Taimiyyah
Taimiyyah
*MABUƊI*
*Ina me farawa da godia ga Allah subhanahu wata'ala,da ya bani ikon fara rubuta wannan littafi
me suna asama,ina roƙo ubangiji yayi riƙo da hannuna wajen rubuta dai-dai,ya kuma yafe
kusakuran da zasu iya kasancewa aciki Ameen.*
*SADAUKARWA*
*Na sadaukar da wannnan littafin gaba ɗayansa zuwa ga duk wata me nakasa,especially masu
matsala irin na TAIMIYYAH,ina roƙo ubangiji yasa nakasan ta zame muku alkhairy da ɗaukaka a
rayuwa.*
*Page 1*
Matashiyan budurwace kwance ƙudundune cikin bargo,jikinta na faman kakkarwa alamun zazzaɓi
ne yai mata kamun me kyau,daga gefenta wata dattijuwa ce wacce shekarunta ya fara nisa
sosai,don a ƙalla zatai shekaru sittin da biyar zuwa sama,farace tas dattijuwan me tsagen kalangu a
fuskanta hagu da dama,kyakykyawace wanda a kallo ɗaya zaka zaci cewa bafulatana ce,sai dai ba
hakan bane bahaushiyace ziryan,wanda ubangiji ne kawai yai mata baiwan kyau da farin
fata,hannu takai tana janye bargon da budurwan ta ƙudundune aciki,cikin muryan da ke nuni da
tsananin kulawa take faɗin "Tashi TAIMIYYAH ki ƙoƙarta kiyi wanka ko zaki daina wannan
rawan sanyin,idan kin karya yanzu sai Sani yazo ku koma asibitin watakila waɗannan
magungunan kaɗai bazasu wadatar da ke ba sai an haɗa da alluran dai da ba'a so."
Ta ƙare maganan tana ƙarisa yaye bargon da budurwan ta rufa dashi,nan take kyakykyawan fuskan
budurwan da aka kira da TAIMIYYAH ya bayyana,tare da jikinta baki ɗaya wanda take sanye da
rigan bacci Ash colour me kauri sosai,kamanninta da tsohuwan daya bayyana sosai zai baka
tabbacin idan ba ƴarta bace to akwai alaƙa ta jini me ƙarfin gaske dake tsakaninta da dattijiyan
matan,abinda kawai dattiyan zata nuna mata shine fuskan manyance ,amma hatta farin fatan nata
irin na Dattijiyan ne,TAIMIYYAH ta yamutse kyakykyawan fuskanta tana sake lumshe manyan
idanunta,muryanta can ƙasa dake ɗauke da ƴar shagwaɓa take faɗin "Wash! Allah Iya baki ji kaina
ba kaman zai cire wallahi."
Iya ta dube ta cike da tausayi da kulawa tana faɗin "Sannu kiyi haƙury zai bari,yanzu tashi ki shiga
wankan na haɗa miki ruwan ɗumi sosai da zakiji daɗinsa,Allah ya baki lafiya TAIMI na."
Budurwan ta amsa da "Ameen." Tana miƙewa tsaye da ƙyar sai lokacin na kula da cewa tana da
tsayi dai-dai misali wanda bai cika yawaba,sam bata da jikin ƙiba sai dai jikin a murje yake cike
da tsoka da cikan halitta me ɗaukan hankali,ta sake lumshe manyan idanunta sabida ciwan da
kanta keyi,kafin a hankali takai hannunta na hagu ta dafa guiwan ƙafanta na hagun tana me fara
takawa zuwa toilet ɗin dake manne cikin ɗakin,Dattijiya Iya tabi bayanta da kallo ƙaunar
budurwan da tausayinta na sake ratsa ilahirin jinin jikinta,tana matuƙar tausayin TAIMIYYAH sai
dai ko kaɗan ba ta nuna mata cewa nakasan da ta samu na ƙafa yana damunta domin ita kaɗaice a
kullum take ba TAIMIYYAN tabbacin haka ubangiji yaso ganinta,tashi tayi tana me ficewa daga
ɗakin mintoci kaɗan ta dawo ɗakin hannunta ɗauke da Mug da ta ciko da zazzafan Kunun gyaɗa
da yaji madara sabida sanin TAIMIYYAH na matuƙar son sa,dai-dai lokacin da TAIMIYYAH ta
fito daga toilet,tana ɗaure da ƙaton towel da tsayinsa ya sauka har zuwa guiwanta,ƙafafunta nabi
da kallo wanda na lura ɗaya ya sirance ɗaya kuma lafiyayye,ta yadda ruwa ke gangara a jikinta
kaɗai zai baka tabbacin Allah yai mata baiwa da sulɓin fata,taiwa Hajiya Iya kallo ɗaya tana sakin
murmushi,a hankali ta ciga da dafa ƙafanta na hagu tana takowa zuwa cikin ɗakin,da alamu
wankan da tayo yasa ta fara jin daɗin jikinta,Iya ta ɗaga kai ta dubeta tana faɗin "Sannu kinji
daɗin jikin ko? ga kununki nan saiki daure ki farasha kafin Ladi ta gama soya miki dankalin."
TAIMIYYAH ta ɗaga manyan idanunta masu haske ta dubi Iya,cikin sanyin muryanta me daɗi
take faɗin "Naji daɗi Iya nagode da kulawa,amma ina ga abar dankalin wannan ɗin kaɗai ya
isa,amma zuwa anjima don Allah ki min faten tsaki da kanki irin wanda kikeyi yayi ɗan tsamin
yakuwannan shi kawai nake son sha." Ta ƙare maganan da shagwaɓa sosai a muryanta."
Hajiya Iya tayi murmushi me faɗi tana faɗin "To shikenan baki da damuwa za'ayi insha
Allah,yanzu dai sha kunun ki sha magungunan,sai a sake kiran Sanin ku koma asibitin,ki tafi da
duka magungunan sabida su gani ki kuma buɗe baki kiyi magana agaban likitan bana son wannan
miskilancin naki idan kina ciwo ki ƙi magana."
Hajiya Iya ta ƙare maganan da mita,wanda hakan yasa murmushi me faɗi suɓucewa daga face ɗin
TAIMIYYAH wacce ta kammala shafa mai tana ƙoƙarin saka rigan da ta ciro,ba tare da tayi
magana ba har Iya ta fice ta sanya doguwan rigan atamfa Red wanda akaiwa adon zanen manyan
Flawer da milk and black,yayi mata kyau sosai tare da haska kalan skin ɗinta,bata shafa komi a
face ɗinta ba sai lip balm me taushi,qamshin Body mist datai anfani dashi ne ya cika ɗakin baki
ɗaya domin ita ɗin ma'abociya son qamshi ce na ajin ƙarshe,zama tayi tana ɗaukan Mug ɗin da Iya
ta aje tana fara shan kunun ahankali cike da nutsuwa,magungunan ta sha bayan ta shanye
kunun,wani zufa ta fara ji na keto mata hakan yasa ta miƙe tana ƙara ƙarfin gudun Fan ɗin dake
aiki a ɗakin,tsaye tayi gaban dogon mirrow ɗin ɗakin tana kallon fuskanta da ya rame sosai a
kwanaki biyu kacal da fara ciwan nata,sai fararen manyan idanunta ma'abota haske da ɗaukan
hankalin mai kallonta,domin wasu irin idanu Allah yai mata baiwansu masu ɗaukan
hankali,ƙirjinta ta kalla tana me waro ido waje ganin cewa ta manta bata sanya Bra ba,gashi fita
zasuyi sam bazata iya fita babu shi ba,sabida Allah yai mata baiwan cikar ƙirji,sai dai bawai irin
sunyi girman da har suka rankwafa bane,kawai dai bata iya fita haka babu Bra dake tare su
ajikinta,wannan sabo ne dataiwa kanta tunda ta isa sanya Bra ɗin,don haka kai tsaye wajen da take
aje su ta nufa ta ɗakko tana sauke zip ɗin riganta zuwa ƙasa ta sanya,wayanta dake aje bisa gado
ya fara ringing,sai ta nufa wajen don ganin me kiran,ganin sunan Sani ya bata tabbacin yazo
kenan,ta ɗaga wayan tana gaida shi tare da bashi tabbacin fitowanta yanzu.
TAIMIYYAH ta amsawa Iya tana miƙewa hannunta ɗaya riƙe da ƙaramin hand bag da ta sanya
magungunan da aka ɗaurata akai,ɗaya hannun na dafe da guiwan ƙafanta na hagu,wanda ke bada
tabbacin sai da taimakon dafa guiwan shanyayyen ƙafan take iya takawa tana tafiya,a dukkanin
cikar halittan ta babu inda ke da naƙasu sai wannan ƙafan na hagu daya shanye ya
silance,kyakykyawace da ta mallaki duk wani cikan halitta me ɗaukan hankali,ahaka ta dinga
takawa har ta fice daga falon Hajiya tayo waje,idanunta suka shiga ƙarewa haraban sasan Iya kallo
kaman me son gano wani abu,kafin ta cigaba da takawa bisa tsarin yadda ubangiji yaso tafiyan
nata ya zamo ahaka har ta fito daga sashin Iya baki ɗaya,ta iso ainihin haraban gidan me ɗauke da
part guda biyu duk da na Hajiya Iya ne cikon na ukun,tafiya ta cigaba dayi zuciyanta na karyewa a
lokacin da idanunta ke hango mata matar da ta fito daga ɗaya part ɗin,bayan matan wani matashi
ne ke biye da ita riƙeda da wata ƙatuwar leda a hannunsa,TAIMIYYAH tayi saurin yin ƙasa da
kanta tana cigaba da tafiya har ta iso dai-dai inda Hajiya Shuwa suke tahowa,hakan yasa
TAIMIYYAH dakatawa daga tafiyan tana jiran ƙarisowan Hajiya Shuwan wacce suke kira da
Umma,matar wan mahaifinta ne wacce taiwa TAIMIYYAN wata irin muguwan tsana.
Sune kalmomin da suka fito daga bakin TAIMIYYAH a lokacin da su Umman suka iso suna shirin
gitta ta su wuce,sai dai gaisuwan da ta aikawa Umman yasa Umman dakatawa tana zubawa
TAIMIYYAH ƙananun idanunta,fuskanta babu ɗigon fara'a ko kaɗan,tai mata wani malalacin
kallo memakon ta amsa gaisuwan TAIMIYYAN sai cewa tayi "Ikon Allah su gurguwa kenan ance
baki da lafiya,ke kuma haka Allah ya yoki irin jaraba ga nakasa ga yawan ciwo da wanne za'aji?
kuma a hakan ake so wani yazo yace zai kwashi jaraba,ga gurgunta ga yawan cuta kaman sikila,to
mu dai kurwan mu kur kada arasa me so ace wataran za'a cinnama lafiyayyun ƴaƴan mu gurguwa
raguwan cuta."
Ta ƙare maganan da jan tsaki tana yin gaba abinta bayan ta kalli ɗan lelen ɗan nata ta maka masa
harara tare da yi masa sign da ido alamun ya shige gabanta,ba tare da ta kuma kallon
TAIMIYYAH da tai ƙasa da kai zuciyanta na shiga wani irin ƙunci mara misaltuwa ba,manyan
idanunta tuni sun fara tara hawaye, ciwan kan da take riritawa taji ya dawo sabo,cikin ɗan hanzari
ta dafa ƙafanta me laluran ta fara cigaba da tafiya,sai dai taku biyu tayi taji sassanyan qamshin
turaren BENTLEY na isowa hancinta,kaman yadda kafin tayi wani yinƙuri yayi saurin tare
gabanta,manyan idanunsa masu kama da nata ya sauke akanta,wani abu na yawatawa cikin
maƙoshinsa,cak! TAIMIYYAH ta tsaya still bata ɗago face ɗinta ba don qamshinsa ya gama bata
tabbacin ko waye domin kaf gidan shi kaɗai ne mamallakin irin wannan turaren me qamshin da ke
kashe jikinta, amon muryansa me cike da ginshira taji cikin kunnuwanta yana faɗin "Kiyi haƙury
Sis da halin Umma please! watarana sai labari ko kaɗan bana so kisa wani damuwa a zuciyanki
haka Allah ya halicceki kuma yaso ya ganki, mu da ita babu me halitta haka kuma babu wanda isa
ya sauya halittan wani face wanda yayisa,ya jikin naki?"
Ya ƙare maganan da jefa mata tambaya,hakan yasa TAIMIYYAH yin jarumtan maida ƙwallan da
suka cika idanunta,sai dai duk yadda ta so ɓoye halin da zuciyanta ke ciki ƙaramar zazzaƙan
muryanta dake rawa ya fallasata,cikin sanyin muryan da ke kashe zuciyansa take faɗin "Naji sauƙi
Yah Sadeeq zazzaɓin ne yaƙi tafiya shine yanzu zamu koma wajen ganin likita,ina kwana dafatan
mun tashi lafiya."
Ta ƙare maganan da gaida shi tana me ɗago manyan idanunta ta sauke akan face ɗinsa,sai dai
ganin ita ɗin yake kallo yasa ta sake ƙasa da kanta,tana jin yadda idanunsa ke cigaba da yawo
akanta,kafin ya furta "Okey! Allah ƙara lafiya yi maza kije tunda yana jiranki zuwa anjima zan
shigo sasan Iya sai muyi magana,take care Angle."
Ya ƙare maganan da wani karyayyen sauti daya motsa zuciyan TAIMIYYAH,hakan yasa ta gyaɗa
kanta tana lumshe idanunta da buɗesu lokaci guda ta cigaba da takawa zuwa parking space inda
take hango motan Sani,ya bi bayanta da kallo tausayinta da matsananciyan ƙaunarta na sake
kassara zuciyansa.
Ko da TAIMIYYAH ta isa wajen motan Sani baya ta buɗe ta shiga don tana buƙatan kwanciyane
sabida yadda kanta ke sarawa,sam baiyi ƙorafi ba domin matsayin driver yake bashi da damuwan
duk inda zata zauna ɗin,sannu yai mata yana tada motan bayan TAIMIYYAH tayi ƙarfin halin
amsa masa,zuciyanta na mata bitan baƙaƙen maganganun Umma wanda inda sabo yaci ace ta saba
da yadda Umma ke kyaran halittan ta da kushe nakasanta tamkar itace tayo kanta a hakan,ba haka
Allah yaso ganinta ba, hawaye masu ɗumi suka silalo mata ta kai hannu ta share tana son ƙarfafa
zuciyanta kaman ko yaushe,don ganin maganganun basuyi tasiri a zuciyanta sosai ba,sai dai har
suka isa asibitin ABU da ke zaria zuciyanta babu daɗi,zuciyanta ya sake nauyi tana tambayan
kanta wai har sai yaushe ne zata daina fuskanta gorin halitta da cin fuska daga wasu cikin ahalinta
akan yadda Allah ya yota? da ƙyar ta lallashi kanta ta samu ƙwarin guiwan shiga cikin asibitin don
ganawa da likita.
A ƙalla ta shafe kusan awa guda kafin ta fito tana faman liliya inda akai mata alluran,domin bayan
dukkanin bayanai da taiwa likitan sai ya sanar da ita dole ta amshi allura guda uku wanda zaa jera
yi kullum guda ɗaya,ba don rai yaso ba ta amince domin allura na daga cikin abinda family ɗinta
suka tsana akira za'aiwa ƴaƴansu tun bayan laluran data samu TAIMIYYAN wanda ta sanadin
allurance ta samu wannan nakasan na shanyewan ƙafa ɗaya,wanda hausawa ke kira da shan inna
wanda kuma take fuskantan ƙalubale me tarin yawa daga ƴan uwanta da wasu baren daban ma,kai
kace itace ta janyowa kanta laluran da kanta ba Allah ne ya ɗauro mata ba.......
Hello! my people gani da sabon salo sabon tafiya irin wanda Ɗansabo bata taɓa zuwa dashi
ba,labarin TAIMIYYAH labari ne mai cike da ban tausayi, haɗi da darasi me tarin yawa ga zallan
ƙauna da soyayya me motsa zukata,kada ki bari abaki labari a wannan karon kowa ta ƙoƙarta ta
mallaki nata akan fara shi me sauƙi da zan faɗi nan gaba kaɗan,ku dai ku cigaba da bibiyata a
shafukan da zasu biyo baya don jin ya rayuwan TAIMIYYAH zai kasance.
#Ɗansabo ce#
[12/14, 3:41 PM] +234 703 040 9541: *TAIMIYYAH*
*Page 2*
Lokacin da TAIMIYYAH suka dawo gida daga asibitin ana ta kiraye-kirayen sallan zuhur
ne,hakan yasa Sani wuce wa masallacin kusa da gidan,ita kuma TAIMIYYAH ta nufo sasan Iya
jikinta gaba ɗaya ya saki ga wani zufa da ke keto mata alamun alluran da akai mata ya fara aiki
sosai wajen saukar da Zazzaɓin gaba ɗaya,kaman ance ta kai dubanta ga sashen adana motoci na
gidan,idanunta suka sauka akan motar Abie ɗinsu,ƙatuwar baƙar LEXUS tuni taji zuciyanta ya
fara gudu wani daɗi ya lulluɓe zuciyanta,domin tayi kewansa matuƙa don sun rabu da shigowa
garin shi da matansa da qanninta ,ta cigaba da takawa cikin takun tafiyanta wanda take dafe da
ƙafanta na hagu,lokacin da ta sanya kanta a sashin Iya shi kuma Abie na shirin fitowa don zuwa
masallaci,kaɗan ya rage suyi karo TAIMIYYAH tai baya don bashi hanya,cikin rashin sa'a
hannunta dake dafe da ƙafanta me lalura ya zame,tai kaman zata kifa Abie ɗin yayi saurin taro ta
yana faɗin "Subhanallah! ki dinga kula Zainab."
TAIMIYYAH da duk murnan ganinsa ya gama cika ta tai murmushin da suka bayyana kyawawan
haƙoranta,cikin zallan murnan daya kasa ɓoyuwa take faɗin "Sannu da zuwa Abie,i miss u so
much tare da su Ummie kazo?"
Alhaji Sameer ya gyaɗa mata kai yana sakin murmushi yake faɗin "We ol miss u too dear,tare
muke ya jikin naki hope kina samun sauƙi sosai?"
Ta gyaɗa kai da shagwaɓa take faɗin "Naji sauƙi sosai Abie bari in shiga daga ciki na ga masallaci
zaka sai ka dawo."
Daga haka ta raɓa shi ta wuce ya bi bayanta da kallo,yana kallon yadda take tafiya wanda shi yake
ganin kaman a wahalce take takawa,tausayin ƴar sa da ƙauna irin ta uba da ƴa ke ratsa sa,sai da ta
ɓacewa idanunsa sannan ya juya ya fice daga sasan baki ɗaya.
A cikin sasan Iya kuwa TAIMIYYAH na shiga falon Iya bakinta ɗauke da sallama,idanunta suka
fara sauka akan qanwarta Nahar,yarinya ƴar shekaru bakwai zuwa takwas,Iya da Ummie da ke
zaune cikin falon ne suka amsa sallaman TAIMIYYAH,yayinda Nahar ta rugo da gudu wajen
TAIMIYYAH tana faɗin "Oyoyo! Anty TAIMIYYAH."
TAIMIYYAH da tayi saurin jingina da jikin kujera don kar Nahar ɗin ta kadata,tayi saurin sakin
murmushi tana ware mata hannuwanta Nahar ta shige,ta rungume yarinyan tana faɗin "Welcome
My Baby i miss u."
Ummie ne tayi saurin buge bakin Nahar ɗin a lokacin da ta iso wajen,yayinda TAIMIYYAH tai
murmushi tana duban Nahar ɗin da muryanta me raunin daya fallasa cewa maganan Nahar ya taɓa
zuciyanta,ta furta "Nahar ba laifin Abie bane domin bashi ne zai iya sawa ƙafan ya gyaru ba,ni
haka Allah yaso ganina karki damu kinji,ni Allah bai nufa in dinga tafiya irin yadda kuke yi bane
kuma ki daina ɗaukan maganan da su Anty Zuhura ke faɗi kina sawa a ranki kinji ko?"
Yarinyan ta gyaɗa kai alamun gamsuwa yayinda TAIMIYYAH tai ƙasa tana gaida
Ummie,Ummien ta amsa da kulawa duk da cewa fuskanta babu wani alamun ɗoki ko murnan
ganin TAIMIYYAN,domin irin matannan ne marasa sakin fuska,sam bawai ta damu da
TAIMIYYAN bane kanta da ƴaƴanta kawai tasani,shiyasa tun lokacin da Abie ɗin ya auro ta ya
nuna son ta riƙe TAIMIYYAN ta bijera masa,domin a ganinta zama da irin su lalurace kawai da
ɗawainiya duk da cewa babu abinda yake gagaran TAIMIYYAN a hakan babu abinda bata
iyawa,hatta da ɗaukar ruwa a bucket da duk wani aikin ƙarfi gwargwado tana iyawa,babu abinda
ake taimakonta dashi sai ƙalilan,sannu da dawowa Iya taiwa TAIMIYYAH tana tambayanta yadda
sukai da likita,TAIMIYYAH ta sanar da ita cewa allurai aka bata uku anyi ɗaya saura gobe da
jibi,Iya tai mata fatan samun sauƙi daga haka ta zame jikinta ta nufi ɗakinta don yin wanka da
sallah sabida yadda take jin zufa ya jiƙe jikinta bazata iya komiba ba tare da ta sake wanka ba.
Lokacin da ta fito wankan samun su Nahar tayi sunyi ɗai-ɗai a bed ɗinta,suna faman kallon ƙaton
photo album dake aje saman Bed side na gado,kallo ɗaya tai musu ta saki murmushi tana wucewa
wajen kayanta,doguwar riga mara nauyi ta saka me taushi bata shafa komi ba a jikinta,ta zura
Hijab ta tada sallah,bayan ta idar ne ta tasa kan su Raudha zuwa falo lokacin Abie ya jima da
dawowa daga masjid,zama sukai gaba ɗaya aka shinfiɗa babban ledan cin abinci wanda aka jera
manyan kulolin abinci duk da cewan zuwan bazata sukai bai hana Iya saka Ladi me aiki shirya
abincika masu sauƙi ba,tare sukai lunch ɗin gunin sha'awa TAIMIYYYAH na jin farin ciki sosai
na ganin ahalinta,duk da cewa sam babu cikakken wani shaƙuwa tsakaninta da Abie ɗin,amma
hakan baya hana ta shiga farin ciki a duk sanda zai zo garin walau shi kaɗai ko da su Ummie
ɗin,Ummie itace ta fara tashi daga wajen cin abinci tana sanar da Iya cewa zata wuce part
ɗinsu,Iya tai mata Allah huta gajiya tai gaba su Nahar ko kallonta basuyi ba bare suyi yinƙurin bin
ta suna nane da TAIMIYYAH domin Allah ya ɗaurawa yaran son Yayar tasu,ko don irin kulawa da
ƙaunar da TAIMIYYAN ke gwada musu ne Allah masani,lokacin da Abie ya kammala cin abincin
yayi hamdala tare da goge bakinsa da tissue,sai ya ɗaura manyan idanunsa akan TAIMIYYAH
wacce itama ta gama cin abincin tana gogewa Nahar baki ne,cikin murya me nuna kulawa yake
faɗin "Zainab yanzu kin gama NCE ɗinki sai kuma miye plan ɗinki na gaba,aure ko karatun zaki
ɗaura?"
Kalman aure daya shigo cikin kalamansa yasa TAIMIYYAH saurin waro idanunta,cikin muryan
da ke nuna kiɗima take faɗin "Abie aure kuma? Karatun dai zan ɗaura ni bazan yi wani aure ba
waye ma zai auri gurguwa kaman yadda Umma ke faɗi."
Ta ƙare maganan tana turo baki alamun shagwaɓa,Iya da ke zaune duk tana jinsu ta ɗago tare da
saukewa TAIMIYYAH harara tana faɗin "Ashe ban hanaki irin waɗannan kalaman na banza ba
TAIMIYYAH,don Allah ya yoki ahaka sai akace shikenan bazaki samu masoyin da zai aureki a
haka ba,to bari kiji wanda suka fiki nakasama sunyi aure har sun haihu bare ke da babu abinda ma
yake gagaranki,kije gidan Malam Inuwa ki kallon gurguwan da bata ko iya tashi ta miƙe a
nannaɗe take amma tayi aure ƴaƴanta goma sha biyu zar sunanan suna taka doran ƙasa,don haka
ki iya bakinki ki kuma daina ƙoƙarin ja da ikon ubangiji,ita wacce kike ji abakin nata tana cewa
bazaki auru ba sai ki zuba mata ido ki ga idan itace ta halicceki da zata hana Allah ikon sa,ni a
nawa ma babu wani karatun da zaki ɗaura Allah ya kawo me so kiyi aurenki kawai ki huta."
Tunda Iya ta fara magana ko tari babu wanda yai har ta dasa aya cike da sababi da jin zafin Hajiya
Saratu a ranta,Abie ne ya dubi mahaifiyan na su yana faɗin "A'a Iya idan har tana son cigaba da
karatun kar a tauyeta,abata dama ta ɗaura idan yaso tana cikin yi Allah ya kawo me son sai ayi
auren,amma zaman haka bazai yiwu ba,Zainab wani skull ɗin kike so gashi yanzu ana cikin
wannan strike ɗin,ni kuma bazan so ki tafi wani gari ba sabida laluranki, karatunki a kusa da gida
zaifi,don haka sai dai ajira aga janyewan yajin aikin malaman sai asan abinyi,idan akwai wani
plan ɗin da kike dashi ina jinki tell me."
Abie ɗin ya ƙare maganan idanunsa akan TAIMIYYAH da daɗi ya cika ta,na jin cewa Abie ɗin
bazai hanata cika burinta na son yin karatu me zurfi ba,cike da ɗoki take faɗin "Abie zan fara yin
wani Computer Skull kafin a dawo daga yajin aikin,ina so in samu certificate na Computer
Training ɗin,kuɗin form da na registration kawai zaka bani,a can wajen Congo ne sai Sani ya
dinga kaini yana ɗakko ni ko Abie?"
Alhaji Sameer ya jinjina kansa cike da gamsuwa yake faɗin "Eh hakan ma yayi kinyi tunani me
kyau,karki damu zan baki kuɗin komi da komi,amma Iya tace an baki allurai uku meyasa kika
yadda aka fara,kinsani sarai bana so ko kina manta alluran shine silan laluranki Zainab."
Ya ƙare maganan da faɗa sosai wanda yasa TAIMIYYAH bashi haƙury,tare da sanar dashi
magungunnan ne basui mata ba dole sai an haɗa da alluran,tare da su Raudha ya bar sashin zuwa
part ɗinsu da suke sauka idan sun zo daga Lagos ɗin.Bayan fitan su Iya ta kalli TAIMIYYAH da
ke ta faman murnan zata shiga Computer skull,ta maka mata harara tana mitan faɗin "Ayi dai
mugani duk son karatun mutum da ƙinsa da aure indai lokacin mutum yayi dole yai auren ba."
Kafin TAIMIYYAH tace komi suka jiyo amon muryansa,wannan dai muryan nasa me cike da isa
yake doka sallama daga bakin ƙofar ɗakin Iyan,Iyan ce ta amsa sallama tare da bada izinin
shigowa,qamshin turaren BENTLEY ya riga isowa cikin ɗakin kafin gangar jikinsa ya
shigo,idanunsa ya sauke akan TAIMIYYAH da ta miƙe tare da dafe ƙafanta ta fara takawa don
komawa ɗaki ta kwanta,baiyi magana ba har ta shige corridor ɗin da zai sadaka da Bedrooms
ɗinsu,illa ɗauke kansa da yai ya maida dubansa kan Iya yana takowa cikin falon,a kujeran 2 seater
ya zauna yana fuskantan Iya ya fara gaida ta,ta amsa fuska a sake tana faɗin "Yanzu Sadeek ka
dawo tun jiya sai yau zaka shigo gaida ni,to kayiwa kanka ne aiko baka shigo ba ka zo don
mutuniyar ka dana tabbatar kaji bata jin daɗi ko da yake naga yanzu ƴar wasan ɓuya kuke tunda
uwarka bata ƙaunar jituwan da ke tsakaninku."
Ta ƙare maganan cike da sababi hakan yasa Sadeeq sake haɗe fuska,yana wani taɓe baki yake
faɗin "Ke dai Iya kin faye son nacin magana ɗaya,waya gaya miki wasan ɓuya muke ita ɗince dai
bansan meyasa bata son haɗuwan mu ba yanzu ko don taga ta gama zama Big Girl ce oho."
Iya ta taɓe baki itama tana faɗin "kadai ji da ƙaryan turancinka,ya wajen aikin naku ina fata dai
komi na tafiya yadda ya dace ko?"
Sadeeq ya gyaɗa mata kai kawai,kafin ya miƙe ya nufi wajen cin abinci yana faɗin "Iya akwai
abincin da zan iya ci anan,cikin gida tuwon shinkafa akayi ni kuma banso,ai na ga motar Abie
ashe sun shigo."
Iya ta amsa da "Eh aiko sai ga su babu sanarwa,sai ka duba akwai ragowan shinkafa da miya sai
dai mayyan Salad ɗin ta juye shi ta kai fridge."
Tuni ya gane wa take nufi don haka baice komi ba sai nufan hanyan ɗakinta da yai,Iya ta bi
bayansa da kallo tana taɓe baki ba yau ta gama gane jikan nata ya kamu da son ƴar uwan nasa
ba,sai dai bata ji ko sama da ƙasa zasu haɗene zata bar TAIMIYYAH ta aure shi,sabida ƙiyayyan
da uwansa take gwadawa TAIMIYYAN,shiyasa tai biris bata taɓa nuna musu daga shi har
TAIMIYYAN tasan abinda suke ciki ba........✍🏻
*Littafin TAIMIYYAH paid book ne da zai zo akan 500 naira only,ga masu buƙatan yin payment
zakui min magana ta wannan number ɗin 08167768704, ko kuma ku turo kuɗin ku kai tsaye ta
wannan account ɗin 0504192664 aisha ibrahim dansabo GTbank.*
_Masu account da Arewa books,zaku dinga siyan sabbin shafuka dalla-dalla akan farashi me
sauƙi,ga yadda zaku siya pages a arewa books kamar haka_ 👇🏻
*DANNA LINK DIN NAN KASHA KARATU👆🏽👆🏽👆🏽*
*Balance* - Zai nuna kudin account dinku da zaku iya sayayyan littafai cikin kasuwar
ArewaBooks.
*Credit/Debit Card* - Hanyar farko kuma mai dadi wajan Recharge din account dinku.
A inda (Enter your amount) za'a saka kudin da akeson Recharge din sai a taba "Proceed". Zaibude
muku inda zaku saka bayanan katin banki, kuna gamawa kudinku zaishiga account dinku kaitsaye
(instant).
--------
*Bank Transfer*
*Airtime Transfer*
Saidai su ba kaitsaye bane (instantly) sai ArewaBooks ta tabbatar da Transfer din, amman bayakai
1hour za'a gansa a Balance.
*Bank Transfer* - kamar yadda akwai bayani a sama da kuma account number ArewaBooks.
*Airtime Transfer* - muna bada shawaran ayi amfani da *Debit Card* kokuma *Bank Transfer*
akan *Airtime Transfer* , amma idan yakama babu mafita saishi tau muna amsar:
MTN,
9Mobile
Glo
Airtel
Amma kamar yadda akayi rubutu a sama afara tuntubar ArewaBooks a WhatsApp domin akwai
percent da ake cirewa na canji(convert) kafin kudinka yashiga Balance.
#Ɗansabo ce#
[12/14, 3:42 PM] +234 703 040 9541: *TAIMIYYAH*
*Page 3*
Yana sanya kansa cikin ɗakin sassayan qamshin daya kama ɗakin ya doki hancinsa,ya ɗan lumshe
idanu yana jinjina tsafta da son qamshi irin na TAIMIYYAH,halayyanta da ke sake saka shi jin ta
aransa sosai da yaba ƙoƙarinta akan kula da kanta, duk da laluran ƙafanta sam bata da ƙyuiya da
son jiki,kwance ya hange ta tayi ruf da ciki tare da tokare hannayenta da pillow waya riƙe a
hannunta,sam bata ji sallamansa ba sai qamshin turaren BENTLEY da ya buɗe ɗakin,hakan yasa
ta saurin tashi zaune tana sauke manyan idanunta akansa,fuskanta a sake take faɗin "Yah Sadeeq
shigowa kayi,ina yini."
Harara ya zabga mata yana takawa zuwa wajen stool da ke gaban madubi ya janyo ya
zauna,idanunsa ya mayar kanta kafin ya buɗe baki cike da ginshira yake faɗin "Wannan yarinyan
kin girma da yawa kin fara raina mutane ko? Ba kina kallo na shigo ba amma ki kai tahowanki
sabida baki ƙaunar haɗuwan mu yanzu ko? to yau sai kin gaya min yadda akai na zama dodo har
da kike guduna."
Ya ƙare magana babu alamun wasa ko sassauci a face ɗinsa,hakan yasa TAIMIYYAH sake
dubansa ya sake jefa mata harara,ganin hakan yasa ta tsuke baki tana faɗin "Kayi haƙury ni fa ba
gudowa nayi ba,kasan banda lafiya to kwanciya na shigo yi ina jin jiri ne."
"Allah ya sauƙe ya baki lafiya,amma meyasa tun wancen week ɗin dana shigo kika ƙi bari mu
haɗu har na koma?"
Yadda ya tsare ta da ido yasa ta kauda kanta,ba tare da tace komi har sai da ya sake maimaita
tambayansa sannan ta ɗago ido ta dube sa kafin ta shagwaɓe murya tana faɗin "Umma ce fa tace
in daina shige maka inba haka ba duk randa ta sake ganina da kai saita ƙarisa ɗayan ƙafan nawa na
zama gurguwan me sosai."
Yadda ta ƙare maganan muryanta na ɗan rawa yasa jikinsa yin sanyi,cikin taushin muryansa me
kauri yake faɗin "Amma sau nawa zance ki daina damuwa da maganganun Umma,haba Baby
meyasa kike son kafa Hujja da Umma ni kuma kina azabtar da zuciyata why?"
TAIMIYYAH da tai ƙasa da kanta ta ɗago tana ƙoƙarin danne hawayen da ke son zubo mata,cikin
rawar murya take faɗin "Dole in saka maganganunta araina Yah Deeku,Umma bata so na bansan
miye laifi na don na kasance gurguwa ba,bani nai kaina ba inda ana ba ɗan Adam zaɓin ya zaɓi
yanda yake son halittansa ya kasance bana ji akwai wanda zai zaɓi nakasa,amma ita sam ta kasa
gane bani ce na zaɓi zamowa a haka ba,yanzu ba da bane Yah Deeku nasan ciwan kaina a
yanzu,maganganunta suna ƙona zuciyata kaman yadda wuta ke ƙona itace,dole in kiyaye duk
abinda zai dinga janyo min gorin halitta,kayi haƙury Umma uwace a guna amma zuciyata bazata
iya juran yawan aibantani da takeyi ba,shiyasa tunda ta nuna bata son shaƙuwan dake tsakaninmu
dole mu koyi nisanta da juna."
Zuwa lokacin da TAIMIYYAH takai ƙarshen magananta tuni hawayen da take dannewa sun
ɓalle,suna zarya a saman kyakykyawan face ɗinta,Yah Sadeeq da tunda ta fara magana ya tsura
mata ido,ransa yai matuƙar sosuwa da hawayen da take zubawar,ya sani tafi shi gaskiya domin
kaman yadda ta faɗi ne babu wanda yasan ciwan kansa da zai so jin yadda Ummansu ke kyaranta
tana aibanta nakasanta kai kace TAIMIYYAN irin guragunnan ne da basa ko iya tafiya,cikin
muryansa da ya bayyana raunin da zuciyansa shi ma yayi yake faɗin "Yanzu kina nufin sabida
Umma ne zaki daina kulani bayan kinsan zuciyata ta riga ta kamu da ƙaunar ki Zainab,ya kike so
inyi da wannan sabuwan ɗabi'an da sam bazan iya jure masa ba?"
Sanin bazata amsa masa ba yasa shi kai tsaye cigaba da faɗin "Lokaci yayi da zan fito fili
insanarwa da Umma ke nake so,so kuma da aure ko hakan zai tabbatar mata da cewa alaƙanmu
dake ya wuce shaƙuwa na ƴan uwantaka,zallan soyayya ce mara algus."
Kukan da TAIMIYYAH ta sanya masa ne yasa shi tsura mata ido cike da mamaki,baki buɗe yake
kallonta wani abu na yawo a cikin zuciyansa,cikin muryan kukan take faɗin "Ka dubi girman
Allah Yah Sadeeq karka faɗawa Umma wannan maganan,wallahi kasheni zatayi nina sani,don
Allah karka shigo da abinda kasan bazai taɓa yiwuwa ba,alaƙanmu ta tsaya iya na ƴan uwantaka,
ka riƙe girmanka na Yayana wanda nafi so da shaƙuwa dashi,me sharemin kuka na da bani
dukkanin ƙwarin guiwa,don Allah kada ka rusa wannan alaƙan ka shigo da batun da bazai taɓa
yiwuwa ba illa jefa rayuwata cikin garari."
Kuka takeyi sosai zuwa lokacin domin ita kaɗai zata iya gayawa duniya irin tsanan da Umma tai
mata,ba ta ji ko za'a tashi duniya zata iya amincewa da Yah Sadeeq ɗin ya zama abokin
rayuwanta,ta sani yana son ta don ya riga ya jima da fallasa mata sirrin zuciyansa,ita ɗince har yau
ya kasa jin taƙamaimai miye a zuciyanta game dashi,baya hango kowace irin soyayya a idanunta
daya wuce na ƴan uwantaka,irin na wanda shaƙuwa ya shiga tsakani,cikin tsananin ɓacin rai ya
daka mata tsawan da yai saurin sata sake rushewa da kuka me ƙarfin gaske,ta kai hannu tana toshe
bakinta ganin yadda ya taso yana nufota,ta shiga matsawa da baya-baya tana cigaba da toshe
bakinta kuka nacin ta,zama yayi daga bakin Bed ɗin yana kai hannu ya janyota baki ɗaya zuwa
jikinsa,kafaɗunta duka ya kamo yana girgizata yake faɗin "TAIMIYYAH me kike nufi da
waɗannan kalaman,kina so ki gaya min tuntuni ni kaɗai nake haukata ke zuciyanki bata kamu da
soyayyata ba? Ki sanar dani ni kaɗai nake shirme na kome?"
Yadda yake magana yana ɗaga murya da sake jijjiga kafaɗunta yasa TAIMIYYAH sake rushewa
da kuka,sai dai kafin tayi wani yinƙuri sai shigowan Iya suka ji cikin ɗakin,ta tafa hannu tana
salati tana faɗin "Me zan gani Saddeeku dukanta kai bata da lafiya kome,ko kaima ka fara kurɓe
kurɓen zamanin nan da samari keyi ne bamu da labari? To sakarta tun ranka bai ida ɓaci ba,ka
kuma sanar dani tun farko ma uban mi ya kawo ka ɗakinta?"
Sadeeq da ransa ya gama ɓaci sai ya saki TAIMIYYAH yana ballawa Iya harara yake faɗin
"Bansani ba miye naki na shigowa nan ɗin kaman an kiraki."
Iya takai hannu ta bige bakinsa tana faɗin "Yi min shiru mara kunya,kuma ka gaya min me tai
maka da zaka tasa ta agaba kana jijjiga kaman ka biya sadakinta sabida tambaɗa da fitsara,to ahir
ɗinka ka kiyayeta ince dai soyayya ce kakema wannan haukan,to inma son ta kake tun wuri ka cire
bazata so ka ba,inma ta fara dole ta daina kowa yai ta kansa,indai ina raye TAIMIYYAH ba zata
aure ka ba uwar ka taje can ta zaɓo maka matan aure amma ba dai Zainab ba,wuce ka kabar min
sasa tun bansa an kira min uwar ka da uban ka sun maka iyaka daga shigowa nan ɗin ba."
Yadda Iya ta rintse ido tana yayyafin masifa yasa Sadeeq ficewa cikin zafin nama,zuciyannan
kaman ya faso ƙirjinsa sabida ɗaukan zafi,Iya ta bishi da tsaki kafin ta koma kan TAIMIYYAH
tana lulluɓeta da faɗa kaman zata duke ta,cikin faɗan take cewa "In banda ke ɗinma banza ce uwar
sa har nan tazo tai miki iyaka da ɗanta,amma shine zai lallaɓo ya tasaki agaba har da kama jikinki
yana girgizawa baki fito kin bar masa ɗakin ba,yo ko dai kema son nasa kike? Aiko da kinyi
asaran duniya kin kuma ba mutane kunya me zakici da mutumin da uwarsa bata da aiki saina
aibanta halittanki tana kyaranki,to ahir ɗinki wallahi idan kika biyesa har ya yaudari zuciyanki sai
dai ku mutu da son juna amma bazaki aure sa ba indai ina numfashi kuma na isa dake,shashashu
kawai marasa hankali."
TAIMIYYAH dai kuka kawai takeyi ba tace uffan ba har iya ta gama bambaminta ta fice,sai ta
zame ta kwanta tana cigaba da kuka me tsuma zuciya,ita sam bata taɓa jin cewa zata iya son
kowani namiji bama bare Yah Sadeeq ɗin,meyasa Iya zata ɗauki zafi da ita har haka? ta cigaba da
kukanta zuciyanta na ƙuna ,kiran wayanta da akai ne yasata tsai da kukan bayan ta ɗauki phone
ɗin ta ga cewa qawarta Haneefa ce me kiran,basu jima suna magana ba sukai sallama da
juna,TAIMIYYAH ta nufi toilet ta wanke face ɗinta ta fito,dogon Hijab ta zura ta ɗauki phone
ɗinta ta fito,a falo taci karo da Iya har lokacin bata fasa ƙananun mitanta da ta saba idan ranta ya
ɓaci ba,kallo ɗaya taiwa Iyan ta ɗauke kai tana takawa zuwa ƙofan fita falon ba tare da tayi niyyan
tankawa Iya ba,ganin da gaske fita TAIMIYYAH zatayi ba tare da ta kula ta ba,ya sanya Iya ɗaga
murya tana faɗin "Au binshi zakiyi don na kore sa,ko kuwa gidan ubanwa zaki kina fama da
kanki?"
TAIMIYYAH da takaicin Iya ya gama cika ta,ta juya ta balla mata harara kafin ta furta "Ni part
ɗin Abie zani tunda yau abin naki akaina zaki sauke shi."
Yadda TAIMIYYAN tayi magana cike da shagwaɓa da jin haushi yasa Iya sakin murmushi,tana
faɗin "Oh'oh'oh me yai zafi daga faɗin gaskiya kuma ƴar nan,dawo kije ki kwanta tunda ba lafiya
ne dake ba,ni ina jiye miki ne yadda uwarsa ta tsaneki me zaki ci dashi Allah na tuba,ko da kike a
haka ai kinfi ƙarfin ajinsa ke ɗin matar manya ce."
Wani hararan TAIMIYYAH ta ballawa Iya tana juyowa ta dawo cikin falon,kujeran kusa da Iya ta
nufa ta kwanta tana faɗin "Nidai Iya wallahi fitinanki idan ya tashi yana bani tsoro,yaushe rabon
da kika ga na kulasa amma sabida son ɗauramin laifi har da faɗin ko na fara son sa ne,ni bana son
sa kuma bazan so kowa bama bare aje ana min gori,auren ma bazanyi ba ko zanyi kuma zanyi
fatane Allah ya bani me nakasa irin tawa ta yadda ƴan uwa da danginsa babu wanda zai min
gori,amma Yah Sadeeq bazan taɓa iya bashi zuciyata ba Iya don Allah ki kwantar da hankalinki,ni
abinda kawai zakiyi ki birgeni ki samu Abbah da maganan kice masa baki son sake jin shi Yah
Deekun ya tada maganan."
Iya da ta tsurawa TAIMIYYAH ido tsananin tausayin ta na faman ɗawainiya da ita,ashe dai
TAIMIYYAN na son auren gori take gudu sabida nakasan ta,zuciyan Iya ya motsa da wani irin
yanayi me wuyan fassara,ji take da komi nata zai ƙare akan TAIMIYYAN ƙafanta ya dawo dai-dai
da zata iya sallamawa,sai dai ita ɗin shaida ce akan irin yawon manyan asibitocin ƙashi da sukai
tun TAIMIYYAN na ƙarama har kawo yanzu,amma ba'a dace ba ƙasar waje ne kawai ba'a fita da
ita ba,ita da kanta TAIMIYYAN da ta gaji da wahala ta roƙi a ƙyaleta haka ubangiji ke son
ganinta,Iya ta furta "To shikenan karki damu zanyi magana da Sanin,ni dai abinda nake so kisawa
ranki gorin da ake miki bazai sauya komi ba,akan duk abinda Allah yai nufin kasancewansa,kada
kisawa zuciyanki lallai sai me lalura irin taki zaki bawa dama,ina fa lura da dake sarai kina samun
masoya kece kike kore su ashe sabida wannan manufan ne dake ranki? To wallahi ki kiyayeni
angaya miki sai me lalura ne irin taki kaɗai zaki aura ki samu kwanciyan hankali da soyayya?
Wannan shirmenki ne kawai ke dai ki dinga addu'an Allah yai miki zaɓi mafi alkhairy kawai."
TAIMIYYAH kai kawai ta gyaɗawa Iya alamun gamsuwa da kalamanta,daga haka suka kulle
wannan babin,Iya ta ɗakko mata zancen aminiyanta Hajiya Juwairiyyah,wacce suka rabu da
saduwa da juna,cikin hiran Iya ke sanar da TAIMIYYAH da zaran ta sake samun sauƙi zasu kaiwa
Hajjajun ziyara,ita dai TAIMIYYAH jin Iya kawai take yi amma sam a ranta bata son zuwa ko'ina,
ita sam tafiye-tafiye basu dame ta ba.......✍🏻
Littafin TAIMIYYAH paid book ne da zai zo akan 500 naira only,ga masu buƙatan yin payment
zakui min magana ta wannan number ɗin 08167768704, ko kuma ku turo kuɗin ku kai tsaye ta
wannan account ɗin 0504192664 aisha ibrahim dansabo GTbank.*
_Masu account da Arewa books,zaku dinga siyan sabbin shafuka dalla-dalla akan farashi me
sauƙi,ga yadda zaku siya pages a arewa books kamar haka_ 👇🏻
*Balance* - Zai nuna kudin account dinku da zaku iya sayayyan littafai cikin kasuwar
ArewaBooks.
*Credit/Debit Card* - Hanyar farko kuma mai dadi wajan Recharge din account dinku.
A inda (Enter your amount) za'a saka kudin da akeson Recharge din sai a taba "Proceed". Zaibude
muku inda zaku saka bayanan katin banki, kuna gamawa kudinku zaishiga account dinku kaitsaye
(instant).
--------
*Bank Transfer*
*Airtime Transfer*
Saidai su ba kaitsaye bane (instantly) sai ArewaBooks ta tabbatar da Transfer din, amman bayakai
1hour za'a gansa a Balance.
#Ɗansabo ce#
[12/14, 3:42 PM] +234 703 040 9541: *TAIMIYYAH*
*Page 4*
Kwanaki biyar da suka biyo baya TAIMIYYAH ta samu sauƙi tayi garas,don ta gama amsan
alluranta har tana harkokinta,tun safiyan yau da ta tashi tana jin cin Meat pie,sai dai basu da nama
ya ƙare dole sai ta aika an siyo gashi Nura almajirin Iya kwana biyu bai zuwa ya tafi gida,bayan
tayi wanka ta shirya wajen ƙarfe sha ɗaya har da rabi,ta samu Iya a ɗaki don sanar mata zata fita
cefanan yin Meat pie ɗin ta dawo,don kuɗi sosai take dashi a hannu,sabida duk idan Abie zai
koma yana barin mata kuɗi sosai a hannunta,gefen gadon Iya ta samu ta zauna ganin Iyan akan
dadduma alamun idar da sallan walhan ta kenan tana addu'a,wayanta da taji yana ring acikin
ƙaramar jakan hannunta ta ciro,ganin sunan Mubarak yasa ta share kiran tare da maida wayan
silent,Mubarak wani course mate ɗinta ne da sukai NCE tare,shi a dole son TAIMIYYAH yake da
gaske sai dai ita kuma bai taɓa birge taba,mutuncinsa da take gani da irin taimakonta da yake yi
akan karatu yasa ta kasa blocking ɗinsa,Iya ta waiwayo ta zubawa TAIMIAYYAH idanu,wacce ke
sanye da Hijab kalan Pusha Pink daya haske farar fatanta,tayi kyau ƙwarai duk da cewa babu komi
akan face ɗin illah manyan fararen idanunta da ta sanyawa kwalli,sai bakinta da sai ka kalla da
kyau zaka gane ta goga lip gloss,wani kuma zaiyi zaton pink ɗin janbaki ta saka domin pink lips
gareta.
Iya ta jefa mata tambayan har lokacin idanun Iyan na kan TAIMIYYAH,TAIMIYYAH ta dubi Iya
tana sanar da ita inda zata da abinda zai kaita,Iya ta gyaɗa kai tana faɗin "To shikenan sai kin
dawo ki kula da kyau,ni bana son yawan zuwa kasuwan da kike da Nura na nan ma babu inda zaki
gaskiya,ga ɗari biyu can saman madubi idan kinga Goro me kyau ki siyo min."
TAIMIYYAH da ta miƙe tana me dafa ƙafanta ta fara tafiya take cewa"Bar shi Iya akwai kuɗi
sosai a hannuna bayan Goran ma har Gautan Yalo idan na gani duk zan siyo miki."
"To Allah yayi albarka TAIMI na,Allah fito min da suruki nagari."
Cewan Iya tana bin bayan TAIMIYYAH da kallo,cike da so da ƙauna haɗi da tausayinta me zurfi,a
ciki TAIMIYYAH ta amsa addu'an Iya tana cigaba da takawa har ta fice daga ɗakin,lokacin da ta
fito haraban gidan sai ta dubi part ɗin Abie da ke kulle,ta cigaba da tafiya tana jin kewan su Nahar
na ratsata don kwanaki biyun da sukai ba ƙaramin ɗebe mata kewa da sanya ta farin ciki sukai
ba,sam bata kula da fitowan su Zuhura daga Sashin su ba,sai da ta kusa fita daga gate ɗin gidan sai
ji tayi kawai an janyo Hijab ɗinta ta baya,ta waiwayo tana sauke idon ta akan Basma,kafin ta buɗe
baki don musu magana Zuhura ta riga ta da faɗin "Dallah! Malama bamu waje mu wuce sauri
muke kinzo kina wannan shegen tafiyan naku na guragu,salon a bangajeki ki faɗi ki janyo ma
mutane masifa,yanzu gaba ɗaya na ga wani tashen girman kai kike ji tunda Yaya ya zubda ajinsa
yace ke yake so,ko mai zaici da gurguwa bansani ba,ko da yake kila kyawu da dirin jikin yake
mawa,inma hakan ne banda abinsa idan Kyan da nonuwan ke ruɗansa ga lafiyayyun ƴan mata nan
da suka haɗa komi mitsuww!"
Zuhura ta ƙare maganan da jan dogon tsaki,Basma na taya ta yayinda TAIMIYYAH da suka ja
gefe tayi saurin durƙusawa ƙasa,tuni hawaye sun fara zarya a face ɗinta,har suka fice daga gate ɗin
ta kasa koda motsawa,kanta na duƙe tana ji zuciyanta na mata wani irin zafi kaman ya kama
wuta,ko kaɗan bata fiya ganin laifin su Zuhuran akan duk irin cin mutuncin da suke mata ba,tafi
ganin laifin Umma domin a wajenta suka fara gani,itace ta koya musu hakan duk da cewa
TAIMIYYAN age mate ɗin Zuhura ne watanni biyu kacal ke tsakaninsu,amma ace har Basma da
take qanwan bayanta ta san taci zarafinta akan kawai ta kasance me nakasa,wasu hawayen masu
tsananin zafi suka sake wanke face ɗinta,tayi saurin buɗe jakanta tana ciro hanki da ke ciki ta
shiga share hawayen ,tana rarrashin kanta kaman yadda ta saba,don wannan ba shine karon farko
ba,idan zasu haɗu so dubu to tana da tabbacin sai sun goranta mata sunci fuskanta,taso fasa fitan
kawai ta koma amma sai tayi tunanin Iya zata tsare ta da tambaya,da zaran ta gaya mata yadda
sukai da su Zuhuran kuma to abin bazai kyau ba domin Iya wanke ƙafa zatai ta je taci mutuncin
Umma da su kansu su Zuhuran,wanda hakan bakomi yake sake janyowa TAIMIYYAN ba sai
tsantsan tsana,don haka kawai ta miƙe duk jikinta yayi sanyi ta cigaba ta kawa har ta fice daga
gate ɗin gidan,idanunta sun rine sabida kukan da tayi amma bata da zaɓi haka ta cigaba da tafiya
bisa yadda Allah ya nufeta da takawa,ta miƙo layin nasu sosai tana cigaba da tafiya,wasu yara da
suka zo wucewa ne suka zuba mata ido suna kallonta,ƙaramin cikin su ne ke cewa "Laah!
Gurguwa ce kunga yadda take tafiya." Ya ƙare maganan yana kwatanta ma ƴan uwansa yadda
TAIMIYYAH ke dafe guiwanta tana takawa,TAIMIYYAH da ke cigaba da tafiya duk tana jinsu
yadda suka biyo bayanta suna ta kwaikwayon tafiyanta,idan tace zuciyanta baya shiga ƙunci to
tayi ƙarya ,sai dai babu yadda ta iya haka ubangiji ya nufe ta da kasancewa,kuma bata isa ta hana a
kwaikwayeta ba,sai dai tunawa tayi da cin mutuncin da ƴan uwanta na jini sukai mata a yanzu
yanzu,yasa takaicin yaran raguwa a ranta domin tana ganin gara su yara ne masu hankali ma sunyi
bare su,har ta iso bakin layin su inda zata iya samun abun hawa zuciyanta a cinkushe yake babu
daɗi sam,bata wani jima a tsaye ba ta samu abin hawa tai gaba abinta.
___________
*GRA,Zaria.*
Babban gida ne wanda tun daga nesa me kallo zai san gidan na manya ne masu hannu da
shuni,tsananin haɗuwan ginin da tsaruwansa zai sa me kallo yasan cewa ƙwararru a harkan ginin
zamani ne suka zana asalin taswiran ginin,ginin upstairs ne da tsayawa misalta tsaruwansa ɓata
lokaci ne,daga cikin ƙaton parking space na gidan motoci manya guda uku ne aje,za kai tafiya me
nisa kafin ka isa asalin main entrance na shiga cikin gidan.
Daga ciki gidan babban falo ne a ƙasa,mai ɗauke da ɗakuna guda uku kowanne manne da toilet a
ciki,an zuba kaya na alatu wanda ƙwararrun Interiors ne suka tsara komi bisa muhallin daya
dace,yanayin yadda aka tsara falon da irin kujerun dake cikinsa da sauran kayan decor na
ɗakin,zai tabbatarwa me kallo ba ƙananun kuɗi aka narkar ba, daga hannun hagu wanda nan ne
aka aje 3 Seater,wani kyakykyawan magidanci ne ma'abocin kyawu da cikar haiba,Black Beauty
ne wanda fatarsa ta rine da hutu da jin daɗin rayuwa,hakan ya haifar ma lafiyayyan fatansa da
wani irin fresh,yana da dogon hanci zar tare da manyan dara-daran idanu,abinda ya ƙarawa
kyawunsa armashi shine gashin giransa baƙi siɗik wanda suke a cinkushe,kame yake cikin kujeran
ya ɗaura ƙafa ɗaya kan ɗaya,a shekaru bazai gaza shekaru talatin da bakwai zuwa da takwas
ba,daga saman cinyansa ƙaramar laptop ne yana faman latsawa,dukkanin nutsuwansa yana ga
aikin da yake a cikin computern,sanye yake cikin wata Farar Jallabiya,wanda kana kallo zaka san
manyan kuɗi aka aje kafin a ɗauke ta,dukkanin wajen ya cika da qamshin turaren RALPH
LAUREN,takun takalman dana fara jiyowa daga ɓangaren matakalan benan dake kallo cikin falon
yasani kai dubana wajen,idanuna suka fara hango min fuskan matar da ke sakkowa daga stairs ɗin
sanye cikin kayan bacci riga da wando da suka fiddo suranta a fili,baƙace sai dai tana da
matsakaicin kyawun fuska,don kai tsaye bazaka kirata kyakykyaba,haka kuma bata da muni akwai
ta da cikar halitta me ɗaukan hankali,ko kaɗan bata da makusa,matashiyace da bazata gaxa
shekaru ashirin da takwas ba a duniya,amma duk wanda yai mata kallo ɗaya zai iya bata shekaru
ashirin da biyu sabida yanayin kula da gyara da jikin ke amsa a kowani lokaci,gaba ɗaya tunda ta
doso tsakiyan falon qamshin turarukan da tai anfani dasu masu sanyi da daɗin qamshi suka cika
wajen,abinda yasa magidancin tsayawa cak! daga latsa Cumputern da yake ya ɗago manyan
idanunsa masu cike da kwarjini ya zube akanta,fuskansa babu yabo ba fallasa yai mata kallo biyu
yana me ɗauke kai ya cigaba da aikinsa,ita kuma ta cigaba da takowa cikin takun da ke nuna
yanga da kwarkwasa don janyo hankalin wanda akeyi dominsa,ko da ta iso inda yake kai tsaye ta
zauna kusa dashi tamkar zata shige jikinsa,gaba ɗaya gangar jikinta ya gama mannuwa da tasa,ta
miƙa hannu da nufin ɗauke Laptop ɗin dake bisa cinyansa,yayi saurin kai hannunsa yana dafe nata
hannun, tare da ɗago ido ya zuba mata,fuskansa na tsukewa hakan yasa ta janye hannun nata,cikin
muryanta me cike da iyayi ta fara faɗin "Haba A.Maleek magana fa mu ke daya kamata ace ka
bani lokacinka ka saurareni,amma shine zaka sakko nan ka zo ka zauna kana faman sabgan
gabanka,meyasa yanzu ni bani da ƙima da darajan da zaka xauna ka saurari matsololina? A
gaskiya A.Maleek na fara gajiya da halin ko inkulan da kake nuna min."
Tunda ta fara magana ya tsaida abinda yake ya zuba mata idanunsa dake rikitata,yana jifanta da
wani irin kallo da ita kaɗai tasan ma'anansa,kafin amon muryansa ya fito cike da Isa da izza yake
faɗin "Suhailah ni za ki zo ki tasa kina ɗagawa murya,si'anki ne ni ko ni ɗin ɗanki ne? karki bari
ki fusata zuciyata a wannan karon har kija in ɗauki matakin da ba zai mana daɗi ba,ke kike ɗaukan
maganan da kika zo dashi tana da muhimmanci,ni a wajena maganan banzace tunda bazaki bi
abinda nake so ba,don haka ki barni inji da tarin matsololi da ciwan kan da kike bani,oya tashi ki
bar nan wajen tun raina bai ɓaci ba,kuma wannan ya zama karo na ƙarshe da xaki sake zuwa min
da raini makamancin wannan."
Ya ƙare maganan yana nuna mata hanyan inda ta fito,idanunta ta sauke akansa kaman zatayi
magana amma yanayin yadda ta ga ya haɗe fuska yana jifanta da kallon da ta fi tsana a wajensa,
yasa ta juyawa da sassarfa ta nufi hanyan stairs ɗin,da bibbiyu take takawa har ta haye,ya bita da
wani mugun kallo kafin yaja ƙaramin tsaki yana miƙewa tare da ɗaukan laptop ɗinsa da wayansa
ya rufa mata baya zuwa saman,ɗakinsa direct ya nufa yana aje Laptop ɗin da wayansa,ya fara cire
jallabiyan jikinsa yai jifa dashi bisa Bed,ɗakin yabi da kallo zuciyansa na ɗaukan zafi,sam
Suhailah bata damu da gyaran ɗakinsa ba,abinda kawai tasani ta ciyo wanka tazo ya biya mata
buƙatanta su sha bidirinsu ta kakkaɓe jikinta tabar masa ɗakin,sai lokacin da ta busa iska sannan
zatai gyaran ɗakin,idan kuma tayi sai ta ɗauki wani dogon lokacin kafin ta sake,sai dai shi idan
yana gari ya dage yai gyaran ɗakin da kansa,don bai lamunci wani ƙato ko ƙatuwa su shigo masa
ɗaki da sunan gyara ba,Bathroom ya nufa don yin wanka kaman yadda saba baya iya bacci idan
baiyi wanka ba,lokacin da ya fito kintsa jikinsa yayi ya sanya wasu kayan bacci masu taushi ya
zura slippers ya fito,kai tsaye kitchen ɗin dake nan upstairs ɗin ya nufa,don haɗo shayin da zai sha
kafin ya kwanta,da kansa ya tafasa ruwan zafin ya zuba duk abubuwan da yake buƙata,cikin Mug
ya juye bayan ya tafasa ya fito zuwa wajen dining ɗin da ke manne da corridor ɗin shiga Kitchen
ɗin,Sugar ya ɗiba da slice bread guda biyu ya nufi ɗakinsa,bayan yayi ma ƙofan shiga ɗakin
Suhailah kallo ɗaya ya ɗauke kansa,koda ya kammala shan shayin nasa bakinsa ya je ya wanko
yazo ya kwanta,ba tare da yana jin cewa zai bi takan Suhailah wajen nemanta zuwa ɗakinsa
kaman yadda yakanyi a wasu lokutan ba,don shi yana ɗaya daga cikin irin mazan da sam basa son
raba shinfiɗa da matansu koda sun samu saɓani ne,sai dai yana ganin a yanzu lokaci yayi daya
kamata ya fara biris da lamuranta ko zata saitu tasan abinda ya dace da ita,addu'an kwanciya bacci
yayi ya shafa yana fata yau yayi bacci ba tare da yayi mafarkin da ya saba yi a ƴan kwanakin nan
ba,mafarkin dake tsaya masa arai ya kuma rasa gane kan inda mafarkin ya dosa,lumshe idanunsa
yayi bayan yaja blanket ya rufe jikinsa........✍🏻
Littafin TAIMIYYAH paid book ne da zai zo akan 500 naira only,ga masu buƙatan yin payment
zakui min magana ta wannan number ɗin 08167768704, ko kuma ku turo kuɗin ku kai tsaye ta
wannan account ɗin 0504192664 aisha ibrahim dansabo GTbank.*
_Masu account da Arewa books,zaku dinga siyan sabbin shafuka dalla-dalla akan farashi me
sauƙi,ga yadda zaku siya pages a arewa books kamar haka_ 👇🏻
https://arewabooks.com/chapter?id=62d29e11aa5f8f19bc9621cb
*Balance* - Zai nuna kudin account dinku da zaku iya sayayyan littafai cikin kasuwar
ArewaBooks.
*Credit/Debit Card* - Hanyar farko kuma mai dadi wajan Recharge din account dinku.
A inda (Enter your amount) za'a saka kudin da akeson Recharge din sai a taba "Proceed". Zaibude
muku inda zaku saka bayanan katin banki, kuna gamawa kudinku zaishiga account dinku kaitsaye
(instant).
--------
*Bank Transfer*
*Airtime Transfer*
Saidai su ba kaitsaye bane (instantly) sai ArewaBooks ta tabbatar da Transfer din, amman bayakai
1hour za'a gansa a Balance.
#Ɗansabo ce#
[12/14, 3:42 PM] +234 703 040 9541: *TAIMIYYAH*
*Page 5*
_________
Ƙarfe goma da rabi na dare TAIMIYYAH ce ke zaune tana kallo a falon Iya,ita da Ladi me aiki ne
da yake nan take kwana Ladin tana da ɗakinta daga waje,wayan TAIMIYYAH ne ya fara haske
alamun kira na shigowa sabida ta sanya wayan a silent,ta kai hannu ta ɗauki wayan tana ganin
sunan Yah Deeku ɓaro-ɓaro kaman yadda tai saving number ɗinsa,ƙaramin numfashi ta sauke
kafin ta danna received takai kunni,zuciyanta na sauya bugu domin rabonta da shi tun ranan da
yabar part ɗinsu a fusace,muryansa ta jiyo yana faɗin "Hello!" sai ta lumshe ido tana amsawa da
faɗin "Hello! Yah Sadeeq ina yini."
Memakon ya amsa sai kawai ya zarce da faɗin "Yanzu Zainab ban isa ki neme ni kiji lafiyata
ba,ina kallo zaki buɗe status ɗina amma ban isa ko gaisuwa ya haɗamu ba,kina ganin hakan shi
zaisa idan ma zan janye manufata ne in janye eyim?"
Ya dakata yana jiran yaji me zata faɗi,TAIMIYYAH da tai kasaƙe rike da waya a kunni sai ta
sauke numfashi tana miƙewa tare da dafa ƙafanta ta fara takawa zuwa hanyan ɗakinta,cikin
muryanta dai dake kashe gaɓɓan jikinsa take faɗin "Sorry Yah Deeku ba haka bane ina ta so in
maka magana Allah ne bai nufa ba,ya kake ya Kaduna ya aiki kuma."
"Duk basu na tambayeki ba malama,kuma bana son wannan sunan kin sani amma bazaki daina
faɗi ba ko? Zan kamaki ne bari dai in shigo gobe,yanzu dai sanar dani me zaki dafa min kafin in
shigo girkin ki kawai nake jin ci Baby kinji?"
Sadeeq ya ƙare magana cikin wani irin salo da shi kansa bai san yanawa TAIMIYYAH illa
ba,zuwa lokacin tayi kwance a bed tana tada kai da pillow,hannunta ɗaya dafe da wayan a
kunni,yanayin salon da yai maganan kawai ya bata tabbacin rigimansa da neman magana ne kawai
ya tashi,inba haka ba ita ta mance rabon daya ƙirƙiri cewa sai girkinta zai ci,sanin idan ta bijire
wani sabon rigiman ne yasa ta faɗin "Baka da Matsala Yayana,faɗi me kake son ci ka ga da yin
safe sai aje cefanen abinda babu."
Ya saki murmushi daga ɓangarensa,kafin ya gyara kwanciyansa yana jin tasirin muryanta da salon
shagwaɓarta na kassara gaɓɓan jikinsa,tuni idanunsa ke hasko masa yadda take maganan ɗan
ƙaramin bakinta na motsawa,ya lumshe idanunsa ya buɗe kafin ya furta "Bani da wani zaɓi ai
kinsan duka irin abincin da nafi so,yanzu me kike yi yau ki ka kai har to 11pm baki bacci ba?"
Ya ƙare maganan da jefa mata tambaya,domin ya santa da baccin wuri wani lokacin tara ma ta
daɗe da yin bacci,TAIMIYYAH ta sake yin ƙasa da murya tana faɗin "Kallo nake na wani film da
ya ɗauke hankalina."
Ya sake jafe mata tambayan,TAIMIYYAH ta waro ido waje kaman tana gabansa,kafin ta wani
kwaɓe face cikin shagwaɓe murya ta furta "Kai Yah Deeku ni dai bance ba kawai dai Film ɗin na
da kyau ne,kasan Korean Films akwai ɗaukan hankali."
"Shikenan Baby idan na zo kya bani labarin Film ɗin,wannan Old Woman ɗin ta jima da yin bacci
kenan,ki gaisheta zuwa da safe kice wallahi idan na iso gobe rigima zamuyi sosai da ita,tunda
yanzu ta daina ƙaunata so take ta zama ƴar ta'addan Soyayya."
Cewan Yah Sadeeq da wani irin salon da yasa TAIMIYYAH fashewa da dariya,sai da tayi me
isanta yana sauraranta da jin kaman ya rufe ido ya ganshi gabanta,kafin ta tsaida dariyan tana
faɗin "Kai Yah Deeku Iyan ce tazama ƴar ta'adda daga faɗin gaskiya."
Ta ƙare maganan da dariya a muryanta,hakan yasa Sadeeq taɓe baki kaman TAIMIYYAN na
kallonsa,kafin ya furta "Okey gaskiya ma take faɗi lallai Baby,any way bye karki ɓata mood ɗina
yanzu in kasa bacci."
Bai jira cewan komi ba yai hanging up,TAIMIYYAH ta sauke wayan daga kunni tana me taɓe
baki,ko kaɗan bata ji duk wani salonsa zata bari yai tasiri akanta,bare ta jefa kanta acikin masifan
da bazata iya fita ba,don a ganinta yin soyayyah da shi babban masifa ne a gareta domin Umma ba
zata taɓa bari ta sami nutsuwan zuciya ba,aje wayan tayi tana hamma alamun baccin yazo da
gaske,sanin Ladi zata kashe kayan kallon idan taji bacci yasa TAIMIYYAH nufan toilet ta ɗauro
alwalan kwanciya bacci,already tana sanye da kayan bacci shiyasa tana fitowa ta kashe fitilan
ɗakin ta haye bed,bata ɗauki lokaci ba kuwa baccin yai gaba da ita.
_________
Ƙarfe goma na safe(10:00am) A.Maleek Ibrahim ya fito daga wanka,tunda ya sanyo kansa cikin
Bedroom ɗin nasa qamshinta daya shaƙo ya sanar dashi wacece,hakan yasa ya ɗauke kai sam bai
kalli inda take ba, ya taka zuwa gaban dogon mirrow ɗin ɗakin,yana cigaba da tsane ruwan jikinsa
yana jin tasirin idanunta da ke biye dashi,amma sam yaƙi duban sashin da ta zauna daga bakin Bed
ɗinsa idanunta akansa "Darling good morning." Cewan Suhailah cikin narke murya,amma
memakon ya amsa sai yai biris da ita yana cigaba da abinda yake,hakan yasa ta miƙewa ta isa
garesa,ba tai magana sai ɗauke man da yake shafawa da tayi,ta lakuta kaɗan ta murza a tafukan
hannunta,tana me kai hannu don fara shafa masa amma sai ya kama hannunta ya riƙe,manyan
idanunsa masu cike da kwarjini ya zuba mata fuskansa a tsuke yake tsaf babu annuri,cikin muryan
da idan yai mata magana dashi take sanin babu alamun wasa ya fara faɗin "Bana so Suhailah,sai
yanzu ne kika san ki ɗakko ƙafa ki shigo ɗakina,meya hanaki zuwa ki kwana da mijinki a daren
jiya?Bayan kinfi kowa sanin na tsani raba shinfiɗa,look! Suhailah wallahi kinji na rantse na fara
kaiwa maƙura da halayyanki da sabbin banzayen ɗabi'un da kike shigowa dasu a zamantakewan
auren mu,idan ma sabbin ƙawaye kikai da suke neman canzaki to kisani bazan ɗauka ba,don haka
tun wuri ki dawo cikin hankalinki ina nan ban canxa ba daga Maleek ɗin da kika sani abaya
ba,karki ga ina nuna miki so ki ɗauka na sauya ne ban sauya ba,kuma zan baki mamaki nan kusa."
Ya ƙare maganan yana sakin hannuwanta,tare da raɓa ta ya wuce zuwa wajen kayansa da ya fiddo
zai saka,Suhailah ta bishi da kallo kafin ta fara faɗin "Haba My A.Maleek duk me yayi zafi haka?
Ni gaba ɗaya wannan dawowan naka na rasa me ke fusata zuciyanka akaina,ni wani sauyawa nayi
don Allah? Gayu iya gayu ina maka ta ina na rage ka,gyaran ɗakinka da girki su kaɗai ne nasan
matsalata,kuma nace maka zan samo masu aikin da zasu dinga yi kaine ka nuna baka so,ni kuma
kasan na tsani aikin gyara da girki tun ina gida,kuma a hakan idan na samu time da kaina nake
zagewa in gyara ko'ina a ɗakinnan,girki kuma kai da kanka ka yaba cewa Ameena ta iya girki,to
me kake so kuma dani Maleek?"
Ta ƙare maganan tamkar zata fashe masa da kuka,tana tsananin son sa bata faye son ɓata ranshi
ba,amma akan wannan matsalan sam bata ji zata iya biye masa ta koma yadda yake so ɗin,bata
son girki a rayuwanta sam tafi gane a girka taci ta kwanta,bata son moriya da yawan aikace-aikace
amma shi Maleek so yake ta zama ƴar bautansa,komi na hidimansa yace sai itace da kanta zatai
masa komi,hatta girki yafi so idan yana nan tayi masa abinci da kanta,ita kuma hakan ne take
ganin bazata iya ba,wani irin kallo ya juyo ya watsa mata kafin cikin kaushin murya ya fara faɗin
"Okey! Kina iya bani waje tunda baki san me nake so da ke ba,amma ina so kisa a ranki duk randa
kika ji nazo da maganan sake aure kiyi kuka da kanki ne,domin na fara ji ajikina dole zan sami
wata abokiyan rayuwan da zata iya sadaukar da lokacinta domin yimin hidima,tare da bin
dukkanin umurnina."
Suhailah da maganansa ya mugun girgizata,game da zancen sake auren daya shigo dashi tayi
saurin kallonsa a razane,za tai magana ya daka mata tsawa yana nuna mata hanyan fita,hakan yasa
Suhailah fashewa da kuka tana ficewa daga ɗakin nasa,ya bita da tsaki yana cigaba da
shirinsa,cikin mintuna biyar ya gama kintsa kansa cikin wani lallausan farin yadi,da yai masa
mugun kyau links ɗin hannun rigan ya gama sawa,ya isa gaban madubi ya ɗauki turarensa na
RALPH LAUREN yana fesawa gaba ɗakin ya sake rinewa da daddaɗan qamshinsa,wayoyinsa ya
kwasa ya fito zuwa down stairs.
A ɓangaren Suhailah kuwa tana fitowa daga ɗakinsa,ta wuce ɗakinta tana ɗaukan waya ta kira
Hajiyansa,kuka ta sanya mata tana sanar da ita cewa Maleek aure zai ƙara ya daina son ta da
ƙaunarta,bata aje wayan ba sai da Hajiyan ta gama rarrashinta da bata tabbacin wasa A.Maleek
yake kawai,sai dai sam ta kasa samun sukuni hakan yasa ta fito ta koma ɗakinsa, ganin baya nan
yasa ta san ya sauka ƙasa kenan,sai kawai ta biyo bayansa zuwa falon ƙasa,direct ɓangaren dining
ta nufa don tana da tabbacin wannan time ɗin yake zaman karya kumallo indai yana ƙasan ko yana
gari,ilai kuwa can ta hangesa riƙe da cup ɗin Tea yana kurɓa,gabansa plate ne daya zuba
chips,Suhailah ta ja kujeran dake kusa dashi ta zauna,tana sake duban yadda ya haɗe fuska kaman
hadarin watan Augusta,cikin narke murya ta fara faɗin "My Maleek don girman Allah kayi
haƙury,insha Allah zan gyara duka kuskurena,amma don Allah karka sake min irin wasan ɗazu wai
zaka iya samo wata bayan ni,wallahi zuciyata zata iya tarwatsewa,kai min rai don Allah ka bar
shigo da irin wannan wasan,in dai abinda kake son in dinga yima da kaina ne zan dingayi Allah
kuwa zan daure kaji Baby."
Ta ƙare maganan tana kwantar da kanta a kafaɗansa tare da kama hannunsa ta shiga
murzawa,hakan yasa ya dubi cikin idanunta tare da watsa mata harara,kafin ya sake kurɓan Tea
ɗinsa ya aje cup ɗin yana faɗin "Ni ɗin ne nake wasa Suhailah?Wato a wasa kika ɗauki maganan
ko Hmm! To maganan Planing ɗin da baki fasa ba kuma fa? Ko kina ɗaukata a sakarai ne bansan
duk wani motsinki ba,to ki sani ni bazan iya cigaba da zama da macen da bata shirya haɗa zuri'a
dani ba,in karatune ina sha kin ƙare har bautan ƙasan duk kin gama,to ina so kisa a ranki nan da
wani lokaci kaɗan komai zai iya faruwa,abinda kike ɗauka wasa zai matuƙar baki mamaki."
Kafin Suhailah ta sami ƙwarin guiwan yin magana,wayan A.Maleek ɗin ya fara kiɗa alamun
shigowan kira,daga yana yin ringing ɗin yasan Hajiyansa ce,don haka yayi hanzarin ɗauka yana
fara gaida ta,memakon ta amsa sai kawai ta shiga tuhumansa akan cewa me zaisa ya fara ɗagawa
Suhailan hankali da zancen cewa zai sake aure,ta rufesa da faɗa ba tare da ta bashi daman kare
kansa ba,daga ƙarshe ta kashe wayanta ta bar Maleek da bin wayan da kallo,kafin ya maida
dubansa kan Suhailah ta dai tsumu alamun rashin gaskiya,ya aika mata da mugun kallo yana faɗin
"Bar kallona kinyi da ido kaman Munafuka,zan baki mamaki wallahi domin sai na sanarwa
Hajiyan abinda kike aikatawa wanda sai tayi fishi da ke,xanga ƙarshen ji dake da take yi alhali ke
ko haɗa jini da ita baki shirya yi ba,sai gayu da ƙaryan kina son ɗanta da kishinsa,haka ake son
Suhailah?"
Suhailah dai tai ƙus zuciyanta na faman bugawa,idan akwai abinda baza ta so ba shine MALEEK
ya tona mata asiri a wajen Hajiyansa ta gane cewa,itace ke anfani da maganin hana ɗaukan
ciki,tasani Hajiya tafi kowa tsanan tsarin Iyali,kuma a ƙagauce take da ta samu jika daga gare
su,ganin yana shirin miƙewa ya bar wajen don tuni ya kammala cin abincinsa,hakan yasa ta tashi
ta ruƙunƙumeshi tana magiyan kada ya faɗiwa Hajiya,ita wallahi ta daɗe da daina anfani da komi
na hana ɗaukan ciki,lokaci ne kawai baiyi ba,sam Maleek fuskansa babu sassauci ya zare ta daga
jikinsa yana takawa ya bar mata wajen,wayoyinsa kawai ya kwasa a falo da mukullin mota yai
waje don barin mata gidan ma baki ɗaya,zuciyansa na tunzurasa akan yaje ya fayyace wa Hajiyan
irin rayuwan da yake yi da Suhailah,ko Hajiyan zata daina goyan bayanta da ɗaure mata
gindi,hakan yasa ko da ya tada mota ya baro gidan kai tsaye hanyan da zai Kaishi Gonan Ganye
ya nufa,inda a nan ne ya tanfatsawa Hajiyan nata ginin.........✍🏻
#Ɗansabo ce#
*TAIMIYYAH*
©️Ayshat Ɗansabo lemu ✍🏻
*Page 6*
Lokacin da ya isa gidan Hajiyan bayan ya gama yin parking a wajen da aka tanaza don adana
motoci,sai ya dakata bai fito ba yana ansa call,lokacin ne kuma Bilya me gadi ya iso tare da
zubewa yana kwasan gaisuwa,hannu kawai A.Maleek da har lokacin ke amsa waya ya ɗaga
masa,hakan ya ankarar da Bilya cewa uban gidan nasa amsa waya yake,sai ya tashi ya bar
wajen,da ido A.Maleek ya bishi tausayin dattijon na sake ratsa shi,lokacin daya kammala ansa call
ɗin sai ya fito yana kulle motan ya fara takawa zuwa cikin gidan,tafiya yake cikin takunsa me cike
da nutsuwa da zafin jini,kallo ɗaya za kaiwa fuskansa da ba ma'abocin fara'a sosai ba kasan cewa
miskili ne na gaske,lokacin da yaiwa falon gidan tsinke bakinsa ɗauke da sallama,dai-dai lokacin
ne Hajiya Aysha ta fito daga wani corridor,hannunta riƙe da waya da wani Cup,amsa sallaman
nasa tayi hancinta na cigaba da shaƙo qamshin turaren RALPH LAUREN,ta ƙariso cikin falon a
lokacin da A.Maleek ɗin yaiwa kansa mausaki a cikin kujeran 2 Seater,kusa da kujeran da ya
zauna nan Hajiya ta zauna itama,domin indai har zatai zaman falo to wannan kujeran dake daura
da inda A.Maleek yake nan ne wajen zamanta,shiyasa ma yaima kansa mazauni anan ɗin,idanunta
fes akansa yake lokacin da take aje wayanta da Cup ɗin da ke hannunta,A.Maleek yayi saurin
zamowa daga kan kujeran ya zube a ƙasan Carpet yana kwasan gaisuwa,Hajiya Aysha da idanunta
ke kansa ta saki lallausan murmushi tana amsa gaisuwan tilon ɗan nata namiji,kafin ta ɗaura da
faɗin "Ina ka baro Suhailan da ka sanyata kuka tunda farin safiya,har da ruɗata da cewa zakai mata
kishiya duk awani dalilin?"
A.Maleek da ya cigaba da zama daga ƙasa ba tare da ya koma bisa kujeran ba,ya ɗaga manyan
idanunsa da ya gada wajen Hajiyan yana faɗin "Hajiya har yanzu dai na lura baki daina ma
Suhailah kallon ƙaramar yarinya ba,kullum cikin goya mata baya kike bakya son laifinta
sam,wallahi Hajiya Suhailah bata jin maganata,sam ba ta ma ɗauki aure da wani muhimmanci
ba,amma a yau ina son warware miki irin zaman da muke ko zaki daina goya mata baya."
Ya dakata da maganan yana kallon Hajiya,wacce ta nutsu tana sauraransa kafin ta gyaɗa kai tana
faɗin "Ina jinka sanar dani menene ke faruwa da rayuwan auren naku?"
A.Maleek yai ƙasa da kansa kafin ya fara da faɗin "Hajiya Suhailah bata kula dani,duk wani aiki
da kika san macen ƙwarai xata tsaya taiwa mijinta Suhailah bata min,ban isa ince ina son abu ka
za ta tashi ta girka min da kanta ba sai dai mai aiki,gyaran ɗakina sai ta bushi iska take yi,shima
ina ga a wata baifi tayi sau biyu ba,ni ne da kaina idan na shigo gari zan zage ingyara komi idan
ina son ganin ɗakin yadda nake buƙatansa,sannan babban matsalata da ita rashin son
haihuwa,Hajiya Suhailah ita da kanta ta kai kanta asibiti ta fara amsan Pills na tsarin iyali ba tare
da sani na ba,a cewanta tana tsaka da karatu akai bikinmu baxata taɓa yadda ta ɗauki ciki ba,yanzu
bikin mu shekaru biyar kenan ta gama karatun tayi Service amma bata daina amsan alluran hana
ɗaukan ciki ba,na ɓoye miki gaskiyan magana cewa babu abinda muke yi ne,sabida na ga idanunki
ya rufe a nuna mata soyayya,sam baki son laifinta san......"
"Dakata Abdul-Maleek kana so kace min ita Suhailan da kanta ne ta yanke ma kanta yin tsarin
iyali ba tare da izininka ba ma, yaushe Suhailah tayi buɗewan ido har haka,ina tarbiyan dana
bata ?"
Hajiya Aysha ta katse A.Maleek a fusace,tare da jero masa waɗannan tambayoyin,fuskanta gaba
ɗaya na rinewa da zallan ɓacin rai,hakan yasa A.Maleek dubanta yana cigaba da faɗin "Nima
abinda na jima ina tambayan kaina kenan Hajiya,ina ga qawaye ƴan duniya tayi da suke son
sauketa akan turban da kika ɗaurata akai tun farko,to ni a gaskiya na gaji da halayyan Suhailah
kuma bazan iya zama da macen da bazata haihu dani ba sai dai ƙaryan nuna min soyayyah,shiyasa
nace a yau zan fayyace miki watakila ke idan kika zaunar da ita kikai mata faɗa zata ji naki,ta
canza banzayen halayyan data fara koya,shiyasa na shigo da maganan sake aure kuma am very
serious idan har bata sauya ba zan tabbatar mata da cewa ni ba zata maida ni sakarai ba,koma ta
canza ɗin ina ji ajikina akwai abinda zai faru nan ba da jimawa ba."
A hankali A.Maleek ya zayyanewa Hajiyan nasa irin mafarkan da yake a ƴan kwanakinnan,da
wata wacce sam ba'a nuna masa zahirinta illah idanunta masu haske da ake nuna masa a
mafarkin,sai hannayenta da take miƙo masa tana kuka alamun neman taimako,amma da zaran
yakai hannunsa don kamo nata yake farkawa daga mafarkin ,Hajiya Aysha bayan gama saurarensa
tai shiru tare da shiga tarin nazari,matsalan Suhailah da mafarkin da A.Maleek ɗin ke yi suka taru
suka kulle kanta,har ta rasa wani tunani ma zatayi sai zuwa wani lokaci ta numfasa,batai masa
magana ba sai wayanta da ta ɗauka ta shiga neman layin Suhailah,bugu biyu ta ɗaga Hajiya bata
jira komi ba ta furta "Ma za yanzu kizo nan gida ki sameni."
Daga haka ta kashe wayanta zuciyanta na cigaba da ɗaukan zafi akan lamarin Suhailah,tabbas tana
ganin a wannan karon dole ta ɓata ran Suhailan don ko kaɗan bazata lamunci irin wannan sakarcin
ba,sannan bata tunanin idan har Suhailah ta cigaba da nuna rashin son haihuwa da gudan jininta to
tabbas ita da kanta ma zata nemo masa wata macen ya aura ko bai so ba,zaman awa ɗaya sukai
suna cigaba da tattauna matsalolin Suhailah,kafin motar Suhailah ta iso gidan Hajiyan,ta shigo
wurjanjan don tunda taji kiran da Hajiyan ke mata tasan ba lafiya ba,A.Maleek ya gama
kwancewa Hajiyan komi,hakan yasa ta shigo jikinta a sanyaye tana faman raba ido,kallo ɗaya
A.Maleek yai mata ya ɗauke kai yana sake haɗe fuskansa tsaf babu alamun wargi,kusa da Hajiya
ta je ta zauna tamkar zata shige jikinta,amma sai Hajiyan ta shiga ture ta tana jifanta da wani
mugun kallo take faɗin "Dallah! Matsa ki bani waje ashe ke ɗin sakaryace mara hankali
Suhailah,irin tarbiyan dana baki kenan,ko ni haka kika taso kika ga inama marigayi rashin albarka
da rashin biyayya? Maxa sanar dani gidan uban da kika kwaso dukkanin halayyan da Maleek ya
sanar dani,har kinyi buɗewan idon da zaki tsarama kanki rayuwa Suhailah,a gidan ubanwa kika
taɓa ganin inda Haihuwa ya hana karatu? Har da zaki je ki cuci kanki ki fara tsarin iyali alhali ko
haihuwan fari baki taɓa yi ba."
Inda Hajiya Aysha ke shiga ba tanan take fita ba,taiwa Suhailah tas wacce zuwa lokacin kuka sosai
takeyi,cike da tarin nadaman Planing ɗin da tai tayi abaya,da gaske takewa Maleek ta daina shan
pills ɗin da takeyi,kusan shekara guda kenan rabonta da shan komi amma ciki yaƙi samuwa,shi
kuma ya kasa yadda ta daina ɗin abinda yasa suke ta samun saɓani dashi kenan,jikin Hajiyan ta
koma tana cigaba da kuka sosai,Hajiyan ta sake ture kanta daga jikinta,don da gaske haushin
Suhailan me zafi take ji,cikin muryan kuka Suhailah ke faɗin "Don girman Allah Hajiya kuyi
haƙury ke da Yah Maleek,wallahi zan gyara duk halayyan da baya so,amma bazan iya ganinsa da
wata mace ba bayan ina raye,wallahi Hajiya na daɗe da daina tsarin iyali shekara guda
kenan,Allah ne bai kawo rabon ba shi kuma ya kasa yadda na daina."
"Ta ya za'ai dama ya yadda kin daina ɗin,tunda lokacin da kika faro ba da yawunsa kika fara
ba,Allah yasa ba illah kikai wa kanki da kanki ba,inko har wani matsalan kika janyowa
kanki,kinga maganan kice baki son ganin mijinki da wata mace ma bai taso ba,don ni da kaina zan
masa wani auren don bazan zuba ido banga ƙwansa a duniya ba,alhali shi kaɗai na mallaka ɗa
namiji da Allah ya bar min ya rayu,tunda ke shashashace baki san inda kanki ke miki ciwo ba,in
banda ke ɗin sakaryace har wani tsoron haihuwa zakiyi don kina boko bayan gani a raye,ki
gayamin wani wahalan raino zaki sani inda kin haihun alhali kinsan kuna dani a raye,to kisawa
ranki zama da kishiya nan ba jimawa ba matuƙar ya tasaki agaba kuka je wajen likita aka tabbatar
alluran da kikai ne ya janyo miki wani matsalan."
Hajiya Aysha ta ƙare maganan cikin fusata tana ji tamkar tun a yanzu ɗin ta rufe Sunailan da
duka,Suhailah da kalaman Hajiyan ke sake kiɗima zuciyanta idan ana shigo da zancen Maleek ɗin
zai iya sake aure,ta sake rushewa da kuka so take ta je ga Maleek ɗin ko shi zai tsaya ya
saurareta,amma kallo ɗaya tai masa taga yadda shi ɗinma ya sake ɗinke fuska yana jifanta da
wannan shu'umin kallon nasa me ɗaga hankali,ai sai ta kifa kanta jikin kujera tana cigaba da
rasgan kuka,yayin da Hajiya ta cigaba da rufeta da faɗa daga baya ta koma nasiha,hakan yasa
Maleek zame jikinsa yai sallama da Hajiyan ya bar gidan,zuciyansa fes don baiyi tunanin Hajiyan
zata iya rufe ido taci zarafin Suhailan har haka ba,idan yana tuna irin son Suhailan da yake rufe
idanun Hajiyan,sabida kawai Suhailan ta fito daga tsatson jinin qanwanta da suka fito ciki guda,ta
rasu ta barwa Hajiyan Suhailan tun tana da shekaru biyar a duniya,tuƙi yake yi yana fata da
addu'an Allah sa dukkanin faɗa da nasihan Hajiyan suyi tasiri a zuciyan Suhailah har ta gyara
ɗabi'unta da baya so,wayansa da yake ruri ya kalla ganin sunan abokinsa Naseer ne yasa shi ɗaga
wayan yana sanar da Naseer ɗin inda zasu haɗu.
___________
Tunda TAIMIYYAH ta tashi take ta tunanin ta yadda zata tsiri yiwa Yah Sadeeq ɗin girkin da ya
buƙata,ba tare da Iya ta gane don shi tayi ba,bare har ta rufe ta da faɗa,dubara ne ya faɗo mata
lokacin da ta kammala shirinta cikin wata rigan atamfa da akaiwa ɗinkin free gown da yai matuƙar
yi mata kyau,ɗankwalin kayan ta ɗaura tana bin jikinta da turarenta me sanyi da daɗin
qamshi,agogo ta kalla taga lokacin ɗaura lunch ɗinsu yayi,hakan yasa ta fita da ƙwarin guiwanta
zuwa falo,kaman yadda tai tunani Iyan na hakince cikin kujera,ta tasa TV agaba tana kallon
wa'azin da ake haskawa a tashar Manara,TAIMIYYAH ta cigaba da takowa cikin irin tafiyanta da
sai da taimakon dafe guiwan ƙafanta me laluran take iya tafiya,ta iso kusa da Iya tana faɗin "Iya
yau kuma me Ladi zata girka ne ko dai in amshi girkin tunda nayi sarai sosai,sai in dafa mana ko
Rice and Stew ne,ke me son wake sai a dafa miki waken daban."
Ta ƙare maganan tana ɗauke idanunta daga kan Iya,ita kuma Iyan sai ta zubawa TAIMIYYAH ido
tana jin ƙaunarta na sake zama a zuciyanta,rashin son jikin TAIMIYYAN da jajircewanta wajen
iya sarrafa nau'in girke-girke na tsananin birgeta,don haka bata kawo komi ba ta gyaɗa kai cike da
gamsuwa take faɗin "Hakan ma yayi TAIMI na indai zaki iya sai ki shiga Kitchen ku haɗu da
Ladin kuyi girkin,amma ni ina son a dafa raguwan Kazan nan da ke cikin Freezer,ayi farfesun ta
kawai ki ɗan saka dankalin turawa irin yadda kike mana yai daɗinnan a zuba kayan qamshi yaji
sosai kinji ko."
TAIMIYYAH ta gyaɗa kai lokacin da take miƙewa,ta dubi Iya tana faɗin "To Iya duk za'ayi yadda
kike so bari inje inga me Ladin take yi."
Daga haka TAIMIYYAH ta nufi Kitchen ɗin nasu,zuciyanta fes kaman ƙanƙara don ta san ta gama
da shafin rigiman Yah Sadeeq ɗin,itace tayi komi Ladi kawai blanding kayan miya tai mata,sai
ganyen Salad da ta sata yanka musu don TAIMIYYAH bata son cin abinci babu ganye,shiyasa
basa rabo da aje kayan Salad ko na Coleslow,bayan kammala abincin TAIMIYYAH ta kwashe su a
kulolin da suka saba zuba abinci Ladi na ɗauka tana fita dasu zuwa falon Iya,tana jerawa a
ɓangaren da suke cin abinci,sam bata wani wahal da kanta ɗibarwa Yah Sadeeq ɗin daban ba,don
tana da tabbacin nan Sasan nasu zai yi masauki yaci abincin,Zoɓon da ta tsaya kammalawa sawa
Flavour ta ƙarisa haɗawa ta miƙawa Ladi tasa shi cikin ƙaramin fridge,ita kuma ta juya tabar
Kitchen ɗin zuwa ɗakinta don yin sallan Zuhur ganin time yaja,lokacin da ta idar memakon ta fita
falo taci abinci sai tayi kwanciyanta a gado,ta ɗauki wayanta tare da kunna Data ta hau
online,shiga nan fita can har ta ɗauki lokaci ba tare da ta damu ba,sai da taji Iya na ƙwalla mata
kira sannan ta fito,a tsaye ta samu Iya riƙe da wani leda a hannu,fitowan TAIMIYYAN yasa Iya
maida dubanta gareta tana faɗin "Maza ɗakko Hijab ki zo ki miƙawa Zuwaira wannan
saƙon,turaren wuta ne aka aiko min na ɗibar musu,ki kuma sanar mata yau bana buƙatan abincin
daren su,Ladi zata tuƙa min tuwan dawa ne zuwa anjima."
TAIMIYYAH ta gyaɗa kai tana faɗin "To Iya bari in ɗakko Hijab ɗin."
Daga haka ta koma ɗaki ta sanyo Hijab ɗin sallanta ta fito,ledan da kwalban turaren wutan yake ta
ɗauka tai waje,tana takawa a hankali har ta isa sasan Baba Sanin........✍🏻
#Ɗansabo ce#
[12/14, 3:42 PM] +234 703 040 9541: *TAIMIYYAH*
*Page 7*
Sallama TAIMIYYAH tai tayi a falon babu amsa,hakan yasa ta sanya kanta cikin falon sosai tana
raba idanu,zuciyanta na tariyo mata baya kaman basuyi dadalmaya a sashin ba,gashi yanzu
shigowa ma tayi hira da ƴan uwanta ya gagareta,ba don bata so ba sai don yadda su ɗin suka juye
suka maida ta tamkar mujiya a cikinsu,zuciyanta yai nauyi tana jin tasirin damuwan hakan da take
dannewa can ƙasan ranta na taso mata,hanyan da zai sada ta da asalin main Kitchen ɗin su Umman
ta nufa,don tana hasashen samun ta acan tunda har ta fito bata ji an kaiwa Iya abincin rana
ba,watakil yau ɗin sunyi ranan girki ne kaman yadda suka saba duk ranan Friday sukan yi ranan
gama abincin rana,sabida yawan aikin da ke ƙaruwa tunda shi ma Baba Sanin sai Weekend yake
dawowa daga can Kano inda yake aiki,kaman yadda tai hasashe haka ya kasance,tana sanya kanta
cikin Kitchen ɗin bakinta ɗauke da sallama,idanunta akan Umma da ke tsaye jikin Cabinet na
Kitchen ɗin ya fara sauka,su Mero me aiki nata faman hidiman kammala abinci ana kwashe su a
manyan kulas,TAIMIYYAH ta gaida su Mero tana cigaba da takawa zuwa inda Umma ke
tsaye,wacce sarai taji shigowan TAIMIYYAN tana kuma jin gaisuwan da take ma su Mero amma
bata juyo ta dube ta ba "Sannu da aiki Umma ina yini."
Cewan TAIMIYYAH lokacin da ta isa daf da Umman,sai lokacin Umma ta juyo ta zuba mata
idanu,fuskanta a haɗe tana faman yatsina,ta amsa gaisuwan da faɗin "Lafiya." A taƙaice daga haka
ta cigaba da rufe tray ɗin da tai raping Salad,ganin hakan yasa kai tsaye TAIMIYYAH ta aje ledan
saƙon a saman Cabinet ɗin tana faɗin "Gashi inji Iya." Daga haka sai ta juyo don baro sashin baki
ɗaya,su Mero na ce mata a gaida Iya,Umma ce tayi saurin dakatar da ita tana faɗin "Ke! zo nan ki
ɗauki wancan kwandon abincin ki kai min dining ɗin falo ."
TAIMIYYAH ta waiwayo tare da sauke manyan idanunta akan ƙaton Basket ɗin,ta nufesa tana
ɗauka ta cigaba da tafiya ahankali dafe da ƙafanta me laluran,ɗaya hannun riƙe da Basket ɗin da
aka jere kulolin abinci ta fito zuwa falo,da Zuhura taci karo wacce ta fito daga ɓangaren ɗakunan
baccin su,TAIMIYYAH ta ɗauke idanunta daga kanta tana wucewa inda aka aiketa,ta aje kwandon
abincin tana shirin juyawa don ficewa daga sashin nasu,sai ga Umma ta baro Kitchen ɗin ta fito
falon,idanunta akan TAIMIYYAH tana dubanta daga sama har ƙasa,takaici da tsanan
TAIMIYYAN na sake kamata,musamman in ta tuna yadda Sadeeq ya iya duban tsakiyan idanunta
ya sanar da ita wai wannan musakan dake gabanta yake so,kuma son ma da aure hakan ba ƙaramin
taɓa zuciyanta yake ba, "Koma ki zauna magana zanyi da ke shu'uma kina faman wani ƙus da kai
munafuka."
Cewan Umma idanunta fes akan TAIMIYYAH,tuni TAIMIYYAH tayi saurin zama daga ƙasan
tiles ɗin wajen,Umma kuma tayi zaune akan Kujeran da ke kusa da ita,yayin da Zuhura ma tayi
zaune kusa da Umma domin bazata so tijaran da Umma zataiwa TAIMIYYAH akan Yayansu ya
wuce taba,Umma ta soma faɗin "Wato ke dai wannan musakan baki jin magana ko,wai haka
gurugu ke da taurin kai ne ni Zuwaira,yo inba taurin kai ba ke da nai miki iyaka da ɗana tun da
daɗewa,shine kika cigaba da ribatan zuciyansa,har ya samu ƙwarin guiwan kallon idanuna yana
sanar dani wai kece zaɓinsa,to bari kiji in gaya miki ni Zuwaira indai ni na kawo Sadeeq
duniya,kuma Nono na ya tsotsa to na haramta soyayya a tsakaninku bare maganan aure ya shigo,in
banda ma shi ɗin sakarai ne duk matan duniya ya rasa wacce zuciyansa zai so sai gurguwa
musaka,me zaici da ke ya aure ki yace ya auri wa? Salon ya kunya tani ya zubda min aji acikin
ƙawaye,to ahir ɗinki ba ki ba shi kije can ki jajibo gurgu irin ki da zaku fi dacewa da juna amma
ba jinin shuwa ba,tashi ki bani waje saura kije ki sanar da Iyan ina dai-dai da kowa ne indai akanki
ne shashasha kawai,sai shegen kyau da idanu kaman na jinnu."
Umma ta ƙare maganan cikin ɗaga murya,TAIMIYYAH da tai ƙasa da kanta tana zubda
hawaye,tayi saurin ɗagowa tai musu kallo ɗaya tana miƙewa,tare da dafa ƙafanta ta fara takawa
don fita daga falon,hatta jikinta rawa yake sabida ɓacin rai da wani irin ƙunci dake cin ranta,a
haka ta fito daga sashin tana danne kukan da ke taho mata,aiko tana tabbatar da cewa ta fito daga
Sashin ta samu bakin inda aka zagaye Flowers tayi zaune tana haɗe kanta da guiwa,ta saki kukan
da take dannewa ko zata samu sauƙin ciwan da zuciyanta keyi,kuka take sosai irin wanda ke
tasowa tun daga ƙasan zuciyan wanda ya jima yana haɗiyan baƙin cikin wani abu dake cin
zuciyansa,sosai zuciyanta ke zafi kalaman Umma na sake ƙona zuciyan tamkar ana zuba
tafasasshen ruwan zafi,ta rasa miye aibunta don ta kasance gurguwa,bata san miye laifinta don ta
zamo a yadda Ubangiji yaso ta kasance ba,bata san meyasa Umma ta kasa gane cewa Sadeeq baya
gabanta ba,ko batai mata gargaɗi akansa ba ita ɗin da kanta bazata taɓa bari zuciyanta tai
gangancin faɗawa tarkonsa ba,meyasa Umma tai mata irin wannan tsanan ne? Sabida kawai ta
kasance gurguwa me lalura ne ,ko kuwa akwai wani dalilinta ne na ƙinta da take ɓoyewa a ranta?
Waɗannan tarin tambayoyin sune suka cigaba da cika kwanyan TAIMIYYAH tana buƙatan amsan
su,kuka tayi sosai tana sauke ajiyan zuciya akai-akai,har lokacin kanta na kife cikin
guiwoyinta,sam bata ji tahowan mutum inda take ba sai da hancinta ya fara shaqo mata qamshin
turaren BENTLEY,sannan tayi saurin ɗago manyan idanunta waɗanda zuwa lokacin suka rine
daga farinsu su ka koma jajur sabida kukan da ta sha,bata sauke idanun a ko'ina ba sai akan
kyakykyawan fuskansa,hakan yasa tayi saurin sauke kanta ta maida shi inda yake tun farko,wasu
hawayen na sake ɓalle mata kaman ana sake ingizo su,qamshin turaren BENTLEY da ya sake
ƙarfi a cikin hancinta ya tabbatar mata Yah Sadeeq ya ƙariso daf da ita kenan,kafin tayi wani motsi
sai jin saukan hannayen shi tayi a jikinta yana me ɗago fuskanta,cikin wani irin murya yake faɗin
"Subhanallah! Kuka Zaynab me akai miki daga ina kike?" Duk ya furta mata tambayoyin har
lokacin yana riƙe da fuskanta a tafukan hannayensa,zuwa lokacin tuni dama ya rage tsawonsa
yana tsugunne gabanta ne,memakon TAIMIYYAH ta bashi amsa sai kawai takai hannunta tana
cire nasa daya riƙe face ɗinta,cikin muryan kuka take faɗin "Babu komi Yah Sadeeq sannu da
zuwa."
"Babu komi ne zan sameki anan kina kuka haka Zaynab,common sanar dani me akai miki kuma
ke da waye?"
Cewan Sadeeq yana sake sanya idanunsa cikin nata,hakan yasa ta lumshe nata idanun tana jin
wani irin ƙunci na sake mamaye zuciyanta,sam ba tayi farin ciki da wannan arangaman da sukai
da shi ba,ta sani matuƙar bata ba shi amsan da zai gamsar da shi ba,zasu yi ta zama ne anan har sai
wani yazo ya gansu yaje ya faɗiwa Umman,hakan yasa ta furta "Ni babu abinda ya haɗani da
kowa na zo fitowa ne kawai daga part ɗinku tsautsayi ya ɗebeni na faɗi,shine naji zafi sosai dama
kuma kaina na ciwo,amma yanzu bari in ƙarisa insha magani."
Yadda ta ƙare maganan cikin rauni da sanyin muryan daya motsa zuciyansa,ya bashi tabbacin daga
wajen Umman sa matsalan yake,baya shakkan cewa tayi mata halin nata da ta saba,TAIMIYYAH
bazata faɗi masa gaskiya bane kawai,hakan yasa shi zuba mata ido kafin ya furta "Kiyi haƙury
Zaynab komi me wucewa ne,watarana Umma da kanta zatai nadaman irin halayyan da take nuna
miki,bana so ko kaɗan ki dinga sanya damuwa a zuciyanki,yanzu tashi ki koma wajen Iya zan
shigo zuwa anjima,ina fata kinyi min girkin da nace?"
Kai kawai TAIMIYYAH ta gyaɗa masa,tana miƙewa tsaye,yayi saurin riƙo hannunta ɗaya har ta
tsayu da kyau,kafin ta dafa ƙafanta don fara tafiya ya riƙe mata ɗaya hannun,ta ɗago manyan
idanunta ta sauke akansa tana son zame hannunta daga nasa amma kallon da ya jefeta dashi yasa
ta barinsa,a haka suke takawa har zuwa ƙofan shiga Sasan Iya,sannan ya sake hannunta ta shige
ciki shi kuma ya juya zuwa part ɗinsu,zuciyansa na matuƙar masa ɗaci da irin halayyan
mahaifiyansa,yana jiye mata ranan da ubangiji zai nuna mata ikonsa akan nata jinin watakila daga
lokacin ne zata gane ubangiji ke yin yadda yaso da bawa,ya kuma halicceshi ta duk irin yadda
yaso bawan ya kasance,ko kaɗan bai taɓa ganin aibun nakasan TAIMIYYAH ba,sai ma dai a
kullum sake ganin irin baiwan da Allah yai mata yake, wanda ke fitowa a hankali don kaf tsakanin
age mate ɗinta su Zuhura tafi so komi,tafi u Brain na karatu boko da islamiya,ta fi su iya kula da
kanta da tsaftan jiki da iya girki,akwai ta da nutsuwa da kamun kai da kuma iya riƙe mutuncinta
na ƴa mace,wanda duk su ba'a ba su wannan baiwan ba,shiyasa a kullum shi baya hango wata
nakasa daga TAIMIYYAH sai tarin abubuwan da ta mallaka wanda ba kowace cikakkiyar me
lafiyan ƙafafun aka baiwa wannan baiwan ba,amma ya rasa dalilin da Umma ta ɗauki karan tsana
ta ɗaurawa TAIMIYYAH,tare da shan alwashin tsine masa idan har ya dage sai TAIMIYYAH
yake so,har ya isa ɓangarensa zuciyansa bata bar masa bitan irin cin mutuncin da Umman tai masa
ba alokacin da ya tare ta da maganan TAIMIYYAH sati ɗaya da suka wuce,yasa mukulli yana
buɗe ƙofan shigewa ɗakinsa kenan wayansa ya fara ringing,ya dakata daga buɗe ɗakin yana zaro
wayan daga aljihun gaban rigansa,ganin sunan My Mum da yayi yasa shi ɗaga kiran kai
tsaye,daga ɓangaren Umman bayan ta amsa gaisuwansa tambayansa take ya iso ne? Ya bata
tabbacin gashi ma acikin gidan yana ɓangarensa ne zai watsa ruwa ya kintsa ne ya shigo ɓangaren
nasu,hakan yasa ta katse kiran shi ma sai ya maida wayan aljihu yana buɗe ɗakin nasa ya shige
ciki.
TAIMIYYAH ko tana shiga ciki ta fara addu'an Allah sa Iya bata falo,sai dai addu'an nata bai ci ba
don tana sanya kanta cikin falon bakinta ɗauke da sallama,idanunta suka sauka a fuskan Iya tayi
saurin sauke kanta ƙasa tana cangala ƙafan da sauri don shigewa ɗakinta Iya ta kirayi sunanta da
cewa "Zainabu zo nan." Cewan Iyan idanunta akan TAIMIYYAH wacce ta juyo ta fara takowa
zuwa wajen da Iya ke zaune cikin kujera,ta kai ƙasa tana zama kusa da ƙafafun Iyan take faɗin
"Iya gani."
Iya takai hannu ta ɗago fuskan TAIMIYYAH da take faman yin ƙasa da kai don kada Iyan ta gane
tayi kuka,cikin wani irin murya a dake Iya ke faɗin "Me ya samu fuskanki,me sukai miki daga
shiga kai saƙo maza sanar dani,kuma idan kikai min ƙarya saina saɓa miki don ban miki wannan
koyin ba."
Iya ta ƙare maganan tana sake tsare TAIMIYYAH da kaifafan idanunta,hakan yasa TAIMIYYAH
sake yin rau-rau da idanu tana me zayyane ma Iya yadda sukai da Umman,ta ƙare maganan da
faɗin "Don Allah Iya kar kice zaki tanka mata,indai akan Yah Sadeeq ne ta kwantar da hankalinta
ni ban taɓa son sa ba bakuma zan fara ba,amma ni bana so kice zaki je kice mata komi,lokaci yayi
da zaki daina tankawa akan komi idan anmin Iya,tunda na kula hakan da kike kaman shi ke sake
janyo min tsana a wajensu."
TAIMIYYAH ta ƙare maganan cike da magiya,abinda ya karya zuciyan Iya kenan,ta dafa kanta
tana faɗin "Naji bazan je ince mata komi ba,amma ke kuma ki daina ƙyalesu akan irin cin fuskan
da suke miki,bance ki tanka Zuwaira ba amma su Zuhura duk wanda ya sake miki gorin
halitta,kice musu idan suke halittan ɗan Adam don Allah su sauyaki daga yadda kike su mayar
dake mara naƙasu,sannan ki daina bari suna ganin hawayenki,domin baka bari maƙiyinka ya gane
lagon ta inda zai dinga saranka koda da kalamai marasa daɗi ne,ko kaɗan ki tsaida zuciyanki tayi
dakewan da ko sauyin fuska zasu daina gani idan sun miki gorin nakasa,hakan zaisa su daina ci
miki fuska,sannan ina so ki kwantar da hankalinki indai mijin aure ne wallahi sai sun sha
mamakin irin mijin da Allah zai kawo miki,ai ba ita ke bayarwa ba don tace bazaki auri ɗan ta ba
sai me? Wallahi ba don bana miki sha'awan rashin kwanciyan hankali ba da saina nunawa Zuwaira
cewa daga ita har ɗanta zan iya iko da su,in kuma haɗa auren da take iƙirarin in tana raye bazai
yiwu ba,sai dai nafi so Allah yai ikonsa da kansa domin ina da tabbacin zaifi ni iya
hukuntata,domin huruminsa take shiga don shi ya halicceki ahakan,shi kuma yasan irin ajiyan da
yai don haka ki cire duk wata damuwa a ranki,ko kaɗan kada kiji cewa zaki ji ƙuncin
kasancewanki a hakan kinji ko?"
Iya ta ƙare magana tana shafa kan TAIMIYYAH wacce ta kwantar bisa ƙafafun Iyan,kalaman Iyan
na shiga kunnuwanta da wani irin tasirin dake ratsa ilahirin zuciya da gangar jikinta,ta gyaɗa kai
alamun gamsuwa da tarin kalaman Iyan,wacce itace gatanta da ta maye mata dukkanin guraben da
uwa zata cikewa ƴar ta,a hankali ta cusa hannuwanta saman fuskanta tana share hawayen dake
gudu,cikin sanyin murya take faɗin "Insha Allah Iya zanyi anfani da dukkanin abinda ki ka ce
nagode Allah ya bar min ke Iya har ƙarshen numfashi na."
Iya da tausayin TAIMIYYAH ya gama cika zuciyanta,ta shafa kanta tana faɗin "Ameen
Zainab,Allah yai miki albarka yasa ki cigaba da biyo halayyan TAIMIYYAH,ita kuma Allah ya
cigaba da kai haske kabarinta,Allah ya nuna min aurenki da zuriyyan da zaki haifa kafin ƙasa ya
rufe idanuna."
Ta ƙare maganan muryanta na rawa cike da raunin zuciya,domin a duk lokacin da ta tuna da
mahaifiyan TAIMIYYAH me suna Zainab sai zuciyanta ya karye,domin bata taɓa ganin
haƙurarriyan mace me tarin nutsuwa da hankali irin ta ba,ga baiwan kyau kaman ita tayi kanta
wanda nagartanta da kyawawan ɗabi'unta suka janyo ake kiranta da TAIMIYYAH,kaman yadda
labarawa basa sakawa ƴar su ko ɗansu suna TAIMIYYAH sai ya mallaki nagarta irin na Zainab
ɗin,shiyasa a lokacin da aka haifi TAIMIYYAH ta sa aka saka mata suna Zainab ɗin kaman tasan
uwar mutuwa zatai,bayan rasuwan Zainab ɗin sai Iya ta cigaba da kiran abinda ta bari da irin
sunan da ake kiran Zainab ɗin dashi wato TAIMIYYAH,tana me fata Zainab ɗin ta gado halayya
da nagartan uwarta,sai gashi ko TAIMIYYAH babu inda ta baro halayyan mahaifiyan nata,Iya ta
sauke ajiyan zuciya tare da dawowa hayyacinta daga faɗawa duniyan tuna baya da ta tafi,muryan
TAIMIYYAH me sanyi tamkar na uwar ta na ratsa kunnuwanta lokacin da TAIMIYYAN ke amsa
addu'an da faɗin "Ameen Iya na,insha Allah bazaki rigani mutuwa bama tare zamu tafi ko zaki
mutu."
Iya ta saki murmushin su na manya,tana sake jin ƙaunar TAIMIYYAN me tsanani yana cigaba da
ratsa jinin jikinta,sai dai kafin tayi magana sallamansa da shigowan sa cikin falon yasa duk suka
bishi da ido,sassanya qamshin nan nasa dai na turaren BENTLEY ya fara kara kaina cikin
falon,Iya gaba ɗaya sai ta koma ta tamke fuska,tana amsa sallaman ya ƙariso cikin falon yana
zama kujeran dake facing Iya,ya zame ya kwashi gaisuwa idanunsa fes akan qanwar tasa da har
lokacin kanta ke saman guiwan Iya,ba yabo ba fallasa Iya ta amsa gaisuwansa sai ya maida
dubansa gaba ɗaya akan TAIMIYYAH yana faɗin "Sis tashi ki bani abinci da yunwa na shigo
garin nan."
Yadda ya ƙare maganan idanunsa akanta yasa Iya da itama ta tsare shi da ido zabga masa
harara,tana riga TAIMIYYAH da faɗin "Kaji min rashin tausayi dai,a memakon ka tashi ka isa
wajen cin abincin tana zamanta sai ka tashe ta wani kawo maka abinci kaman mara ƙafafu,to
bazata tashi ba in bazaka isa wajen kaci ba ka koma wajen uwar ka marasa kunyan qanninka su
zuba maka kaci."
Yadda Iya ta ƙare magana tana faman juya ido ita adole harara take watsawa Yah Sadeeq ɗin,yasa
daga TAIMIYYAH har shi uban gayyan sakin dariya,kafin ko wanne ya maze kaman bashi ke
dariyan ba,Sadeeq ɗin ya tashi yana nufan wajen cin abincin yana faɗin "Maida wuƙan ƴar
tsohuwa amma dai a taimaka ta zo tai sarving ɗina please."
Iya ta ja tsaki tana faɗin "Ka dai ji dashi fitinanne,ke kuma da kike dariya saiki tashi ki zuba masa
waya sani ma kina sane nan zaici abincin shiyasa kika dage sai kinyi girkin da kanki mitsuww!"
TAIMIYYAH da dariya ke cinta arai ganin Iya zata ɗago ta yasa ta haɗe fuska,cike da shagwaɓa
take faɗin "Kai Iya inda haka ne da baki ga na zuba masa a kula daban ba,ni inama nasan zai wani
dawo bare har inyi girki dashi."
Cewan Iya tana taɓe baki ita ko TAIMIYYAH sai ta nufi wajen cin abincin ta fara sarving
ɗinsa,har lokacin Hijab ne sanye ajikinta bata cire ba,plate ɗin ta tura gabansa tana dubansa,ganin
yadda ya tsareta da mayen kallon da yake addabanta dashi yanzu yasa tayi saurin ɗauke kanta tana
faman turo baki,sam ta tsani yawan kallo tun kafin ta girma haka,lemun Fruity Zoɓo da tai ta zuba
masa cikin dogon glass cup ta tura gabansa,kafin ta miƙe tana faɗin "Yah Deeku ni zan shiga daga
ciki ina da karatun hadda kasan gobe Saturday."
Bata jira cewan sa ba tai gaba abinta yabi bayanta da kallo,yana girgiza kansa kawai tare da jin
wani abu na sake fisgansa zuwa gareta,sai dai zuwa yanzu ya fara ji ajikinsa dole ya koyi juriya
akan danne duk wani zazzafan son ta dake ɗawainiya dashi,matuƙar yana son ta sami farin
ciki,domin shi kansa yasan idan ya dage sai ya aureta alhali Ummansa tai mata irin wannnan
tsanan,bazata taɓa samun kwanciyan hankali ba,tabbas kaman yadda TAIMIYYAN ta faɗi ne
haƙura da juna shine kawai mafita su cigaba da zumunci tamkar yadda suka faro,a hankali yake
cin abincin daɗin girkin na ratsa shi,tare da haifar masa da kasala da mutuwan jiki,domin wani
yanayi ke bin jininsa yana yamutsawa,tabbas zaiyi rashi idan ya bar TAIMIYYAH ta suɓuce
masa,ya lumshe idanunsa a lokacin da sanyin Zoɓon da ya zuƙa yabi maƙoshinsa,daɗin ya ratsa
har tsakiyan kansa,sai ya buɗe idanunsa yana cigaba da cin abincin har ya kammala,ya goge
bakinsa tare da tashi a wajen,cikin falon ya dawo har lokacin Iya na zaune ta maida hankalinta ga
kallo,sai yai mata sallama ya fice daga Sasan baki ɗaya..........✍🏻
*Littafin TAIMIYYAH paid book ne akan 500 naira only,ga masu buƙatan yin payment zakui min
magana ta wannan number ɗin 08167768704, ko kuma ku turo kuɗin ku kai tsaye ta wannan
account ɗin 0504192664 aisha ibrahim dansabo GTbank.*
_Masu account da Arewa books,zaku dinga siyan sabbin shafuka dalla-dalla akan farashi me
sauƙi,ga yadda zaku siya pages a arewa books kamar haka_ 👇🏻
https://arewabooks.com/chapter?id=62d29e11aa5f8f19bc9621cb
*Balance* - Zai nuna kudin account dinku da zaku iya sayayyan littafai cikin kasuwar
ArewaBooks.
*Credit/Debit Card* - Hanyar farko kuma mai dadi wajan Recharge din account dinku.
A inda (Enter your amount) za'a saka kudin da akeson Recharge din sai a taba "Proceed". Zaibude
muku inda zaku saka bayanan katin banki, kuna gamawa kudinku zaishiga account dinku kaitsaye
(instant).
--------
*Bank Transfer*
*Airtime Transfer*
Saidai su ba kaitsaye bane (instantly) sai ArewaBooks ta tabbatar da Transfer din, amman bayakai
1hour za'a gansa a Balance.
#Ɗansabo ce#
[12/14, 3:42 PM] +234 703 040 9541: *TAIMIYYAH*
*Page 8*
________Suhailah sai yamma sosai ta koma gida daga gidan Hajiya,bayan ta sha faɗa da nasihun
Hajiyan haɗi da razanarwa,tuƙi take amma gaba ɗaya tunaninta na ga yadda zasu kwashe da
A.Maleek ɗin idan har ta samu matsala,bata ji zuciyanta ko da wasa zata iya ɗaukan ganinsa da
wata mace da sunan matarsa,har ta isa gidanta ranta a jagule yake,mayafinta kawai ta cire ta faɗa
Kitchen,samun Ameena tayi tana aikin ɗaura abincin Dinner,Suhailah ta dubi Ameenan tana faɗin
"Me kike shirin girkawa ne? ina ga yau kiyi abinda zaku ci ke da megadi,ni zan yi girkin da
zamuci da Ogan."
Cike da mamakin Suhailan Ameena ta dube ta,tana risinar da kai alamun girmamawa take faɗin
"Okey Mah ba damuwa,dama tuwan Semo ne zanyi sai Macaroni Salad sabida Oga."
"Bar shi kawai yanzu ki ciro min kaza kiyi marinating ɗinta ki mayar cikin freezer,sai ki gyara
min kayan miya ki fere Dankali kaman guda 6,yanzu zan dawo in ɗaura girkin okey."
Cewan Suhailah tana barin Kitchen ɗin don amsa kiran Raudha da ke shigowa,sun daɗe suna
magana kafin ta saka wayan a silent ta dawo Kitchen ɗin,da taimakon Ameena ta shirya lafiyayyan
gashin Kazan da aka wadata shi da Irish gashin yai wani irin kyau,akai raping cikin foil paper tare
da saka shi a kyakykyawan mazubi,sai haɗin Macaroni Salad da yaji liver da zallan tsokan kaza
shima aciki,da kanta ta ɗauki ƙaton Tray ɗin da aka jera komi ta haura zuwa up stairs,bisa dining
ɗin da ke falon saman ta aje ta wuce zuwa ɗakinsa,yana nan yadda ta gansa da safe,ta fara da
kwashe kayan dake kan bed ta zuba a kwandon adana kayan wanki,sannu a hankali take gyaran
ɗakin tana mita,jikinta ko'ina yana ansawa da gajiya hatta toilet ta daure tai masa kyakykyawan
wanki,sai da ta ga komi ya yayi fes sannan ta fito ta nufi ɗakinta ta ɗakko abun zuba turaren
wuta,ta zuba ta kunna tana kaiwa ɗakin ta turare ko'ina da ina,bisa sofan dake ɗakin ta zube tana
maida numfashi a fili take faɗin "Wai Allah! Anya ko zan jure wannan bautan, gaskiya da kamar
wuya zan dai ta lallaɓa ka har ka yadda asake samo me aikin da zata dinga gyaran ɗakinka
Hubby."
Yadda take maganan can ƙasa cike da mita zaka ɗauka wanda ake yi dominsa yana ɗakin ne,ganin
lokaci na sake tafiya yasa ta miƙewa ta fito daga ɗakin,ko da ta shiga nata ɗakin direct Bathroom
ta nufa tayo wanka,ta fito ana kiran magriba amma sanin fana off yasa kai tsaye ta nufi wajen
mirrow don tsara kwalliya,sosai ko ta fente face ɗinta da light make-up,domin ita ɗin gwanace a
iya kwalliya da son ɗaukan hutuna tana posterwa a media kai ba kace matar aure bace,duk
waɗannan halayyan ke sake haɗata faɗa da Maleek ɗin domin ya tsani hakan sosai amma ta kasa
dainawa,sabida yadda qawaye ke zigata tana kuma samun Followers sosai a shafukan nata
musamman a Instagram,Riga da Skat na wani haɗaɗɗan Voile laces ta saka wanda ɗinkin yai
asalin zama ajikinta,tare da fidda shape ɗinta sosai,tayi anfani da sirirn sarƙan gwal ɗinta da ɗan
kunni wanda suka sake haske kwalliyanta,hannunta warawarai ne guda biyu suma na gwal ne ta
saka,nan da nan tai wani irin kyau tamkar wacce zata wani haɗaɗɗen Dinner Party,ita da kanta ta
yaba kyawun da ta zuba sai fatan miskilin mijin nata ya yaba kawai take,zama tayi bayan ta gama
wadata jikinta da turaren MISS DIOR banda daddaɗan Body Mist da tai anfani dashi,daga ciki
sosai haɗaɗɗen humra ne na DOLCE tai using,gaba ɗaya wani irin qamshi take fitarwa me saukar
da tarin nutsuwa ga duk wanda ya shaqa,wayanta ta ɗauka ta hau online don rage lokaci,bayan tayi
kiran layin Maleek ɗin har su biyu bai ɗaga ba.
A gajiye sosai ya shigo gidan misalin takwas da rabi na dare,lokacin har Suhailah ta gaji da zaman
jiransa a sama ta sakko falon ƙasa,tana kallo a mamaken Smart TV dake manne jikin wani irin
LUXURY TV Stand da ke falon,tunda hancinta ya shaƙo mata qamshin turaren RALPH LAUREN
wanda yakan sirka da ɗayan turaren nasa na AMOUAGE tasan cewa shi ne ya shigo falon,kallo
ɗaya yai mata ita da adonta ya ɗauke kai ya fara takawa zuwa hanyan da zai sada shi da Stairs ɗin
da zai kaishi sama,ganin hakan da yayi yasa Suhailah tabbatar da akwai sauran ƙura kenan,Hajiya
ta gama nata shi kuma yanzu zai hau nasa,cikin baiwa kanta ƙwarin guiwa ta bishi zuwa
saman,samun sa tayi yana rage kayan jikinsa don shiga wanka,sai ta riga shi shiga bayin tana tara
masa ruwan wankan cikin tube,abinda ta mance yaushe rabon da tayi ,shiyasa ko da ya shigo bai
kalleta ba ya fara ƙarisa cire abinda ya rage a jikinsa,ganin hakan yasa ta juyawa ta ba shi waje,ya
saki ƙaramin tsaki yana me jin wani haushinta na kamasa,domin shi mutum ne daya tsani ai masa
abu bada zuciya ɗaya ba,ya riga ya gama sanin duk wannan tarairayan bame ɗaurewa bane ne,tana
yi ne don ta sakko dashi da zaran ya fara sakin jiki zata sake komawa gidan jiya ne,shiyasa shi
kuma ya shirya bata mamaki a wannan karon,lokacin da ya fito samunta yayi kwance bisa
Sofa,ganin fitowansa yasa ta saurin aje wayan da ke hannunta ta nufesa,tana faɗin "My Hubby
bari in taimaka maka da shafan please kar ka gwaleni,don Allah Maleek kayi haƙury wallahi zan
canza dukkanin halayyan da baka so."
Har ta dasa aya bai tanka ba illa ma janye jikinsa da yayi daga gareta,ya fara shafa mansa ganin ta
iso ta amsa man sai ya rabu da ita ta ƙarisa shafa masa,gaba ɗaya sai wani narke masa take tana
komawa kalan tausayi,qamshinta gaba ɗaya ya gama cika hancinsa,yana taso masa da wani irin
feelings akanta,yayi kewanta don rabonsa da gari sati biyu kenan sai a daren shekaran jiya ne ya
dawo,amma rashin samun tarba me kyau yasa suka samu saɓanin da ko nemanta baiyi ba bare ya
sauke nauyin da ya dawo dashi,sai dai ko kaɗan fuskansa ba asake yake ba,sam Suhailah ta kasa
samun yadda take so,jallabiya ta ɗakko masa Milk Colour ya amsa ya saka,ta ɗauki turaren da ta fi
son yai anfani dashi,wato AMOUAGE ta fesa masa tana me kwantar da kanta bisa jikinsa bayan ta
aje kwalban turaren,ahankali ta kai hannunta zuwa bayansa ta rungumeshi sosai tana shaqan
daddaɗan qamshin daya karaɗe ɗakin baki ɗaya, "I Luv u My Maleek." Ta furta cikin wani irin
salon da ya motsa zuciyansa,hakan yasa ya zare ta daga jikinsa yana binta da wani shu'umin
kallo,domin sosai ta taɓo duk wani feeling da ya danne akanta,har lokacin fuskansa a haɗe yake
cikin muryansa me cike da ginshira da izza yake faɗin "Mu je ki bani abinci banci komi ba tun
safe sai ruwan juice da nake ta sha."
Bai jira cewanta ba ya fara takawa don fita daga ɗakin,Suhailah ta rufa masa baya har suka fito
zuwa dining ɗin,da kanta tai Sarving ɗinsu a plate ɗaya don itama bata ci komi ba ta tsaya
jiransa,da farko da kansa ya fara cin abincin amma ganin ta shagwaɓe masa lallai sai ta ciyar dashi
yasa ya sakar mata spoon ɗin,sai da ya nuna ya ƙoshi sannan ta maida hankali taci nata,shi ya fara
barin wajen ya koma ɗaki don akwai abinda yake son aiwatarwa ta Computern sa,hakan yasa
itama Suhailah komawa ɗakinta bayan ta kammala cin abincin,bata sake gigin zuwa garesa ba don
ta gama ganesa idan yana wannan fisge-fisgen to gara itama ta ɗan dinga jan kanta bawai ta zaƙe
ba,sai da agogo ya buga ƙarfe sha ɗaya sannan tayi shiri cikin wasu Nighties masu kyau,Rigan me
transparent ce wanda ita da babu duk ɗaya ne,sai wandon wanda duka tsayinsa iya cinyanta
ne,gaba ɗaya wani irin qamshi take fitarwa me motsa zuciya,wayanta ta ɗauka ta fito xuwa ɗakin
Maleek ɗin,ga tsananin mamakinta har zuwa lokacin yana zaune bisa tsakiyan gadonsa,da Laptop
a gabansa yana ta faman aiki,qamshinta da ya jiyo yasa shi ɗaga manyan idanunsa ya sauke
akanta,ƙirjinsa yai wani irin motsawa nan take dukkanin sha'awansa ya gama tasowa,ya cigaba da
kafe ƙirjinta da ke bayyane cikin Rigan da kallo babu ko ƙiftawa,har ta iso zuwa kan Bed ɗin tare
da yin masauki kusa dashi sosai tamkar zata shige jikinsa,hakan yasa shi sauke ajiyan zuciya yana
ji gaba ɗaya bazai iya cigaba da abinda yake ba,shiyasa yayi hanzarin kashe Computern yana
janyota jikinsa gaba ɗaya ya rungumeta,Suhailah da ta tabbatar ya gama shiga tarkonta sai ta sake
lafewa a jikinsa ta saki kukan kissa,cikin kukan take sake bashi haƙury akan ta tuba wallahi zata
sauya ta koma yadda yake so,A.Maleek da yai nisa a aika mata da gigitattun Kisses tako'ina ya kai
bakinsa ya haɗe da na ta alamun baya son surutu a wannan time ɗin,ai sai Suhailah ta fara maida
martani don itama tayi missing ɗinsa sosai,don ma rashin tsarkin da take ciki dole zai takawa
zalaman su birki,lokacin da Maleek ya fahimci bazai samu zuwa inda yafi muradi ba yaji babu
daɗi amma da taimakonta ya samu gamsuwa,don ita ɗin ba baya bace wajen kula dashi awannan
fannin,shiyasa ko yayi fishin indai aka zo nan ɗin baya ma sanin ya sauka sai komi ya lafa sannan
zai cigaba da ɗauke kai da basarwa,a yanzu ɗin ma hakan ya kasance lokacin daya tabbatar ya
samu gamsuwa,sai ya zareta daga jikinsa da ta kanainayesa ya nufi Bathroom don tsarkake
kansa,ko da ya fito kallo ɗaya yaiwa Suhaila da tai ɗai-ɗai bisa Bed ɗin babu kaya a jikinta ya
ɗauke kai,ya nufi wajen da Jallabiyansa yake ya zura yana kai manyan idanunsa ya dubi babban
agogon bangon da ke ɗakin,lokacin time ke nuna 12:05am na dare,dole sai yasha ruwan zafi kafin
ya kwanta hakan yasa ya nufi inda Suhailah take fuskansa a tamke kaman bashi ya gama mata
kalamai da sambatu ba a ɗazu,ya tsare ta da manyan idanunsa yana faɗin "Suhailah tashi kije ki
wanka ki zo ki haɗo min Shayi okey."
Ya ƙare maganan da janyota ya miƙar har ta sauka daga kan Bed ɗin,bata damu sam data nemi
wani abu ba haka ta wucesa tik ɗinta ta nufi Toilet,ya bi bayanta da kallo yana wani lumshe
idanunsa sabon feeling na fisgansa,sanin bazai samu abinda yake so ba har sai ta samu tsarki yasa
shi danne komi,har ta fito bai sake yadda idanunsa sun sauka akanta ba,har sai da ya tabbar ta
maida kaya a jikinta duk da dai babu maraba da babu wannan rigan nata,ficewa tayi tana faman
zumɓure baki sam bata son takura,lokacin da ta kawo masa shayin sai ya dube ta yana faɗin
"Sorry na manta bance miki i need some lemon aciki ba,jeki ɗakko min in matsa kaɗan."
Yayi maganan ne idanunsa fes akan face ɗinta,don haka akan idanunsa ta saki ƙaramin tsaki tana
juyawa tai waje,ya girgiza kai ransa yana sosuwa,shi dama yasan da wuya Suhailah ta koma masa
yadda yake so,duk rawan ƙafan da takeyi na yaudara ne da ɓacin ran da ta gani a wajen Hajiya,har
ta kawo lemon sai faman cika take yai kaman baisan tana yi ba,yana gama shan shayinsa ya
wanko baki yazo yai kwanciyansa ba tare da ya sake bi takan Suhailan ba,har bacci ya fara
ɗaukansa ya jita cikin jikinsa,hakan yasa shi gyara kwanciyansa yana shigar da ita jikinsa sosai ya
sake jan Duvet ya rufe su.
________
Ƙarfe 9am na safe TAIMIYYAH ta fito cikin shirin zuwa makarantan Hadda,sanye take da dogon
Hijab da ya sauka ƙasa sai dai baya sharan ƙasa sabida laluran ƙafanta,sosai kalan Hijab ɗin da
yake dark Brown yai mata kyau,hannunta Qur'ani ne Izu Sittin ta aje sa daga saman kujera ta nufi
ɗakin Iya,a bakin gado ta samu Iya tana ƙarisa shiryawa alamun wanka ta fito,ta durƙusa ƙasa tana
gaida Iyan,Iya ta amsa da fara'a tana faɗin "Har kin kintsa zaki wuce ɗin TAIMIYYAH,to maza
dai ki karya kafin ki tafi,ki kuma shiga ki gaida Baban ku Sani tunda jiya ya shigo kinyi bacci,idan
su waɗancen sun shirya sai ku wuce tare ma kawai."
Da "Tuh." Kawai TAIMIYYAH ta amsawa Iya,tana juyowa ta fito zuwa falon ta nufi wajen cin
abincin su inda Ladi ta gama shirya komi,Kunun tsamiya ta zuba a Cup ta saka Sugar tana
juyawa,kafin ta aje ta buɗe kulan da aka zuba soyayyan Doya me egg ajiki,ta ɗibi guda 4 ta zuba a
plate ta fara ci ahankali tana shan kunun,lokacin da ta kammala sai ta goge baki bayan ta ɗan sha
ruwa,ta ɗauki Qur'aninta ta fito ta nufi Part ɗin Baba Sani,tana shirin shiga shima Yah Sadeeq da
ya taho daga ɓangarensa yana isowa don shiga Sashin nasu,tunda TAIMIYYAH ta jiyo qamshinsa
ta waiwayo tana sauke manyan idanunta akansa,ta saki murmushi kaɗan lokacin da ya ƙariso inda
take,suna jerawa da juna zuwa cikin gidan,bayan ya amsa gaisuwanta ne ya amshi Qur'anin
hannunta ya riƙe mata,a haka suka ƙarisa zuwa cikin falon gidan,su Zuhura da Basmah ne da
alamun tashin su kenan,ko wanka basuyi ba TAIMIYYAH ta dube su tana faɗin "Sannun ku
dafatan mun tashi lafiya,Basmah baku shirya ba ashe da har ina cewa zamu wuce tare."
TAIMIYYAH ta ƙare maganan tana ɗauke kai daga dubansu,ganin kallon da Zuhura tai mata wai
don ma Yayan su na tsaye a wajen ne,Basmah ta taɓe baki tana faɗin "Ai kinsan mu Malamin mu
bai cika zuwa akan time ba zaki iya wucewanki,ma biyo bayanki."
Daga haka suka haɗa baki wajen gaida Yah Sadeeq ɗin,wanda hankalinsa na kan danna waya sai
dai yana jin duk abinda suke faɗi,ɗago idanunsa yayi lokacin da yake amsa gaisuwan nasu,ya
sauke idanun akan Zuhura yana faɗin "Oya ku tashi kuje ku sanyo Hijab ko bakuyi wanka ba ku
tafi haka,tunda ku ƴan banzan yara ne da bakwa son zuwa makaranta,na baku mintuna goma
kowacce ta fito cikin shiri shashashai kawai."
Yadda ya ƙare maganan da tsawa yasa su miƙewa,suka wuce fuu zuwa ɗakinsu don cika
umurninsa,shi kuma ya maida dubansa kan TAIMIYYAH yana faɗin "Mu je Baby mu gaida
Baban kafin su kintsa."
TAIMIYYAH bata ce komi ba ta fara takawa zuwa hanyan da zai sada su da falon Baba Sanin,a
tare suka shiga bakinsu ɗauke da sallama,Umma da ke zaune tana facing ƙofar shigowa falon,ta
ɗago idanunta ta sauke akan su,xuciyanta na bugawa da wani irin ɓacin rai,amma sai ta danne ta
amsa sallaman nasu,TAIMIYYAH ta zube tana gaida Umman,Umma ta jefa mata harara tana amsa
gaisuwan a wulaƙance,Sadeeq ma ya gaidata ta amsa tana jifansa da wani kallo da shi kaɗai yasan
ma'anansa,Baba Sani ne ya fito daga ɗaki ganin TAIMIYYAH yasa shi sakin murmushi yana faɗin
"Zainab idon ki kenan na dawo jiya ke kaɗaice baki min sannu da zuwa ba,lokacin da na shiga
wajen Iya kuma kinyi bacci."
Ya ƙare maganan yana zama kusa da Umma,TAIMIYYAH ta saki murmushi tana faɗin "Baba kayi
haƙury bacci ne ya ɗauke ni da wuri,ina kwana ka dawo lafiya."
"Lafiya lau Zainab,har anyi shirin Haddan ba sannu da ƙoƙari,ina fata su ƴan uwan naki sun shirya
sarakan shiririta."
Cewan Baba Sani yana maida dubansa kan Sadeeq da ke gaida sa,TAIMIYYAH ta furta "Yanzu
dai zasu shirya Baba."
"Okey! To Allah yayi albarka ya bada ilimi me anfani,zuwa dare zan tara ku akwai maganan da
zanyi da ku don haka kar ki yadda ki bacci da wuri kinji Zainab." Baba Sani ya ƙare maganan da
raha,hakan yasa TAIMIYYAH sakin murmushinta me faɗi tana bashi tabbacin zata jira,daga haka
ta miƙe ta baro falon nasa ta bar Sadeeq ɗin aciki,saman kujera ta ɗosana mazaunanta tana kallon
agogo,ganin lokacin na tafiya yasa ta saki ƙaramin tsaki,Yah Sadeeq da ya fito yana miƙa mata
Qur'aninta,ganin har time ɗin su Zuhura basu fito ba yasa shi nufan ɗakinsu,ko mintu biyu baiyi
da shiga ba sai gasu sun fito kowacce fuska a haɗe suna jefawa TAIMIYYAH mugun kallo,kaman
yasan zasu iya mata wani iskancin a hanya,sai yace su jira shi ya ɗakko mukullin mota zai sauke
su daga bakin hanya su ƙarisa cikin makarantan,tunda makarantan babu nisa yana da daga farkon
shigowa layin su ne,aiko sam basu ji daɗi ba so sukai ya barsu su taka da ƙafafunsu,don su samu
daman cin zarafin TAIMIYYAN akan hanya,amma sai Yah Sadeeq ɗin ya toshe wannan kafan,a
bakin gate ɗin shiga ma ya sauke su yai tafiyansa,suka shige ciki kowacce ta nufi ajinsu,don
TAIMIYYAH ta riga tai musu nisa sosai duka saura Izu huɗu ya rafe su haɗa a yaye su..........✍🏻
#Ɗansabo ce#
[12/14, 3:42 PM] +234 703 040 9541: *TAIMIYYAH*
*Page 9*
Misalin ƙarfe tara da dare Baba Sani ya tara su TAIMIYYAH a babban falonsa,cikin waɗanda ke
wajen akwai Umma da Iya,sai Zuhrah da TAIMIYYAH sai Babban Yaya Sadeeq,dukkanin su
yaran na zaune daga ƙasan Carfet ɗin ɗakin ,sai Iyayen da ke saman Kujeru.Baba Sani shiya buɗe
taron da addu'a kafin ya fara maida dubansa akan Sadeeq wanda yake zaune kusa da shi sosai,ya
soma da faɗin "Kai Sadeeq kai ne babba da kai zan fara,da farko sai muce Alhamdulillahi tunda
Allah yai maka duk wani buɗi dai-dai gwargwado a rayuwa,tunda ga ka da babban aiki hannu ga
kuma gini da saura ƙiris ya rage ka kammala,don haka ina muka kwana akan maganan fito da
matar aure?Nayi ta zuba ido inji ka kawo min zancen aure amma shiru,daga baya saina fara
tunanin ko ƴar gida za'ai tsakaninka da qanwan naka TAIMIYYAH ganin irin shaƙuwan da ke
tsakaninku,amma nan ma banji kace komi ba,har gashi suma sun kammala karatu,me kake
shiryawa ne ko ince me kake jira da har yanzu baka shirya aje iyali ba bayan kullum shekaru
turawa suke."
Ya ƙare maganan da tsaida idanunsa akan Sadeeq,wanda shi kuma idanunsa na kan TAIMIYYAH
wacce ta sake ƙasa da kanta tunda taji Baba Sani ya shigo da sunanta taji ƙirjinta ya shiga
bugawa,Sadeeq ya ɗauke kai daga dubanta yana mayarwa kan Mahaifiyansa Umma,wacce tafi
kowa tsare sa da ƙananun idanunta,tana kuma fatan kada ya bada ita wajen nunawa ubansa yana
son TAIMIYYAN,ganin irin kallon da take masa yasa shi ɗauke idanunsa daga gareta ya mayar
kan Baban nasa yana faɗin "Baba har yanzu ana kan neman matar ne,a kwanakin baya na so
gabatar maka da wacce nake so,sai dai an samu saɓani tsakanina da ita wanda har na haƙura,yanzu
ina kan nema ne da zaran mun dai-daita za'a ji na gabatar da ko wacece."
Yadda ya kai ƙarshen maganan cikin sanyin murya yasa TAIMIYYAH ɗaga manyan idanunta ta
sauke akansa,tana me jin wani irin sanyi ya ratsa zuciyanta,don ba tayi zaton abinda zai faɗiwa
Baban kenan ba,Umma wacce tafi kowa jin farin cikin amsan da Sadeeq ɗin ya baiwa Baba Sani
itama sai da ta sauke numfashi,Baba Sani ya jinjina kai yana faɗin "To madallah,Allah yayi zaɓi
mafi alkhairy ina nan ina sauraran ka,idan kuma ka tsaya ruwan ido ni da kaina zan maka zaɓi."
Baba Sani yai maganan da salon barkwanci wanda ya sanya har Iya murmusawa,kafin ya maida
hankalinsa kan su TAIMIYYAH yana komawa Serious sosai,ya sauke ganinsa akan Zuhurah yana
farawa da faɗin "To Zuhurah na dawo gare ki,kun kammala karatu kuma akwai manema wanne
kika tsayar a cikin tarin maneman da kike tara min a ƙofar gida,kar ki ɗauka don ni ba mazauni
bane bani da masu saka min ido akan duk wani motsinku,sanar dani wa kika tsayar kuma ɗan wani
gida ne? Aure zan muku tunda ke kin kammala Diploma,ga wannan yajin aikin da ba'asan ranan
komawa ba sai a aje batun cigaba da karatu a fuskanci auren don shine cikan mutuncin ku na ɗiya
mace,don haka sanar dani waye gwanin?"
Ya kai ƙarshen maganan yana tsare ta da manyan idanunsa,wanda duk kusan gado sukai wajen Iya
shiyasa hatta jikoki su TAIMIYYAH suka samu nasu kason na gado manyan idanu farare
tas,Zuhurah ta ɗago ta dubi Baban nata cike da kame-kame ta fara faɗin "Umm! Baba ai duk masu
zuwan ba da maganan aure suke zuwa ba,har yanzu dai ban ga wanda xuciyata ta aminta dashi ba
tukunna dai."
Yadda ta kai ƙarshen maganan ya fusata Baba Sani ya soma faɗa yana faɗin "Maganan banza
kenan kice duk samarin da kike tarawa babu wanda zuciyanki ta aminta da shi,to kina sauraransu
da sunan shashanci ne kome? To ki sani ni bazaki maida ni mutumin banza ba,lallai ki tsaida
mutum ɗaya ki turo min shi yazo ya sameni,idan kuma kinƙi zaki ga matakin da zan ɗauka a
gaba."
Zuhurah ta gyaɗa kai tana faɗin "Tuh Baba." Baba Sani ya maida dubansa kan TAIMIYYAH
wacce zuwa lokacin ƙirjinta ke wani irin bugu,sam bata son duk wani abu da zai janyo ai mata
maganan aure,amma ta gama sarewa yau ɗin ba ta da wani mafita tunda Baba Sanin ƴar titsiye
yake jin yi musu,tunaninta ya katsene a lokacin da muryansa ke shiga kunnuwanta yana faɗin "To
Zainabu na dawo kanki,waye Surukin nawa?"
TAIMIYYAH ta sake ƙasa da kai sam ta kasa ɗagowa ta kalli kowa,cikin ɗan rawar murya take
faɗin "Babu kowa Baba,ni bana kula kowa karatu nake so abar ni in cigaba,munyi magana da Abie
zan cike form na wani Computer Training,kafin Asuu su janye Strike ɗin zan samu a ƙalla wata
uku ina yi."
Daga haka tai shiru zuciyanta na cigaba da bugawa,tana me addu'an Allah ya ɗaurata akan Baba
Sanin,Baba Sani da idon sa ke kan TAIMIYYAH ya gyara zama yana faɗin "Eh! Tuh ba zan ce ba
za ki shiga ba tunda kina so kuma abu ne me kyau,sai dai ki sani fito da mijin aure shima abu me
muhimmanci,me yasa bazaki baiwa manema daman da zasu zo gareki ba Zainab? Kada kiyi
anfani da laluran da ubangiji ya ɗaura miki ki tauye kanki,akwai waɗanda laluransu yafi naki wasu
ma sai dai aturasu a keken gurugu,wasu jan gindi suke suna tafiya yayinda wasu a nannaɗe suke
sai an musu komi,kin ga ashe ke ɗin naki me sauƙi ne tunda babu abinda ya gagareki yi,don haka
kamar yadda na sanar da Zuhurah ta fito da miji,kema lallai ne ki fara sauraran manema duk
wanda hankalinki ya tsayu akansa ki turo min shi,kuma yaushe ne za'a fara Computer Training ɗin
sai ku shiga tare da ƴar uwanki kuyi tare."
Baba Sani ya kai ƙarshen maganan idanunsa har lokacin na kan TAIMIYYAH,wacce sai a lokacin
ta ɗago kanta tana duban sashin da Baba Sanin yake,kafin ta sake ƙasa da kanta tana faɗin "Insha
Allah Baba za'ai yadda kace,maganan Training ɗin tuni anfara sai da form ni har na cike online ma
yanzu zanyi Registration ne ranan Monday,tunda Abie ya riga ya bani kuɗin komi kafin ya wuce."
"Amma Zainab baki kyauta min ba,don me ni ba za ki dinga sanar dani abinda kike so ba,sai dai
kima Sameer magana kina ganin ni idan kin tambayeni ba zan baki bane?"
Baba Sani ya jefawa TAIMIYYAH tambayan,muryansa na nuna ɓacin ransa matuƙa,hakan yasa
TAIMIYYAH sake ƙasa da murya cike da ban haƙury take faɗin "Kayi haƙury ba haka bane
Baba,kawai mun riga yin maganan dashi ne kafin ka dawo wannan satin nake so in sanar dakai
dama,to da ya tambayeni abinda ake buƙata ne na faɗi masa sai kawai ya turo min kuɗin,amma ayi
haƙury hakan ba zai sake faruwa ba."
Baba Sani ya gyaɗa kai cike da gamsuwa,da kuma yaba hankali da tarin nutsuwan TAIMIYYAN
da sam yaransa basu samu ba,ya furta "Shikenan ya wuce amma karki sake Zainab duk abinda
kike buƙata na karatu ne ko buƙatun yau da kullum ni zaki sanarwa ko Yayanku basai kin tambayi
Sameer ba kinji ko?"
"Naji Baba kayi haƙuri hakan bazai sake faruwa ba." Cewan TAIMIYYAH muryanta can ƙasa,ta
ɗago ido don duba ko Iya na cikin falon kuwa,don bata ji ko tarin ta ba tunda aka fara maganan,sai
kawai idanunta suka sauka akan Yah Deekun da yake ta kallonta,yana ji a ransa inama Umma zata
janye tsanan da takewa TAIMIYYAN da ayau zai miƙa ƙoƙon baransa wajen Iya da Baba Sani
akan su bashi aurenta,sai dai ko kaɗan baya hango alamun risina a idanun Umman,TAIMIYYAH
tayi saurin ɗauke idanunta akansa ta mayar kan Iya wacce ke hakince tana kallo da sauraren
komi,Baba Sani ya kalli Iya yana faɗin "Iya ko kina da abin cewa?" Iya ta gyara zama tana faɗin
"O'o'o'oh bani da abin cewa sai dai kawai fatan Allah ya fito musu da abokan rayuwa nagari yai
musu albarka,ya tsare mana su da mutuncin su tare da ɗaukacin ƴaƴan musulmi baki ɗaya."
"Ameen ya hayyu ya qayyum,Iya mun gode sosai da addu'a." Cewan Baba Sani kafin ya maida
dubansa ga gimbiyar tasa yana tambayanta ko itama tana da abin faɗi,amma sai ta taɓe masa baki
tare da girgiza kai alamun bata da abin cewa,hakan yasa Baba Sanin ya rufe taron da addu'a ya
sallami kowa yace su je su kwanta,gobe kuma Zuhura ta tuna masa ya bata kuɗin Form taje ta siyo
ta cike,ta amsa masa da "Tuh." Lokacin da suke tashi don barin falon nasa,Sadeeq bai tashi ba don
Baban ya tsaida shi,kusan a jere TAIMIYYAH da Zuhurah suka fito daga falon Baban,Zuhura ta
jefawa TAIMIYYAH wani kallo tana magana ƙasa-ƙasa yadda TAIMIYYAN kawai zata jiyo ta,ta
soma faɗin "Wallahi ke baki isa ki jajibo wani shegen karatu kisa asakani yi dole ba,ni babu wani
Computer Training ɗin da zan yi,ke karatu ya gani don kin rasa madafa inba karatun ba,tunda babu
me zuwa ya taya ki ahaka kina gurguwa,ba dole ki ta jajiban karatu daga wannan ki faɗa wancan
ba,sai kiyi tayi kila a yawon gantalin karatun kya samu ki haɗu da gurgun irin ki da zai kwashe
ki,ko kuma ki samu wani ɗan wahalan da zaice zaiyi maneji dake mitsuww!" Ta ƙare maganan
tana jan dogon tsaki ta wuce TAIMIYYAN fuu! Hakan yasa TAIMIYYAH bin bayan Zuhuran da
kallo,ta saki wani murmushi me ɗaci akaron farko da Zuhuran taci fuskanta hawaye bai nemi zubo
mata ba,ta riga ta ɗaukarwa kanta da Iya alqawarin ba za su sake ganin hawayenta don sun goranta
mata ko sun kirata da kalmar gurguwa ba,ta cigaba da takawa tana baro Sashin na su,can ta hango
Iya wacce ita ta ƙofan Falon Baba Sani ta fice bata biyo ta cikin gidan ba,hakan yasa kusan a tare
suka isa Sasan Iyan da TAIMIYYAH.
"Zainab kin dai ji me Baban ku yace ko? To kaman yadda na sha faɗi miki ne,ki shiga hankalinki
ki baiwa duk wasu masu son ki dama,ta hakane zaki fuskanci me ƙaunarki tsakani da Allah har ku
fahimce juna."
Iya tayi maganan lokacin da TAIMIYYAH ke takawa don shigewa ɗaki ta kwanta,TAIMIYYAH ta
waiwayo tana sauke idanunta akan Iya tare da gyaɗa kai,daga haka ta wuce ɗakinta don sosai take
jin bacci,Iya tabi bayanta da kallo tana tuno wasu shekaru da suka shuɗe abaya....
Bari mu ji miye asalin waɗannan bayin Allan.
_______
Alhaji Amadu haifaffen garin Zaria ne,a wata anguwa da ake kira da Rimin tsiwa,tun asali ya taso
da son karatun zamani dana addini,hakan yasa ya kasance me tsananin ƙwazo da maida
hankali,har yakai matakin shiga jami'a inda ya karanci MASS COMMUNICATION,lokacin da ya
kammala karatun bai wani jima ba ya fara aiki da gidan Radion tarayya da ke Kaduna,a lokacin ne
kuma Allah ya haɗa shi da Fatima wato Iya kenan,ba'a ɗauki lokaci ba suka fahimci juna Iyaye
suka shiga cikin maganan akai aure,Iya itama Iyayenta duk haifaffun Zarian ne suna zaune a
anguwan Juma,lokacin da biki yazo sai ya kama mata haya a wani anguwa da ake jira Tudun
Jukun a cikin birnin Zazzau ɗin,yana tafiya aiki Kaduna ya dawo duk ƙarshen mako ko kwanaki
uku,Fatima wayayyace itama ƴar boko wacce ta kai matakin kammala Sakandiri Skull,sai dai daga
matakin Sakandiri sam bata cigaba da karatun boko ba,sai ta dagewa zuwa islamiya na matam
aure tana kwasan tarin ilimin addini,cikin shekaru biyar da auren su Allah ya azurta su da samun
ƴaƴa uku,na farko me suna Sameer sai Sani sai mace me suna Bilkeesu,daga nan Iya bata sake
samun haihuwa ba,shi kuma Alhaji Ahmad bai kuma wani auren ba,duk da a lokacin ƴan uwa sun
sha zuga shi akan hakan,musamman lokacin da aka ga buɗi ya same shi yayi kuɗi har ga gina
ƙaton gidansa a Gyallesu sun tare,amma yai biris ya maida hankalinsa akan gina rayuwan
ƴaƴansa,da basu nagartaccen ilimin zamani dana addini,hakan yasa yaran suka taso da wani irin
nagarta da tarbiyya me kyau,don Iya ta kasance jajirtacciyar uwa,mara wasa da ɗaukan wargi, ta
tsayu matuƙa akansu har suka kawo lokacin girma,manyan mazan suka shiga jami'a ita kuma
Bilkisu na matakin gama Sakandiri a lokacin,da yake ta taso da jikin girma da kyawun halitta
wanda ta gado a wajen Iya ,sai manema suka fara mata sallama,ganin hakan yasa Alhaji Amadu
cewa da zaran ta kammala Jarabawan kammala Sakandiri aure zai mata,ta cigaba da karatun a
ɗakin mijinta,hakan ko ya kasance bata ɗauki dogon lokaci ba wani ya fito da aka aminta da shi
me suna Ameenu,ɗan Zaria ne amma yana aiki a Kano,aka sanya lokaci kaɗan akai bikinsu tare da
kai Amarya Kano,su kuma su Baba Sani aka cigaba da karatu,lokacin da suka kammala karatu
kowa ya fara kawo ƙarfi don suna sana'a bawai bokon suka tasa agaba ba,musamman Sameer yafi
ɗan uwansa son nema da dogaro da kai,kuma cikin sa'a duk abinda yasa agaba sai ya samu
buɗi,bayan sun kammala bautan ƙasa ne Allah ya haɗa shi da Zainab,wata irin kyakykyawan
budurwa me tarin hankali da nutsuwa,anan ƙasan layinsu take gidan da ake riƙonta,don asalinsu
ƴan Daura ne katsinawa,aure ya kawo Yayarta Zaria da take kira da Anty Mardiyyah shine take
riƙonta,tunda Sameer ya ƙyalla ido akanta su Iya basu sake ganin nutsuwansa ba,har sai da Allah
ya nufi aurensu da ita,wani irin soyayya suke gwadawa juna na ban mamaki,lokacin da akai musu
aure Zainab da ake kiranta da TAIMIYYAH a gidansu tana matakin Degree ne a ABU da ke congo
tana karantar Law,Sameer mahaifinsu Alhaji Amadu ne ya gina masa babban flat a filin da ke
cikin gidan wanda ya siya ne dama sabida su biyun shi da qaninsa Sani,da aka tashi fara ginin sai
aka gina duk biyun a lokaci guda kuma ginin iri ɗaya komi da komi,daga Iya har Baba Amadu
kaman yadda ake kiran mahaifinsu Sameer ɗin,hankalinsu ya kwanta da auren Sameer tun
abinciken farko da sukai game da nagartan Iyayen TAIMIYYAH,sai dai basu sake gasgata hakan
ba sai da TAIMIYYAH ta shigo cikin gidan,sannan Iya ta sake sanin ɗanta yayi dace da mace ta
gari,sam bata da hayaniya ga tsananin kunya kaman ba ƴar boko ba,tana da biyayya matuƙa agun
mijinta da su Iya,hakan yasa cikin ƙanƙanin lokaci ta siye zuciyan Iya,wacce Allah ya ɗaura mata
son matan ɗan nata,har yakai ta daina mata kallon suruka ta koma yi mata kallon ƴar da ta
haifa,kasancewan mace ɗaya ta haifa kuma tayi nesa da ita,don Anty Bilki kaman yadda ake kiran
Bilkisun sam bata cika zuwa gari ba inba da wani abu ba,mijinta me kulle ne sosan gaske shiyasa
Iya da ta samu TAIMIYYAH a matsayin suruka ta gari sai ta maida ta tamkar ƴa,sam bata taɓa
ganin aibun yarinyar ba sabida biyayyan da take mata da yadda ta iya kula da ɗanta,domin cikin
shekaru biyu da aurensu da Sameer ɗin kowa sai tanka irin kyawun da yayi wanda ke alamta yana
samun nutsuwa da kwanciyan hankali,itama TAIMIYYAH tayi wani girma da cika duk da cewa
bawai jikin ƙiba can gareta ba,cikin kwanciyan hankali take cigaba da karatunta,sam Iya bata
sanya musu idanu a lamuran su irin yadda wasu surukan keyi,ba ruwanta da shiga Sasan su sam
sai in wani ba lafiya a cikinsu ta leƙa tace sannu,TAIMIYYAH itace me tarewa a Sashin Iyan da
zaran ta dawo Skull,cikin haka Sameer ya samu aiki a Kaduna a wani ma'aikata me suna
NNDC,don haka sai ya koma zuwa duk Weekend,haihuwa shiru-shiru har sun shiga shekaru uku
da aure,Iya bata taɓa nuna damuwa ba sai binsu da addu'a da take yi,a cikin haka shima Baba Sani
ya gabatar da Zuwaira a matsayin wacce zai aura,sun haɗu da ita tun wajen bautan ƙasa wanda shi
aka tura shi Yobe,a can suka haɗu suka kamu da son juna wanda ƙarfin soyayyan duk ta
wayane,don Yobe ba kusa bane baya samun zuwa,sai da Iyayen Zuwairan suka buƙaci ganinsa
sannan ya wanke ƙafa yaje can Yoben,Maman ta asalinsu Shuwa ne sai Baban ne fulanin
Yobe,lokacin da Sani ya gabatarwa Iya zancen sam ba haka taso ba,ta so ya samu yarinya a kusa
yai aurensa ko don sauƙin bincike amma ya dage shi sai Zuwaira,Alhaji Amadu yace a barsa da
zaɓinsa ya tashi qanninsa da wani abokinsa ya tura su Yobe domin bincike,aka tabbatar musu da
Iyayenta mutanan kirki ne.....✍🏻
#Ɗansabo ce#
[12/14, 3:42 PM] +234 703 040 9541: *TAIMIYYAH*
*Page10*
Ba'a ɗauki wani dogon lokaci ba aka sanya ranan auren Sani da Zuwaira,kwanaki suka cigaba da
shuɗawa har zuwa lokacin da aka ɗaura aure aka ɗakko Amarya daga Yobe aka kawo masa ita
Zaria,Iya da ƴan uwanta sun sha hidima TAIMIYYAH ma ba'a barta abaya ba wajen hidima da
baƙi,har zuwa lokacin da taro ya watse aka bar Amarya da Angonta,Amarya Zuwaira bata wani
jima ba ta fara bayyana halayyanta tsaf,irin matannan ne masu hassada da baƙin hali,tunda ta
fahimci matar wan mijinta wato Zainab TAIMIYYAH ta fita hutawa,mijinta yafi na ta wadata
shikenan ta ɗauki karan tsanan da nuna kishinta afili akan TAIMIYYAN,kai kace sun haɗa miji
ɗaya ne,Iya tun ba ta kula da yadda Zuwairan ta fara nunawa Zainab munanan halaye har ta
karanci inda Zuwairan tasa gaba,hakan yasa ta zaunar da Zainab tai mata nasiha akan cewa sam ko
da wasa kada ta biye ta Zuwairan har wataran aji kansu,ta kama girmanta a matsayin ta na babba
kuma mijinta shine gaba dana Zuwairan,Zainab TAIMIYYAH ta ɗauki nasihan Iya da girma
sosai,kuma sai akai sa'a ita ɗin me tsananin takatsantsan da kauda kaine,sam bata shiga shirgin
Zuwairan tunda ta gane inda tasa gaba,ta maida hankali da kula da karatunta da Mijinta idan yana
gari,a hankali watanni suka fara shuɗawa cikin da Zuwaira ke ɗauke da shi ya fara turowa,wanda
sam babu wanda yasan da samuwansa daga Iya har Zainab ɗin,domin sam Zuwairan bata shiga
shirginsu ko Iya bata damu da zuwa Sasanta ta gaida ta ba,sai ta busa iska wanda sam Baba Sanin
bai san da hakan ba,Sosai Iya har ma da TAIMIYYAH sukai murnan samuwan cikin,Iya ta dage da
yiwa TAIMIYYAH addu'an itama Allah ya kawo mata nata rabon,amma shiru kake ji har zuwa
lokacin da cikin Zuwaira ya isa haihuwa,ta haifo ɗanta Namiji ƙato wanda bai baro komi ba a
kamannin ubansa,Kyakykyawan gaske duk wanda ya zo barka sai yayi santin yaron kaman a
ɗauke a gudu,tunda Zainab TAIMIYYAH ta ɗaura ido akan yaron taji duk wani soyayyanta akan
yara da take dannewa don kada a fahimci rashin samun haihuwan su na damunta,sai ya taso gaba
ɗaya ta ji wani irin son yaron ya dira a zuciyanta,duk wani motsin Zainab TAIMIYYAH akan
yaron ashe Zuwaira na ankare da ita,aiko ana gama shan shagalin suna aka watse aka bar
Zuwairan da wata Innar ta da zatai mata zaman Jego,sai ya zama duk lokacin da Zainab zata shiga
don duba jaririn da yaci suna Abubakar Sadeeq sai Zuwaira ta tsiri ɗaukansa ta riƙe,ko ta ƙirƙiri ba
shi Nono sam bata bari yaje hannun TAIMIYYAH sai idan ta shigo yana hannun Inna shine Innan
zata bata ta ɗauka,tun TAIMIYYAH bata fahimci Zuwaira ba ta son ta da ɗanta ba har ta
gane,hakan kuma ya taɓa zuciyanta matuƙa,har da ta koma sashinta sai da ta zubda hawaye,karon
farko da taji tana tsananin son haihuwa,Iya ma ta daɗe da gane cewa Zainab ɗin tunda Zuwaira ta
haihu ta fito da son haihuwanta a fili,hakan yasa watarana ta zaunar da ita tana mata nasiha da
kwantar mata da hankali akan cewa komi na Duniya rabo ne kuma yana da lokaci,kada ta saka
damuwa a ranta suma nasu rabon nanan zuwa,TAIMIYYAH taji kunya sosai a lokacin amma daga
baya kaman yadda Iyan tace ta dagene da addu'a hakan ya kasance,duk idan tasa goshinta a ƙasa
sai ta roƙi Ubangiji ya basu rabo me anfani,amma fa soyayyan da takewa Sadeeq yaƙi barin
zuciyanta sai dai taja baya sosai da kai kanta Sasan Zuwairan da sunan taje ɗaukan mata yaro
tunda ta nuna bata so,don tana da matuƙar gudun zuciya,takan gansa ta ɗauke shi idan Inna
takaiwa Iya shi,a haka rayuwa ta cigaba da gangara musu sam Sameer bai taɓa nuna damuwansa
akan rashin haihuwan su ba,kuma sosai Allah ke ƙara masa buɗi yana matuƙar samu da
kasuwancinsa da yake,ga kuma ƙarin promotion da yake samu a wajen aiki,lokacin da Sadeeq ya
samu shekaru biyu da watanni a lokacin Zuwaira ta sake samun ciki,a kuma lokacin ne Allah yai
ikonsa akan su Zainab itama ya bata rabo,murna a wajen Iya da ita kanta Zainab ɗin ba'a
magana,hatta da uban gayyan Alhaji Sameer wanda zuwa lokacin yaje Hajji,murnan ba'a
magana,sai dai murnan nasu ya katsene a wani dare da Allah ya ɗauki rayuwan Alhaji Amadu
mahaifin su Sameer ɗin,wanda yai mutuwan farat ɗaya domin sun kwanta da Iya lafiya-
lafiya,cikin dare ciwan kai na ajali ya samesa kafin gari ya waye yace ga garinku nan,mutuwa ne
da ya jijjiga duka Familyn sa,tare da gigita iyalansa domin Iya sai da akai uku ta fara gane
kanta,hatta da TAIMIYYAH mutuwan surukin nasu ya taɓa ta matuƙa,haka aka share zaman
makoki har kowa ya watse,aka bar Iya da takaba wacce cikin ƙanƙanin lokaci duk ta fita
hayyacinta,amma cikin hukuncin Allah tana addu'a kuma ana bata rubutun dangana tana sha,har ta
kwantar da hankalinta zuwa lokacin fitanta takaba,ta gama sarewa da kuma sadaukar da cewa
Amadun ya tafi inda babu dawowa kuma dole rayuwa tacigaba,don haka sai ta sake miƙa wuya ta
cigaba da yi masa addu'a,Alhaji Amadun na da watanni shida da rasuwa,Zuwaira ta haifo ƴar ta
Zuhrah yayinda Zainab ita a lokacin cikinta ya shiga watanni shida,amma girmansa kai kace
yakai watanni takwas,Zuhrah na da watanni huɗu har ta fara koyan zama,wata ranan Juma'a Allah
ya sauki Zainab ta haifo ƴar ta mace ƙatuwan gaske,kyakykywan jinjiran da ta tafi da zuciyoyin
mutane da yawa,ciki har da Iya wacce tunda ta ɗauki yarinyan taji wani irin ƙaunarta me zafi yana
bin jininta,a ranan ne kuma Alahji Sameer ya dawo Weekend ya riski wannan farin cikin na samun
ƙaruwa,lokacin da ya ɗaura ido akan yarinyan sai yaji wani irin soyayyanta na ratsa ilahirin jinin
jikinsa,babu inda ta baro kamannin uwar ta sai manyan idanun ne kawai irin na Sameer ɗin,wanda
suma suka gado wajen Iya,sai dai abin tausayi tunda Zainab ta haihu sai kuma ciwo sam babu
lafiya,aka kwasa aka nufi asibiti da ita nan take aka basu gado,domin tana kuka da ciwan kai me
tsananin gaske,wanda ake tunanin ko hawan jini ne ya sameta,amma bayan gwaje-gwaje aka gano
babu wani hawan jini a tare da ita,kwananta biyar a asibitin Allah ya ɗauki a barsa,wani irin
mutuwa da ya gigita ahalin Alhaji Amadu baki ɗaya,har fiye da yadda suka ji mutuwansa,Iya tayi
wani irin gigicewa da wannan mutuwa da yazo musu a bazata,cikin kuma lokacin da suke tsananin
buƙata da fatan Zainab ta rayu ta raini Kyakykyawan ɗiyar ta,sai dai shi Allah baya barin wani don
wani,da zaran yayi kira dole a amsa kiransa,to hakan ne ta kasance aka ɗauke Zainab aka bar
jinjiran ta,Alhaji Sameer wanwar aka kai shi asibiti baisan wanda ke kansa ba sabida tsaban gigita
da fita hayyaci,jininsa yai wani irin hawa cikin ƙanƙani lokaci,don ko sallan janazanta bai samu ba
yana asibiti aka kaita gidanta na gaskiya,duk wanda ya shiga gidan ta'aziyan Zainab dole ya fito da
kuka sabida tausayin Iyayenta da danginta,da kuma baiwar Allah jaririyan da ta bari,wacce Iya ta
ke riƙe da ita gam ta kankane ta hana kowa,ita ke bata madara idan tai kuka tai mata komi,Yayar
Zainab ɗin ko Anty Mardiyyah ko magana bata iyawa sai kuka,har akai bakwai suna cikin wani
irin yanayi na alhini me taɓa zukatan masu tsoran Allah,a kuma ranan bakwai ɗinne akai zama da
ƴan uwan Zainab ɗin akan son abasu jinjiran su riƙe,amma Iya ta daka tsalle tace bata san wannan
zancen ba,babu me raba ta da jikanta indai tana raye wacce tunda tai kwanaki bakwai aka sanya
mata sunan Mahaifiyanta wato Zainab,kuma nan take aka cigaba da kiranta da TAIMIYYAH
kaman yadda ake kiran Marigayiyan,duk yadda Anty Mardiyyah ta so abata riƙon Little
TAIMIYYAH amma Iya ta ƙeƙashe ƙasa tace bata san zancen ba,shi ma kuma uban yarinya Alhaji
Sameer ya nuna yafi son ƴarsa a wajen Mahaifiyansa,haka suka haƙura aka bar yarinya a wajen
Iya,wanda ya zama sila da kuma tushen tasowan TAIMIYYAH a wajen kakarta Iya,wacce ta maye
mata gurbin uwa ta kuma bata nagartacciyar tarbiyan da uwa tagari zata baiwa ƴar ta,Zuwaira tun
TAIMIYYAH tana ƙarama ta tsane ta sabida irin yadda Iya ta ɗauki son Duniya ta ɗaura akan
TAIMIYYAN,sam bata bi takan Zuhrah da suka taso kusan kai ɗaya da TAIMIYYAN,sai dai shi
ma Sadeeq da zuwa lokacin ya daɗe da shiga makaranta yayi wayo yana da shekaru huɗu,duk inda
yaje ya dawo zaka same sa a Sashin Iya yana nane da ita yana shafa kan TAIMIYYAH,a hankali
rayuwa ya cigaba da garawa yaran suna wayo,soyayyan da Iya ke wa TAIMIYYAH na sake fitowa
fili,lokacin da su TAIMIYYAH ke da shekaru biyu suna gudunsu ko'ina ita da Zuhurah wacce ta
bata watanni huɗu,tare suke wasa da Zuhurah da Sadeeq ma baki ɗaya,tun Iya bata barin
TAIMIYYAH zuwa Sasan Zuwairah don kada ta cutar da ita,har ta haƙura sabida yadda
TAIMIYYAN kullum ke nane da su Sadeeq da Zuhurah,Alhaji Sameer da tun mutuwan matarsa
yaji gaba ɗaya Zaria tai masa zafi,sai ya zamana ya ɗauke ƙafansa daga zuwa sosai,sai a haɗa sati
biyu bai shigo garin ba,duk da cewa soyayyan ƴar sa nanan danƙare a zuciyansa irin soyayyan da
baki bazai iya misaltawa ba,amma zuwan shi Zarian na masa wani irin fami ne idan har yazo ya
buɗe Part ɗinsu ya ga babu Zainab,shi yasa duk son sa da zuwa ya ga ƴar sa da ayanzu soyayyan
da yake wa uwarta ya gama komawa kanta yake dannewa,sai dai duk wani siyayya na abin buƙata
ana jibgewa Iya su,har abin na zarta ƙa'ida sai dai Iya tai ta kwasan rabi tana turawa Zuwairah
taiwa Zuhrah anfani dashi,hakan ya sake janyo wani irin kishi da tsanan TAIMIYYAH a zuciyan
Zuwairan,tana tsananin adawa da yadda yarinyan ta taso da wani irin kyawu me fisgan hankali,da
tarin farin jini, Sadeeq shi ya raɗawa Zuwairan Umma tunda ya buɗi baki,suma su TAIMIYYAH
da bakinsu ya fara buɗuwa sai suka bi bakinsa suna kiranta da Umman,a wani dare lokacin su
TAIMIYYAH na da shekaru uku ta farka da wani zazzafan Zazzaɓi,gari na wayewa Iya ta kira
Alhaji Sameer ta sanar masa,shi kuma ya turo Sani wani yaronsa da ya barwa mota yana kai Iya
anguwa da uzurorin kai TAIMIYYAH asibiti idan buƙatan hakan ya taso,cikin ƙanƙanin lokaci sai
ga Sani ya iso suka wuce asibiti da TAIMIYYAH,tsananin zafin zazzaɓin yasa aka rubuta allurai
biyu da xa'aiwa TAIMIYYAN,anyi na farko ranan lafiya lau Iya ta dawo da ita,a washegari aka
koma akai na biyun,aiko washegari ƙafan yarinya yai lakaf sam bata iya motsa shi bare aje ga
zancen takawanta,babu shiri Iya suka maida TAIMIYYAH asibiti da gaggawa,amma duk iyakan
binciken likitoci an rasa gane daga ina matsalar take,domin likitan da yai alluran kowa ya shaida
ƙwararrene,daga ƙarshe aka bar abin akan cewa anyi rashin sa'a ne alluran ya taɓa jijiya,duk inda
tashin hankali ya kai tuh Iya ta shige shi,a washegari Alhaji Sameer ya diro Zaria hankali tashe
don ganin lafiyan ƴar sa,wasa-wasa sai ƙaramar magana ya fara zama babba,TAIMIYYAH ƙafanta
da akaiwa allura ya fara shanyewa,ta koma sam bata iya tafiya bare motsa ƙafan,wani likita ya
bada shawaran afara mata gashin ƙashi a asibitin ABU da ke Tudun wada Zaria,cikin ikon Allah
ana fara gashin ƙashin ta fara iya motsa ƙafafun,amma fa har lokacin bata iya tafiya,hankalin
kowa a tashe yake da wannan tsautsayi daya gitta a rayuwan kyakykywan ɗiya irin TAIMIYYAH
wacce a duk kwanan duniya kammaninta da mahaifiyanta ke sake fitowa ƙarara,Zuwaira ita ce
kaɗai bata taɓa nuna damuwanta akan wannan lalura ba,wanda hakan yasa Iya sake ƙullatanta a
zuciyanta da ƙinta a ranta,faɗin irin wahala da faɗi tashin da Iya da Alhaji Sameer suka sha akan
TAIMIYYAH bazai misaltu ba,kafin Allah yai ikonsa a samu TAIMIYYAN ta fara taka ƙafan da
taimakon dafa ƙafan da ya shanye,tun ana ganin kaman idan ancigaba da gashin da yawon
asibitocin xata koma da tafiya ba tare da sai ta dafa ƙafanta me laluran ba,har Iya ta fara sarewa ta
cire rai tunda ta ga irin shanyewan da ƙafan daya samu laluran yayi,tuni Zuhrah har an saka ta
makaranta lokacin,ita kuma Zuwaira tana fama da laulayin ciki na uku,Alhaji Sameer a lokacin da
ya sadaƙar ƙafan ƴar sa tabbas ya nakasa sai wani irin ƙaunarta da tausayinsa suka sake kama
ruhinsa,kaman yadda ya kasance ga Iya wacce laluran nakasan ƙafan TAIMIYYAH,ya sake
janyowa TAIMIYYAN wani irin soyayya da tausayi a zuciyan Iya,hatta da Baba Sani wanda a
lokacin ya samu aiki da bankin CBN aka ajesa reshan jihar Kano,ba ƙaramin tausayin
TAIMIYYAH yake ji ba idan ya dawo weekend ya ganta,rayuwa ya cigaba da garawa
TAIMIYYAH na cigaba da taka ƙafanta bisa tsarin halittan da Allah ya nufa,kullum kuma tana
Sasan Baba Sani wajen su Zuhrah,inda abu kaɗan zatayi Umma zata hauta da faɗa tana faɗin "Tafi
can shegiya gurguwa." Tun Zuhurah bata ɗaukan abinda Umma ke faɗi har itama ta fara kiran
TAIMIYYAH da suna gurguwa,Sadeeq ne kawai bai taɓa bin bakinsu ba ko da wasa,saima wani
shaƙuwa da ke sake shiga tsakaninsa da qanwar tasa,don wani lokacin idan TAIMIYYAH sun
haɗu da Zuhurah sun ma Umman ɓanna ta bige su,shi za ka ga ya ja TAIMIYYAH gefe yana
lallashinta,shi yasa Iya tafi ji da shi a yaran Zuwairan ,lokacin da Zuwairah ta haifo Basmah
lokacin Alhaji Sameer ya saka TAIMIYYAH a makarantar boko wani skull da ke tashe a Zaria me
suna JETHRO ACADEMY,Sani shi ya zama Drivern TAIMIYYAH yana kaita ya ɗakko ta,su
Zuhurah su THERBOW Skull Baba Sani ya sanya su,da ƙyar da faɗa da Nasiha Iya ta shawo kan
Alhaji Sameer akan maganan aure,har Allah ya haɗa shi da Samha ƴar nan Kaduna Anguwan
Rimi,ba'a ɗauki lokaci ba akai bikinsu ya kama mata gida anan Kadunan,don a cewansa bazai
kuma sake zaman Zaria ba,sai dai su shigo Weekend ko idan wani abu ya faru su zo su koma,yaso
Iya ta amince masa ya ɗauke TAIMIYYAH ya mayar gabansa,amma sai Samha ta nuna sam
bazata iya riƙe yarinya alhali,ta aure shi a budurwa ɗanya sharaff basu fara moran rayuwansu
ba,itama Iya ta nuna sam bata aminta ba hakan yasa Alhaji Sameer da TAIMIYYAH ke cewa Abie
haƙura,ko kaɗan babu irin shaƙuwa me tsanani tsakaninsa da TAIMIYYAH sabida sunyi nesa da
juna,sai dai kawai idan yazo zai ɗauke ta su je can su je nan yai mata siyayya ya zo ya aje,to haka
rayuwan TAIMIYYAH ya taso Iya kawai tafi sabawa da ita suka shaƙu,sai su Zuhrah da Sadeeq
wanda yake jida TAIMIYYAH sosai,ita kuma Umma ta ɗauki karan tsana ta ɗaura mata,tare da
hantaranta tana sanya su Zuhurah cin xalin TAIMIYYAN wanda hakan ya fara jefa tsoransu a
zuciyan TAIMIYYAH,tun tana ƙawazucin nacewa zuwa Sasan har ta haƙura,daga makarantan
Boko sai zuwa islamiya ke fitar da ita daga Sasan Iya,gashi TAIMIYYAH ta taso da ƙoƙari da son
karatu hakan yasa Abie ɗinta baya jin ciwon kashe kuɗi akan karatunta,tana sake girma da wayo
ne Iya na sake laƙantan hankali da nutsuwan da TAIMIYYAH ta gado wajen uwar ta,gami da tsan-
tsan kyawun halitta,ta taso shiru-shiru mara son haniya da miskilanci,sam in ba ta saba da mutum
ba bazai fahimci halinta na son mutane da faran-faran ba,tana da raunin zuciya da saurin
kuka,musamman idan ana kwaikwayon tafiyanta ko kiranta da suna gurguwa,yanzu zata fashe da
kuka tana kaiwa Iya ƙara........✍🏻
#Ɗansabo ce#
[12/14, 3:42 PM] +234 703 040 9541: *TAIMIYYAH*
*Page 11*
TAIMIYYAH a lokacin da suka girma suka kai matakin gama Secondary School,tun a sannan ta
sake gane irin tsanan da Umma tai mata bana wasa bane,da irin huɗuban da takewa Zuhrah da
Basma akanta, tana cusa musu tsana da kishin TAIMIYYAN a zuciyansu,ko da yaushe tana nuna
ma Zuhrah da take babba cewa,kakarsu Iya tafi son TAIMIYYAH ne kasancewan Abie Baban
TAIMIYYAN yafi Baba Sani kuɗi,abinka da huɗuban uwa tun yaran basa maida kai akan
zantukan ta a hankali suna girma suna sake wayo,har Zuhurah ta fara gasgata hakan tana jin kishin
TAIMIYYAN a zuciyanta da jin haushin yadda TAIMIYYAN ta fita kyawun halitta,a islamiyan da
suke kowa TAIMIYYAH yafi so ba ita ba,haka a dangin su Baba Sani duk idan sun je can Rimi
Family House ɗinsu kowa TAIMIYYAH yafi ja ajiki da yaba kyawun halittanta,hakan ya sake
jefawa Zuhurah ƙin TAIMIYYAH ta ɗauki ɗabi'an ƙuntata zuciyan TAIMIYYAN ta hanyan
kyaranta a bainar jama'a,tana sukan nakasanta da kiranta gurguwa musaka,wanda ta gama gane
hakan shine weakness ɗin TAIMIYYAN,domin bata iya daurewa a duk lokacin da sukai mata
gorin halitta takan ji wani irin ƙunci da ɗaci har ƙasan zuciyanta,wanda take kasa controlling kanta
har sai ta zubar da hawaye,tun Iya bata farga da irin rayuwan da ƴan uwan junan suke ba,har ta
gama gane yadda su Zuhuran ke cin fuskan TAIMIYYAN ko agaban waye,abinda ya fusata
zuciyan Iya har watarana ta haɗa Zuwairan da su Zuhurah tai musu wankin babban bargo,tare da
hana su Zuhuran takowa zuwa sashin ta sai da wani dalili me ƙarfi,itama kuma TAIMIYYAN Iya
tai mata iyaka da shiga Sashin Baba Sanin,sai idan ya dawo taje gaida shi ko ita Iyan ta aiketa ta
fito,amma sam ta hanata zuwa ta zauna bare har su samu daman cigaba da muzantata,wanda hakan
ya sake janyowa TAIMIYYAH wani sabon tsanan a zuciyan Umma da Zuhurah,Alhaji Sameer da
TAIMIYYAH ke kiransa Abie bai taɓa banbanta TAIMIYYAH da Zuhurah a wajen siya musu
tsadaddun Situru na xamani ba,amma sam Umma da Zuhurah basa gani gani suke a komi
TAIMIYYAN sai ta zarta Zuhurah tunda Iya tafi son ta ,ko kaya me tsada aka sai ma Iyan sai ta ce
TAIMIYYAH ta ɗauka ta ɗinka,da kuɗinta ma take siyawa TAIMIYYAN duk abin da tai sha'awa
ta kuma ji tana son TAIMIYYAN da shi,a kwana a tashi su TAIMIYYAH suka kawo lokacin
girma suka shiga shekaran gama secondary skull,zuwa lokacin duk wani kyawu da cikar halitta da
Allah yai mata baiwansa ya gama fitowa fili,Yah Sadeeq lokacin yana shekaran ƙarshe a jami'an
NILE Abuja,wanda Baba Sameer da yai kuɗi sosai zuwa time ɗin shi ya ɗauki nauyin karatunsa
zuwa can ɗin,abinda ya faranta ran Baba Sani matuƙa tare da sake jin ƙaunar Yayan
nasa,TAIMIYYAH ta fito da result me kyau tare da samun manyan kyautuka a ranan Grad ɗin
nasu,sai dai lokacin da suka zo zana Jamb sai akai rashin sa'a bata samu makin da ake nema
ba,domin burin ta shine tana son zama Nurse ko cikakkiyar Lawyer,domin tarihin mahaifiyanta da
taji wacce tana shekaran kusa da ƙarshe ta kammala nata karatun ta haifeta ta rasu,hakan ya dasa
mata son maye gurbin marigayiya TAIMIYYAH,sai dai du ka Allah bai xana hakan a goben
TAIMIYYAN ba sai ta bige da shiga Federal Collage of Education da ke Zaria,kwalejin da suke
kusa sosai aka bata Course ɗin ENGLISH/ECONOMICS course me wuya amma TAIMIYYAH ta
dage akan cewa ya kwanta mata zata yi shi komin wahalansa,don a ganinta idan batai karatun ba
bata san me zatayi ba,musamman a lokacin da take jin kanta cikin wani irin kaɗaici na rashin
abokanan hira a gida,tunda ƴan uwanta na jini da xata raɓe su taji daɗi sun juya mata
baya,tsakaninsu da ita sai kyara da hantara daga su har uwansu,hakan yasa daga kallo sai kallo sai
kuma wayan da Abie ya kawo musu kyautan sa a wani tafiya da yayi xuwa UK,ya zo musu dashi
ita da Zuhurah iri ɗaya samfurin Iphone 12Pro Max,to tunda ta buɗe shafukan sada zumunta nasu
Instagram,Whatsapp,Twitter da sauransu sai suna ɗebe mata kewa sosai,musamman da Maryam
Salis tasa akai adding ɗinta a groups na littafai,sosai take jin daɗin karance-katance especially idan
ba Skull ranan,suna hiran su da Iya sosai domin komi nata kai tsaye take tinkaran Iya,sabida haka
ta hore ta dashi,don riƙon uwa tai mata bana kaka ba,sai dai ita TAIMIYYAH ba hakan tafi so
ba,tafi sha'awan ta jita cikin tsararrakinta,a skull ita ba gwanar tara qawaye bace,daga Maryam
Salis,Murja Gubuci,sai Fatima Lawal, ko kaɗan TAIMIYYAH bata taɓa fuskantan kyara ko gorin
halitta a skull ba,duk da yadda take kame kanta sam bata son shiga cikin mutane sabida gudun gori
ko kyara akan kasancewanta me laluran ƙafa,lokacin da suke primary ne ma take samun irin yara
masu tsokananta suna kiranta da gurguwa-gurguwa,ko yara suyi ta binta suna kwaikwayon
tafiyanta har sai Teachers sun gani sun tsawatar,domin TAIMIYYAH zama take tai ta kuka idan
ana tsokananta,ta sha cewa Iya akaita a gyara mata ƙafanta ko za'a daina kiranta da gurguwa,amma
tunda ta ƙara wayau ta sanya dangana ko an kwaikwayeta bata kuka,duk qawancen da suke yi da
su Maryam ɗin dukkaninsu Iya bata taɓa bari taje gidajensu ba,sai sau ɗaya ne taje gidan su
Maryam Salis dake Gaskiya Layout,su dai sun zazzo nan musamman Murja da Maryama suna
matuƙar son TAIMIYYAH sosai,sai wata ƴar islaminyansu Bushira wacce suke layi ɗaya,amma
itama ɗin Iya bata cika bari taje gidansu ba,a cewanta bata son yawan bin qawaye gara su su
biyoka gida,Yah Sadeeq tun da TAIMIYYAH ta girma ta xama budurwa sai ya sake ninka
kulawan da yake bata,yana janyota a jikinsa sosai tayi sabo da shi ta yadda har yake iya sanin
wasu damuwoyinta,shi kuma duk a lokacin danne Soyayyanta da yake ji yake,har ta kai ta kawo
abin ya fara fin ƙarfinsa,tuni Umma ta lura da irin shaƙuwan da ke tsakanin TAIMIYYAN da
Sadeeq ɗin,watarana ta sa akai mata kiran TAIMIYYAN tai mata kyakykyawan gargaɗi akan ta
fita mata daga harkan ɗa,xagi da cin mutunci ranan TAIMIYYAH ta sha har ta gode Allah,haka ta
baro Sashin ta koma wajen Iya tana kuka sosai,Iya batai ƙasa a guiwa ba bayan ta tirke
TAIMIYYAH taji yadda sukai da Umma,taje tai mata wankin babban bargo,TAIMIYYAH sam
bata damu da zuwa Lagos wajen Abie ba,domin a shekaran da ta shiga FCE a wannan shekaran ne
Abie ya samu canjin wajen aiki aka maida shi Lagos,can Port-authority a kuma babban matsayi
aka kai shi wajen,sai ya ɗauke Samha daga Kaduna suka koma Lagos ɗin da zama,a lokacin an
haifan ma TAIMIYYAH qanni biyu duk mata Raudha da Maryam da ake kira da Nahar,yaran sun
shiga ran TAIMIYYAH amma rashin samun fuska a wajen Ummie matar Abie ɗin yasa sam bata
jin daɗin zuwa wajensu ko ta samu hutu,ta gwammace tai zamanta da Iya duk sanda su suka zo sai
ta ga qanninta wanda suma suke tsananin son ta,sabida yadda take jansu a jiki idan sunzo garin,sau
ɗaya ta taɓa zuwa Lagos ta ga inda su Abie ɗin suke,tai Sati biyu Iya ta matsa akan a dawo da
ita,dama Abie ɗin tabi a jirgi lokacin da zai koma,da zata dawo ma a jirgin ya haɗo ta da wani
abokin aikin sa da zai zo Zaria,tun daga lokacin bata kuma zuwa ba har ta kammala karatun NCE
ɗinta baki ɗaya,ita kuma Zuhurah ta kammala Diploma da tayi a ABU Congo inda ta karanci
Public Administration.Lokacin da Yah Sadeeq ya ga sun kammala karatun ne,ya fallasawa
TAIMIYYAH sirrin zuciyansa akanta,amma sai TAIMIYYAN ta nuna masa rashin yiyuwan
abinda yake muradi,ba ƙaramin ƙiyayya Umma take mata ba,TAIMIYYAN
Duk da kasancewanta nakasashshiya hakan bai hanata cika burinta na samun ingantaccen ilimi
ba,matsi da ƙuncin rayuwa tare da gorin halitta da take fuskanta daga ahalinta su Zuhuran,duka bai
raunata zuciyan TAIMIYYAN ba bare har taji cewa ita ɗin kasashshiyace har ta kasa maida
hankali akan karatun ta.Abu ɗaya ta sawa ranta shine Allah shi ke halittan bawa ta yadda duk yaso
ya gansa,ta kuma sawa zuciyanta cewa nakasan halittan bawa baya tashi abanza domin ubangiji
yai mata baiwa da tarin ni'imomi cikin rayuwanta.Wanda a yanzu ne take sake ganin cewa lokaci
yayi da zata bi shawarwarin Iya wajen dake zuciyanta,ta nuna ma su Zuhuran cewa a yanzu duk
wani gori da cin fuskansu ya daina damunta,zata maida hankali wajen inganta rayuwanta da ilimi
ta kowani fanni,domin tana sha'awan takai wani matakin da zata dogara da kanta har ta tallafi
nakasassu irin ta,waɗanda basu da gata tunda ita Alhamdulillah cikin gata da kyakykyawan
rayuwa ta tsinci kanta .
_To masu karatu mun ji miye asalin TAIMIYYAH da yadda ta taso,yanzu labarin zai fara inda
zamu ji cikakken ya rayuwan TAIMIYYAN zai cigaba da kasancewa da ƴan uwan ta su Zuhurah?
shin burikan ta zasu cika,wani me rabon ne zai yi nasaran shi ga zuciyan TAIMIYYAN har ya cire
mata duk wani tsoro da shakku da take ji akan aure,gurgun ne ɗan uwanta zata samu kaman yadda
su Umma ke faɗi,ko kuma wani ne na daban ubangiji zai jefo shi cikin rayuwanta? Duka zaku ji
amsoshin idan kun cigaba da bibiyan alqalamin Ɗansabon,_
Assalamu alaikum! My peoples duka anan na kawo ƙarshen free pages da zan iya baku,ga duk
wacce take buƙatan karanta cigaban labarin TAIMIYYAH sai ki biya kuɗin ki ta wannan asusun
kai tsaye kamar haka👇🏻
Zaki tura 500 kacal ta wannan account ɗin 0504192664 Aisha Ibrahim Dansabo GTbank,sai ki
turo da shaidan biyan ki ta wannan layin 08167768704.
Masu turo Credit zaku turo ta katin MTN na 500 ta wannan layin 08167768704 shaidan biyanku
ma ta layin zaku tura.
*Balance* - Zai nuna kudin account dinku da zaku iya sayayyan littafai cikin kasuwar
ArewaBooks.
*Credit/Debit Card* - Hanyar farko kuma mai dadi wajan Recharge din account dinku.
A inda (Enter your amount) za'a saka kudin da akeson Recharge din sai a taba "Proceed". Zaibude
muku inda zaku saka bayanan katin banki, kuna gamawa kudinku zaishiga account dinku kaitsaye
(instant).
--------
*Bank Transfer*
*Airtime Transfer*
Saidai su ba kaitsaye bane (instantly) sai ArewaBooks ta tabbatar da Transfer din, amman bayakai
1hour za'a gansa a Balance.
*Bank Transfer* - kamar yadda akwai bayani a sama da kuma account number ArewaBooks.
*Airtime Transfer* - muna bada shawaran ayi amfani da *Debit Card* kokuma *Bank Transfer*
akan *Airtime Transfer* , amma idan yakama babu mafita saishi tau muna amsar:
MTN,
9Mobile
Glo
Airtel
Amma kamar yadda akayi rubutu a sama afara tuntubar ArewaBooks a WhatsApp domin akwai
percent da ake cirewa na canji(convert) kafin kudinka yashiga Balance.
*Page 12 to13*
*CIGABAN LABARI.*
"Wallahi bari kawai wani Computer Training na shiga in gaya miki,shine na je yin Registration
zuwa next week zan fara zuwa."
Cewan TAIMIYYAH har lokacin murmushi yaƙi barin face ɗinta,ta waiwaya wajen Iya tana faɗin
"Iya na dawo,ya ciwan kan na ki ina fata dai ya kama gabansa?"
Iya ta murmusa tana faɗin "Ya kama gabansa kam Alhamdulillah.Na ga ai kin yi saurin dawowa
da har na ce ko za ta kira wayanki,tace a barki dai muna ɗan taɓa hira kin ga gashi har kin dawo
ɗin."
Iya tayi maganan tana tashi don komawa ɗaki,ganin hakan yasa TAIMIYYAH miƙewa tana cewa
Maryam "Mu je ɗaki Besty,gaskiya yau kin biya ni na ji daɗi sosai da wannan ziyara."
Maryam ta saki murmushi tana biye da bayan TAIMIYYAN har zuwa ɗakin ta,Hijab kawai
TAIMIYYAH ta cire ta aje jakanta ta fito zuwa Kitchen don kawowa Maryam wani abu.Duk da ta
ga Iya ma tasa Ladi aje ma Maryam ɗin ruwa da lemu,amma ita tana da raguwan Samosa a Fridge
shiyasa zata soya mata kafin Ladin ta gama abincin Lunch.Cikin minti goma ta gama soya
Samosan ta juye shi a kyakykyawan mazubi,ta ƙara ɗaukan ruwa da lemu ta ɗaura a madaidaicin
Tray ta nufo ɗakin.Maryam ce tayi saurin tashi tana amsan Tray ɗin a hannun TAIMIYYAH tana
faɗin "Haba qawata shine ba zaki kirani in ɗakko ba."
Ta aje Tray ɗin daga saman gadon,idanunta akan TAIMIYYAH da ta saki dariya tana faɗin "Haba
dai zan iya ai, ba gashi na kawo lafiya ba,ke ni fa abubuwa da yawa ba na jin wahalan yin
su,amma ku sai kuita ganin kaman ajigace nake yi ko?"
Ta ƙare maganan cikin low voice,manyan idanunta akan Maryama da ta saki murmushi me
faɗi,kafin ta furta "Wallahi ni haka na ke gani TAIMIYYAH,gaskiya kina da ƙoƙari sosai kam da
son aiki."
Daga haka suka kamo hiran Skull,Maryam ɗin na mitan yadda har yanzu babu wani labari game
da janye yajin aiki,bare su samu su amsa Result ma susan madafa.Daga hiran Skull aka koma na
auren Murja wacce aka sanyawa ranan aure watanni uku masu zuwa.TAIMIYYAH ce ta dubi
Maryam tana dariyan tsokana take faɗin "Mu na gama shan bikin Murja sai kuma naki Besty,ni ba
ki gaya min yanzu waye gwanin ba,tunda kin rabu da Sudais."
Harara Maryama ta zuba mata tana faɗin "Ko kuma sai ke ba,wai TAIMIYYAH ba za ki fito da
miji mu aurar da ke ba,duk irin samarin da ke tare ki a hanya,ba ki sauraransu kar dai kice har
yanzu baki kula kowa?"
"Bana kula su ɗin,kuma ban jin zan ma fara kula sun ba,samarin da ke tare ka a titi dama na arziƙi
ne Maryam? Ai duk me son ka ya biyoka gidan ubanka ne ya gabatar da kansa,ke ni fa babu wani
maganan aure a lassafina,inba gurgu iri na zan samu ba babu wani Namijin da zai ce yana so na in
yarda da shi,ku dai lafiyayyu wanda ba ku da Nakasan da za'a goranta muku don Allah kuyi ku
fito da Mazajen mu sha biki."
TAIMIYYAH ta ƙare maganan tana dariyan hararan da Maryam ke faman zabga mata,kafin
Maryam ɗin ta furta "Okey! Za ki ja da ikon Allah kenan?Don ya jarabceki a hakan shine zaki ce
ke ce za ki zaɓi abinda zai dace da ke ba shi zai miki zaɓin abinda yafi dacewa bako?Kina bani
mamaki TAIMIYYAH don waɗancan shashashan suna miki gori shine ki ke ganin kowa ma
goranta miki zaiyi?To bari ki ji tun wuri ki cire wannan shirmen a ranki,Allah na tuba ke har wani
Nakasa ma ki kai,ga guragu nan da ko tafiya ba sa yi sun kuma yi aure sun haihu.Kuma duk acikin
wanda na sani kar ki ɗauka guragu suka aura,wallahi lafiyayyun maza suka aura don haka kar ki ja
da Allah,ke dai ki bar masa zaɓi shi kaɗai yasan wanda zai zaɓa miki in lokaci yayi,mu dai kawai
muyi addu'a Allah yai mana zaɓi mafi alkhairy,Ke ɗin ma da akaiwa baiwan da mu masu ƙafafun
qalau ma bamu sama ba,ko a kyawunki da cikar halitta aka tsaya TAIMIYYAH ke ɗin matar
manya ce sosai a hakan wallahi,bare azo ɓangaren karatu wannan Brain ɗin naki ba dama
ne,wallahi ki godewa Allah."
Yadda tayi maganan cikin wani narke murya,yasa Maryama dubanta wani abu na motsa
zuciyanta,tana mamakin yadda TAIMIYYAH ta iya shagwaɓa me motsa zuciyan har mata ƴan
uwanta,bare kuma namiji idan tana masa wannan narkewan ai tuni zata gama da shi,ta murmusa
tana duban TAIMIYYAN cikin ido take faɗin "Na ji an bari gimbiyar Yah Deeku wai ina kuka
kwana ne ko auren Zumuncin za'ai ne?"
Maryama ta tsokani TAIMIYYAH tana sakin dariyan taɓara,sabida sun san da labarin Son da Yah
Sadeeq ɗin ke wa TAIMIYYAN,da irin tsanan da su Zuhurah sukai mata,don zuwan Maryam na
farko gidan a gaban idonta Zuhura taci fuskan TAIMIYYAH,wani harara TAIMIYYAH ta watsa
mata kafin ta sanar da ita duk yadda suka kwashe da shi,da umurnin da Baba Sani yai musu akan
fito da miji,ta ƙare maganan tana cewa "Ni kin ga Maryam tunda ba wani nake kulawa ba wallahi
nafi so abar ni nayi karatu na."
Maryam ta taɓe baki tana faɗin "Ke dai kika sani idan Allah ya kawo mijin nan kusa sai mu gani
ko zaki hana mu sha bikin."
TAIMIYYAH ta saki dariya tana taɓe baki itama take faɗin "Oho dai ni dai barni da karanta
littafan Soyayyan muna course,wallahi kuma idan mutum yana karanta littafan sai yayi ta
imagining ina ma kaine star ɗin,ko baki jin hakan Tawan?"
TAIMIYYAH ta ƙare maganan tana sakin dariyan shaƙiyanci,hakan yasa Maryam itama sakin
dariyan tana faɗin "Munafuka mu je dai zuwa,dama irin ku masu gudun faɗawa tarkon luv ai baku
iya kamuwa ba,idan lokaci yazo ni ina matuƙar son in ga wani me sa'an ne zai ɗauke ki."
Itama tayi maganan cike da shaƙiyanci daga haka suka cigaba da hiransu suna baiwa juna
nishaɗi,har zuwa lokacin da sukai Lunch,TAIMIYYAH na jin kaman kada Maryam ta tafi,sai da
Maryama tayi sallan la'asar sannan tayi shirin tafiya,TAIMIYYAH ta yo mata rakiya bayan
Maryam ɗin tayi ma Iya sallama,Iyan har da bada wani haɗaɗɗen turare cikin wanda su Abie ke
yawan kawo mata tsaraban su idan yayi tafiya ko yai mata siyayya a manyan wajeje,sosai
Maryama tayi godia TAIMIYYAH ta rako ta har bakin gate,suna cigaba da hiran da bai ƙarewa
indai an haɗu har a rabu baki bai iya shiru,sallama sukai da Maryam ɗin TAIMIYYAH na bata
tabbacin zata je gidan nasu insha Allah,sai dai kawai taji ta kirata tace gata nan,lokacin da Maryam
ɗin ta fara takawa don barin layin,sai TAIMIYYAH ta juyo tana takawa don komawa cikin
gida,zuciyanta fes da jin daɗin ziyaran da qawar nata ta kawo mata.
________
Tunda suka fito daga gida gabanta ke cigaba da faɗuwa,ta kai dubanta kan A.Maleek ɗin wanda
yake gefenta,ya bala'in haɗe face yana faman danna wayansa,sai ta sake manne masa tana me
ɗaura kanta bisa kafaɗansa,abinda ya janyo hankalinsa har ya ɗago daga latsa wayan nasa yana
sauke manyan idanunsa akanta,yana son jin tausayinta amma yana hana kansa hakan,don yana
lura tun safe da ya tabbatar mata zasu je wajen wani Babban likitan mata,take faman kuka amma
sai bai nuna damuwansa akan kukan nata ba,ya ɗauke kai a yanzu ɗin ma yana sake mayar da
hankalinsa akan Chart da yake da wani manager ɗinsa me kula masa da harkan gidajen gonansa
dake Kaduna,Yusuf Driver ɗinsa ne ke tuƙa su shi da Suhailah suna baya,har suka iso gidan
Doctor Saiff Suhailah bata da wani nutsuwa,kallo ɗaya zakaiwa face ɗinta kasan a ruɗe take,waya
Maleek Ado ya ɗaga ya shiga kiran layin Dr.Saiff ɗin,bugu biyu ya ɗaga Maleek ɗin ya furta "Ga
mu daga bakin gate ɗin mun iso."
Ko mintu biyu baiyi da sauke wayan daga kunni ba,megadin gidan ya buɗe musu gate suka danna
hancin motan ciki,daga can tsaye suka hangi Doctor Saiff ɗin yana jiran shigowansu,ya nufo
motan cikin sauri yana kai hannu ya ƙarisa buɗewa Maleek murfin motan,yana faɗin "Ran
Chairman ya daɗe,barka da ƙarisowa Bismillah mu shiga daga ciki."
Doctor Saiff ɗin ya ƙare maganan da maida dubansa kan Suhailah,wacce ita kuma idanunta nakan
rabin ranta Maleek,daga haka A.Maleek ya miƙe yana sake miƙawa Daktan hannu,cikin muryansa
me cike da ƙasaita yake faɗin "Thank u Dakta,ina ga zamu wuce goben zata sameka a can
ɗin,yadda kuka yi kai tsaye ka nemeni kai min bayanin komi."
"An gama ranka ya daɗe,godia nake zaka jini insha Allah " Cewan Doctor Saiff yana rufawa
A.Maleek ɗin baya wanda tuni ya nufi ƙofan fita falon,Suhailah ta rufa musu baya itama ba tare da
ta tsaya sunyi sallama da matar gidan ba.
Har wajen mota Dr.Saiff yai musu rakiya,shi ne da kansa ya buɗewa A.Maleek murfin motan ya
shiga ya mayar ya kulle yana ɗaga musu hannu,lokacin da Yusuf Driver ya ja motar,Suhailah ta
ɗaga idonta ta dubi A.Maleek,ya balla mata harara lokacin da take matsowa jikinsa,ta haɗe gaf ɗin
da ke tsakaninsu cikin shagwaɓe murya take faɗin "Sweet please mu wuce gidan Hajiya kaina
ciwo yake."
Tayi maganan cike da narke masa face,yai mata kallo ɗaya yana ɗauke kai daga gareta ya mayar
ya saci duban Yusuf Driver,da ya maida hankalinsa kan tuƙin da yake,sannan ya maido da dubansa
kan Suhailah yayi magana cikin wannan dai ƙasaitan nasa "No gida zamu koma i think ina da
Visitors za ku shirya abinci na kaman mutum goma."
"What! Baby mutum goma meyasa ba zaka sa ai order kawai daga Restaurant ba?" Suhailah ta
jefa masa tambayan tana sake narke fuska,sam bata ji zata iya wannan wahalan duk da cewa akwai
Ameena,sannan jiya ma an sake kawo mata wata sabuwar me aikin me suna Salima,yai mata wani
kallo da ita kaɗai tasan ma'anansa kafin yayi magana cikin kausasa murya yana faɗin "Ai baki fini
sanin da Restaurant ɗin ba,idan bazaki shiga ke da masu aiki ku shirya komi ba,sai na sauke su
gidan Hajiya inyi waya ita sai su haɗu da masu aiki suyi komi,tunda ke ba'a isa ace kiyi abu ki
amsa kai tsaye baki gardama ba."
Duk wannan maganan yana yinsa ne can ƙasa-ƙasa,babu ta yadda za'ayi Yusuf Driver yaji me yake
faɗi illa Suhailan kaɗai da ke raɓe da jikinsa,ta ko zunɓure baki gaba tana kwantar da kanta bisa
kafaɗansa,tana faɗin "Allah ya baka haƙury Sweet,abun bai kai Hajia ta ji ba."
Yai mata banza bai kuma sake magana ba har suka isa gidan,ta riga shi fita fuu!...Tana wani irin
cika da batsewa,ta cika tayi fam cike da jin haushin yadda sam Maleek ɗin baya son ta da hutu,irin
ita yadda take so ya kasance tana daga kwance za'a dinga mata komi,sai dai kawai ta dinga bada
umurni,ita sam matan aure masu zagewa suna hana kansu sukuni wajen bautawa miji da ayyuka,a
wahalallu take kallon su sai dai duk yadda ta so burinta ya kasance,indai Maleek ɗin na gari to fa
duk yadda ta kai ga son hutu sai ta zage tayi hidimansa ko bata so,indai tana son ganin farin
cikinsa yadda ya kamata.
Ɗakinsa ya wuce kai tsaye shi ma da ya shigo,yana aje wayoyinsa ya rage kayan jikinsa yana
maida ƙananun kaya,zama yayi yana ɗaukan wayansa yai kira,ya daɗe yana magana kafin ya aje
wayan yana tashi ya fito ya nufi ɗakin Suhailah,tsaye ya sameta tana cire kayan jikinta,idanunsa
ya sauka akan Milk Push-up Bra da ke sanye a jikinta,ya ɗauke kai yana takawa zuwa gare
ta,idanunsa cikin nata yake faɗin "Duk wannan cika da batsewan sabida nace muna da baƙi zakiyi
aikin tarban su?"
Suhailah ta ɗaga ido tana kallonsa itama,lokacin da ya ƙarisa haɗe gaf ɗin dake tsakaninsu yana
kai hannu ya mannata da jikinsa,ta sauke ajiyan zuciya lokacin da hannunsa ya ratsa ta jikinta
zuwa bayanta yana ɓalle maɓallin Bra ɗin ya sake shi zuwa ƙasa,murya can ƙasa cikin marairaita
Suhailah ke faɗin "Ni fa ba fishi nake ba Baby,kawai dai aikin girke-girken nan ne ban faye so
ba."
Memakon yayi magana sai kawai ya ɗauke ta cak! ya aza bisa Bed,yana yin abinda zai fisshesa
don a matuƙar matse yake da ita ɗin,cikin disasshiyar murya yake faɗin "Kinyi wanka ne?"
Suhailah da tai luff tana amsan zafafan saƙonninsa ta gyaɗa kai tana faɗin "Yanzu ne zan yi
wankan."
Bai iya cewa komi ba ya kai bakinsa kan ƙirjinta yana sake mannata da jikinsa sosai,ya shiga
birkita duk wani lissafinta sai daya gama jagulata son ransa kafin ya zare ta daga jikinsa yana
faɗin "Oya jeki ki wankan ki je ku fara aikin ayi komi me kyau please,na saka Fahad ayi ordering
Snack's daga Apple white zai kawo nan ba da jimawa ba." Daga haka ya juya ya bar ɗakin ba tare
da yaji me Suhailan ta faɗi ba......✍🏻
_Salamu alaikum! My luvly fans,kaman yadda na ji ƙorafin ku akan cewa Free Pages da na bayar
1to11 an ce yayi kaɗan,to na duba zan ƙara mu ku yakai zuwa iya 20 Pages for Free daga nan sai
ko wacce ta biya ta shiga Payment Group,don jin cikakken labarin da ya zo da Zazzafan salo.Kada
ku bari a yi ba bu ku Readers._ 😍
*Littafin TAIMIYYAH paid book ne akan 500 naira only,ga masu buƙatan yin payment zakui min
magana ta wannan number ɗin 08167768704, ko kuma ku turo kuɗin ku kai tsaye ta wannan
account ɗin 0504192664 aisha ibrahim dansabo GTbank.*
_Masu account da Arewa books,zaku dinga siyan sabbin shafuka dalla-dalla akan farashi me
sauƙi,ga yadda zaku siya pages a arewa books kamar haka_ 👇🏻
*Balance* - Zai nuna kudin account dinku da zaku iya sayayyan littafai cikin kasuwar
ArewaBooks.
*Credit/Debit Card* - Hanyar farko kuma mai dadi wajan Recharge din account dinku.
A inda (Enter your amount) za'a saka kudin da akeson Recharge din sai a taba "Proceed". Zaibude
muku inda zaku saka bayanan katin banki, kuna gamawa kudinku zaishiga account dinku kaitsaye
(instant).
--------
*Bank Transfer*
*Airtime Transfer*
Saidai su ba kaitsaye bane (instantly) sai ArewaBooks ta tabbatar da Transfer din, amman bayakai
1hour za'a gansa a Balance.
#Ɗansabo ce#
[12/14, 3:42 PM] +234 703 040 9541: *TAIMIYYAH*
*Page 14 to15*
________A washegary kaman yadda A.Maleek suka rabu da Doctor Saiff cewa Suhailah zata
same sa a Hospital,hakance ta kasance ƙarfe takwas da rabi ta gama shiryawa,cikin wani
tsadadden lace Cream Colour da akai masa adon zane da golden ɗin zare,sai touch ɗin Mint Green
wanda ya ƙawata kyawun lace ɗin,ya kuma yiwa lafiyayyen fatanta kyau sosai,da ƙyar ta iya tashi
daga jikin Maleek tai wannan shirin,don a cike take da fargaban me zai je ya dawo,domin a
fuskansa kawai take ganin yadda ya ɗauki lamarin da mugun girma,ɗan kunnaye ta saka ta zuba
zabban Gold guda biyu hagu da dama,kyawun da tayi kai kace wani wajen zata ba Asibiti ganin
Likita ba,gyale ta ɗauka irin wanda ake yayi na zamani me sharan-sharan da baida maraba da
babu,kalan da zai shiga da kayan jikinta ta fesa turarukanta na MISS DIOR haɗe da COROLINA
HERRERA,ɗakin ya buɗe da wani irin qamshi me ratsa zuciya,ƙaramin Hand Bag ta ɗauka ta jefa
wayoyinta a ciki,ta fito kai tsaye ta nufi ɗakin A.Maleek ɗin wanda ta same sa naɗe cikin Duvet,ta
saki wani irin murmushi tana takawa zuwa bakin gadon,tare da ɗosana mazaunanta daga bakin
gadon,ta kai hannu ta ɗan janye Duvet ɗin,kyakykyawan fuskansa ya bayyana idanunsa arufe da
alamun bacci yake sosai,hannu takai tana shafa fuskan a hankali tare da manna masa kiss a saman
goshi, ya buɗe idanunsa daddaɗan qamshinta na gama cika hancinsa,ya sauke ganinsa akan
fuskanta da taiwa kwalliya matsakaici,sai dai lips ɗinnan sun sha janbaki raɗau me asalin tsada,sai
ƙyalli lips ɗin suke yakai hannu zuwa kan lips ɗin ya shafa,yana me yinƙurawa ya tashi zaune
sosai,manyan idanunsa zube akanta babu ko ƙiftawa,cikin wani irin murya na wanda ya taso a
bacci yake faɗin "Suhailah biki zaki ko suna ki kai irin wannan kwalliyan?Sannan sabida kin raina
ni kuma shine zaki fita da wannan abun abakin ki,sau nawa zan sanar da ke bana so,wai ke bakya
kishina ne bare guje ma ɓacin raina? Look at dis Veil da kika sanyo sai kace wata budurwa me
tallan kanta,oya tun raina bai gama ɓaci ba kije ki goge wannan abin da ke bakinki,ki kuma sanyo
Hijab ko Abaya akan wannan shigan okey!"
Yadda yai maganan kawai da yadda idanunsa ke jifanta da wani kallo,yasa ta fahimci ransa ya
gama ɓaci,ta marairaice fuska tana shirin buɗe baki tai magana,ya ɗaga mata hannu cikin kaushin
muryansa me zurfi da ke fita a ƙasaice tamkar basarake yake faɗin "Bana son jin komi getout
please!" Hakan yasa Suhailah cuskule fuska tana barin ɗakin ranta a ɓace,kaman yadda ya buƙata
haka tayi lokacin da ta koma ɗakin yana Toilet,tana shirin fita yana fitowa ya bita da kallo yana
kallon inda tsayin Hijab ɗin da ta sanya ya tsaya,da kaɗan ya wuce cinyoyinta ya ɗauke kai yana
takowa cikin ɗakin,murya a dake yake faɗin "Yusuf na jiranki a waje,kafin ku wuce ki sanar da
masu aiki a shirya abin Breakfast a babban dining dake down stairs ina da baƙi da zamu karya
tare,sannan a ƙara yawan lunch daga nan har zuwa jibi sabida zamuyi ta samun baƙi ƴan taya
murna."
Subailah ta dube sa tana wani ɗan turo baki,cike da takaicin yadda ake so lallai a maidata Busy a
gidanta,sabida yawan baƙi ƴan taya Maleek murnan muƙamin da aka bashi na Chairman na
Shiffing Board na ƙasa baki ɗaya,shi yasa yake ta samun baƙi ƴan taya murna kama daga ƴan uwa
har abokanan arziƙi,ta gyaɗa kawai tana barin ɗakin ba tare da tace komi ba,shi ma sai ya saki
ƙaramin tsaki bai san ranan da Suhailah zatai cikakken hankali irin yadda shi yake so yaga matar
aurensa na bashi Respect sosai ba,Yusuf Drivern sa ta samu yana jiranta kaman yadda Maleek ɗin
ya faɗi,tuni har yai Warming motan da zasu fita aciki,cikin hanzari ya buɗe mata Back seat ta
shiga,ya maida murfin ya rufe bayan ta amsa gaisuwan da yake mata,kafin su fita shima Baba
Megadi sai da ya miƙa gaisuwansa wajen Gimbiyar tasu,wacce take yawan musu ihsani don ba
laifi Suhailah tana da kyauta da sakin fuska wa mutane,ko kaɗan bata da girman kai barta dai da
son girma da son hutawa ta fantama yadda take so ,amma abin hannunta sam baya rufe
idanunta,shi yasa qawanyenta ke ji da ita da yawa kuma acikinsu suke kishin yadda tafi su samun
duniya,ta auri miji na liƙawa a goshi ga kuɗi ga kyawu ga wani irin aji da yake da shi,har suka isa
Asibitin ABU da ke Shika Suhailah na Online tana aikin Chart da Friends,wani lokacin ta kan
amsa call na ƴan uwansu da ke kira don taya ta murnan muƙamin da aka baiwa Maleek ɗin,lokacin
da suka isa Yusuf Driver shi ya ɗaga waya ya kira Doctor Saiff ɗin bisa umurnin ubangidan nasa
Maleek Ado,ba suyi jiran mintuna goma ba Doctor Saiff ya iso wajen,tare da yin ma Suhailah
jagora zuwa Office ɗinsa,da taimakonsa akai duk wasu gwaji da yake buƙata aka fitar da
sakamako,wanda tashin farko ya fahimci akwai babban damuwa,sabida gwajin da Scaning ɗin da
akai mata ya nuna illan da Pills ɗin da ta sha yai mata,ya zaunar da ita yana mata bayani akan irin
haɗarin da tun farko yin planing ke dashi musamman ga mata masu ƙarancin shekaru
kamanta,daɗin daɗawama ita da sam bata taɓa ɗaukan ciki ba,ya cigaba da faɗin "Ranki da daɗe
yin planing ga mace me ƙananun shekaru babban hatsarine ga mace me shekaru ƙanana kama
daga 23years zuwa 24years,musamman ga macen da bata wuce haihuwa 1 zuwa 2 ba,ta saka kanta
ayin family planing ta hanyar shan ƙwayoyi ko kuma yin allura ko saka roba,wannan babban
hatsarine da ke illata mahaifar mace musamman ga wadda bata taɓa haihuwa ba kamar ke,illa ce
da ke hana haihuwan kwata-kwata da maida mace inferlity acikin rukunnan planing da suka kasu
kamar haka
1.DEPO PROVERA_wannan allurace da mata kanyi domin samun tsaikon haihuwa na wata
(3)wanda kafin yinta sai an tabbatar da mace tayi haihuwa kusan 6 ko 7 sabida allurace me
matuƙar ƙarfi da hatsari dake lalata mahaifa da canzawar period ga mata,wannan alluran ba'a yiwa
mace me haihuwa 1 ko 2 zuwa 4 sai wacce tai haihuwa kaman 7 sannan akwai
2.NORISTERAT _wannan allurace da ake yiwa mace ta tazarar wata (2) ita ana iya yiwa mace me
haihuwa 1 ko 2 sabida ita wannan alluran tana da sauƙin sha'anin akan (Depo provera) ta wata
Sannan akwai
3.PILLS_Wato shine ƙwayoyin da mace ke sha don hana ɗaukar ciki,irin wanda ki kai anfani
dashi wanda shima yana da kalan nasa illan na saka zubar jini koba a time ɗin period ba,sannan
shima yana hana haihuwa kwata-kwata."
Doctor Saiff ya dakata yana zubawa Suhailah ido ganin yadda ta firgice,domin an taɓo tsarin da
tabi wato shan pills,cikin tashin hankali ta dubi Doctor Saiff tana faɗin "Yanzu Doctor nima kana
nufin zan iya rasa haihuwa kwata-kwata kenan? Na shiga uku ni Suhailah!"
Tayi maganan muryanta na wani irin rawa tuni wani irin zufa ya fara wanke ta,Doctor Saiff da
tausayinta ya kama shi yayi saurin faɗin "No Madam bazan iya ce miki haka kai tsaye ba domin
Allah shi ke ikonsa a duk sanda yaso,ni dai ina miki bayani ne kan ilimina da aikina,zaki iya rasa
haihuwa za kuma ki iya samu idan Allah ya nufa hakan ya kasance,sai dai ina sake jaddada miki
kinyi wauta me girma da kika illata kanki da kanki,domin fara planing a wajen mace irinki me
ƙarancin shekaru babban illa ce da haɗari me girma,musamman ke da bakima bari kinyi ko da
haihuwa 1 ba,haba Madam me zaisa ki aikata wannan wautan sabida kawai son boko da ke rufe
muku ido da gayu ko? Kin ganni nan matata na aureta ko 100 level bata shiga ba,a gidana ta shiga
jami'a kuma a shekaran da ta shiga ta samu cikin fari,a haka ta haife ta raini yaron tana kuma
cigaba da shiga skull,kuma ko bayan ta haihu ban taɓa tunanin muyi tsarin iyali ba sabida na fi
kowa sanin illan da ke tattare da shi,a haka tana karatu tana haihuwa,ni ke ɗaukan nauyin biyan
masu raino don su rage mata wahalan hidima,amma har ta gama karatu bamu taɓa yin komi da
sunan planing ba,bare ke da kike da Oga kuɗi ba matsalan ku bane,ko masu raino goma kike so
za'a ije miki,gaskiya kinyi wauta me girman gaske,yanzu zan ɗaura ki akan wasu magunguna,da
zaki anfani da su har tsayin wata biyu ko uku,daga nan kuma sai a jira a ga abinda Allah zaiyi."
Ya ƙare maganan yana kallon yadda idanun Suhailah tuni suka fara zubar da hawaye,a matsayinsa
na babban likita a kuma fannin da ya shafi mata,ya sani dole sai yayi aikin lallashi da kwantar da
hankalin Suhailan,yayi mata faɗa da farko ne sabida ta gane kuskuren da tayi abaya me girma ne,a
hankali ya fara kwantar mata da hankali da kalamai masu kyau,yana nuna mata su likitoci ba Allah
bane,da idan suka yanke kaza dole hakan zai faru,a'a Ubangiji na iya nuna ikonsa a duk sanda
yaga dama,duk wani bayaninsa da kalaman da yaita anfani dasu wajen kwantar da hankalin
Suhailah,kusan zan iya cewa baiyi wani tasiri ba domin zuciyanta gaba ɗaya a razane take,tana
hango yadda zasu kwashe da Maleek da kuma Hajja idan har hasashen likitan ya tabbata cewa zata
iya rasa haihuwan baki ɗaya,wani irin kuka ke son ƙwace mata tana dannewa,cikin hanzari ta
miƙe bayan Doctor Saiff ya damƙa mata takaddan da ya rubuta mata magungunan da zatai anfani
da su ɗin,ta fice da sassarfa bata ko ganin gabanta sosai,har ta isa wajen da Yusuf ya faka mota
yana jiranta,tun daga nesa ya hango yanayinta ya tabbatar akwai damuwa,hakan yasa shi saurin
fitowa ya buɗe mata gidan baya ta shige ya maida murfin motan ya rufe,tare da zagayawa
mazaunin Driver ya tashi motan,tunda suka ɗauki hanya Suhailah kuka kawai take,sam bata da mu
da cewa tana tare da Drivern mijinta bane,a can asibitin kuwa bayan fitanta Doctor Saif A.Maleek
Ado ya kira kai tsaye tare da zayyane masa komi,ya kuma sanar dashi magungunan da ya rubuta
da yadda zatai anfani da su,Maleek ɗin yai masa godia sukai sallama,take ya shiga neman line ɗin
Suhailah amma yana ta Ringing taki ɗauka,sai ya maida akalan kiran zuwa ga Yusuf da ke Driving
ɗinsa gently,jin shigowan kira yasa shi ciro wayansa ya duba,ganin sunan Oga ne yasa shi ɗaga
wayan da hanzari,daga ɓangaren Maleek kai tsaye ya furta "Ka wuce da ita gidan Hajiya,ka sanar
mata ta baka takaddan maganin da aka rubuta,yanzu zan saka maka kuɗi a account da zaka cire
kaje ka siyo maganin."
"Okey an gama ranka ya daɗe." Cewan Yusuf bayan ya gama sauraren Maleek ɗin,wanda shi
kuma bai ƙara cewa uffan ba ya kashe wayansa yana furzar da wani irin huci me zafi,tsananin
takaicin abinda Suhailah ta aikata na tafasa zuciyansa matuƙa,domin a cikin ƴan watannin nan
wani irin sha'awa da son haihuwa aka jarabci zuciyansa da ita,ta yadda duk inda ya hangi ƙananan
yara suke bashi sha'awa ya dinga ji kaman ya buɗe ido ya gansa da nasa ɗan ko ƴar,sai dai ga
matsalan da Suhailan ta janyo musu wanda a yanzu basu da tabbacin zata haihun ko bazata haihun
ba kaman yadda bincike ya nuna zata iya rasa haihuwan baki ɗayama.
A ɓangaren Suhailah da ke kuka kasharɓan kuwa,har suka iso gidan Hajiya bata iya cewa Yusuf
uffan ba,domin tun daga yadda yake amsa wayan ta san cewa da Maleek ɗin ne,shine kuma ya
bashi umurnin ya kawo ta gidan Hajiyan,sai dai bata san manufansa na yin hakan ba,murfin motan
ta ɓalle tare da zuro ƙafafunta waje,dai-dai lokacin da Yusuf ke sanar da ita saƙon Maleek ɗin,ba
tayi magana ba sai hannu da ta saka ta ciro takardan maganin daga jaka ta aje masa akan seat
ɗin,ta fice baki ɗaya daga motan ta nufi cikin gidan kuka me ƙarfi na ƙwace mata........✍🏻
*Littafin TAIMIYYAH paid book ne akan 500 naira only,ga masu buƙatan yin payment zakui min
magana ta wannan number ɗin 08167768704, ko kuma ku turo kuɗin ku kai tsaye ta wannan
account ɗin 0504192664 aisha ibrahim dansabo GTbank.*
_Masu account da Arewa books,zaku dinga siyan sabbin shafuka dalla-dalla akan farashi me
sauƙi,ga yadda zaku siya pages a arewa books kamar haka_ 👇🏻
https://arewabooks.com/chapter?id=62d29e11aa5f8f19bc9621cb
*Credit/Debit Card* - Hanyar farko kuma mai dadi wajan Recharge din account dinku.
A inda (Enter your amount) za'a saka kudin da akeson Recharge din sai a taba "Proceed". Zaibude
muku inda zaku saka bayanan katin banki, kuna gamawa kudinku zaishiga account dinku kaitsaye
(instant).
--------
*Bank Transfer*
*Airtime Transfer*
Saidai su ba kaitsaye bane (instantly) sai ArewaBooks ta tabbatar da Transfer din, amman bayakai
1hour za'a gansa a Balance.
#Ɗansabo ce#
[12/14, 3:42 PM] +234 703 040 9541: *TAIMIYYAH*
*Page 16 to17*
_______Ita dai Hajjah tana zaune da wata baƙuwa maƙwafciyanta da suka tare,ta shigo a gaisa
kawai sai faɗowan Suhailah suka gani cikin falon tana rasgan kuka,Hajiya Aysha ta ruɗe tana
faɗin "Suhailah lafiya?" Amma maimakon Suhailah ta tsaya sai wucewa tayi direct zuwa ɗakinta
da tai ƴan matanci,ta faɗa gado tana cigaba da kuka sosai,bayan tayi wurgi da Hijab da jakanta
bisa Bed ɗin,Hajiya Aysha da suke kira da Hajjah ta biyo bayanta tana cigaba da tambayan "Keh!
Lafiya zaki shigo min gida kina kuka,meyafaru ina shi Maleek ɗin me yai miki?" Duka Hajjah ta
jera mata tambayan tana kaiwa zaune bakin gadon da Suhailan ke kwance,kaman jira Suhailan
take Hajjah takai aya ta sake ɓarkewa da kuka,cikin kukan take faɗin "Hajjah na shiga uku na,na
cuci kaina da kaina idan har bazan haihu ba na bani Hajjah,wallahi ina son Yah Maleek irin son da
bazan iya zuba ido in gansa da wata ba,bare har ta bashi abinda ni nakasa bashi,wayyo Hajjah na
bani na shiga uk..."
"Kul! Suhailah bana son alkaba'ai na banza,ki faɗi min kawai meke faruwa?"
Hajjah ta katse Suhailan tana kamo hannunta ta riƙe cikin nata,burinta kawai taji meke faruwa don
sosai taji ƙirjinta na bugawa sam bata son tashin hankali da duk abinda zai sata cikin
damuwa,lokacin da Suhailah ta gama zayyane mata yadda sukai da Doctor Saiff,sai sakin hannun
Suhailah Hajjah tayi tana jifanta da mugun kallo take faɗin "Shine zaki shigo min gida ki ruɗani
kina ta faman kuka kaman anyi mutuwa, ina ce tun farko kece kika kai kanki da kanki kika fara
amsan magungunan kina ɗirkawa cikin ki,ba tare da kinyi zurfin nazari da tunanin irin wannan
ranan zai iya zuwa miki ba,babu abinda zan ce miki Suhailah sai dai ince kinyiwa kanki ne aduk
me zai biyo bayan abinda kika aikata ba tare da amincewan mijinki da shawara da kowa ba,sannan
kisa a ranki ko yau Abdul-Maleek ya kawo mata yace zai aura bazan taɓa hana shi ba."
Daga haka Hajjah ta miƙe fuu...! Ta fice daga ɗakin,ba tare da ta sake sauraran Suhailah wacce
kalaman Hajjan suka sanya ta sake rushewa da kuka,danasanin da bazai mata anfani ba na lulluɓe
zuciyanta,daman Hajjan take da hope akanta itace ke iya sanya Maleek yayi abu ko baya so,to
gashi tana tabbatar mata da cewa ko Maleek zai mata kishiya akan matsalan rashin haihuwa bazata
hana ba,ta sake ɓarkewa da kuka kanta na wani irin juwayawa,gaba ɗaya jin duniyan take tana
mata ɗaurin goro.
Hajjah kuwa tsananin takaicin Suhailan da abinda ta aikata ɗin ne,ya hanata jin tausayinta ko
kaɗan duk da cewa ƙasan zuciyanta da tausayin Suhailan,amma dole ta nuna mata kuskuren da ta
aikata me girma ne,sannan ita da kanta idan har abinda likita ya tabbatar na cewa Suhailan zata iya
rasa haihuwa baki ɗaya ya tabbata,to babu shakka ita da kanta zata sanya Maleek ɗin ya sake
aure,don bazata zuba ido ya ƙare ƙuruciyansa babu haihuwa ba,bata sake bi takan Suhailah da ta
kume kanta a ɗaki taƙi futowa ba,ta cigaba da sabgan gabanta da ma'aikatan ta su Rabi me
aiki,lokacin da aka kammala Lunch ma Hajjah sawa tayi aka haɗa komi aka kaiwa Suhailan
ɗaki,amma ga tsananin mamakinta Suhailah sai ta koro Lubah da abincin wai bata ci,Hajjah
murmushi kawai tayi ta cewa Luban ta kai abincin Dining ta aje,bayan kammala cin abincin da
Hajjah tayi,sai ta ɗaga waya ta kira layin Maleek,wanda a lokacin yana tare da wani abokinsa a
cikin babban falon gidan nasa,bugu biyu tayi ya ɗaga wayan bayan sun gaisa ne take sanar dashi
zuwan Suhailah,tare da tambayan mi yake nufi da sawa akawo ta nan ɗin,ga ta nan ta ƙule a ɗaki
taƙi cin abinci sai faman kuka take,amsan da ya ba Hajjan yasa ta kashe wayanta tana sakin
murmushi,domin tafi kowa sanin halin ɗan nata ciki da bai,sai dai a wannan karon sam bazata
goyawa Suhailah baya akan duk matakin da Maleek ɗin zai ɗauka akanta ba,ta cigaba da harkokin
gabanta ba tare da ko sau ɗaya ta sake komawa ta duba Suhailan ba,wacce ta daɗe da yin baccin
wahalan kukan da ta rasga,tana baccin tana sauke ajiyan zuciya irin na wanda yaci kuka ya
ƙoshi,ƙarfe uku ta farka daga baccin ta kallo agogon ɗakin tana dirowa da sauri,ta nufi toilet don
ɗaura alwala don ko sallan Zuhur bata yi ba,a gurguje ta fito ta gabatar da sallan zuwa lokacin da
ta idar wani irin yinwa take ji sosai,hakan yasa tana cire Hijab ta fito zuwa Dining ɗin falon
Hajjan,lokacin Hajjah na daga kishingeɗe cikin kujera,littafin addu'o'i take dubawa idanunta sanye
cikin medical glass da ke ƙara mata ƙarfin gani,takun fitowan Suhailah baisa ta ɗaga kai ta dube ta
ba,har sai da ta tabbatar ta isa ga wajen cin abincin sannan ta ɗaga kai ta dubeta tana sakin
murmushi sosai,don dama tasan za'a rina fishi da abinci badai Suhailan ta ba,Suhailah tayi nisa
acin abincin Hajjah ta ɗaga murya yadda zata jiyo ta tana faɗin "Oh! Ai ni na ɗauka da gaske fishi
kike da abincin ba zaki ci ba."
Suhailah ta ɗago idanunta da suka ƙanƙace sabida kuka ta dubi Hajjah,tana shagwaɓe fuska take
faɗin "Wallahi ba don ina da ulcer ba banso ta tashi da bazan ci abincin ba,tunda bakya tausayina
kin daina so na Hajjah."
Suhailah ta ƙare maganan tana sakin hawaye sharr...! Abinda ya motsa zuciyan Hajjah sosai,taji
wani irin tausayin Suhailan ya kamata,amma bata nuna ko a fuskaba sai ma haɗe gira da tayi tana
faɗin "Maza ki gama cin abincin sai ki zo muyi magana,ki faɗi min ta inda na daina son naki?"
Daga haka ta ɗauke kai daga Suhailah ta cigaba da duba littafinta,aiko Suhailah na gama cin
abincin ta nufo cikin falon tare da yin masauki akan kujeran da Hajjah ke kai,cikin narke fuska
take faɗin "Hajjah yanzu da gaske sai ki goyawa Yah Maleek baya ya iya sake aure,don na samu
matsala bazan haihu ba,bafa tabbaci aka bayar na bazan haihun ba hasashe ne kawai,kuma ga
magani anbani zan sha na tsayin wata biyu,meyasa bazaku yi addu'an kafin lokacin ma cikin ya
samu ba,ni yanzu wallahi ko ƴan goma yake so in haifa zan iya na shiryawa hakan Hajjah,amma
bazan iya kallonsa da wata ba don Allah karki faɗi hakan agabansa."
Suhailah tayi magana tana zubama Hajjah ido,fuska a maraice zuciyanta na cigaba da shiga ƙunci
na danasanin abinda Zubaida sheɗaniyan qawanta ta zugata ta aikata,Hajjah ta dubi Suhailan tana
faɗin "Suhailah bana fatan hakan nima,sai dai ina so kisani idan har abinda ake hasashe ya
tabbata,to tabbas kome zakice bazan goyi da bayan ki ba, shi kuma a tauyesa ba,ina fata Allah yai
ikonsa ki samu rabo ko da yau ne ko gobe ne,duka me sauƙi ne a wajen Allah,amma kisani akwai
abinda muke aikatawa na son rai,wanda mun san zai cutar da mu amma sabida son zuciya mu rufe
ido mu aikata abin,wanda daga baya zamu zo muna danasanin da bazai mana anfani ba,shi kuma
Allah ya hanamu abin a lokacin da muke da buƙatansa,wanda hakan shine ya faru da ke ko ince
zai farun,don haka maganan ki sanya damuwa ma bai taso ba,kinyi wauta kin tabka kuskure
Suhailah,ni ban taɓa ganin ma sakarya irin ki ba da zaki je ki fara shan maganin hana ɗaukan ciki
alhali ko haihuwan fari baki bari kinyi ba,to yanzu kinga ga samako nan sai ki koki gaba idan ma
Allah ya ji ƙanki ya kawo rabon a lokacin da ake buƙatansa,don haka maganan Maleek ni bazan
shiga tsakani ba,ku je can ku ƙarata ke da shi tunda lokacin da kikai abinki baki shawarceni
ba,kuma maganan na daina son ki da kike faɗi ki cigaba karki fasa."
Hajjah ta ƙare maganan cikin nunawa Suhailah kalman yai mata zafi matuƙa,hakan yasa Suhailah
cigaba da kuka tana baiwa Hajjah haƙury,amma sai Hajjah ta ture hannun Suhailan daga jikinta
tana jifanta da harara,qamshin turaren RALPH LAUREN daya buɗe falon ya ankarar da su Hajjah
wanzuwan Maleek Ado cikin falon,suka ɗaga kai kusan a tare da Suhailah suna sauke ganinsu
akan kyakykyawan fuskansa,wanda take a kirne babu wani alamun fara'a,ya zube hannuwansa
duka biyu cikin aljihun Rigan tsadaddiyar yadin dake jikinsa,wanda kalan yai asalin yi masa kyau
matuƙa,da alamu ya jima tsaye cikin falon basu ankara da shi ba,ganin duk sun xubo masa ido
yasa shi fara takowa zuwa cikin falon,yaiwa kansa masauki cikin kujeran dake kallon wanda
Hajjah da Suhailah ke kai,cikin muryansa me cike da ƙasaita da daɗin amo yake sake gaida
Hajjah,ta amsa da fara'a akan fuskanta,a hankali ya maida kallonsa ga Suhailah wanda yake jin
idanunta na yawo akansa,yai mata kallo ɗaya yana ɗauke kai ya mayar kan Hajjah yana faɗin
"Hajjah ina fata tayi miki bayanin yadda sukai da Dakta? Sakamakon da nake ta guje mata shine
ke shirin faruwa,domin a yadda scaning ɗin da akayi ya nuna magungunan da tasha sunyiwa
mahaifan illan da zata iya rasa haihuwan ma baki ɗaya,kaman yadda na faɗi tun farko yanzu zan
maimaita agaban idanunki Hajjah,bazan iya zama da macen da bazata iya haihuwa ba,don ina
buƙatan ganin ƙwaina a duniya idan ko har zamu cigaba da zaman aure da Suhailah tabbas tana
da buƙatan abokiyan zama,don a yanzu bamu da tabbacin zata samu haihuwa ko bazata samu
ba,zan nema mata Visan zuwa Cairo nan da sati biyu zuwa uku zamu ga wani likitan da aka sanar
dani ƙwararre ne,idan har muka je muka dawo aka sake tabbatar da cewa ta samu illa,to daga
lokacin ni kuma zan fara neman irin macen da zan iya rayuwa da ita akaro na biyu."
Yadda ya ƙare maganan cikin tabbatar da dukkanin kalamansa babu wasa a ciki,sai Suhailah ta
saki kukan da take riƙewa,Hajjah kuma ta tsura masa idanu tana hango tsantsan gaskiyan da ke
cikin idanunsa akan dukkanin kalaman da ya furta,kafin tayi magana tana faɗin "To Maleek naji
dukkanin kalamanka ka kuma yi tunani me kyau,gara ka ɗauke ta ku je can ɗin kada ma ta fara
anfani da magungunan da aka rubuta anan ɗin,ajira har kuje can ɗin aga me bincikensu zai
nuna,maganan ƙarin aure bazan iya cewa komi akai ba sai dai ince a yanzu addu'a shi yafi,daga
mu har kai mu nemi Allah yai ikonsa ya tabbatar mana da dukkan alkhairy,Suhailah ta riga da tayi
kuskure don bazamu kira abinda ta aikata da sunan ƙaddara ba,sai dai mu jingina shi da irin
ƙaddaran da mu hausawa muke faɗi na son zuciya,wanda idan muka aikata son ranmu abu mara
kyau ya biyu baya sai muyi ta kiranshi da ai ƙaddarace,amma idan muka aikata abinda muke so
muka samu kuma biyan buƙata to anan ba Allah ne ya ƙaddara ba,don haka ina addu'a da fatan
Allah yasa asamu mafita ya zamo ba kinyiwa kanki illah bane Suhailah."
"Ameen Hajjah." Cewan Maleek yana maida dubansa kan Suhailah,wacce ta kwantar da kanta
ajikin Hajjah tana cigaba da kuka,cikin low voice yake faɗin "Tashi mu wuce gida."
Suhailah ta sake lafewa a jikin Hajjah tana faɗin "Please Yah Maleek ka barni anan sai dare sai ka
zo mu wuce."
"Idan na fita daga nan bazan sake shigowa ba,sai dai idan kin kai daren Shehu ya maidaki gida,ki
kuma tabbatar da ansamar min tuwan Semo da miyan kuɓewa for Dinner,bana son ƴan aiki su
sanya hannunsu aciki okey!"
Ya ƙare maganan yana miƙewa tsaye,ya maida idanunsa akan Hajjah yana faɗin "Hajjah zan wuce
ina so zan je can Samaru wajen Baba Ali,ya kira yana nema na." Hajjah ta gyaɗa kai da furta
"Hakan yayi ka gaida shi idan ka je ɗin,ina ga akwai ƴan Nasihu da zai maka ne da kuma tayaka
murnan samun wannan muƙami,tunda kasan jikin girma ƙafafun sun matsa masa baya son yawan
fita sai dai a bisa,so nake ma idan ka natsa shima a fitar da shi yaga likita."
"Nima nayi wannan tunanin Hajjah,India zamu fita ni da shi insha Allah bari dai in sake samun
nutsuwa in shiga sabon office ɗinnan sai mu ga abinda zai yiwu." Cewan Maleek yana kai hannu
ya zaro wayansa daga aljihu da ake kira,Hajjah kuma ta amsa da faɗin "To madallah,Allah ya
cigaba da dafa maku yayi albarka."
Maleek ya amsa da Ameen yana kai wayansa kunni,ya fara takawa don barin falon,Suhailah tabi
bayansa da kallo wani zazzafan son sa na sake keta ilahirin jinin jikinta,ta maida idanunta ta
lumshe qamshinsa da ya barwa falon na ratsa kafofin hancinta.
________
Laurat da take autan Ummman su Zuhurah ta tambaya,idanunta akan Zuhuran da rabin hankalinta
ke kan chart ɗin da take yi da sabon saurayinta Ameeru,ta ɗago idanunta ta mayar kan Laurat ɗin
tare da taɓe baki tana faɗin "Wai TAIMIYYAH,tana can Sasan Iya mana."
Laurat ta jinjina kai tana faɗin "Allah sarki,wallahi tausayi take bani gashi dai Allah yai mata
baiwan halitta amma an rageta ta ɓangaren laluran ƙafa,yanzu bata shigo muku hira kenan,na ga
tun jiya dana zo har yau ban ga ta shi go ba." Laurat tayi maganan tana kallon Zuhurah,kafin
Zuhurah ta bata amsa Basmah da ke zaune tana sauraransu tayi zaraf tana faɗin "Taɓ! Tun wani
zamanin ai Iya ta hanata shigowa,hakama Umma kinsan Umma ta tsaneta muma haushinta muke
ji,komi ace ita don anga ta fimu kyau."
Basmah tayi maganan tana wani taɓe baki,hakan yasa Laurat sakin baki tana kallonta,kafin ta furta
"Kai! Basmah to miye abin haushi don ta fiku kyau,kuma banda abin Anty Zuwaira miye aibun
yarinyar don ta kasance gurguwa har da za'a tsaneta?"
Wannan karon Zuhurah ce ta dubi Antyn nasu Laurat,wacce auta ce a wajen su Umman da ita
kaɗai ta rage batai aure ba,ta girmi Zuhurah sosai a ƙallah zatai shekaru ashirin da takwas don dai
Allah bai kawo lokacin aure bane ake zaune har yanzu ba'ayi ba,cikin taɓe baki Zuhuran ke faɗin
"Hmm! Anty kenan don baki san yadda tsowuwar can ke nuna bambamci tsakanin mu da
TAIMIYAH bane,don kawai anga Abie ɗinsu yafi Baban mu kuɗi,sannan ƙarin abin haushi wai da
ita Yah Sadeeq yake so har yana iƙirarin ita zai aura,sai da Umma tace zata tsine masa idan bai
janye maganam ba shine fa ya haƙura,don Allah kamar Yah Sadeeq me zaici da gurguwa ko min
kyanta? Mitsuww...!"
Zuhurah ta ƙare maganan tana jan wani mugun tsaki,ita ko Laurat tai ƙuri da ido tana duban
Zuhuran cike da mamakin yadda duk ɗabi'unsu suka canza,domin ta daɗe bata kawowa Anty
Zuwairan ziyara ba,ta buɗe baki tana faɗin "Zuhurah ku bi ahankali,wallahi shi Allah ba'a masa
haka domin shi yaso maida ta hakan,tunda ke shaida ce tare kuka taso tana tafiyanta qalau dare
ɗaya Allah ya aiko da laluran dayai silar komawarta gurguwan,miye laifinta aciki?Kuma miye
aibun kasancewanta a hakan da har zakuce ba ku son ta da Sadeeq,ni banga wani aibu ba domin
shi soyayyah Allah ke jarabtan bawa dashi kuma babu ruwansa da duba tsarin halitta ko nakasan
mutum,amma ina baku shawara ku bi ahankali domin in mutum yasan farkon sa baisan ƙarshe
ba,yanzu na gane abinda ya sanya ta daina shigowa,kenan kuna mata gori da cin fuska kenan?"
Yadda Anty Laurat ɗin tai maganan cike da jin zafinsu,yasa daga Basmah har Zuhurah tashi tsam
suka bata waje,don sun san ita bata ɗaukan raini yanzu zata ci mutuncinsu,ta girgiza kai kawai
tana bin su da kallo har suka shige ɗakinsu,sai itama ta isa Bedroom ɗin Umma wacce tun safe ta
fita wai zata ɗakko kayanta da suka iso na sayarwa daga park,sabida ta fara business ɗin sai da
kayayyaki irin su atamfofi da kayan yara,ana turo mata daga Lagos shine tunda ta fita har yanzu
bata dawo ba,Laurat ɗin ta zari mayafinta ta yafa,tana fitowa daga Sasan nasu Zuhurah kai tsaye ta
nufo Sasan Iya,don ita dai tunda daɗewa TAIMIYYAH tana mata kyau tana kuma bata tausayi
tunda laluran ƙafanta ya sameta,wayanta riƙe a hannunta take ratso Compound ɗin gidan har ta iso
Sasan Iyan.......✍🏻
Littafin TAIMIYYAH paid book ne da zai zo akan 500 naira only,ga masu buƙatan yin payment
zakui min magana ta wannan number ɗin 08167768704, ko kuma ku turo kuɗin ku kai tsaye ta
wannan account ɗin 0504192664 aisha ibrahim dansabo GTbank.*
_Masu account da Arewa books,zaku dinga siyan sabbin shafuka dalla-dalla akan farashi me
sauƙi,ga yadda zaku siya pages a arewa books kamar haka_ 👇🏻
https://arewabooks.com/chapter?id=62d29e11aa5f8f19bc9621cb
*Balance* - Zai nuna kudin account dinku da zaku iya sayayyan littafai cikin kasuwar
ArewaBooks.
*Credit/Debit Card* - Hanyar farko kuma mai dadi wajan Recharge din account dinku.
A inda (Enter your amount) za'a saka kudin da akeson Recharge din sai a taba "Proceed". Zaibude
muku inda zaku saka bayanan katin banki, kuna gamawa kudinku zaishiga account dinku kaitsaye
(instant).
--------
*Bank Transfer*
*Airtime Transfer*
Saidai su ba kaitsaye bane (instantly) sai ArewaBooks ta tabbatar da Transfer din, amman bayakai
1hour za'a gansa a Balance.
#Ɗansabo ce#
[12/14, 3:42 PM] +234 703 040 9541: *TAIMIYYAH*
*Page 18 to19*
_______Da sallama Anty Laurat ta shiga Sasan Iya,wacce suke zaune daga waje saman lallausan
Carpet da takan shinfiɗa ta zauna tana bitan karatun Qur'ani duk kusan yamma,daga gefen Iyan
Ladi ce zaune itama tana gyaran farce daga gefe guda,Iya da Ladin kusan a tare suka amsa
sallaman Laurat ɗin,wacce ta ƙariso ta zube gaban Iya tana kwasan gaisuwa,Iya ta amsa da fara'a
tana faɗin "Maraba da Lauratu saukan yaushe,ya mutanan can Yoben ina fata duk iyayen na ku
nanan lafiya ko?"
Laurat tayi murmushi tana faɗin "Lafiya Iya duk sunce a gaida ku,wallahi jiya na zo naso shigowa
sai dare yayi ga gajiyan zaman mota,shine sai yanzu nace bari in shigo in miƙo gaisuwa,ya
TAIMIYYAH hala bata nan ne ?" Laurat ta ƙare maganan da tambayan Iya,Iya ta murmusa tana
gyara zaman glass ɗin da take anfani dashi idan zatai karatu sabida ƙara ƙarfin gani,ta amsa da
faɗin "Tana nan ta ƙule a ɗaki tana karatu hala ko ana faman danne-dannen waya da bakwa gajiya
ku yara." Laurat ta saki murmushi tana faɗin "Allah sarki to bari in shiga daga ciki mu gaisa
ankwana biyu ba'a haɗu ba."
"Hakane kam ƴarnan shiga ku gaisa ai kin kyauta da kika taho zumunci."
Cewan Iya tana bin bayan Laurat ɗin da kallo,wacce ta nufi ƙofan shiga falo,Iya na yaba nutsuwan
Laurat ɗin da hankalinta,wacce har Iyan ke ji Laurat ɗin tafi kwanta mata arai ma akan Surukan
nata Umma,da sallama Laurat ta shigo falon Iya tana sake ɗaga murya da kiran sunan
TAIMIYYAH,ita ko TAIMIYYAH na can daga cikin ɗakinta tayi ɗai-ɗai suna kwasan Vid call da
qanninta su Nahar,tana ta biye musu suna bata labarin Lagos da irin wajajen da ake kaisu na
shaƙatawa duk Weekend,can sama-sama take ji kaman ana kiran sunanta hakan yasa tai sallama da
su Nahar tana cewa zata kira su later,ta aje wayan tana miƙewa ta sauko daga Bed ɗin,tana sanye
ne da wani gown me kyau na Material da akaima ɗinkin da ya amshi jikinta sosai,ta dafa ƙafanta
tana takowa zuwa falo,idanunta ya sauka akan Laurat da ke zaune daga hannun kujera,ai da
hanzari TAIMIYYAH ta ƙariso cikin falon,tana faɗin "Laaah! Anty Laurat ce yau a gari,sannu da
zuwa saukan yaushe Anty?"
Laurat ta saki murmushi ta kasa ɗauke idanunta daga kan TAIMIYYAH,tana ganin yadda
TAIMIYYAN tai wani girma kyawunta ya ninka na da,domin a ƙallah zai kai shekaru uku rabonta
da ganinta,har TAIMIYYAH ta ƙariso kusa da ita idanunta na kanta,tana jinjina baiwa da ƙudiran
ubangiji wanda ya ƙagi wannan kyakykyawan halitta,hannu ta miƙawa TAIMIYYAN suka cafke
Laurat ɗin na faɗin "Wow! TAIMIYYAH haka kika koma wata Big Gal,kinga yadda kika sake
zama wata haɗaɗɗiya ta musamman gaskiya ke ɗin matan manyace,Allah kaɗai yasan meyasa ya
ɗan tauyeki kaɗan."
TAIMIYYAH ta saki murmushi tana faɗin "Anty kenan ina yini kin zo lafiya?"
Cewan TAIMIYYAH tana yinƙurin miƙewa tsaye,Laurat tayi saurin dakatar da ita da faɗin
"Wallahi zauna abinki bana jin ƙishi,tun jiya fa na shigo garin nanne bansamu shigowa ba sai
yanzu,ya karatu ana ta strike kuma Allah dai ya kawo ƙarshensa,ko da yike Zuhurah tace duk kun
gama sai jiran a koma ku ɗaura daga inda kuka tsaya,tuh Allah ya taimaka in kuma Allah ya kawo
miji sai mu sha biki kawai ba."
Yadda Laurat ɗin ta kai ƙarshen maganan yasa TAIMIYYAH sakin dariya kawai,ba tare da tace
komi ba Laurat ɗin da yake gwanar iya hirace,ita ke ta janyo zance har TAIMIYYAH ta sake suna
ta hira,sai kusan biyar ta bar Sasan Iyan tana cewa TAIMIYYAH zuwa anjima don Allah ta shiga
can Sasan ayi hira,domin ita har ga Allah ƙaunar TAIMIYYAN take ji da zuciya ɗaya,dariya kawai
TAIMIYYAH tayi don tasan Iya ma bazata bari ba,uwa uba ita kanta ma bazata shigan ba,don
tasan ƙarshenta da ɓacin rai zata fito Sasan,ita ko a yanzu babu abinda take tattali irin farin
cikinta,shiyasa gaba ɗaya ta ɗauki duk wata soyayya da takewa su Zuhuran da qawazucin su ta
adana shi can ƙasan zuciyanta,babu abinda take so da ƙauna da bashi muhimmanci a yanzu irin
karatu,ga kuma wayanta da ke ɗebe mata kewa tana karance-karancenta masu muhimmanci da
take ƙaruwa dasu,ga groups na karatuttukan manyan malamai da ake turowa suna sake wayar da
kanta da samun tarin ilimi,shiyasa ko kaɗan yanzu zaman kaɗaici baya damunta,ko da Anty Laurat
ɗin ta tafi ma ɗaki ta koma ta kunna karatun Qur'ani cikin suran da zata kai hadda sati me
zuwa,tana saurara har akai kiran sallan magriba,sannan ta kashe karatun da yike tana period ba
sallan zatai ba kawai sai ta fito zuwa Kitchen,tana jin sha'awan cin wainan fulawa ko
Pancakes,don ita idan tana al'adah komawa take kaman wata me yaron ciki,bata iya cin abinci
sosai sai kwaɗayi kala-kala, buɗe can rufe can tana tunanin me xata ƙaƙala tayi,har dai zuciyanta
ya tsayu akan yin wainan fulawan,hakan yasa ta ɗebo fulawan ta tankaɗe ta jajjaga tarugu da
albasa kaɗan,haɗi da yanka albasa me dama ta zuba a kwaɓin,ta fasa egg guda biyu ta zuba spices
da maggi ta motsa sosai,sannan ta ɗaura nonstick pan ɗinta a wuta,manja ta zuba me bala'in kyau
irin wanda ake kawowa Iya daga Lagos,nan da nan qamshi ya fara tashi na suyan wainan
fulawan,already tana da dakakken yajin da take dakawa da kanta tana ajewa,don ita Iya bata cin
yaji sam TAIMIYYAN ma da take so kullum cikin yi mata faɗa Iya take,qamshi ne ya ishi Iya da
ke zaune a falo ta ɗaga murya tana faɗin "Wai ni kam me kike soyawa ne haka TAIMIYYAH?"
TAIMIYYAH da ta gama arranging wainan fulawan cikin plate ta wani zubo yaji daga gefe,sai
qamshi ke tashi ta fito hannunta riƙe da plate ɗin,ɗaya hannun na dafe da ƙafatan tana takowa har
zuwa cikin falon,sai lokacin ta saki murmushi tana duban Iya take faɗin "Iya wainar fulawa ce fa
kawai na ɗan soya,in matso mu ci ne tare na ga cewa kike ke bata dame ki."
TAIMIYYAH tayi maganan tana sakin dariya,ganin irin hararan da Iya ke aiko mata,kafin Iyan ta
furta "To sai dai naci wannan irin qamshi haka,wallahi raina ya biya maza matso da shi ince ko
ɗaya ne,ai da ne dai nake cewa bata dameni ba,amma banda yanzu da kika ɗanɗana min irin
wannan haɗin daɗin da kike masa." TAIMIYYAH tana dariya ta ƙarisa gaban Iya suka fara ci
tare,Iya me cewa zata ci ɗaya sai ga shi ta tada guda uku tana faman santi,me TAIMIYYAH xatayi
inba dariya ba,Ladi aka rage ma guda biyu TAIMIYYAN ta fita kai mata ɗakin ta,ita kuma Iya ta
shige ɗaki don gabatar da Sallan isha'i,TAIMIYYAH ɗaki itama ta shige bayan ta dawo kaima
Ladi wainan fulawan,ta ɗauki wayanta tana turawa Abie saƙon Text Message akan tana son ya
siya mata sabuwan Laptop,amma samfurin Apple take so,can zuwa anjima kaɗan kawai taji alert
ya shigo wayanta na kuɗi masu kauri,sai kawai ta shiga kiran line ɗinsa,buga biyu ya ɗaga da yake
vedio call ta kira,yana ɗagawa idanunsa suka sauka akan ƴar nasa da yake matuƙar jinta cikin
zuciyansa,domin duk idan ya ɗaura idanunsa akanta Zaynab ɗinsa yake gani,wata ƙwayan mace
guda ɗaya da bazai taɓa iya haɗa soyayyanta dana kowace ɗiya mace ba "I miss u Abie ka rabu da
shigowa Zaria." Muryan TAIMIYYAH ya shiga kunnuwansa,ya sauke numfashi me sanyi yana
duban ɗan ƙaramin bakinta da ya iya shagwaɓa,ya saki murmushi sosai yana faɗin "Miss u too
Zayab,na ga saƙon ki ina fata kinji alert?"
Yayi maganan idanunsa akanta,ta sake narke masa da shagwaɓa tana faɗin "Eh Abie naji
nagode,Allah ƙara buɗi yasa kafi haka, idan Yah Sadeeq ya dawo shi kawai zan baiwa kuɗin ya
siyo min."
"Hakan yayi Daughter ina Iyan taki take,hope duk kuna lafiya zan shigo garin zuwa next week
insha Allah,har kin fara zuwa Cimputer skull ɗin kenan?"
TAIMIYYAH da ke sauraran Abie ɗin amma bata kalli face ɗinsa ba ta furta "Lafiya lau Abie Iya
tana sallah ne,skull kuma sai monday xa'a fara ina so ne kafin afara na mallaki Computern yadda
duk abinda aka koya mana zan zo in sake gwadawa a nawa."
"Gud gal! to Allah ya taimaka ki gaida Iya ai munyi waya ɗazu bye zan amsa wani call."
Daga haka yai cuting call ɗin,TAIMIYYAH ta sauke ajiyan zuciya tana jin ƙaunar Abie ɗin me
girma a cikin xuciyanta,duk da basu da shaƙuwa me zurfi tsakaninta da shi,amma ita da kanta ta
san yana son ta sosai domin idanunsa basa iya ɓoye hakan,wanda Iya tasha gaya mata cewa
Soyayyar da yakewa Mamanta dole ya shafeta don yayi mata wani irin so me wuyan
misaltawa,ashe rayuwansu bazai yi tsayi tare da juna ba,ta lumshe idanunta tana jin inama ta taso
tare da wannan uwa nata,sai dai ko kaɗan bata maraici don bata ma san daɗinta ba tunda bata rayu
da ita ba,Iya itace ta taso ta gani a matsayin uwarta,sai dai har kullum Iya ta kwaso pic ɗin Maman
nata tana jimawa riƙe da shi,tana kallon tsantsan kaman da suke da juna,hatta a wayanta tayi
snaping copys ɗin hotunan marigayiyan da yawa,ta adana lokaci zuwa lokaci takan shiga folder
ɗin tai ta kallon kyakykyawan fuskan mahaifiyan nata,to a yanzu ma da son ganin pic ɗin ya
motsa take ta shiga ta danno pics ɗin tana gani ɗaya bayan ɗaya.
_________
*9:40pm*
A.Maleek Ado ne zaune daga cikin falon da ke upstairs,yayi zaman dirshan don cin tuwan Semo
da ya sanar da Suhailah yana so,daga gefensa Suhailan ce zaune sanye da wani pencil skat da Riga
me siririn hannu,sosai kayan sukai mata kyau ƙirjinta ya fito sosai ta saman rigan,idanunta har
lokacin basu gama wartsakewa daga uban kukan da ta sha a yau ɗin ba,loman farko da ya kai
bakinsa ya tauna ya haɗiye,ya aje spoon ɗin manyan idanunsa ya sauke akan Suhailah,yana faɗin
"Ɗauke min wannan abincin daga gabana please!"
Yadda yai maganan muryansa na bayyana ɓacin ransa a fili,yasa Suhailah dubansa a razane,ya
cigaba da furta "Mena faɗi Suhailah tun a gidan Hajjah game da yin wannan abincin? Amma
sabida ban isa ba sai da kika baiwa bayinki suka yi sabida ki nuna min iyakata ko?"
Yayi maganan a mugun fusace yana miƙewa ya nufi ɗakinsa,ya bar Suhailah da baki sake gaba
ɗaya ta rasama abin cewa,bata san meyasa yake iya bambamce girkin da tayi dana masu aiki
ba,duk da cewa Ameena da take gani ƙwararriyace ita ta saka tayi masa,amma gashi sai da ya gane
ɗin,ta lumshe idanunta tana jin babu daɗi,dama ya lafiyan giwa ita me laifi ce gashi ta sake ɗaura
wani laifin,jikinta a sanyaye ta miƙe ta nufi ɗakinsa,sai dai tana shirin shiga shi kuma ya
fito,hannunsa riƙe da mukullin mota ya sauya kaya zuwa wasu Riga da Wando na Gucci,saura
kaɗan su gwabza karo Suhailah tayi saurin ja baya tana duban fuskansa da babu annuri take faɗin
"Don Allah kayi haƙury Sweet wallahi kaina ne ya dinga ciwo dana dawo,shiyasa na kasa yi da
kaina gudun karka dawo kuma ka tadda ba'a yi ba yasa nace Ameena tayi,don Al......"
A.Maleek ɗin da ya katseta ya furta,yana raɓata zai wucewansa tayi saurin shan gabansa tare da
riƙo rigansa,wani mugun kallo yai mata yana zare hannunta daga jikinsa,ya wuce da sauri zuwa
Stairs da bibbiyu ya dinga haɗa steps ɗin benan har ya sauka ƙasa,da kansa yake driving ya bar
gidan megadi na ɗaga masa hannu da fatan dawowa lafiya,Apple white ya nufa yayi Ordern wani
irin Tea nasu me daɗi haɗi da Snacks,bai tsaya ci anan ba akai masa take away ya fito zuwa
mota,ya sake isa wani wajen sai da ƙoda ya siya sannan ya wuto gida lokacin da agogo ke buga
sha ɗaya har da mintuna biyu,nan falon ƙasa ya zauna yaci komi iya yadda xai iya ci,yana cikin
ƙarisa shanye tea ɗinsa Suhailah ta sakko,tana sanye cikin kayan bacci Riga da wando da suka
fidda suranta,gaba ɗaya qamshinta ya cika wajen lokacin da ta iso,amma kallo ɗaya yai mata ya
ɗauke kai ita kuma ta zauna idanunta na kansa bayan ta gama kallon yadda ya barbaje packs ɗin
da aka zuba masa komi ciki,cikin wani irin salo na bada haƙury ta buɗe baki zatai magana,yayi
saurin ɗaga mata hannu,yana tashi tsam ya bar mata falon gaba ɗaya ya haura zuwa
sama,murzawa ɗakinsa key yayi don bayama buƙatan damu bare ya saurari ban haƙurinta,sabida
tana sake fusata zuciyansa ne sosai,ya daɗe yana gayawa kansa abubuwa da yawa da yake
shayewa daga gareta tana cin albarkacin Hajjah ne,da kuma ƙarfin zumuncin da ke tsakaninsa da
ita,uwa uba Soyayyan da Inna Kareeman ta gwada masa,wato mahaifiyan Suhailan yana sake taka
rawa wajen danne zafin zuciyansa akan Suhailah,amma baya ji idan aka cigaba da tafiya a yadda
Suhailah take masa yanzu baza'a samu matsalaba,don sosai take son ƙure duk wani haƙurinsa da
kauda kan da yake yi a wasu lamuran,yana ji tana faman nocking yai biris da ita,sai ma wayoyinsa
da ya janyo ya kashe su baki ɗaya,dama baya kwana da waya a kunne sam,har bacci ya ɗauke sa
bayan ya kwanta baisan yadda ta ƙare tsaye abakin ƙofar ɗakin nasa ba.........✍🏻
Littafin TAIMIYYAH paid book ne da zai zo akan 500 naira only,ga masu buƙatan yin payment
zakui min magana ta wannan number ɗin 08167768704, ko kuma ku turo kuɗin ku kai tsaye ta
wannan account ɗin 0504192664 aisha ibrahim dansabo GTbank.*
_Masu account da Arewa books,zaku dinga siyan sabbin shafuka dalla-dalla akan farashi me
sauƙi,ga yadda zaku siya pages a arewa books kamar haka_ 👇🏻
https://arewabooks.com/chapter?id=62d29e11aa5f8f19bc9621cb
*Balance* - Zai nuna kudin account dinku da zaku iya sayayyan littafai cikin kasuwar
ArewaBooks.
*Credit/Debit Card* - Hanyar farko kuma mai dadi wajan Recharge din account dinku.
A inda (Enter your amount) za'a saka kudin da akeson Recharge din sai a taba "Proceed". Zaibude
muku inda zaku saka bayanan katin banki, kuna gamawa kudinku zaishiga account dinku kaitsaye
(instant).
--------
*Bank Transfer*
*Airtime Transfer*
Saidai su ba kaitsaye bane (instantly) sai ArewaBooks ta tabbatar da Transfer din, amman bayakai
1hour za'a gansa a Balance.
#Ɗansabo ce#
[12/14, 3:42 PM] +234 703 040 9541: *TAIMIYYAH*
*Page 20 to21*
*To masu karatu a wannan page ɗin Free pages ya zo ƙarshe.Don haka sai ku hanzarta biyan 500
ɗinku don jin cigaban labarin,domin duk yadda zan gutsira muku ya labarin TAIMIYYAH yake ba
za ku gane inda aka dosa ba har sai kun shiga cikin labarin tsindim sannan za ku gane inda tafiyan
ya dosa.Don haka kar ku bari a barku a baya ku bi sahun masu rubdugun shiga Payment Group
don jin ya labarin TAIMIYYAH zai kasance? Yah Maleek da Suhailah za su kwashe a gaba,shin da
gaske zai iya sake auren wata mace don samun haihuwa,ko bazarana ce kawai yake? Duk za a
warware muku zaren labarin a gaba.Ku dai kawai ku biya ku shige cikin group don kwasan
karatu.Saina ga ruwan ƙauna daga Fans ɗina* 😍
_______Washegary Suhailah da kanta ta tashi ta shiryawa A.Maleek Breakfast,sai dai cikin rashin
sa'a A.Maleek ɗin tun ƙarfe takwas ya bar gidan ba tare da sanin Suhailan ba,sai da ta gama tsara
kwalliya ta nufi ɗakinsa ta tadda babu kowa ciki,sai ɗakin da ya bari a hargitse duk kayan da yai
anfani da su gasu nan zube bisa Bed ɗin,waya ta ɗauka ta kira shi zuciyanta na bugawa da ƙarin
takaicin kanta da kanta,yana ɗaga wayan sai ta nemi sanya masa kuka yayi saurin dakatar da
ita,yana sanar da ita ya wuce Kaduna daga can kuma zai bi jirgi ya wuce Lagos,sai next week zai
dawo bayan an rantsar da shi akan sabon muƙamin da aka bashi,wanda za'a rantsar dasu a Abuja
sati me zuwa, don haka ya bar mata garin tayi yadda take so,ai Suhailah bata san lokacin da ta
rushe da kuka ba shi kuma yai cuting call ɗin yana jan ƙaramin tsaki,zama tayi a ɗakin taci
kukanta ta more kafin ta fice ta koma zuwa nata ɗakin,ta cigaba da neman layin Zuby cikin sa'a
bugu biyu Zubaidan ta ɗauka,sai Suhailah ta sanya mata kuka,cikin nuna kiɗemewa Zubyn ke
tambayan Suhailah abinda ke faruwa amma sai Suhailah ta shaida mata cewa zancen bana waya
bane,don haka idan ta samu lokaci kawai ta zo gidan nata akwai maganganu,daga haka sukai
sallama Suhailah ta aje wayan,zuciyanta sam babu daɗi tana tsoran ace Maleek ya juya mata baya
a dai-dai wannan lokacin,takaicin kanta na yadda take kasa binsa a yadda yake so na sake lulluɓe
zuciyanta.
________
*Monday,10:10am.*
TAIMIYYAH ce tsaye daga bakin titin kwaltan shiga layinsu,sanye take da dogon Hijab kalan
sararin samaniya,kaman yadda kalan Material ɗin jikinta yake,Napep take jira don zuwa wajen
Computer Training ɗin da zasu fara a yau ɗin,sai dai da alama yau ɗin za'ai wahalan abin hawa,ta
sake kallan agogon da ke ɗaure a tsintsiyar hannunta,ta ga lokaci na sake tafiya sai takaicin rashin
barin Sani Drivern Iya ya kaita ya kamata,don ba yadda Iya ba tayi akan ta kira Sanin ba amma ta
nuna tafi so ta dinga zuwa da kanta,tsayuwan mintuna kusan goma ta ƙara bata samu abin
hawanba gashi ita ba gwanar jurewa tsayuwa bace sabida laluran ƙafanta,wayanta take shirin
cirowa a jaka ta kira Sanin ta ji idan yana kusa kawai yazo su wuce,sai dai tsayuwan wani me
Napep a gabanta yana faɗin "Hajiya tafiya ne?" Shi ya katsewa TAIMIYYAH hanzari ta ciro
hannunta daga cikin jakan tana gyaɗa masa kanta,kafin ta furta "Eh tafiya ce,can gaban Congo
kaɗan zaka kaini."
Ta ƙare maganan tana shiga cikin Napep ɗin ta zauna,shi kuma ya ja sukai gaba ko da suka isa
sauka tayi ta nufi cikin wajen bayan ta biya shi kuɗinsa,shi kuma yaja mashin ɗinsa yai gaba,Ƙarfe
ɗaya dai-dai suka tashi kaman yadda aka sanar dasu tsarin karatun,su shiga ten afito one ga
mamakin TAIMIYYAH kuma suna da yawa sosai wanda suke karatun tare maza da mata,cikin
wanda suka fito kusan a tare wata budurwace me yawan fara'a,baƙace sosai sai dai tana da kyau
dai-dai misali,ta dubi TAIMIYYAH lokacin da suka gama fitowa daga cikin ajin ɗaukan karatun,ta
miƙa mata hannu tana faɗin "Salamu alaikum,sunana Zaynab Haroun." TAIMIYYAH itama sai ta
miƙa mata nata hannun sukai musabaha,da murmushi a saman fuskarta take faɗin "Sunana Zaynab
Sameer."
"Wow! nice name Namcy,ina farin cikin haɗuwa da takwarata." Cewan budurwan itama murmushi
kwance saman fuskanta,suka jero a tare da TAIMIYYAH har zuwa bakin titi,budurwan na ta ɗan
jan TAIMIYYAH da magana akan Programme ɗin da zasuyi na Computer Training ɗin,zuciyanta
cike da tausayin yadda TAIMIYYAN ke tafiya,a zuciyanta take ayyana mace har mace
kyakykyawa da ita ga dirin jiki amma Allah ya jarbceta da nakasan ƙafa ɗaya,ita dai TAIMIYYAH
tana amsa mata jefi-jefi,suna tsaye tare har suka samu abin hawa,TAIMIYYAH ta shaida masa
gyallesu zata nufa,yayin da itama Zaynab tace Gaskia ita ta nufa,hakan yasa sukai sallama da juna
TAIMIYYAH ta shiga ya wuce da ita.
Ta iso gida a gajiye sosai burinta bai wuce ta ganta a Sasan Iya ba,tayi wanka ta sawa cikin ta
abinci don yinwu take ji sosai,a hankali take shigowa cikin Compound ɗin gidan,bayan ta tsaya
sun gaisa da sabon megadin da Baba Sani ya kawo a shekaran jiya me suna Tukur,matashi ne
kuma bamai nisan shekaru sosai ba don bazai wuce shekaru arba'in ba,tana cikin tafiya sai ji tayi
ana kiran sunanta,sai ta dakata da tafiyan hannunta dai dafe da ƙafanta me laluran,ta waiwaya
baya idanunta na sauka akan Anty Laurat da ke tahowa daga Sasan su Zuhurah,sai TAIMIYYAH
ta saki murmushi tana cigaba da tsayuwa har Anty Laurat ɗin ta ƙariso wajen,tana furta "Daga ina
ƴan mata da uwar ranannan?"
TAIMIYYAH ta sake faɗaɗa murmushinta tana sanar da Laurat ɗin daga inda take,Laurat ta furta
"Ayyah! Sannu da dowawa tuh,ya karatun hope ya fara daɗi?" Yadda tai maganan da zolaya yasa
TAIMIYYAH sakin murmushi tana faɗin "Anty Laurat kenan sai mu ce Alhamdulillah!"
Laurat itama ta saki dariya kaɗan tana faɗin "Bari na barki ki ƙarisa daga ciki,nima wai na fito zan
ɗan je kasuwa ne akwai abinda zan nemo,zuwa anjima zan shigo ai yau ina so ki ɗan gwada yin
Doughnut irin wanda ki kai shekaranjiya ɗinnan,yayi daɗi ina so na ga yadda kikai kwaɓin."
"Ok ba matsala Anty Laurat,sai kin shigo ɗin bari in ƙarisa na gaji sosai." Cewan TAIMIYYAH
daga haka kuma ta cigaba da takawa zuwa Sasan su inda tafi wayo,a falo ta tadda Iya tayi baƙuwa
qawanta Hajiya Sahura ne ta zo,da alama tazo garin kenan sabida ta bar Zaria da daɗewa,ta koma
can Bauchi wajen Yayanta namiji da ya ɗauke ta tun bayan rasuwan mijinta,TAIMIYYAH ta
durƙusa har ƙasa ta gaida Hajiya Sahuran da ke mata sannu da zuwa,ta amsa da fara'a tana faɗin
"Sannu TAIMIYYAU ai ina zuwa na tambayeki Iya tace kina wani makaranta na koyan
na'urannan me ƙwalƙwala,to Allah ya bada sa'a." TAIMIYYAH ta amsa da "Ameen,amma Hajjaju
ki dinga faɗin sunan dai-dai TAIMIYYAH ne fa ba TAIMIYYAU ba."
Yadda TAIMIYYAH tai maganan a shagwaɓe yasa Iya da Hajiya Sahuran yin dariya,Iya na faɗin
"Ja'irah to ya karatun na ga kin jima nema baki dawo ba."
"Lafiya lau Iya,rashin abin hawa ne wallahi ya tsaidani,don da zani ma da ƙyar na samu,ina ga dai
naki zanbi Sanin kawai ya dinga zuwa ya kaini idan zan dawo na dinga dawowa ni kaɗai ɗin."
Cewan TAIMIYYAH tana tashi don shigewa ɗaki,Iya tabi bayanta da kallo tana faɗin "A tuh! Da
dai yafi miki kam."
Bayan shigan TAIMIYYAH ɗaki ne Hajiya Sahurah ta dubi Iya tana faɗin"Kinga yarinya yadda ta
zama ƙatuwar budurwa kyau kaman ita tai kanta,lallai na jima rabo na da Zaria Iya wallahi
kamanninta da marigayiya uwarta har ya ɓaci,inama ina da ɗa namiji da anyi haɗin zumunci don
ni dai ina ƙaunar wannan ɗiya ina kuma tausayinta matuƙa,Allah yai mata zaɓi ya kareta daga
sharrin samarin zamanin nan." Iya tayi caraf tana amsawa da "Ameen,ke dai bari kawai Hajjaju
kullum addu'an da nake kenan Allah fito mata da nagari,ya kaita inda bazata cutu ba ko dan
laluran ƙafannan nata,kinsan halin mutanan mu koya suka ga mutum da nakasa sai ya zama abin
rainawa,bayan basu san irin baiwan da ubangiji ya aje a garesa ba,Allah dai ya shige mana gaba
yai mata kyakykyawan zaɓi Ameen." Daga haka suka cigaba da hiransu Iya na ba qawan nata
labarin yadda Umma ta ɗauki karan tsana ta ɗaurawa TAIMIYYAN,Hajiya Sahuwa abinka da
mace me saurin ɗaukan zafi,nan take ta dinga la'antan baƙin halin Umma,har tana mata fatan Allah
ya gwada mata samun nakasasshen cikin jikokinta in tana ganin ta gama haihuwa ne a yanzu da
har take nunawa TAIMIYYAH baƙin tsana irin haka,ita dai TAIMIYYAH da ta fito daga wanka
tana jiyo tashin zancen su Iyan sama-sama daga ɗakinta,har ta gama shiri ta fito kai tsaye ta nufi
wajen cin abinci,ta zuba wanda zataci ta fara ci bayan ta kammala ɗaki ta shiga,tana ɗakko
sabuwar Laptop ɗinta da Yah Sadeeq ya taho mata dashi daga Kd,randa yazo Weekend domin
tunda Abie ya turo mata kuɗin sayan sai taiwa Yah Deekun magana ta waya akan tana so ya siyo
mata yazo mata dashi,tayi-tayi ya turo mata details ɗinsa ta saka masa kuɗin,amma sai yai mata
wayau yace ta bari idan ya shigo Weekend zasuyi magana,sai kawai ganinsa dashi tayi randa ya
diro garin ya kawo mata Sasan Iya,yana mata dariya wai Suprising ɗinta yayi,aiko murna a gun
TAIMIYYAH kaman ta rungumeshi haka taji,musamman da ta duba taga Exactly irin wanda ta
tura masa hotonsa ta chart ne tace irin shi take so,hatta Iya tayi murna da wannan kyauta da yaiwa
TAIMIYYAN,tai ta masa godia yana hararanta a lokacin yana faɗin shi baiga abin godia ba don ya
saiwa TAIMIYYAN Laptop kawai.ta saki murmushi lokacin da take buɗe Laptop ɗin ta
kunna,cikin sauƙi ta fara operating ɗin abinta cike da farin ciki,tayi abu me yawa a ciki duk cikin
karatun su na yau ɗin,kafin ta rufe ta mayar ta aje tana komawa gado don ta samu ta ɗanyi bacci
kafin akira sallan La'asar.
Kamar yadda suka rabu da Anty Laurat zata shigo koyan Doughnut,aiko ana idar da sallan la'asar
ta shigo Sasan Iya,bayan sun gaisa da Iya a falo ne ta wuto ɗakin TAIMIYYAH,wacce ke amsa
call ɗin Maryam Salis da ke sanar da ita rashin lafiyan mamansu da aka kwantar a
asibiti,TAIMIYYAH ta bata tabbacin zata sanar da Iya su je su dubo Mum ɗin a asibitin kafin a
sallamesu,ta sauke wayan daga kunni bayan sunyi sallama da Maryam ɗin,manyan idanunta ta
ɗaura akan Anty Laurat da ke bin TAIMIYYAN da kallo,ganin yadda Rigan jikinta yai mata
kyau,tare da fito da kyawun halittan TAIMIYYAN a sarari "Anty Laurat har kin shigo?" Cewan
TAIMIYYAH da murmushi saman face ɗinta,Laurat ɗin itama murmushi tayi tana faɗin "Eh!
Wallahi TAIMIYYAH gani na shigo,gara afara yanzu kada muyi dare ko?"
Daga haka suka fito zuwa kitchen ɗin Iya,da yake babba ne sosai sam babu wani takura,Ladi na ta
hidiman ɗaura abincin dare su kuma suna aikin kwaɓa Doughnut ɗin,wanda TAIMIYYAH tace a
kwaɓa na mudu ɗaya kawai,aci har ayi sadaka da sauran wa maƙwafta,hakan ko akayi ta fiffito da
kayayyakin yin,fulawa mudu ɗaya (8 cups) ta baiwa Anty Laurat ɗin tace ta tankaɗe cikin wani
bowl,ita kuma ta fito da 2 eggs, sai Sugar 1 and half cup, sai 2tbsp na Yeast ,sai 1tsp Salt,sai Half
Simas,sai 2 cups liquid milk(warm),sai 1tsp Vanillah powder.
Bayan duk ta gama arranging Ingredients da take buƙata sai ta ɗakko Mixer ɗinta ta jona jikin
sucket,ta fara da zuba fulawan da aka tankaɗe cikin Mixing bowl ɗinta,sai ta zuba Vanillah powder
ɗinta da Salt and Sugar ɗin,ta juya suka haɗe jikinsu,sannan ta fasa egg ɗin a wani bowl ta zuba
Yeast and Warm milk ɗinta,ta kaɗa sosai ta juye akan fulawa ɗin,sai ta zuba butter ɗin akai ta fara
mixing with high speed,sai da ta tabbar yayi mixing sosai zaku ga tun anan ya fara kunbura yayi
wani irin laushi,tana yi tana zuba butter ɗin har buttern ya ƙare,sai ta kwashe shi cikin wani Bowl
wanda ta shafeshi da Butter,sai ta rufe da clin film ta ajesa yayi some minutes,za ku ga ya kunburo
sosai sannan sai suka fara murzawa a abin murji suna cire shape ɗin Ring Doughnut,wani kuma
sai TAIMIYYAH ta naɗe shi as twisted Doughnut,ita dai Ladi da Laurat bin TAIMIYYAH suke da
kallo tana sake birgesu matuƙa,yadda take kominta a nutse cike kuma da ƙwarewa,lokacin da suka
kammala sai suka bashi some another minutes,za ku ga duk shapes ɗin sunyi doubling sun
kumbura sosai,sannan suka ɗaura mai Anty Laurat ita ta amshi suyan tana faman jerawa
TAIMIYYAH sannu,wanda hakan ya baiwa TAIMIYYAH dariya ma,don ita ta riga da ta saba yin
waɗannan ayyukan don haka ta taso ita me son girke-girke da harkan su snacks ne,shiyasa take
shiga online classes kala kala,kuma duk anan ta sake samun ƙwarewa,abinda bata gane ba sai ta
tafi youtube ta dubo a haka har ta zama ƙwararriya sosai a fannin girkin zamani da haɗa su
Snacks kala kala,wani irin result me kyau Doughnut ɗin ya bada,yayi wani irin laushi da kyau
sosai,kallo ɗaya zakai masa kasan daɗin da zaiyi tun kafin akai baki,yanzu ne kuma Anty Laurat
ɗin ta gane bambamcin da TAIMIYYAH ke faɗi na kwaɓin Mixer yafi na hannu kyau da
laushi,domin duk yadda zakai kneading ɗinsa da hannu ba kaman yadda mixer zaiyi ba don
texture ɗin bazai taɓa zuwa ɗaya ba.
Iya dai da ke can Falo tuni qamshi ya gama cika sasanta,tana alfahari da ƙwarewan TAIMIYYAH
da baiwan da Allah yai mata kashi kashi,tasan ko da wannan baiwan na iya sarrafa girke-girke aka
barta zata mallaki zuciyan miji.Lokacin da suka kammala suyan ya cika wani babban roba domin
sai da suka samu 50pcs cas,don haka TAIMIYYAH ta zuba cikin wani roba me murfi aka baiwa
Ayuba almajirin Iya,ya miƙa gidan Alhaji Bala wani maƙwafcin su Iya,me kirki hakama matarsa
Anty Hannah mutumiyan TAIMIYYAN ce sosai,bayan TAIMIYYAH ta ɗibi wanda zai ishe su ita
da su Iya,sai tace da Anty Laurat ɗin ta wuce da sauran duka kawai Sasan Baba Sanin,Anty Laurat
ɗin tai godia cike da murnan yadda ta samu experience na kwaɓin Doughnut,wanda ita idan tayi
tauri yake sabida rashin ƙwarewa,sai gashi yanzu ta gano bakin zaren cikin sauƙi.
Lokacin da ta isa Sasan su Umman ba kunya su Zuhurah suka tare ta,suna amshe roban Doughnut
ɗin suka shiga ɗauka suna kaiwa baka,babu kunya babu tsoran Allah kaman ba maƙiyiyansu
TAIMIYYAN ce ta sarrafashi ba,ita kanta Umma har cewa tayi Anty Laurat ɗin ta ɗibar mata wani
zuwa dare da shi zata sha Tea kafin ta kwanta,tunda ita mayyan shan Tea ce kafin tai bacci,Anty
Laurat dai kallon su kawai take tana jinjina rashin kunya irin na wasu mutanen,in banda haka
wanda kace kana adawa dashi kana kushe halittansa miye na rawan jikin cin abinda ya fito daga
hannun wacce su ke kira da musaka gurguwa? Ta haɗiye takaicin su Zuhuran da ke cinta arai tana
musu addu'an Allah ya shiryesu kawai.......✍🏻
Littafin TAIMIYYAH paid book ne da zai zo akan 500 naira only,ga masu buƙatan yin payment
zakui min magana ta wannan number ɗin 08167768704, ko kuma ku turo kuɗin ku kai tsaye ta
wannan account ɗin 0504192664 aisha ibrahim dansabo GTbank.*
_Masu account da Arewa books,zaku dinga siyan sabbin shafuka dalla-dalla akan farashi me
sauƙi,ga yadda zaku siya pages a arewa books kamar haka_ 👇🏻
https://arewabooks.com/chapter?id=62d29e11aa5f8f19bc9621cb
*Credit/Debit Card* - Hanyar farko kuma mai dadi wajan Recharge din account dinku.
A inda (Enter your amount) za'a saka kudin da akeson Recharge din sai a taba "Proceed". Zaibude
muku inda zaku saka bayanan katin banki, kuna gamawa kudinku zaishiga account dinku kaitsaye
(instant).
--------
*Bank Transfer*
*Airtime Transfer*
Saidai su ba kaitsaye bane (instantly) sai ArewaBooks ta tabbatar da Transfer din, amman bayakai
1hour za'a gansa a Balance.
#Ɗansabo ce#
[12/14, 3:42 PM] +234 703 040 9541: *TAIMIYYAH*
*Page 22 to23*
________ Satin TAIMIYYAH biyu kenan da fara zuwa Computer training ɗin.Ta saba sosai,tana
kuma sahun farko na ɗaliban da ke matuƙar ƙoƙari,domin duk abinda akayi da ta dawo take zama
ta kunna System ɗinta tana gwadawa.
A hankali kuma suka fara sabo da Zee wacce da gaske ita son su ƙullah ƙawance da TAIMIYYAN
ta ke yi,don tsakaninta da Allah TAIMIYYAN na matuƙar birge ta.Tun TAIMIYYAH ba ta sake
mata har ta fara sabawa da yawan surutun Zee ɗin,don wani lokacin bayan an tashi sukan jima
suna hira daga bakin gate ɗin fita wajen kafin ta samu abin hawa kowacce ta kama gabanta.
Sani shi ke kai TAIMIYYAN ita kuma ta maido kanta gida idan an tashi.To yauma kamar kullum
bayan sun gama zantawa da Zee Haroun ɗin sai ta tare wa TAIMIYYAH Napep.TAIMIYYAN ta
hau sukai sallama suna ɗagawa juna hannu.
Lokacin da TAIMIYYAH suka iso layinsu sam bata kula da motar da ke biye da Napep ɗin data
hawo ba.Bayan ta sauka tana ba me Napep ɗin kuɗinsa ne kaman ance ta ɗaga idanunta zuwa
farkon shigowa layin,sai ta hangi wata farar mota na yin reverse tana komawa da baya.Bata kawo
komi cikin ranta ba ta amshi canjinta da me adaidaitan ke miƙo mata,tayi shigewanta gida. Sallah
kawai tayi ta fito cin abinci,tana jin ɗakin tsit don Iyah bata nan ta fita can ƙasan layin nasu anyi
wani rasuwa.Taje gaisuwa Ladi ce kawai a Sasan,kuma tana ɗakinta da ke daga waje.Don haka
TAIMIYYAH na gama cin abincin ta shige ɗaki don kwanciya,ta riga tayi sabo da yin baccin rana
duk idan ta dawo.
Bata wani jima da kwanciyan ba bacci yai gaba da ita,don haka ta tashi ne ta ga har huɗu na
yamma ta gota.Tayi saurin faɗawa toilet ta ɗauro alwala,ta fito ta gabatar da sallah.Ko data idar
wayanta kawai ta ɗauka ta fito falo,Iyah ta samu da itama fitowanta falon kenan daga ɗaki bayan
tayi sallah.TAIMIYYAH ta dubi Iyah tana faɗin "Iyah ashe har kin dawo, ina ta faman bacci sannu
da dawowa."
"Yauwa sannu Zainabu,aina leƙa ki na ga kina bacci,ya karatun Allah yayi albarka." Cewan Iyah
TAIMIYYAH na amsawa da "Da Ameen." Kafin ta aje wayanta saman kujera tana faɗin "Iyah bari
in zubo furannan na jiya da ban samu sha ba ai nasan bai komai ba tunda yana cikin Fridge.Wani
yinwa nake ji amma na kwaɗayi bana abinci ba." Tayi maganan tana ɗan dariya Iyah ta aika mata
harara tana faɗin "Aifa nan kika fi auki,a wajen kwaɗayi saura ki kwashe min madara duk ki lafta
a cikin furan.Duk da dai ubanki da Sani ke sayan madaran."
TAIMIYYAH dai dariya kawai ta ke yi har ta shige Kitchen ɗin tana ma Ladi sannu da aiki.Ladi
wacce take aikin wanke kuɓewan da xata yanka, ta amsa TAIMIYYAH da fara'a kafin
TAIMIYYAN ta ɗaura da faɗin "Babah Ladi yau kice miyan kuɓewa za mu sha,da tuwan Semo ne
ko tuwan shinkafa?" TAIMIYYAH tayi maganan lokacin da take ciro Jug ɗin data aje furan a
ciki.Ta tsiyayi iya wanda zai mata tana maida sauran cikin Fridge ɗin,Ladi ta saki murmushi tana
faɗin "Ai mutumiyata da tuwan Semo ɗin ne, don itama Iyah ta san kinfi son shi ai."
"Wow! Aiko bari ki gani in gama shan furan nan inzo in amshi yin miyan,ke sai kiji da yin tuwon
Babah Ladi." Cewan TAIMIYYAH tana dafe da ƙafanta me laluran tana tafiya don fita daga
Kitchen ɗin.
Ladi na faɗin "Yauwa ƴar gida na jeki ki dawo ɗin indai miya ne sai ki zo ki mana irin naki me
daɗinnan." Ta ƙare maganan cike da raha ƙaunar TAIMIYYAN na sake kama zuciyanta.Don
baƙaramin birgeta yarinyan ke yiba,gefe guda tana tausayinta har cikin ranta tare da yi mata
addu'an samun mijin da zai ƙaunace ta tsakaninsa da Allah.
Kaman yadda TAIMIYYAH tace tana gama shan furan da ta narkawa uban madara,ta nufo kitchen
ɗin.Ta isa wajen Sink tana wanke cup ɗin da ta ɓata ta kife,direct wajen da Ladi ta aje kayayyakin
yin miyan ta nufa.Tana duba duk abubuwan da Ladin ta aje, tashin farko sai data ƙaro yawan
naman da za'a zuba a cikin miyan.Cikin ƙwarewa ta tada haɗin miyan ɗanyar kuɓewan,wanda ke
ta faman zuba qamshi yaji naman shanu haɗi da ƙashin naman rago.Sosai miyan yai yauƙi yai
kyau a ido sosai.
Bayan ta kammala barin kitchen ɗin tayi Ladi na faman jera mata sannu.basu jima da Iyah ba suna
kallo aka fara kiran Magrib, hakan yasa duk suka nufi ɗaki don yin sallah.Ko da TAIMIYYAH ta
idar karatun Qur'ani ta cigaba da rerowa cikin ƙira'anta me taushi da daɗin amo.Sai da akai kiran
Isha'i tana zaune tana rero karatun ta,kafin ta tashi ta gabatar da sallan ishan.Sannan ta fito
falo,zuwa lokacin itama Iyah ta fito sai suka nufi wajen zaman cin abincinsu.TAIMIYYAH na
zama ta fara buɗe kulolin da aka kawo abincin dare daga Sanan Baba Sani.Ganin Cous Cous da
miya suka yi yasa ta rufe kulolin tana taɓe baki,don ita sam bata fiya son Cous Cous ba.Garama
idan jallop ɗinsa akayi yaji liver da kayan lambu a wadatashi da Irish kuma,to zata ci sosai amma
indai da miya ne bata so.
Ƙullin tuwo ɗaya ta juye a plate ta zuba miya,tana janyo roban yajinta daga saman wani ɗan
cabinet da akai a wajen suna ɗaura tarkacen su cups da su plates.Sunyi nisa a cin abincin su babu
me magana,Tukur mai-gadi yayi sallama daga bakin ƙofan shigowa falon Iyah.Iyah ta tsame
hannunta daga plate ɗin tuwan ta tana amsa sallaman Tukur,tare da faɗin "Malam Tukur lafiya dai
ko?"
Daga waje Tukur ya amsawa Iyah da faɗin "Lafiya lau Hajiya,wani ne dama yazo a wata farar
mota yace inyi masa sallama da TAIMIYYAH.To yadda ya kwatanta min tafiyanta da siffanta ne
na gane TAIMIYYAN yake nufi,shine nazo isar da saƙo."
"To madallah je kace masa tana zuwa.Amma ka shaida masa ya ɗan shigo daga cikin gidan sai ka
sanya fararen kujerun nan daga wajen shigowa nan ya zauna ya jirayi fitowanta.Don tsayuwannan
daga waje akan layi mutane na gilmayya ba mutunci bane,gara ya shigo nan ɗin kana aikinka
idanunka na kansu hakan zaifi."
Cewan Iyah tana kallon yadda TAIMIYYAH ta dakata daga cin abincinta.Fuskannan ta cuskune
shi kaman zata fashe da ihu,shi ko daga waje Tukur ke faɗin "An gama Ranki ya daɗe sai ta fito
ɗin,bari inje inyi yadda kika ce." Daga haka yabar wajen ya fice daga Sasan baki ɗaya don zuwa
isar da saƙon Iyah wajen Matashin saurayin.
"Yanzu Iyah daga cewa ana sallama sai ki wani ce a shigo da mutum ciki,baki san ko waye ba
haka akeyi? Ni gaskiya da kin rabu da shi an sallamesa ni bansan waye ba kawai sai inkama fita
wajen......"
"Dallah! Rufe min baki,ki kuma tashi kije ki samu koma waye ɗin.Ina sha idan kin fitan idanunki
zasu gane miki? Da kike cewa waye waye ba sai an ba mutum dama ake sanin ko shi waye ɗin
ba.Bana son sakarci maza kije ki sanyo Hijab ki fita,kin dinga zama kenan ana zuba miki ido ba za
ki fitar da miji kiyi aure ba,sabida kawai kina da lalura to tun ba'a ji kanmu ba ki tashi ki fita."
Iya tayi maganan cike da faɗa sosai.Idanunta akan TAIMIYYAH da har idanunta sun fara tara
ƙwallah,amma musu da Iyah ta san ba abune da zai yiwu mata ba.Musamman yadda ta ɗauki zafin
nan,sai kawai ta miƙe tana barin plate ɗin tuwan da take ci ba don ta ƙoshi ba.ko da ta shiga
ɗakinta sai data ɗaurayo bakinta da Mouth Wash a toilet,sannan tazo ta zura Hijab ɗin sallan ta.Ta
fito ta wuce Iyah fuskanta ko kaɗan babu annuri,ga ƙirjinta da ke faman dakan lugude har ta fito
daga Sasan Iyah.
Daga gaba kaɗan ta hango inda Tukur ya jera musu fararan Kujeru biyu.Mutumin da sam bata
hango fuskansa ba yana kame saman kujeran.Ta ɗauke kai tana takawa zuwa wajensa bisa tsarin
halittan da Allah ya nufeta da takawa ahakan.
Tun da TAIMIYYAH ta doso shi idanunsa ke kafe akanta ƙur...! Har ta ƙariso ta ja kujeran ta
zauna,kanta a ƙasa take faɗin "Assalamu alaikum." Ya amsa da "Wa'alaikissam warahmatullah
wabarakatuh! Ranki ya daɗe barka da fitowa."
TAIMIYYAH ko kaɗan bata yi gigin ɗago fuskanta daga sunkuyar dashi da ta yi ƙasa ba.Ta amsa
masa da "Barka dai ina yini ina gajiya."
A kallo ɗaya za ka san dogo ne ko bai miƙe ba.Yana sanye da fararan kaya tas da sukai masa
kyau,daga yanayin shigan nasa zaka iya fahimtan ɗan gaye ne sosai,ma'abocin sanin kan iya sanya
kaya.Daddaɗan qamshin turaren AZZARO WANTED ya gama mamaye wajen,duk TAIMIYYAH
ta ƙare masa kallo ne cikin daƙiƙa kaɗan.Ba kuma kai tsaye tayi hakan ba,don sam bata ji ma zai
gane tayi masa kallon da tai masan.
Ta sake yin ƙasa kanta sosai kafin ta fara magana cikin sanyin muryarta tana faɗin "Bawan Allah
naji duk kalamanka,amma sai dai kayi haƙury ni babu maganan yin soyayya da kowa ma a
lissafina.Karatu nake so,shine kuma kaɗai a cikin lissafina.Kuma in banda abinka taya soyayyah
zai ƙullu tsakanin gurguwa da me ƙafafunsa biyu lafiya?Kaga kaman bazai yiwu ba,don haka kayi
haƙury tunda aure kake so zan tayaka da addu'an Allah ya zaɓa maka ta gari lafiyayya wacce ba
gurguwa ba."
Tunda TAIMIYYAH ta fara magana Naseer ya tsura mata ido,wani abu na sake yawo a ilahirin
jinin jikinsa.A yanzu kawai da take gabansa sai ya ga kaman an sake ninka kyawunta ne,gaba ɗaya
sai yaji duk yadda yake hasaso jin muryarta,sai yaji zaƙi da taushin muryan har ya zarce tunaninsa.
Ya saki wani ƙayataccen murmushin da suka bayyana jerarrun haƙoransa,yana faɗin "Malama
TAIMIYYAH kenan,kece kike ganin hakan,amma ni ke na hango a hakan kika kuma tafi da
dukkanin zuciyata da nutsuwata.Idanuna sun fi naki yawatawa akan tarin ƴan mata kala
kala,amma ni gurguwan dai itace zaɓi na.Idan har zaki amince ki bani dama zan tabbatar miki da
gaske ƙaunarki nake da dukkanin zuciyata.Don haka ki aje wannan maganan a gefe,yanzu dai ki
sanar dani wani abu akanki ko da kaɗan ne please TAIMIYYAHH."
Ya kai ƙarshen maganan a wannan ƙaron ma cikin jan ƙarshen harafin sunanta,da wani irin salo da
ya sake fisgan hankalin TAIMIYYAH.Har ta sake ɗago idanunta akaro na biyu ta aza
akansa,amma ganin yadda ya tsura mata nasa idanun ya sata saurin sake yin ƙasa da kanta.Wani
matsanancin kunya na lulluɓeta,ta wani tunzuro baki gaba alamun kallon na bata haushi.Sai dai
duk abinda take yi yana gani kuma tana sake motsa zuciyansa ne ba tare da tasani ba.
Ganin bata da alamun sake tanka masa yasa shi buɗe baki don yin magana,amma sai isowan Anty
Laurat da sallamanta ya katse hanzarinsa.Kusan a tare suka waiwayo suna duban Anty Laurat data
ƙariso wajen sosai,fitowa tayi za ta maida roban da ta tafi da Doughnut aciki.Shine tana dosowa
don shi ga Sasan Iyah ta hango TAIMIYYAN da baƙo shine ta zarto don tayi tsokana.Sallamanta
Naseer ya amsa har da zamowa kaɗan daga kujera yana gaida Anty Laurat ɗin.Ta ko amsa da
fara'a tana faɗin "Sannunka da zuwa sirikina,ina fata dai kaine za ka ci nasaran sace min zuciyan
wannan Daughter ɗin nawa me gudun maza."
Tayi maganan cike da barkwanci,TAIMIYYAH ta kwaɓe fuska cike da shagwaɓa take faɗin "Kai
Anty Laurat."
Yadda tai maganan da salon shagwaɓar ta ba ƙaramin taɓa zuciyan Naseer da idanunsa ke kan
TAIMIYYAN ya yi ba.Yayi saurin faɗin "Yauwa Anty nako gode da Allah ya jefo ki,dama na ga
alaman sai ta wahalar da zuciyata sosai kafin abani dama.Ko tausayina ma ba'a ji sabida bata san
yadda nake jinta a cikin zuciya da gangar jikina ba."
Naseer yayi maganan shi ma yana wani narke murya irin aji tausayinsa ɗinnan.Abinda ya baiwa
Laurat dariya kuma nan take ta gane ɗanyi ne shi,irin sune ke saurin sace zuciyan mace.Don haka
ta biye masa yana sake fallasa mata irin soyayyar TAIMIYYAN da yake ji.Ita ko TAIMIYYAH sai
ta koma ƴar kallo tana jinjina rashin kunya irin ta maza da ake faɗi,da har ya iya zaƙewa yana
sakin zance.Anty Laurat itace ta bashi Number ɗin TAIMIYYAH,wacce ta ji kaman ta sanya ihu
don takaici.Sai kawai ta miƙe tana barin musu wajen bayan tai masa kallo ɗaya tana faɗin "Sai da
safe ni zan shi ga daga ciki."
Ya ɗan ɗaga murya yana faɗin "To ranki ya daɗe amma zuwa anjima don Allah a daure a ɗaga
wayata idan nakira.Don bana ji zan iya bacci ban sake jin golden voice ɗinnan ba,please Luv."
Gaba kawai TAIMIYYAH tayi tana faman taɓe baki,zuciyanta na wani irin bugu da bata san dalili
ba.Sam ko da wasa ita bata son wani ya shigo rayuwanta,wanin ma wai da sunan soyayyah.Kuma
bama gurgu irin ta ba,sam bata ji hakan abu ne me yiwuwa ma.Anty Laurat ne ta cinmata tana gab
da shiga Sasan Iyah,suka ƙarisa jerawa tare tana faman zuzutawa TAIMIYYAH haɗuwan Naseer
ɗin,tare da bata shawaran don Allah ta bashi dama aga iya gudun ruwansa.Idan har da soyayyan
gaskiya yazo ita kam bata ga aibunsa ba, sai ma haɗuwansa.Har da cewa TAIMIYYAN bata ga
yadda za su yi matching da juna bane ita da Naseer ɗin.Ita dai TAIMIYYAN jin Anty Laurat ɗin
kawai take yi,ko da suka shiga ciki TAIMIYYAH wucewanta tai ɗaki tabar Laurat da Iyah a
falo,ita a dole haushin Iyan take ji da ta sanya ta fita wajen Naseer ɗin.
Tana daga ɗaki amma tana jiyo Anty Laurat ɗin nawa Iyah zancen Naseer ɗin.TAIMIYYAH ta
cika tai fam! Wani haushi na kamata,ta rasa meyasa ake son jajibu mata zancen aure tana zamanta
lafiya.Wayanta ta janyo tayi saurin ɗauka ta kashe ta gaba ɗaya,don gudun karma ta manta ta bar
ta a kunne ya samu halin kira don bazata ɗauka ba.Sai kawai ta nufi wajen da take aje littafan
islamiyanta ta ɗauki wani littafi tana dubawa,sai da taji fitan Anty Laurat sannan ta fito ta nufi
kitchen tana sake ɗebo furan ɗazu ta zuba madara tayo ɗakinta.Bata sake bi takan Iyah da ke
zaman jiran ta fito tace mata wani abu game da baƙon ta ba,tana gama shan furan ta nufi toilet ta
wanko baki,tare da ɗauro alwala ta fito tai shirin bacci tabi lafiyan gado........✍🏻
Littafin TAIMIYYAH paid book ne da zai zo akan 500 naira only,ga masu buƙatan yin payment
zakui min magana ta wannan number ɗin 08167768704, ko kuma ku turo kuɗin ku kai tsaye ta
wannan account ɗin 0504192664 aisha ibrahim dansabo GTbank.*
_Masu account da Arewa books,zaku dinga siyan sabbin shafuka dalla-dalla akan farashi me
sauƙi,ga yadda zaku siya pages a arewa books kamar haka_ 👇🏻
https://arewabooks.com/chapter?id=62d29e11aa5f8f19bc9621cb
*Balance* - Zai nuna kudin account dinku da zaku iya sayayyan littafai cikin kasuwar
ArewaBooks.
*Credit/Debit Card* - Hanyar farko kuma mai dadi wajan Recharge din account dinku.
A inda (Enter your amount) za'a saka kudin da akeson Recharge din sai a taba "Proceed". Zaibude
muku inda zaku saka bayanan katin banki, kuna gamawa kudinku zaishiga account dinku kaitsaye
(instant).
--------
*Bank Transfer*
*Airtime Transfer*
Saidai su ba kaitsaye bane (instantly) sai ArewaBooks ta tabbatar da Transfer din, amman bayakai
1hour za'a gansa a Balance.
#Ɗansabo ce#
[12/14, 3:42 PM] +234 703 040 9541: *TAIMIYYAH*
*Page 24*
Ganin lokaci zai tafi sosai yasa TAIMIYYAH saurin sanya Hijab ɗinta kalan da ya shiga da kayan
jikinta.Lokacin data fito falon Iyah na zaune tana kalacin safe,da alamu yau ta makara karyawan
kenan.Don ita bata wuce takwas ba tayi karin safe ba.TAIMIYYAH ta isa wajen tana aje jakanta
daga gefe ta durƙusa har ƙasa tana faɗin "Iyah ina kwana,dafatan mun tashi lafiya?"
"Lafiya lau Zainaba." Cewan Iyah tana cigaba da shan Tea ɗinta.TAIMIYYAH na ganin yadda
Iyah ta amsa gaisuwanta a taƙaice, yasa ta gane fishi Iyah take da ita kenan.Sai kawai ta share Iyan
ta zauna tana duba abinda Ladi ta yi musu yau na karin safen.
Soyayyan dankalin turawa ne da egg,sai kunu da ruwan Tea da aka dafa da kayan qamshi.Hakan
yasa TAIMIYYAH zuba dankali da egg ɗin,memakon ta haɗa Tea ita sai ta zuba kunun,don ba ta
faye son Tea ba.Sam bata son madara a Tea,ko zata sha Tea sai dai ruwan Lipton da kayan
qamshi,ko kuma ta zuba Bounvita ko Milo kaɗai amma ba madara.Babu me magana a cikin su har
suka kammala karin.TAIMIYYAH ta miƙe tana shagwaɓe fuska ta dubi Iyah tana faɗin "Iyah bari
inje kila Sani na waje har ya iso,sai na dawo."
Iyah aka wani taɓe baki ana faɗin "A dawo lafiya." TAIMIYYAH ta saki murmushi me faɗi tana
dafa ƙafanta ta fara takawa don fita daga falon.
A waje sukai kaciɓus da Ladi TAIMIYYAH ta gaishe ta tana mata sai ta dawo.Ladi ta amsa da
fara'a tana ma TAIMIYYYAH fatan dawowa lafiya.
Tun daga nesa TAIMIYYAH ta hangi Sani zaune tare da Baba mai-gadi.Ta cigaba da takawa a
hankali har ta isa bakin gate ɗin,ta gaisar da su suka amsa a lakoci guda.Tana shirin fita daga gate
ɗin ta jiyo muryan Anty Laurat na ƙwalla mata kira.Sai tai tsaye tana jiran ƙarisowan Laurat ɗin,
"Anty Laurat gud morning." Cewan TAIMIYYAH da murmushi saman fuskanta a lokacin da
Laurat ɗin ta ƙariso wajen.Anty Laurat sai ta aikawa TAIMIYYAH da harara tana faɗin "Ban
amsawa wallahi,yanxu TAIMIYYAH don rashin kirki jiya kashe wayanki kika yi duk roƙon da
bawan Allahn nan ya yi akan ki barta a kunne? Ni yanzu ya kirani yana min ƙorafi wai har yanzu
ma ya yi ta neman line ɗin naki a kashe.Shine fa nace masa bari inzo inga ko lafiya,haba
TAIMIYYAH ya da haka please?" Anty Laurat ta kai ƙarshen maganan idanunta akan
TAIMIYYAH da ta wani narke fuska.Kafin tayi magana cike da shagwaɓa tana faɗin "Anty ni fa
bansan me zance masa bane idan ya kira.Shiyasa na kashe wayan kuma dama ni bana kwana da
waya a kunne."
"Kin kyauta to,yanzu sai ki kunna tun da gashi ya damu ya na son yai magana da ke.Please! ki
kunna wayan kafin ku isa skull ɗin,ni bari in koma dama shi ya fito dani,da yake jiya ya amsa
numberta kafin ya wuce.Sai kin dawo bye." Cewan Laurat tana juyawa ta koma inda ta fito,ta bar
TAIMIYYAH na taɓe baki ta juya ta fara takawa don fita daga gate ɗin.Tuni Sani ya fita har ya
tada motan shiyasa tana isa bakin motan ta buɗe gidan baya ta shiga.Sani ya ja motan suna barin
layin,ko kaɗan kuma TAIMIYYAH ba ta yi tunanin zata iya kunna wayan ba kaman yadda Anty
Laurat ɗin ta roƙo.
__________
Suhailah ce zaune ita da qawarta ko ince aminiyarta Zubaida.A cikin falon gidan da ke sama a nan
su kai masauki.
An cika gaban Zubyn da kayan motsa baki,wacce a kallon farko za kaiwa Zubyn ka san cewa irin
ƴan duniyan matannan ne masu buɗewan ido.Baƙace ɗik sai dai tana da matsakaicin kyau,da kuma
dirin jiki me kyau.
Suhailah ta aje cup ɗin hannunta data shanye lemun Chivita,tana faɗin "Zuby yanzu kina ganin
idan Maleek ya jaji bo aure ban gama shiga uku na lalace ba kuwa? Ina cikin matsanancin tashin
hankali Zuby.Burina a yanzu bai wuce in samu ciki ba.Amma ga abinda likita ke faɗi wai
haihuwan ma zan iya rasa ta baki ɗaya.Zuby nayi nadaman fara shan magungunan hana ɗaukan
ciki.Kece duk kika bani wannan gurgun shawaran,ga shi ina shirin shiga masifan da bansan ta
yadda zan iya tinkiransa ba.Ko kaɗan bana hango wasa a idanun Maleek,da gaske yake yi akan
son haihuwa zai iya auro wata macen.Ba tare da yayi la'akari da halin da zan iya shiga ba, ki sanar
da ni miye mafita yanzu?"
Yadda Suhailan tayi maganan hankali a tashe,yasa Zuby aje cup ɗin hannunta da ta cika da lemu ta
shanye.Ta miƙa hannu ta dafa kafaɗan Suhailah tana faɗin "Calm down babbar Yarinya! Nifa ban
ga wani abin ɗaga hankali har haka ba.Ki bari ku je can Egypt ɗin kiji me likitocin can zasu
faɗi.Kuma maganan ya ƙaro aure to sai me tunda ba a kan ki kishiyar za ta zauna ba.Kuma in
banda abinki idan ya auro wata ai tamkar ya auro ta don samun cikar burinsa na samun haihuwa
ne kaɗai.Ba wai don zai yi mata soyayya irin yake miki bane,kinga ashe soyayyar dai tana gareki
ne.Ni abinda nake so da ke ki koyi iya kissa da zaman duniya Suhailah.Ki zama mace me wayo da
iya janyo hankalin miji,ki kwantar da kai ki dinga masa duk abinda ya ke so.Amma ko kaɗan ki
daina nuna damuwanki akan abinda ki ka aikata,domin ba zamu dawo da hannun agogo baya
ba.Ki nuna masa ko auren zai yi za ki goyi bayansa,in yaso idan matar ta haifa masa ɗan sai kiyi
kissan yadda riƙon ɗan zai dawo hannunki.Kin ga zaki ƙarisa janyo hankalinsa kanki ke
ɗaya.Daga shi har Hajjah ki nuna musu kin amshi ƙaddara ko da ance ba za ki haihu ba kin amince
Maleek ɗin ya sake wani auren."
Zuby ta kai ƙarshen maganan tana wani kashewa Suhailah idanu,wacce ita kuma jikinta gaba ɗaya
yai wani irin sanyi da kalaman Zubaidan.Wani sashi na zuciyanta na gaya mata tabi shawaran
aminiyan nata,sai dai tsananin soyayar da take wa Maleek da kishinsa me zafi da take yi.Bata ji
zata iya gani tana raye ya auro wata mace har ta iya dannewa ta nuna rashin damuwanta.Ta tabbar
idan har zanen ƙaddara ya zanawa Maleek ƙarin auren wata mace bayan ita.To tabbas za'ai bikin
tana gadon asibiti ne a kwance.
Suhailah ta dubi Zubyn cikin ido kafin ta soma faɗin "Zuby baki zo da shawaran da zan iya ɗauka
ba a wannan karon.Domin har yau kin kasa gane wani irin zafin kishi na ke dashi akan Maleek
ba.Taya kike iya tunanin zan iya rintse ido in kalli wata mace,a matsayin kishiyata har ta haifa
masa ƴaƴa ba ni ba?Ba zan iya ba Zuby idan ko har na iya to ki tabbatar da zan kwanta ciwon da
zai iya zama ajali na! Ina ma Maleek wani irin so me wuyan bari, sannan baki san waye Maleek a
iya kula da mace bane musamman a shinfiɗa.Tabbas da sam ba zaki kalli idanuna ki bani
shawaran wai in goya masa baya ba." Yadda Suhailah ta kai ƙarshen maganan hawaye na cika
idanunta,yasa Zuby taɓe baki tana jifanta da wani irin kallo.Can ƙasan zuciyanta kishi da takaicin
Suhailan ne kwance sosai,amma ganin Suhailah ta zubo mata ido yasa ta sakin murmushi tana
faɗin "Suhailah shiyasa na ke faɗi miki kanki baya ja har yanzu.Sunan kinyi boko ne kawai amma
sam baki da buɗewan ido,irin na matan zamani da suka san kan duniya.Baki san miye kissa da iya
zaman duniya ba,yanzu fa kike tambayan mafita amma na kawo miki mafitan da zata anfane
ki,kina kawo min zancen kishi da wani so.Ubanwa ya gaya miki dama akwai macen da aka taɓa
mata kishiya da son ranta? Babu wannan macen duk wacce kika ga anyi mawa bata so aka
yi.Amma hakan baya hana matan da suka iya bariki kwantar da kai har su cika burikansu ba tare
da an gano haƙiƙanin manufan da ke zukatansu ba.Kin riga kin aikata abinda ya janyo miki
illa,kina tunanin da Maleek ya ƙaro aure da rashin yardan ki,ba gwara ya ƙaro da yardan ki ba? Ko
banza idan kishiyan ta shigo za ta shigo ne don kawai ta haifa masa ɗa,ba wai don zai yi mata so
irin wanda ke ya ke miki ba.Daga lokacin da zata haifa masa ɗan,ke kuma a lokacin zaki sake
kwantar da kai a baki riƙon ɗan.Kin ga babu me zargin ki sai ma tausayin ki da zai kama zuciyan
Hajjah har ta goya miki baya wajen a baki riƙon ɗan.Daga kuma lokacin da ɗan yazo hannunki
kece zaki raine sa irin yadda kike da burin ya taso.Amma yanzu idan kika bari kishi ya rufe
idanunki har ƙaddara ta zana masa auren wata kina nuna zafin kishi da shirme to zaki ɓata goma
ne ɗaya bai gyaru miki ba.Sannan idan baki aje son jiki da sakaci kin kama mijinki da kyau ba duk
wacce za ta shigo cikin ruwan sanyi za ta gama da zuciyan mijinki.Ta kuma samar da abinda ke
kika kasa samarwa.Yanzu ki bani lambansa zan taya ki bashi haƙury akan cewa kinyi nadaman
abinda kika aikata,sannan zan sanar da shi laifi nane duka domin nice na baki shawara ba tare da
mun san hakan zai iya janyo kowace irin illa ba.Ke kuma da zaran ya diro gari ina so yaga canji,ki
tarairaye shi da kyau tare da samar masa dukkanin nutsuwa.Ko a fuska kada ki sake ki nuna masa
cewa abinda likita ya faɗi yana damunki.Nuna masa za kiyi kin barwa Allah komi,ina fata kin
fahimce ni?"
Zubaida ta ƙare maganan da jefawa Suhailah tambaya.Wacce ta zubawa Zubyn idanu kaman me
son gano gaskiyan dukkanin kalaman Zubyn akan fuskanta.Ta gyaɗa kai kafin ta buɗe baki tana
faɗin "Na gane Zuby gaskiya kin fini sanin kan duniya,kuma kanki yafi nawa ja.Tabbas hakan za a
yi har Hajjah bazan sake nuna mata damuwa ta ba.Zamu bi su a duk yadda suke so.Koda auren zai
ƙaro akwai plan ɗin mu a ƙasa.Idan kuma Allah yayi ikonsa na samu cikin ma kin ga shikenan
komi yazo cikin sauƙi.Amma fa zanyi yaƙi me girma kafin in iya duk waɗannan abubuwan da
kika zano." Suhailah tayi maganan murya a maraice,Zuby da har wani ajiyan zuciyan samun
nasara ta saki,tayi saurin kamo hannun Suhailah tana faɗin "Karki ji komi za ki iya Suhailah sai
dai baki sakawa zuciyanki cewa zaki iyan ba.Yanzu dai bani lambar ranshi ya daɗe ɗin,da zaran na
isa gida zan zauna in tsara masa kalaman da zai gamsu da shi.Ai indai muna tare kisa wa ranki
baki da sauran wani matsala.Irin wannan daula da kike ciki kina fantamawa,yaushe zan miki fatan
wani abu ya raba ki da Maleek ɗin ki.Gashi kuma kina sakar mana muna dangwala ta ina zamu
bari wani abu ya shige gabanki da zai baki matsala?Ki sawa ranki duk wacce za ta shigo to tamkar
za ta zo bautan haihuwa ne ke kuma kina amshe ƴaƴan,kin ga kenan ke ce da riba ba ita ba.Aikin
ki kawai ki cigaba da gyara kanki da jikinki,kina samar da nutsuwa a zuciyansa.Wata kuma tana
aikin ɗaukan ciki tana haifewa,komi nata na yin ƙasa ke kuma na ki yana gyaruwa hhhhh.....!" Ta
kai ƙarshen maganan tana bushewa da wani irin dariya na ƴan duniya,ita kuma sakarya Suhailah
na tayata,lokacin da take karantowa Zuby numbern Maleek ɗin,har wani rawa zuciyan Zubyn ke
yi wani abu na kewaye zuciyanta.Tana gama kwashe numbern tsaf tai saving da suna *My
M.Ado* Suhailah sam bata san ko da wani suna qawar nata dake a matsyin bazawara tai saving
numbern mijinta ba.Zuby ta cigaba da tsarawa Suhailah kalamai son ranta,bata bar gidan ba sai
data tabbatar Suhailah ta hau kan duk wani gadan zare da take ɗaura ta akai.Sannan Suhailan ta
haɗa mata sha tara na arziƙi cike da leda ta raka ta har bakin gate.Sukai sallama tana ji a zuciyanta
bata da aminiya me sonta irin Zubaida Halliru.
Koda ta dawo cikin gida kai tsaye wayanta ta ɗauka ta shiga neman layin Maleek ɗin,amma har
wayan yai ringing ya katse bai ɗauka ba.Hakan yasa Suhailah aje wayan tana gyara kwanciyanta
cikin seater ɗin.Ƙwaƙwalwanta na tariyo mata dukkanin yadda sukai da Zubyn da shawarwarin da
ta bata.Ta lumshe ido tana fata kada ma Allah ya jarabceta da rashin samun haihuwan,bare har
Maleek ɗin ya auro wata mace bayan ita.Sai dai can ƙasan ranta na gaya mata in kuma abinda bata
so ɗin ya kasance to tabbas yadda duk Zubaidan ta tsara mata haka za ta bi...........✍🏻
_Ni dai Ɗansabo cewa na yi anya Suhailah na da man kai kuwa? 😁 amma bari dai mu cigaba da
bibiyan su don ganin yadda wasan zai kaya._
Littafin TAIMIYYAH paid book ne da zai zo akan 500 naira only,ga masu buƙatan yin payment
zakui min magana ta wannan number ɗin 08167768704, ko kuma ku turo kuɗin ku kai tsaye ta
wannan account ɗin 0504192664 aisha ibrahim dansabo GTbank.*
_Masu account da Arewa books,zaku dinga siyan sabbin shafuka dalla-dalla akan farashi me
sauƙi,ga yadda zaku siya pages a arewa books kamar haka_ 👇🏻
https://arewabooks.com/chapter?id=62d29e11aa5f8f19bc9621cb
*Balance* - Zai nuna kudin account dinku da zaku iya sayayyan littafai cikin kasuwar
ArewaBooks.
*Credit/Debit Card* - Hanyar farko kuma mai dadi wajan Recharge din account dinku.
A inda (Enter your amount) za'a saka kudin da akeson Recharge din sai a taba "Proceed". Zaibude
muku inda zaku saka bayanan katin banki, kuna gamawa kudinku zaishiga account dinku kaitsaye
(instant).
--------
*Bank Transfer*
*Airtime Transfer*
Saidai su ba kaitsaye bane (instantly) sai ArewaBooks ta tabbatar da Transfer din, amman bayakai
1hour za'a gansa a Balance.
#Ɗansabo ce#
[12/14, 3:42 PM] +234 703 040 9541: *TAIMIYYAH*
*Page 25*
_______Lokacin dasu TAIMIYYAH suka fito wajen bakin gate,tun daga nesa idanunta ke hango
mata mutum tsaye jingine da jikin mota,ya harɗe hannuwansa a ƙirji tare da kafowa ƙofar fitowa
gate ɗin wajen idanu.
A cikin daƙiƙa kaɗan ƙwaƙwalwanta ya bata tabbacin cewa Naseer ne.Domin kallo ɗaya taiwa
fuskansa ta gano hakan,don kamanninsa ne data gani a daren jiya kwance akan fuskar sa.Tayi
saurin furta "Ya Allah!" A bayyane lokacin da ya fara takowa yana kusanto su.Zee tayi saurin
duban TAIMIYYAH tana faɗin "Lafiya Namcy?" Sai dai kafin TAIMIYYAH taba Zee amsa har ya
ƙariso wajen da sukai tsaye.Hakan yasa TAIMIYYAH ta gagara bai wa Zee amsa,sai kawai ma ta
dafe ƙafanta ta fara tafiya don barin wajen.Hakan yasa Nass da ya ƙariso daf da Zee ɗin ya saki
murmushi yana faɗin "Salamu Alaikum!" Zee ta ɗaga idanunta ta sauke a kansa tana amsa
sallaman da ya yi,kafin ya ɗaura da faɗin "Qawar mu ko zaki taimakeni mu je ki taya ni rarraso
waccar qawan taki please?"
Yadda yai maganan cike da magiya yasa Zee sakin murmushi kaɗan tana faɗin "Eh mu je
badamuwa." Daga haka suka rufawa TAIMIYYAH baya wacce har ta kai bakin titi, tana tsaye
daga gefe guda.Ta jingina da jikin wani ƙarfe don jin daɗin tsayuwa sabida laluran
ƙafanta.Lokacin da su Zee suka iso wajen qamshin turarensa na AZZARO WANTED,ya fara sanar
mata da isowansu wajen.Sai ta yi saurin haɗe fuska cike da zunɓuro baki take duban Zee dake
faɗin "Haba Namcy ya da haka kuma? Zaki taho babu ko jira to ai gashinan na biyo ki,ga baƙo
nan kuma ki ji da shi please!"
Cikin murya me cike da shagwaɓa TAIMIYYAH ta kai dubanta kan Nass tana faɗin "Ina yini." Ya
saki kyakykywan murmushi yana jin wani irin relief! Daga jin muryanta kawai da yayi a
yanzu.Idanunsa a kanta sosai yake faɗin "Ba zan amsa ba Baby,sabida gaba ɗaya yau kin tashi
hankalina,kin kuma shiga hakkin zuciyata ta hanyar hana mata dukkanin sukuni.Har sai yanzu
dana bayyana a gaban ki sannan na samu nutsuwa,kin kyauta kenan eyim Luv?" Ya ƙare maganan
cikin wani irin salo daya saka Zee murmusawa tana duban yadda TAIMIYYAH ta wani kwaɓe
fuska kaman zata saki kuka,ita sai abin ma yaso bata dariya,amma ta maze tana kallon wannan
drama da ake bugawa.Shi ko Nass ganin TAIMIYYAN taƙi amsa shi sai ya ɗaura da faɗin "To
Baby tunda ba za ki magana ba mu ƙarisa ki shiga mota in sauke ki a gida please! Don ba zan so
wannan ranan ya cigaba da taɓa min ke ba.Please! qawarmu kisa baki ko ke zata miki magana."
Ya ƙare maganan yana maida dubansa kan Zee cike da magiya.Zee ta saki murmushi tana matsawa
kusa da TAIMIYYAH sosai,cikin ƙasa ƙasa da murya ta ke faɗin "Qawata ya da shariya haka
kuma,miye laifin wannan Handsome guy ɗin daya mato a kanki? Please mu ƙarisa in raka ki
kawai ki shiga ku wuce,kin ga mutane sai kallo mu mutane suke.Amma fa gaskiya kinyi Babban
kamu Namcy." Zee tayi maganan cike da tsokana,a karon farko da TAIMIYYAH ta ɗago manyan
idanunta masu tsananin haske ta saukewa Zee wani hararan daya sa Zee ɗin kwashewa da
dariya.Ta sake ƙasa da murya yadda Nass daya matsa gefe ya basu wuri ba zai ji ba,ta furta
"Wayyo Qawata wannan harara ai sai ki sa in suma,afuwan please karki gwalesa mu je ku wuce
please!"
"Amma Zee kin san ba mutunci bane aga mace a motar saurayi.Me zance idan wani a cikin ƴan
gidan mu yaga na sauka a motar sa?Duka fa ban san ko shi waye ba,a jiya ɗaya da haɗuwan mu
fa,kawai sai yau a ganni a motarsa gaskiya bazan iya ba.Ki je kawai ki san me zaki faɗi masa ya
kama gabansa." TAIMIYYAH tai wa Zee maganan cikin ƙasa da murya itama,kuma sosai Zee ɗin
ta fahimci me TAIMIYYAN ke nufi.Don ko ita bata ɗauki shiga motan saurayi a mutuncin ƴa
mace ba,har gara gara ma idan ansan da shi a gida,an kuma yar je masa ixinin zuwa zance,Zee ta
gyaɗa kai cike da gamsuwa tana faɗin "Na fahimce ki ina zuwa.Bari naje na san me zan sanar
masa."
Daga haka Zee ɗin ta nufi wajen Nass dake faman danna waya,ya ɗago yana duban Zee ɗin bayan
ya amsa sallaman da tayi masa,ya furta "Mu je ne ta amince Friend ɗin mu?"
Zee ta murmusa kaɗan tana faɗin "Ayyah! Abokin mu kayi haƙuri a she ta riga tayi da me kawo ta
cewa ya zo ɗaukanta.Kaga kuma babu daɗi a ga kaine ka sauke ta hakan zai iya zama abin yi mata
faɗa a gida.Kayi haƙury next time insha Allah ba zamu gwale ƙoƙarin ka ba."
"Alright! Babu damuwa,amma fa ba haka naso ba gaskiya.Kuma ina roƙon alfarma don Allah ki
rarrasar min ita kice ta kunna wayanta da zaran ta isa gida.Wallahi na azabtu haka nan a taimaka
min a kunna wayan." Cewan Nass cike da magiya idanunsa na kan TAIMIYYAH da tayi tsaye a
inda take ko da wasa bata waiwayo in da suke tsaye shi da Zee ba.Ya ɗauke idanunsa daga kanta
lokacin da Zee ɗin ke bashi tabbacin zata sanya TAIMIYYAH ta kunna wayan.Su kai sallama da
Zee ɗin ya juya zuwa wajen motar sa, ita kuma Zee ta nufi wajen TAIMIYYAH tana zayyane mata
yadda tayi da Nass ɗin.Ta ƙare maganan da faɗin "Don Allah Namcy ki bashi dama ki sauraresa ki
ji da wacce ya zo? Ni dai a haka yayi min wallahi kaman zaiyi hankali.Ga shi kyakykyawa ga iya
Dressing gaskiya gayen ya haɗu.Da alamu kuma masu gidan rana sun zauna masa.Ki dubi fa
motar da yake hawa gaskiya kun dace da juna, ki bada kai kawai qawata mu sha biki nan bada
jimawa ba."
TAIMIYYAH wannan karon ma harara ta aika wa Zee ɗin,tana faɗin "Wallahi baki da mutunci
wato in bada kai,lallai ne ni kam tsoron ma bashi dama nake yi don da alamu zai yi baƙin naci,da
takura ni kuma bani son hakan.Dadai ace ma yazo a me lalura irin tawa ne wataƙil dana bashi
space kaɗan in ga ko zan iya gwada ɗanɗana ya soyayyan ta ke.Amma wannan sai ina ga kaman
yafi ƙarfin me lalura iri na,gurguwa dani a ganni da wannan ke kinsan sai anyi da ni an kuma ga
zaƙewata da yawa."
TAIMIYYAN ta ƙare maganan cikin wani irin sanyin murya,me cike da rauni da ya motsa zuciyan
Zee sosai.Taji ƙarin ƙaunan TAIMIYYAN da tausayinta na sake kama ruhinta.Ta dubi
TAIMIYYAN da kulawa sosai take faɗin "Ayyah! Qawata don Allah ki daina irin wannan
maganan.Kada kiyi saɓo ko butulce ma ni'imomin da Allah yai miki,ke dai kawai ki bashi dama
Allah ya fimu sanin yadda ki ke,shi kuma ya san me yasa ya jefo miki shi cikin rayuwanki a
hakan.Kin ko ga yadda nake hango tsantsan ƙaunar ki cikin idanunsa kuwa? Gaskiya bana ji
wannan guy ɗin da wasa ya zo.Da alamu da gaske ya kamu da son ki Namcy.Ki cire duk wani
tunani mara kyau ki bashi dama ki kuma cigaba da Addu'a shi Ubangiji ya fimu sanin hikimansa
na barin ki a yadda kike,ki godewa Allah TAIMIYYAH naki laluran ma mai sauƙi ne,wanda suka
fiki nakasa ma Allah ya basu mijin aure bare ke da Ubangiji yai ma baiwan halitta me fisgan
hankali."
Zee bata bar TAIMIYYAH cewa komi ba,ta cigaba da faɗi mata kalamai na ƙarfafawa,da kawo
mata misalai na nakasassu kala kala.Wanda kuma sun yi aurensu a hakan ba kuma guragu suke
aure ba da yawan su.Har Zee ta tarewa TAIMIYYAN abin hawa ƙarfafata take yi akan ta daure
taba Naseer dama.TAIMIYYAH ta jinjina kai a lokacin da suka isa bakin Napep ɗin, ta shiga ta
zauna tana yiwa Zee godia,me Napep ɗin ya tashe mashin ɗinsa suka harba bisa titi.TAIMIYYAH
ta daɗe tana jin tasirin kalaman Zee na keta zuciyanta,har tana ji cewa za tai ƙoƙarin ganin ta fara
sauraran Nass ta ga da wacce ya zo? Sun iso layin su TAIMIYYAH na jinta a gajiye sosai.Ga
kanta dake ɗan mata ciwo sama sama,a haka ta fito tana zuge jaka ta baiwa Me Napep ɗin
kuɗinsa,ta juya tana nufan gate ɗin shiga gidan,ta ƙaramin ƙofa inda ake shiga ta nufa bayan ta
tsaya ta gaida Me gadi sai ta nufi hanyan isa Sasan su.Sam bata kula da Motar Guggo Bilki da
suka iso garin a yau ba,ta nufi cikin Sasan su bakinta ɗauke da sallama.Yasmeen budurwar ƴar
Guggo Bilki wacce za suyi sa'an juna da su TAIMIYYAN.Itace ta fito a guje tana wa
TAIMIYYAH sannu da xuwa.Da wani irin murna TAIMIYYAH ta washe baki tana duban
Yasmeen data ƙariso ta rungumeta take furta "Wash! Yasmeen sai ki yarda ni ai,kin ga yadda kika
narka uban ƙiba kuwa, sannunku da xuwa." Yasmeen ta saki TAIMIYYAH tana faɗin "Sannu Sis
TAIMY,kin ji yadda na ƙosa ki dawo kuwa,wayyo nayi missing zuwa Zaria irin sosai ɗinnan.Duk
na ƙagu mu iso in sanya ki cikin ido na."
"To ai gashi kin sanya ni a idanun naki,ni ma na yi kewanki My Headache.Yanzu shikenan bani da
sauran hutu sabida sani magana da zaki dinga yi." TAIMIYYAH tayi magana tana sakin dariya
ganin yadda Yasmeen ta cuskune fuska,su ka ƙarisa falon Iyah da sallama idanun TAIMIYYAH na
sauka akan Guggo Bilki.Ta ƙarisa gareta tana faɗawa jikinta tana faɗin "Oyoyo Guggo na sannu
da zuwa." Guggo Bilkisu ta rungume TAIMIYYAH tana faɗin "Oyoyo! ɗiyata sannunki da
dawowa,kin ga yadda kika koma wata baturiya,me Iya wai take baki ne kullum kike sake zama
wata kaman baturiya?" Iyah dake kallon su murmushi yaƙi barin fuskarta sabida murnan zuwan
tilon ƴarta mace sai cewa tayi "Babu abinda nake bata ni,tsabar dai kwanciyan hankali ne da hutu
da take ciki yasa take ƙara kyau da cika kullum.Amma ja'iran a hakan bata ko so ayi zancen kauda
ita,ki duba min yadda kullum take ƙara wani cika ƙirji kaman ya fashe,amma wai bata son zancen
aure." Guggo da Yasmeen ne suka kwashe da dariyan zancen Iyah,hakan yasa TAIMIYYAH
kwaɓe fuska kaman zata saki kuka take faɗin "Kai Iya! Kai Iya! Ni wallahi kinsa min ido da yawa
a gidannan,kawai ki fito fili kice kin fara gajiya dani ko kin daina sona." TAIMIYYAH ta ƙare
maganan tana tashi daga jikin Guggo Bilki.Iyah ta aika mata harara tana faɗin "Kya dai ji da
shi,ba ɗaya cikin duk abinda kika lissafa,zancen aure ne dai sai anyi miki har sai kinyi zuciya kin
tsayar da mijin,ja'ira kawai shagwaɓaɓɓa."
TAIMIYYAH ta miƙe fuu...! dafe da ƙafanta ta fara takawa ta nufi ɗaki.Tana jiyo su Yasmeen na
mata dariya kafin Yasmeen ɗin ta biyo bayanta zuwa ɗakinta.Ta tadda TAIMIYYAH na cire kayan
jikinta zata shiga toilet watsa ruwa,xama tayi daga bakin Bed tana faɗin "Haka kike kwasan
Drama da tsohuwar can Sisi?" TAIMIYYAH ta sake kwaɓe fuska tana faɗin "Rabu da Iyah kawai
ke dai Yasmeen,wallahi ta saka min ido komi maganan aure,ita ko tsoran a wulaƙanta mata ni bata
yi.Ni gurguwa ina naga ta wani xancen aure in ba irina zan aura ba." Yasmeen ta zabga ma
TAIMIYYAH harara tana faɗin "Bismillah! Zaki fara ƙonan rai ba,da anyi maganan aure ki fara
kiran kanki gurguwa.Ke kaza da kaza,to wallahi wannan karon zamu hau sama in baki daina min
banzan zance irin haka ba.Allah sa ke kika fi ko wace mace gurgunta sai mun aurar dake sai dai
mijin bai zo ba."
Yasmeen ta ƙare maganan tana sake tsuke fuska.TAIMIYYAH sanin halin Yasmeen na ɗaukan zafi
yasa ta sakin murmushi tana faɗawa toilet abin ta,tafi kowa sanin Yasmeen ta tsani tana kiran
kanta gurguwa.Shiyasa basa shiri dasu Zuhurah sosai,sabida yadda suke kiran TAIMIYYAH
gurguwa,hakan yasa in dai Yasmeen tazo hutu basa ma yin duk iskancin da suke wa
TAIMIYYAN.Don sosai Yasmeen ke gwaɓa musu ba daɗi su ma,don haka nema basu damu
Yasmeen ɗin ta zo garin ba.A cewan su bata ƙaunar su yadda take ƙaunar TAIMIYYAH,ita kaɗai
take so.
Lokacin da TAIMIYYAH ta fito daga wanka,har lokacin Yasmeen na ɗakin.Tayi kwance akan
gadon TAIMIYYAN,tana faman kallon hotunan girke-girke kala kala acikin wayan
TAIMIYYAH.Da yake ita ba gwanar sanyawa waya code bane don gani take ita kaɗai take
rayuwanta a sasan Iyah.Bata da me zuwa yace zai dinga mata taɓe taɓe a wayan,shiyasa sam bata
sanya ma wayan Code ba.Ta wuce wajen kayanta direct tana ciro doguwar Riga mara nauyi na
shan iska ta saka,ta juyo kenan don yiwa Yasmeen magana wayanta dake hannun Yasmeen ya fara
kuka.Sai Yasmeen ɗin ta tashi daga kwance ta zauna tana miƙowa TAIMIYYAH data iso bakin
gadon wayan tana faɗin "Ungo wani number ne ke kira." TAIMIYYAH ba tayi magana ba ta amsa
wayan tana receiving ta kai wayan kunni bakinta ɗauke da sallama.Daga ɓangaren Nass har wani
ɓoyayyen ajiyan zuciya ya sauke lokacin da sassanyar muryar TAIMIYYAH ta isa ga
kunnuwansa.Ya lumshe ido yana faɗin "Ranki ya daɗe ina fata banyi gaggawan kira ba,na kasa
samun nutsuwan zuciya ne hope kun isa gida lafiya?"
TAIMIYYAH data kai zaune a bakin gadonta,ta ɗan lumshe ido da taɓe baki tana faɗin "Lafiya
lau,amma yanzu abinci zan ci, in babu damuwa later sai mu yi magana please!"
Naseer daga ɓangarensa,ji yayi ina ma suna kusa ne yana kallon yadda ƙaramin bakinta ke furta
kalaman.Ya sauke ajiyan zuciya yana faɗin "To Baby zan barki kici abinci,amma sai kinyi promise
ɗin cewa kina kammalawa zaki min ko da flashing ne saina kira.Inba haka ba kici abincin ina tare
da ke ni bazan gaji ba,sai na dinga sauraran yanayin taunan Babyna.Hakan ya wadatar da ni."
Yadda yayi maganan cikin wani irin salo na jan hankalin me sauraransa,yasa TAIMIYYAH rufe
ido kaɗan tana jinjina rigima da wayo irin na Nass ɗin.Aahankali tayi magana cikin low voice
ɗinta take faɗin "I will call u insha Allah bye!" Daga haka tayi cuting call ɗin tana maida wayan
Silent,ta aje bisa Bed tana miƙewa ta bar ɗakin,tuni dama Yasmeen ta fita ta bata waje tunda ta
fara amsa wayan,hakan kuma ba ƙaramin daɗi yaiwa TAIMIYYAN ba.Wajen cin abinci Direct ta
nufa ta samu Yasmeen ta zuba tana ci itama,da alamu tun da suka iso bata kula taci abincin bane
sai yanzu.TAIMIYYAH tayi joining ɗin Yasmeen suna cin abincin tare, har su ka cinye wanda
Yasmeen ɗin ta ɗiba.Suka ƙara wani suna ci jefi jefi suna taɓa hiran yaushe gamo har suka
kammala cin abincin,su ka tattarro zuwa cikin falon Iyah,inda Guggo Bilki da Iyah suka buɗe
babin hira.......✍🏻
Littafin TAIMIYYAH paid book ne da zai zo akan 500 naira only,ga masu buƙatan yin payment
zakui min magana ta wannan number ɗin 08167768704, ko kuma ku turo kuɗin ku kai tsaye ta
wannan account ɗin 0504192664 aisha ibrahim dansabo GTbank.*
_Masu account da Arewa books,zaku dinga siyan sabbin shafuka dalla-dalla akan farashi me
sauƙi,ga yadda zaku siya pages a arewa books kamar haka_ 👇🏻
https://arewabooks.com/chapter?id=62d29e11aa5f8f19bc9621cb
*Balance* - Zai nuna kudin account dinku da zaku iya sayayyan littafai cikin kasuwar
ArewaBooks.
*Credit/Debit Card* - Hanyar farko kuma mai dadi wajan Recharge din account dinku.
A inda (Enter your amount) za'a saka kudin da akeson Recharge din sai a taba "Proceed". Zaibude
muku inda zaku saka bayanan katin banki, kuna gamawa kudinku zaishiga account dinku kaitsaye
(instant).
--------
*Bank Transfer*
*Airtime Transfer*
Saidai su ba kaitsaye bane (instantly) sai ArewaBooks ta tabbatar da Transfer din, amman bayakai
1hour za'a gansa a Balance.
#Ɗansabo ce#
[12/14, 3:42 PM] +234 703 040 9541: *TAIMIYYAH*
*Page 26*
_______Misalin takwas da rabi na dare Yasmeen ta ja TAIMIYYAH suka nufi can Sasan Baba
Sani.TAIMIYYAH na sanye da Riga doguwa irin na material da ke zuwa Ready made
ɗinnan,ɗinkin Boubou akai masa da yai mata kyau sosai ya fito da cikar ƙirjinta daga sama.
Yasmeen ita ma doguwar Rigan ne a jikinta na Atamfa.Ta yane kanta da ƙaramin Veil,saɓanin
TAIMIYYAH da ke sanye da ƙaramin Hijab.kowannen su hannunsa riƙe da wayansa,su na tafe
suna hiran su gunin ban sha'awa har suka shiga cikin Sasan.Da sallama su ka isa bakin ƙofar shiga
Main-Parlor ɗin su Umman,su Zuhurah dake zaune suna kallo suka haɗa baki wajen amsa
sallaman,tare da bada izinin shiga.
Yasmeen ita ce a farko sai TAIMIYYAH biye da bayanta,suka kutsa kai cikin falon.Basma ce ta
nufo Yasmeen tana faɗin "Oyoyo Yah Yasmeeni,saukan yaushe haka tsidim?" Yasmeen tai
Hugging ɗin Basman tana faɗin "Saukan tun ɗazu da rana mana,tunda kun daina zuwa Sasan
waccar Old Woman ɗin taya zaku san isowan mu."
"Kai Yasmeen haka ma zaki ce?" Cewan Zuhurah tana isowa tare da yin Hugging Yasmeen ɗin
itama,su a dole ga turawa lol.Yasmeen ta furta "Yes haka zan ce mana Sis ƙarya nayi,ba su daina
zuwan bane?" Yasmeen ta yi maganan tana maida duban ta kan TAIMIYYAH,wacce gaba ɗaya
hankalinta na kan kallon da su Zuhurah ke yi.Sanin da ita Yasmeen ɗin take yi yasa ta juyo ta saki
smile kawai ba tare da tace komi ba.Anty Laurat ce ta fito daga ɗakin Umma,ganin su
TAIMIYYAH yasa ta ƙariso da fara'anta idanunta akan TAIMIYYAH ta ke faɗin "Wow! Tawan ke
ce anan yau?"
"Kai! Anty Laurat sai kace irin na daina shigowa kwata-kwata ɗinnan." Cewan TAIMIYYAH tana
duban Anty Laurat ɗin dake jifanta da murmushi,kafin Anty Laurat ta juya wajen Yasmeen suna
gaisawa da juna.
Fitowan Umma daga ɗaki yasa duk hankalinsu ya koma kanta.Yasmeen da TAIMIYYAH suka
gaida Umman ta amsa da sakin fuska,tana duban Yasmeen take faɗin "Yasmeen saukan yaushe a
gari?" Yasmeen ta amsa da cewa "Ɗazu muka iso Umma har da Mamie muke tare ai.Ta gaji ne
shiyasa ba ta shigo ba ina ga sai zuwa da safe."
"Allah sarki to sannun ku da zuwa,ai bansan da zuwan ku ba da an ƙara yawan abincin dare
ai,amma laifin Iya ne da sai ta aiko ko Ayuba tace ya faɗi."
Yasmeen ta ɗan taɓe baki kaɗan tana faɗin "Laah! Bakomi fa Umma abinci ya isa sosai,tunda ga
wanda Ladi ta yi ma duk ya wadata har gashi can ma ba'a cinye wani ba."
Daga haka sai Yasmeen suka maida kai wajen hiransu da su Zuhurah.Ita dai TAIMIYYAH ba ta
sanya baki hankalinta na kan kallo ita da Anty Laurat.
Umma kuma tashi tayi itama ta basu waje.Ta koma can ƙaramin falon dake kusa da Dining Area
ɗinsu tai zamanta,tana faman danna waya abin ta.
Wayan hannun TAIMIYYAH ne ya fara haske alamun shigowan kira.Da yake a silent ta saka
wayan tun ɗazu da rana bayan gama wayanta da Nass,kaman yadda tai masa alqawarin kiransa
bayan ta gama cin abinci.Shine ta kira shi sai ya kashe ya kira ta,ya kuma daɗe ya na sake bayyana
mata sirrin zuciyansa.
A cikin hiran da yai matan ne take jin ashe shi ɗin ɗan cikin gari ne.Gidan iyayensa na nan a
Ƙwarbai can gaban Fadan Mai Martaba Sarkin Zazzau.Ya sanar da ita cewa shi ne Auta wajen
Mamansa,ya kuma sanar mata ya kammala karatun Degree ɗinsa har zuwa Masters a ƙasar
Dubai.Yanzu haka yana aiki da NNRA(Nigerian Nuclear Regulatory Authority.) Reshen su da ke
Abuja.Don ma TAIMIYYAH ta katse hanzarinsa da taga zai dameta,ba don haka ba da hira sosai
zai mata a ɗazu ɗin.Ta sauke ajiyan zuciya a hankali,lokacin da kiran ya yanke ba tare da ta ɗaga
ba.Sai dai wani kiran ne ke sake shigowa,hakan yasa TAIMIYYAH ta zubama Screen ɗin ido, bata
da alamun zata amsa kiran.Saukar muryan Anty Laurat taji cikin kunnuwanta tamkar daga
sama,tana faɗin "TAIMIYYAH kiyi picking call ɗinki mana ha'a." TAIMIYYAH ta zunɓuro baki
kaɗan cike da shagwaɓanta na sabo take faɗin "Anty ɗazu fa muka gama waya,miye kuma na kira
yanzu please!"
"And so what? Na ji min sakarci irin na ƴan fari,wallahi TAIMIYYAH so kike aji kanmu akan
wannan Nass ɗin.Dama ɗazu a chart ya kawo min ƙaran kin yanke masa waya alhali shi bai gama
jin muryanki ba.Oya pick the call my Friend."
Anty Laurat tayi maganan tana zubawa TAIMIYYAH harara.Gaba ɗaya sai TAIMIYYAH ta sake
kwaɓe fuska, ganin yadda duk attension ɗin Zuhurah ya dawo kanta.Ga kuma wayan nata dake
cigaba da Blinking alamun kira ne ke ta shigowa yana yankewa,sai kawai tayi receiving call ɗin
tana kai wayan kunni.
Da shagwaɓaɓɓiyar muryanta take faɗin "Hello!" Sam ita bata san yadda salonta ke kassara
zuciyan Nass ɗin bane.Watakila data rage narke masa murya da shagwaɓa haka,koda yake da
alamu ita bata ma san tana yi ba.Tunda yin shagwaɓa sabonta ne kowa ya santa da shi,wasu har
cewa suke duk laifin Iya ne ita ce ta ɓata TAIMIYYAN.
Nass daga ɓangarensa ya sake gyara kwanciya bisa lallausar Bed ɗinsa.Har wani lumshe idanu
yayi tasirin muryan da shagwaɓar na zagayawa har tsakiyan kwanyansa.Wani irin zazzafar
soyayyan TAIMIYYAN yake ji tamkar ana sake kunna zuciyansa da jan hankalinsa zuwa gareta
ne,abin har ya fara bashi tsoro don bai taɓa jin son mace kaman yadda ya ke ji akan TAIMIYYAN
ba.Duk da cewa ya taɓa soyayya da wata Muneerah suka rabu,amma sam bai ji yadda yake ji irin
haka ba sai daya haɗu da TAIMIYYAN, "My luv shi ne sai kin ja aji kafin ki amsa kiran
nawa.Allah sarki bawan Allah Nass ina shan wahala da wannan Babyn tawa,ina ga sai nazo gaban
Anty Laurat na zubda hawaye,sannan zata sake ƙoƙarin ganin ta kafa gwamnatina a zuciyanki ko
Baby?" Cewan Naseer ɗin shi ma cikin shagwaɓe tasa muryan,salon daya wanzar da
kyakykyawan murmushi saman fuskan TAIMIYYAN.Ta yi magana cikin ƙasa da muryanta sosai
take faɗin "No bama sai hakan ya faru ba,ina yini." ta kai ƙarshen kalamin da gaisar da shi,ya
amsa cikin salon barkwancinsa yana kwaikwayon muryanta,hakan ya sake sanya TAIMIYYAH
sakin murmushi sosai,har Beauty point ɗinta na lotsawa.
Naseer ya cigaba da janta da hira yana sake mata bayanin yadda ya ƙagu yai aure,don ya gama
kammala gininsa a sabuwar GRA ɗin Zaria yanzu,wata anguwa da ake cewa Gonan Ganye.Tuni
har lefe duk ya kammala haɗawa sai abinda ba'a rasa ba,don haka dama shi matar yake jira sai
kuma ga TAIMIYYAN Allah ya haɗasu.
Ita dai TAIMIYYAH jinsa kawai take yi tana ganin komi kaman a film.Wai itace yau take waya da
saurayi da sunan yana son ta,har yana maganan suyi aure? Saurayin ma kuma ba gurgu irin ta
ba.Muryan Nass ɗin ya katse zaren tunaninta lokacin da ya ke faɗin "Baby please allow me to call
u Vid Call please!" TAIMIYYAH tayi saurin girgiza kai kaman yana ganinta,kafin ta narke murya
tana faɗin "No please! Bani kaɗai bace fa ina cikin mutane ne,kuma ma ni bana jin zan iya Vid
Call."
"Meyasa Baby?" Cewan Nass a ƙagauce,amma sai TAIMIYYAH tai shiru bata ce komi ba har sai
daya sake nanata tambayansa,kafin ta furta "Bakomi kawai bana ra'ayi ne shiyasa."
"Gaskiya Baby dole ko ki canza wannan ra'ayin indai muna tare.Yanzu to ki amince inzo har gida
in sake ganin kyakykyawan face ɗin Baby na please!" Nass yayi maganan cike da magiya,hakan
yasa TAIMIYYAN satan kallon Anty Laurat,amma a maimakon idanunta su sauka akan Anty
Laurat ɗin,sai idanunta suka sauka akan fuskokin su Zuhurah da Basmah.Waɗanda gaba ɗaya
attension ɗinsu ya koma kan TAIMIYYAN baki ɗaya.Abinda yasa TAIMIYYAH tayi saurin ɗauke
kanta daga dubansu,tana zagayawa da idanunta ko zata ga Anty Laurat ɗin,amma wayam! Babu ita
da alamu ta bar cikin falon,ba tare da ita TAIMIYYAN ta ankara ba.Ganin hakan sai kawai
TAIMIYYAH ta miƙe tana dafa ƙafanta ta fara tafiya,tana faɗin "Please kar kace haka,bazan iya
fitowa ba koka zo.Sabida na gaya maka ina da baƙuwa,kuma mun jima bamu haɗuba so muna
buƙatan time.Gashi ma sai cinye mana lokacin hira ka ke." TAIMIYYAH ta kai ƙarshen maganan
cike da narke murya,wanda bata san irin tasirin da muryanta ke yi a zuciyan Nass ɗin ba.
Daga can ɓangaren Nass ɗin sake lafe wayan yayi a kunni yana ji tamkar da bata kai aya ba.Don
bai gaji da jin wannan sweet voice ɗin nata ba.
Amma sai ya daure shima cike da salon narke mata murya yake faɗin "To naji Baby amma idan
kina so karna zo,don Allah ki yadda in ga face ɗinki ta Vid call please! Hakan kaɗai zai samar da
nutsuwa a zuciyata har inji zan iya fasa zuwan,please kar kice no Baby!" Yadda ya kai ƙarshen
maganan cike da magiya yasa TAIMIYYAH sauke numfashi a hankali,tana jinjina kalan rigima
irin na Nass ɗin da shegen wayansa.Don ta gama gane duk ta inda ta ɓullo masa yasan shima ta
yadda zaibi tai masa abinda yake so.
Hakanan ba don tana so ba ta amince ya kira vid call ɗin,tana daga zaune bisa wani table da ke
nesa kaɗan da cikin falon.
Tai receiving vid call ɗin tana gyara zaman Hijab ɗin jikinta.Bata wani bari ya jima yana magana
ba tai hanging up! Duk kunya na rufeta sabida rashin sabo,su ko su Zuhurah gaba ɗaya sun rasa
nutsuwa.Hankalinsu gaba ɗaya na kan TAIMIYYAH duk da cewa ta basu waje,amma hakan baisa
hankalinsu ya bar kan TAIMIYYAN ba.Ita Zuhurah tsaban mamakin yadda TAIMIYYAN take
wani shagwaɓa da narke murya take yi,wani kishi da haushi na kasheta.Don a ganinta salon daya
kamata ace ita ta iyane TAIMIYYAN keyi,amma da yake ita buɗaɗɗen murya take da shi sam
muryan nata baya yin irin na TAIMIYYAN.Ita ko Basmah tsabagen takaicin yadda har
TAIMIYYAN da take a gurguwanta ta samu saurayi,ita ko babu wanda ya taɓa cewa yana sonta
shine takaicin da yasa ta kasa ɗauke idanunta daga kan TAIMIYYAN. Har TAIMIYYAH ta gama
amsa call ɗin hankalinsu na kanta, Yasmeen dai na zaune tana kuma ankare da yadda suke bin
TAIMIYYAN da kallo.Wani dariya na cinta a rai amma tana dannewa,har TAIMIYYAH ta dawo
cikin falon ta zauna mamaki bai daina kashe Zuhurah ba.Zaman TAIMIYYAN keda wuya Anty
Zuhurah ta dawo cikin falon,wayane kare a kunninta da alamu tana amsa call ne.
Ta nufi wajen TAIMIYYAH kanta tsaye tana faɗin "TAIMIYYAH ga Amore ɗina zaku gaisa."
TAIMIYYAH tw miƙa hannu ta amshi wayan tana kaiwa kunni,cikin sanyin muryarta me cike da
nutsuwa take gaida saurayin Anty Laurat ɗin,ya amsa da kulawa yana tambayarta ya Zarian? Ai
yana nan zuwa kawo wa gimbiyar tasa ziyara shima yaga gari.TAIMIYYAH dai murmushi tayi
kawai tana furta "To shikenan Allah ya kawo ka lafiya." Daga haka ta miƙa ma Laurat ɗin
wayan,tana maida duban ta kan Yasmeen da hankalinta a yanzu yake kan chart.Ta furta "Yasmeen
mu je ko,na fara jin bacci kinsan halina da saurin bacci gashi har gobe Friday ma sai mun je
skull."
Yasmeen ta miƙe tana faɗin "Okey muje ai an gaisa,saura kuma gobe kar in ga ƙeyan ku a Sasan
Iya anzo min hira." Yasmeen ta ƙare maganan idanunta akan Zuhurah tana aika mata
harara.Zuhurah ta saki murmushi tana faɗin "Haba waneni ai dole ma in shigo,kada ki zauneni da
waɗannan ɗuwaiwukan naki.wai ni Yasmeen yaushe kikai wannan ƙiban haka ne?" Zuhurah tayi
maganan cike da iskanci,hakan yasa Yasmeen dalla mata harara kafin ta furta "Ban sani ba ƴar
rainin wayo,sai kace kema ba ƙiban kika narka ba.TAIMIYYAH ce kawai ta fimu jiki me kyau,ita
ba lukuta can ba kuma babu siranta a tare da ita,ko'ina dai a cike da kayan alatu kaman zasuyi
magana.Wallahi nafi son irin wannan jikin amma ya zanyi tunda jikin ƙiban aka bani." Yasmeen
tayi maganan tana wani watsa hannuwa alamun yata iya ɗinnan....Zuhurah sai baki ya mutu ƙus!
Jin an yabi TAIMIYYAH.Ta wani taɓe baki tana faɗin "Sai da safe jeki abinki saina shigo
goben,in rigimamiyar tsohuwar can ba ta koroni ba,tace na zo taɓa ƴar gwal."
Tuni TAIMIYYAH ta jima da yin gaba abinta.Tana jiran Yasmeen ɗin daga bakin ƙof,amma tana
jin duk abinda suke faɗi.Yasmeen ɗince ta baiwa Zuhuran amsa dai-dai da ita tana faɗin"Eh kam
kinsan zata iya kuwa,don yadda take jin TAIMIYYAH a ranta ai ina ga tafi gwal.Sai dai lu'u
lu'u,kai gud night ɗinku kunji." Daga haka ta nufo wajen TAIMIYYAH suna jerawa da juna suka
fito daga Sasan,suka nufi Sasan Iyah.
Ita Anty Laurat na can suna shan soyayyah da saurayinta ta waya.Sam bata san ma
suTAIMIYYAN sun tafi ba,sai bayan sun ɗan jima da fita ne ta fito falon ta ga wayam! Sai ta
zauna tana maida hankalinta kan TV itama.Zuhurah ce tai zaraf tana duban Anty Laurat ɗin take
faɗin "Anty wai ni kam mutumiyanki babban kamu tayi haka,take zuba wannan uban shagwaɓan
da iyayi a waya? Nifa mamaki ya gama kasheni ɗazu da take waya.Wanene shi ko wannan da yake
biye mata haka?"
Zuhurah tayi tambayan bil hakki idanunta akan Anty Laurat.Wacce ta saki dariyan rainin hankali,
kafin ta dubi Zuhuran cikin ido tana faɗin "Wani Handsome ta samu in gaya miki Daughter.Don
ba kiga haɗuwansa ba,komi yaji gashi ɗan gaye da yasan kan miye iya saka sutura a jika.Kuma ba
ƙaramin matowa akanta gayen yayi ba,sai kinga yadda yake roƙona da safe akan inje in duba miya
hana ta kunna waya.Ai nasha gaya muku ku bar ganinta gurguwa kuna rainata a haka,wallahi
TAIMIYYAH matar manya ce.Domin yarinyan ta mallaki Qaulities ma su yawa a tattare da ita."
Anty Laurat takai ƙarshen maganan tana ji kaman ta saki shewa.Ganin yadda annurin kan fuskan
su Zuhurah da Basmah ya ɗauke,cikin zallan nuna kishi da hassada Zuhurah ke faɗin "Hmm! Anty
amma ke kina ganin ba wani abu ya kawo sa gareta ba?Maza yanzu da suka zama duk ƴan iska.In
kin bibiya wallahi kyawunta da dirin jikinta ya janyo hankalinsa kanta,yana gama mata wayo ya
amshi abinda yake so zai yi gaba abinsa.Ahaf! Nawa akayi kuma wani Guy ne irin wannan zai
wani liƙewa gurguwa musaka,sai dai idan da manufan da ya kawos......"
"Keh! Daughter ki iya bakinki,bana son wannan baƙin halin na ku.Shikenan don tana gurguwa sai
akace bazata yi haɗaɗɗen saurayi ba? Ko kuwa ita ɗin ba mutum bace da Allah ba zai kawo mata
duk irin namijin da yaso ba?Nakasa aiba kasawa bace kune kuke na ku shirmen.Ki faɗi alkwairy
ko kiyi shiru mana haka Annabi yace,amma duk kun bi kun sanyawa baiwar Allah ido kuna
hasada da ita.To wallahi ku kula ni kam ba ruwana,don ni bazan biye muku ba ubanku zanci
wallahi akanta.Don banga abinda ta tare muku ba,kuka ɗauki karan tsana kuka ɗaura a kant....."
Maganan Anty Laurat ɗin ya katse ne lokacin da Umma ta bayyana a wajen.Fuskanta a haɗe babu
rahama take duban Laurat ɗin a fusace tana faɗin "A she ko kema zanci ubanki Laurat.Akan
waccar banzar musakan ne zaki tasa min ƴaƴa kina musu irin wannan tijaran,sai ka ce basu ne
jininki ba?Uban me kika haɗa da ita musakar da har zaki dinga zaƙewa a kanta? Dama kallonki
kawai nake yadda kike wani shige mata sai kace sa'ar ki sabida asara.To ahir ɗinki wallahi ki fita
idona ko ki tattara ki koma gida,indai zaki dinga matsa musu akan wata gurguwa can,aikin banza
kawai."
Umma ta ƙare maganan a fusace tana yin gaba ta wuce ɗakinta direct.Ranta a masifan ɓace yake
da yadda qanwar nata ke son TAIMIYYAH,har tafi damuwa da ita akan su Zuhurah.
Anty Laurat da ke can falo itama ranta ya gama ɓaci sosai.Hakan yasata tashi fuu...! ta bar
falon,zuwa ɗakin da ke kusa da nasu Zuhuran.A nan take sauka dama duk idan tazo ,duk da dai ta
jima ma bata zo garin ba sai wannan karon.Haka ta zauna daga bakin Bed tana dafe
kanta,zuciyanta na tsananin ƙuna da takaicin baƙin hali irin na yayar ta.
Suko su Zuhurah dariya suka sheƙe da shi bayan shigewan Anty Laurat ɗin.Basmah na faɗin "Ke
kiji ƙarfin hali gun Anty dai,ta wani zaƙe sai zuba take akan wata musaka.Waya sani ma ko ita ke
cusa kan nata wajen Guy ɗin,shi kuma yana biye mata don yaji daɗin kwasan banza yaga Body.Ni
inyi saurayin mana Yah Zuhurah." Basmah ta ƙare maganan suna sake bushewa da dariya,Zuhurah
na faɗin "Hmm! Ai zamu zuba ido mu ga waye Guy ɗin,badai yanzu ga Yasmeen tazo ba kwantar
da kai zamu yi,mu riƙa zuwa Sasan da sunan hira daga nan zamu gano komi ai,har ma muci
nasaran ganinsa idan ya zo."
"Very gud idea,Yah Zuhurah hakan ko za'ayi wallahi." Cewan Basmah daga haka suka mai da kai
akan wayoyinsu kowacce na chart da friends ɗinta na online.....✍🏻
Littafin TAIMIYYAH paid book ne da zai zo akan 500 naira only,ga masu buƙatan yin payment
zakui min magana ta wannan number ɗin 08167768704, ko kuma ku turo kuɗin ku kai tsaye ta
wannan account ɗin 0504192664 aisha ibrahim dansabo GTbank.*
_Masu account da Arewa books,zaku dinga siyan sabbin shafuka dalla-dalla akan farashi me
sauƙi,ga yadda zaku siya pages a arewa books kamar haka_ 👇🏻
https://arewabooks.com/chapter?id=62d29e11aa5f8f19bc9621cb
*Balance* - Zai nuna kudin account dinku da zaku iya sayayyan littafai cikin kasuwar
ArewaBooks.
*Credit/Debit Card* - Hanyar farko kuma mai dadi wajan Recharge din account dinku.
A inda (Enter your amount) za'a saka kudin da akeson Recharge din sai a taba "Proceed". Zaibude
muku inda zaku saka bayanan katin banki, kuna gamawa kudinku zaishiga account dinku kaitsaye
(instant).
--------
*Bank Transfer*
*Airtime Transfer*
Saidai su ba kaitsaye bane (instantly) sai ArewaBooks ta tabbatar da Transfer din, amman bayakai
1hour za'a gansa a Balance.
#Ɗansabo ce#
[12/14, 3:42 PM] +234 703 040 9541: *TAIMIYYAH*
*Page 27*
________________
*Lagos,Nigeria.*
*8:35pm*
Kwance yake bisa kafaren gadonsa da ke cikin haɗaɗɗan Bedroom ɗin,wanda komi na cikinsa
kalan White and Blue ne.
Daga gefen bedside na gadon Mug ɗin ruwan Coffee ne na tiriri.Hannunsa riƙe da wayansa da
yake faman duba saƙonnin da suka cika inbox ɗinsa ta Gmail,wanda rabin saƙonnin daga friends
ɗinsa ne, da ke taya shi murnan wannan sabon muƙami da ya samu,wanda aka rantsar da shi satin
da ya wuce a Abuja.
Yana sanye ne cikin fararen Pajamas da suka haska farar fatarsa sosai.
Ya ɗaga kai ya dubi babban agogon da ke manne jikin bangon ɗakin,kafin ya kai hannu ya ɗauki
ɗaya wayansa dake aje daga gefensa.
Ya shiga dialing wata number,tsayin seconds ya ɗauka kafin ayi picking call ɗin.Ya fara magana
cikin harshen nasara, inda ya ɗauki tsayin a ƙalla mintuna biyar kafin yayi hanging up!Yana maida
wayan ya aje inda ya ɗakko.
Sai dai yana ajewa kiran Suhailah ta vid call na shigowa, ta ɗaya wayan nasa.
Ya tsurawa screen ɗin wayan idanu, yana tuna saƙon aminiyarta da ya shigo masa a ɗazu.
Kaman bazai ɗaga kiran ba sai kuma ya ɗaga.Idanunsa ya zuba mata,lokacin da fuskanta ya
bayyana a allon screen ɗin wayansa.Ya wani lumshe ido yana amsa gaisuwan da take masa, kafin
ta ɗaura da faɗin "My Maleek wai yaushe zaka dawo ne? Kace 2 weeks kawai za ka yi gashi yau
har kwananka 15.Please dear come back i miss u so very much." Suhailah tai maganan tana faman
narke masa.Hakan yasa Maleek tsura mata ido,kafin ya ɗan ɓata fuska yana faɗin "U miss me, but
idan na dawo banda ciwan kai me kike bani Suhailah? Any way tomorrow tunda Friday ne, insha
Allah ina bisa hanya." Ya ƙare maganan yana kallon yadda murmushi ya bayyana a face
ɗinta.Cike kuma da shagwaɓa take sanar masa,da yadda tai missing nasa.
Daga ƙarshe tai masa albishir ɗin dawowa ya samu babban tarba daga gareta.
Lokacin da suka gama wayan,gyara kwanciya Maleek yayi yana me lumshe idanunsa.Zuciyansa
na sake tuno masa da saƙon da Zuby ta turo masa,sai ya buɗe idanunsa yana janyo wayansa ya
sake shiga ɓangaren adana saƙonnin.Ya buɗo saƙon yana sake bitan karanta shi, kaman me son
haddace dukkanin kalaman dake rubuce cikin saƙon.
Wani irin takaici da mamakin halin sakarci irin na Suhailah,na sake kama shi.Ko kaɗan yasan ita
Suhailah ba za ta taɓa tunanin cewa,wannan qawar nata za ta iya shirya mata dukkanin abinda ta
rubuto masa ba.Sabida gaba ɗaya daga yadda ya karanta saƙon,da irin kalaman da Zubyn tayi
anfani da su,ya fahimci kome Suhailah ke yi da goyan bayan wannan qawartata take yi.
Ba tare da ƙaramin kwanyanta ya fahimtar da ita cewa wauta take aikawata ba.
Ya lumshe idanunsa a karon farko zuciyansa na kisima masa wasu tarin lamura masu girma da za
su iya biyo baya.
Mafarkinsa na jiya ya shiga kutsowa cikin kwanyansa,kaman a lokacin ya farka daga mafarkin da
yayin.
Idanun yarinyar masu wani irin haske na sake gilmawa ta cikin idanunsa.Kamar yadda sautin
kukan da take yi cikin mafarkin, ke dawo masa tamkar a yanzu ne yake jiyo sautin kukan.
Ya sake maida idanunsa ya lumshe kansa na sake kullewa.Da yadda duk mafarkin da ya ke yi da
yarinyar cikin baccinsa,bai taɓa ganin zahirin fuskanta ba.
Ya rasa meyasa a duk sanda yai mafarkin ya kan jima mafarkin bai bar zuciyansa ba.Abin har ya
fara zama sabo a gareshi,don baya kwana biyu baiyi mafarkin wannan yarinyar ba.Ko yace aljana!
Don bai taɓa ganin fuskanta ba sai idanu kawai.
Wani lokacin yakan ga tana miƙo masa hannuwanta,tana kuka.
Amma ba ya ganin fuskanta da gangar jikinta.Abinda yasa yafi yardarwa kansa cewa aljana ce!
Kila ba dai mutum ba.Gashi kuma ya kasa gayawa kowa yawan mafarkin da ya ke yi da
yarinyar.Sai Hajjah kawai da ya taɓa mata zancen a kwanakin baya.
Ganin zai matsawa kansa da tunani,yasa ya tashi ya nufi mamakeken toilet ɗinsa.Bai jima a ciki ba
ya fito yana komawa ya zauna akan Sofa,yana ɗaura ƙafa ɗaya kan ɗaya ya kunna TV don kallon
labarai.
______________
*Zaria.*
Yau da yake ranan ya kasance Friday ne,tun ƙarfe sha biyu na rana TAIMIYYAH ta dawo daga
skull.
Wanka ta sake yi sabida yadda ake zabga zafi.Shiyasa take tunanin,watakila zuwa anjima a samu
saukan ruwan sama.Don an kwana biyu ba'ayi ruwa a Zarian ba.
Lokacin data fito daga wankan,sai ta nufi wajen kayanta tana zaro wata riga mara nauyi ta saka.Ba
tare data maida lace ɗin da ta saka ta je skull da shi ba ɗazu.
Rigan english gown ne me asalin laushin jiki.Ya zauna ajikinta sosai kaman yadda kalan rigan da
ya zo a Coffee Brown ya haska farar fatarta.
Kanta bata ɗaura komi ba sai gashinta da ya ke a tsife baƙi siɗik! Wanda ta kama shi da babban
Ribbom.Fuskanta yayi fayau sabida bata shafa komi a kan face ɗinba.
Zama tayi daga bakin Bed ta ɗauki wayanta tana kiran layin Yasmeen.Wacce Iyah ta shaida mata
cewa sun fita da Guggo Bilki zuwa Rimi Fam House ɗinsu TAIMIYYAN.
So ta ke yi taiwa Yasmeen ɗin tsiya, don sunyi cewa za su jirata har ta dawo su tafi tare.Amma
gashi ta dawo ta tadda sun yi tafiyansu.
Sai dai har wayan ya gama ringing Yasmeen ba ta ɗaga ba.TAIMIYYAH ta saki ƙaramin tsaki
lokacin da take aje wayan daga gefe,ta miƙe dafe da ƙafanta ta fara takawa don barin ɗakin.
Kitchen ta nufa don samo abin sha kafin a gama girkin rana.Ladi ta samu tana ta faman haɗa
tsakin shinkafa da ta turara shi yai shar!Za ta mayar hawa na biyu bayan ta kammala zuba su
Zogale da Rama.
"Babah Ladi sannu da aiki,Yau Dambu ake haɗa mana ne, Allah sa dai za a yi wannan haɗin
Sauces ɗin?" Cewan TAIMIYYAH lokacin da take buɗe fridge ta ɗakko goran Hollondia Milk me
sanyi.
Babah Ladi ta saki murmushi idanunta akan TAIMIYYAH, da tayi mata kyau cikin rigan da ke
jikinta,ta furta "Aiko dai ƴar gida na sai dai idan ke ce za ki zo ki mana haɗin,don kinsan ban iya
sosai ba tunda ke ce ke yi dama."
TAIMIYYAH ta saki murmushi lokacin data zauna a saman wani kujeran roba da ke kitchen ɗin.
"To Babah Ladi bari mu gani in cikana ya ɗauki madarannan ko zan iya." TAIMIYYAH tayi
maganan tana kai kwalin Hollondian bakinta,ta fara sha a hankali.Sai data sha sosai ta aje tana
hamdala,ta dubi Babah Ladi tana faɗin "To Babah Ladi ko zaki taimako da Dankalin.Ina daga
zaune in fere shi da pillar."
Babah Ladi ta amsawa TAIMIYYAH da "Tuh!" Tana saurin nufan cikin store ta ɗebo Dankalin
Turawa, me ɗan yawa kaɗan cikin kwando,ta haɗo da kayan miya da zata taya TAIMIYYAN
gyarawa.
Suna aikin su suna hira sai gashi nan da nan TAIMIYYAH,ta kammala haɗa lafiyayyan sauces ɗin
Irish with Liver and Vegetables.Da za a ci Dambun shinkafan da shi,gaba ɗaya Kitchen ɗin ya
kaure da qamshin spices da akai anfani dashi.
Babah Ladi ke ta faman jerawa TAIMIYYAH sannu.Lokacin data ke tsane hannunta data wanke
da ƙaramin towel,ta amsa sannun cikin smile tana barin Kitchen ta nufi falo.
Tana isa falon Iyah na fitowa daga ɗakinta riƙe da carbi, da alamu har ta gabatar da sallan Zuhur
ita.
"Iyah sannu da fitowa,har kin yi sallah kenan? Nima bari in shiga daga ciki in yo tawa." Cewan
TAIMIYYAH tana wuce Iyah ta nufi ɗakinta don gabatar da sallan.
Lokacin data idar tana zaune tana addu'a,Yasmeen ta shigo ɗakin da sallama.Hakan yasa
TAIMIYYAH ɗaga idanunta ta sauke akan Yasmeen ɗin,kafin ta danna mata harara ,tana shafa
addu'an data yi take faɗin, "Kin kyauta har kun jirani ai." Yasmeen ta saki dariya tana faɗin,
"Sorry Zaynabu,wallahi laifin Mamie ne da tace kawai mu wuce,kin ga can ma na baro ta wai za
su wani anguwa da Anty Fati,ni keke napep na hawo ya maido gida"
TAIMIYYAH ta taɓe baki tana faɗin "To ai da kema an je da ke kawai unguwar baki dawo ki
dame ni ba." Yasmeen ta saki dariya tana faɗin "Ai ko yanzu kina iya maidani can,ƴar rainin
hankali kawai.Ina sha ba missn ɗina kika fara ba na ga har da min 2 misscall, irin indawo da wuri
ɗinnan." Yadda Yasmeen ta ƙare maganan da kashewa TAIMIYYAH idanu,yasa TAIMIYYAN
sakin dariya sosai tana faɗin "Wannan Babyn wallahi ƴar duniya ce ke."
Kafin Yasmeen tace komi kiran Nass ya shigo wayan TAIMIYYAH.Wannan kuma shine kira na
biyu a yau ɗin da yayi mata, don kafin ta fita skull ma sun yi waya da shi,ta wani narke face da
taɓe baki irin zai takura ta ɗinnan.
Ganin kiran zai yanke yasa ta ɗagawa da kai wayan kunni.Tana amsa sallamansa da sweet voice
ɗinta, da ke sake narkar da Zuciyar Nass ɗin.
"Baby hope kin dawo lafiya,ina fata dai ranan yau bai taɓa min ke ba?" Cewan Nass ɗin bayan ya
amsa gaisuwan da TAIMIYYAH tai masa.TAIMIYYAH ta wani narke murya tana faɗin, "No bai
taɓani sosai ba kam,cox around 12 ma na shigo gida." Yadda tai maganan tana wani shagwaɓa
yasa Yasmeen da ta zuba mata ido kwashewa da dariya.Murya can ƙasa ƙasa ta furta "Wow!
Shegiya luv ta fara aikinta wallahi,duk mutum ya gama cika baki wannan uwar shagwaɓan sace
zuciyan duk ta mecece?" Ta ƙare maganan tana sakin dariya cike da tsokana.Ita ko TAIMIYYAH
sai faman danno mata harara take,ba daman kulata tunda Nass ɗin yana mata magana.
Sun daɗe sosai da Nass ɗin suna waya.Yana faman zuba mata hira,da gaya mata kalamai na sace
zuciya.Daga ƙarshe sukai sallama akan cewa sai ya sake kira zuwa anjima.
TAIMIYYAH bayan ta sauke wayan daga kunni ne,ta dubi Yasmeen tana faɗin "Wallahi Yasmeen
kin shiga uku da sanya ido,in banda gulma ma miye na wani zama ki tasa ni gaba da kallo, har ki
ga me nake yi."
Yasmeen ta saki dariya tana faɗin "An zauna ɗin,nima course nake so inyi, kona samu in iya irin
wannan shagwaɓar da zan sake sace zuciyan Aliyu na."
Suka saki dariya a tare lokacin da Yasmeen ta kai ƙashen maganan,kafin su rankaya su fito zuwa
falon Iyah don yin Lunch.
Suna cin abincin ne suna hiran su kaɗan kaɗan.Sunyi nisa cikin cin abincin, Zuhurah da Anty
Laurat suka shigo ɗauke da abincin Iya.
Direct wajen cin abincin suka nufo suna aje kulolin abincin daga gaba kaɗan.TAIMIYYAH ta
ɗago manyan idanunta tana dubansu kafin ta furta, "Sannunku Anty Laurat."
Laurat ta saki murmushi tana faɗin "Yauwa sannu Besty,ashe kin dawo skull ɗin koda yake yau
Friday, na manta da wuri ku ke tashi." Ta ƙare maganan tana zama kusa da TAIMIYYAN.Ita ko
Zuhurah sai ta samu kusa da Yasmeen ta zauna suna magana, ba tare da tabi ta kan sannnun da
TAIMIYYAH tai musu ba.Yasmeen suka gaisa da Laurat,tana musu tayin cin Dambun da a kallo
ɗaya Laurat ta ji ya shiga ranta.Hakan yasa ba ta wani ɓata lokaci ba wajen ɗaukan spoon ta fara
ci,daɗin Dambun dana sauces ɗin da akai masa na ratsata.
Ita ko Zuhurah cewa tayi bata ci ,sabida ita ƴar gaye ce ba ta cin Dambu.Shiyasa ma ta baro wajen
cin abincin ta nufi cikin falo don gaida Iyah,wacce ke zaune ta kunna TV tana kallon tashar Saudi
Sunnah.
Da sakin fuska ta amsa gaisuwar jikanyan nata tana faɗin "Yau an ga daman shigowa gaida ni
kenan,ya uwar ta ku?"
"Lafiya lau Iyah,ai dama ke ɗin ce baki son muna shigowa.Sai kice wai muna hantaran
TAIMIYYAH,kaman wasu yara ai yanzu an girma Iyah."
Cewan Zuhurah tana hararan Iyah ƙasa ƙasa.Iyah dake kallonta kar! Ta aika mata daƙuwa tana
faɗin "Ungu nan mutumiyar banza,kin harari Zuwairah ne ba Iyah ba.Kuma da kike faɗin kun
girma ina girman yake tunda baku fasa ci mata fuska da kiranta da gurguwaba,daɗin abin dai
kuma mata ne.Ina jiye muku randa Ubangiji zai nuna muku isar sa da ikonsa,shashashai kawai
marasa tunani.Inma banda sakarci ku taso tare gunin sha'awa, lokaci ɗaya don uwar ku na muku
huɗuban tsiya,sai ku biye tata ku watsar da haɗin kan da kuka ta so da shi.A ce Sadeeq ne kawai
me hankali a cikinku da bai biye ta uwar na ku, tunda shi yasan abinda ya ke yi.To ku dai bi a
hankali ni gaskiya na ke faɗa muku,ku da kuke ganin ba'a jarabce ku da nakasanba ba wai kun fita
bane.Haka Allah yaga dama ya bar ku, itama kuma bawai baya son ta bane da ya mayar da ita
hakan.Ni dai ina muku nasiha da ku haɗa kai ku so juna kuyi zumunci a tsakanin ku,idan kuma
baku ji ba akwai ranan da za ku yi nadama yana zuwa."
Daga haka Iyah ta maida hankalinta kan TV. Bata sake bi takan Zuhurah da ke wani kumbure
kumburen fuska ba,daga ƙarshe ma ta koma can ƙarshen kujeran falon ta zauna tana danna waya.
Dawowan su TAIMIYYAH cikin falon yasa Zuhurah maida hankalinta wajen Yasmeen suna
hira.Ita kuma TAIMIYYAH suna hiran su da Anty Laurat, akan wani online class da zasu shiga, na
koyan yadda ake haɗa Graphics.
Su Zuhuran sun daɗe sosai a Sasan Iyah, don har Guggo Bilki ta dawo suna nan,sai da aka kira
la'asar sannan suka bar Sasan Iyah.
*Around,8:45Pm.*
Su TAIMIYYAH ne zaune gaba ɗayansu suna yin Dinner.Bayan ita da Yasmeen sun dawo daga
gaida Baba Sani,da ya dawo ɗazu da Magriba.
TAIMIYYAH ita ce tai sarving Iya da Guggo Bilki tuwan shinkafa miyan taushe.Wanda aka
wadata miyan da naman kan sa,da zallan tsokar kaza sai qamshi yake.
Bayan ta gama zuba ma su Iyah, ita sai ta zuba Rice and Stew da aka kawo daga Sasan Baba
Sani.Ta zabga uban haɗin Salad da ya rinjayi rabin shinkafar da ta zuba ɗin.
Yasmeen kuwa ita tuwan ta zuba tana ci,kaman su Iyah. TAIMIYYYAH kaɗai ce dama bata faye
son tuwan Rice ba sam!
Sunyi nisa cikin cin abincin,sallaman Yah Sadeeq daga can ƙofan shigowa falo ya katse musu ɗan
hiran da suke yi.Iyah ce ta ɗaga murya tana amsa masa sallaman, da bashi izinin shigowa.
Lokacin da ya iso cikin falon tuni qamshinsa na turaren BENTLEY ya gama isowa hancin
TAIMIYYAH.Ta ɗaga manyan idanunta tana kallonsa a lokacin da yake ƙarisowa har wajen da
suke cin abincin,ya samu wajen zama kusa da Guggo Bilki yana gaisheta.Ta amsa cike da kulawa
tana faɗin "Su Sadeeku an zama magidanci auren kawai ya rage,gaskiya ayi a fito min da suruka
haka nan." Ta ƙare maganan cike tsokana,shi ko Yah Sadeeq ɗin sai ya maida dubansa wajen da su
TAIMIYYAH ze zaune yana amsa gaisuwan Yasmeen,kafin ya baiwa ya mai da wa Guggo Bilki
martani da faɗin "Soon zan fito da ita Guggo Bilki ku dai kawai ku taya ni addu'a." Ya ƙare
maganan yana maida hankalinsa wajen Iya ya gaida ta,ta amsa da kulawa kafin muryan
TAIMIYYAH ya ratsa kunnuwansa tana faɗin "Yah Deeku sannu da zuwa ina yini." Sadeeq ya
ɗaura manyan idanunsa akanta yana faɗin "Lafiya lau Baby ya skull?" TAIMIYYAH ta dubesa
tana bashi amsa da "Lafiya lau Yah Deeku." Sai dai kafin Yah Deekun yace komi wayan
TAIMIYYAH ya fara haske alamun shigowan kira,sai tayi saurin duban screen ɗin wayan don
ganin waye me kiran? Idanunta suka sauka akan sunan da tai saving da NASS,sai kawai ta ɗauke
kai ta basar da kiran har ya yanke ba ta ɗaga ba.Lokacin da wani kiran ya shigo dai-dai da
sallaman Megadi ne daga bakin ƙofa,Yasmeen ta amsa sallaman Baba Megadin tana tambayansa
ko lafiya? Kansa tsaye ya furta "Ranki ya daɗe baƙon TAIMIYYAH ne ya iso yana waje,shine
yace don Allah na isar da saƙo ya kira bata ɗaga ba,a shigo da shi kaman wancan lokacin?" Iya
tayi karaf ta amsa da faɗin "Eh! Kace ya shigo sai ka aje musu kujeru kaman yadda ka yi wancan
karon." Tukur Megadi ya amsa da "Angama Hajiya." Daga haka ya bar wajen don zuwa ya aiwatar
da umurnin Iya,daga cikin falon Iyan kuwa Yah Sadeeq ne ya zubawa TAIMIYYAH idanu babu
ko ƙiftwa,zuciyansa na wani irin gudu da baisan dalili ba.Ita ko TAIMIYYAH tai ƙasa da kai
takaicin duniya na rufeta na yadda Nass zai zo bai sanar mata ba,bayan sunyi waya har sau uku a
yau ɗin,ta kasa kallon kowa sabida kunyan da ya mamayeta.Muryan Iya ne ya shiga kunnuwanta
inda take faɗin "Maza tashi ki je kinyi wani zaune kaman mara gaskiya,Yasmeen rakata ku je in
kun gaisa sai ki dawo ki ɗaukar masa ruwa da lemu." Iya tayi maganan cike da bada umurni,hakan
yasa daga Yasmeen har TAIMIYYAN suka miƙe simi simi Suka nufi hanyan ɗakin
TAIMIYYAN,Sadeeq ya bi bayan TAIMIYYAN da kallo tamkar idanunsa za su faɗo ƙasa,tuni
yaji wani irin duhu na mamaye zuciyansa,bai kuma cewa komi ba ya miƙewa ya bar falon.Daga
Iya har Guggo Bilki da tausayin Sadeeq ɗin ya kama su ka bi shi da ido,Iya na faman taɓe
baki.Guggo Bilki ta furta "Allah sarki! Da gaske Sadeeq soyayyar TAIMIYYAH ya yi masa kamu
me kyau,da alamu dannewa kawai yake don yasan hakan shine mafita tunda uwarsa ba ta
so,wallahi tausayi yake bani sosai Iya." Iya ta sake taɓe baki tana faɗin "Sai haƙury Bilkisu don ni
tausayinsa ba zai rufe min ido ayi abinda zai zo ya cuci baiwar Allah ina ji ina gani ba,don yadda
Zuwairah ke nunawa yarinyar ƙiyayyah tun tana ƙarama abin bana lafiya ba ne.To kin ga ina zan
yadda in ɗaure gindi ayi haɗin zumunci su haɗu da uwarsa da qannensa suna cusguna mata,o'o'oh!
Gara kowa Allah ya haɗa shi da dai-dai shi." Iya ta ƙare maganan tana tashi ma ta barwa Guggo
Bilki wajen,don ita sam bata ma son ana ɗakko maganan wai Sadeeq na son TAIMIYYAH.
Sanye da dogon Hijab TAIMIYYAH ta fito kalan Coffee da ya haske fuskarta.Ita kuma Yasmeen
ta yane kanta da babban Veil hannunta riƙe da wayanta,suka wuce Guggo Bilki suka nufi can
wajen Nass,wanda tuni ya jima da shigowa cikin Compound,yana zaune bisa ɗaya daga cikin
fararen roba guda biyu da Tukur ya aje,bayan ya sanya farin tebur daga tsakiya idan za'a iya aje
abin motsa baki akai.
Tunda su TAIMIYYAH suka fito daga Sasan Iya,idanun Nass ke kan TAIMIYYAN yana kallon
yadda suke jerowa da juna cikin nutsuwa,salon tafiyan TAIMIYYAN na motsa zuciyansa
matuƙa.Tare da jin ƙarin ƙaunar ta da tsa-tsan tausayinta na sake ratsa jinin jikinsa.........✍🏻
Littafin TAIMIYYAH paid book ne da zai zo akan 500 naira only,ga masu buƙatan yin payment
zakui min magana ta wannan number ɗin 08167768704, ko kuma ku turo kuɗin ku kai tsaye ta
wannan account ɗin 0504192664 aisha ibrahim dansabo GTbank.*
#Ɗansabo ce#
[12/14, 3:42 PM] +234 703 040 9541: *TAIMIYYAH*
*Page 28*
__________Lokacin da su TAIMIYYAH suka ƙariso wajen.Nass ne yayi saurin tashi yana janye
ɗaya kujeran baya TAIMIYYAH ta zauna,yana faɗin,
Yasmeen ta saki murmushi tana gaida Nass,ya amsa da sakin fuska sosai,sai lokacin TAIMIYAH
ta saci kallonsa.Yana sanye cikin wata Light Brown Wagan-bari,da ya yi masa matuƙar
kyau.Kansa sanye da hulan ƙube daya zauna akan sosai,sai qamshin AZZORO WANTED,ke tashi
a wajen.
Yasmeen komawa tayi cikin gida bayan sun gama da Nass ɗin,don kawo masa lemu da
ruwa,kaman yadda Iyah tace.
Har Yasmeen ta kusa isa bakin ƙofan shiga Sasan Iyah.ta jiyo muryan Yah Sadeeq na kiran
sunanta.
Hakan yasa ta waiwaya tana hangosa daga can wajen parking space na gidan.Yana tsaye ya
jingina da jikin motarsa,sai ta juya tana takawa zuwa wajen nasa.
Ta tsaya daga gefen damansa tana faɗin ,"Yah Sadeeq kaine anan,gani tuh."
Ya ɗaga manyan idanunsa da suka sauya launi.Yana kallon Yasmeen ɗin cikin ido yake faɗin,
Ya yi maganan cikin very low voice,daya sanya Yasmeen saurin dubansa.Ya aika mata harara yana
faɗin "Amsa zaki bani ko kallona zaki tsaya yi?"
"Kayi haƙury Yah Sadeeq,ni ma bansan yaushe ya fara zuwa ba,amma dai bana jin sun kai 2
weeks da haɗuwa."
Yasmeen tayi maganan tana gujewa sake duban fuskarsa.Shi kuma ya wani sauke numfashi a
hankali yana faɗin "Aright! go."
Daga haka bai sake cewa komi ba.Ya buɗe front seat na motansa ya zauna,yana me jingina jikinsa
da jikin seat ɗin sosai,tare da maida idanunsa ya lumshe.Zuciyansa na sake ɗaukan wani irin zafi
da suya,gaba ɗaya soyayyan TAIMIYYAH da yake ƙoƙarin adanawa ya binnesa can ƙasan
zuciyansa ne ya taso baki ɗaya.
Don a yanzu gaba ɗaya wani irin zazzafar soyayyarta haɗi da kishinta me tsananin zafi yake
ji.Irin wanda bai taɓa tunanin zai ji ba.
'Yaushe TAIMIYYAH ta fara soyayyah ba tare da ya sani ba.A ina ta haɗu da gayen kuma shin
tana son shi kenan,da har ta bashi daman zuwa wajenta taɗi?"
Waɗannan tarin tambayoyin ne suka haɗu suna amsa kuwwa! A tsakar kansa.Ba ya ji kuma zai iya
rintsarawa a daren yau ba tare da yaji amsa daga bakin TAIMIYYAH ba.
Yasmeen kuwa bayan ta baro wajen Yah Sadeeq ɗin.Tana tafe ne tana mamakin yadda duk ya wani
birkice daga ganin TAIMIYYAH da wani.Don ita ta ɗauka cewa tunda ya haƙura da TAIMIYYAN
idan ya ganta da wani bazai ji komi ba,har ta kai Sasan Iyah mamaki bai bar zuciyanta sukuni ba.
Direct kitchen ta nufa ta ɗauki madaidaicin Tray.Ta ɗaura ruwa biyu da Juice ɗin 5alive Babba
guda ɗaya,sai ta ɗauki Glass cup guda ɗaya ta ɗaura akai,sannan ta fito don zuwa ta kaima su
TAIMIYYAH.
Ko da ta kai ta aje TAIMIYYAH taso Yasmeen ɗin ta tsaya a wajen,amma fir Yasmeen taƙi tayi
komawanta Sasan Iyah.
Nass ya cigaba da zubawa TAIMIYYAH kalaman Luv masu ratsa zuciya.A lokacin ne kuma yake
sanar mata cewa gobe zai wuce Kd ne,daga can kuma ran Sunday ya wuce Abuja.
Dama hutu ya ɗauka na 2 weeks gashi kuma hutun ya ƙare.Dole Monday zai shiga office, ita dai
TAIMIYYAH jinsa kawai take tana amsa shi da eh! ko umm!
Ya ɗauki a ƙallah awa ɗaya da wasu mintuna kafin yai mata sallama don wucewa
gida.TAIMIYYAH ta miƙe tsaye tana ɗan dafa kujeran da ta tashi,idanunta a ƙasa take faɗin "To
Allah ya kiyaye ya tsare hanya agaida su Mama."
Yadda take magana cikin sanyi da wani irin narke murya,ba ƙaramin motsa zuciyan Nass yake
ba.Ya tsura mata ido yana sake ganin yadda kalan Hijab ɗin da ta sanya yai mata kyau matuƙa,ya
zura hannu cikin aljihu yana faɗin,
"Thank u Luv,za su ji insha Allah,sai dai please ki bar wayanki a kunne, ina isa gida zan kira muyi
gud night call, kafin inyi bacci kinji Baby Luv?" Ya ƙare maganan cikin narke murya,yana ji
kaman kada ya tafi ya bar wannan kyakykyawar halittar da ta gama sace zuciyansa.
Sai dai babu yadda ya iya haka ya aje mata kuɗin daya ciro daga aljihunsa,a saman Tray ɗin da
Yasmeen ta aje,yana faɗin "Baby gashi nan ba yawa ki sayi Recharge Card."
Duk iya magiyan da TAIMIYYAH tayi akan ya ɗauki kuɗinsa, sam bai saurareta ba.Tana ji tana
gani ya bar wajen ya nufi hanya isa gate,idanunta biye da bayansa tana kallon yanayin tafiyansa
abin birgewa.
Zama tayi bayan ta ga fitansa,tana tunanin yadda za ta yi da kuɗin daya aje.Daga ƙarshe haka ta
miƙe tana ɗaukan Tray ɗin da hannu ɗaya,ɗaya hannun na dafe da guiwan ƙafanta mara lafiyan,ta
fara takawa don komawa cikin gida.
Sai dai ko taku biyar bata yi ba qamshin turaren BENTLEY ya fara isowa hancinta.Tayi saurin
ɗaga manyan idanunta tana duban Yah Sadeeq daya ƙariso inda ta yi tsaye cak! Sai ta lumshe ido
tana ji tamkar ta saki Tray ɗin dake hannunta.
Don wani irin faɗuwan gaba ne ya ziyarce ta da bata san daliliba.Kafin tayi wani motsi sai
hannuwansa ta gani akan nata hannun da ke riƙe da Tray ɗin da ta ɗakko.Cikin wani disashshan
murya yake faɗin,
Daga haka yai gaba abinsa,hannunsa riƙe da Tray ɗin da ya amshe daga hannunta.Sai ya bar
TAIMIYYAH da bin bayansa da kallo,tana rasa yadda zata yi,don haka kawai take ji ba ta son
binsa.
Sabida ko bai faɗi ba ta san akan Nass ne zai titsiyeta ta faɗi masa lokacin da fara tsayawa zance
da shi.
Ganin ya dakata daga tafiyan tare da waiwayowa yana dubanta.Yasa TAIMIYYAH fara takawa
tana bin bayansa,har suka isa ɓangarensa,ya saka key ya buɗe ƙofan shiga falon nasa,yana ja baya
kaɗan tare da nuna mata hanya alamun ta shiga.TAIMIYYAH jiki a mace ta raɓa shi ta shige,ya
rufa mata baya hancinsa na shaqo sassayan qamshin da ke fita a jikinta,ya maida ƙofan ya rufe ba
tare da ya saka key ba.
Daga hannun kujeran da ke facing ƙofan shigowa falon nasa,TAIMIYYAH ta ɗan ɗosana
mazaunanta.
Kanta a ƙasa tana wasa da zoben azurfa dake yatsanta na hagu.Sam ta kasa kallonsa sai wani irin
bugawa zuciyarta keyi ba bu ƙaƙƙautawa,shi ko Yah Sadeeq kallo ɗaya yai mata ya gane ba ta
cikin nutsuwa.Hakan yasa shi sake haɗe fuska yana faɗin "Malama zama sosai za ki yi,ko nan ɗin
baƙon kine da zaki wani zauna a hannun kujera kaman na ce zan cinyeki?"
Ya kai ƙarshe maganan cikin masifan da baima san zai iya ma TAIMIYYAN ba.Abinda ya sake
tsorata TAIMIYYAH tayi saurin kallonsa,idanunta suka shige cikin nasa idanun,sai tayi saurin
ɗauke kanta hawaye na taruwa a idanunta.Ta gyara zama sosai a cikin seatern muryanta na rawa
take faɗin "Yah Deeku please! Bacci nake ji don Allah ka barni na koma gida." Wani harara da
Sadeeq ɗin ya jefa mata yasa TAIMIYYAH saurin kauda kanta daga dubansa.Ji take yi tamkar ta
saki kuka kawai ko zai barta. Amma memakon hakan sai gani tayi ya taso ya dawo kujeran da take
kai na 1 seater ga zauna.
Ƙirjinta ya buga da wani irin ƙarfi lokacin da taji hannuwansa duka a jikinta,ya ɗaga ta cak! Ya
zaunar saman hannun kujeran,shi kuma ya zauna daga ciki sosai yana crossing duka leg ɗinsa.
Hannuwansa riƙe da nata yana zuba mata manyan idanunsa.Da suka daɗe da canza launi ,sabida
azaban kishin Nass dake cin zuciyansa,yayi magana cikin wani murya very low,
"Zaynab sanar dani waye shi? A ina ku ka haɗu kuma yaushe har ki ka ba shi zuciyanki?"
Sadeeq ya watsawa TAIMIYYAH tambayan.har lokacin yana riƙe da hannunta bai saki ba,yanayin
da yai masifan ɗaga hankalin TAIMIYYAH da jefata cikin ruɗu.Don kusancin na su da juna yayi
yawa matuƙa.Kuma yau ɗin shine karon farko da hannuwan Sadeeq ɗin suka ratsa jikinta,shiyasa
gaba ɗaya ta firgice,daga zuciyanta har gangar jikinta rawa suke.
Matsanancin tsoro da fargaba ya hana ta duban idanunsa.Saima kuka da ta sakin masa da ƙaramin
sauti,cikin muryan kukan take faɗin,
"Yah Deeku please ka sakeni zan gaya maka koma me kake son ji please!"
Ta ƙare maganan tana kuka sosai,hakan yasa Sadeeq sake hannunta,yana zuba mata mayun
idanunsa,yake faɗin,
TAIMIYYAH ta sauke ajiyan zuciya,tare da sanar da shi komi.Tun daga randa Nass ɗin ya fara
zuwa gidan,har kawo wayan da su ke yi da yadda Iyah ta matsa sai ta fita,duk bata ɓoye masa
komi ba.Ta ƙare maganan da faɗin "Yah Deeku ni Allah ba ni ce na janyosa ba,kuma ina
sauraransa ne sabida bana so Iyah tai fishi dani.Baba kuma yaga kaman naƙi jin maganansa na
cewa infito da wani,amma ni sam babu ma Soyayyah a lissafina, sai karatu kaima kasani ai,amma
kayi haƙury in ranka ya ɓaci please!"
Yadda take bashi haƙury tana kuka ne ya sake karya zuciyan Sadeeq.Wani irin soyayyanta ya
motsa masa wanda har ya kasa controlling kansa,ya janyota jikinsa baki ɗaya ya
rungumeta.Abinda ya tsaida bugun zuciyan TAIMIYYAH cak! Jikinta ya ɗauki wani irin
rawa,kafin ta fashe masa da kuka lokacin da take jin kansa bisa kafaɗunta.Yana sauke wani irin
numfashi kaman wanda yayi gudu,gaba ɗaya qamshin turarensa ya gama cika kafofin
hancinta.Cikin muryan kuka take faɗin "Yah Sadeeq don Allah ka sakeni,kasan dai haramun ne
hakan da kayi ko? Pleas......" Maganan TAIMIYYAH ya maƙaleni ne lokacin da Sadeeq ya sake
shigar da ita jikinsa sosai,yana ƙoƙarin haɗe bakinsu waje ɗaya.Gaba ɗaya huɗuban da sheɗan ke
masa ne ke aiki,don burinsa bai wuce yayi duk abinda zai bashi relief ba.Sai dai kukan da
TAIMIYYAH ta saki me tsananin ƙarfi ne yasa shi janye fuskansa daga gareta,yana maida kansa
ya kwantar bisa kafaɗunta,dukkaninsu jikinsu rawa yakeyi bama kaman TAIMIYYAH, da ke ji
numfashinta na yin sama.
Cikin wani irin murya Sadeeq yake faɗin "Zaynab bansan ta yadda zan sanar dake nakasa cire
soyayyanki daga cikin zuciyata ba.Bansan cewa duk iya ƙoƙarin da nake na danne feeling ɗina
akanki shirme nakeyi ba,sai yau da dana ganki da wani namiji bani ba.Please! Zaynab mu ture duk
wani ƙiyayyan da Umma ke miki,ki amince in samu Baba Sani in gaya masa muna son
junanmu.Nayi miki alqawarin kare ki daga duk wani cutarwa ko tsangwama.Domin bazamu zauna
anan ba bare har Umma ta ganki tai miki abinda ranki zai ɓaci,please Zaynab ki amince dani
bazan iya kallo wani namiji ya aureki alhali ni zuciyata na azabtuwa da soyayyarki."
Sadeeq yayi maganan har lokacin TAIMIYYAH na jikinsa,yai mata wani irin runguma da ta kasa
kwacewa.Kuka kawai takeyi me tsuma zuciya,amma Yah Deekun da alamu sam hakan baya
damunsa.Cikin kuka take faɗin "Ka sakeni tuh sai muyi magana Yah Sadeeq please!"
Bai yi musu ba ya saketa tai baya tana zamewa ta sauka daga kujeran.Kaman yasan shirin da
takeyi na son ta gudu,sai yayi saurin riƙo hannunta yana tsareta da rinannun
idanunsa.TAIMIYYAH tayi saurin faɗin "Yah Sadeeq don girman Allah ka barni in tafi lokaci na
tafiya,zamuyi magana gobe nayi maka alqawari." TAIMIYYAH tayi maganan cike da
magiya,dukkanin jikinta rawa yake burinta bai wuce ta ganta a Sasan Iyah ba.
Kafin Sadeeq ɗin yace wani abu aka buɗo ƙofan shigowa falon nasa haɗe da yin sallama.Muryan
Zuhurah ce ta shigo kanta tsaye tana sauke idanunta akan su TAIMIYYAH.Ta wani waro ido
tsananin mamaki na cika zuciyanta,tuni TAIMIYYAH taji maranta yai wani irin ƙullewa,tana jin
lokacin da fitsari ya zuba cikin pant ɗinta.Tsabagen yadda ta ruɗe da ganin irin kallon da Zuhurah
ke jifanta dashi.Da ƙarfin gaske ta kwace hannunta daga nasa hawaye masu tsananin zafi na sake
ɓalle mata.Dukkanin jikinta babu inda baya rawa sabida tashin hankali,shiko Sadeeq rinannun
idanunsa ya ɗago ya sauke akan Zuhurah dake tsaye daga bakin ƙofan,ta zubo musu ido.
Yayi magana cikin ɓacin rai yana faɗin "Uban me kika zo yi,da zaki shigo min ɗaki ba tare da an
baki iziniba,sabida ke daƙiƙiyace ko?" Ya ƙare maganan da dakawa Zuhurah tsawan daya sake
ruɗa TAIMIYYAH ta sanya masa kuka.Zuhurah ko ta wani kyaɓe fuska tana faɗin "To ai Umma
ce tace inzo in kira mata kai,don ta kira wayanka har sau uku baka ɗaga ba."
"Get out! Stupid kawai,idan kinje kuma ki gaya mata cewa kinga wani abu,kiga idan ban
ɓaɓɓalaki ba!" Yah Sadeeq ɗin yayi magana a fusace idanunsa akan Zuhurah data juya da sassarfa
tana barin ɗakin.TAIMIYYAH da gaba ɗaya ta rasa inda zata sanya kanta,itama sai miƙewa tayi
tana saurin dafa ƙafatan zata fara tafiya,amma sai Yah Deekun yayi saurin isowa wajenta yana
kama hannunta.Ta ɗago manyan idanunta da hawaye suka kasa daina zuba,cikin muryan kuka take
faɗin "Kaga abin da ka janyo min ko Yah Deeku? Yanzu Allah ne kaɗai yasan abinda zata je ta
gayawa Umma,shikenan na shiga uk....." Hannun da Sadeeq yakai bakinta yana faɗin
"Shihhshhhh..!" Shiya katse TAIMIYYAH daga ƙarisa maganan data faro,cikin low voice yake
faɗin "Babu abinda zai faru Zaynab calm down please! Muje in rakaki,amma ki sani duk abinda
na faɗi da gaske nake yi.Bazan iya haƙura da soyayyarki ba Zaynab,don haka ki fara koyawa
zuciyanki yadda za ta so ni,ki kuma dakatar da wancan gayen bana son in sake ganin ku tare."
Yadda ya ƙare maganan cikin wani irin murya,ya tabbatarwa da TAIMIYYAH cewa duk abinda
yake faɗi da gaske yake yi,sam babu alamun wasa ko kaɗan.Ita dai TAIMIYYAH burinta kawai ta
ganta a Sasan Iyah shine kawai samun nutsuwanta,don haka sai kawai ta gyaɗa masa kai ba tare da
tayi magana ba.
Hannunta cikin nasa suka fito daga ɗakin nasa,kobi ta kan Tray ɗin lemu da ruwan TAIMIYYAH
bata yi ba,bare har ta tuna da wani kuɗin da Nass ɗin ya bata.Sai da Sadeeq ya ga shigan
TAIMIYYAH cikin Sasan Iyah,sannan ya juya yana nufan hanyan Sasan su,don amsa kiran
Ummansa.
TAIMIYYAH dake tafiya cikin wani irin slow motion,gaba ɗaya jikinta a sanyaye yake.Zuciyanta
na tsananin bugawa da tsoron abinda zai je ya dawo,don tasan tabbas sai Zuhurah ta sanar da
Umma cewa ta ganta a wajen Sadeeq.Ba kuma zata rage komi akan yadda idanuwanta ya gane
mata su sarƙe da hannun juna ba,har ta shiga cikin falon Iyah bakinta ɗauke da sallama,zuciyanta
babu nutsuwa sam.Da idanun Guggo Bilki ta fara cin karo lokacin data sanya kai cikin falon,sai
tayi saurin yin ƙasa da kanta tana takowa cikin falon.Tana shirin gota su ta wuce muryan Iyah
dake zaune tare da Guggo Bilkin ya shiga kunnuwan TAIMIYYAH ,Iyah na faɗin "Sai yanzu ne
ya tafi Naseerun?" TAIMIYYAH bata jiyo ba ta gyaɗa kai kawai tana yin gaba,domin bata son yin
magana bare Iyah ta gano akwai matsala.Daga Iyah har Guggo Bilki suka bi bayan TAIMIYYAH
da kallo,Iyah na faɗin "Anya lafiya Bilki,naga duk tayi wani sanyi ne gashi ta jima bata shigo ba."
Guggo Bilki ta dubi Iyah tana faɗin "Lafiya lau Iyah,ai kinsan dama bata so fitanba,watakila
daɗewan da yayin ne ya bata haushi."
Iyah sai ta saki rai tana faɗin "Hakane fa kuma,to shine kuma tabar min faranti a waje sabida
taɓara,to ai sai ki kira Yasmeen ta je ta ɗakko min."
TAIMIYYAH kuwa tana shiga ɗaki toilet ta nufa direct.Yasmeen dake kwance akan gado tana
kallo a System ɗin TAIMIYYAH,sai tabi bayan TAIMIYYAN da kallo kawai.
Lokacin da TAIMIYYAH ta fito kan gadon ta nufa tana aje Hijab ɗin data cire shi tun a toilet.Tayi
kwance kawai tana lumshe idanunta ba tare data kula Yasmeen dake ta faman binta da kallo
ba,ganin haka yasa Yasmen danna pause tana ture System ɗin gefe ɗaya.Ta matsa kusa da
TAIMIYYAH da tayi rub da ciki tana faɗin "TAIMIYYAH lafiya,meyafaru?"
TAIMIYYAH kaman jira take Yasmeen tayi magana sai kawai ta saki kuka,tana gayawa Yasmeen
ɗin abinda duk ya faru a part ɗin Yah Sadeeq.Sai dai ta ɓoye mata cewa ya rungumeta,ta taƙare
maganan da cewa "Yasmeen bansan da wani fassara Zuhurah zatai min ba,ban kuma san iya
abinda zata gayawa Umma ba.Sannan bansan me zan cewa Iyah ba idan ta tambayeni yadda akayi
har na biye masa naje ɗakinsa,ni dai Yah Sadeeq na son jefani cikin masifa Yasmeen."
TAIMIYYAH ta ƙare maganan tana sake sakin kuka sosai.Hakan yasa Yasmeen fara lallashinta
tana kwantar mata da hankali,akan cewa babu abinda zai faru ai Zuhuran na tsoran Yah Deekun
bazata sanar da Umma komi ba.Da wannan lallashin na Yasmeen TAIMIYYAH ta ɗan kwantar da
hankalinta,amma har suka kwanta bacci ta rasa wani irin tunani zatayi akan zancen Yah Sadeeq.Na
cewa ta rabu da Nass ɗin,ita dai tasan ko sama da ƙasa zasu haɗe ba zata iya auren Yah Deekun
ba,sannan kuma bata san ta yadda zata iya koran Nass wanda a yanzu ta fara jin zuciyanta na
nutsawa dashi.......✍🏻
Follow this link to join my WhatsApp group:
https://chat.whatsapp.com/FAuxFVUMsQhHYfF5qiGklY
Littafin TAIMIYYAH paid book ne da zai zo akan 500 naira only,ga masu buƙatan yin payment
zakui min magana ta wannan number ɗin 08167768704, ko kuma ku turo kuɗin ku kai tsaye ta
wannan account ɗin 0504192664 aisha ibrahim dansabo GTbank.*
#Ɗansabo ce#
[12/14, 3:42 PM] +234 703 040 9541: *Page 29*
*Friday, 8:49pm.*
Suhailah ce ke ta faman kai-kawo a cikin falonta da ke upstairs,tana jiran isowan Maleek Ado,
wanda ya shaida mata goslow ne ya riƙe su a Kaduna tun ɗazu.
Sanye take cikin wata english straight gown,da ya amshi jikinta sosai tare da fiddo suranta.Make-
up sosai tayi wa fuskanta wanda hakan ne ya sake qawata kwalliyan,ta sanya manyan ɗan kunni
da sukai mata kyau matuƙa,qamshin Turarukan ta masu asalin sanyi da daɗi ke fita daga jikinta.
Tana shirin nufan ɗakinta don ita har ta fara gajiya da jiran isowan nasa.Sai kuma taji buɗe gate
hakan yasa ta isa wajen window,ta zuge labulen dake jiki don ta samu daman kallo harabar
compound ɗin gidan daga waje.Take idanunta suka sauka akan ƙatuwar motarsa da ke shigowa
cikin compound ɗin,kafin a tsaida motan Yusuf na saurin fitowa ya buɗe masa back seat ya
fito.Yana sanye cikin manyan kaya da suka fito da cikar kamalansa,da kyawun da Allah ya
basa.Suhailah ta saki labulan window ɗin tana sauke ajiyan zuciya a bayyane,wata iriyar zazzafan
ƙaunar sa na sake narke zuciyanta,duk ta ƙosa ya ƙariso ciki tai hugging ɗinsa ko zaciyanta zata
samu relief,daga azaban kewansa da ta yi.
Lokacin da Maleek ya iso cikin falon gidan,hannunsa riƙe da brief case da kuma wata ƙaramar
jakan hannu.A bakin matakalan benen da zai kai shi sama su kai kacibus da Suhailah data sakko
don tarbansa.Ya sauke manyan idanunsa akan lips ɗinta da ya sha pink ɗin janbaki raɗau! A
hankali duk wani gajiyan da yake ji ya fara warwarewa,kewanta da ya yi na sake mamayesa.
Suhailah bata jira komi ba ta rungume shi ,tana masa sannu da xuwa cikin salon da ta san yana
motsa zuciyansa.Aiko take ya saki duka abinda ke hannunsa,yai mata wani irin kyakykyawan
runguma,yana sanya kansa tsakanin ƙirjinta da ke fitar da wani irin qamshi me motsa
zuciya.Murya can ƙasa-ƙasa yake faɗin,"I really miss u wife." Yayi maganan yana ɗago kansa
daga wajen ya kai fuskar nasa wani muhalli na daban.
Suhailah cikin low voice ita ma take faɗin, "Miss u too my Maleek,duk na ƙagara ku iso tun
ɗazu." Suhailah ta kai ƙarshen maganan da kai bakinta saman nasa ta haɗe,cikin salon da ke
birkita lissafin Maleek ɗin take labuban harshensa,suka fara ba juna wani irin deep kisses.Wanda
ya sake motsa duk wani kafa da Maleek ɗin yabi ya adana kewanta da yake ji,hannunsa ya kai
yana ƙoƙarin sauke botiran riganta ta gaba,amma sai tayi saurin dakatar da shi ta hanyan raba
jikinta da nasa.Ta ɗauki jakunan daya watsar tana masa sighn da ido, alamun su ƙarisa daga
sama,sannan komi da zai faru sai ya faru...
Maleek da gaba ɗaya jikinsa ya saki da wani irin zazzafan sha'awanta dake sake taso masa.Sai ya
rufa mata baya zuwa saman,inda Suhailah bata tsaya a ko'ina ba sai ɗakinsa.
Lokacin da Maleek ya sanyo kansa cikin ɗakin,wani daddaɗan qamshine ya ziyarci hancinsa.
Ko'ina a gyare yake tsaf! Kaman yadda yake muradin gani,sai ya fara da cire rigan shaddan dake
jikinsa yai jifa da ita saman gado.Suhailah data ƙariso wajen ita ce ta ɗauke rigan tana
ninkewa,kafin ta kai dubanta kan Maleek ɗin da ke binta da kallon da ita kaɗai tasan
ma'anansa.Saita shagwaɓe fuska tana faɗin "Wanka first Darling sannan abinci please!"
Tuni Maleek ɗin ya gane inda magananta ya dosa,amma baiyi magana ba sai miƙa mata hannunsa
da yayi.Babu musu ta ƙarisa kusa da shi yai mata masauki a jikinsa,yana kai bakinsa kunnuwanta
ya raɗa mata wasu kalaman da suka sanyata sakin ƙaramin dariya,tana saurin ɓoye fuskarta a
ƙirjinsa.
Daƙyar ta lallaɓashi ya yo wankan ya fito,ta taya shi ya shirya cikin farar jallabiya suka fito zuwa
falo.Suhailah ce ta isa wajen dining ta fara sakko da kulolin data shirya masa abinci,tana jera su a
ƙasan carfet don ba koda yaushe yake cin abinci a sama ba.Fovourite Food ɗinsa tai masa na
tuwan semo miyan ɗanyar kuɓewa,wanda ta wadata shi da naman shanu da ganda aciki.Sai haɗin
chicken salad da yaji salad cream da kayan haɗi,sai qamshi ke tashi lokacin data ke zuzzuba
abincin cikin plate.
Idanun Maleek ne ke yawo a jikinta ko'ina,tunda ta fara kai-kawo na kwaso kayan abincin,har
zuwa yanzu data gama zuba masa abincin cikin plate.Da kanta ta ciyar da shi itama tana ɗan cin
haɗin salad ɗin kaɗan-kaɗan.
Bai wani ci tuwan da yawa ba sabida dare ne baya son cika cikinsa da abu me nauyi sosai,shiyasa
yafi cin salad ɗin da ɗan yawa sosai,kafin ya kauda kai alamun ya ƙoshi,hakan yasa Suhailah aje
plate ɗin ta tsiyaya masa ruwa da lemun Pineapple da tayi masa,sai ya amshi cup ɗin lemun ya
fara sha da kansa.Ganin hakan yasa Suhailah tashi ta nufi ɗakinta don sauya kayan jikinta,ta maida
wata fingilwan Vest wacce tsayinta da kaɗan ya wuce guiwa.Babu komi a jikinta illa Vest ɗin
kaɗai,wacce ba ta da maraba da ba-bu sabida yadda tabi fatan jikinta ta lafe,tare da bayyana duk
wani suran jikin Suhailan.
Lokacin data sake fitowa falon samun Maleek ɗin tayi yana kallo.Ya ɗago manyan idanunsa ya
sauke akanta,yana jin wani irin feeling na taso masa,na zallan sha'awan ta da ya tara.Domin sati
biyu har da kwanaki biyu ba wasa bane a wajen lafiyayyan namiji kamansa,don haka baƙaramin
tara sha'awanta yayi ya adana a ƙasan zuciyansa ba.
Don haka a yanzu da take gabansa sai komi ya kwance masa,Suhailah ko tun daga nesa ta hango
yadda ya kasa ɗauke idanunsa akanta.Shiyasa tana ƙarisowa sai tayi masauki a laps ɗinsa,tana
kwantar da kanta a ƙirjinsa murya can ƙasa take faɗin, "Sweet wannan kallon fa?"
Maleek da ya sauke ajiyan zuciya me ƙarfi sai ya aje remote ɗin dake hannunsa,yana sake shigar
da ita cikin jikinsa sosai.Gaba ɗaya qamshin da ke tashi a jikinta sake kwance notikan sha'awanta
sukeyi akansa,ya cusa kansa tsakanin wuyanta yana faɗin, "Wife ina tsananin buƙatarki oya muje
Bed ki bani magani." Daga haka ya miƙe da ita ajikinsa,yana takawa kaman ya ɗauki Baby suka
wajen kayan kallon da ke aiki,ya yi anfani da hannu ɗaya wajen kashe kayan kallon.Ita dai
Suhailah sake maƙalƙalesa tayi tana faman bashi kiss a saman face,har suka isa ɗakinsa yai mata
masauki akan tsakiyan gadonsa,yana sakkowa ya nufi toilet don wanko bakinsa.
Lokacin daya fito kai tsaye light off yai musu yana nufan kan gadon,tare da janyo Suhailah zuwa
jikinsa. wacce ta cire masa rigan jikinta gaba ɗaya sabida sauƙaƙa masa wahalan cirewa......
To sai in ce asuba ta gari Maleek Ado tunda na ga,wannan karan da soyayya ka dawo lol.
____________
Tun misalin takwas da rabi na safe,TAIMIYYAH ta gama shirinta tsaf na zuwa haddah.Sanye take
cikin riga da plain zani na wata atamfar Chiganvy,kalan Green da akaiwa adon manyan zane da
Milk and Red kaɗan,ɗinkin yayi mata kyau sosai tare da zama ajikinta ɗas! Fuskanta kaman ko
yaushe babu komi akai sai man leɓe,yau ko kwallin ma bata sanya ba.Cikin sauri-sauri take komi
don bata ma so Yasmeen ta motsa ta ganta,wacce take kwance tana baccinta sadidan.Ta ɗauki
dogon Hijab ɗinta na skull ɗin ta sanya,tare da nufan wajen takalmanta ta zura flat shoe me hanci,
don sune irin takalman da take iya tafiya dasu.Qur'aninta ta ɗauka tana fitowa zuwa falo,ganin
babu kowa yasa TAIMIYYAH nufan ɗakin Iyah,sai dai nan ɗinma Guggo Bilki ce kawai akan
gadon Iyan tana bacci.Jin motsin ruwa daga bayi yasa TAIMIYYAH gane cewa Iyah wanka ta
shiga,sai kawai ta juyo tayi fitowanta don tafiya makarantan.
Daga waje suka haɗu da Ladi ta fito daga ɗakinta.TAIMIYYAH ta gaisheta tana faɗin, "Saina
dawo Babah Ladi,idan Iyah ta fito kice mata sauri na ke yi na wuce,kuma a aje min abin kari na
saina dawo zan karya." Babah Ladi ta amsa da faɗin, "To ƴar gidana adawo lafiya,zan sanar da
Iyan Allah bada sa'a da ilimi me anfani."
TAIMIYYAH da tai gaba ta amsa da "Ameen." Tana fitowa daga Sasan Iyah ta nufi Compound na
gidan,tana fata kar ta haɗu da kowa har ta bar gidan.Cikin sa'a kuwa bata haɗu da kowan ba sai
Tukur da suka gaisa ta fice abinta.Tana tafe ne zuciyanta na tariyo mata abinda ya faru tsakaninta
da Yah Deeku a daren jiya.Ta wani ɗan lumshe ido ta buɗe hankalinta na kan hanyan da take
bi,sanyin safiyan na kaɗa Hijab ɗinta yana ratsa jikinta.Har ta isa makarantan bata bar tunanin da
wani ido zata kalli Zuhurah ba,ba kuma ta san ta yadda za ta yi ta iya dakatar da Nass ba, kaman
yadda Yah Sadeeq ɗin ya buƙata.
A round 10:30am aka tashe su daga skull ɗin,TAIMIYYAH suka jero da wata ƴar ajinsu me suna
Bilkisu.Suna tafe suna magana akan yadda waliman yayensu zai kasance,wanda bazai wuce nan
da wata biyu ba zasu kammala haɗe haddansu baki ɗaya.Sun zo dai-dai kwanan da TAIMIYYAH
za ta nufi hanyan gida sannan sukai sallama da Bilkisun.Sai ya zamana TAIMIYYAH ita kaɗai ke
takawa zuwa cikin layin nasu,kanta a ƙasa take tafiya kaman yadda ta saba.Wani irin ciwan kai
take ji na ɗan taso mata kaɗan-kaɗan,ta kuma san hakan baya rasa nasaba da fitowan da tayi bata
karya ba,har ta ƙariso gida bata haɗu da kowa data sani a layin ba.
Lokacin da ta sanyo kanta cikin compound ɗin gidan,tun daga nesa idanunta suka hango mata
Baba Sani da Yah Sadeeq a tsaye suna magana.Hakan yasa tafiyanta ya sake komawa very
slow,don sam bata so haɗuwa da Yah Deeku ba sam,so tayi har ya gama weekend ɗinsa ya koma
ba za ta bari su sake haɗuwa da juna ba.Babu yadda ta iya haka ta karya kwana zuwa wajen da
suke tsayen,don ta san dole za su ga wucewanta,kuma gashi dama bata je sun gaisa da Baban ba ta
tafi haddah.
"Salamu alaikum!
Ina kwana Baba."
Cewan TAIMIYYAH lokacin data ƙarisa gabansu Baba Sanin,tana me tsugunawa har ƙasa ta gaida
shi.Ya amsa da matuƙar kulawa yana faɗin "Zainab har kin dawo daga haddan,ya dai tabbata ke
kaɗaice ke maida hankali,waɗancan shashashan basama zuwa kenan? Aiko zanci ƙaniyansu
sosai." Baba Sani yayi maganan cike da nuna ɓacin rai,ita dai TAIMIYYAH na tsugunne.Sai daya
kai aya sannan ta miƙe tana satan kallon Yah Sadeeq,da take jin tasirin idanunsa ajikinta.Don
tunda ta ƙariso wajen jikinta ya bata kallonta yake yi,ta gaishe shi cikin sanyin murya tana juyawa
ta fara takawa don barin wajen,ba tare data jira ya amsa ba.
Tana dafda shiga Sasan Iyah ta jiyo muryansa yana faɗin "Wait! Zaynab." Sai TAIMIYYAH ta
tsaya cak! Har ya ƙariso inda take,sannan ta ɗaga manyan idanunta ta sauke akansa,yana sanye da
riga da wando ne irin masu kaurinnan na bacci,da alamu ko wanka baiyi ba kenan.
Ta ɗauke idanunta daga gare shi lokacin da yake matsowa daf-da ita sosai,har tana jin saukan
numfashinsa akan face ɗinta.Abinda yasa tai ɗan baya kaɗan tana sake dubansa da fuska a
shagwaɓe.
Shi kuma sai ya saki ƙaramin smile yana faɗin "Matsoraciya miye na wani saurin yin baya kaman
kin ga dodo,wato shine kika kashe waya tun jiya ko?" Ya jefawa TAIMIYYAH tambayan idanunsa
akanta yana kallon yadda ta sake wani narke fuska,kafin ta dubesa tana faɗin "Ni mantawa nayi
ban kunna ba,sabida da wuri na tafi Haddah."
Yadda TAIMIYYAN tayi maganan cike da shagwaɓan daya riga ya santa da shi,yasa shi sake
matsowa gabanta sosai,cikin ƙasa da murya yake faɗin "Alright! Jiya kin manta baki ɗauki kuɗin
da saurayinki ya baki ba,ki ka barmin a ɗakina saura kaɗan in yayyagasu sabida kishi." Ya ƙare
maganan yana wani tsuke fuska alamun har zuciyansa da gaske kishin yake ji.TAIMIYYAH tayi
saurin dubansa tana sake kwaɓe face take faɗin "Kai! Yah Deeku to ba kaine duk ka janyo hakan
ba,ni har yanzu zuciyata ta kasa nutsuwan cewa Zuhurah ba za ta sanar da Umma a yadda ta
gammu jiya ba."
TAIMIYYAH ta kai ƙarshen maganan komi yana dawo mata,shi ko Yah Sadeeq sai ya tsura mata
ido yana ji tamkar ya sake rungumanta ajikinsa irin na jiyan,ya wani lumshe ido ya buɗe akan
fuskan TAIMIYYAN.Yana ɗan sakin smile yake faɗin "And so what! To idan ta faɗi Baby, Zina ta
ganmu muna yi ko babu kaya a jikinmu ta ganmu?" Yah Sadeeq ɗin yayi maganan yana ƙoƙarin su
haɗa ido da TAIMIYYAH.
Amma sai TAIMIYYAH tayi saurin ɗauke kai,wani uban kunyan maganan da Yah Deekun ya ɓaro
na lulluɓeta.Bai bari tace komi ba ya sanya hannu a aljihunsa yana ciro kuɗin da Nass ya bata jiya
yana miƙa mata,ta sanya hannu ta amsa amma taƙi bari su haɗa ido har lokacin.Cike da kishi yake
faɗin
"Ki tabbatar Iyah kika ba kuɗinsa ta aje masa,kar ki sake ki anfani da su kinji na gaya miki Baby."
Yayi maganan bilhakki idanunsa akan TAIMIYYAN data ɗan zumɓuro baki,kafin ta furta, "Ai da
ma ita zan ba ni bance zan kashe ko sisi ba,kuma ma ai shine ya aje yai tafiyansa,amma tunda ya
bani nace masa bazan amsa ba."
Tana kaiwa ƙarshen maganan ta juya zata bar wajen,amma sai Sadeeq yayi saurin riƙo Hijab
ɗinta.Saura kaɗan hannunta ya goce akan guiwanta da take dafe dashi,tayi saurin sake dafe ƙafan
me laluran.Tana ɗago manyan idanunta ta sauke akan Yah Deekun,ya wani haɗe fuska yana faɗin
"Shine zaki tafi na ce na gama magana dake ne?"
"Yah Sadeeq don Allah ka saki Hijab ɗin to,kada wani ya fito ya ganmu.Yinwa nake ji ban karya
ba na fito don Allah ka barni in ƙarasa ciki please!"
Yadda tai maganan kaman zata sanya masa kuka,yasa ya sake mata Hijab ɗin yana faɗin "Alright!
Baby jeki ki karya amma ki kunna wayanki zamuyi magana."
Kai kawai TAIMIYYAH ta gyaɗa masa tana juyawa ta shige,shi kuma Yah Sadeeq ya juya ya nufi
part ɗinsa,zuciyarsa ba sake cika da soyayyan TAIMIYYAN,da yake ji kaman ƙara shi akeyi a
zuciyarsa kullum.
Da sallama TAIMIYYAH ta shiga falon Iyah,idanunta na sauka akan Yasmeen da Guggo Bilki da
ke zaune cikin falon.Luggage ɗin Guggo Bilkin ne agabanta tana shirya kaya,TAIMIYYAH ta
ƙarisa wajen tana gaida Guggo Bilkin.Ta ɗago tana amsa gaisuwan TAIMIYYAN kafin ta ɗaura da
faɗin "TAIMIYYAH shine kika tafi makarantan baki ko tsaya kin karya ba,zaki ci faɗan Iyah
kuwa don sai mita take yi tun ɗazu." TAIMIYYAH ta saki murmushi tana faɗin "Iyah kenan,dama
na san za ta yi faɗa kam.Guggo Bilki wai da gaske tafiya zakiyi yau ɗin? Gaskiya zamuyi kewa."
TAIMIYYAH ta ƙare maganan cike da nuna irin missing ɗin da za su yi na Guggon nasu,don babu
ruwanta da hayaniya akwai ta da sauƙin kai sosai.
Yasmeen ta dubi TAIMIYYAH tana faɗin "Aike wallahi baki da kirki, kin san za kiyi sammakon
fita makaranta amma baki tasheni ba,ki kai tafiyanki."
Yasmeen ta ƙare maganan tana zabgawa TAIMIYYAH harara.Kafin TAIMIYYAN tace komi Iyah
ta fito daga ɗaki,hannunta riƙe da wayanta ta dubi TAIMIYYAH tana faɗin "Kin kyauta fita babu
karin safe,bayan kin san kina da ulcer." Iyah tayi maganan cike da mita tana hararan TAIMIYYAH
data cire Hijab ta aje saman kujera,kafin ta dubi Iyan tana faɗin "Allah baki haƙury Iyah,sauri
nake yi amma kin san bana fita ban karya ba ai.Ina kwana mun tashi lafiya?" Ta ƙare maganan da
gaida Iyah,wacce ta amsa tana faman taɓe baki,hakan yasa Yasmeen sakin dariya tana faɗin "Iyah
wallahi wajenki TAIMIYYAH ke course ɗin iya harara da shagwaɓa,ke ma da alamu lokacin
ƙuruciya kin taɓa shagwaɓa son ranki." Yasmeen ta ƙare maganan suna kwashewa da dariya ita da
TAIMIYYAH,Iyah ta aikawa Yasmeen daƙuwa tana faɗin "Kin ci gidanku ƴar nema." Guggo Bilki
dai na jinsu tana dariyan draman su Iyah da jikokin nata da bai ƙarewa.TAIMIYYAH ce ta nufi
wajen cin abinci don karyawa,koda ta gama sai ta wuce ɗaki tana ɗaukan wayanta ta kunna.
Haka kawai take son jin muryan Nass ɗin,don tasan yayi ta kiran wayan da safe ya jita a
kashe.Aiko wayan na gama Booting saƙonni suka fara shigowa.Sai ta nufi inbox ɗin don
karantawa,biyu daga MTN ne sai guda ɗaya daga Nass ɗin,ta buɗe na Nass ɗin tana karanta
tsararrun kalaman daya turo mata na gud morning text.Wanda baya fashin turowa duk safe.Daga
ƙarshen saƙon yai mata ƙorafi akan ya kira wayanta a kashe,amma idan ta ga saƙonsa ta kira shi
please!
TAIMIYYAH ta saki smile a lokacin data gama karanta saƙon,tana nufan call log tayi dialling
number ɗinsa.Yana fara ringing zuciyanta ya shiga bugawa,har zuwa lokacin da yai cuting call ɗin
ya biyo bayan kiran.Sai ta gyara zamanta daga bakin Bed ɗin lokacin da sassanyar muryansa ya
shiga kunnuwanta.Ta gaida shi cike da salonta dake sake narkar da zuciyanta Nass ɗin.Sun ɗauki
kusan 15minutes suna waya kafin suyi sallama,Nass ɗin na sanar da ita tuni har ya isa Kd ma.
Bayan TAIMIYYAH ta aje wayan sai ta miƙe tana cire kayan jikinta.Ta maida wata doguwar riga
mara nauyi,sabida bata faye son zama da kaya masu nauyi idan tana zaune a gida ba.
Yasmeen ce ta shigo ɗakin lokacin da TAIMIYYAH ta ɗakko System ɗinta zata kunna.Yasmeen
ɗin ta sauke idanunta akan TAIMIYYAN tana faɗin "To Malama sai ki tashi ki fito mu raka
Mamie don yanzu zata wuce." TAIMIYYAH ta ɗaga manyan idanunta tana duban Yasmeen take
faɗin "Yanzu da wuri haka,kai ita ko Guggo da-dai ta bari sai gobe kawai." Yasmeen ta jefa mata
harara tana faɗin "To Abbah bai ga dama ba,yace yau-yau yake son ganin ta koma gida,nima da
ƙyar ya amince in ƙara one week."
Tare da TAIMIYYAN suka fito zuwa falon Iyah,dukansu sanye da Hijab a jikinsu.Tuni Guggo
Bilki har an kai Luggage ɗinta mota,Driver ɗin da zai tuƙata zuwa Kanon ma iya so ashe tun safe.
Har da Ladi me aiki aka rankaya zuwa wajen compound ɗin gidan,don yiwa Guggo Bilki rakiya
wacce ta nufi Sasan Baba Sani don yi musu sallama.TAIMIYYAH da Yasmeen dai na tsaye
jingine da jikin Motar Guggo Bilkin basu bi ta Sasan su Umman ba,mintuna kaɗan sai ga Guggo
Bilkin sun fito tare dasu Zuhurah,sunyo mata rakiya har zuwa wajen mota.Ta shiga motar su
TAIMIYYAH na ɗaga mata hannu,har Motar ta bar cikin compound ɗin suka juya don komawa
cikin gida.
Zuhurah ce tayi saurin biyo bayansu tana kiran sunan Yasmeen.Hakan yasa su TAIMIYYAH
dakatawa daga tafiyan suna jiran ƙarisowan Zuhuran,koda ta iso idanunta akan TAIMIYYAH
yake wacce tayi saurin ɗauke kai,don bata son ma su haɗa ido da Zuhurah.Tuni Zuhuran ta gane
abinda yasa TAIMIYYAH take ɗauke mata kai,sai ta saki murmushi kawai tana faɗin "Yasmeen
yau fa Ameeru zai iso,shine nace me kike ganin zamu shirya masa na tarba?"
Yasmeen da idanunta ke kan Zuhurah,sai ta juya tana nunawa Zuhurah TAIMIYYAH tana faɗin
"Ga wacce zaki tambaya nan,don ita ce gwanan sanin abubuwan kwaɗayi da Girkunan zamani."
Zuhurah da takaicin maganan Yasmeen ɗin ya ɓata ranta,sai ta maze bata nuna ba.Sai ma tayi taku
biyu tana tsayuwa daga gefen da TAIMIYYAH ta juyar da kanta,murya can ƙasa yadda bama lallai
Yasmeen data zama a gefen Zuhuran taji me zata iya faɗiwa TAIMIYYAN ba.Zuhuran ke faɗin
"Ya da ɗauke kai ƴan matan Yah Sadeeq,ko kuma karuwansa zan ce? Don naga alamu ya gama
amshe budurcin tunda har kike kai kanki garesa kina bashi kayan daɗin har ɗaki.To ya? Zaki
taimaka ki samarma saurayin nawa abinda zamu tarbe shi da shi ɗin ne Babyn Yah Deeku?"
Zuhurah ta ƙare maganan tana sakin dariyan iskanci.Tuni TAIMIYYAH ta gama muzanta da jin
kalaman da Zuhurah ta jefeta da shi,kalmar karuwa data jingina ta dashi yafi komi ɗaga
hankalinta.Tayi saurin ɗago kanta don ganin ko Yasmeen ta ji abinda Zuhuran tace,amma cikin
sa'a sai ta ga Yasmeen ɗin tama yi nesa dasu tana amsa waya.Hakan yasa TAIMIYYAH sauke
manyan idanunta da suka fara tara ƙwallan baƙin ciki a kan Zuhurah,tana faɗin "Zuhurah ni kike
kira da karuwan Yah Sadeeq,sabida kawai kin ganmu riƙe da hannun juna?" Tai tambayan tana ji
hawayen da take son dannewa na son kwacewa su zubo akan fuskanta.Zuhurah ta dubi
TAIMIYYAN tana sakin dariyan rainin hankali take faɗin "To da wacece ke? Karki rainawa kanki
wayau mana,ko daga yadda na ganshi a wani susuce nasan magiya yake miki lokacin,yana so ku
shiga daga ciki ya jisa ajikinki,ke kuma kina wahal dashi irin sai ya gama shiga uku kafin ki bashi
abinda ya saba karɓa,ni dama na san soyayyan da yake miki ba banza ba.Jikin yake so da can
ƙasan tunda an sakar masa komi yaji daɗi shiyasa yake nacin ki zama mallakin nasa baki
ɗaya,kuma wallahi idan kikai wasa kaman na sanar da Umma abinda na gani."
Zuhurah na kai aya TAIMIYYAH tayi saurin juya baya dafe da ƙafanta ta fara tafiya.Kuka take
son yi amma ta danne tana jin wani irin tashin hankali na rufto mata,ga tsananin zafin kalaman da
Zuhurah tai mata na ƙona zuciyanta.Tana jin Yasmeen data biyo bayanta na kiran sunanta,amma
ko waiwaye bata yi ba, don burinta kawai ta isa ɗaki,ko zata kwanta tayi kukan dake neman kwace
mata.Cikin Sa'a babu kowa a falon Iyah hakan yasa ta nufi ɗaki,tana faɗawa kan gado ta saki kuka
me ƙarfin gaske.Dukkanin jikinta rawa yake na tsananin shiga ɓacin rai,domin ba'a taɓa jifanta da
munanan kalamai irin wanda Zuhurah ta jefeta da su a yau ba.
Kalamai ne mafiya munin saurare musamman daga bakin ɗan uwanka na jini.
Har Yasmeen ta ƙariso bakin gadon TAIMIYYAH kuka take yi me asalin motsa zuciya.Daƙyar
Yasmeen ɗin ta ciyo kan TAIMIYYAH ta sanar da ita yadda su ka yi da Zuhurah,ta ƙare maganan
cikin muryan kuka tana faɗin "Yasmeen shikenan na shiga uku idan har Zuhurah wannan sharrin
zata ƙulla min a wajen Umma.Wallahi hannuna kawai ta ga ya riƙe,baya ga haka bata ganmu
muna komi ba."
#Ɗansabo ce#
[12/14, 3:42 PM] +234 703 040 9541: *TAIMIYYAH*
*Page 30*
Yasmeen wani takaicin TAIMIYYAH ne ya kamata,da har zata zo ta kwanta tana rasgan kuka.Bata
ci kutumar uban Zuhuran ba,cike da masifa ta dubi TAIMIYYAN tana faɗin, "Bama dole su
rainaki ba tunda kin kasa kifa mata mari,kin wani zo kina faman kuka kaman wata wawiya
mitsuuuw...!"
Yasmeen ta ƙare maganan tana juyawa fuu...! ta fito daga ɗakin TAIMIYYAN ta nufi ɗakin Iyah.
Iyah na zaune bakin gado,tana gyaran tarkacenta da ke cikin kwallah.Sai ganin Yasmeen tayi
akanta tana faɗin "Iyah taso mu je kiga TAIMIYYAH,yadda ta kifa ciki tana faman kuka,kaman
ance kece kika mutu,sabida kawai waccar mara mutuncin ta kirata wai karuwan Yah Sadeeq."
Iyah ta dafe ƙirji tana waro ido take duban Yasmeen, tana faɗin "Karuwa kuma ni Fatuh! Me
waɗannan yara suke so su zama ne? To uban me ta kamasu suna aikatawa da zata kirata da
wannan jafa'in?" Iyah tana maganan ne tana bin bayan Yasmeen da tai gaba abinta.
Lokacin da Iyah suka shigo ɗakin TAIMIYYAH har lokacin kuka take yi.Iyah ta ƙanƙance ido
tana duban TAIMIYYAN,cike da bada umurni take faɗin "Maza tashi ki zauna ki sanar dani
gaskiyan me yake faruwa,bana son kimin ƙarya don banyi miki wannan koyin ba kema kinsan
haka." Babu musu TAIMIYYAH tabi maganan Iyah ta tashi zaune,idanunta har sun tasa sabida
kuka tana ta faman ajiyan zuciya.
Daga Iyah har Yasmeen suka zuba mata mata na mujiya,lokacin da take zayyano ma Iyah abinda
ya faru a jiya da daddaren.Har kawo yadda Zuhurah ta zo ta samesu Yah Sadeeq na riƙe da
hunnunta,ta ƙare maganan tana cewa, "Iyah wallahi abinda ta gani kenan,dama nina san sai ta juya
magana ta ƙulla min sharrin da ban ji ba ban gani ba."
Iyah da ranta ya gama ɓaci ta dubi TAIMIYYAH, tana sake tsuke fuska take faɗin ,"Shi Sadeeq
ɗin ne ya jaki har ɗakinsa don yai miki gargaɗi akan ki rabu da Naseerun? Ke kuma da yake
sakarya ce kika biye mishi kika bishi ɗakin nasa ko?"
Iyah tayi maganan cike da tsawa idanunta akan TAIMIYYAH,wacce ta sake rushewa da
kuka.Hakan yasa Iyah ɗaura faɗanta da cewa "Kin ga laifinki na farko kenan da kika bisa
ɗakinsa,da ace sheɗan yai muku huɗuba ai zaku iya aikata koma miye,tunda da sonki a cikin
zuciyansa." Iyah ta cigaba da cewa, "Don haka wannan shine karo na ƙarshe,da zaki sake shiga
ɓangarensa.Shi kuma Sadeeq ɗin zan kirasa inma tufkar hanci,ina ce agaban ubansa yace abashi
lokaci zai fito da mata,shine yanzu don ya ga wani ya zo zai ɓullo da sabon salo,to idan so yake
taƙama dashi na bi son da gudu na tattake shi ba takalmi." Iyah ta ƙare maganan cike da masifa,ta
waiwaya tana duban Yasmeen da ke tsaye daga gefe,ta furta "Maza ɗakko min waya ta a ɗaki."
Yasmeen ta juya ta fice ita kuma Iyah ta sake maida dubanta ga TAIMIYYAH,tana faɗin "Zaki
tsaida kukan ki share hawaye ko saina saɓa miki? Ba ma dole su rainaki ba komi kuka,sai kace ke
baki da bakin maida martani sakarya kawai!"
Iyah tayi maganan tamkar ta mangare TAIMIYYAH,don gani take sanyin nata har yayi yawa.Da a
ce tana tsayawa ta maida musu da martani,da tuni sun gane itama ɗin TAIMIYYAN ba kanwan
lasa bace,amma sai tai ta musu kuka shiyasa suka rainata har fiye da kima.
Yasmeen ce ta shigo ɗakin riƙe da wayan Iyah a hannunta,lokacin TAIMIYYAH ta share hawaye
sai faman jan majina take yi.Duk takaicinta ya gama cika Yasmeen itama,don gani take da
agabanta Zuhurah ta yi maganan,babu abinda zai hanata bata kyawawan tafi,ta kuma gaya mata
babu daɗi itama.
"Kira min Sadeeq." Cewan Iyah lokacin da Yasmeen take miƙa mata wayan.
Babu musu Yasmeen ɗin ta kira layin Yah Sadeeq ɗin,yana fara ringing ta miƙama Iyah
wayanta.Lokacin da ya ɗaga kiran gaisuwansa kawai Iyah ta amsa,ta sanar da shi idan yana cikin
gidan yazo tana son magana da shi.Idan kuma baya nan da zaran ya dawo ya sameta a Sashin nata
tana jiransa,daga haka ta kashe wayanta bayan ya sanar mata baya nan,sai ya dawo zai shigo.
Ita dai TAIMIYYAH tai kasaƙe tana faman satan kallon Iyah.Ita ko Iyah tashi tayi tsam ta fice
daga ɗakin,bata kuma tsaya a ko'ina ba sai Sasan Baba Sani,ta shiga ciki bakinta ɗauke da sallama.
Zuhurah da Basmah sune zaune a falon,don haka suka amsa sallaman Iyah jikin Zuhurah na bata
cewa TAIMIYYAH takai ƙaranta wajen Iyah kenan.Babu shiri ta miƙe zata nufi ɗakinsu Iyah tayi
saurin dakatar da ita,lokacin data shigo cikin falon bata kuma jira komi ba ta fara wanke Zuhurah
soso da sabulu,ta inda take shiga bata nan take fita ba.
Umma data fito daga ɗaki ne ta tari numfashin Iyah,tana tambayan Iyah ko lafiya? Aiko nan take
Iyah ta haɗa da Umman ta ci mutuncin su da kyau,Zuhurah sai faman kuka take yi tana sanar da
Iyah,ita sharri TAIMIYYAH tai mata,aiko bata ko rufe baki ba Iyah ta kai mata duka a baki,tana
cigaba da faɗin "Yimin shiru mutuniyar banza kawai,har kece zaki kalli ƴar uwanki ta jini ki
jinginata da kalmar karuwa.Idan akwai ɗan iska ma to ai Sadeeq ɗin ne ba ita ba,mu xuba daga ku
har ke Zuwairah me ɗaura su akan halayya da ɗabi'un banza ina dai-dai da ku ne,kuma aure idan
na so ya yiwu tsakanin Sadeeq da TAIMIYYAH babu uban da ya isa hanawa,shi ma kuma Sanin
xai zo ya sameni." Daga haka Iyah ta juya ta koma Sasanta,ta bar su Umma tsaye carko-
carko.Umma ta dubi Zuhurah tana faɗin "Don ubanki sai ki sanar dani abinda kika ga suna yi."
Zuhurah ta zunɓuro baki tana faɗin, "Wallahi Umma rungume fa na ganta a jikinsa,shi kuma sai
wani faman shafata yake yi ko kunya."
Umma ta saki salati tana faɗin "Shi Sadeeq ɗin kika gani da Gurguwan a haka? Aiko zan ci ubansa
a gidannan,inma iskancin ne ya rasa wacce zai dinga bi sai Gurguwa Musaka? Koda yake ba
laifinsa bane itace take cusa masa kanta,tunda tasan da wuya ta auro gara ta bashi yai ta kwasan
banza,amma zanyi maganinsa zai san cewa da gaske na tsani yarinyar."
Umma ta ƙare maganan cikin tsananin fishi,tana nufan ɗakinta don ɗaukan waya ta kira Sadeeq
ɗin.
Basmah ce bayan shigewan Umma ta dubi Zuhurah tana faɗin "Don Allah Yah Zuhurah da gaske
kike yi abinda kika faɗi,ba sharri ki kai musu ba?"
Basmah tayi maganan idanunta akan Zuhurah.Ita kuwa Zuhurah tsaki ta ja tana faɗin "Eh! Sharrin
nai musu tunda ke banza ce,kina tunanin bazai iya neman nata bane,yana ganin nono da ɗuwawu
available."
Yadda Zuhurah ta kai ƙarshen maganan ne yasa Basmah kwashewa da dariya.Kafin ta furta "No
wonder abu kullum sake cika suke,ashe suna samun taki ne bamu da labari,amma Gurguwarcan
akwai ƴar rainin wayau,kullum zulum-zulum da Hijab ashe shu'uma ce.Shi kuma Yah Sadeeq da
shegen kwaɗayi da son banza,miye na bin Gurguwa inma iskancin zai yi ta bakin Umma
mitsuuww...!" Basmah ta ƙare maganan da jan tsaki.
Daga ɓangaren Iyah kuwa bayan ta koma Sasan nata,zaunar da TAIMIYYAH tayi ta sake mata
faɗa akan yadda kullum take kyale su Zuhurah,na cin kasuwansu akanta ba ta iya maida musu
martani.Daga ƙarshe tai musu faɗa da nasiha daga ita har Yasmeen akan muhimmancin kare
mutumcin kai,ko da wasa kada su bari kowani namiji yai anfani da kusancin da ke tsakaninsu har
yace zai dinga kai hannunsa jikinsu.
Daga Yasmeen har TAIMIYYAN maganganun Iyah sun ratsa jikinsu,hankalin TAIMIYYAH sai ya
kwanta sosai.Amma duk da haka da zaran ta tuno yadda Zuhurah ke gwaɓa mata magana,sai ta ji
zuciyarta ta taɓu.
Duk wannan bidirin da akayi sam Anty Laurat bata da labari,don bata gidan abin ya faru ta je can
samaru kai ɗinki,wajen wani sabon telan da su Zuhurah suka samu.
Yasmeen ce ke bata labarin komi,sanda ta shigo Sasan Iyah da yamma,aiko itama ranta ya ɓaci
sosai da abinda Zuhuran tayi.Hakan yasa tace ta cire hannunta akan yin abincin dasu Zuhuran xasu
tarbi Ameerun dashi,don tuni ma ya ƙariso garin inji Zuhuran.Ya yi masauki a hotel ne ya ɗan
huce gajiya,sai zuwa dare zai ƙariso nan gidan.
Daga Zuhuran sai Basmah da masu aiki,su kai kiɗansu su kai rawansu a Sasan Baba Sanin.Don
Anty Laurat ƙin komawa ma Sasan tayi,don kar ma Umman ta sata shiga ta taya su aikin,sai da
akai kiran Sallar Magriba ta bar Sasan Iyan ta nufi nasu.
Su TAIMIYYAH kowacce sai ta tashi ta nufi ɗaki don ɗaura alwala.
___________
Maleek Ado ne zaune daga ƙasan carfet ɗin Babban falon da ke down stairs,yana sanye cikin
ƙananun kaya mafiya tsada.Dawowansa daga masjid kenan bayan an idar da sallan Isha'i,sai yayi
masauki anan falon ƙasan don hutawa.
Yau ko kaɗan baiyi nesa da gida ba,wajen Hajjah kawai ya je ya gaidata ya dawo gida.
Hatta wayoyinsa yau ɗin a kashe suka yini sai da yamma ya kunna su.Bai wuce minti biyar da
zama ba Suhailah ta sakko daga sama,tana nufo wajensa direct cikin takunta me cike da yauƙi.
Tunda ta doso shi idanunsa ke zube a kanta,tana sanye cikin Straight Gown na English
Wears,rigan yabi jikinta ya lafe sosai tare da fitar da suranta.Bakinta ya sha jan lipstick Red kalan
rigan data sanya ɗin,hannunta riƙe da wayanta tana faman taunan cingam ɗin Orbit me shegen
qamshi.
Lokacin data iso hannu ya miƙa mata ta sanya nata ciki,yana me janyota gaba ɗaya tai masauki a
jikinsa.Ya ɗaga manyan idanunsa ya sauke akan ƙirjinta,kafin ya kai hannnu saman lips ɗinta yana
shafa janbakin daya zauna raɗau akan lips ɗinta.
"Yah Maleek ko a kawo abinci nan ne?" Suhailah tayi maganan tana sake lafewa a jikinsa.Maleek
ya sanya idanunsa cikin nata,murya can ƙasa cike da ƙasaitannan nasa yake faɗin "Yes akawo nan
Wife,amma ba sai anyi wahalan sauko da su duka ba,just ki zubo min iya abinda kika san zan
ci,ina fata kinyi min haɗin Fruit Salad ɗinnan?" Ya ƙare maganan da jefa mata tambaya,yana
saketa ta miƙe tsaye,sai ta gyaɗa masa kai tana faɗin "Nayi tun ɗazu yana cikin fridge bari sai a
haɗo har da shi."
"Alright! Luv thank u." Cewan Maleek cike da basarwa,yana ɗauke ganinsa daga gareta lokacin
da ta nufi hanyan hawa stairs ɗin.
Lokacin da Suhailah ta sakko ɗauke da Tray ɗin da ta ɗauro abincin da tai sarving ɗin Maleek
ɗin,sai ta aje agabansa tana faɗin, "My Maleek ga abincin."
Ya ɗago manyan idanunsa ya sauke akanta,yana nuna mata inda zata kawo masa abincin nan
gabansa sosai.Ta ɗauki Tray ɗin ta matsar gabansa,tana zama kusa dashi ta fara ciyar da shi da
kanta.
Bai ci wani da yawa ba yace ta bashi Bowl ɗin Fruit Salad ɗin,ta miƙa masa tana sake mannuwa
da jikinsa.Qamshin turarenta na shiga hancinsa sosai,yana sake saukar da nutsuwa a zuciyansa,har
ya gama shan Fruit Salad ɗin bai yi magana ba,kamar yadda itama Suhailah ta kame bakinta,don
tasan halin ƴan kayanta sarai.Bai faye son yana cin abinci ana damunsa da hira ba,shiyasa itama
sai ta maida hankali akan chart ɗin da take yi da Zubaida Halliru.Wacce ke tambayanta cewa
Maleek ɗin ya dawo ne? Suhailah ta aika mata da amsan cewa eh! Ya dawo gasu ma tare yana
kusa da ita.
A.Maleek da ya ture Bowl ɗin gefe guda bayan ya shanye haɗin Fruit Salad ɗin,sai ya sauke
manyan idanunsa akan Suhailah da hankalinta ya ɗauku akan chart ɗin da take yi da Zuby.Bai yi
magana ba sai hannu daya kai a bazata ya zare wayan daga hannunta,idanunsa na sauka akan chart
ɗin su,ganin sunan Zuby yasa shi tuno da tarin saƙonnin da take damunsa da turowa,don ma yayi
Blocking ɗinta shine ya samu mafita.
Ya aje wayan daga gefe yana duban Suhailah cikin ido yake faɗin,
"Waye Zuby ,wani matsayi take da shi a wajenki da har zaki ɗauki number ta ki ba ta?"
Ya jefawa Suhailah tambayan yana tsareta da idanunsa,face ɗinsa babu alamun sassauci ko
kaɗan.Hakan yasa Suhailah ɗauke idanunta akansa tana faɗin "Aminiyata ce tare muke a skull tun
daga level one,har muka gama tana da kirki sosai fa Yah Maleek.Kuma ai na bata numbern ne
sabida tace zata tayani baka haƙury ,tunda itace ta bani shawaran fara anfani da Pills ɗin da suka
janyo min matsala." Suhailah tayi maganan tana duban fuskan Maleek,wanda yake jifanta da wani
irin mugun kallo,kafin ya buɗe baki yana faɗin,
"Okey! Tuh ina so kisani in dai zamana kike yi a gidannan,na kuma isa da ke to na soke duk wani
Ƙawancen da ke tsakaninki da ita.Ba ki ba ita, kuma karta sake tako ƙafanta cikin gida na kinji na
gaya miki?"
Suhailah tayi saurin ɗago idanunta da ke nuna zallan kaɗuwa da kalaman Maleek,ta furta "Haba
Yah Maleek me yai zafi har haka,me Zubaidan tai maka?" Tayi maganan tana kallon yadda ya ke
jifanta da harara kafin ya sake jefa mata wata tambayan cikin kaushin murya, "So kike yi kisan me
ta yi min kafin ki bi umurnina Suhailah?"
Yadda ya tsatstsareta da manyan idanunsa yasa Suhailah kasa magana,sai gyaɗa masa kai da tayi
kawai tana jin wani irin haushin kalamansa.
Maleek bai sake magana ba shima,sai wayansa daya ɗauka ya shiga ma'adanan saƙonni yana miƙa
mata wayan,tare da tsare ta da idanunsa da ke kiɗima ta.
Suhailah ta amsa wayan tana sauke idanunta akan numbern Zuby da ta turo saƙon.
Ta fara bin rubutun tana karantawa cikin sauri,amma tun kafin ta yi nisa a karatun wani irin tashin
hankali ya ziyarce ta.Ta ɗago ido ta saci duban A.Maleek da nasa idanun ke kanta,ya watsa mata
wani banzan kallon da yasa ta saurin mai da dubanta kan wayan,tana ƙarisa karanta saƙon da ya
gigita tunaninta.Don bata yi zaton ko da wasa Zubyn data ɗauka a matsayin aminiya za ta iya
shirya mata wannan makircin da sharrin a wajen Maleek ɗin ba.
Hankali tashe Suhailah ta sake matsawa jikin Maleek ɗin,bayan ta aje wayan tana dubansa cikin
rawar murya ta fara faɗin "Wallahi dukkanin abinda ta faɗi sharri ne Yah Maleek,ita ce duk ta bani
shawaran fara planning tana nuna min cewa kada na bari na fara haihuwa tun ban mori ƙuruciyata
ba,ni kuma ganin lokacin ina tsaka da karatu sai na dinga bin shawaranta,har na fara anfani da
maganin hana ɗaukan ciki,wallahi bance bazan haihu da kai ba Yah Malee....."
"Enough! Please." Maleek ya katse Suhailah daga maganan data ke yi cikin fushi,da nuna zallan
ɓacin ransa.Ya ɗaura da faɗin,
"Sabida ke ɗin sakaryace shine kika dinga biye mata tana shirya miki gadar zare ko? To ai yanzu
kin fara fahimtan inda ta dosa.So take ta kashe aurenki ita ta shigo don ta samar da abinda ke kika
kasa samarwa,don haka bana son sake jin sunanta ma a bakinki bare har ta sake tako min cikin
gida.Idan ko hakan ya faru to ki fara shirin amsar ta a matsayin kishiya,tunda ke sakarya ce mara
zurfin tunani,da har zaki ɗauki numbern mijinki ki baiwa qawar ki.Qawar taki ma ƴar iskan da ta
fiki buɗewan ido sabida ke shashasha ce!" Ya ƙare maganan yana ture Suhailah da ke
jikinsa,amma sai ta sake ƙanƙameshi tana sakin kuka me tsuma zuciya.
Dana sani da kuma nadaman biyewa Zuby da tai tayi a baya na mamaye zuciyanta.Cikin kuka take
baiwa Maleek ɗin haƙury tare da roƙonsa yai Blocking layin Zubaidan ma baki ɗaya a
wayansa,don kalamansa na cewa zai iya auren Zubyn idan ta cigaba da Aminta da ita ba ƙaramin
kiɗimata ya yi ba.
Maleek dake sauraren magiyan da Suhailah ke masa,sam baice uffan ba har sai data ɗago tana
duban fuskansa,da idanunta da yai kace-kace da hawaye,ya balla mata wani harara yana faɗin
"Yanzu kin amince zaki rabu da ita ko kina sha'awan ta shigo ku zauna tar......"
Kukan da Suhailah ta saki tana kai hannu ta rufe bakinsa,shi ya hana shi ƙarisa kalamansa,wani
irin dariya ke taso masa yana dannewa.
Cikin muryan kuka Suhailah ke faɗin "Wallahi zan bar ta Yah Maleek,bari na har abada ma kuwa
tunda ita ɗin maciyiya amanace,ba sona take tsakani da Allah ba,don Allah ka daina cewa za ka
iya aurenta zuciyata bugawa za ta yi." Suhailah ta kai ƙarshen maganan tana sake cusa kanta a
ƙirjinsa ta saki kuka,hakan yasa Maleek sakin ƙaramin murmushi yana kai hannu bisa kanta.Ya
zame hulan data sa ya shiga yamutsa lallausan gashinta,kafin ya fara maganan cikin ƙasaitacciyar
muryansa,yana faɗin "It's okey! Kukan ya isa haka,kinga yanzu sai ki fara ɗaukan darasi akan
sakarwa qawaye fuska,bama ita wannan kaɗai ba duk wata qawa kiyi hankali da sakin mata fuska,
bare har ta san wani sirrin abinda ya shafi gidan aurenki da mijinki,har ki iya ɗaukan numbern
mijinki ki bata.Karki sake min irin haka ko da wasa kin ji ko?" Suhailah dake sauraransa ta gyaɗa
kai kawai don bama zata iya magana ba,sabida yadda baƙin cikin Zuby ke kashe zuciyanta.
A Maleek ɗin ya cigaba da faɗin "Nan da 5 days na ke saka ran Visa ɗinki zai fito,zamu tafi Egypt
kaman yadda na sanar da Hajjah,ni nawa har ya fito Visan don haka sai ki addu'a Allah sa asamo
mafita,idan kuma mafitan bata samu ba kaman yadda na faɗi a baya dole ne zan ƙara aure
Subailah.
Zan ƙaro aure ba don na daina son ki ko zan daina ba,sai don kawai ina da buƙatan ganin jinina na
yawo a doran ƙasa,ina buƙatan haihuwa sosai da sosai Suhailah, shiyasa abinda kika yi ya taɓa
zuciyata matuƙa.Ba don dangantaka ta jini me ƙarfi da ke tsakanin mu ba,wallahi da gida zaki
koma har sai kin nemi lafiyan da mahaifanki zata iya ɗaukan ciki.Sannan zaki dawo gida na tunda
lokacin da ki kai ma mahaifar illa ba da izini na kika aikata dukkanin abinda kika yi ba."
A.Maleek ya kai ƙarshen maganan kunnuwansa na jiye masa azababban kukan da Subailah ke
yi.Me asalin motsa zuciyan me saurare wanda hakan ya raunata zuciyansa,har ya sake matseta a
jikinsa sosai,yana jin ɗumin hawayenta da ke jiƙe gaban rigansa.
Bai sake magana ba kamar yadda Suhailah itama bata fasa kuka ba,domin kalamansa ba ƙaramin
rugurguza zuciyarta yayi ba.Wani irin soyayya take wa Maleek ɗin da ya haifar da azababban
kishinsa a zuciyarta,shiyasa kalmar ƙarin auren da yake ambata ta ke jin tamkar yana soka mata
mashi ne a ƙahon zuci.
Shafa lallausan gashin kanta ya cigaba da yi,har zuwa lokacin da Subailah ta yi shiru don
kanta.Tana faman sauke ajiyan zuciya akai-akai,ya ɗago fuskarta daga jikinsa yana tsura mata
ido,kafin ya fara share mata hawayen da yaƙi tsayawa,murya can ƙasa yake faɗin "Ya isa haka
kukan Suhailah,na sanar da ke gaskiyan abinda ke zuciyata ne don bazan iya miki ƙarya ba.Ina son
ki wife ke ma kinsan hakan,sai dai soyayyar da nake miki ba zai sa in iya zuba miki ido mu rayu
babu haihuwa ba.
Musamman yadda na nake jin zafin cewa kece ki kai wa kanki illa,ko da zan ƙara aure ina so ki
sawa ranki zanyi hakan ne ba don son da nake miki ya ragu a zuciyata ba.Kuma nayi miki
alqawarin kare duk wani martabanki,i luv u wife,i luv u so very much! Kuma ina fata in cigaba da
sonki har ƙarshen numfashi na Suhailah."
A.Maleek ya kai ƙarshen maganan yana haɗe fuskokinsu waje guda,kafin a hankali ya haɗe
bakinsa da nata ya fara bata wani irin kisses da suka tsaida gudun hawayen Suhailah cak! Ta wani
sake shigewa jikinsa tare da ƙanƙamesa tamkar zata shige cikin ƙirjinsa.Gaba ɗaya Maleek yayi
nisa wajen nuna wa Suhailah tarin ƙaunanta dake cikin zuciyansa,lamarin da bai tuƙe a ko'ina ba
sai a gadon baccin su.
Don Maleek ɗaukanta yayi cak! Suka haura zuwa sama,ba tare da sun bi takan wayoyinsu dake
zube a falon ba,ban sake jin ɗuriyan su ba sai da komi ya dai-dai ta,sannan Maleek ya zare jikinsa
yana nufan toilet ya tsarkake kansa.
Lokacin da ya fito Suhailah na kwance shame-shame bisa bed ɗin,dukkanin jikinta da zuciyanta
sun gama galabaita da tarin ƙaunar da Maleek ya nuna mata.Kallon ta yayi cikin ido yana nuna
mata hanyan Bathroom da hannu,alamun ta tashi ta je ta tsarkake jikinta ita ma.
Bai kuma jira cewan ta ba ya nufi hanyan fita ɗakin,don sauka down stairs ya kwaso musu
wayoyinsu.
Suhailah ta fito daga wanka agogo na buga ƙarfe 1 dot na dare,sanye ta fito da rigan wanka kanta
na ɗigan ruwa.Direct ɗakinta ta wuce don busar da gashinta sabida gudun kwana da lema akai,don
hakan na sanyata Mura.
Bayan ta busar da gashin,sai ta sanya ƙaramar Vest a jikinta bayan ta fesa Body mist me sanyin
qamshi.Ta fito ta nufi ɗakin Maleek ɗin,ta same shi kwance bisa Bed idanunsa a rufe,hakan yasa
ko da ta hau kan godan sai ta nufesa tana shigewa cikin Duvet ɗin,yai mata masauki a ƙirjinsa
yana ya rungumeta.Hancinsa na shaqo masa sassanyan qamshin Body mist da Suhailan tai anfani
da shi,ita ko Suhailah luff tayi a faffaɗan ƙirjinsa,tana kai fuskanta zuwa nasa ta bashi light
kiss,murya can ƙasa ta furta "Luv u my Maleek."
A.Maleek ya lumshe ido yana mayar mata da martanin kalamanta,ta sigan da zata fi fahimta ba da
baki ba........✍🏻
Littafin TAIMIYYAH paid book ne,ga duk wanda ta tsincesa a kowani irin group ne,kiji tsoran
Allah karki karanta sai kin biya 500 naira only.
Za ku iya min magana ta wannan number ɗin 08167768704, ko kuma ku turo kuɗin ku kai tsaye ta
wannan account ɗin 0504192664 aisha ibrahim dansabo GTbank.*
Masu turo credit za ku turo katin MTN na 500 ta wannan line ɗin 08167768704.
#Ɗansabo ce#
[12/14, 3:42 PM] +234 703 040 9541: *TAIMIYYAH*
*Page 31*
___________
Umma ce zaune a cikin Bedroom ɗinta,ta tasa Sadeeq a gaba tana zazzaga masa ruwan
masifa,akan cewa lallai ya fita a harkan Gurguwan yarinyar nan TAIMIYYAH.
Ta inda take shiga bata nan take fita ba,shi dai Yah Sadeeq yai ƙasa da kansa yana sauraranta,ba
tare da ya tari nunfashinta ko sau ɗaya ba.Umman ta ƙare maganan da cewa "Aure zan maka tunda
abin naka ya fara zama iskanci,ka fara saka Gurguwa a ɗaki kana kwanciya da ita sabida asara,in
banda abinka in ma iskancin zaka yi ka rasa wanda zaka kula sai Gurguwa,Musaka! To tunda ka
kasa fito da zaɓinka ni zan zaɓo maka yarinya dai-dai da ajinka,ƴar gidan qawata Hajiya Hadeeza
za ka je ka nema.Tana nan da budurwar ƴa kyakykyawa me dirin jiki,ita ma fara ce ƙar kaman
waccar Musakar,don haka sai ka shirya wata satin idan ka dawo Weekend za ka ku ga juna,sunan
yariyar Nadeeya."
Umma ta kai ƙarshen maganan tana ɗaura idanunta akan fuskan Sadeeq ɗin,wanda ya haɗe fuska
babu annuri ko kaɗan.Zuciyansa tafasa kawai yake yi yana ji da ba Umma bace ke masa wannan
maganan,tana aibanta TAIMIYYAH a gaban idanunsa,tabbas da wata can dabam ne ba abinda zai
hana shi nuna mata fushinsa.
Amma da yake Uwa ce hakanan ya danne ɓacin ransa,yana faɗin "Umma ni bana son wani haɗe-
haɗe zan zaɓo matar aure da kaina,don Allah kada ma ki yi wa Anty Dijen maganan." Ya kai
ƙarshen maganan cike da roƙo,Umma da ke kallonsa baki buɗe ta dalla masa harara tana faɗin "Ai
ko baka isa ba Sadeeq,wannan umurni ne nake baka ba wai shawaran ka nake nema ba,don haka
na gama magana,kana dawowa wata satin za ka ku ga juna final!"
Daga haka Umma ta miƙe ta bashi waje tana jan tsaki tsuuuw....! Hakan yasa Sadeeq bin bayanta
da kallo,zuciyarsa na matuƙar sake ɗaukan zafi.Tuni idanunsa sun yi mugun kaɗawa ya miƙe yana
ji tamkar ƙafafunsa ba zasu iya ɗaukansa ba,ya rasa da wani ɓacin ran zai ji,na Iyah da itama tai
masa tatas a daren jiya akan lallai ya fita daga harkan TAIMIYYAH,ko kuwa da rigiman da Umma
ta ɗauko yanzu na cewa zata haɗa shi da ƴar aminiyanta Anty Dije? Har ya fito falo bai san
taƙamaimai inda yake jefa ƙafafunsa ba.
Lokacin da ya iso tsakiyan falon ne idanunsa ya sauka akan su Zuhurah.Take Brain ɗinsa ya tuno
masa cewa Zuhuran ita ce silan duk wannan masifan da ake son jefa Zuciyarsa a ciki,sai ya nufi
inda take yana damƙota tare da kifa mata lafiyayyen marin da ya ɗauke jin ta da ganin ta na wasu
ƴan daƙiƙu.
Zuhurah da komi yazo mata a bazata ta ƙwallah wani uban ihu,wanda ya janyo hankalin su Umma
da Anty Laurat da ke ɗaki,suka fito a guje don ganin meke faruwa.
Umma sai tai turus a tsaye tana kallon yadda Sadeeq ya dage yana jibgan Zuhurah,yana zuba mata
masifa akan duk munafunci da cin mutuncin da tai wa TAIMIYYAH a jiya.Umma ganin zai
raunata mata ƴa yasa ta isa wajen da sauri.Ta ɗaga hannu zata ɗauke shi da mari Anty Laurat da ta
ƙariso wajen, tayi saurin shiga tsakiyansu tana faɗin, "Umma kiyi haƙury,Yah Sadeeq oya bar nan
wajen please!"
Babu musu Sadeeq ya juya ya bar Sasan a fusace tamkar zai tashi sama.Zuhurah da Umma take
riƙe da ita sai ta sake sakin wani uban ihu tana faɗin "Wayyo kafaɗata Umma ya karya ni!"
A rikice Umma ta zaunar da ita tana faɗin "Ke don ubanki bansan jafa'i,kar ki tara min mutane
cikin Sasa,ya karya miki kafaɗa ne zaki xauna a haka? Ki yi shiru ki bar ni da shi saina saɓa
masa,ba dai duk akan waccar Gurguwan yake yi ba,to zanci ubansa very soon!"
Umma ta ƙare maganan a fusace,tana juyawa ta bar Zuhurah da su Anty Laurat,wacce ita abinda
Yah Sadeeq ɗin yaiwa Zuhurah ba ƙaramin birgeta ya yi ba.
A can ɓangaran Sasan Iyah kuwa,TAIMIYYAH ce zaune ita da Zee wacce ta kawo mata ziyara a
yau.An cika gaban Zee ɗin da kayan motsa baki,sai hira suke yi har da Yasmeen da ke zaune daga
gefe tana sanya baki cikin hiran.
Wayan TAIMIYYAH ne ya shiga ringing,ta ɗaga wayan tana miƙewa don barin wajen.Ganin Nass
ne me kiran sabida kunyan amsa wayansa ta ke ji a gaban mutane,daga Yasmeen har Zee suka bi
bayanta da kallo suna sakin murmushi.
Ta ɗauki tsayin 15 minutes sannan ta fito ,Zee ta dube ta cike da tsokana ta ke faɗin, "Qawata da
alamu dai wannan Nass ɗin ya ci mu da yaƙi, ya yi nasaran sace zuciyar ki, dama ni na san da ƙyar
zaki iya tsallake tarkon sa,don Guy ɗin ya haɗu kun kuma dace da juna,Allah dai ya tabbatar da
alkhairy a tsakaninku."
Yasmeen ta danna mata harara tana faɗin, "To ai dukkanin reaction ɗinki akansa ya gama fallasaki
yarinya,kowa ya ji yadda kike narke masa ya san kin kamu wallahi,don haka mu bawani gulman
da za a mana a tuh!"
Zee ta saki dariya sosai bayan Yasmeen ta dire magananta,idanun Zee ɗin cikin na TAIMIYYAH
take faɗin "Qawata kawai ki saki an riga an ci ki da yaƙi." TAIMIYYAH ta aikawa Zee ɗin harara
tana faɗin,
"To na ji ƴan saka idanu a ɗakko wani topic ɗin a aje wannan." Daga haka suka shiga wata hiran
har Iyah ta dawo daga anguwan da ta fita,ta tadda Zee ɗin da take jin labarinta a bakin
TAIMIYYAH.Zee ta gaida Iyah cike da ladabi tana faman yi mata sannu da zuwa,Iyah ta amsa da
fara'a sosai cikin Zuciyanta tana yaba nutsuwan Zee ɗin.
Sai around 3pm Zee ta tashi tafiya,Iyah ta bada sinƙin Sabulu me tsada na wanka da turare aba
Zee ɗin.Ita kuma TAIMIYYAH wani Ɗan-kunni da sarƙa me kyau,da take aje da shi bata taɓa
amfani da shi ba,shi ta ɗauka ta haɗa Body Mist me Qamshi,cikin turarukan da Abie ke aiko mata
za ta baiwa Zee ɗin.Har bakin gate ita da Yasmeen su kaiwa Zee rakiya,sai faman godia Zee ɗin
take yi lokacin da TAIMIYYAH ta bata ledan da suka zuba mata sha tara ta arziƙin.
Sai da suka ga Zee ɗin tayi nisa da tafiya,sannan suka juyo zuwa cikin gida.Yasmeen nata yaba
kirkin Zee ɗin da hankalinta,hakan kuma yai wa TAIMIYYAH daɗi a rai,ta ji Zee ɗin ta sake shiga
Zuciyanta musamman da Iyah itama take ta yaba nutsuwan Zee ɗin.
__________
*After One Week*
A cikin sati ɗayannan da ya biyo baya,abubuwa da yawa sun faru.Ciki har da yadda Soyayya me
ƙarfi ya ƙullu tsakanin TAIMIYYAH da Naseer,wanda ke can garin Abuja wajen aiki amma
kullum suna maƙale da juna a waya.
Sunyi wani irin shaƙuwa ta ban mamaki,ta yadda ɗaya baya iya yini guda sur! Bai ji muryan ɗan
uwansa ba.Hatta da yin vid call da TAIMIYYAH ke ƙorafin bata so,yanzu ya fara zame mata jiki
don duk dare kafin su kwanta sai sunyi vedio call da Nass ɗin.
Ita dai Yasmeen na ganin ikon Allah,tare da tasa TAIMIYYAH da tsiya kala kala.Gefe ɗaya kuma
tana jin daɗin yadda TAIMIYYAH ta saki jikinta da Nass ɗin suna kwasan Soyayyah.Zuhurah da
mutuminta Ameeru ɗan mutanen Bauchi itama luv suke bugawa ba kaɗan ba,don da gaske son shi
take yi da dukkanin Zuciyanta.Tuni har maganan ya je kunnin Baba Sani,ya kuma ce a gayawa
Ameerun ya turo manyansa su nema masa izinin fara zuwa zance,duk a bakin Anty Laurat su
TAIMIYYAH ke jin hakan.
Yau ya kama Saturday tun safe su TAIMIYYAH ke shirin tarban zuwan Abie,wanda ya kira wayan
Iyah tun daren jiya ya sanar da ita zai ƙariso Zarian bayan ya tsaya a Kaduna an ɗaura auren da zai
kawo sa garin.
Qanwar Ummie da suke Cousine ne za'ai wa aure shine Abie ɗin zai zo ɗaura aure,ita Ummie da
su Nahar tun Thursday ma suka biyo jirgi zuwa Kaduna.TAIMIYYAH haka kawai take jin duk ta
ƙosa tayi ido biyu da Abie,sabida ya kwana biyu bai shigo garin ba,sai dai su gaisa ta waya wani
zubin su yi vid call.Shiyasa yau ɗin daya sanar zai zo gaba ɗaya farin cikinta ya kasa ɓoyuwa,gefe
guda kuma tun tashinta da safe take fama da faɗuwan gaba,sai ta dinga nanata kalmar
Hasbunallahu wani'imalwakil! Shine ta ɗan samu sauƙi.
Ƙarfe 1:10pm na rana suka kammala shirya abincin da suka yi,a ɓangaren cin abincin da ke falon
Iyah.TAIMIYYAH ɗaki ta nufa ta sake yin wanka,ta fito ɗaure da alwala ta nufi Pray Mat don tada
Sallan Azuhur.Yasmeen ma wankan tayo ta fito ta shirya cikin doguwar rigan Material,ita ma
TAIMIYYAH bayan ta idar mai ta shafawa fatarta,ta nufi wajen kayanta ta ciro wata doguwar riga
na wani Swiss Voile mara nauyi ta saka.Ɗinkin ya yi mata kyau wanda akaiwa A shape,ta ɗaura
ɗankwalin kayan,tana ɗaukan turarenta na GIORGIOS PINK ta fesa kaɗan,ta maida kwalban ta
aje.Idanunta akan Yasmeen take faɗin "Yasmeen zo ki taɓi ƙirjina kiji yadda yake faman
dokawa,na rasa dalilin wannan faɗuwar gaban da nake ji."
Yasmeen ta dubi TAIMIYYAH tana me matsowa gaban ta,ta kai hannu da dafa tsakiyan ƙirjin
TAIMIYYAN, tana jin yadda ƙirjin ke bugawa fat! fat! Ta cire hannunta daga wajen tana faɗin
"Sorry kiyi ta addu'a ne wani lokacin haka ne,sai kai ta jin faɗuwan gaba." TAIMIYYAH ta jinjina
kai tana faɗin "Wallahi tunda safe nake jin hakan,da nayi addu'a sai inji yayi sauƙi amma yanzu
kinji kuma ya dawo."
TAIMIYYAH ta kai ƙarshen maganan tana ɗaukan wayanta, da ke saman madubi dai-dai lokacin
da kiran Nass ke shigowa.Sai ta koma bakin gado ta zauna tana ansa call ɗin,cikin shagwaɓe
murya take masa magana,sun ɗauki wajen 20 minutes suna waya, don har Yasmeen dake jiranta su
ci abinci ta gaji tai ficewanta zuwa falo.
TAIMIYYAH ta sauke wayan daga kunni lokacin da Nass ɗin yai hanging up! Ta saki murmushi
kalaman daya gaya mata na luv na sake narkar da Zuciyarta.
Lokacin da TAIMIYYAH ta isa wajen cin abincin,tuni har Yasmeen ta fara cin abincinta ba tare da
ta jira fitowan TAIMIYYAN ba.Suna cikin cin abincin Iyah ta fito tana amsa waya,da alamu da
aminiyanta Hajiya Rabi take wayan,sabida yadda take ta faman ɗaga murya.Wajen cin abincin ta
iso itama ta zauna kusa da TAIMIYYAH ,tana mata alama da hannu akan ta zuba mata abincin
itama.
TAIMIYYAH ta ɗauki plate tai sarving Iyah Rice and Stew ɗin da yaji zallan tsokar naman
kaza.Ta zuba mata haɗin Salad wanda ba'a riga an sanya masa Salad Cream ba,ta tura gaban Iyah
da har lokacin waya take yi cike da ɗaga murya.Yasmeen tai ƙasa da murya tana cewa
TAIMIYYAH, "Wai wannan tsohuwar tamu bata iya amsa waya a hankali bane halan?"
TAIMIYYAH ta saki dariya tana faɗin "Gashi kuma kin gani,haka take yi indai Babah Rabi ne ta
kirata,kinsan tana cewa Babah Rabin na da matsalan ji,shiyasa take wannan hayagagan."
Iyah data sauke wayan daga kunni,sai ta watsawa su Yasmeen harara don sarai ta san gulmanta
suke yi.Yasmeen ta saki dariya tana faɗin, "Iyah wannan amsa waya kaman kina magana da
kurma." Iyah ta ballawa Yasmeen harara tana faɗin,
"Eh! to ai kusan hakan tunda matsalan kunni gare ta ba ta ji sai anyi magana da ƙarfi."
Yadda Iyah ta kai ƙarshen maganan har lokacin tana hararan Yasmeen,yasa TAIMIYYAH sakin
dariya,suka maida hankali akan cin abincin su har su ka kammala.Yasmeen da TAIMIYYAH sai
suka koma ɗakinsu don TAIMIYYAH cewa tayi bacci za ta yi kafin La'asar tayi.
Suna shiga ɗaki kuwa kwanciya TAIMIYYAH tayi bada jimawa kuwa baccin ya sace ta,ita
Yasmeen sai ta kwanta tana chart don bata cika yin baccin rana ba.
Ƙarfe huɗu dai-dai TAIMIYYAH ta farka daga baccin,kai tsaye toilet ta nufa don yin tsarki da
alwala.Ta fito ta gabatar da Sallan La'asar ɗin,tana idarwa ta fito zuwa falo dai-dai lokacin da kira
ya shigo wayan Iyah dake zaune,tana lazumi ita kuma Yasmeen hankalinta na kan kallon tashar
Bollywood,da ake haska wani Film da take mutuwan so.
Iyah ta ɗaga wayan da sallama a bakinta,tana sauraren maganan da ake sanar mata daga ɓangaren
me kiran.Su dai su TAIMIYYAH kawai gani suka yi Iyah ta saki wayan da ke hannunta,tana
faman jero Salati da Sallallami,jikinta na wani irin rawa kafin jiri ya ɗebeta ya watsar bisa kan
Carfet.TAIMIYYAH tai wani irin tsalle da ƙafa ɗaya sai gata a gaban Iyah,ta shiga girgizata da
dukkanin ƙarfin da take da shi,ƙirjinta na cigaba da bugawa kaman zai fashe.Yasmeen kuma
wayan da Iyah ta jefar ta ɗauka tana bin bayan kiran,TAIMIYYAH kuka take yi tana girgiza Iyah
da tuni ta suma.
Dai-dai lokacin Babah Ladi ta shigo cikin falon,da hanzari ta nufo wajen Iyah dake yashe a ƙasa
babu alamun numfashi,sai kuka TAIMIYYAH take tana faman kiran sunan Iyan.
Yasmeen data bi bayan kiran da aka yowa Iyah,bugu biyu muryan wani namiji ya ɗauki wayan
yana sanar da ita cewa,Abie ne suka samu Accident a dai-dai kwanan Jaji,kuma nan take rai yayi
halinsa sai yara biyu mata da yake tare da su,da suke cikin wani hali mummun......
Ai Yasmeen bata bari ta gama jin ƙarshen maganan ba,ta ƙwallah wani uban ihu tana xubewa
ƙasa.Hakan ya sake tada hankalin TAIMIYYAH da ita ma ta fashe da kuka,Ladi dake faman
shafama Iyah ruwa a fuska don a samu ta farfaɗo,ta dubi Yasmeen tana faɗin "Ƴar nan sanar damu
abinda ke faruwa don Allah."
"A'.a'.a.Abie ne Babah Ladi...!" Yasmeen tayi maganan a rarrabe tana sake fashewa da
kuka,TAIMIYYAH ta ƙariso wajen da Yasmeen take tana faɗin "Me ya samu su Abie
Yasmeen,sanar dani me ke faruwa ne wai?" Tayi magana cikin muryan kuka cike da ƙaraji..! Sai
dai kafin Yasmeen ta buɗe baki sallaman Baba Sani da shigowansa gaba ɗaya cikin falon
Iyah,yasa dukansu suka maida dubansu gare sa.Kallo ɗaya xakai masa kasan cewa a kwai
matsala,don idanunnan nasa sun kaɗa sunyi jajir,ya nufi wajen Iyah da yake hangowa a yashe ana
faman shafa mata ruwan ƙanƙara a fuska.Amma har lokacin bata farfaɗon ba,ya tsuguna kusa da
kan Iyah yana cewa Baba Ladi, "Ladi ai kwara mata ruwan za ki yi gaba ɗaya kawai,ina ga sanyin
ruwan zaifi tasiri wajen sanya numfashin ya dawo cikin sauri."
Ladi nan take tayi yanda Baba Sanin yace,aiko nan da nan sai gashi Iyah ta kawo numfashi.Tana
buɗe idanunta a hankali bakinta ɗauke da Salati,TAIMIYYAH ta iso wajen tana tambayan Baba
Sani meya samu Abie ɗinta?Ganin Iyah ta farfaɗo sai ta nufeta tana sake rushewa da kuka.
Iyah ta rungume TAIMIYYAH tana nanata kalmar Allahummah ajjirni fih musibati
wa'akliflikhairan minha! Idanunta babu alamun hawaye za su zuba,da alamu kukan na zuci take yi
wanda yafi na fili illah.Baba Sani ya share hawaye yana duban Iyah yake faɗin "Iyah xamu tafi
amso su,yanxu kafin in shigo aka sake kira su ma yaran lokaci yayi." Ya ƙarisa maganan yana
fashewa da kuka kaman ƙaramin yaro,mutuwan ɗan uwan nasa da ƴaƴansa na dukan Zuciyarsa.
Iyah ta rintse idanunta da ƙarfi wani abu me tauri na danne Zuciyarta,bata iya cewa komi ba sai
kai data gyaɗa masa kawai.Daga haka Baba Sani ya fice da sassarfa don kama hanyan
Kaduna,zuwa amso gawarwakin su Abie da su Nahar da ajali ya sauka musu a rana guda.
Lokacin dasu Umma suka bazamo Sasan Iyah suna ihun kuka ne,TAIMIYYAH ta fahimci halin da
ake ciki.Nan take ta faɗi ta sume gau! Bata sake sanin inda kanta yake ba sai farkawa tayi ta ganta
akan gadon asibiti.........✍🏻
_Ina maraba da masu son a tallata musu hajarsu cikin wannan Littafin,sai ku tuntuɓeni ta lambar
wayata kamar haka 08167768704._
Littafin TAIMIYYAH paid book ne,ga duk wanda ta tsincesa a kowani irin group ne,kiji tsoran
Allah karki karanta sai kin biya 500 naira only.
Za ku iya min magana ta wannan number ɗin 08167768704, ko kuma ku turo kuɗin ku kai tsaye ta
wannan account ɗin 0504192664 aisha ibrahim dansabo GTbank.*
Masu turo credit za ku turo katin MTN na 500 ta wannan line ɗin 08167768704.
"Ɗansabo ce#
[12/14, 3:42 PM] +234 703 040 9541: *TAIMIYYAH*
*Page 32*
__________ A hankali TAIMIYYAH take buɗe idanunta da su kai matuƙar nauyi,tana bin ɗakin
Asibitin da kallo.Ta sauke ganinta akan Yasmeen da Anty Laurat,waɗanda su ma idanunsu yai
luhu-luhu,ta ke kanta yai wani irin sarawa komi na dawowa Brain ɗinta.
Kukan data fashe da shi shine ya ankarar da su Yasmeen farkawanta.Yasmeen ta isa bakin gadon
da sauri tana faɗin "Sannu TAIMIYYAH kin farko,sorry please! Kukan ya isa haka addu'a kawai
su ke nema,don har an kaisu gidan su na gaskiya."
Yasmeen ta kai ƙarshen maganan cikin rawar murya,tana rungumo TAIMIYYAH zuwa
jikinta.Wacce ta fasa wani sabon kukan,jin cewa da gaske dai ta rasa Abie ɗinta da Qanninta har
biyu Raudha da Nahar,
cikin muryan kuka take faɗin,"Yanzu shikenan ba zan sake ganin Abie da su Nahar ba,don Allah
ku ce min wasa ne ba su mutu ba,meyasa mutuwa za tai min haka Yasmeen? Allah nima ka ɗauki
rai n....."
Rufe bakinta da Yasmeen tayi ya hanata ƙarisa kalamanta.Yasmeen ta fara magana cikin rawar
murya ta ke faɗin "Subhanallah! TAIMIYYAH kar kiyi saɓo please! Mu ma ba jinkiri muka yi
ba,za mu tadda su idan lokacin mu yayi,addu'anki kawai su ke buƙata a yanzu ba waɗannan
surutan da kuka ba,don Allah kiyi tawakkali tamkar yadda Iyah tayi ita ma."
Yasmeen ta kai ƙarshen maganan tana kasa controling hawayen da ke zubo mata,sai lokacin Anty
Laurat da ke share hawayen tausayin TAIMIYYAH,ta iso bakin gadon tana faɗin "Kiyi haƙury
TAIMIYYAH ko wani mai rai da kika gani dole zai mutu watan watarana,Allah ya baki haƙury da
dangana su kuma Abiee Allah ya haskaka makwancinsu,yasa suna kyakykyawan matsayi." Anty
Laurat ta ƙare maganan cikin rawar murya,kafin ta juya ta fice daga ɗakin don zuwa kiran
Likita,wanda yace da zaran TAIMIYYAN ta farko a kira shi.
TAIMIYYAH ta kifa kanta a jikin Yasmeen tana kuka me motsa Zuciya.Ji take yi a lokacin ina ma
Allah zai ɗauki ranta ita ma tabi su Abie ɗin,wani abu me tsananin nauyi ne ya danne
Zuciyanrta,kukan da take yi hawaye na zuba shine kaɗai ke rage mata ɗacin da take ji a
maƙoshinta.
Lokacin da Likitan ya shigo ma ƙin tashi tayi daga jikinYasmeen,sai da ƙyar da rarrashi sannan ta
tashi zaune,yai abinda zai yi ya fice yana cewa Anty Laurat ta bishi office.
A hankali ya taka zuwa bakin gadon da TAIMIYYAH ke kai,ta haɗe kanta da guiwa tana cigaba da
rasgar kuka.Qamshin turaren BENTLEY data shaqa yasa ta saurin ɗago kai ta sauke manyan
idanunta,da zuwa yanzu suka qanqance sukai jajir sabida kukan data kasa dainawa.
Ya zauna daga bakin gadon idanunsa na kanta,Zuciyansa na wani irin matsanancin suya.Tausayin
TAIMIYYAH na zama marainiyan da ba Uwa ba Uba na sake danne Zuciyarsa,ya kai hannu ya
riƙo na TAIMIYYAH idanunsa na sake rinewa.Cikin wani irin murya da bai fita sosai ya fara
rarrashinta,amma memakon tai shiru kaman yadda yake fata,sai kawai ta faɗa jikinsa da dukkanin
sauran kuzarin da ya rage mata,ta saki wani sabon kukan me tsuma Zuciya da raunata Zuciyan duk
wani me saurarenta.
Yah Sadeeq bai yi ƙasa a guiwa ba wajen rungumarta da kyau,yana ji tamkar ya tsaga ƙirjinsa ya
sanya ta ciki.TAIMIYYAH cikin muryan kukan take faɗin "Yah Deeku su Abie sun tafi sun bar ni
ko? Shikenan ni yanzu bani da Uwa bani da Uba,bani da qannin da zan kalla inji daɗi,meyasa
mutuwa ba ta ɗauke ni ta bar su Nahar ba.....?" Kuka ne ya ci ƙarfinta har ta kasa cigaba da
maganan,Sadeeq da ke shafa bayanta hawaye na sauka daga idanuwansa,kamar yadda kaf su
Yasmeen, dake cikin ɗakin su ma kukan su ke taya TAIMIYYAH.
Hatta da Yaseer juya baya yayi yana rufe idanunsa da hanki,yana kukan wannan zazzafan rashi da
ya riske su a yau.Yah Sadeeq ya buɗe baki cikin rawar murya ya ke faɗin "Baby kiyi haƙury,su
Abie addu'a su ke buƙata daga gareki da mu baki ɗaya,kowa da kike gani zai mutu ya tarar da
su,kiyi haƙury kiyi haƙury Zaynab....!!!" Daga haka ya kasa cigaba da faɗin komi,sabida idan ya
cigaba da forcing kansa sai ya rarrasheta da baki,to tabbas shi ma kukan zai fashe da shi.Sai ya
cigaba da rungumarta a jikinsa yana shafa bayanta,ita kuma TAIMIYYAH ta cigaba da sauke
ajiyan Zuciya,ƙirjinta na sake yin nauyi tamkar an danne shi da dutse,
TAIMIYYAH tayi tambayar cikin disasheshshen murya.Yah Sadeeq ya yi ƙasa da kansa wajen
kunninta yana faɗin "Iyah tana gida tana fama da masu ta'aziyyah,amma hankalinta na kanki
Zaynab,kiyi haƙury Allah ya bamu dangana mu da ke baki ɗaya." Ya ƙare maganan yana son ɗago
fuskanta daga jikinsa,amma TAIMIYYAH sai ta sake shigar da kanta ƙirjinsa,tare da sake jefa
masa tambayan ina Ummie ta ke ita ma? Yah Deeku ya sake ƙasa murya yana sanar mata da cewa
Ummie tana Kaduna anyi admitting ɗinta a wani asibiti,tun bayan da aka sanar da ita mutuwan su
Abie ta faɗi bata san inda kanta ya ke ba har kawo yanzu.
TAIMIYYAH na jin hakan sai ta sake fashewa da wani sabon kukan,da ƙyar aka samu tayi shiru
kuma har lokacin tana jikin Yah Sadeeq ɗin, wanda yake jin wani irin tausayinta na narkar da
zuciyarsa.
Likita ne ya sake shigowa ya gwada BP ɗinta,cikin sa'a jininta kaɗan ne ya hau bai yi hawan da
zai zama illa a gareta ba.Yai ma TAIMIYYAH wasu ƴan tambayoyi amma sam bata ba shi amsan
ko ɗaya ba,sai ya rubuta magungunan da za a siya wanda zata yi amfani da su,yana sanar da su
cewa za su iya tafiya gida,tunda babu wani matsala sai na damuwan da take ciki.Ɗumin jikin ma
da Yah Sadeeq yai complain,sai likita yace masa kukan da take yi ne ya kawo ɗumin jikin,da zaran
an samu ta ci wani abu ta sha magunguna ɗumin jikin ma zai tafi.
Yah Sadeeq ya amshi takardan Magungunan da aka rubuta,ya fita zuwa Pharmacy ɗin cikin
asibitin ya siyo,lokacin da ya fito daga ɗakin sai da Magungunan, ya samu har su Yasmeen sun
fito.Anty Laurat ce ke riƙe da hannun TAIMIYYAH har zuwa wajen mota,suka buɗe back seat ta
shiga ciki suma suka shiga ita da Yasmeen,Yaseer kuma ya shiga front seat.Yah Sadeeq da xai yi
driving ya shiga mazaunin driver,bayan ya miƙawa Yasmeen ledan Magungunan,yana jaddada
mata cewa lallai suna isa gida,ta tabbatar TAIMIYYAH ta ci wani abu an bata magungunan.
Lokacin da su TAIMIYYAH suka iso gida.Yasmeen ce ta riƙe hannunta har suka isa Sasan Iya,ita
Anty Laurat Sashin su Umma ta nufa,domin dare ya fara yi don tara har ta wuce.
Da sallama suka isa cikin falon Iyah,wanda yake ɗauke da ƴan uwanta na kusa da suka zo.Sai
wasu daga cikin ƴan Rimi da za su kwana nan,gaba ɗaya sai idon kowa ya dawo kan
TAIMIYYAH da suna sanyo kai falon Iyah,ta ga mutane ta fashe da kuka.
Iyah ta taso da sauri ta iso gaban su TAIMIYYAN tana kama hannunta,suka nufi ɗakinta kai tsaye
wani abu me tauri na sake danne zuciyar Iyah.Wacce tunda aka zo da gawan su Abie ɗin,har zuwa
sanda akai musu sutura ba a ga ɗigon hawaye a idanunta ba.
Zuciyanta yayi wani irin dakewa sai kukan zuci kawai take iya yi,wanda yafi na fiki ciwo.A yanzu
ɗin ma so take yi taji koda kaɗan ne hawaye sun zubo daga idanunta,kaman yadda TAIMIYYAH
ke iya kuka da hawaye,ta zaunar da TAIMIYYAH daga bakin gadon ta,tana zama itama kusa da ita
sosai hannunta har lokacin riƙe dana TAIMIYYAN.Cikin murya me cike da nuna tausayi da
rarrashi take faɗin,
"Zainabu kiyi haƙury,sannan kiyi tawakkali ki ɗauki dangana.Sameer sun riga sun tafi inda ba za
su dawo ba,kuka da nuna damuwa bazai sa su dawo garemu ba,addu'a kawai shine abu mafi
soyuwa da suke da buƙata daga garemu,musamman ke da kike matsayin ɗiyarsa da ya bari a doran
duniya.Don haka kiyi haƙury ki ɗauki dangana duka muma lokaci muke jira Zainab,tabbas mun yi
rashin da har abada ba zamu maida tamka ba,yau mun sake zama marayu na sosai da ba Uwa ba
Uba,amma hakan ba shi ke nuna cewa rayuwa ba za ta cigaba ba....."
Iyah ta ɗan numfasa tana jin shashsheƙan kukan da TAIMIYYAH keyi,wacce maganganun Iyan ke
sake karya zuciyarta,da sake tabbatar mata da cewa da gaske su Abie da su Nahar sun barta bari na
har abada.Iyah ta cigaba da cewa "Ina miki Nasiha da ki ɗauki dangana, kada ki saka damuwan da
zai janyo miki wata illa da ƙarancin shekarunki,kaman yadda kika rayu babu Uwa sai ni haka
yanzu ma zaki cigaba da rayuwa babu Sameer da ƴan uwanki,haka Allah ya tsaro cikin littafin
ƙaddararki Zainab,mu bamu isa canza komi ba nima haka nake rayuwa babu Uwa da Uba duk sun
rasu,kuma haka rayuwa ta cigaba min cikin godian Ubangiji da kaɗaitarwar sa.Don haka haƙury
da tawakkali tare da rungumar ƙaddara shine cikar imanin mumini Zainab,mu yi haƙury ina fata
Allah ya bamu ikon juriya da haƙuryn wannan rashi,ya ba Ummien ku dangana da ƙarfin Zuciyan
jure wannan rashi." Iyah ta kai ƙarshen maganan,wani irin ƙullutu na sake tokare maƙoshinta.
TAIMIYYAH tayi ƙarfin halin buɗe baki tana faɗin "Ameen Iyah,Allah ya jiƙan Abiee dasu
Raudha har da Mamana,Allah yasa suna aljanna...."
Kukan da ya sake ƙwace mata ne ya hanata cigaba da maganan.Ta kwantar da kanta a jikin Iyah
tana yin kukan sosai,a haka Yasmeen ta shigo ta samesu hannunta riƙe da Cup ɗin data haɗowa
TAIMIYYAH Tea yana turiri.Ta aje Cup ɗin daga bakin side drawer tana faɗin "Iyah har yanzu dai
kukan take yi? TAIMIYYAH don Allah kiyi haƙury kiyi shiru kukan yayi yawa.Addu'a ya kamata
ace kina musu ba wannan kukan ba,muma kina sake tayar mana da hankaline da wannan kukan da
yaƙi ƙarewa,don Allah kiyi haƙury yanzu ki tashi ki sha wannan tea ɗin,sai a baki magani daga
nan sai ki samu ƙarfin da zaki rama sallan Magriba da Isha'i da suka wuce ki."
Yasmeen ta ƙare maganan tana tayar da TAIMIYYAH daga jikin Iyah.Ganin hakan yasa Iyah
zamewa ta bar musu ɗakin,tausayin TAIMIYYAH na sake kama Zuciyarta.
*30minutes Later.*
TAIMIYYAH ce zaune daga ƙasan carfet ɗin ɗakin Iyah.Yasmeen na zaune itama kusa da ita,sun
tasa plate ɗin tuwan Semo da miyan Kukah a gaba,wanda Yasmeen ɗin ta zubo musu,wai ko zasu
iya ci amma daga TAIMIYYAN har ita da ƙyar suka iya yin loma uku uku.Wayan TAIMIYYAN
ne da ke kusa da ita ya fara ringing,wanda Yasmeen ce ta ɗakko mata wayan daga ɗakinsu ta kawo
mata nan,ganin Nass ne me kiran yasa TAIMIYYAH turawa Yasmeen wayan tana mata alamu da
hannu akan ta ɗauka.Don sam TAIMIYYAH ji tayi bata son yin magana da kowa ma,duk wanda
suka shigo yi mata gaisuwa da kai kawai take iya amsa musu.
Yasmeen tayi receiving call ɗin tana kai wayan kunni,ta fara da amsa sallaman Nass ɗin.Kafin ta
ɗaura da sanar da shi mummunan rashin da TAIMIYYAH tayi a yammacin yau ɗin,daga haka ta
miƙawa TAIMIYYAH wayan bayan Nass ɗin ya gama yi ma su Abie ɗin addu'an samun Rahama a
wajen Allah.
TAIMIYYAH ko data amsa wayar kara shi kawai tayi a kunni,ba tare da tace uffan ba sai ma wasu
hawaye dake taruwa a idanunta.Har Nass ya gama yi mata ta'aziyyah taƙi buɗe baki tayi masa
magana,daya matsa mata ma sai ta sanya masa kuka kawai,abinda ya ɗaga hankalinsa sosai yana ji
kaman yai tsuntsu ya ganshi a Zaria,domin yana buƙatan ganin halin da take ciki.Sai dai duk iya
yadda zai kai ga son ganinta dole ya jira sai zuwa Thursday,sannan ya samu ya yi squeezing
shigowa Zarian,tunda bai jima da komawa bakin aiki daga hutun da ya ɗauka ba.
Da ƙyar TAIMIYYAH ta yadda ya maida kiran ta vid call,ta yadda zai fi samun nutsuwan
rarrashinta idan yana kallon face ɗinta.Ya jima sosai yana kwantar mata da hankali da kawo mata
misalai na waɗanda su ka rasa iyayensu,ciki har da shi da shima Mahaifinsa ya rasu tun yana
Secondary Skull,sai Mamansa kawai da Yayyinsa mata da ke gidajen aurensu suka rage masa,sai
Qanin Babansa daya maye masa gurbin Uba a yanzu.TAIMIYYAH dai ba umm! ba umm-umm!
Tana dai sauraran Nass ne kawai amma bata ji cewa Zuciyarta zata daina ciwo akan wannan rashi
da tayi har sai ranan da nata mutuwan ya zo.
A ƙallah sun ɗauki tsayin 30minutes kafin Nass yai hanging up! TAIMIYYAH ta sauke wayan
daga kunni,tana me lumshe idanunta sabbin hawayen da suka taru suka samu daman zubowa.A
lokacin ne kuma sallaman su Zuhurah ya doki kunnuwan su,suka ƙariso cikin ɗakin Iyan suna
zubewa a gaban TAIMIYYAH,su kai mata gaisuwa kowacce a cikin su idanunta yayi jawur,da
alamu su ma sun sha kuka ba kaɗan ba.TAIMIYYAH kai kawai ta iya jinjina musu,daga haka su
ka tashi su kai wa Yasmeen sai da safe suna barin ɗakin.
Umma ce itama ta shigo bayan fitan su Zuhuran,ta zauna a kusa da TAIMIYYAN tana mata
ta'aziyyah.Karon farko data ji tausayin TAIMIYYAN ya ɗan taɓa zuciyarta kaɗan,ita ma ɗin dai
TAIMIYYAH kanta kawai ta iya gyaɗa mata ba tare da tayi magana ba,hakan yasa Umma tashi ta
baro ɗakin,Yasmeen na mata sai da safe.
Salati sosai ta saki a lokacin da Yasmeen ta bata tabbacin rasuwan.Sai Yasmeen ta miƙawa
TAIMIYYAH wayan,ta amsa murya a shaƙe taiwa Antyn nata sallama,Anty Mardiyyah ta amsa
daga ɓangarenta,tana wa TAIMIYYAH ta'aziyyah cike da alhini.TAIMIYYAH ta sakin mata kuka
me taɓa Zuciya,nan ta dinga aikin lallashi tare da tabbatar wa TAIMIYYAN cewa zuwa jibi zata
iso Insha Allah.Daga haka sukai sallama da juna TAIMIYYAH na jifa da wayan bisa kan Bed,basu
bar ɗakin Iyah ba sai wajen 11:30pm,sannan suka koma ɗakinsu zuwa lokacin babu motsin kowa,
duk mutanen da za su kwana sun yi bacci.
A kan idanun Iyah su TAIMIYYAH suka fito zuwa ɗakin nasu.Iyah na zaune daga can ƙarshen
kujeran falon, tana faman jan Carbi gaba ɗaya idanunta a ƙyaƙashe suke,babu alamun bacci zai
samu mata a daren yau ɗin,ganin su TAIMIYYAN sun baro mata ɗakin ne yasa ta miƙewa ta isa
ɗakin nata.
Kusan zan iya cewa tsakanin Iyah da TAIMIYYAH,har zuwa kan Baba Sani da Sadeeq babu
wanda ya iya rintsawa a daren,sai dai bacci da ake cewa ɓarawo.Wanda duk iya satansa ya kasa
sace idanun Iyah da TAIMIYYAH,yadda suka ga rana haka suka ga dare,domin da zaran sun kulle
ido fuskan Abie ɗin suke gani da su Nahar.Daga ƙarshe ma kaman haɗin baki sai suka yankewa
kansu shawaran ɗaura alwala,sukai ta sallah suna roƙon Allah ya basu juriya da dangana,tare da
roƙa ma Mamatan gafara.
Washegary kan ace kwabo gida ya cika damƙan da jama'a,ƴan zaman makoki duka ƴan uwa na
kusa dana nesa sun bayyana.Ciki har da Guggo Bilki da Bakwai na safe ma a Zaria yai mata ita da
Abban su Yasmeen ɗin,tare da yayyin Yasmeen ɗin Maza Samari su huɗu,don duk yaranta Maza
ne Yasmeen ita kaɗai ce mace,kaman yadda Guggo Bilkin ita kaɗaice mace a gun Iyah.
Hatta da qawayen TAIMIYYAH su Maryam Sunusi,da su Zee duka babu wacce bata zo mata
gaisuwa a yau ɗin ba.Kuma dukansu sun tausayawa TAIMIYYAH wannan Babban rashi da tayi,
na rasa Uba da Qanni duk a lokaci guda.
Nass ma duk bayan awa ɗaya sai ya kira yayi magana da TAIMIYYAH na sake kwantar mata da
hankali.Hakan kuma ba ƙaramin tasiri yayi wajen sanyawa TAIMIYYAN nutsuwan Zuciya da
dangana ba,duk da cewa idanunta basu fasa zuban hawaye ba,sai dai ba a zo gabanta da sunan yi
mata ta'aziyyah ba.
A ɓangaren Ummie da ke can Kaduna a Asibitin GARKUWA Kaduna,har lokacin bata farfaɗo ba
daga dogon suman da tayi.Shiyasa a yau ɗin su Baba Sani da wasu cikin mata ƴan Family ɗin
Abie ɗin suka nufi Kadunan dubo ta,basu dawo ba sai wajen Zuhur Prayer,suka cigaba da zaman
amsan makoki har zuwa yamma inda kowa ke kama gabansa daga an kira Sallar Magriba.Sai ƴan
uwa na nesa da za su yi ta kwana har sai anyi Uku sannan za a watse zaman makokin,sai dai na
jikin Mamatan kawai da za su yi a ƙallah kwanaki bakwai kafin a watse........✍🏻
Littafin TAIMIYYAH paid book ne,ga duk wanda ta tsincesa a kowani irin group ne,kiji tsoran
Allah karki karanta sai kin biya 500 naira only.
Za ku iya min magana ta wannan number ɗin 08167768704, ko kuma ku turo kuɗin ku kai tsaye ta
wannan account ɗin 0504192664 aisha ibrahim dansabo GTbank.*
Masu turo credit za ku turo katin MTN na 500 ta wannan line ɗin 08167768704.
#Ɗansabo ce#
[12/14, 3:42 PM] +234 703 040 9541: *33*
Ranan da su Abiee ke da kwana uku da rasuwa,ranan aka iso da Ummie zuwa Zaria,wacce sai a
ranan da Abie suke da kwana biyu aka sallameta daga asibiti.
Faɗin irin mummunan yanayin da take ciki ma bazai faɗu ba,don haka sai mutuwan ya dawo sabo
a lokacin da ƴan uwanta suka iso da ita cikin gidan.
Sasan Iyah su ka fara sauka kafin daga nan a wuce da Ummie Sasan su dasu ke sauka duk idan sun
zo garin,wanda a yau da safe aka sanya Babah Ladi ta gyare shi tsaf.
Kwanaki biyar da rasuwan ya kama Thursday ranan ne kuma Nass ya baro Abuja zuwa
Zaria.Ƙarfe huɗu da wasu ƴan mituna motarsa ta tsaya a ƙofar gate ɗin gidan,yayi mamaki da
babu kowa sai tsirarun mutane masu shiga su fita.Don tun randa akai addu'an uku aka dakatar da
zaman makokin,sabida bai da wani anfani in banda zaman gulma da yi da mutane ba abinda ake
yi.
Hakan yasa Iyah ta sanar da Baba Sani adakatar da mutane kawai,sai dai a shigo a fita idan anyi
gaisuwa ya wadatar.
Nass ya ɗaga wayansa yana dialling number ɗin TAIMIYYAH,bugu biyu ta ɗaga wayan cikin
muryanta da a ƴan kwanakin ya sake komawa very low.Bayan ya amsa gaisuwanta ne yake sanar
ita cewa gashi daga bakin gate ko zata fito? TAIMIYYAH ta sauke numfashi tana faɗin,
Daga haka ta sauke wayan daga kunni,tana duban Yasmeen dake kan gado tana faman danna waya
ta furta, "Yasmeen ga Nass nan fa a waje ya iso."
Yasmeen ta aje wayan hannunta tana faɗin "Okey tuh sai ki saka Hijab ki fita,in yaso sai ki shigo
da shi har Iyah yaiwa ta'aziyyah ko?"
Yasmeen tayi maganan idanunta akan TAIMIYYAH,wacce ta nufi wajen kayanta tana ciro
gogaggen Hijab ɗin da zata saka.Sanye take dama da doguwar riga mara nauyi,fuskanta ya rame
kaɗan sabida yawan tunani da zafin mutuwan da ke dukanta.Don ma Iyah ta saka an rubuce musu
Qur'ani tas an wanke suna shan ruwan kullum safe da yamma,hakan kuma ba ƙaramin dangana da
nutsuwa ya samar a zukatansu ba.Domin Qur'ani maganin duk wata irin damuwa ce kuma
warakace daga dukkanin wani ƙunci na rayuwa.
TAIMIYYAH ta sanya Hijab ɗin wanda tsayinsa ya wuce guiwanta da kaɗan.Kalan Hijab ɗin
Army Green ne dark wanda ya haske farar fatarta,yai mata kyau sosai sai ta zura Flat Shoe ɗinta
na Dior,ta dubi Yasmeen tana faɗin "Mu je Yasmeen kinsan dai bazan iya fita in shigo da shi ni
kaɗai ba."
Yasmeen bata ce komi ba ta sakko daga kan gadon,ta ɗauki Hijab ta sanya suka fito don zuwa
wajen Nass ɗin.A falo suka samu Iyah da wasu baƙi uku da suka shigo gaisuwa,sai Guggo Bilki da
wata Innar Iyah dake nan su sai anyi Bakwai za su tafi.Yasmeen ta dubi Mamien nasu tana sanar
da ita inda za su,Guggo Bilki ta jinjina kai kawai daga haka suka fice Iyah na bin bayansu da
kallo.
A tsaye suka tadda Nass ya ginjina da jikin motarsa,yana sanye cikin riga da wando na fararen
Shadda da sukai masa kyau matuƙa.Kansa babu hula sai ƙwantaccen Sumansa da kallo ɗaya zakai
ma gashin kasan yana cin kuɗi ba kaɗan ba,idanunsa akan TAIMIYYAH ya ke tunda suka doso
wajen da yake tsaye.Bayan sun gaisa da Yasmeen ne sukai masa jagora zuwa ciki,Sasan Iyah suka
fara isa da shi yayi mata gaisuwa tare da su Guggo Bilki.Kafin daga nan su nufi falon Baba
Sani,don Iyah tace su raka shi yai masa ta'aziyyah tunda yana nan.
Ita dai TAIMIYYAH ƙin binsu tayi zuwa Sasan Baba Sanin,tace Yasmeen ta kai shi ita zata jira su
a waje.Hakan ko akayi Yasmeen ɗin ce tayi ma Nass ɗin jagora har zuwa falon Baba Sanin,amma
bata yarda ta shiga ba ta tsaya daga waje.
Nass ya shige ya tsuguna har ƙasa ya kwashi gaisuwa tare da yin ta'aziyyah,Baba Sani amsa yana
tambayansa daga ina yake? Nass ya bashi da cewa daga cikin gari yake Ƙwarbai.
Daga haka Baba Sanin bai sake cewa komi ba Nass yai masa sallama ya fito,Yasmeen ta sake
masa jagora zuwa Sasan Ummie ita ma yai mata gaisuwa,sannan suka fito suna dosan inda
TAIMIYYAH take zaune kan ɗaya daga cikin fararen kujerun da Tukur ya aje musu.
Nass ne yaja kujeran dake facing TAIMIYYAH ya zauna,idanunsa akanta yake fes lokacin da yake
faɗin, "My Zee-zee Allah ya ƙara mana haƙury da juriyan rashin su Abie,amma don Allah Baby ki
rage tunani kin ga har kin rame a fuska,kuma ki dinga daurewa kina cin abinci sosai kinji luv?"
Yadda yake maganan cike da kulawa, yasa TAIMIYYAH ta ɗago manyan idanunta ta sauke
akansa.Murya a shagwaɓe take faɗin "Insha Allah! Nagode da kulawa."
Ta ƙare maganan tana kawar da face daga gare shi,ganin irin kallon ƙaunan da yake jifanta da shi
kaman sunyi shekara basu ga juna a zahiri ba.Nass ya sake ƙasa da murya yana faɗin, "Ni bana
son wannan kunyan Luv ki ɗago kawai ki kalli Babyn ki, na san kema kinyi missing ɗina a lot."
Ya ƙare maganan yana son su haɗa ido amma sai TAIMIYYAH tayi saurin kai hannu ta rufe face
ɗinta,tana sakin murmushi.
Yasmeen dake tsaye gefe guda tana danna waya ta saki murmushi kaɗan,lokacin da Nass ya juyo
gareta yana faɗin, "Sis bari in zo in wuce zuwa gida,zan dawo gobe Insha Allah,ki kula min da
Gimbiyar tawa please!"
Yasmeen tayi murmushi tana faɗin, "An gama karka ji komi zan kula maka da ita tamkar egg."
Suka saki ƙaramin dariya dai-dai lokacin dasu Zuhurah ke fitowa daga Sasan Iyah,wasu mata na
biye dasu abaya da alamun sunyi musu rakiya ne su kaiwa Iyah gaisuwa.
Hango su TAIMIYYAH da wani a zaune yasa Zuhurah duban Basmah da itama hankalinta ya tafi
kan su TAIMIYYAN tana faɗin, "Basmah mu ƙarisa mu ga wannan Guy ɗin da Anty Laurah ke
zuzuta shi ne halan."
Daga haka suka nufi wajen su Yasmeen ɗin,idanunsu akan su TAIMIYYAH da suka juya musu
baya.Yasmeen ce da ke tsaye kawai take facing ɗin su Zuhuran,don haka akan idanunta suka
ƙariso wajen.Zuhurah na faɗin "A'a Yasmeen kune anan shiyasa muka ji shiru da muka shiga
Sasan Iyah,mun raka Friends ɗin Umma su yi mata gaisuwa."
Zuhurah ta ƙare maganan tana satan kallon su TAIMIYYAH,wanda da alama basu ma ankara da
tsayuwan su Zuhurah a wajen ba,sai da Yasmeen ta furta, "Eh wallahi,Saurayin TAIMIYYAH ne
yazo yiwa su Iyah ta'aziyyah,shine na raka shi har wajen Ummie da Baba Sani,ku matsa ku gaisa
mana."
Yasmeen tayi maganan tana kallon yadda Basmah ta tsare Nass da ido.Dai-dai lokacin da suka
waiwayo a tare shi da TAIMIYYAH,Zuhurah ta ƙarisa wajen tana faɗin, "Sannu ina yini anzo
lafiya?" Nass ya amsa da "Lafiya lau ya ƙarin haƙurin mu,Allah yai musu rahama ya kyautata
namu zuwan."
Duk suka amsa da "Ameen." Gaba ɗayansu har TAIMIYYAH,Basmah ta gaishe da Nass tana wani
faman maƙe murya.Ya amsa ba yabo ba fallasa daga haka Yasmeen tai masa bayanin cewa,su
Zuhurah Cousines ɗin TAIMIYYAH ne.
Sai ya jinjina kai kawai ba tare da yace komi ba,don haka kawai kallon da Basmah ke faman binsa
da shi yake bashi haushi.Sai ya miƙe yana duban TAIMIYYAH yake cewa "Luv zan wuce sai mun
yi waya,don Allah ki daure ki dinga cin abinci Baby please! Banda yawan tunani kinji ko?"
TAIMIYYAH ta shagwaɓe face murya can ƙasa take faɗin, "Insha Allah,ka gaida su Mama
nagode."
Nass da yake jin wani irin feeling na sake fisgansa akanta,ya ɗan lumshe ido ya buɗe akanta,kafin
ya maida dubansa ga Yasmeen da su Zuhurah yana faɗin, "Hey! Sisis zan wuce bye bye."
Yasmeen tai masa Allah tsare ya nufi hanyan gate,suna bin bayansa da kallo barin ma Basmah da
duk haɗuwan Nass ɗin ya gama sace zuciyarta.
Ji take yi wani abu na malting cikin zuciyarta,tayi saurin maido dubanta kan TAIMIYYAH lokacin
da Nass ɗin ya ɓacewa ganinta tana faɗin, "Wow! Gaskiya Yah TAIMIYYAH guy ɗinnan ya
haɗu,ba ƙarya Anty Laurat ke yi ba,ke ko a ina kika samo sa?"
TAIMIYYAH ta ƙare maganan tana fara takawa don barin wajen ma baki ɗaya.Hakan yasa
Zuhurah taɓe baki tana ballawa Basmah hararan meyasa taiwa TAIMIYYAH magana akan Nass
ɗin.
Yasmeen da itama takaicin Basmah ya cika zuciyarta tun kallon da take ta jifan Nass ɗin da shi, ji
tayi kaman ta kwaɗe Basman da mari,ta dubi su Zuhuran tana faɗin, "Bari mu koma daga ciki
Zuhurah muna dai ta kewan tafiyan Anty Laurat wallahi,su Mama dai basu kyauta ba da suka
matsa sai sun tafi da ita."
Zuhurah ta kyaɓe baki tana faɗin, "Wallahi muma ta bamu kewa,amma idan Umma ta je bikin da
zasu yi a Yoben next month zasu taho tare ai."
Daga haka su Zuhurah suka nufi hanyan komawa Sasan su,ita kuma Yasmeen ta juya tabi bayan
TAIMIYYAH wacce tuni ta kai Sasan Iyah ma.
"TAIMIYYAH kin ga kallon da mara kunyan yarinyan can kuwa ke bin Nass da shi?" Yasmeen ta
jefawa TAIMIYYAH tambayan lokacin da suka dangana da ɗakinsu.
TAIMIYYAH dake ninke Hijab ɗin data cire ta dubi Yasmeen ɗin tana faɗin, "Na gani
Yasmeen,baki ji ma tambayan rainin wayan da tai min bane ,wai ina muka haɗu hmm!"
TAIMIYYAH ta kai ƙarshen maganan cike da takaici,tana aje Hijab ɗin data gama ninkewa akan
gado.Dai-dai lokacin da kira ya shigo wayarta,ganin Anty Mardiyyah ne yasa ta ɗagawa,suka
gaisa.TAIMIYYAH tana tambayanta gajiyan hanya,don jiya suka juya daga Zarian sun zo sunyi
gaisuwa har da mijinta,hatta da dangin Maman TAIMIYYAH da ke garin Daura duk sun zo
gaisuwa cike da mota.
Bayan sun gama magana da Anty Mardiyyan ne, TAIMIYYAH ta aje wayan tana duban Yasmeen
take faɗin, "Yasmeen inata so in tambayeki me Baba Sani yace da kika raka Nass wajensa,ko baki
shiga ba a waje kika tsaya?"
Yasmeen ta dubi TAIMIYYAH tana murmushi ganin yadda TAIMIYYAN ta wani narke face,kafin
ta furta "Ina fa na shiga daga waje na tsaya in gaya miki,amma dai ina jiyo sa yana tambayan Nass
daga ina yake.Nass ɗin ya sanar dashi sunan anguwan su,daga haka bai sake tambayansa komi
ba."
TAIMIYYAH sai ta sauke ajiyan zuciya tana faɗin, "Thank God,wallahi sam bana so Baba Sani ya
san da maganan Nass a yanzu,sai zuwa gaba kaɗan."
Cewan TAIMIYYAH cike da shagwaɓa,Yasmeen ta aika mata harara tana faɗin "Matsoraciya, to
miye abin rashin son ya sanin tunda dai kina son abinki,ko kina tsoran yace ya fito da wuri ne asa
rana mu sha biki?"
TAIMIYYAH ta aikawa Yasmeen harara tana faɗin "Ko ba ku sha biki ba..! Ke wallahi ƴar rainin
wayau ce Yasmeen ɗinnan."
Yasmeen dai dariya kawai tayi,tana yin gaba ta shige toilet don yin fitsarin daya cika mata
mara.TAIMIYYAH sai ta ɗauki wayanta tana kiran layin Anty Laurat,wacce ta tafi tun
shekaranjiya dasu Mamansu suka zo gaisuwa,sai suka tafi tare da ita.Sun daɗe suna magana Anty
Laurat na sake kwantar da hankalin TAIMIYYAH da cewa ta rage tunani ta dinga cin abinci
kuma,don tunda akai rasuwan bata cin wani abincin kirki sai an matsa mata.
Daga ƙarshe sukai sallama TAIMIYYAH na sauke wayan daga kunninta,memakon ta aje wayar sai
ta shiga ma'ajiyar adana hotuna tana kallon pics ɗinsu Nahar.Hawaye na biyo fuskarta yana sauka
akan jikinta,wani irin kewansu take ji na sake baibaye zuciyarta,lokacin data buɗo pic ɗin Abie
kuwa bata san lokacin data fashe da kuka ba.
A haka Yasmeen ta fito ta samu TAIMIYYAH tana kuka sosa,sai ta zauna aikin rarrashi har zuwa
lokacin da TAIMIYYAN ta tsaida kukan tana faman sauke ajiyan zuciya akai-akai.
A can Sasan su Zuhurah kuwa,Zuhuran ce zaune ita da Basmah a cikin ɗakinsu.Basmah ta dubi
Yayarta tana faɗin "Yah Zuhurah a gaskiya Guy ɗinnan ya haɗu fa,ke kinji yadda yake magana
cike da aji,daga gani ɗan boko ne da yasan kan gayu.Wallahi farat ɗaya naji ya shiga raina,shi ko
yana da wannan haɗuwan ya tsaya kula gurguwa? Anya ko ba kyawunta kawai ke jansa ba,ko
kuma sha'awanta ke fisgansa yana son cimma wata manufa akanta,amma in ba haka ba mi zai ci
da gurguwa alhali ga lafiyayyun ƴan mata,da suka mallaki komi na cikar halitta,amma dai zamu
zuba ido mu ga yadda lamarin zai kasance."
Basmah ta kai ƙarshen maganan tana ji ina ma ita Nass yace yana so ba TAIMIYYAH ba! Zuhurah
da itama zuciyarta ke cike da mamakin wannan lamari,ta taɓe baki tana faɗin "Wallahi Basmah
nima sanƙamewa nayi kawai a tsaye,don duk kwarzanta shi da Anty Laurat ke yi ban ɗauka
haɗuwansa ya kai haka ba,to ai wannan ya ma fi Yah Sadeeq haɗuwa da komi.Ita kuma makiran
baki ga wani narke masa da take yi ba,shi kuma duk ya wani susuce yana faman bin ta da mayen
kallo,wallahi TAIMIYYAH ba ƙaramar shu'uma bace Allah ne ma kaɗai yasan meyasa ya maida
ita gurguwan ma."
Zuhurah ta ƙare maganan cike da jin kishin TAIMIYYAN na sukan zuciyarta.Basmah kuwa sai
cewa tayi "Ai Insha Allah wannan guy ɗin sai ya suɓuce mata,ba za ta taɓa auren kaman wannan
alhali mu gamu lafiyayyun ko saurayin bamu da shi,gara ma ke kin kama Ameeru a hannu
mitsuuw...!" Yadda Basmah ta ja tsaki kaman zata tsinke harshe yasa Zuhurah sakin dariya tana
faɗin "Easy Sis ki kwantar da hankalinki ke ma zaki samo mana Handsome guy Soon."
Suka ɓarke da dariyan shaƙiyanci,kafin su kamo wani zancen amma sam Nass yaƙi ɓacewa a
zuciyan Basmah,wani irin feeling take ji akansa na fisgan zuciyarta,gefe guda tana sake jin tsana
da kishin yadda TAIMIYYAH ke kere su a komi tamkar ba Musaka ba....!
Ranan da akai addu'an Bakwai a ranan Guggo Bilki ta koma Kano,ta so ƙwarai su tafi tare da
Yasmeen,amma sai TAIMIYYAH ta sanya mata kuka akan ta bar Yasmeen ɗin ta sake wasu
kwanaki.Iyah ma sai ta goyawa TAIMIYYAH baya akan abar Yasmeen ta zauna,tunda ita ke sake
kwantar ma TAIMIYYAH da hankali da ɗebe mata kewa.Hakanan Guggo Bilki ta koma cike da
alhinin wannan rashi da suka yi me tsananin zafi da ciwo,wanda har abada ba zasu mance ba.
Ummie ita ma dukkanin ƴan uwanta sun tattara sun tafi,sai ita kaɗai da wata Innarta Dattijiya da
aka bari ta zauna da ita.Ranan gaba ɗaya gidan kowa sai daya zubda hawaye, mutuwan ya sake
dawowa sabo,sabida yadda Ummie da TAIMIYYAH ke faman kuka tamkar ranan ne akai
mutuwan.Da ƙyar aka samu sukai shiru ana sake musu nasiha akan muhimmancin tawakkali da
yadda da ƙaddara.
Iyah ce da kanta ta sake sawa akaiwa Ummie saukar Qur'ani a rubuce aka wanke tana shan
ruwan.Tausayinta sosai Iyah ke ji don tasan cewa babu wanda zai kaita jin zafin wannan rashin,ko
ita data kawo Sameer duniya ba zata ce tafi Ummie jin zafin rashinsa ba.
Haka kwanaki suka cigaba da shurawa,su Baba Sani duk suka koma bakin aikinsu ranan
Monday.Sai kuma a ranan TAIMIYYAH ta sake sanya Yah Sadeeq a idanunta,lokacin daya
shigowa yiwa Iyah sallama,sai yasa Yasmeen tai masa kiran TAIMIYYAN.Yana me sake mata
nasiha akan ta kwantar da hankali tayi dangana,shima Baba Sani haka ya tasa TAIMIYYAN a
gaba yayi na shi lallashin da nasiha kafin ya tafi...
Kwanakin da suka biyo baya duk su TAIMIYYAH sun yi shi ne cikin tarin kewa,da alhinin rashin
su Abie ɗin,wanda kullum kwanan duniya ta kwanta bacci sai tayi mafarki da su,takan farka cikin
dare tai ta salloli tana roƙon Ubangiji ya bata juriya da dangana ita dasu Ummie da Iyah,kuma a
hankali ta fara samun nutsuwan zuciya da dangana.......✍🏻
Littafin TAIMIYYAH paid book ne,ga duk wanda ta tsincesa a kowani irin group ne,kiji tsoran
Allah karki karanta sai kin biya 500 naira only.
Za ku iya min magana ta wannan number ɗin 08167768704, ko kuma ku turo kuɗin ku kai tsaye ta
wannan account ɗin 0504192664 aisha ibrahim dansabo GTbank.*
Masu turo credit za ku turo katin MTN na 500 ta wannan line ɗin 08167768704.
#Ɗansabo ce#
[12/14, 3:43 PM] +234 703 040 9541: *34*
*Cairo, Egypt.*
Yau kwanan su A.Maleek uku kenan da isowa ƙasar Cairo wato ( Egypt).Sun sauka ne a wani New
City cikin wani haɗaɗɗen building wanda akai renting ɗinsa da kuɗi masu nauyi.
Single Bedroom ne da babbar falo haɗe da Kichen sai toilet makeke da ke manne cikin Bedroom
ɗin.
Daga yanayin yadda aka tsara ginin gidan da yadda a ka ƙawata ɗakunan,za ka fahimci cewa kama
irin waɗannan wajen sai Manyan ma su Kuɗi.Don ba ƙaramin tsaruwa gidan ya yi ba musamman
yadda aka tsara ɗakunan da kayan more Rayuwa ma su asalin kyau da nauyin kuɗi.
Daga cikin Bedroom ɗin Suhailah ce kwance a jikin Maleek Ado wanda ya ke amsa waya cikin
harshen Nasara.Hannunsa ɗaya na shafa gashin kan Suhailah wanda bata jima da busar da shi
ba,ya sauke wayan daga kunninsa lokacin da ya kammala amsa call ɗin,manyan idanunsa na sauka
akan gashin da ɗaya hannunsa ke kai.Cikin ƙasaitacciyar muryarsa yake cewa, "Wife zuwa anjima
kaɗan Sunusi zai ƙariso ina so mu kammala da Asibitin a yau, zuwa gobe sai mu fara zagayawa
wuraren buɗe ido."
Suhailah ta ɗago idanunta ta sauke akan Maleek kafin ta ce "To Allah ya kai mu anjiman My
Maleek,jikina ya riga da yayi sanyi tun bayanan da likitar tayi jikina na bani na riga na aikata
babban kuskure cikin rayuwata,tunda kaf sakamakon gwaje-gwajen da aka yi babu wanda bai
nuna cewa mahaifata bata samu matsala ba.Ka ga kenan duk wani hope da za a bani na cewa komi
zai iya komawa normal zuciyata ba za ta gamsu ba, har sai lokacin da na ganni ɗauke da ciki a
mahaifata Yah Maleek!"
Yadda Suhailah ta kai ƙarshen maganan tana sakin kuka tare da sake shigewa jikinsa.Ya sanya
Maleek lumshe idanunsa yana sake rungumarta da kyau,hannunsa na shafa bayanta alamun
rarrashi,kafin ya buɗe baki yana cewa "It's okey please! Kuka ba zai yi maganin komi ba
Suhailah,kuskure kin riga kin yi so sai ki rungumi dukkan ƙaddaran da zai biyo baya,har yanzu
kina da sauran hope idan har kin shaye magungunan da aka ce za a ɗaura ki akai,tunda ƙwararriyar
likitar ta bada tabbacin watakila kafin ma ki kammala shanye dose ɗin za ki iya ɗaukan ciki,kin ga
kenan akwai hope.Sai dai mu dage da addu'a tunda shi Allah ba a masa dole,zai iya bayar da rabon
a lokacin da muke saka rai,zai kuma iya hanawa har zuwa wani lokaci koda a ce kuwa komi ya
koma normal ɗin."
A.Maleek ya kai ƙarshen maganan yana share mata hawayen da ke zubowa daga
idanunta.Suhailah tayi lamo a jikinsa tana sauke ajiyan zuciya,wani irin nadama da dana-sanin
biyewa Zuby na sake kama zuciyarta.Sun jima a haka yana lallashinta da kalamai na kwantar da
hankali,don Maleek har cikin zuciyarsa ya ke jin tausayin Suhailan yanzu.Sabida yadda yake
hango tsananin nadaman da tayi a cikin idanunta,shi yasa yake sassauta fushinsa akan kuskuren da
ta riga ta aikata shi.Fushinsa ba zai sauya komi ba amma baya ji da zaran ta shanye magangunan
da za a bata ba a samu wani cigaba ba to dole zai ƙara aure,don da gaske yana buƙatan haihuwa....
Kamar yadda yace Sunusi ne zai zo ya fita da su,hakan ce ta kansance misalin 10:30am Sunusin
ya iso.Cikin wata dalleliyar mota irin wanda manyan masu kuɗi ke zirga-zirga a cikinta.Sunusi
wani yaron A.Maleek ɗinne da yawanci idan ya shigo ƙasar Cairo shi ke masa hidima,tun daga
kan kama masa wajen zama zuwa duk wani zirga-zirgan da zai yi,duk Sunusin ke driving ɗinsa da
yi masa wahalhalu.Sabida shi zaunannan ƙasar Cairo ne da yafi shekaru 15 yana zama cikin
ƙasar,amma ɗan asalin Nigeria ne Bahaushen Jihar Kwantagora.
Suhailah ta shirya cikin wata haɗaɗɗiyar Abaya,Blue Black da akai wa adon zane da golden ɗin
zare.Ta yane kanta da Veil ɗin Abayar wanda ya zagaye face ɗinta,tayi matuƙar yin kyau sai
sassanyan qamshin Turarenta na MISS DIOR da CARROLINA HERRERA ke tashi.
A.Maleek kuma yana sanye cikin wani haɗaɗɗen yadin Filtex Dark Brown me asalin kyau da
tsada.Anyi masa ɗinkin zamani da ya dace da jikinsa,haɗaɗɗan qamshin Turarensa na AMOUAGE
duk ya cika ɗakin.Suhailah ta ƙariso wajen da yake tsaye yana ƙoƙarin sanya Links na hannun
rigarsa,ta amsa tana sanya masa idanunsu na yawo a jikin juna.Ta cikin dogon mirrow ɗin da ke
kafe cikin Bedroom ɗin,ta gama sanya masa Links ɗin tana yin ɗage ta manna masa kyakykyawan
sumba a side face ɗinsa,murya ƙasa-ƙasa ta furta, "Luv u My Yah Maleek."
Maleek Ado ya saki ƙayataccen murmushin da ba kasafai ake gani akan fuskarsa ba.Ya ɗan
rankwafa dai-dai yadda zai iya manna mata kiss saman goshinta,ya sauke mata kyakykyawan kiss
a saman goshi,muryansa very deep yake faɗin "Luv u too sweet wife,and also My lil sis ever."
Suhailah da kalaman da ya kirata dasu su kai mata mugun daɗi.Sai ta lumshe ido ta buɗewa akan
face ɗinsa,kafin ta kai bakinta saman lips ɗinsa,tana sake bashi light kiss.A.Maleek ya tallafi
fuskarta da hannu ɗaya shi ma yana sake manna mata wani kiss ɗin a forehead ɗinta,kafin su fito
suna sarƙe da hannun juna.
Sunusi dake zaune cikin mota yana jiran fitowan ubangidan nasa,yana hango tahowan su yayi
saurin buɗe musu back seat.Idanunsa akan A.Maleek lokacin da suka ƙariso bakin motar ya furta,
"Ranka-ya-daɗe barka da fitowa,Madam mun tashi lafiya?"
Suhailah ta amsa masa gaisuwan shi kuma A.Maleek hannu kawai ya ɗaga ma Sunusin,yana me
gyara zama cikin motar.Sunusi ya rufe motar yana shiga driver seat ya tashi motar,bayan Suhailah
ta rufe nata ɓangaren tana me mannuwa da jikin Maleek.Ƙamshin junan su gaba ɗaya ya haɗe da
ƙamshin da ke tashi a cikin motar,ya bada wani ni'imtaccen ƙamshi me sanyaya zuciya.
Ba su wani jima cikin Asibitin ba suka amsa tarin magungunan da aka baiwa Suhailah,wanda za ta
yi anfani da su tsayin watanni uku kafin ta dawo Asibitin a sake bincikar lafiyar mahaifarta.Jikin
Suhailah a matuƙar sanyaye yake lokacin da Maleek ya aje mata ledan da ke ɗauke da
magungunan da za ta yi anfani da su.Ta langaɓar da kanta a jikinsa cikin murya me cike da rauni
take faɗin, "Yah Maleek yanzu duk ni zan shanye waɗannan tarin magungunan?"
Maleek ya ɗaga manyan idanunsa ya sauke akanta yana cewa, "Yes! Da waye zai taya ki sha?"
Suhailah ta jinjina kai tana cewa "Allah ya bani rabon haihuwa kafin in gama shanye su toh!"
A.Maleek ya amsa da "Ameen wife,Luv u." Suhailah ta ɗaga ido tana kallon cikin idanunsa,kafin
ta furta "Luv u too Yah Maleek,don Allah amma kar kayi gaggawan ƙaro aure koda ban haihu nan
kusa ba please! Wallahi ina tsananin kishinka Yah Maleek,ina cikin matsananciyar nadaman aikata
wautan dana yi a baya."
Yadda ta kai ƙarshen maganan cikin rawar muryan da ke nuna cewa gaf take da sakin kuka,yasa
Maleek rungumota zuwa jikinsa sosai,yana shafa tsakiyar bayanta a hankali.
Memakon su koma gida sai suka nufi wani Shopping Mall don Suhailah na son duba wasu
abubuwan anfani da zata siya,sabida za su samu kaman 2 weeks a ƙasar kafin su koma gida.Ita da
Maleek suka shiga cikin Mall ɗin, sun ɗauki a ƙallah zai kai mintuna talatin,kafin su fito
kowannen su hannunsa riƙe da manyan ledoji.Sunusi ne ya nufesu da sauri yana amsan ledojin
hannun A.Maleek ɗin,shi kuma Maleek ya amshi na hannun Suhailah aka sanya a boot,kafin
Sunusi ya ja motar suka nufi hanyar komawa gida.
Suhailah kaɗai aka sauke lokacin da suka iso gidan,shi Maleek Sunusi zai fita da shi wani
wajen.don akwai abubuwan da yake son dubawa na harkokin Business,wanda yake son fara
aiwatar a ƙasar.Don haka ita kaɗai ta buɗe gidan ta shige Sunusi na biye da ita da tarin ledojin
siyayyar da suka yo a mall ɗin.
Sai daya kai mata kayan har cikin falo sannan ya juyo zuwa mota,sukai gaba shi da Uban-gidan
nasa.
Suhailah Abayar jikinta ta cire bayan ta isa ɗaki,yai saura daga ita sai ƙaramar rigan dake jikinta
mara hannu.Wanda tsayin rigan iya cinyanta ya tsaya gaba ɗaya rabin ƙirjinta a bayyane
yake,sabida wuyan rigan me yankan V-shape ne.
Siyayyan da suka yo ta juye saman gado,tana arranging ɗinsu inda ya dace.Lokacin data kammala
Kitchen ta nufa don ɗaura musu Lunch sabida babu abinda Maleek bai sa Sunusi ya siyo ba na
kayan abinci.Har zuwa kan duk wani abun buƙata kama daga kayan miya har zuwa Kaji da Kifi
duk an damfare su cikin Freezer.Shiyasa basa siyan abinci ita ke musu girki kuma hakan Maleek
ke so shiyasa yaƙi kama Hotel sai gida.
Cikin awa ɗaya ta kammala dafa Jallop ɗin Macaroni da yaji Mince Meat da Potatos with Vegies a
ciki.Sai tayi Pepesoup na Kaza wanda yaji spice sosai da Garlic a ciki,sabida haka Maleek ke son
a cika Garlic a cikin Soup ɗin Kaza idan zai ci.
Ta kammala komi bisa dining area da ke cikin falo,sannan ta koma ta gyara inda ya ɓaci a Kitchen
ɗin kafin ta fito ta nufi Bathroom don yin wanka.
Cikin wasu English Wears riga da pencil skat ta shirya kanta,kayan sunyi mata kyau matuƙa tare
da fidda shape ɗinta.Daddaɗan ƙamshi ke tashi a jikinta duk yadda ta motsa,tana tsaka da da
ɗaure gashinta data warware Maleek ya shigo cikin ɗakin.Suka haɗa ido ta jikin madubin ɗakin
Suhailah na sakin masa murmushi,ya tako a hankali zuwa gare ta yana tsayawa a bayanta ya kai
hannu ya rungumota ta baya, tare da ɗaura kansa bisa kafaɗunta hancinsa na cika da sassayar
ƙamshita.Suhailah data lumshe ido jin ɗumin numfashinsa a wuyanta,sai ta buɗe idon tana faɗin,
"Sannu da zuwa My Maleek."
Bai yi magana ba sai juyo da ita da yayi suna facing juna,ya kai bakinsa a hankali ya sumbaci
ƙirjinta idanunsa a lumshe.Kafin ya buɗe ido yana ɗauke kansa daga ƙirjinta ya mayar saman
fuskarta yana haɗe bakinsu waje guda,cikin wani irin salo ya zura harshensa cikin bakinta yana
laluban harshenta ya fara tsotsa....
Tuni Suhailah ta sarƙe hannuwanta a bayansa tana sake manne ƙirjinta a jikinsa,suka shiga bai wa
juna zazzafan deep kisses.
Da ƙyar ta iya janye jikinta daga garesa jin Maleek ɗin na ƙoƙarin rabata rigan jikinta.Ya ɗago
idanunsa masu cike da zallan rikici ya sauke a kanta yana mata alama da hannu akan ya zata hana
shi abinda yake so? Suhailah ta narke masa tana sanar da shi yinwa take ji ya bari su yi Lunch sai
ta ba shi dukkanin abinda ya ke nema daga gareta. Da haka ta lallaɓashi suka nufi dining don cin
abinci,bayan sun kammala kuwa shi ya ɗauke ta gaba ɗayanta zuwa Bedroom ɗin,bai direta a
ko'ina ba sai saman Bed,yana hanata duk wani motsi har sai da ya tabbatar ya cire rigan jikinta yai
wurgi dashi......
Lamuran da suka biyo baya masu tarin girma ne da alqalamina bazai iya rubutowa ba,ban kuma
sake jin ɗuriyan su ba sai gaf da La'asar.
Kwanakin da suka biyo baya a ƙasar ta Cairo gaba ɗaya shafin soyayya Maleek da Suhailah suka
buɗe,tamkar zasu cinye juna da zallan luv me tsayawa a rai.Gefe guda Suhailah ta fara nisa a shan
magungunan ta,tana kuma addu'an akan cewa Allah yasa ta samu rabo cikin sauri.....
Satinsu biyu cir! Suka biyo Flight don dawowa ƙasar su ta gado wato Nigeria,inda suka sauka a
garin Abuja don nunawa Suhailan sabon gidan da ya saya a Asokoro.wanda tuni aka kammala
zuba komi a ciki na kayan alatun more rayuwar duniya,sabida nan yake so su dawo da zama baki
ɗaya su baro Zaria,sabida wannan sabon muƙamin da aka bashi,zaman shi a yanzu zai fi ƙarfi ne
tsakanin Lagos da Abujan.Shiyasa ya yankewa kansa zaman Abuja don yasan Hajjah ba za ta so
shi da zaman Kudu din-din-din ba.
Suhailah ba ƙaramin ruɗewa da tsaruwan gidan tayi ba,don gini ne da aka tsara shi tamkar ba za a
bar duniya ba.Manya-manyan faluka ne guda biyu daga ƙasa,sai ɗakunan bacci guda biyu,sannan
ƙaton kitchen wanda yake manne da babban Store daga gefen hagu idan ka shige corridor.A kwai
kuma ƙofan da zai kaika Backyard daga cikin Kitchen ɗin,idan ka haura sama kuwa a kwai Ƙaton
falo sai ɗakunan bacci guda uku masu ɗauke da toilet a jikin kowanne Bedroom.Ɗakin da yake
daga can ƙarshe shine na Maleek ɗin,wanda duk yafi sauran Bedrooms ɗin girma da tsaruwa.
Yadda aka qawata gidan da kayan alatu masu asalin kyau da tsada,zai baiwa me kallo tabbacin
cewa,wanda ya mallaki gidan ba ƙaramin arziƙi ya tara ba.
Daga can wajen Compound ƙaton parking space ne,da aka adana manyan motoci sabbi dal guda
huɗu.Hatta sabbin Drivers da aka bashi daga Office sunanan ready suna jirane kawai su tare a
gidan, su fara aikinsu don muƙamin da aka bashi ba ƙarami bane.A kwai BQ me ɗauke da 2
Bedroom da single falo,sai ƙaramin Kitchen daga cikin corridor,sai toilet da ke manne jikim
kowani Bedroom.
Kwanansu biyu a garin Abujan suka biyo jirgi zuwa Kano,daga Kano Yusuf driver ɗin Maleek ya
ɗakko su zuwa Zaria.
____________
*Zaria.*
Yau kwanakin su Abie goma sha biyar kenan da barin gidan duniya.Su TAIMIYYAH sun ɗauki
dangana tare da komawa harkokinsu na yau da kullum,don har TAIMIYYAH ta cigaba da zuwa
Computer Training ɗinta.Sai dai har lokacin ba za a ce alhinin mutuwan ya sake su baki ɗaya ba,
sabida gaba ɗaya TAIMIYYAH ta koma wata irin shiru-shiru mara son yawan magana sosai ba
kaman daba.
Duk yadda Iyah da Yasmeen ke ƙoƙarin ganin ta koma kaman da abin yaci tura.Sai Iyah ta maida
kai wajen yi mata addu'an samun ƙarin dangana,daga ɓangaren Ummie kuma takaba ya fara
nisa,itama kuma ba laifi ta dangana.Sai dai ita ma ta sake zama mara son magana kullum cikin
tunani da mafarkin mijinta da ƴaƴanta ta ke.Iyah har lokacin ba ta fasa sa ana mata rubutu tana sha
ba,tana kuma ƙoƙari matuƙa wajen ganin Ummien ta samu nutsuwan zuciya.
Daga ɓangaren Soyayyar Nass da TAIMIYYAH kuwa kullum daɗa samun cigaba ake yi.Don wani
irin zazzafan soyayyar Nass ɗin ne yai mata mugun kamu,wanda har abin ke bata tsananin
mamaki ta yadda bata iya cikakken awa biyu bata ji muryarsa ba,sabida yadda ya saba mata da
yawan kira.
Bai cika zuwa Weekend ba sai duk bayan Sati biyu,shiyasa rabon su da ganin juna a zahiri tun
ranan da yazo yai mata sallama zai wuce Abuja kwanaki goma sha uku kenan baya.Tun daga
lokacin bai sake shigowa garin ba sai gobe Friday ne yake saka ran shigowa,don an kwantar da
Mamarsa ma a asibiti ciwan Sugar ɗinta ya tashi yau kwana biyu kenan.
Shi yake gayawa TAIMIYYAH hakan a jiya da suke waya da daddare,har yana sanar da ita idan ya
shigo dole zai ɗauke su ita da Yasmeen su je duba Mamar tasa.
Ita dai TAIMIYYAH jinsa kawai tayi a lokacin,amma sam ba ta tunanin za ta iya binsa su je gaida
wata Mamarsa.
"TAIMIYYAH ki zo in ji Iyah."
Cewan Yasmeen data shigo cikin ɗakin dawowanta daga kasuwa kenan,don ita TAIMIYYAH ta
shiga Skull a yau ɗin shiyasa basu tafi tare ba.TAIMIYYAH ta ɗaga manyan idanunta ta sauke
akan Yasmeen ɗin tana cewa, "Yaameen har kin dawo,Allah dai yasa kin samu siyo wiffing cream
ɗinnan da cocoa powder."
Yasmeen data aje jakan hannunta ta dubi TAIMIYYAN tana faɗin, "Hmm! Na siyo amma da ƙyar
wallahi don komai yayi tsada sosai , duk abinda ka taɓa sai ka ji ya ƙara kuɗi wannan tsadan
rayuwa dai kullum gaba ya ke yi TAIMIYYAH,ni wallahi abin har tsoro yake bani fa."
Yasmeen ta kai ƙarshen maganan tana sake jinjina irin yadda kullum ka je kasuwa,sai ka tadda
ƙarin hauhawan farashin kayayyaki.TAIMIYYAH ta miƙe tsaye tare da dafe ƙafanta me laluran
tana cewa, "Hmm! Ke dai Allah yasa mu dace kawai,amma abin sai Addu'a Allah dai ya kawo
mana ɗauki,bari in je wajen Iyan."
Daga haka ta fara takawa don barin ɗakin lokacin da Yasmeen ke amsa Addu'ar da tayi da,
"Ameen."
TAIMIYYAH tayi maganan lokacin da ta iso wajen Iyah da ke zaune a falo tana irga wasu
kuɗi.Iyah ta sauke manyan idanunta akan TAIMIYYAH tana faɗin, "Eh dama waɗannan kuɗin
zaki tayani irgawa,don ni ina yi ina daburcewa na rasa gane ko nawa ne duka kuɗin."
TAIMIYYAH ta zauna kusa da Iyah tana kwashe kuɗin daga gabanta ta fara irgawa tana cewa,"Ke
dai Iyah irgan kuɗi wahala suke baki waye ya kawo miki kuɗi haka masu yawa?"
Iyah ta ɗan taɓe baki tana faɗin, "Kuɗin hayan gidana ne na Samaru ɗazu Kallamu ya kawo kinsan
ai lokacin amsan kuɗin yayi."
"Oh..! Hakane fa na manta wallahi,kice mun yi kuɗi yau zaki siyan mana rousted fish mu ɗanci
ko?"
Cewan TAIMIYYAH cike da tsokana,Iyah ta harareta tana faɗin, "Ai bakinki ne fish ɗin,ki gama
irga kuɗin dai sai ayi magana koma me za'a siya,Allah ya ji ƙan wanda ya siya min gidan yasa
suna kyakykyawan matsayi,su da iyayenmu baki ɗaya da suka rigamu gidan gaskiya."
Iyah ta kai ƙarshen Addu'ar wani abu na motsawa a zuciyarta,tunawa da tayi da Abie don shine ya
siya mata gidan yace a zuba ƴan haya,ta dinga samun kuɗin shiga duk ƙarshen shekara.Banda jarin
kuɗin da ya bata a hannu tana ɗan siyan irin su Barkono da waken Suya idan farashinsu ya hau an
samu riba sai a siyar a sai wani.
TAIMIYYAH ta amsa da "Ameen." Itama zuciyarta na motsawa da wani irin kewa me tarin yawa
na Abiee ɗin,har ta kammala irga kuɗin babu wanda ya sake magana a cikin su.Ta baiwa Iyah
kuɗin tana sanar da ita adadin yawan su,kafin ta tashi ta koma ɗaki tana kwanciya tayi lamo a kan
gado,haka kawai ta ji tana son jin muryan Abie ɗin nata.Hawaye suka fara zarya a fuskarta suna
sauka bisa pillow,amma bata damu data share su ba.
Yasmeen ce ta ƙariso bakin gadon ta zauna tana faɗin, "Haba TAIMIYYAH wai don girman Allah
sai yaushe ne idan kin tuno su Abiee zaki daina kuka sai dai kiyi musu Addu'a? Don Allah ki
sanyawa Zuciyarki cikakkiyar dangana,idan kin tuno su kiyi musu kyakykyawar Addu'a ne ita
suka fi buƙata ba yawan kuka da sanya damuwa a rai ba.Gashi nan shiyasa har yau baki maida
jikinki ba duk kin bi kin rame ba kamar da ba,ina sha kinma Yah Sadeeq alqawarin daina kuka duk
idan kin tuno su yace kiyi musu addu'a ne don haka yanzu zan kira shi in ce gaki nan kina ta
faman kuka."
Jin abinda Yasmeen ɗin tace yasa TAIMIYYAH saurin kai hannu tana share hawayen ta dubi
Yasmeen da face ɗin tausayi kafin ta fara faɗin, "please! Yasmeen kar ki kira shi na bari
wallahi,yanzu ma na kasa controlling tears ɗin ne shiyasa."
Yasmeen da tausayin TAIMIYYAH ya cika Zuciyarta sai ta gyaɗa kai tana faɗin, "Naji ba zan kira
shi ba amma don Allah ki daure ki daina irin haka Baby Sis ɗina kinji ko?"
TAIMIYYAH ta gyaɗa kai tana ɗan sakin ƙaramin murmushin yaƙe jin sunan da Yasmeen ɗin ta
kira ta da shi tamkar wata ƙaramar Baby.......✍🏻
Littafin TAIMIYYAH paid book ne,ga duk wanda ta tsincesa a kowani irin group ne,kiji tsoran
Allah karki karanta sai kin biya 500 naira only.
Za ku iya min magana ta wannan number ɗin 08167768704, ko kuma ku turo kuɗin ku kai tsaye ta
wannan account ɗin 0504192664 aisha ibrahim dansabo GTbank.*
Masu turo credit za ku turo katin MTN na 500 ta wannan line ɗin 08167768704.
_Ina ƴan kasuwa masu buƙatar a tallata muku hajar ku? Maza ku garzayo da kuɗi ƙalilan a tallata
muku kayan siyarwanku sai dai kawai ku ji ana kiran waya don buƙatan sayan kayan ku,ku
tuntuɓeni ta layina kamar haka 08167768704._
#Ɗansabo ce#
[12/14, 3:43 PM] +234 703 040 9541: *35*
Yau ya kama Friday tun misalin sha biyu da rabi TAIMIYYAH ta dawo daga Computer
Skull.Lokacin data shigo gidan ta samu Yasmeen na Sasan Baba Sani don haka kai tsaye kayan
jikinta ta cire ta nufi toilet don watsa ruwa.Duk da anyi ruwa da safe bai hana rana ƙwallarewa
ba,shiyasa ɗan tafiyan da sukan yo daga cikin Class zuwa bakin gate ya gajiyar da ita,shiyasa da ta
dawo tafi gane ta ɗan watsa ruwa sannan take jin daɗi.
Ta fito wankan kenan Yasmeen ta shigo ɗakin hannunta riƙe da wani ƙaramin
kwano.TAIMIYYAH ta dube ta tana faɗin, "Yasmeen me kuma kika samo a Sasan Baba Sani?"
Yasmeen ta aje kwanon a saman drawer tana faɗin,
" Awara ce Mero me aiki tayi ya bani sha'awa shine na amso a ɗanyenta,zan soya da kaina da Egg
in masa sauce.
TAIMIYYAH ta furta, "Wow! Aiko ni ma zan ci wallahi,na rabu da cin Awara ma ni kam."
Kafin kowa ya sake cewa komi wayan TAIMIYYAH ya fara kiɗa,tuni ta gane Nass ne sabida a
yanzu ringing ɗin data sanya masa na daban ne.Don haka ta ɗauki wayan tana faman narke murya
basu wani jima suna magana ba ta aje wayan tana duban Yasmeen take faɗin, "Yasmeen Nass fa ya
dage sai ya zo ni kuma ina tsoran wannan karon suyi arba da Baba Sani,ga Yah Deeku ma duk yau
ɗin za su shigo weekend."
Yasmeen ta saki murmushi tana duban TAIMIYYAH take faɗin, "Waya ce miki zasu dawo yau?
Lagos fa za su wuce don haɗo abubuwan Abiee da suke can,sabida za a fara zaman rabon gado
don sauke masa nauyi,ina ga bama a gobe zasu dawo ba sai zuwa jibi,haka na ji Iyah suna waya da
Baba Sanin bayan kin fita Skull ɗazu da Safe."
TAIMIYYAH sai ta tsaya tai shiru tare da faɗawa duniyan tunani, 'Yanzu har za a fara maganan
raba gado?" Ta tambayi kanta da kanta tana jin wani abu na son tokare mata maƙoshi, jikinta a
sanyaye ta nufi wajen kayanta tana ciro rigar da zata saka.
Doguwar riga ce ta ciro na wata Atamfar Java Holland me kyau.Kalan red and black da akai wa
ƙananun zane da kalan golden and green colour,ɗinkin free gown ne da ya yi mata mugun
kyau,kaman yadda kalan ya haska farar fatarta.
Ta ɗaura ɗankwalin kayan tana ɗaukan Turarenta ta fesa kaɗan ta aje kwalban tana maida dubanta
akan Yasmeen da ke ta faman bin ta da kallo,ta aika mata harara tana faɗin, "Wannan kallon fa
Yasmeen sai kace baki taɓa gani na ba."
Yasmeen ta saki murmushi tana faɗin, "Ke baki ga yadda ki kai kyau bane shiyasa,daga nan har
zuwa lokacin da Nass zai zo karki sauya wannan shigan please,wallahi kayan sun amshi jikinki
sosai Masha Allah!"
TAIMIYYAH ta ɗan taɓe baki kaɗan tana faɗin, "Ke dai Yasmeen ba dama ne wajen iya ziga
mutum,ni tashi mu je ki soya Awaran mu ci tun kafin Babah Ladi ta gama girki in ji Awaran ya fita
kaina."
Daga haka suka fito tare da Yasmeen ɗin zuwa Kitchen,bayan sun ma Babah Ladi da ke ta suyan
Waina sannu da aiki ne sai suka fara hidiman gabansu.Cikin ƙanƙanin lokaci suka kammala suyan
Awaran wanda suka wadata shi da egg,ya ji haɗin Sauces ɗin Albasa sai qamshi ke tashi duk ya
cika kitchen ɗin.
Bayan sun ɗibarwa Babah Ladi ne suka juyo sauran cikin plate su ka nufo falon Iyah,in da suka
samu Iyan a zaune tana faman zuba Sugar a cikin bokitin Nonon da za a yi sadaka da shi haɗe da
Waina, idan an gama soya Wainar.
Ta ɗago tai wa su TAIMIYYAH kallo ɗaya tana faɗin, "Dama na san wannan qamshin da ke ta
zuwar min har nan kune kuke wani abin kwaɗayin.Yanzu Awaran ce ba za a ci ta hakanan ɗinta ba
sai an mata wannan haɗin lallai kam!"
TAIMIYYAH ta shagwaɓe face tana duban Iyah take cewa, "Iyah ai yanzu duk haka ake yi,anfi
iya ci da yawa idan akai irin wannan haɗin,bari dai a baki naki ki ci ki ji yadda yake."
Iyah tayi saurin girgiza kai tana faɗin, "ku ci abinku lafiya ni kam bada ni ba."
TAIMIYYAH su kai dariya suna cin abinsu hankali kwance,bayan sun kammala ne Yasmeen ke
sanar da Iyah Nass zai zo zuwa anjima.Kuma gobe idan Allah ya kaimu zasu je su duba Mamarsa
da aka kwantar a Asibiti, kamar yadda yake ta magiyan su tambayi Iyan izini tun yau.
Iyah ta ɗaga kai ta dubi Yasmeen ɗin da ke mata bayani tana cewa, "To sannu sarkin iya tsari me
kaifin baki,ita Zainabun bata da baki ne halan? To duk ba wannan ba ni a gaskiya bana son irin
wannan sakarcin,wai saurayi ya fara ɗaukan budurwa yana kaita wajen danginsa tun kafin ai aure
ko magana me ƙarfi ya shigo,hakan ba mutuncin ƴa mace bane sam.Amma yanzu tunda ana
maganan rashin lafiya ce ta uwa kuma shine ya roƙi ku tambayeni izini,to zan amince amma da
zaran kun yi mata sannu ku kamo hanya ku dawo gida.Ban amince daga dubiyan ku bishi ko'ina
ba kunji na gaya muku! Don hakan ba mutunci bane sam, ku dinga riƙe martaban ku na ƴaƴa
mata,wayewa duk idan bata musulunci bace halaka ce,don haka ku kula kuma shine karo na
ƙarshe, dama ke Zainab ina son in gaya miki tunda na ga kun fuskanci juna kina sonsa to zuwa
wata satin sai ya zo ya samu Babanki Sani,in yaso sai ya turo magabatansa a zo a yi magana a san
da zamansa."
TAIMIYYAH da tunda Iyah ta fara magana tai ƙasa da kanta,sai yanzu ta ɗago ta dubi Iyan cike
da shagwaɓa take cewa, "To Iyah zan sanar masa Insha Allah! Kiyi haƙury nima wallahi bana son
zuwa duba wata Mamarsa,shi ne ya matsa da maganan ita kuma Yasmeen ta amsa cewa zata
tambayeki,don ni kai tsaye na sanar masa ma ba za ki amince ba."
TAIMIYYAH ta kai ƙarshen maganan tana ƙin yarda su sake haɗa ido da Iyah,ganin haka yasa
Iyah cewa, "Karki damu tunda uwarsa ce sai ku je ɗin,amma daga haka bazai sake cewa ki bishi
ko'ina ba,don ma ga Yasmeen ɗin dai za ta yi muku rakiya da ace ke da shi ne kaɗai bama zan taɓa
amincewa ba sam."
Daga haka suka kulle babin wannan maganan,suka ɗakko maganan zaman rabon gadon da za a
fara idan an gama tattara abinda Abie ɗin ya bari.Jikin TAIMIYYAH duk sai yayi sanyi hankalinta
ya sake tashi,tana jin wani irin kewa me tsanani na danne zuciyarta.
Ganin mood ɗinta ya sauya gaba ɗaya yasa Iyah kawar da maganan,ta hanya sanya TAIMIYYAH
ta tashi ta kai Nonon da Iyan ta gama sanyawa Sugar zuwa Kitchen.Daga nan ta duba idan Babah
Ladi ta tara Wainar da yawa,sai su fita ita da Yasmeen su haɗo kan almajiran da za a baiwa
Sadakan Wainar da Nonon.
Hakan ko akayi su TAIMIYYAH suka fita kiran almajiran da kusan duk Friday sukan taru a ƙofar
gidan.Don sun saba amsar sadaka a Sasan Iyan,mussamman idan Waina ko tuwan shinkafa aka yi.
Sai da suka gama raba ma almajiran sadakan tas sannan suka dawo ciki suka nufi ɗakin su don
ganin lokacin sallan Zuhur ya yi.
*5:35pm*
Motar Nass ne ta faka a ƙofar gate ɗin shiga gidan su TAIMIYYAH.Ya fito sanye cikin shigan
manyan kaya riga da wando na shadda,anyi masa ɗinkin zamani da ya dace da Matashi
kamarsa,wanda ya san daraja da ƙiman iya saka kaya.Kalar shaddar Milk ne daya haska shi sosai
fuskarsa cike da annuri yake takawa zuwa bakin gate ɗin ya buga.
Tukur Mai-gadi ya buɗe suka gaisa yana faɗin, "Ranka-ya-daɗe barka da isowa."
Nass ya saki murmushi yana faɗin, "Barka dai Malam Tukur ya ƙoƙari."
"Lafiya lau wallahi barka da isowa,bari a sanya maku kujerun zama kafin Gimbiyar ta fito."
Cewan Tukur yana nufan inda zai ɗakko fararen kujerun zama ya aje ma Nass ɗin.Nass yabi
bayansa da kallo yana me zaro wayansa ya shiga kiran line ɗin TAIMIYYAH.
Basmah wacce ta fito daga Sasan su zata fita can ƙasan layinsu,sai idanunta suka hango mata Nass
da ke magana da TAIMIYYAH a waya yana sanar da ita gashinan cikin Compound ya iso.Tayi
saurin gyara zaman gyalen jikinta tana wani gyara takun ta cike da yanga,sanye take cikin Riga da
Skat da suka fidda suranta.
Idanunta akan Nass yake har ta ƙariso inda yake tsaye tai masa sallama ya ɗago manyan idanunsa
ya sauke akanta,yana amsa guisuwanta da faɗin, "Basmah ko,ina fata kina lafiya?"
Basmah ta wani kashe murya cike da iyayi take faɗin, "Lafiya lau Bro bari na kira maka Yah
TAIMIYYAN kafin na wuce ko." Daga haka ta juya don zuwa Sasan Iyah ta kira masa
TAIMIYYAH,ba tare data jira Nass ɗin ya sanar da ita cewa TAIMIYYAN ta san da isowan nasa.
Tana sanya kanta a ƙofar shiga Sasan ita kuma Yasmeen na fitowa,hakan yasa saura kaɗan suyi
karo Basmah ta ja baya tana faɗin, "Ayyah! Yah Yasmeen saura kaɗan mu gwabza karo,wai na zo
sanar da TAIMIYYAH cewa guy ɗinta ya iso."
Yasmeen tayi wa Basmah wani sakartaccen kallo tana faɗin, "Okey! Ai tuni ta san da isowan nasa
Basmah,yanzu ma wajensa na nufa kafin ta fito." Daga haka Yasmeen ta ɗaure fuska tana yin gaba
abinta ta bar Basmah da bin bayanta da kallo,tana wani taɓe baki ta juyo itama don tafiya inda za
ta.
Lokacin da Basmah ta fita wajen gate ɗin gidan nasu idanunta akan haɗaɗɗiyar motar Nass suka
fara sauka.Tayi tsaye cak! Tana bin motar da kallo zuciyarta na wani irin kaɗawa,ta cigaba da
tafiya tana ƙarewa motar kallo cikin Zuciyarta take cewa, 'Taɓɗi! Yanzu wannan motar tasa
ce,shine duk haɗuwarsa da ajinsa ya rasa wacce zai so sai Yah TAIMIYYAH,wacce take gurguwa
musaka shi ko me zaici da ita? Alhali ga ƴan mata kamarta lafiyayyu da basu da nasakan komi a
tattare da su."
Ta cigaba da tafiya zuciyar na raya mata wasu tarin lamura, da take ji dole ma tayi anfani da
basirarta wajen karkato da hankalin wannan Zuƙeƙen saurayin zuwa gareta.
Har ta kai gidan su Zeenah wata qawarta anan ƙasan layin, zuciyarta bata bar ta sukuni ba.Don
gaba ɗaya Nass ya tafi da dukkanin nutsuwarta,sai yau ne ma ta sake ƙare masa kallo ta ga
haɗuwarsa sosai.
Allah Sarki ita ko TAIMIYYAH suna can suna shan luv ɗinsu da Nass ɗin,bayan ta fito ta same
shi zaune shi da Yasmeen.
Isowan TAIMIYYAH wajen yasa ta basu waje ta je kawo ma Nass ɗin lafiyayyen samosa da meat
pie ɗin da sukai masa haɗe da lemun Abarba da yaji Kwakwa da Madara.
Koda ta kawo bata sake zama ba ta koma cikin gida ta basu waje don TAIMIYYAH ta sake da
Nass ɗin sosai,wanda gaba ɗaya tun isowan TAIMIYYAH wajen ya wani rikice sai faman bin ta
da azababban kallo yake.
Gyale ta yafa yau ba Hijab ba hakan yasa tai masa kyau sosai fiye da kullum.Shiyasa ya kasa
ɗauke idanunsa akanta har abin ya dinga bama TAIMIYYAH haushi, ta ji dama bata biyewa
Yasmeen ta fito sanye da gyale ba.
Sun ɗauki a ƙallah awa ɗaya da rabi kafin yai mata sallama yana aje mata sabbin kuɗi wai ta sayi
credit.Babu yadda TAIMIYYAH bata yi akan ya ɗauki kuɗinsa ba amma fir! yaƙi,sai ma rigiman
da ya kafa mata akan cewa sai tayi masa rakiya bakin gate.
Hakanan ba don ta so ba ta raka shi sukai sallama da juna,ta juyo don komawa cikin gidan bayan
ta tsaya ta ɗauki kuɗi da tray ɗin abinda Yasmeen ta kawo,wanda kaɗan ya ci ya bar sauran.
Lokacin data isa ciki a falo ta aje tray ɗin hannunta tana nufan ɗakin Iyah don bata kuɗin hannunta
ta aje.Faɗa sosai Iyah ta yi ma TAIMIYYAH akan amso kuɗin da tayi har sai da TAIMIYYAH ta
fara mata alamun za ta yi kuka sannan Iyah ta amsa kuɗin ta adana.
"Yah Zuhurah kin ko ga motar da Guy ɗinnan me son Yah TAIMIYYAH yake hawa? Gaskiya
wallahi guy ɗinnan ya haɗu ƙarshe....Sam bai ma dace da Gurguwa kamar Yah TAIMIYYAH
ba.Gaba ɗaya ya gama tafiya da zuciyata Allah ya sani na kamu da son sa farat ɗaya kuma sai na
san yadda nayi ya zama mallaki na.Don baxan bari ina ji ina gani ya auri wata gurguwa can
musaka,alhali na gani na ƙyasa sam hakan bazai taɓa yiwuwa ba."
Zuhurah da tun fara maganan Basmah ta zuba mata ido,sai yanzu da Basman ta kai aya sannan ta
dube ta cikin ido tana faɗin, "Basmah kinsan me kike faɗi kuwa? Snatching ɗinsa za ki yi ko me
kike nufi da waɗannan kalaman?"
Basmah ta wani watsa hannuwa baya tana faɗin, "Yadda kika faɗin shi za a yi snatching idan nayi
aiba kaina farau ba,wallahi Numbern sa zan sata in gwada sa'ata,idan an dace shikenan sai labari
ya canza,shi ma banda abinsa me zai ci da gurguwa? Duk abinda yake nema a jikinta nima ina da
shi kyau da farar fata kawai zata nuna min."
Yadda Basmah ta kai ƙarshen maganan tana wani jujjuya jiki yasa Zuhurah kwashewa da dariya
dai-dai kuma lokacin da Umma ta fito,tana duban Zuhurah take faɗin, "Dariyan me kuke yi haka
kaman wasu taɓaɓɓu?"
Zuhurah sai ta sake kwashewa da dariya,cikin dariyan take sanar da Umma komi,sai Umman ta
xauna tana faɗin, "Ke Basmah da gaske kike yi motar da yake hawa har ta fi ta Sadeeq kyau? To
ɗan gidan uban waye ta rakito tana gurguwa musaka da ita,anya ko ba Iyah ke shige da ficen da
take nemowa Yarinyar can maganin farin jini ba? Ana kulle idanun Samari su daina ganin nakasan
Yarinyar in banda haka ina hakan zai yiwu kana lafiyayye ka auri me nakasa."
Umma tayi maganan tana jin wani abu na tokareta a ƙirji.Basmah tayi saurin faɗin, "Sai ma kin ga
haɗuwan guy ɗin Umma,wallahi bazai yiwu ace kamansa ya kawo kansa wajen musaka gurguwa
wacce sai da taimakon dafa guiwa take iya tafiya a duƙe,ni dai yanzu da gaske na ke sonsa ya
kama Zuciyata Umma,kuma idan ma muka zuba ido ta aure shi ai mune da kunya tunda kin hana
ya Sadeeq ya aure ta, to kuma kawai sai a ga ta samo wanda ya fi Yah Sadeeq ɗin komi ai mun ji
kunya kenan Umma."
"Ƙwarai maganarki a kan hanya ta ke Basmah,idan har na zuba ido ta auro wanda yafi Sadeeq na
ji kunya,sai Iyah ta zuba ruwa a ƙasa ta sha,don haka idan har da gaske kina son sa kiyi ƙoƙarin
sato numbarsa a wayanta,sauran bayanin duk zan kitsa miki shi,ke inma bazai so ki ba to sai dai
kuyi biyu ba bu,amma In Sha Allah ba za ta auri wani mutum me daraja ba sai musaki ɗan
uwanta,shegiyan yarinya me kama da Aljanu."
Zuhurah data saki baki tana duban Umma sai cewa tayi, "Umma yanzu sai ki goyawa Basmah
baya tayi ƙwacen saurayi,ni aganina hakan duk bai taso ba,ku ma tsaya ku ga yadda tarayyan nasu
da shi zai kaya mana,ku ka sani ma ko jikinta take bashi yana anfana da shi tunda har ta iya
sakewa ya Deeku ya kwashi rabonsa waye za ta ki baiwa kanta,tunda ta san da wuya ta auru ku
kuna ganin kyawun da take ƙarawa na banza ne? Ni hatta cikar ƙirjinnan ban yadda ba hannun
maza yaji ba yake ƙara bunƙasa."
( _Allah ka raba mu da sharrin maƙiyi,readers wannan irin sharri da Zuhurah kewa TAIMIYYAH
na lafiya ne kuwa? Dole ka nemi tsari daga sharrin maƙiya,duk wanda baya son ka babu abinda ba
zai iya yi ma na ɓatanci ba arayuwa,sai dai mu ce Allah ya sakawa Baiwar Allah TAIMIYYAH_
😰).
Umma ta dubi Zuhurah tana cewa, "Oho! Koma dai mene ne tunda ƴar uwanki ta kamu da sonsa
ai sai ki mara mata baya tai iya yinta wajen janyo hankalinsa.To wai ma yaushe kika fara sonta da
har za ki ji tausayinta? Ke abin sonki ne ta auri wanda yafi Yayanki komi,waya sani ma yafi har
Ameerun da kike taƙama da shi tunda ba a ma san ɗan gidan uban waye ba,yanzu haka irin ƴaƴan
attajiran garin nan ne ma waya sani?"
Zuhurah sai taji maganan Umma ya soki Zuciyarta,wani kishi da tsanan TAIMIYYAH na taso
mata,tare da wani tsoro me tsanani tana ji kada fa maganan Umma ya tabbata Nass ɗin yafi
Ameerun ta,aiko da ita da kanta zata iya ƙullawa TAIMIYYAN makircin da ba za ta auri Nass ɗin
ba,tayi saurin haɗe face tana faɗin, "Don Allah Umma ki daina wannan fatan,hakan ma ba zai taɓa
kasancewa ba,Ameeru fa Babansa har Muƙamin ɗan Majalisan Jiha ya yi a baya,kin san ko sun
tara arziƙi ba kaɗan ba."
Umma ta danna ma Zuhuran harara tana cewa, "To shi ma sai ki bari mu san ko shi waye
ɗin,kuma ta ina zamu sani ba tare da Basman ta saci number ɗinsa mun fara bibiyansa ta waya
ba."
Dukansu su kai na'am da maganan Umma,sun daɗe suna tattauna yadda za a yi Basmah ta sato
Number ɗin Nass a wayar TAIMIYYAN,daga ƙarshe Zuhurah ce ta basu tabbacin su bar komi a
hannunta zata samo numbern cikin ruwan sanyi.Daga haka suka rufe maganan zuciyoyinsu cike
fal da ƙyashi da hassadar yadda TAIMIYYAH ta fi su tarin abubuwa masu yawa alhali tana
matsayin gurguwa musaka da suke ganin ita ɗin bakomi bace.
_To masu karatu ya ku ke ganin wannan Cakwakiyan za ta kaya? Su Umma za su yi nasaran raba
soyayyan data riga ta ƙullu tsakanin Nass da TAIMIYYAH ko kuwa wata ƙaddarance za ta raba?
Sai ku cigaba da bibiyan yadda rayuwar TAIMIIYAN zata kasance.......✍🏻_
Littafin TAIMIYYAH paid book ne,ga duk wanda ta tsincesa a kowani irin group ne,kiji tsoran
Allah karki karanta sai kin biya 500 naira only.
Za ku iya min magana ta wannan number ɗin 08167768704, ko kuma ku turo kuɗin ku kai tsaye ta
wannan account ɗin 0504192664 aisha ibrahim dansabo GTbank.*
Masu turo credit za ku turo katin MTN na 500 ta wannan line ɗin 08167768704.
_Ina ƴan kasuwa masu buƙatar a tallata muku hajar ku? Maza ku garzayo da kuɗi ƙalilan a tallata
muku kayan siyarwanku sai dai kawai ku ji ana kiran waya don buƙatan sayan kayan ku,ku
tuntuɓeni ta layina kamar haka 08167768704._
#Ɗansabo ce #
[12/14, 3:43 PM] +234 703 040 9541: *Littafin TAIMIYYAH paid book ne,ga duk wanda ta
tsincesa a kowani irin group ne,kiji tsoran Allah karki karanta sai kin biya 500 naira only.*
*Za ku iya min magana ta wannan number ɗin 08167768704, ko kuma ku turo kuɗin ku kai tsaye
ta wannan account ɗin*👇🏻
0504192664 aisha ibrahim dansabo GTbank.
Masu turo credit za ku turo katin MTN na 500 ta wannan line ɗin 08167768704.
_*Ina ƴan kasuwa masu buƙatar a tallata muku hajar ku? Maza ku garzayo da kuɗi ƙalilan a
tallata muku kayan siyarwanku sai dai kawai ku ji ana kiran waya don buƙatan sayan kayan ku,ku
tuntuɓeni ta layina kamar haka 08167768704.*_
*38*
Amsa gaisuwarsa tayi kafin tayi shiru ya biyo baya tsayin seconds sannan ta furta, "Okey Bala na
santa ba matsala ta shigo kawai."
Daga haka ta sauke wayan daga kunni murmushi na blushing saman face ɗinta tunawa da tayi da
gargaɗin A.Maleek, da kashedin da yace yaiwa Bala akan duk wacce zata zo wajen Suhailah sai ta
faɗi sunanta.Shi kuma Bala sai ya kira Suhailan ya sanar mata, idan ta bada izinin shiga sannan ya
bar kowacece ta shiga.
Amma idan har ya ji cewa sunanta Zubaida to bai yarda ta shigar masa gida ba,kada ma ya kira
Suhailah ya sanar mata kai tsaye ya hana ta shiga masa cikin gida.Suhailah gani take kaman wasa
yake yi a lokacin da ya sanar mata umurnin da ya ba Bala kenan,sai yanzu da Balan ya kira yana
sanar mata da zuwan wata Friend ɗinta Ameena Waziri,sannan tw gane da gaske Maleek ɗin yake
yi bada wasa ya faɗi maganar ba.
Sallaman Meenah Wazir daga bakin ƙofar shigowa falon yasa Suhailah tashi ta nufi bakin ƙofar
falon tayi welcoming Ameenan,sukai Hugging juna kowanne da murmushi saman fuskarta.
Suhailah ta furta, "Welcome dear yaushe kika shigo gari ba labari sai zuwan bazata haka?"
Ameen ta saki murmushi suna sakin juna take cewa,"Mrs.Maleek Ado kenan walllahi shekaranjiya
muka shigo gari da ogan,shine na ce yau dai lallai sai na zo wajenki kafin mu wuce jibi."
"Gaskiya kin kyauta sosai dear cox i miss u so much,ke sam ko a online ba a ganinki sai in mutum
ya ɗaga waya ya kira ki,har yanzu dai harkan social media ɗinnan bata dame ki ba Meenah tun
muna skull ai ta miki ciwan baki."
Suhailah tayi maganan suna jerawa da juna zuwa cikin falon,sukai masauki bisa 3 seater baki
ɗayansu lokacin da Meenah ke faɗin, "Ke rabani da wata harkar online inba Business zan fara
ba.Ni sam wallahi chart bai dameni ba Suhailah bare yanzu da hidiman yara kawai nake ganin ya
isheni banma da time sosai.Ku dai har yanzu amarci kuke ci baku ƙare ba bare ku bamu Babies
ko?" Meenah tayi maganan cike da barkwanci idanunta akan Suhailah.
Suhailah ta saki murmushi tana faɗin,"Wani amarci Meenah ana neman gud 6yrs da aure ke dai
kawai Allah ya kyauta akwai labari sosai gara da kika shigo,dama na rasa da wa zan tattauna
damuwan da ke cikin zuciyata,yanzu dai bari ina zuwa insa akawobmiki wani abu."
Daga haka Suhailah ta miƙe ta nufi hanyar corridor da zai kaita kitchen.Meenah tabi bayanta da
kallo kafin ta fara ƙarewa falon kallo tana jinjina irin daular da qawartata ta samu.Tun tarewan su
Suhailan a gidan sau ɗaya tazo sabida aure da ya kai ita Meenan nesa,tana tare da mijinta ne a
Bauchi sai sun zo gari take samu ta zo ayi zumunci.Tunda itama close friend ɗin Suhailah ce sosai
tun suna Secondary skull har zuwa jami'a suna tare.Daga baya ne su Zuby da suka shegewa
Suhailah har hakan yasa ita Meenah ɗan ja baya, sabida tafi kowa sanin sheɗancin Zubaida Halliru
tunda kusan anguwa ɗaya suke basu da nisa sosai.
Suhailah ta fito daga kitchen ɗin Ameena mai aiki na biye da bayanta ɗauke da ƙaton tray, da aka
shaƙo shi da abubuwan motsa baki.
Ameena ta aje tray ɗin a gaban Meenah tana durƙusawa ta kwashi gaisuwa,kafin ta miƙe ta bar
falon bayan Meenah ta amsa gaisuwan da yi mata sannu.
Suhailah ta zubawa Meenah ido tana ganin yadda ta aje uban ƙiba abinta.Ta saki murmushi tana
faɗin, "Meenah haka kika zama wata big madam shi Asheerun ya barki da wannan jikin?:Ai da
Maleek ne kin bani da mita sai ya ga kin sauka zai sama miki lafiya baya son ƙiba shi sam a wajen
mace.Yafi so ya ganka dai-dai misali kai ba rama kuma babu ƙiba me yawa,so miye labari ina kika
baro yaran?"
Meenah ta saki dariya tana faɗin, "Yara suna Bauchi wajen kakarsu ban taho da kowa ba sabida
jibi zamu juya. Biki muka zo yi fa wallahi Suhailah nima bani son ƙibar amma ya zan yi ina shan
maganin sliming yaƙi amsa ta,na gaji na watsar shima yayi mitansa ya gama wallahi,ai fa ke gaki
nan gunin sha'awa kin zama wata chubby abinki ke ba ƙiba kikai sosai ba kuma baki da rama so
cute."
Meenah tayi magana tana ɗaukan plate ɗin da aka zubo dambun nama ta fara ci a hankali, lokacin
da Suhailah ke cewa, "Amma gaskiya baki kyauta ba da kin zo koda Khalil ne shi da yake
ƙarami."
"Ke rabani da wahala tunda na samu inda za a kula da su na aje su haka yafi min." Cewan Meenah
tana gyara zama ta fuskanci Suhailah sosai.Suhailah ta aika mata harara tana faɗin, "Ai kin kyauta
yanzu miye labari?"
Meenah ta cigaba da tauna dambun data cika baki da shi tana faɗin, "Labari na wajen ku manyan
mata masu duniya,ai sai kawai mu ka ji anbaiwa Maleek Babban muƙami haka gaskiya na yi
murna Allah sanya alkhairy Suhailah,yanzu Lagos za ku wuce kenan ko kina nan dai sai dai ya
dinga zuwa?" Suhailah ta girgiza kai tana faɗin, "Abuja zan koma ina ga zuwa next week ma idan
ya juyo daga Lagos zamu wuce.
Ai Hajjah ba za ta so mu koma Lagos ba kinsan ta tsani garin tunda aka kashe mata Miji a can
shikenan ta tsani jin ko sunan garin,yanzu haka ita bata yi wani murna da wannan muƙamin
ba,tunda aka ce zaman Maleek zai fi yawa a Lagos ɗin.Shiyasa kawai sai ya sayi gida a Abuja sai
ya dinga zuwa duk weekend Abuja ɗin,amma fa ni nama fi so ya bar ni anan ni kaina bana son yin
nesa da Hajjata."
Suhailah ta kai ƙarshen maganan tana wani narke fuska,har ga Allah ita da gaske take yi bata son
komawa wani Abuja.Meenah tayi dariya tana faɗin, "Ai qawata gara dai ki koma ɗin yanzu fa an
daina sakacin barin miji sakaka babu kulawa,gara ko'ina kana nane da abinka ko can Lagos ɗin ya
gayyaceki kar ki sake ki nuna baki son zuwa, bi abinki ki ga halin da yake ciki a can ɗin.Idan ki
kai sanya wasu na nan daga gefe suna jiran su shigo ne,don haka ki aje wannan sakarcin dana
sanki da shi a baya ki kama mijinki gam ki riƙa kula da shi.Ki fita harkan qawaye Suhailah don na
ga suke ɗauke miki hankali kina shirme,wai shin ma ya labarin ta hannun damar naki Zuby,har
yanzu bata yi wani auren ba?"
Meenah ta ƙare maganan da jefawa Suhailah tambaya,idanunta akan Suhailan wacce tayi saurin
taɓe baki kafin ta fara cewa, "Hmm! Meenah kenan wallahi ni har kinsa gabana ya faɗi da kiran
sunanta ma,don sam ko sunan Zuby yanzu bana son inji an kira min."
Da tsananin mamaki Meenah ke kallon Suhailah jin furucin da ke fitowa daga bakinta,kafin ta
buɗe baki tana cewa, "Suhailah duk irin amintar da ke tsakaninku shine zaki ce baki son jin ko
sunanta,meyafaru ne tsakaninku haka?"
Suhailah ta ja numfashi ta sauke tana duban Meenah ta fara bata labarin yadda Zuby ta fara cusa
mata ra'ayin fara shan Pills.Har kawo shawaran data bata bayan an sanar da su mahaifarta ta samu
matsala,da yadda Zubaidan ta amshi number ɗin Maleek har zuwa kan makircin da Zubyn ta so
shirya mata a wajen Maleek ɗin.Da irin textses ɗin da take aiko masa na son ya aureta ta ƙare
maganan da cewa,
"Meenab ai Zuby ta gama sire min ta fita araina kwata-kwata,na daɗe da yin blocking ɗinta ma
bani bata har abada.Dama ansha gaya min shu'uma ce amma lokacin idoma ya rufe tsakanina da
Allah son ta nake da zuciya ɗaya,ashe ita bada zuciya ɗaya take tare da ni ba."
Meenah da sam bata ji wani shock akan duk labarin da Suhailah ta bata ba,don ta riga ta san
wacece Zuby za ta aikata fin hakan ma.Bare tana ganin irin daulan da Suhailah ta samu da irin
mijin da Allah yai mata baiwa da shi.Ita dama tunda ta ga yadda Zuby ke kwantar ma Suhailah da
kai ta san ba a banza ba, akwai wata manufan da take da shi ashe ko hasashenta ya zama
gaskiya.Meenah ta saki murmushin takaici kafin ta dubi Suhailah tana cewa, "Suhailah kenan
dama kece baki san haƙiƙanin wacece Zubaida Halliru ba,ai zata yi fiye da haka don ita bata ɗauki
cin amana a bakin komi ba.Na zura miki ido ne kawai ke da ita don na san sai irin wannan ranan ta
zo Allah ma ya taimakeki da kika samu mijin da ya fargar da ke wautan da kika tafka cikin
sauri.Amma Suhailah kinyi sakarci da wauta da kika biye mata har kika aikatawa kanki irin
wannan Babban kuskuren.Ta ya baki taɓa haihuwa ba zaki fara shan maganin hana ɗaukan ciki
inba wauta da sakarci ba....."
Meenah ta rufe ido taiwa Suhailah tatas akan irin sakarci da wautan data aikata da tare yi mata
gargaɗi akan hattara da biyewa ƙawaye. Musamman a wannan zamanin da mutane suka maida cin
amana ba komi ba,ta cigaba da cewa, "Suhailah ke ce baki san yadda zamani ya sauya ba sabida
bakya shiga cikin mutane.Allah kuma ya yoki da kyakykyawan zuciyar da kike iya sakin jiki da
kowa,to ki sani zamani yayi sauyawan da babu wata wacce zaki iya sakin jiki da ita 100% kice ba
za ta iya cin amanarki ba,ko da ace ko ciki ɗaya kuka fito sabida muna cikin wani irin zamani da
hassada da son kai yayi yawa a cikinsa.Ɗan uwa sai ya ci amanan ɗan uwansa sabida abin
duniya,ƙawa ta ci amanar ƙawarta sabida kuɗi da son duniya.Don haka baka saurin sakin jiki da
kowa yanzu bare har ka dinga buɗe cikinka a wajen wata ƙawa ta san sirrinka da na gidan
aurenka,wallahi Zuby idan ta samu Maleek irin ƴan duniyan mazan nan ne ina tabbatar miki da
cewa cikin ƙanƙanin lokaci za ta janye miki hankalin miji.Ko bai aureta ba suyi ta watsewarsu a
waje tunda ba kamun kai gareta ba,ki godewa Allah Maleek na son ki kuma shi ɗin ɗan halas ne
da ya samu kyakykyawar tarbiyyah.Wanda ruɗin zamani da giyan arziƙi bai sanya ya shiga hanyan
banza ba,don haka idan zaki tashi ki kama mijinki da kyau ki tashi,magana zai ƙara aure ko wani
abu duk ki barwa Allah komi,kuskure kin riga kin yi Suhailah kuma baki da hujja a yanzu ko
dalilin da zaki iya hana shi ƙaro aure kamar yadda ya faɗi.Bama na miki fata ina miki fata ki samu
lafiya ki haihu tamkar kowace mace,sai dai idan ƙaddaranku ce sai ya ƙaro auren kiyi addu'a ki
barwa Allah komi,Insha Allah ko ya ƙaro auren sai ki ga hakan ya zame miki wani alkhairyn na
daban.Amma ki aje duk wani son jiki da sakarci a gafe guda ki kama mijinki kiyi masa
biyayya,yana son ki kuma shi jininki ne bazai taɓa juya miki baya akan duk wata ƙaddaran da zata
sameki ba,amma batun Zuby ki bi duk hanyar da zaki bi ki ga cewa ta daina zuwa inda kike ma
bare har ta sake samun fuska a wajenki,ke garama ki tattara ki bar garin kawai a huta."
Meenah ta ƙare maganan cike da ɓacin rai domin tun farko tayi takaicin yadda Suhailah ta
sakarwa Zuby fuska,har take zuwa gidanta taci karen ta babu babbaka.
Suhailah ta saki ajiyan zuciya tana sake jin nadama da danasanin sakarwa Zuby fuska da tayi tun
farko na ƙona zuciyarta.Ta furzar da iska me zafi daga baki tana cewa, "Meenah nagode ƙwarai da
shawarwarinki tabbas ku ne qawaye nagari da kuke tsagewa mutum gaskiya komin ɗacinta.Haƙiƙa
na cuci kaina na tafka wauta da sakarci hakama Hajjah ta gaya min amma Insha Allah na ɗauki
Babban darasi, har abada bazan sake maimaita kwatankwacin kuskuren da nayi a baya ba.Kuma
Zuby na bar ta kenan har abada na gaya miki ko sunanta bana son ji sabida idan ina tuna irin
maganganun da take aikowa Maleek ji nake zuciyata tamkar zata ƙone sabida baƙin ciki....."
Suhailah ta cigaba da bayyanawa Meenah irin gadar zaren da Zuby ta dinga ɗaura ta akai,ba tare
da ita ta gane cewa cutar da ita take son yi ba sai daga baya.Meenah ta jinjina ma sakarcin
Suhailah sosai don ita ta ɗauka tunda Suhailah tayi aure ta fara hankali,don tun farkon Suhailah ita
irin ƴan farin yarannanne masu wauta da sakarci,don ma Hajjah tayi mata riƙo irin na jajirtattun
iyaye masu baiwa ƴaƴa ingantacciyar tarbiyyah da ba a san irin wauta da sakarcin da Suhailah za
ta dinga yi ba.
Sai wajen ƙarfe biyu da rabi na rana bayan sun yi Lunch sannan Meenah tai shirin tafiya.Suhailah
ta haura zuwa sama ta haɗo mata abin arziƙi har da su uban choculate da bata rabo da su sabida
shan zaƙinta,duk ta zuba cikin leda tace akaiwa yaranta.
Meenah tayi godia me tarin yawa kafin Suhailah ta kira wayan Kabeeru driver ya zo ya maida
Meenah gida.Kabeer ɗin shine driver ɗin da Maleek ya bar mata don ya dinga fita da ita
unguwa,amma ita Suhailan ta fi ganewa yin driving da kanta.Sai idan bata jin yin tuƙin ne ta kan
kira shi sai yazo su fita tare.
Ba a ɗauki mintuna talatin ba ya iso gidan. Suhailah tai wa Meenah rakiya har bakin mota ,sannan
sukai sallama da juna kowacce na ɗagawa ƴar uwanta hannu har Kabeer ya fice daga gate ɗin
gidan.
Sannan Suhailah ta juya zuwa cikin gida tana jin zuciyarta wasai cike da tarin nutsuwa.Domin ta
jima tana neman wacce zata tattauna da ita akan abinda Zuby ta yi mata amma tana tsoron ai mata
Allah shi ƙara.Sai gashi Allah ya jefo mata ƙawarta me son ta Meenah Waziri sun tattauna har ta ji
sirrikan shu'umancin Zubyn wanda bata ma san da su a baya ba.
___________
TAIMIYYAH tana sanye ne cikin wani Black and Red ɗin Laces wanda yai asalin amsar farar
fatarta.An mata ɗinkin half gown da straight skat da ya zauna a jikinta,duk wanda ya kalleta daga
zaune ko daga tsaye babu wanda zai ce tana da wata lalura sai idan ta fara tafiya tana dafa guiwa
ne za a san tana da Nakasa....
Yasmeen ita tana sanye ne cikin wata doguwar rigar atamfar Holland.Wanda ɗinkin yai mata kyau
ya zauna a jikinta sosai, sai ta yafa gyalen da ya shiga da kalan kayan nata,gaba ɗaya ƙamshi ke
fita a jikkunansu me sanyi da daɗi.
Iyah ce ta fito daga ɗakinta hannunta riƙe da kuɗi ta miƙawa TAIMIYYAH tana faɗin, "Ungo ki
riƙe wannan kuɗin ko da za ku dinga fita ki ga wani abin kina so sai ki siya,don tafiya ba kuɗi
babu daɗi."
TAIMIYYAH ta ɗaga manyan idanunta tana duban Iyah kafin ta miƙa hannu ta amshi kuɗin tana
faɗin, "Nagode Iyah amma ina ma fa da kuɗi cikin account ɗina,irin wanda Abie kan turo min duk
ƙarshen wata bana wani kashewa, zan dai amsa wannan ɗin idan na ga abinda kike so in siyo
miki."
Iyah ta jinjina kai tana faɗin, "Ni dai bance ba kena ba,ita ma kuma Yasmeen ga nata nan zan
bata." Iyah tayi maganan tana miƙawa Yasmeen nata kuɗin,Yasmeen ta amsa kuɗin tayi
godia,kafin su miƙe tsaye suna sanar da Iyah zasu Sasan Ummie su yi mata sallama,daga can zasu
shiga har Sasan Baba Sani Yasmeen tai musu sallama.
Da Sasan Ummie suka fara ta baiwa Yasmeen kuɗi da wani turare.Yasmeen ta amsa tai godia ita
kuma TAIMIYYAH ta sanar da Ummien zata bi Yasmeen sai sun dawo.
TAIMIYYAH ta gyaɗa kai tana cewa, "Insha Allah Ummie bazan wuce one week ba zan dawo."
Ummie da Innarta sukai musu fatan Allah kiyaye hanya,sannan suka fito suka nufi Sasan Baba
Sani don yi musu sallama.
Bayan Yasmeen tayi wa Umma sallama ne suka fito gaba ɗaya tare dasu Basmah da za su yi musu
rakiya zuwa wajen mota.
Zuhurah na riƙe da ledan da Umma ta baiwa Yasmeen turmin atamfa.Ita dai TAIMIYYAH ta riga
yin gaba abinta don sam bata so su jera dasu Zuhurah bare su gaya mata wata magana mara
daɗi,don tana ankare da yadda Basmah ke wani binta da wani irin kallo tunda suka shiga Sasan
nasu.
Sun tadda Sani har ya iso yama sanya jakunansu a Boot,hakan yasa sallama kawai suka shiga su
kaiwa Iyah da Babah Ladi.
Iyah ta rako su har waje tana musu fatan isa lafiya.TAIMIYYAH ce ta shiga baya ita kuma
Yasmeen ta kame a gaban motar suka fice su Zuhurah na ɗagawa Yasmeen hannu.......✍🏻
*Salamu alaikum! Ina ma'abota son ƙamshin su ke ne? Uwargida da Amare masu shirin shigewa
daga ciki kai har ma da ƴan mata ma'abota son ƙamshi da ƙamsasa suturunku* *.To ga dama ta
samu don kuwa shahararriyar mai saida turarukan wuta me asalin kyau da inganci wato
RUUSCOLLLECTIONS ta zo muku da turarukan wuta na sawa a ɗaki wanda tun daga kunna shi
baza ki taɓa jin ƙauri ba daga farko har karshensa.*
*Bata tsaya anan kaɗai ba don kuwa akwai jerin gwanon kalolin turarukanta masu ƙamsasa jiki da
gida haɗi da ɗakuna ma baki ɗaya kamar haka* 👇🏻
*Akwai oil koleccha,da cream koleccha,Body butter, white humra,attraction humra, Mehlab
humra, Dufr humra, brown humra, oil humra, golden humra da yellow humra,*
*Turaren wuta dinta kuwa Arabian black bakhoor mai kamshin harami, yemani bakhoor, hemani
flakes, sandal rose, sandal flakes, Arabian spices, Senegalese kajiji, Couscous, special kajiji,
Golden sand, wardrobe balls, Ruus Remix, Exclusive Dufr, cotton candy, Queen of the night,
Bukhur, Alajab.*
*Akwai airfreshner, morphing mist, shampoo, hair cream, Vaseline.* *Harma da su atamfofi, less,
shadda, takalma da mayafai duk zaki same su a wajen RUSS COLLECTION .*
07025393114
#Ɗansabo ce#
[12/14, 3:43 PM] +234 703 040 9541: *Littafin TAIMIYYAH paid book ne,ga duk wanda ta
tsincesa a kowani irin group ne,kiji tsoran Allah karki karanta sai kin biya 500 naira only.*
*Za ku iya min magana ta wannan number ɗin 08167768704, ko kuma ku turo kuɗin ku kai tsaye
ta wannan account ɗin*👇🏻
0504192664 aisha ibrahim dansabo GTbank.
Masu turo credit za ku turo katin MTN na 500 ta wannan line ɗin 08167768704.
_*Ina ƴan kasuwa masu buƙatar a tallata muku hajar ku? Maza ku garzayo da kuɗi ƙalilan a
tallata muku kayan siyarwanku sai dai kawai ku ji ana kiran waya don buƙatan sayan kayan ku,ku
tuntuɓeni ta layina kamar haka 08167768704.*_
*39*
*Kano.*
Ƙarfe huɗu da wasu ƴan mintuna motar Sani ya faka daga bakin gate ɗin shiga gidansu Yasmeen
dake Unguwar Nasarawa GRA Kano.
TAIMIYYAH da bata saba da zaman mota ba sabida rashin sabo tafiye-tafiye da bata cika yi ba.A
gajiye ta zuro ƙafafunta zuwa waje daga cikin motar,bayan ta yiwa Allah godia da ya iso dasu
lafiya.
Yasmeen ce ta baiwa Sani umurnin shiga da motar daga cikin Compound bayan mai gadi ya buɗe
gate ɗin.
Suka rankaya ita da TAIMIYYAH zuwa cikin gidan nasu Yasmeen wanda zuwan TAIMIYYAH na
huɗu kenan zata ce sabida Iyah sam bata son ta ga ta matsa daga kusa da ita.Sai da wani dalili me
ƙarfi,tun ƴan uwa da dangin mahaifiyar TAIMIYYAH na mita har sun gaji sun bari.
Da sallama ɗauke a bakinsu suka isa ƙofar shiga Babbar Main parlor na gidan.Mai aikinsu
Yasmeen Kuluwa itace ta amsa sallaman tana musu barka da zuwa. TAIMIYYAH ta gaida ta cike
da ladabi kasancewarta Dattijiya da zata kusa sa'ar Iyah.
Guggo Bilkice ta fito daga ɗaki tana musu sannu da zuwa tare da rungume TAIMIYYAH a
jikinta.TAIMIYYAH ta gaida Guggo Bilkin tana faman zuba mata shagwaɓar cewa ta gaji.
Guggo Bilki ta dube ta cike da kulawa tana faɗin, "To ai sai ki je ki watsa ruwa yanzu zaki ji duk
gajiyan ta ware, sai ku fito ga abinci can yana jiranku a dining,idan kun kammala duka da abincin
sai ku sameni a part ɗin Abban su Yasmeen, ku gaishe sa kun san yau weekend yana gida."
TAIMIYYAH ta jinjina kai cike da gamsuwa tana cewa, "To Guggo Bilki bari in fara da wankan
wallahi na gaji sosai."
Kafin Guggo Bilki tace wani abu Sani ya shigo ɗauke da jakunansu.Ya gaisa da Guggo Bilki yana
aje jakunan anan cikin falon,tai masa barka da iso lafiya tana me ɗaga murya ta kira ɗaya me aikin
nasu me suna Ramma.
Bayan Ramma ta ƙariso ne Guggo Bilki ta bata umurnin zuwa ta buɗewa Sani ɗakin baƙi,akai
masa abinci da komi da komi.Sani yai godia yana juyawa ya fice daga falon.
Ita TAIMIYYAH tuni har ta isa ɗakin Yasmeen,ta fara da cire kayan jikinta don shiga wanka.
Lokacin data fito wankan har Yasmeen ta kawo musu abincin nan ɗaki.TAIMIYYAH ko mai bata
tsaya shafawa ba ta nufi wajen akwatinta ta ciro wata gown mara nauyi na Material ta saka.
Yasmeen ma wankan ta shiga itama.Lokacin data fito ta samu TAIMIYYAH ta zuba abinci tana
ci,wayanta na hannunta riƙe tana chart da Zee dake tambayarta cewa ko sun isa Kanon?
TAIMIYYAH ta bata amsa da cewa gatanan ma har tayi wanka tana cin abinci ne.Yasmeen ce ta
dubi TAIMIYYAH tana faɗin, "Sis manya ina fata dai har kin kira Iyah don hankalinta ya kwanta
mun iso lafiya."
"Oh God! Gara da kika tuna min wallahi ita nake da niyyan kira,sai kuma hannuna ya kunna data
na hau online,Zee ta tasani da surutunta bari ki gani in kira ta yanzu kuwa."
Daga haka TAIMIYYAH tayi dialing number ɗin Iyah,aiko bugu biyu ta ɗaga suka gaisa.
TAIMIYYAH ta sanar mata cewa sun iso lafiya basu jima sosai suna magana ba TAIMIYYAH
tayi hanging up.Tana shirin aje wayar saƙo ya shigo har zata yi banza taƙi duba saƙon.Sai kuma ta
ga lambar Nass ne data kasa sharewa a wayarta,hakan yasa ta buɗe saƙon,zuciyarta na ingizata ta
buɗe message ɗin message ɗin ta ga ko me ke ciki.
Aiko lokacin data buɗe saƙon ta fara karantawa,bata san lokacin da hawaye suka fara zarya a face
ɗinta ba.Wani irin tausayin kansu da soyayyar Nass ɗin da take ƙoƙarin dannewa na tasowa baki
ɗaya.
Kalamai ne yayi anfani da su masu nuna zallan kewanta da shiga cikin mummunan yanayi da yayi
a sanadiyyar ta daina kula shi,ta daina ɗaukar wayarsa bare ya samu darajan da zata maida masa
reply, na saƙonnin daya dinga turo mata.
Daga ƙarshen saƙon ne ya furta kalaman da suka sanya ta zubda hawaye.Sakamakon sanar da ita
cewa Mummynsa tayi masa Allah ya isa,ta kuma ce idan bar rabu da ita ba sai ta tsine masa.
Sannan bata amince ya cigaba da bibiyan TAIMIYYAN koda ta waya bane.Ya kai ƙarshen
kalamansa da cewa,
" _Zaynab zan barki ne ba don zuciyata ta daina son ki da ƙaunar ba.Sai don gudun kada fushi da
tsinuwar mahaifiya ya tabbata akaina.Ina so kisa a zuciyarki ni Naseer Aliyu Ƙwarbai da
soyayyarki zan mutu,sabida ina miki son da koni bansan adadinsa ba.Don Allah Zaynab ki taya ni
da addu'an Allah ya bani juriya da danganan rabuwarmu da juna,domin ina cikin wani hali da baki
bazai iya furtawa ba,ina miki fatan alkhairy tare da samun masoyin da zai fini sonki da
ƙaunarki,ina fata zan ji koda kalma ɗaya ne tak! Daga gareki bayan kin gama karanta saƙona,_
TAIMIYYAH na kaiwa ƙarshen saƙon ta saki wani irin kuka me cin rai.Tana kai hannu ta dafe
bakinta don gudun sautin kukan kada ya janyo hankalin Yasmeen.Wacce ke can gaban Drawer ɗin
kayanta,tana cire kayanta daga akwati tana jere su a ciki.
Tayi kuka me yawa kafin ta samu ƙwarin guiwan tura masa da reply masu ɗauke da taƙaitattun
kalmomi na fatan alkhairy.Daga ƙarshe bayan ta tura saƙon,sai ta samu kanta da goge dukkanin
lambobinsa biyu dake cikin wayarta baki ɗaya,ta tashi a hankali ta isa kan gadon ɗakin Yasmeen ta
kwanta tana ji wani sabon kukan na zuwar mata. Ta saki kukan da ƙarfi wannan karon,don ji take
yi tamkar ta sanya hannu ta ciro zuciyarta daga ƙirjinta ta cire duk wata soyayyar Nass dake
danƙare a ciki.Amma bata da wannan damar shiyasa ta saki kukanta me sauti,wanda hakan ya
janyo hankalin Yasmeen tayi saurin aje kayan dake hannunta.Ta iso wajen TAIMIYYAH tana
tambayanta abinda ke faruwa,memakon TAIMIYYAH ta bata amsa sai ta sake rushewa da kuka.
Cikin kukan take sanar da Yasmeen saƙon Nass ɗin,ta ƙare maganan da cewa, "Yasmeen ba ina
kuka bane don mahaifiyarsa tace ya barni ba,ina kuka ne sabida zafi da takaicin dalilin ƙina da
take yi da Nass ɗin,sabida kawai Allah ya mayar dani gurguwa.Yasmeen zuciyata zafi take yi idan
ina tuna irin cin fuskan da tai min.Meyasa mutane suka daina duba kyawun halayya da nasaba me
kyau,suka koma duba zubin halitta da ƙyalƙyalin duniya? Miye aibuna a hakan Yasmeen don na
zamo gurguwa...?"
TAIMIYYAH ta sake sakin kuka me cin rai ji take yi ina ma da itace tabi Abie suka bar gidan
duniya ko zata huta da cin fuska da isgilancin da take fuskanta daga wajen wasu mutane,da suke
ɗaukarta a maƙasƙanciya sabida kawai Allah ya jarabceta da zama Gurguwa.
Yasmeen da tausayin TAIMIYYAH ya gama cika zuciyarta har ƙwalla na taruwa a idanunta,tayi
saurin zama kusa da TAIMIYYAH tana fara rarrashinta da kalamai na kwantar da hankali.
Bayan Yasmeen ta ci nasaran tsaida kukan da TAIMIYAH keyi ne sai ta lallaɓata akan ta wanko
face ɗinta.Lolacin da TAIMIYYAH ta fito daga toilet bayan ta wanko fuskarta,sai suka sanya
Hijab suka fito don zuwa Sashin Abban su Yasmeen ɗin su gaishe shi.
Da sallama suka shiga cikin falon nasa yana zaune kusa da Guggo Bilki dake gefensa.Sun maida
hankali wajen kallon TV Guggo Bilkin ce ta amsa sallaman nasu, Yasmeen ta nufi wajen Abbanta
da sauri tana faɗin, "Abbah i miss u." Abban ya shafa kanta yana faɗin "Miss u too my Auta kun
iso lafiya ko? TAIMIYYAN Iyah barka da zuwa Kanon Dabo."
TAIMIYYAH ta isa ta durƙusa a gabansa ta gaishe shi,tana me faɗin, "Lafiya lau Abbah mun
sameku lafiya?"
Abbah ya saki murmushi yana bata amsa da cewa, "Lafiya lau Zaynab barkan ku da zuwa." Daga
haka TAIMIYYAH ta tashi ta fito daga falon ta bar Yasmeen a can tana zubawa Abban
shagwaɓa,don tasan ita ɗin ta gaban goshinsa ce sosai.
Fitowan TAIMIYYAH zuwa main-parlor ɗin yayi dai-dai da shigowan big bros ɗin su Yasmeen
ɗin me suna Emran.TAIMIYYAH ta ɗaga manyan idanunta ta sauke akansa lokacin da shima
idanunsa ke sauka akanta.Sai ta ɗan saki fuska sosai tana cewa, "Sannu da zuwa Yah Emran ina
yini."
Emran ya amsa a taƙaice da faɗin, "Lafiya lau Sis barka da xuwa." Daga haka bai sake cewa komi
ba ya nufi hanyar da zai kaishi kitchen.
TAIMIYYAH tabi bayansa da kallo tana taɓe baki,don batun yau ba ta san shi ɗin miskili ne na
gaske.
Sam baida hayaniya da kula mutane fuskarnan kullum a cuskule yake.
Memakon ta zauna a falon ma sai kawai ta yanke shawaran komawa ɗakin Yasmeen tai
kwanciyarta tana ɗaukar wayarta ta hau online.
Yasmeen data shigo ta ganta a kwance sai ta nufeta tana cewa "Ke yada kwanciya a ɗaka kamam
wata baƙuwa,ki tashi mu fita falo mana ga su Yah Anas can sun shigo ku gaisa."
TAIMIYYAH sai ta tashi zaune tana taɓe baki take cewa, "Ni rabani da wani fita falo wannan Yah
Emran ɗin yaita ma mutane kallon banza.Baki ga fa dana gaida shi yadda amsa gaisuwan a wani
wulaƙance,shi dai akwai baƙin hali wallahi."
Yadda TAIMIYYAH tayi maganan tana faman kwaɓe fuska yasa Yasmeen sakin dariya tana faɗin,
"Ke sai kace baki san hali ba TAIMIYYAH da har zaki wani damu don ya yi miki hakan,shi fa
kowa ya san halin miskilncinsa.Shiyasa gashi nan ko budurwa ya kasa yi har ansawa Yah Anas
rana ashe ina can Zaria,amma shi kin ga ko budurwa bana ji yana da ita,don Allah ki tashi mu je
falo nasan ma bazai zauna ba ya fita abinsa zuwa part ɗinsu."
Ba don TAIMIYYAH taso ba haka tabi Yasmeen suka fita xuwa falon.TAIMIYYAH da fuskan
mutumin nata Yah Emran ta fara cin karo,yana nan zaune babu wani inda ya je.
Sai ta haɗe fuska tana ɗauke kai daga duban sashin da yake zaune.Ta ƙarisa kusa da kujeran da
Yah Anas ke zaune wanda tun fitowan su TAIMIYYAH yake sakar mata murmushi,kafin ya riga ta
da faɗin "Wow! Sis barka da xuwa yau wace rana Iyah ta barki kin shigo Kano,welcome dear
Sisi."
TAIMIYYAH itama sai ta sakar masa murmushinta me kyau tana faɗin," Thank u Yah Anas na
sameku lafiya,ashe kuma an sanya lokaci to Allah ya sanya alkhairy yasa za a yi muna raye,kace
kafin inbar gari za a kaini inga irin zaɓen da kai mana ta Sis in-law."
Anas ya saki dariya yana faɗin, "Karki damu Sis kisa a ranki kin ganta kin gama."
TAIMIYYAH ta maida masa martanin dariyan da yayi ƙasa-ƙasa.Tana maida dubanta kan ɗaya
Yayan su Yasmeen ɗin me suna Ahmad tana faɗin, "Yah Ahmad ya kake?"
Ahmad da idanunsa ke kan TAIMIYYAH ya amsa da faɗin, "Lafiya lau aina ɗauka ba za ki gaishe
ni bane sai Anas kawai kika sani." Yadda yayi maganan yana hararanta yasa duka suka saki dariya
a tare.TAIMIYYAH na faɗin, "Sorry ai abin step by step ake bi,yanzu ba gashi mun gaisa ba ashe
kananan dai kuna buga kishi da juna da Yah Anas ɗin."
Ahmad ya sake aika mata harara yana faɗin, "To ya za a yi kinsan saƙo da saƙo ai." Suka sake
sakin dariya TAIMIYYAH sam bata sake duban inda Yah Emran ke zaune ba.Wanda ya harɗe ƙafa
gaba ɗaya hankalinsa na kan TV amma kunnuwansa na jiyo masa duk abinda akeyi cikin falon.
Hiransu suka yi sosai da su Yah Anas ɗin,Yusuf ne kawai baya nan wai yayi tafiya tare da wani
Cousine ɗinsu xuwa Niger.Sai da aka kira Sallar Magriba sannan suka watse,mazan suka nufi
masallaci su kuma su TAIMIYYAH suka shige ciki don yin nasu sallar.
Kwananta biyu da zuwa Kanon ta ware sosai a gidan Guggo Bilkin.Tana jin daɗin yadda ƴan
uwanta su Anas ke ji da ita,don duk idan zasu dawo daga wajen aiki shi da Ahmad sai sun shigo
mata da Ice Cream da su Shawarma.
Yah Emran ne kawai babu ruwanta da shi daga gaisuwa sai gaisuwa ke haɗa su.
Yasmeen ta kan fita zuwa can gidan da za su yi bikin cousine Sis ɗin tasu.Kasancewar gidan babu
nisa da gidan su Yasmeen ɗin layi ɗaya ne ya raba su,shiyasa da ƙafa ma Yasmeen ke zagayawa ta
je.
Ita dai TAIMIYYAH ko sau ɗaya bata taɓa bin Yasmeen ɗin ba don ita sam bata son shiga cikin
mutanen da bata saba dasu ba.Guggo Bilki tayi mita akan su dinga zuwa ana shirin bikin da su
tare, amma TAIMIYYAH tayi biris taƙi zuwa.
Yauma tun safe Yasmeen ta gama shiri bayan sun karya kumallo.Ta sanar da TAIMIYYAH cewa
zata fita zuwa gidan Babansu Lawal ɗin,don yau Thursday za a yi lalli.
TAIMIYYAH da ke daga kwance sai kawai ta sake gyara kwanciya tana faɗin, "Yasmeen ni
wallahi bana son shiga mutanen da ban sani ba.Dama mun saba da Amaryar ce sai na je to amma
ban santa ba itama ba sanina tayi ba,kawai sai aganni ana nuna ni ana cewa waccar gurguwan
kuma daga ina?Gaskiya ba za ni ba ni ko ranan yinin ma ni kaɗai zaku bari a gidan don ba zuwa
zanyi ba."
Yasmeen data gama jin haushi ta ballawa TAIMIYYAH harara tana cewa,"Ai ke kina da damuwa
wallahi TAIMIYYAH.Inba haka ba miye na kawo wannan maganan,don Allah ki taso muje kema
ai miki lallin mana,ko ja ne zai miki kyau sosai wallahi."
Da ƙyar ta ciyo kan TAIMIYTAH ta yadda zata bita itama ai mata lallin amma a hannu kawai.Ta
tashi ta shirya cikin wata doguwar rigan atamfa da ɗinkin yabi jikinta sosai.Kamar yadda kalar
atamfar me duhu ya haske farar fatarta,ta sanya Hijab irin me kamar riga ɗinnan,wanda zaka zura
hannuwa kai ta sabgarka babu takura.
Suka fito sai faman zuba qamshi suke yi.Sallama sukaiwa Guggo Bilki wacce taji daɗin yadda yau
TAIMIYYAH ta yadda zasu fita zuwa gidan Bikin da Yasmeen.
Tayi musu a dawo lafiya suna jerawa da juna suka fice daga gidan.
"TAIMIYYAH bari kawai mu ƙarisa bakin layin shigowa nan zamu sama Ɗan-sahu,sai mu hau ya
zagaya damu layin gidan Baba Lawal don gaskiya zan wahal dake idan nace mu taka a ƙafa."
Yasmeen tayi maganan idanunta akan TAIMIYYAH da ke dafe da guiwar ƙafarta suna takawa a
hankali.Lokacin da suka ƙarisa bakin titin basu wani daɗe ba suka tare Napep suka shige,ya
zagaya dasu xuwa gidan Baba Lawal ɗin,suka sauka Yasmeen ta biya shi kuɗinsa suka shige zuwa
cikin gidan.
A falon gidan suka tadda Anty Kareema matar Baba Lawal tare da wasu baƙi.Suka gaisheta ta
amsa da fara'a idanunta akan TAIMIYYAH take cewa, "Yasmeen ina kika samo kyakykyawar
budurwa haka,ko itace naji kina cewa kun zo daga Zaria tare?"
Yasmeen ta saki murmushi tana faɗin "Itace Ummah sunanta TAIMIYYAH,bata son shiga
mutanene yanzu ma da ƙyar ta amince ta biyoni,Kausar ɗin na ɗaki ne?"
Anty Kareema dasu Yasmeen ke kira da Ummah,ta dubi Yasmeen ɗin tana bata amsa da cewa,
"Allah sarki wallahi kyakykyawa da ita,Kausar na daga ciki ku ƙarisa mana na san ai sun gama
shiri gara kuje wajen lallinnan da wuri." Daga haka su Yasmeen suka wuce zuwa don ƙarisawa
ɗakin ƴan matan gidan.Anty Kareema da baƙuwarta suka bi bayan su TAIMIYYAH da kallo
baƙuwar na cewa, "Oh! Yarinya kyakykyawa da ita amma ta nakasa wannan da ba gurguwa bace
da anga zallar diri da kyawun halitta,wallahi sai naji duk tausayinta ya kamani."
Anty Kareema ta jinjina kai tana cewa, "Ke dai bari Raliya kin riga ni da baki ne,wallahi yarinyar
ta birgeni a ganin farko,haka Allah ke ikonsa."
Duk wannan maganganun dasu Anty Kareema ke yi akan kunnin TAIMIYYAH ne.Wacce ke bin
bayan Yasmeen a hankali zuwa ƙoafr shiga ɗakin ƴan matan,don haka akan kunninta sukai
maganan.
Ta shige cikin ɗakin daga ƙarshe tana jin wani iri cikin zuciyarta.Ire-iren waɗannan maganganun
da bata rabo da jin su suna ɗaya daga cikin abinda yasa bata faye son shiga mutane ba.Sabida
yawan tanka kyawunta da tausayawa Nakasanta da mutane ke yawan yi,wanda hakan na taɓa
zuciyarta da jefa mata rauni da tausayin kanta da kanta.
Lokacin da suka shige cikin ɗakin ƴan matan wanda su biyu ne ma suka rage ba su yi aure
ba.Yasmeen ce ta nunawa TAIMIYYAH gefen gado tana cewa, "Ga waje TAIMIYYAH
zauna,Kausar ga TAIMIYYAH na janyo muku ita yau zamu tafi Lallin tare."
Daga Amarya Kausar har ƙanwarta me suna Firdausy suka zubowa TAIMIYYAH idanu.Firdausy
na riga Kausar da faɗin, "Sannu da zuwa TAIMIYYAH,Yasmeen gaskiya ƴar uwar taki
kyakykyawace ga sunanta unique, sam ni ban taɓa jin mace da suna TAIMIYYAH ba."
TAIMIYYAH ta sakar musu murmushi suka gaisa cikin fara'a, Yasmeen na cewa Feedoh, "Haka
kowa ke cewa bai taɓa jin sunan ba a wajen mata.Kuma asalin suna TAIMIYYAH mata aka fi
samawa don ko Abul Barakat da Abul Abbas da ake ce musu Ibnu TAIMIYYAH.Toh su
TAIMIYYAN sunan wata kakarsuce na can sama amma macece,sai dai a wajen su labarabawa ba
kowanne irin mutum suke kira da suna TAIMIYYAH ba.Sai wanda ya shahara da ko dai kyau ya
zama mutum kyakykyawaneshi na buga misali,ko kuma irin budurwarnan wacce take da
kyawawan ɗabi'u da iya zama da mutane me haƙury sosai to sai su kirata da suna
TAIMIYYAH.Amma galibi bakasafai suke kiran mutum TAIMIYYAH ba se wanda yake da siffofi
da ɗabi'u masu kyau abun yabo."
Yasmeen ta kai ƙarshen bayaninta,tana sakin murmush ganin irin hararan da TAIMIYYAH ke aika
mata.
Kausar ta furta, "Wow! kice idan na haifi ƴata mace kyakykyawa zan sanya mata suna
TAIMIYYAH kuwa,sai in mata fata ta taso da dukkanin siffofi ababen yabo.Yadda za ta cika
sharuɗan cinye suna TAIMIYYAH,don wannan Sis ɗin taki Yasmeen da alamu ita ta cinye
sunan,don ga kyau nan ga kuma alamun nutsuwa a tare da ita."
Yasmeen ta saki dariya ita da Feedoh suna haɗa baki wajen faɗin, "Amma wannan Amarya baki da
kunya tun kafin ma a ɗaura har kin fara zancen haihuwa,eh lallai gara ayi-ayi mu miƙaki tun kafin
kifi ƙarfin mu."
Wannan karon har da TAIMIYYAH aka saki dariya,kafin su Feedoh su kammala shirinsu Kausar
ta kira wanda zai kaisu wajen yin Lallin.
Lokacin da suka fito jere da junane su Kausar suka kula da yanayin tafiyar TAIMIYYAH.Suka
gane ashe gurguwace me laluran ƙafa,take suka ji wani tausayinta ya kama zuciyarsu,Feedoh tai
ƙasa da murya tana cewa Kausar, "Wayyo Yah Kausar dubi yadda sai ta dafe guiwa take iya
tafiya,ina ma Allah bai jarabceta da laluran ƙafa ba,wannan ai da baƙaramar haɗaɗɗiyar mace za a
yi a wajennan ba.Sabida Allah ya bata kyau da dirin jiki,dama shiyasa ake cewa ɗan Adam tara
yake bai cika goma ba.Duk abinda kake taƙama da shi sai an rageka ta wani fannin toh ita dai da
gurgunta aka jarabceta,amma fa wannan matar manyace gaskiya akwai body da kyau masha
Allah."
Kausar ta jinjina kai tana faɗin, "Wallahi kuwa Feedoh,Allah dai yasa mu dace amma naji
tausayinta ya kama zuciyata."
TAIMIYYAH dai tayi gaba abinta bata san wainar dasu Kausar ke toyawa akanta ba.Don lokacin
da suka fito wajen motar wanda zai kai su kiran Zee ya shigo wayar TAIMIYYAH.Don haka tai
receving call ɗin tana kaiwa kunni lokacin da Yasmeen ta buɗe mata murfin back seat ta shige ta
zauna.Itama Yasmeen da Kausar back seat ɗin suka shiga sai Feedoh ne ta kame agaba. Yellow
yaja motar suna barin layin,har lokacin TAIMIYYAH na amsa wayar Zee dake bata labarin tayi
sabon Saurayi.
Lokacin da suka isa gidan Lallin Amarya Kausar ita aka fara yiwa ja a ƙafa.Sannan akaiwa
TAIMIYYAH a hannu don tace bata son baƙi iya ja kawai za a mata.
Da ƙyar su kausar suka ja ra'ayinta ta yarda ai mata har da ƙafafu.
Basu san ita TAIMIYYAH kunyan yadda zata buɗe ƙafarta aga ɗaya yafi ɗaya girma shi ke hanata
yin Lalli a ƙafa ba.Ko zata yi tafi yarda ta siya salataf na yanka ta manna abinta tayi da kanta.
Amma hakanan ta miƙa ƙaramar ƙafar aka zana mata.Su Kausar na ta satan kallon ƙafafun nata
suna jin wani tausayinta da kaɗaita ƙuduran Allah cikin zukatansu.Don banda Allah wa zai yi
hakan gaka mace har mace kaman TAIMIYYAN amma gashi Allah ya jarabceta da Nasaka na
ƙafa ɗaya.
Lokacin da aka gama zanawa duka ƙafafun ba ƙaramin kyau Lallin yayi ba,tun kafin ma ya kama
a cire.Ita dai TAIMIYYAH na zaune bata wani sanya musu baki a hiran da suke,zuciyarta na can
wajen tunanin Nass wanda har yanzu ta kasa yakice tunaninsa daga zuciyarta sai dai bata zauna
waje ɗaya ba.
Basu baro gidan Lallin ba sai huɗu na yamma.Zuwa lokacin TAIMIYYAH ta gama galabaita da
yinwa,don sam taƙi cin duk abinda aka siyo musu a gidan Lallin.
Sai data ga yinwa zai halakata sannan taiwa Yasmeen raɗa suka tsaya a wani shago aka amso mata
Hollandia Milk da Buns ta ci a motar.
Lokacin da suka iso gidan su Kausar juyin duniya anyi TAIMIYYAH ta shiga ciki suyi sallolin da
ke kansu amma taƙi.
Ta kafe ita kawai su barta Yellow driver ya sauke ta a gida,ita Yasmeen ɗin ta dawo daga baya.
Hakanan su Yasmeen suka bar TAIMIYYAH ta tafi Yellow zai sauke ta a gida.
Suna isa TAIMIYYAH ta sauka ta shige ciki.Tun a waje ta hango motar Yah Emran dama shi huɗu
yake baro office ya dawo gida daga wajen da yake aiki.
Ta isa cikin gidan tana ji kanta har wani ciwo yake mata sabida rashin cin abinci akan lokaci.
Tunda tai sallama taji babu motsin kowa a falon kawai sai ta nufi ɗakin Yasmeen kai tsaye.
Tana shiga tai wurgi da Hijab ɗin data cire akan Bed ta nufi toilet ta yo wanka tare da ɗauro alwala
ta fito.
Idanunta ta zuba akan yatsun hannunta da jan lallin ya kama juwur abin sha'awa,tana kallon irin
kyawun da lallin yayi a yatsun hannunta.
Da sallolin da ke kanta ta fara bayan ta idar ne ta canza rigar jikinta zuwa wata doguwar rigan ta
shan iska mara nauyi.Kalar rigan pich ne sai ya ƙara fito da hasken fatar ta,bata sanya hula a kanta
ba sai ta bar gashinta dake ɗaure da Ribbom a tsakiyar ka.
Ta fito don zuwa ɗakin Guggo Bilki ta sanar da ita ta dawo ta kuma nema abinci.
Sai dai tana sanya kanta cikin corridor ɗin shiga ɗakin Guggo Bilki idanunta ya sauka akan
takalman Yah Emren,dake xube daga bakin ƙofar shiga ɗakin.A hankali amon sautin muryar
Guggo Bilki ya fara shiga kunnuwan TAIMIYYAH.
Jin Guggo Bilki ta ambato sunanta yasa ta jan birki daga bakin ƙofan.Ba tare da tayi yinƙurin
shiga ɗakin ba,haka kawai taji tana son jin dalilin kiran sunanta cikin hiran Guggo Bilki da Yah
Emran ɗin........✍🏻
*Salamu alaikum! Ina ma'abota son ƙamshin su ke ne? Uwargida da Amare masu shirin shigewa
daga ciki kai har ma da ƴan mata ma'abota son ƙamshi da ƙamsasa suturunku* *.To ga dama ta
samu don kuwa shahararriyar mai saida turarukan wuta me asalin kyau da inganci wato
RUUSCOLLLECTIONS ta zo muku da turarukan wuta na sawa a ɗaki wanda tun daga kunna shi
baza ki taɓa jin ƙauri ba daga farko har karshensa.*
*Bata tsaya anan kaɗai ba don kuwa akwai jerin gwanon kalolin turarukanta masu ƙamsasa jiki da
gida haɗi da ɗakuna ma baki ɗaya kamar haka* 👇🏻
*Akwai oil koleccha,da cream koleccha,Body butter, white humra,attraction humra, Mehlab
humra, Dufr humra, brown humra, oil humra, golden humra da yellow humra,*
*Turaren wuta dinta kuwa Arabian black bakhoor mai kamshin harami, yemani bakhoor, hemani
flakes, sandal rose, sandal flakes, Arabian spices, Senegalese kajiji, Couscous, special kajiji,
Golden sand, wardrobe balls, Ruus Remix, Exclusive Dufr, cotton candy, Queen of the night,
Bukhur, Alajab.*
*Akwai airfreshner, morphing mist, shampoo, hair cream, Vaseline.* *Harma da su atamfofi, less,
shadda, takalma da mayafai duk zaki same su a wajen RUSS COLLECTION .*
07025393114
[12/14, 3:43 PM] +234 703 040 9541: *Littafin TAIMIYYAH paid book ne,ga duk wanda ta
tsincesa a kowani irin group ne,kiji tsoran Allah karki karanta sai kin biya 500 naira only.*
*Za ku iya min magana ta wannan number ɗin 08167768704, ko kuma ku turo kuɗin ku kai tsaye
ta wannan account ɗin*👇🏻
0504192664 aisha ibrahim dansabo GTbank.
Masu turo credit za ku turo katin MTN na 500 ta wannan line ɗin 08167768704.
_*Ina ƴan kasuwa masu buƙatar a tallata muku hajar ku? Maza ku garzayo da kuɗi ƙalilan a
tallata muku kayan siyarwanku sai dai kawai ku ji ana kiran waya don buƙatan sayan kayan ku,ku
tuntuɓeni ta layina kamar haka 08167768704.*_
*40*
TAIMIYYAH ta sake jingina da jikin bangon corridor ɗin,ta yadda zata iya jiyo maganganun da su
Guggo Bilkin ke yi da kyau.Kunnuwanta suka cigaba da jiyo maganan da Guggo Bilki keyi inda
take cewa Emran ɗin,
"Emrana ka ga ita ɗin ƴar uwarka ce ta jini,duk wacce zaka je ka auro a waje barin ita
TAIMIYYAR ce.Kaine nake ganin duk kafi sauran zurfin tunani da hankali,kuma kaine baka fito
da matar aure ba ka tsaya shiririta,Anas ya samu mata haka Ahmad shima magana yai nisa,shiyasa
nake ganin kaine ya dace ayi wannan haɗin zumuncin da kai,gadai ta nan ka ganta babu abinda ta
rasa kuma nakasanta ba abinda zai kawo cikas bane don ka aureta,don babu abinda bata iya yi da
kanta,Zaynab tana da tarin nutsuwa da baiwa masu da yawa da zaka ji daɗin kasancewa da
ita.Abbanku kansa yayi na'am shi ya bani ƙwarin guiwan in tinkareka da maganan don aji ta
bakinka,ko kuwa ka samu wata ne bamu sani ba?"
Emran wanda ke zaune kusa da Mamien tasu,ya ɗaga manyan idanunsa ya sauke akanta,cikin
tsananin mamakin dukkanin kalamanta ya fara cewa, "Yanzu Mamie don kawai ban fito da mata
ba daga zuwan Yarinya sai ki fara irin wannan tunanin,arasa wacce za a ce na aura sai
gurguwa,musaka Mamie? Gaskiya bazan iya aurenta ba da dai ace ba gurguwa bace yarinyar ta
haɗa duk wasu abu da nake so a jikin mace,amma tunda tazo a gurguwa gaskia Mamie bazan iya
aurenta ba,haba abokaina ai dariya zasu yi min,ace duk matan garin nan da sauran wurare in rasa
wacce zan aura sai gurguw......"
"Ya isa haka Emrana!" Guggo Bilki ta katsesa cikin fishi me tsanani kafin ta cigaba da faɗin, "A
gabana Emrana,a gabana zaka riƙa aibanta ƴar uwarka don kawai tana da nakasa? Miye aibun
kasancewarta gurguwa kai me lafiyayyun ƙafafu?Ko kana tunanin ka fita gata ne a wajen Allah da
ya barka a yadda ka ke, ita ya jarabceta da zama gurguwan? To shikenan tunda abin naka yazo da
iskanci da rashin mutunci abar zancen gaba ɗaya,amma kasani nan da watanni uku kacal ka fito da
matar aure,sakarai kawai miskilin banza da wofi, da ina maka kallon wanda yasan abinda yake yi
ashe kai ɗin baho ne,duk matar da zaka je ka rakito ɗin ba baki zan maka ba Emrana,amma ba za
ka taɓa samun me nagarta da kyakykyawan hali irin TAIMIYYAH ba.Amma ka je kai nazari ka
kuma sake fuskantar halayyar TAIMIYYAH tunda ga ta nan tana nan tare damu har nan da zuwa
sati ɗaya,idan ka ji kana da ra'ayi zan fi kowa farin ciki tashi ka bani waje."
Guggo Bilki ta kai ƙarshen maganan tana saita masa hanyar fita daga ɗakin.Fuskarta har lokacin a
ɗaure yake don maganganun da Emran ɗin yayi ya ɓata ranta.
Emran ya zube daga gabanta yana cewa, "Mamie kiyi haƙury na ga ranki ya ɓaci,ina gaya miki
gaskiyan abinda ke zuciyata ne amma zan duba inyi tunani kiyi haƙury please...!!"
Iyah abinda TAIMIYYAH ta ji kenan tayi gaggawar juyawa tabar wajen,wani irin yanayi na ɓacin
rai da takaici na lulluɓe zuciyarta.
Itace yau ake wa wani talla yana gudunta don tana matsayin gurguwa? Wasu hawaye masu
tsananin zafi suka cika idanunta,haushi da tsanan Yah Emran ya dira a zuciyarta farat ɗaya.Har ta
isa wajen dining ɗin gidan zuciyarta suya yake yi matuƙa,hatta da Guggo Bilki haushinta take ji
sosai a ranta,tana ayyana me zaisa tai mata haka?Meyasa zata tallata ma Emran ita har ya samu
chance na aibanta nakasanta? Ta kai hannu tana share hawaye masu zafi da suka kwaranyo daga
idanunta,bata so sam ta nuna wani alama na cewa taji zancen nasu shiyasa tayi matuƙar ƙoƙari
wajen danne zuciyarta.Cike da ƙarfin hali ta zuba abinci kaɗan ta fara ci,sabida yadda yinwa ya
dameta kuma bata so ulcer ɗinta ya motsa.
Akan idanunta Yah Emran ya fito daga ɗakin Guggo Bilkin, sai dai shi sam bai kula da ita
ba,sabida bai kallo sashin dining ba har ya fice daga falon.Ba a ɗauki lokaci ba sai ga Guggo Bilki
itama ta fito,dai-dai lokacin da TAIMIYYAH ta aje spoon ɗin hannunta,tana ɗaukan cup ta zuba
ruwan juice kaɗan ta shanye.
Guggo Bilki ta ƙariso wajen dining ɗin tana cewa,"TAIMIYYAH dama har kun dawo ne shine ban
ji motsin ku ba,ina Yasmeen ɗin take ita?"
TAIMIYYAH ta ɗaga manyan idanunta ta sauke akan Guggo Bilki,tana ƙirƙiran murmushi a
saman face ɗinta, lokacin da take baiwa Guggo Bilki amsa da cewa, "Aiko na dawo bada jimawa
ba Guggo Bilki,yinwa ce ta haukatani na yo nan banje na sanar miki mun dawo ba,Yasmeen tana
can gidan zuwa anjima zata dawo tace."
Idanun Guggo Bilki akan Lallin da suka zanu a kyawawan yatsun TAIMIYYAH,lokacin da take
faɗin,
"Shiyasa kice ban ji shigowan naku ba muna ɗaki da Yayanku,aiko Lallin yayi kyau TAIMIYYAH
ina fata har a ƙafa akai miki ko?"
TAIMIYYAH ta jinjina kai tana cewa, "Aiko su Yasmeen sun matsamin da mita Guggo Bilki
hakanan na bada har ƙafafun akayi kin gani ma."
Ta ƙare maganan tana ɗago ƙafanta me lafiyan ta nunawa Guggo Bilki Lallin.Guggo Bilki tabi
zanen da yai raɗau a farar ƙafar TAIMIYYAN tana cewa, "Kai Masha Allah,Lalli yayi kyau kam
ai sun ƙware sosai indai a iya lalli ne."
TAIMIYYAH ta saki murshi yaƙe kaɗan tana cewa, "Ai nan Kano ƙarshe ne wajen iya Lalli
Guggo Bilki,mu Zaria babu ƙwararru sosai gaskiya kaman nan,duk da cewa ba laifi yanzu ana ta
samun wanda suka iya amma basu kai nan ɗin ba gaskiya."
TAIMIYYAH ta kai ƙarshen maganan tana miƙewa tsaye,don so take kawai ta jita a ɗaki daurewa
kawai take yi wajen kula Guggo Bilkin,amma maganganun Yah Emran ne kawai ke kai kawo
cikin zuciyarta.
Guggo Bilki ta bi TAIMIYYAH da kallo lokacin da take ƙoƙarin wuce ta xuwa ɗaki TAIMIYYAN
na cewa, "Guggo Bilki zan je na huta kaɗan kafin yamma ta ƙarisa yi,wallahi na gaji ne sosai
zaman gidan Lallinnan."
"To shikenan TAIMIYYAH a huta lafiya,ai zaman kunshi akwai gajiyarwa shiyasa nima ban damu
da yi ba sam." Daga haka TAIMIYYAH tayi wucewarta zuwa ɗaki.Guggo Bilki na bin bayanta da
kallo da yanayin tafiyarta,wanda sam ita bata hango aibu a cikinsa da har Emran zai ce wai idan
ya auri TAIMIYYAH za ai masa dariya ba,ta jinjina kai kawai kalamansa na sake ɓata zuciyarta.
TAIMIYYAH ko tana shiga ɗakin Yasmeen kwanciya tayi akan gado,ta me lumshe idanunta
kalaman Yah Emran na dawo mata inda yake cewa, " _Da dai ace ba gurguwa bace Mamie ta haɗa
duk wasu abu da nake so a jikin mace."_
'Kenan shiyasa take yawan kama shi yana satar kallonta?" TAIMIYYAH tayi tunanin hakan cikin
xuciyarta,tana sake jin zafin dukkanin kalamansa.Ta lumshe idanunta tana me jin kaman tai
tsuntsu ta ganta a gaban Iyah,gaba ɗaya sai taji zaman Kanon ma ya gundureta.
Amma sai dai bata son ko Yasmeen taji maganan bare har Guggo Bilki ta gane tai musu laɓe, har
ta ji zancen su da Emran ɗin,don haka dole ta daure ta kai iya kwanakin data ambata zata yin.
Tana me shan alwashin ko gaisuwa ba zai sake haɗa ta da Emran ɗin ba.Dama haka kawai ita
jininta bai haɗu dashi ba, girmansa kansa da miskilancinsa sam bai mata ba.
Ta cigaba da kwanciya tunanika kala-kala na kutsowa cikin kwanyarta.So take yi ta gano ko ita
ɗin tana da wani laifine wajen zamantowarta gurguwa? Amma har ta gama tunaninta bata gano
hakan ba. Abu ɗaya kawai ta sani shine Allah haka yaso ganinta,kuma babu wanda zai fi ta son ta
kasance cikin lafiyayyu marasa nakasa,amma bata da yadda zata yi tunda haka Ubangiji ya
jarabceta ya so ta da kasancewa.Kuma tana masa godia tunda ya bata tarin baiwa da ni'imomi,
wanda zata iya alfahari da kanta a hakan.
Ta kai hannu ta share hawayen dake saukowa daga idanunta, zuciyarta na sake shiga ƙunci a duk
sanda ta tuno cewa masu ƙinta duk sabida kasancewarta gurguwace suke gudunta.Ta tuno da irin
cin fuskar da Mummyn Nass tai musu a asibiti, wani irin ƙunci ya cigaba da danne zuciyarta har
bata san sanda ta sanya kuka ba.
Ta cusa kanta a cikin pillow tana kuka sosai har sai da ta gaji don kanta,sannan ta ɗago kai tana
share hawayenta.
A kuma dai-dai lokacin Yasmeen ta shigo ɗakin,kallo ɗaya tai wa TAIMIYYAH tayi saurin
ƙarisowa cikin ɗakin tana faɗin, "Lafiya TAIMIYYAH kika kunshe ke kaɗai a ɗaki kina
kuka,meke faruwa ne?"
TAIMIYYAH tai ƙasa da kanta tana yamutse fuska take faɗin, "Yasmeen kaina ne da cikina ke
ciwo,ina ga sabida yadda na wahala a gidan kunshinnan ne banci abinci ba,ni kinsan ciwan kai na
ɗaga min hankali dana nemi magani ban gani anan ɗaki shine nayi ta kuka abina."
Baki sake Yasmeen take duban TAIMIYYAH tana jinjina shagwaɓarta.Don ita har ga Allah ta
kama da gaske hakan ne,tunda dai tasan babu kowa da zai ɓata ran TAIMIYYAN a gidan, bare ta
kawo cewa ko wani abin akai mata.Ta buɗe baki tana faɗin, "Eh! Lallai ke wannan matar
shagwaɓarki har ta yi yawa,kawai ki fita kiwa Mamie magana abaki magani shine sai ki wani zo
ki kunshe a ɗaki kina kuka,bari inje in samo miki maganin a ɗakin Abbah ki sha." Daga haka
Yasmeen ta juya don zuwa ɗakkowa TAIMIYYAH maganin,ita kuma TAIMIYYAH sai ta miƙe
dafe da guiwar ƙafarta ta fara takawa ta nufi toilet don wanke face ɗinta,idanunta har yaji-yaji
suke sabida kukan data sha.
Lokacin data fito daga toilet ɗin har Yasmeen ta kawo mata magani haɗe da table water ta aje akan
bedside.
Hakan yasa TAIMIYYAH zama daga bakin gadon, tana ɗaukan paracetamol ɗin ta ɓalli guda biyu
ta kai baki tana korawa da ruwan ta shaye.Ta aje goran ruwan tana cewa, "Yasmeen gobe kuma me
zaku yi,hala dai Angon ustaz ne shiyasa ban ji kince za a yi wani bidi'a a bikin ba?"
Yasmeen ta murmusa lokacin da take aje wayarta akan madubi.Ta juyo tana fuskantar
TAIMIYYAH sosai kafin ta fara faɗin, "Aiko dai babu abinda za su yi daya wuce walima gobe da
ƙarfe huɗu za a tafi MIEMAH a can za a yi walimar.Ina fata dai zaki mana tunda walimace dai a
ci a tashi ba wani abu za a yi ba."
TAIMIYYAH ta ɗan taɓe baki kaɗan tana faɗin, "See ur mouth like kece walimar,to bari mu gani
kila in je kila kuma ba za ni ba,nifa ban son shiga mutanene kema kin sani."
"Sai aljanu kike son shiga ko?" Cewan Yasmeen tana ballawa TAIMIYYAH harara.
TAIMIYYAH bata san lokacin data kwashe da dariya tana cewa, "Ki rifa min asiri da jinnu,Allah
yai mana tsari dasu abar zancen zani Insha Allah shikenan ko?"
Wani hararan Yasmeen ta sake aika mata tana faɗin, "Eh shikenan kin tsira tunda kin miƙa wuya
za ki ɗin." Daga haka suka dasa hiran bikin har aka kira sallah kowacce ta ɗauro alwala don bada
faralinta.
Da daddare ƙememe TAIMIYYAH taƙi fita falo zaman hira yadda suka saba zama dasu Yah
Anas.Abincin ma nan ɗaki tasa Yasmeen ta kawo musu suka ci tare.
Guggo Bilki data shigo tana tambayan dalilin da zasu ƙi fitowa falo,sai Yasmeen ta bata amsa da
cewa TAIMIYYAH ce bata jin daɗi,amma ta sha magani,sai Guggo Bilkin tai mata sannu tana
juyawa ta bar ɗakin.
Lokacin da suka iso gida ana ta kiran sallar magriba.Suna sanyo kansu cikin gidan kenan sukai
arba dasu Yah Anas zasu fita zuwa masallaci.
TAIMIYYAH ta ja baya don basu hanya lokacin da Yah Anas ke faɗin, "Wow! Kin ga yadda kika
zama wata balarabiya kuwa Sis,gaskiya shigar Abaya tana miki kyau Sister."
TAIMIYYAH ta saki murmushi tana faɗin, "Kai Yah Anas banda ziga fa."
Anas ya saki dariya yana cewa, "Ba wani ziga fa,da gaske shigar yai miki kyau TAIMIYYAH."
TAIMIYYAH ta ɗago face don yiwa Anas magana, sai idanunta suka shige cikin na Yah Emran da
yai tsaye yana faman ƙare mata kallo.
Tayi saurin fara takawa don barin wajen tana cewa Anas , "Thank u Yah Anas sai kun dawo."
Tuni Anas yayi gaba abinsa ba tare da TAIMIYYAN ta sani ba. Emran daya tsaya kaman wanda
aka dasa.Yabi bayanta da wani irin kallon ƙurilla yana sake jinjina baiwar kyawu da Allah yayi wa
TAIMIYYAN.
amma
Sai dai kasancewarta gurguwa yasa yake jin bazai taɓa iya bata zuciyarsa ba.Wani tunani ne ya
haska cikin kwanyarsa sai ya juya da sassarfa don fita daga gidan, jin za a tada sallah a masallacin
dake kusa dasu inda suke sallah anan.
TAIMIYYAH dai bata san ma yana yi ba,don ita haushin kallonta da ya tsaya yine ma ya
kamata.Ta dinga mita a zuciyarta ita kaɗai akan me zaisa ya tasata da kallo haka kaman wani ɗan
iska.
A fili ta furta, "Mutum sai shegen girman kai da baƙin hali,ga shegen kallon matan tsiya kaman
maye."
Ƙasa-ƙasa tai maganan iya kunnuwanta,shiyasa Yasmeen da ke gefe tana cire Abayar jikinta sam
bata ji me TAIMIYYAN ta faɗi ba.
Yau ɗinma da lokacin yin Dinner yayi TAIMIYYAH ƙin fita tayi.Sai ta fake da cewa Yasmeen
zata ɗan yi tilawa ne sai zuwa can anjima zata ci abincin.
Hakanan Yasmeen ta fita ta bar TAIMIYYAN a ɗaki wacce ta ɗakko Qur'ani ta fara
karantawa.Bata bar karatun ba har sai da Yasmeen ta shigo hannunta riƙe da ledan gasasshen nama
ta ajewa TAIMIYYAH tana cewa, "Gashinan inji Yah Anas kuma Guggo Bilki tace kiyi maza ki
bar karatun haka ki fito kici abinci,don ta kula da gangar kike ƙin fita falo yanzu."
TAIMIYYAH sai ta aje Qur'anin tana duban Yasmeen take faɗin, "To sarkin karaɗi ai dama yanzu
zan fita ɗin don na fara jin yinwa,ɗakko naman muje dashi can ɗin sai muci kilama shi kawai zan
ci in sha madara ya wadaceni."
Yasmeen ta saki dariya tana cewa,"Ai nan kika fi kauri dama, kwaɗayi da son cin nama kamar
wata kura,duk Iyah ce ta sangartaki haka wallahi,yarinya sai shagwaɓa kamar wata babyn goye."
TAIMIYYAH ta juya ta bankawa Yasmeen harara tana faɗin, "Na dai ji wani ma ya koyi
shagwaɓar idan zai iya mana." Daga haka suka jera da juna zuwa falon.Sun samu babu kowa su
Yah Anas ɗin sun kama gabansu zuwa part ɗinsu.
Guggo Bilki kuma da alamu tana ɓangaren Abbah,sai kawai su TAIMIYYAH suka baje naman
suna ci a tsakiyar falon saman carfet.
Yasmeen ce ta ɗakko musu kwalin Hollandia milk cikin fridge ta haɗo da cup suka zuba madaran
suna korawa da shi,suna cin gasasshen naman da yaji kayan haɗi sai qamshi kawai ke tashi.
Koda suka kammala TAIMIYYAH ta riga Yasmeen isa ɗaki don kwanciya bacci,ita Yasmeen ta
tsaya kallo sai wajen 11:30pm ta shigo lokacin tuni TAIMIYYAH ta jima da yin bacci.
Washegari ya kama ɗaurin aure da yini baki ɗaya.Duk iya yadda Guggo Bilki ta matsama
TAIMIYYAH akan ta tashi ta shirya su fita zuwa gidan bikin tare amma ta ƙi,dama ita Yasmeen
tun safe ta bar gidan bayan ta tashi TAIMIYTAH su wuce tare taƙi tashi.
Hakanan Guggo Bilki ta fice zuwa gidan bikin ita kaɗai.Sai ta bar TAIMIYYAH da masu aiki
dake can baya suna hidimansu.
Ita kam TAIMIYYAH ko ajikinta ta gwammaci tayi zamanta ita ɗaya, data je gidan biki ta shiga
taron jama'a daga me cewa Allah sarki dubi gurguwa sai masu yaba kyawunta.
Ko wanka bata tashi yi ba sai wajen 12 na rana.Gidan yai tsit babu kowa don har mazan duk suna
wajen reception tunda ɗaurin auren sha ɗaya na safe ne,shiyasa babu motsin kowa sai su Ramma
masu aiki kuma duk suna ta can baya.
Lokacin da TAIMIYYAH ta fito wanka tana ɗaure ne da towel da tsayinsa ya zarce guiwanta.Ta
nufi wajen madubi tana jan stool ta zauna don fara shafa mai.
Tana tsaka da shafa man aka turo ƙofar ɗakin aka shigo.Sam ita bata damu ba ta cigaba da
shafanta tana cewa, "Yasmeen kin dawo ɗaukan wani abu hal....."
Maganan ta ya katse ne a lokacin da idanunta suka bango mata wanda ke tsaye daga bakin ƙofa ta
cikin mirrow.
Yah Emran ne ta hango tsaye ya zubo mata manyan idanunsa yana kallonta babu ko ƙiftawa.
TAIMIYYAH take ta ji wani matsanancin faɗuwar gaba da takaicin yadda ya risketa babu kaya
ajikinta.Ta rintse idanunta tana rasa ma me zata yi,ita dai ba zata iya tashi a haka ta nufi wajen da
Hijaban sallansu yake ba.Sai ta gwammace ta cigaba da zama a hakan tunda a zaune take da a ce
ta tashi neman abun rufa ya ganta daga ita sai towel.
Ta buɗe idanunta a lokacin da ya gama sanyo kansa cikin ɗakin tare da maida ƙofan ya rufe.Ya
murza key yana zaresa daga jikin ƙofar ya cilla a aljihun dakakkiyar farar shaddar gezner dake
jikinsa.
Ganin hakan yasa TAIMIYYAH dubansa a firgice tana faɗin, "Lafiya Yah Emran zaka shigo ɗaki
babu neman izini,baka ga a halin daka sameni bane? Please ka fita ka bani waje zan shirya tunda
kai ba muharramina bane."
Yadda TAIMIYYAH take magana cike da zallar ɓacin rai,jikinta har wani rawa yake na tsananin
tsoro yasa Emran sakin wani makirin murmushi.
Idanunsa na cigaba da bin jikinta da wani mayen kallo.A hankali ya fara takowa zuwa inda take
zaune ba tare da ya bi umurninta na fita daga ɗakin ya bata waje ba.Ganin yana tahowa wajenta ne
ya sake jefa zuciyar TAIMIYYAH cikin matsanancin fargaba da tsoro.Ta kai hannuwanta duka
biyu tana sarƙesu a ƙirjinta tare da maida idanunta ta rintse,tana nanata kalmar Innalillahi daga
farkonsa har ƙarshe.........✍🏻
#Ɗansabo ce#
[12/14, 3:43 PM] +234 703 040 9541: *Littafin TAIMIYYAH paid book ne,ga duk wanda ta
tsincesa a kowani irin group ne,kiji tsoran Allah karki karanta sai kin biya 500 naira only.*
*Za ku iya min magana ta wannan number ɗin 08167768704, ko kuma ku turo kuɗin ku kai tsaye
ta wannan account ɗin*👇🏻
0504192664 aisha ibrahim dansabo GTbank.
Masu turo credit za ku turo katin MTN na 500 ta wannan line ɗin 08167768704.
_*Ina ƴan kasuwa masu buƙatar a tallata muku hajar ku? Maza ku garzayo da kuɗi ƙalilan a
tallata muku kayan siyarwanku sai dai kawai ku ji ana kiran waya don buƙatan sayan kayan ku,ku
tuntuɓeni ta layina kamar haka 08167768704.*_
*41*
Emran ya cigaba da takawa zuwa wajen da TAIMIYYAH ke zaune idanunsa akanta,ya tsaya daga
bayanta yana kai hannuwansa duka ya dafa kafaɗunta.
Yadda take magana cikin nuna zallan fusata yasa Emran kai hannu ya bige bakinta da
ƙarfi.TAIMIYYAH ta saki kuka tana ture hannunsa daga jikinta,ta yinƙura don ɗakko Hijab ko
wani abu ta suturta jikinta da shi,sai dai tana ƙoƙarin tashi daga kan stool ɗin Emran ya kai hannu
ya ɗagota gaba ɗayanta zuwa jikinsa.
Kafin tayi wani yinƙuri ya kai bakinsa bisa kunninta yana faɗin, "Ashe baki da kunya ni kike wa
tsawa haka? To bari in tabbatar miki da cewa bani da ilimin sanin haramcin."
Yadda yayi maganan yana ƙoƙarin kai ɗaya hannunsa kan towel ɗin dake ɗaure a ƙirjinta yasa
TAIMIYYAH buɗe baki zata saki ihu...Kamar yasan shirinta kawai sai ya kai bakinsa ya rufe
bakinta ruf!
Take bugun numfashin TAIMIYYAH ya tsaya cak! Jikinta ya ɗauki wani irin rawa.Hakan yasa
Emram ɗagata gaba ɗayanta ya kai kan gado,har lokacin bakinsa na manne da nata, ƙamshinsa na
turaren SAUVAGE DIOR gaba ɗaya ya gama buɗe hancin TAIMIYYAH.
Ta kai hannu ta fara dukan ƙirjinsa da yai mata rumfa da iyakan ƙarfinta,amma Emran bai yi ko
gezau ba har sai da yayi nasaran tura harshensa cikin bakinta,cikin sa a TAIMIYYAH ta samu ta
gantsara masa cizon daya sa shi sakinta babu shiri.
Tayi wani irin hantsalawa gefe guda tana damƙo zanin gadon dake shinfiɗe ta rufe jikinta,wani
matsanancin kuka na ƙwace mata har lokacin jikinta rawa yake kaman mazari.
Emran da yai tsaye yana bin ta da kallo, zafin cizon da taiwa harshensa na ratsa shi,sai ya saki
ƙwafa yana binta kan gadon baki ɗaya ,ya damƙota ita da zanen gadon data cimimiye jikinta da
shi.
Ya fara ƙoƙarin zaro ta daga cikin zanin gadon yana cewa, "Allah yau tunda kika cijeni sai na nuna
miki cewa ni ɗin ba kanwar lasa bane."
Cikin kuka TAIMIYYAH ke masa magiyan yayi haƙuri ya barta amma ina...! Sam bai saurareta ba
sai da yayi nasaran rabata da zanin gadon da ya zama sutura a gareta.
Ganin towel ɗin dake ɗaure a jikinta na son kwancewa, yasa TAIMIYYAH kai hannu ta damƙesa
tana sakin kuka me sauti,dukkanin jikinta na sake ɗaukan rawa, zuciyarta tamkar ta fashe sabida
baƙin cikin wannan tozarci da Yah Emran ke shirin aikata mata.
Hannunsa ya kai yana kamo siririn ƙafarta mara lafiyan ya riƙe a hannunsa, yana kallon yadda
zanen jan Lallin da akai mata ya zauna a farar ƙafartata.Ya cigaba da bin ko'ina na jikinta da kallo
sha'awanta na sake fisgar zuciyarsa,musamman da yaji yadda jikinta ke da wani irin laushi.
Cikin disasshiyar murya yake faɗin, "Zaynab kina da kyau da diri daya kamata ace na
mallakeki,sabida kin mallaki duk abinda nake so a jikin mace,cikas ɗaya ne zai hanani amincewa
da ƙudirin Mamie wannan laluran ƙafar daya mayar dake gurguwa.Ba don hakan ba da gudu zan
amince na aureki ko don in more albarkatun jikinnan naki da kyau,amma ko a yanzu bazan iya
barinki ban ɗanɗana koda kaɗan bane naji yadda daɗinki yake ko Babe?"
Yana maganan ne duka hannunsa na yawo a jikin TAIMIYYAH,wacce ke faman rasgar kuka
jikinta na cigaba da ɗaukan rawa ,kaman wacce zazzaɓi ke shirin kamawa.
Kalaman Emran suka haɗu da tsananin ƙunan da zuciyarta ke yi suna neman tsaida gudun
numfashinta.
Ta saki wani gigitaccen ihu a lokacin da taji ya fisge towel ɗin jikinta yayi jifa da shi.
Emran ya kai hannu ya danne bakinta yana ƙoƙarin haɗata da jikinsa ,amma hannun da
TAIMIYYAH tasa ta kai mishi wani nushi a ciki yasa shi sakinta babu shiri,yana me ɗauketa da
wani gigitaccen mari da hannu ɗaya.Wanda ko kaɗan TAIMIYYAH bata ji zafin marin ba, ta
yinƙura tai wani irin tsalle sai gata a bakin toilet.
Jikinta na wani irin kakkarwa ta buɗe ƙofan ta shige tana murza key.Dai-dai lokacin da Emran da
ke dafe da cikinsa ya ƙariso wajen yana cizon yatsa.
Har lokacin hannunsa ɗaya dafe yake da cikinsa,don bada wasa naushin ya shigesa ba,wanda ya
haifar masa da ɗaurewar mararsa a lokaci ɗaya.
Yana jiyo kukan da TAIMIYYAH ta saki daga cikin toilet ɗin,ya juya yana takawa a hankali ya isa
bakin ƙofa.
Da hannu ɗaya ya yi anfani wajen ciro key ɗin dake aljihunsa ya buɗe ɗakin ya fice.Zuciyarsa na
cike da ɓacin rai da jin zafin yadda bai samu nasara akan TAIMIYYAN ba.
Yaso koda kaɗan ne ya murji jikinta koya rage zafi koda ace bai shigeta ba,sai gashi ta
shammacesa da wannan nushin ta kufce masa.
Ya cije lips ɗinsa yana girgiza kai cike da takaici,har ya fice daga falon hannunsa ɗaya na riƙe da
cikinsa, ya nufi ƙofan fita daga sashin baki ɗaya zuwa nasu part ɗin.
TAIMIYYAH dake cikin bayi tana rasgar kuka tana jin lokacin daya fice daga ɗakin.Hakan yasa ta
fitowa da hanzari ta nufi ƙofar ɗakin ta kulle tana me barin key ɗin a jikin ƙofar.
Kuka take yi sosai jikinta kuma bai daina ɓari ba,ta faɗa kan gadon Yasmeen tana sake rushewa da
wani sabon kukan.Bata taɓa tunanin Yah Emran ɗin tantitin ɗan iska bane sai yau da yake ƙoƙarin
tazartata,duk don kasancewarta gurguwa da yake ganin zai iya cin banza akanta.
Hankalinta taji ya yi mummunan tashi, gaba ɗaya sai taji hankalinta ya koma gida,zaman Kanon
ya isheta hakanan,ba kuma taji zata iya wuce gobe bata ganta a gaban Iyah ba.
Ta share fiye da mintuna talatin tana rasgar kuka kaman ranta zai fita.
Da ƙyar ta iya tashi tana layi dafe da ƙafarta me laluran ta nufi toilet tana me sakarwa kanta
shower,ruwa me sanyi na ratsa tsakiyan kanta yana gangara a jikinta.
Ta jima a durkushe ruwan na jiƙe dukkanin jikinta,kafin ta ɗauro wani towel ɗin ta fito daga
bayin,jikinta na ɗaukan wani sabon rawar kamun zazzaɓi.
Ta isa wajen kayanta ta zaro wata riga mara nauyi ta saka, ko bra da pant bata tsaya sakawa ba ta
naɗe akan gado tana sake ɓallewa da kuka.
Nan da nan jikinta ya ɗauki matsananci zafi kanta na wani irin ciwo.Ta janyo wayarta da ƙyar tana
kiran layin Yameen,bugu biyu Yasmeen ta ɗauka.
Da ƙyar TAIMIYYAH ta iya ce mata, "Yasmeen don Allah ki dawo gida banda lafiya." Daga haka
tayi jifa da wayar ba tare da ta tsaya kashewa ba,sai Yasmeen ce tayi hanging up daga ɓangarenta.
Ta dubi ƙawayensu da suka cika ɗakin da suke zaune ta miƙe tana cewa, "Friends ku bani awa
ɗaya zan je gida na dawo TAIMIYYAH ce bata jin daɗi Firdausy."
Yasmeen ta kai ƙarshen maganan tana duban Feedoh,kafin ta ɗauki mayafinta don fita lokacin da
Feedoh ke cewa, "Ayyah..! Ki gaisheta please, zuwa anjima zan zo nima idan muka gama da
jama'a,Allah ya bata lafiya."
Yasmeen ta amsa da "Ameen." Tana saurin ficewa daga ɗakin ta nufi waje,lokacin data fito daga
gidan Baba Lawal sai taci mugun sa a wani mai adaidaita ya sauke wata,kawai sai ta shige tana
sanar masa cewa can layin zai zagaya da ita.
Lokacin da suka ƙariso gidan ta bashi kuɗinsa a guje ta shige,bata ja birki a ko'ina ba sai bakin
ƙofan shiga ɗakinsu.Ganin ƙofar a kulle yasa ta fara bugawa tana faɗin, "TAIMIYYAH gani na
dawo taso ki buɗe ƙofar,in banda abinki ma ya za a yi ki rufe kanki a ɗaki bayan kuma baki da
lafiya." Ita dai TAIMIYYAH dake daga cikin ɗakin jin muryan Yasmeen ne yasa ta tashi da ƙyar ta
dafo ƙafarta tazo wajen ƙofan ta buɗe.
Yasmeen da idanunta suka sauka kan fuskar TAIMIYYAH tayi saurin sakin salati tana faɗin, "Na
shiga uku ni Yasmeen kinga idanunki kuwa TAIMIYYAH,duk ciwan ne yasa ki kuka har idanunki
suka kumbura haka,amma kika kasa kirana sai yanzu?"
TAIMIYYAH gaba kawai tayi ta nufi gado ta kwanta,cikin sanyin murya take cewa, "Yasmeen
please bani abinci da magani kawai, ki aje duk waɗannan question ɗin,jiri nake gani wallahi."
Tayi maganan wasu hawaye masu zafi na sake ɓalle mata.Yasmeen ta juya da sauri don zuwa ta
kawo mata abinci da maganin kamar yadda TAIMIYYAN ta buƙata.
Lokacin data dawo hannunta riƙe da plate ɗin data zubowa TAIMIYYAH Jallop ɗin
shinkafa,wanda ya ji busassshen kifi da nama aciki,sai ta aje plate ɗin akan gado tana cewa, "Ga
abincin ki tashi ki ci bari inje in ɗakko miki magani a ɗakin Abbah."
TAIMIYYAH ta tashi ta zauna tana fara cin abincin a hankali.So take ta ƙarfafa kanta ko zata
samu nasaran barin garin a gobe,don ta san idan ta cigaba da nuna bata da lafiya to Guggo Bilki ba
za ta taɓa bari ta tafi a goben ba.
Shiyasa lokacin da Yasmeen ta kawo mata maganin ciwan kai da zazaɓin,sai ta amsa ta shanye
tana aje cup ɗin ruwan dake hannunta ta dubi yasmeen ɗin tana cewa, "Alhamdulillah! Har na ɗan
ji ciwan kan ya fara sauka,in gaya miki Mamienku na fita ba sai ciwan kai ba,na fara jin sanyi
alamun zazzaɓi shine fa naje na tara kaina a shower ina fitowa kuma sai rawar sanyi ba,na kifa
ciki nai ta kuka ashe ƙarawa kaina wahala nake, kaina ya ɗauki wani irin ciwo,gaskiya gobe sai
gida don na kula kaman zaman garinnan ciwo zai sani in kwanta,na gaji hakanan gobe gida zan
koma gaskiya."
Yasmeen data tsurawa TAIMIYYAH ido ta balla mata harara tana cewa, "Aiko baki isa ba sai next
week zaki tafi,ba wani ciwan da zaki kwanta in Allah ya yarda.Ke ɗince kin cika raki abu kaɗan
duk ki narke ki ta faman kuka,ni wallahi har kin bani tsoro da na ga yadda idanunki suka
kumbura."
TAIMIYYAH ta narke face cike da shagwaɓa take cewa, "Seriously Yasmeen hankalina yayi
gida,ai nayi ƙoƙary yau fa sati na ɗaya kuma dama ai sati ɗaya nace zanyi, monday zamu koma
skull don haka ni da gaske nake yi gobe zan koma, zan ma kira Iyah in sanar mata a turo Sani da
wuri ya ɗauke ni,tunda ku ma kai Amarya za ku tafi goben."
Yadda Yasmeen ta ga TAIMIYYAH tayi maganan da serious sosai yasa ta gama gane rigimi take
ji,kuma da gasken take yi hankalinta ya yi gida.Sai ta dubi TAIMIYYAH tana cewa, "To shikenan
bari Mamie ta dawo sai aji me zata ce."
TAIMIYYAH ta wani kwaɓe fuska take cewa, "Oho! Ni dai babu wani daɗin bakin da za a min
gida zan tafi gobe Allah kuwa."
Kafin Yasmeen tace komi sai ga kiran Iyah ya shigo wayar TAIMIYYAH,ta ɗauka cikin sauri tana
faɗin, "Hello! My Iyah kaman kin san ke zan kira yanzu wallahi,ina yini dafatan kuna lafiya?"
Daga ɓangaren Iyah ta amsa da cewa, "Lafiya lau Zainabu ina fata goben dai zaki dawo ko? Duk
kewanki ya dameni ɗazu ma Ummien ku da ta shigo take tambayan yaushe zaki dawo." Iyah ta
dakata tana sauraran me TAIMIYYAH zata ce daga nata ɓangaren,TAIMIYYAH ta sauke ajiyan
zuciya tana cewa, "Eh gobe zan dawo Iyah Insha Allah,maganan ma muke da Yasmeen kika kira
yanzu,sai ki ma Sani magana tun yau ,gobe idan Allah ya kaimu sai ya taho da wuri mu dawo."
Iyah daga ɓangarenta ta jinjina kai kaman TAIMIYYAH na ganinta kafin ta furta, "Hakane zan
masa magana yanzu ma muna gama wayan da ke,ina su Bilkin suna ta biki tace ke kinƙi shiga
cikin mutane,nace mata to ina ta ga kina zuwa bare ki saki jiki da mutane dama,gara ki yi
dawowarki gida hakanan,dama ai kwana bakwai kika ce za ku yi ku koma makaratar da kike zuwa
ɗin ko?"
TAIMIYYAH ta jinjina kai cike da shagwaɓa take cewa, "Eh Iyah wallahi duk na ƙosa in dawo
nayi kewarki sosai." Daga haka suka ɗan taɓa hira da Iyah kafin suyi sallama da juna akan cewa
Iyan zata kira Sani,gobe da wuri sai ya kamo hanya.Yasmeen da ke zaune tana jin wayan
TAIMIYYAH da Iyah ta zabgawa TAIMIYYAH harara tana cewa, "Ai saiki ta tafiya goben kifi
ruwa gudu ma idan kin so."
TAIMIYYAH ta saki wani murmushin yaƙe, tana jin relief a zuciyarta da Iyah ta goya mata baya
ta koma a goben,ta dubi Yasmeen tana cewa, "Sorry Babyn Aliyu,da gaske hankalina yayi gida
ne."
Yasmeen ta taɓe baki tana faɗin, "To ni bari na koma tunda naga kin ji sauƙi,ko kawai ki tashi ki
shirya mu koma tare,ke kanki idan kika shiga cikin mutane za ki ji daɗi."
Babu musu ko TAIMIYYAH ta tashi, har abin ya so baiwa Yasmeen mamaki,amma sam bata
kawo komi cikin zuciyarta ba illa bin TAIMIYYAH da kallo da tayi,lokacin data isa wajen kayanta
tana ciro rigan da zata saka.
Wani haɗaɗɗen doguwar rigan Swiss Excelsior ta sanya,kalan maroon and milk da akaiwa touch
da black kaɗan-kaɗan a jikin kwalliyar.Kalan yayi wa TAIMIYYAH kyau sosai kasancewarta
fara,gashi ɗinkin ya zauna a jikinta wanda ya kasance yankan A-shape ne.
Ta nufi wajen mirrow tana ɗaukan powder ta murza kaɗan,sai tayi lining manyan idanunta da eye
liner.Take fuskarta ya ɗauki wani irin kyau da ƙyalli don ma idanun nata sun ɗanyi ja sabida kukan
data sha,amma duk da hakan tayi kyau ba kaɗan ba, musamman lokacin data kafa ɗaurin ture kaga
tsiya,tai ɗan baya dashi kaɗan bai cokaro gaban goshi sosai yadda wasu ke yi ba.
Yasmeen data zuba mata ido ta buɗe baki tana faɗin, "Masha Allah,wannan irin kyau haka
TAIMIYYAH gaskiya kullum ki dinga wa Allah godia wanda ya kyautata halittarki,Masha Allah!
Masha Allah! Da wannan kyakykyawar halitta."
TAIMIYYAH ta ɗan harareta kaɗan tana faɗin, "Zaki fara ba,godia kam kullum cikinta muke
Yasmeen,muje don Allah ni karki tasani kina faman yabon kyawu kaman baki taɓa ganin
kyawawaba sai ni."
Yasmeen data miƙe tana ɗaukan mayafinta ta yafa,sai ta dubi TAIMIYYAH tana faɗin, "Ke dai
kawai ayi shiru yanzu dai saka Ɗan-kunni mu wuce,hakan zai sake fito da kwalliyarki, ke baki son
saka Ɗan-kunni."
TAIMIYYAH ta ɗauki wasu Ɗan-kunninta da ke saman mirrow ɗin ta sanya,aiko nan da nan
kwalliyarta ya sake haskawa.
Ta ɗauki wayarta bayan ta yafa gyalen daya shiga da kayan jikinta,ta dubi Yasmeen tana cewa,
"Muje Yasmeen kin tsaya sai kallona kike yi." Yasmeen ta saki murmushi tana yin gaba
TAIMIYYAH ta biyo bayanta.
A falo sukai arba da Yah Emran zaune daga ɓangaren dining,ya sauya shiga daga farar shaddar
ɗazu zuwa ƙananun kaya.
Kallo ɗaya TAIMIYYAH taiwa wajen da yake zaune, ƙirjinta ya buga da wani irin ɓacin rai,da
sauri-sauri take dafa ƙafarta me laluran tana tafiya har ta fice daga falon,yanayin da suka kasance
ciki a ɗazu na dawowa kwanyanta.
Emran da Yasmeen ta tsaya yi masa magana yabi bayan TAIMIYYAH da kallo,yana jin wani
yanayi na sake taso masa,don wankanta ya cijesa matuƙa.Cikin zuciyansa yake faɗin 'Gaskiya
Yarinyar akwai body da laushin jiki,ga kyau babu ƙarya kawai nakasanta shine illarta."
Maganan da Yasmeen tayi ne ya dawo dashi daga zancen-zucin daya tafi,tana cewa, "Yah Emran
ina magana,nace zan samu 5k ɗin ne ko mu wuce kawai?"
Ya sauke manyan idanunsa akan Yasmeen ɗin yana cewa, "Bani da cash a jikina yanzu, amma zan
miki transper ki turo min details ɗinki har dana Zaynab zan saka muku kuɗin." Daga haka ya
maida idanunsa akan abincin da ya zuba bai sake duban Yasmeen dake masa godia ba.
Itama ganin hakan yasa ta fice ta cimma TAIMIYYAH a waje tana tsaye jingine da jikin gate tana
jiran fiwowan Yasmeen ɗin.
Lokacin da Yasmeen ta ƙariso sai da TAIMIYYAH tayi mata mitan daɗewan da tayi bata fito
ba.Yasmeen ta sanar da ita abinda ya tsaidata,sai kawai TAIMIYYAH ta taɓe baki bata kuma
magana ba har suka samu abin hawa suka isa gidan bikin.
Basu dawo gida ba sai dare don tara da rabi ma ta wuce suka shigo gida.Tun a gidan bikin dama
TAIMIYYAH ta sanar da Guggo maganan tafiyarta a goben.
Da Guggo Bilkin tace tayi haƙury har zuwa monday su dawo kai Kausar Amarya,wacce za a kai
Katsina amma sai TAIMIYYAH tace wa Guggo Bilki ai har sun gama magana da Iyah, gobe da
wuri Sani zai zo su wuce.
Tunda Guggo Bilki ta ji cewa Iyah za ta turo Sani tasan zance ya ƙare,hakan yasa ta amsawa
TAIMIYYAH da cewa Allah ya kai su goben lafiya.
Yanzu da suka dawo daga gidan bikin sai kawai TAIMIYYAH ta hau haɗa kayanta.Yasmeen na
taya ta tana mitan yadda TAIMIYYAN ta dage,sai ta tafi kaman wata wadda akai alluran
tuburewa.
Ita dai TAIMIYYAH jin Yasmeen kawai take yi,don ba za ta iya sanar da ita irin halin ƙuncin da
zuciyarta ke ciki, akan tozarcin da Yayansu yai mata a ɗazu bane,shiyasa kawai taja bakinta ta
ɗinke.Suka cigaba da kammala shirya kayanta cikin akwati,Yasmeen ɗin ta fice daga ɗakin ta bar
TAIMIYYAH na yin waya da Maryam Sanusi.
Washegary da wuri TAIMIYYAH ta tashi sukai sallama da Yah Anas da Ahmad kafin su fita wajen
aiki.Kowannensu sai da ya bata kuɗi tai musu godi,mutumin nata Emran ne kawai basu haɗu ba.
Lokacin data je gaida Abbah shi ma kuɗin ya bata dubu goma yace ta sayi kayan kwalliya,ta amsa
tai godia tana fitowa daga ɗakin Abban.
Ta sanyo kai don fitowa kenan Emran da zai shiga ɗakin na sanyo kai, saura kaɗan suyi karo
TAIMIYYAH tayi saurin yin baya ta bashi hanya.Ya shige yana barin mata qamshinsa na turaren
SAUVAGE DIOR.
Ta wuce cikin sauri tana jin daga ƙamshin har mamallakinsa ta tsanesu tsana me tarin yawa.Koda
ta isa ɗaki lokacin Yasmeen ta fito wanka tana shafa ne,TAIMIYYAH ta zauna daga bakin gado
tana zube kuɗin da ke hannunta.
Ta toilet direct itama ta yo wanka ta fito,cikin sauri ta gama shirinta tsaf cikin wasu riga da skat na
atamfa.Suka fito tare da Yasmeen sukai breakfast TAIMIYYAH na ji cikin ranta duk ta ƙosa Sanin
ya iso.
Ƙarfe tara da rabi Sani ya iso garin Kano.Bayan an kai masa abin karyawa ya ci ya huta, wajen 11
suka kamo hanya da TAIMIYYAH,bayan su Yasmeen da Guggo Bilki sun yo mata rakiya har
bakin mota.
Yasmeen har da kukanta lokacin da TAIMIYYAH ke ɗaya mata hannu,itama kanta TAIMIYYAH
sai data share hawaye.
Sun ɗakko hanya da Sani wanda ke tuƙinsa cikin salama da ƙwarewa.Idanun TAIMIYYAH suka
sauka akan wajen ATM machines da ake cire kuɗi.
Tace wa Sani ya tsaya daga bakin hanya ta bashi ATM card ɗinta,ta gaya masa pin ɗin tace ya ciro
mata duka dubu sha biyar ɗin da Yah Emran ya tura musu ita da Yasmeen a jiya.
Sani ya ciro kuɗin ya dawo suka kama hanya bayan ya baiwa TAIMIYYAH kuɗin da ATM card
ɗinta.Sai ta sanar da shi cewa tana son ya kaita inda zata iya ganin nakasassu masu bara akan
hanya,zata basu sadaka ne.
Sani ya kai ta inda yasan masu nakasa suna zama,kama daga gurugu har ma da makafi da kutare.
TAIMIYYAH ta rabar musu da duka kuɗin sannan suka kamo hanyar Zaria.Tana ji zuciyarta na
rage zafi da raɗaɗin baƙin cikin da Yah Emran ɗin ya kimsawa zuciyartata,amma bata ji memory
ɗin abinda ya yi matan zai goge daga kwanyarta har abada.
*Za ku iya min magana ta wannan number ɗin 08167768704, ko kuma ku turo kuɗin ku kai tsaye
ta wannan account ɗin*👇🏻
0504192664 aisha ibrahim dansabo GTbank.
Masu turo credit za ku turo katin MTN na 500 ta wannan line ɗin 08167768704.
_*Ina ƴan kasuwa masu buƙatar a tallata muku hajar ku? Maza ku garzayo da kuɗi ƙalilan a
tallata muku kayan siyarwanku sai dai kawai ku ji ana kiran waya don buƙatan sayan kayan ku,ku
tuntuɓeni ta layina kamar haka 08167768704.*_
*42*
*Zaria,Gonan Ganye.*
Motar Suhailah ce ta faka daga cikin parking space na gidan Hajjah.Ta fito sanye cikin lafaya me
asalin kyau tsada ta yane jikinta daga sama har ƙasa,kai kace irin kanuri ɗinnanne dangin shuwa.
Kalar Lafayar wani irin Blue ne da akaiwa ado da kalan Red and Black haɗe Silver ajiki.Tayi
kyau da shigan sosai hannunta riƙe da key ɗin motarta da hand bag ta nufi cikin gidan.
Da sallama ta isa cikin falon Lubah me aiki ta amsa sallamar tana ma Suhailah sannu da
zuwa,Hajjah ta fito daga ɓangaren kitchen kenan tayi arba da Suhailah.
Sai ta saki murmushi tana faɗin, "Ashe ma gaki kin iso yanzu muka gama maganarki a waya da
Antinku Raliya,tana gaya min kin biya kinyi mata sallama tun ɗazu."
Suhailah ta aje bag ɗinta saman kujera tana ƙoƙarin zama take cewa, "Wallahi Hajjah saloon na
biya shiyasa,da tun ɗazu na iso nan ɗin,kuma na tadda har mutum biyu a wajen shiyasa na daɗe."
Hajjah da itama ta nema waje ta zauna ta jinjina kai tana faɗin, "Ai Maleek yace tafiyan ma ba
gobe ba sai jibi,amma dai angama miki duk abubuwan buƙata har garin kunu dana ɗan-wake duk
an gama,ni kaina har na gama shiri amma na sanar masa kwana ɗaya zanyi na gama ganin wuri sai
a dawo dani,bazan iya wata guda a cikin yara ba kamar mara faɗi haka kawai ba haihuwa ba
bakomi ba."
Suhailah sai ta zumɓure baki tana cewa, "Kai Hajjah don Allah karki ce haka,ni wallahi ji nake yi
kamar kada na koma indai ba za ki yadda ki bimu kiyi wata a can ba,ki daure Hajjah please!"
Hajjah ta girgiza kai tana cewa, "Wallahi bada ni za a yi wannan haukan ba,sai dai ki fasa bin nasa
wannan matsalarku ne ke da shi,au kinga na manta jiya ƙawarki ta zo nan gidan,take tambayata
wai ko kun bar gari ne ta je gidanku yafi sau uku mai gadi na hana ta shiga,baki ga abin arziƙin
data kawo min ba gashi can a ɗaki banma juye su daga ledan ba."
Suhailah taiwa Hajjah ƙuri zuciyarta na ɓaci da jin kalmar sunan Zuby da Hajjah ta faɗa,ta ja tsaki
tana faɗin, " Hajjah ita Zubaidan ce tazo har gidan nan ɗi? Lallai ne wato tanan zata ɓullo sabida
nayi blocking duk wata hanyar haɗuwata da ita,to wallahi tayi kuskure kamar yadda Maleek yasa
ai mata iyaka da shiga gidansa,haka zai sa ai mata iyaka da xuwa nan ɗin ma, banza kawai
maciyiya amana."
Yadda Suhailah take magana cike da ɓacin rai yasa Hajjah sakin baki tana kallonta har ta kai
aya.Kafin ta buɗe baki tana duban Suhailan take cewa, "Lafiya me kuma yafaru tsakaninki da
ita,yadda naga kina jida wannan Zubaidar,me tai maki nacin amana ni Hajjah?"
Suhailah nan take ta zayyanewa Hajjah duk yadda suka yi da Zuby,har kawo ɗaukan numbern
Maleek data yi ta ba Zubyn,da irin saƙonnin iskancin da Zubyn ta dinga tura masa bata rage komi
ba ta zayyanewa Hajjah,ta kai ƙarshen maganan da cewa, "Shine yanzu don an toshe kafan da zata
dinga shiga min gida,ni kuma nayi blocking line ɗinta shine zata zagayo ta ɓangarenki sabida tana
son cusa kai a wajen Maleek taci amanata."
Hajjah da tsananin mamaki da takaicin Suhailah ya rufeta,ta ballawa Suhailah harara tana cewa,
"Ai bai birgeni ba Maleek ɗin da bai amsa tayin aurenta ya aureta ba,tunda ke kin maida kanki
sakarya shashasha..!! Na rasa wani irin wauta kike dashi Suhailah,an gaya miki yanzu ana wani
amintane yadda xamani ya lalace da cin amanan juna,hatta ɗan uwanka na jini baka tsira da ya ci
amanarka ba indai akan abin duniya ne.To wallahi ki kuka da kanki tun wuri ki aje duk wani
sakarci ki kama kanki da mijinki,me ma ya kaiki aminta da Bazawara kamarta da idanu a
tsatstsaye na fitsara,to ai yanzu kinga ta fito miki da halinta dama ba sabida Allah ta shiga jikinki
ba tana da manufa.To kurwanta kur akan ku daga ke har Maleek ɗin,Allah yai min tsari da haɗa
zuri'a da irin su,tsaye kyam nake akanku ba dare ba rana,musamman Maleek da yake namiji
sabida ina jiye masa ruɗin zamani da sharrin kuɗi,domin yanxu idon mutane da yawa na kansa
maza da mata,shiyasa daga ance miki ƙarfe uku tayi na gama bacci kenan,ina kan sallaya ina
miƙama Ubangiji kuka na akan ya tsaremin gaba da bayansa,ya karesa daga dukkanin sharrin
zamani da ruɗinsa,duk wacce xai saukar dashi akan hanya Allah ya shiga tsakaninsa da su.Don
haka ina da yaƙini Ubangiji yana jina kuma yana amsa buƙatuna,daga ke sai shi nake kallo a
matsayin sanyin idanuna Allah yai muku tsari daga dukkan sharrin na mutum da aljan."
Suhailah ta amsa da cewa, "Ameen ya hayyu ya qayyum Hajjah,Allah yaja kwana ya barmu tare
har abada,yadda kike tsaye akanmu Allah ya bamu ikon yi miki biyayya har abada."
Hajjah ta amsa da cewa, "Ameen." Sannan ta cigaba da yiwa Suhailah faɗa da Nasiha akan ta
kula,ta kuma yi hattara da sharrin ƙawayen zamani,ta kama mijinta da kyau ta aje duk wani
sakarci,maganan haihuwa kuma ta dage da addu'a sai ta ga Allah ya kawo mafita cikin sauƙi,idan
ma har ƙaddara zai sa Maleek sake aure duk ta barwa Allah ikonsa,tayi addu'a Allah ba zai kawo
wacce zata cutar da ita ba.
Suhailah dake sauraren Nasihar Hajjah da kunnuwan basira duk sai jikinta ya yi sanyi.Wani irin
ƙaunar Hajjah da ba zai misaltuba na sake mamaye zuciyarta,ta sani Hajjah uwa ce ta gari a
wajenta wacce bata da tamkarta har abada,kuma tayi mata dukkanin gata da ko uwarta na raye
iyakan gatan da za ta yi mata kenan.
Hajjah ta cike mata gurabe da dama cikin rayuwarta ta zame mata uwa kuma uba duk a lokaci
ɗaya.Sannan bata barta haka ba sai da ta ɗauki aurenta ta baiwa nagartaccen tilon ɗanta,wanda duk
duniya ba za ta iya haɗa soyayyarsa da kowa ba.
Hawaye suka cika idanun Suhailah a lokacin da zuciyarta ya tuna baya,tun daga kan tashinta a
hannun Hajjah tun tana ƴar shekaru biyar,har kawo kan aurenta da Maleek wanda akayi lokacin ba
wani son ta yake a zuciyarsa ba.Ya dai amsheta ne sabida Hajjah da kuma soyayyar da ke
tsakaninsa da mahaifiyarta da yake kira da Anty Hauwa.
Itace kaɗai ke masa wata irin azababbiyar soyayyah a lokacin, wanda hakan yasa Hajjah jajircewa
har sai da Maleek ya amince da aurenta.Bayan anyi auren ne a hankali shi ma zuciyarsa ta kamu
da ƙaunarta me ƙarfi.
Ta isa kusa da Hajjah tare da kifa kanta a jikinta tana faɗin, "Hajjah naji dukkanin nasihar ki kuma
ina baki tabbacin zan gyara kusa-kurai na,Hajjah har abada ke ɗin ta dabance cikin zuciya da
ruhina.Allah ya cigaba da bani ikon yin biyayya ga dukkanin umurninki har a zare numfashina
daga gangar jikina."
Hajjah ta rungume Suhailah sosai a jikinta,tana shafa kanta take cewa, "Kar kiyi kuka Suhailah
kome nai miki a rayuwa kaina da ƴar uwata nayi mawa,abinda kawai nake so dake a ko yaushe ki
zama me haƙuri da yawan ibada,tare da riƙe sirrin mijinki komin rintsi kada ki bari aji kanku,ki
kula da mu'amalarki da mutane sabida lalacewar zamani.So da yawa maƙiyanka sune na jikinka
wanda kafi kusanci dasu,dariya ba ƙauna bace Suhailah kar ki ga wasu mutane na buɗe miki
haƙora a waje ki ɗauka ƙaunace.Bance kar kiyi ƙawance ko hulɗa da mutanen arziƙi ba,amma ki
kula kisan wa zaki dinga tarayyah da su,musamman a yanzu da zaki garin masu buɗewan ido sai
fa kin dage kinyi kaman kina yi wajen sake janyo zuciyar mijinki,Allah yai muku albarka duniya
da lahira."
Suhailah ta amsa da, "Ameen Hajjah,nagode Allah ya ƙara girma da tsawancin kwana me albarka
Ameen."
Daga haka suka cigaba da hira da Hajjah gami da tattaunawa akan matsalolin rayuwa,da lalacewar
zamani da irin yadda mutane suka ɗauki cin amana ba a bakin komi ba.Sosai Suhailah ke sake
ɗaukan tarin ilimi a maganganun da Hajjah take yi,wanda rabi hannunka me sanda take sake yiwa
Suhailah.Tana sake tsoratar da ita akan sauyawar zamani, cikin hikima ta yadda zata zabure ta
zama irin macen da take mata fatan zama a wajen mijinta,sabida wautan Suhailah na son yin yawa
ta gama lura tana da sakaci wajen kama miji a hannu,ita kuma ba kasafai take son ta dinga zaƙewa
akan nunawa Suhailah ga yadda zata dinga yiwa Maleek ɗin ba,sabida kada watarana sharrin
zuciya ya kimsawa Suhailah cewa tana matsa mata ne don kasancewan Maleek ɗin jininta tilo da
kowa ya san tana son sa fiye da komi cikin rayuwarta.Shiyasa take kawaici da kauda kai a wasu
tarin abubuwan da Suhailah ke sakaci dasu, tafi yin mata hannunka me sanda ko jirwaye cikin
hikima.
Sai can yamma sosai Suhailah ta baro gidan Hajjah, bayan ta kammale duk abubuwan da zasu
wuce dashi Abuja na anfanin yau da kullum.Sabida jibi da wuri zasu wuce har da Hajjah da zata je
ganin inda zasu tare a Abujan,duk da cewa taƙi amincewa ta zauna dasu koda na wata guda ne a
can ɗin,kafin ta dawo Zaria kamar yadda Maleek ya faɗi.
___________
Tunda TAIMIYYAH suka iso ta gama gaisawa da su Iyah,shikenan sai ta shige ɗakinta tai wanka
tayi sallah ta kwanta bacci.
Bata tashi ba sai yanzu da agogo ke buga uku da kusan rabi.Ta nufi toilet tayi uzurinta tare da
ɗauro alwalan sallan la'asar da aka kusa kira.
Koda ta fito sai data jira aka kira sallah tayi kafin ta fito falo don cin abinci,sabida da wata irin
mahaukaciyar yinwa ta tashi,sabida bata tayi lunch ba ta kwanta bacci.
Tana tsaka da cin abincin Iyah ta fito daga ɗaki cikin shirin fita unguwa.Ta ƙariso wajen cin
abincin nasu tana cewa TAIMIYYAH, "Zainabu zan ɗan je can tudun wada gaisuwan wani rashi
da aka yi,jikan Babah Rabi ƙawata ne suka zo ganin gida ashe ajalin nasa na nan,zani musu
gaisuwa in dawo in kin gama cin abincin sai ki tafi wajen Ummienki ta san cewa kin dawo."
TAIMIYYAH ta ɗaga manyan idanunta ta sauke akan Iyah tana cewa, "To Iyah adawo lafiya Allah
yai masa gafara,dama yanzu nake so idan na gama in shiga can ɗin."
Daga haka Iyah tai tafiyarta ta bar TAIMIYYAH na ƙarisa cin abincinta,koda ta kammala wayarta
kawai da Hijab ta ɗauka ta nufi sasan Ummie.
Da sallama ta shiga cikin sasan, idanunta suka fara sauka akan Inna Larai ,dake waje tana gyara
kayan miya.
TAIMIYYAH ta gaisheta cike da ladabi,Innar ta amsa da fara'a tana ma TAIMIYYAH sannu da
zuwa.
TAIMIYYAH ta wuce ta zuwa ciki tana doka sallama daga bakin ƙofar shiga falon gidan.Ummie
da ke daga zaune cikin falon ta amsa sallamar da cewa, "Oyoyo Zaynab ashe yau ɗin dai zaki
dawo."
TAIMIYYAH ta shiga da fara'a saman fuskarta take cewa, "Wallahi ni ce na matsa saina dawo yau
ɗin,amma dana biyewa Yasmeen da Guggo Bilki aida sai na ƙara sati."
Ummie ta saki murmushi tana faɗin, "Gaskiya kin bamu kewa ni duk sai na ji gidan shiru,don ma
yanzu su Basmah kan shigo min hira."
TAIMIYYAH ta zauna daga kujeran kusa da Ummien suka fara taɓa hira,don yanzu Ummien sosai
take sakar mata fuska da son janyota ajiki,ba kaman lokacin da Abie ke raye da sam bata wani
sakar mata fuska sosai ba.Amma a yanzu tana nuna kulawa akanta sosai har abin na baiwa
TAIMIYYAH mamaki.
Ita ko Ummie tsakaninta da Allah yanzu son TAIMIYYAN ya shiga ranta, musamman data rasa
nata ƴaƴan da mijinta,TAIMIYYAN itace kaɗai jinin Sameer da take gani taji sanyi a zuciyarta
yanzu,shiyasa take jin ƙaunarta har cikin zuciyarta.
TAIMIYYAH ta daɗe sosai a sasan don ta saki jiki ana ta hira da Inna Larai,wacce take da yawan
barkwanci da wasa da dariya,shiyasa take da daɗin zama sosai.
Lokacin da TAIMIYYAH zata fito daga part ɗin Ummie, su kuma su Zuhurah sun iso zasu shiga
kenan,sai TAIMIYYAH ta basu hanya tana cewa, "Zuhurah sannun ku Yasmeen tace tana gaishe
ku."
Ga tsananin mamakin TAIMIYYAH sai ta ga sun amsa ta cike da fara'a suna tambayarta yaushe ta
dawo? ta basu amsa cewa ɗazu da rana ta iso.
Suka wuce ta zuwa ciki ita kuma ta juya ta fara takawa don komawa Sasan Iyah,koda ta shiga ta
samu Iyah ta dawo suna zaune da Babah Ladi a falo suna hira.Itama TAIMIYYAH sai ta zauna aka
cigaba da hiran da ita,kafin shigowan kiran Yasmeen yasa ta tashi ta nufi ɗaki suna waya,inda
Yasmeen take sanar da ita wai Yah Emran har ya amsa lambarta wajen Yasmeen ɗin,shine ta kira
taiwa TAIMIYYAH tsiya akan kodai ta tafi da zuciyar Yayan nasu ne? TAIMIYYAH da takaici ya
isheta sai kashe wayarta tayi baki ɗaya ta zauna daga gefen gado,ta dafa goshinta tana jin wani
matsanancin ɓacin rai na lulluɓe zuciyarta.
'Me yake nufi da amsar lambarta wajen Yasmeen,me xai ce mata idan ya kirata?"
Waɗannan tambayoyin suka dinga damun zuciyar TAIMIYYAH,tunaninta na komawa kan abinda
ya faru tsakaninsu kwana ɗaya daya wuce.Sai ta samu kanta da zubda hawayen da ba za ta iya
tantance asalin dalilin zubansu ba,ta rasa tsakananin kalamansa na raini da nuna ƙasƙanci ga
nakasan dake tare da ita daya furta,da kuma abinda yai mata na son keta alfarmarta wanne yafi yi
mata ciwo a zuciyarta? Ta kai hannu tana share hawayen zuciyarta na wani irin zafi da ƙuna,duk
inta tuna dangantar dake tsakaninta da shi,da yadda ya iya yi mata abinda yayin,sai taji zuciyarta
ya raunana, wani tsoro na lulluɓe ruhinta baki ɗaya.
Tana jin ciwo a zuciyarta,da tsoron anya ko zata samu wanda zai so ta tsakani da Allah har tayi
aure wataran, kamar yadda su Iyah ke kwaɗaita mata? Tarin tunanin da suka dinga cinkushe
kwanyarta da zuciyarta kenan,har lokacin da aka kira sallah sannan ta iya miƙewa ta nufi toilet.
"Yah Zuhurah mutumiyan namu na ga duk ta sake wani sanyi ne,da alamu ta gama saka rai da zata
mallaki handsome Nass ɗinta ne,sai kuma uwarsa tai mata cikas, wallahi duk na ƙosa akai stage
ɗin da zai tako ƙafarsa gidan nan ayi me kankat ɗin.Kin san yanzu lallaɓashi nake tayi muna chart
tamkar babu wata manufa a zuciyata akansa,nuna masa nake yi ina bala'in tausayinsu daga shi har
gurguwar tasa,shiyasa ya saki jiki dani har yake sanar dani irin tarin damuwan da yake ciki akan
rabuwarsa da TAIMIYYAN.
Ashe wai uwarsa ce masa tayi ko a waya ya kirata bata yafe ba,don tafi so kwata-kwata ya shafe
babinta a zuciyarsa.Amma fa da gaske ba ƙaramin so yake wa TAIMIYYAH ba,zan yi aiki kafin in
mantar da zuciyarsa ita koda na mallakesa."
Basmah ce ke wannan maganan suna zaune tare da Zuhurah a falonsu,bayan sun kammala cin
abincin dare.
Zuhurah ta ɗaga kai ta kalli Basmah tana cewa, "Ai baki sani ba,TAIMIYYAH yadda kika san tana
da wani magic na farin jinine a tare da ita,ki duba kiga yadda babu wuya ta shiga ran
mutane,shiyasa ai duk wanda zai so ta ba zai mata so na wasa ba,nima duk na ƙosa in ga yadda
waɗannan idanun nata za su yi randa ta ganki da Nass ɗin,ba dai jibi Umma za ta tafi bikin ba,sai
mu jira dawowarta mu ga yadda za a kaya.Nima cikin wata satin Ameeru yace iyayensa za su turo
a tsaida lokaci kawai."
Basmah tayi wani farr...! Da ido tana cewa, "Wow! kinga idan lokacin an tunkuɗomin ƙeyarsa
mun jone sai kawai a sanya lokaci ɗaya ayi bakinmu tare a huta kawai,tunda shi Yah Sadeeq ya ƙi
wa Umma hannu har yau bai je wajen Nadeeyan ba bare a san abinyi."
Ta ƙare maganan da taɓe baki Zuhurah kuma ta sanya dariya,suka cigaba da tattauna yadda zasu
ƙuntata zuciyar TAIMIYYAH duk randa ta gane cewa Basmah ta kwace mata Nass ɗinta.
Basmah ta lumshe idanunta azababben soyayyar Nass ɗin na sake kama zuciyarta.Tana kuma sake
jinjina wayonta da kaifin ƙwaƙwalwanta, na yadda aka yi ta janyo hankalin Nass har ya saki jiki
da ita.
Ta shiga tuna yadda tayi ta nuna masa cewa, ta ɗauke sa tamkar matsayin Yayanta ne tunda yana
son TAIMIYYAH.Koda wasa bata taɓa nuna masa cewa suna da ƙiyayya da abar sonsa ba,sai ma
nuna masa da take yi kullum cewa kar ya cire rai da samun TAIMIYYAN.......✍🏻
_Lallai Basmah kinyi ƙoƙari inji Ɗansabo,shiyasa aka ce ka rabu da mutum kawai inda ka
gansa,sheɗancin wasu mutanen yafi gaban kwatance,to masu karatu kunji ta inda Basmah ta ɓulla
har ta fara samo hankalin Nass yana magana da ita,ko me zai faru a gaba? Sai mu cigaba da bin
labarin sannu a hankali don jin cikakken ya rayuwar TAIMIYYAH zai kasance baiwar Allah_ 😰
#Ɗansabo ce#
[12/14, 3:43 PM] +234 703 040 9541: *Littafin TAIMIYYAH paid book ne,ga duk wanda ta
tsincesa a kowani irin group ne,kiji tsoran Allah karki karanta sai kin biya 500 naira only.*
*Za ku iya min magana ta wannan number ɗin 08167768704, ko kuma ku turo kuɗin ku kai tsaye
ta wannan account ɗin*👇🏻
0504192664 aisha ibrahim dansabo GTbank.
Masu turo credit za ku turo katin MTN na 500 ta wannan line ɗin 08167768704.
_*Ina ƴan kasuwa masu buƙatar a tallata muku hajar ku? Maza ku garzayo da kuɗi ƙalilan a
tallata muku kayan siyarwanku sai dai kawai ku ji ana kiran waya don buƙatan sayan kayan ku,ku
tuntuɓeni ta layina kamar haka 08167768704.*_
*43*
*Kano*
Kwance yake akan gadon ɗakinsa idanunsa duka a rufe, babu abinda zuciyarsa da gangar jikinsa
ke kwaɗayi irin ya ji ɗumin jikin TAIMIYYAH a cikin jikinsa.
Gaba ɗaya tunda ya ɗaura ido akan tsiraicinta, hannuwansa suka jiye masa laushin fatarta,sannan
bakinsa ya ɗanɗano masa wani irin ɗanɗano me garɗi a mounth ɗinta ,ya rasa dukkanin sukuni da
nutsuwanrsa.
Ya fi kowa sanin sabida shine TAIMIYYAH ta tattara ta bar garin baki ɗaya, don ta tsorata da
maitarsa da ya fitar a fiki akanta.Ya buɗe idanunsa yana Janyo wayansa tare da zubawa lambobin
wayarta ido,wanda tun ɗazu yake gwada kiranta,amma sai yaji ya kasa don bai san me zai ce mata
ba idan ya kira ɗin.
Gabaki ɗaya tunda ta bar garin kaman ana sake ninka masa, sha'awan son kasancewa da ita
ne.Duk neman matansa bai taɓa jin kwaɗayin mace irin na yau ba,kuma babu wacce yake ji zata
iya kashe wutan dake ci a zuciyarsa sai TAIMIYYAH.
Ya sauke wani numfashi me zafi maransa na sake wani irin ɗaurewa, tsabagen wutar jaraba dake
cin zuciyarsa.Ya cije lips ɗinsa yana shahadan danna mata kira, tare da fatan ta ɗauka ko muryanta
ya samu ya ji ko zai samu relief.
Sai dai har kiran ya gama ɓurarinsa ya tsinke ba a ɗaga wayar ba.Sai kawai yayi jifa da wayar
yana tashi da ƙyar ya nufi toilet,bai jima ba ya fito yana nufan ƙofar fita daga ɗakin baki ɗaya,don
zuwa ya haɗo tea me lemon ko zai rage masa nauyin da maransa yayi.
Zuciyarsa na kimsa masa tunanin akan kawai ya samu Mamie a gobe, ya sanar mata cewa ya
amince zai iya auren TAIMIYYAH.
Har ya kai part ɗin Mamie tunanin dake yawo cikin kansa kenan....
___________
TAIMIYYAH na zaune tana danna system ɗinta, a lokacin da kiran Emran ya shigo wayarta.
Tunda kuma ta ɗauki wayar ta ga baƙuwar number ta ji a jikinta cewa shine,shiyasa ta share kiran
bata ɗauka ba har ya tsinke.
Ta saki ƙaramin tsaki tana saka wayan a fly mode, ta cigaba da abinda take yi zuciyarta cike da
ɓacin ran rainin hankalin da ke son shiga tsakaninta da Yah Emran ɗin.
Har ta gama abinda take yi ta kashe system ɗin, don yin shirin kwanciya barci zuciyarta bata daina
tunani,akan abinda ya shiga tsakaninta da shi ba.
Lokacin data ɗauro alwala don kwanciya bacci, sai da ta gabatar da sallar wuturi kafin ta nufi gado
ta kwanta,bata ɗauki dogon lokaci ba bacci ya sure ta.
Washegary ya kama monday tunda wuri TAIMIYYAH ta tashi, don tana son ganin Baba Sani
kafin ya wuce Kano wajen aikinsa.Shiyasa ƙarfe takwas ta isa Sasan su Umma ,a ɗakin Baba
Sanin suka gaisa da Umma wacce ke fifita masa tea da zai sha.
Ya gama shirinsa tsaf yana zaune yana cin chips da aka soya masa,TAIMIYYAH ta tsuguna ta
kwashi gaisuwa tana sanar masa da buƙatarta.
Baba Sani ya amsa cike da kulawa,yana me kai hannu cikin aljihunsa ya irgo adadin kuɗin da take
buƙata ya miƙa mata.
Ta amsa tayi godia tana miƙewa ta fito daga ɗakin,Umma na biyo bayarta da mugun kallo.
Lokacin da ta shigo Sasan Iyah ta tadda har Iyah an sha wanka an fito karyawa.Ta saki murmushi
a lokacin da ta isa gaban Iyah tana cewa, "Iyah barka da fitowa ina kwana."
Iyah ta dubi TAIMIYYAH da manyan idanunta tana cewa, "Lafiya lau Zainabu, daga ina kike da
wuri haka?" TAIMIYYAH ta ɗan shagwaɓe face tana ba Iyah amsa da cewa, "Daga wajen Baba
Sani na amso kuɗi ne kinsan yau an koma skull, ina buƙatan kuɗi a hannuna har zuwa sati me
zuwa."
Iyah ta jinjina kai tana cewa, "Hakane amma da kin min magana ma na riga na tanadar miki kuɗin
duk buƙatunki, kamar yadda Sameer ya saba turo miki lokacin yana raye."
TAIMIYYAH da mood ɗinta ya sauya, fuskarta ya nuna tsananin kewan Abie ɗin, ta dubi Iyah
tana cewa, "To ai ban sani bane Iyah sabida shi yace min lallai duk abinda nake buƙata in dinga
sanar masa."
Iyah ta jinjina kai tana cewa,
"Hakane babu laifi ai, yanzu yau ɗin zaki fara zuwa makarantar, ba zaki bari sai zuwa gobe ba?"
TAIMIYYAH tayi saurin duban Iyah tana cewa, "Sai gobe zan fara zuwa tunda yau aka koma,
bama lallai kowa ya je a yau ɗin ba,don Zee cewa tayi ma sai zuwa Wednesday za ta fara zuwa."
"A toh nima dai haka na gani gara ki bari zuwa goben,kin sake hutawa ma."
Cewan Iyah tana faman cin soyayyan dankali da egg da Babah Ladi ta soya,ta cika cup da kunun
gyaɗa daga gefe guda.
TAIMIYYAH ta fara takawa don komawa ɗakinta,tana cewa Iyah, "Iyah bari in koma in kwanta
zuwa tara zan tashi,yau ni zan yi mana girkin rana idan na gama kwaleman ɗakina."
Iyah ta bi bayanta da kallo tana cewa, "To madallah a tashi lafiya,sai Ladi ta taya ki kwaleman don
rage miki wani wahalan."
Ita dai TAIMIYYAH tuni ta shige ɗaki abinta,kuma tana aje kuɗin da ke hannunta kwanciyar
tayi,don da gaske baccin take son komawa.
Sai ƙarfe tara da rabi sannan ta tashi ,ta yo wanka ta shirya cikin doguwar riga mara nauyi na
material,bata shafa komi akan face ɗinta ba, ta fito zuwa falo don yin kalacin safe.
Lokacin da ta kammala karyawan Iyah ce taiwa Ladi magana akan ta taya TAIMIYYAH suyi
kwaleman ɗakinta.
Hakan ko aka yi cikin lokaci kaɗan suka kammala,wanda rabin aikin Ladin ce kawai tayi ma,don
taki bari TAIMIYYAH tayi komi,in banda shirya kayanta da tayi cikin drawer.
11:30am TAIMIYYAH ta wuce zuwa kitchen don fara shirin ɗaura musu lunch,sabida da wuri
suke gama girkin rana su.
Tuwo Iyah tace tana so ayi amma na dawa da miyar Kukah,don haka TAIMIYYAH ta fara da
ɗaura miyan ne kafin ta ɗaura ruwan tuwan.
Cikin nutsuwa da ƙwarewa take aikinta har ta kammala tuƙa tuwan, ya silala ta sauke don fara
kulla su a leda.Koda Ladi ta shigo don taya ta wani abin ,sai ta amshi kulla tuwan ita kuma
TAIMIYYAH ta ƙarisa miyan ta juye shi cikin cooler.
Store ta nufa ta ɗakko doya madaidaici ta feraye shi,don tana son yin Yam balls ne.
Bayan kammala feraye doyan sai ta wanke shi tas ta ɗauka a wuta.
Ta nufi wajen fridge ta ɗebo carrot da green pepe ta aje su a gefe,sannan ta ɗebo tattasai da tarugu
haɗe da albasa me yawa duk ta gyarasu.
Zuwa lokacin da doyar ya dahu duk ta gama yanke-yanken da zata yi, nasu carrot da green pepe ta
aje a gefe guda,sai ta tsane doyar a colander don barinsa ya huce.
Kafin doyar ya huce ta tafasa nama ta baiwa Ladi ta ɗan daka mata,sai ta juye doyar tasa whisker
ta dagargajeshi.Ta juye su carrot da green pepe haɗe da kayan miyan da tai grating,ta zuba albasa
me yawa da ta yanka, duk ta haɗe su cikin doyar da ta dagargaje ta zuba spices da maggi yadda
take so.
Zuwa lokacin Babah ta kawo mata dakakken naman, shima ta juye akai ta saka hannu ta motsa,
naman yabi ko'ina sannan ta fara mulmulasu zuwa shape ɗin balls.
Babah Ladi dai tsaye tayi kawai tana kallon yadda TAIMIYYAH ke kominta gunin sha'awa.
Bayan ta gama maida su balls ne ta fasa egg ta kaɗashi,ta zuba garin corn flour sabida idan aka
saka corn flour egg ɗin yafi kamawa ya yi kyau sosai.
Tunda TAIMIYYAH ta fara suyan yam balls ɗin,qamshi ya cika ko'ina hatta Iyah dake falo sai da
ƙamshi ya fitineta,ta gane cewa bayan yin tuwon dawan sai da TAIMIYYAH ta ƙirƙira yin wani
abin kenan.
Tana kammala komi ta wuce zuwa ɗaki don gabatar da sallah.Babah Ladi ita ce ta ɗauki kulolin
abincin ta kai falo, ta jere su inda a ke zaman cin abinci.
TAIMIYYAH ta idar da sallah kenan tana cikin ninke Hijab ɗinta, wayarta ya fara ring ta isa
wajen wayar tana kallon sunan Yah Deeku dake rubuce a jikin screen.
Tayi receiving call ɗin tana saka wayar a speeker.Muryan Yah Sadeeq ya fito tar lokacin da yake
furta,
TAIMIYYAH ta zauna daga gefen gadon tana cewa, "Ina jinka Yah Deeku ina yini,kana lafiya?"
Sadeeq yace "Lafiya lau Zaynab kin dawo daga Kano ɗin ne ko kina can? Dis week ban samu
shigowa weekend ba."
TAIMIYYAH ta ɗan shagwaɓe murya kaman yana gabanta tace, "Na dawo jiya Yah Deeku,ai
tunda na ga ban ga motarka ba na san baka samu shigowa ba."
Sadeeq da ke sauraran muryarta yana jin nutsuwa na sauka a ransa, ya lumshe ido yana faɗin, "Eh
Babe! Ban shigo ba yanzu me kike yi ina so ki hau online na tura miki wani pic ne ki gani,but idan
kin gani ki gaya min gaskiya tayi ko bata yi ba,tunda ke an hana min ke bayan zuciyata har yanzu
ke kaɗai take muradi."
TAIMIYYAH dake saurarensa ta sake yin ƙasa da muryarta tana cewa, "Okey Yah Deeku bari in
hau online ɗin."
Sadeeq zai yi magana kenan ya ji tayi cuting call ɗin,sai kawai shima ya hau online ɗin.
Lokacin da TAIMIYYAH ta buɗe pic ɗin, idanunta ne suka sauka akan kyakykyawar fuskar
budurwar dake jikin hoton,ta tsura hoton ido kaman me son gano haƙiƙanin kyawun budurwar.Sai
kawai ta fara typing tana tambayar ya Deeku budurwansa ce? Dai-dai lokacin shi ma ya hawo
online ɗin, ganin tambayar da TAIMIYYAH turo masa yasa shi murmusawa ya fara typing shi
ma,yana bata amsa da cewa,
TAIMIYYAH ta saki murmushi kaman yana gabanta,kafin ta tura masa cewa, "She's very cute Yah
Deeku,gaskiya tayi Allah tabbatar da alkhairy."
Sadeeq ya karanta abinda tace, sai ya aiko mata da emoji na kuka yana rubuta cewa, "Baby daɗi
ma kike ji zan rasaki ko kishi ma ba zaki nuna ba ko?"
TAIMIYYAH ta aika masa da emoji na dariya kawai, ba tare da tace komi ba.
Sai kawai Sadeeq ya sauka daga online yana kiranta vid-call,suka jima suna magana yana sanar da
ita cewa sunan yarinyar Safiyyah.
Ƙanwar wani abokin aikinsu ne suna zaune a Badarawa Kaduna.
Ita dai TAIMIYYAH sai suka gama wayar fuskarta na blushing, don har cikin zuciyarta tayi farin
ciki da Yah Sadeeq zai fitar da matar aure.
Tana kammala cin tuwan da ta zuba kaɗan,ta nufi kitchen ta ɗauki bowl ɗin da ta zubawa Ummie
yam balls, ta fito zuwa falon Iyah.
Bowl ɗin ta aje tana ɗaukan wayarta, sannan ta dubi Iyah tana cewa, "Iyah za ni Sasan Ummie in
kai mata yam balls ɗinnan."
TAIMIYYAH amsa tana yin gaba, hannunta ɗaya dafe da ƙafarta me laluran, ɗaya hannun riƙe da
bowl ɗin da wayarta.
Babu kowa cikin falon Ummien lokacin da TAIMIYYAH ta shiga,sai ta aje bowl ɗin tana zama
cikin seater, dai-dai lokacin da kira ya shigo wayarta.
Ta tsurawa lambobin idanu har kiran ya yanke bata ɗaga ba,wani kiran ya sake shigowa sai ta ɗaga
tana kai wayan kunni.
Jin muryan Yah Emran yasa ta saurin yin hanging up,tana yin blocking lambar baki ɗaya.
TAIMIYYAH ta saki smile tana cewa, "Haka kowa ke cewa bana jin wahalar aiki,wallahi kam
bana ji indai har zan haɗa komi waje ɗaya shikenan,yawan kai kawo ne kawai ke sani inji na jigata
a aiki,amma indai za a aje min komi waje ɗaya inyi aikina daga zaune shikenan."
Ummie ta saki murmushi tana kai yam balls ɗin ɗaya baki, ta gutsira tana cewa, "Allah sarki duk
da haka dai ke ɗin ba mai kyuiyan aikin bace kawai,gashi ko yayi daɗi sosai egg ɗin ya kama
jikinsa.Za ki yi mana a nan sasan wataran in ga yadda kike yi yake yin daɗi haka."
TAIMIYYAH tayi ɗan ƙaramin dariya tana cewa, "To shikenan Ummie duk sanda kika so a yin sai
kiyi magana."
Daga haka suka ɗan taɓa hira kafin TAIMIYYAH ta baro sasan Ummie.
Ta shiga sasan Iyah kenan ta zauna, saƙon text message ya shigo wayarta,da wani baƙuwar lambar
na daban.
Sai ta buɗe text ɗin ta fara karantawa,tana gama karanta saƙon, ta fahimci daga Yah Emran
ne,yana mata magiya ne akan tayi picking call ɗinsa,sai ta share text ɗin baki ɗaya,ta sake tayi
blocking wannan line ɗi daya turo saƙon da shi.
Memakon ta cigaba da zaman falon sai ta nufi ɗaki kawai ta kwanta,tana jin wani ɓacin rai na taso
mata,don ta kasa gane me Yah Emran ke son ɗaukarta da har yake tunanin zata iya
saurararsa,bayan duk irin tozarcin da yayi mata.
Ta lumshe idanunta tunanin Nass na kutsowa cikin kwanyarta,haka kawai taji wasu hawaye masu
ɗumi na sauka suna biyo ƙuncinta.
Soyayyarsa da ke can ƙasan zuciyarta ke son tasowa baki ɗaya,sai ta rintse idanunta sosai tana
tunanin, 'Ko a wani hali yake yanzu,shikenan Mum ɗinsa tayi nasaran tarwatsa duk wata soyayya
da ta gudana tsakaninsu kenan?"
Ta kai hannu tana share hawayen dake zubowa daga idanunta,tana jin zuciyarta na wani irin ƙuna
da shiga ƙunci me tsanani.
Ta gama sallamawa cewa ta rasa Nass har abada, tunda mahaifiyarsa bata sonta sabida kawai ta
kasancewa gurguwa.
TAIMIYYAH ta jima tana kuka da hawaye kafin ta rarrashi kanta tayi shiru,tana faman sauke
ajiyar zuciya, kewan Abie na taso mata.Tana hasaso cewa da yana raye da ta kira shi taji koda
muryansa ne,amma ya riga ya tafi inda bazai dawo ba.
Wani kuka me ƙarfi ya sake kwace mata lokacin da take tuno sautin amon muryar su Nahar,da
yadda suke yawan yin vedio call suna ɗebe mata kewa,yau gashi duka babu ko ɗaya a cikinsu.
Sai kawai ta kifa kanta a jikin pillow tana rushewa da kuka,tamkar za ta haɗiyi zuciyarta ko za ta
huta da jin irin ƙuncin da take ji a yanzu.
Bayan ta rarrashi kanta tayi shiru daga kukan,sai ta zame tana gyara kwanciyarta bisa bed,bata
jima ba sai bacci ya yi nasaran ɗaukar ta,bata kuma farka ba sai la'asar........✍🏻
#Ɗansabo ce #
[12/14, 3:43 PM] +234 703 040 9541: *Littafin TAIMIYYAH paid book ne,ga duk wanda ta
tsincesa a kowani irin group ne,kiji tsoran Allah karki karanta sai kin biya 500 naira only.*
*Za ku iya min magana ta wannan number ɗin 08167768704, ko kuma ku turo kuɗin ku kai tsaye
ta wannan account ɗin*👇🏻
0504192664 aisha ibrahim dansabo GTbank.
Masu turo credit za ku turo katin MTN na 500 ta wannan line ɗin 08167768704.
_*Ina ƴan kasuwa masu buƙatar a tallata muku hajar ku? Maza ku garzayo da kuɗi ƙalilan a
tallata muku kayan siyarwanku sai dai kawai ku ji ana kiran waya don buƙatan sayan kayan ku,ku
tuntuɓeni ta layina kamar haka 08167768704.*_
*44*
_____________
Kwanakin TAIMIYYAH shida da kenan da dawo daga Kano,ya kama ranan Saturday.
Ta dawo daga makarantar haddah kenan a gajiye,tana shigowa falon Iyah hancinta ya shaqo mata
ƙamshin turaren SAUVAGE DIOR.
Sai tayi tsaye daga bakin ƙofar bayan Iyah ta amsa sallamar da ta yi cikin sassanyar muryar
ta.Manyan idanunta ta ɗaga a hankali, tana me sauke su akan bayan Emran da ke zaune yana
facing Iyah,don haka ita da take tsaye daga bakin ƙofa ya bata baya.
Cikin slowly ta dafe ƙafarta ta cigaba da takowa zuwa cikin falon,jikinta ya gama bata koma waye
a zaune tun kafin ta ga face ɗinsa ma.
Emran da tun fara takowan TAIMIYYAH cikin falon ya zubo mata ido,sai ya cigaba da kallonta
har ta ratso tsakiyan falon ta isa wajen Iyah tana cewa, "Iyah na dawo,Yah Emran barka da zuwa."
Daga haka sai ta miƙe ta cigaba da takawa har zuwa ɗakinta.
Tana jikinta na jin tasirin kallon da Emran ya biyo bayanta da shi,zuciyarta ta ji ya ɓaci tunda ta ci
karo da face ɗinsa,ga kuma wani fargaba da zullumi da ke dukan ƙirjinta.
Tambayoyi masu yawa suka dinga kutsowa cikin zuciyarta,tana tambayan kanta, 'Me Yah Emran
Zaria? Don tafi kowa sanin haka kawai, ba kasafai suka cika yo tafiyayya zuwa Zaria su gaida
Iyah ba,sai in da wani dalili suka fi zuwa daga shi har su Yah Anas ɗin,da wacce ya zo,kar dai a ce
tafiyayya ya yo sabida ita?" Waɗannan su ne tarin tambayoyin da suke addabar zuciyarta
TAIMIYYAH har ta gama cire Hijab ɗin da ke jikinta,ta aje Qur'aninta saman drawer.
Shigowar Iyah ɗakin nata ya saka TAIMIYYAH ɗaga manyan idanunta ta sauke akan Iyah,tana
me amsa sallamar da tayi.Iyah ta tako zuwa cikin ɗakin tana kallon TAIMIYYAH cikin ido,tare da
cigaba da nazartan yadda duk tayi wani sanyi daga ganin Emran da tayi.
Ta ɗan tsuke fuska kaɗan tana cewa, "Zainabu sai ga Emran kaman daga sama ya biyo
sahunki,yace yana ta kiran wayarki kin rufe shi baya iya samunki,meyasa zaki haka
TAIMIYYAH? Ke da ɗan uwanki don ya nuna yana da ra'ayi a kanki sai ya zama abin
wulaƙantawa? Ya gaya min komi, yace sabida ya bayayyana miki cewa yana son ki, shine dalilin
da kika matsa sai kin dawo,to maza ki canzo kaya ki fito ki samesa ni yanzu zamu fita da
Sani,zani Rimi amma zan dawo kafin ya wuce,na saka Ladi a shirya abinci sai ki shiga ku yi aikin
tare, ki ɗan masa wani abin na birgewa cikin girkunan zamani da kika Iyah."
TAIMIYYAH da tunda Iyah ta fara magana ta shiga shock...Sai ta ɗaga manyan idanunta ta dubi
Iyah,tana ma rasa abinda zata ce,don tsananin mamaki da tsoran maganan da Yah Emran ɗin ya
shiryawa Iyah,ya gama daskarar da ita a zaune.Amma sai tayi ƙarfin halin cewa Iyah, "Toh
shikenan Iyah za a yi duk yadda kika ce,sai kin dawo ma yi magana,amma ni ba sabida shi na
dawo ba wallahi."
TAIMIYYAH ta ƙare maganan cike da shagwaɓa da raunin murya,wanda ya saka Iyah hararanta
tana cewa, "Koma dai miye ki tashi maza ki same shi bari in je nasan kila Sani na waje ya ƙariso."
TAIMIYYAH ta bi bayan Iyah da kallo lokacin da take ficewa daga ɗakin,ba tare da ta jira cewan
TAIMIYYAH ba.
TAIMIYYAH ta sauke wani zazzafar ajiyar zuciyar, tana ji tamkar ta saki kuka ko zata ji sanyin
takaicin da ya tokare maƙoshinta.Ta cigaba da zama daga bakin gadonta bata da niyyan tashi ta
fito zuwa wajen Emran ɗin, kamar yadda Iyah ke buƙata don ita ya riga ya gama sire mata, ta
kuma tsane shi tsana me tarin yawa,sai dai ta sani tunda ya riga ya tako zuwa nan ɗin,dole ta
fuskancesa ta ji da wacce ya zo?
Sai ta miƙe ta isa bakin mirrow ta tsaya, bayan ta dogare ƙafarta da jikin stool ɗin.Kallon kanta
tayi daga sama har ƙasa, tana sanye ne da doguwar rigan material me irin Silk ɗinnan,anyi masa
ɗinkin boubou da yai mata kyau sosai a jiki.
Fuskarta babu komi sai man leɓe da ta goga tun safe da zata fita zuwa haddah,ta juyo zuwa wajen
kayanta ta ɗauki ƙaramin Hijab ta sanya, ta fita zuwa falon Iyah fuskarta babu ɗigon annuri ko
kaɗan.
Tunda ta fito Emran da ke zaune ya kafe ta da ido,ya ji zuciyarsa na amsawa da tarin begenta da
tsananin soyayyarta da ke fisgan zuciyarsa.
Sai dai ya fi kowa sanin zallar sha'awarta ne ke haifar da zazzafar soyayyarta da yake ji a cikin
zuciyarsa,ya cigaba da kallonta har ta samu waje ta zauna cikin kujeran da ke nesa da shi.
Shiru ya ratsa a cikin falon sai sautin TV da ke kunne ke tashi a hankali,ko kaɗan TAIMIYYAH ba
tayi gigin kallonsa ba,tana dai jin tasirin na shi idanun a jikinta, kafin amon muryarsa ya ratsa
kunnuwarta inda yake cewa, "Zainab gani na biyoki tunda rashin kunyarki har ya kai,ki sanya
duka numbers ɗina a black list ko?"
TAIMIYYAH ta kwaɓe fuska tana me sake jin tsanansa na mamaye ruhinta,ta ɗago manyan
idanunta ta sauke akansa,sai lokacin kuma ta kula da shigan da ke jikinsa.Yana sanye ne da wani
haɗaɗɗen Filtex material na maza,kalan Blue Black da yai masa mugun kyau,don yana da hasken
fata ba za a kira shi baƙi kai tsaye ba, sai dai a kira shi da wankan-tarwaɗa.
Ta ɗauke kai daga dubansa, ganin irin kallon da yake bin ta da shi kamar tsohon maye,tayi magana
cikin sanyin murya tana cewa, "Rashin kunya kuma Yah Emran?"
Emran ya dannan mata harara yana cewa, "Yes rashin kunya mana da raini,sabida kin fahimci
cewa tunda na ga halittarki kin tafi da zuciyata,to gani na biyoki har inda kike.Kuma na zo ne in
baki haƙury akan kalaman da nayi a kanki,da abinda ya faru tsakaninmu a Kano, yanzu son ki
nake ji sosai cikin zuciyata Zaynab,don haka ki amince da soyayyata mu yi aure, dama shine burin
Mamie.Ta son ganin na yi auren zumunci kuma ke ta zaɓa min,zaki amince da Yayanki ya zama
mijinki Zaynab?"
Yadda ya kai ƙarshen maganan cike da narke murya na zallar iya yaudara,yasa TAIMIYYAH
saurin kallonsa with so much shock...! Bakinta har wani rawa yake muryarta na harɗewa lokacin
da take faɗin, "Soyayyah Yah Emran,kana nufin ni kake so a yanzu wai? Kamanta cewa ina nan a
gurguwata har yanzu, wacce ba za ka iya nuna ta a matsayin matarka abokanka su raina ka ba.Ina
nan a musakata ban warke ba, ba kuma zan warke ba har abada idan haka Ubangiji ya so
ganina,don haka ba ni kake so ba Yah Emran tun wuri ma ka gyara kalamanka,kuma kada ma ka
cigaba da yaudaran zuciyarka a kaina,kace kawai jikinki nake so Zaynab amma bani kake so ba."
Yadda TAIMIYYAH tayi maganan cike da gargaɗi tana ɗaga masa murya,yasa Emran daskarewa a
tsaye yana kasa koda motsi,sai idanu da ya zuba mata kawai yana ji tamkar ya nufeta ya
rungumeta da ƙarfin tsiya,kalmar akuyancin da ta furta cikin kalamanta na ƙona zuciyarsa.
Kaman TAIMIYYAH ta san tunanin da ke ransa sai ta miƙe don bashi waje,sabida zuciyarta wani
irin tafarfasa kawai take yi da zallar tsanan Emran ɗin.
Emran ganin da gaske TAIMIYYAH tafiyarta za ta yi ta bar shi, yasa shi cire murya ya kira yi
sunanta Zaynab! Ya ɗaura da faɗin,
"Don Allah ki tsaya ki saurareni Baby wallahi da gaske son ki nake yi,ina sonki a gurguwan da
kike Zaynab,kuma nayi kuskuren sakin kalaman dana furta miki wancan lokacin, amma kiyi
haƙuri a yanzu zuciyata azabtuwa take yi da ƙaunarki me tsanani Sis Zaynab."
TAIMIYYAH da tayi tsaye jingine da jikin kujera, ta ɗaga manyan idanunta tana jifansa da wani
mugun kallo,ta buɗe baki tana faɗin, "Yah Emran please ka daina furta kalmar kana sona,hakan na
sake ƙona zuciyata ne da kimsamin tsananka me tsanani.Ka ɗauka ban ji duk yadda kuka yi da
Mamie akaina bane? Tana roƙonka ka so ni amma kana nuna cewa faɗuwar aji ne lafiyayye
kamarka ka auri gurguwa,har kana faɗin me zaka sanar abokanka idan ka auri gurguwa? Naji
komi Yah Em babu abinda zaka yaudareni da shi, gurgu irina shi yafi cancanta in mallaka masa
soyayyata da zuciyata baki ɗaya.Kada ka ƙara cewa kana sona ko furta wasu kalamanka na
yaudara a kaina,wallahi summa billahi Yah Emran bazan taɓa ƙaunarka ba, sai dai ƙauna irin ta
jini shima bazan ɓoye maka ba a yanzu tsananka nake ji matuƙa,don haka ka daina yaudaran
kanka in dai ni Zaynab ce to banzan taɓa son ka ba,kuma ba zan taɓa aurenka ba Insha Allah."
Daga haka ta juya tana tafiya cikin tsarin yadda Ubangiji ya nufeta da takawa,hannunta dafe da
guiwar ƙafarta na hagu ta nufi hanyar shigewa ɗakinta,hawaye na sintiri a fuskarta har ta isa cikin
ɗakin tayi banging ƙofar da ƙarfi.
A kan gado ta zube tana cigaba da kuka sosai, hawayen baƙin cikin jin kalmar soyayyah daga
bakin Yah Emran ɗin na sake ɓalle mata.
Ko duka jikinta kunnuwa ne ba za ta taɓa aminta da cewa sonta yake yi ba,don ta san ba son
gaskiya da amana zai mata ba, sai dai so irin na sha'awa,tunda bai fara son nata ba sai a lokacin da
ya tozartata ya gama ganin kyawun surarta a zahiri....."
Kukan da ya taho mata ne yasa ta kai hannu tana dafe bakinta,tana ƙoƙarin maida kukan da ke son
kwace mata.
Ta cigaba da sharan hawaye tana jin kewan Nass da Soayyyarsa, na sake kassara duk wata gaɓa da
ke motsi a cikin zuciya da gangar jikinta....
Muryan Iyah data jiyo daga can falon alamun har ta dawo daga unguwar da ta fita,yasa
TAIMIYYAH saurin share hawayenta,ta koma da baya ta kwanta akan gadonta, tana me lumshe
idanunta baki ɗaya tamkar me bacci.
Iyah ta shigo cikin ɗakin kai tsaye tana nufan wajen gadon da TAIMIYYAH ke kwance,ta kai
hannu ta shiga bubbuga ƙafar TAIMIYYAH tana cewa, "Maza ki tashi tun raina bai ɓaci ba
Zainab,ya mutum zai taso takanas saboda ke, ki dinga wulaƙantasa haka kamar ba jininki ba,wato
har yanzu kinƙi cire son wanda uwarsa ta gama tozartaki ta nuna bata ƙaunarki,tace ɗanta ba zai
aureki ba sabida ke gurguwace ko? Shiyasa zaki dinga wulaƙanta ɗan uwanki na jini da zai
ƙaunace ki fiye da duk wani bare,to maza-maza ki je ki zubo masa abinci don ransa ya gama
ɓaci,yace kin gaggaya masa maganganu marasa daɗi,shiyasa kika dawo nan kika kwanta.Yaushe
kika koyi rashin kunya Zainab da har zaki kalli Emran kina gaya masa magana? Sabida kawai
yace yana sonki shine raini zai shiga tsakani, to wallahi ki kiyayi fushina a wannan karon,kuma
baki da miji sai shi don ni naji daɗi da wannan maganar da yazo da it......"
Kukan da TAIMIYYAH ta sanya ne ya hana Iyah ƙarisa kalamanta,tayi sakato da baki tana duban
TAIMIYYAH babu ko ƙiftawa.
TAIMIYYAH ta cigaba da rusa kukanta tana cewa, "Iyah wallahi Yah Emran bani yake so
ba,tsaraki kawai yazo ya yi amma ko Qur'ani akace in dafa akan cewa ƙarya yake bani yake so ba
zan dafa,don Allah Iyah kar ki yadda da zancensa, kuma ni bazan sake fita wajensa ba zuciyata
zafi take yi,in dai ba so kike hawan jini ya kamani ba,don girman Allah ki daina cewa banda miji
sai shi,ki je kawai ki gama da shi ni kuma idan ya tafi zan waraware miki komi."
Iyah da ta kafe TAIMIYYAH da ido sai ta kasa cewa komi,ta juya ta fice daga ɗakin ranta a ɓace
matuƙa.Amma tana isa falo sai ta yi ƙoƙarin saita kanta, ta fuskanci Emran tana bashi haƙury akan
karya da gaskiyar da ya kitsa mata na cewa TAIMIYYAH tai masa rashin kunya.
Babah Ladi ce ta fito ta aje tray me ɗauke da drinks da abinci a gabansa,suka gaisa sannan ta juyo
ta koma zuwa kitchen don ƙarisa aikinta.
Sai around 1:05pm Emran yai sallama da Iyah akan cewa zai koma,yaso ƙwarai Iyah tayi forcing
TAIMIYYAH ta sake fitowa ya ganta, amma hakan bai samu ba.
Hakanan ya ajewa Iyah dubu goma saman kujera, yai mata sallama ya fice zuciyarsa cike da jin
zafin, yadda TAIMIYYAH ta nuna da gaske ƙinsa take yi har cikin zuciyarta.
Lokacin da Iyah ta samu TAIMIYYAH a cikin ɗaki bayan tafiyar Emran.A kwance ta ganta har
lokacin sai faman sharan hawaye take yi,hakan ya sanyayar da jikin Iyah tasan cewa lallai akwai
wani abu, ba banza TAIMIYYAH zata dinga kuka haka don kawai Emran ya zo ya fallasa cewa
yana sonta ba.
Ta nemi bakin gadon ta zauna, tana kai hannu ta ɗago TAIMIYYAH daga kwaciyar da tayi tana
cewa, "Ta shi Zainabu kukan ya isa haka,sanar dani abinda ya faru,ko yake faruwa tsakaninki da
ɗan uwan naki Emran."
TAIMIYYAH ta kai hannu ta share hawayenta, cikin sanyin murya da nutsuwa ta zayyane ma Iyah
duk abinda ya faru a Kano tsakaninta da Yah Emran ɗin.
Bata ragewa Iyah komi ba har hiransu da Guggo Bilki da ta ji duk bata ɓoye komi ba ta sanar da
Iyah,ta ƙare maganan da cewa,
"Iyah wallahi jikina yake so nina gama gane hakan,tunda tun farko ga abinda yace sannan ga
yadda yaso ya tozartani ya keta mutuncina,to taya za a yi a yanzu yazo yace wai in amince son
gaskiya yake min zai aureni,wallahi ƙarya ne ba son gaskiya yake min ba, don Allah Iyah ki kashe
wannan maganan kada ma ya je ya yaudari Guggo Bilki ta ga kaman yayi na'am da ra'ayinta ne,
alhali yaudarace yana da manufarsa akaina ne kawai,ba soyayyar gaskiya yake min ba ta
sha'awace Iyah,don haka don Allah ki rufa min asiri ki dakatar da shi daga duk wani yinƙurinsa
wallahi na tsanesa ya gama zube min,ni soyayyar da kowama ya fita kaina a barni inyi facing
karatuna kawai,duk randa Allah ya kawo min gurgu irina sai afara min maganan auren please
Iyah!"
Yadda TAIMIYYAH ta kai ƙarshen maganan cike da magiya tana kuka,yasa Iyah rungumeta a
jikinta tana jin matsanancin tausayin TAIMIYYAH na keta zuciyarta.Wani irin ɓacin ran abinda
Emran yayi wa TAIMIYYAH na keta zuciyar Iyah.
Cikin murya me cike da rarrashi Iyah ke kwantar da hankalin TAIMIYYAH,har tayi nasaran tsaida
kukan da TAIMIYYAH take yi.
"Kiyi haƙuri Zainab bansan abinda ya faru kenan ba,da ko ganinki ma bazai kuma yi ba bare har
na matsa sai kin je wajensa,zan kuma kira ita Bilkin in sanar da ita komi ta fara cimin mutuncinsa
kafin mu gauraya ni da shi,ashe ina masa kallon kamamme shi ɗin watsatstsene daya ɓata
wayonsa,idan yana iskancinsa a waje sai ya iya keta alfarmanki inda ya samu galaba akanki?
Lallai zamani ya lalace da rashin tsoron Allah,Ubangiji ka shirya mana zuriya dana ɗaukancin
musulmi baki ɗaya,amma gaskiya Emran ya bani mamaki ni ma kuma ya zube min tare da fita a
zuciyata fit..!"
Iyah ta cigaba da bambami cike da ɓacin rai,ita dai TAIMIYYAH sai ta ji ta sama nutsuwar zuciya
a yanzu da Iyah ta san komi,ta kuma fahimce abinda take so ta fahimta ɗin,na cewa jikinta Emran
yake so ba ita ba,soyayyar sha'awace yake mata da zaran ya cika burinsa zai wofintar da ita
ne,tunda tun farko ya nuna zubewar aji ne kamarsa a ce ya auri gurguwa irin ta.
Har Iyah ta gama bambaminta ta fice TAIMIYYAH bata sake cewa komi ba,tayi kwance ne kawai
tana jinjina ƙarfi halin Yah Emran ɗin, da ya iya shiryawa Iyah duk wani ƙarya wai yana son ta.Ta
lumshe ido abinda ya faru tsakaninsu a Kano na dawo mata daki-daki,ta kai hannunta kan bakinta
tana ji kaman bakinsa na tsotsar lips ɗinta ne,hakan yasa tayi saurin buɗe idanunta tar...! Tana ji
wani abu na danne zuciyarta da jin tsanansa me zafi a ranta.
Bata fito daga ɗakinta ba sai bayan da tayi sallah sannan yinwa yasa ta fitowa neman abinci.
Tana cikin cin abincin ne kuma Yah Sadeeq ya shigo,kusan tare da shi ma suka ci abincin da ta
zuba ɗin,suna ci yana mata hiran budurwansa Safiyyah.
TAIMIYYAH ita ce ta sanarwa Iyah cewa Yah Deekun ya samo mata,har da amsar wayar Sadeeq
ɗin tana nunawa Iyah pic ɗin budurwan tasa.
Iyah tayi murna da fatan alkhairy tana jin tausayinsa cikin zuciyarta, don daga kallon da yake bin
TAIMIYYAN da shi zaka gane har yanzu da soyayyarta cikin zuciyarsa.
Ya jima sosai a Sasan suna hira da TAIMIYYAH wacce ke zuba masa shagwaɓar da yayi missing
tsawon lokaci,don ya jima basu sama zama irin haka,TAIMIYYAH ta saki jiki suna hiransu kamar
yau ba,sai kusan la'asar ya bar Sasan Iyah,itama TAIMIYYAH yana fita ta koma zuwa ɗaki don
yin waya da Zee akan assignment ɗin da aka basu a skull.......✍🏻
#Ɗansabo ce#
[12/14, 3:43 PM] +234 703 040 9541: *Littafin TAIMIYYAH paid book ne,ga duk wanda ta
tsincesa a kowani irin group ne,kiji tsoran Allah karki karanta sai kin biya 500 naira only.*
*Za ku iya min magana ta wannan number ɗin 08167768704, ko kuma ku turo kuɗin ku kai tsaye
ta wannan account ɗin*👇🏻
0504192664 aisha ibrahim dansabo GTbank.
Masu turo credit za ku turo katin MTN na 500 ta wannan line ɗin 08167768704.
_*Ina ƴan kasuwa masu buƙatar a tallata muku hajar ku? Maza ku garzayo da kuɗi ƙalilan a
tallata muku kayan siyarwanku sai dai kawai ku ji ana kiran waya don buƙatan sayan kayan ku,ku
tuntuɓeni ta layina kamar haka 08167768704.*_
*45*
*Asokoro,Abuja.*
Suhailah ce zaune daga gefen Maleek Ado,wanda ke kwance baya ɗin Zazzaɓi da ciwan kai ke
damunsa.
Suhailah sai faman Lallaɓasa take yi akan ya tashi ya ci abincin data ɓata lokaci wajen girka
masa,don ya samu idan ya ci ya sha magana,amma shi sai wani narkewa yake yi,dama kuma shi
idan ba shi da lafiya komawa yake yi tamkar wani ƙaramin yaro.
"Please! Luv ka tashi ka ci abincin in baka drugs ka sha,ko sai na kiro maka Hajjah ne wai?"
Suhailah tayi maganan cikin narke masa murya idanunta na kansa.Ya buɗe manyan idanunsa ya
sauke a kan fuskarta, yana jefa mata harara,cikin low voice yake faɗin, "Yes go and call her."
Suhailah ta saki murmushi tana gyara zamanta daga gefen gadon,ta kai hannu tana ɗago face ɗinsa
ta manna masa kiss a goshi tana cewa, "Sorry luv wasa nake yi amma idan baka ci abincinnan ba
zan kira ta gaskiya."
A.Maleek ya lumshe idanunsa yana jin tasirin kiss ɗin da Suhailah ta bashi har ƙasan ransa.Ya
yinƙura ya tashi zaune yana ɗan ɓata fuska yake cewa, "Oya bani inci kaɗan sai ki bani maganin
in sha,kar ki cinyeni da wannan nacin." Suhailah dai murmushi tayi kawai tana ɗakko plate ɗin
abincin ta fara bashi yana ci a hankali,sai da yaci da ɗan yawa sannan ya kauda face alamun ya
ishesa haka,sai ta bashi ruwa ya sha kafin ta fara bashi maganin yana amsa yana sha.Sai faman
wani ɓata fuska yake har ya gama shanye adadin wanda zai sha a lokacin.
Subailah ta maida ledan da drugs ɗin ke ciki ta aje saman side drawer,sannan ta ɗauki plate ɗin
don fita da shi.
"Baby please idan kin kai ki dawo ki min wanka,mu kwanta in ɗan sammaki ɗumin jikin kema kin
ji wife?"
A.Maleek yayi maganar yana daga kwance ya lumshe idanunsa,ba za ka taɓa cewa daga bakinsa
kalaman suka fito ba.
Suhailah sai ta saki murmushi tana cewa, "Ok Luv bari in je zan dawo yanzu in Hajjah bata tsare
ni ba."
Tayi maganar tana fara takawa don barin ɗakin, tana jiyo muryansa a dake lokacin da yake faɗin,
"Alright."
Wani murmushi ta sake yi lokacin da take ficewa daga ɗakin baki ɗaya,tana jinjina rigima irin ta
Maleek in dai akace an taɓo file ɗinsa ba shi da lafiya shikenan magana ta ƙare.Don rigima ce zai
tayi salo-salo har sai ya samu kansa,har ta kai plate ɗin kitchen ɗinta da ke nan upstairs bata bar
murmushi ba.
Bayan ta aje plate ɗin ta fito ɗakinta ta nufa kai tsaye,ta sauya kayan jikinta zuwa wata ƙaramar
riga mara nauyi,don ta san daga yi masa wankannan sunanta sorry,don ita ma sai ya jiƙeta tsaf sun
yi wankan tare sannan zai ji daɗi.
Lokacin da ta koma ɗakin nasa a kwancen dai ta samesa idanunsa a kulle har lokacin,ba kuma
bacci yake yi ba.
Sai ta isa bakin gadon ta zauna tana yaye duvet ɗin da ya rufe jikinsa da shi, ta kai hannu saman
wuyarsa don ta ji ko zazzaɓin na nan,aiko sai taji jikin da sauran zafi sosai.
Maleek ya buɗe manyan idanunsa ya sauke akanta,yana kafe ƙirjinta da ido wanda ko Bra bata
sanya ba,ya kai hannu wajen yana tsareta da idanunsa da suka ɗan shige kaɗan suka rage girma.
Suhailah ta narke fuska tana cire hannunsa daga wajen take cewa, "My Maleek wankan please!
Bari na je na haɗa maka ruwan."
Maleek ya bita da ido lokacin da ta tashi ta nufi hanyar bathroom ɗin,ya maida idanun nasa ya
lumshe har lokacin kansa ciwo yake masa sosai.
Hannunsa cikin na Suhailah suka isa bathroom ɗin, lokacin da ta fito ta sanar masa ta haɗa masa
ruwan wankan.
Da kanta ta cire masa kayan jikinsa,sai faman narke mata yake yi.Kamar yadda ta ruwaita a ranta
cewa ,wankan su biyu zasu yi sa hakan ne ya faru,don Maleek ɗaukarta cak yayi ya sakata cikin
ruwan, bayan ya zare rigar jikinta yayi wurgi da shi.
Wankan da ba a samu yinsa akan time ba kenan,sai da Maleek ya gama bidirinsa son ransa kafin
ayi wankan me dalili,suka fito Suhailah nata faman zunɓure baki,shi kuma yana bin ta da wani
makirin smile.
Suhailar ce ta taya shi ya shirya kansa cikin ƙananun kaya marasa nauyi,kafin itama ta nufi
ɗakinta don shiryawa,ta bar Maleek na amsa kiran da ya shigo wayarsa.
Koda ta gama shiryawa cikin riga da skat na atamfa,wanda ɗinkin ya yi mata cif a jiki tare da
fidda shape ɗinta,sai ta ɗauki turarenta na MISS DIOR ta fesa kaɗan tana ɗaukar wayarta ta fito
zuwa downstairs.
Ɗakin da Hajjah tai masauki tun xuwan su garin, yau kwanakin su bakwai kenan da
tarewa,Suhailah ta shiga ɗakin bakinta ɗauke da sallama.
Hajjah da ke daga kwance tana ɗan hutawa na rashin abin yi, ta ɗago idanunta ta sauke akan
Suhailah,tana amsa sallaman da ta yi.
Ta tashi zaune lokacin da Suhailan ta ƙariso zuwa cikin ɗakin tana cewa, "Kin kintsa kin sakko
ɗin,toh ya jikin Maleek ɗin ina fata da sauƙi sosai?"
Suhailah ta zauna akan sofa dake ɗakin, tana murmushi ta dubi Hajjah tana cewa,
"Ya ji sauƙi Hajjah wanka yayi ma yanzu bayan ya ci abinci,sai ya sha magunguna,yanzu zaki ga
ya sakko zuwa gaida ki ma."
Kafin ko Hajjah tace komi daddaɗan ƙamshin turarensa na AMOUAGE ya gama cika hancinsu,ya
doka sallama cikin muryansa me cike da ƙasaita.
Hajjah ta kai dubanta wajensa tana amsa sallamar tasa, shi kuma ya cigaba takowa zuwa cikin
ɗakin,bai yi masauki a ko'ina ba sai kusa da Hajjah, yana zama daga gefenta kamar zai shige
jikinta.
Murya cike da zallar shagwaɓar da ya saba yi mata yake gaida ita,Hajjah ta saki murmushi tana
ɗaura hannunta saman kansa take amsa gaisuwarsa tare da cewa, "Maleek ya jikin naka ina fata
kana samun sauƙi sosai?"
Maleek ya jinjina kai yana cewa, "Da sauƙi sosai Hajjah kin san zazzaɓin yanzu matsalarsa naci
ne da shi,ɗumin jikin ya hau ya sauka ne haka yake min,amma nan da gobe idan na shanye dose
ɗin bai tafi gaba ɗaya ba, ina ga allura kawai zan amsa zai fi."
Hajjah ta jinjina kai tana faɗin, "Allah ya ƙara lafiya,zai tafi ma insha Allah,ya maganan komawa
ta Zarian a gobe?"
Suhailah dake saurarensu tayi tsagal tana duban Hajjah tace, "Kai Hajjah don Allah ki share
maganan komawarnan sai zuwa wata satin don Allah." Hajjah ta harareta tana cewa, "Aiko sam
baku isa ba gobe zan koma gida, na ga alamun so kuke ku maida ni wata abokiyar wasanku,na bar
bayin Allah a can daga cewa kwana biyu zan yi in juya, sai gashi har na share sati guda sannan
yanzu kice kin sake wasu kwanakin, cikin wannan shegen garin da babu daɗin zama,kana ƙunshe
cikin gida to badani za a yi wannan rayuwar ba,sai ku yara kune kuka dace da irin wannan zaman
amma ba Hajjah ba,ku barni na koma cin ƴan aikina da jama'ar arziƙi dana saba dasu a can,gobe-
gobe babu fashi zan tafi don haka kai Maleek kama sanar da duk wanda zai kaini tun yau,ga
direbobi nan sai wanda aka dar je ya kaini,ai gobe sai kwanan gida ƴar nan da yardar Allah, sai
kuma wani lokacin idan rabo ya kawo mu haka nake fata Insha Allah."
Hajjah ta ƙare maganan tana ɗaga kan Maleek daga kafaɗarta,wanda ya wani narke tamkar jinjirin
goye.
Ganin Hajjah ta ture kansa daga jikinta, yasa shi dubanta fuska a cuskune yake faɗin, "To ni
Hajjah me kuma nayi ake ture kaina ina cikin jin ɗumin jikin uwata,ita zaki ki dungure kanta
tunda ita ce ta takaloki bani ba fa."
Maleek yayi maganar yana faman aikawa Suhailah da ke musu dariya harara.Ita kuma ganin yana
hararanta yasa ta saki dariya me sosai tana cewa, "Hajjah yanzu daga roƙonki ki zauna shine abin
wannan sababin,to ni dai gaskiya sai dai mu koma tare na fasa zaman nan ɗin nima."
Hajjah ta danna mata harara tana miƙewa tsaye take cewa, "To madallah! Ni bari ku ga na baku
waje don na ga so kuke yi ku manna min hauka da girmana,ni dai na gama magana gobe sai gida,
in baki iya zama sai ki bini mu koma,shi kuma sai ya yo sabuwar Amarya ya saka ta cikin
gidan,kin ga an huta da ƙorafi."
Daga haka Hajjah ta fice tana sakin murmushi,tana jiyo Suhailah na cewa, "Wallahi ban yarda ba
Hajjah in haka ne kiyi tafiyar ki kawai bakomi."
Maleek da ya taso daga kan gadon Hajjah, ya dubi Suhailah yana cewa,
"Ashe dai mutum ƙaryan gulma yake yi,ki bita ɗin mana ki gani in ban auro ƙawarki me ƙaton
mazaunai na kawota Abuja ba,tunda ke baki son zama sai da Hajjah,sabida tun farko da ita kika
saba zama gidan miji ko?"
Suhailah da ta cika tai fam da takaicinsa sai kawai ta miƙe zata bar masa ɗakin,yayi saurin riƙota
ya matse a jikinsa, hakan ya sanya ta saka masa kukan shagwaɓa tana cewa, "Ni ka sakeni Yah
Maleek tunda har yanxu ba za ka manta da ƴar iskannan ba."
Maleek ya danne dariyan dake taho masa, yana juyo da face ɗin Suhailah ya haɗe fuskokinsu waje
guda yana cewa,
Suhailah da har lokacin fuskarta a haɗe yake, da jin zafin ambaton sunan Zuby da yayi,sai ta buɗe
baki xata yi magana Maleek ya xura harshensa cikin bakin, yana fara bata wani irin deep kiss da
ya sanya ta sake shigewa jikinsa sosai.
Ya jima yana bata hot kisses tana taya shi itama,sai da ya gaji don kansa ya raba bakinsa da
nata,yana jifanta da wani sassanyar kallo yake cewa, "Baby let go please! Ina so mu ɗan kwanta
tare zuwa la'asar,cox i need u so much dear."
Suhailah ta sake narke masa cikin son tsokanarsa take cewa, "No Luv zan taya Hajjah hira, ka fara
tafiya zan biyo ka daga baya."
Maleek ya jefa mata wani kallo yana haɗe fuska yake faɗin, "Okey idan ma kun gama hiran zaki
iya xama abinki kar ki nemeni."
Daga haka ya raɓa Suhailan zai wuce tayi saurin shan gabansa, tana jifansa da murmushi,murya
can ƙasa take faɗin, "Sorry my Maleek mu je ka sammin ɗumin jikin nima Baby."
Yadda take maganan tana ɗage masa gira, yasa shi kai hannu ya dungure goshinta yana faɗin,
"Let's go Babe!"
Daga haka suka fito daga ɗakin suna ratsowa cikin falon Hajjah da ke zaune,wacce ta maida
hankali wajen kallon tashar Aljazeera.
Ta ɗaga ido ta dube su Maleek sau ɗaya tana ɗauke kanta daga garesu.Maleek ya iso inda take
zaune yana cewa, "Hajjah bari in je na ɗan kwanta xuwa la'asar, idan anyi sallah za ku fita da
Suhailah da driver,sabida ki yi siyayyar tsarabar da zaki tafi da shi."
Hajjah ta taɓe baki tana cewa, "Madallah! Da dai yafi kam,Allah ƙara afuwa je kai kwanciyarka."
Suhailah ta dubi Hajjah cike da shagwaɓa tana faɗin, "Hajjah yanzu don Allah fushi kike dani, ko
kallona baki son yi."
Hajjah ta harareta tana cewa, "Kai ni ku tafi ku bani waje inyi kallona, bansan damu tunda duk
kun haɗu kun maida ni kakar ku."
Suhailah da Maleek duka suka saki murmushi,suna haɗa baki wajen faɗin, "Afuwan Hajjah Allah
baki haƙury mun yi nan."
Daga haka suka nufi hanyar da zai kai su Upstairs, Hajjah na bin bayansu da kallo tana me musu
addu'ar Allah ya dauwamar da zaman lafiya a tsakaninsu, ya baiwa Suhailah mafita da rabo me
anfani kusa ko nesa.
Bayan la'asar kamar yadda Maleek ya faɗi,ya baiwa Subailah da Hajjah kuɗi me yawa suka fita
yin siyayya,tare da ɗaya daga cikin direbobin da aka je musu a gidan.
Washegary Hajjah ta wuce ta bar Suhailah da kewanta me yawa,shi kuma Maleek Monday zai bi
flight ɗin safe zuwa Lagos.
__________
*Zaria,*
*4:15pm.*
Zuhurah da Basmah ne tsaye daga cikin kitchen, suna ƙarisa kammala haɗa abubuwan da za a
tarbi Nass da shi,wanda yace wa Basmah ya kusa ƙarisowa gidan nan ba da jimawa ba.
Basmah ta gama juye lemun Zoɓo da suka cikawa sugar cikin jug, tana duban Zuhurah take faɗin,
"Yah Zuhurah amma fa baki ji yadda gabana ke faɗi ba,sai tunanin yadda zan dubesa ido cikin ido
nake yi a zahiri,bare har in iya sanar da shi irin soyayyar da nake masa."
Zuhurah ta aje plate ɗin da tayi raping Doughnut ɗin da suka siyo,tana duban Basmah da
murmushi saman fuskarta take cewa, "Aiko bai kamata ace kina jin hakan ba, idan akai la'akari da
irin son sa da ya rufe idanunki,sannan Umma ta sanar da ke cewa da zaran kun yi ido biyu da shi
shikenan fa magana ta ƙare,don ji zaiyi ko me kika sanar dashi ba zai iya musawa ba,don an riga
anmantar da shi wata TAIMIYYAH.Bokan fa yace ko sunanta kika kira sai yaji wani ɓacin rai ya
lulluɓe zuciyarsa,ba dai kinyi wankan maganinnan na kwana uku ba,kuma yau ma kinyin turaren
da yace ki yi haɗe kayan da zaki saka idan zaki wajen Nass ɗin,to sai mu zuba ido mu ga me zai
biyo baya...
Zuhurah ta cigaba da cewa, "Ni dai na ga cika aiki wallahi,don yanzu Ameeru sai abinda nace ina
so yake yi, wani irin zazzafan so yake min wanda ya ninka na baya, tunda nai anfani da turarennan
ran da yazo."
Basmah da tai kasaƙe tana sauraran Zuhurah, sai ta saki ƙayataccen murmushi,tana jin wani
ƙwarin guiwa na mamaye zuciyarta.
Shigowan Umma cikin kitchen ɗin yasa duk suka zuba mata ido, Basmah na cewa, "Umma mun
kammala bari na je na shirya yana hanya yace ya kusa ƙarisowa,a falon Baba zamu sauke sa."
Umma ta jinjina kai tana cewa, "Eh hakan yayi,sai kiyi maza ki shirya ɗin ita Zuhurah sai ta je ta
kammala komi a can ɗin,ki tabbatar kin wanke fuskarki da ragowar wannan ruwan rubutun,da aka
ce sai randa za ku yi ido biyu da yaron za ki yi amfani da shi,yana nan na aje miki a ɗakin naku."
Basmah ta gyaɗa kai tana cewa, "To Umma bari in je Allah dai yasa kwalliya ta biya kuɗin
sabulu."
Umma tayi murmushi tana bin bayan Basmah da kallo,kafin ta maida dubanta kan Zuhurah tana
cewa, "Hmm! Yaro man kaza,an gaya miki a banza nake zaune da ubanku shekaru kusan talatin
amma bai taɓa zancen ƙarin aure ba,ki dai yi yadda aka ce ɗin ki ga ikon Allah,amma indai aikin
na bakin rafi ne bai taɓa yi ba a samu nasara ba,in dai zaka saki bakin jaka to za ka ga biyan
buƙata kuwa,ki rabu da fulani kawai inda kika gansu."
Zuhurah tai wani dariya tana saluting Umma take cewa, "Wallahi na yadda Umma don na ga aiki
da cikawa,sabida yanzu Ameeru ko a waya bai son ɓacin raina bare idan yana gabana,wani irin
soyayya yake gwadamin ta ban mamaki, burinsa kawai ayi-ayi a ɗaura auren mu Allah dai ya ja
kwana Umma, ai mu tuntuni baki karanta mana cewa kina zagayawa ta ƙarƙashin ƙasa ba."
Daƙuwa Umma ta aikawa Zuhurah tana cewa, "Zan ci ƙaniyarki Zuhurah kin raina ni ko?"
Zuhurah na dariya take cewa, "Sorry Umma ba haka bane wallahi." Daga haka ta fara kwasan
abubuwan da suka kammala shiryawa tana kaiwa falon Baba Sani,ta shirya komi bisa table tana
sake faffesa roomfreshner cikin falon,nan da nan ko'ina ya ɗauki sassanyar ƙamshi.
Daga ɓangaren Basmah kuwa tuni ta kammala shiryawa,cikin wasu riga da skat na wani atamfar
Chiganvy gold.
Kalar atamfar me duhu ce daya haska ta sosai, don tana da hasken fata tafi Zuhurah haske,ɗinkin
ya zauna a jikinta sosai tare da fiddo shape ɗinta a zahiri.
Push-up Bra ta sanya wanda ya sake turo da cikar ƙirjinta sosai ta saman rigar,sai ta feshe jikinta
da turaruka masu tsananin ƙamshi,ɗakin gaba ɗaya ya buɗe da ƙamshi,tana cikin sanya Ɗankunni
wayarta ya fara ringing.
Sai ta nufi wajen da wayar take aje tana ɗauka, ta kai kunni bayan tayi receiving tana cewa, "Yah
Nass har ka iso ne,ok gani nan fitowa yanzu." Daga haka ta aje wayan ƙirjinta na faman
dokawa,cikin hanzarin ta ɗauki veil ɗinta me shara-shara ta yafa, ta fito daga ɗakin nasu ta nufi
ƙofan fita.
Naseer wanda tun isowarsa ƙofar gate ɗin gidan memories ɗinsu da TAIMIYYAH ya shiga
dawowa kwanyarsa.Sai ya dinga jin wani zumuɗi da shauƙin son ganin kyakykyawan face ɗin
TAIMIYYAH da yayi missing tsayin lokaci.
Sabida Basmah ta yaudare shi da cewa idan ya zo,ita ce zata san yadda za a yi ta jawo masa
TAIMIYYAH zuwa sasan su, ba tare da Iyah tama san ya zo gidan ba.
Ya cigaba da jingina da jikin motarsa hannunwansa duka biyu harɗe saman ƙirjinsa,ya kafe ƙofar
gate ɗin da kallo yana jiran ganin me fitowa daga ciki.
Basmah ta buɗe ƙofar ta fito cikin wani irin taku na ɗaukar hankali,take nufowa inda Nass yake
tsaye.
Nass ya dinga bin ta da kallo yana ji kansa ya fara wani irin sarawa,tun lokacin da ya ɗaura
idanunsa akan Basmah.Ta ƙariso tana kashesa da wani irin murmushi,da har haƙoranta suka
bayyana,kafin tayi magana cikin narke murya tana cewa, "Sannu da zuwa Yah Nass mu je daga
ciki ko."
Nass da gaba ɗaya kansa ke wani irin juyawa, sai yayi saurin dafe goshinsa da hannu yana cewa,
"Okey toh."
Daga haka Basmah tayi gaba shi kuma yana biye da bayanta,idanunsa na yawo akan jikinta yana
kallon yadda take motsa albarkatun jikin nata cike da gayya,take wani irin baƙon abu ya fara
tasowa daga cikin zuciyarsa yana mamaye ilahirin jinin jikinsa,kansa ya yi masa wani irin nauyin
da bazai iya misaltawa ba.
Har suka isa part ɗin su Basmah ya rasa abinda ke masa daɗi.Basmah kuwa sai wani rawar jiki
take yi ta rasa inda zata tsoma ranta, sabida murnan ganin Nass ɗin a gabanta.
Gabaki ɗaya wankan da ya shawo cikin wani dark gray ɗin gezner ya gama tafiya da zuciyarta,ta
zauna kusa da shi idanunsu na sarƙewa cikin na juna.
Nass ya ji wani irin yanayi na ratsa shi har cikin ɓargonsa,ya kai hannu yayi saurin dafe kansa da
ke sara masa, yana son karanto addu'a amma ya kasa.
Basmah da ke lura da yana yinsa sai ta saki murmushi tana cewa, "Bari in zuba maka lemu ka sha
kafin in je in taho maka da TAIMIYYAH."
Tayi maganan tana tsare shi da ido don son ganin reaction ɗin da zai nuna.
Ga tsananin mamakinta kuwa sai gani tayi, ya ɗago yana mata wani irin kallo,kafin yayi magana
cikin sanyin muryarsa yana cewa,
"No Basmah karki kira ta please! Ni ba ita nazo gani ba, yanzu zan koma gidama kaina ciwo yake
me tsanani,tunda ke na ganki its okey please!"
Basmah da taji kamar ta saki ihun murna ta taka rawa,sai ta maze ta wani haɗe face tana cewa,
"Ban gane zaka wuce yanzu-yanzu ba,bayan ba ka ga sahibar taka ba."
Nass da ke ji wani irin duhu na lulluɓe zuciyarsa,yayi saurin duban Basmah yana cewa, "Yes bana
jin ganinta ne kawai,tunda na ɗaura idanuna akanki na ji cewa bama sai na ganta ba,tunda dama
Mum tayi Allah ya isa idan har na cigaba da bibiyarta,please kar ki dage akan sai na ganta
Basmah."
Yadda ya kira yi sunan Basmah ya sake narkar da zuciyarta,ta wani yi masa fari da ido tana cewa,
"Okey Yayana na fahimceka,yanzu dai sha wannan sai mu ɗan taɓa hira kafin ka wuce ɗin."
Tayi maganan tana miƙa masa cup ɗin da ta cika masa da lemun zoɓon,wanda da aka dafa shi da
ruwan magani.
Nass ya amsa ya kai baki yai masa kurɓa biyu ya aje,sabida uban sugar da aka cika, wanda yaji
zaƙin har hawa masa kai yake yi.
Cikin kissa Basmah ke jansa da hira yana biye mata, duk da irin ciwan kan da yake ji amma sai
yaji tamkar wanda aka ɗaure da igiya, sam baya son barinta hasalima muryarta ne yake ji na rikiɗe
masa yana komawa tamkar na TAIMIYYAH.Shiyasa ya sake sakin jiki tana cigaba da hilatarsa da
hira, har zuwa sanda Zuhurah ta shigo suka gaisa da Nass ɗin,ta fita ta basu waje bayan sun haɗa
ido da Basmah sun sakarwa juna ƙayataccen murmushi..........✍🏻
#Ɗansabo ce#
[12/14, 3:43 PM] +234 703 040 9541: *Littafin TAIMIYYAH paid book ne,ga duk wanda ta
tsincesa a kowani irin group ne,kiji tsoran Allah karki karanta sai kin biya 500 naira only.*
*Za ku iya min magana ta wannan number ɗin 08167768704, ko kuma ku turo kuɗin ku kai tsaye
ta wannan account ɗin*👇🏻
0504192664 aisha ibrahim dansabo GTbank.
Masu turo credit za ku turo katin MTN na 500 ta wannan line ɗin 08167768704.
_*Ina ƴan kasuwa masu buƙatar a tallata muku hajar ku? Maza ku garzayo da kuɗi ƙalilan a
tallata muku kayan siyarwanku sai dai kawai ku ji ana kiran waya don buƙatan sayan kayan ku,ku
tuntuɓeni ta layina kamar haka 08167768704.*_
*46*
Lokacin da Basmah da Nass suka fito daga part ɗin Baba Sani ta ƙofar waje, dai-dai lokacin ne
TAIMIYYAH da Shukurah suka fito daga sasan Iyah, TAIMIYYAH za ta yiwa Shukurah rakiya
zuwa bakin gate.
Sun ƙariso bakin gate ɗin ne dai-dai lokacin da TAIMIYYAH ta juyo don komawa cikin
gida.Caraf! Sai sukai ido huɗu da Nass wanda ke tahowa, cikin wannan takun nasa da ta sani, me
cike da nutsuwa.
Idanun TAIMIYYAH suka sake girma,tana sake waro su waje cike da ɗimbin mamakin ganin
Nass shi da Basman,waɗanda ke tahowa Basmah na binsa agindi-agindi tamkar kafaɗunsu za su
yi gogayya juna.
Yadda ta faɗi sunan murya a waje sosai ya sanya Nass da shi ma ya zuba mata ido, kansa na sake
sarawa tamkar zai rabe gida biyu,yayi saurin rintse idanunsa yana ji tamkar kansa zai bar gangar
jikinsa.
Ganin yadda Nass ɗin ya rintse ido, yasa Basmah isa gaban TAIMIYYAH tana cewa,
"Yah TAIMIYYAH miye hakan daga ganinsa zak kira sunansa cike da ɗaga murya haka?Nass
ɗinki ne dai da kuka rabu ba gizo yake miki ba,don haka in mamaki kike yi ki daina."
Basmah ta ƙare maganan tana aika mata wani mugun harara,tana me komawa kusa da Nass tana
faɗin, "Sorry my Nass,har yanzu ciwan kan ne dai?"
Nass da idanunsa har lokacin yake a rintse kansa na juyawa,ya buɗe idon yana sauke su akan
TAIMIYYAH da tai mutuwan tsaye, ta kasa koda ƙwaƙwƙwaran motsi sabida shiga shock da tayi.
"Zay..na.b!"
A rarrabe ya faɗi sunan zuciyarsa na mamayewa da wani irin duhu, ya wuce su TAIMIYYAH
fuu..!!! Tamkar wanda aka dannawa remote control.
Hakan yasa TAIMIYYAH bin bayansa da kallo, zuciyarta na wani irin shaking a ƙirjinta.
Wani irin gagarumin tashin hankali take ji na rufto mata,sai tayi gaggawar maida dubanta ga
Basmah,cike da son jin ƙarin bayani daga gareta.
Kamar Basmah ta san nufinta sai ta tako har xuwa gaban TAIMIYYAN, wacce zuwa lokacin
dukkanin jikinta ya ɗauki rawa,tana dafe da guiwar ƙafarta me laluran.
Basmah ta murmusa tana kai hannu zata dafa kafaɗan TAIMIYYAH, amma sai TAIMIYYAH tayi
saurin yin baya tana jingina da jikin gate ɗin.
Tana ji ƙafafunta na neman gaza ɗaukar nauyin gangar jikinta.Basmah ta sake sakin murmushi
tana cewa, "Yah TAIMIYYAH kiyi haƙury, na san ba za ki taɓa jin daɗin tarayyata da Nass
ba,amma am sorry to say zuciyata ta jima da kamuwa da son abinda zuciyarki ke so,sai kuma akai
sa a baku dace da juna ba tunda ke Allah ya yoki gurguwa,shi kuma Nass lafiyayyan namijin da ya
mallaki duk abubuwan da mace za ta buƙata a wajen ɗa miji."
Basmah ta ɗan dakata da maganar, tana sake shigar da idanunta cikin na TAIMIYYAH,wacce
zuwa lokacin wani irin zufa ya fara wanke fuskarta.Basmah ta cigaba da cewa, "Tun randa na fara
ganinsa a wajenki na faɗa kogin soyayyarsa,amma sai nai ta dannewa sai a yanzu dana bibiyesa na
gane cewa,uwarsa ta raba ku don kasancewarki gurguwa,ba zai yiwu ɗanta ya aure kina a gurguwa
ba,shiyasa ni kuma naga bazan iya bari mu rasa shi duka mu biyu ba......."
Yadda TAIMIYYAH ta jefo mata wani mugun kallo ne ya saka Basmah kasa cigaba da
maganarta,kamar yadda TAIMIYYAH itama ta kasa cewa komi, sai hannu da ta kai ta dafe saitin
zuciyarta tana jin wani irin zafi da ƙuna.
Kanta ne yai wani irin sarawa tana jin duniyar gaba ɗaya na juya mata,cikin sauri ta fara takawa
tana nufan hanyar komawa sasan Iyah.
Basmah tabi bayan TAIMIYYAN da kallo wani abu na motsawa cikin zuciyarta,amma wani sashin
na danne tasirin abinda ke tasowan,sai ma tayi saurin juyawa ta fice daga gate ɗin gidan, ta nufi
wajen motar Nass da ke fake daga waje.
Tana isa ta samesa cikin motar ya haɗe kansa da styering motar idanunsa a rufe ruf! Ta saka hannu
ta buɗe front seat ta shiga ta zauna, tana kiran sunansa cikin narke murya.
Nass ya ɗago idanunsa da suka rine zuwa ja,ya sauke akan fuskar Basmah yana ji tamkar ya fasa
ihu ko zai dawo cikin hayyacinsa,ya gano meke shirin faruwa da shi amma ya kasa.
Ya zubawa Basmah ido zuciyarsa na cigaba da dokawa, tamkar za ta yi tsalle daga ƙirjinsa ta fito
waje,Basmah dake ta faman kallon yanayin da ya shiga, sai tayi ƙasa da murya tana faɗin, "Sorry
My Nass kanne dai har yanzu,kayi haƙury ka ƙarisa zuwa gida ka samu magani ka sha, zuwa
anjima sai muyi waya ko?"
Nass daya zama tamkar wani gunki sai ya samu kansa da gyaɗa mata kai,yana maida idanunsa ya
sake lumshesu,kafin ya sake buɗe su akanta yana cewa, "Okey Basmah, but don Allah meke shirin
faruwa da ni ne?"
Basmah ta aika masa harara ƙasa-ƙasa tana cewa, "Kamar yaya Yah Nass?"
Nass ya cije lips ɗinsa yana kai hannu ya dafe kansa yake cewa, "Basmah zuciyata ciwo take
yi,ga kaina da nake ji tamkar zai rabe gida biyu tunda na iso ƙofar gidannan,gaba ɗaya na rasa
dukkan nutsuwata,a yanzu kuma da nayi ido biyu da Zaynab,ina ji tamkar zuciyata zata yo tsalle
daga ƙirjinane ta fito waje,raina zafi yake yi Basmah meyasa zan ji hakan alhali ina son ta so me
tsanani?"
Yadda ya tsare Basmah da idanunsa da suka sauya kala,yasa Basmah taɓe baki ta sake kwantar da
murya tana cewa, "Naseer bazan iya gane komi ba, tunda nima a haka na ganka sanda ka
iso,amma karka damu yanzu kana buƙatan ka je ka huta, ka sha magani sai muyi magana zuwa
anjima, Allah ya baka lafiya my bro."
Nass ya jinjina kai kawai a lokacin da Basmah ke ficewa daga motar,ta juya don komawa cikin
gida,tana Allah-Allah ta isa zuwa sasansu don baiwa su Umma labari.
Nass ya bi bayanta da kallo zuciyarsa na ɗarsuwa da wani irin feeling da bai taɓa jin irinsa ba,ya
rintse ido tare da cije lips ɗinsa tamkar zai fasa shi,yana me dafe kansa yana furta kalmar,
"La'ilaha'illallah!"
Ya cigaba da zama cikin motar har lokacin hannunsa na dafe da kansa,sai da ya ɗauki lokaci me
tsawo kafin ya iya tada motar ya bar ƙofar gidan.
A ɓangaren TAIMIYYAH kuwa,ikon Allah ne kawai ya ƙarisar da ita zuwa sasan Iyah,sabida ta
turguɗe a tafiyarta babu adadi kafin ta isa cikin sasan.
Gaba ɗaya jikinta da ko'ina ma rawa suke yi, tsabagen shiga shock da tashin hankalin ganin Nass
ɗinta tare da Basmah.
Lokacin da ta iso cikin falon Iyah sai kawai ta zube akan kujeran farko, tana sakin wani irin kuka
me tsuma zuciya.
Iyah da ke zaune ta taso da sauri ta nufo wajan TAIMIYYAH tana faɗin, "Lafiya Zainab, meke
faruwa haka zaki shigo ki xube min kina kuka, daga rakiyar ƙawa maza sanar dani me yafaru?"
TAIMIYYAH sai ta sake rushewa da kuka,tana kama hannun Iyah ta kai saitin ƙirjinta tana cewa,
"Iyah danne min ƙirjina ina kamar zai fashe,zuciyata zafi take yi Iyah kamar numfashina zai
ɗauke."
Yadda take maganar tana rishin kuka ya ɗaga hankalin Iyah,tayi saurin zama cikin kujeran tana
ɗago TAIMIYYAH zuwa jikinta tace, "Subhanallahi! Ni Fatima meke shirin faruwa da marainiyar
Allah,Zainab sanar dani meke damunki? yanzu-yanzu sai Ubangiji ,lafiya kuka fita da Bushira
kuna hiran ku abin sha'awa fa."
Iyah tayi maganar hannunta akan ƙirjin TAIMIYYAH, tana jin yadda zuciyarta ke bugawa tamkar
zai fito daga ƙirjinta.
TAIMIYYAH ko cigaba tayi rasgar kukanta, hannunta na damƙe da ɗaya hannun Iyah,tana ji
tamkar zuciyarta ta fito waje ko zata samu sauƙin abinda take ji.
Iyah data rasa abin cewa sai kawai ta fara janyo duk addu'ar da ya zo bakinta tana tofawa
TAIMIYYAH,suka ɗauki lokaci me tsawo a haka kafin TAIMIYYAH ta tsaida kukan,amma har
lokacin taƙi bari Iyah ta cire hannunta daga kan ƙirjinta da yai masifar yi mata nauyi.
Da ƙyar da kuma rarrashi Iyah ta ciyo kan TAIMIYYAH ta sanar mata da abinda ya faruwa a
waje.
Tun daga kan ganin Nass da Basmah da tayi har zuwa kan maganganun da Basmah ta gaya
mata,bata rage komi ba ta zayyanewa Iyah ta kai ƙarshen maganar tana kuka me tsuma zuciya.
Iyah da itama tai mugun shiga tashin hankali da ruɗu,sai tayi saurin furta kalmar, "Hasbunallahu
wani'imal wakil!" Sannan ta cigaba da cewa, "Yanzu har lalacewar Zuwaira ya kai haka,wace
iriyar ƙiyayyya suke miki da suke so lallai sai sun tozartaki sun ci amanarki har haka? Kiyi haƙuri
Zainab!kiyi haƙury! Shine abu na farko da zan fara gaya miki,sannan ki kwantar da hankalinki ki
baiwa zuciyarki ƙwarin guiwar ɗaukar dukkanin ƙaddaranki na rayuwa.Na sani da ciwo amma ki
daure ki barwa Allah komi,ki kuma zuba musu ido bana so ki nuna komi, koda ace za a kai
matakin da Basmah za ta auri Naseeru,dai-dai da rana ɗaya karki bari su gane cewa sun ƙuntata
zuciyarki,karki bari su ga damuwa akan fuskarki Zainab..."
Iyah ta dakata kaɗan tana ji tamkar itama ta taya TAIMIYYAH kukan,ko zata ji sauƙin baƙin cikin
da ya lulluɓe zuciyarta itama.Amma memakon hakan sai ta ƙarfafi zuciyarta ta cigaba da cewa,
"Tunda dama uwarsa bata son ki,ina so ki danne zuciyarki Zainab,ki zuba musu ido in dai cin
amanace su yi da kyau, Allah zai nuna musu iyakarsu ya kuma yi miki sakayya sabida sun yi
hakan ne don su tozartaki...."
Iyah ta kai ƙarshe tana ƙoƙarin maida hawayen tausayin TAIMIYYAH da suka cika idanunta,ganin
TAIMIYYAH sai cigaban da kukanta take yi,yasa Iyah cigaba da cewa, "Don Allah kiyi haƙury
Zainab, ki zuba ido ni da ke in dai da rayuwa to zamu ga yadda ƙarshen abun zai kasance,kisa a
ranki idan Basmah ta auresa dama can mijinta ne haka Allah ya rubuta,amma kada ki sawa kanki
damuwar da zai illata zuciyarki Zainabu,ki taimakeni ki taimaki maraicinki, ki sanya dangana
cikin zuciyarki don girman Allah."
TAIMIYYAH dai har Iyah ta kai aya kuka take yi ahankali,tana jin dukkanin kalaman Iyan da
suka shiga kunnuwarta suna sake karya zuciyarta.
'Tabbas tana cikin ruɗu da tashin hankali me tsanani,kamar yadda tsantsar mamakin Basmah ke
sake lulluɓe zuciyarta,ta lumshe idanunta tana cigaba da sauraren nasihun Iyah da suka fara rage
mata zafin da zuciyarta ke yi.
Tun hawayen na cigaba da xuba daga cikin idanunta,har suka tsaida kansu sai ajiyar zuciya kawai
da take saukewa akai-akai,har kuma lokacin tana lafe a jikin Iyah ne, ta kaso koda motsawa.
Iyah ta cigaba da shafa kan TAIMIYYAH,tana jin tausayinta me tsanani sake kassara zuciyarta, ta
shiga taɗin zuci tana cewa 'Ta sani da ciwo hakan a wajen ƴa mace, ka ga wata da abinda kai kake
so,koda ace ƙaddara ta rabaku dole sai ka ji wannan kishin,bare TAIMIYYAH da duka-duka basu
ma daɗe da rabuwa da Nass ɗinsa ba,sannan rana tsaka ta tsincesa da ƙanwarta a matsayin
masoya,dole abin ba zai zo mata ta sauƙi ba,kuma ko rantsuwa tayi ba za ta yi kaffara ba har da
haɗin kan uwarsu Zuwaira ,suka shirya hakan don cin amana da son lallai sai sun nunawa duniya
cewa su shaiɗanu ne."
Iyah ta kai ƙarshen maganar zucinta lokacin da TAIMIYYAH ta tashi daga jikinta, tana miƙewa
tsaye ta dafa ƙafarta,cikin sanyin murya irin na wanda yaci kuka ya ƙoshi,TAIMIYYAH ta dubi
Iyah tana cewa, "Iyah zan shiga ciki kaina ciwo yake min ki kawo min magani in sha don Allah."
Daga haka ta fara takawa a hankali ta nufi hanyar ɗakinta,Iyah tabi bayanta da kallo hawaye na
ciki idanunta,na tsananin tausayin TAIMIYYAH.
A cikin zuciyarta take cewa ' Allah ka kawo ma marainiyarka ɗauki,ka bata ikon cinye waɗannan
jarabawoyi da suke kutsowa cikin rayuwarta,Allah kai mata sakayyah da alkhairy tare da miji
nagari, wanda zai ƙaunaceta ya so ta a yadda take."
Ta kai ƙarshen maganar da tayi a zuci tana amsawa da "Ameen." A sarari kafin ta share hawayen
da suka zubo mata, tana miƙewa don zuwa ta ɗakkowa TAIMIYYAH magani ta kai mata ɗaki.
_________
A can Sasan Baba Sani kuwa Basmah ce ta zauna tana zayyanewa Umma da Zuhurah komi daya
faru,har kawo kan ganin da TAIMIYYAH tayi musu tare da Nass ɗin, da yadda ta shiga ruɗu duk
sai da ta sanar musu,ta ƙare maganan tana sheƙewa da dariya.
Zuhurah ma ta saki dariya tana cewa, "Ai ni dama na san dole sai ta shiga shock!Sabida ita duk a
tunaninta bamu san komi akan rabuwarsu da Nass ɗin ba.Ga maganganun da ki kai mata
Basmah,dole zuciyarta ta kusa bugawa,tamkar fa amanarta za ki ci tunda dai tsakani da Allah dole
ce ta raba su, ba son ransu bane yasa ba za su mallaki juna ba,dole da tsananin ciwo ace ƴar uwarta
ta jini kuma ta koma sun jone da abinda zuciyarta ke so,gaskiya ta ɗan bani tausayi tsakani da
Allah."
Zuhurah ta ƙare maganar tana ɗan ɓata fuska,don da gaske ta ji tausayin TAIMIYYAH,sabida tana
hango da ita a kaiwa hakan da bata san irin tashin hankalin da za a yi da ita ba.
Umma ta zabgawa Zuhuran harara tana faɗin, "To sarkin tausayi,sai ki bar mata Ameerun naki ki
share mata hawaye,tunda ta baki tausayi."
Basmah ta amshe da cewa, "Barta kawai Umma tunda tafi son ta dani, aiko sai ta bar mata
Ameeeun mu gani idan zata iya mitsuww...!!!"
Basmah ta ƙare maganan da jan dogon tsaki,tana faman hararar Zuhurah,wacce nan da nan ta haɗe
fuska tana cewa, "Easy please Basmah,abar zancen kawai haka,Allah ya barki da Nass ya juyo da
zuciyarsa gareki shikenan ko?"
Basmah ta sake sakin tsaki tana cewa, "Eh shikenan kuwa kin gama magana,zuciyarsa kuma
kaman na samu na gama tunda ya riga ya shigo hannu ko Umma?"
Umma ta jinjina kai tana faɗin, "Sosai kuwa,yanzu ma zan kira Boka Maharazu in sanar masa da
duk abinda ya gudana,in so samu ne itama gurguwar a yi abinda zata ji ko sunansa bata son ji,a
danne zuciyarta a kuma rufe mana bakin jarababbiyar kakar taku,yadda ko magana yai nisa
tsakaninki da yaron,ba za ta iya taɓuka komi ba sai dai ma ta goyi bayan abin."
"Yauwa Umama wallahi har na ƙara jin ƙaunar ki a raina, i luv u so much." Cewan Basmah tana
rungume Umman suka saki dariya,ita dai Zuhurah sai ta tashi ta basu waje kawai,can ƙasar
zuciyarta danƙare da tausayin TAIMIYYAH.
Umma da Basmha ko cigaba suka yi da tattaunawa akan yadda za a saito musu da zuciyar Nass
ɗin, ta yanda sai abinda suka ce zai yi.
TAIMIYYAH koda ta sha maganin sai ta kwanta,kan kace kwabo kuma zazzaɓi ya rufar
mata,hakan yasa hankalin Iyah ya sake mummunan tashi.
Babu shiri ta sake ɗakko mata maganin zazzaɓi ta bata ta sha,ta rufa mata bargo tana faman jera
mata sannu.
Sai gabda magriba TAIMIYYAH ta iya tashi,da yake tana off ne sai ta nufi toilet ta sakarwa kanta
ruwan ɗumi,tayi wanka ko za ta ji ƙarfin jikinta tunda zazzaɓin ya sauka.
Lokacin da ta fito sai ta kintsa kanta tana zura rigar baccinta me kauri, ta sanya hula akanta ta fito
zuwa falo don cin abinci,har lokacin zuciyarta na mata ciwo,bata kuma fasa ganin komi kaman a
cikin mafarki yake faruwa ba.......✍🏻
#Ɗansabo ce.#
_To masu karatu sai mu je zuwa don ganin yadda wasan zai kaya,amma fa sai da tausayin
TAIMIYYAH ya sani hawaye_ 😰
#Ɗansabo ce#
[12/14, 3:43 PM] +234 703 040 9541: *Littafin TAIMIYYAH paid book ne,ga duk wanda ta
tsincesa a kowani irin group ne,kiji tsoran Allah karki karanta sai kin biya 500 naira only.*
*Za ku iya min magana ta wannan number ɗin 08167768704, ko kuma ku turo kuɗin ku kai tsaye
ta wannan account ɗin*👇🏻
0504192664 aisha ibrahim dansabo GTbank.
Masu turo credit za ku turo katin MTN na 500 ta wannan line ɗin 08167768704.
_*Ina ƴan kasuwa masu buƙatar a tallata muku hajar ku? Maza ku garzayo da kuɗi ƙalilan a
tallata muku kayan siyarwanku sai dai kawai ku ji ana kiran waya don buƙatan sayan kayan ku,ku
tuntuɓeni ta layina kamar haka 08167768704.*_
*47*
*2 Weeks Later*
Cikin biyu ɗinnan da suka wuce abubuwa da yawa sun faru ciki har da sanya ranan auren Zuhura
da Ameeru da aka yi,an sanya watanni uku masu zuwa za a sha biki.
Sai Yah Sadeeq shi ma magana yai nisa har an kai kuɗin gaisuwa ana so nan da lokaci kaɗan a
sanya rana.
Ta ɓangaren Basmah da Nass kuwa tuni sun gama samo kan Nass ɗin,don wani irin azababbiyar
soyayya suke gwadawa juna.Basmah gaba ɗaya ta sake matowa a kansa ta kuma gama saki cewa
asiri gaskiya ne,tunda gashi yayi aiki akan Nass har ya tsunduma a kogin sonta cikin ruwan sanyi.
Duk da cewa tun daga randa ya zo suka haɗu da TAIMIYYAH bai sake zuwa sunyi ido biyu ba,sai
dai ta waya kawai suke shan luv ɗinsu kaman sun shekara da furtawa juna kalmar so.
Umma lokacin da ta ji wajen da Nass ɗin ke aiki a Abuja,sai taji duk ta ƙosama a sanya ranan
auren Basmah da Nass ɗin,don tana saka ran lokaci kaɗan Nass ɗin zai taka wani babbar matsayi.
Gashi binciken da suka yi akansa sun gano cewa Babansa ya rasu ya bar musu ƙaddori
sosai,tsaban kuɗi ne bai bari sosai ba ,duk sai Umma suka sake rikicewa akan son Basmah ta
mallakesa a matsayin miji.
Ta ɓangaren TAIMIYYAH kuwa sati biyunnan tayi shine cike da ƙarfin zuciya, sabida ba ƙaramin
wahala ta sha ba kafin ta iya danne zuciyarta akan cin amanan da Basmah ke son gwada mata.Iyah
ce kullum ke tasa ta a gaba tayi ta mata nasiha akan tayi haƙury ta manta da komi,ta kuma yi
addu'a Allah ya yaye mata dukkanin ƙuncin da take ji a cikin zuciyarta.
Tasirin nasihar da Iyah ke mata da ƙarfin addu'a da tsayuwar dare da take yi,tana kaiwa Allah
kukanta akan ya cire mata duk wata soyayyar Nass da ya rage a zuciyarta,shine ya ƙara taimakawa
wajen samar mata da nutsuwa.
A kuma cikin waɗannan kwanakin ne aka kammala raba gadon Abie gaba ɗaya,aka fitarwa kowa
da kason sa da Allah yace a bashi.
Hatta Baba Sani da Guggo Bilki suma sun shiga cikin magada sabida Abie bai bar ɗa namiji ba sai
TAIMIYYAH ita kaɗai.
Hankalin TAIMIYYAH da na su Iyah ya tashi sosai a ranan,don TAIMIYYAH kusan a kwance ta
yini tana kuka,tare da tsunduma cikin tunanin yadda rayuwa ke juya mata daki-daki da tarin
abubuwa masu taɓa zuciya.
Sai da taci kuka sosai ta gode Allah kafin ta sanyawa zuciyarta dangana,tayi musu kyakykyawar
addu'a kamar yadda Iyah tayi mata nasiha akan yin hakan,lokacin da ta tadda TAIMIYYAR a ɗaki
tana kukan.
__________
Yau ya kama Sunday tun safe TAIMIYYAH ta sanarwa Iyah da maganar zuwan ta Gaskiya Layout
gidansu Zee,kwana biyu kenan da Zee ɗin ta kirata ta sanar mata cewa bata da lafiya sosai.
Hakan yasa TAIMIYYAH ke son zuwa ta duba jikin Zee ɗin,don har ma ta sanar da Sani cewa ya
zo ya kaita idan anyi sallar zuhur,in yaso idan za ta dawo gida sai ta dawo a Napep.
Misalin ƙarfe sha ɗaya da rabi ta kammala shiryawa cikin wata atamfarta kalar dark coffee,wanda
akaiwa ado da milk and gray.Ɗinkin ya zauna a jikinta sosai tare da yi mata kyau ba kaɗan ba,ta
ɗaura ɗankwalin kayan yadda Hijab zai zauna akai sosai,bata shafa ko powder a face ɗinta ba illah
man baki da tozali kaɗai data sanya.
Ta zura hijab ɗinta bayan ta gama feshe jikinta da turarenta na GIORGIO PINK,ta nufi wajen da
take aje takalmanta ta ɗakko wani flat shoe ta zura.
Ƙaramar hand bag ɗinta ta ɗauka ta jefa wayarta a ciki sannan ta fito zuwa falon,don jiran
ƙarisowan Sani su wuce.
Iyah da Ladi ne zaune a falon suna hiran su cike da raha,TAIMIYYAH ta ƙariso cikin falon tana
me zama kusa da Iyah take cewa, "Iyah na shirya Sani kawai nake jira ya iso mu wuce,me xaki
bayar a kaiwa Zee ɗin?"
Iyah da dubi TAIMIYYAH tana jinjina kyawun da ta yi duk cewa Hijab ta saka,ta buɗe baki tana
faɗin,
"Masha Allah Zainabu kin ko fito fes kamar a sace ki a gudu,wannan kalar na kula yana miki kyau
ƙwarai,ki tashi ki shiga ɗakina zaki ga kuɗi a saman madubi, ki ɗauki dubu biyu ki kai mata kice
ta sayi lemu,idan kuma za ku tsaya da Sanin ne ku siya mata duk ba laifi."
TAIMIYYAH ta tashi tana aje bag ɗinta akan kujera tace, "Toh Iyah aiko ta gode,ina ga kawai a
bata kuɗin kin san mara lafiya da ai masa kyautan kayan dubiya gwara an kai masa kuɗin,komin
ciwan da yake sai kin ga yayi murna."
TAIMIYYAH tayi maganan cike da raha tana dafe ƙafarta ta fara takawa don zuwa ɗakko
kuɗin,tana jiyo Iyah da Babah Ladi na dariyan zancen nata.
Tana fitowa Sani na shigowa cikin falon suka gaisa da Iyah, yana sanar da TAIMIYYAH cewa
gashi ya iso.
TAIMIYYAH ta dubesa tana cewa, "Okey mu je kawai Sani ka ga rana tana yi."
Daga haka yai gaba bayan yai sallama da Iyah,itama TAIMIYYAH tayi wa Iyah sai ta dawo ta fito
riƙe da bag ɗinta,ɗaya hannunta kuma na dafe da ƙafarta.
Wayar Zee ta kira lokacin da suka shiga dai-dai kwanar da Zee ɗin tai mata kwatance.Bugu biyu
Zee ɗin ta ɗaga tana sake kwatantawa TAIMIYYAH layin da zasu shiga,basu wani sha wahala ba
suka isa ƙofar bate ɗin gidan nasu Zee.
TAIMIYYAH ta sauka ta sallami Sani ya juya ita kuma ta nufi bakin gate ɗin tana bugawa,ba a
ɗauki lokaci ba mai gadi ya buɗe mata ƙofa ta shige bayan ta sanar masa wajen Zainab ta zo.
Da fara'a Mamar su Zee ta taryi TAIMIYYAH lokacin da tai sallama a bakin ƙofar shiga falon
nasu.
TAIMIYYAH ta durƙusa har ƙasa ta kwashi gaisuwa, kafin tayi masauki akan seater ɗin da
Mamar Zee ɗin ke nuna mata.
Zee ce ta fito daga wani corridor tana faman murmushi cike da murnan ganin TAIMIYYAH take
faɗin, "Oyoyo besty ashe kun gane kwatancen haka da sauri ba ku wahala ba,welcome dear tashi
mu shiga daga ciki."
Ta ƙare maganan tana kama hannun TAIMIIYAH ta miƙar da ita tsaye,ita dai TAIMIYYAH sai
blushing take kafin ta furta, "Zee kenan ya jikin naki?"
"Naji sauƙi sosai namcy sai jiri da nake fama da shi ance jinina yayi ƙasa."
Zee tayi maganar tana yin gaba zuwa ɗakinta TAIMIYYAH na biye da bayanta har suka isa ɗakin
Zee ɗin.
TAIMIYYAH ta samu gefen gado ta zauna tana faɗin, "Kai namcy ki ce kina fama da abu me
wahala jiri bai da daɗi sam wallahi,nayi fama da matsalar wani ciwo da nayi ban ji da daɗi ba ,sai
kin ta shan ORS shi ma yana maganinsa sosai."
Zee ta marairaice fuska tana faɗin, "Ke dai bari kawai TAIMIYYAH wallahi ina jin jiki yanzu
haka ɗan tafiyan nan dana yi baki ji yadda kan ke juya min ba,shiyasa bani son jirgawa ko'ina ina
kwance a ɗaki."
Cike da zallar tausayin Zee ɗin TAIMIYYAH ke faɗin, "Ayyah! Sorry ai dama ba ki fita ba kin
bari an nuna min ɗakin ni sai na shigo da kaina,sannu Allah ya baki lafiya namcy."
Zee ta amsa da "Ameen." Dai-dai lokacin da wata ƙaramar budurwa ta shigo hannunta ɗauke da
tray ta aje gaban TAIMIYYAH.
Ta durƙusa ta gaida TAIMIYYAN cike da ladabi, daga gani ka ga ƴar aiki me hankali da tarin
nutsuwa.
TAIMIYYAH ta amsa gaisuwan da sakin fuska sannan yarinyar ta miƙe ta bar ɗakin.
Hira suka fara da Zee wacce ta jingina da jikin gadon sosai sabida jirin da ke damunta,cikin hiran
take tambayar TAIMIYYAH Nass, sabida ita sam bata san da maganar rabuwar TAIMIYYAH da
Nass ɗin ba.
TAIMIYYAH ta ɗan ɓata fuska tana fara baiwa Zee labarin zuwansu dubiyan Mum ɗinsa da
abinda ya biyo baya,har kawo kan yadda Nass suka yi da Iyah akan cewa rabuwarsu da juna shi
yafi alkhairy, tunda uwarsa ta riga ta furta ba zai auri gurguwa ba.
Zee da abin yai matuƙar bata mamaki da takaici ta buɗe baki tana cewa, "Kai amma ko wannan
Mum nasa jahila ce sai kace ba mace ba,har ta iya kallon tsaban idanunku taci fuskar ku
haka,gaskiya da dani aka je asibitinnan da taji maganganu,amma gaskiya TAIMIYYAH ban ji daɗi
ba wallahi,sabida kun dace da Nass ga shi yana son ki sosai,yanzu shikenan kun rabun da gaske
kenan ko waya ba kwa yi?"
TAIMIYYAH da taji zuciyarta ta ɗan motsa tayi saurin girgiza kai tana cewa, "Wallahi Zee ba ma
yi ni hakan ma yafi min akan mu cigaba da mu'amalar da bai da wani anfani, tunda ba bari za ai
manufa me kyau ya tabbata ba,ina ga ma yanxu ai ya samu matar aure."
"Ki bar wannan maganar namcy wa ya gaya miki har ya manta ki da har zai yi sabuwar budurwa
nan kusa? Koda yake ba abin mamaki bane idan akai la'akari da mazan wannan zamanin,amma ko
idan hakan ya tabbata xan yi mamaki sabida yadda ya mato a kanki."
Zee tayi maganan idanunta akan TAIMIYYAH wacce ke faman sakin murmushin yaƙe,kafin ta
dubi Zee ɗin cikin sanyin murya tana faɗin, "Allah da gaske nake yi Zee ya samu wata wacce ba
gurguwa ba,ai kin san dama shi aure yake son yi da gaske babu ɓata lokaci,kin ga don ya samu
wata cikin gaugawa ba abin mamaki bane."
Yadda TAIMIYYAH tayi maganan muryarta na ɗan rawa na bayyana raunin da ke cikin zuciyarta
yai bala'in taɓa zuciyar Zeee, wani irin tausayin TAIMIYYAH ya lulluɓe zuciyarta,don ita shaida
ce akan cewa TAIMIYYAH ta kamu da soyayyar Nass ɗin sosai,kuma ko a yanzu ta sani ƙarfin
hali kawai TAIMIYYAR take yi.
Ta miƙa hannu ta kamo na TAIMIYYAH tana magana cikin lallashi take cewa, "Sorry ƙawata ki yi
haƙury haka rayuwa take cike da tarin jarabawa da kuma ƙalubale,ki ɗauka cewa kawai Nass ba
alkhairy bane a gareki tunda har hakan ya faru,Allah xai kawo miki mafi alkhairy soon, ni ina ji
ajikina Allah ba zai barki haka ba zai yi miki blessing da abu mafi daraja wanda duk masu rainaki
sai sun sha mamaki.Don haka ki yi haƙury Zaynab Allah sa haka shi yafi alkhairy."
TAIMIYYAH ta sake sakin murmushi cikin ƙarfin halin ɓoye damuwa da raunin da take ciki,tayi
magana cikin dakiya tana cewa, "Hakane Zee rayuwa na cike da abubuwan mamaki da jarabawa
kala-kala,Allah ya bamu ikon cinye ko wace irin jarabawa me daɗi ko marar daɗi."
Zee ta amsa da "Ameen namcy Allah ya ƙara miki ƙarfin imani da ƙarfin zuciya."
Daga haka suka cigaba da hiran rayuwa, koda wasa TAIMIYYAH bata sanar da Zee ɗin cewa
Nass wajen Basmah ƙanwarta ya koma ba.Ta rufe wannan sirrin don tana ganin kaman tonawa kai
asiri ne da tozarta ƴar uwarta idan ta kwashe abinda Basmah tayi mata ta sanarwa Zee ɗin.
Hakan yasa har suka gama hiran samari da irin ƙalubalen da mata ke fuskanta a soyayya, sam
TAIMIYYAH ta kasa sanar da Zee ɗin abinda Basmah ta aikata mata,duk da irin yadda abin ke cin
zuciyarta amma ta danne bata gaya mata Zee ba. ( _Ƙalubale gare ku marasa sirri da ƙiris kuke
jira abu ya faru daku ku je kuna yayatawa ƙawaye,ba ko wani irin sirri bane zaka dinga sanarwa
ƙawa,musamman abinda ya shafi family issue,kun dai ga yadda TAIMIYYAH tayi ƙoƙarin rufe
aibun ƴar uwarta alhali ita ƴar uwartata cin amanarta tayi, amma bata buɗe sirrinta a waje
ba,sabida komin lalacewan jininka jininka ne dai da baka da tamkarsa sai mu kula please!_ )
Sai da TAIMIYYAH ta idar da sallar la'asar sannan tayi shirin tafiya gida.
Zee sabida jirin da take fama dashi ba za ta iya yowa TAIMIYYAH rakiya ba,sai ta haɗata da
Rahane me aiki don tayi mata rakiya zuwa bakin hanya, inda za ta samu Napep cikin sauri,sai
godia take wa TAIMIYYAH akan kuɗin da Iyah ta bayar abata,wanda TAIMIYYAH ta haɗa da
kuɗinta dubu uku ya zama dubu biyar ta baiwa Zee ɗin tace ta sayi lemu.
Mamar su Zee ta bai wa TAIMIYYAH wasu fashion masu kyau,TAIMIYYAH ta amsa tayi godia
sannan suka fito da Rahane da za tai mata rakiya.
Sai da suka fito waje sannan TAIMIYYAH ta kula da hadarin da ke haɗuwa a garin,nan da nan sai
hankalinta ya tashi don bata son dukan ruwa sam!
A hankali suke takowa daga cikin layin gidan su Zee ɗin har suka iso ainihin kan titi inda zata iya
samun abin hawa. Zuwa lokacin hadari ne sosai ke sake haɗuwa a garin,TAIMIYYAH sai ta
sallami Rahane tace ta koma gida kawai bayan ta buɗe jaka ta bata ɗari biyu, Rahane ta amsa tayi
godia tana juyawa don komawa gida.
Ita kuma TAIMIYYAH sai ta ɗan gangara zuwa wajen wani dutse,ta jingina da shi tana sauke
numfashin gajiyar da tayi sabida da ɗan nisa daga gidan su Zee ɗin zuwa bakin titin.
Ta jima a tsaye ƙafarta ɗofane a jikin dutsen don jin daɗin tsayuwa amma bata samu abun hawa
ba.
Duk Napep ɗin da zai zo a cike zata gansa da mutane a ciki, ga kuma hadari da ke sake haɗuwa
sosai har garin ya fara cida, alamun ruwa na gab da sauka,hakan yasa hankalin TAIMIYYAH ya
kai ƙololuwa wajen tashi.
Wani Napep ne ta tsaida daga can tsallaken titi ta yadda dole sai ta tsallaka titin za ta shiga,gashi
motoci da mashina sun ƙi tsagaitawa bare ta tsallaka ta daɗi,zuwa lokacin har yayyafi ya fara
sauka hakan yasa me Napep ɗin fitowa don ya tsallako ya tsallaka da ita, dai-dai lokacin ne kuka
ruwan ya sauka me ƙarfin gaske.
Ita kuma TAIMIYYAH da sam hankalinta bai kai kan me Napep da ke ƙoƙarin tsallakowa wajenta
ba,ganin kamar mota da mashin ɗin dake tahowa a nesa suke,sai kawai ta nufi titin gadan-gadan
tana dafe da ƙafarta don tsallakawa,sai da ta shiga tsakiyan titin ta kula da me mashin ɗin daya
taho a guje,sai tayi baya don komawa ɗaya ɓarayin ba ta san mota ta taho ba, kawai ji tayi an
wantsakali da ita can gefen titin kanta ya bugu da dakalin kwalbatin bakin hanya.
Lokaci guda ita da me Napep ɗin da ya taho don taimakonta suka saki ihu,me motar da ya kaɗe ta
yayi saurin gangarewa gefen hanya ya faka motar suka nufo inda TAIMIYYAH take a yashe shi da
matar da ke cikin motar.
TAIMIYYAY da ke yashe a gefen kwalbatin sai zubar da jini take, da alamu wani waje a fuskarta
ko gefen wuyarta ne ya tsage ko ya fashe shiyasa jini ke zuba sosai.
Gabaki ɗaya kanta yayi wani irin nauyi gingirin,sabida ba ƙaramin bugawa tayi ba tama kasa
kuka,sai idanunta da ta lumshe tana jin wani azaba na ratsa hannunta da ta durƙushe akansa.Sama-
sama take jin maganganun wanda ya kaɗetan da muryar wata mata da ke faman salati tana cewa,
"Shehu maza ku ɗauke ta zuwa mota wannan jinin da take zubarwa yayi yawa."
Babu ɓata lokaci Shehun ya kwashi TAIMIYYAH zuwa mota,wacce jikinta ke faman rawan ɗari
sabida ruwa ake sheƙawa har lokacin.Dama ga shi ita ba mai son ruwa ya taɓa lafiyar jikinta bace,
shiyasa kafin kace kwabo haƙoranta har sun fara karo da juna,ga jinin da yaƙi tsayawa wanda ke
zubowa daga gefen wuyarta da ya tsage sosai.
Hajiya Aysha da ke riƙe da ita a jikinta salati kawai take yi tana ƙarawa, cikin tsantsar tashin
hankalin wannan tsautsayi daya gitta musu.Shehu ne ya miƙo jakar TAIMIYYAH daya ɗakko
daga bakin kwalbatin ya aje kusa da Hajiyan,ya zagaya ya koma mazaunin driver ya tashi motar
yana tambayar Hajiyar wani asibiti za su nufa? Hajiya Aysha dake riƙe da TAIMIYYAH wacce
Hajiyar ta sanya ɗankwalin kan TAIMIYYAH ta ɗaure wajen da jinin ke zubowa tayi saurin cewa
Shehu, "Muje ABU tudun wada kawai Shehu don gara a kaita asibitin da za a duba ta da kyau."
Tana maganan ne cike da tashin hankali musamman yadda taji jikin TAIMIYYAN ya fara ɗaukan
zafi.Har lokacin jikinta rawar sanyi take yi, haƙoranta na faman dukan juna,suna isa asibitin Shehu
yai farking motar lokacin ruwan ya ɗan tsagaita babu laifi.
Cikin ƙanƙanin lokaci aka zo aka ɗauki TAIMIYYAH don ta kasa tafiya sabida yadda jikinta ke
faman rawa,sai a lokacin kuma Hajiya Aysha ta kula da cewa tana lalurar ƙafa ma.Hakan yasa
tausayin halin da yarinyar ke ciki ya ninku a zuciyarta,bata samu nutsuwa ba sai da aka baiwa
TAIMIYYAH gado tare da bata kulawar gaggawa don tsaida jinin dake zuba har lokacin........✍🏻
#Ɗansabo ce#
[12/14, 3:43 PM] +234 703 040 9541: Littafin TAIMIYYAH paid book ne,ga duk wanda ta
tsincesa a kowani irin group ne,kiji tsoran Allah karki karanta sai kin biya 500 naira only.
Za ku iya min magana ta wannan number ɗin 08167768704, ko kuma ku turo kuɗin ku kai tsaye ta
wannan account ɗin 0504192664 aisha ibrahim dansabo GTbank.*
Masu turo credit za ku turo katin MTN na 500 ta wannan line ɗin 08167768704.
_Ina ƴan kasuwa masu buƙatar a tallata muku hajar ku? Maza ku garzayo da kuɗi ƙalilan a tallata
muku kayan siyarwanku sai dai kawai ku ji ana kiran waya don buƙatan sayan kayan ku,ku
tuntuɓeni ta layina kamar haka 08167768704._
*48*
Lokacin da Likitan ya kammala baiwa TAIMIYYAH duk wata kulawa da ta dace,sai ya yi mata
ɗinki a wajen daya tsage daga gefen wuyarta na hagu inda jinin ke zuba,sannan ya yi mata allura
tare da ɗaura mata drip.
Yana juya ya yiwa Hajiya Aysha bayani akan dole admiting ɗin patient ɗinta za a yi ta samu
kaman kwana ɗaya da yini, sabida buguwan da tayi a hannunta na dama,da kuma ciwan kai da
take kuka da shi.
Hajiya Aysha sai ta gyaɗa masa kai cike da gamsuwa tana faɗin, "Okey! Babu damuwa." Tayi
maganar lokacin da take ƙarisawa bakin gadon da TAIMIYYAH ke kwance, idanunta a lumshe
amma hawayene ke zubowa daga idanunta yaba sauka a kan kyakykyawar face ɗinta.
Sai lokacin ne ta samu daman kuka dukkanin inda ta bugu na mata tsananin ciwo,ga kanta da take
ji tamkar xai rabe gida biyu ne.
Muryar Hajiya Aysha da ta jiyo daf da ita yasa ta buɗe idanunta da sukai mata nauyi, ta sauke akan
kyakykyawar face ɗin matar da bata san ko wacece ita ba, Hajiyan ta dubi TAIMIYYAH da ta
zuba mata ido tace, "Sannu Zainab." Don taji lokacin da TAIMIYYAH ke sanar da likita sunanta.
TAIMIYYAH ta maida idanunta ta lumshe bayan ta amsa sannun can ƙasan maƙoshinta, ta sake
buɗe baki a hankali tana cewa, "Don Allah a ɗauki wayata a kira min Iyah."
Hajiya Aysha ta jinjina kai tana cewa, "Nima tunani na kenan,sannu Allah ya baki lafiya kiyi
haƙury komi ya farune bisa tsautsayi da ƙaddara ,don tuƙin ganganci ba halayyar Shehu bane da
alamu ke ce kika shiga titin cikin ruɗu ba yadda ya dace ba,Allah ma ya auna arziƙi da ba wani
mummunar rauni kika ji ba, buguwace kawai inji likitar sai ɗinkin da akai miki a inda kika sami
rauni."
Ita dai TAIMIYYAH jin Hajiyar kawai take yi sama-sama don bacci ya fara rinjayar idanunta,
sabida alluran da akai mata.Hajiya Aysha ta nufi in ta aje jakan TAIMIYYAH kusa da nata,ta buɗe
tana ciro wayarta tai swiping sai ta ga babu lock,hakan yasa ta sauke ajiyar zuciyar tana shiga
contact kai tsaye don lalubo sunan Iyah data ji TAIMIYYAH ta ambata.
Cikin sauƙi ta gano sunan ta kuma dannawa layin kira, kasancewarta wayayya da ta saba anfani da
manyan waya na zamani.
Bugu biyu muryar Iyah ya shiga kunnuwarta lokacin da take faɗin, "Salamu alaikum! Zainab kina
ina ne har kika bari yamma tayi miki a waje?"
Hajiya Aysha tayi saurin cewa, "Barka da yamma Hajiya ba mai wayar bace,wallahi ta haɗu da
tsautsayine gamu nan a asibitin ABU da ke Tudun Wada Zaria."
Tana jiyo yadda Iyah ta rafka salati kafin ta furta, "Subhanallahi! Amma dai da sauƙi ko baiwar
Allah?"
Hajiya Aysha tayi ma Iyah bayani yadda hankalinta zai kwanta,kafin suyi sallama Iyan na sanar da
ita gata nan bisa hanya yanzu Insha Allah.Sai Hajiya Aysha ta sauke wayar daga kunni tana maida
shi cikin jakar TAIMIYYAH ta koma bakin gadon tayi tsaye, tana ƙarewa kyakykyawar face ɗin
TAIMIYYAH wacce barci yai nasaran ɗaukarta kallo.
Hajia Aysha ta dinga yaba kyawun yarinyar cikin zuciyarta, tare da jin tausayinta me tsanani
lokacin da idanunta ya sauka akan ƙafafun TAIMIYYAH,wanda ɗaya ya sirance sai lafiyayyen
dake da ƙibarsa.
Ta sauke numfashi tana kai hannu ta gyara mata rigar jikinta da kyau ya rufe ƙafafun sosai, ta isa
ta zauna a kujeran da ke ɗakin tana sauke zazzafar numfashi.
Shehu driver ne ya shigo yana tambayar jikin TAIMIYYAH Hajiyar ta bashi tabbacin da sauƙi
sosai,tunda buguwace kawai sai ɗinki da akayi a wajen daya tsage.
Shehu ya yi fatan samun sauƙi ga yarinyar yana komawa waje ya zauna cikin mota, kamar yadda
Hajiyar ta bashi umurni tare da sanar da shi zasu jira Mamar TAIMIYYAH ta zo kafin su bar
asibitin.
Mintuna talatin da biyar sai ga Iyah sun iso asibitin tare da Sani da ya kawo su ita da Babah Ladi.
Iyah ta ɗaga waya ta kira layin TAIMIYYAH sai Hajiya Aysha ta ɗauka, tana sanar da Iyah gata
nan fitowa ta taho da su,ta kashe wayar tana fitowa kai tsaye zuwa waje, cikin sa'a sai ta hango
Iyah da Babah Ladi daga can nesa su na faman dube-dube.Ta isa wajensu suka sake gaisawa da
jajanta abinda ya faru,kafin su ƙarisa zuwa ɗakin da aka kwantar da TAIMIYYAN.
Iyah da Babah Ladi suka isa bakin gadon suna kallon TAIMIYYAH dake kwance,hannunta ɗaure
da drip sai bacci take yi sadidan.Iyah ta sauke numfashi tana kai hannu ta taɓa goshin
TAIMIYYAH tana cewa, "Sannu Allah ya baki lafiya Zainab." Ta cigaba da cewa "Nifa na ji
shirun yayi yawa wallahi,sai na ɗauka cewa ruwan da aka yi yasa ta tsayawa bata koma gidan
ba,tunani ma sai ya tafi akan cewa watakila daga gidan ƙawartata ce za a maidota a mota ashe
tsautsayi ne ya gitta,Allah ma ya auna arziƙi babu karaya ko mugun buguwa dama gata da lalurar
ƙafa dana shiga uku ni Iyah"
Iyah ta ƙare maganan cike da damuwa me tarin yawa,Hajiya Aysha ta sauke numfashi tana cewa,
"Wallahi nima inda na godewa Allah kenan da babu wani mugun rauni data ji me ɗaga hankali,sai
a godewa Allah buguwa ce kaɗan da tayi a hannu sai kanta da take kukan yana mata ciwo,shima
kuma likitan ya bada tabbacin tana samun bacci me tsawo zuwa lokacin da za ta farka za ta samu
sauƙi,sai kuma inda akai mata ɗinki da ta zubar da jini sosai amma ɗinkin ma bamai yawa bane
bari ki gani."
Hajiyar ta ƙarisa da Iyah wajen gadon tana nuna mata inda akai ɗinkin daga gefen wuyar
TAIMIYYAR an rufe da plasta.Iyah ta jinjina kai tana cewa, "To Allah ya bada lafiya ku kuma
Ubangiji ya saka muku da alkhairy da kuka kawota asibiti baku gudu kun bar marainiyar Allah a
titi ba."
Hajiya Aysha tayi saurin duban Iyah tana cewa, "Haba Hajiya wallahi babu komi hakkine akan mu
ai kawo ta asibitin, tunda mune muka kaɗe ta,maganan guduwa kuma ai wannan sai mutanen da
basu san darajan ɗan adam ba,amma taya zaka yi sanadiyyan kaɗe mutum kace kuma ka gudu ka
barsa babu tsoran Allah,Allah ya yi mana tsari daga aikata hakan."
Iyah da Babah Ladi suka haɗe baki wajen amsawa da, "Ameen." Iyah na ɗaurawa da faɗin, "Duk
da haka dai mun gode Hajiya Allah saka miki da mafificin alkhairy."
Hajiya Aysha ta murmusa tana jin zuciyarta na sake kwanciya da waɗannan mutane,kafin ta furta
cewa, "Babu komi fa ki bar godia mu ne ya kamata muyi ta bada haƙury Allah ya tsare gaba,sai
dai ai mata faɗa ta ringa kula sosai lokacin da za ta shiga titi." Ta cigaba da sanar da su Iyah yadda
tsautsayin ya faru.
Iyah ta jinjina kai tana cewa, " Ai matsalar TAIMIYYAH shine ruɗewa da zaran ta ga hadari in
dai tana waje ne to shikenan hankalinta zai tashi,sabida bata son dukan ruwan sama ko kaɗan tun
tana ƙarama, yana sanya mata zazzaɓi da mura me zafi,shiyasa ina ga duk ta kiɗime har wannan
tsautsayin ya faru,kuma dai Allah ma ya aiko da hakan ne amma da tunda ta ga hadarin tayi
zamanta gidan ƙawar idan ruwan ya ɗauke ko Sani sai ya je ya ɗakkota."
Iyah ta kai ƙarshen maganar idanunta na kaiwa kan gadon da TAIMIYYAH ke kwance bata ma
san me suke ciki ba.
Hajiya Aysha ta jinjina kai tana cewa, "Ai kinsan ance ƙaddara ya rigayi fata,Allah ya riga ya
rubuto hakan sai dai fatan Allah ya kiyaye gaba,ina ga ni zamu zo mu wuce zuwa goben da safe
Insha Allah zan zo na sake duba jikin nata,nasa Shehu ya biya kuɗin komi babu abinda za a nema
Insha Allah,idan ta tashi a sake mata sannu Hajiya."
Hajiya Aysha tayi maganar tana miƙewa tsaye tareda ɗaukan jakanta dake kan kujera,hakan yasa
Iyah ita ma tashi tana sake mata godia sosai.
Iyah ta raka Hajiya Aysha har waje sannan sukai sallama da juna, Iyah ta dawo ciki tana jinjina
kirki da karamcin matar har cikin zuciyarta.
"Ladi gaskiya matar nan akwaita da kirki na yaba ƙwarai da karamcinta,Allah yasa da alkhairy ya
tsare gaba."
Iyah ke wannan maganar lokacin da ta sake isa bakin gadon da TAIMIYYAH ke kwance,Ladi ta
furta, "Gaskiya Hajiya nima na ga karamcinta,da wasu ne guduwa zasu yi abinsu musamman da
suka ga ruwama ake yi sanda tsautsayin ya faru."
Iyah ta kai hannu tana taɓa jikin TAIMIYYAH don taji ko da zazzaɓi tana cewa, "Hmm! Ke dai
bari kawai Allah ne ya duba yadda TAIMIYYAN take ya taimaketa suka dubeta da idon rahama
har suka kawota asibiti me inganci kuma."
Daga haka suka cigaba da tattauna abinda ya farun.Sai daf da kiran magriba sannan Iyah tace
Babah Ladi ta zauna ita Sani zai maida ita gida ta ɗakko musu abubuwan buƙata ta dawo,sai ita
Babah Ladin ta koma Iyah ta kwana da TAIMIYYAH.
Bayan Iyah ta koma gida ne ta ɗaga waya ta sanar da Baba Sani da ke gari tsautsayin da ya faru da
TAIMIYYAH,tare da sanar da shi cewa yanzu haka TAIMIYYAN na can asibiti sai zuwa gobe za
a sallameta.
Baba Sani ya jinjina lamarin yana faman faɗan cewa a daina barin TAIMIYYAH kwata-kwata tana
fita ita ɗaya a motar haya.Sai dai idan za ta dinga ɗaukan drop duk inda za ta adinga kaita ana
komawa a ɗakko ta idan shi Sani na da uzuri lokacin,Iyah dai dake sauraransa har ya gama
maganar sai cewa tayi, "Kai dai kawai mu doge Allah da abin yazo da sauƙi,amma duk yadda
muka kai da kiyayeta bamu kai Ubangijin da ya halicceta ya kuma jarabeta da lalurar ba,ni a
kullum bana so ta dinga ji a ranta tana da wani nakasan da zai hanata kai kawo yadda kowa ke
yi,tunda dai ba a nannaɗe take ba Allah yasa tana takawa da ƙafafunta da taimakon dafa guiwar da
take yi,idan muna nuna mata cewa komi sai an mata zata dinga jin babu daɗi cikin zuciyarta tunda
ita me ƙoƙarice da son yin komi da kanta a hakan."
Baba Sani da ke sauraren Iyah daga ɓangarensa sai ya jinjina kai cike da gamsuwa da bayanan
Iyan yake cewa, "Hakane kuma Iyah to Allah ya kyauta gaba,bani gida na fita amma da zaran na
dawo zuwa bayan sallar Isha zan ɗauki Zuwairah mu taho asibitin."
Daga haka sukai sallama da Iyah bayan ta sanar masa gata ma a gida tazo ɗaukar musu
kaya,Babah Ladi ta bari da TAIMIYYAH kafin ta koma asibitin ita.
Cikin sauri-sauri Iyah ta kammala haɗa musu duk abinda za su buƙata waje ɗaya,ta nufi kitchen ta
dafa ruwan zafi cikin ƙaton flask ɗinta,sannan ta zuzzuba abinci cikin kuloli ta dama kunun gyaɗa
ta haɗa da kayan shayi, duk ta zuba cikin ƙaton kwandon ɗaukar abinci.
Sai bayan sun yi sallar magariba daga ita har Sani sannan Sanin ya shigo ya kawashi kayan zuwa
mota,Iyah ta fito ta kullo sasan ta nufi sasan Ummi ta sanar mata abinda ke faruwa.Ummie tayi ma
Iyah Allah ya sauƙe ita da Inna Larai,kafin Inna Larai ɗin ta tashi tana sanar da Iyah cewa bari ta
ɗauko mayafi su koma tare ta dubo jikin TAIMIYYAN,sai su dawo tare da Babah Ladi tunda Iyah
ta dage ita zata kwana da TAIMIYYAN.
Lokacin da su Iyah suka isa asibitin har lokacin TAIMIYYAH bata farka ba,a haka Inna Larai ta
isa bakin gadon ta dubata tare da yi mata fatan samun sauƙi.
Sun ɗan taɓa zama kaɗan kafin su yiwa Iyah sallama ita da Babah Ladi suna ma TAIMIYYAH
fatan samun sauƙi cikin gaggawa,Iyah ta raka su har wajen barandar fita ɗakin sannan ta juyo
zuwa ciki.
Ƙarfe takwas da rabi su Baba Sani suka shigo asibitin,Iyah ce ta fita ta zo dasu zuwa ɗakin da aka
kwantar da TAIMIYYAH.Har kuma lokacin TAIMIYYAH bata farka ba likitan kuma yace kar a
tasheta, abarta ta samu isasshen hutu ta yadda idan ta tashi ciwan kan da take kuka da shi zai tafi.
Umma da Baba Sani suka isa bakin gadon suna duba TAIMIYYAH tare da yi mata fatan samun
sauƙi,Umma sai wani yatsina take yi tana kallon Iyah a fakaice tana taɓe baki.
Duk kuma abinda take yi Iyah na kula da ita sarai, tare da jinjina halayyar Umman da sam ba
masu kyau bane.
Iyah sai ta maida kai wajen baiwa Baba Sani labarin duk yadda abin ya faru,da karamcin Hajiya
Aysha na yadda suka kawo TAIMIYYAH asibiti.
Baba Sani ya ji daɗin shi ma yadda su Hajiya Ayshan suka nuna kulawa, basu gudu a lokacin da
abin ya faru sun bar musu marainiyar Allah a titi ba.
Sun ɗan taɓa zama kaɗan kafin su tashi tafiya Iyah ta rakasu bakin ƙofa sukai sallama,ta juyo ta
dawo cikin ɗakin tana ɗauke ledojin fruit da gasashshen naman kaza da Baba Sanin ya kawo.
TAIMIYYAH sai wajen tara da rabi na dare ta farka,tana buɗe idanunta ta sauke akan Iyah dake
zaune saman dadduma da ta shinfiɗa.Ta yinƙura tana son tashi bakinta na furta wash...!!! Hakan ya
jawo hankalin Iyah tayi saurin tashi tana nufowa wajen TAIMIYYAH tana faɗin, "Sannu
TAIMIYYAH kin tashi,ina ke miki ciwo yanzu ?"
TAIMIYYAH ta ɗan ɓata fuska cikin sanyin murya take cewa, "Kaina ne Iyah amma yayi sauƙi
yanzu hannuna ne ya yi min nauyi."
Iyah ta taimaka mata ta tashi zaune tana jin yadda hannunta ke mata ciwo sosai,Iyah ce ta fita
kiran likita ba a jima ba suka shigo tare da likitan ya cire drip ɗin,yana tambayar TAIMIYYAH
inda ke mata ciwo ta sanar da shi.
Sai ya juya ya fice daga ɗakin ba a jima ba ya dawo yana sake gwada BP ɗin TAIMIYYAH,ganin
komi normal yasa shi juyawa yana ma Iyah bayani akan yadda zata bata magungunan da ke aje
daga gefen drawern kusa da gadon da TAIMIYYAH ke kai.
Bayan likitan ya fita ne Iyah ta nufi toilet ta haɗawa TAIMIYYAH ruwan zafi sosai,sannan ta
dawo tana riƙe da hannunta zuwa bakin toilet ɗin, sannan ta barta ta shige don ta yo wanka ta gasa
jikinta.
Sosai TAIMIYYAH ta gasa jikinta da ruwan zafin tayi wanka tare da ɗauro alwala ta fito,tana jin
daɗin jikinta sosai don duk inda ke mata ciwo ya saki,hatta da hannunta da ada yai nauyi yanzu da
ta gasa shi da ruwan zafi taji daɗinsa.
Ta tadda har Iyah ta fito mata da kayan baccin da ta ɗakko mata daga gida,riga da wando ne masu
kauri sosai sabida ruwan da aka yi yasa garin yayi sanyi sosai.
Sallah TAIMIYYAH ta fara gabatarwa bayan ta sanya kayan baccin,lokacin da ta idar har Iyah ta
zuba mata abinci a plate tare da kunun gyaɗan da ta dama don ta san TAIMIYYAH naso.
Da ƙyar da rarrashi sannan TAIMIYYAH taci abincin kaɗan,amma ta sha kunun gyaɗan da ɗan
yawa kafin Iyah ta buɗe mata naman kazan da Baba Sani ya kawo musu.
Da yake TAIMIYYAH akwai son naman kaza taci ba laifi sannan Iyah ta kawo mata
magungunanta ta sha.
Kiran wayar TAIMIYYAH da aka yi yasa Iyah ɗakko wayar ta kai mata,ganin sunan Yah Deeku
yasa TAIMIYYAH ɗauka ta kai kunni.
Cike da shagwaɓa take gaida Yah Deekun, ya yi mata sannu da jiki yana faman faɗa akan meyasa
take fita ita kaɗai ba za ta kira Sani ya kaita ba? Ita dai TAIMIYYAH shiru tayi masa bata ce komi
ba har ya gama faɗansa ya koma kuma yana tambayarta yadda take jin jikinta.
TAIMIYYAH cike da shagwaɓa take sanar da shi cewa taji sauƙi,sukai sallama yana sake mata
fatan samun lafiya sabida yana KD wannan week ɗin bai samu shigowa weekend ba.
Suna gama wayar TAIMIYYAH ta kashe wayarta baki ɗaya ta aje kusa da ita,tana zamewa daga
zaune ta kwanta tare da lumshe idanunta.
Sama-sam TAIMIYYAH ke sauraren Iyah dake ta bata labarin kirkin Hajiyar da suka kaɗe ta,tare
da sanar ita cewa Hajiyar tace zata dawo gobe ta sake duba jikinta.
TAIMIYYAH jin Iyah kawai take yi amma sam bata yi magana ba,sai ma wani baccin da taji yana
fisgar idanunta ba a jima ba kuwa ta ɓingire ta bar Iyah na ta surutunta ita kaɗai.........✍🏻
#Ɗansabo ce#
[12/14, 3:43 PM] +234 703 040 9541: *Littafin TAIMIYYAH paid book ne,ga duk wanda ta
tsincesa a kowani irin group ne,kiji tsoran Allah karki karanta sai kin biya 500 naira only.*
*Za ku iya min magana ta wannan number ɗin 08167768704, ko kuma ku turo kuɗin ku kai tsaye
ta wannan account ɗin*👇🏻
0504192664 aisha ibrahim dansabo GTbank.
Masu turo credit za ku turo katin MTN na 500 ta wannan line ɗin 08167768704.
_*Ina ƴan kasuwa masu buƙatar a tallata muku hajar ku? Maza ku garzayo da kuɗi ƙalilan a
tallata muku kayan siyarwanku sai dai kawai ku ji ana kiran waya don buƙatan sayan kayan ku,ku
tuntuɓeni ta layina kamar haka 08167768704.*_
*49*
Washegari ƙarfe takwas da rabi na safe Baba Sani ya taso su Zuhura da Basmah ɗauke da kayan
breakfast suka iso asibitin.Sun kuma tadda TAIMIYYAH ta taahi daga bacci,kuma ikon Allah
garas ta tashi babu inda tace yana mata ciwo. Zuhurah suka gaida Iyah tare da tambayarta me jiki
ta basu amsa da cewa, "Alhamdullillah! Ta samu sauƙi zuwa anjima kaɗan ma sai gida Insha
Allah."
Baba Sani da ya isa gaban gadon da TAIMIYYAH ke kwance idanunta a buɗe tana jin duk abinda
ake faɗi,isowan Baba Sani wajenta yana mata sannu yasa ta yinƙurawa ta tashi zaune,Baba Sani
ya kama hannunta ɗaya yana ɗagota sosai ta zauna yana tambayarta ya jikin nata? Ta ɗaga manyan
idanunta ta dubesa da ɗan guntun murmushi saman face ɗinta take gaida shi tare da bashi tabbacin
ta samu sauƙi, ya shafa kanta yana faɗin, "Masha Allah Zaynab Allah tsare sai a dinga kulawa da
kyau kinji ko?"
TAIMIYYAH ta gyaɗa kai a hankali tana faɗin, "Insha Allah Baba." Ƙarisowan su Zuhura suna
mata sannu yasa ta dubansu tana amsawa,idanunta akan Basmah wacce rabon da TAIMIYYAH ta
sanya ta a ido tun randa suka haɗu ta ganta tare da Nass.
TAIMIYYAH tayi saurin ɗauke kai daga duban face ɗin Basmah tana jin can ƙasan zuciyarta wani
abu na motsawa.
Iyah ce tace wa TAIMIYYAH ta tashi ta je tayo brush don ta samu ta karya ta sha
magunguna.Babu musu TAIMIYYAN ta sakko daga kan gadon ta nufi toilet,tana jiyo su Baba
Sani na ma Iyah sallama zasu wuce,Iyah ta raka su bakin ƙofa tana sanar da Zuhurah cewa da sun
isa gidan, ta shiga Sasanta ta sanar da Babah Ladi kar tayi wahalan yin abin karyawa tunda ga shi
sun kawo.
TAIMIYYAH bata wani jima sosai ba cikin toilet ɗin ta fito,idanunta akan Iyah da ke zuba abinda
zata ci cikin plate.Ta ƙariso bakin gadon tana gaida Iyah,Iyah ta amsa tana cewa, "Sannu ya jikin
naki kan dai ya daina ciwon ko?"
TAIMIYYAH ta gyaɗa kai tana cewa, "Eh babu inda ke min ciwo sai wajen da akai ɗinki a gefen
wuyarnan ne kawai ke ɗan damuna."
Iyah ta dubeta da kulawa tana cewa, "Ayyah! shi ma ɗin zai bari kin san abu a maƙarfafa dole kiji
ya dameki,da zaran zaren ɗinkin ya fita shikenan zaki samu sauƙi, sannu bari in zuba miki abincin
ki ci, zaki sha tea ɗin ne in haɗa miki babu madara ko kunun zaki sha gashi nan sun haɗo da
kunu?"
TAIMIYYAH ta ɗan ɓata face kaɗan cike da ƴar shagwaɓa take cewa, "A'a Iyah ni ba zan sha
kununsu ba haɗa min tea ɗin kawai,amma zallah milo zaki samin ko sugar kar kisa inba haka ba
zan ji ina jin amai ne da xaran na sha."
Iyah ta jinjina kai tana yin duk yadda TAIMIYYAH ta buƙata.Bayan duk ta kammala zuba mata
soyayyen dankali da egg ɗin ne, ta haɗa mata tea ɗin tana ɗaukan plate da kofin tea ɗin ta kai mata
kan gadon ta aje.
TAIMIYYAH ta fara cin abincin a hankali tana ji gaba ɗaya bakinta babu ɗanɗano sabida muran
da ke son kamata.Dama ta san tunda ruwa ya doke ta sai tayi wannan muran, zazzaɓin ma don ta
amsa allura da magungunan da take sha ne da yanzu ta san tana kwance sosai.
Suna tsaka da karyawa daga ita har Iyah dake zaune daga ƙasa saman babbar dadduma, suka jiyo
sallama daga bakin ƙofan shigowa ɗakin.
Iyah ce ta amsa tana bada izinin shigowa don taso ta gane muryan kamar na Hajiyar jiya ce wacce
suka kaɗe TAIMIYYAH.
Hajiya Aysha da Dattijiyar me aikinta Babah Rabi suka turo ƙofar suka shigo bayan Iyah ta amsa
sallamr tasu da basu izinin shigowa,Babah Rabi hannunta riƙe da ƙaton kwandon ɗaukan abinci.
Cikin fara'a Iyah ke musu barka da zuwa tana me nunawa Hajiya kujera ta zauna,ita kuma Babah
Rabi ta samu saman daddumar da Iyah ke kai ta zauna.
Hajiya Aysha memakon ta zauna sai ta nufi bakin gado kai tsaye wajen TAIMIYYAH,wacce tun
shigowansu ta tsaida cin abincin da take yi.
"Sannu Zainab ya jikin naki,ina fata dai babu wata matsala ko?"
Hajiya Aysha tayi tambayar idanunta akan TAIMIYYAH data ɗan sadda kanta ƙasa,kafin ta ɗago
manyan idanunta ta sauke akan fuskar Hajiya Aysha da ke jifanta da murmushi.
TAIMIYYAH tayi ƙasa da muryarta tana gaida Hajiya Aysha tare da bata tabbacin taji sauƙi babu
wani matsala.
Hajiya Aysha ta jinjina kai tana cewa, "Masha Allah,Allah ya ƙara lafiya ya tsare gaba
kyakykyawar ɗiyata."
Yadda tayi maganan cike da kulawa yasa TAIMIYYAH dubanta da murmushi tana amsawa da
cewa, "Ameen Hajiya na gode."
Daga haka Hajiya Aysha ta koma wajen Iyah suna sake gaisawa, ita kuma Babah Rabi ta isa wajen
TAIMIYYAH tana mata sannu.Iyah ta dubi uban kayan da suka kawo tana cewa, "Haba Hajiya ya
da wannan ɗawainiya haka mu da za a sallama nan bada jimawa ba,wallahi da baku yi wahalan
kawo komi ba, an gode ƙwarai Allah ya fi mu yabawa ya saka da alkhairy sannu da ƙoƙari."
Hajiya Aysha ta jinjina kai tana duban Iyah da murmushi take cewa, "Haba Hajiya babu komi ai
abinda duk ya dace ne ayi ake yin,Allah dai ya ƙara mata lafia ai na ga jikin nata Alhamdulillah."
Iyah da fara'a take baiwa Hajiyar tabbacin jiki fa Alhamdulillah! Kafin ta miƙe ɗauke da flask ɗin
ruwan xafi ta nufi toilet don haɗawa TAIMIYYAH ruwan wanka.
"TAIMIYYAH ta shi ki je ki watsa ruwan ɗumi a jikinki ko kya sake jin daɗin jikin,kafin mu
koma gida kiyi wankan me sosai."
Iyah ce tayi maganar lokacin da ta fito daga banɗakin idanunta akan TAIMIYYAH, wacce zuwa
lokacin ta zame ta kwanta lamo kamar ta koma bacci.
Jin maganar da Iyah tayi yasa ta tashi tana ɗan zumbure baki alamun bata son yin wankan,uwa uba
su Hajiya da ke zaune a ɗakin wanda haka kawai take jin nauyin matar.Amma babu yadda ta iya
haka ta sakko daga kan gadon idanunta a ƙasa,sam bata yadda ta dubi inda suke zaune ba amma
tana jin idanunsu ya yawo akanta.
A hankali ta kai hannu ta dafa guiwar ƙafarta tana tafiya zuwa hanyar banɗakin ta shige,Hajiya
Aysha da me aikinta Babah Rabi suka bi TAIMIYYAH da kallo Hajiya Aysha na jin wani abu na
ratsa zuciyarta akan Yarinyar.
Ta maida dubanta kan Iyah lokacin da TAIMIYYAH ta ɓacewa ganinta tana cewa, "Hajiya
wannan Auta taki ba dai kyau ba,gata komi nata cikin sanyi da nutsuwa take yinsa,amma wannan
laluran ƙafar a haka kika haifeta da shi ne?"
Iyah ta saki murmushi me faɗi tana duban Hajiya Aysha take faɗin, "Ko ɗaya Hajiya wallahi bada
shi aka haifeta ba daga baya ne Ubangiji ya aiko da lalurar,ta fara tafiyarta tana yawo ko'ina sai
zazzaɓi dare ɗaya, washegari daga yin allura ƙafa ya saki shikenan mafarin sanadin ƙaddaran
shanyewan ƙafar da akai ma allurar,mun sha fama sosai kafin ma asamu ta fara takawa da
taimakon dafa guiwar ƙafar...."
Iyah ta cigaba da bayyanawa Hajiya Aysha yadda suka ci wuya akan laluran ƙafar
TAIMIYYAH,kafin a samu ta fara takawa da ƙafar a haka yadda take tafiya.Ta cigaba da faɗin,
"Amma kin ga cikin ikon Allah da taimakon dafa guiwar nan da take tana takawa babu abinda bata
iya yiwa kanta,tana harkokinta komi babu abinda ke gagararta sai kaɗan daga manyan abubuwan
da dole sai an taimaka mata,amma tana da ƙoƙarin ayyuka da son yin komi da kanta bata ma so
ace za a yi mata abu inba gagararta yayi ba."
Hajiya Aysha ta jinjina kai tana cewa, "Allah sarki haka Ubangiji ke ikonsa nata ma da sauƙi ai
tunda tana yawonta ko'ina da ƙafar a haka,wasu a keken guragu ake turasu,wasu basa ma jirgawa
ko'ina sai da taimakon jan gindi,sai a godewa Allah bakomi nakasa so da yawa wani baiwar
ne,mutane ne kawai ke nasu shirmen ki ga ana nuna musu bambamci da kyaran su a wasu
lokutan,ita dai Zainab gashi an mata baiwar kyau da nutsuwa ,lokaci ɗaya na ji ta shiga zuciyata
Hajiya,ina fata dai tayi karatu ba a tauyeta ba an ƙi sakata a makaranta?"
Hajiya Aysha tayi magana idanunta akan Iyah da ke faman murmushi,kafin ta fara faɗin, "Aiko dai
Hajiya tayi karatunta sosai don ma wannan yajin aikin da malaman makarantun jami'a suka tafi ne
yasa bata cigaba daga NCE da ta kammala ba,amma yanzu haka ma wani makarantar Computer
take zuwa,a islamiya ma tayi sauka ta sauke har da manyan littafai,sai makarantar haddah da ake
daf da yayesu sun kusa kammala haddar Qur'ani baki ɗaya,ina ga bazai ma wuce nan da sati uku
ba za a yaye su."
Iyah ta kai ƙarshen maganar dai-dai lokacin da TAIMIYYAH ta fito daga banɗakin,tana ɗaure da
zani a jikinta ta yafo rigar data cire akan kafaɗunta. Hajiya Aysha ta bita da ido tana cewa, "Kai
Masha Allah,Allah yayi wa rayuwarta albarka ya bata mijin aure na gari wanda zai riƙe ta da
amana."
Iyah ta amsa da cewa, "Ameen." Ita dai TAIMIYYAH tuni ta isa bakin gado ta zauna duk kunya
ya isheta tunda ta fahimci hiranta suke yi,cikin sanyin murya ta dubi Iyah tana cewa, "Iyah kayan
fa baki ciro min ba."
Iyah sai ta tashi ta isa wajen jakan da ta sanyo musu kaya ta cirowa TAIMIYYAH doguwar rigar
atamfa,ta haɗa da man shafawarta da ta zo mata dashi ta kai mata bakin gadon ta aje.
TAIMIYYAH sai ta ɗauka kayan da man ta koma banɗakin don shiryawa,sabida ba za ta iya
shiryawa akan idanun su Hajiya Aysha wacce bata iya ɗauke ido daga duban TAIMIYYAN.
Komawar TAIMIYYAH xuwa banɗakin ya saka Hajiya Aysha cigaba da hiran su da Iyah akan
masu lalura iri-iri,cikin hiran ne Hajiya Aysha ke tambayar Iyah bayan TAIMIYYAH tana da wasu
yaran ne? Iyah tayi murmushi tana cewa, "Hajiya kenan wannan ɗin ma ba ni ce na haifa ba jikata
ce ƴar wajen ɗana,mahaifiyarta ta rasu tun tana cimman goyo ni na raineta har kawo yanzu,kuma
cikin hukuncin Ubangiji wata ɗaya da wasu kwanaki kenan da rasuwan mahaifinta da ƙanninta su
biyu duka rana ɗaya ajalinsu ya sauka...
Iyah ta baiwa Hajiya Aysha labarin yadda mutuwarsu Abie ɗin ya kasance,ta ƙare maganan da
cewa, "Yanzu bata da uwa bata da uba sai ni da ƙanin mahaifinta kawai mu ne gatanta, ko fuskar
uwarta bata sani ba sai a hoto, yadda kika ganta haka uwar take har kyawun duk na uwarce ta
ɗakko,da sanyin halin da komi babu inda tabar marigayiya Zainab TAIMIYYAH.Dama kuma
sunan uwar aka saka mata shiyasa muka cigaba da kiranta da TAIMIYYAH yadda ake kiran
marigayiyan."
Hajiya Aysha ta jinjina kai wasu hawaye na taruwa a idanunta,na tsananin tausayin TAIMIYYAH
da taji ya cika zuciyarta.Shiyasa lokacin da TAIMIYYAH ta fito daga banɗakin Hajiya Aysha ta
zuba mata ido,tana sake gano kyawun TAIMIYYAN tare da jin wani ƙaunarta me tsanani na ratsa
zuciyarta,tana cigaba da jinjina ƙudiran Ubangiji me yin yadda ya so a kuma lokacin daya ga
dama.
TAIMIYYAH ta wuce su a kunyace zuwa kan gado ta zauna,bayan ta aje kayan data fito da su a
ninke daga bakin gadon.Ta warware ɗankwalin kayan tana rufe kanta zuwa ƙirjinta da shi,tana me
zamewa ta kwanta ta juya musu baya sabida yadda take jinta a takure musamman kallon da Hajiya
Aysha ke bin ta da shi.
Shigowar Likitan ɗakin yasa TAIMIYYAH sauke ajiyar zuciya tana fata ya kasance
sallamace,aiko cikin sa'a yana sake duba jikinta yayi mata ƴan tambayoyi ta bashi tabbacin babu
wani damuwa,sai ya juya yana wa Hajiya Aysha da Iyah magana akan cewa shikenan yanzu zasu
iya tafiya gida.
Dama already an riga anyi clearing bill tun jiya,sai kawai Iyah ta ɗaga waya ta kira Sani akan ya
zo su wuce zuwa gida an sallame su.
Bayan ta kira Sani driver sai ta kira Baba Sani shi ma ta sanar da shi,ita dai TAIMIYYAH na daga
kwance har lokacin tana sauraran Iyah.
Hajiya Aysha ta dubi Iyah tana cewa, "To Hajiya bari mu amsa lambar wayan juna ko a dinga
zumunci,kuma Insha Allah zan zo har gida idan an kwana biyu in sake duba jikinta,don gaskiya
wannan ɗiya ta shiga raina matuƙa da gaske."
Iyah ta saki murmushi cike da jin daɗin kalaman Hajiyan tace, "Aiko ya kamata kam mu amsa
lambar juna Insha Allah za a riƙa gaisawa akai-akai,idan bikin walimar gama haddarsu ya tashi
ma, kin ga saina sanar miki ki zo mana bikin walimar,ga wayata sai ki sanya taki lambar idan kika
kira sai duk mu yi saving."
Hajiya Aysha ta amsa wayar Iyah ta sanya lambar ta kira, kiran na shigowa ta kashe tayi saving
number ɗin tayi ma Iyah itama saving nata numbar.
Ta miƙawa Iyah wayarta tana takawa zuwa bakin gadon da TAIMIYYAH ke kwance,ta tsaya kusa
da ita sosai tana cewa, "Ɗiyata tashi zaune muyi magana kinji, ki bar jin kunya ta ni yanzu
zumunci nake so mu ƙulla nima ki ɗaukeni kamar Iyar taki kinji ko?"
TAIMIYYAH ta tashi a kunyace tana murmushi kafin ta buɗe baki cikin sanyin murya take cewa,
"To Hajiya nagode da kulawa Allah saka da alkhairy."
Hajiya Aysha ta amsa da, "Ameen Zainab Allah ƙara miki lafiya,yanzu ga wayata nan saka min
number ɗinki zan dinga kiran ki,ke ma kuma sai ki dinga nemana a waya muna gaisawa."
Tayi maganar tana miƙawa TAIMIYYAH wayarta me nauyin kuɗi tamkar ba Dattijiya ba,inji
TAIMIYYAH cikin zuciyarta lokacin da wayar ya je hannunta.
Ta loda lambobinta tana miƙawa Hajiyar wayar don tayi saving da sunan da take so.
Hajiya Aysha ta amsa wayar ta yi saving sukai sallama da TAIMIYYAH akan cewa sai ta ji
kira,daga haka ta juya zuwa wajen Iyah suna magana.
Babah Rabi kuma ta miƙe don ɗaukar kwandon abincin da suka zo da shi wanda ba a taɓa komi
ciki ba,sai Hajiya Aysha ta hanata tana cewa, "Babah Rabi aje kawai su tafi da shi gida,tunda har
mun zo da shi ba za mu koma da abinci gida alhali wacce aka shirya domin ta bata ci ba,gwara su
je dashi duk randa Allah ya nufa na samu lokaci na je gida sake duba ta sai na amsa kulolina."
Iyah dake saurarensu tana jinjina karamci da mutuncin wannan Hajiya sai ta riƙe haɓa tana cewa,
"Ayi haka Hajiya ai ɗawainiyar tayi yawa,da kun koma da shi bakomi wallahi mun gode matuƙa."
Hajiya Aysha ta girgiza kai tana cewa, "Gaskiya Hajiya ba za a koma da abinci TAIMIYYAH da
aka yi dominta bata ci ba."
Hakanan Iyah ta haƙura suka bar kwandon abincin,ta tafi yi musu rakiya zuwa bakin mota.
Ita dai TAIMIYYAH iyakarta bakin ƙofa Hajiya Aysha tace ta koma ta gode da rakiyan ta
yafe,Iyah dai sai da ta ga tafiyarsu sannan ta juya zuciyarta na jinjina kirki da karamcin wannan
Hajiyar, wacce basu san hakiƙanin wacece ita ba.
Amma dai daga yanayin shigar da ke jikinta zuwa ƙatuwar motar da ake janta aciki ya tabbatarwa
Iyah cewa akwai masu gidan rana a tattare da Hajiyar wato (Kuɗi).
Tafiyar su Hajiyar bada jimawa ba Sani ya iso shi ma,suka tattara yanasu-yanasu Sani ya kwashi
kaya da basket ɗin abinci zuwa mota.
TAIMIYYAH ta sakko tana zura hijab ɗin da Iyah ta aje mata suka fito tana takawa a hankali har
zuwa wajen mota.
Iyah sai da ta tabbatar basu manta komi ba sannan ta fito daga ɗakin ta nufo wajen motar,tana
shiga Sani ya tada motar suka baro asibitin zuwa gida..........✍🏻
#Ɗansabo ce#
[12/14, 3:43 PM] +234 703 040 9541: Littafin TAIMIYYAH paid book ne,ga duk wanda ta
tsincesa a kowani irin group ne,kiji tsoran Allah karki karanta sai kin biya 500 naira only.
Za ku iya min magana ta wannan number ɗin 08167768704, ko kuma ku turo kuɗin ku kai tsaye ta
wannan account ɗin 0504192664 aisha ibrahim dansabo GTbank.*
Masu turo credit za ku turo katin MTN na 500 ta wannan line ɗin 08167768704.
_Ina ƴan kasuwa masu buƙatar a tallata muku hajar ku? Maza ku garzayo da kuɗi ƙalilan a tallata
muku kayan siyarwanku sai dai kawai ku ji ana kiran waya don buƙatan sayan kayan ku,ku
tuntuɓeni ta layina kamar haka 08167768704._
*50*
Motar Sani na shigowa cikin gidan ita kuma Umma na fitowa daga Sasan su, hakan yasa ta nufi
wajen motar Sanin kai tsaye don gaida Iyah da yiwa TAIMIYYAH sannu da jiki kada tayi laifi
wajen Iyah.
Bayan sun gaisa da Iyan ne ta dubi TAIMIYYAH wacce ta fito daga cikin motar ta furta, "Sannu
Zainab Allah ƙara lafiya,sai ki dinga kula tunda kinsan kina da matsala ki daina abu irin na masu
lafiyan ƙafafu."
TAIMIYYAH ta jinjina kai kawai ba tare da tace komi ba tayi gaba abinta,Umma ta bi bayan
TAIMIYYAH da harara tana taɓe baki.Iyah ita gaba ɗaya hankalinta ma na kan Sani da ke sauke
kayan da suka dawo da shi ne,sai daga baya ta dubi Umma lokacin da Sani ya aje kwandon
abincin da su Zuhurah suka kai asibiti tana cewa, "Yauwa Zuwaira sai ki wuce da ragowar abincin
aba masu ci,kin ga wani nan ma ko taɓawa ba a yi ba Hajiyar da suka kaɗe TAIMIYYAH ce ta
kawo asibitin."
Umma ta dubi tsadaddun kulolin da ke cikin basket ɗin zuwa shi kansa basket ɗin da ke ɗauke da
kulolin abincin,wanda kana kallo kasan ba ƙananun kuɗi ne suka saye shi ba, ta wani taɓe baki
tana cewa, "Allah sarki ashe dai mutanen kirki ne da wasu ne fa guduwa za su yi Iyah."
Iyah ta tamke face tana faɗin, "To su Allah bai sa haka suke ba,mata ce me mutunci da sanin
darajan ɗan adam,duk arziƙinsu bai sa ta kasance me wulaƙanta halittan Ubangiji ba."
Umma da tuni ta fara jiyo ƙamshin jirwaye cikin maganar Iyah sai tayi saurin ɗaukar basket ɗinta
tayi gaba tana cewa, "To Iyah Allah ƙara sauƙi bari in miƙa kwandon ciki nima fita zanyi na ga
dawowar ku nace bari in tsaya mu gaisa."
Iyah ta taɓe baki tana cewa, "To madallah." Daga haka tayi gaba abinta Sani na biyo bayanta da
kayan zuwa ciki.
Tuni TAIMIYYAH ta isa ɗaki bayan sun gaisa da Babah Ladi da tai mata ya jiki,tana isa kan gado
ta nufa ta zauna tana sauke numfashi.
Bacci-bacci take ji a idanunta shiyasa ta miƙe ta jona wayarta a caji ganin a kwai wuta,ta baro
wajen tana nufan wajen kayanta ta ciro wata doguwar riga me taushin jiki,ta cire na atamfar jikinta
ta sanya wanda ta ciro ɗin.
Direct sai ta nufi gado ta kwanta ba a ɗauki lokaci ba kuwa bacci ya sace ta.
Iyah da ta kammala kintsa kayan da suka dawo dasu sai ta nufi ɗakin TAIMIYYAH, tana son sanar
da ita abubuwan arziƙin da ta gani cikin kulas ɗin da Hajiya suka kawo,sai ta tadda TAIMIYYAH
tayi bacci hakan yasa ta fitowa ta nufi ɗakinta itama don ta huta.
Koda Ummi suka shigo gaida TAIMIYYAH sun samu daga ita har Iyah suna bacci,sai Babah Ladi
kawai suka tadda da ke ta hidiman ɗaura girkin lunch.
Ummie sai ta koma sasanta ta bar Inna Larai za ta taya Babah Ladi aiki,don wataran idan ta shigo
ta kan shiga kitchen suyi aikin tare, tunda Iyah ce take zuba musu abinci ana kuma sanya musu
daga sasan Baba Sani ma,duk da cewa babu abinda ba a aje musu na kayan abinci a sasan su
ba ,sabida idan sunyi ra'ayin dafa abinda ran su ke so su girka abinsu.
TAIMIYYAH da Iyah sai azuhur suka tashi daga bacci,kai tsaye TAIMIYYAH wanka ta shiga ta
fito ɗaure da alwala tana jin daɗin jikinta sosai.
Kanta sayau take jinsa duk ciwan kannan ya tafi sai dai mura dake son damunta kaɗan,shima ta
san tana shan maganinsa da aka haɗo mata daga asibiti za ta samu sauƙi.
Bayan ta idar da sallah ne ta fito falo don cin abinci ta kuma sake shan magani, lokacin ne kuma
ita ma Iyah ta fito daga ɗaki.Hakan yasa Kusan a tare suka isa wajen cin abincin, wanda Babah
Ladi ta aje har kulolin abincin da suka dawo da shi daga asibitin.
TAIMIYYAH ta fara da bubbuɗe kulolin don ganin abinda ke ciki, sai ta ga su chips ne da akai wa
haɗin sauce na musamman da liver,sai farfesun naman kaza da gasasshen naman rago da akai
raping ɗinsa cikin foil paper,wani irin gashi da yayi romo-romo sai azaban ƙamshin spices ke
tashi.
Nan take TAIMIYYAH ta ji gashin naman ya shiga ranta,ta ɗauki plate ta zuba kaɗan tana ɗaura
jallop ɗin shinkafan da Babah Ladi tayi akai.
Iyah ganin naman ragon da ɗan yawa yasa ta zuba itama, suna ci suna santin
daɗinsa,TAIMIYYAH na yabawa duk wanda yayi wannan gashin naman da cewa ƙwararrene.
Tana kammala cin abincin ɗakinta ta koma ta kunna wayarta,don tasan tabbas an nannemeta anji
wayarta a kashe. Aiko tana kunna wayar bada jimawa ba kiran Yasmeen vid call ya fara
shigowa,TAIMIYYAH ta ɗauka tana zama daga gefen gado ta fara da cewa, "Besty sai yanzu zaki
nemeni kiji lafiya ta gaskiya nayi fishi."
Yasmeen da ke kallon fuskar TAIMIYYAH tar a wayarta ta saki murmushi tana faɗin, "Sorry
Tawan kece ai kika kashe wayarki ni kuma ban kira ta line ɗin Iyah ba.Ya jikin naki ina fata dai
babu wani matsala? Kawai sai muka ji wannan tsautsayi Allah ya tsare gaba TAIMIYYAH."
TAIMIYYAH ta amsa da cewa, "Ameen Yasmeen,ai abun ya zo da sauƙi ma tunda ban ji wani
rauni me yawa ba,kuma nayi dace wallahi matar da driver ɗin nata ya kaɗeni me kirki ce,su suka
kaini asibiti yauma kuma ta sake dawowa duba ni, baki ga abincin data zo da safe ta kawo
ba,kuma har sai da aka bani sallama sannan ta tafi, gaskiya Hajiyar tana da mutunci sosai."
TAIMIYYAH ta cigaba da baiwa Yasmeen labarin yadda abin ya faru,Yasmeen ta jinjina kai tana
cewa, "Allah sarki haka ne dama sai ki ga Allah ya haɗaka dana gari wani lokacin,amma ta kyauta
sosai tayi abinda ya dace." Yasmeen ta cigaba da cewa, "TAIMIYYAH dama abinda ya faru
tsakaninki da Yah Emran kenan shi ne baki sanar min ba,sai jiya Mamie ke bani labari kin kyauta
kenan ?"
TAIMIYYAH ta ɓata fuska don ita sunansa kawai da Yasmeen ta kira sai da ranta ya ɓaci,ta
shagwaɓe murya tana faɗin, "Yasmeen to ni banga anfanin sanar miki bane tunda ba abin arziƙi ne
ya faru ba,wallahi ni am sorry to say na tsani jin ko sunansa ba don yana jinina ba.Ai Iyah ta sanar
min wai Guggo Bilki tai masa cin mutunci sosai har da Abbah ta haɗa shi ma."
Yasmeen ta saki tsaki tana cewa, "Hmm! Wallahi abin ya matuƙar bani mamaki da ɗaure min
kai,kinsan bamu taɓa sanin bad side ɗinsa ba sai da hakan ya faru, ashe shi Yah Anas dama ya san
Yah Em ɗin na neman matansa,amma shi kansa cewa yayi bai san abun nasa yayi riƙan da har ke
zai iya cewa zai ketawa mutunc ba,kiyi haƙury TAIMIYYAH ki yafe masa don gaskiya yayi
nadama daga baya,har ni jiya ya sama da daddare yace in sake baki haƙuri wai duk kinyi blocking
line ɗinsa,kiyi haƙuri ki yafe masa maganar soyayyace dai koni ban goyi baya ba,don Abbah cewa
yayi ma kar ya sake jin maganar."
TAIMIYYAH ta sauke numfashi tana cewa, "Shikenan ya wuce Yasmeen,ni bama abinda ya sake
ɓata min rai irin yadda ya lallaɓo yazo ya tsara Iyah wai sona yake da gaske."
Yasmeen ta saki murmushi tana cewa, "Ina ruwan shegen kaya ai ya iya tsari da kike ganinsa a
miskilinnan,to ai Mamie tai masa tas tace in ma son ne na gaske ya kama zuciyarsa sai dai ya
kashesa, kada ma ya sake nufo ta da maganarki tunda shi baida mutunci."
TAIMIYYAH ta ɗan saki murmushi tana faɗin, "Wayyo Guggo Bilki kice dai an masa taron dangi
ne, don Iyah itama tace ta kira shi ta zazzagesa tas!"
Suka saki dariya a lokaci guda Yasmeen na cewa, "Wai ni kam ina mutanenki ne ashe Zuhurah
kuma an sanya lokaci to Allah ya kaimu da rai da lafiya,ita ma Basmah ance ta samu wani za a zo
a sanya lokaci ayi bikin duk gaba ɗaya ko?"
TAIMIYYAH da idanunta ke kan fuskar Yasmeen ta cikin wayarta,tayi saurin ware ido tana jin
wani abu na sukar zuciyarta.Cike da dauriya tai magana tana cewa, "Haka kika ji Yasmeen? Ai ni
bamma sani ba nasan dai ta samu wanin ,amma bansan maganan cewa za a sanya lokacin
ba,Allah ya sanya alkhairy toh."
Yasmeen ta amsa da Ameen tana noticing yadda mood ɗin TAIMIYYAH ya canza,hakan yasa ta
cewa, "TAIMIYYAH lafiya ya dai mood ɗinki na ga kaman ya canza?"
TAIMIYYAH dake ƙoƙarin danne abinda take ji na taso mata daga zuciya, sai tayi saurin duban
Yasmeen ɗin tana cewa, "Yasmeen tsakaninmu babu wani maganan ɓoyo kinsan waye Basmah ke
tare da shi har ake maganar za a sanya musu rana kuwa?"
Yasmeen ta girgiza kai cikin sauri, kafin ta furta, "No bansani ba waye shi ɗin ni naji abun yazo da
gaggawa ne ai, ita dake complain kullum akan rashin masu kulata,waye guy ɗin da yazo cikin
gaggawa haka?"
TAIMIYYAH da ke ji har hawaye ya fara taruwa a idanunta, sabida tsananin ɗacin da take a cikin
zuciyarta tayi ƙarfin halin fara faɗin, "Yasmeen Nass ne fa,Nass nawa da muka rabu shine ya
dawo yana son Basmah,na kasa gaya miki ne tun ranan da mu kai ido biyu da shi yazo wajenta.....
TAIMIYYAH ta kwashe yadda aka yi tana kuka ta sanarwa Yasmeen,har ta kai ƙarshe hawaye na
zuba a idanunta tana jin ciwan wannan cin amana da Basmah za ta yi mata na ƙona ranta.Yasmeen
da gaba ɗaya ta shiga shock! Sai ta yanko wani irin zagi tana cewa, "Kutumar ubancan kayyasa!
TAIMIYYAH ko dai idon ki ne ya gane miki me kama da Nass ,amma ba dai shi Nass ɗinki dana
sani ba?"
TAIMIYYAH sai tayi murmushin yaƙe cikin raunin murya take faɗin, "Wallahi Yasmeen shi na
gani ganin idona ba labari aka bani ba,ni yanzu duk abinda aka ce min mutum zai yi ya daina bani
mamaki,sabida na gama gane halayyar mutane yadda ta lalace kawunansu kawai suka sani,ba a
maida cin amana abakin komi ba, kullum na tuna yadda dama ba sona suke ba sai inji mamakina
ya ragu,amma abinda ke ɗaure min kai shine ta ina har suka haɗu da Basmah suka jone har
soyayyah ya shiga tsakaninsu? Koda dai ta gaya min dama tun randa ta fara ganinsa ta ji ta kamu
da sonsa,sai na tuna irin kallon da take binsa da shi tun a wancan lokacin,amma maganar gaskiya
Yasmeen abin na tsananin min ciwo a zuciyata."
Yasmeen da gaba ɗaya ranta ya gama ɓaci tana ji kamar tayi tsuntsu ta zo Zaria,ta saki wani ashar
ta dannawa Basmah tana cigaba da faɗin, "Kar ki damu kiyi haƙury Besty Allah zai miki
kyakykyawan sakayya ne soon Insha Allah,ita kuma ƴar banzar mara kunyan ki zuba musu ido
kamar yadda Iyah ta faɗi ne,aure indai na cin amana ne wallahi babu inda yake zuwa,ko yayi
ƙarƙo to zaki ga ana fuskantar tarin matsaloli a cikinsa.Kuma tabbas ina ji ajikina ba haka kawai
suka barsa ba, da asiri suka nemesa ko rantsuwa nayi bana ji zan yi kaffara akan hakan,haba abin
da ɗaure kai amma koma miye zai fito fili komin daren da daɗewa,za mu zuba ido mu sha kallo
don Allah ki cire damuwa ki barwa Allah komi, in sunyi ne don su ci amanarki su tazartaki to
kansu zasu ci amana da yardar Ubangiji, ai Allah baya bacci ya kuma san manufan da ke zukatan
dukkan bayinsa."
TAIMIYYAH ta sauke zazzafar numfashi tana kai hannu ta share hawayen da suka zubo mata tana
me cewa, "Hakane Yasmeen wallahi ina iya bakin ƙoƙarina wajen ganin na manta cewa mun taɓa
soyayya da shi,amma na kasa daina jin ciwo a cikin zuciyata duk sanda na tuno wai Basmah ce
xata min haka,amma bakomi koma miye ina musu fatan alkhairy, Allah yasa rakiya tayi nisa,ni
kuma Allah ya bani ƙarfin zuciyar fuskantar kowace irin jarabawa,amma soyayya ya gama fita
daga kaina Yasmeen bana sha'awar in sake ɗanɗanarta."
Daga haka suka cigaba da tattaunawa akan irin yadda ƴan matan wannan zamanin suka kware
wajen iya cin amana.
Lokacin da suka kammala yin vid call ɗin da Yasmeen,TAIMIYYAH sai ta aje wayarta tana sauke
zazzafar numfashi,cikin zuciyarta take al'ajabin yadda rayuwa ke juya mata daki-daki,tare da fatan
Allah ya bata ikon cin jarabawa,amma sam soyayya ya fita ranta baki ɗaya.
Tana cikin duba messages da ke shigowa ta online kiran Zee ya shigo wayarta.
Sai ta kashe data tana receiving call ɗin suka gaisa da Zee,TAIMIYYAH na sake tambayar Zee ɗin
jikinta.
Zee ta sanar da ita cewa ta samu sauƙi,ta ɗaura da yiwa TAIMIYYAH complain akan kashe
wayarta da tayi,don ta kira ta bata sameta ba.
TAIMIYYAH ta sanar da Zee ɗin tsautsayin da ya sameta bayan barowanta gidansu,Zee ta saki
salati tana godewa Allah da TAIMIYYAN bata ji rauni me girma ba.Su kai sallama da juna Zee na
sanar da TAIMIYYAH cewa da zaran ta sake samun sauƙi za ta zo ta duba ta.
TAIMIYYAH ta aje wayarta saman gado tana tashi ta ɗakko system ɗinta ta jona a wuta don yin
chargy.Tunawa da tayi cewa Ummie ta shigo gaidata tana bacci yasa ta yanke shawaran zuwa
Sasan Ummie ɗin,ta fito bayan ta zura hijab akan shigar jikinta, tama sanar da Iyah cewa za ta
Sasan Ummie ta dawo.
Iyah tai mata a dawo lafiya ,TAIMIYYAH ta fito tana tafiya cikin takunta a hankali cike da tarin
nutsuwa har ta isa sasan Ummien.
Bata baro sasan ba sai bayan ta idar da sallar la'asar,cikin tafiyar a hankali take takowa don
komawa zuwa sasan Iyah.Kamar an ce ta ɗaga kai ta dubi sashin gate ,sai ta hango shigowar Nass
cikin compound ɗin gidan daga wajen gate .
Yana sanye cikin ƙananun kaya da sukai masa mugun kyau.TAIMIYYAH sai ta tsaya cak! Kamar
wacce aka saka remote control aka tsaida ta,kirjinta ya shiga bugawa da ƙarfin gaske lokacin da
Nass ɗin ke cigaba da takowa zuwa cikin compound ɗin.
Akan idanunta suka gaisa da Tukur mai gadi Nass ɗin na ɗaga waya ya kai kunni alamun kiran
waya zai yi. Sam hankalinsa bai kai kan inda TAIMIYYYAH ke tsaye dafe da ƙafarta ta zuba
masa manyan idanunta tamkar wacce aka dasa a wajen,gaba ɗaya ta kasa koda ƙwaƙwƙwaran
motsi sabida yadda take ganin komi tamkar a mafarki,so take yi ta sake tabbatarwa kanta wajen
Basmah yazo a wannan karon ma ko kuwa?
Sai dai ko mintuna biyar ba a yi ba ta hango fitowar Basmah daga Sasan su, tana nufan wajen da
Nass ɗin ke tsaye cikin taku na ɗaukar hankali.Nan da nan TAIMIYYAH ta ji kanta ya fara juya
mata, ta shiga nanata kalmar Innalillahi wa'inna'ilaihirraju'un! Ta dinga nanata kalmar, tana ji a
hankali ƙafafunta na yin sanyi lokacin da Basmah da Nass ke neman ɓacewa ganinta,suna takawa
jere da juna suka nufi cikin Sasan Baba Sani.
TAIMIYYAH sai tsinci kanta da silalewa daga tsaye zuwa tsugunne ,tana jin saukar wasu irin
zafafan hawaye daga idanunta zuwa kuncinta.
Ta jima haka a tsugunne bata san ma wani irin tunani zata yi ba, zuciyarta na tsananin zafi da
ciwon wannan lamari da take fata Ubangiji yasa mata ƙarfin zuciyar iya haɗiye abinda take ji a
cikin zuciyarta.
Da ƙyar ta iya tashi tsaye tana ji kanta na mata wani irin ciwo,ta kai hannu ta dafa guiwar ƙafarta
ta fara takawa don isa sasan Iyah,bayan ta tabbatar babu ɗigon hawaye ko kaɗan akan fuskarta.
Sabida bata so Iyah ta sake ganin raunin zuciyarta akan wannan issue ɗin na Nass da Basmah.
Har ta isa sasan Iyah bata daina jin nauyin da ƙirjinta yayi na damunta ba.Shiyasa tana shiga ciki
bata tsaya a falo ba ta shige zuwa ɗakinta ta kwanta,tafi mintuna sha biyar tana jinyar zuciyarta
kafin ta kai hannu ta janyo wayarta,ta shiga wajen da ta adana karatun Qur'ani ta kunna suratul
Rahman,tana fata Ubanjigin rahama da tausayi ya sanyaya zuciyarta cikin gaggawa,idanunta a
lumshe suke lokacin da daddaɗan kira'ar Abdullahil Maɗrooth ke ratsa kunnuwanta.
Hawaye suka fara sauka a hankali daga idanunta suna jiƙe pillow ɗin da kanta ke kai,a haka ta fara
jin nauyin da zuciyarta yayi na raguwa a ƙirjinta ta fara taji tarin nutsuwa na shigarta, bakinta ya
buɗe ta fara bin karatun a hankali cikin muryarta da yai ƙasa sosai sabida yadda zuciyarta babu
daɗi ko kaɗan ........✍🏻
_Allah sarki TAIMIYYAH Insha Allah alkhairy me girma na tafe cikin rayuwarki da
gaggawa.....Irin wannan cin amanar bashi da daɗi ko daga bare ne bare ɗan uwanka na jini.Allah
ya baki juriya da haƙuri Zainab TAIMIYYAH inji Ɗansabo_ 😰
*Hello! Readers what about dis chapter? kun ji tausayin TAIMIYYAH ko bayan Basmah ku ke
bi? Sai na ji tarin comments daga gareku son so domin Allah.*
#Ɗansabo ce#
[12/14, 3:43 PM] +234 703 040 9541: *Littafin TAIMIYYAH paid book ne,ga duk wanda ta
tsincesa a kowani irin group ne,kiji tsoran Allah karki karanta sai kin biya 500 naira only.*
*Za ku iya min magana ta wannan number ɗin 08167768704, ko kuma ku turo kuɗin ku kai tsaye
ta wannan account ɗin*👇🏻
0504192664 aisha ibrahim dansabo GTbank.
Masu turo credit za ku turo katin MTN na 500 ta wannan line ɗin 08167768704.
_*Ina ƴan kasuwa masu buƙatar a tallata muku hajar ku? Maza ku garzayo da kuɗi ƙalilan a
tallata muku kayan siyarwanku sai dai kawai ku ji ana kiran waya don buƙatan sayan kayan ku,ku
tuntuɓeni ta layina kamar haka 08167768704.*_
*51*
"Basmah yanzu duk wannan uban kayayyakin Nass ɗin ne ya kawo miki?"
Zuhurah ke wannan maganar tana faman zaro wasu haɗaɗɗun riguna ready made daga cikin wani
bag, me tambarin sunan wajen da aka sayi kayan.
Basmah ta jinjina kai cike da tsananin murna take faɗin, "Ke dai bari wallahi duk nawa ne guda 2
na zaɓa na tura masa, kawai sai da ya zo naga ashe har guda 4 ya saya min,ai gaskiya za a je da
Cweety ɗinnan nawa Yah Zuhurah,don na ga alamu har ya fi Ameeru hannun kyauta."
Zuhurah da take taji zuciyarta ya sosu sai tayi saurin tamke fuska tana faɗin, "Abin kuma har da
cin fuska Basmah,ke fa baki faye kunya ba wallahi."
Basmah ta saki dariya tana cewa, "Sorry Sis ai gaskiya na faɗi amma, bayan kayannan da zai wuce
10k ya aje min,ni ganin abin nake kaman a mafarki wai ni ce namiji kewa rawar ƙafa haka?
Gaskiya ko nawa Maharaxu Boka yace a biya shi bamu faɗi ba don aiki fa yaci ba kaɗan
ba,wallahi ba kiga yadda duk yake susucewa idan ina kusa da shi ba,cewa yayi duk ya ƙosa ayi
aurennan ko xai hutawa zuciyarsa,ranar Saturday dai magabatansa zasu zo Insha Allah."
Basmah ta kai ƙarshen maganan tana wani blushing cike da tarin farin ciki.Umma da ta fito daga
ɗaki ne ta iso inda su Basmah ke zaune a falon, idanunta akan bag ɗin da Zuhurah ta zazzage
kayan ciki take cewa, "Basmah har Naseer ɗin ya wuce ne,wannan kayan kuma fa?"
Basmah ta dubi Umma tana faman washe baki tace "Umma waɗannan rigunan dana ga ana tallah
a IG ne nace miki na turawa Nass nace ya siya min,to shine ya zo min dasu wannan zuwa
weekend da yayi,kinsan a Abuja me sai da kayan take shine ya je wajenta ya amsa bayan ya tura
mata kuɗin,guda biyu fa na zaɓa amma kin ga guda 4 ya siyo."
Basmah tana maganan ne tana ɗagawa Umma rigunan tana ganin kyawunsu.Umman ta dubi
Basmah bayan ta kammala gani tace, "Masha Allah,gaskiya wannan za a je da shi da alamu
hannunsa a sake yake ba a dunƙule kamar na ƴan dambe ba,to ya maganan turo manyan nasa? Don
ni fa na fiso ai komi gaba ɗaya tare dana Zuhurah ko na huta,sai inji dana Sadeeq da zai biyo baya
tunda shi namiji ne."
Basmah sai ta saki murmushi tana sanar da Umman ai Nass ɗin yace zuwa next week Saturday za
a zo,yana jin ma gaba ɗaya da zuwa da sanya ranar za a yi a lokaci guda,sabida daga shi har
Uwarsa a matse suke ya yi aure,musamman Uwar da take son ganin ya rabu da
gurguwarcan,shiyasa yana zuwa mata da maganata ta amince babu wani dogon bincike,ita dai
burinta ace ya rabu da gurguwar da bata so bata san tuni muka ɗauke tunaninsa daga kan wata
gurguwa ba,ni kaɗai yake ji da gani."
Basmah tayi maganar bil hakki tana sakin dariyar mugunta Umma kuma na taya ta.Zuhura ta ɗan
ja ƙaramin tsaki tana faɗin, "Wallahi Basmah ni har kin fini so kiyi aurennan ma,irin wannan
rawar kan da kike yi haka kamar zaki kai kanki."
Basmah tayi fari da ido tana sakin dariya tace, "To miye a ciki aure ai abin so ne musamman idan
kayi dace da wanda kake so,kinsan yadda nake jin Nass a raina kuwa? Hmm! Ba a magana ke dai
kawai Allah ya ara mana lokaci mu more."
Zuhurah ta amsa da, "Ameen." Suna cigaba da tattauna yadda za su tsara bikinsu idan an sanya
ranar auren Basmah nan da sati me zuwa.....
TAIMIYYAH bayan idar da sallan la'asar da tayi,cigaba da zama tayi a ɗaki tana ta tilawar Qur'ani
sabida so take yi zuciyarta ta sake sanyaya, daga ƙunci da ɗacin da take ji a cikin ranta tun ganin
da ta sake yiwa Nass da Basmah a tare.
Sai ana dafda kiran magriba sannan ta tashi ta fito falo wajen Iyah da ke zaune.
Ta isa kusa da Iyah ta zauna tana faɗin, "Iyah sannu kina ta kallo ne,ni tun ɗaxu ina tilawa ne
kinsan an kusa yayenmu sai da tilawa sabida haddar ya zauna da kyau."
Iyah ta dubi TAIMIYYAH tana cewa, "Hakan yana da kyau,ai ina jiyo karatun naki daga nan nace
to gaki can ana ta ƙoƙari,Allah yasa albarka yasa anyi na tsoran Allah ne."
TAIMIYYAH ta amsa da, "Ameen." Iyah na cigaba da jan ta hira har aka kira sallah suka nufi
ɗakunansu don ɗaura alwala.
____________
*Abuja, 9:05pm.*
Suhailah ce ke tsaye a cikin kitchen ɗinta da ke upstairs,tana ƙarisa haɗawa A.Maleek haɗin Beef
Salad da yace shi zai ci a daren.
Bayan ta kammala haɗawan ne kuma ta nufi Coffee maker, ta haɗa masa ruwan Coffee ta juye
cikin ƙaramin Mug flask me kyau,ta haɗa komi bisa madaidaicin tray ta fito zuwa falo ta aje daga
ƙasan carfet,don ta san ba zai taɓa hawa dining ba.
Tana ƙoƙarin tashi ta nufi ɗakinta don yin wanka,ya fito daga ɗakinsa sanye cikin Pajamas Ash
colour da suka haske fatarsa.Suhailah tayi saurin dubansa tana cewa, "My Maleek na kammala zan
je nayi wanka yanzu, ko in tsaya ka kammala ne?"
Da hannu kawai yayi mata alama ta tafi sabida yau da alamu ƴan miskilancin nasa na kusa
ne,sabida haka suka yini da shi tun rana yana faman shan ƙamshi.
Suhailah ta saki smile tana yin gaba abinta,cikin zuciyarta take jinjina halayyar Maleek ɗin masu
wuyar sabawa.
Lokacin da ta fito yayi nisa wajen cin Salad ɗinsa wanda yayi masa yadda yake so.Ya ɗago
manyan idanunsa ya sauke akan Suhailah lokacin da take takowa zuwa garesa.Tana sanye ne cikin
fararen Nighties riga da wando wanda suka lafe a jikinta tareda bayyana surarta a fili.Sabida kayan
basu da kauri ko kaɗan,hatta ƙirjinta da bata sanya komi ba a na hangosa muraran ta cikin rigar.
Maleek yayi saurin ɗauke idanunsa akanta har ta ƙariso wajen da yake zaune, ta zauna kamar zata
shige jikinsa ƙamshin turarenta dana Humrah da tayi amfani da shi na cika kafofin hancinsa.Ta
miƙa hannu ta amsa fork ɗin da ke hannunsa tana cigaba da ciyar da shi ba tare da tayi magana
ba,kamar yadda shima bai ce uffan ba ya dai sakar mata fork ɗin tana ciyar da shi yana buɗe baki a
ƙasaice yana amsa har ta kammala bashi.
Ta haɗe kayan da suka ɓata ta nufi kitchen ta wanke su ta kife,don bata son kwana da plates da
akai anfani dasu ba a wanke ba.
Lokacin da ta dawo cikin falon samunsa tayi ya miƙe ƙafafunsa sosai yana kallon labarai a tashar
NTA Abuja.
Ta zauna kusa da shi jikinsu na gugar juna kafin tayi ƙasa da murya tace, "Yah Maleek next week
ɗin za ka shiga Zarian ne?"
Bai yi magana ba ya dai ɗago manyan idanunsa ne daga kan TV ya sauke akanta,kafin ya kai
hannunsa duka biyu ya kwanto da ita zuwa jikinsa, yana gyara mata zama bisa laps ɗinsa yake
cewa, "No ina ga sai zuwa upper week zanyi tafiya xuwa Anambra bazan samu shiga Zaria ba,
kina son wani abu ne daga can?"
Yadda yake maganar cike da ƙasaita hannunsa na lalube jikinta yasa Suhailah lumshe
idanunta,dukkanin jikinta na amsan saƙon da yake isarwa a sassan jikinta.Ta buɗe baki murya can
ƙasa tace, "So nake mu je tare dai my Maleek coz nayi missing Hajjah sosai."
Tayi maganar cike da marairaice masa murya,hakan yasa Maleek ɗago face ɗinta da hannu
ɗaya,ɗaya hannun na cikin rigarta ya manna mata harara yana cewa, "Aiko ba za ki Zaria nan kusa
ba sai kin samu kaman 3 month ina ga zaki fi ɗokin ganin Hajjan da kyau,zuwa lokacin kin daɗe
da shaye magungunanki kila ma har kinyi ciki,kinga sai ki je kina mata ɗan amannan da kuke yi
kina tara miyau a baki,sai ta gane cewa ɗan Abuja ya samu."
Suhailah ta waro ido tana duban Maleek sosai,wanda ya haɗe face ba za ka taɓa cewa shine ya
zayyano dukkanin kalaman ba.Ya kai bakinsa yayi kissing idanun nata yana cewa, "Hey! Babe
karki cinyeni da wannan kallon mana."
Yayi maganan har lokacin fuskarsa ɗaure yana jefa mata harara, Suhailah ta saki dariya tana sake
shigewa jikinsa.Ta ɗaga kai tana kai bakinta bisa wuyarsa tayi kissing kafin tayi masa raɗa cikin
kunni wanda sam banji me tace ba.Sai gani kawai nayi Maleek ya dungure mata kai da hannu yana
magana can ƙasa-ƙasa yake cewa, "Zaki yi bayani ne yarinya amma ba a nan ba sai a Bed."
Suhailah dake faman dariya ta ɗan shagwaɓe murya tana faɗin, "Ni kam babu ruwana Yah
Maleek,amma kana ganin zuwa lokacin da zan kammala da magungunan komi zai iya zama
normal har in iya ɗaukar ciki?"
Tayi maganar da wani expression wanda yasa Maleek ɗagota baki ɗaya ya mannata da ƙirjinsa
yana cewa, "If Allah yayi nufin hakan sai ya kasance wife,addu'a zamu cigaba da yi dai sai kuma
in sake zama rigimammen da kike cewa idan rakinki ya tashi,watakila a duba ƙwazona a bamu
rabo kurkusa ko Babe?"
Yayi maganan yana sanya idanunsa cikin nata,da yasan tasirin irin yadda yake dilmiyar da zuciyar
Suhailah idan yayi hakan, daya sassauta mata don wani irin gubar ƙaunarsa yake zuba mata me
asalin ƙarfi dake illata zuciyarta nantake.
Ta lumshe idanunta da sauri tana buɗesu akan kyakykyawar fuskarsa,ba tareda da ta bashi amsa ba
ta kai bakinta saman nasa tana fara manna masa wani irin french kiss,wanda shi ya koyar da ita
amma sai gashi ta fishi ƙwarewa a harkar.
Cikin lokaci kaɗan ta gama kunna zuciyar Maleek,sai da abubuwa sukai nisa ne ta fara danasani.
Don da ƙyar ta kwaci kanta a hannunsa lokacin da ya nuna bai san komi ba, illah ta bashi abinda ta
san shi kaɗai ne zai kashe wutar rikicin da take hangowa cikin idanunsa.
A daddafe suka kai 10:30pm anan falon suka nufi ɗakinsa bayan ya gama shan coffee ɗinsa,yana
fitowa daga toilet yayi musu light up ya nufi kan Bed inda Suhailah ke kwance cikin duvet.
Ya miƙa hannu ya lalubota tare da janyota zuwa jikinsa,jin ta yayi a yadda yafi so don har ta cire
kayan jikinta babu komi a tare da ita,hakan yasa shi manna mata sumba a biki cikin murya can
ƙasa ya furta, "Luv u my sweet wifey."
Daga haka labarin ya fara canzawa zuwa wani salo na daban abinda ya kore ni daga ɗakin kenan
na fito kamar zanyi tuntuɓe......Lol
__________
*3 Weeks Later*
TAIMIYYAH ce zaune tare da Iyah suna tattaunawa akan saka ranan auren Basmah da Nass da
akayi sati biyu da suka wuce.
TAIMIYYAH ta dubi Iyah tana tana faɗin, "Ni Iyah kinsan me ke bani mamaki?" Iyah ta girgiza
kai tana cewa, "Sai kin faɗa TAIMIYYAH." TAIMIYYAH ta ɗan tsuke face alamun koma me
zata faɗi yana hurting ɗinta a zuciya kafin ta furta, "Wallahi Iyah randa na shiga yi musu Allah
sanya alkhairy Umma cewa tayi wai ai dama ban je ba, tunda ta san daga ni har ke baƙin ciki
muke yi sabida uwarsa tace bata sona don ni gurguwace,yanzu kuma mun ga ya dawowa Basmah
har gashi an sanya musu rana ai ta san baƙin ciki muke yi,Allah sanya alkhairin ma na gulma ne
na je yi,wallahi Iyah na ji zafin kalaman sosai a raina."
Iyah dake sauraren TAIMIYYAH ta jinjina kai tana cewa, "Kiyi haƙury Zainab akan koma me
zasu ce miki,ke dai kawai ki musu fatan alkhairi,ki kuma sanya musu ido wanda hausawa kan ce
maganin lalatacce,kuma maganar baƙin ciki da take faɗi da baƙin cikin muke yi,da ni da kaina na
soke batun auren na tona musu asiri,don kuwa idan na sanar da Sani yadda abin ya faro har kawo
dawowarsa wajen Basmah,suna ji suna gani zai yi kora da maganar sai dai kuyi biyu babu,sakarya
wacce bata da lissafi ko kaɗan a cikin kanta,har abada bazan fasa yiwa Sani takaicin kasancewa da
mace jahila me son zuciya irin Zuwairah ba,domin na jima da tsanar halayyarta don ba za ka ce ka
ƙi mutum ba sai dai ka ƙi mugun halinsa,amma ina mata fatan shiriya idan tana da rabo."
Iyah ta kai ƙarshen maganan cike da tsananin ɓacin rai,don har cikin zuciyarta take jin ciwan irin
abubuwan da sukewa TAIMIYYAH ,wacce bata taka musu ba bare ta zubar musu.
Daga wannan hiran suka koma kan shirye-shiryen walimar yayensu TAIMIYYAH da za a gudanar
asabar me zuwa.
TAIMIYYAH na sanar da Iyah cewa tana son sayan sabuwar Abaya da za ta sanya a ranar. Iyah ta
murmusa tana cewa, "To ai sai ki saya ɗin Zainab,nawa ne kuɗin Abayar sai in baki ai,munyi
magana da Babanku Sani ma nace ina so a kayar da ko raguna biyu ne, a gasa kowa yaci
naman,don taro sosai zan yi aci a sha a taya mu farin ciki."
TAIMIYYAH ta saki kyakykyawar murmushin farin ciki tana cewa, "Iyah Allah ya ƙara girma ya
baki tsawon rai me anfani,bani da bakin da zan iya kwatanta adadin ƙaunar da nake miki a duniyar
nan sai dai ince Ubangiji ya baki Jannatul firdaus ,ke da su Abie da Mamata dasu Nahar da mu
baki ɗaya."
Sai kuma hawaye suka fara zubowa TAIMIYYAH sharr...!! Iyah tayi saurin kamo hannunta tana
faɗin, "Ameen Zainabu don Allah bar kukan haka, kiyi haƙury Allah ya gafarta musu ya ƙara
mana dangana,nawa ne kuɗin Abayar maza ki faɗi min kin ji Zainabu na."
TAIMIYYAH ta share hawayen da suka zubo mata tana jin kewar Abie ɗinta me tsanani yana cika
zuciyarta.
Ta yi ƙarfin halin murmusawa tana sanar da Iyah adadin kuɗin Abayar.Iyah ta jinjina kai tana
faɗin, "Karki damu gobe zan baki kuɗin Insha Allah."
TAIMIYYAH tayi godia tana cigaba da cewa, "Iyah ai online na siya Abayar nama tura da kuɗin
ta account ɗina,kawai dai na san zaki yi faɗa ne kice meyasa ban bari kin saya min ba,wajen wata
chuchu na siya na tura mata kuɗin gobe za ta sako min a mota sai Sani ya je tasha ya amso."
Iyah ta aikawa TAIMIYYAH harara tana faɗin, "To ai kin kyauta da baki sanar min ba sai da kika
siya,sai ki amshi kuɗin ai ki mayar cikin asusun naki."
Kafin TAIMIYYAH tayi magana taji kira ya shigo wayarta,ganin sunan Hajiya Aysha yasa ta yi
receiving call ɗin ta kai wayar kunni tana amsa sallamar da Hajiyar tayi.
TAIMIYYAH ta gaida ta cike da ladabi tamkar tana gabanta,kafin tayi jim tana sauraren abinda
Hajiyar ke faɗi daga nata ɓangaren,zuwa can tai ƙasa da murya tace, "Eh Mama ranan Saturday ne
idan Allah ya kaimu,ashe Iyah bata manta ba ta sanar miki."
Ta sake yin jim! Kafin ta furta, "Bakomi Mama duk abinda ake buƙata anyi nagode sosai na
kulawa sai kun zo ɗin."
TAIMIYYAH ta cigaba da blushing tana sauraren abinda Hajiyan ke sake faɗi mata,kafin ta sake
cewa, "To shikenan Mama nagode gama Iyan a kusa dani bari in bata wayar."
Daga haka TAIMIYYAH ta miƙawa Iyah wayar tana mata raɗa da cewa Hajiyar Gonar Ganye
ce,kamar yadda suka raɗawa Hajiyar tun randa sukai waya ta sanar da Iyah cewa a Gonar Ganye
suke zaune.Iyah ta amsa wayar suka gaisa ita dai TAIMIYYAH bata ji me Hajiyar ta sanar da Iyah
ba,ta dai ji Iyah na godia kafin ta miƙo mata wayar sukai sallama da TAIMIYYAH.
Lokacin da TAIMIYYAH ta aje wayar a jikinta ne ta dubi Iyah tana cewa, "Iyah gaskiya Hajiyar
nan akwaita da kirki cewa fa tayi lallai in faɗi me nake son ta kawo min gift ranan walima."
Iyah tayi murmushi tare da jinjina kai tana faɗin, "Wallahi Zainab nima na yaba da kirkin
matarnan Allah kaɗai yasan alkhairyn da yake nufi ya haɗamu ta hanyar gitta tsautsauyi a
tsakaninku,sosai kika shiga zuciyarta na ga alama,ai nina kirata ɗazu kina bacci na cika alƙawarin
dana ɗauka na cewa zan sanar mata idan lokacin walimar ya kusa,shiyasa kika ji ta kira ki yanzu."
TAIMIYYAH ta jinjina kai itama tana jin ƙaunar Hajiyar har cikin ranta,sabida yadda take nuna
mata ƙauna da kulawa.Suka cigaba da tattauna yadda hidiman walimar zai kasance,sai da kiran
Yah Deeku ya shigo wayar TAIMIYYAH ne sannan ta tashi ta nufi ɗaki,don ta san shima dai
zancen walimar yayen nasu zai mata,don tun jiya yake fama akan ta turo masa details ɗinta taƙi
don bata son ɗaura masa ɗawainiyar sai ya bata wani abu.
Sun daɗe suna magana tana faman bashi haƙury da cewa yanzu zata tura masa details ɗin, sabida
yadda ta ji ransa ya ɓaci.Suna ko gama wayar ta tura masa ko minti biyar ba a yi ba k sai ga alert
na 50k.
TAIMIYYAH tayi ta kiransa don tai masa complain akan kuɗin yayi yawa,amma sai yaƙi ɗauka
sai dai ta tura masa text message ɗauke da kalamai masu daɗi na godia.Ta fita da sauri don zuwa
ta sanarwa Iyah don ta taya ta godia wajen Yah Deekun........✍🏻
#Ɗansabo ce#
[12/14, 3:43 PM] +234 703 040 9541: *Littafin TAIMIYYAH paid book ne,ga duk wanda ta
tsincesa a kowani irin group ne,kiji tsoran Allah karki karanta sai kin biya 500 naira only.*
*Za ku iya min magana ta wannan number ɗin 08167768704, ko kuma ku turo kuɗin ku kai tsaye
ta wannan account ɗin*👇🏻
0504192664 aisha ibrahim dansabo GTbank.
Masu turo credit za ku turo katin MTN na 500 ta wannan line ɗin 08167768704.
_*Ina ƴan kasuwa masu buƙatar a tallata muku hajar ku? Maza ku garzayo da kuɗi ƙalilan a
tallata muku kayan siyarwanku sai dai kawai ku ji ana kiran waya don buƙatan sayan kayan ku,ku
tuntuɓeni ta layina kamar haka 08167768704.*_
*52*
Kwanakin da suka biyo baya gaba ɗaya TAIMIYYAH da Iyah sun maida hankali ne wajen shirye-
shiryen walimar kammala Haddar Qur'anin su TAIMIYYAH,ana gobe za a yi walimar Yasmeen da
Guggo Bilki suka iso daga Kano.
TAIMIYYAH suka rungume juna ita da Yasmeen,suna murnan ganin juna tamkar ba kusan kullum
sai sunyi vid call ba.
Da daddare bayan sun kammala cin abinci ne suka ƙule a ɗakin TAIMIYYAH don zantawa da
juna,sabida tunda suka iso ana ta kammala shiri ne sai yanxu ne suka samu time ɗin kaɗaicewa.
Yasmeen ta dubi TAIMIYYAH tace, "Sis kinsan ni duk na ƙosa muyi ido biyu da mara kunyar
Yarinyar can Basmah,ɗazu da naje sasan gaida Baba Sani ban ga kowa cikin su bane,dana tambayi
Umma sai cewa tayi basa nan wai sai gobe da safe za su dawo ma,ni kuma na sha alwashin kafin
in bar garinnan sai naji yadda akayi ta Ƙulla alaƙar soyayya da Nass har ga shi an sanya musu
ranar aure,wannan ai cin amanace kuma ni a yadda tunanina ya bani koda ace baku rabu don
mahaifiyarsa ta nuna ƙinki ba,dama can suna da wani manufa na son cin amanarki ne kawai."
TAIMIYYAH wacce take ta faman kauda kayayyakin gift data fara samu, ta dubi Yasmeen tana
cewa, "Yasmeen wallahi bana son jin zancen Basmah da Nass a yanzu,sabida na sanyasu cikin
wani littafi na daban na kulle dukkanin shafukansu,idan har zan iya baki shawara kema ki ɗauka
to don Allah kada kiyi mata maganar koda wasa,matuƙar ba fatan alkhairy kawai zaki yi ki kulle
bakinki ba,kinsan meyasa nace haka?"
Yasmeen ta girgiza kai alamun bata sani ba,TAIMIYYAH ta cigaba da faɗin, "Sabida babu wani
amfanin yin maganar ko neman ƙarin haske,don komi ya riga ya faru Yasmeen, yanzu ana zancen
irga kwanakin zuwan ranan aurene,don haka ni na daɗe da sallamawa tare da cire duk wani
soyayyar Nass da yai saura cikin zuciyata.Na barwa Allah komi idan har da zuciya biyu aka ƙulla
wannan al'amarin ina roƙo Ubangiji yayi min sakayya da sauyi mafi alkhairy cikin rayuwata,tunda
na rasa su Abie na cigaba da rayuwa cikin godian Ubangiji,to na riga na sawa raina babu wani
mahaluki da zai shigo ya fita cikin rayuwata da bazan iya jure rashinsa ba,tabbas na so Nass irin
soyayyar da ban taɓa tunanin zan yi wa wani ɗa namiji ba,na kuma ji ciwon wannan lamarin fiye
da tunaninki Yasmeen,amma a yanzu ji nake yi komi ya wuce har bani son tuna cewa wata alaƙar
soyayya ya taɓa shiga tsakanina da shi,tun daga randa aka raba goran sanya ranar aurensa da
Basmah na sake sallama cewa Nass ya riga da ya fita cikin rayuwata,don haka kema ina so ki kife
duk wani babi nasa. Wannan lamarin ya daina baki mamaki tunda a duniya muke,duniyar ma irin
wacce ake cikin wata rayuwa na son rai da fifita son zuciya,don haka kome akace ya faru mu
daina mamaki Yasmeen...."
TAIMIYYAH ta dakata da maganar tana duban yadda Yasmeen ta tsura mata ido babu ko
ƙiftawa.Sai ta saki smile tana cigaba da cewa, "Yasmeen duk wannan kallon fa?"
Yasmeen ta sauke numfashi kafin tace, "Hmm! Am Speechless TAIMIYYAH,ban san ma me
zance ba."
TAIMIYYAH ta jinjina kai tana cewa, "Haka nake so dama." Daga haka ta ɗakko wani zancen na
daban suka ɗaura, duk yadda Yasmeen ta so TAIMIYYAH ta bata haɗin kai su tinkari Basmah da
magana akan aurenta da Nass da za a ƙulla,TAIMIYYAH taƙi ba Yasmeen ɗin haɗin kai,ta kuma
roƙeta akan cewa don girman Allah ko a fuska bata son Basmah ta ga canji daga Yasmeen ɗin.
Washegary ƙarfe bakwai da rabi na safe TAIMIYYAH suka fita xuwa makarantar Haddar tasu.Su
Basmah ne dai da ba za a samu yaye su a wannan shekarar ba sabida sun sanya wasa,basu fita
gidan zuwa makarantar ba sai takwas da rabi.
Kafatanin ƴan gidan tun daga kan Iyah har zuwa su Babah Ladi duk sun halarci wajen bikin yayen
Mahaddatan.
Daga Ummie sai Umma da tace babu inda zata su kaɗai aka bari a gidan.Amma hatta Yah Sadeeq
daya shigo weekend don kawai ya halarci taron,duk sun je tare da wasu daga cikin ƴan Rimi can
Fam house ɗin su TAIMIYYAH,duk sun sama halartan taron.
Ƙarfe sha biyu na rana aka fara watsewa daga wajen taron, ɗalibai masu hazaƙa da suka fi sauran
ƴan uwansu Mahaddata ƙwazo sun kwashi uban kyatuttuka daga manyan baƙi mahalarta taron.
Cikin wanda suka samu manyan kyautuka TAIMIYYAH na sahun farko,don ta amsa manyan
kyautuka tun daga kan kuɗaɗe da suturu haɗi Qur'anai. Yah Sadeeq shine ya isa wajen bada
kyaututtukan ya taya TAIMIYYAH amsa,zuciyarsa cike da tarin farin cikin da bazai misaltuba.
Iyah ta kai bakin Hijab ɗinta ta goge hawayen farin cik lokacin da ta ga yadda ake baiwa
TAIMIYYAH kyatuka,tare da kwarzanta kwazonta na zamowarta cikin ɗalibar da ta fi sauran ƴan
uwanta ƙarfin hadda,tare da fitar da Tajweed a cikin ƙira'arta.
TAIMIYYAH sun dawo gida jikinta a matuƙar sanyaye yake,duk wannan tarin ƙaunar da aka nuna
mata,duk irin kara da bajintar da su Baba Sani suka nuna mata na son ganin sun faranta
zuciyarta,ji take yi akwai sauran wani gurbi me girman gaske da suka kasa cike mata shi. Ba kuma
kowane irin gurbi bane sai na kewan Abie da take ji me girma a wannan rana.
Zuciyarta cike take da farin ciki da bazai misaltu ba sabida wannan ranar yana ɗaya daga cikin
ranakun da ba za ta iya daina alfahari da su cikin rayuwarta na duniya ba. Amma tun daga sanda ta
ga Iyayen ƴan uwanta Mahaddata na cike da tarin farin ciki, taji cewa sun yi mata wani fami me
tsanani a cikin zuciyarta.
Kewan Abie me tsanani ya taso ya danne dukkanin tarin farin cikin da take ji a wannan rana,hakan
ya haifar mata da mutuwar jiki da wani irin rauni a zuciya har suka iso gida.
Ta nufi ɗakinta tana shigewa toilet ta rufo,ta jingin da bangon bayin hawaye na zubowa daga
idanunta masu tsananin zafi.
Muryar Abie ɗinta take son ji kamar tayi hauka,amma ta san babu halin hakan don ya riga yayi
mata nisan da ba za ta tadda shi ba sai a kiyama.
Ta sulale daga tsaye ta tsugumna tana kuka sosai,har sai da ta gaji ta rarrashi kanta ta share
hawayen, tare da gabatar da uzurinta ta ɗauro alwalar sallar azuhur ta fito.
Da Idanun su Maryam Sunusi da Zee ta fara cin karo, wanɗanda suka iso kusan a tare da juna.
TAIMIYYAH sai ta saki murmushi tana takowa zuwa cikin ɗakin take cewa, "Welcome my
friends ashe dai da gaske zaku samu zuwa ɗin."
Maryama ta dubi TAIMIYYAH wacce kallo ɗaya za kaiwa face ɗinta kasan ta sha kuka ta furta,
"Haba Besty me zai hanani zuwa ni kam,inba wani babbar uzuri ne ya taso min ba,me kuma ya
sanyaki kuka idanu suka kumbura haka?"
TAIMIYYAH ta sake narke fuska tana baiwa Maryama amsa da cewa, "Maryam na tuna Abie ne
kawai ina hasashen da yana raye wani irin farin ciki zai yi shi ma? Shiyasa na kasa daurewa sai da
nayi kukan na samu sauƙin ciwan da zuciyata ke min,sai yanzu ne nake gane cewa shi mutuwar
iyaye wata babbar jinyace da ba a warkewa sai dai aji sauƙi,Allah ya ƙara mana juriya da haƙury
kawai,su kuma Allah yasa suna Jannatul Firdaus."
Zee da Maryama suka haɗa baki wajen amsawa da cewa, "Ameen ya hayyu ya qayyum." Zee ta
ɗaura da faɗin,
"Sai haƙuri TAIMIYYAH amma tabbas rashin iyaye na da zafi duk da mu bamu san pain ɗin
ba,Mama tace tana gaisheki kuma tana taya ki murna, ga saƙonan ma tace akawo miki babu
yawa."
Zee ta kai ƙarshen maganar tana nunawa TAIMIYYAH ledar da ta aje akan gado.
TAIMIYYAH ta iso bakin gadon ta zauna kusa da Maryama tana cewa, "Allah sarki na gode
ƙwarai,dama ba tayi ɗawainiyar kawo komi ba Zee haba." Tayi maganar hannunta na buɗe
ledar,manyan idanunta suka sauka akan kyakykyawar atamfar da ke ciki.Ta dubi Zee da sauri tana
faɗin, "Kai Zee wannan ɗawainiya ai yayi yawa,an gode Allah saka ya bar zumunci."
Zee ta amsa da cewa, "Ameen qawata ni ma kuma ga nawa babu yawa." Zee tayi maganar tana
ciro wani ƙaramin kwali da akai raping wasu kyawawan Mug guda huɗu,an rubuta sunan
TAIMIYYAH a ciki ana wishing ɗinta Happy Qur'anic Graduation.
Wani irin farin ciki ne ya tsarga a zuciyar TAIMIYYAH sabida sun mata kyau Mugs ɗin,kuma
kana gani zaka san cewa wanda yayi aikin ƙwararrene.
Ta dubi Zee da tarin farin ciki akan fuskarta tana dinga zuba mata godia,Maryama itama tana taya
ta godian kafin ita ma ta ciro envilop daga cikin jaka ta ajewa TAIMIYYAH a jiki tana cewa, "Ga
namu gift ɗinnan babu yawa,ki sai duk abinda kike so inji Mummy. Ni kuma ga wasu fashion nan
kya yi kwalliya,Allah ya sanya albarka yasa anyi na tsoran Allah ne Besty."
Maryama ta ƙare maganr tana ajewa TAIMIYYAH fashions ɗin da ke cikin box
ɗinsu.TAIMIYYAH sai taji gaba ɗaya har ta rasa bakin magana, sabida irin yadda qawayen nata
ke faman nuna mata ƙauna,ta ɗaga manyan idanunta ta sauke akan Maryam tana mata godia har
hawaye na cika idanunta.
Daga haka ta tashi ta gabatar da sallah,ita ma Zee sallar ta gabatar kasancewar da alwalarta ta iso
gidan.
Maryam da ke off ne tayi kwance abinta tana danna wayarta, har zuwa lokacin da Yasmeen ta
shigo ɗakin dai-dai da idarwar TAIMIYYAH daga sallah.
Ta waiwaya ta dubi Yasmeen da ke gaisawa da Maryam tana cewa, "Yasmeen tunda muka dawo
kika ɓace a gidannan ina kuma kika kurɗa?"
Yasmeen ta saki dariya tana duban TAIMIYYAH take cewa, "Ina can sasan Ummie tana nuna min
kayan snacks da ta saka a aiko ta tasha tun daga Kaduna,ba kiji yadda cupcakes ɗin su kai daɗi ba
wallahi,an gode da ƙauna ƙwarai babu abinda zaki ce sai godia,domin an nuna miki ƙauna da kara
me tarin yawa."
TAIMIYYAH ta jinjina kai tana cewa, "Alhamdulillah! Alhamdulillah! Gaskiya an nuna min
ƙauna Allah kuma ya fini yabawa,kin ga abubuwan arziƙin da su Zee ma suka kawo min gasu nan
akan gado,ki ɗauka ki kaiwa Iyah ta gani kafin in fito yanzu,sai akawo musu abinci please
Yasmeen."
Yasmeen ta taya TAIMIYYAH godia tana kwasan kayan da kuɗin, wanda basu ma buɗe sun ga ko
nawa bane ta nufi ɗakin Iyah.
Daga Iyah sai Mamienta ne a ɗakin, Yasmeen ta zube kayan bisa bed ɗin Iyah,tana sanar mata
wanɗanda suka kawo wa TAIMIYYAH.
Iyah da Guggo Bilki suka duba tare da sanya albarka,Yasmeen ta bar kayan anan ɗakin Iyah,ta
wuce zuwa kitchen don kawai su Maryam abinci da lemu,haɗe da snacks ɗin da akayi don rabawa
mutane.
Misalin ƙarfe biyu kira ya shigo wayar TAIMIYYAH, ganin lambar Hajiya Aysha da tayi saving
da suna Hajiyar GG (Hajiyar Gonar Ganye) yasa ta ɗaga wayar ta kai kunni.
Maganan seconds tayi ta sauke wayar daga kunni, ta dubi Yasmeen da suke ta hira dasu Zee tace,
"Yasmeen wannan Hajiyar da nake baki labari wacce suka kaɗeni kwanaki,itace suka ƙariso bakin
layin shigowa nan,don Allah tashi ki rakani mu taho dasu,Allah sa dai kan layin shigowa nan ɗin
suka tsaya kamar yadda na basu address."
Yasmeen sai ta tashi tana zura Hijab akan kayan jikinta,ko wanka basu yi ba sai zuwa la'asar,
sabida ƙarfe huɗu akace za a fara gabatar da walimar.
Cikin sa a suna isa bakin layin TAIMIYYAH ta hango ƙatuwar motar da ta faka daga gefen
hanya.Ta nunawa Yasmeen motar tana cewa, "Yasmeen ga motarsu can mu ƙarisa."
Suka ƙarisa wajen motar lokacin da Shehu driver ya zuge glass ɗin ɓangarensa, yana wa
TAIMIYYAH magana akan cewa su shiga cikin motar kawai su ƙarisa.
Suka buɗe back seat inda Hajiya Aysha ke kame a ciki,TAIMIYYAH fuskarta ɗauke da murmushi
take gaida Hajiya Aysha.Yasmeen ma ta gaisheta ta amsa cike da fara'a idanunta akan
TAIMIYYAH dake kusa da ita take faɗin, "Daughter kice gidan naku ma babu wuyar
ganewa,sannu da ƙoƙari an taso ki ai da kin turo wani yazo ya taho damu kawai."
TAIMIYYAH ita dai sai faman blushing take yi har suka isa bakin gate ɗin gidan.
Yasmeen ce ta cewa Shehu ya tsaida motar sun ƙariso.
Ya tsaida motar duk suka yo waje har Hajiya Ayshan,wacce tace wa Shehu ya wuce da motar zuwa
ƙarfe biyar sai ya dawo ya ɗauke ta.
Suka rankaya zuwa cikin gidan nasu TAIMIYYAH, Hajiya Aysha nata faman bin ko'ina da
kallo,tana yaba tsarin ginin da ganin kyawunsa.Sabida gini ne standard irin na da me
inganci,wanda kuma yake samun kula da gyara akai-akai.
Ta cigaba da bin ƙaton compound ɗin da kallo, wanda ake ta faman arranging fararen kujerun da
mutane za su zauna akai.
Tana biye da bayan su TAIMIYYAH har zuwa ɓangaren Iyah, Yasmeen ce ta amshi jakar hannun
Hajiyar ta riƙe mata sabida nuna girmamawa.
Lokacin da suka dangana zuwa cikin falon Iyah,da tsananin murna ta ƙariso ta tarbi Hajiyar suka
ƙarisa cikin falon.
Iyah da farin cikinta ya kasa ɓoyuwa ta dinga jin ƙaunar Hajiyar da ganin ƙimarta, tare da yaba
karamci da ƙaunar da take nunawa akan TAIMIYYAH.
Su TAIMIYYAH bayan sun sake gaida Hajiyar sai suka shige zuwa ciki,suka barta da Iyah da
Guggo Bilki wacce itama ta fito tana wa Hajiyar barka da isowa.
Kanka ce kwabo an cika gaban Hajiya Aysha da kayan cima kala-kala, cikin abubuwan da aka
shirya don ciyar da mutanen da za a tara.
Iyah ta zauna suka fara hira kai kace sun shekara da sanin juna ne,sabida daga ita har Hajiyar
ma'abota son jama'a ne da faran-faran dasu.
Suna nan zaune suna hira baƙi suka fara zuwa ƴan Rimi da jama'an gari,tare da abokanan arziƙi da
Iyah ta gayyata,ganin hakan yasa Iyah janye Hajiya Aysha zuwa ɗakin baccinta tace tayi zamanta
anan.
"Bilkisu je ki Sasan Sani kice Zuwairah da yaranta su zo,idan kin fito daga nan kije itama Ummie
kice ta zo duk su gaisa da Hajiya Aisha."
Iyah ce ke maganar tana tsaye daga cikin kitchen ita da Guggo Bilki.Guggo Bilki ta duba Iyah
tana cewa, "To Iyah bari in je in kira su,na ga alama wannan Hajiya ta shiga ranki kamar yadda
itama na ga alamun tana ji da ku daga ke har TAIMIYYAH, gaskiya na jima ban ga mace me
mutunci irin ta ba, shiyasa ake cewa bawa ya dinga addu'a akan Allah ya haɗasa da masoyansa,sai
ki ga sanadi kaɗan ya haɗaka da mutanen arziƙi masu son ka da zuciya ɗaya."
Iyah ta jinjina kai tana cewa, "Bari kawai Bilki wallahi matar ta san darajar mutane akwai mutunci
matuƙa."
Guggo Bilki ta je ta isar da saƙon Iyah wajen su Ummie da Umma.Ummie dama ta gama shiryawa
cikin baƙar Abaya da ya amshi jikinta yayi mata kyau matuƙa,tana shirin fita zuwa sasan Iyah ne
Guggo Bilkin ta shigo,sai kawai suka rankaya tare suka fito zuwa sasan Iyan bayan Ummie ta yafa
mayafi a jikinta.
Gaggaisawa da mutanen dake zaune cikin falon Ummie tayi, waɗanda rabi duk ƴan Rimi ne can
FAM house ɗin su Abie,sai ta wuce zuwa ɗakin Iyah don ta miƙa gaisuwa wajen baƙuwar Iyah,
kamar yadda Guggo Bilki ta sanar mata.
Iyah na zaune daga bakin gado sai hira Hajiya Aysha ke mata, tana bata labarin mijinta da aka
kashe a garin Lagos,shekaru goma sha shida baya.Ummie tayi sallama ta shigo,hakan ya katse
hiran na su Iyah ta amsa sallamar Ummie ɗin tare da bata izinin shigowa,ta samu waje daga ƙasan
carfet ta zauna tana gaida Iyah,kafin ta juya tana gaida Hajiya Aysha wacce idanunta ke kan
Ummien.
Iyah ta dubi Hajiyar tana nuna Ummie da hannu take faɗin, "Wannan itace matar ɗan nawa daya
rasu mahaifin TAIMIYYAH,yaransu biyu mata a tsakani,kuma duk ajalin ya sauka musu rana
ɗaya watanni biyu kenan."
Hajiya Aysha ta jinjina kai cike da nuna jimami take cewa, "Allah sarki,Allah ya gafarta musu
yasa suna kyakykyawar matsayi, tabbas an muku rashi me ciwo sannu kinji,Allah ya ƙara miki
dangana."
Ummie da kanta ke ƙasa ta amsa da cewa, "Ameen." Tana miƙewa tace wa Iyah bari ta duba su
TAIMIYYAH a ɗakinsu.
Iyah ta jinjina kai tana cewa, "To badamuwa."
Ummie ta tashi zata fita daga ɗakin sai Hajiya Aysha tayi saurin cewa, "Don Allah ki ce da Zainab
ɗin idan sun gama shirin ta zo ina son ganinta."
Ummie ta amsa tana ficewa daga ɗakin Iyah,ta bar Iyah suna cigaba da magana da Hajiyan, Iyah
na sake bata labarin rasuwan ɗan nata Sameer.
Ummie ta zubawa TAIMIYYAH idanu tana kallon tsantsar kyawun da tayi cikin rantsatstsiyar
Abayar data sanya kalar Dark Coffee,wanda akaiwa ado a wuya da hannu zuwa ƙasar rigar da
kalar zare golden.
Tayi matuƙar yin kyau cikin Abayar yadda baki bazai misalta ba.Yasmeen ce ta siya musu iri ɗaya
sak don su yi anko da TAIMIYYAR,bambamcin kala ne kawai ya raba, amma komi iri ɗaya ne
shiyasa TAIMIYYAH ta aje wanda ta siya ta saka wannan ɗin, don yama fi wanda ta siya tsada
tunda Abban Yasmeen ɗin ne ya bata kuɗi masu nauyi ta siya musu a Algazaru.
Ummie ta dafa kafaɗun TAIMIYYAH tana cewa, "Daughter ki daina min godia ina jin wani iri a
raina,sai in dinga ji tamkar baki ɗauke ni matsayin uwa ba,bayan yanzu duk duniya ke kaɗai nake
ma kallon ƴa ina jin sanyi cikin zuciyata,kinyi kyau matuƙa Zainab Allah ya kawo mijin aure na
gari.Baƙuwar Iyah tace a sanar miki idan kin gama kintsawa ki sameta a ɗakin baccin Iyah,ni zan
koma sai anfara walimar zan sake fitowa,Allah yayi miki albarka ya jiƙan su Abie."
TAIMIYYAH da Yasmeen har ma dasu Maryama dake zaune cikin ɗakin suka amsa da cewa,
"Ameen." TAIMIYYAH na jin wani irin kewan Abie ɗin na danne zuciyarta,Ummie ma cikin sauri
ta bar ɗakin zuciyarta na motsawa da tarin kewa me tsanani na Sameer ɗin da yaranta su Raudha.
TAIMIYYAH ta ƙarisa shiryawa duk jikinta a sanyaye,su Maryama sai bin ta da kallo suke yi suna
yaba kyawun da TAIMIYYAH tayi.Zee ta kasa daurewa sai da ta tanka tana cewa, "Kai Namcy
wannan irin kyau haka,gaskiya ban taɓa ganin shigar da ke ɗaukar jikinki irin shigar Abaya
ba,tana yi miki kyau matuƙa da gaske,duk wanda zai aureki zan bashi shawara ya zubo mana su da
yawa cikin lefe."
TAIMIYYAH ta saki murmushi me faɗi tana faɗin, "Zee baki da dama wallahi."
Daga haka ta gama sanya ɗankunni tana fesa turarenta na GIORGIO PINK bayan body mist ɗin
data sanya daga ciki.Ɗakin ya buɗe da daddaɗan ƙamshi me kwantar da zuciya.
Lokacin da ta isa zuwa ɗakin Iyah, Hajiya Aysha ta samu zaune ita kaɗai,don Iyah na can na fama
da mutanen da suka fara taruwa.
TAIMIYYAH ta shiga cikin ɗakin tana tana takawa dafe da guiwar ƙafarta cikin nutsuwa.Idanun
Hajiya Aysha fes akanta tunda ta shigo har ta ƙariso bakin gadon Iyah ta zube daga ƙasa tana
cewa, "Sannu Hajiya,Ummie tace kina nema na."
Hajiya Aysha ta miƙa mata hannunta tana cewa, "Taho ki zauna nan kusa dani ƴata,tubarkallah
Masha Allah! Kin yi kyau sosai kamar na saceki na gudu da ke zuwa gidana Zainab."
Yadda Hajiya Aysha tayi maganar cike da nuna kulawa yasa TAIMIYYAH sakin murmushi,tana
tashi ta zauna daga bakin gadon,hannunta cikin na Hajiya Aysha da ta riƙe.
Hajiya Aysha ta saki hannun TAIMIYYAH tana janyo jakarta ta buɗe,ta ciro kuɗi rafar ƴan ɗari
biyu sabbi kar ta aje ajikin TAIMIYYAH,tare da ɗaurawa da wani ƙaramin box a saman kuɗin
tana cewa, " Ƴata gashinan babu yawa,wannan box ɗin ɗankunni ne a ciki ki cire wannan ki sanya
in gani, kuɗin kuma ki sayi wani abu tunda kinƙi sanar dani abinda kike so"
TAIMIYYAH baki buɗe take kallon kuɗin tama kasa magana,don bata san me xata cewa wannan
mata da tun haɗuwansu take ta nuna mata ƙauna ta zihiri ba.Ta dubi Hajiyan karon farko cikin ido
kafin ta ɗauke ganinta ta mayar kan box ɗin tana cewa, "Mama na gode Allah ƙara girma da
arziƙi,nama rasa wani irin godia zan yi Allah ya saka da alkhairy." Ta buɗe box ɗin tana ciro
madaidaicin ɗankunnin gwal dake faman sheƙi,ta ciro na kunninta ta sanya na gwal ɗin kamar
yadda Hajiyar ta buƙata.
Take fuskarta ya sake haskawa da wani irin kyawu mara misaltuwa,Hajiya Aysha ta murmusa tana
sake jin ƙaunar TAIMIYYAH na ratsa jinin jikinta.Ta buɗe baki tace, "Masha Allah Zainab Kin yi
kyau tubarkallah! Allah ya kawo miki nagartaccen miji me tsoran Allah."
TAIMIYYAH tayi ƙasa da kanta tana amsawa da "Ameen." cikin zuciyarta dai-dai lokacin kuma
Iyah ta shigo cikin ɗakin,ta tadda wannan abin arziƙi da Hajiya Aysha ta baiwa TAIMIYYAH,tayi
godia me tarin yawa tare da addu'an fatar alkhairy wa Hajiya Ayshan.
TAIMIYYAH sai ta baiwa Iyah kuɗin ta ajiye,ita kuma fito don koma zuwa ɗakinta,ta nunawa su
Yasmeen abin arziƙin da Hajiyan ta kawo mata........✍🏻
#Ɗansabo ce#
[12/14, 3:43 PM] +234 703 040 9541: *Littafin TAIMIYYAH paid book ne,ga duk wanda ta
tsincesa a kowani irin group ne,kiji tsoran Allah karki karanta sai kin biya 500 naira only.*
*Za ku iya min magana ta wannan number ɗin 08167768704, ko kuma ku turo kuɗin ku kai tsaye
ta wannan account ɗin*👇🏻
0504192664 aisha ibrahim dansabo GTbank.
Masu turo credit za ku turo katin MTN na 500 ta wannan line ɗin 08167768704.
_*Ina ƴan kasuwa masu buƙatar a tallata muku hajar ku? Maza ku garzayo da kuɗi ƙalilan a
tallata muku kayan siyarwanku sai dai kawai ku ji ana kiran waya don buƙatan sayan kayan ku,ku
tuntuɓeni ta layina kamar haka 08167768704.*_
*53*
" Yanzu Hajiya Fatima waɗannan ƴan matan ma duka jikokin ki ne?"
Hajiya Aysha ta tambayi Iyah idanunta akan Zuhurah da Basmah da sai yanzu suka busa iska ,suka
ga damar zuwa gaida Hajiya Ayshar bayan an tashi daga walimar.
Iyah ta dubi su Zuhurah tana balla musu hararan yadda suka tsare Hajiya Aysha da ido,kafin ta
furta, "Eh duk jikokina ne ƴan wajen Sani ƙanin mahaifin TAIMIYYAH,ga part ɗinsu can na farko
daga kin shigo gidan, wannan sunanta Zuhurah sai wannan Basmah."
Iyah tayi maganar tana pointing fuskar kowacce a cikinsu.Hajiya Aysha ta jinjina kai tana faɗin,
"Masha Allah,Allah yai musu albarka."
Iyah ta amsa da cewa, "Ameen." Tana me sallamar su Zuhurah da suka zurawa Hajiyan ido,tace su
tashi su tafi abinsu.
Bayan fitarsu ne take baiwa Hajiya Aysha labarin cewa dukansu an saka ranan aurensu watanni
uku masu zuwa ,ta ƙare maganar da cewa, "Mutumiyarki ne dai har yanzu Allah bai kawo
tsayayye ba,amma ina addu'a Allah ya kawo mata itama kafin nasu duk a haɗa ayi gaba ɗaya a
huta."
Hajiya Aysha ta jinjina kai tana cewa, "Insha Allah,Allah zai kawo nata itama,ai aure lokaci ne
kowa ka ga ya yi lokacinsa ne."
"Hakane Hajiya don da lokacin yayi ma da ita da Zuhurah za a fara sanyawa lokacin,sai aka samu
akasi maganar TAIMIYYAH bai je ko'ina ba uwar yaron ta nuna bata so ya auri gurguwa,sanadin
rabuwar tasu kenan,kuma cikin wani ikon Allah yaron ne wai kuma Basmah ƙanwarta za ta
aura....."
Iyah ta shiga zayyanewa Hajiya Aysha abinda ya faru tas,ta ƙare maganan da cewa, "Wallahi
Hajiya sai dana zubda hawayen tausayin Zainab akan wannan lamarin,da ƙyar da lallami na dinga
bata ƙwarin guiwa akan tayi haƙury, ta ɗauki hakan a matsayin ƙaddara da kuma jarabawa,su
kuma idan da gayya suka shirya wannan lamari Ubangiji ba zai barsu haka ba."
Hajiya da jikinta yayi wani irin sanyi, ta dubi Iyah tana faɗin, "Allah sarki Zainab baki ji yadda na
sake jin tausayinta a cikin zuciyata ba,anya ko mutanennan na jin tsoron Mahaliccinsu kuwa?
Meyasa duniya ya zama babu gaskiya ne sai son zuciya da cin amanar juna? Amma bakomi
watakila Ubangiji yayi nufin nuna musu ikonsa ne da nuna musu cewa ita ɗin ba banza bace,Insha
Allah sai ta auri miji na nunawa sa a, wanda sai sun zubda hawayen tausayin kansu da kansu tare
da yin nadaman da bazai taɓa anfanar da su komi ba.Ai shi cin amana duk wanda yayisa ƙarya
yake yace zai samu yadda yake so,kamar yadda kika ce ne a zuba musu ido ai Ubangiji baya bacci
kuma yasan zukatan kowannan mu."
Hajiya Aysha na maganar ne cike da jin ciwo da zafin abinda ya faru da TAIMIYYAH.Iyah ta
ɗaura da nata sharhin suna ta yi har Shehu ya iso don tafiya da Hajiyan,basu daina tattaunawa
akan batun TAIMIYYAH da yadda tun asali dama Umma ke gwada mata ƙiyayyah ba.
Sai da Yasmeen ta shigo ta sanar da Iyah cewa driver ɗin Hajiyan yazo,sannan suka katse hiran
Iyah na tashi ta fito zuwa kitchen tana kiran sunan Guggo Bilki dake zaune a falo.
Guggo Bilki ta samu Iyah a ckin kitchen suka kammala shiryawa Hajiya Aysha abubuwan da suka
tanadar don bata ta tafi da shi.Iyah tayi kiran Babah Ladi ta ɗakko kulolin Hajiyan da suka taho da
shi daga asibiti,aka tattara komi Yasmeen da Ladi suka kai wajen motar Hajiyar dake fake a bakin
gate.
Iyah da TAIMIYYAH suka rako Hajiya Aysha har bakin mota suna mata godia,ta dubi
TAIMIYYAH tana me kama hannunta tac, "Daughter yaushe zaku kawo min ziyara ke da Iyar
taki?"
TAIMIYYAH ta saki murmushi tana duban Iyah dake saurarensu tace, "Insha Allah idan Iyah ta
sanya lokaci sai mu kira waya."
"To Allah ya amince ya baku ikon zuwa ,don kuwa zan yi matuƙar farin ciki da hakan."
Cewan Hajiya Aysha tana duban Iyah ta cigaba da cewa, "To Iyah sai mun waya, Allah ya yi wa
karatunta albarka ya bada miji me tsoran Allah."
Iyah ta amsa da cewa, "Ameen." Tana cigaba da kwararawa Hajiya Aysha godia akan abin arziƙin
da tayi wa TAIMIYYAH.
Sai da suka ga tashin motar su Hajiyar suka juyo zuwa cikin gida,suna ta magana akan kirki da
karamcin matar.
Zuwa magriba taron ya ida watsewa baki ɗaya,su Zee da su Maryam Sunusi duk sun tafi suma,aka
bar su Yasmeen da Babah Ladi da gyaran wuri.
TAIMIYYAH ta samu tarin abin arziƙi daga ƴan uwa da abokan arziƙi.Yasmeen ta dinga bubbuɗe
abubuwan da TAIMIYYAH ta samu suna sanya albarka,su Umma dai ko hanki bata cewa
TAIMIYYAH gashi ba.
Washegarin ranar Guggo Bilki da Yasmeen suka juya zuwa Kano,TAIMIYYAH sai taji tamkar
Yasmeen ta zauna amma babu halin hakan.
Kwanaki sun cigaba da shurawa tarin abubuwa na faruwa cikin aminci da ƙuduran Ubangiji.
TAIMIYYAH sai ta ɗauki hankalinta kacokan ta miƙa ga karatun Computer ɗin ta da take zuwa.Ta
cire duk wani abu da zai damu zuciyarta ta aje sa a gefe,da zaran ta dawo skull to zaka sameta
wajen Ummie, wacce a yanzu sukai wata irin shaƙuwa da TAIMIYYAH.Tana janyo ta ajiki sosai
tare da nuna mata ƙauna ta ban mamaki,hakan kuma ya yiwa Iyah daɗi sosai a zuciyarta.
Hakan sai ya sake jefa kishi da hassadar Ummien cikin zuciyar Umma,ba tayi la'akari da abinda
mijinta shima ya samu ba.Idanunta na kan abinda su TAIMIYYAH suka gada ne kawai,tana sake
sanya jin tsanarsu a zuciyarta me tsanani.
TAIMIYYAH ma kusan duk friday sai ta kira Hajiyan sun gaisa,hakan kuma nawa Hajiya Aysha
daɗi a zuciyarta.Kamar yadda kullum kwanan duniya take jin ƙarin ƙaunar TAIMIYYAH a cikin
ranta,tana kuma kisima abubuwa da yawa cikin zuciyarta dangane da TAIMIYYAR,tare da
addu'an Allah ya gwada mata alkhairy, akan abinda zuciyarta ke kisima mata akan yarinyar sabida
yadda ta shiga ranta farat ɗaya....
____________
*1 Month Later.*
Maleek Ado ne zaune daga cikin falon Hajjah,isowar sa garin kenan ko mintuna goma bai yi ba.
Daga gefensa Hajjah ce zaune tana amsa call, shi kuma yayi zaman dirshan a gabanta.
Lokacin da ta kammala amsa wayar ne ta sauke idanunta akan Maleek ɗin tana cewa,
"Abdulmaleek lafiya dai na ga baka da walwala ko duk gajiya ce?"
A.Maleek ya ɗaga manyan idanunsa ya sauke akan Hajjah yana sake ɓata fuska,ya buɗe baki
kaman me yin raɗa yana cewa, "Wallahi Hajjah na gaji ne, satinnan gaba ɗaya har ya ƙare ban
samu wani isasshen hutu ba,ai dai ta tayamu da addu'a amma wannan muƙami da aka bani ji nake
tamkar in ajesa,gaba ɗaya harka da ƴan kudu akwai haɗari, an sanya min ido sosai a wajen
Hajjah."
Yadda yayi maganar cike da rauni yasa Hajjah dubansa da fuskar tausayi tana cewa, "Kayi haƙury
Maleek shi ɗaukaka ya gaji haka,duk wanda Ubangiji yai wa wata baiwa ko ɗaukaka to fa kullum
rayuwarsa na cikin jarabawane kala-kala,matuƙar akwai imani a zuciyarsa.Don haka kayi haƙury
ka daina zancen cewa kamar a amshe muƙamin daga gareka,hakan tamkar butulcewa Ubangijin da
ya baka ne.Addu'a kuma kullum cikinsa muke ba dare ba rana,muna kuma da yaƙinin Allah na
jinmu kuma zai amsa mana,babu abinda zai faru zaka rabu da su lafiya da izinin Ubangiji,yanzu
dai ga abinci can an shirya maka a dining idan kaci sai ka huta da kyau,don ina da wata
muhimmiyar magana da nake so mu tattauna da kai,shiyasa kaga na ƙagu ka zo garin don mu
tattauna gani ga gaka."
Hajjah ta kai ƙarshen maganar idanunta akan tilon ɗan nata Maleek Ado,wanda ya wani sake
shagwaɓe fuska kamar ƙaramin yaro.
Cikin muryansa me cike da ƙasaita yake faɗin, "To Hajjah bari inci abincin amma a kira Lubah
tazo ta sauko su nan ƙasa bazan hau dining ba."
Hajjah ta ciri murya ta kira Lubah don ta zo tai masa duk yadda yake so ɗin.Cikin ƙanƙanin lokaci
Lubah ta iso cikin falon ta zube a gaban Maleek ta kwashi gaisuwa,hannu kawai ya ɗaga mata
alamun ya amsa, sannan ta tashi ta fara ɗakko kulolin abincin ta jeresu nan tsakiyar carfet.
Tana kammalawa ta wuce ta basu waje,yayi saura daga Hajjah sai shi a cikin falon.
Da kansa ya zuzzuba abinda yayi masa cikin abinci kala uku da aka shirya masa.
Hajjah ta miƙe tana dubansa tace, "Ai ɗazu mun yi waya da Suhailah tana so ka wuce muku da
garin kunu idan zaka juya,Allah yasa jiya Babah Rabi ta kammala tankaɗesa ya yini a rana, tunda
anci sa a anyi ban iska ba ai ruwa ba."
Maleek ya dubi Hajjah kawai ba tare da yace komi ba har Hajjan ta shige ɗaki.Ya cigaba da cin
abincinsa lokaci-lokaci ya kan amsa kiran da ke shigowa wayarsa, a haka har ya ƙare cin
abincin ,ya tashi daga wajen ya koma kan seater ya zauna.
Lokacin da Hajjah ta fito daga ɗaki samun sa tayi yana ta faman amsa waya da harshen Nasara.
Ta ƙariso tana zama cikin seatern da ke facing ɗinsa, hankalinta na kan TV da ke ta faman aiki
cikin falon,har ya kammala amsa call ɗin yana sauke ganinsa akan Hajjan yake cewa, "Hajjah ina
so a sake yin garin ɗan-wakennan wanda akai mana yayi daɗi sosai,sai dai kinsan Suhailah da
kyuiyan yinsa ina ga shiyasa bata sanar miki ya ƙare ba ko?"
Hajjah ta dubesa da murmushi saman fuskarta tace, "Aiko bata faɗi ba amma tunda sai zuwa jibi
zaka wuce za a yi Insha Allah."
Maleek ya jinjina kai yana faɗin, "Okey Hajjah thank u,Allah ƙara muku tsawancin kwana me
anfani."
"Ameen Maleek ku ma Allah ya cigaba da yiwa rayuwarku albarka ya kawo zuriya masu albarka."
Hajjah ta kirayi sunansa kai tsaye kafin ta sake zama so serious tana cewa, "Abdulmaleek ina
buƙatar dukkanin nutsuwarka anan,don abinda zan sanar da kai yana da matuƙar muhimmanci a
wajena."
Maleek ya ɗaga manyan idanunsa ya sauke akan Hajjah,yana ganin yadda taci serious yasan lallai
duk abinda take so su tattauna me muhimmanci ne kamar yadda ta faɗi.Sai ya nutsu sosai tare da
maida dukkanin hankalinsa kanta yana cewa, "Ina jinki Hajjah Bismillah."
Hajjah ta jinjina kai tana me farawa da bashi labari tun daga kan kaɗe TAIMIYYAH da sukai da
mota, har kawo aminci da zumuntar da ya shiga tsakaninta da su.Ta ƙare maganan da cewa,
"Maleek ba wani abu nake so ba illah kai min alfarma ka je ka ga Zainab TAIMIYYAH,idan har
ka ji tayi maka zaka iya zama da ita a matsayin mata,zan so ka nemi aurenta.Wannan shi kaɗai ne
ƙarshen alfarman da nake ji zaka sake min arayuwa ka faranta zuciyata har in cigaba da alfahari da
samun ɗa kamarka.Kai kaɗai na mallaka a duniya da zan iya iko da kai in kuma roƙi alfarma kayi
min ba tare da raina ya ɓaci ba,na so a ce Ubangiji ya bani wani ɗan wanda bai taɓa aure ba don in
saka shi ya aure ta amma Allah kai kaɗai ya mallaka min."
Hajjah ta ɗan dakata kaɗan tana duban fuskar Maleek Ado, wanda ya zuba mata ido yana sauraren
dukkanin kamalamanta. Sai Hajjah ta kasa gane wani yanayi yake ciki, don shi yana cikin irin
mutanen da suka iya riƙe kansu,duk iya yadda zance zai girgiza zuciyarsa zai yi wuya ka gane
hakan akan fuskarsa.Hakan yasa Hajjah cigaba da cewa, "Maleek TAIMIYYAH gurguwace kuma
marainiya da ta rasa uwa da uba,amma ta mallaki tarin abubuwan da duk namijin da yasan kansa
zai yi alfahari da samunta a matsayin matar aurensa,Mahaddaciya Qur'anice me tarin nutsuwa da
hankali,wacce ta samu tarbiyyah me kyau daga kakarta na wajen uba,wacce ta raineta tun tana
taumman goyo,don haka ina so a gobe ka wanke ƙafa ka je ka ganta,dukkanin abinda zuciyarka ta
yanke akanta ka zo ka sameni ka sanar dani."
Maleek da ke sauraren Hajjah yana dinga nanata kalmar gurguwa cikin kwanyansa kafin ya ɗaga
manyan idanunsa yana kallon fuskar Hajjar,Yayi karfin halin fara faɗin, "Shikenan Hajjah zan yi
duk yadda kika ce, amma Hajjah wannan karon kuma da gurguwa kika ga na dace?"
Hajjah ta dubi Maleek cikin ido, tana hango ruɗanin da kamalamanta suka jefa zuciyarsa a
ciki.Ƙarfin hali kawai yayi wajen amsa mata buƙatarta ba tareda yayi mata musu ba,don abune da
bai taɓa yi ba bata taɓa sanya kara ya tsallake ba,shi ɗin me tarin biyayyane akan dukkanin abinda
ta nuna tana so.
Ta jinjina kai tana cewa, "Maleek karka bari kalmar gurguwa ya jefa wani abu a cikin
zuciyarka,don kai da ita duka a wajen Ubangiji ɗaya kuke,bai jarabeta da zama gurguwa don baya
ƙaunarta ba,kamar yadda kai da kake lafiyayye ba zaɓinka bane,shine ya so ka kasance a haka,don
haka abinda za ka fara dubawa da tambayata shine, 'me ya ja hankalina akanta har nake sha'awar
haɗa jini da ita? Wannan amsar kuma kai ne zaka baiwa kanka ita, bayan ka je kun yi ido biyu da
TAIMIYYAH.
Hajjah ta kai ƙarshen maganar idanunta akan Maleek, tana jifansa da wani irin murmushi.Ya
lumshe idanunsa yana jin wani abu na dokawa a cikin kansa,kalmar gurguwa da suna
TAIMIYYAH na amsa-kuwwa cikin kwanyansa da ƙarfin gaske.
Ya buɗe idanun nasa yana sauke su akan Hajjah,cikin son ɓoye dukkanin ruɗanin da ya shiga yake
cewa, "Shikenan Hajjah za a yi yadda kika ce,a kullum mu masu biyayyah ne akan duk abinda
kuke so."
"Allah yayi maka albarka Maleek,Allah kuma ya baku zuriyar da zasu bi ku kamar yadda ku ke
min biyayyah,ban yi maka tayin zuwa ka ga TAIMIYYAH don in tirsasaka aurenta akan dole
ba,duk abinda ka ji a zuciyarka idan ka haɗu da ita ka sanar dani Maleek,kuma ina so ka je a
matsayin kaine ka kai kanka gareta,sam bana so su san ina da alaƙa da kai har sai ka ji cewa tayi
maka,kuma idan ka tashi zuwa kada ka je a motar da zai nuna matsayinka,ina fata ka gane duk
yanda nake nufi?"
Maleek ya jinjina kai cike da gamsuwa yake cewa, "Na gane Hajjah,bari in shiga daga ɗaya
bedroom ɗin in kwanta ina buƙatan hutu zuwa la'asar."
Daga haka ya wuce Hajjah zuwa ɗaya ɗakinta wanda Suhailah ta zauna lokacin tana gida....✍🏻
#Ɗansabo ce#
#Ɗansabo ce"
[12/14, 3:43 PM] +234 703 040 9541: Littafin TAIMIYYAH paid book ne,ga duk wanda ta
tsincesa a kowani irin group ne,kiji tsoran Allah karki karanta sai kin biya 500 naira only.
Za ku iya min magana ta wannan number ɗin 08167768704, ko kuma ku turo kuɗin ku kai tsaye ta
wannan account ɗin 0504192664 aisha ibrahim dansabo GTbank.*
Masu turo credit za ku turo katin MTN na 500 ta wannan line ɗin 08167768704.
_Ina ƴan kasuwa masu buƙatar a tallata muku hajar ku? Maza ku garzayo da kuɗi ƙalilan a tallata
muku kayan siyarwanku sai dai kawai ku ji ana kiran waya don buƙatan sayan kayan ku,ku
tuntuɓeni ta layina kamar haka 08167768704._
*54*
Kwanciya yayi tare da lumshe manyan idanunsa,maganganun Hajjah na dawo masa daki-daki.Ko
kaɗan baccin da yayi tunanin zai iya yi bai samu yi ba,sai ma tarin tunani da suka dabaibaye
kwanyarsa.
Haka ya cigaba da kwanciya time to time ya kan amsa call ɗin da ya ga zai iya ɗagawa,a haka
lokaci ya ja ƙwaƙwalwarsa na cike da tarin tunanin yadda zai fuskanci gobe.
Bayan ya dawo daga masallaci sallar la'asar ne yayi wa Hajjah sallama, akan zai je wajen wani
aminin mahaifinsa ya gaishe shi,daga can kuma zai wuce gidansu na GRA a can zai kwana.
Hajjah tayi masa fatan Allah tsare tare da jaddada masa maganar zuwa Gyallesu a goben,kamar
yadda ta roƙi alfarma ya kuma amsa mata.
___________
TAIMIYYAH da Iyah ne a zaune suna hiran su cikin falon Iyan,daga gefe ɗaya Babah Ladi ce ta
maida hankali kan kallon wa'azin da ake haskawa a tashar ManaraTV.
TAIMIYYAH na sanyene cikin wata free gown na atamfar Chiganvy Gold,kalar atamfar red and
black ne da ya yi matuƙar yi mata kyau tare da haske farar fatarta.Sallamar Zuhurah da shigowarta
cikin falon Iyah,ya sanya TAIMIYYAH ɗaga manyan idanunta ta sauke akan Zuhran,wacce taci
uban ado kamar zata biki.
Fuskarnan ya sha make-up ,kamar yadda kayan jikin natasuka fidda shape ɗinta sosai a waje,ta
ƙariso cikin falon tana gaida Iyah daga tsaye.
Iyah ta dubeta tana amsa gaisuwan a dake,Zuhurah ta ɗaura da faɗin, "Iyah dama Ameeru ne zai
shigo ku gaisa yanzu."
Iyah ta dubi Zuhurah cikin ido kafin ta furta, "To madallah." Daga haka bata sake cewa komi ba
har Zuhurah ta juya ta fice,ba tare da tace wa TAIMIYYAH kanzil ba.
Tsam TAIMIYYAH ta miƙe tana ɗaukar wayarta don shigewa ɗaki,amma sai Iyah ta dakatar da ita
tana cewa, "Koma kiyi zamanki Zainab,kema ke gansa ku gaisa ai."
TAIMIYYAH ta buɗe baki cike da shagwaɓa tace, "Kai Iyah nina ce miki ina son ganinsa? Ni dai
da kin barni na yi shigewata ɗaki."
Kafin Iyah tace komi sallamar su Zuhurah ya karaɗe bakin ƙofar shigowa falon,hakan yasa
TAIMIYYAH sake ɓata face.Iyah ta amsa sallamar tana basu umurunin shigowa cikin falon,suka
shigo Zuhurah na kan gaba Ameerun na biye da bayanta.
Ya zube ya kwashi gaisuwa wajen Iyah wacce take binsa da kallo tun shigowanrsu.
Ta amsa gaisuwar Ameeru cike da fara'a, tana tambayarsa iyayen nasa,ya amsawa Iyah idanunsa a
kan TAIMIYYAH dake zaune cikin kujeran dake facing ɗinsa.
TAIMIYYAH ta buɗe baki ta gaida shi cikin sanyin muryarta,ya amsa yana sake binta da wani irin
kallo na ƙurillah.Hakan yasa ranta ya sake ɓaci da hanata tafiya da Iyah tayi,Iyah ta sanya Babah
Ladi ta kawo masa lemu amma sai ya miƙe yana cewa tafiya zai yi.
Hakan yasa Iyah yi masa fatan alkhairy,ya isa wajen da take zaune ya aje mata kuɗi masu
yawa,duk kuma yadda Iyah tayi da shi akan ya ɗauke kuɗinsa ƙi yayi.
Hakanan Iyah tayi masa godia da sanya albarka,suka fice Zuhurah na biye da bayansa kamar jela.
Suna fita TAIMIYYAH ta miƙe tayi shigewarta ɗaki,don bata ma so Iyah ta ɗakko wani zance
akan Ameerun, wanda ita kallon farko da tayi masa sam bai kwanta mata ba.Bata kuma hango
dacewarsa da ƴar uwar nata ba sam,amma sai tayi musu fatan alkhairy cikin zuciyarta,tare da
addu'an Allah yayi mata zaɓi itama mafi alkhairy cikin nata rayuwar.
Har suka zauna cin abincin dare TAIMIYYAH taƙi tanka Iyah akan zancen Ameeru,wanda Iyah ke
ta faman mitan ita dai yaron yai mata kama da irin mazannan marasa kamun kai.TAIMIYYAH sai
tayi murmushi kawai tana cewa Iyah, "Ke dai Iyah kiyi fatan alkhairy kawai tunda dai an riga an
sanya lokaci,kuma ita shi ta ga yayi mata,shi take so kin ga kenan koma ya yake tana son
kayanta."
"Hakane kuma Zainabu,miye nawa a ciki yaran da basa ganin ƙimarka da darajarka a matsayin
wacce ta kawo ubansu duniya,ai sai suyi tayi Allah bada sa a ya sanya alkhairy."
TAIMIYYAH tayi saurin amsawa da, "Ameen." Tana ɗaurawa da faɗin, "Iyah ya maganar xuwa
gidan Mamar Gonan Ganyen?"
Iyah tayi saurin duban TAIMIYYAH tana cewa, "Oh! Ni Iyah wallahi kaman kinsan abinda nake
ta tunani a raina kenan,ina ga za mu zuwa sati me xuwa Insha Allah,so nake yi ki ɗan yi ko irin
cake ɗinnan na ƴan takaddu da Doughnut ɗinnan me laushi sai akai mata ko baƙi ta dinga ba."
TAIMIYYAH ta jinjina kai tace, "To shikenan Iyah Allah shi kaimu lafiya,sai ayi mata ai tunda
weekend ne za mu Insha Allah."
Daga haka suka cigaba da hira da Iyah,har sai da agogo ya buga ƙarfe tara sannan TAIMIYYAH
tayi wa Iyah sai da safe,ta shige zuwa ɗakinta.
Bata kwanta ba sai da ta gama karanta sabon novel ɗin da ta siya me suna NAHUCE,na Sumayyah
Abdulƙadir Takory, (Gwanata kenan a kaf marubuta littafan Hausa,Allah ya ƙara ɗaukaka Anty
Takory).
Bayan ta kammala ne ta miƙe ta ɗauro alwala ta zo ta kwanta,tana jin wani irin shauƙi na kewaye
zuciyarta,bata jima da kwanciya ba bacci ya saceta ba tare da ɓata lokaci ba.
___________
*GRA,Zaria.*
*09:48am*
Maleek Ado ne zaune cikin falonsa na ƙasa yana karin kumallon safe,wanda Hajjah ce ta shiryo
abincin Shehu ya kawo masa.
Yana cin abincin ne suna vid call da Suhailah,wacce ke ta faman narke masa wai bata da lafiya,ta
tashi da zazzaɓi ne gashi tace masa bata ma sha magani ba.
"Please wife ya isa haka kukan,ki tashi ki sha magani idan bai yi ba,ki wuce asibiti da driver kin ji
ko?"
A.Maleek yayi maganar idanunsa akan face ɗin Suhailah,ta sake zararo hawaye lokacin da ta yaye
duvet ɗin da ta rufe jikinta dashi.Take kuma fingilwan rigar da ke jikinta ya bayyana,hakan yasa
Maleek sake manna idanunsa bisa allon screen ɗin wayarsa,yana kallon yadda ƙirjinta ya bayyana
sosai a waje.Yayi magana cikin low voice yana cewa, "Baby kina son sani a damuwa ne ko?
Bayan kinsan a matse na taho nan ɗin,kin yi tsarki ne?"
Suhailah dake duban face ɗin Maleek ta share hawayen da ke zuba,tana gyaɗa masa kai tace, "Yes
my Maleek ɗazu na yi wanka,goben za ka dawo ko sai jibin?"
Maleek ya ɗan lumshe idanunsa sabida yadda Suhailah ke son kunna shi,gaba ɗaya ta riga ta san
lagonsa babu abinda ke saurin tada sha'awarsa kamar ya ga breast ɗinta a waje.Ya buɗe idanun ya
sauke akan inda yake ɗaukar hankalinsa,sannan ya buɗe baki yace, "No sai jibi daga wajen
meeting zan ƙariso gida,na sanar miki zamuyi meeting da Minister jibi,please wife ki tashi ki je ki
sha magani."
Maleek yayi maganar yana haɗe face yadda Suhailah ba za ta yi masa musu ba,ta kuwa ɓata fuska
tana dubansa tace, "Korata kake yi Baby bayan nima nayi missing ɗinka."
"Suhailah kina son in shiga wani hali ne alhali bama kusa bare in rage zafi,please ki je ki sha
magani za mu yi waya anjima kaɗan, yanzu nima wanka zan yi akwai baƙin da zan gani kafin na
wuce zuwa gidan Hajjah."
Daga haka ya kashe wayar kawai don yasan idan ya biye mata za ta yi ta kunna shi ne kawai,Ya
cigaba da cin abincin yana jin kewarta me yawa na lulluɓe zuciyarsa.
Lokacin da ya kammala cin abincin direct sama ya nufa,ya since kayan jikinsa ya wuce zuwa
toilet don yin wanka.
Koda ya fito cikin sauri-sauri ya shirya cikin manyan kaya da suka amsa jikinsa,ya feshe jikinsa
da tutaren AMOUAGE daddaɗan ƙamshinsa ya cika ɗakin.
Kiran wayarsa da akayi yasa shi isa inda ya zube wayoyin nasa,ya ɗauki wanda kira ya shigo ciki
ya kai kunni.
Maganar minti ɗaya yayi ya aje wayer yana nufan wajen wata drawer, ya ciro kuɗaɗe masu yawa
ya zura cikin aljihu,sannan ya kwashi wayoyinsa ya fito don sauka zuwa falon ƙasa inda zai gana
da mutanen da ke jiransa.
Da wani mutum da zai ba kwangilar kai abinci gidajen marayu ya fara ganawa,ya sallameshi
bayan ya turo masa kuɗi ta account.Daga nan ya fara ganawa da mutanen da ke jiransa daga
waje,yana sallamansu da kuɗi kamar yadda ya saba,in dai ya shigo gari aka san yazo to shikenan
fa bai da sauran sukuni,mutane ƴan maula da masu tarin matsaloli ne za su yi ta zuwa,shi kuma
baya gajiya da bayarwa.Shiyasa shi ma tunda Ubangiji ya yi masa arziƙi bai taɓa gajiya da
bayarwa ba,kuma Allah bai taɓa nuna masa ranan da za a zo a tsaya masa yace ya rasa abin
badawa ba.
Bai samu kansa sai kusan ƙarfe ɗaya na rana,shiyasa bai ma tsaya cewa zai jira yin sallah a
masallacin da dake jikin ƙaton gidan nasa ba,ya wuce kawai don zuwa gidan Hajjah.
Kafin ya ƙarisa cikin Gonar Ganye ɗin sai da ya tsaya ya samu jam'i a masallacin dake bakin titin
shiga kwanar gidan Hajjah ɗin.
Bayan an idar ne ya ƙarisa zuwa gidan Hajjah yayi horn mai gadi ya buɗe masa gate ya shige.
Sai lokacin da yake tinkaran entrance na shiga cikin gidan,zuciyarsa ta tunasar da shi alqawarin da
ya yiwa Hajjah na zuwa ya ga gurguwarta.Wani abu ya taɓa zuciyarsa yana jin gaba ɗaya jikinsa
na mutuwa,don tun daren jiya yake neman hanyar da zai iya sillewa Hajjah amma ya rasa,ya riga
ya amsa mata zai je ɗin dole ne kuma ya cika wannan alqawarin.
Ya samu Hajjah tare da wasu baƙi biyu lokacin da ya shiga,hakan yasa suna gaisawa da baƙin ya
wuce zuwa cikin ɗakin Hajjah.
Akan gadonta ya zauna yana aje wayoyinsa,ya wani lumshe ido yana furzar da iska daga
bakinsa,kafin ya ɗauki wayarsa ɗaya ya shiga neman layin Suhailah.
Bugu biyu ta ɗaga wayar ya fara da tambayarta jikinta,yayi ɗan jim kafin yayi magana cikin isarsa
da ƙasaita yace, "Alright! Sai ki shirya ku wuce zuwa asibiti,ki yi haƙury Suhailah bana son
wannan kukan kina ɗagamin hankali,zan dawo gobe na fasa kaiwa jibin okey."
Ya sake yin jim kafin yace, "Okey sorry zai tafi Insha Allah,ku dai je asibitin in kun isa ki kirani
bye Allah ya baki lafiya."
Daga haka ya yi hanging up yana maida idanunsa ya lumshe,dai-dai lokacin da Hajjah ke sanyo
kanta cikin ɗakin.Ta sauke idanunta akan Maleek ɗin tana cewa, "Maleek lafiya dai?"
A.Maleek ya buɗe manyan idanunsa ya sauke akan Hajjah,kafin ya ɗan saki murmushi kaɗan yana
cewa, "Lafiya lau Hajjah,Suhailah ce ke son dagulamin lissafi zazzaɓi take yi taƙi kuma shan
magani sai kuka,kin san halin ciwanta da raki da shagwaɓar tsiya,yanzu nace lallai su wuce asibiti
tunda ga driver nan a gidan."
Hajjah ta zauna bakin gado tana cewa, "Subhanallah! Allah ya bata lafiya,ai Suhailah ita ciwanta
ban haushi ne da shi,bata son sha magani to ina ko za a samu sauƙi da sauri,gara dai ka matsa mata
su je asibitin a duba ta,zazzaɓin ake tayi ko'ina sai dai fatan Allah yaye wahala kawai."
Maleek ya jinjina kai yana cewa, "Hakane Hajjah,karki damu na sanar mata su wuce asibitin
yanzu,da zaran sun isa za ta kira ni,akwai fura ne a fridge Hajjah?"
Hajjah ta dubesa tana gyaɗa kai take cewa, "Akwai bata da yawa amma,mu je daga falo sai Lubah
ta ɗakko maka,baƙin sun tafi ai."
Suka fito tare da Hajjah zuwa cikin falon nata,ta ciri murya ta kira Lubah tare da bata umurnin
ɗakkowa Maleek Furan da bata da rabo da shi cikin fridge.Lubah ta kawo furan ta aje tana kwasan
gaisuwa,kafin ta miƙe ta bar wajen tana jinjina halin tilon ɗan Hajiyar,wanda suke gulmarsa akan
cewa ya cika miskilanci,sai dai yana da kyauta don suna dafa kuɗaɗe duk idan zai wuce sai ya
musu rabon kuɗi.
"Abdul-maleek ina fata kana sane da zancenmu na jiya,ƙarfe nawa ka yanke shawaran za ku je
ɗin? Ga dai Shehu driver nan da shi zaku don shi ya kaini gidan,amma kamar yadda na sanar
maka bana so ka je da babbar motarka,sabida wasu dalilai don haka a ɗauki ƙaramar motata ta
da,wacce ke aje cikin rumfa yanzu sai a sanar da Shehu ya fito da ita ya goge,so nake ka je ka
ganta ido na ganin ido ba,ba sai da daddare ba."
Maleek dake sauraren Hajjah ya jinjina kai yana cewa, "To shikenan Hajjah duk yadda kika ce
haka za a yi."
Yadda yayi maganar very low yasa Hajjah gane Maleek na cikin damuwa,amma sai ta share ta
dubesa tana cewa, "To bari a sanar da Shehun ya fito da motar zuwa la'asar idan kun yi sallah ba
sai ku je ba kawai,ko akwai inda zaka ne?"
Maleek yayi saurin girgiwa Hajjah kai ba tare da yayi magana ba,sai ta miƙa hannu ta ɗauki
wayarta ta shiga kiran Shehu,don sanar masa ya ciro motar ya goge."
Duk Maleek na zaune yana jin abinda Hajjah ke cewa har ta kammala wayar.Ta dubi Maleek da
yayi shiru ba shi da alamun tanka ta,ta murmusa kaɗan tana cewa, "Maleek ka kwantar da
hankalinka bafa dole zan maka akan Yariyar ba,cewa nayi kawai ka je ku ga juna,duk abinda ka ji
game da ita ka sanar dani,idan tayi maka ka kuma ji a ranka za ka iya zaman aure da ita zan fi
kowa farin ciki,idan kuma ba tayi maka ba zan maka dole ba,sabida ina mata son da bazan so ta
auri wanda baya son ta ba,ko wanda zai ji a ransa an tirsasa shi ne ya aureta don tana da lalura,don
haka ka sanya zuciyarka a inuwa."
Maleek ya dubi Hajjah yana murmushi kaɗan,sabida yadda yake mamakin duk duniya ita kaɗaice
wacce take karantar abinda ke zuciyarsa ko bai furta ba.Ya yi magana cikin shagwaɓe murya
kamar ƙaramin yaro,yana cewa, "Hajjah cewa nayi hankalina ya tashi dama?"
Hajjah ta zabga masa harara tana cewa, "Bansani ba ɗan rainin hankali." Maleek ya saki murmushi
me faɗi a wannan karon,ba tare da yayi magana ba amma.
Kiran Suhailah da ya shigo wayarsa yasa shi ɗagawa cikin sauri,suka jima suna magana kafin ga
miƙa wa Hajjah wayar.
Hajjah tayi wa Suhailah ya jiki suka ɗan jima suna magana,sannan Hajjah ta miƙawa Maleek
wayarsa.
Bayan ya gama da Suhailah a waya ne aka kawo masa lunch nan tsakiyar falon Hajjah.
Da kansa ya zuba abinda zai ci cikin abinci kala biyun da aka shirya a gabansa.Yana cin abincin ne
amma hankalinsa na kan yadda zai je ya ga gurguwar Hajjah.
Zuciyarsa na hasaso masa ko wace irin gurgurwace Hajjah ke nufi? Don bata sanar da shi yanayin
yadda TAIMIYYAH take tafiya ba.Shiyasa yake ji duk ya ƙago ya je shi ma ya ga wacece wannan
gurguwar data sace zuciyar Hajjah,har take so ta ɓallo masa rigimar da bai san ta yadda zai iya
ɗauka ba,don koda yake ma Suhailah zancen ƙarin aure bai yi tunanin Hajjah za ta iya jajibo
maganar aure nan kurkusa ba.
Har ya kammala cin abincin ya kasa samun nutsuwar zuciyarsa,shiyasa abincin ma bai wani iya ci
da yawa ba.
Hajjah dake zaune duk tana kula da yanayinsa, sai tayi murmushi kawai tana dubansa cikin ido
tace, "Maleek yanzu har ka ƙoshi kenan ka ke nufi?"
Maleek ya shagwaɓe face tare da tsukesa yana cewa, "Na ƙoshi Hajjah kin san yau banyi karin
safe da wuri bane,amma anjima ina so amin farfesun Kifi asa yaji sosai da garlic."
Hajjah ta jinjina kai tana cewa, "To Allah ya kaimu anjiman za a yi."
Daga haka sai Hajjah ta kamo wani zancen me muhimmanci suka shiga tattaunawa akai.
Basu tashi daga cikin falon ba sai da akai kiran sallar la'asar,sannan Maleek ya tashi ya fice don
gangarawa zuwa wani ƙaramin masallaci,wanda ke gaba kaɗan da gidan Hajjah.
Ita kuma Hajjah ta shige ciki don gabatar da sallar itama,zuciyarta cike da addu'an Allah ya jefa
son TAIMIYYAH a zuciyar Maleek ɗin.
Lokacin da Maleek ya dawo masallaci sai ya sanar da Hajjah cewa zasu wuce,zuwa gidansu
gurguwanta.Hajjah ta jefa masa harara tana cewa, "Kul! Na sake jin kalmar gurguwar nan,sunanta
Zainab TAIMIYYAH sai ka zaɓi na faɗi aciki ba ka kirata gurguwaba."
Maleek ya taɓe baki yana cewa, "Hajjah wai yaushe kika fara son wannan Yarinyar har haka ne?"
Hajjah ta sake manna masa harara tana cewa, "Babu ruwanka da wannan kai dai kawai ku je Allah
haɗa zukatanku ni shine fata na."
Maleek ya juya ya fice daga falon Hajjah,yana jin zuciyarsa na wani irin dokawa da addu'an da
Hajjah tayi daga ƙarshe..........✍🏻
#Ɗansabo ce#
[12/14, 3:43 PM] +234 703 040 9541: Littafin TAIMIYYAH paid book ne,ga duk wanda ta
tsincesa a kowani irin group ne,kiji tsoran Allah karki karanta sai kin biya 500 naira only.
Za ku iya min magana ta wannan number ɗin 08167768704, ko kuma ku turo kuɗin ku kai tsaye ta
wannan account ɗin 0504192664 aisha ibrahim dansabo GTbank.*
Masu turo credit za ku turo katin MTN na 500 ta wannan line ɗin 08167768704.
_Ina ƴan kasuwa masu buƙatar a tallata muku hajar ku? Maza ku garzayo da kuɗi ƙalilan a tallata
muku kayan siyarwanku sai dai kawai ku ji ana kiran waya don buƙatan sayan kayan ku,ku
tuntuɓeni ta layina kamar haka 08167768704._
*55*
Lokacin da Maleek ya fita har Shehu ya gyara parking cikin tsohuwar motar Hajjah na da,wata
baƙar Vibe wacce har yanzu da kyanta ba wai tayi wani abu bane.
Shehu ya buɗe masa back seat yana masa barka da fitowa,Maleek ya shiga ya zauna yana amsa
Shehu a taƙaice.
Shehu ya rufewa Maleek murfin motar tare da zagayawa ya buɗe driver seat ya shiga,ya tada
motar suka nufi wajen gate.
Bilya ya buɗe musu gate ɗin yana musu fatan dawowa lafiya,zuciyarsa cike da mamakin yau
kuma ubangidan na su ƙaramar mota yake jin hawa.
"Shehu Gyallesu muka nufa,gidan wannan Yarinyar da Hajjah tace kun kaɗeta da mota kwanakin
baya."
A.Maleek ya yi maganan lokacin da suka hau kan kwalta,Shehu ya jinjina kai cike da nuna
gamsuwa yace, "An gama ranka-ya-daɗe Hajiya ta sanar dani."
Daga haka motar ya ɗauki shiru kafin kiran Suhailah ya shigo wayar Maleek,yayi receiving call
ɗin yana jingina da jikin seat ɗin sosai don ya ji daɗin amsa wayar.
Sun jima suna magana kafin ya yi hanging up yana maida wayar ya aje gefe guda.
Motar ya sake ɗaukan shiru zuciyar Maleek cike da tunanin yadda zai yi ido huɗu da gurguwar
Hajjah,ya ɗan saki murmushi kaɗan,lokacin da ya tuna yadda Hajjah ta harare shi don ya kira
Yarinyar da suna gurguwa.
Har suka iso Gyallesu suka ratso kwanar shiga layin gidan su TAIMIYYAH,Maleek na amsa call
ɗin wani abokin aikinsa ne.Hakan yasa Shehu faka motar daga gaban gate ɗin gidan kaɗan,ya
kashe yana jiran Maleek ɗin ya kammala amsa wayar ya ji yadda za a yi.
"Shehu fita ka sanar da mai gadin ya je ya yi mana sallama da Yarinyar, a ce tana da baƙo a
waje,sunanta Zainab in ji Hajjah."
Maleek yayi maganar lokacin da ya sauke wayar daga kunni,Shehu ya amsa da faɗin, "To ranka-
ya-daɗe." Daga haka ya buɗe motar ya fice yana nufan ƙofar gate ɗin gidan direct.
Bayan sun gaisa da Tukur ne ya sanar masa yana so ne ya yi musu sallama da Zainab,Tukur ya
amsa yana nufan sasan Hajjah don isar da saƙo.
Shehu sai ya samu waje ya zauna kan dogon bencin da Tukur ke zama daga bakin gate ɗin,yana
jira Tukur ya dawo ya ji me zai je ya cewa ubangidansa Maleek da ke mota yana jira.
Daga cikin sasan Iyah kuwa,lokacin da Tukur ya yi sallama suna zaune tare da TAIMIYYAH ne
cikin falon Iyan,tana ma Iyah kitso suna hiransu gunin ban sha'awa.
Sallamar Tukur ɗin ya sanya Hajjah amsawa tana tambayarsa abinda ya ke so?Tukur ya buɗe baki
daga waje yana cewa, "Ranki-ya-daɗe baƙo ne aka yi yace a yo masa sallama da Zainab,yana daga
can waje."
Hajjah tace, "Baƙo kuma da yamman nan Tukur?To badamuwa abinda za a yi, je ka maza sasan
Samha ka ce mata na ce a buɗe falon marigayi ta waje,sai ka kai baƙon ya shiga ya zauna ga
Zainab ɗinnan fitowa."
Tukur ya amsawa Iyah yana juyawa don zuwa ya sanar da Ummie saƙon Iyah,kafin ya koma ya
sanar da Shehu yadda ake ciki.
Lokacin da Shehu ya sanar da Maleek cewa ya shiga daga ciki,sai da ya yi ɗan jim yana ɓata
fuska,kafin ya zuru ƙafafunsa zuwa waje ya fito daga cikin motar.Cikin takunsa me cike da aji
yake takawa zuwa cikin gate ɗin gidan,suka gaisa da Tukur a taƙaice,sannan Tukur ɗin ya yi masa
jagora zuwa falon Alhaji Sameer marigayi.
Falon kullum a gyare yake tsaf tunda Ummie ta dawo, kullum ake sharewa a gyara shiyasa yake
fes da shi,sai tashin qamshin turaren da ake sawa ɗakin kullum ke tashi.
Maleek ya samu kujeran 2 seater ya zauna,yana ƙarewa falon kallo tare da jinjina tsaftan masu
gidan,don ƙamshi da ƙyallin da ko'ina ke yi, zai tabbatarwa mutum cewa masu gidan sun san
darajar tsafta.
Daga can sasan Iyah kuwa TAIMIYYAH ce kewa Iyah ƙorafi tana cewa, "Iyah yanzu daga cewa
ga baƙo sai ki ce a kaisa falon Abie,meyasa ba za a ce ya zauna a waje kamar ko yaushe ba?"
Iyah ta fige kanta daga kitsa goran ƙarshe da TAIMIYYAH ke yi,ta aika mata wani kallo tana
cewa, "Haka na ga ya dace kuma ina da dalilina na cewa ya je can,kiyi maza ki tashi ki fita bana
son wani zancen banza."
TAIMIYYAH ta shagwaɓe fuska tare da narke murya tana cewa Iyah, "Gaskiya Iyah ni dai da kin
bar sa a waje,miye na wani cewa a kaisa can sasan kamar wanda ki ka sani,ko ki ka san da
zuwansa, ni waima waye zai zo da yamman nan yace wani ana sallama da ni?"
Iyah ta zabga mata harara tana cewa, "Zainabu ki fita ido na,zaki tashi ki wuce ki kintsa kanki ki
fita, ko sai anji kan mu ni da ke?"
TAIMIYYAH sai ta tashi tana dafa ƙafarta ta nufi hanyar ɗakinta,sai faman mita take yi a
zuciyarta ,ga wani faɗuwar gaba da take ji tunda Tukur ya zo ya sanar cewa wani na sallama da ita
a waje.
Wajen kayanta ta nufa ta ciro dogon Hijab red ta sanya,tsayinsa ya sauka mata har ƙasa dai dai
ƙwaurinta.Ta ƙarisa gaban madubi bayan ta sanya takalmi tana gyara wuyan hijab ɗin ya zauna dai
dai,ta kalli face ɗinta da babu komi a kai sai kwalli da ta sanya tun wankan safe,sai ta ɗan goga
man leɓe me taushi, ta juya ta dafe guiwarta ta fara takawa don barin ɗakin.
Tana ratsowa cikin falon Iyah ta tsareta da idanu,tana kallon yadda jan Hijabin ya haske farar face
ɗin TAIMIYYAN ya yi mata mugun kyau.
Manyan fararen idanunta na haskawa, da ƙyallin baƙin kwalliin da ta sanya a idanun, yana ƙara
ƙawata kyawun fuskarta.
"Masha Allah! Zainabu kin yi kyau matuƙa, sai dai ki saki fuskar mana TAIMIYYAH,wannan irin
ɗaure fuska kamar wacce aka ce ga maƙiyinki na jiran ki,ki sawa zuciyarki salama duk wanda ki
ka ga yazo gare, ki yi fata cewa Allah sa alkhairy ne ya kawo sa,amma ba ki dinga ɓata rai kina
cuskune fuska ba,kin kai munzalin aure Zainab, kuma duk masoyinki zai miki fatan kiyi auren,
don shine cikar mutuncin ƴa mace, don haka ki saki ranki don Allah,ki je an bar shi yana jira tun
ɗazu,zan bai wa Ladi ɗan lemu da ruwa ta kawo masa."
Iyah tayi maganar idanunta akan TAIMIYYAH da ke ta faman zumbure baki,ta dubi Iyah da
muryar shagwaɓa tana cewa, "Ni Iyah wallahi tsoran fita nake yi,bana son abinda ya faru ya sake
faruwa,shiyasa bani sha'awan sake kula kowa a yanzu."
TAIMIYYAH tayi maganar cikin sanyin murya sosai,wani abu na taɓa zuciyarta sosai.Iyah ta
dubeta da fuskar tausayi tana cewa, "A'a Zainabu kada ki karaya komi da ki kaga ya faru da bawa
muƙaddari ne,don uwar Nass ta gujeki don kina gurguwa,hakan ba shi ke nufin ba za ki samu
wanda za su amsheki a yadda Ubangiji ya so ganinki ba.Ki je babu abinda zai biyo baya sai
alkhairy Insha Allah."
Ta tsaya daga bakin ƙofar shiga falon, tana kallon takalmar da ke zube daga bakin ƙofar,wani irin
faɗuwar gaba ke cigaba da riskar zuciyarta.
Ta yi ƙarfin halin yin sallama cikin siririyar muryarta,kafin tayi jim! Don jiran ya bata izinin shiga
amma sai taji tsit! Da alamun ko sallamar nata ma da wuya idan an amsa,don bata ji alamun hakan
ba ko kaɗan.
Ta sake doka wata sallamar nan ma shiru babu amsa,hakan yasa ta yin ƙundubala ta ɗaga labulen
ƙofar ta sanya kanta ciki.
A.Maleek Ado dake zaune yana facing ƙofar shigowa falon,tun sallamar farko ya ji ta, ya kuma
amsa a taƙaice ta yadda ba za ta iya jiyo sa ba.
Ya zubawa ƙofar shigowan idanu yana son ganin halittar da za ta kutso kanta cikin falon,don haka
akan idanunsa TAIMIYYAH da ke dafe da guiwar ƙafarta tana takowa zuwa cikin falon suke.
Wani irin dokawa ƙirjinsa ke yi lokacin da take sake kusantowa cikin falon.
Maleek sai ya samu kansa da kasa ɗauke ido daga gareta, har ta samu waje ta zauna cikin kujeran
da ke daura da inda yake zaune.
Amma ita TAIMIYYAH har lokacin taƙi kallon inda Maleek ɗin yake zaune, sai qamshinsa da
hancinta ke shaqo mata,wanda bata taɓa jin wani mahaluki da irin qamshin ba sai yau.
Sai da ta nutsu cikin kujeran sannan ta ɗago manyan idanunta ta saci dubansa,cikin sa a shi ma na
shi idanun na kanta, ba tare da ita ta san cewa yana kallonta ba.Wani irin abu ya doka a zuciyar
duka su biyun, TAIMIYYAH tayi saurin janye nata idanun daga kansa,bugun ƙirjinta na ƙaruwa
da sauri-sauri.
Shi ko Maleek Ado wani irin abu ne kaman tsawa,ya ji ya doka a tsakar kansa,lokacin da idanunsa
su kai tozali da manyan idanun da yake cin karo dasu cikin barcinsa.Idanun da ke jefashi cikin
ruɗu da tunani me tarin yawa duk lokacin da zai yi mafarki ya gansu a cikin baccinsa,bai san
lokacin da ya miƙe tsaye yana sake tsareta da manyan idanunsa ba.
Jikinsa har wani irin shaking yake, na tsananin shiga ruɗu da kiɗima,ya shiga takawa a hankali
don isa gaban TAIMIYYAH, wacce ta sunkuyar da kanta ƙasa,tana ji kaman ana sanya igiya ana
ɗaure dukkanin jijiyoyin jikinta ne.
Har Maleek ya iso gare ta, bata sani ba sabida kanta na duƙe a ƙasa ne,sai da ta ji ƙamshin
turarensa yayi yawa a hancinta,sannan ne ta ɗago manyan idanunta ,don tabbatar da ko shi ɗin ne
ya taho kusa da ita,aiko sai karaf idanunsu suka sake harɗewa da juna.
Wani irin faɗuwar gaba ya sake ziyartan zuciyar Maleek Ado,wanda ke tsaye kyam a
gabanta,ganin zata sake maida kanta ƙasa ,yasa yayi gaggawar kai hannu ya riƙo fuskarta baki
ɗaya a tafukan lallausar fatar hannunsa.
Lamarin da ya girgiza zuciyar TAIMIYYAH,tare da haifar da matsanancin faɗuwar gaba daga
ƙirjinta,tayi gaggawar lumshe idanunta jikinta da zuciyarta na wani irin rawa.
Maleek Ado da yake jin tamkar an tsaida gudun jini daga jiyoyin jikinsa,sai yayi azamar sakin
face ɗin nata yana ƙoƙarin riƙe kansa.Gaba ki ɗaya kansa yayi wani irin kullewa na ban
mamaki,babu tamtama ko kokonto wannan gurguwar da ke gabansa, irin idanunta yake gani
kullum cikin mafarkinsa,wanda ba a taɓa nuna masa zahirin face ɗin ba illah waɗannan manyan
fararen idanun kawai.
Jikinsa ya yi wani irin sanyi ƙalau, har kuma lokacin yana tsaye a gaban TAIMIYYAH ya kasa
motsawa,sai da yaji ƙafafunsa na neman kasa ɗaukar gangar jikinsa, sannan ya lalubi kujeran da
ke kusa da ita ya zauna, yana me kai hannu ya dafe goshinsa da hannuwa bibbiyu.
Ya lumshe idanunsa zuciyarsa na cigaba da tariyo masa, yawan mafarkan da ya dinga yi da idanun
Yarinyar da ya kasa tantance wacece ita? Sai gashi yau ya ga irin idanun sak akan fuskar wannan
gurguwar da Hajjah ta turo sa zuwa wajenta.
Yayi saurin buɗe idanunsa ya sake zubawa TAIMIYYAH,wacce ta kasa ɗagowa bare ta sake
dubansa,gaba ɗaya itama zuciyarta ta shiga mummunan yanayin da ba za ta iya fassarawa ba.
Ƙamshinsa da laushin tafukan hannayensa da suka sauka akan face ɗinta,ke sake jefa zuciyarta
cikin wani yanayi,jin shiru bai sake wani motsi ba yasa ta ɗago kanta ta saci dubansa ƙasa-ƙasa.
Idanunta su kai masa kallon sakanni kwanyarta na yaba haɗuwarsa.Tayi gaggawar ɗauke ganinta
daga garesa, lokacin da idanunsu ke son sake shiga cikin na juna,sai ta buɗe baki cike da ƙarfin
hali ta gaida shi.
Memakon ya amsa sai ya cigaba da zuba mata idanu,tasirin abinda yake ji a zuciyarsa na sake
hauhawa kamar farashi.Zuwa wani lokaci can ya sauke wata zazzafar numfashi ,yana cigaba da
kallon yadda TAIMIYYAH tayi ƙasa da kanta sosai,kamar wacce take jira yace ket...! Ta arce da
gudu,sai ya buɗe baki cikin ƙasaitacciyar muryarsa yace, "Zaynabb! Ɗago idanunki ki kalleni
please..!"
Yadda ya faɗi sunanta, da yadda muryansa ke fita cike da aji da ƙasaita,yasa TAIMIYYAH ta ɗago
kanta,tare da sanya idanunta cikin nasa.Maleek ya yi saurin sake xubawa kwayar idanun
TAIMIYYAH ido, zuciyarsa na cigaba da girigiza da tarin al'ajabi da shiga ruɗu,ya janye nasa
idanun tare da lumshesu yana kiran sunan Allah a hankali.
Abinda ya yi matuƙar baiwa TAIMIYYAH mamaki da shiga ruɗu kenan,ta dinga mamakin yadda
duk ya wani birkice,tun daga shigowarta cikin falon.Sai ta tashi tsaye tana dafe guiwar ƙafarta
don ficewa daga ɗakin ta bashi waje, ko ita ma zata daina jin abinda take ji daga cikin
zuciyarta,amma sai amon muryarsa a dake ya tsaida ita, inda yake faɗin,
"Koma ki zauna."
Babu musu ta koma ta zauna, tana jin tamkar ta ɗaga waya ta kira wani ya zo,don ya zauna a
tsakaninsu,sabida ta fara tsorata da lamarin wannan mutumin,wanda kallo tayi masa ta ji
kwarjininsa ya cika ɗakin baki ɗaya.
Maleek Ado ya fara da cewa, "Zaynabb sunana Abdulmaleek Ibrahim Ado,na kawo kaina gareki
ne don mu ga juna,kuma ina fata zaki bani dama don sanin cikakken asalinki, koda a taƙaice ne."
Yadda ya yi maganar yana tsareta da manyan idanunsa,ya hana TAIMIYYAH dubansa cikin
ido,amma gaba ɗaya sai ta ji duk wani musu da take son yi masa ta kasa.
Ta buɗe baki cikin sanyin muryarta me daɗin amo tace, "Sunana Zainab kamar yadda naji ka
faɗi,wanda hakan ke nuna kasan sunan tun kafin ka iso zuwa gareni, zan so sanin manufarka na
takowa har zuwa gidanmu."
Maleek da ya tsura mata ido yana kallon kyakykyawar fuskarta da ke cikin hijab,sai ya sake haɗe
miskilalliyar face ɗinsa ,yana cigaba da ƙarewa kwayar idanunta masu haske kallo,wanda yake ji
tamkar ya shekara dubu yana ganinsu ,sabida shi karan kansa ba zai iya irga adadin yawan
mafarkan da ya dinga yi da waɗannan idanun ba,ba zai iya irga sau nawa ya ji irin wannan
sassanyar sautin na rera masa kuka a cikin baccinsa ba.
A hankali kuma ya buɗe baki yana cewa, "Ba wannan ne abinda ya kamata ki buƙaci ji daga gare
ni ba Zaynabb,koma miye ina wa Allah godia daya nuna min wani abu game da ke a zahiri.Yanzu
sauri nake yi amma zan dawo idan na sake samun time, za mu yi waya sai kiji duk abinda kike son
ji daga gareni ɗin."
Daga haka Maleek yayi shiru, idanunsa akan TAIMIYYAH wacce ta kwaɓe face tamkar zata saki
kuka.Ta ɗago manyan idanunta ta sauke akansa tana cewa, "Ni dai don Allah kafin kabar nan,ka
taimaka ka sanar dani wanda ya turo ka zuwa gare ni please!!"
Yadda tayi maganar cike da magiya, ya sanya maleek saurin miƙewa tsaye,don muryarta da
idanunta ba ƙaramin kiɗima zuciyarsa suke yi ba.Yana ji tamkar yayi tsuntsune a yanzu ya gansa a
gaban Hajjah,don ya sanar mata cewa Yarinyar da ake nuna masa idanunta cikin mafarkinsa,ita ce
ta turosa zuwa gareta,ita ce Yarinyar da ya jima yana jin sautin kukanta,da irin dai wannan muryar
da yake ji a yanzu,hakan na nufin ita ce wannan gurguwar dake gabansa.
Ya buɗe baki zai yi magana kenan, Babah Ladi ta shigo hannunta riƙe da tray, da aka ɗauro ruwa
da lemun kwali na 5alive akai.Ta aje tray ɗin akan table dake tsakiyar falon, tana gaida Maleek da
ke daga tsaye.
Ya amsa a gajarce yana zaro wayarsa da kira ya shigo, ya ɗauka ya yi receiving ya kai wayar
kunni.
Babah Ladi ta fice daga falon, tana jinjina ƙasaitan wannan kyakykyawan ingarman najimin da ta
baro a falon Abie.
Tana me tambayar kanta inda TAIMIYYAH ta samo wannan haɗaɗɗan mutumin, ma'abocin
kyawu da ƙasaita tamkar jinin sarakai.
Har ta isa sasan Iyah mamaki bai bar kwanyarta ya huta ba.
Daga can falon Abie kuwa, Maleek ne yake amsa wayar da aka kirasa,yana magana cikin harshen
nasara wanda ba za ka taɓa cewa ya ji hausa ba, idan ka ji yadda yake zubo tatacciyar turanci.
TAIMIYYAH sai ta samu daman ƙare masa kallo cikin tsanaki.Tana mamakin ta yadda haɗaɗɗan
mutum kamarsa zai kawo kansa wajenta,tarin tambayoyi na cika kwanyarta.
'Waya turosa? Kuma wani manufa suke da shi akanta? Waɗannan sune tambayoyin da suka ɗarsa
tsoro da rashin yadda a zuciyar TAIMIYYAH, game da wannan miskilin haɗaɗɗen mutumin dake
gabanta.
Tayi gaggawar ɗauke idanunta daga kallonsa ,lokacin da ya sauke wayarsa daga kunni,yana
ƙoƙarin maido hankalinsa gareta.
Ya yi mata kallo biyu yana fara takowa zuwa gareta,ya tsaya daf da ita sosai tamkar me shirin
faɗawa kanta.Hakan yasa TAIMIYYAH sake shigewa cikin kujeran sosai,ƙirjinta na faman
bugawa da ƙarfi ,cike da tsoro da mamakin ƙarfin halin wanna mutumi.
Maleek ya cigaba da kallonta kafin ya furta, "Zaynabb zan wuce, sai mun yi waya ki gaida mutan
gidan,zan aje saƙo ki baiwa wannan Babar da ta fita yanzu kinji?"
TAIMIYYAH ta dubesa sau ɗaya, tana saurin ɗauke idanunta daga dubansa,ganin irin mayen
kallon da yake bin face ɗinta da shi.
Ta zumbure baki kaɗan,tana gyaɗa masa kai ba tare da tayi magana ba.
Hakan yasa Maleek ja baya kaɗan,yana nuna mata hanya yace, "Oya mu je ina so ki fara yin
gaba ,don na ga tsorona kike ji kada in gudu da ke ko?"
Yadda yayi maganar cikin ginshira, face ɗinsa a haɗe yasa TAIMIYYAH sake kwaɓe fuska.Ta
buɗe baki murya can ƙasa take cewa, "Ok sai anjima,amma kabar abinka bama sai ka bata komi
ba."
TAIMIYYAH tayi maganar tana ƙin kallon face ɗinsa,don jikinta ya gama bata idanunsa akanta
suke,sai kawai ta dafe guiwar ƙafarta,ta fara tafiya don ficewa daga falon.
A.Maleek ya sarƙafe hannuwansa a ƙirji, yana zubawa tafiyarta idanu,wani irin yanayi na gewaye
ilahirin zuciya da gangar jikinsa.
Har ta fice daga falon bai iya ɗauke idanunsa daga gare ta ba,kamar yadda bai fasa jin tasirin
abinda yake ji na zagaye zuciyarsa ba.Sai ya saki hannuwansa, yana zura ɗaya hannun cikin
aljihu,ya irgo kuɗin da baisan adadinsu ba, ya taka zuwa wajen da Babah Ladi ta aje tray ɗin,ya
ɗaura kuɗin akai yana juyawa ya fara takawa don fitowa daga falon.
Can nesa ya hangi TAIMIYYAH tana takawa, cikin tsarin tafiyarta da ya taɓa zuciyarsa.Ya cigaba
da takowa shi ma idanunsa nayi mata rakiya, har ta karya kwanar shiga sasan Iyah,kaman kuma ta
ji ajikinta yana biye da ita da idanunsa,sai ta ɗan dakata daga tafiyar,tayi tsaye dafe da guiwar
ƙafarta ta waiwaya ta dubi bayanta,karaf sai idanunta ya sauka akan Maleek ɗin, wanda yake ta
kallo direction ɗin da take.
TAIMIYYAH sai tayi saurin ɗauke kanta, tana hanzarin cigaba da takawa ta shige cikin sasan
su.Maleek Ado bai san lokacin da murmushi ya ƙwace a saman face ɗinsa ba,ya cigaba da takawa
ya nufi hanyar gate ɗin gidan,yana ji tamkar ya bar wani ɓangare da ke tuno masa da mafarkansa
na baya ne,wanda ada ya dinga ɗauka cewa aljanace yake ta mafarki da idanunta, ashe ba aljana
bace mutum ce kamar kowa.
Bai gane hakan ba sai yau da ya yi arba, da irin idanun da yake gani cikin mafarkinsa, akan fuskar
wannan kyakykyawar gurguwar.
Ya fice daga gate ɗin gidan bayan ya baiwa Tukur kyautan kuɗi me yawa,sai faman zuba godia
Tukur yake yi har Maleek ya yi nisa da barin bakin gate ɗin.
Tukur ya turmutsa kuɗinsa a aljuhu, yana me addu'an Allah ƙullah alkhairy tsakanin wannan
ƙasaitaccen mutumin da TAIMIYYAH........✍🏻
#Ɗansabo ce#
[12/14, 3:43 PM] +234 703 040 9541: Littafin TAIMIYYAH paid book ne,ga duk wanda ta
tsincesa a kowani irin group ne,kiji tsoran Allah karki karanta sai kin biya 500 naira only.
Za ku iya min magana ta wannan number ɗin 08167768704, ko kuma ku turo kuɗin ku kai tsaye ta
wannan account ɗin 0504192664 aisha ibrahim dansabo GTbank.*
_Ina ƴan kasuwa masu buƙatar a tallata muku hajar ku? Maza ku garzayo da kuɗi ƙalilan a tallata
muku kayan siyarwanku sai dai kawai ku ji ana kiran waya don buƙatan sayan kayan ku,ku
tuntuɓeni ta layina kamar haka 08167768704._
*56*
"Zainab me yafaru kika shigo kika zabga uban tagumi haka,har baƙon na ki ya wuce ne?"
Iyah ce ke tambayar TAIMIYYAH, lokacin da ta fito daga ɗaki, ta tadda TAIMIYYAH zaune a
falo,ta rafka uban tagumi.
TAIMIYYAH ta ɗago manyan idanunta, ta sauke akan Iyah tana cewa, "Iyah ya tafi bada jimawa
ba."
Iyah ta zauna daga cikin seater,har lokacin idanunta na kan TAIMIYYAH,wacce gabaki ɗaya
kanta yake a kulle da al'amarin Maleek, wanda ba ta san daga ina yake ba.
Iyah tayi gyarar murya ta ce, "Zainab daga ina baƙon naki yake,kuma me ya kawosa zuwa gareki
ina fata alkhairy ne?"
TAIMIYYAH tayi ƙwal-ƙwal da ido tana duban Iyah ta ce, "Iyah bansan me zan faɗi miki akansa
ba,don ni ma sunansa kawai ya sanar da ni,sai kuma ya ce wai yazo ne kawai ya ganni,amma zai
dawo idan ya sake samun time.Iyah baki gansa bane da alamu babban mutum ne daya mallaki
iyali,kallo ɗaya na yi masa na gane hakan,daga yanayin kwarjini da kamewarsa.Sai dai kaina a
kulle yake, sabida yadda ya dinga nuna kamar dama can, ya daɗe da sanina a wani wajen,amma
kuma yaƙi sanar dani dalilin kawo kansa zuwa gare ni,Iyah ina jin tsoro me tsanani yana lulluɓe
zuciyata,ina ji a jikina kamar wannan mutumin, yafi ƙarfin ya kawo kansa zuwa gareni,akwai
wani abu da yake ɓoyewa."
TAIMIYYAH tana maganar ne cikin tsananin sanyin murya,wanda hakan ya sanya Iyah zuba mata
ido har ta kai aya,kafin ta buɗe baki tana duban TAIMIYYAH cikin ido ta ce, "Zainabu ki nutsu
don Allah,babu komi In sha Allah,koma miye za mu ji daga garesa, tunda yace zai dawo,to sai mu
jira dawowar na sa aji meke tafe dashi?Amma yanzu ki nutsu ki cire duk wani tsoro daga cikin
zuciyarki,in ma bada alkhairy yake tafe ba,sai muyi addu'a kada Allah ya bashi ikon dawowar
ma."
TAIMIYYAH sai ta ɓata fuska ta dubi Iyah ta ce, "Shikenan Iyah,bari in shiga daga cikin
ɗaki,idan Ayuba ya shigo ya je ya ɗakko abinda Babah Ladi ta kai, bai ma sha komi ba."
Daga haka ta miƙe tana dafe da ƙafarta ta nufi ɗaki,Iyah tabi bayanta da kallo tana jin wani abu na
motsawa a zuciyarta game da TAIMIYYAH.
Babah Ladi Iyah ta sanya ta koma can falon Abie, ta ɗakko tray ɗin da ta kai ruwa da lemun.Sai da
Babah Ladi ta kawo ne aka ga kuɗin da Maleek ya aje masu yawa,sai tashin ƙamshinsa kuɗin suke
yi.
Iyah ta ciri murya ta kira TAIMIYYAH, wacce ta ƙule a cikin ɗaki,tana kwance tunani ya
dabaibaye kwanyarta.Jin kiran Iyah ya sanya ta fitowa daga ɗakin zuwa falo,ta yi tsaye daga kusa
da Iyah tana cewa, "Iyah gani."
Iyah ta tsura mata ido, tana nuna kuɗin dake cikin tray ɗin da Babah Ladi ta kawo ta ke cewa,
"Waɗannan kuɗin fa,waya aje su cikin nan?"
TAIMIYYAH ta kwaɓe fuska tare da watsa hannu baya ta ce, "Ina ganin shi ne ya aje su kafin ya
tafi,don dama yace zai aje saƙo a baiwa Babah Ladi da ta kai masa lemu da ruwan."
Iyah sai ta jinjina kai tana kai hannu ta ɗakko kuɗin, ta miƙawa TAIMIYYAH tana cewa, "Irga mu
ga yawansu ,sai ki kai ma Ladin Allah anfana, na ɗauka ke ya ajewa in ce meyasa zaki amsa
kuɗinsa,amma tunda kyauta ce ya yi da sunan Ladi, sai a bata abarta Allah anfana ya yi albarka."
TAIMIYYAH dai bata ce komi ba,sai kuɗin ta amsa ta fara irgawa,ƙamshin AMOUAGE na dukan
hancinta,tare da tsirga wani baƙon yanayi cikin zuciya,har ya zuwa gangar jikinta,tayi saurin
kammala irga kuɗin, wanda suka kai naira dubu sha biyar.Ta miƙawa Iyah tana cewa, "Iyah 15k ne
bari a ba ta ɗin."
Daga haka ta fita zuwa ɗakin Babah Ladi ta kai mata kuɗin,Babah Ladi tayi godia suna fitowa a
tare da TAIMIYYAH, zuwa ɗakin Iyah don tayi godian kuɗin.Ita dai TAIMIYYAH ɗaki ta koma
ta kwanta, zuciyarta na cigaba da tunanin Maleek, da yadda lallausar hannunsa ya tallabo fuskarta.
Ta ɗaga hannu ta shafi face ɗinta, tana ji har lokacin kamar hannunsa ne akan fuskar nata bai cire
ba,tayi saurin lumshe idanunta wani baƙon yanayi na lulluɓe zuciyarta,kamar yadda sunansa ke
amsa kuwwa cikin kunnuwanta.Ta buɗe baki a hankali cikin siririyar muryarta ta furta sunan a
zahiri ' _Maleek Ibrahim Adoo...',_ ta ja ƙarshen sunan akan harshenta, tana jin wani abu na
tsirgawa cikin kanta.
___________
A ɓangaren Maleek Ado kuwa,lokacin da suka isa gidan Hajjah, tun Shehu bai ida gama parking
ba,Maleek ya ɓalle murfin motar ya fice.
Yana taku ne cikin sassarfa da zafin jini, har ya dangana kansa da falon Hajjan,ya yi sallama cikin
muryarsa me cike da ginshiri,lokacin da yake sanya kansa cikin falon.
Hajjah da ke zaune tana duba littafin Hisnul Muslim,idanunta sanye cikin farin gilashi, ta ɗago ta
dubi Maleek ɗin tare da amsa sallamar tasa.
Ya fara takowa zuwa cikin falon a gaggauce, har ya iso kusa da ita ya yi masauki a ƙasan
carfet.Kansa ya ɗaura bisa guiwar ƙafarta ya sauke wani zazzafar ajiyar zuciya,yana ji sai yanzu
ne zuciyarsa ta numfasa,tun bayan ido huɗu da suka yi da TAIMIYYAH.
Hajjah ta aje littafin da ke hannunta tare da zare gilashin idanunta,tana duban Maleek ta ce,
"Maleek lafiya ka ke ta faman sauke numfashi kamar wanda ya yi tsere,kun je ɗin ko wani wajen
ka je daban ne?"
Hajjah ta jefa masa tambayar, tana me ɗago kansa daga guiwarta ƙafarta,inda Maleek ya kwantar
da kansa a kai.
Hakan ya sanya shi zubawa Hajjah manyan idanunsa, kafin ya buɗe baki ya ce, "Can muka je
Hajjah,na ganta,na ga gurguwarki Hajjah,sai dai tunda na yi ido huɗu da ita zuciyata bata huta
ba,na shiga ruɗani da tsoro ba kaɗan ba Hajjah."
Yadda Maleek yake magana cike da sanyi, yasa Hajjah dafa kansa tana cewa, "Me ka gani a tattare
da ita, da har ya jefaka a ruɗani irin haka Maleek,sanar dani meke faruwa ne wai?"
Maleek ya sake sauke numfashi, tare da furzar da zazzafan huci,kafin ya dubi Hajjah yana faɗin,
"Hajjah ko kin san wannan Zaynabb ɗin itace na ke mafarki da me irin idanunta, wacce na taɓa
baki labari watannin baya,har na ke sanar da ke ina yawan mafarki Yarinyar ne tana kuka,sai dai
idanunta kawai ake nuna min, ban taɓa ganin zahirin fuskarta da kammaninta ba,sai dai manyan
idanunta masu haske, da nake gani suna zubar da hawaye,a lokacin ina ɗauka cewa ko dai aljana
ce ke bibiyata a cikin bacci,sai yau nayi ido biyu da irin waɗannan idanun da nake gani cikin
baccina akan fuskar Zaynabb, hakan yasa na gane cewa itace na ke mafarki da ita Hajjah."
Maleek ya ƙarisa maganar yana duban yadda Hajjah ta tsura masa ido with shock,sai ya maida
kansa ya kwantar a jikinta tamkar ƙaramin yaro.
Hajjah ta jinjina kai tana cewa, "Maleek da gaske ka ke yi ko dai kana tsokanata ne kawai?"
Maleek da ke sauraran Hajjah bai ɗago kansa daga jikinta ba ya ce, "Hajjah ke ma kinsan ban iya
ƙarya ba,duk abinda zan faɗi to hakan yake,sabida haka kika horeni,wallahi irin idanun da nake
gani cikin mafarki,shi na gani akan fuskar wannan gurguwar Hajjah,kuma tunda na ɗaura idanuna
akanta nake ji kamar ana uzura zuciyata da wani irin baƙon yanayi a kanta.Na jima ina ji ajikina
cewa,akwai wata ƙaddara dake cikin yawan mafarkan dana dingayi watannin baya,sai dai ban
tabbatar da hakan ba sai a yau, da na yi tozali da waɗannan idanun da siffar Yarinyar,ban san me
ƙaddara za ta zana tsakanina da ita ba Hajjah."
Yayi maganar yana jin yadda zuciyarsa ke cigaba da dokawa akan TAIMIYYAH,shi karan kansa
ba zai iya fassara yanayin da yake ciki,akan ganin TAIMIYYAH da yayi yau ɗaya ba.Yana jin
lokacin da Hajjah ta kai hannunta tana shafa sumar kansa,amma ya kasa ko da motsi kamar yadda
itama Hajjah ba ta ce komi ba,suka ɗauki tsawon lokaci a haka,kafin Hajjah ta fara da cewa,
"Abdulmaleek idan har TAIMIYYAH ta kasance,ita ce ake nuna maka wani ɓangaren na siffarta a
cikin baccinka,to tabbas akwai wani ɓoyayyen al'amari da Ubangiji ya barwa kansa sani,jikina
yayi matuƙar yin sanyi da jin hakan, kamar yadda wani sashi na zuciyata ke farin ciki da jin
hakan,ka duƙufa da addu'a sannan kuma mu yi istikhara, mu nemi zaɓin Allah akan wannan
lamari,duk abinda Ubangiji ya hukunta sai mu amsa a matsayin zaɓinsa ba na mu ba."
Maleek ya ɗago kansa daga jikin Hajjah,yana me zuba mata manyan idanunsa,kafin ya jinjina kai
yana cewa, "Hakane Hajjah,amma baki ji yadda nake ji a cikin zuciyata ba,ba kiji yadda ƙirjina ke
bugawa da wani yanayi da baki ba zai iya miki bayani ba Hajjah,koma miye zai faru na rigama na
sallama, ina kuma ji ajikina da wuya ƙaddaran aure bai haɗani da Zaynab ba,don yadda zuciyata
ke doka mata ban taɓa jin irin hakan akan kowace mace ba,zan aure ta, zan kuma zauna da ita har
ƙarshen numfashi na Hajjah."
Maleek ya yi maganar yana duban yadda wani irin abu ya haska a idanun Hajjah,kafin fuskarta ya
washe da wani irin faffaɗan murmushi,wanda ya jima bai ga irinsa akan fuskar Hajjar ba.Ta cigaba
da kallonsa da tsananin mamaki da murnan jin kalaman da suka fito daga bakinsa,ta kamo
hannunsa ta riƙe tana cewa, "Maleek daga gani ɗaya da ka yi wa TAIMIYYAH har ka yanke cewa
zaka iya aurenta,da gaske ka ke yi za ka iya aurenta ka zauna da ita a yadda take babu cutarwa?
Bana so ka yi gaggawa har sai ka tabbatar da irin ƙaunar da kake mata a zuciyarka,bana so ka ji
tausayin nakasanta ka ce za ka aureta don hakan,ina so ka aureta da zuciya ɗaya ne,kuma kana me
jin so da ƙaunarta, ba wai don tana gurguwaba sai don ɗabi'u da kyawun tarbiyyyah da
nagartarta.Don haka kamar yadda na faɗi ne ka je kayi istikhara ka nemi zaɓin Allah, duk abinda
ka cigaba da ji akanta ka sanar dani,ni kuma na yi alqawarin nema maka aurenta da
gaugawa,Allah shi kaɗai yasan abinda yake nufi da haɗuwata da wannan Yarinyar,don ina jinta a
zuciyata fiye da yadda zan iya misalta maka Maleek."
Hajjah tayi maganar cike da nuna irin ƙarfin ƙaunar da take ji akan TAIMIYYAH,ta cigaba da
cewa, "Ina fata baka sanar da ita wanda ya tura ka xuwa gareta ba,don bana so su san cewa kai
ɗana ne,har sai ka ji da gaske kana ƙaunarta, za ka kuma iya zama da ita tsakaninka da Mahaliccin
sammai da ƙassai,sannan idan har Zaynab ba ta aminta da kai ba, to zamu haƙura da ƙudirinmu
don ba zan so ai mata dole ba."
Kalaman Hajjah na ƙarshe ne suka girgiza zuciyar Maleek Ado,har yayi saurin ɗagowa ya dubi
Hajjah, da wani yanayi akan fuskarsa ya ce, "A'a Hajjah ki daina faɗin hakan don Allah,ban fara
jin irin wannan yanayin da nake ji akanta don in daina ba,tun kafin na yi tozali da ita a zahiri in ga
irin idanun da nake gani a cikin baccina,na ke shiga wani yanayi kafin in koma da walwalata,a yau
dana gansu a zahiri saman kyakykyawar wannan halittar, ba na ji zan sake samun sukunin zuciya
da cikakkiyar nutsuwa,ba tare da na mallaketa gaba ɗayanta ta dawo a ƙarƙashin ikona ba,don
haka don Allah ki daina fatan ba za ta so tilon ɗanki ba please!"
Yadda Maleek ya ƙare maganar cike da magiya,abin har al'ajabi ya bai wa Hajjah.Ta jinjina kai
tana sake sallamawa ƙudiran Ubangiji,don bata taɓa tunanin ganin irin abinda take gani a yanzu
akan fuskar Maleek ba.
Hajjah ta dafa kansa tana faɗin, "Shikenan Maleek ka kwantar da hankalinka, In sha Allah alkhairi
zai biyo bayan wannan lamarin."
Maleek sai ya tashi daga ƙasan carfet,ya nufi kan doguwar kujeran Hajjah ya zauna,yana me
zamewa kaɗan bayansa ya ginjina da jikin kujeran sosai,sannan ya lumshe idanunsa.
Hajjah ta nufi ɓangaren dining,inda aka aje wani ƙaramin fridge,ta ciro goran ruwa me
matsakaicin sanyi,ta nufo wajen da Maleek ke zaune idanunsa a lumshe.Ta ɓalle murfin goran
ruwan tana miƙa masa ta ke cewa, "Maleek karɓi ka sha ruwan sanyi,ko ka dawo cikin nutsuwarka
sosai."
Maleek sai ya buɗe idanunsa yana kallon goran ruwan da Hajjah ke miƙo masa,kafin ya kai hannu
ya amsa goran yana cewa, "Thank u Hajjah." Daga haka ya kai goran ruwan kan bakinsa,ya fara
sha sanyin ruwan na ratsa maƙoshinsa,ya sha fiye da rabin ruwan sannan ya aje goran daga ƙasa
yana sauke numfashi.
Ya dubi direction ɗin da Hajjah ke zaune ta tsura masa ido,ya jefeta da murmushi me sanyi.Hajjah
ta maida masa da martanin murmushin,sannan ta yi magana cike da tsokana ta ce, "Maleek ashe
dai karon ka da gurguwar Hajjah me zafi ne,tunda gashi haɗuwa ɗaya duk ka fita hayyacinka,da
kai ka ɗauka aljanace kake gani da idanun bil'adama a cikin baccin naka?"
Maleek ya jinjina kai yana cewa, "Seriously Hajjah ba za ki gane me nake ji akan wannan yarinyar
ba yanzu, ki taimaka ki bani numbarta zan yi magana da ita zuwa anjima."
Hajjah ta saki murmushi me faɗi,kafin ta tashi ta ɗakko wayarta ta miƙawa Maleek.Ya amsa yana
dubanta da fuskar shagwaɓa yace, "Hajjah to wani suna ki kai saving numbar da shi?"
Hajjah ta aika masa harara tana cewa, "TAIMIYYAH." Daga haka ta koma ta zauna murmushi na
blushing saman fuskarta.Maleek ya shiga contact ɗin wayar Hajjah, ya lalubo sunan
TAIMIYYAH,yana lode lambobin cikin wayarsa wani irin yanayi na kewaye zuciyarsa.
Ya tashi ya isa inda Hajjah ke zaune, ya aje mata wayar a kusa da ita ya ce, "Hajjah Allah ƙara
girma zan fita yanzu,amma zuwa anjima zan dawo kafin in wuce GRA,ina fata zuwa lokacin an yi
min soup ɗin dana ce."
Daga haka sukai sallama da Hajjah,ya taka yana barin cikin falon,gabaki ɗaya yana ji tamkar ana
ingiza zuciyarsa,akan son sake ganin waɗannan idanun a saman fuskar TAIMIYYAH.
Da ƙyar ya iya controllling zuciyarsa, har ta iya haƙura da kiran TAIMIYYAH vid call,ya haƙura
sai zuwa dare idan ya koma can gidansa,ya nutsuwa akan gadon baccinsa sannan sai ya kira ta.
Ya karya kan motarsa da ya ɗauka a gidan Hajjah, ya kamo hanyar shiga cikin City,don zuwa
wajen wani old friend ɗinsa da ke Unguwar Alƙali cikin Zaria City........✍🏻
#Ɗansabo ce#
[12/14, 3:43 PM] +234 703 040 9541: Littafin TAIMIYYAH paid book ne,ga duk wanda ta
tsincesa a kowani irin group ne,kiji tsoran Allah karki karanta sai kin biya 500 naira only.
Za ku iya min magana ta wannan number ɗin 08167768704, ko kuma ku turo kuɗin ku kai tsaye ta
wannan account ɗin 0504192664 aisha ibrahim dansabo GTbank.*
Masu turo credit za ku turo katin MTN na 500 ta wannan line ɗin 08167768704.
_Ina ƴan kasuwa masu buƙatar a tallata muku hajar ku? Maza ku garzayo da kuɗi ƙalilan a tallata
muku kayan siyarwanku sai dai kawai ku ji ana kiran waya don buƙatan sayan kayan ku,ku
tuntuɓeni ta layina kamar haka 08167768704._
*57*
Basmah ta saki ƙayataccen murmushi tana duban cikin idanun Sharifa ta ce, "Ke dai bari kawai
ƙawata,da zafinsa ya zo kam amma maganan long story ne,bari in baku labarin yadda muka
haɗu...."
Basmah ta zayyane ma su Sharifa labarin tun farkon ganinta da Nass tare da TAIMIYYAH,har
kawo yau da ake zancen aurensu,nan da watanni uku masu zuwa.Ta kare maganan tana cewa,
"Friends wallahi ni kaina ganin abin na ke kamar a dream da,amma tunda Umma ta je Yobe ta kai
sunansa wajen oga teacher,shikenan komi ya tafi yadda muke so,kar ku so ku ga yadda Nass ke
nuna min so a yanzu,kamar dama can ni zuciyarsa ta fara so ba wata gurguwaba."
Ta kai ƙarshen maganar tana kwashewa da dariya, su Amna na taya ta.Kafin su tsaida dariyan
Sharifa na faɗin, "Ke bamu mu ga pics ɗinsa inga kalarsa ,da har kika iya rufe ido ki kai wa ƴar
uwarki ta jini ƙwacensa,gaskiya Basmah ba ku da kyau. Ni har tausayin baiwar Allah ya
kamani,da ace uwarsa bata raba alaƙar dake tsakaninsu ba, ahakan zaku farraqa tsakaninsu ki
auresa babu tsoran Allah?"
Sharifa ta ƙare maganar da tambayar Basmah, tana tsare ta da ido.Basmah tayi saurin haɗe fuska
tana dannawa Sharifa harara ta ce, "Eh...! Lallai Sharifa Salis, yaushe kika fara wa'azi bani da
labari? Ke idan ana maganar wanɗanda suka san kan snatching har kya yi motsi ma,kar ki ɓata
min rai please! Bari dai in nuna miki kalar haɗuwarsa,sannan sai ki san cewa ko ke ce, za ki iya
yin komi don ya zama mallakinki."
Basmah tayi maganar tana danno pic ɗin Nass,wanda ya yi azabar kyau.Ya ɗauki pic ɗin ne sanye
da ƙananun kaya,a wani haɗaɗɗen wajen cin abinci a garin Abuja.Ta miƙawa Sharifa wayar tana
cewa, "Amshi ki gani ƙawata."
Sharifa ta miƙa hannu ta amsa wayar Basmah,tana ɗaura idanunta akan screen ɗin wayar,idanunta
suka sauka akan kyakykyawar fuskar Nass Aliyu.Take ta ji wani dumm..! Cikin kanta,ta sake
tsurawa hoton idanu tana sake hango tsantsar kyawunsa da haɗuwarsa,tabbas bata ga laifin
Basmah da ta ruɗe akansa, har suka shiga suka fita za ta mallakesa ya zama nata ba.
Ta ɗauke idanunta daga duban hoton, ta mayar kan Basmah dake ta faman blushing,idanunta akan
Sharifan. Sharifa ta miƙawa Amna wayar tana cewa, "Ungo Amna ki gani,gaskiya guy ɗin ya haɗu
ba karya wallahi."
Amna ta amsa wayar ta kalli pic ɗin per seconds,sannan ta miƙawa Basmah wayarta tana cewa,
"Gaskiya ya haɗu ba karya Basmah,banga laifinki ba don ko ni na samu dama zan iya yin wuff da
shi."
Basmah ta warce wayarta daga hannun Amna, ta tsuke face ta ce, "Ban son iskanci ƙawata, a
gabana ki ke faɗin hakan?"
Sharifa ta amshe da faɗin, "To miye aciki ke ma ai ƙwacensa ki ka yi ƙawata,bare ma wasa Amna
take yi miki,Allah ya sanya alkhairy ya kaimu lokaci,mu ci uwar sabada a ranar."
Suka sheƙe da dariyar shaƙiyanci,Basmah na cigaba da basu labarin yadda tsare-tsaren bikin zai
kasance.Sai can yamma shaƙiƙan ƙawayen Basmah na tun secondary skull,wato Sharifa Salis da
Amna Muktar suka bar gidansu Basmahn,bayan ta yo musu rakiya har bakin gate.
__________
TAIMIYYAH da tunda ta shige ɗaki bayan tafiyar Maleek Ado,ba ta fito ba sai bayan sallan
isha'i.Direct kuma wajen cin abinci ta nufa don yin dinner,ta zauna bada jimawa ba Iyah ta iso
wajen,tana ɗaura idanunta akan TAIMIYYAH ta ke cewa, "Au ashe kin fito,da yanzu ai nake
shirin zuwa ɗakin naki inga ko lafiya,daga tafiyan mutum sai ki ƙule a ɗaki kina faman tunane-
tunane,to ni dai babu ruwana bana son kina sanyawa kanki damuwa akan abinda bai kai ya kawo
ba.Ki yi addu'a a duk abinda kika ga ya shigo cikin rayuwarki,Allah baya taɓa jarabtar bawa sai
akan abinda zai iya ɗauka,don haka ki dinga sanyawa kanki salama don Allah Zainabu."
TAIMIYYAH ta ɗaga kai ta dubi Iyah da manyan idanunta kafin ta ce, "Hakane Iyah nima ba
tunani nake yi ba,kawai na ɗanyi karatu ne sai na tsaya duba wasu littafai,ganin lokacin sallah yayi
yasa na tsaya na gabatar da sallar magriba, na jira akai isha'i sannan na fito cin abinci."
Iyah ta zauna tana faɗin, "To da dai yafi miki Zainabu kar kiji tsoran komi, In sha Allah koma
waye alkhairy ne ya kawo sa ba sharri ba."
Daga haka suka zuzzuba abincin suka fara ci,suna hira kaɗan-kaɗan har suka kammala cin
abincin.TAIMIYYAH ta koma daga cikin falon Iyah ta zauna,tana ɗaukar remote ta sauya tasha
zuwa Bollywood.So take yi ta hana zuciyarta yawan tunanin mutumin ɗazu,ta ƙura ido akan TVn
ba don tana da tabbacin zata fahimci komi ba.Ta rasa meyasa tunaninsa yaƙi fita daga zuciyarta,ya
yi mata tsaye a rai, da ta rufe ido hannuwansa take ji a fuskarta,ta yi saurin sake manna idanunta
akan screen ɗin TV, tana kallon fuskar fararen fatar dake gilmawa a ciki,ba tare da ta san kan film
ɗin ba, bare ta fara fahimtan ina aka dosa ma.
Ƙaran shigowar saƙo cikin wayarta,yasa ta ɗaga ido ta kalli agogon dake manne jikin bango,inda
ya nuna ƙarfe 8:49pm (Takwas da mintuna arba'in da tara na dare).
Sai ta maido dubanta kan wayarta,tana me kai hannu ta yi swiping screen lock ɗin wayar.Idanunta
ya sauka akan baƙin lambobin da aka turo saƙon,sai ta samu kanta da buɗe saƙon don ganin daga
waye?
_"Salam Zaynabbb! Hope u are fine,please zan kira vid call in the next some minutes,ki yi
picking call ɗin please!_ "
Waɗannan sune kalaman dake rubuce cikin saƙon.TAIMIYYAH ta karanta saƙon a ƙallah kusan
sau uku, amma brain ɗinta bai kawo koda wasa cewa daga Maleek bane,don ta san har suka rabu
bata bashi numbarta ba, 'To ko dai Yah Emran ne?', Tunaninta ya haska mata hakan, tana jin wani
abu na taɓa ranta.Sai dai kafin ta sake wani dogon tunani, kira ta vid call ɗin ya shigo wayarta,ta
tsurawa wayar ido tana ji haka kawai zuciyarta na fara dokawa da ƙarfi.
Sai ta miƙe tsam! Tana duban Iyah da ke zaune cikin falon,ta nufi hanyar zuwa ɗakinta tana cewa,
"Iyah bari in amsa call, idan na gama bacci bai zo ba,zan dawo na ƙarisa kallon."
Ta cigaba da dafe ƙafarta tana takawa ta nufi hanyar ɗakinta,Iyah tabi bayanta da kallon tana ɗan
taɓe baki, ta miƙa hannu ta ɗakko remote,ta canza tasha daga Bollywood zuwa Sunnah TV.
TAIMIYYAH na shiga ɗakinta zama tayi daga bakin bed, lokacin da wani kiran ke shigowa,ganin
wannan karon ba vid call bane,sai zuciyarta ta ingizata akan ta ɗaga wayar ta ji ko waye?
Ta yi receving call ɗin tana kai wayan kunni ba tare da tace komi ba,sai ƙirjinta da ke faman doka
mata da wani irin yanayi da bata san dalilin hakan ba.
Ta saki numfashin da bata san ta riƙe ba kafin ta furta, "Na'am wa ke magana please?"
Tayi tambayar cikin sanyin murya sosai,tana jiyo yadda shi ma ya sauke numfashi daga
ɓangarensa, kafin ya furta, "Maleek Ibrahim ne Zaunabb! Meyasa ba ki yi picking vid call ba,ko
ba ki ga message ɗin dana turo miki before in kira ba ne ?"
TAIMIYYAH ta jefa masa tambayar cikin wani irin sanyin muryar ta.
Maleek ya furta hakan yana cuting call ɗin,ya kira ta vid call ɗin.
TAIMIYYAH sai ta janyo Hijab ɗinta da ke saman gado ta sanya, kalar Hijab ɗin blue black ne,sai
da ta gyara zaman wuyan Hijab ɗin sosai sannan tayi receiving vid call ɗin,tana jin yadda bugun
zuciyarta ke ƙaruwa.
Kyakykyawar miskilalliyar fuskar Maleek Ado ne,ya bayyana akan allon screen ɗin wayarta,yana
kwance daga kan makeken bed ɗinsa,yana sanye cikin milk ɗin pajamas da suka haske fatarsa.
TAIMIYYAH tayi saurin ɗauke face ɗinta daga dubansa.Maleek Ado da idanunsa ke kan screen
ɗin wayarsa, lokacin da kyakykyawar fuskar TAIMIYYAH ta bayyana masa,sai ya samu kansa da
lumshe idanunsa, wani abu na sake dokawa cikin kansa.Ya buɗe idanun ya sauke a side face
ɗinta,sabida yadda ta ƙi yadda ta sake kallonsa ta cikin wayartata.Sai yayi magana very low yana
cewa, "Zaynabb ki kalleni don Allah ko zan samu cikakkiyar nutsuwa,idan na sanya idanuna cikin
kwayar idanunki,waɗanda suka jima suna gilmayya cikin barcina."
Waɗannan furucin da Maleek ya furtasu,su suka sanya TAIMIYYAH saurin duban fuskar
wayarta.Manyan idanunta suka sake sauka akan fuskar Maleek,wanda idanunsa ke kafe akan allon
screen ɗin wayarsa,ya sauke ajiyar zuciya yana kallon cikin idanun TAIMIYYAH,wani baƙon
yanayi na sake lulluɓe ruhinsa,tare da aika wani irin zazzafan saƙo,cikin kowacce kafa ta sadarwa
da ke jikinsa.TAIMIYYAH ta sake ƙasa da murya tana cewa, "Don Allah ka daina jefa zuciyata
cikin ruɗani,tun ɗazu ka ke furta wasu kalamai da ke nuna kaman ka taɓa sanina awani
waje,please! waya turo ka zuwa gareni,ko ince a ina ka taɓa ganina da har kake ganin idanuna
acikin baccinka?"
TAIMIYYAH ta kai ƙarshen maganar tana duban fuskar Maleek Ado,cike da son ya fayyace mata
yadda aka yi ya santa, har ya kawo kansa gareta.Sam ita ba ta san irin illar da salon maganarta ya
yiwa zuciyar Maleek Ado ba,wanda tunda ta fara magana yake duban fuskarta da manyan
idanunta,waɗanda suka ƙara girma bisa screen ɗin wayarsa.
Ya wani cije lips ɗinsa, yana ji tamkar ya tsinci TAIMIYYAH a kusa da shi,don kawai ya tasata a
gaba ya yi ta kallon kwayar idanunta,waɗanda suka jima suna ruɗa tunaninsa a cikin
mafarki.Idanun da ya gama sallamawa cewa ,na wata aljanace can daban wacce ke son kawo
ruɗani cikin duniyarsa, a wancan lokacin,amma sai gashi yau Allah ya bayyana masa cikakkiyar
surar mamallakiyarsu a zahiri,cikin lokacin da bai taɓa tunani ko hasashe ba, 'ta ya shi ko zai yi
sakacin da wannan halittar za ta kubce masa?' Tunanin ya haska cikin kansa da wani irin tasirin da
bai taɓa tunani ba.Ya sake duban fuskarta wacce ta sunkuyar da shi ƙasa,da alamu tafin hannunta
take kallo,sai ya sake kiran sunanta 'Zaynabb!' TAIMIYYAH tayi firgigit! Ta ɗago manyan
idanunta da suka sake girma ta sauke akan fuskarsa,tana me shagwaɓe fuskarta da muryarta duka a
lokaci guda,sannan ta furta, "Na'am! Don Allah ka sanar da ni waye kai? A ina ka sanni please!?"
Maleek ya ɗan taɓe baki yana sake miskile fuskarsa ya ce, "Zaynabb meyasa na ke baki tsoro ne
wai? Sunana Maleek Ado na sanar miki tun ɗazu,maganar ki san ko ni waye za ki sani amma ba
yanzu ba,in da na sanki kuwa da kike magana akai,to a cikin mafarkina na fara sanin idanunki ba
fuskarki ba,a cikin mafarki na fara jin wannan muryar taki me kama da magic,a cikin mafarki na
san wani ɓangare naki Zaynab,shiyasa yau da idanuna suka sauka akanki,gaba ɗaya na rasa
dukkanin nutsuwata.Oya tell me wacece Zainab TAIMIYYAH please?"
Maleek ya yi maganar yana duban yadda TAIMIYYAH ta zaro idanunta, cike da zallar mamakin
kalamansa take dubansa,don baƙarmin tsoratata kalamansa na cewa a cikin mafarki ya fara saninta
su kai ba.Ta buɗe baki muryarta na shaking take cewa, "Na ji zan sanar da kai komi game da ni,
amma sai ka fara bani labarin yadda aka yi, ka ke mafarki da irin idanuna."
Karon farko da Maleek Ado ya saki murmushin da bai shirya yinsa ba,idanunsa na zube fes akan
fuskar TAIMIYYAH.Kafin ya maida face ɗinsa ya miskileta kamar yadda take ada, yana farawa
da faɗin. "Zaynab zai kai kaman watanni shida zuwa takwas baya, da na fara mafarki da me siffar
idanunki a cikin baccina,ya zamana kusan kullum ne sai nayi mafarki da Yarinyar me irin
idanunki, amma ba'a taɓa nuna min zahirin fuskar ko wace ce ba,sai dai a nuna min waɗannan
idanun masu haske,suna kuka tana miƙo min hannu kamar tana buƙatan taimako daga gare ni,da
zaran na miƙa hannu zan kama hannun da ta ke miƙomin, sai na mafarka daga baccin ina jin wani
irin yanayi da bana iya fassara shi...."
#Ɗansabo ce#
[12/14, 3:43 PM] +234 703 040 9541: Littafin TAIMIYYAH paid book ne,ga duk wanda ta
tsincesa a kowani irin group ne,kiji tsoran Allah karki karanta sai kin biya 500 naira only.
Za ku iya min magana ta wannan number ɗin 08167768704, ko kuma ku turo kuɗin ku kai tsaye ta
wannan account ɗin 0504192664 aisha ibrahim dansabo GTbank.*
Masu turo credit za ku turo katin MTN na 500 ta wannan line ɗin 08167768704.
_Ina ƴan kasuwa masu buƙatar a tallata muku hajar ku? Maza ku garzayo da kuɗi ƙalilan a tallata
muku kayan siyarwanku sai dai kawai ku ji ana kiran waya don buƙatan sayan kayan ku,ku
tuntuɓeni ta layina kamar haka 08167768704._
*58*
TAIMIYYAH gaba ɗaya kanta kullewa yayi da jin labarin mafarkin da Maleek Ado ya yi tayi a
baya,kuma wai me irin idanunta Maleek ɗin ya ke gani a cikin mafarkin nasa.
Memakon ta tsaya ta cigaba da sauraransa, sai kawai ta kashe wayarta,tana me jingina jikinta da
jikin gadon, ta lumshe idanunta.
Bakomi ke yawo a kanta ba, sai moment ɗin ɗazu da yamma zuwa yanzu,gaba ki ɗaya sai ta ji
tana tsoran Maleek ɗin ma baki ɗaya.Tana ji yana sake kiranta amma tayi biris da wayar,har ta
gama ɓurarinta ta tsinke,zuwa can sai ta ji ƙaran shigowar saƙo cikin wayartata.
Ta miƙa hannu a hankali kamar me tsoron taɓa wayar,ta janyota ta yi swiping tare da buɗo saƙon
kai tsaye,don ganin me ke rubuce a ciki,idanunta suka sauka akan kalaman daya aiko kamar haka,
" _Zaynabb meyasa zaki kashe min waya?Zan barki ki nutsu da kyau, amma kada ki ce za ki damu
kanki da yawan tunanin,cewa sai kin san ko waye ni cikin gaggawa,soon za ki sani Zaynabb.Gud
night wife to be._ "
TAIMIYYAH ta dinga karanta saƙon yafi sau goma,kanta na sake ɗaurewa tare da jin matsanancin
fargaba, da tsoron wannan mutumi.Kalamansa na ƙarshe ke sake gigita tunaninta inda yace "Wife
to be." Tunanin ya haska da wasu irin tarin tambayoyi da suka cika kwanyarta, 'A ina ya san
ni,kuma waye ya bashi numberta har ya kirani,ba tare da na bashi ni a karan kaina ba?"
Waɗannan tambayoyin suka cika zuciyar TAIMIYYAH, tare da sake kulle mata kai,ta ƙurawa
saƙon idanu tana sake karantawa a karo na goma sha ɗaya.Ta ɗauke dubanta daga karanta saƙon,
tana nanata sunansa akan harshenta a bayyane, "Maleek Ado." Kamar yadda ya rubuta daga ƙasan
saƙon,ta maida idanunta ta lumshe abinda ya faru ɗazu a falon Abie na dawowa kwanyarta, 'Kenan
da gaske mafarkin ya ke yi da irin idanunta,shiyasa ya shiga shock lokacin da ya ganta a
zahiri,har yana kasa riƙe kansa sai da ya taɓa fuskarta?" Wannan tunanin ya haska cikin kanta,tana
jin wani irin abu na shiga jikinta yana ratsa ɓargonta.Ta sake rintse idanunta zuciyarta na wani irin
bugu,ta buɗe idanun tana kai hannu ta shafa fuskarta,ji take yi kamar har lokacin lallausar
hannunsa na kan fuskarta ne.
Da ƙyar TAIMIYYAH ta iya yakice tunanin komi, ta sakko daga kan bed ɗin ta nufi toilet,alwala
ta ɗauro ta fito ta nufi kan sallaya don gabatar da shafa'i da wuturi, wanda bata yi sai za ta kwanta
bacci.
Lokacin da ta idar light off kawai ta yi ta bi lafiyar gado,bayan ta canza kayan jikinta zuwa na
bacci,ta jima sosai tana faman tunane-tunane duk akan Maleek Ado.Wanda ya yi mata tsaye a
cikin rai, ta ke kuma da buƙatan sanin cikakken waye shi,ya akayi kuma har ya kawo kansa
gidansu alhali yace mafarki ya ke kawai da me irin idanunta? Sai da TAIMIYYAH ta ga cewa
tunani zai iya halaka kwanyarta, sannan ta lumshe idanunta tana fara karonto azkar na kwanciya
bacci.
_____________
Muryar TAIMIYYAH da salon maganarta ke dawo masa,yana jin wani irin feeling na dabaibaiye
zuciyarsa.Idanunta yake haskowa a lokacin da take waro masa su,bayan ya gama bata labarin
mafarkin da ya dinga yi da mai irin idanunta.Kyakykyawar murmushi ya bayyana a saman
miskilalliyar fuskarsa,ya kai hannu zuwa kansa yana yamutsa sassalkan gashin kansa me matuƙar
ɗaukar ido,sabida kuɗin da suman ke ci ba kaɗan bane.
Kiran Suhailah ne ya shigo cikin wayarsa,hakan ya dawo da shi cikin hayyacinsa,daga duniyar
tunanin TAIMIYYAH da ya lula.
Ya miƙa hannu ya janyo wayar, yana receiving call ɗin tare da gyara kwanciyarsa sosai.Muryar
Suhailah cikin shagwaɓa ya shiga kunnuwansa lokacin da ta ke cewa, "Hello! my Maleek kana
jina?"
Maleek ya buɗe idanunsa yana cuting call ɗin,ya kirata vid call kawai don yana buƙatar ganin
yanayin da take ciki.
Fuskar Suhailah zuwa gangar jikinta ne ya bayyana a allon screen ɗinsa,lokacin da Suhailah tayi
receiving vid call ɗin.Maleek Ado ya sauke ganinsa a kan rigar baccin da ke jikinta kalar pink me
santsi,rigar me faɗin wuya ce hakan yasa ƙirjinta ya fito sosai ta sama.Ya ɗauke idanunsa daga
kallon ƙirjinta ya mayar zuwa kan fuskarta,idanunsu suka gauraya dana Suhailah, wacce ita ma
nata idanun ke kan kallon face ɗinsa.Ta sakar mata kyakykyawar murmushi tana faɗin,
"My Maleek i miss u,tun ɗazu nake kiran line ɗinnan naka ina jin busy,na kira Hajjah ma bata
ɗaga ba,har yanzu fa bana jin daɗin jikina Baby."
Tayi maganar cike da shagwaɓa ganin yadda Maleek ɗin ya tsura mata ido,kafin ya buɗe baki
kamar mara son magana ya ce, "Sorry wife,sauƙi ai a hankali yake samuwa, hope dai kina shan
magungunan yadda ya dace?" Suhailah ta gyaɗa kai cike da tabbatar masa da cewar tana sha,sai
Maleek ya cigaba da cewa,
"Alright! Karki damu zazzaɓin zai tafi soon wife,but i miss u wife so much,oya kiss me wife."
Subailah sai ta saki murmushi, tana aiko masa da kiss ɗin kamar yadda ya buƙata,shi ma sai ya
aiko mata da nasa kiss ɗin, suka saki murmushi a lokaci guda.Kowannensu na jin wani
matsanancin kewar ɗan uwansa na danne zuciyarsa,Suhailah ta sake narke murya tana cewa,
"Sweet ɗazu wata makwafciyarmu ta shigo, ta yi introducing kanta a wajena tana so mu dinga
zumunci, tace su ma basu jima da tarewa ba,goben za ka taho ɗin ne my Maleek?"
A.Maleek Ado ya dubi Suhailah da manyan idanunsa ya ce, "Yes gobe zan dawo wife,na gane
gidan da kike nufi,ina ga matar Captain Aliyu ce indai wanda gidansu ke jikin namu ne ko?"
Subailah ta amsa da cewa, "Yes haka tace kuwa,sunan mijin Aliyu ita kuma Jawahir,matar me
fara'a da son mutane kuwa, daga gani za ta yi kirki sosai Yah Maleek."
Maleek ya ɗaure fuska tare da zama so serious lokacin da ya ce, "Okey daga gani ɗaya da ki kai
mata har kin karanci halinta kenan,look Suhailah ni fa bana son saurin sakin jiki da mutanen da
kike yi,u have to be very very careful akan irin wanɗanda za ki dinga mu'amala dasu,and bazan
yarda da shiga gidan mutane ba,su idan sun shigo miki ba zan hanaki harka da su ba,amma ban
yarda kina shiga gidan kowa ba,Abuja bariki ne ba irin Zaria bane da kika sani,so u have to be
careful."
Suhailah da ke sauraren Maleek, idanunta akansa ta narke murya tana cewa, "Okey my Maleek
zan kiyaye In sha Allah,dama ina gaya maka ne cox tace a gaida ka."
Daga haka suka cigaba da hiransu irin na mata da miji,kafin su yiwa juna gud night, Maleek ya
kashe wayarsa yana jin kewar Suhailar me tsanani na ratsa shi,ga kuma tunanin TAIMIYYAH da
ke addabar zuciyarsa.
Ya miƙe tsaye yana ɗaukar remote ɗin AC ya ƙara ƙarfin aikinsa,sannan ya nufi toilet don yin
uzurinsa,yana fitowa light off yayi ya kwanta, yana ji a zuciyarsa dole gobe kafin ya wuce, ya
sanar da Hajjah yadda yake ji akan wannan gurguwan, don ba zai iya jurewa ba,idan har ba
mallakarta yayi da gaggawa ba.
____________
Washegary TAIMIYYAH ta tashi ne da tunanin Maleek cikin zuciyarta,amma sai ta dinga kwaɓar
zuciyarta akan ta manta da tunaninsa.
Koda ta ga shigowar kiransa vid call, misalin sha ɗaya na safe ƙin ɗauka tayi,duk yadda wani
sashi na zuciyarta ke kwaɗaitar da ita,ta ɗauki wayar bata ɗauka ɗin ba har kiran ya yanke,lokacin
da wani kiran ya sake shigowa ma TAIMIYYAH ƙin ɗauka ta yi,sai ma ta aje wayar bisa bed tana
me fita daga ɗakin baki ɗaya.
_____________
*Gonar Ganye.*
A.Maleek Ado ne zaune a tsakiyar falon Hajjah yana yin breakfast,tun wajen ƙarfe goma ya iso
gidan don yana son suyi magana da Hajjah kafin ya wuce Abuja a yau ɗin.
Duk kiran da ya yiwa TAIMIYYAH suna zaune tare da Hajjan ne,hakan yasa ya dubi Hajjah
lokacin da kiran ƙarshe ya tsinke ba tare da TAIMIYYAH ta ɗaga ba ya ce, "Hajjah ina ta kiran
Yarinyar nan taƙi ta ɗaga wayata,na kirata sau huɗu kenan, gaskiya Hajjah ba zan iya jurar hakan
ba,tun jiya da na bata labarin mafarkin dana dinga yi a baya, ta kashe min waya bata ƙara saurarata
ba.Don Allah Hajjah ki je wajan kakarta ki sanar dasu halin da ake ciki,don ni ba ƙaramin yaro
bane da zan tsaya soyayyar jan aji,tunda na ɗaura idanuna akanta na gane itace yarinyar cikin
mafarkina,shikenan zuciyata bata sake hutawa ba,wani azababben ƙaunarta na ke ji irin wanda
bazan iya misaltawa ba,sannan ina ji a jikina cewa ba zan sake samun sukunin zuciyata ba, in har
ba mallakarta na yi ba Hajjah."
Maleek ya kai ƙarshen maganar cikin marairaice murya,hakan yasa Hajjah dubansa tana faman
sakin murmushi ta ce, "Maleek kana da gaggawa a cikin lamuranka,kamata yayi ka yi haƙury ka
bita a hankali,ina ga ta tsorota da cewa kana mafarki da ita alhali bata san ka ba,bata san ko kai
waye ba. Kawai ta ganka ne rana tsaka ka je gareta,sannan kuma ka ce kana mafarki da irin siffar
idanunta,ka ga hakan dole ya jefata a ruɗani.Zan je gidan zuwa jibi In sha Allah mu tattauna da
Iyah ɗin,zan sanar da ita komi tare da neman alfarman a bamu dama, ka fara neman
TAIMIYYAH,idan har ta ji tana sonka shikenan sai komi ya zo cikin sauƙi,in kuma bata sonka sai
mu haƙura don ba za a yi mata dole ba."
Hajjah tayi maganar idanunta akan Maleek, wanda ya sake tsuke fuska,gaba ɗaya zuciyarsa na ga
TAIMIYYAH,tunda ya tashi yake jin babu abinda yake son ji da gani kamar muryarta, da son
ganin waɗannan sparkle eyes ɗin nata, masu tsananin haske da birgewa.Ya narke murya sosai yana
duban Hajjah da fuskar tausayi yake faɗin, "Please Hajjah ki daina cewa in bata so na,ni ko bata
sona tunda ni naji ina ƙaunarta to hakanan za ta amsheni,ni zan koyar da ita yadda za ta ƙaunace
ni,ni dai kawai Hajjah ki je gobe ba sai jibi ba, sannan ki ɗan kira ta yanzu inji muryarta please
Hajjah, hakan kawai zai bani nutsuwa har na isa Abuja cikin kwanciyar hankali,wallahi Hajjah ba
zan iya misalta miki yadda nake ji akan Zaynab daga ganinta daga jiya zuwa yau ba."
Hajjah ta dubi Maleek da fuskar tausayinsa, don ita kanta ta fahimci cewa,akwai wani ɓoyayyen
lamari da ya jona zuciyar Maleek da TAIMIYYAH, tun akan labarin mafarkin da yace yana yi da
ita.
Ta saki murmushi me faɗi tana miƙawa Maleek wayarta ta ce, "Ungu kirata da kanka,idan ta
ɗauka sai ka bani muyi magana."
Maleek ya amsa wayar hannunsa har rawa yake, lokacin da yake dialing numbar
TAIMIYYAH,bugu biyu ana uku ta ɗaga wayar cikin siriryar muryata.Maleek yayi sauri sanya
wayar a speeker ya miƙawa Hajjah lokacin da TAIMIYYAH ke faɗin,
Hajjah ta amsa da cewa, "Lafiya lau Zainab ya kwana biyu, ya Iyah ina fata kuna lafiya?"
Muryar TAIMIYYAH ya sake fitowa tar lokacin da take amsa Hajjah da cewa, "Lafiya lau
Hajiya,ai muna ta so mu zo ni da Iyah amma har yanzu bamu sama time ba,amma zuwa next week
Saturday za mu zo In sha Allah."
TAIMIYYAH ta ce, "Okey tuh zan sanar da ita Hajiya, mun gode sosai da kulawa."
Hajjah ta murmusa ta ce, "Bakomi Zainab ina fata da wuri kike dawowa daga skull ɗin da kike
zuwa?"
TAIMIYYAH ta baiwa Hajjah amsa da cewa, "Eh da wuri nake dawowa Hajiya."
"To madallah! Allah yayi albarka ya bada ilimi me anfani,sai na zo ɗin ki gaida Hajiya Fatiman da
kyau."
Cewan Hajjah,daga haka kuma sukai sallama da TAIMIYYAH,ta ɗaga idanunta ta sauke akan face
ɗin Maleek,wanda ya wani lumshe idanunsa,yana jin wani irin yanayi na bin ilahirin jinin
jikinsa.Hajjah ta shafa kansa tana cewa, "To Maleek hankalinka ya kwanta yanzu ko?"
Maleek ya ɗago kansa yana faman yamutse fuska ya ce, "Ya kwanta amma kaɗan Hajjah,ba zai
gama kwanciya ba sai kin cika ladanki, wajen ganin na mallaki gurguwarki ta zama tawa,na yi
miki alƙawarin kasancewa da ita har ƙarshen numfashi,na kamu da ƙaunarta me ƙarfi Hajjah,irin
ƙaunar da ban taɓa jin irinsa ba bayan naki da bashi da mahaɗi.Na kasa gane ko dama can da na ke
ɓata lokaci ina tunani idan nayi mafarki da waɗannan idanun nata,cewa na kamu da ƙaunar me
idanun ne tun ban san kowace ce ita ba,tun jiya dana ɗaura idanuna akanta, nake ji zuciyata na
amsawa da wani irin baƙon yana yi ,wanda baki ba zai iya misaltawa ba,don Allah Hajjah ki
taimakeni a bani Zainab,cikin lokaci da ba mai yawa ba,don ina ji ajikina bazan sake samun
nutsuwa ba ,idan har ba na ga an ɗaura mana aure ba."
Yadda yake maganar cikin tabbatar da dukkanin kalamansa, yasa Hajjah sauke numfashi,kafin ta
fara da cewa, "Maleek In sha Allah in dai Zainab rabonka ce za ka sameta,sai dai ina jin tausayin
ƴa ta Suhailah, domin tana maka wani irin so me wahala,tana kuma da kishi me tsanani
akanka,don haka ina roƙon alfarman ka riƙe kanka wajen danne zafin soyayyar Zaynab, don na
lura tun yanzu kana neman ka dinga rasa nutsuwarka akanta."
Karon farko tun shigowarsa gidan, ƙayataccen murmushi ya ƙwace masa,sabida jin furucin Hajjah
na ƙarshe,ya saki murmushin me faɗi har fararen haƙoransa na bayyana,kafin ya dubi Hajjah yana
cewa, "Hajjah kar ki damu zan yi iya yi na, wajen ganin nayi controlling duk wani feeling da na ke
ji akan Zaynabb,Suhailah kuma ke zaki san yadda za ki yi, ki fahimtar da ita komi Hajjah,tunda ke
ce silar haɗuwata da dream gal ɗina, wacce idanunta kawai nake gani a she pretty gal ce a zahiri."
Yayi maganar yana jin wani nishaɗi a cikin zuciyarsa, lokacin da kyakykyawar fuskar
TAIMIYYAH ya bayyana a idanunsa,Hajjah ta saki baki tana kallonsa da tsantsar mamaki, tare da
jinjina ƙudira na Ubangiji.Ta saki murmushi me faɗi lokacin da zuciyarta ta tuno mata da
Suhailah,da irin son da take wa Maleek ɗin, tabbas ta san akwai daru a gaba,idan har ya tabbata
Maleek zai ƙara aure.Ta dubi Maleek cikin ido tana cewa, "Kar ka damu nan za ka taho min da ita,
inyi rarrashi da ban baki tuƙuru,idan har Allah ya ƙulla wani abu a tsakaninka da Zainab
ɗin,Suhailah na da zafin kishi akan ka,shiyasa har addu'a na ke mata akan Allah ya rage mata zafin
kishi,don kishi idan ya cika yawa masifa ne."
Maleek ya jinjina kai yana cewa, "Hakane Hajjah,amma ai za ta fahimceki in dai daga bakinki za
ta ji komi,sabida ni dai a yadda nake ji akan Zaynabb, bana ji ko Nigeria Suhailah za ta yaƙa
sabida zafin kishi,hakan ba zai hana ni mallakar Zainabb ba."
Hajjah ta jinjina kai da tsantsar al'ajabin cewa,wai Maleek ne zaune a gabanta yana furta
waɗannan kamalan duk akan TAIMIYYAH? Ta saki kyakykyawar murmushi tana wa Allah godia,
da zai cika mata burin ta cikin sauƙi,tana kuma fata Iyah da Zainab su yi na'am da tilon ɗanta guda
ɗaya, da take kwaɗayin ya haɗa jini da su,sabida tarbiyar TAIMIYYAN da kuma tausayinta da
take ji,wanda ya haifar da zazzafar ƙaunarta a zuciyar Hajjan.
Sun daɗe suna cigaba da magana tsakanin Hajjah da Maleek Ado, duk akan TAIMIYYAH sai
around 12:30pm yayi sallama da Hajjah,driver ɗinsa Yusuf shi ne zai wuce da shi zuwa Kano,ya bi
flight zuwa Abuja sabida gobe 8 za su shiga meeting,tare da Minister of Transportation.
Hajjah ce ta sanya Lubah fita da saƙon Suhailah, aka sanya komi cikin boot,wanda ya kasance su
garin kunu ne, da na ɗanwake da Maleek ɗin zai wuce da shi. Maleek sai da ya sallami su Babah
Rabi da kuɗi kamar yadda ya saba,sai faman godia su ke yi masa.
Maleek suka fito tare da Hajjah har zuwa wajen mota, suna cigaba da tattaunawa akan
TAIMIYYAH,ta yi masa addu'a na fatan alkhairy,da neman kariya kamar yadda ta saba,sannan ya
shiga mota Yusuf ya ja,suka bar gidan yana jin zuciyarsa, na cike da wani irin nishaɗi mara
misaltuwa............✍🏻
#Ɗansabo ce#
[12/14, 3:43 PM] +234 703 040 9541: Littafin TAIMIYYAH paid book ne,ga duk wanda ta
tsincesa a kowani irin group ne,kiji tsoran Allah karki karanta sai kin biya 500 naira only.
Za ku iya min magana ta wannan number ɗin 08167768704, ko kuma ku turo kuɗin ku kai tsaye ta
wannan account ɗin 0504192664 aisha ibrahim dansabo GTbank.*
Masu turo credit za ku turo katin MTN na 500 ta wannan line ɗin 08167768704.
_Ina ƴan kasuwa masu buƙatar a tallata muku hajar ku? Maza ku garzayo da kuɗi ƙalilan a tallata
muku kayan siyarwanku sai dai kawai ku ji ana kiran waya don buƙatan sayan kayan ku,ku
tuntuɓeni ta layina kamar haka 08167768704._
*59*
Washegari TAIMIYYAH ta dawo daga skull ne kawai,ta tadda danƙareriyar motar Hajiya Aysha
fake a cikin compound ɗin gidansu.
A hankali take takowa daga bakin gate ɗin zuwa ciki,sabida gajiyan da tayi a skull ɗin yau,har za
ta wuce motar sai ta hangi Shehu daga ciki yana zaune,hakan yasa ta nufi wajen motar suka
gaisa,sannan ta wuce zuwa sasan Iyah .
Da sallama ta isa bakin ƙofar shiga falon Iyah,Iyah daga ciki ta amsa sallamar da TAIMIYYAH
tayi,hakan yasa TAIMIYYAH kutsa kanta ciki,idanunta suka sauka akan Hajiya Aysha da ke zaune
cikin falon,an cika gabanta da kayan cima,don tun jiya da TAIMIYYAH ta sanar da Iyah cewa
Hajiyan za ta zo,Iyah ta tashi yau da shirin tarbanta ita da Babah Ladi.
TAIMIYYAH ta isa cikin falon fuskarta na blushing, ta ƙarisa kusa da kujeran da Hajjah ke
zaune,ta durƙusa ta kwashi gaisuwa.Hajjah ta amsa gaisuwar cike da kulawa idanunta akan
TAIMIYYAH da tayi mata kyau sosai, cikin hijab ɗin jikinta kalar maroon,TAIMIYYAH ta dubi
Iyah tana cewa, "IYah ina yini,na dawo".
Iyah ta amsa da cewa, "Lafiya lau, barka da dawowa Zaynab,ai tun ɗazu Hajiya ke tamabayar
yaushe za ki dawo,don tace zuwar naki ne sai ki maza ki shiga ciki, ki kintsa ki fito ki ci abinci."
TAIMIYYAH sai ta dubi Iyah da sauri tana cewa, "Tuh Iyah bari in shiga daga ciki, sallah zan yi
sai in fito."
Daga haka TAIMIYYAH ta miƙe tana dafa ƙafarta, ta fara takawa don isa zuwa ɗakinta,zuciyarta
na cike da mamakin kalaman Iyah na cewa wai Hajiya wajenta ta zo.
Har ta cire hijab ɗin jikinta ta nufi toilet, tunani abinda zai sa Hajiya ta yo takakki zuwa wajenta
take yi,haka nan dai ta yi uzurinta ta ɗauro alwala ta fito ta tada sallah.
Hajiya Aysha ce ta fara da baiwa su Iyah labarin cikakken asalinta in da da soma cewa,
" Sunana Ayshatu Aliyu,haifaffiyar jihar Katsina,mahaifina Alhaji Aliyu shine Magajin Garin
Katsina a wancan lokacin,mahaifiyar mu Hauwa ita kaɗai ce matar mahaifin mu har suka bar
gidan duniya, bai sake wani aure ba kuma mu uku kaɗai suka haifa a duniya,Hadeeza itace
Babba,sai ni Ayshatu sai Autar mu Hauwa'u. Na yi karatuna tun daga kan primary har ya zuwa
jami'a,na kuma yi aure ina da shekaru sha tara a duniya, lokacin ina shekarar ƙarshe a jami'ar
Ahmadu Bello da kenan Zaria,na karanci course ɗin Libarary Science ne.
Mijina marigayi Alhaji Ibrahim Ado haifaffen garin Zaria ne, a wata Unguwa da ake kira Lowcos
cikin lardin birnin Zazzau. Mun haɗu da shi ne a cikin jami'ar Ahmadu Bello, watarana ya kawo
ziyara cikin makarantar, a matsayinsa na tsohon ɗalibin jami'ar. Ba mu jima da haɗuwa ba
soyayyah me ƙarfi ya ƙullo tsakaninmu, har ta kai ga manya sun shiga ciki an sanya mana ranar
aure."
Hajjah ta cigaba da cewa,
" A lokacin Ibrahim Ado yana aiki ne da hukumar Custum, inda har ya fara taka matsayi me girma
a lokacin,don irin mazannan ne da ke tsayawa su samu ilimi me zurfi kafin su yi aure.Mun haɗu
da watanni uku aka yi bikin mu ni da shi,aka ɗakkoni daga Katsina aka kawo ni Zaria,cikin sabon
gidan da ya gina a cikin Unguwar Tukur-Tukur.
Cikin shekaru goma da aurenmu na haifi adadin ƴaƴa biyar,amma duk suna mutuwa sai daga
ƙarshe Ubangiji ya raya min Abdul-maleek, wanda na haife shi muna da shekaru sha biyu da aure.
Hakan yasa ni da mahaifinsa muka ɗauki son duniya muka ɗaura akansa,sai dai hakan bai hana
mu ba shi ingantacciyar tarbiya ba. Gata da kulawar da yake samu hatta daga wajen kakarsa wacce
ta haifi Ubansa, bai sa ya taso a sangarce ba,sabida jajircewata wajen ganin ya samu tarbiya me
kyau. Sam bana nuna masa so a zahiri yadda zai sangarce,yana da shekaru goma muka tattara
muka koma Lagos da zama,sabida lokacin mahaifinsa ya kusa zama Asistant Controler na ƙasa. A
can Lagos Maleek kamar yadda muke kiransa,ya kammala karatunsa na primary,daga nan ya wuce
secondary skull, lokacin ne kuma Autar mu Hauwa ita ma aure ya kawo ta garin Lagos,na yi farin
ciki da hakan a lokacin, domin dama ban san kowa a Lagos ba lokacin da muka koma. Cikin
ƙanƙanin lokaci Maleek ya yi wani irin sabo da Antynsa Hausa,shaƙuwa ya shiga tsakaninsu
sosai,duk idan ya dawo skull zai matsa sai driver ya kaisa gidanta.yana SS 2 ma ya iya driving
sosai abinsa, uban kuma ya ɗaure masa gindi ya siya masa sabuwar mota,sai ya zamana da ya
dawo skull zai ɗauki mota ya wuce gidan Anty Hauwa. Kominsa ita ce hatta abu idan yana so, sai
ya fara sanar mata kafin ni in sani.Bayan ya kammala karatun Secondary ne mahaifinsa ya fita da
shi England, a can ya haɗo deegree ɗinsa na farko da na biyu, duk a fannin da ya shafi siyasa wato
'Political Science'
Hajjah ta kai hannu ta share hawayen da ya zubo mata,na tuna da mummunan ranar da ba za ta
taɓa mantawa da shi, a tarihin rayuwarta ba,ta cigaba da cewa,
"Faɗin irin tashin hankali da giginta da muka shiga ma ɓata baki ne.Mun ɗauki tsayin lokaci kafin
mu dangana,har mu cigaba da rayuw ba don zuciyoyinmu, sun daina jin zafi da raɗaɗin rashin
mutum irin Alhaji Ibrahim Ado ba.
Kuma wannan shine silar tsanata da garin Lagos,ta yadda ko sunan garin aka kira sai na ji zuciyata
ta motsa da ɓacin rai me tsanani.Maleek shi ne ya gina min Sabon gida bayan fitana takaba,na tare
a cikinsa a Gonar Ganye,a lokacin ne kuma aka kammala tattara dukiyar da Ibrahim ya bari aka
raba mana gado,in da ni da tilon ɗana muka lashe kaf dukiya da kadarorin da marigayin ya
tara,sabida lokacin iyayensa sun ɗan jima da rasuwa, a dalilin mummunar gobara da ya tashi a
sabon gidan da Ibrahim ɗin ya gina musu, suka bar cikin Family House ɗinsu.Wannan rabon gado
shi ya janyo mana wata irin tsana daga danginsa,da ƙanninsa maza biyu da suka ci burin ina ma
mace Ibrahim ya haifa,sabida su ma su samu shiga cikin magada,amma sai Allah ya ƙaddara cewa
namiji ya bari. Har a yau da na ke muku wannan maganar, dangin uban Maleek basa
ƙaunarsa,suna matuƙar nuna adawa da irin arziƙin da ya gada,ga kuma na shi ɗaukakan da kullum
cigaba ya ke.
Arziƙi sai dai muce Alhamdulillah! Don ba mu san rashi ba indai na kuɗi ne.Shekaran Ibrahim
uku da rasuwa aka sake rafka min wani rashin me asalin ɗaga hankali, Anty Hauwa ƙanwata da
muka baro a Lagos itace ta rasu,sanadiyar haɗarin mota za su zo wani biki da za mu yi a Katsina a
wancan lokacin, tana cikin mutum na farko da ta fara amsa kiran Ubangiji a cikin motar, ƴar ta
Suhailah kaɗai ta rayu a cikin motar, lokacin ta fara tasawa tana da shekaru biyar a duniya.
Mutuwar Hauwa ya gigitamu ni da Maleek fiye da yadda zan misalta.Don shi Maleek sun yi waya
da ita a lokacin da motarsu ta taso,take sanar da shi gasu cikin mota sun ma taso,don shi mijinta
yace ta bari sai ana gobe bikin su biyo jirgi, amma sai ta nuna tafi son zuwa tun wednesday. Ta
matsa masa sai ta taho,sai yayi mata irin gatsennan yace sai dai ta biyo mota,to da yake ajali na
kira sai ta amince, shi kuma ganin ta nace ya biya mata kuɗin motar suka kamo hanya.
Mu dai sai gawarta aka isa da shi can Katsina,ƴan uwa da dangi suka shiga cikin mummunan
yanayi.Maleek lokacin da muka bar Zaria muka isa Katsina ko magana ba ya yi sai kuka.Don
mutuwar ya gigita shi matuƙa barin ma da muka isa, ya tadda yadda Suhailah ke faman kuka
kamar tasan uwar ta tafi kenan har abada.
Bayan anyi kwana bakwai da rasuwar Hauwa, aka yi bikin da aka ɗaga sabida rasuwartata. An yi
bikin da kwana biyu na haɗo kan mu har Suhailah muka ta ho Zaria, bayan na roƙi mahaifinta
akan ya bani riƙonta,yace in ɗauka amma idan ya yi magana uwarsa bata amince ba, to zai biyoni
har Zaria ya amshi abarsa. Cikin ikon Allah ma sai uwar tasa bata hana ba,hakan shine silar da
riƙon Suhailah ya dawo hannuna tana da shekaru biyar a duniya.
Hajjah ta cigaba da cewa,
"Maleek shi ba mazauni bane, don yana can Lagos ɗinsa sai duk ƙarshen wata ko bayan sati uku
yake zuwa Zaria, ya yi kwanaki biyar ko sati ɗaya ya juya inda ya fito, har kuma lokacin bai taɓa
cemin yana da budurwa ba bare ayi maganar aure. Shekarunsa kuma kullum ƙaruwa suke yi don
har ya shiga shakaru 26 a lokacin,ni kuma bani da burin da ya wuce ya yi auren ,amma shi ko a
jikinsa,tun ina magana har na gaji na koma yi masa addu'a.
Suhailah ta taho cikin gata da kulawa a hannuna, babu me cewa bani na kawo ta duniya ba,gaba
ɗaya ta manta da uwarta sai dai idan ta ganta a hoto.Na sanya ta makaranta mafi tsada na boko da
islamiya, babu abinda ta nema ta rasa,maraicin uwa ma bata san shi ba don yadda na ke ji da ita ko
Hauwa na raye iyakar gatan da za ta bata kenan.
Lokacin da ta girma ta zama budurwa ne na fara lura da zuciyarta ya fara karkata akan
Maleek,sabida yadda take gaza nutsuwa idan ya zo gari.Na cigaba da sanya mata ido har na
tabbatar da hasashena gaskiya ne, soyayyar ɗan uwanta me zafi ne ya kama zuciyarta,shi kuma
wanda ake yi dominsa bai ma san tana yi ba,sabida sam ba yi shiga harkarta sabida ita akwai
surutu da rawar kai, shi kuma miskili ne mara son hayaniya,tana shekaran farko a jami'a na tirketa
akan ta gayamin gaskiya, idan son Maleek ɗin take yi da gaske kuma za ta iya aurensa,aiko
Suhailah babu kunya ta sanar min shi take so,amma sai ta roƙeni akan kada in faɗi masa, sabida
tsoransa take ji sosai,don ba ya sakar mata fuska ko kaɗan.
Ni na san yadda nayi da rarrashi da ban baki har na ciyo kan Maleek ya amince zai aure ƴar
uwarsa, kuma ƙanwarsa Suhailah,ba don yana jin sonta a zuciyarsa ba ,sai don kawai yayi min
biyayya a matsayina na mahaifiyarsa, da ba ya iya saɓa abinda na ke so.
Ba a ja lokaci ba manya suka shigo cikin maganar,mahaifin Suhailah ya fi kowa murna da wannan
haɗin,yayin da su ku ma dangin Maleek suka sake ɗaukar zafi damu.Sabida sun so su yi masa
tallan yaransu ƴan mata ya aura ,sabida kwaɗayin dukiya sai dai basu ga fuska a wajen Maleek ɗin
ba, bare kuma ni da sam na daina shiga sabgar su sai abinda ba a rasa ba.
Haka akai bikin Maleek da Suhailah suka tare a danƙareran gidan da Maleek ɗin ya gina a GRA.
Duk wanda ya je ya ga irin daular da ke cikin gidan Suhailah sai yayi mata murna,dangin ubanta
su kai ta santin gida da murnan cewa ƴar su ta samu gidan daula,masu hassada kuma su kai tayi
mu dai bamu san ma suna yi ba.
Suhailah ta cigaba da karatunta a ɗakin mijinta,amma ma fi zamanta yafi ga gida na,sabida
Maleek baya zuwa sai duk bayan sati uku. Ita kuma Suhailah bata son zaman kaɗaici, hakan yasa
yana tafiya za ta tattaro ta dawo min gidana,sai da nayi da gaske na samar mata ƴan aiki, da kuma
ma'aikatan da Maleek ya zuba maza a gidan,da mai gadi,sannan ne Suhailah ta haƙura ta fara zama
ita da ƴan aiki a gidanta. Anyi auren da shekara ɗaya mahaifin Suhailah ya rasu shi ma,ta zama
cikakkiyar marainiyar da babu uwa ba uba.
Shekararsu biyar kenan zasu shiga da aure,amma Allah bai bada haihuwa ba,wannan shine
taƙaitaccen tarihina dana iyali na Hajiya Fatima."
Hajjah ta kai ƙarshen labarinta tana duban TAIMIYYAH da Iyah da ke saurararta,Iyah ta numfasa
ta ce, "Allah sarki,Allah Ubangiji ya yi musu rahama tare da na mu iyayen da ƴan uwa musulmi
baki ɗaya."
Hajjah ta amsa da cewa, "Ameen." Kafin ta sake amsa gaisuwar da TAIMIYYAH tayi mata, na
rashin mijinta da ƴar uwarta,ta dubi TAIMIYYAH cikin ido wacce ta fara gano in da Hajiya Aysha
ta dosa,don sunan Maleek da ya shigo cikin labarinta ya bata tabbacin cewa ba kowa bane ya zo
wajenta sai ɗan Hajiya Ayshan.
Hajjah ta cigaba da duban TAIMIYYAH tana zayyane musu, yadda suka yi da Maleek akanta,tun
daga maganar da tayi masa akan cewa ya zo ya ga TAIMIYYAR,har kawo yadda suka yi da shi a
jiya kafin ya bar gari,ta ƙare maganar da cewa, "Zainab Maleek ɗa na ne, wanda shi kaɗai na
mallaka a duniya, na so ace ina da wani ɗan wanda bai taɓa aure ba, sabida in saka shi ya zo ya
nemi aurenki,amma ba ni da kowa sai Maleek. Shiyasa shi ɗin dai na ke da burin ya sake samun
nagartacciyar mace me tarbiya a karo na biyu,ina fata za ki amshe sa a matsayin miji,ba tare da kin
yi la'akari da aurensa ko dangantakar da ke tsakaninsa da matarsa ba,Maleek ya kamu da ƙaunarki
ne tun lokacin da yake mafarki da me irin siffar idanunki,bai gane hakan bane sai a shekaranjiya
da ku kai ido huɗu da shi,daga yana yin da ya dawo min a gigice, da irin kamalaman da yake yi
akanki,na gano tarin ƙaunarki da ya taso daga can ƙasar zuciyarsa ya bayyana kansa. Zaynab ina
fata za ki amince mu haɗa jini da ke,domin ɗorewar zumunci da samun iri me kyau daga gare
ki.Ina miki albishir da cewa Maleek zai riƙe ki da amana,zai kuma zame miki mijin marainiya
kamar yadda ya ke shi ma maraya.Sai dai banzo nan don na tirsasa zuciyarki ta amince da abinda
baki da ra'ayi akai ba,idan har kin ji baki son Maleek, ba za a yi miki dole ba,Hajiya ina fata ke ma
za ki amince ɗan ki ya zama surukinki idan Allah ya yi nufin kasancewar hakan?"
Hajjah ta ƙare maganar tana duban Iyah,wacce tayi sakato tana duban Hajjahn,ta rasa ma me zata
ce sai da ƙyar tayi ƙarfin halin faɗin, "Hajiya na rasa da wani baki zan bayyana irin ƙauna da
alkhairin da kike nufin wannan yarinya da shi,tabbas idan har Zainab ta amince da ɗan mu zan yi
farin ciki mara misaltuwa,babu abinda zan ce dangane da wannan lamari, duba da irin mafarkin da
yaron ya fara yi tun farko,don Allah kaɗai ya san me ya ke nufi da hakan,sannan haɗuwar mu da
ke da bayyanar TAIMIYYAH, a matsayin wacce yaron ki ke mafarki da wani ɓangare na siffarta,
shima babban lamari ne da sai dai mu bi da addu'a,kar ki damu Hajiya idan har yaran suka fahimci
juna, ina baki tabbacin zan shige gaba wajen ganin an ƙulla alkhairy ,in dai har zai riƙe min jika da
amana ya kare mata martabarta,su kuma zauna lafiya da matarsa,to ni bani da haufi domin me
sonka da gaskiya ne zai so ɗansa ya haɗa zuriya da naka,babu abinda zance miki sai godia akan
ƙauna da tausayin da kike nunawa Zaynab."
Iyah tayi maganar har muryarta na ɗan rawa,TAIMIYYAH kuwa ƙasa ta yi da kanta, ƙirjinta na
wani dokawa da yanayin da ba za ta iya fassarawa ba.Hajjah ta dubi TAIMIYYAH cike da ƙauna
ta ke cewa, "Ƴa ta tashi ki je daga ciki na ga alamun kin shiga ruɗani,za mu gama magana da Iyah
amma ina roƙarwa Maleek alfarma, a riƙa ɗaga wayarsa idan ya kira,sabida shi mutum ne da bai
iya saka abu ransa da sauƙi ba,ina fata tsoro ya kau tunda kinji waye shi, daga ina kuma ya ke,so
please ki ɗauki wayarsa ki sauraresa, ta hakane za ki gane idan za ki iya amincewa da shi,Allah ya
yi miki albarka ya kuma haɗa zuciyoyinku ke da shi Zainab."
Hajjah ta ƙare maganar tana bin bayan TAIMIYYAH da kallo,wacce ta ke takawa a hankali tamkar
wacce ƙwai ya fashemawa a ciki,sabida yadda zuciyarta ke cikin wani irin ruɗani da kullewar
kai..........✍🏻
#Ɗansabo ce#
[12/14, 3:43 PM] +234 703 040 9541: Littafin TAIMIYYAH paid book ne,ga duk wanda ta
tsincesa a kowani irin group ne,kiji tsoran Allah karki karanta sai kin biya 500 naira only.
Za ku iya min magana ta wannan number ɗin 08167768704, ko kuma ku turo kuɗin ku kai tsaye ta
wannan account ɗin 0504192664 aisha ibrahim dansabo GTbank.*
Masu turo credit za ku turo katin MTN na 500 ta wannan line ɗin 08167768704.
_Ina ƴan kasuwa masu buƙatar a tallata muku hajar ku? Maza ku garzayo da kuɗi ƙalilan a tallata
muku kayan siyarwanku sai dai kawai ku ji ana kiran waya don buƙatan sayan kayan ku,ku
tuntuɓeni ta layina kamar haka 08167768704._
*60*
TAIMIYYAH na isa ɗaki ta nemi bakin gado ta zauna,tana me dafe kanta da hannu bibbiyu,tunani
da tarin ruɗani ya yi wa zuciyarta ƙawanya, don bata san ta yadda za a yi ta iya son wannan
miskilin mutumin ba.Wanda bashi da fara'a sai tarin kwarjini da yake mata a ido, ko a cikin waya
ta kalli fuskarsa sai ta ji kwarjininsa ya cika zuciyarta. Ta zame ta kwanta tana me jingina jikinta
da makarin gadon,dai-dai kuma lokacin da kira ya shigo wayarta,sai ta miƙa hannu ta ɗauki
wayar,wanda ta barshi a ɗakin tun ɗazu. Ganin numbar Yasmeen ce yasa TAIMIYYAH saurin
ɗaga wayar, ta kai kunni tana faɗin,
Yasmeen daga ɓangarenta ta furta, "TAIMIYYAH ina ki ka bar waya ina ta kira tun ɗazu bakya
picking?"
TAIMIYYAH ta gyara kwanciya tana cewa, "Sorry Sis,a ɗaki na bar wayar muna tare da Iyah ne,
da Hajiyar nan a can falon Iyah."
Yasmeen ta furta, "Okey dama zan ce ne ki hau online, ki ga ashobi ɗin da Zuhurah suka fitar,don
na san da wuya sun nuna miki."
TAIMIYYAH ta taɓe baki kamar tana gaban Yasmeen ɗin, sannan ta furta, "Okey zan duba zuwa
anjima Yasmeen,ke ma kin san ba za su nuna min ba ai,amma sun fitar da wuri ba saura 2 month
bane bikin?"
Yasmeen ma ana ta ɓangaren bakin ta taɓe, tana baiwa TAIMIYYAH amsa da faɗin, "Eh saura 2
month mana, kawai ganɗoki ne irin na su,idan kin duba ki min magana don sun ce ne idan bai yi
ba za a sake, ni kuma kin san ba wani iya zaɓe nayi ba."
Daga haka Yasmeen su kai sallama da TAIMIYYAH,ta aje wayar tana sauke a jiyar zuciya,tana
shirin tashi ta nufi toilet kira ya sake shigowa wayarta,sai ta maida idanunta kan wayar tana kallon
numbar A.Maleek,wanda bata yi saving ba na yawo akan screen ɗin. Ta tsurawa wayar ido
zuciyarta na doka mata da wani yanayi, sai daf da kiran zai tsinke ta iya ƙarfin halin ɗaga wayar ta
kai kunni.
"Hello! Zaynabb."
Kalaman A.Maleek kenan da suka shiga kunnuwar TAIMIYYAH, wacce ta sake gyara zamanta da
kyau akan gadon,ta buɗe baki murya can ƙasa ta ce,
"Na'am ina yini ya aiki?"
Memakon Maleek ya amsa gaisuwarta sai ya jefa mata tambayar da ke addabar zuciyarsa,
"Zaynabb Hajjah ta zo gidanku ko?"
Take TAIMIYYAH ta gane wacce yake nufi ɗin, sai ta gyaɗa kai kamar yana ganinta ta furta, "Eh
ga ta can ma tare da Iyah a falo."
"Ke kuma kina ina kenan?" A.Maleek ya sake jefa mata tambayar,zuciyarsa na wani irin dokawa
da jin sassanyar muryarta.
TAIMIYYAH ta ɗan lumshe ido,muryar Maleek Ado me cike da ƙasaita da daɗin amo na ratsa
zuciyarta,cikin ɗan shagwaɓe murya ta bashi amsa da faɗin,
Maleek bai sake magana ba,illah cuting call ɗin da yayi ya kira ta vid call. TAIMIYYAH ta ware
idanunta lokacin da ta fahimci vid call ya kira,sai ta yi saurin miƙa hannu ta janyo hijab ɗinta ta
sanya,sannan ta yi receiving vid call ɗin, tana me cuskule fuska tare da zunɓure baki kaɗan.
A.Maleek kuwa lokacin da kyakykyawar fuskar TAIMIYYAH, ya bayyana masa cikin allon
screen ɗin wayarsa,har wani a jiyar zuciya ya sauke yana me sake ƙuwarawa idanunta da ke da
wani irin tasiri akansa ido,yadda ta zumɓuro baki ya sanya shi gane Yarinyar ƴar shagwaɓace ta
gaske. TAIMIYYAH ita ko ƙin kallon face ɗinsa ta yi, sai ma ta duƙar da kanta ƙasa tana wasa
gefen hijab ɗin da ta sanya,muryar Maleek ya ratsa kunnuwanta lokacin da ya ke faɗin, "Zaynab
ina fata zuwa yanzu kin ji abinda kike da buƙatan ji akaina, sannan ina fata za ki bani dama don
mu fahimci juna, sabida bana ji za a ɗauki dogon lokaci ba tare da na mallake ki ba. Ko ke ba za ki
iya auren me mata ba Zaynabb?"
Yadda ya kai ƙarshen maganar da jefa mata tambayar,ya sanya zuciyarta dokawa da ƙarfi,ta yi
saurin dubansa cikin sa a idanunta ya sauka cikin na A.Maleek ɗin,dukkansu sai da zuciyarsu ta
doka da ƙarfin gaske, kafin TAIMIYYAH ta yi saurin janye idanunta tana bashi amsa da cewa,
"Eh! bana ji zan iya kam, sabida ban san meyasa sai ni ba,duk lafiyayyun matan da ka ke gani
meyasa sai ni gurguwa?"
A.Maleek zuciyarsa ne ta yi wani irin kaɗawa da jin kamalan da suka fito daga bakin
TAIMIYYAH,karon farko kuma da ya ji zafin kalmar gurguwa da ta kira kanta da shi kai tsaye,ba
tare da damuwa akan fuskarta ba, ya sake miskile fuskarsa da tsuketa tamau, kafin ya yi magana a
dake yana cewa, "Zaynabb da kanki ki ke kiran kanki da wannan sunan ? Please kar ki sake faɗa
min hakan,kuma da ki ke tambayar meyasa sai ke? Sabida ke ɗin na gani na ji ina ƙaunar
kasancewa da ke, don haka ni ban damu da zaki iya ko ba za ki iya ba,ba zan damu da cewa za ki
so ni ko ba za ki so ni ba, in dai har an amince za a bani ke hakan ya wadatar dani,daga lokacin
dana mallakeki zan koyar da ke yadda za ki ƙaunace ni kin ji wife."
Maleek ya yi maganar idanunsa har lokacin akan fuskar TAIMIYYAH,wacce ta ƙi ɗago kai ta
dubesa,gaba ɗaya kalamansa na ratsa jijiyoyin jikinta,suna aikawa da wani irin saƙo zuwa zuciya
da gangar jikinta. Kalmar ƙarshe da ya kirata da shi na 'wife' yasa ta ɗaga idanunta a hankali ta
sauke akan kyakykyawar fuskarsa,wanda sam babu ɗigon fara'a akai,sai ta yi gaggawar sauke
kanta ƙasa,wani abu na motsawa a zuciyarta.
Ta kasa cewa komi kamar yadda shi ma Maleek bai sake magana ba, sai kallon side face ɗinta da
ya cigaba da yi,tare da kallon cikin ɗakin nata da yake a tsare fes. Sun ɗauki tsawon lokaci a
haka,babu wanda ya sake magana a cikinsu,shi Maleek ji ya ke yi ko za su shafe awanni a hakan,
ba tare da ta yi magana ba hakan zai wadatar da shi.
Muryar Iyah TAIMIYYAH ta jiyo daga falo tana ƙwallo mata kira,wanda ta tabbatar shi ma
Maleek ya ji hakan,sai ta ɗaga kanta ta sauke manyan idanunta akansa, tana me shagwaɓe murya
ta ce, "Iyah na kira na zan je na amsa kiranta please!"
Maleek ya tsurawa cute mouth ɗinta ido, siririyar muryarta na ratsa zuciyarsa,tare da haifar da
wani zazzafar feeling akanta,ya sauke ƙaramar ajiyar zuciya kafin ya furta, "Okey zan kira zuwa
dare, saura kuma in yi ta kira ba za ki picking ba Zaynab."
TAIMIYYAH ta shagwaɓe fuska tana cewa, "To don Allah kar ka kira ni vid call please!"
TAIMIYYAH ta yi saurin girgiza kanta tana ƙin sake duban face ɗinsa,kiran da Iyah ta sake yi
mata yasa ta saurin yin cuting call ɗin,tana me aje wayar daga kan gado ta amsa kiran da
ƙarfi,yadda Iyah za ta jiyo ta daga can falon.
Lokacin da ta fito falon ta samu Hajiya Aysha a tsaye ne, alamun cewa tafiya za ta yi,sai ta ƙarisa
cikin falon tana faman sunkuyar da kanta ƙasa,sabida wani irin nauyi da kunyar Hajjah ta ji tana
ji.Hajjah da ta fahimci hakan sai ta saki murmushi,tana jin wani ƙarin ƙaunar Yarinyar da
tausayinta,musamman da Iyah ta gama bata labarin yadda uwar Nass ta ƙi TAIMIYYAR,sabida
kawai kasancewarta me lalura.
"Ƴa ta ni zan wuce sai kun zo ke da Iyah har gida ko? Amma don Allah ina so kar kisa wani
tunani a zuciyarki game da maganar Maleek,ki tsaya ku fahimci juna idan har kin ji bai kwanta a
zuciyarki ba, ki sanar da Iyah sai ta faɗi min kin ji ko Zaynab?"
TAIMIYYAH sai ta sake jin wani kunya ya lulluɓeta,ta yi saurin gyaɗawa Hajjah kai ba tare da ta
iya kallon fuskarta ba. Iyah wacce ta fito daga ɗaki ta dubi TAIMIYYAH tana cewa, "Zainabu sai
faman kiranki nake yi, kina mene ne baki fito ba sai yanzu?"
Hajjah ta murmusa tana ji ajikinta cewa Maleek ne ya kira TAIMIYYAH,sabida ta ga missed call
ɗinsa har huɗu a wayarta, kafin TAIMIYYAH ta fito,sai ta dubi TAIMIYYAH tana cewa, "Hala
Maleek ne ko?"
A kunyace TAIMIYYAH ta gyaɗa kai alamun tabbatarwa, Hajjah ta saki murmushi tana cewa,
"Ai tunda na ga missed call ɗinsa na san yana son jin ko na zo ɗin ne.To Zaynabb sai na ga zuwan
ku, Allah ya yi miki albarka ya tabbatar da alkhairy, Allah ya haɗa zuciyoyinku ko burina zai cika
akan son haɗa jini da ke TAIMIYYAH,ina kwaɗayin hakan zan fi kowa murna,idan Maleek ya
sake mallakar mace kamilalliya kamar ki."
Ita dai TAIMIYYAH ta yi ƙasa da kanta sosai tana jigine da jikin kujera,wani irin kunya take ji na
ratsata,da ƙyar ta iya ɗaga kai ta dubi Hajjah, lokacin da Iyah ke mata rakiya don fita daga falon ta
ce, "Hajiya sai anjima mun gode."
Hajjah ta waiwayo tana sakin murmushi ta ce, "To Zaynab sai anjima,ina nan ina zuba ido Iyah ta
ce za ku zo cikin sati me zuwa."
Daga haka Iyah tayi wa Hajjah rakiya har waje,ita dai TAIMIYYAH ta kasa yi wa Hajjah rakiya
sabida nauyi da kunya,sai ta juya ta koma zuwa ɗaki tana jin gaba ɗaya jikinta ya mutu.
Iyah ta yi wa Hajjah rakiya har zuwa wajen mota,suka gaisa da Shehu ya yiwa Iyah godian abinci
da abun sha, da aka fito masa da shi waje.
Basmah ce ta fito daga sasansu za ta fita,sai idanunta ya hango mata danƙareriyar motar
Hajjah,wanda ke fake a cikin compound ɗin gidan nasu, ta cigaba da takowa don nufan hanyar
gate,idanunta na kan Hajjah da Iyah da ke sallama da juna.
Kamar Basmah za ta daure ta wuce sai zuciyarta ya addabeta, akan ta ƙarisa don ganin wace
hamshaƙiyarce Iyah ta samo haka? Lokacin da ta ƙariso kusa da su Iyah ne, ta gane cewa Hajiyar
da Iyah ta sa suka je sasanta suka gaisar ce ranar walimar TAIMIYYAH.
Basmah ta durƙusa ta gaida Hajiya Aysha,Hajjah ta dubi Basmah da fara'a tana amsa gaisuwar
Basman.Iyah ta dubi Basmah tana bin ta da wani kallo, don ta san babu abinda ya iso da ita wajen
sai gulma,amma sai ta danne ɓacin ranta har Basmah ta bar wajen, tana wa Hajjah sallama,Hajjah
ta tsaida Basmah tana ɓalle bakin jaka, ta irgo sabbin kuɗin da bata rabo dasu cikin jakar hannu, ta
irga 5k ta miƙawa Basmah tana faɗin, "Ungo kya sayi credit, ki gaida ƴar uwarki da Mamarku."
Basmah ta miƙa hannu ta amsa kuɗin tayi godia, tana duban Iyah da ke faman doka mata harara ta
ce, "Iyah ki taya ni godia."
Iyah sai ta saki murmushin yaƙe, tana takaicin halayyar jikokin nata da suka gada wajen uwarsu,ta
dubi Hajjah tana cewa, "Hajiya har da wani ɗawainiyar bata kuɗi,to an gode Allah saka da
alkhairy ya ƙara arziƙi."
Cewar Hajjah lokacin da Basmah ta juya don komawa zuwa sasansu,jikinta har ɓari yake yi don
ƙosawa ta isa ta kaiwa su Umma gulma.Iyah su kai sallama da Hajjah ta shiga mota, Shehu ya ja
suka nufi gate. Hajjah ta sake zuge bakin jaka ta baiwa Tukur dubu biyu,ya amsa yana ta godia da
yaba kirki da mutuncin matar, har suka fice daga gate ɗin gidan.
Iyah ta juya don komawa cikin gida, zuciyarta cike da tunanin wannan abin alkhairy da Hajiya
Aysha ta zo musu da shi,don me ƙaunar ka ne zai so haɗa jini da kai,ba tare da ya duba fifikon
ɗaukaka da ratan da ke tsakaninka da shi ba,don daga labarin da Hajjah ta basu ta gane cewa sama
da ƙasa,su Hajjah sun yi musu rata me tarin yawa,duk da cewa su ma suna cikin sahun masu rufin
asiri ne kawai,amma arziƙi na wajen su Hajjah idan har za a duba fifikon da ke tsakani kuwa,za ta
iya cewa Maleek ya fi ƙarfin ajin TAIMIYYAH ko ta wani fanni.Sai dai daga labarin da Hajjah ta
bayar,na irin mafarkin da ya dinga yi yasa jikin Iyah yin sanyi,har take ji a zuciyarta cewa,addu'a
shine kawai abinda lamarin ke buƙata,don ba su san me Ubangiji ya ɓoye ba.Har ta isa cikin
sasanta tunane-tunane kawai take yi a cikin zuciyarta.
__________
Basmah ta dinga ƙwalla kiran sunan Zuhurah,lokacin da ta sanya kanta cikin falon na su,Zuhurah
ta fito daga ɗaki tana cewa, "Basmah lafiya wannan kira haka?"
Basmah ta zauna tana kaɗawa Zuhurah sabbin ƴan 500 da ke hannunta tana cewa, "Zuhurah kalli
ki ga, wannan Hajiyar da muka gaisar ranar walimar TAIMIYYAH,ita ce ta bani su. Ke kin ga
danƙareriyar motar da take hawa kuwa? Hmmm! ni wallahi na rasa inda Iyah ta samo wannan
hamshaƙiyar Hajiyar."
Basmah ta yi maganar fuskarta na nuna alhini me tarin yawa,Zuhurah ta zurawa kuɗin ido tana
cewa, "Wallahi ni ma na rasa ina ta samo matar,daga gani kin san akwai kuɗi a wajen Hajiyar, ko
daga yanayin skin ɗinta zuwa suturar da ta saka a ranar."
Basmah ta gyaɗa kai tana faɗin, "Gaskiya kam matar tayi ga kyauta da fara'a ,amma baki ga yadda
Iyah ke faman zabgamin harara ba, daga na je mun gaisa da matar,Allah kaɗai yasan kuɗin da
matar ta baiwa ƴar gaban goshin Iyar ai,ke kina ganin ko ranar walimar ƙananun kuɗi ta baiwa
TAIMIYYAH? Ai Allah ne kawai ya sani sai su da suka dafa,wallahi Iyah akwai baƙin hali,ba don
na fita Allah ya yi zan wafci rabona ba da shikenan,ba za ta taɓa cewa ta shigo sasan mu, ba tunda
mune bata ƙauna."
Zuhurah ta kyaɓe baki tana cewa, "To ai ta yi banza tunda mu ma dai gidan arziƙin za mu shiga,
duka kwanaki nawa suka rage,sai su yi ta zama ita da gurguwar tata."
Suka saki dariya ita da Basmah,Basmah na miƙewa ta ce, "Bari in je in dawo kin ji,dama gulma ya
dawo dani,ga 1k ke ma ki shaida."
Basmah tayi maganar tana miƙawa Zuhurah kuɗin,Zuhurah ta amsa Basmah ta fice don tafiya inda
za ta.
Daga can ɓangaren sasan Iyah kuwa,lokacin da ta isa cikin falonta sai ta wuce zuwa ɗakin
TAIMIYYAH direct. Ta samu TAIMIYYAH a kwance ta yi zurfi cikin tunani,sai ta zauna daga
gefen gadon tana cewa, "Zainab tashi mu yi magana."
TAIMIYYAH ta yinƙura ta tashi zaune, tana duban Iyah fuskarta a narke,Iyah ta dubi
TAIMIYYAH tana cewa, "Zainabu kin ji dai da maganar da Hajiya ta zo mana da shi ko? Bana so
ki zafafa ko ki hana kanki sukuni da yawan tunani,ki fawwala Allah lamarin mu kuma yi addu'a,
don bamu san abinda Allah ke nufi da haɗamu da waɗannan bayin Allah a rana tsaka ba,jikina ya
yi sanyi da bayanin da Hajiyar ta yi akan mafarkin da ya ke yi da me irin idanunki,kar ki damu
kanki da yawan tunani kamar yadda Hajiyar ta ce, ki saurare shi mu kuma yi addu'a, Allah ya zaɓa
mana mafi alkhairy,idan mijinki ne za ki aure shi ko muna so ko bama so,don haka tun daga yau ki
dage da addu'a, mun rabu da ita akan cewa zan saka Babanki Sani yayi bincike akan su,duk abinda
muka ji zan sanar da ita sai a turo manyansa,don nema masa izinin fara zuwa zance wajenki sabida
ku fahimci juna,ina fata ko don ƙaunar da ta nuna akan ki,ba za ki guji jininta tilo ɗaya da ta
mallaka ba,matuƙar mun same sa da kyawawan halayya,Allah ya duba maraicinki ya yi miki zaɓi
mafi alkhairy."
TAIMIYYAH da duk jikinta yake a sanyaye ta amsa da cewa, "Ameen Iyah amma ni tsoro nake ji,
ina ganin kamar sun fi ƙarfinmu, kuma kar ki manta yana da mata ,kuma jininsa ce matar Iyah,ni
dai gaskiya tsoro nak....."
"Zainabu kar kice za ki ja da yin Allah,ki yi addu'a ne kamar yadda na faɗi,kasancewarsa me mata
ba abin damuwa bane, don Allah ya fiki sanin komi amma kuma ya kawo shi cikin
rayuwarki,Allah ya fi mu sanin abinda yasa ya ƙaddari silar haɗuwarki da mahaifiyarsa,har sanadi
yasa ya gane cewa ke ce yarinyar da ake nuna masa cikin baccinsa,wannan kaɗai ya isa yasa ki
nutsu ki barwa Allah ikon sa,mu jira mu ga abinda Allah zai hukunta kinji ko?"
TAIMIYYAH ta dubi Iyah a sanyaye tana me gyaɗa kai, ba tare da tace komi ba. Iyah ta cigaba da
yi wa TAIMIYYAH ƙarin bayani, akan labarin Maleek ɗin da Hajjah ta dinga bata, da irin yadda
tun ganinsa da TAIMIYYAH ya kasa nutsuwa.Ita dai TAIMIYYAH jin Iyah kawai ta ke yi ,tana
kallon komi kamar mafarki ko almara,tunaninta ya hasko mata yadda suka kwashe da shi ɗazu a
waya,da yadda har ya fara kiranta da wife ɗinsa, kamar wanda akai wa albishir da cewa an basa
ita,wani baƙon yanayi ya doka acikin zuciyarta,idanunta na hasko mata kyakykyawar miskilalliyar
fuskar Maleek Ado ɗin,da yadda yake furta kalamansa cike da ƙasaita. Har Iyah ta gama
bayananta ta tashi ta fice daga ɗakin,zuciyar TAIMIYYAH bata huta daga tunanin Maleek Ado
ba..........✍🏻
#Ɗansabo ce#
[12/14, 3:43 PM] +234 703 040 9541: Littafin TAIMIYYAH paid book ne,ga duk wanda ta
tsincesa a kowani irin group ne,kiji tsoran Allah karki karanta sai kin biya 500 naira only.
Za ku iya min magana ta wannan number ɗin 08167768704, ko kuma ku turo kuɗin ku kai tsaye ta
wannan account ɗin 0504192664 aisha ibrahim dansabo GTbank.*
Masu turo credit za ku turo katin MTN na 500 ta wannan line ɗin 08167768704.
_Ina ƴan kasuwa masu buƙatar a tallata muku hajar ku? Maza ku garzayo da kuɗi ƙalilan a tallata
muku kayan siyarwanku sai dai kawai ku ji ana kiran waya don buƙatan sayan kayan ku,ku
tuntuɓeni ta layina kamar haka 08167768704._
*60*
TAIMIYYAH na isa ɗaki ta nemi bakin gado ta zauna,tana me dafe kanta da hannu bibbiyu,tunani
da tarin ruɗani ya yi wa zuciyarta ƙawanya, don bata san ta yadda za a yi ta iya son wannan
miskilin mutumin ba.Wanda bashi da fara'a sai tarin kwarjini da yake mata a ido, ko a cikin waya
ta kalli fuskarsa sai ta ji kwarjininsa ya cika zuciyarta. Ta zame ta kwanta tana me jingina jikinta
da makarin gadon,dai-dai kuma lokacin da kira ya shigo wayarta,sai ta miƙa hannu ta ɗauki
wayar,wanda ta barshi a ɗakin tun ɗazu. Ganin numbar Yasmeen ce yasa TAIMIYYAH saurin
ɗaga wayar, ta kai kunni tana faɗin,
Yasmeen daga ɓangarenta ta furta, "TAIMIYYAH ina ki ka bar waya ina ta kira tun ɗazu bakya
picking?"
TAIMIYYAH ta gyara kwanciya tana cewa, "Sorry Sis,a ɗaki na bar wayar muna tare da Iyah ne,
da Hajiyar nan a can falon Iyah."
Yasmeen ta furta, "Okey dama zan ce ne ki hau online, ki ga ashobi ɗin da Zuhurah suka fitar,don
na san da wuya sun nuna miki."
TAIMIYYAH ta taɓe baki kamar tana gaban Yasmeen ɗin, sannan ta furta, "Okey zan duba zuwa
anjima Yasmeen,ke ma kin san ba za su nuna min ba ai,amma sun fitar da wuri ba saura 2 month
bane bikin?"
Yasmeen ma ana ta ɓangaren bakin ta taɓe, tana baiwa TAIMIYYAH amsa da faɗin, "Eh saura 2
month mana, kawai ganɗoki ne irin na su,idan kin duba ki min magana don sun ce ne idan bai yi
ba za a sake, ni kuma kin san ba wani iya zaɓe nayi ba."
Daga haka Yasmeen su kai sallama da TAIMIYYAH,ta aje wayar tana sauke a jiyar zuciya,tana
shirin tashi ta nufi toilet kira ya sake shigowa wayarta,sai ta maida idanunta kan wayar tana kallon
numbar A.Maleek,wanda bata yi saving ba na yawo akan screen ɗin. Ta tsurawa wayar ido
zuciyarta na doka mata da wani yanayi, sai daf da kiran zai tsinke ta iya ƙarfin halin ɗaga wayar ta
kai kunni.
"Hello! Zaynabb."
Kalaman A.Maleek kenan da suka shiga kunnuwar TAIMIYYAH, wacce ta sake gyara zamanta da
kyau akan gadon,ta buɗe baki murya can ƙasa ta ce,
"Na'am ina yini ya aiki?"
Memakon Maleek ya amsa gaisuwarta sai ya jefa mata tambayar da ke addabar zuciyarsa,
"Zaynabb Hajjah ta zo gidanku ko?"
Take TAIMIYYAH ta gane wacce yake nufi ɗin, sai ta gyaɗa kai kamar yana ganinta ta furta, "Eh
ga ta can ma tare da Iyah a falo."
"Ke kuma kina ina kenan?" A.Maleek ya sake jefa mata tambayar,zuciyarsa na wani irin dokawa
da jin sassanyar muryarta.
TAIMIYYAH ta ɗan lumshe ido,muryar Maleek Ado me cike da ƙasaita da daɗin amo na ratsa
zuciyarta,cikin ɗan shagwaɓe murya ta bashi amsa da faɗin,
Maleek bai sake magana ba,illah cuting call ɗin da yayi ya kira ta vid call. TAIMIYYAH ta ware
idanunta lokacin da ta fahimci vid call ya kira,sai ta yi saurin miƙa hannu ta janyo hijab ɗinta ta
sanya,sannan ta yi receiving vid call ɗin, tana me cuskule fuska tare da zunɓure baki kaɗan.
A.Maleek kuwa lokacin da kyakykyawar fuskar TAIMIYYAH, ya bayyana masa cikin allon
screen ɗin wayarsa,har wani a jiyar zuciya ya sauke yana me sake ƙuwarawa idanunta da ke da
wani irin tasiri akansa ido,yadda ta zumɓuro baki ya sanya shi gane Yarinyar ƴar shagwaɓace ta
gaske. TAIMIYYAH ita ko ƙin kallon face ɗinsa ta yi, sai ma ta duƙar da kanta ƙasa tana wasa
gefen hijab ɗin da ta sanya,muryar Maleek ya ratsa kunnuwanta lokacin da ya ke faɗin, "Zaynab
ina fata zuwa yanzu kin ji abinda kike da buƙatan ji akaina, sannan ina fata za ki bani dama don
mu fahimci juna, sabida bana ji za a ɗauki dogon lokaci ba tare da na mallake ki ba. Ko ke ba za ki
iya auren me mata ba Zaynabb?"
Yadda ya kai ƙarshen maganar da jefa mata tambayar,ya sanya zuciyarta dokawa da ƙarfi,ta yi
saurin dubansa cikin sa a idanunta ya sauka cikin na A.Maleek ɗin,dukkansu sai da zuciyarsu ta
doka da ƙarfin gaske, kafin TAIMIYYAH ta yi saurin janye idanunta tana bashi amsa da cewa,
"Eh! bana ji zan iya kam, sabida ban san meyasa sai ni ba,duk lafiyayyun matan da ka ke gani
meyasa sai ni gurguwa?"
A.Maleek zuciyarsa ne ta yi wani irin kaɗawa da jin kamalan da suka fito daga bakin
TAIMIYYAH,karon farko kuma da ya ji zafin kalmar gurguwa da ta kira kanta da shi kai tsaye,ba
tare da damuwa akan fuskarta ba, ya sake miskile fuskarsa da tsuketa tamau, kafin ya yi magana a
dake yana cewa, "Zaynabb da kanki ki ke kiran kanki da wannan sunan ? Please kar ki sake faɗa
min hakan,kuma da ki ke tambayar meyasa sai ke? Sabida ke ɗin na gani na ji ina ƙaunar
kasancewa da ke, don haka ni ban damu da zaki iya ko ba za ki iya ba,ba zan damu da cewa za ki
so ni ko ba za ki so ni ba, in dai har an amince za a bani ke hakan ya wadatar dani,daga lokacin
dana mallakeki zan koyar da ke yadda za ki ƙaunace ni kin ji wife."
Maleek ya yi maganar idanunsa har lokacin akan fuskar TAIMIYYAH,wacce ta ƙi ɗago kai ta
dubesa,gaba ɗaya kalamansa na ratsa jijiyoyin jikinta,suna aikawa da wani irin saƙo zuwa zuciya
da gangar jikinta. Kalmar ƙarshe da ya kirata da shi na 'wife' yasa ta ɗaga idanunta a hankali ta
sauke akan kyakykyawar fuskarsa,wanda sam babu ɗigon fara'a akai,sai ta yi gaggawar sauke
kanta ƙasa,wani abu na motsawa a zuciyarta.
Ta kasa cewa komi kamar yadda shi ma Maleek bai sake magana ba, sai kallon side face ɗinta da
ya cigaba da yi,tare da kallon cikin ɗakin nata da yake a tsare fes. Sun ɗauki tsawon lokaci a
haka,babu wanda ya sake magana a cikinsu,shi Maleek ji ya ke yi ko za su shafe awanni a hakan,
ba tare da ta yi magana ba hakan zai wadatar da shi.
Muryar Iyah TAIMIYYAH ta jiyo daga falo tana ƙwallo mata kira,wanda ta tabbatar shi ma
Maleek ya ji hakan,sai ta ɗaga kanta ta sauke manyan idanunta akansa, tana me shagwaɓe murya
ta ce, "Iyah na kira na zan je na amsa kiranta please!"
Maleek ya tsurawa cute mouth ɗinta ido, siririyar muryarta na ratsa zuciyarsa,tare da haifar da
wani zazzafar feeling akanta,ya sauke ƙaramar ajiyar zuciya kafin ya furta, "Okey zan kira zuwa
dare, saura kuma in yi ta kira ba za ki picking ba Zaynab."
TAIMIYYAH ta shagwaɓe fuska tana cewa, "To don Allah kar ka kira ni vid call please!"
TAIMIYYAH ta yi saurin girgiza kanta tana ƙin sake duban face ɗinsa,kiran da Iyah ta sake yi
mata yasa ta saurin yin cuting call ɗin,tana me aje wayar daga kan gado ta amsa kiran da
ƙarfi,yadda Iyah za ta jiyo ta daga can falon.
Lokacin da ta fito falon ta samu Hajiya Aysha a tsaye ne, alamun cewa tafiya za ta yi,sai ta ƙarisa
cikin falon tana faman sunkuyar da kanta ƙasa,sabida wani irin nauyi da kunyar Hajjah ta ji tana
ji.Hajjah da ta fahimci hakan sai ta saki murmushi,tana jin wani ƙarin ƙaunar Yarinyar da
tausayinta,musamman da Iyah ta gama bata labarin yadda uwar Nass ta ƙi TAIMIYYAR,sabida
kawai kasancewarta me lalura.
"Ƴa ta ni zan wuce sai kun zo ke da Iyah har gida ko? Amma don Allah ina so kar kisa wani
tunani a zuciyarki game da maganar Maleek,ki tsaya ku fahimci juna idan har kin ji bai kwanta a
zuciyarki ba, ki sanar da Iyah sai ta faɗi min kin ji ko Zaynab?"
TAIMIYYAH sai ta sake jin wani kunya ya lulluɓeta,ta yi saurin gyaɗawa Hajjah kai ba tare da ta
iya kallon fuskarta ba. Iyah wacce ta fito daga ɗaki ta dubi TAIMIYYAH tana cewa, "Zainabu sai
faman kiranki nake yi, kina mene ne baki fito ba sai yanzu?"
Hajjah ta murmusa tana ji ajikinta cewa Maleek ne ya kira TAIMIYYAH,sabida ta ga missed call
ɗinsa har huɗu a wayarta, kafin TAIMIYYAH ta fito,sai ta dubi TAIMIYYAH tana cewa, "Hala
Maleek ne ko?"
A kunyace TAIMIYYAH ta gyaɗa kai alamun tabbatarwa, Hajjah ta saki murmushi tana cewa,
"Ai tunda na ga missed call ɗinsa na san yana son jin ko na zo ɗin ne.To Zaynabb sai na ga zuwan
ku, Allah ya yi miki albarka ya tabbatar da alkhairy, Allah ya haɗa zuciyoyinku ko burina zai cika
akan son haɗa jini da ke TAIMIYYAH,ina kwaɗayin hakan zan fi kowa murna,idan Maleek ya
sake mallakar mace kamilalliya kamar ki."
Ita dai TAIMIYYAH ta yi ƙasa da kanta sosai tana jigine da jikin kujera,wani irin kunya take ji na
ratsata,da ƙyar ta iya ɗaga kai ta dubi Hajjah, lokacin da Iyah ke mata rakiya don fita daga falon ta
ce, "Hajiya sai anjima mun gode."
Hajjah ta waiwayo tana sakin murmushi ta ce, "To Zaynab sai anjima,ina nan ina zuba ido Iyah ta
ce za ku zo cikin sati me zuwa."
Daga haka Iyah tayi wa Hajjah rakiya har waje,ita dai TAIMIYYAH ta kasa yi wa Hajjah rakiya
sabida nauyi da kunya,sai ta juya ta koma zuwa ɗaki tana jin gaba ɗaya jikinta ya mutu.
Iyah ta yi wa Hajjah rakiya har zuwa wajen mota,suka gaisa da Shehu ya yiwa Iyah godian abinci
da abun sha, da aka fito masa da shi waje.
Basmah ce ta fito daga sasansu za ta fita,sai idanunta ya hango mata danƙareriyar motar
Hajjah,wanda ke fake a cikin compound ɗin gidan nasu, ta cigaba da takowa don nufan hanyar
gate,idanunta na kan Hajjah da Iyah da ke sallama da juna.
Kamar Basmah za ta daure ta wuce sai zuciyarta ya addabeta, akan ta ƙarisa don ganin wace
hamshaƙiyarce Iyah ta samo haka? Lokacin da ta ƙariso kusa da su Iyah ne, ta gane cewa Hajiyar
da Iyah ta sa suka je sasanta suka gaisar ce ranar walimar TAIMIYYAH.
Basmah ta durƙusa ta gaida Hajiya Aysha,Hajjah ta dubi Basmah da fara'a tana amsa gaisuwar
Basman.Iyah ta dubi Basmah tana bin ta da wani kallo, don ta san babu abinda ya iso da ita wajen
sai gulma,amma sai ta danne ɓacin ranta har Basmah ta bar wajen, tana wa Hajjah sallama,Hajjah
ta tsaida Basmah tana ɓalle bakin jaka, ta irgo sabbin kuɗin da bata rabo dasu cikin jakar hannu, ta
irga 5k ta miƙawa Basmah tana faɗin, "Ungo kya sayi credit, ki gaida ƴar uwarki da Mamarku."
Basmah ta miƙa hannu ta amsa kuɗin tayi godia, tana duban Iyah da ke faman doka mata harara ta
ce, "Iyah ki taya ni godia."
Iyah sai ta saki murmushin yaƙe, tana takaicin halayyar jikokin nata da suka gada wajen uwarsu,ta
dubi Hajjah tana cewa, "Hajiya har da wani ɗawainiyar bata kuɗi,to an gode Allah saka da
alkhairy ya ƙara arziƙi."
Cewar Hajjah lokacin da Basmah ta juya don komawa zuwa sasansu,jikinta har ɓari yake yi don
ƙosawa ta isa ta kaiwa su Umma gulma.Iyah su kai sallama da Hajjah ta shiga mota, Shehu ya ja
suka nufi gate. Hajjah ta sake zuge bakin jaka ta baiwa Tukur dubu biyu,ya amsa yana ta godia da
yaba kirki da mutuncin matar, har suka fice daga gate ɗin gidan.
Iyah ta juya don komawa cikin gida, zuciyarta cike da tunanin wannan abin alkhairy da Hajiya
Aysha ta zo musu da shi,don me ƙaunar ka ne zai so haɗa jini da kai,ba tare da ya duba fifikon
ɗaukaka da ratan da ke tsakaninka da shi ba,don daga labarin da Hajjah ta basu ta gane cewa sama
da ƙasa,su Hajjah sun yi musu rata me tarin yawa,duk da cewa su ma suna cikin sahun masu rufin
asiri ne kawai,amma arziƙi na wajen su Hajjah idan har za a duba fifikon da ke tsakani kuwa,za ta
iya cewa Maleek ya fi ƙarfin ajin TAIMIYYAH ko ta wani fanni.Sai dai daga labarin da Hajjah ta
bayar,na irin mafarkin da ya dinga yi yasa jikin Iyah yin sanyi,har take ji a zuciyarta cewa,addu'a
shine kawai abinda lamarin ke buƙata,don ba su san me Ubangiji ya ɓoye ba.Har ta isa cikin
sasanta tunane-tunane kawai take yi a cikin zuciyarta.
__________
Basmah ta dinga ƙwalla kiran sunan Zuhurah,lokacin da ta sanya kanta cikin falon na su,Zuhurah
ta fito daga ɗaki tana cewa, "Basmah lafiya wannan kira haka?"
Basmah ta zauna tana kaɗawa Zuhurah sabbin ƴan 500 da ke hannunta tana cewa, "Zuhurah kalli
ki ga, wannan Hajiyar da muka gaisar ranar walimar TAIMIYYAH,ita ce ta bani su. Ke kin ga
danƙareriyar motar da take hawa kuwa? Hmmm! ni wallahi na rasa inda Iyah ta samo wannan
hamshaƙiyar Hajiyar."
Basmah ta yi maganar fuskarta na nuna alhini me tarin yawa,Zuhurah ta zurawa kuɗin ido tana
cewa, "Wallahi ni ma na rasa ina ta samo matar,daga gani kin san akwai kuɗi a wajen Hajiyar, ko
daga yanayin skin ɗinta zuwa suturar da ta saka a ranar."
Basmah ta gyaɗa kai tana faɗin, "Gaskiya kam matar tayi ga kyauta da fara'a ,amma baki ga yadda
Iyah ke faman zabgamin harara ba, daga na je mun gaisa da matar,Allah kaɗai yasan kuɗin da
matar ta baiwa ƴar gaban goshin Iyar ai,ke kina ganin ko ranar walimar ƙananun kuɗi ta baiwa
TAIMIYYAH? Ai Allah ne kawai ya sani sai su da suka dafa,wallahi Iyah akwai baƙin hali,ba don
na fita Allah ya yi zan wafci rabona ba da shikenan,ba za ta taɓa cewa ta shigo sasan mu, ba tunda
mune bata ƙauna."
Zuhurah ta kyaɓe baki tana cewa, "To ai ta yi banza tunda mu ma dai gidan arziƙin za mu shiga,
duka kwanaki nawa suka rage,sai su yi ta zama ita da gurguwar tata."
Suka saki dariya ita da Basmah,Basmah na miƙewa ta ce, "Bari in je in dawo kin ji,dama gulma ya
dawo dani,ga 1k ke ma ki shaida."
Basmah tayi maganar tana miƙawa Zuhurah kuɗin,Zuhurah ta amsa Basmah ta fice don tafiya inda
za ta.
Daga can ɓangaren sasan Iyah kuwa,lokacin da ta isa cikin falonta sai ta wuce zuwa ɗakin
TAIMIYYAH direct. Ta samu TAIMIYYAH a kwance ta yi zurfi cikin tunani,sai ta zauna daga
gefen gadon tana cewa, "Zainab tashi mu yi magana."
TAIMIYYAH ta yinƙura ta tashi zaune, tana duban Iyah fuskarta a narke,Iyah ta dubi
TAIMIYYAH tana cewa, "Zainabu kin ji dai da maganar da Hajiya ta zo mana da shi ko? Bana so
ki zafafa ko ki hana kanki sukuni da yawan tunani,ki fawwala Allah lamarin mu kuma yi addu'a,
don bamu san abinda Allah ke nufi da haɗamu da waɗannan bayin Allah a rana tsaka ba,jikina ya
yi sanyi da bayanin da Hajiyar ta yi akan mafarkin da ya ke yi da me irin idanunki,kar ki damu
kanki da yawan tunani kamar yadda Hajiyar ta ce, ki saurare shi mu kuma yi addu'a, Allah ya zaɓa
mana mafi alkhairy,idan mijinki ne za ki aure shi ko muna so ko bama so,don haka tun daga yau ki
dage da addu'a, mun rabu da ita akan cewa zan saka Babanki Sani yayi bincike akan su,duk abinda
muka ji zan sanar da ita sai a turo manyansa,don nema masa izinin fara zuwa zance wajenki sabida
ku fahimci juna,ina fata ko don ƙaunar da ta nuna akan ki,ba za ki guji jininta tilo ɗaya da ta
mallaka ba,matuƙar mun same sa da kyawawan halayya,Allah ya duba maraicinki ya yi miki zaɓi
mafi alkhairy."
TAIMIYYAH da duk jikinta yake a sanyaye ta amsa da cewa, "Ameen Iyah amma ni tsoro nake ji,
ina ganin kamar sun fi ƙarfinmu, kuma kar ki manta yana da mata ,kuma jininsa ce matar Iyah,ni
dai gaskiya tsoro nak....."
"Zainabu kar kice za ki ja da yin Allah,ki yi addu'a ne kamar yadda na faɗi,kasancewarsa me mata
ba abin damuwa bane, don Allah ya fiki sanin komi amma kuma ya kawo shi cikin
rayuwarki,Allah ya fi mu sanin abinda yasa ya ƙaddari silar haɗuwarki da mahaifiyarsa,har sanadi
yasa ya gane cewa ke ce yarinyar da ake nuna masa cikin baccinsa,wannan kaɗai ya isa yasa ki
nutsu ki barwa Allah ikon sa,mu jira mu ga abinda Allah zai hukunta kinji ko?"
TAIMIYYAH ta dubi Iyah a sanyaye tana me gyaɗa kai, ba tare da tace komi ba. Iyah ta cigaba da
yi wa TAIMIYYAH ƙarin bayani, akan labarin Maleek ɗin da Hajjah ta dinga bata, da irin yadda
tun ganinsa da TAIMIYYAH ya kasa nutsuwa.Ita dai TAIMIYYAH jin Iyah kawai ta ke yi ,tana
kallon komi kamar mafarki ko almara,tunaninta ya hasko mata yadda suka kwashe da shi ɗazu a
waya,da yadda har ya fara kiranta da wife ɗinsa, kamar wanda akai wa albishir da cewa an basa
ita,wani baƙon yanayi ya doka acikin zuciyarta,idanunta na hasko mata kyakykyawar miskilalliyar
fuskar Maleek Ado ɗin,da yadda yake furta kalamansa cike da ƙasaita. Har Iyah ta gama
bayananta ta tashi ta fice daga ɗakin,zuciyar TAIMIYYAH bata huta daga tunanin Maleek Ado
ba..........✍🏻
#Ɗansabo ce#
[12/14, 3:43 PM] +234 703 040 9541: Littafin TAIMIYYAH paid book ne,ga duk wanda ta
tsincesa a kowani irin group ne,kiji tsoran Allah karki karanta sai kin biya 500 naira only.
Za ku iya min magana ta wannan number ɗin 08167768704, ko kuma ku turo kuɗin ku kai tsaye ta
wannan account ɗin 0504192664 aisha ibrahim dansabo GTbank.*
Masu turo credit za ku turo katin MTN na 500 ta wannan line ɗin 08167768704.
_Ina ƴan kasuwa masu buƙatar a tallata muku hajar ku? Maza ku garzayo da kuɗi ƙalilan a tallata
muku kayan siyarwanku sai dai kawai ku ji ana kiran waya don buƙatan sayan kayan ku,ku
tuntuɓeni ta layina kamar haka 08167768704._
*61*
Kwanakin Hajjah biyar da xuwa gidansu TAIMIYYAH,ya kama ranar Friday. Misalin ƙarfe
takwas na dare, Baba Sani ya shigo sasan Iyah don gaisheta, kamar yadda ya saba duk sanda ya
dawo weekend.
Bayan sun gama gaisawa da Iyah,ita ma TAIMIYYAH ta fito suka gaisa sai ta koma
ɗakinta,kamar yadda ta saba don basu waje shi da Iyah su zanta,Iyah ta ɗaga manyan idanunta ta
sauke akan Baba Sani, kafin ta fara da cewa, "Sani za ka iya tuna labarin Hajiyar nan me kirki
dana baka,wacce suka kaɗe Zainab wata ɗaya da ya wuce?"
Baba Sani ya gyaɗa kai yana cewa Iyah, "Eh Iyah na gane ta, wacce ki ka ce har ta zo nan gidan
ranar walima,har ta baiwa TAIMIYYAH ɗankunnin gwal ko?"
Iyah ta yi saurin faɗin, "Eh tabbas kuwa ita nake nufi Sani,to ita ce ta sake dawowa yau kwanaki
biyar kenan,sai dai wannan karon ta zo da wani lamari me girma ne......"
A hankali Iyah ta zayyanewa Baba Sani yadda suka yi da Hajjah,da kuma wayar da Maleek ɗin
suke yi da TAIMIYYAH,don tun daga ran da Hajjah ta zo ta tafi ,ya maida kiran TAIMIYYAH a
waya tamkar ibada,tun tana wa Iyah ƙorafin ya faye naci da miskilanci,har Iyah ta gaji da jin
ƙorafin ma ita,Iyah ta kai ƙarshe tana cewa maganar da cewa, "To ka ji yadda muka rabu da ita,
don haka ina so daga yau zuwa jibi ka bincika can Family House ɗin nasu, don a ji ya ya
mu'amalarsa da danginsa ya ke? Sannan kuma ka binciki abokanan Sameer na kusa,waɗanda da ke
can Lagos don a binciki halayyar Maleek ɗin da abokanan aikinsa,tunda shi ma duk wajen da
marigayi yayi aiki yake,sai dai shi Hajiya tace a ɓangaren shiffin board yake,wanda a yanzu haka
ma shi ke riƙe da kujeran chairman na shiffing board gaba ɗaya."
Baba Sani ya jinjina kai cike da mamakin wannan lamari ya dubi Iyah ya ce, "Ai Iyah wannan
abu ya kwana gidan sauƙi ,in dai ɗan magariya former Assitant Controler ne da na sani, Yaron
Alhaji Ado Ibrahim da family House ɗinsu ke lowcost, ai maƙotan abokina Alhaji Buhary ne,zai
san komi akan duk wani labari da ya shafesu,zan kira shi mu yi magana anjima nan,sannan kina
nufin shi Chairman ɗin da kansa ma ya tako har nan ya ga Zainab,lallai wannan lamari me girma
ne da Allah kaɗai yasan abinda ya shirya.Sai mu cigaba da addu'a Allah tabbatar mana
alkhairy,amma fa ba ƙananun mutane bane waɗannan."
Iyah ta jinjina kai tana cewa, "Hakane Sani addu'ar mu ke kan yi, sai ka taya mu kaima,amma ina
so wannan maganar ya zama tsakanina da kai ne, ban amince Zuwairah ta ji komi ba har sai
lamarin ya tabbata, sabida bana son surutu da sanya ido."
Baba Sani da tun fil-azal ya san Iyah bata son Umma sabida halayyarta,sai ya jinjina kai yana
cewa, "In sha Allah Iyah babu wanda zai ji daga gareni,Allah ya shige mana gaba ya tabbatar
mana da alkhairy,amma ita Zainab ta amince za ta iya aurensa?"
Iyah ta murmusa ta bai wa Baba Sani amsa da cewa, "To tunda take sauraransa a waya,su shafe
mintuna masu yawa ka ga kenan akwai alamun zai samu kanta,tana dai yawan complain cewa ya
cika miskilanci, ga shi yana da mata ita tana jin tsoro kaza da kaza,amma tunda a hakan dai basu
fasa waya ba, kuma bana ganinta cikin wani damuwa, ka ga akwai alamun ta fara ba shi zuciyarta
kenan."
Baba Sani ya jinjina kai ya ce, "Hakane, to Allah yayi mana jagora ya tabbatar da alkhairy."
Iyah ta amsa da cewa, "Ameen." Daga haka Baba Sanin ya yi mata sallama,ya baro sasan
zuciyarsa na cigaba da al'ajabin wannan labari,sosai ya dinga addu'ar Allah ya ƙulla alkhairy,don
zai fi kowa murna ace Zainab ɗin ta samu gidan hutu da za a kula da ita."
TAIMIYYAH da ke cikin ɗakinta tana operating system ɗinta,ta jiyo muryar Iyah na ƙwallo mata
kira,ta amsa tana tsaida aikin da take yi, ta miƙe ta fice daga ɗakin zuwa falon Iyah.
Iyah da idanunta ke kan TAIMIYYAH har ta ƙariso wajen da ta ke zaune ta furta, "Zainabu zauna
mu yi magana."
TAIMIYYAH ta zauna tana maida dubanta kan Iyah,Iyah ta cigaba da cewa, "TAIMIYYAH so na
ke ki sanar dani za ki iya auren wannan mutum, Abdulmaleek ko kina amsa wayarsa ne don gudun
kar ran Hajiyarsa ya ɓaci? Na san kin yi istikhara kina kuma addu'a kullum, kamar yadda nima na
ke tsaye akan yin addu'ar neman zaɓin Allah,shin kina jin ya kwanta miki a zuciyarki, ko kuwa dai
biye masa kawai kike yi sabida uwarsa ta roƙi alfarman ki riƙa ɗaga kiransa? maza ki sanar dani
gaskiyar abinda ke cikin zuciyarki,don bana so a shiga hakkinki,matuƙar kin ji bakya ra'ayinsa duk
son da Hajiya ke miki da son mu haɗa jini dole za a haƙura,don bazan tilasta ki auren wanda baki
so ba."
TAIMIYYAH sai tayi ƙasa da kanta ta fara faɗin, "Iyah tabbas nayi Istikhara na nemi zaɓin
Allah,sai dai bazan iya cewa kai tsaye ina jin son sa a zuciyata ba,amma dai duk wani tsoro da
fargaba da nake ji ada bana ji yanzu,ina jin nutsuwar zuciyar da ta ruhi a duk lokacin da mu ke
waya da shi,kuma ga dukkan alamu mutum ne daya san abinda ya ke yi,don sam bai taɓa min
zancen banza ba,bani da zaɓi sai na ki Iyah.In dai har ya kwanta miki an kuma yi bincike a kansa,
an samu kyakykyawar shaida akansa shikenan,ba ni da sauran buri akan soyayyah tunda na rasa
Nass."
TAIMIYYAH ta yi maganar kanta a ƙasa don ta kasa duban Iyah,wacce ke faman zabga mata
harara jin sunan Nass da TAIMIYYAN ta furta,kafin ta buɗe baki ta ce, "Au! Zainab har yanzu
kina nan kina ƙawazucin wannan yaron a ranki?Ni na ɗauka tuni kin daɗe da kulle babinsa,to
madallah kada Allah ya sa ki yi lokacin soyayyar wanin, tunda Naseeru shine autan masu iya
soyayyah a duniya ko?"
Iyah ta rufe ido ta cigaba da zazzagawa TAIMIYYAH faɗa,har sai da TAIMIYYAH tayi danasanin
yadda aka yi sunan Nass ya shiga cikin kalamanta.Ta dubi Iyah da fuskar tausayi, hankalinta a
tashe da fassarar da Iyah tai wa kalamanta ta ce, "Iyah don girman Allah ki yi haƙury,ni ba haka na
ke nufi ba baki fahimce ni bane,wallahi na daɗe da cire Nass daga zuciyata,kawai sunansa ne ya
suɓuce akan harshena,ki yi haƙury ki daina wannan faɗan, ni babu Nass a cikin zuciyata a
yanzu,na cire shi har abada daga cikin zuciyata,ina kuma addu'a Allah ya maye min gurbinsa da
mafi alkhairy."
TAIMIYYAH ita dai tashi ta yi ta nufi hanyar ɗakinta, ba tare da ta sake cewa Iyah komi ba,tana
shiga ɗakin kashe system ɗinta ta yi ,sabida bata ji za ta iya cigaba da aikin tunda Iyah ta riga ta
ɓata mood ɗinta a yanzu.Tana cikin saka kayan bacci kiran Maleek ya shigo,sai ta saki ƙaramin
tsaki tana cigaba da sanya kayanta,don ringing ɗin da ta sanya masa daban ne,shiyasa ta gane shi
ne ya kira ɗin.
Tana kammala saka kayan kenan wani kiran ya sake shigowa,sai ta sanya hula akanta tana ɗaukan
ƙaramin hijab ta saka don ta san vid call ne,ilai kuwa tana ɗaukar wayar ta ga vid call ɗin ne, sai ta
zumɓure baki tana receiving call. Kyakyawar fuskar Maleek Ado ya bayyana a allon screen ɗin
wayarta,kamar yadda tata fuskar ya bayyanawa Maleek Ado,wanda ke kishingiɗe daga cikin Sofa
da ke cikin bedroom ɗinsa na gidansa da ke lagos.
TAIMIYYAH ta fara gaida shi cike da zallar shagwaɓa, wanda hakan ke ruruta wutar ƙaunarta a
zuciyar Maleek,har ya ke jin tamkar shekaru biyar suka yi da sanin juna, ba kwanaki biyar zuwa
shida ba.Idanunsa akan kyakykyawar fuskarta yake, lokacin da ya amsa gaisuwar a taƙaice,kafin
ya ɗaura da faɗin, "Zaynabb me ya ɓata mood ɗinki,na ga kamar kina fishi?"
TAIMIYYAH ta yi saurin dubansa cike da mamakin yadda yake saurin karantar yanayinta,ta sake
shagwaɓe murya tana cewa, "Babu komi fa, kawai ni ma haka na ji mood ɗina ya sauya yanzu."
A.Maleek da ya zurawa ƙaramin bakinta,da ke furta kalaman ido,ya wani taɓe baki yana faɗin,
"Tunda ba za ki sanar da ni ba shikenan,yanzu ni yaushe za a bani daman fara zuwa na ganki
ne,cox ina buƙatar hakan da gaggawa ,wannan wayar da mu ke duk bawani gamsar da ni yake ba
Zaynabb,sabida ba ki sakin kiji ki barni na kalli idanunki ,da fuskarki yadda na ke so,amma zan yi
magana da Hajjah in ji halin da ake ciki,sabida na matsu na mallake ki Zaynab don bani da
isasshen lokacin ɓatawa, mu na soyayyar yara gwara a ɗaura ayi me dalili da hujjah ko?"
Ya ƙare maganar cike da son TAIMIYYAH ta ɗago ta kallesa,amma sai ta ƙi yin hakan don
kunyarsa ne ya sake lulluɓeta,tana kuma mamakin yadda ya iya zaro kalamai a miskile, tamkar ba
daga bakinsa kalaman ke fitowa ba. Shi ko Maleek ko a jikinsa ya cigaba da zaro mata manyan
kalamai, TAIMIYYAH na jin kamar ta kashe wayar amma babu halin hakan,don ta fi kowa sanin
ya tsani hakan kuma tun daga randa ta kashe masa waya a karo na biyu, ya nuna ɓacin ransa
sosai,shikenan ta ke kiyaye hakan don a yanzu ji ta ke yi bata ƙaunar ransa ya ɓaci, bata san dalilin
hakan ba kuma don ba za ta ce tana jin soyayyarsa a zuciyarta ba,kuma ba za ta iya cewa tana
ƙinsa ba ,sai dai ma wasu irin feelings da take ji akansa wanda za ta iya cewa ba ta taɓa jin hakan
akan Nass ba.
Sun ɗauki fiye da rabin awa yana mata hira,har sai da kiran Suhailah ya shigo ɗaya
wayarsa,sannan ya ɗauki excuse ya kashe wayar don amsa kiran Suhailah.
TAIMIYYAH sai ta aje wayarta tana jin wani abu me kama da ɓacin rai na danne
zuciyarta,wannan shine karo na biyu da suna cikin waya kiran matarsa ya shigo masa, Maleek na
yanke wayar da ya ke yi da ita don amsa na matarsa,kuma duk abu iri ɗaya take ji yana tasowa ya
danne zuciyarta,ita kuma bata san ko minene ba. Tayi baya a hankali ta gyara kwanciyarta tana me
lumshe idanunta,abinda da take ji na sake danne zuciyarta, tana ji sam ba ta so ya yanke wayar
ba,duk da cewa ita bakomi take cewa ba,da ya wuce umm! ko a'a, ganin ranta na cigaba da shiga
ƙunci ya sanya ta sake janyo wayarta, ta kunna data ta hau oline. Ganin Yasmeen a online yasa ta
ji relief! Suka ɗan fara chart Yasmeen na tambayarta labarin Maleek,sabida TAIMIYYAH ta bata
labarin duk halin da ake ciki. TAIMIYYAH sai ta wani ɓata fuska tamkar Yasmeen na
gabanta,kafin ta danna wajen tura voice note tana faɗin, "Yana can suna soyayya da matarsa
mana,muna fa cikin waya ta kira shi,shi kuma jikinsa na rawa ya yi cuting call ɗin da muke yi,
yana ce min wai zai ɗaga call ɗin wife ɗinsa,wallahi haushi na ji sosai a raina, ba ki ji yadda
zuciyata ke zafi ba Yasmeen,gaskiya soyayyah da me mata sai a slow."
Ta tura voice note ɗin zuwa ga Yasmeen, tana cigaba da zumbure baki,ranta duk babu daɗi.
Yasmeen bayan ta gama jin voice note ɗin, sai ita ma ta aikowa TAIMIYYAH nata voice note ɗin
tana cewa, "Eh! Lallai su Baby an fara zurmawa a son wannan Maleek ɗin, tunda gashi tun ba a je
ko'ina ba,har kin fara jin kishi akan matarsa,to ni dai babu ruwana don Allah ki ko yi riƙe
kanki,kar ki bari ya gane kin fara kishi da matarsa nan kurkusa."
TAIMIYYAH ta wani ɓata fuska lokacin da ta gama jin abinda Yasmeen tace,kafin ta sake aika
mata da wani voice note ɗin in da take cewa, "Ni fa ban son sharri Yasmeen, babu wani kishinsa
da na ke yi,kawai don na ji haushi matarsa ta kira muna cikin waya, sai ki ce wani son sa na fara
ina kishinsa,ke fa ba a abin kirki da ke dama."
TAIMIYYAH ta baiwa Yasmeen amsa suka cigaba da magana ta chart,har sai wajen goma saura
sannan TAIMIYYAH ta kashe data ta kwanta,sabida baccin da ya fara damun idanunta.
Kwanaki biyu bayan maganar Iyah da Baba Sani,game da bincike akan Maleek Ado. Alhaji
Buhary ya zo har gida ya yiwa Iyah gamsasshen bayani, akan asalin waye Alhaji Ado mahaifin
Maleek,tare da zayyane mata kyawawan halayyar marigayin, wanda kuma an yi ittifaƙin Maleek
ya gaji dukkanin kyawawan halayyar mahaifin nasa ne.
Iyah ba ƙaramin farin ciki tayi da samun labari me daɗi, dangane da ahalin Hajiya Aysha ba,su kai
sallama da Alhaji Buhary bayan tayi masa godia me tarin yawa,shi kuma ya sake ɗaukar mata
alqawarin cewa zai cigaba da binciken Maleek ɗin, idan har ya ji wani hali mare kyau a tattare da
shi zai sanar mata,amma a yanzu kada su taɓa bari ya suɓuce musu, don samun mutane masu
karamci da halin dattako kamar Hajiya Aysha da tilon ɗanta,abu ne me wahala don irin su sun yi
ƙaranci a wannan zamanin, musamman idan aka yi la'akari da ɗimbin dukiyar da suka tara, amma
bai sa sun ɗaukaki kansu ba,sai ma ƙarin tausayi da taimakon talaka,da suka ɗaura daga inda
Alhaji Ado ya tsaya.
Bayan tafiyar Alhaji Buhary,Iyah ta samu TAIMIYYAH tana sanar da ita yadda suka yi da Alhaji
Buharyn,ita dai TAIMIYYAH bata iya cewa komi ba,amma can ƙasar zuciyarta ta ji ta sake samun
nutsuwar zuciya akan Maleek Ado,wanda ba za ta iya tantance asalin feeling ɗin da take ji akansa
ba.
Ranar Friday Iyah ta shirya ta je gidan Hajiya Aysha,wacce ita ce da kanta ta turo Shehu driver ya
ɗauki Iyah.TAIMIYYAH babu yadda Iyah bata yi akan ta shirya su je tare ba amma TAIMIYYAH
ta ƙi, ta ce wa Iyah ita kunyar Hajiyar take ji sosai a yanzu,ta dai yi Snacks me yawa ta ce akai wa
Hajjah, kamar yadda Iyah ta buƙata.
Bayan fitar Iyah sai TAIMIYYAH ta tattara ta nufi sasan Ummie,suka sha hiransu sai lokacin da
Iyah ta dawo sannan ta koma Part ɗin Iyah. Iyah ta zauna tana bai wa TAIMIYYAH labarin irin
tarba na karamci, da karramawa da Hajiya Aysha ta yi mata. Tana sanar da ita cewa Hajiyar tace a
gaida ta sosai,kuma za ta aiko a ɗaukar mata ita har gida,ta je ta yi mata yini,don ita a ƴa take
ɗaukarta Maleek ba zai shiga tsakaninsu ya mai da ita suruka ba. TAIMIYYAH dai blushing tai ta
yi tana jin tarin ƙaunar matar na sake ratsa ta,sabida ta sanya a ranta bayan Iyah da su Guggo
Bilki,bata taɓa samun mutanen da suka nuna mata ƙauna irin Hajiya Aysha ba. Don haka matar na
da wani irin ƙima da mutunci a idanunta, koda a ce bata shigo da maganar ɗan ta ya zo ya nemi
aurenta ba.
Ranar Saturday Hajiya Aysha ta bugowa Iyah waya ta sanar da ita cewa,Yayan Mahaifin Maleek
tare da wani Aminin Mahaifinsa Alhaji Aliyu,za su zo nemawa Maleek izinin fara zuwa zance
wajen TAIMIYYAH. Iyah ta ɗaga waya ta sanar da Baba Sani don yana gari ya zo weekend,ta
kuma shaida masa cewa ya sauke su a can Rimi ne, Fam house ɗin su don bata son su zo nan
gidan su samesa. Baba Sani ya amsawa Iyah tare da bata tabbacin za a yi yadda take so ɗin.
___________
*Asokoro, Abuja.*
Suhailah ce zaune a falon su na ƙasa tare da Jawahir, makwaficiyarsu da suka ƙulla ƙawance da ita
a yanzu,don kusan kullum sai ta shigo gidan Suhailah, sabida mijinta Captain Aliyu ba mazauni
bane.
Jawahir ta dubi Suhailah tana cewa, "Matar Maleek anya ba ciki ne gare ki ba? Don na ga sai sake
ɗashewa ki ke yi fa."
Suhailah ta saki murmushi lokacin da take aje cup ɗin da riƙe a hannunta,ta dubi Jawahir tana
cewa, "Tabɗi! Wani ciki Jawahir bayan yanzu haka period na ke yi,kawai zazzaɓin da nayi ya doke
ni shiyasa duk na ɗashe haka,ai ni matsalata babbane Jawahir don ina ma kan shan magunguna
ne,ban sani ba ko kafin in gama sha Allah zai dube ni,ya bani lafiyar da zan iya ɗaukar cikin....."
A hankali Suhailah ta kwashe halin da take ciki ta zayyanewa Jawahir ɗin,Jawahir da ta sake baki
tana duban Suhailah with shock! Ta yi saurin furta,
"Gaskiya Suhailah kin tafka wauta me yawa,amma In sha Allah za ki samu lafiya,maganar ƙarin
aure ki ma daina damun kanki don tsokanarki kawai ya ke yi,so ya ke yi kawai ya ruɗa miki ciki
sabida kin baƙanta zuciyarsa akan abinda ki ka aikata ɗin."
Suhailah ta jinjina kai tana duban Jawahir ta ce, "Hmm! Bana jin Maleek wasa ya ke yi Jawahir,
don kuwa baya furta abinda ba haka ya ke a zuciyarsa ba,sannan Hajjah ta riga ta furta za ta iya
goya masa baya,don daga ita har shi ba su da burin da ya wuce in haihu, sabida shi kaɗai ta
mallaka tana da buƙatar ganin shi ya hayayyafa,ina jin tsoran randa hakan zai tabbata ace Maleek
ya sake auren wata mace, sabida ina da tsananin kishi akansa me zafi."
Suhailah tayi maganar tana jin wani abu na matse zuciyarta,Jawahir ta jinjina kai tana duban
Suhailah cikin ido ta ke cewa, "Suhailah ki kwantar da hankalinki na gama lura ke ɗin kina da ɗan
duhun kai,ai yanzu mace sai ta so zama da kishiya in baki labari,idan baki so ba ko ta shigo za ki
iya korata, ba tare da kowa yasan halin da ki ke ciki ba,kada ki bari kishin mijin ya dameki
musamman ke da kuke da wuta a hannunku,tsayawa kawai za ki yi ki ga cewa kin samarwa kanki
ƴan ci ta ƙarƙashin ƙasa....."
Jawahir ganin irin kallo na rashin fahimta da Suhailah ke jifanta da shi,ya sanya ta yin shiru bata
ƙarisa maganar da ta faro ba,ta saki murmushi tana cewa, "Sorry ƙawata na ɗan saki layi ko? Kar
ki damu in dai muna tare soon za ki gane karatun da nake so ki gane,yanzu kina buƙatar a biki a
sannu ne don na ga kina da ƙarancin buɗewan ido, irin na ƴantattun matan zamani da suka san
kansu."
Suhailah da kanta ke sake kullewa da maganganun da Jawahir ke yi,ta ɓata fuska tana cewa,
"Jawahir ni fa a duhu kawai ki ke saka ni, don sam ban fahimci inda ki ka dosa ba."
Cewar Jawahir tana sakin wani irin dariya na shaƙiyanci,don kana ganinta a kallo ɗaya kawai za
ka fahimci irin matannan ne masu buɗewan ido. Haifaffiyar garin Jos ce daga can Captain Aliyu
ya auro ta,sun cigaba da hira da Suhailah har sai da time ɗin ɗakko yaronta a skull ya yi, sannan ta
yi sallama da Suhailah ta bar gidan.
Suhailah ta daɗe tana jujjuyawa kalaman Jawahir a cikin zuciyarta,amma ta kasa gane inda ta
dosa,ganin za ta damu kanta da tunani yasa ta watsar da zancen, ta cigaba da sabgarta,daga ƙarshe
layin Maleek ta nema amma sai ta ji duka wayoyinsa a kashe su ke,kewansa ta ke ji me tsanani
gashi ya sanar mata ba zai shigo Abuja ba sai next week Friday.
____________
*2 Weeks Later.*
*Zaria, 1:15pm.*
Tunda TAIMIYYAH ta yi waya da Maleek Ado ya sanar mata cewa ya shigo gari, ta ke jin wani
irin baƙon yanayi na lulluɓe zuciyarta, don cikin sati biyu da suka wuce, idan ta ce Maleek bai
kimsa ƙaunarsa a cikin zuciyarta ba ta yi ƙarya.
Yadda ta ke jinsa a zuciyarta a yanzu, ko lokacin da suke tare da Nass bata ji irin haka ba,don wani
irin zazzafan feeling ta ke ji akan Maleek Ado, irin wanda bata taɓa hasashen za ta ji akan wani ɗa
namiji ba.
Ta kan alaƙanta hakan da cewa tarin kwarjininsa da ya yi yawa ne, ke sake haifar mata da jin
yanayi me zafi akansa irin haka, don hatta da Iyah ta gama gane cewa TAIMIYYAH ta kamu da
soyayyar Maleek Ado. Dojewa kawai TAIMIYYAH ta ke yi a gabanta, tana nuna tamkar bata jin
ko wani irin feeling a kansa.
TAIMIYYAH ta ɗaga manyan idanunta ta sauke akan a gogon ɗakinta,tana ƙimanta ragowar
lokacin da ta ke da shi kafin isowar sa gidan,don ya tabbatar mata da cewa ba zai iya kwana a
garin, ba tare da ya zo gareta komin dare ba kuwa.
Ta yi hanzarin tashi tana ji duk jikinta ya saki,zuciyarta ya yi wani irin laushi da ɗokin son ganin
miskilalliyar face ɗinsa a zahiri, a karo na biyu tun bayan zuwansa na farko,wanda lokacin ba ta
samu halin yi masa cikakkiyar kallo ba.
Kitchen ta nufa kai tsaye lokacin da ta fito, tana ayyana irin abinda za ta shirya masa, wanda zai ci
idan ya zo,duk da cewa bata da cikakkiyar tabbacin zai ci wani abu, ko ba zai cin ba. Tunaninta ya
tsaya ne akan ta dafa masa mince meat jallof rice da haɗin chicken breast Salad.........✍🏻
#Ɗansabo ce#
[12/14, 3:43 PM] +234 703 040 9541: Littafin TAIMIYYAH paid book ne,ga duk wanda ta
tsincesa a kowani irin group ne,kiji tsoran Allah karki karanta sai kin biya 500 naira only.
Za ku iya min magana ta wannan number ɗin 08167768704, ko kuma ku turo kuɗin ku kai tsaye ta
wannan account ɗin 0504192664 aisha ibrahim dansabo GTbank.*
Masu turo credit za ku turo katin MTN na 500 ta wannan line ɗin 08167768704.
_Ina ƴan kasuwa masu buƙatar a tallata muku hajar ku? Maza ku garzayo da kuɗi ƙalilan a tallata
muku kayan siyarwanku sai dai kawai ku ji ana kiran waya don buƙatan sayan kayan ku,ku
tuntuɓeni ta layina kamar haka 08167768704._
*62*
TAIMIYYAH bata ɗauki awa biyu ba ta kammala komi, aka nufi sasan Ummie da shi aka shirya
cikin falon Abie.
Wanka ta sake yi sabida gajiyar aikin da ta sha, lokacin da ta fito daga wankan ta jima a tsaye
wajen kayanta, tana nazarin kayan da za ta saka,daga ƙarshe sai ta yanke shawaran saka sabuwar
Abayar da ta siya bata taɓa anfani da shi ba.
Kalar Abayar dark gray ne da akaiwa ado da blue black and golden colour,ya yi matuƙar yi wa
TAIMIYYAH kyau kamar ka sace ta ka gudu.
Bata yi kwalliya a fuskarta ba illah powder da ta shafa, sai ta yi lining idanunta da eye liner,ta
ɗauki man leɓe mai ɗan maiƙo ta shafa a pink lips ɗinta. Nan da nan fuskarta ya sake yin kyau,
manyan idanunta masu wani irin haske suka sake girma, ƙwayar idanun na ta sai sparkling su ke
yi. Ta ɗauki turarenta na GIOGIOR PINK me sanyin qamshi ta fesa ajikinta, bayan ta yi anfani da
body mist na Sugar Girl daga ciki.
Bayan ta kammala shiryawan,komawa ta yi ta zauna daga bakin bed tana kallon lokaci yadda ya
ja,don har biyar ta wuce ga hadari da ke haɗuwa a garin kaɗan-kaɗan.
Wayarta ta janyo tana kunna data ta hau online, don cigaba da karanta novel ɗin da take bibiya,me
suna Baƙar Inuwa na Billyn Abdul. Soyayyar Raudha da Mr. President na matuƙar birgeta, tana
hango tamkar itace da Maleek Ado. Shigowar kiran Maleek cikin wayarta yasa ta dakatawa da
karatun, tayi receiving call ɗin ta kai kunni,muryar Maleek me cike da ƙasaita ya shiga
kunnuwanta, lokacin da ya ke sanar da ita isowar sa.
Ta shagwaɓe murya tana cewa, "Okey! Ka shigo daga ciki part ɗin da ka sauka wancan lokacin,
gani nan fitowa."
Ta ɗanyi jim! Kafin ta saki ƙaramin murmushi, tana sake narke masa murya ta ce, "Alright za ta ji
In sha Allah."
Daga haka ta kashe wayar tana miƙewa ta taka zuwa wajen madubi, don yin rolling gyalen Abayar
a kanta,wani irin kyau ta ga tayi lokacin da ta kammala naɗe fuskarta da gyalen Abayar. Ta saki
wide smile tana sake duban yadda Abayar ta yi kyau a jikinta,sai ta koma ta ɗauki wayarta daga
kan bed ta nufi ƙofar fitowa falo.
"Iyah ya iso na ce ya ƙarisa can Part ɗin Ummie,ya ce in gaidaki zai shigo ku gaisa idan zai
wuce."
TAIMIYYAH ta yi maganar kanta a ƙasa don kunyar haɗa ido da Iyah ta ke yi,Iyah ta saki
murmushi kunyar TAIMIYYAH na sake birgeta ta dubi TAIMIYYAR ta ce, "To madallah ya yi
kyau ki ce ina amsawa ƙwarai. Ki shigar da shi ya gaida har Samhar idan zai tafi."
TAIMIYYAH ta amsa da cewa, "Tuh Iyah." Daga haka ta dafe guiwar ƙafarta ta fara takawa don
ficewa daga falon Iyah baki ɗaya.
Cikin nutsuwa ta ke tafiya zuciyarta cike da wani irin feeling da ba za ta iya fassarawa ba,har ta
isa sasan Ummie ta nufi hanyar da zai kai ta ƙofar falon Abie ta waje, tana sake jin zuciyarta na
wani irin dokawa. Lokacin da ta isa ƙofar shiga falon sai da tayi ɗan jim! Bugun zuciyarta na sake
ƙaruwa,daga ƙarshe ta yi ƙarfin halin buɗe baki ta yi sallama,cikin muryar ta da ya sake yin sanyi
sosai.
A.Maleek da ke kame daga cikin falon,ya na ji duk ya ƙosa ya yi tozali da kyakykyawar fuskar
TAIMIYYAR. Ya buɗe baki ya amsa mata sallamar, yana sake kafe ƙofar shigowa cikin falon da
ido.
TAIMIYYAH ta kai hannu ta ɗage labulen falon, tare da sanyo kanta ciki.Hancinta ya fara shaƙo
mata daddaɗan qamshin Turaren AMOUAGE da ya cika ɗakin baki ɗaya,ta cigaba da takowa
zuwa ciki tana jin tasirin idanunsa akanta. Hakan ya sake sawa ta yi ƙasa da kanta tana isa wajen
kujeran one seater ta yi masauki a kai,sai kuma lokacin ta ɗaga manyan idanunta ta kalli direction
ɗin da, Maleek ya harɗe yana me zubo mata ido babu ko ƙiftawa.
"Barka da zuwa dafatan ka iso lafiya,ya Hajjah ina fata ka same su lafiya?"
Sassayar muryar TAIMIYYAH ta ratsa kunnuwan Maleek Ado, wanda ya kasa ɗauke idanunsa
daga kanta,wani irin kyawunta ya ke gani irin wanda sam a wancan lokacin, bai kula da hakan
ba.Shigar Abayar ta tafi da zuciyarsa baki ɗaya, tare da haifar masa da jin wani irin zazzafar
feeling irin wanda bai taɓa ji ba,ya sake ƙureta da ido lokacin da yake amsata da cewa, "Lafiya lau
wife,Hajjah tana gaida ki ta ce ki kula da ni da kyau ."
Yadda ya yi maganar cikin wani salo,yasa TAIMIYYAH saurin ɗaga manyan idanunta ta sauke a
kansa,sai kuma lokacin ta ga shigar da ke jikinsa. Yana sanye ne da shadda dark gray kalar Abayar
jikinta, kalar ya yi masa kyau sosai. Kansa babu hula sai sumarsa me kyau da sheƙi, ke faman
haskawa cikin hasken fararen fitullun da suka haske falon ƙau!
Ta yi saurin janye idanunta daga dubansa, lokacin da na shi idanun ke ƙoƙarin shigewa cikin na
ta,ta cigaba da murza ƴan yatsun hannunta,tana jin ta very uncomfortable a cikin falon,sabida
idanun Maleek masu cike da kwarjini,wanda suka hanata saƙat! Don har lokacin tana jin idanunsa
akanta.
"Zaynabb ina jin gaba ɗaya so ki ke ki sanya ni, in rasa duk wata nutsuwar zuciya da ta gangar
jikina, idan har banyi gaggawar mallakarki nan kusa ba. Please ki ɗago ki kalleni,kar kice za ki
haramta min ganin waɗannan idanun, da su ke da matuƙar tasiri a gare ni."
Maleek yana maganar ne idanunsa akan TAIMIYYAH, burinsa kawai ta ɗago waɗannan manyan
idanun nata, masu kama da magic ta dubesa da su. TAIMIYYAH sai ta ɗan shagwaɓe fuska,tana
ɗago kanta da tayi ƙasa da shi ta dubesa, cikin sa'a idanunta suka shige cikin na Maleek Ado,
tamkar wacce aka sanya mayen ƙarfe aka ɗane idanun na ta a cikin na sa,sai ta kasa janye na ta
idanun. Suka zubawa juna ido, dukkaninsu wani maganaɗisu na yawo cikin zuciya da gangar
jikinsu.
Sun ɗauki tsayin mintuna biyu a haka, kafin TAIMIYYAH ta janye idanunta ta mayar
ƙasa,zuciyarta na cigaba da doka mata, da wani irin yanayi me wuyar fassara. Shi ko Maleek baya
ya yi da jikinsa ya jinginar a jikin kujerar 3 seater da ya ke kai, ya lumshe idanunsa baki ɗaya,yana
jin yadda zuciyarsa ke doka masa da wani irin baƙon yanayi,wanda bai taɓa jin irinsa akan kowace
mace ba sai TAIMIYYAH.
Ya jima a haka idanunsa a lumshe, kafin ya buɗe baki ya ce, "Zaynabb idan na nemi a ɗaura mana
aure, nan zuwa sati biyu masu zuwa ban yi gaggawa ba?"
Ya ƙare maganar yana buɗe idanunsa tare da ɗago jikinsa daga jinginan da ya yi, yana kafe
TAIMIYYAH da manyan idanunsa masu shegen ƙwarjini.
TAIMIYYAH jin saukar furucinsa ta yi tamkar daga sama,cikin kaɗuwa ta yi saurin dubansa da
idanunta da suka sake girma, sabida firgicin da kalamansa suka haifar a zuciyarta,muryarta har
harɗewa ta ke lokacin da ta furta kalmar, "What....!?"
Maleek Ado ya jinjina kansa cike da tabbatar da kalamansa ya sake faɗin, "Zaynabb da gaske na
ke yi idan za a bani ke nan da sati biyu zan so hakan, sabida abubuwan da nake ji akanki ni kaina
tsoran kaina na ke yi Zaynabb,watakila shiyasa tun farko aka ɓoye min cikakkiyar siffarki,sai
idanun kawai aka jarabe ni da su cikin mafarki,watakila da an nuna min ke sak ɗinki a wancan
lokacin, da na jima da shiga mummunan yanayi, tare da haukacewa a nemanki a ko'ina ki ke a
faɗin duniyar nan don na mallake ki. Please !Zaynab ki taimakeni in roƙi alfarma a ɗaura mana
aure nan da sati biyu mas......"
Kukan da TAIMIYYAH ta sanya masa a bazata ne ya hana Maleek ƙarisa kalamansa, ya kafeta da
ido yana jin zuciyarsa na sake dilmiya cikin ƙaunarta me zafi. A hankali ya kai hannu bisa lips
ɗinsa ya furta, "Shishhhh...!!! Kar ki ƙarisa kunna ni da wannan sautin kukan na ki Zaynabb
please!"
TAIMIYYAH ta yi saurin tsaida kukan nata, wanda dama har da taɓara a cikinsa,ta zuba masa ido
cike da shagwaɓa ta ce, "Don Allah kar ka yi wa kowa wannan maganar,ni ban shirya ai min aure
nan kusa ba na fi son in yi karatu."
Yadda ta yi maganar cike da zallar shagwaɓa with so much confidence, ya sanya Maleek kasa
cewa komi, illa dafe goshinsa da yayi da hannu biyu, yana jinyar zazzafar gubar ƙaunarta da ta
sake kwararawa a zuciyarsa.
TAIMIYYAH ko sam! Bata damu da yanayin da ya shiga ba, sai ma sake narke fuska da ta yi, tana
jira ya sake mata zancen aure nan kusa ne, ta kuma sanya masa wani sabon kukan. Kamar ya san
shirin ta kuwa sai bai sake maganar ba, sai ma duban side ɗin da aka jere kulolin abinci da su ruwa
ya yi,ya ɗauke ido daga wajen yana mayarwa kan TAIMIYYAH ya furta, "Wife bani ruwa me
sanyi please!"
TAIMIYYAH ta miƙe tare da dafa guiwar ƙafarta ta fara takawa don isa wajen table ɗin,in da aka
jere komi a kai ta ɗakko goran table water da glass cup, ta juyo don kai wa Maleek Ado wanda
idanunsa ke kanta, tunda ta tashi ya ke faman ƙarewa yanayin tafiyarta kallo,wani irin abu ya ke ji
na danne zuciyarsa, yana sake haifar da zazzafar ƙaunarta a duk ilahirin jinin jikinsa.
TAIMIYYAH ta aje masa goran ruwan da cup ɗin,daga saman hannun kujeran da ya ke zaune,tana
faman mita cikin zuciyarta na yadda ya ke bin ta da mayen kallo, kamar zai cinye ta. Ta zumɓure
baki cike da shagwaɓa ta ce, "Ga ruwan ko na zuba maka ne?"
Ta ƙare maganar tana ɗaga manyan idanunta ta dubi fuskarsa,ganin ita ya ke kallo yasa ta ɗauke
kai tana sake narke fuska, Maleek murya can ƙasa ya furta, "Da ni ki ke so na zuba da kaina
wife?"
TAIMIYYAH ta kuma dubansa jin yadda ya yi maganar a dake,sai dai yadda fuskarsa ta ke a
miskile, ba za ka taɓa cewa kaf maganganun da yayi daga bakinsa suka fito ba,ta ɗan taɓe baki
kaɗan lokacin da ta ke kai kyakykyawar hunnunta, mai ɗauke da zara-zaran yatsu ta ɗauki goran
ruwan ta buɗe, tare da zuba masa cikin cup ta miƙa masa. Maleek Ado ya zubawa kyawawan
yatsunta ido, yana sake jin tsoran mafarkin da ya yi ta yi da irin waɗannan yatsun, a lokacin da
takan miƙo masa su a cikin bacci tana neman ɗauki daga garesa,sai dai a wancan lokacin da ya
miƙa hannunsa don kamata,ya ke farkawa daga baccinsa a firgice,yau ga hannun a gabansa tana
miƙo masa cup ɗin ruwa a zahiri ba a cikin mafarki ba. Ya sauke zazzafar numfashi yana miƙa
hannunsa, ya amshi cup ɗin ruwan ya kai bakinsa, ita kuma TAIMIYYAH ta yi saurin komawa
mazauninta, tana sake yin ƙasa da kanta don haka kawai ƙamshinsa da ta sake shaƙowa da kyau,
lokacin da suke daf da juna ya dinga kashe jikinta, yana haifar da wani yanayi a cikin zuciyarta.
Maleek ya shanye ruwan tas! Ya dire cup ɗin daga saman kujerar ya dubi TAIMIYYAH,ganin
yadda ta sauke kanta ƙasa ya sa shi furta, "Zaynab yaushe za ku kammala Computer traning ɗin da
kike zuwa?"
TAIMIYYAH ta dube sa ta ce, "Saura one week mu amsa certificate na kammalawa."
"Very good! Zan yi magana da Hajjah, bari na xo na wuce don idan ina cigaba da ganin waɗannan
idanun,ina kuma jin wannan muryar a kusa da ni, to za ki cigaba da illata zuciyata ne kawai,da
ƙaunarki da ke neman ƙure duk wata jarumtar Maleek."
Maleek ya yi maganar idanunsa akan TAIMIYYAH, wacce ta waro masa nata idanun cike da
mamakin kalamansa,ganin sun haɗa ido yasa ta saurin maida kanta ƙasa kunya na lulluɓeta.
Maleek ya saki murmushi kaɗan kafin ya ce , "Zaynabb kin cika kunya da yawa ,anya ko zan
samu irin kulawar da nake buƙata daga mace a gunki?"
TAIMIYYAH ta yi saurin dubansa kamalaman da bata shirya furtasu ba,suka suɓuce akan
harshenta suka yo waje inda ta ce, "Ai ita na san tana baka."
Maleek da idanunsa ke kan bakin TAIMIYYAH, bai san lokacin da murmushi ya haska a samar
fuskarsa ba, yayi saurin cewa, "Ita wa ce Zaynabb?"
TAIMIYYAH da wani kishi da haushin kanta ya gama cika ta,sabida yadda tayi suɓul kalam ta
furta kalaman a fili har ya ji,sai sake narke face ta ce, "Ita matarka mana."
Maleek sai ya miskile face cike da don tsokanarta ya furta, "Oh! Tana bani mana sosai ma,kin san
ta iya luv shiyasa na ke so ke ma ki rage wannan kunyar,sabida ku dinga gasa da juna wajen nuna
min luv ɗin, ko ba haka ba wife?"
TAIMIYYAH tayi kicin-kicin da face tare zumɓuro ɗan ƙaramin bakinta,cike da shagwaɓa ta ke
duban Maleek ta ce, "Ni ban iya ba tunda ita ta iya shikenan sai ta dinga nuna maka luv ɗin."
"No Babe! It's not okey for me, cox ke ma soon za ki zama mallakina, kuma dole ina buƙatar ki
dinga nuna min luv a zahiri."
Maleek ya yi maganar yana sake miskile face, amma can ƙasan zuciyarsa dariyane fal
cikinsa,sabida yadda TAIMIYYAH ke yi da fuska cike da nuna kishi a zahiri,hakan ba ƙaramin
sake kimsa soyayyarta ya yi a zuciyarsa ba.
TAIMIYYAH bata kuma magana ba sai tashi da ta yi,ta isa wajen da aka shirya coolers ɗin
abincin da ta ɓata lokaci ta yi masa. Ta fara da buɗe cooler ɗin farko tana tambayar Maleek me za
ta zuba masa? Ya ɗago manyan idanunsa ya kai kanta yana cewa, "No wife am full ,Hajjah ta cika
min ciki da abincinta."
TAIMIYYAH ta tsuke fuska cike da rashin jin daɗi ta furta, "Please! A zuba maka dai ko kaɗan
ne, ka ga na ɓata lokaci me yawa wajen yin girkin,in zuba please?"
Yadda ta marairaice masa cike da shagwaɓa, yasa Maleek kasa sake gwaleta a karo na biyu,sai ya
ɗaga mata kai yana furta, "Amma ɗan kaɗan Zaynabb."
TAIMIYYAH ta zuba masa shinkafar ɗan kaɗan, ta zuba haɗin Salad ɗin daga gefe guda,sanna ta
taso ta kawo masa tana me aje plate ɗin daga saman kujera.
Maleek kaɗan ya ci abincin amma ya ji daɗinsa ƙwarai,tare da jin mamakin cewa Zaynab ɗin ce
da kanta tayi wannan haɗaɗɗan abincin.
Lokacin da ya tashi tafiya TAIMIYYAH ta shiga da shi wajen Ummie suka gaisa,ya aje mata
kuɗaɗe masu yawa,Ummie ta yi masa godia bayan ta yi iya yinta ya ɗauki kuɗinsa ya ƙi, daga
wajen Ummie TAIMIYYAH ta yi masa jagora zuwa wajen Hajjaju Iyah. Maleek ya zube ya
kwashi gaisuwa tare ajewa Iyah kuɗaɗe ita ma masu yawa, Iyah ta yi maza ta ce TAIMIYYAH ta
kwashe kuɗin ta mayar masa. Maleek ya nunawa Iyah cewa ba zai ji daɗi ba, idan har bata amshi
kuɗin ba,hakan yasa Iyah haƙura ta bar kuɗin suka fito daga falon shi da TAIMIYYAH, wacce za
ta yi masa rakiya zuwa bakin ƙofar fita daga Part ɗin nasu.
Maleek ya dakata daga tafiyar da ya ke yi, lokacin da ya fahimci cewa iya bakin ƙofar fitowa
kawai TAIMIYYAH za ta yi masa rakiyar,ya buɗe baki cike da ƙasaita ya ke furta, "Zaynabb iya
nan kawai za ki yi rakiyar?"
Ta gyaɗa masa kai tana magana cike da shagwaɓa ta ke cewa, "Sorry na gaji ne shiyasa, ka gaida
Hajjah da kyau Allah ya tsare hanya."
Maleek ya ji daɗin kalamanta ƙwarai, shiyasa ya sakar mata ƙaramin smile ya ce, "Ameen wife
thank u, Hajjah za ta ji sosai but ba ki ce in gaida Anty ɗinki ba, tare muka taho fa tana wajen
Hajjah."
Maleek ya sake sakin murmushi yana yin gaba,TAIMIYYAH ta bi bayansa da kallo tana jin wani
irin zazzafan feeling na kwaranya a zuciyarta,ta juya cikin slowly zuwa cikin falon Iyah.
Zamanta bada jimawa ba Tukur ya fara shigowa da manyan ledoji masu ɗauke da tambarin
SAHAD STORE, daga ita har Iyah suka zubawa manyan ledojin har huɗu da Tukur ya aje a falon
ido. Tukur ya juya ya fice bayan sun gaisa da Iyah, ya sanar da ita cewa Maleek da ya fita yanzu
ne yasa shi shigowa da kayan.
Iyah ta jinjina kai kawai tana rasa bakin magana,don ita sam bata son irin waɗannan ɗawainiyar.
TAIMIYYAH sai ta tashi tsam! Ta nufi ɗakinta ba tare da ta bi ta kan sababin da Iyah ta fara yi
akan yawan kayan ba.....✍🏻
#Ɗansabo ce#
[12/14, 3:43 PM] +234 703 040 9541: Littafin TAIMIYYAH paid book ne,ga duk wanda ta
tsincesa a kowani irin group ne,kiji tsoran Allah karki karanta sai kin biya 500 naira only.
Za ku iya min magana ta wannan number ɗin 08167768704, ko kuma ku turo kuɗin ku kai tsaye ta
wannan account ɗin 0504192664 aisha ibrahim dansabo GTbank.*
Masu turo credit za ku turo katin MTN na 500 ta wannan line ɗin 08167768704.
_Ina ƴan kasuwa masu buƙatar a tallata muku hajar ku? Maza ku garzayo da kuɗi ƙalilan a tallata
muku kayan siyarwanku sai dai kawai ku ji ana kiran waya don buƙatan sayan kayan ku,ku
tuntuɓeni ta layina kamar haka 08167768704._
*63*
*Gonar Ganye.*
*09:40pm*
Baka jin sautin komi cikin falon Hajjah sai na kukan da Suhailah ke yi, me taɓa zuciyar duk wani
me saurarenta. Daga Maleek har Hajjah kallonta suke yi cike da tausayi me tarin yawa, Hajjah ta
tashi ta isa wajen da Suhailah ke zaune, ta haɗe kanta da guiwa tana razgar kuka. Ta zauna kusa da
ita tana me ɗago fuskarta ta fara faɗin, "Suhailah haƙury za ki yi, na san akwai ciwo amma bamu
isa mu ja da hukuncin Ubangijiba,Maleek zai sake aure ne ba don ya daina sonki ko ya daina
ƙaunarki ba,haka ba don ba ki haihu zai sake aure ba, zai sake aure ne sabida haka Allah ya rubuta
masa cikin littafin ƙaddaransa, za ki fahimci hakan ne daga labarin da muka baki, tun daga kan
mafarkin da yake yi da Yarinyar, har kawo haɗuwata da ita da sanadin da ya zama silar kulluwar
zumunci a tsakaninmu da su.Suhailah bana so ki ga cewa ba a yi miki adalci ba, shiyasa na zaɓi ku
taho nan don a buɗe miki komi, ba wai ki ji magana daga sama ba,ina baki haƙury tare da tausar
zuciyarki,akan ki ɗauki ƙarin auren da Maleek zai yi a matsayin rubutacciyar ƙaddaranku ke da
shi,wanda mu da ku duka bamu isa ja da hukuncin Ubangiji akan hakan ba,don haka ki nutsu ki
rungumi ƙaddara tare da baiwa mijinki goyan baya, ki yi addu'a Allah ya haɗa kan ku ya ba ku
dauwamammiyar zaman lafiya."
Hajjah ta ƙare maganar tana me rungumo Suhailah zuwa jikinta, ta cigaba da rarrashinta da
kalamai na kwantar da hankali.
Suhailah ta ɗago kanta daga jikin Hajjah, tana kallon direction ɗin da A.Maleek ke zaune, sai
kawai ta sake barkewa da kuka,babu abinda ke amsa kuwwa cikin kanta da kunnuwarta ,sai
maganar ƙarin auren da zai yi nan da lokaci kaɗan, kamar yadda ya sanar mata da bakinsa.
Maleek ya ɗago manyan idanunsa ya sauke akan fuskar Suhailah, yana jin tausayinta me girma na
kassara zuciyarsa. Memakon ya yi magana sai kawai ya miƙe yana barin musu falon ,ya fice baki
ɗaya don ba zai iya zama yana cigaba da sauraren sautin kukan Suhailah ba.
Daga Hajjah har Suhailah suka bi bayansa da kallo, Suhailah ta sake fashewa da kuka tana ji
tamkar zuciyarta za ta fashe,wani mahaukacin kishin Maleek ke sake danne zuciyarta. Duk iya
yadda Hajjah ta kai da son ta ga cewa Suhailah ta fahimce ta abin ya ci tura,sai ma tashi da
Suhailar ta yi ta nufi ɗakinta na tun asali a gidan, ta kulle kanta a ciki don bata son sake jin kowani
irin rarrashi daga wajen Hajjah, ta kuma gama ƙudurcewa a zuciyarta ba za ta bi Maleek zuwa
GRA gidansu su kwana tare ba,don haushinsa take ji daga shi har Hajjan.
Gaba ɗaya daren idan Suhailah ta ce ta rintsa to ta yi ƙarya,tsanar Hajjah da Maleek take ji me zafi
a ranta, tana ganin cewa sun daina ƙaunarta ne kawai,sabida Allah ya jarabceta da rashin haihuwa.
Ko da gari ya waye duk iya bugun ƙofar da Hajjah ta dinga yi, akan Suhailah ta buɗe ta saurareta
abin ya ci tura,sai ma cewa ta yi da Hajjah ta tafi abin ta don ba za ta taɓa buɗe ƙofar ba,gara su
barta ta mutu su ɗauki gawarta tunda sun daina ƙaunarta, don an ga ba idon iyayenta a raye.
Waɗannan kalamai na Suhailah su suka dugunzuma zuciyar Hajjah,ta juya cikin tsananin fushi ta
nufi ɗakinta don kiran Maleek,ta sanar da shi halin da take ciki da Suhailah. Lokacin da Maleek ya
iso gidan Hajjah da ƙyar Suhailah ta yadda ta buɗe ƙofar ɗakin, kallo ɗaya ya yi wa idanunta ya
san ko kaɗan bata samu bacci ba. Sai tausayinta ya kama zuciyarsa,ya isa gareta yana ƙoƙarin
sanyata a jikinsa ya rungumeta, amma sai Suhailah ta yi gaggawar hankaɗe hannunwansa daga
taɓa jikinta,ta fara gaya masa zafafan kalaman da suka hasala zuciyar Maleek. Ya ɗaga hannu zai
ɗauke ta da mari sakamakon zafafan kalaman da ta faɗi na ƙarshe tana cewa, "Kar ka kuskura ka
ce za ka sake taɓani,ka je can wajen gurguwar na sallama mata kai Yaya Maleek, tunda ka tsaneni
ka ci amanata, ka zaɓi auren nakasasshiya sabida ban haihu ba,meyasa idan auren za ka ƙara ba za
a sanyaka ka auro me lafiya ba sai gurguwa, nakasasshiya sabida ku tozarta ni...."
Hannun da ya ɗaga zai zabga mata mari ne ,ya sanya Suhailah gintse kalamanta,Maleek da
idanunsa suka fara sauya launi ko me ya tuna? Sai ya sauke hannunsa ba tare da ya kai mata marin
ba kamar yadda ya yi niyya. Ya juya cikin tsananin fishi ya fito daga ɗakin ya nufi ɗakin Hajjah. A
zaune ya samu Hajjah ranta a matuƙar ɓace ita ma, don kalaman Suhailah sam basu yi mata daɗi
ba ko kaɗan.
Ya isa kusa da ita ya zauna yana buɗe baki ya ce, "Hajjah haƙury za ki yi da Suhailah, ni da ke
duka mun riga mun san sai hakan ya faru,idan har ta ji maganar aurennan,don haka ki yi biris da
ita da duk wani haukar kishin da za ta nuna,ni zan wuce Lagos zuwa anjima,amma ita zan barta
anan ta samu kaman 2 weeks kafin ta koma Abuja,watakila zuwa lokacin ta saduda ta haƙurewa
zuciyarta, don duk wani haukanta ba su isa su hana komi ba,sannan ki gargaɗeta akan aibanta
halittar Zaynab a gaban idanuna,idan har ta cigaba da hakan zan mugun saɓa mata,don ko a yanzu
ma na kai zuciyata nesa ne da sai na kwaɗa mata mari."
Maleek ya yi maganar cikin fishi me tsanani, don a yanzu idan akwai abinda ya tsani ji bai wuce a
kira TAIMIYYAH da suna gurguwaba,hakan na masa ciwo ko da a ce daga bakin ita TAIMIYYAR
kalmar ya fita.
Hajjah ta jinjina kanta kafin ta dubi cikin idanunsa tana faɗin, "Allah ya tsare hanya Maleek,
tabbas barin Suhailah a nan ɗin shi zai fi,don tana buƙatar a bata space ta huce,zan kuma san ta
inda zan ɓullo mata,ai kishi ba hauka bane."
Daga haka Maleek ya yi sallama da Hajjah ya fito daga gidan, ba tare da ya sake bi ta kan
Suhailah ba. Yusuf Driver shi ne zai kai shi Kaduna, ya bi flight ɗin 2 zuwa Lagos.Suna kan hanya
ne ya kira TAIMIYYAH a waya su kai sallama da juna,akan cewa nan da sati biyu masu zuwa zai
sake dawowa,wanda ya ke fata idan ya dawo ɗin kafin ya bar gari an kai kuɗi da kayan sanya
ranar aurensu,don ba ya ji zai iya ƙara watanni biyu ba tare da ya mallaki TAIMIYYAH a
matsayin halaliyarsa ba.
__________
*Saturday, 05:56pm.*
Umma ta dubi Baba Sani hankalinta a matuƙar tashe ta ce, "Yanzu Baban Basmah kana nufin duk
waɗannan uban kwalayen, kamar za a buɗe shago kayan sanya ranar auran TAIMIYYAH ne? Wai
shin ma da yaushe ta samu mijin har magana yayi ƙarfi,ba tare da ko sau ɗaya bakinka ya furta
hakan ba?"
Umma ta kai ƙarshen maganar da jefa masa tambaya, tana jin yadda zuciyarta ke sake rufewa da
wani irin duhun ɓacin rai,idanunta na cigaba da kallon uban kwalaye zuwa katan-katan nasu ruwa
da juice, da suka cinye rabin bango guda na falon daga sama har ƙasa.
Bata taɓama ganin kayan sanya ranar auren da aka haɗo kayayyaki irin wannan ba, ta sake ɗaga
idanunta ta dubi Baba Sani wanda ya tamke fuska tamau, ba shi kuma da niyyar bata amsar
tambayarta. hakan yasa ta sake gyara zama tana fuskantarsa sosai ta ce, "Kana jina fa Baban
Sadeeq,na ce da yaushe ta samu mijin har aka sanya rana da gaggawa haka,mu da muke gida ɗaya
bamu taɓa ganin ko ƙyallinsa ba?sai kawai rana tsaka mu ga waɗannan uban kaya kamar za a buɗe
shagon provition,ina jiye muku tsoron kar ku ɗauki nakasasshiyar marainiyar Allah ku baiwa ɗan
yankan kai, bayan biki ya miƙawa ƙungiya jininta su shanye,don dai daga ganin waɗannan kaya
an san dukiya ne ya ruɗeku, har kuka amsa da gaggawa za ku sallamata,wai shin ma a ina ta samo
mijin ne?"
Umma ta sake jefawa Baba Sani tambayar tana kafeshi da idanunta,sam bata damu da irin mugun
kallon da yake bin ta da shi ba. Ya buɗe baki ya yi magana cikin ɓacin rai yana cewa, "A gabana
Zuwairah, a gabana zaki buɗe baki kina furta irin waɗannan mugayen kalaman akan jinin Sameer?
To kar ki kuskura ki ƙure haƙurina don zan mugun baki mamaki, da ki ke maganar ba ku san da
samun mijinba, dole ne idan Zaynab ta samu miji sai an yi shela duniya ta sani,ko kuma dole sai
kin sani kafin ayi komi sabida ke ce waliyiyarta ko? To bari ki ji ba zan ɗauki duk wani shirme
ba,don ina sane da irin ƙiyayyar da ki ke nuna mata tun asali,kuma maganar kada mu baiwa ɗan
shan jini,idan mun ba shi ki je ki ƙwatota daga hannunsa idan ya tabbata ɗan shan jinin ne,kar ki
kuskura ki sake min magana makamancin wannan Zuwairah kinji na faɗa miki."
Baba Sani ya tashi fuu..! Ya bar mata falon ya shige ɗakin baccinsa, ransa a matuƙar ɓace da
kalaman da Umman ta gaggaya masa. Umma ta bi bayansa da kallo tana jin wani tashin hankali na
sake rufto mata,ga takaicin rashin samun cikakken amsar tambayarta, na son sanin cikakken waye
wanda za su ɗauki auren gurguwar da ta tsana su ba shi? Tana shirin tashi ta bi Baba Sani Sadeeq
ya yi sallama yana shigowa cikin falon, sai ta yi saurin dubansa lokacin da yake takowa zuwa
cikin falon Baba Sanin, idanunsa akan uban kayan sanya ranar auren TAIMIYYAH da su ke tsibe.
Ya samu waje ya zauna yana gaida Umma, wacce gaba ɗaya take jin tamkar ta ari hauka, sabida
baƙin cikin da ke damun zuciyarta. Ta amsa gaisuwar Sadeeq a lalace kafin ta dubi cikin idanunsa
tana jefa masa tambayar da ke cin ranta, "Kai Sadeeq wai wa ye mutumin da waccar gurguwar za
ta aura? Da har ake ɓoye mana maganar tun farko,sai kawai muka ji labarin an sanya ranar
aurensu, kuma don wulaƙanci wai duk gaba ɗaya za a yi bikin da na su Basmah,sabida a
tozartamu a nuna ta samo me arziƙin da ya kere mazajen da ƴaƴana za su aura,don daga ganin
wannan uban kayan an san cewa ba daga ƙaramin gida suka fito ba,sanar dani ɗan gidan uban
waye za ta aura a garinnan?"
Sadeeq ya yi saurin duban Umma yana mamakin yadda ta fusata, tana ɗaga murya cike da zallar
tashin hankalin da ke haskawa akan fuskarta,ya ɗan cije bakinsa yana jin tsanar halayyar
mahaifiyar tasa na ƙona ransa, ya buɗe baki a hankali ya ce, "Umma ni ma ban san shi ba,amma
Baba ya ce ɗan gidan tsohon Asistant Controller ne da ya rasu, Marigayi Alhaji Ibrahim
Ado,sunan guy ɗin Alhaji Abdulmaleek Ado, ana kiran da Maleek Ado kaɗai,gaskiya a yadda
Baba ke bani labari ba ƙananun mutane ba ne, don sun tara arziƙi me ɗinbin yawa,gashi guy ɗin a
yanzu haka shike riƙe da muƙamin Chairman na Shiffing Board na baki ɗaya. Kin ga ko
baƙaramin mutum ba ne ,duk da cewa yaro ne ba wai Babba ba don duka bai ma kai 40yrs ba
thirty something ya ke."
Sadeeq ya gama ratafawa Umma jawabin cike da basarwa, idanunsa akan uban kayan da ke tsibe
cikin falon Baban nasu. Umma da tuni zufa ya gama jiƙe wani ɓangare na jikinta, sai ta dubi
Sadeeq cike da ɓacin rai ta ce, "Eh lallai dole a ɓoye mana ayi komi a munafurce,sabida ni ce da
ƴaƴana ba a so da alkhairy sai musaka gurguwa. Duk kuma ba kowa ke da alhakin hakan ba sai
waccar tsohuwar makiran kakar ta ku Iyah. Sabida na ji ana ƙishin-ƙishin cewa wai ai uwar
Mutumin ce, suka kaɗe TAIMIYYAH ɗin watannin baya,ka ga kenan Iyah ita ce ta kitsawa uwar
tasa wannan munufurcin, akan su haɗa aure tsakanin gurguwarta da ɗan matar,to Allah yasa ba
ɗan ƙungiya bane ya je ya sai da ita bayan auren."
Sadeeq ya yi hanzarin duban Umma yana faɗin, "Subhanallah! Umma wani irin kalami ki ke yi
haka marar daɗin ji? Don Allah ki sanyawa zuciyarki salama, ki yi wa Zaynab fatan alkhairy ne ba
sharri ba,ni dai ina ji a jikina cewa alkhairy ke bibiye da rayuwarta In sha Allah. Kuma ina farin
ciki da wannan auren da za ta yi , Allah ya bashi ikon riƙe ta da amana ita da abokiyar zamanta."
"Au yana ma da aure shi ne za a ɗauki gurguwa a cinna masa? Eh! lallai wannan ya nuna cewa
tsabagen kwaɗayi da son a nuna mana iyakarmu ace ta auri me arziƙi ne,shiyasa makirar ta ƙulla
abin."
Umma ta sake kwaɓowa Sadeeq waɗannan banzayan kalaman,hakan yasa Sadeeq tashi ya baro
falon Baba Sanin, ba tare da ya tsaya tambayar Umman akan cewa ko Baba Sanin na nan ba?
____________
Daga can Part ɗin Ummie kuwa TAIMIYYAH ce zaune ita da Ummie, suna magana akan
Doughnut da TAIMIYYAH za ta yi a raba sadaka, ranar da Ummien za ta fita takaba nan da sati
me zuwa. TAIMIYYAH ta dubi Ummie tana cewa, "Amma dai Ummie za ki zauna anan tare da
mu, ba gida Kd za ki koma ba ko?"
Ummie da gaba ɗaya a ƴan kwanakinnan ta ke sake jin kewar mijinta da yaranta me tsanani na
damun zuciyarta,ta yi murmushin ƙarfin hali tare da cewa, "To ganinan dai Zaynab,zan cigaba da
zama dai har zuwa ayi bikinku sannan sai na tattara na koma gida,sai dai na dinga kowawa Iyah
ziyara time to time,ni duk na ƙosa ma time ya zo mu sha biki in ga cewa na aurar da ɗiyata, ko kya
haifomin jikokin da zan yi alfahari dasu."
TAIMIYYAH ta yi saurin kai bakin gyalenta ta rufe fuskarta, cike da tsananin jin kunyar kalaman
Ummien. Ummie ta saki dariya kunyar TAIMIYYAH na sake birgeta, tare da haifar da tarin
ƙaunarta me tsanani a cikin zuciyarta. Ta buɗe baki cike da son sake tsokanar TAIMIYYAH ta ce,
"Haba daughter ko ke baki son ki haifo little Nahar ne ,wacce za ta dinga ɗebe mana kewar wacce
muka rasa?"
TAIMIYYAH da kalaman Ummie suka motsa zuciyarta,sai ta yi saurin duban fuskar Ummie da ke
faman murmushi ta ce, "Ina so Ummie in dai Allah zai bani ina so,kuma In sha Allah zan roƙa a
maida min sunan Nahar ɗita da na rasa."
Yadda TAIMIYYAH ta yi maganar fuskarta na haskawa da tarin kewar ƴar uwarta,ya sanya
Ummie jin zuciyarta ta taɓu,ta yi saurin kauda zancen ta hanyar faɗin, "In sha Allah Zaynab za ki
haifa,Allah zai ba ki rabo da gaugawa kamar yadda auren ya zo cikin gaugawa."
Daga haka Ummie ta mai da hiran ya koma tattaunawa akan yadda za su shirya shagalin bikin,
idan lokaci ya yi, ita dai TAIMIYYAH kunya ya hanata biyewa Ummien su yi maganar yadda ya
dace.
Kiran Maleek da ya shigo cikin vid call ne ya sanya TAIMIYYAH tashi ta nufi bedroom ɗin
Ummie don amsa wayar.
A kan Sofa da ke cikin ɗakin ta yi masauki lokacin da take receiving call ɗin, tare da gyara zaman
gyalen da ta yafa ajikinta.
Ta saki kyakykyawar murmushi lokacin da face ɗin Maleek ya bayyana a allon screen ɗin sabuwar
wayar da ya siya mata,wani irin soyayyarsa ta ke ji a ƴan kwanakinnan na ƙaruwa a cikin
zuciyarta.
A.Maleek Ado wanda ke kwance akan doguwar kujerar 3 seater,wanda ke cikin haɗaɗɗen falon
gidansa da ke can Lagos,ya sauke idanunsa akan face ɗin TAIMIYYAH, yana jin wani irin sabon
feeling akanta na kewaye jinin jikinsa.
Yadda ya yi maganar a miskile ya sanya TAIMIYYAH zunɓure baki tana sakin murmushi,cike da
shagwaɓa ta narke murya ta ce, "Ni dai Yayana ne kai, tunda ni ƴar Hajjah ce ka ga kenan kai
Yayana ne."
"No wife ni ban yarda ba,tunda soon za a ganki da ƙaton cikin da za ki haifo min twins, don da
nayi mafarki kin yi ciki an ce twins za mu samu. Kin ga kenan ni ba Yayanki bane, ko Yayanki zai
iya yi wa ƙanwarsa ciki ne ta haihu?"
Maleek ya saki ƙaramin smile yana saurin faɗin, "No wife wallahi kar ki fara kashe min
waya,kuma a buɗe min fuskata ni banson wani gulma, wai a dole ana jin kunya ta."
TAIMIYYAH ta buɗe fuskarta har lokacin kunyar kalamansa ta ke ji, shi ko ya basar ko ajikinsa
sai ma cigaba da zaro mata zance ya ke yi. Sun ɗauki lokaci suna waya,kafin Maleek ya yadda su
yi sallama,ganin lokacin kiran sallar magrib ya kusa.
Lokacin da TAIMIYYAH ta koma Sasan Iyah, ta same su ne zaune ita da Baba Sani,da alamu suna
tattauna magana ne me muhimmanci, hakan yasa TAIMIYYAH na gaida Baba Sani ta shige ɗaki.
Sai da daddare ne bayan sun kammmala yin dinner, Iyah ke sanar da TAIMIYYAH maganar da
suka yi da Baba Sani,akan son ya nemi auren Ummie da zaran ta fita takaba nan da sati ɗaya me
zuwa. TAIMIYYAH ta dubi Iyah da wani irin tarin farin ciki daya haska cikin idanunta,bakinta har
rawa yake wajen faɗin, "Wow! Iyah aiko kin yi tunani me kyau, to me Baba Sanin ya ce?"
Iyah ta saki murmushi ta ce, "Cewa ya yi in bashi lokaci ya yi tunani,sannan ita ma Ummie in
sameta da maganar, idan har ta amince a shirye ya ke da ya amsa aurenta." Iyah ta cigaba da cewa
" Wallahi bana so ta kufce mana don sai yanzu na karanci kyawawar halayyar da ta ke da su. A da
ina mata kallo wani iri sabida yadda na ke ganin tana share lamarinki,shiyasa aka ce baka sanin
halin mutum sai ka zauna da shi,zan sameta da maganar zan kuma yi iyakan ƙoƙarina wajen ganin
cewa ta amince da auren Sani,ko ya samu mata me hankali da ta san abinda ta ke yi, Sabida
Zuwairah ba macen arziƙi ba ce sam! Don har yanzu maganar da na ke yi, bata tako ta ce ko Allah
ya sanya alkhairy da sanya ranar aurenki da aka yi ba, sabida tsabar hassada da baƙin hali,daga ita
har ƴaƴan na ta kallonsu kawai na ke yi,kuma baƙin ciki yanzu suka fara in dai a kan aurenki da
Maleeku ne."
Iyah ta kai ƙarshen maganar cike da jin zafin baƙaƙen halayyar Umma da yaranta.TAIMIYYAH ta
taɓe baki tana cewa, "Iyah kenan ni ban taɓa sawa raina cewa suna cikin jerin mutanen da za su
taya ni murna, ko farin ciki don zan yi aure ba, Allah dai yasa Ummie ta amince ta auri Baba Sani
Iyah,idan hakan ya kasance zan fi kowa farin ciki,wallahi har na ƙosa in ga yadda Umma za ta yi."
#Ɗansabo ce#
[12/14, 3:43 PM] +234 703 040 9541: Littafin TAIMIYYAH paid book ne,ga duk wanda ta
tsincesa a kowani irin group ne,kiji tsoran Allah karki karanta sai kin biya 500 naira only.
Za ku iya min magana ta wannan number ɗin 08167768704, ko kuma ku turo kuɗin ku kai tsaye ta
wannan account ɗin 0504192664 aisha ibrahim dansabo GTbank.*
Masu turo credit za ku turo katin MTN na 500 ta wannan line ɗin 08167768704.
_Ina ƴan kasuwa masu buƙatar a tallata muku hajar ku? Maza ku garzayo da kuɗi ƙalilan a tallata
muku kayan siyarwanku sai dai kawai ku ji ana kiran waya don buƙatan sayan kayan ku,ku
tuntuɓeni ta layina kamar haka 08167768704._
*64*
*Abuja*
Jawahir ta dubi Suhailah wacce ta sake ramewa, ta fita hayyacinta sabida kishi,don tunda aka
sanya ranar auren Maleek da TAIMIYYAH, hankalinta ya ke a matuƙar tashe. Duk kwanakin da
ta yi wajen Hajjah da irin yadda Hajjah ta dinga ƙoƙarin ganin Suhailah, ta kwantar da hankalinta
ta fahimci cewa,ƙarin auren da Maleek ɗin zai yi ba yana nufin cewa ya daina sonta ko ƙaunarta
bane,zai ƙara auren ne sabida haka Ubangiji ya tsaro, cikin littafin ƙaddaran kowannensu.
Suhailah sam bata fahimci hakan ba,abinda kawai ta sanya a ranta shine Hajjah ta daina ƙaunarta,
ta nuna mata cewa ta fi son Maleek tunda shi ta haifa ba ita ba,shiyasa ta ke jin zafin Hajjah sosai
game da wannan ƙarin auren,wanda take ganin tamkar farin cikin rayuwarta ake shirin tsaidawa.
"Suhailah ki kwantar da hankalinki don Allah,wannan maganar auren fa ban ga wani big deal a
cikinsa ba, tunda ma musaka zai auro,ina ke ina lalata kanki da zafin kishi akan gurguwa? Wacce
na tabbatar kin fi ta diri da komi,ke da bakinki fa ki ke faɗin uwarsa ce ta haɗa abin,kin ga kenan
shi kansa Maleek ɗin,ya amince ne don kawai yana kwaɗayin ya ɗirka mata ciki ta haihu,ki
kwantar da hankalinki kin nuna cewa komi ya wuce,ni zan shirya miki duk yadda za ki bi da
su,sannan idan akwai kuɗi a wajenki ki kawo ai miki aiki, don ki mallaki mijinki yadda sai abinda
ki ka ce,yanzu an daina zama haka kara zube, ke na ga alamun kan ki har yanzu a kulle ya ke,mu
ai mana kishiyar mana don uban mutum!"
Jawahir ta kai ƙarshen maganar tana wani taɓe baki,idanunta a kan Suhailah da tayi sakato da baki
tana kallonta. Suhailah ta sake zubawa Jawahir idanu kafin ta buɗe baki ta ce, "Jawahir ni sai ki
dinga min magana a dunƙule, ki fahimtar da ni inda kika dosa please!"
Jawahir ta saki murmushin fara samun nasara, kafin ta ɗan tsuke fuska tana kai bakinta kusa da
kunnin Suhailah, ta fara yi mata raɗa a kunni, ni dai sam ban ji me Jawahir ɗin ke raɗawa Suhailah
a kunnin ba.
Jawahir bayan ta gama yi wa Suhailah raɗa ne ta koma ta gyara zamanta tana cewa, "Yanzu
yaushe Maleek ɗin zai shigo miki weekend?"
Suhailah ta taɓe baki kaɗan tana baiwa Jawahir amsa ta ce, "Ina ga nan zuwa jibi zai shigo tunda 2
weeks kenan bai shigo ba."
Jawahir ta yi murmushi ta ce, "Okey to ki dai yi duk yadda na ce ɗin,kar ki taɓa bari ya samu
kanki cikin sauƙi, kin dai gane me na ke nufi ai?"
Suhailah ta jinjina kai tana duban yadda Jawahir ta ci serious sannan ta ce, "Eh duk na gane
ƙawata,kin san yadda na ke jin haushinsa kuwa a yanzu? Hmm! Ni babu abinda ke min ciwo idan
na tuna wai gurguwa Maleek zai amince ya aura, har ya ke nuna rawar ƙafa irin haka,don da gaske
nuna son auren ya ke yi ,ke kya ce lafiyyyace Yarinyar,ni duk na ƙosa in ga shegiyar ma ,na ji
Hajjah ta ce dai wai tana tafiyarta in ta dafa guiwa."
Jawahir ta taɓe baki tana sakin dariyar mugunta ta ce, "To ai za ki ganta ranki-ya-daɗe,kar ki wani
damu da kanta ma za ta sai ta ma kanta hanya, in ta ga cewa kinfi ƙarfinta,ke dai kawai ki yi yadda
na ce ki samu ya amince miki, mu kuma idan hakan ya kasance za mu aiwatar da abinda ya
kamata."
Suhailah ta jinjina kai cike da gamsuwa, sannan suka cigaba da magana da Jawahir,wacce ta ke
ɗaurata akan gadar zaren da ba zai kai Suhailah ko'ina ba sai tashar nadama.
____________
*Zaria*
Kwanaki sun cigaba da shurawa ana cigaba da tsare-tsaren, yadda shagulgulan bikin su
TAIMIYYAH zai gudana,wanda ya rage saura sati uku dai-dai. Iyah sam ba a zama kullum cikin
kai kawo ta ke, na shirye-shiryen yadda za ta fita kunyan baƙi,wanda tuni ta fara aika goro da
sweet na gayyata,hatta dangin Mamar TAIMIYYAH da ke can Daura an aika musu da komi da
komi.
Ta ɓangaren Hajjah uwar Ango ma tuni sun kammala duk wani shirinsu,hatta sabon gidan da za a
aje TAIMIYYAH a cikin GRA ya kammala,an kuma zuba komi na more rayuwa a cikinsa ,sai
ɗakuna biyu ne kacal Hajjah ta ce a barsu, kar a zuba komi sabida a bai wa su Iyah daman nuna
bajintansu su ma,sabida ko yaya ne mace na son a shigo gidanta a nuna wani abu ace daga gidansu
ta taho da shi. Hatta da lefe an kammala haɗawa, kuma duk abinda aka siyawa TAIMIYYAH haka
ta sa aka siyawa Suhailah ita ma,sai dai bambamcin akwatuna biyu da Hajjah ta ƙarawa
TAIMIYYAH, wanda cikin aljihunta ta shiga ta siya kayan da aka zuba aciki,jiran zuwan Maleek
kawai ta ke yi wanda zai iso garin jibi,idan ya ga Lefen sai a ɗauka akai can Fam House ɗin su
TAIMIYYAH, kamar yadda aka sanar da su Hajjan.
___________
"Zee ina ga fa za a cire wani Bridal Shower don ni bana buƙatar yin komi da ya wuce Walima."
TAIMIYYAH ta yi maganar tana duban Zee da ke zaune daga ƙasan carfet ɗin ɗakin
TAIMIYYAH, Zee ta dubi TAIMIYYAH ta ce, "Haba dai Namcy meyasa za ki ce haka,don Allah
mu dai ki bar mu mu raƙashe yadda mu ke so,na ki kawai ki cakare ayi pics, banda haka bamu ce
ki damu kanki akan komi ba,kin san ma Yasmeen ba za ta taɓa yarda a fasa yin Birdal Shower
ɗinnan ba ,yadda taci buri ga kuma kayan mu can wajen ɗinki wanda zamu saka ranar."
Zee ta ƙare maganar tana sakin dariya, ganin yadda TAIMIYYAH ta wani narke face kaman za ta
saki kuka. Ta dubi Zee ɗin ta ce, "Wallahi guys ɗinnan ku na da damuwa, ke dai da Yasmeen ban
san wanda ya fi wani son bidi'a ba,shi kuma Uban Gayyar ne ai ya ɗaure mu ku gindi,da ya turo
muku da kuɗin da za ku yi ta shirme da su,ni kam ko pics ɗin ma ba zan yi ba aje ana nuna ni a
duniya ana cewa, ga wata gurguwa da neman duniya har da su yin Party a biki."
Zee ta dallawa TAIMIYYAH harara ta ce, "Ke dai wallahi ba ki yi ba Zaynab,miye na yin wannan
maganar babu kan gado, to sai me don kin yi Bridal shower don kina da nakasa? baki da labarin
gurguwar da ake turawa akan keken guragu ma anyi ƙasaitaccen Dinner Party da Bikinta,kuma
akan keken gurugun aka turota zuwa wajen,don Allah ki daina kyarar kanki da kanki
TAIMIYYAH please!"
Zee ta ƙare maganar cikin nunawa TAIMIYYAH cewa da gaske, ranta ɓaci ya ke yi idan tana jin
yadda TAIMIYYAN ke zagin kanta da kanta, da an yi magana ta ce ita gurguwace kaza da kaza.
TAIMIYYAH ta saki murmushi tana haɗe hannunta biyu alamun roƙo ta ce, "Sorry Namcy na
daina ,wallahi shi ma Maleek ya hanani kiran kaina da sunan, amma na kasa dainawa don gani na
ke ko ni ban kira kaina da sunan ba, ai dole duniya za ta kira ni da shi,tunda duk wanda ya ga ina
tafiya cewa ake yi ga wata gurguwa can."
TAIMIYYAH ta ƙare maganar wani abu na motsawa cikin zuciyarta, Zee ta sake balla mata harara
cikin son kawar da zancen ta ke cewa, "Su sauran Amaren miye na su shirye-shiryen? Kamata ya
yi ma ku yi komi tare tunda dai duk abun ɗaya ne."
TAIMIYYAH ta ɓata fuska lokacin da ta tuno yadda suka kwashe da su Zuhurah, da irin baƙaƙen
maganganun da suka danƙaramata,lokacin da ta ke tambayarsu ko za a haɗu a tsara yinin bakin
duk tare da juna. Cikin takaicin kalaman da suka gaya mata lokacin ta dubi Zee ta ce, "Hmm! Zee
kenan na gwada son hakan ya kasance, amma sun nuna cewa in yi sabgata su yi tasu,shiyasa ban
ƙara musu magana akan me suke ciki bama,ni da kun bar ni ma iya walima kaɗai idan akayi ana
gobe ɗaura aure ya wadatar."
Zee ta riga ta gama karantar cewa su Zuhurah, ba masu mutunci bane ta taɓe baki ta ce, "To
shikenan sai kowa ya yi sabgar tasa waye a ƙasa? Da sun zo an haɗa kai an yi komi gaba ɗaya, da
sunci arziƙi ma sun bar arziƙi in da suka gansa,don Maleek 1.5 mil abinda ya turawa Yasmeen,ko
bata gaya miki bane?"
TAIMIYYAH ta jinjina kai cikin sanyin murya ta ce, "Ta gaya min ta ma turo min da receipt na
Transaction ɗin da ya tura mata.Ni wallahi Zee kwana biyu ma duk jikina a sanyaye ya ke,idan ina
tuna cewa yana da wata matar, da kuma girman matsayinsa sai in ji wani fargaba na lulluɓe
zuciyata,sai na dinga jin cewa Maleek ya fi ƙarfin aji na nesa ba kusa ba,kawai dai Ubangine ya
haɗa zukatanmu ba don na kai matsayin da zan mallaki mutum kamarsa ba,Allah dai yasa matarsa
ta zama me sauƙin hali ba muguwa ba, don wallahi yana yawan gaya min akwai ta da zafin kishi."
Zee ta murmusa sabida yadda TAIMIYYAH ta yi maganar cike da zallar shagwaɓa,ta dubi
TAIMIYYAH da idanunta ke kanta ta ce, "To ai tunda kin kira Allah kin gama magana Namcy,don
ya fiki sanin fifikon da ke tsananinku da juna, amma a hakan ya haɗa zuciyoyinku tare da jarabtar
zuciyar Maleek ɗin da matsanancin ƙaunarki,maganar matarsa kuma ni ina ga baki da case da ita,
tunda ba gida ɗaya za ku zauna ba,tana Abuja kina Zaria me zai haɗa ku bare har ki ga zafin kishin
nata? Ai sai dai ta yi masa can shi da ya haɗaku, amma ke kam in ba zuwa ta yi ku haɗu anan
Zaria ba miye zai haɗa ki da ita? Babu."
TAIMIYYAH ta jinjina kai cike da gamsuwa, kafin ta ce komi wayarta da ke kusa da ita ya shiga
ringing,ganin Anty Laurat ce me kiranta vid call yasa ta yi saurin yin receiving tana cewa, "Anty
Laurat shiru kwana biyu, sai yaushe za ki iso mana ne,duk na ƙosa ki zo wallahi."
Anty Laurat ta dubi fuskar TAIMIYYAH da ya sake wani kyau da fresh ta ce, "Hey Baby na! Kin
ga ko yadda ki ke ƙara tsatso kyau, wani irin gyara Iyah ta fara yi miki haka da ya amshi jikinki?"
TAIMIYYAH ta saki murmushi kafin ta shagwaɓe murya tana cewa, "Wallahi Anty Laurat Iyah ce
ke min wankan nono da zuma kullum,tun ina jin ƙarnin nonon na damuna ajiki har na daina
ji,haka za ta zuba zuma a cikin nonon shanu ta kwaɓa,sai ta bani in shafe duka jikina da shi,sai ya
ɗauki kamar awa ɗaya sannan ta kai min ruwan lalle da ta dafa shi ya huce dai-dai wanka,sai na
shiga na wanke jikina da ruwan lallin kaɗai,bayan na wanke jikin da ruwan lalli to ba zan ɗauraye
jikin da kowani ruwa ba, sai wannan ruwan lallin ya bushe a jikina ya samu kamar awa ɗaya shi
ma,sannan sai na je na yi wankan sabulu, to shine fa in gaya miki fatata ke wani irin laushi da
glowing,ni kaina na san abin ya amshe ni matuƙa."
Anty Laurat da ke sauraren TAIMIYYAH idanunta na sake ƙarewa fuskar TAIMIYYAR kallo ta
jinjina kai tana cewa, "Gaskiya Iyah ta san ta kan sanin sirrin gyara, wannan ai ko wajen gyaran
jiki ki ka je iyakarta kenan,ni ma ko idan nawa bikin yazo zan jaraba yin hakan, in ga ko zai amshi
fatata dama ke ai fatarki me laushi ce, shiyasa babu wuya gyara ya kama skin ɗin irinku masu
sulɓin fata,su Zuhurah na ji Umma na cewa zuwa next week za a fara musu gyaran ai,ni ma zuwa
next week ɗin zan shigo In sha Allah!Yasmeen ita ma bata iso ba kenan sai ta waya ake ta fafata
shiri,ai na tura mata measurement na ɗinkin gown da za mu saka ranar Bridal ɗin,wallahi sun yi
zaɓe me kyau Material ɗin ya haɗu matuƙa,Allah dai ya kaimu lafiya Mrs.Maleek Ado."
TAIMIYYAH ta amsa da cewa "Ameen." Tana jin wani abu na malting a zuciyarta jin sunan da
Anty Laurat ɗin ta kira ta da shi. Suka cigaba da tattaunawa akan tsare-tsaren bikin,TAIMIYYAH
ta miƙawa Zee wayar suka gaisa da Laurat, sannan ta amshi wayar su kai sallama da juna baki
ɗaya.
Ta aje wayar tana duban Zee ta ce, "Zee don Allah da gaske gyarannan ya amshe ni? Shi ma
Maleek kullum mu kai waya sai ya yi magana ,ya ce duk ya ƙosa ya zo jibi ya ga yadda na koma a
zahiri,ni har kunya na ke ji idan ya fara sakin layinsa wallahi."
Zee ta saki dariya ta ce, "Wallahi da gaske ne nima baki ji ina shigowa sai da na tanka ba,ni ban
san yadda za ki koma ba idan me gyaran jikin da za ta yi ta fara aikinta ita kuma,don wallahi sai
kin kusa sanya Angon na ki ya zautu."
Zee ta yi maganar tana sakin dariyar tsokana,TAIMIYYAH ta kwaɓe fuska cike da shagwaɓa ta
ce, "Don Allah Zee ki daina tsokanata ni fa tsoro na ke ji wallahi,kin san Ummie haka ta dinga
tsoratani jiya tana cewa ,wai wannan Angon ba da wasa ya zo ba,irin su ne wata 9 matar ta haihu
in dai da rabo kusa,ni banma gane me take nufi ba,kawai dai na ji gabana sai da ya faɗi a lokacin."
Zee me zata yi inba dariya ba,ta dinga sheƙa abinta TAIMIYYAH na ji tamkar ta saki ihu don
takaici,cikin dariyar Zee ke faɗin, "Allah sarki Ummie! Wallahi gaskiya ta faɗi don ni kaina yadda
ya ke nuna rawar ƙafa na san akwai shan drama a gaba,zan so ganin idon wata irin washegarin
ranar da ake cewa Ango ya shiga ɗaki ne ko me ne?"
Zee ta ƙare maganar tana sake bushewa da dariya,TAIMIYYAH ta sake ƙulewa daf ta ke da sakin
kuka ta ce , "Zee yaushe ke ma ki ka zama ƴar iska irin Yasmeen ne? Wallahi ni dai babu ruwana
ita Ummie ba nan maganarta ya dosa ba fa,kuma bashi ku ke ci zan rama ne soon ni ma."
Zee ta sake kwashewa da dariya kafin ta yi magana kira ya shigo wayar TAIMIYYAH,ganin
Maleek ne yasa TAIMIYYAH sake narke face lokacin da take receiving call ɗin, ta kai wayar
kunni sabida ba vid call bane.
Sun ɗauki kamar mintuna goma kafin su kammala yin wayar, TAIMIYYAH sai faman zuba masa
shagwaɓa ta ke yi,ita dai Zee sake baki kawai ta yi tana kallon yadda ake buga luv a waya.
"Malama kallon fa?" TAIMIYYAH ta tambayi Zee lokacin da ta ke aje wayarta daga gefenta,Zee
ta saki murshi tana cewa "Ƙalau matar Maleek Ado,kawai ina course ɗin yadda zan koyi irin
wannan shagwaɓar ce, ko nima na dinga yiwa Sahibi irin shi."
TAIMIYYAH ta saki murmushi tana hararan Zee ta ce , "Sanya idanu dai bai yi ba wallahi." Daga
haka Zee ta miƙe don tafiya gida TAIMIYYAH ta raka ta har bakin gate sannan su kai sallama da
juna,lokacin da ta juyo don komawa zuwa cikin gida ne,ta hango fitowar Nass da Basmah jere da
juna. Ta yi saurin yin gaba a bin ta tana faman taɓe baki,don tuni lamarin su Basmah ya daina bata
mamaki don abin na su kullum gaba yake yi ba baya ba,mussamman yadda a yanzu suke tashen
jin tamkar su soketa ita da Iyah, tunda suka ji labarin irin mijin da za ta aura.
___________
*Kusfa Zaria,City.*
Hoton fuskar A.Maleek Ado da kuma na TAIMIYYAH ne, ya bayyana a madubin sihirin da ke
gaban Boko Kallah. Ya ɗaga jajayen idanunsa masu girma da firgitarwa ya sauke su akan Umma
da ƙawarta Hajiya Barirah,wacce ita ce ta yi wa Umman hanyar zuwa wajen Bokan. Ya saki wani
gigitaccen dariya ya ce, "Ba waɗannan su ne mutanen da kike son a tarwatse maganar aurensu,
wanda za a ɗaura nan da kwanaki goma masu zuwa ba?"
Umma ta yi saurin gyaɗa kai tamkar ƙadangaruwa,jikinta ko'ina rawa ya ke yi sabida yadda take
kallon hotunansu TAIMIYYAH, a jikin madubin tsafin tamkar almara. Bakinta har rawa ya ke yi
wajen furta cewa, "Eh Boka su ne,don Allah a hana faruwar auren idan ya so koma waye a nemo a
bata a ranar, amma wannan attajirin bana son a ɗaura da shi."
Boka ya sake sheƙewa da wani dariyar,wanda kafatanin ɗakin da suke zaune a ciki sai da ya
amsa,ya koma ya tsuke fuskarsa tare da zazzarowa Umma ido ya ce, "Duk duniya ban hango wani
Boka ko Hatsabibin malamin duban da zai iya hana faruwar wannan auren ba,kamar yadda
wancan malamin na ki ya sanar da ke sati biyu da suka wuce,to ni ma xan maimaita miki wannan
cewa wannan auren haɗin Allah ne,kuma akwai rabo me ƙarfi a tsakani wanda babu Mahalukin da
ya isa ya hana afkuwar hakan,akwai tarin ɗaukaka da buɗi a cikin auren,duk wanda ya ce zai cika
matsawa akan hana faruwar hakan, to tabbas rabo zai iya zama ajalinsa,don haka ki kawo wata
buƙatar a biya miki amma banda wanda ki ka zo dominsa."
Boka ya ƙare maganar yana sake zazzarowa Umma ido kamar zai cinye ta. Umma da dukkanin
jikinta ya ɗauki rawar tashin hankalin rashin madafa,sai ta dubi Boka cikin rawar murya ta ce,
"Yanzu Boka ina ji ina gani gurguwar,musaka za ta taka wani matsayin da ƴaƴan cikina ba su taka
ba a rayuwa? Don girman Allah da shaharanka a Bokanci ka taimaka ka tarwatsa lamarin
aurennnan ,ya ji ya tsaneta ba zai iya aurenta ba,na yi alqawarin salwantar da duk abinda na
mallaka matuƙar buƙata ta za ta biya."
"Ko da a ce za ki salwantar da ranki akan hana aukuwar wannan rubutaccen auren,to ina tabbatar
miki da cewa sai an ɗaura shi babu makawa,daƙiƙiya me kan kifi kawai."
Boka ya yi maganar a tsawace lokacin da Umma ta sake maimaita buƙatarta,ya cigaba da cewa,
"Kina da sauran ƙalubalen da ya kamata a ce a kansa kika zo nan ba maganar waɗannan mutanen
da duk iya ƙarfin tsafinmu ba za mu iya da su ba,don a jiyar Allah ne su wanda ya haɗa zukatansu,
don ya gwadawa maƙiya irin ku ƙarfin iko da buwayarsa. Ko kina da labarin cewa mijinki zai auri
wata bazawara kuma akwai zazzafar rabo a tsakaninsu?"
Umma ta gwalo idanu tare da dafe ƙirji,cikin kiɗima da mummunan tashin hankali ta ce,
"What...?!! Boka ka san me kake faɗi kuwa,aure fa ka ce Sani zai ƙara to da wata shegiyar?"
Boka Kallah ya sake daka mata tsawar da ya girgiza ƴan hanjinta kafin ya ce, "Ko ma wace ce
bata bayyana min a wannan madubin tsafin ba,don da alamu makaranta masu tsananin ƙarfi
ne,amma ki je ki zuba ido tabbas mijinki zai sake aure nan kusa bada jimawa ba,kuma akwai
zazzafar rabo a tsakaninsu ,wanda shine silar mutuwar mijin matar, duk lokacin da maganar ya
taso ki dawo nan ki sanar dani,maza ku tashi ku ɓace daga nan asararrun duniya."
Boka ya kai ƙarshen maganar cike da tsawa me tsanani,hakan yasa Umma da ƙawarta Hajiya
Barirah tashi a zabure suka nufi ƙofar fita,Hajiya Barirah na faɗin, "A tashi lafiya me gani har
Hanji."
Boka ya tintsere da dariya yana rakasu da wata mummunar ashar cike da ƙaraji,hakan yasa Umma
yin gaɓa tamkar zata ci tuntuɓe sabida firgita.
A cikin Napep ɗin da suka ɗauki drop don komawa da su gida ne Hajiya Barirah ta dubi
Umma,wacce ke faman share hawayen tashin hankali ta ce, "Hajiya Zuwairah ya zuwa yanzu ya ci
a ce kin sallama akan lamarin wannan gurguwar Yarinyar,wacce kika ɗaurawa karan tsana. So da
yawa a wasu lissafe-lissafenmu mu kan lissafa har da abubuwa masu girman da ba za mu iya
cinma wani buri akan su ba. Ki sa a ranki kin lissafa raba auren da babu mahalukin da zai duba
lissafinki ya baki maki dai-dai, don haka ki aje batunsu ki fuskanci sabuwar ƙalubalen da ke shirin
fuskanto ki,ki godewa Allah su ma su Zuhurah duka ba ƙananun gidaje za a kai su ba,don haka ki
sanyawa zuciyarki salama ki cire lissafin wannan gurgurwan cikin littafin tsara-tsarenki."
Umma ta ɗago mitsi-mitsin idanunta da suka rine zuwa ja, ta ɗaurasu akan fuskar Hajiya Barirah.
Ta sake share hawaye tana cewa, Hajiya Barirah ba za ki gane yadda na tsani Yarinyar da Iyah
bane a cikin zuciyata,amma a yanzu tabbas dole na ginjine duk wasu lissafina akan su, in fuskanci
sanin wata shegiyarce ta ke shirin kutso kanta cikin rayuwata da mijina,wanda na daɗe da lissafa
cewa mijina ne ni kaɗai,kuma don ni kaɗai aka haliccesa.Tabbas idan hakan ya faru akwai babbar
yaƙin da zai tashi garin Zaria baki ɗaya,don ba zan taɓa iya zuba ido in ga Sani da kowace irin
mace ba in ba ni ba."
Umma ta ƙare maganar cike da jin wani matsanancin zafi a cikin zuciyarta, har suka iso gida sam
bata cikin nutsuwarta, ji ta ke yi tamkar ta ari hauka ta nanawa kanta, ko za ta samu salama.
Lokacin da suka shigo cikin Compound ɗin gidan,idanunsu ne ya sauka akan danƙareriyar motar
Maleek Ado, wanda ke fake a cikin Compound ɗin gidan. Driver ɗinsa Yusuf na kame daga
mazaunin me tuƙi, yana kora ruwan lemun Chivita a maƙoshinsa. Umma da Hajiya suka sake kai
dubansu ga hanyar Part ɗin su Iyah, dai dai lokacin da ragowar hasken yammacin ya hasko musu
fuskar TAIMIYYAH da Maleek Ado,waɗanda su ke jerowa jere da juna lokacin da suka fito daga
sashin Ummie.
Umma da Hajiya Barirah duka babu wacce zuciyarta ba ta yi wani irin dokawa a ƙirjinta ba.
Lokacin da suka sauke ganinsu akan fuskar TAIMIYYAH,wacce fuskarta ke haskawa da wani irin
tarin annuri da kyawun da ta ƙara yi,sakamakon ingantaccen gyaran jikin da ta fara amsa.
Umma ta yi saurin yin gaba tana ji wani irin duhu na lulluɓe idanunta da zuciyarta baki ɗaya.
Hajiya Barirah ta rufa mata baya ita ma zuciyarta na yaba, haɗuwar wannan matashin attijirin da
ya yi tsaye a zuciyar ƙawarta.
TAIMIYYAH wacce akan idanunta su Umma suka shige zuwa sasan su,sai ta ɗauke kai daga
duban sashin ta mayar kan fuskar Maleek,wanda ya ke tsaye yana ƙare mata kallo. Ta shagwaɓe
masa fuska tare da narke murya ta na cewa, "Yah Maleek wannan kallon ya yi yawa fa."
Ya ƙare maganar yana sake miskile fuskarsa, zuciyarsa na sake cika da matsanancin kishi akan
TAIMIYYAH. TAIMIYYAH ta saki ƙaramin murmushi tana duban bakinsa, wanda ba za ka taɓa
cewa daga nan dukkanin kalaman da ya furta suka fito ba,ta buɗe baki cike da shagwaɓar da ke
narkar da zuciyar Maleek Ado ta ce, "An gama Yah Maleek ."
Maleek ya zabga mata harara zuciyarsa na sake narkewa da ƙaunarta me tsanani, ya buɗe baki ya
ce, "Wife ban san meyasa baki jin maganata akan daina kira na da wannan sunan kareren ba,amma
kar ki damu soon zan bambamce miki cewa ni ba Yayanki bane."
TAIMIYYAH sai ta sake narke masa murya ta ce, "Zan koma ciki Yah Maleek su Yasmeen na
jirana, sai mun yi waya bye...!"
Daga haka ta juya za ta koma zuwa Sasan Iyah,Maleek ya yi saurin dakatar da ita ta hanyar kiran
sunanta, 'Zaynabb' Hakan yasa TAIMIYYAH dakatawa daga tafiyar da fara tana dafe da guiwar
ƙafarta. Maleek ya yi taku uku ya cimmata yana yin ƙasa da muryarsa yadda koni me ɗakko muku
rahoto, ban ji me ya ce ba, ya furtawa TAIMIYYAH wasu ƴan kalmomi, da suka sanyata saurin
rufe fuskarta da Hijab ɗin dake sanye a jikinta. Wani irin feeling ta ke ji na zagaye jinin jikinta,
yana sake narke zuciyarta da dilmiyata a ƙaunar Maleek ɗin me tsanani. Ta buɗe face ɗin tana ƙin
juyowa ta kallesa kamar yadda yaci buri,ta sake shagwaɓe murya tana cewa, "Ni dai babu ruwana
Yah Maleek Bye! Ka gaida min da Hajjah." Daga haka ta fara takawa ta nufi hanyar komawa
Sasan Iyah,Maleek ya bi bayanta da ido yana ƙarewa yanayin tafiyarta da ke bashi tausayi
kallo.Zuciyarsa na sake jin feeling me tsanani akanta,har sai da ta ɓacewa ganinsa ya juya zuwa
wajen motarsa.
Yusuf ya iso da sauri ya buɗe masa back seat ya shiga ya zauna,yana ji tamkar zai bar wani ɓari na
farin cikin rayuwarsa ne daga cikin gidan......✍🏻
#Ɗansabo ce#
[12/14, 3:43 PM] +234 703 040 9541: Littafin TAIMIYYAH paid book ne,ga duk wanda ta
tsincesa a kowani irin group ne,kiji tsoran Allah karki karanta sai kin biya 500 naira only.
Za ku iya min magana ta wannan number ɗin 08167768704, ko kuma ku turo kuɗin ku kai tsaye ta
wannan account ɗin 0504192664 aisha ibrahim dansabo GTbank.*
Masu turo credit za ku turo katin MTN na 500 ta wannan line ɗin 08167768704.
_Ina ƴan kasuwa masu buƙatar a tallata muku hajar ku? Maza ku garzayo da kuɗi ƙalilan a tallata
muku kayan siyarwanku sai dai kawai ku ji ana kiran waya don buƙatan sayan kayan ku,ku
tuntuɓeni ta layina kamar haka 08167768704._
*65*
Umma na isa cikin falonta ta zube a cikin kujera tana faman sauke numfashi,zuciyarta na mata
wani irin suya da ƙona. Su Zuhurah da Basmah da ke zaune suna magana akan tsarin bikinsu suka
ɗaga kai a tare suka dubi Umma suna haɗa baki wajen faɗin, "Umma har kun dawo,lafiya duk ki
ka fita hayyacinki haka?"
Umma ta ɗago ido ta dubi su Zuhurah ta ce, "Zuhurah ina cikin tashin hankali da firgici,ji na ke yi
tamkar zan yi hauka wallahi, wannan hatsabibin Bokan da muka dawo daga wajensa wallahi ya fi
Maharazu shaiɗanci, don ya sanar da ni abinda ya fi gaban auren waccar gurguwar tashin
hankali,don aure ya ce babu fashi sai an ɗaura shi don haka yanzu babu su cikin lissafina,maganar
auren Ubanku yanzu shi ne babbar tashin hankalina."
Umma ta kai ƙarshen maganan tana ji tamkar numfashinta zai sarƙe,Hajiya Barirah da ta ƙariso
cikin falon ne ta dubi Umma ta ce, "Hajiya Zuwairah wannan tashin hankalin duk ba shi ne mafita
ba,sha'ani ne a gabanki nan da ƴan kwanaki za ki fara tara mutane,yakamata a ce kin sanya
nutsuwa cikin lamuranki don kaucewa surutun mutane. Ki nutsu a kammala wannan hidiman kafin
ki kwantar da kai ki binciko wace ce ke shirin kutso kai cikin rayuwarku ke da mijinki."
Su Zuhurah gaba ɗaya sai kan su ya kulle da maganganun su Umma, Zuhurah ta dubi Hajiya
Barirah cike da tarin son ƙarin bayani daga bakin Hajiyan ta ce, "Anty kun samu a duhu wane ne
zai yi auren? Kuma meyasa ba za a iya fasa bikin TAIMIYYAH ba,wallahi Anty ina cikin baƙin
ciki tun daga sanda na san waye za ta aura hankalina ya tashi,bamu sake sarewa da lamarin ba sai
da aka kawo lefenta,wanda hakan yasa babu shiri muka soke kawo namu lefen don kunya kawai
za mu sha,sabida gaba ɗaya babu wanda zai dubi lefenmu da gashi,don duk wata dukiya an gama
zube ta ana waccar shegiyar gurguwar,don Allah Anty a san duk yadda za a yi a fasa bikin ta rasa
shi kowa ya huta."
Zuhurah ta yi maganar idanunta akan Hajiya Barirah,wacce ta ke ta faman murmushi kafin ta dubi
Zuhurah ta ce, "Zuhurah wannan auren ƙaddararren aure ne da babu mahalukin da da zai iya hana
a ɗaura shi,don haka ku yi haƙury ku yi fatan idan ta shiga kada ta samu zaman lafiya da abokiyar
zaman,amma aure kaman an yi an gama in ji Kallah,yanzu abinda za ku fuskanta ya fi gaban
wannan matsalar na ita gurguwar,don Ubanku aka ce zai ƙara aure nan ba da jimawa ba,kuma a
cikin auren na shi akwai zazzafan rabo da zai gitta wanda hakan shi ne silar mutuwar mijin matar
da zai aura ɗin,babbar tashin hankalin shine ba a bayyanawa Boka wace ce matar ba,kun ga kenan
Ummanku na cikin matsala da ku kanku,don ba ku san wata jarabar za a kwaso a kawo muku ba."
Basmah ta danna wata uwar ashar lokacin da Hajiya Barirah ta kai ƙarshen maganarta,kafin ta
maida dubanta kan Umma ta ce, "Umma yanzu sabida Allah da gaske Baba sai ya iya miki
kishiya? Lallai ko wace ce sai ta ci ubanta idan ta shigo gidannan kuwa,don Allah ki kwantar da
hankalinki a gama wannan bikin, mu samu nutsuwa a ɗakin mazajenmu daga baya sai mu maida
hankali wajen gano wace ce wacce zai aura ɗin,ita kuma TAIMIYYAH In sha Allah ba za ta taɓa
samun kwanciyar hankali a gidan aurenta ba,ba dai arziƙi su ke mawa ba to ga ta ga guy
ɗinnan,don wallahi yafi ƙarfin ajin ta kawai Iyah ce da uwarsa suka haɗa abun kamar yadda na ji
labari."
Umma ta dubi Basmah ta ce, "Basmah in ji ubanwa ya ce miki auren haɗi ne? Kin ko ga yadda ya
ke kallonta kamar zai cinyeta,yanzu fa muka wuto su a waje ta yo masa rakiya,kun ga haɗuwar
mutumin kuwa? Motar da ya zo a cikinta kanta abin hankali ya tashi ne idan ku ka ga haɗuwa da
girmanta, don ina ga kuɗinta zai iya siye duka motocin da mazajenku ke hawa,wallahi ina cikin
baƙin ciki da wannnan ƙaddararren auren na TAIMIYYAH,yanzu ne na ke jin tsanarta har cikin
ƙashi da ɓargona domin ban taɓa tunanin musaka kamarta za ta iya taka matsayin auren attajiri irin
wannan mutumin ba,babban tashin hankalina shi ne ta haihu da shi don ance bai taɓa haihuwa
ba,kun ko ga idan ta haihu shikenan sun fara mamaye dukiyarsa don akanta zai talike,ina cikin
tsaka me wuya Hajiya Barirah,na rasa da wanne zan ji? Auren ubansu da Boka ya ce zai tabbata
ko kuwa baƙin cikin auren wannan Yariyar dana tsana tun tana tsumman goyo?"
Umma ta ƙare maganar da jefawa Hajiya Barirah tambayar idanunta na tara ƙwallan baƙin ciki,
zuciyarta na mata wani irin nauyi tamkar an ɗauki bulo an ɗaura mata a ƙirji.
Hajiya Barirah ta dubi Umma cike da jin tausayinta ta ce, "Hajiya Barirah haƙury kawai za ki yi
amma tunda Boka ya furta miki hakan,to ki sawa ranki hakan ne don bai taɓa faɗin abinda ba zai
tabbata ba. Yanxu dai mu kammala da hidiman da ke gabanmu,sannan kada ki sake ki nunawa
Sani cewa kin ji wani magana akan zancen zai ƙara aure,ki zuba masa ido har a ƙare bukukuwan
nan da ke gabanmu. Na tabbatar ko ma wace ce za ta bayyana mana cikin sauƙi idan har ki ka iya
riƙe kanki,ki ka kuma iya danne duk wani kishi da baƙin cikin da ke ta so miki. Sabida rayuwa
duka da kike ganinta iya siyasa ce da kissa na zaman duniya,wanda suka iya suke da riba wanda
basu iya ba kuma sai mu yi ta bulayi muna walagigi ba tare da mun gano bakin zaren ba,don haka
ki adana duk wasu lassafinki akan Sani da waccar gurguwar. Ki fuskanci auren ƴaƴanki da yadda
za ki ɗaurasu akan hanyar da za su mallaki mazajen na su a tafukan hannayensu,wannan shi ne
kawai mafita ba nuna damuwa da baƙin cikinki a fili ba."
Hajiya Barirah ta ƙare maganar idanunta akan Umma, Umma ta dubi Hajiya Barirah ta ce, "Hajiya
Barirah tashi mu je daga ciki mu tattauna da kyau,don gabaki ɗaya kaina a kulle yake bana gane
komi."
Daga haka suka rankaya zuwa ɗakin baccin Umma,su Zuhurah na biye da bayansu da ido,kafin
Basmah ta saki wani mahaucin tsaki,tana jin zafin maganar ƙarin auren Baba Sani da Boka ya faɗi
na taɓa zuciyarta. Ita ko Zuhurah gaba ɗaya baƙin cikin irin mijin da TAIMIYYAH za ta aura , shi
ne abinda yafi damunta da ɗaga hankalinta fiye da komi,sabida tunda wani course mate ɗinta ya yi
mata bayani akan waye Maleek Ado, da irin tarin arziƙin da ya mallaka da muƙakamin da ya ke
riƙe da shi a yanzu,shikenan ta ji duk duniya ta ji babu wanda ya dace da Maleek ɗin irinta. Ta
ɗaga ido ta dubi Basmah ta ce, "Basmah yanzu muna ji muna gani wannan gurguwar za ta shiga
gidan daulan da ya zarce tunaninmu? Wai anya ko Bokayen nan ba wasa da hankalin su Umma
suke yi ba kawai,amma ta ya za a ce ba za a iya hana wannan auren ba?"
Basmah ta ja tsaki tana duban cikin idon Zuhurah ta ce, "Zuhurah don Allah mu aje maganar
TAIMIYYAH a gefe,don ni ji na ke yi kamar zuciyata za ta kama da wuta,aikin gama ya gama
tunda dukkanin Bokayen bakinsu ya zo ɗaya,sun ce aure dole sai an yi babu fashi,kuma an riga an
kawo lefen da ya tabbatar mana da cewa da gaske ta riga ta yi mana zarrah,baki ji yadda Yasmeen
ke koɗa irin tsaruwan gidan da za a kaita a GRA bane? Zuhurah bamu da abin yi yanzu da ya
wuce mu rungumi na mu mazajen ,tunda su ma ba baya bane suna da kuɗinsu daidai su. Ita kuma
kishiya kaɗai ta ishe ta, don ba za ta haɗa kanta da dakariyar matarsa ba don Ubanta. Ba dai
kwaɗayi ba to mu zuba musu ido shi ma guy ɗin kyawunta ne ya ruɗesa kawai,da zaran ya kwanta
da ita shikenan ya gama da ita,don haka ki aje batunta a gefe mu cigaba da shirya yadda za mu
ƙawata yinin mu kawai,kinsan Anty Laurat zuwa nan da 4 days za ta iso,so nake kafin ta iso mun
gama da komi don na san wajen waccar gurguwar za ta tare."
Basmah ta sake jan tsaki suka cigaba da tattaunawa akan auren nasu,da kuma shirin yadda za su
fuskanci bikin wanda ya rage saura kwanaki goma kacal masu zuwa.
____________
Yasmeen ta yi maganar idanunta akan TAIMIYYAH,wacce ta shigo cikin ɗakin tana me zare
Hijab ɗin jikinta. Ta ɗaga manyan idanunta ta sauke akan Yasmeen kafin ta ce, "Wallahi ya wuce
Yasmeen,wai sauri ya ke yi zai ga wani mutum a can gidan Hajjah, a she tare suka iso da matarsa
wai tana gidan Hajjah ɗin. Ni fa wallahi haka kawai na ke jin tsoron haɗuwar mu da ita,don ban
san da wani ido za ta kalle ni ba? Ya sha faɗa min akwai ta da tsananin kishi akansa,ni kuma gashi
gurguwace na san za ta tsaneni sosai domin a matsayinsu da irin ratar arziƙin da ke
tsakaninmu,gani za ta yi tamkar zubewar aji ne a haɗa ta kishi da gurguwa kamata. Wallahi
Yasmeen duk sai in ji jikina ya yi sanyi idan ina tuna hakan,Allah ya sa dai ba gida ɗaya za mu
rayu tare ba da bansan yadda zan yi da fargaba ba."
TAIMIYYAH ta kai ƙarshen maganar cikin sanyin murya da raunin xuciya,hakan yasa Yasmeen
dubanta da fuskar tausayi ta ce, "Ki kwantar da hankalinki TAIMIYYAH babu komi,babu abinda
zai kasance tunda ba tare za ku zauna ba,sannan wannan raina kan naki da ki ke yi bana ƙaunarsa
ko kaɗan,don haka kada ki sake ki nunawa kishiya kasawarki ko gazawarki akan mijinku. Sabida
kawai kina da wata lalura da Ubangiji ne yaso ganinki a hakan,idan ta gane rauninki ta nan
ɓangaren xa ta yaƙe ki ta dinga miki gori. So kada ma ki sake ki dinga nuna cewa nakasanki na
damunki tunda dai mijinki na ƙaunarki a hakan, yana kuma ɗokinki da son kasancewa da ke miye
matsalarki da kishiya? Ki cire ta aranki ki fuskanci abinda zai ɗaga darajarki a zuciyar Maleek ne.
Sannan ki tabbatar masa da cewa nasaka ba kasawa ba ce, wajen bashi dukkanin soyayyah da
kulawar da zai dinga mantar da shi cewa ke ɗin me lalurace. Kada ki bari wannan son da yake
miki ya tafi a banza, ba tare da ke ma kin yi hoɓɓasa wajen mantar da shi kowa a zuciyarsa idan
kuna tare da juna ba."
Yasmeen ta ƙare maganar tana kashewa TAIMIYYAH idanu,hakan yasa TAIMIYYAH sakin
murmushi ta ce, "Yasmeen baki da dama fa,ni idan kina waɗannan kalaman kunya ki ke bani ba
kaɗan ba. Amma fa gaskiya Maleek yana son a nuna masa so a zahiri,shi irin mazan nan ne masu
daraja soyayya da son a nuna musu ko agaban waye.Wallahi idan yana wasu maganganun yanzu
har ji na ke yi kamar na narke sabida kunya,amma shi ko a jikinsa zaro kalamansa ya ke yi kai
tsaye ba tare da jin wata kunya ba."
TAIMIYYAH ta yi maganar cike da zallar shagwaɓa,zuciyarta na sake hasaso mata wasu tarin
kalamai masu nauyi da Maleek ɗin ke faɗi idan suna vid call. Yasmeen ta saki murmushi me faɗi
tana cewa, "Hmm! Ai akwai show wallahi a gaba,don ni har na ƙosa in ga yadda zai maida ke
wata tantiriya a fagen iya luv,dama ke ma ɗin munafuka ce irin ku ba ƙaramin iya nunawa miji luv
ku ka iya ba. Don wannan shagwaɓar kaɗai ta isa ma ta dinga narkar da shi, bare kuma ki buɗe
shafukan litattafan da kika adana don gwada masa madarar ƙauna a zahiri,don na san duk wannan
shagwaɓar ta munafurci ce, waya sani ma ko duk kin ƙosa a ɗaura ki fara bashi pepe."
Yadda Yasmeen ta kai ƙarshen maganar cike da tsokana da shaƙiyanci ne yasa TAIMIYYAH sake
shagwaɓe fuska,kafin ta buɗe baki cike da shagwaɓa ta ce, "Allah ya isa da wannan sharrin da ki
ke Yasmeen. Wallahi ni babu ruwana ban tanadi wasu littafan da zan buɗe shafukansu akan ko
wani namiji ba,ko kin manta ni ɗin ustaziyaciyace ku ma alarammiya,wacce bata san komi ba sai
karatunta,don haka ni ki daina min sharri in ba haka ba zan sanar masa kina min sharri."
Yasmeen ta kwashe da dariya tana duban TAIMIYYAH cikin ido ta ce, "Allahu Akbar! Ustaza
Alarammiya Zainab Maleek Ado,dama ai Ustazai kun fi kowa iya tsula tsiya. Kina san masa kira'a
ne kina narkar da shi a duniyar da bai taɓa tunanin zai je ba. Za dai mu yi kallo idan an ɗaura,
kafin zuwa nan da wata tara mu dawo ɗaukar ɗan Alarammiya TAIMIYYAH da Sheikh Maleek
Ado ko?"
Yasmeen ta jefawa TAIMIYYAH tambayar cike da tsokana,hakan yasa TAIMIYYAH yin dariyar
da bata shirya ba ta ce, "Kin fi ƙarfina Yasmeen,sai dai in miki fatan shiriya wallahi."
Suka saki dariya a tare daidai kuma lokacin Iyah ta shigo ɗakin, tana sauke manyan idanunta akan
TAIMIYYAH ta ce, "Zainabu idon ki kenan? Ba cewa na yi yana tafiya idan kin shigo ki sameni a
ɗaki ba,shine ki ka zo nan kuna ta dararraku da wannan lukutar Yarinyar ko?"
TAIMIYYAH ta dubi Iyah tana shagwaɓe fuska ta ce, "Iyah yanzu fa na shigo ban wani jima ba."
Iyah ta taɓe baki ta ce, "To na ji maza mu je ki shanye ki bani kofi na. Yarinya ana miki gata kina
botsara ki shiga hankalinki da ni wallahi kin ji na gaya miki,kuma Hajjah ta bugo waya ta ce me
gyaran da za ta turo,za ta fara zuwa ne ana saura kwana bakwai biki,so na ke yi kafin ta zo kin
gama shanye magungunan sanyin nan dana haɗa miki,da kuma tsumin da Hajiya Rabi ta aiko,mu
je ki sha yanzu a kan idona."
Iyah ta ƙare maganar tana yin gaba TAIMIYYAH na biye da bayanta,Yasmeen ta raka su da ido
tana dariyar yadda TAIMIYYAH ke ta faman zunɓure baki.
____________
Ana saura kwana bakwai biki aka tafi Bauchi yin jeren Zuhurah. A kuma ranar ne me gyaran jikin
da Hajjah ta ɗakko takanas daga Maidugury ta iso don cigaba da gyare Amarya
TAIMIYYAH,wacce ta sake wani irin fresh da kyau na ban mamaki,sabida gyaran da ta amsa daga
wajen Iyah da aminiyarta Hajiya Rabi.
A ɓangaren Ummie aka sauke Yakurah mai gyaran jikin, mace me fara'a da sanin darajar mutane.
Sosai ta fara aikinta na gyare TAIMIYYAH ciki da wajenta,kamar yadda Hajjah ta buƙata,ta kuma
biya uban kuɗi domin kwalliya ta biya kuɗin sabulu.
Babu irin gulma da surutun da su Umma ba su yi ba,lokacin da suka ji cewa wai uwar Angon ce
da kanta ta turo mai gyaran. Yasmeen da Anty Laurat tare da su Maryam Sunusi, sune kan gaba
akan komi na shirye-shiryen yadda yini da Bridal shower ɗin da suka shirya zai kasance. Ba
ƙaramin kuɗi suke fatali da shi wajen gudanar da shirye-shiryensu ba, wanda zuwa lokacin da ya
rage one week sun kammala komi tsaf!
Ranar Wednesday ne Anty Mardiyyah da wasu daga cikin dangin Mamar TAIMIYYAH suka iso
Zaria. Sun samu kyakykyawar tarba daga Iyah,aka sauke su a sasan Ummie wacce ta kammala
duk wani shirinta na ganin ta tarbi baƙi yadda ya kamata.
A kuma ranar ne aka gudanar da Bridal shower ɗin TAIMIYYAH, wanda aka gudanar bayan isha'i
. Sun cakare sun cake Amarya kuma ta sha kyau na ban mamaki,sabida duk yadda ta zamewa abin
ta kuma nuna bata so ko kwalliya ai mata hakan bai samu ba,don ƙwararriyar me kwalliyace tayi
mata make-up ɗin. TAIMIYYAH ta yi kyau fiye da yadda alƙalamina zai misaltawa me karatu,duk
in da ta gitta sai an kashe mata ruwan flash,su Yasmeen ƙirazan biki su ma sun sha kyau har sun
gaji. Sun yi bidirin su iya son ransu ita dai Amarya na daga gefe a kame a zaune waje ɗaya inda
aka ƙawata da decoration. Su Zuhurah su Kamu suka yi a can wajen Event Centre da suka
kama,wanda rabin Ƴan rimi da dangin Umma ne suka halarta,sai dangin Nass da yake shi ɗan
Zaria ne duk yayyinsa mata da qawayen Hajiya Hajara duk sun halarci wajen.
Ƙarfe goma na dare su Yasmeen suka watse daga shagalin Bridal shower ɗin.
Hotuna ne suka fara bazuwa a kafofin sadarwa na su Instagram da su Twitter zuwa manhajar
Whatsapp,duk su Yasmeen su kai ta ɗaura hotunansu da na Amarya TAIMIYYAH.
Ranar Thursday aka tafi yin jeran ɗakin TAIMIYYAH dana Basmah,in da mutane suka rabu biyu
wasu suka tafi na TAIMIYYAH a can GRA ,wasu kuma suka tafi Gonar Ganye na Basmah tunda
anan Nass ya tamfatsa gininsa daidai ƙarfin arziƙinsa.
Lokacin da aka dawo daga yin jeran ne surutai suka fara tashi , aka dinga koɗa haɗuwar gidan
TAIMIYYAH ana jinjina irin daular da za a kai ta ciki ranan Asabar. Nan fa hankalinsu Umma ya
sake tashi da jin irin dukiyar da aka narka a gidan TAIMIYYAH,don an tabbatar musu da cewa
babu abinda ba a zuba a gidan ba. Ɗakuna biyu kacal aka bari wanda aka jera kayan da Baba Sani
ya yi musu ita da su Basmah, duk wanda ya kalli Umma da su Zuhurah sai ya gane halin da
xukatansu ke ciki, na tsananin damuwa da hassada da ke cin zukatansu.
Ita TAIMIYYAH da mutanen arziƙinta ba su san ma ana yi ba,don harkokin gabansu kawai suke
yi na arziƙi. Iyah duk wanda ya kalleta a ƴan kwanakin nan ya san tana cikin wani irin farin ciki
da ba zai misaltu ba. Kamar yadda shi ma Ya sadeeq da ya iso tun Wednesday ke cikin farin cikin
taya TAIMIYYAH murnar aurenta da za a ɗaura ranar Asabar ɗin,duk da cewa yana jin kishi me
tsanani a ƙasan ransa,amma hakan bai hana shi jin farin ciki da irin mijin da TAIMIYYAH ta samu
ba.
Daga can ɓangaren Hajjah ma gidanta ya fara sauke baki, ƴan uwanta na kusa ne suka iso daga
Katsina, don taya ta murnan ƙarin auren da tilon ɗan ta Maleek Ado zai yi. Daga ɓangaren can
babban gidansu Maleek Ado kuwa komawa gefe suka yi suna gulma da tsegumin cewa Amaryar
ma ashe gurguwace. Ita dai Hajjah ko a jikinta daga ita har uban gayyar murna kawai suke yi da
ɗokin jiran ranar da za a shafa Fatiha,TAIMIYYAH ta zama mallakin Maleek ɗin halak malak.
Daga ɓangaren uwargida Suhailah kuwa tana cikin wani matsanancin hali na kishi,da zallar baƙin
ciki da taraddadin ranan da ke sake kusantowa, wanda za a sake mallakawa mijinta wata mace a
matsayin mata bayan ita. Maganganun Jawahir da irin huɗubobin da ta yi mata kafin isowansu
Zaria kawai take bita a cikin ranta. Gefe guda kuma jakarta na ɗauke da wani sirri da Jawahir ɗin
ta damƙa mata,wanda za ta aiwatar da ƙudirinsu da zaran an ɗaura auren Maleek ɗin da
TAIMIYYAH. Hakan yasa tunda ta iso ta ke kaf-kaf da babbar jakar hannunta,ko kaɗan bata son
yin nesa da shi a kusa da ita. Kullum zuciyarta sake shiga tashin hankali da ruɗu ta ke yi,
musamman da kwanaki suka rage saura 3 days Maleek ɗinta ya zama mallakin wata macen.
Macen ma gurguwa wacce ta ke ganin ƙarshen ƙasƙanci ne a wajenta, a ce Maleek ɗinta ya auro
mata kishiya musaka,gurguwa alhali ya aje mace lafiyayya kamarta,wacce bata rasa komi ba sai
haihuwa kaɗai da ta rasa. Wanda a yanzu ta ke jin zafin rashinsa tamkar ta ari hauka,don ta gama
sallamawa cewa rashin haihuwar shi ne silar ƙarin auren Maleek ɗin. Ba wai ƙaddaransa bace
kamar yadda su Hajjah ke mata daɗin baki,shiyasa ta fita a sabgar kowa tare da ɗaukar fishi me
tsanani da Hajjah, da ma duk wani me goyan bayan auren Maleek ɗinta da gurguwar matarsa. Jira
kawai ta ke yi ranar Asabar ta yi a ɗaura auren,ita kuma ta aiwatar da aikin da Jawahir ta
bata,wanda ta salwantar da kuɗi masu nauyi kafin saƙon ya iso gare ta. (To ko wani irin saƙo ne
wannan Suhailah ta taho da shi? Sai mu zuba ido don ganin me zai faru a ranar).
____________
Ranar Asabar sha shida ga watan Satumban dubu biyu da ashirin da biyu, (16th September
2022),da misalin ƙarfe sha ɗaya da rabi na safe (11:30am). Aka shaida ɗaurin auren ƴan matan
guda uku,
Zainab TAIMIYYAH da Angonta Maleek Ibrahim Ado,sai Basmah da Angonta Naseer Aliyu
Ƙwarbai, sai Amarya Zuhurah da Angonta Ameeru Muhammad Bauchi. An ɗaura Aurarrakin ne a
can Family House ɗin su TAIMIYYAH da ke Rimi. A kan sadaki mabambamta in da dubban nin
mutane ne suka halarci ɗaurin auren. Kama daga kan ƴan siyasa zuwa mayan gwamnati da masu
faɗa ajin Nigeria,duk sun halarci ɗaurin auren. Rabin manya da attajiran sun halarci wajen ne
sabida Maleek Ado,wanda kallo ɗaya za ka masa kasan cewa yana cikin farin ciki mara
misaltuwa. Wannan miskilalliyar fuskar tasa na haskawa da wani annuri da fara'ar da mutane kan
jima ba su ga irin ta akan fuskarsa ba........✍🏻
YADDA AKE BUƊE ACCOUNT A AREWABOOKS*
Bayan kaje play store ka ɗakko ya sauka a kan wayarka. Za'a cike Form ɗin kamar haka: -
*Continue with Google* - Idan kana da gmail/email akan wayarka kawai Continue with Google
za'a taɓa zata buɗe maka account a ArewaBooks kaitsaye.
Masu iPhone
#Ɗansabo ce#
[12/14, 3:43 PM] +234 703 040 9541: Littafin TAIMIYYAH paid book ne,ga duk wanda ta
tsincesa a kowani irin group ne,kiji tsoran Allah karki karanta sai kin biya 500 naira only.
Za ku iya min magana ta wannan number ɗin 08167768704, ko kuma ku turo kuɗin ku kai tsaye ta
wannan account ɗin 0504192664 aisha ibrahim dansabo GTbank.*
Masu turo credit za ku turo katin MTN na 500 ta wannan line ɗin 08167768704.
_Ina ƴan kasuwa masu buƙatar a tallata muku hajar ku? Maza ku garzayo da kuɗi ƙalilan a tallata
muku kayan siyarwanku sai dai kawai ku ji ana kiran waya don buƙatan sayan kayan ku,ku
tuntuɓeni ta layina kamar haka 08167768704._
*65*
Umma na isa cikin falonta ta zube a cikin kujera tana faman sauke numfashi,zuciyarta na mata
wani irin suya da ƙona. Su Zuhurah da Basmah da ke zaune suna magana akan tsarin bikinsu suka
ɗaga kai a tare suka dubi Umma suna haɗa baki wajen faɗin, "Umma har kun dawo,lafiya duk ki
ka fita hayyacinki haka?"
Umma ta ɗago ido ta dubi su Zuhurah ta ce, "Zuhurah ina cikin tashin hankali da firgici,ji na ke yi
tamkar zan yi hauka wallahi, wannan hatsabibin Bokan da muka dawo daga wajensa wallahi ya fi
Maharazu shaiɗanci, don ya sanar da ni abinda ya fi gaban auren waccar gurguwar tashin
hankali,don aure ya ce babu fashi sai an ɗaura shi don haka yanzu babu su cikin lissafina,maganar
auren Ubanku yanzu shi ne babbar tashin hankalina."
Umma ta kai ƙarshen maganan tana ji tamkar numfashinta zai sarƙe,Hajiya Barirah da ta ƙariso
cikin falon ne ta dubi Umma ta ce, "Hajiya Zuwairah wannan tashin hankalin duk ba shi ne mafita
ba,sha'ani ne a gabanki nan da ƴan kwanaki za ki fara tara mutane,yakamata a ce kin sanya
nutsuwa cikin lamuranki don kaucewa surutun mutane. Ki nutsu a kammala wannan hidiman kafin
ki kwantar da kai ki binciko wace ce ke shirin kutso kai cikin rayuwarku ke da mijinki."
Su Zuhurah gaba ɗaya sai kan su ya kulle da maganganun su Umma, Zuhurah ta dubi Hajiya
Barirah cike da tarin son ƙarin bayani daga bakin Hajiyan ta ce, "Anty kun samu a duhu wane ne
zai yi auren? Kuma meyasa ba za a iya fasa bikin TAIMIYYAH ba,wallahi Anty ina cikin baƙin
ciki tun daga sanda na san waye za ta aura hankalina ya tashi,bamu sake sarewa da lamarin ba sai
da aka kawo lefenta,wanda hakan yasa babu shiri muka soke kawo namu lefen don kunya kawai
za mu sha,sabida gaba ɗaya babu wanda zai dubi lefenmu da gashi,don duk wata dukiya an gama
zube ta ana waccar shegiyar gurguwar,don Allah Anty a san duk yadda za a yi a fasa bikin ta rasa
shi kowa ya huta."
Zuhurah ta yi maganar idanunta akan Hajiya Barirah,wacce ta ke ta faman murmushi kafin ta dubi
Zuhurah ta ce, "Zuhurah wannan auren ƙaddararren aure ne da babu mahalukin da da zai iya hana
a ɗaura shi,don haka ku yi haƙury ku yi fatan idan ta shiga kada ta samu zaman lafiya da abokiyar
zaman,amma aure kaman an yi an gama in ji Kallah,yanzu abinda za ku fuskanta ya fi gaban
wannan matsalar na ita gurguwar,don Ubanku aka ce zai ƙara aure nan ba da jimawa ba,kuma a
cikin auren na shi akwai zazzafan rabo da zai gitta wanda hakan shi ne silar mutuwar mijin matar
da zai aura ɗin,babbar tashin hankalin shine ba a bayyanawa Boka wace ce matar ba,kun ga kenan
Ummanku na cikin matsala da ku kanku,don ba ku san wata jarabar za a kwaso a kawo muku ba."
Basmah ta danna wata uwar ashar lokacin da Hajiya Barirah ta kai ƙarshen maganarta,kafin ta
maida dubanta kan Umma ta ce, "Umma yanzu sabida Allah da gaske Baba sai ya iya miki
kishiya? Lallai ko wace ce sai ta ci ubanta idan ta shigo gidannan kuwa,don Allah ki kwantar da
hankalinki a gama wannan bikin, mu samu nutsuwa a ɗakin mazajenmu daga baya sai mu maida
hankali wajen gano wace ce wacce zai aura ɗin,ita kuma TAIMIYYAH In sha Allah ba za ta taɓa
samun kwanciyar hankali a gidan aurenta ba,ba dai arziƙi su ke mawa ba to ga ta ga guy
ɗinnan,don wallahi yafi ƙarfin ajin ta kawai Iyah ce da uwarsa suka haɗa abun kamar yadda na ji
labari."
Umma ta dubi Basmah ta ce, "Basmah in ji ubanwa ya ce miki auren haɗi ne? Kin ko ga yadda ya
ke kallonta kamar zai cinyeta,yanzu fa muka wuto su a waje ta yo masa rakiya,kun ga haɗuwar
mutumin kuwa? Motar da ya zo a cikinta kanta abin hankali ya tashi ne idan ku ka ga haɗuwa da
girmanta, don ina ga kuɗinta zai iya siye duka motocin da mazajenku ke hawa,wallahi ina cikin
baƙin ciki da wannnan ƙaddararren auren na TAIMIYYAH,yanzu ne na ke jin tsanarta har cikin
ƙashi da ɓargona domin ban taɓa tunanin musaka kamarta za ta iya taka matsayin auren attajiri irin
wannan mutumin ba,babban tashin hankalina shi ne ta haihu da shi don ance bai taɓa haihuwa
ba,kun ko ga idan ta haihu shikenan sun fara mamaye dukiyarsa don akanta zai talike,ina cikin
tsaka me wuya Hajiya Barirah,na rasa da wanne zan ji? Auren ubansu da Boka ya ce zai tabbata
ko kuwa baƙin cikin auren wannan Yariyar dana tsana tun tana tsumman goyo?"
Umma ta ƙare maganar da jefawa Hajiya Barirah tambayar idanunta na tara ƙwallan baƙin ciki,
zuciyarta na mata wani irin nauyi tamkar an ɗauki bulo an ɗaura mata a ƙirji.
Hajiya Barirah ta dubi Umma cike da jin tausayinta ta ce, "Hajiya Barirah haƙury kawai za ki yi
amma tunda Boka ya furta miki hakan,to ki sawa ranki hakan ne don bai taɓa faɗin abinda ba zai
tabbata ba. Yanxu dai mu kammala da hidiman da ke gabanmu,sannan kada ki sake ki nunawa
Sani cewa kin ji wani magana akan zancen zai ƙara aure,ki zuba masa ido har a ƙare bukukuwan
nan da ke gabanmu. Na tabbatar ko ma wace ce za ta bayyana mana cikin sauƙi idan har ki ka iya
riƙe kanki,ki ka kuma iya danne duk wani kishi da baƙin cikin da ke ta so miki. Sabida rayuwa
duka da kike ganinta iya siyasa ce da kissa na zaman duniya,wanda suka iya suke da riba wanda
basu iya ba kuma sai mu yi ta bulayi muna walagigi ba tare da mun gano bakin zaren ba,don haka
ki adana duk wasu lassafinki akan Sani da waccar gurguwar. Ki fuskanci auren ƴaƴanki da yadda
za ki ɗaurasu akan hanyar da za su mallaki mazajen na su a tafukan hannayensu,wannan shi ne
kawai mafita ba nuna damuwa da baƙin cikinki a fili ba."
Hajiya Barirah ta ƙare maganar idanunta akan Umma, Umma ta dubi Hajiya Barirah ta ce, "Hajiya
Barirah tashi mu je daga ciki mu tattauna da kyau,don gabaki ɗaya kaina a kulle yake bana gane
komi."
Daga haka suka rankaya zuwa ɗakin baccin Umma,su Zuhurah na biye da bayansu da ido,kafin
Basmah ta saki wani mahaucin tsaki,tana jin zafin maganar ƙarin auren Baba Sani da Boka ya faɗi
na taɓa zuciyarta. Ita ko Zuhurah gaba ɗaya baƙin cikin irin mijin da TAIMIYYAH za ta aura , shi
ne abinda yafi damunta da ɗaga hankalinta fiye da komi,sabida tunda wani course mate ɗinta ya yi
mata bayani akan waye Maleek Ado, da irin tarin arziƙin da ya mallaka da muƙakamin da ya ke
riƙe da shi a yanzu,shikenan ta ji duk duniya ta ji babu wanda ya dace da Maleek ɗin irinta. Ta
ɗaga ido ta dubi Basmah ta ce, "Basmah yanzu muna ji muna gani wannan gurguwar za ta shiga
gidan daulan da ya zarce tunaninmu? Wai anya ko Bokayen nan ba wasa da hankalin su Umma
suke yi ba kawai,amma ta ya za a ce ba za a iya hana wannan auren ba?"
Basmah ta ja tsaki tana duban cikin idon Zuhurah ta ce, "Zuhurah don Allah mu aje maganar
TAIMIYYAH a gefe,don ni ji na ke yi kamar zuciyata za ta kama da wuta,aikin gama ya gama
tunda dukkanin Bokayen bakinsu ya zo ɗaya,sun ce aure dole sai an yi babu fashi,kuma an riga an
kawo lefen da ya tabbatar mana da cewa da gaske ta riga ta yi mana zarrah,baki ji yadda Yasmeen
ke koɗa irin tsaruwan gidan da za a kaita a GRA bane? Zuhurah bamu da abin yi yanzu da ya
wuce mu rungumi na mu mazajen ,tunda su ma ba baya bane suna da kuɗinsu daidai su. Ita kuma
kishiya kaɗai ta ishe ta, don ba za ta haɗa kanta da dakariyar matarsa ba don Ubanta. Ba dai
kwaɗayi ba to mu zuba musu ido shi ma guy ɗin kyawunta ne ya ruɗesa kawai,da zaran ya kwanta
da ita shikenan ya gama da ita,don haka ki aje batunta a gefe mu cigaba da shirya yadda za mu
ƙawata yinin mu kawai,kinsan Anty Laurat zuwa nan da 4 days za ta iso,so nake kafin ta iso mun
gama da komi don na san wajen waccar gurguwar za ta tare."
Basmah ta sake jan tsaki suka cigaba da tattaunawa akan auren nasu,da kuma shirin yadda za su
fuskanci bikin wanda ya rage saura kwanaki goma kacal masu zuwa.
____________
Yasmeen ta yi maganar idanunta akan TAIMIYYAH,wacce ta shigo cikin ɗakin tana me zare
Hijab ɗin jikinta. Ta ɗaga manyan idanunta ta sauke akan Yasmeen kafin ta ce, "Wallahi ya wuce
Yasmeen,wai sauri ya ke yi zai ga wani mutum a can gidan Hajjah, a she tare suka iso da matarsa
wai tana gidan Hajjah ɗin. Ni fa wallahi haka kawai na ke jin tsoron haɗuwar mu da ita,don ban
san da wani ido za ta kalle ni ba? Ya sha faɗa min akwai ta da tsananin kishi akansa,ni kuma gashi
gurguwace na san za ta tsaneni sosai domin a matsayinsu da irin ratar arziƙin da ke
tsakaninmu,gani za ta yi tamkar zubewar aji ne a haɗa ta kishi da gurguwa kamata. Wallahi
Yasmeen duk sai in ji jikina ya yi sanyi idan ina tuna hakan,Allah ya sa dai ba gida ɗaya za mu
rayu tare ba da bansan yadda zan yi da fargaba ba."
TAIMIYYAH ta kai ƙarshen maganar cikin sanyin murya da raunin xuciya,hakan yasa Yasmeen
dubanta da fuskar tausayi ta ce, "Ki kwantar da hankalinki TAIMIYYAH babu komi,babu abinda
zai kasance tunda ba tare za ku zauna ba,sannan wannan raina kan naki da ki ke yi bana ƙaunarsa
ko kaɗan,don haka kada ki sake ki nunawa kishiya kasawarki ko gazawarki akan mijinku. Sabida
kawai kina da wata lalura da Ubangiji ne yaso ganinki a hakan,idan ta gane rauninki ta nan
ɓangaren xa ta yaƙe ki ta dinga miki gori. So kada ma ki sake ki dinga nuna cewa nakasanki na
damunki tunda dai mijinki na ƙaunarki a hakan, yana kuma ɗokinki da son kasancewa da ke miye
matsalarki da kishiya? Ki cire ta aranki ki fuskanci abinda zai ɗaga darajarki a zuciyar Maleek ne.
Sannan ki tabbatar masa da cewa nasaka ba kasawa ba ce, wajen bashi dukkanin soyayyah da
kulawar da zai dinga mantar da shi cewa ke ɗin me lalurace. Kada ki bari wannan son da yake
miki ya tafi a banza, ba tare da ke ma kin yi hoɓɓasa wajen mantar da shi kowa a zuciyarsa idan
kuna tare da juna ba."
Yasmeen ta ƙare maganar tana kashewa TAIMIYYAH idanu,hakan yasa TAIMIYYAH sakin
murmushi ta ce, "Yasmeen baki da dama fa,ni idan kina waɗannan kalaman kunya ki ke bani ba
kaɗan ba. Amma fa gaskiya Maleek yana son a nuna masa so a zahiri,shi irin mazan nan ne masu
daraja soyayya da son a nuna musu ko agaban waye.Wallahi idan yana wasu maganganun yanzu
har ji na ke yi kamar na narke sabida kunya,amma shi ko a jikinsa zaro kalamansa ya ke yi kai
tsaye ba tare da jin wata kunya ba."
TAIMIYYAH ta yi maganar cike da zallar shagwaɓa,zuciyarta na sake hasaso mata wasu tarin
kalamai masu nauyi da Maleek ɗin ke faɗi idan suna vid call. Yasmeen ta saki murmushi me faɗi
tana cewa, "Hmm! Ai akwai show wallahi a gaba,don ni har na ƙosa in ga yadda zai maida ke
wata tantiriya a fagen iya luv,dama ke ma ɗin munafuka ce irin ku ba ƙaramin iya nunawa miji luv
ku ka iya ba. Don wannan shagwaɓar kaɗai ta isa ma ta dinga narkar da shi, bare kuma ki buɗe
shafukan litattafan da kika adana don gwada masa madarar ƙauna a zahiri,don na san duk wannan
shagwaɓar ta munafurci ce, waya sani ma ko duk kin ƙosa a ɗaura ki fara bashi pepe."
Yadda Yasmeen ta kai ƙarshen maganar cike da tsokana da shaƙiyanci ne yasa TAIMIYYAH sake
shagwaɓe fuska,kafin ta buɗe baki cike da shagwaɓa ta ce, "Allah ya isa da wannan sharrin da ki
ke Yasmeen. Wallahi ni babu ruwana ban tanadi wasu littafan da zan buɗe shafukansu akan ko
wani namiji ba,ko kin manta ni ɗin ustaziyaciyace ku ma alarammiya,wacce bata san komi ba sai
karatunta,don haka ni ki daina min sharri in ba haka ba zan sanar masa kina min sharri."
Yasmeen ta kwashe da dariya tana duban TAIMIYYAH cikin ido ta ce, "Allahu Akbar! Ustaza
Alarammiya Zainab Maleek Ado,dama ai Ustazai kun fi kowa iya tsula tsiya. Kina san masa kira'a
ne kina narkar da shi a duniyar da bai taɓa tunanin zai je ba. Za dai mu yi kallo idan an ɗaura,
kafin zuwa nan da wata tara mu dawo ɗaukar ɗan Alarammiya TAIMIYYAH da Sheikh Maleek
Ado ko?"
Yasmeen ta jefawa TAIMIYYAH tambayar cike da tsokana,hakan yasa TAIMIYYAH yin dariyar
da bata shirya ba ta ce, "Kin fi ƙarfina Yasmeen,sai dai in miki fatan shiriya wallahi."
Suka saki dariya a tare daidai kuma lokacin Iyah ta shigo ɗakin, tana sauke manyan idanunta akan
TAIMIYYAH ta ce, "Zainabu idon ki kenan? Ba cewa na yi yana tafiya idan kin shigo ki sameni a
ɗaki ba,shine ki ka zo nan kuna ta dararraku da wannan lukutar Yarinyar ko?"
TAIMIYYAH ta dubi Iyah tana shagwaɓe fuska ta ce, "Iyah yanzu fa na shigo ban wani jima ba."
Iyah ta taɓe baki ta ce, "To na ji maza mu je ki shanye ki bani kofi na. Yarinya ana miki gata kina
botsara ki shiga hankalinki da ni wallahi kin ji na gaya miki,kuma Hajjah ta bugo waya ta ce me
gyaran da za ta turo,za ta fara zuwa ne ana saura kwana bakwai biki,so na ke yi kafin ta zo kin
gama shanye magungunan sanyin nan dana haɗa miki,da kuma tsumin da Hajiya Rabi ta aiko,mu
je ki sha yanzu a kan idona."
Iyah ta ƙare maganar tana yin gaba TAIMIYYAH na biye da bayanta,Yasmeen ta raka su da ido
tana dariyar yadda TAIMIYYAH ke ta faman zunɓure baki.
____________
Ana saura kwana bakwai biki aka tafi Bauchi yin jeren Zuhurah. A kuma ranar ne me gyaran jikin
da Hajjah ta ɗakko takanas daga Maidugury ta iso don cigaba da gyare Amarya
TAIMIYYAH,wacce ta sake wani irin fresh da kyau na ban mamaki,sabida gyaran da ta amsa daga
wajen Iyah da aminiyarta Hajiya Rabi.
A ɓangaren Ummie aka sauke Yakurah mai gyaran jikin, mace me fara'a da sanin darajar mutane.
Sosai ta fara aikinta na gyare TAIMIYYAH ciki da wajenta,kamar yadda Hajjah ta buƙata,ta kuma
biya uban kuɗi domin kwalliya ta biya kuɗin sabulu.
Babu irin gulma da surutun da su Umma ba su yi ba,lokacin da suka ji cewa wai uwar Angon ce
da kanta ta turo mai gyaran. Yasmeen da Anty Laurat tare da su Maryam Sunusi, sune kan gaba
akan komi na shirye-shiryen yadda yini da Bridal shower ɗin da suka shirya zai kasance. Ba
ƙaramin kuɗi suke fatali da shi wajen gudanar da shirye-shiryensu ba, wanda zuwa lokacin da ya
rage one week sun kammala komi tsaf!
Ranar Wednesday ne Anty Mardiyyah da wasu daga cikin dangin Mamar TAIMIYYAH suka iso
Zaria. Sun samu kyakykyawar tarba daga Iyah,aka sauke su a sasan Ummie wacce ta kammala
duk wani shirinta na ganin ta tarbi baƙi yadda ya kamata.
A kuma ranar ne aka gudanar da Bridal shower ɗin TAIMIYYAH, wanda aka gudanar bayan isha'i
. Sun cakare sun cake Amarya kuma ta sha kyau na ban mamaki,sabida duk yadda ta zamewa abin
ta kuma nuna bata so ko kwalliya ai mata hakan bai samu ba,don ƙwararriyar me kwalliyace tayi
mata make-up ɗin. TAIMIYYAH ta yi kyau fiye da yadda alƙalamina zai misaltawa me karatu,duk
in da ta gitta sai an kashe mata ruwan flash,su Yasmeen ƙirazan biki su ma sun sha kyau har sun
gaji. Sun yi bidirin su iya son ransu ita dai Amarya na daga gefe a kame a zaune waje ɗaya inda
aka ƙawata da decoration. Su Zuhurah su Kamu suka yi a can wajen Event Centre da suka
kama,wanda rabin Ƴan rimi da dangin Umma ne suka halarta,sai dangin Nass da yake shi ɗan
Zaria ne duk yayyinsa mata da qawayen Hajiya Hajara duk sun halarci wajen.
Ƙarfe goma na dare su Yasmeen suka watse daga shagalin Bridal shower ɗin.
Hotuna ne suka fara bazuwa a kafofin sadarwa na su Instagram da su Twitter zuwa manhajar
Whatsapp,duk su Yasmeen su kai ta ɗaura hotunansu da na Amarya TAIMIYYAH.
Ranar Thursday aka tafi yin jeran ɗakin TAIMIYYAH dana Basmah,in da mutane suka rabu biyu
wasu suka tafi na TAIMIYYAH a can GRA ,wasu kuma suka tafi Gonar Ganye na Basmah tunda
anan Nass ya tamfatsa gininsa daidai ƙarfin arziƙinsa.
Lokacin da aka dawo daga yin jeran ne surutai suka fara tashi , aka dinga koɗa haɗuwar gidan
TAIMIYYAH ana jinjina irin daular da za a kai ta ciki ranan Asabar. Nan fa hankalinsu Umma ya
sake tashi da jin irin dukiyar da aka narka a gidan TAIMIYYAH,don an tabbatar musu da cewa
babu abinda ba a zuba a gidan ba. Ɗakuna biyu kacal aka bari wanda aka jera kayan da Baba Sani
ya yi musu ita da su Basmah, duk wanda ya kalli Umma da su Zuhurah sai ya gane halin da
xukatansu ke ciki, na tsananin damuwa da hassada da ke cin zukatansu.
Ita TAIMIYYAH da mutanen arziƙinta ba su san ma ana yi ba,don harkokin gabansu kawai suke
yi na arziƙi. Iyah duk wanda ya kalleta a ƴan kwanakin nan ya san tana cikin wani irin farin ciki
da ba zai misaltu ba. Kamar yadda shi ma Ya sadeeq da ya iso tun Wednesday ke cikin farin cikin
taya TAIMIYYAH murnar aurenta da za a ɗaura ranar Asabar ɗin,duk da cewa yana jin kishi me
tsanani a ƙasan ransa,amma hakan bai hana shi jin farin ciki da irin mijin da TAIMIYYAH ta samu
ba.
Daga can ɓangaren Hajjah ma gidanta ya fara sauke baki, ƴan uwanta na kusa ne suka iso daga
Katsina, don taya ta murnan ƙarin auren da tilon ɗan ta Maleek Ado zai yi. Daga ɓangaren can
babban gidansu Maleek Ado kuwa komawa gefe suka yi suna gulma da tsegumin cewa Amaryar
ma ashe gurguwace. Ita dai Hajjah ko a jikinta daga ita har uban gayyar murna kawai suke yi da
ɗokin jiran ranar da za a shafa Fatiha,TAIMIYYAH ta zama mallakin Maleek ɗin halak malak.
Daga ɓangaren uwargida Suhailah kuwa tana cikin wani matsanancin hali na kishi,da zallar baƙin
ciki da taraddadin ranan da ke sake kusantowa, wanda za a sake mallakawa mijinta wata mace a
matsayin mata bayan ita. Maganganun Jawahir da irin huɗubobin da ta yi mata kafin isowansu
Zaria kawai take bita a cikin ranta. Gefe guda kuma jakarta na ɗauke da wani sirri da Jawahir ɗin
ta damƙa mata,wanda za ta aiwatar da ƙudirinsu da zaran an ɗaura auren Maleek ɗin da
TAIMIYYAH. Hakan yasa tunda ta iso ta ke kaf-kaf da babbar jakar hannunta,ko kaɗan bata son
yin nesa da shi a kusa da ita. Kullum zuciyarta sake shiga tashin hankali da ruɗu ta ke yi,
musamman da kwanaki suka rage saura 3 days Maleek ɗinta ya zama mallakin wata macen.
Macen ma gurguwa wacce ta ke ganin ƙarshen ƙasƙanci ne a wajenta, a ce Maleek ɗinta ya auro
mata kishiya musaka,gurguwa alhali ya aje mace lafiyayya kamarta,wacce bata rasa komi ba sai
haihuwa kaɗai da ta rasa. Wanda a yanzu ta ke jin zafin rashinsa tamkar ta ari hauka,don ta gama
sallamawa cewa rashin haihuwar shi ne silar ƙarin auren Maleek ɗin. Ba wai ƙaddaransa bace
kamar yadda su Hajjah ke mata daɗin baki,shiyasa ta fita a sabgar kowa tare da ɗaukar fishi me
tsanani da Hajjah, da ma duk wani me goyan bayan auren Maleek ɗinta da gurguwar matarsa. Jira
kawai ta ke yi ranar Asabar ta yi a ɗaura auren,ita kuma ta aiwatar da aikin da Jawahir ta
bata,wanda ta salwantar da kuɗi masu nauyi kafin saƙon ya iso gare ta. (To ko wani irin saƙo ne
wannan Suhailah ta taho da shi? Sai mu zuba ido don ganin me zai faru a ranar).
____________
Ranar Asabar sha shida ga watan Satumban dubu biyu da ashirin da biyu, (16th September
2022),da misalin ƙarfe sha ɗaya da rabi na safe (11:30am). Aka shaida ɗaurin auren ƴan matan
guda uku,
Zainab TAIMIYYAH da Angonta Maleek Ibrahim Ado,sai Basmah da Angonta Naseer Aliyu
Ƙwarbai, sai Amarya Zuhurah da Angonta Ameeru Muhammad Bauchi. An ɗaura Aurarrakin ne a
can Family House ɗin su TAIMIYYAH da ke Rimi. A kan sadaki mabambamta in da dubban nin
mutane ne suka halarci ɗaurin auren. Kama daga kan ƴan siyasa zuwa mayan gwamnati da masu
faɗa ajin Nigeria,duk sun halarci ɗaurin auren. Rabin manya da attajiran sun halarci wajen ne
sabida Maleek Ado,wanda kallo ɗaya za ka masa kasan cewa yana cikin farin ciki mara
misaltuwa. Wannan miskilalliyar fuskar tasa na haskawa da wani annuri da fara'ar da mutane kan
jima ba su ga irin ta akan fuskarsa ba........✍🏻
Bayan kaje play store ka ɗakko ya sauka a kan wayarka. Za'a cike Form ɗin kamar haka: -
*Continue with Google* - Idan kana da gmail/email akan wayarka kawai Continue with Google
za'a taɓa zata buɗe maka account a ArewaBooks kaitsaye.
Masu iPhone
#Ɗansabo ce#
[12/14, 3:43 PM] +234 703 040 9541: Littafin TAIMIYYAH paid book ne,ga duk wanda ta
tsincesa a kowani irin group ne,kiji tsoran Allah karki karanta sai kin biya 500 naira only.
Za ku iya min magana ta wannan number ɗin 08167768704, ko kuma ku turo kuɗin ku kai tsaye ta
wannan account ɗin 0504192664 aisha ibrahim dansabo GTbank.*
Masu turo credit za ku turo katin MTN na 500 ta wannan line ɗin 08167768704.
_Ina ƴan kasuwa masu buƙatar a tallata muku hajar ku? Maza ku garzayo da kuɗi ƙalilan a tallata
muku kayan siyarwanku sai dai kawai ku ji ana kiran waya don buƙatan sayan kayan ku,ku
tuntuɓeni ta layina kamar haka 08167768704._
*66*
*Gyallesu.*
Daga can uwar ɗakin na ummie ne aka saki guɗar 'Ayyiriyirii...!!!' sai na cigaba da ratsa tsirarun
mutanen da suke cikin falon, na isa zuwa cikin ɗakin baccin Ummien in da ƴan matan huɗu ke
zaune daga bakin gado.
Amarya TAIMIYYAH na zaune akan stool me yi mata kwalliya ta ƙare ana yi mata ɗauri, an
lanƙwasa karin ɗankwali na ƙarshe tare da kalmashe shi daga can ƙarshen ƙeyar kan
TAIMIYYAH, Yasmeen ta sake dagewa ta saki wata guɗar 'Ayyiriyiriii...!!!' Zee ta saki dariya ta
ce "Kai Yasmeen wannan uban guɗa da ki ke saki haka ai sai ki toshe kunnuwar Amaryar ta mu."
TAIMIYYAH wacce me kwalliya ta matsa daga gabanta fuskarta ya bayyana a sarari, su Zee suka
saki baki suna kallon yadda ta koma wata Princess. Tana sanye ne cikin wani rantsatstsen farin
lace,wanda akai wa ado da golden ɗin zare a jikinsa,ɗinkin straight gown akai mata irin na Amare.
Aka kuma yi sa a The Cicada ce ta ɗinka rigar da kanta,shiyasa ɗinkin ya zauna ajikin
TAIMIYYAH tamkar a jikin nata aka halicci rigar.Fuskarta da ya sha make-up irin na Amare
wanda sam ba a cika ba,kuma ƙwararriyace ta yi sa shiyasa fuskar ke haskawa da wani irin sirrin
kyau mara misaltuwa. Ɗan ƙaramin bakinta da ya sha jan baki kalar da ya dace da kwalliyar kan
fuskarta,ya sake ya tsukewa ya zama so cute. Manyan idanunta ya fi komi birgewa sabida yadda
suke wani irin haskawa da shining ɗin baƙin eye liner, da akai lining ɗinsu da shi.Ta yi kyau har
fiye da yadda zan iya misaltawa me karatu,kamar yadda rigar jikin nata ya fiddo duk wani shape
da Ubangiji ya yi mata baiwarsa. Ƙirjinta da ya sha gyara ya sake cika tamkar an hura Baloon ya
tsaya cak abin sha'awa. Jikinta baki ɗaya na tashin daddaɗan ƙamshinta, da ya gama kama ko'ina a
jikinta na tashi.
Dukkanin ƴan matan Amaryan sai kabbara suke yi,lokacin da idanunsu ya sauka akan Amarya
TAIMIYYAH. Sabida yadda suka ga tayi musu mugun kyau,har suna kasa ɗauke idanunsu daga
ƙare mata kallo,Maryam Sunusi ta buɗe baki ta ce, "Fatabarakallahu ahsanulkhaliqin! Allah kai ne
abin kambamawa da ka ƙagi wannan kyakykyawar halitta. Allah ka albarkace ta tare da aurenta,ka
bata zama lafiya da nutsuwa a cikin gidan aurenta. Ya Ubangiji ka kunyata maƙiyanta ka bata
zuriya masu albarka,Congratulation my best friend ever, may urs be among the best In sha Allah
TAIMIYYAH."
Su Yasmeen dukansu suka haɗa baki wajen amsa addu'ar da Maryam tayi da cewa, "Ameen ya
Hayyu ya Qayyum."
TAIMIYYAH ta ɗaga manyan idanunta ta sauke akan Maryam Sunusi,cike da jin daɗin
kyakykyawar addu'ar da Maryam ɗin ta yi mata ta ce, "Ameen Maryama na gode,ku ma Allah ya
yi muku zaɓi mafi alkhairy nan kurkusa."
Suka sake amsawa da faɗin, "Ameen." Yasmeen ta matso kusa da TAIMIYYAH ta sake sakin
ƙaramin guɗa tana cewa, "Finally yau kin xama Mrs.Maleek Ado."
TAIMIYYAH ta saki ƙayataccen murmushi,sai dai kafin ta yi magana wayarta da ke hannun Anty
Laurat,wacce ke faman kashe mata hotuna ya ɗauki ringing. Ta ta so da sauri tana miƙawa
TAIMIYYAH wayar ta ce, "Mrs.Maleek ungo Angon ne da kansa ke kira."
TAIMIYYAH ta amsa wayar zuciyarta na bugawa da wani irin yanayi da ba za ta iya fassarawa
ba. Ta yi receving call ɗin tare da kai wayar bisa kunni,murya can ƙasa ta yi masa sallama. Maleek
Ado daga ɓangarensa ya amsa sallamar sannan ya ce, "Mrs.Maleek Ado!"
TAIMIYYAH ta lumshe idanunta tana jin wani irin abu na malting a cikin zuciyarta,yadda ya furta
kalmar ba ƙaramin tasiri ya yi a zuciyarta ba.Ta buɗe idanunta ta sauke akan su Yasmeen da ke
faman hiransu babu tsagaitawa,sai ta miƙe a hankali ta dafe guiwar ƙafarta ta fara takawa don
barin musu ɗakin. Suka bi ta da ido rii...! Kowacce murmushi na blushing a samar fuskarta,ita ko
TAIMIYYAH direct ɗaya bedroom ɗin Ummie ta nufa,in da ta ke zaton ba za ta ga kowa ba don
bama kasafai ta ke buɗe ɗakin ba.
Kamar yadda ta zatan kuwa haka ya kasance babu kowa cikin ɗakin,amma a gyare ya ke sai tashin
qamshin daddaɗan turaran wuta ke tashi. TAIMIYYAH ta samu bakin gado ta zauna,tana sake
dafe wayar akan kunninta ta ce, "Hello!" Maleek da ya yi shiru yana sauraren takun tafiyarta tun
fitowarta daga ɗakin da suke,ya saki ƙaramin numfashi ya ce, "Wife ina jin ki,kin gudu ma
qawayen na ki ne sabida ke ma kina son ganin fuskar Angon ki ko?"
Bai jiran amsar da TAIMIYYAH za ta bashi ba ya yi cuting call ɗin,ya kirata vid call don dama a
ƙagauce ya ke da ya ga kyakykyawar fuskarta. Ya fara kiran voice call ne sabida sanin cewa dole
tana cikin mutane,amma yanzu tunda ta kaucewa mutanen dole ya kira vid call don baiwa
zuciyarsa abinda ta ke so.
TAIMIYYAH ta kalli kanta kafin ta ɗaga vid call ɗin,cike da jin kunyan yadda karon farko Maleek
ɗin zai fara ɗaura idanunsa akanta babu lulluɓi. Sai ta samu kanta da kasa duban fuskarsa lokacin
da ta tabbatar nata fuskar, zuwa gangar jikinta ya gama bayyana a allon screen ɗin wayarsa.
Cikin muryar shagwaɓa ta ce, "Ina yini ya taro,Allah ya tabbatar mana da alkhairy ya bamu zama
lafiya."
Maleek da idanunsa ke kan TAIMIYYAH ya kasa ɗaukewa,ya buɗe baki cikin muryar da ta fi
waccar yin sanyi ya ce, "Ameen wife, i luv u so very much don Allah ki riƙeni da amana babe!"
Jikin TAIMIYYAH sai ya yi wani irin sanyi da jin kalaman Maleek Ado,ta sake ɗaura manyan
idanunta akan fuskarsa,tana kallon yadda ya ƙurawa waje ɗaya a jikinta ido. Wani haɗaɗɗan kunya
ya taso ya lulluɓe zuciyarta,cikin sauri ta furta, "Yah Maleek don Allah minti biyu zan ɗan ɗakko
mayafi."
Wani kallo Maleek Ado ya watso mata ta cikin wayar,kafin ya buɗe baki kaman me son yin raɗa
ya ce, "No wife! Kar ki fara kashe min waya,yau ba zancen sanya mayafi kin zama mallakina
halak malak! Please kar ki ce za ki haramta min kallon halas ɗina."
Ya ƙare maganar yana sake gyara kwanciyar da ya yi a jikin seat ɗin lafiyayyiyar
motarsa.TAIMIYYAH da kunya ke ɗawainiya da ita sai ta sake narke murya ta ce, "To mu yi voice
call please Yah Maleek,wallahi kunyanka na ke ji."
Maleek Ado ya saki wani ƙayataccen murshi kafin ya ce, "No wife! Ki bani 20 minutes gani nan
tafe zuwa gidanku,idan na iso zan kiraki ki fito ki sameni a mota,but u make sure idan za ki fito
kin rufe min wannan kwalliyar da Hijab,and bana son ɗaukar wasu hotuna ana yawo da ke a
media,shiyasa ni ma bazan shigo ba bare a yi wasu hotuna da aka maida ɗaukarsu fashion,please
tell ur friends su taimakeni kar su ba za ki a duniya ana kallemin sirrikana please!"
Yadda Maleek ya kai ƙarshen maganar cike da nuna magiya da zallar kishin da ke cin zuciyarsa,
yasa TAIMIYYAH dubansa tana sake jin kunyarsa me tsanani na lulluɓeta.Cikin shagwaɓaɓɓiyar
muryarta da ke sake kunna wutar fitina a zuciyar Maleek ta ce, "Zan gaya musu Yah Maleek sai ka
iso ɗin." Daga haka ta yi saurin cuting call ɗin tana sauke numfashi,zuciyarta na sake cika da
ƙaunarsa me tsanani.
Ɗakin da su Yasmeen suke TAIMIYYAH ta koma,suka ko rufar mata da tsiyar cewa ta gudu sun
sha luv da oga Maleek kenan. TAIMIYYAH ta narke musu da shagwaɓa tana kare kanta,ana cikin
haka wata Cousine ɗinsu ƴar Rimi ta shigo ɗakin. Ta dubi TAIMIYYAH tana yaba kyawun da tayi
ta ce, "Ma sha Allah! Amarya kin sha kyau ki zo Iyah na nemanki yanzu."
TAIMIYYAH ta dubi Nusaiba ta ce, "Okey jira ni mu fita tare don ni kunyar shiga jama'a na ke
yi,ina fata dai zuwa yanzu duk mazan da suka dawo ɗaura aure sun watse?"
Nusaiba ta saki murmushi ta ce, "Kai Yah TAIMIYYAH kin cika kunya wallahi,sun watse kam
babu wasu maza a wajen tunda Baba Sani ba zama a gidan zai yi ba,ya tafi can hotel da mutanensa
don su bar mata su sake a cikin gida."
TAIMIYYAH ta jinjina kai cike da gamsuwa sannan ta dubi Yasmeen ta ce, "Sis zo mu je daga can
za ki rakani wani waje."
Yasmeen ta miƙe tana gyara zaman ɗaurinta na ashobin da suka cakare a cikinsa,atamfar kuma ta
yi musu mugun kyau dukansu ƙawayen Amaren. Ta bi bayan TAIMIYYAH da suka rigata yin
gaba,tana ɗaga murya ta cewa Anty Laurat, "Anty Laurat don Allah ga wayata nan a caji kusa da
ke,idan ya cika ki cire min please."
Daga haka ta yi gaba Anty Laurat na amsa mata da cewa, "Tuh shikenan an gama Sis."
__________
Daga can sasan Baba Sani kuwa shirin tafiya da Amarya Zuhurah Bauchi ake yi,don dama haka
aka tsara ana kammala ɗaura aure za a wuce da ita. Ita da Angon da mutane huɗu ne aka biyawa
kuɗin jirgi,sai sauran mutane za su bi dogayen motocin da aka zo ɗaura aure da su don kwasan ƴan
rakiyar Amaryar.
Amarya Zuhurah da ta sha kyau ita ma cikin kayan da ta sanya,sai faman kuka ta ke yi lokacin da
suke sallama da Ummanta. Wacce kallo ɗaya za kai wa Umman kasan cewa akwai manyan
damuwoyi kwance a ƙasan zuciyarta. Ta dubi Zuhurah lokacin da wata ƙanwar su Baba Sani da
suke ƴaƴa maza da ita,ta kama hannun Zuhuran ta miƙar daga gabanta ta ce, "Zuhurah Allah ya
bada sa a,Ubangiji yasa ki shiga gidanki cikin nasara,ki kula da dukkanin huɗubobin da mu kai
miki,sannan kar ki yi sake ba ki yi anfani da waɗannan saƙon kamar yadda aka sanar miki ba,
Allah ya yi miki albarka ƴata."
Zuhurah dai ba baki sai kuka da ta ke sha kamar za ta shiɗe,bata taɓa tunanin wannan ranar za ta
zo ta kasa jin ɗokin barin gida ba,sai gashi tun da aka ce an ɗaura auren hankalinta ya ke a
tashe,tana ji a zuciyarta sam bata son barin gidan,wani irin fargaba ke danne zuciyarta wanda ta
kasa gane dalilin jin hakan da take yi. Ita ko Amarya Basmah kuwa tunda su sai yamma can za a
miƙa su ɗakunansu,sai sabgarta ta ke yi cikin shaƙiƙan ƙawayenta su Amna da Sharifa. Ko kaɗan
bata jin fargaban komi a ranta,sai ma ɗokin son a kai ta gidan Nass ɗin su zama abu ɗaya ita da
shi,don ita haushin Zuhurah ta dinga ji da ta ke wani faman rusa kuka, kamar wacce za a kai gidan
maƙiyinta ba Ameerunta da take ta rawar ƙafa akansa ba.
Aka fito da Zuhurah daga Sasansu aka nufi Sasan Iyah da ita don yin sallama da ita,suna isa Sasan
Iyah ne bada jimawa ba TAIMIYYAH suka shigo don amsa kiran Iyah. Ashe dama Iyan ta aika
akira TAIMIYYAH ne don ta haɗasu su duka ukun ta yi musu faɗa da nasiha duk gaba ɗaya,don
ita ma Basmah an je kiranta ta zo a haɗasu ai musu faɗan tare.
Zuhurah ta zurawa TAIMIYYAH ido lokacin da suka samu waje suka zauna kusa da Iyah,wani
irin kyau ta ga TAIMIYYAH ta yi mata irin wanda bata taɓa gani ba.
TAIMIYYAH ko hankalinta na kan Iyah da su Hajiya Rabi aminanta,ta ɗaga ido ta dubi Iyah ta
ce, "Iyah gani Nusaiba ta ce in zo kina nema na."
Iyah ta dubi TAIMIYYAH da murmushi a samar fuskarta ta ce, "Eh! Zauna nan ku jira Basmah ta
zo,faɗan bankwana za a haɗa ku ai muku. Kin yi kyau Zainabu na Ubangiji ya sanya alkhairy,ya
baku zama lafiya a gidajen mazajenku."
Sauran mutanen da ke cikin ɗakin suka amsa da cewa "Ameen." Guggo Bilki da ke zaune daga
can ƙarshen gadon Iyah ta ɗago kanta ta dubi TAIMIYYAH ta ce, "Zainab kin ko gaisa da su
Yayanki Anas,sun shigo nan suna tambayar ina ki ke na ce su je can Sasan Ummie,sun je ɗin ko
wucewarsu su ka yi?"
TAIMIYYAH ta girgiza kai ta ce, "Aiko dai wucewansu suka yi Guggo Bilki,don ko mai kama da
su ban gani ba wallahi."
"To ai sun kyauta,sa dawo ganin gida wataran ai." Cewan Guggo Bilki daidai lokacin kuma
Basmah suka shigo cikin ɗakin Iyah. Aka haɗu aka fara musu faɗa da nasiha akan muhimmancin
haƙury a zaman aure,TAIMIYYAH tuni idanunta suka raina fata,zuciyarta ta karye ta fara kuka me
motsa zuciya. Gaba ɗaya ji ta yi tamkar a ɗaga auren a ce anfasa sai zuwa gaba,amma ta san hakan
ba mai yiwuwa bane,sosai Iyah da su Guggo Bilki su kai musu nasihu masu ratsa jikin duk wani
me hankali da nutsuwa. Basmah kaɗai ce zan iya cewa bata girgiza ba amma hatta Zuhurah sai da
jikinta ya sake yin sanyi,zuciyarta ta karye ta cigaba da jin lamari me girma na dabaibaye
zuciyarta.
Yasmeen ce ta riƙo TAIMIYYAH zuwa jikinta tana rarrashi,sabida yadda ta ke kuka me asalin
motsa zuciya,kwalliyar fuskarta tuni har ya fara ɓaci.
Zuhurah ta isa gaban Iyah bayan an kammala yi musu nasihan,cikin muryar kuka ta ce da Iyah,
"Iyah ki yafe min duk laifin da na taɓa yi miki don Allah."
Iyah ta dafe kanta ta ce, "Na yafe miki Zuhurah,Allah ya sanya albarka ya baku zama lafiya,ki
kula sosai ki aje duk wasu huɗuba da akai miki na banza,ki kama Allah kaɗai tare da yin biyayyar
aure kamar yadda addini ya shinfiɗa,Allah ya kai ku lafiya yasa ki shiga a sa a."
Daga haka aka janye Zuhurah daga gaban Iyah za a fita da ita,amma sai ta zame hannunta ta isa
wajen da Yasmeen ke zaune tare da TAIMIYYAH da ke faman kuka har lokacin. Zuhurah ta
tsugunna tare da kamo hannun TAIMIYYAH ta riƙe,cikin muryar kuka ta ce, "TAIMIYYAH za a
tafi dani,ina roƙon ki yafe min duk wani abu da na taɓa yi miki mara kyau,sannan ina mana fatan
alkhairy baki ɗayan mu."
TAIMIYYAH jin muryar Zuhurah daf da ita yasa ta buɗe idanunta da suka fara rinewa ta ɗaura
akan fuskar Zuhurah,ganin yadda hawaye ke gudu akan fuskar Zuhurah da yadda ta yi laushi
kamar ba ita ba,sai kawai TAIMIYYAH ta rungumeta tana magana cikin muryar kuka ta ce,
"Zuhurah in ma kin ɓata min wallahi na yafe miki,ban taɓa riƙe ku a raina ba dama. Allah ya kai
ku lafiya ya baki zama lafiya Ameen."
Daga haka suka saki juna kowanne a cikinsu na jin wani irin lamari me girma a cikin
zuciyarsa,kowa a ɗakin sai da ya share hawayen tausayinsu.
Guggo Bilki ce ta ce da Yasmeen ta kama hannun TAIMIYYAH su koma Sasan Ummie, a gyara
mata kwalliyar da ya ɓaci tunda su sai zuwa yamma za a kai su ɗakunansu ita da Basmah.
Yasmeen ta miƙe tana riƙe da hannun TAIMIYYAH na dama,ita kuma TAIMIYYAH na dafe da
guiwar ƙafarta da hannun hagu,suka fara takawa suna ratsowa cikin falon Iyah har suka fito daga
cikin Sasan baki ɗaya.
Yasmeen ta yi maganar tana miƙawa TAIMIYYAH wayarta da har lokacin ya ke kukan neman
ɗauki, TAIMIYYAH ta amsa wayar tana danna receive ta kai kunni. Muryar Maleek ya shiga
kunnuwanta lokacin da ya ce, "Wife gani na iso ina waje,za ki ga wata black ɗin mota daga gaban
gidan kaɗan."
TAIMIYYAH ta jinjina kai kamar yana gabanta,sannan ta yi magana cikin sanyin murya sosai ta
ce, "Okey gani nan zuwa In sha Allah." Daga haka ta yi cuting call ɗin tana maida idanunta akan
Yasmeen ta ce, "Yasmeen wai ya zo ne yana waje,mu je a gyara fuskar sai ki rakani don ba zan iya
zuwa ni kaɗai ba."
Yasmeen ta saki murmushi cike da tsokana ta ce, "Wow! Ki ce Ango ya zo ganawa da Amaryarsa,
amma shi ne ya ƙi yadda ya zo a ɗauki pics bayan ɗaura aure, gaskiya wannan Angon na ki ajinsa
har ya ɓaci,oya mu je a gyara wannan fuskar ta ki da kika jiƙe da hawayen gulma."
TAIMIYYAH ta wurgawa Yasmeen harara,hawaye suka sake zubo mata cike da shagwaɓa ta ce,
"Yasmeen ni ce ke hawayen gulmar ma? Oya mu je kawai kafin ki sake sani a damuwa."
Daga haka suka jera da juna zuwa Sasan Ummie,bayan an gyarawa TAIMIYYAH fuskarta ne ta
samu babban mayafi ta naɗe jikinta da shi. Duk yadda ta motsa wani fitinannan ƙamshine ke ratsa
ko'ina a jikinta,ta zurah flat shoe a ƙafarta tana duban Yasmeen da fuskar shagwaɓa ta ce,
"Yasmeen mu je please kin ga yana sake kira."
TAIMIYYAH ta yi maganar lokacin da kiran Maleek Ado ke sake shigowa wayarta,hakan yasa
Yasmeen ɗaukar wayarta suka fito don yiwa TAIMIYYAH rakiya zuwa wajen Maleek Ado.
Sun fito harabar compound ɗin dai dai lokacin da ake fitowa da Zuhurah daga Sasan su, za a shiga
mota don zuwa Kano su hau jirgi su wuce Bauchi,waɗanda za su bi mota irin su Anty Laurat su
sun wuce tun ɗaxu.
"Yasmeen shikenan Zuhurah za a wuce,ba ki ji yadda jikina ke sake yin sanyi ba,ina jin
tausayinmu mu duka don bamu san wace irin rayuwa za mu je mu taras a gidan auren ba,wallahi ji
na ke yi tamkar a fasa auren a bar ni tare da Iyah ta."
Yasmeen ta saki dariya ta ce, "To sannunki sarkin wauta,don Allah ni mu je in kai ki in yi
dawowata cikin gida,ni fa wallahi duk wannan kukan da wani roƙon yafiyar da Zuhurah ta dinga
yi,sam bata bani tausayi ba don baka saurin sallamawa maƙiyinka,watakili wani salon munafurcin
ne kawai aka shirya mata,ita ƙaramar mara kunyar baki ga ko gezau bata yi ba? Wallahi ina
tausayin Basmah don rawar kan yarinyar da fitsaranta ya yi yawa,amma In sha Allah xa a gyare
mata zama tsaf,ta dai shiga gidan za ta gane Allah ɗaya ne."
Yasmeen tana maganar ne suna takawa a hankali don fita daga gate ɗin gidan,ita dai TAIMIYYAH
jin Yasmeen kawai ta ke yi bata iya cewa komi ba,don bata san ma me za ta ce ɗin ba,amma har
cikin zuciyarta ta ji tausayin Zuhurah,domin ita tana son su a ranta don gani ta ke yi bata da
tamkar su,tunda su ne dai za ta nuna a ko'ina a matsayin ƴan uwanta na jini da iyayensu suka fito
ciki guda.
Lokacin da suka ƙarisa fitowa wajen gate ɗin ne, TAIMIYYAH ta shiga wurga ido don gano inda
Maleek ya parker motarsa. Idanunta ya hango mata wata danƙareriyar baƙar mota daga gaban
gidan kaɗan,kamar yadda ya kwatanta mata,sai ta dubi Yasmeen ta ce, "Yasmeen ina ga waccar
motar ce ya ke nufi,don ya ce daga gaban gidannan kaɗan ya yi parking."
Yasmeen ta jinjina kai suna cigaba da takawa zuwa wajen motar. Maleek da tun da suka doso ya
ke ƙare musu kallo ta cikin madubin motar,sai ya samu kansa da kasa ɗauke ido akan
TAIMIYYAH,wacce tun daga nesa ya ke sake hango irin kyawun da ta yi,sai ya raina mayafin da
ta sanyo domin irin Chantly ɗinnan ne me shara-shara. Ya ɗan lumshe idanunsa ya buɗe akansu
lokacin da suka ƙariso bakin motar. TAIMIYYAH ta jingina jikinta da jikin motar,ta bar Yasmeen
da ƙarisawa bakin driver seat ta yi knocking. Maleek ya sauke tint ɗin glass ɗin motar ya leƙo da
kansa yana cewa, "Sis har kun iso? Ce wa wife ta zagayo front seat ta shigo please!"
Yasmeen ta jinjina kai tana komawa wajen da TAIMIYYAH ke tsaye daga baya ta ce, "Amarya
Angonki na buƙatar ki ƙarisa daga front seat ki shiga."
TAIMIYYAH ta ɗan shagwaɓe fuska ta ce, "Okey mu je." Yasmeen ta balla mata harara ta ce, "Mu
je ko ki je,kin dai ji Yarinya da rainin hankali,in je ina? Ni muna gaisawa yanzu zan juya idan kun
gama kya kira ni in fito,idan kuma ya yo miki rakiya har gida kin ga an hutar dani."
Daga haka Yasmeen bata sake cewa komi ba, ta juya zuwa wajen Maleek suka gaisa ta yi masa
fatan alkhairy ta juyo don komawa cikin gida, ta bar TAIMIYYAH na zagayawa za ta shiga front
seat ɗin,in da har Maleek ya riga ya buɗe mata murfin motar.......✍🏻
#Ɗansabo ce#
[12/14, 3:43 PM] +234 703 040 9541: Littafin TAIMIYYAH paid book ne,ga duk wanda ta
tsincesa a kowani irin group ne,kiji tsoran Allah karki karanta sai kin biya 500 naira only.
Za ku iya min magana ta wannan number ɗin 08167768704, ko kuma ku turo kuɗin ku kai tsaye ta
wannan account ɗin 0504192664 aisha ibrahim dansabo GTbank.*
Masu turo credit za ku turo katin MTN na 500 ta wannan line ɗin 08167768704.
_Ina ƴan kasuwa masu buƙatar a tallata muku hajar ku? Maza ku garzayo da kuɗi ƙalilan a tallata
muku kayan siyarwanku sai dai kawai ku ji ana kiran waya don buƙatan sayan kayan ku,ku
tuntuɓeni ta layina kamar haka 08167768704._
*67*
A hankali TAIMIYYAH ta zura jikinta cikin motar tana me barin murfin motar a buɗe,ƙafarta ɗaya
me lafiyan na daga waje sai ɗayar kawai ta aje daga cikin motar. Ta ɗaga manyan idanunta ta dubi
fuskar Maleek Ado,wanda ke binta da wani irin mayataccen kallo kai ka ce bai taɓa ganinta bane
sai a yau ɗin. TAIMIYYAH sai ta sake narke fuska cike da shagwaɓa ta fara gaida shi,memakon
ya amsa gaisuwar sai cewa ya yi, "Wife ki shigo sosai ki rufe min murfin motar,magana kawai za
mu yi in wuce ba wai cinyeki na zo yi ba."
Yadda ya ke maganar murya can ƙasa da yadda ya miskile fuska,ya sanya TAIMIYYAH bin
umurninsa ta maido ƙafarta ɗaya cikin motar tare da rufo ƙofar motar baki ɗaya. Zuciyarta sai
faman bugu ta ke yi tana jin ta very uncomfortable ,sabida irin kallon da Maleek ya tsareta da
shi.Ta kai dubanta garesa sau ɗaya tana saurin yin ƙasa da kanta,ta fara wasa da yatsun hannunta
da suka sha jan lalli da ya yi wani irin maroon. Kamar a mafarki ta ji hannuwan Maleek Ado akan
jikinta,hakan yasa ta yi saurin ɗago manyan idanunta ta sauke akan fuskarsa,lokacin da ya ke
warware gyalen da ta yane jikinta da shi ya sauke shi zuwa ƙasa.
Jikinta TAIMIYYAH sai ya ɗauki rawa,zuciyarta na wani irin harbawa da matsanancin
fargaba,cikin rawar murya cike da shagwaɓa ta ce, "Yah Maleek a waje fa mu ke,don Allah ka bari
kada wasu su zo wucewa su gan mu please!"
Yadda TAIMIYYAH ta yi maganar tamkar za ta rushe masa da kuka, ba ƙaramin motsa zuciyar
Maleek Ado ya yi ba. Ya sake kafa mata mayun idanunsa yana cewa, "Wife ai babu me ganin
mu,dukkanin gilasan motar tint ne ai so u have to be comfortable kina tare da mijinki ne yanxu ba
wai saurayi ba okey."
TAIMIYYAH sai ta zura masa ido tana sake ɓata fuska,ƙirjinta har lokacin harbawa ya ke yi da
wani irin tsoro me tsanani, ga ƙamshin turarensa da sanyin AC ɗin da ya gama buɗe motar,na sake
haifar mata da wani irin yanayi mara misaltuwa. Ba ta iya cewa komi ba illah yin ƙasa da kanta da
ta yi,tana ji tamkar ta sakin masa kuka ko zai ɗauke idanunsa daga mayen kallon da ya ke bin
jikinta da shi.
"Wife kin yi kyau sosai,irin kyawun da ban taɓa gani akan ko wace mace ba,na gode Allah da ya
mallaka min ke amatsayin halalina,ɗago ki kalle ni babe please cox ina son ganin waɗannan
idanun cikin nawa."
Maleek Ado ya yi maganar da wani irin salon murya,da ya sanya TAIMIYYAH saurin ɗaga
manyan idanunta ta sauke akan fuskarsa,cikin sa a idanunta suka shige cikin na Maleek ɗin. Ta ke
sai wani irin maganaɗisu ya yi aikinsa zukatansu suka buga a lokaci guda,kamar yadda
kowannensu wani abu ya tsirga masa tun daga yatsun ƙafarsu zuwa zuciya da gangar jikinsu baki
ɗaya.
TAIMIYYAH za ta ɗauke fuskarta daga dubansa,amma sai Maleek ya yi saurin miƙa hannu ya
riƙo fuskarta a tafukan hannunsa,cikin wani irin kasalalliyar murya ya ce, "No wife please! Ki
barni na morewa kallon waɗannan idanun masu tasiri akaina."
Sai TAIMIYYAH ta maida ƙwayar idanun ta lumshe su,wani irin abu na gudu a cikin jini da
tsokar jikinta. Zuciyarta ta cigaba da harbawa da gudun gaske,kamar yadda wani abu ke zagaye
jikinta tana jin wani yamm...! A ilahirin jikinta. Bata kuma shiga ruɗu ba sai lokacin da ta ji fuskar
Maleek Ado akan tata fuskar,yana me haɗe fuskarsu waje guda,tare da ɗaura bakinsa akan nata
goshinsu na mannuwa da juna. TAIMIYYAH bata san lokacin da bakinta ya suɓuce ya furta
kalmar 'Hasbunallah!' jikinta ya cigaba da ɗaukar wani irin rawa. Shi ko Maleek Ado ko ajikinsa
bai ma san tana yi ba,burinsa kawai ya bata kiss ya ji irin ɗanɗanon da ke kan harshenta.
Ya miƙa hannuwansa duka ya riƙo TAIMIYYAH zuwa jikinsa ya rungumeta,ta ke ta sakin masa
kuka jikinta na cigaba da ɗaukar rawa,cikin rawar murya ta ce, "Please Yah Maleek don Allah ka
yi haƙury!"
Maleek da maganarta ya bashi dariya sai ya sake mannata da jikinsa sosai,yana me raba fuskarsa
da tata amma idanunsa na kan yadda TAIMIYYAH ta rintse nata idanun ya ce, "Baki min laifi ba
wife, so ki daina bani haƙury kawai ina son jin ɗumin jikin matata ce,ki daina wannan rawar jikin
baby babu abinda zan miki da ya wuce inyi kissing ɗinki,just kiss kawai kin ji babe?"
Yana maganar ne yana sake ƙoƙarin haɗe fuskarsu waje guda,TAIMIYYAH ta sakar masa kuka
jinkinta na kuma ɗaukar rawa.Wannan shi ne karo na biyu da ta ji ta rungume a jikin namiji,tun
bayan karon ta da Yah Deeku a wancan lokacin,amma yadda ta ke ji a yanzu bata ji irinsa a
wancan lokacin ba sam. Maleek Ado ya ɗaura bakinsa akan nata yana aika mata da wasu zafafan
kiss,so ya ke yi ya zura harshensa cikin bakinta amma ta datse ta hana shi daman hakan.Dukkanin
jikinta rawa ya ke yi don lamari ne da bata kawo faruwarsa nan kusa haka ba,ta buɗe baki za ta yi
magiya amma sai Maleek ya yi anfani da wannan daman wajen zura harshensa cikin bakinta. Wani
abu ya doka a tsakar kan TAIMIYYAH lokacin da ta fara amsan wani irin hot kiss daga Maleek
Ado,wanda ke tsotsar harshenta cikin zalama tamkar wanda ya cafki wata alawa me tsananin zaƙi.
TAIMIYYAH ta dinga mutsu-mutsun son kwace jikinta amma ta kasa,don wani irin runguma ya yi
mata yadda ba za ta iya kwace jikinta ba. Ko kaɗan bai saurara mata ba sai da ya tsotsi bakinta son
ransa,sannan ya zare harshensa daga bakinta yana duban yadda hawaye ke gudu akan
kyakykyawar fuskar TAIMIYYAH. Wacce ta rintse idanunta tamau ta ƙi buɗewa sabida ba za ta
iya kallon idanunsa ba, bayan ya gama mata wannan abun kunyar.
Maleek Ado sai ya saki wani killer smile yana sake jin tamkar ana rura masa wutar fitina akan
TAIMIYYAH ne, ya miƙa hannunsa ya fara share mata hawayen da ke sakkowa daga idanunta.
Cikin muryarsa da ya sauya sosai ya ce, "Sorry wife na gama,ba zan sake miki komi ba sai zuwa
anjima idan an kai min ke ko? So please its okey kukan ya isa haka wife."
Memakon TAIMIYYAH ta nutsu ta yi shiru sai ta sake sakin masa kuka,da ƙyar ya rarrashi abarsa
ta yi shiru tana faman sauke a jiyar zuciya,duk ta wani firgice masa sabida gaba ɗaya lamarinsa ya
gigita tunaninta. Da ƙyar ya barta ta kira Yasmeen don yi mata rakiya su koma cikin gidan,bayan
ya gama susuta tunaninta da wasu irin lamura masu nauyi. Lamuran da suka sanya kanta ya so
buga mata,don kuwa a bazata ta ji hannunwansa a kan ƙirjinta,cikin muhallin da tuntuni ya ke da
burin jin hannuwansa a wajen,sabida tun suna waya a ɗazu suka tsone idanunsa. Lokacin da
Yasmeen ta iso wajen motar,har Maleek ya gama gyarawa TAIMIYYAH lulluɓinta, yana ta mitan
cewa gyalen ya yi shara-shara da yawa, ba za ta sake sanya irin su ba. Yasmeen ta yi knocking
ɓangaren da TAIMIYYAH ta ke domin su san ta iso,tunda glass ɗin tint ne ita bata ganinsu sai dai
su suna ganinta,shiyasa ta yi knocking don ta san cewa ba lallai ne hankulansu na kan duban
tahowarta ba. TAIMIYYAH ta ɗaga manyan idanunta ta dubi Maleek,wanda ya tsare ta da mayun
idanunsa yana ji tamkar ya gudu da ita zuwa gidansa, tun kafin a kai masa ita ɗin zuwa anjima.
Cikin murya me cike da zallar shagwaɓa ta ce, "Ta iso Yah Maleek."
Maleek ya cigaba da zura mata ido ba tare da ya yi ko motsi ba,bare ta sanya rai cewa zai yi
unlocking motar. Hakan yasa TAIMIYYAH kwaɓe fuska tamkar za ta sanya masa kuka ta ce,
"Please Yah Maleek ka buɗe min in fita,ga Yasmeen nan tsaye tana jira kar ta ɗauka wani abin mu
ke yi."
Maleek bai shirya yin murmushi ba amma sai da TAIMIYYAH ta sanya shi yin blushing,sabida
yadda ta yi maganar kamar za ta saki kuka ba ƙaramin bashi dariya ta yi ba. Ya miƙa hannunsa ya
kamo nata hannun tare da yin ƙasa da muryarsa ya ce, "Baby i luv u,please ki kula min da kanki
daga nan zuwa anjima, kiss me please! Wife kin ji?"
Yadda ya yi maganar cikin wani irin salonda yadda ya wani miƙo mata fuskarsa, ya sanya
TAIMIYYAH saurin rintse idanunta. Zuciyarta na cigaba da bugawa da matsanancin gudu,ga wani
uban kunya da ke sake yi mata dabaibayi. Cikin shagwaɓaɓɓiyar muryarta ta dinga masa magiya
akan ita dai ya buɗe mata motar ta fice. Maleek sai ya janyota jikinsa baki ɗayanta yana me kai
bakinsa ya manna mata wani hot kiss a saman goshi, ya kamo ƴan yatsunta da zanen lallin da akai
mata ya birgesa, su ma ya sumbacesu kafin ya sake ta yana me sake ƙureta da idanunsa da suka
sauya kala,sabida zallar rigimar da ya ke ji akanta. TAIMIYYAH ban da rawa babu abinda jikinta
ke yi, gani ta ke yi Yasmeen na kallonsu don sam ta manta ma da cewa tint ne glass ɗin motar.
Maleek ya yi unlocking motar yana me yinƙurin sake kai hannunsa jikin TAIMIYYAH,amma sai
ta yi saurin ɓalle murfin motar tana jefo ƙafarta zuwa waje. Yadda ta so fitowa da hanzari ya sanya
ƙafar mara lafiyar gocewa, ta yi kamar za ta kifa sabida bisan da motar ke da shi. Maleek ya yi
saurin dawo da ita baya yana cewa, "Haba wife saurin me ki ke yi haka za ki je ki jiwa kanki
ciwo,don Allah ki rage wannan tsoron nawa da ki ke ji please!"
TAIMIYYAH ta jinjina kai tana me saukowa a hankali daga motar,bayan Maleek ya sake furta
mata kalamai na soyayya masu zafi,wanda yasa TAIMIYYAH sake narke fuska zuciyarta cike da
mamakin lamuran da suka wanzu tsakaninta da Maleek ɗin.
Kallo ɗaya Yasmeen ta yi wa TAIMIYYAH ta ga yadda idanunta suka sha kuka. Fuskarta ta sake
yin ja idanunnan sunyi wuƙi-wuƙi, Yasmeen sai ta ji wani irin dariya na son ƙwace mata,da ƙyar ta
yi controlling kanta har su kai sallama da Maleek ya wuce,sannan ta dubi TAIMIYYAH da ke
tsaye dafe da guiwar ƙafarta ta kwashe da wani irin dariya.
TAIMIYYAH ta sake kwaɓe fuska cike da masifa ta ce, "Yasmeen wai mahaukaciya na zama ne
da za ki tasa ni gaba kina faman tintsira dariya? Allah idan muka shiga gida sai na haɗaki da
Ummie ta yi min iyaka daga iskancin ki."
Yasmeen ta sake kwashewa da dariya ta ce, "Really Matar Maleek Ado? Ke banda abinki daga ina
dariyata sai ki ce da ke nake yi,haka ake yi a Zarian na ku dama?"
TAIMIYYAH ta ballawa Yasmeen harara tana me dafe ƙafarta, ta fara takawa don yowa gaba abin
ta,ta bar Yasmeen a baya tana faman cigaba da kwasar dariyarta. Sai da suka iso bakin gate ɗin
shiga gidan ne Yasmeen ta ce, "Sorry tawan wai fishi ki kai? Ki yi haƙury babyn Maleek idanunki
ne suka bani dariya wallahi,sabida daga gani an san sun sha kukan luv ko ƴan matan Maleek?"
TAIMIYYAH ta dubi Yasmeen cikin ido tana ji tamkar ta saki kuka sabida takaicin kwasarta da
Yasmeen ɗin ke yi.Ta yi magana cike da masifa ta ce, "Yasmeen don Allah ki bar ni inji da abinda
na ke ji,bana son wannan iskancin wallahi. Banda ma sa ido ina ruwanki in ma kukan luv ɗin na
yi?"
Yasmeen ta gimtse dariyar da ke cinta a rai ta ce, "Afuwan Alarammiyar Maleek,haka ne babu
ruwana wallahi kawai wannan bakin nawa ne da ba a gasa min shi ba,baya iya shiru bai tanka ba."
TAIMIYYAH ta saki dariyar da babu shiri tana faman zabgawa Yasmeen harara ta ce, "Allah ya
shiryeki Yasmeen."
Daga haka suka cigaba takawa jere da juna har zuwa cikin part ɗin Ummie.TAIMIYYAH
memakon ta nufi ɗakin da friends ɗinta su Zee su ke,sai ta nufi ɗaya bedroom ɗin Ummien da ta yi
waya da Maleek ɗazu. So ta ke yi ta kaɗaice ko za ta dawo cikin nutsuwarta,sabida gaba ɗaya
lamuran da Maleek ya gudanar akanta sun birkita nutsuwarta baki ɗaya.
Bisa kan gado ta zube tana me yaye lulluɓinta ta yi wurgi da gyalen akan gadon,ta sake gyara
kwanciyarta tare da lumshe idanunta gam! Ta kai hannu ta shafa bakinta zuwa ƙirjinta,har
lokacin jin hannuwan Maleek ta ke ji na yawo a jikinta. Ta sake rintse idanun wani maganaɗisu na
sake zagaye jinin jikinta,ta buɗe idanun tana kai hannunta ta janyo gyalenta,wanda gaba ki ɗaya
ya rine da ƙamshin jikin Maleek Ado. Ta kai hancinta kan gyalen tana shaƙar ƙamshin turaren
AMOUAGE da ya gama kama jikin gyalen,tamkar Maleek ɗin ne a jikin gyalen sabida yadda
mayafin ya kama ƙamshinsa. Wayarta ta fara tsuwwar neman ɗauki sai ta janyo wayar tana
zubawa lambobinsa idanu,daf da kiran zai yanke ta iya ɗaga wayar ta kai kunni. Ba ta yi magana
ba sai shine ya fara sanar da ita yadda ya ke jin kewarta me tsanani daga rabuwarsu. Ita dai
TAIMIYYAH shiru ta yi tana sauraran manyan kalaman da ke fitowa daga bakin Maleek
Ado,waɗanda gaba ɗaya suka girmi kwanyarta da tunaninta. Shi ko Maleek ko ajikinsa don wani
irin fitinanniyar soyayyarta ce ke azalzalar zuciyarsa, ji ya ke yi tamkar ya rufe ido ya buɗe ya ga
an gama duk wani bikin al'ada an barshi da matarsa don ya huta. Sun jima suna wayan kafin ya yi
hanging up ya bar TAIMIYYAH da faɗawa duniyar tunanin yadda rayuwar aurenta da shi zai
kasance,da irin tarin lamura masu girma da nauyin da za su biyo baya,don bata ga alamun cewa
Maleek Ado ya san wani abu wai shi kunya ba. Ta maida idanunta ta lumshe tana sake gyara
kwanciyarta,zuciyarta na cigaba da dawo mata da moment ɗinsu na ɗazu tare da Maleek ɗin cikin
lafiyayyar motarsa, da irin bidirin da ya yi da jikinta da mouth ɗinta da ya sha tsotso. Daga
wannan kwanciyar ne kuma bacci ya sace TAIMIYYAH sabida a gajiye ta ke, sam tunda aka fara
hidiman bikin ba ta samun yin wani isasshen bacci.
__________
*GRA,Zaria.*
Suhailah ce kwance a kan gadon ɗakinta tana faman juyi tana kuka,idanunta sun yi asalin kumbura
don tun daren jiya ta ke aikin kuka.
Duk iya rarrashi da ban baki haɗi da tarairayarta da Maleek ya dinga yi tun a daren jiyan,bai sanya
Suhailah ta saki ranta ta daina kuka ba. Daga ƙarshema sai ta yi ƙaura daga ɗakin Maleek ɗin ta
koma ɗakinta ta kulle kanta,dama kuma ta jima da daina bashi jikinta tun lokacin da aka fara
maganar auren gadan-gadan, sai ta ƙauracewa shinfiɗarsa bisa ga huɗubar Jawahir da Suhailah ta
hau kai ta zauna daram! Don gani ta ke yi duk duniya Jawahir ɗin ce kawai me ƙaunarta da
tausayinta akan lamarin auren Maleek ɗin.
To yau tun safe ta sake kafa wani sabon babin kukan, akan kunnuwanta Maleek ya dinga knocking
yana rarrashinta akan ta buɗe masa ƙofar ɗakin amma ta yi biris da shi. Haka ya gaji ya fita a
sabgarta ya je ya yi shirin zuwa ɗaura aurensa ya bar mata gidan,abinda ya sake ɗaga hankalinta
kenan tare da jefa zuciyarta cikin matsanancin baƙin ciki,sabida akan idanunta motar Maleek ya
fice daga gidan. Tana daga tsaye tana leƙensa ta window ɗin bedroom ɗinta,da ke kallon harabar
parking space ɗinsu ta waje.
Ta ɗaga idanunta ta kalli a gogon ɗakin lokacin da ya buga ƙarfe goma sha biyu na rana. Ta sake
rushewa da wani irin kuka me cin rai,sabida kwakwalwarta ta gama sanar da ita cewa, zuwa yanzu
Maleek ɗinta ya sake zama mallakin wata mace ba ita ba.
Ta sakko daga kan gadonta tana jin yadda wani irin jiri ke neman kayar da ita,sabida yunwar da ke
ɗawainiya da ita don bata sanya komi a bakinta ba tun safe, har kawo yanzu ɗin da agogo ke nuna
sha biyu na rana. Haka ta dinga takawa tana rangaji har ta isa inda jakarta ta ke,wacce ta zo da ita
daga Abuja randa suka iso tare da Maleek ɗin.
Ta ɗauki jakar tana me komawa kan gado ta zauna,tare da buɗe jakar tana ciro wani ƙullin leda ta
warware shi. Ta ke wasu layu guda biyu suka bayyana,Suhailah hannunta na rawa ta ɗauke su tana
juya su a tafin hannunta. Zuciyarta na sake shiga cikin matsanancin ruɗani,tana jin wani
matsanancin tsoro na lulluɓe zuciyarta. Maganar da Jawahir ta gaya mata sanda ta kawo mata
layun na dawo mata cikin kwanyarta,tamkar a lokacin jawahir ɗin ke furta kalaman in da ta ke
cewa,
" _Suhailah da zaran an ɗaura auren ki yi gaggawar birne waɗannan layun, kafin cikar awa ashirin
da huɗu da ɗaura auren,idan har ya wuce waɗannan awannin baki rufe su ba,to shikenan kuɗinki
ya tafi a banza,don ko kin birne bayan cikar awa ashirin da huɗu babu tasirin da hakan zai yi, don
haka da zaran an ɗaura kawai ki san yadda ki ka yi suka shiga ƙarƙashin ƙasa._ "
Suhailah ta sake damƙe layun a cikin hannunta,hawaye masu tsananin zafi da ƙuna na sake biyo
fuskarta. Maganar da Jawahir ta yi akan tasirin birne layun na haskawa a cikin kanta,
" _Da zaran kin birne layunnan Suhailah,shikenan zai ji ya tsaneta ba zai iya rayuwar aure da ita
ba,don suna haɗuwa da juna zai dinga ji tana masa wani irin wari,wanda hakan zai jefa ƙiyayyarta
me tsanani a cikin zuciyarsa,kuma ba zai yi sukuni ba har sai ya sake ta.Don haka ki cire duk wani
tsoro da fargaba Suhailah,da zaran kin yi yadda aka ce shikenan kin gama da matsalar kishiya,ni
kuma daga baya zan kai ki inda za ki mallake zuciyar Maleek,ta yadda ba zai iya sake kallon
kowace mace ya ganta a mace ba ma, bare har ya ji cewa zai iya sake aure._ "
Suhailah ta ƙurawa layun idanu bayan ta dawo daga duniyar tariyo kalaman Jawahir ɗin. Ta dinga
jin wani irin courage na shigarta akan ta aiwatar da wannan aikin kawai,don ba za ta iya zuba ido
ta ga Maleek ɗinta tare da wata mace bayan ita ba.
Sai ta aje layun bisa kan bed ɗinta tana nufan hanyar bathroom, don ta yo wanka sabida ta ji ƙarfin
jikinta kafin ta zo ta nemi abincin da za ta sanyawa cikinta. Har ta murɗa handle ɗin ƙofar shiga
bathroom ɗin ta saki ta juyo ta dawo cikin ɗakin, tana nufar hanyar ƙofa ta buɗe ta fice. Direct
kitchen ɗinta da ke nan up stairs ta shiga,ta nufi wajen fridge ta buɗe tana ciro kwalin Hollandia
milk me matsakaicin sanyi. Ta aje bisa saman island ɗin kitchen ɗin tana matsawa zuwa in da ta ke
aje kayan su Bread da su cookies wanda Maleek ya jido su da yawa daga wani Bakery. Ta ɗibi
cookies ɗin cikin plate ta haɗa da kwalin Hollandia milk ɗin ta fito,ɗakinta ta koma ta aje bisa
saman bedside drawer, sannan ta wuce zuwa bathroom ɗin don sallo wanka. Gaba ki ɗaya ta
manta cewa bata sake kulle ƙofar ɗakin da key ba,burinta kawai ta yo wankan ta fito ta sanyawa
cikinta wani abu, kafin ta aiwatar da aikin birne layun nan biyu,wanda aka bata tabbacin da zaran
sun shiga ƙarƙashin ƙasa shikenan aiki ya ci ya gama..........✍🏻
_To masu karatu ga dai Suhailah ta samo layar tarwatsa wannan auren luv na Maleek Ado da
gurguwarsa TAIMIYYAH. Shin ita ke da nasara ko su TAIMIYYAH wanda suka dogara ga Allah?
Ku cigaba da bin labarin sannu a hankali har ya zo ƙarshe.....Kar ku da mu da ayi rushing domin
bana buƙatar gintse labarin._
_Ina godia da tarin ƙaunar da ku ke nunawa wannan labarin,i really really appreciate it my guys!
Ɗansabo ta yaba, kuma tana ƙaunar ku domin Allah_ 😍
#Ɗansabo ce#
[12/14, 3:44 PM] +234 703 040 9541: Littafin TAIMIYYAH paid book ne,ga duk wanda ta
tsincesa a kowani irin group ne,kiji tsoran Allah karki karanta sai kin biya 500 naira only.
Za ku iya min magana ta wannan number ɗin 08167768704, ko kuma ku turo kuɗin ku kai tsaye ta
wannan account ɗin 0504192664 aisha ibrahim dansabo GTbank.*
Masu turo credit za ku turo katin MTN na 500 ta wannan line ɗin 08167768704.
_Ina ƴan kasuwa masu buƙatar a tallata muku hajar ku? Maza ku garzayo da kuɗi ƙalilan a tallata
muku kayan siyarwanku sai dai kawai ku ji ana kiran waya don buƙatan sayan kayan ku,ku
tuntuɓeni ta layina kamar haka 08167768704._
*68*
Anty Safiya da Anty Radiya ne suka iso gidan Suhailah bisa ga umurnin Hajjah,sabida tunda ta
tambayi Maleek ya sanar mata cewa har ya fito daga gidan, bai sanya Suhailah a idanunsa ba
hankalin Hajjah ya kasa kwanciya. Musamman da ta kira wayar Suhailah amma bata ɗaga
ba,shiyasa ta yanke shawaran turo babbar Ƴar Inna Dije Yayar Hajjah me suna Anty Safiya, tana
aure ne a can Katsinan nasu da yaranta har huɗu, waɗanda bata samu xuwa da su bikin ba duk
suna skull. Sai Anty Radiyar wacce ta ke matsayin Guggon Suhailah don ƙanwar Baban Suhailah
ce uwa ɗaya uba ɗaya,aure ne ita ma ya kawo ta Zaria sai kuma ta yi kyan kai suna zumunci da
Hajjah sosai, tana zaune ne a cikin Tukur-Tukur da yaranta Uku da kishiyoyi har biyu amma
kowacce na zaune a Flat ɗinta daban ne.
Anty Safiya ta dubi Anty Rady bayan sun yi ta rafsa sallama daga downstairs ɗin, amma shiru
babu wanda ya san ma suna yi,don ko Mai aiki ɗaya basu gani ta leƙo ba da alamu suna can ciki
ne.
"Radiya mu wuce zuwa saman kin ji mu ga wani hali Ƴar banzar Yarinyar can ta ke ciki."
Anty Rady ta jinjina kai ta ce, "Hakane kam tunda muna ta sallama shiru,ni wallahi da Hajjah ta
bar ni tun shekaranjiya so na yi in bubbugeta,iskan cin nata ya yi yawa kamar akanta za a fara yin
kishiya,ni da ke da har biyu ashe sai na faɗi na mutu,su kuma Hajjah da Maleek ɗin kansa
lallaɓata suke yi ba sa so ai mata tsiya-tsiya,shiyasa ta ke zuba iskancin nan sabida ta ga ana nuna
tausayinta sosai."
Anty Radiya ta kai ƙarshen maganar cike da sababi,suna fara taka stairs ɗin benen ne Anty Safiya
ta ce, "Hmm! Ke dai bari kawai Radiya,ai shiyasa aka ce idan gata ya yi wa mace yawa tafi hauka
da iskanci. Suhailah tabbas ta bani tausayi don kishiya ko ta buzuzu ce bata da daɗi,kuma babu
macen da ke so tana cikin zamanta da mijinta cikin so da ƙaunar juna ya ce zai yo mata kishiya,to
amma idan har Allah ya ƙaddara hakan ai sai mutum ya sallama ya rungumi ƙaddararsa,amma
Suhailah ta kasa fahimtar hakan gani kawai ta ke yi Maleek ya daina sonta ne shi da Hajjah,sabida
ta samu matsala bata haihu ba. Kar ki so ki ga huɗubar da na yi mata jiya a gidan Hajjah akan ta
kwantar da hankalinta, ta baiwa marar ɗa kunya amma kin ji wai tun safe ta kulle kanta a ɗaki tana
faman kuka."
Anty Safiya ta kai ƙarshen maganar lokacin da suka isa matakalan ƙarshe,Radiya na cewa, "Ai ki
bar ni da ƴar banza idan bata shiga hankalinta ba bubbugeta zan yi,in bi kishin da gudu in tattake
shi babu ko takalmi,tunda ita shashashar Yarinyar ce mara lissafi. Kishi ai ba hauka bane da za ta
bi ta addabi kanta,duk ta fita hayyacinta ba wannan gayu da kwalliyar duk ta zubar sabida shirme
da wauta,ko an gaya mata hakan shi zai sa ya fasa yin auren oho!"
Anty Safiya ta saki murmushin takaici ta ce, "Hmmm! Allah ya ganar da ita gaskiya,ina ne ɗakin
nata don kin san ban taɓa hawo mata sama ba,duk zuwan da na ke yi a gurguje kawai mu ke
gaisawa in wuce."
Anty Radiya ta nufi hanyar ɗakin Suhailar tana cewa, "Nan ne ɗakin in ba kuma ta sauya wani
ba."
Suka tura ƙofar bakunan su ɗauke da sallama suka shiga, jin shiru babu motsinta sai tray da suka
hango a saman drawer ɗin bedside,da kuma jakarta da ke yashe bisa kan gado,hakan yasa Anty
Safiya ta dubi Anty Rady ta ce, "Kin ji ɗakin shiru hala ta ga dama ta shige wanka ne,bari na
ƙarisa daga bakin gadon in ga miye a cikin jakar ja'irar."
Ta yi maganar tana isa bakin gadon Suhailah ta zauna,Anty Rady ta nufi wajen Sofa ta zauna tana
cewa, "Wanka yanzu da rana tsaka sabida shashanci."
Suhailah sai ta ɓata fuska tana ɗagowa ta dubi Anty Rady ta ce, "Anty Rady bakomi fa kawai
sirrina ne ban son a gani."
Anty Safiya ta riga Anty Rady yin magana tana cewa, "Ki rabu da ita Rady ni kuma sai na ga
wannan sirrin da ake wa wannan sufan don ɓoye shi. Oya bani in gani miye sirrin? Idan na
maganin mata ne kin ga muma sai ki sammana mu gwada anfani da shi."
Yadda Anty Safiya ta yi maganar very serious ya sanya ƙirjin Suhailah bugawa,ta yi saurin duban
Anty Safiya ta ce, "Don Allah Anty ki bar wannan maganar,wannan ba magani bane fa wani abu
ne kawai."
"Wani abu bai da suna ne Suhailah? Wallahi sai mun ga ko mene ne ki ke wa wannan uwar sufan
da kika yi wajen ɗauke shi daga kan gadon.don haka tun muna shaida juna ki aje sa kawai mu ga
ko miye."
Suhailah ta dubi Anty Rady cikin mummunar tashin hankali, jikinta har ya fara rawar rashin
gaskiya. Ta yi magana muryarta na rawa ta ce, "Don Allah Anty Rady ku barni wallahi ba zan iya
nunawa ba."
Anty Safiya da jikinta ya gama bata cewa koma miye ba abu me kyau bane shiyasa Suhailah ke
ɓoyewa, sai ta dubi Rady ta ce, "Radiya taso ki gani mu danne ta mu amsa tunda ba fin ƙarfin mu
za ta yi ba."
Suhailah ganin da gaske su Anty Rady danneta za su yi,sai kawai ta saki ledar layun ƙasa. Anty
Safiya tabi ta ɗakko su daga ƙasa cike da zallar tsoro da firgici, ganin layu ne take gani da
idanunta ta dubi Anty Rady ta ce, "Radiya gane min ko idanuna ne basa gani daidai,waɗannan
layu ne nake gani ko kuwa?"
Anty Safiya ta ƙare maganar tana miƙawa Radiya manyan layun guda biyu. Anty Rady ta amsa
tana dubawa cike da firgici ita ma akan fuskarta ta ce, "Da gaske layu ne Safiya ba gizo idanunki
ke yi ba,Suhailah a gidan uban wa ki ka samo layu,yaushe ki ka fara bin Bokaye ba mu sani ba?"
Suhailah da zuwa lokacin ta ke zube akan bed tana kuka,ta ɗago idanunta ta sauke akan Rady.
Wani irin firgici da tashin hankali na sake danne zuciyarta,muryar ta na rawa ta ce, "Wallahi Anty
Rady sharrin shaiɗan ne da kuma zigar Jawahir,amma ni ban taɓa zuwa wajen Boka ba.Na rasa
nutsuwata ne Anty sabida zafin kishin da na ke ji akan Maleek. Shi ne ta ziga ni ta ce wannan
hanyar ita kaɗai ce mafita da za a tarwatsa auren bayan an ɗaura,don Allah ku rifa min asiri kar ku
gayawa Hajjah da Inna Dije,don na san kasheni ne kawai Inna Dije ba za ta yi ba."
Suhailah ta kai ƙarshen maganar tana sake rushewa da wani irin kuka mai cin rai. Dukkanin jikinta
rawa yake sabida shiga ruɗu da tashin hankali,ga yunwa da ke sake kwakular hanjinta na sake
taimakawa wajen sanya jikinta ɗaukar rawar.
Anty Rady da ranta ya gama ɓaci ta dannawa Suhailah wata uwar ashar! Kafin ta ce, "Suhailah da
iliminki na addini akai da komi ki ke kauce hanya, sabida kawai za a miki kishiya? Lallai idan
baki farga kin dawo hayyacinki ba kwanan nan za a fara kiranki da suna bazawara. Don ina sahun
farko da zan ziga Hajjah ta raba aurenki da Maleek tunda kin ɗakko hanyar zama ibilishiya
mushrika. Uban wa ya taɓa gaya miki cewa Boka ya isa ya hana Allah ida nufinsa akan bayinsa?"
Anty Rady ta jefawa Suhailah tambayar cike da tsawa,don ita irin mutanan nan ne masu saurin
ɗaukar zafi. Suhailah ta faɗa jikin Anty Safiya wacce mamaki ya daskarar da ita ta saki kuka tana
cewa, "Don Allah Anty Rady ki yi haƙuri ba zan sake ba wallahi tun a yanzu na yi nadama,sharrin
shaɗain ne da zafin kishi ya kai ni ga biyewa huɗubar Jawahir."
Anty Rady ta ɗaga hannu za ta ɗauke Suhailah da mari,Anty Safiya ta yi saurin tarewa ta ce, "A'a
Rady wannan ba shine mafita ba yanzu dai ta tashi ta kintsa ta ci abinci,don da alamu ko karin safe
bata yi ba,idan ta gama sai mu yi magana da ita cikin tsanaki."
Anty Rady da ke huci ta gyaɗa kai cike da gamsuwa da maganar da Anty Safiya ta yi ta ce,
"Suhailah maza tashi ki kintsa kafin ki sanar da mu wanda ki ka taɓa gani a zuriyar mu yana bin
Bokaye don neman biyan buƙatarsa."
Suhailah jiki na rawa tabi umurninsu wajen tashi ta kintsa jikinta,har lokacin amma kuka ta ke yi
hawaye sun kasa daina zuba akan fuskarta. A haka ta gama shiryawa ba tare da ta iya yin wata aba
wai kwalliya ba,ta dai sanya wani haɗaɗɗan lace mai nauyin kuɗi. Kalar lace ɗin gray ne da
akaiwa ado da red and milk colour, sosai kalar lace ɗin da yanayin ɗinkin boubou da akaiwa rigar
na zamani ya amshi jikin Suhailah. Ta sanya ɗankunni manya da suka sake fiddo kyawunta.
Anty Rady ce ta miƙa mata kwalli tace ta sanya a idanunta,ta kuma tsaida waɗannan hawayen
hakanan. Suhailah ta amshi kwallin ta sanya a idanunta da zuwa lokacin sun kumbura sosai,ta aje
kwallin tana tashi daga gaban mirrow ɗin ta nufi kan sofa ta zauna. Jikinta a sanyaye yake da tarin
nadama da firgicin halin da za ta shiga idan Hajjah ta ga waɗannan layun,kuma aka ce wai ita
Suhailah ce ta amso su don ta binnesu da mugun nufi.Wasu hawayen masu zafi suka sake zubo
mata,ta bar su sukai ta zuba ba tare da tayi yinƙurin share su ba.
"Amshi maza ki ci ki shanye ruwan tea ɗin tas! Empty plate da cup kawai na ke son gani."
Anty Safiya ta yi maganar tana miƙawa Suhailah plate ɗin da ke hannunta,me ɗauke da zazzafan
Noodles da ta dafo mata. Ta soya mata wainar egg a sama tare haɗa mata ruwan tea me kauri.
Suhailah ta amsa ta aje daga kan sofan,ita kuma Anty Safiya ta aje cup ɗin tea ɗin ta juya zuwa
bakin gado ta zauna.
Anty Rady na zaune daga can gefe guda tana kallon Suhailah cike da takaici,don bata ga dalilin da
Suhailah za ta tashi hankalinta haka don Maleek zai sake aure ba.Sabida bata ga abinda ta nema ta
rasa ba,sannan duk wannan haukan kishin da take yi bama waje ɗaya za ta zauna da kishiyar
ba,hasalima ba gari ɗaya za su rayu ba to a wani dalili ne Suhailar za ta damu kanta har haka,har
tana ƙoƙarin jefa kanta a halaka?
Ita dai Suhailah da ƙyar take tura Noodles ɗin sabida gaba ɗaya bata cikin nutsuwar zuciya da ta
gangar jikinta.Hakanan dai ta dinga turawa tana kora ruwan tea ɗin,sai ga shi ta tada plate ɗin
Noodles ɗin baki ɗaya. Ta aje cup ɗin tea ɗin bayan ta shanye tana me yin hamdala,tare da ɗaga
ido ta saci duban su Anty Rady da hankalinsu ke kanta,ta maida kan ƙasa tana ji tamkar ƙasa ta
tsage ta shige,don su kansu kunyar haɗa ido ta ke yi dasu bare kuma su Hajjah.
Anty Safiya ce ta taso daga bakin gadon ta dawo kusa da Suhailah ta zauna,hannunta riƙe da
waɗannan layun biyu ta dubi Suhailah ta ce, "Suhailah kin ga dai daga ni har Rady babu bare a
nan,don haka ki ji tsoran Allah ki sanar damu gaskiyar yadda aka yi waɗannan layun suka zo gare
ki,kuma wani ƙudiri ku ke dashi akan birne su?"
Anty Safiya ta yi tambayar tana tsare Suhailah da idanunta babu ko kiftawa,Suhailah da kanta ke
ƙasa ta sake dankwafar da kanta hawaye na zuba daga idanunta. Takaicin kanta da kanta na sake
lulluɓe zuciyarta,ta yi magana cikin muryar kuka ta zayyane musu duk irin huɗubar da Jawahir ta
dinga mata akan auren Maleek ɗin,har kawo kuɗin da ta baiwa Jawahir ɗin ta je mata wajen Boka
ta amso mata asirin,ta ƙare maganar da cewa, "Wallahi Anty Safiya ba ni ce da kaina na amso su
ba,hasalima ban taɓa zuwa wajen kowa neman taimako ba,ita ce ta je ta amso ta kuma sanar da ni
yadda za a birne su bayan an ɗaura auren,ku taimake ni ku rufa min asiri kar ku sanar da
Hajjah,wallahi ba zan sake ba na tuba na yi nadama wallahi."
Suhailah ta yi maganar tana kuka sosai cike da magiya,amma sam hakan bai sa su Anty Rady jin
tausayinta ba,sai ma tsawa da Anty Rady ta daka mata tana tambayarta wacece Jawahir? Suhailah
ta dubi Anty Rady jikinta har rawa ya ke yi wajen bata amsa ta ce, "Makwafciyata ce a can
Abuja."
"Suhailah wai meyasa ke baki da hankali ne,baki san inda duniya ta sanya gaba ba,baki san illah
da sharrin biyewa ƙawaye da ɗaukar huɗubobinsu na sharri ba ko? Uban wa ya gaya miki ƙaunar
ki take yi da har za ta ɗauraki a irin wannan layin ke kuma ki hau kai? Ba ƙaunarki ta ke yi ba so
ta ke yi ki rasa aurenki don ubanki."
Anty Rady ta yi maganar tana ji tamkar ta taso daga inda take zaune ta kwaɗe Suhailah da mari.
Anty Safiya ta amshe maganar da cewa, "Suhailah kina da wauta gaskiya,kuma baki da wayau ne
ke a rayuwarki ko kaɗan. Shirme da sakarci kawai ki ka sanya a gaba sai zafin kishinki na banza
da wofi,sabida duk zafin kishin mace ba ya hana namiji ƙara aure sai dai idan bai so ba,ko kuma
Allah bai zana masa cikin littafin ƙaddararsa ba.Don haka ki dawo cikin hankalinki ki yi gaggawar
tuba zuwa ga Mahaliccinki, ki gane cewa ƙarin auren da Maleek ya yi bai yi don ya daina son ki
ba. Kuma ba don ba ki haihu bane haka Allah ya rubuta masa cikin littafin ƙaddararsa,sannan ki
gane cewa Hajjah ba za ta taɓa goya baya ayi abunda da zai cutar da rayuwarki ba Suhailah,domin
Hajjah Uwace a gareki da ta baki dukkan gata,ko kaɗan bata cancanci mummunar butulci daga
gare ki ba. Wanda har za a ɗauraki akan layin da za ki iya cutar da gudan jininta,kuma da yake ke
ɗin sakaryace da banzan kishi ya rufe idanunki,ki amince ki bi wannan turbar. To ki sani cewa
kamar Inna Dije da Hajjah sun ga waɗannan layun,don ni ban amince da nadamar da ki ke cewa
kin yi ba,dole su zama shaida don idan wani abu ya faru da tilon ɗan ta ko ƴar mutane ke za a fara
tuhuma."
Anty Safiya na kai aya Suhailah ta sake rushewa da matsanancin kuka,ita kuma Anty Rady ta
ɗaura da cewa, "Yo in banda abin ta ma ni da nake da kishiyoyi har biyu ta taɓa ji ko ganin koda
wasa na ce zan bi hanyar bin Boka ko Malaman tsubbu? Ban taɓa ba kuma bana fata Allah ya
nuna min ranar da zan siyar da imani na sabida ɗa Namiji.Ki nutsu Suhailah ki maida lamuranki
zuwa ga Allah shi kaɗai! Ki kuma gode ma ni'imar da ya yi miki na samun miji nagari kamar
Maleek. Ke ƴar gata ce Suhailah da Ubangiji ya yi miki ni'imomi da dama cikin rayuwarki. Kar ki
manta cewa akwai mata da yawa da basu fi ƙarfin ci da sha ba ma a gidajen aurensu,amma a
hakan mazajensu ke zuwa su jajibo auren kuma su zauna da kishiyoyin dole, basu da yadda suka
iya. Ke kuwa kina cikin daula da gatar uwar mijin da ta raineki da hannunta,ta baki dukkan gata da
kulawar da ko iyayenki na raye ba lallai ki samu hakan daga gare su ba. Sannan bata barki a haka
ba sai da ta ɗauki tilon ɗanta ƙwaya ɗaya da ta mallaka,ta baki shi a matsayin miji ya kuma amshe
ki da hannun bibiyu,tare da baki soyayyarsa da dukkan gata da kulawa. Ya mallaka miki zuciyarsa
da yardansa tare da mayar da ke tauraruwa a idon mata ƴan uwanki,domin Maleek bai rage ki ta
ko'ina ba har kawo yau da aka ɗaura masa aure, bai nuna gazawa akanki wajen rarrashi da son
ganin kin kwantar da hankalinki ba. A she wannan kaɗai bai isa yasa ki danne duk wani zafin kishi
ki rungumi ƙaddara ba Suhailah? Kina tunanin Hajjah za ta iya cutar da ke ko cutar da gudan
jininta ne? Ki ji tsoron Allah wallahi Suhailah. In kuwa ba haka ba za ki zo kina nadamar da ba za
ta anfana miki komi ba sai danasani,domin kishi idan ya yi wa mace yawa babu inda ya ke kaita
sai ga halaka,daga ƙarshe idan ta cika matsawa ma da nuna haukar kishin sai dai mijin ya sake ta.
Don haka ya rage naki ki shiga hankalinki ki watsar da ƙawanyen banza ki kama mijinki,ko kuma
ki cigaba da biyewa ƙawar bariki ta kai ki ta baro.kin yi ilimin addini kin san hukuncin wanda ya
mutu yana haɗa Allah da waninsa,don haka ba sai an sake miki dogon wa'azi ba,idan za ki dawo
cikin hankalinki ki dawo kawai,kishiya ba kanki farau ba kuma ba za a rufe ƙofa daga kanki ba.
Don haka ki rungumi ƙaddaranku ke da shi domin ku zauna lafiya,daga ƙarshe ina miki fatan
Ubangiji ya rage miki wannan zafin kishi da wautar da ke damun kwanyarki."
Anty Rady ta kai ƙarshen maganar idanunta a kan Suhailah, wacce ke ta faman kuka maganganun
Anty Rady na shiga jikinta, tare da motsa zuciyarta matuƙa,dukkanin jikinta ya yi wani irin sanyi
nadama na lulluɓe zuciyarta.
"Yanzu sai ki tashi mu ɗunguma baki ɗaya zuwa gidan Hajjah,don a nuna musu wannan layun
kafin a ƙona su tunda Ubangiji da bai kasance me zalintar bayinsa ba, bai baki ikon aiwatar da
mummunar ƙudirinku ba, ya jefo mu gidan muka ga abinda ki ke shirin birnewa. Don haka maza
ki tashi ki ɗakko mayafi mu wuce,dama ni na tuƙo mu a motar Hajjah don haka sai mu ɗunguma
mu koma can,ki zauna a can gidan ma kawai har a ƙare hidimar komi Amarya ta tare a
ɗakinta,kafin ki tattara ki bar mata garin baki ɗaya. Saura idan kin koma cam ki cigaba da baiwa
ita ƙawar taki fuskar da har za ta sake nufo ki da zancen zuwa wajen Boka. Don Allah ki biye
mata kar ki fasa Suhailah,ina me tabbatar miki da cewa sai kin yi biyu babu in dai kin ce ke
huɗubar ƙawaye za ki riƙa ɗauka."
Suhailah dai ba baka sai kunni kuka kawai ta ke ta rafsawa,a haka ta tashi ta ɗakko mayafinta suka
fito tare da su Anty Rady. Bayan sun ɗaukar mata kaya kala biyu da duk abinda za ta buƙata,sun
sanya shi cikin ƙaramar Luggage. A hankali Suhailah ke biye da bayansu suna tako stairs ɗin
benan don sauka zuwa ƙasa,hannunta riƙe da wayarta da ke faman vibrate alamun shigowar kira
amma ta kasa koda kallon wayar bare ta ga me kiran. Zuciyarta dai na raya mata cewa Jawahir ce
ke kira ta ji ko ta birne layun kamar yadda suka rabu za ta birne ɗin,shiyasa ta kasa duban wayar
ma bare har ta ɗaga kiran.
Sun sakko downstairs ɗin kenan shi kuma Maleek Ado yana shigowa cikin falon,hannunsa riƙe da
babbar rigarsa da ya cire don ba ma'abocin sanya babbar riga bane shi tun fil-azal ɗinsa.
Ya kalli su Anty Safiya lokacin da ya ƙariso cikin falon ya ce, "Sis ki ce ku Hajjah ta turo dannar
ƙirjin?"
Ya yi maganar cike da barkwanci idanunsa na kan Suhailah,wacce ta samu gefen hannun kujera ta
zauna,sabida ciwan da kanta ke yi me tsanani. Anty Safiya sai ta saki murmushi tana cewa, "Ango
ka sha ƙamshi,sai yanzu ku ke dawowa daga wajen Reception ɗin? Ai mu Hajjah ta turo mu danne
ƙirjin wannan sakaryar uwargidan taka mai ban haushi, gashi kuma ƙirjin ba zai dannu a nan ba
sai mun dangana da gidan Hajjah ba."
Maleek ya saki murmushin da ba kasafai ake gani akan fuskar ba,har lokacin idanunsa na kan
Suhailah wacce ta kasa dubansa, ya ɗan taɓe baki kaɗan kafin ya ce, "To fah! Ki ce har yanzu dai
babyn tawa ta ƙi ta ji rarrashi, sai ku je can ɗin ai watakila Hajjar tata ta iya mata tunda ni ma dai
anƙi aji nawa rarrashin."
Maleek ya kai ƙarshen maganar yana takawa don isa wajen Suhailah,suna kuma gaisawa da Anty
Radiya da ke faman jifan Suhailah da harara. Sai kawai su kai gaba abinsu zuwa waje Anty Safiya
na sanarwa Suhailah cewa, ta same su a mota idan sun gama da Maleek ɗin,daga haka suka fice
daga cikin falon baki ɗaya zuwa waje.......✍🏻
#Ɗansabo ce#
[12/14, 3:44 PM] +234 703 040 9541: Littafin TAIMIYYAH paid book ne,ga duk wanda ta
tsincesa a kowani irin group ne,kiji tsoran Allah karki karanta sai kin biya 500 naira only.
Za ku iya min magana ta wannan number ɗin 08167768704, ko kuma ku turo kuɗin ku kai tsaye ta
wannan account ɗin 0504192664 aisha ibrahim dansabo GTbank.*
Masu turo credit za ku turo katin MTN na 500 ta wannan line ɗin 08167768704.
_Ina ƴan kasuwa masu buƙatar a tallata muku hajar ku? Maza ku garzayo da kuɗi ƙalilan a tallata
muku kayan siyarwanku sai dai kawai ku ji ana kiran waya don buƙatan sayan kayan ku,ku
tuntuɓeni ta layina kamar haka 08167768704._
*69*
Maleek ya ƙarisa wajen da Suhailah ke zaune yana me zama cikin seater ɗin,ya miƙa hannu ya
janyota zuwa jikinsa baki ɗaya ya rungumeta. Take wani irin daddaɗan ƙamshi ya bugi hancin
Suhailah,wani irin ƙamshi wanda daga ji kasan daga jikin mace aka same shi,hakan yasa zuciyarta
bugawa da ƙarfin gaske. Wani irin kibiyar kishi ya soke ta a ƙahon zuci, sai ta fara kici-kicin raba
jikinta dana Maleek ɗin amma ta kasa,sabida wani irin riƙo ya yi mata da ba za ta iya ƙwatar kanta
ba. Ganin hakan sai ta sanya masa kuka tana jin wani irin haushinsa na lulluɓe zuciyarta, shi ko
Maleek sai ya ɗaura kansa bisa kafaɗunta tare da kai bakinsa saitin kunnin Suhailah na dama ya
ce, "Please! Wife calm down mana, ki taimakeni ki kwantar min da hankalinki Suhailah. Har cikin
zuciyata bana jin daɗin ganinki kina wannan kukan,duk kin bi kin tsangwami kanki kin ɗaga
hankalinki,duk sabida na yi aure Suhailah? Wa ya gaya miki don na yi aure wani abu ya ragu a
zuciyata game da yadda na ke ƙaunarki? Ban ƙara aure don in sanya ki a damuwa ba
Suhailah,kuma ba don na daina son ki da ƙaunarki bane sai don haka ƙaddara ta zana
min,dukkaninku ina son ku kuma zan rayu da ku har ƙarshen numfashi,don haka ki kwantar da
hankali ki bani goyan baya ne wajen ganin na tabbatar da adalci a tsakaninku kin ji wife?"
Maleek ya yi maganar cikin murya me cike da rarrashi da nuna tsananin kulawa,amma hakan bai
sanyaya zuciyar Suhailah ba,sai ma saƙe zafafa zuciyar kalaman Maleek ɗin suka yi. Sabida ya
tabbatar mata da cewa tare da watan ta za su rayu,har yana faɗin har ƙarshen numfashi. Ta saki
hawaye masu zafi daga idanunta,suna sauka a jikin Maleek yana jin ɗuminsu na keto rigarsa zuwa
fatar jikinsa. Ya kai hannu ya ɗago fuskar Suhailah daga jikinsa yana me tsura mata manyan
idanunsa,ta ɗauke nata idanun da sauri daga dubansa domin bata so wannan kallon ya yi tasiri a
kanta. Maleek sai ya rabu da ita bai matsa akan cewa sai sun haɗa idanunba,ya miƙa hannun ya
fara wiffing tears ɗin da ke zirarowa daga idanunta,ganin hakan yasa Suhailah rintse idanun baki
ɗaya tana me sake shigewa cikin jikinsa.
Ɗumin da jikinta ya yi sosai yasa Maleek sake matseta a jikinsa ya ce, "Please Suhailah ki
taimakeni ki kuma taimaki kanki ki daina wannan kukan haka nan,kin ji jikinki na son kamuwa da
zazzaɓi kuma na san duk yawan koke-koken da kike yi ne."
Nan ma Suhailah shiru ta yi bata tanka shi ba,ya cigaba da rarrashinta da duk salon da ya san zai
yi tasiri akanta,amma sam Suhailah bata nuna masa cewa salonsa ya shige ta ba. Hakan ya sa
Maleek zareta daga jikinsa yana bata umurnin tashi ta bi su Anty Safiya da ke jiranta a waje cikin
mota.
Suhailah ta miƙe daga kan jikinsa tana balla masa harara lokacin da ya yi kissing hannunta da ke
riƙe nasa, wajen taimaka mata tashi tsaye,ta zare hannun tana fara takawa don ficewa daga falon
baki ɗaya. Maleek ya bi bayanta da kallo zuciyarsa na motsawa da tausayinta me tsanani,don ya fi
kowa sanin yadda Suhailah ke ƙaunarsa da kishinsa,ya san dama sai an sha fama kafin zuciyarta ta
risina har ta rungumi ƙaddaran ƙarin auren da ya yi.
Ya zame jikinsa ya kwantar a cikin seater ɗin yana me lumshe idanunsa,moment ɗinsu da
TAIMIYYAH na ɗazu na dawo masa daki-daki. Wani irin fitinan ƙaunarta da shauƙin son
kasancewa da ita na sake azalzalar zuciyarsa. Ya zaro wayarsa daga aljihu domin danna mata
kira,amma sai kira ya shigo daga cikin ɗaya wayarsa,hakan yasa shi fasa kiranta ya yi receiving
call ɗin da ya shigo masa.
Suhailah kuwa tana isa bakin motar Hajjah da Anty Safiya ta zo da ita,sai ta buɗe back seat ta
shige zuciyarta na cigaba da shiga ruɗu da nadama me tarin yawa. Gaba ɗaya fargaba da kunyar
yadda za ta iya duban idanun Hajjah ke sake dagula lissafinta da jefa zuciyarta cikin tsaka me
wuya.
Har suka isa Gonar Ganye gidan Hajjah zuciyarta ba ta huta ba,suna isa ana kiran sallar la'asar a
masallacin da ke ƙasan gidan Hajjah. Suhailah da ƙyar ta iya sanyo ƙafarta waje ta fito daga cikin
motar,tana ji tamkar ƙafafun ba za su iya ɗaukar nauyin gangar jikinta ba, sabida yadda su kai
wani mugun sanyi. A haka ta dinga tafiya cikin slow tana biye da bayan su Anty Rady zuwa cikin
gidan Hajjah. Babu wasu mutane sosai sabida ita ba yau take nata taron ba,sai gobe ne za ta tara
mutane ayi walima tunda a gidanta za a sauke Amarya ta kwana,sai bayan an tara mutane anyi
walima ne sai a wuce da Amarya zuwa GRA ɗakinta.
_____________
Daga can Gyallesu kuwa gidan su Amarya TAIMIYYAH,bayan an idar da la'asar ne me make-up
ta sake gyare fuskar Amarya TAIMIYYAH. Wacce ta sake sauya shiga a karo na uku cikin wani
haɗaɗɗen lace mara nauyi, kalar red and black da ya yi masifar amsar jikinta. Bayan an kafa mata
hular ɗankwalin lace ɗin kamar yadda ake yi a yanzu,sai aka yane jikinta da wani irin haɗaɗɗen
mayafi tamkar naɗin da akewa sari.TAIMIYYAH ta yi kyau har ta gaji su Yasmeen sai kashe mata
hotuna suke yi,suna yana yaba kyawun da ta yi cikin kayan. Anty Laurat ce kawai ba za ta samu yi
mata rakiya ba sabida da ita aka tafi kai Zuhurah Bauchi,sai su Zee da su Maryam Sunusi ne
kawai za su yiwa TAIMIYYAH rakiya zuwa gidan Hajjah. Dukkaninsu sun sauya shiga cikin
kaya na alfarma sun sha make-up na kece raini.
Shigowar Ummie cikin ɗakin yasa TAIMIYYAH ɗaga ido ta dubi Ummien,wacce ta cake ita ma
cikin rantsatstsen lace da ya yi mata mugun kyau,sai ta koma tamkar budurwa irin ƴar 25 yrs
ɗinnan.
"To Amarya sai ki ta so ga motoci can sun iso,za a miƙa ki zuwa gidan miji."
TAIMIYYAH lokacin da suka fito zuwa falon Ummie,sun samu duk su Anty Mardy suna jiran
fitowarsu ne, don a wuce da ita zuwa part ɗin Iyah su yi sallama da juna.
Wani irin ƙaramin film ne ya gudana a part ɗin Iyah,na yadda rabuwarta da TAIMIYYAH zai
kasance, wacce ta ƙanƙame Iyah tana kuka tamkar za ta shiɗe,tana kuka Iyah na kuka kuma cikin
kukan Iyah ke faman rattafo ma TAIMIYYAH addu'o'in sanya albarka.Duk wanda ke ɗakin sai da
ya taya su kuka,sannan kuma ya dara sabida yadda suke kuka tsakanin junansu,da ƙyar aka zare
TAIMIYYAH daga jikin Iyah aka fita da ita.Yasmeen kanta tana kuka ne tana yin musu vedio don
ba ƙaramin tausayin TAIMIYYAH ta ji ba,sabida kowa ya san yadda suke da Iyah zai san cewa
rabuwarsu ba zai zo ta sauƙi ba dama.
Lokacin da aka fito da TAIMIYYAH ita kuma Basmah za a shiga da ita don sake yin sallama da
Iyah ita ma,sabida kusan duk a tare motocin ɗaukar Amaren suka hallara. Ita Basmah can Ƙwarbai
gidan Hajiyar Nass za a fara kaita ita ma ,sai a gobe za a ɗakko ta daga can a kai ta Gonar Ganye
gidan Nass ɗin da ya gina.
Daga yanayin manyan motocin da ke fake a harabar gidan za ka san cewa akwai ratar arziƙi
tsakanin motocin da za su ɗauki TAIMIYYAH da wanda za a ɗauki su Basmah. Ƙawayen Basmah
irin su Sharifa duk sai suka raina arziƙin Nass ɗin,sabida motocin sun ruɗe su don kana kallo
kasan bana ƙananun masu kuɗi bane,ko wace mota ka kallah za ka ganta sabuwa dal ce.
Kallo bai koma sama ba ma sai da motar da za ta ɗauki Amarya TAIMIYYAH ta ƙariso cikin
compound ɗin gidan. Amintaccen driver ɗin Maleek Ado me suna Yusuf ke janye da motar. Wata
iriyar mota da kaf su Sharifa ba su taɓa cin karo da motar da ta ɗauki hankalinsu irin ta ba,motar
ba wani girma ne da ita ba amma kallo ɗaya za ka mata ka san bana ƙananun kuɗi bace,sabuwa ce
dal don ranar aka fara hawanta. Maleek ne ya yi ordern su guda biyu tun daga ƙasar Amurka aka
zo masa da su,domin ya mallakawa matan nasa su kyauta halak malak,shiyasa ya yanke shawaran
a ɗakko masa Amaryarsa TAIMIYYAH a cikin nata.
Surutu ya dinga tashi ana zuzuta irin gidan daular da za a kai gurguwa TAIMIYYAH,kamar yadda
su Sharifa suka dinga faɗin kalmar suna cewa "Kai! Yanzu gurguwace ta auri attajirin mutum irin
haka?"
Suka dinga mamaki suna jinjina lamarin a tsakaninsu kai kace ita gurguwar ba mutum bace,da
Ubangiji ba zai azurta ta kamar yadda ya ke azurta sauran bayinsa ba.
Ita dai TAIMIYYAH bata ma san ana yi ba don kukanta kawai ta ke sha,ko kalar motar aka tsareta
ma ta faɗi ba za ta iya ba don ba abinda ke gabanta kenan ba. Haka Yusuf ya ja motar suka fice
daga cikin compound ɗin gidan,Yasmeen da ke daga gefen TAIMIYYAH riƙe da hannunta na
faman rarrashi,ita ma Anty Mardiyyah da Ummie da suke ta ɗaya gefen na taya Yasmeen
rarrashin. Guggo Lami da ke matsayin ƙanwar su Baba Sani ita ta kame a front seat su Zee da su
Maryam Sunusi suna can cikin ɗaya motar Maleek, wacce ya zo da ita gidan ɗazu. A ciki aka
kwashesu su huɗu daga Maryam sai Zee da Bushira,sai Nusaiba cousine Sis ɗin su TAIMIYYAH.
__________
*Gonar Ganye.*
Daga haka Hajjah ta juya ta bar musu ɗakin,tana jiyo kukan da Suhailah ta saki zuciyarta na sake
ɗaukar zafi da ita. Inna Dije ta dubi Suhailah tana me kai hannu ta bige bakin kukan, cikin zallar
fushi da ɓacin rai ta ce, "Za ki mana shiru ko sai na ɗauke ki da mari, ƴar banzar Yarinya mare jin
magana. Duk irin Nasihar da aka dinga miki ashe ta bayan kunninki suke bi suna fita. Kin bani
kunya Suhailah sannan kin ci amanar ƙauna da tarbiyar da Hajjah ta baki,don baki taso kin ga tana
aikata mummunar abu irin wannan ba,kada ki bari ƙawayen bariki su kai ki su baro Suhailah. Tun
wuri ki dawo cikin hankalinki ki kama mijinki tare da rungumar ƙaddararki da hannu biyu,kishi ba
hauka bane Suhailah don dukkkanmu ni da Radiya gata nan duk kishiyoyin gare mu,amma kin
taɓa ji ko ganin ance ga mu a hanyar amso asiri don mu cutar da su?"
Suhailah ta girgiza kai hawayen tsananin nadama na sake biyo fuskarta,Inna Dije ta cigaba da
cewa, "To ki shiga hankalinki tun wuri, duk wata ƙawa da ba za ta saki a hanyar bin Allah ba ki yi
gaggawar rabuwa da ita,don ba mai ƙaunar ki bace. In da ace kina dagewa da addu'a tare da roƙon
Allah akan ya rage miki wannan zafin kishin,da tuni kin samu nutsuwar zuciyarki. Maleek na
ƙaunarki Suhailah don haka ki yi anfani da damarki wajen kwantar da hankalinki,tun yana
bibiyarki yana rarrashi kafin ki kai shi bango ya tattaraki ke da mummunar kishin banzar ki ya
watsar a gefe guda.Don yanzu sabuwar Amarya ya yi idan kika cigaba da wannan sokoncin da
iskancin da ki ke yi ,wallahi tun kina bashi tausayi yana rarrashinki kina botsarewa, tuh fa zai fita
daga sabgarki ne ya rungumi Amaryarsa da za ta faranta ransa, don haka ki dawo cikin hankalinki
ki aje duk wani zafin kishi. Ki rumgumi mijinki tare da tarairayarsa, ki bashi goyan baya wajen
tabbatar da adalci a tsakaninku. Duk lokacin da ki ka ji kishin ya taso miki ki dinga yawan nanata
wannan addu'ar ' _Allahummah Atinifuh sanahtaqwaha_ wazakkiha Antah Khairumanzakkahah_
Anta waliyyuha_ wamaulahah!_ ' sannan ki dinga yawan faɗin ' _Allahummah lah
sahlan_illahmaja'altuhu sahlan_wa'antah taj'alul haznah_ izahshi'itah sahlan!'_
Idan har ki ka dagewa faɗin waɗannan addu'o'in a duk lokacin da ki ka ji kishin ya taso miki,tuh
ina tabbatar miki da cewa Ubangiji zai sanyaya zuciyarki. Amma bin Boka ko kauce hanya babu
in da zai jefa rayuwarki sai a halaka da danasani marar iyaka. Ga ɗinbin zunubin da zai iya kai ki
wuta,kuma ki daumama a cikinta idan har kika mutu kina shirka baki tuba ba, to ina riba
Suhailah? Ki ji tsoran Allah ki kuma gode masa da ya yi miki baiwa da ni'imar samun miji da
suruka ta gari. Wanda a wannan zamanin da muke ciki samun irin su ya yi ƙaranci. Wallahi Hajjah
bata cancanci butulci daga gare ki ba,don wannan butulci ki ke son nuna mata tun da kin ɗakko
hanyar cutar da gudan jininta da baiwar Allahn da bata ji ba bata gani ba. Sabida Allah ne ya
ƙaddara cewa Maleek shi ne zai zamo mijinta, don haka ya rage naki ki ɗauki dukkanin huɗubobi
da Nasihun da ake miki,ko kuma ki watsar ki kama hanyar da kike ganin ya dace dake. Amma fa
ki sani daga randa kika jefa rayuwarki cikin wani hali kada ki nufo kowa a cikin mu,da sunan
neman ɗauki ko baki shawara. Ki tashi ki je ki wanko fuskarki ki sauya shiga don baƙi ƴan kawo
Amarya suna kan hanyar isowa,kuma lallai ki cigaba da roƙan Hajjah gafara akan ta yafe miki don
ranta a mugun ɓace yake da wannan lamarin da k ika nemi aikatawa me muni."
Inna Dije ta kai ƙarshen maganar tana jin ɗaci da takaicin abinda Suhailah ta yi, ko da wasa bata
taɓa kawo cewa za a iya zuga Suhailah ta kauce hanya sabida zafin kishi ba. Anty Rady ita ce ta
cigaba da yiwa Suhailah faɗa,da nuna mata illar abinda ta so aikatawa,tare da bata misalai na
waɗanda aka yi wa kishiyoyi,amma suka rungumi ƙaddararsu suka kuma zauna lafiya da
mazajensu. Suhailah sosai ta ke jin tasirin Nasihun da suke mata na ratsa zuciyarta, nadama me
tarin yawa na tasowa na sake mamaye zuciyarta, tana jin ɗaci da ƙunci akan yadda ta so sanya
kanta cikin halaka. Burinta kawai a yanzu Hajjah ta sakko daga fishin da take hangowa a cikin
ƙwayar idanunta. Domin wani irin fargaba me tarin yawa take ji, na yadda Hajjah ta ke dojewa
bata so ma ana yawan matsa mata da faɗa akan abinda ta so aikatawan,ta fi kowa sanin halin
Hajjah idan tana irin hakan to ba ƙaramin bango mutum ya kai ta ba,kuma matakin da za ta ɗauka
ba zai yi mata kyau ba ita ta san hakan. Wasu hawaye masu zafi suka sake gangarowa daga idanun
Suhailah, ta miƙe da ƙyar tana jin jiri na neman kada ita, hakan yasa Anty Rady taimaka mata ta
riƙe hannunta suka nufi ƙofar shiga bathroom, don Suhailah ta sako wanka ta zo ta shirya kafin
baƙi su iso.
Suhailah ce a zaune ta gama kintsawa cikin wani haɗaɗɗen Voile lace me nauyin kuɗi,wanda akai
wa ɗinkin straight gown da ya zauna a jikinta. Fuskarta ya sha light make-up da ya taimaka wajen
ɓoye halin da fuskarta ya shiga sabida yawan kukan da ta sha. Ta yi kyau sosai duk da cewa
idanunta har lokacin basu sace daga kumburin da suka yi ba,amma hakan bai hana kyawun da ta yi
bayyana ba.
Ta miƙa hannu ta ɗakko sarƙarta na gwal me asalin kyau ta sanya a wuyarta,kunninta na haskawa
da ƙyallin ɗankunnin gwal ɗin. Hannunta ta zurawa bangles guda biyu duk na gwal, nan da nan ta
sake haskawa da wani irin kyawu me sanyi. Rashin fara'ar da ke kan fuskarta kaɗai ne ya kawo
cikas wajen sake haska annurin kyawun da ta yi ɗin, ta miƙe tana maida box ɗin sarƙarta cikin
jaka, daidai kuma lokacin da wata mata me zaƙin murya ta saki wani irin guɗa, wanda sautinsa ya
ratso har cikin ɗakin da Suhailah ta ke ya shiga kunnuwanta. Sai ta yi saurin sakin jakar hannunta
tana me dafe ƙirjinta da ya buga da ƙarfin gaske, ko ba a faɗi ba ta san cewa Amaren ne suka iso.
Sai ta rintse idanunta tana ambato sunan Allah da karanto addu'ar da Inna Dije ta horeta da yi aduk
lokacin da ta ji kishin ya taso mata.
A hankali ta taka zuwa bakin sofan da ke ɗakin ta zauna,tana cigaba da nanata addu'ar cikin
zuciyarta. Kunnuwanta na cigaba da jiyo guɗar da ake saki tare da jiyo hayaniyan mutanen da
suka rako Amaryar,sai ta ji ina ma bata yadda ta biyo su Anty Safiya ba, da ta sani ta yi zamanta a
can gidanta da yanzu duk ba za ta ji irin waɗannan ayyiyikan ba.
Ta dafe saitin zuciyarta da ke cigaba da bugawa da ƙarfi,tana cigaba da nanata 'Allummah lah
sahlan' har zuwa ƙarshe. A hankali sai ta fara jin sauƙi a cikin zuciyarta, ta dinga jin ƙuncin da ya
danne zuciyarta na raguwa sosai,ta cigaba da zama bisa Sofan tana cigaba da jiyo hayaniyan ƴan
kawo Amaryar, har zuwa lokacin da Anty Safiya ta shigo ɗakin. Ta isa wajen da Suhailah ke zaune
ta zauna tana me kamo hannunta ta riƙe tana cewa, "Kai! Ma Sha Allah! Uwargidan Maleek
gaskiya kin yi kyau matuƙa, saurinki kawai ki saki ranki da zuciyarki Suhailah. Kin ga Amarya ta
iso mutane sun cika gida don haka kar ki yadda ki yi wani abu da zai fallasa halin da zuciyarki ke
ciki.Daurewa ake yi a nuna jarumta wajen danne duk wani kishi da za ki ji,kar ki yadda ki yi
abinda za a tafi da ke a baki ana Allah wadai da zafin kishinki. Don Allah ki ba marar ɗa kunya
daga nan har a watse taron da za a yi zuwa gobe,hakan zai sanyaya zuciyar Hajjah ta jin zafinki a
zuciyarta kin ji ko?"
Suhailah ta gyaɗa kai cike da gamsuwa ta ce, "In Sha Allah! Anty Safiya zan yi duk yadda ku ka
ce, ku taya ni ba Hajjah haƙury don Allah, wallahi na yi nadamar biyewa Jawahir kuma ba zan
sake yin kowace irin alaƙa da ita ba."
"In Sha Allah! Suhailah za mu taya ki ba Hajjah haƙury, kuma na ji daɗin yadda ki kai saurin gane
kuskuren da kika so tafkawa,sai ki roƙi Ubangiji ya yafe miki don shi ne babban wanda ki kai wa
laifi,tunda shi ki kai wa kishiya wajen yadda da cewa akwai wanda zai iya miki wani abu bayan
shi. Don haka ki yi gaggawar tuba izuwa gare shi,Allah ya yaye miki duk wani zafin kishi da zai
kai ki ga halaka."
Suhailah ta amsa da cewa, "Ameen." Cikin sanyin murya me nuna tsananin nadamar da zuciyarta
ke ciki. Daga can ƙasar zuciyarta kuwa so take yi kawai ta yi ido huɗu da Amaryar Maleek ta ga
wace ce ita, da me ta fita da har ya aurota a matsayin gurguwarta?
Anty Safiya ce ta ja Suhailah suka fice zuwa can babbar kitchen ɗin Hajjah, in da ake ta hidimar
kwasan nau'ikan abincin da aka shirya don tarban Amaren. Haɗaɗɗun girke-girke ne zuwa
gasassun kaji da naman rago da aka kawo daga in da aka kai gashin, wajen wani shahararren me
yin gashin da ke can cikin GRA. Da Suhailah akai ta hidimar kammala abubuwan ana baiwa masu
aiki suna wucewa da shi ɗakin da aka sauke Amarya TAIMIYYAH. Wanda akai musu masauki a
cikin ɗaya daga cikin Bedrooms ɗin Hajjah, wanda ba a ma cika amfani da shi ba, sabida 4
bedroom ne ta ke da su kuma wannan da aka sauke Amaren a ciki shi ne daga can ƙarshen
cooridor ɗin da Bedrooms ɗin Hajjah su ke..........✍🏻
#Ɗansabo ce#
[12/14, 3:44 PM] +234 703 040 9541: Littafin TAIMIYYAH paid book ne,ga duk wanda ta
tsincesa a kowani irin group ne,kiji tsoran Allah karki karanta sai kin biya 500 naira only.
Za ku iya min magana ta wannan number ɗin 08167768704, ko kuma ku turo kuɗin ku kai tsaye ta
wannan account ɗin 0504192664 aisha ibrahim dansabo GTbank.*
Masu turo credit za ku turo katin MTN na 500 ta wannan line ɗin 08167768704.
_Ina ƴan kasuwa masu buƙatar a tallata muku hajar ku? Maza ku garzayo da kuɗi ƙalilan a tallata
muku kayan siyarwanku sai dai kawai ku ji ana kiran waya don buƙatan sayan kayan ku,ku
tuntuɓeni ta layina kamar haka 08167768704._
*70*
Daga can ɗakin da aka sauke Amarya TAIMIYYAH, ita ce zaune daga tsakiyar gadon har lokacin
kuka take yi mara sauti. Su Ummie da su Anty Mardy da suka kawo ta duk sun juya sai aka barta
tare da Guggo Lami, sai su Yasmeen da su Maryam su ma duk kwana za su yi sai gobe bayan an
gudanar walima anyi buɗan kai sannan sai su raka TAIMIYYAH zuwa ɗakin ta.
Tarba ce aka yi musu irin na girma da karamci, wanda ya bayyanawa su Yasmeen cewa da gaske
fa gidan girma da arziƙi TAIMIYYAH ta shigo. Irin gidan da suka san ƙima da darajar karrama
mutane, don babu abinda ba a aje musu ba na nau'inka cima da abubuwan sha, babu ne kawai ba a
aje ba ga zallar tarairayan da ake nuna musu tamkar za a ɗauki zani a goya su. Amarya
TAIMIYYAH duk yadda ta dinga noƙewa tana jin kunya haka Anty Safiya ta janye ta zuwa
bedroom ɗin Hajjah, aka cika gabanta da cima kala-kala da abubuwan sha na musamman da
Hajjah ta tanadar dominta. Hajjah da kanta ta tsare ta akan sai ta ci wani gashin naman rago da ta
sanya aka yi sa musamman domin TAIMIYYAH, wanda akai anfani da wani irin sirrin magani me
inganci a cikinsa.
Duk kunyar da TAIMIYYAH ke ji haka nan ta daure ta ci naman, wanda ba mai yawa sosai bane
dama aka yi sa,tunda don cin ta ita kaɗai aka gasa dominta. Bayan Hajjah ta ga cewa ta cinye
naman ne ta fiddo wani ƙaramin gora me ɗauke da wani irin tsumi da aka kawo mata shi daga
Sokoto, ta miƙawa TAIMIYYAH tana cewa, "Ungo shanye wannan ki bani gorar Zaynab,ni
wannan kunyar duk ki aje ta gefe ni uwa ce a gareki ba suruka ba,yadda ki ka ɗauki Iyah haka na
ke so ki ɗauke ni kin ji?"
TAIMIYYAH ta gyaɗa kai a hankali tana sake yin ƙasa da kanta,don ba ta ji wannan kunyar da
take ji na Hajjah a yanzu zai bar ta nan kusa. Ta miƙa hannu ta amsa gorar ta kai baki kamar yadda
Hajjah ta buƙata, ta fara shan tsumin da ke da wani irin daɗi akan harshe,hakan yasa ta shanye tas
tana jinjina daɗinsa, rasa haƙiƙanin ko tsumi ne ko kuma wani abu ne me kama dashi ɗin? Ta dai ji
ya yi mata kama da irin tsumin da Iyah ta dinga ɗura mata,amma sai dai wannnan da ta sha a
yanzu ya fi na Iyah da daɗi da qamshi.
Lokacin da ta aje gorar sai Hajjah ta saki murmushi ci ke da tsokana ta ce, "Ashe dai ɗiyar tawa
me son shan zaƙi ce,kar ki da mu zan san ya a yo miki shi da yawa a kawo, wannan da aka kawo
ba yi da yawa ne don na raba muku biyu ne ke da abokiyar zamanki Suhailah. Zaynab ina me farin
ciki da shigowarki cikin zuriyata, ina kuma fata da addu'ar Allah ya baku zaman lafiya. Sannan ina
roƙon arziƙi da ki riƙe Maleek da Amana,ki zauna da kishiyarki da zuciya ɗaya, kada ki yarda da
duk wani zuga na mutane wanda ba mai kyau ba. Ba gari ɗaya za ku zauna ba don haka babu
ruwanki da ɗaukar duk wani ziga da maganganu irin na mutane, ki toshe kunnuwanki a duk
lokacin da magauta za su nufo ki da wani zance, wanda ba mai daɗi ba akan mijinki ko abokiyar
zamarki. Allah ya haɗa kanku ya baku zama lafiya tare da rabo me anfani, In Sha Allah ba za ki yi
danasanin shigowa cikin zuriyata ba. Na gode Zaynab,na gode da yadda ki ka amince da auren
Maleek Allah ya dauwamar da ƙauna ta har abada a tsakaninku, ina so ki saki jiki da ni sosai ta
yadda duk wani damuwarki za ki iya sanar da ni kafin ki sanar da Iyah, duk abinda ya yi miki
wanda ba ki ji daɗinsa ba ki sanar dani kai tsaye kin ji ko?"
Hajjah ta kai ƙarshen maganar idanunta akan TAIMIYYAH wacce ta sake yin ƙasa da kanta,
kalaman Hajjah na ratsa zuciyarta da haifar mata da nutsuwa sosai a cikin ruhinta. Ta gyaɗa kai a
hankali cikin sanyin muryarta da ya yi can ƙasa sosai ta ce "In Sha Allah, na gode Allah ya ƙara
girma."
Hajjah ta amsa da cewa, "Ameen Zaynab, Allah ya yi miki albarka." TAIMIYYAH ta amsa da
cewa "Ameen." A cikin zuciyarta ba tare da ta furta a fili ba , daga haka Hajjah ta yi kiran Anty
Safiya don ta raka TAIMIYYAH zuwa cikin ƴan uwanta da ƙawayenta don ta sake,sabida yadda ta
ga tana cikin tsananin jin kunyar ta.
Lokacin da Anty Safiya suka fito daga ɗakin Hajjah daidai lokacin ne Suhailah ta shigo cikin
corridor ɗin, ita kuma za ta ɗakin Hajjah don kai wa Hajjah wayarta da ake kira,wanda ta bar shi a
hannun Anty Rady kiran da ake yi mata yasa Anty Radyn baiwa Suhailah ta ce ta kawo wa Hajjar.
Ta sauke idanunta akan yanayin tafiyar TAIMIYYAH tana jin wani abu na motsa zuciyarta,
lokacin da fitinannan ƙamshin da TAIMIYYAH ke yi ya shiga hancinta. Ta haɗiye wani abu me
ɗaci tana sake kafe su da ido lokacin da suke wuce ta suka nufi ɗakin da aka sauke Amaren. Duk
yadda ta so ganin fuskar TAIMIYYAR ba ta samu gani ba sabida sun riga sun bata baya,sai ta juya
ta nufi ɗakin Hajjah zuciyarta na cigaba da matsewa da matsanancin kishi.
*09:35pm*
Maleek Ado ne zaune a cikin ɗakin Hajjah idanunsa akan Inna Dije da ke faman masa tsiyan cewa
ya biyo Amarya ne babu ko kunya? Ya saki murmushi yana me gyara zamansa bisa Sofa ɗin ɗakin
ya ce, "Kai Inna Dije ni ba Amarya na biyo ba,zuwa na yi in ga Ƴar daru na ko ta kwantar da
hankalinta. Sai gashi na sameta ma da su Safiya suna ta hiran su,da alamu kun danne ƙirjin ya
dannu da kyau ke da Hajjah."
Maleek ya kai ƙarshen maganar yana duban side ɗin da Hajjah ke zaune tana murmushi, Inna Dije
ta zabga masa harara ta ce, "Bawani nan ni ban yarda da kai ba, ba Uwargida ka biyo ba Amarya
ka biyo sahu babu ko kunya."
Maleek ya sake sakin murmushi zuciyarsa na sake motsawa da kwaɗayin son sake sanya
TAIMIYYAH a cikin idanunsa, ya dubi Hajjah ya ce, "Hajjah don Allah zan samu abu mara nauyi
haɗe da fura,yinwa na ke ji ban ci abinci ba tun wanda na ci wajen Reception, ni kuma bana son
cin abu me nauyi, idan akwai nama da fura a bani please!"
Hajjah ta dubesa cike da zallar ƙauna ta ce, "Za ka samu nama kam sai kalan wanda kake so,
akwai gasasshe akwai soyayye akwai kuma ragowar farfesun kan rago da Babah Rabi ta gama yi
ɗazunnan. Bari in saka Safiya ta kawo maka nan ko tafiya za ka yi da shi can gida?"
Maleek ya gyaɗa kai yana duban Hajjah ya ce, "Tafiya da shi zan yi Hajjah, ki ce mata ta yi min
take away ɗin gasasshen naman ragon,sai a ɗan soya chips a zuba min akai kaɗan. Furan dai idan
akwai abani da ɗan yawa please!"
Hajjah ta jinjina kai tana miƙa hannu ta janyo wayarta ta kira Safiya, lokacin da ta iso cikin ɗakin
ne ta sanar da ita abinda za ta yi. Ta amsawa Hajjah tana juyawa kan Maleek ta fara masa tsiyan
cewa ita fa bata gane bane, Amarya ya zo gani ba zai iya haƙuryn gobe akai masa ita ɗakinsa
ba,sai ya yo tattaki ya biyo sahu. Shi dai Maleek blushing kawai ya ke yi ba tare da ya ce da
Safiya komi ba, bayan fitarta ne ya dubi Inna Dije ya ce, "Wallahi Safiyya ta gama raina ni da
yawa, ita ko kwarjinin nawa ba ta gani kullum cikin min shaƙiyancin da ta ga dama take yi,don ta
ga cewa girman watanni na yi mata ba na shekaru ba."
Inna Dije ta sanya dariya ganin yadda Maleek ɗin ke wani kwaɓe fuska,ta tsaida dariyar nata tana
cewa, "Kun dai fi kusa ni bazan ce komi ba,don ba a shiga tsakaninku yanzu sai a ganku kuna ƙus-
ƙus za ku ƙulla wata tsiyar."
Maleek ya saki murmushi me faɗi don ya san gaskiya Inna Dije ta faɗi,sabida Anty Safiya
mutuniyarsa ce sosai,suna mugun shiri da ita duk cikin cousines ɗinsa ta ɓangaren Hajjah jininsu
ya fi jituwa da ita. Anty Safiya ta dawo ɗauke da ƙaramin kwandon ɗaukar abinci,wanda ta
shiryawa Maleek coolers biyu da ta zuba gasasshen nama a ɗaya,ɗayan kuma ta zuba masa
farfesun kan ragon da ya ji kayan ƙamshi,daga gefe guda kuma jug ne da ta zuba masa
damammiyar Fura da ta sha kwakwa da madara wajen damun. Sa cup ɗin jug ɗin guda ɗaya da ta
aje daga gefe, ta aje kwandon daga gefensa tana cewa, "Oya gashinan an zubo komi da komi,sai a
tashi a tafi gida idan kuma za ka wuce tare da gimbiyar taka Uwargida ran gida ne,sai na turo
maka ita yanzu don na ga wani basar da kai take yi."
Anty Safiya ta yi maganar cike da tsokana idanunta akan fuskar Maleek Ado da ke faman taɓe
baki. Ya yi magana a ƙasaice ya ce, "No na bar miki ita ki sake danne min ƙirjinta da kyau sosai."
Su Hajjah suka sanya dariya baki ɗaya har Inna Dije, Anty Safiya ta tsaida dariyar tana cewa, "Ok
haka ma za ka ce? Shiyasa na ce Amarya ka biyo wallahi in ba haka ba meyasa ba za ka tasa kan
Uwargida ku wuce tare ba,ka je can kai ka danni ƙirjin nata da kyau."
"No ki rabani da darun Suhailah gara zamanta anan ɗin, ko ta bini ciwan kai kawai za ta bani,
yanzu dai taya ni da ɗaukar kwandonnan mu je ki ɗan ji wata magana daga waje."
Inna Dije ta dubi Hajjah suka saki murmushi a tare,ta maida dubanta kan su maleek ta ce, "Ai
dama na faɗi, ke Safiya ki kiyayemu wallahi Allah idan Amarya ya ke son gani kar ki biye masa,
ya jira har akai masa ita gidan sa."
Anty Safiyyah ta saki dariya lokacin da ta ke ɗaukar kwandon abincin, ta bi bayan Maleek da har
ya fice daga ɗakin, tana me ɗaga murya ta ce, "To Mamah ba zan biyesa ba, amma idan za a cika
min jaka da bugun Abuja gaskiya zan ɗan ci amana."
Daga Hajjah har Inna Dije suka saki dariya,Hajjah na faɗin, "Allah ya shiryaki Safiyyah."
A.Maleek Ado ya ratso cikin falon Hajjah yana sake gaisawa da wasu ƴan Fam House ɗinsu,
waɗanda za su kwana har zuwa gobe taro ya watse, wanda duk rabin su ƴan gulma da ɗaukar
rahoto ne kawai. Ya cigaba da takawa har ya fito daga cikin falon Hajjah, ya yi tsaye daga bakin
barandar waje yana jiran fitowar Anty Safiya. Wayarsa ya ke latsawa yana sake gwada kiran layin
TAIMIYYAH, wanda tun ɗazu ya ke kira amma bata ɗagawa, yanzu ma ɗin har kiran ya tsinke ba
a ɗaga ɗin ba. Sai ya maida wayar cikin aljihu daidai lokacin da Anty Safiya ta fito,hannunta riƙe
da kwandon abincin da ta riƙo masa. Ta dube sa tana yin ƙasa da murya ta ce, "Bro ya aka yi ne,
me kake so?"
Maleek ya ɗan yatsine fuska cike da zallar ƙasaitarsa da ta sani ya ce, "Sisi so nake ki taimaka ki
je ɗakin Amaren can ki taho min da Zaynabb, tun ɗazu na ke son jin muryarta amma Yarinyar nan
ta ƙi ɗaga wayata,na san kuma don tana cikin mutane ne take jin kunyar mu yi doguwar magana
da ita. Ni kuma wallahi ba zan iya kaiwa gobe ban sanya ta a idanuna ba, please ki je ki taho min
da ita amma kar ki bari Hajjah ko Suhailah su ga fitowarku, ki faɗi ko nawa ki ke so zan miki alert
yanzu ba sai anjima ba."
Ya ƙare maganar idanunsa akan Anty Safiya da ta saki murmushin farin ciki,kafin ta buɗe baki ta
ce, "An gama Angon Zaynabu,yanzu ko za ka ga cika aiki ni dai inji alert kawai ko na nawa ne ina
so,me nema ai bashi da zaɓi sai abinda aka bashi."
Maleek ya jinjina kai yana ɗan yin blushing ya ce, "Alright! Karanto min details ɗin tuh."
Anty Safiya ta karanto masa account details ɗinta ya shigar cikin wayarsa, ta juya zuwa ciki bayan
ta miƙa masa kwandon abincinsa da ke riƙe a hannunta. Maleek ya amsa yana fara takawa don isa
wajen parking space inda motarsa ke jirge a wajen. Ko'ina a harabar wajen compound ɗin haske
ne kau! Ya dallare ko'ina ta yadda ko allura ne ya faɗi sai ka gani. Ya buɗe mauzanin driver ya
shiga yana me miƙa kwandon abincin ya aje daga back seat, ya koma ya jingina da jikin seat ɗin
yana miƙa hannu ya saita mirrow ɗin motar, ta yadda zai iya hango tahowar su TAIMIYYAH idan
sun fito daga cikin gidan.
Daga ciki kuwa direct Anty Safiya ɗakin da aka sauke Amaren ta nufa,ta tura ƙofar bakinta ɗauke
da sallama ta shiga ciki. Amarya TAIMIYYAH na daga can ƙarshen gadon sanye da dogon
Hijab,wanda ta ƙi cire sa tunda ta idar da sallar Isha'i su Zee ke mata mitan ta cire amma ta ƙi. Da
suka matsa mata da mita ne ta sanar da su cewa, ita ba za ta iya zama da kayan bacci babu lulluɓi
ba a gidan surukai, hakan yasa suka share ta babu wanda ya sake mata maganar cire Hijab ɗin.
Yasmeen da su Zee ne suka gaida Anty Safiya cike da fara'a, ta ƙarisa zuwa cikin ɗakin tana sake
gaisawa da Guggo Lami, wacce ke kan ɗaya ƙaramin gadon da ke ɗakin ta yi lamo tana kallon ƴan
matan na ta sha'aninsu.
"Guggo za ku ɗan bani aron Amarya ne zan dawo muku da ita nan bada jimawa ba."
Anty Safiya ta yi maganar idanunta akan Guggo Lami, Guggo Lami ta amsa da cewa, "Tuh ai
babu damuwa ga ta can har ta yi shirin kwanciya ai."
Ta yi maganar tana nunawa Anty Safiya can ƙarshen gadon da TAIMIYYAH ke kwance, ta juyawa
su Zee baya tana faman danna wayarta, akan idanunta Maleek ke ta kiran wayarta amma ta kasa
ɗagawa sabida vid call ya ke kira,ita kuma ba za ta iya amsa wayarsa vid call a cikin mutane ba.
Anty Safiya ta matsa daga can direction ɗin da TAIMIYYAH ke kwance tana cewa, "Allah sarki
Amarya har an yi shirin kwanciya haka da wuri, don Allah ki yi haƙury yanzu bada jimawaba za
mu dawo,ta so mu je tunda ma ga Hijab nan a jikinki."
TAIMIYYAH ta tashi a kunyace sai fatam sunkuyar da kanta take yi ƙasa, kunyarta na sake birge
Anty Safiyyah. Ta zura takalminta tana gyara Hijab ɗin jikinta suka fito tare da Anty Safiya. Suna
isowa cikin falon Hajjah duk su Hajiya Laure suka biyo su da ido. Anty Safiya ta yi kamar ba ta
gansu ba suka cigaba da ratsawa ta cikin falon suka fice waje, su Hajiya Laure suka bi su da ido
suna cigaba da gulma akan cewa TAIMIYYAH a she dai gurguwarce da gaske tunda sai da
taimakon dafa guiwa ta ke iya tafiya.
"Amarya wajen Angonki fa zan miki rakiya, ya ce yana ta kiranki ba ki ɗaga ba meyasa? In banda
abinki sai ki shiga ko toilet ne ai ku sha wayarku idan ma kunya ki ke ji na amsa wayarsa cikin
ƙawayenki Zaynab. Gaskiya kunyarki har ta yi yawa dole sai kin rage ta don Maleek shi ɗan life
ne na gaske. Bai san wani abu wai shi kunya ba in dai akan abinda ya ke so ne,dole sai kin rage
wannan kunyar idan kina so ki mallaki zuciyarsa yadda ya dace."
Ita dai TAIMIYYAH jin Anty Safiya kawai ta ke yi, amma zuciyarta sai faman bugu ta ke tunda
Anty Safiya ta ambaci cewa wajen Maleek za ta kai ta. Kwakwalwarta ta shiga haska mata karon
su da shi a ɗazu da rana, zuciyarta ta sake doka mata da wani irin tsoro da firgicin sake
kaɗaicewarta da shi. Sai dai bata da yadda za ta yi don ba za ta iya cewa Anty Safiya ba zata
ba,suka cigaba da takawa TAIMIYYAH na dafe da guiwar ƙafarta,gaba ɗaya ji ta ke yi da zata iya
juyawa cikin gidan da ta juya,don ita yanzu tsoran haɗuwarta da Maleek ɗin ta ke ji, tun
abubuwan da ya yi mata a ɗazu da nauyinsu da kunyarsu ba su bar zuciyarta sukuni ba har kawo
yanzu.
Maleek Ado wanda ke zaune cikin motarsa idanunsa akan mirrow, yana hango tahowar su
TAIMIYYAH xuwa wajen motarsa. Ya lumshe idanunsa ya sake buɗe su akan su lokacin da suka
ƙariso bakin motar, sai ya yi saurin buɗe side ɗin da ya ke zaune yana cewa, "Hey! Sis zo ta nan."
Anty Safiya sai ta nufi ɓangaren da Maleek ke zaune ta ce, "To gata nan dai na kawo maka
ita,amma fa na sanar da Guggonta ba za ta daɗe ba zan maida ta,so ka yi sauri ka ganta mu wuce
kada Hajjah ma ta zagaya yin patrol ta ga an ɗauke musu Amarya."
Anty Safiya ta ƙarisa maganar tana dariya cike da shaƙiyanci,Maleek ya ɗan taɓe baki ya ce, "Ni
dai yanzu tunda kin cika aikin ki,komawa za ki yi ciki nan da minti talatin zan kiraki ki maida ta
inda kika ɗakko ta,za ki ga alert kina buɗe wayarki, so za ki iya tafiya sai na kira ki."
Maleek ya yi maganar yana maida dubansa wajen da TAIMIYYAH ta yi tsaye, ƙirjinta na faman
bugawa da tarin fargaba,ta dubi Anty Safiya lokacin da ta ce, "Amarya bari in shiga daga ciki idan
kun gama zan fito mu koma ciki."
Daga haka Anty Safiyyah ta yi gaba tana sakin murmushi, gaba ɗaya TAIMIYYAH ta bata dariya
yadda ta ke faman zare idanu kamar wacce ta yi ƙarya.
Maleek Ado ya zuro ƙafarsa ya fito daga waje, yana isa wajen da TAIMIYYAH ta yi tsaye ginjine
da jikin motar,ya dubi fuskarta da ta sunkuyar ƙasa ya saki murmushi. Bai yi magana ba illah
kamo hannunta da ya yi,yana zagayawa da ita ɓangaren me zaman banza, ya miƙa hannu ya buɗe
mata ƙofar motar ya ce, "Wife shiga daga ciki."
TAIMIYYAH ta ɗaga manyan idanunta da suka haska da tarin tsoran da ke kan fuskarta ta ce,
"Don Allah Yah Maleek ba sai na shiga ba,bacci na ke ji wallahi ina son in je in kwanta please!"
Maleek bai bi takan maganar da TAIMIYYAH ta yi ba, sai kawai ya ɗauke ta cak! Ya sanya ta
cikin motar, ya maida murfin ya rufe yana saurin zagayawa ɓangarensa ya shiga ya dannawa
motar lock. TAIMIYYAH sai ta haɗe kanta da guiwa tana sakin masa kuka me sauti,dukkanin
jikinta na ɗaukar rawa don har ga Allah ita lamuran Maleek yanzu tsoro suke bata.
Maleek Ado kuwa gaba ɗaya ƙamshin TAIMIYYAH da ya fara cika motar ke motsa zuciyarsa, ya
ɗaga manyan idanunsa ya sauke akanta yana sauraren yadda sautin kukanta ke fita a hankali. Ya
buɗe baki cike da ƙasaita ya ce, "Zainab kina so in wuce da ke gidana ki kwana a can kenan ko?"
Ai bai ma kai ga rufe baki ba TAIMIYYAH ta yi saurin ɗago fuskarta tana sake sakin kuka ta ce ,
"No Please! Yah Maleek don Allah ka yi haƙury."
Maleek ya yi maganar fuskarsa a miskile yana sake tsare ta da idanunsa da ke cike da zallar
rigima, ganin yadda ya yi maganar babu alamun rahama akan fuskarsa,yasa TAIMIYYAH saurin
tsaida kukan hawaye na cigaba da zirarowa daga idanunta.
Ya miƙa hannu ya zari tissue ya miƙa mata yana cewa, "Ungo ki share hawayen nan bana son
kina min a sararsu,don lokacin zubansu bai yi ba ya dai kusa soon Baby."
Yana maganar ne idanunsa a kanta babu ko kiftawa,hakan yasa TAIMIYYAH miƙa hannu ta amshi
tissue ɗin, ta fara share hawayen da ke sake sakkowa daga cikin idanunta. Da ƙyar ta yi nasaran
tsaida hawayen tana faman zumbure baki da sauke ajiyar zuciya, wanda ya sanya Maleek sakin
smile kaɗan yana cigaba da bin ta da wani mayen kallo. Ya buɗe baki cike da zallar ƙasaita ya
ce.........✍🏻
_Hmmm! Maleek Ado ba dama ne,da alamu so ya ke ya gama gigitama Iyah jika da salon luv
ɗinsa,shi baisan cewa Shaikha Alarammiyah TAIMIYYAH ya aure ba ne? Wacce ba ta saba da
fitsaran kalar luv ɗinsa ba lol._ 😒
#Ɗansabo ce#
[12/15, 11:46 AM] +234 703 040 9541: Littafin TAIMIYYAH paid book ne,ga duk wanda ta
tsincesa a kowani irin group ne,kiji tsoran Allah karki karanta sai kin biya 500 naira only.
Za ku iya min magana ta wannan number ɗin 08167768704, ko kuma ku turo kuɗin ku kai tsaye ta
wannan account ɗin 0504192664 aisha ibrahim dansabo GTbank.*
Masu turo credit za ku turo katin MTN na 500 ta wannan line ɗin 08167768704.
_Ina ƴan kasuwa masu buƙatar a tallata muku hajar ku? Maza ku garzayo da kuɗi ƙalilan a tallata
muku kayan siyarwanku sai dai kawai ku ji ana kiran waya don buƙatan sayan kayan ku,ku
tuntuɓeni ta layina kamar haka 08167768704._
*71*
Maleek Ado ya yi maganar can ƙasa idanunsa akan TAIMIYYAH, wacce ta yi saurin ɗago kanta a
razane ta dube sa. Ya gyaɗa kai cike da tabbatar mata da abinda ya faɗi ɗin ba wasa ya ke ba ya ce,
"Please Zaynab ko da kaina ki ke so na cire Hijab ɗin?"
TAIMIYYAH ta sake waro manyan idanunta da suka fara haskawa da ƙyallin ruwan hawaye,
muryarta na rawa ta ce, "Don Allah Yah Maleek ka yi haƙuri, rigar bacci ce kawai a jikina zan iya
ba ka abincin ba ma sai na cire Hijab ba please!"
Ta kai ƙarshen maganar cike da magiya tana duban fuskar Maleek wanda ya sake miskile face
tamkar bai taɓa sanin wani abu wai fara'a ba. Ya miƙa hannu don janyo TAIMIYYAH xuwa
jikinsa sai ta sakar masa kuka me sauti, tana sake dunƙule jikinta tamkar za ta manne da seat ɗin
motar su zama abu guda, hakan ya sanya Maleek sakin murmushin da bai shirya ba ya ce, "Okey
ni kar ki cika min kunni da wannan kukan shagwaɓar ana min asaran hawaye. Ki cire Hijab ki
bani abinci malama in ba so ki ke yanzu mu wuce can gida na in amshi abinda ki ke wa tsoran ba."
Ai da jin hakan sai TAIMIYYAH ta sake sakin kuka,hannunta har rawa ya ke wajen yaye Hijab
ɗin da ke jikinta. Zuciyarta da gangar jikinta gaba ɗaya wani irin rawa su ke, memakon ta cire
Hijab ɗin gaba ɗaya sai ta sake yafa shi ya rufe ƙirjinta kamar wacce ta yafa veil. Maleek da ya
zuba mata ido yana jin wani irin maganaɗisu na yawo a jinin a jikinsa game da ita, sai ya miƙa
mata hannu ya ce, "Bani in aje miki Hijab ɗin Baby, ni rigar baccin kawai na ke son gani a
jikinki."
TAIMIYYAH ta yi saurin dubansa wasu hawayen na wanke face ɗinta ta ce, "Please Yah
Maleek....."
Bai barta ta furta ƙarshen magiyarta ba ya yi saurin katseta da cewa, "Wallahi fa sai kin yi yadda
na ke so Zaynabb cox ban ga abinda za a ɓoye min ba yanzu,tunda kin zama mallakina halak
malak! Ko tsirara na so ganinki dole ki min yadda na ke so, please bana son yawan gardama
Baby."
Ya kai ƙarshen maganar yana fincike Hijab ɗin ya yi can gefe guda da shi, idanunsa suka sauka
akan rigar baccin da ke sanye a jikin TAIMIYYAH kalar dark pink. Sosai rigar ta yi mata kyau
tare da bin jikinta ta lafe sosai, wuyar rigar V-shape ne da ya bayyana asirin cikar ƙirjinta ta sama
kaɗan, duk da kasancewar babu Bra a jikinta don bata iya kwana da ita, hakan bai hana bayyanar
cikar ƙirjinta ba don Allah ya yi mata baiwarsu masu ɗaukar hankali.
Maleek ya sauke wani zazzafar numfashi dukkanin jikinsa na amsawa da wani irin yanayi me
wuyar fassara, ya sake kafe ƙirjinta da ido yana jin wani abu na motsawa a cikin zuciyarsa irin
yadda bai taɓa jin hakan akan kowace mace ba. Ya miƙa hannunsa zuwa back seat ya ɗakko
kwandon abincin da Anty Safiya ta jere coolers a ciki, ya aje daga tsakiyar dashboard na motar,
yana mayar da dubansa kan TAIMIYYAH wacce gaba ɗaya ta ke jinta a wani irin takure, ga
zuciyarta da ta kasa sukuni sabida tsoron abinda zai biyo baya tsakaninta da Maleek ɗin. Sam ta
kasa sake duban side ɗinsa tunda ya yi nasaran amshe Hijab ɗinta, sai dai tana jin tasirin idanunsa
akanta sosai, wanda hakan ke sake haifar mata da jin wani irin yanayi a zuciya da gangar jikinta
baki ɗaya.
Muryar Maleek Ado ya shiga kunnuwanta lokacin da ya ke cewa, "Zaynab ga abincin nan ki xuba
ki bani in ba kina so yinwa ta yi min illah bane,tun rana rabo na da abinci fa Baby."
Ganin babu plate bare spoon a cikin basket ɗin ya sa ta yin magana cike da shagwaɓarta ta ce,
"Babu abin ɗibar abinci da plate ai a ciki."
Maleek da idanunsa ke kan yadda ta ke motsa ɗan ƙaramin bakinta,tana furta kalmomin cike da
shagwaɓar da ke kassara zuciyarsa, sai bai yi magana ba illah ɗaga wayarsa da ya yi ya fara kiran
layin Anty Safiya. Bugu biyu ta ɗaga wayar ya yi magana yana sanar da ita cewa ta kawo masa
plate da spoon yanzu, ya fasa tafiya da abincin a nan zai ci."
Daga haka ya kashe wayarsa yana ajewa akan jikinsa, ya juyo gaba ɗaya yana fuskantar
TAIMIYYAH tare da miƙa hannu ya kamo nata hunnuwan duka biyu. Ya sauke idanunsa akan
zanen jan lallin da suka ƙawata ƴan yatsun hannunta, yana me kai ƴan yatsu bakinsa ya basu wani
light kiss tare da son su haɗa ido da TAIMIYYAH,amma sai ta yi gaggawar lumshe idanunta wani
abu na tsirgawa tun daga tafin ƙafarta zuwa Kwanyarta. Zuciyarta na cigaba da dokawa da sauri-
sauri, jikinta ya cigaba da ɗaukar rawa sosai don gaba ɗaya lamuran Maleek suna zuwar mata a ba
za ta, kuma da wani irin tasiri da ke jijjiga zuciyarta.
Ya saki hannuwarta daidai lokacin da Anty Safiya ta iso riƙe da plate da spoons guda biyu, ta yi
knocking ƙofar motar ta side ɗin da Maleek ya ke. Ya buɗe murfin motar tare da zura hannu ya
amsa plate da spoons ɗin, ya na ji Anty Safiya na masa tsiya ya maida murfin motar ya rufe yana
sake locking ɗin motar. Ta juya ta koma zuwa ciki tana mamakin rashin ta ido irin na Maleek Ado,
ita TAIMIYYAR ne ma ke bata tausayi, very innocent gal da sam bata hango wani matsala a tare
da ita ba,ga kunyar Yarinyar da ke sake birgeta tamkar ba ƴan matan wannan zamanin ba.
Waɗanda suka mai da rashin ta ido tamkar ado ne a wajensu, sai ka ga an kai Yarinya gidan miji
idanu rayas tamkar an soya gyaɗa sabida rashin kunya. Har ta isa zuwa ciki ta nufi ɗakin Hajjah
don janye hankalinsu da hira,zuciyar Anty Safiya na cigaba da yaba kunya da nutsuwar
TAIMIYYAH, tana me taya ɗan uwanta murnan samun natsatstsun mata da ya yi, don Suhailah ita
ma bata na wani matsala me girma da ya wuce rashin wayo da zafin kishinta na banza .
Daga can cikin motar Maleek Ado kuwa TAIMIYYAH ce ta zuba masa haɗin gasasshen naman
rago,wanda da aka soya chips aka watsa a kai sai tashin qamshin spices kawai ke tashi. Ta ɗaga
manyan idanunta da ke walainiya da ƙyallin ruwan hawayen da ta kasa tsaida taruwarsu a
idanunta, ta sauke akan Maleek ɗin wanda ya harɗe hannuwansa duk biyu a saman ƙirjinsa, ya
zuba mata ido tamkar ya cinyeta ɗanya sabida yadda ta yi masa wani irin mugun kyau cikin rigar
baccin da ke jikinta. Ya sake shigar da ƙwayar idanunsa cikin na TAIMIYYAH lokacin da
idanunta suka sauka akan fuskarsa, sai ta yi saurin yin ƙasa da kanta tana tura masa plate ɗin zuwa
gabansa ta ce, "Ga shi ya yi ko a ƙara?"
Maleek ya dubi plate ɗin da ta maƙara masa naman da chips ɗin yana me sakin ƙaramin smile, ya
maida dubansa kanta murya can ƙasa ya ce, "No wife wannan ɗin ya ishe mu ni da ke, oya feed
me please! Wannan kunyar duk ba zai ceto ki ba Yarinya."
Ya yi maganar yana miƙa hannunsa ya ɗago fuskarta sosai,amma ta ƙi dubansa sai shagwaɓe
fuskar da ta sake yi cikin shagwaɓa ta ce, "Ni fa bazan ci ba na riga na ci abinci tun ɗazu,yanzu
bacci kawai na ke son yi Yah Maleek."
Maleek Ado da ƙamshinta ya gama cika hancinsa tare da sake kunna wutar son kasancewata da ita
a zuciyarsa, sai bai yi magana ba illah danna wani abu da ya yi a jikin motar, duka seat ɗin suka
kwanta baya, suka zama flat tamkar masu shirin kwanciya akai. Hakan ya bashi daman ƙarisa
dawo da TAIMIYYAH side ɗinsa,tare da ɗaura plate ɗin naman akan cinyarta ya ce, "Za ki je ki
kwanta idan kin gama cike ladarki wajen ciyar da mijinki kin ji Baby?"
TAIMIYYAH da jikinta ke ɗan rawa ta yi saurin duban idanunsa,shi ko Maleek sai ya ɗage mata
gira guda yana kai bakinsa ya sumbaci manyan idanunta masu wani irin tasiri akansa. Hakan yasa
TAIMIYYAH saurin maida idanunta ta lumshe zuciyarta na cigaba da ɗaukar rawa, jikinta na
amsawa da wani irin baƙon yanayi da ke zagaya ilahirin jinin jikinta. Ƙamshinsa na AMOUAGE
gaba ɗaya ya gama cika kafofin hancinta yana sake jefa zuciyarta a wani hali da ba za ta fassarawa
ba, duk yadda ta kai da son ya ciyar da kansa da kansa ya ƙi hakan,sai da ta aje duk wani jin nauyi
da fargaba ta shiga bashi naman da chips ɗin ya na ci.
Gaba ɗaya sai wani narke mata ya ke yi tamkar ƙaramin yaro, ji ya ke yi tamkar su dawwama a
hakan ba tare da ya barta ta koma cikin gidan ba. Lokacin da ta kammala ba shi sosai ya matsa
mata akan ita ma sai ta ci, duk yadda ta nuna masa cewa a ƙoshe ta ke sai da ya matseta a jikinsa
yana bata da kansa tana ci. Bata ci ya kai yanka biyar na naman ba ta ce masa ya ishe ta,sai ya
barta yana miƙa mata cup ɗin da ya ciko da fura, amma sai ta ce da shi bata shan fura da dare don
yana ɓata mata ciki ne. Hakan da ya ji yasa shi barin ta ya shanye abar sa yana me dire cup ɗin a
side, ya maida dubansa kan TAIMIYYAH da zuwa lokacin ta ke zaune saman laps ɗinsa,ya hanata
dukkan damar da za ta iya barin jikinsa. A bazata TAIMIYYAH ta ji hannuwansa na ƙoƙarin shiga
cikin rigarta, hakan yasa ta yi saurin dubansa tana ƙoƙarin buɗe baki ta sakin masa kuka. Kamar
ya san abinda ta ke shirin aikatawa sai ya yi saurin haɗe bakinsa da nata. Nan da nan jikin
TAIMIYYAH ya sake ɗaukar rawa, ta shiga amsar wasu irin zafafan saƙonnin da ke neman zauta
ƙaramar kwanyarta, da sam bata san kalan waɗannan karatukan da Maleek ya fara biya mata su
ba.
Duk iya yadda ta ke mutsu-mutsun son ƙwatar kanta daga hannunsa ta kasa, tana ji tana gani haka
Maleek ya yi bidirinsa iya son ransa,kafin ya saketa ta bar jikinsa tana faman kukan da ke fita
cikin ƙaramin sauti. Dukkanin jikinta na amsawa da salon saƙonninsa da ya isar zuwa gareta,
bakinta har wani zugi ya ke mata sabida tsotson da ya sha daga Maleek Ado, tana jin dukkanin
hannuwansa na cigaba da yawo a jikinta.
Shi ko Maleek Ado maida jikinsa ya yi ya kwantar bisa seat ɗin da ɗin da kwantar, ƙafafunsa suka
miƙe sosai tamkar yana kan bed. Ya lumshe idanunsa yana jin tamkar ya ja motar ya gudu da
TAIMIYYAH zuwa gidansa,gaba ki ɗaya wutar jarabar son su zama abu ɗaya shi da ita ke sake
ruruwa a cikin zuciyarsa. Bai taɓa jin irin kalar wannan zalamar da ya ke ji akan mace ba sai
akanta, hakan har mamaki da tsoro ya ke bashi don yana tausayin lokacin da haƙurinsa zai gaza
akanta. Ya buɗe idanunsa yana miƙa hannu ya janyo wayarsa, ya shiga kiran layin Anty Safiya don
ta zo ta wuce da TAIMIYYAH zuwa ciki,sabida idan suka cigaba da zama a muhalli ɗaya komi zai
iya faruwa a cikin motar,don baƙaramin abu ya ke ji akanta ba.
Bayan ya sanar da Anty Safiya ta fito ne ya kashe wayarsa yana me tashi zaune,ya maida idanunsa
kan TAIMIYYAH da ta dunƙule jikinta tana cigaba da kukanta a hankali. Ya buɗe baki cikin
muryarsa da ta ɗan shaƙe ya ce, "Baby ba za ki tsaida wannan kukan ba sai Safiya ta zo ta ganki
kina yi, ta ɗauka cewa na fara angwancewa ne tun a mota ko?"
TAIMIYYAH ta yi saurin ɗago idanunta da ke zubar hawaye ta dubi Maleek da wani irin
expression a samar fuskarta, wanda hakan ya sa Maleek sakin mata smile yana sake jinjina mata
kai, alamun tabbatar mata da cewa abinda Anty Safiya za ta zarga kenan idan ta ganta tana kukan.
Sai ta yi magana cike da zallar shagwaɓa ta ce, "Ka bani Hijab ɗina don Allah!"
Maleek ya sake sakin smile yana miƙa hannu ya janyo Hijab ɗin ya yi kamar zai miƙa mata, sai da
ta miƙo hannu don amsa ya yi saurin janyota ta faɗo jikinsa baki ɗaya. Ya sake mannata da ƙirjinsa
ya rungume yana kai bakinsa saitin kunninta ya furta mata wasu zafafan kalamai, kafin ya ɗago
fuskarta yana manna mata wani hot kiss a forehead ɗinta. Ya cire bakin daga nan ya maida
idanunsa bisa ƙirjinta yana kai fuskarsa a hankali zuwa kan ƙirjinta, hakan ya so tsaida bugun
numfashin TAIMIYYAH sabida abun ya zo mata a bazata. Maleek Ado sai da ya yi abinda ya ke
so a muhallin kafin ya saketa yana sanya mata Hijab ɗinta a jikinta, ya dubi idanunta da suka raina
fata ya sakar mata wani killer smile, yana jin farashin ƙaunarta na sake hauhauwa a dukkanin jinin
jikinsa. Lokacin da Anty Safiya ta iso da kansa ya fito ya zagaya side ɗin da TAIMIYYAH ke
zaune, ya buɗe murfin motar yana me kamo hannunta ta sakko daga ciki,kunya duk ya bi ya
addabi zuciyarta kamar ƙasa ta tsage ta shige. Anty Safiyyah kallo ɗaya ta yi wa fuskar
TAIMIYYAH ta san cewa Maleek ya ɗan rage zafi da Amaryar tasa ne, sai ta saki murmushi cike
da tsokana ta ce, "Bro ya aka yi ka sanya Amaryar tamu kuka haka,ni da na san abinda zaka yi
kenan da ban kawo maka ita ba. Kin ji Amaryamu mu je ko sai kin yi haƙury da halin wannan
Angon na ki da bai san inda kunya ya ke ba."
TAIMIYYAH na jiyo sautin dariyar da Maleek ya yi amma ta kasa ɗaga ido ta dubesa,illah
zuciayarta da ke mamakin cewa dama ya iya dariya? Ta dafe guiwar ƙafarta za ta fara takawa
amma sai Maleek ya yi saurin riƙota yana cewa, "Hey wife! Sallamar da za mu yi kenan ba ɗan
gud night kiss ba komi?"
Wani irin kunyar kalamansa da kunyar idanun Anty Safiya da ke kansu ya lulluɓe TAIMIYYAH,
bata san lokacin da ta ɗago manyan idanunta ta balla masa wani irin harara da ya motsa zuciyar
Maleek Ado ɗin. Ya saki dariyar da babu shiri sabida yadda ta yi ba ƙaramin dariya zai sanya duk
me kallonta ba,don Anty Safiyar kanta dariya ta saki tana ballawa Maleek harara. Ita ko
TAIMIYYAH sai ta tsura masa ido tana kallon yadda ya ke dariyar tamkar ba shi ba, abin ya yi
matuƙar bata mamaki shiyasa ta shagala a kallonsa,har sai da ya kai hannu bisa face ɗinta ya ce,
"Malama kallon fa?"
TAIMIYYAH sai ta yi saurin zumɓure baki tana ɗauke idanunta daga kansa, kunya na sake cika
zuciyarta ta dafe ƙafarfa ta yi gaba tana takawa cikin slow motion. Maleek Ado ya ɗaga murya
yadda za ta jiyo sa ya ce, "Gud night Sweet, Allah ya yi miki albarka kin ji."
Ita dai TAIMIYYAH ta cigaba da takawa tana jiyo sautin maganar Anty Safiyyah sanda take cewa
Maleek ɗin, "Allah ya shiryeka Bro gaba ɗaya duk ka gama ruɗa ƴar mutane,wannan ina ga gobe
da wuya ba koran mutane za ka yi ba idan aka ce za a sake kwana a gidan Amarya."
Maleek Ado ya ballawa Anty Safiya harara, cikin ƙasaitacciyar muryarsa ya ce, "Billahi! Babu ma
wannan maganar Sis idan ko aka gwada yin hakan, to ɗaukar matata zan yi mu je can hotel mu
kwana."
Duk maganganun da suka yi akan kunnuwar TAIMIYYAH ce, wacce ta ɗan tsaya daga can nesa
da su tana jira Anty Safiyya ta cin mata su jera zuwa ciki tare. Sai ta wani taɓe baki tana jinjina
rashin kunyar wannan mutumi tamkar ba shi ne miskilin nan ba. Anty Safiya na ƙarisowa in da
take suka jera zuwa cikin gidan tana sake kwantarwa da TAIMIYYAH hankali akan cewa ta rage
wannan tsoran da jin kunyar Maleek ɗin, shi aure haka ya gada akwai tarin abubuwa masu nauyi
da sai a hankali ake sabawa da su. Ita dai TAIMIYYAH duk sai kunya ya bi ya ishe ta har Anty
Safiya ta yi mata rakiya zuwa ɗaki,tana me baiwa Guggo Lami haƙury akan daɗewar da
TAIMIYYAH ta yi.
Babu wanda ya san cewa wajen Maleek Anty Safiyyah ta kai TAIMIYYAH,domin babu wanda ya
ji shigowarsa gidan bare wannan tunanin ya zo ran su. Sun ɗauka dai ta kaita can wajen su Hajjah
ne su yi mata wani nasihar ko dai wani abun. Yasmeen ce kawai ta so ɗago cewa ko dai Maleek ya
zo ne yasa a kai masa ita, ganin yadda TAIMIYYAH ta ƙi kallon kowa a cikinsu,ta nufi can
ƙarshen gado ta ƙudundune jikinta dukkanin zuciyarta na ga Maleek Ado.Wanda ta ke jin tasirin
dukkanin abinda ya wanzu a tsakaninsu na sake bin jikinta da tsayawa a zuciyarta.
Sai da kowa ya gama shirin kwanciya ya kwanta bacci,sannan TAIMIYYAH ta iya tashi ta nufi
toilet don yin fitsarin da ya cika mararta. Lokacin da ta fito ne su kai ido huɗu da Yasmeen da ke
amsa call,da alamu shigar TAIMIYYAH zuwa toilet ne aka kira Yasmeen ɗin shine ta tashi.
TAIMIYYAH ta ɗauke kai daga duban Yasmeen da ta zubo mata ido, ta nufi hanyar komawa
muhallin da ta taso Yasmeen ɗin na cewa, "Amaryar Maleek ko dai shi ne ya zo ya ɗan rage
zafi,shiyasa ki ka dawo kina wani faman noƙewa?"
TAIMIYYAH ta yi saurin waiwayowa ta dallawa Yasmeen harara ta ce, "Ban sani ba ƴar sanya
idanu,sai ki shafa ki ji ko shi ɗin ne ya zo."
Yasmeen ta saki dariya ƙasa-ƙasa tana cewa, "Allah sarki Babyn Maleek,mai da wuƙar ni bazan
iya shafawa in ji komi ba,me shafawan dai Allah kaɗai ya san me ya shafo shiyasa kika dawo kina
faman noƙewa tamkar wata Ustaziyyah, bayan na san bada kai kika yi kuka sha luv ɗinku, mu ma
dai Allah ya aurar da mu."
Yasmeen ta ƙare maganar cike da shaƙiyanci,ita dai TAIMIYYAH gaba ta yi takaicin Yasmeen ɗin
ya kasa bari ta sake tanka mata. Tana isa bakin bed ɗin wayarta ya fara haske alamun kira ne ya
shigo,ta sauke idanunta akan sunan Maleek da ke yawo akan screen ɗin,ta saki ƙaramin tsaki tana
ignoring call ɗin har ya tsinke. Ta yi gaugawar kashe wayar baki ɗaya tana me zamewa ta kwanta
sosai tare da lumshe manyan idanunta, zuciyarta na cigaba da haskawa da tarin al'amuransa masu
tsayawa a rai. Ta miƙa hannunta zuwa kan ƙirjinta tana jin tasirin yadda Maleek ya dinga aika
saƙo a wajen tamkar ba zai daina ba. Ta yi saurin sake rintse idanunta tana jin wani irin yanayi me
wuyar fassara, da ƙyar ta samu bacci ya yi nasaran sace ta a wannan dare cike da mafarkan
Maleek Ado ɗin.
_____________
Washegary tun misalin ƙarfe huɗu na yamma taron haɗaɗɗan walimar da Hajjah ta shirya ya
watse, an ci an sha an kuma bar arziƙi a inda ya ke. Dangin TAIMIYYAH na uwa da uba su ma
duk sun sama halartan taron, wanda su ke can gidajen su Basmah da ma wanda su ke can Bauchi
duk ƴan gulma sun ɗaga waya sun sanar da su irin shagali da abin arziƙin da suka kwasa wajen
walimar. Ga shi Hajjah bata bar kowa a haka ba sai da aka gwangwaje su da turamen atamfofin
Holland ƴan gasken na dubbannin kuɗi, ga kuɗin ƴan saukar Amarya da aka basu masu asalin
nauyi, wanda yawan kuɗin ya sake gigita zukatan ƴan hassada da baƙin ciki.
Ma su yin vedion yadda wajen walimar ya tsaru suka shiga turawa sauran da basu sama halarta ba,
nan da nan abun ya watsu har ya isa ga wayoyin su Zuhurah. Baƙin ciki da hassadar yadda
TAIMIYYAH ke zarta su a komi ya sake cika zukatansu,domin yadda aka shirya mata tsararren
walimar da yanayin yadda aka tsara wajen shi kaɗai zai shaidawa duk wanda ya gani cewa dukiya
ta zauna a wajen.
Daga can ɗakin da Suhailah ta ke kuwa kwance ta ke tana faman kuka tamkar za ta haɗiye ranta,
ta kasa daurewa ta kasa sukuni tun safiyar yau da ta yi tozali da fuskar TAIMIYYAH. Ta ga irin
kyawun da ta ke da shi da cikar halittar da ya zarce nata, shikenan hankalinta ya yi mummunar
tashi. Kishi me xafi da take dannewa ya taso baki ɗaya ya lulluɓe zuciyarta, tsanar TAIMIYYAH
ya ninku a ranta domin bata taɓa tunanin haɗuwar gurguwar da ta raina ajinta ya kai haka ba. Sai
yau ne ta tabbatar da cewa dole Maleek ya ruɗe har ya amshi aurenta ba tare da ya yi la'akari da
nakasarta ba,don ta mallaki abubuwan da ya ke so a jikin mace. Ga kuma tsantsar kyawu da Allah
ya yi mata me ɗaukar hankali, bata sake sarewa da jin kishi da tsanar TAIMIYYAH ba sai lokacin
da aka fita da ita wajen taron walimar. Irin kyawun da ta yi shi ya sake ɗaga hankalin Suhailah har
ta kasa zama wajen taron, ta sulale ta dawo cikin gidan ta ƙule cikin ɗaki tana kukan da ta tabbar
ta farashi kenan, matuƙar bata yaƙi zuciyarta ta rage jin irin wannan zazzafar kishin da ke danne
zuciyarta ba.
Shigowar Anty Safiya ɗakin ne ya tsaida kukan Suhailah, Anty Safiya ta zauna ta fara rarrashinta
tare da kwantar mata da hankali akan cewa ta rungumi ƙaddara. Ta ɗauki TAIMIYYAH a matsayin
ƙanwa ba kishiya ba tunda ba gari ɗaya ma za su zauna ba, ta cigaba da bugawa Suhailah misalai
masu dama na ribar haƙuri da rungumar kowace irin ƙaddara a yadda ya zo wa bawa. Da ƙyar ta
ciyo kan Suhailah ta tashi ta wanko fuskarta tare da gyara kwalliyarta, sabida Hajjah ke kiranta za
ta yi musu nasiha ita da Amarya TAIMIYYAH da ake shirin raka ta ɗakinta bada jimawa ba.
Sun isa ɗakin Hajjah lokacin har an kai TAIMIYYAH tana zaune daga ƙasan carfet ɗin ɗakin
Hajjah, ta rufe fuskarta da lulluɓi hawaye na faman sauka mata akan fuskarta. Don tun wa'azin da
aka gudanar a wajen walimar ya karya zuciyar TAIMIYYAH, tare da tunasar da ita gagarumin
aikin da ke gabanta na girman biyayyah wa miji da sauke dukkanin hakkokinsa da ya hau kanta.
Dole ne duk wata mace da ke wajen in dai ta san abinda ta ke yi to sai wannan wa'azi da
tunasarwar da shahararran Malamin da ya gudanar wa'axin ya yi, ya ratsa jikin mutum tare da
raunata zuciyarsa.
Idanun Suhailah ya sauka akan TAIMIYYAH da ke zaune daga ƙasan carfet, tana amsar nasihun
da Hajjah ta soma yi mata,wanda ke ratsa jiki da zuciyarta suna sake ɓallo ruwan hawaye akan
fuskarta.
Suhailah ta taka a hankali ta isa bakin gado in da Hajjah ke zaune ta zauna, tana ɗauke dubanta
daga kallon wajen da TAIMIYYAH ke zaune. Inna Dije ce ta shigo cikin ɗakin suka haɗu ita da
Hajjah su ka dinga yiwa su TAIMIYYAH nasiha me ratsa jiki.
Hajjah ta jajirce wajen tunasar da su muhimmncin sauke hakkokin juna a tsakaninsu,duk da cewa
ba agari ɗaya za su zauna ba hakan bai hana Hajjah sanar da su hakkokin junansu da ya rataya a
wuyarsu ba. Ta sanar da su cewa su ji tsoran Allah ka da ɗayansu ta yadda ta cutar da abokiyar
zamanta ko da da ƙwayar zarra ne,domin Ubangiji yana ji kuma yana kallon duk abinda bayinsa
ke aikatawa.
Sosai Hajjah da Inna Dije sukai anfani da kalamai na ilimi da hikimar zance, irin na manyan
matan da suka jiya suka ga yau, suke kuma shirin ganin gobe da jibi ma idan Allah ya yar je musu.
TAIMIYYAH kuka ta ke yi sosai mara sauti zuciyarta na sake karyewa, yayin da ita ma Suhailah
wasu kalaman na su Hajjah ya natsar da zuciyarta tare da sanyaya jikinta. Don sun yi mata jirwaye
me kamar wanka sosai cikin zantukansu, wanda ita kaɗai ta fahimci da ita suke yi ba da
TAIMIYYAH ba. Sabida ita ce ta ɗakko hanyar fara cutar da TAIMIYYAH tun farko, hakan yasa
jikinta ya yi matuƙar yin sanyi, nadamar abinda ta so aikatawa a ranar auren na sake lulluɓe
zuciyarta.
Hajjah ta sallami Suhailah bayan sun gama yi musu nasihun da suka dace, ita kuma TAIMIYYAH
Anty Safiya ce ta maida ta ɗakin da suke, in da ƴan uwanta da ƙawayenta ke jiranta don yi mata
rakiya zuwa GRA gidanta. Ba kuma su kaɗai za su yi mata rakiyar ba har da wasu daga cikin
dangin Ango dana Hajjah, za su raka Amarya don ganin ɗaki sabida zuwa gobe kowa zai watse ,
wasu ma tun yau suka kama gabansu tunda taro ya tashi lafiya. Saura dangi na kusa ne kawai za su
watse zuwa gobe,irin su Anty Safiya da su Inna Dije da suka zo daga nesa.......✍🏻
#Ɗansabo ce#
[12/15, 11:46 AM] +234 703 040 9541: Littafin TAIMIYYAH paid book ne,ga duk wanda ta
tsincesa a kowani irin group ne,kiji tsoran Allah karki karanta sai kin biya 500 naira only.
Za ku iya min magana ta wannan number ɗin 08167768704, ko kuma ku turo kuɗin ku kai tsaye ta
wannan account ɗin 0504192664 aisha ibrahim dansabo GTbank.*
Masu turo credit za ku turo katin MTN na 500 ta wannan line ɗin 08167768704.
_Ina ƴan kasuwa masu buƙatar a tallata muku hajar ku? Maza ku garzayo da kuɗi ƙalilan a tallata
muku kayan siyarwanku sai dai kawai ku ji ana kiran waya don buƙatan sayan kayan ku,ku
tuntuɓeni ta layina kamar haka 08167768704._
*72*
Misalin ƙarfe biyar da wasu mintuna motocin da suka ɗakko Amarya TAIMIYYAH, tare da
tawagan masu yi mata rakiya suka parker a cikin tanƙasheshen harabar compound ɗin cikin
gidanta. Tun daga waje masu kallo suka fara jinjina tsaruwar ginin gidan da haɗuwarsa, kafin a
shiga daga ciki kallo ya sake komawa sabo.
Tun daga falon da ke downstairs daddaɗan ƙamshin turaren wutar Nothern Bride ke tashi yana
bada wani irin sihirtaccen ƙamshi me kwantar da zuciya.
Ummie da Anty Mardiyyah da ke riƙe da Amarya TAIMIYAH wacce suka sanyata tsakiya,suna
directing ɗinta tare da bata umurnin yin addu'a da shigowa cikin gidan aurenta da ƙafar dama.
Sune suka cigaba da yi mata rakiya har zuwa ɗaya daga cikin haɗaɗɗun ɗakunan barcinta da ke
upstairs. Suka zaɓar mata ɗakin da ke kusa dana ƙarshe a matsayin na ta bedroom ɗin, don an
kammala shirya kayanta da akwatunan lefenta kaf a cikin ɗakin. Suna shiga wani irin daddaɗan
qamshin Nothern Bride scented ya doki hancinansu, wanda tun rana su Guggo Bilki da suka zo
sake kintsa ɗakin suka bi ko wani lungu da saƙo na gidan suka turare shi da waɗannan daddaɗan
ƙamshin turaren wutar. Amarya TAIMIYYAH da akai wa masauki akan tsakiyar gadonta ita ma
ƙamshin ya gama cika hancinta, har lokacin hawaye bai tsaya daga idanunta ba,kamar yadda bata
buɗe lulluɓin da akai mata wanda ya rufe fuskarta ba .
Dangin Maleek Ado su ne suka fara watsewa bayan sun gama shiga ko'ina sun sha kallo, ƴan
hassada suka dinga ji tamkar su soke kansu su huta da takaici. Masu fatan alkhairy kuma suka
dinga yi suna yaba tsaruwar gidan da haɗuwarsa, waɗanda ke da manyan waya suka dinga vedio
don nunawa sauran ƴan uwansu da basu sama halartan gidan Amaryar ba.
Cikin masu yin vedio ɗin tsaruwar gidan TAIMIYYAH har da ƙawayenta su Zee da su Maryam
Sunusi, waɗanda suka saki tare da sallamawa cewa ƙawar tasu ta tako gidan arziƙi. Don ko
maƙiyinta basa ji ya isa ya kushe tsaruwar wannan aljannar duniyar da TAIMIYYAH ta shigo
cikinsa, babu inda basu shiga sun yi wa vedio ba, suna yi suna yaba kyawu da tsaruwar ko'ina.
Ana kiraye-kirayen sallar Magriba ne aka fara watsewa domin barin Amarya ita kaɗai a ɗakinta,
da ɗaya da ɗaya su Zee suka dinga wa TAIMIYYAH da ke faman kuka sallama suna tafiya, don
tuni Maleek ya sallame su da manyan kuɗi na buɗe fuskar Amarya da siyan baki,wanda ƙawaye ke
kafewa sai anbasu kuɗi akan hakan bisa ga al'ada. To shi sun safe ya yi musu transper na kuɗin da
ya gigita su, sabida ya shaidawa Yasmeen cewa ba ya son kowace ƙawa ta tsaya masa a gida da
sunan wannan al'adar. Shiyasa tunda sun ga ɗaki da tsaruwar gidan Amarya sai kowacce ta kama
gabanta, bayan sun yi sallama da Amarya TAIMIYYAH da ke kukan rabuwa da su.
Hatta su Ummie da su Anty Mardy TAIMIYYAH bata san lokacin da suka silale suka gudu ba,
sabida babu wacce ta yi mata sallama tun da suka ga yadda ta ke kuka abin tausayi. Yasmeen ita
kaɗai ce ta gagara tafiya sabida yadda TAIMIYYAH ta riƙeta tana faman kuka tamkar ranta zai
fita, hakan yasa Anty Safiyya da Anty Rady da suka rage basu tafi ba, sun tsaya sake kintsa ko'ina
da buɗeshi da ƙamshin turaran wutar Traditional Nothern Incense, wanda aka yi ordern su daga
wajen Northern Regalia sabida haɗuwar ƙamshinsu da ke ƙawata waje, tare da narkar da zukatan
duk wanda ya shaƙi ƙamshin.
Bayan sun kammala kintsa wajen ne ana daf da kiran Isha'i lokacin, sai suka ce da Yasmeen ɗin ta
zauna tare da TAIMIYYAH har zuwa lokacin da Ango zai shigo, in ya so sai ya saka a mayar da
Yasmeen ɗin gida. Dama su ne suka so zama zuwa lokacin da Ango zai shigo ɗin, don ba zai yiwu
dama a bar TAIMIYYAH ita kaɗai ba. To ganin yadda TAIMIYYAH ta cukuikuye Yasmeen tana
faman kuka me motsa zuciya, sai hakan ya sanya su Anty Safiya yi musu sallama suka wuce zuwa
gidan Hajjah. Aka bar Yasmeen da TAIMIYYAH su kaɗai a gidan, Yasmeen na faman rarrashin
TAIMIYYAH akan ta tsaida kukan da take yi hakanan kada kanta ya yi ciwo .
Da ƙyar TAIMIYYAH ta tsaida kukan tana faman jan a jiyar zuciya, Yasmeen ita ce ta sanya
TAIMIYYAH ta shi ta ɗauro alwala, don gabatar da Sallar Magriba da bata yi ba har gashi ana
kiran Isha'i.
A hankali TAIMIYYAH ta zuro ƙafafunta zuwa ƙasa tana me yaye lulluɓin jikinta baki ɗaya ta aje
bisa bed ɗin, take kayan jikinta suka bayyana na wani haɗaɗɗan Embroidery lace dark gray da ta
sanya,wanda akaiwa ɗinkin boubou na zamani da ya zauna a jikinta tare da yi mata mugun kyau.
Fuskarta da akaiwa light make-up ya gama ɓaci da ruwan hawaye sabida uban kukan da ta sha, ta
dafe guiwar ƙafarta lokacin da take tsayuwa akan ƙafafunta, ta zube manyan idanunta da suka rine
zuwa ja akan Yasmeen ta ce, "Yasmeen to ina ne toilet ɗin ya ke?"
Yasmeen da hankalinta ke kan wayarta suna chart da Anty Laurat da ta turawa vedio ɗin gidan
TAIMIYYAH, ta ɗago ido ta dubi TAIMIYYAH tana mata pointing ɗin hanyar toilet ɗin,wanda ya
shige daga wani ɗan corridor da aka yi daga cikin bedroom ɗin. TAIMIYYAH ta fara takawa cikin
slow motion ta isa cikin corridor ɗin, idanunta ya sauka akan ƙofar banɗakin da ke facing ɗinta, ta
kai hannu ta buɗe tana sanya kanta cik tana karanto addu'ar shiga banɗakin. Idanunta ya sauka
akan tsaruwar banɗakin wanda ya haɗu kai ka ce ba don a yi buƙatuwa da sauke najasa da kauda
ƙazanta aka gina shi dominsa ba, ta dinga bin ko'ina da kallo tana jinjina yadda ake narka dukiya a
ƙasa. Ta gabatar da uzurinta ta fito zuwa cikin bedroom ɗin don gabatar da sallolinta, idanunta
akan Yasmeen wacce ita tana off shiyasa ta yi zaune tana faman chart abin ta. TAIMIYYAH ta
shagwaɓe muryarta da har ta ɗan dishe sabida kuka ta ce, "Yasmeen Hijab please!"
Yasmeen ta ɗago idanunta ta sauke akan TAIMIYYAH tare da sakin smile,sannan ta miƙe ta nufi
wajen ƙaton wardrobe ɗin da ke manne jikin bangon ɗakin, ta buɗe ta zarowa TAIMIYYAH
Hijab sabo dal daga cikin waɗanda ke jere tsaf a cikin drawer ɗin. Sabida kaf an kammala
kintsawa TAIMIYYAH duk wasu kayanta a ciki, cikin tsari da jera kowani kalar kaya a muhallin
da ya dace da shi.
Lokacin da TAIMIYYAH ta idar da sallar ta kammala yin azkar,sai ta miƙe tare da zare Hijab ɗin
jikinta ta koma bakin haɗaɗɗan gadonta ta zauna. Zuciyarta da jikinta gaba ɗaya a sanyaye suke
tana jin wani irin kewar gida dana Iyah na danne zuciayarta, ta ɗaga kai ta dubi Yasmeen ta na
cewa, "Yasmeen don Allah ki kwana anan kar ki yadda a rabamu please!" Yasmeen ta saki
murmushi cikin son kwantarwa da TAIMIYYAH hankali ta ce, "Kar ki damu Baby kwana zan yi
tunda ga ɗakuna nan birjik sama da ƙasa, kin ga ba sai kawai in yi branching a ƙasa ba, in bar ki
ke da Angonki a sama ku sha Amarcinku."
TAIMIYYAH ta gyaɗa kai cike da gamsuwa hankalinta na kwanciya ta ce, "Yauwa Yasmeen i luv
u."
Yasmeen ta sake sakin murmushi ta ce, "Luv u too Mrs.Maleek Ado, yanzu dai bari in zo in ɗan
sake gyara miki wannan fuskar da ki ka koɗar da kuka, kada Ango ya iso ya ga fuskar Amaryarsa
a ƙuje."
Daga haka Yasmeen ta ɗauki jakarta da ke maƙare da tsadaddun kayan kwalliya, ta nufi wajen
TAIMIYYAH ta gyare mata fuskarta tsaf! Nan da nan TAIMIYYAH ta sake fitowa a Amaryarta
ras! Fuskarnan na haskawa da wani irin sihirtaccen kyau, ga fitinannan ƙamshin da dukkanin
jikinta ke fitarwa me asalin narkar da zuciya. Yasmeen ta miƙe ta isa wajen da aka danka wasu
Aromatic Scented Candles masu a zabar kyau da ƙamshi, ta ɗakko guda ɗaya ta kunna shi ta aje
bisa gefen side drawer na gado. Nan da nan wani irin daddaɗan ƙamshi ya sake cika bedroom ɗin,
ta lumshe idanunta ta buɗe akan TAIMIYYAH tana cewa, "Wow! Gaskiya wannan Scented
Candle ɗin abin saye ne TAIMIYYAH, ke kinji wani ƙamshi me natsa zuciya da ke tashi, gaskiya
Hajjah ba ƙaramin son ki take yi ba,matar ta kashe dukiya akan ki tamkar ke ta haifa ba Maleek
ɗin ba. Don Allah TAIMIYYAH ki baiwa marar ɗa kunya wajen yi wa ɗanta biyayyah tare da
bashi kulawar da ya dace."
TAIMIYYAH ta gyaɗa kai tana jin ƙaunar Hajjah da ɗanta me tsanani na ratsa zuciyarta, ta yi
maganar cikin sanyin murya ta ce, "In sha Allah Yasmeen."
Kafin Yasmeen ɗin ta ce komi wayar TAIMIYYAH da ke aje bisa bed ɗin ya fara ringing, wanda
salon Ringing tone ɗin kaɗai ya shaida mata ko waye me kiran. Ta miƙa hannu ta ɗauki wayar tana
me yin receiving ta kai kunni, cike da shagwaɓa ta yi masa sallama tana maida bakinta ta tsuke,
lokacin da Maleek Ado ke amsa sallamar tare da jefa mata tambayar cewa ita da waye a gidan?
TAIMIYYAH ta sake shagwaɓe murya kamar me shirin yin kuka ta ce, "Ni da Yasmeen ce." Daga
haka ta sake yin shiru tana sauraren abinda ya ke gaya mata,kafin ta shagwaɓe fuska tana ɗan turo
baki kaɗan ta ce, "Okey tuh." Bata sake faɗin komi ba bayan hakan ta yi hanging up tana maida
wayar ta aje in da ya ke, Yasmeen da ta zurawa TAIMIYYAH ido tana kallon yadda ta ke zubawa
Maleek shagwaɓa a cikin waya ta ce, "Kai TAIMIYYAH wannan irin shagwaɓa ai sai ki sanya ya
kore ni in fasa taya ki kwanan da nayi niyya."
TAIMITYAH ta ɗago manyan idanunta da sauri ta dubi Yasmeen, cike da magiya ta ce, "Please!
Yasmeen kar ki fasa kwana don Allah, wallahi tsoro na ke ji ba zan iya kwana daga ni sai shi a
wannan gidan ba,please! Kar ki tafi ki bar ni Sis!"
Yasmeen ta saki murmushi tana jinjina wautar TAIMIYYAH ta ce, "Na ji Babyn Maleek kar ki
damu zan kwana."
Daga haka Yasmeen ta cigaba da ribatan TAIMIYYAH suna hiransu, har zuwa lokacin da Maleek
Ado ya iso gidan.
Yusuf driver da ke janye da motar shi ne ya yi saurin fitowa daga side ɗinsa, yana buɗewa Maleek
ɗin murfin motar ɓangarensa. Maleek ya zuro ƙafafunsa ya fito daga cikin motar, yana sanye
cikin farin shadda me asalin nauyin kuɗi, wanda akai wa ɗinkin riga da wando babu Malum-
Malum, amma duk da hakan ya yi kyau sosai ya fito a Angonsa sak! Sai tashin ƙamshin turarensa
na AMOUAGE ke tashi. Yusuf shi ne ya kwashi manyan ledojin da ke zube a cikin motar,ya
rufawa ubangidan nasa baya har zuwa bakin ƙofar shiga falon gidan. Maleek ya waiwayo ya
amshi ledojin da ke hannun Yusuf ɗin, ya shige zuwa cikin falon bayan Yusuf ya juya ya bar
wajen.
Wani irin qamshin turaren wutar da ya buɗe falon ne ya doki hancinsa, wanda hakan har sai da ya
sanya shi lumshe idanunsa da sake buɗesu, yana sake shaƙo ƙamshin me narkar da zuciya. Ya
cigaba da takawa zuwa wajen da aka aje center table da ke tsakiyar falon ya aje ledojin
hannunsa,ya juya yana nufan hanyar da zai sada shi da matakalan benan da zai kai shi zuwa
upstairs.
Lokacin da ya isa zuwa saman direct ɗakin da ya ke jiyo muryar Yasmeen ya nufa, ya yi knocking
ƙofar Yasmeen ta amsa daga ciki tana cewa ya shigo.
Ya tura ƙofar a hankali tare da sanya kansa cikin ɗakin, wani irin ni'imtaccen ƙamshin da ya fi na
wanda ya shaƙa a ƙasa daɗi da kwantar da zuciya ya bugi hancinsa. Idanunsa ya sauka akan
Amarya TAIMIYYAH wacce ta yi saurin jan mayafi ta lulluɓe jikinta har zuwa fuskarta, tun
lokacin da ta ji ya yi knocking ƙofar ƙirjinta ya yi wani irin doka mata.
Maleek ya cigaba da takawa zuwa cikin ɗakin yana amsa gaisuwar da Yasmeen ke masa, kafin ta
sulale ta baro musu ɗakin ta sauka zuwa ƙasa.
Maleek ya cigaba takawa har zuwa bakin gadon da TAIMIYYAH ke kai, ya zauna daga gefen
gadon yana me kai hannu ya yaye lulluɓin da ya rufe fuskarta. Kyakykyawar fuskarta ta bayyana a
idanunsa, ya saki wani ƙayataccen murmushi tare da yin ƙasa da muryarsa sosai ya ce, "Welcome
to my world wife! Ina fata za ki bani cikakkiyar kulawar da ta dace?"
TAIMIYYAH ta sake yin ƙasa da kanta wani abu na motsawa cikin zuciyarta, ta gyaɗa kai a
hankali ba tare da ta yi magana ba. Hakan yasa Maleek ya kai lallausan hannunsa ya ɗago fuskarta
baki ɗaya, cikin bazata ya kai bakinsa ya mannawa TAIMIYYAH sumba a saman goshi.
Ta lumshe idanunta jikinta na ɗan ɗaukar rawa, ƙamshin jikinsa na sake haifar da wani abu me
ƙarfi a zuciyarta. Maleek ya sake ƙasa da murya ya ce, "Wife bari in sallami Yasmeen in dawo
please! Ko mu je tare ki yi mata rakiya ne?"
TAIMIYYAH ta yi saurin buɗe idanunta ta sauke akan Maleek Ado, wanda ya tsare ta da nasa
idanun yana bin ta da wani irin mayen kallo. Ta buɗe baki cike da shagwaɓa ta ce, "Please ka bar
ta mu kwana tare don Allah Yah Maleek."
TAIMIYYAH ta yi maganar cike da magiya hawaye na taruwa a idanunta, don ita da gaske take yi
har cikin zuciyarta bata son Yasmeen ta tafi ta barta, sabida tana tsoron kasancewa da Maleek Ado,
sabida ya gama kimsa tsoronsa a zuciyarta me yawa. Maleek ya sake sakin murmushi yana kai
hannu ya ɗagota baki ɗayanta ya miƙar tsaye,lokacin da shi ma ya miƙe tsayen idanunsa har
lokacin akanta suke.
Daga haka ya riƙo hannun TAIMIYYAH suna takawa don fitowa daga ɗakin zuwa downstairs,
duk jikinta ya yi wani irin sanyi ga fargaban da ke cin zuciyarta da bata san musabbabin jin hakan
da ta ke yi ba. Lokacin da suka iso cikin falon ƙasan sun samu Yasmeen cikin shiri don ga jakarta
nan a gefe guda ta aje, ta ɗaga ido ta dubi TAIMIYYAH wacce ta kwaɓe fuska daf ta ke da ta saki
kuka. Yasmeen ta ɗauke kai daga duban TAIMIYYAH tana miƙewa tsaye ta ce, "Sis zan wuce
gida na yi miki promise ɗin dawowa gobe in yini miki idan har ba gobe zamu wuce ba kin ji?"
TAIMIYYAH hawaye suka ziraro daga idanunta, ta dubi Yasmeen cikin rawar murya ta ce, "But ai
ba haka muka yi da ke ba Yasmeen, kin ce min za ki kwana don Allah kar ki tafi ki barni Sis."
Tausayin TAIMIYYAH ya kama zuciyar Yasmeen, amma sai ta daure ta dubi TAIMIYYAH ta ce,
"Sorry TAIMIYYAH ni ma haka na so amma yanzu Mamie ta kira ta ce lallai in koma komin dare,
so gobe zan dawo kar ki damu kin ji Baby?"
TAIMIYYAH ta sake matso hawaye ba tare da ta kuma magana ba, akan idanunta Maleek ya
miƙawa Yasmeen rafar kuɗin da bata tantance ko nawa bane. Sukai sallama da juna yana sanar da
Yasmeen cewa Yusuf driver na jiranta a parking space, shi zai maida ta gida. Yasmeen ta yi godia
tana ɗaukar jakarta ta nufi ƙofar fita daga cikin falon, ba tare da ta iya sake duban sashin da
TAIMIYYAH ke daga zaune cikin seater tana kuka ba. Ta fice da sassarfa hawaye na wanke
fuskarta ita ma,don dauriya kawai ta ke yi amma har cikin zuciyarta ita ma tana jin babu daɗi a
ranta.
TAIMIYYAH ta sake ƙara volume ɗin kukanta lokacin da ta tabbatar da cewa Yasmeen ta fice
daga cikin ɗakin, Maleek ya yi saurin kai guiwarsa ƙasa tare da tsugunawa a gaban TAIMIYYAH
ya fara rarrashinta. Ganin bata da alamun tsaida kukan ya sanya shi ɗaukarta cak! Ya nufi makalan
da zai kai su upstairs, dukkanin jikinsa na sake mutuwa sabida daddaɗan ƙamshinta da ke addaban
hancinsa, yana sake kunna wutar fitina a zuciyarsa akan TAIMIYYAH.
TAIMIYYAH ta yi laƙwas a cikin jikinsa tana cigaba da kukanta cikin ƙaramin sauti, har ya isa da
ita zuwa ɗakin baccinsa ba tare da ta san ɗakin nasa ya kai ta ba, sabida fuskart da ke cikin
ƙirjinsa. Sai da ya dire ta a tsakiyar makeken bed ɗinsa sannan ta buɗe idanunta tana kallon
ɗakin,wanda ya ke fitar da wani daddaɗan ƙamshin turaturen Nothern King da ya gama buɗe
ɗakin. Ta yi saurin duban fuskar Maleek Ado tana sake zararo hawaye daga idanunta, ta maida
kanta tsakanin cinyoyinta tana sake sakin wani sabon kukan.
"Wife don Allah ki taimakeni ki tsaida wannan kukan, ko so ki ke ki tunzura zuciyata in yi abinda
ban shirya yinsa nan kusa ba?"
Maleek Ado ya yi maganar lokacin da ya ke aje wayoyinsa daga kan side drawer, ya waiwayowa
ya sake zube idanunsa akan fuskar TAIMIYYAH da ke duƙe cikin cinyoyinta. Ta yi saurin ɗago
kanta tana girgiza masa kai,hakan ya sanya Maleek sakin smile yana faɗin, "Alright! Baby stop
craying ni babu abinda zan miki da ya wuce baki kulawar da ta dace."
Daga haka ya fice daga ɗakin ya bar TAIMIYYAH da bin ko'ina da kallo tana yaba tsaruwar ɗakin
nasa,wanda aka zubawa kayan more rayuwa tamkar ba za a bar gidan duniya ba. Komi na cikin
ɗakin white ne da akaiwa ratsin blue kaɗan, babu abinda ya fi ɗaukar hankalinta irin gadon da take
kai wanda bata taɓa cin karo da irinsa ba ko da a duniyar media ne kuwa.
Ta cigaba da bin ko wani lungu da saƙo da kallo tana sauke ajiyar zuciya, har zuwa lokacin da
Maleek ya dawo cikin ɗakin hannunsa riƙe da manyan ledoji guda biyu. Ɗaya hannun nasa riƙe da
baban plate da ya ɗauro cups biyu akai, ya zube kayan a tsakiyar table ɗin da ke ɗakin yana
juyowa ya sauke ganinsa akan TAIMIYYAH, wacce jin shigowarsa yasa ta maida kanta ƙasa ta
sunkuyar tamkar wata marar gaskiya.
A hankali ya taka zuwa bakin gadon ya zauna yana miƙa hannu ya janyota zuwa jikinsa, ta saki
kukan shagwaɓa tana ƙoƙarin ƙwace jikinta amma ya hana ta dakar hakan. Lulluɓin jikinta ya
rabata da shi yana bin ko'ina na jikinta da kallo, wutar ƙaunarta da zallar zalamar da ya ke ji a
kanta na sake ruruwa a cikin zuciyarsa.
Sakinta ya yi ta koma ta ƙudundune jikinta akan gadon, shi kuma Maleek sai ya miƙe hannunsa
riƙe da mayafin da ya rabata da shi ya nufi hanyar fita daga ɗakin. TAIMIYYAH sam bata san
fitarsa ba sai lokacin da ya dawo ɗauke da kayan bacci a hannunsa, ya zube su akan gadon yana
duban yadda ta dunƙule a tsakiyar gadonsa, abin sai ya bashi dariya ya isa bakin gadon ya ɗakkota
cak! Ɗinta ya yi mata masauki akan cinyarsa. TAIMIYYAH ta buɗe manyan idanunta ta sauke
akan fuskar Maleek, wanda ya miskile fuska babu annuri ko kaɗan a saman fuskar. Ta yi saurin
maida idanunta ta rintse hawaye na silalowa suna saukowa daga idanunta, jikinta gaba ki ɗaya
rawa ya ke tsoransa na sake cika zuciyarta.
Duk iya magiyanta akan ya barta ta cire kayan jikinta da kanta ya hana ta damar hakan, da kansa
ya cire mata rigar jikinta ya sanya mata fingilallun riga da wando na bacci da ya ɗakko mata daga
ɗaki, waɗanda basu da maraba da babu sabida rigar transparent ce da ta bayyana asirin halittar
jikinta,wandon kuma ɗan ƙarami ne wanda tsayinsa ba zai wuce iya cinyarta ba.
TAIMIYYAH ta kasa ɗaga ido ta dubesa lokacin da ya kammala sanya mata kayan, wani irin
kunya ke ɗawainiya da ita yayin da shi gogan babu abinda ya shafesa. Idanu ya zubawa ƙirjinta da
ya zare Bra ɗin da ta ke sanye dashi, ya kai bakinsa a hankali ya sumbaci wajen yana jin wani irin
abu na tsirga masa tunda daga yatsun ƙafafunsa zuwa kwanyarsa.
Ya miƙe yana riƙe da ita a jikinsa ya ke takawa zuwa hanyar bathroom da ke manne cikin bedroom
ɗin nasa, ya dire ta daga bakin ƙofar shiga banɗakin yana cewa, "Wife shiga ki yo alwala please!"
TAIMIYYAH ta kasa ɗagowa ta dubesa lokacin da ya ƙarisa direta a ƙasa, sai ma silalewa da ta yi
ta durƙushe daga ƙasa tana manne ƙirjinta a tsakanin cinyoyinta. Hakan yasa Maleek sakin
murmushi yana juyawa ya bar mata wajen, sabida ya gama gane bakomi ke ɗawainiya da ita sai
kunya,amma yana ji a ransa cewa nan da lokaci kaɗan zai maida ta irin kalar da ya ke so ta zame
masa.
Ɗakinta shi ya koma ya shiga toilet ɗinta ya yo wanka da alwala ya fito, ya koma zuwa nasa ɗakin
bayan ya ɗakkowa TAIMIYYAH Hijab ɗin da za ta yi sallah da shi. Lokacin da ya shiga ya sameta
har ta fito daga banɗakin ta sake naɗewa akan gado, ya taka zuwa bakin bed ɗin yana aje mata
Hijab ɗin ya ce, "Baby ga Hijab nan ki tashi ki sanya mu gabatar da sallah." Daga haka ya taka
zuwa wajen da kayansa ke shirye cikin drawer,ya fiddo wasu fararen Pajamas masu laushi ya
sanya. Nan da nan ya yi wani irin kyau cikin kayan baccin da suka haska shi,ya taka zuwa gaban
mirrow yana ɗaukar turarensa na AMOUAGE ya fesa kaɗan. Ƙamshinsa ya haɗu da ƙamshin
Turaren wutar Nothern King da ya buɗe ɗakin ya sake bada wani sassayar ƙamshi me narkar da
zuciya.
Ya ɗaga manyan idanunsa ya saukesu akan TAIMIYYAH wacce ta yi wuƙi-wuƙi da ido, tana
sanye da Hijab ɗin da ya aje mata. Yadda ta ke zare ido zaka san cewa a tsorace ta ke, ganin irin
kallon da ya ke jifanta da shi yasa ta saurin ɗauke ido daga satan dubansa da ta ke yi. Ya saki
ƙayataccen murmushi yana takawa zuwa bakin gadon da take zaune, ya miƙa mata hannunsa yana
faɗin, "Wife ta so mu gabatar da Sallar Nafila ki bani wani abu in ci don yunwa na ke ji."
TAIMIYYAH ta ƙi miƙa masa hannunta kamar yadda ya so, sai ta sakko daga kan gadon tana
faman zumɓure baki da yin ƙasa da kanta.......✍🏻
#Ɗansabo ce#
[12/15, 11:46 AM] +234 703 040 9541: Littafin TAIMIYYAH paid book ne,ga duk wanda ta
tsincesa a kowani irin group ne,kiji tsoran Allah karki karanta sai kin biya 500 naira only.
Za ku iya min magana ta wannan number ɗin 08167768704, ko kuma ku turo kuɗin ku kai tsaye ta
wannan account ɗin 0504192664 aisha ibrahim dansabo GTbank.*
*Sai ku tura shaidan biyanku ta wannan line ɗin 08167768704.*
Masu turo credit za ku turo katin MTN na 500 ta wannan line ɗin 08167768704.
_Ina ƴan kasuwa masu buƙatar a tallata muku hajar ku? Maza ku garzayo da kuɗi ƙalilan a tallata
muku kayan siyarwanku sai dai kawai ku ji ana kiran waya don buƙatan sayan kayan ku,ku
tuntuɓeni ta layina kamar haka 08167768704._
*73*
Shi ya jasu jam'in sallar nafilar, bayan sun idar ne ya juyo zuwa gareta yana fuskantarta, tare da
miƙa hannunsa na dama ya dafe kanta da shi, ya buɗe baki ya fara karanto wannan addu'ar ya ce,
" َو َش ِّر َم ا َجَبْلَتَها َع َلْيِه، َو َأُعوُذ ِبَك ِم ْن َشِّرَها، َو َخْيَر َم ا َجَبْلَتَها َع َلْيِه،َالَّلُهَّم ِإِّني َأْس َأُلَك َخْيَر َها.
Allahummah innee as-aluka khayraha wakhayra ma jabaltaha 'alayh, wa-a'oothu bika min
sharriha washarri ma jabaltaha 'alayh.
(Ya Allah ina roƙon Ka laherinta da alherin da Ka dabi'antar da ita a kansa, kuma ina neman
tsarinka daga sharrinta da sharrin Da ka dabi'antar da ita a kansa).
Daga haka ya kora da wasu tarin addu'o'in fatan alkhairy, akan Allah Ya albarkaci aurensu Ya
kuma basu zaman lafiya, tare da zuriyya masu albarka.
Bayan ya kammala addu'o'in ne ya yi mata wasu ƴan tambayoyi akan abinda ya shafi addininta,
TAIMIYYAH ta buɗe baki a hankali tana bashi amsar dukkanin tambayoyin da ya ke jefo mata.
Bai ci ta gyara ko guda ɗaya ba har ya gama da yi mata tambayoyin,hakan ya sake haifar da tarin
ƙaunarta me tsananin a cikin zuciyarsa. Yana me sake miƙa godia ga Allah da Ya azurtashi da
samun mace kamar TAIMIYYAH, wacce ta mallakin tarin abubuwan birgewa cikin halittarta da
ɗabi'unta, ga kuma baiwar ilimin sanin addininta daidai gwargwado da Allah Ya azurta ta da shi.
"Zaynab wannan Hijab ɗin cire sa za ki yi, ki matso mu ciyar da juna,don yunwa na ke ji kin ji?"
Maleek Ado ya yi maganar idanunsa akan TAIMIYYAH wacce ta shagwaɓe fuska, dukkanin
jikinta a sanyaye yake ga tarin tsoro da fargaba da ke sake danne zuciyarta. Ta ɗago manyan
idanunta ta sauke akan Maleek tana ɗan zumɓure baki kaɗan ta ce, "Please! Yah Maleek ba sai
na....." Maleek Ado bai barta ta ƙarisa faɗin abinda ta ke so ba ya matsa zuwa gareta tare da
janyota zuwa jikinsa.
Duk iya ƙoƙarinta na son hana shi rabata da Hijab ɗin jikinta, bata samu nasara ba,sai da ya cire
mata shi yana me wurga shi ya isa can ƙarshen bed ɗinsa ya yi masauki.
TAIMIYYAH ta ɓude baki za ta sakar masa kuka ya yi gaggawar haɗe bakinsu waje guda, ya
shiga bata kyakykyawar sumba a uzurce tamkar mayunwacin da ya kwana bai ci ba.
"Baby bana son gardama i think na sanar da ke hakan tun jiya, so kisa a ranki duk idan na ce ki yi
abu ki kai gardama,to za ki biya bashin hakan da abinda baki taɓa za to ba. Oya Bismillah bani
abinci in ci Baby na!"
Maleek Ado ya yi maganar lokacin da ya ke raba bakinsa da na TAIMIYYAH, ya aje ta daga gefen
damarsa yana janyo plate ɗin da ya juye gasassun naman Kaji dana rago, waɗanda suka sha kayan
haɗi da wani irin sauce daga gefe guda, sai tashin ƙamshi suke yi abin sha'awa.
Duk yadda ta so zuƙewa ba shi naman da kanta sai ya turje, sai da ta bashi da kanta sannan ya ci,
bayan ta gama bashi shi kuma ya dage akan da kansa zai ramawa kura aniyarta. TAIMIYYAH na
hawayen shagwaɓa yana bata namar tana ci, a haka ta ci me ɗan yawa kafin ta kawar da fuska
alamun ta ƙoshi. Sai ya ciko cup da fresh milk ya kai bakinta ta ɗan sha kaɗan ta kauda fuska, ya
shanye ragowar yana aje cup ɗin daga ƙasa ya kai bakinsa bisa kunnin TAIMIYYAH, yana raɗa
mata wasu kalamai masu nauyi.
Ta yi saurin haɗe kanta da guiwa tana ji tamkar ƙasa ya tsage ta shige cikinsa, shi ko Maleek sai ya
saki murmushi ya ce, "TAIMIYYAHH oya tashi ki wanko baki ki zo mu kwanta." Karon farko
kenan da TAIMIYYAH ta ji ya kirayeta da wannan sunan, shiyasa ta ɗago da kanta cikin sauri ta
dubesa cikin ido, tana jin wani abu na motsa a zuciyarta sabida yadda ya iya faɗin sunan, da wani
irin salo da bata taɓa jin an kira sunan da shi haka ba. Ya ɗage mata gira guda yana sake shigar da
idanunsa cikin nata, hakan yasa TAIMIYYAH saurin janye idanunta ta miƙe a kunyace tana me
daga guiwar ƙafarta, ta fara takawa don nufar hanyar toilet ɗin ɗakin nasa. Maleek Ado ya bi
bayanta da kallo yana kallon yadda ta ke takawa cikin tafiyarta da ke motsa zuciyarsa matuƙa,
siririn ƙafarta me laluran ya ke kallo yana jin wani abu na danne zuciyarsa.
Lokacin da ta fito shi kuma ya shige banɗakin bayan ya yi locking ƙofar fita daga ɗakin baki ɗaya,
don a jikinsa ya ke jin sai TAIMIYYAH ta nemi guduwa daga ɗakin kafin ya fito.
Aiko hakan ne ya kasance don tana ganin ya shiga toilet ɗin ta yi saurin ɗaukar Hijab ɗinta ta nufi
ƙofar fita, sai dai tana murɗa handle ɗin ta ji sa a kulle, sai ta yi tsaye tana faman sauke ajiyar
zuciya, wani irin tsoro da fargaba na sake lulluɓeta. A haka Maleek Ado ya fito ya same ta a tsaye
daga can bakin ƙofar fita daga ɗakin, sai ya saki murmushi yana takawa ya cimmata a wajen. Bai
yi magana ba illah ɗaukarta cak! Da ya yi ya nufi wajen makunnin fitillun ɗakin ya yi musu light
off! Sannan ya cigaba da takawa da ita ɗauke a jikinsa zuwa bed, ya yi mata masauki a tsakiyar
gadon, yana me hayowa shi ma baki ɗaya zuwa kan gadon, lokacin da TAIMIYYAH ta mirgina ta
yi gefe guda tana sakin masa kuka.
Ya zame ya kwanta yana cigaba da kallon yadda ta cimimiye jikinta da Hijab ɗin da ke hannunta,
bai yi magana ba ya gyara kwanciyarsa yana me juya mata baya, kunnuwansa na sauraren sautin
kukan da ta ke yi.
TAIMIYYAH ganin ya juya mata baya yasa ta sake matsawa can ƙarshen gadon tana takure
jikinta, ta tsaida kukan da ta ke yi tana faman sauke a jiyar zuciya.
Maleek ya yi lamo yana sauraren duk wani motsin da ta ke yi, har zuwa lokacin da ya ji shiru sai
waiwayo da fuskarsa yana duban yadda ta juya masa baya ita ma. Ya saki wani smile yana sake
juya mata baya tamkar wanda bacci ya ɗauka, hakan yasa TAIMIYYAH da ta juyo don ta saci
dubansa ta sauke wani ajiyar zuciya,tana jin releif a ranta don a tunaninta bacci ne ya yi nasaran
ɗauke Maleek Ado. Sai ta juya ta sake gyara kwanciyarta har lokacin Hijab ne a jikinta ta
cimimiye da shi, ta maida idanunta ta rufe tana karanto addu'ar kwanciya bacci.
Maleek Ado sai da ya tabbatar bacci ya ɗauki TAIMIYYAH, sannan a hankali ya matsa zuwa
gareta tare da janyota zuwa jikinsa, ya yi mata wani kyakykyawar runguma da ya sanya
TAIMIYYAH farkawa a firgice, ta buɗe baki za ta sakin masa kuka amma sai ya haɗe bakinsu
waje guda, ya hanata damar hakan. TAIMIYYAH tana ji tana gani ya rabata da Hijab ɗin da ta
cimimiye da shi ya yi wurgi da shi, tare da fara rabata da kayan baccin da ke jikinta baki ɗaya.
Ta saki wani kuka me sauti dukkanin jikinta na ɗaukar rawa, lokacin da ta ji bakinsa akan ƙirjinta
ya na mata wani irin salo,wanda ya nemi tsaida bugun numfashinta na wucin gadi.
Ta firgice ta gigice da salon da take amsa daga wajen Maleek Ado, wanda ke aika mata da zafafan
saƙonninsa masu asalin motsa xuciya, da kiɗima gangar jikin wanda ake aikawa saƙon, duk iya
kuka da magiyan da TAIMIYYAH ke masa sam baya jinta, burinsa kawai su zama abu ɗaya a
wannan daren, domin ba ya ji akwai abinda zai hana sa cinma burinsa.
Musamman da ya kasance ya tara manyan buƙatu masu yawa, sabida Suhailah ta jima da hana shi
kanta, bare ya sauke nauyin sha'awar da ke addabarsa.Dannewa kawai ya ke yi amma a yau ɗin ba
ya ji zai iya zubawa TAIMIYYAH ido,ba tare da ya fara rage manyan buƙatun da suka cika
mararsa ba.
TAIMIYYAH bata sake gigicewa ba sai lokacin da ta ji ya ɗauki hanyar cika burinsa, yana karanto
addu'ar saduwa da iyali yana cewa,
" َو َج ِّنِب الَّش ْيَطاَن َم ا َر َز ْقَتَنا، ِبْس ِم ِهللا الّلُهَّم َج ِّنْبَنا الَّش ْيَطاَن."
Bismillah! Allahummah jannibnash-shaytan, wajannibish-shaytana ma razaqtana.
(Da sunan Allah! Ya Allah! Ka nisantar da shaidan daga garemu, kuma ka nisantar da shaidan daga
abin da za Ka azurta mu da shi).
Daga haka TAIMIYYAH ta ji Maleek ya ɗauki hanyar cillata izuwa wata duniya,wanda bata taɓa
shiga ciki ba.Duk iya kuka da cizo tare da kiraya-kirayen sunan su Iyah kan su zo su ceceta,
hakan bai hana Maleek Ado cika burinsa na maida ta cikakkiyar mace ba. Ta gurzu ta kuma sha
matuƙar wahala, duk da cewa Maleek ɗin ya yi matuƙar ƙoƙari wajen ganin ya iya controlling
kansa, ba tare da ya cutar da ita sosai ba.
Cikin daren ya tabbatar ya fara bata duk wani kulawar da ya kamata, don rage mata raɗaɗin da
take ji domin baƙaramin tausayinta ya ji ba,sabida ta gurzu ba kaɗan ba shi har dauriyarta ma ya
gani sosai a daren.
TAIMIYYAH ba baka sai kunni kukan ma tun tana iyawa har ta kasa, jikinta ya ɗauki wani irin
zafin zazzaɓi sai da Maleek ya bata madara ta sha da ƙyar, sannan ya bata wani pain relief kafin ta
iya kwanciya don yin bacci. Sai lokacin ne kuma hawaye ya ɓalle daga idanunta yana wanke
fuskarta,dukkanin ilahirin jikinta ciwo ya ke mata ba kaɗan ba, tana jin lokacin da ya hayo kan
gadon tare da janyota zuwa jikinsa ya rungumeta.Ta sake sakin kuka ilahirin jikinta na sake ɗaukar
rawa,don a tunanin wani abun zai sake nema daga gareta. Ganin hakan ya sanya Maleek sake
rungumarta, ya buɗe baki yana aikin rarrashinta da furta mata kalamai masu matuƙar nauyi.
Sai da baccin wuya ya sace ta sannan ya kwantar da ita a hankali, tare da rufa mata lallausar duvet
ya sauka daga bed ɗin ya nufi bathroom, don tsarkake jikinsa ya ɗauro alwala ya fito. Sallah ya
gabatar raka'a biyu ya gurfana gaban Ubangiji yana miƙa godiyar sa ga Allah,wanda ya azurta shi
da samun TAIMIYYAH a matsayin matar aurensa. Ya jima yana addu'o'i kafin ya tashi ya koma
zuwa kan gadon, yana shigewa cikin bargon ya dawo da TAIMIYYAH xuwa cikin jikinsa ya
rumgumeta, yadda ba zai takura ta daga bacci me nauyin da ya sace ta ba. A hankali ya kai bakinsa
ya sumbaci goshinta zuwa wuyarta ,yana jin wani wutar ƙaunarta na sake ruruwa a zuciya da
gangar jikinsa.
Wani irin zazzafar soyayyarta ke kwaranya, yana bin duk wani kafar sadarwa na jikinsa yana
mamayewa, bai taɓa gasgata karin maganar da Hausawa ke cewa, " _Gaba da gabantaba wai
aljani ya taka wuta ._ " Sai a yau da ya mallaki TAIMIYYAH gaba ki ɗayanta, ya ɗanɗana kalar
zumarta sannan ya gasgasata cewa tabbas karin maganar haka ta ke, don duniyar da TAIMIYYAH
ta kai shi ba irin wanda ya saba zuwa ba ne. Kalar zumar da ya lasa sam bai yi daidai da irin
wanda ya saba ɗanɗanar zaƙinta daga Suhailah bane. Ita wannan zaƙinta na mussmman ne, da bai
san ta yadda zai iya misalta zaƙi da ɗanɗanonta ba.
Ya sake shigar da ita cikin jikinsa yana kai hannunsa zuwa muhallin da ya fi komi ɗaukar
hankalinsa a jikinta, ganin ta motsa tana shirin farkawa ya sanya Maleek janye hannunsa daga kan
ƙirjinta. Ya cigaba da yawo da shi cikin jikinta, lokacin da hannunsa ya kai kan ƙafarta me laluran
wanda ya sirance, ba kamar lafiyayyen da ke a cike da tsoka ba,sai ya samu kansa da riƙe ƙafar
yana shafa shi a hankali, wani abu me nauyi na tasowa daga ƙasan zuciyarsa yana danne ƙirjinsa.
A haka bacci ya ɗauke Maleek yana rungume da TAIMIYYAH a cikin faffaɗar ƙirjinsa, tamkar zai
maida ita cikin jikinsa baki ɗaya.
*Washegary.*
Maleek Ado shi ne ya fara farkawa ganin lokaci ya ja har sun makara yin sallar asuba akan lokaci,
yasa shi sauka daga kan gadon bayan raba TAIMIYYAH da jikinsa, ya gyara mata kwanciya bisa
bed ɗin. Ya nufi toilet a gaggauce don yin buƙatunsa ya ɗauro alwala ya fito, ya nufi wajen da
sallayar da suka yi sallah jiya ya ke a shinfiɗe, ya hau kai ya tada sallah.
Bayan ya idar ya tsaya ya yi azkar ɗinsa da addu'o'i sannan ya miƙe zuwa bakin bed ɗin, ya zauna
daga gefen gadon yana sauke manyan idanunsa akan TAIMIYYAH. A hankali ya miƙa hannu ya
yaye duvet ɗin da ya rufa mata,yana sauke idanunsa akan kyakykyawar fuskarta da tayi
jajir ,sabida kukan da ta sha a daren jiya. Hannuwansa ya kai kan jikinta yana maidota kan laps
ɗinsa, hakan yasa ta farkawa tana buɗe idanunta a hankali ta sauke akan fuskarsa.
Maleek ya sakar mata smile kafin ya kai bakinsa daidai kan fuskarta ya yi magana cikin sanyi
murya ya ce, "Wife kin tashi? Sannu ko, bari mu je in sake gasaki sai ki zo ki yi sallah time ya
wuce."
TAIMIYYAH sai ta kwaɓe fuska abinda ya faru a daren jiya na dawo mata, ta maida idanunta ta
lumshe ba tare da ta sake kallonsa ba. Ganin hakan da ta yi yasa Maleek ɗaukar TAIMIYYAH
cak! Ya nufi toilet da ita, tana kukan shagwaɓarta tana komi ya sake bata kulawar da ta dace, tare
da sake yi mata wankan sabulu tunda tun daren jiya ta riga tayi wankan tsarkinta. Babban towel ya
ciro daga muhallin da suke a rataye ya naɗota a ciki zuwa bed, sai faman rintse idanu ta ke yi ta
kasa kallonsa sabida nauyi da kunyarsa ta ke ji me girma. Ga matsananciyar ƙauna da soyayyarsa
da ke sake ninkuwa cikin jini da jijiyoyin jikinta, sai da ya aje ta bisa bed ɗin sannan ta buɗe
idanunta tana satan kallon fuskarsa. Ganin sun haɗa ido yasa ta saurin sunkuyar da kanta ƙasa,
tana faman shagwaɓe fuska da zumɓure baki, Maleek ya saki murmushi yana jin ƙaunarta me
yawa a cikin zuciyarsa yadda ba zai misaltu ba.
"Baby na gode, Allah ya yi miki albarka ya barmu tare har abada,babu in da ya ke miki ciwo ko
Zaynabb ?"
Maleek ya furta hakan lokacin da ya ɗauki rigar bacci don sanya mata a jiki, TAIMIYYAH ta yi
saurin riƙe hannunsa cike da shagwaɓa ta ce, "Please Yah Maleek zan sanya da kaina." Maleek
memakon ya barta sai ya sake janyota zuwa jikinsa,yana rabata da towel ɗin ya zura mata riga da
wandon, ya ɗauke ta cak! zuwa wajen sallaya ya aje ta, ya juya ya ɗakko Hijab ya miƙa mata yana
cewa, "Ki maza ki yi sallah Baby lokaci ya tafi sosai, idan kin idar sai ki amsa min tambayoyina
da kyau."
Daga haka ya bar mata wajen yana komawa kan gado ya kwanta, tare da jinginar da jikinsa da
jikin gadon, idanunsa akan direction ɗin da TAIMIYYAH ta tada sallah. Lokacin da ta idar ita ma
sai da ta zauna ta yi azkar da addu'o'inta, sannan ta cigaba da zama a wajen, ba tare da ta yi niyyar
ta shi ta koma kan gadon ba, duk da cewa hakan ta ke buƙata don har lokacin tana jin ciwo a
jikinta da ƙasanta. Sai dai ciwan ba wani sosai ta ke ji ba sabida kulawar da Maleek ɗin ya bata
tun a daren, bai barta ta kwana da tsamin jiki ba, ga kuma maganin da ya bata ta sha shi ma ya
sake taimakawa wajen kawo mata sauƙi.
Maleek da ke jiran ya ga ta taso ta dawo kan bed ɗin ,sai ya ga tana ƙoƙarin zamewa ta kwanta a
kan sallayar, hakan yasa shi sakkowa daga kan bed ɗin ya nufeta yana ɗakkota cak! Ya nufi bed da
ita. Sai da ya cire mata Hijab ɗin ya cillar dashi sannan ya ɗaurata akan gadon, yana me hayewa
shi ma ya kwanta tare da janyota zuwa jikinsa ya rungume. TAIMIYYAH ta shiga mutsu-mutsun
son kwace jikinta amma ya hanata damar hakan.
"Don Allah ka sakeni bacci na ke ji, jikina na min ciwo sosai Yah Maleek."
TAIMIYYAH ta yi maganar a shagwaɓe tamkar me shirin sanya masa kuka, hakan yasa Maleek
tsurawa ɗan ƙaramin bakinta ido, kafin ya kai fuskarsa kan kunninta ya ce, "Sorry wife sanar dani
ina da ina ke ciwon, ko a kira Doctor ne a duba ko nayi ɓarna sosai ne?"
TAIMIYYAH ta yi saurin rintse idanunta wani uban kunya na sake rufe ta, cikin shagwaɓaɓɓiyar
murya ta ce, "No please! Ba sosai bane na ke jin ciwo a wajen, kawai dai duk jikina ya yi min
nauyi ne."
Maleek ya saki smile yana kai baki ya sumbaci saman fuskarta kafin ya ce, "Okey sorry my pure
zuma, amma tunda wajen baya ciwo sosai to ko na ɗan ƙara kaɗan, kafin mu koma bacci kin san
dama ban ƙoshi ba jiya kwaɗayi kawai na tay......"
Ai baima ƙarisa maganarsa ba TAIMIYYAH ta sanya masa kuka, hakan yasa shi sake shigar da ita
zuwa jikinsa yana sakin ƙaramin dariya, cikin muryar rarrashin ya ke cewa, "Sorry Sweet stop dis
crying Zaynabb wasa na ke miki, amma idan ki ka cigaba da kuka zan maimaita abinda za ki yi
kukan me dalili."
"Na bari Yah Maleek, don Allah ka yi haƙury na bar kukan pease!."
TAIMIYYAH ta yi maganar cikin sauri muryarta na faman rawa, hakan ba ƙaramin dariya ya
sanya Maleek ba. Ya shigar da hannunsa cikin rigarta yana cewa, "Gud gal!" Daga haka ya fara
yamutsata son ransa, ita kuma sai shagwaɓa ta ke zuba masa, wanda hakan ke sake narkar da
zuciyarsa, tare da jin sabon sha'awar sake kusantarta na motsa zuciyarsa.
Da ƙyar ya barsu suka koma baccin,ba su tashi ba kuma sai wajen 10:30am, shi ya fara sauka daga
bed ɗin ya nufi toilet ya yo wanka ya fito. Bai tashe ta ba sai da ya kammala shirinsa tsaf cikin
ƙananun kaya masu laushi, waɗanda sukai masa mugun kyau da fiddo ƙuruciyarsa a sarari. Gaba
ɗaya ɗakin ya buɗe da ƙamshin turarensa lokacin da ya fesa, yana aje kwalbar turaren ya nufi in
da ya zube wayoyinsa da ke kashe ya kunna su. Ko mintu biyar ba a yi ba kira ya shigo cikin ɗaya
wayar tasa, ya miƙa hannu ya ɗauki wayar ganin sunan Shehu driver ne. Maganar seconds Maleek
ya yi ya kashe wayar, ya nufar hanyar fita daga ɗakin bayan ya kai dubansa ɓangaren da
TAIMIYYAH ke kwance, har lokacin baccinta ta ke yi sadidan. Ya saki kyakykyawar murmushi
akan fuskarsa,yana fice wa daga ɗakin zuwa downstairs, don amso abincin breakfast da Hajjah ta
aiko Shehu da shi..........✍🏻
#Ɗansabo ce#
[12/15, 11:46 AM] +234 703 040 9541: Littafin TAIMIYYAH paid book ne,ga duk wanda ta
tsincesa a kowani irin group ne,kiji tsoran Allah karki karanta sai kin biya 500 naira only.
Za ku iya min magana ta wannan number ɗin 08167768704, ko kuma ku turo kuɗin ku kai tsaye ta
wannan account ɗin 0504192664 aisha ibrahim dansabo GTbank.*
Masu turo credit za ku turo katin MTN na 500 ta wannan line ɗin 08167768704.
_Ina ƴan kasuwa masu buƙatar a tallata muku hajar ku? Maza ku garzayo da kuɗi ƙalilan a tallata
muku kayan siyarwanku sai dai kawai ku ji ana kiran waya don buƙatan sayan kayan ku,ku
tuntuɓeni ta layina kamar haka 08167768704._
*74*
Lokacin da Maleek ya amso ƙaton kwandon da coolers ɗin abincin ke ciki, direct uptairs ya haura
da shi ya aje bisa dining da ke uptairs ɗin. Yana shirin juyawa don komawa zuwa ɗakinsa ya ga
ko TAIMIYYAH ta farka, sai kawai idanunsa ya sauka akanta tana fitowa daga ɗakin nasa. Ta
dinga takowa a hankali cikin tsarin tafiyar da Allah ya nufeta da shi, dafe da guiwar ƙafarta har ta
ƙariso cikin falon.
Ya tsareta da manyan idanunsa yana me dakatawa daga tafiyarsa, ya tsaya cak! Yana jiran
ƙarisowarta, don dole ta gabansa za ta wuto kafin ta isa nata bedroom ɗin. TAIMIYYAH ko da
take takowa zuwa cikin falon in da Maleek ke tsaye, kallo ɗaya ta yi masa ta sunkuyar da kanta
ƙasa, tana cigaba da takowa a hankali don gabaki ɗaya jikinta na motsawa ne, tana jin ɗan ciwo
daga can ƙasanta. Hakan yasa ta ke tafiyar a hankali gashi kuma yanayin tafiyar nata, na
taimakawa wajen sanya ta jin ciwon daga ciki, a haka ta ƙariso ta gaban Maleek za ta wuce, ya yi
saurin riƙo Hijab ɗin jikinta, tare da janyota zuwa jikinsa a bazata. Hakan ya sanya TAIMIYYAH
buɗe baki za ta sakar masa kukan shagwaɓa, amma sai ya yi gaggawar ɗaura hannunsa ɗaya akan
bakinsa ya ce, "Shishhhhh! Baby bana son jin wannan kukan, idan ba so ki ke yi in maimaita abin
jiya ba. Dama daurewa kawai na ke yi Zaynabb amma sam ban ƙoshi ba ina da buƙatar ƙari, oya
mu je in rakaki zuwa ɗakin tunda kin gudo daga ɗakin miji."
TAIMIYYAH sai ta shigar da kanta cikin ƙirjinsa ƙamshinsa na dukan hancinta, ta yi magana
cikin zallar shagwaɓar da ke narkar da zuciyar Maleek ta ce, "To don Allah ka sake ni zan iya
tafiya zuwa ɗakin ai."
Maleek ya sake mannata da jikinsa yana buɗe baki ya ce, "No wife ni zan ɗauke ki, don wannan
tafiyar da kike yi ina ji ajikina kina jin pain, so ki barni na yi aikina kawai, sai ma na duba na ga
anya ko ban ji miki ciwo ba? Dauriya ce kawai ki ke nunawa."
Ai jin abinda ya faɗi ya sanya TAIMIYYAH sanya masa kuka, cikin kukan ta ke cewa, "Don Allah
ka yi haƙury Yah Maleek ba sai ka duba ba, ni bana jin wani ciwo sosai kaɗan ne, shi ma sai na yi
doguwar tafiya na ke ji wajen na min ciwo."
Yadda ta yi maganar tana kuka kuma cikin muryar shagwaɓa,ya sake kunna zuciyar Maleek, ya
ɗauke ta cak! Ɗinta ba tare da ya yi magana ba ya wuce da ita zuwa bedroom ɗinta. Bai yi mata
masauki a ko'ina ba sai cikin bathroom ɗin ɗakinta, ya aje ta daga bakin tube yana me haɗa mata
ruwan da za ta sake shiga ciki. Lokacin da ya waiwayo kanta ne ta bashi dariya, sabida yadda ta ke
faman haɗe fuskarta da tayi jajir sabida yawan kukan da ta ke yi. Sai ya saki murmushi yana isa
daf da ita ya miƙa hannu zai raba ta da Hijab ɗin da ke jikinta, amma sai ta yi gaggawar riƙewa
cikin narke murya ta ce, "Please! Zan yi da kaina Yah Maleek ba ma sai ka tsaya ba don Allah!"
Maleek ya saki ƙayataccen murmushi kafin ya haɗe gaf ɗin da ke tsakaninsu gaba ɗaya ya ce, "No
wife ban son gardama aikina ne na kula da ke , so please! Ki bar ni na yi aikina yanzu mun riga
mun zama ɗaya, babu wani abinda zamu ɓoyewa juna, wanka kuma tare ma za mu dinga yi sai na
ga ƙarshen jin kunya."
Yadda ya yi maganar fuskarsa a miskile ya sanya TAIMIYYAH matso hawaye, gaba ɗaya tana jin
cewa ta gama shiga uku da wannan rigimammen mutumin da Allah ya haɗata da shi. Wanda sam
ita bata ga alamun yana fahimtar irin kunyar da take ji bane, idan yana mata wasu abubuwan.
Babu yadda ta iya da shi haka ya sake gasata ya yi mata wanka, ya naɗota cikin towel suka fito
zuwa cikin bedroom ɗin nata, sai faman noƙewa TAIMIYYAH ta ke yi ta kasa haɗa ko idanu da
shi amma shi ko a jikinsa. Abinda ya ga dama kawai ya ke aiwatarwa, don shi bai ga abin da za ta
dinga jiwa kunya ba, tunda babu daren da jemage bai riga ya gani ba, sai dai daren mutuwarsa da
ya rage, so shi bai ga abinda za ta dingawa wannan noƙewar ba.
Da kansa ya nufi wajen kayanta ya fito mata da wasu english wears riga da wando, rigar ƙaramace
ƙwarai sai wandon ne ke da faɗi sosai daga samansa har ƙasa. TAIMIYYAH duk yadda ta so ya
barta ta yi komi da kanta ya ƙi bari, hatta da Bra shi ya sanya mata da kansa bayan ya gama yin
yadda ya so da wajen, wanda suke matuƙar gigita zuciyarsa da kunna wutar sha'awarta a
zuciyarsa. Daurewa kawai ya ke yi amma ba ƙaramin sake kunna kansa ya yi ba, shiyasa bai barta
sun fito cin abinci ba sai da ya ɗan sake rage zafi, sai faman hawayen shagwaɓa TAIMIYYAH ta
ke yi.
Hannunta cikin nasa suka fito suna faman zuba ƙamshi, shigar da ya yi mata na ƙananun kayan ba
ƙaramin kyau sukai mata ba. Fuskarta babu kwalliya sai powder da kwalli kawai da ta sanya,
lipstick ɗin da ta gogawa lips ɗinta ma Maleek ɗin ya tsotse kayansa, ya kuma hanata gogo wani
don ya ce ko ta sake gogawa ma shanye abarsa zai yi.
Shi ya yi serving ɗinsu chips wanda akai wa wani haɗin liver sauce da plantain, sai farfesun kan
rago da aka dafosa sai tashin ƙamshin spices, ka ke ji na tashi tunda ya buɗe coolar. Yana cikin
haɗa musu tea a cups wayarsa da ke gaban aljihunsa ya fara ringing, sai ya dakata daga abinda ya
ke yi don ɗaga wayar, wanda daga salon ringing ɗin kawai ya gane cewa Hajjah ce. Ya ɗaga wayar
yana sanya shi a speeker daidai lokacin da Hajjah ta doka sallama, Maleek ya amsa yana me
gaidata tana amsa cike da kulawa,tare da tambayarsa TAIMIYYAH. Maleek ya saki murmushi ya
ce, "Hajjah ga ta a kusa da ni tana jinki ma."
Maleek ya turawa TAIMIYYAH wayar kusa da ita yana faman tsareta da wani sassanyar kallo, ta
buɗe baki a hankali ta gaida Hajjah cike da tsantsar nuna ladabi, kai kace Hajjah na gabanta ne,
hakan sai ya sake birge Maleek Ado. Hajjah ta amsa gaisuwar TAIMIYYAH da kulawa kafin ta
ɗaura da cewa,
" Zainabu ba dai wani matsala ko? Zuwa can anjima idan za a kawo muku lunch za a taho miki da
ƴan aikinki biyu, waɗanda za su dinga taimaka miki da aikin gida zuwa share-share. Allah ya yi
muku albarka ya baku zama lafiya, sai ai ta haƙury da juna kin ji, Allah ya kawo rabo me anfani. A
kwai ƙaramin cooler da za ki gani farfesun kaza ne a ciki don ke kaɗai aka dafa shi, sai ki yi
ƙoƙari ki cinye shi duka ki kuma shanye romon kin ji ko Zaynab?"
TAIMIYYAH dai kunya ya hanata amsawa Hajjah addu'arta, sai Maleek ne ya amsa, ita kuma
TAIMIYYAH ta ce, "To Hajjah In Sha Allah zan yi hakan, sai sun zo ɗin mun gode Allah ƙara
girma." Daga haka sai ta turawa Maleek wayarsa gabansa, tana me ƙin haɗa ido da shi, don sosai
ta ke jin tasirin idanunsa akanta. Maleek ya wani shagwaɓewa Hajjah murya kamar ƙaramin yaro
ya ce, "Yanzu Hajjah har za ki fara nuna wariyar launin fata, meyasa ni ba a dafo farfesun da ni
ba,sai aka haɗoni da na kan rago bayan an san nima nafi son na kazar,gaskiya ni dai ban yarda ba
tare zamu ci da Zaynabb."
Hajjah ta yi murmushin da har suna jiyo sautinsa kafin ta ce, "Sam! Ban amince ka ci mata abunta
ba Maleek, zan sa a dafa maka naka daidai da kai, wannan don ɗiyata kawai na sa aka dafa shi.
Badai wani damuwa ko, ina fata baka yi abinda ka saba ba? Allah ya yi albarka ya baku zama
lafiya, don Allah Maleek ka bi komi a sannu ka dai ga yanayin ta please!"
Hajjah ta yi maganar tana cike da son jin amsar da Makeek zai bata, don sam hankalinta ya gaza
kwanciya tana tsoron kada ace ita ma TAIMIYYAH, Maleek ya yi mata ɓarna kamar yadda ya yi
wa Suhailah a daren farkon su. Maleek da tuni ya gane in da maganar Hajjah ta dosa sai ya saki
murmushi ya ce, "Hajjah babu abinda ya faru, wancan lokacin ma ai ƙuruciyace da kuma rashin
man kai,amma yanzu ai yaron naki ya ƙara hankali."
Hajjah sai ta saki ajiyar zuciya kafin ta ce, "To madallah rasa kunya, duk da haka dai a kula abi ta
a hankali."
Maleek ya amsa da cewa, "Tuh Hajjah In Sha Allah! Suhailah za ta koma gida yau ne ko kuna nan
tare da ita anan gidanki?"
Hajjah ta yi saurin cewa, "A'a gida za ta koma yau ɗinnan zuwa yamma zan kora ta, kowa ma yau
zai kama gabansa ai taro ya watse Maleek, sai dai fatan Allah Ya baku zama lafiya, Ya kuma baka
ikon yin adalci a tsakaninku, ya haɗe maka kansu ku zauna lafiya."
Maleek ya amsa da cewa, "Ameen ya hayyu ya qayyum Hajjah, zan shigo zuwa anjima ita ma
Inna Dije yau za su wuce kenan?"
Hajjah ta bashi amsa da cewa, "Eh gata nan ma har ta fara shiri, Safiya kasan ta bar yara tuh duk
hankalinta ya koma gida."
Maleek ya jinjina kai ya ce, "Okey! Tuh sai na shigo ɗin Hajjah, zan yi waya da Safiya ɗin da
Innar kafin su wuce mun gode." Daga haka ya yi sallama da Hajjah yana maida hankalinsa
katsokan zuwa kan TAIMIYYAH, wacce ke sauraren wayarsu da Hajjah. Sai ta ji hankalinta gaba
ɗaya ya koma kan Iyah, tana son jin muryarta su gaisa amma sai ta daure, har zuwa su gama
karyawar don yunwa ta ke ji da gasken-gaske.
Maleek shi ya dinga bata abincin a baki har ta ƙoshi,amma sai dai bata sha tea ɗin da ya haɗa mata
ba sabida ya zuba madara, ita kuma bata shan madara a cikin tea. Hakan yasa shi shanye wannan
ya haɗa mata zallar ruwar Milo, ko sugar ta hana shi sakawa a ciki, ya dinga kallonta lokacin da ta
ke shan abin ta hankali kwance.
Tashi ta yi tsam! Bayan sun kammala yin kalacin, tana son komawa ɗaki don ta kira Iyah a
waya,sabida gaba ki ɗaya kewarta take ji na danne zuciyarta.
Maleek ya ɗaga manyan idanunsa ya sauke akanta, lokacin da ta ke kai hannu ta dafe guiwar
ƙafarta don fara takawa ya ce, "Wife ina zuwa? Daga gama cin abinci za ki gudu ki bar ni?"
TAIMIYYAH ta shagwaɓe fuska tare da narke murya ta ce, "Ina son yin waya da Iyah ne shiyasa
zan koma ɗaki."
Maleek da idanunsa ke kanta sai ya tashi tsaye yana cewa, "Okey tuh mu je in raka ki, idan kun
gama wayan ni kuma sai abani kaluwar da ta dace ko?"
Ya yi maganar yana ɗage mata gira guda, fuskarsa na haskawa da wani irin killer smile, hakan
yasa zuciyar TAIMIYYAH dokawa da wani irin tarin ƙaunarsa me tsanani. Ta ɗan tsuke baki
kaɗan tana ɗauke idanunta daga kansa, ta fara takawa don nufan hanyar ɗakin baccinta, sai dai
taku biyu ta yi ta ji Maleek ya yi sama da ita. Bai dire ta a ko'ina ba sai tsakiyar gadonta, ta sauke
numfashi a hankali tana sake shagwaɓe fuskarta, tare da zumɓure masa baki. Ya haye kan gadon
yana zama kusa da ita har jikinsu na gugar juna, ya miƙa hannu ya ɗan ɗale bakin yana cewa,
"Wannan bakin shagwaɓar idan ba a daina zumɓure min shi ba yanzu zai amshi quiry."
TAIMIYYAH ta saki murmushi tana matsawa ta ɗakko wayarta, wanda ke aje kan gadon ta shiga
neman layin Iyah.Lokacin da Iyah ta ɗauki wayar Maleek sai ya zubawa TAIMIYYAH ido, yana
kallon yadda ta ke zubawa Iyah shagwaɓa a wayar, har da wani ɗan kukanta tana cewa Iyah wai
ita wajenta za ta dawo. Maleek ya saki murmushin da babu shiri, yana cigaba da tsareta da
idanunsa har ta kammala yin wayar, ta aje wayar tana me ɗaga manyan idanunta ta sauke akansa.
Ganin irin kallon da yake bin ta da shi yasa ta saurin janye idanunta daga dubansa, tana shirin
matsawa ta sauka daga bed ɗin ya yi saurin maido ta baya, tare da mannata da jikinsa. Ya kai
bakinsa bisa kunnuwanta yana raɗa mata wasu kalamai, wanda nauyinsu ya sanya TAIMIYYAH
saurin shigar da kanta cikin ƙirjinsa, zuciyarta na doka masa da wani irin matsanancin feeling.
Hakan da ta yi ya sake kunna Maleek ya fara aika mata da wasu sabbin saƙonnin da suka fara
gigita tunaninta. Cikin lokaci kaɗan idanun TAIMIYYAH suka fara raina fata, tsoro ya lulkuɓe
zuciyarta ta fara ƙoƙarin son raba jikinta da nasa, amma bai bata wannan damar ba. Ta sakin masa
kuka tana fara yi masa magiya akan ya yi haƙury ya sake ta, amma Maleek sam ba ya jiyota ma,
abinda zai bashi nutsuwa kawai ya ke nema, sabida wani zazzafar sha'awarta ke sake kunna
zuciyarsa.
Duk yadda TAIMIYYAH ta kai ga roƙonsa akan kar ya sake maimaita laifinsa na daren jiya,
Maleek bai jiyota ba sai da ya sake isa zuwa cikin sabuwar dubiyar, da ta fara kai shi a daren jiya.
Lokacin da komi ya lafa ne ya rungumeta a cikin jikinsa yana aikin rarrashi, don TAIMIYYAH
narke masa ta yi tana kuka sosai don da gaske wannan karon ma taji ajikinta, don Maleek ɗin bana
wasa bane. Ji ta ke yi tamkar ta gudu ta koma wajen Iyah ,don wannan abu da Maleek ke mata
bata ji za ta iya jurarsa, zuciyarta gaba ɗaya a narke ta ke da tunanin dama wai haka auren ya ke?
Da kansa ya sake gasa mata jiki da bata duk wata kulawar da za ta samar mata da nutsuwa, sai
faman kukan shagwaɓa da raki take zuba masa shi kuma yana sake susucewa akanta.
Cikin wata gown na atamfa dull colour TAIMIYYAH ta shirya, bayan ta gama zuba shagwaɓarta
son rai.Kalar atamfar me duhu ya haske farar fatarta sosai tare da yi mata kyau matuƙa. Fuskarta
ta yi wa simple make-up da ya haska kyakykyawar fuskarta, wanda ya ɗan tasa sabida kukan da ta
yi, ta sanya ɗankunnin gold ɗinta me kyau da ya sake haska kwalliyarta.
Tana cikin fesa sabon turaren da ta fara amfani da shi na Versace, Maleek Ado da ya fita zuwa
ɗakinsa ya dawo.Ta cikin mirrow TAIMIYYAH ta hango shigowarsa, sai ta aje kwalbar turaren
tana wani shagwaɓe fuska, alamun akwai sauran shagwaɓa a gaba.
Maleek da ya ƙariso wajen mirrow ɗin da TAIMIYYAH ke tsaye, sai ya rungumeta ta baya yana
sunsuna wuyarta zuwa saman ƙirjinta, yana shaƙan daddaɗan ƙamshin da ke narkar da zuciyarsa.
A hankali ya kai hannuwansa biyu ya zagaye ƙugunta,yana sake mannata da jikinsa, ya furzar da
wani zazzafan numfashi, yana jin yadda ƙaunarta da soyayyarta me tsanani ke sake narkar da
zuciyarsa.
"Zaynabb i luv u, ina roƙon Ubangiji ya bar mu tare har ƙarshen numfashi, Allah ya yi miki
albarka my pure honey na."
TAIMIYYAH ta sake narkar da fuskarta, ƙaunarsa me tsanani na sake huda zuciyarta, ganin yadda
hannunsa ya fara yawo a jikinta, yana neman dagula lissafinta ,yasa TAIMIYYAH narke masa da
shagwaɓa.
*A round 1:30pm*
Hajjah ta turo Shehu driver da abincin lunch, tare da ƴan aiki biyu da za su dinga taimakon
TAIMIYYAH. TAIMIYYAH tare da Maleek suka sauko zuwa downstairs ɗin, yana riƙe da
hannunta cikin nasa.
Ya isa bakin ƙofar shigowa falon ya buɗe, ƴan matan biyu masu aiki suka shigo cikin falon,
hannun ɗaya riƙe da basket ɗin abincin,ɗayar kuma riƙe da jakar kayansu.
TAIMIYYAH ta tarbe su da fara'a bayan sun aje basket ɗin daga saman table, suka zube suka
kwashi gaisuwa, shi dai Maleek can kujeran da ke facing makeken smart TV da ke falon, ya isa ya
zauna yana ɗaukar remote ya kunna TV.
TAIMIYYAH ce ta dubesa tana me narke murya ta ce, "Yah Maleek ina ne ɓangaren da za a sauke
su?"
Ya ɗago manyan idanunsa ya sauke akanta , yana tuna cewa a she fa bata san kan gidan ba,tunda
ba a zagaya da ita ta ga kan yanayin tsarin gidan ba. Sai ya miƙe daga tsaye yana dubanta da
sassanyar kallo ya ce, "Sorry wife laifina ne da ban zaga da ke kin ga gidan naki ba, oya let's go ki
ga ko'ina da ina ,amma idan tafiyar zai baki matsala a haƙura."
TAIMIYYAH ta ɗan shagwaɓe fuska ta ce, "No zan iya Yah Maleek."
Daga haka ta fara takawa a hankali cikin tsarin halittar tafiyarta, ta isa inda ya ke tsaye yana jiran
ƙarisowarta, ya miƙa hannu ya riƙo hannunta na dama, suka fara takawa don fitowa daga side ɗin
falon suka nufi baya. Masu aikin suka bi su da ido suna kallon junansu , da alamu sun yi mamakin
ganin cewa gurguwace matar gidan, sai dai ba su ce komi ba suka cigaba da zama suna ƙarewa
tsaruwar falon kallo ,wanda ba su taɓa shigowa irin sa ba in ba yau da Allah ya jefo su gidan arziƙi
irin wannan ɗin ba.
Sai da Maleek ya zagaya da ita ko'ina ta gani tana yaba tsaruwa da haɗuwar gidan, tamkar ba za a
mutu ba yadda ake wa ƙasa shinfiɗar zaman duniya. Maleek ya ja ta zuwa parking space yana
nuna mata sabuwar motarta dal, Wanda aka ɗakko ta a cikinsa randa za a kai ta gidan Hajjah.
Maleek ya gyaɗa mata kansa alamun tabbatarwa kafin ya ce, "Yes motarki ce pure honey, cox kin
cancanci ki mallaki fiye da mota."
TAIMIYYAH bata san lokacin da ta faɗa jikinsa ya rungumeta ba, cikin rawar murya ta ke zuba
masa godia tana jin ƙaunarsa me tsanani da sake mamaye jini da tsokar jikinta. Maleek Ado sai ya
kai bakinsa kunni ya raɗa mata wasu kalamai masu azabar nauyi, hakan ya sanya TAIMIYYAH
sake shigar da kanta a jikinsa tana ji kaman ƙasa ya tsage ta shige don kunya.
Da ƙyar Maleek ya iya rabata da jikinsa suka cigaba da takawa yana nunnuna mata ko'ina na
gidan, sun ɗanyi tafiya me nisa ta fara jin gajiya da ciwo daga ƙasanta.
Ta dubesa da fuskar shagwaɓa tana ɗan yatsine fuska, lokacin da suka iso bacyard ta can baya, in
da akwai ƙofar da zai sadaka da kitchen, akwai kuma wani ƙofa da zai kai ka zuwa cikin garden da
ke ta can baya ɗin.
Ya yi maganar yana ƙoƙarin ɗaukarta a hannunsa amma sai tayi gaggawar zamewa ta ce , "No
please! Zan iya ƙarisawa Yah Maleek."
Maleek ya ɗan harareta kaɗan yana cewa, "Baby ba za ki daina kirana da wannan sunan ba ko?"
TAIMIYYAH ta shagwaɓe murya ta ce, "Ni sunan na min daɗi ne ai, kuma bansan wani suna zan
ce ba bayan shi."
Maleek ya kai hannu ya lakace face ɗinta ya ce, "Soon za ki sani baby, don ni bana son jin wani
kalmar Yaya cox ni ba Yayanki bane, ya kamata daga jiya zuwa yau ki gane hakan."
Yadda ya yi maganar yana miskile fuska ya sanya TAIMIYYAH sakin murmushi, bata ce komi ba
har ya ƙarisa da ita zuwa ɓangaren da aka tanadar sabida masu aiki. Ɗakuna biyu ne da ke ɗauke
da toilet a ciki, an sanya komi na kayan ɗaki har da TV babba plasma da center carfet duk an
sanya. Ga gadaje guda biyu masu kyau jere da juna daga cikin bedroom, sosai ɗakin ya yi wa
TAIMIYYAH kyau.
Lokacin da suka dawo zuwa ciki, a inda suka bar ƴan aikin a nan suka tadda su, sun maida
hankalinsu kacokan kan TV suna kwasan kallo.
TAIMIYYAH ta zauna daga cikin seater tana jin gajiya a jikinta sosai, ta ɗaga manyan idanunta ta
sauke akan ƴan aikin nata, waɗanda ba za su gaza shekaru sha biyar ba dukansu.
"Ya sunan ku ?" TAIMIYYAH ta tambaya idanunta akan su, suka ɗago idanunsu daga kan kallon
da suke yi ɗaya na riga ɗayar cewa, "Sunana Harirah." Ɗayar ma ta ce, "Ni sunana Zinatu."
TAIMIYYAH ta jinjina kai ta ce , "Okey ɗauki jakar mu je in nuna muku ɗakin da za ku zauna."
Maleek ya yi saurin duban TAIMIYYAH ya ce, "No Zaynabb ba za ki sake fita ba, kin gaji da
yawa bari ni in nuna musu." Daga ya yi gaba suna biye da shi a baya zuwa side ɗin da za su zauna.
Lokacin da ya dawo cikin falo ya samu har TAIMIYYAH ta shirya coolers ɗin abincin bisa dining,
ya ƙarisa wajen dining ɗin tare da jan kujerar da ke kusa da TAIMIYYAH ya zauna, idanunsa
akanta ya na bin ta da sassayar kallo ya ce, "Luv waɗannan ƴan aikin iyakan su dai aikin shara da
su mopping ne banda girki ko? Ni bana son girkin ƴan aiki in dai har ina gari."
TAIMIYYAH ta jinjina kai ta ce, "Eh iyakan aikin nasu kenan, ni ma bana son a yi min girki zan
iya yi da kaina, sai dai su taimakeni da abinda ba a rasa ba."
"Gud gal! I luv u dear." Cewar Maleek Ado idanunsa fes akan TAIMIYYAH, wacce ta fara buɗe
coolers ɗin abincin don yin serving ɗinsu.
Suna cikin cin abincin ne aka yi knocking ƙofar shigowa falon, Maleek Ado shi ne ya tashi ya isa
wajen ƙofar ya buɗe. Ganin su Yasmeen da Anty Laurat ne yasa shi ba su hanya suka shigo suna
gaida shi cike da ladabi, ya amsa da sakin fuska yana me juyawa ya koma wajen dining ɗin..........
✍🏻
#Ɗansabo ce#
[12/15, 11:46 AM] +234 703 040 9541: Littafin TAIMIYYAH paid book ne,ga duk wanda ta
tsincesa a kowani irin group ne,kiji tsoran Allah karki karanta sai kin biya 500 naira only.
Za ku iya min magana ta wannan number ɗin 08167768704, ko kuma ku turo kuɗin ku kai tsaye ta
wannan account ɗin 0504192664 aisha ibrahim dansabo GTbank.*
Masu turo credit za ku turo katin MTN na 500 ta wannan line ɗin 08167768704.
_Ina ƴan kasuwa masu buƙatar a tallata muku hajar ku? Maza ku garzayo da kuɗi ƙalilan a tallata
muku kayan siyarwanku sai dai kawai ku ji ana kiran waya don buƙatan sayan kayan ku,ku
tuntuɓeni ta layina kamar haka 08167768704._
*75*
TAIMIYYAH ta yi saurin tashi daga kujeran da ta ke kai tana sakin spoon ɗin hannunta, gaba ɗaya
wani farin cikin zuwan su Yasmeen ɗin na cika zuciyarta. Maleek ya zuba mata manyan idanunsa
lokacin da ta ke jan kujerar baya, don fara takawa ta baro wajen dining ɗin zuwa cikin falo, ya
kama hannunta ya riƙe yana me yin ƙasa da muryarsa ya ce, "Zaynab koma ki zauna, babu in da
zaki sai mun ƙare cin abincin nan."
TAIMIYYAH ta shagwaɓe fuska cike da magiya ta ce, "Please! Yah Maleek zan dawo fa, kawai
zan yi welcoming ɗinsu ne ka ji?"
Yadda ta yi maganar da shagwaɓa sosai ya sa Maleek sake damƙe hannunta cikin nasa ya ce,
"Alright! Minti ɗaya kawai na baki, idan baki dawo kin ci abinci ba agabansu zan zo in ɗakko ki,
idan kuma kina ganin wasa ne try me."
Ya yi maganar yana me miskile fuskarsa babu alamun wasa, hakan yasa TAIMIYYAH jinjina kai
tare da sake narke murya ta ce, "In Sha Allah yanzu zan dawo ma bama sai ka yi hakan ba please!"
Daga haka ya sakar mata hannun ta dafe guiwar ƙafarta tana me baro wajen, ta iso cikin falon tana
kallon yadda su Yasmeen duk suka zubo mata ido suna bin ta da kallon ƙurilla. Ta ƙarisa takowa
zuwa kujeran da sukai masauki akai bisa 3 seater tana cewa, "Welcome Anty Laurat! Ashe dai da
gaske ɗin za ku zo."
Yasmeen ta yi ɗan ƙasa da murya ta ce, "Wow! Baby kin ga yadda ki ke wani ƙyalli ne, gaskiya
aure da ban ne da alamu amarcin ba ƙaramin amsarki zai yi ba."
TAIMIYYAH ta wurga mata harara ta ce, "Bismillah! Za ki fara ko Yasmeen, ga dai yi can yana
jinki ni babu ruwana wallahi."
Suka saki dariya a lokaci guda har da Anty Laurat da ke faman bin ko'ina da kallo, cike da yaba
tsaruwan gidan da haɗuwarsa. Ta gama saki cewa TAIMIYYAH ta shigo aljannar duniya, ta kuma
yi wa su Zuhurah rata me tarin yawa a rayuwa, tun da suka iso gidan ta gane cewa TAIMIYYAH
na cikin mata masu sa a a rayuwa.
TAIMIYYAH ta tsaida dariyarta tana duban Anty Laurat ta ce, "Anty Laurat ki ce duk jiya ku ka
gudo ku ka baro Zuhurah a can, Allah sarki auren nesa akwai damuwa fa, amma tun da tana so ita
ba za ta damu ba kila."
Anty Laurat ta buɗe baki za ta yi magana kenan muryar Maleek Ado ya shiga kunnuwansu yana
kiran TAIMIYYAH da cewa, "Zaynabb!" TAIMIYYAH sai ta yi saurin tashi tana duban su
Yasmeen ta ce , "Sorry Yasmeen ina zuwa please!"
Yasmeen ta saki smile tana cewa, "Kar ki damu TAIMIYYAH je ki don Allah."
TAIMIYYAH ta gyaɗa kai tana dafa ƙafarta ta fara takawa don komawa zuwa wajen Maleek Ado,
fuskarta a haɗe ta ke lokacin da ta isa wajen tana jan kujera ta zauna. Ya zuba mata manyan
idanunsa yana nuna mata plate ɗin abincin da hannu ya ce, "Oya maza ki cinye shi bana son zama
da yunwa, ko so ki ke ki kasa ɗaukata anjima?"
TAIMIYYAH ta sake ɓata face tana fara cin abincin a hankali, ba tare da ta tanka shi ba ita gaba ki
ɗaya mamakinsa ta ke yi, yadda ya ke zaro zancen fuskarnan a miskile tamkar ba daga bakinsa
kalaman ke fitowa ba.
Maleek sai da ya tabbatar ta ƙoshi sannan ya barta ta koma wajen su Yasmeen,shi kuma ya kwashi
wayoyinsa ya koma upstairs don hutawa, sabida baya ji zai fita zuwa ko'ina sai zuwa can yamma.
TAIMIYYAH shafin hira suka buɗe bayan ta cikawa Anty Laurat gabanta da kayan gara, ga
abincin gidan Hajjah da ta yi musu ta yi suka ce sun ƙoshi. Ba su bar gidan ba sai can bayan la'asar
lokacin Yasmeen ta gama zagawa da Anty laurat ko'ina na gidan ta sha kallo. TAIMIYYAH dai
bata bisu ba don da gaske idan ta yi tafiya me nisa ciwo take ji, sai da suka dawo daga zaga wajen
gidan ne ta haura da su zuwa upstairs, nan ma Anty Laurat ta sha kallo ɗakin Maleek ne kawai ba
su gani ba don ba hurumin su gani bane ɗin.
TAIMIYYAH kaya sosai ta haɗawa Anty Laurat da Yasmeen cikin kayan lefenta, sabida dukansu
gobe za su wuce kowacce za ta koma in da ta fi wayo.
Har wajen mota in da Sani driver ya ke jiransu ta yi musu rakiya, sukai sallama da juna har suna
hawaye kafin ta juyo a hankali ta dawo zuwa cikin gidan.
Ta nufi ɓangaren masu aikinta ta ƙofar kitchen ta kira Harirah, don ta zo ta kwashe kayan da aka
yi using a falo su gyara wajen, daga haka ta wuce zuwa uptairs tana ji duk jikinta a gajiye. Ɗakinta
ta wuce direct tana zare doguwar rigar jikinta ta nufi bathroom don sake shiga ruwan zafi ko za ta
ji daɗin jikinta, sam bata saka key a ƙofar ba don bata taɓa kawo cewa Maleek zai shigo ɗakin ba.
Tana tsaka da wanke jikinta sai ganinsa ta yi tsidim ya shigo cikin bathroom ɗin, ta saki ƙaramin
ihu tana me dunƙule jikinta waje guda, ta yi magana cike da shagwaɓa ta ce, "Kai Yah Maleek!
Haka ake yi shigowa waje ba notice?"
Maleek Ado ya ƙarisa takawa zuwa bakin tube ɗin yana sakin smile ya ce, "No! Babu maganar
wani sai an bani notice baby, ni fa wannan ɓoyon da kunyan duk ba zai hana ni yin abinda na ga
dama ba, bana son wannan kunyar da alamu har yanzu ban ko fara rage ta ba, amma kar ki damu
kila a daren yau ta fita baki ɗaya ma."
TAIMIYYAH ta ɗago manyan idanunta ta dallah masa harara tana sake kwaɓe fuska kamar za ta
saki kuka ta ce, "Please! Ka fita wanka fa na ke yi, yanzu zan gama in fito ."
"Babu in da zani Zaynabb! Idan za ki gama wankanki ki gama mu je ki sha magani, gayi can
Yusuf ya amso daga wajen Dr. Akwai ma na shafawa da za ki yi using duk pain ɗin da ki ke ji zai
tafi, don Angoci na ke son yi sosai bana buƙatar duk wani raki kin ji pure zuma?"
TAIMIYYAH ta yi banza da shi har kuma lokacin jikinta a dunƙule ya ke, ta hana shi ganin abinda
ke ɗaukar hankalinsa.Ya miƙa hannu yana cirota daga cikin ruwan baki ɗaya, ya nufi in da towels
suke ya xari ɗaya ya rufa mata a jiki, duk yadda ta ke wutsilniya da ƙafafu bai dame shi ba,haka ya
dinga ratsowa da ita ɗauke a jikinsa har suka dangana da ɗakin baccinsa.
A nan sabon dramar ta tashi don TAIMIYYAH kuka ta sanya masa lokacin da ya shinfiɗeta akan
bed ɗin, yana ƙoƙarin ware ƙafafunta wai zai ga wajen yadda ya yi ko dai ta ji ciwo ne take ɓoye
masa?
Duk iya magiyarta bai sa ya barta ba sai da ya buɗe wajen ya ga babu wani raunin da ya yi mata,
sannan ya ɗakko cream ɗin maganin da ke cikin wani ɗan ƙaramin tube, ya matsa a hannunsa ya
shafa mata a wajen, yana me sakin smile jin yadda TAIMIYYAH ta saki kuka bayan ya kai
bakinsa ya sumbaci wajen. Idanunta gam! Ta rintse su sabida mahaukacin kunyarsa da take ji, shi
ko Maleek ko a jikinsa ya ɗagota baki ɗayanta yana sauke idanunsa akan ƙirjinta, wanda ya ga har
sun ɗan ƙara cika daga jiya zuwa yau ɗin.
A hankali ya kai hannuwansa kai yana fara yi mata wani irin salo, wanda ya sanya ta ƙanƙamesa
tana sakin kukan shagwaɓa, ya cigaba da yamutsata son ransa kafin ya aje ta yana fita daga ɗakin,
wai shi da kansa zai zaɓo mata kayan da za ta saka.
Da kansa ya sanya mata rigar da ya zaɓo mata cikin ƙananun kayan da ke shirye cikin sif ɗinta,
wata ƴar filgilwar riga da tsayinta iya guiwa kawai ta tsaya, sai faffaɗan wuya da rigar ke da shi
wanda ya taimaka wajen fallasa asirin cikar ƙirjin TAIMIYYAH, wanda Maleek ya hanata sanya
Bra don ya ce ya fi so ta bar masa abinsa a haka babu Bra ɗin.
Nan cikin falon da ke upstairs ɗin ya ɗakkota suka fito, ya kunna musu kallo yana zama daga
ƙasan carfet ɗin da ke tsakiyar falon. A jikinsa ya kwantar da TAIMIYYAH bisa laps ɗinsa, a haka
suke kallon hannuwansa na yawo a jikinta duk ya hana mata sukuni da salonsa, wanda ke kwance
notikan da ke ɗaure da kanta baki ɗaya.
Bata samu ƴancin kanta ba sai da aka kira sallar magriba, sannan ya barta ta tashi daga jikinsa.
Duk ya gama kashe gaɓoɓin jikinta da salonsa da ke ratsa zuciya, da haifar da zazzafan shauƙi a
cikin zuciyarta.
Ta shi ya yi ya nufi ɗakinsa yana sanar mata cewa zai fita zuwa Masjid da ke jikin gidan nasu,
daga can kuma ba zai shigo ba zai wuce gidan Hajjah ne.
TAIMIYYAH ta yi masa duba ɗaya tana ɗauke kanta cike da kunyar, yadda har lokacin idanun
Maleek ke kan ƙirjinta da rabinsu ke waje,ta buɗe baki cike da shagwaɓa ta ce, "Please! Ka je dani
Yah Maleek ban son zama ni kaɗai ka ji?"
Maleek ya yi saurin girgiza mata kansa ya ce, "No! Sweet Hajjah faɗa za ta yi idan ta ga mun fito
tare, zan dai ce kina gaidata ta bada abin daɗi akawo miki ko?"
TAIMIYYAH ta shagwaɓe fuska tare da zumɓure baki ta ce, "Shikenan tuh! Amma ni babu
ruwana kar ka ce ta bada komi a kawo min, amma idan tana aje zoɓo ka taho min da shi please!"
"Me za ki yi da zoɓo my pure zuma? Ke da ba girki zaki fara ba daga nan har one week."
"Ni dai idan akwai ina so, ina jin sha ne zan dafa Yah Maleek."
TAIMIYYAH ta bashi amsa cike da magiya da shagwaɓa, sai ya jinjina kai yana cewa, "Alright!
Zan taho da shi Allah sa kar na manta amma."
Daga haka ya wuce zuwa ɗakinsa ita kuma ta nufi nata ɗakin don ɗaura alwala.
_____________
*Gonar Ganye.*
Suhailah ce durƙushe a gaban Hajjah tana sauraren tarin faɗa da nasihun da Hajjah ke mata, akan
abinda ta so aikatawa da layun da amso ta ƙare maganar da cewa, "Ki ji tsoron Allah Suhailah ki
gane cewa auren Maleek da Zainab yin Allah ne ba mu ba, kuma hakan yana daga cikin
ƙaddaranku daga ke har shi , don haka ki rungumi mijinki ki maida hankali wajen faranta ransa, da
yi masa biyayyane ba shirme da nuna zafin kishi ba. A yanzu ku biyu kuma kar ki manta cewa duk
wacce a cikinku ta fi zamowa me faranta masa, da yi masa biyayyah ita zuciyarsa zai karkata
akanta. Don haka ki shiga cikin hankalinki ki dawo nutsuwarki tun ba baki saki damarki ba
Suhailah. Ni na san Maleek ba zai bani kunya ba wajen kwatanta adalci a tsakaninku, sannan ba
zai taɓa wofintar da ƙaunar da ya ke miki ba don ya yi aure, sai dai idan ke ce zaki sanya shi ya yi
hakan, wajen cigaba da nuna zafin kishi da wauta da shirmen da kika saba."
Suhailah da ke sauraren Hajjah da kunnin baseera, ta jinjina kai cike da nuna tarin nadamarta ta
ce, "In Sha Allah Hajjah ba zan sake aikata kuskure makamancin wanda na so yi ba, ki yafe min
Hajjah ki kuma dinga ta ya ni da addu'a Allah ya rage min zafin kishin da nake ji a cikin zuciyata
akan Maleek."
Yadda Suhailah ta kai ƙarshen maganar muryarta a raunace, hawaye kuma na biyo fuskarta ba
ƙaramin taɓa zuciyarta Hajjah ya yi ba. Ta kamo hannunta ta riƙe tana cigaba da mata nasiha cikin
rarrashi, bata bar Suhailah ba har sai da ta tabbatar ta kwantar da hankalin Suhailah, tare da ɗaura
ta akan turban da take da tabbacin zai anfani rayuwarta.
Suhailah ta fito daga ɗakin Hajjah tana ji zuciyarta na sake samun nutsuwa, tsanar Jawahir ya
dinga ratsa ruhinta tana sake tabbatarwa kanta cewa ba za ta sake aminta da kowace irin ƙawa ba.
Wanka ta yi ta shirya cikin wasu riga da skat na Atamfa, wanda ya kama jikinta sosai tare da yi
mata kyau, fuskarnan ya sha simple make-up sai tashin ƙamshin turarenta na MISS DIOR ke tashi
a jikinta.
Zuciyarta cike da ɗokin son sanya Maleek a idanunta, ta fito zuwa falon Hajjah lokacin ana ta
kiran sallar isha'i, ita da yake tana off shiyasa ta zauna tana me kunna kallo. Babu kowa a gidan
duk an watse kowa ya koma in da ya fito sai ita kaɗai, ita ɗin ma Maleek ta ke jira ya iso ta bishi
idan zai koma ya sauke ta a gidanta.
Bai samu shigowa gidan Hajjah ba sai wajen takwas da rabi na dare, a falo ya tadda Suhailah da
Hajjah suna kallo bayan sun kammala yin dinner tare.
Ya ƙariso cikin falon yana isa kujeran da ke facing Hajjah ya zauna, idanunsa akan Suhailah da ita
ma ta zubo masa ido tana kallon wani annuri da ke haskawa a saman fuskarsa. Ta ɗauke idanunta
daga dubansa lokacin da suka haɗa ido, tana jin wani abu me nauyi na danne zuciyarta. Maleek ya
dubi Hajjah yana me gaidata cike da ladabi da shagwaɓar da ya saba yi mata. Hajjah ta amsa tana
tambayarsa TAIMIYYAH, ya ɗan saki ƙaramin smile yana cewa, "Ta ce na gaishe ki Hajjah, da
cewa tayi ma sai in zo da ita na ce za ki yi faɗa, but tana son ki bada zoɓo akai mata idan kin yi
ajiyarsa."
Hajjah ta jinjina kai cike da fara'a ta ce, "Allah sarki ina amsawa, aiko akwai zoɓo me yawa ma
kuwa, bari in sanya Babah Rabi ta ɗibar mata, sai a haɗa mata har da kayan ƙamshi ma duk ina da
su."
Maleek ya jinjina kai ya ce, "Okey Hajjah mun gode." Kafin Hajjah ta yi magana Suhailah ta buɗe
baki ta gaida shi, bata jira ya amsa ba fara takawa don barin musu falon, sabida yadda ta ji sun
koma magana akan gurguwarsa. Kishi me zafi take ji na danne zuciyarta shiyasa ko amsa
gaisuwar nata bata tsaya ya yi ba ta juya ta nufi hanyar ɗakinta.
Hajjah da Maleek suka bi bayanta da kallo, Maleek na sakin smile tare da taɓe baki, ita Hajjah
miƙewa ta yi ta nufi hanyar kitchen don isa ɓangaren su Babah Rabi, hakan yasa Maleek miƙewa
ya rufawa Suhailah baya zuwa ɗakin.
A tunanin Suhailah Maleek ya shigo don ya cigaba da rarrashinta ne, amma sai ta ga ya miskile
fuska babu alamun rahama ya dubeta ya ce, "Na baki mintuna biyar kacal ki sameni a mota." Daga
haka ya juya ya yi fitowarsa daga ɗakin ya bar Suhailah da baki sake, wani irin abu me nauyi na
sake danne zuciyarta. Maganganun Inna Dije suka dinga dawo mata, ciki har da in da ta ke ce
mata " _Kiyi anfani da damarki Suhailah tun Maleek na bibiyarki yana rarrashinki,kafin ya yi
watsi da ke ya kama Amaryarsa wacce za ta faranta ransa._ "
Suhailah sai ta yi gaggawar nufan wajen da lugagge ɗinta ya ke a kammale, tana jin wani irin
tashin hankali na rufto mata.
Janye da Luggage ɗin ta fito bayan ta yafa mayafi tare da sanya takalmi a ƙafafunta, idanunta ya
sauka akan Maleek wanda ke tsaye tare da Hajjah da ke miƙa masa wata ƙatuwar leda. Ta maida
dubanta wajen Hajjah ta ce, "Hajjah za mu wuce."
Hajjah ta dubi Suhailah da kulawa ta ce, "To madallah ina fata duk kin ji abubuwan da aka sanar
miki, jibin za ki fara yin gaba ki koma Abujan ko?"
Suhailah sai ta saci duban Maleek da ya ɗauke kansa yana danna waya ta ce, "Eh idan ya ce in
koma ɗin sai na wuce jibin Hajjah."
Maleek ya yi gaba riƙe da ledan kayan su zoɓo da Hajjah ta bayar a kaiwa TAIMIYYAH, Suhailah
ta bi bayansa da kallo zuciyarta na sake narkewa da ƙaunarsa da jin kishinsa me tsanani.
Suka cigaba da magana da Hajjah kafin su yi sallama, Suhailah ta fito janye da ƙaramin luggage
ɗinta, kafaɗarta kuma rataye da hand bag ɗinta ta iso wajen compound ɗin.
Gaban motar Maleek ta buɗe ta shige bayan ta sanya luggage ɗinta a back seat, bai ce mata uffan
ba ya tashi motar suka fice daga cikin gidan Hajjah.
Tunda suka hau bisa titi Suhailah ke sauraren ta ji Maleek ya tanka mata amma sai ta ji shiru,
hakan yasa ta narke murya cikin ƴar shagwaɓar da ba wai ta ƙware a iyata bane ta ce, "My Maleek
wai kai ne ka ce zan koma jibi, to kai kuma sai yaushe za ka bar nan ɗin?" Maleek da hankalinsa
ke kan tuƙi zuciyarsa kuma na ga TAIMIYYAH , ya ɗago manyan idanunsa ya dubi Suhailah har
lokacin fuskarsa a miskile ta ke ya ce, "Eh! Jibi xa ki wuce Yusuf zai kai ki Kano ki bi flight, zan
zo Abuja bayan na gama da kwanakin da shari'a ta ce in yi mata. Ina fata kina shan maganinki
akan time cox ina sane saura sati biyu mu koma zuwa ganin likita, so u have to be careful Suhailah
don idan kika saɓa ƙa'ida aka ce kuma wani abun ya faru kar ki yi kuka da kowa sai kanki okey!"
Suhailah ta jinjina kai wani abu me ɗaci na sake danne zuciyarta, kalaman Maleek na cewa sai ya
gama kwanakin Angoncinsa na sake soya ranta. Ta dubesa fuskarta a narke ta ce, "Ina bin ƙa'ida
ban taɓa kaucewa ba, but meyasa ba za ka bari mu wuce tare ba kawai."
Maleek ya aika mata wani kallo yana sake haɗe fuska ya ce, "Sabida haka na tsara, don haka jibi
za ki wuce za mu biyo bayanki zuwa Saturday, don ina so Zaynab ta yi International Passport tare
da ita na ke so mu wuce Cairo."
Daga haka ya tsuke bakinsa bai sake cewa komi ba, kamar yadda ita ma Suhailah da tsananin
kaɗuwa da kalamansa bai barta ta iya cewa komi ba, sai jinyar zuciyarta da ke mata wani irin suya
kawai ta cigaba da yi har suka isa GRA. Maleek ya tsaya a Apple white ya yi ordering abubuwan
da ya ke da buƙata, sannan ya fito suka sake yin gaba kaɗan daga can ƙasan GTbank ya sake
tsayawa ya sayi rousted fish guda uku, sannan suka ƙarisa gidan Suhailah ya aje ta tare da bata
ledan fish ɗin guda ɗaya. Ta buɗe murfin motar ta fice ba tare da ta ko waiwayosa ba, ya bi
bayanta da kallo yana ɗan taɓe baki kafin ya juya kan motarsa ya fito daga cikin compound ɗin
gidan, bayan mai gadi ya sake wangale masa gate ɗin yana masa a sauka a lafiya.
Tafiyan mintuna biyar kacal ya yi ya iso gidan TAIMIYYAH, mai gadi ya buɗe masa gate ya shigo
cikin compound ɗin, yana nufan parking space ya adana motar. Ya fito yana buɗe back seat ya
kwashi ledojin da ke ciki ya kulle motar yana nufan entrance ɗin shiga gidan.
Daga ciki kuwa TAIMIYYAH ce ke naɗe bisa bed ɗinta suna chart da Zee, tana sanye cikin wata
rigar bacci blue black me santsin jiki. Ta jima tana juyyuya kayan baccin wanda duk babu wasu na
kirki sai fingilallu, da ƙyar ta iya tsamo wannan da ta ke ganin ɗan mutuncinsa ta saka. Fuskarta
ya sha powder da lipstick pink wanda ya zauna a cute lips ɗinta raɗau! Idanunta tayi lining ɗinsu
sai haskawa suke yi da ƙyallin baƙin eye liner. Sosai ta yi kyau cikin rigar baccin wanda ke ɗauke
da gidan Bra jiki, hakan yasa ƙirjinta ya ciko sosai ta saman faffaɗan wuyar rigar.
Hasken ɗakin gaba ɗaya ta maida shi dump ne sai hasken scented candle da ta kunna ne ya sake
baiwa ɗakin wani haske na daban, ga daddaɗan ƙamshin da ɗakin ya buɗe da shi me ratsa zuciya.
Ko'ina tsaf-tsaf ya ke don bayan fitar Maleek ta gyare duka ɗakunan nasu na ta da na shi baki
ɗaya, bayan ta kammala da gyaran ɗakunnan ne kuma ta wuce zuwa downstairs,su Harirah me
aiki suka taya ta kintsa kitchen ta bubbuɗe kayan da ta ke son fara anfani da su ta fito da su sarari.
Sai da suka kammala ne ta nufo upstairs ɗin ta yi wanka ta shirya cikin kayan baccin, ganin time
na tafiya Maleek ɗin bai shigo ba yasa ta naɗewa a bed suna faman chart da Zee wacce ke sanar
mata cewa za ta rako Mom ɗinsu ganin ɗaki.
Maleek Ado tun daga falon ƙasa ni'imtaccen ƙamshin turaran wutan RUSS COLLECTION ke
dukan hancinsa, su Harirah sun sake gyare falon da goge ko'ina sai ƙyalli kawai falon ke yi cikin
hasken fararen fitullun da suka ƙawata ɗakin.
Ya haura zuwa sama hannuwansa riƙe da ledojin da ya ke ɗauke da su, nan ma ɗin hancinsa ne ya
cigaba da shaƙan ni'imtaccen ƙamshin da ke fita daga kowani angles na falon. Ya isa wajen tables
ya aje ledodin yana nufan ɗakin TAIMIYYAH don jikinsa ya gama basa tana ciki. Ya tura ƙofar a
hankali yana sanya kansa cikin ɗakin, wani daddaɗan ƙamshin ya sake dukan hancinsa. Sai ya
ɗan dakata daga tsaye yana ɗaga manyan idanunsa ya sauke akan TAIMIYYAH, wacce jin
shigowarsa ya sata saurin zamewa ta shige cikin duvet tare da lumshe idanunta tamkar wacce ta yi
bacci....✍🏻
*Ga masu buƙatar haɗaɗɗun turarukan wuta masu ƙamshi da inganci, tare da kama waje to ku yi
maza ku garzaya wajen RUSS COLLECTION. Ba ga turarukan wuta kawai ta tsaya ba duk wani
nau'in kayan qamshi na ciki da waje za ku samesa akan farashi me sauƙi, ku tuntuɓe ta wannan
layin don samun ingatattun turaruka zuwa haɗaɗɗun Humrahs da kayan gyara na mata* 👇🏻
#Ɗansabo ce#
[12/15, 11:46 AM] +234 703 040 9541: Littafin TAIMIYYAH paid book ne,ga duk wanda ta
tsincesa a kowani irin group ne,kiji tsoran Allah karki karanta sai kin biya 500 naira only.
Za ku iya min magana ta wannan number ɗin 08167768704, ko kuma ku turo kuɗin ku kai tsaye ta
wannan account ɗin 0504192664 aisha ibrahim dansabo GTbank.*
Masu turo credit za ku turo katin MTN na 500 ta wannan line ɗin 08167768704.
_Ina ƴan kasuwa masu buƙatar a tallata muku hajar ku? Maza ku garzayo da kuɗi ƙalilan a tallata
muku kayan siyarwanku sai dai kawai ku ji ana kiran waya don buƙatan sayan kayan ku,ku
tuntuɓeni ta layina kamar haka 08167768704._
*76*
Maleek ya dinga takawa a hankali har ya isa bakin bed ɗin ya zauna, ya kai hannu ya yaye duvet
ɗin baki ɗaya ya wurga can ƙasa, idanunsa ya sauka akan fuskar TAIMIYYAH da ta lumshe
manyan idanunta ita a dole ta fara bacci. Ya saki smile yana jin wani wutar soyayyarta na sake
narke zuciyarsa, bai jira komi ba ya janyota daga kwancen zuwa jikinsa yana cewa, "Hey! My
pure zuma am back now."
TAIMIYYAH jinta a jikinsa ya sanya ta buɗe manyan idanunta, ta sauke a kansa tana ɗan
zumɓuro bakin da ya sha lipstick, hakan da ta yi kuma ba ƙaramin kunna zuciyar Maleek Ado yayi
ba, sai ya yi gaggawar kai fuskarsa saman nata face ɗin yana bata wani light kiss a forehead
ɗinta,ƙamshi da laushin jikinta na sake kunna zuciyarsa da haifar da yanayi me zafi a cikin jikinsa.
Murya can ƙasa ya ce, "Zaynabb ko welcoming ɗina ba ki iya ba idan na shigo, Sai dai ki naɗe
kina baccin ƙarya ko? Oya kiss me please!"
Ya yi maganar yana sake shigar da ita cikin jikinsa tare da miƙa mata bakinsa, TAIMIYYAHB sai
ta rintse ido wani kunya na sake lulluɓeta, ta yi magana cike da shagwaɓa ta ce, "Please! Yah
Ma....."
Bata kai ga furta kalamanta ba ta ji ya haɗe bakinsu waje guda, ya zura mata harshensa cikin
bakinta wai ko za ta kama, amma sai ta ƙi yin hakan ta barshi ya yi kiɗansa da rawarsa, wajen
susuta ta da zafafan kisses masu motsa zuciya da gangar jiki.
Sai da ya gama yamutsata son ransa kafin ya sake ta ,yana faman jera numfashi a gwame,
idanunsa a lumshe suke gam yana jin wani irin zazzafan yanayi na bin jinin jikinsa. Sam ba zai iya
tafiya yabar TAIMIYYAH a nan ba, haka ya ke ji a cikin zuciyarsa, shiyasa ya ke son Suhailah ta
riga su yin gaba kafin ya yi magana da Hajjah.
TAIMIYYAH wacce ta yi gefe guda tana me dunƙule jikinta, sai ta ɗaga kai ta saci dubansa,
daidai lokacin da ya ke buɗe idanunsa da suka sauya kala ya sauke a kanta, sai ta yi gaggawar
ɗauke idanunta daga kansa tana sake narke fuska.
"My pure zuma ta so mu je ki ci abinci, na san baki yi dinner ba. Hajjah ta aiko Shehu da abinci
ko?"
TAIMIYYAH ta gyaɗa masa kai kafin ta yi magana a shagwaɓe ta ce, "Eh ni har ma na ci abinci,
ga naka can bisa dining da ke nan upstairs."
"Zaynabb shi ne babu jira sai ki ci abinci ba ki jira Babynki ya dawo kin yi feeding ɗinsa ba ko?"
Yadda Maleek ya yi maganar cikin narke murya shi a dole shagwaɓarta ya ke kwaikwayo, ya
sanya TAIMIYYAH sakin dariyar da babu shiri. Maleek ya sake baki yana kallon yadda ta ke
dariya cike da birgewa, sai ya miƙa hannu ya sake janyota zuwa jikinsa yana cewa, "Dariya ma ki
ke min ko Horney? Oya let's go ina buƙatar cin abu mara nauyi kafin mu kwanta."
Daga haka ya riƙo hannun TAIMIYYAH suka fito zuwa falon, ya sakin hannunta ya nufi wajen
TV ya kunna, ita kuma sai ta nufi wajen dining ta zubo masa Chicken Salad with potato,wanda ya
ji haɗin Bama da Salad cream with spices, ta zuba farfesun kayan ciki a ƙaramin bowl ta ɗauro
bisa tray da ke kan dining ɗin, ta nufo shi da shi zuwa nan ƙasan carfet. Maleek da idanunsa ke
kanta yana kallon yadda take takowa hannunta riƙe da tray ɗin,ɗaya hannun kuma dafe da guiwar
ƙafarta, sai ya ji wani abu na motsa zuciyarsa, tausayinta me tsanani na sake huda jinin jikinsa.
TAIMIYYAH ta aje tray ɗin tana me ɗagowa daga tsugunan da tayi wajen aje tray ɗin, ta sauke
manyan idanunta akan Maleek Ado, wanda gaba ki ɗaya idanunsa ke kan ƙirjinta da ya fito waje,
lokacin da ta ke kaiwa ƙasa don aje tray ɗin haunnunta. Ya miƙawa TAIMIYYAH hannu alamun ta
zo garesa amma sai ta noƙe tana nuna masa abincin da ta aje ɗin. Sai ya matso sosai wajen yana
cigaba da bin ilahirin jikinta da mayataccen kallo, ita ya matsamawa ta bashi abincin da kanta,
kafin ya sanyata ɗakko ledojin rousted fish ɗin da ya siyo, suka ɗan ci kaɗan bada yawa ba sannan
TAIMIYYAH ta kwashi ragowar zuwa kitchen da ke nan saman ta sanya cikin fridge.
Lokacin da ta fito bata samu Maleek a falon ba, hakan yasa ta kammala kwashe abubuwan da suka
ɓata duk ta kai kitchen ɗin ta aje, tana fitowa ɗakinta ta wuce ita ma don yin brush.
Tana fitowa daga banɗakin ta jiyo ƙaran wayarta da ke kan bed, sai ta nufi wajen tana ɗaukar
wayar wanda tun daga tone ɗin kiran ta san cewa Maleek ne, sai ta yi receiving tana kai wayar
kunni ba tare da ta yi magana ba.
"Zaynabb am waiting for u fa, ko ni zan biyo ki nan ɗakinki mu kwanta ?"
Muryar Maleek ya shiga kunnuwanta yana jefo mata tambayar da ya sanya zuciyarta doka masa,
ta yi saurin narke masa murya cike da zallar shagwaɓa ta ce, "Ai na ɗauka ka kwanta ne shiyasa,
ni ma gani har na kwanta anan ɗin."
Maleek bai ce komi ba illah murmushi da ya saki yana cuting call ɗin, TAIMIYYAH ta bi wayar
da kallo tana sauke a jiyar zuciya tare da addu'ar Allah yasa ba biyota nan ɗin zai yi ba. Sai dai ko
minti uku bata yi da gyara kwanciyarta ba, ta ji buɗe ƙofarsa da shigowarsa cikin ɗakin, sai ta sake
naɗe jikinta a cikin duvet ɗin, tana lumshe idanunta ƙirjinta na faman dokawa.
Maleek Ado ya raɗawa TAIMIYYAH hakan a kunni lokacin da ya ke kwanto da ita xuwa jikinsa
ya rungumeta, ta sake rintse idanunta tana me kwantar da kanta akan ƙirjinsa ba tare da ta yi
magaba ba.
Maleek ya zura hannunsa cikin rigarta yana sake cewa, "Bana son ko faɗa muka yi ki ce za ki raba
shinfiɗa da ni pure zumata kin ji ko?"
TAIMIYYAH da ke lafe cikin jikinsa ta gyaɗa kanta tana sake haifar da wani yanayi a ilahirin
zuciya da gangar jikin Maleek, sabida yadda ta ke motsa kanta a ƙirjinsa ba ƙaramin kunna shi ta
ke yi ba, ba tare da ita ta san hakan ba. Ya cigaba da yawo da hannunsa a muhallin da ke matuƙar
ɗaukar hankalinsa, yana cibaba da raɗa mata kalaman da ke ratsa zuciyarta.
Maleek ya yi gaggawar katse TAIMIYYAH daga furta kalamanta yana cewa, "No! Zaynabb bana
son wannan sunan, sabon suna na ke so ki raɗamin." TAIMIYYAH sai ta shagwaɓe murya tare da
yin ƙasa da shi sosai ta ce, "Please! Hubby bacci na ke ji, don Allah ka yi haƙury ka barni da
rigata."
Maleek da ya ƙarisa zare rigar baccin jikinta ya cillar ƙasa, sai ya saki smile sunan da ta kirasa da
shi, da yanayin salon da ta furta sunan akan harshenta na sake ratsa zuciyarsa. Ya kai bakinsa bisa
kunninta ya ce, "No Baby na fi son jin wannan lallausar jikin a hakansa, ba tare da sutura ta yi min
shamaki da shi ba.Ki kwantar da mind ɗinki babu abinda zan miki da ya wuce jin ɗumin jikinki,
sai zuwa safe zan yi breakfast da pure zuma na ko ?"
Kunya ne ya lulluɓe TAIMIYYAH ta yi saurin sake shigar da kanta cikin jikinsa, murmushi na
kwacewa a saman face ɗinta wanda Maleek ke jiyo sautin fitarsa, hakan yasa shi ɗago fuskarta ya
haɗe da tasa yana laluban bakinta. Ta rasa meyasa baya gajiya da yin kiss a rayuwarsa, don daga
jiya zuwa yau ta gama fahimtar hakan. Ta zura hannuwanta tana me naɗesu ta bayansa, sabida
yadda jikinta ya fara ɗaukar rawa lokacin da Maleek ɗin ya zare bakinsa daga nata, ya mayar akan
muhallin da ke kiɗima zuciyarsa. TAIMIYYAH ta saki kukan shagwaɓa tana jin wani baƙon
yanayi da ke neman tsaida bugun numfashinta, shi ko Maleek cigaba ya yi da ruɗa jikinta da
zafafan saƙonninsa. TAIMIYYAH hankalinta bai kwanta ba sai da tabbatar ba abinda ta ke tsoro
zai sake maimaitawaba sannan ta samu nutsuwa, tana cigaba da amsan darussan da bata taɓa sanin
da ire-irensu cikin duniyar luv ba.
____________
*Washegary*
*10:30am*
TAIMIYYAH da Maleek Ado suka sakko zuwa downstairs don yin breakfast, tuni su Harirah sun
shirya coolers ɗin abincin breakfast ɗin da Shehu ya kawo bisa dining. Sun gyara ko'ina sai tashin
ƙamshi ya ke kamar yadda aka horas da su yadda za su riƙa yi, tun kafin a kawo su gidan shiyasa
suna tashi suka kammala yin duk abinda ya kamata,sai suka koma zuwa sashin sudon jiran
sakkowan iyayen gidan na su aba su abin karin safe.
TAIMIYYAH ta ɗaga manyan idanunta ta sauke a kan Maleek Ado, wanda ke faman bin shirgar
jikinta da kallo tamkar bai taɓa ganinta ba sai time ɗin. Wasu riga da skat ne ta sanya na wani
material me laushi kalar red and black, wanda ya yi masifar yi mata kyau ɗinkin ya zauna a jikinta
sosai tare da fito da cikar halittarta. Ta shagwaɓe murya tana duban idanunsa ta ce, "Hubby bari in
fara duba yaran can aba su abin karyawa time ya tafi, may be ma sun gama galabaita da yunwa."
Maleek ya zura mata ido yana jin wasu feelings akanta masu ƙarfi, ya gyaɗa mata kai alamun ta je
ɗin sai ta juya ta fara takawa shi kuma ya rakata da idanunsa.
Tare da su ta fito daga side ɗinsu zuwa cikin kutchen tana cewa su jiraye ta anan tana zuwa, sai ta
fito zuwa dining area ɗin ta shiga ɗibar musu abincin yadda zai wadacesu, sannan ta ƙwalawa
harirah kira ta ɗauka, tana sanar da ita idan sun kammala su haura zuwa sama su gyara falon kaɗai
amma banda bedrooms ɗin.
Harirah ta amsa da ladabi tana yin gaba ta bar TAIMIYYAH na jan kujeran dining ɗin ta zauna,
tana me janyo plate ta fara serving ɗinsu abinda za su ci. Maleek ya aje wayarsa da ya ke dannawa
tun isowarta wajen, yana me zuba mata idanunsa masu kaifi akanta, har ta kammala zuba musu
abincin bai ɗauke idanunsa akanta ba.
"Baby sugar guda nawa za a saka?" TAIMIYYAH ta tambayi Maleek da muryar shagwaɓa, sai ya
kashe mata ido guda yana cewa, "Only 3 cubes is okey."
TAIMIYYAH ta saka masa 3 cubes ɗin tana saka tea spoon a cikin cup ta tura zuwa gabansa, ita
kuma ta haɗa only ruwan milo babu ko sugar ta aje a gabanta. Ahankali su ke ciyar da juna har
suka kammala kalacin, Maleek shi ya fara baro dining area ɗin zuwa cikin main parlorn ya zauna
cikin seater. TAIMIYYAH ta kintsa wajen tana me ƙwalla kiran Harirah don ta kwashe sauran
kayan zuwa kitchen, Harirah ta fito cikin hanzari ta iso wajen dining ɗin. TAIMIYYAH ta nuna
mata kayayyakin da suka ɓata da ragowar abincin da ke cikin coolers ɗin ta ce, "Waɗannan kayan
da aka ɓata ku wanke su, shi kuma abincin ku samu plate guda ku ɗibarwa mai gadi a kai masa, ku
haɗa masa da ruwan tea kamar yadda kuka haɗa naku, bayan kun kammala gyaran sama ina so ku
taya ni wani aiki zuwa anjima, but ku tabbatar kun yi wanka kun sauya kaya don bana son zama
da ƙazanta kin ji ko?"
Harirah ta gyaɗa kai ta ce , "Na ji Anty za mu yi wankan da zaran mun kammala ayyukan." Daga
TAIMIYYAH ta baro wajen zuwa cikin falon hannunta riƙe da wayarta, Maleek da ke zaune
hankalinsa akan wayarsa, jin takun isowanta cikin falon ya sanya shi ɗaga ido ya dubeta, yana
nuna mata kusa da shi alamun ta zo nan ta zauna. Bata musa ba ta ƙarisa tana ƙoƙarin ɗosana
jikinta a cikin seater ɗin, Maleek ya yi azamar janyota zuwa kan laps ɗinsa ta yi masauki a kai. Ta
ɗaga manyan idanunta ta sauke akan fuskarsa tana faman narke masa tamkar za ta sanya kuka, shi
ko Maleek sai ya kai baki ya sumbaci wuyanta zuwa ƙirjinta kafin ya ce, "Pure zuma kina fa da
ɗan nauyi kaɗan, nan gaba anya zan iya ɗaga ki ma kuwa?"
Kallon da Maleek ya watsa mata ne yasa ta gyara kalamanta ta ce, "Sorry Hubby, na saba da cewa
hakan kuma ni yana min daɗin faɗi."
Maleek ya dungure goshinta ya ce, "But ni kuma bana so, na fi son a kirani Babyn ko Hubby, ke in
so samune ma ki karani Honey ko bani da sweet ne Baby ?"
Ya yi tambayar yana tsareta da idanunsa fuskarnan a miskile tamkar ba daga bakinsa maganar ta
fito ba, TAIMIYYAH da ta gama shiga kunya ta yi saurin manne kanta a ƙirjinsa, cike da
shagwaɓa ta ce, "Wayyo kunya ni dai gaskiya kar ka lalatawa Iyah jika, wannan maganar tafi
ƙarfina Hubby."
Maleek ya saki dariyar da bai shirya yin ta ba yana me ɗago da face ɗin TAIMIYYAH, wacce ta yi
saurin dubansa tana ganin yadda yake faman dariyar maganarta tamkar ba shi ba. Ta shagala a
kallonsa har zuwa lokacin da ya tsaida dariyar yana cewa, "Really Baby zan lalatawa Iyah ke?
Idan ban lalataki ba ai ke za ki lalatani da wannan salon shagwaɓar naki da ke narka zuciyata, oya
tell me ta ya zan lalata mata ke ɗin?"
Ya yi maganar ne yana riƙo face ɗinta yadda ba za ta iya kaucewa duban idonsa ba, hakan yasa ta
lumshe ido cike da shagwaɓa ta ce, "Please! Hubby a bar zancen kawai wallahi kunya na ke ji."
"Ni kuma gashi in da kunyar ta ke ma ban santa ba pure zuma, don haka ko ki sanar dani ko kuma
yanzu mu koma master room kila za ki fi iya sanar dani a can ko?"
TAIMIYYAH ta yi saurin girgiza kai tana cewa, "No please! Zan faɗi amma sai ka sakar min face
Hubby."
Babu musu ya saki face ɗinta ta maida kanta bisa ƙirjinsa ta kwantar kafin ta ce, "Ni ma bansan ta
yadda za ka yin ba kawai na faɗi ne."
Maleek ya saki dariya kaɗan kafin ya ce, "Aiko baki isa ba tunda ki ka furta sai kin faɗi ta yadda
za ayi, but not now zan biki bashi zuwa dare ko pure zumata?"
TAIMIYYAH ta yi saurin gyaɗa kai tana sake shigewa jikinsa, fitinannan ƙamshinsa na sake
kassara zuciyarta da narkar da ita a ƙaunarsa.
Yinin ranar wata iriyar soyayyane ake ba je kolinsa tsakanin Maleek Ado da TAIMIYYAH, wacce
ta ke amsan tarin darussa masu nauyi daga garesa.
Misalin shida na yamma Ummie ta iso gidan TAIMIYYAH tare da Inna Larai, TAIMIYYAH ta
rungume Ummie cike da tsantar murnar ganinta. Suka saki juna Ummie na faman bin
TAIMIYYAH da ido tana kallon yadda ta ƙara yin wani fresh, alamun amarcin ya fara amsarta.
TAIMIYYAH ta maida dubanta kan Inna Larai wacce ta saki baki tana ƙarewa tsaruwar falon
kallo, ta gaidata cike da ladabi Innar ta amsa da fara'a tana yiwa TAIMIYYAH fatan alkhairy.
Nan da nan TAIMIYYAH da taimakon su Harirah suka cika gaban su Ummie da abubuwan motsa
baki, TAIMIYYAH suka shiga hira da Ummie tana faman jaddada mata yadda ta ke kewansu ita
da Iyah, duk da cewa duk safe sai ta kira Iyah a waya sun gaisa amma hakam baya hanata jin
kewarta me tsanani.
Sai da Ummie ta tambayi TAIMIYYAH cewa Maleek baya nan ne? TAIMIYYAH ta sanar da ita
cewa bai jima da fita ba, daga haka sai suka haura zuwa sama ɗakin baccin TAIMIYYAH. Ummie
ta nufi wajen side drawer na jikin mirrow ta ɗakko wani paper bag, wanda ita ce ta ajesa randa
suka kawo TAIMIYYAH bata samu damar yi mata bayanin kayan da ke ciki ba. Ta zazzagesu
akan bed tana yiwa TAIMIYAH bayanin yadda za ta yi amfani dasu, kayan gyara ne dasu
Humrahs masu kyau, waɗanda take da tabbacin za su taimakawa TAIMIYYAH,musamman a
wannan time ɗin da take tsaka da cin amarci.
Kunya gaba ki ɗaya ya rufe TAIMIYYAH ita ko Ummie ko a jikinta, ta cigaba da koya mata
dibarun da za su sake sanyata ta mallaki zuciyar Maleek ɗin.
Da suka tashi tafiya ne Ummie ke sanar da TAIMIYYAH cewa sallama ta zo suyi, don gobe za ta
koma Kaduna gida baki ɗaya , sai kuma an ɗaura aurenta da Baba Sani sannan za a sake kawota
Zaria.
TAIMIYYAH ta yi farin ciki sosai da jin cewa Ummien sun daidaita kansu da Baba Sani har ana
zancen aure, ta haɗa musu abin arziƙi tare da yi musu rakiya har wajen compound, in da Sani ke
jiransu a mota su kai sallama da juna TAIMIYYAH na faman ɗagawa Ummie hannu , har sai da ta
ga fitar su daga cikin compound sannan ta juya zuwa cikin gida, zuciyarta cike da farin cikin jin
cewa Ummie ta amince da auren Baba Sani, idanunta suka hasko mata fuskar Umma da irin halin
da za ta kasance idan ta ji zancen auren.......✍🏻
#Ɗansabo ce#
[12/15, 11:46 AM] +234 703 040 9541: Littafin TAIMIYYAH paid book ne,ga duk wanda ta
tsincesa a kowani irin group ne,kiji tsoran Allah karki karanta sai kin biya 500 naira only.
Za ku iya min magana ta wannan number ɗin 08167768704, ko kuma ku turo kuɗin ku kai tsaye ta
wannan account ɗin 0504192664 aisha ibrahim dansabo GTbank.*
Masu turo credit za ku turo katin MTN na 500 ta wannan line ɗin 08167768704.
_Ina ƴan kasuwa masu buƙatar a tallata muku hajar ku? Maza ku garzayo da kuɗi ƙalilan a tallata
muku kayan siyarwanku sai dai kawai ku ji ana kiran waya don buƙatan sayan kayan ku,ku
tuntuɓeni ta layina kamar haka 08167768704._
*77*
TAIMIYYAH lokacin da ta koma ciki direct upstairs ta nufa zuwa ɗakin Maleek don kintsawa,
domin idan ba ya fita bane bata samun damar yin komi, suna manne da juna ne baya so ko nan da
can ta matsa daga jikinsa sai da dalili me ƙarfi.
Tana kammala kintsa komi ta kunna burner ta zuba turaren wutar Nothern King ƙamshi ya fara
turare ɗakin, sai ta fito zuwa ɗakinta ta sake kintsawa ta sanya turaren wuta.
A na kiran magriba tana kammala kintsa ko'ina sai tashin daddaɗan ƙamshi kawai ka ke ji. Ta fito
zuwa kitchen ɗin da ke nan upstairs tana ɗakko ledar da Maleek ya zo dashi jiya daga gidan
Hajjah, ta buɗe tana ganin kayan da ke ciki wanda zoɓo ne da kayan ƙamshi masu yawa har da
fresh mint da bata san da shi ba, da ta sanya shi a fridge gudun kar ya yamushe. Murna ya kamata
tana jin kwaɗayin shan fruity zoɓo na kama zuciyarta, ta fitar da komi ta aje a inda ya dace sanna
ta fito ta nufi bedroom ɗinta.
Toilet ta nufa ta ɗauro alwala ta fito ta gabatar da sallar magriba, tana idarwa ta sake fitowa zuwa
kitchen ɗin ta kwashi zoɓon da kayan da zata buƙata ta sakko zuwa downstairs.
Direct kitchen ta nufa ta aje kayan tare da nufan wajen babban fridge me double door, wanda ke
girke cikin kitchen ɗin ta buɗe, ta yi tsaye tana ta dudduba fruit ɗin da aka jeresu a side guda, ta
miƙa hannu ta ɗakko pineapple da Strawberry.
Wajen sink ta nufa ta aje su don sake ɗaurayesu,ta nufi wajen da ta ciro pot ta ɗakko me ɗan girma
ta tari ruwa a ciki, bayan ta ɗauraye tukunyar sai ta tari ruwa ta kunna gas ta ɗaura akai.
Zoɓon ta ɗibi iya yawan da take da buƙatar amfani da shi ta wanke shi tsaf, ta zuba a cikin ruwan
da ta ɗaura a wuta. Ta koma wajen da ta aje kayan ƙamshi ta ɗibi cloves da fresh ginger ta fere
fresh ginger ɗin, ta ɗaurayesu haɗe da cloves ɗin ta zuba cikin blander ta markaɗasu, bayan ta yi
blanding sai ta juye akan dahuwar zoɓon. Ta ɗakko cinnamon stisck ta ɓalli kaɗan ta jefa tare da
yanka lemon guda biyu ta zuba a cikin dahuwar zoɓon shi ma, sai ta dawo kan pineapple ta yanka
shi tare da wanke ɓawon bayan, ta sanya cikin dahuwar zoɓonta. Lokacin da ya fara tafasowa nan
da nan kitchen ɗin ya buɗe da wani irin qamshi, sai ta yayyanka pineapple ɗin da haɗa da
Strawberry with Cocumber ta yi blanding ɗinsu.
Bayan ta ƙammala yin blanding ɗinsu sai ta tace ruwan ta aje a side, ta koma kan zoɓon da ke
dahuwa ta zuba sugar daidai yawan da take da buƙata, ta barshi ya cigaba da dahuwa qamshi na
cigaba da buɗe ko'ina.
Bayan ta tace zoɓon ne ta juye ruwan pineapple with srawberry and cocumber ta sake mayarwa
kan wuta, ya tafasa na minti biyu sannan ta sauke, ta barshi ya wuce tas! Sannan ta juyeshi cikin
wasu bottle masu kyau, wanda aka yi su tamkar jug amma bakin bottles gare su. Cikin freezer ta
jeresu yadda za su yi saurin ɗaukar sanyi sannan ta sake ɗebo fruit, daidai yawan wanda za ta haɗa
fruit salad da shi ta wanke su tas! ta fara yayyankawa.
Haɗin Apples, Pineapple, Strawberry, Banana, Orange and watermelon ta yi. Ta yayyanka su
ƙananu ta juye cikin bowl me kyau,ta nufi wajen freezer in da ta aje haɗin wannan fruity zoɓo ɗin,
ta zuba a cikin haɗin fruit salad ɗin.
Nan da nan ya bada wani irin colour me kyau, tare da bada wani irin flavour me daɗi, sai ta rufe
bowl ɗin ta sanya shi cikin fridge don ya ɗauki sanyi. Ta ciri murya ta kira su Harirah don zuwa su
gyara wajen, Ita kuma ta fito tana nufan uptairs don yin wanka ta gabatar da sallar Isha'i ,lokacin
da ta idar da sallar ne ta kintsa kanta cikin wata doguwar riga na english wears, wanda tsayinsa ya
sauka zuwa guirwarta, rigar me V neck ne wanda ya bayyana ƙirjinta a waje kaɗan. Ta yi kwalliya
me sauƙi akan fuskarta tare gogo red lipstick kalar rigar jikinta, sosai ta yi kyau matuƙa sai fitar da
daddaɗan ƙamshin humrah da turaren VERSACE ta ke yi kota ina. Ta ɗauki wata siririyar saƙar ta
sanya a wuyarta tare da sanya ƙananun barima biyu a kunninta masu azabar kyau, nan da nan
fuskarta ya sake haskawa da wani irin kyawu me ɗaukar hankali.
Ta yi tsaye daga bakin dogon mirrow ɗin tana dafe da guiwar ƙafarta, ta dinga ƙarewa kanta kallo
daga sama har ƙasa, siririn ƙafarta me laluran ta ke kallo wanda take dafe da shi da hannunta. Ta
sauke sassanyar numfashi fuskarta na haskawa da tarin murmushi, tana hango irin kallon da
Maleek zai dinga bin ta da shi, don ita da kanta ta yaba da yadda rigar ta yi mata mugun kyau.
Lokacin da ta fito daga ɗakin downstairs ta nufa, daidai lokacin da Zinatu ke shigowa cikin falon
hannunta riƙe da basket ɗin abinci, wanda Shehu ya kawo yanzu ta fita ta amso.
Zina ta tambaya TAIMIYYAH idanunta akanta ,tana yaba kyawun uwar ɗakin nasu a cikin
zuciyarta, TAIMIYYAH ta dubi Zina ta ce, "Kai kitchen gani nan zuwa in ɗibar muku na ku sai ku
wuce side ɗinku bayan kin kai wa mai gadi nasa."
Daga haka Zina ta wuce da ƙaton kwandon abincin zuwa kitchen, TAIMIYYAH ta rufa mata baya
don ɗibar musu na su kason.
"Hairarah ke ɗauki wannan tray ɗin ki wuce da shi zuwa sama, ki aje bisa kan table ne ba dining
ba. Ke kuma ki kai wa Baba mai gadi wannan, sai ki dawo ki ɗauki naku ku wuce side ɗinku."
Dukansu suka amsa mata da cewa "Tuh." Kowacce na ɗaukar abinda aka ce ta ɗauka suka nufi
inda aka aike su, ita kuma TAIMIYYAH ta matsa daga gaban cabinet ɗin tana ɗaura kwandon a
saman wajen.
Tana fitowa daga kitchen ɗin Maleek Ado na shigowa cikin falon, idanunsa ya sauka akan
TAIMIYYAH wacce take takowa cikin yanayin tafiyarta da ke motsa zuciyarsa.
Ya cigaba da takawa yana nufan direction ɗin da take tahowa don zuwa cikin falon, zuciyarsa na
yaba kyawun da ta yi cikin shigar da ke jikinta.
"Sannu da zuwa Hubby!" Cewar TAIMIYYAH lokacin da Maleek ya ƙariso wajen da ta yi tsaye
jingine da jikin kujera, ya ɗaga manyan idanunsa yana sake bin ilahirin jikinta da kallo, kafin ya
miƙa mata hannu alamun ta taho garesa. Sai ta shagwaɓe fuska tana isowa wajensa tare da miƙa
masa hannunta ya kama, ya mannata da jikinsa ya rumgume murya can ƙasa ya ce, "Wife ba irin
wannan welcoming ɗin na ke so ba, ke da zaki taho ki yi hugging ɗina tare da bani hot kiss,amma
sai ki wani noƙe daga tsaye kina min sannu da zuwa, haka aka ce miki ana welcoming Hubby
ɗin?"
TAIMIYYAH da ke lafe a jikinsa ta ɗago ido ta dubesa kafin ta yi magana cike da shagwaɓa ta ce,
"To zan yi hakan next time Hubby sorry!"
Maleek ya saki smile yana kai baki ya sumbaci wuyanta, ya sauke zazzafar numfashi ya ce, " Gud
gal! Oya kiss me now."
TAIMIYYAH ta sake ɗaura manyan idanunta a kansa ta ce, "Hubby yanzu Harirah za ta sakko
daga sama kar ta ganmu a haka please!"
Yadda ta yi maganar cike da magiya ya sanya Maleek raba jikinsa da nata, sai dai hannunsa cikin
nata ya ke ,suka nufi hanyar hawa upstairs ɗin daidai lokacin ita kuma Harirah ke sakkowa, ganin
Maleek yasa ta yi saurin zubewa ta kwashi gaisuwa, lokacin da ta ƙarisa sakkowa. Ya amsa a
taƙaice fuskarnan babu alamun rahama, ta yi gaba tana gulmar miskilancinsa a zuciyarta, shi kuma
Maleek yana riƙe da hannun TAIMIYYAH suka haura zuwa sama, sun kai steps ɗin ƙarshe ya yi
sama da ita baki ɗayanta. Bai direta a ko'ina ba sai bedroom ɗinsa ya aje ta bisa Sofa yana cewa,
"Wash! Baby wallahi nauyi ki ke ƙarawa koda yaushe."
TAIMIYYAH ta saki murmushi a kunyace tana binsa da wani sassanyar kallo, wanda Maleek ke
jin tasirin idanunta na ratsa ilahirin jinin jikinsa. Ya zauna daga kan Sofan yana kai baki ya yi
kissing eyes ɗinta ya ce, "Luv na gaji wanka na ke son yi za ki min ?"
TAIMIYYAH ta waro idanunta waje kafin ta shagwaɓe murya ta ce, "Pleas..." Hannun da Maleek
ya ɗaura akan lips ɗinta ne ya hanata ƙarisa magiyarta, ya tsare da manyan idanunsa yana cewa,
"Bana son jin wata magiya Luv, mu je ki tayani in yi wankan to Baby."
Duk yadda TAIMIYYAH ta so zamewa haka ya ɗauke ta cak! Zuwa bathroom ɗin, ita ta haɗa
masa ruwan wankan amma sai ya ɗauke ta cak ɗinta ya sanyata cikin tube ɗin. TAIMIYYAH ta
saki kukan shagwaɓa tana masa mitan shikenan ya ɓata kwalliyar da ta yi masa. Maleek ya gama
raba jikinsa da kayansa yana shigowa cikin tube ɗin ya ce, "Ai sabida ni akai kwalliyar don na
ɓata ba matsala bace, sai a sake min wani sabo pure zumata."
Daga haka ya mannota da jikinsa yana zare riga da Bra ɗin ya jefo su ƙasa, ya kai hannunsa yana
juyo da ita suna facing juna. Idanunsa akan ƙirjinta da ke tada dukkanin wutar sha'awarta a zuciya
da gangar jikinsa, sun jima Maleek na yadda ya so kafin ayi wannan wanka.
TAIMIYYAH ita ta fara baro bathroom ɗin tana ɗaure da ƙaramin towel, bata tsaya a ɗakinsa ba ta
gudu zuwa ɗakinta, har lokacin mita take yi akan wankan dole da ya sake sanyata ta yi.
Cikin wasu riga da wando na bacci wannan karon ta shirya, wandon me ɗan faɗi ne wanda
tsayinsa iya cinya ya tsaya, sai rigar wacce take ƙarama ce me faffaɗan wuya,shiyasa rabin ƙirjinta
a waje suke.
Wata kimono ta ɗakko ta sanya akan shigar don kunyar fita a haka take ji, tana cikin fesa turare
Maleek ya shigo cikin ɗakin yana sauke idanunsa a kanta.
Maleek Ado ya furta hakan akan kunnin TAIMIYYAH na hagu, lokacin da ya ƙariso bakin mirrow
ɗin yana rungumeta ta baya,ya cigaba da sunsunan ƙamshinta yana me kai hannu ya kwance igiyar
dake jikin kinomon, wanda ya taimaka wajen rufe jikin TAIMIYYAH. Take shigarta ya bayyana a
sarari yana kafeta da ido ta cikin madubin yana ƙare mata kallo, ya juyo da ita suna facing juna
murya can ƙasa ya ce, "Meyasa sai kin sanya wannan abin Luv?"
TAIMIYYAH ta narke fuska ba tare da ta ce komi ba, hakan yasa Maleek ƙarisa zare hannun
Kimonon a jikinta ya cilla shi bisa kan bed, daga haka ya kama hannunta suka fito zuwa falo.
A.Maleek ya yi tambayar lokacin da ya kai spoon ɗin farko na haɗin fruit salad ɗin da
TAIMIYYAH ta yi bakinsa, TAIMIYYAH ta sakar masa murmushi tana cewa, "Ni ce na yi ɗazu
fah Habibee."
Maleek ya wani waro ido yana jin wani abu na malting a zuciyarsa, game da yadda ta kira shi da
suna Habibee ɗin, ya dubeta da wani irin sassanyar kallo ya ce, "Are u serious Zaynabb ke ce kika
yi wannan haɗin?"
TAIMIYYAH ta sake jifansa da killer smile ,tare da yin masa wani fari da manyan idanunta ta ce,
"Yes am very serious Baby ni ce na yi, kana son fruit salad sosai ne halan?"
Maleek Ado da ke jin tasirin idanunta da kallon da ta yi masa na huda zuciyarsa, sai ya yi
gaggawar matso da ita zuwa jikinsa ya ce, "Yes wife! Ina son sa sosai but ban taɓa shan haɗin da
ya yi daɗi kamar wannan ba, ashe dai da gaske Hajjah ta ke yi da ta ce chef ce ke."
Yana maganar ne yana cigaba da shan haɗin fruit salad ɗin,wanda daɗinsa ke ratsa har kwanyarsa,
TAIMIYYAH da ta lafe daga ɓarin jikinsa na dama sai ta kwantar da kanta a kafaɗunsa,murya can
ƙasa ta ce, "Zan dai zama chef ɗin In Sha Allah Hubby."
Maleek ya ɗago kansa yana kai hannu ya ɗago fuskarta tare da manna mata kiss ya ce, "I luv u my
pure zuma, ke ɗin wata kyauta ce a gareni wanda Allah ya yi min a lokacin da ban taɓa tunani ba,
ina fata mu rayu har ƙarshen numfashi wife!"
TAIMIYYAH ta lumshe idanunta wani irin zazzafar soyayyarsa na kewaye jini da jijiyoyin jikinta,
ta buɗe idanunta tana duban yadda Maleek ya zura mata ido, yana son jin ta bakinta sai ta maida
kanta ta kwantar bisa kafaɗansa, ta buɗe baki cikin wani irin salon murya ta ce, "Ameen ya hayyu
ya qayyum Hubby, i luv u too dear!"
Maleek Ado da dukkanin jikinsa ya saki da tasirin kalamanta, sai ya yi saurin janyota zuwa kan
jikinsa baki ɗaya ya na jin wani irin abu na kewaye jinin jikinsa. Wannan shi ne karon farko da ya
ji TAIMIYYAH ta furta kalmar so a zahiri zuwa garesa, hakan yasa kalaman suka shige shi
matuƙa da gaske. Sai ya haɗe fuskarsu waje guda ya shiga aika mata da wasu zafafan kisses a duk
muhallin da ya ga dama, sai da ya yi ma'ishi kafin ya saketa yana cigaba da shan fruit salad ɗinsa.
Ko minti biyar basu ƙara cikin falon ba bayan kammala cin abincin ya ɗauketa zuwa bedroom
ɗinsa, da alamu yau zuciyoyin amaren cike yake da shauƙin juna me tsanani.
Bisa bed ɗinsa ya yi mata masauki yana nufar toilet don wanko baki, lokacin da ya fito sai ita ma
TAIMIYYAH ta nufi toilet ɗin ta wanko bakinta tare da ɗauro alwala, sabida ta riga ta saba da
kwanciya da alwala, shiyasa ko tana period ne sai ta ɗaura shi kafin ta kwanta bacci. Lokacin da ta
fito har Maleek ya yi musu light off sai haske me duhu da ya bari, don haka akan idanunsa ta fito
tana takowa zuwa bakin bed ɗin ta ɗaya side ɗin. Sai da ya bari ta hawo kan gadon sosai sannan
ya rungumota zuwa jikinsa, ta sakin masa kukan shagwaɓa sai ya rufe bakinta da nasa don ya hana
kukan fitowa, hannuwansa ya kai ya fara zare kayan baccin da ke jikinta ya cillosu zuwa ƙasa,
yana me sake shigar da ita cikin jikinsa.
Daren ranar wani irin sabon shafi ne Maleek Ado ya buɗe na cin duniyarsa da tsinke, tare da rikita
zuciya da gangar jikin TAIMIYYAH. Don Wani salon soyayya ta dinga amsa daga garesa wanda
ya rikita duniyarta, tare da haifar da zazzafar soyayyar Maleek Ado a zuciyarta, Maleek kuwa har
mamakin yadda ta miƙa wuyarta ya yi, komi ya gudana a tsakaninsu tamkar ba ita ba.
___________
Kwanakin da suka biyo baya wani irin shafin luv ne ma'auratan suka buɗe na kula da juna, tare da
morewa lokacinsu tamkar babu gobe, shaƙuwa da wata irin ƙauna me ƙarfi ne ya sake wanzuwa a
tsakaninsu.
Maleek baya fita ko'ina sai can yamma sakaliya sannan ya ke fita, shi ma da zaran anyi isha'i zai
shigo gida ba zai kuma sake fita ba sai wata goben. Suhailah tuni ta wuce Abuja kamar yadda
Maleek ya buƙaci hakan, shi kuma zasu wuce da TAIMIYYAH ranar Saturday.
____________
TAIMIYYAH ta ɗaga ido ta dubi Maleek Ado wanda ya tsareta da manyan idanunsa, yana kallon
shigar da ke jikinta wanda shi ne da kansa ya zaɓar mata kayan don ta saka masa ya morewa
kallonta. Riga da wando ne na english wears masu azabar kyau, wanda suka zauna a jikinta tare da
fitar da suranta a zahiri. Rigar ƙaramace sosai me siririn hannu wuyarta a buɗe ya ke sosai, shiyasa
ƙirjinta ya bayyana sosai kamar yadda Maleek ɗin ke son gani, wandon nada faɗi daga ƙasa amma
daga sama ya ɗan tsuke tare da fiddo shape ɗin mazaunanta sosai.
"Yanzu kana nufin jibi za mu tafi tare da kai can Abujan? Amma ai nan ka ce zan zauna Habibi."
TAIMIYYAH ta yi maganar a shagwaɓe idanunta akan Maleek Ado, wanda ya sake tsareta da
manyan idanunsa yana me miskile fuskarsa, tuni kuma TAIMIYYAH ta fara sabawa da hakan. Ya
buɗe a hankali ya ce, "Haka na ce Baby but yanxu na canza ra'ayi, ba zan iya nesa da ke sosai har
in ɗauki tsayin lokaci bana jinki a jikina ba. Abuja za mu wuce zuwa jibi ina so ai miki passport,
don tare zamu wuce Cairo idan Suhailah za ta koma ganin likita."
TAIMIYYAH ta waro idanunta waje cikin tsananin mamakin kalamansa ta ce, "Tare kuma Habibi
hakan zai yiwu kuwa,ba tare da ga cewa za a shiga rayuwarta da kai sosai ba?"
Maleek ya ɗan taɓe baki yana kai hannu ya janyota zuwa jikinsa, tare da matseta tamkar zai huda
ƙirjinsa ya sanya ta ciki, hakan yasa TAIMIYYAH sakin ƙaramin ihu tana cewa , "Habibi ka
matseni da yawa fa."
Maleek ya sassauta rungumar da ya yi mata yana kai bakinsa kusa da kunninta ya ce, " Ke da ita
dukkanku mallakina ne,ni na ke da damar yin yadda na so daku, so tare na yi niyyar mu tafi don
ba zan iya barinki anan mu kuma muna can ba Baby, cox kin riga kin yiwa zuciyata wani irin
kyakykyawar riƙo, wanda ban san ta yadda zan iya koda sassautawa ba. Yau zamu yi magana da
Hajjah jibi war haka ma muna Abuja In Sha Allah wife, so sai ki fara shiri ke da dawowa zaria
babu ma rana wife."
TAIMIYYAH da zuciyarta ke cigaba da gudu da ƙaunarsa, sai ta yi saurin ɗago kanta tare da zuba
masa idanunsa ta ce, "Ba zan dawo nan kusa ba daɗewa za mu yi ne a can? Zan yi kewar Iyah
Habibi ko dai za ku tafi kai da ita ɗin, ni na fi son zama a kusa da su Iyah please!"
" Wife ba zan iya ba kada ma ki fara ɗakko wannan rigimar, Hajjah ma haƙuri za ta yi dukanku
ɗauke ku zan yi daga zaria. Ko dai ki zauna Abuja Suhailah ta koma Lagos, ko ke ki wuce Lagos
ita tana Abuja dole cikin biyu za a yi ɗaya, but ina ga ke ce za ki zauna Abuja sabida Baze na ke so
ki shiga soon, da zaran kin yi Jamb kin samu makin da ake buƙata, wani course ki ke buƙatar
karantawa Baby ?"
Maleek ya ƙare maganar da tambayar TAIMIYYAH, wacce jin zancen cigaban karatunta ya
faranta zuciyarta, ta sake ƙwakumewa a jikinsa tana jin wani ƙaunarsa na narke zuciyarta, cike da
zallar farin ciki ta ce, "Medicine ko Law Hubby."
Maleek ya saki smile ya ce, "Baby ki karanta Medicine ɗin dai ba Law ba."
TAIMIYYAH ta ɗago kanta karon farko da ta haɗe fuskarta da tasa, tare da haɗe bakinta da nasa ta
fara aika masa zafafan kisses. Maleek ya sake rungumeta da kyau yana amsar salon kiss ɗin da
TAIMIYYAH ke bashi. Ita da kanta sai da lamura suka fara nisa a tsakaninsu sannan kunyar kanta
ya kamata, shi ko Maleek gaba ki ɗaya ta gama susuta shi, tare da birkita duk wani lissafinsa da
salonta, wanda bai taɓa tunanin ta iya shi ba. Idanun TAIMIYYAH suka raina fata lokacin da
Maleek ya yi mata masauki a bed ɗinsa, tare da fara aika mata da nasa salon, wanda ta san
sakamakon da zai biyo bayan hakan.
________
*Gonar Ganye.*
Maleek Ado da Hajjah ne zaune suna tattaunawa, idanunta akan Maleek ɗin ta ke dubansa da
murmushi a samar fuskarta, sai ya ɗauke idanunsa daga kanta ya fara magana a natse yana cewa,
"Hajjah tare da Zaynab na ke so mu wuce Abuja, don ina so ta yi International Passport sabida tare
na ke so mu wuce Egypt ,nan da sati biyu masu zuwa tare da Suhailah. Sai magana na biyu Hajjah,
ina so Zaynab ta koma Abuja sabida skull ɗinta, Baze na ke so ta yi ita Suhailah sai mu wuce
Lagos da ita, sai ya kasance weekend ina Abuja tare da Zaynab. Sai dai mu dinga zuwa duba ku
lokaci bayan lokaci Hajjah, don Allah ki yi min wannan alfarmar kar ki ce sai Zaynab ta zauna
anan."
Yadda Maleek Ado ya kai ƙarshen maganar cike da magiya, ya sanya Hajjah dubansa tana sakin
murmushi me faɗi, kafin ta buɗe baki ta ce, "Maleek kai ke da iko da matanka ai, Allah yasa
hakan ya zama alkhairy kuma idan har kana ganin babu matsala a tafiya da su can Egypt ɗin, su
biyu sai in ce Allah kiyaye muku hanya, ka kula da yin adalci a tsakaninsu Maleek, don gujewa
faɗawa cikin halaka. Na ji daɗin yadda ba ka manta da alƙawarin da aka yi akan cigaban karatunta
ba, don Zaynab tana da buri sosai akan ta yi karatu, kuma ni da kaina na yi mata alƙawarin cewa
za ka barta ta cika burinta. Allah ya haɗa kansu da Suhailah ya baku zama lafiya da kwanciyar
hankali tare da zuriyyah masu albarka."
Maleek da ya ji daɗin addu'ar Hajjah ya amsa da cewa, "Ameen ya hayyu ya qayyum Hajjah,Allah
ya ja kwana ya barmu tare da ku har ƙarshan numfashi."
Hajjah ta amsa da cewa, "Ameen, ina fata zuwa gobe za ka kai ta tayi sallama da Iyah?"
"Eh ina ga ma yau zuwa dare idan na koma za mu je, gobe sai ta yini anan ɗin sabida jibi da wuri
Yusuf zai kai mu Kano, za mu bi flight kawai zuwa Abuja."
Hajjah ta jinjina kai cike da gamsuwa suka cigaba da tattauna muhimman lamura, kafin Maleek ya
yi sallama da ita ya baro gidan misalin shida na yamma...........✍🏻
#Ɗansabo ce#
[12/15, 11:46 AM] +234 703 040 9541: Littafin TAIMIYYAH paid book ne,ga duk wanda ta
tsincesa a kowani irin group ne,kiji tsoran Allah karki karanta sai kin biya 500 naira only.
Za ku iya min magana ta wannan number ɗin 08167768704, ko kuma ku turo kuɗin ku kai tsaye ta
wannan account ɗin 0504192664 aisha ibrahim dansabo GTbank.*
Masu turo credit za ku turo katin MTN na 500 ta wannan line ɗin 08167768704.
_Ina ƴan kasuwa masu buƙatar a tallata muku hajar ku? Maza ku garzayo da kuɗi ƙalilan a tallata
muku kayan siyarwanku sai dai kawai ku ji ana kiran waya don buƙatan sayan kayan ku,ku
tuntuɓeni ta layina kamar haka 08167768704._
*78*
Lokacin da ya koma can GRA ya samu TAIMIYYAH ta yi baƙi, Zee ne ta rako Mamarta ganin
ɗaki,bayan sun gaisa da Maleek sai ya wuce zuwa upstairs.
Mamar Zee ganin shigowar Maleek ya sanyata tashi, ta ce da Zee su wuce kawai tunda magriba
ma ta kusa, TAIMIYYAH ta haura zuwa sama ta buɗe a kwatin lefenta na kayan shafa, ta samarwa
Mamarsu Zee sabulai da turare ta sanya a leda ta sakko zuwa downstairs ɗin.
"Zee ga shi ki riƙewa Mum, na gode ƙwarai da ziyara Allah ya bar zumunci."
TAIMIYYAH ta yi maganar tana miƙawa Zee ledar da ke hannunta, tuni ita Mum ɗin har ta yi
gaba ta fice daga falon. Zee ta amshi ledar ta yi godia suna jerawa da TAIMIYYAH har zuwa
wajen compound, in da driver ɗin su Zee ke jiransu.
TAIMIYYAH ta yi wa Mum ɗin godia su kai sallama ta juyo zuwa ciki, ta sanya Harirah ta
kawashe kayan cimar da aka cika gaban su Zee da shi, ita kuma TAIMIYYAH ta wuce zuwa sama.
TAIMIYYAH ta yi maganar tana zama kusa da Maleek, wanda ke zaune bisa Sofan da ke ɗakinsa,
System ne a gabansa ya buɗe yana duba wasu ayyuka.
Ya ɗago manyan idanunsa ya sauke akan TAIMIYYAH,wacce ke fitar da wani sassayar ƙamshi
daga jikinta, kafin ya buɗe baki a hankali ya ce, "Lafiya lau tana gaishe ki."
TAIMIYYAH ta saki smile ta ce, "Ina amsawa Habibi, yaushe za ka kai ni wajensu ita da Iyah?"
Maleek ya zuba mata ido yana wani taɓe baki ya ce, "Anjima za mu wajen Iyah, Hajjah kuma yini
zamu yi mata gobe a can gida."
A bazata ya ji TAIMIYYAH ta rungumeshi tare da bashi kiss a forehead ɗinsa, ta yi magana cikin
narke murya ta ce, "Thank u Hubby, i luv u!"
Maleek Ado ya sake rungumeta da kyau a cikin jikinsa kafin ya buɗe baki ya ce, "Luv u too my
pure zuma, but tukuici babba na ke so daga gareki a daren yau, bayan mun dawo if not kuma sai a
fasa fitar."
"No please! Habibi kar ka ce haka, na yi promise zan yi maka duk abinda ka ke so."
Maleek ya saki murmushi yana ɗago fuskarta yana kasheta da wannan kallon nasa da ke narke
zuciyarta ya ce, "Really Baby?"
TAIMIYYAH ta gyaɗa kanta a kunyace tana maida fuskarta ta kwantar a jikinsa, sai ya mannata
kiss a side face ɗinta yana cigaba da Shafa System ɗinsa, ba tare da ya bata damar tashi daga cikin
jikinsa ba.
____________
*Gyallesu*
*Around 08:35pm*
Motar Maleek Ado ta faka a cikin compound ɗin gidan su TAIMIYYAH, bayan Tukur ya wangale
musu ƙofar gate ɗin sun shigo ciki.
TAIMIYYAH ta kai hannu za ta ɓalle murfin motar ta fice, amma sai ta ji a kulle ta yi saurin ɗago
manyan idanunta ta sauke akan Maleek.
Ya ɗage mata gira guda yana rigata yin magana ya ce, "Saurin me ki ke yi haka wife?"
TAIMIYYAH sai ta shagwaɓe murya ta ce, "Na ƙosa ne in ganta Habibi cox am really miss her,
please! ka buɗe min in fita Hubby."
Maleek bai yi magana ba ya buɗe lock ɗin motar yana cewa, "Wait for me Baby, tare zamu jera
okey!"
TAIMIYYAH da jikinta ke faman ɓari ta gyaɗa masa kai tana sakkowa daga cikin motar, Maleek
ya zagayo yana rufe murfin motar da bata kai ga rufewa ba, sannan ya kama hannunta na dama
suka fara takawa zuwa part ɗin Iyah.
Gaba ɗaya TAIMIYYAH duk ta ƙosa ta yi tozali da fuskar Iyah, wacce ta ke ji aranta tamkar
watanni biyar ta yi bata ganta ba, ba kwanaki biyar ba.
Suna shiga cikin part ɗin Iyah TAIMIYYAH ta ƙwace hannunta daga na Maleek tana yin gaba
tare da ƙwalla kiran, " Iyah! Iyah!"
Iyah da ke zaune tare da Babah Ladi suka jiyo muryar TAIMIYYAH kamar daga sama, sai Iyah ta
yi saurin amsa kiran tana duban Babah Ladi ta ce, "Zainabu ce fah anya lafiya kuwa?"
Kafin Babah Ladi ta ce komi TAIMIYYAH ta shigo falon fuskarta a washe, ta cigaba da takowa
har zuwa wajen da Iyah ke zaune wacce ta saki baki tana kallon TAIMIYYAH.
Wani irin kyawu ta ga TAIMIYYAH ta yi mata cikin shigar Green ɗin Abayar da ke jikinta,
fuskarta ya cika ya yi ɓul abin sha'awa sai faman glowing ta ke yi.
TAIMIYYAH ta faɗi hakan lokacin da faɗa jikin Iyah tare da rungumeta, Iyah ta saki murmushi
tana cewa, "Na bani ni Fatima wannan runguma haka kamar za ki ɓallani Zainabu, daga ina ki ke
da darennan kwana biyar da kai ki ɗakin miji?"
TAIMIYYAH ta saki Iyah har lokacin fuskarta na haskawa da farin cikin ganinta a kusa da Iyah, ta
yi magana cikin shagwaɓaɓɓiyar muryarta ta ce, "Iyah ni da shi ne fa, mun zo gaishe ku ne mu yi
muku sallama, jibi zamu wuce tare da shi Abuja, daga can kuma zamu wuce Egypt."
Iyah ta jinjina kai ta ce, "Ma Sha Allah! Amma shi ne zaki shigo ki barsa, yana ina yanzu?"
Kafin TAIMIYYAH ta ce komi suka jiyo sallamar Maleek daga bakin ƙofar shigowa falon, Babah
Ladi ne ta amsa sallamar nasa tare da bashi izinin shigowa.
Maleek ya shigo cikin falon daidai lokacin da TAIMIYYAH ta maida dubanta kan Babah Ladi
suna gaisawa, Babah Ladi ta amsa da fara'a tana cewa, "Ai kin shigo idanunki a rufe ƴar gidana,
burinki kawai ki jiki a jikin Iyah,shiyasa sam baki ma kula dani a cikin ɗakin ba."
TAIMIYYAH ta narke murya ta ce, "Sorry Babah Ladi, na yi missing ɗinku ne sosai wallahi."
Maleek da ya zube yana kwasan gaisuwa wajen Iyah sai ya kalli TAIMIYYAH, zuciyarsa na cika
da mamakin yadda ita sam shagwaɓa baya mata wuya,da alamu nature ɗinta ne hakan tunda gashi
har Babah Ladi take ma wa.
Iyah ta amsa gaisuwarsa cike da fara'a tana tambayarsa Hajjah, ya sanar mata da cewa tana lafiya.
Babah Ladi ta gaida shi ya amsa da kulawa, sai ta zame ta fice zuwa ɗakinta don ba su waje, Iyah
ta dubi TAIMIYYAH wacce ke manne da jikinta ta ce, "Zainabu maza tashi ki kawo masa lemu da
ruwa, akwai dambun nama ma a ɗaki na ki ɗakko plate ki ɗebo masa."
TAIMIYYAH ta miƙe don cika umurnin Iyah ta bar Maleek Ado da bin bayanta da kallo, yana
sake yaba kyawun da shigar Abaya ke mata a jikinta.
" Iyah mun zo muku sallama ne zamu wuce tare da ita zuwa Abuja, daga can zamu yi tafiya idan
mun dawo kuma ina ga can Abuja za ta tsaya gaba ɗaya ,sabida can na ke son samar mata
makarantar da za ta fara."
Maleek Ado ya yi maganar cike da ladabi sosai, Iyah ta dubesa ta ce, "To madallah! Ubangiji yasa
hakan shi ne mafi alkhairy, Allah ya kai ku lafiya ya dawo da ku lafiya. Sai ai ta haƙury da juna
domin zaman tare sai an yi haƙury da juna, Allah ya haɗa kanku ya baka ikon kwatanta adalci a
tsakaninsu ,Allah kuma ya yi albarka ya bada zuriyyah masu albarka."
Maleek ya sake ƙasa da kansa yana amsawa da cewa, "Ameen mun gode Iyah Allah ya ja kwana."
TAIMIYYAH da ta ratso cikin falon hannunta riƙe da tray ta amsa da cewa, "Ameen Ya Allah."
Maleek ya sauke idanunsa akanta lokacin da ta ke aje tray ɗin a gabansa, wanda ta ɗauro plate ɗin
dambun nama da lemun Chivita da table water a kai.
Bayan ta zuba masa lemun ne ta koma wajen Iyah ta zauna,tana wani nanewa da jikinta tana
faman zuba shagwaɓa, shi dai Maleek sai satan kallonta ya ke yana jifanta da wani sassanyar
kallo. Yana shanye lemun ya ɗan ci dambun naman kaɗan ya tashi ya yi ma Iyah sallama, yana aje
mata kuɗi masu yawa ya fice daga falon.
Iyah ta raka bayansa da godia da addu'an fatan alkhairy, kafin ta maido da dubanta kan
TAIMIYYAH ta fara sake kwakwkwafa mata nasiha,tare da tunasar da ita muhimmanci haƙury, da
yiwa miji biyayyah akan dukkan umurninsa matuƙar bai saɓawa mahalicci ba. Sosai TAIMIYYAH
kalaman Iyah suka ratsa kwanyarta, ta dube ta da shagwaɓa ta ce, "Yanzu Iyah shikenan zan jima
ban ganki ba sai dai waya, wallahi ji nake yi ba don ina son na yi karatu ba, da an barni anan garin
da na ji ganinki sai dai kawai in zo, amma yanzu zamu yi nesa da juna....."
TAIMIYYAH sai ta sanyawa Iyah kuka har cikin zuciyarta ta ke jin za ta yi kewarta me tsanani,
Iyah ta rungumo TAIMIYYAH zuwa jikinta tana cewa, "Miye haka Zainabu, kin zo tayar min da
hankaline ba sallama ba ko? Haƙury za ki yi shi aure ya gaji haka ya kan kai mace inda duk ba
tayi tunani ba. Don haka kada ki zama me yawan ƙorafi akan umurnin mijinki, kada ki zama me yi
masa gardama ko musu akan duk abinda ya nuna yana so, ko da ace ke bai miki ba in dai ba saɓon
Allah bane to ki danne zuciayarki ki taya shi son abin. Allah Ya yi muku albarka Zainabu ya baku
zama lafiya, ayi ta haƙury da juna ki kuma zama mace me biyayyah kada ki bani kunya Zainabu
kin ji ko?"
TAIMIYYAH ta jinjina kai tana tsaida hawayen da ke saukowa daga fuskarta ta ce, "Na gode Iyah
In Sha Allah bazan baki kunya ba."
"Yauwa Zainabuna haka nake son ji, maza tashi ki je yana jira amma ku shiga sasan Babanki Sani
yana nan ya zo ɗazu."
TAIMIYYAH sai ta miƙe tsaye tana duban Iyah da ita ma ta tashi tana nufan hanyar ɗakin
baccinta ta ce, "To Iyah bari mu je mu gaishe shi zan sake shigowa mu yi sallama ko?"
Iyah ta balla mata harara tana cewa, "Ban ce ba, kar ki sake shigowa yanzu zan juye miki ragowar
dambun naman nan ne,Ladi za ta kai muku wajen mota sai ku wuce da shi. Ba kiyi magana da
wuri bane ai da an tanadar miki wani abin kun wuce da shi."
TAIMIYYAH ta ɗan zumɓure baki ta ce, "Yanzu Iyah ko kewata ba za ki yi bane ki ke faman
korata haka? "
Iyah ta yi banza da TAIMIYYAH tana shigewa ɗakinta ta barta a tsaye, sai kawai ta dafe guiwar
ƙafarta ta nufi hanyar fita falon.
TAIMIYYAH ta yi maganar idanunta akan Maleek Ado, wanda ke jingine da jikin motarsa yana
danna waya, ya ɗago manyan idanunsa ya sauke akan TAIMIYYAH kafin ya buɗe baki ya ce,
"Alright Sweet!"
Daga haka suka jera da juna zuwa part ɗin Baba Sanin, hannunta riƙe cikin na Maleek Ado, ta
cikin part ɗin suka shiga yadda za su fara isa main-parlor na gidan.
TAIMIYYAH ta dinga ƙwalla sallama amma babu amsa, sabida babu kowa cikin falon masu aiki
kuma suna can sashinsu ba jiyo ta za su yi ba. Sai ta ɗaga manyan idanunta ta sauke akan Maleek
da ke bin falon da kallo, ta yi magana cikin sanyin murya ta ce, "Baby ina ga Umma tana can
falon Baban, bari kawai mu fita ta waje mu shiga ta can."
Maleek ya jinjina kai kawai ba tare da yace komi ba suka fito jere da juna zuwa waje, ta ƙofar
shiga falon Baba Sanin ta waje suka isa zuwa bakin ƙofar shiga falon, TAIMIYYAH ta rafsa
sallama daga waje tare da jiran a basu izinin shiga.
Baba Sani da ya jiyo murya kamar nata sai ya yi gaugawar amsa sallamar yana bada izinin
shigowa, TAIMIYYAH ta kutsa kanta cikin falon Maleek na biye da bayanta.
Umma da ke hakimce cikin seater sai ta waro idanunta waje, lokacin da tayi tozali da
kyakykyawar fuskar TAIMIYYAH, wacce fuskarta ke haskawa da wani irin smiling. Ta ɗauke
dubanta daga TAIMIYYAH ta mayar kan Maleek Ado, tana jin wani abu na matse zuciyarta.
TAIMIYYAH ta zube a gaban Baba Sani ta kwashi gaisuwa, Baba Sani ya amsa da fara'a akan
fuskarsa yana cewa, "Zainab daga ina ku ke haka, kwana biyar kacal har kin fara fitowa waje?"
TAIMIYYAH ta yi ƙasa da kanta cike da jin nauyi ta ce, "Baba Sallama ne muka zo yi muku, jibi
zamu wuce Abuja tare da shi daga can kuma za mu yi tafiya zuwa Egypt."
"To madallah! Zainab, Allah tsare hanya ya baku zaman haƙury, sai ai ta haƙury da juna kin ji ko?"
Baba Sani ya yi magana cike da fara'a akan fuskarsa, ita kuma TAIMIYYAH sai ta gyaɗa kai ta ce,
"In Sha Allah Baba."
Maleek ya tsuguna ya kwashi gaisuwa wajen Baba Sani, lokacin da ita kuma TAIMIYYAH ta
maida dubanta sashin da Umma ke zaune, wacce gaba ki ɗaya ta ji maganar fitan TAIMIYYAH
zuwa wata ƙasa tamkar saukar aradu a zuciyarta. Wani abu me nauyi ya taso ya danne ƙirjinta, da
ƙyar ta ƙaƙaro murmushin yaƙe ta ɗaura kan fuskarta, ta amsa gaisuwar TAIMIYYAH idanunta na
yawo a ilihirin jikin TAIMIYYAR, sai duban yadda TAIMIYYAR ta sake yin wani irin mugun
kyau da fresh Umma ke yi. Abayar jikinta kawai ka duba zaka san bana ƙananun kuɗi bane,ga
wani fitinannan ƙamshinsu da ya gama cika falon Baban Sanin.
Da ƙyar Umma ta iya tsayawa ta amsa gaisuwar Maleek Ado, kafin ta miƙe ta bar musu falon
zuwa ɗakinta ,domin ba za ta iya jure ganin TAIMIYYAH da Maleek Ado cikin wannan
kyakykyawar yanayin ba, wanda ke bayyana kwanciyar hankalin da TAIMIYYAH ta fara tsinta a
gidan aurenta.
Daga TAIMIYYAH har Baba Sani suka bi bayan Umma da kallo, suna rasa gano dalilinta na tashi
ta bar musu falon tamkar wata bare.
Maleek da kansa ya yi wa Baba Sani bayanin cewa TAIMIYYAH za ta koma Abuja da zama,
sabida a jami'ar Baze zai sanyata da zaran ta yi jamb, ta samu secores ɗin da ake nema.
Baba Sani ya nuna farin cikinsa sosai tare da yi musu fatan alkhairy, Maleek ya tashi ya yi masa
sallama bayan ya aje masa kuɗi daga gabansa. Baba Sani ya zare masa ido yana cewa, "Kar muyi
haka da kai Abdulmaleek, zo ka ɗauki kuɗinka."
Lokacin da TAIMIYYAH ta fito zuwa waje sai idanunta ya sauka akan Maleek Ado, wanda ke
tsaye daga can gaba kaɗan yana amsa waya. Ta dinga takawa dafe da guiwar ƙafarta har ta isa in
da ya ke tsaye, jin takunta ya sanya shi ɗago manyan idanunsa ya sauke a kanta, yana cigaba da
amsa wayarsa bayan ya miƙa mata hannunsa na hagu don ta kama. Babu musu ta miƙa masa
hannun ya riƙe suka cigaba da takawa zuwa wajen motarsa, idanun TAIMIYYAH ya sauka akan
babbar robar da Iyah ta juye musu dambun namanta. Ta saki murmushi tana duban fuskar Maleek
daidai lokacin da ya ke sauke wayarsa daga kunni, cike da zallar shagwaɓa take dubansa ta ce,
"Habibi minti biyar please! Ina so in sake yin sallama da Iyah ne"
Maleek ya zuba mata ido kafin ya ce, "Okey karki wuce time Baby kin ga dare na yi."
TAIMIYYAH ta gyaɗa kai tana nufan part ɗin Iyah, suka sake yin sallama da juna Iyah ta rakota
har wajen compound, TAIMIYYAH na faman share hawayen kewar Iyah da za ta yi, Iyah ta juya
zuwa cikin part ɗinta, ita ma zuciyarta na motsawa da wani irin yanayi me girma, don a jikinta
take jin yadda za ta yi kewar TAIMIYYARTA, sabida sam bata kawo cewa Maleek ɗin zai ɗauketa
daga Zaria nan kusa ba. TAIMIYYAH na isa wajen motar ta tadda har Maleek ya buɗe mata front
seat, yana jiran ƙarisowarta ta shiga ya maida murfin ya rufe, yana zagawa ya shiga driver seat ya
tashi motar, basu fita daga gate ɗin gidan ba sai da Maleek ya yi wa Tukur kyautan kuɗi shi ma,
sanan suka fice daga cikin gate ɗin gidan,TAIMIYYAH na sake jin zuciyarta na matsewa da kewa
me tsanani.
Daga can part ɗin Baba Sani kuwa, Umma ce ke zaune daga bakin bed ɗin ɗakin baccinta, sai
faman gwada kiran layin Hajiya Barirah take yi. Sai da ta kira sau huɗu ba a ɗaga ba sai ana biyar
ɗinne Hajiya Barirah ta ɗaga wayar, Umma ta sanya wayar a speeker lokacin da Hajiya Barirah ke
cewa,
"Lafiya Hajiya Zuwaira kira har biyar a daren nan, kin manta Oga yana gari ne halan?"
Umma ta sauke ajiyar zuciya me ƙarfi tana cewa, "Yi haƙury Hajiya Barirah hankalina ne yake a
tashe wallahi, yanzu wannan gurguwar da mijinta suka fita, wai sun zo yi ma Sani sallama za su
tafi Egypt da mijin. Ke kinga yadda ta koma a kwanaki biyar kacal Hajiya Barirah? tamkar ki taɓa
ta jini ya yi tsartuwa, wallahi da na ji sallamar shegiyar na zata wani masifar ne ya afka mata, ta
kamo hanyar gida sai da na yi tozali da fuskar dakaren mijin nata jikina ya yi sanyi. Ya zama dole
mu koma wajen Bokannan Hajiya Barirah, domin ya sake lalubowa ko da wani aikin da za a iya a
lalata wannan auren, don wannan zuƙeƙen mijin bada ita ya dace ba, sannan ga maganar ƙarin
auren Sani da har yau na kasa samo bakin zaren, duk iya bin ƙwaƙwƙwafina Barirah na kasa gano
gaskiyar lamarin."
Umma ta kai ƙarshen maganar zuciyarta na cigaba da kamawa da wutar baƙin ciki, tare da takaicin
yadda lamura ke son kwaɓe mata a rana tsaka.
Hajiya Barirah ta saki ƙaramin tsaki kafin ta ce, "Hajiya Zuwaira na sha gaya miki kin faye ci da
zuci a cikin lamuranki, shiyasa baki faye ganin nasaraba, sannan kina da muguwar hassadar da ke
hana kwanyarki aikin da ya dace. Ni fa sam haushi ki ke bani a kan yadda ki ke nuna tsana da
hassadar wannan gurguwar, bayan tun farko ke ce baki yi anfani da kwanyarki ta fannin da ya
dace ba, da yanzu ke ce zaki dinga juya lamuranta yadda ki ka ga dama. Maganar bata waya bace
Hajiya Zuwaira don ga Oga can na jirana, zan bashi abinci zan dai shigo gidan naki zuwa jibi idan
Allah ya kai mu."
Daga haka Hajiya Barirah ta yi cuting call ɗinta ba tare da ta sake bai wa Umma damar cewa komi
ba, sai Umma ta bi wayarta da kallo kanta na kullewa da maganar da Hajiya Barirah ta yi, akan
cewa wai sakacinta ne da yanzu ita ke juya lamuran TAIMIYYAH, to ta yaya? Amsar na ga Hajiya
Barirah hakan yasa Umma kai hannu ta dafe saitin zuciyarta, wanda ke faman bugawa da sauri-
sauri. Tana shirin tashi ta koma zuwa falon Baba Sani kiran Zuhurah ya shigo cikin wayarta, sai ta
sake gyara kwanciya tana receving call ɗin ta kai kunni........✍🏻
"Ɗansabo ce#
[12/15, 11:46 AM] +234 703 040 9541: Littafin TAIMIYYAH paid book ne,ga duk wanda ta
tsincesa a kowani irin group ne,kiji tsoran Allah karki karanta sai kin biya 500 naira only.
Za ku iya min magana ta wannan number ɗin 08167768704, ko kuma ku turo kuɗin ku kai tsaye ta
wannan account ɗin 0504192664 aisha ibrahim dansabo GTbank.*
Masu turo credit za ku turo katin MTN na 500 ta wannan line ɗin 08167768704.
_Ina ƴan kasuwa masu buƙatar a tallata muku hajar ku? Maza ku garzayo da kuɗi ƙalilan a tallata
muku kayan siyarwanku sai dai kawai ku ji ana kiran waya don buƙatan sayan kayan ku,ku
tuntuɓeni ta layina kamar haka 08167768704._
*79*
Tunda Umma ta ji muryar Zuhrah cikin kuka sai ta yi gaggawar sanya wayar a speeker ƙirjinta na
faman dokawa, Zuhurah cikin muryar kuka ta ce, "Umma ina cikin wani hali, ashe Ameeru
mashayi ne ban sani ba, kwanaki uku kenan kullum a buge ya ke shigomin ya yi mankas da giya.
Sannan Umma ashe shi ba yaron Honourable ɗin bane ma, ɗan me aikin gidan ne da ta rasu.
Wallahi bazan iya zama da mashayi yana duka na ba Umma......"
Zuhurah ta sake rushewa da kuka, dama kuma cikin kukan duk ta zayyano wa Umma wannan
jawabin, Umma da ta yi kasaƙe tana sauraren Zuhurah sai ta ji tamkar zuciyarta bugawa za ta yi,
sabida yadda ta ke jin ƙirjinta na mata nauyi da ƙuna. Ta buɗe baki cikin zallar kaɗuwa da tashin
hankali ta ce, "Zuhurah ki dubi girman Allah ki tsaida kukan nan ki min cikakken bayani, ban
gane cewa Ameeru ba ɗan Honourable bane ɗan me aiki ne, in ji wani shegen? Sannan maganar
shaye-shaye ana raba ƴaƴan manya da shaye-shaye ne Zuhrah? Matuƙar akwai kaya hakanan ake
daurewa, za ki saba da yanayin ki kuma san yadda za ki dinga tarairayarsa a hakan, har a samu
abin ya yi sauƙi ya daina shigo miki a bugen."
Zuhurah sai ta sake rushewa Umma da kuka cikin kukan ta ke faɗin, "Wallahi Umma ba zan iya
rayuwa da mashayi kuma ɗan me aikin gida ba, haba faɗuwar sai ta yi yawa Umma yaron me
boyi-boyine fa, shi mahaifiyarsa amintacciyar me aikin uwargidan Honourable ɗin ce, shine ta
rasu a nan garin cikin gidan Honourable ɗin ,ta bar Ameeru tun yana ƙarami shine Hajiya Aynah ta
riƙe shi har girma, ba tare da sun san ma cikakken asalin Ameerun da in da gidan ubansa ya ke
ba."
Zuhurah ta kai ƙarshen maganar tana sake sakin kuka me motsa zuciya, Umma ta saki salati tana
sake jin duniyar na mata ƙunci. Ta buɗe baki cikin kiɗima ta ce, "Zuhurah duk wa ya sanar da ke
hakan, bayan iya binciken da aka yi ba a gano hakan ba kafin auren?"
"Wallahi Umma ɓoyewa aka yi shiyasa ake cewa bincike ya yi wuya a wannan zamanin, ita
Hajiyar da ta riƙesan da bakinta ta sanar min da hakan, sabida na yi zaton mahaifiyarsa ce kamar
yadda ake nunawa, na kirata a waya na sanar da ita halin da na ke ciki da Ameeru, akan shigowa
gida a buge da yake yi, shine jiya ta zo har nan gida ta buɗe min komi, tana cewa in yi haƙury
watarana zai daina shaye-shayen, wallahi Umma ba zan iya jura ba. Yanzu haka gayi can a falo ya
yi mankas daga yin magana ya kai min mari, shi ne na gudo na kulle kaina a ɗaki muna wannan
wayar, ta ya zan iya zama da ɗan me aikin gida kuma a matsayin ɗan shawu? Wallahi ba zan
zauna ba."
Umma da ke ji zuciyarta tamkar za ta kama da wuta, ta saki wata uwar ashar ta ce, "Amma
wannan yaron ya yaudare mu, shi ma kuma Honourable ɗin da uwar riƙon nasa duk sun
yaudaremu, in ba haka ba meyasa ba su faɗi cewa ba ɗan cikinsu bane? Yanzu Zuhurah da ki ke
faɗin ba za ki zauna ba, dawowa za ki yi ai mana dariya a samu a bakin duniya, ana cewa kwana
kaza da aure har kin fito ? Alhali ga waccar musakar can ta samu duniya ƙasarma za su bari,yanzu
bada jimawa ba ta zo yi wa munafukar kakarku da Baba Sani sallama, kin ga yadda ta koma cikin
kwanaki biyar kacal Zuhurah? Don Allah kar ki yi gaggawar ɓallo wannan auren ki dawo min gida
maƙiya su yi mana dariya, tun da dai mu kaɗai muka san hakan duk dangi a matsayin ɗan tsohon
ɗan majalisa suka san sa, a bar zancen a hakan ki yi haƙury mu ga abinda zai yiwu a gaba, amma
kar ki ce za ki dawo Zuhurah."
Umma ta kai ƙarshen maganar cike da magiya zuciyarta na sake ɗaukar zafi, da yi mata nauyi
tamkar an ɗaura bulu, Zuhurah ta sake rushewa da kuka ta ce, "Umma yanzu kin gwammace
rayuwata ta lalace sabida gudun kar ai mana dariya? To ni wallahi ba zan iya cigaba da zama da
Ameeru, alhali na gano cewa shi ɗin bakomi bane face ɗan fafa da cin arziƙi, ga shi mashayi so ki
ke in cigaba da zama da shi a hakan, yana shawo giya yana shigo min gida a buge, in yi masifa ya
hau ni da duka sannan ya kwanta dani ? Ba zan taɓa iyawa ba Umma wallahi ba zan lalata
rayuwata sabida gudun dariyar mutane ba."
Daga haka Zuhurah ta kashe wayarta ta bar Umma na rushewa da kuka, zuciyarta na cigaba da
shiga ƙunci da tashin hankali mara misaltuwa. Duk yadda ta rintse idanunta, fuskar TAIMIYYAH
da A.Maleek Ado ta ke gani suna gilma mata, cikin shiga ta alfarma da kyawun yanayin da ke
tabbatar da cewa, suna cikin kwanciyar hankali da jin shauƙin juna.
Ta saki kuka me sauti tana saurin kai hannu ta dafe bakinta,gaba ki ɗaya duniyar ta yi mata wani
irin ƙunci. Da wanne za ta ji ne wai? Irin wannan masifu da ke shirin biyota bi da bi, ga maganar
auren Sani da ta kasa shinshino komi game da batun, yanzu kuma ga Zuhurah na shirin ɓallo wani
ruwar. Umma sai ta sake sakin kuka tana tunanin yadda maƙiya za su yi musu dariya, to ko ita
Basmah a wani hali take? Tunanin ya haska cikin kanta sai ta yi saurin tashi ta janyo wayarta. Har
ta danno lambar Basmah don kiranta amma sai wani irin tsoro da fargaban abinda za ta ji ya kama
zuciyarta, ta yi jifa da wayar akan gado tana sake jin wani ɗaci na mamaye zuciyarta. Muryar
Baba Sani da ta jiyo daga falo yana kiranta, ya sanya ta saurin dira daga gadon ta faɗa toilet ta
kulle, don bata so ya ganta a wannan yanayin ya tambayi ba'asin kukan da take yi,sabida ba za ta
iya sanar da shi zancen Zuhurah a yanzu ba.
Ko da ya shigo bedroom ɗin yana kiran sunanta sai ya jiyo gyaran muryarta daga cikin toilet,
hakan yasa shi juyawa ya fice daga ɗakin baki ɗaya.
Umma na jin fitarsa ta yi saurin wanko fuska ta fito daga toilet ɗin, ta nufi wajen kayanta ta zaro
rigar bacci me santsi ta sanya tare da gyara fuskarta, ta bulbula turare ta fito ta nufi ɓangaren Baba
Sani zuciyarta har lokacin na cikin garari.
____________
Washegary kamar yadda A. Maleek ya sanarwa TAIMIYYAH cewa gidan Hajjah za su yini, hakan
ce ta kasance tun 11:30am suka nufi gidan Hajjah tare da masu aikinta su Harirah, waɗanda zu su
zauna a wajen Hajjah har zuwa lokacin da TAIMIYYAH za su dawo daga tafiyar da za su yi, sai a
tura mata su can Abuja .
Kusan duk tare da shi aka yi yinin yana takurawa TAIMIYYAH da salonsa, ko kunyar idanun
Hajjah ma baya ji, sai da ya fita sallar la'asar ne ya wuce cikin gari can Fam House ɗinsu.
Bai dawo gidan Hajjah ya ɗauki su TAIMIYYAH ba sai bayan Magriba, lokacin da ya shigo ya
samu TAIMIYYAH har ta kintsa shi kawai suke jira. Hajjah ta so su tsaya su yi dinner amma sai
Maleek ya ce a zuba musu su wuce da shi, hakan yasa Hajjah sanya Babah Rabi zuba musu
abincin cikin coolers, aka jere coolers ɗin cikin basket ɗin ɗaukar abinci, su Harirah suka fita da
shi zuwa wajen motar Maleek Ado.
Hajjah ta rako su har wajen compound suna sake sallama da TAIMIYYAH, wacce Hajjah ke sake
jin ƙaunarta me tsanani na sake zama a zuciyarta.
Lokacin da suka isa gida TAIMIYYAH direct upstairs wuce zuwa ɗakinta, ta cire kayan jikinta ta
nufi bathroom don watsa ruwa, lokacin da ta fito a gaggauce ta shirya cikin wata ƙaramar riga na
bacci, wanda tsayin rigar iyakansa cinyarta, tana fesa turare Maleek ya shigo cikin ɗakin, yana
sanye cikin fararen Pajamas da alamu shi ma har ya watsa ruwa ya kintsa kenan.
TAIMIYYAH ta ɗago ta yi masa kallo ɗaya tana ɗauke idanunta daga garesa, lokacin da ya cigaba
da takowa zuwa wajen mirrow ɗin. Ya kai hannu ya amshi Band ɗin da ke hannunta tana ƙoƙarin
ɗaure sassalkan gashinta, ya ɗaure mata da kansa irin yadda ya ke so, ya juyo da ita suna fuskanta
juna, idanunsa gaba ɗaya ya zubesu akan ƙirjinta da bata sanya Bra ba, yana jin wani abu na motsa
zuciyarsa. A hankali ya kai bakinsa ya yi kissing wajen kafin ya zagaye hannuwansa akan ƙugunta
yana cewa, "Zaynabb u look so sexy, rigar ta yi miki kyau Baby. Oya let's go ki bani abinci am
feeling hungry Sweet."
Ya kai ƙarshen maganar yana manna mata kiss a goshi, yana riƙe da hannunta suka fito zuwa falo
ta yi serving ɗinsu abincin, suka ciyar da juna cike da shauƙi Maleek sai faman narke mata ya ke
yi da salonsa,wanda ta tabbatar da cewa yau a kwai rigima kenan.
Suna kammala cin abincin ko minti goma bai bari sun ƙara ba a cikin falon, ya janyeta zuwa
bedroom ɗinsa, ita ce ta kammala shirya masa kayansa da za su wuce da shi. Don ita tun safe ta
gama shirya duk abinda za ta wuce da su, sabida ya sanar mata cewa fitan safe zasu yi a goben,
shiyasa ta kintsa komi tun kafin su fita zuwa gidan Hajjah.
Sai da ta kammala kintsa masa komi sannan ya yi musu light off suka kwanta, yana me janyota
zuwa jikinsa, TAIMIYYAH ta fara zuba masa shagwaɓar da ke sake kunna zuciyarsa a kanta,aiko
nan da nan A.Maleek ya fara aika mata da zafafan saƙonninsa, kuma cikin tsananin mamakinsa sai
TAIMIYYAH ta fara maida masa da martani, cikin salon da shi ɗin ne ya ke karantar da ita hakan.
Ya gigice tare da sake haukacewa wajen nuna mata zallar ƙaunar da ya ke mata me wuyan fassara,
wani irin dare ne da Maleek Ado ya sanya shi cikin kundin tarihin dararen da bazai taɓa mantawa
da su ba, sabida TAIMIYYAH ta susuta zuciyarsa tare da sake dilmiya zuciyar cikin ƙaunarta da
soyayyarta da bai da iyaka. Ya dinga ji a zuciyarsa cewa ba zai taɓa iya rayuwa ba tare da
TAIMIYYAH ba, sabida ita ɗin wata kyauta ce da Ubangiji ya yi masa ba tare da ya taɓa tunani
ba.
Washegary ƙarfe takwas daidai suka bar Zaria cikin ƙatuwar motar Maleek Ado, Yusuf driver ke
jan motar yayin da TAIMIYYAH da Maleek Ado ke back seat manne da juna.
Suna isa Kano bai fi da 30minutes ba jirginsu ya tashi zuwa Abuja, Yusuf sai ya juyo da motar
Zaria ya aje a gidan Maleek kamar yadda ya saba.
________
*Abuja.*
Suna sauka a Airport ɗin Abuja TAIMIYYAH ta dinga jin wani irin fargaba na kama zuciyarta,
sabida bata san irin tarban da za ta samu daga wajen Suhailah ba.
A hankali ta ke biye da Maleek Ado wanda ke riƙe da hannunta, tuni ɗaya daga cikin drivers ɗinsu
da ke nan Abuja har ya iso don ɗaukarsu, shi ne kuma ya ke janye da Luggage ɗinsu zuwa wajen
motar Maleek ɗin, wanda ita yafi hawa idan ya shigo Abuja.
TAIMIYYAH na manne jikin Maleek Ado a cikin motar, yana faman shafa kanta da yi mata
magana, amma sam ita hankalinta na ga yadda za ta yi ido huɗu da matarsa ne. Ya ɗago fuskarta
ya tsura mata ido ya ce, "Wife are okey kuwa? Na ji kin yi shiru baki ko iya magana ne, kina jin
yunwa ko? Ki yi haƙury soon za mu isa gida breakfast na juran mu a can."
TAIMIYYAH ta dubesa tana ɗan sake shagwaɓe fuska ta ce, "Lafiya lau Hubby kawai kaina ke
ciwo, ga ɗan tsoran da na ji na hawan jirgi cox wannan shi ne karo na farko da na fara shiga
flight."
Maleek sai ya murmusa kaɗan yana shafa bayanta ya ce, "Ga shi kuma kin fara hawa kenan baki
san ranar dainawa ba, tunda za ki dinga raka mijinki duk inda ya yi muradi idan buƙatar hakan ya
taso."
TAIMIYYAH ta kwantar da kanta a ƙirjinsa tana sake shagwaɓe murya ta ce, "Gaskiya ni dai na ji
bana son hawa jirgin ma, dama haka ake ji shi ne wasu ke maida hawansa kamar wani abin
birgewa? Ni kam gwara in yi ta hawa mota babu ruwana da wani jirgi."
Maleek ya saki murmushi yana jin wani ƙaunarta me yawa a ransa, ya sanya hannunsa ya lakace
face ɗinta ya ce, "Ni dai na faɗi miki ki ajiye tsoran a gefe, flight yanzu ki ka fara hawansa."
TAIMIYYAH sai ta yi shiru bata sake cewa komi ,ba har lokacin kuma rabin jikinta na manne
dana Maleek ne, wanda ke faman kai hannunsa muhallin da ya ga dama a jikinta, don ma
doguwar riga ce a jikinta na wani lace mara nauyi, ɗinkin kuma highneck ne babu yadda zai yi,ya
iya sanya hannunsa cikin rigarta shiyasa ya ke ta faman shafa saman ƙirjinta, wanda ya sake cika
sosai a kwanaki bakwai ɗinnan na amarcinsu.
Sun iso gidansa da ake Asokoro TAIMIYYAH na faman yaba kyawun garin, musamman wannan
anguwar da ko ba a faɗi mata ta san mallakar gidaje a wajen sai manyan attajiran da suka tara.
Bata sake sakankacewa ba sai da driver ya tsaida motar a bakin gate ɗin wani haɗaɗɗan gida,
wanda duk rukunin estate ɗin ginaginen gidajen suka tafi iri ɗaya sak, sai dai daga ciki girma ko
tsaruwarsu su bambanta da juna.
Mai gadi ne ya buɗe gate ɗin driver ya danna hancin motar zuwa ciki, TAIMIYYAH ta dinga bin
tsaruwar ƙaton compound ɗin da kallo har suka isa parking space, driver ɗin ya tsaida motar yana
saurin fitowa don buɗewa ubangidansu murfin motar ta side ɗinsa. Maleek Ado ya zuro ƙafafunsa
waje ya fito daga cikin motar, yana zagawa ya buɗewa TAIMIYYAH ɓangarenta ta fito, ya miƙa
hannu ya riƙo hannunta suka fara takawa zuwa wajen entrance na shiga gidan.
Daga cikin gidan kuwa Suhailah da ke tsaye jikin window ɗin ɗakin baccinta, ta yi saurin sakin
labulen da ta riƙe tana jin wani abu me nauyi na danne zuciyarta. Akan idanunta Maleek da
TAIMIYYAH suka fara takowa jere da juna, sabida tunda ta ji tsayuwar mota a cikin compound
ɗin ta gane su ne suka iso, shiyasa ta miƙe ta isa ga tagan da mutum ke iya kallon komi da ke
wanzuwa a wajen compound ɗin gidan ta sama ta yi tsaye a wajen tana hangensu.
Ta taka a hankali ta dawo wajen mirrow ta yi tsaye tana sake ƙarewa kanta kallo, tana sanye ne
cikin wasu riga da skat na Atamfar Embilished, ɗinkin ya zauna a jikinta tare da fito da shape
ɗinta, kamar yadda fuskarta da ta sha light make-up ke bayyana kyawun da ta yi. Ta sake ɗaukar
kwalbar turaren MISS DIOR ta fesa a jikinta, tana me aje kwalbar ta fito cikin sassarfa, da
bibbiyu ta dinga haɗe stairs ɗin benen tana sakkowa har ta ƙariso zuwa ƙasa.
Ta nufi wajen ƙofar shigowa falon da ke downstairs ɗin, jin ana knociking wanda ta tabbatar da
cewa A.Maleek ne, sai da ta karanto addu'ar Allahummah laah sahlan! Sannan ta yi ƙarfin halin
buɗe ƙofar, tana sake aro dakiya da jarumta ta azawa kanta. Idanunta akan fuskar A.Maleek ya
fara sauka kafin kyakykyawar fuskar TAIMIYYAH ya bayyana a idanunta, wacce ke daga gefensa
jikinsu na gugar jun, Suhailah sai ta yi gaggawar ɗauke idanunta daga kan TAIMIYYAH, tana
mayarwa kan A.Maleek da idanunsa ke kanta. Sai ta sakar masa murmushi tana ƙarisawa ta
rungumeshi ta ce, "Welcome my Maleek, sannunku da zuwa."
Maleek Ado ya sakar mata smile yana sake rungumarta ya ce, "Thank u wife!" Daga haka ya sake
ta yana sanya kansa cikin falon, bayan ya maida dubansa kan TAIMIYYAH da ta daskare a tsaye,
zuciyarta na faman bugawa da wani irin yanayin da ba za ta iya misaltawa ba. Suhailah tuni ta yi
gaba zuwa ciki hakan yasa Maleek dakatawa har TAIMIYYAH ta ƙarisa shigowa, suka jera da
juna zuwa cikin tanƙasheshen falon, wanda tsaruwarsa ya gama tafiya da zuciyarta sosai, sabida
babu ƙarya gidan ya haɗu matuƙa.
"Wife sannu ko! Bari ki isa ciki ki watsa ruwa sai ki fito mu yi breakfast ko?"
Maleek ya waiwaya ya dubi Suhailah da ke tsaye daga can bakin stairs, da alamu ƙarisowarsa
wajen ta ke jira su haura zuwa sama ya ce, "Suhailah come please!"
Suhailah ta tako xuwa cikin falon tana ƙin duban side ɗin da TAIMIYYAH ke zaune, don wani
mahaukacin kishinta take ji na sake sukar zuciyarta.
Suhailah ta tsuke fuska jin sunan da ya kira TAIMIYYAH da shi, sai ta gyaɗa masa kai tana cewa,
"Eh an gyara ko'ina can ma upstairs na sanya an sake gyara single room ɗinnan."
Daga haka ya maida dubansa kan TAIMIYYAH ya ce, "Sweet oya let's go."
TAIMIYYAH ta miƙe tare da dafe guiwar ƙafarta ta fara takawa zuwa wajen da Maleek ke tsaye,
har sun fara tafiya don zuwa ɗaya daga cikin bedrooms ɗin da ke downstairs ɗin, TAIMIYYAH ta
tuna cewa bata gaida Suhailah ba, sai ta zame hannunta daga na Maleek,tana me waiwayawa ta
sauke idanunta akan Suhailah, wacce idanunta ke kan su fes sai buɗe baki ta ce,
TAIMIYYAH ta furta hakan tana me ɗauke idanunta daga kallon Suhailah, wacce ke bin ta da
wani mugun kallo. Suhailah ta wani taɓe baki kafin ta amsa gaisuwar a taƙaice ta ce, "Lafiya lau."
Daga haka TAIMIYYAH ta juya zuwa wajen A. Maleek suka nufi ɗakin da zuciyarsa ya bashi ya
zaɓar mata, cikin jerin 3 bedroom ɗin da ke downstairs ɗin.
Komi na cikin ɗakin pink and white ne hatta cottens ɗin da aka sanya a ɗakin kalar su kenan,
ɗakin ya yi wa TAIMIYYAH kyau sosai sai tashin ƙamshin turaren wuta ka ke ji.
Maleek ya juya ya fice daga ɗakin bayan ya nuna mata hanyar corridor ɗin da zai sada ta da
bathroom, TAIMIYYAH ta bi bayansa da ido tana jin wani abu me girma game da shi na sake
danne zuciyarta.
A hankali ta ke takawa zuwa cikin bathroom ɗin, ta shiga ƙare ma ko'ina kallo da yaba tsaruwarsa,
kafin ta fara cire kayan jikinta don yin wankan.
Ta fito ta tadda Luggage ɗinta jera daga gefe guda na ɗakin, hakan ya bata tabbacin Maleek ne ya
shigo mata da su.
Cikin lokaci kaɗan ta gama shirya kanta cikin wata simple boubou na material mara nauyi, ta
shafa powder a fuskarta tare da gogo lipstick kaɗan kalar red da ya haske farar fuskarta,yanayin
yadda bakin ya sake zama cute dole ya baka sha'awa. Tana cikin fesa turarenta bayan ta murza
haɗaɗɗiyar humrarta daga ciki, wayarta ya ɗauki tsuwwa! Tone ɗin kawai ya sanar da cewa
Maleek ne.
Bata ƙarisa abinda take son faɗi ba ta ji Maleek ya yi cuting call, sai ta taɓe baki tana sake
shagwaɓe fuskarta tamkar tana gabansa. Ko minti biyu ba a rufa sai ganin Maleek ta yi ya shigo
cikin ɗakin, fuskarnan a miskile babu alamun fara'a ko kaɗan. Ta sauke idanunta ƙasa bayan ta yi
mai kallo ɗaya sabida yadda ta ga babu alamun wasa a fuskarsa, Maleek ya aika mata wani kallo
kafin ya yi magana a miskile ya ce, "Sweet wuce mu je."
Babu musu TAIMIYYAH ta miƙe tana me zumɓuro baki kaɗan,wanda hakan da ta yi baƙaramin
kunna zuciyar Maleek ya yi ba. Ya yi saurin riƙota tare da rungumota zuwa jikinsa, ƙamshinta na
sake dukan hancinsa da narkar da zuciyarsa, TAIMIYYAH ta narke a jikinsa tare da shagwaɓe
murya ta ce "Habibi ni nafi so na ci abincin a nan."
Cewar A.Maleek yana ɗago fuskarta ya zurawa cute lips ɗinta ido, kafin ya kai bakinsa ya haɗe da
nata yana laluban harshenta. Sai da ya shanye jan bakin tas sannan ya sake ta, yana riƙe da
hannunta suka fito falon, TAIMIYYAH na jin zuciyarta na raurawa lokacin da ta hango Suhailah
da ke kame a ɗaya daga cikin kujerun dining ɗin.
Sai da Maleek ya zaunar da TAIMIYYAH a seat ɗin da ke gefensa, kafin ya ja kujera ya zauna, sai
ya zamana sun sanya shi a tsakiya kenan. Suhailah ita ce ta yi serving Maleek ta turo plate ɗin
zuwa gabansa, tana me ɗago ido ta sauke akan TAIMIYYAH wacce kyawunta ke ƙona zuciyar
Suhailah, da sanya ta jin kishinta me tsanani na danne zuciyarta.
Ta furtawa TAIMIYYAH hakan tana gyara zamarta, tare da duban fuskar Maleek wanda ya sake
haɗe girar sama da ta ƙasa, kafin ya tsare Suhailah da ido yana son ganin iyakar gudun ruwarta.
TAIMIYYAH da maganar sam ba tai mata ba sai ta kasa ko da motsawa, don a tunaninta Suhailah
za ta yi serving ɗinsu gaba ɗaya ne a matsayinta na baƙuwa da ta zo yau. Maleek da shi ma abinda
Suhailah tayi ya ƙona zuciyarsa sai bai ce komi ba, ya turawa TAIMIYYAH plate ɗin da Suhailah
ta yi serving ɗinsa chips, yana miƙa hannu ya janyo wani plate ɗin don serving kansa. Ganin
hakan yasa Suhailah kai hannu za ta matso da plate ɗin gabanta, amma wani kallo da Maleek ya
aika mata ya sanya ta janye hannunta, tana jin wani ɓacin rai da tsanar TAIMIYYAH da ta kutso
cikin rayuwarsu na ƙona ranta.
A sanyaye TAIMIYYAH ta dinga cusa chips ɗin tana korawa da ruwan milon da Maleek da kansa
ya haɗa mata, tana ji gaba ɗaya zaman dining ɗin ya yi mata ƙunci, don duk duban da za ta yi wa
ɓangaren da Suhailah ke zaune,sai ta ga irin kallon tsanar da take jefo mata.
"Hubby am okey, zani na ɗan kwanta please!"
TAIMIYYAH ta yi maganar cike da zallar shagwaɓar da tasan yana kunna zuciyar Maleek Ado,
Maleek da idanunsa ke kanta yana tuhumanta akan don me zai sa ta tashi bata ci wani abin kirki
ba, sai ya sake manna idanunsa akan fuskarta ya ce, "But Baby baki ci da yawa ba fa, ko kina
buƙatar wani abin ne bayan wannan?"
TAIMIYYAH ta yi saurin gyaɗa kai tana sake narke masa da shagwaɓa ta ce, "Bana buƙatar komi,
kawai kwanciya na ke son yi na ƙoshi Habibi."
Daga haka TAIMIYYAH ta dafe ƙafarta ta fara takawa don baro dining area ɗin, Suhailah da
Maleek suka rakata da ido A.Maleek ɗin na jin wani abu na taɓa zuciyarsa. Ita ko Suhailah wani
azababben kishin TAIMIYYAH da mamakin salon shagwaɓarta,wanda ta fahimci yana tasiri sosai
akan Maleek ɗinta, ya dinga ƙona zuciyarta.
Ita TAIMIYYAH lokacin da ta isa masaukinta kwanciya ta yi da gasken , tana jin wani irin kewar
gida dana Iyah na lulluɓe zuciyarta . Sai ta ɗaga wayarta ta kira layin Iyah suka daɗe suna magana,
tana sanar da Iyah cewa sun iso Abujan bada jimawa can ba. Bayan sun yi sallama da juna sai ta
kira Yasmeen vid call suka jima suna magana, kafin TAIMIYYAH ta yi cuting call ɗin.
Har za ta aje wayar ta tuno da Ya Deeku, wanda tunda ta yi aure ko sau ɗaya ba su yi waya ba, sai
ta kira layinsa bugu biyu ya ɗauka ,ta fara zuba masa ƙorafin cewa ya manta da ita, bai taɓa kira
ya ji lafiyarta ba tunda suka korota gidan miji. Ya Deeku ya dinga bata haƙury tare da ce mata zai
zo ya ga ɗaki ai, TAIMIYYAH ta sanar masa cewa ai ta baro Zaria tana Abuja yanzu haka, ya yi
mata fatan alkhairy tare da addu'ar samun kyakykyawar rayuwa a gidan aurenta, su kai sallama da
juna TAIMIYYAh na jin zuciyarta na washewa daga takaicin da Suhailah ta kimsa a zuciyarta.
Ta aje wayar tana zamewa ta kwanta a lafiyayyen bed ɗin da ke ɗakin, wanda kana kallo kasan
bana ƙananun kuɗi bane. Bada jimawaba ko bacci ya ɗauketa sabida bata samu isasshe da safe ba,
ga gajiyan zaman motan da tayi na zuwa Kano su hawo jirgi. Hakan yasa nan da nan bacci ya sure
ta bata farka ba sai wajen 1 na rana........✍🏻
_To fah! Ga TAIMIYYAH a garin Abuja ga kuma sarkin kishi Suhailah, ko ya rayuwarsu zai
kasance a guri ɗaya tare da gwarzon mijin nasu A.Maleek Ado? Da alamu dai za a ɗan yi wani
ƙwarƙwaryan film da zai ƙayatar , kafin kuma su wuce zuwa ƙasar Cairo mu ga me zai faru a can
kuma?_
_Littafi dai na ta zuwa gangara sau ƙiris mu ƙarisa In Sha Allah! Ina godia da tarin ƙauna masoya
litfafin TAIMIYYAH . Na gode ƙwarai Allah ya bar ƙauna_
#Ɗansabo ce#
[12/15, 11:46 AM] +234 703 040 9541: Littafin TAIMIYYAH paid book ne,ga duk wanda ta
tsincesa a kowani irin group ne,kiji tsoran Allah karki karanta sai kin biya 500 naira only.
Za ku iya min magana ta wannan number ɗin 08167768704, ko kuma ku turo kuɗin ku kai tsaye ta
wannan account ɗin 0504192664 aisha ibrahim dansabo GTbank.*
Masu turo credit za ku turo katin MTN na 500 ta wannan line ɗin 08167768704.
_Ina ƴan kasuwa masu buƙatar a tallata muku hajar ku? Maza ku garzayo da kuɗi ƙalilan a tallata
muku kayan siyarwanku sai dai kawai ku ji ana kiran waya don buƙatan sayan kayan ku,ku
tuntuɓeni ta layina kamar haka 08167768704._
*80*
*Gyallesu, Zaria.*
" Hajiya Zuwaira kamar yadda na gaya miki ne tun farko, ke ce ki ka saki damarki akan wannan
gurguwar, gashi yanzu ta zame miki ƙadangaren bakin tulu. Da yanzu ke ce yakamata a ce kina
juya rayuwarta yadda ki ka ga dama, duk wani daula da ɗaukakar da za ta samu ke ce da ƴaƴanki
za ku fara mora, amma sai ki ka ɗauki karan tsana ki ka ɗaura akanta kina nuna mata ƙiyayya ta
zahiri."
Hajiya Barirah ke wannan maganar idanunta akan Umma, wacce ta nutsu tana saurarenta kafin ta
buɗe baki ta ce, "Hajiya Barirah ban gane ina ki ka dosa ba har yanzu, ta ya zan juya rayuwarta
alhani tun asali na tsaneta ita da uwarta?"
Hajiya Barirah ta saki murmushi ta ce, "Shi ne sakarcin da ki ka yi tun farko ai, ke yakamata a ce
kin riƙi yarinyar a hannunki tun farko, kin ga da yanzu ke ce za ki ci gajiyarta don ke za ta kallah a
matsayin uwa,amma sai ki ka nuna mata ƙiyayya tun tana ƙarama har girma. ki ka rabata da
ƴaƴanki tare da cusa musu ƙiyayyarta a zuciyarsu, da a ce kin yi amfani da ƙwaƙwalwa wajen
nuna kissa da kisisinan rungumarta da janyo ta a jikinki, ina me tabbatar miki da cewa da ke ce
zata kallah a matsayin uwa, kuma da yanzu wannan baƙin ciki da hassadar da ki ke ji ba zai damu
zuciyarki kamar haka ba. Sabida ku ne zaku fara cin gajiyar duk irin daula da ɗaukakar da za ta
samu a rayuwa, amma kin riga kin saki damarki sai dai ki yi kallo ke da ƴaƴan naki."
Hajiya Barirah ta kai ƙarshen maganar tana ɗan sakin dariyar mugunta, Umma ta ɓata fuska tana
jin maganganun Hajiya Basirah na tasiri a zuciyarta, tare da sanya zuciyarta cikin dana sanin
wautan da ta tafka tun farko. Ta jinjina kai tana cewa, "Tabbas na yi wauta Hajiya Barirah, kuma a
yanzu bakin alƙalami ya riga ya bushe, don ko na ce zan nuna mata so a yanzu na makara, sabida
ta rayu ne da sanin cewa bani ƙaunarta tun asali, sannan kowa ma ya shaidi hakan kin ga duk
wanda ya ga a yanzu na fara nuna mata so, ya san cewa ina da wata manufa a ƙasa. Mu tafi zancen
Zuhurah a aje batun gurguwar a gefe guda, ya zan yi in taushi zuciyarta kar ta dawo garin nan a
samu a bakin duniya Hajiya Barirah? Ina cikin matsanancin tashin hankali gashi tun safe na ke
kiran layinta a kashe ina mafita?"
Hajiya Barirah ta jinji kai ta ce, "Ni ina ganin ki barta ta dawo Hajiya Zuwaira, sabida ko ni ce ita
ba zan zauna da mashayi mara asali ba, to mara asali mana tunda sun ce basu san ma haƙiƙanin
inda dangin ubansa su ke ba, waya sani ma shege ta yi ta kawosa duniya. Kar ki kashe rayuwar ƴar
ki sabida gudun kunyar duniya da surutun mutane, ni na ga auren da ya mutu cikin kwana uku da
ɗaura shi, kuma yarinyar mijin ya kwanta da ita ta zama bazawara."
Umma ta zurawa Hajiya Barirah ido tana jin wani abu me nauyi na sake danne zuciyarta, sam bata
so Zuhurah ta kaso wannan auren don tasan sai an musu dariya.To amma kamar yadda Hajiya
Barirah ta ce ne babu anfanin zama da Ameeru, tunda bai fito a ɗan Honourable ba bare su
tursasata ta zauna da shi sabida kwaɗayin dukiya,ta furzar da iska me zafi daga cikin bakinta kafin
ta ce, "Gaskiya ne Hajiya Barirah zama da shi ba shi da sauran amfani, amma ya cuce mu ya
yaudare mu wannan yaron wallahi, takaicina irin kuɗin da na dinga narkawa wajen sake karkato
da hankalinsa kan Zuhurah."
Hajiya Barirah ta ɗan taɓe baki ta ce, "Ai halin maza yanzu abin tsoro ne Hajiya Zuwairah, sannan
yanzu fa ba a faɗin gaskiy wajen binciken aure sai dai a rufe mutun a bai-bai kawai. To ita kuma
Basmah wata wainar a ke toyawa da nata mijin?"
Umma da jikinta ya gama yin sanyi, damuwa da takaicin duniya ya gama lulluɓe zuciyarta, sai ta
watsa hannuwanta baya kafin ta ce, "Wallahi ban sani ba Hajiya Barirah, bata taɓa kirana ba tun
da aka kai ta, ni kuma jiya har na ɗaga waya zan kirata fargaba ya sanya ni fasawa,don bansan me
zan ji daga nata ɓangaren ba kuma,amma bari a kira ta yanzu a ji."
Daga haka Umma ta ɗaga waya ta kira layin Basmah, wayar ya daɗe yana ringin kafin ta ɗaga.
Umma ta sanya wayar a speeker tana ajewa akan jikinta lokacin da muryar Basmah ya ratsa
kunnuwarsu tana cewa, "Hello Umma ina yini ya ku ke?"
Umma da ta ji muryar Basmah very low sai da ƙirjinta ya yi wani irin doka mata, kafin ta amsa da
cewa, "Lafiya lau Basmah ya ku ke badai wani damuwa ko? Kuma a ce tunda ki ka tafi shiru babu
kira ki gaishe mu, Basmah kin ga ya dace kenan hakan?"
Basmah ta yi saurin faɗin, "Umma ki yi haƙuri ya amshe wayar ne sai yau da safe ya bani, tun
washegarin da aka kawoni ya ƙwace wayar sabida kawai wani friend ɗina ya kira ya yi min
murnar biki. Akwai fa damuwa Umma don Nass ya gama dawowa cikin hayyacinsa, ya kuma
tabbatar min da cewa wani malami ya sanar masa asiri mu ka yi, muka janyo hankalinsa har ya
aureni, wallahi wulaƙanci me tsanani na ke fuskanta daga garesa Umma, har cewa ya yi ba zai
taɓa sona ba, zai cigaba da zama da ni ne don kawai ya dinga kauda sha'awarsa a kaina amma ba
don so ba, dole a koma wajen Boka Umma don sake sabon aiki akan Nass, ni har ya fara bani
tsoro ga shi Hajiyarsa tun shekaranjiya ta zo ta tare a ɗakin da ya gina don ita a gidan, da alamu
bata da ranar barin gidan gaba ɗaya a takure na ke, ga hantara da wulaƙancin dana ke fuskanta
daga garesa Umma, gaba ɗaya duk na fara fita a hayyacina sabida fargaba da tsoran me zai je ya
dawo."
Basmah ta ƙare maganar tamkar za ta rushe da kuka, Umma da Hajiya Barirah da ke sauraren
Basmah duk jikinsu ya gama yin sanyi. Umma ta haɗiye wani abu me ɗaci da ƙuna daga
maƙoshinta kafin ta ce, "Shi Naseerun ne ya sanar da ke hakan Basmah? Meyasa lamura da dama
a wannan karon ke son kwaɓemin ne, da me zan ji ne wai ni Zuwairah?"
Umma ta yi maganar cikin zallar tashin hankali da firgici, wanda hakan ya sanya Basmah sakin
kukan da ta ke riƙewa, cikin kukan kuma ta ce, "Umma ni dai ki taimakeni kar wata tanganɗa ta sa
in rasa Nass, wallahi ina matuƙar ƙaunarsa sosai, duk yadda za ai a sake juyo min da hankalinsa
kaina a yi hakan Ummana."
Umma da ke jin kanta na juyawa mata ta yi ƙarfin halin cewa , "Ki yi shiru Auta yanzu za mu
koma Kusfa don zama bai kama ni ba, ga Zuhurah can na shirin dawowa ta ce ba za ta zauna da
Ameeru ba, ashe ɗan me aikin gidan Honourable Ahmed Attah ne ba ɗan cikinsa ba ne."
Basmah ta yi saurin cewa, "What!!!!?" Umma ta zayyanewa Basmah komi tana kai ƙarshen
maganar da cewa, "Basmah Ameeru ya ha'ince mu ya yaudari Zuhurah, yanzu ina zan kai kunyar
maƙiya da wannan annamimiyar tsohuwar da ke jiran ƙiris ne ta yi mana dariya, tun da dama ba
ƙaunarku take yi ba sai waccar tsinanniyar gurguwar."
Basmah a ɓangarenta sai ta rasa ma abin cewa illah wani irin tashin hankali da ya sake rufta mata,
Umma ta katse wayar tana duban Hajiya Barirah da ta yi kasaƙe tana sauraren duk abinda su ke
zantawa akai tsakanin Umma da Basmah.
"Hajiya Barirah tashi za ki yi mu tafi Kusfah yanzu-yanzu wajen Boka Kallah, don ban ga ta zama
ƴaƴa biyu duka na shirin ɓallo min ruwa, ga rashin madafa akan sanin wacce ubansu ke shirin
kawo min, ina zan saka kaina ne Barirah, meyasa lamura ke neman juyemin da abinda ban lissafa
da su cikin rayuwata da ta ƴaƴana ba?"
Hajiya Barirah ta jinjina kai ba tare da jin ko ɗar na tausayin aminiyar nata ba ta ce, "Hajiya
Barirah so da yawa aiki da ƙwaƙwalwa wajen samarwa kai mafita ya fi ka sadaukarwa Boka da
Malaman tsibbu ragamar komi, sabida ba komi ne za su iya sama ma mafita akai ba. Ni na koya
miki bin Bokaye amma ni ina aiki da ƙwaƙwalwata a lissafa-lissafe da dama, kafin na sanya Boka
a cikin sabgata, amma bari mu je ya gano mana me ke shirin faruwa ,sai mu dawo mu san yadda
za mu ɓullowa lamuran."
Daga haka basu sake zantawa akan komi ba, Umma ta zari mayafi suka fito don zuwa Kusfa,
bayan ta sallami ƴan aikinta da sallahun abinda za su girka na lunch, don Baba Sani bayanan ya
tafi Kaduna, bai kuma shaidawa Umma me zai je yi ba,shiyasa ta yi zaton ko wani ɗaura aure ko
wata sabgarce ta kaisa, bata san cewa ya je nemo auren Amaryar ta bane.
__________
Boka Kallah ya buga ƙasa tare da shafa madubin sihirin da ke bayyana masa lamura da dama,
sannan ya ɗago kansa ya dubi Umma wacce sam bata cikin nutsuwarta ya ce, "Matso nan ki sanya
idanunki akan wannan madubin." Ya yi maganar cikin wani irin tsawa da ya kiɗima zuciyar
Umma, ta yi gaggawar matsawa gabansa tana ɗaura idanunta akan wannan madubin sihirin.
Dukkanin jikinta ya sake ɗaukar rawa lokacin da idanunta su kai tozali da fuskar Naseer da wata
mata, ta dubi Boka Kallah da gaggawa wanda sam bayi da kyawun gani, sabida asirin muninsa.
Cikin rawar murya umma ta ce, "Boka wannan shi ne mijin ƴa ta Basman , sai dai bansan wace ce
wannan matar ba."
Boka ya tuntsure da wani irin dariya da sai da ɗakin ya amsa da sautinsa, kafin ya tsuke fuska
yana kallon Umma ya ce, "Wannan ita ce mahaifiyarsa da ke tsaye akan lamuransa a yanzu, domin
kwanaki biyu kafin ɗaura aurensa da yarinyar ta ki, wani malaminta ya sanar da su cewa asiri akai
wa ɗanta, kuma ko kaɗan ba ita zuciyar ɗan ta ke so ba, tun daga nan hankalinta ya tashi suka
lalata duk wani aiki da kuka yi don ku mallaki zuciyarsa, yanzu haka tana can ta tare domin sanya
idanu akan ɗanta, tare da bashi dukkan kariya daga farmakin da za ku sake kai wa rayuwarsa. Don
haka a yanzu babu wani aiki da za mu iya yi akansa ya yi tasiri , har sai ta kauce ta ɗan bada waje
sannan sai mu yi wuff mu damƙo zuciyarsa, ta yadda zai yi wuya ya iya komawa hayyacinsa cikin
sauri, amma fa sai mun bada lokaci. Sai maganar auren mijinki babu makawa ana daf da ɗaura
auren, don haka ki yi gaggawar gano ko wace ce kafin wankin hula ya kai ki ga dare, maganar
ɗaya ƴar taki tabbas akwai rabuwa a kwai kuma rabo da zai gitta a tsakani bayan rabuwar."
Umma da zufa ya gama jiƙe rigarta ta dubi Boka a gigice ta ce, "Yanzu shugaban ɓatattu babu
abinda za a iya yi don hana aukuwar auren Sani da koma wace ce? Sannan maganar Zuhurah don
Allah a dakatar da kowani irin rabo ne don bama buƙatarsa, sannan uwar wannan Nass ka taimaka
Boka ka lalata yinƙurinta domin mu shigar da aikinmu da gaggawa, na yi alƙawarin sadaukar da
ko nawa ne akan samun biyan buƙatata."
Boka ya sake tintsirewa da dariya ya ce, "Ban ga mahalukin da zai iya dakatar da wannan auren
ba, domin akwai zazzafar rabo kamar yadda na sanar miki a baya, wanda shi ne silar rasa mijin
matar don haka duk wanda ya ce zai ja da wannan auren zai iya rasa ransa, don dole sai rabon da
ke tsakaninsu sun taka doran duniya. Sannan maganar ƴar ki kada ki ce zaki ja da rabon da zai
gitta a tsakani domin sai ya zo duniya, ko da zaki ƙarar da numfashin da ya yi saura a rayuwarki
ne don ki hana aukuwar hakan. Don haka ki sanya kan ki cikin lissafin marasa rabo domin a duk
lamuranki babu sa a sai faɗuwa, sabida zuciyarki ba ta nufin kowa da alkhairy sai kanki da
ƴaƴanki."
Boka ya kai ƙarshen maganar yana sake ruɗa ɗakin da mahaukaciyar dariyarsa, kafin ya tsaida
dariyar yana sake duban yadda Umma ke sharce zufa, dukkanin jikinta na ɗaukar rawar rashin
sanin madafa.
Hajiya Barirah ta yi ƙarfin halin yin tambayar, tausayin Umma na kama zuciyarta, Boka ya daka
mata tsawa ya ce, "Ba rashin nasara ba ce Barirah domin dukkanin ayyukata akwai nasara, sai dai
idan wanda ya kawo aikin ne mare nasara a rayuwa tamkar aminiyarki. Mafita ɗaya ta ke dashi
akan auren mijinta da zai yi, shi ne ta je ta gano wace ce zai aura ɗin, bayan ta gano sai ta yi
ƙoƙarin samo farcen ƙafarta na dama, da shi zan mata wani aikin da ba za su jima ba za su rabu."
Umma ta sake sharce wani uban zufa zuciyarta na sake shiga wani yanayi mara misaltuwa, cikin
son bai wa kanta jarumta ta dubi Boka ta ce, "An gama Boka zan yi ƙoƙarin gano ko wace ce,
sannan duk yadda za a yi na samo farcen zan samo na kawo."
Boka ya sake bushewa da dariya kafin ya sallame su daga gabansa, bayan Umma ta aje masa kuɗi
masu yawa. Suka fito daga gidan nasa jikin Umma na cigaba da ɗaukar rawa, zuciyarta tamkar za
ta rabu da ƙirjinta haka ta ke ji sabida tsananin zafin da take mata.
"Hajiya Barirah meyasa sai da rayuwa ta zo gangara sannan rashin nasara za su shigo cikin lissafa-
lissafe ne ? Meyasa zan zamo cikin marasa nasara alhali a baya komi na sa agaba sai na yi nasara
akansa? Ta ina zan gano wace ce wannan baƙar hatsabibiyar da ke shirin kutsowa cikin rayuwar
Sani? Na yi dukkani yina ban gano komi da zai alamta min cewa yana neman aure ba Barirah."
Umma ta kai ƙarshen furta tarin tambayoyin da suka cika kwanyarta, tare da hautsina kwanyarta
da duniyarta baki ɗaya. Hajiya Barirah ta dubi Umma lokacin da ta yi wa motar ta key ta ce,
"Hajiya Barirah ki nutsu ki don mu fuskanci abinda ke gabanmu na gano koma wace ce ɗin, dole a
yau idan ya dawo ki fasa masa maganar idan har da gaske yana neman auren, daga kallon
idanunsa ma za ki fahimci hakan, daga lokacin ke kuma za ki yi anfani da kwanyarki wajen danne
duk wani kishi da zai ta so miki, ki zama shahararriyar kisisinanniyar macen da ta iya kwantar da
kanta a gaban miji, domin cin ma manufa da cikar burinta na samo abinda ta ke so daga garesa."
Umma ta zurawa Hajiya Barirah ido ta ce, "Ta yaya zan yi hakan Hajiya Barirah?"
Hajiya Barirah da ta cigaba da murza kan styering motarta ta ce, "Nuna masa za ki yi idan auren
da gaske zai yi, to kina maraba da duk wacce za ta shigo ɗin, kar ki nuna kishi ko bada wata kafan
da zai gano akwai wata mummunar manufa a zuciyarki, daga lokacin da kika kwantar da kai kika
nuna kina supporting ɗinsa, to duk tambayoyin da zaki jefa masa a lokacin za ki iya samun
amsarsu ba tare da ya ɗago manufarki ba ko kaɗan. Ina fata yanzu kin fara ɗaukar haske don na
lura sam ke kwanyarki bata ja Hajiya Barirah, abinda kawai ki ka fi amanna da shi shine sihiri,
wanda na faɗa miki a ɗazu ba a kowani muhalli ya ke aikin da ƙwaƙwalwa ke yi ba, wajen samo
mafita cikin sauƙi. Don haka ki gwada wannan idan an ci nasara mun gano bakin zaren, sai mu san
hanyar da zamu bi wajen isa gareta ko tura ɗan saƙo, wanda zai kawo mana cikakkiyar bayani a
kanta, watakilama har ya iya samo mana abinda Boka Kallah ke buƙata cikin ruwan sanyi."
Hajiya Barirah ta yi maganar tana duban fuskar Umma da ke washewa da wani irin murmushi,
kafin ta dubi Hajiya Barirah ta ce, "Gaskiya Hajiya Barirah kwanyarki ta fi tawa ja nesa ba kusa
ba, tabbas hakan za a yi a yau ba sai gobe ba zan gwada wannan sa ar, watakila matakin nasarace
cikin ruwan sanyi."
Hajiya Barirah ta saki dariya suna cigaba da tattauna yadda za su ɓullowa lamura da dama, har
suka ƙariso gyallesu ta sauke Umma ta juya don komawa nata gidan, ba tare da ta sake shiga gidan
Umman ba. Umma ta nufi gate don shiga gidan zuciyarta na cigaba da samun rangwamen tashin
hankalin da ta shiga, koma ta ce tana kan shiga don hankalinta ba zai taɓa kwanciya duka ba, har
sai ta gano wacce Baba Sani zai aura.
___________
*Asokora, Abuja.*
*09:05pm.*
A.Maleek Ado ne zaune bisa ɗaya daga cikin kujerun dining ɗin don yin Dinner, daga gefensa
Suhailah ce ta ci uban ado cikin wasu riga da wando na english wears da suka bayyana surar
jikinta ta ko'ina, sai fitinannan ƙamshi ke tashi a jikinta. Fuskarta ya sha light make-up ta yi kyau
matuƙa kamar yadda kayan suka amshi jikinta sosai.
Maleek Ado ya ɗaga kai ya dubeta lokacin da take shirin fara serving ɗinsa ya ce, "Wait wife, bari
ta fito please!"
Suhailah ta jefa masa tambayar rainin hankalin, da ya sanya shi ɓatar da duk wani annurin da ke
kan fuskarsa, ya buɗe baki cikin ƙasaitacciyar muryarsa ya ce, "Zaynabb!"
Yadda ya ambaci sunan da wani irin tone sai da ya sanya Suhailah saurin dubansa, tana jin wani
kishi me tsanani na danne zuciyarta, ta taɓe baki kaɗan tana komawa ta zauna bisa kujeran dining
ɗin ta ce, "Amma Yah Maleek kasan dai yau kwanana ne tunda ka gama mata kwanaki bakwai
ɗinta, don za mu ci abinci tare baya nufin cewa sai an jira ta tana ɓatawa mutane lokaci, ni gaskiya
na ƙosa na kwanta kuma yunwa na ke ji."
Suhailah ta yi maganar muryarta na bayyana kishi da halin da zuciyarta ke ciki, Maleek ya sake
haɗe fuska ya ce, "Okey ke za ki gaya min abinda ya dace Suhailah, wa ya gaya miki ɓata lokaci
ta ke yi ba a gabanki na yi waya da ita ta ce wanka ta fito tana kintsawa yanzu za ta fito ba? Kar ki
sake ki fusata zuciyata da kalamai marasa kan gado please!"
A.Maleek ya yi maganar cikin zallar nuna gargaɗi ga Suhailah, wacce ta sake cika ta yi fam tare
da sake jin tsanar gurguwar matarsa na sake girma a zuciyarta. Kafin ta buɗe baki ta iya cewa
komi TAIMIYYAH ta ratso cikin falon, hannunta na dafe da guiwar ƙafarta take takowa zuwa
ɓangaren dining ɗin kanta a ƙasa. Tana sanye cikin wasu nighties masu a zabar kyau kalar dark
purple, da a kaiwa adon zane da pusha pink, tsayin rigar iya guiwa ne da ke ɗauke da faffaɗan
wuya V-shape, wanda ya bayyana cikar ƙirjinta daga sama kaɗan, sai ta ɗauki wata kimono me
taushin jiki ta sanya don sakaya shigar da ke ciki. Fuskarta babu komi sai powder da kuma kwalli
da ta sanya wa manyan idanunta masu wani irin haske, cute lips ɗinta na haskawa da ƙyallin
lipbalm me maiƙo, cikin hasken fararen fitullun da suka dallare ko'ina a cikin falon zuwa dining
area ɗin.
Tunda ta doso idanun Maleek Ado da na Suhailah ke kanta, sai ta dinga jin kaifin idanunsu na
ratsa jikinta, yana haifar mata jin wani yanayi a zuciya da gangar jikinta, ta ja kujeran da ke gefen
Maleek ta ɓarin damarsa ta zauna, tana me ɗago idanunta ta sauke a kansa. Idanunsu suka shige
cikin na juna, kamar yadda ƙamshin kowannensu ya bugi hancin ɗan uwansa, TAIMIYYAH ta yi
saurin janye idanunta daga garesa ta maida saitin Suhailah, ta ɗan shagwaɓe murya kaɗan ta ce,
"Sorry na barku da jira don Allah ku yi haƙury, shirina ne babu sauri ban kuma ɗauka cewa tare za
a ci abincin ba."
Suhailah da zallar kishi da takaicin TAIMIYYAH ya gama cika zuciyarta, sai ta yi ƙarfin halin
saita kanta ta ce, "Okey badamuwa amma dai next time, a dinga ƙoƙarin ganin ba a shiga hakkin
juna ba please! Don jira babu daɗi kam."
TAIMIYYAH sai ta jinjina kai ta ce, "In Sha Allah! Sorry please!"
Daga haka ta maida dubanta zuwa ga gogan wanda ya tsare Suhailah da ido, yana jifanta da wani
irin kallo amma ta ƙi waigo da kanta ta dubesa, bare ta ga irin kallon da ya ke jifanta da shi, sai ya
ja ƙwafa kaɗan yana maido dubansa kan TAIMIYYAH. Idanunsu suka sake sarƙewa da juna sai ta
sakar masa kyakykyawar murmushi tare da sake narke masa fuska, cike da zallar shagwaɓa ta yi
ƙasa da muryarta ta ce , "Sorry Hubby na bar ku kuna jira, da kun sani kun fara cin abincin ni idan
na zo sai na ci nawa ko?"
Maleek da TAIMIYYAH ta gama kunna zuciyarsa da salonta, sai ya saki smile kaɗan yana sake
tsuke face ɗinsa ya ce, "No Sweet babu komi kar ki damu kan ki da yawan bada haƙury."
TAIMIYYAH ta sake sakar masa murmushi kafin ta ɗauke idanunta akan sa ta ce, "Okey!"
Suhailah da hankalinta ke kansu ji ta yi tamkar zuciyarta za ta yo waje, wani irin abu me ɗaci ta
dinga ji yana wucewa ta maƙoshinta, mamakin shaharan wannan gurguwa a iya shagwaɓar da ke
sace zuciyar miji na sake soya zuciyarta, bata san lokacin da ta ballawa Maleek harara ba, ganin
yadda kaf hankali ya koma kan TAIMIYYAH yana faman bin jikinta da kallo. Wani abu ya soki
zuciyarta lokacin da ta kai dubanta kan inda idanunsa ke kai, ta ke ta ji wani irin abu me nauyi ya
sake danne zuciyarta, lokacin da idanunta ya sauka a ƙirjin TAIMIYYAH, wanda breast ɗinta ya
leƙo kaɗan ta saman wuyar rigar.
Ta yi gaggawar ɗauke idanunta daga gareta, tana tura plate ɗin da ta yi serving Maleek Beef Salad
with grilled patato, ta sake ɗaukar plate ta zuba Jallop ɗin pasta da yaji kayan lambu da naman
kaza a ciki, sai ta zuba haɗin Salad daga gefe ta tura gaban TAIMIYYAH. Ita ma tayi serving
kanta jallof ɗin pasta ɗin ta cika Salad daga gefe, ta ɗauki cup ta tsiyayawa Maleek juice ɗinsa na
5alive da ya fi sha ta tura gabansa, sai ta koma ta zauna tana ƙoƙarin controlling kanta sabida
yadda ta ke jin zuciyarta na mata suya.
A hankali suke cin abincin babu me magana a cikinsu, lokaci bayan lokaci TAIMIYYAH da
Maleek kan haɗa ido su sakarwa juna smile, duk kuma hakan da suke yi akan idanun Suhailah
suke yi, wacce ke jin tsananin kishi tamkar zuciyarta za ta kama da wuta. TAIMIYYAH ita ta fara
kammala cin abincin, wanda ita sam bawani daɗi ya yi mata ba, ta miƙe don baro dining ɗin ne
Maleek ya yi saurin riƙo hannunta ya ce, "Wife ina zuwa daga gama cin abinci kuma, ni duk yau
ma banga kin ci wani abin kirki ba, are u not feeling fine?"
TAIMIYYAH ta saci duban yadda Suhailah ke jefosu da mugun kallo ta shagwaɓe murya ta ce,
"Lafiya ta lau Habibi, zan koma ɗaki ne bacci na ke ji da wuri kawai."
Maleek ya sake tsare ta da manyan idanunsa ya ce, "No ba za ki kwanta ba sai na yi magana da ku,
so ki jira mu daga cikin falon ga mu nan ƙarisowa kin ji?
TAIMIYYAH ta gyaɗa kai ba tare da ta ce komi ba, ya saki hannunta ta dafe guiwar ƙafarta ta fara
takawa zuwa cikin falon, ta zauna cikin seater ɗin da ke fuskantar TV ta zauna, tana me lumshe
idanunta ta jingina da jikin kujeran sosai. Gabaki ɗaya ta rasa meyasa bata jin daɗin irin kallon
tsanar da Suhailah ke jifanta da shi, duk da cewa ita irin wannan kallon ba baƙonta bane, don ta
saba da ire-irensu daga wajen Umma tun kafin ta san kanta, har ta mallaki hankalinta. But wannan
ɗin yana mata ciwo da sanyata jin duk ta zumunta,ta cigaba da zama shiru idanunta a lumshe tana
jiran isowarsu cikin falon...........✍🏻
#Ɗansabo ce#
[12/15, 11:46 AM] +234 703 040 9541: Littafin TAIMIYYAH paid book ne,ga duk wanda ta
tsincesa a kowani irin group ne,kiji tsoran Allah karki karanta sai kin biya 500 naira only.
Za ku iya min magana ta wannan number ɗin 08167768704, ko kuma ku turo kuɗin ku kai tsaye ta
wannan account ɗin 0504192664 aisha ibrahim dansabo GTbank.*
Masu turo credit za ku turo katin MTN na 500 ta wannan line ɗin 08167768704.
_Ina ƴan kasuwa masu buƙatar a tallata muku hajar ku? Maza ku garzayo da kuɗi ƙalilan a tallata
muku kayan siyarwanku sai dai kawai ku ji ana kiran waya don buƙatan sayan kayan ku,ku
tuntuɓeni ta layina kamar haka 08167768704._
*81*
Ta yi zaman da ya kai mintuna biyar sannan Maleek ya fara ƙarisowa cikin falon, daga baya
Suhailah ta ƙariso tana faman takowa cikin wani irin taku me fisgar hankali, sai wani juya jiki take
yi don ta nunawa TAIMIYYAH cewa ita ɗin lafiyayyace da za ta fita iya sarrafa taku wajen jan
hankalin miji. Kallo ɗaya TAIMIYYAH ta yi wa Suhailah ta ga yaddda wandon jikinta ya bayyana
surar mazaunanta a sarari, ta yi gaggawar ɗauke idanunta zuciyarta na matsewa da wani irin
yanayi da ba za ta iya fassarawa ba.
Suhailah ta isa kujeran da Maleek ke zaune cikin seater,ta zauna tana me manne jikinta da nasa,
sai faman wani yatsina take yi tana ɓata fuska.
Maleek da Idanunsa da hankalinsa ke kan TAIMIYYAH wacce ya ga mood ɗinta ya sauya, sai ya
gyara zamansa yana raba jikinsa dana Suhailah amma sai ta sake manne masa, hakan yasa shi
rabuwa da ita ya maida hankalinsa ga TAIMIYYAH da sam taƙi duban sashin da suke zaune, ya
fara da kiran sunan ta, "Zaynabb!" Ta ɗaga manyan idanunta ta sauke akansa ta na amsawa da
cewa, "Na'am Hubby!"
Salon da ta kira yi sunan da yadda ta furtashi cike da zallar narke murya da shagwaɓa, ya daki
zukatan Maleek da Suhailah a tare,Suhailah ta ji tamkar ta tashi ta je ta shaƙure TAIMIYYAH, ko
zata huce takaicin baƙin cikin da take ƙunsawa zuciyarta, da wannan salon shagwaɓar tata da ke
narkar da zuciyar A.Maleek ɗinta.
Ya maida dubansa ga Suhailah ita ma ya kira yi sunanta, "Suhailah!" Suhailah aka wani yi fari da
ido ana wani maƙale murya aka amsa da cewa, "Na'am my Maleek!"
A.Maleek Ado sai ya sake miskile fuskarsa da sake zama so serious, sannan ya buɗe zaman da
addu'a kafin ya fara da cewa, "Zan fara ne da jawo hankalinku tare da tunasar da ku muhimmancin
zaman lafiya da kuma haɗin kan juna, dukkaninku a yanzu mun zama wani ɓangare na rayuwar
juna, da zamu zauna a ƙarƙashin inuwar aure. Duk da cewa ba za ku rayu a muhalli ɗaya ba,
amma a matsayina na shugaba kuma miji a gareku, tabbas ina buƙatar haɗin kanku tare da
wanzuwar zaman lafiya a tsakaninku, domin hakan kaɗai shi ne zai bani dama wajen wanzar da
kwatanta adalci a tsakaninku. Suhailah ke ce babba don haka da ke zan fara, ina so ki kama
girmanki tare da jin tsoran Allah wajen ganin baki shi ga hakkin abokiyar zamanki ba, idan an
samu wani saɓani a tsakanin junanku ku zama masu yafiya da yawan yiwa juna uzuri. Bazan
amince da faɗa ko tashin hankali a cikin gidana ba, don na aureku ne don na ji daɗin zama daku,
kuma ku zame min farin ciki a rayuwa ba wai ku zame min tashin hankali ba. Dukkaninku na
aureku ne don ina sonku ina ƙaunarku, ina kuma sha'awar mu rayu da juna har ƙarshen numfashi,
don haka kar wata ta ji cewa ta fi ƴar uwarta a zuciyata, har sai idan kin tabbatar da cewa
biyayyarki gare ni da bani farin ciki ya zarta na ƴar uwarki. Ina fata a matsayinki na babba za ki
bani goyan baya wajen ganin kun haɗa kan juna, don a samu zama na fahimta da samun
kwanciyar hankali me ɗaurewa?"
Suhailah ta jinjina kai tare da kwantar da kanta a saman kafaɗarsa ta ce, "In Sha Allah my Maleek,
Allah ya bani ikon yin duk abinda ya ke shi ne daidai."
Maleek ya amsa da cewa, "Ameen." Kafin ya mai da dubansa kan TAIMIYYAH da kanta ke ƙasa
ya ce, "Zaynab ina fata hankalinki na nan? "
TAIMIYYAH ta ɗago kanta tare da zuba masa manyan idanunta ta ce, "Ina ji Hubby!"
Maleek ya jinjina kai ya cigaba da cewa, "Zaynab a matsayinki na ƙarama ina fata za ki haɗa kai
da ƴar uwarki ku zauna lafiya, sannan ki zama me girmamata a matsayinta na wacce ko a shekaru
ta baki rata me yawa. Bana buƙatar raini ko rashin kunya ya shiga tsakaninki da ita, idan har hakan
ya faru zan saɓa fiye da yadda za ki yi tunani,ina fata zaku haɗa kai don bani goyan baya wajen
tabbatar da adalci a tsakaninku?"
Maleek ya ɗaura da yi musu bayanin yadda za su rayu da juna a inuwa ɗaya har su je su dawo
daga tafiyar da za su yi, daga nan kowacce sai ta rayu a muhallinta ita kaɗai.
Daga ƙarshe ya nemi shawaran junansu akan yadda rabon kwana zai kasance daga nan har su je
Egypy su dawo, suka amince akan kwana bibbiyu ya yi musu. Daga haka Maleek ya rufe taron da
addu'a TAIMIYYAH ta fara tashi don barin musu falon, sabida yadda Suhailah ta gama kwanciya
a jikin Maleek tana wani faman narke masa ba ƙaramin sosa zuciyarta ya yi ba.
Ta fara takawa a hankali dafe da guiwar ƙafarta ta nufi hanyar ɗakin da za ta rayu a ciki, kafin
gidan ya zama nata ita kaɗai da za ta rayu a cikinsa ba tare da Suhailah ba. Ta ƙi duban sashin da
su Maleek ke zaune har ta gota su ta miƙi hanyar ɗakinta, sai dai tana jin rakiyar idanunsa akanta
amma duk da hakan ta kasa waiwayo ta dubesa, duk da cewa hakan zuciyarta ke da muradi amma
kishin da ke tafasa zuciyarta, na yadda Suhailah ta yi ale-ale a jikin Maleek ɗin ya hana ta damar
juyowa ta sake duban fuskarsa.
Wasu hawaye suka taru a idanunta tana jinjina cewa 'Dama haka kishi ya ke?' har ta kai kanta
cikin ɗakin zuciyarta suya ta ke yi, hakan yasa ta zama a bakin gadon tare dafe kanta. Gaba ɗaya ji
ta ke yi tamkar ta yi tsuntsuwa kawai ta koma Zaria, da ƙyar ta yi controlling kanta ta rarrashi
zuciyarta tare da tunasar da kanta cewa, Maleek ba nata bane ita kaɗai dole idanunta su ɗauki
ɗammaran ganin kowace irin salo daga matarsa. Kuma idan gaskiya za a bi bai dace a ce ta ji irin
zazzafar kishi haka don kawai matarsa ta kwanta a jikinsa ba, tunda tare ta gansu da juna ita ce ta
shigo mata rayuwar miji, don haka bai kamata ta ji zafin abinda Suhailar ta yi ba. Da wannan
tunanin ta samu ƙwarin guiwar ta shi zuwa toilet ta wanko bakinta tare da ɗauro alwala ta fito, ta
nufi wajen ƙaton wardrobe ɗin jikin bango da ta kammale rabin kayanta a ciki, ta zare kimonon da
ke jikinta ya rage daga ita sai rigar baccin jikinta. A hankali ta take takawa don isa bed ta kwanta
sai ta ji an murɗo ƙofar ɗakin an shigo, qamshin turarensa kaɗai ya shaida mata ko waye, sai ta
ɗaga manyan idanunta ta sauke akansa lokacin da ya ke takowa zuwa cikin ɗakin, bayan ya maida
ƙofar ya rufe. Ta janye idanunta tana ƙarisawa gaban gadon ta haye abin ta, tana shirin jan duvet ta
rufe jikinta Maleek ya ƙariso wajen, yana me zama daga bakin bed ɗin ya janyota zuwa jikinsa
baki ɗaya, ya rungumeta tare da sauke wani zazzafan ajiyar zuciya. Cikin wani irin salon murya ya
yi magana ya ce, "Zaynabb shi ne ki ka taho ba tare da kin ce min ko gud night ba haka ake yi
Sweet, kin san yadda na ji a zuciyata kuwa? tell me laifin me nayi akai min irin wannan shariyar
eyim?"
TAIMIYYAH da ta lafe a jikinsa zuciyarta na sake bugawa da ƙaunarsa me zafi, sai ta shagwaɓe
murya ta ce, "Babu komi mantawa na yi ka yi haƙury Baby."
"Na ji but ba zan haƙura ba sai kin bani gud night kiss please!"
Maleek ya furta kalaman yana ɗago fuskar TAIMIYYAH daga ƙirjinsa ya haɗe fuskarsu wa je
guda, ta sake narke masa tare da shagwaɓe murya ta ce, "Habibi ka manta yau ranarta ne please!
Kar mu shiga hakkinta, idan akai min hakan ba zan so ba, so ka yi haƙury time ɗina ya zo ba kiss
ba ko me kake so i promise zan yi maka ka ji Hubby?"
Yadda ta ke maganar a hankali cikin kwantar da murya da zallar shagwaɓa, sai ya sake kashe jikin
Maleek tare da haifar da zazzafar shauƙinta a zuciyarsa. Ya saketa a hankali ta koma kan gadon ta
zauna, har lokacin tana jifansa da wani sassanyar kallo, ya ɗan sake matsawa gare ta ya manna
mata kiss a goshi yana cewa, "Na ji Sweet but ki tabbatar sai kin cika promise, only kiss fa na
buƙata Baby ban ce abin daɗin za a bani ba, oya kiss me please ko small ne ina so."
TAIMIYYAH ta narke fuska tana jin yadda zuciyarta ke sake narkewa a kansa, ta sani tunda ya
fara wannan nacin ba zai bar ɗakinba sai ta yi yadda yake so ɗin, sai ta kai bakinta a hankali zuwa
fuskarsa tare da manna masa light kiss a goshi, ta raba fuskarta da tasa tana ɗan zumɓure baki
alamun ya takurata. Maleek ya wani lumshe ido tare da sake buɗe su akanta, ya kamo hannunta ya
sumbata ya ce, "Luv u my pure zuma, gud night!"
Daga haka ya saki hannunta yana ƙoƙarin sauka daga bed ɗin, dukkanin jikinsa ya gama saki da
soyayyarta, muryarta ya jiyo lokacin da ta ke faɗin,
Maleek sai ya cak! sunan da salon yadda ta furta shi na ratsa ilahirin zuciya da jinin jikinsa, ya
waiwayo yana aika mata da wani sassaryar kallo me narkar da zuciya, sannan ya juya ya fice daga
ɗakin zuciyarsa na cigaba da narkewa da ƙaunarta. Ya dinga addu'a cikin zuciyarsa akan cewa
Allah ya bashi ikon iya kwantata adalci a tsakaninsu, ya kuma bashi ikon iya riƙe kansa akan irin
zazzafar soyayyar TAIMIYYAH da ke son fin ƙarfinsa.
A ɓangaren TAIMIYYAH kuwa sai ta saki murmushi tana jin wani zazzafar ƙaunarsa na sake
mamaye zuciyarta, ta sakko daga kan gadon ta nufi ƙofar shigowa ɗakin ta murza key tare da
kashe wutan ɗakin baki ɗaya ta kwanta.
*Washegary...*
A round 10:05am TAIMIYYAH ta kammala shiryawa, sanye take cin riga da zani na atamfar
holland dull colour da ya haske farar fatarta. Fuskarta simple make-up ne daga powder sai lipstick
da ta gogawa leɓenta kalar red me duhu, manyan idanunta ta yi lining ɗinsu suna haskawa ba
ƙyalin bakin eye liner ɗin. Jikinta na fitar da wani irin ni'imataccen ƙamshin Humrah na RUSS
COLLECTION, wanda Ummy ta siya mata cikin kayan da ta nuna mata randa ta je su kai
sallama,wani irin ƙamshi take yi me asalin motsa zuciya da sanya shauƙi a zuciyar duk wanda ya
shaƙi wannan ni'imatccem ƙamshin Humrar. Ga kuma ƙamshin turarenta na yanzu me suna
VERSACE da ya haɗe dana Humrah ɗin ya sake bada wani ƙayataccen ƙamshi me kwantar da
zuciya,
0703 318 6060 shine number da zaku tuntuɓeta ga duk me buƙatar sayan kayanta.
Wayarta ta ɗauka ta kira layin Iyah suka gaisa, sannan ta kira Hajjah ita ma ta gaidata hakan kuma
baƙaramin faranta zuciyar Hajjah ya yi ba. Tana aje wayar Maleek Ado na sanyo kansa cikin
ɗakin, ya bi ko'ina da kallo hancinsa na shaƙo masa daddaɗan ƙamshin da ke tashi a ɗakin, na
turaren wutar Russ da ta sanya cikin burner. ya cigaba da takowa cikin ɗakin idanunsa akan
TAIMIYYAH, wacce ta yi masa kallo ɗaya ta ɗauke kanta daga dubansa har ya ƙariso bakin bed
ɗin in da take zaune.
Ƙafansa ɗaya ya ɗaura akan bed ɗin yayinda ɗayar ke daga ƙasa, hakan yasa jikinsa rankwafawa
daidai kan fuskar TAIMIYYAH tamkar me shirin faɗa mata. Ta shagwaɓe fuska tana ɗago manyan
idanunta da ke da wani irin tasirin a zuciyar Maleek, ta sauke dubanta akansa tana faɗin, "Gud
morning Sweet Amore!"
Maleek Ado ya kai hannu yana ɗago fuskarta da kyau, idanunsu na sake gauraya da juna yayinda
daddaɗan ƙamshin da bai taɓa ji ajikinta ba sai yau ɗin ke narkar da zuciyarsa, ya buɗe baki a
hankali ya amsa gaisuwarta ya ce, "Morning my pure zuma i miss u so very much!"
Ya yi maganar yana kai bakinsa ya sumbaci idanunta, hakan yasa ta lumshe su tana jin zuciyarta
na sake narkewa a so da ƙaunarsa me zafi.
Maleek sai ya saki fuskarta yana miƙar da ita tsaye ya ce, "Oya let's go Baby Suhailah na jiran mu
a dining, muna gamawa fita za mu yi ki fara ganin gari ko?"
TAIMIYYAH ta jinjina kai kawai ba tare da ta yi magana ba, suka jera da juna don fita daga ɗakin
zuwa dining area don yin kalaci,zuciyoyinsu baki ɗaya na sake cika da shauƙin juna me tsanani.
"Salamu alaimum!"
TAIMIYYAH ta furta hakan lokacin da suka dining area ɗin, tana satan kallon Suhailah wacce ta
ɗauki wanka cikin wasu riga da skat ƴan kanty, da suka kama jikinta ƙwarai tare da fito da surarta.
Ta ɗaga kai ta dubi TAIMIYYAH tana amsa sallamar da ta yi, kafin ta ɗauke ido daga kan
TAIMIYYAH wacce ta ja kujeran da ke kusa da Maleek ta zauna. Suhailah gaba ki ɗaya sai ta ji ta
raina shigarta da take ganin ta yi don ta birge Maleek ɗin, sabida kallo ɗayan da ta yiwa
TAIMIYYAH ita kanta sai da ta yaba irin kyawun da atamfar jikinta da ɗinkin ya yi mata. Wani
kishin yadda TAIMIYYAH ta fita kyawun halitta na cin zuciyarta, Maleek ya dubi TAIMIYYAH
ya ce, "Zaynabb ke za ki yi serving ɗin mu yau."
Daga Maleek har Suhailah suka bi bayanta da kallo, Suhailah tafiyarta take kallo yayinda Maleek
shi kuma zuciyarsa ne ke motsawa da tarin lamura masu yawa a kanta.
Tana shi ga ɗakinta ta nufi kan Sofa ta kwanta tana ɗaukar wayarta ta kunna Data ta hau online,
zuciyarta har lokacin suya ya ke da zallar kishin da bata taɓa tunanin tana da shi har haka ba.
Account ɗin book ɗin NOOR ALBI na Mamue gee da take bi ta shiga, ta fara karanta pages ɗin da
aka turo labarin,labarin na matuƙar ɗaukar hankalinta kamar yadda soyayyar sugar daddy ɗin da
ƴar abokinsa ke matuƙar tafiya da zuciyarta.
Ta yi nisa cikin karatun Maleek Ado ya shigo, amma sam bata kula ba ta cigaba da karanta page
ɗin da take bi, a bazata ta ji anyi sama da wayarta sai ta ɗago idanunta ta sauke akan Maleek tare
da shagwaɓe murya ta ce, "Please! Habibee ka bani wayata."
Maleek da ke karanta daidai inda take karantawa ya saki murmushi me faɗi, yana miƙa mata
wayarta ya zauna akan sofa ɗin jikinsu na gugar juna ya ce, "Zaynabb a she karatun soyayyah ki
ke yi, shiyasa kullum ake sake narkar da zuciyar Maleek ko?"
Kunya ya kama TAIMIYYAH ta sake narke masa tana cewa, "A'a ni kawai yanzu ne na ke koyan
karatun sabida ya dinga ɗebemin kewa."
Maleek ya sake sakin murmushi yana kai bakinsa ya raɗa mata wasu kalamai masu nauyi,
wanɗanda tsananin kunyar jin kalaman daga bakinsa, ya sanya TAIMIYYAH saurin kwantar da
kanta a jikinsa tana me lumshe idanunta. A.Maleek da dama hakan yake so sai ya zura hannunsa
cikin rigarta zuwa muhallin da yafi ko'ina ɗaukar hankalinsa, TAIMIYYAH ta kai hannu ta yi
saurin riƙe nasa hannun da ya fara dagula lissafinta, ta shiga yi masa magiya akan cewa ya barta
don Allah tunda ba kwananta bane, kada matarsa ta biyo sahunsa ta ga abinda ya ke aikatawa. Da
ƙyar Maleek ya iya ƙyaleta yana tashi daga kan sofa ɗin ya ce ta shirya fita za su yi yanzu har da
Suhailah, daga haka ya fice daga ɗakin ya bata waje.
Ta tashi ta nufi wajen kayanta tana ɗakko wata brown ɗin Abayar da za ta saka, ta nufi bakin
gadon ta aje tana cire riga da zanin da ke jikinta, ta sanya wasu ƙananun kaya daga ciki sannan ta
ɗaura Abayar a sama. Sosai ta yi mugun kyau cikin shigar Abayar wanda ita kanta ta gama saki
cewa shigar yana mata kyau matuƙa, tayi rolling gyalen Abayar sai ta fito tamkar wata budurwa
sweet 16, sai tashin sassayar ƙamshi kawai ke fita daga jikinta.
Lokacin da ta fito falon Suhailah ta tadda ta sakko kenan daga upstairs, sanye cikin shigar Abayar
ita ma tamkar haɗin baki, sai dai na Suhailah blue black ne da yaji ado sosai fiye dana jikin
TAIMIYYAH, wanda shi adonsa iya wuya ne da saman hannunwan rigar, ita Suhailah har ƙasar
rigar anyi wani irin ado me ƙyalli sosai.
Kusan a tare jere da juna suka fito daga falon amma babu wacce ta tanka ƴar uwarta, ita
TAIMIYYAH wulaƙanci da ƙasƙanci ne bata buƙata, sabida tun daga yanayin kallon tsanar da
Suhailah ke mata, ta gane cewa ba irin wacce za ta shigewa bace, shiyasa daga gaisuwa bata ji
akwai abinda za ta iya ɗaurawa akai, don gujewa cin fuska da gorin halitta, don ta fahimci akwai
take-taken hakan daga Suhailar.
Suhailah ita ta yi saurin shiga front seat ta kame sai TAIMIYYAH ta shiga back seat, tana sakin
ƙaramin murmushi don ita wani abin idan Suhailar ta yi mamaki ta ke bata. A. Maleek Ado da zai
yi driving ɗinsu da kansa ya ja motar bayan ya saita mirrow ɗin motar yadda zai dinga ganin
TAIMIYYAH da kyau, wacce ta lafe a back seat ɗin tana cigaba da karatun novel ɗinta hankali
kwance......✍🏻
#Ɗansabo ce#
[12/15, 11:46 AM] +234 703 040 9541: Littafin TAIMIYYAH paid book ne,ga duk wanda ta
tsincesa a kowani irin group ne,kiji tsoran Allah karki karanta sai kin biya 500 naira only.
Za ku iya min magana ta wannan number ɗin 08167768704, ko kuma ku turo kuɗin ku kai tsaye ta
wannan account ɗin 0504192664 aisha ibrahim dansabo GTbank.*
Masu turo credit za ku turo katin MTN na 500 ta wannan line ɗin 08167768704.
_Ina ƴan kasuwa masu buƙatar a tallata muku hajar ku? Maza ku garzayo da kuɗi ƙalilan a tallata
muku kayan siyarwanku sai dai kawai ku ji ana kiran waya don buƙatan sayan kayan ku,ku
tuntuɓeni ta layina kamar haka 08167768704._
*82*
*Gyallesu, Zaria.*
Umma ce kalmashe a gaban Baba Sani bayan kammala yin breakfast ɗinsu, waya ya ke yi ita
kuma ta maida hankali akan TV da ke kunne badon hankalinta na kan abinda ke wanxuwa cikin
TV ɗin ba, sabida burinta kawai ya gama wayar ta fara gwada sa ar ta don jiya bata samu zantawa
da shi da dare ba.
"Baban Basmah wani magana na ke ta ji yana tasowa, shi ne na ce ni dai ba zan gasgata kowa ba
sai na ji daga gareka."
Umma ta yi maganar idanunta akan Baba Sani da ya kammala yin wayar, ya maido hankalinsa
gareta sabida yadda ta kwantar da murya tana magana, jin ta dakata da alamu tana son jin ta
bakinsa ne sai ya ce, "Wani magana ki ka ji Zuwairah?"
Umma ta sake nutsuwa sosai tare da kwantar da murya ta ce, "Ji na yi wai za ka sake aure, shi ne
abin ya ɗaure min kai don dai na san da gaske ne, ni ya kamata na fara sanin hakan ba wai in tsinci
magana a gari ba. Da gaske Baban Basmah kai ne za ka yi auren ko kuma auren Sadeeq ne ake
jujjuya zancen ana cewa kai ne za ka auro min abokiyar zama?"
Umma ta kai ƙarshen maganar da tambayarsa tana sake aro jarumta da nutsuwa ta sanyawa kanta,
Baba Sani ya dubeta da kyau kafin ya saki ƙaramin murmushi ya ce, "Zuwairah a bakin wa ki ka
fara jin wannan jita-jitar?"
Umma sai ta rasa abin cewa don kuwa bata san a wajen wanda za ta ce ta ji wannan maganarba,
sabida babu wanda ya tare ta da magana akan wai Baba Sani zai sake aure, a bakin Boka Kallah
kawai suka ji hakan, ganin yadda ya tsareta da ido yasa ta tsuke fuska ta ce, "Maganar duniya ai
bata ɓuya Baban Basmah, kuma shi ƙarin aure ai lokaci ne amma ni abinda na ke son ji kawai shi
ne da gaske ne ko bada gaske bane?"
"Da gaske ne Zuwairah tabbas zan ƙara aure, dama ina shirin nufarki da maganar cikin wannan
satin."
Baba Sani ya yi maganar idanunsa akan Umma,wacce zallar kaɗuwa ya sanyata zubar da duk wani
jarumtar bogi da ta ara ta yafa, cikin rawar murya ta ce, "Da gaske ne Baban Basmah amma shi ne
ka kasa sanar dani hakan, sai da na tsinto maganar daga waje, wace ce wacce za ka aura ɗin tuh?"
Baba Sani ya ɗan haɗe fuska yana duban Umma da wani irin kallo ya ce, "Zuwairah ba wai na
ɓoye miki maganar bane sabida abin ne zai zo da gaggawa, kuma maganar wace ce duk ba
huruminki bane, za ki sani idan lokaci ya yi abinda kawai na ke so ki sawa ranki shi ne, aure
lokaci garesa kuma ina fata za ki goya min baya ku zauna lafiya, duk da cewa ba waje ɗaya za ku
zauna ba ita zan tafi da ita can Kano ne."
"Kutumar ubancan kai!!! Sani kasan me kake faɗa kuwa, kana nufin ni zaka bari a Zaria zaman
jiran gida, ka ɗauki Amarya ka maida kusa da kai kuna holewarku ni ina zaman jira sai weekend
ya zo ka leƙo ka koma?"
"Haka na ke nufi Zuwairah kuma babu wanda ya isa ya sauya hakan, tun da fari babu yadda ban yi
da ke akan mu tattara mu koma can da zama ba, amma kika nuna cewa ke ba za ki iya zama da
kanawa ba kin fi son zaman Zaria. Don haka a yanzu ma ba za ta canza zani ba, anan ɗin za ki
cigaba da zama."
Umma da ta tsurawa Baba Sani ido tana jin tamkar ta fasa ihu sai ta yi ƙoƙarin danne zuciyarta,
sabida tunowa da huɗubar Hajiya Barirah da ta yi, ta buɗe baki cikin son danne zuciyarta ta ce,
"Ni yanzu abinda ya fi damuna wace ce budurwace ko bazawara?"
"Bazawarace Zuwairah sanin wace ce ita idan kin kwantar da hankali nan da lokaci kaɗan za ki
sani."
Daga haka Baba Sani bai sake buɗewa Umma komi ba, duk iya nacinta akan ta san ko wace ce
wacce zai aura da kuma sanin yaushe ne auren ya ƙi bata damar hakan, daga ƙarshema sai ya tashi
ya ce mata fita zai yi zuwa can Fam House ɗin su.
Yana barin gidan Ummah ta ƙule a ɗakinta ta kira layin Hajiya Barirah, ta zayyane mata yadda
suka yi da Baba Sani ta ƙare maganar da cewa, "Hajiya Barirah tabbas kwanan nan hawan jini zai
mun mummunar kamu, domin bana iya bacci sabida ruɗu da shiga tashin hankali, na rasa da wani
kalar masifan zan ji, da ta ƴaƴa ko ta Sani da ƙarin aurensa? Duk iya yadda na yi akan ya sanar
dani ko wace ce wallahi kaucewa ya yi, sannan babbar tashin hankalina shi ne tafiyar da zai yi da
ita can Kanon, Hajiya Barirah ki dubi girman Allah ki sanar da ni menene mafita ?"
Hajiya Barirah daga ɓangarenta ta ja numfashi ta ce, "Hajiya Zuwairah har kullum ina sanar da ke
illar gaggawa a yayinda da ka ke son lamura su daidaita, ko ka gano bakin zaren wani abu da ka
ke so. Ki sanya nutsuwa ki cigaba da bin sa a hankali, ko kaɗan kada ki nuna masa hankalinki ya
tashi da zancen aurensa, maganar tafiya da ita can in da yake aiki kuwa, ni banga abin tashin
hankali ba su tafi ma bangon duniya, ke dai idan akai aikin da zai dawo tafin hannunki ba
shikenan ba."
Umma ta numfasa tana cigaba da sauraren Hajiya Barirah, wacce ke cigaba da bata shawarar
yadda za ta kwantar da hankalinta, har zuwa lokacin da za su gano wace ce Baba Sani zai auro
ɗin.
Lokacin da suka gama waya da Hajiya Barirah ne ta kira layin Zuhurah amma wayarta a kashe, sai
ta dafe goshinta tana jin zuciyarta na sake ɗaukar zafi. Gaba ki ɗaya bata san yadda za ta kwatanta
irin ruɗanin da ta ke ciki ba, burinta kawai ta san wace ce ke shirin kutso kanta cikin rayuwarta da
gaggawa haka?
Misalin ƙarfe uku na yammah Ummah na zaune tare da wata maƙwafciyarsu, wacce suke business
ɗin siyar da atamfofi tare me suna Hajiya Jummai, sai ganin shigowar Zuhurah suka yi kamar
daga sama.
Ummah ta yi saurin tashi tsaye a firgice tana sauke idanunta akan Zuhurah da ke janye da ƙatuwar
luggage, duk fuskarta ya koɗe ta yi wani firgai-firgai alamun tana cikin rashin kwanciyar hankali,
ta buɗe baki ta ce, "Zuhurah sannu da isowa."
Umma ta yi maganar tana son ɓoye tashin hankalinta don gudun kada Hajiya Jummai ta fahimci
wani abu, Zuhurah da ta fahimci in da Umma ta dosa sai ta saki murmushin ƴaƙe ta ce, "Umma
sannunku mun iso a gajiye ne bari in shiga daga ciki, Hajjaju ina yini mun sameku lafiya?"
Hajiya Jummai da ke bin Zuhurah da kallon ƙurillah ta amsa gaisuwar da fara'a tana cewa,
"Amarya ce a gari haka sannu da zuwa barka da hanya."
Zuhurah ta amsa tana cigaba da jan Luggage ɗinta ta nufi hanyar corridor ɗin da zai sadata da
ɗakinsu, Ummah ta rakata da ido kafin ta maido dubanta kan Hajiya Jummai tana ƙaƙaro
murmushi ta ce, "Hmm! Yaran yanzu dai basa son zaman gidan miji idan ba suna tare da juna
bane, wai tafiya ce ta kama shi zuwa wata ƙasa shine ta matsa sai dai ta dawo gida kafin ya dawo,
tunda tafiyar ta zo daga sama ne babu yadda za a yi su wuce tare. Na ce ta yi zamanta ko ƙannin
mijin ne sai ta roƙa a tura mata su gidanta su tayata zama, amma kin ga sai da ta kamo hanya ta
dawo gidan dai."
Hajiya ta saki murmushi ba don ta yadda da abinda Umma ta faɗi ba ta ce, "Allah sarki kin san
kowa da irinsa ne, ita me ƙawazucin gida ce shiyasa, Allah ya dawo da shi lafiya aiba wani abin
aibu bane."
Daga haka Ummah ta ɓatar da maganar suka koma tattaunawa akan kayan da za a turo musu cikin
satin da za a shiga, rabin hankalin Ummah na ga Zuhurah duk ta ƙosa Hajiya Jummai ta tashi ta
bar gidan.
Lokacin da sukai sallama da Hajjya Jummai ta tafi, cikin sauri Umma ta nufi ɗakin su Zuhurah
zuciyarta na sake ɗaukar zafi.
A tsaye ta samu Zuhurah har ta fara jere kayanta cikin sif ɗinta, Umma ta zauna daga bakin bed
tana cewa, "Yanzu Zuhurah sai da kika taho bayan na ce ki zauna mu ga abinda zai iya yuwuwa,
kin fi so mu ji kunyar maƙiya kenan?"
Zuhurah ta dakata daga shirya kayan ta tako xuwa bakin bed ɗin ta zauna, ta dubi Umma cikin ido
ta ce, "Ummah gara in ji kunyar jama'ar duka duniya da in cigaba da zama da Ameeru, don Allah
ki dubi yadda na koma kwana takwas kawai da kaini gidansa. Tun da aka kaini kwanaki biyu kacal
na yi cikin farin ciki yana tarairayata, shi ma don yasan ya rabani da budurcina ne ya dinga rawar
ƙafa, amma duk sauran kwanakin na yi su ne cikin ƙunci da tashin hankali, sabida sai ya shawo
giyarsa daga waje zai shigo min a buge, kuma da zaran giyar ta sake sa akaina zai ƙarar da kuzarin
da ya rage masa, da na yi magana ya ce zai doke ni,don haka ni kam ba zan iya wannan rayuwar
ba Umma, sannan babbar abinda yasa na tsani Ameeru ya fita a raina shi ne, ba yaron Honourable
bane ba a ma san cikakken asalinsa ba, ɗan me shara da wanke-wanken gidan ne, tsabagen samun
waje ne ya ke abu tamkar ɗan cikin gida, sabida ya ga Allah bai ba Honourable ɗin haihuwar ƴaƴa
maza ba, shiyasa uwargidarsa ta riƙesa tamkar ɗan cikinta, tana ɗaure masa gindi yana famtamawa
tamkar ɗan mai gidan. Ba zan taɓa cigaba da aurensa ba ko a kotu ne sai ya bani takardata Umma,
gara mu ji kunyar koma su waye da in cigaba da zama da shi rayuwata ta lalace."
Zuhurah ta kai ƙarshen maganar zuciyarta na sake ƙeƙashewa da jin tsanar Ameeru me tsanani,
Umma da ta zura mata ido ita ma nata zuciyar ce ke sake cika da tarin baƙin ciki da jin tsanar
Ameerun me zafi, sabida yadda ya rufesu a baibai bai taɓa sanar da su koda wasa, cewa bashi da
wata alaƙa ta jini da Honourable Attah ba.
Ta buɗe baki ta ce, "Shikenan Zuhurah sai ki share ɗaki ki ɗauki aniyar zaman zawarci, ki kuma
jirayi hukuncin da Babanku zai yanke idan ya ce ki koma kin ga dole ki koma ɗin, ni ma yanzu
haka ina cikin masifar tashin hankali akan maganar auren da uban naku zai yi ne."
Umma ta kai ƙarshen maganar tana ji zuciyarta na mata wani irin nauyi, sabida yadda wani abu ya
taso ya danne zuciyarta. Zuhurah ta miƙe tana nuna rashin kulawa da abinda Umman ta faɗi, ta
cigaba da shirya kayanta tana ji a ranta cewa ko sama da ƙasa za su haɗe, bata ga wanda ya isa ya
sata komawa ta yi zaman aure da Ameeru ba, cutarta ne ya riga ya gama tunda ya rabata da
budurcinta, ya kuma more ta yadda ya ga dama cikin kwanaki bakwai ɗin da tayi tare da shi.
Umma ta miƙe ta baro ɗakin tana jin kanta na mata nauyi, har wani jiri ta ke gani kafin ta kai
kanta ɗaki, ta zube bisa bed tana son yin kuka ko za ta ji sauƙin nauyin da zuciyarta ta yi, amma ta
kasa kukan sai ta kwanta lamo tana kai hannu ta dafe saitin zuciyarta.
__________
*Abuja.*
Tun wajen azuhur su TAIMIYYAH suka dawo daga yin shopping ɗin da suka fita, sabida Maleek
ya kasa jurewa zagawa da su wurare sosai,don ya saba Suhailah da driver ya ke haɗa ta ko ita ta
fita da kanta tunda ta fara sanin kan gari sosai.
TAIMIYYAH kwanciya ta yi bayan ta yi sallah sun yi lunch tare da juna,bata jima can da
kwanciya ba bacci ya sace ta sai wajen la'asar ta tashi, shi ma ringing ɗin wayarta da ke kusa da
kanta a gefen pillow ne ya tashe ta. Ta tashi zaune tana murje idanunta ta janyo wayar don ganin
me kiran, ganin sunan Ummie ne yasa ta saurin ɗaga wayar tare da sanya shi a speeker.
Muryar Ummie ya ratsa kunnuwar TAIMIYYAH, sai ta saki murmushi tana bai wa Ummie amsa
da cewa, "Lafiya lau Ummie i miss u so much!"
Ummie ta saki murmushi daga ɓangarenta kafin ta ce, "Miss u too Zaynabb ya amarci?"
TAIMIYYAH kunya ya kamata sai ta kasa bata amsa ta kauda maganar da cewa, "Ummie an
tsaida ranar ɗaura auren ne da Baba Sani?"
Ummie ta ce , "An tsayar daughter shiyasa na kira in miki albishir kafin Iyah ta rigani, next week
Saturday za a ɗaura auren da tariya baki ɗaya."
TAIMIYYAH ta saki wani ƙaramin ihun murna kafin ta ce, "Wow! Allah ya kai mu ya tabbatar da
alkhairy Ummie, gaskiya na ji daɗin jin wannan daddaɗan labarin."
Daga haka suka ɗan taɓa hira wanda duk rabi akan auren Ummien da Baba Sani ne, kafin suyi
sallama da juna TAIMIYYAH ta miƙe ta nufi toilet don ɗaura alwala ganin time ɗin sallar La'asar
ya yi.
Bayan ta idar da sallar ne ta yi zaune akan sallayar ta fara karatun Qur'ani cikin ƙira'arta me
matuƙar daɗi da sanyi, tana cikin karatun ne kuma A.Maleek Ado ya shigo cikin ɗakin, ya nufi kan
gadonta ya zauna yana me zuba mata ido da sauraren ƙira'arta mai matuƙar daɗi, wanda duk
lokacin da take karatun a gabansa zuciyarsa narkewa ya ke sake yi a kanta.
Sai da ta kai ƙarshen suratul Ahqaf da ta faro sannan ta tashi tana zare Hijab ɗin jikinta, ta
waiwaya tare da sauke manyan idanunta a kansa, ta cigaba da takowa zuwa garesa. Daga bakin
bed ɗin ta zauna nesa da shi ta ce, "Thank u Hubby!"
Maleek ya sake tsareta da ido kafin ya ce, "For what?" TAIMIYYAH sai ta ɗan shagwaɓe face
tana nuna masa ƙatuwar ledar shopping ɗin da suka yi, wanda duk rabin kayan ciki ne shi ne ya
zaɓar mata don ita kasa ɗibar komi ta yi, don bata ga abinda ta nema ta rasa ba shiyasa kawai ta
ɗibi su choculate kaɗai, da wasu irin crakers biscuit, shi ne ya dinga kwasar mata duk abinda ya yi
masa. Ya saki smile yana matsawa kusa da ita tare da haɗe gaf ɗin da ke tsakaninsu ya ce, "Okey
ni ba irin wannan godiar na ke so ba Sweet,bari ki ji irin wanda na ke so....."
Ya kai bakinsa bisa kunninta ya raɗa mata kalaman da ban san me ya faɗi ba, ni dai kawai gani na
yi TAIMIYYAH ta yi saurin kai kanta bisa ƙirjinsa tana ɓoye fuska, ya ɗago face ɗinta yana sake
narkar da zuciyarta da salon smile ɗinsa, ya kai bakinsa ya sumbaci bakinta zuwa idanunta ya ce,
"My pure zuma wannan haɗin fruit salad ɗin na ke son sha anjima, zan turo Ameena ki sanar mata
ingredient ɗin da ake buƙata na haɗin zoɓon da ki ke sawa a ciki, tunda akwai fruit kin ji?"
TAIMIYYAH ta gyaɗa masa kai ta ce, "Babu abinda za a nemo na zo da zoɓon ai da duk
abubuwan da zan iya buƙata, gasu can cikin waccar bag ɗin ban san inda zan aje su bane kawai."
Yadda ta yi maganar a shagwaɓe ya sanya Maleek sake bata peck a goshi kafin ya ce, "Alright bari
Ameena ta zo ta kai kitchen, zuwa an jima sai ki same su a kitchen su nuna miki komi da in da za
su aje miki kayayyakin."
TAIMIYYAH ta ce , "Okey tuh!" Maleek ya miƙe yana tada ta tsaye ita ma ya ce, "Wife ki daina
zama ke kaɗai a ɗaki ki saki jikinki gidan mijinki ne, ki fita ki zaga duk in da ki ke son shiga bana
son wannan noƙewar da ki ke yi, gobe zan je wani taron Meeting a Lagos duk da ina hutu ne,
amma dole zan halarci zaman ina ga tare zamu wuce don bazan iya bari kwananki ya ƙare bamu
tare ba,tunda gobe ke ce dani ko Sweet?"
TAIMIYYAH ta gyaɗa kai a kunyace tana jin wani matsanancin shauƙi na dabaibaye zuciyarta,
Maleek ya kama hannunta suka fito zuwa falo ya zaunar da ita cikin seater, yana ɗaukar remote ya
kunna TV tare da saita channel ɗin zuwa Bollywood. Ya ɗago ya dubi TAIMIYYAH da ke faman
ɓata fuska don ita tafi sha'awar zaman ɗaki ta yi karatun novel ɗinta, hakan ya fi mata akan ta
dinga haɗuwa da matarsa tana jifanta da mummunar kallon tsana.
Maleek ya furta hakan yana nufan hanyar da zai kai shi upstairs, TAIMIYYAH ta raka shi da ido
kawai tana ji kamar ta gudu ta koma zuwa ɗaki.
Daga can upstairs kuwa Suhailah ce ke kwance suna vid call da Meenah Wazeer, ƙawarta ta amana
wacce ta ke yadawa ta kama marasa man kai sai lamura sun kwaɓe mata tafi tunawa da ita. Ta
dubi Meenah da ke bata shawaran fara manyan business tunda Maleek ba zai amince da aiki ba ta
ce, "Meenah ni babbar damuwata da wannan gurguwar tasa yarinyar idanunta tamkar a buɗe suke,
kin ga yadda wai ta iya janye hankalinsa da salon shagwaɓarta ne ? Ga shegen kyau kamar ita tayi
kanta wallahi.Ina jin tsanarta da kishinta me zafi a raina ban san meyasa Maleek ke son lallai sai
mun haɗa tafiya tare ba, idan honeymoon ya ke son zuwa su tafi can wata ƙasa mana bayan mun
dawo."
Suhailah ta kai ƙarshen maganar cike da ƙorafi, Meenah ta saki dariya ta ce, "Easy ƙawata ni duk
ban ga abin damuwa ba tunda kowa sabgarta za ta yi, babu wacce za ta zauna akan ƴar uwarta.
Suhailah na faɗi miki dole ki koyi danne duk wani zafin kishinki, da ɗauke kai a lamuransu
matuƙar kina son siyawa kan ki girma da daraja a idanun Yarinyar, tunda ba sa'arki bace kin
girmeta ko a shekaru, so kar ki bari ta gane cewa kina da zafin kishi a kanta, in ba haka ba da
gayya za ta dinga yin abinda zai dinga ƙona zuciyarki. Mu mata wani lokacin mu ke fara bada
kafar da kishiya za ta raina mu, idan kika iya riƙe kanki da ɓoye zafin kishi, ki ka kama girmanki
za ki ga babu ta yadda kishiya za ta samu kafar rainaki, mussamman ke da A.Maleek bai bada
wata kafar da raini zai shiga tsakaninku ba.So ki iya takunki ki ɗauke kai daga duk wata soyayya
da tarairayar juna da zaki gani, dama shi namiji idan ya yi sabon aure duk son da ya ke miki dole
sai kin yi haƙury, tare da bashi time kafin ya dawo gareki da nutsuwarsa baki ɗaya.Ki maida kanki
very busy ta hanyar fara business, duk wani zafin kishi zaki ragesa da zaran kun raba gari ma
shikenan, sai kin so ki dinga tuna cewa kina da kishiya, musamman da zai kasance ke ce tare da
shi koda yaushe, ita sai weekend ko wani abu ya kai sa Abuja za su dinga zama da juna, so me zai
dameki idan ba kin so sanya kanki a damuwa ba Suhailah?"
Meenah ta kai ƙarshen maganar tana sakin smile da kallon yadda Suhailah ta nutsu tana
saurarenta, Suhailah ta ɗan ɓata face ta ce, "Shikenan Meenah zan gwadayin duk abinda ki ka ce,
duk yadda ta kasance za ki jini, na gode da shawarwarin da ki ke bani, tabbas ke ce ƙawa ta gari
ba irin su Jawahir ba."
Meenah ta sake sakin smile ta ce, "Kar ki damu Suhailah ai mun zama ɗaya, tun farko ke ce ki kai
baya dani ki ka kama ƙawaye masu buɗewar ido, amma ina sake gargaɗinki da ki sake kulawa ba
ko wace mace bace zata ƙulla ƙawance da ke, ta zama me ɗauraki akan turba nagari, kuma nagarin
su ne sukai ƙaranci cikin wannan zamanin."
Daga haka Meenah ta cigaba da yiwa Suhailah faɗa akan illar sakacin da ta ke dashi, wajen saurin
yarda da mutane har ta ding buɗe musu sirrikanta, Suhailah ta dinga ma Meenah godia tare da bata
tabbacin za ta kula, daga haka su kai sallama da juna daidai lokacin da Maleek ya turo ƙofar
ɗakinta ya shigo.
Ya sauke manyan idanunsa akan Suhailah yana takawa zuwa cikin ɗakin, ya tsaya daga bakin bed
ɗin da ta ke kwance ya ce, "Suhailah ya kamata a ce kina sauka downstairs ku yi hira da Zaynab
don ku saba da juna, ni ban ce lallai dole sai kun yi mu'amala da juna tamkar qawaye ba, but bana
son kuma irin wannan rayuwar na basar da juna, musamman ita da ta ke matsayin baƙuwa, ba
rayuwa za ku yi dindin ba yamakamata ki sake mata, ta ji daɗin zama da ke bawai ki dinga nuna
mata halin ko in kulaba.Ina kula da duk irin kallon ƙasƙancin da ki ke mata, ki ji tsoron Allah
Suhailah idan akan laluranta ne ba wai kin fita gata bane a wajen Allah, da ya yo ki a mai lafiyan
ƙafafu, ita kuma ya jarabeta na nakasa. Don haka ki shiga hankalinki kada ki bari zafin kishi da
shaiɗan su kai ki su baro, don haka ki shiga hankalinki tare da kama girmanki, don bazan ɗauki ko
wane irin nonsense ba akan matata. Dukkaninku ina son ku kuma kowacce da irin matsayin da
take dashi a zuciyata. Zaynabb bata da damuwa idan har kika kama girmanki za ku zauna lafiya,
daga nan har mu je mu dawo kowacce ta zauna a muhallinta, bana so wata matsala ya fara ɓullowa
daga gare ki, ita ma kuma ina sanya idanu a kanta, da zaran na ga ba daidai ba za ki ga matakin da
zan ɗauka, so ki kula ki kama girmanki wannan kallon ƙasƙacin da nuna ƙiyayyar da ki ke mata ki
daina bana so, if not za ki ga order side ɗina da baki taɓa gani ba wallahi!"
Maleek ya kai ƙarshen maganarsa cike da gargaɗi, Suhailah da maganganunsa suka shigeta tare da
sanya jikinta yin sanyi,sai ta rewace da bashi haƙury ,don ita bata taɓa kawo cewa yana kula da
yadda ta ke bin matarsa da kallon tsana ba.
Ya fara takawa don barin ɗakin ya ce, "Ki sameni a downstairs mu zauna tare kafin magrib, ita ma
gata can na sanyata fitowa, don bana son ɗayanku ya dinga takura kansa akan ɗan uwansa, sabida
kishin banza kishin da zaku yi, shi ne ku faranta min rai da bani nutsuwa ta yadda zan ji daɗin yin
adalci a tsakaninku."
Daga haka ya ƙarisa fita daga ɗakin ya bar Suhailah da bin bayansa da kallo, kafin ta nufi bakin
mirrow ta sake fesa turare ta fito ta nufi downstairs.
Tun daga nesa take hango yadda Maleek ya manne a jikin TAIMIYYAH, wacce ke faman zuba
masa shagwaɓa akan ya tashi daga wajen, kafin Suhailah ta sakko ta gansu a haka alhali ba ranar
ta bane. Amma sai A.Maleek ɗin ya yi biris da ita,sai ma sake shinshinar ƙamshin Humrar RUSS
da ta fara amfani dashi daga jiya ya ke, wanda ƙamshin baƙaramin narkar da zuciyarsa ya ke ba.
Jin takun takalman Suhailah da ke sakkowa daga stairs ya sanya TAIMIYYAH saurin ɗaga
manyan idanunta ta dubi side ɗin, ta yi saurin maido dubanta zuwa ga A.Maleek wanda ya yi
tamkar bai jiyo sakkowar Suhailah ba, ta narke murya tana ture hannunsa daga jikinta ta ce,
"Please Hubby ka tashi ka koma seat ɗin can, gatanan fa ni dai babu ruwana kuma hakan babu
kyau, tunda ba kwana na bane please ka tashi kafin ta ƙariso!"
Yadda TAIMIYYAH ta yi maganar duk a daburce, idanunta na haskawa da zallar rashin jin daɗin
abinda ya ke yi, ya sanya Maleek dungure mata goshi yana tashi daga cikin seater ɗin, ya koma
ƙasan carfet ya zauna yana wani miskile fuska.......✍🏻
#Ɗansabo ce#
[12/15, 11:46 AM] +234 703 040 9541: *83*
Tunda TAIMIYYAH ta gama haɗawa A.Maleek Ado fruit salad ta saka a cikin fridge, ta koma
ɗaki ta don ɗaura alwalar sallar Magriba da time ya yi.
Bayan ta idar sai da ta tsaya yin karatun Qur'an har time ɗin Isha'i ya shiga ta bada faralinsa,
sannan ta tashi ta nufi bathroom don yin wanka. Lokacin da ta fito a gaggauce ta kammala
shiryawa cikin kayan bacci, riga da wando marasa nauyi da suka fitar da surarta a zahiri. Rigar irin
me shara shara ne daga wuya zuwa ƙirji, sai daga ƙasa ya zama silk, hakan yasa tun daga
kafaɗunta zuwa ƙirjinta a fili suke, don babu maraba da babu riga a jikinta. Wandon shi ma silk ne
wanda ya bi jikinta ya yi mata kyau matuƙa, sai ƙamshi ta ke zubawa kamar yadda ɗakin ke fidda
ƙamshi me kwantar da zuciya. Ta ɗauki remote ɗin AC ta ƙara ƙarfinsa sabida zafi ake yi a garin
Abuja, an rabu da yin ruwa kamar yadda ta ji Suhailah na faɗiwa Maleek a ɗazu.
Direct gado ta nufa ta shige cikin duvet don tasha alwashi cikin zuciyarta cewa, ba za ta halarci
wajen cin abincin ba a daren yau, sabida sam bata son irin yadda Suhailah ke shigewa Maleek,
tare da yi masa abubuwan taɓara don kawai ta ƙuntata zuciyarta.
Sai ta kunna data tana hawa online ta fara karatun novel wanda yanzu ta ƙware, tana kuma ƙaruwa
sosai tare da ɗaukar darusa masu tarin yawa.
Shigowar kiran A.Maleek cikin wayarta vid call yasa ta dakatar da karatun ta ɗaga kiran, tana me
narke fuska da muryarta baki ɗaya lokacin da fuskokin junansu ya bayyana a allon screen ɗin
wayoyinsu. Maleek Ado da ya kafeta da ido ne ya rigata cewa, "Wife baki fito ba muna jiran ki
kiyi serving ɗin mu dinner."
TAIMIYYAH ta zame duvet ɗin da ta rufa ya yi ƙasa, ta sake narke murya da yatsine fuska ta ce,
"Sorry Sweet kaina ke ciwo sosai, ba zan iya fitowa ba."
Yadda ta yi maganar tana shirin sanya masa kukan shagwaɓa, ba ƙaramin motsa zuciyar Maleek
ya yi ba, ya waro idanunsa waje cike da zallar damuwa akan face ɗinsa ya ce, "But shi ne ki ke
kwance ba za ki kira ni a kawo miki magani ki sha ba Luv? Gani nan kawo miki abincin da
magani."
Daga haka ya kashe wayar yana maida dubansa kan Suhailah,wacce ta tsaresa da idanunta tun fara
wayarsa da TAIMIYYAH, ya miƙe daga tsaye yana ɗaukar plate don zubawa TAIMIYYAH abinci
ya ke cewa, "Suhailah kina iya zuba abincin ki fara ci kafin in dawo, Zaynab ce kanta ke ciwo ba
za ta iya fitowa ba, so zan kai mata abincin ɗaki, yanzu fara ɗakko min maganin ciwan kai da
table water mara sanyi."
Daga haka ya cigaba da zubawa TAIMIYYAH Jallof ɗin couscous da aka dafa shi ya ji kayan
lambu da liver, sai ya zuba mata haɗin chicken salad da yaji salad cream. Suhailah ta taɓe baki
tana tashi ta je ta ɗakko maganin ta kawo masa, ya haɗa da abincin ya nufi ɗakin TAIMIYYAH.
Da kansa ya bata abincin a baki sai faman narke masa da shagwaɓa take yi, kai ka ce da gaske kan
nata ciwo ya ke yi sosai. Bayan ta ƙoshi ne ya bata maganin ta sha sannan hankalinsa ya kwanta,
ya kai baki ya sumbaci goshinta yana faɗin, "Sorry my pure zuma, ciwan kan zai ta fi soon kin ji
ko?"
A.Maleek ya zaunar da ita akan bed yana cewa, "Kar ki kwanta yanzu please har abincin ya faɗa
miki sosai, and u make sure idan kan bai daina ciwo ba kin kira ni kin faɗa min okey!"
TAIMIYYAH ta gyaɗa masa kai tana jin wani nutsuwa da zazzafar ƙaunarsa na sake bin jinin
jikinta, A.Maleek ya sake sumbatan lips ɗinta kafin ya juya ya bar ɗakin don komawa zuwa dining
area ɗin.
Ya samu har Suhailah ta kusa ƙarasa cin abincinta, fuskarta ya cika ya yi fam da fishi da takaicin
irin daɗewar da ya yi a ɗakin TAIMIYYAH, daga cewa zai kai mata magani da ruwa kawai ya
dawo. Amma da ta tuna da shawarwarin da Meenah ta bata sai ta danne zuciyarta wajen ƙirƙiro
smile, tana duban idanun Maleek ɗin ta ce, "Ya jikin nata ?"
Maleek da ya ji daɗin kulawar da ta nuna ya maida mata martanin murmushin yana cewa, "Da
sauki it's just headache."
"Allah ya ƙara lafiya." Suhailah ta sake faɗi tana ture plate ɗin gabanta ta ɗauki cup ɗin da ta zuba
ruwa ta kai baki, A.Maleek ya amsa da cewa, "Ameen." Yana sauke idanunsa akan Suhailah da ta
miƙe don zuba masa abincin, sai da ya kammala ci sannan suka nufi upstairs zuciyarsa na ga
TAIMIYYAH.
Har sun yi shirin kwanciya ya sake ɗaga waya ya ji lafiyarta, sai da ta tabbatar masa cewa kan ya
daina ciwo sannan hankalinsa ya kwanta, har ya ji cewa zai iya jurewa ba tare da ya sake sauka
zuwa downstairs don duba lafiyarta ba.
Daga ɓangaren TAIMIYYAH kuwa chart ɗinta ta sha da su Yasmeen da Zee da suke online, sai
wajen 10:30pm ta yi sallama da su ta sauka online, ta je ta wanko baki tare da ɗauro alwala ta bi
lafiyar gado.
___________
Baba Sani ya sauke idanunsa akan Zuhurah bayan duk ya gama jin jawabin da Umma ta koro
masa, akan yadda aka yi Zuhurah ta zo garin da kuma abinda ta ke cewa a kan Ameeru ɗin.Ya
buɗe baki cike da zallar fushi da nuna ɓacin rai ya ce, "Zuhurah dukkanin abinda mahaifiyarku ta
faɗa kin tabbatar gaskiya ki ka faɗi, ko kuwa kin shiryo zancenki sabida ki watsa mana ƙasa a
idon duniya tare da janyo mana surutan jama'a? a ce kwana takwas da kai Yarinyar ɗakin miji ta
dawo gida ai wannan masifa ce, kin tabbatar duk abinda ki ka faɗi akansa gaskiya ne?"
Zuhurah ta jinjina kai alamun tabbatar da cewa hakan ne, Baba Sani ya sauke numfashi ya ce,
"Okey zan kira shi Ameerun tare da Honourable ɗin sai a zo a zauna, ga ki ga shi ga iyayensa a
daddale zance, kasancewarsa ɗan me aikin gida ba zai shafi aurenki da shi har a ce ya zama silar
mutuwar auren ba, sabida akwai mutane da yawa da suka rayu a doran duniya, ba tare da sun san
cikakken asalinsu ba sai na mariƙansu, don haka wannan ba aibu bane ko da ace shege ne shi,
tunda ba laifinsa ne na zamowarsa a shegen ba, haka ya buɗi ido ya gansa babbar aibun kawai shi
ne shaye-shayen da ya ke yi."
Baba Sani ya kai ƙarshen maganar yana me jin ɗaci a zuciyarsa, tabbas shi ma ya ji zafin yadda
Ameeru ya ɓoye asalinsa bai bayyana cewa shi ɗin ba ɗan Honourable Attah bane, duk da cewa
shi ba wannan ne damuwarsa ba, don baya cikin irin iyayen da ke bada auren ƴaƴansu don
kwaɗayin duniya, ko kuma don kasancewar wanda zai basu auren sun fito a masu arziƙi, ko sun yi
fice irin yadda Honourable ɗin ya yi fice a harkar siyasarsa. Abinda ya bashi haushi kawai ɓoye
gaskiya don ba a son ƙulla alaƙar aure da ƙarya da rashin gaskiya, domin zama ne ake son a yisa
na gaskiya da amana tare da yarda da juna.
Zuhurah ta sauke numfashi tana jin daɗin yadda Baba Sani ya gane cewa shaye-shayen Ameerun
zai iya zama babbar illar da zai kawo ƙarshen zamanta da shi, shiyasa lokacin da ya sallameta ta
miƙe da kuzarinta sosai, tana ji tamkar ta gama da rabin matsalarta ne akan Ameeru.Umma ta
rakata da ido tana jin ciwo da wani irin zafi a cikin zuciyarta me tsanani, sam bata so wani matsala
ya gitto a rayuwar auren ƴaƴan nata ba, domin akan TAIMIIYYAH ta lissafa aukuwan tarin
matsaloli su biyo baya a gidan aurenta, sai gashi tun ba a je ko'ina ba matsalolin sun ɓullo daga
nata ɓangaren ne bana TAIMIYYAH ba. Idanunta suka hasko mata irin tarin annuri da shauƙin
juna da ta gani akan fuskokinsu, lokacin da suka zo gaida Baba Sanin da yi masa sallama, wani
abu me girma da nauyi ya danne zuciyarta, tana ji tamkar ta saki ihu ko zata samu sauƙin irin
ciwon da zuciyarta ke yi.
Washegary Baba Sani ya samu iya da magana akan Zuhurah, tare da sanar da ita shawaran da ya
yanke na kiran Ameerun da uban riƙon nasa domin a zo a zauna. Idan har ya tabbata cewa
Ameerun na shaye-shaye tabbas ba zai tirsasa Zuhurah zama da mashayi ba, sai dai idan har ita ce
ta sakko da kanta ta nuna cewa ta ji ta gani za ta koma hannunsa.
Iyah ta numfasa tana jin ko kaɗan babu daɗi cikin zuciyarta, domin duk yadda su Zuhurah za su
lalace suna nan dai a matsayin jininta, kuma jikokinta da take jin ƙaunarsu har cikin zuciyarta. Ta
buɗe baki cike da nuna alhini ta ce, "Allah ya kyauta Sani, amma sam abu bai yi daɗi ba, tun asali
na ji ajikina cewa za a rina don ni kallo ɗaya na yi masa na sha jinin jikina, cewa baya cikin sahun
kintsatstsun samari, amma kasancewar ban isa da su ba kuma basa ganin girmana yasa na tsuke
bakina, don kar a ce na kore mata saurayi ɗan masu arziƙi. Yanzu Fisabilillahi ina ranar hakan ace
aure kwana takwas kacal amma matsaloli sun fara biyo baya? Allah ya yi mana mafita shi ne
kawai abin cewa."
Baba Sani ya numfasa yana jinjina kai ya ce, "Babu ranar hakan kam Iyah, kuma wallahi iya
bincike na sanya anyi akan yaron amma babu wanda ya ce an sameshi da wani hali marar kyau,
shiyasa abin ya ɗaure min kai da sani a damuwa!"
"Ahaf! Ai faɗin gaskiyar halayyar mutum a binciken aure yanzu ya yi matuƙar wahala Sani, ana
dai yi ne don a samu nutsuwar zuciya da sanya kyakykyawan zaton cewa naka ya zai dace da
gidan mutunci, amma babbar makamin binciken bawa a wannan zamanin shi ne addu'a, da kuma
zamowa me kyakykyawar zuciya, wanda baka nufin kowa da sharri sai alkhairy, to idan ka
kasance a hakan sai Allah ya dubeka ba zai sanya ka faɗa hannun banza ba sai wajen nagari,
amma ka gafarceni Sani ko wannan auren na Zuhurah ya mutu, ina so ka sanya a ranka cewa
shukan da Zuwairah ta yi ne za ta fara girbansa, kuma ramin da ta jima tana jinawan don ƴar wasu
ta faɗa ciki shi ne nata ƴaƴan za su rufta a ciki, domin babu yadda za a yi ka nufi ɗan wani da
sharri kai ka ce zaka ga alkhairy akan naka ƴaƴan, wannan ƙaryace wallahi domin Ubangiji baya
zalinci. Allah ya shiryar da mu ya gyara zukatanmu ya rabamu da hassada da yiwa juna mugunta,
ya maganar ɗaurin auren naku kai da Samha yana nan a asabar me zuwa ɗin?"
Iyah ta kai ƙarshen maganar da jefawa Baba Sani tambayar, wanda jikinsa ya mutu da kalaman
Iyah ya dube ta ya ce, "Eh! Yana nan Iyah an riga an tsaida magana za a ɗaura ɗin, zuwa sati me
zuwa a kawota nan Zaria, daga nan za mu wuce Kano tare,ina na so daga gobe a fara gyaran part
ɗin, don so nake yi ayi sabon fenti sai a maida kayan ciki tunda sabbi ne ba jimawa sukai can ba."
Iyah ta jinjina kai cike da gamsuwa ta ce, "To Allah ya kai mu ya tabbatar mana da alkhairy."
Baba Sani ya amsa da cewa, "Ameen." Daga haka ya yi sallama da Iyah ya baro part ɗin nata
zuciyarsa cike da begen son jin muryar Ummie, wacce tunda aka fara maganar aurensu wani
ƙaunarta me zafi ke bin jinin jikinsa.
___________
*Gonar Ganye.*
*Gidan Basmah.*
Kana sanyo kai cikin falonta za ka fara jiyo dararrakun ƙawayenta Sharifah da Amnah, waɗanda
sai yau suka sake waiwayota tun bayan da suka yo mata rakiya zuwa ɗakin nata.
Basmah da ke zaune daga kusa da Sharifah ta taɓe baki ta ce, "Yanzu Sharifah miye anfanin
wannan dararrakun da ku ke yi, matsalar da na ke ciki fa na ke sanar da ku. Yanzu Fisabilillah ya
dace ace uwarsa ta zo ta tare mana a gida daga yin aure, idan dawowa nan ɗin za ta yi gaba ɗaya ai
ba a irin wannan lokacin da mu ke buƙatan a barmu mu sakata mu wala za ta dawo ba, da na yi
magana sai Nass ya hauni da faɗa wai so na ke na kori uwarsa a gidansa ko me na ke nufi? Jiya
ma har zagina ya yi yana cewa idan na sake magana akan zamar uwarsa a gidansa sai ya bani
mamaki. Don Allah ku dubi yadda ko irin kyawun amarcin nan da ake yi ni ban yi ba, sabida bani
da kwanciyar hankali Sharifah, kullum cikin yi min gorin cewa ba zai taɓa so na ba sai dai na
zama sex machine ɗinsa, tun da na zaɓi aurensa har da masa asiri, ya kuma tabbatar min da cewa
ba don albarkacin irin soyayyar da ya yi wa TAIMIYYAH ba, wallahi sakina zai yi ya auro wacce
za ta iya maye masa gurbinta a zuciyarsa tun da ya riga ya rasata."
Basmah ta kai ƙarshen maganar cikin rawar murya, sabida ba ƙaramin zafi da ciwo kalaman Nass
ke mata a zuciyarta ba,sabida yadda ita take fama da zazzafar soyayyarsa amma shi sam bata
gabansa.
Sharifah da Amnah suka haɗa ido tare da sakarwa juna murmushi, kafin Sharifah ta dafa kafaɗar
Basmah ta ce, "Ayyah! Ƙawata gaskiya kina cikin garari domin na san illar ka so amma kai aƙi
sonka, domin na gama fahimtar ke ɗin ce baya so, kuma bana ji tunda bai so ki a waɗannan
kwanakin ba watarana zai zo da zai so ki ɗin, amma ina Bokan da ya yi muku aiki akansa wancan
lokacin?"
Basmah ta taɓe baki tare da jan ƙaramin tsaki ta ce, "Yana nan ƙawata sai dai daga shi har sabon
Bokan da Umma ta samo, duk bakinsu ya zo ɗaya, sun ce a yanzu babu wani aiki da zai yi tasiri
akansa, sabida waccar makirar uwar tasa na tsaye akansa ne yanzu, tunda daga ita har shi sun gano
cewa da asiri muka nemesa har ya amince da aurena."
Sharifah ta sake waro ido waje ta ce, "Kai! Gaskiya sunanki sorry Basmah, tunda har ku ka yi
saken da uwarsa ta gane kuna bin Bokaye, no wonder za ta kalmashe muku a gida taƙi tafiya,
gaskiya kina ruwa sai dai na ce Allah ya fiddo ki, ga dai guy har guy kin samu amma kuma babu
amfani, tunda sai dai ya kwanta da ke ya tashi, babu ƙauna da soyayyarki a zuciyarsa, anya
wannan ba hakkin gurguwar Yayar taki ba ce Basmah?"
Basmah ta yitsene fuska ta ce, "Don Allah sharifah ki bar ɗakko min wani ɓacin ran kina jibga
min, ki bar ni na ji da halin da na ke ciki idan ba za ku samar min mafita ba."
Wannan karon Amnah da bata tanka su ba sai wannan karon ta ce, "Basmah mafita ɗaya ki ke da
shi, shi ne ki tashi wajen ganin kin janyo hankalinsa da kyawawan ɗabi'u, ki kwantar da kai ki riƙa
yi masa biyayyah da girmama uwarsa, duk da dai ba za ki taɓa daraja a idonta ba, tunda ta riga ta
gane cewa ba don ɗanta na son ki ya auro ki ba aikin asiri ne. Amma shi biyayyah da kyawawan
ɗabi'u su kan saurin siyowa mace soyayyah a zuciyar namiji."
Basmah ta jinjina kai ta ce, "Hakane Amnah, ina ƙoƙarina akan hakan, amma kin san hali na ban
iya ɓoye ƙiyayyah ba, so a fili na ke nuna masa bani son uwarsa wallahi, sabida ba ƙaramin haushi
ta ke bani ba."
"Ai ko ba za ki taɓa samun kansa ba tunda ya san ciwo da zafin uwarsa, duk soyayyar da za ki
nuna masa, matuƙar za ki cigaba da nuna ƙiyayyah da rashin biyayyah ga uwarsa, wallahi ba zai
ƙaunace ki ba."
Cewar Sharifah kenan tana ballawa Basmah harara, Basmah ta gimtse fuska ta ce, "Hmmm! Ba za
ku gane yadda na ke jin haushinta bane, ta fiye takura da sanya ido hatta kallo fa a falon nan ta ke
yi da dare, duk ta bi ta kurani ina son yin shigar ɗaukar magana amma haka nan sai dai in bari sai
ta bar falon wajen 10 na dare sannan zan samu sakewa."
Kafin kowa ya ce komi cikin su Sharifah suka jiyo ƙauri na fitowa daga kitchen alamun girki ya
kama, hakan yasa Basmah tashi a guje ta nufi hanyar kitchen ɗin, tana zuwa ta tadda jallof ɗin da
ta ɗaura duk ya kama yana ƙauri. Shinkafar ta cika mata ruwa duk ta wani kwaɓe, ga uban kayan
jallof da ta jibga a ciki,ta ɓata fuska lokacin da ta ke juya shinkafar, ƙaurin da girkin ya yi ya haɗe
da ƙamshin uban currry da ta sanya, ya bada wani irin ƙamshi marar daɗi. Haka ta ɗakko cooler
ɗin da ta ke zubawa Nass abinci,ta zuba masa hakanan ba tare da damuwan cewa zai iya ci ko ba
zai iya ci ba. Ita dai kawai ta wuce wajen tunda ta yi girkin, ba zai dawo ya tadda bata yi ba, ta
samu babban plate ta zuba musu ita da su Sharifah, duk rabin naman da ke cikin abincin su ta
kwashewa.
Wani ƙaramin cooler ta ɗakko wanda ta ke zubawa Hajiya Hajara abinci a ciki, ta kwashe mata na
can ƙasa-ƙasan tukunyar, in da yafi fito da ƙaurin girkin ta zuba mata tana yi tana zaginta a
zuciyarta.
Lokacin da ta aje plate ɗin abincin a gaban su Sharifah, sai Amnah ta dubi jallof ɗin da ke surfa
uban ƙauri ta ce, "Basmah amma dai da faten shinkafa ki ka yi niyyar yi ko?"
Basmah ta ɓata fuska ta ce, "Wallahi ba shi na yi niyyar yi ba, na cika sanwar ne kin san bawani
iya girkin na yi ba,don ko a gida daga ni har Zuhurah sai ta ƙure za ki ganmu a kitchen, amma
yanzu dole na koya don Sweetyn nawa mayen girki ne, har da takaicin rashin iya girkin kuma ke
sake tunzura zuciyarsa a kaina. Kullum na aje abinci da ƙyar ya ke iya ci kusan duk da dare sai dai
ya yo mana take away a waje fa, muna ci ya danna min gori da baƙaƙen maganganu, kuma uwar
na ji wani bin tunda sai goma ta ke barin nan ta koma part ɗinta."
Sharifah ta jinjina kai ta ce, "Gaskiya Basmah lamuranki akwai gyara me tarin yawa a cikinsa,
dole ki tashi tsaye in ba haka ba nan da lokaci kaɗan za ki ga katin ɗaura aurensa da wata."
Basmah ta zaro idanu waje tana jin wani matsanancin tashin hankali na rufto mata ta ce, "Don
Allah Sharifah ki daina min wannan mummunar fatan, haba sai ka ce ke ɗin ba aminiyata ba me
ƙaunata haba don Allah!"
Sharifah ta saki smile kafin ta ce komi Nass ya doka sallama ya shigo cikin falon, hannunsa riƙe
da ledan fruit da siyo musu. Idanunsa ya sauka akan su Sharifah, waɗanda su ma jin muyarsa da
shigowarsa ya sanya su ɗago kai don ganinsa a zahiri.
Idanun Sharifah suka sarƙe da na Nass wanda shi ma nasa idanun akanta ya fara sauka, sabida ita
ce a farko Amnah na daga gefenta. Wani irin abu ne ya doka a zukatansu su duka biyun, Sharifah
na sake shigar da idanunsa cikin nasa tana ƙarewa kyawunsa da haɗuwarsa kallo. Sai ta ga gaba
ɗaya a fili ma yafi kyau da haɗuwa akan ganin da ta yi masa a hoto, gashi ƙananun kaya ne a
jikinsa na GUCCI da suka yi masa masifar kyau da fito da zallar ƙuruciyarsa.
Nass shi ya fara janye idanunsa daga kan Sharifah yana jin wani irin abu na tsaya masa a zuci,
Sharifah ganin ya fara taku don shigewa ciki yasa suka haɗa baki wajen gaida shi. Sai ya waiwayo
yana amsa gaisuwar ta su cike da basarwa, Basmah da tuni ta miƙe don rufa masa baya sam bata
kula da irin kallon da Sharifah ke biyo bayan su da shi ba.
"Kai! Amnah guy ɗinnan ya haɗu ba ƙarya, gaskiya Basmah ta samo miji na nunawa sa a amma
sai dai a banza tunda bata samu zuciyarsa ba."
Amnah da ita ma kyawun Nass ɗin ya tafi da ita ta jinjina kai ta ce, "Gaskiyarki ƙawata, guy ɗin
ya haɗu babu ƙarya, amma Basmah ta faɗo tunda bata gabansa."
Suka cigaba da gulmar Basmah ƙasa ƙasa, suna yi suna tsakalar jallof ɗin da sam bai musu daɗi ba
ko kaɗan, daga ƙarshema tashi suka yi tsam suka koma saman seater suna cigaba da hiransu.
Mintuna kusan goma da shigewar su Basmah da Nass cikin ɗaki suka fito, Basmah sai faman nane
masa take yi a jiki har suka isa wajen dining in da ta shirya abincinsa akai, ta yi serving ɗinsa
jallof ɗin da tunda ta ɓuɗe ƙaurinsa ya doki hancin Nass ɗin, ya zuba mata har ta turo abincin
gabansa bai ɗauke ido a kanta ba.
Basmah ta narke fuska ta ce, "Sorry Luv wallahi na cika ruwar sanwar ne, sannan muna can muna
hira da su Sharifah girkin ya kama shiyasa abincin ya yi ƙauri."
Nass ya sake kafe plate ɗin abincin da ido, kafin ya ja dogon tsaki ya ce, "Look Basmah! Ni fa ba
zan ɗauki wannan dabbancin ba, a ce mace har mace amma ba iya girki kullum da irin abinda za
ki faɗi."
Basmah dai ta taɓe baki zuciyarta na sake ɓaci da jin yadda Nass ke ta ɗaga murya,ta kuma
tabbatar su Sharifah na jinsa.
Ture plate ɗin abincin Nass ya yi bayan ya yi spoon biyu, gaba ɗaya ji ya yi ba zai iya cin abincin
ba. Ya dubi Basmah ya ce, "An kai wa Hajiya ne?"
Ta yi saurin girgiza kai ta ce, " Yanzu na ke son kai mata dai."
"Okay kar ki kai don ba za ta iya cin wannan shirmen ba, bari in je in yo mana take away kawai."
Daga haka ya nufi hanyar baro dining area ɗin Basmah na rufo masa baya, suna ƙarisowa cikin
falon su Sharifah na miƙewa tsaye. Basmah ta dube su tana cewa, "Sharifah ya dai na ga kun tashi
ba dai tafiya za ku yi ba?"
Sharifah ta wani kashe murya ta ce, "Aiko dai ƙawata tafiya za mu yi ,Amnah za ta yi baƙo zai iso
da la'asar."
Ta yi maganar tana satan duban Nass da ya yi gaba zuwa ƙofar fita daga falon, Basmah ta ce,
"Okey to bari kawai sweety ya sauke ku ko daga bakin hanya ne."
Basmah ta yi saurin yin gaba don tsaida Nass tana cewa, "Okey bari in gayo masa."
Lokacin da Basmah ta sanarwa Nass zai aje su Sharifah daga bakin hanya, bai musu ba ya ce su
fito hakan yasa Basmah komawa ta sanar da su Sharifah cewa su fito.
Tare suka fito da Basmah har zuwa wajen motar Nass, tana riƙe musu da babbar ledar da ta zuba
musu kayan kwalliya, na cikin lefen ta wanda sai sanda ta zo gidan Nass ya kawo mata su, tunda
sun hana akai kafin biki sabida tunda suka ga an kawo na TAIMIYYAH , suka san cewa ko an
kawo nasu ba zai isa a kallah ba.
"Sharifah ta buɗe front seat ta shige, ita kuma Amnah ta shiga back seat ,Basmah ta aje musu ledar
tana cewa, "To friends na gode da ziyara sai mun yi waya."
Daga haka su kai sallama da juna Nass ya ja motar yana jin wani irin feeling na jan zuciyarsa akan
Sharifah, Basmah ta juya zuwa cikin gidan zuciyarta na jaddada mata cewa dole ta tashi ta ko yi
girke-girken don birge Nass da sace zuciyarsa.
Nass daga can bakin hanya daidai makarantar Albani ya sauke su, sabida ba hanya ɗaya za su nufa
ba. Sharifah lokacin da ta sakko daga motar ne ta ɗaga ido ta dubi Nass ta ce, "To ogan Basmah
mun gode ko."
Nass ya zuba mata ido yana yaba kyawunta da cikar halittarta ya ce, "Okey! Ga wannan ku biya
kuɗin Napep ko."
Sharifah ta amsa kuɗin tana shirin rufe murfin motar Nass ya sake cewa, "Please ko za ki bani
phone number ɗin ki idan babu damuwa?"
Sharifah da ta ji wani yarr....! Sai ta dubesa da wani irin expression akan fuskarta ta ce, "Babu
damuwa bari in baka...."
Ta shiga karanto masa numbarta yana shigarwa a wayarsa, su kai sallama da juna ta yi gaba zuwa
in da Amnah ta yi tsaye tana jiran ƙarisowarta. Sam bata sanar da Amnah cewa Nass ya amshi
numbarta ba, sai kuɗin da ya basu 2k kawai ta nuna mata, suka tare abin hawa suka hau suna
cigaba da labari akan halin da Basmah take ciki a gidan Nass ɗin........✍🏻
Littafin TAIMIYYAH paid book ne,ga duk wanda ta tsincesa a kowani irin group ne,kiji tsoran
Allah karki karanta sai kin biya 500 naira only.
Za ku iya min magana ta wannan number ɗin 08167768704, ko kuma ku turo kuɗin ku kai tsaye ta
wannan account ɗin 0504192664 aisha ibrahim dansabo GTbank.*
Masu turo credit za ku turo katin MTN na 500 ta wannan line ɗin 08167768704.
_Ina ƴan kasuwa masu buƙatar a tallata muku hajar ku? Maza ku garzayo da kuɗi ƙalilan a tallata
muku kayan siyarwanku sai dai kawai ku ji ana kiran waya don buƙatan sayan kayan ku,ku
tuntuɓeni ta layina kamar haka 08167768704._
#Ɗansabo ce#
[12/15, 11:47 AM] +234 703 040 9541: Littafin TAIMIYYAH paid book ne,ga duk wanda ta
tsincesa a kowani irin group ne,kiji tsoran Allah karki karanta sai kin biya 500 naira only.
Za ku iya min magana ta wannan number ɗin 08167768704, ko kuma ku turo kuɗin ku kai tsaye ta
wannan account ɗin 0504192664 aisha ibrahim dansabo GTbank.*
*Sai ku tura shaidan biyanku ta wannan line ɗin 08167768704.*
Masu turo credit za ku turo katin MTN na 500 ta wannan line ɗin 08167768704.
_Ina ƴan kasuwa masu buƙatar a tallata muku hajar ku? Maza ku garzayo da kuɗi ƙalilan a tallata
muku kayan siyarwanku sai dai kawai ku ji ana kiran waya don buƙatan sayan kayan ku,ku
tuntuɓeni ta layina kamar haka 08167768704._
*84*
*Abuja.*
Tun safe TAIMIYYAH ta tashi da shirin amsar girki don Suhailah ta gama da kwanaki biyun ta,
ita ta haɗa musu abincin breakfast me rai da motsi. Daga Suhailah har A.Maleek Ado sun yi santin
girkin sosai, Suhailah ta dinga mamakin yadda TAIMIYYAH ta iya yin duk abubuwan da ta yi
ɗin. Kishinta me tsanani ya dinga kamata, sabida tun kan aje ko'ina ta fara gano cewa gurguwar da
ta ke rainawar akwai ta da tarin baiwa.
Da rana ne A.Maleek ya hanata yin girkin lunch ya ce TULIP BISTRO za su, hakan ko aka yi don
da kansa ya yi driving ɗinsu zuwa ƙayataccen wajen cin abincin, wanda ake ji da shi a garin Abuja
yanzu. Dukkaninsu kowacce ta yi kwalliya na ɗaukar hankalin mijin nasu, TAIMIYYAH dai
shigar Abayarta da ta fi jinta comfortable a ciki ta yi, sai Suhailah da ta sanya wata boubou na
voile da ya amsa jikinta, sai ta yane kanta ba babban mayafi kamar yadda A.Maleek ya fi so.
Wajen ba ƙaramin ƙayatar da TAIMIYYAH ya yi ba, ta dinga jin ina ma daga ita sai A.Maleek ɗin
ne suka zo wajen, sabida yadda ta dinga jin shauƙin su mori wajen ta hanyar nunawa juna zallar
kulawa, amma idanun Suhailah sun yi mata shamaki da sakin jiki a wajen sosai, bare ta samu
sakewan da zata gwadawa Maleek luv a wajen.
Sai wajen la'asar suka shigo gida sabida ya ɗan zaga dasu wasu wuraren, sabida TAIMIYYAH ta
fara buɗe ido da garin. Suna shigowa gidan TAIMIYYAH ta nufi ɗaki tana jin jikinta a gajiye
tamkar wacce tayi tafiyar ƙasa, hakan yasa ta zare kayan jikinta ta nufi bathroom ta watsa ruwa,
tare da ɗauro alwala ta fito ta sanya riga mara nauyi ta feshe jikinta da turaruka. Ganin time ɗin
sallah ya yi ta gabatar, bayan ta idar ne ta nufi bed ta ɗan miƙe jikinta tana ɗaukar waya ta kira line
ɗin Yasmeen.
Sun jima suna waya Yasmeen na sanar mata da yadda shirye-shiryen bikin Yah Anas zai kasance,
wanda za a yi nan da 2weeks me zuwa, don ma an ɗaga bikin ne da tuni an yi kafin ayi na su
TAIMIYYAR. TAIMIYYAH sai ta sanar da Yasmeen cewa da ƙyar a yi bikin suna ƙasar ma, ta
labarta mata maganar tafiyarsu zuwa Egypt nan da bai fi 2 week ba ɗin, ba ma ta ji zai kai hakan
don ta ji Maleek na cewa da zaran ta yi passport za a tura don neman Visa .
Ko da suka kammala yin wayar da Yasmeen sai ta cigaba da hutawarta, sai wajen 5 na yamma
sannan ta fito don shiga kitchen ta ɗaura musu abincin dinner.
Ana daf da kiran magriba suka gama jera coolers ɗin girke-girken da TAIMIYYAH ta yi musu na
dinner ɗin, wanda sam babu abinci me nauyi a ciki sosai don ta fahimce tsarinsa da al'adarsa
kenan rashin cin abu me nauyi da dare.
Yam balls ne da yaji nama a ciki da su carrot, sai ta yi haɗin beef salad da shi ma ta lura Maleek
ɗin na so sosai, sai ta gasa musu rousted fish da ya ji Irish a ciki da tarugu da onions me yawa a
ciki.
Ta ɓangaren abin sha kuwa sassanyar lemun fruity zoɓo ta haɗa, wanda ya ji kayan haɗi sai
ƙamshin su pineaple ke tashi gunin daɗi, tun daga kan ƙamshinsa me son zoɓo zai fara jin miyansa
ya tsinke. Ta haɗa da lemukan zamani duk suka jere bisa dining ɗin in style, suna kammala shirya
dining ɗin ta koma zuwa ɗaki don gabatar da sallar Magrib.
Bata tashi a wajen ba sai da ta jira time ɗin Isha'i ya shiga sannan ta gabatar da shi, tana idarwa
wanka ta faɗa ta fito a gaggauce don kammala shiri kafin time ɗin fita yin dinner ɗin ya yi.
Wata haɗaɗɗiyar doguwar riga ta sanya wanda A.Maleek ne ya zaɓar mata shi, a wani boutique da
suka shiga randa suka fita yin shopping, sosai rigar ta yi mata kyau tare da bin jikinta ta fiddow da
shape ɗin halittarta a zahiri. Ƙirjinta da ya fi ko'ina ɗaukar hankalin A.Maleek ya fito sosai, kuma
sam bata sanya Bra a ciki ba shiyasa hatta nipples ɗin sun bayyana kansu a zahiri, sabida yanayin
yadda rigar ta bi jikinta ta lafe.
Daddaɗan ƙamshin Humrar nan na Russ ke tashi a jikinta, wanda ya haɗe da ƙamshin turaren
VERSACE ya sake bada wani ni'imatacce ƙamshi me kwantar da zuciya.
Tana cikin sanya ɗankunni ne A.Maleek Ado wanda shigowarsa gidan kenan ya sanyo kansa cikin
ɗakin, don tun da ya aje su bai shigo ba fita ya kuma yi sai yanzu ya shigo gidan.
Ya dinga takowa a hankali zuwa gareta idanunsa na sake mannewa akan shigar jikinta, wanda tun
daga nesa ya fara hango yadda mutanan nasa suka bayyana a fili. TAIMIYYAH jin ta kawai ta yi a
cikin jikinsa lokacin da ya ƙariso zuwa gareta, ya yi mata wani kyakykyawar runguma yana kai
bakinsa zuwa tsakiyar ƙirjinta ya sumbata. Wani yanayi me wuyar fassara ya ratsa jinin jikin
TAIMIYYAH, ta yi saurin ƙanƙamesa lokacin da bakinsa ke sauka bisa dokin wuyarta, hancinsa
na mannuwa a fatar wajen yana sunsunar fitinannan ƙamshin da ke sake kunna zuciyarsa.
Da ƙyar TAIMIYYAH ta ƙwaci kanta a hannunsa bayan ta sanar da shi time ɗin cin abinci ya yi,
kada ya kasance Suhailah ta sakko tana jiran fitar su.
Hannunsa cikin nata suka dinga ratsowa ta cikin falon har suka iso dining area ɗin, TAIMIYYAH
na jinta a wani mugun takure ga uban kunyar yadda Suhailah za ta ganta da wannan fitsararriyar
rigar na sake kassara zuciyarta.
Babu yadda bata yi da A.Maleek akan ya barta ta sanyo kimono akan shirgar ba, amma ya ƙi ya ce
shi a haka yake son ganinta, babu ruwansa don Suhailah ta ganta a hakan, don ita ma shigar da ta
so take yi ta fito wajen cin abincin,don haka bai ga aibu don ita ma TAIMIYYAH yau ɗaya ta ɗana
hakan ba.
Ita dai TAIMIYYAH da ya ke akwai ta jin nauyi duk sai ta ji kunya tamkar ta nutse, lokacin da
suka isa ga dining ɗin ta fara jin yadda idanun Suhailah ke yawo a kanta. TAIMIYYAH sai ta kasa
kallon direction ɗin da Suhailah take, ta yi tsaye tare da fara yin serving ɗinsu abincin, in da ta
fara da A.Maleek ta tura gabansa. Sai ta ɗaga ido da ƙyar ta dubi Suhailah ta ce, "Anty me za a
zuba miki?"
Suhailah da gaba ɗaya ƙirjinta ya yi nauyi da wani irin zazzafar kishin da ta ke ji, ta fisgo magana
da ƙyar daga bakinta ta ce, "Ki zuba yam balls ɗin sai fish ɗin is okey."
TAIMIYYAH ta jinjina kai tana zuba mata abinda ta ce ɗin ta tura gabanta, ita kuma sai ta zuba
haɗin salad ɗin da rousted fish kaɗan,ta kwashe dankalin da ke cikin rousted fish ɗin ta zuba akan
haɗin salad ɗin.
Tunda suka fara cin abincin Suhailah ta gama lura da cewa gaba ɗaya hankalin A.Maleek ba shi
akan kowa da komi sai TAIMIYYAH,wacce shigarta gaba ɗaya ya gama kunna shi tare da tayar da
kwaɗayinsa a kanta.
Suhailah ta dinga cusa abincin da ƙyar,gaba ɗaya zuciyarta wani irin suya ta ke mata, tsabagen
kishi da mamakin yadda TAIMIYYAH ta iya fitowa da irin wannan shigar a gaban idanunta, (Ta
manta cewa ita ma ta fito da ire-iren shigar da TAIMIYYAR ta yi, su Suhailah a ji tsoran Allah).
Tashi ta yi tsam! Ta bar musu wajen ba don ta ƙoshi da cin daddaɗan gashin kifin ko yam balls ɗin
ba, sai don sabida yadda kishi ke cin zuciyarta. Ta dinga jin duk ta raina kanta da uban kwalliyar
da ta ɓata lokaci ta yi don ta birge A.Maleek ɗin, amma bata birge ɗin ba hasalima sam bai nuna
ya san da wanzuwarta a wajen ba, hankalinsa na ga TAIMIYYAH ce ita kaɗai.
Har ta isa ɗakinta ta kwanta a bed zuciyarta b ta bar yi mata suya da zafi ba, hawaye suka dinga
biyo ƙuncinta suna sauka akan pillow,ba tare da ta damu da ta tsaida su ba. A hankali ta dinga
karanto addu'ar ' Allahummah laah sahlan! har zuwa ƙarshensa. Ta dinga nanatawa har sai da ta ji
ta samu nutsuwa, sannan ta dakata da karantawar,tana me janyo wayarta ta kira line ɗin Anty
Safiya.
Daga can downstairs kuwa tun daga wajen cin abincin, bayan Suhailah ta bar wajen A.Maleek
Ado ya fara baje kolin rigimarsa, kafin su kwasa zuwa upstairs ɗin cikin ɗakin baccinsa da ya gaji
da haɗuwa, TAIMIYYAH daren ta amshi tarin darussa tare da zazzafar salon luv, irin wanda bata
taɓa sanin da su. Shi ko A.Maleek Ado gaba ki ɗaya sake gigicewa ya ke akan TAIMIYYAH,
sabida kullum ya shiga duniyarta ji ya ke yi tamkar kada ya fito, yafi so ya yi ta ninƙaya a cikinta
domin wata iriyar duniyar zazzaƙar zuma ce, da bai taɓa kwankwaɗar me zaƙi da garɗinta ba.
Washegary flight ɗin 9am suka bi zuwa Lagos sabida A.Maleek za su shiga meeting 11am, kuma
ya fiso su isa har ya ɗan huta da zumarsa kafin ya isa wajen meeting ɗin.
Babbar gidansa da ke Lekki anan su kai masauki, wanda babu ne kawai ba a zuba na jin daɗin
rayuwa a cikinsa ba, TAIMIYYAH bin ko'ina ta dinga yi da kallo tana jinjina yadda ake narka
dukiya a ƙasa, tamkar ba za a bar gidan duniyar ba. Ta dinga mamakin ƙuduran Ubangiji me sauya
rayuwar bawa da kai shi matsayin da bai taɓa zato ba, domin bata taɓa tunanin koda wasa za ta
taɓa iya mallakan namiji kamar A.Maleek Ado a matsayin miji ba, bata taɓa kawo cewa yadda ta
ke a gurguwarta zai ƙaunace ta, har ya mallaka mata zuciyarsa kamar yadda ya yi a yanzu ba.
Ta dinga bin sa suna ratsa tanƙasheshen falon da ke downstairs ɗin hannunta cikin nasa, kafin su
malkwaɗa su yi wani kwana in da zai sada mutum ga matakalan da zai kai shi xuwa upstairs. Wani
irin gini ne da idanunta bai taɓa cin karo da irin sa ba, domin duk haɗuwar gidansa na Abuja sai
TAIMIYYAH ta ga wannan ya shafesa a kyawu da tsaruwa.
Bata sake tsinkewa ba sai da suka dangana da ɗakin baccin A.Maleek Ado ɗin, sosai ta yaba
kyawu da tsaruwarsa komi na cikin ɗakin white ne babu sirkin ko wani kala a cikin ɗakin.
Maleek ne ya ɗaga waya ya kira kukunsa da ke masa girki idan yana gari, ya sanar masa ya hawo
musu da abincin breakfast xuwa upstairs ɗin.
Ya dubi TAIMIYYAH da ke zare After dress ɗin da ta sanya a jikinta tana ninkewa, ya zuba mata
manyan idanunsa bisa ƙirjinta da ya bayyana, sabida ƙaramar vest ce ta sanya kawai da dogon
wando daga ciki, kafin ta ɗaura Abayar a sama.
Ya miƙa mata hannunsa alamun ta ƙariso garesa,TAIMIYYAH ta taka ta isa zuwa in da ya ke tana
miƙa masa hannunta, ya janyota zuwa jikinsa tare da yi mata masauki akan laps ɗinsa. Ya kai
bakinsa a hankali ya sumbaci ƙirjinta yana shaƙo wani fitinannen ƙamshin Humrar da ta yi anfani
dashi a wajen, ya sake cusa kansa a muhallin tare da fara aika mata saƙo me zafi,wanda ya sanyata
sake rungumarsa tana zuba masa shagwaɓar da ke narkar da shi.
Da ƙyar ya barta suka fito zuwa falon da kukunsa ya gama shirya musu abincin da zasu yi
breakfast daga saman dining, suka zauna A.Maleek na kai hannu ya sake yin ƙasa da wuyar vest
ɗin da ke sanye a jikin TAIMIYYAH, ta dubesa tana mairairaice face ɗinta tare da kai hannu za
ta ja wuyar vest ɗin sama, amma sai A.Maleek ya miskile fuska yana jifanta da wani irin kallo da
ya sanya zuciyarta kaɗawa, ta zumɓure baki tana sauke hannunta ƙasa, ta ja plate ta fara serving
ɗinsu abinda za su ci.
Bayan sun kammala ne A.Maleek ya janyeta zuwa ɗakinsa suka kwanta, amma duk yadda
TAIMIYYAH ta so ya barta su yi bacci bai samu ba, bidirinsa ya yi son ransa kafin ya rungumeta
a jikinsa yana sanya mata albarka, tare da raɗa mata manyan kalaman da har sun fara zama a
kwanyarta, tare da fara sabawa da nauyinsu a cikin zuciya da gangar jikinta.
11:10am ya bar gidan driver ɗinsa da ya ɗakko su daga airport ne ke jansa don kai shi wajen da za
su yi meeting ɗin, ya bar TAIMIYYAH ita kaɗai a gidan sai Kukunsa wanda ke can ɓangaren da
ya ke zama daga BQ ɗin gidan.
Baccinta ta sha sosai bayan fitarsa sai wajen 01:30pm na rana ta tashi, hakan yasa a gaggauce ta
nufi toilet ta yo wanka tare da ɗauro alwala ta fito, bayan ta idar da sallah ne ta kintsa kanta cikin
ƙananun kaya marasa nauyi, waɗanda su kai matuƙar yi mata sai ƙamshi kawai take zubawa
kamar babu gobe.
Ta tadda Petter har ya shirya abincin lunch a dining, hakan yasa ta isa wajen tana bubbuɗe coolers
don ganin mi ya girka musu for lunch ɗin? Kular farko sai ta ga soyayyiyar shinkaface da ta sha
kayan haɗi da wadatacciyar liver a ciki, ta buɗe cooler na biyu ta ga tuwan semo ne da miyar
ɗanyar kuɓewa,wanda akai amfani da kifi da zallar tsokar kaza a cikin miyar. Yadda miyar ya yi
kyau a ido da irin aroma ɗin da yake bayarwa, ya sanya ta jin tuwan kawai ta ke son ci, sai ta saka
ƙulli guda a plate tare da zuba miyar ta fara ci. Sosai ta yaba da ƙwarewar Kukun wajen iya sarrafa
nau'ikan abinci, amma can ƙasan zuciyarta kuma kishin yadda za a yi mijinsu ya dinga cin abincin
iren-iren waɗannan yaren da bama musulmi ba ya dinga sukar zuciyarta, ta dinga ganin sakarcin
Suhailah da ta gwammaci zama a can Abuja ba tare da ta dinga biyosa nan ɗin, tana kulawa da
cimarsa da ba shi kulawar da ta dace ba, sakacinta da sakarcinta ta dinga hangowa, tana jin cewa
in da ita ce a matsayinta sam ba za ta aminta da hakan ba, sai dai su dinga shigowa weekend
Abujan idan ya zama ƙa'ida ne, amma ba za ta iya barinsa a irin wannan garin da buɗewar ido yayi
yawa ba shi kaɗai.
Bayan ta kammala cin abincin ne ta baro dining ɗin ta dawo zuwa cikin falo ta kunna kallo, Iyah
da ta faɗo mata a rai ne ya sanya ta kiran layin wayarta suka sha hiran su kafin su yi sallama da
juna, TAIMIYYAH na jin kewar Iyah me tsanani na sake kamata.
A.Maleek Ado bai shigo gidan ba sai a round 2:30pm,da taimakon TAIMIYYAH ya yi wanka ya
shirya cikin kaya mara nauyi, suka fito zuwa dining don ba shi abinci ya ci.
Yana kammala cin abincin suka nufi bedroom ɗinsa don ya ce mata a gajiye ya ke yana buƙatar
hutu, sai dai lokacin da sukai masauki a kan bed ɗin nasa ne ta gane irin hutun da yake da buƙatan.
Sai around 4:15pm suka farka daga baccin da ya sace su bayan A.Maleek ɗin ya gama huce
gajiyarsa da kyau a jikin TAIMIYYAH, tare suka yo wanka suka fito don gabatar da sallar La'asar.
Bayan sun idar ne suka shirya cikin ƙananun kaya marasa nauyi, sun yi kyau matuƙa sai faman
jifan juna suke da murmushi, zuciyoyinsa cike da wani irin shauƙi da ƙaunar juna.
"My pure honey, fita zamu yi ina so ki ɗan fara ganin gari kafin gobe mu yini a waje, ina ga sai
jibi za mu koma Abuja."
A.Maleek Ado ya yi maganar idanunsa akan TAIMIYYAH, lokacin da ta ke zama kusa da shi akan
Sofa, ta ɗago manyan idanunta ta sauke akansa, kafin ta shagwaɓa murya ta ce, "Jibi kuma Hubby,
yau fa kwanana zai ƙare gobe da jibi duk kwanakin Anty ne, gaskiya mu dai wuce a goben kar mu
shiga ranarta hakan babu kya......"
Bakinsa da ya ɗaura kan nata ya hanata ƙarisa kalamanta, ya tsotsi mouth ɗin sosai kafin ya zare
bakinsa daga nata yana mayarwa kan kunnuninta ya ce, "Na sani sweet but ba zamu koma ba sai
na yi ƙara'i na son rai a nan garin, akwai wuraren hutawa da zamu morewa amarcin mu ko
Zumata?"
TAIMIYYAH ta narke fuska tare da zumɓure baki ta ce, "Ni dai babu ruwana."
A.Maleek ya saki murmushi yana sake matseta a jikinsa ya raɗa mata wasu kalamai, sai ga
TAIMIYYAH na faman ƙyalƙyala dariya bayan ta rufe fuskarta da tafukan hannyenta.
Ya zare hannunta daga kan fuskarta yana kai baki ya sumbaci saman ƙirjinta, ta yi gaggawar ture
hannunsa tana cewa, "My Amore ka ce fa fita za mu yi ka barni na shirya please!"
A.maleek ya yi maganar yana sake cusa kansa cikin ƙirjinta, da ƙyar ya barta ta shirya cikin Navy
blue ɗin Abaya da ya amshi jikinta tare da yi mata wani mugun kyau,fuskarta babu kwalliya daga
powder sai lipbalm da ta goga kaɗan, manyan idanunta ta sanya musu kwalli suna wani irin
sparkling.
Shi ya ke driving ɗinsu cikin wata ƙaramar motarsa me azabar kyau nauyin kuɗin, TAIMIYYAH
ta dinga kallon ko'ina tana yaba kyawun garin Lagos ɗin.
Sai wajen goman dare suka shigo gida domin bayan ya zaga da ita manyan wuraren buɗe ido, sai
da su kai branching a wani haɗaɗɗen hotel, wanda manyan mutane suka fi ziyartarsa sabida
haɗuwa da tsaruwansa, tun daga habarabar shiga hotel ɗin za ka ɗauka tamkar ba cikin 9ja ka ke
ba.ita dai TAIMIYYAH ware ido ta yi ta sha kallo, a nan hotel ɗin su kai dinner bayan sun
gabatar da sallar Magriba da Isha'i.
Shiyasa lokacin da suka shigo gidan wanka kawai TAIMIYYAH ta yi, ta zura kayan bacci ta bi
lafiyar gado. Shi ko A.Maleek zama ya yi bisa Sofa ya kunna system ɗinsa, yana shigar da wasu
bayanai akan zaman meeting ɗin da suka yi a yau ɗin.
Sai wajen 11:30pm ya kashe system ɗin ya nufi bathroom, bai jimaba ya fito ya yi musu light off
ya haye bisa ɗin, yana miƙa hannu ya janyo TAIMIYYAH zuwa jikinsa.
Washegaryn ranar ma tun safe suka fice daga gidan, bayan duk ya gama kai ta wuraren buɗe ido
sun shana, sai suka sake branching a wani 5star hotel wanda kusan zan iya cewa har ya fi hotel ɗin
jiya tsaruwa, don wannan a wani sabon waje ne da attajiran 9ja sukai gasar yin gina-gine irin
wanda ba a samun ire-iren su sai a ƙasar Dubai.
Basu baro cikin hotel ɗin ba sai 11pm shi ma don babu yadda A.Maleek zai yi ne, sabida morning
ticket ya siya musu kuma kayansu na can gida, amma da anan hotel ɗin zasu kwana in yaso sai su
wuce airport daga nan.
TAIMIYYAH ta gurzu ta kuma sake dilmiya a tafkin ƙauna da soyayyarsa me wuyar bari, don
daga jiya zuwa yau ɗin ne ta sake tabbatarwa kanta cewa A.Maleek ɗin, irin mazannan ne ƴan son
rayuwa ba kaɗan ba.
Ya san salon tafiyar da mace sosai tare da dilmiyar da zuciyarta a soyayyarsa, ba tare da ta ankare
ba domin a kwana biyu ɗin da suka yi, ba ƙaramar wata ƴar ƙwarya-ƙwayar mara kunya ya mayar
da ita ba, a fannin nuna masa luv da kulawa.
Ta dubesa da idanunta da ke cike da bacci da gajiya, a lokacin da take kwantar da kanta a ƙirjinsa
ta ce, "Sweet Amore amma idan muka koma ita ce zata amsa girki tunda kwanakinta muka cinye
ko?"
A.Maleek Ado ya lumshe idanunsa tare da sake bulesu akan fuskar TAIMIYYAH, ƙamshinta na
sake narkar da zuciyarsa yana jin wani zazzafar feeling na sake kama shi. Ya buɗi baki cike da
ƙasaita ya ce, "My pure zuma har kin gaji da ni ne kina neman kai da ni?"
Yadda ya yi maganar a ƙasaice cike da narke mata murya, ya sanya TAIMIYYAH kai hannu ta
shafo face ɗinsa, kafin ta sake shagwaɓe murya ta ce, "No! Sweet Amore, kawai dai gani na yi
cewa hakan shi ne adalci tunda kwana ɗaya ka ce za mu yi, mukai 3 days ka ga a ƙa'idah jiya da
yau duk ranarta ce kuma duka ranakun ka mori abarka, so gobe dole a bata kwanakina amadadin
nata da muka cinye, wannan shi ne gaskiya da kuma kwatanta adalci. Sannan ka haɗa da rarrashi
da ban baki domin abin xai yi mata ciwo na sani, don mu mata muna da zafin kishi akan hakan."
TAIMIYYAH ta kai ƙarshen maganar tana sanya idanunta cikin nasa, tare da sake shagwaɓe masa
fuska tana jiran jin ta bakinsa.
A.Makeek ya sake mannata da ƙirjinsa wani irin matsanancin ƙaunarta ne ke sake samun wajen
zama a zuciyarsa, kalamanta sun ratsa shi tare da tunasar da shi girman hakkin da ke kansa wajen
kwatanta adalci a tsakaninsu. Ya kai baki a hankali ya sumbaci forehead ɗinta kafin ya ce, "My
pure zuma, ban san da wani baki zan iya kwatanta miki iyakar ƙaunarki da ke dilmiyar da zuciyata
ba,na gode da ki ka tunasar da ni abinda na so mantawa, haƙiƙa ke ɗin mace ce ta gari kuma
wacce ta san girman hakkin abokiyar zamanta akanta, na gode da baki kasance cikin mata masu
taimakawa wajen danne hakkin abokan zamansu ba. I luv u Zaynabb! Ina fata za ki cigaba da
tunasar da ni tare da ɗaurani akan hanya idan na kauce, wajen ganin kin taimakeni na zama adali a
tsakaninku."
Ya kai ƙarshen maganar yana sake manne bakinsu waje guda, tare da cigaba da nuna mata ƙarfin
soyayyarta da ya gama da zuciyarsa. TAIMIYYAH ta kama harshensa da ke cikin bakinta, ta fara
masa wani irin salo da ya cigaba da gigita kwanyarsa, kafin ta saki harshensa tare da zare bakinta
daga nasa ta mayar kan kunninsa ta ce, "I luv u too sweet Amore, kuma ka daina gode min domin
hakkina ne sanar da kai gaskiya, tare da ɗaura ka akan hanya idan ka sauka, matuƙar Allah ya bani
sani a wannan fannin. Ina fata za ka zama cikin maza masu tsananin kwatanta adalci, domin in da
ni ce akai wa hakan a yadda na ke jin kishinka a raina, zan iya jimawa ban sakko daga dokin fishin
da zan hau ba, domin duk uzurin da zaka bani gani zan yi da gangar ka ɗauketa ku ka tafi ku ka
cinyo kwanakina, don ka nuna min kafi son ta dani. So please! Ka bata haƙury tare da rarrashinta
ta hanyar da ba za ta sake tsanata a zuciyarta ba,domin na sani dole za ta ji ciwon a bin matuƙa a
ranta."
A.Maleek ya saki murmushi me faɗi ƙaunar TAIMIYYAH na sake bin jinin jikinsa, ya yi magana
murya can ƙasa ya ce, "Wow! My pure zuma a she dai ana ƙaunata da kishina har haka? Ki ce
dole in kiyaye aikata hakan don duk randa ki ka ɗauki kalar wannan fishin ban san in da zan saka
kaina ba."
Suka saki dariya a lokaci guda domin salon yadda ya yi maganar dole ne ya baka dariya, daga nan
kuma sai lamura suka fara sauya salo, TAIMIYYAH ta ji wani irin tsoro da fargaba na shigarta,
don ta yi matuƙar gajiya da amsarsa dauriya kawai da jarumta ta ke gwada masa, amma ta kula
tamkar baya gane hakan ko kaɗan, shi baya nuna gajiyawa akanta in dai za ta bashi to fa zai amsa
da gudu ne.
Ta sauke wani zazzafar numfashi lokacin da fahimci cewa ba in da take tunani zai dosa ba, ya
shigar da ita cikin jikinsa bayan ya gama bidirinsa da in da suka fiso tsole idanunsa, ta kwantar da
kanta tare da sake shigewa jikinsa tana fata bacci ya sace ta da gaggawa.
Washegary sai da suka kusa makara don Maleek bai barta sun yi wanka ba, sai da ya fanshe ɗaga
mata leg ɗin da ya yi a daren jiya, aiko ya sha kukan shagwaɓa sosai kafin su yo wanka a
gaggauce su shirya.
Driver ɗinsa ya wuce da su zuwa airport da misalin ƙarfe 8am na safen, sabida flight ɗin 9 za su bi
zuwa Abuja ɗin.
___________
*Gyallesu, Zaria.*
Umma ta kai dubanta kan Baba Sani wanda ya yi shigowar safe a yau friday ɗin,ba kamar yadda
ya saba zuwar yamma ko dare ba daga Kano ɗin.
Ta cigaba da zuba masa abincin breakfast ɗin da zai ci, kafin ta buɗe baki ta ce, "Amma Baban
Basmah na yi mamakin shigowarka da sassafe haka, ko dai yau su Ameerun za su zo a zauna akan
maganar su da Zuhurar ne?"
Baba Sani ya girgiza kai yana ɗaukar cup ɗin tea ya kai bakinsa, ya yi masa kurɓa biyu ya aje yana
duban cikin idanun Umma ya ce, "Ko ɗaya, ba yau za su samu xuwa a zauna ba sai jibi Sunday,
domin mun yi waya da shi Honourable ɗin na yi masa bayani akan duk abinda Yarinyar ta ce, ya
kuma gamsu shi ma ya bada haƙury akan cewa basu san Ameeru bai gaya mana cewa shi ɗan riƙo
bane, kuma maganar shaye-shayensa ya tabbatar da yina ɗin, amma sun ɗauka idan da mace a
kusa da shi abin zai fara yin sauƙi ne. Ya sanar min shi ba zai samu zuwa ba amma zai turo
wakilinsa tare da Ameerun su zo a tattauna."
Umma ta jinjina kai cike da gamsuwa da bayanan Baba Sanin, zuciyarta na cigaba da jin tsanar
Ameeru me tsanani tare da danasanin irin kuɗin da ta narkar akansa don su mallakesa. Sai gashi
tun ba a je ko'ina ba auren zai girɗiɗe tun daga tushensa,ta buɗe baki cikin nuna zallar takaici ta
ce, "To ai shikenan, Allah ya kaimu jibin lafiya ni ma a yanzu ina bayan Zuhurah, a raba auren
kawai ya bata takardarta tunda ta ce bata yi. Allah zai fito mata da wani cikin gaggawa In Sha
Allah!"
Baba Sani ya saki murmushi zuciyarsa na taɓuwa, da wannan lamari na auren Zuhuran da ke son
mutuwa, ya buɗe baki ya ce, "To Allah ya yi zaɓin abinda ya fi alkhairy Zuwairah, sai ki iya ganin
kuma idan ya zo ya rarrasheta ta amince za ta koma ɗin."
"Inaa..!!! Baban Basmah! Zuhurah ta riga ta tsanesa sosai in gaya maka, don haka ba za ta taɓa yin
hakan ba wallahi."
Umma ta yi maganar da ɗaga sautin muryarta, hakan yasa Baba Sani balla mata harara ya ce, "To
miye abin ɗaga min murya anan Zuwairah? Na ga alama zafi na ki ke ji tamkar ni ne na sanya
duk abinda ya faru."
Umma sai ta shiga nutsuwarta tana bashi haƙury, ya sake ɗaure fuska yana cigaba da yin kalacinsa
har ya kammala.
Ya ture plate ɗin daga gabanaa yana duban Umma ya ce, "Maza kwashe kayan ki fita da su, ki
dawo ina da magana da ke yanzu."
Umma ta yi yadda ya ce ɗin tana ji duk ta ƙosa ta ji wani magana zai yi da ita? Don haka kawai
dama zuciyarta ta kasa nutsuwa da wannan uwar sammakon da ya yi ya baro Kano a yau.
Bayan ta dawo ta nutsu a gabansa ne Baba Sani ya gyara zamansa tare da zura mata ido ya ce,
"Zuwairah kamar yadda na sanar da ke maganar ƙarin aurena kwanaki, to yanzu ma maganarce ta
taso da gaggawa don kuwa gobe ne za a ɗaura auren. Abun ne ya zo da gaggawa domin mahaifinta
ya ce a ɗaura kawai ta tare, duk da cewa dai nan za a fara kawo ta sai daga baya za mu wuce Kano
tare, za ta zauna wancan part ɗin tunda da ma ni ne na gada wajen."
Baba Sani ya ɗan dakata yana kallon yadda Umma ta zura masa ido, ta kasa koda ƙwaƙwƙwaran
motsi da alamu dukkanin kalamansa jinsu take yi tamkar cikin mafarki ne. Ya kira yi sunanta don
ta dawo hayyacinta, aiko sai ta yi firgigit tana cewa, "Me kace Sani, ban fahimci abinda ka faɗi ba
me ka ke nufi ?"
Baba Sani ya sake maimaita mata dukkanin bayanansa, ai sai Umma ta saki wani irin ihu tana dira
a gabansa ta riƙo hannayensa, dukkanin jikinta rawa ya ke lokacin da ta ke cewa, "Sani gobe ɗaura
aurenka fa ka ce? Don Allah ka sanar da hakan ba gaskiya ba ne, da wace ƴar kutumar uban ne
wai za a ɗaura, don Allah ka sanar da ni wace ce ?"
Baba Sani ya rungume Umma a jikinsa yana shafa bayanta don ta nutsu amma ina, ita burinta
kawai ta san da wace ce za a ɗaura masa aure a gobe? Ta cigaba da kuka tana tambayarsa har sai
da ya buɗe baki ya ce, "Calm down Zuwairah! Ba da wata bare bace can da baki sani ba. Samha ce
matar da za a ɗaura mana aure, ina so ki kwatar da hankalinki ki ɗauki hakan a matsayin ƙaddara
wanda ta rigayi fata, ki ɗauka cewa haka Allah ya ƙaddara matar ɗan uwana ita ce za ta sake zama
matat......"
Wani irin cakuma da Umma ta yiwa wuyar rigarsa ya hanashi ƙarisa kalamansa, ya kai hannu yana
finciketa daga jikinsa baki ɗaya, lokacin da Umma ta sake buɗe murya ta saki wani gigitaccen
ihun da kaf mutanen da ke cikin part ɗinta sai da suka jiyo ta. Gaba ɗaya sai yanzu da Baba Sani
ya sako cewa matar ɗan uwansa a maganarsa, sannan kwanyarta ta gano wace ce Samhar da ya ke
faɗi, don ita gaba ɗaya har ta shafe Ummie da babin ta cikin lissafinta.
Cikin matsanancin tashin hankali ta fara buɗe masa faifan tijara da zage-zage, akan cewa ko sama
da ƙasa za su haɗe ne ba za ta taɓa amincewa Samha ta zama kishiyarta ba.
"Wallahi ƙarya ka ke yi Sani, ka yi kaɗan ka yi min irin wannan tozarcin, ka rasa wacce za ka aura
sai matar da ɗan uwanka ya mutu ya bari, ragowar ɗan uwanka za ka aura sabida ka tozartani
Sani? To wallahi daga kai har munafukar da ta ƙulla abin ƙarya ku ke yi, don na san babu wacce ta
kitsa hakan sai munafukar tsohuwar can Iy......."
Marin da Baba Sani ya ɗauke fuskar Umma da shi ya sanyata kasa ƙarisa muggan kalamanta, ya
nuna ta da yatsa cikin tsananin fushi da fusata ya ce, "A gabana Zuwairah, a gabana ki ke kiran
mahaifiyata da munafuka? To bari ki ji aure babu fashi kamar an ɗaura shi an gama shashasha!
Mara mutunci. Wallahi ba zan ɗauki ko wani irin tozarci akan mahaifiyata ba, kuma ki sanya
speeker ki gayawa duniya cewa ita ce ta sanyani auren Samha, ta isa da ni ne tunda ita ta kawo ni
duniya, kuma na amshi tayinta da hannu bibbiyu tare da ɗaura ɗamarar zama da zaɓinta har
ƙarshen numfashi!"
Daga haka Baba Sani ya kwashi wayoyinsa da mukullin motarsa ya fice daga falon baki ɗaya,
hakan ya sanya Umma da ta miƙe tsaye dafe da fuskarta da yasha mari, ta saki wani razananniyar
ihu tana zubewa a ƙasa kanta ya bugu da jikin table. Zuhurah wacce ta jiyo ihun Umma a karo na
biyu ne ta san cewa babu lafiya, shiyasa ta shigo a guje cikin falon Baba Sanin don ganin abinda
ke faruwa.
Ganin Umma yashe a ƙasa bata numfashi ya sanyata ƙwalla wani ihu tana fara jijjiga Ummar, faɗi
take yi , "Umma! Umma! Umma don Allah ki tashi ki sanar da ni abinda ke yafaru."
Ganin cewa Umma bata ma san tana yi ba yasa Zuhurah tunawa da ruwa, sai ta ruga a guje ta
ɗakko goran ruwa me sanyi ta zo ta diddilewa Umma akan fuskarta, ba a ɗauki dogon lokaci ba
kuwa numfashin Umma ya dawo. Zuhurah ta yi jifa da goran ruwar tana riƙo hannun Umma ta ce,
"Sannu Umma wai me yake faruwa ne?"
Umma ta ja numfashi kanta na wani irin sake ɗaukar nauyi gingirin...! Ƙirjinta na cigaba da yin
nauyi tamkar an ɗora bula an danne mata shi. Hawaye masu tsananin zafi suka fara wanke
fuskarta, ta yi magana murya a shaƙe ta ce, "Zuhurah zan mutu, wallahi mutuwa zan yi ko na
kamu da ciwan zuciya idan har ya tabbata ubanku Samha zai auro min a matsayin kishiya."
Umma ta kai ƙarshen maganar tana son ta rushe da kuka ko zata ji sauƙin nauyin da ƙirjinta ke
mata amma ta kasa kukan, sai dai hawaye kawai da ke iya zubo mata. Zuhurah ta dubeta cikin
rashin fahimta ta ce, "Umma wace ce Samha kuma? Maganar auren ya taso ne yaushe za a ɗaura
auren?"
Da ƙyar Umma ta iya sanar da Zuhurah abinda ke shirin faruwa, ta ƙare maganar da cewa,
"Zuhurah ki gaya min ta ya zuciyata za ta iya amsar Samha a matsayin kishiya? Matar da babu
abinda zan iya nuna mata game da buɗewar ido, ta fini yarinta ta fini buɗewar ido domin ita
tashin bariki ce, kowa ya san matan Kaduna da buɗewar idon su daban suke. Ta fini kuɗi ta fini
kyawu babu ta in da zamu yi gogaggiya da juna,sai ta fannin ilimi wanda matsayin kwalin mu
guda ya ke da juna, amma waya sani ma ko kwanyarta tafi nawa ja ? Ba zan iya ba Zuhurah
matuƙar hakan ya kasance ciwan zuciyace zai zama ajalina ."
Umma ta kai ƙarshen maganar tana dafe saitin zuciyarta da ke mata wani irin zafi da ƙuna,
Zuhurah da gaba ɗaya kanta ya gama kullewa sai ta yi ƙarfin halin cewa, "Umma to me Boka ya
sanar da ku akan zancen auren ,babu abinda za a iya yi ne a rabasu koda abin ya tabbata?"
Umma wani abu me nauyi ya sake danne zuciyarta lokacin da tambayar da Zuhurah ta yi mata, ya
sanyata tunowa da kalaman Boka Kallah, " _Ban ga mahalukin da zai iya dakatar da wannan auren
ba, domin akwai zazzafar rabo kamar yadda na sanar miki a baya,rabon shi ya yi silar mutuwar
mijin matar, don haka duk wanda ya ce zai ja da wannan auren zai iya rasa ransa,sabida dole sai
rabon da ke tsakaninsu sun taka doran duniya...._"
Kuka me tsananin ƙarfi ya ƙwacewa Umma, lokacin da ta tuno waɗannan kalaman na Boka
Kallah, ta dubi Zuhurah tana zayyane mata yadda suka yi da Boka Kallah,ta kai ƙarshen maganar
da cewa, "Zuhurah ina cikin tashin hankali, ki kira min Hajiya Barirah please!"
Babu musu Zuhurah ta ɗakko wayar Umma ta kira Hajiya Barirah, lokacin da Hajiya Barirah ta
ɗauki wayar sai Zuhurah ta miƙawa Umma wayar, tana me barin falon ta koma zuwa ɗaki don
kiran Basmah ta sanar da ita bala'in da ke shirin samunsu a gobe, na ɗaura auren Ummie da za a yi
da Babansu.......✍🏻
#Ɗansabo ce#
[12/15, 11:46 AM] +234 703 040 9541: Littafin TAIMIYYAH paid book ne,ga duk wanda ta
tsincesa a kowani irin group ne,kiji tsoran Allah karki karanta sai kin biya 500 naira only.
Za ku iya min magana ta wannan number ɗin 08167768704, ko kuma ku turo kuɗin ku kai tsaye ta
wannan account ɗin 0504192664 aisha ibrahim dansabo GTbank.*
Masu turo credit za ku turo katin MTN na 500 ta wannan line ɗin 08167768704.
_Ina ƴan kasuwa masu buƙatar a tallata muku hajar ku? Maza ku garzayo da kuɗi ƙalilan a tallata
muku kayan siyarwanku sai dai kawai ku ji ana kiran waya don buƙatan sayan kayan ku,ku
tuntuɓeni ta layina kamar haka 08167768704._
*85*
*Abuja*
A.Maleek Ado ne zaune tare da iyalan nasa gaba ɗayansu a saman dining, suna yin breakfast har
da Suhailah, wacce ita ce da kanta ta girka abincin kalacin. Duk wani zafi da kishi da take ji akan
yadda Maleek ɗin ya ɗauki TAIMIYYAH, suka je suka cinyo har da kwanakinta wajen faranta ran
juna, bata nuna ɓacin ranta a fili ba ta yi anfani da shawaran da Meenah ta bata wajen danne ɓacin
ranta.
Babu yabo babu fallasa ta amsa gaisuwar TAIMIYYAH lokacin da ta gaidata, har ma ta ɗaura da
yi wa TAIMIYYAH sannu da hanya, daga haka suka yi kalacin babu me cewa komi sai ƙaran
spoons kawai ke tashi.
TAIMIYYAH ita ce ta fara tashi daga wajen ta nufi ɗaki bayan ta kammala cin abincin, Maleek ya
bi bayanta da kallo wani murmushi na ƙwacewa a saman face ɗinsa.
Suhailah da ta tsaresa da idanunta tana kallon yadda yabi bayan gurguwar tasa da ido, sai ta ji
zuciyarta ta sosu wani ɓacin rai na tasowa na lulluɓe xuciyarta. Ta miƙe a hankali ita ma ta bar
wajen tana haurawa zuwa upstairs ɗin, ta nufi ɗakinta tana nufan wajen tagar ɗakin ta ya ye
labulen tare da yin tsaye a wajen, wasu hawaye na tsananin kishi da jin zafin A.Maleek suka fara
zubowa daga idanunta.
A.Maleek da ya biyo bayanta ya cigaba da takowa zuwa bakin window ɗin da tayi tsaye wajen, ba
tare da Suhailah ta waiwayo ta dubesa ba, duk da cewa tun shigowarsa cikin ɗakin, ƙamshinsa ya
bayyana mata wanzuwarsa cikin ɗakin.
Yana isa wajen ya rungumeta ta baya yana ɗaura kansa bisa kafuɗunta ya ce, "Sorry wife! Ban
kyautaba na sani amma ki yi haƙuri, meeting ɗin ne bai kammala ba sai da muka sake zama a
washegarin randa na so mu dawo, zan rama miki kwanakinki da muka shiga don haka yau da gobe
duk ranarki ce Baby, miss u dear!"
A.Maleek ya kai ƙarshen maganar yana juyo Suhailah suka fuskanci juna, kafin ya kai bakinsa ya
haɗe da nata ya shiga bata wasu irin deep kisses, waɗanda suka sauke duk wani fushi da ɓacin ran
da ta shiga, ba tare da sanya ba ta sake rungumarsa tana maida masa martani ta hanyar da ta san za
ta kunna zuciyarsa.
Bata samu bakin yi masa magana da maida martani ba, sai bayan da A.Maleek ɗin ya dawo daga
duniyar cire mata ƙishirwarta a kansa, don da gaske ta yi missing ɗinsa shiyasa bata cuci kanta ba
nunar masa a matse take da shi ɗin. Jikinsa ne ya yi sanyi tausayinta ya shigesa da ya tuna cewa,
da TAIMIYYAH ba ta tunasar da shi akan abinda ya so aikatawa idan sun iso ba, tabbas da sun
shiga hakkin Suhailah ba kaɗan ba, don shi da ta rabu da shi da ita zai sake kasancewa har ya
cinye kwanaki biyunta, ba tare da an barwa Suhailah su don su maye gurbin nata da suka cinye ba.
Ya sake rungumarta da kyau a jikinsa lokacin da take cewa, "But amma meyasa da ka san za ku
sake kwanaki har ku shiga ranata baka sanar min ko a waya ba my Maleek? Ka kyauta kenan tare
da kwantanta adalci?"
A.Maleek Ado ya kai hannunsa ya shafa lallausar fatar jikinta ya ce, "Suhailah am very sorry!
Hakan ba zai sake faruwa ba ki min uzuri please!"
Suhailah sai ta sake shigewa jikinsa ba tare da ta sake yin wani ƙorafi ba, don ta san halinsa ba ya
son ai ta nanata abu ɗaya, tunda har ya iya buɗe baki ya bata haƙury ma ta gode.
TAIMIYYAH tunda ta shige ɗaki chart su ke yi da Yasmeen, daga ƙarshema suka kafa yin vid call,
daf da zasu yanke wayar Yasmeen ta tuna cewa, basu yi zancen Zuhurah da TAIMIYYAH ba, ta yi
saurin duban TAIMIYYAH ta ce, "Sis Iyah ko ta sanar miki Zuhurah na nan ta dawo gida, za a
raba auren?"
TAIMIYYAH ta waro ido tare da ɗaukar salati, ƙirjinta na faman dokawa da matsanancin firgici,
cikin zallar damuwa ta ce, "Yasmeen raba aure kuma, da Ameerun nata wannan wace irin magana
ki ke yi haka?"
Yasmeen ta wani taɓe baki ta ce, "Au! Ba ki ma yadda ba kenan? Aiko ɗaxu dai Iyah ta kira
Mamie ta sanar da ita komi, wai yana shaye-shaye kuma ya ɓoye musu asalinsa, ashe ba ɗan
Honourable Attah bane ɗan me aikin gidan ne, ta rasu ta bar shi a hannun uwargidan Honourable
ya tashi. Shiyasa ya ke ɗaukar kansa tamkar ɗan gida sabida Honourable Attah Allah bai bashi
haihuwan ƴaƴa maza ba, shiyasa ina ga ake tattalinsa tamkar jinin gidan. Abu dai babu daɗi
TAIMIYYAH amma ace aure ko cikakken sati biyu ba a yi ba ana taɗin rabuwa."
TAIMIYYAH da ke cikin matuƙar damuwa da tashin hankalin jin wannan mummunar labari, ta
dubi Yasmeen ta ce, "Allah Ubangiji ya kyauta am speechless Yasmeen, gaba ɗaya kaina ya kulle
ban san me zan iya cewa ba. But kin san Iyah tun ganinta da guy ɗin ta fara so ta ce min ba
kintsatstse bane, a lokacin na yi banza da ita na ce ta fita batun kawai, amma idan soyayyar
gaskiya ta ke masa ai ko a wani yanayi ya ke za ta iya jurewa ta zauna da shi."
Yasmeen ta sake taɓe baki ta ce, "To wa ya gaya miki soyayyar gaskiyarce? Ai dama ta kwaɗayi
ne da bin ƙyalƙyalin duniya, da sun ɗauka ɗan Honourable ne tunda attajiri ne ya tara
dukiya,sannan shi ya nuna mata cewa shi ke kan dukiyar ma yana yadda ya so, to yanzu dai to cut
the story short aure zai lalace, don ta ce ba za ta taɓa zama da shi ba."
TAIMIYYAH ta jinjina kai har zuciyarta ta ke jin babu daɗi, ta buɗe baki ta ce, "To Allah sa
rabuwar ya zama alkhairy ne, amma Umma ba za ta ji daɗi ba, ga mutuwar auren Zuhurah ga
ɗaura auren Baba Sani gobe anya abin bai yi mata yawa ba Yasmeen? Wallahi har na ji tausayinta
ya kamani."
Yadda TAIMIYYAH ta yi maganar bilhakki cike da nuna zallar alhini akan fuskarta, ya sanya
Yasmeen jan tsaki ta ce, "Wallahi bata bani tausayi ba TAIMIYYAH, abinda ta shuka ne za ta fara
girba, ba dai sun ce ke ce ba za ki cigaba ba to ai gashinan tun ba a je ko'ina za su fara ganin aya.
Don ni babu tausayin Umma a raina ko kaɗan, kuma auren Baba Sani da Ummie ina ga babu
wanda ya kaini murna da wannan haɗin, ziga ta zan ta yi ta tabbatar ta kwance duka notikan kan
Baba Sani da salon luv ɗin ba bai taɓa sanin da shi ba."
Yasmeen ta kai ƙarshen maganar suna kwashewa da dariya tare da TAIMIYYAH, kafin
TAIMIYYAH ta tsaida dariyar tana cewa, "Wallahi Yasmeen baki da kirki, yanzu don baki da
kunya sai ki iya gaya mata hakan?"
Yasmeen ta taɓe baki ta ce, "Naki wasa ne Yarinya, ke yanzu ba kwance na A.Maleek ki ke yi ba
munafuka."
Suka sake sakin dariya TAIMIYYAH na cewa, "Allah sarki ni babu abinda na kwance akan Sweet
Amore ɗina."
Yasmeen ta sake sanya dariyar yadda TAIMIYYAH ta wani narke murya wajen kiran sunan, ta
buɗe baki cike da tsokana ta ce, "Ke ni rabani da wannan narke muryar, ni duk na ƙosa in ji kin
fara laulayi, ko ɗan Egypt za a samo mana ne?"
TAIMIYYAH ta bankawa Yasmeen harara ta yi cuting call ɗin tana faman sakin murmushi, ta kai
hannu ta shafa cikinta tana jin ƙirjinta na faman doka mata da wani yanayi me wuyar fassara. Ta
buɗe baki a hankali ta ce, "Ciki kai no! Ba yanzu ba Yasmeen am too young a ce zan iya haihuwa
yanzu."
Ta yi maganar tamkar wata taɓaɓɓa kai ka ce Yasmeen na jin ta ne,ta cigaba da blushing tana
zamewa ta kwanta sosai bisa bed ɗin.
Kamar wacce aka tsikara da allura ta yi saurin tashi, ta janyo wayarta ta kira layin Iyah, suka daɗe
suna magana akan Zuhurah da kuma zancen ɗaura auren Ummie a gobe, daga ƙarshe su kai
sallama da Iyah TAIMIYYAH ta kashe wayarta, zuciyarta na hasaso mata irin mummunar yanayin
da Umma za su shiga ciki.
Sai kusan 2pm suka haɗu a dining don yin lunch, A.Maleek Ado shi ne ya ɗaga waya ya kirata
akan ta fito. Lokacin da ta ƙariso wajen dining ɗin kallo ɗaya ta yi masa ta yi saurin ɗauke kanta,ta
miƙe ta yi serving ɗinsu tare da komawa ta zauna, tana jin tasirin idanun A.Maleek a kanta sosai.
Suhailah ko tunda TAIMIYYAH ta fito take satan kallon yadda kullum ta ke sake wani glowing,
kyawunta na sake fitowa matuƙa ga wani cika da ta yi a fuska da ƙirjinta. Ita kanta da ta ke mace
tana ganin kyawun yana kuma tsaya mata a rai ina ga A.Maleek ɗin kuma? Wani irin kishi ya taso
ya danne zuciyarta, hakan yasa hiran ma da taso jan Maleek ɗin da shi ta kasa, ta dinga tura
abincin a baki ba tare da yin ko tari a wajen ba.
Wannan karon ma TAIMIYYAH ta riga tashi ta bar wajen ta koma ɗaki,ta ɗauki wayarta ta fara
karatun novel don ɗebe kewa.
Tana tsaka da karatun ya shigo cikin ɗakin yana takowa zuwa bakin bed ɗin ya zauna,
TAIMIYYAH ta ɗaga manyan idanunta ta sauke akansa tana maida dubanta kan wayarta.
A.Maleek ya saki smile yana miƙa hannu ya ƙwace wayar yana cewa, "My pure zuma wai laifi na
yi ne ake ta faman basar da ni haka?"
TAIMIYYAH ta shagwaɓe fuska cike da zallar shagwaɓa ta ce, "Ni ce na ke basar da kai Sweet
Amore?"
A.Maleek ya sake sakin smile yana sake hayewa kan bed ɗin ya janyota zuwa jikinsa, ta buɗe baki
za ta yi magana ya yi saurin rufe bakin da nasa ya bata wani deep kiss, ya zare bakinsa daga nata
ya ce, "Ba za ki daina amsa min tambaya da wata tambayar ba ko pure zuma?"
TAIMIYYAH ta zame daga jikinsa tana gyara wuyar rigarta ta ce, "Sorry! To ai ni ban san ina
basar da kai ɗin bane Hubby."
Maleek ya jinjina kai ya ce, "Okey! But meyasa ba ki son cin abinci sosai idan aka haɗu a dining
ana ci gaba ɗaya, akwai abinda ke takuraki ne?"
TAIMIYYAH ta yi saurin girgiza kai ta ce, "No! Babu komi fa, kawai kwana biyu bana jin cin
abinci ne,sai su Biscuit na ke ci idan na shigo ɗaki."
Maleek ya sake janyota zuwa jikinsa ya rungume yana cewa, "Ohh! To kodai har na yi ajiya ne a
nan Baby?"
Ya yi maganar yana zura hannunsa ya shafo lafaffen cikinta, hakan yasa TAIMIYYAH saurin kai
hannu ta ture nasa, cike da zallar shagwaɓa ta ce, "No! Sweet babu komi fa, don Allah kabar min
waiwayi a ciki."
Da ƙyar A.Maleek ya barta kafin ya bar ɗakin yana jaddada mata cewa ta fito falo, ta daina zama a
ɗaki tana takura kanta, memakon ta fito falon sai ta cigaba da kwanciya tana karatun novel ɗinta,
bata san yana falon ba shiyasa bata fitan ba har sai da ya kira wayarta sannan ta fito.
A hankali ta ke takowa zuwa cikin falon idanunta akan Suhailah da tayi matashin kai da laps ɗin
Maleek Ado, hakan yasa TAIMIYYAH jin wani abu ya soki zuciyarta, ta yi gaggawar ɗauke
idanunta akan su tana ji kamar ta koma ɗaki, amma ta riga ta kawo tsakiyar falon. Sai ta nemi
kujerar da ke kusa da ita ta zauna zuciyarta na sake matsewa, Maleek ya ɗaga ido ya sauke akan
TAIMIYYAH wacce ta ɗauke kai daga dubansa cikin sauri. Suhailah ganin fitowar TAIMIYYAH
yasa ta sake narkewa a jikinsa tana faman masa wani irin salo don ɗauke hankalinsa, duk abinda ta
ke yi TAIMIYYAH na satan dubanta zuciyarta na sake cika da zazzafar kishi. Kiran wayarta da
aka yi yasa ta duban wayar ta ga Zee ce me kiran, sai kawai ta tashi tana barin musu falon ta koma
ɗaki, duk su ka bi bayanta da kallo, A.Maleek na jin wani haushi na kama shi,don ya fi son ta
zauna yana kallonta a kusa da shi ko da ba zai mata komi ba.
Da dare TAIMIYYAH ce ta yi girkin dinner suka shirya komi bisa dining ita da su Rabecca, kafin
ta wuce ɗaki don yin wanka ta ɗauro alwalar sallar Magriba.
Sai da ta jira aka yi sallar Isha'i sannan ta shirya cikin wata doguwar riga mara nauyi, daga samar
rigar ya kamata tare da fiddo cikar ƙirjinta da babu Bra, sai daga ƙasa rigar ta buɗe sosai. Tsayin
rigar iya guiwarta ya tsaya ta yi kyau sosai kamar wata Ƴar 16yrs, bata shafa komi akan fuskarta
ba sai kwalli, baya ga shi ko powder bata shafa ba bare aje ga man baki don bata son ɗaukar
magana,tunda ba ranarta bace bare ta saki jiki ta tsara masa kwalliyar ɗaukar hankali.
08:40pm ta ji kiran A.Maleek ya shigo wayarta, bata ɗauka ba sai kawai ta fito daga ɗakin tana
riƙe da wayar a hannu ɗaya, ɗaya hannun na dafe da guiwar ƙafarta dukkanin jikinta na fitar da
sassanyar ƙamshinta me narkar da zuciya.
Tun daga nesa Suhailah da ta hango tahowar TAIMIYYAH ƙirjinta ya doka da wani matsanancin
kishi, gaba ɗaya sai ta raina rigar da ke jikinta wanda ta ke ganin ta kai maƙura wajen bayyana
surarta, amma sai gashi ta jikin TAIMIYYAH ta ɗauki hankalinta, tare da bayyana kyawun
TAIMIYYAH a zahiri. Ta rasa meyasa kyawu da cikar halittar gurguwar ke ɗaukar hankalinta, ta
ɗauke idanunta daga kanta tana dawo da dubanta kan uban gayyar, sai ta ga gaba ki ɗaya
hankalinsa na kan TAIMIYYAH,da ke daf da ƙarisowa wajen dining ɗin. Wani azababben kishi ya
sake turnuƙe zuciyarta, ta maida kanta ga duban yadda aka tsara table ɗin tana ji zuciyarta na sake
shiga ƙunci.
TAIMIYYAH ta faɗi hakan lokacin da take jan kujeran dining ɗin baya, tana me aje wayarta ta
jingina ƙafarta me laluran don jin daɗin tsayuwa, ko kaɗan bata kalli side ɗin da A.Maleek ke
zaune ba, wanda ya kafeta da mayun idanunsa zuciyarsa na sake narkewa akanta, don shigar ba
ƙaramin tsokano shi ya yi ba musamman yadda kayansa suka cika ƙirjinta kamar wacce ke sanye
da Bra.
Shi ta fara serving ta tura plate ɗin gabansa tana ƙin duban fuskarsa, ta ɗauki wani plate ɗin ta yi
serving Suhailah potato salad with rousted chicken, sai ta ɗauki wani ƙaramin bowl ta zuba mata
soup ɗin fish a ciki ta tura gabanta. Ita kuma soup ɗin ta zuba da potato salad ɗin ta yanki rousted
chicken ɗin kaɗan daga gefen salad ɗin, sai lokacin ta ɗaga manyan idanunta ta sauke akansa
lokacin da ya ke kai spoon ɗin soup ɗin fish baki. Idanunsu ya sarƙe da juna ta yi saurin ɗauke
dubanta ta mayar kan abincinta, har lokacin tana jin idanunsa na yawo a jikinta.
A.Maleek wanda daɗin soup ɗin ya ratsashi, sai ya sake ɗebo wani ya kai baki, yana jin wani
wutar ƙaunarta na sake bin jininsa. Suhailah kanta ba ƙaramin daɗin abincin ta ke ji ba,tana
mamakin yadda gurguwar ta san kan sarrafa nau'ikan abinci masu daɗi da birgewa ko a ido, tana
cin abincin ne amma zuciyarta na cigaba da couting, tarin abubuwan da take gani a wajen
gugrguwar Maleek ɗin, da ke tsaya mata arai yana kuma bata mamaki, sabida bata taɓa tunanin za
ta sameta da wani baiwa ko iyawar da zai hana zuciyarta sukuni ba.
Ita dai TAIMIYYAH cin abincinta ta ke yi hankali kwance, ko kaɗan bata kuma damuwa da duban
side ɗin da suke ba, har ta kammala cin abincin ta xari tissue ta goge mouth ɗinta, sai ta miƙe tana
ɗaukar wayarta ta ce, "Gud night!"
A.Maleek da Suhailah suka dubeta a tare Suhailah na cewa, "Okey! Allah huta gajiyar girki."
TAIMIYYAH ta saki smile ɗin da ya sake motsa zuciyar gogan nata, bata ce komi ba ta defe
guiwar ƙafarta ta fara takawa don baro dining area ɗin, tana jin rakiyar idanun A .Maleek a kanta
har ta ɓacewa ganinsu.
Lokacin da ta isa ɗaki sai ta zauna a bakin bed ɗin tana sauke numfashi, tare da jinjina yadda ta
iya riƙe kanta wajen ƙin dubansa lokacin da take baro dining area ɗin, duk da cewa zuciyarta na
cike da kwaɗayin kallonsa da son ganin wannan kyakykyawar smile ɗin da zai jefe ta dashi. Ta
sake sauke numfashi zazzafar ƙaunarsa da shauƙi na sake kassara zuciyarta, ta zame hankali ta
kwanta rigingine tana tunanin yadda rayuwa za ta kasance musu tare da juna idan sun bar ƙasar.
Sosai ta ke hango zafin kishinta a idanun Suhailah da irin kallon da take bin ta da shi duk idan sun
zo cin abinci, ta lumshe idanunta tana kisima lamura da yawa a cikin zuciyarta. Sam bata ji
shigowarsa ba sabida ta yi nisa a duniyar tunani, hannuwansa kawai ta ji ajikinta yana me ɗagota
baki ɗaya ya azata bisa cinyarsa,ƙamshin junansu ya bugi hancinsu,A.Maleek na kai hannu ya
shafa saman ƙirjinta murya can ƙasa ya ce, "Sweet shi ne ko gud night ɗin ni ba a ce min ba,ki kai
tahowarki ko kallo ma ban ishe ki ba ko? Baki san yadda ki ka ɓata zuciyata ba da yin hakan ko?"
TAIMIYYAH ta dubesa cike da narke murya ta ce, "Sorry! Luv ban yi don ka ji haushi ba, kawai
bana son irin kallon da kake min a gabanta ne,duk sai in ji na tsargi kaina."
A.Maleek ya lakace face ɗinta yana cewa, "Wannan ba hujja bane da za a dinga basar dani my
pure zuma, next time kar ki ƙara irin hakan kin ji wife?"
TAIMIYYAH ta ɗaga ido ta dubesa tare da jinjina kanta ta ce, "Na ji Hubby ba zan kuma ba
Sorry!"
A.Maleek ya kai bakinsa ya sumbaci goshinta ya ce, "Gud gal, but give me a kiss luv please!"
TAIMIYYAH ta bashi light kiss a side face ɗinsa tana cewa, "Please my Amore ka tafi kar ta ga ka
biyoni ka daɗe hakan babu kyau."
Yadda ta yi maganar cike da magiya tana narke masa yasa shi tashi yana cewa, "Korata ma kike yi
ko Luv? Shikenan zan tafi but za ki zo hannu ai, za ki biya bashin da ki ke ci ne dalla-dalla."
A.Maleek na murmushi ya bar ɗakin yana jin ƙaunarta me yawa na bin jininsa, yana fita
TAIMIYYAH ta kulle ɗakinta ta yi shirin kwanciya bacci.
_____________
*Gyallesu, Zaria.*
Baba Sani bai shigo gida daga fitan da ya yi tun safe ba, sai wajen goman dare yana tunanin zuwa
time ɗin Umma ta gama duk wata tijararta ita kaɗai ta yi laushi. Sai dai bai sani ba shigowarsa
kawai ta je jira ta sake ɓallewa da wata sabuwar tashin hankalin, wai don ma Hajiya Barirah ta zo
gidan da rana ta ɗan taushi zuciyarta, don da har cewa ta yi za ta wajen Iyah ta yi mata ruwan
tijaran da sai dai ta sanya ɗan nata ya sake ta ƙarshen rashin ƙauna kenan, sai da Hajiya Barirah ta
yi wa Umma tatas tare da tsinewa yadda kanta kwata-kwata baya ja, sannan Umma ta shiga
hankalinta ta fasa zuwa sashin Iyah.
Duk iya yadda ta so Baba Sani ya kulata a yi tashin hankali bai yi hakan ba, hasalima shigewa
ɗakin baccinsa ya yi ya kulle ya bar Umma a falo tana zuba ruwan tijara, tare da zubar da muggan
kalamai da ɗaukar alwashi masu yawa akan Ummie. Ya toshe kunnuwarsa bai kulata ba duk da
yadda wasu kalaman su ka dinga ƙona zuciyarsa,amma haka ya shanye ya danne zuciyarsa tare da
ba banza a jiyarta, dama ya riga da ya ci abinci a waje so bai nemi komi ba bare ta samu kafan da
za ta sake kunna shi.
Umma hakan da Baba Sani ya yi mata sai ya sake sanyata jin kamar za ta ari hauka, sabida ta so
ace ya kulata ne ta sake samun damar amayar masa da tijaran da bai taɓa tunani ba,ta yi zaman
ƴan bori a tsakar falon tana rushewa da kuka tare da cigaba da maganganu tamkar zata zare,
idanun nan sun sake ƙanƙacewa sunyi mitsi-mitsi da ruwan bala'i.
Da ƙyar ta iya baro side ɗin Baba Sani ta kai kanta ɗaki, tana jin zuciyarta da ƙirjinta na sake
ɗaukar zafi. Kanta ya yi wani irin gingirin tamkar an ɗaura mata dutsen dala akai, koda ta kwanta
don ta samu bacci ya ɗauketa hakan ya gagara.
Kusan yadda ta ga rana haka ta ga dare ko kaɗan bata samu wani bacci ba, sai goshin asuba baccin
ya sace ta shiyasa ko sallah bata samu yi ba sai goman safe.
Zuwa lokacin tuni Baba Sani da tawagan ƴan Rimi sun kama hanyar Kaduna, sabida ɗaura auren
sha ɗaya na sefe za a yi, shiyasa suka fita tun tara na safe.
A bakin Zuhurah Umma ta ji cewa su Baba Sani sun wuce, shi dama Sadeeq Baba Sani ya hana
shi zuwa weekend a jiya, ya ce ya jira yau a ɗaura aure sai a ɗakko Amarya Ummie a taho Zaria.
Umma kuka ya ƙwace mata tana sake jin matsanancin ciwo a zuciyarta da kanta da ke faman sara
mata, idanunta sun sake zurmawa tare da ƙanƙacewa, Zuhurah ta dube ta ta ce, "Umma don
girman Allah ki sawa zuciyarki salama, don Baba ya auro Ummie ba fa ƙarshen rayuwarki ce ta zo
ba,ki yiwa Allah ki kwantar da hankalinki kafin ta zo ta fahimci cewa kin ɗaga hankalinki akanta
ta ji daɗin raina ki."
Umma ta dannawa Zuhurah wata uwar a shar tana cewa, "Ta daɗe bata ce na ɗaga hankalina ba
Zuhurah, ke baki san bala'in da nake ciki bane abubuwa sun yi min yawa, da wani takaicin ake so
in ji? Ga matsalar fitowarki ɗakin miji, gata Basmah da ke can ta kasa mallakar zuciyar mijin sai
fuskantar wulaƙanci da raini, sannan ga wannan masifar na auro min Samha da wanne ki ke so in
ji?"
Umma ta kai ƙarshen maganar tana dafe saitin zuciyarta da ke barazanar yowa waje, Zuhurah da
tausayin Umma ya kamata sai ta kai hannu ta share hawayen da suka zubo mata ta ce, "Allah shi
kyauta kawai shi ne abin cewa Umma, amma da alamu duniya so take yi ta juya mana baya a
lokacin da muke tsaka da buƙatar muyi gaba da gaba da ita."
Umma ta sake danne saitin zuciyarta da ƙarfin gaske kafin ta yi ƙarfin halin cewa, "Allah ya isa
tsakanina da Iyah, domin duk ita ce silar jefamu cikin wannan masifar, babu wacce ta ƙulla
wannan auren sai ita, waya sani ma ko matsiyaciyar gurgurwar can ta bata shawaran a haɗa auren,
tunda na ga sun ƙulle da samhar yanzu, ji da gurguwar ta ke yi tamkar ƴar cikinta, sabida tsabar
iya bariki da neman gindin zama a wajen Iyar, gashi kuma ta samu gindin zamar tunda anyi
nasarar cusawa Sani aurenta."
Zuhurah sai da Umma ta ambaci kalmar gurguwa sannan ta tuno da TAIMIYYAH, wani abu ya
matse zuciyarta me ɗaci tana jin son sanin a wani hali TAIMIYYAH ke ciki yanzu? Ta tuno da
chart ɗinsu da Anty Laurat wacce ke zuzuta mata haɗuwar da TAIMIYYAH ta sake yi, don ta ga
wani pic ɗinta data ɗauka a Lagos tare da Maleek Ado.
Zuwan Hajiya Barirah gidan ne ya fanshi Zuhrah daga aikin rarrashin Umma, sai ta koma ɗaki
suka dinga vid call da Basmah suna tattauna halin da Umma ke ciki, Basmah na ji tamkar ta yi
tsuntsuwa ta zo gidan amma babu hali, don tayi iya yin ta akan Nass ya kawota amma ya ce ba za
ta fara fita ba sai ta yi watanni shida a gidansa.
Shiyasa ta ci kukanta ta share hawaye babu halin fitowa ta zo ɗin, sabida ya kasa ya tsare ko nisa
bai yi don ma kar ta fito bada izininsa ba, ga kuma Hajiya Hajara da ita ma ke sanye da idanunta
akan Basman.
_____________
Ƙarfe huɗu da rabi aka zo da Amarya Ummie Zaria, in da akai mata masauki a part ɗin Iyah,
wacce bata tara kowa ba sai ƴan Rimi ne kaɗai suka taru da la'asar ɗin don tarban Amarya. Bayan
ƴan rakiyar Amarya sun tafi ne su Inna Lami suka rakata zuwa sashinta wanda yake mallakin Baba
Sani ne a yanzu don shi ya ci gadon wajen,an sake sabon fenti tare da gyara ko'ina sai ƙamshi
kawai ke tashi.
Babu mutum ɗaya da zai kwana cikin dangin Ummie duk juyawa suka yi a ranar aka barta ita
kaɗai, sai faman zare ido ta ke yi tana tunanin yadda za ta dubi Baba Sani a matsayin Angonta,
bayan alaƙa ta jini me ƙarfi da ke tsakaninsa da marigayi Sameer, wannan tunanin ya dawo mata
da mutuwar Sameer sabo a zuciyarta, sai ta kifa ciki tana kuka me motsa zuciya............✍🏻
#Ɗansabo ce#
[12/15, 11:47 AM] +234 703 040 9541: Littafin TAIMIYYAH paid book ne,ga duk wanda ta
tsincesa a kowani irin group ne,kiji tsoran Allah karki karanta sai kin biya 500 naira only.
Za ku iya min magana ta wannan number ɗin 08167768704, ko kuma ku turo kuɗin ku kai tsaye ta
wannan account ɗin 0504192664 aisha ibrahim dansabo GTbank.*
Masu turo credit za ku turo katin MTN na 500 ta wannan line ɗin 08167768704.
_Ina ƴan kasuwa masu buƙatar a tallata muku hajar ku? Maza ku garzayo da kuɗi ƙalilan a tallata
muku kayan siyarwanku sai dai kawai ku ji ana kiran waya don buƙatan sayan kayan ku,ku
tuntuɓeni ta layina kamar haka 08167768704._
*86*
Daga can ɓangaren Umma kuwa su Hajiya Barirah ne da wata ƙawarsu Hajiya Lubah, ke ta faman
dannar ƙirjin Umma wacce tunda suka ji an kawo Amarya, hankalin Umma ya sake tashi ta fashe
musu da kuka tana faman surutai tamkar zautacciya.
Da ƙyar Hajiya Barirah da Lubah suka shawo kan Umma ta yo wanka ta shirya cikin wani
haɗaɗɗen lace, kalar mint green ne da ya haska fatarta, sai dai fuskarta gaba ɗaya ya kumbura,
idanunnan sun yi mitsi mitsi da su.
Hajiya Barirah ta dubi Umma lokacin da suke shirin tafiya ta ce, "Hajiya Zuwairah matsonan ki ji
wata shawara."
Umma ta matsa kusa da Hajiya Barirah har jikinsu na gugar juna, Hajiya Barirah ta shiga raɗa
mata wasu kalamai wanda duk bin ƙwaƙwƙwafina na kasa jiyo me take raɗawa Umma. Umma
tayi kasaƙe tana sauraren Hajiya Barirah kafin Hajiya Barirah ta kai ƙarshen raɗar nata da cewa,
"To kin dai ji na gaya miki, idan kuma har kika bari wannan damar ta wuce ki to ke ce a ruwa don
na kula ke ɗin bakisan abinda ya dace ba, haukan kishinki da sakarcinki ke sa sam bakya nasara
Hajiya Zuwairah, ina ce akan idanunki na ke yadda na so a gidan Alahji Lado, ina juya dukkanin
Yaransa a tafin hannuna, kuma wallahi da kwanyanta kawai na ke aiki babu Boka babu Malam,
tsabar kissa da iya kwantar da kai amma ke kin gaza yin hakan, tun akan waccar gurguwar na
raina kwanyarki Hajiya Zuwairah, da yanzu Yarinyar ke ki ka maye mata gurbin uwa, kin ga da
har mu sai mun ci arziƙin mijin mun famtama yadda mu ke so, amma ƙaramar daƙiƙiyar
kwanyarki bata bar ki kin yi abinda ya kamata ba tun farko. Don haka idan har ki ka bari Samha ta
bar garinnan ba ki bi shawaran dana baki mun samu abinda mu ke nema ba, to kar ma ki nemi
idan lamura suka sake kwaɓe miki."
Umma ta jinjina kai ta ce, "Hakan ma ba zai faru ba Hajiya Barirah, zan bi duk yadda ki ka ce
amma da yiwuwar yau ba zan iya rintsawa ba sai jinina ya hau, domin zuciyata ba za ta taɓa
hutawaba,bayan Sani zai kwanta da wata mace bayan ni, kai! Wallahi mutuwa zan yi ......"
Hajiya Lubah ce ta bige bakin Umma ta hanata ƙarisa kalamanta, cike da takaicin Umma ta ce,
"Amma Hajiya Zuwairah baki da man kai ko? Wai akan ki aka fara kishiya ne? To wallahi idan
baki iya takunki ba cikin ruwar sanyi wannan Amaryar za ta ƙwace Sani a hannunki."
Umma ta rintse ido tana ji zuciyarta tamkar za ta buga ta ce, "Ba za ku gane me nake ji bane
shiyasa, amma na gode da kulawarku a kaina ku tafi kawai in ji da kaina Hajiya Lubah, amma ku
tabbatar kun bar wayoyinku a kunne don za a iya kiranku a ce gani can a gadon asibiti."
Umma ta kai ƙarshen maganar tana rushewa da kuka, ƙirjinta na sake mata nauyi da ƙuna hakanan
su Hajiya Lubah su kai sallama da ita suka bar gidan.
Bayan tafiyansu ne Zuhurah ta shigo ɗakin baccin Umma, hannunta riƙe da plate ɗin indomie da
kofin shayi, wanda ta haɗowa Umma don ta samu ta ci ta sha shayin don tun safe rabonta da
abinci. Da ƙyar ta shawo kan Umman ta ci noodles ɗin kaɗan ta shanye shayin, ta cigaba da
rarrashinta don ta kwantar da hankali amma Umma ta gaza yin hakan, kukanta ta ke yi tamkar
ƙaramar Yarinya.
A haka Baba Sani ya shigo ya samesu misalin tara da rabi na dare, ya samu bakin gadon da Umma
ke kai ya zauna, Zuhurah ta gaida shi tana tashi ta bar musu ɗakin zuciyarta cike da takaicin
Baban nasu.
Umma ta sake barkewa da kuka ganin yadda Baba Sani ya yi mata wani masifar kyau, cikin
shigar farar gezner da ke jikinsa, ya ɗaga ido ya dubi Umma kafin ya buɗe baki ya ce, "Zuwairah
yanzu halin da ki ka zaɓi ki jefa kanki kenan sabida kawai na yi aure? Kin ga yadda ki ka fita
hayyacinki kuwa ki ka jeme tamkar wacce ta yi jinyar shekara guda. Samha ce fa aka auro miki
kin santa ta sanki, ku ba bare bane a idanun juna, to meyasa za ki ɗauki tashin hankali ki sanyawa
rayuwarki har ki gallabi kanki har haka? Aure an riga an ɗaura shi mu da ke duka ya zama tilas mu
rungumi ƙaddara mu zauna da juna lafiya, haka ubangiji ya rubata Zuwairah don haka babu wanda
zai kaucewa rubutacciyar ƙaddararsa. Ke ba ƙaramar yarinya ba ce da ki ke da buƙatar sai an
zauna an dinga kwakwkwafa rarrashi da yi miki wa'azi, ki yi haƙury Zuwairah ban yi wannan
auren don in tozarta ki ba."
Baba Sani ya kai ƙarshen maganar yana tashi tsaye, Umma ta dubi idanunsa ta ce, "Yanzu Sani ni
ka ke cewa bana buƙatar a rarrasheni, eh! Lallai Samha ta samu zuciyarka sai dai Allah ya yi min
sakayya."
Daga haka ta sake rushewa da kuka tana kallo Baba Sani ya je falo ya ɗakko ledar manyan
gasassun kaji da fresh milk da ya shigo da su, ya kawo mata ya aje bisa bed ɗin tare da yi mata sai
da safe ya yi fitowarsa.
Umma ta saki wani razanannan kuka ta kai hannu ta watso ledojin ƙasa suka tarwatse, ta shiga
sumbatu tana sakin maganganu tamkar wacce za ta zare.
A can ɓangaren Amarya Ummie kuwa Baba Sani ya shiga ya taddata har lokacin tana kuka, sai ya
aje ledojin hannunsa daga kan side drawer ya nemi bakin bed ɗin ya zauna. A hankali ya kai hannu
ya ɗago da Ummie daga ruf da cikin da ta yi yana cewa, "Haba Samha kukan ya isa haka please!
Ka da kanki ya yi ciwo, koma mene ne kika tuna ki sani addu'a shi ne magani, kuma shi ne abinda
yafi buƙata daga gare mu baki ɗaya."
Yadda Baba Sani ya yi maganar cikin raunin murya, ya sanya Ummie dubansa da idanunta da
sukai jajir, zuciyarta na cika da mamakin yadda ya yi saurin gano akan me ta ke kukan, kusancin
da ke tsakaninsu ya sanyata sake jin wani abu na gudu a jinin jikinta, musamman da hancinta ya
cika da daddaɗan ƙamshinsa.
Ta zame jikinta a hankali daga garesa tana cigaba da jan ajiyar zuciya, Baba Sani da ke jin wani
yanayi na sake fisgar zuciyarsa zuwa gareta, sai ya lumshe idanunsa tare da sake buɗe su akan
Ummie ya ce, "Please Samha ki taimakeni ki tsaida kukan hakanan, kin yi sallah ma kuwa?"
Ummie ta gyaɗa masa kai alamun ta yi, sai ya miƙe tsaye yana zare babbar rigarsa ya aje bisa bed
ɗin , ya sake dubanta ya ce, "To tashi ki ɗauro alwala mu yi sallar nafila sai ki zo ki ci wani abu
ko?"
Nan ma kai kawai ta gyaɗa masa tana zamowa daga kan gadon a hankali ta nufi hanyar toilet, ba
tare da ta cire lulluɓin da ke jikinta ba. Baba Sani ya bi ta da kallo yana sake jin wani yanayi me
wuyar fassara, ya cigaba da tsayuwa yana ƙarewa ɗakin kallo tare da shaƙan daddaɗan ƙamshin da
ke tashi a cikin ɗakin.
A kan idanunsa Ummie ta fito wacce a tunaninta ya bar ɗakin ne, shiyasa ta cire lulluɓinta ta riƙo
shi a hannu, sai ya bi ta da ido yana ƙarewa shigar jikinta kallo wanda ya tafi da zuciyarsa.
Ta sadda kanta ƙasa tana ƙarisa takowa cikin ɗakin ba tare da ta yadda sun sake haɗa ido da shi ba,
ta isa bakin gadon ta zauna tare da bin bayan Baba Sani da kallo wanda ya nufi hanyar toilet ɗin
da ta fito, ga tsananin mamakinta shi har da wanka ya yo ba alwala kaɗai ba. Ya fito ɗaure da
babban towel da tsayinsa ya kai masa iya guiwa, Ummie ta yi saurin ɗauke kanta daga dubansa
ƙirjinta na faman bugawa da sauri-sauri. Baba Sani ya wuce ya fito yana nufan ɗakin da zai zama
mallakinsa, wanda tun a jiya ya shirya kayayyakin da zai buƙata a ciki, ya shirya kansa cikin
fararen pajamas ya fito ya koma zuwa ɗakin Ummie.
Shi ya ja su sallar nafila ra'aka biyu bayan sun idar ne ya dafa kanta ya karanto addu'a kamar
yadda shari'a ta koyar, sannan daga ƙarshe ya yi mata wasu ƴan tambayoyi tana bashi bashi amsa
kanta a ƙasa.
Da kansa ya fita zuwa kitchen ya samo plate da cups ya dawo ɗakin, ya ɗakko ledar gasassun
kajin da ya shigo da su ya dire akan tsakiyar carfet ɗin ɗakin, ya bubbuɗe tare da juye ƙatuwar
kazar guda ɗaya da taji kayan haɗi da wani irin sauce sai ƙamshi ke tashi, ya ɗaga manyan
idanunsa ya dubi yadda Ummie ta takure jikinta, kafin ya miƙe ya isa in da ya barta akan sallaya
ya riƙo hannunta,a kunyace take biye da shi har zuwa wajen da ya aje kayan ƙwalam ɗin.
Duk iya jin nauyi da kunyarta haka ya dinga ciyar da ita naman abaki, sai da ta ci me yawa sannan
ya barta ya ci nasa yayi ƙat! Ya sha fresh milk me yawa ya yi hamdala, yana kwashe kayan ya kai
kitchen ya sake dawowa cikin ɗakin.
"Wife ko sai na taimaka miki wajen sauya kayan jikinki zuwa na bacci ne?"
Baba Sani ya jefawa Ummie tambayar idanunsa akanta, ta yi saurin girgiza kai wani bahagon
kunya na lulluɓeta, sai ta tashi ta fita zuwa ɗakin da ta tabbatar nan aka aje kayanta, ta sauya
kayan jikinta zuwa na bacci tare da hayewa gado ta yi kwanciyarta.
Baba Sani jin shirun yayi yawa ne ya sanya shi bin bayanta zuwa ɗaya bedroom ɗin, tunda ya
hangota akan bed ɗin ya saki murmushi yana ji tamkar ana azalzalar zuciyarsa ne akanta, wani irin
shauƙi ke fisagarsa me tsananin ƙarfi. Ya cigaba da takawa zuwa bakin bed bayan ya yi musu light
off, Ummie na jin takunsa ta sake dunƙule jikinta a cikin duvet, ƙirjinta na cigaba dakowa da wani
irin tsoro da bata san na mine ne ba.
Tana jin time ɗin da ya ƙarisa hawowa bed ɗin yana lalubarta, sai ta sake matsawa can ƙarshen
gadon zuciyata na dokawa da firgici me tsanani. Jin hannuwansa a jikinta yana shirin janta zuwa
jikinsa, ya sanyata sakin kukan da bata san daliliba, Baba Sani ya ƙarisa mannata da jikinsa yana
kai bakinsa ya rufe nata bakin da ke kukan.
Daganan ne lamura suka fara kankama wanda a daren Ango Baba Sani sam bai ɗaga leg ba, sai da
ya tabbatar Ummie ta zama shi ya zama ita halak malak!
A ɓangaren Umma kuwa yadda ta ga rana haka ta ga dare, sam bata rintsa ba tun tana kuka da
hawaye har suka ƙafe ta koma yin na zuci kawai, hakan ya haifar mata da shiga mummunar
yanayi,kanta ya yi mata wani irin nauyi, da ta tashi sai jiri ya ɗebeta ya maida ta kan gado.
Hakan ya tilasta ta yin lamo a kan bed ɗinta tana jin yadda ciwan kanta ke sake hauhauwa,
zuciyarta na cigaba da yi mata nauyi matuƙa.
*Washegary.*
Baba Sani tare da Amaryarsa Ummie suka sallo wanka, sai faman noƙewa ta ke tana zuba masa
shagwaɓar da bai saba gani a wajen mace ba, duk ta sake susutashi da jefa zuciyarsa cikin wani
shauƙi me zafi.Koda suka fito shi ya ja su jam'i suka gabatar da sallar asuba, daga kan sallar ya
sake ɗaukar Ummie cak! Ɗinta zuwa bed yana kai hannu ya zare rigar baccin da ke jikinta. Duk
iya magiya da shagwaɓar da take zuba masa akan ya barta bai jita ba,sai da ya tafi second round
sannan ya rungumeta a cikin jikinsa yana sanya mata albarka, zuciyarsa gaba ɗaya ta gama
narkewa a ƙaunarta da jin wani irin zazzafar yanayi da bai taɓa hasasowa ba.
Sosai ya ke jin soyayyarta me zafi na sake fisgar zuciyarsa, wani irin runguma ya yi mata a cikin
jikinsa suka koma bacci cike da shauƙin juna.
Daga ɓangaren Umma da ƙyar ta iya tashi tana jin wani jiri na ɗibarta, hakanan ta dinga dafa
bango har ta kai kanta toilet, bayan ta gama uzurinta ta yo wanka don ta ji ƙarfin jikinta, sai ta
ɗauro babbar towel ta nufo ƙofar fitowa toilet ɗin.
Ta ku biyu ya rage ta ƙarisa bakin ƙofar jiri ya ɗebeta ta zube ƙasa, kanta na cigaba da sara mata
da wani irin ciwo me tsanani, hakan ya sa ta saki ƙaramin ihu wanda ya faɗa kan kunnin Zuhurah
da shigowarta cikin ɗakin kenan. Ta nufo bakin toilet ɗin a guje tana kiran, "Umma! Umma!
Umma lafiya meyafaru?"
Daga cikin toilet ɗin Umma ta ce, "Zuhurah zan mutu maza ki kari min Sani, ki ce masa banda
lafiya kaina na barazanar rabewa gida biyu."
Zuhurah cikin tashin hankali ta murɗa handle ɗin ƙofar, cikin sa a Umma bata sanya key ba hakan
yasa ta tura ƙofar ta shiga. Ganin Umma wanwar a ƙasan tiles ɗin bayin, ya sanya Zuhurah
fashewa da kuka tana faɗin, "Kin gani ko Umma! Umma kina neman kashe kanki akan wata banza
da bata ma san kina yi ba ko? Don Allah Umma ki dawo cikin hayyacinki kada ki jefa rayuwarki
da namu cikin garari akan wata banzar kishiya."
Zuhurah ta kai ƙarshan maganar tana ɗago Umma zaune, da ƙyar da taimakonta suka fito zuwa
ɗakin ta kwantar da Umma a kan gado, ta fito da sassarfa daga part ɗinsu ta nufi na Baba Sani don
kiransa ya ga halin da Umma ke ciki.
Zuhurah ta dinga knocking ƙofar shiga falon Ummie amma ba a buɗe ba, ta sake yin knocking a
karo na huɗu sannan ta jiyo takun tafiya. Hakan ya sanyata zubawa ƙofar idanu don ganin wa zai
buɗe ƙofar, idanunta suka sauka akan Ummie lokacin da ta buɗe ƙofar, Zuhurah ta zura mata ido
tana kallon ɗamammun kayan da ke jikin Ummie ɗin. Ummie ta yi saurin juyawa tana cewa,
"Shigo mana Zuhurah kin tsaya daga bakin ƙofa."
Zuhurah da zallar takaici ya cika zuciyarta sai ta ɗaga murya ta ce, "Ni wajen Baba na zo yana ina
ne?"
"Gani nan ki shigo daga ciki aka ce, kin tsaya daga bakin ƙofa ana wasa da ke ne Zuhurah?"
Baba Sani ya yi maganar daga cikin falon yana zaune daga ƙasan carfet, Ummie ta cika gabansa
da kayan karyawa da Iyah ta sanya Babah Ladi girkawa a kawo part ɗin, don ta san ko giyar wake
suka sha Zuwairah ba za ta taɓa sanya wa akai abinci sashin Ummie ba.
Zuhurah ta taka a hankali ta shiga daga cikin falon zuciyarta na cigaba da ɗaukar zafi, ta durƙusa
ta gaida Baba Sani tare da sanar da shi halin da Umma ke ciki,ta miƙe za ta bar ɗakin ta jiyo
muryarsa cikin tsawa yana cewa, "Dawo nan Zuhurah."
Zuhurah ta dawo da baya tana ji tamkar ta saki ihu, Baba Sani ya nuna ta da yatsa ya ce, "Baki iya
gaisuwa bane Zuhurah?"
Zuhurah ta tunzure baki tana duban side ɗin da Ummie ke zaune ta ce, "Ina kwana."
Ummie ta amsa fuskarta a sake ta ce, "Lafiya lau Zuhurah an zo ganin gida ne?"
Zuhurah da takaici ya kawota iya wuya sai kawai ta juya a guje ta fito daga falon baki ɗaya, tana
tafe tana taya Umma kukan takaicin wannan aure da Baba Sani ya yi, wanda tun kafin akai ko'ina
ta fara hango ƙurar da zai ta shi agaba,don ba ƙarya Umma ta yi ba Ummie akwai ta da buɗewar
ido, kwannanan za ta fara mai da Baban nasu wani susu akanta.
Bata rufa mintuna goma da komawa wajen Umma ba, Baba Sani ya shigo sashin ganin halin da
Umma ke ciki ya tashi hankalinsa, don bai yi tunanin abin ya kai haka ba. Cikin gaugawa ya
taimaka Umma ta sanya kaya da Hijab suka fito don wucewa asibiti, Zuhurah na gaba sai Umma
da aka kwantar a back seat ɗin tana nishi tana kiran kanta zai fashe. A haka suka nufo asibitin
ABU da ita da ke tudun wada, cikin ikon Allah suka samu aka amshe ta da gaggawa don fara bata
kulawar da ta dace.
Dole admiting ɗinta za a yi kamar yadda likita ya yiwa Baba Sani bayani, sabida jinin Umman ya
yi mummunar hawa shiyasa dole tana buƙatar kulawa a ƙarƙashin likita.
Baba Sani ya ɗaga waya ya kira Iyah ya sanar mata halin da ake ciki, Iyah kanta hankalinta ya
tashi suna aje wayar ta sanya Babah Ladi shirya abin breakfast, ita kuma ta kira Sani don ya kai su
asibitin da gaggawa.
Lokacin da Iyah suka iso asibitin sun samu Umma ta samu bacci, hannunta ɗaure da drip
fuskarnan duk ta jeme ta fita hayyacinta tamkar ba ita ba. Iyah ta ƙarisa bakin bed ɗin tana ƙare
mata kallo, tare da Allah wadai da halayya da zafin kishi irin na Zuwairah, daga ƙarshe ta yi mata
fatan samun sauƙi, tana komawa ta zauna cikin ɗaya daga cikin fafaren kujerun da aka aje don
zama a cikin ɗakin.
Babah Sani da Zuhurah suka juya zuwa gida domin Zuhurah ta ɗebo musu kaya da abubuwan
buƙata, Iyah da Babah Ladi suka cigaba da zama har zuwa lokacin da Zuhurah za ta dawo su sai
su koma gida.
Hankalin Baba Sani sai ya rabu biyu domin suna da zama akan case ɗin Zuhurah a yau ɗin, amma
sai ya kira Baba Labaran da Baba Salisu don sanar da su halin rashin sukunin da ya same shi, tare
da basu tabbacin ba za a samu yin zaman tare da shi ba.
Zuhurah ita ce ta ɗaga waya ta sanar da Basmah halin da Umma ke ciki, ta kuma kira layin Hajiya
Barirah ta sanar da ita cewa Umma na asibiti.
Daga ƙarshe Anty Laurat ta kira ta labarta mata komi, tun daga ɗaura auren Ummie da Baba Sani
har zuwa kan halin da Umma ta sanya kanta ciki, gashi mummunar hawan jini ya sameta rana
tsaka. Anty Laurat ta jinjina lamarin a ranta tare da yin Allah shi kyauta, ta kashe wayarta don
zuwa ta sanar da iyayensu halin da Ummar ke ciki.
Lokacin da Zuhurah ta dawo asibitin sai su Iyah suka juya zuwa gida, a motar Baba Sani don ba
zama zai yi ba shi ma gida zai koma, tunda ya gama biyan duk abinda ya kamata, kuma likitar ta
tabbatar musu da cewa dama kada a dinga hayaniya a ɗakin da patient ɗin ta ke, don ana so ta
samu isasshen hutu da bacci sabida yadda jininta ya hau sosai.
Don haka Zuhurah kaɗai aka bari wacce ta fito daga barandar shiga ɗakunan marasa lafiyar ta
zauna cikin kujera, tana kallo motar Baba Sani ta fice daga asibitin sai ta maida idanunta kan
wayarta tana kiran Layin Yah Sadeeq, wanda bai biyo ƴan ɗaura aure ya dawo Zaria ba ya yi
zamansa a Kaduna.
Bayan sun gama waya da shi ta sanar masa halin da Umma ke ciki sai ta kashe wayarta, tana
kunna data ta hau online rabin hankalinta na ga tunanin yadda za a kwashe da Ameeru a yau ɗin,
shin zai bata takardarta cikin salama ne ko sai an kai ruwa rana? Ganin tunani zai mata yawa ne
sai kawai ta kashe datar ma ta sake neman layin Basmah ta ji ko ɗan gagarin nata zai samu damar
kawota ta duba jikin Ummar?
*08:30pm*
Motar Baba Sani ne ta shigo asibitin yana tare da Amaryarsa a gefe, kuma tamkar haɗin baki bai
kai ga gama yin parking ba motar Nass da ke tare da Basmah ya shigo.
Hakan yasa kusan tare da juna suka jera zuwa ɗakin da aka kwantar da Umma, zuciyarta Basmah
na faman rawa duk ta ƙosa su iso ciki ta ƙarewa fuskar Ummie kallo.
Baba Sani shi ne ya fara shiga ɗakin Ummie na take masa baya, ko zama basu yi ba su Basmah
suka ƙariso suma wanda sam Baba Sani bai kula su ɗin ne daga bayansu ba,sai da sukai sallama
suka shigo sannan.
Yah Deeku da ya iso garin tunda la'asar shi da Zuhurah ne tare da Umman, Hajiya Barirah ma bata
jima da komawa gida ba. Yah Sadeeq ɗin shi ne daga zauna a bakin bed ɗin da Umma ke kai, yana
bata tea a baki tana amsa idanunta sunyi firgai-firgai.
Nass ya tsuguna har ƙasa ya gaida Baba Sani yana tambayarsa me jiki, Baba Sani ya amsa da
fara'a yana cewa, "Me jiki Alhamdulillahi! Ta ji sauƙi sannunku da zuwa."
Basmah ma ta kwashi gaisuwa wajen Baban idanunta akan Ummie, wacce ta ci kwalliya cikin
wani simple zani da riga na atamfar holland, tayi matuƙar yin kyau fuskarta na haskawa da wani
irin glowing da annuri. Basmah ta buɗe baki ta gaida Ummie da ƙyar, ganin yadda Baba Sani ke
zabga mata harara, daga haka ta ƙarisa wajen Umma wacce tun shigowar Baba Sani tare da
Ummie ta ji kanta ya sara mata, da wani irin ciwo me tsanani, shiyasa ta kasa cigaba da amsar tea
ɗin da Yah Deeku ke bata, zuciyarta sai harbawa ta ke tamkar za ta yo waje.
Ummie ta yi maganar lokacin da suke isa bakin bed ɗin jere da juna da Baba Sani, Umma ta
haɗiye wani abu me ɗaci tana jinjina kai alamun amsawa, ba tare da ta iya buɗe baki ta yi
maganaba.
Yah Deeku ya gaida Ummie cike da girmamawa, ita ma ta amsa da matsanancin fara'a tana sake
jin ƙaunarsa da yaba hankalinsa, yadda ya fita zakkah cikin yaran Umman, don shi sam baya shiga
duk wani shirmen da za ta shi ciki, yana da hankali sosai da sanin yakamata.
Nass ya iso ya gaida Umma yana aje mata kuɗi daga gefen bed ɗin, ya juya ya yiwa Baba Sani da
Sadeeq sallama ya baro ɗakin, Basmah ta raka shi da ido tana jin wani abu me nauyi a zuciyarta.
Umma ta dubi Baba Sani da ke tsaye a kanta bayan Ummie ta koma daga gefe guda ta zauna akan
kujera, su Zuhurah sai faman zabga mata harara suke,ba tare da ita tama san suna yi ba, don gaba
ɗaya hankalinta ta mayar kan wayar hannunta,tana ɗaura wasu takalma da ta yi order za su iso nan
da one week, tunda tana taɓa business sosai musamman yanzu da ta samu gadon Abie sai ta sake
zuba jari me kauri.
Umma ta jefawa Baba Sani tambayar da yafi damun zuciyarta a yanzu,tana cigaba da jin ƙirjinta
na mata zafi da ƙuna. Baba Sani ya dubeta yana mamakin yadda ta koma cikin kwanaki biyu kacal
da fara maganar aurensa da Ummie, ya buɗe baki yana cewa, "Sun zo Zuwairah, kuma Ameeru ya
rubuta mata saki ɗaya takardan na wajen Iyah na ce ta aje. An dai so akai ruwa rana kafin ya bada
takardan kamar yadda Alhaji Salisu ya sanar min,amma Alhamdulillah tunda an samu ya rubuta
ɗin."
Daga haka bata sake cewa komi ba ta maida idanunta ta kulle tana jin matsanancin kishi na bin
jininta, Basmah ta dubi wayarta da kiran Nass ya shigo ta ɗaga wayar da sauri ta kai kunni, "Da
wuri haka my Nass bafa mu yi magana ma da ita ba ina jira su Baba su wuce ne."
Basmah ta yi maganar tana yin ɗan jim alamun sauraran abinda Nass ke faɗi, kafin ta ɓata fuska ta
sake cewa, "Okey! gani nan Allah ya baka haƙury luv."
Daga haka ta sauke wayar daga kunni ranta a ɓace ta dubi Zuhurah wacce ta tsura mata ido, tana
mamakin yadda Basmah ta yi laushi haka, tana ma Nass magana cike da tsantsar kwantar da
kai,duk rashin kunyar nan babu shi ta jinjina kai lokacin da Basmah ta ce, "Kin jin wai in fito ko
ya yi tafiyarsa."
Zuhurah ta taɓe baki ta ce, "Lallai Nass na zuba miki iko Basmah, ke kuma gashi soyayyarsa ta
gama miki muguwar kamu, kin ga yadda ki ke kwantar da kai wajen yi masa magana kuwa?"
Basmah ta sake ƙasa da murya yadda Ummie ba za ta jiyo su ba ta ce, "Hmm! Sis ba za ki gane
bane, wallahi Nass ya wuce tunaninki ban taɓa sanin ɗan garari bane sai da na je hannunsa, abu
kaɗan yanzu sai ya ce idan ba zan jure zama da shi ba ƙofa a buɗe ta ke, ni kuma ina tsananin son
sa Zuhurah domin ya san ta kan iya sarrafa mace,wallahi zan iya jurar ko wani irin wulaƙanci akan
ace in rabu da Nass, bari ki ga in yi sauri kada ya fusata da yawa ya yi tafiyarsa."
Zuhurah ta ja tsaki takaicin Basmah na cika zuciyarta, cike da ɓacin rai ta ce, "Lallai Basmah aiko
sai ki ɗaura ɗammaran shan wulaƙanci da takaici a rayuwar aurenki, in dai har haka za ki saki
kanki yana taka ki da gasa miki maganganu na rashin ƙauna."
"Na ji dai hakan yafi min akan in fito mu dawo mu zube tare a gida, ayi ba wan ba ƙanin gara in
lallaɓa a hakan."
Cewar Basmah tana yin gaba wajen gadon Umma ta bar Zuhurah da baki sake, maganganun
Basmah na ƙona zuciyarta da jefa ta a tsantsar mamaki da tsoro. Wasu hawaye masu zafi suka taru
a idanunta, tana cigaba da kallon Basmah lokacin da take wa Umma sallama.
Cewar Basmah tana duban Baba Sani da ke magana da Nass akan zancen sanya ranarsa da za a
turo gobe a tsaida lokaci, Baba Sani ya jinjina kai ya ce, "To madallah a sauka lafiya Basmah."
Basmah ta yi saurin ficewa ba tare da ta sake bi takan Ummie da Zuhurah ba, Ummie ma tashi tayi
ta isa gaban gadon Umma ta yi mata sallama tare da fatan samun sauƙi, Umma ta rintse ido ba tare
da tankawa Ummie ba har ta baro wajen, ta saki hawayen da take riƙewa suka zubo tana me buɗe
idanunta ta sauke akan Ummie, lokacin da ta isa wajen Baba Sani ta tsaya har jikinsu na gugar
juna, Ummie ta yi ƙasa da murya ta ce, "Yallaɓai zan je daga waje kafin ka fito."
Baba Sani ya bita da wani sassanyar kallo ya ce, "To ga key ki jira ni a mota gani nan fitowa
yanzu wife!"
Ummie ta jinjina kai tana amsar mukullin motar ta fice, Zuhurah ta rakata da ido tana taya Umma
jin kishi me tsanani kan Ummien.
Umma ta danne saitin zuciyarta tana jin wani abu me nauyi na sake danneta, ta maida idanun ta
lumshe hawaye masu tsananin zafi na sake zubo mata.
"Zuwairah Allah ya ƙara lafiya, zamu wuce ko kina da buƙatar wani abu da ki ke son ci, ga dai
nama nan da fruit ga kuma souf ɗin fish da potato Samha ta yo miki."
Umma ta buɗe baki da ƙyar ta ce, "Ku koma da shi bana ci Sani, bana buƙatar komi kuma don
Allah idan zaka dawo kar ka sake zuwa min da ita, in dai kana buƙatar ɗorewar lafiya ta."
Baba Sani ya jinjina kai ya ce, "Okey zan kiyaye Allah ya baki lafiya, amma abinci ba za a koma
da shi ba yanzu Sadeeq zai shigo da shi."
Daga baka Baba Sani suka fice tare da Sadeeq ya ɗakko kwandon abinci,da kayan fruit da
gasasshen naman da Baba Sani ya siya,lokacin da ya aje basket ɗin a gaban gadon ne Umma ta
buɗe ido ta balla masa harara tana cewa, "Sadeeq wato kai ne baka jin tausayina kana goyawa
ubanka baya ku ga ƙarshena ko?"
Sadeeq ya kwantar da murya ya ce, "Ki yi haƙury Umma ba haka bane, don Allah ki kwantar da
hankalinki please!"
Kafin Umma ta yi magana kiran TAIMIYYAH ya shigo wayarsa, sai ya yi receiving call ɗin yana
sanya wayar a speeker, sassanyar muryar TAIMIYYAH ya karaɗe kunnuwar su Umma, lokacin da
take magana a shagwaɓe tana cewa, "Hello! Yah Deeku ina yini, ashe Umma bata ji daɗi ba an ce
tana ma hospital ya jikin nata?"
Yah Sadeeq ya ce , "Lafiya lau Zaynab, jikin Umma da sauƙi ina ma asibitin yanzu haka, bari in
bata wayar ki masa sannu."
Daga haka ya matsar da wayar kusa da Umma, lokacin da TAIMIYYAH ke cewa, "Okey bata
wayar."
Umma da wani abu ke sukar zuciyarta ta yi ƙarfin halin cewa, "Da sauƙi."
TAIMIYYAH ta ce, "Allah ya ƙara lafiya Umma, yasa kaffara ne, Zuhurah kuma aure ya ƙare
Allah yasa hakan ya zama alkhairy ,ya fito mata da wani nagari."
Daga haka su Umma suka jiyo ƙasaitacciyar muryar A.Maleek na cewa, "Salamu alaikum, Umma
ya jiki Allah ya baku lafiya ya kawo afuwa."
Umma wannan karon sai da ta rintse ido kafin ta iya amsawa da cewa, "Da sauƙi, na gode."
Daga haka A.Maleek ya miƙawa TAIMIYYAH wayarta, yana sake mannata da jikinsa, ta amshi
wayar tana cewa, "To shikenan Yah Deeku sai mun sake waya, Allah ya bata lafiya ka sake mata
sannu."
TAIMIYYAH na shirin cuting call ɗin A.Maleek Ado ya sanya hannunsa cikin rigarta ,ya ɗan
mintsi ƙirjinta hakan yasa ta cewa cewa, "Ash...!! Sweet zafi ....."
Yah Sadeeq sai ya yi saurin cuting call ɗin don ya gane cewa TAIMIYYAH ta ɗauka ya yi hanging
up ne, Zuhurah da akan kunnuwanta komi ke faruwa ta ji wani kibiya ya cake ta a ƙahon
zuci,Umma kuwa sai da ta maida idanunta ta rintse tana kai hannu ta dafe saitin zuciyarta.
Sadeeq shi ne ya ɗauki bincin da Ummie ta kawo, ya tafi da shi zai ci don tunda ya shigo garin bai
ci abincin kirki ba.
*Washegary*
Iyah da Babah Ladi a nan asibitin suka kusa yini, bayan Iyah ta sanya Babah Ladi girka
wadataccen abinci, a kuma ranar da yamma Mahaifiyar Umma da Anty Laurat suka iso don duba
jikin Umma, cikin mutunci da karamci suka gaisa da juna tsanakin Iyah da Mahaifiyar Umma da
suke kira da suna Guggo.
Bayan tafiyar su Iyah ne kuma Guggo ta tasa Umma da faɗa, akan yadda ta jefa rayuwarta cikin
haɗari, daga faɗa ta koma nasiha da nusar da ita akan cewa ta gyara munanar halayyarta, Umma ta
dinga kuka tana sanar da Guggo yadda ta ke jin zafin kishi akan wacce Baba Sani ya auro mata
ɗin.
Sai dare Baba Sani ya kwashi su Guggo zuwa gida, shi Yah Sadeeq ya koma bakin aikinsa, shi ma
Baba Sani don ya ɗauki hutu ne shiyasa bai koma a yau ɗin ba..........✍🏻
#Ɗansabo ce#
[12/15, 11:47 AM] +234 703 040 9541: Littafin TAIMIYYAH paid book ne,ga duk wanda ta
tsincesa a kowani irin group ne,kiji tsoran Allah karki karanta sai kin biya 500 naira only.
Za ku iya min magana ta wannan number ɗin 08167768704, ko kuma ku turo kuɗin ku kai tsaye ta
wannan account ɗin 0504192664 aisha ibrahim dansabo GTbank.*
Masu turo credit za ku turo katin MTN na 500 ta wannan line ɗin 08167768704.
_Ina ƴan kasuwa masu buƙatar a tallata muku hajar ku? Maza ku garzayo da kuɗi ƙalilan a tallata
muku kayan siyarwanku sai dai kawai ku ji ana kiran waya don buƙatan sayan kayan ku,ku
tuntuɓeni ta layina kamar haka 08167768704._
*87*
Kwanakin Umma huɗu a asibiti aka sallameta ta koma gida, tuni su Guggo da Anty Laurat sun
juya Yobe tun da suka ga Umman ta samu sauƙi.
Baba Sani da Amaryarsa Ummie cikin waɗannan kwanakin da Umma ta yi a gadon asibiti ,ba
ƙaramin morewa junansu suka yi ba, wani irin shafin soyayyah da tarairayar juna suka buɗe,
wanda Baba Sani bai taɓa sanin da irin su ba, don gaba ɗaya Ummie ta gama kwancen notikan
kansa da salonta masu sace zuciya.
Ranar da Umma ta dawo Baba Sani ya tattar ya koma part ɗinta, zuciyarsa cike da matsananciyar
kewar Ummie da soyayyarta, ita kanta Ummie sai da ta ji babu daɗi a ranta domin tana jin Baba
Sani a zuciyarta fiye da yadda za ta misalta. Har mamaki take yi akan hakan don bata zaci za ta ji
ƙaunarsa me ƙarfi cikin ƙanƙanin lokaci kamar yadda ta ke ji a yanzu ba.
Zuhurah hankalinta ne ya kwanta da jin cewa takardan sakinta na hannu, ta dinga ji a ranta lokaci
ya yi da za ta tsaya ta darje wani mijin na kerewa sa a, sai ta buɗe sabon shafin gyara kanta don ta
dawo cikin hayyacinta sosai, ko ta sami wani me hatimun nasaran ya kulata.
Kwanan Baba Sani biyu ya koma Kano bayan ya tara matan nasa ya yi musu faɗa da nasiha akan
su zauna lafiya, amma sai dai a gaban idanunsa Umma ta saki baƙaƙen maganganu akan cewa ba
ta ba Ummi har abada, ya ma daina tunanin in dai suna inuwa ɗaya za a samu zaman lafiya, daga
haka ta tashi bar musu wajen cike da zallar fusata. Hakan yasa Ummie ɗaura ɗammaran ba
Umman mamaki,tare da jinjina rashin man kanta da daƙiƙancinta a zahiri, don ita a tunaninta tuni
an daina irin wannan kishin na dabbanci, sai dai ayi na ilimi da iya kissa da kisisina wajen ƙwace
mijin.
Shiyasa Ummie tun bayan tafiyar Baba Sani ta kama kanta, ko da wasa bata kuma shiga sashin
Umma ba, iyakarta part ɗin Iyah da ta ke jin ƙaunarta a ranta me tsanani fiye da baya.
Sau biyu Umma na tura Zuhurah don ta ya Ummi kwana don su samu damar sanya mata maganin
bacci me ƙarfi, ta yadda Zuhurah za ta samu damar yanko musu ƙunbar ƙafar Ummien, amma ba
su ci nasara ba don kuwa Ummien cewa ta ke yi ta gode Zuhurah ta koma kawai bata buƙatar ƴar
tayin kwana, don kuwa gidan da part ɗin gaba ɗaya ba baƙinta bane.
Hakan ya sake jefa tsanar Ummien a zuciyar Umma, lokacin da ta sanar da Hajiya Barirah cewa
haƙansu bai cimma ruwa ba, cewa ta yi, "Allah dai ya yi wadaran rashin sa ar ki a rayuwa Hajiya
Zuwairah, amma ace mutum kullum bashi da sa a ina daɗinsa."
Umma da kanta ta koma wajen Boka Kallah don kai masa ƙorafi akan rashin samun yanko farcen
da ba a yi ba, Boka sai ya sanar mata cewa ta koma idan an kwana biyu ta san yadda za'a yi ta
samo gashin kan Ummie ta kawo masa.
Amma cikin rashin sa a Baba Sani na dawowa weekend ya tattara Ummie suka wuce Kano.
___________
*Abuja.*
A.Maleek Ado ne rungume da Samha a jikinsa yana sanar da ita samuwar visa ɗinsu gaba ɗaya har
da TAIMIYYAH, zuwa jibi za su wuce zuwa Egypt ɗin.
Samha ta sake lafewa a jikinsa ta ce, "Amma Yah Abdul duk gida ɗaya za mu sauka idan mun je?"
A.Maleek ya shafa gashin kanta ya ce, "Yes gida ɗaya ne zamu sauka wife, har ma na turawa
Sunusi kuɗin komi ya biya ba ki ga gidan da ya samar mana a wani new city ba, har ma na sanya a
bincika min kuɗin da zan iya mallakar gidan ya zama nawa gabaki ɗaya."
Samha ta jinjina kai tana cewa, "Amma ni dai zan so kabar ni ko a hotel ne don Allah!"
A.Maleek ya miskile fuska ya ce , "Look! Suhailah meyasa kullum ina neman ku haɗe kanku
amma ke kina bauɗewa ne, miye aibun Zaynab da ba za ki iya sakin jiki da ita ku zauna a muhalli
ɗaya ba?"
Yadda ya yi maganar a fusace ya sanya Suhailah sake shigewa jikinsa ta kwantar da murya ta ce,
"Allah ya baka haƙury Sweet, but ni kafi kowa sanin ina da tsananin kishi akanka, wallahi da ƙyar
na ke iya cotrolling kaina duk sanda zan ga kuna tare da juna. Yakamata ka gane hakan ka yi min
uzuri wajen raba mana muhalli idan mun je can, idan ni ba za ka bar ni a hotel ba to ita ka ɗauke ta
ku yi masauki a hotel please!"
"Suhailah hakan ba zai yiwu ba ki ma cirewa zuciyarki wannan, gida me girman gaske da ke
ɗauke da 3 bedroom kowacce za ta ɗauki guda, ni kuma in yi anfani da guda a matsayin nawa,
babu ruwan wata da wata a cikinku kowacce ta girka abinda ta ke so, bare ma a waje zamu dinga
cin abinci sai dai dinner kaɗai ne duk me girki za ta yi a haɗu a dining a ci, miye zai dame ki da
hakan?"
Suhailah ta sake kwantar da murya cike da sarewa ta ce, "Shikenan Allah ya bani juriyar rintse
idanu akan abinda zan ji ko in gani."
Tausayinta sai ya kama zuciyar A.Maleek amma bai nuna ba, sabida baya son buɗe mata ƙofar da
za ta dinga amfani da zafin kishi, wajen son wargaza haɗin kan gidansa.
Ya zare ta daga jikinsa ganin time ɗin Magriba ta kusa,kuma yau kwanan TAIMIYYAH ne ita
Suhailah yau ta ƙare nata kwanar. Ya nufi hanyar fita daga ɗakin yana cewa, "U make sure zuwa
gobe kin kammala duk wasu shirye-shiryenki, cox morning flight za mu bi okey!"
Suhailah ta bi bayansa da kallo tana jinjina kai ba tare da ta ce komi ba,ya ƙarisa fita daga ɗakin
nata ya nufi downstairs.
Can ɓangaren dining ya hango TAIMIYYAH da Rabeca suna arranging coolers ɗin abincin da
TAIMIYYAH ta ɓata lokaci wajen shiryawa, ya bi ta da sassayar kallo lokacin da Rabeca ta bar
wajen ya ƙarisa bakin dining ɗin yana cewa, "Hey! My pure zuma."
TAIMIYYAH ta ɗago manyan idanunta tana jifansa da smile ta ce, "My Sweet Amore how far?"
A.Maleek ya ƙarisa gareta yana rungumeta ta baya ya ce, "Daidai my sweet, me aka tanadar min
yau bayan waɗannan daɗaɗan girke-girken?"
TAIMIYYAH ta shagwaɓe murya tare da yin ƙasa da shi ta ce "Komi ma an tanadar maka Sweet
Amore."
A.Maleek ya yi maganar yana juyo da TAIMIYYAH suka fuskanci juna, ta kai bakinta ta sumbaci
kumatunsa tana cewa, "Luv u too my sweet Amore, its time for pray Baby sakarni in je ɗaki
please!"
Maleek ya saketa yana riƙe da hannunta suka nufi ɗakinta, a can ya ɗaura alwala ya fito don zuwa
Masjid ɗin da ke manne da jikin gidansa, don da wuya ya yi gini bai gina har masjid a jikin gidan
ba.
Sai da aka idar da sallar Isha'i sannan ya shigo gidan, diract kuma ɗakin TAIMIYAH ya wuce, ya
sameta ta gama cancanɗa masa kwalliya cikin kayan da suka fitar da surarta, musamman twins
ɗinsa da suka fito sosai suna tsokanarsa, ya kai hannunsa kansu lokacin da ya rungumota zuwa
jikinsa, ta saki ɗan kukan shagwaɓa tana ture hannunsa tare da cewa, "Sweet Amore its time for
dinner fa, kar Anty ta sakko tana jira please!"
Maleek ya balla mata harara kafin ya kai bakinsa ya sumbaci in da ta ture hannunwansa a kansu,
ya ɗago fuskarta yana tsareta da manyan idanunsa da suka fara bayyanar zallar rigimar ya ce,
"Baby ko dai har na yi ajiya ne, na ga kullum kayana sake cika suke yi da yin fresh, miye sirrin?
Tell me please!"
TAIMIYYAH kunya ya lulluɓeta ta nemi zillewa daga jikinsa tana cewa, "Kai! Sweet Amore ni
dai ba ruwana ba kai wata ajiya ba."
Maleek ya sake ta yana sakin dariya kaɗan ya rufa mata baya zuwa wajen da ta rataye kimono
ɗinta, da za ta ɗaura akan shigar jikinta, ya zare kimonon daga hannunta yana cewa, "No Sweet
mu je kawai a haka."
TAIMIYYAH ta tirje tana masa magiya akan ya barta ta suturta wannan shigar , da ƙyar ya amince
ta sanya suka fita zuwa dining ɗin. Sun isa kenan ita ma Suhailah ta sakko zuwa wajen,
TAIMIYYAH ta yi serving ɗinsu suka fara cin abincin, jefi-jefi A.Maleek na sako zancen tafiyarsu
a jibi.
Suhailah ita ta fara barin wajen ta haura zuwa sama don fara shirya kayanta a tsanaki sabida gudun
yin mantuwa, ta bar su TAIMIYYAH a dining area ɗin suna zuba shiririta wajen ƙarisa cin
abincin. Bayan sun kammala ne ya yi mata rakiya zuwa ɗakinta don ɗaukar abinda za ta buƙata
suka fito, ya ɗauke cak! Akan hannuwansa suka haura zuwa upstairs ɗakin baccinsa.
Washegari TAIMIYYAH ita ma ta fara kintsa musu kayayyakin da zasu wuce da su, bayan ta
kammala ne ta sakko zuwa kitchen don yin snacks da ta ke son su wuce da shi.
Samosa da meat pie me yawa ta yi, sai ta yi packaging ta sanya cikin freezer, sai ta kwaɓa milky
cin-cin ta baiwa Ameena ta murza ta yanka mata, ita kuma ta fara aikin ɗaura abincin lunch
Rabeca na taimakonta da abubuwan da suka kamata.
Koda suka kammala aikin abincin sai ta bar su Ameena da shirya dining ɗin ta wuce ɗaki don yin
wanka, sabida ta gaji matuƙa shiyasa koda ta zo yin wankan ta yi amfani da ruwa me zafi sosai,
bayan ta fito ta gabatar da sallah ne ta fita zuwa dining ɗin.
Ita kaɗai ta yi serving kanta abincin da za ta ci, don A.Maleek tun safe da ya fita bai shigo gidan
ba, shiyasa ba za su yi zaman cin abincin tare ba.
Tana kammalawa ta koma ɗaki ta kwanta bada jimawa ba kuma bacci ya sace ta, can cikin baccin
ne ta ji mutum a jikinta yana janyeta ya mayar da ita kan faffaɗan ƙirjinsa, sai ta sake gyara
kwanci a jikinsa sukai baccin tare manne da jikin juna. Basu tashi ba sai after 4 lokacin sallah har
wuce, hakan yasa suka ɗauro alwala a gaggauce ya jasu jam'i, bayan sun ɗ idar ne ta yi masa
rakiya zuwa dining don bashi abinci, cox ya ce bai ci komi ba tun breakfast ɗin safe.
Da dare fita sukai zuwa TULIP don yin dinner a can, amma Suhailah ta ƙi bin su daga shi sai
TAIMIYYAH suka je wajen, wanda tun zuwan farko wajen ya tafi da zuciyarta, hakan yasa da
suka isa ta saki jiki sosai, suna cin abincin suna zuba luv tamkar ba bu gobe, babu ruwan wani da
wani a wajen kowa sha'anin gabansa ya ke tamkar a turai. Da kanta ta saita camera ta kashe musu
hotuna masu kyau a wajen, shi da kansa A.Maleek ya ji daɗin fitar tare da yaba soyayyar da
TAIMIYYAH ta ke gwada masa.
Sai to 11 suka koma gida shiyasa suka faɗa bathroom a tare suka watso ruwa tare da sanya kayan
bacci suka nufi bed, bayan TAIMIYYAH ta tabbatar da cewa komi na su ya kammala tsaf wanda
za su wuce da shi.
*Washegary*
Flight ɗin ƙarfe tara da rabi goma saura ya tashi dasu zuwa ƙasar Cairo(Egypt). Karo na farko da
TAIMIYYAH za ta fara cillawa zuwa wata ƙasa. Zuciyarta na cike da farin ciki mara misaltuwa,
tun sassafe ta kira su Iyah ta yi musu sallama hatta Ummi da Baba Sani sai da ta kira su, Yasmeen
ne last wacce sukai waya da ita kafin jirginsu ya tashi.
A first class seat suke zaune su duka ukun, daga TAIMIYYAH har Suhailah shigar Abaya ce a
jikinsa different design and colour. TAIMIYYAH sanye da Brown colour Suhailah na sanye da
wani irin dark gray wanda ya ji aiki wuya da hannu, dukkaninsu sun yi kyau matuƙa,amma fuskar
Suhailah sam babu cikakken annuri. Gogan na su na sanye ne cikin manyan kaya riga da dogon
wando na wata ɗanyar gezner kalar brown, ɗinkin ya yi masa matuƙar kyau tare da fito da
ƙuruciyarsa tamkar wani ɗan 30yrs.
Lokacin da jirgi ya sauke su a airport ɗin ƙasar Cairo, sun samu har Sunusi ya isa da mota don
ɗaukar su zuwa masauki,tafiyar 60 km suka yi daga Cairo International Airport, zuwa Sixth of
October City, Egypt. (Wani new city ne a garin Cairo da hausawan mu ke sha'awan zuwa su zauna
da iyalansu).
Lokacin da suka isa ƙaton gidan da Sunusi ya yi renting ɗinsa da kuɗaɗe masu nauyi, gaba ɗaya
TAIMIYYAH a gajiye ta ke domin wannan shi ne karon farko da ta baro ƙasarta na haihuwa, ta
taho wata duniya ta daban shiyasa ta ke jin gajiya me tarin yawa.
Bata bi takan tsaruwar gidan da haɗuwarsa ba, burinta kawai ta dangana ga makwanci ta warware
gajiyar da take ji, A.Maleek na kai ta ɗakin da zai zama mallakinta har su bar ƙasar ta nufi
bathroom, a daddafe ta yi wanka ta fito ɗaure da towel ta nufi bed, komi ba ta tsaya sanyawa a
jikinta ba ta shige cikin duvet sai bacci.
A.Maleek da Suhailah ce ke dashi don a yau ɗin ne za ta amshi girki suka baro ƙasar, suma wanka
suka yi suka bi lafiyan bed. Lokacin da suka tashi ne suka gababar da Sallah suka fito don cin
abinci, sai lokacin TAIMIYYAH ta zuro ƙaramar riga mara nauyi ta fito, tana faman ƙarewa
tsaruwar gidan kallo.
Bayan sun kammala cin abincin ne Maleek ya zaga dasu suka ga tsarin gidan da haɗuwarsa, yana
sanar dasu cewa yana son mallakar gidan ya zama mallakinsa ne kafin su bar ƙasar, sabida sabon
gini ne dal da ba a jima da kammala sa ba, su ne farkon wanda suka kama hayarsa. Sosai
dukkansu suka yaba da kyawun gidan tare da yi masa fatan gidan ya zama mallakinsa, lokacin da
suka koma zuwa ciki a babban falon su kai masauki.
TAIMIYYAH ta dinga so ta yi magana da su Iyah amma sai ta wayar Maleek ta samu ta yi magana
da su, kafin ta sayi layin ƙasar zuwa gobe.
Sabida gajiya ranar baccin wuri ta yi ko dinner a daddafe ta tsaya suka yi gaba ɗaya, duk kuma
Sunusi ne ke musu ordering abincin ya kawo musu gidan.
Washegary da shiga shopping malls suka fara, kowacce ta yi siyayyar abubuwan da za ta buƙata,
shi kuma Sunusi da A.Maleek suka yi siyayyar kayan abinci da komi da za su buƙata har su bar
ƙasar. A wani haɗaɗɗan Restaurant sukai lunch sai can yamma suka koma gida, tare da tarin
shopping bags ɗin da sukai siyayyah.
Washegary Suhailah da A.Maleek tare da Sunusi da ke driving ɗinsu ne suka nufi asibitin da
Suhailah ta fara ganin likita tun farko, wanda tafiyar one hour ne daga in da suka sauka zuwa
wancen garin da hospital ɗin ya ke.
Ita TAIMIYYAH sai ta tsaya a gida bata bisu ba, shiyasa da ta ga rana ta yi sai ta shiga kitchen ta
ɗaura musu lunch na abinci me sauƙi, ta yayyanka fruit ta shirya komi bisa dining sannan ta wuce
ɗakinta don yin wanka.
Lokacin da ta fito sai ta shirya cikin kaya masu ɗan kauri, sabida garin sanyi ake musu sosai kuma
duk rabin weather ɗinsu dama sanyi ne zallah.Shiyasa ta zaɓi kaya masu kauri ta sanya don tana
da jin sanyi sosai ita, tana tsaka da yin kallo suka shigo hannun Maleek riƙe da na Suhailah suka
shigo cikin falon, hakan yasa TAIMIYYAH ta yi musu kallo ɗaya ta ɗauke kai bayan ta yi musu
barka da dawowa.
Sun ɗauki a ƙallah 20minutes da shiga ɗaki kafin su fito babban falon in da dining area ya ke,
A.Maleek na duban TAIMIYYAH tare da shagwaɓe murya ya ce, "Sweet zo ki bani abinci am
feeling hungry."
TAIMIYYAH ta ɗan taɓe baki tana miƙewa ta dafa ƙafarta ta fara takawa zuwa dining area ɗin, ta
ɗauki plate ta yi serving A.Maleek ita Suhailah da kanta ta yi serving kanta, suka zauna suka ci
abincin tare da TAIMIYYAH. Bayan sun kammala ne Suhailah ta yi shigewarta ɗaki sabida yau
TAIMIYYAH za ta amshi mijin.
Zuciyarta a wanke take da sakamakon gwajin da akaiwa mahaifarta, aka tabbatar musu da samun
lafiyarta, sai dai su jira Allah ya yi ikon sa don likitar ta tabbatar musu da cewa, a kowani lokaci
Suhailah za ta iya ɗaukar ciki. Shiyasa ta ke jin zuciyarta a wanke matuƙa, ta ɗaga waya ta kira
Hajjah ta labarta mata komi, Hajjah ta taya ta murna tare da addu'ar Allah ya kawo rabo me anfani.
Daga can falon kuwa bayan sun kammala cin abinci ne A.Maleek ya janye TAIMIYYAH zuwa
ɗakinsa suka kwanta, bai bar su sun sama bacci ba sai da ya gama rikita jikinta da zafafan
saƙonninsa.
Washegarin ranar suka buɗe shafin yawon hutawa da zagaye garin, tare da halarta duk wasu
manyar wurare na hutawa da ke cikin garin Sixth of October City, sosai TAIMIYYAH ke buɗe ido
tana kallon wurare da tarin gina-ginen na tarihi.
Tun daga ranar kullum basu zama a gida suna aikin zaga garuruwa masu ɗinbin tarihi suna yin
hotuna na tarihi, duk wasu muhimaman wurare na tarihi sun halarcesa cikin kwanaki biyar da
zuwarsu ƙasar Cairo, banda wuraren hutawa da shaƙatawa da suka halarta, A.Maleek sosai ya ke
morewa matan nasa a duk lokacin da suka fita wuraren hutawan, duk me girki a ranar baya jin
kunyar nuna mata zallar luv da kulawa, tun TAIMIYYAH na jin kunya har ta fara fitsare idanunta
ita ma wajen mayar da martani, haka a ɓangaren Suhailah tun tana jin takaici da matsananci kishi
har ta haƙura ta ko yi shanyewa, musamman da ta ga yadda Maleek ɗin ke matuƙar ƙoƙarin
kwatanta adalci, da nunawa kowaccensu ita ɗin wani ɓangarene na rayuwarsa.
Yau kwanakinsu bakwai da zuwa ƙasar Cairo, tun safe TAIMIYYAH ta kulle ɗakinta tana faman
kuka, sabida kawai A.Maleek ɗin ya ce ta shirya za su ganin wani likitan ƙashi a ALEX, a
tunaninta ya gaji da zama da ita a matsayin gurguwarta ne, shiyasa ya ke neman hanyar da zai ce a
gyara mata ƙafarta, alhahi ita ta jima da rungumar ƙaddararta tare da sallamawa cewa haka
Ubangiji yake son ta rayu, shiyasa ya jarabceta na laluran alhali har ya ara mata damar da ta fara
takawa da ƙafafunta lafiya lau.
Ta kai hannu ta share wasu hawaye masu zafi tana ji yana sake knocking ɗakin, cikin dakakkiyar
muryarsa ya ke cewa, "Zaynabb ki taso ki buɗe ƙofar ɗakinnan, kar ki bari raina ya sake ɓaci
okey!"
TAIMIYYAH ta sakko daga bed ɗin ta zo ta buɗe ƙofar,ta juya zuwa bed ɗin ta kwanta tana sake
sakin kuka me sauti. A.Maleek ya iso bakin bed ɗin ya zauna yana cewa, "Tashi zaune please!"
TAIMIYYAH ta ƙi tashi sai ma kukan da ta sake sakin masa, hakan ya sake ɓata ransa ya miƙa
hannu ya fisgota zuwa jikinsa yana cewa, "Zaynab yanzu don ina so ki samu lafiya shi ne na zama
abin wulaƙantawa kina min irin wannan kafiyar?"
"Don Allah Hubby idan tausayina da ka ke ji ne akan lalurar ƙafata ne ka ke son a gyara min, ka
yi haƙury ka cire tausayin ka zauna da ni a yadda Ubangijina yaso in rayu, ban taɓa sha'awar cewa
sai na koma da tafiyata kamar yadda na faro ba, sai dai idan kai ma ka fara ji aranka cewa faɗuwar
aji ne ka cigaba da zama da gurguwa a matsayin matarka, ina son kaina a hakan ina kuma
sha'awan cigaba da kasancewa a matsayin gurguwata, domin duk wanda zai ji tausayina baya ga
wanda ya halicceni ne,please! ka janye maganar zuwa ganin wani likita ba za ni ba, sai dai idan ka
daina so na a hakan ne ka mayar da ni gi........"
Bakinta da A.Maleek ya bige ne ya sanyata sake sanya kuka ba tare da ta ƙarisa faɗin abinda ta ke
son faɗi ba,ransa a matuƙar ɓace ya ce, "Zaynab ni ki ke gaggayawa waɗannan maganganun? Na
ji an fasa ganin likitar tunda kin jahilci manufata. But who told u na daina son ki ne a hakan
Zaynabb?"
TAIMIYYAH babu bakin magana sai kuka, hakan yasa ya cigaba da cewa, "Ina son ki Zaynabb
irin soyayyar da baki ya yi kaɗan ya misalta, ina ƙaunarki irin ƙaunar da ban taɓa ji akan halittar
kowace mace ba baya ga mahaifiyata. Sannan ban taɓa jin kasancewarki me lalura zai sa watarana
in ji na rage son ki ko zan gajiya da zama da ke a hakan ba. Ina alfahari da samunki a hakan
Zaynabb, na yi sha'awar a duba lafiyar ƙafar ne idan da yiwuwan zai koma daidai sai ayi aikin, ba
don na daina ƙaunarki a yadda ki ke ba, sai donba tunanina hakan zai faranta ranki. Amma tunda
kin min mummunar fassara na yi alƙawarin ba zan sake kawo miki magana makamancin wannan
ba. U hurt me very much Zaynabb da yadda ki ka fassarani, amma ba laifinki ba ne thank u!"
Daga haka ya zareta daga jikinsa yana juyawa da sauri ya bar ɗakin zuciyarsa na tafasa da
kalamanta, ko kaɗan bai yi tunanin haka za ta fassarashi ba da bai fara ɗakko maganar ba, ya yi
tunanin murna za ta yi tana yaba masa akan son ya ga lafiyar ƙafarta ta dawo daidai.
Ɗakinsa ya shiga ya kwanta rigingine tare da lumshe idanunsa, yana jin yadda kowani bugun
numfashinsa ke fita tare da zazzafar soyayyarta me tsanani, ya sake lumshe idanunsa yana ji
zuciyarsa sam babu daɗi, ita yake son ji a cikin jikinsa amma dole ya danne kwaɗayin hakan, don
nuna mata cewa ta ɓata zuciyarsa.
TAIMIYYAH bayan fitarsa daga ɗakin sai ta koma ta kwanta hawaye masu zafi na biyo face ɗinta,
jikinta ya yi mugun sanyi da yadda ta jahilci manufarsa, ta dinga recalling kalaman da ta furta
masa tana sake jin nadama na ratsa zuciyarta. Tamkar wacce aka bai wa umurni haka ta yi saurin
tashi tana kallon shigar da ke jikinta, ƙaramar riga ce me hannun vest wanda akai wa gidan Bro a
jiki, tsayinta duka iya guiwarta ne sai ta miƙe tana dafe ƙafar ta fara takowa don fitowa daga
ɗakin.
Ɗakin A.Maleek ta nufa ta tura ƙofar ta shiga sabida dama ranarta ce, tasan cewa ba za ta ga
Suhailah a ɗakin ba tana ɗakinta, shiyasa ta shiga kai tsaye bayan ta yi sallama bai amsa ba.
Ta dinga takawa har ta isa bakin bed ɗin da yake a kwance, ya yi rigigine idanunsa a lumshe
tamkar me yin bacci, ta hau gadon baki ɗaya tana zamewa ta kwantar da kanta a saman ƙirjinsa, ta
kai hannu samar fuskarsa amma sai ya ture tare da tashi zaune yana sauke ta a jikinsa ya juya mata
baya.
TAIMIYYAH sai ta ji hankalinta ya kai ƙololuwa wajen tashi, ta sake binsa tare xura hannu ta
ƙanƙameshi ta baya tana sakin masa kuka me sauti.
A.Maleek ya yi saurin tashi yana finciketa daga jikinsa cikin murya me cike da masifa ya ce,
"Why Zaynabb, meyasa za ki biyoni kina min wannan kukan da kika san bana so yana ɗagar min
da hankali? Kin biyoni ne ki sake gaya min maganganun da ranki ke so,sabida raini ya fara shiga
tsakanina da ke ko? Oya get out please!"
Ya yi maganar yana nuna mata hanyar fita daga ɗakin, aiko sai ta sake rushe masa da kuka tana
faɗawa jikinsa baki ɗaya ta rungumesa, cikin muryar kuka ta ce, "Don girman Allah ka yi haƙury
ka yafemin Baby! Ba zan ƙaraba na yi nadaman duk kalaman dana faɗi maka, hankalina ne ya
tashi sabida na yi tunanin ka fara gajiya da zama dani a gurguwata ne, alhali zuciyata ta gama
shiga garari a ƙaunarka. Don Allah ka yi haƙury sweet na yi maka mummunar fahimta, ni nafi son
in ga cewa mun rayu a hakan, domin yaran da zan haifa su taso suna masu tinƙaho da nakakkasu
tare da girmamasu, sabida kasancewar uwarsu me nakasa ce. Ina so ƴan uwa na masu nakasa irin
tawa su dinga jin cewa nakasa ba kasawa bace, kuma Ubangiji zai iya ɗaga darajarsu ya kai su ko
wani irin matsayi da ɗaukaka na rayuwa, ba kamar yadda ake kyaran mu da nuna cewa mu ba
komi bane. Shiyasa na ke da burin yin ilimi me zurfi ta yadda zan sake yin alfahari da kaina da
kasancewata me nakasa, don Allah Habibi ka yafe min ka fahimci manufar da yasa bana sha'awar
a gyaramin ƙafafuna, domin na riga na nakasa ko baka lura da yadda ƙafar ya shanye bane? Ko an
taɓa ƙafar ba mu da tabbacin zai dawo daidai idan har haka Ubangiji ya so ganina, mu haƙura mu
zauna da juna a hakan cikin soyayya da ƙauna juna Habibi. Idan kuma akwai ina gaza ne wajen
baka abinda ka ke nema na san Anty Suhailah na cike maka wannan gurbin kasancewarta
lafiyayya. I luv my sweet Amore, don Allah ka fahimce ni ka kuma yafe min ɓacin ran dana sanya
ka ciki ka ji Luv please!"
TAIMIYYAY ta kai ƙarshen maganar cike da magiya tana sake shigewa jikinsa, tare da manna
ƙirjinta akan nasa, hakan ya sanya Maleek kai hannu ya sake matseta a ƙirjinsa suna jin bugun
numfashi juna, ya kwanto da kansa bisa kafaɗarta ya ce, "Ya wuce Baby na yafe miki, na kuma
fahimci manufarki but kar ki sake tunanin wai ni Abdulmaleek akwai ranar da zan ji kin gundureni
ko na gaji da ganinki a yadda ki ke, ni ne na amince da aurenki a hakan ba tare da ko sau ɗaya na
taɓa jin cewa akwai randa zan gajiya da kallonki a hakan ba, kin riga kin zama wani ɓangare na
rayuwata Zaynabb, duk yadda zan misalta miki yadda na ke jinki a zuciyata ba za ki fahimta ba, so
please kar ki sake tunanin gazawarki a kowani fanni wajen faranta raina, domin kina min abinda
lafiyayyun mata biyu ba za su iya maye min gurbinki ba."
Yadda A.Maleek ya kai ƙarshen maganar da wani irin sanyin murya, ya sanya TAIMIYYAH ɗago
da kanta tana duban tsakiyar idanunsa, wani irin abu take hangowa me girma a cikin idanunsa. Sai
ta haɗe fuskarsu waje guda tana lalubar bakinsa ta haɗe da nata, A.Maleek ya sake matseta a
jikinsa yana amsar wasu irin zafafan kisses daga gareta, ya kai hannuwansa duka biyu ya ɓalle
maɓallan gaban rigarta tare da zare rigar gabaki ɗaya daga jikinta. TAIMIYYAH sai ta zare
bakinta daga nasa tana jifansa da wani irin kallo,wanda ke nuna zallar ƙaunarsa da ya yiwa
zuciyarta mugun kamu,lokacin da ta ji bakinsa kan ƙirjinta sai ta kai hannu tana sake tallabo kansa
zuwa gareta, hakan ya bashi damar ƙarisa cusa kan nasa a tsakiyar ƙirjinta da ke gigita duk wani
nutsuwarsa.
Daga haka lamura suka kankama a tsakaninsu,in da TAIMIYYAH ta zage wajen ganin ta ɓatar da
duk wani fishi da ɓacin ran da ta kimsa a zuciyar A.Maleek Ado, sai da ta tabbatar ta gama ɓatar
da duk wani tattaunawarsa da likitar ƙashinsa da ya jajibo ta watsar da su a gefe guda.
A.Maleek da ke rungume da ita a jikinsa bayan ya dawo cikin nutsuwarsa, sai ya dafa kanta yana
faman sanya mata albarka tamkar ba hakkinsa bane aka bashi. TAIMIYYAH ta yi laƙwas a jikinsa
kai bakace ita ce ta rufe ido ta sarrafashi son ranta ba,daga haka bacci ya sace su sai after La'asar
suka tashi.
TAIMIYYAH ɗakinta ta gudu ta yi wanka ta fito ta gabatar da sallah, tana jin zuciyarta wasai sai
tarin shauƙi da soyayyar Maleek ɗin ke sake nuƙurƙusar zuciyarta.
Tana tsaka da sanya kaya A.Maleek ya shigo, ya shirya fes cikin ƙananun kaya da sukai masa
mugun kyau, ya isa bakin bed ya zauna yana zurawa TAIMIYYAH ido, wacce ke ɗaure maɗaurin
gaban rigar wani english gown da ta sanya, kalar red da ya haska farar fatarta tare da yi mata
mugun kyau, ta gogawa ƙaramin cute lips ɗinta jambaki kalar red kaɗan, sai idanunta da tayi
lining ɗinsu suna faman haskawa da wani irin kyau me fisgar hankali.
A.Maleek sai ya kasa daurewa ta kammala laƙaiƙaitar da ya kula da gangar take yi, ya miƙe ya isa
bakin mirrow ɗin yana amshe kwalbar turaren VERSACE da ta ɗakko za ta fesa, ya fesa mata
kaɗan ya aje yana juyo da ita ya rungumeta, ya kai bakinsa ya yi kissing wuyarta zuwa ƙirjinta,
yana riƙo hannunta suka isa bakin bed ɗin ya zaunar da ita yana faɗin, "Wait Sweet!"
Daga haka ya nufi wajen kayanta ya ciro mata wani madaidaicin Egyptian Jilbabs da suka siye su
kala-kala, ya zaro mata black colour ya zo ya sanya mata.
Nan da nan ta sake yin wani mugun kyau tamkar ka sace ka gudu, ya dinga kallonta yana jin
yadda zuciyarsa ke sake narkewa akanta.
TAIMIYYAH ta narke face cike da shagwaɓa ta ce, "No Sweet please! Kai fa ka yi mana
alqawarin Sunusi zai kaimu wajen tunda company ne mu zaɓi design kawai a buga mana su, ni fa
da gaske business ɗin su zan fara, ina son shigar Abaya kuma ina da waɗanda za su iya sarar ko
guda dubu ne idan na turasu zuwa kano, kasan yaran guggo Bilki duka suna taɓa business bayan
aikin gwamnati."
Maleek ya zura mata ido kafin ya ce, "My pure zuma kenan, bakin ku ya zo ɗaya da Suhailah, ita
ma abinda ta ce kenan za a buga mata designs unique ta sarar dasu,kar ku damu zan yi magana da
Sunusi amma ina fata account ɗinku da nauyinsa ko?"
Yayi tambayar yana ɗage mata gira guda, hakan yasa ta saki dariya tana kai baki ta manna masa
kiss kafin ta ce, "Ko babu nauyi my sweet Amore zai cika mana ya yi nauyin ai, ko ba haka ba
luv?"
A.Maleek ya lakace face ɗinta ya ce, "Hakane my pure zuma let's go Sunusi ya iso na ji kamar
muryarsa daga falo."
Daga haka suka fito zuwa falon ilai kuwa Sunusi ne ya iso, suka gaisa da TAIMIYYAH cikin
mutunci, ya gaida A.Maleek ɗin kafin ya miƙe ya fice.
Suhailah ta fito cikin shiri ita ma tana sanye da doguwar rigar boubou na material da ta siye shi
ready made, ta yane kanta zuwa jikinta da babban veil me kauri wanda companyn da ke yin irin
Hijab ɗin da TAIMIYYAH ta sanya, su suke yin veils masu kauri da kyawu sosai.
Wani ƙaton companyn sarrafa Abayas ne me suna AL-ASLY dake Ataba Market Cairo nan suka
fara isa, Companyn suna buga haɗaɗɗun Abayas design-desighn masu asalin kyau da nagarta.
Tunda suka iso wajen in da aka ware wani babban waje da ake aje samples ɗinsu, su TAIMIYYAH
duk suka ruɗe suna rasa irin design ɗin da zasu zaɓa, mayan albums na samfuri kala-kala aka
dinga jibge musu suna kalla, Sunusi wanda duk cikinsu shi ne ya ji larabci shi ya ke magana da
ma'aikatan yana sanar da su TAIMIYYAH.
A.Maleek ne ya ce kowacce cikinsu ta zaɓi design ɗin da take so guda sha biyar, su biyu guda 30
kenan suka zaɓa akai bill ya biya sannan aka je ga maganar wanda su ke so abuga musu, su wuce
da su 9ja don fara business ɗinsu.
Suhailah ko kaɗan bata nuna kishinta ko ƙyashi don mind ɗinsu ya zo ɗaya da TAIMIYYAH
wajen son yin business ɗin abu iri ɗaya ba, domin tasan kowacce da hanyar da za ta shigar da
abarta so ko ajikinta, kusan ma TAIMIYYAH da ta fita iya zaɓi duk ita ce ta zaɓar masu haɗaɗɗun
desighns masu kyau da ba a buga ire irensu ba, sai a wata me kamawa suke shirin fitar da desighns
ɗin, shiyasa balaraben ya jinjina ma iya zaɓinta, akai estimate na kuɗi masu matuƙar nauyi domin
guda ɗari huɗu suke so a buga musu, difference desighn duk design ɗaya ya zamana an buga sha
bibbiyunsa.
A.Maleek shi ne ya tura kuɗin zuwa asusun companyn, sannan akai packaging na su
TAIMIYYAH suka fito daga wajen.
Daga nan wajen sun shiga wasu malls sun yi siyayya kafin su wuce gida, bayan sun tsaya sun yo
take away ɗin abincin dinner,sabida sun riga sun yi yamma ga gajiyar zaman mota daga Ataba
zuwa City ɗin da suka sauka.........✍🏻
#Ɗansabo ce#
[12/15, 11:47 AM] +234 703 040 9541: Littafin TAIMIYYAH paid book ne,ga duk wanda ta
tsincesa a kowani irin group ne,kiji tsoran Allah karki karanta sai kin biya 500 naira only.
Za ku iya min magana ta wannan number ɗin 08167768704, ko kuma ku turo kuɗin ku kai tsaye ta
wannan account ɗin 0504192664 aisha ibrahim dansabo GTbank.*
Masu turo credit za ku turo katin MTN na 500 ta wannan line ɗin 08167768704.
_Ina ƴan kasuwa masu buƙatar a tallata muku hajar ku? Maza ku garzayo da kuɗi ƙalilan a tallata
muku kayan siyarwanku sai dai kawai ku ji ana kiran waya don buƙatan sayan kayan ku,ku
tuntuɓeni ta layina kamar haka 08167768704._
*88*
Wanka da sallah suka fara yi basu fito wajen dining ɗin ba ma sai after sun yi sallar Isha'i,
A.Maleek tare da TAIMIYYAH suka iso wajen sai daga baya Suhailah ta fito, taci kwalliya da
wasu nighties masu kyau.TAIMIYYAH ita ce ta fara bubbuɗe packs ɗin da suka shigo da su na
abincin, tana serving ɗinsu tare da turawa kowa zuwa gabansa.Ta miƙa hannu ta janyo ledar
rousted fish don warwarewa, ta ke ƙamshin spices ɗin da akai anfani da shi ya doki hancinta,
cikinta ya yi wani irin hautsinawa zuciyarta ta tashi. Nan da nan ta yi sauri ture ledar wani
bahagon amai na taso mata, cikin sauri ta ja kujeran baya tana juyawa da sauri cikin yanayin
tafiyarta da idan tana gudu za ka ga kamar tsalle kawai take da ƙafa guda, ta nufi ɗakinta amma ko
kafin ta kai toilet ta saki aman. Ta durƙushe ta dinga kelaya aman tamkar za ta amayo da kayan
cikinta, A.Maleek da ya rufo mata baya aguje yana tambayar lafiya? Ganin ta durƙushe tana zabga
uban amai sai nishi take yi, babu shiri ya ƙariso wajen tare da riƙeta a jikinsa yana faman yi mata
sannu.
Sai da ya tabbatar ta gama aman tas ya ɗauke ta cak! Zuwa toilet, sai faman nishi take yi yana
mata sannu da tambayarta dama bata da lafiya ne? Ita dai TAIMIYYAH nishi kawai take yi don ta
gama galabaita, ya wanke mata baki da jikinta da ya ɗan ɓaci, ya naɗota a towel suka fito yana
kwantar da ita akan bed.
Da ƙyar ya iya daurewa ya gyara wajen bayan ya ɗakko kayan shara ya kwashe aman,Suhailah ce
ta biyo bayansa don ganin ko lafiya? Ganin TAIMIYYAH naɗe a bed ɗaure da towel A.Maleek na
aikin gyara wajen da ta yi amai sai ta ji hankalinta ya tashi, ta dubesa tana cewa, "Sweet lafiya,
meyafaru kuma?"
A.Maleek da zallar damuwa ya bayyana a fuskarsa, sai ya ɗago ya saci duban TAIMIYYAH da ke
kwance bisa bed ya ce, "Suhailah bansan meke damunta ba, na shigo na samu tana ta amai ne dai."
Suhailah sai taka zuwa bakin bed tana duban TAIMIYYAH ta ce, "Sannu Zaynab baki da lafiya ne
dama?"
TAIMIYYAH ta ɗago manyan idanunta ta sauke akan Suhailah ta ce, "Wallahi ƙalau muka dawo
kawai kifin can ne dana buɗe aroma ɗinsa ya tayar min da hankali."
Suhailah da ta ji wani abu ya rufto kanta, ta aro jarumta ta danne zuciyarta ta sake cewa, "Eyyah!
Amma ai na ga kina son fish, ko dai mun sama ƙaruwa ne my Maleek?"
Ta yi maganar tana maida dubanta kan A.Maleek da ya yi tsaye yana saurarensu, jin abinda
Suhailah ta ce yasa shi saurin sakin mopper da ke hannunsa ya iso bakin bed ɗin, ya zauna yana
janyo TAIMIYYAH zuwa jikinsa ya ce, "Zaynabb when last ki kai period, an ya ma tunda mu kai
aure kin yi kuwa?"
Ya jefa mata tambayar a gigice gaba ɗaya duk ya wani kiɗeme, ya ma manta cewa har lokacin
Suhailah na cikin ɗin, TAIMIYYAH ta sake narkewa a jikinsa cikin sanyin murya ta ce, "Rabo na
da gani tun sati biyu before wedding."
"Oya let's go to the hospital now Baby."
A.Maleek ya yi maganar yana miƙar da ita zaune, ganin hakan yasa Suhailah juyawa da sassrfa ta
baro ɗakin, wasu hawaye na ciko idanunta cikin zuciyarta ta ke cewa, "Shikenan ta faru ta ƙare,
wai anyi wa me dami ɗaya sata. Shikenan idan ya tabbata gurguwar ciki gareta ta gama yawo,don
bata san kalar soyayyar kuma da A.Maleek zai riɓanya akan wanda ya ke gwada mata a yanzu ba."
Ta wuce ɗakinta tana sakin kuka mara sauti dukkanin jikinta na ɗaukar rawa, tana jiyo sautin
takunsu lokacin da suka fito don tafiya asibitin, sai ta kifa kici ta rushe da kuka wani irin nadamar
wautarta na can baya na sake danne zuciyarta, don ma idan ta nuna cewa likita ta basu tabbacin
samun lafiyarta sai ta ji zuciyarta ta ɗanyi sanyi.
Suhailah bayan ta ci kukanta ne ta rarrashi kanta ta wanko fuskarta ta fito zuwa falo, don zaman
jiran dawowarsu A.Makek ɗin ta ji da wacce za su dawo.
A.Maleek Ado ya dubi likitan da ke sanar da shi sakamakon gwajin da ya fito ya ce, "Doctor kana
nufin matata na ɗauke da cikin sati huɗu har da wasu kwanaki akai?"
Yayi tambayar cikin harshen nasara don likitar ɗan asalin ƙasar India ne ya ji turanci sosai,
Likitan ya jinjina kai tare da miƙawa A.Maleek sakamakon gwajin, hannunsa har rawa ya ke yi
lokacin da takardan ta zo hannunsa. Ya zubawa rubutun da ke jiki idanu wanda bai fahimci komi
akai ba, sabida da larabci ne aka rubuta dukkanin bayanan. Ya ɗauke ido daga kan takardan ya
mayar direction ɗin da TAIMIYYAH ke zaune,ta kasa kunni tana jin dukkanin abinda suke faɗi.
Zuciyarta ta cika da wani irin farin cikin jin cewa tana ɗauke da cikin A.Maleek ɗin, ta dubesa
lokacin da idanunsa ke shiga cikin nata, sai ta yi saurin yin ƙasa da kanta tana jiyo takunsa zuwa
gare ta.
Abazata ta jita a jikinsa ya yi mata wata iriyar runguma yana furta kalaman godia ga Allah
Maɗaukakin sarki, wanda ya azurtashi da samum rabo daga jikin TAIMIYYAH.
Likitar abin ya yi matuƙar birgesa don bai saba ganin irin wannan soyayyar a wajen ƴan Nigeria
ba, ya dinga sakin murmushi lokacin da A.Maleek ya kai bakinsa ya sumbaci lafaffen cikin
TAIMIYYAH, kafin ya zaunar da ita yana komawa gaban Doctor ɗin, don neman ƙarin bayani
akan yadda za su raini cikin.
A hannuwansa ya ɗakkota daga cikin hospital ɗin zuwa mota,babu kuma me kallonsu bare a sanya
musu idanu,Sunusi da shi ne ya kawo su asibitin, ya yi saurin fitowa ya buɗewa Ubangidansa back
seat ya sanya TAIMIYYAH a ciki, ya gyara mata zaman Hijab ɗin da ke jikinta.
Sun shigo gida wajen 9pm na dare har lokacin Suhailah na zaune cikin falon, rabin hankalinta na
ga kallo rabi na kan wayarta tana chart. Ta ɗago ido ta dubi A.Maleek da ya riƙo TAIMIYYAH a
cikin jikinsa suna takowa a hankali zuwa cikin falon, don ma ta ƙi ya sake ɗaukarta da ba zai barta
ta yo tafiyar da kanta ba.
"Sannu Zaynab ya jikin naki?"
Suhailah ta furta hakan lokacin da A.Maleek ya zaunar da TAIMIYYAH cikin seater, ta saki
murmushi tana duban Suhailah ta ce, "Wallahi jiki Alhamdulillah! Ba ma fa in da ke min ciwo
kawai aman da na yi ne ya galabaitar dani amma yanzu bana jin komi."
Suhailah ta jinjina kai ta ce, "To Ma Sha Allah! Allah ya ƙara lafiya."
TAIMIYYAH ta amsa da cewa, "Ameen." Idanunta akan A.Maleek da ya zura mata ido tamkar bai
taɓa ganinta ba, duk sai kunya ya rufeta ta miƙe tana dafe guiwar ƙafarta ta dubi side da Suhailah
ke zaune ta ce, "Bari in shiga daga ciki Anty sai da safe."
Suhailah ta jinjina kai ba tare da ta yi magana ba illah kallon yadda A.Maleek da ya yi zaraf ya
tashi yana riƙo hannun TAIMIYYAH, ganin za su shige su barta a zaune ya sanya ta ciri murya ta
ce, "My Maleek!"
A.Maleek ya waiwayo ya dubeta yana cewa, "Suhailah ina zuwa bari in rakata ɗaki sorry!"
Ya cigaba da riƙe hannun TAIMIYYAH har suka isa ɗakin baccinta,Suhailah ta raka su da ido tana
jin wasu hawaye na taruwa a idanunta.
Bai jima ba ya fito fuskarsa na faman blushing, ya zauna cikin seater ɗin da Suhailah ke kai yana
janyota jikinsa ya ce, "Suhailah ki ta ya mu murna za mu samu Baby ,Zaynabb na ɗauke da cikin 4
weeks."
Wani abu ya doka a tsakar kan Suhailah, ta yi saurin rintse idanunta tana son controlling kanta,ta
ƙirƙiro murmushi tana dubansa cikin ido ta ce, "Wow! Congratulations my Maleek, Allah ya
ingata ya raba lafiya ni ma Allah ya kawo min nawa rabon."
Suhailah ta kai ƙarshen maganar cikin rawar murya, idanunta na sake cika da ƙwalla, hakan ya
sanya A.Maleek sake rungumarta a cikin jikinsa ya ce, "Ameen Suhailah, soon ke ma za ki samu
ki kwantar da hankalinki please! Ki sani komi lokaci ne ke ma naki na zuwa, don Allah kar ki
sanya damuwa a ranki Suhailah....."
Ya cigaba da rarrashinta da kalamai masu daɗi don ta kwantar da hankalinta,domin sosai ya ke jin
tausayinta akan yadda ta ke son ta haihu gashi har yanzu Allah bai kawo rabon ba.
ya jima yana rarrashinta kafin ya baro ɗakin ya nufi ɗakin TAIMIYYAH , zuciyarsa cike da ƙauna
da tausayin ƴar uwarsa kuma matarsa Suhailah.
Ya isa ɗakin TAIMIYYAH daidai lokacin da ta fito daga bathroom ɗaure da towel iya cinya,
A.Maleek Ado ya isa zuwa gareta yana ɗakkota cak! Ya kai ta bisa bed ya kwantar. Da kansa ya
murza mata lotion a jiki tare da ɗakko kayan bacci ya sanya mata, ya ɗage rigar yana kallon kallon
lafaffen cikinta, wani abu me ƙarfi na huda jininsa. Cikin wata iriyar murya ya kai bakinsa bisa
kunninta ya ce, "Zaynabb ban san ta yadda zan misalta miki farin cikin da na ke ji a yau ba, sai dai
in ce Allah ya yi miki albarka tare da inganta wannan rabon da ya shiga tsakaninmu, i luv u wife!"
TAIMIYYAH ta lumshe idanunta tana jin yadda hannuwan A.Maleek ke yawo a jikinta, sai ta
buɗe idanunta tana sauke manyan fararen eyes balls ɗinta akan fuskar A.Maleek ta ce, "I luv u too
my sweet Amore! Allah ya tabbatar mana da alkhairy da lafiya me ɗaurewa."
A.Maleek ya ɗago ta baki ɗayanta ya rungumeta har sai da ta ce, "Wash!!! Sweet za ka matse
Babyn ai."
A.Maleek ya yi saurin sakinta yana zaro idanu waje, hakan yasa TAIMIYYAH sakin dariyar da
babu shiri tana yi masa gwalo, sai ya sake janyoya zuwa jikinsa yana cewa, "Oh! My pure zuma
abin ma har da zolayata za a riƙa yi kenan, oya tashi mu je ki haɗamin Coffee in sha sai mu zo mu
kwanta in yi welcoming Baby na ko?"
TAIMIYYAH ta shagwaɓe face ta ce, "No Sweet ba ma sai ka yi welcoming ɗinsa ba please!"
A.Maleek ya yi gaba yana cewa, "Wallahi pure zuma baki isa ba sai na yi ɗin, na ga alama kwana
biyu kin koyi raki sai kukan shagwaɓa ki ka iya, ko dama duk Baby ne ke sanya ki bamu gano
hakan ba?"
TAIMIYYAH da ke faman murmushi ta ɗan ɗaga sautin muryarta a shagwaɓe ta ce, "I don't know
my sweet."
"Kar ki damu zai faɗa min idan muna gaisawa my pure zuma."
TAIMIYYAH ta saki smile tana biyo bayansa don haɗa masa ruwan coffee, ta kuma yi masa
toasting bread slice biyu ya ci da shi.
Hajjah ta daɗe tana jan kunninsa akan ya kula sosai da Zaynab ɗin, sannan kuma ya zama me iya
riƙe kansa agaban Suhailah domin yanzu abu ƙuris zai faru, zata ɗaukesa a matsayin cin fuska don
ita bata samu cikin ba har yanzu.
Lokacin da ya kammala waya da Hajjah ya yi musu light off yana lalubota zuwa jikinsa,
TAIMIYYAH ta dinga zuba taɓara son ranta kafin ta je hannunsa, idanunta suka raina fata don tun
daga salon da yake nuna mata tasan akwai ƙura .
___________
*Nigeria.*
*Gyallesu, Zaria.*
Tun safe Zuhurah ta tashi da wani irin zazzaɓi me zafin gaske, hakan yasa Baba Sani da ya shigo
weekend ɗaukarta zuwa hospital, gwajin farko aka gano ciki ɗan sati huɗu a jikinta.
Lokacin da likitan ya sanar da su tare da miƙawa Baba Sani result ɗin test ɗin, rushewa da kuka
Zuhurah ta yi tana kiran ta shiga uku, Baba Sani ya daka mata tsawa ya ce, "Zuhurah kina hauka
ne ana miki albishir da samun ƙaruwa kina kiran kin shiga uku, shin cikin shege ki ka yi ko
kuwa?"
Ta girgiza kai cike da zallar tashin hankali ta ce, "Baba don girman Allah a cire wallahi bana so, ba
zan taɓa fatan na haɗa zuriya da Ameeru ba, ka taimakeni a cire cikin nan don......."
Kyakykyawar marin da Baba Sani ya sauke mata ne ya sanya ta sake rushewa da kuka, ya nuna ta
da yatsa cikin zallar fishi ya ce, "Wallahi summa billahi! Sai kin haife cikinnan Zuhurah matuƙar
ina numfashi, idan ki ka sake maganar zubar da shi ban yafe miki ba, kuma ki sani daga yau duk
abinda ya samu cikin nan sai mun yi shari'a da ke agaban alƙali, domin sai na kai ki ƙara akan
zubar da shi ki kai matuƙar ba akan idanuna ƙaddaran fitar ya sauka ba, ko kuma daga bakin likita
sahihi na ji cewa Allah ne ya zubda shi ba, don haka ki sawa ranki kin haɗa zuriya da Ameeru kin
gama."
Daga haka ya fito a fusace daga ofishin likitar yana cigaba da bambamin faɗa, Zunurah ta biyo
bayansa tana gunjin kuka dukkanin duniyar na juya mata da wani irin matsanancin tashin hankali.
Lokacin da suka iso gida da ihu ta nufi part ɗinsu tana faman kiran sunan Umma, Umma ta fito da
hanzari daga ɗaki ƙirjinta na faman bugu, dama har yanzu ba wani isashshiyar lafiya ce da ita ba
tunda aka ce hawan jininnan ya sameta, ta dubi Zuhurah da ta zube a kujeran falo tana kuka ta ce,
"Zuhurah lafiya za ki shigo min gida da kururuwa, meyafaru da ke?"
Kafin Zuhurah ta bata amsa Baba Sani da ya sanyo kansa cikin falon ya riga ta da cewa, "Babu
abinda ya sameta sai alkhairy, ciki aka ce tana da shi na wata ɗaya, kuma ke da ita ku sani sai ta
haife wannan cikin koda zai zama ajalinta, don haka duk wanda ya ciresa sai munyi shari'a da shi
a gaban alƙali."
Daga haka ya wuce su zuwa side ɗinsa ransa na cigaba da ƙuna, Umma kuwa ƙirji ta dafe ta saki
salati tana ji kanta na juya mata da wani matsanincin ruɗani, maganan Boka Kallah ya dawo mata
tarr cikin kwanyarta in da ya ke cewa, " _Maganar ƴar ki kada ki ce za ki ja da rabon da zai gitta a
tsakani domin sai ya zo dubiya, koda ace za ki ƙarar da numfashin da ya yi saura a rayuwarki don
ki hana aukuwar hakan, Don haka ki sanya kan ki a cikin lissafin marasa rabo, domin a duk
lamuranki babu sa a sai faɗuwa....._ "
Maganganun Boka Kallah suka gama haskawa fresh cikin kwanyar Umma, tamkar a lokacin ya ke
furta mata su, sai ta dafe saitin zuciyarta da ke mata zafi ta zame ta zauna cikin seater ɗin ita ma.
Idanunta akan Zuhurah da ke sheƙa kuka ta ce, "Zuhurah dole ne wannan a karon mu amince
bamu cikin lissafin mutanen da ke da sa ar rayuwa, domin kaf lissafin da Boka Kallah ya gama yi
min babu wanda bai tabbata ba, kuma ko wanne za a ɗakko a ɗaura shi a teburin bada maki to ba
za mu taɓa yin nasarar cinye lissafin daidai ba sai dai mu faɗi, wace iriyar rayuwace ke shirin
riskar mu?"
Ta kai ƙarshen maganar hawaye na wanke mata fuskah, Zuhurah ta ɗago a zare ta ce, "Me Bokan
ya ce Umma?"
Umma ta sanar da ita yadda suka yi da Boka Kallah, ai sai Zuhurah ta sake sakin kuka me gunji
faɗi ta ke, "Na shiga uku Umma wallahi bana ƙaunar wannan cikin, kamar yadda na daina ƙaunar
wanda ya yi sa. Ameeru ka cuceni ka gama da rayuwata!"
Ta cigaba da kuka me cin rai Umma na taya ta da zubar da hawaye, kafin ta ɗaga waya ta kira
Hajiya Barirah don neman mafita, Hajiya Barirah ta yi musu gargaɗi me kauri akan kada su sake
su ce za su yi yinƙurin zubda cikin nan, su haƙura har a haifesa don tunda Boka yace sai cikin ya
zo duniya to ko me za su yi bata ji cikin xai fi ta, don haka maganin kada ayi ta kar afara kawai."
Maganganun Hajiya Barirah su ka shigi Umma tare da ɗarsa tsoro me tsanani a zuciyarta, ta dinga
rarrashin zuhurah akan ta haƙura ta raini cikin da zaran an haife, sai su tattara abinda aka samu
sukai musu can Bauchin su ƙarata da shi. Da ire-iren waɗannan kalaman ta ciyo kan Zuhurah ta
haƙura akan batun fitar da cikin, suka cigaba da kokawa juna akan yadda abubuwa marasa daɗi ke
kutso kai cikin rayuwarsu.
Daga ɓangaren Iyah kuwa bayan sun gama waya da Hajjah ta yi mata zancen samun ciki a jikin
TAIMIYYAH,sai Iyah ta shiga matsanancin farin ciki suna gama wayar da Hajjah ta kira layin
TAIMIYYAH, wanda take kiranta da shi kullum daga can Cairo ɗin.
Bugu biyu TAIMIYYAH ta ɗaga wayar tana faman zubawa Iyah shagwaɓa, Iyah ta tambayi
lafiyarta tare da yi mata murnar rabon da aka samu, TAIMIYYAH ta dinga jin kunya tamkar tana
gaban Iyah ne, daga ƙarshe Iyah ta bata shawaran yadda za ta kula da kanta, ta sanar da ita zancen
sanya ranar Yah Deeku da aka yi za a yi bikin nan da watanni biyu masu zuwa. TAIMIYYAH ta
dinga murna tare da fatan alkhairy kafin su yi sallama da Iyah tana ji a ranta duk ta ƙosa ta dawo
9ja ɗin.
___________
*Gonar Ganye.*
*Gidan Basmah.*
Basman ce durƙushe tana faman kwara amai daga bakin tube, Nass na tsaye akanta yana faman
yatsina fuska cike da nuna ƙyanƙyami, ya dubeta bayan ta gama aman ta kurkure ba ki ya ce,
"Ke lafiyarki kuwa daga jin ƙamshin turare sai amai me ki ke nufi?"
Basmah ta dubesa a galabaice ta ce, "Don girman Allah Naseer ka fita wallahi bana son jin
ƙamshin turarenka shi ke ɗaga min zuciya, yakamata ka gane cewa ba ƙarya nake yi ba."
Nass ya watsa mata wani kallo yana cewa, "Daga dawowata weekend jiya ne wannan tsirfan zai
fara Basmah? To bazan ɗauka ba in ma don karna moreki ki ka tsiro da hakan to wallahi baki isa
ba, dole ki bani hakkina don anfaninki kenan dama kauda sha'awata, kafin in auro wacce za ta
maye min gurbin Zaynabb, kuma soon za ta shigo don na sameta."
Daga haka ya bar cikin toilet ɗin yana jan tsaki, Basmah ta rushe da kuka tana bin bayan Nass da
kallo,ta miƙe da ƙyar tana kora aman ya wuce ta sake wanko fuskarta ta fito.
A falo ta samesa yana waya yadda ya ke ƙasa da murya kawai ya sanya ta gane da mace ya ke
wayar, wani abu me girma ya taso ya danne zuciyarta, ta cigaba da takawa ta shige ɗakin baccinta
tana sakin kuka.
Duk tabi ta fige sabida rashin kwanciyar hankali, ga wannan yawan aman da take yi da ta fara
zargin ko ciki ta ke da shi? Tana nan zaune tana sharan hawaye ya shigo ɗakin, direct in da take
zaune ya nufo ya zauna yana janyo ta zuwa jikinsa ya ce, "Basmah tun jiya fa a matse na dawo
garinnan amma ban biya buƙatata ba, don haka yanzu dole ki bani wallahi sai dai ina yi kina aman
har na gamsu."
Daga haka ya fara cire mata kayan jikinta, yana jifa da su ita kuma hannuwanta duka biyu ta sanya
ta rufe hancinta, zuciyarta na cigaba da tashi tana jin kamar wani aman zai kufce mata.
Nass ya yi fatali da kayan jikinsa kafin ya jefa ta a gado yana bin bayanta, iya wahala Basmah ta
sha a hannun Nass har lokacin da ya gamsu,ta dinga kwara amai a tsakar ɗakin kamar zata amayo
kayan cikinta.
Ganin abin da gaske ne na Basmah ya sanya Nass jin tausayinta, har ya taimaka mata ta yo wanka,
ya haɗo mata tea mara madara ta sha sannan ya ɗauketa suka wuce asibiti,bayan gwaji da
tambayoyin da ta amsawa likita aka gano ciki na wata ɗaya ke wahal da ita.
Nass ya nuna ɗoki da murna sosai don yana son yara,hakan ya rage damuwar da ke cinkushe a
zuciyar Basmah, amma har lokacin maganar da ya yi na cewa soon zai auro wacce za ta maye
masa gurbin TAIMIYYAH a zuciyarsa ya tsaya mata arai, har suka iso gida babu wani walwala
akan fuskarta.
Ta ɓalle murfin motar za ta fita Nass ya riƙo hannunta yana duban cikin idon ta ya ce, "Baby ashe
ƙaruwa muka samu no wonder na ji kin ƙara sweet kwana biyu, dole a nemo maganin da aman
nan zai tsaya, don moranki zan yi sosai Babe!"
Basmah da takaici ya cika zuciyarta ta saki hawayen da ta riƙe suka zubo, bata yi magana ba illah
ƙwace hannunta da ta yi ta fice daga cikin motar tana kuka, Nass ya bi ta da ido yana faman taɓe
baki bai fito daga motar ba sai da ya kira Shairfah, wacce suke buga soyayyah da juna don ba
ƙaramin kama zuciyarsa ta yi ba.
Tun wancen satin ya tura manya suka je nema masa izinin fara zuwa zance, a can hanwa gidan su
Sharifah, Babanta banufe ne sai mamarta ta kasance fulani.
Sun daɗe suna waya yana sanar mata cewa ƙawarta fa ciki gare ta, saura ita don ba zai taɓa ɗaga
mata leg ba yadda soyayyarta ke wahal da zuciyarsa. Koda ya fito daga motar ya kulle side ɗin
Hajiyarsa ya nufa ya sanar da ita zancen cikin, ba laifi ta nuna murnarta a gaban idanunsa ,amma
yana fita ta ja tsaki don ba ƙaramin tsanar Basmah ta yi a zuciyarta ba, musamman da Nass ya
fayyace mata cewa ƙanwar musakar Yarinyar da ta raba shi da ita ne, sukai asiri suka aure mata ɗa
sai ta ji tsanar Basmah ya ninku a zuciyarta, shiyasa ta goyi bayan Nass ɗin akan zancen Sharifah.
Basmah na shiga ɗaki Umma ta kira ta sanar da ita zancen cikinta, Umma ta yi murna ba laifi
amma sam zuciyarta babu daɗi, ta sanar da Basmah cewa ita ma Zuhurah cikin ne da ita, ta gaya
mata duk yadda suka yi da Boka kallah da furucin Baba Sani. Basmah ta taɓe baki ta ce, "Allah ya
kyauta Umma, ni yanzu abinda ke damuna furucin da Nass ya yi ya ce wai ya samu wacce za ta
maye masa gurbin gurgurwar nan a zuciyarsa, Umma ina jin tsoran ya auro min kishiya alhali ko
shekara bamu dosa ba, wallahi mutuwa zan yi Umma don ina tsananin kishinsa."
Ta rushewa Umma da kuka lokacin da ta kai ƙarshen maganarta,Umma ta dinga aikin rarrashin
Basmah, shigowar Nass ɗakin ya sata yanke wayar baki ɗaya tana sauke ajiyar zuciya.
__________
*Cairo, Egypt.*
TAIMIYYAH ce tsaye a kitchen tana haɗa musu abin breakfast,fuskarta sai blushing yake tana
tuna yadda ta zame daga jikin A.Maleek ta gudo zuwa kitchen ɗin.
Ta buɗe drawer ta ciro gwagwanin siden da zata haɗa tayi sandwich, ta ɗakko ƙaramin bowl don
juye kifin gwangwanin a ciki, tana buɗewa ƙamshin ya bugi hancinta ta ji hankalinta ya tashi.
Ta yatsine fuska tana cigaba da zazzageshi cikin bowl ɗin hankalinta na sake tashi, ta buɗe na
biyun kenan smell ɗinsa ya sake bugunta, take ta ji wani ƙaƙƙarfa amai ya taho mata.
Ta nufi wajen sink da sauri ta fara kwara amai, wani irin amai ta dinga sheƙawa me wahala, wanda
kakarinsa ya sanya Suhailah da ta tashi a lokacin saurin nufowa kitchen. Ganin yadda
TAIMIYYAH ta galabaita tana faman nishi ya sanyata saurin isa bakin sink ɗin tana cewa,
"Subhanallah! Sannu Zaynab wani aman ne kuma?"
TAIMIYYAH ta gyaɗa kai kawai tana ƙoƙarin kunna famfo don ɗauraye bakinta da face ɗinta,
Suhailah na tsaye na faman jera mata sannu tana jin wani tausayinta na kamata kaɗan-kaɗan.
Bayan TAIMIYYAH ta gama wanke face ɗinta ne Suhailah ta dubeta tace, "Ki je kawai ki kwanta
zan ƙarisa aikin please, ki daina damun kanki tunda yanzu baki da isasshiyar lafiya."
Kafin TAIMIYYAH ta ce komi suka jiyo takun A.Maleek da ƙamshinsa, suka ɗaga ido a tare suka
sauke akansa lokacin da ya ke takowa zuwa cikin kitchen ɗin, idanunsa akan TAIMIYYAH ya ke
har ya ƙariso ciki yana cewa, "Zaynab whats wrong with u?"
TAIMIYYAH ta dubesa tana jin ƙirjinta na bugawa ganin yadda ya haɗe fuskarsa tamkar bai taɓa
sanin miye dariya ba, ta shagwaɓe fuska tare da narke murya ta ce, "Bakomi fa amai ne kawai na
yi, kuma lafiya lau na ke aikina daga buɗe Siden ɗin can ne amai ya taho min."
A.Maleek ya sake haɗe fuska cikin dakakkiyar muryarsa ya sake cewa, "But waya ce ki shigo
kitchen ki ce zaki wani abu Zaynab, mena gaya miki jiya akan yin duk wani aiki?"
TAIMIYYAH ta sake narke murya ta ce, "Cewa ka yi kada na sake yin duk wani aiki,but....."
Bai barta ta ƙarisa maganarta ba ya katseta da cewa, "Sabida ban isa ba shiyasa ki ka taso muna
kwance ki ka zo kina stressing kanki, har da janyo sanadin da ki kai amai ko? Wuce ki koma
ɗaki."
Ya yi maganar da ɗan ɗaga sautin muryarsa, TAIMIYYAH sai ta ji ranta ya sosu har hawaye na
taruwa a cikin idanunta, ta dafa ƙafarta ta fara takawa ta fice daga kitchen ta nufi ɗakinta.
A.Maleek ya rakata da ido yana jin haushin yadda ta ƙi jin maganarsa, ya maida dubansa kan
Suhailah da ke tsaye tana kallon ikon Allah ya ce, "Wife don Allah kar ki sake barinta ta ce za ta yi
wani girki koda na fita, na soke yin girkinma gaba ɗaya har mu wuce zuwa jibi, ordering za mu
dinga yi ko mu fita mu ci a waje."
Suhailah ta ɗan taɓe baki ta gaida shi kafin ta ɗaura da cewa, "Ai ma nata abin da sauƙi sweety, ita
na lura ƙamshin kifi ne cikin bayaso kaman, but tana cikin koshin lafiya ba kaman wasu da ke
ciwo sosai idan ciki ya shiga ba."
A.Maleek ya taɓe baki ya ce, "Duk da haka wife bana son ta dinga stressing kanta, ga yanayin
tafiyarta da sauransu so hankalina zai fi kwanciya ta dinga nutsuwa guri ɗaya ta daina duk wani
aiki , da zai sanya ta jin gajiya a jikinta sosai, kuma doctor ma abinda ya faɗi kenan don meyasa
ba za ta kula ba ?"
Ganin yadda ya hau sosai ya sanya Suhailah taɓe baki ta ce, "Easy please my Man, don Allah a yi
mata haƙury ba wai da faɗa za ka nuna mata baka so ba, ita gani ta ke lafiyarta lau shiyasa."
A.Maleek bai sake cewa komi ba ya baro kitchen ɗin Suhailah ta bishi da harara, tana jin wani abu
me nauyi na danne zuciyarta.
" Zaynab sabida na ce ki daina aiki don kula da lafiyarki shi ne za ki zo nan kina kuka haka?"
A.Maleek ya yi maganar lokacin da ya ke zama daga bed ɗin da TAIMIYYAH ta yi kwance tana
kuka, ta ɗago manyan idanunta ta ce, "Don Allah ka yi haƙury ni bansan ƙamshin za ya sani amai
ba da bazan ce zan yi ba ai, ni lafiya lau na ke Hubby shiyasa.Kuma abinda ya sani kuka kawai
yadda ya ka yi min faɗa a gabanta."
Yadda ta yi maganar da shagwaɓa tana sake matso hawaye ya sanya A.Maleek janyota zuwa
jikinsa, ya kai hannunsa yana share mata hawayen ya ce, "Sorry my pure zuma, raina ne ya ɓaci
tunda tun jiya na ce kar ki ce zaki sake yin wani aiki baki ji ba, muna cikin baccinmu kika gudu
gashi nan har jikinki ya yi ɗumi sabida galabaitar da kika yi wajen yin amai ɗin, please ki dinga
jin maganata Baby."
TAIMIYYAH ta sake shigewa jikinsa ta ce, "Sorry!" A.Maleek ya cigaba da sanar da ita
dokokinsa akan cikinsa don ta kiyaye masa lafiyar Babynsa, wanda tun kafin ya zo duniya ya ke
jin ƙaunarsa da ba zai misaltu ba.
Tare suka shiga bathroom don yin wanka, bayan A.Maleek ya gama zuba taɓararsa akai wankan,
suka fito duka ɗaure da ƙaramin towel,TAIMIYYAH sai faman shagwaɓa ta ke zuba masa shi
kuma yana sake susucewa akanta.
Sun riga Suhailah isa dining ɗin don zaman yin kalacin, sai daga baya ta fito ta ci uban ado cikin
ƙananun kaya da suka fitar da surarta, sai dai kallo ɗaya ta yiwa shigar jikin TAIMIYYAH ta ji
kibiyar kishi ya soki zuciyarta.
Wata ƙaramar riga ce TAIMIYYAH ta saka wanda ya kamata daga sama daga ƙasa kuma ya
buɗe,daga wuyar rigar har hannunwansa net ne daya bayyana jikinta daga sama har zuwa ƙirjinta
da bata sanya Bra ba, Suhailah ta yi saurin ɗauke idanunta daga kan su daga ita har Maleek ɗin. Ta
tashi ta fara serving ɗinsu suka fara cin abincin babu me magana, TAIMIYYAH spoon biyu ta kai
na plantain Sauces da Suhailah ta yi musu ta aje spoon ɗin, don ji ta yi gaba ɗaya ba za ta iya ci ba
ɗanwake kawai take jin ci.
A.Maleek ya tambaya ganin yadda ta ke juya spoon a cikin plate ta kasa cin abincin, TAIMIYYAH
ta ɗaga manyan idanunta ta sauke akansa, cike da zallar shagwaɓa da narke murya ta ce,
"Ɗanwake na ke son ci Hubby!"
Suhailah ta haɗiye tea ɗin da ta kurɓa da sauri, tana jin wani abu na tokare maƙoshinta, A.Maleek
ya jinjina kai ya ce, "Okey! Sorry bari in kira Sunusi ya taho da shi."
Ya ɗaga waya ya sanar da Sunusi cewa ya yo masa ordering Ɗanwake, ya aje wayan yana maida
dubansa kan TAIMIYYAH yana rarrashinta ta daure ta sha tea.
Suhailah da duk ta ji ta muzanta a wajen sabida yadda gaba ɗaya bata ishi A.Maleek kallo ba a
wajen, hankalinsa na kan gurguwar matarsa yana faman rarrashinta akan ta sha tea, ita kuma
TAIMIYYAH sai faman shagwaɓa ta ke zuba masa, sai kawai Suhailah ta ja ƙaramin tsaki tana
tashi fuu...! Ta wuce ɗakinta hawaye na fara taruwa a idanunta.
TAIMIYYAH da A.Maleek suka bi bayanta da kallo, A.Maleek ɗin na jin babu daɗi a zuciyarsa,
amma shi kansa bai san meyasa idan yana gaban TAIMIYYAH ya ke rasa duk wani nutsuwarsa
ba, musamman a yanzu da ta ke da cikinnan wani mahaukacin ƙaunarta aka ruɓanya a cikin
zuciyarsa.
Bayan Sunusi ya iso awa ɗaya da wasu mintuna da yin wayarsa da A.Maleek, ya aje pack ɗin
Ɗanwaken da ya sayo a in da suka saba siya wajen wasu ƴan 9ja, sai Maleek ya ɗauka ya wucewa
TAIMIYYAH da shi zuwa ɗaki.
A kan idanunsa ta dinga cin Ɗanwaken wanda ya ji kayan haɗi da yajin tafarnuwa, ga haɗin Salad
da akai masa wanda ya sanya ta sake jin shauƙin cin sa tamkar wacce ta yini bata ci ba. Ya zura
mata ido yana jin wani irin abu na zagaye jinin jikinsa, TAIMIYYAH da ta tada pack ɗaya duka na
Ɗanwaken ta dubesa da shagwaɓa ta ce, "Habibi wannan kallon ai sai ka shaƙemu ni da unborn
ɗin."
A.Maleek ya saki murmushi yana kai hannu ya janyota zuwa jikinsa ya ce, "I luv u wife!"
TAIMIYYAH ta lunshe ido wani zazzafar soyayyarsa na kewaye jinin jikinta, ta buɗe baki tare da
riƙo kansa ta sumbaci bakinsa ta ce, "Luv u too my Maleek,sakarni na yo brush sabida ƙamshin
garlic ɗin da naci a yajin nan, but ya yi daɗi Baby thank u!"
A.Maleek ya sumbaci idanunta da ke da tasiri akansa kafin ya barta ta tashi zuwa toilet, shi kuma
ya koma falo wajen Sunusi suka fara tattauna muhimman lamura akan Business ɗin da yake son
kafawa a ƙasar.
Da rana fita suka yi su kai lunch a wani haɗaɗɗan Restaurant, daga can suka sake zaga wasu
wurare sai yamma suka shigo gida. Da daddare Sunusi ne ya yi musu order ɗin abincin dinner,
suka haɗu a dining suka ci kafin A.Maleek ya bi TAIMIYYAH zuwa ɗakinta, cox ta riga su tashi
ta shige sabida yadda ta ke jin bacci da wuri.
Washegary suka kammala duk wasu kayansu da zasu wuto da shi, sabida jirgin 11am za su biyo
zuwa 9ja a gobe. TAIMIYYAH ta kammala haɗa kayanta dana A.Maleek tun safe, don haka tana
wanka suka yi breakfast baccinta ta koma don kwana biyu wani irin bacci ta koya da bata gajiya
da yinsa, har A.Maleek ya yi complain akan hakan amma ta tabbatar masa da cewa lafiya ce.
Washegary suka baro ƙasar Cairo cike da jin kewa me tarin yawa, TAIMIYYAH ta dinga jin cewa
memory ɗin irin rayuwar luv ɗin da suka sha a ƙasar ba zai taɓa gogewa a cikin kwanyarta
ba.Suhailah kanta ta ji daɗin tafiyar duk da cewa ta haɗiɗiyi tarin abubuwa masu ɗaci game da
zazzafar kishin da ta ke ji duk lokacin da A.Maleek ke susucewa akan TAIMIYYAH a gaban
idanunta.
___________
*Abuja.*
Lokacin da girji ya sauka a Airport ɗin Abuja already har Obi driver ya iso don ɗaukar su zuwa
gida,shi ya dinga kwashe manyan jakunan kayan da suka taho da shi zuwa mota, su kuma su
TAIMIYYAH na biye da bayan A.Maleek ɗin zuwa in da Obi ya yi parking.
Daga TAIMIYYAH har Suhailah sun sake yin kyau da wani irin fresh, sabida hutu da jin daɗi tare
da kwanciyar hankali da suka samu a ƙasar Cairo. Amma kyawun da TAIMIYYAH ta ƙaro na
daban ne sabida yaron ciki da take ɗauke da shi, ta sake cika musamman ƙirjinta wanda ke
matuƙar ɗaukar hankalin Maleek Ado. Fuskarta ta sake yin wani irin fresh sai glowing ta ke me
fisgar hankali, ta cika ta yi fes da ita tamkar ka saceta ka gudu.
Lokacin da suka isa gida kasancewar ba ita ke da A.Maleek ɗinba yasa ta wucewa ɗakinta, wanda
su Ameena suka gama gyare ko'ina sai tashin ƙamshin turarukan wutar Northern Regalia ke tashi,
wanda ƙamshin ya cakuɗu da na Russ ya ruɗa ko'ina da wani irin fitinannan ƙamshi me kwantar
da zuciya, tare da kama waje da kayan da ke wajen ma baki ɗaya .
Wanka kawai ta iya yi tabi lafiyar gado wani daddaɗan bacci na tafiya da ita, bata san iya lokacin
da ta ɗauka tana baccinba har zuwa lokacin da A.Maleek ya shigo ya tashe ta, ta yo brush da
alwala ta zo ta gabatar da sallar Zuhur ganin har lokaci ya ja sosai. Yana zaune yana amsa call har
ta idar da sallar ta miƙe tana zare Hijab ɗin jikinta, yabi cinyoyinta da kallo ta cikin dogon vest ɗin
da ta sanya ta zumbula Hijab akai.
Ta taka zuwa wajen kayanta tana ciro wata boubou na material ta zare vest ɗin ta zura,ko Bra bata
sanya ba sai ƙaramin underwear daga ciki, ta tako zuwa bakin bed in da Maleek ke zaune ya zubo
mata ido kamar zai cinyeta da mayen kallonsa.
Ta yi maganar a shagwaɓe tana shafa lafaffen cikinta, A.Maleek ya aika mata wani sassayar kallo
da ke kiɗima zuciyarta, kafin ya rungumota zuwa jikinsa yana kai bakinsa bisa ƙirjinta ya yi
kissing ɗinsu. Ya ɗago kansa ya mayar kan fuskarta ya sumbaci mouth ɗinta ya ce, "Oya let's go
my pure zuma,yanzu za ki ci abinci ki daina jin yunwar okey!"
Daga haka suka fito zuwa dining tuni har Suhailah ta yi serving kanta ta fara cin abincin, don
tunda ta ga ya tashi ya je kiran TAIMIYYAH tasan sai an gansa kuma. Kallo ɗaya ta yi musu
lokacin da suka ƙariso ta ɗauke kai tana cigaba da cin abincinta, TAIMIYYAH ita ta bubbuɗe
coolers ɗin ta yi serving ɗinsu abinda za su ci, ta turawa A.Maleek nasa ita kuma ta zauna tana
fara cin nata. Koda suka kammala wani baccin ta ji tana son sake yi amma ba ta kwanta ba, sai da
ta maida line ɗinta ta kira Iyah da su Yasmeen ta sanar musu sun dawo, Hajjah ta kira daga ƙarshe
wacce suka jima suna magana da TAIMIYYAH, tana tambayarta lafiyar jikinta da tambayarta ko
da abinda take sha'awar a aiko mata dashi? Sai TAIMIYYAH ta ce tana son garin ɗanwake da na
tuwo. Hajjah ta tabbatar mata cewa za a yi a turo mata ko idan Maleek zai shigo cikin week ɗin sai
ya taho mata da shi.
Kwanakinsu biyar da dawowa daga Cairo Suhailah ta gama parking duk wasu kayanta da za ta
wuce da su Lagos, kayan sawa ne kawai dama sai abubuwan da ba a rasa ba tunda babu abinda za
a kwance da ya dangacin kayan ɗaki ko makamantasu, don can a tsare yake har fiye da nan ɗin .
Duk ta ƙosa ta kuma ƙagu su bar garin ko idanunta sa huta da ganin zallar tarairayar da
TAIMIYYAH ke samu daga wajen A.Maleek ita da cikin jikinta, wanda hakan ba ƙaramin ɗaga
hankalin Suhailah da sanyata a damuwa da kishi me tsanani da ta ke ji ba. Ta sha shiga ɗaki ta yi
kuka ta yi nadamar wautar da ta aikata a baya akan yiwa kanta illah, wata kila da yanzu da yaranta
biyu ko uku a gabanta a daidai wannan lokacin.
Ta ɓangare ɗaya ta ke samun sauƙi shi ne idan A.Maleek na kwantar mata da hankali akan rashin
haihuwar, da kuma nusar da ita cewa a kowani lokaci ita ma nata rabon na iya samuwa. Ta kan ji
relief da kuma ƙwarin zuciyar da ke sanya ta cigaba da riƙe kanta da zuciyarta, bata taɓa nuna
halin da zuciyarta ke ciki a gaban idanun TAIMIYYAH ba, haka TAIMIYYAH na iyakan
ƙoƙarinta wajen ganin ta kaucewa yin wani abu da zai sosa zuciyar Suhailah.
Ana jibi za su wuce Lagos ɗin ne ya kama weekend hakan ya sanya A.Maleek yankar musu ticket
na flight zuwa Kano, daga can Yusuf zai ɗakko su zuwa Zaria. TAIMIYYAH ta yi murna matuƙa
lokacin da A.Maleek ya sanar mata maganar tafiyar, don a cike ta take dama da ɗokin son ganin
Iyah ta kuma kai mata tarin tsarabar da ta jibgo mata daga Cairo.
Ƙarfe biyu na rana suka iso kano sun kuma samu already Yusuf na jiransu, a wani haɗaɗɗan
Restaurant suka tsaya suka ci abinci sannan suka kamo hanyar Zaria, TAIMIYYAH ta dinga ji
tamkar ta yi tsuntsun ta biya gidan Guggo Bilki amma babu halin hakan..........✍🏻
#Ɗansabo ce#
[12/15, 11:47 AM] +234 703 040 9541: Littafin TAIMIYYAH paid book ne,ga duk wanda ta
tsincesa a kowani irin group ne,kiji tsoran Allah karki karanta sai kin biya 500 naira only.
Za ku iya min magana ta wannan number ɗin 08167768704, ko kuma ku turo kuɗin ku kai tsaye ta
wannan account ɗin 0504192664 aisha ibrahim dansabo GTbank.*
Masu turo credit za ku turo katin MTN na 500 ta wannan line ɗin 08167768704.
_Ina ƴan kasuwa masu buƙatar a tallata muku hajar ku? Maza ku garzayo da kuɗi ƙalilan a tallata
muku kayan siyarwanku sai dai kawai ku ji ana kiran waya don buƙatan sayan kayan ku,ku
tuntuɓeni ta layina kamar haka 08167768704._
*89*
*GRA,Zaria.*
Ƙarfe biyar da wasu mintuna suka shigo gida bayan sun sauke Suhailah a gidanta,
kasancewar TAIMIYYAH ita ke da A.Maleek yasa suka wuto gidanta tare.
A gajiye ta ke sosai duk da irin baccin da ta kwasa a mota hakan bai hanata jin gajiya ba, shiyasa
ta fara wanka kafin ta gabatar da sallar La'asar da ya samesu a hanya.
Tana idarwa A.Maleek na shigowa cikin ɗakin hannunsa riƙe da ledar take away na farfesun kayan
ciki da su snacks da ya sanya Yusuf wucewa ya siyo bayan ya aje su, ya dire ledojin akan table
yana cigaba da takowa wajen da TAIMIYYAH ke zaune bakin bed ya zauna. Idanunsa a kanta ya
dinga bin ta da wani sassanyar kallo kafin ya ce, "My pure zuma shi ne ki kai wankanki ba ki jira
ni mun yi tare ba ko?"
TAIMIYYAH ta sakar masa smile tana cewa, "Sorry Luv anjima zan jira ka sai mu yi tare, me aka
siyo? Unborn na jin yinwu Hubby!"
Yadda ta yi maganar da zallar shagwaɓa ya sanya A.Maleek rungumota zuwa jikinsa, ya kai hannu
ya ɗage fingilwar vest ɗin da ke jikinta yana kai bakinsa ya sumbaci cikin, murya can ƙasa ya ce,
"Wai haka unborn?"
TAIMIYYAH ta saki dariya tana ture hannunsa da ke mata waiwayi a ciki ta ce, "Au sai ma ka
tambayesa Hubby, bayan Mamah ta faɗi maka gaskiya ne?"
Ya saki murmushi tare da sumbatar goshinta ya ce, "Oya mu je unborn ya ci abinci sai mu ɗan
gaisa 2 days ya yi missing Papa ko sweet?"
TAIMIYYAH ta yi saurin dubansa ta ce, "No Hubby unborn ya bai yi missing Papa ba."
A.Maleek ya yi maganar yana hararar TAIMIYYAH,ta saki dariya sosai tana faɗin, "Sorry Habibi
ni ba sharri na yi masa ba fa."
Daga haka suka ƙarisa ƙasan carfet ya zaunar da ita yana ɗakko ledodin da packs ɗin suke ya dire
a gabanta, bata da mu da a ɗakko plate a ciki suka ci suka bar sauran, don shi kaɗan ya ci snacks
ɗin ita ce dai ta ci da yawa tamkar ba sai da suka suka yi Lunch a Kano kafin su zo ba.
*08:40pm*
TAIMIYYAH ta kalli jakar da ta ɗibi tsaraban da za ta kai wa Iyah, har da su Umma da Babah
Ladi duk ta cire musu. Hatta Basmah da Zuhurah ta siya musu Abaya masu kyau kala bibbiyu,
Yasmeen da Ummie ma haka ta siya masu Abayas bibbiyu da turaruka masu ƙamshi Arabians.
Tsaraban Ummie da na Yasmeen ne kawai bata saka cikin bag ɗin ba, sabida tana son ta roƙi
A.Maleek su tsaya a Kanon ta je ta ga gidan Ummie su kuma gaida Guggo Bilki.
A.Maleek Ado ya zuba mata manyan idanunsa lokacin da ya shigo cikin ɗakin,kafin ya ɗauke idon
daga kanta ya mayar kan jakar da ke gabanta ya saki smile. TAIMIYYAH ta shagwaɓe face ta ce,
"Hubby na gama shirin mu je ne?"
A.Maleek ya sake sakin smile yana kallon yadda doguwar rigar jikinta ta yi mata, wata iriyar
gownce da ta siyeta ready made a wani mall a Cairo. Rigar me ɗan faɗi ce tamkar boubou amma
kuma daga saman ƙirji ya tsuke ya baiwa cikar halittar wajen damar bayyana kaɗan, sai daga
hannu zuwa ƙasa ya saki gaba ɗaya tamkar boubou, kalar rigar dark purple ne da akaiwa ado da
pink jefi-jefi a jikinsa. Sai ta samu gyale me kauri pink ta yane kanta zuwa ƙirjinta da shi, ta yi
kyau matuƙa fuskarta da ya yi bul sai faman glowing ya ke yi cikin hasken fitullun da suka haske
ɗakin.
Ya saki sassanyar ajiyar zuciya lokacin da ya sanya manyan idanunsa cikin nata idanun, waɗanɗa
suka sha kwalli suna wani irin sparkling, har yau har gobe A.Maleek bai taɓa cin karo da me irin
idanun nata ba sai ita ɗin dai, don wani irin haske suke da shi da ke haskawa da wani irin ƙyalli ta
cikin ƙwayar idon.
Ya taka a hankali ya isa ya zauna tare da kai bakinsa ya ba idanun light kiss yana cewa, "My pure
zuma kin faye rigima yanzu duk gajiyar da ki ke cewa kin yi, shi ne kuma ki ke so mu fita yanzu
ba za ki bari sai gobe ba Sweet?"
TAIMIYYAH da ta gama sanya ran ganin Iyah a yau ɗin sai ta sake narke masa a jiki cike da
shagwaɓa ta ce, "Don Allah Habibi mu je yau ɗin, wallahi na gama sanya rai zan ga Iyah, mu je
please ka ji!"
A.Maleek ya ɗago fuskarta yana cewa, "To me za a bani idan mun dawo, don gaskiya sai an bani
tukuicin wannan fitar idan har ana so gobe mu sake fita."
TAIMIYYAH sai ta kai bakinta daidai kunninsa ta raɗa masa wasu words masu zafi, wanda ya
sanya A.Maleek sake manna ta da jikinsa yana shigar da ƙwayar idanunsa cikin nata ya ce, "Really
pure zuma?"
TAIMIYYAH ta jinjina masa kai ta ce, "Yes Sweet Amore! Kai dai ka kaini in ga tsohuwata mu
dawo in baka mamaki."
A.Maleek bai san lokacin da ya miƙe tare ɗaukarta ya dire a ƙasa yana cewa, "Oya let's go Babe!"
Suka jera da juna yana riƙe da bag ɗin tsarabarta har zuwa parking space, ya buɗe mata front seat
ta shiga ya maida murfin ya rufe tare da sanya bag ɗin back seat, ya zagaya ya shiga mazaunin
driver ya tada motar suka nufi gate, Mai gadi ya buɗe musu gate ɗin tare da musu fatan dawowa
lafiya suka fice.
Lokacin da suka iso gyallesu TAIMIYYAH gaba ɗaya ji ta yi ta ƙosa su isa cikin gidab nasu, shi
kuma A.Maleek da gangar ya dinga gangarawa da motar cikin layin nasu very slow.
TAIMIYYAH ta yi maganar a shagwaɓe tana kallon yadda ya ke smilling, ya dube yana narke
murya cikin son ya kwaikwayi muryarta ya ce, "Lafiyarta lau my pure zuma."
TAIMIYYAH ba ta kuma cewa komi don ta gane da gangar yake tafiya slowly, suna shiga cikin
compound ɗin ta hango motar Baba Sani da na Yah Deeku a parking space, sai ta ji wani farin ciki
da ɗoki ya sake kama zuciyarta. Ta miƙa hannu za ta buɗe motar ta fice A.Maleek ya yi saurin
furta, "Wait Sweet."
Sai ta dakata har ya zagayo ya buɗe mata murfin motar ta fito, yana riƙe da jakar tsarabarta ɗaya
hannun kuma na riƙe da nata suka isa part ɗin Iyah.
TAIMIYYAH tun daga nesa za ta fara ƙwalla kiran Iyah A.Maleek ya yi saurin harararta ya ce,
"Kina buɗe min murya za mu juya gida wallahi kin ji na rantse!"
Sai ta yi saurin rufe bakin tana ji kamar ta fincike daga hannunsa ta ruga da gudu, A.Maleek ya
sake dalla mata harara ganin yadda duk ta wani birkice kamar wacce ta shekara bata zo gida ba.
Shiya fara doka sallama daga bakin ƙofar shiga falon har lokacin ya ƙi sakin hannun
TAIMIYYAH, daga cikin ɗakin Iyah da Yah Sadeeq da ke zaune cikin falon suka amsa sallamar,
kafin Iyah ta bada izinin su shiga TAIMIYTAH ta yi nasaran fincike hannunta daga Maleek ta
runtumo cikin falon, cikin wannan gudun nata me kama da tsalle ta isa wajen Iyah tana cewa,
"Washh! Allah Iyah i miss u wallahi duk na ƙosa in ɗaura idanuna akan ki."
Iyah da murnar ganin TAIMIYYAH ya kamata ta yi saurin dubanta tana cewa, "Oh! Iyah Zaynabu
lafiyarki lau kuwa za ki shigo da wannan hanzarin yanzu fa ba irin da bane kuma kin san ba ke
kaɗai ba ce ko?"
Kafin TAIMIYYAH ta ce komi A.Maleek shi ma ya shigo cikin falon, yana riƙe da bag ɗin
tsarabar TAIMIYYAH, ya sauke idanunsa akanta yana jifanta da harara. Iyah ta dubesa cikin farin
ciki ta ce, "Barka da zuwa a she ma tare ku ke, sannunku da zuwa lale marhabin dafatan kun dawo
lafiya?"
A.Maleek ya tsuguna daga ƙasa ya gaida Iyah cike da girmamawa kafin ya bata tabbacin sun dawo
lafiya Alhamdulillah! Yah Deeku ya taso cikin hanzari yana miƙawa A.Maleek hannu sukai
musabaha, yana mai da dubansa kan TAIMIYYAH da ta sake masa wani mugun kyau a ido ta sake
cika sosai, sai ya yi saurin ɗauke idanunsa akanta yana cewa, "Baby idanunki ya rufe ko ni baki
gani ba sai Iyar ki kawai kin kyauta."
"Please! Yah Deeku ka yi haƙury idanuna a rufe da son ganin tsohuwata na shigo, ina yini ya Anty
na kuma? An sanya time Allah ya sanya alkhairy ya kai mu lafiya."
Daga haka Sadeeq ya fice ya baro part ɗin Iyah ya nufi nasa, zuciyarsa cike da zallar farin cikin
ganin TAIMIYYAH cikin kwnciyar hankali tare da samun nagartaccen miji kuma attajiri irin
A.Maleek Ado, wanda kallo ɗaya za kai masa ka ga irin yadda ya ke bin TAIMIYYAH da kallo, za
ka fahimce cewa ba ƙaramar ƙauna da soyayyarta ne ya damƙi zuciyarsa ba.
Daga cikin part ɗin Iyah kuwa ita ce da kanta ta tashi don zuwa ta kawowa surukin nata ruwa da
abin kaiwa baka, ganin Iyah ta bar musu falon ya sanya shi isa wajen da TAIMIYYAH ke zaune
ya ce, "Zaynabb yanzu da unborn ɗin a jikinki ki kai wannan tsallen da ki ka yi sabida baki da
man kai ko?"
TAIMIYYAH ta shagwaɓe fuska tare narke murya ta ce, "Don Allah ka yi haƙury Habibee na kasa
controlling kaina ne, but ba zan kuma ba ka ji!"
Yadda ta kai ƙarshen maganar cike da magiya ya sanya shi kai hannu ya ɗan bige bakinta da ta
zumɓuro ya ce, "Idan ma ki ka saken za ki ga yadda zan yi da ke, sai in hana fitar ma gaba ɗaya
mutum ya zauna a gida in ga yadda za a yi."
TAIMIYYAH ta sake bashi haƙury cike da zallar taɓarar da ke sake narkar da shi, suna cikin haka
Iyah ta fito daga kitchen ɗauke da tray da aka ɗauro plate ɗin dambun nama da bata rabo da shi,
sai ruwa da lemu haɗe da glass cup. A.Maleek ya yi saurin tashi ya amsa tray ɗin daga hannunta
yana mata sannu, Iyah ta saki murmushi cike da farin cikin ganin yadda TAIMIYYARta ta sake
zama wata saraunuyar kyau ta ce, "Sannun ku dai ina fata kun samu su Hajjar lafiya?"
A.Maleek ya murmusa ya ce, "Lafiya lau ta ke duk da dai ba mu isa can ba sai gobe, nan muka
fara zuwa da ya ke shigowar yamma muka yi kuma gobe za mu juya don jibi da safe zamu wuce
Lagos da ita Suhailah."
Daga haka A.Maleek ya ɗanci dambun naman kaɗan,ya miƙe yana cewa TAIMIYYAH zai jira ta
daga mota.
Bayan fitarsa ne Iyah ta dubeta ta ce, "Zaynabu kin ga yadda ki ka dawo wata balarabiya kuwa,
gaskia garin ya amsheki matuƙa, don Allah ki dinga kulawa banda cikawa kanki aiki me wahala ki
kafe ki ce sai da kanki za ki yi, kin ga yanxu bakya kaɗai ba ce. Ya abokiyar zamar ta ki ina fara
dai babu wani matsala har ku ka je kuka dawo ko?"
TAIMIYYAH ta jinjina kai ta ce, "Lafiya lau Iyah, babu wata matsala don na san yadda na ke
zama da kowa idan na karanci halinsa, bana shiga sabgarta bata shiga nawa sai an haɗu wajen cin
abinci ko zamu fita tare ma mu ke ganin juna."
Iyah ta jinjina kai ta ce, "To adai kula Zaynabu banda raini ko rashin ɗa'a duk ba halinki bane,
babu ruwanki da matarsa tsakaninki da ita girmamawa da mutuntawa don ko babu aure tsakaninta
da shi jininsa ce ita,ki riƙe kanki kar kuma ki yadda a shiga hakkinta da goyan bayanki kin ji ko?
Ki tsare gaskiya akan duk abinda ki ka san zai shiga hakkinta ki kiyaye hakan."
TAIMIYYAH ta jinjina kai cike da gamsuwa ta ce, "Na gode Iyah In Sha Allah zan kiyaye, Allah
ya bamu zaman lafiya."
Daga haka TAIMIYYAH ta janyo jakar tsabar Iyah ta buɗe ta fitar mata da nata, ta fitar da na
Babah Ladi wacce ke can ɗaki sai da Iyah ta ciri murya ta kirata sannan ta iso ɗakin Iyah, cike da
murnar ganin TAIMIYYAH ta ƙarisao cikin falon, TAIMITYAH ta gaida suka taɓa barkwanci
kafin Iyah ta bata tsarabarta ta dinga zuba godia.
Bayan fitar Babah Ladi ne TAIMIYYAH ta nunawa Iyah tsarabar da za ta ba su Umma, Iyah ta
jinjina kai cike da nuna yaba kyawun hali da zurfin tunani irin na TAIMIYYAH ta ce, "Madallah!
Zaynabu na, haka nake son ganin cewa baki riƙe su a zuciyarki ba bare har ki kasa tunawa da su
da musu alkhairy idan har kin ga ya dace, na ji daɗi da ki kai tuna da su tare da yi musu tsaraban,
Allah ya bada lada ya ƙara ɗaukaka, ki cigaba da tunawa da su tare da yi musu alkhairy ba tare da
kin tuna rashib kirkin da suka shuka miki a baya ba. Baki da kamarsu Zaynabu duk iya yadda suka
tsaneki ba za su sauya alaƙan jini da ke tsakaninku ba, don haka ki yi zumunci da su iyakan
iyawarki ko da ba za su baki fuska ba, ki taimakesu idan suna da buƙatan hakan koda ba xa su
amsa ba kin fisu har wajen Ubangiji. Ko ƙasa ya rufe idanuna bana son ki wofintar da su a kowani
matakin rayuwa za ki taka Zaynabu Allah!"
Iyah ta kai ƙarshen maganar idanunta akan TAIMIYYAH, wacce ta nutsu tana sauraren Iyah da
kunnin baseera, ta jinjina kai ta ce, "In Sha Allah, ni wallahi ban taɓa riƙe su a zuciyata ba , ko da
na ja baya da su na yi hakan ne don kare martaba, amma na san bani kamarsu tunda su zan nuna a
matsayin ƴan uwana na jini."
Iyah ta jinjina kai ta ce, "Hakane Zaynabu, Allah ya yi wa rayuwa albarka, sai ki tashi ku ƙarisa
sasan nasu Sani ma nanan ya zo ai, Ummienki na can bata jin daɗi in ji Sanin."
TAIMIYYAH ta waro ida ta ce, "Ayyah! Amma mun yi waya fa bata ce min bata jin daɗi ba Iyah."
TAIMIYYAH ta miƙe tana maida lulluɓin gyalenta ta dubi Iyah ta ce, "Bari mu je Iyah amma
wannan dambun naman zan tafi da shi ya yi daɗi, zan ma bar kuɗi ayi a turo min please!"
Iyah murmusa tana jin wani ƙaunar TAIMIYYAH na sake lulluɓe zuciyarta, ta dubi TAIMIYYAH
lokacin da ta ke kai hannu ta bag ɗin tsarabarsu Umma ta ce, "Bama sai kin bar komi ba kaman
wancan karon juye muku wanda na ke da shi kawai zan yi, a sake min wani tunda muna gari ɗaya
da me yi ni."
TAIMIYYAH ta yi godia tana fita daga falon Iyah ta fito zuwa compound, A.Maleek da ya hango
fitowarta sai ya fito daga mota yana jiran ƙarisowarta.
TAIMIYYAH ta yi maganar idanunta a kansa, ya jefa mata harara yana ɗan taɓe baki ya ce, "Ai
Baby yau zane ki me kawai ba zan yi ba, oya mu je mu gaida Baba mu wuce gida na gaji matuƙa
hutu na ke so."
TAIMIYYAH ta saki murmushi tana bashi haƙuryn zaman jiranta da ya sha, suka jera zuwa part
ɗin Baba Sani ta na waje suka shiga, TAIMIYYAH ta doka sallama Baba Sani ya amsa yana
zubawa ƙofar shigowa falon idanu.
TAIMIYYAH suka sanya kansu ciki bayan ya basu izinin shiga, idanunta ya sauka akan Baba Sani
da ya yi wani irin fresh har ƴar ƙiba ta ga ya yi mata,ta isa gabansa tare da durƙusawa ta kwashi
gaisuwa. Baba Sani da farin cikin ganin TAIMIYYAH ya lulluɓe shi ya amsa gaisuwar da fara'a,
yana musu barka da dawowa lafiya. TAIMIYYAH ta amsa tana cewa, "Baba Ya Ummie na, ai idan
za mu wuce gobe zamu tsaya a Kanon."
Baba Sani ya saki smile yana jin wani kewa da shauƙi akan Ummie na danne zuciyarsa, ya buɗe
baki ya ce, "Yakamata kam Zaynabu ku tsaya, har wajen Bilkisu ki kaisa a gaisa shi ne zumuncin."
"In Sha Allah Baba." Cewar TAIMIYYAH tana murmushi, A.Maleek ya matsa ya kwashi gaisuwa
cike da nuna girmamawa ga Baba Sani, Baba Sani ya amsa yana tambayarsa lafiyar Hajjah.
A.Maleek ya tabbatar masa da cewa lafiya lau ta ke, daga haka TAIMIYYAH ta miƙe tana duban
Baba Sani ta ce, "Baba bari mu shiga daga ciki mu gaida Umma sauri mu ke yi, ga wannan ba
yawa tsaraba."
TAIMIYYAH ta aje masa wani kwalin turare me azabar ƙamshi da ta siyesa da kuɗi me nauyi ko a
can, Baba Sani ya amsa yana sanya mata albarka su kai sallama da juna.
Ta cikin falon Baba Sanin suka ratsa don isa side ɗin Umma, TAIMIYYAH ita ce ta yi gaba zuwa
ciki, A.Maleek na tsaye daga bakin corridor da zai shigo da mutum falon Umma ta ɗakin Baba
Sani.
"Assalamu alaikum!
TAIMIYYAH ta furta lokacin da ta sanya kanta cikin falon Umma,Zuhurah da ke zaune cikin
falon hankalinta akan wayarta ta yi saurin ɗago idanunta jin muryar TAIMIYYAH, ta akanta
lokacin da ta cigaba da ratsowa cikin falon.
Wani irin kibiya ya cake ta a ƙahon zuci lokacin da idanun nata suka cigaba da yiwa TAIMIYYAH
rakiya har wajen seaten da ta nufa, ta cigaba da kallonta tamkar ranar ta saninta wani irin yanayi
ke tasowa daga ƙasan zuciyarta yana bayyana a kan fuskarta.
"Zuhurah sannu da gida dafatan kuna lafiya? Ashe haka abu ya kasance to Allah yasa hakan shi ne
mafi alkhairy."
TAIMIYYAH ta yi maganar lokacin da mazaunanta suka daidaita a cikin seater ɗin, kafin Zuhurah
ta ce komi Umma ta fito daga cikin ɗakinta da alamu wanka ta yo, don kuwa gashi nan ta sha uban
ado sai ƙamshi ke tashi a jikinta.
Idanunta ya sauka akan TAIMIYYAH da ke zaune cikin seater, lokacin da Zuhurah ta yi ƙarfin
halin cewa, "Ameen na gode!"
Umma ta ƙariso ta zauna akan kujera tana ƙoƙarin saita kanta da zuciyarta da ke faman bugu,
TAIMIYYAH ta zamo kaɗan tana gaida Umma ta ce, "Umma ina yini mun sameku lafiya, ya ƙarin
jiki kuma? Allah ya ƙara lafiya yasa kaffara ne."
Umma ta tsurawa TAIMIYAH ido tana jin wani abu na matse zuciyarta, da ƙyar ta fisgo kalmomi
daga bakinta ta furta, "Lafia lau, jiki Alhamduillah! Yaushe ku ka dawo kenan?"
TAIMIYYAH ta koma ta zauna sosai kafin ta ba Umma amsa da faɗin, "Yau kwanan mu biyar
kenan Umma."
Umma ta kasa cewa komi illah cigaba da ƙarewa TAIMIYYAH kallo ita da shigar jikinta, gashi
gaba ɗaya falon ya kaure da wani ƙamshin turaren TAIMIYYAH da ya kama komi nata, jin shiru
babu wanda ya sake tanka ta tsakanin Zuhurah da Umma yasa ta miƙewa ta dubi Umma ta ce,
"Umma in ce ya ƙariso ciki zai gaida ki."
Umma ta dubeta ta ce, "Shi wa fa?"
Daga haka ta nufi wajen corridor ɗin ta kora A.Maleek suka dawo cikin falon, yana riƙe da jakar
tsabar da TAIMIYYAH za ta bai wa su Umma, daga Zuhurah har Umma wani abu ne ya daki
zukatansu, ganin yadda ya ke biye da TAIMIYYAH riƙe mata da bag a hannu.
A.Maleek ya kwashi gaisuwa wajen Umma, Zuhurah ta gaida shi tana faman ƙarewa haɗuwarsa
kallo, ya amsa da kulawa yana sanya hannu a aljihu ya irgo kuɗin da bai san adadinsu ba ya ajewa
Umma yana cewa, "Umma ga shi a siya lemu, Allah ya ƙaro afuwa."
Umma ta haɗiye wani abu me nauyi da ke neman danne ƙirjinta, ta miƙa hannu ta janye kuɗin tana
cewa, "An gode madallah! Ai jiki ya warware gaba ɗaya Alhamdulillah!"
Ganin A.Maleek ya tashi don barin falon ya sanya TAIMIYYAH dubansa ta ce, "Hubby wannan
ita ce Sis ɗina Zuhurah ba ka gane ta ba ko?"
A.Maleek ya dakata daga tafiya yana juyowa ya zube idanunsa akan Zuhurah da ta ƙura masa ido
ya ce, "Ayyah! Sorry Sis ai ban gane ba, da ya ke har akai biki ba mu haɗu ba ya ki ke?"
Zuhurah ta ji tamkar ta sanya ihu yadda salon muryar A.Maleek ɗin ke dukan zuciyarta, ta yi
ƙarfin saita kanta ta ce, "Lafiya ƙalau wallahi!"
A.Maleek sai ya sake zura hannu a aljihu ya irgo kuɗi ya miƙawa TAIMIYYAH ya ce, "My pure
zuwa bata wannan."
TAIMIYYAH da jin kunyar sunan da ya kirata da shi agabansu ya sanyata sadda kai ƙasa ta amsa
kuɗin tana cewa, "Thank u!"
Daga haka ya yi gaba abinsa yana jiyo Zuhurah na biyo bayansa da godia, TAIMIYYAH ta
miƙawa Zuhurah kuɗin ta amshe, ita kuma sai ta ɗauki bag ɗin da Maleek ya aje ta ciro ƙullin
tsabar Umma ta aje a kusa da ita tana cewa, "Umma ga tsaraba ba yawa."
Umma ta sake haɗiye wani abu me ɗaci ta ce, "Madallah an gode, har da mu kuma a tsaraba lallai
kam!"
TAIMIYYAH ta miƙawa Zuhurah bag ɗin tana faɗin, "Sis ga naku ke biyu Basmah biyu, sai ki
zaɓa desighn ɗin da ya yi miki a aje mata nata, na so ace zan samu zuwa gidanta amma gobe za
mu juya, sai na zo bikin Yah Deeku kenan zan sama time In Sha Allah."
Zuhurah ta amsa bag ɗin tana cewa, "Allah sarki mun gode TAIMIYYAH, Allah kai mu bikin
lafiya ai ba damuwa."
Daga haka TAIMIYYAH ta yi sallama da su ta fito, suka yo mata rakiya da idanunsu tamkar za su
cinyeta ɗanya.
Sai da TAIMIYYAH ta koma part ɗin Iyah sannan ta fito riƙe da robar dambun ta, ta nufi motar
Maleek da ke tsaye ya buɗe mata seat yana jiran ƙarisowarta, ya amsa robar ya sanya a back seat
bayan ta shiga ya rufe mata murfin motar.
*
"Umma ke kin ga yadda TAIMIYYAH ta koma kuwa, dama haka Mijin mata ya haɗu? Tabbas ba
mu kasance masu sa a ba kambala'i! Aini duk kuɗinsa sunan da ya yi ban ɗauka ajinsa da
haɗuwarsa ya kai har haka ba shiyasa har aure a gurguwarta."
Zuhurah ta yi maganar wutar hassad na sake cinye zuciyarta, Umma ta haɗiye wani abu me nauyi
ta ce, "Hmmm! Zuhurah kenan ke ta haɗuwar mijin ki ke yi bata yadda ya fara zama boyi-boyinta
ba, baki ga shike riƙo mata jaka tabbacin sun gama samun kansa, bansan wasu irin Malamai Iyah
ke bi akan wannan gurguwarba wallahi. Don abin ya yi yawa kamarta musaka ace ta taka irin
wannan matsayin alhali ku ba taka ba, tabbas rayuwata daga farkonta ne kawai na samu sa a,
amma gashi yanzu da aka zo tsakiya za a tafi gangara gaba ɗaya abubuwa sun juye, dukkanin
lissafina babu wand na yi nasaran lissafashi daidai Zuhurah!"
Umma ta kai ƙarshan maganar da wani irin tone me taɓa zuciya,wasu hawaye masu ɗumi suka
zubo mata, ta kai hannu ta share tana buɗe ledar tsabarta lokacin da Zuhurah ke cewa, "Wallahi
Umma wannan karon ba zan taɓa yin saken da ba zan shiga irin arziƙi ba ni ma, sai na dar je
wallahi inaaa! Ai ba zan sake wannan saken ba, dole mu ma ace ga wata a cikin ta taka gidan
girma ta fantama."
Umma ta jinjina kai lokacin da idanunta ke sauka akan dalleliyar doguwar rigar da ke cikin ledar,
ta zaro ta tana jin ƙaunar rigar na ɗarsuwa a ranta don ta san baƙaramin kyau za ta yi a ciki ba,
ƙamshin da TAIMIYYAH da A.Maleek suka bar musu a cikin falon irin dai ta ke ji daga jikin
rigar, wanda hakan ke alamta musu cewa ƙamshin ya kama komi nasu ne.
Zuhurah ta ciro nasu tana dubawa ita ma suna sake sakin zance da jin hassada da kishi me tsanani
na danne zukatansu, Zuhurah ta kira Basmah ta labarta mata zuwan TAIMIYYAH, tare da zuzuta
mata yadda ta koma wata irin classy woman, daga ƙarshen ta yi snaping haɗaɗɗun Abayar da ta
kawo musu tsara ta turawa Basmah. (Ni dai na ce an ji kunya, na ɗauka sabida hassada ba za ma
ku karɓa tsarabarba).
Washegary TAIMIYYAH gidan Hajjah suka isa tunda safe, sai da suka tsaya suka ɗauki Suhailah
a gidanta sannan suka wuce. Hajjah ta tarbesu cike zallar farin ciki, ta dinga ji ina za ta sanya
kanta da farin cikin ganin yadda TAIMIYYAH ta yi wani irin kyau da cika, da zaran kuma ta tuna
jikarta ko jikan na ɗauke a mahaifar TAIMIYYAR sai ta farin cikin ya ninku.
A gidan su ka yi breakfast gaba ɗayansu bisa babban dining, bayan sun kammala ne Suhailah suka
keɓe da Hajjah a ɗaki, suna tattauna maganar business ɗin da Suhailah za ta fara, don ta cewa
Hajjah tana bada jimawa ta buɗe shago ne a garin Lagos, wanda za a dinga shigo mata da Abayoyi
ƴan gaske zuwa su Veils da takalma. Hajjah ta bata goyan baya domin dukiyar gadon Suhailah na
uwa da uba duk a hannun Hajjah suke a na ɗan juya mata su, kuma sun hauhawa babu laifi, daga
ƙarsha Hajjah ta ce ta bar komi a hannunta za ta yi magana da A.Maleek ɗin.
Hajjah ta jima tana ma Suhailah nasiha akan ta kwantar da hankalinta game da jinkirin rashin
haihuwa, kada ta ce za ta sanya damuwa a ranta don Allah ya ba abokiyar zamanta rabo, In Sha
Allah ita ma nata na tafe. Suhailah ta rungume Hajjah tana kuka tare da sanar da ita cewa ta jima
da sanyawa zuciyarta dangana, Hajjah dai ta dinga rarrashinta da kalamai na kwantar da hankali,
shi ma kuma A.Maleek Hajjah ta yi mai magana akan ya kula wajen kwatanta adalci, sannan ya
zama me rarrashi da ƙarfafa zuciyar Suhailah, hakan zai sa hankalinta ya kwanta ta gane cewa ko
bata haihu ba ba zai kasance me wofintar da ita da rashin nuna damuwa kanta ba.
Ƙarfe ɗaya suka bar Zaria bayan Hajjah ta cika su da tsaraban kayayyin amfani da za su nema, ita
TAIMIYYAH har da su kayan ciye-ciye irin wanda ba a rasa me ciiki da cin su duk an tanadar
mata.
Da yake flight ɗin 6pm za su bi zuwa Abuja, hakan a gurguje suka tsaya a gidan Ummie suka
gaisa, tare da bata tsarabarta ko mintuna sha biyar ba su yi a gidan ba suka tafi, bayan A.Maleek
shi ma ya yi mata alkhairy ya bata kuɗi masu kauri.
A gidan guggo Bilkine kaɗai suka ɗan zauna har Suhailah ta ci dambun shinkafa da ya ɗauki
hankalinta,tare da yi mata mugun daɗi shi A.Maleek ruwa kawai ya sha ya jira su a mota tare da
Yusuf driver, bayan ya aje wa Guggo Bilki kuɗi ita ma.
Yasmeen ta sanya TAIMIYYAH a ɗaki tana faman yi mata sharhi akan irin kyawun da ta ƙaro, sai
da Guggo Bilkisu ta jira TAIMIYYAH don za su wuce sannan suka fito, TAIMIYYAH ta cewa
Guggo ita dai a zuba mata dambun ta tafi da shi, Yasmeen ta yi mata packing ɗinsa ta yo musu
rakiyar har wajen mota, Maleek ya yi mata kyautar kuɗi yana cewa yaushe za ta je can Abuja ta
taya Babynsa zama ? Yasmeen ta dinga dariya tare da sanar da shi cewa soon In Sha Allah!
Daga haka sukai sallama suna ɗagawa juna hannu, Suhailah kanta ta yaba da yadda dangin
TAIMIYYAH suka amshe ta hannu bibbiyu cikin mutunci da girmamawa, zuciyarta sai ya sake
kwanciya da nasihun Hajjah ta amince cewa tabbas TAIMIYYAR ƴar gidan mutunci ce da suka
san darajan mutane.
Direct Airport suka wuce ko mintuna sha biyar ba suyi ba suka tashi zuwa Abuja, Yusuf driver
kuma ya juya don komawa Zaria kuma zuwa jibi zai ɗakko motar TAIMIYYAH, ya wuce mata da
shi Abuja don za ta fata koyan driving tare da Obi.
___________
*Abuja.*
A gajiye ta TAIMIYYAH ta shige zuwa ɗakinta da ƙyar ta yo wanka ta fito, ta zura riga mara
nauyi ta time ɗin magrib ya yi ta gabatar da Sallah.
Sai 8:30pm suka fito zuwa dining don yin lunch kamar yadda suka saba haɗuwa, bayan sun
kammala cin abincin ne TAIMIYYAH ta miƙe don komawa ɗaki, sabida wani bacci ta ke ji yana
fisgar idanunta. Suhailah ta ɗaga idanunta ta sauke akan TAIMIYYAH tana kiran sunanta,
"Zaynabb!"
TAIMIYYAH ta waiwayo ta sauke idanunta da ke cike da jin bacci ta amsa da cewa, "Na'am!"
Suhailah ta sake dubanta ta ce, "To ni gobe zan wuce watakila kafin zama ya sake haɗamu waje
ɗaya kamar haka zai yi wahala, ina fata a zaman da muka yi da juna ban yi wani da ya ɓata miki
ba, in ma na yi ina roƙon afuwa saboda halin rai da zaman tare da dama dole ka saɓawa mutum ko
cikin rashin sani ne, sai ya fi juna don Allah."
TAIMIYYAH da ta ji xuciyarta ya karye sai ta langaɓe kanta tana cewa, "Babu komi Anty baki
min komi ba in ma an saɓa cikin ajizanci irin na ɗan adam, wallahi na yafe Allah ya yafe mana
baki ɗaya ya dauwamar da zaman lafiya a tsakanin mu."
Suka haɗa baki har A.Maleek da ke sauraransu wajen amsa da "Ameen." Daga haka TAIMIYYAH
ta yi musu sai da safe ta wuce zuwa ɗaki, tana ji zuciyarta sam babu daɗi ta dinga kisima yadda za
ta yi zaman kwanaki biyar babu A.Maleek ɗin a cikin gidan, ƙarshema bashi garin ne baki ɗaya sai
kawai ta ji hawaye sun fara zubo mata.
A haka ta isa ɗaki ta kwanta lamo bisa bed hawaye na bin idanunta,bata ji shigowarsa har sai ya
ƙariso bakin bed ɗin sannan ƙamshinsa ya bata tabbacin zanzuwarsa a cikin ɗakin.
Ta yi saurin kai hannu za ta sharen hawayen don kar ya gani, amma ta makaro don ya riga ya gani
hakan yasa shi saurin zama yana janyota zuwa jikinsa ya rungumeta tsam, dukkaninsu zuciyoyinsu
na bugawa da tsananin damuwar kewar juna da za su yi, TAIMIYYAH wasu hawaye suka sake
ɓalle mata ta yi magana cikin rawar murya ta ce, "Hubby yanzu idan ku ka tafi sai Friday za ka
zo?"
A.Maleek ya sake shigar da ita cikin jikinsa kafin ya yi magana cikin low voice ya ce, "My pure
zuma ya yi nisa ko?"
TAIMIYYAH ta gyaɗa masa kai alamun tabbatar da cewa ya yi mata nisa kwanakin babu shi a
tare da ita, sai ya ɗago face ɗinsa yana kai harshensa ya fara ɗauke hawayen da ke zubowa daga
idanunta, cikin wani irin sanyin murya ya ce, "Za ki bini mu tafi tare ki haƙura da karatun kawai
Baby babu abinda za ki nema ki rasa daga gare ni na yi miki wannan promise ɗin."
TAIMIYYAH sai ta tsaida kukan cak! Ta shiga girgiza kai tana cewa, "No Hubby kar ka ce haka
please! Ina son cika buri na na yi karatu me zurfi koda iya deegree ne, ina so in zama cikakkiyar
lawyer don in cika burin mahaifiyata da bata samu cikawa ba rayuwarta ta ƙare, don Allah ka cika
alƙawari wajen ganin na cika burina akan hakan."
Ta kai ƙarshen maganar zuciyarta na motsawa da alhinin rashin uwa da bata san daɗinta ba, bata ji
ɗumin jikinta ba bata kuma rayu da ita. Wasu hawaye masu tsananin zafi suka sake ɓalle mata,
hakan ya sanya A.Maleek sake matseta a jikinsa ya fara aikin rarrashi yana cewa, "Sorry wife it's
okey please! Kukan ya isa haka Allah ya gafarta musu yasa suna Jannatul Firdaus, in dai karatu za
ki yi In Sha Allah met month za a za ki zana jamb kin ji ?"
TAIMIYYAH ta gyaɗa kai tana faɗin , "Thank u sweet Amore, i luv u"
A.Maleek ya kai bakinsa ya sumbaceta yana mayar mata da martani a aikace bada baki ba, da ƙyar
ya iya barin ɗakinta lokacin da bacci ya sace ta tana cikin jikinsa,ya sumbace yana baro ɗakin ya
nufi upstairs zuciyarsa na kisima yadda zai yi kewar kafin ya juyo garin nan da 5 days.
Washegary flight ɗin 9am ya wuce da su zuwa Lagos bayan sun sake sallama da juna tsakanin
TAIMIYYAH da Suhailah, TAIMIYYAH sai da ta zubda hawaye lokacin da suke sallama da juna.
Da Ameena Mai aiki Suhailah ta wuce aka barwa TAIMIYYAH Rabecca kafin zuwa jibi Yusuf ya
iso tare da su Harirah,yini bacci TAIMIYYAH ta yi ranar bayan ta ɗaɗɗaga wayoyin A.Maleek vid
call babu adadi.
Washegaryn randa suka wuce Lagos Yusuf ya iso da motarta tara da su Harirah, kwanansa ɗaya ya
juya Zaria bayan TAIMIYYAH ta yi masa alkhairy me yawa.
Sai gidan ya sake rage mata kaɗaici sabida ta san tana tare da mutane ƴan aikinta, musamman
Rabecca da ta kasance babba kuma me hankali.
TAIMIYYAH bata aikin komi da wuce gyaran ɗakinta, sai idan tana jin kwaɗayi ta sakko zuwa
downstairs ta yi girka ta koma sama, bata faye yin girki a kitchen ɗin upstairs ba tafi gane ta sakko
ƙasa.
Rabeeca ke girkin gidan baki ɗaya a zubawa har Mai gadi, ma wanki da kuka har da drivers biyu
da aka aje Obi da Samuel, duk ba musulmai bane.
Kullum cikin yin vid call su ke da A.Maleek ɗin wanda a ranar da suka isa Lagos ma ya shiga
office, sam ya yi busy ba shi da time amma hakan baya hanashi samun lokacin kiranta vid call
koda ko ba za su jima suna magana ba, sai hakan ya ragewa TAIMIYYAH kewar da ta ke tunanin
za ta ji me zafi idan basu kusa.
Ranar Friday ɗin farko da ya fara zuwa mata weekend ba ƙaramin mamaki ya sha na irin tarban da
ya samu daga gare ta, har a bed ya sha mamakin yadda ta aje kunya ta shayar da shi ruwan luv irin
wanda taɓa tunani ba, nan da nan ya sake narkewa a nuna mata tsantsar ƙauna da soyayya me
wuyar bari.
Ranar Monday da safe ya bi flight ya juya Lagos ya bar TAIMIYYAH da unborn ɗinsa da
kewarsa me tsanani, ranar kuma da rana suka fara fita da Obi da ke zai koya mata driving,
TAIMIYYAH ta ji daɗin hakan kuwa don zaman gidan na damunta.
___________
*3 month Later.*
*Zaria.*
*Gonar Ganye.*
Basmah kwance tana rasgar kuka tamkar zata haɗi ranta, daga gefenta Nass ne zaune yana shan
ruwan coffee ɗinsa hankali kwance.
Ya dire cup ɗin bayan ya shanye yana maida dubansa kan Basmah da duk ta fita hayyacinta, tun
daga daren jiya da ya sanar mata cewa Sharifa Aminiyarta, ita ce Amaryar da za a ɗaura masa aure
da nan da sati me zuwa.
Basmah ta ɗago dubesa cikin rishin kuka ta ce, "Nass don darajar Allah da manzons kar ka auro
min Sharifah ta zama kishiyasa alhali duk wani sirri nawa ta gama saninsa, na gwammace ka auro
mata uku na yadda zan zauna da su amma banda Sharifah, wallahi mutuwa zan yi Naseer....!"
Basmah ta kasa ƙarisa magiyarta sabida yadda wani kuka me ƙarfi y sake ƙwace mata, wani irin
firgici da tsoro tare da tsanar Sharifah ne ke sake rugurguza zuciyarta. Ta kai hannu ta dafe saitin
zuciyarta da ke barazanar rabewa gida biyu tana faɗin, "Wayyo! Zuciyata Nass, Zuciyata za ta
buga wayyo cikina, marata Nass wash.....!"
Basmah ta yi maganar cikin fitar hayyaci tana jin yadda maranta ya ƙulle, ta saki wani razanan ihu
lokacin da ɗumin jini ya ratsa ƙasanta. Ta mirgina gefe guda tana kai hannu ta dafe mararta, kafin
ta yi magana Nass da idanunsa ya kai bed ɗin ya saki wani ƙara yana nufota, bai jira komi ba y
sanya mata Hijab ya ɗauke ta zuwa mota suka wuce hospital.
Basmah ta sha matuƙar wahala kafin a yi nasarar tsaida bleeding ɗin da take yi,da ƙyar cikin ya
tsaya bata yi ɓarinsa ba ga jininta da ya yi mummunar hawa.Likitar ya dingawa Nass faɗa akan
yadda zai bari matarsa ta kamu da matsananciyar damuwan da zai janyo jininta ya hau irin haka,
bayan ya san illar hawan jini a wajen mace me ciki.Shi dai Nass haƙury kawai ya ke ba likitar,
amma cikin xuciyarsa ya je faɗim, 'Ba hawan jini Basmah za ta kamu da shi ba ko ciwan zuciyace
sai ya cika burinsa na mallakar Sharifah a matsayin matarsa, ba zai taɓa bari ta suɓuce masa yadda
TAIMIYYAH ta suɓuce masa ba, domin ba ƙaramin kamu Sharifah ta yiwa zuciyarsa ba, kamar
yadda ya ke da tabbacin shi ma ya yi wa zuciyarta kamu me tsanani."
Lokacin da ya baro office ɗin likitar ya koma ɗakin da Basmah ke kwance ta samu bacci,
hannunta ɗaure da drip sai taka zuwa bakin bed yana kai hannu ya shafa fuskarta da ta zurma cikin
kwana ɗaya kacal ya ce, "Sorry Basmah, zuciyata Sharifah ta gani tana so ita ce wacce na ke za ta
iya maye min gurbin ƴar uwarki dana rasa, don haka sai dai ki yi haƙury aure tsakanina da
Sharifah babu fashi, za ki cigaba da zama a asibiti har a ɗaura auren sai ki yi jinyar zuciyarki da
kyau. Allah ya tsare min unborn ɗina ya zo duniya cikin ƙoshin lafiya."
Ya kai ƙarshen maganar yana zare hannunsa daga kan fuskarta ya mayar kan cikinta, ya shafo fatar
cikin yana ganin yadda Basmah ta motsa tare da yatsine fuska alamun baccin ma ba mai daɗi ta ke
yi ba.
Ya zare hannunsa yana koma kan kujeran da ke ɗakin ya zauna,ya me ɗaga waya ya kira layin
Hajiya Hajara ya sanar da ita cewa suna asibiti, daga haka ya yi cutinb call ɗin ya kira layin
Umman Basmah kamar yadda ya yi saving. Bugu biyu Umma ta ɗauka hankalinta a tashe don
daren jiya da Basmah ta kirasu tana kuka ta sanar musu Nass zai auri Sharifah, shikenan ta shiga
tashin hankali da taraddadin jin mummunar labari don ta ayyana a ranta da wuya baƙin ciki bai
sanya Basmah yin ɓarin cikinta ɗan watanni uku da kwanaki ba.
"Umma muna asibiti da Basmah ne, jini ne ya ɓalle mata amma an yi nasarar tsaida shi cikin bai
fita ba, na kira ne ko Zuhurah za ta zo ta kwana da ita please!"
Nass ya sanar da Umma hakan bayan ya gaidata ta tambayesa Basmah, Umma ta haɗiye wani abu
me ɗaci kafin ta ce, "Okey wani asibiti ku ka je kenan?"
"AL-MADINAH."
Cewar Nass a dake daga haka kuma ya yi cuting call ɗin ya kira gimbiyarsa Sharifah, ya sanar
mata cewa Basmah na gadon asibiti, ta sakin masa kukan kissa tana nuna tsantsar tausayin
Basmah da ke cin zuciyarsa, ya lalace wajen rarrashinta da sanar da ita cewa ta samu sauƙi fa ɓari
ta so yi amma Allah ya kare cikin bai fita ba.
Sai da ya jira isowar Zuhurah ita da ke fama da kanta, don tun bayan gama kacaniyar bikin Yah
Deeku take fama da kanta, yau ciwo gobe lafiya ita kuma nata cikin da haka ya zo mata.
Bayan tafiyar Nass ɗin ne Zuhurah ta zubawa Basmah ido tausayinsu su duka na dukan
zuciyarta,idanunta suka hasko mata yadda TAIMIYYAH ta sake komawa wata haɗaɗɗiyar mace
da irin ƙatuwar motar da ta zo bikin Nass a cikinta, kaf danginsu babu wanda bai tanka irin daular
da ta samu ba sai cewa ake yi Gurguwar Iyah ta sama duniya.
Hawaye masu zafi suka zubo daga idanun Zuhurah lokacin da tuna zancen su da Yasmeen akan
irin tarairayar da Yasmeen ta basu labari A.Maleek na yiwa TAIMIYYAH, domin ita Yasmeen ɗin
ta je Abujan ta yi sati biyu tare ma da TAIMIYYAH ya biya musu kuɗin ticket suka zo Kano, daga
nan ne Yusuf ya zo da mota ya wuto da su Zaria su kai bikin.
Ta lumshe idanunta lokacin da wani vedio ɗin da Yasmeen ta yiwa TAIMIYYAH tare da A.Maleek
ɗin, lokacin da ya ke bata ice cream a baki ita kuma tana zubo da shi daga bakinta, shi yana sa
bakinsa yana lashe wanda ta zubo da shi ɗin.
Kuka me ƙarfi ya ƙwacewa Zuhurah wanda a wancen lokacin bata samu damar yinsa agaban
Yasmeen da Anty Laurat ba, sai yanzu ne data tariyo abin daga kwanyarta ta samu chance ɗin da
zata koka.
Kukanta ne ya tashi Basmah ta buɗe idanunta a hankali tana ƙarewa ɗakin da ta ke ciki
kallo,lokacin da ta fahimci tana kan gadon asibiti ne ta ji hawaye na ɓalle mata.
Zuhurah ta yi saurin tsaida nata kukan tana nufan Basmah ta ce, "Sannu Basmah kin ta shi?"
Basmah ba bakin magana sai kuka ganin hakan yasa Zuhurah fita ta kira lkitan da ya ke on duty,
suka dawo tare ya duba jikin Basmah tare da sake gwada BP ɗinta, ya dinga rarrashinta da kalamai
masu daɗi akan ta kwantar da hankalinta a samu jininta ya sauka, in ba haka ba za ta sanya kanta
cikin haɗari da ƙarancin shekarunta.
Ita dai Basmah jinsa kawai take yi amma bata ga yadda hankalinta zai kwanta ba, alhali ga
Aminiyarta can za ta ci amanarta ta aure mata miji nan da sati zuwa ba. Tuno hakan da ta yi ya
sanya ta fashewa da kuka, ƙarshe dai sai alluran bacci akai mata don ta samu hutun zuciya da
ƙwaƙwalwa, Zuhurah ta ɗaga waya ta kira Umma, tana kuka ta sanar da ita halin da Basmah ta ke
ciki.
Ummah yadda ta ga rana haka ta ga dare sam bata rintsa ba, gashi Baba Sani bai samu shigowa
weekend ba yana can ya tare wajen Ummie, wacce ke gadon asibiti bata da lafiya ciki ya zo mata
da laulayi me zafi, shi ne duk ya bi ya susuce akanta tamkar wanda ba a taɓa haifa masa ƴaƴa ba
sai akanta zai samu, kamar yadda Umma ta dinga bambami tana faɗi.
Ta fashe da kuka me tsanani tana ji kanta na fara sarawa alamun ita hawan jinin nata na daf da
tashi, sai daf da asuba ta samu rintsawa bayan ta yi sallah da ƙyar.
Ƙarfe tara ta gama shiri ta aka haɗa komi na buƙata na karin safe, ta kira Sani driver ɗin Iyah don
shi zai kai ta kamar yadda Baba Sani ya ce, sai da ta kai zuciyarta nesa ta iya shi ga ta sanar da
Iyah halin da ake ciki, Iyah ta zari mayafi kuwa ta ce bata ga ta zama gara su je tare ta duba jikin
Basman.
Sun isa asibitin daidai lokacin da shi ma Nass ya iso tare da Hajiya Hajarah, duk kusan a tare suka
shiga ɗakin da aka kwantar da Basmah ɗin.
Kallon-kallo aka shiga yi tsakanin Hajiya Zuwairah suna jin wani tsanar junansu a zukatansu na
sake ninkuwa, da ƙyar suka gayar da juna lokacin da Nass ya sanar da Hajiya Hajara cewa Umma
ita ce mahaifiyar Basmah, ya nuna mata Iyah a matsayin Kakarsu Basmah ɗin.
Ita dai Iyah ba yabo ba fallasa suka gaisa da Hajiya Hajara, wacce kallo ɗaya Iyah ta yi mata ta
gane cewa bata da mutunci, duk abinda aka ce za ta aikata ba za ta musa ba. Ta cigaba da kallon
yadda suke jifan juna da harara tsakanin Hajiya Hajara da Umman, Zuhurah ce suka fito daga
toilet ɗin cikin ɗakin asibitin, tana riƙe da hannun Basmah wacce ta raka don ta yi brush.
Dukkansu suka zuba musu ido har Zuhurah ta kai Basmah zuwa bakin bed ɗin ta zauna, sabida tun
da ta farka ta ke kuka da kanta ga jiri da ke damunta.
Iyah ta dubi yadda Basmah duk ta fita hayyacinta, tana mamakin me yake damunta haka don
wannan ya wuce ace laulayin ciki kaɗai ne.
Basmah ta dubi Umma tana fara zubar da hawaye,cikin rawar murya ta gaida Hajiyar Nass da Iyah
suka amsa suna mata sannu da jiki, Basmah tama kasa amsawa sai kuka da ta fashe da shi. Cikin
kukan ta dubi Umma da Hajiyar Nass ta soma cewa, "Don Allah ku roƙe ya janye batun wannan
auren da Sharifah, idan ma auren ne ya auro wasu matan ko biyu na yadda zan zauna da su amma
banda aminiyata da ta gama sanin sirrikana, don Allah Mamah ki min rai ki hana shi wannan auren
cin amanar da suke shirin yi mini."
Hajiya Hajara ta wurgawa Basmah wani banzar kallon kafin ta dubi fuskar Umma ta ce, "Har
abada ba zan haramta masa abinda Allah ya halas ta masa ba, don tana aminiyarki sai me? Ashe ke
babu daɗi ku kai asirin da ya auroki ba don yana son ki ba, ke ma ai amanar musakar ƴar uwarki ki
ka ci kin ga kenan don za a miki ramuwar gayya bai kamata ki tashi hankalinki ba, aure babu fashi
za a ɗaura shi sati me zuwa tunda ita zuciyarsa ke so na kuma yaba da tarbiyarta da nasabar gidan
su, don haka idan za ki kwantar da hankali ko dan abinda ke cikinki ki kwantar ehe!"
Umma ta saki wani uban tsaki tana duban cikin idon Hajiya Hajarah ta ce, "Allah zai mata
sakayya kuma wallahi idan kafiyar ƴata ya salwanta akan auren cin amanar da ɗanki zai ƙaro sai
na yi shari'a daku, kuma maganar asiri ai duk jirgi ɗaya ya kwaso mu tunda ke ma kina kan layi
ne. Kuma Basmah ba amanar ƴar uwarta ta ci ba tunda da ma can kin raba su kin ce ba zai auro
miki musaka ba, ashe kenan ba cin amana muka aikata mata ba."
Iyah da zuwa yanzu ta gama fahimtar in da film ɗin ya dosa sai ta saki wani murmushin takaici, ta
dubi Basmah da su Umma ta girgiza kai ta ce, "Allah sarki duniya! Wato shi dai rayuwa idan kana
son cin ribarsa to kar ka sake ace ka zalinci wani,ko ka shiga hakkin wani ka ace yau ba ka son
cigaban wani sai kanka. To tabbas idan ka aikata hakan sai ka ga samako ko min daren daɗewa,
dama ai shi cin amana tamkar ɗan aike ya ke shi ma, duk in ka aika shi to ka jirayi dawowarsa
kanka, kuma duk wanda ya ci amana wallahi sai amana ta ci sa shi ma. Zuwairah ku ji tsoron
Allah daga ke har ita Hajiyar duka,ke kuma Basmah ki yi gaggawar sanyawa zuciyarki salama ki
rungumi ƙaddararki da hannu bibbiyu, abinda ki ka shuka ne lokacin girbansa ya yi don haka bai
kamata ki ɗaga hankalinki ba,don kuwa kun ci amanar Zaynabu kun jefa zuciyarta cikin garari a
lokacin da naku zukatan ke wanke fes, kuna ganin cewa ita bakomi ba ne bata cancanci samun
kowani irin miji me nagarta ba sai ku, sabida ku ne baku nakasa ba, to yau wa gari ya waya?
Zaynabu ta yi jinyar zuciyarta bata mutu ba a lokacin da ku ka ƙunsa mata baƙin ciki, don haka ke
ma ba za ki mutu don ya auri aminiyarki ba Basmah,za ki yi jinyar zuciyarki ne kawai na ɗan wani
lokaci kafin ki warke kamar yadda Zaynabu ta yi a baya. Amma yau ga ta can cikin kwanciyar
hankali da cikakkiyar nutsuwar zuciya."
#Ɗansabo ce#
[12/15, 11:47 AM] +234 703 040 9541: Littafin TAIMIYYAH paid book ne,ga duk wanda ta
tsincesa a kowani irin group ne,kiji tsoran Allah karki karanta sai kin biya 500 naira only.
Za ku iya min magana ta wannan number ɗin 08167768704, ko kuma ku turo kuɗin ku kai tsaye ta
wannan account ɗin 0504192664 aisha ibrahim dansabo GTbank.*
Masu turo credit za ku turo katin MTN na 500 ta wannan line ɗin 08167768704.
_Ina ƴan kasuwa masu buƙatar a tallata muku hajar ku? Maza ku garzayo da kuɗi ƙalilan a tallata
muku kayan siyarwanku sai dai kawai ku ji ana kiran waya don buƙatan sayan kayan ku,ku
tuntuɓeni ta layina kamar haka 08167768704._
*90*
Umma da Hajiya Hajara da suka saki baki suna sauraran Iyah, sai Umma ta ja dogon tsaki ba tare
da ta iya cewa komi ba, don tasan duk maganar da Iyah ta faɗi gaskiya ne, ita ko Hajiya Hajara
tsanar su Umman ce ya sake danne zuciyarta. Nass kuwa tuni dama ya bar musu ɗakin tun fara
maganganun da suka fara tsakanin Umma da Hajiyar tasa, ya koma can mota suna shan wayarsu
da Sharifah.
Zuwan Hajiya Barirah asibitin ya sanya Iyah yi musu sallama Sani ya juya da ita gida, zuciyarta
cike da alhini da tsanar halayyar Umma da ƴaƴanta. Ta wani ɓangaren kuma godia ta dinga yi wa
Allah da ya nuna mata irin wannan lokacin da suka fara girban abinda suka shuka, sharrinsu da
mummunar nufin da sukewa TAIMIYYAH ya fara juyowa kansu a lokacin da basu taɓa tunani ba.
Koda ta isa gida Guggo Bilki ta kira ta labarta komi, suka dinga jimami tare da Allah wadai da
halayyar Umma, da har za ta biyewa uwar mijin ƴa suna wa juna gorin biye-biyen gidajen Bokaye,
wannan abu yafi komi yi wa Iyah ciwo ta dinga ji zuciyarta na ƙuna. Har suka gama waya da
Guggo Bilki Iyah zuciyarta bata yi sanyi ba, sai da ta kira TAIMIYYAH ta bata labari tare da sanar
da ita cewa Aminiyar Basmah ce Naseeru zai aure nan da sati ɗaya.
Cikin kiɗima TAIMIYYAH ta tambayi sunar ƙawar Iyah ta ce mata 'Sharifah.' TAIMIYYAH sai ta
ji wani shock ya kamata, don kuwa ta san yadda Basmah ke ji da Sharifah cikin ƙawayenta.
A can asibitin kuwa Nass ne ya yi nasarar tasa Hajiyarsa da suke ta raba hali da Hajiya Barirah, ya
maida ta gida sai faman zage-zage take yi tana cewa ya sakar musu ƴar su kawai ma kawai, Nass
ya dinga bata haƙuri tare da nunar da ita mutunci da dattako irin na mahaifin Basmah, da nagartar
Iyah da yake ganin girma da mutuncinta a idanunsa har yanzu. Don haka Basmah za ta ci
albarkacin su ne kawai ya cigaba da zama da ita, sannan ko bakomi tana matuƙar ƙaunarsa ya san
hakan,shiyasa ba zai saketa ba zai cigaba da zama da ita har zuwa lokacin da za ta buƙaci rabuwa
da shi don kanta.
Da wannan maganganun ya kashe bakin Hajiya Hajarah ta janye kalamanta na cewa sai ya saki
Basmar, yana aje ta a gida ya juya ya nufi Hanwa gidansu Sharifah.
Kwanan Basmah biyar a asibiti aka buƙaci bata sallama, amma sai Nass ya yi magana da Likitan
cewa abarta ta sake samun wasu kwanaki, zai cigaba da biyan ko nawane ana kula da ita don ya
san ko sun koma sai sun dawo, don ana cewa an ɗaura aurensa jibi ya san cewa za ta sake
birkicewa ne, tunda har yanzu jinin nata ma baya koma normal yadda ake buƙatar saukarsa bane.
Da wannan yasa aka fasa sallamar Basmah suka cigaba da zama Zuhurah na jinyarta, sai dai
kullum Umma ta zo su yini tare ta koma gida idan dare ya yi.
Ranar Friday ana gobe ɗaurin auren Nass da Sharifah Baba Sani ya zo weekend, tare kuma da
Ummie suka zo wacce ta matsa akan ita ma za ta biyo shi ta gaida Basmah.
Umma sam bata san tare za su iso ba kawai ganinsu tare su kai kamar daga sama, sabida suna
shigowa garin asibitin Baba Sani ya wuto dasu direct.
Umma ta ji wani takaici da ɓacin ya lulluɓe zuciyarta,ƙirjinta ya dinga mata wani irin zafi lokacin
da idanunta suka sauka akan Ummie,wacce ta sake cika ta yi wani irin fresh. Kyawunta ya sake
fitowa matuƙa da gaske, kuma kallo ɗaya za kai mata ka gane cewa tana da shigar ciki, sabida irin
hasken da ta yi fuskarta ya yi wani muku-muku.
Umma ta haɗiye wani abu me ɗaci tana aro jarumta ta amsa gaisuwar da Ummie ta ke mata,tare da
tambayarta me jiki Umma ta amsa da cewa, "Me jiki ta ji sauƙi."
Ummie ta amsa gaisuwar Zuhurah tana matsawa bakin gadon da Basmah ke kwance ta yi mata
sannu, Basmah ta amsa da ƙyar tana jin wani ƙarin ciwo a zuciyarta.
Baba Sani ya matsa yana ma Basmah ya jiki ta amsa da ƙyar tana sakin masa kuka, ya tambayi
abinda ke faruwa ta buɗe baki za ta sanar masa, Umma ta yi gaggawar daka mata tsawa ta ce,
"Basmah baki da hankali ashe,a gaban kishiya za ki tona mana asiri? Kina cewa tak! Sai ta so na
kwaɗeki da mari shashasha! Kawai."
Basmah ta rintse ido wasu hawaye na sake ɓalle mata, ganin hakan yasa Ummie da ta zauna akan
kujeran da Baba Sani ya aje mata, ta tashi tana dubansa da sassanyar kallo ta ce, "Baby zan jira ka
a mota please! Bani key ɗin kawai."
Daga Umma har su Zuhurah wani abu ya daki zuciyarsu jin kalmar da Ummie ta kira Baba Sani
da shi, shi kansa ya ji kunya amma sai ya basar yana haɗe fuska ya miƙa mata key ɗin yana cewa,
"Okey wife zan fito mu wuce gida ki huta."
Ummie ta amsa key tana maida dubanta kan Umma ta ce, "Allah ya ƙara mata lafiya."
Umma da kukan takaicin ke shirin ƙwace mata sai ta kasa cewa komi illah jan dogon tsaki da ta yi,
Ummie ta sakar mata wani smile tana maida dubanta kan Baba Sani, ta sake kashe murya ta ce,
"Baby Yallaɓai sai ka fito."
Baba Sani ya rakata da ido yana jin wani feeling na fisgar zuciyarsa, Ummie na jiyo ashar ɗin da
Umma ta saki ta yi saurin ƙarisa ficewa tana sakin dariyar mugunta.
"Yanzu sabida asara Baban Basmah agaban ƴaƴanka wata ƙatuwa za ta kiraka Baby ka amsa?
Wannan wace iriyar cin fuska ce haka wallahi Allah ya isa tsakanina da wannan auren da ka yo,mu
za a fara wa bariki ana nuna mana cewa tashin bariki ne marasa kuny......."
Baba Sani ya yi saurin ɗagawa Umma hannu ya ce, "Ya isa haka Zuwairah bana son shirme."
Ta ja ƙwafa tana ji tamkar zuciyarta za ta yo waje sabida kishi da tsanar Ummie da ke cin
zuciyarta,lokacin da Baba Sani ya ce za su wuce sai Umma ta zari mayafi da jakarta ta ce ita ma
sai dai su wuce tare, babu ƴar iskar da za ta shiga lokacinta ai ita ya zo wa weekend, don haka
ƙafarta ƙafarsa za su koma gidan.
Murmushi kawai Baba Sani ya yi yana jinjina kansa, ba tare da ya ce komi ba suka jera da juna
zuwa wajen motarsa,Ummie na hakimce a gaban motar ta hango tahowarsu sai kawai ta saki
murmushi, tana cigaba da kallon yadda Umma ke takowa a fusace.
Umma ta buɗe back seat ta shige zuciyarnan tamkar ta kama da wuta, ita dai Ummie banda
blushing babu abinda ta ke yi, har Baba Sani ya shiga ya tada motar suka baro asibitin.
Sun yi nisa a tafiya ta hango wani me sai da Yalo da ke turawa a baro ya tsaya, sai ta dubi Baba
Sani tare da narke murya ta ce, "Baby ga me Yalo a tsaya a siya please!"
Baba Sani ya dubeta da kulawa ya ce, "Okey! but shi kaɗai ki ke so, ko kina buƙatar wani abun?"
Ummie ta sake narke murya cike da shagwaɓa ta ce, "No Sweet shi kaɗai na ke sha'awa."
Daga haka Baba Sani ya parker motar daga gefen hanya ya fito zuwa in da me yalon ya tsaya,
Umma da har hawaye suka cika idanunta na zallar baƙin ciki ta saki wani uban tsaki tare da cewa,
"Aikin banza in dai iskanci da bariki ne a cigaba da yi akwai Allah."
Ummie ta saki murmushi bata tankawa Umma ba, sai wayarta da ta ɗaga ta kira layin
TAIMIYYAH, suka sha wayarsu suna kwasar dariya tamkar wasu ƙawaye, hakan ya sake jefa
zuciyar Umma cikin matsanancin yanayi, har sai da ta zubda hawaye masu ƙuna.
Lokacin da Baba Sani ya shigo motar sai ya ajewa Ummie ledar Yalon akan cinyarta yana cewa,
"Gashi wife." Ummie ta dafe ledar tana dubansa cikin ido ta ce, "Thank u Baby, i luv u."
Umma ta ji wani kuka me ƙarfi ya taho mata amma sai ta yi gaggawar dafe bakinta, tana jin wani
abu me nauyi na sake danne zuciyarta, 'Wai ita ce yau ake gwadawa wannan buɗewar idon babu
kunya bare tsoran Allah?'
Ta ayyana hakan a cikin zuciyarta tana jin ƙirjinta na mata wani irin zafi, kanta ya cigaba da
sarawa tana jin lallai suna isa gida sai ta danna maganin hawan jininta, don yadda kanta ke
juyawar nan da wuya ta samu bacci a daren yau.
Suna isa gida Ummie part ɗin Iyah ta wuce, shi kuma Baba Sani suka wuce part ɗin Umma, yana
son ya watsa ruwa kafin ya fito zuwa part ɗin Iyah su gaisa.
Daga can asibitin kuwa Sharifah ce ta kira wayar Basmah don ta gaida ta da jiki, sai Zuhurah ta
ɗauki wayar ta shiga danna mata zagi bayan ta saka wayar a speeker, memakon Sharifah ta kashe
wayar ko ta ji haushi sai ta saki dariya tana cewa, "Easy Yah Zuhurah miye abin zagi da cin
mutunci don zan auri mijin ƙanwarki? Bafa ni na janyosa zuwa gare ni ba shi ya kawo kansa, ni
kuma na ga ya yi min zan iya aurensa to sai me, haramun ne ko kuwa akaina aka fara cin amana?
Ina ce ita ma anamar gurguwar gidanku kuka ci ta auresa bayan kun nemesa da asiri kun samu
kansa, ni kuwa babu Boka ba Malam soyayyace min indillahi ya ke min ina masa, to kuma sai me
don zamu auri juna? Don haka kar ki ƙara zagina da kirana maciyiya amana,ina Basmar ta ke?"
Zuhurah ta saki wata uwar ashar lokacin da Basmah ta fisge wayar tana kuka ta ce, "Sharifah ni za
ki ci amana har kina kiran hakan ba a bakin komi ba? Meyasa sai Nass za ki aura bayan ga
mazanan da suka fi shi komai? Meyasa sai mijin ni aminiyarki ki ka ga ya dace ki aura don ki
sanya min ciwon zuciya,bayan kin gama sanin sirrina, meyasa hakan Sharifah? Me nayi miki dana
cancanci wannan sakayyar ta cin amana daga gareki?"
Basmah ta kai ƙarshen tambayoyin tana kai ɗaya hannunta ta dafe sautin zuciyarta,wanda ke
bazanar rabewa gida biyu. Sharifah ta ja numfashi tausayin Basmah na son danne ta amma ta
yakicesa tana cewa, "Basmah haƙury za ki yi don tsakani da Allah tun randa ki ka fara nuna min
hoton Nass zuciyata ta kamu da ƙaunarsa, shiyasa lokacin da ya taya ni kuma ban tsaya sanya ba
wajen bashi zuciyata, ina miki bushara da cewa zamu zauna lafiya ba zan taɓa cutar da ke ba,
hasalima ba za mu rayu inuwa ɗaya ba Basmah , ki yi haƙuri ni da ke ƙaddararmu kenan bye!"
Daga haka Sharifah ta kashe wayarta ta bar Basmah da rushewa da wani irin kuka tana shure-
shure tamkar za ta zare, sai da Zuhurah ta kira Doctor ya zo ya danna mata allurar bacci sannan
suka samu sukuni.
Washegary ƙarfe sha ɗaya na safe aka ɗaura auren Nass da Sharifah akan sadaki naira dubu ɗari,
aka zarce da shagalin biki har zuwa lokacin da aka ɗakko Amarya Sharifa, aka kai ta Fam house
ɗin su Nass ɗin da ke Ƙwarbai cikin City.
Hajiya Hajara da aminanta an sha shagali, don murna ta ke da wannan auren sosai da sosai,
shiyasa ta zage wajen ganin an tarbi amaren yadda ya dace, sai zuwa next week Ango zai wuce da
Amaryarsa Abuja, in da ya kama haya a Jabi nan zasu zauna sai dai ya dinga shigowa Basmah
weekend Zaria.
Basmah ba don a ƙarƙashin kulawar likitoci ta ke ba da Allah kaɗai ya san irin mummunar
yanayin da zata shiga, don kuwa hauka kawai ne bata yi ba lokacin da ta tabbatar cewa an ɗaura
auren, Sharifa yanzu ita ce za ta amsa sunan kishiyarta. Hatta Zuhurah sai da ta taya Basmah
kokawa tana jin tausayin junansu na ratsa zuciyarta, da ƙyar aka samu Basmah ta dangana bayan
an sanyata yin baccin dole don samun hutun ƙwaƙwalwarta, cikin jikinta kansa ba don Allah shi
ne me iko akan komi ba, kuma bai ƙaddari fitarsa ba tabbas da tuni ya daɗe da zubewa.
_____________
*Abuja.*
TAIMIYYAH da ke da watanni uku a garin Abuja, zuwa lokacin ta jima da sabawa da garin tana
kuma jin daɗinsa matuƙa, hannunta ya jima da fara nuna a iya driving don kusan yanzu da kanta ta
ke fita duk in da to, duk da cewa har lokacin ba a cire Laner daga jikin motar ba.
Ta kammala yin duk wasu jarabawa da za su kaita matakin shiga Jami'a, kuma ta samu nasarar
tsallakewa yanzu zaman jiran addimision later kawai su ke yi ta fara Registration.
Cikin jikinta da ita kanta suna cikin ƙoshin lafiya da samun cikakkiyar kulawa daga A.Maleek
Ado, wanda duk ran duniya sake ninka kulawarsa akansu da nuna musu ƙauna ta zahiri da baɗini
ya ke yi.
TAIMIYYAH ta sake cika ta yi wani irin kyau me fisgar hankali,duk weekend A.Maleek na kan
hanyar zuwa dubasu, su sha soyayyarsu monday ya bi flight ya juya, haka rayuwar ta dinga
garawa har kawo yau ya da ya kama Friday.
Tun safe ta kintsa ɗakin baccinsa tare da buɗesa da turarukan wuta masu ƙamshi na Northern
Regalia, ta gyara ko'ina fes tana jin wani shauƙi da ɗokin son ganinsa tamkar sunyi watanni ba su
ga juna ba.
Ita ta taimakawa Rabecca suka gama shirya abincin Lunch don bata iya zama bata aikin komi, tun
A.Maleek ɗin na masifa har ya gaji ya daina ya gane cewa haka nature ɗinta ya ke, kuma tana da
ƙoshin lafiya ne don haka Hajjah ta sanar masa lokacin da ya kai ƙarar TAIMIYYAH wajenta.
Shiyasa ya haƙura ya barta tana yin ƙananun ayyukar da ba za su jigatar da ita ba, sun kammala
shirya dining ɗin da ke upstairs ɗin ne ta wuce ɗakinta don yin wanka da sallah.
Tana cikin shiryawa A.Maleek ɗin ya iso, shi ya ƙarisa shafa mata mai da sanya mata kayan da ta
ciro riga da wando na shan iska marasa nauyi, kalar pich and black masu laushin jiki. Wuyar rigar
me faɗi ne da ya fito da dukiyar fulaninfa a fili, ta yi kyau matuƙa cikin kayan, A.Maleek ya kai
bakinsa ya sumbaci wajen yana wani lumshe idanunsa, tare da sake rungumota zuwa jikinsa.
TAIMIYYAH ta sake shigewa jikinsa tana lalubar bakinsa ta haɗe da nata, a hankali take aiki
masa da deep kisses da suka fara birkita lissafinsa.
Da ƙyar ta kwaci kanta tana magiyar ya tashi ya yi wanka ta bashi abinci , ya dinga aika mata
harara bayan ya raɗa mata wasu kalamai masu nauyi a kunni.
Bayan ya fito daga wankar ne ta taimaka mai ya shirya sannan suka fito zuwa dining, ita ce ta
ciyar da shi abincin kafin shi ma ya ciyar da ita da kansa.
Bayan sun kammala me ya ɗauke ta cak! Zuwa bedroom ɗinsa, ban sake jin ɗuriyarsu ba sai can
yamma da suka tashi don yin sallar la'asar. Kwanaki biyun da ya yi na weekend ɗin kullum sai sun
fita wajen hutawa abin su, sai yamma liƙis suke shigowa gida duk a waje suke yin Lunch sai
dinner ne kawai TAIMIYYAH ke dafa musu abu mara nauyi su ci su kwanta.
Monday ya juya zuwa Lagos ya barta da tarin kewarsa, don ma yanzu business ɗin da suka fara na
sake ɗauke hankalinta da rage mata kewa, sabida sun fara abin a sa'a daga shigo da Abayun nan su
Yah Anas suka tallatawa ƴan kasuwa, take wani me shagon sayar dasu ya sare duka guda 150 ɗin.
Yasmeen kanta sai wajensa ta je ta darza wanda za a zuba a lefenta, sabida ita ke haɗa kayan auren
da kanta wanda bikin ya rage saura 4weeks wata biyu kacal aka saka, za ta auri Aliyunta ɗan nan
Kano ne amma haifaffen Yola ne, yana aiki a Nasarawa can za a kaita.
Kamar da wasa sai TAIMIYYAH ta sake ordern wasu har ma da Hijabai da gyaluluwa, su ma
bugun farko suna isowa duk aka sare su daga haka sai abu ya fara yin gaba,ita ma Suhailah abin ya
amsheta don yawan nata ma sun zarce na TAIMIYYAH, don ita ta yi renting shago ne a Ikoyi ta
zuba kayan, tun daga kan Abayas da takalma zuwa jakuna, duk tana order daga Dubai da Egypt
duka, tana kuma sararwa ƴan kasuwa akan farashi me sauƙi. Nan da nan sai suka ji son yin
business ɗin na sake bunƙasa a ransu, shi kuma A.Maleek sai ya ƙara musu jari don yana jin daɗin
yadda abin ya amshe su shi ma, kuma bashi da burin barin su suyi aiki sai dai business ɗin dama.
Sai ya zamana Subailah yanzu duk wani kishi da wauta ta aje sa a gefe ta kama mijinta da
business ɗinta hannu biyu, sai yanzu da ta fara business ɗin ga kuma mijin a kusa da ita,sai take
gane cewa tabbas shawarwarin Meenah da Anty Safiya sune masu inganci, don gashi yanzu
hankalinta ya fi karka akan nawa za su shigo nawa kuma ta fitar, ba tunani kishiya da son sanin
wani hali take ciki ba.
Cikin TAIMIYYAH na da 5month ta fara ɗaukar lacture a Jami'ar Baze, ta fara karantar Law cikin
ɗoki tare da ɗinbin maida hankali, musamman da ya kasance tana cikin wanda Ubangiji ya yi wa
baiwar kwanya, tana sahun gifted da aka fara ji da ita a faculty ɗin tun a semestern farko. Ita ke
driving kanta zuwa skull ɗin ta kuma dawo gida cikin kwanciyar hankali, sosai ta ke jin daɗin
course ɗin tare da shan ɗammaran fitowa da first class idan Allah ya bata nasara. Dukkanin
dokokin A.Maleek ɗin daya kafa mata akan sanya dogayen Hijabai duk ta ɗauka, ta kuma kiyaye
domin a zauna lafiya.
Tunda ta fara zuwa bata saki jiki da kowa cikin ƴan matan ajin nasu ba, har ma da matan aure don
suna da yawa mata dake karantar course ɗin a shekarar, don za su kai su 20 mata kawai.Mace ɗaya
ce ta fara sabo da ita daf da za su fara exams na first semester ita ce Hannah Bashir, matar aure ce
ita ma me kwanya da maida hankali akan abinda ya kawota, ustaziyace da ke da matuƙar kamun
kai da riƙe mutuncinta, abinda ya fara janyo hankalin TAIMIYYAH kenan akanta sai ta fara sakin
jiki da ita, don Allah ya haɗa jinin Hannah da ita tana shige mata sosai don ta ga cewa ta saki jiki
da jita. A hankali sukai sabo da juna tare da exchanging numbar juna, bayan hutu ne kuma Hannah
ta kaiwa TAIMIYYAH ziyara sau ɗaya, hakan yasa suka sake ƙullewa amma TAIMIYYAH ba ta
taɓa zuwa gidan Hannah ba, wacce ita tana zaune a Wuse 2 da mijinta.
Haka rayuwa ya cigaba da garawa TAIMIYYAH cikin nasara da cigaba me tarin yawa cikin
rayuwarta, cikinta ya yi girman gaske sanda ya shiga watanni takwas, sai ya zama jikinta ya yi
nauyi sosai ko skull ɗin bata iya zuwa, daga asibiti sai gida shiyasa ta roƙi Iyah akan ta zo ta zauna
da ita, tunda A.Maleek ɗin ya yi rantsuwar ba za ta koma Zaria ta haihu ba, shi ma hutu zai ɗauka
da zaran ta haihun su dawo Abuja har Suhailah sai an gama hidiman suna sai su koma Lagos ɗin.
Hakan ko aka yi da ƙyar Iyah ta amince ta haɗo kan kayanta aka biya mata kuɗin flight ,tunda
Train ya zama labari tun da akai attaciking mutane suka daina shigarsa, hanya kuma masu kuɗi na
tsoro basa ma son bi an gwamace abi flight daga Kano zuwa Abuja ɗin.
Ana saura one week EDD ɗin TAIMIYYAH ya cika, Suhailah da A.Maleek suka tattaro daga
Lagos zuwa Abuja, Suhailah sai ta yi branching a downstairs cikin ɗakunan baccin da ke nan ɗin,
ta zaɓi na can ƙarshen cikin corridor ɗin sai Iyah da ke ɗakin farko.
Hajjah ta iso ana gobe EDD ɗin zai cika, amma cikin ikon Allah har suka yi kwana kusan biyar
haihuwar bai zo ba.
____________
*National Hospital,Abuja.*
Hajjah da Iyah tare da A.Maleek Ado ne ke faman kai-kawo daga ɓangaren Labour room ɗin, suna
fata da addu'ar saukar TAIMIYYAH lafiya wacce aka kawo tun safe amma gashi har agogo ya
buga 11am ba ta haihu ba.
A.Maleek duba ɗaya za kai masa ka karanci zallar rashin nutsuwa a tattare da shi, ya yi nacin a
barsa ya shiga Labour room ɗin amma Likitan da zai amsa haihuwar Doctor Safwan ya hanashi
damar hakan.
Addu'a kawai suka duƙufa yi daga shi har su Hajjah da hankalinsu suma ya gaza kwanciya,
kowacce ka duba za ka karanci zallar damuwar da ke akan fuskarta.
Fitowar Doctor Safwan daga ɗakin haihuwar ya sanya A.Maleek saurin nufansa yana tambayar ta
haihu ne? Doctor Safwan ya shafa kan A.Maleek yana sakin murmushi ya ce, "Congratulation Sir!
Ta haihu with so much suprised twins muka samu ba guda ɗaya kamar yadda duk scanning ɗin da
ta yi ta yi ke nuna Baby boy ne guda ɗaya ba."
A.Maleek ya dubi Doctor Safwan with shock! Wani abu na keta zuciyarsa na zallar farin ciki, ya
buɗe baki ya ce, "Twins Doctor?"
Doctor Safwan ya jinjina kai ya ce, "Yes kuma dukan su suna cikin ƙoshin lafiya, nan da 20
minutes za mu gama gyaresu su fito zuwa ɗaki hutu, ita ce ake ɗinkewa yanzu don ta ƙaru sosai
but tana cikin ƙoshin lafiya Alhamdulillah!"
A.Maleek da bakinsa ya kasa rufuwa sai ya kalli gabas ya kafa goshinsa a ƙasa yana godewa
Ubangijinsa, akan wannan kyauta da ya yi masa na samun ƴaƴa har guda biyu a lokaci ɗaya ba
tare da za to ko tsammani ba.
Su Iyah da tunda suka ga ya sanya goshinsa a ƙasa suka ganewa cewa an sauka lafiya, sai su kai
hamdala suna nufo wajen da A.Maleek ya ke Hajjah na cewa, "Alhamdillah! Me muka samu
Abdulmaleek?"
A.Maleek ya furta hakan cikin matsanancin farin ciki, Hajjah da fuskarta ke washewa da
matsanancin murna ta ɗaga hannu ta yi wa Ubangiji kirari tare da gode masa Iyah na taya ta.
Dukkaninsu sun shiga mamaki domin ko a girman da cikin ya yi babu wanda zai ɗauka biyu za a
samu, Iya ta jinjina kai ta ce, "Allah kenan! Me yin yadda ya so a kuma sadda ya ga dama, Allah
ka raya mana su bisa sunnah ka baiwa uwarsu lafiyar shayarwa."
Ta ɗaga waya ta kira Suhhailah ta sanar mata cewa TAIMIYYAH ta haihu an samu twins ɓace da
namiji, Suhailah ta ji wani farin ciki da mamaki ya lulluɓe zuciyarta. Ɗokin son ganin yaran na
bijiro mata hakan yasa ta saurin cewa, "Gani nan zuwa yanzu Hajjah, amma zan tsaya in sayo
kayan Baby girl tunda siyayyar maza aka yi kafin ayi ordern na mata yau-yau ɗinnan."
Hajjah ta jinjina kai ta ce, "Kin yi tunani me kyau Suhailah sai ki hanzarta Allah Ya yi albarka, Ya
kawo miki naki rabon ke ma me amfani."
Daga haka suka kashe wayar daidai lokacin da aka basu izinin shiga don duba TAIMIYYAH da
yaranta kyawawan gaske, babu in da suka baro kamannin iyayensu don macen sak! TAIMIYYAH
ce shi kuma Namijin A.Maleek ne sak! Kamar an tsaga kara hasken fata kawai zai fisa don ya biyo
farin TAIMIYYAH ne sosai.
Babu kunya ya rungume yaransa a gaban Iyah da Hajjah, yana jin ƙaunarsu me tsanani na ratsa
zuciyars, an goge su tas! An sanya musu kayan sanyi kala daban amma duk colour ɗin maza don
namiji hoton ke nuna wa.
Lokacin da ya baiwa su Hajjah yaran ne ya nufi wajen TAIMIYYAH, wacce ta gama jigata da
galabaita idanunta a lumshe suke, amma tana jin duk bidirin da ake yi tsakaninsa da Hajjah da take
masa faɗan rashin kunya.
TAIMIYYAH da ke saurarensa sai ta buɗe manyan idanunta ta sauke akansa, dukkanin kalamansa
na ratsa ɓargonta, cikin murya me cike da shagwaɓa da narkewa ta ce, "Thank u Zauj!"
Daga haka ta maida idanunta ta lumshe ƙaunarsa da na yaranta waɗanda ba ta kai ga ƙare musu
kallo ba, na sake mamaye zuciyarta da jinin jikinta baki ɗaya.
Iyah da Hajjah suka ƙariso wajen suna mata sannu, ta buɗe idanunta ta sauke akan Iyah tana gyaɗa
kai ba tare da ta ce komi ba.
Hajjah ta tambaya cikin tsantsar nuna kulawa, TAIMIYYAH ta girgiza kai ta ce, "A'a Hajjah babu
komi."
Daga haka suka fito daga ɗakin don bai wa uban gayyar damar sakewa da matar tasa, aiko kaman
jira ya ke yi su fita ya kwaso yaran ya kawowa TAIMIYYAH su, bayan ya zaunar da ita tare da
sanya mata pillow a baya yadda za ta ji daɗin zama.
Ya riƙe macen a hannun ya bata namijin yana zama sosai jikinsu na gugar juna, sabida gado ne me
yalwa na zamani na kwanciyar patient.
"Zaynabb da wa suke kama ne wai?"
Ya tambaya da wani irin salon murya da ke bayyana tsantsar ƙaunar su gare shi, TAIMIYYAH ta
ɗago manyan idanunta daga ƙare musu kallo ta dubesa tana blushing ta ce, "Damu duka, Boy ɗin
kai ya biyo Macen kuma ni ko?"
A.Maleek ya saki wide smile ya ce, "Yes! My pure zuma haka ne kam, har wannan ɗan ƙaramin
bakin shagwaɓar taki ce wallahi."
Ya yi maganar yana kai hannu ya shafa cute pink lips ɗin Baby gal ɗin, TAIMIYYAH saki dariya
daidai lokacin da Suhailah ta sanyo kanta cikin ɗakin, hannunta duka biyu riƙe manyan bags da ta
tsaya ta yi shopping.
A.Maleek ya dinga kallonta har ta ƙariso bakin gadon da suke zaune, fuskarta ɗauke da wide smile
ta ce, "Congratulations! My Maleek ashe kuma twins muka samu?"
Maleek ya jinjina kai yana tashi ya isa gareta ya miƙa mata macen yana cewa, "Thank u luv, twins
muka samu."
Suhailah hannunta na rawa ta amsa Babyn zuciyarta na shiga wani yanayi da ba za ta iya
fassarawa ba, ba baƙin ciki ta ke ji ba sai ma zallar ɗoki da murnan ganin twins ɗin, amma dai can
ƙasan zuciyarta akwai wani pain da ke motsa mata wanda ba za ta iya kwatantawa ba.
Ta tsurawa Yarinyar ido tana kallon zallar kammanin TAIMIYYAH akan fuskar Yarinyar,
kyakykyawar gaske tamkar a sace ta a gudu, ta sake tsura mata ido tana jin wani abu ma motsa
zuciyarta, har cikin ƙashinta ta ke jin ƙauna da sha'awar Babyn na ratsata. A.Maleek da ya amso
Namijin daga wajen TAIMIYYAH sai ya zauna kusa da Suhailah yana kara mata shi ya ce, "Wife
ta ya gani waya yafi wani kyawu a cikinsu, an dai raba mana gardama Wannan A.Maleek ne sak!
Ita kuma Zaynab ce ko?"
Suhailah ta ɗaga ido ta dubi namiji wani abu me ƙarfi na harbawa cikin zuciyarta, ta yi saurin aje
macen a hankali daga gefe tana amsar namijin ta tsura masa ido, tana jin wani irin ƙaunar Yaron na
ratsa zuciyarta, cikin wani irin murya ta ce, "My Maleek dukansu kyawawane da babu wanda ba
za a sace a gudu da shi ba idan ana sata, but dis bouncing Boy ɗin is my Fav!"
Yadda ta yi maganar tana sake manna idanunta akan Babyn ya motsa zuciyar A.Maleek ɗin, ya ji
wani irin tausayinta na ratsashi sabida ya san ƙarfin soyayyar da take masa da kamanninsa da
Yaron ya yo ne yasa ta ce shi ne Fav ɗinta.
Ya rungumesu ita da yaron yana kai bakinsa bisa kunninta ya ce, "Suhailah in dai shi ne Fav ɗinki
to ki fara shirin rainonsa bayan an yaye sa, ni Maleek na baki shi har abada!"
Daga Suhailah har TAIMIYYAH da ke saurarensu suka ɗago a razane suka dubesa, kowacce
zuciyarta na bugawa da ƙarfin gaske, A.Maleek bai kalli side ɗin TAIMIYYAH ba sam ya cigaba
da kallon Suhailah ya ce, "Da gaske na ke yi Suhailah na baki Muhammad Sameer, a hannunki zai
tashi da izinin Allah."
Suhailah sai ta sake rungume yaron tana sakin kuka mara sauti, wani irin abu ke kewaye jinin
jikinta, ta dubi A.Maleek muryarta na rawa ta ce, "Thank u luv, but ita bata ce za ta bani ba, kar ka
yi saurin yin kyauta da abinda ba kai kaɗai ka ke da hakki akansa ba."
Sai lokacin A.Maleek ya ɗago ido ya dubi side ɗin da TAIMIYYAH ta ke, wacce ta tsura musu ido
shi da matar tasa tana kallon ikon, zuciyarta na sake shiga tashin hankali da wani irin fargaba me
tarin yawa. 'Me A.Maleek ke shirin yi ne haka?'
Ta tambayi zuciyarta tana ji hawaye na taruwa a idanunta, ganin ya fara takowa zuwa gareta ya
sanya ta yi saurin sadda kanta ƙasa.
A.Maleek ya zauna daga bakin bed ɗin yana riƙo hannuwanta tare da ɗago da face ɗinta,ya buɗe
baki zai yi magana ta riga shi da faɗin, "Kar ka cemin komi Hubby! Idan har abinda ka furta mata
hakane har a cikin zuciyarka, ba sai ka yi magani da ni don Allah!"
TAIMIYYAH ta kai ƙarshen maganar tana zame jikinta ta kwanta, hawaye na zuba daga idanunta
wani irin abu na cigaba da danne zuciyarta,hakan yasa A.Maleek tsura mata ido with so much
shock! Ya sake kai hannu zai riƙo nata ta yi saurin janyewa, murya can ƙasa ta ce, "Don Allah ku
barni na samu hutu please! Ka kwashesu A.Maleek tunda kana da ikon yin hakan sabida kai ne
mahaifinsu, but now ina da buƙatar ku bar ni da huta please!"
Ta yi maganar tana juya masa baya tare da sakin kukan da take riƙewa, Suhailah da ta zuba musu
ido tana kallon komi sai ta taso tana nufo bakin bed ɗin ta tsaya. Ta zubawa jaririn da ke hannunta
ido ƙaunarsa da na A.Maleek na sake huda zuciyarta, cikin wani irin raunin murya ta ce, "Yah
Maleek na gode da tarin karamci da nuna tausayinka gare ni, wanda shi ne jigon da yasa ka ke
ganin za ka iya min irin wannan sadaukarwa, sai dai kash! Ba zan taɓa goyan bayan raba uwa da
ɗanta, ba tare da amincewarta ba, na haƙurah Yah Maleek kai ma ka haƙura ka janye wannan
maganar, ba za ta bani ba koma ta bayar za ta bayar ne bisa tirsasawarka gare ta, don haka na
haƙura Allah ya san dani kuma ban cire rai daga rahamarsa ba, Allah ya raya mana su cikin
musulunci. Zaynabb ki yi haƙury ba zai rabaki ɗanki ya bani ba alhali baki yi na'am da hakan ba!"
Suhailah ta ƙare maganar tana sakin kukan tausayin kanta,hakan ya soki zuciyar Maleek tare da
TAIMIYYAH wacce tun fara maganar Suhailah ta ji jikinta ya ɗauki rawa, wani irin tausayinta ya
lulluɓe zuciyarta.
"Na baki shi Suhailah, kamar yadda ya furta miki hakan ne zai kasance, abinda na ke so ku gane
kawai ina buƙatar hutu ne a yanzu, ki yi haƙury!"
TAIMIYYAH ta furta hakan cikin rawar murya, Suhailah ta lumshe idanunta tana wa A.Maleek
sign da ido akan ya je ga TAIMIYYAH, ita kuma ta taka a hankali ta koma wajen gadon da aka
kwantar da Baby gal ɗin, ta sanya Baby boy ɗin a cikin nasa gadon ta fice daga ɗakin, tana kasa
fassara wani yanayi zuciyarta ke ciki.
"Zaynab ki yafe min idan abinda na yi ya ɓata ranki, ban yi don in nuna isa ko ƙarfi iko ba sai don
ina jin tsananin tausayin Suhailah, na san baki san issue ɗinta akan rashin haihuwa ba ko?"
TAIMIYYAH ta gyaɗa masa kai hawaye na cigaba da biyo face ɗinta, A.Maleek ya sanar da ita
tun farkon matsalar da Suhailah ta samu har kawo yanzu, da suke jiran rabo ya samu a gare ta
amma Allah bai kawo ba. Ya ƙare maganar da cewa, "Shiyasa na ke tsananin jin tausayinta
Zaynab, ki taimakeni in cika wannan promise ɗin a gareta, ba don na isa ba sai don ke ma ki nuna
mata sadaukarwa, ko babu aure a tsakanina da ita wallahi zan iya sadaukar mata da abinda na
haifa, domin mahaifiyarta ta nuna min so da gata Zaynab, kuma ta bar duniya ba tare da na cika
burina akanta na nuna mata gata da kulawar da naci buri ba, so akan Suhailah kaɗai zan kyautata
mata domin ita kaɗai ta bari a duniya, please TAIMIYYAH ki taimak......."
Hannun da TAIMIYYAH ta kai ta rufe bakinsa ya hana shi ƙarisa kalamansa,ta buɗe baki a
hankali ta ce, "Ka daina roƙona Hubby in dai yadda ta ka ke nema na amince, Allah ya raya su
cikin aminci zan bata shi kamar yadda kasanar mata sai an yayesu za ka bata."
A.Maleek ya rumgume TAIMIYYAH yana gaya mata maganganu masu nauyi na nuna zallar
ƙauna,tare da farin cikin yadda ta kasance me son duk wani abinda ya ke so, cike da nuna jarumta
da ɓoye damuwar da ke zuciyarta ta cigaba da biye masa, har zuwa lokacin da Hajjah ta shigo ta
korashi akan cewa ya barta ta huta.
Sai washegaryn ranar aka sallamesu daga asibiti zuwa gida,har lokacin kuma bata sake sanya
Suhailah a idanunta ba, sai can dare ta shigo ɗakin riƙe da Baby Boy ɗin a hannunta, A.Maleek
riƙe da macen sun dawo da su don a basu nono.
TAIMIYYAH ta ɗaga manyan idanunta ta sauke akan Suhailah, tausayinta na sake huda zuciyarta
sosai, Suhailah ta aje Babyn a kusa da TAIMIYYAH tana cewa, "Zaynabb yana buƙatar nono in ji
Hajjah."
Har Suhailah ta nufi ƙofa don fita daga ɗakin TAIMIYYAH ta kira yi sunanta ta dawo, ta dubeta
cikin ido ta ce, "Ki yi haƙury Anty jiya na ga kamar baki fahimceni ba game da alƙawarin da
Hubby ya yi miki, ni da yaran duka ikonsa ne yana da damar ya sarrafamu yadda ya ke so, na
amimce za mu mallaka miki Abbana ki raineshi a matsayin ɗan cikinki, ina fata za ki ƙaunacesa
tamkar yadda ki ke ƙaunar mahaifinsa, ina miki addu'ar ke ma Allah ya kawo miki rabo me
amfani."
TAIMIYYAH ta kai ƙarshen maganar tana jifan Suhailah da murmushi, Suhailah sai ta tako ta
zauna daga bakin bed ɗin tana duban TAIMIYYAH cikin ido ta ce, "Zaynab da gaske za ki iya
sadaukarmin da ɗanki na rainesa?"
TAIMIYYAH ta gyaɗa kai ta ce, "Me zai hana ?"
Suhailah sai fuskarta ya washe da wani irin wide smile, gaba ɗaya sai ta rasa kalar farin cikin da
za ta nuna, ta ɗakko Yaron ta rungumeshi tana jin wani ƙaunarsa na sake huda jinin jikinta, ta
sumbacesa ta ɗago ta dubi TAIMIYYAH ta ce, "Na gode Zaynabb, na gode da wannan
sadaukarwan ina roƙon Allah ya bani ikon bashi ingatacciyar tarbiyya, haƙiƙa ke ɗin ba kishiya ba
ce abokiyar zama ce. Luv say something please!"
Ta kai ƙarshen maganar tana kallon A.Maleek da ke blushing, zuciyarsa cike da zallar ƙaunarsu da
soyayyarsu me zafi, ya isa wajen TAIMIYYAH ya rungumeta ya ce, "Thank u Luv, Allah ya
faranta ranki ya baki Aljanna Firdaus."
Daga haka ya sake ta ya koma wajen Suhailah ita ma ya rumgumeta ya ce, "Luv u Wife, ina fata
Abban mu ba zai ture gwamnatina anan ba?"
Ya yi tambayar yana kai hannu bisa ƙirjin Suhailah daidai saitin zuciyarta,suka saki dariya a tare
har TAIMIYYAH, kafin su tsaida dariyar Suhailah na cewa, "Ai ko da wuya bai ture ba sweety, na
ji kuna ta cewa Abba an sa musu suna ne?"
Maleek ya jinjina kai ya ce, "An saka musu suna Muhammad Sameer da Nana Aysha,amma za mu
kira ta da Nahar."
Suhailah ta jinjina kai ta ce, "Wow! Nice names Sweet ka ce princess Hajjah mu ka samu."
Da ƙyar Suhailah ta iya barin ɗakin bayan TAIMIYYAH ta gama shayar da yaran tana kallo cike
da birgewa,har cikin zuciyarta take jin kyawun zuciya irin na TAIMIYYAH, sai ta ji jikinta ya
sake sanyi akan zazzafar kishin da ya ɗebeta a baya har ta yi yinƙurin binne layun da ta amso, ta
dinga jin tarin nadama tana sake yin Istigfari akan Allah ya yafe mata.
Da dare A.Maleek suka keɓe da Hajjah ya sanar mata yadda suka yi da TAIMIYYAH,akan cewa
idan Allah ya raya twins har aka ya ye su zai ɗauki Sameer da suka kira da 'Abbah ' ya baiwa
Suhailah. Hajjah ta yi farin ciki sosai tare da zuwa ta yi wa TAIMIYYAH godia me tarin yawa, sai
lokacin Iyah ta ji maganar ita ma kuma ta yi na'am tare da jin daɗin yadda TAIMIYYAH ta baiwa
A.Maleek haɗin kai su yi wannan sadaukarwan.
Kwanakin da suka biyo baya su TAIMIYYAH da yaranta na samun tsananin gata da kulawa daga
wajen Hajjah da Iya, ana jibi suna garin Abuja ya fara ɗaukar baƙi ƴan Zaria da za su halarci taron
gagarumin shagalin sunan da za a gudanar.
Su Guggo Bilki da Amarya Yasmeen da akai bikinta lokacin TAIMIYYAH na da tsohon ciki, sun
iso ana gobe suna ne don ta Kano Yasmeen ta fara tsaya suka biyo flight zuwa Abuja.
Sauran dangin TAIMIYYAH da abokanan arzikin Iyah da su Anty Mardy dangin Mamar
TAIMIYYAH, duk ana gobe suna suka bayyana har da Ummie da ita ma ta fara yin nauyi........✍🏻
#Ɗansabo ce#
[12/15, 11:47 AM] +234 703 040 9541: Littafin TAIMIYYAH paid book ne,ga duk wanda ta
tsincesa a kowani irin group ne,kiji tsoran Allah karki karanta sai kin biya 500 naira only.
Za ku iya min magana ta wannan number ɗin 08167768704, ko kuma ku turo kuɗin ku kai tsaye ta
wannan account ɗin 0504192664 aisha ibrahim dansabo GTbank.*
Masu turo credit za ku turo katin MTN na 500 ta wannan line ɗin 08167768704.
_Ina ƴan kasuwa masu buƙatar a tallata muku hajar ku? Maza ku garzayo da kuɗi ƙalilan a tallata
muku kayan siyarwanku sai dai kawai ku ji ana kiran waya don buƙatan sayan kayan ku,ku
tuntuɓeni ta layina kamar haka 08167768704._
*91*
Umma dai babu halin zuwa a ga ƙwaf sabida Zururah da ita ma ake jiran na su haihuwar ita da
Basmah, waɗanda duk wata ya shiga lokaci ake jira kawai.
Yah Deeku ne ya kai matarsa da ke da ƙaramin ciki ita ma, daga Kd in da suke zama direct ya
wuce da ita Abujan,gida fa ya cika don ma akwai ƙaton BQ ta baya shiyasa aka samu wadatan
wajen kwana.
Wani irin shagali ne aka gudanar a wani babban wajen yin tarukan suna da biki da aka kama, tare
da yin haɗaɗɗan Naming decoration da ake ya yi yanzu. An ci an sha an kashe dukiya sosai wajen
wannan bikin Suna, Mai jego da Babies sun sama kaya da abin duniya kamar ba gobe, Suhailah
kanta akwatin kaya ta yiwa Jenior da Princess Nahar kamar yadda ta raɗawa yaran sunan da za a
riƙa kiransu da shi.
Duk wanda ke bin status ɗinta a ranar zai yi zaton ita ce Mai jegon ma, sabida yadda ta ci ado tana
ɓarke sabbin ɗinkuna ana kashe musu pics da Babies ɗin.
Su Anty Safiya da Anty Nadeey suka dinga mamakin yadda Suhailah ta koma, tamkar ba ita bace
me zafin kishinnan da wauta, yanzu duk ta zubar ta shiga nutsuwarta tamkar ba ita ba.
Zuwa can Yamma taron ya watse aka dawo gida, misalin takwas da rabi sai Baba Sani ya kira
Ummie da Iyah ya sanar da su cewa Zuhrah ita ma ta sauka. An sama ɗa namiji suna asibiti cikin
ƙoshin lafiya, Ummie ita ce ta shigo ɗakin TAIMIYYAH ta sanar da su haihuwar, TAIMIYYAH
suka dinga murna da yiwa Zuhurah fatan samun lafiya.
Bayan fitar Ummie Yasmeen suka ɗakko zancen Basmah, Yasmeen na baiwa TAIMIYYAH
labarin yadda aka ce duk ta lalace, sabida ta sawa kanta zafin kishi me tsanani shi kuma Nass ɗin
baya bi ta kanta, yana can da Sharifarsa iyakarsa da ita ya shigo weekend ya yi kwana biyu ya
juya, har kuma lokacin Hajiya Hajarah na gidan Basmah ta ce mutu karaba, ta dawo kenan sai
randa aka fita da gawarta amma zama daram, tunda ya riga ya gina mata part a cikin gidan bata ga
uban da ya isa hanata zama ba.
Washegary sai Ummie ta wuce Kano tare da su Yasmeen da su Guggo Bilki, duk kuma A.Maleek
ne ya siya musu ticket.
Iyah ta so ta dawo ta bar Hajjah da Anty Mardy wacce za ta zauna ta kula da TAIMIYYAH, amma
sai Hajjah ta ƙi amincewa ta ce lallai tare za su yi zaman jegon nan. Idan don duba masu haihuwa
ne za su iya zuwa su dawo abun su, da haka ta kashe bakin Iyah ta haƙura za ta zauna ɗin.
Washegarin suna da kwana biyu kowa ya watse ya kasance daga Me jego sai su Iyah, Suhailah
yadda ta ke kula da Babies ɗin dole a yaba mata, kuma tsakani da Allah ta ke yi don da gaske jin
yaran ta ke yi har cikin zuciyarta, kullum ƙara ganin kyawunsu ta ke yi musamman princess da ke
sake zarowa kamanninta da Mamanta na sake fitowa.
__________
*Gyallesu,Zaria.*
Zuhurah ce ke faman kuka tana riƙe da kyakykyawan Babynta me kama da ubansa Ameeru tamkar
kwabo da kwabo, tun jiya da ya zo duniya suka ga haliitar ƙafafunsa su ke kuka daga ita har
Umma, don kuwa irin nannaɗaɗɗun ƴaƴan nan ne wanda duka ƙafafunsa biyu a dunƙule suke,
babu zancen ma ayi maganar tafiya sai dai ko ya rayu ya riƙa jan gindi ko a tura shi a keken
guragu.
Hajiya Barirah da ke zaune ta dubeta da tausayi ta ce, "Zuhurah kar ki ja Ubangiji Ya yi fishi da
ke, ki iya bakinki ki rungumi ƙaddararki da hannu biyu, kun tafka kusakurai wanda duka hurumin
Allah ku ka shiga dole ku ga sakamako, waccar gurguwar da ku ka dinga ma gorin halitta kuna
aibatata hakkinta kaɗai ya isa Ubangiji ya saukar muku da Aya. Yadda ki ke ji a zuciyarki fiye da
haka ta ke ji, yadda za ki ji idan aka fara tsangwaman wannan Yaron ki sani cewa fiye da irin
ciwan da za ki ji Kakarku ta dinga ji a zuciyarta, lokacin da ku ke tasa ta gaba da gorin
halitta.Shiyasa ba a son aibanta halittan Ubangiji domin duk wanda ka gani da nakasa ba shi ya
sanyawa kansa ba, haka Allah Ya so ganinsa."
Zuhurah ta rushe da kuka maganganun Hajiya Barirah na sake tuno mata da baya, lokacin da suke
tashen tsangwamar TAIMIYYAH da kushe nakasarta, yau gashi ta haifo wanda ya dameta a
nakasa ya shaye, wanda ba zai moru har ya taka doran ƙasa da ƙafafunsa ya yi tafiya ba, sai dai ya
ja gindi ko a tura shi a keken guragu. Wani irin ɗaci ya mamaye zuciyarta ta dinga jin wani irin
nadama da danasani na kewaye jinin jikinta, mahaukaciyar soyayyar ɗanta da tausayin yadda zai
taso ya dinga keta zuciyarta yana shiga ɓargonta.
Umma da ke daga gefe tana sauraran dukkanin maganganun Hajiya Barirah, sai lokacin ta samu
halin tankawa ta ce, "Hajiya Barirah tabbas ni Zuwairah ina cikin ganin Aya da jarabawar rayuwa,
na tafka kusukuren da ba zai gogu ba gashi ina ganin aikina daki da daki, tunda ya zo duniya a
haka na fahimci cewa shi ɗin Aya ce Ubangiji ya saukar akan zuriyata don ya nuna min
iyakata....."
Kuka ya ƙwacewa Umma ta dinga yinsa tamkar ba za ta daina ba, nadamar da baida anfani ke
cigaba da cika zuciyarta. Hajiya Barirah ta cigaba da tunasar da su kuskurensu na baya akan yadda
suka tsangwami TAIMIYYAH, abin har ya yi yawa alhali ita bata taɓa ganin aibun Yarinyar ba,sai
ma nutsuwa da hankakinta da ta ke gani.
Umma da Zuhurah jikinsu ya yi mugun sanyi, da zaran ƴan barka sun zo sai a nannaɗe yaron da
kyau cikin showel, don gudun surutun mutane, hakan yasa da yawa waɗanda suka zo barka ba su
kula da yadda ƙafafun Yaron suka zo a nannaɗe ba.
Randa Zuhurah ta kwana biyu da haihuwa su Ummie suka iso har da Yasmeen da za ta jira ayi
sunan Zuhurah kafin ta koma, suka dinga santin kyawun Yaron don Ameeru kyakykyawane.
Sai da aka zo yiwa Yaro wanka da yamma ne su Guggo Bilki suka ga abinda ake ɓoyewa, ita dai ta
yi mamakin yadda ake kanannaɗe yaro da showel,ashe akwai magana jikinta ya yi mugun sanyi
lokacin da ta fahimci cewa Ubangiji ne zai nuna wa su Umma iyakarsu.
Ta sake jinjina ƙudiran Ubangiji da yadda ya iya hukunta bayinsa daidai da laifukansu, wanda idan
mutum ne ya ce zai maida martani ya yi kaɗan ya iya mayarwa daidai da yadda ɗan uwansa ɗan
adam ya zalincesa, amma idan ka barwa Ubangiji shi Ya san ta yadda zai kama bawansa cikin
ruwan sanyi.
Yasmeen da Ummie duka sai da su ma jikinsu ya yi sanyi, suka sake jin tsoran Allah tare da
neman tsari daga aibanta halittar Ubangiji, Yasmeen ita ce ta kira Iyah ta sanar mata komi, Iyah ta
saki salati tare da yiwa Ubangiji kirari ta ce "Allah ya raya musu shi tamkar yadda ya raya
Zaynabu, yau gata da tsala-tsalan lafiyayyun ƴaƴanta har guda biyu, haƙiƙa Yasmeen Ubangiji shi
ne mafi iya hukunta bayinsa, yanzu sai su bashi lafiya su ciresa daga nakasa mu gani."
Yasmeen ta jinjina kai ta ce, "Hakane Iyah ni ma abinda na faɗi kenan, Allah dai Ya yi mana tsari
daga bin son zuciyoyinmu da aibanta halittar bayinsa."
Iyah ta amsa da cewa, "Ameen Ya Hayyu Ya Qayyum! Za mu shigo zarian da Hajiya Aysha ana
gobe suna In Sha Allah."
Daga haka sukai sallama da Yasmeen Iyah na maida dubanta kan TAIMIYYAH, ta labarta mata
komi kafin Yasmeen ta kira vid call suna sake magana, TAIMIYYAH sai ta ji tausayin yaron da
ƙaunarsa ya shiga ranta tun kafin ta gansa, ta dubi Yasmeen ta ce, "Yasmeen ki shafa min kansa ki
ce ina ƙaunarsa, idan basu sonsa ni su bani shi zan rainesa tamkar ni na kawo shi duniya."
Yasmeen da ta ji zuciyarta ita ma ta karye ta dubi TAIMIYYAH ta ce, "Waya gaya miki ba sa
sonsa, ai irin waɗannan ƴaƴan ba ƙaramin shiga rai suke da shi ba, kar ki so ki ga yadda uwar ke
nuna ƙaunarsa."
TAIMIYYAH ta dubi Yasmeen ta ce, "Allah ya raya shi, ki turo min pic ɗinsa please! Bari in kira
Zuhuran yanzu."
Daga haka TAIMIYYAH ta yi cuting call ɗin ta kira Zuhrah, bugu biyu Zuhrah ta ɗaga wayar suka
gaisa da TAIMIYYAH, ta yi mata barka tare da addu'an Allah ya raya musu abinda suka samu,
Zuhurah ta amsa a sanyaye ta ce, "Ameen TAIMIYYAH don Allah ki yafe mana, haƙiƙa mun ci
fuskarki a baya gashi Allah ya saukar da Aya akaina TAIMIYYAH, ki yafe min Zaynab don
girman Allah!"
Zuhurah ta kai ƙarshen maganar tana sakin kuka, TAIMIYYAH zuciyarta ya karye cikin rawar
murya ta ce, "Na yafe muku Zuhurah sai ku roƙi Ubangiji shi ma Ya yafe muku, don huruminsa ku
ka shiga ba nawa ni kaɗai ba, sabida shi ya mayar dani gurguwar ba ni na mayar da kaina ba, ki
shafa min kan Babyn ki ce masa ina ƙaunarsa matuƙa!"
TAIMIYYAH ta kai ƙarshen maganar hawaye na zuba daga idanunta, Zuhurah ta sake rushewa da
kuka tana jin matsananciyar nadama na sake lulluɓe zuciyarta, TAIMIYYAH ta yi cutin call ɗin
tana jin zuciyarta na cika da wani irin yanayi me wuyar fassara.
Kwanan Zuhurah biyar da haihuwa ana jibi suna, ita kuma Basmah ta haifo ƴarta mace a asibitin
AL-Madinah, su Guggo Bilki da su Ummie ne suka rankaya asibitin lokacin da Nass ya kira ya
faɗi haihuwar, don ya shigo weekend yana gari haihuwar ya zo.
Lafiya ƙalau suka tadda Mai jegon da ƙatuwar ƴarta, me kama da ita sak! babu in da ta baro ta a
kammanni.
Suna asibitin Hajiya Hajarah ta iso da Aminiyarta Hajiya Murja, sam Yasmeen bata gane Hajiya
Murja ba ita ce ta ganeta lokacin da ake gaggaisawa, Hajiya Murja ganin Yasmeen bata gane ta ba
yasa ta dubanta ta ce, "Ƴan mata baki gane ni ba ko?"
Hajiya Murja ta yi murmushi ta ce, "Ni ce wacce kuka samu tare da Hajiya Hajara lokacin da ku
ka je gaisheta ke da ƴar uwarki me lalurar ƙafa da Nass ya kai ku don gaida Hajiyarsa ta yi muku
cin zarafi, na dinga baku baki lokacin."
Yasmeen da sai lokacin ta gano tabbas ta ga wannan fuskar, sai ta saki murmushi ta ce, "Allah
sarki ai sai yanzu na gane. Kinsan ai wannan ɗin ma ƴar uwata ce ƙanwar mu ce ni da
TAIMIYYAH."
Hajiya Murja ta ce, "Allah sarki haka Hajiya Hajarah ta sanar min, ashe ƙanwarta ce ta aure mata
saurayi yanzu ita tana ina ne?"
Yasmeen ta sanar da Hajiya Murja cewa TAIMIYYAH ta yi aure tana Abuja, ta buɗe wayarta ta
nuna mata pics ɗin suna. Hajiya Murja ta amsa wayar tana duban hotunan wanda tun daga yanayin
tsaruwar wajen ta gane cewa TAIMIYYAR ba gidan banza ta shiga ba, kuma ba ƙaramin mutum ta
ke aure ba, hakan yasa ta jefawa Yasmeen tambayar cewa waye mijin ? Yasmeen ta ce, "Sunansa
Abdulmaleek Ibrahim Ado, ɗan Marigayi Alhaji Ibrahim Ado da ya riƙe Assistant Controller na
ƙasa lokacin yana raye "
Hajiya Murja with shock ta ce, "Kina nufin ɗansa ƙwaya ɗaya da ya mallaka a duniya shi ta aura?"
Hajiya Murja ta jinjina kai ta ce, "Allah na gode maka, ai dama ni na ji ajikina wannan Yarinyar
wallahi ba ta banza ba ce, Ubangiji shi kaɗai yasan hikimarsa na tauyeta da nakasan da ya yi, don
Allah ki ce ina gaidata kin ji ko, Allah Ya raya twins Ya yi musu albarka."
Daga haka Hajiya Murja ta ƙarisa wajen da Hajiya Hajarah ta kame kan kujera riƙe Baby, ta shiga
labarta mata zancen TAIMIYYAH, Hajiya Hajarah ita ma ta yi mamakin jin wanda TAIMIYYAH
ta aura ɗin, ta dubi Hajiya Murja da mamaki ta ce, "Kina nufin gurguwar Yarinyar nan ya aura duk
tarin dukiyarsa da ficen da ya yi?"
Hajiya Murja ta ce, "Ƙwarai da gaske ba don kar su ce na zo na yi gulma ba da na amso wayar kin
ga uban dukiyar da aka kashe wajen bikin sunan twins ɗin da ta haifa masa,duk ta riga ƴan uwan
nata haihuwa ashe."
Su dai su Yasmeen suka kai sallama dasu suka baro asibitin,don Hajiya Hajara ce za ta kwana da
Mai jegon zuwa da safe a sallameta.
Ana gobe sunan Zuhurah su Iyah suka iso Zaria tare da Hajjah, tare suka je har gidan Basmah
suka ga Baby, Hajjah ta aje musu kayan barka har da kuɗi .
Zuhurah ma kaya sosai Hajjah ta kai mata tare da kuɗi sai faman godia Umma ta ke zubawa, don
gaba ɗaya ta fara yin laushi abubuwa sun fara shan kanta, ga rashin ƙoshin lafiya tunda hawan
jinin nan ya sameta.
An yi shagalin suna sosai ƴan Bauchi ma sun zo sun kuma kawo kayan arziƙi sosai, Ameeru ya zo
sau ɗaya ya ga Baby baya ga haka ko waya bai sake yi ba bare ya ji lafiyar Babyn.
Zuhurah ko ajikinta don ada ne ma take ji da zaran ta haihuwa za ta sallama musu abinda ta haifa,
ta zo ta buɗe sabon shafin rayuwa, amma tunda ta haifi Muhammad Sani, (Sunan Baba Sani aka
sawa Yaron) shikenan ta ji cewa ba za ta taɓa iya bai wa kowa shi ya riƙe mata ba.
Ranar sunan Basmah Yarinya ta ci sunan Hajiya Hajarah, za su riƙa ce mata (Ummi) sosai Hajiya
Hajarah ta ɗauki son duniya ta ɗaurawa Ummi. Ta yi kayan suna na gani na faɗa sai a ranar sunar
ne kuma Basmah sukai ido biyu da Sharifah, wacce ke ɗauke da ciki ɗan watanni huɗu, ta sake
zama wata classy woman,sabida Sharifah dama akwai iya gyara da sanin kan gayu, ta zube kayan
suna wanda Basmah takaici ya sanya ta yin watsi da su ta ce bata so, Sharifah dariya kawai ta yi ta
tattare kayan ta kaiwa Hajiyar Nass, sai gashi ita da kanta ta kawowa Basmah kayan ta zageta tas
ta ce lallai asawa Ummi kaya, ai ba don ita Sharifah ta bada kayan ba. Basmah ta amsa tana kuka
tana jin tamkar ta haɗiyi zuciya ta mutu sabida baƙin ciki da kishi me zafi da ke cin zuciyarta.
__________
*Abuja.*
TAIMIYYAH ita wanka ya fara nisa tuni Suhailah sun juya Lagos tun suna da 2 weeks, amma
kullum sai ta kira vid call an nuna mata yaran, da gaske ta ke ƙaunarsu tare da jin su acikin
zuciyarta, hakan ba ƙaramin yi wa TAIMIYYAH daɗi ya ke ba, dama an ce 'me ɗa wawah' duk
wanda ke son nasa sai ya so shi.
A.Maleek Ado shi ma baya iya cikakkun awa uku ba tare da ya yi waya da TAIMIYYAH vid call
ya ga yaransa ba, wata irin soyayyah suke sha ta waya suna musayar zafafan kalamai, don
TAIMIYYAH kullum kanta sake buɗewa ya ke yi idanunta na sake soyewa da tarin ƙaunarsa da
kan makantar da idanunta wajen nuna masa soyayya ko a gaban waye.
Duk weekend sai ya shigo Abuja su yi ta faɗa da Hajjah idan ya shige ɗakin TAIMIYYAH ya
jima, za ta biyosa ta kora shi tana masa faɗan shi ko kunyar idanun Iyayenta baya ji ne? Idan ita ya
rainata ta saba da fitsararsa ai su basu saba gani ba. Sai dai ya yi dariya yana sosa kai kuma hakan
ba zai hana shi idan ya kuma jin son ganinsu ya lallaɓa ya shige ɗakin ba.
Downstairs gaba ɗaya Hajjah ta sanya TAIMIYYAH ta dawo ana jegon anan, idan ta hau sama to
wani abin ta je ɗakkowa ta dawo downstairsa abin ta.
Wani irin jego take yi irin ƴan gata don kulawar da take samu ma har ya yi yawa, sam bata san
wahalar yaran ba iyakar ta dasu basu nono, shiyasa suna da 20days ta fara shiga skull sabida sun
fara yin testsis an shiga tsakiyar second semester, Hajjah da Iyah da faɗa suka fara randa ta shirya
ta ce za ta shiga skull, sai da ta kira A.Maleek ta shagwaɓe masa tare da yi masa bayani, sannan ya
fahimtar da su Hajjah suka haƙurah,ta tafi ta bar Yaran bata ma jima ba test kawai ta yi tare da
signing attendance ta dawo gida.
Hannah ta zo mata barka har da siyayyar kayan Babies, ta tafi tana santin kyawun rayan kamar ta
gudu da su.
*MURFI*
*After 7 Years*
Barrister Zaynab Sameer (TAIMIYYAH) ita ce ke sakkowa daga stairs hannunta cikin na
A.Maleek Ado Ibrahim, wanda ya sake zama wani irgarman namiji da shekarunsa suka fara nisa.
Ita kuma ta zama wata babbar mace me tsananin aji da kamewa, kana kallonta za ka san ilimi da
wayewa na zamani da na addini sun zauna mata matuƙa, ta sake zama wata haɗaɗɗiyar mace
masaniya kuma ƙwararriyar Lawyern da ta san kanta, wacce ta fito da kwalin first class.
Sanye take cikin shigar Abaya da ya zame mata tamkar ibada duk idan za ta fita shigarta kenan,
kuma hakan A.Maleek ya fi buƙata domin yana mata kyau yana kuma ɓoye masa sirrikan
albarkatun jikinta daga ciki, shi kuma yana sanye cikin ɗanyar BUA kalar sky blue da ya yi
masifar amsar fatar jikinsa.
Suka dinga jerowa a tare har suka iso cikin tsakiyar falon ƙaton gidansa sabo dal da suka sake
sauyawa anan Asokoro, don shekaru biyu kenan da bashi muƙamin ƙaramin Ministern Sufuri cikin
sabuwar gwamnatin da aka fa, kasancewarsu jigo kuma manyan da suka bada tarin gudumuwa
suka yi aiki da aljihunsu da mutanensu wajen ganin gwamnatin ta kafu.
TAIMIYYAH ta ɗaga manyan idanunta masu haske ta dubesa tana ƙasa da murya ta ce, "My
sweet amma dai ba zamu fita da yarannan ba?"
TAIMIYYAH ta ɓata fuskah ta ce, "Amma kasan muna ɗaukarsa Hudah ba za ta taɓa barin
kunnuwanmu su huta ba sabida kuka."
Kafin ma A.Maleek ya yi magana kyawawan twins ɗin ƴan shekaru biyu suka fito da gudu daga
ɗakin wasan su dake nan downstairs, hannunsu riƙe da ledar choculate ɗin kit kat suna sha, macen
ta kawo hannu za ta damƙi rigar TAIMIYYAH, ta yi saurin riƙe hannuwanta tana cewa, "No
Hudah! Kar ki ɓata ma Mamah kaya, oya mu je a wanke a hannun."
TAIMIYYAH ta yi maganar tana jan hannun kyakykyawar Yarinyar ,suka nufi toilet da ke corridor
ta wanke mata hannu, shi ko Haidar wajen Papan nasu ya nufa ya ɗaga shi sama ya dire yana
sumbatarsa ya ce, "My boy how fer?"
A.Maleek ya saki smile yana sake jin ƙaunar yaron a ransa ya ce, "Okey bari Mamah ta zo sai
muyi dropping na ku a wajen Momy."
TAIMIYYAH ta dawo riƙe da hannun Hudah da ta sauyawa riga, ta dubi A.Maleek tana cewa ,
"Mu je Hubby please!"
A.Maleek ya aika mata wani sassanyar kallo ya ce, "Okey my pure zuma, amma za mu yi
dropping nasu wajen Momyn su, Haidar ya ce wajen Momy za shi."
TAIMIYYAH ta saki smile ta ce, "Thank god, wallahi ya ma fi hakan mu je mu dawo babu wani
hayaniya da yara."
Ya balla mata harara yana cewa, "Ni bansan meyasa baki son fita da yara ba wallahi."
TAIMIYYAH ta shagwaɓe murya ta ce, "Takura ce ban so, ita ko Momy ka ga babu ruwanta."
Suna ta hiransu har suka isa wajen motar A.Maleek driver ya yi saurin buɗe musu back seat suka
shige, ya maida murfin motar ya rufe tare da shiga mazauninsa ya tashi motar suka fice.
Zagayawa ne kawai suka yi sabida gidan Suhailah na daga bayan estate ɗinsu TAIMIYYAH ne ta
baya, da gugu yaran suka nufi ciki suna kiran, "Momy! Momy!"
TAIMIYYAH da A.Maleek suka saki dariya suna rufawa yaran baya zuwa ciki, a falo suka tadda
Suhailah da ƙaton cikinta a gaba wanda ya kusa shiga watan haihuwa, ta sake buɗewa ta zama big
madam sosai.
Ta sauke idanunta akan A.Maleek da TAIMIYYAH ta sake gyarawa su Hudah zama a kusa da ita
ta ce, "Au ku ce tare ku ke da su na ɗauka dirver ne ya kawo su ai?"
TAIMIYYAH ta saki smile tana zama daga bakin seater ta ce, "Momy ina yini, ya nauyin jiki?"
Suhailah ta ɓata fuska ta ce, "Wallahi nauyi jikin kam akwai sa."
Cike da tausayinta TAIMIYYAH ta ce, "Ayyah! Allah ya raba lafiya, ai an kusa dai."
Kafin Suhailah ta yi magana Jenior ya fito daga ɗaki, ganin su TAIMIYYAH ya sa shi ƙarisowa da
sauri ya rungume A.Maleek yana cewa, "Welcom Pa." A.Maleek ya shafa kan yaron nasa me
shekaru shida amma sabida girman jikinsa za ka ɗauka ɗan shekaru takwas ne ya ce, "My son ya
ku ke, ina Princess ina fata kuna maida hankali a skull sosai ko?"
TAIMIYYAH ta balla masa harara ta ce, "Koma an tambayeta ai ba gaskiya za ta faɗi ba, tunda
bakin ku ɗaya."
Suhailah ta saki murmushi ta ce, "Mun dai ji, ke ma kin san Yarona in dai kwanyace wallahi ko
waccar Princess ɗin ba za ta nuna masa komi ba, a Qur'ani ne kawai ta yi masa zarrah, amma za
mu kamota soon ko Son?"
Daga haka ya gaida TAIMIYYAH ta amsa tana wani basar da shi, Fitowar Nahar daga ɗakin ya
sanyata maida idanunta kan Yarinyar, wacce kamanninsu da ita har ya ɓaci hatta shagwaɓar babu
abinda da baro nata.
"Oyoyo my Pa." Nahar ta faɗi lokacin da ta rugo ta rungume A.Maleek, ya rungumeta da kyau shi
ma ya ce, "My Mum ya ki ke?"
"Mamah welcome!"
Ta cewa TAIMIYYAH tana rungumeta ita ma, ta amsa da kulawa tana duban A.Maleek ta ce, "Mu
je Papa please! Ka da ayi ta jiran mu."
A.Maleek su kai sallama da Suhailah suna sanar da ita cewa, wajen Yayen ɗaliban da za a yi na
Foundation ɗinta za su a Jabi.
Suhailah ta yi musu a dawo lafiya suka fito sukai tafiyar su tare da barin yaran wajen Suhailah,
wacce suka yi sabo da ita sosai sabida tana nuna musu kulawa tamkar ita ce ta haifesu.
Sun isa Jabi taro ya yi taro sai tashin karatun ɗaliban ake ji waɗanda sukai saukar ALQUR'ANI
Mai Girma, ƙarƙashin makarantar Islamiyar ƙungiyar TAIMIYYAH'S FOUNDATION. Ƙungiyace
da ta kafata da kuɗinta ta ke kuma hidimtawa ƙungiyar da jikinta,da lafiyarta har ta kafu ta kawo
yadda ta ke a yanzu cikin shekaru huɗu da kafata, ƙaton gini ne me ɗauke da wajen kwanan
Marayu da Nakasassu guragu da makafi, duk ana kula da su tare da basu ingantaccen ilimin
zamani dana addini, an gina azuzuwar ɗaukar karatu na Boko da Islamiyya duk a cikin wajen. Ga
wajen kwanan Ma'aikata masu yi musu hidima maza da mata, ana biyansu albashi duk ƙarshen
wata. Kaf gadonta na kadara da Abie ya bar musu, ta sanya aka sai da komi ta xo ta zuba kuɗin
wajen kafa wannan Foundation, tana kuma fata da addu'ar Ubangiji ya amsa a matsayin sadaƙatul
jariya ita da Abie ɗinta.
Ɗalibai guda ashirin da huɗu ne suka sauke Qur'ani ake bikin ya ye su, shi ne su TAIMIYYAH
suka halarta wajen don sun tara manyan baƙi da suka gayyata, har ma da manyan Malamai da suka
yaba tare da jinjinawa ƙoƙarinta na ƙafa wannan Foudation don inganta rayuwar Nasakasassu da
marasa galihu.
Da yawan masu kuɗin da suka halarci wajen sun sanya tallafi me kauri don cigaban wannan
Foundation da ƙara bunƙasashi, an ci an sha Malamai kuma sun yi wa'azi da janyo hankalin masu
kuɗi Maza da Mata,akan su zo a haɗu wajen sake ɗaga wannan Foudation da bunƙasata ta yadda
Nasassu da marasa galihu za su yi alfahari da su. Daga ƙarshe aka nemi TAIMIYYAH da ta zo ta
rufe taron da addu'a bayan ta rero ƙi'arta me daɗi, ta karanta ayoyi goma na ƙarshen suratul
baƙarah, ta rufe taron da addu'a bayan an baiwa ɗaliban tarin kyaututtuka.
TAIMIYYAH a gajiye suka dawo daga wajen taron, shiyasa ba su biya sun ɗauki su Hudah ba
suka wuce gida, sai dare Suhailah ta sanya driver ya kawo su gida, don su mayun uwarsu ce duk
yadda za su damu akawo su basa taɓa yarda su kwana a wajenta.
Wani irin rayuwa suke yi na kishi me tsafta da sanin ciwan kai, kowacce burinta kawai ta yi zarrah
a zuciyar Maleek ɗin, basu da lokacin ɓatawa wajen faɗa da juna ko ƙananun magana. Kowacce
business ɗinta da hidimomin gabanta sun ishe ta, Suhailah sai yanzu ne Allah ya nufeta da samun
rabo, kuma cikin ya zo mata da wahala ne tun farkonsa ta ke fama, yau lafiya gobe ciwo har kawo
yanzu da saura watanni biyu ta haihu.
Nahar kusan ita ma ta dawo hannunta sabida rabin zamanta na gidan,dalilin shaƙuwarta da ɗan
uwan haihuwarta.
Su Hudah ne kawai na Mamah ɗinsu, don tun TAIMIYAH na ƙawazucin Nahar ɗin, har ta gaji ta
haƙurah ta rungumi su Hudah da ta ke kira da autanta.
__________
Hajiya Hajarah an ya ko Yarinyar nan ba za ku kaita wajen sarkin rafi ba, a ce Yarinya shekara
biyar sai dai a kwantar sai dai a tayar, ko zama bata yi bare rarrafe ballantana kuma a yi zancen
tafiya, har an yi mata ƙanni biyu amma babu wani can ji?"
Hajiya Malliya ɗaya daga cikin ƙawayen Hajiya ke wannan maganar, Hajiya Hajarah ta dubi
Ummi da ke kwance bisa cinyarta ta ce, "To Hajiya Malliya wallahi ni na rasa ma ina za mu kai ta
a dace, duk in da muka ji me magani muna tafe amma har yau ba a dace ba, ni kanta nema da ya yi
uban girmannan ke bani tsoro, daga faɗowa akan gado kai ya kumbura ɗim!"
Hajiya Malliya ta ce, "Hmm! Shiyasa na ke tsoro Allah sa ba aljanu ne suka shafeta irin waɗanda
ake cewa ƴan ruwa ɗinnan, amma koma miye ai ishara ce ki ke gani sabida shegan kyaran halittar
ƴaƴan jama'a da ki ka iya, ƙiri-ƙiri ki ka ƙi Kyakykyawar gurguwarnan ki ka ce Allah kyauta ɗanki
ya auro miki nakasassa, yo Allah na tuba da irin waɗannan ƴaƴan ai gwamma nasassu dubu irin
gurguwar, tunda ita tana yawanta ko'ina da cikar halittar ta da komi, amma wannan fah? fuska
kamar bana bil'adama ba Yarinya duk ta sauya kamanni Allah dai ya kyauta."
Hajiyar Nass da baki ya mutu ta ɓata fuska ta ce, "Ameen" Amma abin na damuna Hajiya Malliya
gashi an ɗauki son duniya an kimsawa zuciyata akan wannan yarinyar, wallahi ni kaina wani zubin
sai in dinga jin tsoranta haka kawai in ji kamar ba mutum bace, tabbas gwara guragu dubu da ire-
irenta Allah na tuba!"
Ta kai ƙarshen maganar wani abu na danne zuciyarta, shigowar Basmah ɗakin ɗauke coolers ɗin
abincin Hajiyar ya sanya su rufe zancen, ta aje abincin tana durƙusawa ta gaida Hajia Malliya, ta
amsa a wulaƙance tana faman taɓe baki.
"Ke kin sanar da Naseer zancen me maganin nan da naga ana talla a TV?"
Hajiya Hajarah ta jefawa Basmah tambayar a dake, Basmah ta jinjina kai ta ce, "Eh na faɗa mishi,
ya ce shi ya gaji a haƙura a barta kawai."
Ta yi maganar murya na rawa, idanunta akan Ummie da ke kwance ba ta ma san me take ciki ba,
sai dai ta yi ta zare idanu kawai. Hajiya ta jinjina kai ta ce, "Okey to xai dawo ya sameni ai jeki
abin ki."
Basmah ta baro ɗakin tana ji hawaye na biyo fuskarta, kullum cikin danasani da nadama su ke ita
da Zuhuarah, akan irin cin fuskar da suka dingawa TAIMIYYAH a baya, suna aibanta halittarta
gashi Allah ya jarabce su da masu lalurar da suka nata a gindinsu.
*Gyallesu.*
"Zuhurah ɗakko masa keken mana yana son fita waje ya yi hidimansa da yara."
Umma da takaici ya lulluɓe zuciyarta sai cewa ta yi, "Sun ma kansu, da gangar ne ai tsabagen su
ci zarafinsa ne kawai."
Zuhurah ta turo haɗaɗɗan keken tura gurugu wanda TAIMIYYAH ita ce fa siya masa ta turo masa,
tare da tarin tsadaddun suturu na ƴaƴan gata zuwa kayan ciye-ciye. Duk idan sun fita yi wa su
Nahar siyayyah sai ta yo masa nasa daban, sabida yadda take son Yaron da tausayinsa, tun su
Umma na jin haushi har suka saki tare da sallama cewa da zuciya ɗaya take yi. Nadama sun yi yafi
kwando dubu har sai da Umma ta roƙi TAIMIYYAH gafara akan ta yafe mata, ranar TAIMIYYAH
sai da ta zubda hawayen ganin yadda rayuwa ta sauya wa Umma, duk ta yi sanyi wannan jin kan
duk ta aje sa gefe, ga Baba Sani Ummie ta gama da zuciyarsa ita kawai ya ke gani agabansa,
tsakaninsa da Umma sai dai kawai ya zo musu weekend ya sauke hakkinta ya juya, yana dai kula
dasu da sauke duk wani hakkinsu amma zallar soyayyah na ga Ummie da yaranta twins da ta
haifa, wanda suka ci suna SAMEER da AHMAD sunan Baban TAIMIYYAH da na Mahaifin su
Baba Sanin.
Matar Yah Sadeeq ma ta haifi ƴarta mace, me sunan Umma suna kiranta (Ammie) ita ma Yasmeen
ta haihuwa shekara ɗaya da ya wuce ta haifi namiji me suna Mahmud. Su Zee da Maryam Sunusi
ne har yanzu aure shiru Allah bai kawo lokaci ba,dukkaninsu karatu suka sanya a gaba kafin Allah
ya kawo mazajen aure na gari.
Hajjah kusan rabin zamanta ya koma Abuja, ta kan je ta jima sannan ta dawo Zaria su ma su
TAIMIYYAH duk hutu sukan zo kowacce ta buɗe gidanta, su yi hutu su koma abin su.
Zuhurah zawarah na ta zuwa amma har yau bata samu wanda ya kwanta mata ba, shi ko Ameeru
har ya sake wani auren ya zo da matar don su ɗauki Muhammad, amma matar na ganin Yaron ta
daka tsalle ta ce ba za ta taɓa riƙon musaki ba, wanda ko mi sai an taimaka masa, ranan Zuhurah
da Umma sai da suka zubda hawayen baƙin ciki da takaici.
Zuwa yanzu Zuhurah da Umma sun yi nadama tare da fara ɗaukar darasi a rayuwa, don Umma
yanzu bata da matsalar da ya sha kanta irin Zuhurah da Basmah, waɗanda laluran ƴaƴansu kawai
ya gama daibaibaye zukatansu, tare da haifar da nadama me tsanani a zuciyoyinsu, sun gamsu sun
kuma gane cewa Ubangiji na halittar bawa ne a yadda ya so, ya kuma ɗaukaka shi ba tare da duba
fifikon halitta ba. Basmah ba ta da wani power sai abinda Sharifah ta shinfiɗa Nass ke aiki da shi,
wacce zuwa yanzu yaranta biyu da Nass duk maza, Aliyu da Hamdan. Tsakanin Basmah da shi sai
dai ya zo weekend ya juya kamar yadda Baba Sani ke zuwa wa uwarsu. Ta yi sanyi da laushi duk
wannan iskancin Hajiyar Nass ta gama ko ya mata hankali tare da natsata, don ma ita kanta
Hajiyar rashin lafiyarta dana Ummi ya sanya ta yin sanyi ba kamar da ba.
Iyah ko ta gama zama ƴar gatan A.Maleek da TAIMIYYAH, don baƙaramin yi mata hidima suke
ba, zuwanta Umrah tare da Hajjah sau uku kuma duk A.Maleek ke kaisu, zuwan ƙarshe ma da
suka yi tare da su TAIMIYYAH suka yi sai da suka wuce Dubai sukai sati biyu kafin su dawo.
A kwana a tashi watan haihuwar Suhailah ya yi ta haifo ɗanta namiji me kama da A.Maleek Ado,
ranar suna Yaro ya ci suna Ibrahim za a dinga ce masa (Khaleel). Anyi shagali sosai kamar yadda
aka yi a duka haihuwar da TAIMIYYAH ta yi guda biyu, TAIMIYYAH ta yi bajinta wajen nuna
wa me jego da ɗanta kulawa tare da kashe musu kuɗi wajen siyayyar kayan barka.
Kowa sha'awan yadda suka haɗe kai ya ke yi, suna harkan arziƙi irin na wayayyun mata, waɗanda
suka san kan duniya.
Hajjah ita ce ta tattaro don yin zaman jego, Iyah ma ta yi kara ta zo ta yi sati biyu ta koma, ana daf
da fara azumin watan Radaman Suhailar ta haihu shiyasa ma Iyah ta yi sati biyu ta juya, don ta ce
ta fi son yin azumi a ɗakinta.
A.Maleek da TAIMIYYAH sai suka buɗe sabon shafin rayuwa da faranta ran juna, tunda Suhailah
ana jego ita ke da mijin yanxu har zuwa masu jegon su yi arba'in.
Ya ɗauke ta cak! zuwa bed tana faman zuba masa shagwaɓar cewa bata gama yi masa kwalliyar ba
fa, ya shinfiɗeta bisa bed ɗin yana cewa, "Na yafe my pure zuma, ni ba kwalliya na ke so ga
abinda na ke so nan ana min ƙwalelensu."
Ya yi maganar yana cusa kansa a tsakiyar ƙirjinta, wani ƙamshi ya doki hancinsa ya ɗago kansa
tare da mannata kiss a goshi ya ce, "Sweet yau fa wasu twins ɗin na ke so mu farauto, tunda na ga
ke ɗin ƴar baiwace da bibbiyu ki ke bani sanyin idanun nawa ko ba haka ba?"
Ya kai ƙarshen maganar yana kai hannu zai zare rigar jikinta, ta yi saurin riƙewa tare da shagwaɓe
murya ta ce, "No my sweet Amore na yafe wallahi su Hudah sun ishe mu haka ai."
A.Maleek ya balla mata harara ya ce, "Ai ba ki isa ba Yarinya yau ɗinnan zan samar da wasu twins
ɗin, gara ki shirya yau till down ne kawai my pure zuma."
Ya yi maganar yana ɗage mata gira guda, TAIMIYYAH ta sakar masa kukan shagwaɓa yana mata
dariya, kafin ya yi musu light off ya hayo kan gadon baki ɗaya yana kai hannu ya janyo ta zuwa
jikinsa don rarrashi.......✍🏻
ALHAMDULILLAH!
Duka anan na kawo ƙarshen wannan littafin me suna TAIMIYYAH, ina fata za a amfana da
darussan da ke cikin littafin, kuskuren da na yi ina roƙo Ubangiji ya yafe mini.
Waɗanda ƙarshen littafin bai yi musu ba ina fata za ku yi min uzuri, don dama ba lallai ƙarshen ya
zo wa me karatu a yadda ya ke so ba, abinda za ku fahimta kawai na gina labarin ne tun asalin don
na faɗakar akan illar wulaƙanta nakassu da illar aibanta halittar Allah. Nakasassu suma mutane ne
kamar kowa, kuma suna da ƙima da darajar a wajen Mahaliccinsu.Sannan Ubangiji yana
ɗaukakasu kamar yadda ya ke ɗaukaka masu lafiya koma fiye.
Ina fata duk wata me nakasa da za ta ci karo da wannan labarin na TAIMIYYAH, za ta yi alfahary
da kanta tare da jin cewa ita ma halittace me daraja da zata iya taka kowani irin mataki na rayuwa,
ta kuma samu miji na kerewa sa a kamar yadda TAIMIYYAH ta samu, domin hakan huwacewa ne
na Ubangiji don yana ɗaukaka wanda ya so,ba tare da la'akari da nasakasar mutum ko lafiyarsa ba.
Wassalamu alaikum warahmatullah! Allah ya haɗu mu a littafina na gaba me zuwa In Sha Allah!
Na gode da tarin ƙaunar da aka nunawa wannan littafin, na yaba ina kuma godia matuƙa da gaske
masoya. Ɗansabo na ƙaunarku Fisabillah!