BIZCORE WITH AYUUSH
Da
Hanya UKU domin Maida STATUS Viewers
zuwa Customers
FEBRUARY, 2024
©Bizcorewithayuush 2024
annan littafin mallakin BizCore With Ayuush
W
ne. Ba a yarda a siyar da shi ba ko amfani da
wani sashe na littafin ba tare da neman Izinin
ba.
Designed by Acube Graphicx
2ND EDITION. FEB, 2024
i
Abubuwan da ke ciki
Gabatarwa 01
Online Markerting 03
I na Matsalar Take? 0 6
R ainon Sabbin Contacts 09
Hanyoyi Guda 3 Da Zaki Maida Status 1 0
Viewers Zuwa Customers
Y adda Ake Posting A Status 15
Lokacin Da Ya Kamata Asa Status. 17
ii
O1
Gabatarwa
Assalamu alaikum
Tabbas zan yi alfahri ƴar kasuwa kamar ki duk da
ƙarancin lokaci da kuma ayyuka amma duk da
haka kika sami lokaci don ki karanta wannan
littafin nawa. Hajiya, nagode da girmamawa. .
Nima shi yasa na taƙaita littafin kuma na fito da
ainihin abunda littafin ya ƙunsa domin kar na
ɓata miki lokaci.
Na rubuta Wannan littafin ne bisa tambayoyin
da ƴan uwa na ƴan kasuwa mata suke akan
yawan status viewers amma ba ciniki. Na rubuta
shi daga iya abunda da nasani da kuma abunda
na koya daga shekaru huɗun da nai ina koyar
yadda ake digital marketing.
Wannan littafin mai suna CUSTOMER DA STATUS
na yi bayani dalla dalla akan hanyoyi guda uku
da zaki bi domin maida WhatsApp Status Viewers
Zuwa Customers In shaa Allah.
Da fatan zaki karanta littafin sannu a hankali har
zuwa ƙarshe yadda ba wani sirri da za ki rasa
samu.
02
Domin samin ƙarin bayani ko kuma wata hulɗa
ta kasuwanci zaki iya nema na ta WhatsApp
Number ta +234 814 547 4518
Ko ki danna wannan rubutun
Asha karatu lafiya.
Aisha Abubakar
Owner of Bizcorewithayuush.
Customer da status
03
Online Marketing
Kasuwanci a yanar gizo ita ce hanya mafi sauki
domin bunƙasa kasuwanci. A wannan zamanin
babu wata rana da za ace ta zo ta wuce ba tare
da an yi amfani da yanar gizo ba wajen siye da
siyarwa. Masana suna harsashen cewa nan
zuwa shekara ta 2025 Kashi 80% a cikin 100% na
kasuwanci zai kuma ana yin shine a yanar gizo.
Social media marketing ya fi ko wace hanya
sauƙi wajen siye da siyarwa musamman ga ƴan
kasuwa ma su tasowa. To wannan ya zama
ƙalubale ga duk wanda yake son cigaban
kasuwancin shi kuma bai maida hankali wajen
samin ilimi akan yadda zai tafi da zamani ba.
Customer da status
04
Da yawan ƴan kasuwa kan koka babu ciniki
alhali cewa su ne dalilin rashin samin cinikin su,
domin su kan shiga kansuwanci sama taka ba
tare da bibiyar masana ko wanda sukai suna a
fannin su ba.Ta kai har wasu gani suke asarar
kuɗi ne siyan wani online class ko bata lokaci .
Matuƙar baza ki kashe kuɗi ki koyi kasuwanci ba
musamman online to tabbas ba za ki rabu da
kukan rashin motsawar kasuwancin ki ba. Ai ilimi
ne zai zamar miki ɗan jagora a gudanar da
kasuwancin ki, shi kuma kuɗi ba'a neman sa sai
da kuɗi.
Matsalar rashin samun cinki ko customer yana
da alaƙa da yadda kika san abunda kike siyarwa
da kuma wa zai siya. Idan kika san wannan to
tabbas ke da kukan ba ciniki to ba akai akai ba.
An san kasuwa daman wataran ayi cinki wata
ran kuma akasi.
Customer da status
O5
WhatsApp ya zama tamkar wani fage na
bajakolin kayan sana'a, kuma shi ne hanyar da
tafi kowa ce hanya sukuni wajen hulɗa da
customer.
Ƴan kasuwa da yawa su kan koka da cewa duk
da yawan Contact Gain din da suke shiga
kullum abun dai jiya iyau, a farko dai kamar da
gaske bayan kwana biyu kuma sai an haɗa da
don Allah ku siya abunda na ke siyarwa !
Ance mutane sune kasuwa to kuma fa ga
status viewers amma ba ciniki. Nasan kin fara
tinanin ke ma dai akwai matsala amma kin rasa
ganota, Idan kika bini sannu a hankali zan
bayyana miki matsalar har ma na baki Dabarun
Har Guda 3 Wanda Za Su Maida Miki Status
Viewers Zuwa Customers In shaa Allah.
Customer da status
06
INA MATSALAR TAKE?
Matsalar a tun farko take CEO, ta fara tun
lokacin da kike neman ƙarin mutanen da kike
fatan nan gaba su zamar miki Customers (lead
generation).
Da yawan ƴan kasuwa sukan ɗauka kowa ma
customer ne sai suke bin hanyar da WhatsApp
TV ko WhatsApp influencers suke amfani da shi
wajen tara mutane. Su WhatsApp Tvs da
Influencers yawan masu kallon suke nema, kin
ga case din ku ba ɗaya bane.
Ke kin ga a matsayinki na ƴar kasuwa mai
neman customers dole ke kina buƙatar ki tsaya
kiyi bincike domin sanin wasu mutane ne suke
neman kayan da kike siyarwa ruwa a jallo! .
Customer da status
07
Idan kina saida sabulun goge ƙuraje akwai ƴan
mata da yawa da ke ta neman sabulu irin na ki.
To haka ko me kike siyarwa akwai wanda neman
kayan ki su ke. To irin wannan su ya kamata ki
jefawa signal don ko a'ina su ke su garzayo don
zama abokan kasuwanci.
Saboda haka, ki sami lokaci kiyi karatu mai
kyau akan su wane ne customers ɗin ki ta
hanyar haɗa wannan bayanai:
Mata ne ko maza,
Shekarunsu nawa ,
Inda suke zaune,
Yaren su,
Inda suke da interest, da lifestyle din su,
Wani lokacin har ma da Addinin su.
To ina fata dai daga yau ba kowa ce number
za ki dinga saurin saving ba.
Customer da status
08
Maganar Target audience tana da tsawo
wanda in shaa Allah nayi bayani akan ta dalla
dalla a cikin online class ɗina mai suna
WhatsApp Markerting Techniques For Business
Growth
Zaki sami ƙarin bayani game da class ɗin a
ƙarshen wannan littafin.
Customer da status
09
RAINON CUSTOMERS
Yawwa! Bari mu cigaba.
Bayan kin yi iya binciken ki kuma kin nemo
sabbin contacts. To raino ne ya kama ki, don
zaki dinga musu yayyafi da ilimin ki da
gwanancewar ki akan sana'ar ki. Ba kawai za ki
fara musu talla ba, ina sai da wannan da
wannan, a'ah suna buƙatar ki basu lokaci domin
ki gamsar da su cewa kayan ki su ne maganin
matsalar su, za ki tabbatar musu da haka ne
kuma ta hanyar contents ɗin ki (abubuwan da
kike talla da su kamar video, photos da kuma
rubutu).
Zaki musu bayani akan ki, sannan me kike
siyarwa haɗe de faɗa musu yadda kayanki za su
taimaka musu wajen rabuwa da matsalar su.
Ki sani cewa da yawan customer basa siyen
kaya sai bayan sun yarda da kayan da za su
siya da kuma mai siyarwa. Shi yasa yake da
kyau ki bi hanyoyi domin ki ƙarawa kasuwancin
ki kwarjini a idon customers kuma ki guje bin
hanyar da zai sa su ji shakku akan sana'ar ki.
Customer da status
10
HANYA GUDA 3 DA ZAKI MAIDA STATUS
VIEWERS ZUWA CUSTOMERS.
Sau ta ri sai ki yiwa mutum magana bai duba ba
amma sai ki tsince shi ya kalli status ɗin ki.
Wannan ya nuna cewa mutane sun fi son zuwa
cen kallo. Kasuwa daman mutane ta ke buƙata
kuma ga shi an samu, saboda haka yana da
kyau ki yi amfani da wannan damar.
Nan gaba kaɗan in shaa Allah zan bayyana
miki hanya guda 3 da zaki bi domin ki maida
masu kallo zuwa Viewers.
Customer da status
11
1. Wayar Da kan Su Akan Sana'ar ki:
Shi kin san da cewa da yawan customers ba su
san suna buƙatar kayan da kike siyarwa ba sai
kin faɗa musu?
Idan kin sani to za ki dinga faɗakar da su akan
yadda sana'ar ki take da kuma abunda da ki ke
siyarwa. Wannan zai taimaka miki wajen jawo
hankalin su na su sayi kayanki ki don sun san
amfani da zai su musu.
Misali kamar mai siyar da Atamfofi ce, za ki iya
yi musu bayani akan yadda ake gane Atamfa
Leather da cotton, faɗa musu wani company ne
suke Atamfa da kin ga mai irin ta kin san hajiya
ce ke tafe, yadda ake wanke da goge Atamfa.
Akwai irina da yawa da ba musan kan Atamfa
ba, a dinga ma na bayani don mu ga ne.
Customer da status
12
Na yi misali da masu Atamfa saboda yawanci
sune suke da ƙarancin ƙirƙirar contents ɗin da
za su jawo hankali .
Da fatan na baki idea akan yadda zaki yi na naki
sana'ar.
Customer da status
13
2.Yi Musu Kyauta:
Ina nufin kyauta daga cikin wani bangare na
abunda kike siyarwa ko kuma services ɗin ki.
Maƙasudin dai customers suyi amfani da kayan
ki don su san yana da inganci ko kuma
ƙwarewar ki tasa su yadda ba za ki saida musu
da jabu ba.
Misali: zaki iya musu free class, ko ki ba su free
recipes ko Ebook. Idan kina da hali zaki iya musu
ma kyautar abunda kike siyarwa Kamar yadda
masu giveaway suke yi.
Customer da status
14
3.Yi Musu Discount:
Duk da a shawarce ba'a san yiwa sabbin
customers arha, amma nan kamawa tai, Ka da
ki manta a baya daman na ce maƙasudin shi ne
su san inganci abun da kike siyarwa . Kuma ai
daman ita arha bata nufin baka ci riba ba.
Za ki iya kuma barin yadda kuɗin yake ki hada
musu da kyauta amma ga sabbin customers.
Zaki ga ko Apps ko wasu kamfani idan suna so
su karɓu suna abu da arha a farko daga baya
kuma su fanshe. To shi ne abunda nake so nayi
bayani.
Customer da status
15
YADDA AKE POSTING A STATUS
Status shine babbar hanyar da ake tallata kaya
a WhatsApp, rashin sani yadda ake tallata kaya
a Status zai sa ki ta ɓata lokacin ki da data kina
talla amma ba a siya.
Ga abubuwan da ya kamata ki guji yin su.
1.KADA KI DINGA SA STATUS A-Z
TALLAN KAYAN KI KIKE YI
Mutane za su ƙosa,mutane basa son su dinga
ganin Status din ki kullum talla ne, yana sa su
daina zuwa kallon status dinki daga nan kuma
ki rasa ciniki.
2.KI DINGA SA CAPTION
Sa caption yana sa mutane su tsaya suna
kallon photon ki.
Caption dinki ya kasance kullum yana
ƙarfafawa mutane guiwa akan su sayi kayan ki.
Idan kika bar kayan ki ba caption mutane
sukan rasa me za ma su ce miki, amma idan
kika sa wani dan rubutun sai su sami abunda
za su yi miki reply.
Rashin sa caption ne zai sa ki ta sa posting
amma shiru ba a kula ka.
Customer da status
16
3.KI DINGA SAKA PRICE :
Rashin sa farashi, ba shi da wani amfani, domin
sau da yawa sai mutane su ga abunda za su iya
siya amma basu siya ba, saboda suna tsoron su
tambaya kuɗin su bai kai ba.
Sa farashi yana sa mafi yawan yawan wanda
zai miki magana zai iya siyan kayan ki ne.
Kin ga ki huta da masu tambayar nawa nawa.
4.KI DINGA AMFANI DA HOTUNA
MASU KYAU
Duk photo da kika sa yana wakiltar kayan da
kike talla, to ki dinga sa hotunan da za su bada
sha'awa da har a siya kayan ki.
Customer da status
17
LOKACIN DA YA KAMATA AKE SA
STATUS
Status shi ba shi da takamaimai lokacin da ake
sa shi, za ki iya sa wa ko yaushe musamman ma
yanzu da sai mutum yana online zai ga updates
ɗin ka,
Abunda ya kamata kiyi idan kina so ki samu
mutane da yawa su gani shine ki bari sai lokacin
da kika fahimci cewa mutanen ki sai su fi hawa
online lokacin sai kisa.
Lokutan sun bambamta amma mafi yawa
mutane sun fi hawa online da sassafe, yamma
sai dare.
Customer da status
18
A taƙaice dai, kafin ki ce status viewers din ki
ba sa siyan abunda ki ke siyarwa , sai kin fa
tabbatar da cewa kin yi abunda ya dace kuma
dai abun ba cigaba. Saboda haka idan kinga
kuskuren ki yana da kyau ki gyara.
Kaso 50% a cikin 100 % na samun cinki a
kasuwanci ne ya dogara akan cewa wanda
kike wa tallan masu buƙatar abunda kike
siyarwa (Target Audience) ne , sai kuma sauran
kaso 50 % ɗin aka raba wa abunda kike siyarwa
(products) da offer ko wane ya ɗau kaso 25%. Ki
lura da wannan.
Na ji wata masaniya akan kasuwanci tana
cewa Kasuwanci ba Sa'a ba ne koya ake.
Saboda haka matuƙar kina so ki cigaba sai kin
zamana kina karatu, bincike da koya daga
wurin ƙwararro. Zama haka kawai ba inda zai
kai ki.
Customer da status
19
Kafin na rufe wannan littafi, ina gabatar miki da
Class ɗin na mai suna WhatsApp Markerting
Techniques For Business Growth.
Business kike amma kullum jiya iyau.
Fama kike da matsalar banda contacts ko kuma
kina da su basa wani engaging bare su siya
kayan ki?
Ko kuma advert kike bayarwa ayi miki amma ba
mai danna link ɗin.
Idan kina fama da ɗaya ko duka daga cikin
matsalolin nan kuma kin shirya fara ingantaccen
kasuwanci musamman a WhatsApps to kin zo
inda za a share miki hawayen ki.
WhatsApp Marketing Techniques for business
Growth wani course ne da akayi na musamman
don koyar da yadda zaki inganta kasuwancin ki
online, inda za a koya miki:
Customer da status
20
✅ Mene WhatsApp Markerting, amfanin da
ƙalubalen sa.
✅ Yadda zaki jan hankalin Customers ta hanyar
gyara profile ɗin ki kawai.
✅ Yadda ake amfani da WhatsApp business
features
✅ Sirrin yadda ake samun Contacts ɗin
mutanen da a shiye suke tsaf don zama
Customers
✅ Hanyar da zaki bi domin sanya customers ɗin
da ba su sanki ba su yarda da ke.
✅ Yadda Ake posting a status da dabarun da
ake bi domin samun high Status viewes.
✅ Yadda ake rubuta attention
grabbing caption writing
✅ The effective strategies da ake bi wajen
tallata kaya online .
✅ Abu guda 10 da dole sai kin sani kafin
bayarwa a miki Advert.
✅ Hanyoyin da zaki bi domin zama cikin
business ɗin da ƴan kasuwa suke sha'awa.
✅ Dabarun da in dai kin bisu ke da ƙorafin ba
ciniki to ba akai akai ba.
Ba iya nan ba
✅ Zaki koyi yadda zaki dinga yiwa customers
reply ba tare da kinyi typing.
✅ Yadda zaki saving numbers ɗin mutane ba
tare kin bata lokaci ba
Customer da status
21
Akwai kuma certificate bayan kin kammala
wannan Class din.
Zaki sami wannan class a naira 5,000 kachal
Idan kikai registration zaki sami bonuses kamar
haka:
🎁Yadda ake SMEADAN certificate
🎁Yadda ake listing business a Google
🎁 E-LIBRARY da ya taimaka min na koyi
kasuwancin online.
🎁 10 plus Ai sites da za su taimaka miki wajen
inganta kasuwancin ki online.
🎁 Sites ɗin da zaki dowloading premium
Applications kyauta.
🎁 A secret site da zaki sami affiliated products,
wanda zaki sami sama da product 30 kuma ki
siyar da kayanki online ki sami.
🎁 Site din da zaki koyi digital marketing kyauta
har da certificate
Bari ki ji abunda wanda sukai registering
register da Class din suke cewa.
Customer da status
22
Yanzu ta koyi yadda zata tafiyar da
kasuwancin ta da Customers ɗin ta.
uk abunda da ta koya ta
D
gwada sai ta ga canji.
Customer da status
23
Ta ƙaru da abunda aka koyar, ta ce ma
abunda suka koya ya fi karfin kuɗin da suka
biya.
a sami ƙarin Customers sossai, sanadin
T
wannan class da ta shiga.
Customer da status
24
Matuƙar kin san baki san yadda ake kasuwanci
a WhatsApp ba, to kar ki bari wannan aji ya
wuce ki. Don yin Register
Ko ki danna wannan rubutun
Da haka nake cewa fatan alkhairi tare da
fatan kasuwanci mai albarka.
Aisha Abubakar Abdullahi
BizCore With Ayuush
Customer da status
Bizcorewithayuush
2024