0% found this document useful (0 votes)
407 views59 pages

Miskilanci Ko Gidadanci

The document is a fictional narrative titled 'Miskilanci Ko Gidanci' written by Manshart, focusing on the life of a young man named Abubakar and his family dynamics. It explores themes of familial love, personal struggles, and societal expectations as Abubakar navigates his education and relationships, particularly with his mother and future wife. The story is set in Nigeria and highlights cultural elements, including marriage traditions and the importance of education.
Copyright
© © All Rights Reserved
We take content rights seriously. If you suspect this is your content, claim it here.
Available Formats
Download as TXT, PDF, TXT or read online on Scribd
0% found this document useful (0 votes)
407 views59 pages

Miskilanci Ko Gidadanci

The document is a fictional narrative titled 'Miskilanci Ko Gidanci' written by Manshart, focusing on the life of a young man named Abubakar and his family dynamics. It explores themes of familial love, personal struggles, and societal expectations as Abubakar navigates his education and relationships, particularly with his mother and future wife. The story is set in Nigeria and highlights cultural elements, including marriage traditions and the importance of education.
Copyright
© © All Rights Reserved
We take content rights seriously. If you suspect this is your content, claim it here.
Available Formats
Download as TXT, PDF, TXT or read online on Scribd
You are on page 1/ 59

[3/18, 10:59 AM] Manshart: *MISKILANCI KO GIDADANCI*❓

```Written by Manshart```💘

~In dedicated to my luvly Dad (Alhaji😍) nd (Bissalam)~

*{Đíş íș mý şęçºŋð ŋºvęłş👌🏽}*

*Part 1*

*BISMILLAHIR-RAHMANI-RAHIM*

Da shirinsa yafito, sanye d kananan kaya riga white da wando red color, kayan sunyi
matu'kar dai-dai da halittar jikinsa. Farine dogo bacan ba, kuma yanada karfaffin
kirji ba sosai ba guy ya hadu matuk'ar haduwa.

Sauri² yake yana saukowa daga benen dake cikin k'ayataccin falon nasu. Wata dacci
juwa hakan nagani da shekarunta bazasu daramma 45 b tafito daga wani daki. "Daga
ina haka sai famar sauri kake kamar wanda zai bar 9ja?" Cikin murmushi ya dubeta
yace "Mummy barka da sfia" tace "Yawwa, nace ina zuwa haka sai famar zuba sauri
kake? Incedai gurin daurin auren kayi?" "Daurin aure kuma?" "Ohh harka manta kenan?
Toh na wannan abokin naku Sadiq yake ko wa?" "Ohh Mummy na tina, aa ba daurin auren
zani ba Mummy , yaya Sabir ne ya aikeni skul akan maganar saka Junior a makaranta,
ko jiyama ya tunamin amma na shaafa kinga sai yanzu na fito" yakara sa maganar
tareda dubin agogon dake a hannusa" "ok, naji, bazakaje daurin auren bane?"
"Mummy zanje idan nadawo da huri" Mummy ta kalleshi kallon rashin yarda tace "Hmm
wlhy ka gyara rayuwarka Alhaji! ace mutum baya shiga mutane, sai kace wanda za'a
cinye, idan bakaje nasuba kana ganin idan naka yazo su zasu takoma ne? Wlhy ka
gyara rayuwar ka, mtwss" ta huce kitchen batareda ta ko sake kulashiba.

Shi kanshi yasan Mummy ta fusata, sanin Mummy bazata kulashi yanzu b yasaka shi
kaba kai yahuce.

Pkg spc ya zarce yadauko mota ash, yashiga ya fice batareda ya kula yan uwansa
dake nan harabar gidan suna tattaunawa ba.

15mints ya isa gate din makarantar, mai suna *Brilliant Footsteps Academy*
batareda bata lokaci ba akayimasa iso zuwa office din principal din mkrntr.

Baayi wani wstn tm ba komai ya daidaita, kasan cewar Alhaji yazo da cash ba wata
matsala. Nan aka bashi komai har uniform da littattafan da zai fara karatu dasu.
Godiya yayima principal din yafito.

Tafiya yake tinanin maganar Mummy yake, yasan idan yakoma gida yanzu zatamai fada
baije daurin auren ba. Juyarda akalar motar sa yayi yanufe gidan gonar Dady'n su
dake bye pas.

Horn yayi masu garin gidan suka wangale gate din, sanin ko waye ke horn. Shiga
yayi gadangadan sai inda aka tanadar na ajiye motoci, anan ya tsara tashi yafito
cikin takunsa mai daukar hankali.

Masu gadin gidan sai sannu da zuwa suke masa amma ko yajuyo ya kallesu, hasalima
murtuke fuskarsa yayi, kai kace wani kumarci ne.

Inda aka tanadar na shan iska ya nufa, runfunonine gewaye ta ko ina, can bangarin
na dama wasu stones ne anmusu adu da paint green sak da fulawoyin dake hurin, daya
bangarin hurine dake manne da glass ga tsuntsaye kanana wurin sai kuka suke cikin
muryarsu mai dadi tsoi-tsoi-tsoi🐧

Can daga nesa gadina ce faffada, mai cike da plants kala-da-iri, sai sanyi ke
fesowa tako ina kace cikin a,c ne kake. Kasan cewar hurin kusa da teku ne ga kuma
stream ta bayan gidan.

Cikin runfunan yanufa cike da shauqi, danshi a rayuwar sa yafiso yaganshi irin
wannan hurin da ba wani bil'adam dazai takuramasa. Nan fa ya wuni sai da misalin
karfe 3:30 yafito daga gidan, yakama hanya ya nife gida.

A layin nasune ya hadu da group² na yan unguwar tasu, kasancewar unguwar GRA ce,
baka ganin kowa sai yan kwarorin samari, sun fito shak'atawa. Banda Alhaji danshi
bashida wani aboki ko daya wanda zaace azo a gani. Shi a rayuwar sa yafiso
yakadaita shikadai tillo!

Tafiya yake ko ina yakai cikin layin zai hadu da gungun samari ana zaman layi,
zaman kashe wando, zaman kallon yan mata aga wacece tafi aji ko tafi iya dressing,
hannu kawai yake musu, shima sai idan sune suka dagamai yadaga musu idan ya lura,
dan ko gefensu baya kallo.

Haka yahuce hurin gungun wasu samari sai firar girlfriends dinsu suke. Rage
gudun motar yayi tana tafiya slow².

Har yakawo inda suke, wucewa yayi batareda yace dasu uffan b. Can wani daga cikin
guys din yace "Mazaa gafa nakunnan ya doso!" daya yace "Hmm wai Alhaji kake nufi?"
Guda yace "ai JB ni a rayuwata ban taba ganin mutun irin wancan guy'n ba wlhy,
shikadai yake rayuwarsa, idan ma kakada kanka kayimai mgn toh fa yarfaka zaiyi" nan
wani yanisa yace "ohhh ni duniya! ba aiwa dan Adam dai-dai! Yanzu da ace yana kula
mutane kuma ace ga abinda yayi, miye naku na wani baya kulalaku waye² nd other? Ni
kunga wlhy rayuwar sa tana mugun burgeni, musamman rashin surutunsa, guy'n so
silent miye na damuwarku akan wanda bai damu da kuba".

Sai can dayan yaci "gaskiyar ka Shafson, nima yana burgeni wlhy sosai, shidai
baya zaman layi, baya da surutu bale kace yayi gulmar wani, idan kaganshi yafito
toh masallaci zashi ko fita zaiyi" Shafson yace "toh kagani just face our business
mana" nan fa suka hada baki sukace "hakane fa wizzy"

Shi gogan baimasan miyar da akeshaba, haka ya isa gida a gajiye.

Dadi sosai yaji ganin ba kowa a falo, ya haura sama abinsa. Da shigarsa
birthroom yanufa yatube tufafin dake jikinsa ya sake washa, haka ya kammala wankan
ya fito, waldrop yabude yadauko wata jallabiya milk ya saka, fitowa yayi yanufe
dakin Mummy dayasan sarai ya gama bata mata rai a yau.

Da sallama ya shiga, yatarad tafito daga toilet da alamu wanka tayi ta fito.

Ko kallon inda yake batayiba tacigaba da shafa manta, nufota yayi, yayi hugging
dinta tabaya yace "pls Mummy nasan na bata miki rai, amma dan Allah kiyi hakuri,
dont b sed with me pls" yagama maganar a shagwabe. Ita kanta Mummy yabata dariya
irin yadda ya isa maganar. Amma ta daure tace "Alhaji kenan, kai ba yaro ba amma a
koda yaushi matsalar ka bata k'arewa, nifa mahaifiyarka ce! Idan akwai abinda ke
damunka kasanar min mana".

Cikin ladabi yasauko daga kan gadun yace "wlhy Mummy ba abinda ke damuna, idan
ma akwai kinsan am told u, bazan boye miki komai ba" Mummy ta girgiza kai tace
"dole akwai abinda ke damunka, ni a iya rayuwata bantaba ganin mutun like u b
Alhaji, wannan abin yana jazama karan tsana tsakaninka da mutane. Yakamata kagyara
mana" takai karshe maganar tana kallon sa.
"Toh Mummy, in shaa Allahu i will change" Mummy tasake murmushi irin nasu na
manya tace "Yawwa Baba nah!, wai ina kashiga ne yau tun safe sai yanzu" tabe baki
yayi yace "Mummy naje gidan gona ne nadan rage zango" yafada tareda tashi yakoma
kan gadun, kusa da ita.

Mummy tayi dariya tace "nasan zaayi haka shiyassa ma ban wani nemekaba, nasanka
da gidan gonan nan, zuwa ma zanyi na kerama makekin gida acan kazauna kaida
surukata" "dagaske Mummy zaki? Wlhy ina matu'kar son gidan gonan nan " Mummy tayi
dariya tace "wasa nake kasan sarai Daddynku bazai yarda ba" "Zai yarda man Mummy
idan kika gayama sa" Mummy tace "kaga ban iyawa da sagartannan taka. Kaci abinci
ne?"

Yatsina fuska yayi yace "Yap Mom " Mummy ta dubeshi tace "Ban yarda ba, nasanka
ai bakasan cin abinci ko nan gida nice mai matsama nabaka abaki bale can gidan
gonar waxai baka" "Mummyy, nacifa wlhy" Mummy takai tsaye zata saka tufafinta tace
"Can da kaida cikinka, tunda baka tsoron ulcer" "Bazama ta kamaniba"

Dai² nan aka kira sallar magriba, tsam yamike tsaye yace "Mummy bara naje nayi
sallah" Mummy tace "toh adawo lfy, ayo muna addu'a" yakai k'ofa yana cewa "kullum
anai muku ai Mummy, fatan mu dai Allah yasa munayi a bakin mala'iku" Mummy tace
"Ameen Baba nah" yafita.

```Nasan masu karatu zasuso sanin wanene wannan ALHAJI❓Musamman Manshart novels
akwai son jin kwakwaf😉 toh kubiyo BASAKKWATA```😜

*Ⓜªŋşħªŕŧ ŋºvęłş📚*
[3/18, 10:59 AM] Manshart: *MISKILANCI KO GIDADANCI*❓

```Written by Manshart💘```

~In dedicated to my luvly Dady (Alhaji) nd Mummy (Bissalam)~

*{Đïş ïş mý şęĉºŋð ŋºvęłş}*👌🏽

*Part 2*

*Usman Abubakar Ibrahim*


Shine asalin sunansa. Mahaifinsa Alh. Abubakar , dan asalin garin Bissilam ne,
acikin babban birnin sakkwato. Mahaifinsu sunansa Ibrahim wanda ake kira da IBRO
yanada mata 1 mai suma khadija, khadija yar uwar IBRO ce, auren Zumunci ne akai
musu.

Inda ankayi aure wata tara ta zankado danta mai kyau na ji da fada. Kasancewar
fulani ne dukkansu, haka ran suna yaron Inna khadija yace suna Abubakar, bayan
shekara biyu ta haihu mai bima Abubakar wato Sulaiman, bayan wasu shekaru Allah
yabata zankadediyar budurwa wacce taci sunan mahaifiyar Ibrahim wato A'isha.

Sun samu gata da kulawa sosai, dan kuwa malam IBRO mutun ne mai zafin nema, baya
wasa da iyalansa ko kadan. Aduk fadin garin ansan malam IBRO mutun ne na mutane, ga
mutunci da karramawa. Haka kuma dansa Abubakar yagadosa, sai Sulaiman shima
baabarsa a bayaba. Haka Aisha yar autarsu wadda dagareta Inna khadija bata sake
daukar wani cikiba, Allah yawa Aisha kunya sosai.

Rayuwar su suke cikin jin dadi da kwanciyar hankali, malam IBRO yasakasu
makarantar yaki da jahilci ta garin, ba laifi suna ganewa duk da makarantar
government ce bawani kulawa sosai akeyi ba.

Inda Abubakar yana primary 5, Sulaiman na primary 4, auta na primary 1. Inna


khadija tana matu'kar son yar tata, a cewarta auta ce har tamaidata auta. Abubakar
yana ji da A'isha, komai yasiyo A'isha dai A'isha, ba abinda ke rabashi da ita.
Bacci ma a daki daya sukeyi, idan yafita yayo kwadagonsa A'isha zai yoma siyayya
yakawo mata, shiyassa itama takeson hamma Abubakar, idan yafita komai hamma
Sulaiman yayi mata idan Abubakar yadawo zata sanarmai sai ya ramo mata.

A kwana atashi Abubakar yakammala primary skul, kuma jarabawarsa tayi kyau, haka
ya shiga bording school Jss 1 a *Government day secondary school Bissilam* karatu
yake sosai. Yana final exams dinsa mahaifinsa yarasu.

Inna Khadija tayi rashin mijinta mlm IBRO wanda kowa a garin yasan shi mutunin
kirki ne. Bayan Abubakar yakammala jarabawarsa yadawo gida yatarad da mugun labari
na rasuwar mahaifinsa! Wanda yayi kuka sosai da bakin cikin rasa mahaifinsu.

Bayan wata 1 result dinsa yafito na waec da neco dinsu. Kuma yace credit sosai
kusan duk credits dinsa A ne sai can zakasamu B. Gomnati ce tadauke nauyin
karatunsu kasancewar Abubakar yanada kokarin sosai, yana dai daga cikin wadanda ake
alfahari dasu a makarantar.

*USMANU DAN FODIO UNIVERSITY SOKOTO (UDUS)* acan yajona yacigaba da karatunsa a
Inda yakarance business education. A can ya hadu da Shafa'u wadda suka fara
soyayya! Shafa'u yar asalin skt ce. Bayan sun kammala degree ne Abubakar yasanar ma
iyayensa akan maganar Shafa'u, Inna Khadijat ta amince da maganar kuma ta yaba da
hankalin ta. Baba Hamza ne kanin margayi Ibrahim yajagorance auren, Inda aka biya
sadaki aka saka ranar aure.

Ba laifi Abubakar ya hada kayan lefe duk da ba wasu kaya ne akeyiba, kasancewar
ma su Shafa'u a birni suke, suna irin yar riyar nan ta aure. Abubakar baiyi wata
riyaba cos kar-tasan-karce tsakanin sa da Shafa'u, tasan ko waye Abubakar ba wani
haline dashiba.

Haka akasaka ranar aure Rabi'ul-auwal. Shirye²n aure akafara tsakanin bangarin nan
guda biyu. Barin su Inna Khadijat da wannan shine farko, su auta sai murna akeyi
hamma Abubakar zai aure yar burni, lolz.

Akwana atashi asarar mai rai! Yau takama Asabar acikin watan Rabi'ul-auwal.
Dinbin alumma suka shede dauren auren *Abubakar Ibrahim* da *Shafa'atu Usman* anyi
taro lafiya, inda yan uwan Inna Khadijat sukazo sokoto dan ganin gidan amarya
sakamakon skt Abubakar yazauna Dan yanaso ya cigaba da masters dinsa anan. Auta
tayi tsayin daka akan sai anje da ita taga matar hamma Abubakar, badason Inna
Khadijat ba, yan uwata suka turza akan abarta taje tunda suna tare ai zasu sawota a
gaba su dawo da ita.

Kaddara ta rigaye fata! Bayan sun iso sokoto garin fitowa mota auta ta subuce
musu, aka nema aka rasa Auta, yan uwan Inna Khadijat kasa komawa sukayi Bissilam
sbd jin kunyar yanda zasu tunkare Inna Khadijat da maganar batan yarta!

Haka aka sanar ma Abubakar da har kwanci saida yayi asibiti sbd girgizar dayayi
na rashin kanwarsa tillo wadda yafiso fiye da komai na duniya. Barin Inna Khadijat
wadda shine sanadiyar jininta yayi up! Daga karshe dai shine musabbabin rasuwar
Inna Khadijat!

Abubawa goma-da-goma suka tararrama Abubakar, bakin ciki baya kwana kullum sallah
yake yana rokon Allah yasake hada tozalin idanunsa Dana Auta. Abubakar dai rayuwar
auren zan iya cewa alhamdulillahi dai! Sulaiman yadauko suka dawo nan skt din da
zama.

Allah majirokon bawansa (akoda yaushe abinda Allah yabawa Dan adam shine mafi
alkhairi agareshi! So dayawa mutun zaiyi addu'a yadawo cewa: wlhy nayitayin addu'a
amma Allah bai amsaba! Toh musani Allah yayi alkawarin duk lokacin da bawansa
yarokesa da ihlasi zai amsa masa. Wani zai iyayin addu'a ta Allah ya azurtashi,
shiko Allah yafika sanin abinda yafi dacewa dakai. Mai yuwa idan Allah yabaka
arzikin yazamoma hanyar dazata jaka zuwa wuta! Zaka iyayin sabon Allah cikin
arzikin ka, kasha giya, kaje gidan rawa, kayi zina, da sauransu. Amma sai Allah
yajuyema wannan addu'a dakayi ta dukiya tazamto# idan Allah yarubuta cewa zaka fita
kayi accident ka kakkarye a k'afa da hannu! Toh sakamakon wannan addu'ar dakayi sai
Allah yasa kana tafiya kadanyi karo da dutsi kan hanya ya jima cewo kadan! Kaga ai
ko nan Allah ya amshe addu'ar ka. SBD hk yan uwa ako yaushe mukasance masu komawa
ga Allah masu kaskantar dakai ga Allah, masu kyautata zato ga Allah.)

Allah yabaiwa Abubakar aiki awani company ba laifi yana samun albashi mai tsoka
wanda yake ciyarda matarsa da dan uwansa.

*Ⓜªŋşħªřŧ ŋºvęłş📚*
[3/18, 10:59 AM] Manshart: *MISKILANCI KO GIDADANCI*❓

```Written by Manshart ```💘

~In dedicated to my luvly Dady (Alhaji) nd Mummy (Bissalam)~

*{Đïş ïş mý şęĉºŋð ŋºvėłş}*👌🏽

*Part 3*

Haka rayuwa taci gaba da tafiya yau dadi gobe ba dadi! Har Allah ya baiwa Shafa'u
ciki, wata tara ta haihu danta mai suna Sabir, sai kuma bayan shekara biyu tasake
haiho yarta mai suna Zainab. Ta jima bata koma haihuwa ba.

Abubakar arziki sai karuwa yakeyi, har yasake wani aure. Yanzu mata biyu ne
dashi, Shafa'u da Saratu.

Saratu tanada 'ya'ya 2 itama amma duk mazane Jabir da Saddiq.

Bayan wadansu shekaru Allah yabaiwa Shafa'u ciki mai cike da laulayi, tunda tasamu
cikin bata aiki ko kadan, wani fitinannin cikine Allah yabata, Shafa'u tadai gode
Allah da wanga cikin, har ta fidda rai ga rayuwa a duniya.

Sai da aka samo mata mai aiki tadinga tayata aikin gida da rainun yaranta 2.
Kasancewar itama Saratu cikin ne da ita, kusan duk watansu daya.

Zuwa² ciki yakai watannin haihuwa! Ohohooo! Ranar wahala tadawo sabuwa, duk wanda
yadube Shafa'u da wannan cikin sai ya tausaya mata. Ranar jumu'a da misalin karfe
11am nakuda tataso gadan²n, kuma Abubakar yafita aiki, sai Saratu da mai aiki
kawai. Hankalin su yayi matu'kar tashi ganin Shafa'u tana cikin tsananin wahalar
naquda, da taimakon Allah Shafa'u ta haihu da misalin 3pm.

Tirkashiiii karkuso ganin wannan hadaddin baby'n, masha'Allah! Haka akayima yaron
wanka aka kimtsashi, tsintsar kyaunsa yakara bayyana, duk wanda yazo ganin yaron
sai ya fita da maganar kyawonsa. Abubakar yaji dadin ganin wannan baby'n nashi mai
kama da kanwar sa A'isha sosai, lokacin batan auta yadawo mai a rai. Ran suna dan
yaci sunan mahaifin Shafa'u, wato *Usman* kasancewar Abubakar yayi mata alkawarin
saka sunan mahaifinta. Amma Alhaji suke kiransa, sbd shima mahaifin Shafa'u haka
ake kiransa. Shafa'u taji dadi sosai na saka sunan mahaifinta.

Sati 1 da haihuwar Shafa'u Saratu tahaiho yarta tubarkalla! Wadda ake kira
Labila. Bayan Labila Saratu ta haihu twins mace da namiji Husnah da Alhasan.
Haj Shafa'u tana matu'kar ji da wannan dan nata, batasan ganin bacin ransa ko
kadan. Duk da bayan hauhuwarsa Shafa'u tayi haihuwa 2 A'isha wadda Abubakar ya
sakamata, sa'annan autar Mummy Shafa'u mai suna Sajida .

Shekaru sunja, Sabir yayi aure da matarsa mai suna Kubra har ta samu haihuwa da
namiji Abdullah, Zainab ma tayi aure a Kaduna. Tanada yara biyu, Musaddiq da
Sadiqa.

Jabir ma yayi aure da diyarsa Munawwara. Sai sadiq dayake kanyi a yanzu.

So da gata Mummy take bawa Baban nata sosai.


Amma sai dai kash!!! Alhaji yanada wata rayuwa, wadda kowa a familynsu yakejin
haushinsa bayason surutu, baya magana sai tazama dole, ko waye kai Alhaji baya
zama yayi fira dakai, Mummy ce kawai yake iya zama suyi fira, itama sai idan ba
kowa a dakinta zai shiga suyi fira, ga matsananciyar kunya harta tashin hankali!
Duk yadda zan zayyana muku irin kunyar Alhaji toh ya d'aramma can. *Miskiline* na
karshe! Dariya ma wahala take bashi, bale ya zauna ayi fira dashi.

Wannan shine cikakkin tarihin Usman wanda akafi sani da *Alhaji*

*Mun dawo labari*💃🏿💃🏿💃🏿

Misalin karfe 8 na dare, kwance yake kan bed dinsa, yana duba wadansu takardu, ga
alama wani abun yake nema.

Guntun tsaki yaja tareda daukar takardun ya tusasu a locker, yadawo yakwanta
yajawo wayarsa ya kunna data. Sakone turoro suke famar shigowa ba full stop, jiran
su yayi saida suka gama shigowar dasuke yafara chart abinsa.

Duk da ba kowanne grp yake magana ba, grp daya yake magana shima gaisu kawai
yake yafito nanufe istgrm ko Facebook IMO da BBM da sauran su.

Yau kam fitowa yayi yanufe browser domin yin browsing, karar shigowar message
yajiya ta WhatsApp dinsa. Sharewa yayi yaci gaba da aikin gabansa. Bayan minti 5
wani yakara shigowa, tsaki yaja yafito daga browser yanufe WhatsApp din dan ganin
wannan no din data dameshi. Yatsine fuska yayi ya dallama no din harara, yafito
yaci gaba da browsing dinsa.

Sai karfe 10:15pm yakashe data yahau baccinsa cikin kwanciyar hankali.

Ita kuwa haushi taji. a ranta tace "wannan wani irin dan rainin hankali ne? Ko
waye mai wannan no yacika MISKILI! Mtwssss" taja tsaki ta kashe datar ganin shima
yadade da sauka. Littattafan ta tajanyo taci gaba da muraji'ar ta dan gobe zasuyi
jarabawa a islamiyya.

*Ⓜªŋşħªŗŧ ŋºvėłş📚*
[3/18, 10:59 AM] Manshart: *MISKILANCI KO GIDADANCI*❓

```Written by Manshart ```💘

~In dedicated to my luvly Dady (Alhaji) nd Mummy (Bissalam)~

*{Đïş ïş mý şęĉºŋð ŋºvełş}*👌🏽

*Part 4*

Washe gari tun da sassafe tashirya, cikin shigarta ta uniform na islamiya. Kafin
lokaci yacika, karfe 10 zasu shiga jarabawa. Kan gado ta haura tajawo wayarta P6
tahau chart.
Prvt dinsa ta nufa ganin yana online tasake turamai sako kamar haka:
*Barka da asuba*
Bai duba sakon ba kasancewar yau ma yana Instagram. Tsaki yaja ganin wannan no
dince tajiya tadameshi! Sherewa yaso yayi amma sai zuciyar sa tace dashi "tayu
alkairine ke bebiyarka! Kaduba" a fili ya furta "wani alkairi kuma"

Shiga yayi takan mssg dinta yadubasu kamar haka:


*Assalamu alaikum*
*Wai baa magana ne😏*
Sai kuma nayau data tura shima na barka da safiya.

Murmushi kawai yayi, yashiga yimata reply:

*Wslm*
*Wake mgn?*

Farin ciki fal a zuciyarta, dan ita ko ba komai tanaso tasan waye mai wannan no din
datasamu kan wayarta. Amma saida taja tsawon minti 5 kafin ta mayar da reply.

*mutun ne🙄*

Dariya ma tabashi, ganin wannan karfin halin irin nata, domin kowa dagani wannan
mace ce. Shima mayar mata yayi da nashi martanin;

*Ke kikama kanki😏 wakike nema ne?*

Ido waje take kallon wayar, ta tuntsore da dariya, tace a fili "Ashe ma shidin dan
duniya ne! Toh nafika iyawa wlhy muje zuwa" tamai reply:
*Mai wayar nake nema🙄 idan ba damuwa abashi wayar muyi mgn*

A fusace yace;.
*"Ke kikama kanki😡 waye mai wayar idan baniba? Kajimin yarinya sai kace tasamu
warinta"😏*

Itama din a fusace tace:


*"wacece yarinyar"😡?*
*"Ke mana😏"*
*"Hmm...lallai ma yaro bakasan dawa kake mgn ba"*🤒
*"Kece zance bakisan dawa kike mgn b, ni nan nafi jika dake"*
*kutumar!....😳 kakuwasan koni wacece😳"???*
*"Toh wacece ke? Koke ifritu ce bazanji shakkarki ba yarinya"*😏
"😔😭😰"
*"Hhhh lfy dai"?*🤔
*"Banasan ana kirana da yarinya😟"*

Dariya tabashi sosai a zuciyar sa yace "wannan wace irin yarinya ce da barkwanci
hk" reply yamata;

*"Idan bakyaso akiraki da yarinya me kikeso akiraki dashi ne?"*🤔


*"Babba💃🏿💃🏿💃🏿"*
*"😂😂😂ke bakiji kunya bama?"*
*"Kunya tami kuma😳 ni ba yarinya bace😏"*
*"toh tsohowa😜"*
*"😳 uhmm ni...ni..nii banaso😰"*

Dariya takara bashi a karo nabiyu daya kara tabbatar cewa wannan yarinya duk yadda
akai sagartacciya ce.
*"😂😂😂😂😂An fada tsohowa😝"*
*"sai nagayama yaya na kace dani tsowowa😒"*
*"Koma kin gaya masa bazai yardaba ai😅"*
*"😳😳zai yarda man, nifa yar gatace👯"*
*"Yarinya nafiki zama dan gata😏"*
*"Huum🙄ni banyarda faa" 🤒*"

Nan fa sukayi fira sosai.

Wani yaro ne yashigo yace "Aunty kizo muje skul har lokaci yayi fa" "toh Ladib
ina zuwa" yace "to" yafita.

Juyawa tai takan wayar tata tace:


*Zanje skul bye🙋🏼*
*Toh adawo lfy 😏"*

Kashe wayar tayi tabarta a nan tafige papers dazata amfani dashi tafito.

A falo tasume wata daccijuwa ta sunkuya tagaidata "Mama barka da asuba" kallon up
nd down tamata tace "barka, kinacan tushe a daki sai kace mayya! Yara duk sun fito
amma ke a koda yaushe kina cikin daki dauke da wannan mugun hijabi, tashe kifice
tun kan sutafi" "toh mama" kawai tafada tatashe tafara tafiyarta mai cike da
natsuwa da daukar hankali.

A mota tasamesu, kowa yashiga ita kurum ake jira ta iso. A gaba tashiga, dama kowa
da permanent set dinsa, driver yajasu suka nufe skul.

Alhaji kuwa bayan tasauka shima yasauka. Fitowa yayi yanufe dakin Mummy, koda
yashiga batanan yafito yanufe falo. Nan ma shiru sai junior kawai daya mayarda
hankalinsa da games.

Nufoshi yayi, yashafa sumar Kansa, a tsorace yadubeshi yasaukar mai murmushi tare
da cewa "uncle morning" "morning hw par" "5yn uncle" "Gud! What're u doing?" Dariya
Abdallah yayi yace "games nakeyi" "Mummy fa?" "Suna can suna breakfast a dining"
"Ok, kaifa?" "Ina jiranka ne" "ok, wait let me come, yanzu zanzo muyi breakfast
din" Abdallah yace "zan bika muje"

Hannun sa yaja suka nufe part din Daddy. Knock sukaji dady yabasu izinin shigowa.
Shigowa sukayi yana janye da hannun junior, Sabir da Jabir suna cikin falon na dady
harda Saddiq ma. Suna tattaunawa kasancewar yau weekend ba aiki, sai dady dazaije
kasuwa zuwa anjima.

Ba haka Alhaji yasoba, dan shi bayasan idan yaje wurin daddy yatarad da mutane a
ciki, ko yanzu ma dan yariga yashigo ne. Sunkuyawa yayi yace "Dady barka da asuba"
"Alhaji antashi lfy" "lafiya klu dady" "Masha'Allah" junior yanufe kan dady
yarikeshi. Shima suka gaisa.

Komawa yayi kan Sabir yagaidashi, ya amsa cikin kulawa yace "bazakaje ka gaida
momyn kaba?" Junior ya girgiza kai yace "bazan jeba sai tareda uncle junior😥"
Jabir yayi dariya yace "Ohhh! Lallai kana dauke da babban aiki" Sabir yace "babba
ma kuwa, Alhajin ne zai tafi gidan momyn ka" junior yace "eh, yace zaikaini mutafi
a tare😒" Daddy dake saurare dasu yana dariya yadube Alhaji daya sunkuyar da kansa
a k'asa ko murmushi bayayi. Sadiq kuwa ko tankawa baiyiba yasan ko waye Alhaji.

Mekewa yayi a tsaye yajuya zai fita, dady yace "ina zuwa koma Alhaji?" Hannun sa
yasaka a sumar kansa yafara murjawa yace "Breakfast zanje nayi" dady yace "Ok, yayi
kyau" junior yabishi a baya yanaima su Dady hannun a baya alamar zasu tafi.

"Hmm... Waini wannan wani irin yaro ne🤔 narasa abinda ke damunsa" dady ya fada
hade da kallon su Sabir dake falon. Sabir yace "Duk zai wuce *MISKILANCI*😏" dady
yace "Aiko zanyi maganin wannan *Miskilancin* nashi"

Da fitowar su dinnig area suka nufa, nan suka tarad da su mummy suna breakfast
suna fira cikin farin ciki tareda Haj Saratu wadda suke kira da Umma, sai su Labila
daAisha tare da su twin's.

Kasa isowa yayi kan dining din, yana k'okarin komawa. Mummy ce ta kwala masa kira
yadawo, ya sunkuya ya gaidasu, Umma ce ta amsa domin kuwa Mummy a fusace take tace
"Da komawa zakayi ne? Wato kaga makiyanka ko?" "Haba Haj Shafa'u kidaina fadin haka
mana, kidaina biyewa masa, harkace ta yaro" Umma tafada.

A fusace mummy tace "dan Allah Haj Saratu kidaina kamamasa, Alhaji ne yaro? Aishi
yakamata yadinga yima kanninsa fada idan suna irin wannan abun" Umma tanisa tace
"Haka ne kinsan kowa tashi rayuwa daban Allah yayi masa" Mummy taja tsaki. Hannun
junior yaja dayaketa famar games suka bar gurin.

Umma tace da Labila takai masa can dakinsa. Mummy tanisa tace "Ohhh ni Shafa'u🤔
narasa mike damun yaron nan *MISKILANCI KO GIDADANCI*❓🤔🤔

*Toh nima dai Manshart tambaya nake*😉😜

*Ⓜªŋşħªŗŧ ŋºvęłş📚*
[3/18, 10:59 AM] Manshart: *MISKILANCI KO GIDADANCI*❓

```Written by Manshart💘```

~In dedicated to my luvly Dady (Alhaji) nd Mummy (Bissalam)~

*{Đïş ïş mý şęĉºŋð ŋºvęł}*👌🏽

*Slm...fans part 4 najiyane daban samu damar typing ba😌 amma gana yau good9yt😴*

*Part 5*

Sai bayan shigarsu skul da 30mints aka fara jarabawa. Tsit kakejin skul din kowa
yana cikin aikin rubuta jarabawa ba kama k'afar yaro.

Zauna take kan set dinsu dama su 2 suke zama itada kawarta Fairuza. Fairuza
itakadai ce frnd din ta duk fadin skul din, tasan halin mutuniyar tata batasan
surutu, akai saa itama Fairuza ba gwanar surutu bace. Zana jarabawar ta take cikin
kwanciyar hankali, 5mints takammala tatashi takaiwa mlm Yusuf dayake shine yake
tsaron class dinsu.

Ido waje yake kallon ta yace "M Bissalam har kin gama ne" batare da tako kalleshi
ba tace "Eh" tafita. Da kallo yabita yana mamakin k'okari irin na M. Bissalam. Duk
yan class din suka bita da kallon tsana, sai Fairuza kawai datake binsu da kallon
tuhuma. Can wata a kusa da set din su Fairuza tace da kawarta "Fatima wai kinga mlm
Yusuf yanda yake ma M. Bissalam?" Wadda aka kira da Fatima tace "Hmmm naji kawata!
Harda wani cewa harkin gama, baisan dacewa dama anyi copy a gida b😅" wadda tai
maganar tace "kedai fadi, aimu munsan kar! Ba abinda za'a nuna muna"

Fairuza duk tana jinsu kaf har sukasa kai aya. Tajuyo a fusace tace "tsofaffin
algumgumai, toh inajinku, kuma bakin cikine kukeyi da ita dan kunga tanada k'okari
ba kamar kuba masu dak'ik'in kai, munafukai!" Fatima tace "ke kuma awa? Da shigar
sharu ba shanu😏, ai naga kemadin ba wani kulaki takeba, kece kike makale da ita"
Nan danan ran Fairuza ya tafarfaso tawawaso huyan Fatima. Nan fa class ya surnike
da fada.
Mlm Yusuf da shi tinaninsa baya kansa, yafada tinanin wannan dalibar tasa dayake
matu'kar so a rayuwarsa. Can yajiyo hayaniya class yasurmuke, "Kaiiii mike faruwa
ne?" Ganin Fairuza takama huyan Fatima sosai har idanuwanta sun canza kala yasa mlm
Yusuf k'arasowa yace da Fairuza tasake huyan Fatima.

Dakyar tasake, sai saukar da numfashi take tana cika tamkar wata damisa. Waje
yafiddasu duk yace suyi kneel down, ya amshe papers dinsu, Allah yasa Fairuza saura
Q1 takarasa dama 10Qs ne answer 8Q kasancewar jarabawar karshe ce sukeyi.

Fita sukayi waje acan ma bakin Fatima bai karaya ba duk da zazzafar shaqar
datasha. M Bissalam kuwa batasan wainar da ake tuyawa ba, sbd bayan tafito ne sako
yazo mata cewa principal dinsu yana nemanta tatafi.

Sai bayan kowa yakammala mlm Yusuf yafito yatuna dasu, danshi harya manta dasu
ma. Warning yamusu akan idan suka sake fada acikin class ana jarabawa sai yakoresu
mkrntr baki daya.

6:00pm
Bayan sun fito ne Fairuza take gayama M Bissalam abinda yafaru. M Bissalam tace
"haba Fairuza, miyakaiki kulasu ma har takaiku gayin fada a class, gashi yanzu
kinyi asarar first exam dinki kuma kinsan muna term din karshe ne a mkrntr nan"
Fairuza tadubeta taturmuke fuska tace "dan muna term din karshe sai nabari acimiki
mutunci😡" M Bissalam tace "Aa ba hk nake nufeba, kinsan fa dama ni black blood ne
dani a class din Fairuza yakamata ace kin saba da tsangomar da yan class dinmu
sukemin kamar yadda Nima narigaya na saba" Fairuza tace "wlhy bazan iyaba, bazan
taba zuba ido naga ana kuntatamiki ba a rayuwa, me kikaka tare musu ne? Kodan kawai
bakya kulasu ne?" M Bissalam tace "kema kinsani ai Fairuza, kinsan rashin mgn ta
ita take jawomin bakin jini ko ga yan uwana, da ace inada yadda zanyi nagyara
zamana da mutane danayi Fairuza" takai mgn kamar zatai kuka.

Tausayi tabaiwa Fairuza tace "karki damu kawata, in shaa Allah komai zaikoma
normal wata rana. Nan fa Safara'u takwalla mata kira saida ta juyo a tsorace.
Fairuza tabuga tsaki tace " wlhy wannan sis taki haushi take bani, irin yadda take
miki dinnan yayi yawa Bissalam " murmushi tayi tace "karki damu Fairuza, wata rana
sai labari.

Haka suka kai gate, sukayi sallama kowa yanufe motar su da drivers din su duk sun
iso tun tuni. A cikin mota kuwa su safara'u da Ummi sai fada suke ma M Bissalam,
wai tana walakanta mutane. Itadai ko uffan batace dasuba kamar Ladib dashima bai
kulasuba yanadai saurare.

Da isar su suka tarad da mama falo tana hutawa. Ita ce tafara shigowa ta sunkuya
tayimata barka da gida. Fuskar mama ba yabo ba fallasa ta amsa " lfy" tahuce
dakinsu, Ladib ma hk ya gaisheta shi ko kulasa batayiba yagaji yabi yayarsa
dakinsu.

Su Ummi da Safara'u kuwa da shigowar su ba ko sallama Safara'u tahau kan mama


Ummi ta yarda bag dinta kan kujera tazauna tareda cewa "wash!" Mama takalle yaran
nata cikin jin dadi tace "sannunku da zuwa, ya jarabawar?" Safara'u dake kan
cinyarta tace "mama jarabawa sai a slow wlhy" Ummi tace "ke zaki fadi hk ko ni,
nifa mama Q10 fa kuma duk sai mun amsa duka" mama ta fito da ido tace" sbd tsabar
mugunta? Toh yaya kin amsa gaba daya"? Ummi tayatsina fuska tace "nadai amsa
abinda ya sawwaka mama" mama tace "toh ita waccan fa?" Ummi tace "Hmm kinsan fa ita
copying takeyi dataje sai kawai ta fidda ta bayar, sai aita ganin k'okari ne da
ita" a fusace mama tace "su malaman basa ganewa ne? Wadanne irin malamai ne
wadannan?" Ummi tace "kamar sonta sukeyi mama, shiyassa duk akai jarabawa itace mai
debo ta daya a class dinmu" mama tace "tabdi! Lallai zanyi maganinta, ku tashi
kushiga ciki ku watsa ruwa kufito muci abinci" duk sukace "toh mama"
Ita kuwa da shigarta daki bathroom tanufa tawatsa ruwa tafito. Shirya wa tayi
cikin wata red gown, abinci sukaci itada Ladib yafita, tazo ta kwanta kan kujerar
dake dakin tafara nazarin jarabar da zasuyi gobe.

Ladib ne yashigo yazo kan kujerar ya kwanta kan ruwan cikin ta. Cikin sanyayyar
muryarta tace "haba Ladib, ai wannan sai ka fasamin ciki🙄" Ladib yayi dariya yace
"lalala! Taya zan fasa cikin ki narasa Aunty nah😉 kinsan nasaba ne" "toh amma ai
yanzu ka girma kayi nauyi kazama tula😚" "uhm...ni aunty maryam ban girmaba, har
yanzu ni yarone 12yrs fa😒" ring din wayar ta ce takatse firar.

Dubawa tai bata gantaba, Ladib yashiga dube² ko zai ganta. Can yaga hasken
flashlight dinta a karkashin filo. Kan gadun yadira yadauko yakawo mata, kafin
lokacin takatse. Duba mai kiran tayi ganin Yaya Ma'aruf tagane manne kan screen din
wayar. Tashi tayi zata fita tajuyo tace da Ladib "ina yaya Ma'aruf yake?" Ladib
yace "yana dakin sa, yanzu na karbo mai credit kantin Ya'u". " Ok, kashiga kayi
wanka kafin nadawo muyi muraji'a" "toh" Ladib yafada yafada bathroom.

Fita tai bata sameshi ba tadawo tadau wayar t tafara chart. Ganin yana online
yasa ta cikin hanzari tamai mgn kmr HK......

*Kubiyo BASAKKWATA*😜

*Ⓜªŋşħªŗŧ ŋºvęłş📚*
[3/18, 10:59 AM] Manshart: *MISKILANCI KO GIDADANCI*❓

```Written by Manshart ```💘

~In dedicated to my luvly Dady (Alhaji) nd Mummy (Bissalam)~

*{Đïş ïş mý şęĉºŋð ŋºvęłş}*👌🏽

*Part 6*

Zata turamai ne taji kiran Yaya Ma'aruf, datar takashe da hanxari tatashi
tafita.

A tsaye ta tarad dashi bayan ta gaidashi yace "kisameni dakina" tana sunkuye
dakai tace "toh". Gaba yashiga tabishi a baya, har suka iso dakin nasa. " dama
typing zakimin, na wahala yau a skul" murmushi tayi tace "OK..."

Fita yayi daga dakin, tajawo system din tafara aikin typing din project dinda
yasakata. Kiran sallah taji, ta ajiye tanufe toilet dinsa ta dauro alwala tafito ta
shimfida sallaya ta fara sallah.

Shima kiran sallah dayaji ne yasakashi kashe data yafito. A kofa ya haduda junior
yana k'okarin shigowa. "Laaa uncle junior dama kai nazo kira muje masallaci" "Nima
kai nake kokarin kira, hp kayi alwala?" "Tun tuni ma" hannunsa yariko suka sauko a
tare.

"Ina zuwa?" "Zamuje masallaci ne Mummy" "toh adawo lfy. Ohhh Abdallah akwai son
zuwa masallaci🤔" dariya junior yayi yace da Alhaji "uncle zo muje kada Mummyn nan
tasa mu makara🙄" dariya Mummy tayi harsu Labila ma dasuke falon. Watsa musu harara
Alhaji yayi sanin halinsa yasaka su tashi kowacce ta nufe dakin su domin yin
sallah. Suko suka fita.

Bayan ta kammala sallah takoma kan system din tacigaba da typing. Ladib ne
yashigo, "Shine kika barni acan sai jiranki nake muyi karatun😒" batareda ta
kalloshi ba tace "am sorry my Ladib, yaya Ma'aruf ne yasakani typing" karasowa yayi
kan kujerar ya zabce papers din datake typing dasu yamayar bayan sa "bani nima nayi
typing din🤕" "kaga, kabarni na idamai mana Ladib" "gaskiya ni aunty Sadiqa sai na
koya😟" "nace kabani, zan koyama wata rana mana" "promise?😥" "I promise u".

Handouts din yabata, yasamu guri yazauna yana kallon ta. Ita kuwa typing taci
gaba, sai surutu yake mata yana bata lbrn jarabawar tasu, sai jifa² take tankamai.
Ya Ma'aruf ne yashigo, yakaraso inda suke yace " dis is god my sweet sis😍"
murmushi tasakar mai, shine babban goronta da mutun, dariya kyautace babba agareta.

Ladib yaduba daya mayar da attention dinsa a system din kace shine ke typing
din. "Ladib" da sauri yajuyo yakallesa yace "naam yaya😎" "Kai ke aikin ne naga
kawani mayar da hankali ga system din?" "Aa ya Ma'aruf😅 koya nake😢" dariya
Ma'aruf yayi yace "toh kada katakura mata dai nasanka da surutu kamar aku".

Tashi tayi a tsaye, tace " Ai yaya nama kammala" godiya Ma'aruf yamata tafita
batare da taĉe uffan b, Ladib yabiyota suka fito a tare. Falo suka tarad da mama da
iyalanta suna kallo, dama shine kawai aikinsu. "Kee zo nan" jikinta na bari tazo ta
durkusa "daga ina kike?" "Mama yaya Ma'aruf ne yasakani ai..." "Rufamin baki
munafuka, dama kinyo gado a..." "Haba mama! Wannan wani irin abune hk, dan Allah
kidinga safsaftawa yarinyar nan mana" "iyaaa lallai Ma'aruf😳! Ni zaka nunawa sonta
kake🤔 Toh ai sai ka aure ta na tabbatar da sonta kake" "haba mama wannan wace irin
maganace kike dan Allah? Maryam fa kanwata ce taya zan aureta?" "Eh to, son natane
naga yayi yawa. Ai nazata aurenta zakayi" Safara'u tace "Nima dai abunda nagano
kenan" Fyyyyyau kakeji sautin mari! "Ma'aruf ka mareta akan wannan kucakar
yarinyar *BAGIDAJIYA*?" Ma'aruf sai huce yake yace "wlhy idan takara saka baki
cikin maganar nan saina kakkaryata" "ehhh lallai Ma'aruf! Albasa batai halin ruwa
ba wlhy, inaga mamana dakasha furzar dashi kayi."

Bai kara tankawaba yadube maryam da tune hijab dinta yayi sharkaf da hawaye yace
"ke tashi kifice" tashi tayi kamar wadda kwai yamatamma a ciki ta nufe dainsu,
Ladib da shima kukan yakeyi yabita da baya. Tsaki Ma'aruf yayi yafice zuwa dakinsa.
"Wlhy dani kake zancin Ma'aruf, zan gwadama ko wacece Rakiya a gidannan, matu'kar
kasake tabamin 'ya'ya" baiko kulata ba yafice daki da takai cin mahaifiyar tashi
fal a zuciyar sa. Irin yadda take wahalar da marainiyar Allah!

Da shigarta dakin, gado ta fada tayi kuka mai isarta, Ladib sai hakuri yake bata
shima kukan yakeyi dakyar tayi shiru. Karatun darasin da zasuyi jarabawar sa gobe
tayimai bita, yaci gaba da muraji'ar ita kuma tahau chart.

Su Alhaji basuda shigowa gidaba sai da akai sallar isha. Dakinsa yashiga shida
junior dayayi tsayin daka lallai² sai dakin uncle junior zai kwana a yau. Duk fadin
gidan ba wanda Abdullah yashaku dashi irin Alhaji, duk da *MISKILANCIN* Alhaji yana
kula Abdallah, wanda yake kira da junior, shima yake kiransa uncle junior. Abdallah
baya kula da kowa har mahaifinsa Sabir idan yana tareda Alhaji, har mahaifyarsa ma
sai tayi wata bata saka Abdallah a ido ba! sai idan shine yatafi dashi gidan suka
gaisa sudawo sakamakon gidan yake dazama.

Bayan sun gama fira junior yayi bacci yadauko wayarsa, dan idan har junior na
falke toh ba mgnr chart, zai ishesa da tambaya ne.

Yau sati daya kenan da haduwar su a social media, amma har yau ba wanda yasan
sunan wani a cikinsu. Kamar kullum yauma tun da saffafe ta hau online domin yanzu
har sun saba sosai dashi. Amma har yau *MISKILANCIN* su yagagara barinsu tambayar
juna sunayensu.

Amma ayau ta kudurce sanin ko waye wannan da kullum cikin tunaninsa take!

Itace tafara masa mgn, bayan sun gama gaisawa da barkwancin su irin wanda suka
saba kullum tace. "dan Allah zan iya tambayarka?" "mizai hana" yace da ita. Juya
idanuwanta tashiga yi kamar tana a gabansa kan tace "Sunanka nakeso nasane idan ba
😉 dariya tabashi sosai yace "sunana tsada ne dashi sai an biya😒" "hw mc?😒 "
damuwa"
"Hhhh....bakida darhamin da zaki siyar kisaye sunan nawa😚" "waya gayama😳" "nasani
ne😜" "Lolz...Yanxu hk sunan ba dadi ma😏" "ko dai ya yake kece kika neme kisani😅"
😂 "Da yafi kam😍 , ni sunana Usman😳" "whattttt😳 ?" Ido waje ta
"Am sowie gayamin pls"
kwallama sunan ido tana maimai tawa "Usman...Usman...Usman!" "Ohhh har kin
tsoratane😉 tell me ur nm, naji ko yana da dadi irin nawa😜" "Hmmm....ai sunan naka
babba ne😫" "dama na gaya miki😏" "wlh sunan Dady nah ne dakai😥" "😂😂😂kice
😒 "sosai ma😎" "hhhh.....nasamu daughter kenan😎 , toh miye sunan
respect dole"
daughter tawa?" "Maryam Sadiqa" "nc nm😘, a wani gari" "Skt, kaifa?" "Ohhhh munyi
nisa sosai ni ina kano".

Nan fa suka share kusan 2hrs suna fira, daga kisani sukai sallama. KO wannan su
da kyawar dan uwansa.

*BASAKKWATAR KUCE*😜

*Ⓜªŋşħªŗŧ ŋºvęłş📚*
[3/18, 10:59 AM] Manshart: *MISKILANCI KO GIDADANCI*❓

```Written by Manshart```💘

~In dedicated to my luvly Dady (Alhaji) nd Mummy (Bissalam)~

*{Đïş ïş mý şęĉºŋð ŋºvęł}*👌🏽

*Part 7*

Yau takama wed, kwance yake a dakinsa. Ringing din wayarsa ce ta tadashi.
Sunan Mummy yagani ta kan screen din. "Kazo ina nemanka yanzu" batareda tajira
amsar dazai bayarba ta katse.

A dakin ta yatarad da ita sai shirye2 take, Sajida da A'isha suna gyefinta sai
aikin kintsa tufafi suke acikin trolley. Mummy kuwa sai waya take da Aunty Zainab
wadda take aure a kaduna.

Guri yasamu yazauna yana jiran mummy tagama wayar da take. Waya tayi sosai
kafin ta katse ta juyo ta kansa. "Alhaji!" Takira sunansa, "Naam Mummy" ya amsa
cikin ladabi. "Dama maganar tafiya skt nakeso nagayama. Nasan duk yaran gidannan
zasuje dauren auren nan, amma nasan kai idan ba najama kunneba bazakaje ba! Toh
inaso kasani wlhy idan har kayarda akai dauren auren nan bakaje ba ranka inyayi
dubu zai bace! Fatan kaji abinda nake gayama" sunkuyar da kai yayi a k'asa yace "in
shaa Allah Mummy zanje tareda su" "Yawwa hk nakesan ji baba nah! Kaga yanzu nida
A'isha da Sajida da Labila zamuje yau, jibi idan Allah yakaimu Haj Saratu zataje
itada su twins da Kubra. Ita Zainab daga kaduna zata wuce itada yaranta MusaddiQ da
Sadiqa. Sai yan uwanka zasu shiga dauren aure Assabar kenan" "Toh Mummy adawo lfy"
"Ameen Allah yasa"

K'arfe 11 na safe su Mummy sufa fito, dama driver yayi parking su kadai yake
jira. Su Sajida andau na kuti zaaje skt bikin uncle Mubarak.

Har zuwa gate su Umma suka rako su, Alhaji da Sadiq suma sunyo musu rakiya. Suna
tafiya suna sallama har suka kawo mota, Alhaji yabude booth yasaka musu trollys
dinsu tareda sauran kayansu . nan fa su twins sukayi tsayin daka sai antafi dasu.
Mummy ta rarrashesu tareda basu chocolate, sunason chocolate shiyassa a koda yaushe
mummy bata rabo da chocolate domin bawa su Husnah da Alhasan twins din Umma kenan.

Umma kuwa sai fatan alkhairi takewa abokiyar zaman ta wato Mummy, kasancewar
suna zaman lfy kwanin shaawa ga amana a tsakanin su. Tareda tabbatar mata da
zuwansu ranar Jumu'a, Mummy tamusu sallama driver yajasu suka dau hanya su twins
suna ma Mummy hannu.

Alhaji yakama hanyar cikin gidan, Umma tace "wato yanzu Alhaji Haj Shafa'u
tatafi nida ganinka sai anyi walkiya" Sadiq dake dauke da Husnah yace "lallai kam"
murmushi kawai Alhaji yayi musu yashige abinsa. Kan su shigo falon har ya haura
sama dakinsa. Umma tayi murmushi tare da fatan alkhairi ga wannan dan nasu, haka ta
shige part dinta cike da tambayar zuciyarta mike damun wannan yaron *MISKILANCI KO
GIDADANCI*❓.

Shiko da shigarsa kan touch dinda ke dakin yafada, cike da abu biyu a zuciyarsa.
Na farko dama Mummy ce take sakashi dole yayi wasu abubuwan kuma yanzu batanan,
amma yana cike da kewarta. Sai kuma haushin zuwa dauren auren da Mummy ta cilasta
masa dole! Kuma yasan yazamo wajibi akansa yashiga garin skt domin bin umurnin
mahaifiyar sa.

Wayar sa yadauka yahau chart, yanzu yazame masa jiki ma, saboda daughter sa
wato Maryam. Akai rashin saa bata online! Baiji dadi ba dan daughter itace mai
sashi farin ciki aduk lokacin da buk'atar hakan tataso. Sun shako da ita sosai
yanzu, ta daukeshi tamkar mahaifinta na hakkun, sbd darajar sunansa. Tun lokacin da
taji ainahin sunansa tafara kiransa da Dady, shima yake kiranta da daughter.

Shakuwar su tayi yawa shida Maryam, har ta zaman musu tamkar a huri daya suke.
Abinci ma a tare sukeci a waya, basa iya kwana 1 basu hadu a online ba. Musamman
Alhaji tana matu'kar bashi tausayi da ta sanarmai mahaifiyar su ta rasu itada
kaninta Ladib, wanda kusan kullum sai Alhaji ya tambaye lafiyar Ladib.

Yau tun da sassafe yatashi, bai fito ba domin yau mummy bata nan. Chart sukeyi
da maryam yana gaya mata zaiyi tafiya gobe daurin aure, fatan alkhairi tamai tareda
addu'o'in ta, na zuwa lfy da dawowa lfy.

Duk da zasu hadu online amma ko wannan su bayajin dadi, gani suke kamar nesa
zasuyi da junansu.

Yau su Umma zasutafi itada twins da Kubra matar Sabir da tsohon cikinta
7mouth, sai Safiya matar Jabir tareda yarta Munawwara.

Haka suka kama hanyar zuwa skt, driver'n Jabir ne yakaisu. Yau gidan ba kowa sai
Alhaji da Sadiq, da kuma dady, shima zaije skt din dauren aure. sauran suna gidan
matansu dayake ba nisa koma gobe ne tafiyarsu suma.

3:40pm
A gidan su Maryam kuwa. Zaune take a falo ita da Ladib yana games a wayarta itako
tana karatun wani novel mai suna *AMANNAH*

Yaya Ma'aruf ne yashigo dauke da system dinsa da alama daga skul yake duk ya
jigata. Sallama yayi ta amsa dauke da murmushi a fuskar ta. Kujera daya yakama ya
zauna yana fuskantar ta, "Ina yan gidan ne sai ku kadai a falo?" "Ladib yayi sauri
ya ce "Sunje party" "party kuma?" Hararar Ladib tayi tace "waya gayama party
sukaje? Yaya Ma'aruf sunje Kamu ne na Yaya Mubarak dan abokin Abba" "Ohhh ok, amma
duk su duka suka tafi ina mama?" "Duk sun tafi" "toh kefa?" Ma'aruf yatambaya.

Ladib yayi karaf yace "bata zuwa party ne🙊" "wai waya tambaika ne Ladib?" Ta
tambaishi tareda watsamai harara. "Yakamata kije mana little" Ma'aruf ya fada.
"Yaya Ma'aruf zanje gobe biki ne" "OK....hakan ma yayi daidai" yafada tareda nufar
dining domin cikin sa sai kiran zamfara yake, Lolz.

"Yaya Ma'aruf gobe ni kadai za'a bari a gidan kenan?" Ladib yafada a shagwabe ya
ajiye wayar da yake games da ita yahau murtuke fuska sai kace ya hade sabulu. "Kai
ba skul zaka tafiba miye hadinka da biki kuma na mata" karaf yayi yace "laaa ka
manta gobe weekend ne yaya?" "Ohhh! Kai dan Allah kabarni naci abinci duk kawani
cazamin kai da surutun nan naka" dariya tayi musu kawai tacigaba da karatun ta "pls
yaya kace sutafi dani" "toh zanje dakai daurin aure, shekenan ko?" Tsalle yahau yi
daga bisani ya dauke wayar yakoma zuwa game dinsa.

*BAHAUSARKU CE*😜

*Ⓜªŋşħªŗŧ ŋºvęłş📚*
[3/18, 10:59 AM] Manshart: *MISKILANCI KO GIDADANCI*❓

```Written by Manshart```💘

~In dedicated to my luvly Dady (Alhaji) nd Mummy (Bissalam)~

```wannan part din nakine dear Reefat (Kishiya)😜 Thanks 4 dedicated me ur novels
(Rayuwar yau) luv u alout😘```

*{Đïş ïş mý şęĉºŋð ŋºvęł}*👌🏽

*Part 8*

Yau tun da asuba su Dady da kanin sa Sulaiman Jabir, Sabir, Sadiq, da kuma
Alhaji. Suka kama hanyar skt. Sai 2:00pm suka sauka birnin sakkwato. Kasan cewar
motarsu tana gudu sosai. Hotel suka yada zango, dady yakama musu daki 3 daya shida
Sulaiman sai kuma daya Jabir da Sabir, dayan kuma Sadiq da Alhaji.

Basuwani bata lokaci ba sbd dady yasanar musu suyi saurin shirya wa 3zaai
dauren auren. Har SadiQ yashirya Alhaji yana zaune ko wankan bai shi gaba, sadiQ
yafahimce dole kawai akaiwa Alhaji zuwa dauren auren, danshi bazai ma iya kawo
yaushine marba dayaga Alhaji gurin daurin aure ba har ya manta. Dan shi duk wata
harka dazata hada dubban al'umma babushi a gurin.

Kasa daure wa SadiQ yayi yazo kan gadun dayake zaune dauke da hannu saman ka,
yabuga tagumi, "Alhaji" yakira sunansa, batareda ya dago kansaba yace "naam" kusa
dashi yadawo ya zauna yace "haba, waimi ke damunka ne? Naga tun gida baka cikin
walwala, kuma tun isowar mu hotel dinnan kake gurin nan kadaura hannuwa aka, gashi
kowa ya shirya ko ka manta yadda Dady yace ne?" Batareda yatankashi ba yatashi
yanufe toilet.

Girgiza kai kawai SadiQ yayi yana mamakin irin *MISKILANCIN* wannan guy'n. Duk
da yasaba da halin sa, amma wani lokaci yana mugun bashi mamaki da al'ajabi, ace
mutun bayasan shiga mutane? Kuma shi dai ba *BAGIDAJE* ba bale kace *GIDADANCI* ke
damunsa, toh Allah dai ya kyauta.

Fitowar sace ta katsema SadiQ tinanin dayakeyi, ya kalleshi sama da k'asa,


yadauke kai. Shiryawa yayi shima cikin k'ananan kaya, Dady ne yakira SadiQ yace
sufito.

Fitowa sukai Dady ya fahimce Alhaji basan zuwa yakeyiba, yasan sarai lamarinnan
akwai abin shinshina acikinsa, in shaa Allah Shafa'u ce mai cilasta masa. Hanyar
*Gwaiwa AK* suka kama, bada jimawaba ta sadasu gidan su Shafa'u. Dama sunyi waya da
Dady yasanar mata cewa sun iso suna hotel, yanzu ma kafin su fito yasanar mata
zasuzo yanzu.

Koda suka isa gidansu Mummy taro ne iya taro ba masoka tsintsiya, dubun al'umma
ne suka taro, ango kawai ake jira akama hanyar zuwa dauren auren. Can daga nesa
suka samu huri sukai parkin, suka fito suka nufe harabar gidan. Dady yaso yasamu
ganin Mummy amma yasan hakan bazata samuba, cinkoso yayi yawa, sai dai idan andawo
daka dauren auren. Ango kenan Mubarak! Yasha malun-malun sai sheki yake, ganin su
Dady tacan gefen yasa shi zuwa suka gaggaisa tareda yimai fatan alkhairi aka huce
*MABERA* gidan su amarya kenan.

Ladib ko sai shiri yakeyi cikin hadaddiyar shaddarsa giznah tasha mayen aiki,
Maryam kuwa sai dariya take masa ganin yadda yake zagwadi kamar shine angon.
Ma'aruf yashigo yakirasa suka fita suma suka nufe *MABERA*.

Karfe 3:00 aka daura auren *MUBARAK USMAN* da *AMINA MUSA* Cikin farinciki.
Aka dawo gida domin yin liyafa😋 su Dady ma gidan suka dawo, sbd hankalinsa bazai
kwanta ba sai yaga matansa😜.

Bayan angama liyafa mutane sun fara tsiyayewa, dady yasamu ganin Mummy. Ta musu
iso suka shigo cikin gidan domin gaisawa da mahaifiyar ta. Taji dadi sosai ganin
Alhaji ya halarce dauren auren kanin nata, amma tasan dalili, da batai rantsuwa ba
da bazai jeba. Har Umma ma ta gaisa da mai gidanta, inda yake sheda musu karfe 6pm
zasu huce shida Sulaiman, amma su Jabir sai zuwa gobe. Mummy bataji komai ba ganin
irin ayyukan daya kashe yau yazo dauren auren, tayaba kuma tasaka albarka tareda
fatan Allah yak'ara budi da arziki mai amfani.

Biki ake dangi da yan uwa duk sun halarce bikin, kasan cewar shine namiji auta
wanda baiyi aure ba.

Bangarin su Maryam kuwa tana cikin kitchen mama tashigo "Maryam kinga mu
munshirya zamuje, kada kiyarda kije bikin nan batareda kin kammala min aikina ba
kinajina?" "Eh mama" "atoh nasan bakar munafukar kawar nan taki Fairuza zata
tadamiki hankali akan sai kin maza kinshigo tunda yayan tane angon" mama tafada
tareda barin kitchen din.

Falo tasamu su Ummi da Safara'u an matsa ado sai jujjuya idanuwa suke sai kace
karuwa taga maza😛. Guda mama tafara tace "gaskiya kunyi kyau twins dina, kunganku
kuwa?" Safara'u takara juyawa tareda cewa "yakika gani mama" "aaa Ai baa mgn,
Safara'u nah. Allah dai yasa nasamu surukai acan" "Ameen mama" Ummi tayi karaf
tace. Dariya mama tayi tareda sake rangada wata gudar suka bar gidan. Driver ne
yajasu suka dau hanya.

Karfe 4:00pm Ma'aruf yashigo baiga kowa a falo ba yashiga part din mama nan ma
bakowa, dakin Maryam yahuce yatarad da ita kwance yazata bacci take, sunanta yakira
tamaza ta juyo yace "lfy dai little?" "A ya Ma'aruf har kun dawo ne?" "Eh, nace lfy
kike kwance ke kadai a gida" "lfy klu yaya, kawai nadan gajine nakeso na kwanta na
h..." Karar wayar ta yakatse mata mgnr. *Besty* tagani a rubuce, dauka tayi takara
a kunne, "wai shin kina ina ne Maryam? Wannan wani irin abune kin barni sai famar
jiranki nake, kinsan fa nagayamiki abinda zamuyi, kuma bazan iyayiba bakya nan
haba" tarasa karyar da zatai mata tabarta sai famar hello hello take.

Signal Ma'aruf yamata alamar tace tana zuwa yanzu, haka kuwa akayi tace tabata
5mints, tayi tsaki ta kashe wayar. Yaya Ma'aruf yace "kitashi kishirya zan saukeki"
"to" tace tanufe toilet.

Koda tasameshi ya parka ita kawai yake jira. Bude motar tayi tashiga, Ma'aruf
yabita da kallo. Tayi kyau sosai, sanye take da wani lesi pink mai dauke da wani
ratsi2n fari a ciki. Dinkin riga da siket ne, duk da tana cikin hijab bai hana
nagano ko wanne irin kyau ya mata ba. Abin sai dai nace Masha'Allah.

Basu wani jimaba 4:40 suka isa, Ma'aruf ya ajiye ta, da zimmar anjima driver
zaizo ya daukeso itada mama dasu Ummi.

Dady da Sulaiman sunyi ma su Mummy sallama zasu tafi. Su Jabir kuwa suna can
tareda abokanan ango su sai gobe asubanci zasuyi. Dady sai waya yakeyi yana tafiya.
Kicibis yayi da amininsa a tsaye a harabar gidan, ba shiri yatattako zuwa gurin
motarsa dayake tsaye.

"Alh. Shehu" Dady yakira sunansa "Alh. Abubakar ya gida, ai naganku dauren aure
amma cikin tarone bansamu mun haduba" "eh haka ne, gida lfy klu ya kowa da kowa"
"Alhamdulillah" gaisuwa sukai ta bayan rabu kan suka fada wata mgnr ta daban koma.

Kanta a k'asa take tafiya, sunkiyawa tai cikin ladabi tagaisheda Abban nata
tareda Dady dasuke tsaye. Cikin fara'a Abba ya amsa tareda sakamata albarka. Dady
kuwa binta da kallo yayi, Abba yace "lafiya dai Alh. Abubakar?" "Wannan wacece?"
Dady ya tambaya cikin mamaki. "Wacece fa kake tambaya, ita Maryam din yar wajena ce
baka ganeba?" "Eh gaskiya bansan da itaba kasan ni Ma'aruf kawai nasani sai yayar
sa Rashida wadda take aure can kano" dariya Abba yayi yace "lallai kuwa munjima
bamu haduba, toh ai wannan yarinya tace Maryam" "Dan Allah idan bazaka damuba inaso
muyi wata muhimmiyar mgn dakai."

*Ko wacce irin magana ce Dady zaiyi da Abba🤔🤔🤔*

*HAR YAU DAI, BASAKKWATAR KUCE*💃🏿

*Ⓜªŋşħªŗŧ ŋºvęłş📚*
[3/18, 10:59 AM] Manshart: *MISKILANCI KO GIDADANCI*❓

```Written by Manshart ```💘

~In dedicated to my luvly Dady (Alhaji) nd Mummy (Bissalam)~

*{Đïş ïş mý şęĉºŋð ŋºvęł}*👌🏽

*Part 9*

Abba yace "Toh ba komai inajinka" gyaran murya Dady yayi yace "da farko dai zan
tambayeka, kuma na neme alfarmar ka" "Haba Alh. Abubakar, sai kace dai ba abokanai
bane mu. Ka tambaya komai kakeso , batun alfarma ko sai idan tafi karfina" Dady
yanisa yace "kayiwa yarinyar ka miji ne?" "Wai Maryam?" Jinjina mai kai Dady yayi
tareda murmusawa "Aa Maryam batada tsayayyen miji a yanzu, sai dai maza da yawa
sunason ta amma ko wanne sai yazo tace bataso, niko bazan iya cilasta mataba sbd
tausayinta danake, kuma yarinyar tanada hankali ga ladabi" murmushi Dady yasakeyi a
karo na biyu.

"Faduwa tazo daidai zama Alh. Shehu, idan har zaka yarda, inaso mu hada auren
Maryam da dan wajena" cikin fara'a Abba yace "mizai hana Alh. Abubakar, ai Maryam
yarka ce, kuma na amince da wannan maganar a matsayina na uban yarinya" Dady bai
iya boye tsabagen dadin da yajima. Godiya sosai yayima Abba.

Shiga tai cikin gidan idonta noce sbd mutanin da sukai yawa a harabar gidan.
Wayar ta ta dauka tasanar ma Fairuza cewa ta iso, baafi 2mints ba Fairuza tafito,
"amma yarinyar nan kin iya walakanci fa, kin wani shanyani sai faman jiranki nake,
har su Ummi na tambaya ke suka ce basusan inda kike ba" "sorry mana Besty nah, koda
kika kira ina kan hanya kinsan napep wahala take a skt irin yau da dauren aure
sukai yawa" "kuma fa haka ne, mushiga daga ciki ki gaisa dasu Hajiya sai tambayar
ki take" to tace da ita suka shiga ciki.

A parlo ta tatarad da su Ummi sai famar surutu sukeyi, sallama tamusu Safara'u
tai tsaki Ummi ta kauce kai gefe. Fairuza kam ta jata suka shiga falon Hajiya
mahaifiyar su kenan.

Duk kowa da kowa yana parlon Mummy, Umma, Hajiya, Aunty Zainab, Kubura, da kuma
safiya, duk suna farlo sai fira ake. Shigowa sukai Fairuza na janye da hannun
Maryam kamar rakumi da akala, durkusawa tai cikin ladabi ta gaishe su, ta kuma yima
Hajiya tata gaisuwar special. Cikin kulawa Hajiya ta amsa tareda tambayar ta ya
gida, duk ta amsa lfy lau. Fairuza tajata suka shige dakinta.

Tun shigowar su idon Mummy yake kan Maryam, itadai haka kawai taji yarinyar
tashiga ranta, musamman ladabin ta datagani kuma da kamunkai, ga shigarta ta
mutunci. Aunty Zainab ta lura da kallon da Mummy takewa Maryam a ranta tace "toh
kodai kame Mummy zataiwa danta🤔?" Hajiya ce ta katsewa Mummy tinanin da take da
cewa "yarinyar nan duk cikin abokanan Fairuza hankalina yafi kwanciya a kanta, sbd
tanada hankali da natsuwa" "gaskiya ne Hajiya nima shigowar ta iya yanzu kawai na
fahimce haka" Mummy ta fada tareda sauke sassanyar ajiyar zuciya. Hajiya tace "amma
fa akwai wani abu *MISKILANCI*👌🏽"

Dakin Fairuza kuwa sai kyas akeyi, tsakanin Fairuza da da Maryam. Fairuza ta
fiddo musu da kayan da Hajiya ta siya musu wanda zasu saka anyima idan za'ai party
amma fur Maryam tace bazata sakaba ta fito sak arniya. Labila da Sajida suna
dakin, suma duk suka saka baki akan tasa tunda yau ne kawai, kuma ma tufafin basuda
wata mishkila. K'nanan kayane daga dubai Hajiya tasiyo musu itada Fairuza. Dakyar
tayarda tayi na'am zata saka sukaji dadin hakan.

Alhaji kuwa duk ya susuce, wani abokin Mubarak ne yadinga mai surutu har akai
saa yadan fara sakin jikinsa, har yana dan fira cikinsu. Amma hankalinsa baya
gangar jikinsa, sbd tun jiya da sukai chart da Maryam da safe bai koma ganinta
online ba. Duk yabi ya tada hankalinsa ko lfy oho! Itama bangarin Maryam hk domin
ko wayarta babu chaji tun jiya da Ladib yayi games tayi low, yakai locker ya ajiye.
Yar Nokia ce take using da ita a yanzu, kuma ba dama ta kirashi da ita sbd basa
waya Sam basu taba waya da itaba sai dai chart kawai.

Bayan anyi sallar magrib a bangare biyu aka fara shirye²n tafiya party. Ango da
amarya kenan. Su Fairuza sai shiri akeyi andau na kuti an kule wanka, wankan nan
wanda gayu suke kira *No respect😜* Maryam dai sai jinta take ba dadi sbd bata
sababa.

Labila ce tai mata simple makeup tayi kyau kamar ba gobe sai "Wowww! Nice! So
sweet! Nuture beauty!" Su Fairuza suke cemata, itako murmushi kawai take. Sajida
tazo daidai kunnuwanta tace "kinyi kyau gaskiya, Allah ya hadaki da yaya nah😍"
dariya tai mata kurum Fairuza tace "Hmm....rufama yayanki asiri indai Maryam ce,
shegen nacin tsiyane da ita, har yau ba namijin da yagama tafiya da imaninta ne"
harara Maryam ta galla mata tace "kinsan banaso ko🙄" "sorry" kawai Fairuza tace da
ita daganan tacigaba da gyaran gyalinta da taketa aikin rolling dinsa tun dazu.

Hall ne cike da maza da mata, amarya da ango kuwa sunyi kyau bana wasaba.
Table suka samu suka zazzauna Fairuza da Maryam daya, sai Sajida da Labila daya, Su
Ummi da Safara'u da Aisha daya. Dan tunda suka hadu da Safara'u ran Kamu, suka
k'ulla k'awance, dan kuwa Safara'u akwaita da son abokanai yayan manya, duk da suma
din mahaifinsu ba bayaba.

Shigowa yayi tareda abokin ango Saifu wanda yaketa shigema Alhaji tun zuwansu.
Kujerin da aka jerama abokanan ango Saifu yanufa dashi, suka zauna su biyo da yake
kujerun ukku ne wannan gefe ukku wannan gefen ukku na amarya da abokananta biyu sai
ango da nasa biyu.

Tun da suka shigo hall din gabansa ke faduwa, ji yake kamar wani abu zai faru
dashi. Su Ummi kuwa sai rawar kai akeyi taga handsome. Harda Aisha ta tambaya
tagayamata yayanta ne, amma ta kama kanta cos *MISKILANCIN* sa yayi over, ko
budurwa bashida ita.

Dady yasanar wa Sulaiman akan batun maganar da sukayi da Abba, kuma yayi na'am
da maganar. Maganar koma wa kano yau ta yanke musu, domin kuwa sun tsaida maganar
gobe da safe za'a yanka sadaki. Dady yaso ayanka da yau din, amma Abba yace bayayin
abu bada yan uwansa ba, sai ya sanar musu tukun, zuwa gobe sai suzo ayanka sa
dakin, kuma suma su Dady sun yarda da maganar.

Sai shagali ake a hall din ana ciye-ciye, amma banda Maryam da cikin ta sai
ciwo yake mata, "Subhanallah!" Ta furta, ta tsorata sosai, sanin ko menene ke
shirin zomata, kuma ita ba ashirye takeba. Fairuza ta fahimce halinda Maryam take
ciki, sai cije baki take tana ballar hannunwan ta, alamar tanajin zafi a cikin da
ta yima wawan rigo.

Cikin firgice Fairuza tazo kusan ta "Maryam lafiya? Mike faruwa?" Kasa magana
Maryam tayi sai kwallar dake zubuwa takan idanuwanta. Gigicewa Fairuza tayi tace
"bakida lfy ne Maryam? Pls gayamin dan Allah mike damunki?" Ganin batada niyar amsa
mata yasata saukowa daga kan kujerar ta durkusa kasa tareda kamu hannun ta.

Ganin Fairuza ta durkusa yasa Labila da Sajida tasowa cikin azama suka nufota.
"Lafiya dai aunty Fairuza? Mike damunta?" "Oho, wlhy bansani ba, nima nayita
tambayar ta tamin shiru" Labila takai durkushe tace "pls Maryam kisanar muna mike
damunki dan Allah" Maryam bata iya mgn ba sai nune kawai tamusu da hannu alamar
cikinta ne ke mata ciwo.

Atake Fairuza tagane damuwar Maryam, dakuma abinda yasaka ta tashin hankali.
Dama tasan yadda yakewa Maryam idan yazo mata, yana matu'kar bata wahala, sbd
tatabayin hk a skul. Nan danan hawaye suka sauka daga fuskar Fairuza.

"Pls kufitar damu duhu mana aunty Fairuza, naga kema sai kukan kike, mike
faruwa ne"? Sajida ta tambaya, itama ga alama kukan yana shirin zomata. "Kwanakin
watan tane sukazo, kuma tana tsananin wahala idan tanayi" Fairuza tagayamusu cikin
sigar tausayi.

Sun tausaya mata sosai, dansu tunda Fairuza tana basu lbrn ta hk kawai sukaji
ta burgesu, barin dasukaganta, takara shiga rayuwar su. Maryam kuwa sai famar matse
baki take tana girgiza kai alamar zafi sosai tajeji.

Labila tace "toh yanzu aunty Fairuza yazamuyi?" "Wlhy bansan yadda zamuyi ba
Labila" "ina zuwa 2mints" Sajida tace dasu. Kallo sukabi Sajida dashi kawai, daga
bisani suka koma kan Maryam suna lallashinta.

*Ⓜªŋşħªŗŧ ŋºvęłş📚*
[3/18, 11:00 AM] Manshart: *MISKILANCI KO GIDADANCI*❓

```Written by Manshart💘 ```

~In dedicated to my luvly Dady (Alhaji) & Mummy (Bissalam)~

*{Đïş ïş mý şęĉºŋð ŋºvęł }*

*SLM...frndz kumin afwa, a sakamakon rashin jina da kukayi jiya, nadanyi rashin lfy
ne, but now, Alhamdulillah. Don't 4get me, I need ur prayers pls thanks u all fans
I luv u wujiga2*

*Part 10*

Fitowa tai harabar hall din, motocine birjik ta ko ina. Lambobin motocin tabi da
kallon 1by1 dayake hurin haskake yake da fitillo ta ko ina. Akai saa taga motar
gidan su an rubutamata *A I no.5* dadi sosai taji, musamman ganin mutun a motar ya
kifa kansa da sitarin motar, ga Alama tinani yake. Kamar barauniya take tattakawa
takai ga motar, tafi 3mints a tsaye gaban motar sai kallon sa take,sai da ta
tabbatar baimasan da zuwanta ba kan ta shiga knock din motar ta gilas. Dago kansa
yayi ya kalleta yamayar da kansa kawai.

"Uhm...uhm...yaya" sake dago kansa yayi yadubeta. "Dan


Allah yaya wata alfarma nakeso kamin" sai a lokacin
yadubeta yace "what it?" "Uhm...yaya wata frnd dinace
batada lfy sosai, inaso ka sauketa a gidan su" tafi minti 5
a tsaye baice da ita uffan ba, hasalima cigaba yayi da
latsar wayarsa, wadda yaketa neman daughter dinsa da
tun jiya da safe, rabunsa da ita.
"Pls yaya kataimaka mata wlhy serious takejin jiki" tsaki
yaja yace "dayake kinsan ni nasan garin" "A'a yaya, ba
haka nake nufi ba, zamuyima kwatance ne pls!" Jiyake
kamar yace aa amma yakasa, baisan lokacin dayayi
na'am akan alfarmar taba.
Hall din Sajida takoma, kowa sai sabgarsa yakeyi, masu
rawa nayi, masu likin kudi nayi. Gunsu Fairuza ta isa,
cike da farincikin samun nasara!
Koda ta tarad Maryam abu yak'ara rikicewa. Fairuza
tacewa suzo da ita, tasamu wanda zai sauketa gidan su.
Koda ta tashi duk jikinta ya lalace! Sai kuka takeyi na
ban tausayi.
Fitowa sukai da ita har bakin motar, Fairuza na rike da
hannunta, tafiya ma dakyar takeyi. Labila ta bude bayan
motar tasakata, ko tsayi bata iyayi. Fairuza taje tamai
kwatancin gidan a can *Sama road*. Batareda ya basu
amsar ya gane kwatancin ba ko bai ganeba, yaja motar
suka bar harabar hall din. Fairuza sai mamakin
*MISKILANCI* irin na wannan guy take. Toh nima dai
*Manshart* am very surprise
Kan titi yahau, batareda yasan inda zai dosaba, itako sai
kuka take, tana rike da marar tata, ji take kamar fashewa
zatai! Duk ta gama bashi haushi, duk da baiko juyaba
bale yaga halinda take ciki, amma kansa har yadau zafi,
shida ko surutu ake saidai yabar gurin amma baya jure
surutu, memorial dinsa basa daukar irin wannan
koramniyar. A fusace ya parka gefin titi yace "Keee.....ya
isa haka, idan bazakiyi shiru ba kifita kibarmin mota ta"
wani bakin ciki da tsanar sa taji ya ziyarce zuciyar ta
lokaci daya. Tsawa yakara daka mata, wanda yasa ta
firgita, a rayuwar ta batasan fada ko amata tsawa, wani
sabon kuka ya kara fito mata.
Fitowa yayi da azama ya budo kofar motar, ta inda take,
ya fincikota yayi ball da ita a waje tareda cewa "zaki iya
kuka a nan din, useless kawai" ya tada motar tare baza
mata kurar gurin yafice abinsa. Kuka takeyi sosai tana
kiran Umman ta tazo ta taimaketa.
Driving yake sai jujjuyawa kansa yakeyi, ga wani
azababbin ciwo da yake masa. Gurin party'n yakoma dan
yanason ganin Sajida. Bai iya shiga hall dinba, wayar
Sajida yakira, ringing 1 ta dauka, batare da yayi mgn ba
yak'atse wayar. Sajida tace "to ko kwatancin ne bai
ganeba?" Tatashi tafita harabar hall din.
Ganin ta fito, yasa shima yafito, karasowa tayi yabude
marfin motar yanuna mata da hannu "See, wannan
k'azamar yarinya tasakamin k'azanta a mota, mtwsss"
kuka da kunya hadeda haushi suka mamaye Sajida a
gurin, takasa motsawa. Daga bisani tajuya ta nufe hall
din. "Ina zakije koma?" Yatambayeta cikin fusata. "Zan
samu abune" tabashi amsa batareda ta juyo ta kallesa
ba, takoma hall din.
Gurin su Fairuza takoma, fuskar ta dauke da hawaye,
"lafiya Sajida" suka tambaita a tare. Bata kulasuba. Inda
Aunty Samira kanwar Mummy tanufa, ta buda jakarta
tazaro tissue, dayake bata jima da haihuwa ba, tazo
dashi dan amfanin baby'n ta yar 4mouths.
Gorar ruwan da suke kan table dinsu ta zira, b
daukar jakarta. A tsaye ta tarad dashi, ya rungume
hannuwa, hade da jinginawa da motar. Shiga tayi cikin
motar tabuda ruwan tazuba hadeda dauko tissue tafara
gogewa. Shiko duk abinda take idonsa na kanta, kunya
duk tagama kama Sajida. Ohhh su Sajida an girma .
Bayan ta goge tsab, takawo turarenta BlackBerry ta saka,
a take motar ta dau kamshi. Fitowa tai batako bi ta
kansa ba, ta koma ciki, koda ta shiga angama shagali
kowa na kama gabansa.
Shiga yayi motar, duk da turaren da Sajida tasa bai
hanasa dauko nashi car fresh yasaka ba. Motar ta
sirnane na kamshi, yaja yabar gurin.
Bangarin Maryam kuwa, har yanzu tana inda ya barta, sai
kuka take, bata iya tafiya. Mota ce taketa horn a daidai
inda take, daga karshe dai fitowa yayi yazo inda take.
"Lafiya dai emmata? kike zaune a kan titi? Bakya tsoron
wani yazo ya bigeki?" Ganin batada niyar amsa mai
tambayoyin sa, yasaka shi cewa "idan bazaki damuba,
kizo na saukeki a gida" batada mafita wadda tahuce
tashiga, dole ta yadda tashiga motar, da kwatancin da
take mai ne yagane gidan nasu ya sauketa.
Godiya sosai tamai, nan ya tambaye sunansa tace dashi
SadiQa, murmushin jin dadi yayi yace "wow! Suna mai
dani, kuma yanada halak'a da nawa sunan, SadiQ"
"thank!" Kawai tace dashi, daga bisani yaja motar yabar
huri. Gida ta shiga, Saar ta daya ba kowa, Ladib yayi
bacci, kan gado harda minshari.
Toilet tashiga ta gyara jikinta tsab tafito, tasaka kayan
bacci, ta haura gado.
Tinanin abinda yafaru ita da wannan guy take. Wata
tsanar shi taji yak'aru a cikin zuciyar ta, duk da bawani
ganeshi takeba, amma zata gane gefen fuskar sa daya
matu'kar mata kyau sosai. Tsaki taja tareda cewa
"bantaba tsanar wani namiji ba irin yadda na tsaneka!
Mugu , mara tausayi, *BAGIDAJE*" sai kuma kuka yaci
karfenta, ahaka har bacci yayi gaba da ita.
Yau ta kama lahadi, tun da farar safiya Dady yayi waya
da Abba, ya shida mai yasanar da yan uwansa, zuwa
karfe 10 zasu zo. Dady ma yace suma zasuzo shida
Sulaiman kafin su huce.
*2hours latter*
Dady ne da Abba, Sulaiman da yan uwan Abba su 3,
zaune a katafarin falon Abba. Bayan anyi yan gaishe2
daganan aka yanka sadaki 50k domin samun ladar aure.
Duk da yam uwan Abba basuso hakan ba, anasu son,
sadakin yafi hakan, amma Abba yace shi ba kudin yake
soba, asamu albarka acikin auren yafi komai. Abba ya
dogara ne a hadisin manzon Allah (SAW) cewa "albarka
aure tana daga k'arancin sadaki".
Anyanka sadakin, cikin aminci, kuma akasaka rana 1ga
watan march. Anyi komai lfy, daga karshe su Dady suka
kama hanya, tareda su Jabir. Su Mummy ma yau zasu
huce, amma sai da yamma.
A cikin mota Sulaiman yakema Dady magana akan auren
nan. " amma yaya, kana ganin wannan yaron zai yarda da
maganar auren nan da kakeso ka hada?" Murmushi Dady
yamai daga bisani yace "ba shawara zan nema a gurin sa
ba, umurni zan bashi" "eh, amma wannan *MISKILIN*
yaron zai iya bijirema fa" "kai kake ganin haka, kuma
mgnr *MISKILANCI*'n sa, wannan bai shafeniba. Dole
nabashi umurni kuma sai yabi" "toh yaya, Allah ya
taimaka" "Ameen, zanmai *Bazata* ne" (Rash kardam).
Sulaiman yayi dariya yace " Akwai kwarya-kwaryar drama
kenan........"

*BASAKKWATAR KUCE*🤒

*Ⓜªŋşħªŗŧ ŋºvęłş📚*
[3/18, 11:01 AM] Manshart: *MISKILANCI KO GIDADANCI*❓

```Written by Manshart💘```

~In dedicated to my luvly Dady (Alhaji) nd Mummy (Bissalam)~

*{Đïş ïş mý şęĉºŋð ŋºvęł👌🏻}*

*Sallama....frndz 🙋🏻kuyi min uzuri zaku dinga jina shiru nadan kwana biyu, sbd
Aunty's dina ne suka haihu zamudanyi didima😋 luv u all INA TARE DAKU❣*

*Part 11*

Yau Maryam ansamu chaji, sai dadi takeji zataga dadyn ta. Sai bayan takammala
aikin ta ne tadawo daki tafara chart, akai sa'a tasameshi online! Batai k'asa a
gwaiwa ba tamai sallama.

Cikin farinciki ya mayar mata da martani. "My daughter I really miss u wlh,
ina kika shiga?" "Miss u too luvly Dady, fatan kana cikin koshin lfy?" "Klu nake
daughter, sai dai kewarki kawai danake, daughter ina kika shiga" "wlhy nadanyi
zazzabi ne dady😰 amma yanzu alhamdulillah nasamu lfy" "zazzabi daughter😳 Allah
sarki, Allah yakara baki lfy, amma naji kamar zazzabin yadawo kaina, sbd banasan ki
wahala daughter😪" "a'a Dady nah, ai yanzu komai yakoma normal, nima ai banasan ka
wahala Dady nah" "toh Allah yakaro sauki, amma banasan wani abu yasameki daughter"
"Ameen luvly Dady" nan dai sukaci fira sosai, har su Mummy saida ta tambaya da kuma
junior. Sai karfe 10am suka tafi zuwa breakfast domin sun sabawa juna da yi a tare.

Dady kuwa sai shirye2n aure yakeyi, ba gudu ba jada baya! Amma har yanzu Mummy
batasan ko anayi ba, sai yau yayanke shawarar sanar mata.

Dama yau Mummy itace da mai gida, shigowa tai dauke da flask tareda sallama,
Dady ya amsa a far'ance tareda dauko agogon hannun sa ya saka. Zaunawa tai a dining
table din tana gyaggara hadaddan breakfast din na mai gidanta.

Karasowa yayi, yazauna da basmala, tareda dubin uwar gidan tasa, "Uhm yau dai
mai gida da alama akwai magana a bakin ka" Mummy ta fada tareda juyomai da kayan a
gabansa. "Haka ne uwar gida, inaso nai wata muhimmiyar mgn dake" "toh" Mummy tace
hade da k'ara gyara zamanta.

Dady yayi gyaran murya "dama inaso na sanar mikine cewa nasamowa Alhaji mata,
kuma zaayi auren bada jimawa ba" "aure kuma mai gida?" "Eh, harma anyanka sadaki da
komai ansaka rana wannan watan" "Amm.." "Dakata Shafa'u! Nagayamiki ne dan
kincincinta da kisani, hakkinki ne na sanar miki, amma ba shawara nake nemanki ba,
kisani umurni nake zartarwa" "amma gaskiya mai gida, wannan hukuncin da kakeso
kayanki yayimuna tsauri nida d'a na, bazaiyu ace yaro kamar Alhaji ba ace yayi aure
a yanzu just 27yrs old fa haba mai gida" "Shafa'u!!!" Dady yakira sunanta a fusace.
"Ina so kisani, wannan hukunci nariga na yanka, kuma ya zaunu, kuma mgnr dakike ta
cewa Alhaji bai isa aure ba, hauka ce kikeyi, ba k'asar da bazaaiwa kamar Alhaji
aure ba" "Amma kasan da cewa sauran yan uwansa ba wanda yayi aure har saida yacika
shekara 30, sa'annan ma ai bashine yaga yarinyar yace yanaso ba, kana nufin *Auren
dole* zakayimai ne?" " amma kuma kinsan su sunfitar da matar da sukeso kafin sukai
shekarun, shi wannan *MISKILANCI*'n sa bazai barshi yaneme mata ba, kuma ni bazan
zauna na zuba masa idoba. Ko kina nufin ni ban isa nabashi umurni bane" "aa maigida
n...." "Shhhhh..... Banasan kice komai, nariga na tsaida mgn, SBD hk ni kinga
tafiya ta"

Binshi da ido tayi, har ya fita dakin, daga bisani itama tafito ta nufe nata
dakin, cike da bakin ciki.

Bayan ta kama breakfast ne ta gyara dakin, Ladib yana zaune yana games a wayar
ta. "Kaga Ladib kada ka canyemin chaji inaso nayi chart anjima" "ai bazan cinyeva
aunty SadiQa, da sunmin game over zan ajiye" Ladib yafada yana cigaba da game din
tasa.

Ringing din wayar ce ta k'atse mishi game din, yaja tsaki ya kashe! Haka wayar
tasake daukar k'ara, yaja wawan tsaki hade da cewa "OMG!😁" daga bisani ya dauka
yace "aunty Fairuza tana toil..." Kafin ya isar ta amshe wayar ta kara a kunne
"Hlo! Besty nah ykk" "klu nake, yar rainin hankali, shine kika shukamu jiya ya
jikin naki" "dadai yafi kam, kinwani hauni da fada toh banji sauki ba" Maryam ta
fada hade da murtuke faska kamar tana gaban ta, har saida Ladib yayi dariya yafita.
"Hhhh sorry mana tawan, ya jikin" "Alhamdulillah" "wai ya kuka kaya keda wannan
*Miskilin*?" Wani bakin ciki hade da kunci da tsananin takaicinshi taji ya tokare
mata a zuciya. Kashe wayar kawai tayi tafada kan gado ta fara reru kuka marar
sauti.

Tunda Mummy tashiga daki bata fito ba, tanacan ta sak'a ta kwance, a cikin
dakin ita kadai. Daga karshe ta yanke hukuncin bazata sanar ma dan nata abinda ke
faruwa ba, harsai abin ya tabbata yaganema idunsa.

Umma ganin yau tun safe Mummy bata fitoba , gashi yanzu har 4:30 yasa ta nufar
dakinta taji ko lfy.

A kwance ta sameta, da alama tinani take. Karasawa tayi da sallama, Mummy ta


amsa tareda tashi daga kwancin da take.

"Lafiya dai yau najiki shiru tun safe?" Umma ta tambaye ta hadeda kallonta
cikin damuwa. "Hmm lfy ta lau, sai dai wani abu ke shirin faruwa a gidannan!" Cikin
faduwar gaba Umma ta tambaya "na miye haj Shafa'u?" Nan fa Mummy ta kwashe komai
ta sanar wa Umma, ba abinda ta ragar mata har yadda sukayi da Dady.

"Amma gaskiya idan hakane mai gida bai kyautaba, yakama ya neme amincewar sa,
baikamata ace dan ka haife da kace zakamai abinda kaga damaba, musamman ma shaanin
aure" Mummy tanisa tace "Nima haka nake nunamai amma sam yakasa fahimtata, daga
karshe ma tashi yayi yabarmin dakin" "hakane, amma kiyi hakuri, in shaa Allah komai
zai zamo tarihi, kawai mudage da addu'a in shaa Allahu Allah zai dube kukan mu
yazaba muna abinda yafi zama alkhairi" haka Umma taita bawa Mummy shawarwari hadeda
kwantar mata da hankali, har Mummy taji wasai, kamar ba damuwa a ranta, sabanin
dazu da takeji kamar zuciyarta ta fito. (Hmm..... Kishiya ta gari kenan👌🏻 wadda kuwa
ke fata😊 amma nasan wasu ko irinta basaso😂 Nima dai........🙊toh Allah dai ka
zabamuna na gari)

Godiya sosai Mummy tayima Umma, daga bisani tafita, Mummy takama wasu yan
ayukka taji jikinta yayi mata dadi, dayake su Sajida suntafi gidan Kubra matar
Sabir.......!

*YAR MUTAN MARNAWA CE*👯

*Ⓜªŋşħªŗŧ ŋºvęłş📚*
[3/18, 11:01 AM] Manshart: *MISKILANCI KO GIDADANCI*❓

```Written by Manshart```

~In dedicated to my luvly Dady (Alhaji) & Mummy (Bissalam)~

*{Đïş ïş mý şęĉºŋð ŋºvęł}*👌🏼

*A/N. Sorry readers kwana biyu kun daina jina, banida lfy ne, fatan kuna biye dani
acikin wannan littafin, wanda zai dinga zo muku a kowacce safiya da yardar
ubangiji. Thank u all ILYSM❤*

*Part 12*

Yau takama asabar, Maryam sai aiki takeyi kasan cewar weekend ne. Kitchen
tashiga ta hada musu breakfast, tafito takoma daki bayan ta jajjera kan dining.

Kan gadun da Ladib yake ta haura ta bubbugashi, yatashi tareda mek'a yana
murza ido alamar baccin bai gama asarsaba.

"Aunty SadiQa har rana ta fito ne?" "Taya zakasan ta fito kana bacci ko
motsawa bakayi" "uhm..aunty nah kenan, yau baccin da dadi yake wlhy, kamar kar na
tashi" "kaga, je kai wanka kazo muyi breakfast yunwa nakeji"

Dariya Ladib yayi kan yafice toilet. Dakin ta hau gyarawa, tsab tama dakin
kafin kace me, dakin yahau kamshi. Shaf2 Ladib yafito daga wankan, "Ladib me zan
gani?" Duba jikinsa yayi sama da k'asansa dauke da 3Q, ba abinda ya gani yadawo da
dubansa kanta.

"Me kika gani ko?" "Hmm am not surprising, je ka shirya ina zuwa" ta fita daga
dakin. Waldrop ya bude ya dauko tufafinsa riga da wando pencil yasaka, yazauna
zaman jiranta.

Zaune ta tarad da dady a dining shi da Mama, sai kwasar girki yake da alama
yanajin dadin farfesun kan ragon😋. Sunkuyawa tai ta gaisheshi, da far'a Abba ya
amsa cike da kulawa ta d'a da mahaifi. Mama ta gaisuwa tamata banza sai kwasar
girki take itama, ga alama su Ummi suna can suna sana'arsu wato bacci, dayake ba
dakinsu dayaba.

"Am maryam" Abba yakira sunanta, ta tsorata jin kiran sunan ta dayayi,
kasancewar SadiQa yake kiranta. "Na'am Abba" ta amsa cikin ladabi. "Idan na dawo
anjima inaso zanyi magana dake" "toh Abba, Allah yakiyaye hanya adawo lfy" "ameen"
Abba ya amsa. Tashi tayi tanufe kitchen.

"Yarinyar nan tausayi take bani wlhy" Abba yafada yana kallon mama, wani kallo
tabishi dashi cike da takaici tace "can taji dashi" spoon din ya ajiye tareda
kallon mama cikin mamaki, yabar gurin.

Shigowa tai cikin dakin hadi da sallama, Ladib ta harara ganin yakoma kan gado
yayi arsheshe2 kace wani babba. Ajiye kayan tayi kan center carpet din dake
tsakiyar dakin, hadi da kallonshi. Games ce yakeyi, ko motsawa bayayi, "Uhm... Idan
kagama kazo muyi breakfast din" tafara bude2n hadaddin breakfast din data shirya
musu.

Dariya Ladib yayi, hade da kashe watar, yazo ya zauna, sukai breakfast din sai
surutu Ladib yake mata, kai kawai take gyada masa, amma ita sam baya gabanta.
Tinanin maganar Abba kawai takeyi.

Bangarin su Alhaji kuwa, yau kowa bacci yasha a gidan. Basu tashiba sai 11 bayan
Dady yafita, dan yanzu Dady baya zama hidindimu yakeyi, SBD yadau BABBAN aiki,
shine zaiyi komai na bikin nan, batareda sa hannun ango ko wani ba. Shida Sulaiman
suke shirye2n su, dan yau saura 2week auren.

Parlo su Mummy suka baje, sai fira suke cikin nishadi da jin dadi, dan Mummy
yanzu ta cire damuwa a ranta, kamar yadda Umma ta nema. Su Sajida kuwa sai firar
Maryam suke, Mummy dai saurarar su kawai take, daga bisani tanadan murmusawa.

Karfe 2pm Mummy tashiga daki domin yin sallah, bayan ta watsa ruwa tayi sallah
tana kan sallaya yashigo da sallama. Cikin kulawa Mummy ta amsa, yanemi guri
yazauna, suna dan taba fira da Mummy. Daga bisani yasanar mata yanaso yaje ya
kwanta ya huta, Mummy tayi na'am da kudurinsa tareda masa fatan alkhairi, cike da
tausayinsa.

Dakinsa ya haura, yaneme gado ya kwanta, sam bacci yaki zuwa, yabuga2 yaki zuwa,
karshe hakura yai yajawo wayarsa, ya balla data ko zai samu daughter dinsa a
online, ko banza yayi missing dinta a yau, duk da sunyi chart 8-10. Akai sa'a
yasameta a online, sai dai kash! bata kusa da wayar. Badan yasoba ya hakura ya
kashe data shima yasamu wani aiki yafara dan yasan itama aikin take.

Karfe 8:30pm, Abba yadawo, bayan yaci abinci ya huta ya aiki Ladib dayake tare
dashi a falo, yakira masa ita. Kwance taki a daki tana bitar karatun ta.

Kanta Ladib yafada "aunty Abba yace kizo" tasss gavanta yafadi, tashi
tayi tazura hijab dinta batareda ta tanka Ladib ba, ta fita. Wayarta Ladib yaja
yafara games.

Cikin ladabi ta isa gareshi, tareda sunkuyawa ta bada gaisuwa. Bayan ya amsa
gaisuwar ya nuna mata guri alamar ta rage tsayinta. Zaunawa tayi ta kama jikinta.
News papers Abba ya aje kan center table hadeda Gyaran murya, yafara da cewa
"Maryam inaso ki tattaro hankalinki gareni, domin ki fahimce abinda zan gayamiki.
Dafarko dai kinsani cewa ke marainiya ce, mahaifiyarki ta rasu tun tuni! Kuma kinfi
kowa sanin halin da kuke ciki keda dan uwanki a gidannan" ruwa Abba yakura kan
yacigaba da cewa "a kullum burina bai huce naga na aurar dakuba keda yan uwanki,
shine dalilin dayasa ban karaba daku ba daga scdry, badan banasan kuyi karatu bane,
sai dai inaso na aurar daku kucigaba idan mazajinku sun yarda sun amince" Abba
yakara gyaran murya.

"Abinda yasa nakiraki a nan shine, inaso nagayamiki cewa natsaidamiki da miji!
Kuma kwanan nan za'ai auren bada jimawaba" tunkan ya kai karshin maganar sa, bugun
zuciya ya ziyarceta!

Ba abinda take furtawa face "Hasbunallahi wani'imal waken! Lahaula wala quwati
illabillah!" Namfa ta lalabu addu'ar da ake karatanwa yayin faruwar wata musiba ko
tashin hankali! Wato "Allahumma ajjirni fe musibati, wa ahliqli khairan minhaa!"

Jin tayi shiru batace komai ba yasa Abba cewa "Kinyi shiru Maryam, bakice komai
ba" cikin ladabi ta tattaro natsuwar ta tace "ba komai Abba, Allah kazaba muna
abinda yafi zama alkhairi" dadi sosai Abba yaji, bai iya boye farin cikin saba,
harsai da yanuna shi a bayyane, wanda hakan tasa fararin hakuransa suka bayyana.
Albarka, da fatan gamawa lafiya, hadeda zaman lafiya, da kunciyar hankali, a gidan
miji, Abba yashiga sakawa Maryam, daga bisani ya umurceta da tafiya. Tafiya take
Abba sai albarka yake zankada mata, hadeda godemata.

Dakin su takoma, ganin Ladib ya shige blanket sai numfashi yake saki, alamar
yayi bacci, yasata jin dadin kukan ta. Kuka tayi sosai, daga bisani ta tuna da
halin da take ciki a gidan, tasan yin aurenta shine kwanciyar hankinta, kuma uwa
uba shine burin mahaifinta, musamman ganin irin farin cikin daya nuna na ganin tayi
na'am da qudurinsa. Hakan yasan ya ta hakura tareda tashi ta nufe toilet. Alwala
tayo tazo tayi nafila raka'a biyu, bayan ta gama tayi addu'a tareda neman zabin
Allah (SWA). Daga bisani ta hau gado ta kwanta, cike da tinanin wannan mijin da
Abba yazaba mata. Da haka har bacci yayi gaba da ita.

Mummy da Dady ne zaune a cikin k'ayatatcin palon Dady, suna kallon news a TV
sai can suke taba fira. Kumai Dady yatina? Yace "yawwa, Haj Shafa'u, dama inaso na
sanar miki, ku fara shirye2n aure, wani sati mai zuwa za'ai bikin." "Biki kuma?"
Mummy ta tambaya, batareda ta kalleshi ba. "Haj Shafa'u kenan. Wato so kike ki
batamin rai a auren nan, nafahimce kin canzamin kwata2 kamar kar nafara batun auren
yaron nan, duk abubuwan da bansanki dasuba ada su kikeyi a yanzu" cup din dake
hannun ta ta ajiye, hade da cewa "ba haka bane mai gida, naga wani BABBAN al-amari
ne kakeso ka tono muna, yaron nan fa baisan da wannan maganar ba, hasilima baisan
wace yarinya bace, kana ganin kuwa zai yi na'am da wannan a.....?" "Ya isaa haka
Haj Shafa'u, nagane inda zancin ki ya dusa. Wato kece zaki goya masa baya akan ya
bijiremin? Toh wlhy wlhy idan kikaga baa daura auren nan ba karkiyi farinciki,
domin bana raye, amma matu'kar ina lumfashi sai anyi auren nan" cikin bacin rai
Dady yagama maganar, yatashi yashiga dakinsa tareda bugo kofar kappp! "Ikon Allah!"
Mummy ta furta.

"Gaskiya wannan bazai yuba, yazaace ita tayi aure bayan ga yan uwanta Ummi da
Safara'u su ko mijin basuda, a'a sai aje saboda tsabar munafurci ace Maryam yakeso,
bayan nasan Ummi yace yanaso ko Safara'u amma kabashi ita. Toh wlhy bazata
sab'uba, bazaiyu tayi aure ga yayyunta a zaune gida ko mashinshine babu ba" mama ce
taketa zabga masifa, kasancewar Abba yasanar mata zancin auren Maryam.

"Haba Rakiya, yakamata ace kina ciremin haki a ido, amatsayina na mijin ki.
Baikamata ace kina abinda kikaga damaba a gidan, toh naji! dama kike maganar su
Ummi basuyi aure ba nine nahanasu auren? Ai naga maza suna fito musu amma ke kike
hanawa, ke adole 'ya'yanki bazasu aure talaka..." "Kwarai kuwa, fadi ka k'ara fada,
'ya'yana bazasu taba auren talaka wa ba, yadda suke 'ya'yan masu kudi hk zasu aure
'ya'yan manya"

"Toh inaso kisani, Maryam dai nariga nabayar, aure kuma nanda wata asabar za'a
daura da yardar ubangiji" "Niko ina tabbatar maka matu'kar ina raye da sunana
Rakiya, Maryam bazayi aure ba a gidannan harsai 'ya'yana sunyi. Wannan ka rubuta a
ajiye" Mama tafada tana mai barin dakin. Tagumi Abba yayi da alajabin wannan hali
na matar sa, tareda neman tsarin Allah a kan sharrin ta......!

*YAR MUTAN SAKKWATAWA*👯

*Ⓜªŋşħªŗŧ ŋºvęłş📚*
[3/18, 11:01 AM] Manshart: *MISKILANCI KO GIDADANCI*❓

```Written by Manshart💘```

~In dedicated to my luvly Dady (Alhaji) & Mummy (Bissalam)~

*{Đïş ïş mý şęĉºŋð ŋºvęł}*👌🏼

*Part 13*
Yau sai karfe 12am Maryam tatashi daga bacci, kasancewar jiya batayi bacci
ba, sbd tinanin maganar Abba. Koda ta tashi Ladib yagyara daki tsab, yayi wanka ya
fara games a wayarta.

Toilet ta fada tayi wanka tadauro brush, tafito. Bayan ta fito, ta shirya cikin
wata super riga da siket, ba laifi tayi kyau. "Wai aunty lfy dai yau sai bacci
kike?" Ladib yatambayeta batareda ya dubeta yana games. "Klu nake Ladib, waya gyara
dakin nan?" "Hhhhh, nine man, yau na dauke miki ne kinsan kullum ke kikeyi" "very
good! Kayi breakfast ne?" "Aa, ke nake jira muyi a tare" "OK, jirani ina zuwa"
batareda ta jira amsar shiba tafita.

Zaune tatarad da Mama da su Ummi, suna kallon films. Sunkuyawa tayi ta gaisheda
Mama, harara ta watsa mata ta cigaba da kallon ta. "Mtwssss" Safara'u taja tsaki,
tacigaba da kallon ta itama. Tashi tayi ta nufe kitchen domin dauko breakfast
dinta, sbd hanjinta sai vibration suke.

Shigarta kitchen din taga komai wayam, ba alamar an girka wani abuma a kitchen
din. Sai a lokacin ta tuna cewa, Jamma mai aiki tatafi kauye, tasan ita kadaice
zatayi musu girki a gidan. Fitowa tai tanufe dining place, ba abinda tagani kan
dining, sai kayan tea kawai babbaje, gurinma yayi kacha2!

Dariyar da taji anyice ta dawo da ita duniyar tinanin data lula, Safara'u
tagani tsaye rike da qogunta, sai kwasar dariya take "lallai ma yarinyar nan, wato
kinje yawon Daren ki kinsha bacci sai da rana ta hantse zakizo kina neman breakfast
ko?" Safara'u tafada tana mai mannawa Maryam harara. "Ki barta kawai autana, wa
kika aji wanda zai girka miki abinci kiware duwawu kici? Kega yar gata" Mama ta
fada tareda karasowa garesu. " fice ki girka mana na rana, dan mu munyi take away
tun tuni" juyawa tayi kamar wadda kwai yamatarma a ciki!

Daki takoma batareda ta kula Ladib ba dake famar aikin sa wato games, dan shi
bashida wani aiki da yawuce games sai karatu, idan har baya karatu toh fa yana bisa
games. Kayan jikinta ta sauya tareda fitowa ta nufe kitchen, tafara aiki tukuru,
dama can ta saba. Ai kuwa hanjinta sai lissafi suke saboda yunwa.

Sai karfe 3pm ta gama girki, ruwa ta watsa ta fito, koda ta fito Ladib
yashirya musu abincin, ita kurum yake jira ya fara aiki. Bayan ta saka tufafi tazo
sukaci abincin hankali ya kwanta! Sai yanzu suka samu natsuwa, dan yau kam sunyi
rabin azumi, duk da wannan ba sabo bane, haka Mama take musu wata rana idan
tanajin mugun halinta!

Bayan sun gama cin abincin, ta umurce Ladib tayaje yayi wanka sbd 3:30 zai
tafi islamiya. Ita kuma ta dau wayarta tafara neman Dadyn nata a watApp, mssgs ta
turamasa ganin yana online. "Dady nah nayi miss dinka sosai" duk da baya kan watApp
din, amma ganin shigowar mssg ta watApp dinshi, dauke da tambarin *DAUGHTER NAH*
yasaka shi hanzari daukeda farinciki yabuda mssg din.

Lokaci daya yasake murmushi hadeda jin dadi a zuciyar sa yace "Nima nayi miss
dinki daughter, ina kyewarki duk bayan dak'ik'a daya a rayuwata daughter nah"
takan mssg dinta kuwa ya mayar mata kamar haka "me too daughter, ina kika shiga ne
yau? Tun safe nake nemanki" "nashiga busy ne yau Dady nah, ykk" "klu nake sai
kyewarki kawai ke damuna, amma yanzu komai normal tunda lafiyarki lau" hawayen
bakin ciki suka kwararo mata, idan har zata tuna rabuwar ta da dady dole zatayi
rashin sa, tasan ta rasa Dady a rayuwar ta, gashi son sa da kaunar sa sunyi katutu
a cikin zuciyar ta, ita kanta tana mamakin lokacin da tafara son wanda bata taba
gani ba, kuma bata taba tunanin zasu hadu daidai da rana daya ba. "Toh wannan me
yake nufi? Anya kuwa ma Dady yana so nah? Idan ma yanasona to meyasa ya boyemin?
Wannan yana nufin baya sona kenan?" Haka taita jero ma kanta tambayoyi a fili,
wadanda batada amsar ko daya daga cikinsu.
"Daughter" yakira sunanta, sam hannun ta yakasa daukar wayar bale yayi reply.
"Daughter yau nafahimce kina cikin damuwa gaskiya, dan Allah idan da wani abu
kigayamin" ya turomata tareda furta "OMG! Pls daughter Kiyi mgn mana" a fili,
cikeda damuwa kamar yana gabanta.

Kukane yayi galaba a kanta, duk da tayi bakin k'okarinta akan rashin zuwansa,
wayar takashe tareda rera kukanta mai rai da motsi! Tafi awa tana kuka, idanuwanta
suka rine sukayi jajir dasu, fuskar ta ta kumbura, kanta yadinga juyamata kan kace
me yafara ciwo!; kan kujerar bacci yayi gaba da ita.

Shikuwa hankalinsa yayi matu'kar tashi, yafahimce yau daughter'n tasa tana
cikin wani hali, shima nan take yaji yatsunduma cikin bakin ciki da tashin hankali!
Junior ne yashigo dauke da ball, sai cillata yake a k'asa, ganin fuskar uncle
junior yau ba walwala yasanyashi yada ball din ya hauro kan gadun "uncle junior
bakada lfy ne?" Kai kawai ya girgizamai, baice dashi uffan ba. "Uncle nagayawa
Hajiya bakada lfy?" Junior yafada cikin sigar dausayi "kaga! Ni lafiyata lumui, je
kacigaba da ball dinka" baki junior ya turo "toh amma ai yau kace zamuje gidan momy
nah ko ka manta?" Idanuwan sa ya rufe dasuka soma canza kala yace "haka ne, ban
mantaba, amma sai zuwa 4 nace zamuje ko" "hakane fa na manta" junior yafada hadeda
toshi baki. "Kaje Mummy ta shirya ka kafin nima na shirya mutafi" "yeeerhhhh"
junior yawashe baki, yadau ball dinsa ya fita da gudu.

"Iyee! Lallai yarinya, wato kinga dazu na daga miki k'afa, shine yanzu kikazo
kikasamu guri kikayi arsheshe2 kina bacci" Mama ke famar yiwa Maryam masifa, bayan
tayi mata jagab da ruwa masu dan karin sanyi. Tashi tayi fuskar ta a kumbure,
hawaye na kwarara a idanunta, tafito falo. Bayan ta mama tabiyo, sai masifa take
"saura kuma idan kika shiga kitchen din kisamu katifa ki shimfida ki kwanta, dan
nasan yanzu sai mukai karfe 9 baki gama girkin dare ba a gidannan, sannan ko wlhy
ki haduda fushina, kindai san koni wacece, kin kuma san danyin aikina" tana karasa
maganar tata saiga Ladib tareda yaya Ma'aruf sun shigo.

Kallon tsana yaya Ma'aruf yabi Mama dashi, gameda kallon Maryam datake
famar goge hawayenta. "ke ina zakije haka?" Ma'aruf yatambaya fuskar nan turmuke
"Awooo lallai! Yau ga Ubanta ko? Toh aiki nasakata ko bazatayi bane" kallon takaici
ya wulgama ta, cike da tsana, daga bisani yamayar da kallon sa ga Maryam datake
k'okarin shiga kitchen. Hawaye ne suka kwararoma Ladib, dan shi a rayuwar sa bayaso
yaga yar uwarsa ta zubda hawaye, domin jinta yake tamkar mahaifiyarsa. Daki yawuce
cike da kunar rai tareda k'ara tsanar Mama a ransa! Yaya Ma'aruf yabi Maryam
kitchen yana mai tirr da abinda mahaifiyar sa ke aikatawa na marasa imani.

Aiki tafara tukuru, tana zubarda hawaye, shigowar mutun dataje ne yasanyata
k'okarin share hawayenta. Yaya Ma'aruf tagani fuskar sa ba annuri, Hakuri sosai
yabata tareda nuna mata dinbin ladarda zata samu idan taci wannan jarabawar, domin
kuwa jarabawace Daga ubangiji ma daukaki, duk wanda Allah ya daukewa Uwa yakuma
hadashi da kishiyar Uwa mara imani toh hakika yana jarabashi ne (ALLAH SARKI UWA😪
WE REALLY MISS U MY MOMY😰 WE NEVER FORGET U IN OUR PRAYER😭) sosai Ma'aruf
yakwantar mata da hankali tareda nunamata
*{‫الصبرين‬ ‫مع‬ ‫الله‬ ‫*ان‬.

*BASAKKWATAR KUCE*👯

*Ⓜªŋşħªŗŧ ŋºvęłş📚*
[3/18, 11:01 AM] Manshart: *MISKILANCI KO GIDADANCI*❓

```Written by Manshart💘```

~In dedicated to my luvly Dady (Alhaji) & Mummy (Bissalam)~


*{Đïş ïş mý şęĉºŋð ŋºvęł}*👌🏼

*Part 14*

Yau kusan kwana biyu, basuyi chart ba, kota hau online bata yimasa magana.
Ita a nata tunanin hakane kadai zaisa ta manta dashi! Tunda tasan ta rasashi har
abada. Shima yakasa yimata magana tun lokacin data ki ta gayamai damuwarta.

A bangarin Alhaji kuwa, Mummy ma bata ganekansa, duk yabi ya zuzuce! Abinci ma
yadainaci, yadda aka ajiye haka ake tarad dashi, drinks kawai yakesha shima Mummy
ce ke cilastashi. Duk a tsammanin Mummy Daddy yasanar wa Alhaji maganar auren,
shiyasa ya shiga damuwa, dalilin dayasa bata wani neme tasan abinda kedamunsa ba,
sai dai kawai tace dashi yayi hakuri komai zai koma story, kuma ya dage da addu'a
Allah zaiyi mafita.

Fairuza da Maryam ne zaune a daki, yau tazo kawomata ziyara, kasancewar tun
bikin Yaya Mubarak basu haduba sai waya kawai. Fairuza ta fahimce dimbin damuwa a
fuskar amaniyar tata, duk da Maryam tana daremata, amma a shakuwarsu takai ta gane
kankanuwar damuwa idan Maryam tana da ita.

"Besty wai yau lafiyar ki kuwa? Naga kin canza ba kamar yadda nake ganinkiba"
murmushin karfin hali ta lalabu, daga bisani tace "ba komai Besty karki damu"
hannayinta data daura kan kafar Fairuza ta watsar "kinga, wlhy ban yardaba, dole
akwai abinda ke damunki, sai dai idan zaki boyemin, kuma yin hakan BABBAN KUSKIRE
ne (AUNTY RASH KARDAM)! Domin kuwa nasan kaf duniyar nan bakida wadda zaki gayama
damuwarki, wadda ta huce ni, kuma naga Maryam abokin kuka baa boye masa mutuwa"
tagumi Maryam ta zuba, hadeda lumshe kyawawan idanuwanta masu kamada gold, "I told
u bakomai Besty" tashi Fairuza tayi tareda daukar handbag dinta, "tunda bankai
matsayin ki sanarmin damuwarki ba, toh ni kinga tafiya ta" ta juya a fusace!

Gabanta Maryam ta tara, "am sorry Besty nah, koma ki zauna, zan gayamiki"
amshe hannunta tayi daga riqon da Maryam tayimata, tareda komawa kan gadun tabuga
faster, fuskar nan turmuk'e!

Maryam ta kwashe komai ta sanarmata, maganar da Abba yayi, har rayuwar su da


Dady, dakuma halinda take ciki a yanzu. "Amma Besty me yasa baki gayamai cewa
kinada wanda kike soba?" Hawaye na ambaliya a kumatunta tace "Hmmm... Besty kenan!
Taya zan sanarwa Abba inada wanda nakeso, dai2 da rana baitaba furtamin kalma mai
halak'a da SO ba, tun haduwarmu, sai dai abinda nasani shine, akwai Tausayi,
Aminci, Yarda, Kulawa, da kuma Shakuwa, a tsakanin mu, taya zan ce yanasona?"
Fairuza ta dubeta cikin kulawa hadeda son gano wani abu a fuskar ta tace "kin jero
abubuwa 5, wadanda a cikinsu akwai abu 3, wadanda idan aka samesu acikin zuciyar
mutane biyu wato mace da namiji, toh wannan ko shakka babu akwai *BOYAYYIN
AL'AMARI* a cikin zuciyar su, SO da Kauna kenan! Sai dai *MISKILANCI* zai iya hana
ma'abuta su bayyana kansu ga junansu, saboda haka Maryam ina tabbatar miki cewa
yadda kike azabtuwa da son sa! shima na tabbata duk inda yake a duniya yana
azabtuwa sosai ta dalilin Shakuwar dake tsakaninku" "hakane Besty, amma yanzu komai
yazo karshe Ai, tunda satin nan zaayi auren" zaro ido Fairuza tayi "a satin nan
Besty fa kikace?" Jinjina mata kai tayi tareda cewa "haka Abba yafada, kuma ba
alamar wasa a tattare dashi ko kadan" Fairuza ta jinjina al'amarin, a zahirin
gaskiya tana mai jin dadin Besty'n ta zata fita daga cikin K'angin bautar da take
ciki, amma kuma tana tausayin ta, kasancewar batasan wanda zata aura ba, maybe ma
zai walakanta tane. Ba irin shawarar da Fairuza bata bataba, takuma nuna mata ta
dauka *KADARAR TACE*, kuma ta dauketa hannu bibbiyu, kuma tayi na'am da shawarta,
harma ta sake jikinta suka fara meeting din yadda zasu gudanarda shagalin biki.
Fairuza batabar gidan ba sai 6 na marece, dan har girki saida ta tayata kafin
tatafi.

Kuyi hakuri da wannan pls🙏🏼am very busy today.


*Ⓜªŋşħªŗŧ ŋºvęłş📚*
[3/18, 11:01 AM] Manshart: *MISKILANCI KO GIDADANCI*❓

```Written by Manshart💘```

~In dedicated to my luvly Dady (Alhaji) & Mummy (Bissalam)~

*{Đïş ïş mý şęĉºŋð ŋºvęł}*👌🏼

*Part 15*

Yau takama saura kwana biyar adaura aure, su Dady kuwa sai shiri akeyi,
inda ya kera makekin gida nagani na fada, na kuma nunawa tsara. Haka ma Mummy da
Umma, sunata shirin biki, dangi da yan uwa kowa yasamu labarin gagarumin bikin da
zaai. Banda Alhaji dashi har yanzu baisan wainar da ake tuyawaba, saidai gaya
mutane dayawa a familyn suna mai wani kallo, wanda bai yarda dashiba, kallon biri
yakemusu sukuma sunamai kallon aiba😂, Kuma shi bai neme yasan daliliba.

Bangarin su Maryam kuwa, shirye2 sukeyi sosai, su Fairuza ba zama, kullum


suna bisa hanya, kuma yau zaayi Kamu, duk yau basu zauna ba hidima tayi yawa.

Mama ce da su Ummi suna zaune cikin dakin Mama, fuskar mama Sam ba annuri,
domin kuwa taje gurin malum2n dinta (domin bazan kirashi malami ba, dan duk mai
bugun k'asa, komai aiki da jinnu toh bokane!) Kuma yatabbatar mata cewa, aure kan
saidai tayi hakuri, amma abisa duban dayayi mata, yagano cewa harma anyi auren,
wato buk'ata dai bata biyaba, kawai tayi hakuri, wannan auren hadin Allah ne!

"Haba Mama, mizaisa kidamar da kanki ga wannan auren? Bayan kinsan yadda
tushinsa yake, wannan mijin bashine yaganta yace yanasoba, Abba nefa ya hada
aurennan" "ai kuwa gaya mata dai Ummi, ni wannan auren ai ko a k'afa aka daura min
shi zan kwance shi, kina ganinfa, ba ko kare wanda yazo gidannan da cewa yazo a
matsayin dan uwan mijin ba, sunansa mafa bata saniba, ba Lefe, kuma wai ace a satin
nan za'ai, to wama yasani ko sadaka ya bayar da ita a masallaci" Ummi da Safara'u
kefada suna kallon Mama data buga takumi! Murmushin mugunta Mama ta sake, hadeda
kallonsu tace "wannan maganar taku abun aduba ce kuma fa, banyi wannan tunanin ba,
amma gaskiya kun kawo shawara" Dariya sosai Mama da 'ya'yan nata sukayi, daga
bisani tabasu kudi makudai suka fita shopping mall, domin yau so suke suyi wankan
rashin yarda.

K'arfe 3:30Pm,
Maryam ce zaune kan gado, sai kuka take, domin kuwa taji maganar su Mama
kaf, a kunnuwanta. "Haba Besty, har sau nawa zan gayamiki kiyi hakuri kibar kukan
nan?" Fairuza ta fada tana kan dressing mirror, wanda take makeup akai. Ganin
Maryam batada neyar dainawa, yasata tashi ta dawo gurinta, zauna wa tayi ta daura
hannuwanta kan cinyar Maryam, "kinga Besty, dan Allah mana kidaina kuka, yaufa ba
ranar kuka bane a gareki, ranar farinciki....." "Dole nayi kuka Faizy, kinfi kowa
sanin halinda nake ciki, ki dubafa kigani yaufa saura kwana 5, a daura aurena, amma
bansan dawa za'a daura min wannan auren ba, sa'annan ba laife, ba kayanda zan saka,
kuma kinfi kowa sanin idan baa kawo wadannan kayanba, sai nasha gori da habaici
agurin su Mama, sa'annan kice ba zanyi kukaba" takai maganar tana mai sakin
azababbin lumfashi!

Duk tagama bawa Fairuza tausayi, tasan maganar ta hakkun ce, dole ayimata
gori, domin kuwa yanzu duk amaryar da zaakai ba laife, dole zatasha surutu a cikin
gari, bare Maryam da tatara makiya, musamman su Mama. Rungumeta tayi sbd batasan
saurarin kukan ta ko kadan, tace "hakuri zamuyi Besty, insha'allah Allah bazai
tozartakiba, kuma bazai taba bari wani bil'adam ya tozartaki ba, kiyi tawakkali ga
Allah, domin kuwa Allah (SWA) yana cewa; duk wanda ya dogara (tawakkali) ga Allah,
toh Allah zai isarmasa. SBD haka Besty pls kidaina kuka, kibarma Allah komai na
rayuwarki, tunda yayi alkawarin zaiyi miki mafita idan kika dogara gareshi" wani
sanyi Maryam taji, taji kuma ta tsunduma cikin farinciki. Godiya tayima Faizy
sosai, dakuma fatar Allah yabarsu tare, dan kuwa itakam tagams dacin k'awa.

Wayar Maryam ce ta dauke k'ara, Fairuza tamata nuni data daga. Daukar wayar
tayi ta kara a kunne, hade da sallama, bansan me yace da itaba, naji tace "toh
Abba, na gode sosai Allah yakara bude" ta kashe wayar. Murmushi tasakarwa Faizy,
Fairuza ta manna mata signal, kasancewar Faizy taji abinda Abba yafada sbd speaker
tasaka. Bayan minti 5 saiga Shamsudeen yashigo, dauke da ledodi tigini2, Ladib ma
ya rigomai wasu. Suka shigo da sallama, Fairuza ta amsa cikin fara'a, huri
shamsudeen yasamu ya ajiye kayan, hadeda cewa "gasu inji mai gida yace akawo miki"
godiya tamai, ya fita. Cikin farinciki Fairuza ta isa ga kayan, fiddo da kayan
tayi, ta babbajesu, "wowwww!" Fairuza tafada, hadeda kallon Maryam data zuba tagumi
tana kallon ta, murmushi ta sakar mata hadeda karasowa suka da kayan. Wedding
Gown's ne kala2, hadeda da under wears, sai sarkokine gold masu shegin tsada da da
kyau, ga daukar hankali! Kayan dai sun hadu matu'ka, Ladib yace "yayi aunty SadiQa,
wadannan kaya haka, ai sai k'asar turai idan kika saka su" Dariya dukkansu sukayi,
Fairuza tace " kinga Besty, yanzu kowa mu ake jira, za'a fara Kamun nan, sbd haka
kiyi sauri ki shirya kafin afara kiran afito2" to tace mata, Fairuza ta zabamata
wadanda zata saka, wata gown ce coffe brown, mai ratsin hannu, hadeda kayan sarka
da handbag, komai iri daya. Tirkashi! Tayi masifar kyau sosai, gown din ta fiddo da
ita, tayi parking din gashin kanta, da ribbon, gashin sai sheki yake, a Teema's
Hair Saloon & henns, akai mata gyaran kai da kunshi, dama sun kware gurin gyaran
kan amare, barin maryam da gashinta har gadon bayanta. Masha'Allah!

Karfe 4:00Pm suka fito, dama can kowa yayi ready amarya kawai ake jira a nufe
Bafarawa institute da ita, can old airport gidan Gwoggo Sa'adatŭ kanwar Abba kenan.
Motocin suka shiga aka nufe gidan da ita, koda suka isa jama'a tawaga2 antaru,
shigowar amarya kawai ake jiya, DJ kuwa sai zuba zance yake, ganin motoci na
shigowa yayi shela akan ga amarya ta iso.

Wai wai wai! Karkuso kuga yadda ake kallon ta, domin kuwa kyau tayi bana wasa ba.
Yan bakin ciki kuwa su Ummi da kawayinsu wadanda suka gyayyato domin sutayasu ganin
kwaf zan iya cewa har zawwa saida sukayi, irin yadda sukaga Maryam. Mamaki suke a
ina ta samu wadannan tufafin? ga alama ma a turai akai Oderring dinsu, dan kuwa
sai wane-da-wane zaka gani da irinsu. Nan DJ ya umurce amarya data zauna, itada
babbar aminyarta wato Faizy, bakin fairuza baya rufuwa, domin taga fuskar yan bakin
ciki ta canza color.

Can fa na hango Manshart GRP sai shagali ake, an samu zazzafa. Su Reefat
(Maisona) da M fkyht ansamu kujeru anbaje, can kuma na hango Hafcy london da Billy
AA sai zuk'ar 5Alive akeyi, ansamu banza😜 luvly ma da nafspretty da Fareeda baa
barsu a bayaba, can na hangosu suma sai brush ske da chicken ba sassafci😂dama
sauran yan grp din, duk na ganku👀. Anci ansha an dancee, sai 8 na dare aka watse,
su Safara'u kuwa, tuni sun kai gida, sun baiwa Mama labari, daren a bakin ciki suka
kwana su kadai, dan kuwa Maryam gidan gwaggo Sa'adatŭ suka kwana itada su Fairuza
da Ladib.

Haka aka share kwanakinnan 4 kullum da events dinda ake hadawa, kuma ko wannan
su na kece raini, har village day saida sukayi, da Arabic night, inda aka zuzzube
basiru na yarin Larabci da hindi, abindai zan iya cewa Sai wanda yagano. Domin
hausawa suna cewa "Gani yakore ji".

Alhaji ne kwance a daki, kamar marar lafiya. Wayarsa ce tadau ruri, tsaye
yatashi daga kwancin dayake, ganin kiran babba ne. Dagawa yayi gameda sallama. Duk
yadda nakai gason jin labari banji me suka fadaba, naji yace " toh, Dady gani nan
zuwa yanzu. Wayar ya ajiye, hade da daukar hularsa ya zura takalminsa yafita.
Kishingide ya tarad da Dady cikin falon sa, da sallama ya iso gareshi, cikin ladabi
da girmamawa. Amsawa Dady yayi shima cikin kulawa, hadeda yimai nuni daya zauna kan
kujera. Badan bayason yimai musuba, dabazai zauna ba, sbd ladabi, ya tashi ya koma
kan kujera, wadda ke gefin Dady, ya sunkuyar da kanshi kasa. Ledar dake kusa dashi
ya dauko ya bashi "wannan nakane, gobe zakasa mutafi dauren auren SadiQ skt idan
Allah yakaimu" cikeda mamaki Alhaji ya nufe shi, batareda yaja dashiba ya amsa yana
mai godiya, sa'annan yabashi izinin tafiya. Tashi yayi jiki ba kwari, yimai fatan
tashi lfy, yaja kofar yafita.

Bai dire ko inaba sai dakinsa, kan gadu ya cilla ledar, ya koma ya kwanta abinsa,
batareda yasan sirrinda ledar take tattare dashiba, ya kwanta abinsa bako tunani a
ransa. Saidai yayi tunanin me yasa Dady yazabe sai shi dole zashina dauren auren,
bayan kuma basu jima da zuwa garinba.

Yau takama Asabar 1 ga watan jamadha sani, shekara ta dubu daya da dari daya da
goma sha bakwai, hijirar manzon Allah (SAW) daga makka zuwa madina. Tun da sassafe
gidan yatashi da hayaniya, yan uwa da abokanan arziki duk sun hallara, aunty Zainab
ma ta kd tazo, itada yaranta musaddiq da SadiQa, tareda kanwar mijinta Haiza.

Har karfe 8 Dady baiga Alhaji ya fitoba, kuma 8:30 zasu tashi, kusan kowa ya
shirya, mutane ma wadanda Dady ya gayyato da abokanan su SadiQ dana su Jabir da
Sabir duk sun hallara, a harabar gidan. Amma Alhaji bai fitoba, waya Dady ya dauka
yakirashi, kusan 10missed calls bai dauka ba, SadiQ ya aima dayaje ya kira masa
Alhaji.

Kwance yake, sai bacci yake abin shi, cikin kunciyar hankali, knock din dakin
SadiQ yashigayi, ganin bazata kareba yasashi kara knock din sosai, yadda ko suma
kayi kaji wannan bugun dakin dole ka farfado. Tsaki yaja, jin bugun kofar da akeyi,
kamar wani makawo. Lalubo wayarsa yayi, domin ganin ko karfe nawa yanzu, "OMG! 10
missed calls, wanne irin bacci ne nakeyi har Dady yamin wadannan missed calls
haka?" Ya tambaye kanshi, tareda tashi ya bude kofar. Tsaki SadiQ yaja ganin threeQ
sanye da jikin shi, alamar yanzu yatashi daga bacci. "Waikai me ke damunka ne
Alhaji? Kodai ka mantane cewa yaune dauren auren, dazakazo kanata bacci, gashi kowa
ya shirya sai kai ake jira" juyawa yayi tareda cewa "Nasani mana, dayake ka
sanarmin cewa zakayi aure, har yau dauren aure, sa'annan ma kace ni kawai ake jira,
nine angon dabaza'a jeba sai tareda ni?" Cike da mamaki SadiQ yake kallonshi, yace
"Toh bakaine angon ba nine ko" cikin ko in kula yace dashi "kasan da haka zakace ni
kawai ake jira, kaga malam, kafita kuje tun huri, tunkan lokaci bai yakorema ba"
SadiQ kam yagamayin mutuwar tsaye tuni, lalubo natsuwarsa yayi yace "Kaga man,
Dady ne yace kazo yana nemanka, SBD haka kashirya mu tafi, Allah kaikadai ake jira"
sai a lokacin ya tuna da ledar da Dady yabashi jiya, daukota yayi yabaje kayan kan
gado, SadiQ yace "kaga kabarsu zan shiryama komai, je kawai ka watsa ruwa kafito"
batareda ya amsamai ba, yabar kayan yanufe toilet. A toilet din yakai kusan 15mins
bai fitoba, kala ran SadiQ bai baceba har takai ga yayi mugun baci, Barin ma karyar
dayakewa Dady cewa shirine suke, gasu tafe. Nan fa SadiQ yahau gewayar dakin, yana
mai fargabar kiran Dady, dan yanzu kam baisan wace karya zaiyimai ba.

Sai can yafito, daure da towel, ya daura daya yana goge sumar kansa data
kwanta lumau, da daya, sai sheki take abinta. Guntun tsaki SadiQ yaja, kafin nan
yakaraso kusadashi, dayake tsaye kan mirror, yana shafa mai. "Pls Alhaji, dan Allah
kayi da sauri mana, wlhy Dady yayita kira, yace mu kadai suke jira, dan harsun
shiga motoci" batareda ya tankashiba yafice weldrobe yadauko suite, zai saka, SadiQ
yayi saurin kawowa gareshi, ya amshe suite din "wai dan Allah kai wane irin
*BAGIDAJE*ne? Wadancan kayanfa Dady yaci kasaka, kuma miye na dauko wannan?" SadiQ
yafad'a a fusace "Toh wai kai why not kake restricted dina, wadannan kayan ko yaune
dauren aurena iyakacinsu kenan, toh meyasa kake wahalar da kanka akan saina saka
wadannan kayan?" Murmushin takaici SadiQ yayi, ganin yana k'okarin sakawa yasaka
SadiQ amshe tufafin yace, "bazaiyu ka saka wadannan tufafi ba gaskiya, dan Allah
kasaka wadanda Dady yabaka pls n pls" wani iska yasake a bakinsa, mai zafi, ya koma
kan kadon ya dauko tufafin, shaddace tsadadda light blue, rigace da malum2, dan
guntun tsaki yaja, ganin babbar rigar, danshi ya tsane babbar riga, badan yanasoba
yadaka, yasa blue takalmi Italy, da designer watch hadeda links set, yayi kyau bana
wasaba, yadauko hula itama light blue yasaka, yakaita 0. Wayyo! Karkuso ganin
yadda tsintsar kyaunsa ya bayyana a zahiri, wow! SadiQ ya furta, lokacin dasukayi
2eyes dashi. "Kaga yadda kayi kyau kuwa? Wlhy kamar akshe khumar, wannan kyau haka"
Tsaki yaja yafice, SadiQ yagoya masa baya sukafita.

A falo suka tarad da yan uwa, kowa sai murna yake, suna yava irin kyauda
Alhaji yayi. Batareda ya tankasu ba ya gaisheda Mummy, ta sakarmai murmushi, ya
gaisheda Umma, itama ta amsa a far'ance tareda yimai fatan alkhairi. SadiQ yana
beye dashi, suka fita.

Mototin dasukayi parking sai jeransu suke suka nufa. Jabir da Sabir suka fito
suka nufosu dauke da murmushi a fuskokinsu. Hannu suka bashi tareda cewa
"congratulation" suna jinjina hannun nashi, a zuciyarshi yace "toh miye na congrat?
Bayan banine angon ba, amma kuma SadiQ is my bross, za'a iya min congrat domin
zaiyi aure" suka k'arasa dashi motarda zai shiga, mutanema sun fito kowa sai
congrat yakemai. Baiyi wani mamaki ba dan sun yimai congrat, yashiga motar suka
nufe SOKOTO.

*YAR MUTAN MARNAWA*😍

*Ⓜªŋşħªŗŧ ŋºvęłş📚*
[3/18, 11:01 AM] Manshart: *MISKILANCI KO GIDADANCI*❓

```Written by Manshart💘```

~In dedicated to my luvly Dady (Alhaji) & Mummy (Bissalam)~

*{Đïş ïş mý şęĉºŋð ŋºvęł}*👌🏼

~Wannan part din nakine Naja'atu💃🏼Aisar, hakika kinfi kowa daukin wannan littafin,
sbd hk wannan kyautace gareki. ILYSM❤😘~

*Part 16*

Maryam ce da gwaggo sa'adatu a cikin daki, tareda Fairuza da aunty


Rasheedat wadda take yayarsu ce, itace babbar yar Mama, wacce sam bata dauko halin
Mama ba, itada Ma'aruf suna alawadai da abinda Mama takeyi.

Sai daga ake da Maryam wurin cin dafaffar kazar da gwaggo Sa'adatu tayo mata,
bayan kullum saita tsimata da hadaddun kayan, amma sai ankai ruwa rana Maryam
kesha. Yau ma haka ake da ita, dan har aunty Rasheda tazo mata da wasu, dagyar aka
samu Maryam taci Rabin kazar, gwaggo sa'adatu tabaiwa aunty Rasheda cup cikeda
tsimi tace idan tagamaci tatsareta saitasha. Haka kuwa akayi, tanasha tana yamutse
fuska, Fairuza kuwa sai dariya take mata, ta tsumu sosai, an gyarata in & out.

K'arfe 2:00pm suka iso garin sokoto, dama can su Abba antara tawaga2 ta
al'umma sai su kawai ake jira, tafiya suke cikin mota Alhaji sai tsaki yake, danshi
duk yaji an takura masa, barin ma wannan malum2 dayake sanye da ita. Gaban shine
yayi mugun faduwa, ganin inda ya yada yarinyar da su Sajida suka hadashi da ita,
wani sabon tsanar tane yaji ya tasomai lokaci daya. "Mtcsss, Allah karya hadani da
wannan k'azamar yarinyar, useless" ya fada yana girgiza kansa.

SadiQ kuwa, sosai yagane unguwar dasuka dosa, ganin su Dady dasuke gaba sunyi
parking da motarsu, yasan ya SadiQ sakin murmushi, a zuciyar shi yace "Allah kasa
SadiQa ce matar Alhaji, domin kuwa idan ba karya taminba, nanne gidan su data
nunamin lokacin da na taimaketa kuma yarinyar tanada kirki sosai" kafin nan motocin
suka gama parking, suka fito.

Dady ne ya nufo su Jabir dasuke jaye da hannun Alhaji, sai kamshi yake zubawa,
ya rigo hannun shi yanufe harabar gidan dashi. Cikin rumfunonin da suke cikin
harabar gidan ya shiga yana janye da hannun Alhaji, cike da mamaki Alhaji yake
kallon Dady, shikowa Dady sai murmushi yake sakarmai. Nanfa yaji gaban shi sai
faduwa yake, damashi bayason shiga cikin taro, huri Dady yasamu ya zaunar dashi,
yan daurin auren kuwa sai kallon shi suke, suna yaba kyau irinnan wannan angon,
domin kuwa daka ganin shigarshi basai ka tambaya ba kasan shine angon.

Mai dauren auren yafara shela, ga ango ya iso, batareda bata lokaci ba aka fara
gudanar da abinda ya tarasu. Sunkuye yake da kansa, sai tunani yake kala2, bai
ankaraba yaji mai gabatarwa yace ".......DAURA AUREN USMAN ABUBAKAR IBRAHIM, TAREDA
AMARYAR SA MARYAM SHEHU AL'HASSAN, AKAN SADAKI........" Gabansa ne yayi rassssssss
yafadi, tsaye ya tashi, yana mai kallon Dady, nan take zufa ya karyomai, kansa ya
fara jujjuya, "Da....da....ddyy, aure kuma? Wanne Usman kenan? Badai ni Usman ba?"
Haka yajeruma Dady tambayoyi, atake idanuwansa suka bada kala, hawaye na
kwararomai, tsaye Dady yatashi, hadeda dafa kafadarsa, yasakarmai murmushi, kauce
fuskarsa Alhaji yayi, daga kallon da Dady yake masa "Kaga Alhaji, dan Allah ka
natsu, kabani hadin kai plx, karka tarabin mutane, idan mun koma zanyima bayani,
amma dan Allah karka tada hankali har wani yagane abinda ake ciki". A take yajike
da zufa sharkaf! Sai jujjuya kansa yake, ba wanda ya ankara da abinda ke faruwa,
sai SadiQ kawai datun shigowar su idonshi suke kan Alhaji, yaga duk ya fita
hayyacinshi. Ganin komai zai iya faruwa dashi, yasan ya shi kwace hannun sa ga Dady
yafara kutsawa cikin mutane, domin kuwa jiyake tamkar zuciyarsa zata baro gangar
jikin shi ta fito, saboda bakin ciki!. Fita yayi daga harabar gidan, Dady nabiye
dashi da ido, ya rasa yadda zai bulloma al'amarin. SadiQ dayaga fitarshi, yabishi a
baya, koda ya isa haryatashi mota yana kokarin barin wurin.

" Alhaji! Alhaji!!!" Yakira sunansa, gameda shiga gaban motar, ya ware
hannuwansa, tsaida motar yayi, yabuga kansa ga sitarin motar, nan take lumfashi sa
yafara kaiwa da komowa, tamkar wani mai fitarrai! Cikin hanzari SadiQ ya bude motar
yashiga, rigoshi yayi yana girgizashi, yana "Alhaji! Alhaji!!! Pls karka mutu dan
Allah! Alhaji!!!!!!!" Ganin lumfashin shi yatsaya, a gigice SadiQ yajawo gorar
Faro'n dake ajiye saman motar, yashiga kwaramak a fuska, nan lumfashin yafara
dawowa, hadeda ajiyar heart! Ruwan ya zubamai a baki, a take ya hadiye ruwan
tareda saukarda wahaltaccin lumfashi! Farfadowa yayi yana kiran sunan Allah! SadiQ
yace "sannu" jaye jikinsa yayi kan SadiQ yace "leave me pls, Ashe dakai aka hada
baki aka cuceni?, dama danshi kasakani a gaba akan dole saina zaka wadannan
tufafin?" Girgiza mai kai SadiQ yayi tareda cewa "wannan abun Dady ne ya hada shi,
wlhy banida masaniya akai Alhaji trust me pls" "bazan taba yarda da wannan auren ba
SadiQ, koda kuwa hakan yana nufin zan koma ga mahaliccina, amma gaskiya Dady ya
cuce..." "Haba Alhaji, d u know wat a u saying? Dady nefa" "Yes, I know, wlhy i
can't not SadiQ, bazan iya zama da wannan yarinyar ba, koda kuwa na zauna da ita
bazan iya mata adalciba" "toh naji, koma menene idan muka koma gida sai muyi
solving dinsa, amma yanzu mukoma daga ciki, kasan dole za'a neme kafa" girkiza kai
yayi yana fadin "stop suffering urself, bazan komaba wlhy, kafitamin daga mota
pls". Ba yadda SadiQ baiba akan ya shawo kan Alhaji, amma fir yaki, dole ya fita
motar yabarshi.

Jan motar yayi hadeda bad'a kura, yana rike da k'irjinshi, domin wani
azababbin radadi yakeji. Yana barin wurin su Sabir na karasowa, SadiQ kawai suka
gani a tsaye, ya buga tagumi yana kallon motar Alhaji da har tabar layen, cike da
tunanin yanzu ina zai dosa.

Karasowa sukayi Jabir yace " ina Alhajin?" SadiQ yace "yatafi" Sabir yace "Oh
sheet! Yakamarshi yatafi?" SadiQ yace "me kukeso namai? Rikeshi zanyi nace
baxaitafi ba ko yaya?" Jabir yace "innalillahi wa'innan ilaihirraji'un! Amma
gaskiya Alhaji bai kyau taba, wannan wani irin *GIDADANCI* ce?" SadiQ yace "Alhaji
ne bai kyautaba ko dai Dady? Gaskiya Dady ba haka yakamata yayiba" Sabir yace "koma
meye, *MISKILANCI*'n sane yaja masa, sbd hk kuxo mukoma daga ciki, kar muma Dady
yanememu bamanan" Jabir yace "toh me zamuce da Dady?" Sabir yace "Nasan yadda
za'ai, kawai kuzo muje" "Toh" sukace suka goyamai baya.

Dady ko ba irin kunyar da baijiba, haka aka watse taron, tareda yima ango da
amarya fatan alkhairi. Dady da Abba sun hadu, sunyi gaisuwa gameda godiya sosai ga
junansu, sai karfe 3:30Pm suka tashi, tareda amarya suka koma da Fairuza domin kuwa
Hajiya tabar ta har sati daya, sbd zata zauna gidan yayarta Shafa'u. Sai su Ummi da
Safara'u da Aunty Rasheeda wadda a gidanta amarya zata sauka, kafin dare akaita
dakinta. Da gwaggo sha'adatu akatafi, tareda Ladib da diyan kannin Abba su 3,
Zahra, Yusra, Shareefa. Huduba sosai Abba yayima Maryam, cewa tabi miji tayimasa
biyayya, karta sake yaji wata matsala daga gareta, kuma tayi alkawarin hakan
bazata faruba. Mama kam ko kulata batayiba,amma Maryam ta roke gafararta koda ta
yimata wani laifi.

Sai karfe 6na marece suka isa garin kano, a gidan aunty Rasheeda aka saukesu,
wanda yake cikin Nasarawa, acan suka yada zango. Dady kuwa, a cikin mota sai hakuri
Sulaiman yake bashi, amma Dady yadau alkawarin saiya nunama Alhaji kuskurinsa.

A fusace Dady yashigo gida , dakin shi ya huce yadauke waya yakira Mummy,
yagayamata tazo falonsa yana son ganinta. Baa dau dogon lokaci ba saiga Mummy
tashigo da sallama, bai jira amsa sallamarta ba yatashi a fusace yace "wato ke kika
daure masa gindi akan yatozartani a cikin mutane? Toh wlhy Haj Shafa'u ki kiyayeni
keda d'anki, kuma zanyi maganinku dukkanku" yafita daga falon, yabar Mummy tsaye
cike da taslima.

Dakinta ta koma, su aunty Zainab naciki tareda su Sajida da Aisha andau wanka.
Wayarta ta dauka tayi dialing numbar Alhaji, amma tajita a kashe, lambar Sabir
tayi dialing, bugu daya yadauka, "kana tareda Alhaji" ta tambaya, "Aa Mummy, dama
baidawo gidaba ne?" "Yazaka tambayeni baidawo gidaba, bayan a tare kuka tafi?"
"Amma Mummy...." "Kaga, kazo inason ganinka yanzu2" ta kashe wayar. "Mummy meke
faruwa ne?" Zainab ta tambaya tana sakama junior tufafi, Mummy bata tanka taba
domin ranta a bace yake, kafin nan Sabir yashigo hadeda sallama. "Miya faru gurin
dauren auren ne?" Mummy ta tambaya batareda ta amsamai sallamar saba. Sabir
yakwashe komai ya sanar mata.

Ajiyar zuciya Mummy tayi gameda cewa "shine abinda nake gujema Dadyn ku, amma
yanunamin ban isa na hanashi abinda yayi niyaba, yanzu gashi abinda ya faru, toh
yanzu ina shi Alhajin yake?" "Wlhy Mummy muma bamu saniba, na daukama yadawo gida
wlhy" Mummy ma kasa magana tayi, sai Zainab ce tace "wai dama Alhaji baisan da
auren bane?" Sabir yace "ga alamakam bai saniba" sai lokacin mummy tayi magana
"Wlhy bai saniba Zainab, hasalima baisan wacece za'a aura masa ba" Zainab tazaro
ido gameda cewa "LALLAI AKWAI BABBAN AIKI!".........

*BASAKKWATAR KUCE*👯

*Ⓜªŋşħªŗŧ ŋºvęłş📚*
[3/18, 11:01 AM] Manshart: *MISKILANCI KO GIDADANCI*❓

```Written by Manshart💘```

~In dedicated to my luvly Dady (Alhaji) & Mummy (Bissalam)~

*{Đïş ïş mý şęĉºŋð ŋºvęł}*👌🏼

*Part 17*
Karfe 8:00PM
Aunty Rasheeda sai shirya amarya take, itada Fairuza ne a cikin dakin, sai su Ummi
suna parlor suna jiran fitowar amarya, Maryam kuwa tayi kyau sosai, abuga fulanin
asuli. Maryam kyakkyawar mace ce, farace sosai kasantuwar bafulatana ce, gata da
gashi har gadun baya, idan tayi murmushi har dimple dinta ke fitowa, bansan yadda
zan zaiyane muku kyau irin na Maryam ba, sai dai abinda zan iya cewa daku, Maryam
irin matan nanne kyawawa.

Aunty Rasheeda ta shirya ta sosai, Fairuza ma tasaka tata bajintar, domin


itace ta zubamata makeup, sbd ta iya sosai. Fitowa sukai da ita falo, sai kamshi
take zuba.

Tirkashi!!! Kallo yakoma sama, su Safara'u sai kallonta suke baki bude. Nan fa
suka shiga mototi suka nufe gidan amarya.

Wani mayen gida akashiga dasu, ko wajen gidan abin kallone, barinma dasuka
shiga harabar gidan, nan fa kallo yake. Cikin zumudi su Ummi suka shiga cikin
gidan, su Gwoggo sa'adatu suka shiga da amarya. Falo ne mai fadin gaske, ga dakuna
tako ina, nan fa su Ummi suka koma bakauyun gaske, dan kuwa wani abin ma basu taba
ganinshiba zaman su duniya, sai tattabawa suke suna mamaki da al'ajabi.

Bangare biyu suka gani, daya suka fara shiga wanda ya tabbatar musu shine na
amarya, Kaiii Allah sarkin sammai! ALLAH ka wadatamu duniya da lahira. Dakin ya
hadu, komai na dakin pink ne, ga dressing mirror ya cika da kayan kwalliya kamar ba
gobe, gadun nata Royal ne pink mai dan karin tsada da daukar hankali. Nan fa su
Ummi sukai 2eyes da mayyun akwatuna wurin set 3, akwatunan ma abin kallone, bare
abinda ke ciki. Fairuza taji dadin ganin yadda fuskarsu Ummi tacanza, cike da bakin
ciki, taji dadi sosai dan ko ba komai tasan zaku kaima Mama labari.

Maryam kuwa sai kuka take ganin za'a tafi abarta, damacan taci kukan tun kafin
suzo. Hakuri sosai su Gwoggo suka bata, Fairuza ma tamata alkawarin gobe zata dawo
insha'allahu. Nan dai suka barta suka tafi, dan kuwa dare yayi sosai, kuma ango bai
shigoba. Nan suka barta sai tsoro takeji, dama can ita gwanar tsoroce.

Mummy ce a daki, sai safa-da-marwa take, domin kuwa Dady sai fada yake mata,
wai itace ta bawa Alhaji shawarar ya gudu, kuma tayita kiran layenshi a kashe. Ta
sak'a ta kwance take, tarasa yadda zatai, kuma tadau alwashin saita batawa Alhaji
rai yau a gidannan.

12:00Pm yashigo gidan, bako fargaba a zuciyarsa, sai dai bayaso ya hadu da
kowa a gida, domin bayason asan cewa yadawo. Kunnu kan motarsa yayi cikin gidan,
bayan horn dinda yaitayi kafin mai gadi ya bude. Haskin fitillun motar sane suka
haskakamai idanuwan Dady, dasuka rine suka koma jajir. Daidai inda zaiyi parking da
motar Dady yabuga fasta, gameda rungume hannuwansa, yana jiran fitowarsa.

Fitowa yayi ya sunkuya zaikai gaisuwa, saukar marukka yaji a kuncinsa, saida
ya dafe kunce. Kafin ya ankara Dady yajashi izuwa falon sa, hadeda kwalawa Mummy
kira. Mummy datake gewayen dakin taji kiran Dady, nufar dakin tayi cikin azama.
Tsaye tayi ganin Dady rike da kwalar Alhaji, sai huce yakeyi kamar namiji zaki!

"Ga dan naki yadawo, dama Ai nagayamiki zaizo yasameni" isa Mummy tayi garesu
batace uffan ba. Kwalarsa yasaki hadeda juyawa yabasu baya. "Wato ni zaka tozarta a
cikin dubban al-umma? Kana nufin ni ban isa garekaba ko? Toh ina mai tabbatar ma
wlhy ko bayan raina banyarda ka sake Maryam ba, idan kuma ka k'untata mata wlhy ban
yafemaba har abada" sa'annan ya juyo ya kalleshi "kuma banyarda ka kwana min a
gidaba, katafi duk inda kaga ya fiyema" Dady ya juya yabar gurin. Mummy ma juyawa
tayi tabar falon, suka barshi shi kadai a falon, daga bisani shima yatashi yabar
gidan baki daya.
Fita yayi batareda yasan inda zai nufaba, hasalima baisan inane gidan amaryar
tasaba. Daga karshe ya yanki hukuncin yabar gidan ma kawai. Grand Central Hotel
yanufa, da isarshi Reception yanufa yasamu Receptionist suka bashi information akan
hotel din, nan fa yayi komai suka bashi key mai dauke da room number dinshi ya nufe
can. Yana k'okarin bude dakin itama zata bude nata dakin, wanda ke dubin nashi
dakin. Kallo tabishi dashi har ya shige abinsa baima kula da itaba, zata shiga ne
yarufo dakin dole ta koma ta bude nata tashiga, cike da tunanin wannan handsome.

Bangarin Maryam kuwa, sai kuka take ita kadai, sai budar ido take inda zataji
motsin wani amma shiru. Ko motsi batayi saboda tsoron da takeji, a haka har bacci
yayi awon gaba da ita. Asuba ta gariiiiii.

*YAR MUTAN MARNAWA CE😘*

*Ⓜªŋşħªŗŧ ŋºvęłş📚*
[3/18, 11:01 AM] Manshart: *MISKILANCI KO GIDADANCI*❓

```Written by Manshart💘```

~In dedicated to my luvly Dady (Alhaji) & Mummy (Bissalam)~

*{Đïş ïş mý şęĉºŋð ŋºvęł}*👌🏼

*Part 18*

*Allah readers har kunyar ku nake🙈 Nasan wata zatace Manshart tacika J class,gaskiya
ba haka bane. Amma kuyi hakuri, gaskiya ba lalle bane kuna ganin post dinaba a
kullum, sbd karatu, kuma yanzu sai a slow nake.......abubuwa sunyi yawa, yau lfy

gobe akasin haka, amma inasonku masoyana harma......*

Washi gashi tunda sassafe ta tashi, fitowa tayi tagyara gidan tsaf, tashiga
kitchen domin tanajin yunwa, tun skt rabonta da abinci. Cikin sa'a kuwa ta taradda
kaya tigini2 a store, kayan abincine kala2, ba abinda babu a ciki, harsai ta darje.
Tea & fried egg with baked beans tahada, bayan ta kammala takoma daki ta tsola
wanka. Wayarta ta dauka tayi dialing number Fairuza, ring daya ta dauka, "Hlo
amarya? Ykk ya first night din?" Tsaki taja gameda cewa "bansani ba, wai sai yaushe
zaki shigo ne?" "Karki damu amarya, yanzu breakfast nagama, wanka kawai zanyi
natafi gidan aunty Shafa'u, sai muxo tareda su Sajida" "haba Besty kiyo sauri mana,
har na hada muna breakfast ke kadai nake jira" cikin rashin fahimta Faizy tace
"banganeba, ina angon dazakice nazo muyi breakfast?" Wani bakin cikine ya mamaye
Maryam tace "kinga, nidai dan Allah kizo" "zanzo amma ba yanzuba, dan bazan dako
muku saukoba" Fairuza tafada gameda kashi wayar tana dariya. Haushi tabawa Maryam
itama ta yada wayar kan gado tafada tana rero kuka marar sauti.

Sai karfe 11am yatashi daga bacci, bayan yatashi karfe 6 yayi sallah asba. A
lokacin abinda ya faru jiya yadawo mai a rai, maganar Dady take ta yawo a kansa,
dakin yabi da kallo, a ranshi yace "wai yau ni Alhaji da kwana hotel? Ya ilahi!" A
fili kuwa ya furta "its compulsory 4 me to hate this girl, na tsaneki, yau kin
hadani da iyayena, bantaba bijire ma umurnin iyayena ba koya suka gindayasu, amma
yau.... Kuma kece sila, Kece ......." Kafin ya ida maganar yaji ana knock din
dakin, yakai kusan 5mints kafin yatashi ya isa kofar, "Waye?" Ya tambaya da
raunanniyar murya. "Nice" batareda ya tanka ba ya bude kofar hadeda juyawa yabada
baya. Shigowa tayi sai karairaya take, tana wata tafiya kace ba k'ashi a jikinta.
Ba tareda ya dubeta ba yakoma kan gadon ya zauna, hadeda noce kansa yadaura hannuwa
aka. Wuri tasamu ta zauna a dai2 inda yake zaune, harsuna hada jiki, tsam yatashi
yakai tsaye, sai a lokacin ya dubeta. Yar silinda ce, fara ba sosai ba, tanada kyau
sosai kamar itace ta kera kanta, batada k'iba ko kadan, sanye take da mini siket,
sai wata Riga mai daukeda siririn hannu, rigar bata sauko ta rufe surar taba, sai
wani hirkakin gyale data saba, shigardai Allah wadai. Kauda kansa yayi daga kallon
dayake mata, tareda furta subhanallah! "katashi lfy?" Ta fada cikin wata siririyar
murya mai cike da zak'i, da taushi, hadeda kallon shi tana jujjuya idanuwa. Jin
muryarta yasashi lumshe idanuwansa lokaci daya. "Wakike nema ne? Kuma meya kawoki
dakin nan?" Murmushi tasakar mai tareda tashi tanufeshi, kallo yabita dashi
hartakai gaban shi, ido cikin ido suke kallon juna, nakusan mintota, daga besani
yakauda fuskarsa gefe hadeda sakin iska a bakinsa. Jin an tabe sumar kansa
yasakashi juyowa a fusace tareda yarfe hannun ta "Wai ke ba musulma bace?" Da
sauri ta dubeshi, tana girgiza kanta, so take tayi magana amma ta kasa, girgiza
kanta kawai take, hawaye ne suka ziyarto fuskar ta a lokaci daya, k'ofa ta nufa a
da sauri, mabudin kofar ta jawo hadeda juyowa ta kalleshi tafita. Mamaki fal
zuciyar sa, ganin abubuwan da takeyi "amma kuma meya sakata kuka a lokaci daya? Ko
nine na batamata rai? Toh ko kalmar dana jefeta da itace ta bata mata rai? Amma
kuma idan hakane itace Kalmar data cincinta da ita" haka yaita jerowa a fili, daga
bisani yakoma kan gado yadaura hannuwa yana sak'awa da warwarewa, ganin bazata
fiddashiba yasakashi tashi ya nufe toilet dan watsa ruwa.

Kan touch dinda ke dakin ta fada hawaye na bin kumatunta, cike da bakin cikin
wannan maganar da guy nan yamata. "Me yasa wannan guy yakirani da ba musulmaba? Ko
dan yaga nashiga dakinsa ne?" Deen kaine ka mayarda rayuwata haka, har ake ganin
niba musulma bace" kuka take sosai tana fadin sunan Deen, wanda bansan ko waye
Shiba.

12am Faizy tafito daga gidan aunty Rasheedah, itada Ladib, gidan aunty Shafa'u ta
nufa cike da dauke ta taradda su Sajida. A gate din gidan napep ta saukesu a falo
ta tarad da Labila, tsalle Labila tayi ganin aunty faizy, sosai taji dadin zuwanta,
faizy tace "INA sauran mutanin gidan, naji kowa shiru" Labila tace "Nima yau shiru
nakejin gidan, amma Mummy tana daki" dakin Mummy Faizy ta nufa, janye da hannun
Ladib cikeda jin dadi. Su sajida tasamu suna gyara daki, kanta sukai sukayi hoggin
dinta cike da murna. Faizy tasamu guri ta zauna, Sajida tace "shine aunty faizy ko
kizo biki" Faizy tace "biki kukai ne?" Hadeda zaro ido, Aisha tace "au bakisan
Alhaji'n Mummy yayi aure ba kenan?" Dariya faizy tai tace "kice *Miskilin*yayanku
yai aure, amma fa abun da mam..." Bata k'arasaba Mummy da aunty Zainab suka shigo.
"Ah Fairuza ce yau a gidan namu? Saukar yaushe?" Mummy tafada, dariya Faizy tai
tace "laaa aunty sai kace bana zuwa" "yaushe ko, kinfi 2yrs rabunki da garin nan"
Zainab ta zaro ido tace "lallai aunty Faizy wato ko mummy baa ziyara toh inaga mu
yan kd" duk sukayi dariya. Mummy tace "yanzu ma nasan ba yau kikazo ba daga ina
haka?" Faizy tayi dariya tace "Besty nah aka kawo nan garin, shine mukazo nace zan
saukanan" Mummy tace "nikam nasan da walakin" Sajida tayi karaf tace "Aunty Faizy
ko Maryam ce?" Faizy tace "itafa, Ai shine nazo muje kurakani dan nasan zakuso
hakan" Mummy tace "Allah sarki, wannan dan uwantane?" Ladib yakai k'asa ya gaishe
da ita. Sajida tace "sunada kama kuwa sosai" Wayar Faizy tashiga ring, batareda ta
dagaba tace "kunga kushirya muje, gata sai kirana take wai tsoro takeji ita kadai"
nan fa su Sajida suka shiga shiryawa, aka chaba ado, driver'n su Mummy ya kaisu
itada Aisha da Labila.

A falo suka yada zanzo, shiru kakeji ba kowa, zaunawa sukayi su Sajida na yaba
kyau irin na gidan, Faizy takirata a waya, basuwani jimaba ta fito sanye da hijab,
tsaki Faizy tai takauda kai gefe, Ladib yaje ya rungume ta. Ba laifi ta tarbesu
kuma taji dadin zuwansu, sai dai abinda Faizy bata ganeba shine, ba ango ba labarin
ango, ko yafito yatarbesu. Faizy bata iya boye damuwartaba har saida taja Maryam a
daki.

"Wai Besty ni bangane ba, ina angon naki ne?" Murmushin takaici Maryam tayi, ta
dube Faizy da ta wani tsura mata ido tana saurarenta, "Besty kenan, wlhy Nima har
yanzu bansaka shi a idona bah, tun jiya da kuka fita kuka barni ni kadai har yanzu
ni kadaice a gidan" cikin tashin hankali Faizy tace "bangane ba, kina nufin kice
baki ga shigowar sa bane? Kodai halinki ne kika nuna masa, yasaka shi fushi har ya
bar gidan tun safe?" Hawaye na ambaliya a kumcinta tace "haba Besty kiyarda dani
mana, wlhy baizoba" tagumi Faizy ta buga, hadeda nisawa tace "lallai wannan babban
magana ce, amma wani irin *BAGIDAJE* ne wannan ango, ace amarya ta tare a gidan ka
tun jiya,kakasa zuwa kaga ko lfy ta tashi, gaskiya akwai matsala" rungume ta
Faizy tayi tashiga lallashinta, tareda bata shawarar tacigaba da aikin ta wato
hakuri. Kuma ta bata shawarar tadaina zama da hijab, SBD yanzu gidan mijinta take
ba gidansuba, kuma maxan yanzu saida ADO. Basubar gidan ba sai kusan marece, Maryam
taji kamar karsu tafi, SBD ko banza sun debemata kyewa.

Su Ummi kuwa tun safe suka koma skt, sun baiwa Mama labarin gidan Maryam dakuma
duniyar dake ciki, kut, Mama kam zuciyarta tamkar zata fito saboda bakin ciki, Kuma
tadau alkawarin raba auren.

*ALKALAMIN YAR MUTAN MARNAWA*🤒

*Ⓜªŋşħªŗŧ ŋºvęłş📚*
[3/18, 11:01 AM] Manshart: *MISKILANCI KO GIDADANCI*❓

```Written by Manshart💘```

~In dedicated to my luvly Dady (Alhaji) & Mummy (Bissalam)~

*{Đïş ïş mý şęĉºŋð ŋºvęł}*👌🏼

*Part 19*

Bayan ya fito daga wanka, yana zaune kan bed yajiyo bugun kofa, tashi yayi
ya nufe kofar ya bude, wani mutun yagani dauke da leda a hannu, lfy?" Ya tambaya,
klu dama madan ce tace na kawo" inji mutunin, batareda ya tambaishi ba yace kakoma
dashi" ya kulle kofar, kofar dan sakon yabi da kallo, daga bisani yasani inda dare
yamai. Komawa yayi yasa akai mai odern take away, ya kora da lemo duk da ba sosai
yaciba, yakoma kan gado yana tunanin daughter, sosai yake kyewarta, sai a lokacin
ya tuna da wayarsa, ya lalubota yakunna yafara neman daughter'n tasa.

Kwance take a falo, ganin zamanta haka zaija mata wata matsalar yasaka ta
kunna data dan tagaisa da mutaninta. Ganin shigowar mssg dauke da sunansa yasaka ta
yin hamdala ta godewa Allah, 'dady ina kashiga ne kwana biyu" Maryam ta fada,
"nasan namiki laifi daughter amma kiyi hakuri, wasu abubuwa ne suka min yawa kwanan
nan, amma yanzu alhamdulillah" godiya taima Allah, suka share kusan awa biyu suna
fira, daga bisani sukai sallama, ta shiga aikin kimtsa gidan, duk da ba komai yaiba
amma tasaba da aiki ne, bata gajiya, dama ita gwanar tsafta ce. Bayan ta kammala
wurarin 6 tashiga kitchen ta girka indomie ta hada lemon ta na Coconut n milk ta
fito, tashiga daki ta chab'a wanka. Falo ta dawo ta zauna karfe 8pm Faizy ta kirata
sukasha fira itada Ladib dan gobe zasu shigo sumata bankwana zasu wuce jibi, sai
kusan 9 suka rabu a waya.

Yau da sassafe su Faizy na dakin Mummy ana fira, su Sajida na tsokanar Mummy
danta daya manta da ita tunda yai aure bai dawo gidan ba,Mummy tace anjima daga
gidan Maryam su biya suga amaryar tashi, basu gama maganar ba sukaji muryar Dady
yana kiran Mummy "Shafa'u!! Ke Shafa'u!!!!" Bai daina kiran sunanta ba saida ta
bayyana falon, su Sajida suka goya mata baya, Umma ma ta fito jin kiran Dady daji
ba lafiya ba. Dady kuwa sai huci yake "Mai gida lfy ka...." Kafin Mummy ta ida
maganar Dady yai cikinta yana surfa mata matsifa "ina kika kai Alhaji, nasamu lbrn
baimaje gidan matar sa ba, tun lokacin daya fita gidannan nan yanufe wani gurin,
badai gidan matarsa ba" Mummy tace "haba mai gida, ni ina zankai Alhaji, kafi kowa
sananin duk wannan abu kai kaja, laifina kawai kake gani amma ni banida laifi ko
daya a ciki, idan har zaka min adalci" eh wato adalci ma kikeso nai miki, ni
kunmin adalci ne? Bakiga illar da danki ya minba. Wlhy Shafa'u gameda auren nan
komai zai iya faruwa da naki auren" gaban kowa ne ya fadi har Umma datake famar
bashi hakuri, tace "haba mai gida meya kawo wannan magana kuma a gaban yara" harara
Dady ya watsa mata daga bisani ya juyo kan Mummy "wlhy nabaki nan da kafin na dawo
daga tafiyar da zanyi kin nemo shi duk inda kika kaishi, idan ba haka ba wlhy a
bakin auren ki!!!!" Yabuga babbar rigarshi ya bar falon. Kan kujera Mummy ta fada
tana jero innalillahi wa'aina ilaihirraji'un! Allahumma ajjirni fe musibatee.
Alhaji yanaso yasani cikin wani hali, Umma tadawo kanta tana bata hakuri, Faizy
kuwa duk tagama fadawa duniyar tunani, toh kodai wannan *MISKILIN* ne mijin k'awar
tata, kai bazai ma taba yuwaba, amma in kuwa hakane yazama dole yau takoma gidan
Maryam.

Karfe 3 su Faizy suka isa gidan Maryam, yau kam a falo suka tarad da ita,taci
kwalliya sai kamshe take, bayan sun gama gaisuwa Ladib ya dau wayarta yashige daki,
Faizy tace "Besty wai inane dakin mijinki?" Kallon tuhuma Maryam tabita dashi
hadeda harara, "ban ganeba, duka2 yaushe nazo gidan, ni ba inda na shiga a gidan
nan" Faizy ta tabe baki ta tashi ta shiga dube2 lungu2, har ta kamo wani kayataccin
falo, Wanda yake babba ne, ya hadu matuka, gaban tane ya fadi lokacin da tayi
2eyes da warjagegin pics din su Maryam da Alhaji, wanda daka gani edtn akayi,
sunyi kyau sosai, da sauri ta fito ta baro dakin, inda tabar Maryam a nan ta tarad
da ita, "kingano dakin ne?" "Aa" kawai Faizy tace da ita, taga bisani suka baro
gidan, da dinbin 19 ta arziki, Ladib harda hawaye yai zaibar aunty Maryam, alkawari
tamai idan sukai Holliday zatazo ta tafi dashi, sa'annan fa yashiga murna da
tsalle.

Allah2 Faizy take su isa gidan dan ta sanarwa Mummy, haka kuwa akayi, ita
kadai tasama a daki su Sajida sun fita, kayan da Maryam ta basu ta sauke k'asa
hadeda cire hijab dinta ta fada kan gadon da Mummy take tana tunani, "Aunty
Shafa'u, Ashe dama Maryam ce matar dan nak .." Kafin ta ida maganar mummy takai
zaune, "dagaske kike Fairuza?" Mummy ta tambaya, Faizy tace "wlhy kuwa" Mummy tace
"ke waya gaya miki?" "A falon shi naga makekin PIC dinsu itadashi, amma kinsan wani
abu, ita kanta batasan da pic dinba" Mummy tace "kamar ya batasani ba" nan fa Faizy
takwashe komai ta sanarwa Mummy yadda auren yake, sosai mummy tatausayawa Maryam,
kuma jinjinawa hakiri irin na maryam, taji dadi dan kuwa dama tanada burin hakan,
amma bata samu damaba, Ashe Allah yacikamin burina. Ba laifi Mummy taji sanyi a
zuciyarta, yanzu abinda takeso daya ne, tagano inda Alhaji yashiga, sai kiran no
dinshi take baya received. Faizy ce ta katse tunanin Mummy da cewa "ina su Sajida?"
Mummy tanisa tace "suntafi gidan Kubra ta haihune dazu bayan fitarki" Faizy tace
"ahhh me akasamu ne" mummy tace "mace" Faizy tace "toh bara naje tunda ba nisa,
gashi gobe zan wuce da munci zazzafa ran biki" Mummy tace "Ai kuwa" gyale taja tayi
kiran Ladib dayake falo shida su twins suna wasa, dan shikam akwaishi da son wasa
musamman idan cikin yarane, uwa uba ga games, dan kuwa ko Junior mayen games ne,
Mummy tace "kibarshi mana a gajiye yake yadan sarara" tace toh ta fita. A falo ta
sameshi suna kallon yadda yake buga Mario dan ya kwarai sosai, su twins duk sun
rufeshi suna kallo, zata fita yace "aunty Fairuza fita zaki nazo muje" Husnah tai
karab tace "aa aunty baza'aje dashiba munason wasa dashi" Faizy tai murmushi tace
"toh kaji abinda Husnah ta fada SBD haka kucigaba da wasa dama ba nisa zanyi ba"

Karfe 6:30pm. Yana kwance kan gado yayi ruf da ciki, yana chart da daughter'n
sa, sosai yakejin dadin yadda yake chart da ita, duk tagaba debemasa kyewa, ji
yakai kamar yana gidan Mummy. budin kofa yajiyo, sai lokacin yatuna da bude yabar
kofar da aka kawomai sako. Shigowa tai yau kam shigar da dama2 dan gown ce take
sanye da ita milk color, Gajerin tsaki yai, yasaka hannun shi yajanyo rigarshi
yasaka, guntun murmushi tayi gameda samun guri ta zauna tana kallon shi, ko kallon
ta baiba yacigaba da chart dinshi, ta lura jimi2 yana murmusawa, takai 10mnts a
dakin amma ko a kwalar rigarsa, hasalima ko kallon ta baiba. Ganin bazata
fishshetaba yasanyata cewa "barka da marece, kaikadai kake a dakin? Nazo tayaka
fira ne" batareda ya kalleta ba yace "thanks" murmushin jin dadi tai, ko ba komai
ya kulata, "uhmm....idan bazaka damuba, zan iya tambayar ka?" Sai a lokacin ya juyo
ya dubeta, gaskiya tai matu'kar masa kyau sosai, amma kuma ya murtuke fuska, dan
bayasan ta raina shi, duk da ya tsinci kansa dason amsata, yace "gameda me zaki
tambaini, Allah yasa na sani" ameen tace hadeda cewa "Naga kaikadai ne tun zuwanka
hotel dinnan, banganka tare da wata mace ba, ko saboda me?" Kauda kansa yayi, daga
bisani ya mayarda dubansa gareta lokacin da tace dashi "kabani izinin na tambaika,
amma kuma bakace komai ba" duk da haka yaja wani lokaci kafin yace "ba abunda
yakawoni hotel dinba kenan" ajiyar zuciya ta sauke kan tace "ko zan iya sanin
meyakawoka" "ba hurimin kibane sanin wannan" yafada a tak'aice. Kafin nan aka kwala
kiran sallar magariba, da sauri ta dube agogon wayarta gameda tashi ta kai tsaye,
"lokacin sallah yayi, zanje nai sallah, amma inaso idan nagama zanzo na tayaka fira
saboda ni kadaice" ba musu yace toh" domin kuwa ta burgeshi, ganin tana kula da
addininta.

Karfe 8:30 tashigo dakin, "yakamata kiyo sallama kafin ki shigo" Alhaji yafada
batareda ya jiyo ya kalletaba, yana kan sallaya yana lazimi. "Uhm" kawai tace
tafita tayo sallamar cikin muryarta mai dadin sauraro, ya amsa, kan gado tazauna
tana kallonshi, ya bala'in mata kyau yadda taga sumarsa sai shek'i take, ga sajensa
tubarkallah! Dan ita tanason hadaddin namiji, barin irinsu Alhaji ba sauki. Bayan
ya gama yai addu'a zai shafa suka shafa a tare, tashe yai ya nufo kurera zai zauna
ta tashi daga kan gadon tamai nuni daya zauna, "zauna kawai, ni nanma is OK"
"yazaai haka ta faru, kazo ka zauna ni zan zauna kan kujerar" bajewa yai kan
kujerar idonshi sama,batareda yatankataba, ta lura bayasan surutu bare gardama,
yasata komawa kan gado ta zauna suna fuskantar juna. Sunshare mintota ba wanda yace
da wani uffan, daga bisani ta k'atse shirun da cewa "Nazata fira zamuyi Ai" bai
tankata ba saida ta maimaita kan yace "Inaso naimiki wasu tambayoyi" cikin fara'a
tace "inajinka fada koma wacce irice" "ko wacce irice zaki amsamin"? Jinjinamai kai
tayi yafara da cewa, "da farko inaso nasan ke wacece? Meya kawoki hotel kina
matsayin mace kuma musulma? Kuma waye kuke taredashi a hotel dinnan?" Hawaye ne
suka shiga ambaliya a fuskarta, wanda har saida yai nadamar tambayar ta, duk da
bayasan jin kukan mace, amma yatsinci kansa da jin dadin sautin kukan nata, amma
kuma hankalin shi yatashi, ganin yadda take kukan, hanky yaciro yabata, ta karba ta
goge hawayen tafara da cewa.

"Da fari dai ni Sunana Sairah, mahaifina Alh. Tahir mai kudin gaske ne, mu
yan nan garin ne, muna zama a unguwar Nasarawa, mahaifina Alh. Tahir bafulatini ne,
a cikin kauyen da ake kira (Dan batta) Su biyu ne mahaifiyarsu ta Haifa, shine
babba mahaifinsu sai kanwarsa me suna Hafsa, sai diyan kishiyarta wato IYa, itako
diya ukku ne da ita maza biyu mace daya, Baba Salisu da Baba Abdu, sai macen mai
suna meero. Dukkansu Baba Ilo yasaka su a makarantar boko, amma fur sukak'i sai
Dady na kawai ya daure yai, su duk sukace kiyo sukeso suyi, Inna (uwar Dady) ta
goyamasa baya 100% dan tanaso yai karatun zamani, ba laifi tana yan sana'o'in ta,
na cikin gida gishiri,omo,maggi,kubewa,dss, tana biyamasa kudin sha'anin makarantar
sa idan buk'atar hakan ta taso, SBD IYa ta hana Baba Ilo daukar dawainiyar
makarantar Dady nah, SBD ita nata diyan basu tsaya sun mayarda hankaliba, duk
lokacin da za'ai exams su suke kulle aji..." Nisawa tai hadida kallon shi daya
bayarda komai nashi yana saurarinta, da kuma irin yadda take fitarma ko wanne
harabi hakkinsa. Ta dube agogo 4:15am agogon 9ja, "lokaci yatafi Ashe" ta fada tana
dubanshi dayakasa koda motsi, iska ta hura masa a fuska kasancewar basuda tazara
tsakani, firgigit ya sauko daga tunaninsa, yadube a gogo, dubansa ya mayar gareta,
"bara na barka kai bacci, naga alamar bacci kakeji, zan cigaba gobe idan Allah
yakaimu" Kai ya girgiza mata hadeda cewa "ba bacci nakeba, amma kamar yadda kikace
mubari zuwa goben idan Allah ya kaimu" "toh shikinan asuba ta gari" tafada tana
nufar kofa, har tabuda kofar yace "Asuba ta gariiii"

*Nima Ⓜªŋşħªŗŧ nace ASUBA TA GARIII matan ZAZA😜*

*Ⓜªŋşħªŗŧ ŋºvęłş📚*
[3/18, 11:01 AM] Manshart: *MISKILANCI KO GIDADANCI*❓

```Written by Manshart💘```
~In dedicated to my luvly Dady (Alhaji) & Mummy (Bissalam)~

*{Đïş ïş mý şęĉºŋð ŋºvęł}*👌🏼

*Part 20*
Yau tun da asuba su Faizy suka kama hanyar skt itada Ladib,
acikin mota kuwa sai waya suke da Maryam, tana tsokanarta, su Sajida kuwa ana gidan
aunty Kubra, kuma yaune Dady zaiyi tafiya zuwa German. Umma na dakin shi tana
sharya masa kaya a trolley dinshi dazai je ta su, Umma ta sassafta murya cikin
ladabi tace "mai gida yakamata kasanar wa Shafa'u zaka tafi, SBD baa San ta raiba"
jinjina Kai Dady yai tareda cewa "haka ne, amma wlhy da ba dan tafiya zanyi ba, da
bazan gayama ta ba, dan so nake na hukuntasu itada Dan nata" Umma tace "kama dai
menene yaci ace ka sanar mata, ko ba komai akwai rai a kwai mutuwa" yana saka watch
dinshi yace "je kikirata"Umma tace toh ta tashi. A zaune ta tarad da ita itada
junior, sai damunta yake ina uncle junior, sallama tai ta amsa tasanar mata da
kiran Dady, a tare suka shigo dakin da sallama, Dady ya amsa a takaice, Umma ta
fito falo tabarsu, Mummy ta zauna kan gado tare cewa " antashi lfy" "alhamdulillah"
Dady ya ansata, "dama zan wuceni shine zan sanar miki, kuma inaso kisani, inanan
kan bakata, ba gudu ba jadabaya, nan da sati biyu, kafin na dawo kitabbatar kin
nemoshi duk inda yake" bai tsaya jin me zata fadaba ya dau kayan shi yai waje,
tashi tai hadeda jinjina kai ta dauke trolley'n tashi ta bishi a baya, zaune suka
samu Umma a falo, ganin su sun fito yasaka ta tashi ta nufe Mummy ta amshe
trolley'n tareda sakar mata murmushi, Mummy ma tmaida mata nata murmushin. Dady ya
fita Umma ta bishi Mummy ta koma dakinta, cike da kunci da takaici hadeda bacin
rai, da tasan inda zata samu Alhaji a yau da tayi mugun bata masa rai, amma ku
yanzu ta kudurce nuna masa kuskurinsa.

Karfe 10am ta shigo dakinsa, hadeda sallama, yana kan gado yana chart
da daughter'n sa, sallamar ya amsa hadeda neman izini ga daughter cewa tabashi nan
da minti 30, juyowa yai gareta ta ware idanuwanta tace "sannu da fira" "yawwa" yace
a takaice gameda cewa "mu daura daga inda muka tsaya" zamanta ta gyara ta ajiye
wayarta tecno Y6 a gefe hadeda noce fuskar ta da hawaye ke kokarin saukowa garesu
tafara, "lokaci sai tafiya yake akwana a tashi, Dady na kuwa ilimi sai karuwa yake,
har takai ya fita Manchester gurin karatu, zai karance business Administration,
shekaran shi 6 a k'asar, bayan ya dawo ne ya hadu da mahaifiyata, sukai aure, bayan
sunyi aure, suka tare a Abuja, kasantuwar can yake aiki, abubuwa sun bude masa, yau
suna wannan k'asa gobe suna waccan k'asa yawon honeymoon, hakan yasanya yan uwanshi
jin haushi abun, watan su 5 da aure mahaifinsu (Baba Ilo) yace ga garinku, haka
yasaka Dady nah yadau dawai niyar mahaifiyar sa dama sauran yan uwansa, yana
matu'kar ji dasu, yana kyau tata musu sosai, shine kula dasu da matan su da ma
yayan su, ya daukesu yan uwansa na jini, amma su Sam ba haka bane a zuciyarsu, duk
da suna nunamai so a gaban idon shi, amma daya bada baya zamu dinga zundinshi, zagi
ba irin wanda basa yimasa, duk da yana kyau tata masu,. Mahaifiyata wacce nake kira
Ummeetah, ta jima Allah bai bata haihuwaba, ba asibitin da Dady nah bai je da
itaba, har k'asashin turawa ya fita da ita amma shiru kakeji, likitoti sun tabbatar
mai bazata taba haihuwa ba, hakan yasaka mata karan tsana a gurin yan uwanshi, wata
rana sunje bikin gwaggo Hassi (kanwar Dady) yan uwan shi suka sakata a gaba sai
gori suke mata, haka aka gama bikin bayan sun dawo gida tasamu Dady take cemai
yakara aure dan bataso yan uwanshi suna ganin kamar itace ta hanashi aure, Dady
yace bazai kara aure ba dan baya da muradin ajiye mace sama da daya, kawai tayi
hakuri lokaci ne baiba. Akwana a tashi mahaifina sai gaba arziki yakeyi, ya buda
gidajin man fetur da company's, suna safarar kayayyaki, arziki sai gaba yaki tsanar
da yan uwansa sukemasa sai karuwa take, barin baba Salisu, shine babban makiyin
Dady nah" nisawa tai tadubeshi hadeda murmushi, shikuwa har idanuwansa sun fara
rinewa, dan dajin labarinta akwai ban tausayi a ciki. "Wata rana kwatsam, Ummeetah
tafara ciwon kai mai tsanani, Dady nah yafita office, sai yan aikin gidan mu dake
ta jirga2 suna kaikomo a gidan, dayake ba aikin da Ummeetah takeyi a gidan, masu
aiki keyi. Waya takira Dady cikin azama yadawo gida, ya dauketa suka tafi asibiti,
Alhamdulillah! Dady ya fada, lokacin da akai test Dr yatabbatar mai matarsa tana
dauke da juna biyu, wowowooo! Dadi ba a mgn wanda yasaka Dady rashin boye dinbin
farincikin sa, har kyauta saida yama Dr ta makudan kudi, Dr sai dadi takeji yanaima
Dady godiya. Haka suka dawo gida, ba wanda Dady bai sanarwa Ummeetah tana dauke da
ciki naba, haka ya dauketa suka fita shopping mall, badan sun san me zasu Haifa ba,
Mace ko namiji? Allah ne kawai masanin gaibu, siyayya sosai sukai inda Dady
yakashe makuddan kudi, suka dawo gida, daga nan Ummeetah tacigaba da laulayi, wata
tara cib, ta haihu yarta kyakkyawa, ajin farko, hmmm murna gurin Dady nah baa mgn,
sabanin yan uwansa, da suketa jin haushin murnar da yake, Dady ya dauke wani
tankatsetsin gida yabaiwa Ummeetah a matsalin gift. Sati ya zagewayo suka radamin
suna (Sairah), ancashe naira tai kuka, dan kuwa Dady ya baje kudi shower yadingayi
da kudi, saboda murna. Akwana a tashi har nai shekara daya da haihuwa, Dady nah
kuwa ya hadamin kayataccin birthday, a ranar dad ya mayar da sunan company's da
gidajin mai fetur dayake dasu da sunana *Sairah Industry limited* wanda yake a
cikin garin nan, da kuma *Sairah Internationa PLC* sai gidan man sa shima ya mayar
dashi *SAIRAH T.H LTD* sosai yan uwansa sukai bakin cikin haka, saboda gani suke
yanzu idan dady ya kuma ga Allah shikenan basuda kaso tunda ya mayarda komai nashi
da sunana. Hakan tasakasu kasa boye hasadarsu saida Baba Salisu yaima Dady mgn akan
hakan, dady baice dashi komai ba, hakan yasasu kara jin haushi da tsanar Ummeetah
da Dady. Zuwa2 nafara tasawa kasancewar inada babban jiki, nan da kake ganina
yarinya ce sosai ni, just 19yrs old, Ina girma tsantsar kyauna na kara bayyana, so
da gata Dady nah yake nunamin ainun, baya bari Ummeetah ta dakeni komai girman
laifin dana mata, niko Allah yaini da muguwar barna, ga fada, bana ganin girman na
sama dani ko waye, bare na k'asa dani, kuma banason talaka ko kadan, na tsane
talaka, ma'aikatan gidan mu kowa yasan halina, sau da kafa suke bina, dan saina sa
a Kore mutun bakomai bane a gurina, domin kuwa nashasa ana korar ma'aikata har
bansan iyakabama, tunda nakai 6yrs Dady nah yasakani skul mai tsada sosai, kuma
duk shekara sai Dady nah yamin celebrating birthday, duk abinda Dady yakemin bada
amincewar Ummeetah ba, dan ita tana ganin ba tarbiya bace Dady yake daurani akaiba,
SBD Dady yadauko AL'ADUN WASU (Batul maman) yadaurawa kansa, kuma a kuda yaushe
Dady cewa yake ni *Yar Gata ce* (Miemie bee👄) kuma ni kadai Allah yabashi yazama
wajibi yabani gata wadda ba'a taba bawa wata mace ba a duniya. Hakan yasa bana
daukar Ummeetah da girma ko kadan, duk abinda tamin idan Dady bayanan saina sanar
masa, danaji horn din motarsa nake fitowa na daura hannuwa aka ina kuka, a gigice
Dady yake fitowa, bayama jira securitys su buda masa kofa, idan yafito yashiga dani
gida yaitama masu aikin gidan mu maza da mata fada, dan me zasu barni ina kuka,
Ummeetah kuwa yaita mata fada, kamar zai cinyeta, har kuka take watarana, Niko ko a
jikina dan gani nake kamar sonane batayi Dady kadai ke sona" tana Kai nan ta
girgiza kanta hadeda cewa "Allah sarki Ummeetah, kinsha wahala a kaina. Tun ina
primary skull nake da samari da masoya (friends) kala da iri, kar nakai secondry
gani da k'okari sosai dan kaf class dinmu ba Irina, nice first class upper amma sam
bana mayarda hankali, islamiya ma tuni na daina zuwa, saboda banaji tsokana nake
kuma duka suke, nagayawa Dady yace nadaina zuwa tunda duka suke, Ummeetah tasaka
baki Dady yace ba ruwanta, amma gameda boko kam Dady a tsaye yake, dan yanada burin
nai karatu sosai. Tun da nashiga secondry dady yasakarmin kudi, yasiyamin mota, ni
nake driving dakaina, duk a skul dinmu ba macinda takeda mota saini, ganin haka
yasani daukar kaina yess nakai, nafara girman kai, har wasu sukemin kallon
*MISKILA*, saboda *MISKILANCI* na. Garin su Dady kuwa, bantaba zuwaba, dan banason
zuwa kauye, haka nakecewa Dady kuma baya cilastaman. Bayan na kammala secondry Dady
nah ya hadamin kayataccin party na Candy, da birthday na 17yrs, inda na gayyato
frnds dina mukai rawa mukai shagali tareda abokina kuma boyfriend dina wato
Nuraddeen, wanda tun muna ss1 muke taredashi, yau muna wannan club gobe muna wancan
club jibi muna wannan hotel, a tareda shi, duka a cikin dukiyar Dady muke fafatawa
abunmu, domin kuwa duk wata sai yasaka min kudi a Acount. Munyi party a yau jibi
zamuje umurar mauludi k'asa mai tsalki, wato saudia, nayi farin ciki sosai duk da
ba yaune fariba, tun ina primary 3 muke zuwa hajji da umara. Munje munsauke nauyi
muka dawo, a Daren da muka dawo a daren Dady yakira lawyer'n sa, bansan abinda suka
tattaunaba, Ashe Dady ya mayarda sunan komai nashi har gidajinsa da kadarorinshi da
sunana, bayan lawyer'n sa yafita ni dashi da Ummeetah muka sha fira a falonsa, sai
12pm nakoma dakina hadeda yimusu sallama ta fatan alkhairi, Ashe sallamar
bankwanace" hawayen da suka kwanta a idanuwanta ta matse wanda yasaka shi ganin
zara2n gashin idonta sun yi sharkaf da ruwan hawaye, tausayi ta bashi sosai, cikin
raunaniyar muryarsa yace "kiyi hakuri Sairah...." Sosai taji dadin irin yadda
yakira sunanta, jitai kamar sarewa ake dukamata a kunnuwanta, dan yadda yafadi
sunan harda k'alk'ala. murmushi tasakar mai hadeda cewa "komawa ta dakina keda
wahala, bacci bai daukeniba naji harbin bindiga, ta ko ina, a gigice na tashi
nanufe kofa, bude kofar keda wahala naji jibgegin k'ato ya dakeni a ka da
bindigarsa, nasaka yar k'ara, a firgice nake, dakin Dady suka nufa dani, wanda suke
kwakkwance kan carpet din dakin, sunyi tsit kamar ruwa yacisu, ban ankaraba naji
ogansu yace " me kuke jira dasune?" Nanfa suka saita bindigoginsu suna kokarin cika
umurnin ogan nasu, tsaidasu yai yace sujira, nan yataso yai kaina kamar zai
cinyeni, yatazgo gashin kaina danai parking dinshi da ribbon, sosai naji zafi na
kwala ihu, ina kiran sunan Dady. Dady yai tamaza yace "dan Allah kada ka taba min
yarinya ni komai zakuyimin kuyi min amma kada ku tabata" kan bindiga yabugamasa
wanda yasa Dady sunkuyarda Kansa, Ummeetah ko sai ambaton Allah take, ban auneba
naji sun tashi dasu da bindiga, nanfa na kwala ihu, na daura hannuwa aka. Kukan
motar police suka jiya, kasancewar kukan bindigar tasu takai ko ina, kuma darene
komai amshe yake. Suka rance nakare, ba abinda suka dauka gidan suka gudu".

*Ⓜªŋşħªŗŧ ŋºvęłş📚*
[3/18, 11:01 AM] Manshart: *MISKILANCI KO GIDADANCI*❓

```Written by Manshart💘```

~In dedicated to my luvly Dady (Alhaji) & Mummy (Bissalam)~

*{Đïş ïş mý şęĉºŋð ŋºvęł}*👌🏼

*Part 22*

Nisawa Alhaji yai hadeda kallon ta, yace "gaskiya labarin ki yana cike
da bantaysayi, kuma kina neman taimako sosai a rayuwar ki, domin kuwa a yadda kike
yanzun nan yaci ace kina gidan miji, shi wannan Deen din me zai hana ya aureki
tunda shine ya bata maki rayuwa" kwalla na zuba a idonta ta dubeshi tace "nagane
Deen ba son aure na yake ba, bukatarsa kawai yai mu'amala dani kawai, ni yanzu
abinda ke gabana shine, yadda zan dawoda dukiyar mahaifina a hannuna, domin cikar
burin Dady nah" Cikin kulawa yadubeta "ki hakuri Sairah, insha'allahu zan
taimakeki gwargwadon ikon danake dashi, amma abinda nake so dake, ki daina amincewa
da Deen, domin kuwa ba aikin kwarai kuke aikata wa ba, zina ce kukeyi, kuma Allah
ya haramta zina a cikin Qur'ani Allah yana cewa " WA'AQRABUZ- ZINA!" dama hadissan
manzon Allah (SAW) hani yazo k'arara akan zina, da kuma illarta" sosai yai mata
wa'azi har saida taci kuka wanda ya amsa sunansa, Daga bisani taimai godiya, hadida
masa alkawarin cewa daga yau zata kauracewa Deen insha'allah. "Kaji asalin lbr na,
sbd haka nima inaso nasan ko kai waye, kuma miye sunanka, meya kawoka hotel haka
kawai" ta tambaya tana kallom shi, "Sairah kenan, ni sunana Usman but amfi kirana
da Alhaji, ni dan nan garin ne, wani dalili kawai yasani zuwa nan, wanda lokaci
k'alila zaki sanshi insha'allah" "Alhaji! Alhaji!" Ta maimaita sunan "suna mai
dadi, but ni zan dinga kiranka Elhaj zaka so?" Ta tambaya tana sakarmai signal, "ur
wlcm" yace da ita yana murmushi" Tashi tai zata fita, yana binta da kallo, ta yuyo
tace "Yaya Elhaj zan dawo anjima" gyada mata kai kawai yai, ta fita. Sosai yakejin
wani abu gameda Sairah, musamman da tabashi ainahin lbrnta, "gaskiya Sairah tana
buk'atar taimako a gurina, wanda sanadiyar hakan zan iya fadawa wani hali, amma
zanyi iya k'okarina akan hakan" yafada shida zuciyarsa.

Yau kwanan Dady biyu da tafiya, kafin ya tafi saida ya biya ta gidan Maryam
yabata hakuri tareda tambayar tana buk'atar wani abu, tace a'a sa'annan yatafi.
Kwance take a dakinta sai famar tunanin Elhaj take, gaskiya ta kamu da sonsa, so
bana wasaba, bata tabajin tana son wani namiji ba irin yadda taje tanason Elhaj.
Amma kuma a zuciyar ta tunani take anya kuwa Elhaj zai aure ni? Bayan yagama sanin
ko ni wacece, koma ya zanyi da Deen dayake masifar kishina?. Tana cikin tunanin
taji karar wayarta, Deen tagani kan screen din, dagawa tai "Hllo Deen, Allah? Kai
am very happy wlhy, zuwa yaushe? Atoh Allah yadawo dakai lfy" takatse wayar tareda
jan guntun tsaki. Wayarta ta dauka tai dialing no din Elhaj, yana kwance yana chart
da Maryam, yadaga "Elhaj, kashirya yanzu zanzo mutafi gidana, yau Kaine zaka kawon
ziyara" batareda musuba yace "toh sai kinzo" kwance ta tarad dashi baiko d'aga daga
inda yakeba, murguda baki tai "au ko shiryawa bakaiba?" Yadubeta cikin murmushi,
"na shirya mana" yafada yana kai tsaye, dama a shirye yake, suka fito. Jere suke
tafiya Sairah kamar zata rungume shi, sai matsawa take a jikin shi, shiko sai
karabawa yake domin shi bai sababa, hasalima tsoron mata yake😜. Haka suka fito,
kowa sai kallon su suke, har suka kai bakin motar ta, ita ta budame gaba ya shiga ,
ita kuma ta koma tai jasu. Tafe yake da yar baby'n shi, suna makale, Ai kuwa yabisu
da kallon mamaki da al'ajabi, har suka bar hotel din yana biyar motar Sairah da
kallo, wadda take driving cikin kwarewa. Sai karfe 6pm suka dawo, kowa yawuce
dakinsa domin watsa ruwa, dan kuwa a gajiye suke.

Yau sati daya kenan da tafiyar Dady, SadiQ na zaune shida Sabir a falo, tareda
Mummy da Umma, suna meeting din yadda zasu fara neman Elhaj, wayar SadiQ tahau
ruri. Fita yai domin ganin sunan abokin sa Nasir, wanda ya dameshi da kira tun safe
akan yanaso su hadu. "Yah dai Nasir, yau sai tayarmin da hankali kake" dubinshi
Nasir yai "SadiQ wani abun mamaki nagani, wanda ya tayarmin da hankali tun jiya,
nakasa bacci wlhy" SadiQ yaja tsaki yace "duk zai wuce yan matanka ne suka
yaudareka, kazo kana damuna. Kaga nifa inada very issue a gabana" Nasir yace
"katsaya ka saurareni dan Allah" SadiQ yasake Jan tsaki yace "wai meye? Gayamin
shafshaf" Nasir yai gyaran murya "wai dama SadiQ bross dinka yana biyar mata ne?"
Cikin mamaki SadiQ yake kallon sa "ban ganeba, cikin bross din nawa waye a ciki"
Nasir yace "Alhaji mana" dauke da tashin hankali SadiQ yace "kaga, iskancin naka ya
baro ko ina yau yazo takan bross dina? Wanda yau kusan sati biyu kenan rabon shi da
garin nan" Nasir yace "Hmm..dadina dakai SadiQ akwaika dason karyata mutun wlhy,
toh wlhy idan ma zaka yarda ko bazaka yardaba oho, nidai naga Alhaji da idona,
ganau ba jiyauba a Grand central hotel, shida wata yarinya, da alamu budurwarsa ce,
kuma har da yamma nagansu a tare sun dawo, sun shiga wani daki, idan ka musa kaje
kaganoma idanuwanka SadiQ kaga tafiyata, sai anjima" Nasir ya juya zai tafi. SadiQ
yai saurin jayoshi "haba Nasir, ina kuma zaka tafi? Pls gayamin no din dakin dakaga
sun shiga" Nasir yace Ban luraba da no din dakin, but zan iya gane dakin" SadiQ
yace "hakan ma yayi daidai, pls zan nemeka anjima, but wannan yazamo sirri tsakanin
ni da kai pls" Nasir ya juyarda kansa "wama zan sanarwa, da inaso Ai a masallaci
zan tafi nai shela" yafada yana juyawa cikin tafiyar su ta gayu. SadiQ kuwa a
gigice yashiga gida, ya tarad da su Mummy a inda ya barsu. Guri yasamu ya zauna,
Umma tace "ya naganka duk kayi wani iri haka SadiQ" SadiQ yakwashe komai ya sanar
masu. Cikin firgice Mummy ta tashi, "yanzu abinda Alhaji ya zabarwa kanshi kenan na
zama hotel da yan mata? Innalillahi wa'ainnah ilaihirraji'un!" Umma ta tashi tace
"Ai ba abinda zamu zauna muna fadaba kenan, kamata yai mu tafi hotel din muzo
dashi" Mummy tace "taya zamuje hotel haj Saratu? Kinsan mutane bazasu taba dubin
abinda yakawo mu ba, zasui mana wata fassarar daban" Umma tace "haka ne, amma kuma
Ai Allah zai dube manufarmu, domin kuwa shi da zuciya yake aiki, kuma Ai zamu
sanarwa Mai gida idan abun ya sasantu" Mummy tace "hakan ma yayi muje" Sabir ma
kasa magana yai. Haka suka kama hanyar hotel sabir yana driver'n dinsu.

Zaune suke a dakin Sairah, dan yau tace a dakinta zasui fira. Budin kofa suka
jiyu, cikin firgice Sairah ta kai tsaye, ya shigo sai wuce yake "Sairah waye
wannan?" Kasa magana tai sai kallon su take, idan ta dube wannan ta dube wancan.
Kyakkyawan mari yakai mata a kumce "nace waye wannan?" kan kujera tafada tana kuka
mai tsuma rai. Zai koma kai mata wani marin Elhaj ya rike hannun. Deen yana wuce
yace "kai waye da har zaka rikemin hannu?" Elhaj ya fizge hannun sa yace "koda
bansan waye kaiba, amma na gano kaine Deen" cikin mamaki Deen yake kallon sa "waye
kai nace????" Sai lokacin Elhaj ya dubeshi sama da kasa, "ba wannan tambayar
zakamin ba, idan kai baka sanniba ni nasamu lbrn ka kuma...." Kafin ya isa maganar
Deen ya tada hannu zai mareshi Sairah tai saurin rike hannun, "karka sake ka
mareshi Deen, wannan dan uwana ne, kuma nafison sa sama da kowa a duniya, domin
kuwa shine yadaurani akan hanya" mari yaso yakai mata Elhaj yace "karka sake ka
kara marinta, idan ba hakaba ina tabbatar ma zakai zaman firzin na tsawon shakaru
aro2" Deen yace "ka kuwa san koni waye?" Elhaj yace "bandamu danasan wannan ba,
saidai kai kana buk'atar kasan ko waye ni" Deen ya cije baki yana kokarin yai wani
abun amma ba yakasa. Elhaj yace da Sairah "dauke kayan ki mu tafi" Sairah tatashi
tana kuka ta shirya kayanta tsab tabi Elhaj, suka bar Deen a tsaye. Nan fa Deen
yashiga gewayan dakin yana kaiwa hannayensa naushi. Yarasa abinda zai aikata wa
wannan guy, daga bisani shima ya bar dakin.

Dakin shi suka koma, tazauna kan kujera sai rera kuka take. Sukuwa su Mummy
sunzo harabar hotel din Sabir yai parking suka fito suka nufe ciki, Nasir ne mai
musu jagora. Saida ya nuna musu dakin kafin nan yajuyo. Kuka take marar sauti, haka
yaji yagaji da sauraren kukan nata ya sauko ya nufota yai kneel yazaro hanky a
aljihunsa yafara shafemata kwallan dake zuba, dago kai tai tana kallonshi, ido
cikin ido suke kallon junaaa. Daidai nan su Mummy suka banko kofar.

Tirk'ashiiiiiiii!!!!!!!!!!!!💃🏼

*Ⓜªŋşħªŗŧ ŋºvęłş📚*
[3/18, 11:01 AM] Manshart: *MISKILANCI KO GIDADANCI*❓

```Written by Manshart💘```

~In dedicated to my luvly Dady (Alhaji) & Mummy (Bissalam)~

*{Đïş ïş mý şęĉºŋð ŋºvęł}*👌🏼

Dear friends, I am really appreciate the way ur showing an interest to my novel,


more especially, u my mom (BISSALAM)😍I am truly happy for that wlh😊. Words alone
can not express my appreciation to u. Thank u, thank u, thank u once again. ILYCM❤

*Part 21*

Nan da nan fuskar ta tai sharkaf da hawaye ta matse kwalla,


tarufe idanuwata kan ta saukesu a kan nashi. Yayi shiru sai ita yake saurari,
shima din kukan yake, daga bisani yace "Allah sarki Allah kajikansu da rahma,
mukuma ya kyau tata namu karshen, ki daina kuka Sairah Allah yana saneda muyagon
mutanen da suka kashe iyayenki, kuma Allah bazai barsuba, komai daran dadewa, share
hawayenki" ya bata hanky, ta karba ta goge hawayen, koda suka lura lokacin sallah
ya wuce har 2:30pm ake magana
Shi yafara tashi yaje ya dauro alwala, koda ya fito bata dakin, sallaya ya
shimfita yana kokarin tadawa tashigo da sallama, juyowa yai ya amsa, sanye take da
hijab half iya gwaiwa, pink, ta iso gaban shi, "Me zai hana muyi jam'i domin samun
ladar jam'i" tafada tana kallon shi ido cikin ido, gaskiya Sairah tana da kyau
yafada a zuciyar shi, sake maimaitawa tai a karo na biyu dayasakashi sauke
sanyayyar ajiyar zuciya. Gyada mata kyau yai sau biyu, kan ya juya yashiga gaba
tana bayanshi har suka gama, saida suka shafe 10mints ba wanda ya motsa daga inda
yake, har saida yai addu'a ya shafa itama ta shafa. Tashi yai ya nufe kan gado, ta
juya cikin muryarta mai zaki tace "Ina wuni Yaya nah" cikin mamaki yake kallon ta
ya amsa da "lafiya lau nd u" "Alhamdulillah" ta amsa hadida tashi ta nufe kujera ta
zauna, kallo yabita dashi a zuciyar sa yace "Ashe tanada tarbiya, amma kuma a cikin
labarinta ba inda naga tarbiya a ciki, itama ta tabbatar min da haka, Toh ya wannan
abun?" Ya tambaye zuciyarsa. waya yaji tanayi da wani, bada jimawaba akai knock
taje ta bude tareda amsu kayan ta komo ta zauna, kayan ta fiddo dasu, freid Rice ce
da drink sai gorar swan biyu, kallon shi tai da yake famar latsa wayarsa, taga
alamun chart yake, amma kuma cikin kankanin lokaci taji zuciyarta ta sosa ganin
yadda yake murmusawa, nan take taji wani kishinsa ya taso mata, duk da basonsa
takeba amma ita tanada kishi gaskiya, idan tanason abu bataso wani yai tarayya
dashi. Daurewa tai tace "ka sauko muyi launch nasan kaima kaji junwa" kallon ta
yake kawai daga bisani ya sauko. Ba wani abincin kirki sukaciba dukkansu,
kasancewar daganinsu jirgi daya ya saukesu fagin abinci. Kan bed yakoma ya zauna
hadeda jawo filo ya rungume. Dubinta yai dauke da murmushi, yace "bayan iyayenki
sun rasu a ina kika zauna?" Nisawa tai gami da hadeye yawo tace "bayan sun gudu,
jami'an tsaro suka yau cikin gidan, suna dubin ko ina har suka zo dakin Dady nah
danake rungume da su ina kuka, suka neme susamu bayanai ta wurina amma inaa, bana
ko mgn sai kuka nake. Nan aka dauke su Dady akai musu sutura tareda su Baba Salisu
kanninshi, aka kaisu makwancinsu. Haka akaita bikin kwana uku, kasancewar yanzu
mutuwa tazamo biki, nikuwa sai kuka nake ina kiran sunan Dady. Bayan anyi sadakar
sati, su Baba Salisu sukace zasu koma dani can kauyen mahaifina (Dan batta) domin
kuwa babu wanda zai zauna dani anan, nace subarni a nan, bazan iya zuwa kauyeba,
sukai tsayin daka lallai2 sai sun tafe dani, Umar kuwa dadi kawai yakeji. Umar dan
Baba Salisu ne, yana sona sosai, Niko ko kallon shi banayi, dan ba ajina bane.

Haka suka tsareni na dibe kayana nasaka a trolley, yan kadan, dan nasa a
raina ko munje zan gudo nadawo, dan bazan iya rayuwar kauye ba. Acikin abubuwan
dana dauko akwai envelope wanda ke dauke da takardun gidan da Dady yabaiwa Ummeetah
a matsayin gift, lokacin da ta haifeni. Ummeetah tabani shi kwana biyu kafin
tafiyar mu baitillah, nasakashi qasan kayana da yan wasu kudade wadanda zan yi
amfani dasu kafin na dawo. Muka kama hanyar dan batta, karfe 4pm muka isa, nasauka
a gidan Baba Salisu. Matar Baba Salisu Asabe muguwar matace, inasamun labarin ta
gun Ummeetah tana daya daga cikin masu kishi da hassada ga Ummeetah, batasan ta ko
kadan. Inna Asabe 'ya'yanta 2, Umar, shine babba, ba wanda baisan Umar ba a
karkarar, dan iskan gaske ne, shaye2 yake da neman mata, sai Bilkisu kanwar sa
wacce kusan sa'ata ce. Da zuwana nafara ganin azaba da wahala iri2, nice wankin su,
nice abincin su, dakan fara ma nice" kuka ne yaci karfin ta, tadube hannayenta, ta
girgiza kai tacigaba da cewa, "kullum cikin kuka nake da kuma Allah ya isa ga duk
macucin dayasaka aka kashemin IYAYE. SBD irin wahalar da nake sha a gidan, abinci
ma ninake girkawa tun ban iyaba har na iya, saboda a gida bana ko kauda kare, aiki
na kawai ci na kwanta, abinci ma a baki ake bani, da akwai halin taunamin
ahadiyemin da anyi min. Amma sai gani a inda ni nake girkawa nabaiwa qattin banza,
sai kanzo ne nakeci, wata rana ma ko kanzo bana samu, wanka kuwa sai nai sati
banyiba, sbd Inna Asabe bata bari, kuma ko nai wankan ba tufafin canza wa, duk
tufafin danaxo dasu inna Asabe ta dauke wa yarta Bilkisu, sai wanka take dauka
dasu, inaji ina gani bana iya mgn, sai ragga ne daure dani. Kuma duk abinda akemin
a gidan da goyon bayan Baba Salisu akemin, baya cewa komai. Idan dare yai wani
akurkin kaji ne nake kwanciya, ga Umar sai nemana yakeyi, yanaso yasamu sa'a a
kaina, akuda yaushi idan yashigo gidan yana kallona yana lashe baki, kace maye yayi
bako. Ganin haka yasanyani zama da wani hijab da akai sa'a nasiyo a Umarar da
mukaje tareda Dady naga kyaunshi na siyo, banasa hijab ma, amma ganin kyaunshi
yasanya ni siyoshi. Dashi nake wuni a gidan, tunzuwana ko waje ban taba lek'awaba
bare na fita, inanan cikin gida, a cewar inna Asabe wai bazan fitaba nakorewa yarta
Bilki samari, domin kuwa idan samarinta sukaganni zasu dawo gareni, kuma bazaiyu
nai aure ga yartaba, niko dadi ma nakeji, dan banaso wani yaganni yace yanaso su
Baba Salisu su aura min shi. Akwana a tashi, har nai kusan wata biyu a can, su Baba
salisu da Baba Abdu suka fara shirin auramin Umar, Umar kuwa sai dadi yakeji, idan
yashigo gida yadinga cewa amaryata2. Saura kwana biyu a daura aure, da dare na
kudurce guduwa, duk da bansan hanyar kauyen ba, kuma banida kudi, kudin danazo dasu
Inna Asabe ta karbesu kaf. Haka na kudurce guduwa koda kuwa hakan tana nufin zan
rasa rainane, amma bazan iya auren Umar ba. A ranar da dare su inna Asabe suna
daki, dama ni dakina da kashigo gidan ne, bantsaya daukar komai ba sai envelope din
danazo dashi, da kuma wayata da nazo da ita na kashe ta dan nasan Inna Asabe zata
iya karbeta. Nasaka envelope din a k'uguna nasha uwar damara kamar wadda zatayi
dambe, nakulle wayata cikin dan kwalina nasaka hijab dina, sussussus....nafito
tsakiyar gida ba motsin kowa na fita. Har na baro gidan ba wanda yaganni. Nashiga
gudun famfalaqi, sai ketar karkara nake, ba kowa tsoro kawai nakeji kar na haduda
yan iskan garin danaji ana fada,masu tare yam mata suna musu fyade! Haka kuwa ta
faru, ina cikin gudu, naje nai karo da wani warjagegin mutun, take na fadi ina
k'okarin komawa da baya, can nai karo da kafar wani gefena, suka sakani tsaki ya,
sai kuka nake ina rokonsu, amma inaaaaa! Suka shiga kokarin rabani da hijab dina,
ina kuka ina kiran sunan Dady yazo ya taimakeni, ba kowa sai su sai Allah
mahaliccin mu. Nan suka samu nasarar rabani da hijab din, na dukunkune hannayena
ina tare jikina, dayan ogansu yace "Hhhhhhh.....yarinya kinzo hannu, ba mai
kwatarki yau" ya kece da wata razananniyar dariya data sakani razana, daya yace
"yanzu oga yazamui da ita ne?" Tsawa ya dakamai akan cewa "yadda akasaba mana" daga
bisani yace "Amma ku dakata, naga alamar wannan ba irin sauran bace, wannan zatafi
dadin harka, dan da ganinta ba yar karkarar nan bace" dukkansu su 3 sukace "wannan
haka yake oga" yacigaba da cewa "yadda zamui muje da ita dakin mu acan zamufi jin
dadi" suka kwashe da wata dariya hadeda cewa "SAI OGAAA". ni kuwa sai kuka nake ina
addu'a ko wacce iri nasamu yi nake, ban ankaraba naje sundakamin tsawa, agigice na
kai tsaye, suka sakani a gaba, ina tafe ina waigosu, har muka isa wani akurki, dan
bashida maraba da akurki, kofar dakin ma kamar zakai ruku'i idan zaka shiga. Acan
suka ajiye ni, duk suka fita suka barni sai ogan nasu, wanda shike farawa ya
ragarmusu. Suka kulle mai dakin, nikowa sai jero innalillahi wa'inna
ilaihirraji'un! nake, ina karanto addu'o'i, sai lokacin nake mamakin yadda na iya
addu'o'i haka, Ashe wai na iya Addu'a, Allah sarki!. "Sheeeeeiiiit....." Naji yace
da qarfi, "ya isa haka, idan kika kara daga wadannan saina raunanaki a daren nan,
kuma ba wanda ya isa ya kwaceki a hannuna" duk da a tsorace nake amma bai hanani
cewa "sai Allah! Domin kuwa Allah shine mai iko ga dukkan komai, kai baka isa kamin
abinda Allah bai rubuto a kainaba, kanada iko daka aikatamin duk abinda kaso amma
saida iko na Allah. Kuma duk abinda zaka aikata yanzu dama kullum kasani Allah yana
kallonka, domin kuwa manzon Allah (S,A,W) yana cewa: "FA'ABUDUL-LAHA, KA'ANNAKA
TARAWO, BA ILLAM TAKUN TA RAWO, FA'INNAHU YARAKA" ma'ana, "Kabautawa ALLAH kamar
kana ganinsa, idan kai baka ganinsa, toh shi yana ganinka". SBD haka duk inda bawa
yashiga ya aikata wani abu, toh Allah yana ganinsa" nisawa yai cikin sigar nadama
yace "kina nufin yanzu duk abinda zanyi Allah yana kallona?" Nace "tabbas yana
kallon ka, domin shi baya bacci" yace "koda na kashe fitillo?" Nai murmushi nace
"hmmm, ai Allah sami'un basir ne, ko a ina kashiga ka aikata abu yana ganinka
saidai yana jinkirtamuna ne domin kuwa a cikin Qur'ani cikin suratul Nun ‫ ن‬ayata
45 Allah (S,W,A) yana cewa: " WA UMLI LAHUM, INNA KAIDI MATEEN!" maana "Jinkiri ne
nake musu, hakika dabarata mai k'arfice!" Shiyasa a koda yaushe mutane mukeyin abu
muna ganin kamar Allah baya sane damune, har muke mantawa da akwai ranar da Uwa
take gudun danta, duk yadda uwa takaiga son danta a wannan yinin sai takai da
batasoma ta hadu da dan nata da nan duniya bataso taga ko bacin ransa. Ranar da
Allah yace a cikin suratul ma'arij ayata 10, Allah yake cewa; "WALA YAS'ALU
HAMIMAN HAMIMA. YUBASIRU NAHUM, YUWADDUL MUJRIMUNA LAU YAFTAGI MIN AZABI
YAUMA'IZIN. WA SAHIBATIHI WA'AHIH. WA FASILLATIHIL-LATI TU'UWIN. WAMAN FIL ARDI
JAMI'A, SUMMA YUNJIHIM" ma'ana "Ranar da masoyi baya tambayar masoyinsa" (duk
soyayyarki/ka da mutun nan duniyace kawai, sai idan kun hadu aljannah) Allah
yacigaba da cewa "KUMA SUNA GANIN JUNANSU, RANAR DA MUJIRUMI ZAIYI GORIN INAMA A
FANSHEHI DA AZABAR WANNAN WUNIN DA 'YA'YANSA. DA MATARSA DA DAN UWANSA. DA KUMA
DANGINSA DA SUKE MASA HIDIMA NAN DUNIYA, SHIDAI A TSIRATAR DASHI". (Innalillahi
wa'inna ilaihirraji'un!!! Kuduba fa kugani, duk irin soyayyar dake tsakanin da da
mahaifi. Mata da miji. K'awa da k'awa, Aboki da Aboki, amma ranar lahira idan mutun
bai aikata abun kwarai ba zaiyi gurin zaiso a dauke wadannan amusu azaba saboda
tsananin tashin hankali! Subhalallah! Yah Allah kasa mu aikata kyakkyawa. ALLA'UMMA
RABBANAH ATINA FIDDUNYA HASANA! WAFIL AHIRATI HASANA! WAQINA AZABAN NARRR!!! AMEEN
YAH ALLAH.) Nan fa idanuwanshi suka zubo da hawaye, yahau kuka mai ban tausayi,
wanda Nima saida na tausayamai. Yajima yana kuka kan ya dago da jajayen idanuwansa
yace " gaskiya naji dadin hadu wata dake yau, domin kuwa najima ina wannan aika2 a
karkararnan, amma bantaba haduwa da wata macen da tamin wannan wa'azinba sai yau
Allah ya hadani dake, Ashe kece silar shiryuwata" sai kuma ya fashe da raunannin
kuka, na safsafta muryata nai hamdala ga Allah da wannan arzikin da yabani, domin
kuwa Annabi (S,A,W) yana cewa "MUTUN YASHIRYU TA HANYARKA YAFI ALKAIRI DA ABAKA
JAJAYIN RAKUMMA" godiya sosai nama Allah daga bisani na dubeshi nace "ba kuka
zakaiba, godiya zakaiwa Allah daya nufeka da shiryuwa ayau, kuma tareda tuba
gareshi da rokon yafeya domin kuwa Allah Gafurun ne Raheem, yana gafartawa wanda
yaso a kuma lokacin dayaso domin shi YAF'ALU MA YASHA'U ne bamai cilasta masa"
lokaci daya mutumin ya roke yafiya ga Allah sai dai Allah yana yafema bawa abinda
ke tsakanin shi da bawansa ne, baya yafe lefin dake tsakanin bawa da bawa. Ganin
mun jima a dakin yaran shi suka fara dukan dakin akan ya bude, na tsorata amma
ganin shine ogansu abin zaizo da sauki yasanaji dadi. Fita yai yasamesu, ya sheda
musu cewa shi ya tuba daga yau ya daina, kuma idan zasu tuba su zauna a tare idan
ba haka ba kowa ya kama gaban shi, duk sukai na'am sukai nadama tareda tuba ga
Allah. Duk abinda suke ina kashe da kunne ina saurare, sai gashi ya dawo dakin ya
zauna, yake tambaya ta ni ba yar garin nan bace Koma daga ina nake ina zanije?.
Nace eh, ni yar kano ce, nabashi lbrn auren da zaamin na gudo, yace na kwantar da
hankalina ba abinda zai faru dani. Yace na kwanta a dakin nikadai, su zasuyi gadina
a waje zuwa safe, dan lokacin 2 nadare yayi. Haka kuwa akayi na kwanta hankalina a
kwance, dan nafijin dadin bacci a dakin sama da dakin da nake kwanciya a gidan Inna
Asabe, duk da sumadin wata tsohuwar katiface. Safiya ta waye tun da dahu2 suka tafi
dani tashar mota, suka hadani da driver direct kano. Su suka biya driver'n kuma
suka bani 5k nai guzuri, da kuka na nake musu godiya, suma sai godiya sukemin
tareda jaddadamin nice silar shiriyarsu bazasu taba mantawa daniba. Muka kama hanya
sai kano, muka yada zango, anan na rasa ina zan dosa, nan na yanke shawarar tafiya
tsohon gidan mu, nan na tarad da gidan a rufe, ba kowa a ciki, narasa wanda zan
gayama damu wata. Naje company'n
Dady sukaimin wulakanci wai umurni aka basu kada su sake su barni na shiga. Daga
karshe na dauke wayata na kunna nakira Deen, yayi murnar ganin kirana ya daga yace
ina naje na gujeshi kuma yazo gidanmu akace mun bar k'asar. Nan na zayyanemai
komai, ya tausayamin yamin jajin rashin iyayena, daga karshe namai kwatancin Inda
nake yazo, na dauke takardun gidan da Ummeetah tabani na bashi, nan ya nemo gidan
dayake akwai address din unguwar da no din gidan a jikin takardun. Mukaje a tare,
gidane iya zaman mutun daya, amma yanada kyau kasancewar duk shekara sai Dady
yasaka anmai sabon gyara wanda ake yayi, sosai yake dakyau, nan nacigaba da zama
tareda Deen. Duk da inada gida ni kadai lokaci bayan lokaci muna zowa dashi
hotel,tun bana yarda dashi har takai da nafara yarda dashi, Deen yamayar dani
tamkar matarsa ta sunnah, kuma bai yarda nai tarayya da wasu mazan ba, yana
matu'kar kishina yadda kasan matarsa, yanzu ma Dady'n shine ya aikeshi Dubai,
shiyasa kaganni ni kadai, amma duk da hk na gaji da zaman banzar da nake da Deen,
naita masa magana akan muyi aure tunda muna son juna amma akullum SAI yace nabashi
lokaci haryau bawata mgn ta aure wadda tashigo tsakanin mu. Toh kaji karshen
labarina ni Sairah."

*Ⓜªŋşħªŗŧ ŋºvęłş📚*
[3/18, 11:01 AM] Manshart: *MISKILANCI KO GIDADANCI*❓

```Written by Manshart💘```

~In dedicated to my luvly Dady (Alhaji) & Mummy (Bissalam)~

*{Đïş ïş mý şęĉºŋð ŋºvęł}*👌🏼

*Part 23*

A gigice yakai tsaye, ganin yakai tsaye yasaka Sairah


waiwayawa dan ganin meke faruwa. Ganin mutane sunyi turus a tsaye yasakata mekewa
takai tsaye tana kallon su. Da sauri Mummy ta nufosu tawawaso wuyan Sairah, tahada
da bangon dakin gaffff....kakeji, sosai Mummy takama wuyan nata tana wuce tace "yar
iska karuwar banza, shine kika kawomin yaro a hotel? Dama ke kike son L🅰L🅰T🅰 min
shi kenan? Matsiyaciya kawai yar matsiyata. Mummy takai mata wawan mari hadeda
wilgata k'asa. Elhaj kuwa yama rikice yarasa me zai aikata, sai zufa ke karyo mara,
jiyake kamar yabuda k'asa yashiga. Ganin Mummy tana k'okarin hallaka Sairah yasaka
shi saurin kaiwa ga resu. K'okarin janye Mummy yake daga kan Sairah da ta hauta sai
jibga take. Mummy tai mugun tureshi hadeda bashi kyakkyawan mari. Umma da tarasa
abinda zata aikata tai saurin amshe Sairah daga kan Mummy da tai jina2 saboda
wahala, dankan taji maza. Mummy tana wuci tana karawa tace " Haj Saratu ki barni na
hallaka wannan karuwar banzar, irin karuwan nanne masu wargaje ma tarbiyar 'yaran
ka dakai shekaru kana aikin basu, k'askantacciya kawai" Sabir dayake bin Elhaj da
kallon tsana yayo inda Mummy take tsaye "Ai Mummy ba ita yaci ace kinyiwa wukunci
ba, domin kuwa ba laifin tabane, idan bai gayyaceta ba zata zo ne? Ai bazata zoba,
sbd hk shine mai laifi shiyaci ace kin wukunta HK" Mummy tana wuce tace "Ai ita zan
fara wukuntawa tokon, kafin shi, domin kuwa nata mai sauki ne" ta kalle Sairah
datake kwance a kasa kamar matatta tadube Elhaj tace "Amma wlhy kaji kunya, ace
karasa abinda zaka aikata da girmanka sai zaman hotel da yam mata, kuna zaman
dadiru, wlh ko a mafalki akabijiromin dakai cewa kana neman mata zan falka na
karyata mafalkin, mu a iya kallon *MISKILI* kawai mukema, Ashe wuce nan" hawaye
na kwarara a fuskar sa yace "Mummy wlh ba zaman banza muke da itaba ita......"
Kafin ya ida maganar Sabir ya wankamai mari har biyu a kumce, "Mummy tana magana
kana magana, dan kakoma dan iska, kana biyema irin wadannan matan, wannan yarinya
waye bai santaba? Kaima saboda tsabar *MISKILANCI*'n kane yasa bakasantaba. Harfa
gida take dashi ita kadai tana tara maza iri2 suna aikata masha'a, amma kai......?
Cikin bakin ciki Elhaj ya tsaidashi " Yah isa hk Sabir, Sairah ba karuwa bace, ita
zan aura saboda hk kadaina kiranta karuwa, Kuma....." Kafin ya ida Mummy tai kukan
kura tai cikinsa takamo wuyan rigarshi, tashiga marinshi ta kowane kumce, "Har
kanada bakin cewa ita zaka aura? Ashe haka ka lalace ban saniba Alhaji, har zaka
dube wannan karuwar kace itace ita zaka aura?" Da sauri yace " ba karuwa bace
Mummy, kidaina kiranta karuwa" sakinshi Mummy tai tace "lallai kafi karfina Usman,
karigaya ka lalace ka....." Kafin ta ida Umma ta rufe mata baki "Haba haj Shafa'u,
karkice zaki raka tatashi mana, Alhaji fa har yanzu yarone" cikin bacin rai Mummy
tace "yarofa kikace? Wlh zaizo yasameni zan nunamai kuruciya" takama hanyar fita,
Sabir yaja tsaki yace "amma wlh Alhaji kaji kunya" Umma tabisu da kallo, shida
Sairah da take kwance sai kuka take marar sauti. Sunkai kofar fita Mummy batareda
ta juyoba tace "karka yarda ka kwana a hotel dinnan komai dare ka sameni gida, kuma
idan ba haka bawlhy saina tsinema albarka!" Tabuda kofa ta fita suma suka maramata
baya. Zuciyar shi kamar zata baro gangar jikinsa, yanufe Sairah, ganin jini na zuba
ta fuskar ta yasanya shi firgice yaciro hanky yana k'okarin shafe jinin. Tureshi
tai tatashi tsaye, "meyasa kake maida musu mgn sbd ne Elhaj? Yazama wajibi kabi
mahaifiyarka Elhaj, bazanyi sanadiyar rabaka da yan uwanka ba, yazama domin
komunaso ko bamaso murabu" Cikin bakin ciki, kwala na zuba a idonsa yace "Haba
Sairah, taya zan bari a cimutuncinki, kinfasan ni nai alkawarin baki kariya koda
zan rasa raina. Dan Allah ki...." "Shiiiiiittt.... Ya isa haka, dan Allah katafi
kabarn, bazan iya zama dakai ba Elhaj, koda inaso yan uwanka bazasu barina" "taya
zan tafi nabarki, bayan nine silar shiriyarki, kuma yanzu ace na barki a haka,
aisai bakin ciki yakara kaiki ga aikata abinda yai wanda kika aikata baya hatsari!
Kinga Sairah kizo muje asibiti, sbd jinin nan dake zuba". Batada dabara domin kuwa
tasan idan tarabu da Elhaj bazata koma samun wani irinshiba, dole haka ta bishi.
Fitowa sukai, suka shiga mota yajasu, suka nufe asibiti. Driving yake yana tunanin
waye yasanarma su Mummy cewa yana hotel? Kuma har yasan hotel dinda yaje, dakuma
dakin da yake. Ta lura hankalinsa sam baya gareshi, sbd yarage gudun motarsa.
Hannun ta ta karamai ga ido, " me kake tunani ne HK?" Ajiyar zuciya yasauki tareda
cewa "bakomai" murmushi tai takwantar da kanta jikin motar, da jini yaketa famar
zuba. Kara gudun motar yai har suka isa. Basui wata wahala ba akai mata treatment,
suka bata gado sukace sai zuwa gobe zasu sallameta, sbd tana buk'atar Hutu. Tana
kan gado kwance, yashigo da ledodin fruits da drinks ya ajiye hadeda yimata sunnu,
ta amsa "Ya jikin dai?" Tasakar mai murmushi "dasauki sosai" yace "toh
alhamdulillah, Allah yakara sauki" ta amsa da "Ameen ngd" "shiiit, nagaya maki
banason godiya fa" tai dariya tace "toh na daina yaya Elhaj" yai murmushi, yadauko
fruits din daya siyo yafara bata, dakyar takeci, saida ya matsa mata sosai kan
taci, shima bada yawaba. Nan take bacci ya dauketa, shiko ya janyo wayar shi yana
latsawa, jimi2 yana kallon ta, yadda take baccin yai matu'kar masa kyau sosai,
yasaita camera wayarshi yafara daukarta pics, yana dauka yana murmushi. Can misalin
karfe 10pm ta farka, tabishi da kallo, har bacci yafara daukar sa, jin saukar ido
akan fuskarsa yasaka shi bude idonsa yasaukar a kan nata, "sannu" yace da ita tace
"yawwa, har kafara bacci ne?" Yace "a'a ina tunani ne kawai" tadubeshi cikin kulawa
tace "tunanin me kake?" Yace "ba komai" tace "bakomai kake tunani? Nasan abinda ya
farune dazu kake tinani, kuma nasan Dole zakai tunanin abun, dan ko ba komai nasan
mahaifiyar ka ce, yazama dole katashi kaje kabi umurninta" saurin kallon ta yai
yace "kefa? Sai nabarki ke kadai?" Ta girgiza kai, yace "toh dawa zan barki?" Tace
"ga Allah!" Yai shiru nadan mintota kan yace "hakane, amma idan abinda kikaji Mummy
ta fadane karki damu, domin kuwa nasan ko wacece Mummy nah, tafada ne kawai saboda
natafi" Sairah ta girgiza kai "A'a Elhaj, kada ka yaudare kanka, ba alamun wasa a
tattareda Mummy'n ka, yazama dole katafi, domin cika umurnin mahaifiyar ka, dan
Allah plssss" cikin mamaki yake kallonta a ransa yace "lallai Sairah kin tsorata da
Mummy" a fili yace "ba matsala, zan tafi yanzu, amma dan Allah inaso kiyi hakuri
akan abinda Mummy nah tai miki pls, wlhy rashin sanine, amma na tabbata zata
fahimceni" Sairah tai murmushi tace "karka damu wlh komai ya wuce, katafi kada dare
yama a hanya" yace "toh" sukai sallama yatafi.

Bayan dawowar su Mummy, suna falo wayar Mummy tahau ruri, ganin no din Dady
yasaka ta dauka da sauri tana kallon Umma, "Wacce uwa kukaje dauka a hotel keda haj
Saratu?" Dady ya fada har kana jiyo hucinsa a wayar. Cikin kunar rai Mummy tace
"waya gayama munje hotel?" Ta tambaya tana kallon Umma, Umma takai tsaye kamar
yadda Mummy takai. "Yanzu wani abokina yakirani yake sanarmin yaganku a Grand
central hotel, me kukaje yi acan?" Mummy ta hade rai tace "amma dai kasan ba abinda
zamuje mui acan, dan mu ba karuwai bane" ganin abun zai zamo wata matsala yasanya
Umma karbar wayar hadeda sallama "haba mai gida, kai kanka kasan lafiya ko jin dadi
bazai kaimu hotel ba muna matan aure" Dady yace "kamar ya ba lafiya ba? Meke
faruwa?" Umma tagayamai abinda ake Dady kuwa kamar yai tsuntsu yadawo yana wuci
yace "kbata wayar" Mummy ta karba kamar zata fashe yace "idan ya dawo ki kirani
kice zanyi waya dashi" Mummy tace "toh" yakatse wayar Umma tace "kaii mutun! yau ba
dabba ake kiyoba mutane, yanzu har ansamu munafukin da yakira ya gayamasa" Mummy
tace "hmm, shiyasa tun farko nafada" Umma tace "lallai, Allah toh ya kyauta".

Hanyar gida ya nufa, mai gadi yabude masa gate ya shigo, baibi takan kowa ba
ya wuce dakin Mummy, tsaye ya tarad da ita sai safa-da-marwa take dakin, ganin
yashigo yasaka ta tsayawa chak! Tabishi da kallon tsana. Karasowa yai zai durkusa
ya kwashe gaisuwa Mummy ta tsaidashi "bana buk'atar gaisuwar ka, ka'adana maybe nan
gaba zataima amfani, amma ba yauba" tsaye yai ya sunkuyar da kai, Mummy tabashi
waya da take famar ring, ganin sunan Dady gabansa ya fadi! Haka ya daure ya daga
ba sallama Dady yace "inaso kafin na dawo ka tabbatar kabayar da takardar Maryam
domin ita nake buk'ata, dama ba idda a tareda ita, dana dawo inaso na daura mata
aure, kuma wlh idan nadawo baka saketaba zaka haduda fushina" bai jira mai zai
fadaba Dady ya kashe wayar. Mummy tace "ka tabbata gobe ka bani takardar ta, idan
ba hakaba duk lokacin da yadawo haduwar ku bazatai kyauba, kuma Nima haka. Domin
kuwa bazaiyu a rabo yarinya da iyayenta ba azo a girketa a cikin gida ba'a
saukemata hakki, wlhy bazaiyu ba. Tunda har bazaka iya sauke mata hakkin ta da ya
rataya a huyanka ba so kabani takardarta, ma'ana ka saketa!" Wani farin ciki ya
ziyarto zuciyarsa lokaci daya. Yana kokarin mgn Mummy tace "katafi kabani wuri tun
muna sheda juna" cikin jin dadi yabar dakin, yafito yashiga mota yanufe gidan, jin
kanshi yake kamar yaune ranar haihuwar sa sbd murna. Can me yatuna yace "kai bazai
yuba, bazaiyu na sake taba batareda na raunana taba, yazama dole na koya mata
hankali, yazama wajibi nai mata illa da ba wani namiji dazai sota, yazama wajibi na
sakata idda, iddar wuce wata ukku zansakata, idda shekara Ukku! ". Motar sa
yakarama wuta baiyi birki ko inaba sai gidan, yadinga horn saida mai gadi ya bude
gidan. Binsa da kallo mai gadi yai, yaga abinda bai taba ganiba. Sosai gidan yamasa
kyau, domin kuwa irin yadda yakeson tsarin gidan sane, a zuciyar sa yace " kamar
Dady yasan inason irin wannan gidan" can kuma yatunada abinda yakawo shi, da kwarin
gwaiwa ya haura ciki.

Bangarin Maryam kuwa, ta rurrufe ko ina ta fesa ado da kwalliya, sai kamshi ke
fesawa ta ko ina, sleep gown ce take sanye da ita iya gwaiwa, kasancewar ita kadai
ce a gidan, bako dankwali a kanta, tana kwance falo tana kallon wani American film.
Har bacci yafara gaba da ita tajiyo budin kofa da sauri ta tashi daga kwancin da
take takai tsaye. Cikin tashin hankali take kallonshi, tanaso ta tuna inda ta taba
ganin wannan fuskar amma ta kasa ganewa. Shikuwa cikin mamaki yake kallon ta, a
zuciyar shi yana farincikin sake haduwa da ita, idan kuwa itace, yazama wajibi ma
nai mata uban abinda zan mata a yanzu. Nufota yai itakuwa sai jadabaya take tana
daukeda hannuwa a ka. Juyawa yai yakashe wutar falon. Ihu ta kurma ina rokon shi
amma inaaaaaaaaa.

*Ⓜ ªŋşħªŗŧ ŋºvęłş📚*
[3/18, 11:01 AM] Manshart: *MISKILANCI KO GIDADANCI*❓

```Written by Manshart💘```

~In dedicated to my luvly Dady (Alhaji) & Mummy (Bissalam)~

*{Đïş ïş mý şęĉºŋð ŋºvęł}*👌🏼

*©HIKAYA ONLINE WRITER'S (HOW)*

*Part 24*

Rufe mata baki yai hadeda mannata a kirjinsa, daga bisani


yadauketa firrrrr...... Sosai Elhaj yai mata kace2, kuka take ihu take but banza,
daga bisani ta some, bata motsi ko kadan. Duk da yafahimce bata motsi amma hakan
baisa ya ragar mata ba. Kiran sallar asuba ne ya mayar dashi hayyacinsa, yabi jikin
ta da kallo irin yadda yai mata jina-jina. Elhaj ya razana ganin jini na zuba, sai
lokacin ya fahimce yadda wurin ya baci, duk wurin yai kace2! Jikin ta yabi da kallo
lokacin da yazo daidai ita, yana k'okarin taba jikinta, zaune yai ya tsareta da ido
irin yadda halittar jikinta take, "gaskiya Allah yai halitta ga wannan yarinyar"
yafada a zuciyar sa, bai taba haduwa da wata mace ba a duniya irin wannan yarinyar,
"gaskiya tanada kyau". Juyar da kansa yai gefe hadida guntun tsaki, a fili yace "
me zanyi da wannan yarinyar? Dahar zan tsaya bata lokaci na akanta, na tabbata
Sairah tafita kyau sosai" yakuma Jan tsaki a karo na biyu. Tashi yai yanufe
bangarin sa, daya tabbata nan ne nashi. Sosai yaga kyau palon, ido waje yake kallon
pic dinsu dake manne da bangon dakin. Da hanzari ya isa gareshi, kallonsa yake ko
kyaftawa bayayi, "badai wannan itace yarinyar ba?" Ya tambaye zuciyar sa, daga
bisani wani bakin ciki ya tasomai ya nufe room dinshi. Birth room ya nufa yagyara
jikinsa, yashirya cikin kananan kaya yafito. Yaduba lokacin sallah yayi, yasaka
sallaya ya gabatar da sallah. Bai ko koma ta kan Maryam ba, yafada dakin sa ya
kwanta. Bacci bai iya daukarsaba sai tunanin yarinyar yake, taya zan saketa yanzu?
Gaskiya yarinyar tanada kyau, amma bazan taba nuna mata so ba, sai dai zan nunama
su Dady sonta nake sosai, domin kuwa inaso na hukuntata, ta yadda gobe bazata sake
ta yadda a aura mata wanda bata saniba. Amma daga baya zan saketa, domin kuwa ni
har yau bana sonta!. Haka yaita surutan sa, sai karfe 8am yashirya yafito, yanufe
asibiti gurin Sairah. Maryam kuwa sai karfe 7:25 ta tashi, sosai ta firgita ganin
yadda take cikin jini "innalillahi wa'inna ilaihirraji'un!" Ta furta, cikin
tsintsar tashin hankali, "me yazoyi a gidan aurena ne ni Maryam? Dama nan garin
yake? Allah kasa ba fyade yamin ba ya gudu," kuka take sosai, daga bisani tai
yunkurin tashi amma ina, ta kasa, bata iya koda motsi, zafi takeji sosai. Daga nan
bata sake sanin inda takeba.

A zaune ya tarad da ita kan kujera, ta kifa kanta ga alama tunani take. Har ya
zauna batasan ma ya isoba "me kike tinani haka?" A firgice ta dubeshi ta sakarmai
murmushi "kai mana" yai murmushi shima yace "toh gani nazo. Ya jikin naki" juya
idanuwan ta tai tace "da sauki Sosai, Dr ma yazo zai sallameni but bai gankaba
shiyasa yace abari sai ka zo" yace "OK" da sallama Dr I.S ya shigo dauke da file a
hannu, yamata ya jikin Elhaj ya amsa da "taji sauki Sosai Dr" yace "yawwa, dama tun
dazu nake jiran isowarka" yabasu sallama suka baro asibitin. Suna tafiya Elhaj yace
"Sairah, inaso ki fidda miji ki aure sbd zama haka bazai yuba" ajiyar zuciya ta
sauke, nan take idanuwanta suka fiddo da kwalla tace "hakane, ni inada wanda nakeso
a yanzu, saidai bansan shi ko yana sona b" kallon ta yake har ta ita, tabashi
tausayi, amma kuma baiso tafadi hakan ba, domin kuwa soyayyarta ta gama shiga
zuciyar sa. Shiru yai baibata amsaba har suka isa gidanta. A tare suka shiga suka
dire a parlor, kusa dashi tazo ta zauna ya dubeta yace "wanene kikeso haka Sairah"
noce fuskar ta tai daga bisani ta saukesu akan nasa. Suna cikin haka wayarsa ta hau
ring, sunan Mummy ya bayyana takan screen din,kallon Sairah yai da ta bishi da
kallo a tsorace yad'aga "ina alkawarin da mukai dakai zaka?" Rasa yai me zai fada
yafara "Mum....mmn...." Kafin ya ida mummy ta dakamai wata uwar tsawa da saida ya
razana "me kake nufine? Wlhy nabaka nan da minti 30 ka tabbata ka kawo min konai
mugun sabama" ta kashe wayar. Sairah tabishi da kallo, "meke faruwa?" Murmushin
karfin hali yai yace "ba komai karki damu" tabe baki tai yace "zantafi wani wajan
amma bazan jimaba zan dawo" tace "OK" a tare suka tashi ta rakoshi har saida ya bar
gidan kan ta juya ta koma cikin gidan tashiga kimtsashi.

Ganin har 10 na safe baizoba yasanya Mummy tashigo mota ta nufe gidan. Wangale
mata gate mai gadi yai ta haura ciki. Sallama Mummy tadinga kwalawa shiru ba kowa,
ta isa ciki. Da sauri Mummy ta nufe ta ganin ta sheme Mummy ta shiga tambayarta,
Da sauri Mummy tadauketa yar firit da ita tasaka a mota. Sosai take tuki har ta isa
asibiti, da sauri suka amsheta suka nufe emergency da ita, domin bata taimakon
gaggawa!. Umma Mummy ta kira ta sanar mata, baai minti 20 ba Umma ta iso asibitin,
tana daukeda damuwa itada SadiQ. Suna zazzaune Dr Nafeesa ta fito takira Mummy da
Umma tasanar masu halin da Maryam take ciki. Nan take Mummy tashiga tashin hankali
da alawadai da abinda Elhaj ya aikata, domin kuwa tasan cewa aikin sane wannan.
Waya ta dauka ta kirashi, yana driving zaije gidan, ya dauka, bako sallama mummy
tace "inaso nan da minti 30 kazomin da Maryam gida" ta kashe wayar ta. Sai lokacin
ya tunada inda ya bar ta, sheme a daki. "Toh yanzu taya zan kaima Mummy ita tana
cikin wannan halin?" Ko nace batajin dadi? Amma kuma nasan Mummy zata iya aikowa a
dubatafa" sitiyarin motar sa yakaima duka tareda furta "OMG! Yazanyi yanzu?" Gidan
ya nufa baiko tsaya shiga da motar ba ya barta waje yafito ya nufe cikin gidan.
Tashin hankali ne karara ya bayyana a fuskarsa, lokacin da ya duba ko ina ba Maryam
babu alamunta. Safa-da-marwa yafara a falo, yana cikin hakan wayar Mummy ta shigo.
Saida tai ring sau ukku kafin ya daga, a gideme yake, yarasa me zai fadama Mummy da
sai Hlo take! Can ya daure yace "wlhy Mummy ba inda ban dubaba a gidan amma bata
nan" Mummy tace "whattttt? Me kake nufi ne Alhaji? Toh kasani wlhy daga nan zuwa
yamma ka tabbatar ka nemota duk inda take, idan ba haka ba kasan saurn" ta katse!
Sosai ya firgita da maganar Mummy, ganin yanzu ina zai samu Maryam, fitowa yai
yashiga mota, batareda yasan inda zai nufaba. Hasalima baisan a ina zai fara
nemanta ba, tunda va yar garin bace a ina tasani da zata je. Yana tafiya yana
tunani mssg yashigo ta no Sairah, mssg din soyayya ne taturo, habawa, yana gama
karanta wa yaji duk kan damuwarsa ta yaye, domin kuwa yakamu da son Sairah sosai,
Kuma ya kudurce zai aureta komai rintsi dan ya taimakamata. Bai samu ya mayar
mataba, yaja mota yashiga tunanin inda zai fara neman Maryam. Har yamma ta gabato
amma ba Maryam ba alamunta, kuma Mummy ta tabbata mai kada yai kuskurin takowa
gidan ta ba tareda ya nemo Maryam ba!. Can wurarin karfe 6 wayar Mummy ta shigo,
ya daga mummy tace "wai me kake nufine har yanzu?" Cikin sarkewa yace "wlh Mummy ba
inda baijeba amma ban sametaba, kuma bansan inatajeba" Mummy tace "karka gayamin
zancin banza, ka tabbatar ka nemota duk inda ka kaita wlh" yana k'okarin mgn Mummy
ta katse wayar. Umma dake zaune tareda Mummy tace "me yasa zaki wahalar dashi hk?
Kigayamai yazo muna asibiti mana, idan yaso idan yazo sai kimai duk hukuncin da
yakamata, amma yanzu ina mu kasan zai dosa yanzu" Mummy ta saukar da lumfashi tace
"yazama dole na koyawa wannan yaron hankali haj Saratu, bazaiyu ace yana wahalar da
muba, ki duba kigani yadda ya aikatama wannan yarinyar, kina ganinfa tun zuwan mu
asibitin nan ko motsi batayi" Umma ta kalle Maryam datake kwance bako alamar motsi
tace "hakane, gaskiya bai kyautaba, amma kuma hakan da zaki bai kamataba, kinsan fa
irin wahalar da akasha kafin mu nemo wannan yaron, yanzu idan kika tunzurar dashi
yaje wani wurin fa, ina mukasan zamu neme shi?" suna cikin maganar Dady yakira
Mummy ta daga cikin tsoro, dan ita yanzu Dady har tsoro yake bata. "Ya aki ciki haj
Shafa'u? Tun safe nake saurare daga wajanki, kinsan fa nagayamiki dana dawo nakeso
na hada auren nan, bayarda takardar?" Mummy tasaukar da ajiyar zuciya tace "A'a
bai bayarba amma nakirashi yace zaizo yanzu" a fusace Dady yace "Me yake nufine?
Toh gobe zan dawo, yazama dole yasaketa wlh" Dady ya katse wayar. Mummy tabi wayar
da kallo tareda kallon Umma.

Maryam bata farkaba sai wajan karfe 8, da innalillahi ta farka tana binsu Mummy
da ido. Da sauri mummy tayo kanta tareda mata sannu, kallo kawai take biyar ta
dashi tanaso ta tuna inda ta santa amma ta kasa. "Waya kawoni wannan wurin, kuma me
nakeyi a ciki?" Ta tambaye Mummy. Mummy tace "ki kwantar da hankalinki Maryam munan
iyayenki ne, mu muka kawoki asibiti" cikin mamaki take kallon Mummy a zuciyar ta
tace taya tasan sunana? A fili tace "asibiti kuma? Me nazoyi a ciki?" Umma datake
gyefe tace, "Sannu Maryam, ki kwantar da hankalin ki kisamu lfy, in yaso daga baya
zamui miki bayani kinji" gyeda mata kai kawai tai tareda juyarda kanta gyefe daya
tana kuka cikin raunanniyar murya. Jim! Sukai suna binta da kallo, daga bisani su
Sajida sukai sallama suka shigo itada su Aisha da Labila. Suka gaisheda su Mummy
tareda tambayar ya mai jiki suka amsa da sauki. Sajida ce tai saurin nufar inda
Maryam take a kwance ta juyarda kanta. "Sannu, ya jikin?" Sajida tace, sai lokacin
Maryam ta juyo ta dubeta, lokaci daya tai hogging din Sajida tana kuka tana cewa
"ya cuceni ya cuce rayuwata ya gudu Sajida" hawaye ne suka saukoma Sajida, su Mummy
suka bisu da kallo, Sajida ta share hawayenta tace "karki damu Maryam, Allah zai
saka miki koma wanene" kasan cewar baa sanar masu Sajida aikin Elhaj bane. Dakyar
tasamu shawo kan ta itada Labila, suka samu tai shiru tana saukar da lumfashi, har
saida ta bawa su mummy tausayi. Mummy ta fita waje ta kira shi, tace yasamesu
asibiti, yana k'okarin mgn Mummy takatseshi. Cikin minti 30 yashigo da sallama
Maryam tana kwance saman cinyar Mummy, har bacci yafara gaba da ita, kasancewar su
Sajida sun koma gida tareda Umma. Domin gobe da sassafe Dady zai dawo zasu
shiryamai kayan tarba. Karasowa yai kusa da Mummy ya sunkuya yabada gaisuwa, Mummy
ta amsa ciki2, gabanshi sai faduwa yake. Mummy ta watsamai harara dole yashiga
k'okarin gaisheda Maryam da gaisuwar sa ce ta tasheta daga bacci. Wani razanannin
ihu ta kurma ta shige cikin Mummy tana cewa "Dan Allah ki taimakeni karki bari
yakoma yimin abinda yamin wlh kashe ni zai! Dan Allah kice ya tafi mugune sh.."
Kafin ta ida maganar takoma somewa.

*Ⓜªŋşħªŗŧ ŋºvęłş📚*
[3/18, 11:01 AM] Manshart: *MISKILANCI KO GIDADANCI*❓

```Written by Manshart💘```

~In dedicated to my luvly Dady (Alhaji) & Mummy (Bissalam)~

*{Đïş ïş mý şęĉºŋð ŋºvęł}*👌🏼

*✍🏻
✍🏻✍🏻
✍🏻 ✍🏻HIKAYA ONLINE WRITER'S✍🏻(HOW)*

my readers. Thank you for being so passionate about my novel and wanting to
connect with me. Thank you for interacting with me, sharing your lives with me, and
being the reason I can continue doing what I love. I get messages from many of you
everyday telling me "thank you" for writing my novel, but really this is my THAN
YOU, THANK YOU, THANK YOU😍from me to you from the bottom of my heart!💔Thank you
once again #onelove😘😍

*Part 25*

Sosai Mummy ta firgita ganin bata lumfashi, cikin


tsoro tashiga jijjigata tana "Maryam! Maryam!!" Ganin hankalin Mummy yatashi
yasashi karasowa kan gadun zai tabata, Mummy ta wanka mai lafiyayyen mari da yasaka
shi kaiwa k'asa ya rike kumce. "Duk waya ja wannan abin bayan kai? Wato so kake ka
kashe yar mutane ko? Toh wlh idan har ta mutu kaima kasiye file dinka ne na mutuwa"
Mummy tafada tana nunin shi. "Wlh Mummy ba hak....." Cikin wata irin tsawa Mummy
tace "Rufe min baki shashasha kawai" ta hankadashi ta tashi da sauri taje kiran Dr.
Da fitar ta yatashi ya nufe Maryam kan gado yana wani shu'umin murmushi. Jin budin
kofa yasaka shi rungumo ta yana jijjigata. Da sauri Mummy ta iso wurin shi ta
janyemai hannu daga kan Maryam, Dr Nafeesa datake tareda Mummy a baya tai gaggawar
isowa kusa da gadun tashiga a'a'aunata da stethoscope tana lalubo lumfashin ta.
Mummy ta watsamai harara dole ya fita dakin, a zuciyar shi sai dadi yakeji. Da
fitar shi yaja mota yawuce gidan Sairah. A kwance ya tarad da ita a falo tana
kallon ball a MBC, ya karaso da sallama ta amsa cikin fara'a da murmushin ta
maikara mata kauna a zuciyar sa, shima ya sakar mata yazauna tareda cewa "dama kina
kallon ball ne?" Tai dariya tace "eh mana, sosai ma, Ai inason wasar ball" yace
"sai kace namiji" takara fashewa da wata dariya tace "aini namafi mazan son ball,
sbd lokacin da Dady nah yana raye taredashi mukeyi shima yanasan ball, shinema ya
koyamin" murmushi yai yace "lallai kin kware" tai dariya tatashi tana taku dai2
tashiga kitchen ta daukomai abinci, dareda drinks tazo takawo, yana zaune tazo ta
aje, a tare sukaci. Ba laifi yanzu Elhaj ya fara sakewa da Sairah, har suna zaunawa
sui fira sosai, sbd tana nishadantar dashi, shiyasa yakejin dadin zama da ita.

Dakyar Dr ta shawo kan Maryam, da taimakon Allah lumfashinta ya dawo, Mummy ta


godema Allah. Tun da sassafe Mummy ta neme likita data barsu su tafi, sbd batasan
Dady ya tarad da Maryam a asibiti, tasan ran kowa sai ya bace a gidan. Dakyar Dr ta
barsu suka koma gida, tabasu maguggunan da za'ai mata amfani dasu, kuma tace Mummy
ta tabbata ta kula da ita sosai SBD tana buk'atar hakan. Koda suka shigo gidan masu
aiki sai safa-da-marwa suke a falon, suna harhada kayan da za'a tarbe Dady dasu.
Mummy na janye da hannun Maryam da take tafiya a hankali sbd jikin ta har yau bai
sakiba. Sajida da Labila sun fito daga dakin Umma sukai kanta suna mata ya jiki.
Mummy tace "da sauki, ku barta ta huta. Kuje kucigaba da aikinku" sukace toh suka
tafi.

Karfe 12 Dady ya iso k'asa 9ja, direct gida akayo dashi dan yana buk'atar ya
huta. Kowa yaji dakin dawowar Dady lfy. Dining Umma ta nufa dashi bayan ya watsa
ruwa ta huta. Suna zaune yana kwasar girki yace da Umma "wai nikam ina haj Shafa'u
ne? Naga tunda na dawo ban gantaba" Umma tace "aiko tana ciki, maybe wani abun ne
ya riketa shiyasa bata fitoba, amma nasan yanzun zaka ganta" Dady ya jinjina kai
yacigaba da cin abincin shi, yana tunanin ko abinda yai matane yasa har yau bata
huceba. Har yagama cin abinci ba Mummy, itako Mummy fargabar haduwa dashi take
shiyasa bata fitoba. Tashi yai yanufe dakin ta, dan kuwa koba komai yai mssn dinta.
Rike da Maryam ya tarad da ita a dakin, fitowar su kenan daga toilet, dan tunda
suka dawo daga asibiti Mummy tashiga gyaran Maryam, dan jinta take tamkat yarta ta
ciki. Da sauri Mummy tace "sannu da zuwa" mamaki fal fuskar Dady yace "yawwa sannu,
meya sameta ne?" Gaban Mummy na dardar tace "batajin dadi ne" Dady ya fito da ido
waye tareda saurin karasowa yace "toh meyasa baa sanar daniba tun wuri" Mummy tace
"jiya ne zuwa yau, kuma ma kaida baka k'asa taya zamu sanar ma" Dady yace "dan bana
k'asa shiyasa baza'a sanar daniba, haj Shafa'u ki kiyayeni fa" Mummy ta sunkuyar
dakai hadida rungume hannuwa tace "Allah yabaka hakuri" yaja tsaki yace "Ya jikin
naki" sai lokacin Maryam tagaiseda shi tareda cewa "da sauki" sunkuye da kai,
itakam ko Mummy kunyarta take, dan yanzuma a toilet saida akai daga kafin mummy tai
treatment dinta. Dady yace "bari naje nagayama driver yazo muje asibiti, Ai bazaiyu
mu zauna a gida ba" Mummy tace "ai munje asibiti yanzu muka dawo ma, kuma jikin da
sauki sosai". Dady yace " kin tabbata ba wata matsala?" Mummy tace "babu
insha'allah" yace "toh kisameni a daki inaso muyi wata mgn" yafice. Mummy tabawa
Maryam tufafin dazata saka, takira Sajida tace ta kawo mata abinci idan taci sai
tasha magani. Ta fita.

Tsaye ta tarad da shi kusada TV yana rike da remote yana k'okarin canza tasha.
Da sallama ta isa tasamu guri ta zauna. Saida yacanza tashar kafin ya juyo yace
"ina yadda mukai dake?" Mummy tarasa mezata fada, Dady yafahimce manufar Mummy
tayin shiru yace "nagane manufarki" waya yajanyo a aljihunsa yai dialing no din
Elhaj, akai sa'a yana kan hanyar zuwa gidan, domin yaje asibitin bai samesu a
canba. Da sallama ya shigo, ya sunkuya yakwashe gaisuwa. Mummy ce kawai ta amsa shi
can k'asan ranta. Dady ya juyo yace " kai ina takardar Maryam?" Sosa keya yashiga
yi daga bisani yace "Dady dan Allah kai hakuri wlh inason ta, bazan iya sakintaba"
da sauri Mummy da Dady suka kalloshi, Mummy tai murmushi dan taji dadi. Maganar
Dady ce ta katse mata jin dadin "Inaaa! Ai baka isaba! Bayan ka walakanta ni cikin
mutane, ka nuna banida kema da darajja a idonka, saannan yanzu zakazo kace wani
kana sonta. Ai wlh bazai yuba, dolinka ka saketa, dama Ai nina aurama ita, kuma
nace kobayan raina banyarda ka saketaba, toh yanzu da rai nama nace ka saketa"
Sunkuyar da kai Elhaj yai yace "dan Allah dady kayi hakuri" Mummy tace "tunda yace
tanason matar sa ni a ganina kabar masa mana" Dady yace "nagayama nariga na yanke
wukunci zan auradda ita cikin satin nan, dama ba idda a tareda ita" Mummy tace "sai
maganar ba idda a tareda ita kake, waya gayama ba idda a tareda ita? Naga Ai
auradda ita kai" a fusace Dady yace "taya zatai idda bayan kinsan tun aurensu yasa
k'afa yabar gida, ko gidan shifa bai taba zuwaba yaron nan" tashin hankali ya
bayyana a fuskar Alhaji yana kallon Mummy sai faduwar gaba yake Allah kasa Mummy
bata gano abinda ya aikatama Maryam ba. Bai ankaraba yaji Mummy tace "Koda ya
saketa burinka bazai taba cikaba na aurad da ita, dan kuwa Maryam tana daukeda
idda" Da sauri Dady ya dube Mummy daga bisani yakai zaune, shi kowa Elhaj saurin
sunkuyar da kansa k'asa yai, dan kowa duk kunya tagama baibayeshi. Kallon tsana
Dady yabishi dashi daga bisani yace "koma miye yazama dole kasake Maryam wlh" Elhaj
rasa yai abinda zai Dady dan kasa magana ma yai, nan wayarsa ta fara ruri kiran
Sairah yashigo, tirkashi! Nan Mummy tatashi tabarsu a dakin. Daga bisani Dady
yashige daki Elhaj ma fitowa yai yanufe gidan Sairah.

Daki Mummy ta koma ta tarad Sajida na zaune tareda Maryam suna dan taba fira
Maryam na kwance kan gado. Mummy takaraso tace "Sajida taci abincin kuwa?" Sajida
tace "eh taci amma ba sosai ba" Mummy tace "a hankali zata fara ci sosai. Ya jikin
dai?" Maryam tace "da sauki" tana sunkuya da kai. Mummy ta jinjina kai dan ta lura
Maryam ma irin Elhaj ce da *MISKILANCI*.

Yau sati biyu kenan da faruwar al'amarin. Dan yanzu Maryam lafiya ta samu, sbd
Mummy bata wasa wurin gyaranta, kuma ba laifi ta sake dasu Sajida suna zaunawa sui
fira, saidai su Umma ne takemin kunyarsu. Amma da zaran Elhaj yashigo ko suna falo
zatai tsumut tatashi ta shige dakin Mummy, dan ita har tau tsoron shi take. Yauma
kamar kullum suna falo itada su Sajida da Labila, Aisha tashigo daukeda plate na
abinci, ta dauko daya ta rufe daya. Nan ma Maryam tashiga hangin plate din, har
Aisha ta kawo kusa da ita ta zauna. Bude plates din Aisha tai Maryam tadan ja
guntun tsaki, Aisha tai dariya tace "kinzace wani abunne ko?" Maryam tace "wlh ke
kwanan nan kwadayi nak......" Kafin ta ida taji sallamar Elhaj tareda junior aikuwa
nan ta tashi da gudu ta haura dakin Mummy kamar zata fadi. Dukkansu suka bita da
kallo kan su mayarda kallon su kofar. Elhaj suka gani kowa ya saita zamanshi Aisha
ta dauke plate dinta ta shige dakin su. Harara ya wargamasu Sajida yai sama shida
junior. Da gudu tashiga dakin Mummy har saida Mummy ta tsorata tace "ke lafiyarki
kuwa?" Tana mayarda lumfashi tace "klu Mummy" takoma ta zauna. Kafin ta ankara taji
budin kofa, aikuwa nan ta kai tsaye tana kallon Mummy da take kallon shi. Da
sallama ya karaso, yaneme guri ya zauna, nan fa tasamu tafito da sauri ta rufo musu
kofar. Binta yai da kallo, tayimai kyau sosai cikin shigarta ta atamfa Riga da
siket sunyi matu'kar kar barta. Daga bisani ya mayarda hankalinsa da Mummy. Mummy
tace "dama na kiraka ne akan maganar yarinyar nan Maryam, inaso tacigaba da
karatunta, tagayamin midwifery takeso tayi, domin ta taimake yan uwanta mata a
bangarin haihuwa. SBD haka zakuje da ita kakarbo mata form din makarantar ta cika,
inyaso sai tafara zuwa yafi zamanta haka" tunda Mummy tafara maganar yake biyarta
da ido harta kai aya, yasaukarda lumfashi yace "amma fa ni Mummy banasan tai
karatun nan gaskiya. Mezai hana kibarta takoma gidana tacigaba da zaman auren ta
ainaga zaifi" Mummy ta dubeshi sama-da-kasa tace "taka kafada ko? Toh ni tawa na
yanke kuma umurni nake baka a matsayina na mahaifiyar ka bawai shawara ba. Kuma
karatu ko kanaso ko bakaso sai tai" sunkuyar da kanshi kawai yai daga bisani tace
"toh Mummy duk yadda kikace haka za'ai" mummy tace "da yafi kam. Gobe kazo da safe
sai kadauketa kutafi" yace "toh" yafita.

Maryam kuwa da fitarta dakin su Sajida tashiga tana saukar sa lumfashi, Aisha
tace "Maryam na fahimce kina tsoron Alhaji da yawa fa" Maryam ta watsa mata harara
tace "ba doleba, Wannan yayan naku da bashida imani Ai dole na tsoraceshi" Labila
tace "Ai kuwa zanso naganku a gida daya" Maryam ta zaro ido waje tace "Allah
yakiyaye, tab ni Maryam nazauna gida daya da wannan mara imanin" sosai tabasu
dariya harda Aisha datake cin abinci takasa hadiye abincin saboda dariya.

*Ⓜªŋşħªŗŧ ŋºvęłş📚*
[3/18, 11:01 AM] Manshart: *MISKILANCI KO GIDADANCI*❓

```Written by Manshart💘```

~In dedicated to my luvly Dady (Alhaji) & Mummy (Bissalam)~

*{Đïş ïş mý şęĉºŋð ŋºvęł}*👌🏼

*✍🏻
✍🏻
✍🏻✍🏻
✍🏻HIQAYA ONLINE WRITER's✍🏻 (HOW)*

*Ina tayaku murnar kammala novel dinku Aunty Badi'at & Kairat Up. Allah yakara
basira lodi2 yakaro zakin hannu zakwai2 kamar zuma😋 gaskiya kuna nishadantar damu,
TUNALIN TOKA (Badi't) ya fadakar hakama Takwarana AISHA HUMAIRA (Kairat up) so all
sweet. Muna jiraye daku a new novels dinku. LYCM❤ wujiga2😍😜*

*Part 26*

Elhaj ne kwance acikin k'ayatattin dakin sa, sai bacci


yake, kasancewar jiya bai samu isasshin bacci ba. Karar wayarsa ce ta tadashi
yadube a gogo bayan ya dube mai kiran. Karfe 8:30 yagani. Tsum yameke tsaye ya nufe
toilet yayo wanka yafito. Tufafin sa yazura tareda fitowa falo yadau keys dinshi
kan center table dinda ke falon yafito. Parking space yanufa yadauko motarsa yazo
mai gadi ya buda masa gate ya fita, yanufe gidan Mummy. Ba kowa a falo duk suna can
suna bacci ya haura dakin Mummy. Da sallama ya isa, yasamu guri ya zauna yana
kallon ta da take kan mirror tana daukar pics a waya, dan kuwa yau wankan ta ba
k'arya. Yafi 5mints yana kallon ta tajuya nan ta juya nan tana bada selfie. Sosai
taimai kyau ganin yadda take daukar pics din cikin kwarewa. Wayarsa yasaka yafara
daukarta ta inda yake zaune, batareda ya karasaba. Saida ya dauka har sau 5 kafin
nan ya mayarda wayar a aljihunsa yabita da kallo. Ganin pics din bazasu kareba a
zuciyarsa yace "wai bata gajiya ne?" Sai kuma yabasar. Har yafara jin haushin abin,
itako sai dauka take, ta dauka sunkai 20, sai a na karshe ne tawani d'aga hannun ta
sosai sama, nan fa tai ido da mutun cikin camera'n. Aikuwa nan take tayada wayar ta
juyo tana binshi da kallo, k'okarin fita take Daga dakin amma ba hali, kasancewar
batada hijab a kusa da ita, yana weldrobe tamanta bata daukoba lokacin da ta dauko
tufafin ta. V gown ce take sanye da ita black da ratsin stones a jikin rigar. Rigar
tai mata kyau dama gata fara sol, tai rolling kanta da mayafi fari, kanta a kwance
tai parking dinshi tasako harshin gashin suka zubo ta gabanta. Kauda kanshi yai
daga kallon da yake mata, tareda Jan tsaki ya murtuke fuska kace wani damisa. Nan
fa Maryam tasamu ta isa da baya baya takai ga weldrobe tabude tabaya, taiwani
shigewa ciki tajanyo hijab dinta tazira. Tana zirawa da gudu tanufe kofa, ai kuwa
yakamota yace "dan ubanki baki iya gaisuwa bane?" Jikinta na bari cikin sarkewa
tace "I...iii...ina kwana" ido ya fidda waje yace "haka ake gaisheda babba a
gidanku?" Sulalewa tai daga wawan rigon da yai mata tace "antashi lfy" kunnayinta
yakama yace "daga yau haka zaki dinga gaisheda ni, idan ba haka ba hmmm kindaisan
abunda yafaru...." Cikin rawar murya tace "to...toh" kafin ta tashi Mummy ta turo
kofar tashigo. A durkushe ta taradda ita shiko gogan yana tsaye sai sosa keya
yake. Mummy tace "me kuma kai mata?" Da sauri yace "ba abinda namata Mummy kawai
gashinta ne bazata iya parking dinshi ita kadaiba, shine tace na tayata" cikin
rashin gamsuwa Mummy tace "OK" itakam Maryam kasa tashi tai, dan tune kunya ta
mamayeta, wannan sharri haka! Tafada a zuciyarta tana kallonshi dayake sakar mata
shu'umin murmushi. Mummy tace "Tun tuni ta shirya kai kawai take jira, saboda hk
karka sake ta gayamin ga abinda kaimata, nabaka amanarta" Elhaj yace "haba Mummy
sai kace wani banida imani" yafada yana wargama Maryam harara. Cikin zuciyarta tace
"ina ko kaga imani" Mummy tace "Maryam kutafi" Maryam tace "toh Mummy" zata dauke
jakarta yai saurin dauka yasakar mata murmushi data sake baki tana kallonshi. Daga
bisani tahadeyi yawu a ranta tace "lallai wannan yaciga munafuki" daga nan suka
fita.

Inda yai parking yanufa tana biye dashi a baya. Ganin sunyi nisa inda ba mai
hangosu yasa ya wurgomata jakar, Allah yasa ta iya gola takarbe, tana kallon ikon
Allah. Suna isa motar yabuda yashiga yai zamanshi, batareda ya buda mataba. Sundau
mintota a haka kan ya ziro kanshi ta glass yace "wai wakike jira ne?" Tabe baki tai
tareda gewayowa ta bude baya ta shiga. Guntun tsaki yaja aransa yace "gaskiya
yarinyar nan ta rainani, amma zan gyaramata zama" daga bisani ya fige motar da
karfin tsiya yabar gidan.

Tafiya suke bamai cewa da wani uffan, daga bisani yakunna karatun Qur'ani
kira'ar manshawai, suka cigaba da tafiya. Maryam kuwa sosai taji dadi sbd tanason
kira'ar, aikuwa tabishi suna tafiya, dama kuma tanason ayar cikin Tawbah, sosai
takejin dadin Surat. Elhaj kuwa baisan lokacin daya rage muryar spekr karatun ba
yashiga saurarar nata karatun, gaskiya ta burgeshi, ko makomai yanaso yaga mace
mahardaciya alqur'ani uwa uba ma ta iya kira'a zamzam. Ita kuwa kanta a sama sai
rero karatun take. Jin an tsaida karatun yasanyata dagokai ta dubeshi, daga bisani
ta mayarda kallon ta sama. Da haka dai har suka kai. Anasiye foam din tacika tayi
komai, sati mai zuwa zata fara fita. Basu dawo gidaba sai bayan la'asar. Daga
tsayawar mota tabude tafito da gudu tashiga gida. Yana binta da kallo har ta shige
gidan, kafin nan ya mayarda hankalinsa kan motar yafito shima yashiga gidan. A falo
ta tarad da su Sajida sun baje sai fira suke. Sallama tamusu ta haura dakin Mummy,
sukabita da kallo. A zaune ta tarad da ita tana shafa mai Mummy ta dubeta tace "har
kun dawo ne?" Maryam tace "eh Mummy sannu da gida" hadeda ajiye jakarta ta dire a
k'asa. Mummy tace "ohhh, sannu, kundibo gajiya kam" Maryam tai murmushi, daga nan
ya shigo. Tashi tai tanufe bayan Mummy tai kamar ta boya. Yashigo hadeda gaisheda
Mummy yagaya mata yadda suka k'are da malaman. Nan fa Mummy tashiga farin ciki, ko
ba komai yaga dariyar Mummy. Dan tunda akai abin Mummy ta daina sakewa dashi. Tashi
yai zai fita Mummy tace "kadawo kaci abinci mana" yatsine fuska yai yace "A koshe
nake Mummy" Mummy tace "haryau dai bazaka canzaba" yai murmushi ya fita. Mumm y ta
kalle Maryam tace "ke kije dining kisamu kici abinci, dan nasan ba abinda kukaci
acan" Maryam tace "eh Mummy munsha drink" Mummy tace "drink ai bazai rikekuba har
zuwa yanzu, kije kici abinci karki daka ta wancan" Maryam tace "toh" tatashi a
zuciyarta tana cewa "taya zan daka ta tashi, ina ruwan biri da gada ma" tafita.
Bayan ta kammala cin abinci tayo nan falon gurin su Sajida tazauna. Labila tace
"wai tawan yau ina aka shiga keda nakin?" Maryam taja tsaki "wani nawa kuma. Kinga
munje nacika form ne wani sati zan fara fita skul" Sajida da hankalinta na akan TV
tace "Allah ko tawan?" Maryam tace "sai kiyi" Labila dake kusa da ita tatabota tace
"kice can zaasha luv" Maryam ta harareta "dawaye?" Aisha da tun farawarsu batace
uffan ba tace "da Ya Alhaji mana" Maryam taja tsaki "wannan *Miskilin* a inama
yasan wani soyayya? Kuma ma nidawa zanyi soyayya bayan mijina dayake turai"
dukkansu suka hada baki sukace "Turaiii" daga nan akai kiran sallar magrub suka
tashi kowacce tatafi zuwa sallah.

Yau Maryam zata fara fita skul. Sosai ta caba ado najan hankali, bada
jimawaba yazo yadauketa suka tafi. A gate din skul din ya ajiyeta, kuma tsakanin
gate da hall din da zasui lecture da nisa sosai, kafin ma kashiga cikin farfajiyar
skul din da nisa. Kallo kawai tabishi dashi lokacin dayai parking da mota. Ganin
bata fitoba yasanya shi cewa "me kike jira ne?" Kallonshi tai ta marairaici murya
tace "amma...." Kafin tace wani abu yafito yabude motar yayo waje da ita yaja mota
yabar gurin. Maryam kuwa tabi motar da kallo. Daga bisani tashiga cikin gate din.
Tafe take da motatta mai kyau babba, ta kawo daidai Maryam tai parking Maryam tabi
motar da ido tan kallon me motar datake kokarin janye glass din. "Boyar Allah idan
ciki zaki kishigo mu karasa mana" Maryam tace "Aa wlh nagode" ganin bazata shigoba
yasanyata fitowa tace "haba boyar Allah, nifa mace ce yar uwanki, kuma ai naga ba
wani abu a ciki dan na ragemiki hanya SBD nasan kema din badan babu abinda zakizo
nan dinbane a gidanku" Maryam tace "hakane, amm...." Matar tace "karkice komai mana
mutafi dan Allah" ganin wannan matar ta nace yasanya Maryam cewa "toh bakomai" tace
"yawwa kokefa" tabuda mata gaba ta shiga ta zaga ta shiga itama taja. Ganin Maryam
tai shiru yasanyata cewa "boyar Allah ko zan iya sanin sunanki?" Maryam tace
"sunana Maryam Shehu Bissalam" tace "wow! Very nice. Am ni sunana Sairah Tahir"
Maryam tace "nice name" tacigaba da cewa "kina karatu ne a nan?" Maryam tace "eh ni
new student ce, yauma zan fara daukar lectures" Sairah tace "abu mai kyau. Wanne
course kenan?" Maryam tace "midwifery" Sairah ta jinjina kai hadeda murmushi tace
"kune masu taimakonmu nan gaba kenan. Shiyasa na dauko ki a mota ta nasan kema wata
rana zan neme hakan a gurin ki" Maryam tai murmushi kawai tamayarda kallon ta waye.
Sairah tace "kinga ni nazo neman wata friend ditace, sunanta Ameera, itace
tajajibomin zuwa skul dinnan yanzu, ashe rabon zamu hadu ne" Maryam takalleta
takara sakin murmushi a karo na biyu. Sairah tace "sai kinyi hakuri danifa, dan
kuwa akwai surutu" Maryam tace "bakomai" kafin nan suka kawo daidai inda zasu rabu.
Basu rabuba saida sukai exchanging no da ita, daga bisani sukai sallama kowa ya
kama gabansa. Da tunanin matar Maryam ta isa hall din, harma anfara, dakyar
lecturng din yabarta tashiga.

*Ⓜªŋşħªŗŧ ŋºvęłş📚*u

You might also like