Wannan Rubutu Ne me Tsayi saboda Zan koro Cikakken Bayani ne a kan Ilimin Taurarin Dan-
Adam Da na Yanayi, (Bashariyyan) Da Kuma Badiliyyan da kuma Zahiriyyan, A Daure a bi
rubutun A sannu a sannu yana da tsayi sosai, In an zo karatu za a dinga ganin Read more a karshe
da launin Shudi wato (Blue)🔵 Sai a dangwala👇🏻 za a ga ya bude sai a cigana da Karantawa haka
za a yitayi har zuwa Karshe a whatsapp kenan, amma a facebook ba Lallaine ya zo da read more a
karshe ba.
ILIMIN TAURARI⭐⭐ SUN KASU DA YAWA AMMA ZAN DAUKI KASHI BIYU ✌🏻MASU
MUHIMMANCI INYI BAYANINSU
1. Akwai Ilimin Taurarin⭐⭐ Dan-Adam👤
2. Akwai Ilimin Taurari⭐⭐ Na Yanayi
1. ILIMIN TAURARIN⭐⭐ DAN-ADAM👤
MENENE TAURARI⭐ ⭐ DAN-ADAM👤❓
Ma'anar Taurari⭐⭐ dai shine Wasu Halittune da Allahu Subhanahu Wa ta'ala ya Halitta a jikin
Ruhin Mutum👤 (Arwah) a turance (Spirit), Da hausa Kuma Kurwa, Ita Kurwa itace take Dauke
Da Tauratinka Guda tara⭐⭐ ⭐⭐⭐⭐ ⭐⭐⭐
Wadannan Taurari Guda tara da Allah ya haliccesu a jikin Ruhin Dan-adam sune ake cewa Dan-
adam Tara yake bai cika Goma ba, Abinda ya kewaye Taurari tara cikon Na Goman shine Ajalin
Mutum
Wadannan Taurari guda tara da ake Magana sune Rayuwar Mutum, Dukkan abinda mutum zai
samu ko ya rasa ko farinciki ko bakinciki a nan Duniya toh ya ta'allaka/Danganta ne da haskawar
ko disashewar Hasken Tauraron da yake wakilcin Wannan Abin
SUNAYEN TAURARI GUDA 9 DA WAKILCINSU
1. Tauraron Arziki ⭐💰
2. Tauraron Lafiya ⭐💪🏻
3. Tauraron Daukaka ⭐🤴🏻👸🏻
4. Tauraron So (Rihatul-Hub) ⭐💞
5. Tauraron Haihuwa ⭐🤰🏻🤱🏻
6. Tauraron Aure ⭐💏
7. Tauraron Jama'a
8. Tauraron Farinciki 😃
9. Tauraron Ilimi
Wadannan sune Taurari guda tara da Dan-adam ke rayuwa da su tare da Ruhinsa kuma suke
Gudana da tasiri a cikin Rayuwarsa, Kowanne Tauraro yana Dauke da ga6a Tara ne wato (Five
Joint), Shiyasa zakaga a rayuwa wani yafi wani, misali wani yafi wani Arziki, Saboda wani
Tauraron Arzikinsa ya haska masa Iya ga6a uku ne, wani kuma ga6a biyar ne keda haske, wani
kuma ga6a taran na tauraron arzikin duk ya haska, irinsu ne basa Talauci, Sune Tun zamanin
Annabi Sulaiman, su Dan-Karuna💰, wani Kuma Tauraron Arzikin nasa ma Iya Ga6a Dayane Tak
keda Haske, sbd Haka Kullum Sai ya nemo kafin ya ci, in bai nemo ba zai kwan da yunwa a haka
zai ta rayuwa in ba Allah ya hadashi da masu ilimin Taurari da gyaran Taurari ba saidai yata
wahala a Duniya 😭
Haka kuma Dukkan Abinda Dan-adam zai nema ko ya Rasa yana Karkashin Haskawar ko
Disashewar Daya daga cikin Tauraron⭐ da yake wakilcin wannan Abin, Dukkan Abinda Allah ya
Rubuta cewa zaka samu toh Rubutacce ne a Qaddararka cewa zaka samu ko zaka Rasa? Amma
Addu'a tana Chanza Qaddara Inji Annabi S.A.W🤲🏻
Idan Allah ya soka da Arziki da Da Mulki toh sai Taurarinka na Mulki da Arzikin Sai su haska
sama da Ga6a Biyu ko uku ko ma ga6a tara duka, Dukkan Abinda zaka samu ko ka rasa sai
tauraron da ke Wakilcin wannan abin ya haska ko ya disashe wannan wata Qudura ce da isa daga
☝🏻
Allah
TAURARIN⭐ DAN ADAM👤 KAN SAMI MATSALA SU DISASHE
Taurarin Dan'adam kan Sami Matsala su Disashe Al'amuransa su chakude 😭 Ta hanyar Tasirin
Shigar Sihiri ko Shafar Aljanu👹👺 ko Makaru ko Kambun ido👀 ko Kambun baka👄🗣️ Ko Tasirin
Baki😠Da Hassada😡
MENENE SIHIRI KUMA YAYA YAKE BATA TAURARON DAN'ADAM❓
AL-SIHIR= Huwa Udgimatush-shay'i Fil-Nafsi, Shi sihiri Shine Shigar Mummunan wani Abu
Cikin Ruhi, Al-Nasi Ayyi Ma'ana Arwah, Ma'anar Rai shine Kurwa wato Spirit, Kurwa kuma itace
Take Dauke da Taurarin Dan'Adam Guda tara wanda dukkan Abinda zai samu ko ya rasashi a
duniya🌍 yana Karkashin Haskawar ko Disashewar Daya daga Cikin Tauraron da yake wakilcin
Wannan Abin
Idan Sihiri ko Aljani shedani Ko Kambun baka ko jifa ya shiga jikin Ruhin mutum, toh A nan
Taurarin Rayuwarsa suke saboda haka sai su Lalace a sababin shigar wannan Mummunan abin
Jikin Ruhin, Daga nan Sai Taurarin su disashe sai Al'amura su fara Tabarbarewa suna Lalacewa
bisa kowanne irin Sanadi bayyananne ko Boyayye, Saukakakke ko Kuntatacce,
Idan Sihiri ya shiga Yakan Tunkari Tauraron so da Tauraron Arziki da Tauraron jama'a da na lafiya
sai ya harbesu duka sai su disashe sai aga abubuwa marassa kyau suna ta faruwa da mutum, ko me
ya sa a gaba sai abin ya lalace Saboda tasirin sihirin da ya shiga ruhinsa ya disashar da Hasken
Taurarinsa, Toh fa a nan matukar ana so komi ya tafi Daidai Sai an yi abu 3
1. Karya wannan sihirin
2. Gyara 6arnar da Sihirin yayi wajen Disashar da Taurarin Sa wato Gyaran Taurarin da sihirin ya
bata kenan
3. Yin Wani magani ko addu'a na Dafa'i wanda za a samu Kariya saboda gaba
Da yawan Mutane Suna fadawa hadarin Sihiri ko shigar Aljanu amma saidai basu iya Jinyar Bane,
kokuma suna zuwa Gun masu magani da basu san kan Abin ba ko basu ma San ya zasu yi ba
damuwarsu kawai a basu kudi, kai marar Lafiya ko bukatarka ta Biya ko kar ta biya ohonka
sudai sun Ci kudinka Allah ya tsaremu🤲🏻
Shiyasa sai Kaji Marassa lafiya suna ta cewa wai sunyi Magani sunyi magani sun gaji da kashe
kudi, Kokuma abin sai ya tafi sai kuma ya dawo, A Ka'ida fa Ita Jinyar Sihiri ko shafar Aljanu ko
wani abu me kama da haka, idan aka gano matsalar sai a Magance ta, Sannan a gyara Taurarin da
matsalar ta Shafa, Sannan a yi na tsari ta yadda kar Abin ya kara Afkuwa, Amma mafi yawa kawai
maganin ake sai matsakar ta kau kuma sai a kara yima mutum wani jifan ko asirin sai ya kara
Kamashi har sai ya dauka Dama wanchan din bai warke bane Alhali ya warke kawai bai katange
taurarinsa da ruhinsa da Dafa'i na Addu'a ko Magani Bane yasa aka kara jifansa kuma aka
sameshi, Haka kuma da yawa sai kaga Anyi maganin sihirin Amma dai har wayau Al'amuran suna
a tabarbare, wannan kuma Matsalar itace An yi maganin Sihiri ko jifa ya karye Amma ba a gyara
Taurarin sun dawo hayyacinsu ba suna a lalace ba haske, Dole ne sai an samu Masanin Gyaran
Tauraro domin Zaka iya Samun me magani shi kawai yana da Maganin Jinnu, Sihiri, Maita da
sauransu Amma Baida ilimi a kan Taurari sam sam, saboda haka shi kawai zai baka Maganin Jifa
ko sammu ko jinnu, Kuma da gaske ya baka Maganin saidai kawai Yakamata ace Bayan Magani
an gyara Taurarinka Sabida komai ya tafi Daidai,
Misalin Karya sihiri ba tare da Gyara Taurarin da sihirin ya Bata ba Daidai yake da Misalin
Gobara Ta kama Cin Gida Sai a zo a kashe wutar bayan ta kokkona Kayan cikin gidan sunyi baki
kaikuma ka ce zaka shiga gidan a haka cikin bakin gawayin da wannan Gobarar ta ci, Ashe kenan
bayan an kashe Gobarar dole a zo a share Dattin da Gobara ta haifar Sannan kayan da suka Kone a
chanza na Chanzawa a gyara na gyarawa, Toh kamar Hakane Gyaran Tauraro ga Mutumin da Aka
masa sihiri Bayan an karya sihirin sai a gyara Taurarin da sihirin ya Bata su.
a takaice wannan shine Bayani a kan Taurari ⭐ da sunayensu da wakilcinsu da kuma Yadda suke
Lalacewa, Abinda na Fada Daidai Allah ka Karba Min ka Bamu ikon Amfana da shi, wanda nayi
Kuskure kuma saboda Ajizanci Na Dan'adam Allah ka gafartamin 🤲🏻
2. ILIMIN TAURARI NA ⭐⭐⭐ YANAYI KO RAYUWA
ILLIMIN TAURARI⭐⭐NA YANAYI DA RAYUWA
Da Sunan Allah wanda ya sanya taurari su zama jagora ga rayuwar ɗan Adam, Tsira da Amincin
Allah su tabbata ga khairil Anam, Sayyidina Muhammadu Imamuna Badarut tamam🤲🏻 Wa Alihi
Wa Sahabihi Ahlil kiram, S.A.W🤲🏻
Wannan ilimi na taurari, yana hana mutum shiga garari, da samun alheri da kaucewa hatsari.
TUSHENTA
Daga Annabi Idris (Enoch) A.S yake. Allah ya sanar dashi mafi yawa daga cikin Abubuwan da
Annabi Adam ya lissafo a gaban mala'iku.
✍🏻
Shine Annabin Allah na biyu, shi ya fara amfani da alqalami wurin rubutu, shi ya fara dinka
kayan sawa🥼🩲👕👚 shi ya fara amfani da tafiyar taurari dan gane al'amura.
Ayoyi sun zo a cikin Al-qur'ani wayanda suke nuna alaqar rayuwa da taurari. Bisa taqaitawa ba
zan kawo su ba.
Amma mu sani, Komai yana da alaqa da taurari ⭐⭐⭐
RABE-RABEN TA
Ilimin taurari ya rabu kashi kashi amma ni saboda taqaitawa, Fannin Hisabi zan dauka inyi bayani.
Amma akwai su FALAKI, ILMUL KAFFI da sauran su.
ILIMIN HISABI
Shine ilimin amfani da harrufan Arabiya guda Ashirin da takwas wurin samun kusanci da Allah da
neman alherin duniya da lahira🤲🏻 ko tsari daga sharrinsu.
HARUFFAN ARABIYyA
Kowani Harafi yana dauke da lambar da yake wakilta. Misali Alif, yana daukan daya, Ba biyu, Ta
400, Tha 500. Haka haka dai har Ya wanda yake daukan lamba goma.
HARUFFA DA ADADINSU
10- ي.9- ط.8- ح.7- ز.6- و.5- ه.4- د.3- ج.2- ب.1-أ
200- ر.100- ق.90- ص.80- ف.70- ع.60- س.50- ن.40- م.30- ل.20-ك.
1000- غ.900- ظ.800- ض.700- ذ.600- خ.500- ث.400- ت.300-ش.
Wannan Shine tsarin yadda ake rubuta su ba kamar yadda ake jera su a rubutun Alif Ba Ta Tha Jim
zuwa Ya'un ba. Ana kiran wannan tsarin ABJA-DIYYA.
BANBANCIN ADADI
Akwai wasu haruffa wayanda suke da banbanci wurin adadin su a wurin malaman taurari na gabas
(Larabawa) da na yamma (Baqaqen fata) da kuma wayanda suka shahara a fannin irin su IBN
ARABIY AL KHATIMI wanda shi adadin da yake amfani dasu daban ne da na Gabas ko Yamma.
Haruffan da suke da banbanci guda shida ne kamar haka
1. صA gabas 90 ne, A yamma 60 ne.
2. ضA gabas 800 ne A yamma 90 ne.
3. سA gabas 60 ne a yamma 300 ne.
4. ظA gabas 900 ne A yamma 800 ne
5. غA gabas 1000 ne a yamma 900 ne
6. شA gabas 300 ne a yamma 1000 ne.
Duk wanda ka ɗauka kayi amfani dashi kayi daidai domin a shari'ar Musulunci ma ance
SAƁANIN FAHIMTAR MALAMAI, RAHMANE GA AL'UMMA.
WANNAN SHINE ADADIN HARUFFA NA ZAHIRI, AKWAI NA BAƊINI DA BAƊININ
BAƊINI AMMA WANNAN SAI NAN GABA ZAMU KAWO SHI INSHA ALLAH.
MISALI
Yan'uwa da yawa zakuji a wurin Addu'a akance a karanta abu kaza adadi kaza. Misali, a karanta
HASBUNALLAHU 450, Ladifu 129, Ya Kafiy 111, Da sauran su. Meyasa?
Ana tawassali da sirrin adadin haruffan abinda za a karanta din ne don samun bakin zaren addu'ar
wato mustajaba. Idan muka dauki Ladifu a arabiya zai bamu لطيف
30 -ل
9 -ط
10 -ي
80 -ف
Idan muka ce 30+9+10+80 zai bamu 129. Kunga ashe adadin haruffan ladifu din ake karantawa.
Ga qarin wasu kalmomi da adadinsu
1. 66 -الله
2. 92 -محمد
3. 53 -احمد
4 165 -الاله اال الله
5. 454 -محمد رسول الله
Duk in kuka yi musu abinda muka yiwa ladifu, adadin da zaku samu kenan amma fa nayi Amfani
da Adadin gabas ne ba na yamma ba saboda shi mutanen yanzu suka fi amfani dashi.
Sai dai naga Diwanin Sheikh shehu Ibrahim Inyas RTA bisa tsarin Yamma ya rubuta ta. Harafin
qarshe a wurinsa ,SHIN MAI RUWA (Shinun) ne ba GALLIKAFA (gainun) BA. Dan haka ina
amfani da Na yamma sosai.
ƊABI'AR MUTUM
Mutum Allah ya halicce shi ya sanya masa ɗabi'ar daya daga cikin abubuwan nan guda hudu
kamar haka:
1. Wuta/Haske
2. Iska
3. Ruwa
4. Qasa/yumɓu
A turanci ana kiransu ELEMENTS OF CREATION (Sinadaran halitta) saboda rayuwar mutum
bata kasantuwa in babu daya daga cikinsu. Allah ya halicce ka da qasa, ranka daga haske, ruwa ke
raya jikinka, iska ke raya ruhinka.
Toh kowani mutum dabi'ar sa in ka lura zaka ga yana kama da daya daga cikin hudun nan, wannan
yana nufin wannan sinadarin ya rinjayi sauran ukun kenan.
Abubuwa hudu din nan kowannen su ya rabu kashi uku. Zaka iya samun mutane biyu masu dabi'ar
wuta amma daya daga cikin su yafi dayan su zafi. Dalili kuwa shine sun banbanta a wurin taurarin
da ake kira BURUJI da KAUKABU da MANZILA (Amma bazanyi bayanin manzinlai ba tunda
ba Falaki muke yi ba).
BURUJI
Allah SWT yana cewa "wassama'i zatil buruj". Toh buruj din nan wasu taurari ne guda goma sha
biyu. Kowani dan Adam yana dauke da daya daga cikinsu, gasu sunayensu:
1. HIMLU
2. SAURU
3. JAUZA
4. SURƊAN
5. USDU/ASADU
6. AZ'RAA
7. MIZAN
8. AQRABU
9. QAUSU
10. JADYU
11. DALLU/DALWU
12. HUTU
Hadisi Ingantacce ya bamu labarin cewa mutum shine yake zabar arziki ko talauci, rabauta ko
tabewa da sauransu. Bayanin baki daya yana rubuce a tauraron ka.
Kowani buruji yana dauke da mala'ika da Shaiɗani/aljani wayanda suke hidimatawa tauraron.
Annabi SAW yana cewa "kowani mutum yana da shaiɗani har dani amma nawa ya musulunta"
Ibada ke qarfafa mala'ikan ka ya tauye shaiɗanin ka, shagala ke qarfafa shaiɗanin ka ya tauye
mala'ikan ka.
Mala'ika shi yake maka ilhama
Shaidaninka ke jefa maka wasuwasi
KAUKABU: Taurari ne wayanda suke tamkar motar dake daukar burujai daga nan zuwa can cikin
ranaku bakwai da watanni sha biyu. kowannen su yana rataye ne a daya daga cikin sammai
bakwai. Gasu kamar haka:
1. SHAMS (Shine jagora a Lahadi)
2. QAMAR (Shine jagora a Litinin)
3. MARIKHA (Shine jagora a talata)
4. UƊARIDA (Shine jagora a laraba)
5. MUSH-TARI (Shine jagora a Alhamis)
6. ZUHRA (Shine jagora a juma'a)
7. ZUHAL (Shine jagora a asabar)
Ta hanyar kaukabu mutum yake iya sanin wani kaya ya dace ya dinga sanyawa, menene sana'ar da
ya dace yayi, da sauransu. Abin nufi, ta hanyar kaukabu mutum yake gane hanyar da zai bi dan ya
riski abinda burujinsa ya qunsa Wato yadda zaka gane wacce sana'a ce ta dace da Kai da sauransu,
Domin da yawan Mutane suna Tafiya cikin duhu shiyasa suke wahala a rayuwa
Subhanakallahumma wa bihamdik Ashhadu Anlaa ilaaha illaa anta Astagfiruka wa atubu Ilaik🤲🏻
A nan zan tsaya sai nan gaba zamuyi bayanin yadda mutum zai gane burujinsa da dabi'arsa da
kaukabun sa.
YADDA AKE GANE 'DABI'AR MUTUM👤
Assalamu Alaikum!
Kar ku manta Ɗabi'a daban, Buruji daban, Kaukabu Daban, Manzila daban. Saidai kowannen su
yana da alaqa da kowanne.
HALIN KOWANE DAƁI'A
1. NARI (Wuta)🔥: Mutum ne mai saurin faɗin ra'ayinsa in ana magana, mai son nishaɗi, mai son
ya samu rinjaye a komai, mai ji-ji da kai, marar rikon sirri, mai tsatsauran ra'ayi, mai mugun
neman kudi, mai zafin rai😠😡 da faɗa amma ba wuya ya huce😁
2. TURABI (ƙasa): Mai yawan haquri😀👏🏻 da zurfin ciki😷 mai sanyin jiki da danasani kan
abinda ya aikata, mai yawan sha'awa, mai tunani mai amfani mai tawadi'u, mai hawa da sauka a
lamarin son dukiya, mai fasahar magana da daukar hankalin jama'a.
3. HAWA'I (Iska): Mai zafin nama💪🏻 da tsananin tafakkuri cikin maganganun da akayi dashi, mai
yawan tashin hankali, mai yawan tafiye-tafiye🚘🛫✈️da rashin zama wuri ɗaya na lokaci mai tsawo,
mai nuna banbanci tsakanin abubuwa, mai fasahar qirqire-qirqire tareda nasara a abinda yasa a
gaba saidai bashi da magana ɗaya, yanzu eh, anjima A'a.
4. MA'I (Ruwa): Shahararre ne a duk fannin da yasa a gaba tareda samun rinjaye ko da yaushe💪🏻,
mai son yin kakaci da jama'a, iya siyasa da zolayar mutane, mai rashin karaya, mai tawadi'u wurin
taimakon wasu.
KU LURA: Kowannen suna anyi bayani ne a taqaice sosai.
YADDA AKE GANE DABI'AR MUTUM
Akwai hanyoyi da yawa amma zan fadi kwaya daya kuma shine mafi sauqi daga ciki, gashi:
1. Ka haɗa sunan ka da na Mahaifiyar ka sai ka dinga ɗebe huɗu-huɗu, idan 1 yayi saura, kai
NARI ne. Idan 2 yayi saura, kai TURABI ne. Idan 3 yayi saura, Kai HAWA'I ne. Idan 4 yayi
saura, kai MA'I ne.
Misali, Sunanka Adam (Adadinsa 45) mahaifiyarka Hauwa (Adadinta 15). 45+15=60. Idan ka
dinga ɗebe huɗu-huɗu cikin sittin 4 zai yi saura, dan haka kai MA'I ne.
QARIN BAYANI
Idan ka bi wasu hanyoyin wurin gane Dabi'ar ka ba lallai bane ta baka amsa irin na wannan domin
kowanne da irin yadda aka bi aka gano shi. Amma sam babu laifi, kana iya daukar kowanne kayi
amfani dashi.
Sau tari ko a shari'a ne zakaga ga wannan mazhabar tace ga yadda abu kaza yake, wancan
mazhabar kuma tace A'a ba haka bane. Kowannen su yayi daidai tunda saɓanin fahimta ne ba son
Zuciya ba.
YADDA AKE GANE BURUJIN MUTUM
Ka hada sunanka da na mahaifiyar ka sai ka raba da 12-12-12, abinda yayi saura daga 1-12 shine
tauraron burujinka.
Misali, Adam (45), mahaifiyar ka Hauwa (15). 45+15=60. A sittin ɗin sai kayita cire 12-12-12,
abinda zaiyi saura shine 12, dan haka burujin ka buruji ne na sha biyu. (Dan sanin burujai da
sunayensu, Wanda yake buqatar cikakken bayani akan kowani buruji, ya nemi littafin ABU
MA'ASHAR.
BINCIKE AKAN RASHIN LAFIYA
Ka haɗa sunan mara lafiyan da adadin sunan ranar da kake binciken a ciki sannan ka qara 10. Sai
ka cire 7-7-7. Idan 1 yayi saura, ciwon aljanu ne👺👹. Idan 2 yayi saura, ciwon daga iska aka shaqa
😷 Idan 3 ne, Sihiri ne. Idan 4 ne, maita ne👿👽, idan 5 ne, a jini🩸💉 ciwon yake. Idan 6 ne, zazzabi
ne.🤒 Idan 7 ne, Sanyi ne.
Misali, Sunanka Adam (45), ranar bincike laraba ( )اربعه278. Sai ka qara da 10. 45+278+10=333.
A cikin 333 ka dinga cire 7-7-7... 4 zai rage. Dan haka ciwon maita ne.
BINCIKE🔍🔎 AKAN AURE 💏
Ka hada sunanka da nata ka qara bakwai. Idan ya rage:
1. Za ayi shagali lokacin auren amma za a rabu daga baya ba jimawa
2. Aurene mai cike da alheri da arzikin ya'ya saidai sai an toshe kunne daga surutan mutane kafin
ayi auren.
3. Babu alheri ko kaɗan kuma mijin ba lallai bane yayi tsawon rai.
4. Zai yiwu amma akwai matsala daga wurin matar ko iyayenta ko iyayenka mata.
5. Akwai alheri da samun ya'ya mata da zaman lafiya.
6. Farkonsa da kyau, karshensa rabuwa ko mutuwa.
7. Akwai alheri amma babu sulalla sosai saidai kadarori amma yara zasu shahara.
8. Komai daidai babu talauci babu arziki mai yawa.
9. Tashin hankali da Bala'i da kisa da da da...
Misali, Adam 45, Hauwa 15, A qara 7. 45+15+7=67.
67 a cire 9-9-9... Hudu zaiyi saura.
Toh ya kuka ga zaman Annabi Adam da hauwa, Daga wurin wa aka fara samun matsala? Hisabi
wulaya ce mai zaman kanta!