0% found this document useful (0 votes)
103 views3 pages

Attachment

The document narrates the story of Hadiza, a young woman whose life takes a tumultuous turn due to her choices in marriage and the consequences of her actions against others. It highlights the moral and spiritual lessons about adhering to divine guidance in relationships and the repercussions of straying from it. Ultimately, Hadiza is urged to seek forgiveness and rectify her wrongdoings as she reflects on her past decisions.

Uploaded by

Zaynerb Eerderm
Copyright
© © All Rights Reserved
We take content rights seriously. If you suspect this is your content, claim it here.
Available Formats
Download as DOCX, PDF, TXT or read online on Scribd
0% found this document useful (0 votes)
103 views3 pages

Attachment

The document narrates the story of Hadiza, a young woman whose life takes a tumultuous turn due to her choices in marriage and the consequences of her actions against others. It highlights the moral and spiritual lessons about adhering to divine guidance in relationships and the repercussions of straying from it. Ultimately, Hadiza is urged to seek forgiveness and rectify her wrongdoings as she reflects on her past decisions.

Uploaded by

Zaynerb Eerderm
Copyright
© © All Rights Reserved
We take content rights seriously. If you suspect this is your content, claim it here.
Available Formats
Download as DOCX, PDF, TXT or read online on Scribd
You are on page 1/ 3

*😰MACE-MACEN AURE😰*

*(GAJEREN LABARI ME ILIMANTARWA TARE DA SANYA NISHAƊI🙌🏻)*

*DA SUNAN ALLAH MAI RAHAMA MAI JIN ƘAI.ALLAH YA YI SALATAI MARASA IYAKA GA
SHUGABAN ANNABAWA DA MANZANNI ANNABI MUHAMMAD SALLALLAHU ALAIHI WASALLAMA
AMIN*

****

*Haƙiƙa aure a wannan Lokacin/Zamanin yana taɓarɓarewa saboda abubuwa masu tarin yawa,kuma duka ba komai
ya taka muhimmiyar rawa ba kamar barin hanyoyin Allah da akayi,ba'a neman mace ko miji kamar yadda Ubangiji
ya tsara a musulunci,ga taƙaitaccen labarin Hadiza me sakin reshe ta kama ganye....*

*SHAFI NA FARKO DA ƘARSHE*

****

Yarinya budurwa me kimanin shekara goma sha takwas,tana zaune akan wani dandamali wanda aka siminceshi irin
yadda mutanen da zamanin kakanninmu suke yi domin cin abinci da maƙota,ba ita kaɗai bace ba,domin wani
saurayi ne acan gefenta a zaune da alama zance suke yi.

Hira suke sosai da soyayyace me ƙarfi a tsakaninsu kasancewar har baiko anyimusu da ita rana kawai ake jira,wayar
salularsa ce tai ƙara wanda hakan yasa ya miƙe tsaye a gaggauce jin ɗan uwansa na masa magana kamar haka...

"Jafar duk inda ka ke kayi ƙoƙarin zuwa yanzu jikin Baba ya motsa sosai"

Abinda ya iya ji kenan aka yanke wayar.Duban Hadiza ya yi wadda itama jikinta yai sanyi dan daman ta kwana da
sanin baban nashi baida lafiya,kafin ya yi mata magana tace masa ya tafi karya daɗe a hanya bai isa gida ba,haka
kuwa ya tafi duk jiki ba ƙwari inda itama ta shiga gida.

Ajali in yai kira ko ba ciwo aje,aikuwadai haka Baban Jafar ya amsa kira,ranar sadakar uku gidansu Hadiza suka
shirya sukaje suka yi musu gaisuwa.Bayan sun fito ne daga gidan wani a cikin ƴan zaman makoki ya biyo Hadiza
yaga gidansu,aikuwa da dare yayi se gashi a gidan nasu,kasancewar baban Hadiza baya gida babarta tace ta fita,jin
ance mutumin da mota yazo,ko da ya shirgawa Hadiza ƙarya se ta yarda dashi ta kuma sanya a ranta se ta rabu da
Jafar ta aureshi dan ita yanzu ba ajin talaka bace ba.

Wane tudu wane gangare haka Hadiza da babarta suka ƙulla makircinsu na mata sukai abinda sukai aka mayarwa da
Jafar kuɗinshi Alhaji Bala ya kawo kuɗaɗe masu yawa da kaya na manyan mutane sannan yace baya buƙatar komai
se matarsa.
Jin wannan magana da kuma jin labarin irin kuɗin da Alhaji ke dasu yasa KATTUME mahaifiyar Hadiza ta gigice ta
sanya dole MALAM mahaifin Hadizan ya yadda akai wannan aure.

Kafin auren ya faɗamata bashi da wata mace matarsa ɗaya ce kuma ta rasu lokacin haihuwar fari shiyasa bai kuma
aure ba se a kanta,amma me? Hadiza na tarewa taji labarin matan Alhaji huɗu,randa aka ɗaura aurenta dashi ranar ya
saki matarsa ɗaya da safe.

Iya tashin hankali Hadiza ta shigeshi amma da ke akwai dukiya haka Mama Kattume ta kwantar mata da hankali
akan duk zasu koresu ita kaɗai zata ci gaba da zama a gidan.

Kwanci tashi asarar mai rai se ga Hadiza da ciki,murna a wajanta da babarta ba'a magana saboda zasu gaji Alhaji,su
fatansu a yanzu bai wuce ace namiji Hadiza zata haifa ba.

Yawon ƴan bori da ƴan tsibbu shi Hadiza suka tasa gaba suke yi akan matan Alhaji da ma shi kansa,sannan kuma ga
shegen makirci da sharri da ta ke ƙullawa kullum cikin rigima ake a gidan.

Wani shu'umin boka ta samu ya dinga yimata aiki cikin ikon Allah se da ta fitar da matan Alhaji biyu,yayinda ɗayar
me suna Karimatu ko ciwon kai bataiba balle taju ciwon saki,kasancewar ita mace ce mai matuƙar tsoron Allah,inhar
bata da aiki zaka taddata da ƙur'aninta ko carbi da Azkar ɗinta tana yi safe da yamma,babu addu'ar da ta ke
wuceta,dan haka Allah ya tsayamata sharrin Hadiza baibi ta kanta ba.

Wata rana Hadiza da Babarta sunje wajan boka yace dole se sun kawo wasu manyan kuɗaɗe da kayan abinci da
busasshiyar ganda me yawa wadda zata ishi aljanun da ke masa aiki sannan za'a samu nasarar fitar da Karima daga
gidan.

Haka kuwa Mama Kattume taje ta ɗaga kayanta ɗakinta kaf bata bar komaiba ta siyar,ba yadda Malam baiba akan ta
faɗamai me zatai amma taƙi tace...

"Malam bazaka gane ba"

Nan ta haɗa komai na abinci da Boka ya buƙata sannan ta haɗe guri ɗaya da kuɗin ta kaiwa boka,nan yai ihu yai
zage-zagensu sannan ya bata wata ƴar kwalba da shuɗin ruwa a ciki yace ta kaiwa Hadiza,idan taje ta faɗamata ta
samu ta lallaɓa ta asko gashin bakin da gashin Hammatarsa guda bakwai ta zuba a kwalbar a dawo masa dashi....lol.

Aikuwa tana kaiwa Hadiza se da ta girgiza,amma da ke sheɗan ya buga mata gangar nasara haka ta yadda zatai.

Dare nayi Alhaji ya kwanta ta tashi tana ta tunanin yadda zata ɗaga hannunsa ta yanki gashin Hammatarsa guda
bakwai,wata dabara ce tazo mata,nan da nan taje ta ɗaga hannunsa sama tare da sanya kanta tsakankanin hannun
nasa,saida ta tabbatar baccinsa ta yi nisa sannan ta zame kanta ta ɗakko rezarta ta sanya tafara askowa inda a ƙarshe
se ihun Alhaji taji ta yankeshi.

Cikin tashin hankali Alhaji yake ihu inda bai sani ba ya bige kwalbar gun boka ta faɗi ya taka ƙafarsa ta fashe,koda
likita ya duba Alhaji ya bashi magani ya nutsu se ya danƙarawa Hadiza saki ɗai-ɗai har uku.

Bayan ta dawo gida ne se ta miƙa lamuranta ga Allah ta koma zama inda babanta yake yana ƙara tunatar da ita
abinda Allah ya faɗa.

Sa ke kallonta Malam yai tare da faɗin...

*"Daga Abu Hurairata Allah ya yarda dashi,daga Annabi (S A W) ya ce: 'Allah Maɗaukaki yana da kishi,amma
kishin Allah Maɗaukaki yana motsawa ne lokacin da mutum ya afkawa abinda Allah ya haramta' (Shaikhani suka
ruwaitoshi.*
Kinji dai,kamata yai dukkanin wanda ya yarda da Allah da ranar lahira ya yi daga abinda Allah yace ayi,ya bari daga
abinda Allah yace a bari.Amma ke anan me kika yi kenan?,kinje kin tarar da mata a gidansu kin rabasu da farin
cikinsu da iyalansu.

Shin ke kina tunanin Ubangiji zai barki ne?, karfa ki manta Ubangiji da kanshi ya faɗa a cikin Suratu Gafir
cewa...*'Allah yasan yaudarar idanu da abinda ƙiraza suke ɓoyewa'*.Ubangiji ya san baki ɗaya sha'anin aurenki
baku ƙullashi da niyyar arziƙi ba,se da kuka yaudari ɗan marayan Allah Jafar saboda ganin kuɗi,yanzu ina kuɗin
yake?,gashi uwarkima komai nata ya ƙare ba ku da taro bare sisi,yayin da shi kuma Jafar kinga yaje ya auri
aminiyarki gashin Ubangiji yasa wani attajiri ya ɗaukeshi aiki a Lagos yanzu hakama shirin gyaran gidansu yake yi
saboda Allah ya sanyamai albarka acikin sha'aninsa.

Sannan inason ki sanya maganar da Ubangiji ya faɗa da kansa a Sura Alfajri cewa ...*'Lallai Allah yana nan a
madakata'*. Kinji dai,kisani a yanzuma wannan abu da ya sameki bashi ke nufin Allah ya miki hukuncin laifukanki
ba! A'a yana madakata yana jiran bayinsa yai musu husabi bisa al'amuransu da suka aikata,kuma a sannan ne zai
hukuntaki ke da mahaifiyarki,idan kuma kinji tsoron haɗuwa da Ubangijinki kinyi nadama ingantacciya,to kije ki
nemu afuwar waɗanda kika zalunta sannan kici gaba da Istigfari Allah zai yafemiki,dan Allah Gafurur'rahimu ne
shi,sedai baya yafe laifi tsakanin mutum da mutum,a yanzu lokaci bai ƙuremiki ba tunda kina da rai suma waɗanda
kika zalunta suna da rai."

Kuka Hadiza ta fashe dashi sabida bayanan Malam sun ratsata matuƙa,kuma ta ɗaukar masa alƙawarin lallai zata je
ta nemi yafiyarsu,ita babban abinda ya tsayemata ma bai wuce arziƙin da Jafar yai ita kuma ta tsiyace ba,kenan dai
yanzu a taƙaice ita ta saki reshe ta kama ganye.

*Tammat bi Hamdillahi.*

You might also like