0% found this document useful (0 votes)
8K views31 pages

Yarima Jalal (WWW - Thn.com - NG)

Yes

Uploaded by

maryamyusufuba
Copyright
© © All Rights Reserved
We take content rights seriously. If you suspect this is your content, claim it here.
Available Formats
Download as TXT, PDF, TXT or read online on Scribd
0% found this document useful (0 votes)
8K views31 pages

Yarima Jalal (WWW - Thn.com - NG)

Yes

Uploaded by

maryamyusufuba
Copyright
© © All Rights Reserved
We take content rights seriously. If you suspect this is your content, claim it here.
Available Formats
Download as TXT, PDF, TXT or read online on Scribd
You are on page 1/ 31

[3/21, 5:45 PM] +234 703 003 6037: (11:40am,01/01/2016)

*************************⬇**********************
************* Top Hausa Novels ****************
*************************⬆ **********************

DOWNLOAD More complete Hausa Novels, Education Books, Adventure, Drama, Mystery,
Religion, Fiction, Non-Fiction, Romance, Meimor, True Life Stories & Others from
our blog.

Visit > https://www.thn.com.ng

Ka tura mana sako ta adireshinmu na email, domin tuntubarmu ko turo mana hausa
novel ko kuma post.

Email > tophausanovels@gmail.com

******* FOLLOW US ******

Facebook: Top Hausa Novels

Twitter: Top Hausa Novels

Telegram Channel: https://t.me/tophausanovels

Telegram Group: https://t.me/tophausa

Haka kuma domin shiga kowanne daga cikinsu za ku iya ziyartar shafin ku yi search
na TOP HAUSA NOVELS, hatta facebook group dinmu ma za ku samu.

********************** ⬇ **************************
*************** Top Hausa Novels ****************
********************** ⬆ **************************

!Y@RIM@ J@L@L!

Nah halima musa akano(leeemat)💮

Jalal! Jalal! Jalal! Jalal! Sai kiransa nake amma shi wanda na kira da jalal din ko
motsi baiyi ba,sai da na karaso wajansa kafin yace min so nawa nake fada Miki idan
zaki rinka kirana kizo inda nake kafin ba tun kina nisa ba..kallonsa naki cikin
mamaki a cikin zuciya ta kuwa cewa nake wlhy dad ne ya daure masa gindin ya mana
abinda yagadama a gidannan amma zan koya masa hankali.makaranta zaka kaini magana
nake cikin isa da gadara idonsa a gefe yace min ina driver dinku cikin masifa nace
oho watan idan nace ka kaini makaranta ko da driver bazaka kaini ba koh to ganin
gida yaji..
Jalal kuwa idan you asan da wata a gun to dotse yayi magana ganin zai bata min
lokaci yasa na Fara magana a sanyaye domin nasan in zamu kwana a gun bazaya tashi
ba cos yana min kasheji akan idan zan masa toh insan yanda zana tauna harshena..
Ina gama masa maganan cikin natsuwa ya tashi ya nufe wajan adana motoci ya dauki
mecedec,idan akwai moton da na tsana to itace amma saboda idan na tsaya masa magana
bata ma kaina lokaci zanayi sai na shiga kawai. Tafiya muke babu Wanda ya kula dan
uwansa kamar ance masa ya juya ya kalleni saiya ganni daga ni sai wando da riga da
dan karamin gyalle wani birki yaja da har na saka wani kara daga ido nayi saina ga
ashe har mun karaso. A cikin zuciyata magana nake yau kuma salon wulakancin da
za'amin kenan a waje zai ajeni wani dogon tsaki nayi na budi kofar moton najita a
kulle daga ido nayi ina mai kallonsa.jalal kuwa ko kallona baiyi ba sai ma kara
kauda kansa dayayi yace min me nafada miki ranar nan bace miki nayi duk ranar da ya
kasance ni zan fitar da ku to ku rinka saka hijab ba,ina mai tabbatar miki da cewa
yanzu zamu koma gida ki saka saina dawo da ke..kamar zanayi hauka amma saboda hali
irin nawa na bashi hakuri ina ganin kamar ci baya ne.haka inaji ina gani yayi
reverse muka koma gida gashi sai kirana ake tayi wai za'a mana text...a gate ya
tsaya da sauri na fito na shiga ciki ko minti biyar banyi ba na fita da sauri sanye
da hijab toyobo mai ruwan powder (pink )..
Wow abinda yafada kenan saboda kyaun da nayi cos acewarsa yau ce rana ta farko da
ya fara ganina da hijab.tafiya nake bakina a ture,sai yaga na masa kyau sosai ina
karasowa ya kauda fuskarsa..yana tsayar da moton kafin ya gyara parking na fito
nayi tafiyata shi kuwa bina yayi da kallo yana murmushi yarinya sai girman kai haka
zana koya miki hankali.ya juya ya fice a makarantar ya huce gida..dawowa yayi ya
dauko ni a makaranta amma yaita jirana banfito ba jalal kuwa idan akwai abinda ya
tsana itace a bata masa lokaci shiyasa ma baya African tym saboda duk lokacinda ka
fada masa abu to yana zuwa kafin lokacin tayi..yanzu dai Sun tashi da kusan minti
daya kenan😏ni kuwa da gangar na masa saboda ya batamin nawa lokacinda safe..ina
zuwa baya na budi na shiga ina mai murmushi ciki2 domin nasan zanja magana amma
abin mamaki ko uffan baice min ba saima gyara kwanciyar da yayi a moton.gyara zama
nima nayi tun ana minti talatin har an gangaru hour daya hmmm an kira asr,cewa nayi
a zuciyata kila yayi sallar azahar ni kuwa banyi ba gashi har LA'asar tayi bude
kofar nayi na kumo gidan gaba...leeemat kuwa cewa tayi kin ma kanki kiyamullaini ba
wai sunan wani sallan dare..ina zaune na dan kalle shi ta gefen ido abin mamaki
idonsa biyu, saida ya kara kusan minti talatin kafin ya ta da motar suka tafi gida
yana mai dariyar keta a zuciyarsa daya fahimce inajin yunwa domin cikina har
kururuwar yunwa takeyi......

Written
By
Leeemat💮...

[3/21, 5:45 PM] +234 703 003 6037: !Y@RIM@ J@L@L!

Nah halima musa akano (leeemat)💮

Alhaji nasir bammali shine mahaifina, hajiya naja'atu itace mahaifiyata mu biyar ta
mahaifemu nakasance ya ta farko a gunta inda tasakamin sunan simra ina da shekara
uku ta haife jalilah sai kuma yan biyu dahir da dahira sai autan mu ummu kulsum
amma ummu muke kiranta.mahaifana haifaffun garin zaria ne wato kaduna State kenan a
gun suke zama har aka haife mu nayi primary har secondary dina a zaria yanzu ina
University of Zaria wato Abu kenan inda nake karanta medicine and surgery jalilah
ita ma tana abu inda take karanta bsc nursing yan biyu kuma na secondary ummu na
playclaas..ina shekara ta biyar kenan jalilah kuma na shekara daya a university
din,duk da karatun mu bai hana mu aiyukan gida ba irin su kwankeke da abinci kai
har da shareshare domin mahaifiyar mu ta hana a dauko mana Mai aiki anata cewar
batason a kora mata yara a gidan miji duk sanda mahaifinmu ya mata korafi abinda
take cemasa kenan saiyace idan sun tafi makaranta wa zaiyi aiyukan saitace ni
zanayi har su dawo saiyace in kin tsofa da aiki amarya zan kawo miki sai suyi
dariya kawai.kwankin kaya da guga kuwa mahaifinmu yace bazamuyi ba jalal she ke
mana da mu da mahaifinmu da mahaifiyar mu sai idi driver sa'annan baba Mai
gadi.rayuwa muke cikin sakewa amma bai hanamu biyayya ga iyayenmu ba duk kayan da
muka gadama muke sakawa sai zuwan jalal rayuwar mu ya hanamu sakewa,zana iyacewa ni
yafi tsana saboda bana masa ta dadi haushin sa nake ji, akwai ranar da zamu tafi
ziyara a gidan kakaninmu idi driver dad dinmu yayi aikansa a banki layi yayi yawa
sai bai dawo da wuri ba ni kuwa na kagu na ga hajiya tsohowa mahaifiyar dad dinmu
saina ce ma dad dinmu yafada ma jalal ya kaimu muna shiga cikin moton saiyace wai
nafito tambayansa nayi meyasa saiyace na canja kaya ko kuma na saka hijab na duba
shigarda nayi doguwar rigace da mayafinsa saidai fitted ce,dan Allah wannan rigar
me yamasa da zakace na canja,ni gaskiya babu wani rigar da zan canja na gyara zama
ina maijin haushin halinsa na takura tsawa ya daka min har bansan lokacinda na fita
ba na shiga ciki ina kuka side na dad na nufa ina fada masa abinda jalal yamin hau
ni da fada yayi na tashi na nufe wajan mom ita ma fadan taimin dakina na huce nayi
kuka har na godiwa Allah tun daga wannan ranar na tsane sa bana masa kallon mutunci
saboda da shi iyayena suka min fada wannan shine musabbabin rashin jituwa a
tsakanin mu dukkanmu muna nuna wa juna miskilanci amma daga karshe ni nake sauke
nawa na bi nasa ra'ayin saboda wani tsoronsa da nake ji amma baya hanani na masa
rashin mutunci.....

Written
By
Leeemat💮....
[3/21, 5:45 PM] +234 703 003 6037: !Y@RIM@ J@L@L!

Nah halima musa akano (leeemat)💮

Babu irin wulakanci da tozarcinda bana masa amma duk bandaina jin haushinsa
ba.jalal kuwa duk lokacinda ya zauna saiyayi tunanin wai meyasa na tsane shi bayan
ga su idi da baba maigadi mts kawai yayi ya cigaba da harkansa
Yau ya kasance graduation dinmu na gama makaranta an bani shaidar na zama
cikakkiyar likita murna kuwa ba'acewa komai munyi hoto sosai domin har da jalal
nayi hoton,da aka kawo mana hotonan kuwa sunyi kyau sosai saima wanda mukayi da
jalal domin yana kallona ne cikin wani salo da na kasa cire idona a hoton
Anyi sha'ani lfy muka dawo gida washegari na tafi gaida dad dinmu ina gaidashi na
Mike zana fita ya kira ne na dawo na zauna yafara da cewa simra nace na'am,yace duk
abinda uba yake ma danshi na miki ko ban miki ba nace kayimin saina yace sauran me
gabana yayi mummunan faduwa.
Aure ya fada,aure yanzu ya rage min na miki Kuma na baki daman ki fitar da mijin da
kike so duk da dai ne yadace na fitar miki da miji a matsayin ki na budurwa amma
kinyi wasa da damar ki dun haka ni zan fitar miki da miji nan da kwana uku idan
baki fitar da wanda kike so ba,nan na mike jiki a sanyaye na huce dakina gashi bana
kula samari na tuna da numbar wani da muka hadu a wajan bikin uncle dinmu da sauri
na nufe jakata amma abin takaici bangani ba sa'annan na tuna a lokacinda yake bani
numbar na yaga takardan domin nace masa bazan iya bashi wayata ba saiya rubutu min
a paper.
Haka dai har kwana ukun yayi amma babu komai nayi kuka harna gode Allah
Da safe saboda tsoron jin mijinda dad ya zabamin ya hanani tafiya gaidashi saida ya
saka a kirani,na tashi na tafi ido a kunbure saboda kuka na zauna tare da gaida shi
ko amsawa baiyi ba yacemin tunda kin kasa kawo miji to na zaba miki jalal...

Päge 4

!.Y@RIM@ J@L@L!

Nah halima musa akano (leeemat)💮

A razane na kallesa ina kuka dad jalal fa kace,kwarai kuwa haka nace idan Kuma ban
isa da ke bane saina sani koh tashuwa nayi na huce dakin mom na fadi a jikinta ina
kuka tambayata take amma na kasa bata amsa sai dad da nake ta cewa mom kuwa rudewa
tayi a zatonta wani abune ya same sa da sauri ta fita daga daki ta shiga side dinsa
saboda akwai wani coridor da za'abi a shiga falonsa tana shigowa wani ajiyan zuciya
tayi kafin ta tambaya me ya same simra,magana yake cikin bacin rai wai ace wannan
yarinyar bata da sayayye ga kanwanta tana da miji jiranta akeyi amma babu, shine na
zaba mata jalal a matsayin mijinta mom ita ma a razane tace wani jalal din badai na
gidannan mai kwanki da guga ba. shi ya bata amsa ko kema gardaman zakimin,a'a na
isa Allah ya huce zuciyar ka ta tashi ta fice abinta ta sameni inata kuka ina
ganinta nace wallahi mom banasonsa dan Allah kifadama dad ni bana sonsa ya zabamin
wani na yarda amma ba jalal ba.mom kuwa babu abinda take sai aikin lallashi tare da
bani bakin nayi hakuri dad bazaya min zabin tumun dare ba amma na ki sai kuka nake
Mom kuwa irin matan nan ne masu bin maganan mazajansu idan yace ga abinda yake so
to haka zatayi ko da kuwa batason abin Allah yasa muma muyi kuyi da wannaan halin
ameen

Päge 5

Written

By

Leeemat💮....

..
[3/21, 5:45 PM] +234 703 003 6037: Y@RIM@ J@L@L

Nah halima musa akano (leeemat )💮

Yau ya kasance weekend babu makaranta inason na dan fita shopping na saya
abubuwanda bandashi amma babu idi driver tsaki nayi saboda na tuna da jalal dan
girman kai bansan yaya zan masa magana ya kaini ba side din mom na huce na tarar
tana gyare2 dakin ta na fara tayata tare da mata maganan inason taima jalal magana
ya kaini shopping bude bakinta tacemin daga yau shine yau idan kina da bukatar
tafiya wani gu karki sake ki zo wajena saboda ni ba sa'arki bace sai girman kan
tsiya kinason ki fita amma girman kai ya hanaki masa magana,na marairaice fuska
sa'annan nace mata wallhi mom dan rashin mutunci ne wai inzaka masa magana kuma
saika tausasa harshen ka nikuma gaskiya bazana tsaya ina tausasa masa harshe kamar
wani mijina ba bayan kuma dan aikin mu ne,jalal na shiguwa falon mom da niyar zai
kawo mata tsako a gidan hajiya tsohowa kenan yaji abinda simra ke cewa girgiza kai
kawai yayi ya fice. Yana shiga dakinsa wayarsa tayi kara yana daukowa yaga abokinsa
ne hello dude ya kake wallahi Kalau inson mu hadu yau ok to babu damuwa ina zowa
yanzu jalal ya kashe wayarsa sai wani kirar ta shiga yana dubawa yaga mom ce da
sauri ya dauka to to kawai naji yana cewa sa'an ya kimtsa jikinsa ya fita ya tarar
simra na jiransa shiga moton yayi Suka tafi,suna tafiya babu abinda ke tashi a
motar sai karatun alqur'ani na sheikh sudais surar AL'imran simra kuwa sai bin
karatun take a zuciyata saboda ta sauke tun tana ss1,tama mance bata fada masa inda
zaya kaita ba ji kawai tayi ya sayar da moton daga ido tayi domin ta ga ina ya kawo
ta saita gansu a wani gida mai bala'in a ranta cewa tayi nan kuma inane tabe baki
tayi irin I dont Care din nan fita yayi ya shiga gidan ya tarar da abokinsa mai
suna kamal suka bude shafin hira.
Simra kuwa tun tana zaman dadi har ta fara na wuya ana hour daya har anzo biyu uku
kuma taki kiransa saboda girman kai numbarsa ma batta da shi haka ta zauna godiya
Allah ac a kunne take amma fa cikinta ya gayamata saboda yunwa.jalal kuwa ganin
azahar ta gabato yasa shi yin sallama da kamal ya fito ya tarar da ita ta kunbura
saura kadan ta fashe yana shiga yace mata ina kike son na kaiki tundake bazaki
fadamin ba ni bara na tambaye ki amma fa karkiyi tunanin tsoron ki nake a sanyaye
nace masa shopping zanaje,muka tafi mun dawo gida kusan karfe biyu ina shiga mom na
tambayata meyasa muka dade haka na zayyana mata abinda ya faru ina hawaye,cewa tayi
maganinki kenan amma fa na gode masa domin ya kuya miki hankali hucewata daki nayi
na cigaba da kukata....

Päge 3

Written

By
Leeemat 💮....
.
[3/21, 5:45 PM] +234 703 003 6037: !Y@RIM@ J@L@L!

Nah halima musa akano (leeemat)💮

Tun daga wannan ranar na tsiro da ma jalal wulakanci, aika duk da dai nasan idi
driver ake aikan sa amma saina bawa jalal amma abin mamaki zaya harma yamin abinda
nace ya kawo min wanki kuwa ya kwanke kayan akwatina Sun fi so goma anawa tunanin
wai saboda yace ya fasa aure na
Bangaran Iyayena kuwa sunyi fadan sunyi nasiha amma na kiya jalilah itama tamin
nata maganan amma na zagzageta nace mata kar ta karamin maganan jalal,har da wani
cewa yana da kyau ga aji da miskilance mts idan yana da kyau ke ki aure sa mana na
fada raina a bace ita ko tacemim Allah ya baki hakuri ta fice abinta domin jamal
yazo mijin da zata aura banker ne sa'annan shima a Zaria yake Sun hadu a lokacinda
ta tafi bank bude account dinta amma saboda bata sa akeyi ba domin na bani hakuri
akan na rakata naki shine ta tafi da kanta,jamal ya taimaka bata da sauran
prossesses da akeyi harta gama ganin taimakonda ya mata ya saka ta karba numbarsa
domin su rinka gaisawa har zumunci ya zama soyayya,haka dai rayuwa ya cigaba da
tafiya,dad dinmu dayaga abin nawa gaba yake yi ya saka mana ranar auranmu a ranar
kuwa har nayi zazzabi saboda kuka..
IV aka kawo mana saboda biki ya rage sati biyu kannena nata yabun iv din amma ko
kallonsa banyi ba har cewa suke lah har da rubutun India a ciki a raina kuwa cewa
nake a ina wannan dan rigimar ya saka an mishi iv har da wani India a ciki wa ya
iya India da za'a karanta bangama maganan zuci ba naji dahir nacewa ai uncle jalal
ya iya India ai inajinsa yana waya da wani wai abokinsa ne ya koya masa a raina
kuwa cewa nayi makaryacin banza a ina yaga aboki da har zayace abokinsa ne ya kuya
masa kila ma a kauyansu ko radio basu da shi...

Päge 6

!Y@RIM@ J@L@L!

Nah halima musa akano (leeemat )💮

Saita raba iv jalilah take amma ko kallon nawa banyi ba saboda a cewata abin kunya
ne ace wai zan aure jalal da jalilah taga ban da iya in zata fito zaita dauko har
da nawa sa'annan ta dauko wayata ta rubuta sms na gayyatar auran ta sending ma all
contact dina bansani ba har satin auran yayi an tambaya me zana yi nace mata babu
abinda zanayi haka jalilah sunyi kamu da friends day nima nayi bikin amma in ba an
fada maka bane bazaka gane nima amarya bace domin ankon da akayi shine na saka kyau
kuwa ba'a cewa komai saidan ramar da nai dama ba kiba ce dani ba jalilah ce dai mai
kiba kadan gobe za'a daura aure dad dinmu ya kirani yamin nasiha sosai simra wato
dai kin nunamin ban isa dake ba tunda na miki miji shikenan kin hana wa kanki
sukuni bayan kinsan ko wani uba bazaya zaba wa dan sa zabin da baida kyau ba amma
babu komai inhar ban isa dake ba gobe idan a kaiki ki saka shi ya sake ki ki dawo
gida magana yake rai a bace babu abinda nake yi sai kuka yana gama ya fita abinsa a
ranar akayi walimah WA'azi akayi Wanda naji kamar da ni ake nayi kuka har a ranar
da zazzabi da kwana na kwana
Washegari ya kasance dauren aure jama'a kuwa kamar ana hawan sallah kai da yan
kasashen waje da ma sarakuna na gari daban daban irin su isa mustapha agwai na daya
sarkin lafia nasarawa state da sarkin Zaria da sunusi lamido sunusi sarkin kano
kenan dama wanda baxana iya lissafa ba an daura aure da gwalagulai da ba'asan nawa
ne kudin su ba na simra kenan yanda Kuma na jalilah kudi aka bayar,
Mahaifinmu baiso haka ba amma babu yanda ya iya domin yace albarkar aure ake so..
Ana daura kuwa magana yazo har gida an daura mana aure wani kuka na sake dama banda
lfy sai jikin ya karatashi mom dinmu ta shiga ta sameni tamin nasiha tare da cewa
bamusan abinda yasaka dad dinmu bawa jalal ke ba amma munafatan Allah yasa alkhairi
ne domin nasan insha Allah zakiyi alfahari da zabinda dad dunku ya miki sa'annan
naji dan sauki cewa tayi na tashi na shiga nayi wanka ina gama na saka wani shadda
a cikin kayan dad da daddare aka zo daukan amarya jalilah domin ance ni sai gobe
garin su jalal da nesa baza'a kaini yau ba sai gobe muka tafi kai jalilah gidanta
dake g.r.a da zamu dawo kuwa munyi kukan rabuwa domin nima gobe zan tafi yafeyar ta
na nima saboda bansan wani irin rayuwa zanyi a can ba...

Written
By
Leeemat 💮
.....

[3/21, 5:45 PM] +234 703 003 6037: !Y@RIM@ J@L@L!

Nah halima musa akano (leeemat )??

Washegari aka kawo min kaya kamar na sarauta na saka sa'annan na dura da alkyabba
kamar wata sarauniya na ce a raina motoci kuwa Sun kai goma,ni duk abin mamaki yake
da ban domin har na kasa cewa komai aka kaine wajan mom tamin nasiha mai rasa jiki
na kuka sosai na rumgumeta ina cewa umma ki gafarceni nasan na muku gardama da dad
inason ki yafemin kuka nake kamar za'a kaini gidan ajalina,domin har na saka
mutanin falon kuka mom ta kasa daurewa ita ma sai kuka takeyi tare da cewa nayafe
miki simra dama bakimin komai ba da kyar aka babbare daga jikinta domin inaga kamar
bazana sake ganinta kuma ba side din dad aka nufu dani dad shima yamin nasiha tare
da cewa yasan bazan bashi kunya ba domin yasan sainayi alfahari da zabinda yaymin
wata rana,nima na masa alkawarin insha Allah zanyi biyayya ga jalal bazan bashi
kunya ba natashi muka fita a gidan sai kuka nake tare da ma gidan mu kallon
karshe,mota na biyar aka saka ni ina shiga muka tafi ina kuka tare da kallon
gidanmu, munyi tafiya mai dan tsaho sainaga mum tsaya saboda tsakani na da driver
akwai wani abinda ya rabamu maganan zuce nake wai har mun iso kenan amma kuwa garin
babu nesa kofar aka bude min na fito gabana yayi mummunan faduwa sakamakon abinda
nagani.....

Päge 8

!Y@RIM@ J@L@L!

Nah halima musa akano (leeemat )??


Me zan gani,ganinmu nayi a gidan sarkin Zaria me muka zo yi anan nayi tambaya a
raina amma babu amsa wani bamgarin cemin yayi kila kunzo gaisuwa ne ko kin mance
sarkin Zaria aminin dad dinki ne,gimbiya mutafi naji muryar wata na mace namin
magana tafiya take ina binta a baya har muka iso wani side muna shigowa muka tarar
da wata mata daga ganinta kaga Mace mai sarauta saboda yanayin zamanta cikin
kasaita fuskar ta a daure yanda naga matan sukayi haka nima nayi muka gaida ita
amsawa take kamar dole nan da nan haushi ya kamani Allah yasa nima ba talaka bace
da za'a raina min wayo muna zauni kusan minti talatin amma batace mana komai ba ni
kuwa na kumbura saura kadan yarage na fashe ina shirin zan mike kenan sainga wacce
muka shigo da ita tace uwargijiya samu shiga can,ban ma tsaya sauraron abinda
zatace ba na fita muka danyi yin tafiya sosai sa'annan muka shiga Wow abinda na
fada kenan sakamakon daular da nagani a falon sai kamshin turare ke tashi a falon
muka zauna saiga wata mace kyakyawa ta fito daga wani daki da Fara'ar ta ta karaso
sannu da zuwa tashi tashi ki zauna a kujera tacemin amma nace mata a'a nan ma ya
isa kaina a kasa cikin jin kunya,ai nan gidan ku ne kar kiji kunya kinji murmushi
kawai nayi aka kawomin kayan shaye2 da na ciye2 ruwa kawai na sha,muka cigaba da
hira da ita inda take tambayata ance nagama karatu koh eh nace mata sa'annan tace
ai munso muzo amma fu'ad ya kiya a raina nace waye mai wannan sunan kuma har wajan
karfe 8na dare ina wajan sa'an muka nufe wani gu nisa da gidan sarkin ko Kuma nace
a baya gidan yake katoton gida aka shigar dani sa'an matar tace min nan ne gidanki
na daga ido ina mai kallonta saitace sunan indo amma anfi sanina da jakadiya duk
abinda kike da bukata zaki iya aikowa a kirani ta fice ta barni a gun da tambayoyi
a zuciyata...

Päge 9

Written
By
Leeemat??.....

[3/21, 5:45 PM] +234 703 003 6037: !Y@RIM@ J@L@L!

Nah halima musa akano(leeemat)??

Na shiga toilet nayi wanka ina fitowa na sauna a kan stool na dressing mirror ina
shafa mai domin komai yana gun abin mamaki duk maiyukanda nake anfani da shi ina
gama shafawa na zauna inata tunani bangane abinda ke faruwa ba jiran jalal kawai
nakeyi yazo yamin bayanin mekefaruwa ina cikin tunani naji an budi kofa gashi Kuma
banda komai a jikina na mike da niyyar dauko wani abu na rufe jikina amma is too
late me kikeyi haka kamar wacce bata da gaskiya naji yafada na juya da niyyar masa
rashin mutunci amma saina tuna da alkawarinda nama dad dinmu sainayi shuru matsowa
yayi kusa dani najada baya ya kamamin baki ya murda kara na saka domin wani azama
naji rashin kunyan da kika saba zakimin?kin dai san da da yanzu ba daya bane yanzu
sai abinda nace Kuma sai abinda naso,banason gardama idan nayi magana sa'annan idan
na kiraki kar ki bata min lokaci ko me kikeyi ki barshi kizo inba abinci kike
kikedafawa ki barta kizo inya so ya kune zaiki dafa wani tunda dai abinci na ne
kindai ji abinda na fadamiki koh? Daga masa kai nayi ya kara matse min baki da baki
na miki magana ko da kai kara na sake saboda yanda yake min da bakin hawaye na bin
kunci na sa'annan ya sake min bakin saina ce masa babu yanda zana amsa maka bane ai
saboda hannun ka na baki na juyawa yayi ya fice abinsa jalal nace masa ya juya yana
zuwa inaja da baya hannuna ya kama ya saka farcinsa a fatar hannunta kara na sake
sa'annan yace baki da kunya koh?jalal kika kirani yanzu mijinki nake ba mai kwanki
da guga ba ki san sunanda zakina kirana ba jalal ba,me ke tafe dake na sassauta
muryata sa'annan nace kaya nake son na saka ya nufe drower ya cire min night gown
mai kyaun gaske ya bani yayi yafiyar sa yana kaiwa bakin kofa ya cemin daga yau
abincina ya dawo hannun ki kai har dama wanki na yayi tafiyarsa,zaunawa nayi a
bakin gado na sake kuka mai tsuma rai oh ni simra na shiga uku meke shirin faruwa
dani ne kar dai ace Y@RIM@ J@L@L na aura? Ku biyone domin jin wanine jalal....

Written
By
Leeemat ??..

[3/21, 5:45 PM] +234 703 003 6037: !Y@RIM@ J@L@L!

Nah halima musa akano(leeemat)💮

Päge 1⃣1⃣

Na kasa bacci sai juye juye nake tayi ga yanayin garin Zaria da sanyi ni kuma ban
iya kwanciya ni daya ba tare da naji dumin jikin wani ba,ko a gida haka nake manne
wa jalilah saboda banason sanyi ga kuma tunanin auran da nayi bansan a zahiri jalal
mai wanki da gugan gidan mu na aura ko kuma yarima jalal dan sarki na aura ba,haka
dai tunani yamin yawa ga sanyi ya daman kamar nayi kuka bani dayin bacci ba sai da
asubah(kunsan dai shaidan babu abinda bazaya iya ba sai lokacin sallah na samu Mai
dadin gaskiya).ban tashi ba saida naji saukan ruwan zafi a jikina kuma kunsan Allah
inaga tafashashshan ruwa ya xuba min domin naji xafin ruwan har zuciyata dama ga
jikina baida kyau nan da nan wajan ya tasa kamar wuta ya kuna ni a gun,maganan da
yake yi yadawo dani maganan zuci da nakiyi,haka aka kuya miki a gidan ku da safe
bazaki gaida mijinki ki hada masa karin kumallo ba,wai ma tsaya kinma yi sallah
kuwa domin nasan a gida bakya sallah da wuri wai ke sanyi ko rau rau da ido nayi
nace masa wlhy sanyi yayi yawa banyi sallah ba fincikoni yayi ya fitar da ni waje
na dibo ruwa a wani randar da ake sallah a masallacin da ke gefen gidan ya zaunar
dani oya Fara alwala mugani ina taba ruwan hannuna yayi wani shocking na yarfa
hannuna ina mai bashi hakuri ya barni na shiga ciki nayi In kuma bai yarda ba na
dibo ruwan zafi nayi dashi,ga jikina duk a jike sakamakon ruwanda ya zuba min a
jiki,haka nake alwalar ina kyarma jikina sai rawa yake kamar wacce ake kada da
ruwan bazari ina gama nakasa tashi saboda yanda jikina ke rawa dibo wani ruwan yayi
yace tunda sanyi bai isheki ba bari ba karo miki a guje na shiga ciki ina idar da
sallah kichen na nufa na masa breakfast mai sauki na kawo masa da ruwan zafi a
flask ina ajiyewa yace nashiga kichen In bude kichen cabinet zanaga garin coffee na
kawo masa,ina kawo masa na juya zan tafi yace daga yau abinda zaki rinka kawo min
kenan in kin kawo min breakfast to kawai nace na juya na shiga ciki wanka na fada
ina fita na saka leshi mai ruwan pauda da ruwan kwai sai da ratsin purple gaskiya
favourite colour dina kenan(pink yellow and purple ) ina gama na fita na tarar da
bayanan na dan leko waje na aika a kirawomin jakadiya na komu ciki na tarar da
abinci a kan dining table na zauna sainaga note a gefen cooler din ina budewa
sainaga a rubuta abinci ne daga gun hajiya ina budewa naga su kayan mu da gargajiya
ne naci sosai na kai saura kichen na zauna a falo ina jiran jakadiya ta karaso
banfi minti biyar da zama a falon ba sainaji salama na bada umurnin a shigo tana
shigowa tafara kwasar gaisuwa na amsa sa'ananan na gaida ita tare da fada mata
bukatata nason ta fadamin labarin jalal murmusawa tayi sa'annan tace tohhh..

!Y@RIM@ J@L@L!

Nah halima musa akano(leeemat)💮

Päge 1⃣2⃣
Sarki jalaludden muhammad shine mahaifin yarima yana da mata biyu sarauniya amina
itace uwargida kuma matarsa ta farko auran gida aka musu inda sarki bayasonta itace
ke so asiri suka mar har ya aure ta anyi aure shekara daya ta haife masa na mace
yayi murna sosai ta biyu ma haka mace bai damu ba saboda masanin adini ne sosai, ta
uku ma mace duk bai damu ba mutanin fada suka bashi shawara akan ya kara aure mana
murmushi yayi sa'annan yace mu kara hakuri mana dodo yaran nawa ne uku fa insha
Allah mu tsaya muga abinda Allah zayayi nan gaba mana sarauniya amina kuwa magana
yazo kunnin ta akan ana shirin sarki ya kara aure idan bata haife magajin sarki ba
hankalinta ya tashi ta fara shige shige domin ta samu na miji har Allah ya bata
wani cikin murna ba'acewa komai domin wani malami yace mata zata haife na miji haka
dai kowa a masarautar yana jira sammanin na miji zata haifa haka dai ranar da zata
haihu gidan sarki ko ina shuru kake ji domin kowa ya kasa kunne domin yaji me za'a
fada haka dai ta haihu lafiya anata sanarwa ni kuwa leeemat na kagu naji me aka
samu abinda kunnuwa na suka jiyu ya saka wayata faduwa....

Written
By
Leeemat💮....

[3/21, 5:45 PM] +234 703 003 6037: !Y@RIM@ J@L@L!

Nah halima musa akano(leeemat)??

Päge 1⃣3⃣

Kunnuwa suka jiyu min Allah ya raya mana gimbiya yar sarki bari mu leka dakin mai
jego sarauniya amina kuwa babu abinda take sai kuka tana Allah ya isa wa malamin da
yace mata na miji zata haifi saboda ba'udan kudin da ta bashi babu yanda aka iya
anyi suna amma ba'a dadin rai ba bayan sati biyu an hadu a pada waziri ya fada ma
sarki akwai wata yarinyar da ya yaba da hankalin ta a gidan wani makocina ko za'a
daura muku aure da ita insha Allah za'a samu abinda ake so,sarki yace za'ayi haka
waziri yace babu abinda baza'ayi ba yallabai sarki yace to amma zanji mu dan gana
da ita,waziri yace babu damuwa basai ka tafi ba sarki yace a'a zan tafi kar ka damu
haka dai sarki ya shirya suka tafi saiga sarki a gaban budurwa ana hira abin gwanin
sha'awa,sarki ya kasa kwanciya sai tunanin fa'iza haka dai ba'a dauki wani lokaci
ba aka daura aure amarya fa'iza ta tare a gidan mijinta saidai wani abun mamaki
tunda aka kawo ta bata kara ganin angonnata ba kusan wata daya kenan ta rame saboda
damuwa sallah kuwa babu dare babu rana tana kai kukanta ga rabbin izzati ya karkato
mata da kan mijinta kareta saboda tanajin lbr uwargidan ta da biye biye gefen
sarauniya amina kuwa tunda taji lbrn sarki na tafiya hira da tashi tsaye da shige
shige har Allah ya bata sa'a asirin ya kamashi a ranar da aka kawo amarya,fa'iza
kuwa babu irin abinda bata gani da dare intana barci amma sakamakon adu'a datakeyi
aka dai take ta fama wulakancin Kala kala babu wanda bata gani daga gun sarauniya
har kuyanganta haka dai take hakuri har Allah ya amshi adu'ar ta.....

!Y@RIM@ J@L@L!

Nah halima musa akano(leeemat)??


Päge 1⃣4⃣

Ranar AL'amis da dare ta idar da sallah isha'i kenan tana adu'a saitaji anyi salama
har tsoro ya kamota tana tunanin waye kenan da Daren nan ta mike ta budi kofar wa
zata gani sarki tayi wani ajiyar zuciya sa'annan ta mashi gu ya shiga ciki ya zauna
ta kulle kofar ta kawo masa ruwa da abinci domin bata rasa da abinci a gidanta yayi
murmushi yace amarya bakya laifi kamar ko kinsan banci abinci ba murmushi tayi ta
gaidashi ya amsa yana mai kallonta tare dacin abinci yana santi ita ku mezatayi sai
dariya ya gamaci ta Karo masa ya cinye ya karace a karo masa binsa kawai tayi da
ido ta tashi da kawo masa yankakkyan kayan marmari yasha sosai sa'annan ya dan
kishingide,yallabai yallabai tashi ka tafi dare yayi fa sosai domin har ya Fara
bacci lumshe idonsa yayi yace korata kike tace waneni yayi murmushi yace to yau a
anan zan kwana zuciyarta yayi fari tare da godiwa Allah daya amsa mata adu'ar
ta,cikin damuwa tace anty amina fa yace tana bangaranta mana ai tasan inada amarya
ai murmushi nayi cikin jin dadi nace to tashi kayi wanka yallabai na hada masa ruwa
yayi kwanka kafin ya gama kwankan na fitar masa da rigar bacci na ajiye masa a kan
gado yana fita ya ganni a kwance cewa yayi har zaki kwanta eh kawai nace masa ya
gama saka kayansa ya kwanta kusa dani,inda yafara sarrafani nikuwa mezanyi sai
adu'ar mijina ya dawo gareni har yana niman hakkinsa kayana ya fara cirewa sa'annan
tsoro ya dirar min amma ban nuna masa ba saboda inajiran ranar da zaidawo gareni
kuma ace ban kwata ma kaina yanci ba haka dai na daure ya kawar da budurcina kuka
nake na farin ciki domin adu'a nake wa iyayena da suka bani tarbiya mai kyau har na
kawo abinda kowacce mace take burin kawowa gidan mijinta,sarki kuwa sai hakuri yake
bani tare da lallashina a daran ya min wanka yayi nasa muka sake kwanta bacci har
washegari sa'annan na tashi na hada masa kari yace ya huce pada......

Written
By
Leeemat ??

[3/21, 5:45 PM] +234 703 003 6037: !Y@RIM@ J@L@L!

Nah halima musa akano(leeemat)💮

Päge1⃣5⃣

Haka dai sarki ke zowa gidan har sahon sati daya kafin ya koma bangaren
sarauniya,haka dai rayuwa ta cigaba da tafiya wani rana fari wani baki,yau da gobe
babu wuya a gun Allah na waye gari da son cin goroba a rana daya sainaci guda goma
ko fin haka sa'annan Allah ya taimakeni babu wani rashin lafiya ko Kuma wani
laulayi shiyasa ma cikin ya haura wata bakwai babu wanda ya sani sai sarki haka dai
muke rainon cikin har ya kai watan haihuwa sarki yace bazan haihu a Nigeria ba aka
mana shirye2 tafiya India kafin sarauniya amina tasan ina da ciki nan da nan ta
huce gidan malaminta inda take fada masa abinda yafaro murmushi kawai yayi yace
mata yanzo me kike so tace masa ita tanason indan suka tafi kar su dawo su mutu
daga ita har abinda yake cikinta,malamin dariya yayi yace bazayaji ba saboda matan
tana da kariya sosai amma abinda zan iya miki shine idan ta haihu saimu karkata
hankalin mijinki ya dawo gareki bakince tare zasu tafi ba ta daga masa kai yace to
zaki iya tafiya ta danka masa kudi masu yawa tayi tafiyar ta.kafin ta dawo amarya
fa'iza Sun tafi tana dawowa ta kira wayan sarki take fada masa akan mamanta ne bata
da lfy ta tafi gaida ita to kawai yace tare da cewa Allah shi bata lfy tace ameen.
Sun sauka garin India inda suka tafi masaukinsu saboda sarki yana da gida a gun
haka dai suka cigaba da rainon cikin har ranar haihuwar ta yayi ta haife yaron ta
na miji mai kama da ita murna kuwa ba'a cewa komai ya kira waziri yafada masa
abinda aka samu masarautar kowa na cikin farinciki inda sarauniya amina na cikin
bakin ciki har kuka sanda tayi...

!Y@RIM@ J@L@L!

Nah halima musa akano(leeemat)💮

Päge1⃣6⃣

Sarki ya masa huduba da fu'adudden inda suke kiransa da fu'ad bayan sati daya suna
shirin dawowa domin ayi suna amma fu'ad ya tashi da masakaicin ciwo suka dakatar da
tafiyan su aka kaishi asibiti yayi kusan wata daya a asibiti yana warkewa doctors
din suka basu shawara Akan su guje abinda zai saka shi kwanciya wai da sunan baida
lafiya saboda shi irin mutaninda in rashin lfy ya kwantar da su sai Sun kasance a
kwance na sahon wani lokaci kafin su farfadu suka dawo gida,haka dai suke kula
dashi har ya kai shekara uku suka saka shi a makaranta a Indian tare da saka shi a
islamiyya.sarki kuwa anata kiransa a gida akan ya dawo kan milkinsa yanajin su
saida yaga idan ya musu haka bai kyauta WA kansa ba sa'annan ya fara shirin bar
India a ranar da zaya dawo ya fadawa amarya fa'iza akan da zarar ya kammala primary
dinsa itama ta dawo gida ta barshi ya cigaba da karatun sa ta masa korafi akan
lafiyansa yace mata akwai wanda zasuna kula dashi Kuma bayason tayi nisa da shi
haka dai ta hakura tacigaba da zama da danta har ya gama primary an masa komai na
secondary sa'annan tayi shirin dawowa gida Nigeria inda sunyi kukan rabuwa,fu'ad
kuwa yayi kuka sosai saida ta hanashi kafin yayi shiru tana tsoron kar kukanda yayi
ya saka masa wani rashin lafiya,haka dai ta tafi ta barsa dashi da masu zama da
shi.
A lokacin sarki ya dawo gida kuwa sarauniya ta rinka murna ita a nata tunanin
maganin da aka masa ne bata kuwa san saboda mutaninsa ya dawo ba...

Written
By
Leeemat 💮......
.
[3/21, 5:45 PM] +234 703 003 6037: !Y@RIM@ J@L@L!

Nah halima musa akano(leeemat)💮

Päge 1⃣7⃣

Amarya fa'iza kuwa tundaga kan fu'ad bata kara koda batan wata ba,bata nuna
damuwanta ba saima godiwa Allah tayi tunda har ya bata fu'ad,inda kuwa a bangaren
sarauniya taci alwashin sai ta halaka fu'ad ko badade ko bajima toh yaya kenan
za'ayi mundai ji furucin sarauniya amina,bari mu leka India.
India kuwa fu'ad tun yana damuwa har ya dawo ya daina damun kansa inda ya mayar da
hankalinsa kan karatun sa yana gama jss three sai aka applying masa school of army
dake New Delhi saboda fu'ad akwai son soja ya fara daga ss1 har Allah ya taimaka ya
gama sa'annan yacigaba daga inda ya tsaya yayi karatunsa har ya gama lafiya sukayi
passing out parred ya fita da second leutinant suka dauke sa aiki inda suke zama a
barriki,aiki yake cikin gaskiya da rikon amana inzasu tafi yaki kuwa a koda yaushe
suna cikin nasara idan wayansun su Sun samu rauni shi yake musu treatment saboda
Allah ya bashi wannan baiwar....
!Y@RIM@ J@L@L!

Nah halima musa akano(leeemat)💮

Päge 1⃣8⃣

Akwai wani yakin da suka tafi duk da dai su sukayi nasara amma mutaninsu sunji
rauni sosai bayan fu'ad ya gama treating dinsu sai major dinsu yayi kiransa a
office dinsa yanatafi ya sara masa yanda dai munsan sojoji ke yi yace masa ya zauna
yana zaunawa saiya fara da cewa dama wani sharawa na kawo amma bansan ya zaka dauke
a abinba murmushi fu'ad yayi yace sir ai shawara kace ai nasan mai kyau ce fada min
ina saurarunka sai yace masa naga kana da baiwar treating mutani to me zaisa bazaka
tafi course na likitanci ba iyaso dai idan ka dawo sai ka cigaba da aikin ka anan
kana duba mana marasa lafiya,fu'ad kuwa ya amince suka turashi course na shekara
hudu a California yaso ya tafi Nigeria ya sallame ma'a dinsa amma amarya fa'iza
tace ita tafi son idan zaya taho ya taho gabadaya haka dai ya hakura tare da
missing dinta.....

!Y@RIM@ J@L@L!

Nah halima musa akano(leeemat)💮

Päge1⃣9⃣

Ya tafi California tare da samun nasarar karatunsa har ya gaima saidai karatun yaso
yadan bashi wuya kadan amma da taimakon Allah da ta adu'a ya gama ya dawo India na
nasarori sosai inda yayi kudi sosai abin sai wanda kagani kawai,yayi aiki a India
saida ya kai matsayin major kafin ya dawo Nigeria inda aka hada masa liyafa ta ban
girma saboda tunda amarya fa'iza ta tafi India da cikinsa sai a ranar aka Fara
ganinsa amma a garin Zaria babu wanda baisan labarin dan sarki ba duk da ba wanda
ya taba ganinsa haka dai a ranar da ya sauka garin Zaria cewa zakiyi shugaban kasa
ne yazo haka dai suka masa liyafa akaci aka sha,inda mata kuwa sai kawo kansu suke
amma duk sonda suke ikirarin suke masa na karya ne wasu saboda kudinsa wasu Kuma
saboda mulki,haka dai ya tayi har ya auro ki amma bansan ya akayi har ya yarda an
muku aure ba saigashi kina tambayata labarinsa nasan duk yanda akayi bakisan waye
yarima dan sarki ba.daga mata kai nayi tare da cewa tabbas bansan shi ba amma
jakadiya meyasa ake kiransa da jalal bayan sunan sa fu'ad toh me karatu ku biyomu
domin jin meyasa ake kiransa da jalal taku mai son nishadantar da ku leeemat

Written
By
Leeemat💮.....

[3/21, 5:45 PM] +234 703 003 6037: !Y@RIM@ J@L@L!

Nah halima musa akano(leeemat)??

2⃣0⃣
Yarima fu'ad Wanda akafi sani da yarima jalal duk da dai ban zauna da shi a
lokacinda yake India ba amma yarone mai hankali ya tashi da taimakon na kasa da
shi,ko a makarantar su in zasu zana jarabawa yakan taimake wanda basu sani ba duk
da yana fuskance matsala saboda ana hukuntashi amma bai hanashi taimako ba sa'annan
tun bai mallake hankalin kansa ba yake bayar da zakkah saboda malaminsu yamusu
WA'azi akan idan mutun yana da arziki da kudi sosai to Allah yace ya bayar da
zakkah tun daga lokacin ya fara zakkah saboda anasa tunanin shima yana da kudin da
zaya iya baida zakkah,da azimi kuwa abin ba'acewa komai saboda yana saka a dafa
abinci kullum ana kaiwa masallatai tare da gidan marayu da yamma kuwa idan za'ayi
breakfast watan lokacin sha ruwa kenan tea ake da bread a bawa basu bukata,yayi
gidan marayun da bazana iya lissafa miki ba da yake daukan nauyin komai nasu cin su
da shan su duk tare masallatai,lokacinda ya dawo Nigeria kuwa abinda yake a
masarautar nan sai san barka saboda duk wani abinda mai martaba sarki keyi haka
yarima yakeyi kamar yanda bayi sa'annan ya hada musu aure da mazajansu bayi
yantattu sa'annan shi yake komai na auran ya kuma bawa mazajan aikin yi.
Saboda hali irin na yarima fu'ad babu abinda bai dauka ba a hali irin na mahaifinsa
shiyasa muka lankaya masa ko kuma nace muna kiransa da sunan mahaifinsa wato
❗Y@RIM@ J@L@L❗.......

Written
By
Leeemat??

[3/21, 5:45 PM] +234 703 003 6037: !Y@RIM@ J@L@L!

Nah halima musa akano(leeemat)??

2⃣1⃣

A ranar na dafa masa abincin da ni kaina bansan na iya dafa abinci mai dadi sosai
haka ba,ina kammalawa wanka na fada nayi sallar asr na fito falo na zauna ina kallo
domin inada tabbacin zaya shigo idan ya dawo daga gun aiki saboda duk da dai ban
zauna da shi sosai ba amma irin mutanin nan ne da idan nauyi na kansu suna kokarin
saukewa ban idar da tunanin da nake ba na jiyu sallamar sa na amsa ya shigo na
gaida shi ya amsa sa'annan na kawo mar abincin sa ina ajewa na shige daki mintina
kadan naji yakirani (R@NI S@HIB@)a raina nace na yau kuma kenan na gobe saiyafi
haka yau kuma sunan da za'a kirani dashi kenan a gidan mu SONI@ yake kirana oho ai
na ma mance dan India ne jin wani kiran nayi da sauri na fito gani wai ke wacce
irin mara hankali ce ke sau nawa na fada miki akan a duk lokacin da zaki kawo min
abinci inason ki kawo da coffee ya hakuri na mance ne shiyasa kafansa ya dura akan
kafata ya matse wani kara na saka sa'annan yace kinga wannan zaya tunatar dake a
duk lokacin da zaki kawo min abinci kichen na huce na kawo masa zan huce daki yace
dawo nan ki zauna haka kike ganin mom keyi a duk lokacin da ta kawo ma dad abinci?
na dawo na zauna a kujeran da ke fuskartansa ina mai kallon irin halittar da Allah
ya masa.....

!Y@RIM@ J@L@L!

Nah halima musa akano(leeemat)??


2⃣2⃣

Fu'ad dogo ne sosai na nuna wa sa'a fari ne shi irin dai fatar indiyawa sa'annan
ga sumar sa inda dai kuka ga na India a raina nace dole komai naka ya fita irin
tasu ko saboda komai naka da rayuwan ka a garin kayi shi Wow beauty point dinsa
kuwa ba'a magana saboda duk abinda yake ko magana yake ko karatu zakaga ya lutsa
baton idanunsaa kuwa sleeping eyes gareshi ga idon manyan2 dasu kamar an masa gorin
idon shiyasa idan ya daga ido ya kalleka duk fitsarancinka sai ka natsu saboda
yanda idon keyi like magic,fatar jikinsa kuwa kina ganinsa kawai kinsan dan hoto ne
saboda yanda skin dinshi yake fresh ga wani sheki da yake yi kamar ba soja
ba,kirjinsa kuwa a bude yake tafiya yake a baude kamar dai soja.idan an zo batun
magana kuwa kamar ana saka shi dole ne kafin yayi wani magana mai tsayi sai da wani
kwararrar dalili sa'annan yana maganar tare da lumshe ido kamar mai shirin bacci
kai dole ne ma idan yana magana ya bake sha'awa.mari na ji amma hannun nasa kamar
auduga naji a firgice na kallesa yace me haka da wani kallo kamar tsohowar mayya
kallonsa kawai baki a budi saboda yanda idonsa keyi a raina nace maiyasa ban taba
lura da fu'ad kyakyawa bane sai yau......
Leeemat ??

[3/21, 5:45 PM] +234 703 003 6037: !Y@RIM@ J@L@L!

Nah halima musa akano (leeemat)💮

2⃣3⃣
Inma maitar kika ci to kurwata kur yafada, bude bakina nace masa ai haka mom takewa
dad in yana cin abinci ko ba kai kace min inyi abinda mom ke ma dad ba nayi maganan
cikin shagwaba kamar zanayi kuka kallo yake saboda yanda na masa kyau tashuwa nayi
nace masa nima kurwata kur yanda yafada da hausansa kamar na makoya amma fa idan
kaji zakayi zaton slangs na hausa yakeyi amma hausan ne bai tsaya masa a baki sosai
ba Cup ya dauka ya jefeni dashi kafin na shiga daki Cup din ya saman a kafa faduwa
nayi a gun ina mai yarfar da hannu na alamar zafi nan da nan jini ya fara
gangarowa.fu'ad kuwa ko a jikinsa saima kama gabansa da yayi a haka na shiga bayi
na wanke ina saka ruwan dettol ina ihu kamar wanda aka sakani dole saboda zafi.haka
dai nayi jinyar kafata har ya warke fu'ad kuwa ko sannu bai taba hadani da shi ba a
cewar sa ai nima likitace zana iya kula da kaina basai an kula dani ba.

*************************⬇**********************
************* Top Hausa Novels ****************
*************************⬆ **********************

DOWNLOAD More complete Hausa Novels, Education Books, Adventure, Drama, Mystery,
Religion, Fiction, Non-Fiction, Romance, Meimor, True Life Stories & Others from
our blog.

Visit > https://www.thn.com.ng

Ka tura mana sako ta adireshinmu na email, domin tuntubarmu ko turo mana hausa
novel ko kuma post.

Email > tophausanovels@gmail.com

******* FOLLOW US ******


Facebook: Top Hausa Novels

Twitter: Top Hausa Novels

Telegram Channel: https://t.me/tophausanovels

Telegram Group: https://t.me/tophausa

Haka kuma domin shiga kowanne daga cikinsu za ku iya ziyartar shafin ku yi search
na TOP HAUSA NOVELS, hatta facebook group dinmu ma za ku samu.

********************** ⬇ **************************
*************** Top Hausa Novels ****************
********************** ⬆ **************************

!Y@RIM@ J@L@L!

Nah halima musa akano(leeemat)💮

2⃣4⃣

Tashuwar asuba kuwa babu abinda ya janza domin kuwa kullum shi yake tashina nayi
sallah sa'annan da ruwan zafi haka dai har na saba tashuwa da ruwan zafi a jikina
ni kuwa wai na irin tashi wani rana kafin yazo din nan bana iyawa saboda sanyi
masarautar ko ina bishiya kamar wani dauji.nayi wata daya chaf kafin na fita a
gidan muka nufa fadan sarki jalal muhammad mulki akwai wahala sannan akwai dadi
tafiya muke cikin kaya ta alfarma duk inda muka huce gaisuwa ake mana fu'ad kuwa
sai amsawa kawai yake cikin Fara'a da kamala kawai sainaji sonsa ya kara tasiri a
cikin zuciyata muna isa fada muka tarar babu kowa sai sarki yana jiran mu muna
shiguwa da murmushi a fuskarsa yace yau na bawa kowa hutu ya zauna da iyalansa
inason na gana da ya ta murmushi kawai nayi muka gaida shi cikin girmamawa yace ma
fu'ad babu ruwana da kai fu'aduddeen tunda kanamin rauwar yata sai yau kaga damar
kawo min ita susa keya yayi alamar kunya ni kuwa kamar na nitse a kasa saboda kunya
ya juya ya fuskanceni bari muyi maganan da da mahaifi fu'ad yawani tura baki kamar
wani karamin yaro Papa wato anyi sabuwar ya shine kuka manta dani daga kai har ma'a
ko to shikenan babu damuwa kowa da ranar shi,sarki kuwa ko sauraransa baiyi ba yace
min ya ta nace na'am babu wani matsala ba ko na juya na kalle fu'ad yanda yamin da
idonsa ya saka ni saurin kawar da fuskata.sarki yace min kar kiji tsoro ki fadamin
idan da wani abu budi bakina sainace.......

Written
By
Leeemat💮....
[3/21, 5:45 PM] +234 703 003 6037: !Y@RIM@ J@L@L!

Nah halima musa akano(leeemat)💮


2⃣5⃣

Babu komai fu'ad ya sauke wani ajiyan zuciya sa'annan yayi murmushi yace Papa kana
shakku da irin rikonda nake mata ne sarki yace a'a bada kai nake ba kamin shuru
amma ya ta kamar da magana a bakinki amma kin kasa fada min nayi murmushin da bai
kai zuci ba na rasa wani karya zana masa sai wani dabara ya fadu min sainace masa
dama so nake na ga mom da dad amma yace ba yanzu ba nan da nan fuskar sarki ya
sauya ya fara fada amma fu'ad ka ban kunya ace yarinya nason ganin iyayenta amma ka
kasa kaita su gana ina kai kullum saikaga naka iyayen amma kar ka sake yin haka
Kuma ko kullu yaumin take son ganinsu to ka tabbata ka gaita.kai daga yau na kafa
doka duk ranar jumma'a a kaita itama ta gaida iyayenta godiya mukayi sa'annan muka
nufa bangaran sarauniya amina,sallama mukayi fu'ad ya zauna tare da cewa mamuji
ganinta mukayi ta fito a daki cikin shiga ta alfarma tana ganinmu da Fara'arta ta
karaso tana fadin a'a yata tashi ki zauna a kujera mana saboda a kasa na zauna tun
farkon zowana a kasan ma naga irin tarbar da ta min ballatana zowana ta biyu amma
mamaki ya hanani rufe baki.cikin mamaki nace a'a nan ma ya isa ta hada fuska tare
da cewa nace miki ki tashi ki zauna sa'annnan na tashi na zauna ta saka aka kawo
mana abin mutsa baki dukkan mu mukace mun koshi saita ce oho my son yau Kuma baza'a
ci abinci a gidana bako saboda an taho da amarya ko Kuma dai kana tsoron karta xane
ka inkun koma gida ne dariya kawai mukayi muka sallameta sai gidan mahaifiyansa
muna shigowa na cire rigarda ke cikina saboda zafi na kwanta a three seater.....

!Y@RIM@ J@L@L!

Nah halima musa akano(leeemat)💮

2⃣6⃣

Muna komawa gida yana bude kofa na shiga daki a guje domin nasan nayi laifi amma me
kafin na kulle kofata ya shiga dakin ya cafkoni ya jani zuwa bangon dakin yana
kokarin sunbatata ina kokarin kwace kaina hannunsa ya tallafe kaina ya fara kissing
dina,naji dadi amma sai zafi nake ji kamar labban bakina zai fito saboda zafi yana
gama yace ki kara saka papa yamin fada saboda ke sa'annan karki san irin maganan da
zaki rinka fada masa wannan kadan na miki yafice a dakin hannu na saka a labbana
ina taba saboda zafin da nakeji.washegari na kai masa abin kari tare da coffee
dinsa na mance da kashejin da yake min na gaisuwa bugu naji a bakina wani kara na
sake saboda zafin da ya ziyarce ni da sauri na gaida shi sa'annan na saka hannuna a
baki naga jini da sauri na shiga daki na nufe gaban mirror ina duba bakina sainaga
ya kumbura a raina nace me ya saka bakina yin haka ba zanace dai bugun bakina da
yayi ne ya saka bakina haka ba,ok ko dai kiss da yamin jiya ne yasaka bakina yin
haka amma kuwa Allah ya isa na fada tare da cire anpiclox na sha,
Ina zaune a falo da kumburarran bakina yace min yau jumma'a amma bazaki tafi gida
ba sai bakinki ya warke saboda kar suce ban iya riko ba a raina nace dama ka iya
ne,amma fili sai nace masa to Allah ya kaimu ya kalle ni cikin mamaki yace hmm baki
ya mutu ko da kuwa na nuna miki ko ni waye da kin min wani rashin kunya....
!Y@RIM@ J@L@L!

Nah halima musa akano(leeemat)💮

2⃣7⃣

Cikin ikon Allah har bakina ya samu sauki jumma'a ta kewayo ya kaini gidan mu na
shiga da ihu ina mom domin nasan tana gida saboda ranar jumma 'a bata dadewa a
office bayan mun gaisa nake fada mata abin AL'ajabi jalal yaron aminin dad ne
sarkin Zaria mom itama kanta tayi mamaki domin yan uwanta babu wanda ya fada mata
murmushi tayi cikin cin dadi tare da cewa kai amma nagode wa Allah amma dad dinku
bai taba cin min komai ba kullum ina cikin damuwa ya tura ko su hassan da hussaini
ne su duba ke amma saiyace lafiyan ki kalau amma meyasa kika rame haka nasan ki da
rashin cin abinci ko Kuma dai kina da wani matsala ne ki sanar dani murmushi nayi
nace mata wlhy babu komai mom komai lfy kalau kinsan yau da gobe sai Allah bare ni
da na tsince kaina a cikin sarauta kinga kuwa sai a hankali zana saba muka hira
kafin na ce mata zani gidan jalilah tacemin abincin fa nacemata in na tafi gidan
jalilah zanace mom tace da take fama da rashin lfy shine zaki sakata wani aikin ko
domin nasanki da Sun jikin babu gara babu dalili a raina nace da kuwa kinsan irin
aikin da nakeyi yanzu da baki cemin mai son jiki ba ina shiguwa gidan sainaga
jalilah a jikin mijinta saina koma baya nayi sallama ganin jalilah nayi tana oyoyo
sis simra cikin dariya nace ya akayi kika gane muryata tace amma ai ko a cikin
magagin bacci ne san gane muryanki,mijinta kuwa ya gaida ni sa'annan yace hmm yau
anga yaya simra na huta da kuka kullum waini inkai gun ki batasan a wani hali kike
ciki ba dukkan mu mukayi dariya sa'annan ya fice a gidan to ni bari na fita tunda
ga yayanmu ta zo ko cikin shagwaba tace masa yaushe zaka dawo cikin lallashi yace
nan bada jimawa ba,kallon such as nake cikin sha'awa saboda yanda suke tafiya da
rayuwansu ta birgeni sosai......

!Y@RIM@ J@L@L!

Nah halima musa akano (leeemat)💮

2⃣8⃣

Sis simra ina magana kinyi shuru na juya ina kallonta ina mai murmushi rayuwanku ne
abin sha'awa jalilah tace yaya simra mu bar wannanan maganan yaya gidan yake ko
kuma nace kauyan yake cikin murmushi tace jalilah a garin nan muke gidan ma a gidan
sarki aminin dad jalilah cikin cikin mamaki tace kina kardai nace jalal shima yana
daga cikin bayin gidan ne amma yantacce simra tace ko daya jalilah ina munajin
labarin yarima jalal a lokacin da muke gida da har kike damuna da kinason kuwa ki
ganshi saboda irin labarin da ake bayarwa akansa to ba wani bane yarima jalal sai
jalal mai mana kwanke da guga.cikin kaduwa jalilah tace kina nufin jalal shine
yarima jalal dan sarki jalaluddeen muhammad! Murmushi nayi na tace mata kwarai da
gaske kina mamaki ko sa'annan na fara bata labarin shi amma bansan ya akayi har
yazo gidan mu ba sa'annan na fada mata irin abinda yake min saboda bama boyewa
junan mu sirrin mu ina kuka har na gama fada mata tare da cewa kinga abinda na masa
Allah ya juya lamarin ya zama mijina kuma walhy tunda an daura mana aure nayi
alkawarin masa biyayya amma shi babu irin wulakancinda bayamin hakuri jalilah ta
rinka bani tare da cewa kar ki damu wata rana sai labari saikinyi alfahari da auran
sa godiya na mata muka shigaba da hiranmu wanda duk nasa ne da tuna irin abubuwanda
yake mana lokacinda muke gida amma bamu taba lura da irin abubuwanda yake yi kamar
na jinin sarauta amma bamu taba gane ba har kusan magriba kafin na bar gidan ina
shiguwa gida na tarar da fu'ad na jirana gabana sai faduwa yake tayi kichen na
nufa na kawo masa abinci ina ajewa ya kama hannuna ya matse da farcansa nayi kaman
banji ba saboda mom na gun amma fa ina shiga kichen na duba hannuna naga har yana
jini ina shiga falo na tarar ko taba abincin baiyi ba haka muka tafi gida gabana
sai faduwa yake saboda fargaban abinda zan Tarar.....

Written
By
Leeemat 💮
[3/21, 5:45 PM] +234 703 003 6037: !Y@RIM@ Y@RIM@!

Nah halima musa akano (leeemat )??

2⃣9⃣

Muna isa gida yace na dafa masa abinci yunwa yake ji cikin mamaki nace masa amma na
kawo maka abinci kace bazakaci ba ka koshi saiyace to yanzu zanci ko kuma ban isa
na sakaki bane Allah ya baka hakuri na shiga kichen na masa indomie na kawo masa
yauwa wa ya baki izinin tafiya gidan jalilah cikin inna inna nace masa babu kowa
oho saboda kin rainani shine kika tafi ba Tare da izinina ba koh to yau zana
hukunta ke dai dai da laifin ki cikin kuka nace dan Allah ka yahakuri bazan sake ba
ko ta kaina baiyi ba ya huce side dinsa ya kawo kayansa ya watsa min a jiki tare da
cewa yanzu nake son ki wanke sa'annan ki goga saboda gobe zana fita radin suna
cikin hawaye na mike tare da kwashe kayan na nufa toilet na fara wanke kayan har
hannuna na jini saboda alkyabba ce akwai karfe2 a ciki amma haka na wanke ga idona
kamar zaya fada a kasa saboda baccinda nake ji ban gama wankin ba sai sha biyu na
dare saboda tsoro ban iya fita waje na shanya kayan ba a toilet na shanya nayi
zaman hour biyu amma kayan kamar yanzu na shanyata ganin karfe biyu ya huce har da
kwata ya sakani kwanciya nayi bacci da niyar da safe zan tashi na goga kafin ya
shigo. amma me cikin barci naji kamar ana zuba min ruwan zafi da sauri na mike tare
da bude ido amma hasken ranar da ya kashe min ido ya sakani rufe idona cikin sauri,
cikin fada yace har na fita suna na dawo amma baki tashi daga bacci ba ina kayanda
na sakaki wanki da guga cikin sauri na nuna masa hannuna daya tashi saboda wanki
nace masa wlhy na wanke amma ban guge ba fincikoni yayi muka fita falo yace oya
maza dauko ki taho nan ki goga yanzunnan ina shiguwa daki kuwa alwala nayi na yi
sallah da sauri sa'annan na fito da kayan na saka iron na Fara guga amma kamar
banayi fu'ad cikin sauri yace min ki danna hannunki sosai ko bakisan wannan
alkyabba bace cikin hawaye nace wlhy ina dannawa hannuna zafi yake min, nuna min
hannunsa yayi yace kinga kayanki abinda yamin?tun ban iya guga ba har na iya duk da
dai wani lokaci ina badawa a wanke tare da goga amma saida na kune saboda jaraba
irin nake cikin kuka na cigaba da gugan har na gama......

!Y@RIM@ Y@RIM@!

Nah halima musa akano (leeemat )??

3⃣0⃣

Amma duk da irin cin mutuncin da fu'ad ke min bai taba zagen iyayena ba shiyasa ma
ban taba nuna damuwata ba saboda nasan ni na masa laifi ba su ba kuma yana
hukuntani ba tare da su a ciki ba haka dai na cigaba da rayuwa a gidan fu'ad babu
abinda na nima na rasa ta fannin abinci har ma sitira sa'annan ko wani jumma'a ina
tafiya gaida iyayena abu daya ko kuma nace biyu shine kawai damuwata amma ni daya
yafi damuna wai ace ina matsayin matarsa amma ban taba tafiya side dinsa wai da
sunan gyarawa ba sai na biyu wani abu bai taba hadani da shi ba wai da sunan
tarayyar aure saboda yace saiya gyara min zama sa'annan zayayi zaman aure dani ni
wannan bayama damuna kamar hanani gyara masa makwancinsa sai bayin gidan su suke
gyara masa ni kuwa abin haushi yake ban amma babu yanda na iya saboda ya ce a duk
ranar da ya tarar dani a side dinsa ko kuma an fada masa saiya karairaya min kafata
kamar na muciyan nan shiyasa nake wa kaina kiyamallaini.....

Written
By
Leeemat ??...

[3/21, 5:45 PM] +234 703 003 6037: !Y@RIM@ J@L@L!

Nah halima musa akano (leeemat )??

3⃣1⃣
Yau ta kasance ranar juma'a mun dawo daga gidan mu kenan fu'ad na zaune a falo da
kofin coffee a hannunsa na zauna a kasa a gefensa nace masa dama so nake na maka
magana inajinki ya fada tare da cigaba da shan coffee dinsa dama dad ne ya min
magana akan aiki wai ya samu min aiki shine yace na fada maka saika amince kafin na
fara tafiya ina gama fada masa ya juya sosai yana mai kallona da sleeping eye dinsa
ya lumshe su saiyace min ina miki murna da samon aiki amma inason kimin wani aiki
guda daya kafin ki fara zuwa aiki sa'annan zuwanki aiki bazaya canja daga
abubuwanda kike min ba cikin murna nace masa me kake son na maka ka fadamin kuma
nayi alkawarin insha Allah zan maka shi,toh mai karatu saiku biyomu domin jin me
yarima jalal ke son a masa taku har kullum leeemat ??.

!Y@RIM@ J@L@L!

Nah halima musa akano (leeemat )??


3⃣2⃣

Kallonsa nake ina jiran ya fadamin me yake son na masa amma bai fada ba saima
cigaba da shan coffee dinsa da yayi ina zaune har ya kammala shanyewa saiyace min
wani baba nake son ki masa aiki a kafa ina medicine and surgery kika karanta na
daga masa kai yace magana nake miki da baaki ba da kai ba eh na amsa masa,ya cigaba
da cewa maciji ya sare shi babu inda ba'a kaishi ba amma idan kafar ya dauke
warkewa saiya sake dawo kamar sabo kuma wata uku kawai na baki kije kiyi tunani in
zaki iya to zaki fara tafiya aiki da zarar kin gama aikin amma in bazaki iya ba to
kinga zaman gida ya kamaki daman inda kika fi dace kenan yana gama yace to zaki iya
tafiya ina jiranki nan da two days mikewa nayi cikin kasala na huce dakina ina mai
tunanin abinyi, idan na tuna da kalmar da yake cewa wai daman zaman gida ya kamace
ni da gurbataccan hausa dinsa dinnan sainace raina ya kara bace (amma fa yanda yake
hausan ma abin a tsaya saurarune ).kai zana maka cewa mu mata zaman gida bamu ya
kamace ba ina gama tunanin abinda zana fada masa na kwanta sai barci.....hmmmmmmm
ku biyomu

Written
By
Leeemat ??

[3/21, 5:45 PM] +234 703 003 6037: !Y@RIM@ J@L@L!

Nah halima musa akano (leeemat )💮

3⃣3⃣

Washegari na gama hada masa breakfast na kawo masa da coffee dinsa ina zaune har ya
gama ya tashi ya koma falo ya zauna na bishi a falon nace masa maganan jiya ne nake
son nace maka na amince, cigaba da kallonsa yayi kamar babu mutun a wajan. daga
bisani yace min to Alhamdulillah gobe za'a kawo shi a dakin wajan nan zai zauna
bude bakina sainace masa ah meyasa baza'a kawo shi yau kawai ba nayi maganan ne
cikin gatsi har saida ya juya yayi kallona ni kuwa a raina murna nake saboda inada
nawa kimar tunda har an juya anyi kallona.cemin yayi abinda yasa ban kawo shi yau
ba saboda inason na gyara masa dakin ne tare da kayan aikin da zaki mishi kwabe
baki nayi na tashi alamun I don't care dinnnan na huce dakina tare da cewa Allah ya
kaimu fu'ad kuwa kallona yake baki bude saboda mamakin da na bashi. Washegari
abinda na saba yi kullum aka yau ma nayi ina jiran patient dina ba'a kawo shi ba
sai da yamma lokacinda ma na gama komai na gida nayi wanka sallah nake yi naji
sallamar fu'ad daya ga ina sallah ya fito falo ya xauna ina idarwa na gama adu'o
ina a raina nace wato ina sallahr ma bazaya jirani a daki ba sai ya bani wahalar
biyosa falo bayan abinda yake nima a guna bukatarsa ne ba nawa ba.na shiga falon na
xauna nesa dashi nace masa sannu da dawowa amsar da yabani wlhy haushi ya kamani
cewa yayi gashi an kawo shi zaki iya zuwa kiganshi ko ya tashi ya huce, raina a
jagule na tashi na bi bayansa

Oh ni leeemat bansan me ya same gimbiya simra ba ganinta kawai nayi tanata kwarara
amai 😳 ko dai abin ne an samu 🙈

Written
By
Leeeemancy💮

📢👏🏽📢👏🏽🎂🍰🍦🍕🍟🍔🍺🍺🍻🍡🍗🍣🍲🍞🍘HAPPY Birthday MAMAN ALEESHA wishing you happy many many


returns and may u celebrate more and more of it........
[3/21, 5:45 PM] +234 703 003 6037: !Y@RIM@ J@L@L!

Nah halima musa akano (leeemat )💮

3⃣4⃣

Ina dosowa kofar dakin nafara jin wari muna shiga dakin kuwa sai abinda ma ya karu
cikina har wani koowa yake na dan kalle fu'ad ta gefen ido abin mamaki kamar
bayajin warin ni kuwa kamar zanyi amai amma na daure saboda kar na bashi kunya
ballanta da naji yana cewa baba ga mamata wacce zata kula da kai murmushi yayi yace
falalu haka yake kiransa ko kuma yace muhammadu saboda yace sunansa da wuyan fadi
haba haba duk dawainiyyar da mai martaba yayi dani kaima ka gwada naka bajintar
ba'ace sa'a ba da ka bari ai har Allah yayi halinsa cikin dauriya nace haba baba ai
ciwo ba mutuwa bane zamu gwada wannan mugani insha Allah zaka samu lfy nayi shuru
domin ina gab dayin amai na juya gun fu'ad nace masa sai gobe kenan zan fara
dubashi Baba yace Allah ya kaimu na gode sosai Allah yayi muku albarka mukace
ameen.fu'ad ya mike tare da cewa to baba saida safe ko yace Allah ya tashemu muka
fita a dakin fu'ad yayi side dinshi nima nayi nawa,da gudu na karasa toilet dina
saboda amai da ya tahomin nayi ta kwararan amai kamar hanjin cikina sai fito, a
ranar dai baccina rabi da rabi ne saboda amai har na galaibaita da naga ban samu
nayi baccin ba sainayi alwala kawai na cigaba da sallah(anan nake son ja hankalin
mata a duk lokacin da kin since kanki da dare bakyajin bacci to kiyi alwala kinyi
nafilfili kiyi ta rokon Allah basai kina cikin matsala kawai zaki na tashi sallah
ba domin akwai wasu matan da masusan akwai Allah ba sai suna cikin matsala kafin
zaku ga Suna ibada which is not ryt Allah yasa mu dace ameen.) ina idarwa na kwanta
sai wani zuciyan nace min ki fasa aikin idan zaya zamu miki matsala Allah ma nacewa
a cikin qur'ani akwai abinda bazakayi ba in zaya zame maka matsala ko zaya baka
wahala wani zuciya kuma nace mata kiyi Allah zai baki ladah hakuri da juriya kawai
zakiyi tunda ma mijinki ne ma ya sakaki kinga kuwa lada biyu kenan gana mijinki
gana taimakon da kikayi ba tare da an baki ko kwandala ba kinga kuwa ladan mai yawa
ne har bacci barawo ya sace ta bata sani ba

Toh ku biyu mu don jin yadda abinda zaya kasance tsakanin likitar da patient dinta.

Written
By
Leeemancy 💮
🍡Maman aleeesha happy birthday once again 🍣🍘🍞🍞🍲
[3/21, 5:45 PM] +234 703 003 6037: !Y@RIM@ J@L@L!

Nah halima musa akano (leeemat )??

3⃣5⃣

Washegari bayan na gama breakfast nayi wanka na saka labcoat dina da mask na huce
dakin tare da kayan aikina ina shiga na gaida shi na tambaye shi ko ya ci abinci
yace min eh na masa allura sa'annan na wanke masa kafar da concentrated hydrogen
(wanda ba'a diluting dinshi da ruwa ba )ina gama na masa dressing din kafar na
bashi magunguna nace mishi sai da yamma kuma zana sake wanke maka kafar.haka zamu
rinka wanke kafar har muga inda Allah zayayi sai muyi maganan surgery ya ce to tare
da saka min albarka na fita ina fita daga dakin toilet na huce nayi wanka yau ma
nayi amai amma bai kai na jiya ba saboda mask dinda na saka.haka dai na shiga da
attending ma patience dina alhamdullilah kafar na improving har muka shiga watan
Ramadan abinda fu'ad yace min ayau har ya saka ni kuka saboda takaici...

!Y@RIM@ Y@RIM@!

Nah halima musa akano(leeemat)??

3⃣6⃣

Ya kasance gobe za'a fara azimi bayan ya gama cin abincin dare ya kirani na taho na
zauna nace masa gani sai yace min gobe za'a fara azimi koh nace masa eh saiyace ok
dat means a daren yau kenan za'a tashi sahur koh nace eh saiyace min to zaki rinka
tashuwa kina min abinci da asuba saboda bazana iya cin dumame ba na naga ido ina
kallonsa nace masa nifa bana tashuwa nayi sahur kafin na gama maganata yace ni ina
tashuwa da asuba don haka a rinka tashi ana dafa min abinci saikuma abu na biyu
banason ready made juice inason wanda za'a min a gida ne with fresh fruits kin gane
idona na zubar da hawaye nace masa eh saiyace abu na karshe kuma abokanaina anan
zasu rinka zuwa sunayin breakfast don haka a kara hannun girkin I hope i made
myself clear nace masa eh na tashi na shige daki na fadi a gado kuka nake sosai
saboda takaicin tashuwar asuba dafa masa abincin nayi kukana mai isata kafin na
setting alarm a karfe 3 na kwanta.karfe ukun nayi na tashi na masa tuwo da miyan
kuka taji man shanu na ajiye masa da coffee dinsa na huce daki na kwanta amma saida
nayi sallah kafin na samu na kwanta saboda fitina irin na fu'ad,da safe na tafi gun
patient dina na masa dressing kafar sa na dawo daki na kwanta domin nayi bacci
kafin lokacin abinci tayi godiyar Allah a watan azimi nake da yaushe naga ta hutu
har da baccin rana nasaka alarm dina a 12......

[3/21, 5:45 PM] +234 703 003 6037: !Y@RIM@ J@L@L@!

Nah halima musa akano (leeemat )💮

3⃣8⃣

Haka dai rayuwa ta cigaba da tafiya har aka gama ramadan kullum banda hutu har na
rame saboda aiki ga azumi ga aiki kamar na gidan biki ga kuma baba wato patience
dina.bayan sallah na masa aiki inda naci nasaran aikin domin kafar tayi sauki har
yana iya takawa da sanda yanzu magani kawai yake sha, kafar na warke wa nayi wani
ciwon da kamar zana mutu wato da asuba na tashi sallah sainaji na kasa tashuwa
jikina yayi zafi sosai da rurrufe na shiga toilet ina idar da sallah na hau gadona
kwanta nida idan na tashi da asuba to babu ni babu komawa barci sai fu'ad ya fita
amma yau na kasa ina kwance amma na kasa bacci saboda tunanin abin da zaya biyo
baya idan ya tarar ban hada masa breakfast ba ban gama tunanin da nakeyi ba naji
kiransa (RANI SAHIBA) da kyar na iya mikewa na fito falon ina mai tafiya kamar
wanda ta sha kayan maye saboda jikina babu karfi hada fuska yayi yace ina break
dina nace masa wallahi bana jin dadi bane shiyasa ina jiran saukan mari sainaga
yanayin fuskar sa ta sauya alamun tausayi a cikin tarihin aurena yau ne mijina ya
kalle ni da fuskar tausayi saiyace ok kinsha magani nace a'a saiyace mai yasa nayi
shuru ok kawo min coffee na sha nayi late sauri nake to nace kawai ina juyawa kawai
sainaji wani jiri kawai ganin falo nake yana juyamin nayi suuu na fa.......

!Y@RIM@ J@L@L!

Nah halima musa akano(leeemat)💮

3⃣9⃣

Suuu nayi zana fadi sainaji ni a jikin mutun yaune ta kasance rana ta farko da
najini a jikin mijina nasan ma saboda rashin lafiya ne amma da babu abinda zaya
kaini jikinsa bansan inda kaina yake ba.jin sanyi sanyi ajikina yasaka ni bude
idona caraf idona ya sauka a fuskar fu'ad ganin yanda duk yabi ya sukurkuce kamar
ba mijina mai gayu ba saina kirkiro murmushi sainaga ya mayar min kokarin tashuwa
nake son nayi na kasa saboda yanda jikina taimin nauyi kamar an dora dotse sainaga
ya tashi da sauri ya taba wani guri a jikin gadon sainaga gadon yana tashuwa a
hankali nikuwa sai cije baki nake saboda yanda jikina ke mikewa sai inajin zafi ya
tsayar da gadon ganin yanda nake yi.ya dauka briefcase dinsa na aiki yana dubani
yana gamawa ya dan gyaran min gashin kaina ya baida su baya yana shafa kaina tare
da cewa every thing is ok alryt u are fyn now murmushi kawai nayi saboda mamaki wai
mafarki nake ko kuma a zahiri fu'ad mijina ko kuma wani fu'ad din ne yake min haka
jin yana magana yasa na dawo daga tunaninda nake yi zaki iya tashi ko kuma saina
dauke ki ce masa nayi a'a zan iya tashi na yunkuro zan tashi sainaji.....

!Y@RIM@ J@L@L!

nah halima musa akano(leeemat)💮

4⃣0⃣

Sainji ya dauko ni sai bayin gida sakani yayi a cikin bath sai a lokacin ma na
fahimce babu kaya a jikina kunya duk ya kamani na sunkuyar da kaina kasa yace zaki
yi wankan ne ko kuma na miki da sauri nace zan iya yayi murmushi yayi yace
(TA'ABANA) a raina nace wannan yare nawa ya iya ne murmushi kawai nayi na cigaba na
wanka na ina gama babu abinda zan rufe jikina ina daga ido sainaganshi yana kallona
sunkuyar da kainayi cikin tsananin jin kunya ya towel ya dauka ya lullube ni ya
dauke ni kamar wata karamar yarinya ya zaunar da ni a kujera yace na zauna na
gajina da kwanciya mai ya shafa min ya saka min kaya ya bani tea na sha ina gama
sha kuwa nayi amai ya share gun ni kuwa in banda mamaki babu abinda nakeji wai
yarima kenan yana abubuwan nan saboda wancce ta masa rashin mutunci yana shiga
toilet wanke hannunsa na sha ruwa ina cire bakina a gorar na sake kwarara wani amai
daga baya naji ance min sannu juyawan da zanyi wa zan gani.......

Written
By
Leeeeemat💮
[3/21, 5:45 PM] +234 703 003 6037: !Y@RIM@ J@L@L!

nah halima musa akano(leeemat)??

4⃣1⃣

Wa zan gani mahaifiyar fu'ad nagani wato MA'A kenan kamar na nutse a gun saboda
kunya rusunawa nayi ina gaida ita tashi tashi ke da baki da lfy na tashi ban iya
zama a kujera kuma ba kwanciya nayi saboda tsananin jin kunya maganan zuci nake
wai yanzu ta shigo ko kuma tana cikin dakin nan bansani ba amma kuwa mun cika
marasa kunya in tana cikin dakin nan ne fu'ad yamin wannan abubuwan.haka dai jikina
babu sauki sai amai nake tayi na sha ruwa kuwa kamar wacce bata da ruwan a jiki,har
naxo na samu lfy abin mamaki gida jiya muka sake komuwa kamar yau na masa abinci
saboda yayi baki ina gama abinci na kwanta bani da tashuwa ba saida naji saukan
ruwan zafi na tashi a firgice before u knw banganshi ba ya fice a dakin.....

!Y@RIM@ J@L@L!

nah halima musa akano(leeemat)??

4⃣2⃣

Yau ina zaune a falo na abin duniya duk ta isheni na rasa me yake min dadi naji
sallamar sa tashuwa nayi na masa sannu da zuwa yace min ki shirya monday zaki fara
zuwa aiki wani ihu na saka mai karar gaske har ya rufe kunnensa yana mai murmushi
ganin yanda nake murna saiyaji dadi a ransa saboda tunda muke da shi bai taba min
abinda ya saka ni farin ciki kamar yau ba bansan lokacin da na bashi tyd hug ba ina
thank u very much i wil never forget dis ina gamawa na ce masa ga abincin ka a
dinnin is ready murmushi kawai yayi ya tashi ya nufe table.a daran saboda murna na
kasa bacci salloli na cigaba da jirowa ina rokon allah ya sa na fara aiki cikin
sa'a tare da rokon allah ya karkato da hankalin mijina gareni domin babu abinda
banyi ba tafannin jawo hankalin miji irin su dafa masa abinji,kwalliya,saftar gida
babu abinda banyi ba yanzu kawai adu'a zan cigaba dayi har allah ya amsa min adu'a
ta ina idarwa na fara niman kayan da zan saka na ma mance akan gobe jumma'a ne
saida ina cikin duba kayan da zanasa sai tunanin labcoat ya fadumin ina tunanin ya
zan fara zuwa aiki babu labcoat sai na tuna akan ai gobe friday ne saina dinka a
unguwar mu idan muka tafi......

Written
By
Leeeeemat??

[3/21, 5:45 PM] +234 703 003 6037: !Y@RIM@ J@L@L!

nah halima musa akano(leeemat)??

4⃣3⃣
Washegari na tafi gida aka dinko min labcoat dina na dawo gida da wuri saboda
banason nayi laifi.ina dawowa na dafa masa abinci na fara shiryeshirye na, haka dai
har ranar monday na fara zuwa aiki amma wani abin mamaki duk lokacin cin abincinsa
sai na dawo na masa kafin na koma asibiti amma abin baya damuna tunda nasamu ina
zuwa aikin,in wani lokaci ina night ne haka zana dawo na saka masa abinci saiya ci
kafin na koma asibiti saboda ina kammala abinci kafin ya dawo idan ya dawo kuma
saiya kirani yana kirani kawai nasan abinda yake nufi saina dawo gida na saka masa
abinci kafin na koma.haka dai rayuwa ta cigaba da tafiya akwai wani ranar da nake
shirin tafiya aiki da safe sauri nake na saka pant da bra kenan ina gyara gashina
domin na saka kaya na tsaya a bakin gado saboda kayan na zuba su a kan gado ne ban
ji sallamar mutum ba kawai na ga mutum ya shigo ina daga ido sainaga fu'ad.fu'ad
kuwa rikicewa yayi saboda ganin albarkatun kirjina saboda gaskiya ina da boost
sosai saima na saka bra irin mai karfe dina kuma duk bra dina kanana nake sakawa
wanda zaya kamani ni sosai, na kasa musawa ina tsaye a gurin kamar wata gunki saida
naga ina zuwa a hankali towards me saina fara komawa da baya a hankali hankali
saime?..

!Y@RIM@ J@L@L!

nah halima musa akano(leeemat)??

4⃣4⃣

*************************⬇**********************
************* Top Hausa Novels ****************
*************************⬆ **********************

DOWNLOAD More complete Hausa Novels, Education Books, Adventure, Drama, Mystery,
Religion, Fiction, Non-Fiction, Romance, Meimor, True Life Stories & Others from
our blog.

Visit > https://www.thn.com.ng

Ka tura mana sako ta adireshinmu na email, domin tuntubarmu ko turo mana hausa
novel ko kuma post.

Email > tophausanovels@gmail.com

******* FOLLOW US ******

Facebook: Top Hausa Novels

Twitter: Top Hausa Novels

Telegram Channel: https://t.me/tophausanovels

Telegram Group: https://t.me/tophausa

Haka kuma domin shiga kowanne daga cikinsu za ku iya ziyartar shafin ku yi search
na TOP HAUSA NOVELS, hatta facebook group dinmu ma za ku samu.

********************** ⬇ **************************
*************** Top Hausa Novels ****************
********************** ⬆ **************************

Ina komawa baya a hankali hankali sainaji ni na zauna a kan gado fu'ad da ganin
haka saiya sakayani da hannunsa ya daura hannunsa a kan gado yana matsuwa ni kuwa
ina komawa da jikina baya yana kan karasowa kafana a kasa yana ta matsuwa da
fuskarsa a fuskata duk fadin jikinsa ta hanani motsi ina zaune yana zuwa da fuskar
sa dai dan bakina kamar zaya sunbace ni labbansa yana karasowa dai dai bakina ni
kuwa babu abinda nake yi sai rawar jiki gabana sai faduwa yake tayi rufe idona nayi
da karfi ina jiran inji bakinsa cikin nawa sallama mukaji ta falo mikewa yayi cikin
mutuwan jiki ya fita ni kuma wani mahaukacin ajiyan zuciya na sauke da sauri na
saka kayana na fita wa zan gani su hassan da hussaini ne nace musu ya dai da safe
haka sai suka ce min ai jalilah ce ta haihu wani ihu na saka sai suka ce min wai
anata niman ki a waya is off shiyasa mukace bara mu zo kawai mu sanar da ke nace me
aka samu ne suka ce min mace nace musu to mu tafi ko saina dubata before na huce
aiki wani kallo naga fu'ad ya min sainayi shuru na huce daki domin dauko gyale na
ina juyawa naga mutum a bayana na damke hannuna yayi yace bance ki tafi ko ina ba
ki huce gun aikin ki kawai ya juya ya fice a dakin na fita da sauri domin na fada
masu hassan wani karya saina tarar basanan nayi kuka har naji babu dadi kafin na
huce gurin aiki ina office dina na kira jalilah na bata hakurin insha allah mayb
gobe zana shigo aiki yamin yawa ne tace babu komai sister simra ya naji kamar
muryarki ta canja ne nace mata babu kamai kinsan aiki tace to allah ya taimaka nace
amin ina kashewa na sake wani kuka....

!Y@RIM@ J@L@L!

nah halima musa akano(leeemat)??

4⃣5⃣

Kuka na sake nayi kuka mai isata kafin nace wannan abin yafara isata wallahi har da
kannuwata ma ta haihu amma saboda wulakanci amma ace ya hanani tafiya,a ranar dai
nayi aiki cikin dauriya ne kawai amma duk jikina a mace yake ina gamawa gida na
huce jakana da gyalle na duk na zuba su a falo na huce kichen na dafa masa abinci
nayi sallar magriba nayi isha'i ina dan duba wasu takarda naji sallamarsa na daga
kai na masa sannu da zowa ya fita falo na fahimce me yake nufi saina tashi nima na
fita na ganshi a coshin ya zauna na nufe dining area ina shirin kawo masa abinci
sai naji yace saboda kin mayar dani acici ko na saya cak saiyace ki shirya na kaiki
gidan jalilah saina dawo zana ci nace masa bazana tafi ba kallona yake baki bude na
huce daki na fada a gado ina kuka wato ma ni da yar uwata sai an gama min milki
kafin za'a barni naji na ganta to baza'a tafi ba wata zuciya kuma tace min to shi
ina ruwansa ai kece mai yar'uwan idan ma baki tafi ba duk lalurarki ne da sauri na
tashi na nufe dressing mirror na dan murza powder na dan shafa lipgloss a bakina na
nufe falo domin nasan akwai gyalle da jakata a falon ina fita na dauka gyalle da
jaka naji an jani zuwa bango bakinsa naji cikin nawa gabana sai faduwa yake domin
ina zatun amsar da na bashi dazunne zaya hukuntani yamin irin na ranar daya
kumburar min da baki saboda da mugunta wani kara na sake......

Writtten
By
Leeemat??
[3/21, 5:45 PM] +234 703 003 6037: !Y@RIM@ J@L@L!

Nah halima musa akano(leeemat)??

4⃣6⃣

Kissing dina yake kamar ya samu sweet lips dina yake latsawa cikin kwarewa har naso
na mance a wani duniya nake,naji tsoron kar yamin na ranar ya sakani sake kara
amma shi ko a jikinsa(wai an duke bango yace ko jikinsa) aikinsa yacigaba dayi
dayaga basaya iya jure tsayuwan ba saiya cire bakinsa cikin nawa yayi hanyar
waje,ni bansan lokacinda na zame jiki na zauna a kasa ba ina mayar da numfashi a
hankali wai haka sumbata take da dadi magana nake a zuciyata sa'annan na mike na
biyo bayansa na tarar ya kishingide a gefen mai zaman banza a raina nace me wannan
bawan allah yake nufi ya bude baya na zauna munkai kusan minti goma kafin yacemin
ki dawo gaba ke zaki driving dinmu nayi kamar badani yake ba RANI SAHIBAH dake nake
magana fa na fito na zagaya na shiga muka kama hanya muna cikin tafiya yake cemin
daga yau idan zamu fita tare dake ke zaki rinka driving dinmu uffan bance ba saiya
kara cewa wato zamu tafi gidan kannuwanmu shine kika saka lipgloss wa zaki nuna
mawa ya dan kalle fuskata tare da cewa let me check ko kuma har yanzu bai kare ba
saina share miki kiiiiii kake ji na mutu fu'ad kuwa babu abinda yake furtawa sai
innalillahi wainnahilaihirajiun....

Writteen.
By
Leeeemat??

!Y@RIM@ J@L@L!

Nah halima musa akano(leeemat)??

4⃣7⃣

Sha biyu nayi na tashi na fira dankalin turawa zuba a kwando saboda ya tsane na
saka ganda a pressure cooker saboda tayi da sauri a lokacin asr yayi na tafi nayi
sallah na dawo na fara aikin fruit salad, fruit salad ya dauke ni har LA'asar ina
gamawa na saka a fredge na gama miyan ganda na zuba a foodflask na saka frying pan
a wuta na zuba mai na tafi sallah na dawo a lokacin mai yayi zafi na fara soya
dankalin sa'annan na saka tukunyan farfesun kifi a wuta nan da nan na gama amma na
saka mishi sinadarin kamshi irin su cinta da dai sauraran su saboda karni ina
gamawa na zuba a flasks na fira doya na saka a wuta sa'annan nayi mango fruit juice
na zuba a jug na saka a fredge already akwai ruwan zafi a flask wanda zaya so
tea.har an kira sallah na shirya musu table na huce daki nayi sallah nima na ci
abinci na daki inata jin hayaniyar su a falo amma ban fita ba can naji shuru da
alamar Sun tafi sallar isha na koma kichen na sauke doyar da na saka a wuta na zuba
a injin nika doya nan da nan na gama na mulmula masu a leda na saka a cooler na kai
musu falo da miyan ganda da na musu da kuma mango juice na huce nayi sallah a
gajiye ina shirin wanka saina tuna da baba yau ban masa dressing kafa ba gashi na
gaji saina fara kuka kawai saboda gajiyan da nayi haka I don't have a choice na
huce ina gama masa na dawo na kwanta na saka alarm 3 saboda tashuwar asuba
Hmmm har ni kaina leeemat na gaji ina kuma gimbiya simra zataji a jikinta irin
wannan aiki haka amma fa lada ne kam bamusan irin ladan da take kwasa ba saidai
kawai nace Allah ya bamu juriya irin na simra muma mu rinka yiwa maigidan mu haka
domin tsira daga shiga wuta ameen.....

Written
By
Leeeemat ??
.

[3/21, 5:45 PM] +234 703 003 6037: !Y@RIM@ J@L@L!

Nah halima musa akano(leeemat)💮

4⃣7⃣

Na jin abinda ya fada sai na daga brek din moton ji kake kiiiii!fu'ad kuwa babu
abinda yake sai innalillahi wainnahillaihirajiun,ni kuwa cikin sauri na share
sauran wanda ya dan rage a labbata.cikin bacin rai yace wai so kike kimin asarar
kanki shuru nayi ina kallonsa cikin mamaki da jin furucinsa fu'ad kuwa bansan subul
da baka yayi ba sai yayi sauri ya canja maganan da cewa duk da dai banda asara idan
ma mutuwar kikayi wai ma wa yasakaki kiyi wannan shirmen okey saboda nace zan share
sauran?to kiyi reverse mu koma gida tunda dama kwalliyar kina ma wa mutan waje ne
yau bazaki nuna musu kwalliyar ba bansani lokacinda na matsa kusa dashi na tura
masa bakina tare dacewa gashi kayi duk abinda zakayi dashi amma dan allah kar ka
hanani tafiya gidan jalilah,dariya na bashi amma ya daure sai kuma na banshi
tausayi yace huce to mu tafi na share fuskata nayi saboda har na fara zubar da
kwalla.muna isa gidan na fita a guje na shiga na tarar da yan zuwa barka na tafi
na rungume ta sa'annan nace ina baby dina mutanin falo sukayi dariya tace tana
dakin ki aka sake wani dariyar dakinta na huce na dauka babin ina kallonta cikin
sha'awa naji kamar motsin na daga kaina ganin fu'ad nayi yana shigowa da kaya a
leda amma bansan me yake ciki ba yana zaunawa nima zaunawan nayi na cigaba da
kallon babin inda jalilah tace min sis simra ki bashi babin mana sai sa'annan na
tuna dashi na tashi na mika masa ita ya mata adu'a wayar sa tayi kara ya mika min
babin ya fita a waje amsa kiran yana fitowa na nufe gun ledar da ya shigo da ita na
bude wani kamshi naji kaza nagani irin na mai jego dinnan da sauran abubuwan ci da
shi.haka dai na shigaba da zuwa gidan in na tashi daga gun aiki har ranar suna inda
aka saka sunana hmmmm fada muku abinda fu'ad yayi a ranar sunan zaku ganin kamar
karya nake abin mamaki ya ban haka dai aka gama suna lafiya kowa ya tafi gidansa
inda maijego ta samu abubuwa sosai da kudi domin har bude account tayi ma babin...

Written
By
Leeemat💮
[3/21, 5:45 PM] +234 703 003 6037: !Y@RIM@ J@L@L!
Nah halima musa akano(leeemat)💮

4⃣8⃣

Fu'ad kwance yake a kan gadonsa wanda zana iya kiransa da royal bed saboda yanda
aka kayata gadon da abubuwa mai kama da gold sai sheki gadon yake duk da dakin yana
cikin duhu ne amma bazaya hanaka ganin shekin da gadon ke yi ba.doom light ya saka
yana son yayi bacci amma abin ya gagara gashi yau ya gaji sosai a gun aiki
sakamakon babu armies duk sun tafi yaki a wani garin da suke fuskantar azzalumai
masu sace masu mata da rasa.ya kasance fu'ad bayanan a cikin masu tafiyan dan haka
aiyukan suna masa yawa sosai kamar ma yau da ya gaji sosai amma ya kasa bacci.sai
tunanin simra yake wanda tun ranar sunan A'shadieeyah waton yarinyar jalilah kenan
takwaran simra ya kasa tsukuni tunanin ta yake saboda ta bashi tausayi mutuka
saboda yanda takeyi kamar sunanta ne na yarinyar ta sa'annan duk da ba'a gida ta
kwana ba tasan halin mijinnata tana tashuwa da safe ta nufe gida ta masa breakfast
ta jira ya shigo ya ci kafin ta dawo gidan sunan haka da rana ta kumo gidanta ta
masa abincin rana domin intace zata diba masa na gidan sunan kila kifa mata zayayi
a jiki domin bazaya tabaciba yana ganin abincinda dunbin mutani sukayi sa'annan ta
ce zata saka mishi yace tana gama masa abincin rana ta dawo suka cigaba da
sunansu.yasan ya hukuntata daidai da laifinta amma bari ya dan bata tym kadan
saboda yanzu ya shirya zaman aure da ita cikin soyayya,har bacci yayi awon gaba
dashi amma tunanin simra yake da irin soyayyar da zasu kasance idan sun fara zaman
aure daga karshe yayi wani mummunan mafarkin da ya firgita shi,mafarki yayi akan
yana wani sahara mai girman gaske inda yake hangin simra nesa dashi tana kiran
sunanshi amma ta kasa karasowa wajensa kamar ana koma da ita baya inda take ta
kokarin zuwa har allah yasa ta karaso sai tana ce masa fu'ad wai meyasa bazaka yafe
min laifin da na maka lokacinda nake gida bane wani yanzu na canja ba kamar da ba
kuma bana wulakanta mara arziki kawai dai a lokacin jinin mu bai hadu da kai bane
magana take tana kuka sosai har da majina inda take cewa dan allah ka yahakuri ka
gafarceni muyi zaman mu na ma'aurata saboda makiya suna sun su rabamu tana cikin
maganan taga kamar yana komawa da baya tana pls fu'ad ka tsaya mana tana kuka tare
da mika hannunta amma me saitaga katon rami a bayansa tana fu'ad no fu'ad no
bayanka zuwa take da gudu amma saijinsa tayi ya fadi cikin ramin wani ihu ta saka a
dai dai lokacin fu'ad ya tashi zufa cabe cabe a jikinsa

.written
By
Leeemat💮

[3/21, 5:45 PM] +234 703 003 6037: !Y@RIM@ J@L@L!

Nah halima musa akano(leeemat)??

4⃣9⃣

Adu'a yafara kafin ya shiga bayi domin yajin kamar har anfara sallah a masallatai
yana idarwa ya fara tunanin mafarkinda yayi yau kamar an tsikare ya tashi toilet ya
shiga yayi wanka yana saka kaya tare da tunanin yaya zaya fara fuskance ta da
maganan domin gaskiya yau dinnan zaya kasance da matar sa abin kaunarsa yana
murmushin jin dadi yana gama ya dauke turare yana sakawa domin yasan yanzu tana
kichen a cikin ransa yace abincin yau dani za'a dafa sa'annan muci tare cikin
kaunar juna ya murmusa ya fita yana kai bakin kofa yaji wayar sa tana ringim kamar
ma bazaya dawo ba saiya juya ya koma cikin dakin sunanda yagani ya saka shi saurin
dauko wa hello yace basan me aka fada masa ba kawai ganinsa nayi ya dauka car key
dinsa ya fice cikin tashin hankali.baza mu koma ta bangaran sarauniya amina idan
mai karatu bai mance ba sarauniya tayi alkawarin saitaga bayan yarima fu'ad to
abinda yafaru yau tana son tafiya gida gaida iyayenta domin tayi kwana biyu saita
nufe padan mai martaba sarki saita juyo wani magananda ya tayar mata da hankali mai
martaba taji yana cewa jibi zamu rada fu'aduddeen saboda yafara aikinsa tun yanzu
duk da dai nasan yanayi amma zan rada masa ko bai zauna a pada cikin mu ba ya fara
sanin matsalolin mutaninsa yana biya musu bukatansu magananda bata shiga tayi ba
kenan ta huce gida suka huce gidan boka ta fada masa matsala ta yana dubawa yace
gaskiya wannan yaron yana da kariya sosai akwai wasu adu'oin da yake yi idan zayayi
barci kuma da addo'ar iyayensa amma yau zamu jaraba mugani ko za'a dace ba kisa
kike son a masa ba? ta ce eh yace to shikenan ta bashi kudi da bazana iya san
adadin su ba suka fice sai murna..
Ta gefen fu'ad kuwa gudu yake kamar zaya tashi sama ganinsa nayi ya shiga bariki
dinsu na sojoji abinda nagani har ya firgitani mutani nagani a kasa wadansu a mace
wadansu a raye amma sunji rauni ba kadan ba sai jujejuye suke alamun suna cikin
azaba da rauni yana karasowa aka sara mashi yace ya dai wani daga cikin sojan yace
munci nasara amma sun kashemu sosai sabida suna da kayan aiki.alhamdullilah yace
sa'annan yace musu su kwashe su a kaisu ciki zaya duba su aka shiga dasu yafara
duba su wadannan basu da rai a fitar da su wadannana suka ji mummunan rauni kuwa
babu adadi aiki kawai yakeyi saidai in lokacin sallah tayi ya fita yayi ya dawo ko
ruwa bai sha ba har goma na tare waninda yake tayashi aikin yace ka tafi gida haka
mana gobe saika karasa ai ko murmushi yayi yace a'a duk yau zan musu aka kuwa akayi
saida ya gama musu kaf kafin ya dawo a lokacin biyu ta wuce yana zuwa kuwa kwanciya
kawai yayi saboda yayi kwanka a barikin bacci mai nauyin gaske ya dauke shi yana
tunanin sai gobe zaya ga matanshi

Written
By
Leeemat??

[3/21, 5:45 PM] +234 703 003 6037: !Y@RIM@ J@L@L!

Nah halima musa akano(leeemat)💮

*************************⬇**********************
************* Top Hausa Novels ****************
*************************⬆ **********************

DOWNLOAD More complete Hausa Novels, Education Books, Adventure, Drama, Mystery,
Religion, Fiction, Non-Fiction, Romance, Meimor, True Life Stories & Others from
our blog.

Visit > https://www.thn.com.ng

Ka tura mana sako ta adireshinmu na email, domin tuntubarmu ko turo mana hausa
novel ko kuma post.

Email > tophausanovels@gmail.com

******* FOLLOW US ******

Facebook: Top Hausa Novels

Twitter: Top Hausa Novels

Telegram Channel: https://t.me/tophausanovels


Telegram Group: https://t.me/tophausa

Haka kuma domin shiga kowanne daga cikinsu za ku iya ziyartar shafin ku yi search
na TOP HAUSA NOVELS, hatta facebook group dinmu ma za ku samu.

********************** ⬇ **************************
*************** Top Hausa Novels ****************
********************** ⬆ **************************

5⃣0⃣

Washegari simra tashi da tunani mai yawa a kwakwalwarta tun jiya bata gan fu'ad ba
gashi yanzu har goman safe bai shigo ba ko mai yafaru ita bata sani ba har shabiyu
tayi kai da taga abin bana karewa bane saita tashi cikin faduwar gaba ta nufe side
dinsa tare da niyyar duk abinda zaya mata saidai ya mata amma yau zata shiga side
dinsa tafiya take cikin tsoro da fargaba abinda zata ji ta tarar tana tsaye a bakin
kofan kusan minti talatin sa'anan tayi adu'a ta shigo a hankali ta bude kofar bata
komai ba sai katon falo tana shiga numfashinta yan niman daukewa saboda kyau da
tsaruwan falon kawai da yake ba abinda ya kawota ba kenan bata tsaya kallon yanda
falon yake ba ta huce wani kofar da ta gani a gefen falon saita nufe kofar ta bude
shi a hankali tare da sallamar tsoro taji shuru tayi sallama sau uku taji shuru
saita shiga ganinsa tayi a kwance yana bacci ta karaso kusa da shi fu'ad fu'ad
fu'ad shuru babu motsi ballantana har ya amsa sai ta shiga rudani tafara kiransa
cikin tsoro domin yanayin kwanciyar sa ma da tambaya bude bargo tayi hau kan gadon
ta tabashi taji kamar babu rai a tare da shi ta fara bubbuga shi tana kiran
sunansa tana hawaye fu'ad pls wake up banason irin bacci dinnan fa shuru babu
magana saita fara kuka a jikinsa ta kwanta tana kuka kamar ance ta daga kanta
saitaga hawaye na fita a gefen idonsa sai a lokacin tunanin kira likita ya zo mata
minti kadan sai kuwa gashi yana mata korafin gidan da kyar aka barshi ya shiga
bayan ya gama dubashi yace mata nidai ban fahimce komai ba amma gaskiya jikinsa is
weak baxaya iya komai ba in ba abinci yace ba kafin zamu san me ke damunsa godiya
na masa kafin na dawo na cigaba da kuka fu'ad tell me wat is happening to u pls
tell if u dont my heart will be shatered pls fu'ad
Wani tunani yazo min kuka na ya tsananta dana tuna da labarin da jakadiya ta bani
akan ba'ason fu'ad yayi ciwo saboda yana iya daukansa wata ko shekara kafin ya samu
lafiya idan kuma wannan ya kasance yaya kenan zanayi ban gama da damuwan aure ba ga
ciwo wayyo allah na...

Written
By
Leeemat💮

You might also like