[9/6, 6:36 AM] +234 816 142 6063: *PAPPER SOUP SPICES*
Citta gwangwani 3
Coriander gwangwani 2
Barkono chokali 4
Masoro chokali 2
Kimba guda 5
Fennel chokali 2
[9/6, 6:39 AM] +234 816 142 6063: Gyadar miya guda 10
Tafarnuwa chokali 3
Cardamom chokali 2
Cumin chokali 2
Lemon grass
Thyme chokali 1
[9/6, 6:45 AM] +234 816 142 6063: *YAJIN TSIRE*
Kuli kuli gwangwani 4 uku
masoro Rabin gwangwani 1
Coriander Rabin gwangwani
cardamom chokali 3
Onga
Maggie star
Gishiri
Barkono gwangwani 1
Citta chokali 3
Kanumfari chokali 2
Ajino moto idan kunaso shi ba dole bane saboda ba kowa bane yakeci
[9/6, 6:49 AM] +234 816 142 6063: *DADDAWA MIX*
Daddawa gwangwani 4
Citta gwangwani 1
Kanunfari kwatan gwangwani
Masoro chokali 2
Nutmeg rabin gwangwani
Tafarnuwa kwatan gwangwani
Kimba guda 10
Barkono gwangwani 2
[9/4, 7:05 PM] Oumhaneefah: Yau dabaru da sinadaran girki zamu gabatar
MENENE KAYAN KANSHI NA ABINCI?
Spices kamar yadda mukasani Ana amfanidashine wuri Kara armashin abinci sannnan kuma da yawa
acikin spices din suna Kara lafiya.
Yana zuwa nau’ika da dama kamar ganye,Itace,fruit,seeds/kwayoyi,flowers dadai sauransu.
Idan kinaso ki ajiye spices yadade Miki dole yazamana a bushe wasu suna iya kaiwa shekara 2-3 a bushe
basu canza kamshi ko dandanoba amma kuma wasu spices din Idan ya bushe shikenan amfaninshi ya tafi
misali parsley shi da fresh 1 kawai ake amfani.
HOT SPICES/KAYAN KAMSHI MASU YAJI:Black pepper/masoro,White pepper,Mustard
Su wadannnan suna cikin spices masu yaji
Sai spices da suke flower:
Thyme,lemon grass,coriander,saffron,levender,sweet basil.
Sai spices masu karfin kamshi
Ginger,Garlic,Onion,All spices da dai sauransu.
Akwai spices masu bada Kala :Turmeric/kurkur,Paprika/Garin tattasai,Safron dadai sauransu
Sai kuma Wanda suke zuwa a iri/Seed:Mustard seed,Fenugreek/Hulba,Cumin seed da kuma garin
kantu /sesame seed.
Sannnna kuma akwai single spices misali
Ginger powder,Onion powder,Garlic powder, dadai sauransu
Sannnnan akwai mix spices/Hadi ;Kamar Taco seasoning,Utalian seasoning,Gram masala da dai sauransu
Mungama introduction na spices yanzu zamu shiga ainahin yadda ake hadasu.😍❤️
[9/4, 7:05 PM] Oumhaneefah: CURRY:- Curry sinadarin girki ne da kowa ya sanshi amma ba lallai yadda
yakamat kike anfani dashi ba, hanya mafi kyau yadda zakiyi anfani da curry shine ki sakashi a farkon
girkinki da kuma tsakiyar girki,misala idan jollof rice zakiyi ana saka shi a farko wajen bayan kin tsaida
ruwan jollof dinki,idanya tafasa,kika zuba shinkafarki,tayi tafasa kamar biyu sai ki qara..
[9/4, 7:05 PM] Oumhaneefah: THYME:- thyme yawanci anfi anfani da na kanti,amma akwai ganyen
sa,wanda shima zaki iya anfani dashi ki saka a nama,kifi ko kaza, ana anfani da ganyen thyme a recipes
na dankali yana matukar kawata abinci.
[9/4, 7:05 PM] Oumhaneefah: White pepper: Zan iya ce masa qanin masoro saboda dukkan su 'yaya ne
na pepper plant kuma wuri daya ake ciro su, saboda hatta girmansu daya a colour ne suka banbanta
wannan baqi wannan fari. White pepper yafi masoro yaji, kuma yana gyara haqori, rage qiba, gyaran fata
da disease
[9/4, 7:05 PM] Oumhaneefah: Star Anise: Ya samo sunan sa ne daga yanayin sa kamar star mai shape 8,
kuma yana daga cikin abun da Chinese suke amfani dashi hade da cloves, fennel seeds, Chinese
cinnamon da Sichuan pepper su hada Chinese five-spice powder, kuma ana shan sa a tea yana maganin
cutuka dayawa.
[9/4, 7:05 PM] Oumhaneefah: Fennel Seed: Yana da qamshi mai dadi kuma qamshin sa yana tafiya ne
tare da Anise. A yanayi kuma yana mutuqar kama da Cumin, Shima a familyn parsley yake, ana amfani
dashi a abinci da kuma yin magani dashi. Yana qara yawan ruwan nono ga nursing mothers, kuma ana
bawa jarirai ruwan sa don rage kumburi da ciwon ciki, yana taimakawa wurin narkar da abinci da kuma
rage cholestral.
[9/4, 7:05 PM] Oumhaneefah: Fenugreek (hulba): Spice ne wanda yan south Asia suke sanya shi a cikin
girki, amma a nan dai amfanin da muke dashi daban gaskiya, don masu sashi a girki basu da yawa
[9/4, 7:05 PM] Oumhaneefah: Cummin: Shima a family parsley yake, ana amfani dashi a qamshin abinci,
ana sashi a dakakke ko kuma a yanda yake
[9/4, 7:05 PM] Oumhaneefah: Negro Pepper (kimba): Ana sanya cikin spices especially farfesu zaki hada
shi tare dasu citta da kanunfari haka nan in zaki yi yaji.
[9/4, 7:05 PM] Oumhaneefah: Sis wlh mgnrki akan Business na yaji is true I hv been in the business for
more than 7yrs kuma sosai ya karbu
[9/4, 7:05 PM] Oumhaneefah: PAPRIkA:- yana da dadi sosai a girki, gashi zaki ganshi da jar kala,ana saka
shi stew,ana zaka shi a gashi kamar idan zakiyi gashin nama,kifi,kaza da sauransu,zakiga namanki yayi
wani jar kala mai kyau,ana saka chi kuma a blend spice,idan zaki hada home made spices dinki
CHILL POWDER:- chill combination ne na wasu spice,irinsu chili ,cumin ,oregano,cayyene da sauransu,
zaki ji chill powder yana kamshi na musamman,kuma ana anfani da shi a miya da kuma kashin nama
ALL SPICES:- all spice sinadarin girki ne mai zaman kansa,wanda da yawa mutane suna zaton wasu
combination ne na spice,haka yake round kamae masoro ko kanunfari,yana da dadin kamshi a girki,ana
saka shi a dahuwar nama,soup da kuma brown rice,ana saka shi a salad dressing da kuma spice mix.
OREGANO:- sinadrin girki ne,zakiji shi da lemony flavor yana going perfectly da garlic da kuma curry a
girki.
[9/4, 7:05 PM] Oumhaneefah: GINGER(citta):- basai nace komai ba game da citta ba saboda duk inda
zaayi anfani da kanunfari,masoro toh tabbas citta tana da matsuguni a wurin, ita citta tana da banbancin
kamshi da fresh ginger,fresh ginger yafi dadi a lokacin da zakiyi anfani da tafarnuwa,ita kuma citta
alokacin da zakiyi anfani da ragowae yen uwanta su masoro da kanunfari.
KIMBA:-kimba itama tana cikin kayan kamshin da yawa mutane basu waye daita ba,tana matukar dadi
idan zaki hada garin kununki na gero,ki tabbata tana ciki,ko kuma idan markaden kunune na
hasara,shima a jefa ta ciki a markado da ita tare da sauran kayan kamshi su citta,kanunfari da masoro
NUTMEG(gyadarmiya) :--
Idan ma bakya anfani da nutmeg to ki fara,saboda sinadari ce matukar kamshi a miyar
yauki,kuka,kubewa karkashi da sauransu,tafi dadi ida kika hada ta da daddawa da masoro da yer citta
kadan kika dakasu liqwi,ki saka a ruwan namanki idan zakiyi miyar yauki,kuma a farkon girki ake anfani
ita,saboda idan ta dahu sosai,shine kamshinta zaifito sosai.
[9/4, 7:05 PM] Oumhaneefah: CINNAMON (girfa):- Ina son girki da cinnamon,akwai na gari akwai kuma
na stick,yana matukar dadi a shyi mai kyan kanshi,kuma yana dadi a home made drinks kamar su
tamarind drink,milk shakes,ana saka cinnamon a baked foods kamar chocolates
cakes,swissrolls,cinnamon rolls ,ana garnishing dashi,ana matukar dadi a soup na kayan ciki da kuma
soup din nama. Shi na stick din guda daya zai iya yi miki 2 weeks ko fiye kina amfani da shi.saboda haka
idan kika saka shi a duk abinda kike bukata ya kai 5 minutes yana dahuwa sai ki cire