'KANGIN RAYUWA (1to70) - 1-2
'KANGIN RAYUWA (1to70) - 1-2
_NA_
_SAMIRA HAROUNA_
_My Happiness *Amnoor*, barka da fara sabon novel mai sunan *matar farko*
(dandab'asa), wannan novel kam namu ne domin damu ake, matan farko ba ba kamar su
o'o ba, ina nufin momyn D....tasan sauran, su kam d'ogalawa ne.😁 Allah yasa ki
gama lafiya kamar yanda kika fara lafiya._
💘💘💘💘💘💘💘💘💘💘
_My BK, nasan babu godiya tsakaninmu, to amma ya zama dole yaba kyauta, ina godiya
BK ta Allah ya bar zumunci._
💘💘💘💘💘💘💘💘💘💘
🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾
_My Heenat, na rasa me zance ma, sai dai kawai nace Allah ya barmu tare, qauna ta
gaskiya kam kina nunawa Sameera ita._🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾
_💘Mamien mu *(Maman Labyb)*, gaskiya ke uwace ta gari wacce ko wace d'iya ko d'a
zaiyi alfaharin samunki a matsayin uwa, yanzu haka har na d'an fara kishi da BK ina
ji inama nice 'yarki , to amma ba damuwa zan zauna a matsayin 'kawa kuma rabin ran
d'iyarki._💘
_DEDICATED TO_
*MA FAMILLE*
_Bismmilahir-rahman-rahim_
1⃣
Da alama ranta a b'ace yake ga k'aguwa a zahirinta ya bayyana, sake kallon agogo
tayi na karo ba adadi sannan ta kalli k'ofar douche d'in taja dogon tsaki tana
magana k'asa k'asa "wannan wulak'anci dame yayi kama, sama da awa d'aya kina wanka,
ki bani wani banzan serviette (towel) na rik'e kamar ke wata musaka ce."
Sake kallon agogon tayi sai dai kafin ta maido kallonta taji an bud'e k'ofar douche
ana fitowa, da sauri ta kalleta amma saboda ganin santaleliyar budurwar ta fito
daga ita sai d'an k'aramin silip (pant) d'inta ko soutien ( bras) babu yasa tayi
k"asa da kanta, ita kam ko a jikinta takowa tayi ta zo gabanta ta karb'i serviette
d'in ta d'aura a k'irji sannan ta karb'i dayan ta d'aura a kanta, gaban coiffeuse
taja kujera ta zauna tana kallon madubi ita kuma mai aikin ta matso ta d'auki mai
ta fara shafa mata, bayan ta gama ta shafa mata powder da pink d'in jan baki, ta
fito mata da wani silp d'in da soutien ta bata ta saka sannan ta fito mata da riga
da siket na atamfa, d'inki ne na yan zamani yayi kyau sosai gashi ya zauna a
jikinta daram , mai aikince ta zuge mata zip d'in dake bayan siket d'in wanda ya
kamata sosai komai nata ya fito masha Allah, d'an kwali ta kashe d'aurinshi sannan
ta fito mata da sarka da yan kunnai da gani kasan sunji kud'i, sannan ta fito mata
da jaka da takalmin da suka dace ta aje mata gabanta, sakawa tayi sannan ta d'auki
turare ta fesheta dashi ita kam tana tsaye kamar gunki, tana kamalawa ko jiranta
bata tsaya ba kawai tayi k'ofar fita abinta.
Binta tayi da harara tana fad'in "wannan zanso naga gidan aurenki , mijinki ne zai
miki wannan hidimar ko kuma mai aiki zai samar maki."
Gyara d'akin tayi kamar yanda maishi zata buk'aci ganinshi sannan ta fito ta rufe
mata d'akin.
Ba tare data kalli kowa dake kan table a manger (dinning) d'in ba taja kujera ta
zauna, wata mai aikince dake tsaye kusansu ta matso ta fara zuba mata abincin, ta
zuba mata fritte zata bud'a wani kwanon kawai ta d'aga mata hannu tare da kallonta
cike da wulak'anci tace,
"Ya isa haka, ni ba jaka bace kamarku da zan zauna ina had'iyar abinci haka."
Ja baya tayi kanta k'asa bata kalleta ba ita kuma ta fara cin fritte d'in,
mahaifiyarta ce tace "mu kike so mu fara gaidaki kenan?"
Kallon saurayin da suke fuskantar juna tayi, amma ganin wani kallo da yake mata
tare da murmushi yasa ta zabga masa harara, maida kallonta tayi ga mahaifinta,
d'auke kai tayi ta kalli mahaifiyar tata tace "ki tabbatar min jiya bai shigo cikin
maye ba, ni kuma saina gaisheshi."
A tsawace uwar tace "ke, ashe baki da mutunci, wannan ba mahaifinki bane da zaki
fad'a masa haka?"
A wulak'ance ta kalli uwar tace "shi kenan mutunci ne yake sashi shigowa cikin gida
a buge? kinga nifa karki b'ata min rai da safiyar nan."
Duk da k'ok'arin rik'e hawayen da tayi saida suka zubo, cikin muryar kuka tace "ba
laifinki bane, kiyi yanda kike so."
Tana fad'a ta juya ta nufi d'akinta tana zubar da hawayen takaici, ita kuma ko
kulata ba tayi ba bare taji ba dad'i, saima mahaifinta data kalla tace "zaifi maki
kyau ki daina saka damuwa a ranki akan wannan da baisan kina yi ba."
Tashi tayi ta bar abincin zata fita ,mahaifinta ne kalleta a marairaice yace "kiyi
hak'uri mana gimbiyata, nayi alk'awari ba zan sake ba."
Kallonshi tayi ta kalli saurayin dake zaune kusanshi tace "ka fad'awa wannan wawan
watak'ila shi zai yarda da abinda ka fad'a, amma bani ba *Khairat*."
Fita tayi ta nufi wajen motarta, d'aya daga cikin jami'an dake kula da mahaifinta
ne ya taho shima a gadarance ya karb'i jakar hannunta da makullin mota ya nufi
motarta dasu, dan in baiyi ba to masifa zaisha amma ba k'aramin d"aci ba abin ke
mishi, har zata shiga mota taji saurayin nan yace "nine wawan?"
Nunashi tayi da yatsa tace "wallahi harka gama wa'adin daka dibarwa kanka ba zan
tab'a kallonka a matsayin mutum ma bare harna fara tunanin soyayya da kai, désolé."
Tana fad'a ta shiga motarta ta bar gidan cikin matsanancin gudu, shi kuma taushe
b'acin ranshi yayi da har yanzu yana ji a jikinshi zata iya zama tashi, a ranar da
kuma hakan ta faru zata gane wanene shi.
********************
Kafin ta fara gudanar da komai saida tasa masinger ya siyo mata fritte mai had'e da
soyayyen nik'akk'en nama da jus d'in albasa da moutarde, tasa *Habiba* ta had'a
mata kakkauran tea da zuma sannan ta fara wani sabon petis de jeûner d'in, tana
fara ci Habiba ta sake shigowa cikin ladabi tace "madame, manager ne ke son
ganinki."
Juyawa tayi dan cika umarninta, takai wata lomar bakinta taji shigowarsu, amma jiji
da kai yasa ta kasa koda kallonsu da ido, tsaye sukayi a kanta hakan yasa ta musu
nuni da hannu akan su zauna, saida suka zauna sannan ta kallesu gaba d'aya ta kuma
kalli manager tace "kai kad'ai aka ce kana son ganina, yana ganku ku biyu?"
"Eh madame, wannan shine wanda za muyi magana akan ci gaban daya kawo mana."
Sake kallon saurayin tayi wanda idonshi ke kan kallon yatsun hannayenta da take cin
abinci dasu, jan lallen da suka sha da dogayen akaihu na kanti wanda suma ta
lullub'esu da pink couleur d'in vernie, sosai suka birgeshi duk da dai ya tsani mai
su d'in, maida kallonta tayi ga plate d'in abincinta taci gaba da ci har saida ta
gama sannan ta d'auki bidon (gora) d'in ruwa ta zura hannunta ta tagar dake
bayanta ta wanke hannu ta juyo da nufin aje bidon d'in ta d'auki lotus dan goge
hannu, karaf idonta suka sauka akan gayen nan daya kasa d'auke idonshi akan
kyakyawar hallitarta, da sauri ya d'auke idonshi tare da had'e fuska tamkar hadarin
gabas, dan tunda ta fara aiki anan take tak'ama wajen mahaifinta ne ya lura tana da
raini shi kuma ba zai d'auka ba, saida ta goge hannun ta tsaya ba yare data zauna
ba ta kallesu tace "ina jinku."
Hannu manager yasa a jaka ya fito da takalma ya mik'a mata yana fad'in "wannan
shine sabon sanfarin da wannan ma'aikacin namu ya fito mana dashi, shine nace kafin
muci gaba da bugawa sai mun samu izininki."
Karb'a tayi bayan ya gama mata bayanin ta kallesu da kyau, tabbas sanfurin ya
birgeta dan kuwa basu da maraba dana maza harda gidan babban yatsa, ga kuma
tudunsu shima kamar dai na maza, ajesu tayi qasa ta cire na qafarta tasa
wad'annan, su kam kallo suka bi qafar da ita yayin da saurayin ke ma qafar kallon
qurilla wacce tasha jan lalle sai dogayen akaihu itama data saka masu kamar dai na
hannuwa, ganin yanda suka zauna a qafarta suka mata kyau yasa ta cire ta zauna a
kujerarta tace" kuje kawai ku ci gaba da bugawa, ku bar min wannan zanyi publié a
Internet nasan zamu samu masu so."
Cikin farin ciki bayan sunyi godiya suka tashi zasu fita, muryarta ta tsayar dasu
tace "fasahar waye?"
Juyowa sukayi manager kuma yace "wannan ne madame." ya fad'a tare da nuna na kusa
dashi.
Takowa yayi tare da k'ara d'aure fuskarshi, saida ya tsaya gaban tebur d'inta yana
kallon idonta, jujjuya kujerar ta fara yi tana juyawa da ita ta fara magana "karka
bari mu sake had'a ido da kai da sunan had'arin kallo, karka sake bari na maka
magana so d'aya har sai an maimaita maka, karka bari na sake jin raina ya b'ace a
kanka, sannan karka sake kallon min bayana idan na juya."
Tsaye ta mik'e tare da d'aukar lotus d'in data goge hannu ta saka masa shi a
aljihun gaban riga tace "ka aje min shi, gobe zan tambayeka."
Saida ya gama mata kallon raini kafin ya gyara tsyuwarsa yace "idan baki son ana
kallonki, to ki zama kamilar mace ta yanda ba zaki rinjayi shed'anun dake cikin
zuk'atanmu ba bare har mu kalleki , ni kaina nasan nayi zunubi kuma dole na nemi
gafarar ubangijina akan hakan, sannan ki sani ni ba d'anki bane da zaki takani
yanda kike so, haka kuma talaucina bai k'ask'antar dani izuwa matakin dake kike
k'ok'arin d'orani a kai ba, ina fata kin fahimta."
Yana fad'a ya juya bar bureaux d'in, ita kuma ta bishi da kallo tare da tunanin
koya masa hankali.
Kasancewar bata jima da fara aiki a wajen ba yasa har yanzu akwai rashin sabo,
yanzu haka tattara kayanta tayi Habiba ta biyota dasu ta nufi gida saboda bacci
kawai take so tayi.
********************
Tunda ta shiga gidan taga guardcord (bodyguard) d'in mahaifinta kuma taji shiru
dan haka ta shiga babban falon da zai sadata da nata d'akin, duk da ba bak'on abu
bane a wajenta amma dai ta tsorata, tunda taji sautin tasan mahaifinta ne ke dukan
mahaifiyarta, da gudu ta nufi d'akinshi ta jefar da jakarta, bata tsaya komai ba ta
kutsa kai cikin d'akin ai kuwa bata tsaya ba wajen kaiwa mahaifiyarta d'oki , saman
gadon ta fad'a ta rumgumo mahaifiyarta tana k'ok'arin kare jikinta, tunda ya ganta
ya jefar da wayar hannunshi ya fara zare ido, yana kakkare jikinshi saboda daga shi
sai gajeran wando, kama mamanta tayi suka sauko daga gadon ta d'auki rigarta a
k'asa daya ketata da qarfi ta rufe mata jiki, tana rik'e da mahaifiyarta ta
kalleshi sai k'yabta ido yake tace "wallahi idan ka sake dakar min uwa, to ka sani
justice (kotu) ce zata rabani da kai, dan ba zai yiyuba ka dinga shak'o giyarka
kana zuwa kana narkar min uwa ba."
Tana fad'a suka fita daga d'akin saida ta kaita har d'akinta ta d'auko mata riga
doguwa ta sauya ta d'auko mata maganinta ta bata tasha sannan ta kwantar da ita
tana rufeta tana fad'in "banga abinda kike tsinta a gidan nan ba da ba zaki barshi
ba, amma da nayi magana sai kice saboda ni kike zaune, ni zan kula da kaina ki
koma wajensu Mammie ki zauna."
Tana fad'a ta juya itama ta koma nata d'akin ta cire kayan jikinta ta watsa ruwa
sannan ta d'auki kayan data fi jin dad'in zama dasu a cikin gida ta saka, wando ne
na jeans fari tas sai dai iya cinyoyinta ya tsaya sai kuma riga ta dan sauko har
cibiya amma k'ananan hannuwa gareta, kwance tayi ba jimawa bacci ya d'auketa.
*******************
Tana tashi bayan la'asar brush tayi kawai ta fito bata damu dayin sallolin dake
kanta ba, a falo ta zauna saman lunstumemiyar kujerar dake kai tana kallon tv, mai
aiki ce ta kawo mata abinci tana ci mamarta ta fito rik'eda carbi , zaune tayi tace
"kinyi sallah?"
Haka suka kasance wunin ranar ba wani dad'i, sai dai takalmin data d'ora a internet
sun samu masoya, anan wasu manyan 'yan kasuwa suka ce suna son dayawa akan sari,
anan suka tsayar akan gobe zasu zo ma'aikatar tasu sai suyi magana, kasancewar
manyan mutane ne yasa tace wa mahaifiyarta ta tasheta k'arfe takwas na safe danta
shirya da wuri, cikin dare sosai tana kwance tana chat taji motsi a falo, lek'owa
tayi abin mamaki *Mujahhid* ne yake shiga d'akinshi cikin tsananin maye tare da
wata budurwa, tsaki taja tace "dubunka ta cika, wallahi saika bar gidan nan tunda
bana ubanka bane."
Komawa tayi d'aki ta ci gaba da abinda take har bacci ya d'auketa da ecouteur a
kunne tana sauraren wak'ok'i iri iri.
*********************
*Da safe* zaune take a tsakiyar wani faffad'an gado na alfarma cike da magagin
bacci da har yanzu bai saketa tace "nifa wallahi kun takura min, wai dole saina
tashi ne?"
Sake komawa tayi ta kwanta taja wata kakkabrar zanin rufa ta rufe, matar dake tsaye
gefenta ta sake yaye zanin tana fad'in "dole ki tashi, ke da kanki kika ce na
tasheki takwas daidai saboda bak'in da zasu zo."
Tana jin haka ta tashi firgigit tana zare ido tare da kallon mahaifiyar tata tace
"k'arfe nawa yanzun?"
Ai kuwa kamar zata bige uwar haka ta diro daga kan gadon ta nufi k'ofar fita, ta
bud'e k'ofar matar tace "ina kuma zaki je da wannan kayan?"
Tsayawa yayi ya juyo yana kallonta, sai dai bashi kad'ai ba harda masu tsaron
lafiyarsa dake cikin tenue d'insu na sojoji su hud'u, kayan baccine wando iya
cinyoyinta sai kuma k'arama kuma siririyar riga mai kamar puscier, abinka ga fara
kuma doguwa kyakyawa, ba tare data kulasu ba kawai tace wa mahaifinta "papa, ku
jirani na shirya saiku ajeni a service d'in."
Juyawa kawai tayi ta nufi cikin gidan tana fad'in "bana jin tuk'i yau."
Ajiyar zuciya ya sauke dan babu yanda zaiyi dole ya jirata, yayin da jami'an suka
bita da kallo iri iri suna kallon mazaunanta dake juyawa gwanin ban sha'awa.
Kasancewar tana sauri yau shi yasa bata jima douche ba ta fito cikin k'ank'anin
lokaci ta shirya, doguwar rigar tattausan tissue (matériel), wacce ta kama jikinta
sosai k'asa kuma ta bud'e, kallabin rigar kawai ta d'aura ta d'auki jakarta tasa
takalmi ta fito bayan fessa tsadaddun turarukanta masu d'aukar hankali dayawa, duk
da jan jan-baki ne ta shafa kad'ai amma hakan bai hana kyawunta fitowa ba sai
k'ananun kitsonta da suka kwanta a gadon bayanta.
Tana fitowa matar na zaune a d'aya daga cikin kujerun falon ta kalleta, cike da
nuna rashin jin dad'i tace "me yasa kullum kike burin mu dinga nanata kalma d'aya,
yanzu ko nauyi ba kiji ki fita haka babu gyale bare hijabi."
Wata babbar fridge ta bud'a tana fad'in "kece kike sha'awar bawa kanki wahala da
kike maimaita abu guda kullum."
Tana fad'a ta d'auki wani gateau da holandia yagourt ta fice abinta, tana zuwa
jami'in ya bud'e mata gidan baya kusa da mahaifinta, shagalta da yayi da kallonta
yasa bai bud'e k'ofar da kyau ba, cikin jin haushi ta daka masa tsawar da saida
kowa ya zabura dake wajen tana fad'in,
Da sauri ya bud'e mata ta shiga tana jan tsaki tana fad'in "sakarkarin banza kawai,
ni banga abinda suke tsinana maka ba da har yanzu kake tare dasu, in banda
k'yauyenci da shirme babu abinda suka sani."
Haka suka ja motocin, mota d'aya ce a gabansu sai kuma wata d'ayar a baya tasu a
tsakiya, saboda tsaro.
Gâteau ta fara ci tana korawa da tana ci gaba da mita, shi dai mahaifinta
saurarenta kawai yake,amma hankalinshi baya wajenta, har saida suka isa suna
tsayawa a babban masana'antar ta sake kallensu tace "kenan babarku ce zata bud'e
min k'ofar ko me?"
Wanda baya tuk'in ne ya fito ya bud'e mata, tana fita ta kalli mahaifin nata tace
"idan kaje mashayar ka shawu son ranka, kaga saika shigo mana gida a buge."
Kallonta kawai yayi baice da ita k'ala ba, ita kuma ta wuce ta tunkari ma'aikatar,
tana shiga ma'aikatan suka fara shan jinin jikinsu yayin da kowa ke gaisheta, sai
dai babu mai sa'ar da zata amsa mashi gaisuwar , secretaire d'inta mai sunan
*Habiba* ce ta karb'i jakar hannunta ta fara take mata baya tare da fad'a mata
programme d'insu na yau bayan sun sallami bak'in, juyowa tayi a hassale ta kalleta
tace,
"Ki soke duk wani programme na yau dan babu abinda zan iya, bak'in nan kawai zan
gani na koma gida."
Shiru tayi suka haura sama a cikin acessaire in da zai sadasu da d'akin da bakin
suke, tana shiga kallon mutanen ya dawo kanta in da kowa ke yaba kyawun fuskarta
dana hallita da Allah yayi mata, bakin turawa ne duka ta mikawa hannu cikin sakin
fuska suka gaisa kafin ta zaune kujerar dake tsakiyar sauran kuberun , saida kowa
ya zauna mazauninshi harda secretaire d'inta ta zaune daga bayanta danta d'auki
rahoton abinda zasu tattauna, sai lokacin kuma kallonta ya kai ga wata kujera da
babu mazauninta, kallon habiba tayi tace,
Za tayo magana suka ji an bud'e k'ofar wajen, ganin saurayin cikin hanzari yake
yasa ta tashi tsaye cike da raini tace "sannu da zuwa yallab'ai."
Kallonta yayo ya kalli mutanen dake wajen, take ya fahimci abinda take nufi dan
haka yace "je demande vos esxuze, je..."
Tsawar data masa yasa yayi shiru "yi mana shiru, kenan muna zaune nan dan ka zo ka
bamu hak'uri, kai mahaukacin ina ne da baka san mahimmancin lokaci ba? kawai mutane
jahilai daku babu abinda kuka iya sai tumasanci da banlag...."
Cikin b'acin rai ya ci gaba da cewa "me kika d'auki kanki? su waye jahilan? fad'a
min matakin karatunki da har kike fad'a min haka, to bari kiji wallahi kika sake
kirana jahilai saina fasa miki baki a wurin nan, ke in ba jahilce ke damunki ba me
yasa zaki kira wasu da jahilai, kuma bari kiji aikine da nake a service d'inku
zaisa kimin kallon banza ko? to na daina daga yau, saiki zauna ki cinye wurin idan
zaki iya."
Yana fad'a ya juya ya barta nan tsaye sake da baki, a fusace ya bar wurin kayanshi
ya had'a dake kan teburd'inshi yana shirin fita, ta baya yaji an dafa kafad'arshi,
juyowa yayi ya sauke idonshi akan babban abokinshi....
_NA_
_SAMIRA HAROUNA_
_DEDICATED TO_
*MA FAMILLE*
_Bismmilahir-rahman-rahim_
_Manzo (S.A.W) yace "Imanin d'ayanku ba zai cika ba har saiya soma dan uwansa
abinda yake so ma kansa."_ *Imamul Bukhari da muslim suka ruwaitoshi*
2⃣
"Me kuwa ya faru, na baro mata wurin,kuma daga nan gidanmu nayi dan ba zan iya aiki
a k'arkashin yarinyar nan ba."
Da sauri ya rik'e hannunshi daga shirin rataya jakar da yake shirin yi yana fad'in
"me kace? Faruk kana da hankali kuwa? kasan me kake shirin aikatawa?"
"To bari kaji in fad'a maka kuskuren da kake shirin aikatawa, wannan aiki shekara
hud'u mukayi muna neman abinyi amma bamu samu ba, ka sani kafin mu sameshi munsha
wahala sosai, bama wannan ba Faruk me yasa ba kayi tunanin mutanen da suka ci suke
sha ta dalilinka ba, ko ka manta da irin nauyin dake kanka ne, sannan ka sani
wannan aikin da kake neman watsarwa a yanzun, to ka sani akwai dubbun nan mutanen
dake qaunarshi kuma d'aruruwan mutane ne zasu so da burin samun kujerar daka tashi,
dan haka kayi tunani kafin ka yanke hukunci."
Barinshi yayi tsaye yana tunanin abinda ya fad'a, ganin baida wata mafita data
wuce ya zauna yasa ya ajiye jakar cikin sanyin jiki ya koma sale d'in bak'in, a
hankali ya bud'e kofar yayi daidai da har sun gama tattauna abinda ya tarasu,
kallonshi take sosai da mamakin abinda ya maidoshi, saida ta bawa bakin nata hannu
sukayi musabaha sannan suka wuce, saida ta gama kallonshi shi kuma ya kasa cewa
komai, wayarta ta dauka Habiba ta biyota da jakarta suka fita daga wajen, acessaire
(lift) suka shiga Habiba na shirin rufewa ya kutsa kai ciki, tana ganin haka ta
fito cikin zafin rai ta nufi matattakalar bene da sauri ta fara sauka, da sauri
shima ya fito harda gudu gudu ya tari gabanta ya soma sauka ta baya yana kallonta
yana fad'in "magana zamuyi dan Allah ki saurareni."
Bata saurareshi harta sauka suna kaiwa tsakiyar ma'aikatar ya sake tare gabanta
yana fad'in "dan Allah ki saurareni, hak'uri zan baki...."
Marin daya sauka a kunci ne yasa yayi d'uf, dafe yake da kunci yana kallonta, itama
shi d'in take kallo haka kuma duk mutanen wajen ita su suke kallo, kafin wani abu
ya sake faruwa sai kuwa Faruk ya zabgeta da marin da yafi wanda ta mishi.
Dafe kuncinta tayi baki bud'e tana kallonshi saboda mamaki, kasa motsawa tayi daga
wajen yayin da shi kuma ya d'ora mata da wani sabon bayani "wallahi ke baki isa ba
kisa hannu ki mareni, akan me? saboda kawai muna k'asanki."
D'aukar kayanshi yayi ya bar ma'aikatar gaba d'aya, cikin fushi da ba zata iya
misaltashi ba ta bar wajen, gudu take sosai a mota ba tare da tunanin wani abu ya
sameta ba.
Tana shiga ko rufe motar ba tayi ba ta wuce cikin gidan da gudu, daf da k'ofar
shiga ta fad'a saman mutum, kallon kallon suka tsaya yi tana gama gane waye ya
rik'eta ta fizge jikinta tana tureshi baya, shi kuma murmushi kawai yake mata,
cikin masifa da son sauke bala'inta a kanshi ta fara magana,
"Meye haka, kai mahaukacin ina ne? baka ganine da zaka bigeni harda wani tab'a
jikina? to bari kaji wallahi yau duk uban daya tsaya maka a garin nan saika bar
gidan nan, tunda bana ubanka bane."
Duk da maganganunta sun masa zafi amma daurewa yayi yace "bake kika kawoni ba, ba
kuma zaki fitar dani ba idan banyi niyya ba."
Sake fizge hannunta tayi ta tureshi iya k'arfinta tace "banza kawai, wani arzik'i
mahaifin naka yake da da har zaka fad'a min, to bari kaji yau dole ka bar gidan
nan, dan ba zai yiyuba ka zauna kana kawo mana mata a gida ba bayan kasha giyarka."
Muryar Mamie ce suka ji tace "Khairat dama rashin mutuncin naki har ya kai haka?
waike wace irin yarinya ce marar ganin girman na gaba da ita? me yasa kika zab'arwa
kanki wannan kakkaussar rayuwar da ba zata kaiki ko ina ba a matsayinki na mace?"
K'arasa shigowa tayi cikin falo tana kallon uwar tace "nice ai ya kamata na miki
wannan tambayar, me yasa kika auri mutumin da kinsan baya da hallaye masu kyau?
sannan karki sake cemin bana da mutunci, dan inma hakane to gadone nayi"
Kafin tayi wata magana ta d'ora da "kinga, wallahi yaron nan ya bar gidan nan yau,
idan kuma ba haka ba zansa Papa yayi rashin mutunci a gidan nan, idan kuma shiya
kasa saboda yana tsoronki, toni da kaina zanyi kuma zaku sha mamaki."
A fusace ta rab'a uwar tayi d'akinta ta barsu nan, hawayen da suka fara taho mata
ne tayi saurin saka hannu ta share tana kallon Mujahhid, murmushin yak'e ta masa
tace "kana ji ko yarona, kayi hak'uri dan Allah k....."
Katseta yayi ya matso kusanta da sauri yana fad'in "karki damu Mamie, ba komai
wallahi, zan tafi, amma ni ke nake tunani yanda zaki ci gaba da rayuwa a gidan nan
cikin kad'aici."
Kallonshi tayi tace "a'a, karka damu dani, aini na saba, zan ci gaba da zama a
haka, har lokacin da Khairat zata fitar da mijin aure, dan aurenta ne ya tsayar
dani gidan nan."
Tana shiga d'aki ta jefar da jakarta ta k'arasa gaban coiffeuse tasa hannu tayi
watsi da kayan dake wajen, matuk'a ranta a b'ace yake kuma tana so tayi abinda yafi
wanda aka mata ciwo, a hankali ta fara zamewa a jikin bango tana sulalewa har takai
qasa, fashewa tayi da kuka sosai, ta jima a gurin tana kuka har saida mai aiki ta
bud'a d'akin zata shigo, cikin daka tsawa tace "ki fita ki bani wuri, bana son
ganin kowa."
Abinda ba'a so ne ya faru, saboda tsananin damuwa da kuka yasa qirjinta ya fara
matsanancin ciwo haka kuma kanta ya fara mata bala'en'en ciwon da tafi fatan
mutuwarta a kanshi, jin haka yasa ta rarrafa ta bud'a coffre ta d'auki maganinta,
duk da dishidishi take gani hakan ta duba amma bata ga ruwa ba ba a d'akin ,
k'arfin hali tayi ta tashi ta nufi k'ofa danta samu ruwan, tana kusa ga kaiwa kawai
ta fad'i a guri numfashinta kad'an yake fita, hannayenta ne duk bisa kanta saboda
yanda yake fizgarta, daga haka kuma bata sake sanin meya k'ara faruwa ba a gaba.
*Da misalin* 16:30 Papa ya shigo gidan, Mamie na zaune akan kujera cikin damuwa da
tunanin halin da Khairat take ciki, ba tare da sallama ba kawai ya zauna kusa da
ita yana fad'in "sannu da gida."
"Ba dai Khairat bata dawo ba?" ya fad'a yana cire hular kanshi.
Saida ta sauke ajiyar zuciya tace "bata wuce awa d'aya ba da fita ta dawo, tana
d'akinta."
"Bacci take?"
A sanyaye tace "gaskiya ban sani ba, ta shigo kamar ranta a bace yake, harma suka
samu matsala da Mujahhid wanda yayi sanadiyar komawarsa gida, amma tunda ta shiga
d'aki bata fito ba, kuma mai aiki taje ta dubo halin da take ciki ta korota."
Jin tayi shiru yasa ya kalleta yace "ina jinki, sai akayi yaya?"
Tsaye ya mik'e yana girgiza kai yace "ban san me yasa kike nuna mata rashin
kulawarki ba kamar ba 'yar da kika haifa ba, da bake kika haifeta ba sai nace ba
kya sonta, kinfi kowa sanin duk baccin da Khairat za tayi ba zata kai wannan
lokacin tana bacci ba, amma ki kasa duba halin da take ciki."
Yana bud'e k'ofar ya k'arasa a guje yana fad'in "oh mon Dieu, Khairat, Khairat!!!."
Maida kallonshi yayi ga Mamie wacce ta shigo yanzu, cikin b'acin rai yace "kin gani
ko, kin gani abinda kika jawo mana, wai me yasa kike nunawa yarinyar nan rashin
kulawa ne? ki dubi sakacinki abinda yake nema yaja mana."
Mamie da bata san meya faru ba itama cikin fad'a tace "to miye anfanin kulawar da
zan dinga nuna mata, naga kaima da kake nuna mata kulawar ba wani girmanka take
gani ba, bare kuma ni à banza...."
Duk da ta kai k'arshen aya amma saida ta dire kalmar ba daidai ba saboda tsawar
daya mata, cikin d'aga murya yace "dallah ki min shiru, zaki kama min ita ne ko
kuma burinki ta mutu?"
Qafafunta ta kama shi kuma ya d'auki duka rabin jikinta suka nufo da ita waje,
ma'aikatan gidan na ganin haka suka fara tambayar lafiya meya sameta, biyarsu suke
a baya har chauffeur ya bud'e musu k'ofar mota suka kwantar da ita a baya sannan
suka shiga suka bar gidan, ma'aikatan kowa jini kan akaifa , ba zasu ce suna jin
dad'i ba saboda rashin lafiyarta , amma dai sun san sun d'an samu hutu na wani d'an
lokaci.
********************
*Faruk* ne zaune akan taburma shi da abokinshi *Ishaq*, yayin da wata dattijuwar
mata mai kamala ke gefensu akan kujera yar tsugunno, sai kuma babban malamin dake
tsaye ya tisasu a gaba yana fad'a akan aikinshi daya baro, cikin fad'a ya sake
cewa,
"Kai yanzu badan baka da hankali ba, daga k'aramin abu sai kawai kayi hushi, kai
gaka uban zuciya ko? to bari kaji wallahi wannan aikin idan har ka bari ya kubuce
maka, to wallahi za kayi nadama da daka sani, kai kafi kowa sanin kaine kusan rabin
k'arfin gidan nan, to idan kace ka daina aikin kenan duk yayanka ne zai had'a ya
d'auki har nauyinka.?"
D'ago kanshi yayi yace "Baba bafa k'aramin abu bane, marina fa tayi a fuska,
wallahi ko k....."
Tsawar da Baba ya masa yana fad'in "ta mareka d'in, nace ta mareka saime? idan baka
rama ba mutuwa za kayi, kuma tun farko ai kai kaja komai."
"Dan haka ka jini da kyau, ka tashi yanzun nan ga Ishaq nan ya rankaka kuje ka
sameta ka bata hak'uri, karka yarda ka rasa wannan aikin, in kuma kayi sake to ka
sani, wallahi abincin gidan nan ma ka daina ci tunda kai sarkin zuciya ne, waika
gaka *Umar Faruk* ko?"
Sake d'ago kai yayi yace "Baba, cewa fa kake naje na...."
"K'warai haka nake nufi, dole sai kaje ka bata hak'uri, in kuma ba haka ba to duk
matakin dana d'auka kanka, kai ka siyo da kud'inka."
Sai lokacin mahaifiyarshi tace "in banda abin Umar faruk ma, kaida maganar aure ka
keyi amma kake k'ok'arin aje aikin da shine gatanka."
"To, fad'a masa dai, tunda naga shi baya da hankali zuciya ce kawai yasa a gaba."
Ishaq ne yace "kaga, ba wani abin damuwa bane, yanzu ya tashi mu tafi mu koma
service d'in mu samu manager, nasan insha Allah zai taimaka mana kamar yanda ya
taimaka mana muka samu aikin nan da farko."
Ajiyar zuciya ya sauke mai nauyi kafin ya kalli Baba yace " kuyi hak'uri Baba,
insha Allah zanje na bata hak'uri kamar yanda kuka ce."
Addu'a Mama ta bishi da ita da fatan samun dacewa, Baba kuma na sake jaddada masa
ya tabbatar ya bata hak'uri sosai harta hak'ura, haka suka fito da niyyar tafiya
ma'aikatar wajen manager.
Sun samu manager kuma Ishaq ya fad'a masa komai daya faru, yayi mamaki sosai dan
baisan wainar da aka toya ba, yayi jimami sosai tare da k'ara tsorata Faruk akan
karma ya fara tunkararta ya jira hukuncin da mahaifinta zai d'auka a kanshi ko kuma
ita da kanta, baiji shakka ko d'ard'ar ba akan matakin da zasu d'auka, matsalarshi
d'aya shine yanda mahaifinshi ya d'auka da zafi sosai, ganin baice komai ba yasa
manager cewa,
"A gaskiya *Umar Faruk* ba zan yarda a dalilinka na rasa nawa aikin ba, kayi
hak'uri, amma taimakon da zan iya maka na riga da nayi maka shi, shawara d'aya da
zan baka kawai shine, idan har ta dawo d'aukar fansa to ka qasqantar da kanka, ka
nuna mata kayi nadama kuma a bisa kuskuren rashin sanin ko wacece ita ka mareta,
idan kayi sa'a ta iya yafe maka, amma gaskiya bana tunanin zata hak'ura, dan
wallahi yarinyar nan rashin mutuncinta ya kai mak'ura, bata kallon kowa da idon
daraja babu tausayi ko imani a zuciyarta, kuma tun ranar da mahaifinta ya mallaka
mata masana'antar nan na fad'a muku dukanmu sai munyi hak'uri da ita, saboda
kaushinta yayi yawa."
A sanyaye Umar faruk yace "zan jaraba na gani, bara naje bureau d'in nata."
Murmushi manager yayi yace "ta yaya kake tunanin zata zauna a wajen nan, ina jin a
lokacin da naga tafiyarta to a lokacin ne abun ya faru."
Faruk ne yace "a'a fa Ishaq, gaskiya bana so naje gidansu, idan taga haka zata san
nadamu sosai, zata d'auka gaba d'aya na bada rayuwata wa aikin nan, hakan kuma
zaisa ta qara wani rashin mutuncin."
"Muji ta d'auka a hakan in har ba zata koreka ba, meye a ciki?"
Kai Faruk ya girgiza yace "waiku me yasa ne kuke shakkarta har haka? mutum ce fa
kamarku kuma mace mai rauni a kanku, me yasa zaku dinga tsoronta har haka, nifa
wallahi bana son irin haka gaskiya, dan wannan ai bayar da maza kuke, yarinyar da
da zaku bud'e mata ido sau d'aya dole zata fara shakkarku itama, amma duk kubi kuna
wani tsoronta kamar ita ta halliceku."
Fuskar manager d'auke da murmushi yace "bawai muna jin tsoronta bane, sai dai ka
sani kowane d'an adam a rayuwa yana buqatar ci da sha kafin ya rayu, to tamu
k'addarar ta damka cin mu da shanmu ta sanadiyarta ne, ita kuma bata da kirki duk
da bata jima a garin nan ba, amma na samu labarinta sosai kamar wanda yayi rayuwa a
gidansu, dan ba tun yau muke tare da mahaifinta ba, kaga dole mubi a sannu."
Faruk ne ya tashi tsaye yace "zamu je gidan, ina fatan ta amince kodan saboda
Baba."
Cikin tsokana Ishaq daya mik'e shima yace "da kana so amma kake wani nuna baka damu
ba."
"Amma ai kaji me nace, ina fata ta amince saboda Baba." ya fad'a ba tare daya
kalleshi ba.
Suna fita akan mashin d'in Faruk suka kama hanyar zuwa gidansu Khairat......
_Shin kuna ganin za suyi nasara kuwa? to wai zama su samu ganin Khairat d'in ko
kuwa dai...???_
*********************
Suna zuwa k'ofar gidan suka tsaya suka sauka akan mashin d'in suka nufi k'ofar
gidan, mai gadin gidan ne mai sanye da kaki irin na sojawa ya taresu yana fad'in
"yadai malamai, daga ina, wa kuke nema?"
Ishaq ne yace "sannun ko, dan Allah munzo ganin Hajia Khairat ne."
Kallon tuhuma ya musu yace " Hajia Khairat? to tasan da zuwanku ne?"
Kallon juna sukayi tare da yin shiru na 'yan dak'ik'u kafin Ishaq ya sake cewa
"gaskiya bata san da zuwanmu, mu daga service d'inta muke, manager ne ya turo mu
saboda wani aiki daya d'an taso."
Kallonshi Faruk yayi saboda jin abinda ya fad'a , mai gadin ne yace "kuyi hak'uri
mazaje, duk wanda ku kaga ya shiga gidan nan to an san da zuwanshi koda kuwa d'an
uwane, kunsan gidan manyan mutane."
"Yanzu kenan babu wata dama da zata saka mu ganinta?" cewar Faruk.
"Gaskiya babu, dan Hajia Khairat ko tasan da zuwan mutun ma zata iya tsayar dashi a
k'ofar gidan nan na tsawon awa uku, idan na barku kuka shiga zan iya rasa aikina."
Mai gadin ne yace "in dai abu mai mahimmaci ne, to zan iya fad'a muku wurin da zaku
sameta, yanzu dai kunga ta shiga gida, kuma da alama ranta a b'ace ta shigo."
Da mamaki Faruk ya kalleshi yace "malam, mufa a ma'aikatarta muke aiki, ba wani abu
bane a tsakaninmu da ita ba, amma ta yaya zamu sameta a wannan wajen kuma fa sai
cikin dare."
D'aure fuska mutumin yayi yace "kunga dan Allah kubar nan, taimako kuka ce kuma shi
nayi muku."
Yana fad'a ya koma mazauninshi ya barsu tsaye, mashin d'insu suka hau akan hanya
suna tunanin wata shawarar, amma Faruk yace shi bai tab'a zuwa gidan rawa ba ba
kuma zai fara zuwa yau ba.
Suna zuwa gida suka fad'awa Baba yanda ake ciki, fafur Baba ya rufe ido yace bai
yarda su tashi su koma, ganin basu son tafiya yasa Baba ya tisa k'eyar Umar faruk
gaba yace su tafi, haka kuwa akayi akan mashin d'inshi suka tafi, amma wannan karan
suna zuwa mai gadin yace musu an tafi da ita likita babu lafiya, da alama ma kamar
babu rai a tare da ita, tabbas Umar faruk yaji ba dad'i kuma yana tsoron ace abinda
ya faru tsakaninsu ne ya janyo faruwar hakan, likitar aka fad'a musu suka nufi can
shi da Baba.
Cikin sa'a kuwa suna zuwa sukaga masu tsaron mahaifinta a kusa da d'akin da aka
shigar da ita cikin gaggawa, kusa da d'akin suka tsaya amma ba suyi magana ba
saboda ganin mahaifin nata nata kai komo a wajen ya gagara nutsuwa, duk da baisan
mahaifiyarta ba amma da gani yasan ita ta haifeta saboda tsananin kamar da suke,
kuma dama tun daga fatar jiki zaka san uwace tayi ba mahaifinta ba dake tillik'ik'e
kuma bak'i wulik dashi,🤣 had'in gambiza ba, duk da akwai damuwa sosai a fuskarta
amma dai babu alamun hawaye a tare da ita.
D'auke kai sukayi kamar ba wajensu suka zo ba, amma abin mamaki shine muryar Baba
da sukaji yace "kina zaune hankali kwance, da alama so kike ta mutu ki huta ko? to
ta Allah ba taki ba wallahi."
Tsaye ta mik'e cikin jin zafi tace "eh, so nake ta mutu na huta, kai a ganinka idan
ta mutu ba zan samu salama ba? idan da abinda ya janyo mata wannan halin bai wuce
kai ba, wallahi duk kai kaja mana halin da muke ciki saboda bak'in halinka,
yarinyar nan tun tana k'arama ta fara fahimtar halayenka, amma hakan baisa ka daina
ba, me kake so ta zama? wallahi ka sani alhakin lalacewar rayuwarta yana wuyanka
ne, addu'a d'aya nake mata yanzu shine, kar Allah yasa ta fara shaye shaye da bin
maza kamar yanda kake lalata 'ya'yan wasu."
Fizgota yayi daf dashi cikin hassala yace "ke ya isa haka, ke me yasa baki da kunya
ne? a cikin mutane zaki nime tozarta ni, kuma ni ai nasan 'yata, wallahi ba zata
tab'a bin maza ba."
Fizge hannunta tayi tasa gyalenta ta share hawayen idonta tayi murmushin takaici
tace "kenan baka so ta fara bin maza ko, ka manta da fad'ar Manzo (S.A.W) ne,
_cewar duk abinda kayi sai an maka_? kayi gaggawar aurar da ita, idan kuma ba haka
ba to wallahi ni zan barka na koma wajen iyayena, dan ba zan iya supporter naji
kona ga wani abu ya sameta ba."
"Ke marar mutunci, wallahi zai karyaki a warin nan, shashashar banza kawai."
Duk maganar nan yayita ne da d'aga hannu kamar zai mareta, zaburowa tayi tace "ka
dakeni mana, ina jin tsorone ? dukanka wane irine ban gani ba ai sai dai kuma na
gaba."
Hannu ya d'aga kam da nufin kai mata mari sai kawai ya tsaya cak saboda ganin
Khairat d'in da aka shiga da ita ranga ranga amma ta fito da k'afafunta, kamar dai
yanda suka taho da ita haka ta fito babu takalmi ba kallabi, kallon iyayen nata
kawai take sai huci take saukewa, takowa ta farayi gabansu docteur kuma ya biyo
bayanta yana neman ta tsaya dan farfad'owarta kenan taji hayaniyar iyayenta, saida
ta tsaya gabansu ta kallesu da kyau sannan ta kalli drivensu tace "muje ka mayar
dani gida."
Wucewa tayi mahaifin nata ya rik'e hannunta yana fad'in "gimbiyata, ina kuma zaki
je ya jikin naki?"
Da iya k'arfinta ta fizgo hannunta tana mashi jan kallo tace "lache moi ma main."
ta k'arashe da d'aga murya.
Wucewa tayi suka bi bayanta Papa na kiran sunanta harta shiga mota ta rufe, haka
suka shiga motar ba tare da kowa yayi magana ba har suka kai gidan.
Faruk kam da Babanshi mutuwar tsaye sukayi, mamaki ya gama kashesu a wurin, tabbas
akwai wasu abubuwa a cikin rayuwar gidan, da alama arzik'i ne Allah ya musu amma
babu kwanciyar hankali.
_Wallahi da auren wani mai kud'in gwara auren talaka in dai da kwanciyar hankali,
Allah ka k'ara mana kwanciyar hankali da ni'ima a qasarmu dama sauren qasashe baki
d'aya._
*********************
Gida suka koma dan sunga babu alamun nasara, amma duk da haka Baba bai hak'ura ba
yace koma da safe ya shirya ya tafi gurin aikinshi kamar yanda ya saba, watak'ila
idan da rabo ma ba zata masa magana.
_NA_
_SAMIRA HAROUNA_
_DEDICATED TO_
*MA FAMILLE*
*Manzo Allah tsira da amincin Allah su tabbata a garesa yace* " _Kaji tsoron Allah
a duk inda kake_"
*Rawahu muslim*
3⃣
Tunda ta shiga d'aki wanka tayi ta saka kayan data saba sakawa wato k'aramin wando
iya cinya da k'aramar riga, zaune tayi akan gado tana tunanin abinyi, har akayi
sallah magrib da isha amma bata tashi daga in da take ba, wani tunani da tayi yasa
ta tashi ta fito daga d'akin, duk da duka iyayen nata na zaune a falon amma babu
wanda ta kula bare ta masa magana, farfajiyar gidan ta fita, masu tsaron mahaifinta
ne zaune a kusa da mai gadi suna hira, tsaye tayi nesa dasu cike da raini tace
"kuzo nan."
Kallon juna sukayi cike da raini suka tashi a kasalance suka nufi wajenta, tsaye
sukayi kowa ya d'auke kai babu mai kallonta, cikin jin haushi ta daka musu tsawa
"kai, ni kuke wa wannan kallon? to ku saurareni da kyau kuji aiki zan saku."
Shirun da sukayi yasa ranta ya sake b'aci , a harrzuk'e ta shak'o uwan rigar d'aya
daga cikinsu tana fad'in "kai matsiyacin banza, ku har kun isa ina magana daku kuna
wani d'auke kai, ko kun manta k'ark'ashin mahaifina kuke, kufa ba komai bane face
maqasqanta wanda suke wuni dare da rana a bayan iyayenmu domin tsare lafiyarsu,
yaushe kuka fara tunanin kuna da matsayi da har zaku rainani?"
Mai sauk'in cikin sune yace "kiyi hak'uri Hajia, ki fad'i aikin da zamu miki."
Tureshi tayi yayi baya baya kamar zai fad'i sannan ta kalli wanda yayi maganar tace
"ku nutsu ku jini da kyau, akwai wani saurayi da nake so ku d'auko min shi gobe,
ina so ku kaishi d'aya daga cikin gidajen Papa, idan kun d'aukoshi saiku kirani zan
sameku acan, amma kafin nazo ku tabbatar kun canzamin kammaninshi ta yanda ba zai
iya gane kanshi ba bare kuma wani."
D'aya daga cikine yace "amma ta yaya zamu iya ganeshi kenan?"
Sai lokacin ta tuna da hakan, a wulak'ance ta kallesu tace "ku jirani anan, yanzun
nan zan samo photonshi."
Tana wucewa wanda ta shak'e ma wuyan riga yayi wani huci tare da rik'e gudu yana
kallonta, a hassale yace "wallahi saina ma yarinyar nan rashin mutunci ta yanda
gobe ba zata sake sha'awar wulak'anta wani ba, dan muna aiki qasan mahaifinta bashi
ke nuna maqasqanta bane kamar yanda take d'auka, wallahi na gaji dan abinda take
mana ko wannan banzan mashayin uban nata bai isa ya mana ba bare kuma ita banza."
D'aya daga cikine yayi dariya yace "toya zamuyi tunda Allah ya d'orasu akanmu, kuma
da kake cewa zaka mata rashin mutunci, ita fa 'yar akuya kai kasan haka, kenan me
kake tunanin yi mata?"
Da sauri ya bashi amsa da "dukan tsiya zan mata wallahi har saina sab'a mata
kammaninta."
Shak'iyin cikin ne ya lashe baki tare da d'an cije leb'e yace "ku naku duk wasa ne,
irin yaran nan ai duka baya gyarasu, karfa ku manta gatane ta gani shi yasa take
abinda take so, ni wallahi ban tab'a jin wai na daketa ba, dan duka ba shine mafita
ba."
"Miye mafita to? danni dai na gaji da rainin hankalin yarinyar nan."
Saida ya kalleshu yana murmushi kafin yace "kona fad'a ma ba zaku iya ba, dan haka
ku barni kawai ni zanji da komai."
"Kamar ya ba zamu iya ba? ka fad'a in dai har za muyi maganinta wallahi za muyi."
Ajiyar zuciya yayi yace "kullum tana cikin qananan kaya, hakan kuma na tayar min da
sha'awata, abinda za muyi kawai mu takurata ta hanyar samun biyan buk'atarmu, ta
hakane kad'ai zamu iya huce abinda ta mana."
Tuni d'aya daga ciki har shaid'an ya k'awata masa abin, cewa yayi "kuma fa hakane
wallahi, dan shi fyad'e idan kayiwa mace ba zata tab'a mantawa ba har abada, kaga
zamu tashi 1-1 mu da ita ,ita ba zata manta ba muma ba zamu manta irin wannan cin
kashin data mana ba."
Hannu ya bashi suka bige suna dariya yace "da kyau mutumina ka fahimceni daidai,
kuma ma wannan yarinyar ai da gani kasan ba mune zamu fara ba, da alama wasu sun
rigamu kai da gani kasan ba budurwa bace, a idone kawai muke ganin haka."
"Gaskiya ne kuma."
"To amma ni gaskiya ina d'an jin tsoro, gaskiya ban tab'a yi ba tunda nake, kuma
kaga za ayi binciki akan lamarin nan idan aka ganemu, kunga fa shikenan munyi
asarar rayuwarmu mun b'ata k'uruciyarmu a banza."
"Bama za'a ganemu ba, ai za muyi anfani ne da kasancewarmu sojiji miyi aiki da
ilimi, insha Allah komai zai wuce babu abinda zai faru, kuma muma ai bamu tab'a yi
ba."
"Abu mai sauk'i, kawai za muyi anfani da gidan rawar da take zuwa duk kwana uku sai
muyi komai acan, kunga ta haka zamu fita daga zargi kuma babu wani bincike, domin
kuwa cikin biyu dole suyi tunanin d'aya."
"Na farko za suyi tunanin kodai ita da samarinta ne da suka saba shek'e ayarsu, ko
kuma dai tunda wajen rawa na b'ata garine , kaga za'a ce ta had'u da marasa jine
kawai suka mata fyad'e wannan shine."
Cikin dariya d'aya ya bashi hannu yana fad'in "gaskiya Musa kanka naja sosai,
wannan tsarin fa yayi."
Cikin dariyar mugunta yace "ko baiyi ba dole zan fito da wani, dan burina kawai
buk'atata ta biya a kanta."
Musa ne yace " ku zama cikin shiri , dan ko yau bata fita saboda abinda ya faru,
watak'ila kwana uku mai zuwa ta fita."
Da wannan shawara suka tsaya akai.
_Allah ya kiyaye_👏
Tana shiga d'aki wayarta ta d'auka a saman gado k'irar IPhone XMax, kira ta aikawa
manager yana d'auka cike da salon bada umarni tace "ina so cikin 5 minute ka aiko
min da adreshin gidansu yaron nan tare da photonshi."
Tana gama fad'a ta kashe wayar, zaune tayi tsakiyar gadon tana jiran shigowar
sak'on manager, 2 minute saiga sak'on ya shigo adreshi da kuma photonshi, a hankali
ta furta sunan unguwar tasu " *Bassora*"
Take ta tuna marin daya mata, bata san lokacin data goge photon ba daga wayar
saboda b'acin rai, ajiye wayar tayi a gefenta ta fara sauke nunfarfashi ita kad'ai,
jin qirjinta ya fara nauyi yasa ta tashi ta bud'a coffre ta d'auki maganinta tasha
sannan ta koma gado ta kwanta, bacci harya fara d'aukarta wayarta ta fara k'ara,
tana dubawa taga sunan *Macho* ya fito, d'auka tayi ta d'ora a kunne tare da jan
zanin rufarta ta rufe tace "hello macho."
Daga d'aya b'angaren tace "yane macho? naganki shiru, yau kin fito ne?"
"To in dai hakane, nima saina bari har goben sai muje kawai."
Tana gam fad'a ta kashe wayarta gaba d'aya ta koma baccinta, a cikin bacci taji
kamar ana tab'ata, bud'a ido tayi taga mahaifiyarta ce ke shafar kanta sai kuma
mahifinta daga gefenta a tsaye, cike da masifa ta tashi zaune tace....
Da sauri Mama ta rufe mata baki tace "kiyi hak'uri Khairat, na yarda nayi kuskure,
amma ki sani mufa iyayenki ne dole mu damu da halin da kike ciki, mun kasa bacci
saboda tunanin damuwar dake damunki."
A raunane ta kalleta tana shirin fashewa da kuka tace "Mamie, ya kike so nayi?
kince na daina shiga harkarki kuma na daina, yanzu me kike so nayi to?"
Shiru sukayi kafin ta sake cewa "Mamie, ki fad'a min tunda muke dake kin tab'a nuna
min soyayyarki, kullum hantara kike da yimin fad'a tare da kokarin aibatani, ban
tab'a yin daidai ba a wajenki idan nayi ma bakya yabawa, babu abinda kuka koya min
babu abinda kuke koya min wanda zai anfane ni, da fadanku na bud'e idona kune
kullum cikin fad'a da aibata junanku, duk da kunsan matsalar da hakan ya janyo min
amma baku daina ba, shin so kuke sai ranar da kuka bud'e ido baku ganni a duniya
sannan zaku daina?"
Kuka Mamie ta fashe dashi tace "a'a Khairat, wallahi ina sonki, kinsan babu yanda
uwa za tak'i yar data haifa, ni ina so ki zama yarinyar kirki amma mahaifinki bai
damu da rayuwarki ba, ina damuwa da halin da kike ciki, kawai dai akwai dalilin da
suka sakani nuna miki rashin kulawa, amma ki yafe min kinji yata ba zan sake
nesantarki ba."
Ta fad'a tana rumgumeta, itama rumgumeta tayi cikin kuka tace "Mamie na riga dana
b'ata rayuwata."
Kafin ta k'arasa uban dake tsaye yace "wato kullum laifina ne ko, kullum burinki
shine ki d'ora min laifi ni kad'ai ko? to wallahi baki isa ki rabani da yata ba
muguwa kawai."
Kallonshi Mamie tayi tace "eh naji, in ni muguwa ce kai kuma fa? ai kaine babban
mugu tunda duk kaine ka jefamu halin da muke ciki, kuma wallahi in har baka tuba
zuwa ga Allah ba sai kayi *nadama*."
Matsowa yayi kusanta a hassale yace "wallahi kika sake magana a wajen nan saina
tattakaki, saboda kin rainani ina fad'a kina fad'a ko?"
"Allah yana gani bai rainaka ba kaine dai ka raina kanka, kuma nasan Allah ma ba
zai kamani da laifi ba."
"Ke..." wata k'ara da Khairat tayi yasa suka maida hankalinsu kanta, saukowa tayi
daga kan gadon ta kama hannayen iyayen nata ta tisa k'eyarsu suka fita daga d'akin,
saida ta kallesu kafin ta rufe k'ofar tace "ba zaku tab'a gyaruwa ba, wannan shine
babbar damuwata, baku damu daku tozartani ba ko a dinga yayatani ba, a duk in da
kuka samu kanku fad'a ku keyi da junanku."
Tana fad'a ta rufe k'ofarta ta koma gado ta dinga kuka da takaicin rayuwar
iyayenta.
_Novel hausa akace, dan haka kuyi hak'uri 'yan uwa, ba zan sake saka muku wani
harshe ba insha Allah domin kowa ya fahimta._
_Kafin sanin amsoshin bara mu koma baya mu fara sanin tushen labarin._
_Ku biyoni😍_
05/07/2019 à 15:14 - ~NANA KHADIJA~😍: 💑💑💑💑💑💑💑💑💑💑
*JIHADI*
_Umar faruk_
💑💑💑💑💑💑💑💑💑💑
_NA_
_SAMIRA HAROUNA_
_DEDICATED TO_
*MA FAMILLE*
_Bismmilahir-rahman-rahim_
4⃣
*TUSHEN LABARIN*
*Alhaji Mani Bukar* babban mutum kuma mai babban dangi, asalinshi haifaffan garin
*Maradi* ne kasuwancine ya kaishi *niamey* daga nan kuma harya tsunduma siyasa,
mahaifinsu mutum ne daya sha boko sosai ya k'oshi, hakan yasa yake da kula da
takatsantsan da yaranshi, matan mahaifinshi biyu amma gaba d'aya yaranshi guda
biyar saboda tazara da ake sawa, mahaifinsu irin tsofaffin masu kud'in nan ne,
hakan yasa bayan rasuwarsa yaransa suka kwashi rabonsu bayan rabon gado.
Bayan rasuwar mahaifin sai kowa ya fara abinda yaga dama, haka ma Alhaji Ousmane
wanda sukafi kiranshi da *Mani*, bana ce muku mutumin kirki ne ba amma dai yana da
wasu manyan halaye wanda muke da tabbacin duk mai aikatasu, to tabbas babu abinda
zai iya gagararsa kuma zai iya yin komai, wannan halaye kuwa sune *zina* da shan
*giya*, duk da wannan halayen amma ubangiji ya masa talala ta hanyar k'ara sakawa
dukiyarsa albarka, yana cikin holewarsa tare da abokai kuma sai Allah ya had'ashi
da *Na'ima*.
*Na'ima Bilal Abdallah*, yarinya mai hankali nutsuwa da kuma tarbiya, ta samu duk
wannan ne a wajen iyayenta saboda yanda suke tsaye a kanta, asalinsu mutanen
*Arlit* ne amma aiki ya kai mahaifinta qasashe da dama tun kafin aurenshi da kuma
lokacin da yayi auren harda cikinta ma, wanda daga qarshe dai a *India* aka
haifeta, bayan wasu shekaru sai mahaifin nata ya rasu, kasancewar a ma'aikatar ana
kula da ma'aikatan da kuma iyalensu yasa basu bari mahaifiyar da yarinyar sunsha
wahala ba, sunci gaba da zama a gidan compagnie tare da d'aukar d'awainiyarsu, a
lokacin tana da shekara ashirin suka zo Arlit ganin danginsu, wanda kuma suka tarar
da auren cousine d'inta wacce za'a kawota Maradi, dole tasa suka zo anan kuma
qaddararta ta fad'a dan anan suka had'u da Mani.
Tunda ya d'ora ido a kanta sai Allah ya jarabceshi da sonta har cikin zuciyarshi
kuma karo na farko da yaji yayi sha'awar aure, Na'ima kam tunda ta ganshi ita kuma
sai taji bai mata ba, bugu da qari da taji k'awayen amarya na fad'in halinshi na
son mata saiya dinga lasar baki yana maka kallon iskanci, gashi kuma Allah ya masa
muni dan babu wani abun birgewa a tare dashi, bak'i k'irin yake ga kuma k'iba da
yayi saboda hutu, haka ya fara nuna mata abinda ke ranshi amma bata bashi dama ba,
bayan shagalin ya kammala haka ya nemi sanin komai a kanta, rana kwatsam saiga Mani
Arlit kamar daga sama.
In dai tak'aice muku, abinka ga mai kud'i wanda dama zamanin nan masu kud'i suke
auren kyawawan mata, haka ya shiga ya fita tare da kutsawa duk cikin wani danginta
mai ruwa da tsaki a kanta har saida ya samu Na'ima, babu irin kuka da bala'in da ba
tayi ba ta kuma fad'a musu ba mutumin kirki bane, amma su basu ga haka ba dan yanda
ya nuna musu, a qarshe dai amarya ta tare gidanta a Maradi, bayan qalubalen data
fiskanta tun daga darenta na farko har zuwa sauran darare, bayan wani lokaci kuma
sai suka koma niamey da zama to tun daga shi sai dai suzo gaishe da dangi Maradi da
Arlit, bayan lokacin kad'an kuma sai mahaifiyarshi ta rasu itama.
Komawarsu niamey yasa ya k'ara tandarewa babu uwa babu uba babu mafad'i sai abinda
yaga dama yake yi, kuka a wajen Na'ima harya zama jiki dan a wannan lokacin baya
neman mata idan ba cikin gidanshi ba bayan ya shigo a bige, abun na matuk'ar
damunta sosai ga rashin sonshi ga kuma bak'in cikin da yake d'ura mata, wani abin
takaici shine lokacin data gama gane halinsa saita fara masa qiyo a shinfid'a in
har ya nemeta, abinka ga mashayi kuma haka zai zage qarfinshi ya daketa son ranshi
idan ta jikkata sannan ya turmusheta da qarfinshi ya biya buqatarsa, yarinya mai
kama da indien sai gashi ta fara fita hayyacinta ta fara lalacewa, wata uku ta
d'auka a wannan rayuwa, a lokacin data rame sosai saiya fara zargin ko cikine da
ita shi kuma bai shirya hakan ba yanzu, daya tambayeta sai tace bata da komai dan
itama bata sani ba, domin d'aukar mataki saiya fara bata qwayoyin hana d'aukar
ciki, kwana uku da fara shan maganin saita fara ciwon mara kafin kace me sai jini
ya fara mata zuba, bayan zuwa asibiti aka tabbatar ta cikin jikinta ya zube
sakamakon shan magani ba abisa qa'ida ba , duk da taji tayi asarar beby amma kuma
taji dad'i ko ba komai bata fatan haihuwa dashi.
Wata babbar dama ce ya bata dan tun daga lokacin saita fara shan maganin ba
qaqqautawa, tun bai fara saka abin a kanshi ba harya fara damuwa saboda ganin an
d'auki lokaci mai tsayi, wasa wasa sai gashi ta d'auki shekara biyar ba tare da
nadama ko data sanin abinda take yi ba, a lokacin ne kuma Mani ya dakatar da ita
tare da cewa ya shirya haihuwa, hakan baisa ta daina ba dan ranar ya shigo a bazata
ya samu za tasha maganin, a ranar dukan tsiya ya mata bana wasa ba sannan ya karb'e
duka maganin, cikin ikon Allah wata biyar saita samu ciki, amma kuma mai matuk'ar
had'ari da wahala.
Saboda shan maganin data dinga yi yasa mahaifarta a had'ari hakan yasa cikinta ke
buk'atar kulawa dan komai zai iya faruwa da bebynta, a lokacin da cikin ya fara
girma aka mata scanning aka tabbatar da macace a cikinta, take sai Mani yaji
qaunar yarinyar tun ba'a haifeta ba, visa ya samar musu suka koma India tare wajen
mahaifiyarta wacce tafi jin dad'in zamanta acan.
A lokacin data haihu aka tabbatar da mahaifarta ta lalace ba zata sake samun wata
haihuwar ba, babu yanda ta iya dole aka cire mata mahaifar domin rage mata nauyi,
Allah kuma ya jarabcesu da son *Khairat*, da k'yar Na'ima ta dawo gida niger amma
zamanta gaban mahaifiyarta ya mata dad'i sosai, dan tunda suka tai bai nemeta ba,
sai dai daga yanda yake fita ya jima yasa take jin ya samu wasu masu d'ebe masa
kewa.
*Rayuwa bayan haihuwar Khairat* tafi mata k'unci akan kafin haihuwarta, dan a
wannan lokacin ya fara harkar siyasa, baya zama gida harkoki sunsha gabanshi,
harkar mata ta k'aru sai dai shan giya ya d'an ragu sai daddare kawai, duk wannan
bai damunta kamar yanda idan yayi shigowar dare yake ritsata a gaban Khairat ya
nemeta, duk k'ok'arin da zatayi na samun dama baya barinta, haka zai kwanta da ita
a gaban Khairat duk da tana bacci, ta d'auka kodan tana qarama ne yake haka duk da
ba a hayyacinshi yake ba, amma sai gashi Khairat tayi wayo da girmanta da komai zai
fara k'ok'arin nemanta, yarinyar ce kawai ke barin wurin saboda tsoro.
Duk da haka Khairat na ganin soyayya a wajen mahaifinta da k'auna , babu wanda ya
isa ya harareta baiga wulak'anci ba gata take samu a wajenshi sosai, sai dai duk da
haka takan ji tsoronshi kuma bata zuwan wajenshi sai inshi ya zo wajenta, ta fara
karatu a ecole (school) d'in da tafi kowace a garin, sai dai duk k'ok'arin Na'ima
na ya barta taci gaba da zuwa makaranta amma ya k'iya saboda ta fara zuwa ranar ta
dawo tace malam ya daketa, bai bari ta sake zuwa ba kuma Na'ima data fara koya mata
a gida, ranar ya samu tana kuka bayan ya tambayeta tace mama ta daketa dan bata iya
karatun data koya mata ba, bayan fad'a da Na'ima tasha y kuma ce karta sake shiga
harkar 'yarshi, saboda b'acin rai sai yasa Na'ima yin alk'awarinba zata sake
kulashi da yarshi ba, idan Allah ya nufeta da shirya ta shiryu, idan kuma akasin
hakane to matsalarsu ce.
_Kash, wannan ba mafita bace, duk inda aka je aka dawo ke uwace kin fishi asara ,
dan ko gidan aure taje za'a ce laifin uwane._
Kallonta Khairat tayi a matuk'ar tsoro ta kalli mahaifin nata, bayan mahaifiyarta
ta koma ta b'oye, lokacin kuma ya kawowa uwar cabka ya fara k'ok'arin keta rigarta,
sake turata tayi ta nufi k'ofa tace "kije nace ko."
Duk da tsawar data mata baisa ta tafi ba, wani mari ya kifa mata a cikin muryar
'yan shaye shaye yace "d'iyar tawa zaki ma wannan tsawar, ita sa'arki ce, nace
sa'arki ce ita, tsararki ce da zaki mata wannan tsawar?"
Duk ya k'are tambayoyin ne da marinta, belt (ceinture) d'inshi ya fiddo zai fara
dukanta Khairat ta fita a guje tana kuka, bakin k'ofar d'akin ta tsaya tana
sauraren kukan mhaifiyarta da kuma sambatu da kukan mahaifinta keyi, kamar abu yayi
sauk'i sai taji k'arar belt d'in nan da kuma kukan mamarta, ta tabbatar itace yake
duka, kasa jura tayi kawai saita shigo d'akin a hankali, ganin mahaifinta babu
komai a jikinsa haka ma mahaifiyarta kawai sai tayi k'ara mai tsanani ta fad'i qasa
somammiya, shine ya fara kai mata d'auki kafin uwar tasa kayanta ta nufi wajenta
itama, a daren ba suyi bacci ba ko kad'an bayan sun samu Khairat ta farfad'o, daga
lokacin sai abubuwa suka fara canzawa amma fa na d'an wani lokaci.
Khairat ta daina walwala a gidan mahaifinta, tafi so ta zauna shiru ko kuma tasa
écouteur (hearpeas) a kunne tana sauraro, Na'ima kuma ta fita harkarta daidai da
gaisuwa bata had'ata da ita, ko abinci bata ce mata fito kici ta dinga nuna mata
rashin kulawa, mahaifin kad'ai ke kulata ke kuma bata farin ciki.
Khairat nada *shekara sha shida* ta fahimci abinda iyayenta keyi a kowane dare
wanda kesa mahaifiyarta kuka, kowane dare da abin sauraro take saboda kar taji
abinda ke faruwa a wajen iyayen nata, a hankali sai damuwa da kad'aici da kuma
tsoro yayi tasiri sosai a rayuwar Khairat, hakan kuma ya janyo mata matsanancin
ciwon qirki da kuma ciwon kai dake damunta duk lokacin da ta shiga b'acin rai ko
damuwa, bayan Mani ya fahimci hakan saiya kaita asibiti anan aka d'orata akan
magunguna, amma matsalar ba daga ita bace daga garesu ne, ganin abin ba sauk'i yasa
Mani ya mayar da ita india wajen mahaifiyar Na'ima, komawarta can kuma yafi mata
kwanciyar hankali da jin dad'i, gata da lele ta sake samu acan saboda ita d'in ta
zama 'yar gudaliya a wajen kakar tata, sannu sannu sai Khairat ta fara zama mai
tsauri da rashin kunya kuma marar qaunar talakawa mai wulak'anci gana k'asa da ita,
taci gaba da karatunta acan kuma ta shiga gidan koyan rawa wanda hakan baima Na'ima
dad'i ba ,amma tunda tace ta daina shiga harkarta yasa bata mata magana ba, a kwana
a tashi saiga Khairat har akan je da ita wajen concert ko wani competition na rawa
kuma ta zama zak'ak'urar 'yar rawa da shugabansu ke ji da ita, soyayyar data fara
da wani yaro abokin rawarta mai sunan *Rajveer* yasa hankalin Na'ima ya tashi
lokacin da ta zo ganin mahaifiyarta, ganin basu da shamaki sukan tab'a juna ba tare
da jin wani abu ba yasa bata tafi ba sai tare da ita, duk da ita bata so ba amma
haka suka tafi, yayin da Raj yaji mahaifiyar bata gyara masa ba danshi yana sonta
sosai.
*Shekara d'aya* da dawowarta kuma Mani ya mallaka mata wannan compagnie nashi a
matsayin kyautar anniversaire d'inta na cika shekara ashirin da biyar, a lokacin ne
kuma ta fara aiki a ma'aikatar, duka duka sati uku kenan da fara aikinta, amma
gashi *Umar Faruk ya b'ata mata rai.*
_SAMIRA HAROUNA_
_DEDICATED TO_
*MA FAMILLE*
_Bismmilahir-rahman-rahim_
*BILQEES*
5⃣
A hankali ta farka daga baccinta, saida ta tashi zaune tayi hamma sannan ta d'auki
wayarta ta duba agogo, 10:40 tashi tayi ta fito sai dai bata sauko ba daga sama ta
dinga hangen falon harta hango d'aya daga cikin mai aikinsu, daga saman ta kwallo
mata kira "Biba."
Juyawa tayi kawai ta koma d'akinta ta zauna saman gado tana wasa da kitson kanta,
Biba ce ta shigo ta durk'usa tace "gani Hajia."
Saida ta gama had'a mata da duk wasu turaruka da take aiki dasu sannan ta fito ita
kuma ta shiga, saida ta d'auki awa d'aya sannan ta fito daga bayin, d'aya mai aikin
ta samu wacce take tayata shiryawa, kamar yanda suka saba yanzu ma hakane ya faru,
da taimakonta ta shirya cikin riga da siket na shadda wanda suka kama jikinta sosai
suka fito da k'irarta, d'an k'aramin gyale ta d'auka sai dai a d'aya kafad'a kawai
ta d'orashi tare da rik'e jaka a hannu da wayarta sannan ta fita, a falo ta samu
duka iyayen nata a tsaye da alama magana suke, wucewa tayi ba tare data kallesuba
tace "da alama kun tashi lafiya."
Bata jira amsarsu ba tayi gaba, Mamie ce tace "Khairat abincinki fa?"
Bata ji ba bare ta amsa saboda ta rigayi da tayi nisa, motarta ta shiga k'irar
RENGE ROVER ta nufi ma'aikatarsu da tunanin had'uwarta da Umar faruk.
Ai kuwa kamar yanda ta saba da shan k'amshinta ta shigo wajen, a gadarance take
kallon kowa har saida idonta ya sauka akan Faruk, murmushi ta farayi tana takowa
wajenshi har saida ta tsaya gabanshi, jin tattausan k'amshin turare a bayanshi yasa
ya juyo a hankali, da sauri ya mik'e tsaye gabanshi na fad'uwa dan baisan me zai
biyo baya ba, dama ya zone saboda umarnin mahaifinshi, cikin rainin wayo tasa
yatsarta ta shafi sajen fuskarshi tana fad'in "Umar Faruk ko?"
"Sannu jarumi, sai dai kuma nayi mamakin ganinka anan, na d'auka ai ka daina aiki,
amma kuma saina ganka nan, meya faru?"
Bata bari yayi magana ta kama mab'ullin rigarshi ta fara b'alle masa tana fad'in
"karka d'auka ka mareni ka ci bulus kenan, ka kula da kanka dan babu abinda zai
hanani *d'aukar fansata* a kanka ba, kayi abinda ko iyayena ba suyi ba, da wannan
nayi alk'awarin cin mutuncinka ko ta wace irin hanya, ina fata ka fahimta?"
Wasa wasa ashe ta cire duka mab'allan rigarshi, saida ta wuce bureau d'inta sannan
ya fahimci hakan, maida mab'allanshi ya farayi yana kallon mutanen dake kallonshi,
saida kowa ya fara aikinshi ya sulale ya nufi bureau d'in nata, Habiba ce ta shigo
tace yana son ganinta amma tace ta fad'a masa bata son ganin kowa, rok'on alfarma
yayi akan ta barshi ya shiga, a gadarance tace ta barshi ya shigo, shigowa yayi
yana kallon fuskarta har ya tsaya gabanta, saida ta kallesa rai b'ace tace "kayi
kuskure, kafin ka bar nan wajen zan saka wani aiki."
Kud'i ta fito dashi 'yan goma goma guda uku ta bashi tace "karb'i wannan, kaje ka
samu masinger ka tambayeshi komai akan abinda yake siyo min, saika siyo min dan
banyi kari ba."
Wani kallo ya mata yana lumshe ido d'aya kamar zai sake bigeta amma saiya dake ya
juya ya fita, haka yaje ya samu masinger ya tambayeshi, tsaf ya fad'a masa komai
sannan ya hau mashin d'inshi ya tafi.
Cikin awa d'aya ya dawo, har bureau ya kawo mata ya aje, kallonshi tayi cike da
mugunta tace "kaga plateau ( plate)can d'auko ka saka min."
Kallonta yayi amma babu yanda ya isa sai d'aukowa ya zo ya zuba mata, tura mata
plate d'in tayi tasa hannu ta fara ci ya fito da kud'i ya aje gabanta tare da cewa
"canjinki."
Fuska a had'e tace "aini bana karb'ar canji, ka rik'e wanjenka nasan zasu maka
anfani."
Ganin kamar ba zai d'auka ba yasa ta kalleshi tace "ba kaji mena ce ba?"
Dauka yayi ya rik'e a hannunshi sannan yace "dan Allah kiyi hak'uri akan abinda ya
faru, wallahi kuskure ne insha Allah ba zan sake maimaita kamarsa ba."
Saida ya gama ta kalleshi tace "ka d'auko min ruwa masu sanyi a fridge."
Yanda yayi tsaye baida niyyar yin abinda tace yasa ta jingina da kujerarta ta
lumshe ido, idonta ya kalla wanda sukasha mascara sai sukayi kamar fossile, fridge
d'in ya nufa yana fad'i a ransa "kyawunta hallinta babu kyan hali, ina ma zaki
gyara d'abi'unki da kin more kyawunki duniya da lahira."
Daukowa yayi ya aje mata, cikin marairaicewa ya sake cewa "dan Allah kiyi hak'uri,
wallahi idan na rasa aikin nan mahaifina zai iya yin hushi dani, ki taimaka min dan
Allah kar....."
Kallonta yayi ya kalli telephone d'in dake kusanta wanda anfaninshi kenan kiran
wanda take so, juyawa yayi rai b'ace ya fita ya kira mata manager, tare suka shigo
sukayi tsaye suna kallonta, ji yake kamar ya gaggabjeta da wasu marikan yanzu haka,
kallon manager tayi tace "ka turo min takardar sallamarsa zansa hannu a kai da
kaina."
Manager kallonta yayi ya kalli Faruk babu damar da zai bada hak'uri, cewa yayi "to
Hajia."
Zai juya Faruk ya rik'e rigarsa yana kallonta yace "dan Allah kiyi hak'uri wallahi
ba zan sake ba, da aikin nan na dogara, dan Allah karki koreni wallahi zanyi duk
abinda kike so."
Lotus ta d'auka ta goge hannunta ta jingina bayanta a kujera tana juyata tace "to
ka durk'usa ka ban hak'uri, ni kuma saina yafe maka."
Shiru yayi yana tunanin abinda zaiyi, amma tuna hukuncin da Baba ke shirin d'auka a
kanshi yasa yayi kasa da kanshi, a hankali ya sulale gwiwoyinshi ya zube qasa kamar
yanda take so, kasa had'a ido yayi da ita saboda tafasar da zuciyarshi keyi, abune
da bai tab'a faruwa dashi ba sai yau, haka kawai yaji hawaye na fitowa a idonshi
dan Baba ko Mama ce kad'ai idan suka masa fad'a bada hakk'inshi ba yake sashi zubar
da hawaye, ganin ya kasa furta komai yasa ta mik'e tsaye da wayarta a hannu tace
"tunda ka zama kurma ni zan fita waje."
Tsayawa tayi ta dawo ta zauna tana kallonshi tana murmushi, cike da raini tace
"tashi, kaje gida ka kwanta ka huta, ba zan hak'ura cikin sauk'i haka ba."
Tsaye ya mik'e ba tare daya bari sun had'a ido ba ya juya ya fita,manager ma zai
fita tace "zan turo maka da adreshin club d'in da zanje an jima, ka fad'a masa ya
sameni acan."
"To Hajia."
Yana fita tayi dariya tace "zaka gane kuranka, zan had'aka da macho tamin
maganinka."
Misalin *14:00* tayi parking a wata restaurant mai sunan *Amandine* dan taci abinci
kafin ta wuce gida, saida taci ta k'oshi kafin ta mik'e zata fita, juyowar da za
tayi sukayi karo da juna ita da wani had'add'en matashi, ware manyan idonta tayi ta
kalleshi kafin ta fara k'ok'arin wuceshi, saurayin kam da yayi mutuwar tsaye saboda
ganinta saurin rik'e hannunta yayi, a fusace ta fizge hannunta ta kalleshi tace
"akan me zaka tab'ani?"
Saida ya kalli tsayayyan qirjinta ya lashe leb'e sannan yace "yi hak'uri, ban
tambayi izini ba kafin na tab'a."
"Mtsssss." taja dogon tsaki ta wuceshi, biyo bayanta yayi yana kallon k'ugunta ya
kasa magana, bud'a motarta tayi ta aje jakarta da wayarta sannan ta shiga ta tayar,
zata fara tafiya ya tari gabanta yace "ko zamu iya yin magana?"
"Babu lokaci." ta fad'a tana sake taka motarta, rik'e k'ugu yayi yace "in baki bani
dama ba, to sai dai mu kwana anan."
Tana fad'a ta tako motar ta nufo kanshi gadan gadan, ganin da gaske take yasa yayi
saurin kaucewa sai dai ina saida motar ta bugi gwiwarshi, rik'e gwiwar yayi yace
"kuttt, wannan fa yar akuya ce ta gaske." yaji zafi sosai dan da qyar ya taka qafar
ya koma cikin restaurant d'in yana tunanin sanin ko wacece ita da kuma k'arasa
abinda yayi niyyar yi a kanta.
Yana zaunawa akan kujera abokinshi wanda shigowarshi kenan a wajen kamar yanda
sukayi akan su had'u anan, ko zaune baiyi ba yace "kai wa naganka da ita yanzu?"
Wata uwar harara ya wurga masa yace "wace tambayar iskanci ce kuma, daga zuwa ko
zama ba kayi ba sai tambaya akan wata cika, wallahi tafi mu shed'anci wannan daka
gani."
Zaune yayi yana kallonshi da mamaki yace "ba saika fad'a ba nasan da haka, ina so
nasan meya had'aka da Khairat?"
Shima da mamaki ya kalleshi yace "ka santa ne, dan Allah fad'a min gidansu, wallahi
saina tarfa yarinyar nan, kasan meta min kuwa?"
Tab'e baki yayi yace "koma meta maka in dai Khairat ce ta wuce haka, danta wuce duk
in da kake tunaninta, ka ganni nan ko gaisuwa bata tab'a had'ani da ita ba, kuma
unguwarmu d'aya da ita."
"Kai dan Allah, kenan itama a *Présidentielle* take? kenan kace babbar yarinya ce?"
"Gaskiya me? kai hin wallahi fita idona in rufe, karka ja mana abinda yafi
k'arfinmu , karka d'auka mu yayan manyan mutane ne, to ubanta wallahi ya take
ubanninmu ya jikesu ya shanye, domin kuwa d'iyar *Mani Bukar* ce."
Ido ya fiddo yace "ashe abun babba ne, ah dole tayi rashin mutunci saboda sune
gwamnati."
Da haka suka rufe shafin maganar suka fad'a abinda ya kawosu , ita kuma tana kaiwa
k'ofar gida ta tsaya saboda wani dattijo daya taho kanta da dugu gudu yana mata
sannu da zuwa, kashe motar tayi ta fito a kasalance tana wani yak'una fuska, duk
gaisuwar da tsohon keyi babu wacce ta amsa saida yayi shiru tace "lafiya ko?"
Cikin muryar kuka ya fara magana "Hajia dama 'yata ce ke asibiti babu lafiya, mun
kaita an rubuta mana magani, sai dai bamu da halin siyan maganin, shi yasa na zo ki
taimaka mana kamar yanda Allah ya taimakeki."
Takardar dake hannunshi tasa hannu ta amsa ta bud'a, saida ta d'auki kusan 2 minute
sannan ta kalleshi tace "Baba, me yasa kuka yiwa yarinya aure da qananan shekaru?
yanzu gashi kun jefa rayuwarta a matsala, ina mijinta yanzu?"
Cikin kuka dattijon yace "ai tunda ta kamu da ciwon yoyon fitsari mijin ya saketa."
Ajiyar zuciya ta sauke ta mika masa takardar ta bud'a motarta ta d'auko jakarta ta
fito da kudi, mika masa tayi tace "na duba kudin maganin, jikka talatin da shida da
rabi ne, nan kuma jikka hamsin ne, kaje ka siyi maganin sauran kuyi wani abun
dasu, idan kuma wani abun ya taso kayi gaggawar zuwa ka sanar dani."
Tana gama fad'a ta shige motar mai gadi ya bud'e mata ta shige ciki, godiya sosai
dattijon keyi mata yana hawaye tare da saka mata albarka, wani abu daya k'ara
birgeshi shine, wannan shine karo na biyu daya zo neman taimako kuma ta taimaka
masa.
_Duk da Khairat bata da halin qwarai, amma akwai wani babban arzik'i da Allah yayi
mata, shine *taimako*, duk wanda Allah ya bawa zuciyar taimako to hak'ik'a yayi
dace, dan ko baya da abun bayarwa zaiyi iya qoqarin da zaiyi yaga ya kyautatama
wani, wani kuma idan Allah bai bashi zuciyar taimako, sai kaga Allah ya wadatashi
da abin duniya amma sai yaji baya iya cire ko sile ya taimaki wanda baya da, Allah
ka wadata zuciyarmu._
Babu kowa a falon sai masu aiki a farfajiyar gida suka mata sannu da zuwa, kai
tsaye d'akinta ta nufa ta cire kayan jikinta ta watsa ruwa ta saka kayan da tafi
so, wayarta ta d'auka da abin sauraro ta laka a kunne sannan ta fito da silipas a
qafarta, Mamie ta samu zaune a kujera tana kallo, zaune tayi kusanta tare da fad'in
"sannu Mamie."
"Yawwa sannu, yaushe kika shigo?" cewar Mamie cikin sakin fuska.
Ita kam mamakin ganin sakin fuskar yasa ba tace komai ba, sake cewa tayi "kinci
abinci kuwa?"
Janyo kanta Mamie tayi ta d'ora saman cinyarta ta fara shafar kanta, mamaki duk ya
ishi Khairat dan rabon da haka ta faru harta manta, sun jima a haka kafin Mamie
tace "ni kam Khairat wai sai yaushe zaki kawo mana sirikina ne?"
Gyara kwanciyarta tayi ta fuskanci Mamie tace "Mamie, nifa har yanzu ban shirya
aure ba saboda ban samu wanda ya dace dani ba."
Cikin zolaya Mamie tace "haba gimbiyar Papa, yanzu duk samarin nan naki ace babu
wanda ya dace dake? amma ai naga duk kyawawane masu aji da ilimi, ki duba kiga d'an
uwanki fa Mujahhid, ga kuma *Muzaffar* ga *Ahmadi*, ace duk cikinsu babu wanda ya
miki."
Tashi tayi zaune tace "Mamie, Mujahhid bai dace dani ba, eh shi kyakyawane ajin
farko amma idan na auresa zanyi irin rayuwar da ki keyi ce yanzu, Muzaffar kuma
yana da wani hali da ban sonshi, yana da son mata da kuma qyamar talakawa, Ahmadi
kuma gaskiya shi yana da babban familly ne masu yawa, ni kuma ba zan iya d'aukar
kwaramniyar danginshi ba."
Komawa tayi ta kwanta qafarta tana fad'in "kawai kici gaba da min addu'a na samu
wanda ya dace, ni ban damu sai mai kyawu ba, ina son samun namijin da kallo d'aya
zaka samu tabbacin lalle cikakken namiji ne shi."
Mamie dai bata sake magana ba tana saurarenta tana biyar wak'ok'in da take saurare
har bacci ya d'auketa, ci gaba tayi da shafar kanta bata gushe a wajen ba har saida
la'asar tayi ta tashi sannan tace taje tayi sallah itama ta nufi nata d'akin dan
yin sallah.
Misalin *22: 30* ta fito cikin shirin tafiya club, kallonta Mamie tayi sosai tace
"Khairat dan Allah ki zauna gida karki fita wurin nan bai dace ba."
Cikin sakin fuska tace "karki damu Mamie, akwai wanda zamu had'u dashi ne, ba
jimawa zanyi ba."
Tana fad'a ta fita ta shiga motarta, tana d'aukar hanya su Musa suka bi bayanta
cikin bak'ak'en kaya da rufaffiyar fuska ta yanda ba zata iya shaidasu ba, a hanya
kuma ta turawa manager adresse d'in in da Umar zai sameta, sannan ta kira macho
amma sai tace tuni tana wajen.
_NA_
_SAMIRA HAROUNA_
_DEDICATED TO_
*MA FAMILLE*
_Bismmilahir-rahman-rahim_
6⃣
Umar Faruk na k'ofar gida saman dakali yana chat yaga sak'on manager, zaune yayi
daga kishingid'ar da yayi yana kallon sak'on, bud'ar bakinshi yayi yace "kodai
akwai abinda yarinyar nan ke nufi danine, me yasa ba zamu had'u a wani wajen ba?
Ganin babu wata mafita yasa ya shiga gida yayi wanka ya shirya cikin kayan da yafi
ta'ammali dasu qanana, turarenshi ya d'auka *Gold* ya fesa bayan yayi anfani da
*nivea men* sannan ya d'auki makullin mashin d'inshi ya fita, yayi doguwar tafiya
kafin ya isa club d'in, yana sauka daga mashin d'in ya hangi motarta, tsaki yayi
sannan ya nufi k'ofar masu tsaron k'ofar ne suka tareshi, ganin kallon da suke masa
yasa kafin suyi magana yace "Khairat na ciki?"
Bud'a mashi hanya sukayi ya wuce, yana shiga yaji ranshi ya sake b'acewa, hayak'i
da wari ne kala kala na kayan shaye shaye, ga masifaffen kid'in dake tashi duk da a
wurinsu mai tab'a zuciya ne, yanda mata da maza ke cakud'e ya sake harzuk'ashi wasu
tsirarane kawai baka kirasu amma da kayan dake jikinsu basu da maraba da tsirara,
ga hasken wurin mai jane sai sauran fitilun dake bayar da haske mai kala kala, haka
yake kutsawa yana shiga har ya tsaya cak saboda hango Khairat da yayi, tsakiyar
fili take tana tik'ar rawa abinta tare da wani dogo kuma had'add'en guy, tabbas ta
iya rawa sosai dan daga yanda take sarrafa jikinta zaka gane haka, shima matashin
da alama ya iya rawar sosai, abun haushi shine yanda suka rik'e da juna suna tab'a
jikinsu duk yanda suka so har wani cirata yake sama, ran Faruk kam k'ara b'acewa
yayi daya kalli kayan jikinta, rigace a jikinta bak'a mai kyau da walk'iya amma mai
siraren hannaye iya cinyoyinta, duk wutsilniyar da take har pant d'inta na ciki ake
gani fari shima bai wuce cinyarta ba, balerine ne a k'afarta sai dogayen kitsonta
data sakeshi yake kad'awa yanda yake so shima, kid'in da suke takawa ne ya zo
qarshe dan haka suka k'arar da kid'in tare da rungume juna suna sauke numfashi,
tapi aka musu da shewa sannan suka raba jikinsu dana juna, sakinshi tayi zata koma
mazauninta ya fizgota ta sake komawa qirjinshi, kallon juna suke kamar daga sama ya
kalli kwayar idonta yace " *ina sonki* Khairat."
Yana fad'a ya kai bakinshi a nata ya sumbata, da sauri ta raba bakinsu tana
kallonshi, amma saita kasa cewa komai ta nufi mazauninta, babbar kujerace a wajen
ita kad'ai zaune, haushine ya nemi kashe Faruk dan haka kawai yaji ranshi ya
matuk'ar b'acewa, jiki a sanyaye ya fara d'aga qafarsa zai nufi wajenta, cak ya
sake tsayawa saboda wani sabon saurayin daya zauna kusa da Khairat suka rumgume
juna, da alama babban yaro ne dan harda masu tsaronsa a bayanshi.
K'ura masu ido yayi yana kallo cikin takaici yana ji kamar zuciyarshi zata fashe, a
hankali ta raba jikinta da nashi, kallonta yayi yace "Khairat, me yasa baki so ina
kusantoki?"
Saida ta harareshi tace "to me yasa kai kuma saika kusanceni, mu zauna a haka
mana."
Cikin wata irin murya yace "Khairat ba kowa bane zai iya, in dai namiji lafiyayyene
ya ganki dole yaso kasancewa dake, wallahi Khairat kasa bacci nake, kece ke zuwa
min a cikin tunani na."
Hannu ta d'aga masa tace "kaga Muzaffar, nifa saboda kaine yasa har yanzu na kasa
tsayawa waje d'aya, kullum da club d'in da nake zuwa amma na rasa ta yaya kake
sanin in da nake, me yasa kake takurawa rayuwata ne, dan Allah ka rabu dani bana
sonka."
Kasancewarshi mutum ne mai saurin fushi kawai saiya mik'e tsaye yace "ke baki isa
ki wulak'antani ba wallahi, ina sonki Khairat kuma ko zaki mutu wallahi saina
mallakeki koda kuwa bayan darenmu na farko zamu rabu dake."
Tsaye tayi itama tace "oho, kenan burinka kawai daren farko, kaga ka nuna min kai
jikina ne kawai a gabanka, to kaji wallahi yafi k'arfinka har abada ba zaka sameni
ba."
Baiyi magana ba sai wucewa da yayi da k'arfi har saida ya bangaje Umar tsabar
hushi, binshi da tayi da kallo yasa ta sauke idonta akan Umar Faruk dake kallonta,
da d'an yatsa ta masa alamar ya taho, takowa ya farayi sai dai d'uffff, wutar wajen
ta d'auke, wayoyi wasu suka fara k'ok'arin kunna fitila kafin haka ta faru kuma,
Musa ya toshe bakin Khairat ya d'auketa daga wajen.
Kasancewar sun shirya abun hakan yasa babu wanda ko yaji faruwar wani abu, bayan
'yan mintuna wutar ta dawo amma babu Khairat a in da take, rik'e kugu Faruk yayi
yace "dama danta raina min hankaline yasa tace na zo nan."
K'wafa yayi tare da juyawa ya fita daga wajen, k'awarta kam tana can tana
soyewarta bata san wainar da ake toyawa ba, tafiya yake akan mashin d'inshi yana
tsaki yana sake hangota a jikin mazan da ba maharramanta ba, k'ok'ari yake ya share
kawai amma ya kasa sai dawo masa take a kwakwalwa.
Kallon motar dake gabanshi yayi ganin yanda take gudu, yana kallo har motar ta
shiga wata kwana ta ratsi wata hanyar kamar zata bar gari, wucewa yayi shima amma
abun mamaki saida ya sake juyawa ya kalli motar sai yaji gabanshi ya fad'i, tsayawa
yayi yana kallon da motar tabi kawai kuma saiya tayar da mashin d'inshi yayi gaba
abinshi.
Tunda yaje gida ya shiga d'akinshi kasa samun nutsuwa yayi, haka kawai yake jin
gabanshi yata fad'uwa ba kuma shine abinda yafi damunshi ba, shine yanda Khairat ta
kasa barin tunaninshi, ganinta kawai yake a idonshi , kasa samun nutsuwa yayi sai
gashi ya raya darenshi da tunani da k'ara jin tsanar Khairat da haushinta, ba kamar
yanda ya saba rayashi da anbaton ubangijinshi ba.
Wani gida suka kaita suka jefata saman k'aramin gadon dake ciki, tun a cikin mota
suka d'aure mata baki da qafafu lokacin da zasu d'aure mata hannuwa saita fara
kokawa dasu, hakan yasa ba tare da tausayi ba suka bank'are mata hannu har saida
taji k'arar hannu kuma ta tabbatar ya karye, tana ganin sun jefata ta fara kallonsu
cikin tsoro sai dai ba zata iya fahimtar kosu waye ba, so take tayi magana amma ina
babu baki sai gunguni kawai kake ji, baya baya ta fara ja daga kwance saboda ganin
d'ayan yana nufota yana zare zip d'in wandonshi, kuka ta fashe dashi mai tsanani
tana ci gaba da ja baya kamar tafiyar tsutsa, kusan fad'uwa tayi hakan yasa Auwal
dake bayanta ya turota da k'arfi ta dawo tsakiyar gadon, Musa na ganin haka ya
k'arasa janyota ya haye sannan ya kallesu yace "ku bamu wuri ko, zan kiraku."
Suna fita ya kwance mata d'aurin qafafun ya bud'e qafarta da k'arfi yana shirin
zare pant d'inta, k'ok'arin tashi tayi saiko ya kama gashinta ya fizgota , fashewa
tayi da k'ara sai dai bata fito ba ma bare aji, cikin jin zafi tasa qafafunta ta
fara harbinshi, shima cikin b'acin rai ya wanketa da mari ya kuma janyo kanta ya
had'ashi da kan gado, tuni kanta ya fashe sai jini duk da haka bata sasuda ba tayi
nasarar yakushinshi ta bayan hannu, saboda dogayen akaihu da tasa yasa har saida
jini ya fito masa, ai kuwa sai yasa hannu da iya karfi da tsabar mugunta ya fizgo
akaihun, wani ihu ta saki saboda azabar da taji, akaihunta uku ne suka fita tare da
asalin akaihunta, shak'e mata wuya yayi ya sunkuya cikin kunne ya rad'a mata "zaki
mutu a banza kuma ba zamu fasa abinda mukayi niyya ba."
Yana fad'a ya janye pant d'inta daga jikinta, ware qafafunta yayi ya fara k'ok'arin
shigarta, bille bille take tana kuka amma ina ko saurarenta baya yi, hanya yake
nema amma abun ya gagara, ya d'auki lokaci yana so ya shiga amma shiru, ganin abun
bana lafiya bane yasa ya sake buda qafafunta sosai har saida magangamar cinyarta
tayi qara, da gaba d'aya karfinshi ya tusa kanshi ciki, duk da bakinta d'aure yake
amma data fasa ihu saida sauran dake waje suka ji, ganin ya samu hanya saiya fara
aiki tuburan.
Saida ya nutsu sannan ya barta, yana fita d'aya ma ya shigo a haka suka dinga
shigowa d'aya bayan d'aya har suka kammala, kuma duk wanda ya shigo cikinsu saiya
nemi k'ofarshi da kanshi saboda matsewar da take, wannan itace hallitar Khairat,
tun tana motsi harta daina gaba d'aya bata san meke faruwa ba, tsaye sukayi akanta
suna kallonta Bello yace "wallahi ban d'auka budurwa bace da ban fara ba."
Musa ne yace "kai dallah fita harkarta, ba dai mun gama ba, to ku tsaya ku gani."
A hankali ya cire belt d'in k'ugunshi kafin suyi magana harya fara labta mata shi,
tambayarshi suke me yasa amma bai iya ce musu komai ba, saida yaga ya mata ligaliga
harta sauya kammani sannan ya maida belt d'inshi ya kallesu yace "ubanta da yake
lalata 'ya'yan wasu aishi baya musu haka, kuma duk lokacin da za'a rama mugunta to
ka rama fiye da wacce aka maka."
_Wannan ba gaskiya bane, ba kuma koyarwar shari'a kenan ba, Allah ka shiryemu
shirin addininmusulunci_
K'aramar rigarta data yagalgale cire rigar sukayi suka kwasheta a haka suka fita
da ita, a mota suka sata bayan sunyi tafiya mai nisa suka tsaye, Musa da Auwal ne
suka fito suka kamota, a gefen hanya suka jefar da a ita suka tafiyarsu.
😭😭😭😭😭😭😭
Kwance take kamar gawa babu alamun rai, a haka ta zauna bakin titin na tsawon
lokaci, sallah asuba tasa mutanen dake wajen suka fita sukayi sallah, wani dattijo
ne da gidanshi ke bakin kwalbati yazo tsallakawa da fitila a hannu yaga mutum
kwance tsirara, tsorata yayi da farko amma saiya daure ya sake haskawa , gaba d'aya
yaga mutum duk da kalarta harta fara sauyawa , nan ya fara kwaroroto yana d'aga
murya har mutane cikin gida da waje suka hallara.
Nan fa suka fara shawarar yanda za ayi, wani matashi ne mai zafin nama ya k'arasa
wajenta, rigarshi ya cire ya rufe mata k'asanta zuwa k'irji, kallon mutanen yayi
yace "dan Allah ku samo abin hawa mu kaita asibiti."
Basu b'ata lokaci ba suka suka samu mota aka saita suka nufi asibiti da ita koda
ta mutu ma sai a nemi danginta.
😭😭😭😭😭😭My Khairat.
08/07/2019 à 11:16 - ~NANA KHADIJA~😍: 💑💑💑💑💑💑💑💑💑💑
*JIHADI*
_Umar faruk_
💑💑💑💑💑💑💑💑💑💑
_NA_
_SAMIRA HAROUNA_
_DEDICATED TO_
*MA FAMILLE*
_Bismmilahir-rahman-rahim_
7⃣
Ganin halin da take ciki yasa likotoci suka amsheta tare da umarta da sukai report
a wajen police, matashin nan ne ya tafi dan cika umarnin, baisha wahala ba ya samo
takardar izini a dubata, yana kawowa likitoci suka duk'ufa kanta, tun matashin nan
na kai da kawowa harya fara zaune yana jiran fitowar likotocin, mutanen da suka
taho tare ma jira suke tare da jimami, ana haka wata docteur ta fito tana tambayar
wanda suka kawota, a sukwane suka rufeta suna fad'in sune, a nitse tace "kune 'yan
uwanta?"
Matashin ne yayi karaf yace "a'a, muma tsitarta mukayi, ina fatan dai lafiya ko?"
Wani kallo ta masa tace "kai baka ga yanda kuka kawota bane har kake maganar
lafiya, muna buk'atar dan ginta dan akwai aiki da za'a mata ana buk'atar saka
hannunsu."
A raunane yace "gaskiya bamu san kowa nata ba, amma in ba damuwa mu saimu saka
hannun."
Juyowa matashin yayi yace "dan Allah iyayena kuyi hak'uri, ina so ku bani had'in
kai mu taimakawa baiwar Allah nan."
Wani dattijo ne yace "ba komai yaro, muma fa iyayene, fatanmu dai Allah ya bata
lafiya."
Fitowar docteur d'in tasa suka maida hankalinsu a kanta, matashin ta kalla tace "ka
biyoni tare da wani dattijo d'aya a cikinku sai kusa hannun."
Binta sukayi ta kuma nuna musu suka saka hannu, saida suka tashi zasu fita matashin
yace "dan Allah wane irin aikine za'a mata?"
"Kai baka san aikin da za'a mata ba kasa hannu, saboda ba yar uwarka bace kenan?"
Kai ya girgiza yace "ba haka bane, kawai dai muna so ne mu taimaketa."
Tsaye ta mik'e ta wuce tana fad'in "d'inki za'a mata saboda tana zubar da jini
dayawa."
A haka suka kasance har rana ta take sosai amma ba wani labari, ganin haka yasa
dattijawa biyu suka bar wajen ya rage sai su uku a wurin.
*Tun daren jiya* Mamie ta kasa bacci saboda ganin k'arfe d'aya tayi, a al'adar
Khairat kuma bata kai wannan lokacin, kai kawo ta dinga yi a tsakiyar falo ita
kad'ai duk hankalinta a tashe, *03: 17* Papa ya bud'o k'ofar d'akin ya shigo a
halin daya fi shigowa, tsaye tayi tana kallonshi harya k'araso ya zube saman kujera
yana maganganun dashi kanshi baisan me yake fad'a ba, durk'ushe tayi gabanshi
cikin kuka tace "Alhaji, Khairat fa bata dawo gidan nan ba har yanzu, dan Allah
kayi wani abu kar komai ya samu 'yata, dan in haka ta faru wallahi ba zan yafe maka
ba."
Wani fizgo hannu ya fara a cikin muryarshi ta maye yana fad'in "to saime idan bata
dawo ba, ita d'in yarinya ce? ki barta tayi sha'aninta taji dad'in rayuwarta, ke
kad'ai ce a duniyar nan baki waye ba ai."
Cike da damuwa ta sake cewa "dan Allah Alhaji ka taimaka ka dubo min ita ko kasa a
dubota, wallahi nasan Khairat ba zata jima haka kawai ba a waje saida dalili,
jikina yana bani kamar akwai wani abu dake shirin faruwa, wallahi hankalina ya kasa
kwantawa gabana fad'uwa yake."
Abin takaici ashe duk maganar da take yayi bacci, dole ta gyara zamanta a k'asa
tana ci gaba da kiran wayar Khairat gashi tana kururuwa amma ba'a d'auka ba, haka
ta kasa rintsawa har gari ya waye lokacin kuma Papa ya farka a cikin hayyacinshi, a
lokacin data fad'a masa halin da ake ciki hankalinshi ya tashi sosai kuma harya
fara mata fad'a wai bata fad'a masa ba, nan ta fad'a masa halin daya shigo da
abinda suka tattauna kafin bacci ya d'aukeshi.
Aifa hankaline ya tashi dama na Mamie tuni a tashe yake, a lokacin kuma su Musa
sunzo wajen aikinsu cikin kaki, nanfa ya sasu nemo mashi Khairat duk in da take,
saboda su sun san komai kawai sai suka fara tafiya gidan rawar suna binciken
k'arya, anan kuma suka samu wayarta , haka a wajen da suka jefar da ita suka tsaya
suna tambayan mutanen wajen ko basu ga wani bak'on al'amari ba, saboda ganinsu da
kayan soja yasa aka fad'a musu abinda ya faru, nan fa suka dawo gida da qarfin
gwiwa sun samu labarinta, Papa da Mamie basu zauna ba suka rankaya zuwa asibitin,
kai tsaye asibitin *Clinic Poudrière* anan suka samu mutanen da suka kawo Khairat
asibitin, matashin ne ya fad'a musu halin da suka kawota, cikin fitar hayyaci Papa
ya shak'i wuyan matashin yana fad'in,
"Wallahi baku isa ba sai kun fad'a min abinda kukawa 'yata, ka fad'a min me kuka
mata?"
Matashin kam zare ido ya fara yi baisan me zaice ba, suna haka likitoci biyu maza
da d'aya mace suka fito daga d'akin da Khairat take, da sauri suka nufi wajensu
banda Mamie data zube wajen kamar gawa sai hawaye kawai dake zuba a idonta, "likita
meya faru da yarinyata?"
A tsanake likitocin suka kalleshi kafin babban docteur d'in yace "kaine
mahaifinta?"
Kamar zai tashi sama haka ya bishi har kamar zai shiga gabanshi, sun d'auki 'yan
mintuna da shiga Mamie ta dawo hankalinta ta tashi tabi bayansu dan taji abinda
za'a fad'a, da isarta yayi daidai da bayan kwantar da hankalin da likitan yayiwa
Papa ya kalleshi yace "kayi hak'uri yallabai, fyad'e akawa 'yarka."
Mamie na jin haka ta k'arasa fad'uwa a gurin somammiya, Papa kuma wani kuka ya saki
kamar yaro yana kiran "a'a, a'a, ba dai akan 'yata, me yasa ba za'a rama a kaina
ba, na shiga uku na lalace."
Kallonshi yayi yana goge hawaye da babbar rigarshi yace "ina jinka."
A hankali kuma a nutse likitan ya fara magana "'yarka tana cikin wani hali da take
buk'atar kulawa, bawai fyad'en ne ba abun tashin hankali, yawan mutanen da suka
mata fyad'en sune abun dubawa, duk da mun rasa wasu hujjoji saboda ba'a kawata da
wuri ba a asibiti, amma dai munyi k'ok'arin gano wasu abubuwan, mun bata duk wata
kulawar da take buk'ata a yanzu tare da taimakon wanda suka kawota, mun mata gwaje
gwaje na cutuka da akan iya d'auka ta hanyar saduwa, kuma alhamdulillah a yanzu dai
babu wani abu mai yiyuwa ko nan gaba, sai kuma akwai raunika da dama da aka ji mata
mai yiwuwa tayi fad'a da mutanen sosai, dan mun samu karaya a hannunta da tsakanin
cinyarta da k'ugunta, sai kuma gocewa a yatsunta biyu da kuma wasu raunika da suke
nuna dukanta akayi, akwai ciwo a kanta daya ja mata matsala sai dai munyi k'ok'arin
shawo kanta, badan ciwon a cikin gashinta yake ba da iska ya shiga akwai yiyuwar
ta kamu da ciwon mantau.
"Ciwon daya bamu wahala, shine ciwon da suka ji mata a gabanta, 'yarka tana d'aya
daga cikin irin matan nan masu tsukakken gaba, wasu daga ciki zaka ga ko haihuwa
basa iya yi da kansu sai an masu aiki, wasu kuma ba zasu haihu da farko ba amma sai
kaga cikin ikon Allah sun haihu a gaba da kansu, gaskiya 'yarka bana jin tana daga
cikin masu samun damar haihuwa da kansu ko a gaba in ba wani iko na ubangiji ba, ko
mijinta ne na aure zai shigeta dole saiya had'a da dabaru, amma kasancewar sun mata
ta k'arfi hakan yasa sun b'arkata sosai, idan kaga gabanta kafin a mata aiki zaka
d'auka *anus* d'inta da *vessie* (gabanta da duburarta) a had'e suke, amma cikin
ikon Allah mun di'nketa sosai d'inki kuma ba adadi, sai kuma jini da muka d'auka a
lab muka saka mata dan tana buk'atarshi."
"Inna lillahi wa'inna ilaihir raju'un." abinda Papa ya dinga maimaitawa kenan,
hawaye taf da ido ya dag'o yace "kana ganin zata rayu ma? danni na cire rai da
ita."
"Haba yallab'ai, ya zaka cire rai da rahamar ubangiji? ai insha Allah babu abinda
zai sameta, zata tashi in Allah ya yarda ma."
Cikin i'ina yace "eh...to, yanzu dai..tana kwance...insha Allahu,zata farka , amma
dai har yanzu a some take bata san in da kanta yake ba, kawai muna gane tana raye
da ta hanyar na'urar dake nuna mana numfashinta."
"Eh yanzu kam babu wani abu, akwai magungunan da za'a d'orata ne kawai idan aka
siyo, sai kuma kud'in duka aikin da aka mata, gashi nan a rubuce." ya fad'a tare da
mik'a masa takardar.
A sanyaye ya amshi takardar ya mik'e ya fara takawa, yana bud'e k'ofar yaci karo da
Mamie kwance a wajen, da sauri ya zube yana jijjigata yana kiran "Na'ima, Na'ima,
dan Allah ki tashi, meya faru dake?"
Likitane ya k'araso ya kiran likita mace suka kamata aka shiga da ita emergency dan
bata taimakon gaggawa, Papa ji yake shima kamar zai fad'i amma da taimakon su Musa
ya samu ya zauna numfashinshi na fita d'aya d'aya, saida suka d'auki kusan awa
d'aya sannan likitan ya tsaya gaban Papa, ganin halin da yake ciki yasa yace masa
"ka kwantar da hankalinka yallab'ai, Hajia na samun sauki, zata farfad'o nan da
zuwa yamma."
Sake sunkuyar da kai yayi yana ci gaba da zubar hawaye, wucewa likitan yayi shi
kuma ya bawa su Musa takardar maganin yace su duba mota akwai kud'i su siyo, saida
suka tafi ya nufi wajen mutanen da suka kawo Khairat asibiti ya basu hannu yana
musu godiya, wani dattijo ne yace,
Idon nan jawur ya kalleshi yace "ameen na gode, amma dan Allah kun shaidani?"
Murmushi sukayi d'aya yace "yallab'ai waye bai sanka ba, ai mun shaidaka tun
shigowarka."
Duk da baiji dad'i ba amma haka yace "to dan Allah wata alfarma nake nema a
wajenku? ina so dan Allah abin nan daya faru akan yata ya zama sirri tsakanina
daku, idan maganar nan ta fita wallahi zamu shiga uku, ko yarfen siyasa saiya
addabemu bare kuma jama'ar gari."
Had'e hannaye yayi alamar rok'o ya sake cewa "dan Allah, ku rufa mana asiri, kar
maganar nan ta fita waje, wallahi za'a mana dariya ne ana fad'in munanan kalmomi a
kanmu."
Matashin saurayin nan ne yace "yallab'ai karka damu, wallahi babu wanda zaiji
maganar nan, insha Allah zamu rik'e wannan sirrin tunda ba wani abun fad'a bane,
duba da zamanin da muke ciki, idan bai faru akan k'anwarka ko yayarka ba, to zai
iya faruwa da wata shak'ik'iyarka."
"Na gode sosai, Allah ya saka muku da alkairinsa, Allah ya taimakeku kamar yanda
kuka taimakeni."
Haka suka bar wajen suna mata fatan samun lafiya, shi kuma ya zauna zuciyarshi na
tafasa, sai dai a yau yana ji har abada ya daina neman mata da kuma shan giya,
kanshi qasa a hankali ya furta "in dai anyi duniya dan Manzon Allah S.A.W, to nabar
giya da matan banza har abada, domin abinda nayi da yaran wasu yau gashi an ninka
wannan abun akan yata, ban tab'a ma 'yar kowa fyad'e ba tunda nake, kowace mace na
kusanta to da son ranta ne na kuma biyata, amma yau sai gashi namiji fiye da d'aya
ya kusanci 'yata da k'arfi, wannan cin zarafi yayi yawa, Allah ina rok'onka gafara
abisa zunubaina, wannan tuba tubane na gaskiya, wallahi ba zan sake ba har duniya
ta nad'e."
Bayan su Musa sun kawo maganin da wasu allurai an kaiwa likitan, Papa kuma ya tara
su Musa yayi tsaye gabansu yace "ku jini da kyau, ina so ku koma gidan rawar nan ku
bincika min komai daya faru a wajen, ina so ku zage damtse ku samo min wad'annan
'yan iskan da suka lalata min rayuwar ya, dan wallahi ba zasu ci banza ba dole na
d'auki mataki a kansu, dan haka kuyi da jiki ku gaggauta kawo min su cikin kwana
uku, ina so kafin Khairat ta dawo hayyacinta su fuskanci hukunci."
"To ku motsa, ni ku barni da driver, yanzu wannan shine aikinku kuma yafi tsarona
mahimanci."
Anan ya basu umarni shi kuma ya shiga d'akin da Mamie take, k'ura mata ido yayi
yana tunano rayuwar da sukayi, hakika yana k'aunar Na'ima fiye da yanda yake
k'aunar kanshi, abubuwan da yake kawai sabone yasa kasa dainawa duk da bata so,
amma yau kam yayi tuba na gaskiya, likitace ta shigo tana fad'in "sannan yallab'ai,
ya mai jiki?"
Kai ya girgiza yace "ku zaku fad'a min, dan har yanzu banga ta farka ba."
Murmushi tayi tace "zata farka yallab'ai, saboda hawan jininta yasa aka mata
allurar bacci, kuma gashi jininta ya hau, amma yanzu zan sake dubawa na gani."
Sake awo ta mata sannan tace masa "mu gode Allah yallab'ai, jininta ya koma daidai,
amma dole a guji abinda zai tayar mata da hankali idan ta farka."
Shiru yayi dan yasan ba lallai taso ganinshi ba idan ta farka, dan kullum maganarta
kar abinda yake ya shafi yarsa, kuma yanzu yasan da bai tab'a kusantar 'yar kowa ba
ba abisa sadaki ba, to da duk rashin kunyar Khairat babu wanda ya isa ya mata irin
wannan cin zarafin , dan haka ya tashi ya fita daga d'akin, a lokacin 'yan uwa na
kusa dana nesa har sun fara samun labarin Khairat ba lafiya da Hajia Na'ima, zuwa
bayan magrib yan uwa sun fara zuwa ganinsu, Mamie kad'ai suke gani su koma hakan
yasa Papa ya shawarci likitan suka k'ara tsaurara tsaro akan Khairat.
_SAMIRA HAROUNA_
_DEDICATED TO_
*MA FAMILLE*
_Bismmilahir-rahman-rahim_
8⃣
*India* tun jiya Mammie ke kiran shalelenta Khairat amma bata dagawa, bayan gari ya
waye ta sake doka mata kira amma shiru, abinne ya dameta dan haka ta fara kiran
Mamie, amma itama ba'a dauka saboda wayar na gida, ganin itama an kasa dauka yasa
ta fara kiran Papa cikin b'acin rai, shi kuma tun daren jiya yasa wayar vibration
saboda kar a takura masa, nan ma ba amsa dan haka Mammie take jin in har aka sake
riskar gobe a haka to tabbas zata shigo gida niger.
Wani jami'i ne aka tsayar dashi a kofar d'akin da Khairat take ba'a bari kowa ya
ganta, kannan Papa da Mamie ne kad'ai suka ganta shima sau d'aya, tunda Mamie ta
farka take kuka tana wa Papa Allah ya isa cikin fitar hayyaci, hakan yasa itama ta
zama cikin tsaro tunda ya zama kamar suna fallasa sirrin gidansu ne, har yanzu Papa
baije gida ba haka ma Mamie gaba d'aya basa cikin nutsuwarsu, hakan yasa kuma sai
maganganu suka fara fita musamman daga wajen yan uwa wanda suka ga jikin Khairat
d'in
Nan suka fara fad'in kila wa kala ama dai suna gani kamar fyade aka mata, dama duk
abinda aka ce ya fara da jitajita to dole a samu banbancin kalamai, a cikin *kwana
uku* sai gashi manganu suna yaduwa akan amma Khairat fyade, duk da tsaro da kuma
boye abinda ake amma bai hana maganar fita ba.
Wasu kuma suna cewa ba wani fyade kawai dai dubunta ce ta cika watakila sun samu
matsala da abokanan shekewarta ne kawai, to haka dai aka dinga yada wannan magana,
kuma abu ga manyan mutane dan danan sai labari ya game gari, mutane nata tururuwar
zuwa dan ganin kwam amma babu mai ganinta koda kuwa cousine d'inta ne, haka labari
ya samu masana'antarta kuma suma sun zo ganinta sai Papa kawai suka ma jaje, amma
manager Papa yace a barshi ya ganta saboda sun jima tare ya aminta dashi.
*Duk badakalar nan* da ake Khairat bata san me ake ba, tana kwance da na'urori a
jikinta kamar wacce ta shiga halin doguwar suma, ruwa da sassaukan abinci duk ta
tiyo ake bata su, duniya kenan.
*Umar Faruk* ma tun ranar bai sake zuwa masana'antar ba, sai dai ya shirya ya fita
kamar ya tafi aikin saboda Babanshi amma kuma fafutukar samun wani aikin yake zuwa,
dan ya riga daya cire rai da aiki a karkashin Khairat.
Yau ta kama *lahadi* Faruk na kwance d'akinshi akan kafarshi Baba ya shigo, yana
ganinshi ya mike zaune yana fad'in "sannu da zuwa Baba."
Bai amsa mashi ba sai kallonshi da yake, tsarguwa yayi da kallon dan haka yace
"Baba, da wata matsala ne?"
"Eh, da matsala."
Gyara tsayuwarsa yayi yace "Faruk, yanzu har kiyayyar da kake ma yarinyar nan ta
kai haka, da har zata kwanta rashin lafiya amma ka kasa fad'a mana ko dai mu mata
addu'ar samun sauki?"
Duk da bai fahimci Baban ba amma haka yace "kayi hak'uri Baba, wace yarinya kenan?"
Dakuwa Baba ya masa yace "ban sani ba, har ni zaka tambaya wace yarinya? aiku ku
kafi kowa labarin abinda ke faruwa tunda ku ke aiki a ma'aikatarta."
Cikin mamaki yace "Baba wai, Khairat kake nufi? meya sameta to? ni bana da labari."
Shima da mamaki ya kalleshi yace "Umar Faruk kamar ya baka da labari, kai yanzu
kace baka san meke faruwa ba? bayan kullum kana fita."
Ganin karya ballowa kansa wani liki kawai sai yace "a'a Baba, kasan da yake ina da
aiki sosai shi yasa bana da lokacin wani shirme , amma wallahi bansan meya faru da
ita ba."
Juyawa Baba yayi zai fita yace "amma Baba me yake damunta?"
Yana fad'a ya bar d'akin shi kuma ya fad'a duniyar tunanin abinda ya samu Khairat,
gashi dama har yanzu yana ganinta a idonshi a cikin wannan shigar, tsaki yayi kawai
ya kwanta amma ya kasa komai sai tunanin wannan daren yake.
*Safiya* nayi ya shirya kamar yanda ya saba ya fita sai dai yau ma'aikatar ya tafi
dan jin meke faruwa, da sameshi ko sai yayi sa'ar ganin manager a farfajiyar wajen
zai shiga mota da alama fita zaiyi, da sauri ya karasa suka gaisa kafin manager
yace "Faruk ashe kana nan ka daina zuwa aiki?"
Kai ya shafa yace "eh yallabai ina nan, nasan ko nazo ba zata barni ba shi yasa ma
bana zuwa."
Nan ma kai ya shafa yace "yallabai nazo ne naji meke faruwa anan? dan jiya Baba ya
sameni yana fad'an wasu maganganu da ban gane ba."
"Kamar me kenan?"
Shiru ya d'anyi sai kuma ya kalli saman ginin yace "Hajiar tana ciki?"
Da mamaki yace "Umar Faruk, kar dai kace min baka san meke faruwa ba? Hajia Khairat
ai yau kwananta hud'u bata fitowa."
Dammm , yaji gabanshi ya tsinke ya fad'i, saida ya had'e yawu yace "to meya
sameta?"
Ajiyar zuciya manager ya sauke yace "yanzu dai kaga ganinta ne zanje, idan zaka iya
mutafi tare mana?"
"Asibiti."
Zagayawa yayi ya shiga motarshi suka d'auki hanya tare, amma ya rasa dalili sai
yaji zuciyarshi na bugawa d k'arfi ga gabanshi dake ta fad'uwa babu gaira babu
dalili, a haka suka isa asibitin jami'in dake tsaron k'ofar d'akin yana ganin
manager ya kauce masa ya wuce amma saiya hana Faruk, manager ne yace "dan Allah
abokina ka barshi ya wuce, dani dashi duk d'aya ne."
Cewar jami'in "gaskiya ba zai wuce ba wannan doka ce, kayi hak'uri ka koma."
Papa ne yaji maganarsu daga cikin d'akin dan haka ya lek'o duk da baiga ko suwaye
ba amma kawai sai yace "barsu su shigo kawai."
Da sallama suka shiga amma sallamar Faruk saita tsaya cak saboda ganin Khairat a
wani hali na daban, cikin sanyin jiki da rauni ya k'arasa gaban gadonta ya tsaya
yana kallon fuskarta dake d'aure da bandeji , Papa kuma d'akin kusa dana Khairat ya
shiga in da Mamie take kwance, a hankali ya kalli manager yace "meya sameta haka,
hatsari tayi?"
Kai kawai ya girgiza masa, sake maida kallonshi yayi gareta yana k'ara jin tsoron
ubangiji na shigarshi, wai wannan matashiyar mai tsiwa da girman kai da raina
mutane yau gata kwance, ta sauya kamanni kamar ba ita ba duk kusan rabin jikinta
bandeji ne sai jini, bin qafarta yayi da kallo wacce tayi sumtum da ita ta
kunbura , kallon yatsun qafar yayi wanda suka sha akaihu da kalar pink, kallon
fuskarta yayi idonta rufe gashin idonta duk ya kwanka luf kamar na kanti, wata har
sharasharar rigace fara aka lak'aba mata.
Suna haka wayar manager tayi k'ara dan haka ya fito da ita ganin mai kira yasa ya
fita daga d'akin dan amsa wayar, kujerar dage gaban gadon Faruk ya zauna yana
kallon k'afarta dake rataye da gado tasha k'arafa saboda dorin da aka mata haka ma
hannu, sosai zuciyarshi ta karye saboda ganin halin da take ciki, sama sama ya fara
jiyo murya daga d'aya d'akin ko ba'a fad'a masa ba yasan muryar iyayenta ne, tsaye
ya tashi saboda ji da yayi muryoyin na sake sama kuma kamar zasu fito daga d'akin.
Juyawa yayi da nufin barin d'akin kawai yaji har sun fito, muryar Mamie ce ta fara
magana cikin tsananin kuka da fitar hayyaci ta nuna Khairat dake kwance tace "ka
dubi yarinyar nan dake kwance waya ja mata shiga wannan halin? kaine duk kaine
sila."
"Ka sani wallahi jira kawai nake 'yata ta samu sauk'i mu raba kanmu da kai , dan
in har zamu ci gaba da zama da kai , to ya zama dole sai mun shirya karb'ar bala'en
da suka fi wannan, bansan me yasa nayi wannan kuskuren ba duk da na karanta cewa
bai hallata ba zama da fasik'i ba, yau gashi abinda ka shuka yarka ta fara
girbarshi, gashi gyaran kuskurenka zai zama alhakin 'yarka, to sam ba zan yarda ba
wallahi, dole ka sakeni nayi nesa da kai da yata dan mu tsira da rayuwarmu da
lafiyarmu."
"Ka dubi k'ask'ancin da aka mata, nasan ko kai baka tab'a shigar da 'yar wani a
wannan halin ba, amma yau gashi yarka mutum d'aya d'aya har guda hud'u ne suka keta
mata haddi , yanzu haka ya maka daidai kenan? kaji dad'i?"
Duk da kuka yake amma cikin dakakkiyar zuciya yace "Na'ima, wai me yasa kike da
taurin kaine? me yasa baki da yafiya a rayuwarki? tunda abin nan ya faru nake baki
hak'uri amma kinki hak'ura, na rantse miki da Allah Na'ima nayi nadama kuma na tuba
ga Allah, wallahi ba zan sake aikata sab'o irin wanda nayi a baya ba, dan Allah
Na'ima ki sake bani dama mu sake sabuwar rayuwa, muyi fatan ganin Khairat ta samu
lafiya, ni kuma na miki alk'awarin saku farin ciki sannan zan samar ma Khairat miji
na gari na had'ata dashi, kuma wallahi daga yanzu duk abinda ki kace nayi zanyi
Na'ima amma banda rabuwa dani."
Murmushi tayi tace "oho , kenan sai yanzu zaka fara maganar yi mata aure, kenan
yanzu ne kake ganin Khairat ta isa aure? to kai a ganinka waye zai yarda ya aureta
a yanzu bayan ta rasa kimarta , ai kowane namiji yana alfahari ace shiya fara sanin
matar daya aura, wallahi Mani duk wanda kaga ya auri Khairat a yanzu to abu d'aya
ne, shine dukiyarka, amma duk wanda ya auri Khairat dan Allah to ka sani wallahi
taimakonta yayi kuma *JIHADI* yayi."
Juyawa tayi ta zauna kusa da Khairat ta fara shafar kanta tana zubar da hawaye,
shima Papa hawayen yake yi yana kallonsu, Umar Faruk kuma ya kasa motsawa saboda
tunanin kamar basu lura dashi ba ma a wajen, baya baya ya fara ja yana so ya sulale
daga wajen kawai yaji an bud'o k'ofar an shigo, ya dauka manager ne ashe Kakar
Khairat ce ta zo daga India, maida kallonsu sukayi gareta da sauri duk suka tashi
kowa na fad'i "Mammie, yaushe kika zo?"
Hannu ta d'aga musu tana kallon Khairat dake kwance a tsananin mamaki, bata d'auke
idonta akan Khairat ba tace "meya samu gimbiyata? me kuka mata?"
Mamie ce ta fara kame kame tace "Mammie babu komai fa, ta samu wani d'an hatsari
ne."
Cikin d'aga murya tace "wane irin hatsari ne wannan? zaku fad'a min gaskiya ko
saina tsine muku albarka."
Da sauri Papa yace "a'a Mama, dan Allah kiyi hak'uri, wallahi..."
Kuma sai yayi shiru, ganin Mammie ta kafe Mamie da ido yasa ta fara i'ina tana
fad'in "Ma...ma wa...sune..suka , wasu ne....suka, suka mata fyad'e." ta k'arasa da
fashewa da kuka.
A nitse Mammie ta k'arasa gaban gadonta ta durk'usa tana shafa kanta tana zubar da
hawaye, kuka suke sosai babu wanda yake bawa wani hak'uri a cikin wannan hali Umar
Faruk ya sulale ya fita, a farfajiyar wajen ya samu manager yana waya , saida ya
jira ya gama suka shiga mota suka wuce in banda tunanin halin daya ga Khairat da
abinda yaji mahaifiyarta ta fad'a babu abinda yake, a haka har suka kai ma'aikatar
manager yace kawai ya shigo yaci gaba da aikinshi kafin Allah ya bata lafiya.
Nan ya shiga ya kuma zauna mazauninshi, abokinshi Ishaq da wasu ma'aikatan mata da
maza ne suka taru suna tattauna abinda ya faru da Khairat d'in, d'aya daga ciki ne
yace,
"Koda dai har yanzu babu tabbas, amma duk mai hankali ai zaiyi zaton wani abu."
"Gaskiya ne, wallahi abar tausayi, nasan tana cikin wani hali ne shi yasa ma ba'a
bari a ganta."
Wata matashiya ce tace "wacece abar tausayin? Khairat d'in, ni kuma wallahi ko
kad'an banji tausayinta ba, dan nasan ba wani mummunan abu bane a wajenta."
Faruk ne ya kalli matashiyar ya taso ya tsaya gabanta, duk da yana k'ok'arin tausar
kanshi, amma haka kawai yaji zuciyarsa na masa zafi akan abinda suke fad'a, basu
san da zuwanshi ba sai muryarshi suka ji yace "wannan maganar bata dace ace ta fito
daga bakinki ba a matsayinki na mace, tausayi da jimami ya kamata a gani a tare
dake, kamata yayi ace kinji cewar an tab'a kimarki kema saboda 'yar uwarki mace aka
tab'a, ki tuna fa kema macece kuma bana miki fata, amma kema kina cikin wannan
k'alubalen dan haka zata iya faruwa dake, dan Allah ku dinga kyautatawa juna zato."
Tab'e baki tayi ta kau da kai tana fad'in " ni dai nasan ina zaune da kowa lafiya,
kuma kamar yanda na fad'a a baya bana jin Khairat wani sabon abune ya sameta bare
kuma taji zafinshi."
Sake gyara tsayuwa yayi cikin b'acin rai da d'aga murya ya fara magana "bata jin
zafi kike cewa? kinsan me fyad'e yake nufi? shin kin tona zuciyarta kinga me take
ji? shin kin tab'a kwatanta me zaki ji a zuciyarki ace namijin da baki had'a komai
dashi ba ya tursasaki ya kusanceki? kefa macece, ki misalta kona second goma kiji
me zaki ji a zuciyarki."
"Shin kinsan halin da take ciki? kin ganta da idonki bare kisan me take ji? kije,
kije kiga halin da take ciki, kina gani nasan dole ki yarda tana cikin wani hali,
kinsan zafin karaya a hannu bare kuma a qafa? shin kin tab'a yin hatsarin da yasa
kika ji raunika? to ita a sanadiyar abinda ya faru tana can kamar wacce babbar
motar ta bige, dan Allah ki sawa zuciyarki tausayi kodan kasantuwarki mace."
Yana fad'a ya bar wajen ya fita farfajiya zuciyarshi in banda tafasa ba abinda
take, ji yake kamar zai fashe da kuka amma kuma ya kasa, a hankali ya tambayi
kanshi "wai me yasa ka damune? Khairat ce fa."
Saida yasa hannu ya goge idonshi da yaji sun cika da k'walla sannan yace "rashin
imanina bai kai na kasa tausaya mata ba."
*Haka* Faruk ya kasance cikin wannan damuwa da tunani har yaje gida, haka ya dinga
tunanin abinda idonshi suka gane mishi a ranar, kai da kawo yake a tsakiyar
d'akinshi yana fad'in "rigarta, wannan saurayin, matashin da yazo daga baya,
d'aukewar wuta, dawowar wuta bayan qanqanin lokaci, b'atan Khairat, sai
kuma....sai...sai kuma me?"
Ci gaba yake da kai da kawowa har saida ya tsaya cak baki bud'e ido waje, a
hankali ya furta "wannan motar, wannan *CRV Honda* d'in, tabbas akwai alamun
tambaya akan wannan motar, me yasa take gudu a cikin wannan daren, sannan ina suka
nufa da suka ratsi wannan jejin?"
"Dole nasan wani abu a game da motar nan, dole na koma wajen nan."
Wata zuciyar ce kuma tace "to wai akan me? ka barsu da matsalarsu mana."
"A'a, ka tuna fa kana k'annai mata dayawa, ya zaka ji idan d'aya daga cikinsu ce?
koda namiji d'aya ne ba zaka ji dad'i b bare har hud'u saboda rashin imani, zanyi
wannan taimakon a matsayin *jihadi* fisabilillah."
_NA_
_SAMIRA HAROUNA_
_DEDICATED TO_
*MA FAMILLE*
💃💃💃💃💃💃💃
_Farin ciki auntynmu ta dawo, *ASMA'U GALADIMA* (ummu Maryam), marubuciyar *Dijah
Qaya* ina miki barka da dawowa._
_Bismmilahir-rahman-rahim_
9⃣
Har gaggawa yake gari ya waye, alwala yayi ya fara tsayuwar dare kamar yanda ya
saba, ya jima yana sallah har aka kira asuba sannan ya nufi masallaci tare da
sauran 'yan uwanshi, saida gari yayi haske suka dawo yana zuwa shiryawa yayi ya
fita ko kari baiyi ba, kai tsaye asibiti ya nufa dan yana so ya d'an samu wata
makama da zai iya dafawa a matsayin k'warin gwiwarshi.
Sammakon da yayi yasa ya tarar da Papa a k'ofar d'akin da Khairat da Mamie suke
tare dasu Musa bayan sun fad'a masa har yanzu basu samu wani abu ba, cikin b'acin
rai da sassauta murya yace,
"Wannan ai maganar banza ce, ba zai yiwu ba, ku dubi Khairat nan fa kwance har
yanzu bata farka ba, me kuke so nace mata idan ta kalleni? to kuji wallahi ku shiga
duk in da zaku shiga ku nemo min 'yan iskan nan, idan ba haka ba ranku ne zai
b'ace, kunji na fad'a muku."
Yana fad'a ya koma cikin d'akin su kuma suka jiyo Musa na fad'in "kaji d'an wahala,
to ya zaiyi in bamu samosu ba? dole dai a qarshe ya hak'ura tunda ba mik'a k'anmu
zamuyi ba muce mune muka mata fyad'en."
Da sauri Faruk ya juya yana binsu da kallo matuk'ar tsoro ya bayyana a fuskarshi
sosai, yana kallo har suka shiga motarsu CRV Honda, hannu yasa ya rufe bakinshi
yana fad'in "inna lillahi wa'inna ilaihir-raju'un."
Juyawa yayi ya koma ya hau mashin d'inshi dan baya da hujjar da zaice sune kai
tsaye dole ya samu wata makama da zai nuna eh sune, saida ya koma har club d'in nan
sannan ya fito ya d'auko hanyar, a hankali yake tafiya yana dube dube har saida ya
kawo wajen da motarnan ta shiga kwana, nan yabi yana waige waige yana dubawa ko
zaiga gida da makamantansu, wasa wasa dai bai samu komai ba har saida hanya ta
b'illo dashi kusa da unguwar airport, ganin idan ya koma baya zai maida kansa baya
ne kawai saiya shiga kwanar da zata sadashi da titi, zai hau titi kenan motar su
Musa ta shigo kwanar suka nufi hanyar daya fito, da sauri ya taka birki ya juya
yana kallonsu, bai b'ata lokaci ba yabi bayansu har suka tsaya k'ofar gidan da Papa
ya basu duk lokacin da suke bakin aiki.
Nesa da gidan ya tsaya da tunanin ko zasu fito, amma shiru shiru su Musa basu fito
ba har suka kwashe awanni uku, tun yana gyara zama akan mashin d'in har ya kai
gayin kwance a sama nan ma ya gaji ya sauka ya aza takalminshi ya zauna qasa.
Su kuma suna ciki dama duk lokacin da Papa ya matsa musu lamba nan suke dawowa suyi
kwancinsu su huta sannan su koma suce masa babu labari, _(rainin wayo)_, sai
lokacin suka fito suka shiga motarsu sukayi gaba abinsu, anan ya bar mashin d'in ya
nufi gidan, ganin k'ofar rufe take amma katangar gajera ce yasa ya tuna yarinta
d'araf ya haye katangar ya haura gidan.
🤣🤣🤣🤣🤣🤣🤣
Ganin k'ofar falon itama a rufe take kawai yasa ya dinga bangazar k'ofar har saida
ta bud'e da k'arfi, nan ya shiga d'akuna hud'u ne a ciki, kowane d'aki b'alle
k'ofar yayi ya dinga bincikawa ko zaiga wani abu amma shiru, d'aki na qarshe daya
shiga ganin bai samu komai ba yasa ranshi ya b'ace ya daki armoire (wradrob) d'in
da k'arfi, abinka ga d'akin maza ba'a kimtsa komai, kayane suka zubo daga ciki.
Durk'usawa yayi zai kwashe kawai yaga wata bak'ar mask ta fuska, d'auka yayi ya
kalleta da kyau yana tunanin ko meye anfaninta, zai mayar da kayan saiya sake ganin
wata, dan haka ya sake dubawa saiga guda hud'u ras sun bayyana, kai ya girgiza ya
mayar da kayan har da mask d'in sannan ya rufe wradrob d'in fito ya daga d'akin,
maida k'ofar falon yayi ya rufe duk da bata rufu ba.
Har zai wuce kuma ya tsaya yana kallon poubelle (abun zuba shara) d'in wajen, cike
da mamaki yasa hannu ya ciro rigar da koba a fad'a masa ba yasan ta Khairat ce dan
itace a jikinta a ranar, duk rigar ta yage sosai ga jini a jikinta har da pant
dinta da kuma takalminta duk a cikin sharar, ji yayi idonshi sun kawo ruwa amma
saiya aje rigar ya da kayan ya fita ya bar wajen, gudu yake sosai akan mashin d'in
har saida ya kai asibiti.
Ya samu 'yan uwa dayawa a wajen wanda ba'a bari shiga ba, mai tsaron k'ofar Umar ya
cewa "dan Allah ko zan iya ganin yallab'ai?"
"Kaga wallahi magana ce zamuyi mai mahimmanci, dan Allah ka barni na ganshi."
"Ka fad'a min ko miye saina fad'a masa." cewar jami'in yana d'auke kai.
"Maganar nan sirri ce, dan Allah kace ina son ganinshi."
A hassale jami'in yace "kai, wai kai wane irin mutum ne? nace maka yace kar a
takura masa ko, kai baka ga yan uwa ba duk gasu nan amma ba'a bari sun shiga ba sai
kai, dallah ka b'ace min da gani."
Ganin fa ba zai barshi ba yasa dole ya yanke shawarar fad'a masa, d'an sassauta
murya yayi yace "kaga abokina, wata masaniya na samo akan mutanen da yallab'ai yake
nema, dan Allah ka barni na ganshi kar lokaci ya qure mana."
Ido ya zaro yace "kenan kasan mutanan da ake nema? to su waye, kuma me sukayi?"
Kallon rainin wayo ya masa yace "kana nan kace baka san akan me ake nemansu ba?"
Cike da son jin gulma yace "wallahi ban sani ba, ba'a yarda kowa yasan meke faruwa
ba."
Cike da k'osawa yace "yanzu zaka iya yimin magana dashi d'in ko kuwa na tafi?"
"A'a jira ina zuwa."
Yana fad'a ya shiga d'akin dan fad'a ma yallab'ai Papa, zaune ya samesu shiru dasu
abin tausayi suna kallon Khairat, sunkuyawa yayi kusan kunnen Papa yace "yallab'ai
wani saurayine a waje kesan ganinka, kuma yace akan maganar mutanen da ake nema
ne."
Tsaki yayi yace "yanzu haka d'an jarida ne yayi basaja ko kuma masu son sanin meke
faruwa, kawai kace masa ina wani uzuri ba zanga kowa ba."
Duk abinda ya fad'a a kunne Mamie dan haka bata ce k'ala ba ba ta mik'e zunbur ta
fita daga d'akin, tsaye ta samu Umar Faruk yana jira, saida ta kalleshi da kyau
tace "sannu bawan Allah, kaine kake son ganin Alhaji?"
Cikin muryar tausayi tace "ka fad'a min wani abu da zaisa naji dad'i dan Allah."
Ajiyar zuciya ya sauke tare da gyara tsyuwa yace "kiyi hak'uri Mama, bansan taya
zaki fahimci abun ba, amma dai tabbas anci amanarku, wanda suka ketawa yarku haddi
suna nan tare daku, hasali ma sune kuke sawa nemo muku masu laifin."
A jujjuye ta fahimceshi dan haka tace "ban fahimceka ba yaro? ko zaka iya yimin
dalla dalla?"
"Mama ba zan iya fad'a muku komai ba, amma ku aika wasu jami'an na daban ba wanda
kuke tare dasu ba, suje unguwar airport daga farkon shiga unguwar a gida mai number
8, suyi bincike da kyau karsu bar komai, ina tabbatar muku zaku samu hojojjin da
suke nuna masu laifin anan suke."
Tuni hawaye suka wanke fuskar Mamie tana kallon Umar Faruk tace "jirani ina zuwa
kaji yarona."
Tana fad'a ta juya ta shiga ciki da gudu, Umar Faruk na ganin haka shima yayi
murmushi kawai ya juya bar wajen, tare da Papa Mamie ta fito amma basu ga Faruk ba,
nan Papa ya ciro waya jiki na rawa yasa aka turo mashi wasu jami'an, dan danan
asibiti ta cika da jami'an kama daga police soldier da gendarme, nan fa suka basu
jawabin abinda Umar ya fad'a musu, ina Papa ma ba'a barshi ba saida ya bisu.
Suna gaf da fita daga k'ofar asibitin motar su Musa tazo shigowa, nan suka tsaya
suka fito suka sarama manyansu suma wasu suka sara musu, nan Papa yace su shiga
mota su tafi an samu labarin in da mutanen nan suke, ganin yanda ya masu magana
bai nuna wani abu ba yasa ransu yayi fari suna tunanin wasu ne aka lak'ama sharrin,
amma tunda suka ga ana nufa unguwarsu gabansu ya fara fad'uwa, babu wanda baiji
gudawa ba lokacin da aka tsaya k'ofar gidansu.
Duk da unguwa ce da babu mutane sosai amma saida jama'a suka fito kallo ganin yanda
jami'an suka cika unguwar, Papa na fitowa ya duba yaga kwatancen daidai ne kawai ya
juya ya kalli su Musa da sukayi sukayi sharkaf da zufa, hannu Papa ya nuna musu
yace "ku kama min su."
Tuni aka cika aikin yallab'ai akayi ram dasu Musa aka d'aure su , gidan suka shiga
nan fa suka fara shiga kusfa kusfa ana bincike, saboda Umar Faruk ya rage musu
wahala hakan yasa suka samu hujjojin da Faruk ya gani har dama wanda shi bai gani
ba kamar bras d'inta da d'an kunnai, haba su Musa ai tun daga nan suka fara shan
duka.
Kasancewarsu jami'an yasa ba'a tausaya musu ba, cikin k'ank'anin lokaci har sun
canza kama wai wannan somin tab'i ne kafin su gurfana a gaban kotu, tuni labari ya
karad'e gari akan abinda ya faru da Khairat da kuma kama masu laifin, duk mai
zuciyar imani ya tausaya mata sosai ace har mutum hud'u.
*02: 40* na dare Khairat ta farka da ihu tana fad'in a taimaketa zasu kasheta,
Mamie da Mammie ne suka rik'eta sosai suna tofa mata addu'a harta nutsu, kuka take
sosai tana d'aga murya kamar ranta zai fita, haka har suka wayi gari bata daina
kuka ba, tunda likitoci suka nufi wajenta ta dinga kuka tana fad'in karsu tab'a ta
su saketa ta koma gida, babu abinda suke ji kamar d'orin qafarta dan yafi hatsari,
ganin abin ba qarami bane yasa Papa ma yace su sallamesu kawai.
Duk da ba haka aka so ba haka aka sallameta aka koma gida da ita, a d'akinta aka
sake mata wani tanadin na ci gaba da jinyarta , amma duk da sunzo gida ma ba'a bari
kowa ya ganta saboda kukan da take.
*Bayan sati d'aya* jikinta yayi dama dama sai dai har yanzu bata fara taka qafar
ba, qananan raunikanta ne suka warke har akaihunta guda biyu sun toho, in banda
shiru da tunani da hawaye babu abinda Khairat keyi hakan kuma na damun iyayenta.
Da farko an fara barin 'yan uwa na zuwa dubata, amma ranar da Mujahhid yazo da
abokanshi su uku saita firgita sosai tana fad'in sune sune, tun ranar sai Mammie ta
yanke shawarar tafiya da ita india danta samu ta dawo daidai.
Umar Faruk ya ci gaba da zuwa wajen aikinshi sai dai i zuwa yanzu babu wata damuwa
a tare dashi, gaba d'aya ma mantawa yake da wata Khairat bare ta dameshi , yayin da
d'aya b'angaren kuma yake soyayyarshi hankali kwance da 'yar uwarshi *Zubaida*
wacce suka fi kira da *Zuby*, kuma suna jiran hutun 'yan makaranta domin shi zai
basu damar zama miji da mata.
An shigar dasu Musa kotu kuma sun samu hukuncin shekarun da doka ta tanadar ga duk
wanda ya keta haddin wata, tun akan akan hayarsu ta zuwa sabon gidansu suka fara
tuhumar juna suna dorawa Musa laifin, shi kuma yace ba gaskiya bane tunda bai
tilasta kowa ba.
_Allah ka karemu da yayenmu daga fuskantar qasqanci irin wanda Khairat ta fuskanta,
Allah ka shirya mana zuri'armu shirin addinin musulunci._👏
Mamie da Mammie ce suka kama Khairat daga bisa kujerar guragunta suka cire mata
kaya sannan suka sata cikin bahon wanka dake d'auke da magunguna na ice kala kala,
suna zaunar da ita ta rintse ido saboda zafin dake da ruwan, duk da kullum ake mata
tunda suka komo gida amma ta kasa sabawa , a hankali ta bud'a ido hawaye suka
gangaro, Mamie ce ta fita daga ban d'akin sai Mammie ta dinga tausarta da kalaman
har saida ruwan suka huce sannan ta kira Mamie suka kamata suka fito da ita.
Mamie ce ta shiryata cikin doguwar rigar kantie iya gwiwa sannan suka zaunar da ita
akan kujerarta, abinci Mamie ta d'auka ta fara bata a baki, da sun had'a ido Mamie
take saurin dauke nata, ganin kuma ta kafeta da ido yasa duk ta tsargu , a raunane
ta kalleta tace "akwai abinda kike so ki fad'a ko?"
Lumshe ido kawai tayi ta kawar da kai, Papa ne ya shigo cikin shiri da alama fita
zaiyi, saida ya sumbaci goshinta yace "shalele ya kike?"
Da ido kawai ta kalleshi, sake fad'in "ya jikin naki? da sauk'i dai ko?"
Ganin dai ba za tayi magana yasa yace "shaleleta kiyi hak'uri kinji da abinda ya
faru, ina tabbatar miki hakan ba zata koma faruwa ba."
Take idonta ya kawo ruwa cikin mamakin abinda ba suyi tsammani ba suka ji Khairat
tace "wane mai hankalin ne zai sake sha'awata kuma? akwai wani abinda ya rage min
ne da har zan birge wani?"
Maida kallonta tayi ga Mammie tace "Mammie, ki kaini waje dan Allah ina so nasha
iska."
A hankali ta tuka kujerarta ta fitar da ita kamar yanda tace, lambun dake bayan
gidan ta kaita ta barota kamar yanda ta buk'ata, shiru tayi tana kallon firanni na
kad'awa ga iska mai dad'i.
Papa da Mamie ne suka fito daga d'akin nata suna zuwa falo yayi daidai da shigowar
manager, bayan sun gaisa ya fad'a musu tare da sauran ma'aikata yake suna so suga
jikin Hajia, Papa ne yace su shigo sannan yace Biba mai aiki taje ta taho da
Khairat, zaune sukayi suna jiran shigowarta, Mamie kuma ko kad'an bata lura da
Faruk ba yaron da take nema danta gode masa, madafa ta nufa domin samo musu d'an
abun tab'awa.
Shigowar Khairat a keken guragu yasa kowa maida kallonshi gareta, mamaki al'ajabi
duka a tare da ganin Khairat, ita kam ido ta kafesu dashi tana kallon kowa, a
lokacin da kallonta ya sauka kan Umar Faruk kuma sai gabanta ya mugun fad'i, duk da
haka kuma bata d'auke idonta ba, shima a nashi b'angaren gabanshi ne yayi mummunar
tsinkewa ya fad'i, d'auke kanshi yayi ita kuma suka k'arasa shiga falon, sannu kowa
ke mata da jiki amma babu wanda ya amsa, Papa ne ya shafi kanta yana kallonsu yace,
"Sai hak'uri fa, har yanzu magana na mata wuya, muma haka muke zaune da ita."
A bazata Umar Faruk ya sake satar kallonta amma sai idonsu ya sake had'ewa , suna
haka har Mamie ta fito amma da qyar wasu suka sha ruwa dan ganin Khairat ya
girgizasu sosai, tashi sukayi gaba d'aya suka fita, amma Umar Faruk dake daf da
barin falon sai yaji kamar muryar Khairat a bayanshi, dan haka yayi saurin juyowa
ya kalleta, dama itama shi d'in take kallo dan haka suka kalli juna, d'an sakin
fuskarshi yayi daga had'ewar daya mata baisan sanda ya saki wani basaraken murmushi
ba, ita kum sai taji haushi ya kamata dan tunaninta yayi farin ciki da abinda ya
sameta.
_NA_
_SAMIRA HAROUNA_
_DEDICATED TO_
*MA FAMILLE*
🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾
*Raina Fansane gareta*
🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾
_My sweet Heenat, ina tayaki murnar kammala wannan littafi, tabbas ya qayatar tare
da nishadantarwa, ga ilima da muka samu a ciki, wannan shine labari ina fatan
ubangiji ya yafe miki kurakuranki sannan ya baki ladar dake cikin wannan fad'akarwa
da ki kayi._ sai mun jiki a next novel.
_Bismmilahir-rahman-rahim_
1⃣0⃣
*Haka* kwanaki suka dinga tafiya sati ma ya fara shud'ewa har aka fara lissafa
abinda ya faru da sati uku, a *sati uku* kuma duk wasu qananan raunika sunyi sauk'i
sosai sai qafarta da har yanzu takata ya zama aiki, har yanzu Mammie na gasata a
ruwan zafi tare da wasu saiwar magunguna da zai taimaka mata, haka ma an sake
maidata asibiti an mata gwaje gwaje amma cikin ikon Allah babu wata matsala har
yanzu.
A lokacin data cika wata d'aya sai suka fara shirye shiryen tafiya india, a lokacin
kuma Mamie ta matsawa Papa akan ya bata takardarta, shi kuma ya dage ba zai bayar
ba, amma ita taci alhwashin tafiya ko babu takardar saki, Mammie bata fahimci komai
ba dan basa nuna da wata matsala a gabanta, Papa kam yayi tuba na gaskiya ya daina
duk abinda yake yanzu, sai dai akwai barazana da wasu matan ke kawo masa saboda
suna samun arzik'i sosai a hannunshi, duk da Khairat bata cika magana ba a yanzu
amma dai bata kula Papa sosai haka ma Mamie.
Yau ta kama ranar *juma'a* Papa ya fito cikin shirin massallaci misalin k'arfe
*10:00*, zaune suke a falo yayin da suka bishi da ido, durk'usawa yayi gaban Mammie
ya gaisheta tare da fad'in "Mama zan tafi masallaci sai a mana addu'a."
Murmushi tayi dan ita har ranta tana ganin d'iyarta tayi sa'ar miji na gari, cikin
sakin fuska tace "Allah ya tsare ya kareka daga sharrin masharranta, insha Allah ba
zaka tab'e ba, domin kai mutumin kirki ne, duk da ban haifeka ba amma ka d'aukeni
tamkar mahaifiyar data haifeka, babu abinda zance sai dai nace Allah ya saka maka
da alkairi."
"Ameen ameen Mama, na gode da addu'ar nan Allah ya bar mana ke."
"Ameen." itama ta fad'a sannan ya mik'e yana kallon Mamie yace "ni zan wuce."
Cike da murmushi tace "to abban Khairat Allah ya tsare, saika dawo."
Shima cikin murmushi yace "ameen na gode."
Maida kallonshi yayi ga Khairat ya dafa kanta yace "shalele ni zan wuce, kiwa Papa
addu'a kinji."
Sanin ba za tayi magana sai kawai ya wuce, muryar Khairat yaji tace "Allah ya
kiyaye, a dawo lafiya."
Da sauri ya juyo ya taho a sukwane ua zube gwiwoyinshi gaban kujerarta, cikin farin
ciki yace "Khairat, yau kece ki kawa Papanki addu'a? kai Allah na gode maka."
Duk da hawaye sun fara taho mata haka tace "Papa, duk munin halinka kai mahaifina
ne, Papa ku yafe min da duk abinda na muku wanda ya b'ata muku rai, nasan hada
hakk'inku dana kasa saukewa da kyau shi yasa haka ta faru dani."
Hannunta ya rik'e da sauri yace "a'a shaleleta, ba laifinki bane, laifina ne duk ni
na ja miki, amma ki sani Papanki yayi nadama sosai kuma ya daina duk abinda yake
yanzu."
Shiru sukayi babu mai magana dan haka Papa ya tashi yana goge hawaye ya fita, Mamie
ce ta matso kusanta ta rik'e hannunta tana shafawa tace "Khairat, ki yafe mana a
bisa kurakurenmu, nima na taka rawa wajen faruwar komai a matsayina na uwa, amma
yanzu mun shirya gyara kuskurenmu."
Da ido kawai ta kafe Mamie ba tace komai ba har Mamie ta gama surutunta ta koma
mazauninta, haka suka zauna shiru dan yanayin da gidan yafi zama kenan tun faruwar
abinda ya faru.
Bayan Papa ya dawo daga masallaci sunci abinci Mamie taje d'akinsa ta zauna dan
kawar da duk wani shakku da zai nuna basa zaune lafiya, yana cire kayan jikinsa ya
kalleta ta madubi yace,
Ba tare data kalleshi ba tace "kana tunanin akwai abinda zaisa na fasa ne, kayana a
shirye suke ranar kawai nake jira."
Gabanta ya zo ya tsaya ya kamo hannayenta suna kallon juna, kai ya girgiza mata
yace "Na'ima, ke musulma ce kuma mai ilimi, nasan kinsan ba daidai bane aibata
wanda ya musulunta, haka ma bai dace ak'i karb'ar yafiyar wanda ya nemi afuwa ba,
hakan nasa da dama su kasa shiryiwa saboda tunanin haka, dan Allah Na'ima ki yafe
min laifina wallahi ba sani da kika min da bane."
Ganin ta kawar da kai gefe yasa hannu ya tallabo fuskarta yana kallo, a hankali
cikin tsoro ya had'ata da jikinshi, 😁wasa fa saita fara canzawa to ni dai nayi
nan, bana kallon k'aramar harka bare kuma wannan babbar harka.
Kamar yanda Mamie tayi niyyar tafiya ko babu takarda hakane ta faru, ta shirya
itama kuma tace wa Mammie shine yace su tafi tare danta kama mata kula da Khairat,
ya gama shirya musu komai amma banda Mamie, in da itama ta shiryawa kanta komai ba
tare da saninshi ba.
Sun gama shirin tafiyarsu tsaf ranar talata kawai suke jira ta zo, yau *litinin*
da dare Mamie na zaune matashin saurayin nan ya fad'o mata a rai, wayarta ta d'auka
ta kira manager ta tambayeshi akan yaron da suka zo tare a ranar, ya fad'a mata
sunanshi dama matsayinshi a ma'aikatar tare, ta kuma tambayeshi koda wata alaka
tsakaninshi da Khairat yace a'a, amma ya fad'a mata abinda ya shiga tsakaninsu.
Nan tace da safe ya turo mata shi kafin lokacin tashin jirginsu, bayan sunyi
sallama ya kira Umar Faruk ya fad'a masa, hakan yasa ya kwana yana tunanin abinda
zai faru da kuma dalilin da yasa matar ke nemanshi, haka dai ya wayi *gari* sannan
ya shirya ya tafi gidan.
Khairat ce zaune akan kujerarta ta kira Biba, tana zuwa tace mata ta turata ta
kaita lambu tasha iska, haka akayi ta kaita can ta barota yayin da ta toshe
kunnuwanta da abin sauraro tana sauraron wak'ok'i, Umar Faruk ne ya shigo gidan sai
dai kafin ya shiga ciki sai wayarshi ta fara ruri, yana fito da wayar yaga Zuby ce
ke kira dan haka ya d'auka ya fara tafiya ya nufi kwanar cikin gidan duk da baisan
ina zata kaishi ba, a hankali yake takawa harya riski lambun dake bayan gidan,
jingina yayi a bishiyar daya fara gani cikin taushin murya ya mayar da martanin
abinda Zuby ta fad'a masa,
"Ina sonki, ina qaunarki , na matsu ranar nan tazo domin a ranar burina na gidan
duniya ya cika, na gaji da mafarkinki a kullum, ina so mu fara rayuwar gaske."
Khairat dake sauraren wak'ok'i bata jin me yake fad'a, amma shi duk da yana magana
ne amma yana jin wata siririyar murya na tashi a kusa dashi ana rera waka , juyawa
yayi ya kashe wayar yasa aljihu tare da rumgume bishiyar ya lek'a kanshi a hankali
dan ganin me wakar, yanda ya rumgume bishiyar yasa hannunshi ya d'an shafi
kafad'arta hakan kuma yasa ta juyo da sauri, manyan idanunsu ne suka sarke dana
juna suna kallon kallo, babu wanda baiji fad'uwar gaba ba a cikinsu amma sai suka
basar.
Babu wanda yace wani abu kuma babu wanda ya d'auke kanshi, Khairat ce taja tsaki
tare da maida kallonta ga wayarta ta ci gaba da abinda take, yana ganin haka ya
tab'e baki shima ya koma hanyar daya fito, Biba ce ta masa izinin zama sannan taje
ta sanar da Mamie bak'onta ya zo.
Yana cikin kallon hadadden falon yaji bud'a k'ofa, maida kallonshi yayi ga
nutsatsiyar matar mai dattako, tsaye ya mike yana murmushi ita kuma ta masa izinin
zama, cike da girmama juna suka gaisa kafin Mamie ta kalleshi a tsanake.
Hakika Umar Faruk ba zaka kirasa da kyakyawa ba ajin farko, amma dai dole ka
kirashi kyakyawa na farko a aji na biyu, manyan idanunshi masu firgita mai kallonsu
da kuma saka kwarjini, haka kuma bak'i kuma yalwataccen sajenshi ma ya k'ara masa
kyau, kana ganinshi zaka san jarumin namiji dan suffarshi ma ta zaratan maza ce,
daga tafiyarshi kuma zaka gane ingarman dokine mai tashen k'uruciya a jika.
Murmushi Mamie tayi tace "Umar Faruk, ranar ka taimakemu amma kuma saika tafi ba
tare da mun maka godiya ba, kome yasa kayi haka?"
D'an murmushi yayi yace "Hajia ni na taimakeku ne saboda Allah, bana buk'atar ku
gode min."
"Duk da haka Umar Faruk muna godiya sosai da irin taimakon daka mana, amma dan
Allah tayaya akayi kasan da mutanen nan?"
Kallonta yayi yace "Hajia da mun bar duk wannan maganar, tunda dai masu laifin sun
shiga hannu."
"Hakane, amma zan iya sanin meke tsakaninka da Khairat?"
"Uhum, ba damuwa."
Kallonshi tayi tace "amma misali, idan nace zan da Khairat, kana ganin zaka yarda
ka aureta?"
Kafeta yayi da ido da tsananin mamaki, ba zai iya yi mata qarya ba kamar yanda ba
zai yarda ya lalata rayuwarshi ba ta hanyar auren Khairat, ko kyauta za'a bashi ita
to ba zai karb'a ba, shima da ido ya kalleta yace "kiyi hak'uri Hajia, amma gaskiya
ba zan iya ba, kiyi hak'uri idan abinda na fad'a ya b'ata miki rai, ina da wacce
nake so kuma hutu kawai muke jira a d'aura mana aure."
Murmushin takaici tayi tace "karka damu raina bai b'ace ba, dama tunda abun nan ya
faru na sawa kaina dole haka zata fara faruwa damu, nasan a yanzu ba kowa bane zai
iya yarda ya aureta, amma ba komai zamu ci gaba da hak'uri har komai ya zo qarshe,
kuma ina so ku sani Khairat bata da laifi, duk laifin namu ne iyayenta musamman ma
ni uwa."
"Shari'a ta nuna mana yanda zamu samu yaya na gari tun kafin aure, amma sai
kaddarata ta zo da tangarda na kasa samar mata uban daya dace, ba komai karka damu
kanka kaji."
Shi dai baice komai ba yana kallo ta fara tafiya kuma ta tsaya ta juyo tace "bansan
ko kana buk'atar kuyi ban kwana da Khairat ba, dan baifi awa d'aya daya rage mana
ba mu koma India da zama tare da mahaifiyata."
Tana fad'a ta juya saboda hawayen da suka taho mata, yau gashi *halin rayuwa* yasa
harta yiwa namiji tayin 'yarta a cikin wasa amma yace baya so, shi kuma jikinshi ne
yayi sanyi duk yaji ba dad'i, amma kuma baiyi nadama dan ba zai yarda koda a
misaline ba a dinga had'ashi da Khairat.
Tashi yayi shima ya bar gidan dan baiga wani ban kwana da za suyi ba da ita, haka
ya d'auki hanya yana tunanin maganganun mahaifiyar Khairat, uwar mutuniyar kirki ce
amma diyar da uban sai a hankali kam , inji Umar Faruk.
10/07/2019 à 12:39 - ~NANA KHADIJA~😍: 💑💑💑💑💑💑💑💑💑💑
*JIHADI*
_Umar faruk_
💑💑💑💑💑💑💑💑💑💑
_NA_
_SAMIRA HAROUNA_
_DEDICATED TO_
*MA FAMILLE*
TTTTTTTT
*MARAYU MA 'YA'YANE*
TTTTTTTT
_A gaskiya littafin nan ya ilmantar sosai, kuma da za'a dinga yin labari irinshi to
za'a samu ci gaba, my Lissa na tayaki murnar kammalashi, ubangiji ya yafe miki
kurakurenki ya baki ladar fad'akarwar da ki kayi._ sai mun had'u a labari na gaba.
_Bismmilahir-rahman-rahim_
1⃣1⃣
Lokaci nayi suka fito cikin shirin tafiya, Papa na ganin Mamie ya janyeta gefe
cikin rad'a yace "wai me kike shirin yi ne Na'ima, da gaske tafiya za kiyi?"
Fizge hannunta tayi tace "ka rabu dani, aina fad'a maka babu abinda zai hanani
tafiya wallahi, kaji na rantse."
Jinjina kai yayi yace "naji, tunda kince dole zaki tafi to ki tafi, amma ki barmin
'yata zan kula da ita."
Dariya tayi tace "'yarka, wallahi idan kaga nabar Khairat a hannunka to ka tabbata
aure zaka mata, amma in ba haka to wallahi ba zan bar maka ita ba."
Wucewa taje yi ya sake rik'eta yace "naji tunda haka kika ce, ki bar Khairat anan,
na miki alk'awarin samo mata miji na gari na had'ata dashi."
Kallon sama da qasa ta masa tace "idan ka samu mijin saika kirani ka fad'a min, ni
kuma zan kawo maka ita da kaina."
Tana fad'a tayi gaba, haka suka tafi tare ya rakasu babu mai magana har jirginsu ya
tashi yana kallonsu, haka suka tashi yana ji kamar ya bisu amma tunda bai shirya
hakan ba dole ya hak'ura, haka ya juya ya koma gida zuciyarshi na tafasa kamar
zata fashe, yana son Na'ima kuma yasan ba zai samu mace kamarta ba, amma
hallayarshi taja mashi rasata a lokacin daya fi buk'atarta.
Ita kanta Mamie saida jirgi ya tashi sai taji kamar bata kyauta ba , kamata yayi
ace ta hakura su rumgumi 'yarsu su maida hankali kan tarbiyarta, ba kuma wannan ne
yafi d'agawa Mamie hankali ba shine ji da tayi kamar itama ta kamu da son Papa ba
tare data sani ba, haka dai har suka sauka a india Mamie na hawaye, Khairat kuma na
ganin haka saita dinga jin haushin Mamie saboda tana ganin ai farin ciki ya kamata
tayi data rabu dashi na d'an wani lokaci, to amma ta rasa kukan miye take.
*SOYAYYA KENAN*😁
Tunda suka sauka abokan arzik'i da aka saba suka fara zuwa musu sannu da zuwa, kuma
sai lokacin suke ganin halin da Khairat ke ciki, haka dai ake ce musu hatsari tayi
nan zasu mata addu'ar samun lafiya sannan su tafi.
Haka ma dai masoyin nata Raj ba'a barshi a baya ba, a sukwane yazo domin ganin
Khairat cikin farin ciki tare da shirinshi na neman aurenta a yau d'in, amma
ganinta a wannan hali saiya sare masa gwiwa dole ya hak'ura, amma yayi niyyar
bayyana mata k'udirinshi bada dad'ewa ba koda tana cikin wannan halin ne dan yana
sonta so mai tsanani.
*Daga* wannan rana sai Raj ya fara taimakawa su Mamie wajen jinyar Khairat, duk da
Mamie bata so ko kad'an amma da yake mutum ne mai barkwanci da son mutane gashi da
aiki ko ba'a sashi ba, hakan yasa ya shiga ran Mammie kuma ya qara girma a idon
Khairat, kowace safiya saiya zo gidan ya tayasu had'a abin kari kuma da kanshi yake
bawa Khairat nata , haka kuma da dare zai zo su jima suna hira da Khairat saboda
kusan unguwa d'aya suke, Khairat najin dad'in haka hakan yasa yanzu harta fara
canzawa yanzu tana magana sosai tana dariya in dai Raj na nan.
A haka sai shakuwa ta sake shiga tsakaninsu fiye da baya, duk da raunin dake
jikinta tare da rashin tafiya hakan baya hana Raj fita da ita wuraren shaqatawa,
kuma hakan na mata dad'i tana d'ebe kewa sosai.
*A b'angaren* Papa kuwa an duk'ufa an maida al'amura ga ubangiji, sallah kan lokaci
tsayuwar dare yana neman gafarar ubangiji, azumi kullum sadaka da taimakawa marasa
galihu duk wannan yanzu shine aikinshi, damuwar rashin iyalinshi na damunshi
musamman Na'ima wacce yake ganin ta tafi kenan, duk kiran da yake mata bata dauka
Khairat kad'ai da Mammie suke waya dasu amma banda ita, idan ka ganshi yanzu yayi
kalar tausayi sosai kana ganinshi za kasan yana rayuwar kad'aici, sai ma'aikata
kawai dake hidima da gidan.
*Bayan wata uku* Umar Faruk ne a tsakar gidansu Zuby suna hira, Zuby ce ta nunfasa
tace "yaya Umar, a gaskiya kaban mamaki sosai daka iya b'oye min abu mai mahimmanci
haka."
Gyara zama yayi yana kallonta sosai yace "uhum, ina jinki, me nayi kuma?"
Cewa tayi "yaya Umar, jiya da naje gida wajensu Mama nake jin abinda ya faru a
wajen aiki, wai matar da kuke aiki a qasanta ta mareka, a gaskiya raina ya bace
sosai, ganin duk kwarjinin nan naka ace mace ta daga hannu ta mareka, ai sai dai
mai zarra."
Shiru ya d'anyi na wani lokaci dan sai yanzu da tayi maganar ya tuna da wata
Khairat, a hankali ba tare da sanin maganarshi ta fito fili ba yace "ko ya jikinta
yanzu?"
Dorawa tayi da "amma ai kamar itace na gani a Whatsapp ana magana akai, wai in dai
har za'a dinga keta haddi yayan manya ma to ina ga talakawa da marasa 'yanci."
Kallonta kawai yayi da ido, dan haka ta sake cewa "kuma naji ance har mutum hud'u
ne ko, gaskiya ta ban tausayi, nikam yaya da zaka kaini gidansu ma na ganta
wallahi."
"Keeee." tsawar daya mata tasata zabura da k'arfi.
Tsaye ya mike yana masifa "ita d'in cinema ce da za kice na kaiki ki ganta, wani
abun dad'i ne ya sameta da har zaki dinga magana haka cikin shauki , to ba zan
kaiki d'in ba kije da kanki saiki ganta, hada wani wai mutum hud'u, to sai akayi me
dan mutum hud'u ne? zata fasa rayuwa ne ko kuma zata rasa mijin aure ne?"
Yana gama fad'a kuma ya koma ya zauna yana huci, ruwan dake kusa dashi a cup ya
d'auka ya kai bakinshi , kamar dirar mikiya ya tsinci muryar Zuby tace "zata rasa
mijin aure, dan a mahawarar dana gani a Whatsapp, kowane namiji yana cewa shi ko
kyauta ba zai aureta ba, wasu kuma suna cewa idan za'a had'a musu da kud'i da mota
da gida to zasu amince, watak'ila kaine kake ganin ba komai bane, amma wannan ba
k'aramar matsala bace."
Kasa shan ruwan yayi ya qura mata ido, ita kuma tashi tayi ta shige d'akinsu wai
ita ya d'aga mata murya akan wata banza.
Ai baiko bi ta kanta ba ya fita daga gidan shima ya hau mashin d'inshi, bai zame ko
ina ba sai majalisar da manage ke zama bayan an tashi daga aiki, zaune ya samesu
wasu akan tabarma wasu akan benci, gaidasu yayi cikin girmamawa dan duk ba
sa'anshi, manager ne yasa takalmi ya tashi suka keb'e.
Shiru ya d'anyi shi kuma yana kallonshi kamar mai nazartarshi, kai ya shafa yace
"manager wai dan Allah ya jikin Hajia Khairat ne? naga har yanzu babu wani labari
tunda suka tafi basu dawo ba."
Ajiyar zuciya ya sauke yace "wannan sirrin gidan Alhaji Mani ne, bai kamata na
fitar dashi ba, amma dai ka sani mahaifiyarta ba zata sake dawowa ba sai dai wani
iko na ubangiji kuma."
A tsanake ya kalli manager yace "hakan nada alak'a da abinda ya faru da 'yarsu
kenan?"
Kai Umar Faruk ya girgiza ya bawa manager hannu yace "na gode manager, ni zan
wuce."
Harya tafi manager ya kira sunanshi, juyowa yayi yace masa "ko dai na baka lambarta
ne saika kirata kaji."
Kamar wanda aka ba tsoro saiko yace "a'a a'a, ni kuma me zanyi da lambarta."
Yana fad'a ya juya ya hau mashin d'inshi yana fad'in "ina ruwana da ita, tana can
fa ita da masoyinta."
Tafiya ya fara amma ya rasa dalilin da yasa ranshi b'acewa, da k'arfi sake fizgar
mashin d'in tare da jan dogon tsaki yace "Raj d'in banza da wofi, miye matsalata
dashi da zai dameni."
😛😛😛😛😛😛😛
*A wannan* lokacin Khairat jiki yayi dama sosai tafiyarta ma lafiya lau, da
taimakon Raj ta fara takawa dan kullum shike rik'e da hannayenta yana koya mata
tafiya harta fara sosai, yanzu dai da kaga Khairat to ta baya ce dan ba zaka tab'a
cewa tayi wata larura ba.
Mammie Mamie da Khairat duka suna zaune a falo suka ji ana buga kofa, Khairat ce ta
tashi ta bud'e, da farin ciki ta rumgume Raj wanda ya shirya cikin pink d'in riga
da bakin wando, sosai yayi kyau dan dama akwai kyau d'in, sakin juna sukayi ya
shigo ciki ta rufe kofar, hannun juna suka rik'e cikin yaran india take cewa,
Murmushi kawai ya mata ya mik'a mata flowers daya taho da ita ja mai kyau, karb'a
tayi tace "na gode."
Mamie da tunda ta ganshi ta had'e rai dan ko kad'an bata san ganinshi tare da
Khairat, bata musa akan cewar yaran kirki ne ba,amma tafiyarshi da Khairat bata
dace ba, saboda shine namiji kuma ba musulmi ba, d'aya bayan d'aya ya sunkuya ya
tab'a qafafun Mammie da Mamie d'in dan neman tabarruki, Mammie ce tace ya zauna,
kallon kallon aka shiga yi har saida Khairat tace,
Kai kawai ya girgiza mata alamar ba komai, Mammie da Mamie ya kalla cikin
harshenshi yace "ina neman izininku akan ku bani damar neman auren Khairat."
Khairat ce ta kalleshi da mamaki, kai ya jinjina mata dan haka ta taso ta dawo
wurinshi ta zauna murya qasa qasa tace "kana haukane? nifa ban shirya aure ba
yanzu."
Hannunta ya kama ya rik'e yana mata shu'umin kallo yace "me yasa Khairat? baki sona
ne?"
Cikin sanyin jiki tace "ba haka bane Raj, amma ba...."
11/07/2019 à 22:43 - ~NANA KHADIJA~😍: 💑💑💑💑💑💑💑💑💑💑
*JIHADI*
_Umar faruk_
💑💑💑💑💑💑💑💑💑💑
_NA_
_SAMIRA HAROUNA_
_DEDICATED TO_
*MA FAMILLE*
1⃣2⃣
Bai bari ta k'arasa ba ya rufe mata baki yana fad'in "shiiii, Khairat, in dai har
kina sona, to ki tabbatar min da hakan yanzu ta hanyar saka wannan zoben, alamar
munyi baiko dake." ya fad'a tare da fito da zobe daga aljihun rigarshi ya bud'e
mata.
Da mamaki ya kalleta tana tunanin mafita, hak'ik'a Raj shine namiji na farko da
take jinshi a ranta, ganin bata da wani dalili na kin amincewa yasa tayi murmushi
ta mik'a masa hannunta tace "eh, na amince."
Cikin farin ciki ya fito da zoben jiki na rawa ya fara k'ok'arin saka mata,
"Khairat!"
Kira da Mamieta mata yasa suka kalleta a matuk'ar razane, tsaye suka mik'e suna ci
gaba da kallonta, d'orawa Mamie tayi da "ashe baki da hankali Khairat, ke yanzu
amince masa za kiyi ki aureshi kike nufi kome? kinsan hukuncin kuskuren da kike
shirin aikatawa kuwa?"
Maida kallonta tayi ga Raj da bai fahimci komai ba ta fara masa magana a harshen
india duk da yanzu indiancin nata yayi rauni sosai amma haka ta dage tace masa,
"Kaga Raj, kai yaron kirki ne, amma ka sani alak'arka da Khairat ba mai dorewa bace
domin kuwa ita musulma ce kai kuma ba musulmi ba, addininmu kuma ya haramtawa mace
musulma auren namiji da ba musulmi ba, dan Allah ina so ka fita a harkarta ka manta
da ita a rayuwarka, kaje ka samu mace yar uwarka ka aura, dan Khairat ma an fitar
mata da miji fad'a maka ne ba tayi ba."
Duk da ta fad'i hakane danya rabu da ita, amma dai bata ji dad'in abinda ta fad'a
ba saboda ba gaskiya bane, had'e hannayenta tayi tace "na rok'eka da ka tafi, ka
tafi dan Allah karka sake dawowa, dan Allah."
Tunda Mamie ta fara magana ya zama kamar gunki, jin ta gama fad'an abinda take son
fad'a yasa ya juya ya kalli Khairat, gefen fuskarta ya shafa yayi murmushi wanda
yasa hawayenshi suka fito, da qyar ya iya furta mata "zanyi kewarki Khairat, naso
na sameki, amma dole na barki, ba zanso ki sab'a umarnin addinninki ba a kaina,
kibi zab'in iyayenki."
Yana fad'a yayi hanyar fita, da sauri Khairat tabi bayanshi, fizgowar da Mamie ta
mata tasa ta fad'a saman kujera, a hassale ta tashi cikin harshen zarma
(zabarmanci,😁inji k'anwata zamarmanci) ta fara magana,
"Wai meye haka, me yake damunki ne, kinsan me kika aikata kuwa? aurena fa ya nema a
gabanku, akan me zaki masa haka?"
"Khairat, kin manta ke musulma ce, bai halatta gareki ba auren wanda ba musulmi
ba."
"Mamie saime, nifa zan zauna dashi bake ba, me yasa zaki min haka?"
_WAI'IYAZU BILLAH_😭
A fusace ta shige d'aki ta barsu, Mamie kuma fad'awa tayi saman kujera ta fashe da
kuka sosai har saida Mammie ta taso ta zauna kusanta ta dafata tace,
"Na'ima kiyi hak'uri, kici gaba da yiwa Khairat addu'a, insha Allah zata canja."
"Yaushe, Mama sai yaushe Khairat zata san mu iyayen tane, Mama munyi kuskure da
bamu d'ora Khairat a tafarkin ilimin addini ba, yafi kowane ilimi a rayuwa, na
tabbata da tayi karatu da zata san girman hukuncin iyaye sannan zata san girman
zunubin da take shirin aikatawa."
"A gaskiya Mama ba zan jure ba, aure kawai nake so Khairat tayi Mama, akwai matsala
zamanta anan dan haka gobe zamu koma wajen mahaifinta, na gaji da ganinta a gabana
Mama."
Tana gama fad'a itama ta tashi ta nufi d'akinta, kwance tayi tana tunanin rayuwa da
kuskurensu da kuma kuskuren da 'yarta ke cikin aikatawa, Khairat ma na d'akinta
tayi kiran wayar Raj harta gaji, ganin ta aika sak'o ba amsa yasa kawai ranta ya
b'ace ta fita harkarshi shima, abin sauraronta tasa a kunne tasa sanyayyen waka
domin d'ebe mata kewa.
*Tunda gari ya waye* Mamie taje ta ciro musu ticket kuma tayi sa'ar samun jirgin da
zai tashi da yamma, tana zuwa ta shirya kayanta dana Khairat dake bacci a d'akinta,
tana gamawa ganin lokaci ya fara tafiya yasa Mamie tashin Khairat.
Da mik'a ta farka tare da hamma, ganin Mamie tsaye yasa ta gyara zamanta tana
kallonta, "ki tashi ki shirya zamu tafi."
Dariya tayi tace "kije kawai idan kinyi kewar mijinki ne, ni nafi jin dad'in zamana
anan tare da kakata."
Gabanta Mamieta tare tace "Khairat tare zamu tafi dake, kiyi sauri ki shirya ki
fito ki sameni."
"Bansan me yasa kike so ki bawa kanki wahala ba, na fad'a miki ba zanje ba."
Da sauri Mamie ta fita daga d'akin ta koma falo ta bud'a jakar kayan Khairat d'in
ta d'auko wata doguwar rigar atamfa ta dawo d'akin da zafinta, tana zuwa zaune ta
samu Khairat akan kujerar dake gaban madubi tana kallon kanta, da k'arfi Mamie ta
kamo hannunta ta tsayar da ita gabanta ta cire mata qaramar rigar dake jikinta,
ganin tana kare qirjinta yasa Mamie tayi tsaki taci gaba da abinda take, saida ta
barta da silip kad'ai sannan ta rataya mata wannan rigar, wani irin d'auri ne Mamie
ta mata mai ban dariya sannan ta d'ora mata gyale a kafad'a dan tasan haka tafi so.
Hannunta ta fizga zasu fita daga d'akin Khairat ta tirje tace "wai Mamie miye haka,
nifa ba yarinya bace?"
Mammie na zaune taga sun fito kamar ankorosu, tsaye ta mike tace "ku kuma lafiya,
miye haka kike janta kamar yarinya?"
Jakunkunansu Mamie ta d'auka zasu fita Mammie tace "saikin dawo kuma, ina kuma
yaushe, ki zo kiyi me?"
Saida Mamieta bud'e k'ofar fita tace "idan na dawo za muyi magana, sai kinzo bikin
gimbiyarki."
Dariya Mammie tayi lokacin da taji Khairat tace "biki kuma, aure zaki min?"
Haka suka fita suka shiga taxi d'in dake jiransu a k'ofar gidan, Mamie bata saki
hannunta Khairat ba har saida suka shiga jirgi sannan.
*Dare ya fara tafiya* suka shigo garin, suna cikin taxi Khairat na kallon gefen
titi kwatsam ta hango Papanta zai shiga wani super market tare da wata wayayyar
mata sun shiga ciki, da sauri Khairat ta daddab'a kafad'ar driven taxi tace ya
tsaya, tsayawa yayi Mamie kuma tambayarta ta fara yi ko lafiya, fita tayi daga
motar da sauri ta fita ta rufe motar ta lek'o kai tace wa Mamie "kije gida, zanje
na taho miki da mijin naki."
Da gudu ta tsallaka d'aya titin, zata tsallaka na biyu wani mai mota da bata kula
dashi ba ya danna mata wata irin oder da saida ta zabura, cak ta tsaya tana kallon
motar, ganin mai motar ya tsaya yasa ta kwada tsaki zata wuce kawai taji yace "yan
mata lafiya, da matsala ne?"
Hararanshi tayi tace " dallah gafara can, wai kai mai mota sai iya oder tsiya,
hamago yanzu haka ma motar aro ce."
Umar Faruk ne a d'aya b'angaren data tsallako zai wuce yaga kamar idonshi na mishi
gizo, amma daga ganin kayan jikinta da yanda takewa mutumin nan magana yasa yasan
Khairat ce da kanta ba mai kama da ita ba, tsallakowa yayi ya tsaya daga gefe yana
kallonsu kamar wasu mutanen da suma har sun fara kallonsu, mai motar nan ne yace
"da alama baki da tarbiya, amma tunda kika had'u dani kin gama, wallahi daga yau ba
zaki sake wulak'anta wani ba."
A zabure ta matso kusanshi tace "me za kayi, dukana za kayi, ko kuma kaima za kayi
abinda kuka iya ne, to ka sani ba kaine farko ba?"
Zaiyi magana ta mashi wata irin kyara tace "tafi dallah ni bana da lokacinka."
Zata wuce ya tari gabanta ya zaro mata ido yace "ke har kin isa kice zaki ci
mutunci na, kinsan ko waye ni? ke yar gidan uban waye? da alama fa karuwanci kika
fito amma har kike so ki rainani, to yau sai naga uban daya d'aure miki gindi a
garin nan."
Waya ya fito da ita da alama kamar wata lamba yake nema, Umar Faruk ne yaga
al'amarin zaiyi tsamari dan haka ya matso tare da rik'e hannun mutumin yace "sannu
abokina, dan Allah kayi hak'uri ka rabu da ita, qwaqwalwarta ce ta samu matsala
tunda ta samu wani hatsari."
A hassale mutumin yace "ina so ne naga uban daya d'aure mata gindi a garin nan da
har take wa mutane rashin kunya, ka bari kawai na koya mata hankali."
"Ka koya min hankali kaga yanda zamu kare da kai, wallahi sai kayi nadaman zuwanka
duniya." cewar Khairat.
Gyara tsayuwa tayi ta rik'e k'ugu da hannu d'aya tana nunashi da d'aya hannun tace
"kasan ni kuma wacece, duk kasancewarka a cikin gwamnati nasan baka kai mahaifina
ba, kasan koni yar wacece? to ni yar Mani Bukar ce, kuma nasan kasanshi."
Jim ya d'anyi kafin ya basar yace "to saime dan kina d'iyar Mani Bukar, cemin za
kiyi ragowar sojoji, ke yanzu duk da abinda ya faru dake amma kike wannan bud'a
hanci, kamar wata wacce take cike da budurci."
Ranta ne ya b'ace duk da hawayen da suka taho mata, matsowa ta sakeyi daf dashi za
tayi magana amma sai Umar Faruk ya d'auka ko zata mareshi kamar yanda shima ta
masa, da sauri ya shiga tsakaninta dashi yana kallonta yace "waike me yake damunki
ne?"
Kallon sani tama Umar Faruk amma kuma tana ji ba zata iya tunashi ba, wani tsakin
ta kuma ja ta bisu da harara ta wuce abinta, Umar Faruk binta yayi da kallo kafin
yaga in da ta shiga shima ya juya ya hau mashin d'inshi yana tunanin maganganun da
mutumin ya fad'a mata.
Tana shiga ta fara waige waige ta in da za taga mahaifin nata, can ta hangoshi da
wata qosashiyar mace da gani kasan ba qarya babbar macece, a hankali ta fara takawa
harta tsaya bayansu basu sani ba, cikin taushin murya tace "sannu da jin dad'i."
Juyowa sukayi dukansu in da jikin Papa ya d'auki rawa, matar kam a wulak'ance ta
fara kallon Khairat, matsowa tayi kusan matar za tayi magana Papa ya gaggauta jan
hannunta yayi gefe da ita ya fara magana cikin rad'a.
"Papa wacece waccen matar, kenan har yanzu baka daina abinda kake ba?"
Hannunta ya rik'e yace "a'a shalele, wallahi na daina duk abinda nake, na riga dana
tuba da duk wani aikata zunubi, wannan matar ma ba wani abu bane tsakaninmu a
yanzu, kawai tana so ta b'ata min suna ne, shi yasa nake binta a hankali."
Kai ta girgiza tace "Papa, kamar ya kake binta a hankali? me take maka?"
"Khairat, wannan matar tace tana d'auke da cikina, kuma ta kaini asibiti an
tabbatar min da hakan, kinga dole na bi a sannu."
Juyawa tayi ta kalli matar sannan ta kalli Papa tace "wannan matar bata da wani
ciki, kuma yanzu zan tabbatar maka da haka."
Tana fad'a ta tunkari matar, tsaye tayi gabanta tana murmushi tace "Papana ya fad'a
min na kusa samun kani , rashin yarda da banyi ba yasa nace bara duba da kaina na
gani."
Tana fad'a ta kamo hannun matar ta fara kallon tafin hannunta wai ita tana so ta
gano ciki🤣, sakin hannunta tayi tana mata kallon tuhuma, k'ara matsawa tayi kusanta
ta bud'a ijiyarta tana kallo, matar kam duk tsoro ya kamata dan haka ta tsaya ma,
sakinta tayi ta kalli Papa tace "babu wani ciki a tare da ita, wahalar da kai kawai
take yi, da alama ma kamar ba zata iya d'aukar ciki ba."
"Inji uban wa? wallahi ko banda ciki yanzu ni nasan ina haihuwa."
Kallon Papa tayi tace "ka gani ko, ko makarantar koyan likitanci ban tab'a shiga
ba, amma ta bayar da kanta saboda tana tunanin ni ma'aikaciyar lafiya ce."
Soshe soshe matar ta fara na rashin gaskiya a hankali ta aje kwandon hannunta wanda
take zuba kayan data d'auka, tafiya ta fara yi su kuma suna kallonta, saida ta
d'anyi nisa ta juyo tace ma Khairat "kin kub'utar da ubanki."
Murmushi ta mata tace "sai dai ki kama uban wani amma ba nawa ba."
Tana fita Papa ya shafa kan Khairat yace "Allah miki albarka shalele, gashi kin
kub'utar da Papanki."
Ba tace komai ba har suka shiga mota yana tuki har suka isa gida, zaune suka samu
Mamie a falo ko hijab d'in jikinta bata cire ba haka ma kayansu na gabanta, zaune
Papa yayi yace "ya kike zaune haka?"
Kallon Khairat Mamie tayi tace "ki shiga ciki za muyi magana."
Wucewa kawai tayi ta shiga d'akinta, wanka ta fara tana tunanin fuskar data gani,
bud'e idonta tayi duk da ruwa na sauka a kanta tace "Umar Faruk ko? tabbas shine."
Tab'e baki tayi ta ci gaba da wankanta harta fito ta shirya cikin dogon wando fari
da pink d'in riga mai siraren hannuwa, turare kawai ta shafa ta d'auki abin
sauraronta ta makala a kunne ta fara tik'ar rawa abinta.
11/07/2019 à 22:43 - ~NANA KHADIJA~😍: 💑💑💑💑💑💑💑💑💑💑
*JIHADI*
_Umar faruk_
💑💑💑💑💑💑💑💑💑💑
_NA_
_SAMIRA HAROUNA_
_DEDICATED TO_
*MA FAMILLE*
_Bismmilahir-rahman-rahim_
1⃣3⃣
Papa ne ya gyara zama yace "ina jinki, dan da alama akwai magana sosai a bakinki."
"Eh, in har mukayi wasa wallahi Khairat zata iya auren wannan yaron Raj, wanda
hakan kuma bai dace ba, ni kuma bana so wani abu ya faru dan yaran yanzu zasu iya
yin komai akan abinda suke so, shi yasa nake so ka d'auki maganar da mahimmanci,
dan a gaskiya wata d'aya ya wuce banga Khairat a d'akin mijinta ba, tofa zan koma
in da na fito dan aurenka ne zai mutu."
Yanda tayi maganar ya bashi dariya, amma saiya had'eta yace "Mamien Khairat kenan,
yau da alama da rigima kika shigo garin nan, amma fa karki manta abinda kike so ayi
kamar za'a tilastata ne akan abinda bata so."
"Ba wani nan, ya zama dole ka kauda ganinka daga b'acin ranta, in ba haka ba dama
babu abinda za kayi."
"To naji, yanzu bara na kirata naji koda wanda take so."
Yana fad'a ya fara kwalla mata kira, amma ina ta toshe kunnuwa da abin sauraro koji
ba tayi, saida Papa ya tashi ya bubbuga k'ofar da qarfi sannan ta bud'e tana
kallonshi, "kizo." kawai yace ya koma falon.
Bayanshi ta biyo harta zauna kujera mai fuskantar tasu, ganin sun kafeta da ido
yasa ta cire abin kunnuwanta tana kallonsu, Papa ne ya kalli Mamie ya kalli Khairat
yace,
Da kai ta masa alama da me kenan, d'orawa yayi da "ina so naji ko akwai wanda kike
so a cikin zuciyarki? saimu tattauna dashi."
Wata shek'akk'ar dariya tayi tace "wai kun gaji dani ne da kuke son aurar dani
kome?"
Papa ne yace "a'a shalele, aishi aure shine darajar 'ya mace."
Mamie kuma tace "ai kin kai munzalin da za'a gaji dake d'in, shekara ashirin da
biyar ai ba shekara sha biyar bace."
Tsaye Khairat ta mik'e tace "kaji ko, to wallahi babu wanda zai min aure ban shirya
ba, kuma me yasa baki fad'a masa abinda ya faru a jiya ba, baikona fa kika
dakatar."
Wucewa taje tayi Papa ya kalleta yace "to baki fad'a min wanda kike so ba?"
Tsaye tayi ta kalli Papa tace "ni babu wanda nake so, har yanzu ban samu wanda ya
dace ba."
Tana fad'a ta juya Mamie ta bita da ido tana fad'in "kaji kuma, jiya fa hannu ta
mik'a wani zaisa mata zobe, amma yau tana cewa bata son kowa."
Papa ta kalla dake dariya tayi tsaye tace "shikenan tunda kun mayar dani
mahaukaciya."
Da sauri ya tashi ya rik'o jakar data d'auka yana fad'in "haba madam, kiyi hak'uri
ki bar min komai a hanuna, insha Allah za kiga auren Khairat da idonki harki saka
mata albarka."
Zuciyarta ce ta karye ta kalleshi tana zubar da hawaye tace "dan Allah kayi wani
abu dan ganin Khairat tayi aure, wallahi ina jin tsoron faruwar wani abun marar
kyau, ka sama mata miji na gari daya dace, wanda zai d'orata akan addininta sannan
ta gyara rayuwarta."
Hannunta Papa ya rik'e yana kallonta yace "zan iya baki zab'i?"
"A gaskiya Na'ima a yanzu babu abinda nake so kamar naga Khairat ta fara sabuwar
rayuwa mai kyau da tsabta, in hai muna so haka ta faru sai mun had'ata da jigo,
kinga kuma a duk cikin masarinta dana sani banga mai wannan nagartar ba, amma
bansan ko ke zaki iya samoshi koda a cikin danginki ne?"
Shiru Mamie tayi dan sosai ta gamsu da bayaninshi, amma kuma saita kasa tuna komai
dan haka tace "a'a, karfa muje wajen neman na gari kuma mu had'ata da bata gari,
kawai ina ganin tunda ga Mujahhid nan d'an uwanta ai sai a had'asu."
"Umm hakane, to ki kwantar da hankalinki insha Allah gobe da safe zanje na samu
yaya *Suleiman* sai muyi magana."
"Amma kana ganin Khairat ba zata bada matsala ba? danni yarinyar nan halinta sai
ita fa."
"Ki barta, wannan karan dai kam zan nuna mata ni mahaifine, zan shawo kanta da
yardar Allah."
Cike da jin dad'i Mamie tace "gaskiya naji dad'in haka, Allah ya k'ara mana
shiriya."
"Ameen, ban fad'a miki bane, amma harna fara zuwa islamiyya ta manya, daga sallah
magrib zuwa insha, kuma a yanzu babu abinda ke min dad'i kamar kasancewata a
majlisi na ganni gaban malam ina d'aukar karatu."
Cikin nuna tsatsan farin ciki Mamie ta fad'a jikinshi tace "hakan yayi kyau,
gaskiya ka kyauta, Allah ubangiji ya yafe kurakurenka na baya."
*Tunda safe* koda Papa ya gama kari ya fita bayan Mamie ta bishi da addu'ar fatan
nasara, Khairat kuma na d'aki na bacci lokacin tashinta baiyi ba.
Yaya Suleiman yayi matukar mamakin ganinshi a bazata haka, amma kuma farin cikin
ganin d'an uwan nashi wanda yake masa wuyar gani yasa bai nuna a fuska ba har saida
ya samar masa masaukin daya dace sannan, yana zuba masa lemon a cup yace "gaskiya
fa ka shammaceni sosai, irin wannan bazata haka kuma da sassafe."
Cikin dariya yace "gaskiya dama nasan zansha wannan maganar, wallahi kawai cewa
nayi zaifi nazo da safe dan wannan lokacin ne zan iya samunka gida."
"Babu komai yaya, ba wata matsala bace, nazo ne akan maganar 'yarka da kuma d'ana."
Kai ya girgiza yace "eh su, naga kamar lokaci yayi daya kamata ace mun had'asu
tunda ba yara bane."
Duk da yaya Suleiman ya d'anji wani abu amma dai kuma ba komai bane, cikin farin
ciki yace "ranar daka saka kazo ka fad'a min, ko kuma ka zo kawai ka sanar danine
dan nasa albarka a ciki?"
Dariya yayi yace "yaya kenan, ai kaine uban 'ya, dan haka kai muke jira kasa mana
rana."
Dariya shima yayi da k'arfi yace "haba dai wasa kake, ai duk diyanka ne dan haka
kasa ranar data maka kawai."
Papa ne yace "amma kafin musa ranar aida munji ta bakin Mujahhid d'in ko? dan kasan
yara fa, watakila bai shirya ba ko kuma yana da wani tsarin a ransa."
"Haba dai Mani, yaranmu ne fa mu muka haifesu basu suka haifemu ba, kawai ka fitar
mana da ranar, tunda yana da aikinyi kawai aurene ya gagara sai yawo a gari tare da
abokai, idan kuma kai kana jin tsoronsu ba zaka iya ba ni saina saka ranar."
Dad'i Papa yaji dan haka yace "to ba komai hakan ma ai yayi, kawai ka tsayar mana
da lokacin, sai muyi fatan Allah ya nuna mana ranar da alkairi."
"To tunda kace haka, yanzu mu barshi nan da wata d'aya, hakan ya maka?"
Wani sabon dad'i ne ya sake kashe Papa dan jin ansa daidai da lokacin da Mamie ta
diba , da sauri yace "hakan ai yayi yaya, Allah ya nuna mana ranar, Allah ya
tabbatar mana da alkairinsa."
"Ameen ameen, kawai kuje ku fara shirye shirye, muma tanan wajen zamu fara, duk da
ma dai abun duk gidane."
"Gaskiya ne yaya, kuma da wannan nake maka albishir d'in dauke muku duk wata
dawainiya, hatta gida da zasu zauna a ciki ni zan bayar insha Allah."
*A haka* suka tsayar da maganar auren Khairat da Mujahhid, tun a hanya Papa ya kira
Mamie ya fad'a mata, wai zo kaga farin ciki wajen Mamie marar misaltuwa, sai dai
Papa yace karta fad'ama Khairat sai zai fad'a mata yanda zata fahimta, suna gama
waya Mamie na zaune kawar Khairat ta shigo da sallama, amsawa Mamie tayi cikin
daure fuska saboda tasan k'awacen 'yarta da *Rashida* ba alkairi bane, cikin ladabi
ta zauna gefen Mamie tace.
Saboda jin tambayar wata iri yasa ta d'ansha jinin jikinta tace "eh Mamie daga gida
nake, dama nazo ganin Khairat ne, jiya take cemin ta dawo gari."
"Ina fata dai ba fita za kuyi ba ko?"
Kallonta Mamie tayi tace "Rashida, me zai ku nutsu kusan cewa annabi ya faku,
Rashida zaifi muku ku fara neman ilimin addini, ku koma islamiyya tunda ba'a tsufa
da neman ilimi, kuma bokon nan kunyishi keda k'awarki iya gwargwado, dan Allah ku
koma in da zaku san ubangijinku da yanda zaku bauta masa domin tsiranku duniya da
lahira."
A kunyace tace "insha Allah zamu koma Mamie, mun gode sosai."
Tashi tayi tace "bara na shiga ciki, nasan mutuniyar bacci take har yanzu."
"Umm." kawai Mamieta fad'a danta lura Rashida bata wani d'auki zancen da muhimmanci
ba, binta tayi da kallo ganin kayan dake jikinta itama dai kamar Khairat d'in sai
dai ita ta fita jiki hakan yasa matsatsin kayan ko kyau basa mata.
Kwance take akan makeken gadonta rufe ruf da zanin rufa pink saboda sanyin da
d'akin ya d'auka na ac, zaune tayi akan gadon ta daddab'ata tana fad'in "macho,
machota tashi gani na zo."
Dogon tsaki taja tana bud'e zanin daga kanta, saida ta tashi zaune sannan ma ta
kalleta, jingina tayi da kan gadon ta kalleta cikin muryar bacci tace "infa gaki
saime, me zaki min? hada wani zuwa ki tasheni."
Shiru tayi ba amsa dan tasan ta tab'o dala ba ganmo, ganin ba tayi magana ba yasa
ta sauka daga kan gadon ta nufi ban d'aki tana tattare gashinta daya bazu wanda tun
tana kwance aka since matashi.
Jin qarar ruwa yasa Rashida ta tabbatar wanka ta fara hakan kuma yasa ta gyara
zama, dan tasan awa d'aya ce zata fito da ita daga bayin, bugu da qari itama ba
zata iya barin gidan ba har saita samu abinda take so, dan in bata jira ba zata ma
kanta asarar kud'i kuma tana da tabbacin zata samu.
13/07/2019 à 14:47 - ~NANA KHADIJA~😍: 💑💑💑💑💑💑💑💑💑💑
*JIHADI*
_Umar faruk_
💑💑💑💑💑💑💑💑💑💑
_NA_
_SAMIRA HAROUNA_
_DEDICATED TO_
*MA FAMILLE*
_Bismmilahir-rahman-rahim_
1⃣4⃣
Fitowa tayi da d'aurin qirji iya cinyoyinta taja kujera ta zauna a kai tana kallon
kanta a madubi, mai take so ta shafa amma tana jin k'iwa, Rashida ce ta taso ta
tsaya bayanta tasa hannu tana shafar kanta tana murmushi, ta madubi ta kalleta tayi
qaramin tsaki, sun jima a haka babu wanda yayi magana, saida ta gaji da
miskilancinta sannan tace "me kike so?"
Kallonta tayi ta madubi amma ba tayi magana ba, sake cewa tayi "kiyi magana macho,
nasan wani abu kike so shi yasa kika zo."
Kai ta sosa ta fara magana "eh to, wallahi macho, gidane babu kudi gashi babu kayan
abinci, mun shiga wani hali saboda ba kya nan, yanzu ma banso na zo wallahi dole ce
tasa na zo."
Juyawa tayi ta nufi wajen kayan nata tana hararanta ta qasan ido, da hannu ta nuna
mata wanda zata d'auko mata, tana kawo mata tace "ki kira min Biba."
Nan ma a qufule ta juya ta fita, Khairat ma nayin hakanne da gangan dan abotarta da
Rashida bata da wata mamora, shi yasa wani lokacin take sata aikin ma da bai kamata
tasa ta ba idan ta lura akwai abinda take so a wajenta.
Ciki ciki tace "ki wanke hannuwanki a ban d'aki kizo ki shafa min mai."
Saida ta kalleta sannan ta shiga dan wanke hannuwan, haka ta fito ta fara shafa
mata man a jiki har suka ida Rashida na zaune, da taimakon Biba tasa kaya sannan ta
zauna gaban madubi ta murza powder kad'ai sannan tasa Rashida ta d'aura mata d'an
kwali, masha Allah tsaf ta fito cikin riga da siket d'in atamfa wacce tasha d'inki
tsadadden.
Saida ta gama kallon kanta a madubi sannan ta juya ta bud'a wani coffre ta d'auko
poshet (post) ta tsaya gaban Rashida, budawa tayi ta d'auko kudi yan jikka goma
goma sababbi guda biyar ta mika mata, tana sa hannu ta karba Khairat ta juya zata
fita Rashida tayi saurin rumgumota ta baya tana fad'in,
Murmushi kawai tayi ta janye kanta daga jikinta ta fice, binta tayi a baya haka ta
sauka daga kan matakala kamar wata sarauniya, kai tsaye wajen cin abinci ta nufa ta
zauna saman kujera, Rabi ce tayi saurin zuwa ta fara zuba mata farfesun kayan cikin
rago da kuma soyayyar kaza ga kuma doya da aka mirginata cikin k'wai, fresh milk ta
d'auko mata ta zuba mata sannan ta fara ci, Rashida kam an samu kud'i ko ta abincin
bata bita, sallama tama Mamie sannan ta kalli Khairat tace "macho na tafi, sai mun
had'u."
Ba wani sosai taci ba, dan Khairat a rayuwa bata san k'iba, dan d'an kumarin dake
gareta ma yanzu jinshi take a wani babbar matsala, dan haka take kula da jikinta
sosai amma bata son motsa jiki saboda ragwantaka, tana kammalawa ta komo falo ta
zauna kusan Mamie, hankalinta na a wayarta Mamie kuma na kallo tana d'an satar
kallonta wani lokacin tana murmushi.
*****************
*Umar Faruk* kuma tun jiya daya ga Khairat ya kwana cikin tunanin halin daya ganta,
sam baiyi tunanin haka daga gareta ba, ya d'auka zata canza ko dan abinda ya faru
da ita amma sai yaga akasin haka, ta wani b'angaren kuma haushin abinda wannan
mutumin ya fad'a yake ji, da haka har safiya tayi ba tare da yayi wani baccin kirki
ba, duk lokacin daya farka Khairat ce zata ziyarci tunaninshi da ganinshi.
Haka kawai yaji yana burin ya sameta a wajen aiki, shiri yayi sosai cikin qananan
kayanshi bak'ar riga mai dogayen hannu da wando kalar qasa, yana shiga ma'aikatar
ya fara duba wajen ajiye motoci ko zaiga motarta amma babu, duk da haka bai sare ba
bayan ya shiga ciki ya aje jakarshi cikin dubara da sand'a ya nufi bureaunta,
lekawa yayi ta madubi amma babu kowa kamar dai yanda yake, wata ajiyar zuciya ya
sauke cikin sanyin jiki ya dawo mazauninshi, yana zaunawa ya fara tambayar kanshi
wai me yasa ya damu da son ganinta ne, tsaki yayi kawai ya fara aikin gabanshi.
****************
Khairat ce ta 'kwalla kiran Biba, tana zuwa tace ta d'auko mata jaka a d'aki da
gyale, cikin 'yan mintuna ta dawo da jaka da takalma da gyale duk kalar atamfar
dake jikinta, tana sakawa tayi hanyar fita Mamie tayi saurin cewa "sai ina kuma
Khairat?"
"Mamie zan lek'a bureau ne naga meke faruwa acan, saina dawo."
Dawowa tayi ta tsaya gabanta, tashi tayi tsaye ta shafi fuskarta tace "Allah ya
miki albarka Khairat, Allah ya baki yaya na gari, Allah ya kiyaye hanya kinji ko."
Cikin jin dad'i ta rumgume Mamie tace "yau dai da wayona naji addu'ar sa albarka ta
fito daga bakinki, na gode Mamiena, saina dawo ba zan jima ba."
Sumbatar goshin Mamie tayi ta fita cike da farin ciki yau Mamie ta mata addu'a, ita
kanta Mamie sai taji ba dad'i dan in zata iya tunawa gaskiya ta jima rabon data
mata addu'a irin haka.
*Kuskure da iyaye mukeyi sakacin yiwa yara addu'a, wasu na ganin laifin Khairat
data zama fitsararriya, amma bansa Khairat ta zama haka ba har saida na samu
dalili, Mamie ta kasance mai zuciya da yanke hukunci cikin hushi, hakan ya janyo
tun Khairat na qarama ta daina daina janta a jiki bare tasata a hanyar data dace,
hakan kuma bai dace ba ko kad'an, yaro ko yana qarami kake masa addu'a zan sai kana
masa, uwa uba kuma addu'ar na bibiyarsa ta alkairi ko akasin haka, mu kula iyaye
Allah ya bamu ikon tarbiyantar da yaranmu.*
Da takonta na qasaita ta shigo wajen, kallon Abba yayi kowa da komai take da kyau,
Umar Faruk daya duqufa da aiki, gabanshi ne yaji ya tsinke ya fad'i hakan ya
tilasta masa juyowa da k'arfi, kasa dauke idonshi yayi daga kanta, duk da ba
murmushi a tare dashi amma kuma fuskarshi a sake take, ganin yanda kowa ke kallonta
kamar da wani abu a jikinta yasa ta tsaya waje d'aya, sake kallon kowa tayi dake
wajen ta girgiza kai tayi murmushin takaici.
A hankali tace "kowa ni yake kallo saboda yanzu kuna ganin kamar na zama daban a
cikin mutane, kowa so yake yaga ina cikin damuwa, ni kuma abinda nayi alk'awarin ba
zan shiga ba kenan har abada."
Tana fad'a ta juya a fusace ta nufi in da ta aje motarta, Umar kuma buga tebur d'in
dake gabanshi yayi tare da fad'in "kai."
Da gudu ya tashi yabi bayanta mutanen kuma suka bishi da kallo, Ishaq abokinshi ne
yayi murmushi ya kalli na kusa dashi yace "dama ace duk soyayyar da aka fara da
qiyayya to tafi zafi."
"Kai ai basai an fad'a ba kasan akwai soyayya wannan wajen, watakila basu fahimci
hakan ba."
"Lallai ko abokinka ya d'auko dala ba gammo, to ina had'in kifi da kaska? ai wannan
qarmanje ne."
Cewar mutumin "ai ko ban sani ba aikinta ya nuna abokinka baya da wani girma da
qima a idonta, tunda nidai banga ko kallonshi tayi ba, zaifi ka bashi shawara ma
tun wuri ya fitar da abinda ke ranshi, dan wahalar banza zaisha."
"Ai kuwa in dai har gaskene, to wallahi zaka sha mamaki, dan kana nan zaune za'a
gayyaceka daurin aure."
"Tare dani dashi da kai za'a gayyata." cewar mutumin yana kama aikin gabanshi.
Tana daf da shiga mota Umar Faruk ya fito da gudu, juyawa tayi ta kalleshi ta tsaya
saida ya karaso, tsaye yayi ya kuma rasa me zaiyi sai yanzu yake jin haushin abinda
yayi, juyawa yayi zai koma ciki tace "kazo ka tambayeni me nake ji ne?"
Dogon tsaki taja ta bud'e motarta ta shiga taja tayi gaba, shima ciki ya koma yana
tsananin jin takaicin abinda ya aikata, shin me yasa yayi haka???
*****************
Tun yamma da Mujaheed ya dawo gida mahaifiyarshi ta fad'a mashi halin da ake ciki
tare da zigashi akan karya yarda, bud'ar bakinshi cewa yayi "Mama bama sai kince
ba, wato ni zasu rainawa wayo ko? kafin ta zama ragowa ina biyarta amma tana
wulak'anta ni, su kuma sun biye mata aka su ba zasu bata wanda bata so ba, yanzu
kenan sun saduda ne shine za'a kawo min ita ni d'an iska ko, to wallahi basu isa
ba."
Tunda mahaifinshi ya dawo da dare suka sameshi da mahaifiyar tashi akan basu son
wannan maganar auren, Baban baiji dad'i ba haka sauran matanshi guda biyu sun bada
tasu shawara akan Mujaheed yayi hak'uri tunda yer uwa ce, amma mahaifiyarshi tace
su rufe musu baki dan ba yayansu bane, an jima ana tattaunawa har saida Mujaheed
yace in dai har aka takurashi wallahi zai shiga duniya, sanin halinshi da Baban
yayi wanda dama ya ake dashi yanzu ma bare ya sake shiga wata duniyar, hakan yasa
yace an fasa sai dai yana jin nauyin yanda zai fukanci d'an uwanshi.
Ganin baida wata mafita yasa ya kira Papa a waya ya fad'a masa yanda sukayi cikin
raunin murya, a zahiri Papa ya nuna babu komai amma da suka gama waya bak'in
cikinshi ya bayyana, bayan ya shigo gida shima bai iya fad'awa Mamie ba saboda
gudun matsala, amma kuma ya kwanta da wani sabon shirin a ranshi, safiya kawai yake
jira ta waye ya gudanar dashi.
_To Papa muji alkairi._
Kamar yanda Khairat tayi niyyar ba zata bari damuwa ta samu muhalli a zuciyarta ba,
tunda ta dawo take d'akinta bayan tasha bacci ta tashi da yamma, da dare kuma tana
d'aki tana tik'ar rawa abinta duk dan karta damu.
Ko kari Papa baiyi ba ya fita Mamie bata sani ba Khairat kuma na bacci, hanya Papa
ya d'auka shi da drivenshi cikin awa d'aya suka isa fadar shugaban....fan's ku
k'arasa min _(bana son tabo mukamin kowa, amma ku kuyanke hukunci ku d'auka babban
Muzaffar shine qarshe a mulki baban Khairat kuma na binshi baya)._
Tarba ya samu sosai a babban falon bak'i na palace d'in shugaban , hamshakin
shugaban mai dattako cikin fara'a ya kalli Papa yace "sai kuma gaka da safiyar nan,
kamar da wata matsala ko?"
"Alhamdulillah."
Shiru ne ya d'an biyo baya kafin shugaban yace "ya yarinyata da jiki, taji sauk'i
ko? dan har yanzu bamu sake komawa ba."
Dariya yayi yace "shugaba ai dan mun kwana biyu bamu had'u ba, amma Khairat taji
sauk'i sosai."
"Ah to alhamdulillah."
"Muzaffar ai yau kwananshi uku baya nan, na turashi saudi arabia dan halartar wani
taro na qarawa juna sani akan yanda za'a inganta rayuwar matasa."
"Da kyau shugaba, in da kake birgeni kenan, kowane abu kana azashi a muhallinshi,
Allah ya taimaka ya dawo dashi lafiya."
Wani shirun ne ya sake biyo baya kafin shugaba yace "'yata dai tak'i yarona, da
yanzu mun gama da maganarsu."
Cikin dariya Papa yace "ah haba shugaba, taya zata k'i d'anmu, yanzu haka ma
maganar aurensu ya kawoni, dan nayi tunani zamanta a gida haka yayi yawa sosai,
kuma tunda suna fahimtar junansu naga zaifi kawai mu had'asu."
Gyara zama yayi a cikin lunstumemiyar kujerar yana fara'a yace "haba dai, kai amma
naji dad'i sosai da maganar nan."
D'orawa yayi da "Muzaffar zaiyi farin ciki da wannan magana, gaskiya naji dad'i
sosai, danni kaina burina bai wuce naga yayi aure ba."
"Hakane shugaba, dan haka yanzu wuk'a da nama na hannunku, kasa lokacin da kaga ya
maka."
"Kuma dai? dad'in ai saiya mana yawa."
"A'a wallahi baya komai, idan kunsa ranar ku fad'a mana, iyakarmu addu'a kawai."
"Umm, to yanda mai zai hana asa nan da wata d'aya, tunda kaga akwai wani babban
taro da za ayi 15 ga watan da za'a shiga, kuma dole mu dasu yaran duka zamu
halarceshi, kaga zaifi dad'i suje a matsayin ma'aurata, koya ka gani?"
A haka dai Papa ya baro gidan cikin farin ciki, take kuma shugaba ya dannawa
Muzaffar kira, yana d'auka daga d'aya b'angaren yace "Papana ya kake?"
"Nasan baka min albishir marar dad'i, goro fari tas Papana."
"Yanzun nan Mani ya fita daga nan, kuma bai bar nan ba saida muka tsayar da aurenku
kai da Khairat."
"Wow, da gaske Papa? kai amma naji dad'i sosai, Papa yaushe kuka saka?"
"Sosai ma Papa, gashi dai Allah yayi zaifita zama mijin Khairat, to dan Allah Papa
kuyi duk abinda ya dace kafin na dawo."
"Karka damu yarona, yanzu zan shiga ciki muyi magana da mamarka akan yanda za'a
tafiyar da komai."
"yawwa Papana, a fara shirya komai kafin nazo, idan na zo zamu ci gaba da shiri,
dan dole bikina da Khairat ya amsa duk gari a samu labarinshi, saboda kaga fa
babbar yarinya ce nima kuma haka."
A haka suma sukayi sallama, haka ma a ciki ya fad'a ma mahaifiyar Muzaffar, sosai
itama tayi farin ciki da alamarin dan a rayuwarta tana son bariki da tsare kai,
hakan yasa Khairat ke birgeta sosai, dan lokuta da dama suna had'uwa a wasu
tarurruka ta wakilci mahaifinta ita kuma ta wakilci shugaba, hakan yasa take
sha'awar aurenta da d'anta.
Lokacin da Papa ya dawo Mamie ta gama karinta tana tunanin in da ya tafi bata sani
ba, ganinshi yasa ta mike tana tambayar lafiya, saida ya zauna yace ta zauna, zaune
tayi tana kallonshi kafin yace "daga gidan shugaba nake."
Suna gama maganar Khairat ta fito da riga da wando farare tas ta zauna, "ina
kwananku?"
Kallon juna sukayi dan haka bata tab'a faruwa ba, amsawa sukayi Papa ya dora da
"shalele kin tashi lafiya?"
Da sauri Biba ta fito ta zube gabanta, cikin yauki tace "ki kawo min abinci na."
Anan ta kawo mata ta fara cin abincin Papa kuma fita yayi gabatar da harkokinshi,
Mamie ce tace "ki kammala cin abincin ki shirya zamu tafi dake gidan *Safiya*."
Kallonta tayi tace "Mamie nifa kinsan bana son zuwa gidan nan, wannan d'an iskan
yaron da yake min maganar banza wai yana sona, bana son ganinshi ma."
Dariya Mamie tayi tace "ki shirya muje kedai, kinsan na jima banje ba, kuma yanzu
nasan ba zai miki maganar soyayya ba."
Kallon Mamie tayi danta fahimci me take nufi da abinda ta fad'a, maida kallonta
tayi ga abincinta tana tunanin yanda za tayi rayuwa a cikin mutanen da take kewaye
dasu ba tare data iya tuna abinda ya faru da ita ba.
Da qyar Mamie ta lallabata ta shiga danta shirya, saida ta d'auki awa d'aya kafin
ta shirya ta fito Mamie harta gaji da jira, a motar Mamie suka tafi tare da
driventa suka nufi unguwar *yantala* (gidan Safiya diyace ga magajiyar mamar
Na'ima, ma'ana cousine d'inta.), da sallama Mamie ta shiga gidan sab'anin Khairat
dake binta kawai, da farin ciki matar ta taresu sai dai Khairat fuskarta a had'e
take saboda hayaniyar gidan tayi yawa, saboda matan gidan hud'une yara kuma manya
da qanana barkatai, haka suka shiga ciki suka zauna, matar ce ta fara gaishe da
Khairat kafin tace "ina wuni."
Wata matashiyar budurwa ce ta shigo ta kawo musu ruwa, Mamie ce tasha ita kuma ko
kallo, dama Mamie ta mik'a mata girgiza kai tayi tana b'ata fuska, ganin Mamie na
janyo hirar da zata sa su jima yasa ta mik'e tsaye tace "Mamie ki sameni a mota, ba
zan iya zama cikin zafin nan ba."
Kallonta kawai tayi ta fice a soron gidan suka had'u da *Aqilu*, wucewa taje yi ya
tare gabanta yana fad'in "ya dai, yau kece a gidan?"
"Kar kace zaka min maganar banzan daka saba, dan bana da lokaci."
Wata irin dariya yayi yace "wai maganar so kike nufi, ai wannan tsohon yayi ne,
abinda nake son fad'a miki yanzu kuma shine, dan in gaya miki cewa na janye son da
nake miki ne, dan ba zan...."
Bai k'arasa ba tace "shashasha."
_NA_
_SAMIRA HAROUNA_
_DEDICATED TO_
*MA FAMILLE*
1⃣5⃣
Ba jimawa Mamie ta fito ta sameta a mota, suna fara tafiya ta kalli Mamie tace "kin
fad'i gaskiya, Aqilu yace baya sona yanzu."
Murmushi tayi kawai ta fito da abin sauraronta ta manne kunnuwanta suka ci gaba da
tafiya, suna isa gida ta nufi d'akinta bata kuma sake fitowa ba sai da aka fara
kiran sallah magrib, har tayi zaune Mamie tace "ki tashi kiyi alwala kizo muyi
sallah."
Cike da nuna rashin jin dad'i tayi shiru, a tsawace Mamie tace "dake nake magana
kina jina kinyi shiru."
Ganin ta tashi ta wuce cikin kasala Mamie ta dora da fad'in "kuma wallahi ya zama
na qarshe da zan miki magana akan sallah, inba rainin wayo ba kamarki shekara
ashirin da biyar amma ba zaki iya gaishe da unangijiki ba sai kinga dama."
*Wallahi a zamanin nan da muke ciki, matasanmu musamman yan mata bamu cika tsayar
da sallah ba, musamman idan sunyi kwalliya a fuskarsu ba'a son asa ruwa a wanke, ya
kamata muji tsoron Allah mu gane saida sallah ne muke iya banbanta kanmu da
kafirai, Allah ka bamu ikon kyautata ibadunka, Allah kasa mu zama masu tsayar da
sallah domin samun sassauk'an hisabi, Allah kasa mu tsayar da sallah domin ta zama
abokiyar zamanmu a qabari dan haskaka makwancinmu.*
*Da sallah ne muke cika cikakki musulmi, idan sallanmu tayi kyaune ake kyautata
mana zaton sauk'in hisabi, sallah itace take tayamu zama a qabarinmu kafin lokacin
da za'a tashi qiyama, sannan mai tsayar da sallah ko a cikin al'uma zaka ga
fuskarshi na annuri, sannan hadisi ne ingantance cewar wuta bata tab'a duk wata
gab'a da take samun ruwan alwala, wannan 'yar qaramar tunatarwa ce badan na fiku
sani ba.*👏
Babu wata matsala a game da alwalarta sai dai a game da sallah kam akwai yar
mishkila, saboda cikin minti biyu ta gama sallah ta fito falo, hakan yayi daidai da
fitowar Papa zashi makaranta, ganin littafi a hannunshi yasa tace "Papa sai ina
kuma?"
Wata dariya tayi ta nufi fridge tana fad'in "wasa kake Papa, haka dani na shiga
makaranta."
Papa ma wucewa yayi dan lokaci nayi yana fad'in "ba'a girma da neman ilimi, tunda
ki kaga na fara zuwa to kema ki shirya dan kin kusa."
Yau ma dai kamar kusan kullum ita kad'ai taci abinci bayan iyayenta sunci, tana
kammalawa ta koma d'aki tana chat tana sauraron waqoqi har dare yayi sosai tana
bacci cikin kwanciyar hankali.
Mamie ce ta shigo d'akin ta zauna kusa da ita, ta jima tana kallonta tana murmushi
kafin ta tofa mata addu'a ta sumbaci goshinta, zani taja mata ta rufeta ta tashi
saida ta kashe mata wutar d'akin kafin ta fita, tun fil'azal Khairat bata bacci da
duhu a d'aki hakan yasa ma bata kashewa.
Kusan abune daya zamar mata jiki mafarkin abinda ya faru da ita, kamar a zahiri
haka ta dinga tuna lokacin da take kokawa da Musa har lokacin da yayi nasarar kutsa
kanshi a tsakiyar matancinta, razananniyar qarar da tayi a mafarkinta itace ta
bayyana har a zahirin baccinta.
"Ahhhhhhhhh, Mamiena, Papa wayyo Allah, Papa, Papa zasu kasheni, Papa gasunan fa,
zasu sake min fyad'e, dan Allah kuzo ku taimakeni, Mamie, wai baki jina ne? wallahi
gasu nan."
Wannan duhun d'akin shi ya qara firgitata haka ta dinga kiran su Mamie da Papa,
kasancewar d'akinsu a qasa yake hakan yasa basu ji da wuri ba, Mamie ce ta fara ji
ta tayar da Papa, a sukwane suka shigo d'akin nata Mamie ce ta kunna wuta Papa kuma
ya tunkareta, tana ganin haske ya mamaye d'akin tayi saurin rarrafowa ta nufo Papa,
fad'uwa tayi wajen tahowa Papa ne yayi saurin tashinta ya rumgumata a jikinshi yana
shafa kanta yana fad'in "shiiiiii, shalele, gani nan Papanki ne kinji, ya isa
haka."
A haka suka taka ya qarasa da ita bakin gado suka zauna yana ci gaba da fad'in "ya
isa kinji gimbiya, ba kowa anan, d'ago idonki ki gani, nine Papanki da kuma
Mamienki, ki nutsu kinji."
A hankali kuwa ta daga ta kalli Papa sannan ta kalli Mamie dake gefenshi, da sauri
ta kamo hannun Mamie ta sake fashewa da kuka tace "dan Allah Mamie ki kwanta anan,
wallahi zasu iya dawowa su sake min fy......" Mamie tayi saurin rufe mata baki.
A haka suka ci gaba da rarrashinta har Mamie ta d'ora kanta a qafafunta bacci ya
d'auketa, a zaune Mamie ta kwana tana shafar kanta tare da mata addu'a.
Suna a haka Papa ya shigo ya tashesu suyi sallah asuba, tare da Mamie sukayi sallah
sannan Mamie ta sauka ta shiga madafa, Papa na zauna yana hutawa a lambu tare da
linttafinshi yana bitar karatu wayarshi tayi qara, ganin mai kira yasa ya rufe
littafin ya d'auka, bayan sun gama a sukwane ya shigo cikin falo yana kiran sunan
Mamie.
Da sauri ta fito tana fad'in "gani Alhaji, lafiya dai irin wannan kira haka?"
"Yanzu mukayi waya da shugaba, kuma tabbatar min suna so ayi komai a gama, dan haka
goben nan zasu kawo lefen Khairat."
Cike da tsantsar farin ciki tace "kai, Alhamdulillah, amma naji dad'in wannan
albishir, Allah ya nuna mana goben yasa alkairi."
"Ameen, yanzu kije ki lissafa mana duk abinda za'a buqata dan tarbar bak'i, tunda
kinsan fa harkar babba ce."
"Ah sosai kam, kar kaji komai, ba buk'atar kashe kud'inka, ni zan d'auki wannan
nauyin insha Allah."
Cikin dariya tace "a'a ba duka ba, dole ai kasan zamu shiga cikin aljihunka idan
biki ya matso."
💃💃💃💃💃💃💃
Misalin 11:35 Khairat ta tashi ta fito falo, Mamie na madafa tare da masu kama mata
aiki, cikin takon mai nuna magagin bacci ta shiga madafa, ma'aikatan ne suka
gaisheta amma babu wanda tako kalla bare ta amsa, wajen kayan lambu ta nufa ta
d'auki kokomba ta wanke ta fara kaiwa bakinta, sai lokacin ta kalli Mamie tace "ina
kwana Mamie."
"Um." ta fad'a tare da fito ta koma d'akinta tayi wanka ta shirya cikin riga da
siket na kanti kanta ba d'an kwali ta fito falo ta zauna, 12:30 su Mamie suka
kammala abincin rana, jerawa sukayi a dinning sannan Mamie ta shiga wanka, 13:00
Papa ya shigo gidan tare da sabin masu tsaron lafiyarsa su biyu, suma da qyar ya
yarda aka had'ashi dasu.
Hannunta ya kamo yana fad'in "muje ki zuba min naci gimbiya, yunwa nake ji sosai."
Itama cewa tayi "amma ai ban iya zubawa ba, bari na kira Biba ko Saude su zuba
maka."
Kallonshi tayi ta kalli kwanukan abincin ajiye wayarta tayi a gefe zata d'auki
plate wayar Papa tayi qara, d'auka yayi yana fad'in "hello, manager har kun karaso
ne?"
Jim yayi na d'an lokaci kafin yace "to ku shigo kawai ina ciki nima yanzu na
shigo."
Aje wayar yayi ya kalli Khairat yace "wallahi wani hazik'in matashi ne aka samu a
masana'antarki, baifi wata biyar zuwa shida da fara aiki ba, amma harya fito da
sanfirin takalmin da suka karb'u a duniya, shine nace manager ya kawoshi nan mu
gaisa na kuma masa godiya, sannan zan shirya masa qarin girma a ma'aikatar."
Ko qala ba tace ba, kwanon farar maca ta bud'a wacce tasha kwalliya da waken
gwangwani, cokali ta d'auka ta fara k'walbatowa rabi na zubewa qasa rabi na shiga
plate d'in, da qyar ta zuba a plate d'in har Mamie ta fito ta samesu, kwanan miya
ta bud'e wacce tasha kaji daga-daga, (😁mutuniya ba) tana saka cokalin miyar ta
fallatso mata sai a ido, qara ta saki tare da sakin cokalin a miyar, sake
fallatsowa yayi sai kuwa a fuskarta da jikinta, zafin da taji yasa ta dinga tsala
ihu tana fad'in "na k'one , na k'one, zafi Mamie ki goge min."
Mamie da hankalinta ya koma kan manager da matashin saurayin nan, Umar Faruk daya
tsaya ya kasa gudawa yana kallon Khairat na tsalle tsalle duk jikinta na kadawa, da
qyar ya had'e yawu suka fara takawa suka zauna inda Papa ya nuna musu, sai lokacin
Khairat tayi shiru ta sauke idonta akan Umar Faruk.
Kallonshi take sosai shi kuma ya d'auke idonshi daga kanta, Mamie ce ta katseta da
fad'in "ki zuba musu abinci mana shalele."
Da sauri ta kalli Mamie, da ido ta mata alama ta zuba musu, turo baki tayi gaba
tace "nifa Mamie ban iya ba, kina gani abinda ya faru yanzu na k'ona kaina."
Wayarta ta d'auka ta juya zata bar wajen Papa yace "gimbiya baki zuba min ba."
Lokacin data juyo idonsu suka had'u dana Umar yana mamakin abinda ta fad'a wai bata
iya zuba abinci ba, to kenan ya zata dafashi??? ya tambayi kanshi.
Zagayawa tayi wajen da yake zaune ta mik'a masa hannunta tace "zo."
Da mamaki yake kallonta yana mamakin fitsararta, kallon Mamie da Papa tayi wanda
suma ita suke kallo tayi murmushi tace "kunyarku yake ji fa."
Tana fad'a ta ja hannunshi suka nufi d'akinta, tana shirin bud'a k'ofar d'akin ta
tsaya cak saboda ji da tayi ya qara matse hannunta, kasa juyowa tayi saboda yanda
taji tattausan hannunshi ga kuma gabanta daya fad'i, a hankali ta fara zame
hannunta daga nashi shi kuma baisan ya akayi ya kasa rik'e kanshi ba harya qara
matse hannunta, saida ta raba hannunta da nashi sannan ta ta bud'e d'akin ta shiga,
kallonshi tayi ganin yaki shigowa, alama ta masa da ido akan ya shigo, a hankali
yake takawa yana jin bugun zuciyarshi na k'ara tsananta, da sauri ya juya ya
kalleta saboda ganin ta rufe k'ofa.
Gabanshi ta tsaya tace "ranar na tambayeka amma baka bani amsa ba, amma daga baya
sai nayi tunani naga cewa, ai ko ban tambayeka nasan kai kana daga cikin mak'iyana,
kuma kayi farin ciki da abinda ya sameni, kuma nasan ko kai ka samu dama zaka iya
yin abinda wad'ancen sukayi."
"To ba komai, kuma ku sani ni Khairat ba zan nuna gazawa ba, ba kuma zan nuna bana
da daraja ba, kamar yanda ba zan saka damuwa a raina ba, dan haka duk mai bak'in
ciki sai dai ya mutu."
Wucewa tayi ban d'aki tana fad'in "zaka iya tafiya."
Shi kuma ya kasa komai gaba d'aya ji yake yayi sanyi ya rasa duk kuzarinshi, binta
yayi da kallo ya kasa fita, Khairat ce daga ciki ta jefo da gaba d'aya kayanta data
cire harda qananan ciki saboda bata tunanin yana nan har yanzu, yana ganin haka
yayi saurin juyawa zuciyarshi kamar zata fito daga qirjinshi, saurin fita yayi daga
d'akin hannunshi a kan saitin zuciyarshi a hankali yake takawa yana tambayar
kanshi.
Khairat na sakar ma kanta ruwa ta lumshe ido, da sauri ta bud'e idonta saboda ji da
tayi kamar hannun Umar Faruk a nata hannun, ajiyar zuciya ta sauke ta sake rufe ido
saboda yanda ruwa ke sauka a kanta, Umar Faruk dai ta sake gani yana mata wannan
kallon da fassararshi sai _my aunty Aishan Umma_, haka ta fito daga wanka wannan
tunanin ya kasa barin qwaqwalwarta harta d'auki riga da wando ta saka qanana sannan
ta sake fitowa.
Tare suka ci abinci dasu banda Umar Faruk da ruwa kad'ai yake d'an kurb'awa suma
sai Papa ya mishi magana, anan Papa ya masa godiya tare dasa albarka sannan yace
"kaci gada da k'wazonka, insha Allah za kayi nasara a duk inda ka samu kanka, Umar
Faruk..ko?"
Da mamaki Papa ya kalleshi yace "Ahmad Adam, kai d'an malam Ahmad ne?"
Mamie Papa ya kalla yace "Allah sarki, kinga fa yaron nan d'an malamin da nake
d'aukar karatu wajenshi ne, haba shi yasa ka zama mai hazak'a da basira."
Dariya Mamie tayi tace "yaron kirki ne kam, Allah ya maka albarka."
Kiran daya shigo wayar Khairat ne yasa ta tashi daga wajen, Mamie ce tace "baki ci
komai ba fa tun safe."
Mamie da Papa ne quka kalli juna suna murmushi, sabanin Umar Faruk da gabanshi ya
buga ranshi kuma ya b'ace, cup d'in ruwa ya d'auka ya kifa saida ya shanye sannan
ya mik'e yace "ni zan wuce, na gode."
Ficewa yana jin tsanar Muzaffar a zuciyarshi ba tare da sanin shi Muzaffar d'in ba,
kasa jiran manager yayi dan haka ya tari taxi ya mayar dashi ma'aikata, haka ya
isa ya zauna yana kallon tafin hannunshi da Khairat ta rik'e, wani hamshak'in
murmushi ya saki saboda tuna da yayi lokacin da take tsalle tana ihu, sake fashewa
yayi da dariya haka kawai ya rasa dalili amma farin ciki yake ji har k'ark'ashin
zuciyarshi, Ishaq daya lura da hakane ya tab'oshi ta gefe yana fad'in,
"Da alama fitar nan tayi kyau ko?"
B'ata fuska yayi yace "ban gane ba, kai baka san ina muka je bane?"
Dariya Ishaq yayi ya maida hankalinshi ga aikinshi yana fad'in "da alama ka fad'a
soyayya abokina."
Da k'arfi ya kalleshi yace "me? soyayya fa kace? to aini dama ba sabon shiga bane,
ko ka manta ina da Zuby?"
Saida Ishaq ya kalli k'wayar idonshi yace "watak'ila yanzu ne ka fad'a soyayyar
gaskiya kuma wacce ta dace, idan kuma ba haka to zai iya yiwuwa yanzu ne zuciyarka
ta kamu da so."
"Son wa?"
Sake kallonshi yayi dan baiyi tsammanin yaji abinda yace ba a fili, zunbur ya tashi
daga wajen ya fita filin ma'aikatar, maganar Ishaq ce kawai ke dawo masa a
qwaqwalwa ta cewa "son Khairat mana."
A zafafe ya furta "ina, hakan ba zai yiwuba, bata dace dani ba, zuciyata ba zata
tab'a min wannan rashin adalcin ba."
Daga yanda Muzaffar yake wa Khairat magana yasa ta fahimci akwai wani dake faruwa,
musamman da yace ya matsu gobe tayi a kawo kaya a tabbatar mishi ita tashi ce,
kashe wayar tayi ta dawo falon lokacin manager ma harya tafi, tsaye tayi gabansu
tana kallonsu tace "me yake faruwa? me Muzaffar yake fad'a?"
Papa ne yace "kinga shalele ki zauna kici abincinki , an jima za muyi magana."
Cikin d'aga murya tace "wane naci abinci bayan abinda wannan mahaukacin yake fad'a,
kawai ku fad'a min koma miye naji."
Mamie ce ta d'aga murya itama ta tashi tsaye tace "Khairat!!! mu kuke d'agawa
murya? kece kika haifemu ko mune muka haufeki? idan bamu fad'a miki ba me za kiyi?"
Kallon Mamie tayi fuska ba annuri tace "maganar aure yake, kuma nasan kinsan babu
wanda zai min aure ba tare da ina so ba, idan alk'awarina kuka mishi to ku janye
danni ba 'yar roba bace da za'a min haka."
Zata wuce Mamie ta fizgota da k'arfi za tayi magana Khairat ta fizge hannunta da
k'arfi tana fad'in "ki sake ni, karki sake tab'ani, ki fita a harkarta."
Duk da qoqarin b'oye hawayenta kasawa tayi saida kukan ya k'wace mata ta fara
magana cikin kuka "na sani kuma dake iyayena kuna ganin yanzu bana da wata kima da
daraja ta 'ya mace, inba haka ba babu ta yadda zaku fara min maganar aure ba tare
da sanina ba.:
Wucewa tayi ta barsu nan Papa kuma ya kalli Mamie cikin b'acin rai yace "....😁
15/07/2019 à 16:38 - ~NANA KHADIJA~😍: 💑💑💑💑💑💑💑💑💑💑
*JIHADI*
_Umar faruk_
💑💑💑💑💑💑💑💑💑💑
_NA_
_SAMIRA HAROUNA_
_DEDICATED TO_
*MA FAMILLE*
_Wallahi har qasan raina ina jin dad'in addu'arki sister Alawiyyah, gaskiya ke ta
dabance, samun fan's irinki abin alfahari ne kuma burin kowace marubuciya, duk da
soyayyar da kike nuna min bata isa ba saida kika nunawa my Heenat d'ina itama tata
soyayyar, lallai muna yinki over, luv u dear.😘_
_My aunty *Aishan Umma* ina mik'a godiyata sosai a gareki, kinsa naji cewar ni mai
sa'a ce a rayuwa😊 muna alfahari dake a matsayin shugabar k'ungiyarmu._
_Bismmilahir-rahman-rahim_
1⃣6⃣
"Wai me yasa kike wa yarinyar nan haka, akan me zaki dinga d'aga mata murya, me
yasa kika cika b'acin rai ne Na'ima?"
"Au, nice ma na daga mata murya kenan? kai yanzu baka ga abinda tayi ba? wai me
yasa kake hakane? Khairat fa 'yarmu ce mu muka haifeta ba ita ta haifemu ba, to
akan me zata dinga tsaya gabanmu haka tana fad'a mana abinda ranta yake so?"
Tsaye ya mike yace "koma dai miye kinsan muna da laifi, kamar Khairat ace mun
tsayar da maganar aurenta ba tare da saninta ba a wannan qarnin da muke ciki, kinga
dole ranta ya b'ace."
D'akin Khairat d'in ya nufa yana ci gaba da mita, tundada ta shiga d'aki ta kwanta
kan gado tana kuka, jin kanta na sarawa yasa tasan yanzu zai fara mata azababben
ciwon daya saba, tashi tayi da nufin d'auko magani tasha amma bata kai ga wajen ba
jiri ya d'ebeta ya yadda, rintsegudu ido tayi ta dafe kanta sosai tana fad'in
"wayyo Allah kaina, kaina zai fashe, kaina Papa ciwo yake, dan Allah kazo kai
kad'ai ke sona, Papa kaina zai fashe, wayyo, ahhhh, wash."
Papa na shigowa ya ganta kwance a qasa, da gudu ya k'arasa wajenta yana tambayar
"shalele lafiya, meya faru, kanne ke ciwo halan?"
Kamata yayi ta tashi ya taimakata ta zauna akan gado yana fad'in "wallahi shi yasa
bana qaunar abinda zai b'ata miki rai saboda irin haka."
Da sauri ya nufi wajen maganinta ya d'auko ya kawo mata tare da ruwa ya taimaka
mata tasha, kwantar da ita yayi yana fad'in "kwanta ki huta kinji."
Kai ta girgiza har yanzu hannunta na saman kanta tana matsewa tace "dan Allah Papa
ka d'aure min kaina fashewa zaiyi, ka taimaka ka d'aure min dan Allah."
Ya tashi kenan zai bud'a kayanta Mamie ta shigo d'akin, wata harara ya dalla mata
dan ranshi ya b'ace sosai, kayan ya bud'a ya d'auko wani qaramin gyalenta ya dawo
ya zauna kusa da ita ya d'aure mata kan sosai, sake cewa tayi ya d'aure mata sosai,
shi kuma yana ganin ya d'aureshi qwarai haka ya sake tamke mata kan, duk da haka ba
sauk'i Mamie dake tsaye tana kallon yanda jijiyoyin kanta suka fito sai harbawa
suke kai kasan ba qaramar azaba take ji ba, cikin muryar kuka tace "dan Allah
Alhaji ko zamu fita da yarinyar nan waje ne, kasan fa babu kyau ciwon kai ga 'ya
mace? gaskiya ni ina jin tsoro."
Wata tsawa Papa ya daka mata ba tare da saninshi ba "dallah rufe min baki, duk waya
janyo yanzu in ba ke ba, ke wai har abada ba zaki iya mu'amulantar yarinya da
kyakywar mu'amula ba, sai hushi kawai na banza da wofi, to idan kika kasheta ai
kinga saiki huta, kinsan dai ba zaki sake haihuwa ba har abada dan mahaifar ma baki
da ita, ni kuma wallahi aure zanyi da ba zan zauna ba magaji ba."
Kasa hak'ura tayi da abinda ya fad'a saida tace " to kayi auren mana saime? nace
saime idan kayi aure? namiji goma aiba uba goma bane, wato ka lalata min rayuwa
yanzu kuma burinka kenan na rasa 'yar tawa guda d'aya kai kuma kayi aure, to
wallahi baka isa ba, yanda ka b'ata min rayuwa kaima a haka zaka tabbata ba d'a ba
jika."
Tsaye ya mike "ni kike fad'awa haka Na'ima, waike me yasa baki da kunya? yanzu a
gaban 'yarki kike fad'a min haka? kenan tarbiya ce kike so ta d'auka a haka?"
"Kai tarbiyarce kake so ta d'auka daka fad'a min abinda ka fad'a min, kasan kaine
silar lalacewar mahaifata, to miye na fad'a min wai zan kashe 'yata?"
"Naki nayi shiru, kayi abinda za kayi mana, an fad'a maka tsoronka nake ji? aini
dama nasan ba tuban gaske za kayi ba, kawai dai parpaganda ce irin taku 'yan
siyasa."
Tatsssss, Papa ya d'auketa da gigitancen mari yana fad'in "ke har kin isa kici
mutunci na, wallahi bari gani ina d'aga miki qafa, ruwane suka daki babban zakara
wallahi, idan kuma kinfi son in dawo Mani na nada to mu zuba dani dake."
Dauke hannu tayi daga kunci tace "ka dawo Mani mana dama ai baka canza ba, kuma da
kake maganar mutunci, kai har mutuncine da kai da za'a ci? kuma wallahi ka sake
dukana ramawa zanyi, tunda ni ba jaka bace."
Nunata yayi da hannu yace "kici albarkacin 'yarki dake kwance a wurin n...." bai
k'arasa ba saboda ganin Khairat zaune tana kallonsu kamar ba mai ciwon kan nan ba.
Kunya ce ta tureshi dan baiji dad'in abinda ya faru ba ko kad'an, kawai ta kaishi
bangone, zai zauna a kusa da ita kenan ta fashe da kuka tace "karka zauna, dan
Allah ku fitar min daga d'aki, ku barni zanci gaba da ratuwata a haka, ba zaku
tab'a sauyawa ba saboda ya riga daya zama jikinku, ba zan iya zama daku na minti
d'aya ba ba tare da kun samu sab'ani ba, ku fita dan Allah, zan kula da kaina ko
bakwa nan."
Papa ne ya sake marairaicewa yace "shalele ki saurare ni kiji."
Jiki a sanyaye suka fita, amma tana jinsu ko nisa ba suyi ba Papa ya fara tuhumar
Mamie akan ita ta janyo komai, haka suka jima suna wannan fad'an harya fita ya bar
gidan, Khairat kam turmutsutsu ta dinga yi saman gado tana tusa kanta pillow saboda
rad'ad'in da yake mata.
*Wallahi yan uwa akwai iyayen da basa iya rik'e b'acin ransu, ko a ina ko a gaban
waye idan ransu ya b'ace sai suyi musayar yawu, wallahi iyaye muji tsoron Allah,
dan dole zamu tsaya a gabansa kuma mu amsatambayoyi.*
*Yana da kyau ace ke uwa mace kina da hak'uri fiye dana namiji , domin kece mai
tarbiyar yara maza da mata, idan ranshi ya b'ace ke kiyi hak'uri ki taushi naki
b'acin ran, yara tun suna qanana suna lura da zamantakewar iyayensu kuma hakan nada
tasiri a rayuwarsu sosai, wannan d'an qaramin jan hankali ne, Allah ya bamu ikon
kiyayewa, ameen.*
*****************
Umar Faruk ne da Zuby suke waya, amma shirunshi yayi yawa ba kamar kullum ba,
tunanin Khairat da lokacin data rik'e hannunshi kawai yake yi, ga kuma tuna abinda
Ishaq ya fad'a, a hankali ya saki wani tattausan murmushi daya bayyanar da
kywunshi, sannu sannu ya bud'a bakinshi ya furta kalmar " *shalele*".
Wani murmushin ya koma saki, muryar Zuby ce ta katseshi da tace "yau kuma sabon
sunan na samu?"
Shi kuma harga Allah sunan daya ji Papa y kira Khairat dashi ne ya maimaita, cikin
sauri yace "am kina ji? zan sake kiranki."
Yana fad'a ya kashe wayar tare da fad'awa duniyar tunani, ya jima a wannan halin
kafin ya fara magana da kanshi "haba Umar Faruk, ka dawo hankalinka mana, wannan fa
bata dace kai ba ko kad'an, me yasa kake damun kanka a kanta? ko ka manta wacece
ita? kai da ita fa kamar mota da jirgin sama ne."
"Kai kana son mace mai kunya, ita kuma bata da kunya, kai kana son mace mai kamun
kai da aji, ita kuma sai ajin amma ba kamun kai, kana son samun mace wacce zata
kula maka da mutuncinta ko bayan idonka, amma ita ko a gaban idonka ma zata zubar
maka dashi bare kuma bayan idonka, kana son mace mai ilimin addini, amma baka da
tabbacin sahihancin addininta, kai namijine mai kishi, ita kuma ta riga da tayi
tallar surar jikinta a waje kowa ya gani, bugu da qari baka da tabbacin ita d'in
saliha ce tun ma kafin a mata fyad'e, dan haka ka fita a harkarta daga tunaninta ma
haka."
UUUUUUU
Sai dare ciwon kan ya lafa mata amma kuma bata fito ko falo ba bare farfajiyar
gidan, tana d'aki zamanta tana sauraran waqoqinta, Papa ma yayi yayi ta fito taci
abinci amma tak'i, dole sai nan aka kawo mata shima bata ci wani mai yawa ba sosai
kamar yanda ta saba, daga nan kuma bacci ya d'auketa.
*Washe gari* gidan an tashi anata qoqarin shirin tarbar bak'i, Khairat na bacci
Papa yasa Mamie ta tasheta, dan dole tasan halin da ake ciki, tana bud'a ido taga
Mamie kawai ta tashi ta shiga ban d'aki tayi wanka, ta jima kafin ta fito ta shirya
cikin rigar shadda dan fita take so tayi daga gidan, falo ta fito da gyalenta a
kafad'a da jakarta a hannu, tana shirin kaiwa k'ofa Mamie ta fito daga d'akin Papa,
a hanzarce tace "Khairat."
Saida ta sauke ajiyar zuciya sannan ta juyo bata yarda sun had'a ido da ita ba
kawai ta nufi d'akin Papan.
Kamar yanda bata saba ba haka yanzu ma ta shiga d'akin ba sallama, zaune tayi
bakin gado saboda Papa na zaune a d'aya daga cikin kujerun d'akin, kallonshi take
tana jiran taji me zaice Mamie itama ta shigo ta zauna gefenta, babu wanda ya kalli
wani bare suyi magana har Papa ya gyara murya yace....
"Khairat."
Jin yanda ya kira sunanta kuma yayi shiru yasa dole ta amsa da "na'am."
"Da kyau."
Sannan ya d'ora da "a tunani da hankalin da Allah ya miki Khairat, nasan kinsan
iyaye suna da daraja sosai, hakane?"
"Hakane."
"Shin kina ganin mun kai matsayin da zamu iya yanke miki hukunci daya shafi
rayuwarki ba tare da saninki ba, ko kuwa dai dole sai mun nemi izininki kafin mu
nuna mu iyayenki ne?"
"Ba wannan nake son ji ba Khairat, zamu iya ko ba zamu iya ba?"
"Zaku iya."
"To Alhamdulillah."
"Khairat, yau za'a kawo kayan lefenki daga gidansu Muzaffar, mun amince a
matsayinmu na iyayenki, kuma muna da yak'ini akan ba zaki bamu kunya ba."
Tsaye ta mik'e tayi wata dariyar yan daba tace "nasan dama za ayi haka, yanzu me
kuka daukeni da har zaku yanke wannan hukuncin a kaina? taya zaku had'ani da
mutumin da tsarina da nashi ma daban ne? ni bana son Muzaffar kuma ba zan aureshi."
Jakarta ta dauka zata fita Papa ya daka mata tsawar da tasa ta tsaya wuri d'aya "ke
Khairat, ina magana kina magana, maza wuce ki zauna magana nake dake."
Sum sum sum ta koma ta zauna Papa ya dora da "a tunani mummunar kalma bata tab'a
shiga tsakanina dake ba, amma ki sani Khairat idan har kika shirya bani kunya da
tozartani, to hakika zaki fara jin kalma marar dad'i ta fara fitowa daga bakina
kuma a kanki, bana fatan na tsine miki albarka, amma dai ba zaki ji dad'in abinda
zai fito daga bakina ba, ke ba yarinya bace kin isa aure har kin wuce ma, burinmu
shine mu kaiki d'akin mijinki kema."
Kallon Mamie tayi ta kalli Papa shi kuma yace "burinta kawai taga aurenki, kullum
cikin fargaba take a kanki, saboda yanda take son taga kinyi aure Khairat har
rabuwa tayi dani kuma ta dawo, yanzu haka mahaifiyarki wata d'aya ta bani dan na
aurar dake, idan kuma ba haka ba to zamu rabu kuma rabuwa ta har abada, yanzu ki
fad'a min Khairat."
"Shin kina son muci gaba da zama ni da mahaifiyarki, ko kuma kinfi son mu rabu?"
Shiru tayi tana tunanin mafita, tabbas bata son Muzaffar saboda basu dace ba, amma
kuma ba zata yarda iyayenta su rabu ba saboda maganar aurenta, dan haka ta samawa
kanta mafita, a hankali ta kalli Papa tace "in dai wannan shi zai saku farin ciki,
tona amince."
Tana fad'a ta sake d'aukar jakarta zata fita Mamie tace "da gaske kike Khairat?"
Kura mata ido tayi tana kallon tsantsan farin cikin dake fuskar Mamie kafin tace
"eh Mamie, na amince."
Danne zuciyarta tayi ta qaqaro murmushi tace "yau fa za'a kawo kayana Papa, ai bai
kamata na zauna gida ba har sai kowa ya ganni."
Dariya suka saka mata dukansu itama ta wuce tana dariyar, yayin da suka bita dasa
albarka, tana fita motarta ta shiga ta fara tuk'i kuma Mamie ta kirata, tana d'auka
tace mata "shalelen Papa, dama cewa nayi me zai hana kije gidansu *Hibba*, kinga
saiku zauna acan tunda mahaifiyarta ma nanan zuwa nan d'in."
"Ok, zanje." tana fad'a ta kashe wayar Mamie kuma tayi murmushi.
A hanya ta kira k'awayenta *Rashida, Sarina, Farida, Mamy* akan su sameta gidansu
Hibba, duka suka amsa kiranta dan sun san akwai labari, hannun riga sukayi da Mamar
Hibba hakan yasa basu gaisa ba, kafin su Rashida suzo ta fad'a mata abinda ke
faruwa, dan ita kad'ai ke bata shawarar data dace, yanzu ma sake jadadda mata tayi
tabi iyayenta, sannan ta nunawa Muzaffar kamar tana sonshi har tayi nasarar samun
soyayyarshi ta gaskiya, tunda shi ya fad'a da bakinshi ko da ranar darensu na farko
ne bai damu ba dan sun rabu, haka ta bata shawarwari masu kyau, sannan su Rashida
suka zo.
Tana fad'a musu za'a kawo kayanta suka saka shewa da murna dan sun san babban
bidiri ne, nan suka wuni har Muzaffar ma ya kirata yana tambayarta abubuwa da zasu
shirya, kamar yanda Hibba ta bata shawara akan tayi dan ta b'oye sirrin zuciyarya
sosai, ta fad'a mishi bata gida za suyi shawara da k'awayenta idan taje gida saita
fad'a masa yanda sukayi dasu, a haka sukayi sallama su kuma suka ci gaba da shirye
shiryensu.
*A gida* kuwa Mamie farin ciki take sosai hakan yasa suke ta kujuba kujuba, 'yan
uwa mak'ota da mutanen arzik'i tuni suka cika gidan, hada hada kawai ake an soya na
soyawa , an gasa na gasawa , an dafa na dafawa , an motsa na motsawa haka ma na
jik'awa an jik'a.
*16:35* unguwar ta shaida bak'i sun shigo cikinta, jiniya kawai kake ji na motocin
matan manya uwa uba ga mahaifiyar Muzaffar da kanta tace ba za'a barta a baya
(abinka ga 'yan bariki.😁), motoci ne ba adadi suka tunkaro k'ofar gidan kama daga
na matan manya da abokan arzik'i, sai kuma na abokan Muzaffar duk da baya gari amma
sun masa kara, abinfa ba'a cewa komai ba'a kuma ga komai ba, saida masu tsaron
lafiya suka fara bud'e motoci manyan mata na fitowa daga ciki.
Dala tayi kuka a wajen harka ta girma ce akayi sosai, sai dai wata matashiyar mota
kyakyawa wacce aka shiga da ita har farfajiyar gidan, masu tsaronne suka dinga fito
da akwatina kowace mak'il da kaya d'aya d'aya har dozin biyu da rabi, ga kuma
wannan mota da aka azo akan lefan.
Ciki aka shiga masu gulma nayi masu saka albarka na sakawa masu d'aukar photuna
suna d'auka, acan kuwa na hango muku Mamar Mujaheed 🤣ta rumgume jakarta tana kallon
manyan mata suna yagar kaji da qafafun rak'umi 😁, haka dai aka ga abin arzik'i
tari guda sannan aka sake tsayar da ranar kwana ashirin da biyar ya rage.
**************
Tunda Khairat ta dawo gida taga kayan ita kanta taji dad'i, dan burinta kenan ta
samu babban mutum ta aura, bata wani kalli kayan duka ba kwai ta shiga d'aki tayi
wanka tasa kayan bacci sannan ta kwanta dan bacci take ji.
*Washe gari* da safe kiran Muzaffar ne ya tasheta, cikin magagin bacci ta d'auka ta
aza a kunne da fad'in "hello."
Sai lokacin ma ta tuna shine fa wanda zata aura, zaune tayi tace "lafiya lau, ya
kake?"
Tashi tayi ta fara rage kayan jikinta tace "ok, to yanzu zaka min uzuri na shiga
bayi, dan tashina kenan."
A hassale tace "muryar lafiya, tashina fa kenan, so kake nayi fitsarin anan? haba
nifa bana son irin haka."
Ji tayi ya fashe da dariya yana fad'in "ashe fitsari kike ji, kinga kuwa da zaran
munyi aure, da kaina zan dinga jaye miki fitsarin nan😛."
Da sauri ta wani qaqaro amai tana fad'in "kai, wannan qazamtar fa? kaga sai an
jima."
Kashe wayar tayi ta cilla saman gado tayi bayin da gudu, ko wanka ba tayi ba ta
fito kai tsaye falo ta nufa, binsu take da kallo ganin mata zaune suna kallon kayan
lefen, cikin risunawa suka ce "sannu da fitowa Hajia."
Kai kawai ta daga musu ta nufi madafa, had'uwa sukayi da Mamie da kula abinci a
hannunta, "yawwa dama yanzu zanje na tasoki , zo muje to ga abincinki."
Hannunta ta kamo suka dawo falo suka zauna, buda kula tayi wani b'ata rai Khairat
tayi tace "wannan fa? Mamie karfa zaki fara min wannan tashin hankalin ne? wallahi
ba zan iya ba."
Dariya sukayi Mamie kuma tace "kwanciyar hankali dai Khairat, wannan shine
gudumuwar da zan iya baki, dan nima shi kakarki ta bani."
Diba Mamie tayi tasa mata a baki, da qyar ta had'e tana b'ata rai sannan tace "haba
Mamie ba dad'i ba."
"Yi hak'uri kinji shalelen Papa, ki saba da cinta kullum, kuma wannan fa had'in
tattabaru ne, sai an jima zan miki na kaza."
Haka Mamie ta dinga bata tana rarrashinta har saida ta cinye wanda aka zuba mata
sannan ta tashi ta shiga wanka.
*Tofa daga wannan rana* Khairat aka shiga sahun masu kurbe kurbe da tamne tamne,
duk abinda Mamie zata had'a mata baya wuce na kayan itatuwa saboda sunfi lafiya,
wannan kazar da tattabaru namiji da mace kad'ai ake hadawa da wasu sinadarin wajen
dahuwarsu, abinka ga lafiyayya sai hakan ya d'an fara damunta saboda wasu itatuwa
sun k'ara mata k'arfin sha'awa wanda da bata da ita, wasu kuma suna saukar mata da
ni'ima.
Kowace safiya take jan foyer wajen gyaran jiki cikin k'ank'anin lokaci ta koma
kamar sabuwar haihuwa, kuma haka ake kullum ba'a daina ba, yan mata da samari sun
had'u sun tattauna abinda zasuyi, daga ciki akwai arabian night wanda ango yake
bala'in son partyn , sai indian night wato b'angarenmu ba yan india😁, sai kuma
party wanda za'a gayyaci kowa da kowa, sai cocktail daya zama kamar al'ada.
Kasancewar Khairat ta karanci zane hakan yasa ma ta zana kalar abayar da zata saka
a arabian night d'in, amma kayan indian night Mammie tawa magana aka fara aiko mata
da photuna ta zaba sannan Mammie zata taho dasu.
*Shirye shirye sunyi nisa sosai, kuma ango ya dawo sai dai Khairat tak'i yarda su
had'u, hakan kuma ya dameshi dan haka ya fara tunanin ko da matsala ne.
Yau ta kama ranar *Asabar* kwana bakwai ya rage a daura aurensu, shiryawa yayi
kawai yace shi zai tafi ya gant, mamarshi ce tace "Allah ya kiyaye hanya, amma dan
Allah banda saurin hushi."
Yana fad'a yasa kai tare da rakiyar masu tsaron lafiyarsa sai gidansu Khairat....
_FAN'S JIHADI, ku kawo kud'in ankonku , dan yau zan siyo tawa, kuma babu wanda za
muma alfarma ya shiga idan baya da anko musamman 'yan team d'in Umar Faruk, dan
zasu iya b'ata mana taro.😊😁😎_
16/07/2019 à 16:47 - ~NANA KHADIJA~😍: 💑💑💑💑💑💑💑💑💑💑
*JIHADI*
_Umar faruk_
💑💑💑💑💑💑💑💑💑💑
_NA_
_SAMIRA HAROUNA_
_DEDICATED TO_
*MA FAMILLE*
_Bismmilahir-rahman-rahim_
1⃣7⃣
Babu kowa a falon kasancewar sanyin safiya ce, Mamie yau bata fito wajen girki ba,
sai masu aikin kad'ai suke abinsu, ganin babu kowa yasa shi sallama da k'arfi, da
sauri Saude ta fito ganin ko wanene yasata zube qasa tana gaisheshi, saida yayi
qaramin tsaki sannan yace "ina Mamie?"
"Khairat fa?"
Tashi tayi ta nufi madafa tana fad'in "ikon Allah kenan, sai kuma Allah ya had'ata
da daidai ita."
Shima sama ya haura d'akin Khairat, a hankali ya bud'a k'ofar yana kallon gadon da
yake da tabbacin tana nan, (kunsan mutuniyar dama ba kwana take da manyan kaya ba)
hakan yasa Muzaffar ya kusa kallon rabin sadakinshi😂, saboda wata irin riga ce
bata da maraba da bras, sai kuma wandon rigar kad'an ya wuce mazaunanta, takowa
yayi harya tsaya gaf da ita yana had'iye yawu masu nauyin gaske, da qyar ya lumshe
idonshi sannan ya sake bud'ewa ya saukesu a kanta, hannu ya kai zai daddab'ata ta
bud'e ido tare da juyawa, karaf idonsu suka sark'e dana juna, a zabure ta tashi
zaune taja dara ta rufe jikinta tana mashi kallon tuhuma.
"Wannan wane irin jahilci ne, miye haka Muzaffar, ya zaka shigo min har cikin d'aki
kana tab'ani?"
K'ara matsowa yayi yana fad'in "kinga Khairat dan Allah kiyi shiru, karki tara min
jama'a, wallahi bada wata manufa na tai tab'aki ba."
"Haba Khairat w...." katseshi tayi da fad'in "dallah ni nace k...." kuma sai tayi
shiru saboda tuna abinda Hibba tace mata.
Hararanshi tayi ta turo baki gaba tace "to dan Allah kawai ka shigo min haka duk ka
bani tsoro."
"To naji, wai mema ya kawoka nan? bayan nace maka ba zamu had'u ba har sai an fara
shirya shiryen bikinmu."
"Kiyi hak'uri my Khairiri, wallahi na kasa hak'ura ne shi yasa, matuk'ar so nake na
ganki sosai."
"To naji ni dai yanzu ka fita ka jirani falo zanyi wanka na fito."
Cikin wani shu'umin kallo yace "to muje na miki wankan mana."
Pillow ta dauka ta jefa masa tare da masa kallon kai shashasha kuma hamago ne, amma
da yake hamagon ne na gaske saiya kasa fahimtar kallon, hannu ya mik'o mata tare da
sake fad'in "kizo na rakaki to idan ba zaki yarda na miki wankan ba."
Saida ta had'e fuska sannan ta mik'a masa hannunta ta sauko daga kan gadon, ci gaba
yayi da k'arewa surarta kallo ita kuma ko a jikinta, har saida ya kaita bakin ban
d'akin sannan yayi murmushi yana cewa "insha Allah nan da rana kamar ta yau kin
zama tawa, kuma daga wannan ranar ni zan dinga miki wanka."
Itama murmushin tayi tace "zaka dinga min, ko zamu dinga yi tare?"
Tana shiga shima ya bar gidan gaba d'aya ba tare daya jirata ba dan akwai abubuwa
gabanshi, itama kuma ta jima bata fito ba bayan ta shirya ta fito falo, bata
sameshi ba kuma bata damu ba, harkokin gabanta ta shiga yi bayan Mamie ta had'a
mata kayanta tasha nasha taci naci, foyer ta nufa wajen gyaran jiki kamar kullum.
***************
Cikin farin ciki ya fito daga gida zuwa wajen aikinshi, tunda ya shiga yaga gungun
su Ishaq sunata hira, saida ya tsaya bayanshi bai sani ba ya kai masa duka yana
fad'in "iskancin banza, wajen neman kud'in naku kuka mayar kamar kasuwa?"
Dariya Ishaq yayi lokacin daya juyo ya kamo hannunsa yace "kai haba zo ka gani
kaima."
Matsowa yayi shi kuma ya d'auko wata had'add'iyar shadda gizna kalar ruwan qasa ya
bashi, hannu yasa ya karb'a yana kallo yace "na miye wannan?"
Saida ya kalleshi yace "ankon Hajia Khairat ne ta aiko manager ya kawo, kuma tace
duk wanda bai siya ba to yasan sauran, dan tace tana buk'atar ganin kowa dake wajen
nan ya hallara duka shagulgulan da za ayi."
D'orawa yayi da "kuma kasan halinta dai, k'aramin aikinta ta tsige mutum daga aikin
nan, dan haka kayi sauri ka siya dan kwana hud'u ya rage a fara shagulgulan bikin."
Wata uwar harara ya zabga masa tare da jan tsaki ya cilla masa shaddar a qirji ya
fita ya bar wajen, saida ya hau mashin d'inshi ya tambayi kanshi "ina kuma zaka
je?"
Ai kuwa gida ya nufa da tunanin samun sauki, yana shiga a soro ya aje mashin d'in
ya shiga ciki, duk da mutanen daya gani a farfajiyar gidan bai kula kowa ba yana
shirin shiga d'aki mahaifiyarshi tace...
Zai wuce ta sake cewa "Umar faruk, ashe yarinyar nan za tayi aure wacce kuke aiki a
masana'antarta, shine kuma baka fad'a ba, kuma kaga ko mahaifinka bana tunanin ua
sani dan daya fad'a min."
Rai b'ace ya kalli Mamar yace "Mama kuma waya fad'a miki maganar nan?"
A zafafe ya kalleta yace "ke kuma gidan uban wa kika ji?" ya tambaya a harahen
zarma.
Tuni Ruk'ayya ta fara rawar jiki saboda tsoro tace "wallahi yaya Umar nima a
Whatsapp ne na gani ana d'ora photonta da akwati talatin da makullin mota,amma ni
bansan komai ba."
Sama da qasa ya harareta ya rangada dogon tsaki sannan ya kalli Mama yace "wallahi
shi yasa banso aka bar yarinyar nan ta rik'e wayar nan ba, kawai salon yara su
lalace."
D'akinshi ya wuce zuciyarshi kamar zata kama da wuta, wani irin haushin kanshi ne
yake ji daya takura kanshi akan tunanin wata banzar Khairat (a cewarshi), bai sake
fita ba har saida Ishaq yazo gida ya sameshi da yamma.
Gaishe da matan gidan yayi kafin ya d'ora ma Mama da "Mama mutumin kuwa yana ciki?"
Dariya yayi ya mike yana fad'in "mutumin fa ba dama, kamar gobene auren nan."
Itama dariyar tayi tace "ka barshi kawai, a doleshi k'uryar d'aki yake so a fitar
masa, kuma wuri ba zai isa ba, in dai baso yake na fita daga d'akina ba dan yayi
k'uryar d'akin."
Yana shiga ya sameshi cikin falon d'akin wanda ke shafe kayane kawai babu, falon
babba ne sosai amma babu wani d'aki a ciki, d'an k'aramin kewayene daga waje sai
matsakaiciyar ban d'aki , gaisawa sukayi Ishaq ya d'ora da "kai haka ake? kawai
saika sa kai kayi gaba kuma baka komawa, shi yasa ai na fad'a musu wallahi son
yarinyar nan kake, dan inba...."
Katseshi yayi da fad'in "kai kai kai, dakata dan Allah, wacece nake so d'in?"
"Khairat mana."
"Mtssss, yanzu wannan sakaryar kake had'ani da ita, wannan mahaukaciyar yarinyar?
gaskiya ka cuceni Ishaq, wallahi da zan san zuciyata na sonta, toda babu abinda zai
hanani hukunta kaina ta hanyar da tafi kowace hanya zafi."
Shiru ya masa ya ci gaba da kallon d'akin shi kuma yace "to aini banga wani aibunta
ba yarinyar, kaifa kasan *wacece ita*."
"Sanin wacece ita yasa ba zan iya yarda na bari zuciyata ta fara sonta ba, da
bansan ita yar d'an giya bace ko kuma manemin mata, da ace bansan ita
fiysararriyace wace bata d'auki cud'anya da maza ba a bakin komai, da ace bansan
ita mai wulak'anta mutane bace, da ace bansan tana soyayya da arne ba, sannan da
bansan itace yarinyar da namiji majiya k'arfi guda biyar suka sauke sha'awarsu a
kanta ba, to da zan iya tunaninta."
Da mamaki Ishaq ke kallonshi dan b'acin rai ne kawai ya gani a idonshi da tafasar
zuciya, girgiza kai yayi yace "wallahi wannan ba Umar Faruk d'ina bane, tabbas
akwai abinda ke damunka kuma baka shirya fad'a min ba, Umar d'in dana sani yana da
ilimin addini dana zamantakewar rayuwa, wannan maganganun bai kamata su fito daga
bakinka ba, amma saboda b'acin ran da kake ciki yasa ka fad'esu, amma duk da haka
ni ban yarda baka son Khairat ba, sai in har ka siyi ankon bikinta kuma ka halarci
taron sannan na yarda."
"Sosai ma."
Kamar wasa Umar faruk ya shiga d'akinshi ya k'wamuso kud'ad'enshi suka fita, tare
suka siye kuma suka biya suka bada d'inki, Umar harda siyan takalmi 😏kaji sai kace
shine angon.
Saida dare yayi suka dawo gida, dama kuma gida biyu ne ya raba gidansu, k'arar
mashin d'inshi yasa Baba dake zaune a d'akinshi dake farkon shigowa gidan yasa ya
kira sunansa , bayan ya shigo nan ma dai maganar d'aya ce akan aure Khairat ne, sai
dai shi Baba Papa ne yazo da kanshi ya gayyaci malaminshi a matsayin wanda zai
wakilceshi ya bada auren Khairat, a tsorace Umar Faruk ya d'ago kai yace "Baba, wai
kai zaka d'aura auren?"
"Ba damuwa kaje, amma ka sani dole zaku je wannan d'aurin auren, na fad'awa duka
yan uwanka maza masu wayo , zamu tafi tare daku."
Da qyar yakai kansa d'aki yayi kwance yana ji kamar yayi kuka, amma kuma yana
tambayar kansa to kukun me kenan zaiyi😆😆😆.
*****************
*Komai* na tafiya yanda suke tsarashi a haka kuma Khairat ta fara d'aukan haske
saboda k'unshi da gyaran kai mai masifar kyau da aka yanyara mata gwanin sha'awa,
ranar *laraba* aka fara da indian night, a ranar an rak'ashe sosai shagali yayi
shagali, yayin da ya tara dubban mutane manyan yara da manyan mata, kusan kowa yayi
qoqarin yin shigar indiawa, amma kana ganin amarya zaka ganeta saboda kayan data
d'auka jar kala da golden, riga da siket ne hannayenta sun sauko akan damatsenta
amma ta kamata sosai, sai k'aton siket d'in da yake jan qasa yasha duwatsu ga
walk'iya, mayafin kayan ne aka d'ora mata akai, ba laifi gana gani zasu birgeka dan
had'insu yayi, sai dai duk kyan Muzaffar Khairat ta takeshi ta shanye, haka akayita
walima har aka buk'aci da amarya da ango su shigo fili su d'an taka, sai lokacin
kad'ai nida ma chérie Hakeema da sister Chappa muka tsagaita da rawa muka ba
Khairat d'inmu fili dan munsan tanan b'angaren gwanace ta qarshe.
Ai kuwa bata bamu kunya ba, dan kuwa wata waqa ce aka baza mata d'aya daga cikin
film d'in *dilwale* mai taken *janam janam*, Muzaffar tsaye yayi amma fa amarya ta
taka ba laifi sai lik'i da tafi da aka dinga mata, a haka aka tashi taron ango ya
maida amarya gida shima suka wuce gida kowa yayi baccin gajiya.
_Har yanzu kunkumina ciwo yake😂 can naga yan team d'in Umar faruk ta taga suna
lek'enmu muna yagar kaji, ah to ai dama na fad'a muku dan babu alfarma a wannan
ranar_.
*Washe gari* ma sabon shiri aka d'auka na arabian night, abayar da Khairat ta
zanawa kanta ta saka, sosai rigar ta dace da ita, dogayen hannuwa kuma matsatsu
hakama ta kamata wajen qirki abinda yayi kunkuminta, sai dai daga nan kuma saita
bud'e sosai har tana jan qasa a baya, kwalliya akama rigar sosai ga d'an kwallinta
ma, tana d'orawa ta fito kamar balarabiyar gasken, dogayen takalmi aka d'auko mata
zata saka kawai taga ba zata iya ba, in da take ajiyar takalmin ta bud'a sai idonta
ya sauka akan wasu tapet masu kyau masu kamar na maza , murmusawa tayi data tuna
ranar farko da manager ya shigo tare da Umar Faruk suka gabatar mata da takalmin
kuma tace su bar mata su, tana sawa suka tsaya a qafarta d'aram gwanin sha'awa
dasu, haka suka nufi hall d'in taron amma idon Khairat sun kasa barin takalmin nan,
yau ma haka akayi wannan taro aka ci aka sha baja baja (an samu na banza ba),
22:15 kowa yasan in da dare ya masa, sai dai tun kafin abar taron photon amarya da
ango suka rigasu fita daga wajen, masu d'orawa a fecebook, Whatsapp, Instagram, kai
da sauransu, cikin qanqanin lokaci sai photunan suka shiga duniya, maganganu iri
iri wasu na yaba dacewarsu, wasu na yaba kyawun matar, wasu na yaba kyawun namijin,
wasu na fad'in ai an mata fyad'e, yayin da maza suka fara tabka mahawara a shafukan
sada zumunta iri iri, wasu na cewa ya kyauta kuma yayi jarumta tare da *Jihadi*,
wasu kuma suna ganin ba zasu iya ba kuma shima da yayi bai birgesu ba.
*Al'amarin aure kenan, dole sai ace nan yayi daidai, nan baiyi daidai ba, mutum
d'ari na iya maganar aurenka, amma da wuya ka samu goma da zasu ce Allah dai ya
sanya albarka, kashi saba'in masu kushewa ne, ashirin masu yabawa, goma ne masu
addu'ar fatan zaman lafiya, Allah ka rabamu da sharrin mutane da aljanu , Allah ka
bamu ikon yin komai da kai.👏*
A cikin haka Allah ya had'a Umar Faruk da videon Khairat a Indian night tana
rak'ashewarta, wanda anan ma mahawarar ake , wai idan kaine ya za kayi azo party
amaryarka na wannan rawar kamar baindian gaskiya, wasu na fad'in kafin a d'aura
auren zasu ce sun fasa, wasu kuma na cewa aiba komai bane zamani ne, yayin da Umar
Faruk ya sake jin haushin Khairat sosai a zuciyarshi, tunanin yake yanda zaije
partyn gobe da aka ce dole suje kuma gashi manager ya rok'esu akan suje danshi.
Photo d'aya ya zubawa idanu shine in da take cikin abaya ta yane kanta, meuk-up
d'in da tasha ta sake canza mata kammani tayi bala'in kyau, saika santa zaka iya
ganeta abinka ga farar fata, da alama bata san an d'auki photon ba saboda babu
murmushi a fuskarta kuma bata kallon mai d'aukarta, kanta na kallon qasa baka iya
ganin idonta sai golden da pink d'in eyshadow d'in dake saman idon, zoom d'in
photon yayi yana kallon kyawun fuskarta, a hankali furta "dama labarina dake gajere
ne, gashi ya datse tun bamu kai ko ina ba." da kallon wannan photo har bacci ya
d'aukeshi.
A b'angaren Khairat kuwa har tayi shirin kwanciya bacci Mamie ta shigo da 'yan tame
tamenta, tun kafin tayi magana Khairat tace "ohh Mamie, wai dan Allah abun nan ba
zai qare bane? nifa wallahi na gaji da shan kayan nan suna takura min."
Cikin dariya Mamie tace "kiyi hak'uri kinji, keda nake tunanin na had'a miki su
idan ki kaje can kiyita anfani da kayanki."
"Wa, ni? ba zan iya Mamie, na yanzu ma wallahi komawa za kiyi dasu."
Kafad'arta ta dafa tace "Khairat, burin kowace uwace, taga yarta tayi rayuwar farin
a gidanta, kiyi hak'uri nasan ba zaki ji dad'i ba amma ya zama dole na tuna miki,
'yata, akwai wani abu mai mahimmaci da kika rasa wanda ba zaki iya yiwa mijinki
tink'aho dashi ba, amma duk da haka ina so naga kin samu kyautar da ake samu a
daren farko."
A hankali Khairat ta girgiza kai alamar a'a, murmushi tayi tace "wasu na bada
kyautar kud'i, kadara ko tasa albarka, amma ni ina so a daren farkonki , mijinki ya
mallaka miki kanshi ke kad'ai, ina so ya mallaka miki zuciyarshi ki zama mai
alhakin kula da ita, duk abubuwan da kika ga ina baki, wannan ne sirrinsu, ki
rik'esu da kyau su zama sirrinki, duk in da mijinki zaije to wallahi zai dawo
matuk'ar kin rik'esu, natural ne ga lafiya a jiki ga dad'i a baki, kuma zasu dinga
tsumaa jikinki koda kin zama raguwar mace, to zasu jima a jikinki ba tare da kin
rage d'and'ano ba, idan kuma kina yi akai akai, to kullum d'and'anonki zai dinga
haukata mijinki tamkar qaramin yaro ."
Kai ta sake girgiza alamar eh, Mamie na bata ta amsa ta kifa kai saida ta shanye
sannan ta ajiye cup d'in Mamie ta d'auka sukayi sallama ta bar d'akin zuciyarta
fari qal.
*Mamie nima na rik'e sirrin nan, shi yasa ban fad'a musu ba😎, nifa har kyautar
yaran da zan haifa aka min😁.*
*Washe gari* haka aka tashi da sabuwar hada hada kasancewar gobe d'aurin aure,
bak'i na nesa dana kusa sun hallara kuma kowa na shirin tafiya partyn da za ayi na
kowa da kowa, yamma nayi aka fara tafiya bayan wankan da amarya ta d'auka cikin
shadda irinta ango, sunyi masifar kyau masha Allah, yau kam hall d'in cika yayi
sosai dansu Umar Faruk ma na hangosu da sauran ma'aikatan, da qyar ake iya ganin
amarya da ango saboda masu d'auka da waya nayi masu camera ma nayi, haka ake taro
har mc ya kira amarya da ango suka yanka babban cake d'in da aka masa siffar amarya
da ango , suka ba junansu a baki sannan suka shigo fili suka fara d'an rausayawa,
naira tayi kuka domin wasu kamar a cikin shara suka deb'ota yanda suke zubawa ango
da amarya, Umar Faruk ya kasa d'auke idonshi akan Khairat amma da kallonshi ya kai
ga Muzaffar, 🤣sai naga ya bishi da harara da dogon tsaki, wannan tsakin ne ya ishi
Ishaq yace su tafi su tafi tunda dai an gama ai, ko ruwa baisha ba bare jus sai
Ishaq yayo oder abinshi a leda ya taho dasu.
*Can naga yan team d'in Umar Faruk suna kokawa wajen d'aukar kwalban jus d'aya,
amma da yake team d'in Khairat akwai imani, haka muka cika musu jakunkunansu da
kayan k'walam😁*
*Hak'ik'a kun min kara, dan kun cashe sosai fiye da tunani na.*
******************
Koda ya shigo gida kai tsaye d'akin mahaifiyarshi ya nufa sai dai tuni sunyi nisa a
bacci, kamar yanda ya sani dama ko yayi dare to abincinshi na gefen mahaifiyarshi,
kwanan ya d'auka ya zauna kusa da ita ya fara ci yana kallonta tana baccinta, sai
dai baici mai yawa ba ya barshi ya fito daga d'akin, d'akinshi ya shiga ya cire
kayanshi ya fito zai shiga wanka, yayanshi ne *Abbakar* ya shigo shima bayan ya
yiwa mashin d'inshi wajen zama, hannu ya bashi suka gaisa yana fad'in "yadai
abokina, ina ka shiga ne haka?"
Cikin sanyin jiki Umar Faruk yace "wallahi abokina ina nan, kai dai ka b'ace,
waccen matar ta b'oyeka."
Nunashi yayi da hannu yace "kai ka fita idona, ina ruwanta kuma."
Bokitin ya d'auka ya nufi ban d'akin yana fad'in "idan ka shiga kace mata na dawa
ta zo ta gaisheni."
"Lallai ma, sai dai ka kama layi to harta gama dani, kasan ance in ana dara fidda
uwa ake."
Baice komai ba saboda harya fara cire kayan jikinshi, yana fitowa kuma yayi alwala
ya shiga d'akinshi, doguwar riga yasa ya kabbara sallah ya fara nafilfili har saida
kiran sallah asuba ya riski kunnuwanshi sannan ya dakata, fitowa yayi saboda jin
motsin mutane sun tashi suma , tare suka nufi masallaci da yan uwanshi da kuma
mahaifinsu, bayan sun idar da sallah suka dawo gida, kuma kamar yanda mahaifin nasu
ya koya musu wasu karatun littafi mai girma suka fara, wasu kuma tasbihi da hailala
da kuma istigfari, Umar Faruk ma karatu yayi saida 06:00 tayi sannan ya rufe ya
d'an kwanta kafin k'arfe 09:00 auren Khairat.
********************
*Yau ne fa*😂
Yau ta kama ranar *asabar* ranar d'aurin aure, Umariri ma 😂baiyi qasa a gwiwa ba
wajen shiryawa kamar yanda yaga yayanshi Abbakar da k'annanshi guda biyu *Usman da
Aliyu* suna yi dan cika umarnin mahaifinsu, wani abun mamaki shine, haka kawai Umar
Faruk kejin wani nishad'i da farin ciki na baibaye mishi zuciya, ga murmushi mai
matuk'ar tsada daya kasa barin fuskarshi, duk da yana d'an jin fad'uwar gaba da
kuma tsoro, amma dai yafi farin ciki hakan kuma yasa ya ta'alak'ashi da karatun da
yayi ne dan yafi komai samarwa mutum da nutsuwa.
Cikin wata shaddarshi gizna fara ya shirya wacce suka d'inkata a bikin abokinsu ,
kasancewar ba mutum ne mai sha'awar manyan kaya ba yasa tun ranar bai kuma sawa ba,
kamar yau ne ya fara saka shaddar saboda yanda take d'aukar ido, dogayen hannuwa ne
da ita da kuma wasu da aka aza daga iya kafad'u hakan zaisa kayi tunanin rigar
ninki biyu ce, bak'ar hula takalmi qafa ciki bak'ak'e da agogo ya d'aura kamar dai
yanda aikin rigar yake, shi kanshi yasan ya had'u masha Allah sai tafiya kawai.
Yana fitowa ya samu duka sun shirya suna tsakiyar gidan, rufe d'aki yayi ya kallesu
yace "muje ko."
Duka da kallo suka bishi saboda ganin bak'on al'amari a tare dashi, ganin kallon
yayi yawa yasa Umar faruk sake cewa "muje ko."
Baba ne yace "wai Umar faruk kaine da wani murmushin haka mai tsada, meya faru ne
haka kake farin ciki?"
Murmushin kawai ya ci gaba dayi ba tare da yace komai ba, Abbakar ne yace "wannan
farin cikin dai akwai wani abu a qasa gaskiya, mutumin da kullum fuska a had'e."
Cikin dariya yace "dan Allah ni ku wuce mu tafi, lokaci fa tafiya yake."
*Saratu* matar Abbakar dake zaune tare dasu Mama a tsakar gidan ce tace "wannan
sauri da kake Allah yasa ba wani abun kake shiryawa ba."
Kallonta yayi yace "baki iya gaida miji ba amma kin iya katsa landa, to me zan
shirya ni kuma?"
Cike da zolaya tace "tona sani ko amaryar zaka sace , ko kuma kasa a d'aura auren
da kai."
Dariya duka aka saka saishi daya ce "wata d'iyar robace da kike tunanin haka ta
faru?"
Mama ce tace "yarinya fa tsadane da ita tunda ita ta...." sai kuma tayi shiru.
Ke Ruk'ayya uwar d'umi sai kika ce "ita ta tallabeshi da mari fa duk wannan d'acin
da yake mana a gida."
Da gudu tayi d'aki saboda biyota da yayi duk da kiranshi da Mama keyi saida yakai ,
yana shiga ya tallabeta da marin itama😂 sannan ya kama kunnenta ya murd'e yace
"wallahi na sake jin bakinki manya na magana, saina lahira ya fiki jin dad'i."
Kuka take sosai shi kuma yana fitowa ya kalli Saratu yace "ki shirya tarban sabuwar
amarya."
Fita sukayi suka hau taxi dukansu suka nufi d'aurin auren, dandazon jama'a manya da
qanana masu mulki masu sarauta, masu kud'i na nesa dana kusa ga kuma bak'i daga
k'asashe da dama na gida dana waje, ganin irin d'ubbin jama'a yasa Umar Faruk jin
haushi ma ya kamashi, haka dai suka samu suka kutsa tare da mahaifinsu harya shiga
babban masallacin dake d'an nesa da gidan su kuma suka tsaya daga bakin masallacin.
********************
*A b'angaren* Muzaffar ma farin ciki yake da d'okin zuwa wajen d'aurin auren, ya
gama shirinsa tsaf ya d'auki babbar rigarshi zai saka amininshi da suke kira da
*Basta* ya kalleshi yace "sai farin ciki kake da zumud'i zaka samu Khairat, amma mu
kuma bak'in ciki muke dan koba komai munsan mun kusa rasaka kenan har abada."
Cike da mamaki yace " Basta, yanzu dama bak'in cikin aurena da Khairat kake? amma
gaskiya ka bani mamaki."
"Ba haka bane abokina, ina nufin ina bak'in cikin rasaka da za muyi."
"Nasan kasan komai game da Khairat, amma sai gashi ka yarda da aurenta kamar wanda
mata quka k'are a gari, baka tsaya kayi bincike ba bare ka tabbatar da lafiyarta,
haba abokina kayi tunani mana ka gani, kai da kanka ka fad'a min mahaifin yarinyar
nan ne yaje ya samu mahaifinka da maganar aurenku, kenan akwai wani abu a qasa."
Shiru ya d'anyi yana tunani sai dai bai iya tunani komai ba, a hankali ya
tambayeshi "kamar me kenan?"
Shu'umin murmushi yayi yace "kasan ko suwaye suka mata fyad'e, ai kuwa ba zata rasa
cuta mai karya garkuwar jiki ba, ko kuma dai wata cutar ko kuma ciki."
"Ciki kuma? amma ai ba yau bane aka mata fyad'e, wata nawa aka d'auka da cikin ya
kasa bayyana har yanzu?"
"Kai baka san mata ba wallahi, amma idan baka yarda da abinda na fad'a maka ba , to
ga wuri nan."
Yana fad'a ya fita ya barshi dan yasan zaifi yin tunani da kyau, haka ne kuwa ya
faru ya jima yana tunanin abinda ya fad'a har lokaci ya tafi sosai, agogon daya
kalla yasa shi d'aukar wayarshi saboda ganin 08:57, shugaba ya kira yana d'auka
cikin sauri yace "Papa an d'aura auren?"
Murya qasa qasa cikin dariya yace "wai saurin me kake? harna bayar da sadakinka fa,
d'aurawa kawai za ayi."
"Wai kasan me kake fad'a kuwa, baka da hankali ne? yanzu haka fa d'aura auren nan
ne za ayi."
"To ni dai nine za'a d'aurawa auren, kuma nace na fasa dan haka ba zanyi ba."
Shugaba ne ya saci kallon Papa da bakinshi ke bud'e sannan tasa babbar rigarshi ya
goge zufa, aje wayar yayi yana kallon mutane malam ne yace "to zamu iya farawa
yanzu."
Shirun da shugaban yayi yasa aka fara shirin d'aura aure, sannu sannu murya na
rawa yace "a dakatar da d'aurin auren."
Kallonshi akayi amma babu wanda yayi magana , "Muzaffar ne ya kirani yanzu, kuma
yace a dakatar da auren."
Papa ne da gabanshi ya fara dukan uku uku yace "a dakatar kamar ya, gaba d'aya za'a
dakatar ko kuma na wani d'an lokaci?"
"Eh to, nidai yace min a dakatar ya fasa baya so."
Da sauri Papa ya dafe kanshi, yana jin mutanen cikin masallacin na hayaniya amma
bai iya cewa komai ba, kusan minti ashirin aka d'auka wasu na waje sun fara qaguwa
akan meke faruwa, na cikin masallacin ne da suka tabbatar ba za'a d'aura ba suka
fara fitowa, shugaba ma kallon Papa yayi yace "kayi hak'uri Mani, wallahi bansan
meya faru ba,amma idan na koma gida zanji meye matsalar."
A wulak'ance Papa ya kalleshi yace "ba damuwa, ba saika takurashi ba, allah zai
kawo mana d'auki."
Fita shima yayi ya rage daga Papa da malam sai yaya Suleiman da sauran k'annan
Papa, su Umar Faruk dake tsaye k'ofar masallacin ne suka shigo ciki, wajen malam
suka nufa suna tambayar lafiya har yanzu ba a d'aura auren ba, a raunane malam
yace musu "yaran ne ya fasa."
Kallon kallo suka shiga yi suma har muryar Papa ta daki kunnuwansu yana fad'in
"bansan me zance mata ba, tafi kowa damuwa da auren nan, tana matuk'ar son ganin
Khairat tayi aure, yanzu gashi ba lafiya ne da ita ba, watak'ila idan na fad'a mata
hawan jininta ya tashi, Khairat ma na fama da rashin lafiya, itama zata iya shiga
matsala duk da dai nasan biyayya ta mana ta yarda zata aureshi."
A hankali ya furta "Allah ka kawo mana agaji." sai kuma kuka ya k'wace mishi, ganin
haka yasa hankalin Umar faruk tashi babba na kuka a gaban idonshi, akan abinda zai
iya taimaka masa, dole ne ma yayi wannan *Jihadin* kodan ceton mutunci da rayukan
wasu, watak'ila kuma labarinshi da Khairat dama baizo qarshe ba, kuma zai iya
yiyuwa akwai wani *b'oyayyen al'amari* dasu basu sonshi ba .
Matsowa yayi kusan Papa ya rik'e hannayenshi yace "yallab'ai, ni ba kowa bane, kuma
ba d'an kowa ba, bansan ko zaka iya bani auren 'yarka ba."
Take farin ciki ya lullub'e Papa ya rumgume Umar faruk yana ci gaba da kuka, godiya
kawai yake masa yayin da mutane suke mamaki malam kuma yana farin ciki haka ma
'yan uwanshi.
Anan take aka d'aura auren *UMAR FARUQ AHMAD ADAM* da *KHAIRAT MANI BUKAR* Papa da
kanshi ya wakilci Umar Faruk, anan ango ya tattara duk abinda yake da aka biya
sadaki, malam kuma ya wakilci Khairat.
_NA_
_SAMIRA HAROUNA_
_DEDICATED TO_
*MA FAMILLE*
1⃣8⃣
Ana gama d'aurin aure sai kuma labari yasha bam bam, amma a wajen Papa farin cikine
zalla yake saboda faruwar hakan, Papa ne ya keb'e da ango da Abbakar da kuma Baba
yana tambayar lokacin da zata tare, Umar Faruk dai cewa yayi duk lokacin da suka
shirya, amma Baba yace a basu sati d'aya, sosai Papa yaji dad'i ya kuma ce ya bawa
Umar Faruk kyautar gidan da zasu zauna da kuma mota, murmushi Umar faruk yayi yace
"wallahi bana buk'atar komai, shi yasa ma na fad'a maka koni waye dan matsayinmu ba
d'aya bane, ba zan bar gidanmu ba, kuma ina da wajen da zan ajiyeta, idan kuma taga
hakan bai mata ba, toni banda matsala tun kafin tafiya tayi nisa zan iya sss..."
Bai k'arasa ba saboda taushe mishi baki da Abbakar yayi, Papa ne yace "ba komai
Umar faruk, ai ba sai ankai ga haka ba, ko rumbu ka ajeta dole ai zata zauna, mudai
muna godiya sosai."
Papa ne yama Umar faruk iso a cikin gida yaga sauran iyaye da kakannin Khairat ya
gaishesu, abinka ga idan Allah ya aiko abu, duk uwayen masu hankali idan suka kalli
Umar Faruk sai suji ya kwanta musu a rai saboda hankali nutsuwa da kunya, haka suka
kamo hanyar komawa gida yana wasi wasi yana ji kamar yayi kuskure hukuncin daya
d'auka.
******************
*Khairat* na d'aki tare da k'awayenta tanti (aunty) Safiya ta shigo ta fita da ita
bayan ta rufeta ruf da daren amare bleue wacce ta mata kyau, babban falon da Papa
ke sauke manyan bak'inshi suka shiga, duk da kanta na qasa kuma cikin dara amma
saida taga yawan mutanen dake d'akin, gaba d'aya kannan da yayun mahaifinta ne,
Mamie kuma dama ita d'aya ce ga iyayenta, hakan yasa sai Safiya da *Ramlatou* itama
cousine d'inta ce, sai kuma matar margayi babansu Papa da kuma Mammie, zaunar da
ita tayi a tsakiyarsu sannan itama ta zauna.
*Nan fa* aka fara sambado ma Khairat nasihoji ta ko ina bayan sun fad'a mata yanzu
ita ba budurwa bace mai aure ce, kuma ita ba matar Muzaffar bace, matar *Umar Faruk
ce*, an jawo mata ayoyi hadisai da kuma karatun *duniya*, sosai nasihar ta shiga
jikin Khairat sai gata da kuka tare da bawa kowa dake wurin hak'uri na ayafi juna,
dan duk rashin kunyarta bata kai tama mutanen dake wajen ba saboda girma da
matsayinsu gareta, haka suka bita da sa albarka bayan ta musu alk'awarin bin Umar
Faruk sau da qafa, tanti Safiya ce ta mayar da ita d'akinta.
Tunda ta zauna ta fara wani sabon kuka dan babu yanda za tayi ne kawai ta amsa
musu, amma ko kad'an Umar Faruk baya da tsari irin na mazan da take so (a cewarta
fa)😎, gashi kuma baya da komai hasalima a qarqashinta yake samu, to tayaya zata
rik'eshi a matsayin miji, gaskiya zata hak'ura taje gidanshi danta musu biyayya,
amma dole zata dawo dan rainine ma a had'ata da wani wai Umar Faruk, haka dai bayan
'yan d'aurin aure sunsha lagwadarsu wasu har sun tafi da guziri, aka fara biki
gadan gadan aka sha casu sosai.
Tun yamma mutane suka fara watsewa zuwa dare kuma babu kowa sai bak'i da suka zo,
kowa ya kwanta dan yayi bacci ya huta gajiya amma banda Khairat dake tunanin yanda
rayuwar aurenta zata kasance, yanda taga safe haka taga rana ba tare data rintsa
ba, kiran sallah asuba kad'ai yasa ta tashi tayi alwala tayi sallah sannan ta
kwanta rama baccin da bata samu tayi ba.
******************
*A b'angaren* Umar Faruk kuma suna shiga gida yanda duk suka shiga da kazar kazar
amma banda shi yasa mahaifiyarshi ta fara tambayar lafiya, fad'a mata yayi ita da
yan uwanta (matanshi guda biyu) su sameshi d'akinshi, ba b'ata lokaci suka hallara
tare da Abbakar da Umariri😂, nan Baba ya fad'a musu abinda ya faru sannan ya d'ora
da "wannan na tabbata itace k'addarar yaranku, kuma wannan abun *rubutatten
al'amarine* da ubangiji ya rubutashi tun kafin a samar dashi kanshi Umar d'in, dan
haka ku shirya tarbar sarakuwarku ban da rana irin ta yau insha Allah, sannan ku
saka musu albarka."
Saida suka gama jimami sannan mahaifiyarshi ta sauke ajiyar zuciya tace "gaskiyane
malam, kuma insha Allah ba za'a samu matsala daga garemu ba, kuma muna musu fatan
alkairi Allah ya basu zaman lafiya."
"Ameen ameen." cewar malam kafin ya kalli sauran yace "ku kuma me zaku ce?"
Tab'e baki *Sa'a* tayi tace "ah to me zamu ce, tunda kun riga da kun gama yanke
hukuncinku."
Mik'ewa tayi ta kama hannun *Maimuna* tana fad'in "nifa ba zan iya zama wajen nan
ba."
Itama Maimuna saida suka mike ta kalli Umar Faruk da kanshi ke qasa shi abin duniya
ma ya dameshi tace "wallahi dai kayi abin kunya, in banda kwad'ayin dukiya ta uban
yarinyar nan, ince kaine nan kazo kwanan baya kana huci akan ta mareka kuma ka
rama, shine yanzu dan tsabar rashin zuciya wai kai uban taimako ka taimaketa, kai
yanzu ba abin kunya bane a wajenka ace ka auri macen da wasu garada suka raga?"
Sa'a ce tace "ke rabu dashi dan Allah, yana tunanin zai samu abin duniya shi yasa,
amma ka sani ba lallai ka mori abinda za'a baka ba, dan cutar da waccen ya guje ma
kai zata sama, wannan itace k'addararka."
Bushewa sukayi da dariya suka tafa hannu suka wuce abinsu, ba sabon abu bane wannan
dan haka babu wanda ya dama a cikinsu, Baba ne yace "Umar Faruk."
D'agowa yayi ido jawur kamar zai fashe da kuka yace "na'am Baba."
"Kayi hak'uri kaji, wallahi Allah ba zai barka haka kawai ba saiya dafa mata, kuma
ni nayi farin ciki da abinda kayi, kuma nayi alfahari da kai a matsayin D'ana,
Allah ya maka albarka."
"Ameen Baba."
Baba ne ya kalli Umar Faruk d'in shima kallonshi yayi, cikin muryar tausayi yace
"Mama ba zan iya barin gidan nan ba, idan sunga nan ya musu, to su kawota idan kuma
ba haka ba, to gaskiya sai dai mu rabu, danni dama kawai saboda na fitar dasu daga
halin da zasu shiga nayi."
Mama ce tace "haba Umar Faruk, me yasa zaka fara maganar rabuwarku tun yanzu, bana
so ka daina, kuma ba komai ai sai a qarasa gyara abinda ya rage, idan har ya musu
saisu kawota nan d'in."
Abbakar ne yace "Mama, saida fa mahaifinta yace zai bashi gida da mota, amma yaron
nan da taurin kai yak'i amincewa."
Umar Faruk ne yace "idan na amince na amsa kenan me nayi? me kake so al'umma suce a
kaina? na aureta saboda dukiya? to wallahi babu abinda mahaifinta zai bani a
duniyar nan na amsa, ni taimako nayi *jihadi* nayi na auri 'yarsa, dan haka bana
buk'atar komai daga gareshi."
Tashi yayi ya fita daga d'akin Baba kuma ya kalli Abbakar yace "nifa naji dad'i da
bai karbi komai ba, dan yanayin haka jama'a za suce dama abinda yasa yayi taimakon
kenan, duk da bansan yarinyar ba nasan dai tana da rawar kai, kana ganin idan ya
amshi wani abu daga mahaifinta zata yarda ya tank'warata a matsayinshi na mijinta?"
Mama ce tace "nidai wallahi a tsorace nake, dan zamanshi da yarinyar nan fa akwai
matsala."
"Kaifa kasan halin Umar Faruk da zuciyar tsiya, ina jin tsoron yanda zasu zauna
gaskiya ba tare da sun samu matsala ba."
"Kinga dan Allah, ki cire tsoro a ranki sannan ki bishi da addu'a, insha Allah
komai zaiyi daidai."
Cikin dariya Baba yace "ban gane kuma dai ba? kina ganin zamu zauna hakane ba muyi
komai ba bayan amaryar da muka samu a sauk'ak'e, kema kinsan dole za muyi koda
walima ce mu godewa Allah."
Abbakar ne yace "ina ga ayi walimar zaifi, kunga sai ayi wa'azi ma tare da musu
addu'ar zaman lafiya."
Suna fitowa Abbakar yaga matarshi a tsakar gidan tana shirin d'ora abincin rana ,
saida ya tsaya gabanta yace "ashe haka bakinki keda k'arfi, lallai Allah ya miki
baiwa, tunda gashi abinda kika fad'a ya faru."
Duk da gabanta ya fad'i dan bata fahimceshi ba haka tace "lafiya, meya faru, mena
fad'a kuma?"
Murmushi yayi yace "da zamu fita ba kince Umar faruk zai sace amarya ba ko a d'aura
dashi?"
Dariya yayi ya nufi kewayensu dake kusa da d'akin amaryar Umar Zuby😂yana fad'in
"dashi muka d'aura auren."
Wata irin bud'a ta rangada data sashi tsayawa cak yana kallonta, wato ita farin
cikinta ma harya kai haka, wucewa yayi ita kuma da gudu ta lek'a d'akin Umar daya
cire kayan jikinshi ya kwanta, amma ganinshi ba riga yasa ta dawo baya ta koma ga
aikinta.
Umar Faruk kuma in banda tunanin irin kuskuren da yayi babu abinda yake, ji yake
kamar fa ya sauke ma kanshi nauyin daya d'auka ya aza ba tare da an tilastashi ba.
Tunda kannanshi suka dawo daga islamiyya aka fad'a musu suma dai murna suke yayansu
yayi aure, nan kuma Mama ta siyo goro ta bawa yaran suka dinga rabawa makota ana
fad'a musu Umar ne yayi aure, haka ma a waya Mama tasa Rukayya da Ali suna kiran
yan uwa suna fad'a musu, wani yaji dad'i wani yaji haushi, dan ma ba'a fad'a musu
wacece amaryar, duk da a kurarran lokaci ne amma zama lafiya da mutane da Mama keyi
yayi tasiri sosai a yau, dan gidan turuwa aka dinga yi ana zuwa tayasu murna, Umar
Faruk kuma ganin ba za'a barshi ya huta ba yasa ya sake shiri ya fita zuwa gidansu
Ishaq dake kusa dasu.
*****************
Tunda Ruk'ayya ta kira tanti *Ma'u* (Mamar Zuby) ta fad'a mata ta fara bala'i tun a
waya, ganin haka yasa Ruk'ayya kashe wayar taci gaba da kiran wasu, duk da haka
bata hakura ci gaba tayi da masifa ita kad'ai Zuby kuma da taji meya faru kuka ta
fashe dashi, Mama ko nata bala'i ko sauraronta ba tayi ba, jin kukan nata yayi yawa
yasa tace,
"Dan ubanki rufe min baki kafin inci uwaki , yar banza kawai duk bake kika jawo ba,
Umar Faruk wace irin jaraba ce baiyi ba ki bari ayi aurenku amma kika k'i yarda,
waike sai kin gama jarabawarki, to yanzu gashi nan ya samu dama kuma yayi anfani da
damarsa, yanzu kafin wata biyu yayi a d'aura aurenki dashi ita lokacin ta fara
laulayin ciki, kinga ta riga ta tsere miki."
Zaby na jin haka ta sake fashewa da kuka tace "na shiga uku Mama, yanzu Umar faruk
saiya had'a jikinshi da wannan tsohuwar kilakin."
"Wayyo Allah, dan Allah Mama ki taimaka min wallahi ba zan iya jura rasa Umar Faruk
ba, Mama kinsan ina sonshi sosai, bana so wata ta rab'eshi ma bare harya had'a
jikinshi da wata."
"Uwarki ma, yo wane irin taimako zan miki? ai kin riga da kin cuci kanki."
"Dan Allah Mama kiyi hak'uri." kwance tayi tana kuka hakan yasa taji ba dad'i,
tadata tayi ta zauna tace "kwantar da hankalinki kinji, Umar fa d'an uwanki ne kuma
naki ke kad'ai, sai kinso ne zaki bashi dama harya kusanci wacce karuwar sauran
sojawa (da yake Zuby ta fad'awa Mama komai akan Khairat d'in tun ranar da Umar ya
d'aga mata murya akanta.)."
Murmushi tayi tace "idan da zaki yarda da sai nace a d'aura aurenki dashi ranar
juma'a da za ayi walima, to daga nan fa sai labari ya fara shan bambam."
Murmushi ne ya bayyana kan fuskarta tace "da gaske Mama, kina ganin Umar zai yarda
ya aureni ranar juma'a?"
"Umar Faruk d'in banza, ni uwanshi nake iko dasu, dan haka kwantar da hankalinki
tsaf za'a d'aura aukenku."
"Wallahi Mama na amince, danni bana so na rabu dashi."
"Ba zaku rabu ba, amma fa ki sani ba zaki tare a gidansa ba har sai munga kamun
ludayinshi a matsayinshi na me mata biyu, kinga zaki samu damar raba tsakaninsu ta
zaman da za kiyi anan, sauran karatun kuma na biya miki shi daga baya."
Alk'awari ta mata gobe za taje gidan ta sanar dasu halin da Zuby take ciki, dan
haka kawai a d'aura musu aure.
*********************
*Muzaffar* manyan duniya😂 wallahi dariya yake bani,😎 abokananshi na zuwa gidan
suka fara balbaleshi da masifa, wannan bai dameshi kamar da wani yace "dallah ku
rabu dashi, tunda shi bai aureta ai wani ya aureta ko."
"Kwarai, wani ne a cikin taron auren yayi *jihadi* ya rufa mata asirin da kai kake
kokarin tona mata, kuma yanzu Khairat ta zama *matar Umar Faruk*, dan haka zaifi
maka kaje ka samu mahaifinta danya biyaka duk abinda ka kashe a kanta."
"Kutumar uba, wane dan haune ya auri *matata*? wallahi k'aryane , babu wanda ya isa
ya auri Khairat ina raye, na riga dana tsara rayuwata da ita kuma ita kad'ai nake
tunani, dan haka dole a kwance wannan auren."
Ire iren irin wannan magnganun yake tayi duk suka watse suka barshi yana sambatu,
bai tab'a tunanin yana son Khairat haka ba sai yau daya rasata, dafe kai yayi da
hannu yace "na shiga uku, Basta ka cuceni, gashi banma san ina kake ba yanzu, Allah
ya tsine maka albarka shege tsinanne."😛
Yan uwa da iyayenshi takaicine ya hanasu zuwa inda yake, haka baki kowa ya tattara
kayanshi ya koma inda ya fito rai a b'ace, shi kuma damuwa ta mishi yawa saida ya
zubar da hawaye kad'ai yaji dama dama, haka ya wuni cikin d'akinshi bai fita ba bai
kuma cire kayan jikinshi ba har yayi bacci dasu tare da daukar dangana da komai
daya kashe akan Khairat amma ba da ita kanta ba, dan har yanzu yana ji zai iya
samunta tunda a tunaninshi tana sonshi.
******************
Gyara zama tayi ta kalli su Baba tace "to ni dama ba wani abu bane ya kawoni sai
maganar Umar faruk da Zubeida."
Rudududu yaji kayan cikinshi sun kada , yawu ya had'e ya daga kai ya kalleta, ci
gaba tayi da "tun jiya da Zuby taji abinda ke faruwa ta daga hakakinta da nawa, har
yau kuka take tak'i ci tak'i sha, daren jiya da zazzabi ta kwana gashi yau ma tak'i
hakura, maganarta d'aya shine zata rasa Umar Faruk, shine nace to da a tsaya haka
me zai hana a daura musu aure? tunda dai dama an gama komai lokaci kawai ake jira,
hakan zaisa ta samu tabbacin ba zata rasashi ba, amma shawara ce ya kuka gani?"
Mama da Baba tausayin Zuby ne ya kamasu saboda dole za taji ba dad'i saboda
shak'uwar dake tsakaninsu, da firgici ya kalleta yana tunanin girman maganar data
zo da ita, a ranshi ne yace "ni kum gidan uban wa zan kai mace biyu a wannan
qarnin, a zanyi dasu?"
_Umariri kenan,😂kafi kowa sanin yanda za kayi dasu idan ka gansu gabanka._
Baba ya amshi tayin data zo dashi yace ba matsala, kuma za'a d'aura auren ranar
juma'a, ita kuma tace ba yanzu zata tare ba sai bayan ta gama karatun, haka tanti
ta koma gida cikin farin ciki Umar kuma ya kalli Baba yace "amma Baba, mata biyu a
lokaci d'aya, duka ni d'in nawa nake da zan auri mace biyu, kuma idan suka tare ina
zan ajesu? gaskiya Baba nauyin yamin yawa ba zan iya ba."
"Haba Umar faruk, da jarumta fa akasan mai wannan sunan, karka bari mana mata su
baka tsoro da wuri haka, zaka iya da yardar Allah, kuma Allah zai baka yanda za
kayi dasu insha Allah, zai dubi zuciyarka ya taimaka maka wajen d'aukar nauyin ko
wacce."
"Maganar wuri kuma da kake, ai abune mai sauki, tunda itama Zubeida ba yanzu zata
tare ba, kaga ita Khairat d'in dake uwar gida saika ajeta acan b'angaren daka
gyara, d'akinka na yanzu kuma da muke tunanin saka k'annanka a ciki idan ka tashi,
sai a gyara Zubeida ta shiga ciki, abinda zasu ci kuma wannan Allah ba zai hanasu
ba, nasan za kayi k'ok'arin yin adalci a tsakaninsu, kuma zamu maka addu'a Allah ya
baka ikon yin adalci a tsakaninsu."
Mama ce tace "Allah ma ya yardar maka kafin lokacin da Zubeida zata tare ka mallaki
naka gidan na kanka."
"A'a." yana fad'a ya tashi jiki ba kwari ya shiga wanka ya fito ya shirya cikin
qananan kaya, fita yayi ya gidansu Ishaq ya sameshi kwance yana bacci, ware hannu
yayi ya kai masa duka, a tsorace ya farka yana ganinshi yace...
18/07/2019 à 13:08 - ~NANA KHADIJA~😍: 💑💑💑💑💑💑💑💑💑💑
*JIHADI*
_Umar faruk_
💑💑💑💑💑💑💑💑💑💑
_NA_
_SAMIRA HAROUNA_
_DEDICATED TO_
*MA FAMILLE*
_Bismmilahir-rahman-rahim_
1⃣9⃣
"Dallah malam tashi, wato kai duk girgizar qasarnan da ake baka ji kana nan kana
bacci, ni ina can cikin ibtila'i kai kuma hutawa ma kake."
Gyara zamanshi yayi yana murza ido yana fad'in "lafiya, meya faru?"
Saida ya zauna shima akan katifa sannan yace "akwai matsala fa mutumina."
Bushewa da dariya Ishaq yayi yace "ai koda kace yaran nan na fahimci da matarka da
kuma budurwarka kake, dan kasan mu maza ko mace ta girmemu muna so muce mata
yarinya."
Harara ya cilla masa yace "toni fad'a min a cikinsu wacece ta girme min? ka daina
ganin wannan da kabri ga kuma tsayi, wallahi ba zata wuce ashirin da uku zuwa da
biyar ba."
"Humm, nidai yanzu fad'a min me yake faruwa da kace akwai matsala? danni bana
tunanin abin nan zai fara damunka tun yanzu, tunda Zuby nanan tafe."
"To ai akan Zuby d'in ne, tanti fa tazo gida kuma sun gama magana akan za'a sake
wani d'aurin auren ranar juma'ar nan."
"Juma'a kuma? amma me yasa zasu mai dashi juma'a? bayan wata biyu ne nan gaba."
"Kaima kasan halin tanti, wallahi ni nasan dagangan tayi haka, kawai akwai bala'in
da suke so su kunno min shi yasa tayi haka."
"Ai kuwa in hakane wallahi saika tashi tsaye, ka nuna musu kai namiji ne na gaske,
dan inba haka ba sai kazo ka rasa yanda za kayi, wata rana ka kwana d'akina wata
rana kuma kaje wajen Mama kana hawaye."
"Wa? ni Umar zanyi kuka akan mace tamin wani abu, ai kaima kasan halina, duk wacce
tamin ba daidai ba wallahi daidai nake da ita, tsaf zan zane yarinya."
Dariya Ishaq yayi yace "sai dai Zuby, amma Khairat ba zata daku a hannunka ba."
"Wai wasa kake dani ko? gani kake tafi k'arfina ne? ai kuwa za kasha mamaki, dan
sai nasa yarinyar nan tayi laushi fiye da tunaninka."
"Allah yasa, dan in haka ta faru kaine za kafi kowa cin moriyar hakan."
"Kai, karfa ka d'auka wata rayuwar jin dad'i zanyi da ita, taimak...."
Ishaq ya katseshi da "bana son cika baki mutumina, bari ya shigo tukun muga iya
gudun ruwanka, nasan mata kuma zata iya canza maka tunani cikin qanqanin lokaci,
dan haka bari har naga tafiyar taku sannan."
Tashi Ishaq yayi ya d'auki doguwar rigarshi yasa ya d'auki maclean da brush zai
fita yace "ka jira na fito saina rakaka wajen amarsu."
Dan k'uwa ya masa yace "amaryo ba amarsu ba."
Yana ganin ya shiga shima ya fito zai tafiyarsa ya had'u da Baban Ishaq zai fita
shima, har k'asa ya zube ya gaisheshi ya amsa cikin sakin fuska tare dasa masa
albarka, sannan ya d'ora "jiya sai mu kaji abin alkairi, gaskiya ka kyauta Allah ya
maka albarka ya taimakeka a duka al'amuranka, saura wannan sakaran shima kasa ya
samu mata yayi aure."
Dariya kawai yayi ya tashi tsaye shima tsohon ya wuce, saida ya koma gida ya d'auki
mashin d'inshi sai dai bansan ina ma zashi ba, yau *lahadi* yau ne dama suke hutu a
wajen aiki, mashin d'inshi ya tuk'a bai zame ko ina ba sai gidansu Zuby.
Taji dad'in ganinshi amma kishi yasa ta kasa bayyanawa, d'aki ta shige ta barshi
zaune gaban tanti, ganin haka yasa tantin tace "tashi ka wuce ka sameta mana, gidan
ai ba bak'onka bane."
Yana wucewa ta bishi da harara, zaune ya sameta a bakin gado ta had'e hannaye,
zaune yayi kusanta yana kallon fuskarta, sun jima a haka kafin ya sake kallonta
yace "amaryata hushi take dani?"
Da mamaki ta kalleshi tace "lallai ma yaya Umar, yanzu daga d'aura auren naka
shine harka kaini matsayin amarya tun ma bata tare ba a gidanka? lallai da
matsala."
Shima dai da mamakin ya bita da kallo, taushe zuciyarshi yayi yace "ko da ita ko ba
ita, ke amaryata ce kuma kinsan haka."
Hawaye ne suka ciko idonta ta kalleshi tace "wallahi yaya Umar ni dama tun ranar
daka d'aga min murya akan banzan yarinyar nan nasan kana sonta, kawai raina min
hankali kayi ka nuna ba komai, shine yanzu wai za'a ce ta zama matarka ta farko
bani ba, bayan lokacin da muka d'auka muna tare da kai, wallahi kaci amanata yaya
Umar, tunda muke da kai ban tab'a kallon wani a matsayin saurayi ba na kare maka
kaina,amma shine kai ka kasa hakan, dama ku maza h......"
"Mu maza me? mayaudara ko maciya amana? kinga ki hukuntani ni kad'ai saboda ni miki
laifi, amma karya shafi kowa, sannan ni kaina bana jin abinda nayi laifine, saboda
ni namiji kuma *mijin mace hud'u*, saboda nayi ta farko kuma zan aureki a matsayin
ta biyu ni banga wani aibu a ciki ba."
"Sannan kinsan abinda ke tsakanina da ita, so bashi ya sani nayi abinda nayi ba."
Cike da rashin wayo tace "ba wani nan wallahi, idan da gaske taimakonta kake son
yi, meya hana ka rok'i yaya Abbakar ya aureta, ko kuma shi Baban ya aurrr."
Qamewa tayi ta rintse ido tana jiran taji saukar hannun, Umar faruk kam daya d'aga
hannu zai wanketa da mari tsayawa yayi saboda tunawa a cikin gidansu yake, nunata
yayi da hannu yace "maganar data shafi ni dake, karki sake saka iyayenmu a ciki,
idan ba haka ba ranki zai dinga b'acewa."
D'orawa yayi da "karki kuskura kice zaki raina min mata bare iyayena, ita ke gaba
dake kuma dole ki bita in har kina son zama dani, in kuma ba haka ba to mu hak'ura
da junanmu, dan duk abinda zai shafi mutuncina bana k'aunarshi, a yanzu kuma itace
tabbas d'ita tunda ta shiga hannuna , kuma kare mutuncinta yana wuyana ne, dan haka
ki kiyaye, sannan idan kin shirya aurena to ki shirya dabarun zama dani lafiya."
Yana fad'a ya fito daga d'akin yayi wa tanti sallama yayi gaba ranshi na quna , wai
tun yanzu kenan za'a fara caza masa kai, sai lokacin kuma ya dinga tunano abinda ya
fad'a mata akan Khairat, duk da ba sonta yake ba amma yaji dad'i dan ko ba komai
dai dole ya kare mutuncin kowace a cikinsu idan har suka zama nasa dukansu.
*****************
Khairat na bacci ka tasheta saboda bak'i na shirin tafiya, sallama suka dinga mata
ana sake mata addu'a Allah ya bada zaman lafiya, ita kuma tana yak'e tana amsawa da
ameen ameen 😁, har suka gama tafiya ya rage sai Mammie a gidan, bayan sallah
azahar suka tafi da Hibba salon aka cire mata akaihun data saka dogaye da kuma
gyaran da aka mata aka aka gyara mata aka mata kitso manya, bayan la'asar suka dawo
gida tayi wanka tayi sallah taci abinci, ita da kakarta sai farin ciki suna hira
cikin nishad'i.
*Bayan sallah magrib* Papa ya tafi masallaci d'aukar karatu, kamar kullum saida
sukayi sallah isha'i aka sallami kowa, anan Baba ya tsayar da Papa ya fad'a masa
maganar auren Umar faruk, farin ciki Papa yayi tare dasa albarka kuma yace zasu
halarci d'aurin aure insha Allah.
Bayan yazo gida ya fad'a ma Mamie da Mammie, Mamie ce kawai tace "Allah ya basu
zaman lafiya ya basu hak'urin zama da junansu, a fad'a mata kawai tasan halin da
ake ciki."
"A'a." cewar Papa sannan ya d'ora da "ba hurumin mu bane, ki bari mijinta zai fad'a
mata da kanshi, shi yasan ta yanda zai tarota."
"To shikenan, amma ni dai wallahi ina son yaron nan sosai, dan nasan shi kad'ai ne
zai iya tafiyar da Khairat a matsayin miji, kuma ina ji a jikina zata gyaru ta
dalilinshi ne insha Allah."
Papa ne yace "nima yaron ai ya kwanta min a rai sosai, dan ba kowa bane zai iya yin
*jihadin* da yayi."
"Sosai kam, dan da yanzu bamu san halin da muke ciki ba dukanmu, nadai tabbatar
bama cikin yanayin dad'i." cewar Mammie.
Dariya Mamie tayi tace "ai yaron kirki ne kuma ya samu tarbiya, tunda ba shine karo
na farko ba daya taimakemu."
"Kin sanshi dama? wane irin taimako yayi mana?" inji Papa.
"Shine fa yaron daya je asibiti yana son ganinka, wanda ni na fito na ganshi kuma
shiya fad'a min inda aka samu masu laifin nan, kaga ba danshi ba da yanzu muna nan
tare dasu."
"Allahu Akbar, lallai ya mana taimako, babu abinda zamu saka masa dashi sai dai
addu'a da fatan alkairi, Allah kuma yasa kar yarinyar nan ta bamu kunya."
Mamie ce tace "ameen, amma dai nasan zaiyi wuya a samu sauk'in al'amari daga wajen
Khairat."
"Allah yasa."
*Haka* aka dinga tafiyar da rayuwar ba dad'i ba wuya, Khairat rayuwarta take
kamar babu auren kowa a kanta, sai dai Mamie ta hanata fita ko k'ofar gida, itama
kuma bata damu ba tunda tana sakewa a cikin gidan, zuwan Mammie ya sata farin ciki
sosai kullum suna tare suna shirmensu kamar yanda suka saba.
Sai dai kuma har yau basu had'u da Umar Faruk ba, kamar yanda basa da lambar juna
bare wani ya kira wani, sau d'aya yazo da sassafe tana bacci, yace agaisheta kawai
zai dawo har yau kuma bai koma ba.
*****************
Umar Faruk ma shirye shiryen wani sabon auren yake tayi hakan yasa ma baya da
lokacin kanshi sosai, sai dare yayi kuma sai Khairat ta sallamo mishi ta hanashi
bacci, tunaninta na takura masa yana hanashi sukuni sosai, wani lokaci har yakan
manta da Zuby a rayuwarshi saboda katutun da Khairat tayi a zuciyarshi.
*Kwana hud'u* yau da auren, Mamie ta tura Mamar Hibba da tanti Safiya gidansu Umar
Faruk ganin d'akin Khairat, su kad'ai ne ta yarda dasu da kuma hallayarsu shi yasa
ma ta turasu su kad'ai, sunje cikin aminci kuma sun dawo cikin farin ciki saboda
tarbar da aka musu, sun fad'ama Mamie komai akan gidan dama d'akin inda tanti
Safiya ta qara da cewa "gaskiya rayuwa dai ta mai qaramin k'arfi, to wannan d'akin
na Khairat ya ishi bawa rayuwa kuma cikin farin ciki."
Sai dai Mamar Hibba tace "amma ko kad'an kayan da aka saka mata a d'akin Muzaffar
ba za suyi a wannan d'akin ba."
Hakan yasa Mamie turawa aka d'auko kayan Khairat daga gidansu Muzaffar aka sasu
kasuwa, a take kuma aka siyo mata wasu sabbi yan zamani masu bala'in kyau, *ranar
alhamis* aka mata jere a d'akinta, masha Allah yayi kyau sosai duk da d'aki d'aya
ne amma zai birge, haka yan gidan suka lek'a suka ga d'aki yayi tsaf dashi, ga
kayan kallo da aka lak'a mata panka da k'aramar fridge, matasan kujeru ne aka aza a
d'an k'aramin farfajiyar kewayenta , sai babbar kujera a cikin d'akin ta zaman
mutun uku, saman wradrob kam cike yake da manyan darori da bargo , ciki kuma bayan
kayan jiki sai kwanoni da sauran kayan aikin gida, a kusa da taga ma wasu darorin
ne aka jerasu har suna kusan tab'a rufin d'akin saboda yawa, haka aka rufe d'akin
ana jiran asabar tayi maishi ta shiga.
Duk wani abu da Muzaffar ya kawo saida Khairat ta tabbatar ta mayar masashi a cikin
akwatinshi, duk wani abu data d'inka saida tasa aka nemo irinshi sannan tasa aka
mayar masa, kamar dai yanda yayi itama motoci ta samu suka kai kayan har gidansu,
had'e kuma da makullin motarshi, tunda yaga haka ya tabbatar da aikin Khairat ne
ma'ana tayi hushi kenan, bai k'ara tsinkewa da al'amarin ba saida ya bud'e k'aramar
motar ya samu goron daya bada da kuma enveloppe, yana bud'awa yaga kud'i ne a ciki
kamar yanda ya bada, sai kuma k'aramar takadar data rubuta wasik'a da harshen
french cewar,
_"Bani ba kai, ba kai bani har abada, yunk'urin sake shigowa rayuwata a karo na
biyu, daidai yake da yak'in duniya na uku, dan ba shakka yak'i ne zai b'arke
tsakanin gidanmu da gidanku, *K'ARAMIN MUTUM* kawai._
Hawayen da yaji suna son zubo mashi yasa ya koma cikin gida ranshi b'ace,
hamshak'iyar mahaifiyarshi dake zaune a d'akinta tana waya ya fad'a saman jikinta
yana kuka, kashe wayar tayi tare da tureshi daga jikinta cikin jin haushi tace
"dallah ni dagani shashasha kawai, kasan kana sonta uban wa ya aikeka d'aukar zigar
aboki ana daf da d'aura aurenka? kawai saboda rashin tunani da lissafi saika yarda
da abinda ya fad'a, yanzu gashi har yau bai sake zuwa inda kake ba, tunda burinshi
ya cika."
Ganin mahaifiyar tashi ma ta d'auki zafi yasa ta tashi ya fita ya koma b'angarenshi
zuciyarshi kamar zata buga.
****************
Tun ranar Umar Faruk bai sake zuwa gidansu Zuby ba bai kuma kirata ba, shirin
d'aurin auren kawai yake yi amma sam ya daina jinta a cikin ranshi, musamman idan
ya tuna abinda ta fad'a masa, haka kawai yake jin ba dad'i idan ya tunata yafi
farin ciki kawai idan yana tunanin Khairat wacce yake da yak'inin ko sau d'aya bata
tab'a tunaninshi ba.
*Yau juma'a* gidan an tashi da shirye shirye da kimtse kimtse, kamar yanda muka
sani lokaci na gudu, dan-danan sai aka fara tafiya masallaci, bayan gama sallah
kuma aka sake d'aurawa Umar Faruk wani auren, *Umar Faruk Ahmad Adam* da *Zubeida
Hamza*, daga masallaci gidan wani abokinshi *Abdul Azeez* suka wuce inda akasha
gara tare da tayashi murna, Ishaq dai dariya yake masa duk lokacin da suka had'a
ido dashi saboda tamke fuskar da yayi, bidiri sosai abokanshi suka shirya wanda ya
kaisu har magrib, suna sallah kuma suka dawo gida inda aka fara shirin walima.
Shiryawa yayi cikin wata sabuwar shadda ruwan toka had'e da takalma sai dai bai
d'ora hula ba, yana fitowa ya samu taro harya fara cika, Abdul Azeez ne ya takura
masa ya rakashi asibiti yanzu aka kirashi ankai kakarsu ba lafiya, jin uzurinshi
kuma tunda bai nemi kowa ba saishi yasa suka shiga mota suka tafi.
****************
*Amarya Khairat* ce zaune a falo a saman qafafun Mammie tana latsa wayarta, kirane
ya shigo ta d'auka da "hello macho."
"Kai Khairat, kina b'ata mana lokaci fa, asibiti zamu wuce tare da Farida muke."
Mik'ewa tayi daga jikin Mammie ta d'auki kallabin doguwar bleue rigarta ta d'ora a
kai tace ma Mammie "su Rashida ne waje wai asibiti zasu, bara naje naji kiran me
suke min."
Tana fita Mamie ta fito cikin shirin tarban Papa, zaune tayi tana fad'in "ina ta
shiga kuma?"
Zunbur Mamie ta tashi tace "Rashida? na shiga uku, nifa bana qaunar yarinyar nan,
wallahi ita ke qara lalata min yarinya."
K'ofa ta nufa Mammie na kiran "ina kuma za kije? yanzu zata dawo fa."
K'ofa ta nufa tana fad'awa mai gadi "kai duba min Khairat, maza ce nace ta shigo
ciki."
Dafe kai Mamie tayi tace "na shiga, ina zasu je kuma? me zan fad'awa mahaifinta?"
Dawowa tayi tace "Mama kin gani ko? Khairat bata nan wai sun fita."
Kafin Mammie tayi magana ta d'auki wayarta ta fara kiranta, Khairat kuma da tana
fita ta samesu a cikin taxi Rashida ce tace "yawwa zo muje."
Ta fad'a tana matsa mata nufin ta zauna, "ina kuma zanje bayan kinsan ba'a barina
fita?"
"Kinga asibiti zamu je k'anan Farida ne ba lafiya, dazu aka kaishi ya k'one da
ruwan zafi, kizo muje yanzu zamu dawo daga nan sai muyi magana."
Hannunta ta janyo ta fad'a cikin taxi d'in suka ja suka tafi, ba suyi nisa ba kuma
kiran Mamie ya shigo wayarta, tana d'auka Mamie tace "kina ina?"
Da sauri Mamie tace "amma kinsan ba kya fita ko ina ko? me yasa zaki fita haka
kawai, idan mahaifinki ya dawo ya zance masa?"
Tana fad'a ta kashe wayar ta kalli Rashida tace "wace magana za muyi?"
Kallon juna sukayi kafin Rashida tace "am Khairat, wallahi mutuminki yana cikin
wani hali, yana buk'atar taimakonki sosai."
Farida ce tace "Muzaffar mana, kinga yanda ya koma saboda damuwa, wallahi sai
addabarmu yake wai mu taimaka masa."
"Yanzu dama akan maganar waccen banzan ne kuka saka na baro gidanmu ba tare da
izinin kowa ba? kinga tsayar da mai taxin nan na koma gida in dai wannan ce
maganar."
Rik'eta sukayi suna fad'in "kinga shikenan to, ba zamu sake miki maganarshi ba, yi
hak'uri."
Harara tabi kowace a cikinsu tana fad'in "aikin banza kawai, mutumin daya ci min
mutunci har zaku wani zomin da maganarsa , shi bai fad'a muku ba komai tsakanina
dashi ba, ko sile baya bina bare ya takura min, mak'uddan kud'ad'e na kashe wajen
biyanshi abinda ya min."
Babu wanda sake magana har suka isa asibitin suka duba yaron da qafarshi ce kad'ai
ta k'one sannan suka tashi zasu koma, bayan mahaifiyar Farida ta gargad'eta akan ta
kula da gida da sauran k'annanta, fitowa sukayi suka tsaya a bakin titi suna jiran
samun taxi.
*Umar faruk* ne suka fito zasu tafi suma sun shiga mota suka tayar, bakin titi suka
tsaya suna so kai kawon motoci ya tsagaita su samu su hau titi suma, a cikin waige
waigen da suke sai kuwa Abdul Azeez yace "masha Allah, abokina da alama nima
lokacin aurena ya kusa, domin kuwa naga wacce tamin."
Haka kawai sai Umar Faruk yaji gabanshi ya fad'i, daurewa yayi yace "toh , wace mai
sa'ar ce wannan?"
Sai lokacin Umar faruk ya kai kallonshi ga yan mata ukun dake tsaye, hakan yayi
daidai da Khairat ta juyo saboda motar dake bayansu ba haskesu sosai, saida ya
rintse ido saboda takaici da bak'in ciki, sam fitowa bada izininshi bai dameshi ba
kamar rigar dake jikinta.
Duk da bata kamata ba amma da yake tana da 'yar k'iba kuma yadin rigar yadine mai
bin jiki, hakan yasa ya hango shatin kwanciyar pants d'inta da kuma bras d'inta, ga
kuma kallabin k'aramin hakan yasa gashinta ya fito har ya kusan rufe shatin bras
d'inta, duk da dai baida tabbacin gashin kanta ne, ranshi ya b'ace sosai musamman
da abokin nashi ya haskesu da mota yana mata kallon k'wak'waf, dan suma k'awayen
nata duk shigar tasu babu mai dama dama a cikinsu.
A fusace ya fita daga motar ya tsaya bayanta ba tare da yayi magana ba, jin kamar
mutum a bayanta yasa ta juyo dan ganin wane d'an rainin wayone, a take gabansu ya
tsinke ya fad'i sai kallon kallo da sukewa juna, kasa magana tayi dan har cikin
zuciyarta taji bata ji dad'in ganin daya mata a haka ba, kasa d'auke idonta tayi
daga kanshi shima kuma haka.
Had'iye yawu tayi ta kalli Rashida, muryarshi ta dawo da ita da yace "wuce muje."
Kallonshi tayi amma wani irin bala'in kwarjini daya mata sai yasa ta nuna su
Rashida da hannu, wani sabon kallo daya mata da idonshi fuskar nan ba hasken annuri
ya sake cewa "wuce muje gida."
"Amma ai....."
"Nace ki wuce mu tafi ko." tsawar daya mata yasa ta kama hanya ba shiri , ganin
haka yasa yabi bayanta ya bud'e mata bayan motar ta shiga, tana kallonsu Rashida
suka wuce suka barsu, su kuma mamaki suke ko wanene shi, Farida ce tace "nifa ina
tunanin ko shine mijin nata."
"In kuwa shine gaskiya yarinyar nan mai sa'a ce, danni kin sanni fa ina son namiji
irin wacce wallahi, da irinsu sunfi dad'in harka.
Farida ce tace "ki daibi a sannu, dan kinsan yarinyar can ta fiki akuyanci, mijinta
kuma yafi k'arfinki."
******************
Tunda suka d'auki hanya babu wanda yace tak , tafiya kawai suke Abdul Azeez kuma da
kanshi ke kulle bai samu damar magana, dan yasan tabbas akwai wani abu a qasa
saboda yanda yaga Umar faruk ya mu'amulanci Khairat d'in yasan ba sanin yanzu bane
a tsakaninsu, Khairat kam tayi iya k'ok'arinta wajen ganin gabanta ya daina fad'uwa
amma ta kasa, kamar yanda Umar faruk kejin haushinta da takaicin aurenta da yayi, a
haka suka isa gida da kanshi ya fito ya bud'e mata k'ofar ta fito babu wanda ya
kalli wani, izuwa yanzu kuma Abdul Azeez ya gane kuskure yayi dan ko ba'a fad'a ba
wannan itace 'yar Mani Bukar.
Wucewa tayi zata shiga shima yabi bayanta, tana daf da shiga gidan yace "kina
haukane da kika da wannan kayan a jikinki, sannan da izinin wa kika fita?"
_NA_
_SAMIRA HAROUNA_
_DEDICATED TO_
*MA FAMILLE*
_Bismmilahir-rahman-rahim_
😭😭😭😭😭😭😭😭
_ALLAH KA SHIRYA MANA YARANMU MAZA DA MATA, ALLAH KA BAMU IKON TARBIYANTAR DASU,
AL'AMARIN NAN YA FARA BANI TSORO WALLAHI, YARA QANANA SUN D'AUKI D'ABI'A MARAR
KYAU, WASU GANI SUKE WASU KUMA YIN KANSU NE KAWAI, ALLAH UBANGIJI KA KARE MANA
'YA'YANMU DAGA B'ATA GARIN ABOKAI, ALLAH KA BAMU IKON KIYAYE DUK WANI ABU DA ZAI
HASKU A IDON 'YA'YANMU HAR SUYI SHA'AWAR KWAIKWAYA._👏👏
😭😭😭😭😭😭😭😭
2⃣0⃣
"Ban gane ba, me kake nufi, me kayan jikina sukayi, wai ikone zaka min tun ban tare
gidan naka ba? ina ruwanka da kayan jikina to? kana da matsala da hakan ne? karfa
kace zaka rainani saboda kaji ance an daura mana aure, wallahi ba dauka zanyi ba
kaji na fad'a maka, haka kawai zaka wani tsareni harda tambayar wai da izinin wa na
fita, bayan a gidan mu nake har zaka min wannan tambayar, ko kana ganin iyayena
basu da ikon da zasu bani damar fita? to in dai kai zan dinga tambaya kafin na fita
da sai dai karna fita har abada, dan ba zan iya qasqantar da kaina har haka ba,
kuma wallahi ka fita idona, kar kace zaka sake min irin tsawar da kamin d'azu
musamman a cikin mutane, in kuma ba haka ba."
K'wafa tayi mai k'arfin gaske ta juya zata shiga gida, wata fizgowa ya mata saida
ta kai mashi karo a qirji, turata yayi ta kaima bango karo ya mata runfa da
faffad'an jikinshi, kafeta yayi da ido sunyi ja saboda zafin maganganunta fuska a
d'aure ba alamar wasa cikin dakakkiyar murya yace "waye ni?"
Cike da tsiwa tace "waye fa daya wuce d'aya daga cikin gama garin mutane."
"Nace waye ni a wajenki?" tsawar daya mata har saida mai gadi ya leko, amma ganin
Khairat da angonta yasa ya koma, ita kam yanda muryarshi ta daki k'ok'on kanta yasa
ta zabura da k'arfi tare da fashewa da qara har wayarta ta sub'uce ta fad'i,
hannayenshi yasa a jikin bango kamar zai rumgumeta ya sake tsareta da ido yace "ina
jiran amsarki."
A hankali ta daga idonta ta kalleshi amma sai hawaye suka zubo mata, kau da kai
tayi ta sauke ajiyar zuciya ba tace komai ba, sake matso da kanshi yayi daf da
fuskarta yace "zamu kwana anan in har baki fad'a min ba."
Cikin daga murya da jin zafi tace "to waye kai? me kake so nace? so kake nace
*mijina*? to naji kaine *Umar faruk mijina*, shikenan? to kauce min a hanya zan
wuce."
Wani d'an iskan murmushi yayi mai kama da kuka tare da fad'in "humm." kafin yace
"daga yau ina so na dinga jin muryarki k'asa da tawa, idan kuma kika bari k'uruciya
da hauka irin naki yasa kika d'aga min murya, to ki kuka da kanki, dan zan miki
abinda kaf a tarihi babu wanda ya kwatanta yi miki shi."
Sunkuyawa yayi ya d'auki wayarta ya dangwara mata a hannu sannan ya juya ya shiga
mota tana kallonshi har suka b'acema ganinta, juyawa tayi ta shiga gida kamar zata
tashi sama, har Papa na falo suna jiran dawowarta, a tare suka mik'e ganin ta shigo
da sauri tana share hawaye, Papa ne ya fara tambayar "shalele lafiya, meya faru
kike kuka."
Mammie ma d'orawa tayi da "shalele meya sameki, wani abu aka miki?"
"Ya zaki ce ba komai? bayan kin fita cikin farin ciki kin dawo kina kuka, kuma an
fad'a min wad'ancen yan iskan yaran ne suka fita dake."
Ganin zasu takurata yasa tace "Mamie ba komai fa, tare dashi muke."
Fuska kowa ya saki yana murmushi har Mammie tace "to kuma a waje kika baroshi?"
_Abinka ga manya_ duk sai sukayi tunanin ko zaman da tayi na sati d'aya ne yasa ya
gagara hak'uri, shi yasa suka fita ya d'an rage zafi, 😂 masu hangen nesa kenan,
wannan hasashen naku ba yau ba ba kuma gobe ba.
Cikin b'acin rai da bak'in cikin abinda Umar Faruk ya mata ta shiga wanka ta fito
ta shirya cikin rigar bacci doguwa, dole ta toshe kunnuwanta da abin sauraro danta
rage zafi.
*******************
Tunda suka d'auki hanya babu wanda yayi magana, amma saboda ya nuna masa baisan
komai ba yasa Abdul Azeez cewa " *wacece ita*?"
Kamar ba zai amsa ba amma kuma ba tare daya kalleshi ba yace " *matata ce*"
Shiru yayi dan duk wata magana da zaiyi yanzu zai iya janyo b'acin rai fiye da
yanzu, har suka isa babu wanda ya sake magana, suna zuwa tuni taro yayi taro *ustaz
Khalid* nata bada wuta, nan ya fara gaishe da malamanshi da uwaye da kuma kakanni ,
tare da sake miki gargad'i da nasiha akan rik'e adalci da gaskiya, wuri ya samu ya
zauna kamar mai sauraron abinda ake amma a gaskiyar lamarin ba haka bane, harya
fara hango irin rayuwar da zaiyi a tsakanin d'akin Khairat da d'akin Zuby, Zuby
akwai k'arancin wayo, Khairat kuma da wayonta zata b'ata maka rai, amma dole ya
d'auki matakin gyara tun kafin lokaci ya k'ure masa.
****************
Zuby ce tsakiyar aunyt's d'inta guda uku, sun gama zigata tare da hure mata kunne,
sun cire mata soyayya da tausayin Umar Faruk a ranta tun kafin aje ko ina, tilasta
mata sukayi ta kurashi ta bashi hak'uri akan abinda ta masa, saboda akwai wani
magani da suka siya mata, kuma dole aiki dashi sai suna shiri dan suna son ya
kusanceta, wayar ta d'auka ta kirashi lokacin yana tsaka da tunani, yayi mamakin
ganin kiranta sosai dan abune da bai tab'a faruwa ba suyi fad'a ta kirashi sai dai
shi ya kira, dauka yayi baice komai ba, cikin taushin murya tace,
Cikin shagwab'a tace "kenan ba zan samu ko wane irin suna daga gareka ba?"
Murmushi tayi yace "ina tsoron nace amaryata kuma kiyi hushi ne."
Cike da wayencewa tace "ba komai yayah Umar, ka kirani amarya zan amsa, tunda aunty
Khairat ta rigani zama taka."
"A'a, har yanzu fa babu wacce ta shigo hannuna, dukanku dai ina jira ku gama
wainani sannan ku shigo gidan."
Haushi ne ya kamata danta lura soma yake Khairat ta shigo gidan bayan yace taimako
yayi, shi kuma baya so ne ya bada wata k'ofa da zata sa Zuby ta raina Khairat
musamman ace ta dalilinshi, koba komai itama matarshi ce kuma uwar gida, a dak'ile
tace "dama na kirane na baka hak'uri abisa abinda ya faru, dan Allah ka yafe min ba
zan sake ba."
Haka taro ya tashi lafiya bayan addu'o'in da aka zuba musu, dare yayi kowa ya
kwanta amma banda Umar Faruk, a qarshema d'akin Khairat ya bud'e ya shiga, fitilar
d'akin ya kunna a hankali ya dinga sauke numfashi saboda wani baqaraken k'amshi
dake shigar hancinshi, had'e yake da kamshin turaren wuta da kuma turaukan dake
zube a saman coiffeuse da mayuka har babu wurin aza wani abun, bin d'akin yake da
kallo ko ina yana kallon irin kayan da aka cika d'akin dashi, wai nan danma yana
ba'a samu irin wurin da ake so bane, kusan komai na d'akin pink couleur ne hakan
yasa yace "da alama shine couleur préféré (best coulor) d'inta."
A sannu yake tunanin ranar daya fara shiga d'akinta yana fad'in "girman d'akinta
shine kaso d'aya na bisa ukun gidan nan, girman gadonta kuma d'akin nan ba zai
daukeshi ba, duk da banga ban d'akinta ba, amma na tabbata ta kusa girman d'akin
nan."
Ajiyar zuciya ya sauke tare da sakin murmushi yace "taya zata iya rayuwa a d'akin
nan? bayan gashi tagar dake akwai ma kaya sun rufeta, taya zata iya rayuwa da
wannan pankar? bayan acan ac take kunnawa , taya zata iya rayuwa a gidan nan da
mutane haka? bayan ita acan ita kad'aice ba k'ane ba k'anwa ba yaya ba aunty."
********************
*A b'angaren* tunda aka tashi da safe ta tashi jiki ba k'wari, gashi Mamie ta kira
mai kitso amma sam tace bata so, ayi juyin duniya tace ba taso dole aka barta, da
qyar ta bari aka mata jan lalle tunda waccen ya goge dan jikinta baya da kama
lalle, duk da mutanen da suka zo dan rakiyar amarya Papa yace sam bashi ba wannan
bidi'a, dan haka da kanshi zai kai yarshi gidanta tare da rakiyar kakanninta.
Abin yama Khairat yawa dan haka tun yamma ta fara kuka, amma sai tace musu kukan
rabuwa ne dasu, haka akayi magrib akayi isha'i, ba wani shiri tayi ba atamfa ce ta
zabga riga da zane d'inki simple, kasancewar bata tab'a saka zane simple ba saiya
mata kyau d'as, Mammie da Hajia *Maryama* ne suka kamata Papa da kanshi ya tuk'a
mota suka nufi gidan amarya bayan d'an jan kunne da Mamie ta sake mata, sai bayan
fitarsu Mamie kuma ta fashe da kuka saboda tunanin rayuwar da yarta za tayi a gidan
yawa.
Kasancewar a gidan Baba Papa ya koyi *sunna* hakan yasa basu tarar da wasu 'yan
tarban amarya ba bare abincinsu, mutanen gidan ne kawai kuma yara na islamiyyar
dare dan haka sai uwayen, tarba aka musu sosai tare da Baba aka musu iso zuwa
d'akinta, Papa ne ya kama hannun Khairat ya zaunar da ita bakin gado sannan ya
zauna zauna kujerar dake kallonta, su Mammie ma zaune sukayi kusa da ita kafin Papa
ya kalli Baba yace "surukin namu yana nan? ina so zan d'anyi magana dashi."
"Ba damuwa, ina jin ai baiyi nisa ba, bara na dubo muku shi." Baba ya fad'a tare da
fita waje.
A gidansu Ishaq aka kira Umar Faruk tun saman hanya gabanshi ke faduwa, haka ya
shigo cikin gidan har kuma d'akin, Papa ne ya masa nuni daya zauna kusa da Khairat,
kallon Papan yayi ya kalli wajen da zai zauna sannan ya matsa a hankali ya tsoma
k'ugunshi, duk da fuskarta a rufe take da mayafi amma sai yake ji a jikinshi
hararanshi take, kuma kuwa hakane😂dan bayan harara harda murgud'a baki da
gunaguni.
Papa ne ya fara da "Umar Faruk, ga Khairat nan, mun kawo maka ita, kuma amana muka
baka, muna fatan zaka rik'e mana ita abisa gaskiya da amana, Umar Faruk na yarda da
kai, bana jin akwai ranar da zata zo ka bud'i baki ka gorantawa Khairat akan
taimakon daka mana, ka sani Umar Faruk akwai ranar da Allah zai tashemu kuma ya
tambayemu yanda muka zauna da iyalenmu , kayi adalci a tsakanin matanka domin hakan
ne kad'ai zaisa ka samu rabo a ranar gobe k'iyama, kasan wani abu Umar Faruk, ba
wai gaggawar aurar da Khairat bane muke da har yasa muka baka ita a waccen ranar,
kawai dai na yarda da tsatson daka fito, kuma ina da yak'ini akan tarbiyar daka
samu, ina son Khairat sosai fiye da komai a duniya, domin ita kad'ai na mallaka,
bawai ina son zamanta anan bane dan nasan dole kafin ta saba zata sha wuya, amma
darasin da zata koya a zamanta anan d'in shine yafi min komai dad'i, dan nasan
*tarayyarku* zata zamar mana alkairi."
"Daga qarshe kuma, ina sake jaddada muku da kuyi hak'uri da junanku, Umar Faruk,
akwai abinda ya kamata ka sani a game da Khairat, tana fama da wata muguwar rashin
lafiya wacce idan ta taso mata takan shiga tsakanin halin rayuwa da mutuwa, duk da
ince kusan nine silar wannan rashin lafiyar, amma dai a yanzu ina fatan kai ka zama
maganin wannan cutar, wacce damuwa da kad'aici ne suka janyo mata ita, da fatan
zaku zauna lafiya, Allah ya muku albarka, Allah ya baka abinda zaka ciyar da
matanka, Allah kuma ya baka ikon yin adalci a tsakaninsu."
"Insha Allahu Baba zanyi k'ok'arina wajen kawar da kowace damuwa a tare da ita."
cewar Umar Faruk yana satar kallonta.
Murmushi Papa yayi yace "Allah ya baka iko , ke kuma baki ce komai ba?" inji Papa
yana kallon Khairat.
A hankali ta d'ago da kanta tana d'aga mayafinta tare da kafe Umar Faruk da ido,
shima ita ya kalla amma ganin kallon da take masa bana arzik'i ne yasa ya kawar da
kanshi, maida kallonta tayi ga Papa tace "nayi muku alk'awarin zama dashi...." sai
kuma tayi shiru ta sake kallonshi, sai dai shima a lokacin ya kafeta da ido yana
jiran yaji me za tace, ba tare data d'auke kai daga gareshi ba tace "har abada."
Wani irin farin cikine Umar Faruk yaji ya mamayeshi ba tare da yasan dalili ba, su
kaka kuma hak'uri dai suka sake jaddaja musu suyi da junansu, nan suka tashi zasu
tafi Umar ma ya mik'e dan rakasu, da gudu Khairat ta k'arasa ta rumgume Papa ta
fashe da kuka, nan ya shiga rarrashi da ban magana tare da k'ok'arin yakiceta a
jikinshi amma ta cije , a lokacin kuma Mammie ta janyo hannun Umar Faruk ba tare da
kowa ya gani ba ta bashi magungunan Khairat tace masa,
"Wannan sune maganinta idan ciwonta ya tashi, ina fata zaka zamar mata waraka , a
k'arshe ma ku jefar da maganin saboda rashin anfaninshi gareku."
Kai ya girgiza yana mamakin wane irin ciwo ne, ko dai aljanu gareta? ya tambayi
kanshi, murmushi yayi ya rik'e hannun Mammie yace "na miki alk'awarin haka, insha
Allah."
Lokacin kuma muryar Baba ta dawo dasu yana fad'in "kai Umar Faruk, kamata dan Allah
su samu su tafi."
Kallon Baban nashi yayi yana tunanin ta yanda zai fara rik'eta, wasu yawu ya
had'iya tare da yin k'unar bak'in wake yayi kansu zai b'anb'areta, ita kuma tunda
taji ance ya rik'eta ta sake sark'afe Papa tare da lab'ewa bayanshi tana fad'in "ni
wallahi ba zan zauna, kawai ku tafi dani, wannan fa mugune ba imanine dashi ba."
Papa ne ya kalli Umar Faruk da yayi tsaye yana sauraronta yace "dan Allah ka rik'e
matarka kaji."
Umar Faruk bai dawo gidan ba saida *23:30* tayi sannan, yana shigowa ya shiga
d'akinshi ya cire kayan sannan ya shiga wanka a ban d'akinsu ta tsakar gidan, yana
fitowa kuma ya sake shiga d'akin a shirya cikin doguwar riga fara qal duk kai da
kawon nan yayi shine cikin sand'a kar Baba yaji, sannan ya fito ya nufi d'akin
amarya.
Yana shigowa ya sameta yanda ya barta sai ajiyar zuciya take saukewa a hankali
alamar bacci ya d'auketa, kashe mata wutar d'akin yayi ya fita ya rufe k'ofar tare
da rufe gaba d'aya kewaye sannan ya koma d'akin tuzurai 😁Umariri kenan.
Ya jima baiyi bacci ba suna waya da amarya Zuby wacce take farin ciki take ganin
kamar ta hanashi gabatar da daren farkonshi , nikam nace 😏 _kin rako mata duniya
dai, lokacin da zai yishi ma sai kin shigo gidan_, suna gama waya kuma saiya d'auro
alwala ya fara jera nafilfili har asuba, kiran farko ya bud'e k'ofa a hankali danya
koma d'akin amarya ya tasheta, amma ina duk hanzarinshi Baba ya rigashi , domin
kuwa yana bud'e k'ofar sai kuwa Baba a bakin panpo yana d'ibar ruwa a buta , cike
da kunya da sanyin jiki ya nufi d'akin ya bud'e ya shiga ciki, tana nan har yanzu
kwanciyarta kawai ta gyara, saida ya gama kallon qafafunta da suka sha lalle suka
yi tsaf dasu sannan ya tab'a qafar, a hankali ta fara motsawa harta tashi zaune ta
wartsake sosai, kau da kai yayi yana shan k'amshi yace "ki tashi kiyi sallah,
lokaci yayi."
Wata muguwar harara ta dalla masa tare da juya baki, qasa da sama ya kalleta sannan
ya wuce abinshi, har tayi kwance kuma taji gumi ma ya isheta, tashi tayi ta cire
mayafin jikinta da d'an kwali sannan ta mik'e ta cire rigar atamfar sannan ta
d'auki t-shirt matsatsa mai k'ananan hannuwa tasa, bata cire zanin ba dashi ta fito
d'an k'aramin kewayen nata, duk da duhun asuba saida ta gama kallon ko ina, tabb',
wai itace zata rayuwa a wannan gidan, hayaniyar da take ji yasa ta lek'a ta
gajeruwar katangar saboda ta fita tsayi, kai komo kawai mutanen gidan keyi yara da
manya sunata alwala, da mamaki take kallon mutanen da ko ganinta ba suyi ba, a
ranta tace "duk mutanen gidan ne wannan kamar ana biki, lallai ma.", a qalla sunkai
ashirin kosu haura ashirin, kujerun da aka jera a wajen ta zauna duk da fitsarin da
take ji amma tana so ya zo ya nuna mata ban d'akin.
Ana gama sallah suka kamo hanyar zuwa gidan, a hanya kuma Baba saida yama Umar
Faruk fad'a akan abinda yayi, anan take ya bada hak'uri tare da alk'awarin kiyaye
gaba, suna shigowa Baba ya tsaya d'akinshi na soro, Abbakar yayi kewayenshi dake
had'e da nasu Umar, su Usman ma suka shiga d'akinsu dake kusa da kewayen iyayensu
mata, saida ya shiga tsohon d'aki ya had'a kaf abin buk'atarshi dan tarewa d'akin
amarya sannan ya fito da kaya nik'i nik'i, yana shigowa ya tsaya kallonta ganinta
zaune da alama ba tayi sallah ba.
Tashi tayi daga kishingid'ar da yayi ta fara rabka hannuwa tana jujjuyasu tana
fad'in "toh malam, ina zanyi sallah? ka nuna min inda zan kama koda ruwa ma bare
nayi alwala, naga gidan naku har yanzu bak'in da suka zo biki basu tafi ba, to ina
zan fita bansan kowa ba."
Ya gane akwai cin zarafi a maganarta, amma saiya dake ya nuna mata da hannu yace
"ga ban d'akin nan."
Yana fad'a ya wuce da kayanshi ya shige d'akin ya ajesu a inda yaga wuri kafin yayi
zaune yana tilarwar karatu, tunda ta lek'a taga matsatsan bayin ta fito ta sameshi
d'akin tace "wai malam me kake nufi? waccen abar itace wurin wanka, da komai da
komai?"
"Itace, idan zaki shiga ki shiga, idan ba zaki shiga ba ki zauna a haka matsalarki
ce." ya fad'a ba tare daya kalleta ba.
Cikin d'aga murya tace "inaaa, wallahi ba zan iya ba, to wannan idan na shiga zan
iya tsayuwa ma kuwa? tunda ni dai ba gajera bace, uwa uba kuma kai, ya za kayi
kenan?"
"To dama me yayi ruwan nawa da kai, ni dai ka samo min gurin da zanyi wanka a
wale , amma ba wannan kurkukun ba."
Tana fad'a ta koma gado ta zauna, ganin da gaske take kuma gari na haske yasa yace
"ki tashi kiyi sallah, in yaso kyazo kici gaba da zaman har sarkin zama ya sameki."
"Ki tashi nace." duk da jin amon muryarshi ba wasa amma bata tashi ba.
A zafafe ya taso yayo kanta yana fad'in "dake fa nake magana kina jina kinyi shiru,
zaki tashi ko saina b'allaki?"
Gabanta ya tsaya yana kallonta itama kuma shi take kallo, tsaye ta mik'e fuska a
had'e tace "wai me? dukana za kayi? hahaha, kai dai kasan da ganina wallahi ba zan
daku gareka ba, dan ba zan tsaya sanya ba wajen zage k'arfina mu daku da kai ba,
idan kuma hakan ya gagara tofa akwai k'ungiyoyi da dama masu kare hakk'in mata,
wallahi tsaf zansa a d'aure min kai."
Saida ya shafi kansa yace "idan harna tashi dukanki, to ki sani dukan da zan miki
bama zaki iya tuna meya faru dake ba bare har kiyi k'arata ba, shi yasa nake so ki
bini a hankali mu zauna lafiya."
"Yanzu wuce kiyi sallah, dan akan wasa da sallah wallahi sai ajimu dake a kaf garin
nan."
Ba yanda ta iya dole ta wuce ta shiga ban d'akin ta kama ruwa sannan ta fito tayi
alwala ta koma d'akin, saida ta jima kafin ta samu hijab d'in da Mamie ta d'inka
mata sabbi sannan ta d'auki sallaya zata shinfid'a ta kallesa da harara tace "ina
ne gabas?"
A tunaninshi iskanci ne kawai amma ta sani dan haka yace "ki kalleni kiyi sallahn."
Ai kuwa shinfid'awa tayi tana kallonshi ta kabbara sallah, ganin da gaske take
sallaceshi za tayi yasa yayi saurin cewa "wai ke bahaguwar inace, yanzu nan shine
gabas? dallah malama can zaki kalla."
Wata hararar ta sake banka masa sannan ta juya ta daidaita ta ci gaba da sallahta,
tun daga sallah ya fahimci akwai matsala kuma yayi niyyar gyara mata, tana idawa
shi kuma ya shiga wanka kasancewar akwai k'aramin panpo ciki, yana fitowa ya samu
ta koma kan gado tayi kwance, gashi yana so ya canza amma ya kasa, lura da tayi da
hakan yasa ta tab'e baki ta juya masa baya tana fad'in "me zan kalla a jikin? sai
kace wata mayya."
Bai kulata ba harya gama shirinsa cikin jan raiga mai dogayen hannu da bak'in wando
da takalma qafa ciki bak'ak'e, yayi kyau sosai sai turarenshi daya fesa sannan ya
juya zai fita daga d'akin dan yau babu aiki , saurin juyowa tana fad'in,
"Kaga malam, wannan shirgin kayan naka ka tattaresu daga nan, ka bud'a armoire
(drower) nan na qarshe akwai wuri ka zubasu."
Ajiyar zuciya ya sauke mai k'arfi kafin ya fara d'iban kayan yana jerawa, duk kayan
saida ya samar musu matsuguni sannan ya rufe, ya sake juyawa zai fita kenan
Ruk'ayya ta rabka sallama daga k'ofar d'akin....
_Ina sonku masoyana , addu'o'inku ma kad'ai sun ishemu farin ciki._ Allah barmu
daku.💐
19/07/2019 à 21:41 - ~NANA KHADIJA~😍: 💑💑💑💑💑💑💑💑💑💑
*JIHADI*
_Umar faruk_
💑💑💑💑💑💑💑💑💑💑
_NA_
_SAMIRA HAROUNA_
_DEDICATED TO_
*MA FAMILLE*
_My 🅱K, ina tayaki murnar kammala wannan novel mai suna, 💘 *NA BAKI RAYUWATA* 💘,
wallahi Allah har cikin raina nake ji kamar na gani da idona a lokacin mutuwar
Affan, sosai wannan labarin ya shigeni dan saida na zubar da hawaye na gaske😭,
Allah yasa wannan fad'akarwa da ki kayi taje inda muke so kuma ayi anfani da
darasin ciki, Allah ya baki ladar tare da sakamakon gidan aljanna, Allah kuma ya
qara miki lafiya sai mun jiki a next novel._ *ina yinki tawan.*
_My Seeya, barka da fara sabon novel mai suna *QADDARATA*, daga jin sunan kasan zai
bada kala dan kowa da tashi qaddarar, Allah ya baki ikon kammalashi lafiya kamar
yanda kika fara lafiya, fatan nasara my see see._😘
_Bismmilahir-rahman-rahim_
2⃣1⃣
Wata sallamar ta sake yi tare da bud'a labulan d'akin ta shigo, saida ta sunkuya ta
aje kwanukan dake hannunta sannan ta d'ago tace " ina kwana yah Umar, ina kwana
aunty Khairat." ta fad'a tana kallonta.
Umar Faruk dai ya amsa amma banda Khairat da take tunanin itace matar tashi, jin
bata amsa ba yasa ta kalli Umar Faruk tace "dama Mama ce tace na kawo muku abin
karinku."
Kwanukan ya d'auka a aza saman karamin tebur d'in dake tsakanin gado da doguwar
kujerar nan sannan ya zauna yana kallonta, ita kam ta d'aure fuska dan haushin
Ruk'ayya taji sosai, ganin shirun ba zai gyarashi ba yasa yace "ki taso ki zuba
mana abinci muci."
Cikin jin zafi tace "nice zan zuba maka abincin? to kar Allah yasa kaci, ni kaga
nayi kama da masu zuba abinci, ka tab'a jin koda labari cewa an ganni ina zuba
abinci ko a gidanmu, ai kaima ka gani ranar, dan haka in zaka zuba ka zuba kaci."
Shiru ya d'anyi na dakiku kafin ya tashi inda yaga tarin kayan anfani ya d'auko
plate da cokali guda biyu ya zo ya fara zubawa, saida ya gama ya kalleta yace "ki
taso kici."
Sai lokacin ta juyo ta kalleshi, plate d'in ta kalla ganin malku ne (naman kan
rago) yasa ta yamutsa fuska tace "wacece? ni zanci wannan abun? bana cin a wannan
lokacin, kawai kaci abunka."
Banza yayi da ita kawai ya d'auki bred ya fara ci, yana cikin ci yaji tace "wannan
itace matar taka?"
Cak ya tsaya daga kai lomar da zaiyi, cikin rashin fahimta ya kalleta amma sai tace
"wallahi ban tab'a tunanin zan iya auren mutumin da bai min alk'awarin zama dani ba
ni kad'ai, amma sai gashi wai na auri mai mata, mtssss, rayuwa kenan."
Shi kam tunani yake ko bata san jiya ne aka daura masa auren ba, to kenan iyayenta
basu fad'a mata ba kome? ji yayi abincin ya fita a ransa kawai ya fita ya wanke
hannu ya dawo d'akin, zaune ya sake yi a inda ya tashi yana kallonta yace "wannan
ba *matata* bace, kanwata ce, jiya ne aka daura aurena kuma bata tare ba sai nan da
wata biyu."
Kallonshi tayi amma saboda harbawar da zuciyarta keyi yasa ta kau da kai tana guna
guni, ganin ba za tayi magana yasa ya mik'e ya d'auki turare ya fesa a hannayenshi
sannan ya fice ya barta.
Wani bala'in haushinshi take ji dama matar duk da bata ganta ba, ta jima cikin
d'akin har rana ta take sosai sannan ta mik'e ta nufi waje, tana fitowa daga
'karamin kewayen nata ta ja ta tsaya tana 'kerewa gidan kallo, yana da girma amma
yawan mutanen gidan yasa duk an matseshi , duk yara na islamiyya sai Ruk'ayya
kad'ai dake k'ok'arin hura wuta dan d'ora abincin rana, sai kuma Saratu dake kamata
da alama a tare ake girkin , iyayen kuma su uku suna zaune duk da dai biyu sun
had'e kai waje d'aya, ta jima tsaye babu wanda ya lura da ita har saida haushi ya
kamata yanda Ruk'ayya keson wutar ta kama amma tak'i kunnuwa.
Cikin d'aga murya tace "waike dan Allah ba zaki bar hura wutar nan bane, duk kibi
kin cika mutane da hayak'i, wai dama da ice kuke d'ori? tabb'."
Sai lokacin kowa dake wajen ya kalleta, Ruk'ayya ma juyowa tayi sai dai kafin tayi
magana ke Mama Maimuna sai kika ce "kaji kuma wani iyayi , to in tabar hura wutar
dame za ayi d'orin kenan, ko kin tanadar mata wani abun ne? kiji rashin kunya kai."
Mama Sa'a ce tace "ah to dai ganin min hanya, mu za'a yiwa fitsara anan."
Takowa Khairat ta fara yi saida tazo har gabansu ta tsaya tace "daku nake magana?
kunji nace kune da kuka samin baki? to karku sake min irin haka in baso kuke na
muku rashin mutunci ba, ku in banda ma qaddara kun isa ku ganni cikin gidan nan
bare har kumin katsalandan a harkata."
K'wafa tayi ta juya zata wuce Sa'a tace "ke mu kike wa rashin kunya? kinsan komu su
waye? muma fa iyayen Umar Faruk ne."
"Saime? idan ku iyayenshi ne nace saime? na shiga harkarku ne? ko kuma shi yace ku
dinga shiga tawa sabgar? to bana so."
Tana fad'a ta juya su Mama da Saratu kam mamaki ma ya gama kashesu daga inda suke,
sun d'auka ta tafi ne amma sai suka ga ta sake fitowa da wayarta a hannu da da
d'aya daga cikin kujerun nan, ta zauna a bakin k'ofar shiga b'angaren nata, waya
take sai dai basa jin me take fad'a, Ruk'ayya dai ta samu wutarta ta kama bayan
wuya da tasha ta fara aikinta gadan gadan, su Mama Sa'a kuma sai satar kallonta
suke daga nan amma baki ya mutu murus, a qalla awa d'aya aka d'auka tana zaune ta
d'auki wayarta ta kara a kunne saboda kiran daya shigo, tana d'auka tace "ok ina
zuwa." ta kashe wayar.
Mik'ewa tayi ta nufi hanyar da take tsinkayan mutane na wucewa ba kallabi a kanta
sai wannan k'aramar rigar da zane ta fita, a k'ofar gidan ta tsaya wasu samari ne
guda biyu, "yawwa ku shigo dashi." ta fad'a tana komawa cikin gidan, Umar Faruk
dama ba wane wurin yaje ba suna k'ofar gida shida Ishaq da wasu abokansu su hud'u,
ji yayi kamar zai fashe daya tsinkayeta amma ya zaiyi, sharewa kawai yayi ya basar,
suna shiga gidan ta kalli Ruk'ayya tace "ki nuna musu inda zasu aje miki."
Kowa da mamaki yake kallonta da samarin nan saboda ganinsu sun shigo da cuisinière
mai guda hud'u da kuma butalin gas 5kilo, duk da suna cikin zulumin abinda tayi
saida kowa yayi farin ciki, sai dai mahaifiyar Umar Faruk najin d'ard'ar, da ba
lallai malam ya amince ba, nan Ruk'ayya ta nuna musu cikin wata rufa suka had'a
mata shi sannan suka juya inda Khairat ke tsaye, dama ta shiga d'aki ta fito kudi
ta mika musu masu yawa sukayi godiya suka tafi, itama d'akin ta koma tayi kwance
Ruk'ayya da Saratu kam ai sai suka mayar da tukanansu sama cikin jin dad'i, ai sai
suka manta da rashin kunyar da tayi, yayin da Mama Sa'a da Mama Maimuna suka waro
ido suke tunanin sunci arzik'i dan haka su kwantar da kai kawai.
Yara na dawowa kowa baki bud'e sai farin ciki, nan suka rankaya suka nufi d'akin
dan ganin amarya, suna zuwa sun sameta ta kasa bacci tunda ta shiga zafi ya dameta
duk da pankar data aje gabanta, binsu take da wani kallon tsana da qyama suma yaran
kallonta suke saboda kallon da take musu, ganin sunyi zaune wasu qasa wasu akan
kujera yasa tace "ku kuma fa daga ina?"
Mai wayon cikin ne yace "ina kwana aunty amarya, mu kannan yah Umar ne, jiya bamu
ganki ba kuma kuma da safe muka tafi islamiyya, shine yanzu muka zo mu ganki."
Sauka tayi daga kan gadon ta nufi wata coffre ta bud'a ta d'auko chocolat tazo ta
bawa kowa d'aya d'aya, haba ai da gudu aka fita ana murna ana ji wannan amarya mai
ja ce, 😂haba kudai baku sani ba, dan ita ta basu ne dansu tafi su barta, suna fita
cikin farin ciki suka had'u da Umar ya shigo gidan shima, cike da murna sukayi
kanshi Zeinab na fad'in "yah Umar, kalla aunty amarya ta bamu."
Shiru sukayi suka kalli juna dan sun manta, ai da gudu suka sake komawa shi kuma ya
nufi wajen Ruk'ayya da Saratu dake girki baki bud'e har sun kusa kammalawa, "wannan
fa 'yan mata?"
Saratu ce ta harareshi tace "na fad'a maka ka daina kirana yan mata fa."
Baice komai ba sai juyawa da yayi ya nufi b'angaren nasu ya rasa wane hali
zuciyarshi ke ciki, farin ciki ko k'unci, yaran na fitowa shi kuma ya shiga, tana
ganinshi ta sauko daga kan gadon tana fad'in "yawwa, dama kai nake jira dan Allah
ka nuna min inda zanyi wanka, tun jira rabona da wanka fa."
Kallon kwanukan daya ci abincin safe yayi yace "amma aina nuna miki ban d'akin,
watak'ila dama wankan bai dameki ba shi yasa kike so ki d'ora laifin ga ban
d'akin."
"Humm, nida nake shiga cikin baho cike da ruwa nayi link'ayata son raina, shine
zaka nuna min wannan banzan douche d'in kace wai a ciki zanyi wankan, kaima kasan
ba zai yiwu ba wallahi, koka nuna min inda zanyi, ko kuma na tub'e a tsakar gidan
nan nayi wanka na dan nan ne kad'ai zai isheni , in yaso sai kace ma kowa ya rufe
idonshi."
"Kije kiyi mana ga wajen nan, inkin fasa ba sunanki Khairat ba."
Yana fad'a ya juya ya bar d'akin saboda rashin sanin wacece Khairat, bayanshi ta
biyo ya dauka shi take bi hakan yasa ya tsaya yana kallonta, wuceshi tayi ta fito
tsakar gidan ta fara kalle kalle, Ruk'ayya ce ta hanga tana kashe wuta da alama ta
gama, "ke." ta kira Ruk'ayya dashi.
"Zo nan." da sauri ta taho ta tsaya gabanta, babban bokiti nake so ki cika minshi
da ruwa ki aje min nan, saiki fad'awa iyayenku su koma d'aki zanyi wanka."
Da mamaki fal a fuskarta ta kalli Umar Faruk dake bayansu, ce mata yayi "kije kici
gaba da aikinki."
Wucewa tayi Khairat kuma ta kalleshi tace "aini ba musaka bace zan iya da kaina."
Kewayen nasu ta shiga ta samu bokiti ta fito da nufin d'ebo ruwa a bakin panpo
kawai ya rik'e hannunta yace "ke mahaukaciyar inace ne? me yasa baki da h...."
Bai k'arasa ba tace "wallahi karka kuskura ka k'ara kirana bana da hankali ko
mahaukaciya, wai ka mantani ne da kake fad'a min haka, ko dan kaga ana kiranka da
mijina shi yasa, to bana so wallahi kaji na fad'a maka."
Fizge hannunta tayi zata wuce yayi saurin tare gabanta yace "kinga saurareni, kiyi
hak'uri ki shiga nan kiyi wankan , daga baya zansa a gyara miki tunda ba kya so,
kinji?"
Zuyawa tayi ta kalli douche d'in sannan ta kalleshi tace "idan ma baka gyara ba
wallahi ni zansa a gyara, kawai douche sai kace gidan b'eraye."
Wucewa tayi ta fad'a douche d'in ta cire kaya ta cillo kamar yanda ta saba, rigar
data jefo qarshe sai a fuskar Umar Faruk da zai shiga d'akin, a hankali ya janye
rigar ya kalli sauran kayan pants bras da zanin, sunkuyawa yayi ya kwashesu ya
shiga dasu d'akin ya aje mata, ruwa ta makama jikinta ta d'auki sabulu ashe bata
d'auko ba ta d'auka douche d'inta ce wacce ke akwai komai da komai, cikin d'aga
murya tace "ka d'auko min sabulu."
Shirun da taji yasa ta sake bud'a murya tace "ka d'auki min sabulu, kona fito na
d'auka."
Tun maganar farko ya jita ya kuma tashi d'auka, jin abinda ta fad'a a qarshe yasa
yana fitowa daga d'akin yana b'are sabulun a cikin kwalishin yace "kizo ki d'auka
mana."
Yana daf da kaiwa bakin douche d'in ita kuma ta zuro da kai za tayi magana, da
sauri ta dage qirjinta saboda bayyanar da yayi tare da komawa ciki tayi shiru, yana
ganin haka ya juya bayanshi ya mik'a mata sabulun yana fad'in "gashi."
Amsa tayi sannan ta fara wankan shi kuma ya fita daga gidan, Ruk'ayya ya turo ta
d'auki kwanunan ta wanke sannan ta zubo musu wani abincin ta kawo ta aje, duk
lokacin Ruk'ayya na mamakin irin wankan da take data jima haka, amma a b'angaren
Khairat fad'a da guna guni kawai take rusawa daga cikin douche d'in, sai gashi ta
fito ba tare da tayi abinda ta saba yi ba, ta fito daga wanka cikin minti sha biyar
zuwa ashirin, d'aki ta shiga ta fara shiri tana ci gaba da masifa akan douche d'in.
K'aramar riga ce mai siraran hannaye ta kamata sosai duk ta fito mata da mamanta ,
sai kuma jan siket data d'ora a saman rigar har kusa da qirkinta, a bud'e yake
siket d'in sai dai iya gwiwa ya tsaya mata, raba gashinta tayi gida biyu tasa
k'ananan chouchou (ribom) ta d'aureshi, bata wani kwalliya ba sai turare data shafa
ta kuma fesa sannan ta d'auki wayarta tasa takalma ta fito farfajiyar gidan.
Wata kujerar ta d'auka ta aza 'kofar kewayen nasu ta zauna dan zafi ya isheta, daga
yaran har iyaye satar kallonta kawai suke babu wanda yayi magana, mahaifiyar Umar
Faruk kuma tana so tayi magana amma tana jin tsoron wulak'ancin da zata mata, waqa
tasa a wayar ta fara biyarta tana rausaya daga zaune, mak'ota da yan uwa suka fara
shigowa ganin amarya, amma duk wanda ya shigo saiya nufi wajen mahaifiyar Umar
Faruk ya zauna yana tambayar ina amarya, da an nuna masa Khairat saiya tashi yana
addu'a Allah ya kyauta, a qarshe da taga kowa ita yake kallo, aje wayar tayi ta
zuba tagumin rainin hankali tana bin kowa da ido itama, hakan yasa gidan yayi shiru
sai magana qasa qasa.
Baba da Abbakar ne suka taho zasu shigo gidan ganinsu yasa Umar Faruk ya biyosu
suka shigo, da sallama suka shigo amma ta Umar Faruk saita tsaya saboda ganin
Khairat da wannan kayan a jikinta, Abbakar ma dai duk'e kai yayi qasa ya nufi inda
mahaifiyarsu take zaune ya tsugunna, Baba ma haka ya k'araso jiki ba k'wari saboda
ya riga daya shigo, kamar wanda k'wai ya fashema a ciki Umar Faruk ya tako ya nufi
wajenta, yana kaiwa cikin zafin nama ya finciko hannunta yayi cikin d'akin da ita.
Qarar da tayi lokacin daya fizgi hannunta yasa Baba ya kalli Mama yace "kinga,
tashi dan Allah kira minshi, sai yayi b'anna yaron nan kin sanshi da bak'ar zuciya,
karya lahanta 'yar mutane."
Da sauri ta tashi ta nufi d'akin nasu, suna shiga ya jefata saman gado cikin b'acin
rai, zaiyi magana ta rigashi da cewa "meye haka wai, kana haukane? ni sa'arka ce da
zaka min wannan pigar kazar mahaukaciyar."
"Mtssssss." tsaki tayi ta fito daga d'akin zata sake komawa inda take, shi kuma
dama tsakin yafi bashi ma haushi, da azama ya biyota ya cakumo hannunta ya juyo da
ita da k'arfi, wani irin zafine daya ratsata saboda rik'on daya mata yasa ta janye
hannunta daga gareshi hawaye fal idonta, kasancewar shima yayi niyyar sakinta yasa
ta fad'a saman kujerun dake wajen, kuma bata fad'a da kyau ba kawai sai kujerar ta
wuntsila da ita ta fad'i qasa, qara ta saki mai k'arfin gaske hakan yasa Baba dake
can tsaye hankalinshi ya sake tashi, Mama kuma ta karasa danno kai ciki, samu tayi
Khairat na kokarin tashi tsaye hakan yasa ta kamata ta tashi tana kallon Umar
Faruk, "meye haka Umar Faruk, kana lafiya kuwa?"
Kai kawai Mama ta d'aga mata, kallon bayan hannunta tayi da har gurin ya karce jini
ya fara fitowa saboda hannun ya had'u da bango, maida hawayenta tayi ta fizge
hannunta daga Mama kawai ta koma d'aki, Mama kuma harara ta bishi da ita tace "ai
saika fito mahaifinka na nemanka."
Juyawa tayi zata fita ya kamo hannunta ya rik'e ya marairaice yace "wallahi Mama
ban mata komai ba, dan Allah ki fad'awa malam."
Wucewa tayi ta barshi kawai dole ya biyo bayanta, da hannu Baba kawai ya masa alama
ya boyoshi d'akinshi, cikin sanyin jiki ya bishi d'akin suka zauna, cikin hikima
Baba ya dinga mashi nasiha da gargadi har a qarshe ya dora da "ba haka ake ba Umar
Faruk, a matsayinka na namiji, dole akwai bukatar kafi matanka hak'uri, saboda su
matane kuma masu rauni , mace zata iya yin abu, kai a ganinka waouta tayi amma ita
sai tace kuskure ne, dan haka dole ka dinga hak'uri wannan zuciyar taka ka dinga
tausarta, musamman kai daka fara da mata biyu, duk ranar da Allah ya had'aku zama
gida d'aya, dole zaka gane ba kada wayo dan dole sai sun gwara maka kai, nasan ka
sani dan kai shedane akan zaman da nake da iyayenku, dan haka dan Allah bana son
wannan yawan hushi da zafin zuciya, ka rage kaji ko?"
"To Allah yasa, yanzu kaje ka bata hak'uri dan Allah, sannan ka mata godiya akan
d'awainiyar da tayi, dan mahaifiyarka ta fad'a min, tashi kaje Allah ya maka
albarka."
A haka ya tashi ya tunkari b'angaren nasu yana tunanin ya bata hak'uri kamar yanda
Baba yace, ko kuma dai ya shareta kawai.
_Ya kuka ce? kuna ganin zai bada hak'uri, ko kuma zaiyi taurin kai?_😎😏
*Ina barar addu'arku yan uwa, Allah yaba mahaifiyata lafiya, tana jin jiki, yer
uwata ma na fama da tasku na rayuwar aure, gidan miji da tsangwamar kishiya , plss
ku tayamu da addu'a.*
_NA_
_SAMIRA HAROUNA_
_DEDICATED TO_
*MA FAMILLE*
_Bismmilahir-rahman-rahim_
2⃣2⃣
Da sallama ya shiga ya sameta zaune a tsakiyar gado tana share hawaye, har ga Allah
har zuciyarshi yaji ba dad'i kuma yaji bai kyauta ba, bata amsa sallamar ba harya
zauna kan kujera yana kallonta, hannunta na dama da yake fitar da jini ya gani, shi
kanshi baisan lokacin daya zaburo ba yayo kanta yana fad'in "subhanallah, kinga
jini kike fitarwa."
Zai kama hannun tayi saurin janye hannunta ta d'aga masa hannu tana fad'in " karka
kuskura ka tab'ani, mugu kawai azzalumi, wallahi Allah saika sakeni na koma
gidanmu, ba zan iya zaman wannan takaicin ba."
Wani tafarfasa yaji zuciyarshi nayi tare da bugawa da k'arfi, wajen kayanshi ya
nufa ya bud'e ya d'auko wani magani pommade ya bud'e ya lak'ata a hannunshi ya
matso zai shafa mata, tsaye ta mik'e akan gadon tana fad'in "nace karka tab'ani ko,
ko ana dole ne? ban son taimakon naka."
Danya nuna mata ba damuwa yayi da ita ba kawai ya cilla mata maganin a jiki yace
"idan kinga dama ki shafa da kanki, yarinya sai taurin kan tsiya."
"Nice yarinyar? Umar Faruk ni kake fad'ama yarinya? lallai *zaka gane kurenka*
wallahi."
Zaune tayi akan gado shi kuma ya matso kusanta yace "yaushe aka haifeki to?"
Sama da qasa ta wurga masa harara tare da jan tsaki, bata daidaita bakinta ba ya
kama labb'an nata ya matse sosai wanda yayi silar sake fito da wasu hawayen daga
idonta saboda masifar zafi, duk da idonta daya ga sunyi ja saida ya qara murd'e
bakin yace "zaki sake min tsaki?"
Rintse idonta tayi sosai hawaye na zuba, sake murd'ewa yayi yana fad'in "za kiyi
magana ko saina cire bakin? fad'a min naji zaki sake hararata ko tsaki?"
Kasa magana tayi saboda ya rik'e bakin sosai, cikin fashewa da kuka ta girgiza masa
kai a hankali cike da takaici, shima harara ya dalla mata ya saki bakin yana fad'in
"marar kunyar banza kawai, wallahi ki yarda na sake gani kiga yanda zamu kwashe
dake."
Zaune yayi akan kujera ya fara zuba abincin da Ruk'ayya ta kawo ta aje, ita kam
hannu tasa ta dafe bakinta gam tana kallonshi, had'a ido da sukayi yasa ta sake
banka masa wata hararar, danya tsorata yasa ya taso da azama yana fad'in "baki
daddara ba kenan? bari kiga yanda zanyi dake."
Da gudu ta wuntsila daga kan gadon tayi d'aya b'angaren tana nunashi da hannu tace
"wallahi ka matso kusa dani zan illataka."
Murmushi kawai yayi ya koma ya zauna ya gama zuba abinci ya kalleta har yanzu tana
tsaye yace "kizo kici abinci."
Tab'e baki yayi ya fara cin abincin, amma bai kai ko ina ba sai wata zuciyar tace
masa "da safe ma bata ci komai ba, a hakane Umar Faruk zaka tafiyar da iyalinka?
kai kaci ita kuma baka damu da taci ko karta ci ba."
Ajiye cokalin yayi ya kalleta yace "ki fad'a min me zaki ci?"
Sai lokacin ta zauna bakin gadon tana fad'in "karka damu dani, ka d'auka zamana a
gidan nan kamar naje k'auyen kakanni na ziyara ne, dan haka zan kula da kaina."
" *Khairat*."
Saida taji gabanta ya buga tare da sanyin jiki saboda yanda ya kira sunanta, bata
kalleshi sai dai tana sauraro taji me zaice, ganin bata kallonshi yasa kawai ya
qyaleta shima, saida ya gama cin abincinshi sannan ya tashi ya fita ko kallonta
baiyi ba, ita kuma tana ganin ya fita ta sake kama bakinta saboda har yanzu zafi
yake mata sannan ta bishi da harara tace "mugu kawai." sake haye gadon tayi ta
kwanta, taso tayi bacci amma ina zafi da matsatsi sun hanata, dole tashi tayi ta
sake fitowa farfajiyar gidan, lokacin wasu na d'aki wasu na tsakar gidan, zaune
tayi dan har yanzu kujerar na nan inda take.
Usman ne ya doso cikin gidan, da matuk'ar mamaki yake kallonta ganin bak'uwar
hallita a gidansu, ko kad'an baya tunanin matar Umar Faruk ta kasance haka, cike da
fara'a yace "sannu ko."
Da hannu ta masa alamar yazo, ba musu kam kamar sakarai ya nufi wajenta, tsaye yayi
gabanta yayin da mutanen dake wajen kallo ya koma kansu, rik'e hab'a tayi ta
tangale hannu da kujerar tana kallonshi tace "kana da abin hawa?"
Mik'ewa tayi tsaye tace "ka bari idan wanda nake zaune dominshi yazo ya fad'a maka
koni wacece, amma yanzu ka fara zuwa aiken nawa."
D'akin data nufa ya tabbatar masa matar Umar Faruk ce, kuma wannan itace Khairat,
kai kawai ya girgiza ya juya ya kalli mahaifiyarshi da yasan sarkin surutu ce amma
tayi shiru, tunkararta yayi ya tsugunna gabanta yana fad'in "Mama, ita kuma haka
take?"
"Kai, tashi kaje abinda ta saka bana son surutu, kuma kayi sauri ka dawo." cewar
Mama Sa'a tana yi tana kallon k'ofar da Khairat zata fito.
Fitowa tayi amma ganinshi gaban wacce take tunanin mahaifiyarshi ce yasa tayi zaune
saman kujerar tana jiranshi, da k'arfi Mama Sa'a ta turoshi ya dawo gaban Khairat
ya tsaya, jikka goma guda uku ta bashi ta fad'a masa abinda take so, wucewa yayi
yana tsananin mamaki akan abincin da zata ci zaka kashe duk wannan kud'in, lallai
yaran nan iyayensu sun kwashe mana kud'i suna facaka yanda suke so😎 inji Usman
fa😂.
Ta jima tana jiranshi amma bai dawo ba, har saida ranta ya gama b'acewa taji abinda
take so d'in ya fita a ranta, ta tashi kenan zata shiga d'aki Usman ya danno kai
cikin gidan, wani wawan tsaki taja tare da nunashi tace "saika zauna kaci ai, ni
bana so."
Shigewa tayi d'akin shi kuma ya tsaya da leda a hannu yana kallon k'ofar, da gudu
gudu Mama Sa'a ta taso ta karb'i ledar zata shiga d'akin Usman yace "canjin fa."
Dawowa tayi ta karb'a ta wuce d'akin Khairat mahaifiyar Umar Faruk na kallonta tana
jin tsoron abinda zai biyo baya, da sallama ta shiga cike da ladabi🤔 sau hud'u tayi
sallama ana biyar ne Khairat tace "ki shigo."
Da murmushi ta shigo tana k'arewa d'akin kallo tana ji kamar ace d'akin tane ko
kuma na 'ya'yanta mata masu aure, aje wayarta tayi tana kallonta cike da tsana da
wulak'anci amma ita bata damu ba, ledar ta mik'o mata tana fad'in "gashi 'yata ,
kiyi hak'uri kici kinji, kinsan yaran yanzu sai hak'uri, inka aikesu sai sun b'ata
lokaci kafin su dawo, amma na miki alk'awarin ba zai sake ba daga yau."
Gatse gatse Khairat tace "baki ji me nace mishi bane? nace yaci idan kuma ba zai ci
ba, ke kici ko kuma ku zubar a shara, amma ni na gama da babin wannan kuma, zaki
iya tafiya."
Ba tare data damu ba ta sake murmushi ta mik'o mata kud'in tace "to ga canjinki."
"Suma ku rik'e bana so." ta fad'a tana maida abin sauraronta a kunne.
Da dariya cike da farin ciki ta juya ta fita, amma abin mamaki saita d'auki kwano
ta juyo abincin ta zauna Usman da sauran yaran dake nan suna kallo da mahaifiyar
Umar Faruk ta fara ci tana fad'in "harkar arzik'i aida mutanen arzik'i ake yinta."
Usman da haushi ya kamashi ficewa yayi daga gidan, ita kam ko a jikinta cin abinta
tayi tasha ruwa saura ta bawa yara, amma kasancewar sun samu tarbiya sai basu
karb'a ba suka ce sun k'oshi, masifa ta fara tana fad'in "yara an koya muku bak'in
hali tun kuna k'anananku, to ku aje kar Allah yasa ku ci d'in ."
Kud'inta kuma bata bari ma kowa ya gani ba, ko abokiyar cin mushen nata dan dama
tana d'aki tana bacci.
******************
Mamie da Papa sosai suke cikin damuwar rashin 'yar gudaliyarsu, haka duk suke zama
shiru kowa da abinda yake tunanin a kanta, haka ma ma'aikatan gidan suna damuwa ta
b'angaren kyauta da taimako, amma ta b'angaren wulak'anci da yawan aiki kuma suna
farin ciki da hakan, amma dai kam tabbas suna kewarta saboda ita kad'aice 'ya a
wajensu.
*******************
Ana gama sallah isha'i Umar Faruk ya shigo gidan danya shirya saboda yace ma Zuby
yana nan zuwa, da sallama ya shigo tare da leda a hannunshi, bata amsa ba kuma bata
kalleshi ba sai ayabarta data d'auko a fridge take ci tana korawa da fresh milk,
aje ledar yayi saman tebur ya d'auki maclean da brush ya shiga wanka, ya d'an
d'auki lokaci kafin ya fito sanye da dogon wando fari da kuma towel ya rufe
jikinshi dashi, ya jima tsaye yana shafawa yana fesawa kafin ya fara k'ok'arin saka
kaya, ganin yana zame wandon daga jikinshi yasa Khairat saukowa daga kan gadon da
duk ta ya mutseshi ta fito a d'an kewayen nasu ta zauna, saida ta daidaici ya gama
shiryawa sannan ta shigo, gaban madubi ta ganshi yana daidaita hularshi, da kuma
waya a kunnenshi ya danneta da kafad'a.
Muryarshi taji qasa qasa yana fad'in "to ki shirya min kanki, dan gani nan zuwa
yanzu, kinga tunda aka d'aura mana aure bamu had'u ba."
Juyowa yayi yaga Khairat tsaye tana kallonshi, wuceta kawai yayi yana sa wayarshi
aljihu sannan yasa takalmi ya d'auki leda d'aya a cikin wanda ya aje ya kalleta
yace "wannan taki ce."
Juyawa da yayi zai fita yasa Khairat tayi saurin cewa "wannan fa ta wacece?"
"Zubeida, amaryata."
Kai tsaye kuma ya fita daga gidan ba tare daya sake kulata ba, tab'a ledar tayi
taji kaza ce😋(ina sonki kaza), a hankali ta fara d'aga qafafunta harta koma kan
gado, sai dai ta rasa meke damunta da taji zuciyarta na mata k'unci duk taji ba
dad'i, haka ta rasa me za tayi gaba d'aya kalmar Zubeida amaryata ta tsaya mata a
rai, daga ta dafe baki saita dafe goshi ko kuma k'ugu, a hankali ta lumshe idonta
amma sai tayi saurin bud'ewa saboda jin hawaye sun zubo mata, hannu tasa ta share
ta tashi ta shiga 'yar k'aramar douche d'in ta cire kayan jikinta ta jefosu kamar
yanda ta saba ta fara wanka, saida ta gama ta fito kuma ashe babu towel, kamar
yanda tayi da rana haka ma yanzu tayi, da gudu ta fito ta shigo d'akin sannan tayi
shirin bacci, rigace mai 'yan hannuwa sai wandon dogo har qasa amma bai kamata ba
sannan ta kwanta, bacci ne ya gagareta saboda zafi fitowa tayi farfajiyar gidan,
kowa yayi shinfid'arsa ya d'aura gidan sauro ya kwanta, kewayenta ta koma ta zauna
akan kujera tana sauraron waqoqi daga nan kuma bacci ya d'auketa zuciyarta na
tsananta bugawa, gashi tunanin Umar da Zuby ya kasa barin qawqwalwarta.
****************
Tunda yace zaizo tanti Ma'u tayi farin ciki Zuby kuma ta shiga wanka, tun kafin ta
fito kuma Umar yazo, koda ta fito mahaifiyar tata harta had'a mata 'yan tame tame
da tsarabe tsarabe, saida tayi kwalliya sosai ta shirya cikin riga da siket na
shadda sannan Mama ta zaunar da ita bakin gado ita kuma tana tsaye ta mik'a mata
roba mai cike da nono da magunguna masu k'arfin gaske ta shanye, wani farin magani
ta bata tace "tashi ki matsashi a gabanki."
Tashi tayi kamar yanda tace haka tayi sannan ta aje mata kaskon wuta ta zuba wani
turaren tace ta sake tsugunnawa, gyara jikinta tayi sannan Mama tace "kina jina ko?
kiyi duk abinda kika san zaija hankalinki ya kwanta dake, dan wannan abinda kika
gani bana wasa bane, nasan dai duk gaggawarshi bai riga ya kusanci waccen karuwar
ba, dan haka kar kiyi wasa da wannan damar."
Ganin Zuby tayi qasa da kanta alamar kunya yasa tace "to kuma miye na kunya? nifa
uwarki ce dan haka karki damu."
A sanyaye ta kalleta tace "wallahi Mama tsoro nake ji, gabana ma fad'uwa yake."
"Saboda me? mijinki ne fa, kasheki zaiyi? keni nama ci uwaki idan kika b'ata min
rai, to in banda abinki kowace mace ba saida tazo wannan gurin ba kafin nan ta
wuce, muma duk bata haka muka sameku ba."
Lemon da Mama tasa aka siyo mata ta d'auka ta fito ta shiga d'akin da aka gyara
mata ta zauna kafin lokacin tariyarta, zaune yake akan k'atuwar katifar dake
tsakiyar d'akin, k'ura mata ido yayi harta zauna kusa daf dashi duk da irin ruwan
da take jin gabanta na fitarwa, sosai ta masa kyau kasancewarta siririya kuma kayan
sunbi jikinta, ga kwalliyar da tayi sosai hakan yasa ta masa kyau.
Wani kashe ido ne da tayi yasa jin tsikar jikinshi ta tashi had'e da fad'uwar gaba,
itace tayi k'arfin halin cewa "sannu da zuwa angona, na barka kana ta jirana ko?
kayi hak'uri to na tsaya maka shirine."
Cikin wani irin yanayi da shi kad'ai yasan me yake ji yace "ba komai, ai girmanki
ne."
Lemon ta d'auka ta bud'e sannan ta kai masa a baki tana sake rikirkitashi da wani
sabon kallon, kurb'a d'aya yayi ya kau da kansa gefe tare da d'auko ledar daya
shigo da ita mai d'auke da kaza da kuma lemuka masu sanyi, bata yayi ta karb'a tana
fad'in "meye kuma?"
"Ki diba ki gani mana, kazar amarcinki ce."
Ya fad'a yana dariya, ita kam gabanta ne ya fad'i dan haka tace "na shiga uku, nifa
bana son cin kazar nan."
Cikin tsoro tace "wallahi ina ji k'awayena suka fad'a wai duk wanda yaci kazar nan,
to shima dole sai an...." kuma sai tayi shiru.
Cike da zolaya yace "ke kuma biyanne kike jin bak'in ciki ko?"
Tuna abinda Mama ta fad'a mata yasa ta fad'a jikinshi tare dasa hannunta ta shafo
qirjinshi amma ba tace komai ba, tunda ta fara shafarshi ta kwance masa lissafi ido
ya rufe yana sauraronta, bata daina ba saima botir d'inshi data b'alle ta zura
hannu tana shafoshi, cikin wata rikitaciyar murya ya kira sunanta da,
"Z..u....beid...a."
D'ago kan da tayi ta kalleshi tana marmad'a ido yasa ya sake fita hayyacinshi, a
hankali ya had'a bakinshi da nata ya fara tsotsa, tun yana aika sak'on a hankali
harya fara da sauri sauri, sai kuwa ya kwantar da ita akan katifar ya hau samanta
ya cire hularsa da riga da.....🙊BK za tace waya aikeni.
Umar Faruk dai ya manta da ina yake sai faman aiki yake, rana ta farko daya fara
sanin 'ya mace kenan, shaye shayen da Zuby tayi yasa Umar Faruk bai sarara mata ba
ko kad'an, hakan ya janyo ya mata babbar k'ofa😂shiga gari, wacce ba lallai Khairat
nada ita ba, ya jima sosai kafin ya d'agawa Zuby k'afa , kwance yayi yana kallon
sama yana sauke numfashi duk da gumin daya had'a, Zuby na ganin haka ta yunk'ura ta
tashi zaune ta d'auki rigarta ta yab'a tare da saka siket d'inta ta mik'e zata
fita, da sauri ya tashi ya d'auki wandonshi qarami ya saka ya rik'ota yana fad'in
"ina zaki je haka Zubeida, miye haka?"
Cikin layi da shan wahala tace "dan Allah ka k'yaleni na tafi, wallahi ciwo nake
ji, zanje wajen Mama ta taimaka min."
Tare gabanta yayi yace "haba Zuby, ya kike nema ki tona min asiri? ki bari dan
Allah ki gyara jikinki, karki fita haka."
Zip d'in rigarta ya saka mata tare da bata d'an kwalinta ta d'aura sannan ya saka
nashi kayan shima, sallama ya mata ya bar gidan dan ba zai iya had'a ido da Mama
ba, haka ya bar gidan gabanshi fad'uwa kawai yake kamar bai samu nutsuwa ba, a haka
harya isa gida.
Zuby na shiga d'aki ta fad'a saman gado, da sauri Mama ta d'auko babban roba da
ruwan d'umin data d'ora musu tunda ta kara kunne a k'ofar d'akin taji nishi da
sambatun Umar Faruk da kuma kukan Zuby ta dafasu , da taimakonta ta samu ta gasa
jikinta sannan tayi wanka kafin baccin wahala ya d'auketa.😂
******************
00:30 ya shigo da mashin d'inshi a cikin gidan bayan ya kasheshi yanda Baba ba
zaiji ba, yana daidaita zaman mashi d'in yana sad'af sad'af zai shiga ciki muryar
Baba ta daki kunnuwanshi da kiran sunan "Umar Faruk."
Rintse ido yayi sosai yana jin bugu zuciyarshi na qaruwa, a hankali ya juyo ya
kalli Baba dake qofar d'akinshi, kallon da yake masa yasashi zubewa k'asa ya
durk'usa yana sauraran Baba.
"Umar Faruk, ya ina yabanka sallah zaka kasa alwala, kai da kanka Umar Faruk, yanzu
ka kyauta kenan? to waima daga ina kake?"
Yana shafa kai cikin rashin gaskiya yace "kayi hak'uri Baba, daga gidansu tanti
Ma'u nake."
"Au, yanzu acan kayi dare kenan haka? Umar Faruk yanzu yarinyar mutane daka bari
fa? ya kayi da ita?"
Shiru yayi ba magana dan haka Baba yace "to kaje ka bata hak'uri, dan kamar ka
d'auki kwananta ne ka kaiwa wata, ko ban tambayeka ba nasan akwai abinda ya shiga
tsakaninka da Zubeida, dan yanayinka ya nuna hakan, ka tashi ka ka b'ace min da
gani, kuma wallahi ka kiyaye shiga hakk'in matanka, dan mugun kamu Allah zai maka."
yana fad'a ya shiga d'akinshi ya barshi.
Jiki ba k'wari haka ya tashi yana k'arewa kanshi kallo dan baya so ya shiga da
wannan yanayin da Baba yace ya gani a tare dashi, kallon ahlin nashi yayi da sukayi
nisa a bacci, k'ofar kewayen nasu a bud'e take haka ma wuta ba'a kashe ba, yana
dosa kai ciki ya tsaya cak saboda ganin Khairat zaune akan kujera harta langab'e
kamar zata fad'i, ga abin sauraronta a kunne wayar kuma ta fad'a a d'aya saman
kujerar, abinda ya d'aga mashi hankali shine yawan motsin da take saboda sauron
dake ta cizonta sai sosar jiki take, a hankali ya sunkuya daf da ita ya saka
hannayenshi ya .....
_NA_
_SAMIRA HAROUNA_
_DEDICATED TO_
*MA FAMILLE*
_Bismmilahir-rahman-rahim_
2⃣3⃣
Hannu yasa ya zare abin sauraron daga kunnenta ya d'auki wayar ya kashe, a hankali
ya daddab'a hannunta kafin yayi na biyu kuma ta bud'a ido, zunbur ta tashi tsaye
tana zare ido sai kuma ta fara sosar jiki kamar mai k'yaya, jin gaba d'aya jikinta
ya d'auki rad'ad'i na cizon sauro yasa ta lab'e baki kamar jaririya ta fashe da
kuka tana ci gaba da sosar duk inda take jin kyaikayi, Umar Faruk kuma mutuwa yayi
da kallonta cike da birgewa yanda tayi kalar yara, wani murmushi ya saki ya nufi
kayanta data jefo lokacin da za tayi wanka ya d'auke ya shiga dasu d'aki, jim
kad'an ya fito ya fad'a douche danya tsarkake kanshi, kallon juna sukayi ita kuma
ta wurga masa harara da tsaki dan sai lokacin ta tuna rabuwarsu dashi, douche ya
shiga ita kuma ta shige d'akin amma ta kasa komawa ta kwanta.
Fitowa yayi cikin doguwar riga ya sameta zaune tana kukan shagwab'arta, zaune yayi
akan kujerar yana kallonta, ganin har yanzu sosar jiki take yasa ya taso a hankali
ya zauna bakin gadon tare da sauke ajiyar zuciya, waigawa yayi ya kalleta cikin
taushin murya yace "Khairat."
Cikin kukan shagwab'a ta fara magana "wallahi Allah ni dai ka mayar dani gidanmu,
ba zan iya zama anan ba sauro ma kasheni zaiyi, dan Allah ka taimaka ka bani izini
na tafi gidanmu."
"Ni ina maganar ka kaini gida, kai kuma kana maganar naje nayi alwala." ta fad'a a
matuk'ar harzuk'e.
Saboda ibada ne yasa ta tashi ta fita ta d'auro alwala ta dawo ta sameshi, tunda ta
fita ya duba ledar daya aje tana nan yanda take, yana ganinta ya tashi ya shinfid'a
sallaya yace "kisa hijab d'inki ki tsaya bayana."
Kallon daya mata yasa ta d'auki hijab d'in ta saka ta tsaya daga gefenshi a
bayanshi, kabbara sallah sukayi, raka'a biyu sukayi tare da jimawa zaune Umar Faruk
yana jero musu addu'a, suna sallamewa zaune yayi sosai tare da juyowa ya kalleta,
cikin nutsuwa da hikima ya fara magana,
"Khairat, da farko na d'auka labarina dake gajeran labari ne, amma daga ranar da
zuciyata ta yanke min hukuncin na amince da aurenki, saina yarda labarinmu dogone,
hak'ik'a aurena dake Allah ya qaddara faruwarsa bamu ba, idan har za ayi maganar
gaskiya, to kin wuce tsarin aurena, matsayinki da nawa ba d'aya bane, amma duk da
haka sai kuma Allah ya hukunta aure tsakanina dake, hakan na nufin akwai abinda
Allah ya tsara mana a rayuwarmu, dan haka zaifi mu jira hukuncin ubangiji, amma
maganar saki ki daina ba kyau, sannan ina so kiyi hak'uri dan nasan na b'ata miki
sosai saboda aurenki da nayi, amma dan Allah Khairat ki bani dama na cika
alk'awarin dana d'aukarwa iyayenki ta hanyar samar maki ingantacciyar ruyuwar da
suke miki fata da kuma burin samu."
"Khairat akwai tambayoyin da nake son yi miki a game da addininki , kuma ina fatan
zaki amsa minsu kamar yanda suke, ina so na d'ora miki daga inda kika tsaya, dan
haka ina son fara sanin yanda kike tsarkake kanki, domin kuwa saida tsarki ne zaka
fuskanci ubangijinki, idan har kina wankan tsarki kamar yanda aka koyar to
alhamdulillah, dan haka ina jinki ki fad'a min."
Hannu ta zura a cikin hijab d'inta ta d'an sosa damtsenta da duk k'urajen sauro
suka fito mata, shiru tayi kamar bada ita yake ba, hakan yasa yace "Khairat dake
nake fa."
"Toni me zance maka? kana ganin sauro duk ya b'ata min jikina, ya kake so nayi."
Tsaye ta mik'e ta cire hijab d'in tana shirin hayewa gado taji ya rik'e qafarta,
juyowa tayi tace "dallah sakeni malam."
Tana turo baki gaba ta koma ta zauna shi kuma yana bin hannayenta da kallo, saiya
ji tausayinta saboda duk fatarta tayi ja sai shatin cizon sauro a jikinta.
Ajiyar zuciya ta sauke tana kallonshi tace "bansan me zance maka ba, zan fad'a maka
rabona da islamiyya tun ina 'yar shekara bakwai, ko kuma zan fad'a maka ni bansan
komai ba, abinda na koya daga wankan tsarki a wa'azi naji a gurin malamai da dama,
duk da sunce wankan akwai wanda zaka iya zuba ruwa tun daga samanka har qafafunka
tare da cud'a jikinka ma ya hallata , to amma ni hankalina yafi kwanciya ga wanda
yake tare da alwala, dan haka ni shi nake yi."
Kallonshi tayi tace "wai dan Allah ba zaka bari harda safe ba, yanzu bacci nake ji
ga wannan masifar sauron."
Hararanshi tayi taja tsaki, da sauri ya kalleta ya kai hannu zai kamo bakinta ta
tuno da karonsu da rana, da sauri ta jaye daga wajen tayi baya tana fad'in "to naji
zan fad'a maka."
"Nakan fara da niyyar yin wanka sannan na tanadi ruwana masu tsarki da tsarkakewa,
sannan na wanke gabana da kyau ta yanda duk wata qazanta zata fita har izuwa
gwiwoyina zuwa cibiya, sannan nasa sabulu na wanke hannayena da kyau, sannan na
fara d'aura alwala sau d'aya d'aya har saina zo shafar kai, ana so ya samu ruwa
sosai sannan na k'walk'wale kunnuwana, daga nan kuma zan fara wanke barin damana
tun daga sama har qasa, sannan na koma barin hagu shima tun daga sama har qasa,
sannan na wanke qafar dama sai kuma ta hagu, wankana ya kammala kuma idan lokacin
sallah yayi ma zan iya yin sallah dashi in dai har banyi wanka da sabulu ba, to
yanzu zan iya kwantawa *malam Umar Faruk mai tambayar wankan tsarki*?"
Yaji dad'i sosai da har wankanta ya zamana yanda sunna ta koyar ne, dan haka ya
dinga mata tambayoyi tun daga lokacin daka gama alwala har lokacin da zaka shiga
sallah, kuma cikin ikon ubangiji ta amsa saboda tambayoyi ne masu sauk'i, abu d'aya
shine ko hizib d'aya ba zata iya karanta maka ba daga farko zuwa qarshe, dan haka
Umar Faruk yace "karki damu, in dai har zaki bani goyon baya, to kema zaki samu
hasken qwaqwalwa dana zuciya, ina so zan fara miki karatu daga gobe daga inda nake
ganin ya kamata a d'oraki, kuma ina so kisa abin a ranki ta yanda ko bana nan zaki
iya tambayar wani ko wata, a cikin gidan nan Khairat ko *Fateema, da Alqasim* kika
tambaya zasu iya d'oraki daga hizib d'aya zuwa talatin, dan haka kije ki kwanta
gobe insha Allah zan fara miki da littafin *AL'AKHDARI, HUSNUL MUSLIM, KHAMSUNA
HADITH, DA KUMA LITTAFI MAI TSAKI DAGA HIZIB D'AYA ZUWA GOMA*, idan har kika saka
abin a ranki to Allah zai taimakeki cikin sauk'i ki dinga fahimtar abinda kike
koya, saida safe."
Ya fad'a yana tashi tsaye tare da kabbara wata sallah, duk da taga sallah yake amma
bai hanata cewa ba "na d'auka ba zan tab'a samun hasken rayuwa ba, ina son sanin
addinina sosai, amma duk lokacin da nayi yunkurin zuwa inda za'a koyar dani, sai
k'awayena da zuciyata su nuna min na wuce wannan wurin ko kad'an ba ajina bane,
kuma ma ai ina da ilimi na zamani ga wayewa ga kuma kudi, sai dai na manta dashi
ilimi ba'a tsufa da nemanshi, kuma wannan ilimi saida shine zan samu tsira ranar
gobe qiyama, insha Allah zan koya kuma lokacin ya kusa zuwa da zanje gaban Mamie
na karanta mata sura mai tsayi wacce za tasa tayi mamaki harma ta saka min
albarka."
Tana fad'a ita kuma tayi kwance a gado sai dai ina bacci bai samu ba, kiran sallah
ne ya daki kunnuwansu dan haka Khairat taji wani sabon shauk'i a game da son ibada
ya shigeta, tun kafin ya sallame ta tashi ta fita tayi alwala, zata shigo d'aki shi
kuma zai fita masallaci, tsaye tayi ta fita sannan ta shigo saida ta fara da
*salatul fijir* sannan tayi sallah, tun bata tashi ba bacci ya fara fizgarta daga
nan, jingina tayi da gado kawai ta dunk'ule cikin hijab ta fara gyangyad'i, a haka
Umar Faruk ya shigo ya sameta, zaune yayi yana tasbihi yana kallon fuskarta,
murmushi kawai ke bayyana a fuskar tashi saboda tuna tambayoyin daya mata kuma ta
amsa, ga kuma abinda yaji tace a game da son karatun, a cikin ranshi yace "taya zan
bata hak'uri kenan?"
Bai samu amsa ba kuma bai daina kallonta ba har gari haske yana kallon yanda take
bacci kuma ko motsawa ba tayi ba, a sama sama yake iya jin hayaniya a tsakar gidan,
dan haka ya d'auka ko masifa ce dasu Mama Sa'a suka saba da ita, hayaniyar ce ke
sake yin sama ga kuma kuka da yake ji wanda yake tunanin na *Yusuf* ne d'an
Abbakar, wannan kukan ne yasa Khairat bud'a ido ta sauke akan Umar faruk dake
kallonta, zaune tayi da kyau tana mike qafafu tana murza ido shi kuma tuni ya
d'auke kai daga kallonta, jin kukan da hayaniyar mutane yasa ta kalli Umar Faruk
tace "waiku gidanku ba kwa baccin safe ne? suna damuna fa."
Kafin yayi magana ta mike tsaye ta cire hijab zata kwanta kenan taji ana kiran
sunan Umar Faruk, da sauri ya fita daga d'akin tana binshi da harara da jin haushin
mutanen gidan da basa barin bacci, da azama ya sake shigowa taga yana lalabar
aljihun rigarshi daya cire jiya, yana d'aukar makulli yace "zanje na dawo."
Jin haka yasa Khairat biyo bayanshi da sauri itama ko kallabi bata d'ora a kai ba
bare takalma, Yusuf na rik'e a hannun Abbakar sai kuka yake Umar Faruk kuma yana
gaba danya fitar da moto, duk kowa yayi cirko cirko Ruk'ayya ce Khairat ta dafa
tace "meya sameshi."
Saida ta kalli kayan jikinta sannan tace "wallahi wata 'yar k'aramar lula ce mai
kamar ball ya samu yake wasa da ita, shine ya saka a hanci ta shige masa, kuma gata
ana gani amma tak'i fitowa."
Jin haka yasa Khairat rugawa a guje ta tari gaban Abbakar ta finciko Yusuf daga
gareshi ta zaune dashi a qasa ba tare data damu ba, ganin haka sai kowa ya matso
inda take duka suka rufesu suna kallon ikon Allah, Umar Faruk ma zai fitar da moto
yaga kuma an taru dan haka ya dawo shima, amma abin mamaki da bai tab'a tunanin ko
a mafarki ya faru bane ya faru, Khairat ya gani duk da hawaye da miyo ga majina
data b'ata fuskar Yusuf bai hanata saka bakinta a hancinshi ba a inda babu lular
tana busawa, sosai take busawa kafin ta d'ago kai ta kalli Abbakar tace "ace duk
yawankun nan kun kasa taimaka mishi, sai wani maganar asibiti kuke."
Sake maida bakinta tayi da k'arfi tana busawa, sai kuwa lular nan tayi b'ul ta fito
daga hancin Yusuf, wata irin sa'ida da salama da yaron yaji yasashi saurin rumgume
Khairat ya manna kanta a qirjinta dake k'yam dashi yana hararan Umar Faruk daga
nan😉, d'an shafa kanshi tayi sannan ta mik'awa Abbakar shi yana amsa ya kalleta
sosai yace "mun gode sosai k'anwata."
Mik'ewa tayi amma sai Saratu ta rik'e hannayenta duka biyu ta had'e tana kuka tace
"na gode sosai yer uwa, tashin hankalin dana shiga yasa na manta ta yanda zan fara
taimaka masa, na gode sosai."
"Ba komai." ta fad'a kamar dai wacce aka saka dole, kakkab'e wandonta tayi ta juya
ta nufi kewayenta kowa kuma na binta da kallo saboda abinda tayi babu wanda yayi
tsammanin yinshi, saida kowa ya kama harkar gabansa Umar Faruk na tsaye, daga baya
yaji an dafa kafad'arshi, juyawa yayi sai yaga Mama ce, murmushi yayi zai wuce yaji
Mama tace "zuciyarta mai kyau ce, tana da abinda ba kowa yake dashi ba, wato
*tausayi da taimako*, duk wanda yake da wannan halayen to mai imani ne shi, d'an
duhun dake cikin rayuwarta nake so naga ga yaye matashi ka mayeshi da da haske ,
kaje Allah ya muku albarka."
Wucewa Mama tayi shima kuma ya nufi kewayen yana jin wani irin nishadi da farin
ciki na lullub'e zuciyarshi, yana shiga ya ganta ta d'ibi ruwa tanata wanke baki
wai ita majina, murmushi kawai yayi ya shiga d'aki, tana shiga itama tayi zaune
tare da d'aukar wayarta tana aika kira, ba jimawa aka d'auka a daqile tace "ka kawo
min mota ina jiranka."
Duk da wanda ta kira yaso ya tambayi gidan nata, amma ta riga data kashe wayar,
Umar Faruk kuma tashi yayi ya shiga wanka, koda ya fito ta tashi zata shiga itama
tace masa "aiki zanje, idan ka rigani zuwa kace Habiba ta share min bureau
(office)."
Tana fad'a ta wuce abinta shi kuma yayi shiru yana tunanin kuma ta yanda zaiyi ya
dakatar da ita, harta cire kayan jikinta sai kuma taji wani irin sanyi ya
lullub'eta, dafa wuyanta tayi sai taji zafi ruf, tsaki tayi dan tasan sauron nanne
kawai ya zuba mata zazzabi dan haka ta d'auko kayanta a hannu ta manta da inda take
rayuwa yanzu, duk da ta raumgume kayan amma dai kallo d'aya zaka mata kasan babu
komai a jikinta, tana dosowa zata shiga Umar Faruk ya bud'e labule zai fita gaida
iyayensu, da sauri ta durk'ushe qasa ta rintse ido tare da rufe fuska da kayan,
kasa gaba yayi sai baya da yayi ya dawo cikin d'akin ya fad'a saman kujera kamar an
turashi, yana hangenta ta labule bata tashi ba yasa ya tashi ya d'auki towel d'inta
daya gani rataye ya bud'e ya cilla mata a jiki, sai lokacin ta mik'e ta d'aurashi
sannan ta shigo, zaune tayi ta sake d'aukar waya ta danna wani kiran, kasalance
tace ,
Shiru alamar tana saurare kafin tace "wallahi zazzab'i ne ke son rufeni, zanzo
yanzu."
Aje wayar tayi duk yana kallonta amma baice komai ba, tashi tayi ta bud'a kayanta
ta d'auko doguwar rigar atamfa ta saka tabi jikinta sosai kuma ta mata kyau, d'an
kwali ta d'aura sannan ta d'auki qaramin mayafin daya dace da kayan ta aza a
kafad'a, poshet (post) d'inta ta d'auka ta bud'a wata jakar ta d'ibi kud'i ta zuba
a ciki sannan ta d'auki wayarta tasa takalmi ta d'auki turare ta feshe jiki dashi,
takowa tayi har gabanshi ta tsaya tace "idan driver Mamie ya kawo min motar ka
karb'a ka aje min ni zan hau taxi."
Juyowa tayi tace "iko? wai iko kake so ka min? to ban tab'a fita dashi ba ba kuma
zan fara yau ba."
Tsaye ya mik'e yana fad'in "kuma dole kisan cewa da dah da yanzu ba d'aya bane,
wallahi ke baki isa ki zubar min da mutunci ba, idan kika fita a haka to mamaki da
zulumi ne zasu hana mutanen unguwar nan samun shak'at, ace surukar malam Ahmad a
haka, ina ba dani za ayi wannan fitsarar ba."
"Wato ma nice fitsararriya ko? to ba zanyi ba naga me za kayi, idan kuma zaka
tursasani ne na gani."
Sallamar Ruk'ayya ce yauma tasa ya amsa tare da bata izinin shiga, yau ma gaishesu
tayi sai dai Umar Faruk kad'ai ya amsa kamar dai jiya, aje kwanukan tayi ta fita
abinta Khairat kuma ta juya har zata fita kuma ta tsaya ta sake kallonshi tace
"idan iko kake so kaima a matsayinka na namiji, toka bari har figaggiyar matarka ta
shigo gidan saika mulketa, amma bani ba *Hajia Khairat*."
Gyara tsayuwa tayi tace "duk da bana da ilimin addini, amma ka sani na kare
mutuncina, kuma duk da bana da sani akai amma nasan abinda kayi jiya baka kyauta
ba, ka raba dare a wajen amaryarka, kuma daga yanda ka shiga wanka a wannan tsohon
daren ya tabbatar min da wani abu ya faru, amma karka damu na yafe maka badan komai
ba saboda ni ba sonka nake ba, kuma bana qaunarka kamar yanda ba son auranka nake
ba."
Bakinshi ne ya mutu dan haka dole yayi shiru yana kallo harta fita daga gidan,
mutanen dake tsakar gidan kuma kowa kasa motsi yayi yana kallonta harta fita, sai
dai Mamar Umar Faruk tayi niyyar fad'a mata gaskiya dan wannan ba abu bane mai
yiwuwa, malam ma dake k'ofar gida suna tattaunawa da mak'otanshi yana ganinta ya
d'auke kai dan karya nuna ma ya santa, amma dai shima dole yaji a ranshi zai
tsawatar mata da kanshi, bata sha wahalar samun taxi ba ta d'auketa kai tsaye sai
asibitin kud'i asibitin da suke da familly docteurn su, *Clinique d'an magori* kai
tsaye bureaun docteur d'in ta shiga, kasancewar suna ganema juna sosai yasa ta
kwantar da ita ta saka mata sérum (drip), tana kwance amma suna hira baka ce
Khairat ce ba mai ganin dama kafin tayi magana.
*****************
Tana fita shima ya fito ya fara shiga d'akin Mama Maimuna ya gaisheta saboda shine
farko, kuma an nuna musu duka iyayensu ne dan haka d'aya ne, yana fitowa kuma ya
shiga na Mama Sa'a, abin mamaki shine cewa da tayi "Umar Faruk ya 'yata, da fatan
dai ta tashi lafiya?"
Kallonta ya d'anyi a fakaice sannan yace "da sauk'i Mama, dan yanzu haka ma ta tafi
asibiti, zazzab'ine ya rufeta."
"Ameen Mama."
"Ai Umar Faruk kayi dacen mata wallahi, Allah dai ya baku zaman lafiya."
Yana fita daga nan ma d'akin mahaifiyarshi ya nufa, bayan sun gaisa ne tace "Umar
Faruk ina ne matarka ta fita tunda safe haka? kuma kana kallonta ta fita da wannan
kayan, kuma naga duka yaushe ne tazo da har zata fara fita."
"Kuyi hak'uri Mama, duk ni naja muku, amma insha Allah zan d'auki mataki akan
hakan."
"To shikenan, amma dai banda duka ko wannan muguntar taka ka kama bakin mutum ka
murd'e ko mintsini, ka mata cikin ruwan sanyi harta fahimta."
Daga nan kuma yayi d'akin Baba kuma ya sameshi yana karin kummalo, kuma Abbakar da
Aliyu ma duk sunje gaisheshi, a tare ya musu nasihar daya saba na suji tsoron Allah
su kyautata ibadarsu, sannan su guji d'aukar hakk'in wanda Allah ya had'asu zama
dashi kona minti d'aya ne, daga nan kuma ya sallamesu suka tafi Umar faruk yayi
tunanin sai Baba ya masa magana amma yaji shiru, yana fitowa yaga motarta a k'ofar
gida, fita yayi suka gaisa da driver wanda Mamie ta fad'a masa unguwar shi kuma
yayi tambaya, makullin ya amsa driver kuma ya koma dan ya hau taxi, shima d'aki ya
dawo ya aje mata makullin sannan ya zuba abinci ya ci, Ruk'ayya ya tura ta gyara
d'akin ta kuma d'auko kwanuka da kazar da bata ci ba.
Tunda ya nufi wajen aiki yake tunanin yanda mutane zasu kalleshi, kuma kam hakane
ya faru dan yana shiga suka dinga zuwa suna masa wai barka, da qyar ya zauna
mazauninshi Ishaq ya zuro kai yace "mutumina ina amaryar, ba dai ka hana ta fito
ba?
Wata harara ya wurga masa yayi banza dashi, dan tunaninshi na gareta yana so yaji
ya take a yanzun, gashi kuma baya da lambar wayarta, dubara ce ta fad'o masa daya
tuna manager, kai tsaye bureaunshi ya nufa, yana bashi izinin shiga ya shiga ya
samu wuri ya zauna, kai fa fara sosawa ya kasa magana.
Ganin haka yasa manager cewa "angon Hajiarmu, ya kuma kayi shiru? ina Hajiar tamu
take? ko dai har yanzu baku gama cin amarcin bane?"
Wani tarr yayi da ido yace "kai manager, amarci fa? da Hajiar taku ? kamar dai ka
mantata, nifa kaga ba wannan ne ya kawoni ba, lambarta ma nazo ka bani ina so zan
kira."
"Me!? lambarta fa? kwananka nawa a matsayin mijinta? amma kace baka da lambar
wayarta? anya Umar faruk."
Shiru yayi kawai yana jira ya bashi, ba yanda ya iya shima dole ya bashi lambar
sannan ya fito yana doka mata kira, tunda taga lambar ta shigo wayarta taji gabanta
ya fad'i ba gaira ba dalili, gashi kuma lambar sassauk'a hakan yasa ta birgeta,
saida ta tsinke ya sake kira sannan ta d'auka, shiru dukansu sukayi kafin shi yace,
"Hello."
Lumshe ido tayi saboda yanda muryarshi ta daki kunnuwanta cikin nutsuwa, "hello."
tace a matuk'ar sanyaye.
Shima dafe qirji yayi saboda wani irin bugawa da yaji yayi, da qyar yace "kina
ina?"
"Mai gida kenan, ina asibiti har yanzu, sérum aka saka min."
Cike da nuna kulawa yace "subhanallah, amma kuma shine baki kira ba?"
"Dame zan kira? bana da lambarka ai, kuma kaima nasan yanzu ka samu tawa."
"Ina Clinic d'an magori." tana fad'a ta kashe wayar, shi kuma yabi wayar da kallo.
Fita yayi ya hau mashin d'inshi ya koma gida sannan ya d'auki motarta ya tafi da
ita dan ba zai dawo ba sai tare da ita 😂kasan kuma ba zata hau *Utu utu* ba.
_Kuna ganin zata yarda ta taho tare dashi a motarta, ko kuma shi zai dawo a qafane
ya kai mata motar kenan?_😂
_NA_
_SAMIRA HAROUNA_
_DEDICATED TO_
*MA FAMILLE*
_Bismmilahir-rahman-rahim_
2⃣4⃣
Saida ya kirata ta kwatanta mishi wajen da take, yana kaiwa kofar d'akin docteur
d'in ta fito danta basu wuri, gaisawa sukayi kafin ta fice tana yaba mijin na
Khairat, koba komai a yanda ta ganshi tasan zaiyi wuya Khairat ta rainashi, kallon
juna sukayi lokaci d'aya kuma suka d'auke idonsu, zaune yayi bakin gadon ita kuma
ta nad'e qafafunta, kallon ruwan yayi yaga harma sun kusa qarewa, shiru sukayi babu
mai magana har wayarshi tayi qara, yana ganin Zuby ce sai yaji wani haushi ya
kamashi, tunawa da yayi abinda ya faru, amma kuma sai yaji tausayinta a wani
b'angaren ganin yanayin daya barota, muryar Khairat ce ta katse masa shiru da "ka
d'auka mana, ko sai tayi hushi, zaifi maka ka lallab'ata dan ita kad'ai gareka."
D'auka yayi baice mata komai ba, a daqile yake amsa gaisuwarta, da qyar yace mata
"ya kike, da fatan kinji sauk'i?"
Zuby dake gaban Mama tana kallonta tace "da sauk'i dai, amma fa har yanzu ina jin
ciwo."
"Ayya, sannu kinji, zai bari insha Allah, yanzu ki kashe waya zan kiraki ina wani
wuri ne."
Saida ya kalli Khairat ta gefen ido sannan ya rage sautin murya yace "ina asibiti."
Wannan karan kallon idon Khairat yayi wacce take latsa wayarta sai dai zuciyarta
bugawa take da k'arfi, haushi take ji yana taso mata tana ji kamar ta bugeshi tare
da wayar, sannan yace "auntynki ce ba lafiya, amma yanzu zamu koma gida serum d'in
ta kusa qarewa."
Zaro ido tayi ta kalli Mama sai kuma tace "tana kusanka ne?"
"Zata ji."
"Sumbata nake so kamin wacce baka min ba jiya ka tafiyarka, kuma na d'auka zaka
kirani amma baka kira ba."
"Wallahi ban yarda ni saika min." ta fad'a cikin shagwab'a harda kukanta.
A hankali ya tashi ya fita bakin k'ofar d'akin ya danna mata sumbar sannan ya kashe
wayar, sai dai kuma Khairat tajishi hakan ya qara harzuk'ata.
Tana aje wayar tace "shikenan Mama, na shiga uku, wallahi harta fara laulayi."
"Waifa suna asibiti bata lafiya, kinsan dai ba haka kawai za tayi rashin lafiya ba,
gashi abinda muke gudu ya faru, kuma ni na riga na bashi kaina tun ban tare ba."
Ajiyar zuciya Mama ta sauke tace "to kin gani, wallahi ba zan iya wannan kayan
takaicin ba, dan haka shiryawa za kiyi kawai ki tare gidansa kema, in yaso duk
abinda suke ayi a gabanki, dan zai iya mantawa dake anan d'in, yana can ya samu mai
kud'i kenan ya fita harkarki, dan haka ki koma can ki zauna duk abinda suka ci kema
kici wanda sukasha kema kisha, kinji ko?"
"Amma me? dan ubanki ana nuna miki annabi kina rintse ido, duk abinda nake yi ba
saboda ke bane nake yinshi, dan haka ki fara shiri wallahi kin kusa komawa
gidanki."
Tashi tayi ta barta ita kuma ta koma ta kwanta dan har yanzu ba dad'in jikinta take
ji ba, dan ba qaramar wahala tasha ba abinka ga sabbin shiga.
******************
Ran Khairat a matuk'ar b'ace ba tare data kalleshi ba tace "ka kira min *Sadiya*
tazo ta cire min na koma gida."
Bata san me yake damunta ba amma bata kosan had'a ido dashi, a zafafe tasa d'aya
hannun ta janye sirinjin daga hannunta hakan kuma yasa jini ya fito tunda bata cire
yanda akeyi ba, kallonta kawai yake ita kuma ta d'auki mayafinta ta laga a kafad'a
tasa takalmi tayi hanyar fita, da kallo ya bita yana k'ok'arin kiran sunanta.
"Khai...k.k..." tuni ta fita dan haka ya biyota da sauri, har zai tari gabanta
saiya tuna lokacin data maresa,😁( ba kyau), cak ya tsaya sai kuma ya fara binta a
baya har suka fita, Sadiya ce taga fitarsu a ranta tace "Allah ya had'aka sai
hak'uri."
Tana fita farfajiyar ta tsaya saboda ganin motarta, juyowa tayi ta kalleshi lokacin
daya tsaya gabanta, hannu ta tara masa tace " bani makullin motata."
D'ago hannu yayi zai mik'a mata sai dai kuma baya so ya bata, da k'arfi ta fizgi
makullin tana fad'in "ka bani nan, ko taka ce?"
Tana karb'a ta dalla masa harara tace "inma kanayi ne dan naji haushi to ba zanji
ba, da kai da matarka baku isheni kallo ba, kana k'ok'arin kaci mutuncina a gaban
k'aramar yarinya saboda kaga damata, to kaje ka had'iyeta mana iyakar sumba , ba
shikenan ba saiku huta."
Motar ta nufa ta bud'e ta shiga ta tako da k'arfinta tayi kwana domin ta hau kan
titi, saida ta tsaya inda yake ta zuge galss tace "ka tari taxi ta mayar da kai
inda ka fito."
Rik'e kugu yayi da hannu d'aya d'ayan kuma ya rik'e wuya, yana so ya fahimci wani
abu amma ya kasa, to duk miye na wannan harzuk'ar? qarasawa yayi gaban titi ya tari
taxi yace ya mayar dashi ma'aikata, abin mamaki shine baijin komai dan gane da
abinda ta masa, ranshi bai b'ace ba kuma baijin haushinta, to me yasa?😉ka tambayi
Hasfat A A, haka ya koma jiki ba k'wari wata zuciyar na raya mishi ya dinga taka
tsantsan ya daina waya da Zuby a gabanta, wata zuciyar tace masa to akan me? ai
matarka ce, haka dai har yamma tayi ya tashi ya nufi gida yana tunanin yau kuma
wacce zai isko.
***************
Da qyar takai kanta shagon wani *Saminou* saboda jiri dan dama ba'a tashi lokaci
d'aya idan aka gama sérum, kuma gashi ba wani abu bane a cikinta, tana zuwa ta paka
motar anan, fad'a mishi da tayi bata jin dad'i yasa ya shiga motar ya tukata ya
kaita gida, tare suka fita ya bata makullin motar a shiga gida shi kuma ya hau
acaba ya mayar dashi, ganin layin da take yasa suka fara tunanin ko shaye shaye
take, Ruk'ayya ce ta taso da Umar Faruk ya bata makullin d'akin ta bud'e mata
sannan ta shiga, da k'arfi ta fad'a saman gado ta fashe da kuka tana fad'in "wayyo
Mamie, zuciyata zafi take, ji nake kamar zata fasa qirjina ta fito, dan Allah Papa
kazo ka d'aukeni mu kuma gida."
Ruk'ayya da taji haka yasa ta shigo a hankali ta fara cewa "aunty Khairat,
lafiyarki k'alau? me yake damunki? ko baki da lafiya ne?"
Da qyar tayi zaune tana kallonta hawaye na ci gaba da zuba mata tace "ki bud'a
fridge akwai madara a ciki ki d'auko min nasha."
Da sauri ta juya ta d'auko ta kawo mata saida ta bud'e murfin sannan ta bata ta
kifa kai, saida ta shanye duka sannan ta jefar da kwalin , Ruk'ayya kuma d'aukar
kwalin tayi ta rik'e ta sake tsayawa gabanta tana kallonta tace "aunty kina
buk'atar wani abun?"
Saida ta goge hawayen dake fuskarta cikin shagwab'a tace "kin iya dafa indomie?"
Nuna mata tayi da hannu tace "ki bud'a coffre d'in nan akwai indomie, ki d'auki
guda biyu ki dafa min, idan akwai k'wai ki had'a min dashi guda uku."
"Ai kuwa aunty babu k'wai, sai dai in za'a siyo ne?"
Tana fad'a ta kwanta saboda jiri, d'aukar indomin tayi ta fita nan ta fara dafa
mata, cikin k'ank'anin lokaci ta gama ta kawo mata kuma taji dad'inta sosai, hakan
yasa ta kalli Ruk'ayya tace "ke ba kamar yayanki ba, kina da kirki."
"Shima yana da kirki aunty Khairat, kawai dai baki fahimceshi bane."
Yar qaramar dariya Ruk'ayya tayi tace "ba zance miki a'a ba, yaya kam akwai zafi
kuma akwai salon k'eta, amma kuma in dai har zaka dinga jin maganarsa sannan baka
rainashi ba, to gaskiya zaku zauna lafiya dashi."
Cike da basarwa tace "ok, kije, idan na fita zan siyo k'wan saiku aje."
****************
Yana shigowa gidan tanti Ma'u ya samu tare da Mama suna hira, har qasa ya tsugunna
ya gaishesu sai dai bai bari sun had'a ido da tantin ba, dan yasan tasan me yayi
kuma tana kallonshi da abun, Mama ce tace masa "akan maganar tarewar Zubeida ne, ta
yarda ta dawo gidan mijinta ta zauna itama tayi karatunta."
Kallon Mama yayi ya kuma kalli tantin, tanti Ma'u ce ta katseshi da "ko dai baka
shirya tariyarta bane, kafi son ka dinga zuwan can gida kana....."
"Na amince tanti, yaushe ne?" ya katseta dan yaga zata tona mishi asiri, ita kuma
dama ba ruwa bane a idonta, dan haka ba komai bane a wajenta danta fad'a kowa yaji.
Tashi yayi ya nufi kewayen nasu yana mamakin canzawarsu, tunda ya tunkari d'akin
yaji kid' na tashi, can cikin mak'oshi yayi sallama dan haka ma bata ji ba, shiga
kawai yayi tare da tsayawa k'ofar d'akin yana kallonta tana tiqar rawarta, kayan
jikinta su suka d'aga masa hankali tare da tayar masa da wata kafirar sha'awa da
bai tab'a jin irinta ba a rayuwarsa, iya cinyoyinta wandon yake sai rigar da ba
za'a kirata da bras ba haka kuma bata fi bras girma ba, rintse idonshi yayi sosai
ya cije labb'enshi , bud'e ido yayi ya sake saukesu a kanta, da k'arfi ta juyo
hakan yasa gashinta dake sake saida ya tashi sama shima ya juya sosai, duk da
ganinshi da tayi ba tayi wani yunk'urin kare jikinta ba sai dai dakatar da rawar da
tayi, gumin data had'a yasa ta fara takowa itama da nufin fita, tsaye tayi saboda
ya tare hanyar fitar kuma har yanzu idonshi na kanta ya kasa d'aukewa , hannayenta
ta d'aga tana tattare gashinta tana kallonshi tace,
Ganin ya kasa gusawa kuma har yanzu kallonta yake yasa ta matso daf dashi ta d'aga
kanta tana kallonshi saboda ya fita tsawo sosai, wani mayan kallo ta masa tana
murmushi tace "yadai, kana jin wani abu ne?"
Da sauri ya dawo hayyacinshi hakan yasa girgiza kai, wani murmushin ta sake yi tace
"hakan yafi maka."
Saida tayi kamar zata fad'a jikinshi kafin ta samu ta wuce saboda ya kasa matsawa a
hanyar, takalmi tasa ta shiga douche tayi wanka duk da ta d'auki lokaci hakan yasa
ma Umar Faruk tafiya masallaci saboda idan ya tsaya jiranta zai b'ata lokaci, harya
dawo bata shirya ba sai d'aurin qirji daya sameta dashi tana shirin saka kaya, bai
sake kallonta ba harya saka doguwar rigarshi zai shiga wanka tace "kayi hak'uri fa,
d'azu na baroka acan wajen." ta fad'a tana dariya.
Saida ta nufo wajenshi ta bud'e fridge ta d'auki ruwa sannan ta fara bud'ewa tana
fad'in "da sauki, amma dai ba zaka sake bari na kwana a cikin sauron nan ba ko? dan
nan gaba nasan mutuwa zanyi."
Sallamar tanti Ma'u ce ta katsesu ta shigo ganin amarya, Umar Faruk ne ya leko yana
fad'in "tanti shigo mana."
Khairat kuma wajen kayanta ta nufa ta fara neman wanda zata saka har tanti Ma'u ta
shigo, Umar Faruk ne ya bata wajen zama amma Khairat ko kallo, cikin taushin murya
yace "Khairat, wannan itace magajiyar Mama kuma mahaifiyar Zubeida."
Tana fad'a ta tashi tace "Umar ni zan wuce, zaka zo ganin matar taka?"
Tanti Ma'u kam mutanen nan ne da bakinsu baya da linzamin, kawai sai cewa tayi "da
alama karuwancin harya fara tasiri a kanka, tunda gashi har saika kalleta kafin ka
yanke hukunci."
Labule ta bud'a zata fita Khairat ta rufe wajen kayanta ta matso tana fad'in "yadai
tsohuwa, me kika ce? sai naji kamar kince karuwanci ko?"
"Eh, haka nace, ko k'arya nayi ba karuwar bace ke? me ake kiran mace irinki inba
karuwa ba? ke kar kice zaki min fitsara dan wallahi ba mutunci ne dani ba, ba zan
duba cewa ke sarakuwata bace ko kuma kishiyar 'yata, tsaf zan kwab'e kayana na
dakeki son raina."
Dariya kawai Khairat tayi, kasancewar ba mai son hayaniya bace hakan yasa kawai
tace "bansan me kika sani akaina ba da har kike kirana da karuwa, amma ga dukkan
alama 'yarki kike tayawa kishi tunma bata shigo gidan ba, to ba komai kije, amma ki
sani ni Khairat da karuwa ce, wallahi da Umar Faruk bai kusanci 'yarki ba a daren
jiya, ki dinga sanin me kike fad'a dan baki san me za'a fad'a miki ba idon kin
b'arota da zafi, Umar Faruk kuma gashi nan ki d'auka ki kaiwa 'yarki, amma nasan
saiya dawo gareni, koba haka ba...... *Faruk*?"
Ta fad'a tana fad'awa jikinshi tare da shafo fuskarshi, tsikar jikinta ne ta tashi
haka shima, a take yaji zufa na tsattsafo masa, ba abinda ya masa dad'i kamar
kiransa da tayi da *Faruk* dan babu wanda ya tab'a kiranshi da haka sai yau, bai
iya cewa komai ba saboda mamaki, tanti Ma'u kuma cewa tayi "ke dai wallahi anyi
tsinanniya marar kunya, yanzu a gabana kike rik'eshi haka kamar wata uwarki ce ta
haifeshi."
"To wace kunya kuma? mijina ne fa, nan da qananin lokaci ma cikinshi zaki gani
jikina." duk tayi maganar ne tana sake cukwikuye Umar Faruk.
"Mtsssss, Allah ya wadaranki 'yar iska kawai, wato kinzo kin samu wuri harda mik'e
qafa, kamar ba kece yar d'an siyasan nan ba da ba'a fadanshi da alkhairi , ke da
gani nasan baki samu tarbiyya ba daga wajenki uwarki, kuma nasan hakan ba zai rasa
nasaba da tasu rashin tarbiyyar suma iyayen naki."
D'agawa tayi daga jikin Umar Faruk tace "ke tsohuwa, kifa kama girmanki, ba mutunci
ne dani ba wallahi saina zubar miki da...."
Yayi saurin saka hannunshi ya rufe mata baki yana kallon tanti yana fad'in "dan
Allah tanti kiyi hak'uri ki tafi, nace zanzo."
"A'a, saketa ka barta ta fad'i abinda take son fad'a danta nuna min ita yar zamani
ce, da wallahi nima saina nuna miki ni tsohuwar zamani ce, wai har wani cika baki
kike zaki raba Umar Faruk da Zubeida ko? to bismillah, idan kika fasa raba tsakanin
nasu ke ba *'yar halak* bace, baki haihu cikin uwarki da ubanki ba, shed'aniya
kawai marar kunya."
Jin abun na tanti wuce ya gona da iri yasa ya dafa kafadunta ya fitar da ita daga
d'akin, Khairat kuma kanta ne taji yana sarawa da k'arfi sosai ga qirjinta da take
jin yana d'an zafi ga kuma dukan da yake mata, hannu biyu tasa ta dafe kanta sosai
ta rintse ido dan kamar saukar guduma take ji a cikin qoqon kanta, da qyar Umar
Faruk ya fita da tanti daga gidan ya had'ata da Aliyou dake kofar gida yace ya
rakata ta shiga taxi, wannan masifa data dinga yi yasa mahaifiyar Umar Faruk itama
kanta ya fara sarawa saboda hawan jini ne da ita, ko kad'an bata qaunar hayaniya
koya take.
Mikewa tayi da qyar badan tana ganin gabanta ba ta fara bud'a duk wani abinda take
ganin za'a aje abu ciki mai mahimmanci kota samu taga maganinta, tana cikin dubawa
Umar Faruk ya dawo d'akin, binta yake da kallo saboda ganin tana abu kamar
makauniya dan ba daidai ba ma take tafiya, ganinshi a bayanta yasa ta dago hannunta
dafe da kai tana ganin dishi dishi ta fara masa magana cikin yanayin matukar shan
wahala,
Bata qarasa ba tayi luuu ta fad'i kasa, da gudu Umar Faruk yayo kanta ya zube qasa
ya fara kiran sunanta, shiru bata amsa ba, cike da damuwa yace "na shiga uku, tanti
ta kwanto min bala'i, yanzu gashi bansan meye matsalar ba, ya zanyi da ita?"
Tashi yayi da sauri ya d'auki ruwan data aje akan fridge yazo ya zuba a hannu ya
fara shafa mata a fuska, da qyar ta farfad'o sai dai da wani sabon ciwon kan, da
kuka ta farka tare da saka hannaye biyu akai tana fad'in,
"Kaina zai fashe, ka taimaka dan Allah ka d'aure min, zai fashe, kaina zai
tarwatse, ciwo yake min sosai, dan Allah ka d'aure minshi *Faruk*."
Itama cikin kuka tace "qirjina ma fashewa zaiyi, amma nafi jin ciwon kan nan, dan
Allah ka taimaka min ka samo abu ka d'aure minshi."
Rufe ido yayi lokaci d'aya kuma ya bud'e ya saukesu a kanta, tsaye yayi tare da
sungumarta ya rumguma a jikinshi, yanda ta kwantar da kanta a qirjinshiya yasa
hankalinshi ya sake tsananta tashi, domin kuwa tsaf yake jiyo yanda jijiyoyin kanta
ke harbawa, a hankali yake takawa da ita harya direta akan gado, ya qura mata ido
yana ganin jijiyoyinta duk sun fito, alamu ne qarara suka bayyana masa irin wahalar
da take ciki, haka kawai sai yaji inama ciwon ya koma kansa, koba komai zai fita
juriya da hak'uri, gyara zamanshi yayi a kan gadon yasa hannayenshi biyu ya fara
shafa kanta daga farkon inda take aza goshinta wajen sallah, har zuwa inda gashinta
ya tsaya kusa da kunne, ya jima yana shafa mata kamar yana wasa jin haka kuma yasa
Khairat shako wuyar rigarshi cikin azaba da rad'ad'i ta bud'e ido danta masa magana
amma sai taga dishi dishin ma har yafi d'azu, dan haka ta d'ago kanta ta kai
bakinta har saman hanshinshi sannan tace "ka d'aure min kaina nace, ko so kake na
mutu? mugu kawai azzalumi."
Shidai baice qala ba harta saki wuyan rigarshi, yana cikin shafa mata ya matse
daidai inda gashinta ya tsaya sosai da yatsa biyu, wata siririyar qara tare da
zabura ta cakumi rigarshi ta shige qirjinshi tana rik'e hannunshi daya matse mata
kai da k'arfi sosai, k'ok'arin k'wace hannunshi take dan ba qaramin matsa ya mata
ba, shi kuma ya rik'e sosai hakan yasa ta kasa k'watar kanta, turmutsutsu kawai
take a jikinshi tana zubar da hawaye, gashi tana rok'on ya saketa amma bata jin
muryarta na fita, da qyar yayi dauriya ya k'arasa addu'o'in da yake karanta mata
saboda yanda take had'a jikinshi da nata tana murzawa, ba tare daya d'auke
yatsunshi ba yaja yatsun nashi da k'arfi har saida ya diresu akan inda take aza
goshinta wajen sallah sannan ya saketa, tana jin wani sauk'i ya zirnyarceta ta
fad'a saman pillow tana sauke numfashi amma idonta rufe, sai lokacin taji kan yana
mata sauk'i sosai sai kuma taji qirjinta kamar zai tsage, hannaye ta d'ora akai
tana murzawa, ganin haka yasa ya d'auke hannayenta yace "bara na taimaka miki,
shima zai bari da yardar Allah."
Kallonta yake yana tunanin yanda zaiyi wannan taimakon, kiran sallah isha'i ne ya
riske kunnuwanshi, a hankali ya fara k'ok'arin sauka daga kan gado amma sai yaga ta
dunk'ule waje d'aya tana dafe qirjinta sosai, wani sauk'ak'ak'en numfashiya sauke
sannan ya dawo ya zauna, gyara mata kwanciyarta yayi ta mik'e sosai kamar wata gawa
sannan ya d'auke hannayenta daga qirjinta, "um um, Umar faruk, karka fara." cewar
wani b'angare na zuciyarshi.
"Ba komai, matarka ce ai, ka d'auka yanzu ma wani *Jihadi* ne za kayi, domin tana
cikin halin rayuwa ne da mutuwa."
A hankali ya kai hannu ya sab'ule d'aurin qirjin dake jikinta, wata 'yar k'aramar
numfashi yaja tare da saka tafikan hannayenshi ya rufe fuskarshi, ba k'aramin
rikita mashi lissafi sukayi ba, kasancewar Allah ya horesu gasu kuma b'ul b'ul dasu
kamar na mai k'aramin ciki, jawur suke har sunfi fatarta haske uwa uba kuma kan😎,
kamar wani abu ya cijesu saboda yanda suke jawur dasu kamar an sulb'esu, gasu giri
giri suke babu alamar kunya a idonsu😉, bud'e idonshi yayi ya sauke a fuskarta sai
dai idonta a rufe suke, da alama bata ma cikin hayyacinta, "k'uk'ut." ya had'iye
yawu kafin ya kai hannunshi da tuni suka fara karkarwa ga gumi dake tsattsafo masa,
dan tuni ya shiga masifa network kuma ya kawo service, awazarta duka biyu ya soka
hannayenshi a qarqashi ya tallabosu, wata irin bank'arewa tayi ta tusa masa
qirkinta a nashi qirjin saboda masifar zafin da taji, kwantar da ita yayi saita
kuma tasowa tana kara 'kwak'umeshi, sake mayar da ita yayi yana fad'in "ki tsaya
mana, bana son mugunta fa."
_To wai fan's, me Umar Faruk ke nufi da baya son mugunta, mema aka masa na
muguntar?_
Nan ma dai addu'a ya mata ya tofa mata sannan ya rabu da ita yana ji yana gani
jam'i ya wuceshi, sauka yayi daga gadon ya bud'a wajen kayanta ya d'auko wata rigar
bacci da wandonta silip ya aje mata yana fad'in "ki tashi ki saka."
Sai dai bansan Khairat azabar ciwon kai yasa ji da ganinta sun d'auke ba na wucen
gadi , ko alamar taji ma ba tayi ba hakan yasa ya d'auki kayan ya warware rigar
yana kallo........
💋luv u my Meelat.👄
23/07/2019 à 09:55 - ~NANA KHADIJA~😍: 💑💑💑💑💑💑💑💑💑💑
*JIHADI*
_Umar faruk_
💑💑💑💑💑💑💑💑💑💑
_NA_
_SAMIRA HAROUNA_
_DEDICATED TO_
*MA FAMILLE*
*Sadaukarwa ga*
_Bismmilahir-rahman-rahim_
2⃣5⃣
Kamar zai fita daga d'akin kuma saiya kashe wutar d'akin ya dawo da rigar a
hannunshi, duk da ba'a gani amma haka ya lalabata ya qarasa zame towel d'in, wandon
ya d'auka ya fara saka mata sannan ya zura mata rigar, saida ya tabbatar komai yayi
daidai sannan ya kunna hasken d'akin, daga inda yake ya kalleta ganin kayan sun
mata d'as gwanin kyau, fita yayi daga d'akin danya tafi masallaci sai dai kuma
yasan alwalarshi ta karye dole saiya d'anyi wanka😂 ko sama sama ne😛, haka kam
akayi saida yayi wanka ya fito ya bud'a kayanshi zai ciro wasu kayan ya saka kawai
yaga maganin da kakarta ta bashi, a hankali ya fara tuna maganganun iyayenta dama
kakarta d'in, hakan yasa ya ya fad'a a fili "kenan wannan ne abinda ke damunta? to
me yake janyo mata shi?"
Maganar kaka ya sake tarowa baya kawai sai yace "uhum, kenan b'acin rai da damuwa
ne kamar yanda mahaifinta ya fad'a? ikon Allah."
Maida kallonshi yayi gareta tana bacci hankali nutse, shiryawa yayi ya aje
magungunan kusa da ita ya fita ya nufi masallaci, shi kad'ai yayi sallah shi sannan
ya hau mashin d'inshi ya d'an fita, baifi awa d'aya ba kuma ya dawo, har yanzu
bacci take dan haka ya fito da clé USB daya siyo ya mak'ala a tv ya jona ya fara
sauraren k'ira'o'in, wannan karatun ne ya tasheta yana ganin haka ya taso zunbur
yayi kanta, tana dafe da kanta ta fara k'ok'arin bud'e idonta, a kanshi ta saukesu
tana kallonshi, saida ta saisaita kanta sannan ta kalli d'akin da kyau ta kuma
kalli jikinta, da sauri ta dafe qirjinta ta kalleshi a tsorace.
"Ba wannan kayan bane jikina, waya canza min kayana?" ta tambaya tana kallonshi.
Da sauri ta sauka daga kan gadon tana fad'in "waya canza min kayan jikina, ka fad'a
min gaskiya Faruk, kaine? yanzu kenan ka kalleni saboda kaga bana cikin hayyacina?
kamin adalci kenan? saboda kawai kana mijina."
"Kinga dan Allah, bafa abinda kike tunani bane, ba..ni ba...bane ba sauya miki
kaya."
Kallonta kam yayi sai dai gaba d'aya gabansu dukan uku uku yake, a hankali tace "ka
rantse ba kai bane, ni kuma saina yarda."
Kuka ta saka da k'arfin gaske harda bubbuga qafafu tana fad'in "shikenan ya gama
dani wallahi, ace kamar wannan yaron ne zai saka min kaya a jikina, shikenan ta
qare miki Khairat, baki da bakin magana kuma tunda haka ta faru, nan gaba kuma
kusantarki zaiyi daga nan kuma saiki d'auki cikinshi sannan ki haifeshi , bayan nan
kuma saiya...."
Da sauri Umar Faruk ya janyo k'ugunta ya had'e da nashi ya d'ora yatsarshi akan
labb'ata suna kallon juna, wani yanayi yake ji dashi kad'ai yasan me yake ji,
dakewa yayi ya kama gashinta ya fara wasa dashi kamar gaske harda murmushi kafin
yace mata "kiyi shiru, bana so mutanen dake waje su d'auka wani abu ne nake miki,
dan haka kuskure ne, ki cire wannan tunanin a qwaqwalwarki dan haka ba zata faru
ba, ni Umar Faruk ba zan iya had'a jikina da naki ba."
"Saboda me? ni karuwa ce? kaima haka kake gani? amma me yasa ka aureni to?"
Ganin hawaye sun cika idonta sai kuma ta bashi tausayi sosai, a hankali ba tare
daya raba jikinshi ba yace "ni ba haka nake nufi ba, kawai dai ba zan iya had'a
jikina da naki bane, saboda ina da matuk'ar kishi."
Qasa tayi da idonta tace "kenan yanzu da ice ka had'a jikinka? ko kuma kana nufin
daga wannan had'awar da kayi yanzu ne ba zaka sake had'awa ba?"
Har zai wuce tace "baka ji mena fad'awa mahaifiyar matarka ba kenan? idan naso
Faruk zaka zama nawa, idan nayi niyya zaka zama kamar raqumi da akala sai yanda
nayi da kai, ka daina cika baki."
"Ka tabbata?"
"Qwarai ma kuwa."
"Ok, zamu gani, ni kuma zan ruguje wannan yarda da kai d'in."
"Kinga maganinki nan ki d'auka kisha yafi miki mahimmanci."
Juyawa tayi inda ya nuna mata ta kalla, maido kallonta tayi gareshi tace "ina ka
samu magani na?"
"Matata ce ta bani."
Wani irin murd'awar kayan ciki taji lokaci d'aya kuma zuciyarta ta turnuk'o, a dake
tace "wace matar taka? ba dai wannan d'iyar masifafiyar matar ba?"
Dariya ce ta kama Umar Faruk, karo na farko da Khairat taga dariyarshi, kafeshi
tayi da ido harya tsagaita yace "wannan ta dabance , duk cikin matan nawa babu mai
qaunata kamar ita, shi yasa nima na mata waje na musamman a zuciyata."
Duk da Khairat ta fahimci Umar faruk zaiyi dad'in zama kuma kamar yanda Ruk'ayya
tace ta fad'a ne, amma kuma wani bala'i da taji ne a zuciyarta yasa ta rasa meke
damunta, haka kawai taji bata so yana danganta kanshi da kowace mace a duniya, ba
tare daya ankara ba Khairat ta kai masa duka a qirji harda fad'in "aisai kaje gaka
gata ku cinye junanku."
Juyawa tayi zata haye gado tana fad'in "aikin banza kawai, ni gidanmu ma zan koma."
Da k'arfi taji ya janyota har saida ta fad'a qirjinshi, kafe juna sukayi da ido na
d'an lokaci kafin yayi k'arfin halin cewa "meye wannan nake gani a idonki?"
Tsaki tayi mai k'arfi ta janye kanta daga jikinshi, fizgota yayi niyyar yin sai
kuma,
"Assalama alaikum." sallamar Ruk'ayya ta katsesu.
Shigowa tayi tana aje kwanukan Khairat tace "kina zuwa a lokacin da bai dace ba
fa."
Ruk'ayya dai sakin ido tayi tana kallonta, har zata fita kuma tace "kina ji? ki
dafa min."
Hannu d'aya ta rumgume a qirji ta mike qafafunta tana girgizawa tana murmushi tace
"to meye a ciki, naga jikina ne ba bana ka ba, kuma kace baka qaunarshi ba zaka
tab'a had'ashi da jikinka ba, to miye na damuwa?"
Muryar Mamie ta daki kunnuwanta dan haka tace "Mamie ya kike, shine kun manta dani
ko kirana ba kuyi ba?"
Shiru tayi kafin tace "ba wani nan, kudai kuna can kuna soyayyarku da Papa, tunda
yanzu babu kowa a gabanku, dama nice kuma kun kawar dani."
Turo baki tayi cikin shagwab'a tace "wallahi Mamie nayi kewar Papa, nan fa gaba
d'aya ba dad'i, yau fa har zazzab'i ya kamani, amma dai da sauki."
Nan suka dinga hira har Ruk'ayya ta shigo ta kawo mata sannan ta kashe wayar, sauka
tayi daga kan gadon ta zauna kujerar da Umar Faruk ke cin abinci harda turashi take
da k'ugu tana fad'in "duk kabi ka matse waje kai kad'ai."
Plate d'in imdomin ta ta aza ta fara ci itama, satar kallon hannunta yake wanda
suka sha jan lalle, tana ci tana kallonshi ta wutsiyar ido tana kuma tunanin
abubuwan da matar nan ta fad'a mata, alwashi taci saita saka matar nan tayi nadamar
abinda ta mata, to amma tayaya? dole saita samu kusanci da Umar Faruk, to shima
tayaya? abu mai sauk'i, namiji neshi ke kuma macce, kawai ki samu kusanci dashi, a
hankali ta juya ta kalleshi, caraf idonsu suka had'u, kallon baka da hankali ta
masa yayin da shi kuma ya bita da harara, tunawa da plan d'inta yasa ta turo baki
gaba cikin sigar shagwab'a ta d'an mangareshi da kanta, hannu tasa ta debo lomar
indomie ta nufi bakinshi da ita, ganin yana mata kallon rashin fahimta yasa ta sake
langab'e kai tace "bud'a bakinka mana."
Kai ya gurgiza mata alamar a'a, a bakinta ta saka lomar ba tare data kallesa ba
tace "hum, kama daina kallona haka."
Wata sallamar ce ta katsesu daga k'ofar kewayen nasu, Umar faruk ne ya fita jim
kad'an ya dawo, tsaye yayi a kanta yace "ki canza kaya Baba nasan ganinmu."
Ba yanda ya iya saida ta gama sannan ta wanke hannu ta d'auki doguwar riga tasa ta
d'auki kallabi ta yafa, yana kallonta yace "hijab zaki saka."
"A'a, nifa bana iya zama dashi, kuma ba kace wajen Baba ne zamu ba."
Hijab d'inta da take sallah ya d'auka ya matso kusanta ya gyarashi , bai b'ata
lokaci ba wajen saka mata, k'ok'arin 'kwacewa tayi ya mata wani jan kallo dole ta
tsaya, gaba ya sata suka fita daga d'akin bayan ya rufe, suna daf da shiga d'akin
Baba inda gaba d'aya mutanen gidan suke, hannunta Umar Faruk ya kama ya gyarawa
yatsunsu waje d'aya tare da murzawa har suka shiga yayin da yayi sallama, amma suna
shiga ya saki hannunta suka samu wuri suka zauna, tunda ya rik'e hannunta taji wani
*baqon yanayi* a tare da ita da bata tab'a jin irinshi ba, kamar yanda shima
abubuwan da yaji sunfi k'arfin wasa, dan saida ya tuna da maganar Ishaq cewar
*wataqila yanzu ne ya fara soyayar gaskiya.*
Kallon kowa take yayin da su kuma suke sauraran nasihar da Baba ke musu akan rik'o
da zumunci, sun jima sosai kafin Baba yaba Zeinab damar rufe musu taron da addu'a,
sosai yarinyar ta shiga ran Khairat saboda ganinta bata fi yar shekara bakwai ba,
amma sink'i sink'i addu'o'i na fitowa daga bakinta, haka suka tashi suka fito, kowa
makwancinshi ya nufa sai Umar Faruk daya kalli Khairat yace "muje kiga Mama."
Binshi kawai tayi suka nufi d'akin Mama, da sallama ya shiga ita kuma tun k'ofar
d'akin take kalle kalle har suka shiga, zaune yayi kusa da Mama dake kwance amma
ganinsu tare yasa ta tashi zaune tana fad'in "ah, ashe tare kuke da 'yata."
Sai lokacin ta d'anyi zaune akan kujera tana kallon d'akin da kyau, k'aramar panka
take kallo a ganinta ba zata musu komai ba, muryar Umar Faruk ce ta katse yana
fad'in "ya jikin Mama?"
Umar Faruk ta kalla dan haka yace "hawan jininsu ne ya tashi, amma sunsha
maganinsu."
"Eh, akwai maganin da aka rubuta musu, to shine suke anfani dashi." cewar Ruk'ayya
dake gyara shinfid'a.
"Amma ai hakan bai dace ba, me zai hana ku dinga kaita asibiti duk lokacin da bata
jin dad'i? amma zama da ciwo ana shan magani barkatai."
Tsam ta mik'e daga kujerar ta durk'usa kusan Mama ta tallabota ta zauna daidai,
kallon Ruk'ayya tayi tace "ki bani hijab d'insu."
Ba tace komai ba sai hijab d'in data mik'o mata, saka mata tayi sannan tayi tsaye
tana ciccib'ar Mama tana fad'in "muje asibiti Mama, lafiyarki tafi komai
mahimmanci, kuma suma kansu yayanki nasan sun san da haka, amma babu mai fasahar
kaiki asibiti, sai sun rasaki kuma za kiga sunfi kowa damuwa da kuka."
Kallonta kawai Umar Faruk da Ruk'ayya da sauran yaran suke, tsaye yayi yana fad'in
"ba wai bamu damu bane, muma muna...."
Mama ce tace "'yata dama kin barshi wallahi, naji sauk'i ai da dama jikin ba kamar
d'azu ba."
"A'a Mama muje kawai, sai dai kuma ko kina so ki nuna min ni ba 'yarki bace."
Suna fitowa farfajiyar gidan ta kalli Umar Faruk tace "ka rik'e Mama, zan d'auko
makullin mota."
Tana fitowa kuma da makullin da post d'inta ta kuwa haka ta rik'e Mama har suka
fita inda Baba ya fito da su tafi tare amma Khairat tace kawai yayi zamanshi, tare
da Umar Faruk suka tafi suna gaba ita dashi tana tuk'i, Mama na baya in banda
addu'a da qaunar Khairat babu abinda take ji, bata san kuma me yasa ba amma taji
daga haka son sarakuwar tata ya kamata, suna zuwa asibitin da taje da safe docteur
Sadiya ta tafi sai wani docteur d'in, cikin qwarewa ya duba Mama kuma ya fad'a musu
jininta ya hau, allura aka mata na saukar da hawan jinin sannan aka rubuta wasu
magunguna masu matuk'ar tsadar gaske, ita ta biya kud'in sannan suka kamo hanyar
gida, saida ta tsaya babban pharmacie ta siyo duka magungunan sannan suka tafi gida
dare yayi sosai lokacin.
Har d'aki suka kai Mama ta kwanta Khairat taja zanin rufa ta rufeta, gefen fuskar
Mama ta shafa tace "kiyi bacci Mama, dan Allah banda damuwa da tunani, ki more
baccinki babu mai takuraki."
Hannunta taji ta rik'e hakan yasa ta koma ta durk'usa tana kallonta, cike da jin
dad'i da tsantsar qauna Mama tace "na gode yata, ubangiji ya saka miki da mafificin
alkairinsa, Allah ya kareki daga sharrin masharranta, Allah ya baki abinda kike so,
Allah ya saka miki da gidan aljanna, Allah ya albarkaci rayuwarki da zuri'arki baki
d'aya, Allah ya sakawa iyayenki da alkairi, Allah ya kareki daga bakin duniya,
Allah....."
Rufe bakinta Khairat tayi ta fashe da kuka ta fad'a jikin Mama ta rumgume, saida
tayi mai isarta ba wanda ya bata hak'uri kafin ta d'ago ta share hawayenta ta rik'e
hannun Mama sosai tace "Mama, kin kusa kasheni da farin ciki saboda wannan addu'ar
taki, tunda nake a rayuwata ban tab'a jin addu'a irin wannan ba, ko mahaifiyar data
haifeni bata tab'a kwatanta yimin irin wannan addu'ar ba, Mama nice da godiya bake
ba, ina da yak'inin wannan addu'ar taki ba zata fad'i k'asa banza ba, a yanzun nan
sai nake ji kamar ni 'yar aljanna ce kuma zan gama da duniya lafiya, Mama Allah ya
bar mana ke, kuma nayi alk'awarin zama a gidan nan har qarshen rayuwata in dai har
zan dinga samun irin wannan addu'a a wajenki."
Tana fad'a ta bar d'akin tana kuka, Umar Faruk ma bayanta yabi bayan sunyi sallama
da Mama, yana shiga ya sameta kamar ba ita bace mai kukan nan harta murje idonta
tayi kwance, sai dai abinda Umar Faruk bai sani ba ta rufe ido ne amma addu'a Mama
ce ke yawo a qwaqwalwarta, kashe wutar d'akin yayi bayan yayi shirin kwanciya
sannan ya kwanta a saman kujera, zunbur ta tashi zaune tana lalubar wayarta ta
kunna haske, a daqile tace "malam nifa bana bacci a cikin duhu, ka kunna fitilar
mana in dai ba wani abu bane a ranka."
Wayarshi ce a hannunshi yana duba kiran da Zuby tayi bai d'aga ba, ba tare daya
kalleta ba yace "ni kuma gashi bana bacci a cikin haske, ya kenan za ayi?"
_Idan an kashe akwai d'an dannau mai taushe mutun cikin dare😎😂, idan an bari kuma
shed'anun aljanu na anfani da hasken su cutar da bil'adama._
24/07/2019 à 12:27 - ~NANA KHADIJA~😍: 💑💑💑💑💑💑💑💑💑💑
*JIHADI*
_Umar faruk_
💑💑💑💑💑💑💑💑💑💑
_NA_
_SAMIRA HAROUNA_
_DEDICATED TO_
*MA FAMILLE*
*_Masoyana💖, kune abin alfahari na, ina matuk'ar ji daku fiye da tunaninku, fatana
Rabbi ya bar qauna tare da soyayya, nasan ba zamu iya had'uwa daku ba dukanku, amma
ina fatan Allah ya sadamu da alkairinsa sannan ya taramu a aljannatul-firdausi._*👏👏
_Bismmilahir-rahman-rahim_
2⃣6⃣
Wajen makunnin ta nufa tana shirin kunnawa yayi saurin tare gabanta, d'auke idonshi
yayi daga nata saboda masha Allah akwai girma kamar idon Barbie ga kuma kyau da
yalwataccen gashi, "dan Allah ka matsa min na kunna, bana iya bacci a cikin duhu,
tsoro nake ji."
Da kanshi ya nuna mata gado yace "kije kiyi addu'a saiki kwanta, babu abinda zai
sameki da yardar Allah."
"Ba zaka gane ba, dan Allah..." bata qarasa ba saboda hannunta data kai ta kunna
wutar shi kuma ya rik'e.
Janye hannunta tayi tana sauke ajiyar zuciya tace "shikenan, kar Allah yasa ka
kunna, amma wallahi naji hannun mutum a jikina ana lalubata, to zaka sha mamaki dan
saina fasa maka kai wallahi."
Dariya ce ta subece masa komawa yayi kawai ya kwanta, harta kwanta itama amma data
rufe ido saita ga su Musa a idonta, sosai ta rintse ido amma duk da haka bata daina
gani ba, bud'e idon tayi taga duhu sosai, zaune tayi ta kalli wajen da Umar Faruk
yake tace "malam nasan ba kayi bacci ba, dan Allah ka taimaka ka kunna ko hasken
fitalar wayarka ne."
"Haka kawai zan kunna harsken wayata har safe, ai tunda ka hana a kunna wallahi na
wayarka zaka kunna."
"Kaji kamar mai wata wayar million d'aya, wallahi saika kunnata ko kuma."
Ta fad'a tana saukowa daga kan gadon, jin tahowarta yasa ya tashi zaune yana fad'in
"ko kuma me?"
Da hasken wayarta taga wayar tashi akan qaramin teburin dake tsakanin gadon da
kujerar da yake, tunkararta tayi gadan gadan tare da kai hannu zata d'auka, da
sauri ya d'auki wayar tare da ajeta bayanshi ya rumgume hannaye yace "ki d'auka
idan ke jan wuyace."
"Dan Allah ka bani, wallahi bana iya bacci a duhu, kuma gashi dare keyi har yanzu
banyi bacci ba, zanfa maka kuka wallahi ko kuma na fad'awa Mama."
Kallonta yayi dan ya mata tambayar ne dan yaji me zata ce, a hankali ya zura hannu
ya d'auko wayar ya mik'o mata kamar sakarai, hararanshi tayi tace "ka kunna mana,
meye saika wani bani a hannuna."
Baiyi magana ba kuma bai bar mik'a mata ba, cike da haushi tasa hannu ta karb'a ta
kunna fitilar, murmushi tayi ta kalleshi tace "kaga tasirina ya fara aiki a kanka,
tun ma ba'a je ko ina ba kenan."
Zaune yayi yana fad'in "ke bani wayata, tasirin me? kin d'auka dabararki ce tasa na
baki?"
Juyowa tayi tana kallon qwayar idonshi ta soka wayar a cikin rigarta tsakiyar
mamanta sannan ta rik'e k'ugu tace "kazo ka d'auka idan ka isa."
Murgud'a baki tayi ta koma gado ta haye tare da fitowa da wayar ta aje gefenta,
baki sake ta barshi yana kallonta har bacci ya d'auketa, saida ya tabbatar tayi
nisa sannan ya taso zauna bakin gadon yana kallon fuskarta, baisan menene asalin
abinda yake ji ba, sai dai yana ji kamar a yanzu haka baya so ta masa nisa, to amma
me yasa? *my aunt Aishan Umma* ce zata baka amsa a gaba, wata irin nutsuwa ce yake
ji tana sauko masa, ga kuma taimakon da tawa mahaifiyarshi wanda yafi komai faranta
masa rai, ya jima a wajen sosai yana tunani akanta kafin ya tashi ya koma wajenshi,
ko bacci bai d'aukeshi ba yaji Khairat ta farka a tsorace.
Da sauri ya dawo kanta yana kallonta, numfashi kawai take saukewa kamar wacce tayi
tseren gudu, a hankali ya furta "Khairat, lafiya? meya faru dake?"
Kallonshi tayi a firgice sai kuma ta rufe bakinta da hannu tana fashewa da kuka,
wata nauyayyen ajiyar zuciya ya sauke ya kau da kansa danya lura tana da saurin
kuka akan komai, sake cewa yayi "Khairat, meya faru?"
Share hawayenta tayi tana kallonshi tace "ba komai, kaje ka kwanta kawai."
"To me kake so nace? na fad'a maka bana son duhu, sune ke sake zuwa min duk da
qoqarina nasan ganin na manta komai, fyad'e ba abu bane mai sauk'i, amma duk da
haka ina so na manta dan nayi rayuwata ba tare da damuwa ba, naso na zama marar
tsoro da fargaba, amma su sun saka na zama mai tsoro, sunsa min fargaban da bana
iya sakewa a kowane lokaci, kullum ji nake kamar zasu qara dawowa gareni ne."
Hawaye ta goge tace "ka kwanta kawai." tana fad'a ta koma ta kwanta ta bashi baya.
Kallonshi tayi kuma lokaci d'aya ta dauke idonta, a hankali yace "baki iya bane?"
Nanma shiru tayi kawai sai yace "to ki d'aga hannayenki, saiki dinga fad'ar duk
abinda na fad'a, kinji?"
Yanda yace tayi, *ayatul kursiyu* ya fara karantawa sannan *ammana rasul*, kafin
suka karanta *falaq* da *nas* sannan ya karanta mata *Allahuma aslaftu nafsi
ilaikh, wa fawadhatu amri ilaikh, wa wajahtu wajhi ilaikh, wa aljahtu zahri ilaikh,
ragabatan wa rahabatan ilaikh, lamalja'a wala manja minka illa ilaikh, amantu bi
kitabikal-lazi anzalta wabi nabiyikal-lazi arsalta.*
Shafawa tayi sannan ta koma ta kwanta, a hankali ya tashi yana sake nanata kalmar
fyad'e a bakinshi, karo na farko daya ji haushin masu laifi kuma yaji inama shiya
d'auki mataki akansu , wutar d'akin ya kunna tare da komawa shima ya kwanta, ganin
haske yasa ta kashe na wayarsa sannan ta sake rufe ido sai bacci.
******************
Koda tanti ta koma gida tasa Zuby ta kira mata sauran 'yan uwanta a waya kasancewar
duka matane 'ya'yanta guda hud'u, nan fa ta fad'a musu matar Umar Faruk taci
mutuncinta tare da fad'a musu qudirin Khairat, nan fa suka fara zaginta suna
aibatata tare da cin alwashin fitar da ita daga gidan, sannan suka qara kitsama
Zuby wani sabon shiri a kanta tare da alk'awarta mata sabon had'in magani na
musamman domin yaqar Khairat.
Sai dai tanti ita burinta ya wuce nasu dan haka safiya ma take jira kawai tayi,
danta lura yarinyar dole sai an had'a da malamai.
******************
Tunda Khairat take a gaba d'aya tsawon rayuwarta, bata tab'a bacci mai dad'in na
yau ba, bata tab'a jin natsuwa da farin ciki ba a cikin bacci kamar yau, gashi kuma
ubangijinta ya nuna mata wani abu da ko kad'an bai firgitata ba saboda nutsuwar
data farka da ita, a baccinta Allah ya haska mata tanti Ma'u tana matuk'ar biyarta
da sharri , sai dai ta rasa waye kuma me yasa ya fad'a mata cewar ta rik'e addu'a
tafi komai mahimmanci, koda Umar Faruk ya tasheta tayi sallah zaune tayi ta murje
idonta kafin yace mata "ki fad'i abinda zan fad'a."
Kai ta jinjina alamar tana sauraro, *Alhamdulillahi lazi ahyana, ba'ada ma'ama tana
wa'ilaihir-nushur.*
Nanma fad'a tayi kafin ta shafa ta sauka daga kan gadon shi kuma ya nufi masallaci,
har tayi alwala tazo ta kabbara sallah tana tunanin akan me matar nan zata nemeta
da sharri, shin akan yarta ne ko kuma akan abinda ya faru tsakaninsu? da qyar ta
saita nutsuwarta ta samu tayi sallah tana gamawa kuma ko hijab bata cire ba ta
zauna bakin gado, a hankali take tunano addu'a da Umar Faruk ya fad'a mata jiya,
tana haka kuma ya shigo d'akin.
Kayanshi ya bud'a ya d'auko duk litattafan daya fad'a jiya sannan ya zauna akan
kujera, kallonta yayi yace "dawo nan ki zauna."
Ba musu tayi yanda yace, littafi mai tsarki ya bata sannan yace ta bud'e, a farko
ta bud'e sannan ya fara biya mata daga qananan surori har guda goma, kallonshi tayi
jin daga nan yake tsayawa yasa tace "to wai meka d'aukeni, iya haka zaka tsaya min?
kaga ni qara min kawai ai zan iya."
"Da farko dai ina so ki d'aukeni a matsayin malaminki, dan ta hakane za kiga haske
da albarka a karatun, sannan ki girmamani domin samun sauk'i, sai kuma jin maganata
a duk lokacin dana miki, kin fahimta?"
"In dai sai nayi haka zan samu albarka a karatuna, to na shirya zama dalib'a 'yar
shekara biyar a gaban malaminta."
"Da kyau." ya fad'a kafin yace "idan kina so na qara miki, ki fad'a min wanda na
fad'a miki sannan."
Gyara zama tayi kamar zata kwanta jikinshi sannan ta d'ora yatsarta a littafin ta
fara biya masa, duk da a cikin salon koyo take karatun, amma abin abin birgewa da
sha'awa, bakinta yake kallo wanda take motsashi a hankali tana biya karatun domin
gudun kar tayi sauri tayi b'ata kuma, sosai Umar Faruk ya girgiza domin kaf a cikin
waje d'aya kawai ya mata gyara, shima kuma ta fad'a ne ba daidai ba, murmushi yayi
har hak'oransa suka fito fili yace "kinyi qoqari sosai, kuma ina fatan zaki kasance
haka, har ranar da zaki hardace al'Qur-ani a kanki."
Wata irin lallausan dariya tayi data tafi da imanin Umar Faruk dan bai tab'a ganin
irinta ba a fuskarta, cike da jin dad'i tace "nima zan hardace a kaina, na zama
kamar k'anwar nan taka?"
Nan ya sake dora mata har suka kai suratul *Qari'a* sannan yace ta rufe littafin
tare da cewa "ki tabbatar kin kawosu gobe, idan ba haka ba kuma."
Kunnanta ya kama ba zato ba tammani ya murd'e fuska a had'e yace "ni kike fad'awa
haka? anya kina neman albarka kuwa?"
Hannayenshi ta kama duka biyu tana rokon ya saketa tana fad'in "dan Allah kayi
hak'uri wallahi ba zan sake ba malam, dan Allah kasa min albarka ko nayi saurin
fahimta."
Sakinta yayi yana tunanin ya samu hanyar da zaibi da ita cikin sauk'i dan haka yace
"idan akayiwa malam laifi har qasa ake duk'awa a bashi hak'uri, dan haka ki fara in
dai har da gaske dalib'a ce mai neman albarka."
Ita kuma yanzun nan taji a ranta bata da wani buri daya wuce na karatu, musamman da
taji wai yau itace take karatun littafi mai tsarki haka, shaukin abin ya shigeta
sosai dan haka bako tunani ta zube qasa ta kamo hannunshi ta rik'e tana murzawa ba
tare dama tasan me take yi ba tace "naji to kayi hak'uri dan Allah, ba zan sake ba,
nidai ina sonna samu albarkar karatuna."
Shima biye mata yayi ya dinga murza tattausan hannunta yace "ba albarkata kad'ai
kike buqata ba, akwai ta iyayenki, dama mutanen da kike zaune dasu."
Saida suka fita sun nufi d'akin Mama Maimuna yace "za muje ne mu gaida iyayenmu,
sai kice kina neman albarkarsu."
Kallonshi tayi kamar zata fashe da kuka tace "zafa ka rusa min jiji da kaina,
gaskiya ba zan iya ba."
"Shikenan, koma ki zauna, amma ki sani za kiyita karatu bakya fahimta, saboda ba
albarkar manya a ciki."
Bubbuga k'afafu tayi cikin shagwab'a ta kutsa kai d'akin Mama Maimuna, ganinta
kawai tayi ta fad'o mata dan haka ta tsorata, da sallama ya shiga sosai ya gaisheta
duk idonshi na kan Khairat da har yanzu ta b'ata rai, da ido ya mata alama kafin ta
fahimta ta kalli Mama Maimuna tace "ina...kwana, an tashi lafiya, ina neman albarka
dan Allah ki saka min."
Mama Maimuna mamaki ne ya hanata magana, saida Khairat ta sake cewa "ba zaki samin
bane kome?"
Kai ta girgiza da sauri tace "a'a 'yata, kin tashi lafiya? Allah ya miki albarka."
"To na gode, sai an jima." tana fad'a ta tashi ta fita shi kuma ya mata sallama ya
fita.
Kewayensu ta nufa shi kuma ya janyo hijab d'inta ya nuna mata kewayen Mama Sa'a,
ciki suka shiga amma Mama Sa'a harda rumgume Khairat tanata wasar baki tana
gaisheta, haushi ne yasa Khairat yin shiru ta kasa gaisheta, danta lura irin
mutanen nan ne masu shishigi, Umar Faruk kad'ai ya gaisheta kuma yanawa Khairat
alama da ido akan tarbiyar gaisheta amma tak'i, fitowa sukayi suka shiga d'akin
Mamanshi, suna shiga da sauri ta qarasa ta durk'usa gaban Mama tana rik'o hannunta
da fad'in "Mama ya jikinki?"
Cikin sakin fuska tace "da sauk'i 'yata, kin tashi lafiya."
"Ina kwana aunty Khairat." murayr duka yaran dake d'akin ta daki kunnuwanta.
D'an murmushin gefen labb'a kawai ta musu kafin suka juya kan Umar Faruk suka ce
"ina kwana yah Umar."
Juyawa tayi ta kalli Ruk'ayya dake shirin fita tace "har yanzu baku gama bane?"
"Me? yanzu fa? kuma Mama ta zauna tana jiranki? me yasa ne wai kuke haka? kamar dai
baku damu da ita ba."
Mtsssss, taja tsaki tare da tashi rai bace ta fita daga d'akin har tana karo da
Abbakar da Saratu da zasu shigo suma, wayarta ta d'auko ta dawo d'akin tana ci gaba
da kira amma ba'a d'auka, saida ta aika kira na hud'u sannan mutumin ya d'auka jiki
na rawa, tana jin ya d'auka tace "ka kyauta, amma yanzu bata kai nake ba, ka
gaggauta had'a min duk wani abinda kake dashi yanzu, amma karka saka arom
(d'and'ano) a ciki na mai tension ne, da zaran ga kama ka kirani."
Umar Faruk ta kalla wanda suma dukansu kallonta suke tace "dan Allah ka d'auki
makullin motata kaje *riva side* ka karb'owa Mama abinci."
Fita tayi shi kuma yabi bayanta, makullin ta d'auka ta bashi ta bud'a post d'inta
ta d'auki kud'i ta bashi, kai ya girgiza mata yace "ki barshi zan biya."
"Kai kayi magana a maka oder koni? kaine ka sani koni nayi niyya? dan haka karb'i
kawai."
Karb'a yayi ya cire doguwar rigarshi ya sake kayan sannan ya fita, yana fita ita
kuma ta shiga wanka ta fito ta shirya cikin riga da siket na shadda, kwalliya tayi
sosai kafin ta d'ora gyale a kafad'a ta d'auki jaka da takalmi, wayarta ta d'auka
da nufin kiranshi sai gashi ya shigo, hannu kawai ta tara masa ya bata makullin
sannan ta fita.
Bayanta yabi amma sai yaga ta shiga d'akin Mama, Mama ce kad'ai a d'akin dan haka
ta sake zubewa qasa tace "ga abinci nan kici Mama, sannan ki saka min albarka zan
fita wajen aiki."
"Allah yayi albarka yata ,daga yanzu har zuwa fitar numfashina na qarshe sanya
albarkata ba zai tab'a nesanta dake ba."
"Na gode Mama." ta fad'a tana yunk'urin tashi.
Komawa tayi yanda take tace "na'am Mama, akwai abinda kike sone?"
" 'Yata, wannan kayan na jikinki, bai kamata ki fita dasu ba a matsayinki na matar
aure, ki sani Allah ya umarcemu damu dinga rufe jikinmu a duk lokacin da zamu fita
daga cikin gidajenmu, kuma hakan nada alfanu sosai, hakan da zaki fita baiyi ba
sannan shi kanshi mijinki zaiji ba dad'i, yata, ina so ki zama salihar mace kuma
yar aljanna, amma fa ki sani ba'a zama salihar mace a haka, dan Allah yata ki kare
mutuncinki ko dan gudun sake faruwar abinda ya faru dake a baya, ki kame kanki ba
kowa jaki da alade bane ya kamata ace sunga surar jikinki, idan zai yiwu ki gwada
saka hijab ki gani, na tabbata zai miki kyau, dan sutura ce mai rufa asirin mace
tare da qara mata kwarjina da haiba."
Murmushi Khairat tayi ta sake makale hannun Mama tace "na gode Mama, kullum
mahaifiyata na fad'a min na dinga rufe jikina, yau kema gashi kin fad'a min, hakan
na nuna irin soyayyar da kike min."
Nan ta bar jakarta ta fita ta koma d'akinsu, cikin hijabban da Mama tasa aka d'inka
mata ta d'auko kalar aikin shaddarta ruwan qasa, tana saka hijab d'in ta kalli
kanta a madubi, wani murmushi ta saki ganin yanda ya d'auki jikinta ga hannayenta
da suka fito ya tsaya iya gwiwarta, fita tayi daga d'akin ta koma na Mama, su Mama
Sa'a mamaki ne ya kamasu ganin tana safa da marwa a d'akin, tana shiga Umar Faruk
da Mama suka sakar mata ido, tsaye tayi gaban Mama tace "Mama haka yayi, nayi
kyau?"
Tana fad'a ta d'auki jakarta ta bar d'akin ko kallon Umar Faruk, tana fita ta
d'auki hanya amma saboda rashin sabo yasa taji kamar an d'aureta , kasa jurewa tayi
hakan yasa ta cire ta ajeshi saman kujera harta isa ma'aikatar, d'aukar hijab d'in
tayi ta saka ta d'auki jakarta sannan ta fito, da gudu massinger yazo ya tareta
yana gaisheta, hannu kawai ta d'aga masa tayi gaba, tunda ta shiga idon kowa ke
kanta suna gaisheta da mamaki, kowa da abinda yake sak'awa a ransa, Khairat a wajen
aiki tunda safe haka gashi ko Umar Faruk d'in bai zo ba, sannan da sabuwar shiga,
harta tunkari office d'inta, dago ido Habiba tayi amma saita saukesu ba tare data
mik'e tsaye ba kamar yanda ta saba, saida Khairat ta tsaya gaban tebur d'in tana
kallonta, k'amshin turaren da taji ya tabbatar mata Khairat ce, a zabure ta tashi
tsaye tana fad'in,
"Wato *arniya kafira* yau ta shigo da hijabi, shi yasa har zaki kasa ganeni? dama
wad'ancen shashanshun sun bini da ido, shine kema zaki min fitsara."
Wucewa tayi mazauninta tana shiga ta zauna kuma ta cire hijab d'in ta rataye, a
gaba d'aya ma'aikatar kuma maganganu aka d'auka, wasu na ganin Umar Faruk yayi
namijin qoqari da har ya iya canza Khairat a qanqanin lokaci haka, wasu kuma na
mamakin ta yanda ya iya juyata harta zama haka.
_FAN'S ya kuka ce? nifa sai nake ganin kamar qoqarin na Mama ne ba Umar Faruk ba._
Abun mamaki jakarta naga ta d'auka kawai ta fito da littafin da Umar Faruk ya bata,
budawa tayi ta fara karatunta a hankali daki daki , dan bata so gobe ya tambayeta
ta kasa fad'a mashi, kodan gudun bulala.🤪
_Shin kuna ganin zai iya dukanta idan ta kasa kawo karatun daya koya mata?_
25/07/2019 à 09:22 - My BK est parti(e)
26/07/2019 à 08:04 - My Heenat: 🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾
💑💑💑💑💑💑💑💑💑💑
*ƘANGIN RAYUWA*
_(labarin Raheenat da Abdul Hakeem)_
🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾
💑💑💑💑💑💑💑💑💑💑
*RAHEENAT M ABBAKAR*
AND
*SAMEERA HAROUNA*
*DUKKAN YABO DA GODIYA SUN TABBATA GA ALLAH SUBHANAHU WATA'ALA DA YA BAMU IKON
RUBUTA WANNAN LITTAFIN NAMU, TSIRA DA AMINCI SU ƘARA TABBATA GA ANNABINMU FARKON
ƘAGA ƘARSHEN AIKA WATO ANNABI MUHAMMADU S.A.W*
```WANNAN LABARIN ƘIRƘIRARRAN LABARI NE, ƘIRƘIRAR RAHEENAT CE DA SAMEERA DAN HAKA A
GUJI JUYA MANA SHI TA KO WANI IRIN SIGA, DUK WANDA LABARINMU YAYI DAIDAI DA
RAYUWARSA TO AKASI AKA SAMU👏```
_WANNAN LITTAFIN ƊUNGURUGUM ƊINSA SADAUKARWA CE GAREKI ALAWIYYA, HAƘIKA KINA NUNAWA
RAHEENAT DA SAMEERA SOYAYYA, BAMU TA KAMARKI A DUK FANS ƊINMU, SHI YASA MA MUKA
BAKI LITTAFIN GABA ƊAYANSA, IN KIKA CE BABU WANDA ZAI KARANTA YA ZAUNU, DOMIN
GIRMANKI NE, KI HUTA KAWAI KIJI DAƊINKI MY LOVELY SISTER RAHEENAT DA SAMEERAT SUNA
SONKI HAR CIKIN ƘALBINSU❤ LOVE YOU TO ALL MY HEART❤_
*JINJINA IRIN TA BAN GIRMA GAREKU ƳAN ƘUNGIYARMU, HAƘIƘA MUNA MATUƘAR JIN DAƊIN
ZAMA CIKINKU, GIDANMU YA AMSA SUNANSA GIDAN ZAMAN LAFIYA DA AMANA KAMAR YANDA MUKA
KIRASHI. HAƘIƘA KU ƊIN MUTANE NE MASU KARAMCI DA SANIN YA KAMATA, KU HUTA KAWAI
❤
KUJI DAƊINKU RAHEENA DA SAMEERA SUNA YI MUKU FATAN ALKHAIRI*
*GAISUWA TABAN GIRMA GAREKI SHUGABA KUMA AINTƳNMU WATO AUNTY AISHAN UMMU, HAƘIƘA
KECE GINSHIƘIN KAFUWAR ƘUNGIYARMU. KIN KASANCE SHUGABA TA GARI GAREMU, MUNA JINJINA
MIKI👍 KI HUTA KAWAI AUNTYNMU RAHEENAT DA SAMEERA NA YINKI, FATAN ALKHAIRI DAKE DA
ZURI'ARKI ALLAH YAJA DA KAWANKI❤*
Page 1 to 5
" *Raheenat*! *Raheenat*!! , wai baki jina ne ? matsiyaciyar yarinya kawai. "
Cewar matar dake tsaye bakin murhu, wata matashiyar yarinyar da ba zata gaza
shekara sha shida zuwa sha bakwai ba ta fito daga wani d'aki tana d'aura d'an
kwali, abun mamaki a tare da ita shine duk da kyawun halittarta amma kayan jikinta
sai hamdala, doguwar riga ce ta shadda, amma fa tasha jiki sosai duk da kalarta
bleue ce, amma har tayi fari fari saboda tsabar wahala, durk'usawa tayi alamar
girmamawa tace "Inna gani."
"Raheenat me yasa hankalinki baya kwantawa idan ba ji kikayi ina kwaroroton daga
muryata a kanki ba ?, Ke kurma ce da kira d'aya biyu duk bai isa yasa kiji ba.?"
A ladabce tace "kiyi hak'uri Inna, wallahi tun kira na farko naji kuma na taso, to
d'an kwalina ne na tsaya nema...."
"Rufe min baki dallah, yau aka fara ne bare na yarda dake? ni dallah d'auki abincin
*Sadik* gashi nan ki kai masa d'akinsa."
D'ago ido tayi ta kalleta, a sanyaye ta tashi tsaye tace "bara na d'auko hijab."
"Ke!"
Ta dasa mata tsawa, a tsorace ta zabura ta juyo tana kallonta, "ke awa da har zan
aikeki kice wai sai kin d'auko wani banzan hijabi, wata tsiyace a jikin naki da
za'a kalla? dubeki fa."
Ta sake wata sallamar, muryar Sadik d'in ce yace "ki shigo mana."
Bud'a labulen d'akin tayi tare da sake wata sallamar, bata yarda ta had'a ido da
kowa dake d'akin ba harta aje kwanan, ta juyo zata fita taji an rik'e hannunta,
wata irin tsinkewa ne gabanta yayi ya fad'i ga tsoro daya bayyana a tare da ita,
juyowa tayi a hankali cikin rawar murya tace "dan...dan...Allah...yah Sadik ka.....
sake min hannuna na tafi."
Cikin wata dariya matashin saurayin yace "Raheenat na gaji da wannan jiran, me zai
hana ki bani abinda nake so a wuce wurin kawai? kefa ba yarinya ba ce nima kuma
haka, amma sai ki dinga yin abu kamar wata marar ilimi kuma yar qauye."
Mutsu mutsun ƙwatar hannunta kawai take amma ba tace komai ba, sake rik'e hannun
yayi gam yace "Raheenat, ki amince da buk'atata mana, ni kuma na miki alk'awarin
zanyi miki duk abinda kike so, wallahi za kiji dad'in rayuwarki, kuma zan saka Inna
ta daina miki duk abinda take miki, kinji?"
Ba tare data daina ƙoƙarin kwatar hannunta ba ta kawar da kanta gefe ta rufe ido
tace "dan Allah ka sakeni, na fad'a maka ba zaka tab'a samun abinda kake so ba daga
gareni, rayuwar da muke ciki bata kai na salwantar da mutuncina ba."
Sakin hannunta yayi ya nunata da yatsa yace "kiji nan da kyau, ni kuma saina nuna
miki nafi k'arfinki, wallahi saina sameki tunda har na k'wallafa rai a kanki, ko
kina so ko baki so saina cinma burina, koda kuwa hakan yana nufin numfashinki na
qarshe."
Jin haka yasa ta kalleshi da mamaki amma ba tace ƙala ba ta juya ta bar d'akin,
ƙannanshi dake kallon ikon Allah d'ayan ne yace "dan Allah yah Sadik ka fita harkar
yarinyar nan, karfa kaje kayi wani abinda za kasa kanka a matsala damu ma."
Hannu ya d'ora akan bakinshi yana kallon *Nuhu* yace "yimin shiru da bakinka, ba
matsalarka bace, idan kuma nasa kaina bance kowa ya shiga ba."
➡➡➡➡➡➡➡
Tana shiga d'akin nasu ta fara canza kayanta izuwa na islamiyya, riga da wando ne
da hijab, amma wandon har yana neman ya d'age mata gashi sunyi wani sid'ik dasu
kayan, musamman hijab da saman kanshi yayi fari tas ga wasu qananan hudodi akan
alamar zafin rana ta kusa kasheshi, haka ma 'yar doguwar rigar dake bakin gwiwa ita
kam a mazaunin duk ta tumurmushe sai wani k'aton d'inki da akayi a wajen, ba komai
a d'akin sai kayan jikinsu da kuma katifar baccinsu, kyakkyawa kuma matashiyar
matar dake zaune a bakin katifar ce ta lura da yanayinta dan haka ta d'anyi
murmushi tace "tunda naji tace ki kaiwa Sadik abinci, nasan shine silar wannan
shirun naki."
Da sauri ta tsaya daga saka hijab d'in ta nufo matar ta durk'usa gabanta ta rik'e
hannayenta tace " *Mama*, dan Allah mubar gidan nan, wallahi ina jin tsoron Sadik,
ya fara bani tsoro Mama."
Jaye hannunta tayi ta dafa kafad'arta tace "muje ina Raheenat ? Na d'auka nan ma da
muke taimakonmu ne akayi, kuma kinsan komai, toya kike so muyi?"
Kamar zata fashe da kuka tace "Mama za'a sake taimaka mana, amma dan Allah mubar
gidan nan dan komai zai iya faruwa, Sadik ba imanine dashi ba."
Kai matar ta girgiza tace "a wannan duniya tamu da taimako yayi wuya, taya kike
tunanin da mun fita daga nan za'a taimaka mana, Raheenat nasha fad'a miki cewar ki
kwantar da hankalinki, wallahi Sadik ko waninshi basu isa su cutar dake ba, saboda
kina tare da addu'ata, dan haka haka Allah ba zai bawa duk wani mai
ƙoƙarin son yaga ya cutar dake nasara ba, dan haka tashi ki shirya lokaci na
tafiya."
Rumgume mahaifiyar tata tayi tace "shi yasa nake alfahari dake Mamana, har kinsa
naji zuciyata ta washe."
Murmushi tayi itama tace "nima ina alfahari dake 'yata, tashi ki shirya to."
Qarasa shirin tayi ta d'auki wata irin bak'ar jaka da duk ta yamutsu ta kece ta
rataya a kafad'a sannan ta dawo gaban mahaifiyartata ta sunkuya tace "Mama kimin
addu'a tare dasa albarka?"
Kanta ta dafa tace "Allah ya miki albarka Raheenat, Allah ya kaiki lafiya ya dawo
min dake lafiya, ya baki ilimi me albarka wanda zai amfani al'umma, Allah ya
tsareki daga duk wani abun cutarwa ko sharri, ubangiji ya rufe idon mak'iya daga
ganin kyakyawar 'yata."
Ta k'arashe maganar da kama kumatunta, dariya dukansu sukayi kafin tace "na gode
Mama, ina miki fatan zama cikin aminci har izuwa lokacin da zan dawo gida."
Daga haka sukayi sallama ta fito ta kama hanyar islamiyyarsu, tana tafe tana
tilarwar karatu a kai saboda mahardaciyar ALQUR'ANI ce.
Da isarta ta taras har Sameera ƙawarta ta rigata zuwa, zama tayi kusa da Sameerar
tana faɗin "yau kin rigani zuwa Sam. "
Murmushi Sameera tayi tace "nima ɗin yanzun nan na shigo, naso shigowa gidanku sai
kuma nace ƙila kin wuce tun ɗazun. "
Littafin Hallul masa'i Raheenat ta ciro cikin jakarta ta fara ƙokarin dubawa domin
shine darasinsu na farko a yau tana cewa "wallahi kin ganni sai yanzu. "
Sameera bata ƙara cewa komai ba sai ga malam ya shigo ajin, nan itama ta ɗauki
littafinta dake kan tebur ɗinsu tana buɗawa, ba tare da ɓata lokaci ba malamin ya
fara gabatar musu da abinda ya kawo shi, nan duk ajin suka nutsu suna sauraronsa.
Ƙarfe shida daidai aka tashesu daga makarantar, jerowa Raheenat da Sameera sukayi
zuwa gida, domin unguwarsu ɗaya, duk da cewa Raheenat basu wani daɗe da zuwa
unguwar ba.
Tafe suke suna hirar karatunsu, faɗin wahalar littafan da aka sanya musu yanzun
sukeyi, Raheenat ce tace "ni fa duk wahalarsu be dameni ba tunda ina fahimta, kuma
akwai karuwa sosai a cikinsu, abinda yafi burgeni ma shine ayoyin alqur'anin da
suke cikin littafan. "
Murmushi Sameera tayi tace "akwai fa ƙaruwa wallahi, fata dai Allah ya amfanar damu
abinda muke karanta. "
"Ameen dai" cewar Raheenat, wanda faɗin hakan kuma yayi daidai da zuwa ƙofar
gidansu.
Sallama sukayiwa juna Sameera tayi gaba dan gidansu na gaban nasu Raheenat ne,
shiga gidan Raheenat tayi da sallama a bakinta, Inna dake zaune tare da ƴaƴanta
mata ko su ɗago su kalli Raheenat ba suyi ba balle ta saka ran su amsa sallamar da
tayi, nufar hanyar ɗakinsu tayi cikin sanyin jiki, daidai ta buɗe labulan ɗakin
nasu ta jiyo muryar Inna na cewa "ki shiga ki cire uniform ɗin ki zo ga wanke-wanke
nan na jiranki, ki gama kuma ki share gidan gaba ɗaya, sannan ɗakin su Farida ma
nason gyara, saura ki shiga ki ƙi fitowa da wuri, dan nasan munafukar uwar nan taki
in ta sakaki a ɗaki babu abinda takeyi miki sai huɗubar tsiya. "
Lumshe ido Raheenat tayi ta buɗe cike da jin ɗacin kalamar Inna akan Mamanta, cikin
mutuwar jiki tace "to Inna"
Tana faɗin haka ta ƙarasa shigewa cikin ɗakin nasu da sallama a bakinta.
Mama dake zaune ne ta amsa mata cikin sakin fuska tace "ƴar albarka kin dawo. ?"
Murmushi Raheenat ta saki wanda saida duka kumatunta suka lotsa ta ƙarasa kusa da
Maman nata ta zauna tana faɗin "eh na dawo Mamana, ina fatan dai kina cikin ƙoshin
lafiya kamar yanda na barki.?"
Murmushin jin daɗi Mama tayi tace "lafiya ƙalau nake ƴar Mamanta, saboda lafiya ma
zan iya zuwa makka da gudu in dawo."
Dariyar da bata shirya ba Raheenat ta saki tare da miƙewa ta fara ƙoƙarin cire
uniform ɗinta dan zuwa gabatar da aikin da Inna tace suna jiranta, kafin yanzu a
fara mata tijara ita da Mamanta, tana cewa "haka nakeso ai Mamana, Allah ya kara
miki lafiya.?"
Ameen Mama tace tana kallon ƴar tata cike da so da ƙauna, a kullum tafi son taga ƴa
nata tana farin ciki, sam bata son ganin damuwa a fuskar ɗiyartata kamar yanda
itama Raheenat bata son ganin damuwar Mamanta wacce ita kaɗai ce gareta.
*ƘANGIN RAYUWA*
_(labarin Raheenat da Abdul-Hakeem)_
🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾
💑💑💑💑💑💑💑💑💑💑💑
*RAHEENAT M ABBAKAR*
AND
*SAMEERA HAROUNA*
DEDICATED TO ALAWIYYA❤
*Bismilallahi-rahamanir-rahim.*
Page _5 to 10_
Shara ta fara saboda ba taso magriba tayi tana sharar, tana karasawa kuma ta had'a
kwanuka ta wanke, ruwan wanke wanken ta had'a ta fita zubarwa a waje, bata an
karaba a cikin soro ta had'u da mutum har ruwan suka zuba sosai, muryar Farida
kawai taji tace "kutumar uba, yau ana shirin yinta."
Sai kawai ta shak'o wuyanta tayi yarb'i da ita tare da rufa mata baya ta fara
shirgarta tana fad'in "marar mutunci, ke yanzu ni zaki jika da ruwa in ba iskanci
ba? turoki akai ko?"
Saurayin da suke tare dashi ne a soron ya rik'e Farida yasa hannu ya tallabo
Raheenat yana fad'in "haba ke kuwa ya isa haka, ruwane fa ba wani abu ba."
"Ruwa ne ba wani abu ba? ruwan wanke wake ne fa, wallahi da gangan tayi munafukar,
saboda kawai ita bata da saurayi." duk tayi maganar ne a hassale.
Raheenat da share hawaye kawai take tace "dan Allah kuyi hak'uri, wallahi ban kula
bane, sam ba'a ganin mutum shi yasa."
Wani duka ta sake kai mata a fuska hakan yasa ta zube qasa ta dafe wajen saboda
zafin da taji, qafa tasa ta harbeta tana fad'in "zaki tashi ki wuce ko saina
illataki, banza kawai."
Tana zubar da hawaye ta tashi ta fita ta zubar da ruwa ta dawo, koda zata wuce ma
saida ta sake dangwararta a baya tana fad'in "shegiya kawai."
Tana aje bokitin ta nufi d'akinsu Farida danta gyara kamar yanda aka ce, nanta fara
da gayaran shibfidarsu dake kamar ta mahaukata saboda basa iya gyarawa, sannan tayi
goge goge tayi shara, saida ta saka turaren tsintsiya sannan ta bar d'akin shi
kanshi yana samun nutsuwa.
Ta fito kenan zata nufi d'akinsu Inna dake zaune ta kirata, karasawa tayi jiki a
sanyaye ta tsugunna, saida ta gama kallonta tace "d'akinsu Sadik zaki je ki share
musu, tunda rana ya fad'a min na fad'a miki amma na manta."
Hawayen da suka taho matane ta mayar dasu kafin tace "Inna dan Allah ki taimaka ki
bani abinci na kaiwa Mama, wallahi nasan tana jin yunwa."
Kujerar dake kusa da ita yar tsugunno ta dauka, ba tare da tausayi ko tunani ba ta
kuwa gabza mata ita, kasancewar ta kare kanta hakan yasa ta sauka a hannunta,
rintse ido tayi sosai tuni hawaye suka b'alle mata, masifa Inna ta fara "marar
kunya fitsararriya, yarinya sai iya shege da kinibibi, ni har in saki abu amma ba
za kiyi ba saikin kawo min uzurinki, wallahi dani dake nan a gidan, kuma bari shi
wanda ya kawoku gidan ya dawo kiga yanda za muyi dashi."
Raheenat kam tuni ta shige d'akinsu Sadik ta fara gyara musu shinfida , tana gamawa
tayi shara sannan ta musu turare, fita tayi ta maida kofar ta kara musu ita sannan
ta koma wajen Inna, dan dama bata basu abinci har sai ta tabbatar Raheenat ta gama
musu aikin da duk yasha gabansu sannan, tun kafin tayi magana ta d'auko wani
yamushashen kwano ta dangwaro mata har miyar kukan na fallatsuwa k'asa.
Dauka tayi ta nufi d'akin nasu inda Mama take, da sallama ta shiga d'akin Mama ta
amsa tana aje carbin dake hannunta.
Ajiye kwanan abincin tayi gaban Mama sannan ta zauna itama, kallon ƴar nata Mama
tayi cike ta tausayi tace "sannu da aiki Raheenat. "
Murmushi ta saki tace "wani aiki Mama, ba wani wahala fa, ga abinci nan ciki Mama
nasan kina jin yunwa sosai. "
Kallonta Mama tayi sosai sannan ta kalli kwanan tuwon da yake can ƙasar kwano tace
"kefa Raheenat.?"
Murmushi ta kuma tace "ni bana jin yunwa Mama, kedai kawai kici. "
Waro fararen idonta tayi tace "dan Allah Mama ki ci, wallahi nasan kina jin yunwa.
"
Kallonta Mama tayi tace "bazan ci ba har sai kema zaki ci, Raheenat ta yaya kike
tunanin zan iya cin abinci ke baki ci ba. ?"
Sun kusa ƙarasawa Mama ta cire hannunta badan ta ƙoshi ba saidan tabar wa ƴarta ta
ƙarasa duk da tasan itama ɗin ba ƙoshin zatayi ba, domin tuwan ko mutum ɗaya yaci
shi kaɗai ba ƙoshi zaiyi ba, ɗago kai Raheenat tayi ta kalli Maman nata, murmushi
Mama ta sakar mata tace "Alhamdulillahi. "
Raheenat ba tace komai ba ta maida kanta ta ƙarasa cinye sauran sannan tayi hamdala
ta miƙe ta ɗibowa Mama ruwan sha cikin wata tsohuwar randar dake ɗakin.
Saida Mama tasha ta wanke hannunta sannan itama tasha ruwan ta miƙe ta fice daga
ɗakin ɗauke da kwanan a hannu.
Wanke kwanan tayi taje ta ajiye a majiyarsa sannan ta ɗauki buta ta nufi rijiya
taja ruwa, bayi ta shiga tayi tsarki sannan ta duƙa ta ɗaura alola, saboda kiran
sallah da aka fara a masallatan dake unguwar.
Bayan ta idar da alolan ƙara cika butan tayi da ruwa ta nufi ɗakin nasu dashi,
bakin ƙofa ta samu Mama na shirin fitowa itama dan ɗaura alolar, miƙawa Mama butan
tayi ita kuma ta shige ɗakin domin yin sallar.
Sai da sukayi isha'i tare da shafa'i da wuturi sannan suka tashi daga kan sallaya,
memakon kwanciya bacci sai Raheenat ta ɗauko littafanta ta fara muraji'a, saida ta
tabbatar da iya duk karatun da akayi masu yau sannan ta mayar da littafai cikin
jaka ta ajiye, bata tsaya nan ba ta fara rero ƙira'ar karatun al'qur'ani cikin
daddaɗar muryarta me daɗin sauraro, kamar yanda muka ce muku Raheenat hafizace, dan
haka ta ɗinga rero karatu babu tsayawa saida ta karanto surori har uku, sannan tayi
addu'ar kwanciya bacci ta kwanta, zuwa lokacin tuni Mama ta daɗe dayin bacci.
*************
Washe gari tana yin sallah ko tsayawa azkar ɗin safiya ba tayi ba ta fito ta fara
ƙoƙarin hura wuta, wanda tasan dama aikinta ne, daƙyar ta samu wutar ta kama mata
sannan ta ɗaura ruwan koko, bata tsaya ba ta fara haɗa wanke-wanken da akaci da
daran jiya ta wankesu tas, tana kammalawa ta ɗauki tsintsiya ya share gidan ƙyal,
daidai kammala sharar ruwan da ta ɗaura ya tafasa.
Nufar ɗakin Inna tayi domin amso ƙullun da zata dama, sallama tayi bakin ƙofar
ɗakin har daki uku amma ba'a amsa mata ba, ta buɗe baki kenan zatayi na huɗun kenan
sai ga Inna ta fito cikin hargowa tana faɗin "dan jaraba kana bacci ma sai an
addabeka, tsaban baƙin ciki ba za'a barka kayi bacci ka huta ba, wannan masifa har
ina," mttsss taja godon tsaki.
Raheenat dai dake tsaye haɗiye wani mugun yawo tayi ta duƙa har ƙasa tace "ina
kwana Inna."
Wani mugun harara Inna ta wurga mata tace "daba kwana ba zaki ganni ne uwar
kinibibi, meye kika zo da wani sassafen nan ki na ƙwaɗa min sallama.?"
Cikin sanyin murya Raheenat tace "dama kamu nazo amsa na dama koko. "
Kallonta takai ga murhun wanda yake ci ganga-ganga da alamu ruwan tukunyar ya daɗe
ta tafasa sannan ta juya a fusace ta shige ɗaki ta ɗauko botikin kamun ta
dangwarawa Raheenat a gaba tace "gashinan kije ki dama gangin jaraba kawai. "
Ɗauka kwai Raheenat tayi ba tare da yace komai ba ta nufi bakin murhun dan dama
kokon, domin inda sabo ta saba da irin hakan.
My meera ce ta kalleni idanu cike da ƙwalla tace "my heenat ina matuƙar tausayawa
takwarar nan taki wallahi. "
Dariya nayi nace "da yake ka tausayi yayi miki yawa ba."
Dariya nayi nace "tunda ke kin gane ai kamar Raheenat ta gane ne. "
Raheenat tana kammala dama kokon ta mayar masu Farida da ruwan wanka akan wutan
cikin wata ƙatuwar tukunya, ɗaukar kokon tayi wacce tafi rabin kafilas (babban
farin roban fanti) ta nufi ɗakin Inna dashi.
Muje zuwa🥰
Meeraheenat ne💋
26/07/2019 à 08:08 - My Heenat: 🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾
💑💑💑💑💑💑💑💑💑💑💑
*ƘANGIN RAYUWA*
_(labarin Raheenat da Abdul-Hakeem)_
🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾
💑💑💑💑💑💑💑💑💑💑💑
*RAHEENAT M ABBAKAR*
AND
*SAMEERA HAROUNA*
DEDICATED TO ALAWIYYA❤
_NA_
_SAMIRA HAROUNA_
_DEDICATED TO_
*MA FAMILLE*
_Bismmilahir-rahman-rahim_
2⃣8⃣
Shima wani littafi ya bud'a ya fara karantawa, ya jima sosai kafin ya aje ya tashi
yayi wanka ya fito ya fara shiryawa, ganin zai saka kaya yasa Khairat sauka daga
kan gadon zata fita, tana saukowa tari gabanta yana mata wani irin kallo yana
warware rigar dake hannunshi zai saka, giftashi tayi zata wuce ya sake tareta,
numfashi ta sauke ta kalleshi fuska ba annuri tace "meye matsalar?"
Saida yaja wani dogon numfashin kafin yace "d'azu kin sumbaceni, me yasa?"
Zata fice ya janyo hannunta, wani kallo da sukawa junansu lokaci d'aya kuma Khairat
ta d'auke idonta, cikin kissa da mazantaka Umar Faruk ya rumgumo kugunta ya had'a
da nashi yasa hannunshi d'aya ya cire hular dake kanta ya fara wasa da gashinta,
kafeta yayi da ido akan yasa ta kasa kallonshi, qirjinshi kawai take kallo gabanta
na faduwa sai dai kuma shima tana jin yanda zuciyarshi ke bugawa saboda hannunta na
kan saitin zuciyarshi, a hankali ya sunkuyo da kanshi ya kalli fuskarta, ganin tayi
quri da ido tana kallon qirjinshi yasa ya hura mata iska a ido, da sauri ta
lumshesu kai tsaye kuma ta bud'e ta kalleshi, saida ta had'e yawu masu daci sannan
tace "me ka keyi haka, ka manta meka fad'a jiya?"
Wani shu'umin murmushi yayi yace "ke kika tab'oni ai, akan me kika sumbaceni? dan
haka ramawa zanyi."
A k'arfi ta kwaci kanta tayi baya ta nunashi da hannu tana fad'in "karma ka fara
wallahi, karka dauka nayi ne dan jin dad'i, kawai ni nayi ne saboda mutanen dake
wurin, idan kuma kace zaka tab'ani harka sumbaceni, wallahi...."
D'orawa yayi da "meye na rantsuwa, karki wahalar da kanki, kece zaki kwana a ciki
danni ina da mata, yanzu haka ma wajenta zanje."
Wani dammm, taji gabanta yayi amma saita dake tace "to ina ruwana da matarka ni,
kuma wallahi kaje ka kai mata kwana na, to ban yafe ba."
Duk da ganin ya zame towel d'in jikinshi sai qaramin wandon dake jikinshi baisa ta
daina fad'ar abinda take fad'a ba ta rufe ido sai masifa take "wallahi ba zan yafe
ba ko mutuwa za kayi, haka kawai ka mayar dani wata ballagaza kana cin amanata,
toni ba sakarya bace wallahi, kuma kaje daga kai har matarka zaku shigo hannuna,
aikin banza kawai kace waini na janyo komai, ba wani nan dama kana so kawai baka
samu damar tafiya bane inda za'a baka."
Yana cikin d'aure belt d'inshi ya kalleta yace "kema ai nasan kinji wani abu a
lokacin, watak'ila har yanzu kina jin shauk'i tunda mutum ce ke, sai dai ko in kina
da k'arancin isassar lafiya."
"Kuutt, ni d'in ce ma banda lafiya? wallahi lafiyata k'alau ni, sai dai in kaine
baka da lafiyar."
"Ni ai dama bance miki bana da ba, ke dai nake tunanin ba kyada ita."
"Wallahi ina so da." ta fad'a tana juya baki.
"Kin tabbatar?"
Matsowa yayi kusanta yace "kenan kema kinji wani abu d'azu."
Saida ya b'alla botir d'in rigarshi yace "to in kina so na yarda babu abinda ki
kaji, ki bani dama na bincika da kaina saina gane, amma in ba haka ba to qarya kika
fad'a kina b'oye wani abu a ranki."
Babbar yatsarta tasa a bakinta tana kallonshi tana tunani, fito da yatsar tayi tace
"ka rantse babu cuta a ciki."
Matsowa ya sakeyi kusanta yana fad'in "ok, bani minti d'aya tak ya isa na gano
gaskiyar komai."
Kafin tayi magana taji bakin Umar Faruk a nata bakin, "ahhhh." kuma sai tayi shiru
tare da lumshe ido.
Shi kanshi ji yake kamar bashi ba dan bai shirya yin hakan ba, zuciyarshi kawai
yaji tana izashi akan yin komai, bayanta yake shafa a hankali yana latsawa har
lokacin daya zura tafikan hannayenshi ta cikin rigarta, bras dake jikinta ya balle
ba tare daya cireta ba yakai hannayenshi a mamanta, jin yanda yake shafasu ne yasa
Khairat qamqame Umar Faruk sosai tare da turo masa gabanta, shi kanshi sake fita
hayyacinshi yayi yanda yaji gaban tsam tsam dashi kamar an hura mata iska, wani
numfarfashi yake saukewa yana ji yana so yakai wata gab'a da baisan ko zai iya
jarumtar hakan ba.
Yanda ta qamqameshi tare da cabko harshenshi ta fara tsutsa yasa gaba d'aya ya rasa
wanene shi me kuma yake yi, biye mata yayi suka fad'a kan gado, harya fara shirin
rabata da rigarta sai kuma ya tuna minti d'aya ne gareshi, a zabure ya tashi tsaye
yana gyara jikinsa da saisaita nutsuwarsa, Khairat ma a firgice ta tashi zaune tana
ganin an fara cire mab'allan rigarta tayi saurin rufe qirjinta tare da duk'e kanta
qasa, kasa had'a ido sukayi harya d'aga qafafunshi ya bar gidan.
Kasa motsawa tayi daga wajen tana tunani har bacci ya fara fizgarta, daga nan kuma
ta kwanta sai bacci.
***************
Yana fita daga nan siyayya yayi ta yan kayan motsa baki ya wuce gidansu Zuby, dan
tun ranar daya rabata da budurcinta bai sake komawa ba, bai samu tanti a gidan ba
sai Zuby kad'ai, yayi mamakin rashin tanti a gida a wannan lokacin amma ya zaiyi,
da gudu Zuby ta qaraso ta rumgumeshi, shima rumgumeta yayi dan dama a tafashe yake,
amma abin mamaki shine, abinda yaso yaji bashi yaji ba, ga dukkan alama ba tayi
wanka ba kodan bata san da zuwanshi bane oho, a hankali ya raba jikinta da nashi
yana murmushin yak'e, "sannu da zuwa yah Umar, shine ko ka sanar dani kana zuwa?"
"Ina so na miki bazata ne." ya fad'a suna nufa d'akin da aka ware mata.
Tsaye yayi yana kallon d'akin ganinshi a yamutse, da hannu ya nuna mata yace "meye
haka Zubeid? na d'auka nan shine muhallinki."
"Eh yah Umar, ai an fara tattare min kayana ne gobe za'a kaisu can gida ayi gyara
d'akin, jibi kuma saina tare." ta k'arashe maganar da jin kunya.
Ya karb'i uzurinta hakan yasa ya bata ledar hannunshi yana fad'in "ya jikinki."
"Kai yah Umar, yayi sauk'i fa." ta fad'a cikin rufe fuska.
Hannunta ya kamo ya sake rumgumeta a jikinshi cikin sanyayen muryar da baima san
yana da ita ba yace "kinyi kewata kuwa?"
Cikin tsoro ta bud'e baki tace "yah Umar, ba yanzu ba gaskiya, ka bari saina dawo
gidanka."
Cikin shagwab'ar da tunda yake a rayuwa bai tab'a irinta ba yace "kenan tsoro kike
ji? zafi ke akwai ne har yanzu?"
"Eh to yah Umar, akwai zafi kuma akwai wahala, amma dai ba sosai ba."
Kafin tayi wata magana yace "ni zan koma gida, ki gaida tanti idan ta dawo."
Sallama sukayi ya fita, fitarshi kuma tanti ta tsinkayeshi sai dai shi bai ganta
ba, tun daga soron gidan ta fara kiran "Zuby, Zuby, ke kina ina fito fad'a min
waccen mara mutuncin me yazo ya miki, injin dai baki yarda dashi ba? dan na lura
yaron nan so yake saina mashi rashin mutunci."
Zuby dake tsaye tana kallonta tare da sauraronta ne tace "kai Mama, bafa abinda ya
kawoshi kenan ba, kawai yazo ganina ne."
Dorawa tayi da "kinga abinda nake fad'a miki ko, tunda ki kayi aure nake fad'a miki
ki saba da yawon wanka amma ba kyaji, yanzu gashi ya miki zuwan bazata, ke ko kunya
baki ji ba?"
Ganin zata maida bala'in a kanta yasa ta shigewarta d'akin ta d'auki ledar tsirenta
ta fara ci, shigowa tayi tana ganinta ta fizge ledar tana fad'in "shegiya
matsiyaciya , wato ke kad'ai zaki ci saboda baki da mutunci."
Fita tayi da ledar Zuby kuma ta bita tana fad'in "wai Mama me yake damunki ne, to
kema ke kad'ai zaki ci, dan Allah ki bani kayana."
_Ganin uwa da d'iya zasu botsare akan ledar tsire yasa na fito,danni ba wajen kuka
na bane, da kaza ce😁 da sunga sabon tashin hankali *amma fa shima ina sonshi,
musamman na madugu mai nama*._😂maman Dady.
*************
Ishaq ya samu a kofar gida dan haka ya tsaya suka gaisa, "kaga mijin mace biyu,
matashin yaro mai sa'a a duniya, wanda ya fara da zankad'a zankad"an mata a lokaci
guda, kai Umar Faruk ina fatan Allah ya bani irin taka."
"Humm, ba wata shiririta, kai dai kawai kace za kaje ne tana jiranka, aini na gama
sanin komai wallahi."
"Kuma, ka manta dazu a ma'aikata kun nuna mana sanfiri a fili mun gani."
Duka ya kai masa ya goce yana fad'in "kaifa d'an iska ne wallahi, to an fad'a maka
sone ya kawo hakan? kawai tayi ne saboda ire irenku 'yan gulma."
Rik'e kan mashin d'inshi yayi yace "kaii , amma fa Umar Faruk kana more rayuwa
wallahi, ace ko ina jin dad'i ne ya baibayeka, ka fita daga gida kabar santaleliyar
lace kaje wajen wata santaleliyar, gashi kuma zaka sake shiga ciki waje wata
zankad'aziyar."
"Allah ya shiryaka Ishaq, wallahi kayi sauri kayi aure, inba haka ba zaka mutu."
Tayar da mashin d'in yayi zai wuce cikin gida Ishaq yace "za kasha mamaki idan na
fad'a maka wacce nake so."
Hararanshi yayi yace "ya wuce kace Ruk'ayya kake so, banza kawai dake tsoron fad'an
abinda ke ransa."
Da k'arfi ya rik'e moton yana fad'in "waye ke tsoro d'in? naga ai bani kad'ai bane
ya kasa fad'a, kaima ka kasa fad'a."
Sake kashe moton yayi yace "wa wai? ni kake nufi? ai kasan ni tuni na wuce wajen
wallahi."
"Me yasa kake sha'awar mayar dani baya, kasan sau nawa ina fad'awa Zuby kalmar so?
yafi sau dubu."
Sosai Ishaq ya kalleshi tare da nuna ba wasa a abinda zai fad'a yace "saboda ba
ainihin sonta kake ba, Khairat itace wacce zuciyarka ta kamu da sonta, watak'ila ka
fahimci hakan, ko kuma ka sani kana take sanin ne, amma ka sani tun fil'azal dama
Zuby ba sonta kake ba, kawai sone na 'yan uwantaka da kuma shak'uwa."
"Kasan me kake fad'a? kaifa kasan Zuby da Khairat, kuma kasan matsayin kowace a
zuciyata, to me yasa kake so ka nuna bana qaunar Zuby?"
Rumgume hannayenshi yace "sanin haka ma yasa nace maka Khairat itace masoyiyar
zuciyarka, amma ba Zuby ba, kayi tunani hakan haka da kanka zaka fahimci gaskiyar
da kake b'oyewa, kayi tunani da kyau zuciyarka zata bayyana maka alamomin a fili
wanda take fad'awa a duk lokacin da tayi tozali da Khairat."
***************
Saida ya shiga yaga Baba ya mishi sallama haka ma d'akin Mama sannan ya wuce
d'akin, ganinta kwance tana bacci yasa ya cire kayan jikinshi ya watsa ruwa ya
sauya kayan bacci sannan ya zauna makwacinshi, remonte ya dauka ya kunna qira'a ya
fara biya.
Sautin k'ira'ar daya kunnane yasa ta farka, saida ta murje ido sannan ta zuro da
qafafunta ta sauko daga kan gadon duk yana kallonta, tana kallonshi taji haushi ya
lullubeta wato ya dawo daga wajen matarshi, hararanshi tayi ta bud'a ma'ajiyar
kayanta ta d'auko qaramin wando iya cinya da rigarshi hannayen sun d'an sauko zuwa
damtse, yana kallo ta cire rigarta sai bras d'in daya b'alle mata ko gyarawa ba
tayi ba, juyowa tayi sai kuwa sukayi ido takwas takwas, hararanshi tayi ta juya ta
zage bras d'in ta d'auki rigar baccin ta saka, juyawa tayi ta sake kallonshi tace
"zan saka wando fa."
"Miye nawa a ciki to?" ya fad'a yana d'auke kai daga barin kallonta.
"Nak'i d'in, idan zaki saka ki saka, kuma ma ai naga ke ba lafiya ne dake ba." ya
fad'a kamar bashi ke maganar ba.
Da hannu a nunashi tace "kai, karka qara cemin bana da lafiya, Allah ranka zai
b'ace."
"To kina da lafiyar ne? aini ba zan tabbatar ba har sai jarabaki na gani."
"Hahahahaha, kaji yaro, waini zai mayar shashasha mahaukaciya, to an fad'a maka ni
d'in yar shekara goma ce da zaka mayar dani abar wasarka, to bari kaji, inma wani
abu kake nema a wajena ka sani ba zaka samu ba, ka jira amaryarka tazo sai kuje ku
cinye kanku, tunda naga ita d'in marar aji ce da har zata bada kanta tun bata tare
ba."
Maida kanshi yayi ça tv yace "kedai kiyi fatan kar Umar Faruk ya buk'aceki, dan
hakan na faruwa to ki sani kin zama sorry."
"Dan Allah Faruk ka buk'aceni, ni kuma a lokacin zan nuna maka nawa d'anyan kan."
"To waima me kake tunanin zaka min? tausheni ta k'arfi kamin fyad'e."
Saida ya kalleta yace "kina ganin ba zan iya bane?"
Tana fad'a ta juya ta fara zuge dogon wandonta, bata kai ga cirewa ba taji an
hankad'ata saman gadon ta fad'a, kafin taga wanda yayi aika aikar kuma aka tausheta
, duk da dai ta gane Umar Faruk ne amma bata fahimci yanayinshi ba, had'e
hannayenta yayi da katifar ya taushe tare da sakar mata gaba d'aya nauyinshi,
taushe mata qafafu yayi da nashi qafafu sannan ya had'a goshinsu wuri d'aya yana
kallon qwayar idonta, yunk'urawa tayi da nufin ta tashi amma taji ko matsawa ta
kasa yi dan ba qaramar matsa ya mata ba, bata san lokacin da hawaye suka zubo mata
ba suka fara gangarowa ta kunnuwanta, da qyar take fitar da numfashi sama sama ga
zuciyarta dake barazanar fitowa waje, tausar daya mata yasa yake iya jiyo bugawar
da zuciyarta keyi, cikin muryar kuka tace,
"Dan Allah Faruk ka d'agani, wallahi ni ba dakai nake ba, ina jin tsoron abinda
za'a aikata, zaka iya jimin ciwo kamar yanda suma suka min."
Wani mugun tausayinta ne ya rufeshi dan take qwaqwalwarshi ta hasko mashi photonta
kwance a gadon asibiti bata san inda kanta yake ba, basarwa yayi ya mata kallon ki
shiga hankalinki sannan yace "wannan sanfiri ne na nuna miki, idan kika qara
qalubalantar mazantaka ta, to zan wuce inda bakya zato kuma nayi kaca kaca dake."
D'agata yayi ya koma mazauninshi yana fad'in "sai tsoron tsiya amma kuma ba hus,
hada wani wai zaka jimin ciwo, ko ciwon me zanji ma wacce ke a bud...."
Sai kuma yayi shiru dan yasan ba lallai maganar ta mata dad'in ji ba, ba abinda
bata jiba hakan yasa ta share qwallanta tace "eh naji, nasan idan ka kusanceni ba
zan galabaita ba, amma kuma nasan dole zansan ka shigeni, saboda na yarda da kaina,
kuma nasan cika bakin ba zai rasa nasaba da waccen figaggiyar matar taka ba, ita
dake budurwa ai banga kayi sammakon zuwa kai mata d'auki ba."
Saida ta sauke numfashi sannan tace "wallahi ka sake cin zarafin matsayina saina
had'aka da mahaifinka ya shiga tsakaninmu."
Bata damu dashi ba ta zage wandon ta saka na bacci sannan ta kwanta, tunowa da
addu'a yasa ta tashi ta kalleshi tace "ka taimaka ka koya min addu'ar kwanciya
bacci."
A wulak'ance ya kalleta tare da harara, itama hararar ta banka masa had'e da juya
baki , tasowa yayi yazo kan gadon ita kuma tana ganinshi ta wuntsila ta sauka, ta
kan gadon ya taka ya ritsata saboda bata da hanyar bi, hannu ya kai zai shak'o
bakinta ita kuma tasa hannu ta rufe bakin tana fad'in "na tuba, wallahi mantawa
nayi ba zan sake ba."
Kunnenta ya kama sosai ya murd'e yana fad'in "zaki koma kenan in dai har kina
mantawa."
"A'a wallahi, a'a ba zan sake ba, na shiga uku kunnena , dan Allah kayi hak'uri
kunnena zai cire, dan Allah Faruk kunnena."
Duk tana maganar ne tana tsalle tsalle da yarfa hannaye ya saketa , "sai kinyi
alk'awarin ba zaki sa...."
"Nayi nayi, wallahi nayi, ba zan sake ba." ta fad'a tun bai qarasa ba.
Sakinta yayi ya sake kafeta da ido yace "me sunana?"
Da k'arfi ya bugi bangon dake bayanta yace "sunana kenan na yanka, amma ba sunan
daya kamata ki kirani dashi ba kenan, ina so naji sabon sunana."
Kallon gefenshi tayi tana sharb'ar majina😁irinta ansha kukan nan ta fara girgiza
kai tana fad'in "dan Allah ka bari zanyi tunani akai."
"Me? sunan ne sai kinyi tunani? zan zubar miki da hak'ora ma."
Ya fad'a kamar zai kai mata mazga, dafe kai tayi ta durk'ushe, "tashi tashi." ya
fad'a yana mata alama da hannu.
Tsaye ta mik'e duk tayi kalar tausayi sannan yace "ina jinki."
Gashinta dake kwance kan wuyanta ta kama tana wasa dashi tana ta rarraba ido, can
ta tuna ta kalleshi cikin lab'e baki tace "baby."
Wata shegiyar dariya Umar faruk ya kece da ita kafin yace "baby? ki aje wannan
sunan har ranar da kika shirya d'aukata a matsayin mijinki, amma ba yanzu ba."
Hannunta ya janyo ya zaunar da ita a inda ta tashi yaja zanin rufa ya rufa mata
sannan yace ta d'aga hannayenta suyi addu'a, haka sukayi har suka gama sannan ta
shafa ta kwanta, kallonshi tayi tana mamakin izzarshi da kwarjini, ko ba tayi
niyyar abu ba inda ya canza yanayinshi to dole take yi, tunawa tayi da sak'on Papa
hakan yasa tace,
Kallonta yayi yace "Germany kuma? wajen me? kuma dole sai dani?"
A hassale ta sauko daga kan gadon ta fara nunashi da yatsa tana fad'in ".....
_NA_
_SAMIRA HAROUNA_
_DEDICATED TO_
*MA FAMILLE*
_Bismmilahir-rahman-rahim_
2⃣9⃣
"Anya Faruk zaka iya zama shugaba mai adalci kuwa, waini meka d'aukeni ne? dabba ko
marar anfani? ace matarka zata tare amma ni na kasa sani sai tana jibi zuwa, shima
kuma bawai ka fad'a min ne ba a'a maganar dana d'auko ce tasa ka fad'a min, to
wallahi ba zan yarda da wani wulak'ancin ba, kai in banda ma k'addara nida nake so
na auri wanda zaimin alk'awarin ba zai tab'a min kishiya ba, sai gashi nazo na
aureka, amma kuma har kake kokarin wulak'antani akan wata figaggiya, to ba zai yiwu
ba wallahi, gari na wayewa zanje na samu Baba na fad'a masa duk abinda kake, na
fad'a masa a rage maka nauyi d'aya dan ba zaka iya zama mijin mace biyu ba,
jarumtarka bata kai can...."
Shiru tayi saboda hararar daya watso mata, kallonta yake bako qyabtawa ita kuma
tace "ko kasheni za kayi saina fad'a, tunda abun rainin wayo ne."
Shi fa harga Allah ba wai yaki amincewa bane saboda Zuby, kawai dai baya so da wuri
haka ace ya fita qasar waje kuma tare da ita, yasan zaisha maganganu da tsirfa iri
iri, yafi so idan Allah ya hore masa nashi na kanshi, saiya d'auketasu keta hazo a
duk inda suke so, amma ba irin haka ba kuma daya zama tarone ba wani biki ko
zumunci ba, to amma ya zaiyi tunda tana barazanar fad'awa Baba, bari ya mata abinda
take so kawai tunda dai laifinshi ne da bai fad'a mata ba.
Shima tasowa yayi ya tsaya gabanta tare da sakin fuska ya kamo hannunta yace "me
kike so nayi Baby?"
Hararan wasa ta wurga masa tare da turo baki gaba tace "wacece babyn? ka nemi
babynka ma tun wuri.
"To naji zan nema idan lokaci yayi, yanzu fad'a min me kike so nayi da zai goge
laifina?"
"Sai dai in zaka yarda ka biyoni muje." ta fad'a tana d'an rausayawa.
"To na yarda za muje, amma ba zan wuce kwana biyu ba zuwa uku."
Juyowa yayi ya kalleta "na lura kamar baka san kusantar ahlina da kuma dukiyarmu,
dan tun ranar da akace min anbaka gida da mota amma kak'i karb'a na fahimci hakan,
amma ka sani iyayena ba k'ananan mutane bane da zasuyi abu kuma su goranta , haka
nima duk wanda taimaka to bana iya tuna koda fuskarshi bare na tuna me nayi masa,
ka saki jikinka ka babu abinda zai faru, ka d'auka kamar kaine ka biya mana kud'in
jirgi, sannan kasa a ranka kamar zaka tafi cin amarci ne da uwar gidanka."
Murmushi kawai ya sakar mata ya kwanta akan kujerarshi yana qara gyara kwanciya,
ganin sai juye juye yake yasa ta taka har gabanshi cike da kissa ta kamo hannunshi
ta tako dashi har gaban gado ta zaunar dashi, kwantar dashi tayi ta dora kanshi
akan pillow kamar jariri taja zanin rufa ta rufe masa rabin jiki, haurawa tayi ta
kanshi ta kwanta gefe itama taja zanin ta rufa, kallon juna suke amma ita ta rufe
idonta, tunani ne take indai har kishiyarta zata tare jibi a maimakon wata biyu da
akace, tofa ba zai rasa nasaba da ita ba, in kuwa hakane ya zama dole ta tashi
tsaye koda bata samu soyayyar Umar Faruk ba, to ta samu koda tunaninsa ta yanda
zata addabeshi, kuma ba zata samu hakan ba harsai ta kusanta kanta dashi.
A hankali ta bud'a idonta sai kuwa taga ashe shima idonshi na kanta, ji yake kamar
ya dinga tsotsar bakinta harya gaji da kanshi, murmushi ta masa tare da dora
hannunta a bayanshi ta qara had'a jikinta da nashi, daga haka kuma bacci ya
d'auketa, yayin da tabar Umariri ido bud'e abinda duniya ya isheshi, had'e
cinyoyinshi kawai yake saboda ji yake kamar wani abu zai b'illo daga nan😂, saida
yaga tayi nisa a bacci ya sake tausa kanta a qirjinshi yana shinshinar wani
daddad'an k'amshin tuffa ga numfashinta dake fitar da k'amshin kanunfari, sannan
k'amshin jikinta kuma ya rasa dame zai misaltashi ma kamar sabulu kamar turare, kai
koma dai miye yana da dad'in shak'a da kwantar da hankali da kuma tayar da
hankalin.....jijiya."
Ko alama bai rintsa da idonshi ba, daf da a kira sallah asuba Umar Faruk yaji kamar
zai mutu saboda bala'in abinda yake ji, ga mararshi data d'aure take ciwo ga
azababben zabbab'in daya rufeshi, sake matse Khairat yayi sosai a jikinshi ya d'ago
da kanta ya fara sumbatar fuskarta, a tsorace ta zabura zata mike yayi saurin sake
damk'arta ya had'e bakinsu, tsotsar bakinta yake sosai yaki bata damar da zata
'kwaci kanta, dukanshi ta fara yi tana ihu sai dai ba'a jinta, abu d'aya ne ke mata
yawo a tunani shine su Musa, shi kuma mafita kawai yake nema, wata cakuma daya
kaiwa mamanta yasa ta zabura tare da k'amewa, dauke bakinshi yayi daga bakinta ya
saukeshi kan d'aya daga mamanta ya fara tsotsa d'aya hannun kuma yana murzar
d'ayan, mafita d'aya ta rage mata shine tayi ihu , ai kuwa zage damtse tayi ta
rumtuma wata qara da shi kanshi saida ya tsorata, a wahalce ya dago da jajayen
idanunshi cike da rauni ya tallabota gaba d'aya ya had'ata da jikinshi ya kai
bakinshi cikin kunnenta yace,
"Ni, ni dai ka sakeni dan Allah." ta fad'a tana shirin k'watar kanta.
Sake kai bakinshi yayi ga mamanta yana tsutsa ita kuma tasa hannaye tana ture
kanshi da k'arfi, bille bille take sosai yanda dole ba yanda ya iya daya rabu da
ita ya kife a wajen ya kwanta, ruf da ciki yayi ya tusa kanshi a pillow yana sauke
numfashin wahala, tana ganin haka ta sauka daga kan gadon tana fad'in "jaraba
kawai, kaine fa harda cika baki wai kai ba zaka had'a jikinka da nawa ba, kenan
raina min hankali za kayi."
Hannu ta dora kan qirjinta ta tab'a taji yanda suka fara mata zafi saboda bala'in
matsar da suka sha, tsaki tayi kawai ta wuce douche lokacin kuma an fara kiran
sallah.
Har tayi wanka ta fito yana yanda yake , shiryawa tayi cikin doguwar riga ta
shinfida sallaya sannan ta kai hannu ta daddab'a qafarsa tana cewa "ka tashi fa an
kusa tayar da sallah."
A hassale ya tashi zaune yana fad'in "karki sake tab'ani kinji na fad'a miki,
muguwa mai bak'in hali."
Yana fad'a ya fita ya bar dakin cikin k'arfin hali ba dan ko yana ganin inda yake
takawa ba, da qyar yayi wanka shima ya fito amma saboda bala'in abinda yake ji yasa
ya kasa saka kaya a jikinshi ya koma ya kwanta, abin ya dameshi sosai kuma baisan
miye mafita ba tunda bai tab'a jin irin haka ba, ita kam ko a jikinta saida tayi
raka'atanil fijir sannan tayi sannan ta kuma jima zaune tana addu'a da tasbihi
kafin ta tashi, cire hijab d'in tayi ta nade sallayar duk tana kallonshi kuma sarai
tasan miye matsalar saboda tana da wayewa ta wannan fannin, amma dai ba zata iya
taimaka masa ba take ji, littafinta ta d'auko ta kwanta saman kujerarshi ta bud'a
ta fara karatu, jefi jefi tana kallonshi tana basarwa, gari ya fara haske ta sake
juyawa ta kalleshi ganin mutum mai ibada amma har yanzu ya kasa tashi yayi sallar
farilla, aje littafin tayi ta qarasa wajenshi ta d'an daddab'a faffad'an bayanshi
tana fad'in "Faruk."
Bata fad'i abinda taso fad'a ba saboda jin atsakanin zafi a jikinshi, bata wani
daga hankalinta ba saboda tasan a ina matsalar take, fitilar d'akin ta kashe tazo
taja zanin rufa tare da haurawa kan gadon ta kwanta kusa dashi ta rufesu sosai, da
qyar ta birkitoshi sannan ta rumgumeshi a jikinta sosai ta matseshi, a hankali tasa
hannu ta zame rigarta daga jikinta ya zama daga ita sai pants, a hankali ta saka
mashi mamanta a bakinshi kamar 👶, da qyar ya iya bud'a bakinshi ya fara tsotsar
mamanta a hankali ido rufe.
Duk da itama tana jin abin na ratsata amma dai had'e tata zalamar tayi ta dinga
shafar kanshi da duk ilahirin gab'a ta jikinshi, sai waje d'aya da bata fatan
hannunta ya kai can, Umar Faruk kuma da yake jin yana neman shidewa can kawai yake
so takai , a hankali ta kwantar dashi tare da haye ruwan cikinshi tana murza mishi
kan....kai kuyi hak'uri wannan rubutu yafi k'arfin alk'alamina.
_Suturtawa_
Sosai Khairat ta samarwa Umar Faruk da nutsuwa, har inda bata so takai saida ya
tilasta mata zuwa, tsorata dashi sosai saboda jin girmanshi da rik'ewarshi, take
fargaba ya shigeta tare da fatan kar Allah ya kawo ranar da zai kusanceta, tun Umar
Faruk na nishi da numfarfashi da ihu😁harya fara had'awa da kuka, kalamai dai ba
wata tsiya ba Khairat tasha su, ita kanta ta lundu ta kuma gurzu amma bata yarda ya
shigeta ba, dan irin haka take so ya fara jin banbacin salo kafin yaji banbancin
hq, dan da hakane kad'ai zata zama tauraruwa itama a wajenshi, tunda tasan ta rasa
abinda za tayi tink'aho dashi.
*Wannan shine dalilina na saka akawa Khairat fyad'e, shifa budurci ba shine mace
ba, amma wasu na ganin daka rasashi ka rasa komai, baka da martaba da qima, to ba
haka abin yake ba akwai abubuwan da inka rik'esu za kafi mai budurci bakali a gurin
miji, tabbas ka rasa burduci kuma ba zaice na sameta budurwa ba, amma ace ka rasa
salon kwantarwa miji da hankali shine abin gudu.*
Juya mashi baya tayi a lokacin shi kuma yaji nutsuwa na zuwa mishi tare da
tsatsafowar zufa daga jikinshi, a hankali ya matsa kusa da ita ya rumgumeta ta baya
yana sumbatar kanta, da qyar a bud'a bakinshi ya rad'a mata a kunne yace "na gode
Khairat, kin taimaki rayuwata."
Tashi yayi ya fad'a douche ya suburbud'a ma kanshi ruwa yayi wanka k'arfi 😂,
sannan ya fito ya zura doguwar riga ya shinfida sallaya ya kabbara sallah, harya
gama Khairat na yanda take itama dan haka ya tashi ya kunna mata chauf eaux
(heater), har ruwan suka tafasa ya juye mata a bokiti bata motsa ba, a hankali ya
rad'a mata a kunne "ki tashi kiyi wanka."
Khairat ko daga nan kwance ba komai take ba illa karanta karatun rashin kunya 😂,
dan inba fitar da kunyar tayi ba a yanda take ji yanzu sam ba zata sake had'a ido
dashi ba, ai kuwa dai murje ido tayi ta tashi zaune kamar wacce tayi bacci, towel
d'inta ta d'auka ta d'aura ta nufi douche ya bita da kallon *so* da *qauna*.
Tana gama wankan ta fito ta sameshi harya shirya abinshi, itama shirin tayi lokacin
Ruk'ayya ta kawo musu abin kari, har Ruk'ayya zata fita Khairat tace "idan an jima
ki share mana d'akin nan."
Yau ma hijab ta dora akan shirin atamfar da tayi kuma hakan ya masa dad'i sosai,
saida ta rigashi fita ta fara shiga d'akin Mama ta gaisheta sannan ta wuce wajen
aiki, tun a hanya ta yanke shawarar ba zata bari kishiyarta ta k'wace miji ita
kad'ai ba, dole itama ta samu.
*******************
Tana cikin ayyukanta Habiba tace ana son ganinta wata k'awarta, izini ta bata ta
shigo da koma wacece, jim kad'an macho ta shigo, gyara zama tayi tayi kalar rashin
mutumci tana kallonta harta zauna, "meya kawoki?"
"Kiyi hak'uri macho, wallahi ban samu damar zuwa gidanki bane, amma nida Farida da
Hibba munyi shawarar zuwa insha Allah."
"Ke dallah karki raina min wayo, kinga Rashida, a gaskiya na gane *tarayyata* bata
da wani anfani, tunda na tare babu shegiyar data taka qafarta gidan nan, kuma tunda
na ganki anan kuma a yanzu , nasan wani abu kike so, dan haka dama dai abota daku
kune kuke qaruwa dani amma banda ni, dan haka ina ganin daga nan ya kamata mu raba
kaya daku."
Ko kad'an al'amarin bai yiwa Rashida dad'i ba, dan wata hidima ce ta taso mata
kuma a gun Khairat kad'ai zata samu kudi, in wajen samari ne to dole saita bada
wani abu itama kafin ta samu, "amma macho wane irin hukunci ne wannan? wallahi zamu
gyara dan Allah kiyi hak'uri."
Hak'uri da magiya ba irin wanda bata mata amma ta kafeta da ido ko magana tak'i
tayi bare tasa ran ta hak'ura, dole ta tashi ta fita rai a bace tana dura mata
ashar, ba ita kad'ai ba harda Umar Faruk da take ganin shine silar suyawarta.
Tana fita ta dora kanta akan makeken tebur d'in tana hasko irin wasan da sukayi da
Umariri, murmushi ta saki tana jin wani farin ciki zuciyarta na ratsata, da sauri
ta lumshe ido saboda tuna irin....🙈tana tausayin kanta ranar data shiga hannunshi🤓
karki damu tawan, aunty Aishan Umma tana nan tare dake.😉
Shima dai a b'angarenshi haka abin yake, *daren jiya* ya kasa fita a qwaqwalwarsa
da zuciyarsa , murmushi ne kawai akan fuskarshi mai tsada, tunani yake wace irin
nutsuwa ce to zai samu in har zai iya jin irin wannan farin cikin da kwanciyar
hankali saboda taimakon data masa, ko kuwa dai mutuwa zaiyi ma gaba d'aya tsabar
farin ciki da jin dad'i, _mutuwar lafiya_😏.
Daga shi har ita babu wanda ya tsinana wani abun kirki har aka gama sallah azahar
Khairat ta nufi gida, yauma saida ta tsaya gabanshi tace "ni zan wuce gida."
Har zata wuce taji ya janyo hannunta,tana juyowa ya tashi tsaye ya manna mata
kiss😘a goshi , yau ita mamaki ya shek'e shi kuma baiji komai ba saima aikin
gabanshi daya kama.
Fita tyi tana sakin murmushi jama'a ma dai yau basu saka musu idon nan ba kamar
jiya, har taje gida bata daina tunanin Umariri ba, shima kuma dama ba wani aiki
yake yi ba, tana fita ya kwanta akan tebur d'in yana murmushi tare da wasa da
alk'alamin dake gabanshi.
******************
Tun fitarsu ba dad'ewa yan uwan Zuby suka zo gyaran d'aki tare da kaya, tun kafin
su fara gyaran suka kalli kewayen Khairat *Uwani* tace "hum, ina zubarwa da kai
mutunci ba, kewayen nan da sunan Zuby akayishi amma ku d'auka kuba wata, ai wannan
rashin adalcine."
*Zabba'u* ce tace "waike kina mantawa da kud'i sunfi tasiri fiye da aikin boka ko
malam? ai kar kiyi mamaki kud'i suka gani fa."
"Kuma fa hakane, Allah ya shiryemu to , amma ni ko duniya zaka d'auka ka bani, aiba
zan qasqantar da kaina gareka ba wallahi."
"Ke kika san haka ai, baki ga harda sabon abin sanhwa aka sake ba?" cewar
*Zulfa'u*.
Da wanna kananan maganganun suka gama gyaran, ba laifi an cika d'akin da kaya, sai
dai tsari da qualitie ya banbanta dana Khairat, suna gamawa suka shekama d'akin
turaren wuta sannan suka rufe, ana kiran sallah azahar sukayi alwala sukayi sallah
sannan Ruk'ayya ta kawo musu abinci.
Sunacin abincin Hajja Khairat ta shigo, ta tarar kowa na tsakar gidan ana cin
abinci , ko kallon su Uwani ba tayi ba ta wuce wajen da Mama ke zaune tana bawa su
Yusuf da Fateema abinci, gwiwoyinta ta d'ora akan taburmar da suke zaune tace "Mama
sannu da gida, ya jikinki?"
Cikin sakin fuska da fara'a Mama tace "jiki alhamdulillah 'yata, har kin dawo?"
Cikin dariya Mama tace "albarkata na tare dake 'yata a koda yaushe, kije ki huta
yanzu Ruk'ayya zata kai miki abincinki."
"A'a Mama, ki barshi kawai." tana fad'a ta mik'e zata wuce ciki, Uwani ce tace
"koda nace, gashi dai da idona na gani."
"Hum, aini da wani ne ya fad'a mana ma ba zan yarda ba wallahi." cewar Zulfa'u.
"Nifa abin takaicin anan, yanda k'anwarmu zata zauna a wannan gida a wannan rayuwar
takaici, taya za tayi kishi da karuwa? yake ya k'wak'walo cutarshi yazo ya
mak'alawa yar uwarmu, ni shine yafi damuna."
Cak Khairat ta tsaya tare da juyowa ta kalli Ruk'ayya tace "sabbin mahaukata akayi
kuma a gidan?"
Maida kallonta tayi gareta ba alaman wasa a tare da ita tace "kin fahimci hakan
kenan?"
A take kula ta kalli Uwani tace "dama ku tunaninku zaku kawo yar uwarku ne haka
kawai ba tare da kun bata training d'in zama da karuwa ba? karuwar ma kamar
Khairat."
"In dai har baku shiryata ba, to ku ware mata d'aki dan har yanzu bata gama zaman
gida ba, domin kuwa ba dad'ewa za tayi ba zata koma inda ta fito."
Juyawa tayi Ruk'ayya ta taso ta d'auko makullin k'ofar ta soma bud'e mata, Zabba'u
ce ta nuna ita bata da hak'uri, hakan yasa ta taso tazo har gaban Khairat tace
"idan gadararki fitsari, to ki sani ni zan miki maganinta, wallahi ba yar Mani
Bukar kike ba, ko kece 'yar shugaba gaba d'aya ni sai naci kutumar ub...."
Tasss, kake ji Khairat ta nuna mata ta fita hauka, da hannu Khairat ta nunata tace
"idan haukane a kanki ki sani asibiti ce akan Khairat, idan rashin kunya ce
tak'amarki ki sani Khairat harta siyarwa take da, idan fitsara ce tink'ahonki ki
sani Khairat dab'i'arta ce haka, ki yaye nan gaba idan za kiyi magana, ba dan a
cikin qaddarar aurena ba akwai auren Umar Faruk, ke da baki isa ko kamata ki gani
ba koda a mafarkinki , banza kawai."
Da k'arfi ta zura kai ciki ciki tana shiga d'aki Ruk'ayya ta gyarashi tsaf sai
kamshi yake, fad'awa tayi saman gado tana jin zuciyarta kamar zata fito, maganar
kishiya na tab'a ranta sosai kuma yana dagula mata lissafi, bawai zafin maganar da
Zabba'u ta fad'a baneya harzuk'ata, zafin kishi ne kawai ya rinjayeta.
Nan fa sauran suka mike wai sai sunyiwa Khairat dukan tsiya, Mama Sa'a da yanzu
bata san ana takurawa Khairat da kuma Mama da Saratu ne suka dinga basu hak'uri, da
qyar suka rabu dasusuka bar gidan, amma dai al'amarin baima kowa dad'i ba, amma
Ruk'ayya taji dad'in haka sosai tunda da farko iyayensu suka dinga ciwa mutunci.
Saida ta jima kwance tana kuka kafin ta tashi ta watsa ruwa ta zura doguwar riga
iya gwiwa ta d'ebo kayan marmari da biscuit da chocolat tasha ta k'oshi sannan tayi
kwance, bacci bai d'auketa sai tunanin daren jiya kawai hakan yasa ta kira Ruk'ayya
ta d'auko littatafanta ta fara mata wani sabon darasi, sai kiran sallah la'asarya
tsayar dasu suka tashi zasuyi alwala Ruk'ayya cikin kunya tace "wallahi aunty
Khairat rigarki tamin kyau."
Murmushi kawai tayi ta fara alwala tace mata "idan kinyi sallah ki had'a min
ordevre."
Babu abinda bata siyo ba a kayan abincin data siyo musu, hakan yasa babu abinda aka
buk'ata wajen had'awa, minti kusan arba'in ta dauka kafin ta kawo mata, tana zuwa
ta sameta da wata riga da wando iya gwiwa kayan sai suka fi birgeta akan rigar
dazu, ajewa tayi tace "aunty gashi."
Da farin ciki ta d'auki rigar tana gwadawa a jikinta, tsayi dai Khairat ta fita
amma jiki kam zasu iya zuwa daidai ko kuma Khairat ta fita da kad'an, "na gode
aunty Khairat."
Ko kulata ba tayi ba bare ta amsa, tana fita ita kuma ta fara cin abincinta, bayan
ta kammala kuma ta sake d'aukar littafi tana karatu, *18:30* Umar Faruk ya dawo
gidan, tunda ya shiga d'akin ko kallonshi ba tayi ba harya cire kaya ya shiya
wanka, sai lokacin kuma wata zuciyar tace mata "to a hakane kuma kike so ki addabi
tunaninshi, idan ya gane kina kishinshi zai d'auka sonshi kike kuma ya rainaki ,
kawai ki basar harki samu kuje Germany ku dawo wata dama ce da zata qara kusantashi
dake, kuma me meye na hushin kin manta ya gama ganin komai na jikinki."
Tashi tayi ta bud'a kayanshi ta d'auko wata shemise fara qal da bak'in wando slim
da takalma farare slipas, tana cikin duba agogo ya shigo d'akin...
*Meerah*
28/07/2019 à 13:42 - ~NANA KHADIJA~😍: 🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾
💑💑💑💑💑💑💑💑💑💑💑
*ƘANGIN RAYUWA*
_(labarin Raheenat da Abdul-Hakeem)_
🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾
💑💑💑💑💑💑💑💑💑💑💑
*RAHEENAT M ABBAKAR*
AND
*SAMEERA HAROUNA*
_GAISUWA GAREKU MASOYA, HAƘIƘA MUNA JIN DAƊIN COMMENT ƊINKU AKAN WANNAN NOVEL ƊIN,
KU SANI MEERAHEENAT SUNA YINKU IRIN SOSAI SOSAI ƊINNAN FA😉_
DEDICATED TO ALAWIYYA❤
*🇸🇦ZAMAN AMANA WRITER'S*
*(Z.A.W)*
```(Gidan zaman lafiya da amana insha Allah)🤜🤛```
*Bismillahir-rahamanir-rahim*
Page 15 to 20
Yana ji a ransa ina ma lafiyarsa ƙalau da ya tafi a sukwane yasha ruwan nan sha ba
na wasa ba, saboda irin matsanancin ƙishir ruwan da yake ji, saidai kash ba zai iya
ko motsa ƙafarsa ba balle ya miƙe, kallonsa Raheenat takeyi sosai a ranta tana
yabawa da kyaunsa, duk shigowarta da takeyi gidan ɗiban ruwa bata taɓa ganinsa ba,
amma tasan babu shakka wannan kyakkyawar matashin saurayin shine Abdul-Hakeem ɗa
ɗaya tilo ga Alhaji Naseer buzu wanda take jin labarin rashin lafiyarsa a cikin
unguwa, wani lokacin kuma a bakin su Farida in suna hira labarinsa, ganin da tayi
shi Abdul-Hakeem sam ba ita yake kallo ba ruwan da yake zuba a panpon ya tsurawa
ido yasa tayi tunanin ko ruwan yake son sha ne, kau da idanta daga kallonsa tayi ta
fara neman abinda zata ɗiba ruwan ta bashi yasha, ganin babu wani mazubi a kusa
yasa ta nufi bakin get gurin Baba megadi da sauri dan samun kofi.
Baba na zaune kan bencinsa da ƴar redionsa a hannu ya yana saurara yaga Raheenat ta
nufo inda yake, murmushi yayi yace "ƴata Raheenat ya akayi ne banga kin ɗebo ruwan
ba.?"
Murmushi Raheenat tayi tace "Baba kofi nake son ka taimaka min dashi na tara ruwa
nasha. "
Miƙewa Baba yayi ya shiga ɗakinsa ya ɗauko mata kofi yana faɗin "ayya kice ƙishi
kika ji. "
Raheenat dai bata tsaya bashi amsa ba ta koma gurin ponpon da sauri tara ruwan a
kofin sannan ta nufi gurin Abdul-Hakeem, da zuwanta ta kafa masa ruwan a baki tana
faɗin "nasan duk yanda akayi kishi kake ji tunda naga kana kallon ruwan. "
Nan Abdul-Hakeem ya kama shan ruwan babu ƙaƙƙautawa, domin kishin yake ji sosai.
Hajiya Luba ce wacce dama ɓangaren mahaifin Abdul-Hakeem ta shiga sai gashi sun
fito tare dashi suna hira cikin nishaɗi, karaf idanunsu ya sauka kan Raheenat wacce
ke bawa Abdul-Hakeem ruwa, nan take annurin fuskar hajiya Luba ya ɗauke haushin
Raheenat da tsanarta taji nan take, shiko Alhaji Naseer abin birgesa yayi yaji
yarinyar ta shiga ransa, hajiya Luba kuwa a ranta take faɗin "akan me wannan
yarinyar zata shiga hurumin da ba nata ba, akan me zata taimaka masa, me yasa ba ta
bari ƙishir ruwan ya galabaitashi koma ya kasheshi kafin waccen shashashar uwar
tashi ta zo ta bashi ruwan ba, lallai wannan yarinyar ta shiga al'amarinna, ya kuma
zama ɗole ta ɗauki matakin da ya dace a kanta, dole ne ma na hukuntata. "
Muryar Alhaji Naseer ne ya katse mata tunaninta taji yana cewa "hajiya kinga wani
abin burgewa, gaskiya yarinyar ta samu nagartacciyar tarbiya, wallahi naji ta
birgeni sosai, yanzu daga shigowarta har ta fahimci Abdul na son shan ruwa. "
Saurin wayancewa tayi ta saki murmushin da bai kai zuci ba tace "Raheenat kenan ai
tafi da haka, gaskiya nima ta burgeni matuƙa, gaskiya kam ta samu tarbiyya sosai
wajen mahaifiyarta" cikin suɓutar baki tare da nuna ita ɗin tana tausayinsa, ta
ɗaura da cewa "ni har nayi wa ɗana sha'awarta, ina ma ace zaka nemawa Abdul-Hakeem
aurenta, kaga ko ba komai mahaifiyarsa zata samu sausacin wasu abubuwa, dan gaskiya
akwai abinda ya kamata yanzu ace matarsa ce zatayi masa, kamar wanka, wankin ba
hayanshi da fitsari dan akwai nauyi matuƙa mahaifiyarka nayi maka irin waɗannan
abubabuwa, matarshi ce kawai zatayi masa ba tare da jin nauyi ba. "
A kakkauce tace masa "eh , ai yar gidan malam Habu ce wacce suke zaune a gidanshi."
Wani basaraken murmushi Alhaji Naseer yayi ya ƙara kai kallonsa ga Raheenat wacce
ta gama bawa Abdul ruwan, kuma tas ya shanye sai kofin, har ranshi yaji daɗin
maganar Hajiya Luba tare da ƙudurawa a ranshi zai nemi iyayan yarinyar ya nemawa
Abdul auren Raheenat domin yanayin yarinyar kaɗai da ya gani yasan zatayi hankali
sannan zata kula da ɗansa sosai, sai dai ko da wasa be nunawa Hajiya Luba ya ɗauki
shawararta ba, dan haka kawai yaji baya son sanar da ita amincewarshi akan batun.
Ita kuwa Hajiya Luba dariyar mugunta tayi ganin Alhaji Naseer bece komai ba, a
ranta tace "aikin banza, wacce macen ce zata yarda ta auri masaki ta zo tayi zaman
bauta, to koni naji wacce ta yarda wallahi sai nayi yanda zanyi na hana abin
faruwa, domin ba zan yarda Abdul-Hakeem ya samu kulawa ba, nafi son naga yana
wahala kafin ranar da zai margaya. "
*************
Tana shiga gidan ta ajiye ruwan, ko sauraren masifar da Fa'iza takeyi mata na ta
daɗe ba tayi ba ta shigewarta ɗakinsu da sauri domin cire uniform ɗinta tazo ta
ɗaura girkin rana.
Zaune ta iske Mama akan sallaya da alama kiran sallah azahar take jira, "sannu
Mama." ta fad'a cikin hanzari tana cire kayan jikinta.
Doguwar rigar jiya ce ta zura a jikinta tana fad'in "eh Mama na d'ebo, zanje ne na
d'ora girki rana nayi."
Tana fad'a ta fita daga d'akin tana d'aura d'an kwalinta, tana fita ta fara zura
itace a murhu ta k'yasta ashana, kafin wutar ta kama Inna dake fitowa daga d'aki
tazo ta aje mata shinkafa da kayan miyan da za tayi aiki dasu tana fad'in "gashi
nan saura ki munafurceni kamar yanda kika saba."
Kallonta kawai tayi ba tayi magana ba har Inna ta d'auki gyalenta a rataye ta aza a
kafad'a ta kalli Raheenat tace "na gaji da wannan ranar tuwon, wallahi daga gobe
idan baki shigo gidan nan qarfe sha biyu ba kuma kika d'ora min abinci, to ki sani
ba zaki sake zuwa makarantar ba tunda ai dama ba ubanki bane ya biya miki kud'in
ba."
Cikin raunin murya Raheenat tace "dan Allah Inna kiyi hak'uri karki hanani, wallahi
na miki alk'awarin zan dinga dawowa da wuri, zan nemi izini a gurin malam."
"Aikin banza, shi kuma malam d'in saiya barki kiyi yanda kike so? saboda kece
shafaffiya da mai." cewar Farida daga zaune.
Fa'iza ce ta tare da cewar "to kinsan meke tsakaninsu da malam d'in ne, watak'ila
akwai karatun da suke na musamman a bayan aji."
A hankali Raheenat ta kalleta tace "Faiza, ka fad'i alkairi ko kayi shiru, hakan
bai dace ba ki zargemu a bisa abinda baki gani ba da idonki."
"To waliyiya ustaziya, wato ma zarginku ne ake? to ai kura ba tayi gudu ba d'anta
yayi rarrafe." cewar Inna.
Kafin wani yayi magana Inna ta kalli su Farida tace "ni zan shiga wajen Hajia tun
jiya rabona da ita."
Dakk'uwa Inna ta mata tace "shegiya, idan da lafiyarshi k'alau ke kina ganin ba sai
nabi duk hanyar da zan biba danna had'aki dashi aure ba."
Farida ce tace "lallai ma Inna, wato ni ko oho ko? ni dake nan kullum ina masa
fatan samun sauk'i kodan ya aureni, amma ke kuma kina so ki had'ashi da wacce take
masa iskanci."
Dorawa tayi da "wallahi karki yarda koda wasa Hajia Luba taji kinawa Abdul fatan
samun lafiya, idan ba haka ba kema zaki zama kamarshi, ko kuma ma ya fiki kyan
ganuwa."
Tana fad'a ta juya ta bar gidan, duk maganar nan da suke akan kunnuwan Raheenat,
tana aikinta tana sake mamakin wannan Hajia Luba to miye matsalarta da samun
lafiyar Abdul, watak'ila tana da hannu a rashin lafiyar tasa, wata zuciyar ce ta
gargad'eta ta daina zargin haka dan babu kyau tunda bata tabbatar ba.
Tana cikin aikin Sameera ta shigo gidan d'auke da kwanon abinci, ko kallon banza su
Farida basu isheta ba, kai tsaye wajen Raheenat ta nufa ta dafa kafad'arta, juyowa
tayi cikin dauriyar matsanciyar yunwar da take ji ta kalli Sameera d'in, "my Meera,
kece?"
Fuska ba annuri tace mata " karb'i wannan ki tashi kije d'aki ke da Inna kuci , ni
zan qarasa miki aikin."
Murmushi kawai Raheenat tayi dan tasan zaiyi wuya ta fita daga gidan nan haka
kawai, hannunta ta rik'e tace "Meera, kije ki kaiwa Inna, nima na kusa qarasawa,
shinkafa kawai zan zuba."
Cikin d'aga murya Sameera tace "dallah miye haka? kasheki zasuyi ne idan kin tashi
daga nan? yunwa fa kike ji."
Farida ce tayi tsal tace "to yunwar ta kasheta mata, ke yarinyar nan fa na lura in
dai kika shigo gidan nan saikin nemi tashin hankali, to bari kiji wallahi kin kusa
daina shigowa cikin gidan nan."
Sunkuyawa Sameera tayi ta aje kwanon hannunta ta dago, Raheenat da tasan meye zai
faru tayi saurin tashi daga kujerarta ta rik'e Sameera sosai tana magana qasa qasa
tace "pls my Meera, kar kiyi dan Allah rabu dasu, ki shiga ciki ki bawa Inna
abinci, ni idan na gama zanci."
Cikin tsawa da masifa Sameera tace "dallah ki sake my Heenat, ki bari na nuna musu
da banbanci tsakanin Meera da Heenat, 'yan iska kawai da kuka raina mutane."
"A'a Meera na rok'eki dan Allah, in dai har zan iya fad'a miki kiji to kiyi abinda
nace, in kuma ban isa ba to ki nuna min yanzun nan." cewar Raheenat cikin rarrashi.
Fincike kanta tayi daga rik'on data mata ta sunkuya ta d'auki kwanon rai bace ta
d'ago ta kalli Farida tace "wallahi kinci albarkacin masu albarkaci, badan haka ba,
da kin gane shayi zalla ruwa ne."
A hassale ta shiga d'akin nasu ta samu Mama a tsaye kuma da alama taji me yake
faruwa, kawai dai bata fita bane dan tana zuwa za ace ta shigar musu,
_Meeraheenat_😍
28/07/2019 à 14:18 - My Heenat: 🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾
💑💑💑💑💑💑💑💑💑💑
*ƘANGIN RAYUWA*
_(labarin Raheenat da Abdul Hakeem)_
🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾
💑💑💑💑💑💑💑💑💑💑
*RAHEENAT M ABBAKAR*
AND
*SAMEERA HAROUNA*
*DUKKAN YABO DA GODIYA SUN TABBATA GA ALLAH SUBHANAHU WATA'ALA DA YA BAMU IKON
RUBUTA WANNAN LITTAFIN NAMU, TSIRA DA AMINCI SU ƘARA TABBATA GA ANNABINMU FARKON
ƘAGA ƘARSHEN AIKA WATO ANNABI MUHAMMADU S.A.W*
```WANNAN LABARIN ƘIRƘIRARRAN LABARI NE, ƘIRƘIRAR RAHEENAT CE DA SAMEERA DAN HAKA A
GUJI JUYA MANA SHI TA KO WANI IRIN SIGA, DUK WANDA LABARINMU YAYI DAIDAI DA
RAYUWARSA TO AKASI AKA SAMU👏```
_WANNAN LITTAFIN ƊUNGURUGUM ƊINSA SADAUKARWA CE GAREKI ALAWIYYA, HAƘIKA KINA NUNAWA
RAHEENAT DA SAMEERA SOYAYYA, BAMU TA KAMARKI A DUK FANS ƊINMU, SHI YASA MA MUKA
BAKI LITTAFIN GABA ƊAYANSA, IN KIKA CE BABU WANDA ZAI KARANTA YA ZAUNU, DOMIN
GIRMANKI NE, KI HUTA KAWAI KIJI DAƊINKI MY LOVELY SISTER RAHEENAT DA SAMEERAT SUNA
SONKI HAR CIKIN ƘALBINSU❤ LOVE YOU TO ALL MY HEART❤_
*JINJINA IRIN TA BAN GIRMA GAREKU ƳAN ƘUNGIYARMU, HAƘIƘA MUNA MATUƘAR JIN DAƊIN
ZAMA CIKINKU, GIDANMU YA AMSA SUNANSA GIDAN ZAMAN LAFIYA DA AMANA KAMAR YANDA MUKA
KIRASHI. HAƘIƘA KU ƊIN MUTANE NE MASU KARAMCI DA SANIN YA KAMATA, KU HUTA KAWAI
❤
KUJI DAƊINKU RAHEENA DA SAMEERA SUNA YI MUKU FATAN ALKHAIRI*
*GAISUWA TABAN GIRMA GAREKI SHUGABA KUMA AINTƳNMU WATO AUNTY AISHAN UMMU, HAƘIƘA
KECE GINSHIƘIN KAFUWAR ƘUNGIYARMU. KIN KASANCE SHUGABA TA GARI GAREMU, MUNA JINJINA
MIKI👍 KI HUTA KAWAI AUNTYNMU RAHEENAT DA SAMEERA NA YINKI, FATAN ALKHAIRI DAKE DA
ZURI'ARKI ALLAH YAJA DA KAWANKI❤*
Page 1 to 5
" *Raheenat*! *Raheenat*!! , wai baki jina ne ? matsiyaciyar yarinya kawai. "
Cewar matar dake tsaye bakin murhu, wata matashiyar yarinyar da ba zata gaza
shekara sha shida zuwa sha bakwai ba ta fito daga wani d'aki tana d'aura d'an
kwali, abun mamaki a tare da ita shine duk da kyawun halittarta amma kayan jikinta
sai hamdala, doguwar riga ce ta shadda, amma fa tasha jiki sosai duk da kalarta
bleue ce, amma har tayi fari fari saboda tsabar wahala, durk'usawa tayi alamar
girmamawa tace "Inna gani."
"Raheenat me yasa hankalinki baya kwantawa idan ba ji kikayi ina kwaroroton daga
muryata a kanki ba ?, Ke kurma ce da kira d'aya biyu duk bai isa yasa kiji ba.?"
A ladabce tace "kiyi hak'uri Inna, wallahi tun kira na farko naji kuma na taso, to
d'an kwalina ne na tsaya nema...."
"Rufe min baki dallah, yau aka fara ne bare na yarda dake? ni dallah d'auki abincin
*Sadik* gashi nan ki kai masa d'akinsa."
D'ago ido tayi ta kalleta, a sanyaye ta tashi tsaye tace "bara na d'auko hijab."
"Ke!"
Ta dasa mata tsawa, a tsorace ta zabura ta juyo tana kallonta, "ke awa da har zan
aikeki kice wai sai kin d'auko wani banzan hijabi, wata tsiyace a jikin naki da
za'a kalla? dubeki fa."
Ta sake wata sallamar, muryar Sadik d'in ce yace "ki shigo mana."
Bud'a labulen d'akin tayi tare da sake wata sallamar, bata yarda ta had'a ido da
kowa dake d'akin ba harta aje kwanan, ta juyo zata fita taji an rik'e hannunta,
wata irin tsinkewa ne gabanta yayi ya fad'i ga tsoro daya bayyana a tare da ita,
juyowa tayi a hankali cikin rawar murya tace "dan...dan...Allah...yah Sadik ka.....
sake min hannuna na tafi."
Cikin wata dariya matashin saurayin yace "Raheenat na gaji da wannan jiran, me zai
hana ki bani abinda nake so a wuce wurin kawai? kefa ba yarinya ba ce nima kuma
haka, amma sai ki dinga yin abu kamar wata marar ilimi kuma yar qauye."
Mutsu mutsun ƙwatar hannunta kawai take amma ba tace komai ba, sake rik'e hannun
yayi gam yace "Raheenat, ki amince da buk'atata mana, ni kuma na miki alk'awarin
zanyi miki duk abinda kike so, wallahi za kiji dad'in rayuwarki, kuma zan saka Inna
ta daina miki duk abinda take miki, kinji?"
Ba tare data daina ƙoƙarin kwatar hannunta ba ta kawar da kanta gefe ta rufe ido
tace "dan Allah ka sakeni, na fad'a maka ba zaka tab'a samun abinda kake so ba daga
gareni, rayuwar da muke ciki bata kai na salwantar da mutuncina ba."
Sakin hannunta yayi ya nunata da yatsa yace "kiji nan da kyau, ni kuma saina nuna
miki nafi k'arfinki, wallahi saina sameki tunda har na k'wallafa rai a kanki, ko
kina so ko baki so saina cinma burina, koda kuwa hakan yana nufin numfashinki na
qarshe."
Jin haka yasa ta kalleshi da mamaki amma ba tace ƙala ba ta juya ta bar d'akin,
ƙannanshi dake kallon ikon Allah d'ayan ne yace "dan Allah yah Sadik ka fita harkar
yarinyar nan, karfa kaje kayi wani abinda za kasa kanka a matsala damu ma."
Hannu ya d'ora akan bakinshi yana kallon *Nuhu* yace "yimin shiru da bakinka, ba
matsalarka bace, idan kuma nasa kaina bance kowa ya shiga ba."
➡➡➡➡➡➡➡
Tana shiga d'akin nasu ta fara canza kayanta izuwa na islamiyya, riga da wando ne
da hijab, amma wandon har yana neman ya d'age mata gashi sunyi wani sid'ik dasu
kayan, musamman hijab da saman kanshi yayi fari tas ga wasu qananan hudodi akan
alamar zafin rana ta kusa kasheshi, haka ma 'yar doguwar rigar dake bakin gwiwa ita
kam a mazaunin duk ta tumurmushe sai wani k'aton d'inki da akayi a wajen, ba komai
a d'akin sai kayan jikinsu da kuma katifar baccinsu, kyakkyawa kuma matashiyar
matar dake zaune a bakin katifar ce ta lura da yanayinta dan haka ta d'anyi
murmushi tace "tunda naji tace ki kaiwa Sadik abinci, nasan shine silar wannan
shirun naki."
Da sauri ta tsaya daga saka hijab d'in ta nufo matar ta durk'usa gabanta ta rik'e
hannayenta tace " *Mama*, dan Allah mubar gidan nan, wallahi ina jin tsoron Sadik,
ya fara bani tsoro Mama."
Jaye hannunta tayi ta dafa kafad'arta tace "muje ina Raheenat ? Na d'auka nan ma da
muke taimakonmu ne akayi, kuma kinsan komai, toya kike so muyi?"
Kamar zata fashe da kuka tace "Mama za'a sake taimaka mana, amma dan Allah mubar
gidan nan dan komai zai iya faruwa, Sadik ba imanine dashi ba."
Kai matar ta girgiza tace "a wannan duniya tamu da taimako yayi wuya, taya kike
tunanin da mun fita daga nan za'a taimaka mana, Raheenat nasha fad'a miki cewar ki
kwantar da hankalinki, wallahi Sadik ko waninshi basu isa su cutar dake ba, saboda
kina tare da addu'ata, dan haka haka Allah ba zai bawa duk wani mai
ƙoƙarin son yaga ya cutar dake nasara ba, dan haka tashi ki shirya lokaci na
tafiya."
Rumgume mahaifiyar tata tayi tace "shi yasa nake alfahari dake Mamana, har kinsa
naji zuciyata ta washe."
Murmushi tayi itama tace "nima ina alfahari dake 'yata, tashi ki shirya to."
Qarasa shirin tayi ta d'auki wata irin bak'ar jaka da duk ta yamutsu ta kece ta
rataya a kafad'a sannan ta dawo gaban mahaifiyartata ta sunkuya tace "Mama kimin
addu'a tare dasa albarka?"
Kanta ta dafa tace "Allah ya miki albarka Raheenat, Allah ya kaiki lafiya ya dawo
min dake lafiya, ya baki ilimi me albarka wanda zai amfani al'umma, Allah ya
tsareki daga duk wani abun cutarwa ko sharri, ubangiji ya rufe idon mak'iya daga
ganin kyakyawar 'yata."
Ta k'arashe maganar da kama kumatunta, dariya dukansu sukayi kafin tace "na gode
Mama, ina miki fatan zama cikin aminci har izuwa lokacin da zan dawo gida."
Daga haka sukayi sallama ta fito ta kama hanyar islamiyyarsu, tana tafe tana
tilarwar karatu a kai saboda mahardaciyar ALQUR'ANI ce.
Da isarta ta taras har Sameera ƙawarta ta rigata zuwa, zama tayi kusa da Sameerar
tana faɗin "yau kin rigani zuwa Sam. "
Murmushi Sameera tayi tace "nima ɗin yanzun nan na shigo, naso shigowa gidanku sai
kuma nace ƙila kin wuce tun ɗazun. "
Littafin Hallul masa'i Raheenat ta ciro cikin jakarta ta fara ƙokarin dubawa domin
shine darasinsu na farko a yau tana cewa "wallahi kin ganni sai yanzu. "
Sameera bata ƙara cewa komai ba sai ga malam ya shigo ajin, nan itama ta ɗauki
littafinta dake kan tebur ɗinsu tana buɗawa, ba tare da ɓata lokaci ba malamin ya
fara gabatar musu da abinda ya kawo shi, nan duk ajin suka nutsu suna sauraronsa.
Ƙarfe shida daidai aka tashesu daga makarantar, jerowa Raheenat da Sameera sukayi
zuwa gida, domin unguwarsu ɗaya, duk da cewa Raheenat basu wani daɗe da zuwa
unguwar ba.
Tafe suke suna hirar karatunsu, faɗin wahalar littafan da aka sanya musu yanzun
sukeyi, Raheenat ce tace "ni fa duk wahalarsu be dameni ba tunda ina fahimta, kuma
akwai karuwa sosai a cikinsu, abinda yafi burgeni ma shine ayoyin alqur'anin da
suke cikin littafan. "
Murmushi Sameera tayi tace "akwai fa ƙaruwa wallahi, fata dai Allah ya amfanar damu
abinda muke karanta. "
"Ameen dai" cewar Raheenat, wanda faɗin hakan kuma yayi daidai da zuwa ƙofar
gidansu.
Sallama sukayiwa juna Sameera tayi gaba dan gidansu na gaban nasu Raheenat ne,
shiga gidan Raheenat tayi da sallama a bakinta, Inna dake zaune tare da ƴaƴanta
mata ko su ɗago su kalli Raheenat ba suyi ba balle ta saka ran su amsa sallamar da
tayi, nufar hanyar ɗakinsu tayi cikin sanyin jiki, daidai ta buɗe labulan ɗakin
nasu ta jiyo muryar Inna na cewa "ki shiga ki cire uniform ɗin ki zo ga wanke-wanke
nan na jiranki, ki gama kuma ki share gidan gaba ɗaya, sannan ɗakin su Farida ma
nason gyara, saura ki shiga ki ƙi fitowa da wuri, dan nasan munafukar uwar nan taki
in ta sakaki a ɗaki babu abinda takeyi miki sai huɗubar tsiya. "
Lumshe ido Raheenat tayi ta buɗe cike da jin ɗacin kalamar Inna akan Mamanta, cikin
mutuwar jiki tace "to Inna"
Tana faɗin haka ta ƙarasa shigewa cikin ɗakin nasu da sallama a bakinta.
Mama dake zaune ne ta amsa mata cikin sakin fuska tace "ƴar albarka kin dawo. ?"
Murmushi Raheenat ta saki wanda saida duka kumatunta suka lotsa ta ƙarasa kusa da
Maman nata ta zauna tana faɗin "eh na dawo Mamana, ina fatan dai kina cikin ƙoshin
lafiya kamar yanda na barki.?"
Murmushin jin daɗi Mama tayi tace "lafiya ƙalau nake ƴar Mamanta, saboda lafiya ma
zan iya zuwa makka da gudu in dawo."
Dariyar da bata shirya ba Raheenat ta saki tare da miƙewa ta fara ƙoƙarin cire
uniform ɗinta dan zuwa gabatar da aikin da Inna tace suna jiranta, kafin yanzu a
fara mata tijara ita da Mamanta, tana cewa "haka nakeso ai Mamana, Allah ya kara
miki lafiya.?"
Ameen Mama tace tana kallon ƴar tata cike da so da ƙauna, a kullum tafi son taga ƴa
nata tana farin ciki, sam bata son ganin damuwa a fuskar ɗiyartata kamar yanda
itama Raheenat bata son ganin damuwar Mamanta wacce ita kaɗai ce gareta.
*ƘANGIN RAYUWA*
_(labarin Raheenat da Abdul-Hakeem)_
🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾
💑💑💑💑💑💑💑💑💑💑💑
*RAHEENAT M ABBAKAR*
AND
*SAMEERA HAROUNA*
DEDICATED TO ALAWIYYA❤
*Bismilallahi-rahamanir-rahim.*
Page _5 to 10_
Shara ta fara saboda ba taso magriba tayi tana sharar, tana karasawa kuma ta had'a
kwanuka ta wanke, ruwan wanke wanken ta had'a ta fita zubarwa a waje, bata an
karaba a cikin soro ta had'u da mutum har ruwan suka zuba sosai, muryar Farida
kawai taji tace "kutumar uba, yau ana shirin yinta."
Sai kawai ta shak'o wuyanta tayi yarb'i da ita tare da rufa mata baya ta fara
shirgarta tana fad'in "marar mutunci, ke yanzu ni zaki jika da ruwa in ba iskanci
ba? turoki akai ko?"
Saurayin da suke tare dashi ne a soron ya rik'e Farida yasa hannu ya tallabo
Raheenat yana fad'in "haba ke kuwa ya isa haka, ruwane fa ba wani abu ba."
"Ruwa ne ba wani abu ba? ruwan wanke wake ne fa, wallahi da gangan tayi munafukar,
saboda kawai ita bata da saurayi." duk tayi maganar ne a hassale.
Raheenat da share hawaye kawai take tace "dan Allah kuyi hak'uri, wallahi ban kula
bane, sam ba'a ganin mutum shi yasa."
Wani duka ta sake kai mata a fuska hakan yasa ta zube qasa ta dafe wajen saboda
zafin da taji, qafa tasa ta harbeta tana fad'in "zaki tashi ki wuce ko saina
illataki, banza kawai."
Tana zubar da hawaye ta tashi ta fita ta zubar da ruwa ta dawo, koda zata wuce ma
saida ta sake dangwararta a baya tana fad'in "shegiya kawai."
Tana aje bokitin ta nufi d'akinsu Farida danta gyara kamar yanda aka ce, nanta fara
da gayaran shibfidarsu dake kamar ta mahaukata saboda basa iya gyarawa, sannan tayi
goge goge tayi shara, saida ta saka turaren tsintsiya sannan ta bar d'akin shi
kanshi yana samun nutsuwa.
Ta fito kenan zata nufi d'akinsu Inna dake zaune ta kirata, karasawa tayi jiki a
sanyaye ta tsugunna, saida ta gama kallonta tace "d'akinsu Sadik zaki je ki share
musu, tunda rana ya fad'a min na fad'a miki amma na manta."
Hawayen da suka taho matane ta mayar dasu kafin tace "Inna dan Allah ki taimaka ki
bani abinci na kaiwa Mama, wallahi nasan tana jin yunwa."
Kujerar dake kusa da ita yar tsugunno ta dauka, ba tare da tausayi ko tunani ba ta
kuwa gabza mata ita, kasancewar ta kare kanta hakan yasa ta sauka a hannunta,
rintse ido tayi sosai tuni hawaye suka b'alle mata, masifa Inna ta fara "marar
kunya fitsararriya, yarinya sai iya shege da kinibibi, ni har in saki abu amma ba
za kiyi ba saikin kawo min uzurinki, wallahi dani dake nan a gidan, kuma bari shi
wanda ya kawoku gidan ya dawo kiga yanda za muyi dashi."
Raheenat kam tuni ta shige d'akinsu Sadik ta fara gyara musu shinfida , tana gamawa
tayi shara sannan ta musu turare, fita tayi ta maida kofar ta kara musu ita sannan
ta koma wajen Inna, dan dama bata basu abinci har sai ta tabbatar Raheenat ta gama
musu aikin da duk yasha gabansu sannan, tun kafin tayi magana ta d'auko wani
yamushashen kwano ta dangwaro mata har miyar kukan na fallatsuwa k'asa.
Dauka tayi ta nufi d'akin nasu inda Mama take, da sallama ta shiga d'akin Mama ta
amsa tana aje carbin dake hannunta.
Ajiye kwanan abincin tayi gaban Mama sannan ta zauna itama, kallon ƴar nata Mama
tayi cike ta tausayi tace "sannu da aiki Raheenat. "
Murmushi ta saki tace "wani aiki Mama, ba wani wahala fa, ga abinci nan ciki Mama
nasan kina jin yunwa sosai. "
Kallonta Mama tayi sosai sannan ta kalli kwanan tuwon da yake can ƙasar kwano tace
"kefa Raheenat.?"
Murmushi ta kuma tace "ni bana jin yunwa Mama, kedai kawai kici. "
Waro fararen idonta tayi tace "dan Allah Mama ki ci, wallahi nasan kina jin yunwa.
"
Kallonta Mama tayi tace "bazan ci ba har sai kema zaki ci, Raheenat ta yaya kike
tunanin zan iya cin abinci ke baki ci ba. ?"
Raheenat ba tace komai ba ta maida kanta ta ƙarasa cinye sauran sannan tayi hamdala
ta miƙe ta ɗibowa Mama ruwan sha cikin wata tsohuwar randar dake ɗakin.
Saida Mama tasha ta wanke hannunta sannan itama tasha ruwan ta miƙe ta fice daga
ɗakin ɗauke da kwanan a hannu.
Wanke kwanan tayi taje ta ajiye a majiyarsa sannan ta ɗauki buta ta nufi rijiya
taja ruwa, bayi ta shiga tayi tsarki sannan ta duƙa ta ɗaura alola, saboda kiran
sallah da aka fara a masallatan dake unguwar.
Bayan ta idar da alolan ƙara cika butan tayi da ruwa ta nufi ɗakin nasu dashi,
bakin ƙofa ta samu Mama na shirin fitowa itama dan ɗaura alolar, miƙawa Mama butan
tayi ita kuma ta shige ɗakin domin yin sallar.
Sai da sukayi isha'i tare da shafa'i da wuturi sannan suka tashi daga kan sallaya,
memakon kwanciya bacci sai Raheenat ta ɗauko littafanta ta fara muraji'a, saida ta
tabbatar da iya duk karatun da akayi masu yau sannan ta mayar da littafai cikin
jaka ta ajiye, bata tsaya nan ba ta fara rero ƙira'ar karatun al'qur'ani cikin
daddaɗar muryarta me daɗin sauraro, kamar yanda muka ce muku Raheenat hafizace, dan
haka ta ɗinga rero karatu babu tsayawa saida ta karanto surori har uku, sannan tayi
addu'ar kwanciya bacci ta kwanta, zuwa lokacin tuni Mama ta daɗe dayin bacci.
*************
Washe gari tana yin sallah ko tsayawa azkar ɗin safiya ba tayi ba ta fito ta fara
ƙoƙarin hura wuta, wanda tasan dama aikinta ne, daƙyar ta samu wutar ta kama mata
sannan ta ɗaura ruwan koko, bata tsaya ba ta fara haɗa wanke-wanken da akaci da
daran jiya ta wankesu tas, tana kammalawa ta ɗauki tsintsiya ya share gidan ƙyal,
daidai kammala sharar ruwan da ta ɗaura ya tafasa.
Nufar ɗakin Inna tayi domin amso ƙullun da zata dama, sallama tayi bakin ƙofar
ɗakin har daki uku amma ba'a amsa mata ba, ta buɗe baki kenan zatayi na huɗun kenan
sai ga Inna ta fito cikin hargowa tana faɗin "dan jaraba kana bacci ma sai an
addabeka, tsaban baƙin ciki ba za'a barka kayi bacci ka huta ba, wannan masifa har
ina," mttsss taja godon tsaki.
Raheenat dai dake tsaye haɗiye wani mugun yawo tayi ta duƙa har ƙasa tace "ina
kwana Inna."
Wani mugun harara Inna ta wurga mata tace "daba kwana ba zaki ganni ne uwar
kinibibi, meye kika zo da wani sassafen nan ki na ƙwaɗa min sallama.?"
Cikin sanyin murya Raheenat tace "dama kamu nazo amsa na dama koko. "
Kallonta takai ga murhun wanda yake ci ganga-ganga da alamu ruwan tukunyar ya daɗe
ta tafasa sannan ta juya a fusace ta shige ɗaki ta ɗauko botikin kamun ta
dangwarawa Raheenat a gaba tace "gashinan kije ki dama gangin jaraba kawai. "
Ɗauka kwai Raheenat tayi ba tare da yace komai ba ta nufi bakin murhun dan dama
kokon, domin inda sabo ta saba da irin hakan.
My meera ce ta kalleni idanu cike da ƙwalla tace "my heenat ina matuƙar tausayawa
takwarar nan taki wallahi. "
Dariya nayi nace "da yake ka tausayi yayi miki yawa ba."
Dariya nayi nace "tunda ke kin gane ai kamar Raheenat ta gane ne. "
Raheenat tana kammala dama kokon ta mayar masu Farida da ruwan wanka akan wutan
cikin wata ƙatuwar tukunya, ɗaukar kokon tayi wacce tafi rabin kafilas (babban
farin roban fanti) ta nufi ɗakin Inna dashi.
Muje zuwa🥰
Meeraheenat ne💋
28/07/2019 à 14:18 - My Heenat: 🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾
💑💑💑💑💑💑💑💑💑💑💑
*ƘANGIN RAYUWA*
_(labarin Raheenat da Abdul-Hakeem)_
🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾
💑💑💑💑💑💑💑💑💑💑💑
*RAHEENAT M ABBAKAR*
AND
*SAMEERA HAROUNA*
DEDICATED TO ALAWIYYA❤
_Bismillahir- rahamanir-rahim_
Daga k'ofar d'akin tayi sallama kamar yanda aka gindaya mata tsayawa nan, Inna ce
ta fito cikin jin haushi tana zuwa ta tsaya ta qare hararanta tas kafin tace
"jaraba, to ina wajen da zan zuba miki? ko kuma zanina kike so na zuba miki a
ciki?"
"A'a Inna." ta fad'a tare da juyawa ta nufi d'akinsu, wata qaramar mod'a ta dauka
wacce ta zama ta zuba musu kokon sannan ta fito duk Mama na kallonta, tana zuwa ta
aje mod'ar Inna kuma ta d'auki babban ludayin ta zuba mata biyu dashi.
Tana zuba mata ta d'auki bokiyin tayi d'akinta dashi ita kuma ta d'auka tayi nasu
d'akin, tun kafin ta shiga d'akin wata dubara ta fad'o mata a rai, dan haka ta
canza yanayinta kamar mai gaggawa ta shiga d'akin, da sauri ta qarasa gurin Mama ta
aje modar tana fad'in "Mama ga kokonki kisha, ni zan wuce islamiyya."
Bata jira me za tace ba ta nufi wajen tsohon uniform d'inta ta fara sakawa, harta
gama bata kalli Mama ba sai dai Mama ita take kallo, "Raheenat kizo kisha kokan
mana karya huce." cewar Mama.
"Mama kisha, Sameera na jirana a waje zamu wuce, idan naje zan samu wani abu naci."
duk tayi maganar ne tana saka hijab d'inta da d'aukar jakarta.
Kafin Mama tayi wata magana kuma ta durk'usa gabanta ta sunkuyar da kanta tace
"Mama sa albarkarki."
Cikin murmushi Mama ta dafa kanta tace "albarkata na tare dake 'yar albarka, kina
cikin kariyar ubangiji har kije ki dawo."
Yatsu biyu ta saka taja kumatun mahaifiyarta ta tana dariya tace "uwa mai dad'in
zama uwa abar alfahari, na gode Allah daya bani ke, nafi kowa sa'a."
Tashi tayi a sukwane tare da sumbatar kumatun mamanta tace "ina sonki Mamana."
"Ina sonki, Allah ya tsare saikin dawo." Mama ta fad'a saboda harta kusan fita daga
d'akin.
Girgiza kai Mama tayi tare da share wasu wahalallin qwalla, tasan babu abinda zata
samu taci, hakan yasa ta d'auki modar ta samu wani d'an murfi ta rufe da tunanin
aje mata harta dawo, tashi tayi ta fito daga d'akin dan ganin meke wakana a wajen,
dan tasan Raheenat bata so saboda rashin mutuncin Inna, haka yasa tace ta dinga
zamanta a d'aki.
Ai kuwa Inna ce ta fito daga d'aki bayan su Farida sun tafi school, ganinta yasa
tayi saurin juyawa zata koma d'aki amma sai Inna tace "dakata mana, ai saiki fito
kisha iska, wato munafirci da kinibibi baya tashi sai mai gidan na nan, idan kuma
baya nan saiki wuni baki lek'o tsakar gida ba."
Shiru dai tayi ita kuma ta qara da "an daiji haushi, kilaki kawai, waiku kun b'ige
da neman taimako, ba gaira ba dalili kin d'orawa mijina nauyin daba nashi ba, a
banza sai ciyar daku yake ba lada ba zunubi."
"Allah ya baki hak'uri, muma rayuwa ce tasa har muka zauna tare daku."
"Uhum, da anyi magana sai kice rayuwa rayuwa, kamar ku kad'ai ne a cikin *K'angin
rayuwa*, bayan akwai wanda suka fiku shiga wani hali a cikin rayuwar."
"Humm, ai kuwa duk wanda ya fimu matsi da k'uncin rayuwa, to ki sani baya numfashi,
yana cikin k'abarinsa da munanan ayyukansa."
Juyawa tayi zata koma ciki tace "aikin banza aikin wofi, in har gaske ne me zai
hana ki sada yarinyar nan da dangin ubantan in har ya mutu da gaske, ai da gani ba
sai kin fad'a ba cewar a yawon ta zubar kika samu wannan 'yar, hakan yasa ma kowa
ya gujeku, kuma kamar yanda kika sameta ta hanyar da bata dace ba, to ki shirya
itama saita samo miki d'an dakan kuka, wallahi saikin goyi d'an shege a bayanki."
Zafin da kalaman suka mata yasa ta qarasa shiga da gudu d'akin tana zubar da
hawaye, in banda sauyin rayuwa har ace ana sheganta mata 'yar data haifa ta hanyar
sunna, lallai yau za taji maganar Raheenat ba zata sake fita ba in dai bada wani
dalili ba, dan zuciyarta ba zata iya d'aukar bak'ak'en maganganu akan 'yarta ba.
***************
Hajiya Maryam ce take gunguro ɗanta Abdul-Heema saman kekensa zuwa farfajiyar gidan
domin yasha iska, daidai gurin wani ɗan madaidaicin gurin hutawa da aka ƙawata shi
da fararen kujeru kusa da gurin adana motocin gidan ta ajiyesa, kallonsa tayi da
murmushi a fuskarta tace "to Abdul ni zan koma ciki na ƙarasa aiyuka. "
Da ido ya bi mahaifiyar nasa kawai, tasan ba zai iya magana ba amma tana da
tabbacin yaji abinda ta faɗa, juya kawai tayi ta koma ciki ta barsa a gurin yana
shan iskar da take kaɗawa me daɗi.
Lumshe ido yayi wanda su kaɗai ne suke motsawa a jikinsa ya buɗesu fes a akan wasu
tsintsaye da suke saman bishiyoyin fulawar da aka ƙawata gidan nasu dashi, da ganin
yanda yake kallonsu zaka fahimci yana cikin nishad'i.
Shekarunsa ba zasu gaza ashirin da hud'u ba zuwa da biyar, kana ganinshi zaka
fahimci hutu ya ratsashi sosai saboda tattausa kuma lallausar fatar jikinshi wacce
ke shek'i da kyali , sumar kanshi dake bak'a sid'ik ta qara fito da farin fatarshi,
ga kuma sajen daya sake k'awata fuskarshi, tako ina dai Abdul-Hakeem ya had'u,
nak'asunshi d'aya tak shine, *ido ne kad'ai ke motsi a jikinshi*.
Wata rantsetsiyar matace ta fito daga wani katafaran b'angaren da duk gidan ba
b'angare mai kyau kamarshi, suturarta da sauran kayan adon dake jikinta zasu
fahimtar da kai tana fad'a aji a gidan kuma dukiya ta kwanta mata sosai, wani
b'angaren ta tunkara amma ganin Abdul zaune yasa ta tunkari wajenshi, da takon
k'asaita ta isa ta tsaya gabanshi tana murmushi, giftawar wata ma'aikaciyar gidan
yasa ta dafa kanshi tare da d'an rank'wafawa tana murmushi tace,
"Yadai musaki, an fito shan iska ne? To yayi kyau, aci gaba da zama a haka har
lokacin da zaka qarasa inda ya dace."
Har zata wuce kuma tace "ehem, nasan kana jin haushina, amma hak'uri ya zama dole,
nima hak'uri nake da nake iya jurar kallonka kai da tsinanniyar mahaifiyarka a
gidan nan, amma komai ya kusan zuwa qarshe kamar yanda boka ya fad'a min."
Kumatunshi ta shafa ta sake sakin wani murmushin tace "see you my son."
Tana wucewa ya lumshe idonshi da sukayi jawur yana so ya zubar da hawaye amma ya
kasa, hakika matar na bala'in kasheshi da bak'in ciki, amma ba yanda ya iya, ko
alama ba zai iya yima wani ba bare kuma a fahimceshi, yasan abubuwa da dama a tare
da ita saboda tana wayan sakin baki a gabanshi saboda tunaninta dashi da gawa duk
d'aya, sai dai komai na cikin kanshi kuma yana mayar mata da martani a zuciyarshi,
lafiya kawai yake fatan samu ya rabata da mahaifinshi.
*****************
Da qyar Raheenat ta kai kanta islamiyya saboda azababbiyar yunwa, amma fa babu
abinda ta fahimta a game da karatun da aka musu, suna tashi suka d'auko hanya ita
da Sameera, fahimtar halin da take ciki da tayi yasa Sameera cewa "my Heenat, kizo
muje gida idan muka ci abinci saiki wuce gida."
Tana girgiza kai cikin tsananin yunwa tace "a'a my Meera, ki barshi kawai zanje
gida, aiki na jira a gida idan na makara zansha masifar Inna ne kawai."
"A hakan za kiyi wani aiki? To ai bana ganin zaki iya moruwa a haka, kinga kizo
muje dan Allah, idan masifarta kike gudu ni zanje mu tafi tare gidan."
Qarasawa da sukayi inda zasu rabu yasa suka tsaya, kafadarta Raheenat ta dafa tace
"karki damu my Meera, idan naje nasan ba zan rasa abinda zanci ba."
Cikin jin haushi Sameera tace "me zaki samu kici, a ina ne zaki samu abinda zaki ci
d'in, wanda ko abincin da ake baku ba isarku yake ba, taya kike tunanin samun wanda
zaki ci yanzu?"
Dafe cikinta tayi tace "my Meera, idan har baki so na shiga matsala, to dan Allah
kiyi hak'uri ki barni, na fad'a miki zan samu abinda zanci."
Tsaki Sameera tayi ta nufi hanyar nasu gidan dake kallon nasu Raheenat d'in
zuciyarta na k'una , itama hanyar gidan ta nufa tana murmushi dan tafi kowa sanin
halin aminiyarta ta, hakan yasa bata cika son tana zuwa gidan ba, in har taje sai
an samu matsala ko dai tsakaninta da Inna kosu Farida.
"Sallamu alai..." bata qarasa ba taji an jefo mata bokiti a qirji ana fad'in "saiki
d'ebo mana ruwa tunda kin dawo daga gantalin."
Sai lokacin ta kalli Farida ce ke maganar, za tayi magana kuma saita dafe cikinta
saboda kukan da yake, Inna ce ta fito daga d'akin tana fad'in "wai har yanzu bata
dawo ba?"
Jin haka yasa tayi saurin cire jakarta ta aje a qasa gefen tabarmar dasu Faiza dake
latsar waya, d'aukar bokitin tayi zata fita Inna tace "kuma kiyi sauri ki dawo kizo
ki d'ora mana abinci."
Juyawa tayi ko ganin gabanta ba tayi da kyau sai sharar qwalla take, duk da rijiyar
dake akwai a cikin gidan, amma idan suka niyyar muzguna mata sai suce saita d'ebo
ruwa a panpo a gidan *Alhaji Naseer Buzu*.
Tana zuwa mai gadin ya bud'e mata gate d'in yana fad'in "Raheenat d'iban ruwa aka
zo?"
Aje bokitin tayi a bakin panpon dake kusa da wajen ajiyar motoci, kan panpon ta
rik'e hannu d'aya kuma ta dafe 'kugu saboda bala'in yunwa dake cinta.
D'an kalle kalle ta shiga yi har idonta suka sauka akan idon Abdul daya kafe ruwan
dake zuba da ido....
_Meeraheenat_😍
28/07/2019 à 14:18 - My Heenat: 🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾
💑💑💑💑💑💑💑💑💑💑💑
*ƘANGIN RAYUWA*
_(labarin Raheenat da Abdul-Hakeem)_
🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾
💑💑💑💑💑💑💑💑💑💑💑
*RAHEENAT M ABBAKAR*
AND
*SAMEERA HAROUNA*
_GAISUWA GAREKU MASOYA, HAƘIƘA MUNA JIN DAƊIN COMMENT ƊINKU AKAN WANNAN NOVEL ƊIN,
KU SANI MEERAHEENAT SUNA YINKU IRIN SOSAI SOSAI ƊINNAN FA😉_
DEDICATED TO ALAWIYYA❤
*Bismillahir-rahamanir-rahim*
Page 15 to 20
Yana ji a ransa ina ma lafiyarsa ƙalau da ya tafi a sukwane yasha ruwan nan sha ba
na wasa ba, saboda irin matsanancin ƙishir ruwan da yake ji, saidai kash ba zai iya
ko motsa ƙafarsa ba balle ya miƙe, kallonsa Raheenat takeyi sosai a ranta tana
yabawa da kyaunsa, duk shigowarta da takeyi gidan ɗiban ruwa bata taɓa ganinsa ba,
amma tasan babu shakka wannan kyakkyawar matashin saurayin shine Abdul-Hakeem ɗa
ɗaya tilo ga Alhaji Naseer buzu wanda take jin labarin rashin lafiyarsa a cikin
unguwa, wani lokacin kuma a bakin su Farida in suna hira labarinsa, ganin da tayi
shi Abdul-Hakeem sam ba ita yake kallo ba ruwan da yake zuba a panpon ya tsurawa
ido yasa tayi tunanin ko ruwan yake son sha ne, kau da idanta daga kallonsa tayi ta
fara neman abinda zata ɗiba ruwan ta bashi yasha, ganin babu wani mazubi a kusa
yasa ta nufi bakin get gurin Baba megadi da sauri dan samun kofi.
Baba na zaune kan bencinsa da ƴar redionsa a hannu ya yana saurara yaga Raheenat ta
nufo inda yake, murmushi yayi yace "ƴata Raheenat ya akayi ne banga kin ɗebo ruwan
ba.?"
Murmushi Raheenat tayi tace "Baba kofi nake son ka taimaka min dashi na tara ruwa
nasha. "
Miƙewa Baba yayi ya shiga ɗakinsa ya ɗauko mata kofi yana faɗin "ayya kice ƙishi
kika ji. "
Raheenat dai bata tsaya bashi amsa ba ta koma gurin ponpon da sauri tara ruwan a
kofin sannan ta nufi gurin Abdul-Hakeem, da zuwanta ta kafa masa ruwan a baki tana
faɗin "nasan duk yanda akayi kishi kake ji tunda naga kana kallon ruwan. "
Nan Abdul-Hakeem ya kama shan ruwan babu ƙaƙƙautawa, domin kishin yake ji sosai.
Hajiya Luba ce wacce dama ɓangaren mahaifin Abdul-Hakeem ta shiga sai gashi sun
fito tare dashi suna hira cikin nishaɗi, karaf idanunsu ya sauka kan Raheenat wacce
ke bawa Abdul-Hakeem ruwa, nan take annurin fuskar hajiya Luba ya ɗauke haushin
Raheenat da tsanarta taji nan take, shiko Alhaji Naseer abin birgesa yayi yaji
yarinyar ta shiga ransa, hajiya Luba kuwa a ranta take faɗin "akan me wannan
yarinyar zata shiga hurumin da ba nata ba, akan me zata taimaka masa, me yasa ba ta
bari ƙishir ruwan ya galabaitashi koma ya kasheshi kafin waccen shashashar uwar
tashi ta zo ta bashi ruwan ba, lallai wannan yarinyar ta shiga al'amarinna, ya kuma
zama ɗole ta ɗauki matakin da ya dace a kanta, dole ne ma na hukuntata. "
Muryar Alhaji Naseer ne ya katse mata tunaninta taji yana cewa "hajiya kinga wani
abin burgewa, gaskiya yarinyar ta samu nagartacciyar tarbiya, wallahi naji ta
birgeni sosai, yanzu daga shigowarta har ta fahimci Abdul na son shan ruwa. "
Saurin wayancewa tayi ta saki murmushin da bai kai zuci ba tace "Raheenat kenan ai
tafi da haka, gaskiya nima ta burgeni matuƙa, gaskiya kam ta samu tarbiyya sosai
wajen mahaifiyarta" cikin suɓutar baki tare da nuna ita ɗin tana tausayinsa, ta
ɗaura da cewa "ni har nayi wa ɗana sha'awarta, ina ma ace zaka nemawa Abdul-Hakeem
aurenta, kaga ko ba komai mahaifiyarsa zata samu sausacin wasu abubuwa, dan gaskiya
akwai abinda ya kamata yanzu ace matarsa ce zatayi masa, kamar wanka, wankin ba
hayanshi da fitsari dan akwai nauyi matuƙa mahaifiyarka nayi maka irin waɗannan
abubabuwa, matarshi ce kawai zatayi masa ba tare da jin nauyi ba. "
A kakkauce tace masa "eh , ai yar gidan malam Habu ce wacce suke zaune a gidanshi."
Wani basaraken murmushi Alhaji Naseer yayi ya ƙara kai kallonsa ga Raheenat wacce
ta gama bawa Abdul ruwan, kuma tas ya shanye sai kofin, har ranshi yaji daɗin
maganar Hajiya Luba tare da ƙudurawa a ranshi zai nemi iyayan yarinyar ya nemawa
Abdul auren Raheenat domin yanayin yarinyar kaɗai da ya gani yasan zatayi hankali
sannan zata kula da ɗansa sosai, sai dai ko da wasa be nunawa Hajiya Luba ya ɗauki
shawararta ba, dan haka kawai yaji baya son sanar da ita amincewarshi akan batun.
Ita kuwa Hajiya Luba dariyar mugunta tayi ganin Alhaji Naseer bece komai ba, a
ranta tace "aikin banza, wacce macen ce zata yarda ta auri masaki ta zo tayi zaman
bauta, to koni naji wacce ta yarda wallahi sai nayi yanda zanyi na hana abin
faruwa, domin ba zan yarda Abdul-Hakeem ya samu kulawa ba, nafi son naga yana
wahala kafin ranar da zai margaya. "
*************
Tana shiga gidan ta ajiye ruwan, ko sauraren masifar da Fa'iza takeyi mata na ta
daɗe ba tayi ba ta shigewarta ɗakinsu da sauri domin cire uniform ɗinta tazo ta
ɗaura girkin rana.
Zaune ta iske Mama akan sallaya da alama kiran sallah azahar take jira, "sannu
Mama." ta fad'a cikin hanzari tana cire kayan jikinta.
Doguwar rigar jiya ce ta zura a jikinta tana fad'in "eh Mama na d'ebo, zanje ne na
d'ora girki rana nayi."
Tana fad'a ta fita daga d'akin tana d'aura d'an kwalinta, tana fita ta fara zura
itace a murhu ta k'yasta ashana, kafin wutar ta kama Inna dake fitowa daga d'aki
tazo ta aje mata shinkafa da kayan miyan da za tayi aiki dasu tana fad'in "gashi
nan saura ki munafurceni kamar yanda kika saba."
Kallonta kawai tayi ba tayi magana ba har Inna ta d'auki gyalenta a rataye ta aza a
kafad'a ta kalli Raheenat tace "na gaji da wannan ranar tuwon, wallahi daga gobe
idan baki shigo gidan nan qarfe sha biyu ba kuma kika d'ora min abinci, to ki sani
ba zaki sake zuwa makarantar ba tunda ai dama ba ubanki bane ya biya miki kud'in
ba."
Cikin raunin murya Raheenat tace "dan Allah Inna kiyi hak'uri karki hanani, wallahi
na miki alk'awarin zan dinga dawowa da wuri, zan nemi izini a gurin malam."
"Aikin banza, shi kuma malam d'in saiya barki kiyi yanda kike so? saboda kece
shafaffiya da mai." cewar Farida daga zaune.
Fa'iza ce ta tare da cewar "to kinsan meke tsakaninsu da malam d'in ne, watak'ila
akwai karatun da suke na musamman a bayan aji."
A hankali Raheenat ta kalleta tace "Faiza, ka fad'i alkairi ko kayi shiru, hakan
bai dace ba ki zargemu a bisa abinda baki gani ba da idonki."
"To waliyiya ustaziya, wato ma zarginku ne ake? to ai kura ba tayi gudu ba d'anta
yayi rarrafe." cewar Inna.
Kafin wani yayi magana Inna ta kalli su Farida tace "ni zan shiga wajen Hajia tun
jiya rabona da ita."
Dakk'uwa Inna ta mata tace "shegiya, idan da lafiyarshi k'alau ke kina ganin ba sai
nabi duk hanyar da zan biba danna had'aki dashi aure ba."
Farida ce tace "lallai ma Inna, wato ni ko oho ko? ni dake nan kullum ina masa
fatan samun sauk'i kodan ya aureni, amma ke kuma kina so ki had'ashi da wacce take
masa iskanci."
Dorawa tayi da "wallahi karki yarda koda wasa Hajia Luba taji kinawa Abdul fatan
samun lafiya, idan ba haka ba kema zaki zama kamarshi, ko kuma ma ya fiki kyan
ganuwa."
Tana fad'a ta juya ta bar gidan, duk maganar nan da suke akan kunnuwan Raheenat,
tana aikinta tana sake mamakin wannan Hajia Luba to miye matsalarta da samun
lafiyar Abdul, watak'ila tana da hannu a rashin lafiyar tasa, wata zuciyar ce ta
gargad'eta ta daina zargin haka dan babu kyau tunda bata tabbatar ba.
Tana cikin aikin Sameera ta shigo gidan d'auke da kwanon abinci, ko kallon banza su
Farida basu isheta ba, kai tsaye wajen Raheenat ta nufa ta dafa kafad'arta, juyowa
tayi cikin dauriyar matsanciyar yunwar da take ji ta kalli Sameera d'in, "my Meera,
kece?"
Fuska ba annuri tace mata " karb'i wannan ki tashi kije d'aki ke da Inna kuci , ni
zan qarasa miki aikin."
Murmushi kawai Raheenat tayi dan tasan zaiyi wuya ta fita daga gidan nan haka
kawai, hannunta ta rik'e tace "Meera, kije ki kaiwa Inna, nima na kusa qarasawa,
shinkafa kawai zan zuba."
Cikin d'aga murya Sameera tace "dallah miye haka? kasheki zasuyi ne idan kin tashi
daga nan? yunwa fa kike ji."
Farida ce tayi tsal tace "to yunwar ta kasheta mata, ke yarinyar nan fa na lura in
dai kika shigo gidan nan saikin nemi tashin hankali, to bari kiji wallahi kin kusa
daina shigowa cikin gidan nan."
Sunkuyawa Sameera tayi ta aje kwanon hannunta ta dago, Raheenat da tasan meye zai
faru tayi saurin tashi daga kujerarta ta rik'e Sameera sosai tana magana qasa qasa
tace "pls my Meera, kar kiyi dan Allah rabu dasu, ki shiga ciki ki bawa Inna
abinci, ni idan na gama zanci."
Cikin tsawa da masifa Sameera tace "dallah ki sake my Heenat, ki bari na nuna musu
da banbanci tsakanin Meera da Heenat, 'yan iska kawai da kuka raina mutane."
"A'a Meera na rok'eki dan Allah, in dai har zan iya fad'a miki kiji to kiyi abinda
nace, in kuma ban isa ba to ki nuna min yanzun nan." cewar Raheenat cikin rarrashi.
Fincike kanta tayi daga rik'on data mata ta sunkuya ta d'auki kwanon rai bace ta
d'ago ta kalli Farida tace "wallahi kinci albarkacin masu albarkaci, badan haka ba,
da kin gane shayi zalla ruwa ne."
A hassale ta shiga d'akin nasu ta samu Mama a tsaye kuma da alama taji me yake
faruwa, kawai dai bata fita bane dan tana zuwa za ace ta shigar musu,
_Meeraheenat_😍
29/07/2019 à 13:11 - ~NANA KHADIJA~😍: 💑💑💑💑💑💑💑💑💑💑
*JIHADI*
_Umar faruk_
💑💑💑💑💑💑💑💑💑💑
_NA_
_SAMIRA HAROUNA_
_DEDICATED TO_
*MA FAMILLE*
_Bismmilahir-rahman-rahim_
3⃣2⃣
Wanka ya shiga ba tare da sun kula juna ba, saida ya shiga sannan ta tuna da
tsarinta, tashi tayi yanzu ma ta fito mashi da wata watsetsiyar shadda fara qal da
alama bai tab'a sakata ba, takalma agogo ta fito dasu tare da hula bak'ak'e, tana
gamawa ya shigo yana tsane ruwan jikinshi, karb'ar towel d'in tayi ta fara goge
masa shi kuma yana kallonta yana tunanin kodai tana da aljanu, a haka ta gama
shiryashi tsaf dashi yau ma ta d'aukesu selfie sannan ya fita zuwa masallaci, harya
fita ya kuma dawowa yace "wannan shirin fa na miye?"
Murmushi kawai yayi ya fita zuciyarshi na qara kamuwa da qaunarta, ana kiran sallah
itama tayi sallah sannan ta shiga wanka ta shirya cikin riga da siket masu shegen
kyau na kantie sun fito mata da komai a fili, kwalliya tayi sosai tana gamawa kuma
ta mayar da sallah isha'i da ake kiran, harta gama ta zauna akan kujera amma bai
dawo ba, ranta na tafarfasa haushi ya gama isarta tunaninta ko yana can da motarta
ma ya tafi d'aukar figaggiyar amaryarshi.
***************
Tanti Ma'u ce ta tisa Zuby gaba ta bata wani kullin magani tace "wannan wanka za
kiyi dashi na tsawon kwana uku, wannan kuma kisan hanyar da za kibi Umar Faruk
yaci a abinci, wannan kuma na tsinnaniyar matarshi ce, a abinsha zaki zuba
matashi."
"Ke can dallah, wannan da kinyi aiki dashi, to ke zai dinga gani da daraja , ita
kuma ta fita a ranshi, wannan kuma idan yaci a abinci, to zaki malleshi ne sai
yanda ki kayi dashi, wannan kuma da tasha ita kuma, to ba haihuwa a gidan Umar
Faruk har saita mutu."
***************
Umar Faruk kuma yana can ya tura abokananshi d'aukar Zuby amma yana k'ofar gida
tare da Ishaq, ana cikin haka an kawo amarya suka hallaro, nanfa aka fara hayaniya
aka shiga da amarya aka bud'e d'akinta aka zurata ciki, saida aka gama bidi'o'i da
kwanjil kwanjil sannan mutane aka fara watsewa, anan yan uwan Zuby suka sake bata
wasu sinadaran na yak'ar Khairat danta cinye gida, yayin da Zabba'u take addu'ar
Allah ya had'ata da Khairat a tsakar gida ta rama marinta.
Ganin har zasu tafi bata fito ba yasa suka dinga d'ura mata ashar suna habaici iri
iri had'e da kiranta karuwa, to nidai lek'awa nayi d'akin Khairat d'in naga tana
jinsu kuma tayi shiru.
😂 _Kun sanfa mutuniyar akwai son casu, can na hangota kwance akan kujera ta danne
kunnuwa da masub'urb'ud'ar sauti tana holewarta._
Haka dai aka watse aka bar amarya da ita da halinta, sai kusan 22:45 Umar Faruk
ango ya shigo, kai tsaye d'akin amarya ya nufa inda ya zuro k'eyarta gaba izuwa
d'akin amarya danya ja musu kunne😂, tun a labule Khairat ta hangi tahowarshi hakan
yasa ta cire abin sauraron ta aje, yana bud'e labulen tare da sallama tayi saurin
fad'awa jikinshi tare da fad'in "sannu da zuwa."
Hannunshi ta kamo suka qarasa shiga ta zaunar dashi akan kujera tare da zama akan
cinyoyinshi ta sagala hannunta ta wuyanshi, cike da kissa tace "ka tafi ka barni
kana can wajen amaryarka, tun yanzu harna fara kewarka."
Saida ya sumbaci nonuwanta dake barazanar fitowa daga rigarta kafin ya lumshe ido
yace "da gaske? ashe dama za kiyi kewata?"
_Hum😎 duk wacce taso ai ita take zama banza a wajen miji._
Yatsar hannunta tasa tana shafa gefan fuskarshi ta cije leb'e tana wani kakkashe
masa ido tare da d'an jujjuya mazaunanta akan cinyoyinshi, hakan kuma yasa take
tsokano babbar harkar daga qasa😂, ido Umar Faruk ya rufe kamar zai fashe da kuka
yana fad'in "wayyo ni Ummaru na shiga uku, Khairat kasheni za kiyi fa wallahi."
Matseta yayi a jikinshi ya tusa kanshi a mamanta dansu suka fi d'aukar hankalinshi,
itama matse kanshi tayi tana mishi cakulkuli tana fad'in "kana mutuwa zan sake dawo
da kai ai, dan yanzu na fara jin dad'in rayuwata da kai."
😂😂😂😂😂😂
Da sauri Umar Faruk ya kalli Zuby dake tsaye yama manta da ita harga Allah, "inna
lillahi." ya fad'a tare da d'aga Khairat daga jikinshi ya mayar da ita ta zauna
gefenshi ya zura hannu ya janyo hannun Zuby ya zaunar da ita d'aya gefenshi.
Saida ya saci kallon Zuby tare da saisaita nutsuwarsa kafin yayi gyaran murya ya
fara da " *KHAIRAT*."
"Na'am baby." ta fad'a da dafa kafad'arsa, dan tunda ta sauke idonta akan Zuby ta
fahimci akwai tazara a tsakaninsu mai yawa.
"Ga Zubeida, k'anwarki, kuma ina fata zan samu had'in kanku domin ku fahimceni na
fahimceku, dan ta hakane zamu samu zaman lafiya da kwanciyar hankali, Khairat, kece
babba, dan haka akwai buk'atar ki kama girmanki ta yanda zaku zauna lafiya, duk da
bamu jima tare ba, amma nasan kin fahimci ni ba mutum bane mai son hayaniya da
tashin hankali, kamar yanda dukanku kun sanni bana d'aukan raini da rashin hankali,
dan haka ina so kowace ta tsaya matsayinta, bana so naga ko naji raini a tsakaninku
bare har yakai ga sa in sa ya had'aku wata rana, ina fata kin fahimceni?"
Ajiyar zuciya ta sauke ta kalli Zuby tace "Allah sarki, wannan itace Zuby? karka
damu baby, insha Allah ba zaka tab'a samun matsala daga gareni ba, kuma zan
d'auketa kamar k'aramar k'anwata dan dama bana da kowa."
"Saike Zubeida, wannan itace Khairat kuma tana gaba dake a shekaru dama kasancewa
matata, buk'atata a gareki shine ki kama kanki kema sannan ki d'auketa a matsayin
yayarki, nasan Khairat, bata da hayaniya da tashin hankali, dan haka nake rokon da
ki kiyaye duk wani abinda zai kawo tashin hankali a tsakaninku, Zubeida a sanin
sanin dana miki ke ma...."
"Ni masifafiyar ce? ai tun tuni daka fito sak ka fad'a min, da kace kasanta ita ba
mai hayaniya bace, kenan nice mai hayaniya? yah Umar wai yaushe ka canza ne haka?
da fari ka kirani kuma kazo kuna karuwanci a gabana, amma kuma bai isheka ba shine
kake fad'a min matarka ba mai hayaniya bace, to naji saika barni da hayaniyata ni."
Kallon Khairat tayi tace "ke kuma, karma kiji dad'i saboda kinji yace na d'aukeki a
yayata ke kuma har kike jin dad'i, wallahi bani bake kuma bana da had'i dake da har
zaki zama yar uwata, kuma ki sani tashin hankali masifa da bala'i, yanzu kika fara
ganinsu cikin gidan nan, dan ba zan tab'a yarda nayi kishi da karuwa ba."
A hassale Umar Faruk ya mik'e zaiyi magana Khairat ta rik'e hannunshi d'aya hannu
kuma tana shafa qirjinshi tace "ya isa haka baby, ka rabu da ita mana, yarinya ce
fa."
Tureta Umar Faruk yayi daga jikinshi cikin jin zafi ya cabko Zuby da k'arfi ya fara
magana "wacece ke Zubeida da har nake magana kina katseni, yaushe aka haifeki da
har zaki d'aga murya akan yawa, fad'a min ina jinki akan me? yaushe wuyanki yayi
kauri haka?"
Jiki na rawa ta zauna kowa ya zauna wajenshi sannan yace "abinda ki kayi yanzu
hauka ne, kuma bana d'aukar irin wannan, akwai kishin da zan iya yiwa mace uzuri a
kanshi, amma banda irin wanda ki kayi yanzun, dan haka a kiyaye nan gaba, bana
buk'atar tashin hankali da qananun maganganu, zan sab'ama duk wacce ta tayar min da
tarazma a gida ba tare dana d'aga qafa ba, dan haka ku had'a kanku shine zaifi muku
alkairi dani kaina, dan saida had'in kanku zan iya samun farin ciki, kwantar da
hankalinku shine zai zama silar nasarata a rayuwa, da wannan nake mana fatan samun
zaman lafiya."
Addu'a ya dinga kwaranyowa ta fatan zaman lafiya tare da neman tsari daga shed'an
daga garesu, kafin daga bisani ya d'ora da "akan maganar kwana kuma, kamar yanda
muka sani ne, zan dinga yin kwana bibbiyu a d'akin ko wacce."
Yana fad'a ya fita ya bar d'akin ranshi a b'ace yana tunanin abinda Zuby tayi,
Khairat ma ta bishi a sannu bare kuma ita k'aramar alhaki banza a banza😂inji ni fa
ba Umar Faruk ba.
Juyawa Zuby tayi zata fita Khairat ta rik'e mayafinta ta tako a hankali gabanta ta
tsaya, kallonta tayi sosai kafin tace "hum, wai kishiyata , kinyi wasu maganganu
d'azu amma bansan ko zaki iya maimaitawa ba? nasan ma ba zaki iya ba domin karyaki
zanyi, amma bari kiji in fad'a miki, ni *karuwa* ce kuma ta Umar Faruk, dan haka
zan baki shawara kamar yanda na bawa mahaifiyarki, ki koyi karuwaci kema ko zaki
iya samun wani kaso a zuciyar Umar Faruk, idan kuma ki kayi wasa, to ki sani kin
rasashi kenan har abada, sai dai kiyi rayuwar k'unci a gidan Umar Faruk ko kuma
kiyi rayuwar 'yanci a gidanku a gaban mahaifiyarki, ma'ana zawarci."
Da hannu ta mata alama tace "zaki iya tafiya, idan kin fita ki turo min baby na
rarrasheshi, dan kin b'ata masa rai daga zuwanki gidan."
"Dama Mama ta fad'a min baki da kunya, amma ni zan koya miki hankali." cewar Zuby
tana shirin fita.
Rik'ota tayi tace "au, dama kuna tunanin samun karuwa da kunya ne? ai kawai ki
tanadi maganin hawan jini dana ciwon kai, domin daga yau salon bugun zuciyarki zai
canza."
Tana fad'a ta haye gado ta kwanta ita kuma ta fita daga d'akin ta koma nata, ko
kayan jikinta bata cire ba ta kwanta tana kuka saboda bak'in cikin abinda ta gani
da idonta.
D'akin Mama ya nufa ya samu abinci yaci kafin ya mata sallama ya komo d'akin
sahiba😉, tana ganinshi ta sauko daga kan gado ta sake rumgumeshi kafin ta d'ago ta
kalli fuskarshi cikin shagwab'a tace "kayi hak'uri baby, ta b'ata maka rai, muje na
maka wanka to."
Sake rumgumata yayi a jikinshi murya can cikin mak'oshi yace "zaki iya yimin
wanka?"
"Me zai hana? kaifa nawa ne."
Kafeta yayi da ido harta rabashi da kayan jikinshi ta d'aura mishi towel, hannunshi
ta kama dan zuwa douche ya rik'e hannunta ya fizgota ta fad'o kanshi, kallon juna
suke sosai kafin ya fara magana cikin sigar tausayi kamar zaiyi kuka yace,
"Khairat, dan Allah ki fad'a min me yasa kika canza daga yanda na sanki? Khairat me
yasa kike min duk wannan kyautatawar? bayan nasan ba sona kike ba, Khairat dan
Allah ki fad'a min me kike shiryawa a kaina? dan ina ji zuciyata zata iya bugawa
idan har kika gujeni daga baya, ni kaina bansan me nake ji ba, ban kuma san me
zance yake damuna ba a kanki, amma dai ina jin bugun zuciyata yana qaruwa idan ina
tare dake, sannan ina shiga farin ciki idan na ganki a kusa dani, Khairat nakan ji
daban a tare dani idan jikinmu ya had'u wuri d'aya, Khairat ina jin matsanancin
kishi a kanki, kuma ina yawan tunaninki kamar yanda kike yawan zuwa min à
qwaqwalwata, tunaninki na hanani sukuni, fuskarki takan hanani shak'at saboda yawan
ganinta da nake a idona, Khairat, wasu na tunanin na kamu da sonki ne, amma ni
kaina na kasa tantacewa sonki nake ko kuma ba haka bane, kinsan me yasa na kasa
tantacewa?"
Kai kawai ta girgiza masa shi kuma yace "domin ban tab'a shiga irin wannan yanayin
ba har saida na had'u dake, a sanadinki ne na fara jin komai na canza min, Khairat,
a yanzun in har zan iya fad'in gaskiyar abinda yake raina, to zan iya cewa *ina
sonki*, tabbas Khairat *ina qaunarki*, bana jin zan iya rabuwa dake a yanzun, dan
Allah kema karki gujeni, nasan ni talaka ne kuma ba zan iya d'aukar nauyinki ba,
amma Khairat zanyi iya qoqarina wajen ganin na samar miki duk abinda kike buk'ata,
Khairat zan iya bada rayuwata dan ganin walwala da farin cikinki, yanzu abu d'aya
nake so naji shine, kema kina sona?"
Rarraba ido ta shiga yi tare da had'iyar yawu tana k'yabta mishi ido, abinda za
tace masa take tunani, koda bata sonshi tasan dai taji dad'in abinda ya fad'a
yanzu, idan kuma ta fad'a mishi bata sonshi to zata rasa duk wani abu da take
shiryawa, dan haka mafita d'aya ta nuna itama sonshi take, maye murmushi tayi a
gurbin da mamakin kalamanshi suka bayyana sannan ta riko hannunshi sosai ta sumbata
kafin tace...
"Na d'auka ni kad'ai nake jin abinda nake ji a game dakai, bansan wani irin farin
ciki zan nuna ba, Faruk, kayi min abubuwa da dama wanda babu wanda ya tab'a min har
iyayena ma, tun daga ranar na fara jin abubuwa daban a game da kai, amma dayake
shashasha ce ni, saina kasa fahimtar halin da nake ciki, sai yanzu da naga wata
zata shiga tsakanina da farin cikina, naga ba zan iya hak'ura ba zaifi nima na
tashi tsaye na nuna maka soyayyata a zahiri."
Amsawa yayi ta hanyar sake kafeta da ido, dorawa tayi da " *ina sonka*, ina
qaunarka, ina sonka so mai tsanani , son da babu wanda zai iya ganin qarshensa sai
mahallicin sammai da qassai."
Qasa yayi da kanshi yana dariya saboda wani kuntumemmen farin ciki daya tokare
zuciyarshi, tabbas ya yarda yanzu ne ya fara soyayya, kuma da Khairat, hannayenta
tasa ta tallabo kanshi , abin mamaki ba dariya bace kad'ai harda hawayen farin
ciki, ita kanta wani farin cikin ne taji yana nuk'urk'usarta a zuciya, rumgumeshi
tayi sosai suka mak'alewa juna kowa kuma hawaye yake zubarwa.
_My Khairat ki yarda kawai, kema kin fad'a tarkon guy nan, auntyna Aisha, ina ga
maganar team tazo qarshe, mu nemi 'yan adawa mu sasanta kanmu, dan muji dad'in
farmakar Hajja Zuby._😉
Tare sukayi wanka kai kace shekararsu arba'in suna zuba love, haka suka fito a
towel d'aya kowa ya shafa na shafawa ya murza na murzawa, Umar Faruk na kallon
Khairat tana shafa humra takai kala bakwai wacce ta shafa, ta bayanta ya rumgumota
ya shinshina wuyanta ido lumshe kafin yace "miye sirrin turarukan nan? danna lura
akwai al'ajabi a tare dasu."
"Me yasa to?" ya tambaya yana qara tusa kanshi a tsakiyar wuyanta yana shak'ar
daddad'an k'amshin.
Juyowa tayi da nufi d'auko kayan baccinta ta saka kawai ya sureta yayi kan gado da
ita, saida ya kwantar da ita sannan ya sauka ya kashe wutar d'akin ya dawo tare da
zame towel d'in jikinshi ya wurgo mata, kan jikinta ya kwanta ya fara lagudarta
yana sarrafata son ranshi, to itama fa ba kwance kawai tayi ba aikin ta tayashi yi,
duk da ita kanta tasa takai mak'ura kuma tana buk'atar tallafi domin gabanta ya
nuna hakan, amma ba zata bari ya shigeta tun yanzu ba, tana jin ya fara bud'e mata
qafafu ta tashi zaune a firgice.
Janyota yayi jikinshi yace "Khairat, wallahi taimakonki kad'ai nake nema, dan Allah
ki barni nayi."
Cikin kukan shagwab'a tace "um um, gaskiya ni tsoro nake ji, wallahi ciwo zanji."
Da sauri ya rik'ota yace "a'a Khairat, na miki alk'awarin ba zaki ji ciwo ba,
wallahi a hankali zan biki."
"Ka manta meya faru ne, ba qaramin rauni suka min ba fa, gaskiya ba zan yarda na
sake kai kaina mahallaka ba."
Janyeta yayi daga jikinshi rai b'ace ya sauka daga kan gadon, kayanshi ya bud'a ya
samu doguwar riga ya zura da qaramin wando ya kwanta akan kujera, ranshi kam in
yayi dubu ya b'ace dan wani irin kishin bala'i ne yaji ya taso mishi akan su Musa,
kawai saiya dinga haskota kwance su kuma suna juyata son ransu, tunani yake yanzu
nan wasu sun rigashi isa bakin bodar, tuk'uk'i kawai ke taso masa a zuciya har
Khairat ta d'auro towel d'in tazo kusanshi, zata sunkuya kenan ya tsayar da ita ta
hanyar d'aga mata hannu yace "dan Allah ki rabu dani, kije ki kwanta."
Yanda yayi maganar yasa bata da wani zab'i daya wuce ta koma kan gadon tayi zaune
sai kuma ta fara kuka, yana jin shashek'arta kuma duk sai hankalinshi ya watse,
alk'awarin daya d'auka na ba zai bari ta zubar da hawaye ba yasa ya koma kusanta ya
fara rarrashi, a cikin rarrashin yace "ke kika tsokano min kishina Khairat, dan
Allah idan zai yiwu? bana so na sake jin wannan kalmar a bakinki, ina so ki manta
nima kuma zanyi qoqari naga na manta, kinji ko shalelen Papa."
Murmushi tayi tace "kayi hak'uri to , insha Allah ba zan sake ba."
_NA_
_SAMIRA HAROUNA_
_DEDICATED TO_
*MA FAMILLE*
_Bansan me zan iya cewa masoyana ba, hak'ik'a kuna sakani farin ciki, comment
d'inku na nishad'antar dani, tsakanina daku sai dai ince Rabbi ya bar qauna._ 💞💕💗
_Bismmilahir-rahman-rahim_
3⃣4⃣
Kamar saukar aradu Umar Faruk yaji saukar wani gundumemen bahagon makahon kiss a
kumatunshi, ji kake
"Muahhhhhhhhh."
😂😂😂😂😂😂
Sakin fuskarshi tayi data rik'e tace "idan kaga hannun Khairat ya tab'a fuskarka
yanzu, toka sani shafata ne za tayi."
D'aukarta yayi ya dinga juyi da ita a tsakaiyar d'akin yana dariya yana fad'in "har
kinsa zuciyar maza ta tsinke, na d'auka fa marina za kiyi, ashe dai sanin da nayiwa
Khairat."
Itama dariyar take kafin tace "kaga saukeni kaje ka shirya lokaci na tafiya."
Sauketa yayi ya qarasa cire kayan jikinshi kafin ya shiga wanka, koda ya fito ta
fito mishi da kayan da zai saka, da taimakonta ya shirya tsaf cikin farar shadda da
hula da takalmi, kallon kanshi yayi a madubi yana qara daidaita hularshi, saurin
d'auke hular tayi a kanshi ta d'ora a kanta tace "kenan ban iya sakawa ba? shine
har kake gyarawa."
K'ugunta ya janyo ya had'a da nashi yasa hannayenshi ya fara daidaita mata zaman
hular a kanta, murmushi ya sakar mata yace "dubi madubi kiga yanda kika gama
had'uwa, shi yasa nace miki ni mai sa'a ne."
A tare suka kalli madubin yana bayanta ita tana gaba, wani irin bala'in kyau ne
sukayi ga matuk'ar dacewa da junansu, wayarshi ya ciro a aljihu ya d'auketa photo
ita kad'ai sannan ya musu tare, cire hular yayi ya mayar a kanshi yana fad'in
"kinsan me zai faru?"
Goyeta yayi yana fad'in "kawai kizo muje tare, saina biya na ajeki gida wajen
Mamie, idan na dawo saina biyo na d'aukoki."
Da k'arfi ta wuntsilo ta sauko daga bayanshi tana fad'in "da gaske baby, Allah kuwa
ina son zuwa, ina kewar Mammie."
D'aukowa tayi ta rik'e a hannunta, shi kuma ya kama hannunta suka fita, saida ya
saki hannunta ya rufe k'ofarsu hakan kuma yayi daidai da fitowar Abbakar shima ya
shirya zai tafi, Zuby da Saratu kam kallon ikon Allah suke, wato masallacin ma tare
zasu tafi kome? anya Umar Faruk bai haukace ba😉 ku shinshina kuji, cikin taushin
murya Khairat tace,
Kallonta yayi ya juya ya kalli Abbakar dan baiga fitowarshi ba, cike da k'aunar
juna Umar Faruk yace "abokina ka jirani saimu tafi ko?"
Abbakar dake nad'e sallayar hannunshi ne yace "amma ai naga kamar tare zaku fita?
taya zan shiga wannan harka ta amare."
Wani wawan tsaki da Zuby taja tare da tashi tabi ta gaban Khairat ta wuce d'akinta,
Umar Faruk kam ko kulata baiyi ba yace "kaga muje, dama akwai maganar da nake so
muyi da kai."
Saratu dake zaune acan tace "Allah yasa dai ba cewa za kayi ya qara aure ba."
Kafin suyi magana Mama Sa'a tace "ke kuma shine matsalarki, kenan mu nan mutuwa
mukayi da muke zaune da kishiyoyin?"
Umar Faruk ne yace "rabu da ita Mama, aure ai ya zama dole yah Abbakar ya qara,
tunda ita yanzu ta tsufa."
Saida ya kama hannun Abbakar suka nufi hanyar fita yace "da bakinki kika fad'a, ko
awa d'aya ba ayi ba."
Khairat ma bayansu tabi ko murmushi ba tayi ba bare dariya, Mama Sa'a kuma harda
daga murya tana fad'in "saikin dawo 'yar albarka."
"Mtsssss, tusa kai ba kwarjini." cewar Mama Maimuna dake zaune akan tabarma.
A hassale Mama Sa'a tace "dawa kike Maimuna? ni kike fad'awa haka? ni tsararki ce
da zaki shiga harkata?"
"Eh, dake nake kiyi abinda za kiyi, aikin banza kawai, duk kibi kina wani nanik'ewa
yarinya ita kuma tana wulak'antaki, kawai saboda tsinannan kwad'ayi."
Aifa tsaye aka mik'e suka fara surfa bala'i Mama Umar Faruk dasu Saratu Ruk'ayya
hak'uri kawai suke basu, dan duka mazan sun tafi masallaci Zuby kuma naji tayi
banza dasu, saida suka kusan dakuwa sannan suka hak'ura kowace ta shiga d'akinta,
amma duk da haka kowace na jefo magana daga d'akin nata.
**************
A mota kam Abbakar da Umar Faruk hira suke sosai data shafesu, Khairat na baya tana
jinsu amma tana latsa wayarta har suka isa, tare suka fita da Umar Faruk suka tsaya
a k'ofar gidan, saida ya d'an saci kallon Abbakar dake mota kafin ya shafi fukarta
yace "ki gaishe dasu Mamie, idan muka taso zan biyo."
Cikin shagwab'a tace "amma fa nidai daka barni har zuwa dare, kaga idan ka dawo
daga wajen aiki sai kazo muje."
Tana fad'a ta matsa kusa dashi ta sumbaci bakinshi tana kallonshi ta kece da
dariya, "meye?" cewar Umar Faruk.
"Ba komai, saika dawo." duk tayi maganar ne a cikin dariya tare da tura k'ofar
gidan ta shiga.
Mai gadi dake alwala cikin shirinshi na masallaci ya taso da nufin gaisheta ta daga
masa hannu tare da tsayawa tace "kaci gaba da alwalanka, ba'a so ana tsayawa idan
ana alwala, komai mahimmanci abu kar yasa ka dakatar da alwalarka, musamman ma idan
abun ya shafi harkar duniya ne."
Tana fad'a ta shige ciki shi kuma ya biya da kallo tare da tunanin yaushe Hajia
Khairat ta zama Ustaza haka, yauma farin ciki sosai Mamie da Mammie sukayi,
musamman data fad'a musu shiya kawota kuma yace zai biyo idan ya taso, hak'ik'a
sunga shiriya sosai a tare da yarsu, kuma sunyi farin ciki marar misaltuwa."
*************
Yana shiga mota ya tayar suka wuce, Abbakar kam kallonshi yake yana dariya, ganin
dariyar tayi yawa yasa kalleshi yace "wai miye haka dan Allah? ya zaka sani a gaba
kana dariya."
Yanda yayi maganar yasa ya fahimci rai zai iya b'acewa dan haka yace "kalli madubi
ka gani."
Gyara madubin yayi ya kalli kanshi a ciki, ganin bakinshi yayi ja kamar yasa jan
baki yasa ya fahimci me yake wa dariya, a lokacin kuma ya fahimci dariyar da
Khairat take masa, lotus ya d'auka a motar ya goge bakinshi yana hararan Abbakar
yana cin magani, girgiza Abbakar yayi yace "Umar Faruk kenan, kamar ba kai ba
wallahi duk ka canza."
"Dama wata tafiya ce ta taso mai mahimmanci, kuma Khairat tace mahaifinta yace dole
sai dai mu tafi tare, in kuma banje ba ba zasuji dad'i ba, ni kuma harna ce mata na
amince, saboda akwai wani laifi da nayi mata tace zata fad'awa Baba, saboda haka
yasa nace na amince, amma ni gaskiya har yanzu bana jin zan iya tafiya tare da ita
haka kawai a dinga nuna ni a gari."
Saida ya gama nazartarshi kafin yace "to ita dai rayuwar duniya da kake gani inka
biya ta abinda mutane zasu fad'a to babu inda zaka je, sannan a matsayinka na
mijinta kuma kace zaka, amma daga baya kace a'a hakan zai iya tab'a darajarka da
mutuncinka a wajenta, iyayenta kuma tunda suka ce suna buk'atarka a wajen, tofa
akwai buk'atar son ganinka ne a wajen, dan haka ni ina ganin kawai ka bita ku tafi
tunda dai ba siyar da kai za tayi ba, matsala d'aya ce kawai nake tunanin za'a
samu."
"Matsalar me kenan?"
"Zubeida mana, da ace kafin ta tare ne, amma a yanzu data tare kuma na lura kan
yarinyar yana rawa, bai zama lallai ta amince ka tafi ba."
"Nima yaya nayi wannan tunanin tun kafin kayi, amma da yake tamin alk'awarin idan
har mun kwana biyu to ba zamu wuce uku ba, a lissafina ranar talata ne tafiyar ta
kama, daga gobe kuma kwanan Khairat zai qare, kaga kenan a ranar da zan koma
d'akinta ne za ayi tafiyar, kenan ko an shiga kwanan Zuby to kwana d'aya ne."
"Eh to da sauk'i idan hakane, dan haka ka fara shiri kawai ni zanji dasu Baba, sai
kuma ka nemi izinin matarka."
"A wannan qadamin kam kusan itace, dan ka sani in bata amince ba ba zaka tafi ba,
idan kuma ka tafi bada amincewarta ba, tofa ka sani ranar gobe Allah zai tsayar da
kai a gabanshi."
"Sheik Umar Faruk dai, kuma kayi k'ok'ari kafin ku dawo kuzo mana da babban
tsaraba."
Dariyar da yake yasa yace "wane irin k'ok'ari kuma, wace irin tsaraba?"
Bushewa sukayi da dariya harda tapa hannu kafin Umar Faruk yace "baka da dama
wallahi, taro ne fa zai kaimu ba lune da miel (honeymoon) ba."
Da haka suka isa masallaci kamar wasu abokanai suna hirarsu cikin raha, saida aka
gama hud'uba kafin akayi sallah daga nan kuma suka dawo tare suka komo gidansu
Khairat dan d'aukarta kamar yanda yace.
*****************
Suna zuwa tare suka shiga da Abbakar har ciki, a lokacin masu aiki na k'awata wajen
cin abinci da kalolin girke girke, Khairat da fitowarta kenan daga d'akinta ta gama
sallah ta dako da gudu ta rumgume Umar Faruk, "sannu baby , har kun taso?"
Kasa aiwatar da komai yayi saboda fitowar Mamie itama daga d'aki wanda Mammie dama
tana zaune a falon, abinka ga yan bariki😂 ba wanda yaji wani abu, sai Umar Faruk
daya ji kunya ta rufeshi, suna shirin zubewa qasa dan kwasar gaisuwa Mamie ta
qaraso da sauri ta dafa kafad'un Umar Faruk duka biyun tana fuskantarshi tace "a'a
a'a, haba d'ana, ai ka wuce wannan a gidan nan, kaima fa d'an gidan nan ne."
Hannunshi ta rik'e tayi hanyar wajen cin abincin dashi tana fad'in "muje ga abinci
an gama kuci."
Umar Faruk dai kanshi na qasa ya kasa kallonta sai Abbakar dake kallon falon irin
tsari da dukiyar da aka zuba, da kanta taja mishi kujera ya zauna ita kuma mai aiki
taja mata ta zauna, Khairat ma da Mammie duka sun zauna, Biba da Saude ne suka
bud'a kwanukan suka fara zuba musu abincin, suna gamawa suka koma mafakarsu su kuma
suka fara cin abincin.
Ba ruwan Khairat haka kawai take jin son Umar Faruk na gaskiyar na shirgarta, da
kanta take d'ibar abincin tana saka mishi a baki saboda taga baya ci, haka yasa ya
fara diba kad'an kad'an yana ci, Khairat d'in da Mammie kuma hira suke sosai irin
na kaka da jika , Abbakar dai kallon ikon Allah yake yana qara ganin girman
Khairat, dan inba mai hak'uri ba babu ta yanda za ace kana rayuwa cikin wannan
daular kamar a masarauta, abinci ma na rana kana cin kusan kala uku zuwa hud'u amma
ka yarda ka fara rayuwa a gida kamar nasu, haka ma a wajen Umar Faruk abinda yake
rayawa kenan a zuciyarshi tare da sake jaddada irin taushin zuciyar Khairat, lallai
baka sanin asalin mutum saika zauna dashi sannan zaka fahimceshi.
Suna kammalawa kafin su tashi Mamie ta kalli Khairat tace "ki tashi kije ki shirya
kizo ku tafi."
Umar Faruk ne yace "a'a Mama, ku barta kawai ta zauna, naga kunyi kewarta sosai,
idan na taso daga aiki zan biyo saina d'auketa."
Cike da farin ciki ta kalleshi tace "da gaske baby? gaskiya naji dad'i."
Mak'ale wuyanshi tayi tare da janyoshi kusanta ta sumbaci kumatunshi tare da fad'in
"na gode baby."
Mammie dake kusan Khairat ce ta zura hannu ta kama kumatunshi tace "yaron kirki,
gaskiya ka kyauta, dan dama muna so muyi shirye shiryen tafiyarmu a gabanta."
Ture hannunta Khairat tayi tana fad'in "kuma shine saikin tab'a min miji , nifa
bana son haka."
"Allah sarki, yo mijinki ko mijina? kaji min yarinya kai, kawai dan na ara mikishi
saiki wani zak'e dayawa."
Kallon Umar Faruk tayi ta kalli Mammie tace "zak'ewa ma nake? to ai mijin naki ne
ke rawar qafa a kaina."
"Kaji wani d'aurin duniya kuma, to nidai ban gani ba, kuma nasan yafi sona."
"To ai gashi nan ki tambayeshi kiji." Khairat ta fad'a tana nunashi da hannu
"Ba buk'ata, danni zai zab'a, bana so kiji kunya a gaban mutane."
Cikin taushin murya cike da jin kunya Umar Faruk yace " gaskiya ne, za tasha a
wajenki."
Mammie kam bushewa tayi da dariya had'e da yiwa Khairat gwalo, turo baki tayi tana
kallon Umar Faruk, shi kam kasa kallonta yayi saboda wutar tartsatsin da yake ji a
kanta, haka suka mik'e gaba d'ayansu zasu tafi, bayan sunyi sallama Mammie tace
"nasan dai sai mun had'u a lokacin tafiyarmu ko?
A hankali Khairat ta taka musu har zuwa k'ofar d'aki sannan suka tsaya, sumbatar
bakinshi tayi tare da kumatunshi kafin ta kalleshi tace "Allah ya tsare, saika zo."
Su Mamie dake hangensu yasa ya d'an shafi fuskarta kawai yayi gaba, suna fita suka
d'auki hanya saida ya aje Abbakar gida ko shiga baiyi ba ya juya ma'aikata dan
lokaci yayi sosai, sai dai zuciyarshi ta qara narkewa da tsananin son Khairat, haka
ya koma duk baijin dad'in aikin saboda manyan kayan dake jikinshi, ga kuma motsi da
k'amshin Khairat daya isheshi duk sanda ya motsa, ji yake kamar tana jikinshi ko
kuma tana sumbatartashi, a haka dai ya gama aikin a daddafe har aka tashi.
Bai wuce gida ba har saida ya tsaya ya siyawa Zuby kayan data buk'ata kafin ya wuce
gida, yana isa ana kiran sallah magrib hakan yasa yana shiga d'akinta ya aje mata
kayan ya fito yayi alwala cikin gaggawa ya tafi masallaci, bai dawo gidan ba har
saida akayi sallah isha'i saboda lokacin qurarre ne kuma suna tare da Ishaq suna
hira, suna gamawa ya shigo gidan saida ya fara shiga wajen Baba suka gaisa kafin ya
shiga d'akin Mama da sauran iyayen, yana fitowa ya wuce d'akin Zuby.
Ya samu tana nad'e sallayar da tayi sallah, abinda ya qona masa rai da haushi
shine, d'akin dai tsaf dashi sai kamshin turaren wuta amma kayan jikinta, tun
atamfar safe ce daya fita ya barta da ita ya kuma dawo ya sameta da ita, kuma yanzu
ma ita dai ce, ya d'auka kafin ya dawo daga masallaci zai samu ta canza, amma ina
alamu dai na ba tayi wanka ba tun na safe, zaune yayi a kukerar robar dake
fuskantar gadon ya kalleta fuska ba yabo ba fallasa yace, cike da ladabi tace
"sannu da zuwa."
Aje sallayar tayi ta tsaya tana kallonshi, a d'an dak'ile yace "zauna mana."
Zaune tayi bakin gadon tana kallonshi shima wuyanta yake kallo dake tsattsafo da
zufa , a shak'e yace "kin duba kayan?"
Cikin sanyin murya tace "eh to, kusan abinda babu kad'an ne gaskiya."
Da d'an k'arfi yace "to yanzu kamar nawa zai isheki ki siyo abinda babun?"
D'aga gira yayi sama ya d'an zame daga kan kujerar yasa hannu aljihu ya fito da
kud'i, jikka biyar biyar guda biyu ya bata yace "gashi, sai kiyi manage dashi dan
kinsan nauyi dayawa ne a kaina."
Sauran canjin ya mayar aljihu kafin ya sake gyara zama ya kalleta sosai yace "ina
son yin wata muhimmiyar magana dake, ina fatan zaki bani hankalinki kuma ki
fahimceni?"
"Zubeida, akwai wani babban taro da aka shirya a Germany, taro ne na manyan mutane
wanda zai had'a da iyalensu, mahaifin Khairat na d'aya daga ciki, kuma ya gayyaceni
a matsayina na surukinsa, tafiyar zata iya d'aukanmu kwana biyu zuwa uku, shi yasa
nake neman alfarmarki kwanan d'ayan, domin zai iya yiwuwa na shiga cikin kwananki
domin kinsan tafiyar hali, kosu Mama basu sani ba domin ina so na kammala daku
iyalina, ina fatan zaki min wannan alfarmar ki bani kwananki d'aya tak."
Cikin mamakin kalamansa tace "tafiya kuma, har qasar waje, amma kuma kai yaya ka
amince ka tafi? ba ka tsoron ko wani abu aka shirya maka."
"Darammm." taji gabanta ya fad'i, cike da kasa b'oye abinda ke ranta ta mik'e tsaye
tace "uhum, yanzu naji magana, kace dai tare da karuwarka zaku tafi, wato harta
bud'e maka idon da har kake tunanin fara biyarta a duk inda tayi ko? yah Umar wai
yaushe ka zama haka ne? gaba d'aya ka canza kamar ba kai ba, to wallahi in dai
izinina ne ake nema ban yarda ba."
Wata wawura daya ma hannunta har yayi qara cikin d'aga murya yace "Zubeida , akan
miye ina magana dake har zaki mik'e tsaye kina min ihu, rainani ne ki kayi kome, me
yasa zaki d'aga muryarki akan tawa? wai tambaya ma kike yaushe na canza? to a ranar
da kika canza na canza nima, akan miye zan zaunar dake ina miki magana cikin
nutsuwa ke kuma zaki d'aga min hankali, waye ya koyar dake wannan d'abi'ar? nace
waye yace kizo nan ki dinga min abinda ranki yake so, waye." ya qarashe da d'aga
murya tare da hankad'ata saman gado.
D'orawa yayi da "kina tunanin izininki nake nema? to baki fahimta daidai ba, ni
alfarma na nema kimin ta kwana d'aya wanda shima qila waqala na yishi a can, da har
zaki wani ce wai baki yarda ba, to karki yarda mana saime? naga idan zamanki nake a
gidan."
"Ba dai alfarmar dana nema bace har tasa kika min haka, to bari ki gani yanzu zanyi
maganin abin."
Wayarshi ya ciro daga aljihu ya danna kira, daga d'aya b'angaren ana d'auka cike da
karsashi da kashe murya tace "hello baby."
Saida ya lumshe ido saboda yanda yaji har tsikar jikinshi ta tashi, saita
nutsuwarsa yayi tare da sauke ajiyar zuciya kafin yace "hello, ya kike?"
Cikin shagwab'a da wata shegiyar kissa tace "ba dad'i, ka tafi ka barni inata
jiranka, duk da ina kewar gida amma har kasa naji gidan ya gundureni saboda kayi
nesa dani, a gaskiya Faruk sai yanzu nake qara tabbatarwa cewa soyayya *had'in
Allah ce*, yanzu fad'a min yaushe zaka taho?"
Baisan sanda wani basaraken murmushi ya sub'uce masa ba, a hankali ya furta "zanzo,
yanzu fad'a min tafiyar nan da zamuyi, kina ganin zamu iya dawowa a kwana biyu?"
"Eh baby , dan a ranar da za muje ma a ranar za'a gabatar da taron, kawai dai akwai
gajiyar tafiya da kuma ganin gari da zai iya kaimu kwana ukun."
Yanda muryarta ke fita yasa yasa hannunshi yana shafar saitin zuciyarsa da yake jin
bugunta yana canzawa , cikin basarwa yace "to a kwana biyu nake so mu dawo, ki
shirya zanzo d'aukarki yanzu."
Cike da zumud'i da qwarin murya danta daki dodon kunnensa tace "an gama ranka shi
dad'e."
Kashe wayar yayi ya maida kallonsa ga Zuby dake zaune tana sauraranshi, kallon sama
da qasa ya mata yace "wai duk wanda ya samu dama ba zai tsaya wasa ba sai k'ok'arin
ya dama damarsa, to in dan kwana d'aya ne ki rik'e na yafe miki bana buk'ata, zan
tafi a ranar da kwanan Khairat zai zagayo, naga kuma mai hanani abinda naga dama."
Wucewa yayi ya barta a zaune yana fad'in "aikin banza kawai, yara da zaran sun
ganka ba kaya a jikinka saisu nemi su rainaka."
Yana fita d'akin Khairat ya nufa ya bud'e da makullan wajensa ya shiga, kayansa ya
cire ya shiga wanka, bai jima ba ya fito ya shirya cikin qananun kaya yayi wanka da
turare kafin ya d'auki makullin mashin d'inshi dan dashi yake so ya d'auko
gimbiyar.
*****************
Duk da yaso ta fito amma saida tasa ya sake shiga ciki ya gaishe dasu Mamie kafin
ta fito, cak ta tsaya saboda ganin Dream a maimakon Renge rover😂, matsowa tayi
kusanshi tace "baby, ina motar take?"
Gemunshi ya tattaro ya had'e guri d'aya yana murmushi, a tunaninta so yake ya gwada
soyayyar da take fad'in tana masa shi yasa ya taho da mashin d'in, ba zata bari
shirinta ya watse ba dan haka ta saki murmushi ta rumgumeshi taré da sumbatar
kumatunshi kafin tace,
"Karo na farko a rayuwata zan hau mashin, a gaskiya soyayya za tayi dad'i akan
mashin."
Cikin dariya ya fara qoqarin hawa yana fad'in "saima kin hau zaki tabbatar."
Rik'e rigarsa tayi tace "ka taimaka min na hau kafin ka hau."
Hannun damansa ya mika mata ta rik'e sannan ta tattare rigarta kafin ta hau, yana
hawa ya tayar suka d'auki hanya, tintserewa tayi da dariya ta fara masa cakulkuli
tana fad'in,
"Ashe haka mashin yake? gaskiya daga yau ba zan sake hawa mota ba, nima mashin zan
siya sabo."
"Ke ke, dan Allah ki bari, za kisa mu fad'i fa, ki bari mana, hhhhhhh." ya qarashe
da dariya.
Saida suka hau titi kad'ai ta rabu dashi amma fa tana makale a bayanshi tayi luf
kamar mai bacci, surutu kawai take zuba masa shi dai nishadi da farin ciki ma ya
hanashi magana, da sauri ta nuna masa wata babban restaurant da zasu wuce ta
gabanta tace ai saiya tsaya sunci abinci.
"Dan Allah me zamu tsaya muyi anan? idan yunwa kike ji muke gida sai kisa Ruk'ayya
ta dafa miki duk abinda kike so." cewar Umar Faruk.
Cikin raha tace "a'a ni bana jin yunwa , kawai zamu je ne a matsayin masoya kuma
muci abinci."
"Um um , nifa bana son shiga irin guraren nan." ya fad'a cikin shagwab'a.
Saida ya rank'wafo bayanta ya kwantota yace "an gama ranki shi dad'e."
Tsayawa yayi kamar yanda take so suka shiga babban restaurant d'in, d'aya daga
cikin ma'aikatan ne suka tarbesu da kyakyawar mu'amula har suka samar musu da wajen
zama, ana aka basu takardar da zasu duba abinda suke so, Khairat ce ta zaba Umar
Faruk kuma yace abinda take so shi zaici, cikin k'ank'anin lokaci aka wadata
gabansu da kayan tab'awa, suna ci suna hira kamar masoyan tun a ranar farko, suna
daf da gamawa ma'aikacin ya dawo ya basu bill d'insu, ganin kudin da zasu biya yasa
Khairat kallon Umar Faruk, shima kallonta yayi saita bawa ma'aikacin takardar ta
nuna Umar Faruk tace "kaba baby zai biya." tana fad'a ta bud'a post d'inta ta
d'auko kud'i ko dubawa ba tayi ba cikin dubara ba tare da kowa ya gani ba.
Nufa wajen Umar Faruk ma'aikacin yayi amma sai Khairat ta rigashi isa ta sunkuya
kamar ta mishi sumba ta kamo hannunshi ta dank'a masa kud'in kafin ta dago ta kalli
ma'aikacin cikin harshen frensh tace "dan Allah ina zan samu douche?"
Kwatanta mata yayi ta nufi wajen Umar Faruk kuma ya kalli a hannunshi yaga kud'i,
karb'ar takardar bill d'in yayi sai yaga kud'in da aka rubuta ko kasheshi za ayi ba
zai iya biyansu ba, sai lokacin ya fahimci abinda Khairat tayi, murmushi kawai yayi
yayi kamar ya fito da kud'in daga aljihunshi ya bawa ma'aikacin, godiya yayi ya
wuce Umar Faruk kuma ya maida kallonshi ta inda habibiyar zata fito.
Ai kuwa sai gata dama ba abinda taje tayi kawai dan tabar wurin ne, tana zuwa ya
mik'e itama post d'inta ta d'auka sannan suka wuce, suna fita waje ya kalleta yace
"me yasa zaki biya? bayan nine ya dace na biya."
Kallonta yayi yaga raina masa wayo kawai za tayi dan haka yace "daga yau bana so ki
sake shiga aikin daba naki ba, wannan ba huruminki bane, yin hakan kamar kina nuna
ba zan iya d'aukar nauyinki bane."
Saida suka hau mashin d'in tace "duk da bana da ilimin addini, amma nasan abune mai
kyau mata ta taimakawa mijinta, nice nace muzo nan badan kana so ba, taya zan bari
kayi asarar mak'odan kud'ad'e har haka."
Jin yayi shiru yasa ta bishi da wata kissar ta hanyar rumgumeshi ta baya tana sauke
numfashi tace "kayi hak'uri to idan ranka ya b'ace, zan kiyaye anan gaba, amma ban
maka alk'awari ba."
Da sauri ta d'aga daga jikinshi cikin daga murya kamar ta manta inda suke tace
"wayyo Allah, yau mijina ne yake saka min albarka, gaskiya na gode baby, dan Allah
kayi min alk'awarin kullum zaka dinga saka min albarka, kaji?"
A haka suka kai gida cikin nishad'i da farin ciki, saida suka shiga wanka suka fito
kafin ya saka doguwar riga ya shiga yiwa iyayensu saida safe, d'akin Zuby ne ya
shiga qarshe ya tarar da ita kwance tana chat a wayarta, ko kallonshi ba tayi ba
saboda ta nuna masa ranta a b'ace yake, shi kuma domin ya nuna mata yana farin ciki
sai yace "ni zanje na kwanta, ina fatan dai ba wani abu ko?"
"Ok, saida safe to." yana fad'a ya wuce ya barta, ta d'auka zai rarrasheta ne koya
tsaya tab'a jikinta, hakan kuma ya mata zafi sosai dan haka ma ta fara matso wasu
hawaye masu zafi.
Shi kam yana komawa can Khairat tasa ya manta da wata Zuby soyayya da salo ta dinga
kasheshi dasu, har saida ya goge hawayen dake idonshi ya k'amk'ameta sosai yace
"dan Allah Khairat ki bani dama na shiga rayuwarki shiga ta har abada, Khairat ki
amince ki bani kanki mana ta hakane kad'ai zamu sake zama d'aya, dan Allah Khairat
ki taimakeni , ina kusa da kaiwa k'adamin da ba zan iya rik'e kaina ba, ki taimaka
ki bani kanki kafin kwananki ya qare daga gobe."
Shiru tayi a qirjinshi dan sam ta manta da wani rabon kwana, basarwa tayi ta fara
shafar kanshi tana fad'in "kayi hak'uri baby zan baka, d'an lokaci kad'an zaka
qaramin."
"Yana iya to , dole nayi hak'uri, na riga dana saba da wannan jikin naki Khairat da
salonki , zaiyi yuwa na iya *rayuwa ba tare dake ba*." duk yayi maganar nan yana
shafar qirjinta kamar zai ciresu.
Ita kam wani murmushin gefen labb'a ta masa dan kuwa hak'arta ta cinma ruwa, kuma
ko iya haka aka tsaya, to tayi nasara akan Umar Faruk.
*ƘANGIN RAYUWA*
_(labarin Raheenat da Abdul-Hakeem)_
🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾
💑💑💑💑💑💑💑💑💑💑💑
*RAHEENAT M ABBAKAR*
AND
*SAMEERA HAROUNA*
DEDICATED TO ALAWIYYA❤
Page 20 to 25
A jiye kwanan abincin tayi sannan ta zauna tana ci gaba da cika tana batsewa, dan
ita taso Raheenat ta barta taci uwarsu Farida, ita sam ta rasa wani irin sanyin
hali ne ke ga Raheenat ayi tacin mutumcinta ba zata iya ramawa ba, ita fa bata iya
juran irin wannan rashin mutumcin da rashin imanin wallahi, murmushi Mama tayi taje
ta zauna gefen yaƙunanniyar katifarsu tana kallon Sameera, a hankali ta buɗe baki
tace "ƴata me yasa kike son biye wa su Farida ne kuna rigima, su fa dama burinsu
kenan, dan ba sabon abu bane a gurinsu, dan Allah ki rinƙa tausar zuciyarki kinji
ƴata. "
Wani nannauyar numfashi Sameera ta sauke ta kalli Mama idanunta cike da ƙwalla tace
"Mama ba zan iya juran ganin ana wulaƙantaku nayi shiru ba, Mama sufa sam basu da
imani, ace tun safe baka ci komai ba a cikinka, sun kuma san kuna jin yunwar nan
amma su sam babu ruwansu, kuma dan rashin tausayi da imani ba zasu bar Raheenat ta
huta ba sai sun haɗata da aikin da yafi ƙarfinta, da wanne za taji Mama ? Da yunwar
dake damunta ko kuma da aikin da suke sakata, gaskiya Mama ba zan iya yin shiru ba
ina kallon wannan rashin imanin. "
Murmushi Mama ta kumayi tana jinjina irin soyayyar da Sameera takeyiwa Raheenat
tace "to bacin abinki Sameera maganar naki zai hanasu yin abinda sukeyi ne, yau ne
kika fara nuna ɓacin ranki a akan hakan, kuma sun bar abinda sukeyi, ina ce ma sai
wanda ya ƙaru ? Sameera ya zamar mana dole muyi haƙuri da duk wani abinda zasuyi
mana saboda muna cikin gidansu ne. "
Kamar Sameera zatayi kuka tace "to Mama dan kuna gidansu sai aka ce su wulaƙantaku,
ku bar musu gidan mana, wallahi mutanen nan basu da imani da tausayi ko ƙanƙani. "
Mama tace "mu bar musu gidansu muje ina Sameera, kin ko san irin wahalar da muka
sha kafin mu samu nan ɗin ma?, kina sane da *Halin Rayuwar* da muke ciki a wannan
zamani namu, taimako yayi ƙaranci, rayuwar ya zama ramin kura, kowa daga shi sai
ƴaƴansa, Sameera ki bar faɗin mu bar gidan nan dan bamu da inda za muje in muka bar
nan ɗin."
Sameera tace "wallahi Mama da da ɗaki a gidanmu da na roƙi Babana ya baku, to babu
ɗaki shi yasa, amma insha Allahu komai ya kusan zama tarihi. "
Murmushi Mama tayi cike da ƙaunar yarinyar tace "to Allah yasa ƴata. "
Janyo kwanar abincin Sameera tayi tace "yauwa Mama sauko ki ci abinci kafin
Raheenat ta ƙarasa aikin ta zo. "
Cikin jin daɗi Mama tace "Sameera ba dai zaki bar wahalar da kanki ba ko akan kawo
mana abinci. "
Turo baki Sameera tayi tace "Mama meya abin wahala a cikin kawo muku abinci, dan
Allah kibar cewa haka, yanzu dai dan Allah zo ki ci. "
Ta ƙarasa maganar tana buɗa ƙwanan abincin.
Riƙe hannunta Mama tayi tace "rufe ƴata, bari Raheenat tazo sai muci tare, nasan ta
fini jin yunwa. "
Cike da matuƙar tausayinsu Sameera take kallon Mama, wannan soyayya tsakanin uwa da
ɗiyartan yana burgeta, da wahala kaga ɗaya ya saka wani abu a bakinsa ba tare da ya
tabbatar ɗayan ya ci ba, bata ƙara wani maganar ba sai ga Raheenat ta shigo ɗakin,
daƙyar sallamar ma ta fito saboda yunwar da takeji, har wani jiri-jiri take gani,
da kallo suke binta har tazo ta zauna kusa da Mama, Mama ba tayi wani magana ba ta
janyo kwanan abincin ta buɗe tare da turawa gaban Raheenat, ɗago ido Raheenat tayi
ta kalli Mama, Mama tasan ma'anar kallon hakan yasa ta saka hannunta tare da yin
bismillah ta ɗibo loma, itama Raheenat ɗin sai ta saka hannu tare da bismillar suka
fara cin abincin, ƙwallar da ya ciko idanun Sameera ta saka hannu ta share tana ci
gaba da kallonsu, miƙewa tayi tsam ta ɗebo musu ruwa a randa tazo ta ajiye musu a
gabansu sannan ta koma ta zauna.
Murmushi Raheenat tayi tace "mun gode my meera, Allah ya biyaki da gidan aljanna,
yanda kike jin tausayinmu ubangiji kema yaji tausayinki. "
Itama murmushi Sameerar tayi tace "ameen ameen my Heenat, karki damu matuƙar muna
tare to sai inda ƙarfina ya ƙare gurin taimakonku. "
Murmushi kawai Raheenat tayi ta ci gaba da cin abincin, suna kammalawa ta ɗauki
ruwa tasha tace "Alhamdulillahi. "
Tana faɗin hakan ta miƙe da sauri ta nufi hanyar fita daga ɗakin.
Itama Sameera miƙewa tayi tabi bayan ƙawar nata suka fice.
Har lokacin su Farida na zaune suna aikin matsar waya, ko kallon inda suke Sameera
ba tayi ba danji takeyi kamar taje ta rufesu da duka ko taji sanyi a ranta, nan ta
taimaka wa Raheenat suka sauke tukunyar daga kan murhu domin shinkafar ta tsanye,
ganin Inna har lokacin bata shigo daga gidan Alhaji Naseer buzu bane yasa Raheenat
ta kalli Farida cikin sanyin murya tace "Farida na gama abincin. "
Ba tare da Farida ta ɗago ta kalleta ba tace "to dangin yunwa kije ki ɗauko
kwananku na zuba muku ke da munafukar uwarki. "
Rintse ido Raheenat tayi cikin jin zafin kalaman Farida tace "Farida ki iya bakinki
akan mahaifiyata, wallahi ina iya juran komai amma banda cin mutumcin mahaifiyata.
"
Tana gama faɗin hakan ta nufi hanyar ɗakinsu tana share hawayenta, Farida kuwa
cikin ɗaga murya tace "naƙi in iya bakin nawa, dukana zakiyi ne Raheenat, nace
dukana zakiyi, ai da kin tsaya kin saka min hannu shine zansan ranki ya ɓaci da
kalamai na, banza kawai dangin mayu. " ran Sameera fa in yayi dubu to ya ɓace,
cikin fusata take kallon Farida, wallahi taci darajar Mama tayi mata magana yau da
zai ta koyawa Farida hankali a gidan nan, sai dai kome zai faru ya faru, amma ta
ɗauki alƙwari a ranta sai ta koyawa Farida hankali ko ba yau ba.
Dariya Fa'iza tayi tace "gashi dai duk gorin da za'ayi muku bakwa zuciya da abincin
kuce baza ku ci ba. "
Farida ta amshe da cewa "to su mayi zuciyar ai sune zasu zauna da yunwar ba wani
ba. "
Raheenat dai ba tace komai ba har Faridar ta taso ta zuba mata abincin tare da
ɗaukar tukunyar ta nufi ɗakin Inna dashi, itama ɗaukar nasu tayi takai ɗaki sannan
ta dawo ta haɗa wanke wanke Sameera ta tayata suka wanke, sai da Sameera ta
tabbatar ta gama aikinta a wannan lokacin sannan tayi masu sallama ta tafi gida
tare da cewa zata biyo mata islamiyya in ta shiryo...
****************
Koda Inna ta shiga gidan kai tsaye b'angaren Hajia Luba ta nufa kamar yanda ta
saba, ta sameta akan lumtsumemiyar kujera 3 seater tana waya, qasa ta zauna kusa da
qafafun Hajia Luba kamar yanda take kullum tana kallonta tana murmushi tana ji
kamar Allah ya ara mata lokaci itama ta dama wannan damar, saida ta d'auki kusan
minti ashirin kafin ta gama wayar kuma duk maganar kud'i ce take kafin ta kashe
wayar, ba tare data kalleta ba tace "Ramatou."
Cike da qasaita da isa take magana d'aya bayan d'aya "wannan yarinyar dake zaune a
gidanki, ta shiga aikin daba nata ba d'azun, shin ke kika aikota ko kuma gaban
kanta ne tayi?"
Shiru ta d'anyi kafin tace "aiko ina jin Raheenat, Hajiata wani abun tayi halan?"
Saida ta sauke numfashi tace " kamar yanda na fad'a miki ta shiga aikin daba nata
ba, domin kuwa ta taimakawa Abdul Hakeem da ruwa, kuma ke sanin kanki ne duk wanda
ya taimaki Abdul koda da addu'a ne, to yakan samu hukunci daga wajen Hajia Luba."
Cikin washe baki tace "ni kam na sani Hajia, saboda hakan ma yasa kika saka boka ya
rufewa duk wani d'an uwanshi baki dan gudun karsu bishi da addu'a."
Sai lokacin kad'ai ta kalleta a wulak'ance, hakan yasa ta kama bakinta tayi shiru,
shiru d'akin ya d'auka na 'yan wasu dak'ik'u, mahaifiyar Abdul Hakeem ce ta fito
daga kicthen d'in dake gefe dasu d'auke da faranti ta k'awatashi da kayan ciye ciye
iri iri ta nufo Hajia Luba dashi, tana zuwa ta sunkuya har qasa ta aje farantin
tare da fad'in "Hajia gashi."
Shiru tayi kamar ba zata amsa ba kafin tace "ok, idan kin shiga ciki, saiki d'ora
mana tuwon shinkafa da miyar kuka, kisa busashen kifi a ciki shi nake sha'awar naci
da dare."
"To Hajia, amma dan Allah ki ban dama zanje na mayar da Abdul Hakeem d'akinshi?
nasan yanzu ya 'kosa da zaman can d'in."
Saida ta gama hararanta sama da qasa kafin tace "kije, kuma karki wuce minti uku."
"Na gode Hajia." ta fad'a ta tashi ta fita da sauri, sam ba zaka rabata da mai aiki
ba saboda kayan jikinta da gaba d'aya yanayinta.
Tana zuwa ta sameshi kam ya gaji da zama wuri d'aya, abinda ya tayar mata da
hankali wanda take da tabbaci saiya d'auketa tsawon lokaci shine, b'ata jikinshi da
yayi da bahaya, saida ta goge hawayen dake idonta ta shafi kanshi tace "kayi
hak'uri Abdul, nima ba'a son raina na barka nan ba, yanzu ma minti uku aka bani
nazo na mayar da kai, gashi kuma ka matsu harka b'ata jikinka."
Qara share qwalla tayi sannan ta tura kujerarsa izuwa b'angarensa, ba laifi baban
falo da kuma d'akuna guda uku a ciki sai kicthen da toilet a falon bayan ko wane
d'aki akwai toilet d'in, d'akin tsakiya ta shiga dashi anan ne d'akinshi, kai tsaye
toilet ta wuce dashi, saida ta cire masa kayan jikinsa ba tare da tana kallon
jikinshi ba kafin ta wanke masa jiki, fitowa sukayi ta sake mishi wasu kayan ta
fesheshi da turare kafin ta tallaboshi da qyar ta zaunar dashi saman gado, duk abin
nan da take masa idonshi rufe dan yakai munzalin da yake jin kunyar mahaifiyarshi
duk lokacin da take masa irin wannan d'awainiyar, ganin idonshi rufe yasa ta shafi
gefen fuskarshi tace,
"Kayi hak'uri Abdul, wata rana sai labari, ni mahaifiyarka ce kuma ni kad'ai ce zan
iya maka wannan hidimar, nasan kana jin kunya amma fa ka sani zaka fi jin kunya
idan akace matarka ko wani ne ke maka wannan abun, dan haka kayi hak'uri kaji, ni
zan koma na d'ora abincin dare, zanzo na baka abinci sannan na wanke kayan daka
b'ata, nasan kana jin yunwa, amma ba'a bani damar da zan baka abincinka ba."
Ganin yaki bud'e ido yasa ta fita ta barshi cike da tausayi, d'akin Hajia ta koma
ta samu suna hira qasa qasa ita da Inna, wucewa tayi kicthen yayin da suka ci gaba
da hirarsu.
Inna ce tace "aini Hajia wallahi da zaki amince ma, Allah dasai a had'a tsinanniyar
yarinyar nan da waccen musakin aure, kinga ni zanyi maganinta ita da uwarta, ke
kuma kin qara samun wata 'yar aikin, bauta kawai zata zo tayi."
"Haba Ramatou, ni zan yarda a yiwa Abdul aure a yanzu, miye anfanin hakan to?
taimakonsa za tayi ni kuma bana so."
"Hajia ai saikin so zata taimakeshi, da zaran ta shigo gidan kika gindaya mata
sharrud'anki da aiyukanta a cikin gidan ai kin gama da ita, ita fa kamar jaka ce
shegen aikine da ita."
Shiru ta d'anyi duk da dai bata ga wani anfani a auren ba, amma koba komai zata
hukuntata saboda taimakon data masa, kuma zata iya zama mai aikin 'ya'yanta, tunda
dama tak'i d'aukar masu aiki mata saboda bata san matsala.
_Meeraheenat_😘
02/08/2019 à 07:09 - My Heenat: 🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾
💑💑💑💑💑💑💑💑💑💑💑
*ƘANGIN RAYUWA*
_(labarin Raheenat da Abdul-Hakeem)_
🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾
💑💑💑💑💑💑💑💑💑💑💑
*RAHEENAT M ABBAKAR*
AND
*SAMEERA HAROUNA*
DEDICATED TO ALAWIYYA❤
Inna kuwa ganin shirun na hajiya Luba yayi yawa ne yasa ta ƙara gyara zama cike da
makirci ta neman tusa kai tace "
02/08/2019 à 22:19 - ~NANA KHADIJA~😍: 🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾
💑💑💑💑💑💑💑💑💑💑💑
*ƘANGIN RAYUWA*
_(labarin Raheenat da Abdul-Hakeem)_
🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾
💑💑💑💑💑💑💑💑💑💑💑
*RAHEENAT M ABBAKAR*
AND
*SAMEERA HAROUNA*
DEDICATED TO ALAWIYYA❤
Page 25 to 30
Wani irin murmushi Hajiya Luba tayi, cike da isa ta ƙasaita tace "naji shawararki
Ramatou, zan duba nayi shawara akai, abinda na yanke zan sanar dake. "
Cikin jin daɗi Inna tace "Allah yasa muji Alkhairi Hajiyar Allah, uwargida a gidan
Alhaji Naseer, Allah yaja da ranki ki daɗe kina zuba mulkinki. "
Murmushin gefen kumatu hajiya Luba tayi tana jin kanta na fasuwa tace "Ramatou ga
abin taɓawa nan ki ci."
Ai Inna kamar jira takeyi ta fara aikawa cikinta babu ƙaƙƙautawa, ita kuwa hajiya
Luba remote ta ɗauka ta mayar da hankalinta kan tanƙamemen tvn dake manne a falon
tana kallo.
**********
Misalin ƙarfe huɗu Sameera ta biyowa Raheenat zuwa makaranta, lokacin da Sameera ta
shigo gidan bata samu kowa a tsakar gidan ba, hakan yasa kai tsaye ta shige ɗakinsu
Raheenat, gaisawa sukayi da Mama cikin sauri Raheenat ta shirya cikin koɗaɗɗun
uniform ɗinta suka fito suka wuce islamiyyar, suna tafe a hanya suna hirarsu har
suka isa.
Sun samu har malam ya shiga aji, cikin sauri suka nemi guri suka zauna tare da ciro
littafansu, dan yau ba ranar taran latti bane.
**********
Sai gurin ƙarfe biyar hajiya Maryam ta kammala girkin da Hajiya Luba ta sanyata ta
zuzzuba a kula, ɗauko abincin Abdul-Hakeem tayi sannan ta fito ta duƙa har ƙasa
cike da girmamawa tace "na kammala da komai Hajiya, babu wani abu da za'ayi.?"
Cike da isa da wulaƙanci Hajiya Luba tace "babu" ba tare da ta kalli hajiya Maryam
ba.
Cikin sanyin murya hajiya Maryam tace "to hajiya zanje na bawa Abdul abinci, nasan
yana can yana jirana. "
"Ok, kije, sai dai karki manta akwai gogan kayana da zakiyi, da zaran kin kammala
bashi abincin sai kizo kiyi aikinki bana son ɓata time, kinji na faɗa miki. "
Cike da girmamawa tace "to hajiya, insha Allahu bazan ɓata lokaci ba. "
Tana gama faɗin hakan ta fice falon da sauri ta nufi ɓangaren Abdul dan bashi
abinci, tasan yanzu ya riga da ya galabaita da yunwa, hawaye ne taji sun tawo mata
tayi sauri sa hannu ta sharesu a fili tace "akwai Allah. "
Hajiya Maryam na fita Inna ta kalli hajiya Luba tace "aikinki na kyau hajiyar
Allah, gaba ɗaya kishiyarki ta zama baiwarki, gaskiya ke babba ce hajjaju. "
Taɓe baki hajiya Luba tayi tace "an gaya miki Luba ta wasa ce ?, kaɗan daga aikina
kenan Ramatou, ace kamarni bacin ƙaddara taya ma za'ace anyi min kishiya, kishiyar
ma har tazo ta haihu, haihuwar ma ɗa namiji wanda ni ban haifa ba, ke kanki kinsan
ba zan barsu haka ba. "
Murmushi Inna tayi tace "na sani hajiya, kinfi gaban nan, babu wanda zai ja dake ya
zauna lafiya, in ko mutum ya zauna lafiya ke kika so, ni bari na zo na koma gida,
dama gaisuwa ce nace bari na kawo, naga kwana biyu ban zo na kawo gaisuwa ba. "
Cike da ƙasaita tace "kin kyauta kuwa Ramatou, " jakarta ta ɗauka dake kusanta ta
buɗa ta ɗauko 5000 ta miƙawa Inna tace "ga wannan Ramatuo ayi hidimar gida dasu. "
Nan fa Inna ta zube ta dinga zuba godiya, har saida hajiya Luba ta ɗaga mata hannu
alamun isa sannan ta dakata, ta miƙe tayi mata sallama ta fito daga gidan ranta
fes.
*******
Hajiya Maryam na shiga ɗakin Abdul-hakeem ta iskeshi gar lokacin kwance yanda ta
barshi idanunsa lumshe yana hango kyakkyawar fuskar Raheenat lokacin da take bashi
ruwa, da sauri ta ƙarasa kusa dashi tana faɗin "yi haƙuri ɗan Mommynsa, ga Mommynka
ta dawo baka abinci buɗe idanunka kaji ɗan albarka. "
Buɗe idanun yayi yana kallon Mommyn nasa, wani irin zafi tare da tuƙuƙi ya keji
cikin ransa ganin yanda muguwar matar nan ta mayar da Mommynsa ƴar aiki da ƙarfi da
yaji, be san sanda hawaye ya zubo masa ba, ganin hawayensa ne yasa hajiya Maryam
ruɗewa, cike ta tausayin ɗan nata da ita kanta tace "subhanallahi, Abdul kuka
kuma.?"
**********
Biyar da rabi daidai yau aka tashi su Raheenat daga islamiyar, hakan yayiwa
Raheenat daɗi sosai, dan zata samu damar kammala aikinta da wuri yau, dan tasan
yanzu tana komawa wanke-wanken kwanukan da suka ci abinci nanan na jiranta da kuma
gyaran ɗakinsu Farida da na wannan ɗan iskar Sadiq.
Daidai ƙofar gidan su Raheenat Sameera tayiwa Heenat sallama ta wuce gida ita kuma
Raheenat ta saka kanta cikin gidan kanta tsaye.
Karo kawai taji tayi da mutum ba tare da taji zuwansa ba, da sauri ta ɗago kanta
dan ganin wanene, aiko sai ta sauke idanunta kan Sadiq da yake tsaye yana binta da
wani mayen kallo yana lashe laɓɓa......
Ja tayi da baya amma saiya rik'o hijabinta yana janyota, duk da Raheenat nada
hak'uri, amma ba zata iya zuba ido aci mutuncinta ba ta hanyar keta mata haddi ko
kuma muzanta mahaifiyarta, hakan yasa tayi k'arfin halin fizge hijabinta daga
gareshi tana fad'in "haba yah Sadik, wai me yasa ne kake haka? me yasa ba zaka duba
girma da darajar yaya da nake baka ba? kai kullum burinka ka zubar min da mutunci."
Sake kashe mata ido yayi yana ci gaba da lashe labb'anshi harda d'an tsizawa yake
kafin yace "matsalata dake kenan, wannan gidadancin naki, bansan yaushe zaki waye
ba?"
A hassale tace "in dai abinda kake nema a guna ne na hanaka shine wayewa, to ka
sani har abada ba zan tab'a wayewa ba, zanci gada da zama a cikin wannan duhun kai,
dan shine kad'ai zaisa na tsira da mutunci na."
"Ai kuwa kota k'arfi saina rabaki da mutuncin, dan banga anfanin da kuke mana a
gida ba, kufa kamar bayi ne a garemu, kinga kuwa dole kuyi abinda muke so."
"Ba dole, kamar yanda mu ba bayi bane, kuma Allah shine zai tayani kare mutunci na
daga ire irenku marasa tsoronshi."
Matsowa yayi kusanta tare da zura hannu yana shirin rik'o k'ugunta, ganin abinda
yake shirin yi yasa tayi saurin tureshi da iya k'arfinta harya kusan faduwa tare da
kaiwa bango karo, zafi yaji sosai hakan yasa yana d'agowa ya wanketa da wani
bazawarin mari, qara ta fasa mai k'arfi saboda yanda taji marin, kafin ta dawo
hayyacinta ta kuma jin wani sabon marin, duk'ewa tayi a wajen ta fashe da kuka
sosai.
Mama dake zaune a d'aki tun a marin farko taji gabanta ya fad'i, da sauri ta mik'e
tsaye jin qarar Raheenat kuma ya tabbatar mata da wani abu ya samu 'yarta, amma
tunda cikin gidan ne ba yanda za tayi daya wuce taja baki tayi shiru.
Inna dake fitowa daga ban d'aki duk taji meya faru, kuma taji laifin na d'anta ne,
amma saita rufe ido ta shigo soron ta samesu, "meya faru, meka mata Sadik?"
Jin muryar Inna yasa Raheenat mikewa da k'arfin gwiwa ta fara cewa "Inna, yah Sadik
ne yake min maganar banza, kuma ba tun yau ba ya jima yana haka, na fad'a mishi ya
daina amma yak'i, shine yanzu....."
"Ke dallah rufe min baki." wannan tsawar ce tasa tayi shiru kamar an d'auke wuta.
Kafinta ankara ta finciko hijabinta bata tsaya da ita ko ina ba sai tsakar gidan,
Inna ce ta ci gaba da cewa "ke har kina da wani abinda Sadik zai dinga bibiyarki?
wacece ke da zakiwa d'ana qazafi? kenan yanzu abun naku ma harda sharri a ciki? to
bari kuji daga ke har bakar uwar taki , wallahi kika sake shiga hanyar d'ana saina
wulak'antaki, haka kawai saboda jaraba kin tsotsa a nono shine kike bibiyar Sadik."
"Kenan ni kike so kice na nemiki? to me zanyi dake? mata sun qare a duniyar ne da
zan rasa wacce zan nema saike?" Sadik ne ya katse.
Share hawayenta tayi tace "naji, tunda haka kace, kaje akwai Allah kuma shi zai
mana sakayya , amma idan har kai d'an halak ne Sadik karka sake nemana."
Bawai Inna da Sadik ba, ita kanta Raheenat saida ta fad'a tayi mamakin kanta, Inna
ce tayi kanta ba tare da tunanin komai ba ta fara kai mata duka tana fad'in
"Raheenat ni? ni Raheenat kike shegantar min da yaro kuma a gabana, ke yanzu Sadik
ne zaki kalla har kice in d'an halak ne shi? yau saina ci ubanki, koda yake bama
uban gareki ba, sai naci uwarki a gidan nan."
Haka take fad'a tana dukanta, kuka da ihu kawai Raheenat keyi yayin da su Farida ke
tsaye suna kallo suna mata dariya, shima Sadik d'in haka sai yake jin inama shine
ke dukanta saboda yanda take shigewa jikin Inna, kamar daga sama sukaji sallamar da
tasa Inna tsayawa cak yaran kuma kowa yasha jinin jikinshi.. .
05/08/2019 à 19:47 - My Heenat: 🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾
💑💑💑💑💑💑💑💑💑💑💑
*ƘANGIN RAYUWA*
_(labarin Raheenat da Abdul-Hakeem)_
🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾
💑💑💑💑💑💑💑💑💑💑💑
*RAHEENAT M ABBAKAR*
AND
*SAMEERA HAROUNA*
```Muna godiya gareku makaranta wannan litttafin, haƙiƙa muna jin daɗin comment
ɗinku, yana sanya mu nishaɗi sosai, har ma my meera take ce min my heenat anya ko
baza mu ƙara musu yawan typing ba ko dan mu saka su nishaɗi suma kamar yanda suke
saka mu ? Murmushi nayi kawai nace my meera duk yanda kika ce haka za'ayi😊, to
fans ku huta kawai kuji daɗinku muna yinku sosai sosai, ku ci gaba da sambaɗa mana
comment mu kuma zamu ci gaba da sambaɗo muku typing da yardan me duka🥰```
DEDICATED TO ALAWIYYA❤
30 to 35
Ƙara lumshe idanunsa yayi, hakan yasa wasu hawayen saukowa, a hankali hajiya Maryam
ta saka tafin hannunta ta fara goge masa hawayen itama idanunta cike da ƙwalla,
magana ta fara cikin sanyin murya tace "kayi haƙuri Abdul, haƙiƙa *komai yayi
farko* to yana da ƙarshe, ina me tabbatar maka kamai zai zama tarihi watarana,
nasan me kakeyiwa hawaye, to ka sani Allah yana sane da halin da muke ciki kuma ba
zai barmu hakanan ba, ina ji a jikina zaka samu lafiya nan ba da daɗewa ba, ina ji
ajikina Abdul ka kusa takawa da ƙafafunka, ka kusa buɗe baki kayi min magana da
daddaɗan muryar nan naka me daɗin sauraro, dan Allah kabar kuka, bana son ganin
hawayenka ko ƙanƙani, hakan na ɗaga min hankali, nasan Abdul ɗina ba rago bane
jarumi ne, jarumi kuwa ba'a sanshi da saurin karaya ba. "
Kamar saukar ruwan sama da ɗaukewarsa haka hawayen Abdul suka ɗauke nan take,
kalaman Mummynsa ba ƙaramin daɗi sukayi masa ba, sai dai baya da damar nuna mata
hakan, ko murmushi baya da ikon yinsa wanda zai iya nuna mata yana farin ciki,
idanunsa ne kaɗai suke iya fahimtar da ita farin cikinsa da baƙin cikinsa, kuma ta
cikinsu ne kaɗai take iya gano abinda yake buƙata.
Ajiyar zuciya ta sauke ganin yabar kukan, taimaka masa tayi ta zaunar dashi sosai
sannan ta buɗe kular abincinsa ta ɗebo da hannayenta ta nufi bakinsa dashi.
Cikin hikima take bashi abincin, wani na shiga wani na fitowa, a haka ta kammala
bashi abincin sannan ta bashi ruwa yasha, goge masa bakinsa tayi sannan ta miƙewa
tayi ta nufi toilet domin wanke kayan da ya ɓata ɗazun.
Abudul-Hakeem yana ganin shigewar Mummynsa toilet ɗin ya mayar da idanunsa ya rufe
ruf, fuskar Raheenat yaƙi barin ƙwak'walwarsa, yanzu ma da ya rufe ido ita yake
hangowa, wacece ita ? shine tambayar da yake yi a zuciyarshi.
***********
"Subhanallahi! me nake gani haka Innar su Sadiq?" malam Habu ya faɗa yana ƙarasa
shigowa cikin gidan.
Kame-kame Inna ta farayi saboda bata san me zata faɗi ba, gashi sam ba tayi
tsammanin dawowan Malam Habu a wannan lokacin ba saboda balaguro ya tafi.
Cikin ɓacin rai ya zo ya ɗago Raheenat da take duƙe ƙasa tana kuka ya kalli Inna
yace "yanzu Ramatou me yarinyar nan tayi miki ne kike mata irin wannan dukan na
rashin imani ?, budurwa irin wannan kome za tayi miki ya dace ace kin kamata kina
bugu haka, saboda Allah ke kin ga dacewan abinda ki kayi ?, wallahi Ramatou kiji
tsoran Allah, ki sani zaki mutu. "
Kallon su Farida yayi cikin tsawa yace "ku ɓacen da gani anan gurin sakarkarun
banza kawai shashashai. "
Aiko a guje sukayi ɗakinsu saboda suna matuƙar tsoron Babansu, Inna kuwa kasa
magana tayi domin duk iskancinta tana shakkar me gidan nata.
Kallonsa ya mayar kan Raheenat da har lokacin take kuka cike da tausayawa yace "
kiyi hak'uri kinji Raheenat, ina mahaifiyarki take?"
Da hannu kawai ta nuna masa d'akin nasu alamar tana nan, kama hannunta yayi suka
nufi d'akin nasu yana hararan Inna dake d'arare har yanzu.
Tsaye suka samu Mama k'ofar d'akin tana hawaye, tana jin shigowarsu tayi saurin
k'arasawa wajen yar katifarsu ta zaune tana share hawaye, kallonta yake harya
karasa wajenta ya zaunar da Raheenat kusanta shi kuma ya tsugunna yana ci gaba da
kallonta, "dama kina cikin gidan take dukanta haka? kuma kina ji kin kasa komai."
Shiru tayi kanta qasa, sake magana yayi " *Fateema* dake nake, me yasa za kiyi
shiru kina gani tana neman sabauta miki 'ya? ko bake kika haifeta ba baici ace
kinyi magana ba."
A matuk'ar tsorace ta kalleshi ganin yanda yake kallonta yasa ta tsorata sosai,
cikin kuka tace "wallahi Baba bana da laifi, laifin yah Sadik ne, shine yake min
maganarrr...."
Kallon da Mama ta mata yasa tayi cak da maganarta, fuska a had'e ya kalli Mama
kafin ya mayar da kallonshi ga Raheenat yace "ki fad'a min ina jinki, meya faru
tsakaninki da Sadik?"
Saida ta had'e yawu ta kalli Mama da kanta ke qasa kafin tace "tunda muka zo nan
yah Sadik yake yawan yimin maganganun banza, kullum ina fad'a masa ya daina amma
baya ji, yanzu har takai yana cewa kota k'arfi ne saiya....."
Sai kuma tayi shiru saboda nauyin maganar, a fusace Baba ya tashi bai tsaya ko ina
ba sai d'akinsu Sadik, Sadik na kwance akan qaramin gadonshi yana danna wayarshi
bai ankara ba yaji saukar wani mahaukacin dundu a bayanshi, wata irin qara yayi mai
kamar amai tare da yunk'urawa ya tashi zaune yana kallon mahaifin nashi da kana
gani kasan sai dai Allah ya gyara kawai.
Kwalar rigarshi ya cabko ya fito dashi tsakar gidan yayi wurgi dashi ya zube qasa,
cikin zafin nama ya d'auki d'aya daga cikin icen da Raheenat tayi d'ori ya kai
masa duka a jiki yana fad'in "ni Sadik? ni? ni zaka zubarwa da mutumci a idon
duniya? ni zaka zubarwa da mutumci a cikin unguwa? akan me zaka dinga yiwa
marainiyar Allah maganar banza, rashin imani da gurb'acewar tarbiyarka har yakai
haka dama? tirr , nayi bak'in cikin wannan ranar, Sadik yau d'in nan kasa naji ina
nadamar haihuwarka da nayi, ina ma b'arinkkk."
Inna ce ta fito daga d'akin tana fad'in "a'a malam, akan me zaka dinga aibata
d'anka akan wasu bare banzaye? saboda kawai sun fad'a maka qarya da gaskiya, a
gaskiya bai dace ba ai kamata yayi ka tarasu kaji meya faru."
"Ke Ramatou, wallahi ki fita idona in rufe, ki kiyayeni fa, ki bari na gama dashi
zanzo kanki, zanji dalilin dukanta da kike kamar jaka." duk yayi maganar ne yana
nunata da icen hannunshi.
Komawa yayi kan Sadik ya d'aga iccen zai sake gabza masa yayi saurin rik'ewa yana
neman afuwar Baba "dan Allah Baba kayi hak'uri ka yafe min na tuba, na tuba wallahi
ba zan sake ba daga yau, ka yafe min dan Allah Baba wallahi ba zan sake ba."
Fizge iccen yayi amma yaji ya rik'e gam , da hannu ya nunasa yace "zaka gane dani
kake magana, ka kuma shirya dan babu abinda zai hana na maka aure tunda na fahimci
burinka shine ka tozartani."
Yana fad'a ya shiga d'akin Inna badan ransa naso ba sai dai kawai shine kawai
d'akin da zai iya shiga, dan d'akin nashi shine ya kwashe kayanshi ya bawa su
Raheenat suka zauna, Sadik ma tashi yayi cike da kunya da takaicin zafin rai irin
na mahaifinsu , da girmanshi da komai ace ana dukanshi, ai sam bai kamata ba kuma
ma saboda wata banzar yarinya.
_Ohhh, my Heenat, me yasa zaki hanani na qarasa? da kin barni na nuna mishi_😏
******************
Hajia Maryam ce ta fito daga toilet tana goge hannayenta da hijabinta ta tunkaro
wajen Abdul Hakeem, sunkuyawa tayi ta shafi fuskarshi tana murmushi tace "d'an
albarka ana kwance, toni na gama zanje na d'anyi wanka dan magriba ta gabato, gaji
sosai Abdul, amma dai zan dawo kafin na kwanta kaji."
Duk da mahaifiyarshi ce amma yasan ba gaskiya ta fad'a masa ba, yasan dole akwai
wani aiki dake gabanta yanzun haka, d'an lumshe ido yayi alamar to kafin ta sake
sakin murmushi tace "da kyau yaron Mamanshi."
D'agawa tayi ta juya zata fita taji an bud'o k'ofar d'akin, mahaifin Abdul Hakeem
ne hakan kuma yasa gabanta ya tsinke ya fad'i tare da yin qasa da kanta lokaci
d'aya alamar tsoro da fargaba ya rufeta, kanshi tsaye ya wuce wajen Abdul Hakeem ko
kallonta baiyi ba dan inya kalleta ranshi ne zai b'ace, kuma da yasan zai sameta da
bai shigo ba yanzun.
Tana ganin ya zaune kusan Abdul Hakeem tare da shafa kansa tayi wuf ta fita daga
d'akin, kallon Abdul yake sosai ba tare da yace komai ba, yana jin soyayyar d'an
nashi qwaya d'aya tak daya mallaka a duniya, kullum ya sauke idonshi a kan d'ansa
saiya sake jin burin samun magaji , yana ganin da Abdul yana da lafiya da yanzu
shike kula da kusan kashi biyu daga cikin uku na harkokinshi, amma kash larura ta
masa cikas , *Raheenat*, itace yarinyar data fad'o masa a rai a daidai wannan
lokacin da yake kallon Abdul shima kuma shi yake kallo, yana tausayawa mahaifinshi
rayuwar da yake ciki, yasan abubuwa da dama dangane da rayuwar gidansu, yasan Hajia
Luba itace mai alhakin tarwatsa zaman lafiya da farin cikin gidansu, domin kuwa
tana fad'a masa haka sai dai ba damar da zai iya koda nunawa, kuma sanin hakane
yasa itama take sakin jiki tana fad'a masa duk abinda yazo bakinta ba tare da
shakku ba.
***************
Ruwa Inna ta d'auka ta shiga d'akin dashi, durk'usawa tayi zata aje masa yace "
ashe Ramatou dama amanata kike ci idan bana gidan nan? akan me zaki min haka
Ramatou? wallahi ko kad'an banyi tsammanin haka daga gareki ba"
Cikin sigar makirci tace "dan Allah malam kayi hak'uri, tabbas nayi kuskure amma ba
zan sake maimaita kamarsa ba insha Allah."
Shiru yayi ganin haka yasa ta zuba ruwan ta bashi tare da fad'in "fatana dai Allah
ya huci zuciyarka, dan kafi kowa sanin ba son ganin b'acin ranka ba nake."
Bashi ruwan tayi ya karb'a yasha sosai kafin yace "ki zuba min ruwa a buta zan wuce
masallaci."
Raheenat ce tsaye a bakin rijiyar tana jan ruwa itama zata zuba a buta, harara Inna
ta wurga mata tare da fizge gugar a hannunta, bata tsaya ba ta wuce d'aki ta kaiwa
Mama ruwan kafin ta fito tayi alwala.
******************
Ganin yanda Abdul d'in ke kallonshi yasa ya tsaya da shafa kanshi da yake yace "ya
jikinka Abdul?"
Ko kad'an bai motsa idonshi ba hakan yasa ya sake cewa "baka jin komai?"
Nanma ba wata alama, d'an murmushi yayi yace "akwai tunanin da nake yi a kanka, sai
dai ba lallai ne ya yiwu ba, dan akwai tawaya sosai daga d'aya b'angaren, amma duk
da haka zan jaraba."
Sai lokacin Abdul ya lumshe idonshi kafin ya sake bud'ewa akan mahaifin nashi,
kiran sallah ne yasa mahaifin nashi mik'ewa tare da cewa " ni zan tafi masallaci
Abdul, saina dawo."
Bai jira amsarshi ba kai tsaye ya bar gidan ya nufi masallaci dan dama da
alwalarshi, had'uwa sukayi da malam Habu suka gaisa sannan suka shiga ciki, haka ma
bayan yan idar tare suka fito, a jere suke takawa a hankali suna yar hira sama sama
har suka zo k'ofar gidan Alhaji Naseer d'in kafin ya tsayar da malam Habu......
_Meeraheenat_😍
08/08/2019 à 12:23 - My Heenat: 🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾
💑💑💑💑💑💑💑💑💑💑💑
*ƘANGIN RAYUWA*
_(labarin Raheenat da Abdul-Hakeem)_
🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾
💑💑💑💑💑💑💑💑💑💑💑
*RAHEENAT M ABBAKAR*
AND
*SAMEERA HAROUNA*
DEDICATED TO ALAWIYYA❤
Page 35 to 40
Shima dai malam Habu gyara nasa tsayuwar yayi yace "gaskiya ban sani ba Alhaji. "
Murmushi Alhaji Naseer yayi yace "magana ne akan yarinyar gidanka. "
Cike da rashin fahimta malam Habu yace "Alhaji ai yaran gidan nawa suna da yawa,
wacce a ciki kenan. ?"
Alhaji Naseer yace "ina nufin yarinyar da suke zaune gidanka ita da mahaifiyarta,
Raheenat take ne ko wa."
"Ayyo Raheenat kenan, Allah yasa dai ba wani laifi tayi ba. "
Faɗin malam Habu yana kallon fuskar Alhaji Naseer.
Murmurshi Alhaji Naseer yayi yace "a'a ba tayi laifin komai ba, sai ma neman
taimakonta da mukeyi. "
Alhaji Naseer yace "ƙwarai taimakonta malam Habu, kuma wannan taimakon ba zai samu
ba har sai kai ma da taimakawanka. "
Wani irin murmushi Alhaji Naseer yayi me ciwo yace "in ba zaka damu ba mu shiga
daga ciki sai muyi maganar, dan be kamata ace munyi maganar a nan tsaye ba. "
Nan suka ƙara jerawa zuwa cikin gidan Alhaji Naseer ɗin, basu ya da zango a ko ina
ba sai cikin tanƙameme ko ƙawataccen falon Alhaji Naseer, izinin zama yayiwa Malam
Babu sannan ya nufi Fridge ya ɗauko masa lemo ya ajiye masa a gabansa sannan shima
ya nemi guri ya zauna.
Malam Habu ne ya kalli Alhaji Naseer yace "ina sauraronka Alhaji. "
Nisawa Alhaji Naseer yayi sannan yace "Malam Habu kadai san komai game da lallurar
ɗana guda ɗaya tilo dana mallaka a rayuwa ba sai nayi masa bayani ba, yau kimanin
shekara goma kenan Abdul-Hakeem yake zaune saman kujera baya iya motsa koda yatsar
hannunsa, anyi maganin anyi maganin amma har yau babu wani canji, sanin kanka ne
ƙasashen dana fita da Abdul dan neman lafiyarsa ba zasu ƙirgu ba, amma abin mamakim
yanda muje haka muke dawowa, maganar gaskiya ba sai na faɗawa kowa ba ansan ina
cikin matsanancin damuwa game da ciwonsa, sannan ina matuƙar tausayawa masa, na
daɗe ina neman hanyar da Abdul zai samu sausaucin akan ƙuncin da yake ciki amma na
kasa, sai shekaran jiya na samu hanyar da na tabbatar Abdul ɗina ko be warke ba zai
zauna cikin farin ciki saɓanin yanzu da kullum bana hangen komai a fuskarshi sai
ƙunci da baƙin ciki, kuma ba wata hanya bace sai na aura masa Raheenat. "
Da sauri malam Habu ya kalli Alhaji Naseer yace "aura masa Raheenat kuma Alhaji.?"
Ɗan murmushi Alhaji Naseer yayi yace "ƙwarai malam Habu, a shekaran jiya Raheenat
ta shigo gidannan ɗibar ruwa, a lokacin Abdul na zaune yana shan iska a farfajiyar
gidan nan, basan me ya faru ba, amma mun fito mun iske Raheenat tana bawa Abdul
ruwa yana sha, lokaci ɗaya naji yarinyar ta burgeni, daga shigowarta har ta fahimci
yana son ruwa alhali ba magana yakeyi ba ? Hakan ne ya tabbatar mun in na aura masa
yarinyar zata kula dashi sosai, sannan ni na hango wani abu cikin idanun Abdul game
da yarinyar lokacin da take bashi ruwan, malam Habu dan Allah dan annabi ina neman
alfarmanka ka bawa ɗana Abdul-Hakeem auren yarinyar nan, ta hakanne kawai
mahaifiyarsa zata samu sausauci shima ya samu me kwana tare dashi, na tabbatar
Abdul zaiyi farin ciki, duk da nasan kamar cutar da rayuwar yarinyar ne amma ku
taimaka ku taimaki yarona, ina ji ajikina aurenta da Abdul zai zamo mana alkhairi
dan Allah kuyi min wannan alfarman. "
Ya ƙarasa maganar yana haɗa hannayensa alamar roƙo, ga hawaye da suka cicciko
idanunsa.
Shiru malam Habu yayi yana wani tunani, haƙiƙa Raheenat yarinya ce me ilimi, tabbas
zata bada gudummuwarta sosai akan Abdul, saboda shi a iya hasashenshi ya gane ciwon
Abdul bana asibiti ba ne, sannan ɓangare ɗaya yarinyar tana cikin haɗari a cikin
gidansa, dan yasan ba lalene Sadiq ya ƙyaleta ba tunda sheɗan ya riga ya buga masa
ganga, yana matuƙar tsoron abinda zaije ya dawo, a halin da ake ciki yanzu aurenta
da Abdul wata hanyace ta tsiratar da mutuncinta daga farmakin ɗansa Sadiq, ajiyar
zuciya ya sauke ya kalli Alhaji Naseer yace "naji duk abinda kace Alhaji, sai dai
karka manta wannan yarinyar marainiya ce, taimakonsu nayi ita da mahaifiyarta,
saboda basu da kowa, koda ba zance haka ba dan dangin mahaifin yarinyar suna nan,
zumunci ne dai da yanzu ya zama sai addu'a, da zaran aka ce mutum ya faɗi ya mutu
to da wahala ka ga ƴan uwansa sun tallafi ƴaƴansa, sai dai abarsu su wulaƙanta, to
hakanne suma ya faru dasu Raheenat har Allah ya haɗani dasu na taimakesu na kawosu
gidana, bana da iko akan Raheenat, sai dai zan iya taimakawa wajen ganin burinka ya
cika."
"Kai, amma malam na gode sosai kuma naji dad'i, Allah ya taimakeka kaima kamar
yanda ka taimakeni, Allah ya sanya farin ciki a cikin rayuwarka kamar yanda ka
faranta mana, kuma Allah ya saka maka da mafificin alkairinsa."
"Ba komai Alhaji, ai yiwa kaine, yanzu zan samu mahaifiyar yarinyar da maganar, duk
yanda mukayi da ita insha Allah za kaji, inhar ta amince nasan zata sadamu da
dangin mahaifin yarinyar insha Allah."
"Na gode sosai malam Habu, ba zan tab'a mantawa da wannan taimakon ba a rayuwata
ba, sai naji daga gareka."
Mik'ewa malam Habu yayi tare da fad'in "gashi kuma har an fara kiran sallah
isha'i."
"Gaskiya ne, kasan lokacin wannan sallolin shi yafi zama tak'aitacce, inaga kawai
muje saimu mayar da sallah." cewar Alhaji Naseer
Tare suka koma fita suka tafi masallaci dan gabatar da sallah isha'i, ko da aka
idar da sallah suka fito sallama suka ƙarayi wa juna kowa ya nufi gidansa.
***********
Saida Malam Habu ya gama ci abinci sannan ya kalli Inna yace "Ramatou jeki ki kira
min Fateema a ɗakinsu. "
Wani kallo Inna tayi masa kafin tace "wacce Fateeman kake nufi malam. ?"
Cikin jin haushi tace "wai malam Maman Raheenat kake nufin inje in kira maka.?"
Malam Habu cikin ɓacin rai yace "Ramatou bana son jan magana, zaki je ne ki kira
min ita ko kuma naje da kaina."
Ganin ransa ya fara ɓaci ne yasa ta miƙe cikin itama nata ɓacin ran ta fice daga
ɗakin ba tare da ta ƙara magana ba, ita haushinta ɗaya aikenta da malam yayi ta
kira masa Maman Raheenat, yanzu har ita ce za'a aika kiran wancen banzar matar, ko
me malam zai faɗa mata ? Abinda Inna take faɗi kenan har ta isa ɗakin su Raheenat,
daga ƙofa ta tsaya ta hankaɗe labulan ɗakin ba tare da tayi sallama ba tace "uwar
manafunci kizo malam na kiranki, kullum dan salon munafunci kina ƙunshe a ɗaki sai
kace daddawa, ko kuma sabuwar amarya, duk munafincinki da karuwancinki wallahi
mijina yafi ƙarfinki ki, inma wani abu kike ƙullawa tun wuri ki kwanceshi, dan
kishi da Ramatou ba zai miki daɗi ba, banza kawai dangin mayu, marasa asali. "
Tana gama faɗin hakan ta saki labulan ta juya ta koma inda ta fito.
Kallon kallo akeyi tsakanin Mama da Raheenat dake zaune riƙe da al'qur'ani a hannu
tana karantawa, kalaman Inna matuƙa sunyi masu zafi, amma ya zasuyi tunda suna
zaune a gidansu ne, duk wani abu da zata faɗa musu yanzu dole suyi haƙuri su jure,
miƙewa Mama tayi jiki a sanyaye ta ɗauki hijjabinta ta saka ta nufi hanyar fita
ɗakin dan jin kiran da Malam Habu keyi mata tare da cewa Raheenat "bari naje nazo
ƴar albarka. "
Raheenat bata iya amsa wa Maman nata ba har ta fice daga ɗakin.
Sallama tayi a bakin ƙofar ɗakin Inna, malam Habu ne ya amsa tare da cewa "shigo
mana Fateema. "
Buɗa labulan tayi ta shiga tare da ƙara wani sallamar, guri ta samu can gefe ɗaya
ta zauna, yayin da Inna take ta aika mata da harara.
Saida ya matsar da kwanukan gabanshi qara tanqwashe qafafunsa yana kallon Mama
kafin yace "Fateema dama wata magana ce nake so muyi dake mai mahimmanci, shi yasa
nace kizo."
Cikin ladabi kanta qasa tace "to Allah yasa muji alkairi."
Gyara murya yayi yace "kafin na shigo gida makocinmu Alhaji Naseer ya tsayar dani
akan wata mata mai mahimmanci, maganar kuwa itace akan 'yarki Raheenat."
Sai lokacin ta kalleshi tace "toh, Raheenat kuma, Allah yasa ba wani abun ba tayi?"
D'an qaramin murmushi yayi yace "a'a Fateema, ba laifi tayi ba, ya sameni ne akan
yana so abawa Abdul Hakeem d'ansa auren Raheenat, amma na fad'a masa bana da iko
akan haka, kuma nace zan miki magana tunda kece mahaifiyarta."
Tunda yace aure tsakanin Raheenat da Abdul take kallonsa harya gama, da mamaki tace
"d'ansa dai dana sani marar lafiya?"
"Eh, shi."
Ajiyar zuciya ta sauke mai nauyi amma ba tace komai ba, kallonta ya sake yi a nutse
yace "Fateema, wannan fa ba dole bane, idan kinga zaki iya to , idan kinga da
tawaya a ciki ma ba za'a miki dole ba tunda 'yarki ce."
Tsal, Inna dake gefe ta karbe da cewa "yo wace tawaya ce a ciki? taimako fa zasuyi
su dubi halin da yaron yake ciki, na tabbata da lafiyarsa k'alau dako wannan
tunanin ba zata tsaya ba, kuma naga yarinyar da babu wanda yasan asalinta harma an
samu babban gida irin wanan suce suna so, amma har a tsaya wani jan aji."
Wani kallo Baba ya mata yace "dan Allah jiramu a waje, maganar fahimta muke."
"Nace ki fita ki jiramu." yanda yayi maganar yasa dole ta tashi ta fita tana
gunaguni.
Tana fita ya mayar da kallonsa ga Maman Raheenat yace "ina jinki maman Raheenat, me
kika yanke."
A cikin nutsuwa ta fara magana "kayi hak'uri Baban Sadik, ina kallonka kamar yaya,
zaka iya yanke hukunci a kaina ma bare kuma 'yar dana haifa, amma a gaskiya ina
ganin kamar akwai babbar matsala a auren Raheenat da Abdul, domin kuwa shi yana da
matsala ita kuma lafiyarta lau, hakan na nufin za'a tauyeta sosai, domin maganar
aure ake bawai wacce zata masa aiki ba, ana aurene da saran zama har abada, har
abada na nufin har qarshen rayuwa, Raheenat kuma duka yanzu ne ta shiga shekara ta
sha bakwai a duniya, idan aka had'ata da Abdul wanda ko magana baya iya yi, sai
naga kamar an cutar da ita, amma kayi hak'uri Baban Sadik idan abinda na fad'a bai
maka dad'i ba."
_Hmmmmmmm_
_Meeraheenat_😍
08/08/2019 à 12:23 - My Heenat: 🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾
💑💑💑💑💑💑💑💑💑💑💑
*ƘANGIN RAYUWA*
_(labarin Raheenat da Abdul-Hakeem)_
🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾
💑💑💑💑💑💑💑💑💑💑💑
*RAHEENAT M ABBAKAR*
AND
*SAMEERA HAROUNA*
DEDICATED TO ALAWIYYA❤
*🇸🇦ZAMAN AMANA WRITER'S*
*(Z.A.W)*
```(Gidan zaman lafiya da amana insha Allah)🤜🤛```
_Bismillahir_rahaman_rahim._
"Ba komai Fateema, kuma naji dad'in hangen nesanki wanda ni da mahaifin yaron duk
ba muyi ba, tabbas Raheenat zata cutu a zamansu, dan haka ki kwantar da hankalinki
kuma ki d'auka maganar nan kamar ba'a tab'a yinta ba, dama nazo miki da maganarne
da tunanin samun maslaha tsakanin Raheenat da Sadik, dan d'an yau ka haifeshi ne
baka haifi halinshi ba."
Cike da jin dad'i tace "na gode Baban Sadik, Allah ya shige mana gaba, kuma dan
Allah ina nemawa Sadik afuwa akan abinda ya faru, kasan yara sai hak'uri."
"Haba Fateema, wane irin yara? wanda yake wa mace wannan maganganun ne za'a kirashi
da yaro."
Shiru dai tayi hakan yasa yace "ba komai, zaki iya tafiya."
Inna ce k'ofar d'akin ta kasa kunne tana jin me suke fad'a, tana ganinta ta
harareta tare da tsaki, Mama dai wucewa tayi d'aki ta samu har yanzu Raheenat na
karatu, ganin Mama yasa ta rufe ALQUR'ANIN tana fad'in "Mama, lafiya dai ko, ba
wani abu bane ya faru?"
Ajiyar zuciya ta sauke tare da cire hijabinta ta aje akan katifa tace "lafiya lau
Raheenat, ba wani abu bane, magana kawai mukayi."
Tarbiyar da Raheenat ta samu ba zata barta ta tambayi akan me suka tattauna ba, a
hankali ta aje Alqur'anin hannunta ta cire hijabi ta kwanta akan katifar tare da
d'aukar littafin Husnul muslim ta fara karantawa, Mama ce ta kwanta gefenta itama
tana fad'in "Raheenat kenan, ba kya gajiya da karatu."
Murmushi tayi tace "Mama kenan, ai duk musulmi na qwarai ba zai gaji da karanta
abinda zai anfaneshi ba, wannan karatun nafi jin dad'inshi akan komai, yafi d'ebe
min kewa da sakani nishad'i."
Bacci ne ya d'auki Mama Raheenat kuma saida ta daina jin motsin bil'adama a
kunnenta kafin ta aje littafin tayi addu'ar kwanciya bacci ta shafe jikin Mama duk
da a gabanta tayi addu'a, sannan itama ta shafe jikinta ta kwanta.
▶▶▶▶▶▶
Kamar yanda Abdul yayi tunani hakane ta kasance, fitarta daga nan sallah kawai tayi
ko wanka ba tayi ba ta shiga gugar kayan Hajia Luba, saida ta gama ta shiga d'akin
*Nabeela* domin gyara mata d'akinta, kasancewar itace auta yan uwanta kuma suna
qasar waje suna karatu, cikin sauri ta kammala gyaran ta bar d'akin dan bata fatan
yarinyar tazo ta sameta ta fad'a mata magana marar dad'i, fitowarta kuma yayi
daidai da shigowar Alhaji sun dawo daga masallaci, da sauri Hajia Luba ta tashi ta
tarbeshi cikin shirin riga da siket da suka mugun kamata sosai, rumgume juna sukayi
kamar yanda ta sama mishi tana masa sannu da zuwa, wucewa tayi kicthen ta d'auko
abincinta dana Abdul sannan ta fito, kamar zata wuce sai taga ya kawar da kansa
daga barin kallon inda take, sunkuyawa tayi tace "Hajia na gama, ina so zanje
b'angarena."
A wulak'ance ta kalleta tana shafar jikin Alhajin tace "kije, kuma ki tabbatar
kinyi sammakon tashi gobe."
Tana fad'a ta tashi ta wuce ba tare data kalleshi ba ko tayi masa magana, tana
wucewa yaja tsaki dan jin muryarta yake kamar tana watsa mishi ruwan zafi a jiki,
ya tsani ganinta a rayuwa ba kuma yasan rayuwarta a cikin gidanshi, kawai tana
zaune ne saboda Hajia Luba ta buk'aci hakan.
B'angarenta ta nufa dake buk'atar gyara sosai ta wuce d'akinta tayi wanka sannan
tayi sallah isha'i, tsofaffin kayanta ta saka ko man da zata shafa bata dashi bare
turare haka ta nufi d'akin Abdul, kamar dai yanda ta barshi haka ta sameshi, da
qyar ta cuccub'ashi ta aza a kujerarshi ta nufi toilet dashi dan tasan zai buk'aci
hakan, ai kuwa kamar jira yake ya fara zunduma fitsari, saida ta zuba masa ruwa
sannan ta fito dashi, akan kujerar ta bashi abinci sannan ta mayar dashi ta
kwantar, zaune take tana shafar kanshi saita fara gyangyad'i, da ido ya kafeta yana
so yace taje ta kwanta amma ba hali, langab'owar da kanta yayi har tana neman fad'a
masa yasata zabura ta bud'a ido, kallonshi tayi tana murmushi amma ganin kallon da
yake mata yasa ta sake shafar kanshi tace "naje na kwanta kake nufi?"
A hankali ya lumshe idon alamar Eh, sumbatar kanshi tayi sannan ta mik'e taja masa
zanin rufa tace "saida safe d'ana."
Yana ganin ta kashe masa wutar d'akin ta fita ya maida idonshi ya rufe, kyakyawar
yarinyar data bashi ruwa ce ta fito a majigin qwaqwalwarshi, bud'a ido yayi ya
fad'a a zuciyarshi *wacece ita*?.
"Haba my Meerah, ina ruwanki to? ki bari zai sani da kansa mana." cewar my Heenat.
Turo baki nayi gaba nace "hum, nifa kinsan bana son jira, zaifi kawai ayita ta
qare.
_Zamu fara jin asalin labarin gidan Alhaji Naseer, kafin muci gaba_
Alhaji Naseer buzu haifaffen najeriya ne cikin garin kano, mahaifinshi Alhaji Musa
ɗan siyasa ne kuma ɗan kasuwa, ya tara dukiya me yawan gaske, yana da matar aure
ɗaya me suna hajiya Rabi, hajiya Rabi buzuwa ce ƴar ƙasar niger, harkan siyasarsa
ce ta kaishi can ya aurota, sun haifi yara uku tare, Alhaji Naseer shine babba, sai
ƙaninsa me bi masa me Suna Ahmed sai auta Hajara, sun taso cikin gata da tarbiyya,
iyayansu suna matuƙar ƙaunarsu, Alhaji Naseer yayi karatunsa tun daga primary har
zuwa jami'a duk a cikin garin kano, business ya karanta saboda shine burin
mahaifinsa, bayan kammala karatunsa mahaifinsa ya mallaka masa ɗaya daga cikin
kampanoninsa, nan shima ya kutsa cikin kasuwanci sosai kuma Allah ya albarkaci
kasuwancin nasa, ba'afi shekara biyu ba da kammala karatunsa Allah yayi wa
mahaifinsu rasuwa sakamakon jinya da yayi, sunyi kukan rashin mahaifinsu sosai,
amma babu yanda suka iya dole suka sakawa zuciyarsu haƙuri suka bisa da addu'a.
Bayan rabon gado ne Alhaji Naseer ya ƙara bunƙasa harkokin kasuwancinsa, sosai
Allah ya saka masa nasibi a ciki, ɗan uwansa Ahmed kuwa harkan siyasa ya faɗa
gadan-gadan, shima sai Allah ya dafa masa cikin harkokin nasa, ya zamana kula da
mahaifiyarsu da ƴar ƙanwarsu ya dawo hannunsu, bayan rasuwar mahaifin nasu da
watanni goma sukayi wa ƙanwarsu Hajara aure da wani me kuɗi, haka rayuwar ta ci
gaba da tafiya musu cikin nasarori, cikin haka ne Allah ya haɗashi da Lubabatu,
soyayya sosai sukayi da Luba wanda har ta kaisu ga aure, lokacin ne shima Ahmed ya
mallaki nasa iyalin.
Lubabatu ƴar wani hamshaƙi ne anan kano, mahaifiyarta Hajiya Kilishi macece me ji
da kanta tare da son abin duniya, sam bata son wani ya raɓi me gidanta harta da
danginsa, duk tabi ta kakkane komai daga ita sai ƴaƴanta, Hajiya Kilishi irin ƴan
ɗuniyar matan nan ne, bin bokaye gurin hajiya Kilishi ba'a magana, duk wani damuwa
nata to tayi amanna bokaye ne zasuyi mata maganinsa, ta mallake Alhaji Bashir sai
yanda tayi dashi, komai ta faɗi ya zaunu babu ja, ta zama itace me jan ragamar
gidan gaba ɗaya, Luba ta taso yarinya mara tarbiya, duk abinda takeso shi takeyi,
duk wani halayyar mahaifiyarta babu abinda ta bari, tun tana budurwarta take bin
bokaye dan samun biyan buƙatarta gurin samari, domin hakaɗin horan mahaifiyarta ce.
Shi yasa kafin shigowarta gidan Alhaji Naseer suka bi duk wani hanya da zai saka ta
mallakeshi a hannunta, kuma burinsu ya cika, domin ta samu yanda take so, zamane da
soyayya sukeyi tsakaninsu, komai take so Alhaji Naseer nayi mata shi, sam baya son
damuwar Lubabatunsa, shekararsu ɗaya da aure Hajiya Luba ta samu ciki, zo kaga
murna gurin Alhaji Naseer, ciki na shiga watan haihu ta haifi ƴarta mace, ba haka
Luba ta so ba, taso ta haifi namiji ne saboda ya zamo ta mallake gida gaba ɗaya,
haka dai ta saka wa zuciyarta haƙuri tare da fatan gaba ta samu ɗa namji, ranar
suna na zagayowa yarinya taci suna Rabi'atu sunan mahaifiyar Alhaji Naseer, suna
kiranta da Mimie.
Haka rayuwa ta ci gaba da tafiya musu sai dai hajiya Luba sam ta kasa samun abinda
takeso, saboda bayan haihuwar Rabi'a mata biyu ta sake haifa, Salma da Nabeela,
hakan beyi mata daɗi ba amma sai ta saka wa zuciyarta haƙuri ganinta ai ta riga da
ta gama mallakar gidan Alhaji Naseer, saboda sai abinda tace tana so ita ɗa ƴaƴanta
yakeyi, haka take zuba milkinta yanda yakeso a cikin gidan ba tare da damuwar komai
ba, kuma tun daga kan Nabeela haihuwa ya tsaya mata cak.
Ɓangaren Alhaji Naseer kuwa, son samun ɗa namiji ne ya mamaye zuciyarsa, kasancewar
kasuwancinsa na ƙara bunƙasa, domin zuwa yanzu ya mallaki kamfanoni zasu kai goma
bayan super market's da store's da ya mallaka masu yawa, hakan yasa yake son samun
magaji, wanda zai kama masa wasu harkokin nasa, kuma ko bayan ba ransa zai samu
magaji.
Maryam yarinya ce me tarbiya, ta haɗa komai, kyau, hankali, nutsuwa tare da nasaba,
iyayanta masu ƙaramin ƙarfi ne, saidai sunfi ƙarfin komai, maƙota suke da gidan
Alhaji Musa, wato gidan Hajiya Rabi mahaifiyar Alhaji Naseer.
Hajia Rabi ta gamsu da tarbiyar Maryam hakan yasa ta nemi aurenta a wajen
mahaifinta, magana ce tayi qarfi har maza suka shiga ciki, cikin ikon Allah kuma
komai ya tafi yanda ake so, Alhaji Naseer yakan fake da zuwa wajen mahaifiyarshi ne
sannan yaje wajen Maryam zance, a haka kuma soyayya saita shiga tsakaninsu, saboda
Maryam nada hankali sosai kuma tana da barkwanci, Alhaji Naseer kuma yana samun
farin ciki da annashuwa idan yana tare da ita, a haka har lokaci ya matso ya rage
saura kwana biyar, fargaba da tashin hankali Alhaji Naseer ya shiga a wannan
lokacin saboda baisan ta yanda zai fad'awa Hajia Luba maganar auren ba.
Yau ta kama ranar *juma'a* kwana biyu ya rage d'aurin aure, Alhaji Naseer ne ya
zaune a bakin gado yana kallon Hajia Luba dake tsefe kai a gaban madubi cikin
shirin kwanciya bacci, saida ta qarasa ta taso cikin kwarkwasa ta zauna akan
cinyarshi, duk da ta fara rikitashi da kalar salonta haka ya saita kanshi ya rik'e
hannunta ya fara magana murya na rawa, dan harga Allah yana jin shakkarta...
_Meeraheenat_😍
21/08/2019 à 06:21 - My Heenat: 🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾
💑💑💑💑💑💑💑💑💑💑💑
*ƘANGIN RAYUWA*
_(labarin Raheenat da Abdul-Hakeem)_
🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾
💑💑💑💑💑💑💑💑💑💑💑
*RAHEENAT M ABBAKAR*
AND
*SAMEERA HAROUNA*
DEDICATED TO ALAWIYYA❤
*🇸🇦ZAMAN AMANA WRITER'S*
*(Z.A.W)*
```(Gidan zaman lafiya da amana insha Allah)🤜🤛```
_Bismillahi_rahaman_rahim._
Gyara murya yayi yana jin bugun zuciyarshi na qara tsananta bugawa yace "dama ba
wata magana bace sai...um...sai.."
Sake matse hannunta yayi yace "kinsan yanzu a rayuwar nan duk maison ya gama da
duniya lafiya, to hak'ik'a sai yabi iyayenshi sannan zaiga daidai, kuma kinsan ace
bin na gaba bin Allah, to a gaskiyar magana akwai wani hukunci da Hajia ta yanke a
kaina wanda na kasa musa mata."
Tunda taji yace Hajia ta b'ata rai, dan tasan matar ba sonta take ba, a daqile tace
"ka fito kamin bayani yanda zan fahimta."
Saida ya dauke idonshi daga ganinta yace "dama akwai wata yarinyar mak'otanta ce
Maryam, to ta gamsu da nutsuwa da tarbiyarta, shine dai ta nema min aurenta, yanzu
haka maganar da nake miki jibi ne d'aurin auren insha Allah."
Ba tare daya kalleta ba yace "da gaske mana, ya zan miki maganar aure da wasa?
bayan nasan ba kya so."
Tabb',zunbur ta mik'e daga kan cinyarshi kamar mahaukaciya tace "jar uban can,
kishiya wai kake nufi, ni Hajia Luba ce kake tunanin had'awa da wata mace a doran
duniya? to bari kaji, ko a lahira wallahi ni kad'ai zan zauna da kai bare a duniyar
nan, gidan nan nawa ne ni kad'ai banga wacce ta isa ta shigo da sunan kishiyata ba
wallahi, babu wacce ta isa ta shigo gidan nan harta had'a kafad'a dani wajen
tarayya da kai, wallahi gidan nan nawa ne daga ni sai 'ya'yana, ina nan kuma zanga
'yar iskar fitsararra marar kunyar da zata shigo min gida, wallahi saina halakata
ko 'yar gidan uban wacece, kai ka sani kuma kasan wacece ni, nafi k'arfin wannan
tozarcin da kake neman yimin, ko gidanmu mahaifiyata kad'ai na gani tana rayuwarta,
saini zanzo na had'a gida da wata banza wai a matsayin kishiyata, to mu zuba mu
gani d'an halak ka fasa, zanga wacce ta isa ta shigo gidan harta wanke qafa tasa
kayan bacci taje turakarka da sunan ta kai maka kwananta, wallahi zan maimaita
maka, sai nayi ajalin kowace 'yar iska ce, aikin banza kawai."
A sanyaye ya mike tsaye shima yace " haba mamar Nabeela, ya kamata ki gane shifa
aure nufin Allah, idan har Allah ya nufeka da qarawa to ba makawa sai kayi, kuma
k...."
"Aiba wani abinda zaka fad'a min, kuma kamar yanda na fad'a maka, ina nan ina zaman
jira naga shed'aniyar da zata shigo min gida, wallahi zanyi maganinku daga kai har
ita Hajiar data kitsa maka maganar k'ara auren cikin qwaqwalwa."
Tana fad'a ta fita ta bar d'akin ta koma b'angarenta kamar za tayi hauka, shi kuma
hanakalinshi ne ya tashi ganin ran Hajia Luba ya 'bace kuma ta sanadiyarshi,
b'angarenta yaje ya fara buga k'ofa amma ko jinshi ba tayi saboda tana can bedroom
d'inta, haka ya gaji ya koma nashi ya kasa zaune ya kasa tsaye, haka dai gari ya
waye ba tare da dukansu sun rintsa ba, yana dawowa daga sallah asuba ma part d'inta
ya koma yaci gaba da bugawa, a lokacin kuma tana shiryawa dan tafiya wajen wanda
take ganin zai mata maganin matsalarta, shiru tayi bata kulashi ba saida taji ya
daina bugawa sannan ta d'auko makullin mota da jakarta tare da waya ta fito, saida
ta farawa mai gadi magana akan ya bud'e mata gate a hankali dan bata so Alhaji yaji
fitarta sannan ta shiga mota, cikin sauri ta fita daga gidan cikin wannan duhun
asuba ta kama hanyar wani qaramin qauye dake kusa dasu.
Zaune take a gaban mutumin kai da gani ba sai an fad'a ba kasan mushriki ne ajin
farko saboda shigar dake jikinshi, cikin fitar hayyaci da b'acin rai Hajia Luba
tace "boka *bandaru*, wannan ma ai maganar banza ce, ya za kace wannan aikin yafi
qarfinka, yaune muka fara aiki dakai? naga kayi aikin da yafi wannan ma wahala, to
me yasa ba zaka hanashi qara auren nan ba? akwai matsala babba inhar yayi auren
nan, dan ina tunanin saboda tsayawar da haihuwa tamin ne yasa mahaifiyarshi tasa ya
qara auren nan, kuma kaga akwai yiwuwar matar da zai aura tazo ta haifa masa d'a
namiji, haka kuma ta faru wallahi zan iya kashe Alhaji ma baki d'aya, dan ba zan
yarda ina ji ina gani ba wata tazo ta qwace gidan nan, alhalin ina tare dashi
arzik'inshi ya qara bunk'asa."
A tsawace bokan yace "ke Luba!, ba'a daga mana murya anan, kuma kamar yanda na
fad'a miki, wannan auren da mijinki tabbatancen aure ne kuma rubutacce, ba zamu iya
ruguzashi ba saboda dole saiya faru, dan haka ki tashi ki koma gidanki ki jira
amaryarki, idan kina buk'atar wani abu bayan auren kin dawo, duk da dai yarinyar
akwai addini, amma ba za'a rasa yanda za ayi ba."
Jin abinda Boka yace ne yasa hajiya Luba cewa "Allah ya wuce zuciyar boka Bandaru,
dole ne ma in dawo ai, domin wallahi bazan taɓa barinsu suyi farin ciki ba. "
Wata irin dariya boka yayi yace "shegiya Luba, ai nasan halinki bakya da imani,
tashi kije sai kin sake dawowa."
Miƙewa tayi jiki a sanyaye ta fice daga cikin ƴar bukkar nashi tana jera masa
kikarari har ta fita.
Koda hajiya Luba ta koma gida ɓangarenta ta shiga ta fara zirga-zirga hankalinta a
matuƙar tashe, "yanzu dole sai anyi auren nan, ta yaya ni Luba zan zauna da kishiya
? Ina! ba zai yiwu ba. "
Ta faɗa da ƙarfi tare da buga hannunta jikin ba bangon ɗakin.
Alhaji Naseer kuwa jin hajiya Luba taƙi buɗe ƙofar hankalinshi ba ƙaramin tashi
yayi ba, dan ya tsani ɓacin ran Hajiya Luba ko ƙanƙani, komawa part ɗinsa yayi ya
zauna ya rasa me zaiyi, da zai iya da ya fasa auren nan dan farin cikin hajiya
Luba, sai dai baya jin zai iya fasa auren nan, yana jin son Maryam sosai a ranshi,
ta yanda yake ji inda yabarta zai shiga cikin wani hali, daɗin daɗawa yana matuƙar
son samun ɗa namiji, duk da baya da tabbacin samun ɗa namijin in anyi auren.
Miƙewa yayi ya ƙara fitowa zuwa part ɗin nata ko zaiyi sa'a ta buɗe, cikin sa'a
yana tura ƙofar part ɗin nata yajita a buɗe.
Cikin sanɗa ya shiga kamar mara gaskiyya, kai tsaye ɗakinta ya nufa, a hankali ya
turo ƙofar ɗakin ya shiga da sallama, a tsaye ya sameta tana takai da kawo har
yanzu, kamar me safa da marwa, suna haɗa ido dashi tace "Naseer ka fita min daga
ɗaki bana son ganinka, wallahi na tsaneka maci amana kawai. "
Rintse ido Alhaji Naseer yayi ya taka a hankali kusa da ita ya rungumota jikinsa,
fisge-fisge takeyi tana son ƙwace kanta daga jikinsa shi kuma yaƙi bata damar
hakan, cikin kunninta yake taɗa maya "ki nutsu hajiyata, dan Allah ki tsaya ki
saurareni nayi miki bayani, kamar yanda nace miki ne ba laifina bane, hajiyace
kawai ta neman min auren, kuma sanin kanki me ba na iya musu da hajiyarmu, amma ke
kanki kin sani ke kaɗai ce macen da nakeso kuma nake burin zama da ita, sanin kanki
ne kece farin cikina, bana son ɓacin ranki ko kaɗan, to ta yaya kike tsammanin zan
nemi auren wata macen alhali kina tare dani, ki yarda dani Luba ba a san raina
za'ayi auren nan ba. "
Waɗannan kalaman na Alhaji Naseer ne ya dakatar da hajiya Luba daga ƙoƙarin raba
jikinsa da nata, haƙiƙa tasan ko wani kalmar nasa ba gaskiya bane wani gaskiya ne,
amma yanda take jin zuciyarta ba ta jin zata iya haƙurin ganin mijinta da wata
mace, yanzu mafitarta ɗaya ce kawai ta kwantar da kanta ga Alhaji ta nuna masa
komai ya wuce, daga baya tazo ta ɗauki matakin da ya dace akan tsinanniyar yarinyar
da zata shigo mata gida, ba ita kaɗai ba har hajiyar sai ta ɗauki mataki akanta dan
taga matar na neman shiga rayuwarta sosai.
A hankali ta raba jikinsa da nata cikin taushin murya tace "ok Alhajina, na yarda
da abinda ka fad'a kuma na gamsu, fatana yanzu kawai Allah ya bamu zaman lafiya,
kai kuma Allah ya baka ikon yi mana adalci."
Wata nauyayyar ajiyar zuciya ya sauke yace "my Hajiata, i really proud of you, that
why i like you."
Daga ranar Hajia Luba ta fara nuna masa kamar ba komai, har aka daura auren Alhaji
Naseer da Maryam......
_Meeraheenat_😍
*ƘANGIN RAYUWA*
_(labarin Raheenat da Abdul-Hakeem)_
🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾
💑💑💑💑💑💑💑💑💑💑💑
*MUNA BAKU HAƘURI MASOYAN WANNAN LITTAFI DA RASHIN POSTING AKAI AKAI DA BA BAYI
YANZU, HAKAN NA FARUWA NE SAKAMAKON WASU UZIRI DA SUKA SHA MANA KAI MU DUKA, KU
ƘARA HAƘURI INSHA ALLAHU KOMAI ZAI DAIDAITA NAN BADA DAƊEWA BA, MEERAHEENAT SUNA YI
MUKU FATAN ALKHAIRI.*
DEDICATED TO ALAWIYYA❤
Daran da aka kawo amarya ƙiri-ƙiri hajiya Luba ta hana Alhaji Naseer shiga ɓangaren
amarya ta tilasta masa kwana anata ɓangaren, amarya kuwa tana can tana jiran ango
babu ango babu labarinsa, haka ta gaji da jira har bacci ya kwasheta, haka aka ɗibi
kwanaki huɗu da ɗaura auren nan amma hajiya Luba sam taƙi bada wani ƙofa da Alhaji
Naseer zai keɓe da amaryarsa, gaba ɗaya tabi ta kankane komai, Maryam amarya ta
shiga damuwa matuƙa ganin an kawota gidan mijinta amma ganin mijin yayi mata
wahala, shi kanshi Alhaji Naseer cikin damuwar yake, yana matuƙar so ya keɓe da
amaryarsa amma sarautar matar ta hanasa.
Yau ma zaune suke a falonshi hajiya Luba duk tabi ta kanenayeshi, kusan rabin
jikinta yana jikinshi sai faman zuba masa shagwaɓa takeyi kamar wata karamar
yarinya, shafo fuskarshi tayi cikin kissa tace "Alhajina ina so kayi min wani
alƙawari ne dan Allah. "
Kallonta yayi cikin sakin fuska yace "ina jinki hajiyata, faɗi ko wani irin
alƙawari ne ni me yi miki shine. "
Ƙara lanƙwashe murya tayi cikin salon makirci tace "alƙawari nakeso kayi min ba
zaka taɓa kusantar amaryarka ba, kaga kai kanka ba sonta kakeyi ba dole akayi maka
ka aureta, ni kuma sam ba nason sharing ɗinka da wata macen, wallahi Alhaji zan iya
mutuwa duk randa ka kusanci wata mace bani ba, dan Allah kayi min wannan alƙawarin
ba zaka taɓa kusantarta ba Alhajina."
Ta ƙarasa maganar cikin salon makirci da kitihi tana wani shafa jikinsa tare da
kashe masa idanuwa.
Salon da takeyiwa Alhaji Naseer gaba ɗaya ta rikitashi ya fara fita a haiyacinsa,
cikin wani irin amon murya wanda kana jinsa kasan yana cikin matukar sha'awa yace
"amma hajiyata bakya ganin hakan zai zamo cutarwa ga ita yarinyar, amanace ita ɗin
aka bani fa, ina naci amanarta Allah fa ba zai barni ba. "
Ɗan haɗe rai hajiya Luba tayi tace "me kake nufi Alhaji, kar dai kace min ka fara
son yarinyar ne.?"
Cikin in ina yace "a'a hajiyata ba haka nake nufi ba, amma kin...."
Katseshi tayi kafin ya ƙarasa tace "amma me Alhaji, nufinka dai yanzu ba zaka iya
min alƙawarin ba kenan ?, hmmmm, ai sai yanzu na ganoka Alhaji, wato dai kana son
yarinyar kuma kana son kusantanta, hakan ne yasa ba zaka iya yimin alƙwari ba ko.?"
Tayi maganar tana tsaresa da idanunta.
Janyota yayi jikinsa ya rungume cikin sanyin murya yace "ba haka nake nufi ba
hajiyata, sanin kanki ne ke kaɗai kin isheni ba sai na haɗaki da wata ba, abinda
ina so ne ki gane shine Maryam amana ce aka bani, be kamata ace na watsar da amanar
ba tun kafin akai ko'ina, dan Allah zai iya kamani da laifin cutar da ita."
Shafa ƙirjinsa ta fara cikin wani irin salo, gaba ɗaya riga ta rikita Alhajin cikin
raɗa raɗa tace "indai da gaske baka sonta wannan hanya shine kawai mafita Alhajina,
kaga ita kanta in taga baka kulata ba zata zauna ba, da kanta zata nemi takardanta,
kaga shikenan sai ka sallameta mu ci gaba da zamanmu mu kaɗai kamar yanda muke ada.
"
Cikin fitar haiyaci Alhaji Naseer yace "shikenan Hajiyata, duk yanda kika ce haka
za'ayi."
Cike dajin daɗi hajiya Luba ta ci gaba dayiwa Alhaji wani irin salo tare da raɗa
masa a kunni cewa "shi yasa nake sonka Alhajina. "
Daga nan kuma komai ya kwance musu suka lula wata duniyar.
Haka rayuwa ta ci gaba da tafiya musu har aka samu tsawon sati uku da kawo Maryam
gidan amma hajiya Luba ta hana Alhaji Naseer shiga ɓangarenta ya dubata ma balle
ayi wani maganar haƙƙinta na aure, zuwa lokacin kuwa hankalim Alhaji Naseer in yayi
dubu to ya tashi, ya rasa hanyar da zaibi ya ga amaryarsa, idon hajiya Luba na
kansa gaba ɗaya, ga wani sabon tsoranta da gudun ɓacin ranta da ya keji yanzu ,
ɓangaren Maryam ko tayi kuka har ta gaji, ta rasa wani irin jarabawa ce wannan, da
farko dai ta shiga cikin damuwa tare da tunanin me Alhaji Naseer yake nufi da ita,
dama ba sonta yakeyi bane ya aureta, ko dama ya aureta ne dan ya wulaƙantata ? Amma
sai zarginsa da ƙudirin da tayi akansa duk randa yazo gareta ya kau a lokacin da ta
samu baƙuncin hajiya Luba cikin falonta, ranar tana zauna ta rafka tagumi tana
hawaye tare da tunanin halin da take ciki hajiya Luba ta shigo, bayan ta gama ƙare
mata kallo ita da falon nata a wulaƙance ta fara mata gargaɗi akan mijinsu, tare da
yi mata ikirari da cewa Alhaji nata ne ita kaɗai, babu wacce ta isa ta shigo
tsakaninsu, sannan ta ƙara da ce mata ita take da iko dashi, sai abinda tace yayi
yakeyi, dan haka ta saka a ranta tazo mata bautane kawai nan da ɗan lokaci ƙanƙani,
amma ba zaman aure ba, domin Alhaji baya da wata mata bayan ita kaɗai, nan dai ta
gama yi mata tijara kafin ta fice tabar Maryam na rusar kuka, tun daga wannan rana
Maryam ta dage gurin miƙawa Allah kukanta, Allah maji roƙon bayinsa, cikin satin
wani biki ya tasowa Hajiya Luba na ƴar aminiyarta dake Kaduna, nan ta fara shirin
tafiya, ranar da zata tafi haka ta dinga yiwa Alhaji gargaɗi kan kar yaje ga
Maryam, shidai da to yake amsa mata har sukayi sallama direba ya jata suka kama
hanyar Kaduna, ai Alhaji Naseer kamar jira yakeyi da saurinsa ya juya ya nufi
ɓangaren Maryamu.
Kwance ya sameta saman kujera three seater hannunta riƙe da carbi tana ja yayin da
idanunta suke a lumshe, wani irin tausayinta ne yaji ta taso masa tun daga ƙasan
ransa, da ɗan sassarfa ya ƙarasa kusa da ita.
Saida taji tsoro saboda jin an tab'ata, a zabure ta tashi har d'an kwalinta ya zame
ya fad'i, ido tsaye take kalleshi ba ko k'yabtawa, qasa yayi da nashi idon yana
tunanin abinda zaice mata, da qyar ya fara da "Maryam kina lafiya?"
Wasu ƙwalla ne taji sun zubo mata, dakewa tayi tace "abinda kazo tambaya kenan.?"
Da sauri ya kama hannunta yana matsawa alamar rarrashi yana fad'in "Maryam, dan
Allah kiyi hak'uri ki gafarceni, nasan ni mai laifine a gareki, amma dan Allah ki
taimaka ki yafe min, wallahi nima ba'a son raina bane, kullum ina tunaninki kuma da
tunaninki nake wuni, amma na kasa samun damar da zan iya zuwa inda kike, Maryam ki
gafarta min dan girman Allah, wallahi idan baki yafe min ba zan shiga tashin
hankali, kuma kema kinsan haka a matsayinki na mai ilimi."
Kallonta yake yana jiran yaji me za tace, ita kam tayi qasa da idonta kuka ne ya
qwace mata, hankalinshi ne tashi dan haka ya matso kusa da ita ya rumgumota
jikinshi ya fara rarrashi, da qyar ya samu ta tsagaita da kukan kafin yace "yanzu
fad'a min me kike so?"
Cikin shashek'ar kuka tace "yanzu dai yunwa nake ji, kasa mamin abinci naci."
Cike da kunya ya d'an cije lips d'inshi yana satar kallonta, ace matarshi tana zama
da yunwa saboda rashin abinci, duk da yana da dukiyar da zai iya ciyar da milyoyin
mutane, murya qasa qasa yace "dama wai baki cin komai?"
Cikin muryar kuka tace "akwai cincin da mahaifiyata tasa aka kawo min shine nake
ci, kuma ina ina da yan kud'i a jikina ina siyan wani abu, amma tun jiya komai nawa
ya qare har yanzu banci komai ba."
Wani irin tausayinta ne ya sake ji, rumgumeta yayi sosai a jikinshi baisan lokacin
da qwalla ta matso mishi ba a ido, sakinta yayi yana goge qwallan yana fad'in "bara
na samo miki abinda zaki ci, kiyi hak'uri kinji Maryam d'ina."
B'angaren Hajia Luba ya nufa, cikin qanqanin lokaci sai gashi da kayan ciye ciye,
nan ya zube mata gabanta ta fara ci, saida ta qoshi tayi hamdala kafin ta tashi ta
d'auke kwanukan, duk lokacin idon Alhaji Naseer na kanta, a lokacin kuma yaji wata
yana buk'atar matarshi a kusa dashi.
A wunin ranar dai tare sukayi shi yana riritata kamar qwai , gashi dama masu aiki
basu zo ba kuma Hajia Luba ta tafi da yaran duka , sallah kawai ke fitar dashi kuma
kuma da yayi zai dawo haka har isha'i ta samesu, koda yayi sallah isha'i da kanshi
yaje ya siyo kaza guda biyu😋 da lemunmuka masu sanyi sannan ya dawo, saida sukayi
sallah ya mata tambayoyi akan addininta ,duk da Maryam ta nuna tsoro da fargaba,
amma cikin dubara da siyasa Alhaji Naseer ya mayar da ita babbar mace, wannan dare
kuma ya shiga cikin tarihin rayuwarsu , dare ne da Alhaji Naseer ba zai tab'a
mantawa dashi ba.
A kwana ukun da Hajia Luba tayi bata nan, sosai Alhaji ya gurji amarcinshi da
Maryam, amma ranar da Hajia Luba ta diro daga ranar kuma komai ya lalace ya koma
kamar farko, al'amura basu sake watsewa ba saida Maryam ta fara laulayi, Hajia Luba
ta sani ne ta hanyar 'yar aikinta lokacin da taga Maryam nacin d'ata, saida ta mata
kallon qwqwaf sannan taje ta fad'awa Luba, nanfa hankali ya tashi a take ta nufi
wajen boka danya tabbatar mata, ya kuma tabbatar mata anan ta nemi a lalatashi,
amma saiya fad'a mata tana cikin kariyar ubangiji ba zai iya musu komai ba, amma ya
bata shawara ta jira harta haihu sai a kashe d'an, da wannan ne yasa ta kwantar da
hankalinta harta haihu, a lokacin da Alhaji yaji tana da ciki yayi farin ciki, amma
bai bari Hajia Luba taji ba, dan a tunaninshi bata sani ba kuma baya so ta sani, da
taimakon mahaifiyarshi Maryam ta dinga rainon cikin Abdul Hakeem.
Lokacin mahaifiyar Hajia Luba ta dawo daga qasar waje wajen harkokinta, nanfa tace
ai Luba tayi wasa sosai, data fad'a mata yanda boka yace sai tace sam bata yarda
ba, nanta d'auketa suka je wanjen wani bokan, duk da basuyi nasarar fitar da cikin
ba, amma sunyi nasarar saka Maryam shan wahala, har saida ta fita daga hayyacinta
ta rasa gane wacece ita, kuma sunyi sihirin da har abada ba zata sake haihuwa ba,
yan uwa da iyaye aka dage wajen addu'a har lokacin haihuwarta yayi, saida Maryam
tayi kwana goma sha biyu tana nak'udar Abdul Hakeem, gashi dai haihuwa kusa kuma
zata iya haihuwa da kanta, amma sam ta kasa haihuwar sai azaba da wahala da take
sha, da qyar take samun baccin minti biyar zuwa goma, da qyar da taimakon Allah da
taimakon addu'a aka samu ta haifi Abdul Hakeem, haihuwar d'a namiji shine silar
faruwar lalacewar komai, Alhaji Naseer dai yayi farin ciki kamar zai kasheshi haka
ma mahaifiyarshi, amma a b'angaren Hajia Luba da mahaifiyarta kamar bak'in ciki ne
zai kashesu.
Anyi hidima, kuma irin hidimar da Alhaji yayi yasa Hajia Luba ta qara tunzura ,
mataki na qarshe suka d'auka akan wannan al'amarin, dan kuwa kafin Maryam tayi
arba'in mahaifiyar Alhaji Naseer Allah ya mata rasuwa itama, Maryam tafi kowa jin
mutuwar, domin kuwa itace ke taimaka mata akan komai, abubuwa sun qara had'e mata
ta yanda ko abinda zata ci wani lokaci yakan bata wahala, dan saita d'auki wata
d'aya ba taga Alhaji Naseer da idonta ba, musamman idan baya gari ma saita d'auki
wata kusan biyu, ga tsangwamar yaran Luba da suka rainata kamar ba matar mahaifinsu
ba.
Duk da baya kula Maryam amma baya hana ya aiko ya amsar mishi Abdul Hakeem, yana
matuk'ar son yaran, da wannan kad'ai take jin dad'i saboda soyayyar da yakewa
yaron, amma duk da haka ba'a barsu ba, bayan *shekara goma sha biyar*, abubuwa sun
faru marasa dad'i kuma su sukafi yawa a b'angaren Maryam, yana daga cikin rashin
kulawar da yake nuna ma Maryam rashin zuwanta qasa mai tsarki, hakan kuma ya tab'a
qaninshi Ahmad sosai, ba tare da shawarar Alhaji Naseer ba yabiya mata kujerar
makka, amma hakan baiwa Alhaji Naseer dad'i ba musamman da Hajia Luba ta qara
zugashi, sosai sukayi fad'a da d'an uwanshi har yace ya fita harkar iyalinshi, duk
da bai fita harkar iyalin nashi ba amma dai ya rage zuwa inda suke, saidai Maryam
ta samu nasarar tafiya ɗakin Allah ta sauke farali, daga lokacin ta tashi daga
Maryam zuwa Hajiya Maryam.
Abdul Hakeem an girma, kuma Allah ya bawa yaron qwaqwalwa sosai, yakan hardace
komai cikin sauk'i, kuma a lokacin sai mahaifinshi ya fara janshi a jiki sosai
wajen harkokinshi, daya taso daga school ko islamiyya Alhaji Naseer zaice ya
sameshi office, harta kai ta kawo Alhaji Naseer idan zaiyi tafiya saiya tafi da
Abdul Hakeem, hakan ba qaramin tab'a Luba yake ba, Abdul Hakeem yana kallon irin
rashin adalcin da mahaifinshi ke nunawa tsakanin mahaifiyarshi da mahaifiyarsu
Mimie, haka baya masa dad'i amma babu yanda ya iya, sai dai ya tsani Hajia Luba
sosai, baya ko qaunar ganinta dan yana ji a jikinshi ba mutuniyar kirki bace, hakan
yasa ko gaisheta zaiyi sai dai ya gaisheta kamar mai ciwon baki, kuma da abinda
yake samu ne wajen mahaifinshi yake yiwa mahaifiarshi abubuwan buk'atar rayuwa,
ranar da hajiya Luba ta kusa mutuwa saboda bak'in ciki itace ranar da Abdul Hakeem
ya kawo result d'inshi kuma yayi kyau, a lokacin Alhaji Naseer ya fara mishi
tanadin shiga jami'a tare da kyautar tartsetsen gida da kuma mota da zai fara
tafiya da ita school, koda ta fad'awa mahaifiyarta nan suka shirya domin zuwa
d'aukar mataki.
A wannan karon sunyi nasara sosai, anyi nasarar nakasa Abdul Hakeem ta yanda aka
hanashi koda ta motsa yatsarshi, yayin da aka suka rufe bakunan mutane daga yi musu
addu'a, tayi nasarar mayar da Maryam yar aikinta, kuma an sakawa Alhaji Naseer
tsanarta fiye da komai, a lokacin kawai lafiya yake nemawa Abdul Hakeem gari gari
qasa qasa, amma shiru babu labari daga hakan komai ya tab'arb'are, bawai dangi na
nesa ba ko Hajia Maryam da Alhaji Naseer babu wanda ya tab'a cewa Allah ya bashi
lafiya, bare kuma dangi na nesa dana kusa, d'aid'aikun mutane kad'ai ke iya mishi
addu'a wanda ansan ba kullum zasu mishi ba, kuma a lokacin sai Hajia Luba ta fara
sakin baki a gaban Abdul Hakeem, dan akwai wata rana ta shiga d'akin tare da Alhaji
da nufin ganinshi, kwance yake kamar yanda yake tunda larurar ta sameshi, Alhaji ne
ya fara fita bayan mishi magana kafin ta matso tana kallonshi tana dariya tace,
"Yaron babanshi kenan ana kwance, toya kake ji a halin yanzu? humm, kayi hak'uri
duk da dai nasan ba laifinka bane, amma mahaifiyarka taja maka, domin kuwa ta had'a
hanya dani har takai ga kaiwa wajen dani kad'ai keda ikon kaiwa can, kasan inane
wannan wajen?" ta tambaya cike da iskanci.
Murmushi tayi ba tare da kunya ba tace "ina nufin ta bari mahaifinka yayi anfani da
kanshi a wajenta kamar yanda yake yi a wajena, alhalin nayi alk'awari ni kad'ai zan
zama tashi, wannan shiya janyo maka kwanciya anan kamar gawa, kuma za kaci gaba da
zama a haka har lokacin da mala'ikan d'aukan rai zai sameka, idan kaje lahira kuma
ka had'u da yan matan aljanna, toka fad'a musu Alhaji Naseer mijin Hajia Luba, nata
ne ita kad'ai ba zata iya sharing d'inshi da wata ba, ka gane.?"
Daga haka Abdul Hakeem ya fara rayuwar k'unci da takaici, fatan Allah ya baka
lafiya Abdul😭....
Malam Muhammadu da Rasheeda ƴan asalin garin agadaz ne dake ƙasar niger, talauci da
rashin qwqwaran abinyi ne ya fito dasu daga garinsu zuwa Maradi, inda Muhammadu ya
samu aiki a gidan wani Alhaji yana masa aikin gadi, da kanshi ya basu wani fili a
cikin filayen da yake dasu a cikin unguwar *Ali d'an sofo*, da qyar malam Muhammadu
ya samu ya tayar musu da bukka a tsakiyar filin, a lokacin Fateema nada shekara
biyu ne a duniya, a haka suka fara rayuwarsu a wannan yar bukka , kasancewar
Alhaji mutum ne ba mai zama ba yasa suke shan wahala ko wajen samun abinda zasu ci.
*Shekararsu d'aya* a garin Maradi suna paputuka, ta yanda har Rasheeda saida ta
fara shiga gidajen masu kud'i, wani wurin ta kanyi dace a bata wankin kaya wani
wurin kuma sai dai a bata hak'uri ta dawo, wani mak'ocinsu mai sunan *Salisu* ne ya
bawa Muhammadu shawarar ko zai fara fita *Nigeria* domin samun abinda zai rufawa
kai asiri, da wannan shawarar sukayi anfani ya shirya tsaf kuma ya tafi, cikin ikon
ubangiji sai sana'ar lebarenci ta karb'eshi, *wata biyu* yayi acan ya dawo, ya samu
iyalenshi sun jikkata sosai saboda rashin abinci da kayan masarufi, a lokacin kuma
Alhaji ya dawo daga wata tafiya saiya sallameshi tunda yaga ba niyyar zamane dashi
ba a waje d'aya, hakan yaba Muhammadu damar sake komawa garin *Kano* domin nema....
*Muje zuwa tare da*
_Meeraheenat_😍
21/08/2019 à 06:21 - My Heenat: 🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾
💑💑💑💑💑💑💑💑💑💑💑
*ƘANGIN RAYUWA*
_(labarin Raheenat da Abdul-Hakeem)_
🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾
💑💑💑💑💑💑💑💑💑💑💑
*RAHEENAT M ABBAKAR*
AND
*SAMEERA HAROUNA*
DEDICATED TO ALAWIYYA❤
Domin neman halalinsa, be bar ƙasar niger ba sai tare da matarsa da ƴarsu guda ɗaya
wato Fateema, koda suka iso garin Kano sunsha wahala matuƙa kafin ya samar musu
gidan hayan da zasu zauna shi da iyalinsa, gida ne irin ginin ƙasar nan me ɗauke da
d'akuna kusan goma cikinsa, haka dai suke rayuwa cikin gidan yana fita yana
leburancinsa domin samarwa kansu abinda za suci, haka rayuwa take tafiya musu cikin
rufin asiri domin kam babu laifi yana samu, rayuwa ba fara yi musu zafi ba sai
lokacin da ƴarsu Fateema ta shekara biyar a duniya, a lokacin ne komai ya kwaɓe wa
malam Muhammadu, ko ya fita da ƙyar yake iya samo abinda zasu ci, wata rana ma
yanda ya fita haka zai dawo, suna cikin wannan hali na ƙangi da talauci ne Allah ya
haɗashi da wani Alhaji, Alhaji Isma'il mutum ne me son mutane da tausayawa na ƙasa
dashi, ranar Malam Muhammadu ya fita neman abinda za suci shi da iyalansa ne, domin
tun ranar jiya rabonsu da abinci, ga ɗiyarsu Fateema sai kukan yunwa takeyi, kuma
cikin gidan nasu babu wanda yaga Allah ya jefesu da ko lomar abinci ne, a cewarsu
kowa ta kansa yakeyi, yayi yawon amma be samu komai ba, ga rana ta take hakan ne ya
tilas ta masa samun guri a jikin wani katon gida ya zauna yana hutawa, yana zaune
ya shiga duniyar tunani be san sanda hawaye yake zuba masa ba, tausaya wa kansu
yakeyi da *Halin rayuwar* da suka tsinci kansu a ciki, ko'ina babu sauƙi, be san da
zuwan mutum ba saboda yayi zurfi cikin tunani kawai sai jin magana yayi, da sauri
ya ɗago da kansa yana kallon Alhajin dake tsaye.
Cikin taushin murya Alhaji Isma'il yace "bawan Allah kai ko me yayi zafi haka da
zaka zo cikin rana ka zauna kana hawaye, komai yayi zafi maganinsa Allah ne. "
Wasu hawayen ne suka tawowa Malam Muhammadu, cikin muryar kuka yace "ba zaka gane
bane Alhaji tunda kai Allah yayi maka ni'ima, tun jiya kamar iwar haka rabonmu da
abinci ni da iyali, nayi biɗar nayi biɗar ban samu ba, har kwasan bola na nemi a
bani abin ya gagara, dako nan ma cikin kasuwa na gaza samunshi, yanzu haka ƴarmu
ƴar shekara biyar na can tana kuka babu abinda zata ci, to ka faɗa min in banyi
kuka ba me ka keso nayi. "
Ya ƙarasa maganar wasu hawayen na zubo masa, cikin matuƙar tausayawa Alhaji Isma'il
ya duƙa gabansa yace "kayi haƙuri kabar kuka dan Allah, zaka iya gadi.?"
Washe baki malam Muhammadu yayi cikin farin ciki yace "me zai hanani ni kuwa,
wallahi zan iya. "
Murmushi Alhaji Isma'il yayi yace "masha Allah, dama ina neman me gadi saboda me
gadina yayi tafiya, yanzu bari na shiga gida na kawo maka abincin da zakaje kuci da
iyalanka kafin gobe sai kazo ka fara gudanar da aiki. "
Cikin tsananin farin ciki malam Muhammadu ya dinga zubawa Alhaji Isma'il godiya,
miƙewa Alhaji yayi ya shige wannan gidan, be daɗe ba sai gashi ya fito da ƙaton
kula a hannunsa, meƙawa Malam Muhammadu yayi yace "gashi ko, haka kawai naji na
yarda dakai, shi yasa ma har nayi maka tayin gadin gidana, ina fatan zaka zama me
amana. "
"Insha Allahu Alhaji zaka sameni fiye da tsammaninka, nagode, nagode, Allah ya
jiƙan mahaifa. "
Nan dai Malam Muhammadu ya dinga zuba ma Alhaji Isma'il godiya kafin ya miƙe ya
nufi hanyar gida zuciyarsa cike da farin ciki.
Koda ya koma yake faɗawa Rashida yanda sukayi da Alhaji tayi farin ciki sosai, tun
daga wannan rana malam Muhammadu ya fara gadi a gidan Alhaji Isma'il,
alhamdulillahi rayuwa tayi musu daɗi, domin kullum sai hajiya juwairiyya ta bashi
abinci tare da kaya ya kaiwa iyalanshi, mace me kirki kenan da sanin ya kamata, da
tafiya yayi tafiya ma sai Alhaji Isma'il yace ya ɗauko matarshi ya dawo da ita
gidan, nan ya basu ɗaki a b/q na gidan, rayuwa sukeyi cikin mutunta juna tsakanin
hajiya Juwairiyya da Rashida, kasancewar Allah be bawa hajiya Juwairiyya haihuwa ba
yasa ta ɗauki Fateema kamar ƴar da ta haifa, ya zamana Fateema ta koma hannunta,
makaranta me kyau ta nema wa yarinyar ta sanyata tare da taimakon Alhaji Isma'il,
duk wani gata sunayiwa Fateema kai kace su ne suka haifeta, hakanne ya ƙara musu
matsayi da ƙima a idanun Malam Muhammadu da Rashida, ko tsinke Rasheeda bata bari
hajiya ta ɗaga, ta ɗauke mata komai ita takeyi mata, zaman nasu dai gwanin sha'awa.
Fateema na girma kyawunta na ƙara fitowa, Allah ya sakawa Fateema son karatu sosai,
shi yasa ta mayar da hankalinta ga karatu ba na bokon ba bana islamiyyar ba, hajiya
Juwairiyya tana son Fateema sosai, bata son damuwar yarinyar, shi yasa itama
Fateemar take sonta, komai Momy wani lokacin har mantawa takeyi da cewa Rashida ce
mahaifiyarta, shekarar Fateema goma sha biyu a duniya Allah yayiwa malam Muhammadu
rasuwa, sakamakon mota da ta bigeshi ya fita yiwa hajiya cefane, ranar me zuwa mata
cefanan ne be zo ba ta fito tana neman ɗan aika, abinka da tsausayi da ƙarar kwana
yace ta kawo yaje mata, yaje yayo cefenan zai dawo mota ta bankeshi, ko shurawa
beyi ba a gurin, sai gawarshi aka kawo musu..
Rashida ta shiga tashin hankali da ba zai iya misaltuwa ba, haka Fateema duk da
qaranci shekaru amma tasan tayi rashin mahaifi , shi kanshi Alhaji Isma'il yaji
mutuwar kamar d'an uwanshi ne ya rasa, uwa uba kuma Juwairiya da take gani kamar
silarta ne, damuwa da tunani ne sukayi tasiri a gurin Rashida sosai, wanda harya
janyo mata matsanancin hawan jini, Juwairiya da mai gidanta na iya qoqarinsu wajen
ganin sun bawa Rashida kukala, amma ina haka Allah ya tsara, ranar itama tana
fitowa daga d'aki tayi alwala zata koma kawai ta fad'i qasa, Fateema dake rik'e da
littafin karatunta ce tayi saurin ajewa takai mata d'auki, anyi sa'a Alhaji na gida
suka kaita asibiti, har an rubuta magungunan da zai siyo kuma ya tafi siyowa koda
ya dawo babu Rashida itama ta cika.
Fateema na jin haka ta yanki jiki ta fad'i sumammiya, kwananta biyu kamin tasan
inda kanta yake, haka itama dai suka dinga jimaminta yayin da kullum mutuwar ke
dawo musu sabuwa , saboda ganin Fateema cikin damuwa, gaba d'aya yarinyar saita
fita a hayyacinta duk da irin kulawar da take samu, karatunta ma saiya zamana tana
saku-saku dashi, dan tunani da kuka yafi yawa a cikin al'amuranta, Alhaji kuma na
nuna damuwarshi akan haka, kullum cikin janta a jiki yake yana rarrashi, yau da
gobe sai Allah sai shed'an ya farawa Juwairiya hud'uba akan cewar ai Alhaji zai iya
cewa yana son auren Fateema, a lokacin saita fara canzawa Fateema, amma abin baiyi
nisa ba Allah ya turo mata *Abdullahi*.
Tana da shekara *goma sha biyar* a lokacin suka had'u da Abdullahi, kuma yaron
Alhaji Isma'il ne da yake aike, koda ya nuna sha'awar aurenta Fateema ta amince,
dan a lokacin ta fara jin d'acin zaman gidan, da taimakon Alhaji akayi komai aka
gama, duk da yaso yarinyar tayi karatu, amma tunda tace tana sonshi kuma tana son
aure babu yanda ya iya, lokacin har ta kammala secondry ɗinta, cikin wata shida aka
d'aura musu aure suka tare a unguwar sabon gari tare da mahaifiyarshi da qannanshi
uku maza mata biyu, sosai Alhaji ya mata bajinta, dan saida ya cika mata d'akinta
maqil da kaya masu kyau da tsada, qarancin shekarunta yasa ta kasa amincewa dashi
da wuri har saida yayi hak'urin wasu kwanaki, ranar ma da dubara da wayo ya samu ya
mayar da ita babbar mace, kasancewarshi shima matashi yasa suke matuqar qaunar
junansu da kuma nunawa juna soyayya, sai dai hakan kuma yasa mahaifiyarshi ta fara
saka musu ido tare da nunawa Fateema tsangwama.
Fateema kuma na hak'uri sosai kuma bata fad'a mishi duk abinda zasu mata, dan har
qannanshi basu raga mata ba, wani lokaci har dukanta mahaifiyarshi keyi amma bata
tab'a koda tunanin fad'a masa ba, ranar kuma mahaifiyarshi da qannanshi mata su
biyu suna dukanta ya shigo gidan, nanya taimaka mata tashi ya kuma tambayi dalilin
dukan, mahaifiyar ce ta fad'a mishi waita rainata, haushi ne yasa ya kama qannanshi
suma ya dakesu dansu kiyaye gaba, amma furucin da suka fito daga bakin
mahaifiyarshi sam ba dad'i, kuma a ranar tace ta cire hannu a al'amuranshi, tun
daga ranar hankalin Fateema ya kasa kwanciya take lallab'ar mahaifiyarshi data yafe
mishi, shima haka yake bata hak'uri amma sam tace bata bashi, wata uku kuma cikin
*Raheenat* ya bayyana a jikin Fateema, kasancewar cikin bamai wahala da matsanancin
laulayi bane yasa bata san tana d'auke dashi ba, Abdullahi ne ya fara ganewa daga
ranar kuma salon tarairayarta ya canza, kulawa sosai take samu ita da abinda ke
cikinta, matsalar d'aya mahaifiyarshi da bata shiga sabgarsu, a haka dai har cikin
ya shiga watan haihuwa.
Ranar *Laraba* aka haifi Raheenat, santaleliyar yarinya wacce ta d'auko uwa da
uba , koba komai Mama tayi farin cikin ganin yarinyar, duk da bata musu magana ba
amma dai ta kula da yarinyar yanda ya kamata, duk wani abu da uba zaiyi Abdullahi
yayi wa Fateema da 'yarta shi bakin gwalgwado, sai dai ance _ALLAH baya barin wani
dan wani yaji dad'i_, washe garin ranar da akayi sunan Raheenat a ranar shima ya
koma ga ubangiji, kafin ya fita haka kawai yake ji wata sabuwar qaunar iyalinshi na
qara mamayeshi, harya fita ya dawo ya d'auki Raheenat yana mata wasa, kallonshi
Fateema tayi tace "anya kuwa zaka fita yau?"
Kallonta yayi shima yace "aida zan samu Alhaji yace na zauna gida, wallahi dana ji
dad'i matuqa."
Murmushi kawai tayi taci gaba da ninke kayanta, bata ankara ba taji ya rumgumeta ta
baya yana sumbatarta , nok'ewa ta farayi gabanta na fad'uwa dan tana gudun yace zai
zarce daga haka, tunda tana cikin jinin bik'i, da qyar ta samu ya rabu da ita kafin
yace "ba zaki barni na rage zafi ba ko, ke kad'ai fa gareni."
"Ke wannan fa al'ada ce ba addini ba, taya zan iya hak'ura har wannan lokacin? kema
kin sani ai."
Raheenat ce tayi kuka yasa ta d'auketa tasa masa nono a baki, durk'usawa yayi yana
kallonsu cike da so da qauna, cike da kunya Fateema ta kalleshi tace "ka tashi ka
fita mana, rana fa takewa take."
Mik'ewa yayi yana fad'in "to na tashi, tunda baki so ina kallonku."
Kafin tayi magana kuma ya sumbaci goshinta tare da cewa "ina godiya a gareki abisa
wannan babbar kyautar."
Sumbatar Raheenat yayi dake tsotsar nononta ido rufe, kafin ya fita yana kallonsu
itama tana kallonshi, awa d'aya da fitarshi labarin mutuwarshi ta samesu, wanda
yake tare dasu ne sukace yadai ce musu kanshi na ciwo, daga nan kuma sai yace zaije
ya sha magani ya ɗan kwanta, to kwanciyar da be tashi ba kenan.
Fateema tayi kuka kamar hawayenta zasu ƙare, ta shiga matsanancin damuwa, Abdullahi
shi kaɗai ya rage mata wanda take kallo taji daɗi, wanda in tayi kuka yake share
mata hawayenta, yau gashi shima wanda ya fita sonshi ya ɗauke abinsa, yanzu ƴarta
guda ɗaya tilo ita kaɗai ce danginta kuma sanyin idaniyarta.
Haka akayi zaman makokin Abdullahi aka ƙare, mahaifiyarsa kanta tayi kukan rashin
ɗan nata me tsananin biyayya a gareta, ta kuma yi nadamar abinda ta dinga yi masa
lokacin rayuwarsa, bayan kwana arba'in da mutuwar Abdullahi komai ya ƙara
taɓarɓarewa Fateema, domin kuwa sam bata jin daɗin zama da uwar mijin nata da ƴan
uwansa, abincin da zata ci kanshi basa bata sai tayi wankau ko daka wani lokacin
take samu ta ci, haka dai zaman nasu ya dinga gudana, Fateema duk tabi ta fita a
hayyacinta, wahala da rashin abinci duk ya galaɓaitar da ita, lokacin da ta fita
takaba taje gidan Alhaji Isma'il neman taimako gurin hajiya Juwairiya, ƙiri-ƙiri ta
koreta a gidan, tare da mata gargaɗin kar ta ƙara ganin ƙafarta ako ƙofar gidan ne,
sai ka rantse bata taɓa sanin Fateema ba a rayuwarta, kuma wai duk hakan akan
kishin mijinta ne wai kar Fateema ta aureshi, ko kuma shi yace yana so, domin Allah
yayi wa Fateema kyau.
_Hnmm, shaiɗan kenan me raya mana abubuwan da be kamata ba, yanzu dai duk kirki
irin na hajiya Juwairiya shaiɗan yy galaba akanta, Allah yasa mufi ƙarfin
zuciyarmu, ya karemu daga sharrin shaiɗani ameeen._
Tun daga wannan rana rayuwa ta ƙarayiwa Fateema ƙunci ita da jaririyarta ƴar wata
biyar, ta shiga *ƙangin rayuwa* wanda Allah ne kawai zai fitar da ita, ga babu
dangin uwa bare na uba a gari, yanzu ita ko wuƙa aka sanya mata a wuya ba zata iya
kai kanta agadaz ba balle ta nuna danginta.
*ƘANGIN RAYUWA*
_(labarin Raheenat da Abdul-Hakeem)_
🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾
💑💑💑💑💑💑💑💑💑💑💑
*RAHEENAT M ABBAKAR*
AND
*SAMEERA HAROUNA*
DEDICATED TO ALAWIYYA❤
*ƘANGIN RAYUWA*
_(labarin Raheenat da Abdul-Hakeem)_
🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾
💑💑💑💑💑💑💑💑💑💑💑
*RAHEENAT M ABBAKAR*
AND
*SAMEERA HAROUNA*
DEDICATED TO ALAWIYYA❤
_Bismillahi_rahaman_rahim._
Haka rayuwar take tafiya musu ba dad'in yau bana gobe, abin tashin hankalin shine
tattara komai da mahaifiyarshi tayi wanda ya mallaka ta rik'e, yanzu haka daga
cikin gadon ne take siyan kayan tana tafiya qauye tana siyarwa, idan kuma tayi
wannan tafiya komai yafi qara lalacewa, dan tana bawa yaranta kud'in abinci ne, ita
kuma ko oho haka ma jikanyarta, tun daga ranar da zata tafi harta dawo ita zata
dinga neman abinda zata ci ita da 'yarta, a sannu sannu sai watanni suke shud'e aka
fara lissafa shekaru.
*Bayan shekara biyar* Raheenat tayi wayo, kyakyawan yarinya mai kama da
mahaifiyarta a fuska, amma a suffa mahaifinta ne sak hatta yatsun qafa dana
hannayenta, lallausan hanaye da tsayi, Fateema ta dage sosai har saida ta sata boko
da islamiyya, kuma sosai ake ganin ci gaba a karatun yarinyar, a lokacin Fateema ba
abinda ba tayi na sana'a danta taimaki 'yarta da kanta, kullum qannan Abdullahi da
mahaifiyarsu goranta mata suke akan ta tafi ta basu gida, da farko tace zaman
Raheenat take dan bata san inda zata je da ita ba, amma da abin yayi yawa sai tace
to subata gadon Raheenat zata tafi, koba komai zata gina rayuwar yarta dashi, daga
lokacin sai suka daina maganar, dan insun matsa magana zata iya girma.
A haka aka sake shanye wasu shekarun, Raheenat nada *shekara koma sha biyar* ranar
kakarta ta tafi qauye, wannan tafiyar da tayi bata dawo ba tsawon lokaci,
kasancewar kuma duka qannan mahaifinta sunyi aure kuma dama babu wanda suke gani
idan ba kakarta kenan ba, hakan yasa basu damu ba dan dama ba taimakonsu suke ba
inba baqar magana zasu fad'a musu.
Rana tsaka wani Alhaji ya sallamo gidan, Mama ce ta fita ta ganshi nan yake fad'a
mata wai ya siyi gidan wajen mahaifiyar Abdullahi, notice ya basu na kwana uku akan
subar gidan, d'aurewar kai da Mama ta samu yasa tama kasa maganar da Raheenat, a
daren ranar da washe gari mutumin zaizo sam Mama bata rintsa ba, da safe kuwa
Raheenat na shirin tafiya islamiyya mutumin yayi sallama, tsoro da fargaba yasa
Mama yin shiru tak'i amsawa, shi kuma daba mutunci ne dashi ba yasa yaran da yazo
dasu suka shiga gidan, cike da wulaqanci suka dinga fito musu da kayansu suna
watsi dasu akan hanya, Mama tayi magiya tayi kuka ita da Raheenat amma ko jinsu
basuyi ba, mutane kuma na kallo babu mai *zuciyar taimako*, tofa ana hakane Allah
ya kawo Malam Habu wajen yaga wannan cin zarafi, daga nan ya d'aukesu ya tafi dasu
gidanshi har suke zaune cikin wannan tsangwamar ta Inna.
*Cigaban labari*
Kamar kullum Raheenat bata kwanta ba ta fara shirya abin karyawa, sai dai ba tayi
mamakin ganin su Farida a wajen ba har suna kama mata tunda Babansu yana nan, duk
da ba wani aiki sukayi ba saida suka gama a tare sannan ta shiga wanka tayi shirin
islamiyya, haka suma su Farida shirin islamiyya sukayi tunda mahaifinsu nanan dole
yau zasu tafi ko basu so.
Baba na d'aki zaune yana karyawa Inna na gefenshi yaran suka shigo da sallama,
amsawa sukayi a tare suka durk'usa suka gaisheshi, amsawa yayi tare da d'orawa "har
kun gama shiri kenan?"
Raheenat ma ta gama shiri ta kalli Mama tace "uwa mai dad'i ni zan wuce."
Rumgumo wuyan Mama tayi tana dariya tace "zaki fasa min kaina fa."
"Ni kike nema ki fasa min nawa." Mama ta fad'a cikin dariya itama, sumbatar kumatun
Mamanta tayi tace "saina dawo Mama, ki kula da kanki."
"Ameen Mamana."
Ta fad'a ta fita, saida ta tsaya qofar d'akin Inna tayi sallama Baba ya amsa, shiga
tayi kanta qasa cike da ladabi ta gaishesu, Baba kad'ai ya amsa banda Inna dake
hararanta kamar idonta zasu fad'o qasa, addu'a Baba ya mata sannan ta tashi ta wuce
itama, cikin sa'a kuma sai suka had'u da Sameera itama zata wuce, gaisawa sukayi
sannan suka rankaya tare.
Bayan an taso ma tare suka tawo, suna jiyo su Farida ta bayansu suna aika musu da
zagi amma ko su kulasu, sai ma suka mai dasu mahaukata, a haka har suka ƙaraso
ƙofar gidan, sallama Sameera da Raheena sukayi sannan Raheenat ta shige gida ɗauke
da sallama a bakinta su Farida na mara mata baya.
*************
Kamar kullum dai hajiya Maryam tana tashi salla ta gabatar sannan ta nufi ɓangaren
Abdul da sauri dan ganin yanda ya kwana, tana shiga ta sameshi kwance yanda ta
barshi jiya idanunsa a lumshe, sai dai ta tabbatar ba bacci yakeyi ba, shafa kanshi
tayi cike da tausayinsa tace "barka da tashi ɗan albarka. "
Buɗe idanunsa yayi ya kalleta sannan ya mayar ya rufe, cikin taushin murya tace
"bari na taimaka maka na kaika toilet Abdul, nasan zaka buƙaci hakan. "
Tana gama faɗin hakan ta ɗauko wheel chair ɗinsa ta aje a gefen gadon, nan ta fara
ƙokarin cicciɓansa, daƙyar ta ɗaurasa saman keken tana nishi, turashi tayi a
hankali ta nufi toilet ɗin dashi.
Da taimakonta dai yayi fitsari tayi masa tsarki sannan ta kuma gunguro sa suka
fito, kuskure ɗaya hajiya Maryam takeyi a cikin jinyar Abdul Hakeem, kuskuren kuwa
shine ba ko yaushe ne take ɗaura masa alola tace yayi sallah a cikin zuciyarsa ba,
wanda muke ganin hakan babban kuskure ne, Abdul sallah be ɗauke a kansa ba, saboda
yana cikin hankalinsa yana iya jin duk wani abu da za'a faɗa yana kuma gani, saidai
kawai ba zai iya motsa duk wata gaɓa na jikinsa bane, kunga kuwa ai zai iya yin
sallah a cikin zuciyarsa matuƙar aka ɗaura masa alola, to Hajiya Maryam ba ko
yaushe ne take hakan ba sai ya ɗauro.
Shafa kansa tayi tace "ɗan gidan Momynsa ni bari naje na haɗa abin kari kar hajiya
ta jini shiru, zan barka saman kujeran nasan zaka fi buƙatar hakan tunda ka kwana
kwance, ko na kaika falo ne na kunna maka tv ya ɗebe maka kewa.?"
Lumshe ido yayi ya buɗe, hakan yasa ta fahimci eh yake nufi, gungurosa tayi ta
ajiye a falo sannan ta kunna masa tv, tashar sunna tv ta kama masa sannan ta fice
daga falon da sauri sabida gudun samun matsala gurin hajiya Luba, da idanunsa yabi
Momyn nasa cike da tausayin rayuwarsu, haƙiƙa yana matuƙar tausayawa Momynsa saboda
irin wahalar da take sha cikin gidan, wai kuma a hakan gidan mijinta ne, amma
marabarta da ƴar aiki babu.
Kai tsaye katafaren kitchen ɗin hajiya Luba ta nufa domin ɗaura break fast, cikin
sauri takeyi komai har ta kammala, kai tsaye dining table ta nufa ta fara jeresu,
tana cikin jerawa su hakima hajiya Luba aka fito hannunta sarke cikin na Alhaji
Naseer, cikin rawar jiki hajiya Maryam ta zube tana faɗin "barka da fitowa hajiya.
"
Sai da ta zauna tukunna cikin ya tsina da wulaƙanci tace "me kika girka ne.?"
Cikin rawar baki tace "ruwan zafi ne, sai doya dana suya cikin kwai na haɗa da
farfesun kan saniya. "
Hajiya maryam cikin sanyin jiki dajin ita ba komai bace a gidan sai ƙasƙantacciya
ta fara saving nasu tana riƙe hawayen dake ƙoƙarin zubo mata, tana gamawa tabar
gurin cikin sauri domin wani irin kuka ne ta tawo mata da ƙarfi.
Kitchen ta shige taci kukanta ta ƙoshi sannan ta ɗauki kular abincin nasu ta nufi
ɓangaren Abdul-Hakeem, zuciyarya nayi mata ƙuna tare da raɗaɗi.
************
Raheenat kuwa kamar yanda ya zame mata jiki tana cire uniform ɗinta fitowa tayi ta
fara ƙoƙarin ɗaura masu girkin rana tare da taimakok su Farida, sosai yau ta samu
sausaucin aikin saboda tayen da ta samu gurinsu Farida, shi yasa take son ace Baba
na gari kodan samun sauƙinta, domin kuwa duk wani hantara da tijara rageshi sukeyi.
Haka dai rayuwar ta ci gaba da tafiya ta ko wani ɓangare cike da ƙuncin rayuwa, ba
ga Raheenat ɗin ba ba ga hajiya Maryam da ɗanta ba, suko iyayan gayyar babu abinda
yayi musu zafi dangane da rayuwa, cikin karensu kawai sukeyi babu babbaka, Raheenat
ta samu sauƙi sosai gurin Sadiq, domin tun daga ranar da Baba ya bigeshi be ƙara
taranta da wata maganar banza ɓa, dan yana matuƙar tsoran Babansa.
Yau ta kama juma'a babu islamiyya, Inna ce take ƙwalawa Raheenat kira kamar zata
tashi gidan, da sauri Raheenat ta fito daga ɗakin nasu tana faɗin "na'am Inna gani.
".
Wani mugun harara Inna ta jefa mata tace "in kinga dama ki ɗauki botikin nan kije
gidan Alhaji Naseer buzu ki ɗebo min ruwa. "
Tayi maganar tana nuni da botikin gabanta.
Juyawa ɗaki Raheenat tayi ta ɗauko hijjabinta sannan ta fito ta ɗauki botikin ta
nufi gidan Alhaji Naseer buzu cike da fata da burin ganin Abdul-Hakeem, abin mamaki
malamin islamiyyarsu ne ta gaji a k'ofar gidan Alhaji Naseer tare dashi suna hira,
cike da nutsuwa ta sunkuya tana dafe da bokitin ta gaishesu, amsawa sukayi cikin
sakin fuska da yabawa da tarbiyar yarinyar, mik'ewa tayi ta shiga cikin gidan bayan
sun gaisa da mai gadin, kalle kalle take tana so taga ta inda zata hango bawan
Allah Abdul Hakeem amma shiru, dole ta d'ibi ruwan ta fito ba tare data gansa ba,
saida ta sake cewa malaminsu "sai anjima malam." kafinta wuce.
Abinda bata sani Abdul Hakeem na hangenta ta madubin daya lullub'e qofar falonshi,
yanda take kalle kalle shima kallonta yake kamar ya tashi ya mata magana, yana
kallo harta fita daga gidan yana jin ba dad'i.....
Meeraheenat😘
24/08/2019 à 11:51 - ~NANA KHADIJA~😍: 🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾
💑💑💑💑💑💑💑💑💑💑💑
*ƘANGIN RAYUWA*
_(labarin Raheenat da Abdul-Hakeem)_
🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾
💑💑💑💑💑💑💑💑💑💑💑
*RAHEENAT M ABBAKAR*
AND
*SAMEERA HAROUNA*
DEDICATED TO ALAWIYYA❤
*🇸🇦ZAMAN AMANA WRITER'S*
*(Z.A.W)*
```(Gidan zaman lafiya da amana insha Allah)🤜🤛```
Page 65 to 70
Lumshe idonsa yayi yana jin wani irin ɗaci a zuciyarsa, fata yakeyi Allah ya bashi
lafiya shima ya miƙe kamar kowa, wannan wani irin rayuwa ce, mutum ko yana son abu
baya da bakin da zai faɗa, ko da yake ya ɗauki hakan a matsayin kaddararsa ce.
Murnushi Malam Saminu yayi yace "eh, Raheenat ba, yarinyar akwai nutsuwa ga tarbiya
data samu daga gida. "
Ɗan ɓata fuska Alhaji Naseer yayi yace "ai kwanakin baya naso nemawa ɗana Abdul
aurenta saboda yabawa da tarbiyar nata da nayi, amma saidai babu nasara. "
Kallonsa Malam Saminu yayi sosai yace "wai kana nufin Abdul-Hakeem. ?"
Ɗaga kansa Alhaji Naseer yayi yace "banda abinka Malam ina da wani ɗanne bayan shi.
"
Ɗan shiru Alhaji Naseer yayi kafin ya gyara zama yace "ka gane ne Malam, wato dai
kwanakin baya ne na fito.....nan ya bawa Malam Saminu labarin duk abinda ya faruwa
tun daga lokacin da Raheenat ta bawa Abdul ruwa zuwa maganarsu da Malam Habu, da
shi abinda Malam Habun yazo ya sanar dashi na rashin amincewar mahaifiyar yarinyar,
kafin ya ɗaura da cewa "sam abin beyi min daɗi ba da Mamanta taƙi amincewa, nasan
dai tabbas akwai cutarwa ga yarinyar amma taimaka min zasuyi, dan ina saka ran
Abdul zai tashi nan bada daɗewa ba, amma babu yanda na iya na haƙura. "
Nisawa Malam Saminu yayi yace "gaskiya ne Alhaji ba ko wacce uwa ce zata so ganin
ƴarta cikin wahala ba, shi aure ana yinsa ne domin bautar Allah da kuma jin daɗi,
amma a yanzu duk wacce zata auri Abdul to tabbas sai ta wahalta masa, to kaga ko ba
ko wacce uwa ce zata yarda da hakan ba, saidai karka damu, zan tayaka da addu'a,
insha Allahu in akwai aure tsakanin Raheenat da Abdul komai zai zamo mana cikin
sauƙi. "
Cike da jin daɗi Alhaji Naseer ya dinga zubawa malam Saminu godiya, nan sukayi
sallama malam Saminu ya tafi shi kuma ya shige gida.
Alhaji Naseer sun haɗu ne da Malam Saminu ta hanyar wani abokinsa da yayi masa
hanya akan shi Malam Saminun zai taimaka masa akan ciwon Abdul ɗin, dududu ba afi
sati biyu ba da haɗuwar nasu, yanzun ma yazo ganin Abdul ɗin ne, saboda be taɓa
ganinsa ba sai labarin ciwon nasa da Alhaji Naseer yake bashi, duk da ya fara bada
wani taimako a ringa bawa Abdul hakan be samu ba saboda hajiya Luba ta hana, da
yake komai sai Alhaji Naseer ya faɗa mata, to yana faɗa mata ta rinƙa faɗa tace sam
ba malamin gaskiya bane kar ya yarda ya bawa ɗansa duk wani magani da zai bashi, to
hakanne ta kasance ba abawa Abdul magani ko ɗaya ba cikin wanda Malam Saminu ya
bayar, sai dai shi Alhaji Naseer har cikin ransa ya gamsu da Malam Saminu, shi yasa
ma ya kasa rabuwa dashi, kallo ɗaya Malam Saminu yayiwa Abdul ya gane akwai sihiri
a jikinsa, yanzu ma tsayuwar da Raheenat ta gansu sunayi akan lallurar tashi suke
tattaunawa.
_Wannan kenan_
*********
Malam Saminu ne yayi kiran Raheenat office ɗinsa bayan tashi daga makaranta, da
sallama ta shiga office ɗin kanta a ƙasa, nuna mata kujera Malam yayi yace ta
zauna, zama tayi kamar yanda ya umurceta gabanta na faɗuwa dan zatonta wani laifi
tayi.
Gyaran murya Malam Saminu yayi yace "Raheenat dama kina shiga gidan Alhaji Naseer
ne.?"
Ɗagowa tayi ta kalleshi tace "eh malam ina shiga, amma ruwa ne kawai nake zuwa
ɗibowa, shima ba ko yaushe bane. "
Girgiza kanta tayi tace "eh, amma so ɗaya na taɓa ganinshi. "
Ɗan murnushi yayi yace "kenan baki san taimakon da mahaifinsa ya nema a gurinki
ba.?"
Cike da mamaki Raheenat ta kalli Malam tace "taimako! A gurina kuma, wani irin
taimako ne ni kuma Alhaji Naseer zai nima a gurina ? Ni bansan komai ba wallahi
malam. "
Gyara zamanshi Malam yayi yace "kenan mahaifiyarki bata faɗa miki komai ba. "
"Kwantar da hankalinki Raheenat ba wani abu bane, dama aurenki ya nema a bawa ɗansa
Abdul. "
Waro ido tayi tare da dafe ƙirji tace "aurena kuma, ni Raheenat akeso na auri
Abdul-Hakeem, kuma malam kace mahaifiyyata ta sani.?"
"Kuma ta yarda.?"
Murmushi Malam Saminu yayi ya fara mata bayanin duk yanda sukayi da Alhaji Naseer
har abinda mahaifiyarta tace kafin ya ɗaura da cewa "Raheenat ni a ganina taimako
zakiyi tare da *Jihadi*, saboda na gano lallurar yaron akwai sihiri cikinsa, kuma
ina ji ajikina aurenki dashi Alkhairi ne, Raheenat nasan ke malama ce, zaki bada
gudunmuwarki sosai gurin samun lafiyarshi, na fahimci wani abu da yake faruwa a
cikin gidan Alhaji Naseer tun lokacin da yazo gurina neman taimako, kuma wannan
abin da yardan Allah zai zo ƙarshe sanadin shigarki gidan, saidai bansan ta yaya
al'amuran zasu kasance ba, Raheeenat ina so ki bani nan da kwanaki uku zan ƙarayi
miki istihara akan al'amarin, abinda na gani zan sanar dake, kema kuma ya kamata
kiyi istiharar nan da kwanakin sai ki faɗa min me kika gani. "
Jiki a matuƙar sanyaye Raheenat tace "to malam, insha Allahu zanyi yanda akace,
Allah ubangiji ya tabbatar mana da alkhairi. "
"Ameen ameen" cewar Malam Saminu, kafin ya ƙara da cewa "zaki iya tafiya, amma
karki saka wani damuwa a ranki fa. "
Murmushi tayi tace "kar ka damu Malam babu komai wallahi. "
Shima murmushin yayi mata yace "kina da zuciya me kyau Raheenat, nasan Allah ba zai
taɓa bari ki wulaƙanta ba. "
Nan tayi masa sallama ta fito daga office ɗin, bakin office ɗin ta iske Sameera na
jiranta, murmushi suka sakarwa juna sannan Sameera tace "my heenat ina fatan ba
wani laifi kikayi ba. "
Tafiya Raheenat tayi tace "karki damu my Meera tamabayata kawai yayi, kisan rannan
nace miki na haɗu dashi a gidan Alhaji Naseer ai. "
Bayanta Sameera ta biyo suna tafiya tace "ok har naji sanyi, kinsan ko kaɗan bana
son naji ance kinyi wani abu barar daɗi. "
Murmushi Raheenat tayi ta kamo hannu Sameera ta riƙe tace "na yarda Allah ne me
haɗa bayinsa my Meera, kina nuna min soyayya wacce ko ƴan uwa jini ɗaya muke sai
haka, nagode da soyayyarki Allah ya barmu tare har mutuwa, ya kau da idon maƙiya a
kanmu. "
Haka suka ci gaba da tafiya suna hirarsu har suka zo inda zasu rabu Sameera ta nufi
gidansu ita kuma ta shige nasu.