Akidata
Akidata
*PART1* _Page 1_
*written and edited by*
_*AYSHERCOOL*(Daddy's girl)*_
The experience writer of *ABDUL JALAL*
Bismillahir rahmanirrahim, da sunan Allah me Rahama me jin ƙai, Wannan littafi
ƙirƙirarren labari ne banyi shi dan cin zarafi ko cin fuska ga wani ko wata ko wata
ƙabila ba, idan har wani ko wata yaga wani abu daya yi kaman ceceniya da rayuwar sa
ko ƙabilar sa Amin Afuwa banyi dan cin zarafin wani ko wata ba. Wannan littafin
mallaka tane, ban yadda a juyamin labari ta kowane fanni ba ba tare da izinina ba.
What's App : 07063065680 Facebook : real Humaira Watpad : Ayshercool7724 Gmail :
Www.ayshertadam@gmail.com
Katafaren ɗakin Bacci ne me ɗauke da kayan alatu na more Rayuwa da jin daɗi, idan
ka ƙarewa ɗakin kallo zaka tabattar da ma'abocin wannan ɗakin Allah yayi masa
Ni'imar Dukiya dan ya ƙawatu da dukkan wasu kayan more rayuwa, kallo ɗaya zakayiwa
ɗakin kasan mamalakin ɗakin mace ce, saboda kan madubin dake ɗakin shaƙe yake da
kayan kwalliya da gyaran jiki, ga wani show glass ɗauke da takalma da jakunkuna na
adon mata kamar wani kantin saida kayan ado, kai da ganin takalma da jakunkunan nan
kasan bana talaka bane, Makeken Gadon dake ɗakin ne ɗauke da wata kyakywar
matashiyar budurwa ta baje gashin kanta tana bacci cikin nutsuwa.
Hasken ranar da ya ratso ta tagar ɗakin ne yake dukan fuskarta wanda hakan yasa ta
motsa a hankali, ta buɗe idanuwanta. Ɗan ya mutsa fuska tayi, ta miƙe zaune ta
kalli Agogon bangon dake ɗakin nata, ƙarfe tara da rabi na Safiya, a hankali ta
zuro ƙafafuwanta ƙasa ta miƙe ta nufi banɗakin dake cikin ɗakin nata. Aljannar
Duniya shi kansa ba ɗaya nata ya isa a tsaya a kalla.
Wanka matashiyar tayi ta fito daga ita se towel, abun mamaki har an gyara mata inda
ta tashi, ta zauna a gaban mudubi, ta shafa wannan ta goga wancan, gashi komai nata
a hankali cikin nutsuwa take aiwatar dashi, riga da skirt na blouse ta ɗakko ta
saka da ɗan guntun mayafi, ta ɗora akanta tasaka takalmin ta me matuƙar tsini da
jakarsa, seda ta kalli agogon hannun ta ƙarfe goma da rabi dai dai sannaan ta buɗe
ɗakin ta fito.
Wani irin taku take na ƙasaita, takalmin ta na bada sauti ƙwas, ƙwas, ta fito wani
irin ƙaton falo ta zauna, ba ta daɗe da zama ba, me aiki ta kawo fruit gabanta ta
ajiye, bata kalli inda fruits ɗin suke ba, se kallon tsintsyar hannun ta da ta
ɗaurawa Agogo take yi.
"wato Isa rayuwar ƙauye akwai daɗi akwai wahala" Wanda aka kira Isa yace
"Haba ɗan uwa wani irin daɗi a ƙauye? Kai ka taɓa ganin wanda yake birni ya koma
ƙauye banda zunzurutun wahala mene ne a ƙauyen?"
"to ai Rayuwar ƙauye tafi ta birni kwanciyar hankali, ba tashin hankali ba fargaba,
amma kaga birni a nan rashin gaskiya ya ƙare"
"tabdijan lallai ma sani, ai tunda Allah ya kawoni birni na samu aikin gadin nan,
idan naje ƙauye to ziyara na kai Amma bani babu zaman ƙauye ina daf da dawo da
iyalina nan ma"
"kai gidan nan zaka dawo da iyalin naka, kaifa kace min zaman fargaba kake a kowane
lokaci za'a iya sallamar ka fa"
Isa yace "rufamin Asiri in kawo iyalina gidan nan Haya zan kama"
Suka ci gaba da hirar su tare da yin taɗi akan rayuwar birni da ta ƙauye
Sake kallon Agogon ta tayi har sha biyu saura minti goma sha biyar, miƙewa tayi
cikin takunta na isa ta fito harabar gidan, kai tsaye ta nufi bakin gate, inda me
gadi ke zaune yana hira da abokin sa sani suna cin gyaɗa.
Isa Yana hangota ya miƙe jiki na rawa yace "Allah ya temake ki, barka da fitowa"
bata amsa masa ba tace
"har yanzu Sabo driver bezo bane?"
Cikin girmamawa yace "Eh ranki ya daɗe be ƙaraso ba"
Haɗe rai tayi ta jinjina kai ta koma cikin gidan
Sani yace "Isa ita kuma wannan wacece naga jikin ka se rawa yake dan tazo" sani ya
tambaye shi
Isa yace"kai bari kawai, itace 'yar masu gida bata da wa, bata da ƙani shalelen
Alhaji kenan, watan ta uku da dawowa daga ƙasashen Turai, yarinyar nan sam bata
taɓuwa, gaba ɗaya halin turawa shi take yi, yau kam kashin sabo ya bushe wallahi "
Sani yace "kamar ya kashin Sabo ya bushe meze faru?"
Be ƙarasa maganar ba aka fara bubbuga gate ɗin gidan, da sauri Isa yaje ya buɗe,
wani mutum ne a ƙalla ze shekara Arba'in ya shigo kaman an koro shi.
Isa ya kalle shi yace "Taɓɗijan sabo yau kashin ka ya bushe, yanzu ta fito gurin
nan neman ka"
Wanda aka kira da Sabo ya shiga rafka salati "na shiga uku yanzu ya zanyi, wallahi
yarona ne babu lafiya na kaishi chemist"
Isa yace "ai bani za kayi wa bayani ba, seka je ka same ta"
Suna cikin maganar ta kuma fitowa, Fuskarta a haɗe babu annuri ta kalli sabo tace
"ƙarfe nawa nace maka zan fita?"
Jiki na rawa yace "ƙarfe sha ɗaya ranki ya daɗe"
"yanzu ƙarfe nawa ne?"
"shabiyu da minti goma"
"good, bani mukullayen motocina"
Sabo yace"dan girman Allah kiyi hakuri ranki ya daɗe, wallahi yarona ne ba lafiya
na kaishi chemist"
Cikin tsawa tace "shut up, did I ask you? Kabani keys ɗina"
Durƙusawa yake ƙoƙarin yi amma ta dakatar dashi "kai motocin na ubanka ne ko nawa?"
"naki ne Hajiya"
"idan har nawa ne, ka kawomin makullayena, na sallameka za'a bawa me gadi kuɗinka
ya baka, daga yau se ya zama izina a gare ka, Alƙawari yana da mahimmanci cika shi
alamace ta amana, lokacin aiki dana ɗauke ka mallakina ne ba mallakin ka ba tunda
biyan ka nake, dan haka seda izinina za kayi duk wani abu komai girmansa in ba
ibada ba tunda biyan ka nake"tana gama maganar ta juya ta koma cikin gidan. guri
sabo ya nema ya zauna ya dafe kansa yana salati.
Isa yace "Sabo se dai haƙuri, Allah ya baka aikin da yafi wannan"
Cike da damuwa Sabo yace "Ameen Isa, Nagode sosai Allah yasaka da alkhairi, idan ta
bada sauran haƙƙin nawa nazo in karɓa" Sukayi sallama Sabo ya fice daga cikin gidan
zuciyar sa a cunkushe babu daɗi.
Bayan tafiyar Sabo,
Sani cikin damuwa yace "wai Bala in tambaye ka mana, ita bata da mafaɗi bata san
dai dai ba, bata san Afuwa da uzuri ba?"
Bala yace "Taɓɗijan kai kasan su amma ita kam bata sansu ba, wannan da kake gani
tana da wata irin muguwar AƘIDA da ta tashi akai saboda rayuwa da turawa, zuciyar
ta kaman Arniya gaba ɗaya Aƙidun turawa ne da ita bana musulunci ba, babu wanda ze
iya raɓarta su zauna lafiya, Akwai matar mahaifin ta dake gidan nan ita da 'ya'yan
ta, seta yi sati biyu seta ga dama za su ganta balle maganar fatar baki ta haɗa su,
ta maida su tamkar bayin ta, idan kaga dariyar ta to da Mahaifin ta ne, da wani
babban Aminin sa, ko wasu ƙalilan daga ƙawayen ta, bata da yadda sam, gani take duk
wanda ya fiye raɓarta ba shi da gaskiya, Sabo shine driver na huɗu da tayi bayan
dawowar ta Nigeria, ga Albashi me kyau ga mahaifinta da kyauta, amma kowanne
ma'aikaci da ƙafarsa yake guduwa saboda izza da bala'in ta, 'yan aiki kuwa koni na
kawo shida daga garin mu amma da ƙafarsu suke guduwa, yanzu kalli duk haƙuri da
ƙoƙari irin na Sabo kaga yau yadda ta wulaƙanta shi ta kore shi"
Sani ya sauke nannauyar Ajiyar zuciya yace "to ina mahaifiyar ta? Ya aka yi aka
bari ta tashi da wannan AƘIDA wadda tayi hannun riga da Akidunmu na musulunci da
kuma na Al'adar mu?"
Isa yace "Mahaifiyar ta ta rasu, shi kuwa mahaifin ta duk abunda tayi dai dai ne a
gurin sa, yace ɓata mata rai tamkar zuba wuta ne a zuciyarsa"
Sani ya dinga juya maganganun Isa a ransa yana tunani, Sallama yayi wa Isa ya fito
ya tura wheelbarrow ɗin mangwaronsa ya bar arear.
************************************
Wani matashine da baze gaza shekaru talatin ba zaune akan kujera ya tattara dukkan
hankalin sa da tunanin sa akan allon na'ura me ƙwaƙwalwa dake kan teburin gaban sa
ko ƙyafta ido ba yayi da alama wani abu ne me mahimmanci yake wa wannan kallon
ƙurrilar.
Ƙwanƙwasa ƙofar ofishin da'aka yi ne yasa shi dawo wa hankalin sa a hankali yace
"yes bismillah"
Turo ƙofar ofishin akayi aka shigo, wata matashiyar budurwa ce ta shigo jikin ta
sanye da suit baƙaƙe da ɗan ƙaramin veil shima baƙi hatta takalmin ƙafarta baƙine,
cikin taku na ɗaukar hankali ta ƙaraso gaban teburin sa tace
"barka da hutawa ranka ya daɗe"
Fuskarsa babu yabo ba fallasa yace "yawwa sannunki ya aka yi?"
Cikin iyayi da yauƙi tace
"dama Yallaɓai ne yace yana son ganinka a office dinsa" Ɗan jinjina kai yayi yace
"Alright zanje Insha Allah" Cikin sigar shagwaba tace
"can i offer you something to eat, naga yau kaman ba kaci komai ba?" Girgiza kai
yayi tare da faɗin
"No thank you"
"Amma Yallabai dan Allah Yusuf fa?"
Ba tare da ya ɗago ba yace mata "be shigo ba"
Haka ta fita ta bar office ɗin gwiwa a saɓule tana tunani "komai za'ayi ba'a taɓa
birge gayen nan daga shi har Yusuf, gara ma wannan akan waccan me kama da saƙagon
da magana ma se ya ga dama yake yi" tai maganar a fili da sigar mita
Ya tattara system din ya kashe, ya ɗauki wayarsa da mukullin motar sa, ya ɗora top
ɗin kayansa a kafaɗa da jakar sa ya fito ya nufi wani ofishin.
Yana shiga dayan ofishin ya ƙame cikin girmamawa ya sarawa wanda ke office ɗin da
alama shugaban sa ne, be zauna ba seda aka yi masa izini sannan ya zauna suka sake
gaisawa.
Mutumin ya ɗago ya kalle shi yace"Abbas kana ganin babu matsala a wannan aikin
da'aka baka kasan hatsarin dake cikin aikin zaku iya kuwa? Kana ganin akwai wani
cigaba akan case ɗin?"
Wanda aka kira da Abbas yai murmushi cikin girmamawa yace "karka ji komai ranka ya
daɗe Insha Allah zan iya, zamu yi nasara, kuma ina fatan nasara Insha Allah yanzu
idan na bar nan zanje in samu Yusuf ne kasan shine jigon aikin"
"hakane to shikenan Allah ya tabbatar da Alkhairi ya baku sa'a na yadda da ƙwazon
ku, Allah ya bada sa'a"
"Ameen yallabai muna godiya".
**********************************
Zaune yake Ya barbaza takaddu da na'urori masu ƙwaƙwalwa har biyu akan gadon sa ya
tattaɓa wannan ya taɓa waccan, kafin daga baya yayi zugum yana kallon hotunan wata
tsaleliyar yarinya, yarinyar wadda zata yi kimanin shekaru goma sha takwas sanye
take da farin gajeren wando, se wata 'yar riga a jikin ta itama fara, ta saka farar
hula hat ta baza gashin da ya kasa tantance nata ne ko na sawa ne, ga ƙaton baƙin
tabarau a idonta ta buɗe fararen haƙoran ta tana dariya, bayan ta wani irin makeken
ruwa ne shuɗi sosai, hannun ta na hagu riƙe da igiya da aka saƙalo wuyan wani
jibgegen kare, jikinsa fal farin gashi ƙal, ba ƙaramin kyau yarinyar tayi a hoton
ba. ko ƙwakwaran motsi ba yayi hotunan kawai yake dubawa kaman yana ƙoƙarin gano
wani abu a jikin hotunan.
Wayarsa ce ta fara ruri, wanda ya sashi dawowa daga dongon nazarin da yake yi, ya
duba wanda yake kiran wayar tasa yaga sunan Abbas akan Allon wayar tasa, yasa hannu
ya kai wayar kunnen sa yace "Assalamu Alaikum warahmatullah"
Daga ɗaya bangaren aka amsa sallamar sannan wanda ya amsa din ya ɗora da cewa " ina
ƙofar ɗakin ka kana cikine in shigo? akwai labari da nazo maka dashi"
"eh ina ciki shigo kawai" Kafin ya kashe wayar aka turo ƙofar akayi sallama a ɗakin
nasa, tashi yayi zaune ya aje wayar yana faɗin
"kai tun shekaran jiya daka turomin hotunan wata yarinya bamu kuma haɗuwa ba, kuma
ka kashe wayarka, gashi saboda aikin nan ko Office bana zuwa ina ta ƙara bincike,
ina ka shiga haka?"
Abbas yace "ka bari in zauna se in maka bayani sarkin ƙorafi"
"to zauna maza ka koramin bayani, wani labari kake tafe dashi?"
Abbas Ya samu guri ya zauna ya ajiye jakarsa ya tattara hankalinsa kan Yusuf sannan
yace
" Yusuf kaga hotunan yarinyar dana turo maka dasu ta email ɗinka?"
"Eh nagani, su nake ta nazari ban san dalilin da yasa ka turo su ba"
Abbas ya gyara zama yace "hotunan 'yar gidan Alhaji Nasir Daula ce, kusan aikin mu
gaba ɗaya akan ta yake, sati biyu kenan ina zuwa ina gidan su a matsayin me saida
mangwaro da yankan farce, na samu karɓuwa a gurin megadin gidan su, hakan yasa idan
naje se in zauna muyi ta hira da megadin su sannaan in tafi"
Yusuf ya gyara zama yace "to aini banga Alƙar binkicen mu da ita ba"
"Injiwa ai ta hanyar ta zamu samu duk abunda muke so, ita kaɗaice 'yar Alhaji
Nasiru, kuma itace target ɗin maƙiyan sa, aikin mu ba' a akan iya bincike bane
hadda bata Kariya"
Yusuf yace"Abbas sanin kanka ne binciken nan na sirri ne, shi kansa Alhaji Nasir be
san ana yin shi ba ta yaya zamu bawa 'yarsa kariya"
Abbas yace "Yawwa ɗan gari bazata taɓa sanin Aikin da muke ba, yadda mahaifinta be
sani ba itama baza ta sani ba, a hirar da muke dame gadin su yau watan ta uku da
dawo wa daga America a can take Rayuwar ta, maman ta ta rasu a hannun step mum ɗin
ta take, a tsawon lokacin nan mahaifinta ya sangar tata da kuɗi a taƙaice dai
muguwar taɓararriya ce me wata irin AƘIDA ta kafiya da taurin kai ga mugun
tsatstauran ra'ayi kamar baturiya, yarinya ce da bata da yadda tafi bawa mage da
kare mahimmanci fiye da mutanen dake kusa da ita, bata san zafin talauci ba balle
tayi wa wani talaka uzuri ko ɗaga ƙafa hasali ma gani take kaman talakawa bayin
sune masu kuɗi bata ɗaga ƙafa ko sassauta wa na ƙasan ta san.....
"kaga dakata wannan dogon labari haka, kamin bayani a taƙaice" Yusuf ya katse shi
Abbas yace "Dadina da kai ƙosawa, hotunan dana turo maka hotunan tane"
Yusuf yace "to me zanyi dasu?"
Abbas yace "Yawwa anzo gurin, da dawowar ta a wata ukun nan direbobi biyar aka
sallama saboda baza su iya jure halin ta ba, tana da gadara da wulaƙanci, a gabana
tayi wa direban ta korara wulakanci jiya, Yanzu haka megadin ya bani labarin
mahaifinta yasa shi ya samo mata wani direban daze dinga kaita unguwa, yake gayamin
ya gaji da samo mutane tana wulaƙanta su, akwai Albashi me kyau amma halin ta da
AƘIDAR TA kesa mutum ya gudu da kansa, dan haka nace ni ya barni zan samo mata
direba, kuma kai nake so ka zama direban nata!!"
Wani mugun kallo Yusuf yayi wa Abbas "Ashe baka da hankali, kaime ya hana kaje ka
zama direban nata?, ni zanje in dinga tuƙa ƙaramar yarinya tana wulaƙanta ni akan
me? Bazan yi ba gaskiya, ai kaine gaba dani a gurin Aikin kai kaje mana"
Cikin sigar rarrashi Abbas yace
"Calm down brother, nasan zaka iyane kai ƙarshe ne gurin haƙuri, kaga ni bani da
haƙuri zan iya lakaɗa mata duka idan tayi min ba daɗi ƙarshe in ƙare a prison in
shiga uku, kaikuma kowa ya san ka akan haƙuri da hikima, dan haka zaka iya, ɗazu
mukayi magana da Yallaɓai na tabattar masa zamu iya aikin nan, ita kanta yarinyar a
cikin gagarumin hatsari take, akwai bukatar a bata kariya da kulawa "
Ɗan tsaki Yusuf yayi yace" gaskiya ni bana son wulakanci ne, yarinya ƙarama ta
wulaƙanta ni dan ni talaka ne, gaskiya ni ka gama dani daka haɗani da wannan aikin,
daka barni da kayan computers ɗina da damuwar da nake ciki da se yafi min"
Abbas ya kuma gyara zama yace "cigaban mu ne idan mukayi nasara dan Allah ka daure,
Sannan Yusuf lokaci yayi da zaka cire damuwa ka fuskanci Rayuwa ka manta da
ƙalubale ka gina Rayuwar ka"
Cikin takaici Yusuf yace"Abbas kenan kana yiwa matsala ta kallon ƙaramar matsala,
amma Allah shi ka ɗai yasan zugi da Raɗaɗin da nake ji a raina idan na tuna ni wane
ne, wace Rayuwa zan gina bayan bani da dirakun da zasu riƙe min ginin Rayuwar tawa?
Abunda ya faru dani yasa naji komai yafi ta daga raina, yanzu na barwa Allah
al'amura na, in riƙe mahallici na, in rungumi ummana da Aikina nasan bani da
kamarsu"
Abbas ya dafa kafaɗar Yusuf yace "Yusuf nasara bata samuwa ba tare da an jarabci
ɗan adam ba, kayi haƙuri da taka ƙaddarar, Allah yana sane da kai"
Yusuf yace "Hakane Allah yabani ikon cin jarrabawa"
Abbas ya amsa da Ameen, sannan ya ɗora da cewa "Aiki na gaba se bayan ka zama
direban ta sannan zan sanar da kai shiri na gaba, zan gaya maka aikin da'a ke so
kayi"
Yusuf yace "to Allah ya bani iko ya tabattar da alkhairi ya bamu nasara"
"Ameen ya Allah, ɗazu fa mutuniyar ka tazo office ɗina tana ta kwarkwasa, take
tambaya ta kana ina?"
Yusuf yace "wa kenan?"
"kafini sani ai, wacece in ba Sakina ba"
Tsaki Yusuf yayi yace "dan Allah Abbas ka dena sa kamin wannan yarinyar cikin
lamurana, ni tun abunda ya faru dani duk wata harka da mata gudun ta nake yi,
wannan aikin ma da kuka bani kaida yallaɓai dan ba yadda zanyi ne harka ce ta aiki,
balle wata Sakina, ni ina tsoron mata nafi ƙaunar tsira da mutunci na da kuma
tsayawa matsayin da Allah ya ajiye ni, nayi darasi akan abunda ya faru dani"
Abbas yace "hakane kana da gaskiya Yusuf, Amma ka sani idan har mukayi nasara a
Aikin nan cigabanka ne, sekafi kowa benefitting gaba kaɗan in aikin ya kankama zan
ƙara sanar da kai wasu abubuwan" Abbas ya ci gaba da kwantarwa da yusuf hankali
tare da lallaɓa shi har ya ƙara gamsuwa ya Amince Amince akan zasu je gidan Alhaji
Nasiru Daula da weekends domin a tantance shi in ze iya zama direban Wannan yarinya
me muguwar AƘIDA sannan a gabatar da Yusuf a matsayin Sabon direban wannan 'yar
Hamshaƙin Attajiri Me murɗaɗiyar AƘIDA!!!.
Tun bayan da Abbas ya tafi, Yusuf yake ta tunani akan wannan gagarumin Aiki, yana
ƙara duba kyawawan hotunan wannan yarinyar da ko sunan ta be sani ba, she has an
innocent face a hoto, gata very young and beautiful amma ya akayi take da halaye
marasa kyau haka? Idan har ya kasance da gaske tana da duk wannan halaye da'aka
faɗa masa anya ze iya aikin kuwa? Amma meyasa Abbas be warware masa yadda aikin
yake ba gaba ɗaya yace se ya fara yi wa yarinyar aiki ze gaya masa? "Allah yasa ba
cikin wata cakwakiyar zasu jefa ni ba" yai maganar a fili tare da miƙewa ya tattare
kayan da ya baza a kan Katifar sa ya fito daga ɗakin nasa. Kasancewar Yamma ce
bashi da gurin zuwa da yake shi bame yawan shiga sabgar mutane bane, ya shiga ɗakin
Umman sa ya ɗakko kayan wankin ta ya wanke tsaf, ya share ko ina, ya ɗora girki se
kace mace, cikin nutsuwa yake Al'amuran sa ya kammala dafa shinkafa da miya ya zuba
a flask, lokacin ana ta kiraye kirayen sallar magariba yayi Alwala ya fice
Masallaci.
Ayshercool 07063065680
_*AƘIDA TA*_
*PART1* _Page 2_
*written and edited by*
_*AISHA HUMAIRA (Daddy's girl)*_
The experience writer of *ABDUL JALAL*
Bismillahir rahmanirrahim, da sunan Allah me Rahama me jin ƙai, Wannan littafi
ƙirƙirarren labari ne banyi shi dan cin zarafi ko cin fuska ga wani ko wata ko wata
ƙabila ba, idan har wani ko wata yaga wani abu daya yi kaman ceceniya da rayuwar sa
ko ƙabilar sa Amin Afuwa banyi dan cin zarafin wani ko wata ba. Wannan littafin
mallaka tane, ban yadda a juyamin labari ta kowane fanni ba ba tare da izinina ba.
What's App : 07063065680 Watpad : Ayshercool7724 Gmail : Www.ayshertadam@gmail.com
************************************
Wata Babbar Mace ce Zaune a cikin wani katafaren falo me girma sosai, cike yake da
kayan more Rayuwa, Aƙalla zata kai shakaru hamsin, Amma kaman 'yar shekara talatin
da biyar saboda hutu idonta sanye da glashi ta nutsu sosai tana danna Computer tana
shan tea.
Wata matsashiya ce ta shigo falon a ƙalla za ta kai shekaru Ashirin da bakwai, tazo
ta zauna a kusa da Matar. Ba tare da Matar ta ɗago ba tace "Ya a kayi ne? Nasan
akwai damuwa tunda na ganki yanzu meya faru?" ta ƙarasa maganar tana kallon
matashiyar.
Ta ɗan yatsuna fuska tace " Mummy kin san wani abu?"
"A'a sekin faɗa" matar ta bata Amsa
Cikin shagwaba tace "Mummy ki duba girman gidan nan da cikar sa, kalli dukiyar dake
cikin gidan nan, Amma mota ɗaya tak na mallaka, ko ɗan direba ma ba'a sama min ba,
Amma kalli 'yar masu gida motocin ta nawa? Direbobi nawa ta wulaƙanta ta sallama a
dawowar nan tata? Har motocin me gidan nan take hawa in ta ga dama gaskiya ana nuna
mana wariyar launin fata, banda cin fuska da wulakanci da muke fuskanta seka ce
wasu Bayi"
Matar ta cire glashin fuskarta tace
"Ramlah me kike so inyi? Alhaji Baya jin magana ko ganin girman kowa sena 'yar sa,
abunda take so shi yake yi, Sannan duk abubuwan nan da suke faruwa na ɗan lokaci
ne, Amma me kike so ayi? "
"Mum Mota nake so a canzamin sannan nima a ɗaukar min direba, bama mota ba motoci
nima in dinga kece raini yadda yakamata, kalli daular da muke ciki, Amma a ce se
abunda yarinya ƙarama take so akeyi, Mummy ina son inyi birthday ina buƙatar kuɗaɗe
masu yawa fa wanda zan burge ƙawaye na dasu, Sannan naji labarin Akwai filayen da
gwamnati za ta yi gwanjonsu a GRA ya kamata ace kin mallaka"
"Hmm Ramlah kenan samun wannan abubuwane masu Sauƙin samu a hannun me gidan nan,
Amma kin san seda izini kokuma ince yaddar 'yarsa ko?"
Ramlah tace "Amma Mummy ba yadda za' ayi in samu kuɗin a hannun ki? Kina matarsa
amma ace se Abunda 'yarsa take so haba dan Allah, yakamata ace Akwai wata Dama da
zaki dinga mallakar kuɗaɗe bayan wanda yake baki"
"babu wannan damar, dan duk kuɗin dazan fitar seda sanin Lawyern sa, dan haka ba
yadda zanyi, Karki manta muna da kyakkyawan shiri a ƙasa shiyasa sam bana damuwa,
ni yanzu so nake in lallaɓa shi Amal me ta tafi turkey ta ci gaba da karatu a can"
Ramlah tace"shikenan Amma yakamata kiyi wani abu akai kar wannan damar ta wuce mu,
Amma kafin wannan ya batun canza motarfa?"
Mummy tace "Wannan kuma sekin yi tsani da 'yar masu gida, tana magana ko mota goma
kike so kamar kin samu, batun kuɗi kuma zan tura miki kuɗi Account ɗinki base
munjira ba, Amma ki same ta in ta yadda za tayi masa magana a baki wata motar"
Ramlah ta yamutsa fuska tace"A' a Mummy ke zaki mata magana, kin san ba shiga
sabgarta nake ba, bana son wulaƙanci da rainin hankali, kin san bama shiri da ita"
Mummy tace "ke kina tunanin idan nayi mata magana zata saurare nine? Yau kwana
biyar rabon da in sata a idona fa yarinyar nan barta kawai"
Ramlah tace "bari in kira miki ita dan Allah ki mata magana ko zata sa baki, ni kin
san bama jituwa da ita"
Mummy ta ɗan jinjina kai tace "shikenan Allah yabada sa'a"
Tana zaune akan stool a gaban dressing mirror ɗin ta wanda yake shaƙe da kayan
shafe shafe na mata, towel ne a jikin ta tana ta ƙoƙarin tsane gashin kanta. Ƙofar
ɗakin aka turo aka shigo, wata matashiyar budurwar ce ta shigo ɗakin ba tare da
tayi sallama ba ko wata doguwar maganaba tace
"Mum nasan ganin ki a cikin gida, zakuyi magana"
Wadda akewa maganar se kace da gini ake, ko gezau ba tayi ba ta ci gaba da abunda
take yi, bata kalli me mata maganar ba ta cigaba da abunda take yi . Cikin ƙosawa
da fushi matashiyar wadda aƙalla ta girmi wadda take wa maganar nesa ba kusa ba
tace
"wai ba kyaji ina miki magana ne? Kin min banza kaman baki san na shigo ba?"
Cikin isa yarinyar ta Ajiye Ƙaramin Towel ɗin hannun ta, ta miƙe ta nufi wardrobe
ɗin ta, Subhanallah koda ta buɗe wardrobe ɗin sutura ce a ciki kaman shara, kamar
inji ne ya shirya kayan ba hannu ba, kai in akace suturar mutum ɗaya ce seka riƙe
baki tareda tunanin ina mamallakin suturar ze kai ta?
Ta saka hannu ta janyo wata 'yar riga ja mara hannu, tana ƙoƙarin sakawa ba tare da
ta waigo ba cikin ƙasaita tace
"Ramla ki koma ki gayawa wadda ta aiko ki banyi budget da lokacin da zan bata ba a
yanzu, ko menene idan ta damu tazo da kanta ta sameni in gani ko zan iya saurarta,
idan kuma bame mahimmanci bane zata iya haƙura har se lokacin da Allah yasa na
shigo cikin gidan, you can go out i need privacy"
Cikin ɓacin rai Ramla tace "Waike wace irin mara ɗa'a ce haka? Mahaifiyar tawa ce
zata zo ta same ki? Kika san me yasa ta kira ki? Se kace sa'ar ki?"
"koma me zesa ta kira ni nasan baze wuce biyan wata buƙata tata ba kokuma ta 'ya'
yan ta, ni kuma da ku da ita bani da lokacin ku a yanzu, ɗan fitar min daga ɗaki,
zan kaɗaice inyi tunani"
Ramla tace "Amma baki da kirki, a gabana kike faɗan maganganu akan uwata, ke har
Abada girma da shekarun mutum baya sa ki bashi girma, Ko ance miki rayuwar Turai
hauka ce? Rayuwar turai fa ta saɓa da Al'adunmu, Ko kuma akanki aka fara Arziki?"
"Enough Ramlah" Yarinyar ta katse ta ta nuna Ramlah da yatsa ta ɗora da cewa
"Amma kamar kin san ba'amin shouting ko? You know the consequences of doing that.
Mahaifiyar ku, ku ta haifa, ni kuma Babana take Aure bata haifeni ba, what's the
meaning of respect according to you ne Ramla? Your mother is just a human being
like everyone, she don't deserve any special respect, i will treat her the same way
i treat every human being, and mark you This is my father's house, if you are
tired of what am doing, go back to your father's house, nan gidan mahaifina ne ina
da right inyi abunda nake so, and no one should stop me from doing what I want, if
you are tired of what am doing park your things and go, madam get out from my room,
kaina ya fara ciwo ki fitar min daga ɗaki "
Cikin faɗa take maganar, hannun ta ɗaya riƙe da kanta, tana nunawa Ramlah ƙofar
fita
Ramla ta ƙulu matuka ta fice a fusace tare da buga ƙofar ɗakin da ƙarfi.
Falo ta koma inda tabar mahaifiyar ta, kallo ɗaya Mummy tayi mata ta ɗanyi murmushi
tace "yana ganki a fusace?"
"Mummy wallahi yarinyar nan bata da mutunci, kinga rashin mutuncin da tamin kuwa,
wallahi badan ina gudun abunda ze biyo baya ba sena shaƙeta kowa ya huta"
"hmm Ramla kenan, baki ga komai akan halin ta ba, ni da nake tare da ita ni nake
ƙunsar takaici da baƙin ciki, Amma ina jiran lokaci ne wanda... Bata ƙarasa ba tai
shiru tareda yin murmushi ta dafa kafaɗar Ramla tace "karki damu daughter, saura
ƙiris komai ya canza, na sama ya koma ƙasa, na tudu ya koma ruwa, a wannan lokaci
da dariya zata gagari kare, hmm kiyi hakuri ni da kaina zan canza miki mota, in
ɗaukar miki driver kinji?"Shiru Ramla tayi ba tace komai ba se faman huci da take
yi. kaman an mintsine ta tace
"wallahi na tsani yarinyar nan Mummy, bana ƙaunar ganin ta ji yadda aka maida ke da
mu kaman wasu bayi ko 'yan Alfarma a gidan nan, ai ko Albarkacin kina Auren
mahaifinta ya kamata ace muna da matsayi na musamman"
Mummy tace"nifa nace kiyi hakuri ko? Komai ya kusa zama tarihi"
********
Yusuf Yana zaune har Bayan sallar isha'i yana kallon labarai, yaji anyi Sallama
amsa sallamar yayi tareda ɗan ɓata rai. Me sallamar ta shigo falon ta ajiye jakarta
da mayafi ta ɗan kalli inda Yusuf yake tace "fushi kuma ake dani, ko a kalli inda
nake? Ai gani na dawo"
Yusuf yace "haba Umma tun azahar kika fita se yanzu bayan isha'i duk kaɗaici ya
dameni"
Umma tace "kai tafi can, sekace wanda nake shayarwa ba damar in ɗan fita, ka dinga
damuwa kenan"
Cikin shagwaba yace "wana keda shi inba Ummana ba? Dole in shiga damuwa duk lokacin
da kikayi nisa dani ummana, daga Allah seke se kuma Aikina ku kenan nake da su,
niba Abokai ba ko wasu mutane na musamman ke ɗin ce dai, Allah ya jiƙan Abba na,
tun abunda ya faru Umma ke kaɗai nake da yaƙinin ƙaunar ki a gare ni baza ta gushe
ba, shiyasa bana son kiyi nisa dani"
Tausayin Yusuf ne ya mamaye ta, har zuciyar ta ta karaya hawaye na ƙoƙarin fita
daga idon ta, da sauri ta fice ta bar ɗakin da nufin yin Alwala.
Bayan Umman Yusuf ta idar da sallar isha'i suka ci Abincin dare tare suna hira,
Yusuf yana ta so ya sanar da Umman sa batun Aikin da'aka bashi a Office amma ya
kasa, dan yasan idan har ya gaya mata ranta zata ji babu daɗi, ace ɗanta Yazama
direban yarinya, Yarinyar ma mara tarbiyya wadda bata san darajar ɗan Adam ba, dan
haka ya bar abun a ransa be gaya mata ba.
Haka ya kwana yana tunanin wace karɓa ze samu a gurin yarinyar nan? Ya aikin ze
kasance? Haka yaita tunani har bacci ya ɗauke shi.
Washegari ma Yusuf yayi ƙoƙarin yiwa Umman sa zanncen amma ya kasa, haka yai
breakfast ya tafi gurin Aiki.
A office ma kasa wani aikin kirki yayi, wayar sa ya ɗakko yana kuma duba hotunan
wannan tsaleliyar yarinyar, ya kuma tuna irin halayen ta da Abbas ya bashi labari.
Ɗan tsaki yayi ya ajiye wayar ya jingina da kujera ya dafe kansa yana tunani.
Sallamar Abbas ce tasa ya ɗago kansa, Abbas yace "Yusuf dama ka shigo yau baka
nemeni ba?"
"na shigo tun ɗazu ina aiki ne shiyasa ban neme ka ba"
"OK tashi muje, Yallaɓai Suleiman na son ganin mu yanzu"
Yusuf ya miƙe yabi Abbas suka fice, suna zuwa suka gaisa cikin girmamawa, yai musu
umarni suka zauna.
Yallaɓai Sulaiman yace "Yusuf nace kuzo tare da Abbas ne dan tabattar da cewar
aikin da muka ɗora muku zaku iya, mussman kai Yusuf nasan kana da kula da aiki kuma
kana da haƙuri matuƙa"
Cikin girmamawa Yusuf yace "Insha Allah Yallaɓai baza'a samu matsala ba"
"Good kayi taka tsan2 kabi a hankali, karka kuskura wani yasan bincike ne ya kaika
gidan, kasan aikin ka base na gaya maka ba, samun matsala a wannan aikin gagarumin
hatsari ne da kuma Asara ina fatan kun san hakan"
Yusuf ya risinar da kai yace "Insha Allah ba zamu baka kunya ba sir"
"kai kuma Abbas ku kula yadda ya kamata"
Abbas yace "Insha Allah sir za muyi iya ƙoƙarin mu"
Haka suka ci gaba da tattauna wa akan harkar aiki, sannan Yallabai Suleiman ya
sallame su.
Bayan fitowar su Abbas yaita bawa Yusuf ƙwarin gwiwa tareda bashi shawarwari, suka
tsara yadda tafiyar tasu zata kasance ranar Asabar zuwa gidan Alhaji Nasir Daula.
Tunda gari ya waye Asabar gaban Yusuf yake faɗuwa, ya rasa dalilin da yasa tun
da'aka gaya masa Aikin daze yi yaji gaban sa na faɗuwa a duk sa'ar daya tuna, har
seda Umman sa ta fuskanci ya rage walwala, ta tambayeshi yace mata "bakomai" haka
Yusuf yaci gaba da Adduo'i.
Yana nan zaune a ɗakin sa ya rasa abunda yake masa daɗi, misalin ƙarfe sha ɗaya na
safe Abbas yazo, ya tsaya a tsakar gida suka gaisa da Umman Yusuf sannan ya shiga
ɗakin ya same shi. Abbas ya kalleshi daga sama har ƙasa yace
"gaskiya Yusuf wannan kayan naka ba suyi kama da wanda zeyi aikin direba ba,
gaskiya ka canza kaya, ni baka ga kayan da na saka ba" Se lokacin Yusuf ya lura da
koɗaɗɗen Yadin dake jikin Abbas, Yusuf ya ɗanyi murmushi yace "Taɓɗijan, wannan
wane irin kaya ne?, ni ban san wani kaya zan saka ba"
Abbas ya buɗe wardrobe ɗin Yusuf, duk kayan Yusuf masu kyaune, da ƙyar ya ɗakko
masa wasu ƙananan kaya ya bashi ya saka suma dai basu ji jiki ba, Yusuf ya karɓa ya
saka, yace "Allah yasa kar Umma tayi min magana akan kayan nan"
har zasu fita Abbas yace "ɗan tsaya idan muka je gidan Sunana Sani me mangwaro ba
Abbas ba "
Yusuf ya jinjina masa kai sannan suka fito, Yusuf ya kalli Ummansa dake kwashe
kayan wanke2 yace "Umma zamu fita" Umma tace "to Yusuf, Abbas ka gaida gida sekun
dawo"
Har zasu fita Umma ta kira yusuf tace "Yusuf zo nan" Dawowa yayi tace "Wannan wace
irin shiga kukayi, kalli kayan jikinka be kamata ace ka fita da su ba, Allah ya
rufa maka Asiri amma kasa wannan kayan kana yawo a gari"
"Umma shima hakan cikin harkar Aiki ne, idan na dawo zan miki bayani Insha Allah"
Umma tace "Amma harkar aiki shine zaka fita da wannan suturar kamar mara galihu"
"haba Umma wallahi kayan nan da kyansu, kiyi min Addu'a sena dawo"
Ɗan girgiza kai tayi yayin da Yusuf yayi waje da sauri.
Napep suka tara suka hau zuwa gidan Alhaji Nasir, yayin da gaban Yusuf keta faɗuwa.
Tun daga bakin layin shiga rukunin gidan jam'ian tsaro ne ke kaiwa suna komo wa,
seda aka musu tambayoyi kafin su wuce da yake sun gane Abbas yana zuwa, aka barsu
suka wuce.
Koda suka je gidan Abbas ne ya sallami me Napep ɗin, tun daga waje Yusuf ya fara
ƙarewa gidan kallo tirƙash lallai mamallakin gidan yaci ai masa inkiya da Daula.
Suka ƙarasa ƙofara katafaren gate ɗin suka tsaya, Abbas ya ɗakko wayarsa ya kira
Isa me gadi, yace masa suna waje. Befi mintuna uku ba aka buɗe ƙaramar ƙofar dake
jikin gate ɗin ya leƙo yana ganin su Abbas ya washe baki yace
"bismillah ku shigo Ashe kaine" Suka shiga suka tsaya suka gaisa da Isa. Isa yace
"Sani wannan ne ɗan uwan naka daze aikin?"
Abbas yace "Eh shine" Isa yace "Ya sunan shi?"
"Sunana Yusuf" Yusuf ya bashi amsa
Isa yace "masha Allah to Allah yaba ka iko, dan seka yi haƙuri aikin akwai samu
amma babu sauƙi, bari inje in sanar wa da Alhaji zuwanku"
Abbas yace "shikenan babu laifi"
Bayan tafiyar Isa, Yusuf ya kalli harabar gidan, wasu irin motoci ne masu rai da
lafiya a tsaye a gefe ɗaya, yayin da ainihin ƙofar shiga katafaren gidan se kayi
wani gajeren tattaki daga gate ɗin kafin ka kai ga ƙofar. Yusuf ya numfasa yace
"wai ni Abbas ya aka yi rukunin gidajen nan jam'ian tsaro ke gadi, Amma kuma nan
gidan naga wannan ma shiriricin ke gadi"
Abbas yace "Sani dai ba Abbas ba"
Yusuf yace "Am sorry, Sani"
Abbas yace "duk yana cikin binciken da za kayi, ka kula kayi taka tsan2, banda
sakin jiki da kowa dama nasan kai ba me son hayaniya bane"
Isa ya dawo yace "bismillah ku taho mu shiga, Alhaji yace a shiga daku"
Tunda suka kama hanyar shiga cikin gidan Yusuf yake ƙarewa ko ina kallo, an
danƙarawa gidan dukiya kaman ba'a san ciwon ta ba.
Wasu irin faluka suka dinga ratsawa, kowanne da kalar sa da irin tsaruwar da yayi,
shikan sa Abbas be san haka cikin gidan yake ba.
Sunyi doguwar tafiya kafin su iso wata ƙatuwar ƙofar glashi,Isa yasa hannu ya murɗa
suka shiga da sallama.
Iya girman falon nan ya ishi wani talakan gina wadataccen gidan da ze zauna, Yusuf
ya fara tambayar kansa shi kuwa wannan wane irin sana'a yake yi da har ya gina
wannan gidan kamar baze mutu ba?
Babban mutum ne a zaune akan wata luntsumemiyar kujera yana karanta jarida gefen sa
da wata mata, se 'yan mata biyu zaune akan kujerar dake facing ɗin su.
Aka amsa musu Sallamar, cikin girmamawa suka gaisa da me gidan tare da iyalan sa,
yanayin gaisawar tasu ze nuna maka mutum ne me fara' a, dan kuwa fuskarsa ɗauke da
murmushi ya amsa musu.
Isa yace "Yallaɓai sabon driver ne da kace a samo, shine suka zo yanzu"
Ya ajiye Jaridar hannun sa yace "Masha Allah wanne ne daga cikin su?"
Cikin girmamawa Yusuf yace "Nine"
Alhaji Nasir ya ɗan ƙura masa ido yace "masha Allah, ya sunan ka?"
"Suna na Yusuf"
Alhaji Nasir ya jinjina kai yace "Hajiya Halima kinji me sunan Yaya na ko?"
"Aikam dai me sunan shi" ta amsa
Alhaji Nasir yace "Allah sarki, Allah yasa me irin halin sa ne, ni duk Yusuf ɗin
dana sani mutanen kirki ne, ina fatan kaima haka?"
Abbas yace "Alhaji ba ganin ido ba Shima mutumin kirki ne sosai"
Alhaji yace "ai dama na sani, ban taɓa ganin Yusuf mutumin kawai ba"
Ya kalli 'yan matan nan dake zaune yace "Amal jeki part ɗin gimbiya ta, ki gani
idan idon ta biyu bata komai ki gaya mata Daddy na son ganin ta, idan kuma da
abunda take yi ki ƙyaleta"
Wadda aka kira Amal ta miƙe tare da cewa "to Daddy" .
Babban abunda ya bawa Yusuf mamaki be wuce tun lokacin da' aka ce shine ze zama
direban, matar da 'yan matan nan suke binsa da kallo ba, mussman wadda aka kira
Amal yadda ta tsare shi da idanuwa.
Seda akayi Minti goma sha biyu da tafiyar Amal, sannan ta dawo tace "Daddy tace
tana zuwa"
Alhaji Nasir yace "to babu laifi"
Wasa2 seda sukayi minti Arba'in ba suga Alamar wadda aka kira ɗin zata fito ba,
iyalan suka ci gaba da hirar su aka bar su Yusuf shiru kamar mayu.
Gaba ɗaya Yusuf ya gaji da zaman, ga sanyin A. C da kallon ƙurillar da'ake masa duk
yabi ya takure.
Alhaji Nasir ya kuma cewa "Ramla bawa baƙin nan Abinci kafin ta zo"
Ba tare da Ramla tace komai ba ta miƙe ta fice, ruwa da fruits ta kawo ta ajiye
musu.
Abbas da Isa suka dinga ɗauka suna ci suna kallon tv, shikam Yusuf ya kasa cin
komai, gaba ɗaya a takure yake, gashi ko ɗaga kai baya son yi saboda kallon da'ake
masa.
Kaman ance ya ɗaga kai idonsa yayi tozali da wata irin kyakywar halitta, babu
shakka itace a jikin hoton da Abbas ya tura masa, Amma a zahiri tafi haka kyau,
gabansa ne ya dinga faɗuwa ƙirjinsa yana bugawa da ƙarfi, yarinya ce sharaf amma se
kwarjini fara ce ƙal tana sanye da skin tied iya gwiwarta, se wata over size shirt
data saka har wajen gwiwarta, kanta babu ɗan kwali gashin ta a hargitse babu
ribbon, ta sake shi a kafaɗun ta.
Fuskarta a haɗe babu annuri, ta ƙaraso cikin falon ta zauna kusa da mahaifin ta.
Tana zama Hajiya Halima ta miƙe ta canza wata kujerar
Alhaji Nasir yace "Lovely daughter ina fatan ba'a takura miki ba?"
Girgiza masa kai tayi alamar A'a
Alhaji Nasir yace "Sabon driver ne gashi nan, yazo ki gani in yayi miki"
Kamar baza tace komai ba ta ɗago ta kalle su ɗaya bayan ɗaya ta tsaida idon ta akan
Yusuf ta ɗan ɗau lokaci tana kallon sa kaman tana ƙoƙarin gano wani abu. Ɗauke kai
tayi ta haɗe rai cikin isa tace
"Ramla kawo min madara da cup, sannan kije falona ki kawomin wata folder akan
kujera"
Waigawa Yusuf yayi ya Kalli wadda aka kira Ramla, ta girmi yarinyar da har yanzu
be san sunan ta banesa ba kusa ba, dan shi har yanzu beji wanda ya faɗi sunan ta
ba, ramla ta miƙe ta tafi cika umarnin ta.
Yarinyar da dudu bata fi shekaru sha takwas zuwa sha tara ba, a idon ta da yadda
take magana zaka gano tsabar izza, da isa, Ta kalli Abbas tace "kai kaman na sanka
ko?"
Abbas yace "eh ni abokin Bala ne, ina zuwa gurin sa"
"good, kai Bala meye aikin ka?"
Cikin Rawar jiki yace "gadi ranki ya daɗe"
"to ka tashi da kai da shi ku fita ka koma kan aikin ka" Ba musu bala ya miƙe,
Abbas ma ya miƙe, kafin su bar falon ta kalli Hajiya Halima tace
"Madam i need privacy you can leave"
Ɗan taɓe baki Hajiya Halima tayi ta miƙe ta nufi wata ƙofar daban.
Ta kalli inda Amal take ta mata wani kallo, tun kafin ta furta komai Amal ita ma ta
miƙe ta nufi barin falon.
Gaba ɗaya mamaki ya cika Yusuf, yadda take wannan izzar take wa manya magana babu
respect kuma a gaban mahaifin ta amma bece komai ba, ya ma maida hankali akan
jaridar sa kaman be san me take yi ba.
Ramlah ta dawo ɗakin ɗauke da cup da madara tazo ta ajiye, sannan ta miƙa mata
folder, taje ta nemi guri akan kujerar da ta tashi zata zauna, Amma suka jiyo
zazzaƙara muryar ta tace
"wait don't sit, get out from here, bana buƙatar wani a falon zan gana da shi"
Wata irin Ajiyar zuciya Ramlah tayi ta ɗan jinjina kai ba tare da ta waigo ba ta
miƙe ta fita ta bar falon itama.
Madarar ta ɗauka ta zuba a cup tana sha, tana kaɗa ƙafa kaman tama manta da Yusuf
a gurin.
Alhaji Nasir ya kalle ta yace "gimbiyar Daddy bari inje in ɗan watsa ruwa zan fita
anjima, yadda kuka yi dashi kya gayamin in na dawo, in yayi miki.
Ɗan ɗaga girar ta ɗaya tayi ta lumshe ido ba tare da tace komai ba.
Bayan tafiyar mahaifinta haka suka ci gaba da zaman kurame ita da Yusuf
Can ba zato ba tsammani yaji tace
"what's the level of your Education?"
Yusuf ya ɗanyi jim sannan yace "secondary school" yai maganar ƙirjinsa na bugawa
Shiru ta kuma yi tana kallon tv seda aka kuma jan wani lokacin sannan ta kuma cewa
"Meye sana'arka?" Gumi ne ya fara tsatstsafo masa dukda sanyin AC da yake ɗakin,
Yusuf baya son kuma yin ƙarya, Amma yace
"Eh ina ɗan zuwa kasuwa ne ina yaron shago"
Cikin Tsara magana da take daki daki, da muryarta me sanyi tace
"Anyway naga kaman za kayi hankali, zan iya yadda ka zama direba na amma ina da
sharuɗai" Ta ɗanyi shiru kaman ba zata kuma magana ba, sannan ta ɗora
"bana son ƙarya, duk ranar da na gano kayi min ƙarya zaka fuskanci hukunci me
tsauri, bana son sa ido da shishigi a cikin lamurana, bana yafewa maƙaryaci ko
wanda yaci amana ta, babu ruwan ka da irin mutanen da nake hulɗa dasu, bana yadda
da mutum kowaye ni kaina wani lokacin bana yadda da kaina balle wani, dan haka duk
lokacin da kayi motsin da ban yadda da shi bama zan iya sawa a kulle ka, ban yadda
da saɓa lokaci ko Alƙawari ba, sannan lokacin dana ɗauke ka aiki mallaki na ne bana
ka ba, ibada kaɗai kake da 'yancin yi, bayan wannan baka da hurumin yin wani aiki
idan ba nawa ba, se dai idan ni na baka dama, in ka amince da sharuɗai na" ta ajiye
wata takadda
"kayi signing anan, salary 200k and your hard work determines your salary
promotions"
Shiruu Yusuf yayi yana tunani, gaba ɗaya ya rasa abun yiYusuf yace"ranki ya daɗe ko
zaki iya bani dama inje inyi shawara"
"I don't gives second chance, and I don't want too much waste of time" ta bashi
amsa tana maida hankalinta kan talabijin
Shiru Yusuf ya kuma yi ya ɗauki takardar yana jujjuya ta ba tare da ya karanta meye
a jiki ba, gumi se karyo masa yake ya ciro biro a Aljihun sa, hannun sa na rawa ze
sa hannu yaji tace
"that means you accept the terms and conditions i have mentioned?"
Jinjina kai yayi alamar yana ƙoƙarin ya saka hannu tace
"if you are here to spy don't sign this paper"
(idan kazo nan ne dan leƙen Asiri kar kasa hannu a takardar nan)
Ras! Gaban Yusuf ya faɗi, Anya babu wata a ƙasa, yarinyar nan bata san komai ba?
Cikin ƙwarewar Aikin sa ya dake yace
"ranki ya daɗe menene Spy kuma?"
Banza tayi masa ba tace komai ba.
Seda Yusuf yayi Addu'a a zuciyar sa sannaan yasa hannu akan takardar.
Ta sa hannu ta ɗauki takardar ta jujjuya ta sannan tace
"signing this paper is like signing on your death contract!!! Jeka sena neme ka"
Tana gama faɗin haka ta miƙe ta bar falon
Ras! Ras!! Ras!!! Gaban Yusuf ya faɗi A fili yace "My death Contract kuma?"!!!
Ayshercool07063065680
_*AƘIDA TA*_
*PART1* _Page 3_
*Story and written by*
_*AISHA HUMAIRA (Daddy's girl)*_
The experience writer of *ABDUL JALAL*
I dedicated this book to my Mum (Malama Nafisat Adam Muhammad) i love you mum
Special thanks to my Association Members Perfect writers Association
Maimaita death contract Yusuf ya dinga yi, ya rasa abunda ya kamata yayi, a hankali
ya miƙe ya biyo hanyar da Isa ya biyo da su ya fice.
Abbas yana tare da Isa yana jiran fitowar Yusuf, kallo ɗaya Abbas yayi masa yasan
akwai matsala, da ƙyar Yusuf yake ɗaga ƙafarsa, Isa da Abbas suka dinga tambayar
sa meyafaru? Amma yaƙi cewa uffan, Abbas yayi wa Isa Sallama ya ja Yusuf suka tafi,
be ƙara tambayar Yusuf ba har suka je gidan su Yusuf.
Da suka je gidan ma Yusuf yai mursisi yaƙi faɗa wa Abbas yadda suka yi, daga ƙarshe
dai Abbas ya ƙyale Yusuf ya ɗauka ire iren wulaƙanci ya fara fuskanta, dan haka
yaita bashi haƙuri yana kuma rarrashin sa kan ya daure kar ya karaya.
Sam hankalin Yusuf baya kan Abbas, gaba ɗaya ƙwaƙwalwar sa ta shiga lissafe lissafe
daban2, a karon farko da shigar sa Aiki wannan ne aiki me matuƙar wahala da
sarƙaƙiya a gare shi, yana buƙatar nutsuwa da taka tsantsan akan komai.
"Yusuf naga kaman hankalin ka baya kaina fa?" Yusuf yayi ajiyar zuciya yace "ta
yaya zaka samu hankali na, tace ba'a mata ƙarya bata yafe wa wanda yayi mata ƙarya,
Nikuma akan ƙaryar ma naje nake aikin, yanzu idan ta gane gaskiya fa?"
Abbas yace "karka damu kayi abunda ya kamata kawai tana ƙoƙarin yi maka ba razana
ne, idan kabi a hankali ba zata gane komai ba"
"to Allah yasa?"
Abbas yace "Ameen"
Bayan tafiyar Abbas fa tunani ya auri Yusuf, kasa jurewa yayi seda ya gayawa Umman
sa aikin daze jeyi a matsayin direba gidan Alhaji Nasir Daula amma ya ɓoye mata
gaskiyar halin yarinyar da sharuɗai da ta saka masa.
"Yusuf wace irin lalacewa ce kana aikin ka gwanin sha'awa zaka koma wani direba?"
"Umma ba lalacewa bace, harkar aiki ce ta kawo haka"
"hakane amma ni bana son sabga da masu kuɗin nan yaran su ba tarbiyya suka cika ba,
bana so a wulaƙanta min ɗa a banza, gurin aikin naku babu wanda zasu saka se kai"
Yusuf yace "Umma Addu'arki da goyon bayanki nake buƙata, idan kika soki abun zaki
kashe mun gwiwa ne"
Umma ta numfasa tace "shikenan Allah ya tabattar da Alkhairi, Allah yabada sa'a, ka
kula da kanka"
"insha Allah umma na nagode sosai"
'yan kwankin nan Gaba ɗaya bacci ya ƙauracewa idaniyar ta, duk motsin da zata yi
surar Yusuf take gani, rashin walwalarta da yawan son kaɗai cewa ne yasa 'yar
uwatta lura da akwai abunda yake damun ta kasancewar ta me surutu da san hira.
Ramla ta dubi yadda' yar uwar tata tayi shiru tana jujjuya spoon a cikin cup ko sau
ɗaya bata kai abunda ke kofin bakin ta ba, bayan shafe kusan mintuna goma da zaman
da tayi da niyyar cin Abinci.
"Amal wai me yake damunki haka ne, na lura tun jiya kin zama wata iri"
Amal ta ajiye spoon ɗin hannun ta a ranta tace "Mhmm Yaya Ramla ina cikin damuwa
tabbas, kuma na shiga damuwa ne domin ƙoƙarin samo mafita akan gagarumin lamarin
dake barazanar jefani wani bigire da be kamata ba, Amma nasan bazaki taɓa bani
goyon baya ba" Amma a zahiri tace "karki damu bana jin daɗi ne kawai"
"Amma yakamata kije kiga likita"
Amal tace "ba abun damuwa bane, zan ware Insha Allah"
Tun Yusuf yana fama da tunani tareda sauraren kira daga uwaɗakkinsa har ya fidda
rai, ya fara mantawa ya shiga sabgogin sa.
Kusan sati uku kenan da zuwan Yusuf gidan daga nan Amal bata ƙara saka shi a idon
ta ba, wasa wasa abu ya ci gaba da damun zuciyar ta, gashi abu na ta faman damun
zuciyar ta.
Alhaji Nasir Daula ne zaune a wani ƙaton falo shida wani mutum wanda zeyi sa' ansa,
sukw hira tareda ƙyaƙyata dariya kai da gani kasan akwai kyakkyawan kusanci da
fahimtar juna a tsakanin su.
"Alhaji Nasir nikam daughter tunda ta dawo ƙasar nan bata zo mun gaisa ba, kota
manta dani ne?"
Alhaji Nasir yace "haba Bulama yaza'ayi daughter ta manta da kai, kawai dai kasan
halin ta ne Nason kaɗaici har yanzu a haka take, Amma insha Allah zan turo maka ita
har gida ku gaisa"
Alhaji Bulama yace "kana nufin har yanzu bata dena wannan ɗabi'ar ba, ba ta warke
ba kenan?"
"kai dai bari kawai, lamarin daughter yana damuna, ace kaf rayuwar ɗan adam be
yadda da kowa ba, ba za ta sake da kowa ba, to koni wataran ina ƙasar nan idan bata
ga dama ba se tace bata son inje inda take, narasa menene mafita "
Jinjina kai Alhaji bulama yayi yace" "wai shekarun ta nawa ne yanzun?"
"18 to 19, amma menene ma fitar?"
Alhaji Bulama yace "mafita ɗaya ce shine kayi mata Aure, idan har aka yi mata Aure
zata dena wannan halin nata"
Alhaji Nasir yace "Aure kuma? Dudu du guda nawa daughter take? Yarinya ce ƙarama
kuma waze iya jure halayen ta?"
Alhaji Bulama yayi murmushi yace "kai kake ganin yarintarta idan ka aurar da ita
daram zata zauna, samun wanda ze zauna da ita da halin ta abune me sauƙi, semu haɗa
ta Aure da Fahad yaron guri na da yake karatu a china, dama bata sanshi ba kaga se
a haɗa su, hakan ze ƙara zumunci dake tsakanin mu, kuma kaga tunda ita kaɗai Allah
ya baka seka samu 'yan jikoki"
"Masha Allah gaskiya naji daɗin wannan shawarar taka, amma kasan semun bi a sannu
idan nace zan tursa sata, za' a iya samun matsala"
"bakomai mu bi komai a sannu insha Allah babu wata matsala"
Suka cigaba da hirarrakin su.
Misalin ƙarfe goma na dare Yusuf yayi shirin sa tsaf ze kwan ta, wayar sa ta fara
ringing, Sunan Abbas ne akan screen ɗin wayar, ya ɗaga suka gaisa
Abbas yace "Yusuf ɗazu Isa megadi ya kirani, yace min yarinyar nan ta bada saƙo
tace zaka kaita unguwa gobe misalin ƙarfe goma na safe, ta jadadda goma na safen
nan dan haka ka kiyaye"
"Shikenan zan je Insha Allah"
Tunda Yusuf ya kwanta ya gagara cikakken bacci, da yaje sallar Asuba sam be koma
bacci ba, ya zauna ya ci gaba da lazumi, da sassafe ya tashi yayi wa mahaifiyarsa
aikace2, kaman yadda 'ya mace za tayi haka Yusuf ya share ko' ina yai wanke2 yai
girkin karin kumallo.
Koda Ummansa ta tashi tayi mamakin inda Yusuf yake gaggawar zuwa, bata son yawan
takura masa dan haka ta ƙyaleshi.
Ƙarfe tara dai2 na safe Yusuf ya isa gidan Alhaji Nasir.
Isa na ganin sa yace "kai sannu da ƙoƙari Allah yasa ka ɗore, idan ka ɗore da zuwa
akan lokaci saura kuma ƙalubale na gaba"
Yusuf yayi murmushi yace "Malam Isa kenan, Kowace sana'a tana da ƙalubale, sedai
fatan Allah ya bamu ikon aikata dai2"
Da yake Isa akwai surutu kaman an ƙona shi aka, haka ya dinga zubawa Yusuf surutu
kuma surutun nasa ba'aakan kowa bane se kan 'yar masu gida
Yusuf yace "wai ya sunan ta ne?, nifa har yanzu ko sunan ta ban sani ba"
Isa yace "Ai abune me wuya kaji sun kira sunan ta, ban san sunan ta na gaskiya ba,
amma sunan ma dai da' ake kiran ta dashi akwai wuya dan ban riƙe ba"
Yusuf yace "ikon Allah wahalar sunan ta kai ka kasa riƙewa"
"haba Malam Yusuf kaman baka san iyayinku na 'yan binni ba? Wasu sunayen ma karasa
sunan tumakine kona taurari"
Ba ƙaramin dariya Isa ya bawa Yusuf ba.
Suna ta ɗan taɓa taɗi, Isa yace "Aff gata can ta fito"
Yusuf ya ɗaga kai ya hango ta, ba ƙaramin kwarjini take da shi ba, taku take na
ƙasaita akan wani dogon takalmi, dogon wando ne a jikin ta dark blue da riga light
blue me dogon hannu, ta ɗaure kanta da ɗan kwali, amma gashin ta seda ya fito ta
baya, fuskarta sanye da wani ƙaton glashi, wayar tace kawai a hannun ta babu jaka
se key ɗin mota. Guri ta samu ta tsaya, yayin da Yusuf yai sauri ya ƙarasa inda
take tsaye, gaban sa na ta dukan uku2, yaje gabanta ya ɗan risina yace "barka da
safiya ranki ya daɗe"
Bata amsa ba, ta miƙa masa mukullin mota, yasa hannu biyu ya karɓa a hankali ta
furta masa Lambar motar da zata hau, kowace mota dake parking space tana da lamba,
dan haka be sha wuya gurin gano wadda take nufi ba, abun da ya ɗaure masa kai shine
kaddai a haka da wannan shigar zata fita?.
Ya fito da motar, ya fito ya buɗe mata ƙofar Bayan motar, wuce shi tayi taje ta
buɗe gaba ta shige ta zauna. Ya zagayo ya buɗe shima ya zauna yana ta Addu'a, gashi
besan inda za suje ba, haka yai shahada ya kunna motar Isa ya buɗe musu gate, taiwa
Isa Alama da hannun ta yazo, a guje jiki na rawa Isa ya ƙaraso gefen window ɗin da
take zaune ya risina
"kwatanta masa gidan Bulama" ta furta kaman wadda aka yi wa dole, Isa yace "kina
nufin Alhaji Bulama Abokin Alhaji?" Ɗauke kai tayi tana kallon wani gurin daban, se
Yanzu Isa ya tuna bata maimaita magana, ya gyara tsayuwa yayi wa Yusuf kwatancen
gidan.
A hankali Yusuf yaja motar suka bar gidan, tunda suka fara tafiya babu wanda yayi
wa wani magana, Yusuf ya dinga bin kwatancen gidan da Isa yayi masa, har zuwa ƙofar
wani katafaren gida da suka zo ƙofar gate ɗin Yusuf ya kalle ta yace "Nan ne ranki
ya daɗe?" Shiru tai masa ko motsawa ba tayi ba balle ta kalle shi, ɗan taɓe baki
yayi, yai horn megadi ya buɗe ƙofa ya leƙo yana ganin motar ya ja da baya da sauri,
ya koma ya buɗe gate ɗin gidan, gidan yayi kyau ya tsaru matuƙa sedai be kai gidan
Alhaji Nasir ba. Yusuf yaje parking space yayi parking, kafin ya sakko ya buɗe mata
ta buɗe motar ta fita. Fitowa yayi shima ko da wani abu dazata buƙata ya fito ya
tsaya a bayan ta, me gadi ya ƙaraso cikin girmamawa yana gaishe ta, bata amsa ba
tace "Bulama yana nan ne?"
"Eh ranki ya daɗe, Amma bana jin ya tashi"
"Ace masa gani na zo, ya tashi ko be tashi ba be dameni ba, bazan haura mintuna
talatin a gidan nan ba"
Da sauri megadin yace "Angama ranki ya daɗe" nufi cikin gidan.
Ba tare da ta kalli inda Yusuf yake ba tace "biyo ni" ba musu yabi bayan ta, Wata
rumfa dake harabar gidan me ɗauke da fararen kujeru ta nufa taje ta zauna akan
kujera, bayan ta yusuf ya tsaya ba tare da ya zauna ba.
Me gadi ne ya fito tare da wani matashi, matashin na ganin ta ya fara murmushi ya
ƙara so inda take zaune
Matashin yace "Manya maganin ƙanana, Dama yaran talaka irin mu na ganin ku?"
Ɗan taɓe baki tayi tace "Gurin Alhaji Bulama nazo, yace yana son gani na, a ce masa
gani nazo"
Matashin yayi murmushi yace "Yau kuma a Alhaji Bulama yake ba Daddyn ba, WIDAD
kenan, to ki shiga ciki mana ku gaisa da su Hajiya da Iman mana"
Yusuf a ransa ya maimaita "Ikon Allah wani irin suna ne wannan? Widad?
Widad tace "banzo da niyyar ganin su ba a yanzu"
"Shikenan bari ayiwa Daddy magana"
Har ze wuce ya kalli Yusuf yace "am Sorry young man bamu gaisa ba"
Ya miƙawa Yusuf hannu, Yusuf yayi murmushi ya miƙo masa hannu da nufin suyi
musabiha, Amma Widad ta kalli Yusuf ta haɗe rai tace"don't try it" A hankali Yusuf
ya janye hannun sa suka fasa gaisawar, saurayin ya girgiza kai yace "Hmm bari in
kira Daddy"
Yusuf a ransa yace "wai ita wannan shikenan kowa se dai yabi abunda take so? Kowa
ma wulaƙanci take masa?"
Sunan a harabar gurin, aka turo 'yar aiki da kayan drinks da fruit ta kawo musu,
yadda aka ajiye kayan ko kallon su ba tayi ba.
Ba tare da ta kalli inda Yusuf yake ba tace "duk wanda yazo gurin nan ban yadda ka
kula shi ba, ba ruwan ka da kowa"
Yusuf yace "angama ranki ya daɗe"
Wani babban mutum ne ya fito sanye da jallabiya fara ƙal, aƙalla zeyi sa' an
mahaifin widad.
Ya ƙaraso gurin fuskarsa ɗauke da murmushi, yaja kujera ya zauna ya kalli widad
yace "daughter yau kuma cikin gidan nawa ne baza'a shiga ba?"
"Eh bazan shiga ba banyi niyya ba, yanzu ma Daddy ne yace kana nemana nazo" ta
bashi amsa kai tsaye
Alhaji Bulama yace "yanzu daughter ace kina Nigeria amma ki kasa zuwa ki ganni mu
gaisa, ko na miki laifi ne?"
Ɗan girgiza kai tayi tace "nafison zamana ni kaɗai ne"
Alhaji Bulama ya kalli Yusuf yace "daughter shi kuma wannan fa?"
"driver nane, ba ruwan ka da shi"
"Shikenan naji ba ruwana da shi, amma idan bodyguards kike buƙata ai za'a iya samo
miki, wannan ba abunda ze iyayi miki"
Ba kunya Widad Ta kalli tsabar idon mutumin nan a gadaran ce tace "bana buƙata,
bana son kowa ya raɓeni"
Alhaji Bulama yace "A'a daughter sama miki masu tsaron ki yana da mahimmanci,
musamman tunda kin san amfanin hakan a tare da ke"
"Bana buƙatar kowa a tare da ni, bana buƙatar saka rayuwar kowa a hatsari, ban
yadda da kowa ba dan haka bana buƙatar su"
Alhaji Bulama ya jinjina kai yace"Amma daughter kin san likita ya hana ki wannan
ɗabi'ar kaɗaice kan naki, rayuwa ba zata taɓa yuwuwa a ce kina gudun mutane ba, ya
kamata ki samu kiyi aure zaki samu nutsuwa, da kuma farinciki zaki rage kaɗaicin
nan"
Karon farko da Yusuf yaga dariya a fuskar ta, ba ƙaramin kyau tayi ba da tayi
Dariya ta wani jinjina kai cike da rainin hankali tace
"Alhaji Bulama kenan, an gaya maka rayuwar kaɗaicin da nakeyi tana damuna ne?
Karnuka na da maguna suna ɗebe min kewa sosai fiye da yadda mutane zasu yi min,
tunda nasan sun baza su cutar dani ba"
Ta miƙe tsaye tsam ta kalli Alhaji Bulama ta haɗe rai kaman ba ita ta gama dariya
ba tace
"Ka cire wa zuciyar ka cewar ni widad zanyi Aure, ban yadda in zauna a ƙarƙashin
wani ba yana juyani yadda yake so ba, in anyi Aure ana neman Aljanna ne, ni kuma
idan nayi Aure sedai Rahamar Allah ta shigar dani Aljannah, ba dan zanyi wa wanda
nake tare da shi biyayya ba, na faɗa bazan zauna ƙarƙashin wani ba, babu wani
farinciki da'ake a tsinta a Aure, babu komai cikin rayuwar aure se takura da
matsaloli, NO MARRIAGE IN MY POLICY!!! Rayuwa ta da nake nika ɗai ta fiye min bazan
gayyato wa kaina matsala ba bayan wadda nake ciki"
Ba Alhaji Bulama ba hatta Yusuf maganganun Widad sun ɗaure masa kai, ita kam wannan
wace irin zuciya ce da ita haka?
Inda motar su take ta nufa, hakan yasa Yusuf bin ta da sauri ya riga ta ƙara sawa
inda motar take ya buɗe mata.
Suna tafe yana lura da ita, ranta a ɓace yake sosai, haka yayi tuƙi a hankali koda
suka je gida part ɗin ta ta nufa ba tare da ta kula kowa ba.
Yusuf kam rasa abunyi yayi, ita ba tace ta sallame shi ba ko A'a, ga mukullin mota
bata karɓa ba.
Bayan ya kulle motar Isa ya nufoshi yana murmushi yana zuwa yace "har kun dawo
kenan?"
"Eh min dawo malam Isa"
"to yaya, fatan dai bata maka halin ba?"
Yusuf yayi murmushi yace "niba abunda tayi min, ni yanzu damuwa ta ban sani ba ko
ta sallameni ba tace min komai ba, ina son tafiya gida ne"
Isa yace "kaje ina? ai zama zakayi setace ta sallame ka"
Harar Isa Yusuf yayi yace"shikenan ni bani da Abunyi na kaita inda zan kaita meya
rage banda in tafi tawa sabgar, mahaifiya ta Nason ganina dan haka bazan zauna ba"
Yana gama maganar ya nufi ƙofar shiga cikin gidan, yana jin Isa yana kiransa amma
yai masa banza.
Yana shiga yayi karo da Amal ta taho da sauri zata fkta.
Tana ganin sa ta tsaya tana ajiyar zuciya, taji wani farinciki na ratsa zuciyar ta
Yusuf yace "barka da rana"
"Yawwa barka ya kake ya aikin?"
"Alhamdilillah, ga key ɗin mota nan bata karɓa ba ta tafi, ina son zan tafi gida
ne inga mahaifiya ta"
Ya miƙawa Amal, be jira me zata ce ba yai waje abun sa. Jinjina kai Amal tayi tace
"lallai wannan besan wacece Widad ba, da alama shima kansa yana ɗan rawa" Babban
abunda ya bata haushi irin yadda be tsaya ko gaisawar kirki sunyi ba.
Koda Yusuf ya koma gida ya sha tambayoyi a gurin Ummansa, seda ya tabattar mata da
babu wata matsala sannan hankalin ta ya kwanta.
Tunda ya shiga ɗakinsa yake saƙawa yana warwarewa, abubuwa da yawa sun bashi mamaki
yana da tarin tambayoyin da besan me bashi amsar su ba, Amma kusan akwai alamar
tambaya akan dukkanin iyalan gidan akwai wani ɓoyayyen abu da kowa yake ɓoyewa a
ransa.
"Amma me yasa Widad ta zaɓi rayuwar kaɗaici akan rayuwa da mutane? Me yasa tayi wa
Aure mummunar fahimta haka? Me yasa kowa yake biyayya ga Umarnin ta abunda take so,
ko da kuwa hakan na nufin ɓacin ran mutane ne?"
Bashi da Amsar tambayoyin nan, Shi ze nemowa kansa amsoshin tambayoyin.
Widad tana kan gadon ta ta ƙurawa sama ido, Hawaye na bin gefen idon ta, Mahaifin
ta yayi Sallama a ɗakinta, tana jinsa amma tayi masa shiru, ta miƙe zaune a
hankali, ya ƙaraso gefen gadon ta ya zauna ya kalli idon ta yace
"daughter ya akayi ne? Meke faruwa? Abbanki ya gayamin ko gidansa baki shiga ba
iyakarki harabar gidan, daughter me yasa?"
"Bana son hayaniya ne, shiyasa na tsaya kawai a harabar gidan" ta bashi Amsa
Alhaji Nasir yayi ajiyar zuciya yace
"Alhaji Bulama ya gayamin yadda kuka yi, Lovely bamu yanke shawarar batun yi miki
aure ba sedan na gaji da ganin halin dake ciki, Widad zuciya ta na shiga ƙunci da
irin wannan rayuwar da kike yi, kin san larura dake damunki, likita ya hana ki
kaɗaicewa, idan kika cigaba a haka fa ze cigaba da taɓa ƙwaƙwalwar ki, dan Allah
daughter ki amince da roƙona, kiyi Aure ina son ganin farincikin ki, ko baki yadda
da kowa ba, idan dai zaki buɗe ido kiga 'ya' yanki da mijinki zakiji daɗi sosai,
dan Allah Widad bani da kowa yanzu seke, se kuma Aminina Bukar Bulama, naso Inkuma
samun yara bayan ke, Allah be bani ba, zanji daɗi idan naga 'ya' yanki, please
Widad help your Dad, nasan bana tunanin akwai wanda kika tsayar kike so, Amma nida
Bulama mun yanke shawarar zaɓa miki mijin da zakiyi Alfahari da shi, wanda ze nuna
miki so ya kula dake ko bayan raina, Widad a yau idan na faɗi na mutu bayan Alhaji
Bulama bana tunanin Akwai wanda ze kulamin da Rayuwar ki, sannan kinsan a haɗarin
da muke daga ni har ke, please Widad ki Amincewa batun Auren nan, am sure if you
got true love you will never regret been married, Akwai Soyayya da tausayi a cikin
rayuwa da wanda yake son ka, na tabattar da Aure ze wanke miki dukkanin wani pain
da yake ranki"
Tunda ta ƙura masa ido ko ƙyaftawa ba tayi, seda ta bari ya gama, ta miƙe tsaye ta
fice ta bar masa ɗakin ba tare da tace komai ba.
Alhaji Nasir ya jinjina kai, babu alamar Nasara, Amma ya yanke wa zuciyar sa ze
cigaba da lallaɓata yana bin kanta, dan babu wata mafita da ta rage masa se
Amincewa da shawarar Alhaji Bulama. A fili yace "Wannan karon ke zakiyi biyayya ga
unarnina daughter, duk wannan abun inayi ne saboda ke"
Widad kam gaba ɗaya maganganun mahaifinta haushi suka bata, kaman korarriya haka ta
sakko daga kan bene, ta samu corridor ta tsaya tana zancen zuci, "wai Aure, waya
gaya musu akwai Aure a tsarin Rayuwar ta? Taɓɗijan inyi Aure in zauna a ƙarƙashin
wani yana juya ni yadda yake so? Ko kuma a haɗa kai da shi a cutar dani, kaman
yanda yake ɗabi'ar mutane ne cin amanar wanda ya yadda da su, idan har Akwai mutane
masu amana da suka rage a doron ƙasa to sunyi nisa da duniyar da ni Widad nake
ciki, waima waye ake cewa za'a haɗa da shi ne Aure? Idan kuma ya zamana yana ɗaya
daga cikin mutanen da nake nema fa, hakan yana nufin in masa Alfarma ko in ɗaga
masa ƙafa?
A fili tace
"Baze yuwu ba wallahi, ba wani Aure da zanyi, what is their in marriage apart from
pains!, hurting each other!, tensions!, regrets and restriction of rights,!! No
Impossible i want free life, i can't live under someone's control, i better live
alone and die alone than to got married to irresponsible man of now a day's,
bazanyi Aure ba, idan har Soyayya da shaƙuwa basa hana ɗan Adam ya cutar da ɗan
uwan sa, to tabbas Love doesn't exist is just an imagination, love does not exist
talk less of true love, So shike sa ayi Aure, kuma yadda ce ke kawo so ban yadda
da kowa ba, Daddy Bulama kayi min katsalandan bisa ga kawo wannan shawarar da ɗaya
take da ƙarasa gurgunta rayuwa ta" hawaye ne ya wanke mata fuska sharkaf se ajiyar
zuciya take yayin da take maganar.
Ramla da tazo wucewa ta tsaya taji surutan da Widad take yi, ta jinjina kai a ranta
tace "to Aure kuma? Waye ze auri wannan Jarababbiyar? Kuma mahaukaciya? Anya Mummy
ta san zancen nan kuwa?
Widad kam ji tayi zuciyar ta tana wani irin raɗaɗi, ta fito harabar gidan da sauri
kanta ko ɗan kwali babu, dan gaba ɗaya ji tayi kaman tana cikin wuta dole ta fita
dan ta samu sassauci, Tana fitowa harabar gidan ta nufi inda Isa yake tace
"ina direban nan yake, yazo ya fita dani ya bar arear nan dani"
Isa ya kalleta ya kalli kayan jikin ta, mini skirt ne a jikin ta se wata riga
armless, gashin kanta a baje kaman ta zare, Isa ya ɗan ƙare mata kallo, a ransa
yace "Masha Allah, Allah ya yi halitta anan" yace"Ranki ya daɗe a hakan za'a fita
dake?" Kallon da yake mata ne da tambayar da ya tsareta da shi, yasa ta ƙara fusata
ba zato ba tsammani Isa yaji saukar lafiyayyen mari a fuskar sa.
Gigicewa yayi ya dafe kuncin sa yace "ranki ya daɗe ya tafi tun ɗazu, nace ya tsaya
amma yace baze tsaya ba yana da uzuri"
Ƙanƙance ido tayi ta dubi Isa, a hankali tayi ƙasa sa muryar ta tace "ɗan uban waye
shi da ze saka hannu akan dukkan sharuɗai na, kuma yau da ya fara min aiki har ya
fara saɓamin doka?"
Shiru Isa yayi yana sake shafa kumatunsa dan bashi da amsar da ze bata
"Wallahi sena masa wulaƙancin da babu wata halitta data taɓa yi masa, sena sauke
dukkan baƙin cikin da nake ciki akansa, waye ubansa? Yana ƙasƙantacce zeyi watsi da
dokokin da shi yasa hannu da kansa, Matsiyatan banza marasa Alƙawari, shiyasa wani
talakan har ya mutu baze Arziki ba saboda rashin sanin mahimmancin Alƙawari da
Amana, ya shirya karɓar hukuncin da ba'a taɓa masa makamancin sa ba"
(Nikam nace masu kuɗi ne kawai suka san Alƙawari da Amana? Ko kuwa Alƙawari da
Amana ce tasa suka yi Arziki? Shikenan idan mutum yana aiki a ƙarƙashin wani me
kuɗi se ya zama kaman Bawa? Shi besan jin daɗi ba se Bauta? Bashi da wani 'yanci na
walwala da jin daɗi kenan? Tabbas da ba talaka ƙaryar me kuɗi yaji daɗin Rayuwar sa
komai Arziƙin sa kuwa, Naga kowane ɗan Adam dai ajizine babu wanda baya kuskure, ke
Widad ba kya kuskure ne ko kuwa? A ce mutum ya zabi Rayuwa shi kaɗai ƙwal ba
mutane? Kowa be iya komai ba ciki hada mahaifinki, Gaskiya kin zafafa Aƙidojin ki,
wata sabuwa kuma Widad tace "Love doesn't exist, is just an imagination talk less
of getting true love" masu karatu wannan kaɗanne daga Aƙidojin Widad
TIRƘASHI!!!
Yaseen Akwai cakwakiya, Hassada, Munafunci, tsantsar Soyayya, Fuska biyu, kutsen
ƙaddara me sauya rayuwar bawa ko be shirya mata ba, da sarƙaƙiyar gaske a cikin
wannan littafin kar ku bari a baku labari dan ya haɗu.
Insha Allah ze cigaba da zuwar muku 1 ga watan September
Domin sharhi, gyara, ƙorafi ko makamancin haka ku tuntuɓeni akanWannan lambar ta
what's app kawai 07063065680
Masu bina private akan in tura musu ABDUL JALAL dan Allah kumin afuwa, Abubuwa
sunmin Yawa na kammala part two a document na sake shima, idan baku samu ba ku duba
manhajar watpad a account ɗina Ayshercool7724 insha Allah zaku samu dama sauran
litattaafai na.
Masoya a cigaba da haƙuri dani, sakamakon harkar makaranta da wasu abubuwan da suka
sani gaba Insha Allah wannan littafi ze fara zuwar muku 1 ga watan September, a
what's App, da telegram groups ɗina, da kuma Facebook a shafin mu na perfect
writers Association, ko kuma YouTube channel dinmu
Ina godiya da Adduoin ku.
_*AƘIDA TA*_
*Story and written by*
_*AISHA HUMAIRA (Daddy's girl)*_
The experience writer of *ABDUL JALAL** WATA KISSAR.... (SAI MATA) *And now *AƘIDA
TA *
I dedicated this book to my Mum (Malama Nafisat Adam Muhammad) i love you mum
Special thanks to all members of my Association Perfect writers Association may
Allah subhanahu wata'ala bless our pens and grant us wisdom to write what will
bring positive changes to our Community.
I won't forget you my fans 😍😍😍 you are always in my heart, my love to you is
endless, especially those that shows me love support and follow me with prayers
since my first Novel to date, i can't mentioned you all but am proud of you all 😍
HAUSAWA SUKACE KYAN ALƘAWARI CIKAWA, KAMAR YADDA YAKE KOYAR WAR ADDININ MU CIKA
ALƘAWARI ABU NE ME MATUƘAR MAHIMMANCI, NAZO DOMIN CIKA MUKU ALƘAWARI, A BAYA NASAKA
RAN KAMMALAWA DA MAKARANTA A AUGUST, KATSAM AKA ƊAGA JARRABAWA AKA MAIDA ITA 20 GA
WATAN SATUMBA, AMMA TUNDA NI NAYI MUKU ALƘAWARIN CIGABA DA KAWO MUKU WANNAN LITTAFI
A WANNAN WATA, NA SHIRYA TSAF DAN CIKA ALƘAWARIN KU 'YAN AMANA, WATTANI HUƊU KUNA
SAURARE NA, INSHA ALLAH BAZAN BAKU KUNYA BA, KU SHIRYA DOMIN SALON NA DABAN NE,
AKWAI TUFKA DA WARWARARA ME MATUƘAR SARƘAƘIYA A WANNAN LITTAFI DA KUKA DAƊE KUNA
JIRA. KARA ƊAYA ZAKUYI MIN, SHINE NUNAMIN JIN DAƊIN KU TA HANYAR YIMIN COMMENT TARE
DA SHARE, LITTAFIN NAN KYAUTA NE DOMIN JIN DAƊIN KU MASOYA NA, AMMA A DALILIN
RASHIN COMMENT ƊINKU KOMAI NA IYA CANZAWA, GA MASU MANHAJAR WATPAD KU GARZAYA KU
NEMENI@AYSHERCOOL7724 KU NEMI LITTAFIN A FACEBOOK A GROUP ƊIN PERFECT WRITERS
ASSOCIATION ƘOFA TA A BUƊE TAKE DOMIN GYARA SHARHI KOKUMA SHAWARA AYSHERCOOL
07063065680
YADDA NA FARA LAFIYA ALLAH YASA IN KAMMALA LAFIYA
Haƙƙin Mallaka ⚠ : Littafin nan mallaki nane, tun daga sunan labarin zuwa abunda ya
ƙunsa, ban yadda wani ko wata ya sauyamin ko yin Amfani da wani ɓangare na labarin
ba ba tare da izinina ba, Nagode
BISMILLAHIRAHMANIRRAHIM
ELEGANT ONLINE WRITER'S
*PART1* _Page 4_
Babu alamar sassauci fuskar Widad, yanayin fuskarta ze tabattar maka da gaske har
cikin zuciyar ta zata aikata abunda ta faɗa, ta juya ta koma cikin gidan da
hanzari.
Jinjina kai Isa ya dinga yi yana kuma sake shafa kumatunsa yadda yske masa raɗaɗi,
tare da tausayawa wulaƙancin da Yusuf ze fuskanta.
Ramla kam cikin sassarfa ta nufi ɗakin mahaifiyar ta, tun daga waje take kiran
"Mummy"
Hajiya Halima tace "Ramla wannan wane irin kira ne haka? Ke kam bakya girma"
Ramla ta ƙarasa kusa da mahaifiyar ta ta zauna tace "wai nikam nace me akayiwa 'yar
gwal ne? Naga kaman ciwon nata na ƙoƙarin tashi fa? Kuma ga dukkanin alamu yau ta
kwaɓe mata itada uban tane"
Ɗan tsaki Mummy tayi tace "sakani yake cikin sha' aninsa shida 'yar sa ne? Ai sedai
inga suna lamauran su ta yaya zan san meya sameta?"
Ramla ta sake gyara zama "hmm kinsan dai halin ciwon ta, a corridor ɗin ƙasa na
haɗu da ita, tana ta surutai, wai Daddy Aure zeyi mata, se safa da marwa take tana
zufa"
Zaro ido Mummy tayi tace "Aure kuma? Wane irin Aure ana zaman lafiya? Waye ze Auri
mahaukaciya mara tarbiyya kamar wannan Yarinyar? Shi mijin da haukan zeji ko kuma
da rashin tarbiyya?"
Ramla tace "waya sani musu?, sedai ki jiyo mana kanun Labaran muma ki fesa mana,
Amma ina tunanin wanda ze kwashi wannan Mahaukaciyar"
"To nidai a iya sanina bata yadda da mutane ma, to ta yaya ta samo wanda ze Aure
ta?"
Ramlah tace "Ai samun miji ba wuya ze mata ba, ko dan wannan haɗaɗiyar Daular, dan
haka ko'a turu take dan hauka, za'a iya samun me sonta yace ze aureta a haka"
Mummy tace "hakane, Amma ya zama dole musan waye ze Aureta, dole in gano" Haka Suka
ci gaba da tattauna wa akan lamarin.
Yusuf kam kashe wayoyin sa yayi ya shiga sabgoginsa, duk yadda Isa yaso kiran Yusuf
a waya ya gaya masa Saƙon Widad abu ya gagara wayar sa taƙi shiga, ƙarshe se haƙura
Isa yayi.
Widad kam baranda ta samu ta kwanta, akan tiles ga sanyin tiles na ratsa ta amma
sam bata ji, tayi ruf da ciki tana jin yadda zuciyar ta take mata raɗaɗi, kamar ta
tsaga ƙirjinta ta fito, Babban Abunda ya ƙara bata mamaki shine yadda mahaifin nata
be biyo sahunta ba balle ya rarrashe ta kaman yadda yake yi abaya, shima kamar yayi
fushi da ita karon farko ya barta cikin damuwa, lallai wannan karon mahaifin nata
dagaske yake.
Washegari Yusuf ba shida Niyyar zuwa gidan su Widad Sam, da ya tashi da safe ma
shirin tafiya Office yayi abun sa, ya shirya ya fito Umman sa ta kalle shi tace "Ya
haka kuma? Yau ina zakane?"
Murmushi yayi yace "Yau Office zanje Umma"
"Kacemin kuma, an turaka aiki gidan Alhaji Nasir Daula, yanzu kuma kace min zaka
gurin aiki ya haka?"
Yusuf yace "hakane Umma, an turani aiki gidan Alhaji Nasir Daula, Amma dole zan
dinga leƙawa Office, ina documenting findings ɗina sannan indinga presenting
sakamakon bincike na"
"shikenan a sauka lafiya, Allah ya tsare ya kiyaye hanya"
"Allah yasa Umma, dan Allah yau ki mana dambu kinji Umma na"
Umma tace "banyi Alƙawari ba, ka bari ranar da kake nan se kayi"
Noƙe kafaɗa Yusuf yayi yace "dan Allah Umma, ni gaskiya idan ba dambu kika yi yau
ba bana cin Abincin"
"kar kaci ɗin, ai cikin ka ba nawa ba"
Haka yaita zolayar umman nasa sannan yai mata sallama ya tafi.
Da yaje Office ɗin ma Ayyuka sun ɗanyi masa Yawa, ya duƙufa sosai yana ta shigar da
ayyukan sa cikin system.
Sallamar da'akayi a office ɗin ne ya sashi ɗagowa yaga me Sallamar, kamar yadda ya
zata sakine ce ta shigo.
Kallo ɗaya yayi mata, ya Amsa sallamar ya maida kansa ya cigaba da danna system ɗin
shi.Yauma cikin baƙaƙen suit Sakina take, amma skirt ga ƙaramin hijjabi da ta saka,
gaba ɗaya kayan sun bayyanar da surar jikin ta. Kujera ta ja ta zauna tana facing
ɗin sa.
"Yusuf sannu da Aiki" Ba tare da ya kalle ta ba yace "lafiya kalau Alhamdilillah"
"kwana biyu baka shigowa Aiki, lafiya dai ko?"
Ɗan ɗagowa yayi yace "Eh an bani wani Assignment ne"
Cikin iyayi da lumshe ido tace "to Allah yaba da sa'a"
Ya amsa da "Ameen"
"Can i offer you something to eat?"
Ba tare da yace komai ba ya girgiza mata kai, Alamar A'a.
Miƙewa tayi ta zagayo inda yake tace"ko Akwai abunda zan taya ka ne?"
Ɗagowa yayi ya kalleta a hankali yace "dan Allah ki fitar min daga Office inada
Ayyuka da yawa kina takuramin fa"
A Shagwaɓe tace "Yusuf meyasa kake son yi mun wulaƙanci ne?"
"ba wulaƙanci bane, gaskiya ce, Aikine ya kawo ni gurin nan ki barni inyi aikina
mana"
"Amma Yusuf meyasa zaka maida Soyayya ƙiyayya, tunda na nuna ina sonka kake
wulaƙantani haba Yusuf"
"Sakina niba wulaƙantaki nake ba, yanzu lokacin aiki nane, dan Allah ki tashi ki
tafi, bearable in shiga lokacin aiki ba"
"Yusuf" ta kira sunansa, ɗaga mata Hannu yayi ya dakatar da ita tare da faɗin
"Sakina dan Allah ki barmin office, kalli shigar jikin ki, kuma kinzo kin sani
gaba, dan Allah ki tafi"
Suna cikin Jayayyar ne Abbas ya shigo, Sakina ta miƙe ta bar office ɗin a fusace.
Abbas ya kalli Yusuf yace
"Anya Sakina bata fara kama zuciyar ka ba Yusuf?"
Ɗan girgiza kai Yusuf yayi yace
"Abbas kenan anyi na farko, baza'ayi na biyu dani ba, bana son yi mata wulaƙanci ne
amma taƙi ganewa, Soyayya kam sedai inga anayi, bazan sake ba, in Allah yayi zanyi
Aure shikenan, Amma na gama Soyayya"
Abbas ya jinjina kai yace "shikenan Allah ya kyauta, na kiraka tun jiya bata shiga
ya labarin mutuniyar ne?"
Shafa Aljihun sa Yusuf yayi, sannan ya jingina da jikin kujera yace
"Aini tun jiya dana dawo na kashe waya ta, bana son a dameni ne sam"
Abbas yace "kayi mata aikine jiya?"
"Eh munfi ta, na kaita wani gida, inaga gidan ɗan uwan mahaifinta ne ko makamancin
haka"
Abbas yace "babu dai wata matsala ko?"
"Babu wata matsala, ba tayi min dai wulaƙanci ba, Amma fa naga izza wadda ban taɓa
ganin makamanciyarta ba, dan cikin isa da gadara take wa kowa magana, bata shakkar
kowa bata girmama kowa, kai ko Dariya banga tayi ba Jiyan nan, magana ma aiki ce a
gurin ta"
Abbas yace "taɓ, aishi yasa nace bazan iya ba, saboda na samu labarin yarinyar,
shikenan ka dai kula sosai akan abunda muke son ganowa"
Jinjina kai Yusuf yayi, tare da cewa "Insha Allah, komai ze tafi dai dai"
***********
Ƙarfe goma na safe Yusuf ya bar gurin aikin, ya koma gida seda yayi wa Umman sa
cefane, ya kai mata markaɗe ya kama mata Ayyukan gida sannan ya sauya kaya, ya nufi
gidan Alhaji Nasir.
Yau da yaje ya tarar da Isa mai gadi dashi da wani, Suka gaisa, Isa yayi farat yace
"Yusuf ga Nura shine direban megidan nan, lokacin da kazo yaje garin su ne, amma
gashi ya dawo, shike kai Alhaji unguwa"
Yusuf ya miƙa wa Nura hannu suka gaisa.Isa ya nisa yace "Yusuf kayi gangancin
tafiya jiya, nan ta fito a birkice jiya kaman mara hankali tazo nan tana neman ka
wai ka fita da ita, baka ga shigar jikin ta ba, daga tambayar ta a haka zaka fita
da ita ta mareni, wallahi har yanzu ko ƙuda bana so ya taɓa fuskata dan ba ƙaramin
shiga marin nan yayi min ba"
Zaro ido Yusuf yayi yace "mari kuma?"
"Wallahi Yusuf mari na tayi"
Nura yace "aiba abun mamaki bane, dama wani lokacin haka take birkice wa, kun san
abunka dame rangwamen Ƙwaƙwalwa, aini tunda naji zata dawo naji aikin gidan nan ya
fita daga kaina, Allah ya temakeni aka samo mata nata direban"
Kallon su Yusuf yake dan be fuskanci inda zancen nasu ya dosa ba.
Isa yayi ƙasa da muryar sa yacewa Yusuf "wani lokacin birkicewa take kaman hauka
hauka, shiyasa kaga bata son mutane suje inda take, tana da larurar ƙwaƙwalwa
shiyasa....
Yusuf ya katse shi ta hanyar cewa"Shikenan shikenan, Allah ya bata lafiya be kamata
a dinga yayatawa ba, Addu'a ya dace ayi mata, faɗar bashi da Amfani sam"
Widad ce ta fito ƙaton falon gidan, ta tarar da matar gidan da yaran ta Suna ta
ciye ciye suna hira, tana fitowa suka yi tsit suka shiga taitayin su, suka dena
hirar.
Ta dube su ɗaya bayan ɗaya, kamar me nazari, sannan ta yatsuna fuska tace
"Amal jeki kira min wancan matsiyacin talakan direban, yau in fara gwada masa
wacece ni"
Sam Amal ba taji daɗin kalaman da Widad tayi amfani da su akan Yusuf ba, Amma babu
yadda ta iya ta miƙe ta tafi kiran sa.
Tunda Amal ta fito ta hangi Yusuf yana hira da su Nura, yayi kyau sosai komai nasa
gwanin sha'awa, kamar ba direba ba.
Amal Ta ƙaraso inda suke bata kula su Isa dake ƙoƙarin gaishe ta ba, ta dubi Yusuf
tace
"barka da rana Yusuf"
Fuskarsa ba yabo ba fallasa yace"Yawwa barka, ina uwa ɗakina?"
Bata jin daɗin yadda koda yaushe yake taƙaita magana da ita, Amma ta basar tace
"itace tace in kira ka ma"
Yusuf ya miƙe yace "shikenan muje"
Yabi bayan Amal, tsananin kwarjinin Yusuf ne yasa Amal sam ta kasa kuma ce masa
komai, se ƙamshin turare yake fitarwa me daɗin ƙamshi kaman ba direba ba.
A falon suka tarar da hakimar ta harɗe da alewa me tsinke a bakin ta, tana danna
waya tareda kaɗa ƙafafuwan ta.Kamar kullum yanzu ma kanta babu ɗan kwali, ta baje
gashin ta, Amma yau anyi sa'a skirt ne dogo a jikin ta da wata 'yar ƙaramar riga
shara shara.Tunda Yusuf ya shigo ɗakin ƙamshin turaren sa ya daki hancin ta taji ya
saukar mata da wata muguwar kasala, a duk lokacin da Yusuf zezo gidan nan taji
wannan ƙamshin turaren a jikin sa se kasala ta saukar mata.
Kallo ɗaya Yusuf yayi mata yaji ƙirjin sa ya buga da ƙarfi, da sauri ya ɗauke idon
sa daga kanta, Sam fuskar ta babu alamar afuwa.
Ya kalli matar gidan yace "barka da yamma Hajiya"
"Yawwa barka sannu ya aikin?"
"Alhamdilillah"Ya juya ga Widad yace "sannu da hutawa ranki ya daɗe"
Dama be zaci zata amsa ba, dan haka be kuma cewa komai ba se sunkuyar da kansa ƙasa
da yayi.
Ya shafe mintuna Arba'in a durƙushe a gaban ta ba tare da tace komai ba, shi kuma
ko kansa be ɗaga ba.
Amal ji take tamkar ita ce a durƙushe a gurin, gaba ɗaya taji kaman ta cewa Yusuf
ya tashi yayi tafiyar sa.
Ba zato ba tsammani ya tsinkayi maganar ta
"Waye ya baka iznin tafiya jiya?"
"ba kowa Ranki ya daɗe"
Seda ta kuma jan wasu mintunan sannan tace"meyasa ka tafi?"
Ba tare da ya ɗago kansa ba yace
"na zata na gama aikina na jiyane shiyasa, Amma hakan ba zata sake faruwa ba Insha
Allah, kiyi haƙu....
Cikin tsawa tace"Shut up, what the hell are you trying to say? Do you sign my
conditions based on Assumption? Don't you read what is in that paper? Why are you
trying to applogise? Talaka baze canza hali ba, baku da Alƙawari baku san ƙa'idar
Aiki ba, se an jima ku buɗe baki kuna zagin shugabanni da masu kuɗi, waye kai da
zaka karyamin doka? Me kake taƙama dashi da zaka nemi ka raina min hankali? Ɗan
uban waye kai? Ko ban gaya maka lokacin aiki nawane ba? Har da zaka fara da
rainamin hankali"
Tunda Widad ta fara zazzaga rashin mutuncin ta Yusuf be ɗaga kai ba, dukda yadda
zuciyar sa ke harbawa jijiyoyin kansa suka miƙe saboda ɓacin rai, Amma ya dake.
Amal kaman ta ɗora hannu akai tayi ihu, ji take tamkar ita Widad ke ciwa mutunci,
ita kuwa matar gidan da Ramlah ko a jikin su dan babu wanda Widad ta bari a rashin
mutunci.
"kasan tsanani baƙin cikin da na shiga zama na a gidan nan bayan an ɓata min rai,
daka nan ka fita dani da ban shiga damuwar dana shiga ba, tun jiya nake fama da
damuwa saboda sakacinka, nayi kwanan baƙin ciki da ɓacin rai, this is my last
warning to you, idan makamancin haka ya kuma faruwa, sena nuna maka wace ce Widad"
Risinawa ya kuma yi da kai
"zan kiyaye ba zana kuma ba insha Allah"
Jefo masa key tayi fuskar sa tare da faɗin"Car Number 8, to bulama's residence"
Yaji zafin yadda ta jefa masa key a fuska, da maganganu marasa daɗi da tayi masa,
amma yasa hannu ya ɗauka, kaman wanda ƙwai ya fashewa a ciki ya nufi hanyar fita.
Fakar idon Widad Amal tayi ta biyo bayan Yusuf, wajen ƙofar fita ta cin masa, yana
ta sauri fuskarsa babu Annuri, Amal ta kira sunan sa, dan tsayawa yayi ya waigo
yana kallon ta
"Dan Allah kayi haƙuri da abunda Widad tayi maka, haka halin ta yake muma duk
haƙuri muke da ita, dan Allah kayi hakuri"
Ga mamakin ta se taga murmushi akan fuskarsa yace
"aini banji haushi ba, tabbas laifi nane da banbi komai a ƙa'ida ba, bayan nasan
hakan ya saɓawa Yarjejeniyar dana sakawa hannu, kuma nasan yana daga AƘIDAR uwa
ɗakina girmama Alƙawari, ya kamata in nemi Afuwa ne ba jin haushi ba"
Ɗan zare ido Amal tayi "yanzu duk abunda tayi maka kana nufin ba kaji haushin hakan
ba?"
Jinjina mata kai yayi alamar eh tareda faɗin,
"bari in hanzarta in fito da motar karta fito ta sameni anan ranta ya kuma ɓaci"
yayi gaba abun sa yayin da shi kaɗai yasan me yake ji a ransa.
Yaje ya fito da motar da ce masa, ya buɗe ya shiga ya zauna ya kifa kansa akan
sitiyari, tabbas badan duk cikin aikin sa yake wannan abun ba to da ko Gidan su
Widad gold ake sarrafawa baze kuma aiki a gidan ba.
Jin ƙamshin turaren ta yasa shi saurin ɗagowa, ta buɗe gaban motar ta zauna, tace
"jeka falo inda na zauna ka ɗakko min wayata"
Ikon Allah wayar ma bazata fito da ita ba seya ɗakko mata? Bece komai ba ya fita
daga motar ya koma cikin gidan, yana zuwa ya tarar falon ba kowa wayar tana kan
center table, ya ɗakko ya fito ya kawo mata.
Tasa hannu ta karɓa ba tare da ta kalle shi ba tace "A ina kaga wayar"
"Akan center table"
Murmushin gefen baki tayi tace "let's go"
Kamar yadda tace gidan Bulama ya kai ta, ya samu guri yayi parking ya fito ya buɗe
mata ƙofa ta fito, ƙafarta sanye da takalmi me tsini sosai shigar nan tata baka ce
musulma ce ba, kayan sun kamata tsam a jikin ta a hankali ta furta "do not accept
any gift from anyone"Gyaɗa mata kai yayi yace "Insha Allah" "Follow me"
Haka yabi bayan ta, cikin hanzari take tafiyar yau.
Yau kai tsaye bata nemi iso ba cikin gidan ta nufa, Yusuf na bin bayan ta.A babban
falon dake gidan suka ga wata budurwa da wannan matashin da suka tarar jiya, da
wata babbar mace da alama itace matar gidan.
Maimakon Widad tayi Sallama se tace "Hi how are you doing guys?"
Matar tace "Widad dama kina garin nan amma ko ganin ki ba'ayi"
Budurwar tace "Wallahi Mum Ramadan yace tazo jiya amma taƙi shigowa" Yusuf dai bece
komai ba saboda jan kunnen da tayi masa jiya.
Ramadan ya kalli Widad yace "you look so Cute in this outfit Dear"
Ba ta amsa musu maganganun su ba tace "Is Daddy Around?"
Yusuf ya kalli kayan dake jikin Widad, da kuma abunda Ramadan yace kawai ya girgiza
kai
Ramadan yace "yeah yana nan"
Ƙoƙarin hawa bene Widad take yi, budurwar tace
"hey Baby who is this gentleman with you?"
Aiko tsaya ba tayi ba balle bada amsa, ta haye saman benen da sauri, Yusuf bashi da
zaɓin daya fi yabi bayan ta.
Wata ƙatuwar ƙofa ta buɗe, ta kutsa kai Yusuf yabi bayan ta, shima wani haɗaɗɗen
falo ne me girman gaske, sanyi Ac ke rasa ko ina na ɗakin.
Alhaji Bulama ne ke zaune akan ɗaya daga cikin kujerun falon, yana shan tea tareda
dannan system, Yusuf ne yayi sallama, Alhaji Bulama ya ɗago ya kalle su.
Murmushi yayi ya amsa sallamar Yusuf, yana ƙarewa Widad kallo, guri ta nema ta
zauna tana fuskantar Bulama.
Bulama yace "Daughter wai shi wannan duk inda zaki se tare da shine? Ina direba ne
kawai? Kodai Allah ya karɓi Addu'armu kin fara sakin jiki da mutane?"
Haɗe rai tayi tace "my policies remain constant, babu abunda ya canza, babu ruwan
ka da dalilin da yasa duk inda zani yake bina"
Alhaji Bulama ya murmusa yace "shikenan Allah ya baki haƙuri"
Ya kalli Yusuf yace "Sannu ɗan Samari, daughter ɗin tamu seka na haƙuri, muma
lallaɓata muke"
Da ido ta kalli Yusuf, dan haka Yusuf bece komai ba se ɗan murmusawa da yayi.
Alhaji Bulama ya maida kallon sa ga Widad yace "ina jinki?"
"Meyasa ka turawa Daddy na ra'ayin ayimin Aure?"
Ɗan girgiza kai Bulama yayi tareda murmushi "yaro yaro ne, Widad Aure shine ya dace
dake, domin shine ze gusar miki da wannan larurar ki zama kaman sauran mutane"
"na taɓa ce maka ina son Aure ne? Ko kuma akwai shi a cikin tsarin Rayuwa ta?"
"look daughter, Aure shi ze gusar miki da dukkanin wannan halin da kike ciki, babu
yadda za'ayi lafiyayyen mutum ya rayu ba tare da mutane a cikin Rayuwar sa ba, shi
yasa muka yanke shawarar Aurar dake"
"ka dai yanke shawara sannan ka cusawa Daddy na ra'ayin hakan, ace har Daddy yamin
laifi sannan ya fita harka ta dan naƙi yadda da batun Auren nan, duk kai ka jamin,
sannan nida ban yadda da soyayya ba balle inyi ta har in samu mijin Aure, wazaku
aura min?"
Gyara Zama Bulama yayi yace"Fuhad mana first born ɗina, kun dace sosai, ze soki
tsakani da Allah ya zauna dake, tunda ke 'yar uwassa ce"
Shiru tayi ta kalli Bulama sannan tace "what the fucking shit are you talking
about? meye wani ze soni tsakani da Allah? Let me tell you something, i don't
believe in Love talk less of true love, Love is just an imagination full of bull
shits and stupidity, so ke sa ayi aure ko? To ban yadda yayi existing ba, dan haka
ka gaggauta warware wannan maganar, dan ko aure zanyi bazan auri namiji bahaushe
ba, you people that are not romantic at all, babu abunda kuka iya banda iko da
ɗaukar matayen ku tamkar bayinku, baku damu da halin da zasu shiga ba idan har taku
buƙatar zata biya, baku iya komai ba se masifa da hantara, don't you see how women
are complaining about you? How Hausa women's are suffering because of your poor
marital life? Women's are always complaining about marriage issues, this is type of
life you want me to do? Do you think I can live with someone that will be shouting
at me?"
Shiru Bulama yayi yana kallon ta, Ta gyara zama ta kalli cikin idon Bulama tace"
idan baso kuke ku ƙara tunzura haukan nawa ba kaman yadda kuke iƙrari ba, ya kamata
ku ƙyaleni da maganar nan"
Numfasawa Bulama yayi yace "Amma kin san mahaifinki ma bahaushe ne, kike wannan
maganganun akan mazan hausawa"
"da nace ban dashi a ciki ne? Shima badan yayi rayuwar Turai ba he will have the
same negative habits on his wife, it seems it is in your genes, Alhaji Bulama daga
yarin tata sanina da kai mata nawa ka aura bakwa tare yanzu? Go back to your senses
Sir, Am not ready to ruin mad, i don't have interest of getting marriage, i don't
know maybe later, but I can't married a man from hausa people, they don't value
their wives "
Ba Bulama ba, Yusuf kansa yaji haushin cin mutuncin da Widad tayi wa ƙabilar
Hausawa, duk lalacewar Al'umma akwai mutanen kirki ai, Amma ba shida ta cewa, tunda
shi ɗan karere ne.
Ta miƙe tsaye tayi gaba abun ta, Yusuf ya rufa mata Baya, yauma har suka je gida ba
wanda ya kula wani, sedai da suka koma gidan, a mota ta bar jakarta da wayarta,
dole Yusuf ya ɗauka ya bita da su ba dan yana so ba, dan sam baya son shiga cikin
gidan, ba ƙaramin tsarguwa yake da irin kallon da mutan gidan ke masa yake ba.
Yanzu kam ba 'a hankali take tafiya ba cikin gaggawa take tafiya, kaman tana son
tayi wani abune, ta falon da zata bi ta wuce ta tarar da Mahaifinta a zaune da shi
da matarsa, ko kallon su batayi ba tasa kai zata wuce.
"Widad" Mahaifinta ya kira sunan ta ba tare da juyo ba ta tsaya cak, be damu ba ya
ɗora da cewa "Munyi waya da Bulama ya gayamin abunda kika je kika ce masa, ki sani
wannan karon dole kibi abunda nake so, bani zan biki ba, am doing all this for your
benefit, in the next two Months insha Allah Fahad zezo ƙasar nan, ina son ayi Auren
ku kafin ya koma" Cigaba tayi da tafiyar ta ba tare da cewa Mahaifinta komai ba.
Yusuf dake tsaye yana jinsu ya ƙarasa ya gaida mahaifin Widad da matarsa Hajiya
Halima. Ya amsa masa cikin, yayin da Hajiya Halima ta Amsa masa a ciki.
Yusuf ya miƙa wa Mahaifin Widad jakar ta da keys ɗin motar ta, yayi musu Sallama ya
fice.
"Yaya Yusuf" yaji an kira sunan sa, tsayawa yayi ya waigo, Amal ce take tahowa da
sauri hada ɗan haɗawa da gudu.
"Sannu ashe kun dawo?" "Eh mun dawo, akwai wani abu ne?"
Ɗan sosa kai tayi tace "dan Allah in babu damuwa so nake ka raka ni Shopping"
"Shopping kuma? Niɗin?""Eh amma idan ban takura maka ba" "ina batun takura ni da
nake muku aiki, idan kin shirya kimin magana" Murmushi tayi tace "nagode sosai Yaya
Yusuf" Shima murmushi ya mayar mata yai gaba abun sa.
(WASA FARIN GIRKI)
Share please 🙏 🙏 🙏
Comment nake so ba sticker ba ko kuma thanks ba, inda suka fi Comment su zasu dinga
fara samun posting Domin gyara, sharhi, kokuma ƙorafi a tuntube ni akan wannan
lambar 07063065680Watpad Ayshercool7724
_*AƘIDA TA*_
*Story and written by*
_*AISHA HUMAIRA (Daddy's girl)*_
The experience writer of *ABDUL JALAL** WATA KISSAR.... (SAI MATA) *And now *AƘIDA
TA *
Haƙƙin Mallaka ⚠ : Littafin nan mallaki nane, tun daga sunan labarin zuwa abunda ya
ƙunsa, ban yadda wani ko wata ya sauyamin ko yin Amfani da wani ɓangare na labarin
ba ba tare da izinina ba, Nagode
ELEGANT ONLINE WRITER'S
PART1 Page 5
Yusuf ya fita yaje yai alwala yai salla saboda lokacin salla yayi.
Widad kam tana zuwa ɗakin ta ta jefar da Jakarta da wayar ta akan gado ta fara safa
da marwa a ɗakin ta
"Bulama ina ganin girman ka, ina maka kallon uba amma kana ƙoƙarin ƙetare gona da
iri, kana ƙoƙarin tsallake iyakokinka, a tunanin ka yin Aure ze sa in canza
ra'ayina? Daddy kunyi kuskure daga kai har Bulama, kuma bazan taɓa bari wannan
kuskuren naku yayi tasiri a kaina ba, dole inyi wani abu" haka ta cigaba da surutai
ita kaɗai.
Hajiya Halima ta kalli maigidan ta tace "Nikam wai Alhaji dagaske Widad zakayi wa
Aure ko kuma yaya? Na kasa gane kan lamarin"
Ɗan shiru yayi sannan yace "Eh hakane, Bulama ya bani shawarar akan cewa muyi mata
Aure hakan ne kawai zesa ta canza wannan halin nata, Amma yarinyar nan kin san
halin ta da kafiya da taurin kai, ta tirje tace sam bata san zancen ba, Amma a
wannan karon bazan canza ra'ayi ba, ina son inga ta dawo da walwalarta, wannan
karon dole tayi biyayya ga umarni na"
"Amma Alhaji baka ganin yin hakan tamkar ze ƙara tunzura rashin lafiyar ta ne, zaka
ƙara sawa rashin lafiyar ta ya tsanan ta, ko ka manta sharuɗan da likitoci suka
gindaya ne akanta?"
Alhaji Nasir Ya numfasa sannan yace
"Shima zaman ta a hakan bakomai ze ƙara mata ba face cigaba da dawwama a cikin
damuwa da rashin walwala, akwai buƙatar ko bayan raina Widad ya zama na tana da
kafaɗar da zata tada kai, ya zamana tana da wanda ze kula da rayuwar ta"
"Amma Alhaji wa zaku bawa Auren ta? ina fatan wanda zaku bawa yasan yanayin larurar
ta? Tunda kaga ba shiga mutane take ba balle a ce tana da wanda take so, kar a bawa
wanda besan ya take ba abu yazo ya ɓaci"
Alhaji Nasir yace "Ai ba wani bane za'a aura matan, fahad ɗin Bulama ne, itace dai
batayi wayon saninshi sosai ba, rabon da su haɗu tun tana yarinya ƙarama, Amma shi
ya santa kuma nasan baze bamu kunya ba Insha Allah, tunda itama tamkar ƙanwa take a
gurin sa"
Jinjina kai kawai tayi ba tare da ta kuma cewa komai ba.
Wajejen la'asar Amal ta shiryo cikin wata irin doguwar riga wadda ta kama jikin ta
matuƙa, se zuba ƙamshin turare take wanda turaren har hawa ka yake yi saboda ƙarfin
sa ta hau kan wani takalmi me uban tsini, duwatsun jikin rigarta se ƙyalli suke
suna rawa.
Cikin iyayi ta ƙarasa inda Yusuf yake zaune da su Nura da sauran ma'aikatan gidan
tace "Yaya Yusuf mu tafi ko na shirya" Ba musu Yusuf ya miƙe yayi wa su Isa
sallama.
Ya karɓi mukullin Motar Amal, suka shiga mota suka fice.
Yusuf na barin gurin Murtala me bawa shukoki ruwa yace "wai kunga abunda na gani ko
kuwa?"
Nura yace "mun gani, kai kaga wata irin kwarkwasa da take masa? , anya yarinyar nan
Amal ba san shi take ba? Kaga wani iyayi da take yi tana fari da idi"
Murtala yace "Amma kuwa da ta faɗo, duk zuƙa zuƙan Samarin dake zuwa gurin ta? duk
iya yin da wulaƙancin nata ta ƙare a direba, wallahi da tayi faɗuwar baƙar tasa"
Isa yace "to ai gara Amal ɗin akan yayar ta Ramla, kun san agola musamman in aka
samu guri akwai iskanci, yadda suke hura hanci suna Wulaƙanta mutane kai kace gidan
ubansu ne, Amma fa duk da haka gara nasu lafiya ne akan 'yar masu gida wai wa yaga
Azaba, idan bata ga dama ba fuskarta idan ka kalla seka yi fitsari a wando, saboda
sam bata da rangwame, Azababbiyar Yarinya idonta fiƙi fiƙi kamar me maye"
Nura yace "wallahi ko san haɗa hanya da yarinyar nan bana yi, nagode Allah da yasa
ba ita nake tuƙawa ba baban ta nake tuƙawa, ni nayi mamaki ma yadda Yusuf ɗin nan
har yanzu basu samu saɓani taci mutuncin sa ba, dan naga wani jin kan sa yake
shima, musamman idan yana jan manyan motocin nan se kace na gadon ubansa, kamar har
mantawa yake direba ne shi"
Isa ya gyara zama ya waiga sannan ya ƙara ƙasa da muryar sa yace
"ku nifa ban gama yadda da Yusuf ɗin nan ba, kuna ganin sa wani haɗaɗɗe da shi,
kullum tsaf tsaf da shi, babu alamar wahala a tare da shi, ga jan aji duk yafi mu
kyan gani sannan ace ya ƙare a direba anya babu lauje cikin naɗi a wannan harkar
kuwa?"
Murtalah yace "Nima nayi wannan tunanin, amma ya zamu san gaskiyar lamarin? Dan ya
fara bani haushi wallahi, yadda megidan nan ya fara wani girmama shi wai yana da
sunan yayan sa, har wani Yaya na yake ce masa shi kuma yana washe baki yana
sunkuyar da kai, damabidan mutum yavfiye sunkuyar da kai munafuki ne"
Isa yace "ku ƙyale shi zan bugi cikin sani inji ko zamu samu wani bayanin muji, ai
duniya seda labari, Amma ina tunanin ta yadda za'ayi kamar wannan da beyi kama da
wanda yake cikin wahala ba yazo yana aikin direba"
Yusuf ya ƙudurcewa ransa ze ɗan dinga sakarwa Amal, domin samun sanin wasu abubuwa
da suka shige masa duhu game da yanayin tsarin Rayuwar mutanen gidan. Suna tafiya a
hanya Amal tace
"Yusuf dan Allah ka dinga haƙuri da abunda Widad take maka, sam abunda tayi maka
ɗazu banji daɗi ba wallahi haka take bata san darajar ɗan Adam ba mussman talaka,
bata da mutunci, mu kanmu haƙuri kawai muke da ita sam bama jin daɗin zama da ita,
shiyasa babu wanda yayi farinciki da dawowarta"
Yusuf da sauri yace "A'a uwa ɗakina ce fa ranki ya daɗe, ya zaki ce bata da mutunci
a gabana? ai bazan ji daɗi ba gaskiya banji daɗin yadda kika aibata ta ba"
Kallon Yusuf tayi galala cike da mamaki tace "kana nufin baka ji haushin abunda
tayi maka bane? Ai ba ƙarya nayi mata ba, da tana da mutunci da bata muzanta maka
ba, harta jefe ka da key a fuska ba"
Yusuf yayi murmushi yace "yana da kyau mu dinga girmama doka kafin muyi ƙorafin
anci zarafin mu, ko ba'ayi mana adalci ba, da hannu na na saka hannu akan dokokin
ta kafin in fara mata aiki, na saka hannu na amince da zanbi sharuɗan data gindaya
min, dan haka tunda ni na saɓa abunda na sakawa hannu, komai tayi min be kamata
inji haushi ba, ko kuma ince bata da kirki ba, idan nayi haka banyi wa kaina adalci
ba"
Amal tayi ajiyar zuciya tace "indai wannan ce kai da kanka zaka dawo daga rakiyar
ta saboda wulaƙancin ta, dan wataran seta maka abunda zesa ka tsaneta tamkar
mutuwar ka, tun bamu kai haka ba mahaifiyar mu ta auri mahaifin ta muke zaune tare,
Amma bamu da daraja ko ƙima a idon ta, kai bamu ba har mahaifiyar mu bata ɗagawa
ƙafa, Alhaji Bulama ne ya bada shawarar a bar ƙasar nan da ita, shine ma muka samu
muka huta na wasu shekaru kafin ta dawo, se a dinga fakewa da bata da lafiya, tana
taka mutane tana nuna isa da Izza"
Yusuf yace "bata da lafiya kuma? Kamar ya bata da lafiya, Meke damun ta?"
Ɗan taɓe baki Amal tayi tace "wai bata da lafiyar ƙwaƙwalwa, ko da yake me lafiyar
ƙwaƙwalwa baze abunda take ba, wannan dukiyar ta mahaifin ta, da ita take taƙama da
ita take wulaƙanta mutane, ta yaga duk wanda yayi mata abunda yake saɓanin raa'yin
ta, aikin banza, dukiyar da'ake farautar ranta akanta, Amma take da damar Wulaƙanta
mutane saboda ita"
Da sauri Yusuf yace "kamar ya farautar rai? Ranwa ake farauta, saboda dukiya?"
"Ran Widad ɗin mana, yana ɗaya daga cikin dalilin da yasa ta bar ƙasar nan fa,
bayan larurar Ƙwaƙwalwa da take dashi ana farautar ranta ne, tunda maman ta ta rasu
take fama da larurar ƙwaƙwalwa, kuma a kazo ana nema a kashe ta, abundai gashi nan,
Amma kodan wulaƙanta mutane da take dole wani yai ƙudurin kashe ta ya huce
takaicinsa, bayan wulaƙancin da take wa mutane, har ɗaure mutane take sa ayi"
Jinjina kai Yusuf yayi yana kuma nazarin maganganun Amal, baya so ya cika ta da
tambayoyi, karta fuskanci wani abu dan haka yayi shiru yana ɗan satar kallon Amal
yana tunani a ransa.
Yusuf ya kai Amal wani katafaren mall kaman yadda ta buƙata ta dinga ɗibar kaya,
sannan tace Yusuf ya ɗauki abunda ya keso. "A'a nagode amma ni bana buƙatar komai"
Amal tace "haba Yusuf dan Allah ka ɗauka, karka ji komai" Fafur Yusuf yaƙi yadda ya
ɗau komai se haƙura tayi.
Bayan sun dawo gida tace dan Allah ya taya ta ɗaukar kayan da ta siyo, babu musu ya
ɗau kayan yabi bayan ta kamar yadda suke da Widad, Sedai tun a babban falon ƙasa
suka ci karo da hakimar ƙafar ta ɗaya kan ɗaya tana shan tea, gefen ta kuma tana
bawa magenta madara, bata kula su ba su kayi gaba za su wuce, muryar ta suka jiyo
tace
"Stop there" ta faɗa kai tsaye cikin bada umarni, gaba ɗaya suka tsaya suna jiran
me za tace.
Se da ta ja wasu seconds sannan tace
"Amal yaushe muka fara sharing ɗin abu nida ke ne ban sani ba? Ya akayi matsayinki
har ya kai kiyi amfani da abina ba tare da kin nemi izini na ba?" tai maganar tare
da miƙewa tsaye, tavtako ta zo har inda suke tsaye ta kalli Amal, ta tsaida dubanta
kan Amal, Amma tace wa Yusu
"waye ya ɗauke ka aiki a cikin gidan nan?"
"kece ranki ya daɗe" ya faɗa cikin girmamawa
"Wa kayi wa aiki yanzu?" tai maganar me cike da bayyanar da tsantsar Izzar ta
" 'yar uwarki ranki ya daɗe" ya bata amsa
Ta ɗan lumshe ido sannan ta buɗe tace "Na taɓa gaya maka ina da ɗan uwan ko' yar
uwa ne?"
"A'a"
"lokacin dana ɗauke ka aiki na gaya maka nida wani zakayiwa aiki?"
"A'a" ya sake bata amsa
Ta maida idon ta kan Yusuf cikin ɗaga sauti tace
"Ka karyamin doka karo na biyu da wani suna ya kamata in kira kane? Bagidajen ina
ne kai? Ko kuma ince daga wani jejin kake? a haka you look civilized amma kwata2
shashasha ne kai, hala ka manta akan death contract kayi signing? Inaga ka manta
ne, ko kuma ka ɗauka wasa ne shiyasa kake wasa da rayuwar ka"
Ya girgiza mata kai alamar A'a
Hayaniyar da Hajiya Halima take ji sama sama ne ya sa ta fito ita da ramlah suka
tsaya suka yi cirko cirko a falon Widad tana ta zuba tsiyata kunta san ranta.
Widad tace "Yanzu ina maka hukunci se ka kirani azzaluma ko? Saboda haka ɗabi'ar ku
ta matsiyatan mutane take, ku kullum akan daidai kuke masu kuɗi kuma Azzalumi ko?,
dukda bana maimaita magana yau zaka sani na maimaita, Ni Widad ban yadda da kowa
ba, duk yadda muke da mutum karyamin dokoki na daidai suke da yunƙurin cin amana
ta, kuma penalty ɗin wanda yaci amana ta, bana jin tantirin talaka wanda bashi da
komai kamar ka ze iya ɗauka "
Amal tace " haba Widad be kama......
Ɗaga mata hannu Widad tayi ba tare da ta kalli Amal ba tace "har yanzu 'yar alfarma
ce ke a cikin gidan nan, matsayinki be kai na 'yar masu gida ba, karki ƙara
gangancin ina magana ki katseni ko kisamin baki, idan ba haka ba kin san sauran,
kai kuma daga yau nikaɗai kake wa aiki a cikin gidan nan, ban yadda wani ya saka
aiki kayi ba, duk wanda yace kai wani abu kace Widad kake wa aiki ba wani ba,
sannan kayi a rabin salary ɗinka shine hukuncin karya min doka da kayi har sau biyu
dismiss from here"
Yusuf ya risina ya ɗanyi murmushi yace "godiya nake uwaɗakina, Allah ya ƙara girma
Insha Allah zanyi ƙoƙari in kiyaye dokokin ki, bazan ƙara karya miki doka ba, Allah
ya huci zuciyar ki"
Gaba ɗaya suka bi Yusuf da kallo wato shi duk wannan cin zarafin da aka yi masa
godiya yayi, lallai wani talakan Jaki ne, besan ciwon kansa ba, Ramlah ta faɗa a
ranta.
Widad ta kallesu ɗaya bayan ɗaya tace "bana buƙatar kowa a falon nan, madam zaki
iya jan zugarki ku ɓace min daga nan"
Saboda tsabar baƙinciki da takaici Amal watsi tayi da kayan shopping ɗin da tayi a
falon, tai cikin part ɗinsu da gudu tana kuka, abun yayi yawa taji zafin cin
mutuncin da akayiwa Yusuf ga tsabar wulaƙanci da suke fuskanta a gidan nan se kace
Almajirai, kokuma wasu bayi.
Ramlah ta kalli mahaifiyar su tace"Mummy am tired wallahi enough is enough are we
slaves? see how this little baby is shouting at both of us including you, Mummy you
have to do something"Kafin Mummy tayi magana Amal ta shigo tana kuka.
Mummy tace "Amal meya saki kuka?"
"gaskiya ni Mummy zan tattara kaya na in bar gidan nan na gaji, wannan wane irin
cin zarafi ne?"
Mummy tace "duk nasan da haka amma kuyi haƙuri ku ƙara wataran se labari da munsamu
abunda muke so shikenan fa an wuce gurin"
Amal tace "dan Allah Mummy yaushe wataran ɗin nan zata zo, shekara nawa muna zama
kaman bayi? Wallahi nagaji kalli cin mutuncin da tayi wa wannan bawan Allah dan
kawai ya kaini unguwa"
A fusace Ramlah tace "dallah rufewa mutane baki, dan taci masa mutunci seme ina
ruwan wani? Shi ta fara yiwa cin mutunci? Dama naga yadda kike wani zaƙewa a kansa
tun wuri ki nutsu dan ni natsane shi wallahi sam ban yadda da shi ba"
Amal tace "Malama ba ruwan ki da abunda nake yi seki ta tsanar tasa ai, seki kashe
shi tunda kin tsane shi"
Mummy tace "kunga dan Allah ya isa haka kar kuyi min faɗa, ni kaina ban yadda da
wannan Yusuf ɗin ba, narasa yadda aka yi megidan nan ya wani ɗaukake shi haka, ina
son sanin daga ina yake"
Haɗe rai Amal tayi ta zumɓura baki
Mummy tace "ku kuke tada hankalinku, Ramlah zancen da kika yi min ranan na tambayi
babanta ya tabbatar min da cewa Aurar da ita zeyi"
Da yake Amal bata san zancen ba da sauri ta waigo tace "Aure kuma? A hakan za ai
mata Aure? Waze kwashi wannan Jarabar"
Ramlah tace "Mummy dama na gaya miki, Amma wane me tsautsayin za'a liƙawa wannan
Mahaukaciyar? Nasan dai bata da saurayi to waze ma kulata taci masa zarafi"
Mummy tace "ba wani bane Fahad ɗin Alhaji Bulama ne"
Asahar Ramla ta saki tace "Wane Fahad ɗin?"
Murmushi Amal tayi tace "Bulama nawa muke da shi? Fahad dai da kika sani, Fahad
naki shine me tsautsayin"
Ramlah tace "Taɓɗijan wallahi da sake, baze yuwu ba akan me? Ita Hajiyar sa tana me
za'a aura masa wannan tantiriyar ga hauka gashi maybe ta gama watsewa da turawa,
shekararta nawa a turai, Allah kaɗai yasan me take acan baze yuwu ba"
Ta miƙe ta bar ɗakin tana masifa.
Yusuf be bar gidan ba ranar se bayan sallar isha'i. Koda yaje gida ya tarar Umman
sa ba taci Abincin dare ba shi take jira, seda sukaci Abinci suka yi hira sannan ya
koma ɗakin sa. Ya ɗakko laptop ɗin sa ya shigar da duk abunda ya faru da date da
komai, dukkanin hirar da suka yi da Amla seda ya rubuta sannan ya kwanta.
Tun daga ranar Yusuf yake taka tsantsan gurin bin dokokin Widad, Sannan yana ta
ƙara lura da yanayin mutanen gidan da ɗabi'ar kowa daga cikin su.
Widad ta aika Ramla ta kira mata Yusuf. Ramlah tana zuwa inda suke zama ta kalle
shi a wulaƙance tace "kai wa kake kazo inji waccan yarinyar"
Yauma Yusuf ya shirya tsaf ze kai Widad Store za tayi siyayya bayan fitar su,
Hajiya Halima ta aika aka kira mata Isa mai gadi, yaje ya same ta a ya durƙusa ya
gaishe ta, ta amsa masa a wulaƙance sannan tace
"kaine ka kawo wa Widad direba ko?"
"Eh nine Ranki ya daɗe"
"Good, ina son sanin daga ina yake?"
Isa ya risina sosai sannan yace "Wallahi ranki ya daɗe ban san daga inda yake zuwa
ba, nima wani abokina ne Sani ya kawomin shi yace ɗan uwan sane amma ban daga ina
yake ba"
"ka buɗe kunnen ka da kyau ka saurareni"
Isa yace "to Hajiya"
"Ina so duk yadda za'ayi in san daga ina yake? Daga ina yake zuwa gidan nan, sannan
ina so ka ƙara samun ido akan sa sosai ina tunanin akwai wani ɓoyayyen abu a tare
da shi"
"An gama ranki ya daɗe insha Allah zanyi yadda kike so"
"sannan wannan maganar ina so ta tsaya daga ni se kaine, bana son wani ya san munyi
ta"
"babu me ji ranki ya daɗe"
"tashi ka tafi" Isa ya tashi fita.
Yusuf kam wani katafaren shago ya kai Widad, ta siyi kayan da take buƙata, hatta
ruwan roba da zata sha seda ta siya abun ta.Banda kayan ciye2 da sauran kayan
ƙyale2
Seda sukaje gurin biyan kuɗi ta kalli Yusuf tace "jeka mota ka ɗakko jaka ta"
Ba musu yaje ya ɗakko 'yar ƙaramar jakar ta ya kawo mata"
"buɗe ka ɗakko ATM card ɗina"
Ya ɗakko ya riƙe aka lissafa kuɗi, kuɗi ne masu yawan gaske, ko a jikin ta tace
"basu ATM ɗin" ya miƙa musu suka saka a POS suka miƙo masa yasa ka password ya sa
hannu ya karɓa ya miƙo mata domin ta saka lambobin da zasu bada damar cirar kuɗin,
a hankali tai ƙasa da muryar ta tace
"7724" Yusuf ya gane me take nufi haka ya danna lambobin ya miƙa musu. Suka ciri
kuɗin su yana mamakin me yasa ta gaya masa password ɗin cirar kuɗin ta.
Sun fito harabar Store ɗin zasu tafi suka wuce ta gefen wani mutum dake ƙoƙarin
rufe motar sa yabi Widad da kallo tare da faɗin subhanallah.
Da sauri yabi bayan su Widad, Yusuf yayi gaba yana zuba kaya a mota mutumin ya sha
gaban Widad yace
"Ahh excuse me Madam you look so hot"
Zare glashin fuskarta tayi tai masa kallon sama da ƙasa ta mayar da glass ɗin ta,
tai gaba abunta.
Sake binta mutumin yayi ya sha gaban ta zeyi magana Widad tace "wai me kake nema
ne?"
Yusuf kam ganin ta tsaya ya sashi komawa inda take tsayen dan ganin meke faruwa.
Mutumin yace "Wow ashe bahaushiya ce? Gaskiya beb bazan ɓoye miki ba kin tafi da
imanina, kin min ina sonki, ki bani contact ɗinki mana se muyi magana, you look
sexy" yai maganar yana wani kashe ido irin na 'yan bariki tare da miƙowa Widad
wayar sa
Karɓar rantsatsiyar wayar tayi kaman gaske, ta sake ta a ƙasa ta fashe sannan tace
"waya gaya maka samun lamabr mace kamar ni a gurin ƙasƙantattun mutane marasa
amfani irinka abu ne me sauƙi, dalla matsa a gabana ko in tsinka maka mari sakarai
kawai"
Waro ido mutumin yayi "ni zaki tsinkawa mari? Kin san waye ni kuwa? In baki wayata
ki fasa min"
"Waye kai banda banza wofi, matsiyaci mara amfani? Kauce a gaban kafin inyi maganin
ka"
Kan Widad mutumin yayo yana kumfar baki "Wallahi sena nuna miki koni waye a garin
nan, 'yar uban waye ke da zaki min haka? Sena ci zarafin ki na wulaƙanta ki"
Tuni Attention ɗin mutane ya fara yowa kansu kaman ze daki Widad, Yusuf ya shiga
tsakanin Widad da mutumin ya kalli mutumin yace
"kana ta mana kumfar bakin ba' a san waye kai ba, ita kasan wacece? Ina ruwan ka da
ita da zaka biyo ta kafaɗi maganar banza akan ta, ka kiyaye harshen ka kafin a nuna
maka ƙarfin ikon data ke dashi"
"Kaikuma waye kai waye ya sakoka a cikin wannan maganar?" mutumin yasa hannu a
aljihu ya miƙowa Yusuf id card ɗinsa, kafin Yusuf ya karɓa Widad tasa hannu ta
karɓe ta duba id card ɗin nasa sannan tace
"Ashema matsiyaci ne taƙamarka kaki ko? Zan iya sawa a keta kakin naka a gaban
mutane a wulaƙanta ka, a tozarta min kai, sannan in ɗaure ka, kuɗi sunfi wannan
kakin banzar da kake tin ƙaho dashi, Widad Nasir Daula inada Arzikin da zan
wulaƙanta ka ka ƙare a gidan yari sakarai kawai " tayi jifa da ID card ɗin nasa ta
tofa miyau akai
Ai Sunan ta data faɗa yasa mutumin nan wani mummunan zare ido tare da sauke
numfashi yana kuma maimaita sunan nata.
Widad ta wuce mota Yusuf ya bita suka tafi, suna tafe tana ƙwafa tareda yin tsaki
jefi2 kallon ta kawai Yusuf yake.
Suka isa gida ta buɗe murfin motar ta fice abunta, Yusuf ya ɗebo kayan ya bita
dasu, matar gidan tana falo tana kallo, Yusuf ya shigo yabi bayan Widad har ɗakinta
ya ajiye mata kayan, ze juya ya ɗebo sauran tace "ɗan tsaya" Yusuf yaja ya tsaya
tazo ta duba kayan, ta ɗakko wata Jaka da turaruka a ciki ta ajewa Yusuf, cike da
iko da kashedi tace
"daga yau karka ƙara saka wannan banzan turaren da kake sawa in zaka zo inda nake,
ga wannan turarukan kar in kuma jin kasa wannan turaren dan yana samin tashin
zuciya ina fatan ka gane?" jinjina mata kai yayi alamar Eh.
Ya ɗau ledar turaruka ya fita ya kwaso mata sauran kayan ya kawo mata, yana zuwa ya
tarar ta shiga wanka, dan haka ya haɗa da ledar turarukan da ta bashi, ya ajiye
mata akan gadonta yai ficewarsa.
Bayan Yusuf yayi sallar Azahar ya nemi guri ya zauna a inda suka saba zama da
sauran ma'aikatan gidan, Isa mai gadi yace "Yusuf manyan ƙasa, gaskiya ka ciri tuta
a gidan nan, ina jinjina maka"
Yusuf yace "Mena yi na cancanci jinjina haka"?
"Ahh irin yadda kake jure cin mutuncin wannan yarinyar mana, naga da alama kaman
kai bata yi maka wulaƙsncin, amma dukda haka kana haƙuri wallahi yarinya se kace
sheɗaniya, zuciyar ta babu Imani se miyagun Aƙidun turawa to aibtama ci uwar turawa
wannan"
Yusuf yace "kaga dakata Isa, kana gidan mahaifinta kana cin Arzikin su sannan kuma
ka dinga zagin ta? Aiba'a haka a rayuwa, ni duk wannan abubuwan da kuke faɗa akan
ta ni bana gani, danni ba ta yi min ba"
Isa yace "ni na rasa me yasa kullum kake ƙoƙarin kare ta, da anyi magana ka hau
kare ta, ina tausayawa ranar da zata maka mugun halin nata, naga yadda zaka yi ai"
"kaga Isa abar wannan maganar dan Allah"
Isa yace "shikenan tunda haka kace, nikam nace ina Sani kuwa? kwana biyu baya zuwa
gidan nan ko a waya bana samun sa, nasan kai kuna haɗuwa tunda unguwar ku ɗaya"
Yusuf yace "waye ya gaya maka unguwar mu ɗaya?"
"Ai gani nayi ɗan uwanka ne shiya kawo ka gidan nan, dan haka nayi zaton unguwar ku
ɗaya"
Yusuf ya murmusa yace "A'a ba unguwar mu ɗaya ba"
"to kai a wace unguwa kake? Ko ince inane ƙauyen ku? Dukda baka yi kama da 'yan
karkara ba, ni mamaki ma nake yadda matashi kamar kai yake aikin direba"
Yusuf yayi murmushi yace "Isa kenan, dama su' yan ƙauyen wata kamace dadu ta daban
ne? meyasa ka damu da sanin unguwar da nake?, indai Sani ne zan nemo maka shi dukda
ba unguwar mu ɗaya ba, zan kawo maka shi har nan yazo"
Yusuf ya basar da zancen yaƙi gayawa Isa unguwar da yake.
Duk wasu hikimomi Isa yabi, Amma Yusuf ya nuna masa ƙwarewa irin ta jami'in sirri
ya basar da zancen ya shiga wani. Daga ƙarshe ma ya miƙe ya bar gurin, Isa yace
"wannan anyi Jarababbe me taurin kan masifa, ƙiri Ƙiri yaƙi gayamin, amma zaka ga
tsiya, in kasan wata baka san wata ba, zan biyo maka ta inda koka ƙi Allah seka
faɗa"
Share please 🙏🙏🙏
Masoya masu Comment ina godiya, Allah ya bar ƙauna 😍 😍 😍 ku sani yanzu aka fara
wasan, amma gaskiya idan ba'a Comment yadda nake so zan ɗau matakin da ya dace, dan
Allah idan kin karanta idan kin san Tanks kawai zakice koki turamin sticker ki riƙe
abun ki please 🙏🙏🙏
Domin sharhi, gyara ko shawara ƙofata a buɗe take, feel free to contact me, sedai
in ban buɗe saƙon da wuri ba ayimin afuwa, ina godiya 😍
Ayshercool 07063065680
_*AƘIDATA*_
PERFECT WRITERS ASSOCIATION
(WE AIN'T PERFECT BUT WE ARE ALWAYS TRYING OUR BEST, TO MOTIVATE AND ENTERTAIN OUR
READERS)
https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/
P. W. A
*Story and written by*
_*AISHA HUMAIRA (Daddy's girl)*_
The experience writer of *ABDUL JALAL** WATA KISSAR.... (SAI MATA) *And now *AƘIDA
TA *
I dedicated this book to my Mum (Malama Nafisat Adam Muhammad) i love you mum
Haƙƙin Mallaka ⚠ : Littafin nan mallaki nane, tun daga sunan labarin zuwa abunda ya
ƙunsa, ban yadda wani ko wata ya sauyamin ko yin Amfani da wani ɓangare na labarin
ba ba tare da izinina ba, Nagode
https://www.wattpad.com/user/Ayshercool7724?
utm_source=android&utm_medium=link&utm_campaign=invitefriends
ELEGANT ONLINE WRITER'S
PART1 Page 6
Widad kam koda ta fito daga banɗaki, da jakar turarukan nan data bawa Yusuf ta fara
yin arba akan gadon ta, ta ƙarasa a hankali ta duba, sune dai turarukan da ta
bashi, "lallai wannan ɗan rainin hankali ne, ni zan bashi abu yazo ya ajiye min?"
Fita tayi falo ba kowa dan haka ta wuce part ɗinsu Amal, tana zuwa ta tarar da su a
kitchen suna ta girki suna hirarsu, Wai Ramlah zata yi baƙi, se hada hada suke da
kaji da sauran kayan masarufi.
Basu san da zuwan Widad ba se muryarta da suka ji cikin isa tace"Ramlah kije gate
ki kiramin driver na yanzu"Cike da ɓacin rai, ba tare da Ramlah ta kalleta ba tace
"to"Haka Ramlah ta fita tana ƙunƙuni ta nufi bakin gate.
Tana zuwa ta tarar Yusuf ya siyo Abinci ze fara ci, Ramlah tazo kansa ta tsaya ta
ƙare masa kallon up and down a wulaƙance, ta kalli gurasar gaban sa ta masu balango
da nama ta kuma kallon sa ta taɓe baki ta ɗanyi tsaji taxe
"kai kazo inji waccan yarinyar"
Banza Yusuf yayi mata ya cigaba da ƙoƙarin cin Abincin sa.
"Wai baka ji ne?" ta masa magana cikin tsawa.
Nura direban Alhaji yace "Yusuf da kaifa take magana"
Yusuf ya ɗago ya kalli Nura yace "yawwa Sunana ka ambata, meze hana ta kirani da
Sunana dan me zata cemin kai, kuma ni ban san wata yarinya a gidan nan ba"
Mamakine ya kama Ramlah, dama yana magana haka da wulaƙanci amma yake iya tsayawa
Widad taci zarafin sa? Ba mamaki saboda kwaɗayin abun duniya kar a kore shi shiyasa
yake shnaye wulaƙancin Widad, amma har ita wannan talakan ze buɗe baki ya gayawa
magana a fusace tace
"kai saurara bazan kira sunan naka ba, uban waye kai da zaka dinga tambayar ban san
sunan ka bane? Kai a wa? Ka kiyaye ni wallahi bana son shirme idan kace zakamin
rashin mutunci zaka ga abunda ze biyo baya, sannan idan kaga dama kaje, in baka ga
dama ba karka je ka san sauran"
Yusuf yayi kaman ba da shi take ba ya ci gaba da antaya gurasar sa. Ran Ramlah ne
yai mugun ɓaci da ganin wannan rainin hankalin na Yusuf, ƙwafa tayi ta koma cikin
gida.
Nura yace "Yusuf dan me zakayiwa Ramlah haka? So kake kaja wa kanka a kore ka?"
Yusuf yace "Nura kenan, to a korenin mana seme?" ya ci gaba da cin gurasar sa seda
ya gama cin Abincin sa, Sannan ya miƙe ba tare da ya kuma cewa komai ba ya nufi
cikin gidan.
Yana zuwa ya tarar da hakimar ta ɗora kafarta akan centre table tana jiran isowar
sa.
Yusuf ya ƙaraso cikin girmamawa yace "gani ranki ya daɗe"
Widad tace "se yanzu ka ga damar zuwa? Na tura a kira ka kace bazaka zo ba seka
gama abunda kake?"
Da confidence ɗin sa yace "bance ba zanzo ba ina cin Abinci ne lokacin"
"ba tun ɗazu aka kaiwa ma'aikatan gidan nan Abinci ba?"
"Aini ban sani ba munfita tare da ke, kuma ni ba'a taɓa Abinci ba"
Tsuke Fuska Sosai Widad tayi tace "Ramlah kiramin larai" Ramlah ta juya ta tafi
kiran larai, Widad ta kalli Yusuf a wulaƙance tace
"me kake nufi da in baka abu ka ajiyemin kayi tafiyar ka? Me kake nufi da hakan?
Harni zan baka abu saboda wulaƙanci da girman kai irin na talaka harni zaka
gwadamin halin naku na talakawa na girman kan banza akan abunda baku dashi"
Yusuf ya ɗanyi murmushi yace "ba girman kai bane Madam, bakomai ne yasa na ajiye ba
face abunda kika bani yafi ƙarfin talaka kaman ni in saka, duk wanda yaji ƙamshin
wannan rantsatsun turarukan to tabbas zan zama abun tuhuma ga al'umma, kiyi hakuri
wannan turaren seke"
Wani irin murmushi Widad tayi wanda ita kaɗai tasan ma'anar sa, sannan ta tsuke
fuska tace
"Amma fa ka iya rainin wayo sosai, shikenan amma idan na kuma jin tashin wannan
banzan turaren a jikin ka kasan sauran"
"Insha Allah bazan sake saka turaren da shugaba ba taso ba"
Ramlah ce ta dawo tareda 'yar aiki larai na biye da ita, jikin larai se tsuma yake
tazo gaban Widad ta durƙusa.
"Larai Me yasa ake hana direba na Abinci?"
Larai ta kalli Ramlah a ɗan dirirce sannan ta dawo da kallon ta kan Widad za tayi
magana, Widad tace "Idan kikamin ƙarya sena hukunta ki"
"Wallahi ranki ya daɗe Hajiya ce tace kar a sake a bashi Abinci, ba a cikin
ma'aikatan gidan nan yake ba"
Widad tace "hmmm tunda ita ta siyo ta kawo ko? Ke Ramlah kije ki gayawa
mahaifiyarku, ko kare na ajiye a gidan nan ya zama dole a bashi duk abunda yake
buƙata tunda lokacin da'ake tara dukiyar gidan nan bada gumin ta aka tara ba,
sannan....
Yusuf katseta ta hanyar cewa "Amma uwa ɗakina ina ganin idan kika yi haka baki kyau
ta ba, ki bari...
"Shut up....., do you think am doing it because of you?, let me tell you something,
ba nace a baka Abinci a gidan nan dan komai ba sedan kauce wa hatsarin dake tattare
da hakan, karka manta YOU SIGN ON YOUR DEATH CONTRACT ya rage naka kula da rayuwar
ka"
Ta miƙe ta nufi part ɗinta cikin takunta na isa.
Jiki a sanyaye Yusuf ya fice yana mamakin waime take nufi da wannan death contract
ɗin ne?
**********************
Manyan Mutane maza su uku, zaune a wani ƙaton falo, da ganinsu kasan suna da kuɗi
saboda yanayin suturar jikin su, zaune suke suna tattaunawa fuskarsu ɗauke da
damuwa Ɗaya yace "nifa Al'amarin nan ya fara isa ta, tsawon shekaru muna fama akan
abu ɗaya, amma abu yaƙi ci yaƙi cinyewa nifa na fara karaya"
"haba Alhaji Haruna, akan me zaka karaya haka? Ai ba gudu ba ja da baya, se burinmu
ya cika se mun samu abunda muke nema, abun baƙin cikin yarinyar nan muguwar
gaddamammiya ce, wani irin mugun Aƙida ne da ita tamkar tasan abunda muke nema, sam
bata da wani mutum data aminta da shi ya shiga jikin ta balle mu samu abunda muke
so"
Alhaji Haruna yace "kai bari kawai Alhaji Musa, Yarinya kaman ba jinsin mutane ba,
duk na kusa da ita ba wanda bamu bi ba amma bamu samu abunda muke buƙata ba, Kalli
yadda shirin mu na jiya ya wargaje.
"Hmmm bari kawai kaga jiya yadda ta wulakanta Jamil a harabar Store ɗin nan, ina
zaune a mota na ɗauka zeyi ƙoƙari ta bashi lambar wayarta amma ta fasa wayar ta
ƙare masa zagi a gaban mutane"
Alhaji Haruna ya girgiza kai "yanzu meye abunyi ko mu kashe yarinyar nan mu huta mu
kama Nasir daula ta ƙarfin tsiya mu samu abun nan"
Alhaji Munir yace "kul Haruna, in baka iya kama ɓarawo ba shi seya kama ka, wannan
ai wauta ne, kasan yarinyar nan a gurin sa ta gaji wannan taurin kan, idan muka
kashe ta tamkar mun kashe Nasiru Daula ne, kuma kasan akwai hatsari sace
shahararren mutum kaman Nasiru a ƙasar nan, dan haka ita yarinyar ya kamata mu ci
gaba da farauta "
Alhaji Musa yace " to sace ta zamuyi ko yaya? Duk hanyoyin da ya kamata mubi munbi
amma abu ya gagara, idan muka bari ta koma ƙasar waje aikin mu ze kuma komawa baya
ne"
"to sace ta zamuyi ko kuwa?"
Alhaji Munir yace "A'a a yanzu ba sace ta ya kamata mu yi ba, zamu ci gaba da bin
diddigin ta, kun san sace wannan yarinyar se anyi kyakykyawan shiri"
Alhaji Musa yace "Anya Alhaji Bulama be san komai akan abun nan ba? naga amintaccen
Nasiru Daula ne ko zamu gayyato shi cikin mu?"
"Taɓɗijan ashe tamkar mu fita mutonawa kanmu asiri ne, kome zamuyi kar mu shigo da
bare cikin mu, zamu ci gaba da yin zagon ƙasa ne a sirri har mu samu abunda muke
so"
Haka suka ci gaba da tattauna wa a tsakanin su.
**********************
Yusuf na bakin gate ya bada hankalin sa akan wayar sa, Amal ta fito yana ganin ta
yai murmushi tace "Sannu da hutawa"
"Yawwa ranki ya daɗe ya gidan?"
"lafiya ƙalau, Widad na nemanka"
"to shikenan muje" ya tashi ya bita har part ɗin Widad, suna shiga Widad ta tsira
musu ido, ta sauke idon ta akan Amal ta ƙura mata ido ko ƙyaftawa ba tayi, Sum sum
Amal ta fita ta basu guri, zuciyar ta ɗauke da zazzafan kishin barin Yusuf daga shi
se Widad a ɗaki.
Widad ta ƙare Yusuf kallo kaman bata sanshi ba kallo ɗaya yayi mata ya ɗauke kai,
dogon wando ne a jikin ta da vest ko kunya ba taji a irin shigar data keyi Widad
tace "zan fita anjima ƙarfe huɗu zanje gurin birthday, ƙarfe huɗu, in kaga dama ka
tafi yawon ka"
Ya jinjina mata kai yace "Insha Allah zan kiyaye lokacin" daga nan ya fice.
Ƙarfe huɗu saura kwata akayi sallar la'asar, Yusuf ya gabatar da sallar la'asar,
sannan ya shiga cikin gidan.
Yana zuwa ya tarar da Alhaji Nasir da iyalan gidan, gefen sa ga trolley alamun
tafiya zeyi.
Yusuf yace "barka da rana Yallaɓai"
Alhaji Nasir yace "Yawwa Yusuf ya aikin, ya haƙuri da Daughter"?
Murmushi Yusuf yayi yace "ai mune take haƙuri damu, Aiki kuma Alhamdilillah,
mungode Allah"
Alhaji Nasir ya jinjina kai yace "tafiya ta kamani zani Paris, se shagwaba take wai
bazan tafi ba, Yusuf ga amana ta nan, na bar amanar daughter na a hannun ka, har
inje in dawo kar a bari tayi kuka, idan tana buƙatar wani abun akula ayi mata dan
Allah"
Widad da sauri ta kalli mahaifin ta sannan ta kalli Yusuf a wulaƙance tace "Allah
ya kiyaye Ina da komai da nake buƙata, dan haka bana buƙatar taimako daga gurin
kowa balle talaka kaman direba na"
Gaba ɗaya suka ɗauke wuta, shi kansa Alhaji beji daɗin abunda Widad ɗin ta faɗa ba.
Yusuf kuwa yai murmushi yace "indai wannan Amanar ce Alhaji na yadda na karɓa,
Insha Allah zaka je lafiya ka dawo ka tarar da ita, Allah ya bani ikon kula da ita"
Alhaji Nasir yace "Ai dama nasani duk me sunan Yaya na mutumin kirki ne, ban taɓa
ganin Yusuf wanda ba shi da kirki ba, Allah yayi wa Rayuwar ka Albarka"
Yusuf ya amsa da Ameen
Ita kuwa Maman su Ramla tamkar ta haɗiye zuciya, wai direba ake bawa amanar 'yar
masu gida, tunda ita cinye ta zata yi ai dole a ce direba ya kula da ita, shikenan
direba ya kula da ita in yasan wata ai be san wata ba. Ba ƙaramin haushi take ji
yadda Alhaji Nasir ke nuna wa Yusuf kulawa ba.
Yusuf ya ɗaukar wa Alhaji Nasir trolley ɗin sa suka fito harabar gidan, Nura ya
taho jiki na rawa ya buɗewa Alhaji Nasir bayan mota ya shiga.
Ramlah ce ta taho da nufin itama ta shiga motar ayi rakiyar Alhaji Nasir da ita.
Widad ta kalli Ramlah tace "ba gurin ki a motar nan, dan bama buƙatar rakiyar ki"
ta kalli Yusuf tace "shiga gaban motar" .
Nura ya tsaya ya kalli Widad ya kalli Yusuf, Yusuf ma saroro yayi yana kallon
Widad, Waidad tace"ba kaji ba? ko sena maimaita" Yusuf ya buɗe gaban mota ya
zauna, yayin da ita da mahaifin ta suka shiga baya suka zauna.
Nura ya ja mota suka tafi, Ramlah ta rasa me zata yi ne, Mummy tace "yi haƙuri
ƙyalesu, in sun san wata basu san wata ba" Haka ta rarrashi Ramlah suka wuce cikin
gida.
Jefi2 Alhaji Nasir da Widad suke hira, yayin da Yusuf da Nura suka yi shiru kowa da
abunda yake saƙawa a ransa
Suna cikin tafiyar ne, Alhaji Nasir yace "daughter na dan Allah ina sake roƙon ki,
karki watsamin ƙasa a ido, idan fahad ya dawo ku daidaita, ina son ganin ki cikin
farin ciki ne daughter bana son irin wannan rayuwar takura kan da kike yi"
Banza tayi da Daddyn, seda aka ja lokaci sannan tace "Daddy na fara tunanin ka
dena sona, idan har kana tunanin yi mun aure ne ze sani farinciki, to tabbas zaka
sake jefani ne cikin wata damuwar, kafi kowa sanin meye buri na, Aure ze zama
tamkar barrier ne a cimma buri na"
"Daughter yanzu abun nan baze wuce a gurin ki ba? Ba zamuyi haƙuri ba mu barwa
Allah, ba zamu yadda komai ya faru damu muƙaddari ne daga Allah ba?"
"Daddy bazan taɓa mantawa ba, kuma bazan yafe ba sena cika buri na, kuma ka dena
min batun Auren nan bana so, bazan iya zama a ƙarƙashin wani ba inyi masa biyayya
ko waye shi, ku ƙyaleni da zancen Auren nan please bana so"
Ta mirror Yusuf yake ganin Widad yadda Hawaye ya wanke mata fuska, ta rintse ido
tana magana cikin kuka.
Alhaji Nasir ya rungume ta a jikin, sa cikin sigar rarrashi yace
"Am sorry my dear, i don't mean to hurt you, nasan tamkar na fama miki wani ciwo ne
dake cin zuciyar ki, amma kiyi haƙuri ina ƙoƙarin wanke miki wannan damuwar ne, ina
son komai ya wuce kema ki fuskanci rayuwar ki"
"No Daddy i can't, ta yaya zan manta da abunda ya faru, Daddy bazan ƙara yadda da
kowa ba, yin aure na tamkar ƙara kusanto da maƙiya jikin mune, ni bazan yadda da
kowa ba balle a sake cutar dani a karo na biyu ba, Daddy i repeat my self bana son
kowa a kusa dani, bana so" sosai kukan nata yake ƙara ƙarfi harda sheshsheƙa.
"yi haƙuri daughter na, Amma ina sa ran Insha Allah zakiyi alfahari da auren fahad,
yana da kirki sosai ɗan uwanki ne, tunda jinin Alhaji Bulama ne, bana tunanin akwai
wata cutarwa da Alhaji Bulama ze mana"
Haka nan Yusuf yaji ta bashi tausayi, duk abunda zesa Widad ta sauke wannan izzarta
ta, ta dinga irin wannan kukan lallai ba abune ƙarami ba.
Har suka je airport Widad kuka take, har kyawawan idanuwan ta sunyi ja, haka suka
yi Sallama da mahaifin ta. Alhaji Nasir ya dubi Yusuf yace "Yaya na a kulamin da
amana ta"
A fusace Widad tace "Daddy karka ƙara cewa ka bar amana ta a hannun wani , ka barni
a hannun Allah zaka je ka dawo ka tarar dani lafiya Insha Allah, amma zuwa yanzu
yaci ace kayi darasin da bazaka ƙara bawa mutum yadda da Amana ba, narasa me yasa
Daddy ka kasa fahimta ta"
Alhaji Nasir yai murmushi ya riƙo hannayen ta yai mata raɗa a kunnen ta, sannan a
fili yace "ina da surprise a gare ki idan na dawo, ku koma karku yi dare my
lovely"
Haka Widad suka juya zuwa mota, yanzu ma Nura ne ke jan Motar
Widad tace "yi parking anan" Nura ya tsaida motar, tace masa
"gaya masa inda farm house yake"
Nura ya gane abunda take nufi, dan haka yaiwa Yusuf kwatancen inda tace.
Daga nan ta ɗaga idon ta wanda suka jiƙe da hawaye tacewa Nura
"fita ka bar motar nan ka hau ta haya ka koma gida, Kaikuma ka karɓi tuƙin mu tafi"
Nura yace "Amma ranki ya daɗe motar Alhaji ce kuma....
"motar Alhaji ta ubanka ce? Ko ta Ubana?" ta jefo masa tambayar
"A'a amma ban fito da kuɗi ba"
"Idan ka bari na sake magana, zan ɓata maka rai fiye da tunanin ka, fita daga motar
nan nace, idan ba tare muka haɗa kuɗi muka siya ba"
Haka Nura ya fice daga motar, Yusuf ya karɓi tuƙin.
Yusuf ya dinga bin kwatancen da Nura yayi masa, har sukaje gidan gonar Widad bata
dena kuka ba, Sam Yusuf yaji beji daɗin yadda take kukan ba, gashi ita ba'a iya
mata balle ya rarrashe taWani irin tangamemen gida ne har yaso yafi gidan da su
Widad ke Rayuwa a ciki girma, Yusuf ya fara tunanin anya wannan gidan gona ne? Horn
Yayi aka buɗe masa wani jibgegen gate me matuƙar nauyi ya shiga da Motar cikin
gidan.
Ma'aikatan gidan ne suka dinga tahowa cikin matuƙar sauri inda motar su Widad take,
Kallon gurin Yusuf yake yi, dabbobi kala kala a ɓangarori daban daban wanda idon sa
yake iya gani, gefe kuma gida ne sosai ginanne a ciki, cikin zafin Nama ta fito
daga motar tana ta Hawaye, cikin girmamawa ma'aikatan ke zubewa suna gaishe ta,
babu wanda ya samu Arziƙin kallo balle ta kula shi.
Cikin matuƙar sauri ta nufi ɓangaren da yake gida ne a cikin gurin, Yusuf ya bita
shima cikin sauri, binsu ma'aikatan suka yi da kallo mussman Yusuf, Wani irin
murgujejen kare ne fari da baƙi a jikin sa ya nufo inda Widad take yana wani irin
gurnani gami da sufa.
Durƙusawa tayi ƙasa Karen yazo yana zagaye Widad yana shanshana jikin ta, shafa
gashin karen tayi tana kuka tace "I miss you Miz"Karen ya kwantar da kansa a jikin
Widad yana zaro harshe, ko tsoron sa bataji balle ƙyama.
Haka karen yai lamo a jikin ta tareda ƙurawa Yusuf ido, ita kuma tana cigaba da
kuka, can kuma ta shafa kan karen tace "Excuse me Miz, I will see you later"
Ta miƙe zata yi gaba Yusuf ya bita, Karen nan ya bishi yana masa wani irin haushi
da gurnani yana zubar da yawu, Yusuf a ransa yace "Wane irin jarababben kare ne
wannan se kace zaki?"
Widad ta juyo ta kalli karen tace"don't Worry, I trust him Miz"
Daga nan ta miƙe ta ci gaba da tafiya, Aikuwa tana faɗar hakan karen ya dena bin
Yusuf.
Sunyi doguwar tafiya sosai a cikin gidan, dabbobi daban daban wasu daka gansu kasan
sun sha banban da kalar namu na Nigeria.
Gida ne sosai a ciki ginanne me matukar kyau, ya tsaru sosai sedai da alama babu
mutane a ciki.
Wani ɗaki Widad ta nufa ya bita, suna shiga ɗakin Widad ta ƙara sautin Kukan ta,
wani katafaren gado ta nufa ta zube a gaban gadon ta ci gaba da rera kukan ta, daga
jin yadda take fidda sautin kukan kasan kuka ne me taɓa zuciya.
Yusuf se binta yake da ido cikin tausayawa halin da take ciki, amma bashi da damar
yayi mata magana ko ya rarrashe ta dan bata son shisshigi, yanzu zata masa rashin
mutunci.
Ba tare da ta kalli Yusuf ba, a hankali tace "Excuse me please" Yusuf ya jinjina
kai ya fice ya tsaya a wajen ɗakin, kusan mintuna talatin yana tsaye yana jiran ta.
Fitowa tayi ɗauke da wata shigar ta daban, kamar ba ita ba, shigar jikin ta ba kace
musulma ce ba.
Kallon ta Yusuf ya tsaya yanayi duk wani ilahirin surar jikin ta seda ta bayyana,
Farar fatar ta se ɗaukar ido take.
"let's go" shine abunda ta cewa Yusuf, haka yabi bayan ta zuwa inda motar su take,
nan ma ma'aikatan ne suka kuma biyo ta suna mata Fatan Alkhairi, gaban motar ta
buɗe ta ɗebo kuɗi bandir bandir ta basu, ta shige motar Yusuf yaja motar.
Wani ƙaramin kati ta miƙawa Yusuf, kwatancen inda gurin partyn yake ne, shi sam ya
manta tace ze kai ta gurin birthday ne, ga yamma tayi sosai, se dai bashi da ikon
magana haka ya bi kwatancen.
"Hello ranka ya daɗe, bayan tsawon shekaru yaufa tazo gidan gona"
"Me tazo tayi?"
"Nima ban sani ba Yallaɓai"
"ta fita da wani abu daga gidan ne?"
"A'a bata fita da komai ba, kaya kawai ta canza sannan ita da wani matashi suka zo
yana tuƙota"
"Direban tane kokuma waye?"
"Gaskiya ina tunanin ba direban tane ba kawai, dan a biye yake da ita, har cikin
gida duk inda ta shiga yana binta"
"Good, ina so aje anemo min waye wannan matashin, me yake yi a tare da ita, Akwai
yuwuwar ze mana Amfani"
"shikenan Oga an gama"
*******************
Koda sukaje gurin birthday ɗin a harabar wani katafaren gida, da ganin yaran da
suke shiga suna fita a harabar gurin kasan sun jiƙu da kuɗi, fitowa Widad tayi daga
motar, Yusuf ma ya fito ya kulle motar.
Wata 'yar siriryar Murya suka ji tace "hey beb you are here?"
Da sauri Widad ta juya suka rungume juna da matashiyar Yarinyar da zata yi sa' ar
Widad, suna murmushi
Widad tace "Happy born day baby"
"Thank you sweetheart"
Wani matashi ne ya biyo bayan Yarinyar ya kalle ta yace "Sweetheart who is this
beb?"
"She's My best friend in UK, we take part in the same school, She's Alhaji Nasir
daula's daughter"
Ta kalli Widad tace "Baby wannan cousin ɗina ne"
Matashin yai murmushi yace "wow Nice to meet you baby"
Ya miƙa mata hannu da nufin su gaisa, Amma cikin zafin nama Yusuf ya saka hannun sa
a na Matashin wanda hakan ya hana Widad gaisawa da Matashin.
Kallon sa sukayi gaba ɗaya da mamaki, Widad kam mazewa tayi kamar ba taga Abunda
Yusuf yayi ba, suka nufi gurin da ake Shagalin birthday ɗin.
Yusuf bin bayan su yayi, Nurat ta kalli Widad tace
"Beb waye wannan ne wai?"
"Why are you asking?" Widad ta tambaye ta
"Abunne ya bani mamaki, nasan baki da brother, Amma me yasa ze miki haka? Lallai
kinyi sanyi ko kin fara sauka daga kan AƘIDAR taki ne?"
Widad ta girgiza kai tace "babu abunda ya canza, sedai kin san komai na Widad a
lissafe yake"
Jinjina kai Nurat tayi tace
"Wannan ma cikin lissafin ne kenan?"
Widad tace "Maybe"
Nurat tayi murmushi tace "You are wonder lady"
Sukayi Murmushi suka nufi kan stage ɗin, Widad na Hawa kan stage ɗin tare da Nurat
aka ɗauki tafi ana shewa.
Cake Nurat ta yanka, aka dinga tafi ana ihu, tare da waƙoƙin birthday. Kyautar Mota
Widad tayi wa Nurat, a matsayin birthday gift, gurin ya hagirtse da shewa anawa
Widad kirari, suka shiga cashewa a stage din nan kaman ba yaran musulmi ba.
Kiran Yusuf akayi a waya, ya fita waje domin amsa Wayar saboda hayaniyar da take
tashi a gurin.
Yana ɗaga wayar yasa a kunnen sa tare da yin Sallama
"Idan har kana son tsira da Rayuwar ka, to ka tafi ka bar gurin nan a yanzu, in ba
haka ba ko kai ko Uwarɗakin naka ɗaya ze iya rasa ransa"
SHARE PLEASE 🙏🙏🙏
Ayshercool07063065680
_*AƘIDA TA*_
PERFECT WRITERS ASSOCIATION
(WE AIN'T PERFECT BUT WE ARE ALWAYS TRYING OUR BEST, TO MOTIVATE AND ENTERTAIN OUR
READERS)
https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/
*Story and written by*
_*AISHA HUMAIRA (Daddy's girl)*_
The experience writer of *ABDUL JALAL** WATA KISSAR.... (SAI MATA) *And now *AƘIDA
TA *
I dedicated this book to my Mum (Malama Nafisat Adam Muhammad) i love you mum
Haƙƙin Mallaka ⚠ : Littafin nan mallaki nane, tun daga sunan labarin zuwa abunda ya
ƙunsa, ban yadda wani ko wata ya sauyamin ko yin Amfani da wani ɓangare na labarin
ba ba tare da izinina ba, Nagode
https://www.wattpad.com/user/Ayshercool7724?
utm_source=android&utm_medium=link&utm_campaign=invitefriends
PART1 Page 7
Da sauri Yusuf ya koma gurin partyn ba tare da fargabar komai ba ya shiga kutsawa
yana neman Widad, amma babu ita babu alamar ta a gurin, can ya hango Nurat tana
ƙoƙarin fita, seda ya bari ta fito daga gurin party, sannan yabi bayan ta a guje ya
sha gaban ta, seda ta tsorata da ganin sa ta ɗan tsaya ta kalle shi tace "Are you
ok?"
"Ina Widad?" ya jefo mata tambayar
"ban sani ba na barta akan stage tana rawa" tai maganar cikin wata irin
gurɓatacciyar hausa.
Subhanallah shine abunda Yusuf ya furta, yai gaba yana sake duba gurin.
ba zato ba tsammani ya shammaci Nur ya fizgota ya shiga cikin duhuwar flowers da
ita, yasa hannu ya shaƙeta, ya kalle ta a hasale kamar wani mahaukacin zaki yace
"Ko ki gayamin gaskiya ko kuma zan fita dake daga gurin nan, zan riƙe ki a matsayin
garkuwa harse Naga Widad, idan kuwa rayuwar Widad ta salwanta taki ma ta salwanta,
ki gayamin ina take?" Yai maganar cikin ɗaga murya tare da shaƙe Nurat.
"Dan Allah, please don't kill me I will tell you, please secure my life"
"Your life will be secured if you tell me the truth" ya faɗa yana zare mata ido
Cikin kokawa da numfashi tace "Ok zan gaya maka, Dad ne yasa aka busa mata wani
abu, yanzu tana harabar gurin nan a ɓoye, wasu zasu zo su ɗauke ta, idan baka
hanzarta ba komai ze iya faruwa"
"Meyasa Mahaifinki yake ƙoƙarin sace ta?"
Cikin kuka tace "I sure to the Almighty ban sani ba, trust me"
Tasa Nurat yayi a gaba ta nuna masa ƙarƙashin bishiyar da aka ajiye Widad, tana
kwance helplessly a ƙasa, unconscious kaman babu rai a jikin ta, ga jakar ta a
gefen ta.
Ya waiga ba kowa a gurin, Yasa hannu ya sunkuce ta ya tafi da ita motar su da
sauri, ya buɗe bayan motar ya kwantar da ita, yaja motar da gudun tsiya ya bar
gurin.
Da gudu Nurat ta koma cikin gidan su tana haki, da yake hall ɗin party a cikin
gidansu yake, ɗakin ta ta tafi kai tsaye ta shige banɗaki tana sauke numfashi, ta
wanke fuskarta, ta buɗe fridge ta sha ruwa me sanyin gaske, sannan ɗakko wayarta ta
kira layin mahaifinta.
Seda ta kusa tsinkewa sannan ya ɗaga yace "Yaya i hope everything is going
according to how it's planned?"
Cikin rawar baki tace "No Daddy something is going wrong"
Cikin sauri yace "meya faru?"
Cikin Rawar Murya Nurat tace "Daddy basu ƙaraso da wuri ba, nayi abunda kace Amma..
" Amma me? Ki gayamin menene? "" Daddy ita da wani tazo, nayi abunda kace, but
someone intimidate me, yace in ban faɗi inda take ba ze kashe ni""Waye shi?" ya
faɗa a fusace"Ban sani ba Daddy, Amma tare suka zo" "Wace irin wawuya ce ke haka?
Kinsan lokacin dana ɗauka ina wannan shirin? Idan wasu suka rigani mallakar Abun
nan mun kaɗe" "Daddy ba laifi na bane, laifin wanda ka turo su ɗauke ta nefa" "Shut
up, kin ɓata min shiri kina gayamin maganar banza" "Am Sorry Dad is not my fault,
but.... " Common Keep quiet " ya faɗa a Hasale, tare da katse wayar yana tsaki,
tabbas ba dan wawancin nan 'yar cikin sa ce ta aikata masa ba da ba abunda ze hana
yasa a Kashe ta. A fili Yace"dole in toshe duk wata kafa da zesa su Alhaji Haruna
su san nayi yunƙurin sace Yarinyar nan ni kaɗai, kuma dole in gano wane yaron ne
suka je gurin tare"
Yusuf kam gudu yake bana wasa ba, ya dinga kauce wa dukkanin hanyoyin da zesa ya
haɗu da cunkoson ababen hawa, ko kuma jam'ian tsaro, be sassauta da gudu ba seda
yaga ya shigo layin su Widad, a hankali ya ƙara sa tuƙin yana zuwa ƙofar gate ɗin
ya saki wani irin horn me gigitarwa, duk a ƙoƙarin sa na ganin ya kai Widad gida
lafiya.
A gigice Isa ya buɗe ƙofar dake jikin tangamemen Gate ɗin ya leƙo ya fara masifa
"haba Yusufa, wannan wani irin horn ne kaman me shirin sanar da tashin duniya"
Cikin harzuƙa Yusuf yace "Open the Gate" Dukda Isa ba turanci yake ji ba amma ya
gane Yusuf na magana ne akan ya buɗe masa ƙofa, Cikin Sauri Isa ya buɗe masa Gate
Yusuf ya shiga da motar yayi parking, ya sakko da sauri daga cikin Motar ya buɗe
inda ya Kwantar da Widad, har yanzu bata hayyacin ta, Yasa hannu ya ɗakko ta tareda
Jakar ta ya nufi Cikin gidan da ita, Isa ya biyo bayan sa da Sauri yana ƙasa da
murya cike da gulma yake Faɗin
"Yusufa meyasami Uwar ɗakin naka kuma? Kodai Shaye2 tayi ne? Naganta kamar a buge"
Cikin tsawa Yusuf yace "Idan ka ƙara taku ɗaya daga inda kake zan ɓata maka rai"
Gaba ɗaya Isa mamaki ya kama shi yadda Yusuf ɗin ke wani magana cikin Izza da isa.
Babu kowa a babban Falon dan haka Kai tsaye part ɗin ta ya nufa da ita, Ya kwantar
da ita akan gadon ta. Yasa hannu a aljihunsa, ya ɗau wayarsa ya kira Abbas, bugu
ɗaya ya ɗauka yace "Kai ya haka? Zaka kirani a wannan daren?" "Kai akwai matsala
fa" "Matsalar meke nan?" "Widad na kai gurin birthday akayi barazanar za'a kasheni
idan ban bar gurin ba, ina komawa na neme ta na rasa, da ƙyar na ganta, yanzu haka
na dawo da ita gida Amma bata san inda kanta yake ba, I thinks they Use sedative
substance on her, nayi niyyar in tsaya da ita a Asibiti Amma naga hakan hatsari ne
babba"
Abbas ya numfasa yace "Gaskiya kam zata farfaɗo Insha Allah, gobe in Allah ya
kaimu ka shigo Office kawai za muyi magana"
"Shikenan Allah ya kaimu" suka yi Sallama, ya maida Wayar Aljihunsa ya kalli Widad
da take ta bacci bata san meke faruwa ba se sauke numfashi take, Yusuf ya ɗauki
bargon dake gefen ta ya rufe ta dashi saboda yanayin Sanyi, wayarta ce keta ringing
a Jakarta ya buɗe Jakar ya ɗakko wayar ya kashe ta gaba ɗaya, Sannan ya kama hanyar
fita.
Yusuf ya fito ya nufi hanyar fita, yaci karo da Ramlah a babban falo, share ta yayi
ze wuce.
"Daga ina kuke a daren nan? Me kake a ɗakin Widad a wannan lokacin?" muryar Matar
gidan ce, dake tsaye a ƙafar bene.
Yusuf ya juyo ya kalle ta sannan yace "Na kaita unguwa ne" "Me kake a ɗakin ta a
wannan lokacin? Bata da lafiya ne, na kaita ɗakin ta ne" "Ka kaita ɗakin ta kai a
wa?" Ramla ta tambaye shi.
"Ni ba a kowa ba, ni a ɗan uwan ta musulmi, kuma ma'aikacinta"
"Kai shashasha rufemin baki" Hajiya Halima ta katse shi cikin tsawa.
"Naga kanka yana rawa, to bari in tuna maka kai ba kowa bane face matsiyacin
talaka, ka dena jin kanka kamar wani me iko dan kaga mai gidan nan yana wani baka
girma na musamman kai ɗin ba kowa bane ba"
Amal da take jiyo hayaniya ta fito daga ɗakin ta, tana zuwa ta tarar da mahaifiyar
ta ta saka Yusuf a gaba tana zagin sa"Haba Mummy, me Yusuf yayi miki kike masa
wannan cin mutunci haka?" Ramla tace "An zage shi ɗin, meye alaƙar ki dashi? Ɗan
uban waye shi da ze dinga wani jin kansa, dan yaga ya samu gindin zama, saboda
tsabar cin fuska akan wannan banzan waccan mara mutuncin ta dizgani"
Yusuf ya ɗan murmusa yace "Nasani niba kowa bane, talaka ne ni gaba da baya, dan
haka ku kwantar da hankalin ku,kuma ni bana sawa kaina ni wani ne" yana gama faɗin
haka ya juya ya fice.
Amal tace "Mummy koma menene laifin Widad ne, ni banga abunda Yusuf yayi ba"
Hajiya Halima cikin tsawa tace "dalla rufemin baki banza, naga zaƙewar ki kema tana
yawa akan yaron nan, ki shiga hankalin ki tunda wuri, ni sam yaron nan be minba, ya
fiye kalar munafukai"
Ramla tai caraf tace "wallahi kuwa Mummy, ni kaina ban yadda dashi ba, Ina jiran
sakamakon binciken da kika sa ayi a kansa ne"
Amal tace "Mummy koma menene Yusuf bare ne aiki ne ya kawo shi gidan nan, bekamata
a saka shi a wannan sabgar ba"
"Amal kenan ke har yanzu yarinya ce, baki san inda rayuwa tasa gaba ba, kashedina
dake shine, tun wuri ki fita daga sabgar yaron nan, dan muddin na gano wani abu
saɓanin abunda nayi zato a tattare dashi ba abunda ze hana insa ayi masa abunda ya
dace da shi"
"Amma mum....
"Ke rufemin baki, shashasha kawai" Mummy tayi maganar tare da juyawa zuwa ɓangaren
ta, Ramla ma tabi bayan ta suka bar Amal a falon tsaye.
Yusuf na fitowa, Nura ya biyo shi yace"A'a kaga ɗan gatan 'yar masu gida, gaskiya
Yusuf ka ciri tuta, naga' yar masu gida tana yi da kai, ƙiri Ƙiri ta koreni kuka
tafi unguwa, naga duk inda zaka tare kuke tafiya"
Kafin Yusuf ya bashi amsa, Isa mai gadi ma ya nufosu yana cewa "Nikam Malam Yusuf
baka gayamin meyasami Uwar ɗakin ka ba, nifa abun ya bani mamaki, iya sanina dai
bata shaye2, sedai taɓun hankali amma meyafaru da ita haka?"
Kallon su yayi ɗaya bayan ɗaya yana karantar tsantsar munafunci da son jin gulma a
fuskokin su, sharesu yayi bece musu komai ba yai gaba abunsa ya fice ya bar gidan.
Yusuf na fita, Nura yace"Ji shi se kace ɗan uban wani, muna masa magana amma yayi
mana banza, da Alhaji ne uban sa bansan wulaƙancin da ze ba"
Isa yace "Bar mara mutunci, ji yadda muna masa magana ya share mu, Anya Nura
mutumin nan ba Asiri yayi wa me gidan nan ba?"
"Ni zance maka Asiri yayi masa hadda 'yar sa ma, kana gani ɗazu ta hana Ramla binsu
saboda shi, da muka dawo daga filin jirgi se cewa tayi ni in sauka in hau motar
haya in tafi gida, shi kuma ya kaita unguwa"
Isa ya jinjina kai yace "Kana gani duk jin kai da izzar ta, duk Aƙidar ta ta
rashin yadda da mutane Amma duk inda zata tare dashi suke tafiya, dudu yaushe yazo
gidan nan? Ko wata ɗaya be cika ba ya samu wannan gindin zaman, mu kuwa shekara
nawa muna aiki a gidan nan? Ba abunda yake haɗamu da ita se cin mutunci da
wulaƙanci "
Nura yace "to ai magana ce a buɗe, Allah kaɗai yasan abunda suke yi"
Isa yace "kuma fa hakane zancen ka Nura, taɓ aikuwa zamu ƙara saka ido sosai,
zamuyi maganin wannan gani-ganin da yake mana"
Haka suka zauna suka cigaba da gulma, suna muzanta Yusuf da miyagun kalamai.
Yusuf kam kansa ya kulle Sosai, daya koma gida ma kasa bacci yayi, yana ta nazari
akan abubuwa da dama yana son gano bakin zaren amma ya rasa ta ina ze fara, gaba
ɗaya Al'amuran a cukurkuɗe suke, me zesa Baban Nurat yunƙurin sace Widad? Waye
mahaifin Nurat? Dole Akwai dalilin da yasa Widad take da wannan AƘIDA na ƙyamar
talaka da nesanta kanta da mutane, yanayin Abubuwan da take yi wasu lokutan yasa
Yusuf ya fara gazgata cewar tana da taɓin ƙwaƙwalwa, tunani ya haɗu ya cunkushe
massarafar gangar jikinsa wato ƙwaƙwalwarsa, ba shiri ya tsagaita tunanin ya kwanta
da ƙudurin dole yaje Office da safe, akwai buƙatar yaga Abbas.
A hankali ta motsa daga nannauyan Baccin da take, ji tayi kanta kamar an ɗora mata
wani nannauyan dutse, gaba ɗaya gaɓoɓinta sun mata nauyi, a hankali ta buɗe idon ta
ta ƙarewa ɗakin nata kallo, ta mayar da idanunta ta lumshe na wasu daƙiƙu sannan ta
sake buɗe su, a hankali taja jikin ta ta miƙe zaune, kallon jikin ta tayi tare da
ƙoƙarin son tuna abunda ya faru, sosai take takura ƙwaƙwalwarta don ta tuna mata
abunda ya faru, Amma fafur ta kasa tuna komai, dafe kanta tayi wanda taji yana sara
mata, ta miƙe jiri na kwasar ta ta tafi banɗaki.
Da sassafe ko karyawa Yusuf beyi ba ya fito ze fita. Umma dake kitchen tana ƙoƙarin
haɗa Abinci ta leƙo tace"Yusuf me zan gani haka? Ba zaka tsaya ka karya bane?"
Yusuf yace "Umma sauri nake ne, bana son in makara akwai aikin da nake son yi"
"Yusuf nifa gaskiya wannan aikin da kake a gidan masu kuɗin nan ba sonsa nake ba,
nasan halin masu kuɗi da rashin mutunci da wulaƙanta talaka, nidai gaskiya su canza
maka wannan aikin su baka wani, danni gaskiya bana son kaje inda za'a wulaƙanta min
kai" Kallon Umman sa yayi, ya ɗanyi murmushi ya tako gaban ta ya riƙe hannayen ta
yace"Kyakkyawar Uwa, Uwa da babu irin ta, ina Alfahari dake Umma na, yadda kike
kula dani Allah ya kulamin dake ko bayan raina, ki kwantar da hankalin ki, basa
wulaƙanta ni, kuma yanayin aiki ne yazo a haka, dana Kamm zan koma Office, idan
kuma kince ba kyason aikin se in haƙura gaba ɗaya"
Badan ranta yaso ba tace "Yusuf ba aikin ne bana so ba, ni wannan aikin da suka
baka ne bana so, yaushe rabon da muci Abinci tare, in ka fita tun safe se dare,
Amma shikenan dai, Allah yayi maka Albarka, Allah ya sadaka da Alkhairi a duk inda
kake"
"Ameen Umma na, bari in sauri sena dawo"
"Allah ya kiyaye hanya" Ya amsa da "Ameen" ya fice.
Kai tsaye headquarters su ta jam'ian tsaro na farin kaya ya tafi. Kasancewar Yusuf
mutumin kirki yasa tun daga gate masu gadi suke gaida shi, ya tsaya suka gama
gaisawa sannan ya shige ciki. Ofishin sa ya nufa kai tsaye, yana zuwa ya tarar da
shi tsaf ana shiga a gyara masa dukda baya nan, Na'ura me ƙwaƙwalwarsa ya ɗakko ya
kunna, ya ɗan jira kaɗan sannan ya fara daddanawa. Gaba ɗaya ya nutsu sosai
hankalinsa kacokan yana kan Computer, da gani kasan ƙoƙarin gano wani abu yake me
mahimmanci.
Sallamar da'akayi a office ɗin ne yasa shi ɗagowa, Sakina ce sanye da suit na aiki
kamar yadda ta saba, fuskar ta ɗauke da murmushi ta ƙaraso tana wani fari da ido,
Sam Yusuf baya ƙaunar mace mara kamun kai, shiyasa sam Sakina bata burgeshi.
Kujera taja ta zauna, ta kalle shi tace "wata sabon gani, aiki ya ɓoye mana kai
gaba ɗaya haka, ba'a jin ɗuriyar ka ko a waya, na kira ka harna gaji baka ɗagawa"
Yusuf "Aikine ya ɗanmin yawa shiyasa, Ya aikin?"
Cikin iyayi tace "Alhamdilillah, Fatan dai kana lafiya?"
Cike da basarwa yace "Lafiya ƙalau" Ya cigaba da latsa computer sa.
"Kwana biyu da baka zuwa duk gurin nan ba daɗi, nayi farincikin zuwan ka sosai"
Bece mata komai ba ya ɗakko wayarsa ya ɗan daddana ya kanga a kunnen sa, ya ɗanyi
shiru na wasu daƙiƙu sannan yace"Ya Abbas ka shigo ne?"
Ya sake yin shiru sannan yace "Ok nima na shigo yau akwai buƙatar in ganka, bari
inzo office ɗin naka"
Yana gama wayar ya miƙe ya fice ya bar Sakina a gurin, ba tare da yace mata komai
ba.
Wani ƙululun baƙin ciki ne ya tokarewa Sakina zuciya, tabi bayan sa da kallo tare
da yin ƙwafa.
Yana fita ya nufi Office ɗin Abbas, yaje ya tarar da shi yana karin kumallo, ya
zauna suka gaisa, Abbas ya zubawa Yusuf shayi ya miƙa masa sannan yace "Mutumin ya?
Yau ka samu chance ɗin ɓullowa kenan? Meye labari ne?"
Yusuf yace "labari kam akwai shi Abbas, nifa gaba ɗaya a rikice nake wallahi, gaba
ɗaya na rasa bakin zaren"
"Take it easy man, bi komai a sannu, me ake ciki?"
Nan Yusuf ya warware masa irin abubuwan da suka faru har zuwa ga yunƙurin sace
Widad da'akayi jiya.
Shiru Abbas yayi yace "Lallai lamarin akwai rikitarwa, Mahaifin Nurat ze shiga
cikin suspects ɗinmu, yanzu abunda za'ayi ka bani Adress ɗin gidan, zamu je muyi
bincike, semun fara gano waye ma mahaifin Nurat ɗin"
Shikenan zan turomaka Complete Adress ɗin ta Email ɗinka. Suka zauna suka cigaba da
tattaunawa. Wayar Yusuf ce ta fara ringing ya ɗakko ya duba, lambar Isa megadi ce a
akan allon wayar tasa, ya ɗaga ya kara a kunnen sa, suka gaisa Isa yace masa "Ana
neman ka"
"Shikenan gani nan zuwa"
Yusuf ya kalli Abbas yace "Abbas bari in canza kaya, waccan rigimammiyar tana
nemana yau nasan zan sha tijara, dan titsiyeni za tayi tace sena gayamata meyafaru"
Dariya Abbas yayi yace "Ina jinjina maka Yusuf, yadda kake iya aiki da wannan
Yarinyar mara alƙibla" "to ya zanyi tunda kun takura kunce se nayi, dole in kwantar
da kai inyi haƙuri da halin ta, Amma kasan wani abu Abbas?"
"A'a seka faɗa"
"Ni yanzu gaba ɗaya tausayi take bani, gaba ɗaya rayuwar ta ba irin yadda kowa ke
gudanar da rayuwar sa take yi ba, duk yadda zan kwatanta naka ba zaka gane ba, ina
kyauta ta zaton akwai wani pain a zuciyar ta, da yake ƙara assasa condition ɗin da
take ciki "
"Hmm Yusuf kenan ba wani pain, kawai iskanci ne na yaran masu kuɗi, ta taka wanda
take so tayi rashin mutunci saboda tana da masu gidan rana"
Yusuf yace "Haba Abbas, su talakawan me suka yi take musu haka? Wai waya gaya maka
talakawa kawai take wa haka? Hmm ni nasan abunda nake gani kawai, ba iya Wulaƙanta
mutane ba, Akwai wani ɓoyayyen abu da yake damun ta, ina jin tausayinta sosai"
Abbas ya ƙyalƙyale da dariya yace "Kai mutumina, ko dai ka koma ruwa ne?"
"Na koma ruwa kamar Yaya?"
"To naji kace kana tausayinta, na sani ko babbar magana zaka janyo mana"
Shiru Yusuf ya ɗanyi jiki a sanyaye ya kalli Abbas yace"Abbas ai na rufe wannan
babin har Abada, sedai wani ikon na Allah, just recently ka manta abunda ya faru
dani ne? Ina ni ina Widad, as i told you before i give up gaskiya babu yarinyar da
zan ƙara cewa ina so, zanyi haƙuri da ƙaddara ta, in zauna Yadda Allah ya ajiye ni,
ni yanzu bari in tafi kar in ƙarawa kaina laifi, dukda yanzu ma nasan laifi na riga
nayi shi, zan sha tijara a gurin Widad" yai maganar tare da miƙewa ya fice.
Abbas yayi shiru yabi bayan Yusuf da kallo, he's very gentle and innocent, abubuwa
da yawa marasa daɗi sun faru da Yusuf, gashi shi kullum zuciyar sa a wanke take,
baya nufin cutar da kowa. A fili Abbas yace "Anya kuwa nayi adalci idan aka haɗa
kai dani, aka cutar da Yusuf, Kai Amma kuma Alherin da zan samu a wannan sabgar ya
isa in ajiye wannan wahalallen aikin in more rayuwa ta"
Yusuf ya canza kaya ya tafi gidan su Widad, ya tsaya suka gaisa da ma'aikatan gidan
sannan ya nufi cikin gidan, babu wanda yake da wannan damar ta shiga cikin gidan
kai tsaye, ko ba Aiken sa akayi ba se Yusuf, shi Yusuf be san da wannan dokar ba ma
sam, kai tsaye ya shiga Babban falon da yake shine mahaɗar iyalan gidan.Ya shiga da
sallama a bakin sa, ya tarar da Amal a zaune tana kallon zee world, tana ganin sa
tayi murmushi tace "Sannu da zuwa, yau ka makara fa"Murmushi yayi yace "Allah ya
bada haƙuri, Madam ta tashi ne?"
Amal ta kwaɓe baki tace "waya san mata, ka zauna mana ka tsaya a tsaye"
"karki damu nidai ace mata nazo"
"Ni ban zanjeba seka zauna"
Yusuf ya zauna a ƙasan carfet, Amal ta ɓata fuska tace "ya zaka zauna a ƙasa kuma,
haba Yusuf dan Allah ka zauna"
Haka Amal ta uzzura masa seda ya zauna akan kujera, ta miƙe tsaye tace"bari in kawo
maka ruwa, kafin ta fito bana so inje ta Wulaƙanta ni, idan ta ga dama zata fito da
kanta" tana gama faɗin haka ta miƙe ta shiga wani ɓangaren.
Yusuf na nan zaune, ya ɗakko wayarsa yana ɗan daddanawa, sega Nura direba ya shigo
da wata babbar jaka a hannun sa, da alama Aiken sa akayi yana ganin Yusuf a zaune
akan kujera yayi turus yana kallon Yusuf.
Yusuf ya ɗaga kai ya dube shi yace "ya dai Nura? Naga ka tsaya kana kallo na kamar
baka sanni ba"
Kafin Nura yayi magana, sega Ramla da mahaifiyar ta sun fito, idon Ramla ya sauka
akan Yusuf dake zaune akan kujera, buɗe baki tayi tace"iyeee samun guri, ɗan kuturu
da gaɗa cikin Rama, wato isarka da ƙasaitar taka harta kai ka dinga zama akan
kujera sannu fa" Rai a ɓace Mummy tace "Kai ubanwa ya baka izinin shigowa falon
nan harka zauna akan kujera, gidan ubanka ne kona uwarka da zaka shigo min falo ka
zauna akan kujera, kai na fuskanci kanka na rawa fa"
Amal ce ta fito da ruwa da cup a hannun ta, ta ƙaraso falon tace "Haba Mummy dan
Allah kiyi haƙuri, wallahi ni nace ya zauna"
Yusuf kam shiru yayi bece komai ba, zama akaan kujera kawai yaja masa zagi da cin
mutunci.
"dalla rufe min baki, se nayi maganin yaron nan, saboda jin kansa yake kamar ɗan
uban wani, matsiyacin banza ɗan talaka, dama haka kuke baku iya samun guri ba, kana
wani sumi sumi da kai mara mutunci, dama gaba ɗaya siffofifinka na munafukai ne
bari Alhajin ya dawo, sena sa anyi maganin ka, bazaka tashi ba kana jina ina magana
"
Gaba ɗaya ran Yusuf ya gama ɓaci, kujera kawai wannan akanta ake masa wannan cin
zarafin. A hankali ya yunƙura ze tashi rai a ɓace, cikin tsawa da rashin mutunci
Ramla tace"ba magana ake maka ba ba zaka tashi ba, banza kawai ɗan talakawa, an
kusa korarka kowama ya huta, dalla tashi sakarai"
"baze tashi ba, Kujerar ba wani ya kawo ta ya ajiye ba se mamallakin gidan, dan
haka babu wanda yake da ikon cin zarafi ko korara wanda ni yakewa aiki a gidan nan,
baku kuka ɗauke shi aiki ba, Kuma duk wanda yake tunanin ze kori wanda na ɗauka
aiki sedai ya bar gidan nan tunda mutum ba gidan nasa uban bane"
Widad ce tsaye sanye da gajeren wando, da vest a jikin ta gashin kanta a kwance a
kafaɗarta kamar yadda ta saba shigar ta, cike da isa da nuna tsantsar iko tayi
maganar. Ramla ta harzuƙa za tayiwa Widad rashin mutunci Amma Mummy ta hana ta.
Widad tace "ki ƙyaleta ta faɗi abunda take so mana, keda ita kun sani banbancin ku
da masu gadi da direbobin nan kaɗan ne ai, dan haka ku tsaya iya matsayin ku, kar
wanda ya ƙara shiga hurumi na da wanda yakemin aiki, wannan ya zama kashe dina da
gargaɗi na na ƙarshe a gareku, babu ruwan ku da ma'aikata na, wallahi duk wanda ya
kuma karyamin doka zanyi ba dai dai ba, na gaya muku"
Wani ƙululun baƙin cikine ya ƙule zukatan su, a gaban masu aiki tayi musu wannan
cin zarafin da wulaƙanci, saboda wannan sakaran talakan.
Widad ta ɗago idanunta cike da rashin mutunci da tsantsar izza ta kalli Yusuf tace
"kai kuma biyo ni" Jiki a matuƙar sanyaye Yusuf ya miƙe yabi bayan ta, kamar kazar
da ƙwai ya fashewa a ciki, dan yasan tistiye shi zata yi da tambayoyi.
Share please
Ayshercool 07063065680
_*AƘIDA TA*_
*Story and written by*
_*AISHA HUMAIRA (Daddy's girl)*_
The experience writer of *ABDUL JALAL** WATA KISSAR.... (SAI MATA) *And now *AƘIDA
TA *
I dedicated this book to my Mum (Malama Nafisat Adam Muhammad) i love you mum
Special thanks to all members of my Association Perfect writers Association may
Allah subhanahu wata'ala bless our pens and grant us wisdom to write what will
bring positive changes to our Community.
PART1 Page 8
Jinjina kai Mummy tayi ta juya ta nufi part ɗinta, jiki a saɓule yaranta na suka bi
bayanta. Koda taje ɗakin ta safa da marwa ta shiga yi tana sauke wata nannuyar
Ajiyar zuciya me bayyanar da tsantsar baƙin ciki da takaici.
Ramla ta numfasa tace "Mummy akwai buƙatar ɗaukar matakin gaggawa akan wannan ɗan
iskan mutumin, na rasa Wani asiri yayi wa wannan daƙiƙiyar da take tozarta ki
akansa, kawai kisa a kawar da shi daga hanyar ki mana"
A gigice Amal tace "A'a Ramla, meye laifin sa? Laifin sa fa kawai ya hau kan
kujera, shikenan Amma Widad ce tayi laifi anan bashi ba, kiyi tunani mana"
Ramla ta daka mata tsawa ta hanyar cewa "dalla rufe mana baki, dalilin wa akayi
mana haka, a gaban masu aiki aka Wulaƙanta mu? saboda wanna ɗan matsiyatan ne me
kama da mataccen silifas, wallahi Mummy ko baki ɗau mataki akan sa ba ni zan ɗauka,
zan ɗau matakin da ya dace da shi da gaggawa"
Cikin hanzari Mummy tace "A'a Ramla da alama akwai Amfanin daze iya yi mana a nan
gaba, nasa Isa mai gadi ya binciko min ɗan wace unguwa ne"
Ramala tace "Mama Isa megadin me? Me ze iya tsinanawa, kawai Kisa abi bayan sa
kawai a gano inda yake, kuma ɗan uban waye shi"
Amal cikin sanyin jiki tace "dan Allah Mummy karkisa a masa wani abu dan Allah, abi
komai a hankali"
Mummy tace "dalla rufemin baki sakarya!"
Ramla tace "Mummy ƙyaleta dan Allah, me abun haushi kawai, Amma Mummy ta yaya ze
iya mana amfani a nan gaba?"
Murmushi Mummy tayi tace "zan miki bayani Ramla, ba zanyi a gaban wannan shashashar
ba, dan yanzu na kasa gane inda tasa gaba"
Widad kam, suna zuwa falonta ta tsaya ta juyo ta kalli Yusuf, ta ƙure shi da ido
tun daga sama har ƙasa, yayin da shi kuma ya ƙi yadda ya ɗago ido ya kalle ta, ta
daɗe tana kallon sa tana nazarinsa.
"Look up" ta faɗa a taƙaice, ɗan ɗagowa yayi ya kalleta ya maida kansa ƙasa.
"Ya aka yi na dawo gidan nan jiya? Meyafaru dani a gurin party jiya?"
Dama Yusuf yasan a rina, dan haka a dake yace
"Eh kin faɗi ne akan stage, shine muka taho gida"
"Malam ƙarya kake, ka gayamin meyafaru? Ko kaima kazo ne dan a haɗa kai da kai a
cutar dani?"
Yusuf ya girgiza kai yace "Me yasa kike tunanin za'a haɗa kai dani a cutar dake?
Meye riba ta in an haɗa kai dani an cutar dake?"
"Saboda talaka ba abunda baze iyayi akan kuɗi ba, An haɗa kai da kai an turo ka ka
cutar dani, in ba hakaba meyasa lokacin da nace kasa hannu a death contract ka
yadda ba tare da ko ɗar ba ka cigaba da aiki dani? Wannan shi ne karo na biyu kana
min ƙarya, meyasa? Ta yaya zan faɗi haka kurum bani da wani special case, se taɓin
hankali, shima kuma ƙaƙabamin shi akayi, ta yaya haka zata faru? Bana tunanin na
samu mental attack ne haka kurum a gurin nan, Ka gayamin gaskiya you are here to
kill me, you were sent by someone to kill me " cikin ɗaga murya, tare da tsantsar
rashin yadda take maganar.
Gaba ɗaya ta birkice, Yusuf yai shiru ya ƙura mata ido yaƙi cewa komai.
A fusace tace "talk to me!!"
"Am not here to kill you, na karɓi aikin nan ne saboda shine last option ɗina, idan
banyi aikin nan ba babu wata hanya da zan samu abunda zan kula da kaina da
mahaifiya ta, talaka ze iya komai akan kuɗi, Amma be kai yadda me kuɗi zeyi ba, me
kuɗi yafi talaka son kuɗi da aikata komai dan ya mallake su, da zan cutar dake da
tuni nayi tunda kika amince kije ko ina tare dani, someone attempts to kidnap you
yesterday night, that's all I know"
Dafe kai Widad tayi ta shiga sintiri a gurin, gaba ɗaya idonta yayi Ja se gumi
take, a hankali ta furta "Jeka falo ka jirani, zamuje gidan Bulama yanzu" Yusuf ya
jinjina kai ya koma babban falon.
Kusan mintuna sha biyar yana jiran ta sannan ta fito, yauma dai babu batun mayafi
balle hijjabi a jikin ta, haka suka fita.
Alhaji Haruna ne mahaifin Nurat ɗauke da waya a kunnen sa yana waya, yana yi yana
sharce gumi duk da sanyin Na'urar sanyaya ɗaki dake ɗakin amma gumi yake yakicewa,
cikin inda inda yake cewa"wallahi ranka ya daɗe seda aka shirya komai, dan yarinya
ta Nurat ta tabbatar min da taje gurin party, taje gidana, dan an gama komai an
sumar da ita, ana jiran sahu ya ɗauke azo a ɗauke ta, wani matashi yayiwa Yarinya
ta barazana ya ɗauke ta ya tafi da ita, kuma ni a iya sanina ko su Alhaji Musa da
muke komai tare dasu muke neman abu ɗaya basu san mun ƙulla alaƙa da kaiba balle
ince haɗin baki ne"
Ɗaya ɓangaren yace "Shikenan zanyi wani shirin na mussman, Amma idan ka bari muka
kuma rasa damar mu a karo na biyu zan ajiye ka a gefe in nemo wani"
"Insha Allah baza'a sake samun matsala ba Alhaji Bukar"
Alhaji Bukar yace "Allah yasa, sannan batun wannan matashin kabar komai a hannu na,
nasan abunda zanyi" "Shikenan godiya nake ranka ya daɗe " daga nan suka yi sallama.
************************Bayan fitar su Widad, Mummy tasa aka kira mata Isa mai
gadi. Isa yaje ya same ta a falo, cikin rawar jiki ya gaida ita ta amsa masa a
wulaƙance ta kalle shi tace"Kai na baka aiki amma har yanzu nani shiru ko bazaka
iya bane?" "A'a ranki ya daɗe, yaron ne gaba ɗaya baya sakin jiki damu yanzu, wani
mugun jin kansa yake kamar wani basarake"
Ta jinjina kai tace "tabbas nima naga hakan, kuma da sannu zan kawo ƙarshen wannan
izzar da yake ji da ita, talakan banza asararre, kaje kayi abunda na saka, bana so
yasan nasa a bibiye shi ne, ka nemo min inda yake zaune, zan sa ayi maganin sa,
tashi ka koma bakin aikin ka"
Ya tashi sumi sumi ya fice.
***********************
Yusuf suna zuwa gidan Bulama suka yi sa'a yana nan, a harabar gidan suka ganshi
yana shan lemo, hannun sa ɗauke da Jarida. Ɗago idon da yayi ya sauke akan Widad
yasa shi sakin murmushi, itakam fuskar nan a murtuke ba annuri.
Alhaji Bulama yace "barka da zuwa lovely daughter"
A ɗan ciki tace "barka da hutawa Daddy"
"Yawwa barka lovely daughter, ya akayi ne na ganki a haka? Meke faruwane? Ko ciki
zamu shiga?"
Yusuf a ransa yace "wata sabuwa, yau kuma Alhaji Bulama take kira da Daddy, idan
taga dama kai tsaye take kiran sa da Bulama, wannan yarinya akwai ta da rikici,
bata da Alƙibila sam"
Ta yamutsa Fuska tace
"A'a nan ma ya isa, Amma Daddy akwai matsala fa"
Ya tattaro hankalin sa kanta yace "matsalar me daughter"
"Ana farautar rayuwa ta har yanzu, daga fita jiya aka kusa saceni, nidai tunda
Daddy baya nan kamin visa zan bar ƙasar nan, gara in ƙarasa Rayuwa ta a can
ƙasashen wajen"
Alhaji Bulama yace "waye yayi attemptin ɗin sace ki, kuma a ina? Shiyasa tuntuni
nace a samo masu tsaron lafiyar ki"
"Bashi da mahimmanci kasan inda naje, da wanda yai yunƙurin saceni, duba da tsawon
shekaru kun gaza maida hankali ku gano hakan, kuna ɗaukar wasu maganganun nawa a
matsayin maganganub hauka, kawai ka nema min visa zan bar ƙasar nan"
"Haba lovely, saboda me zaki bar ƙasar ki ta haihuwa? kije ki cigaba da rayuwa ke
kaɗai a wata uwa duniya? Nace a ɗaukar miki masu tsaron lafiyar ki da zasu dinga
miki rakiya kinƙi, kin ɗakko wannan dogarin duk inda zaki yana biye dake kamar
inuwa, shiba soja ba, shiba wata tsiya ba ta ina ze iya tsare lafiyar ki?" yai
maganar yana nuna Yusuf
Widad ta haɗe fuska tace "kaikam wani lokacin se in rasa meke damun ka, aini babu
me tsaron lafiya ta se Allah, Akan me zan ɗau masu tsaron lafiya ta, haka kurum a
haɗa kai da masu tsaron nawa a cutar dani? I don't trust anyone"
Alhaji Bulama yace "shi wannan ɗin kina da tabbacin baza'a haɗa kai dashi a cuce ki
ba?"
Ta juya ta kalli Yusuf dake tsaye, sannan ta kalli Bulama tace "Ba'a kansa muke
magana ba yanzu , babu ruwanka kasancewarsa tare dani, muna magana akan Visa
zakamin in bar ƙasar nan kawai"
"wai tayaya zan miki visa ki bar ƙasar nan? Keda muke saka ran Dawowar Fahad in
next couple of weeks a fara zancen Auren ku, meya.......
"shut up please! " ta faɗa a hasale tana ɗaga masa hannu sannan ta ɗora da cewar
" wai har yanzu baka janye wannan banzan ƙudurin naka ba ko? Kana tunanin abunda na
gaya maka ƙarya nake, let me repeat myself, bazan yi Aure ba, babu namijin daya
dace dani, ni ba zanyi Aure in zauna a ƙarƙashin wani ba, Allah ya bani dukiya
wadda ta isheni rayuwa, bana buƙatar wani Aure, hankalina na kan son ganin bayan
maƙiya na, koni ko su, ko kuma muyi mutuwar kasko"
"Widad, dukiya shirme ce idan babu Soyayya da kulawa, ban hanaki gano wanda suka
rusa farincikin rayuwar ki ba, Amma aure yana da mahimmanci a rayuwar ki, bakya son
ganin 'ya' yan ki a duniya? Aure garkuwa ne Widad"
"Soyayyar banza, is just stupidity and form of mental disorder, an imagination and
bunch of problems, bana buƙatar soyayyar kowa, nikaɗai zan gudanar da rayuwa ta, na
ishi kaina rayuwa bana buƙatar kowa yayi min garkuwa"
Zuwa yanzu Yusuf ya saba jin ire iren wannan maganganun na Widad, Amma yana kallon
ta a wani iri idan yaji tana faɗin wannan kalaman, ta yaya mutum zece ze rayu shi
kaɗai, ba abokin rayuwa ba 'yan uwa ba Abokan Arziki? Kafin ya bawa kansa amsar
tambayoyin ya tsinkayi murayarta tana cewa
"Wallahi ko kana so ko baka so, ba zan cigaba da zama a ƙasar nan ana farautar
rayuwa ta ba, kuma ba zanyi Aure ba babu shi a tsarina"
Bukama yace "Aini bance dama ki zauna a ƙasar nan dole ba, da zarar an ɗaura miki
Aure ƙasar nan zaku bari gaba ɗaya keda mijinki, kinga kin tsallake tarkon
maƙiyanki"
Cikin izza me bayyanar da tsantsar ikon da take dashi tace"Wani tabbaci kake da shi
shi ɗan naka baza'a haɗa kai dashi a cutar dani ba?"
"Idan har ɗan dana haifa ze cutar dake, da nine mutum na farko da ze cutar dake da
mahaifinki, dan a yanzu mahaifinki bashi da ka mata"
Widad ta miƙe tsaye ta dafa teburin ta kalli idon Bulama tace"Zan bar ƙasar nan ko
kana so ko baka so, kuma bazan Auri ɗanka ba, babu Aure a tsari na, ina fatan
wannan ya zama karo na ƙarshe da zan gaya maka babu Aure a tsarin Rayuwa ta, Ganin
bayan maƙiya na shine a gaba na"
Ta juya ta nufi inda Yusuf yayi parking ɗin mota, da sauri Yusuf ya riga ta
ƙarasawa ya buɗe mata gaban mota, dan bata zama a bayan Mota.
Yusuf ya fara tuƙi ba tare da ta kalle shi ba tace "Muje Farm House" shima be ce
mata komai ba, ya ɗauke kan motar zuwa hanyar gidan gona. Suna tafe Yusuf yana
tunanin wani dalili ne yasa kowa yake tsoron Widad haka? Take faɗawa kowa abunda ta
ga dama komai tsufan sa kuwa? Indan Mahaifinta yana da kuɗi ne, suma ai masu kuɗi
ne.
Bayan tafiyar su Widad Bulama na nan inda suka barshi yana zaune yayi shiru,
Matarsa Hajiya Sarah ce ta fito da shirin ta tsaf, da alama fita zata yi. Inda
Alhaji Bulama ke zaune ta nufa, ta samu kujera ta zauna ta kalle shi tace "Ya dai?
Wannan dogon tunanin fa? Shekaru sun fara ja, dogon tunani be kamace ka ba"
Ya sauke Ajiyar zuciya ya kalle ta yace "dole inyi dogon tunani, Yanzun nnan Widad
ta bar gidan nan, lamarin yarinyar nan kullum ƙara taɓarɓarewa yake, wai ita ba
zata yi Aure ba kwata2, haka zata ci gaba da zama, Rayuwa zata yuwu a haka? "
Ɗan taɓe baki tayi tace "waini Alhaji meye nasa damuwar 'yar wani a ranka? Naga
dai ba kaine ubanta ba, taje tayi abunda taga dama mana"
"A' a Sara, Kin san yadda nake da Mahaifinta, damuwata tasa ce, damuwar sa ta wace,
kuma har yanzu ana kainata hari, nace a samo mata masu tsaron lafiyar ta, taƙi se
wannan yaron da take yawo da shi, kome ze tsare mata oho?"
"to ku ƙyaleta tayi abunda ta ga dama mana, tunda bata san abun Arziki ba, dama ba
dole a cigaba da kai mata hari ba wannan Wulaƙanta mutane da take, Yarinya ƙarama
se baƙar Aƙida"
"A'a be kamata a ƙyaleta ba Sarah, nifa mun yanke shawarar zamu haɗa ta Aure ne da
Fahad"
Kallon sa tayi galala sannan tace "ban gane haɗa ta Aure da Fahad ba? Wannan
Yarinyar mara tarbiyya da bata san Darajar mutane ba zaku haɗa da Fahad, ko manta
Fahda ɗin shima yadda yake da saurin Fushi da zuciya? Tabbas babu inda wannan Auden
zeje, gara ma karka fara"
"Babu ruwan ki, Insha Allah zasu zauna lafiya"
Miƙewa tayi tsaye tace "Ai se ayi in gani, ni na haifi abuna ba wani ya haifar min
ba, bame Aura masa Mahaukaciya mara tarbiyya"
Ta ɗau jakarta ta bar gurin tana ƙunƙuni.
Yusuf ne zaune ya zubawa sarautar Allah ido, Widad ce take zaga dabbobin gidan,
wanda mafi Akasari karnuka ne da maguna se tsuntsaye, Abunda ya bashi mamaki shine
yadda tasa aka fito mata da wani jibgegen ingarmar doki, aka ɗaura masa linzami, ta
ajiye Wayarta ta da 'yar ƙaramar Jakarta, ba tare da an taimaka mata ba ta haye kan
dokin nan.
Kasancewar harabar gidan ƙatuwa ce sosai, hakan yabawa Widad damar yin sukuwa akan
dokin nan yadda take so, ba ƙaramin ɗaurewa Yusuf kai tayi ba, yadda take sukuwa
akan dokin tana sarrafa akalar sa yadda take so, ze tabattar maka ta saba hawan
dokin, kuma ga dukkan Alamu hakan yana bata Nishaɗi.
Seda tayi me isar ta sannan taci birki ta sauka daga kan dokin, ta shiga cikin
gidan. Yusuf yana nan zaune ɗaya daga cikin ma'aikatan gidan wanda Aƙalla ze
shakara talatin da wani abun ya ƙaraso inda Yusuf yake zaune shima ya zauna kusa
dashi. Ya miƙawa Yusuf hannu suka gaisa, ya kalli Yusuf yace "ɗan Samari daga wani
gari kake ne?" Yusuf ya ɗan ƙura masa ido Sannan yace "Kano" Mutumin Yayi
Murmushi yace "Ashema ɗan garin nan ne kai, a wace unguwa kake?" Yusuf yace "Me
yasa kake tambaya ta ne?"
"Ahh karka damu kawai dai na tambaya ne, Amma idan ba zaka damu ba, dan Allah wani
irin aiki kakewa Madam haka da take yawo da kai ko ina? A iya sanina da ita tun
shekarun baya bata sake wa da mutane haka, Amma kai gashi tana yawo da kai ko ina"
Yusuf yayi Murmushi yace "Ita yakamata ta baka wannan Amsar bani ba"
Suna cikin maganar ne Widad ta fito sanye da wasu kayan daban. Ƙure Yusuf da Saleh
tayi ido, tana musu kallo irin na tuhuma, ba tace komai ba ta nufi inda Motar su
take, Ma'aikatan gidan suka biyo ta suna mata kirari suna Allah ya kiyaye, bata
kula kowa a cikin su ba ta hau motar Yusuf ya ja suka bar gidan.
Suna cikin tafiya yaji tace "Me Sale yace maka?"
"Waye Sale?" Yusuf ya tambaye ta, shiru tayi masa tsawon wasu daƙiƙu sannan cikin
maganar ta ta isa, tace "Kana jin daɗin rainamin hankali a lokuta da yawa, na kan
ƙyaleka ne saboda ina jin nauyin hukunta ka a lokuta da yawa, saboda hatsarin da
rayuwar ka ke ciki Kasancewar ka tare dani, Amma hakan baze hanani koya maka
hankali idan ka saɓawa Yarjejeniyar mu ba, na tambaye ka ɗazu da Safe baka bani
haƙiƙanin Amsar tambaya ta ba, ka rainamin hankali, yanzu ma na tambaye ka kana
sake tambaya ta, wannan abubuwan da kake kana jawowa kanka zargi ne a gurina, karo
na biyu Me Sale yace maka? "
Murmushi Yusuf yayi yace "Ya tambaye ni Sunana ne, da kuma aikin danake miki, na
gaya masa sunana, Amma aikin da nake miki nace ya tambaye ki"
Jinjina kai tayi tace "Amma kamar na gaya maka duk inda muka je, ba zakayi magana
da kowa ba se idan ni nayi maka izinin yin hakan"
Juyowa yayi ya kalli Widad, Yarinya ƙarama se izza da jin kai.
Yusuf ya ɗan rausayar da kai yace"Allah ya baki yawan rai ya kare ki daga sharrin
maƙiyanki, banyi hakan da saɓa dokarki ba, sedai idan nayi hakan mutane zasu ga
tamkar wulaƙanci ne, nasan tsoron ki kar a haɗa kai dani a cutar dake, Amma ina
tabbatar miki da cewa bazaki taɓa samuna da cin amanar ki ba"
Ba tare da ta kalle shi ba tace "Zan gani ai"
Sunyi shiru na wani lokaci, can ta jinjina kai tace "Lallai Sale, kar nake kallon
sa, yana son ganin bayana saboda abunda nayiwa ɗan uwan sa, duk randa na kama shi
red handed wallahi se yaje inda ɗan uwansa yaje, babu Amfani zama da maƙaryaci me
cin Amana"
Yusuf ya juya yana kallon ta, yana tunanin randa ta gano waye shi, wane irin mataki
zata ɗauka akan sa?
****************************A kwana a tashi Yusuf yayi wata guda cif yanawa Widad
aiki, kullum cikin hantarar sa take da wulaƙanci amma sam seya nuna mata ko a jikin
sa, duk abunda yayi baze burgeta ba, yayin da Amal keta ƙara tura kai a gurin
Yusuf, dan ita nan duniya babu wanda yayi mata kamar shi tana matuƙar ƙaunar Yusuf
saboda nutsuwar sa, Yusuf yana ta ganin Abubuwa na ban mamaki a game da uwar ɗakin
sa yayin da gefe guda ya kasa gane bakin zare al'amuran gidan nan, gaba ɗaya
yanayin yadda mutanen gidan ke gudanar da mu'amalarsa da ban mamaki dan kowa da
inda yasa gaba kuma kowa akwai wani boyayyen abu da yake ɓoyewa a ransa.Har wata ya
cika, aka shiga wani watan Widad bata biya Yusuf haƙƙin sa ba, shi kuma bece mata
komai ba, sannan duk lokacin da ta buƙaci zuwa wani guri, zeje ya kaita ba tare da
ɓata lokaci ba.
Isa me gadi yana ta ƙoƙarin bugun cikin Yusuf yaji wani abu game da shi amma Yusuf
yaƙi gaya masa komai.
Gaba ɗaya ma'aikatan gidan suka tsangwami Yusuf suna ganin ana fifita shi akan su.
Shikam ko a jikin sa, shima ya dena shiga harkar su, har gara Murtalah me kuka da
shuke shuken gidan suna hira da Yusuf wasu lokutan.
Hajiya Halima na zaune a falo tana aiki a System, gefen ta kuma Amal ce ke cin
Abinci, mai aiki ta fito daga sashin Widad, ta durƙusa a gaban Mummy tace"Hajiya,
Anty Widad fa tun jiya ɗakin ta a rufe, na ƙwanƙwasa taƙi buɗewa, tun jiya da safe
naje in gyara mata amma ɗakin a rufe" Tsaki Hajiya Halima tayi tace "To ina
ruwana, yarinya ce ita ƙarama da zan dinga binta, in taji yunwa zata kashe ta ta
fito"
Amal tace "Mummy kina tunanin Yunwa zata saka ta fito ne? In baki wasa ba sedai
kiga gawar ta kin san halin ta, idan ta mutu da wani kalamai zaki ƙwaci kanki a
gurin me gidan nan? Bama ke kaɗai ba dukkan mu, sannan Burinmu baze cika ba, ƙarshe
ma dukkanmu sedai mu mutu a prison"
Ɗan zaro ido Mummy tayi tace "Kuma fa hakane, tashi muje mu gani"
Suka nufi part ɗin Widad, Amma suka tarar ta rufe bedroom ɗinta, suka yi bugun
duniya taƙi ta buɗe.
Rasa abunyi suka yi, suka kira Alhaji Bulama suka sanar masa da abunda ke faruwa,
da kiran wayar tasa beyi mintuna Arba'in ba se gashi.
Yaje ya tarar dasu sunyi cirko cirko a ƙofar ɗakin Widad, ya taka yaje gaban ƙofar
ya fara ƙwanƙwasawa"Lovely daughter, Dad ɗinki ne, ki buɗe ƙofa kinji, karkiwa
kanki illa" Still Widad ba tayi responding ba, dan ko motsin ta basaji.
Alhaji Bulama yace "Kuma babu wani abu daya haɗaku da ita? Kowani saɓani ko ayi
mata wani abun?"
Ramlah tace "waze nata wani abu kuwa? Ita wannan se an mata wani abu? Ai sedai tayi
wa wanima,wataƙila haukan nata ne ya motsa"
Alhaji Bulama yace "ku bani mukullin ɗakin ta, a buɗe ɗakin karta"
Mummy tace "taɓ wake da mukullin ɗakin basarakiya, ita da bata yadda da kowa ba,
wa zata bari ya mallaki mukullin ɗakin ta ba wanda yake da mukullin ta"
Alhaji Bulama yace "to ko maza za'a kirawo su ɓalla ƙofar a gani"
Ramlah tace "A'a karka jamana Jaraba, a ɓalla mata ƙofa ka samu a tashin hankali
da masifarta, a kira Baban ta aji meze ce"
Alhaji Bulama yace "Keba babanki bane Ramlah"?
Cikin tsiwa Ramlah tace "Niba baba na bane, kullum bata da gori seba gidan ubanmu
bane, dan haka ubanta ita ya haifa bani ba"
Yau Yusuf ya makara dan se sha ɗaya ya tashi na safe, tunda ya koma bacci ƙarfe
takwas na safe, dan haka a gurguje ya kintsa ya fito, yayi sa'a Umma bata nan ta
fita, dan haka ya kulle gidan ya fita, ya nufi gidan su Widad.
Yana zuwa suka gaisa dasu Nura sama sama,suna masa wani kallon banza
Yusuf ya kalli Murtalah yace "Murtalah Madam ta fito kuwa? Ko tazo nema na naga yau
na makara sosai"
Murtalah yace "ina fa, tana can tun jiya taƙi buɗe ƙofa, ana can anata fama da
ita, ba wanda yasan tana raye kota mutu, gashi babu wanda yake da mukullin ƙofar
ta, ana tunanin ko ɓalla ƙofar za'ayi
Zaro Ido Yusuf yayi ba tare da yace komai ba, ya tashi da sauri ba tare da tunani
komai ba ya tun kari cikin gidan.
Isa ya taɓe baji yace "kalli uban shisshigi, Allah yasa yana zuwa su Wulaƙanta shi
su koro shi, banza me rawar kai kawai"
Murtalah yace "Haba Isa, ka sawa Yusuf ido da yawa wallahi, gashi kullum ƙara
samun matsayi yake a gidan nan fiye da kai"
"dalla rabu dani, se kace baka ganin yadda aka fifita shi akanmu a gidan nan, danma
mun samu mu Hajiya tana bayan mu, duk yadda muka so samun gindin zama a gurin
yarinyar nan muka kasa, Amma shi daga zuwan sa ga yadda ya samu sake yake wani
zaƙewa kamar gidan ubansa"
Yusuf kuwa na shiga Babban falo ya gansu a zazzaune suna tattaunawa, Ya durƙusa ya
gaishe su.
Alhaji Bulama ne kawai ya amsa, se Amal da tace "Sannu da zuwa"
Hajiya Halima tace "To Munafuki me ka shigo yi uban iya"
Yusuf yace "Naji ance Madam bata fito daga ɗaki ba yau kwana biyu shine nace.....
Cikin hantara Ramla tace "shine me, mezaka iya? Bama son munafunci malam jeka
mungode, Anjima baban ta ze dawo, yasan yadda zeyi da ita uban shishshigi"
Yusuf yace "Amma be kamata a barta har se ya dawo ba, babu wanda yasan halin da
take ciki, ta rufe kanta a cikin ɗaki yakamata a duba halin da take ciki"
Hajiya Halima tace "kai bana son rawar kai irin naku na matsiyata, ka fimu sanin
abunda ya dace ne? Dalla ɓacemin daga nan"
Alhaji Bulama yace "A'a Hajiya Halima, kika san Alaƙar dake tsakanin su?, ki ƙyale
shi ya Jarraba mana wataƙila kiga ta buɗe ƙofar, kaga tashi kaje ko zata buɗe"
Yusuf ya miƙe ya nufi hanyar ɗakin ta.
Yana zuwa ƙofar ɗakin ba tare da ɓata lokaci ba, yasa hannu a aljihunsa ya ɗakko
mukullayen motocin ta dake gurin sa, ya saka key ya buɗe ɗakin nata, da yake yasan
mukullin ƙofarta ta falo da ta bedroom tunda tana aiko shi ɗakin.
"Innalillahi wa inna ialaihi raji'un!!!"
Shine abunda Yusuf ya faɗa
07063065680 Ayshercool
_*AƘIDA TA*_
*Story and written by*
_*AISHA HUMAIRA (Daddy's girl)*_
The experience writer of *ABDUL JALAL** WATA KISSAR.... (SAI MATA) *And now *AƘIDA
TA *
I dedicated this book to my Mum (Malama Nafisat Adam Muhammad) i love you mum
https://www.wattpad.com/user/Ayshercool7724?
utm_source=android&utm_medium=link&utm_campaign=in
PART1 Page 9
_Asslam Alaikum warahmatullah_da _fari dai zanyi wata magana_ _tun page ɗin farko
nayi bayani_, _nace ina da Jarrabawar ƙarshe_, _ina ƙoƙarin cika Alƙawari ne yasa
na cigaba da kawo_ _littafin nan ɗaya ga watan October_ _nace bazan samu yin
posting kullum ba_ _amma ina iya ƙoƙarina inga nayi duk dan faranta muku_ _amma
wasu na ƙorafi hadda gayamin baƙar magana_ _dan bana posting kullum_ _littafin
nan dai nina sa kaina_ _kuma nace free ne balle ace siya akayi nake jan rai_ _babu
wanda nayiwa dole seya karanta_ kuma ban karɓi kuɗin kowa ba, _ni nake saka data in
ɓata lokacina inyi typing sannan inyi posting_ _dan haka wanda baze iya haƙuri ba
ze iya dena karantawa_ ba zanyi _typing kullum ba tunda ba siyarwa nayi be__Ni bana
Wulaƙanta kowa nasan soyayya ce tasa ake karanta littafina
_ _Masoya har kullum ina sake godiya da Comments ɗinku da Addu'oinku_ _zancigaba da
ƙoƙarin faranta muku Insha Allah_
Widad ya hango zaune acan ƙarshen gado kamar Mahaukaciya tuburan, rigar jikin ta
iya cinyar ta, gaba ɗaya gashin kanta a hargitse, ta sunkuyar da kanta jikin ta se
rawa yake tana kuka, ta rufe ko ina babu haske a ɗakin, seda ya buɗe ɗakin sannan
haske ya bayyana a ɗakin.
Babban abunda ya bawa mutan gidan mamaki be wuce yadda akayi Yusuf ya mallaki
mukullayen ɗakin Widad ba, alhalin su raɓar ɗakin nata ma basu isa suyi ba, balle
samun mukullayen.
Da sauri ya ƙarasa gaban gadon ta yana ambaton Subhanallah,tana ɗagowa taga Yusuf
ta gigice ta fara ja da baya tana girgiza kai.
Yusuf yace "Meya sameki haka? Ki kwantar da hankalin ki, Yusuf ne direban ki fa"
Girgiza masa kai tayi tana kuka tace "Ni karka kasheni"
"No ba kashe ki zanyi ba"
Ɗaga kai tayi ta kalli su Alhaji Bulama dake tsaye suna kallon su, riƙo rigar Yusuf
tayi kamar zata yagata tace "Suwaye wannan? kace su fita bana son ganin su, kace
su fita su bar nan" ta faɗa cikin ɗaga murya da zubda hawaye.
Yusuf ya zauna yace
"Calm down, kinga fa wancan Dad ɗinki ne Alhaji Bulama, ga Mummy, ga Ramlah ga
Amal, sune baki gane ba?"
Alhaji Bulama ya tako yazo inda suke, ya miƙa hannu ze riƙo Widad.
Wata irin ƙara ta saki, ta rirrƙe Yusuf tana ɓuya a bayan sa tana girgiza kai,
cikin ƙaraji take cewa"Ni su fita, su fita su bar nan gurin, kasheni za suyi, kana
kallo nima zasu kasheni, bana son ganin su ba wannan ne Daddyna ba kuma bashi ne
Bulama ba"
Yusuf yace "buɗe ido ki kalle su fa, ga Daddy Bulaman nan s tsaye a gaban ki"
Girgiza kai tayi tace "bashi bane ba, na gaya maka bashi bane" Ta rungume Yusuf gam
tana ci gaba da zubar da Hawaye.
Yusuf a ransa yace "ta tabbata kenan Widad tana da taɓin hankali? In ba haka ba
meze sa ta koma haka?"
Alhaji Bulama yace "Karka damu dama tana yin hakan wani lokacin, ciwonta ne ya
tashi"
Ihun da take yi ne iya ƙarfinta, kai kace wadda ake yankawa, ba shiri suka bar
ɗakin Amal wani irin baƙin kishi ne ya cunkushe zuciyarta, yadda Widad ta rungume
Yusuf yafi komai yi mata ciwo.
A hankali Yusuf yace "Kinga sun fita ba kashe ki za suyi ba, cikani ki ga wani
abu"
Girgiza masa kai tayi "tace ni A'a tsoro nake ji, kasheni za'ayi nima an kashe Ammi
nima kasheni za'ayi"
Yusuf ya girgiza mata kai cike da damuwa yace "Ai ina nan tare da ke, ba inda zani
babu me taɓa ki idan ina nan insha Allah , ba wani abun tsoro fa"
A hankali ta cika Yusuf tana sauke Ajiyar zuciya, hawaye na cigaba da bin fuskarta.
Yusuf ya kalle ta yace "je kiyi brush se kici Abinci, ance tun jiya baki ci Abinci
ba"
Girgiza masa kai tayi Alamar A'a.
"Idan baki abunda nace ba, zan tafi in barki anan suzo su tafi dake"
A firgice ta kalle shi, ya jinjina mata kai alamar eh, rigarsa ta kuma riƙewa gam
ya rakata banɗaki ta wanke baki, ta fito, tana ta binsa da kallo kamar taga wata
halitta daban.
Da yayi hanyar fita seta biyo shi tana sake rirriƙe shi, gaba ɗaya tausayinta ya
kama shi, ya ɗauki bedsheet ɗin dake kan gadon ta ya ɗaura mata, ya ɗakko hula ya
saka mata.
Alhaji Bulama ya kalli Hajiya Halima yace "Nayi mamakin abunda ya tayar da ciwon
Widad, na zata tuni ta warke?"
Hajiya Halima ta taɓe baki tace "to ni ina zan sani, daga ita se ubanta se kuma
kai suke sakawa a lamarin su, ta yaya zan san kota warke ko bata warke ba"
"Amma abun da mamaki, Akwai buƙatar ta cigaba da ganin likitan ƙwaƙwalwa kenan?"
"Wannan kuma ya rage shawararka kai da Mahaifinta, ni 'yar kallo ce ai tunda alamu
sun nuna haukan yana nan tuburan"
Bulama yace "Hajiya Halima ai ba kyace haka ba ɗa na kowane"
"A'a wannan dai bata kowa bace, ta babanta ce kawi, ka dena wannan maganar nawa'
ya'yan dai nawane, itama 'yar wasu ce"
Ƙyalƙyalewa da dariya Alhaji Bulama yayi yace "Shikenan tunda haka kikace, ni dai
na tafi, Munyi waya dashi Megida kafin inzo nan yace yana kan hanyar dawowa, zezo
ya dubata idan jikin da sauƙi ya koma, idan kuma da yuwuwar a maida ita ga
likitocin ƙwaƙwalwa shikenan, dan be gama abunda yake ba ze yanke ya dawo, kin san
idan bata da lafiya baze iya komai ba, Allah ya bata lafiya"
Hajiya Halima tace "Karma Allah yasa tayi lafiyar, Ita da ubanta ya shafa bani ba"
Alhaji Bulama ya girgiza kai ya fice.
Yusuf Ya kira Amal a waya, ta ɗaga tana tura baki, dan gaba ɗaya kishin Yusuf take,
Yusuf yace "Amal dan Allah ki kawo Abu me ɗan ɗumi a bata taci, da alama tana jin
yunwa sosai"
"wallahi Yusuf ba dan kai ba ko zata mutu ba zan kawo komai taci ba, kaima ɗin dai
kawai zan kawo ne"
"Yi haƙuri, Nagode sosai da kika min Alfarma"
Amal ta shiga kitchen ta haɗa kayan tea, Mummy tace "Me zakiyi da tea ranar nan?"
"Widad za'a bawa" ta bata amsa
"ke meye naki a ciki to?"
"Mummy wai so kike se duniya tasan halin da muke ciki ne? Kar hankali ya dawo
kanmu, Ai se munayi muna ɓadda sahu"
Mummy tai murmushi tace "daɗina dake wani lokacin akwai hankali, ɗakkomin Jakata a
ɗaki"
Amal taje ta ɗakko mata jaka ta dawo, sannan ta ɗau tray ɗin ta tafi part ɗin
Widad.
Yusuf ya miƙe da nufin karɓo kayan tea ɗin, Amma Widad ta riƙe rigar sa tabi bayan
sa tana zare ido.
Yusuf ya kalli Amal yace "dama Amal dagaske Widad nada taɓin hankali?"
Amal tace "gashi kuwa kana gani tana yinsa tuburan"
Cikin tsawa Widad tace"niba mahaukaciya bace, ka gaya musu niba mahaukaciya bace,
su suka haɗani da hauka, su suke maida ni mahaukaciya, Amma niba mahaukaciya bace"
Gaba ɗaya Yusuf ya rikice, yace "is Ok ai dama ke ba mahaukaciya bace, ki kwantar
da hankalin ki"
Amal ta kalli Widad tace "kina wannan tamɓelen kike cewa ke ba mahaukaciya bace?
Kalli fa abunda kike yi mahaukaciya ce ke tuburan, dan me hankali baze abunda kike
ba"
Yusuf yace "Haba Amal, ya ana ƙoƙarin kwantar mata da hankali Amma kike tinzira
ta"
Amal ta zumɓura baki tace "kaga ni karɓi kayan nan, kalli yadda take wani riƙe ka
aikin banza kawai"
Widad ta shammace ta, tasa hannu ta kifar da farantin ruwan zafin, aikuwa ya zube a
ƙafar Amal, Ihu Amal ta saki, wanda ya janyo hankalin Mahaifiyar ta da Ramlah suka
taho da sauri.
Idan ba gizo idon Yusuf yake masa ba, tabbas kamar ragowar ƙwayar magani ya gani a
ƙasan kofin da'aka zuba tea ɗin, sedai kafin yayi wani yuƙuri
Hajiya Halima taƙarsaso tana cewa "lafiya, meye haka?"
Cikin kuka da azaba Amal tace "Mummy, Widad ta ƙonani da ruwan zafi, Mummy ƙafata"
Mummy ta kalli inda Yusuf ke tsaye, Widad na riƙe da shi tace
"To maye Jarababbe, ka lallaɓa ka Asirce ta ita da uban ta, shine ka koma da baya
zaka illatamin 'ya ko? Wallahi ka kiyayeni, kuma kafin kasa kwaɓata tayi ruwa ni
zanyi maganin ka, ke kuma" ta nuna Widad dake bayan Yusuf tace "dan Ubanki ba dai
hauka ba, a haka zaki ƙare, Hauka yanzu kika fara shi, daga nan har ƙarshen rayuwar
ki, keda hankali sedai ki ganshi a gurin wasu, wannan haukan haka zaki mutu kina
yinsa"
Widad ta Jijjiga Yusuf tace "kai ka gaya musu niba mahaukaciya bace, kuma wallahi
idan ta kasheni itama sena kashe ta, gaba ɗayansu sune zasu kasheni, suna tace min
mahaukaciya zasu kasheni, wallahi in baka hana su ba ni zan kashe su"
Ramla tace "kaga Malam dalla cikata kazo ka bar gidan nan, tunda babu gadon ka a
ciki, ba'a haɗa kuɗi da matsiyacin uban ka an gina ba"
Wani irin kallo Widad takewa Ramla daga bayan Yusuf.Kallon da Widad kewa Ramla ne
yasa taga kamar Widad ta dawo hankalin ta.
Widad tace "idan ka tafi ka barni kasheni za suyi, kashe mutane suke yi fa"
Mummy tace "uwarwa muka kashe miki? Mu bama kisa kumako bamu kashe ki ba mutanen
da kike Wulaƙantawa suna nan suna bibiyar ki zasu kashe ki, Mahaukaciyar banza da
ta wofi, Allah kaɗai yasan me sukeyi da harta yarda da shi haka, dalla kuzo mu tafi
suje su ƙarata, Allah ya ƙara birkita ƙwaƙwalwar ki zauna a haka koma samu mu huta,
in ƙwaƙwalwar ki ta birki ce ta Ubanki ma ta birkice kowa ya huta da iskancin ki"
Ramla tace " Mummy watch your words fa, kina ta sakin layi mu tafi kema Amal Allah
ya ƙara, maganinki kina ma wannan ɗan isakan direban shisshigi, gashi ai sun ƙonaki
a banza nan gaba ma illataki zasuyi"
Shiru Yusuf yayi yabi bayan su da kallo, gaba ɗaya tausayin Widad da Mahaifinta ya
kama shi.
Ya lallaɓa Widad ya bata youghurt da ƙyar ta sha, tana sha tana masa surutai na
shirme, irin na masu taɓin hankali.
"Menene dalilin samun taɓun hankalin Widad?" Yusuf ya tambayi kansa
Kwanciya tayi a jikin sa tana lumshe ido alamar bacci take ji, ƙirjin Yusuf se
bugun uku uku yake, Kasancewar ya keɓance da Widad, abunda be taɓa yi ba, a duk
lokacin da yayi yunƙurin rabata da jikin sa seta saka ihu kamar ƙaramar yarinya.
Yusuf yayi mamakin iri maganganun da Hajiya Halima da 'ya' yanta suka dinga faɗa
akan Widad, koda yake ba abun mamaki bane, duba da Yadda Widad ɗin ke Wulaƙanta su,
Amma me sukayi mata take musu haka? " Yusuf yayi Alwashin tone duk wani abubuwa da
ake ɓoyewa, kuma ya ƙudurce a ransa zeyi duk me yuwuwa ya jure wulaƙancin Widad
yaga ta ina ze temaki rayuwar ta.
Yusuf yai shiru yayi zurfi a cikin tunani, yaji Widad tana ajiyar zuciya alamun
tayi bacci, a hankali ya zame ta daga jikin sa, ya kwantar da ita ya lulluɓeta ya
fita ya kulle ta a ɗakin yaje yai salla.
Ana idar da Salla Isa yace " Yusuf ashe uwar ɗakinka ce babu lafiya? Ance taƙi
buɗewa kowa ƙofa amma tana jin muryar ka ta buɗe, gaskiya kai ɗan baiwa ne, Amma
naji ance haukan nata ne ya tashi ko?"
Yusuf ji yayi kamar ya kwaɗawa Isa mari, Amma ya ƙyaleshi ba tare da yace masa
komai ba.
Ya koma ɗakin nata ya tarar bata farka daga baccin ba.
Falon ta ya koma yana tunani, Ba zato ba tsammani yaji sallamar Mahaifin Widad a
falon, Amsawa Yusuf yayi cikin girmamawa tare da risinawa.
Alhaji Nasir a ɗan ruɗe yace "Sannu babban Mutum, ya me jikin kuma?"
"Alhamdilillah, ta samu bacci"
"Masha Allah"
Yasa kai ya shiga bedroom ɗin, ya taka a hankali zuwa gaban gadon Widad ya zauna a
gefen ta ya ɗagota, idon ta a rufe tana bacci, ya shafa kanta yace "Allah ya baki
lafiya my daughter" ya kalli Yusuf yace "Nayi mamaki data iya yadda da kai, idan
ciwon nan ya tayar mata bata yadda da kowa seni, ko Bulama wani lokacin muɗinma
bata yadda damu gaba ɗaya se an mata allurai"
Yusuf yace "Wane irin ciwo ne haka?"
Alhaji Nasir ya ɗan na Numfashi cike da damuwa yace "Yusuf, nasan mutane da yawa
suna mata kallon bata da kirki, wasu suna zargina da barin 'yata ta lalace, kawai
ina kallon sune, ba tare da nace wa kowa komai ba, Yusuf Widad ita kaɗaice' yata
dana mallaka, larurar nan ta same ta ne sakamakon kashe mahaifiyar ta akan idon ta"
Zaro ido Yusuf yayi yace "Innalillahi wa inna ialaihi raji'un" Alhaji Nasir ya
jinjina kai yace "ƙwarai kuwa, Akwai abunda ya faru da Widad, wanda tun daga
lokacin take gudun mutane, ta haɗu da larurar ƙwaƙwalwa, dukda partially ne larurar
tata da farko, Amma daga depression ya zarce mata ta samu Arthropophobia,larurar
ƙwaƙwalwa me sa mutum ya dinga jin tsoron mutane, ba mutane ba wani lokacin idan
tana cikin larurar ko haske bata so, muna ta magani Sedai har yanzu na gaza samun
abunda zesa ta farinciki, kana gani ko fara'ar kirki ba tayi, na yanke shawarar in
mata Aure amma tace bata so, dan Allah Yusuf na san kana haƙuri haka nan naji ka
kwantamin, dan Allah ka tayani Addu'a, Allah ya bawa 'yata lafiya, ita kaɗai nake
da ita, ba uwa ba uba"
Gaba ɗaya tausayin Alhaji Nasir da' yar sa suka cika shi, Yusuf ya numfasa yace
"Insha Allah Alhaji, Amma ba kayi......
"Yallaɓai ya akayi harka shigo ban sani ba? muna can part ɗina muna fafutukar a
kira likita yazo ya duba ta, gaba ɗaya yau kwana mukayi ba muyi bacci ba saboda
yadda jikin Widad ya rikice, ko Abinci ba wanda ya iya ci yanzu ma mun shiga muyi
salla ne ka dawo ban sani ba" Hajiya Halima ke wannan maganar cike da salon bariki
da Kissa.
Alhaji Nasir yace "Allah sarki, nasan kina ƙoƙari akan Yarinyar nan, Allah ya saka
miki da Alkhairi, ina su Baby Amal ɗinne ko basu san na dawo ba?"
"Amal ma bata jin daɗi, Ramla kuma salla take, ina jiran Widad ta farka ne a bata
Abinci, mun samu da ƙyar tayi bacci"
Yusuf kam bin Hajiya Halima yayi da kallo, yana mamakin wannan iya salon barikanci
nata, gaba ɗaya ta juye kamar tana cikin damuwar gaske.
Yusuf yace "Bari inje gida Alhaji tunda ka dawo"
"Shikenan Yusuf ka gaida gida, nagode sosai Allah yasaka da alkhairi"
"A'a bakomai Yallaɓai" Yusuf yasa kai ya fice, Hajiya Halima tabi bayan sa da
harara.
Kan Yusuf ya ƙara ɗaurewa da maganganun da Alhaji Nasir ya gaya masa, yana daf da
fita kawai yaga Ramla ta sha gaban sa.Tsayawa yayi yana kallon ta, ta kalle shi
cikin Isa tace "Bani mukullayen Motar Widad dana ɗakin ta dake gurin ka"Yusuf ya
tsuke Fuska yace "ɗan bani hanya zan wuce mana""Ni kake kallo kakewa wannan gadarar
haka? Zaka bani ko sena maka rashin mutunci?""bake kika bani ba, ba kuma ke nakewa
aiki ba, dan haka babu ruwan ki dani""Kai kalli tsabar Idona, karka kuskura kace
zakayi Jayayya dani, naga se wani shisshigi kake kana cusa kai a gurin waccan
Mahaukaciyar da ita da Ubanta, to bari kaji in gaya maka, idan ma wani abu kake
kwaɗayin samu wallahi ba zaka samu ba, Kuma hauka yanzu Widad ta fara shi daga nan
har ƙarshen Rayuwar ta, ba zata sake moruwa ba, gara ka cire wa kanka ƙwalamar
wannan daular da dukiyar, yadda kazo a talaka haka zaka koma a matsiyaci, idan kaga
dama kaje ka faɗawa duk wanda zaka faɗawa, shawara ta ƙarshe da zan iya baka itace,
ka gaggauta Ajiye aikin nan ka ƙara gaba ya fiye maka Alkhairi akan wasa da rayuwar
ka"
Murmushi Yusuf yayi ya dubi Ramla yace "in kinga na bar aiki a gidan nan wanda
nakewa aikin ne suka sallameni, kina wani iƙrarin dukiya, dukiya nawace taki a
dukiyar nan? Ki kiyayi Yusuf, matsi da takura babu wanda Yusuf be gani ba a rayuwar
sa, dan haka ƙaramar barazana irin taki ba zata hanani Aiki na ba, ni babu ruwana
da rayuwar da kuke a cikin gidan nan ni aikina kawai nasani, ban guri in wuce ko in
hankaɗeki"Galala tabi Yusuf da kallo, da ma akwai Yadda yake mata magana cikin Izza
shima, Me yasa ba yayiwa Widad da take Wulaƙanta shi, lallai maganar Mummy gaskiya
ce, ya kamata ayi maganin Yusuf.
Yusuf fa kai ya sake ɗaukar wuta, abun da ya faru yau, ya ƙara tabbatarwa Yusuf
akwai wani mugun nufi a zuciyar Hajiya Halima da 'ya' yanta. Umman Yusuf ta lura da
yanayin Yusuf ko iya sakewa yaci Abinci ba yayi, Umma ta kalle shi tace"Yusuf wai
meke damunka ne haka? Naga gaba ɗaya kwanan nan na kasa gane kanka, Allah yasa ba
wani abun aka kuma yi maka ba?"
"Umma ni a rayuwa ta wani irin ƙalubale ne ban gani ba? Aini lamarin rayuwa ta na
miƙawa Allah, aikin da aka bani ne me matuƙar rikitarwa"
Nan ya kwashe komai ya gayawa Umman sa, Umms tayi shiru na wasu 'yan mintuna sannan
tace "lallai wannan lamarine me sarƙaƙiya, nidai fatana ka kula da kanka Yusuf,
kayi taka tsan tsan ka cigaba da Addu'a, Amma waye yazo ya nemi da a dinga bawa ita
Yarinyar kariya?"
Shiruu Yusuf yayi sannan ya girgiza kai yace "Wallahi Umma ban sani ba"
"Ta yaya za'a bawa mutum kariya ba tare da sanin sa ba? Kaima kamar baka san aikin
naka ba?"
"Umma nasan aiki na, Amma nima umarnin manya na nake bi, wataƙila be kamata in sani
bane"
"Hakane amma kayi taka tsan tsan, naji tausayin yarinyar nan, Amma ni jikina yana
bani wani abu game da aikin nan da aka saka, Amma kasa gane ko menene, ina dai yi
maka addu'a a duk inda kake Yusuf, ni dai fatana ka kula da kyau"
"Insha Allah Umma na"
Haka suka cigaba da taɓa hirarrakin su na ɗa da uwa.
Sosai tunani ya auri Yusuf, maganar Umma tana bisa hanya, waye wannan da ya nemi a
bawa Widad kariya a ɓoye, dole akwai wata a ƙasa.
*******************
Washegari da safe, Yusuf ya koma gidan su Widad, bayan sun gaisa da su Nura, Yusuf
yace "Nura ya jikin uwa ɗakina kuwa?"
Nura yace "ta yaya zamu sani? Kaine dama aka ɗauka mutum a gidan nan, da kai ake
komai mu ina zamu san wani abu? Ai kaine mutum a cikin mu"
Yusuf yayi Murmushi ya samu guri ya zauna. Murtalah ya ƙaraso inda Yusuf yake yana
faɗin "Malam Yusuf, ɗazu Alhaji ya leƙo yana tambayar ko kazo, dama yace in kazo a
shiga da kai ɓangaren sa"
Yusuf yace "shikenan babu laifi, muje"
Murtalah yayi gaba Yusuf ya bishi a baya, Sam Yusuf be taɓa sanin da wannan
ɓangaren a cikin gidan ba, gjda se kace ba'a duniya ba, Yusuf ya buɗe ido yana bawa
idonsa Abinci. Suna shiga Ƙaton falon, Murtalah yace "to ni na tsaya daga nan, dan
bani da ikon ƙarasawa ciki, seka fito" Seda Yusuf ya gama waige2 sannan ya kalli
ƙatuwar ƙofar dake cikin falon, a hankali ya taka yaje ƙofar ɗakin ya ƙwanƙwasa
tare da yin sallama.
Alhaji Nasir ne ya amsa tare da cewa "Shigo" Yusuf ya tura ƙofar ɗakin ya shiga,
Alhaji Nasir ne zaune Widad ta ɗora kanta akan cinyar sa, idonta biyu tana ta
jujjuya ƙwayar idon ta, gefe kuma Alhaji Bulama ne zaune a kusa da Alhaji Nasir.
Yusuf ya durƙusa yana gaishe su, Alhaji Nasir ya faɗaɗa murmushinsa yace "Me
babban suna, ashe kazo?" "Eh nazo ranka ya daɗe, yame jiki" Alhaji Nasir yace "Jiki
da sauƙi, Alhamdilillah an samu ta dawo hayyacin ta, Amma taƙi magana sam" Yusuf ya
kalle ta yace "Sannu ya jikin naki?" Haɗe rai tayi ta tura baki tace "Malam ni
lafiya ta ƙalau" Alhaji Bulama ya jinjina kai yace "gaskiya akwai ka da sa'a, tun
ɗazu muke magana taƙi kulamu amma kai gashi tayi maka magana"
Alhaji Nasir yace "My lovely, kin san wannan?" yai maganar yana nuna mata Yusuf
"Daddy nifa ba mahaukaciya bace"
Daddy yace "Ai na sani Babyna, tambayar ki kawai nayi"
Ta tura baki tace "Nasan shi"
Alhaji Bulama yace "to waye?"
"Direba ne" ta bashi amsa a taƙaice.
Daddy yace "direban wanne daga ciki?"
Maimakon ta basu amsa seta kalli Yusuf tace "kai ka gaya musu niba mahaukaciya
bace, naga suna yadda da maganar ka, wallahi ni ina da hankali"
Yusuf yace "ai dama basu ce ke mahaukaciya bace, kina da hankali"
Ta kuma cewa "ka gaya musu wani na ƙoƙarin kasheni a gidan nan, ka cewa Daddy dan
Allah ya ƙyaleni in koma England"
Yusuf yace "Shikenan ki kwantar da hankalin ki, zan gaya musu Insha Allah"
Alhaji Nasir yace "Naga taku tazo ɗaya da Yusuf Lovely, kamar shi kin yadda da
shi ko?"
"Allah ya kiyaye, direba ne kawai, yana nan a matsayin sa na direba, karma ka faɗi
wani abu da zesa yaji cewa shi na musamman ne, ko yana da wani matsayi, i don't
trust anyone"
Alhaji Nasir ya girgiza kai yace "Yusuf nagode sosai, zaka iya tafiya abunka kaje
ka huta, dama na kiraka ne in ƙara maka godiya nagode"
Yusuf yace "Ai babu wani abun godiya da nayi Yallaɓai, Allah ya bata lafiya"
Suka yi Sallama ze tafi, sedai yana ƙoƙarin barin ɗakin, Hajiya Halima ta shigo da
tray da kayan marmari a kai, tana ganin Yusuf ta haɗe rai ta bishi da wata uwar
harara ba tare da ta bari Alhaji Nasir yaga hakan ba.
Yusuf ya kama hanyar fita, yaji ance "Yusuf ashe kazo?" Ya juyo ya kalli inda Amal
ke masa magana yace "Eh nazo, tun ina ciki na duba jikin Madam ne" Amal tace
"shikenan ɗan jirani ina zuwa" "to shikenan bari in jiraki a waje" Yusuf ya koma
harabar gidan yana jiran fitowar Amal, mintuna kaɗan sega Amal tazo, kaya ne a
jikin ta wanda sukai matuƙar matsarta, ta dube shi tace "dan Allah so nake muje
gurin shan ice cream tare, Akwai maganar da nake so muyi" "Kina ganin ba matsala
kuwa? Kinga wancan karon, Madam bata ji daɗin fita da mukayi tare ba" "Shikenan
idan ba zaka iya min Alfarma ba, na fasa zuwa"
Ɗan shiru Yusuf yayi yana nazari a ransa, tabbas Amal bata da wayo sosai, idan ya
bugi cikin ta ze samu bayanai, dan haka ze iya shanye masifa da tsiwar Widad, a
fili yace "shikenan kawo car keys ɗin naki mu tafi" Ta kalle shi tayi fari da ido
tace "Dan Allah meye matakin karatun ka ne? Ka iya turanci Yusuf" Ɗan basarwa
kawai yayi murmushi ya nufi inda motocin suke.
Wani Joint tasa ya kaita, tayi ordering Pizza da tea, ta tambayi Yusuf me zeci yace
shi baya cin komai.
Yusuf ya kalleta yace "Wai ya naganki duk wata iri ne yau?"
Ɗan taɓe baki tayi tace "ba lafiya ba, shine ko ka tambayeni ya jikina? bayan a
gabanka Widad ta ƙonani jiya ba abunda kayi, baka damu dani ba, Amma nasan saboda
rashin lafiyar ta yasa kazo da wuri yau" ta ƙarasa maganar tana tura baki
Yusuf ya ɗanyi Murmushi yace "kiyi haƙuri, kinga bata da lafiya wani mataki zan
ɗauka akanta? kuma kinga kaman mamanki da Yayar ki basa Son ina yawan shiga
al'amuran gidan ku"
Amal tace "ba Al'amuran gidan nan ne basa son kana shiga ba, Al'amarin Widad ne da
kake nuna damuwa dashi sosai ne basa so, ko baka ga Yadda take Wulaƙanta mutane
ba?"
"Eh amma, ita ina maman ta ne take rayuwa ita kaɗai?"
Amal ta ɗan taɓe baki tace "Kashe ta akayi fa, shine dalilin da yasa ta zama
mahaukaciya bata son mutane"
Zare ido Yusuf yayi kamar besan komai ba yace "waye ya kashe ta?"
Amal ta taɓe baki tace "Oho wayasani? Kana gani dukda mahaifinta yana da kuɗi amma
a binciko wanda yayi laifin abu ya gagara, shi ne ita kuma tace zata nemo wanda
suka kashe mahaifiyar ta, akwai mutanen data sa aka kama aka kulle a prison ba tare
data nada wata cikkakiyar hujja ba, dan haka itama ake farmakinta, sannan akwai
wani abu da'ake so a karɓa a gurin ta wanda nima ban san komenene ba, Shiyasa nake
gujemaka yawan Shiga lamarin ta bayan Aƙidarta ta Wulaƙanta mutane, duk randa ka
bari wani kusanci me ƙarfi ya shiga tsakanin ka da ita, ba shakka za'a fara
farmakin rayuwar ka domin za'ace kasan inda abunda ake nema a gurin ta yake, shine
death Contract ɗin data gaya maka ai!!!"
IN AN KARANTA AYI SHARHI PLEASE SANNAN AYI SHARE
07063065680 Ayshercool
_*AƘIDATA*_
PERFECT WRITERS ASSOCIATION
(WE AIN'T PERFECT BUT WE ARE ALWAYS TRYING OUR BEST, TO MOTIVATE AND ENTERTAIN OUR
READERS)
https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/
P. W. A
*Story and written by*
_*AISHA HUMAIRA (Daddy's girl)*_
The experience writer of *ABDUL JALAL** WATA KISSAR.... (SAI MATA) *And now *AƘIDA
TA *
I dedicated this book to my Mum (Malama Nafisat Adam Muhammad) i love you mum
ELEGANT ONLINE WRITER'S
PART1 Page 10
Shiru Yusuf yayi yana bin Amal da kallo, tare da nazarin maganganun ta.
"Waye ya kashe Mahaifiyar Widad? Me yasa aka kasheta!!? Meyasa ake bibiya da
barazana ga dukkanin wanda yake da kusanci da ita!!!? Meye dalilin rushewar
binciken wanda suka kashe mahaifiyar Widad? Meye Alaƙar kisan Mahaifiyar Widad da
wanda Widad tasa aka ɗaure!!!? Meye alaƙar ciwon Widad da ƙwayar dake cikin tea ɗin
da'aka kawo mata?
Wannan sune jerin tambayoyin da suka shiga kaiwa suna komowa a cikin ƙwaƙwalwar
Yusuf.
Ta ɗago ta kalli Yusuf tace "let's keep this aside, Yusuf ka taɓayin budurwa? Ko
kana da budurwa a halin yanzu?"
Jin tambayar Yusuf yayi wani banbarakwai, ta tuna masa da abu mafi ciwo a rayuwar
sa da baze manta ba har ya koma ga Allah, ya kalle ta ya ɓoye damuwar sa yayi
murmushi yace "Budurwa kuma? Wacece zata so talakan mutum kamata? Ni bani da wata
budurwa ni kaɗai ne, ai nayi ƙarami inyi budurwa" Murmushi tayi tace "ka fiye abun
dariya, a haka kamar baka magana, Amma ka iya sa mutum dariya, yanzu babba da kai
kace kayi ƙarami da budurwa?" "Eh mana ko dan kin gani ƙato? Yarone ni ƙarami" Ta
sake yi masa wani murmushin tace "hmm Shikenan, kodai Widad kake so?"Zare ido yayi
kamar idon ze faɗo yace "Ni, rufamin Asiri, inani ina 'ya' yan manya, ai iyakacin
talaka daku yayi muku aiki ku biyashi""Amma meyasa kake nuna damuwar ka a kanta
haka? Dukda tarin wulaƙanci da rashin mutunci da take maka a wasu lokutan?""Saboda
batamin wulaƙanci se idan na saɓawa umarnin ta, kuma mahaifinta yana matuƙar
mutuntani, kuma kinga nine a ƙarƙashin ta, dole inyi haƙuri da duk abunda zata yi
min"Amal ta numfasa tace "hakane, Amma ina shiga matuƙar baƙin ciki a duk lokacin
da naga tana cin zarafin ka, shiyasa nake ganin meze hana ka ajiye mata aikin ta,
in samo maka wani aikin ka huta da wulaƙanci?"
Yusuf yayi Murmushi yace "Inajin daɗin wannan aikin a hakan, bana so kiyi wani abu
da ze ɓata ran mahaifiyar ki, Amma ina godiya da karamcinki a kowane lokaci, tunda
kin gama, muje in sauke ki a gida nima in tafi, kafin Madam ta farga tare muka fita
dake" yai maganar cike da ƙoƙarin basar da maganganun Amal
Amal ta jinjina kai ta miƙe, suka bar gurin.
***************************
"Bayanai sun sameni cewar, Akwai yuwuwar Bala ya tona mana Asiri, yayi iƙrarin cewa
tunda aka kaishi prison babu wani ƙoƙari da muke dan fitar dashi, munawa kabmu
ƙoƙarine kawai, dan haka na yanke shawarar in kiraka muyi wata magana, fatan zaka
buɗe kunnenka ka saurereni"
"To Yallaɓai, ina saurarenka"
"Hashim, Abunda nake so da kai shine, So nake a zuba magani a Abincin daza'a bawa
Bala, wanda ze sashi rashin lafiya, daga nan se a kaishi Asibitin doctor Mukhtar, a
can nake so a ƙarasamin shi, a kauda shi daga duniyar gaba ɗaya dan baze ɓata mana
shiri ba"
Hashim Yace "Amma Yallaɓai aikin nan fa yana da hatsari sosai, kasada ne me girma,
idan aka gano da hannuna a ciki zan rasa aikina, kuma za'a kamani"
A hasle mutumin yace "Kowace irin kasada ce gara ayita matuƙar Sunana baze fito ba,
bazan zuba ido suna na ya ɓaci a banza ba ba tare da na cimma burina ba, Amfanin
Bala ya ƙare dan haka a kauda shi bashi da sauran amfani a gareni, kana da damar
yin hakan, kana da dama a hannunka dan haka kayi yadda nace, tun kafin raina ya
ɓaci"
Hashim yace "Amma Yallaɓai......
"Sadakin aikinka naira million biyu ne, idan ba zaka iya ba zan saka a gefe in saka
wani yayi min, Amma kasani kaima bazan barka a doron ƙasa ba tunda kasan sirrina,
tashi ka fita na gama magana da kai "
**********************
Widad ta koma normal kamar ba ita ba, dan haka Daddy ya fara shirin komawa saboda
Ayyukan da yake dasu, sedai sun fafata da Widad sosai dan ya sake yi mata batun
Aure, ita kuma ta ƙara tabbatar masa tana nan akan bakarta ba gudu ba ja da baya,
hakan yasa suka ɗan samu saɓani, ya tafi ba tare da tayi masa rakiya ba.
Yusuf yaje ya tsananta bincike akan gano waye mahaifin Nurat, wadda suka je gurin
birthday ɗinta shi da Widad, ya samu bayanin wasu abubuwan ne daga gurin Amal,
wadda ta riga ta gama narkewa a ƙaunar Yusuf. Mahaifin Nurat babban ɗan siyasa ne,
sukan haɗu da mahaifin Widad a gurin kasuwanci, amma bayanai sun nuna akwai
tsohuwar Alaƙa dake tsakaninsu wadda daga baya tayi rauni, 'yarsa da Widad sun haɗu
a gurin karatu ne a ƙasar waje, ita kaɗaice ƙawar Widad a Nigeria, se 'ya'yan
Alhaji Bulama, shima ba wata alaƙace ta kusa tsakanin su ba, dan bata yarda a
raɓeta, ba kowa ke iya jure halinta ba.
Tsangwama ta yau daban ta gobe daban, haka Hajiya Halima, Ramla da ma'aikatan gidan
suke nunawa Yusuf, shi kuma ko a jikin sa, aikin da yaje yi shi kawai yake.
Isa mai gadi yayi yayi yasan daga ina Yusuf yake zuwa, Amma fafur Yusuf yaƙi
gayamasa, daga baya ma se ya janye jikin sa, bayan gaisawa babu abunda ke shiga
tsakankanin su.
Wasa2 aka shiga wata na uku, Amma Widad bata biya Yusuf haƙƙinsa ba, shi kuma koda
wasa be taɓa magana ba. Yusuf yana zaune a harabar gidan yana danna wayar sa, daga
sama yaji ance "Ssss" ɗaga kai yayi ya hango Widad ta saman bene, tayi masa alama
da hannun ta yaje.
Yusuf ya miƙe ya shiga, tana zaune a falo tana cin gugguru, tana ci tana bawa
magenta, Su Hajiya Halima na falon ita da su Ramla gaba ɗaya.
Yana shigowa Amal ta kalle shi tana kashe masa ido, seda yakusa faɗuwa dan gani
yake gaba ɗaya sunga abunda Amal tayi, Widad dake kaɗa ƙafa tana kallon Abunda Amal
tayi, bata tanka ba ta cigaba da watsa popcorn ɗinta.
Gefen kujerar da Widad ke zaune yaje ya zauna a ƙasan carfet yace "Gani ranki ya
daɗe" Ta kalle shi ta yamutse tace "Kai nifa bana son all such kind of names,
Malam sunana Widad, ka dinga kirana da sunana" Murmushi yayi mata tare da ɗan
girgiza kai yace "Bazan iya ba, nafi jin daɗin ince Madam, ko ranki ya daɗe"
"to bana so, niba basarakiya bace, ka kira ni da sunana kawai"
"Aike kinfi basarakiya ma gimbiyar Daddynta"
Wani ɗan guntun Murmushi tayi, wanda ita kaɗai tasan ma'anar sa.
Wani uban tsaki Amal tayi wanda bata san ya fito ba, ta miƙe a fusace da nufin ta
bar falon saboda haushi.
"Amal!" Widad ta kira sunan ta. cak ta tsaya ba tare da ta waigo ba.
"Me nayi miki ne?" Widad ta jefa mata tambayar
Fuska a cunkushe Amal tace "bakomai"
Murmushi Widad tayi wanda ya ƙara fito da kyawunta, tana girgiza santala santalan
ƙafafuwanta, sannan tace
"Kin san Widad bata Soyayya, balle ince zan so abunda kike so, shi kansa Son ban
yadda dashi ba balle inyi shi, koda zanyi so bazan so maƙasƙancin Mutum kamar
direba na ba, balle inyi wani abu da zesa kiji haushi saboda shi, ki kwantar da
hankalinki ba abunda zanyi da wannan abun, rainin hankalinsa da ƙwarin gwiwarsa
gurin karyamin dokoki ne ke burgeni wasu lokutan, ban taɓa ma'aikacin da yake
rainamin hankali da son yimin katsaladan a cikin lamaurana yadda yakeso kamarsa ba,
wani abu dana fuskanta shine, ze iya jure duk wani hali da AƘIDATA, hmm ki huta beb
ba wani abun damuwa a cikin abunda nake" ta ƙarasa maganar tare da wani murmushi na
rainin hankali.
Yusuf ya kalli Widad, yaji haushin maganganun ta, ya ƙudurce wani abu a ransa.
Ta kalli Yusuf cike da kashedi tace "Kaikuma tara ka kawai nake, ina sane da duk
abunda kake yi, ina gargaɗinka akan contract ɗin daka sawa hannu, Ni kaɗai na
ɗaukeka aiki, ni kaɗai zakayiwa Aiki, idan har zakayi soyayya or what ever Rubbish
you call it, kayishi bayan ka bar gidan nan, hope I made my self clear "
Yusuf ya jinjina kai, a fusace Mummy tace "Aikuwa se naci uban Amal akan yaron nan,
ka kiyayi 'yata ba kai ba ita, banda tsiyar ɗan talaka ina kai ina Amal, ƙwarya
tabi ƙwarya mana, wallahi duk lokacin da ka kuma shiga sabgarta sena saɓa maka"
"Cewa akayi ana sonsa bashi yace yana so ba, ko ba kya gani ne? Kina zaƙewa gurin
ci masa mutunci wasu lokutan, na lura Daddy yana matuƙar ji dashi saboda
biyayyarsa, yana girmama shi sosai, ko dan haka at least dole a ɗagamasa ƙafa
saboda yana matsayi me girma a gurin megida, dan haka a dinga ɗaga masa ƙafa a dena
son shiga hurumin dabe dace ba"
Ta kalli Yusuf tace "Aiken ka zanyi, kaje ɗakina, ka ɗauki key a drower mudubi, ka
buɗe wardrobe ɗina ta ƙarshe, ka ɗakko ATM ɗina kazo"
Ba Hajiya Halima ba har Ramla da Yusuf seda suka kalle ta da sauri. Ta basar ta
maida hankali kan talabijin, kamar ba ita tayi magana ba, jiki a sanyaye Yusuf ya
miƙe ya nufi ɗakin ta, gaban sa se faɗuwa yake, inda ta kwatanta masa yaje ya ɗau
key ɗin ya buɗe wardrobe ɗin da tace.
Ramla ta kalli Widad tace "Amma Widad kamar be kamata kitura ƙato kamar wannan
ɗakinki ba"
Widad bata kalle ta ba tace "gayamin abunda ya kamata Uwata"
Ramla taja bakin ta ta tsuke, dan tasan idan taja maganar se ranta ya ɓaci.
"Subhanallah" shine abunda Yusuf ya furta, dan bayan sutura dake cikin wardrobe ɗin
Widad, hadda bandir bandir na kuɗi na Nigeria dana ƙasashen ƙetare. A gagguce ya
ɗau abunda ze ɗauka ya fita ya kai mata, maimakon ta karɓa se ce masa tayi "Kaje na
baka hutu na sati ɗaya dan ba inda zanje a kwanan nan, ina so kaje da ATM card ɗin
nan, ka cire kuɗi, ka siyomin latest trending phone me kyau guda biyu"
Yusuf yace "Yanzu zan siyo in kawo miki?"
Ƙura masa ido tayi ba tace komai ba, kallon gargaɗi take masa akan bata son rainin
hankali, dan haja Yusuf ya girgiza kai ze fita, Widad tace "Ji mana" ya tsaya tare
da waigowa ya kalle ta"Yanzu idan na tambaye ka kasan inda rai yake, wace amsa zaka
bani?"
Ɓoye mamakin tambayar da tayi masa yayi yace "Allah Mahalicci shikaɗai yasan wannan
Amsar"
Ta jinjina kai tace "Good you can go"
Hajiya Halima a gigice tace "Widad baki da hankali ne? Ya zaki bawa baƙo wanda baki
san daga inda yake ba ki ɗau ATM wanda Account ɗin cike yake da kuɗi, Yallaɓai ma
yana zuba dukiyar sa a ciki, kodan baki san zafin dukiyar ba sama taka aka tara aka
baki, yanzu idan ya gudu yaƙi dawowa fa?"
"Kalma ta farko kin faɗi abunda ya dace a kaina, kin faɗa daidai ba kuskure, bani
da hankali ni mahaukaciya ce kamar yadda kuka saba faɗa, dukiya kuma ta ubana ce,
idan na salwantar da ita ba abunda zece tunda nima akwai tawa a ciki, ki dena tada
jijiyar wuya akan dukiyar daba taki ba, idan tunanin ki abunda zaki samu bayan me
ita ya mutu, sena tabattar da na ƙarar da komai kafin ya mutu koni na mutu, shine
hanyar da zan baƙantawa masu harin dukiyar nan rai, and Mark you idan wani abu ya
samu dukiya ta a yanzu to ba shakka kece, saboda babu wanda yasan da ATM ɗina a
hannun sa seke da iyalanki"
Widad ta miƙe ta barmusu falon suna kallon kallo.
***********************"Mummy, me yasa Daddy yayi yunƙurin sawa a sace Widad ne? Am
so much Confused fa, tunda akayi abun nan ta bar gidan nan bata ƙara kirana a waya
ba"
Mahaifiyar Nurat tayi ajiyar zuciya tace "Nurat nima ban sani ba gaskiya, ni banda
yanzu da kika gayamin ma ban san abunda yake shiryawa ba, yanzu ina magana ze iya
ɗaukar mummunan mataki a kaina, kin san halin sa"
"Amma Mummy abun ya ɗauremin kai, kinji yadda ya dingamin masifa dan na bari an
ɗauke ta, kuma fa wani ne yayi barazanar ze saceni nima in har ban gaya masa inda
take ba"
"Mhmm Nurat, kija bakinki kiyi shiru da wannan maganar, dan muddin kika bari wani
yaji maganar nan mun kaɗe a gurin mahaifinki"
"Insha Allah Mum ba wanda zan gayawa"
*************************Tunda Yusuf ya tafi da ATM ɗin nan Hajiya Halima ke cikin
zullumi, dan ba ƙaramar dukiya ce danƙare a account ɗin nan ba, tunani take yadda
zata gano inda Yusuf yake, tasa a ƙwato mata ATM card ɗin nan. Ramla ta aika ta
kira mata Isa me gadi, ba tare da ɓata lokaci ba ya biyo Ramla jikin sa na tsuma
zuwa falon Matar gidan.
"Kai wani irin sokon gara ne haka? Har yanzu ace ka kasa gano inda wannan talakan
banzan yake?"
"Wallahi ranki ya daɗe ya dena zama a cikin mu ma, wani girman kai yake ji da shi,
yanzu shi kaɗai yake al'amuransa ko inda muke ya dena zuwa, iyakacinmu da shi
gaisawa" Dogon tsaki Hajiya Halima taja tace "dallacan sakarai ni rufemin baki,
tashi ka bar nan sakarai kawai, ni na tsaya bi ta kanka, zan nemi wanda zasu yi min
aikin".Isa ya tashi jiki a sanyaye ya bar falon, Mummy ta kalli Ramla tace "Ramla
meye abunyi ne? Me ya kamata muyi?"
"wallahi Mummy kaina ya kulle, na rasa abunyi, yarinyar nan ta tabbata mahaukaciya,
Mummy idan dukiyar nan ta salwanta ya zamuyi?"
Hajiya Halima tayi ajiyar zuciya tace "bana tunanin yaron nan ze gudu da ATM ɗin
nan, Widad tana da wayo ze iya yuwuwa tarko tayi masa, Amma tunda harta yadda dashi
haka, dole mu janyo shi cikin mu"
"Hakane Mummy zeyi mana Amfani, idan har ya kasance a ɓangaren mu, Ammafa kamar
zeyi taurin kai gayen"
'idan yaƙi yin yadda muke so, then we should exact power over him, you know what I
mean "
Ramla ta jinjina kai tare da yin murmushi tace "Am proud of you Momma "
*****************************
Kwance yake akan makeken gado a wani tangamemen ɗaki me ɗauke da kayan alatu, ya
mimmiƙe ƙafafuwan sa hannun sa riƙe da waya yana kallon hotuna. Gefen sa wani
matashin ne zaune a gefen gado yana tattaɓa System.
Hotunan Widad ne akan screen ɗin wayar kala kala yana kallo yana murmushi, kowanne
se ya tsaya yayi zooming ɗinsa ya ƙare mata kallo, yanayi yana shafa sajensa tare
da tattausan murmushi, ga dukkan alamu yana jin daɗin kallon hotunan nata. A
hankali ya furta "Can't wait to see you darling" Matashin da ke gefen sa ne ya
waigo ya kalle shi yace "Nifa ka isheni, se kace akanka aka fara Soyayya, kullum
se kayi zancen yarinyar nan seka kalli hotunan ta, kuma ban taɓa jin ko waya kayi
da ita ba" Shafa sumar kansa yayi tare da yin murmushi yace "bazaka gane bane
Fahad, yarinyar ce 'yar daru se hankali, dukda ƙanwa tace amma halinta daban yake,
ina tunanin yadda zata karɓi soyayya ta idan na bayyana mata"
"saboda me kake wannan tunanin?"
"saboda tace shi kansa son bata yadda dashi ba"
Ƙyalƙyalewa da dariya Fahad yayi yace "Wallahi Anwar kana ruwa, se kace ita
kaɗaice mace kaje ka nemi wata mana, dama da ganin ta zatayi izza, nifa rabona da
ita tun tana yarinya ƙarama sosai"
Anwar yace "hmm tabbas da zaka ga Widad a yanzu ba zaka taɓa cewa in haƙura da ita
ba, Ina matuƙar sonta, na ƙagu in koma gida, wallahi yadda na ƙagu in ganta be kai
yadda nake son ganin su Amal da Ramla ba, gashi seka rigani komawa da sati biyu"
Fahad yace "lallai ka tsunduma da yawa, nima ina son in koma inga Ramla, dukda ni
muna waya da chatting da ita"
"Aishi yasa nake ta Addu'a, Allah ya bani Widad a matsayin mata"
Fahad yace "Hmm Allah dai ya baka me sonka"
***********************Gaba ɗaya hankalin Hajiya Halima yaƙi kwanciya, gashi duk
wanda ze kaiwa Alhaji Nasir ƙarar Widad to lallai zasu ɓata, ranar kwana na bakwai
da tafiyar Yusuf, Hajiya Halima se sintiri take tsakanin part ɗinta da babban falo,
Widad kam ko a jikin ta shagalin ta kawai take.
Yusuf ne yayi Sallama a falon, Hajiya Halima na zaune a falon tun safe ta kasa
sukuni seda Yusuf yazo. Abunda ya ɗaurewa Yusuf kai be wuce yadda yau ta sakar
masa fuska ta amsa masa gaisuwar cikin mutunci ba.
Zeyi magana kenan yaji ƙamshin turaren Widad, wanda ya alamta masa ta fito falon,
waiwayawa yayi ita ɗin ce kuwa cikin shigarta ta ƙananan kaya kamar yadda ta saba,
bakin ta ɗauke da chew gum tana taunawa tare da lumshe ido, a hankali tana taku me
ɗaukar hankali ta tako ta ƙarasa shigowa falon, ta samu guri ta zauna ba tare da
tace komai ba.
Yusuf ya tako zuwa gaban kujerar da take zaune ya durƙusa a gabanta ze fara magana,
katse shi tayi ta hanyar yi masa alama da hannun ta na ya zauna akan kujerar dake
kusa da wadda take kai.
Seda ya ɗaga ido ya kalli Hajiya Halima sannan ya tashi ya zauna yace "Ranki ya
daɗe ga saƙon"
Ya miƙa mata ledar wayoyin da receipt ɗinsu da kuma ATM card ɗin. Tasa hannu ta
karɓa, ta buɗe ta ciro wayoyin manya masu kyau, ta jujjuya su a hannunta sannan ta
kalli Yusuf tace "can i have your phone?"
Kallon ta yayi, tare da yin sororo"are you deaf?" ta tambaye shi tana tsare shi da
ido.
Ciro wayarsa yayi daga aljihu ya miƙa mata, Android phone ce, dukda ba wata me
tsada bace Amma hoton sane da Ummansa akan wallpaper ɗin wayar, seda tayi nazarin
hoton na wasu seconds sannan ta buɗe wayar Yusuf ta cire sim cards ɗinsa da memory
ta haɗa da sabuwar waya guda ɗaya, da tsohuwar wayarsa ta bashi sannan tace
"i want see you tomorrow by 9:am Insha Allah, you will get your salary alert today,
you can leave"
"amma ranki ya daɗe, wannan wayar ai tayi min girma, kuma..."
Ai ko kallon inda yake bata sake yiba ta miƙe ta nufi part ɗin ta.
Gaba ɗaya hankalin Hajiya Halima akan Yusuf yake, Yusuf ya fita daga falon, ganin
bashi da wani aikin da zeyi ya sashi ya ƙudure tafiya gida, yana ta ƙara jinjina
kyautar wayar da Widad ta bashi.
Yayiwa su Nura Sallama ya fice ba tare da ya gaya musu abunda Widad ta bashi ba,
yana cikin tafiya kafin ya kai ƙarshen layin aka sha gaban sa da mota, tsayawa yayi
cak yaga waye wannan.Ramla ce ta fito daga motar tana masa wani irin kallo, ta
kalle shi a yatsine tace "Nasan zakayi mamakin ganina anan, saboda bakamata mace
kamarni ta tsaya tana ɓata yawunta akan talaka mutum maƙasƙanci kamar ka ba, sedai
ita kasuwar buƙata idan ta taso tamkar guguwa take bata da shamaki, magana nake so
muyi da kai me mahimmanci, wadda zata amfaneka, idan ba zaka damu ba ina so ka
shiga mota muyi magana"
"talakan mutum maƙasƙanci a gurin ki, amma wataƙila me matsayi a gurin Allah be
cancanci ya shiga motar mace me girman kai da tinƙaho ko ince tagumi da haɓar wani
ba, bana buƙatar dukkan wani abun Amfani da ze taso daga gare ki komai mahimmancin
sa kuwa, a gurin Allah nake nema dan haka ki bar abunki koma menene kuma komai
amfaninsa"
"karkayiwa kanka gaggawa, ƙarshe kazo kana cizon yatsa, da da nasanin fatali da
abunda ya tunkaro ka kayi masa shinge da riskarka saboda girman kai na banza,
talakan mutum me dakakkiya zuciya irinka, zuciyarsa cike take buƙatar samun
damarmaki, dama irin wadda kowa ke lalube a duhu ko a sarari, katsam se gashi ka
sameta a sarari, Amma ka kasa ƙafa kai fatali da ita, me yasa kayi hakan? "
"lokaci abune me mahimmanci a gurina, ina bashi mahimmanci fiye da yadda kike
tunani, zefi kyau ki taƙaita wannan dogon surutan naki marasa amfani, a cikin
taƙaitattun kalmomi kimin bayani gwari gwari kamar yadda Uwargida Widad keyi, hakan
zefi min sauƙi, kuma ze adana lokacin mu".
Wani kallon banza ta watsa masa sannan tace "ko Uwargida ko ubangida wannan kai ta
shafa, ni daban ita daban, dama ta sameka amma ka watsar da ita a yadda kake gaka
matashi har matashi, kai dai ba muni ba kuma ba nakasa ba, a wannan shekarun naka
da ƙirar da Allah yayi maka kamata yayi ace kana wani ɗan ƙwalisa meji da kansa,
katsam sega shi ka ƙare a direba, direban ma maƙasƙanci, kana tuƙa ƙaramar Yarinya
tana cin zarafinka yadda taso, bata ganin gjrmanka da aikin da kake mata, da kasan
maƙudan kuɗaɗen dake cikin Account ɗin nan da tabbas baka dawo gidan nan ba, dan da
kai da talauci har gaban Abada, ba kaiba har 'ya'yan ka da jikokin ka ba zasuyi
talauci ba, sedai kash garin yin gwaninta kayiwa kanka mugunta"
Yusuf yace "har yanzu jira nake ki faɗi abunda kike tafe dashi, na gaji da sauraren
wannan salon maganar taki me tafiyar kura, kiyi gaba kiyi baya kamar kema baki
yadda da kanki ba"
"Babu batun rashin yadda da kai sedai ina so muyi tarayya gurin temakon juna ne,
ina son ka gayamin password ɗin Widad ne na banki, nayi maka Alƙawarin samun wani
gwagwaɓan sakamako indai kayi abunda nace, hakan ze zama madadin wannan shiritar da
kayi nayin wasarere da damar daka samu, kuma ze baka damar samun 'yantuwa daga
wannan aikin dakake ƙarƙashin wannan Yarinyar me Baƙar Aƙida"
Wani irin kallo Yusuf yayi mata sannan yace"dukda kasancewa ta talaka maƙasƙanci
kamar yadda kuke kirana, Yusuf yafi ƙarfin karɓar abunda zaku bashi saboda wannan
baƙin aikin da kuke so inyi, ku tara dukiya da guminku seku yi barazana da ita ko
tinƙaho, Bana danasanin aiki na ƙarƙashin Widad, duk inda tayi faɗa ko tsiwa to
tabbas an mata ba daidai bane, shiyasa komai tayi take birgeni, kasancewata meyi
mata aiki be sa naji cewar ni maƙasƙanci bane, kasancewata me aiki a ƙarƙashinta na
sani ƙara samun ilimin rayuwa, dan haka kece maƙasƙanciya da kika ƙallafa rai akan
abunda ba naki ba, ni talaka ne me wadatar zuci, dukiyar Widad bata isa ta yanken
talauci ba"
"haka kace ko, to shikenan zakaga abunda bijirewa buƙata ta ze haifar maka, ba dai
shishshigewa wannan mahaukaciyar ka zaɓa ba, a haka zata ƙare a hauka, kuma death
contract data gaya maka zaka ganshi dan kusancinka da ita tamkar kusancinka da
mutuwar Kane, Akwai mutanen dake farautar mutane irin ka, wanda suka raɓeta, zasu
cigaba da farautarka da bibiyar ka, zasu nemi wani abu a gurin ka, muddin ka gaza
yi musu zaka ga abunda ze biyo ba, ka rubuta ka ajiye zaka ce na gaya maka, sakarai
mara rabo kawai "
"Ke rabon ne yasa kike zaune a gidan mutane kina harin yin zamba cikin Aminci ai,
dukda irin gata da sutura da akai muku"
Wani murmushi tayi me ciwo, badan Widad tana Wulaƙanta su a gaban Yusuf ba ya isa
ya kalli idon ta ya gaya mata wannan maganganun, ta ɗaga ido ta kalle shi tace "ka
faɗi abunda kake so a yanzu, amma ka saurari ƙalubalen dake fuskantar ka" ta shige
ta kunna motarta ta bar gurin a guje.
Ayshercool07063065680
_*AƘIDA TA*_
PERFECT WRITERS ASSOCIATION
(WE AIN'T PERFECT BUT WE ARE ALWAYS TRYING OUR BEST, TO MOTIVATE AND ENTERTAIN OUR
READERS)
https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/
P. W. A
*Story and written by*
_*AISHA HUMAIRA (Daddy's girl)*_
The experience writer of *ABDUL JALAL** WATA KISSAR.... (SAI MATA) *And now *AƘIDA
TA *
I dedicated this book to my Mum (Malama Nafisat Adam Muhammad) i love you mum
Special thanks to all members of my Association Perfect writers Association may
Allah subhanahu wata'ala bless our pens and grant us wisdom to write what will
bring positive changes to our Community.
PART1 Page 11
Bin motar Yusuf yayi da kallo harta ƙure, sannan a sannu yaja ƙafar sa ya ci gaba
da tafiya abubuwa daban daban na yawo a kwanyarsa.
Maimakon ya tafi gida seya tsaya yayi sallar azahar ya wuce gurin aiki, office ɗin
Abbas ya tafi yaje ya tarar da shi yana tsaka da wani aiki, Abbas na ganin Yusuf
yai murmushi suka gaisa sannan yace "Yane mutmina? Akwai wani latest update ne?"
Yusuf ya ɗan ɓata rai yace "na baka abu kayi assisting ɗina kaƙi, seni nayi abuna
bakomai nagode"
"wane abu kace inyi assisting ɗin naka naƙi?" Abbas ya tambaya
"Akan mahaifin yarinyar nan Nurat mana, Nace ka tayani bincike akansa amma ƙarshe
ni nayi abina"
Dafe kai Abbas yayi yace "Sorry my man, wallahi aiki yayi min yawa na manta shaf"
"Shikenan amma ina tafe da Labari ne"
Abbas ya tattara hankalin sa yace "ina jinka, dama kamar kasan jiya Oga Suleiman
yayi min maganarka"
Yusuf yace "Abbas ina kyautata zaton akwai sa hannun matar Mahaifin Widad a
farmakin da'ake kai musu"
Abbas ya ture System ɗin gabanshi ya sake tattara hankalinsa yace "ta yaya kenan?
Meka gano?"
Nan Yusuf ya gaya masa abubuwan da Su Hajiya Halima keyi, da kuma Yadda suka yi da
Ramla"
Jinjina kai Abbas ya shiga yi yace "Lallai biri yayi kama da mutum, amma kaga Oga
yana Abuja akan wani case, Amma idan hakane meye alaƙar iyalan Alhaji Nasir da
Mahaifin Nurat?"
Yusuf yace "Abunda zan ɗora da bincike na akai kenan"
Waya ce ta fara ringing, Abbas da Yusuf suka shiga waige waigen wayar da take
ringing ɗin, Abbas yace "kamar daga jikin ka ringing ɗin ke tashi fa"Se yanzu
Yusuf ya tuna an bashi sabuwar waya, hannu yasa ya ɗakko wayar ya ɗaga, suka gama
magana Umma ce ta kira shi. ssebayan Yusuf ya gama Abbas yace
"jar uba mutumina wannan latest phone ɗinfa? Miƙomin in ganta, yaushe ka siyi waya
haka, kaida manyan wayoyi basu dame ka ba?"
Yusuf ya miƙa masa wayar yace "Widad ce ta aikeni na siyo mata wayoyi masu tsada
guda biyu, ina kai mata ta bani wannan"
Abbas ya dinga jinjina kai yana jujjuya wayar yace "Lallai ka faso gari, amma
kamata yayi ka siyar da ita kai sabgar gabanka da kuɗin"
"Idan kuma ta tambayeni wayar nace na siyar taji daɗin Yimin wulaƙanci ko?"
Abbas yace "A'a ba haka nake nufi ba, Ashe dai har yanzu halin nata na nan, ai
kwanan nan Insha Allah zan ɓullo gurin naku"
"to nidai in kazo ka kula, karka sake ka gaya wa wani unguwar da nake, haka kurun
sun matsa da son sanin daga inda nake zuwa, dan nima kaina ban yadda da mutanen
gidan ba"
Abbas ya kwashe da dariya yace "ashe dai ta koya maka halin nata"
Alert ne ya shigo sabuwar wayar Yusuf dake hannun Abbas, zare ido Abbas yayi yace
"Yusuf an turo maka kuɗi"
Yusuf yace "waye ze turomin kuɗi tsakiyar wata haka?"
"wallahi dagaske nake, dubu ɗari shida"
Miƙewa tsaye Yusuf yayi yace "ni a wa? Waze turomin kuɗi haka?tabbas anyi kuskuren
lambar account"
Abbas yace "dakata, kuma ba uwaɗakinka bace?"
Shiru Yusuf yayi yace "to aini bata da Account number ɗina, sedai idan naje gobe
in Allah ya kaimu in tambaye ta, Amma inma itace gaskiya kuskurene, Kaga Abbas se
anjima akwai inda nake son zuwa"
Gaba ɗaya Yusuf ya ruɗe, mamaki ya cika zuciyarsa yafi tunanin ko Ramla ce, dan
tana son ta siye shi yayi mata aikin data keso? Amma daga rabuwarsu ta ina zata
samu Account number ɗinsa?.
***********************
A mugun fusace Ramla ta koma gida, tana zuwa bata tsaya ko ina bs se ɗakin
mahaifiyar su, taje ta tarar da ita suna magana da Amal.
"Mummy akwai matsala fa"
"matsalar me?"
"Mummy this guy is very rude, we have to exact power over him, how dare will he
look into my eyes and tells me that he won't do what i ask him to do?" ta ƙarasa
maganar tana ta gauraya Numfashi.
"Kinga nutsu kiyi min bayani ya kukayi dashi?"
Ramla ta warware mata komai, Amal tace "da anyi shawara dani da baza'a tun kare
shi ba saboda nasan ba zeyi ba, Mutum ne me kafiya da dagewa akan gaskiyar sa"
Cikin fushi Ramla tace "A beg shut up Malama, wayafi kafiya talakan banza mara
amfani, ni ya tsaya ya kalli cikin idanuna ya cimin mutunci, shikenan dani yake
zancen wallahi se nasa zaman garin nan ya gagare shi banza da kansa kamar lemo"
Amal tace "Wai kansa kamar lemo, kekuma naki fa"?
"dan Allah kuyi min shiru karku yi min faɗa anan, mafita ya kamata munema ba surutu
ba, sannan Amal wallahi idan baki kiyayeni akan yaron nan ba sena saɓa miki fiye da
tunanin ki wallahi, bazan taɓa aurawa maƙasaƙancin mutum ɗana ba, dan haka ki shiga
hankalin ki, zaƙewar da kike masa tayi yawa "
Zumɓura baki Amal tayi ta bar ɗakin.
"Mummy inaga mubi Amal a hankali, tabbas son gayen nan take, Amma cikin hikima zata
iya samo mana abunda muke so, ki dena yawan hantarar ta a kansa, karta zo ta bijire
mana daga baya fa"
"Bazan bari alaƙar tasu tayi nisa ba, saboda yaron kalar mayaudaran mazane, yana da
mu'amala me kyau, daɗin Soyayya ze iya sa Amal ta tona komai, kin san bata da
hankali, Amma zan sanar dake mataki na gaba da zan ɗauka.
**************************
Safa da marwa yake yana kaiwa yana komowa a cikin wani matsakaicin Office, yana ta
sake nanata maganganun da Oga ya gaya masa game da poisoning ɗin Bala a prison,
wani mutum ne yayi Sallama a office ɗin yace "Yallaɓai Hisham lafiya kake nemana?"
Hisham yayi ajiyar zuciya yace "Oga Bukar ne ya bada wani aiki, kuma muddin aka
samu kuskure bamuyi ba ze halaka mu"
"Kamar Yaya? Wai shi meyasa be maida kisan kai komai ba saboda buƙatunsa? Wallahi
nayi dana sanin sabga dashi"
"Kwantar da hankalin ka Bashir, mu lallaɓa muyi masa wannan aikin bisa Yarjejeniyar
shine na ƙarshe, idan ya cigaba da takuramu, semu ma mu ɗana masa tarko"
Tsaki Bashir yayi yace "ina jinka, me kuma zamuyi masa?"
"yace so yake ayi poisoning ɗin Bala, yadda ze fara rashin lafiya, da an kai shi
Asibiti kuma zesa a ƙarasa shi, saboda Balan yayi barazanar tona Musu Asiri, sun
barshi a gidan yari tsawon shekaru takwas, sunƙi fitar da shi"
"wallahi Hashim mutanen nan basu da Imani, tsaf muma zasu iyayi mana abunda suka yi
wa Bala, amma salin alin muyi abunda suke so, muna dafe kan madarar kawai zan ajiye
aikin gidan nan in fece"
Hisham yace "shikenan but you have to focus"
Bashir ya jinjina kai ya fice daga office ɗin.
*********************************Dogayen kaya ne a jikin Yusuf, yayi kyau sosai ya
shiga falon da sallama, ba'a amsa ba kasancewar ba kowa a ciki, ɓangaren Widad ya
nufa kansa tsaye, yaje ƙofara falonta ya tsaya, tare da yin knocking.
Ƙasa ƙasa ya jiyo muryar ta tace "Come in" da Sallama ya shiga falon, tana zaune
tana shan tea, ya kalleta yace "barka da Safiya ranki ya daɗe" jinjina masa kai
tayi ba tare da ta amsa ba, ta cigaba da abunda take ba tare da tace uffan ba.
Haka ya shuɗe tsayin wasu lokuta yana zaune yana jiranta, ga shan tea ɗin take
kamar tana shan magani.
Yusuf ya gyara zama yace "Ranki ya daɗe jiya naga an turomin kuɗi a account ɗina
masu yawan gaske, ban sani ba koke ce, shine nace bari in tambaye ki"
"Kana expecting ɗin kuɗi daga gurin wani ne?" tai maganar tana ajiye cup ɗin
hannunta
"A'a, bana yi" ya bata amsa
"Anyway salary ɗinka ne na 3 months da ban baka ba"
Zare ido Yusuf yayi yace "Amma sunyi yawa fa, ya zanyi da wannan maƙudan kuɗaɗen?"
"Zaka iya zubarwa, wannan kai ta shafa"
"A'a Madam, banyi aikin da zan karɓi wannan kuɗaɗen ba, sun yi yawa ban san....
"Kai ɗan Yimin shiru mana, idan ban manta ba kafin in ɗauke ka aiki na gaya maka
salary ɗinka, kasan sunyi yawa meyasa kace zaka yi aikin? A beg keep this aside
follow me"Tayi maganar tana miƙewa tsaye ta nufi bedroom ɗin ta, jiki ba ƙwari
Yusuf yabi bayan ta.
Wardrobe ɗinta ta buɗe ta ɗakko wayar nan da tasa ya siyo, ta tako zuwa gaban
Yusuf, sedai tana zuwa suka ji wani shock a tare, ƙamshin turaren da Yusuf yake
yasha banban da wanda ta hana shi sakawa, amma muddin zata ji ƙamshi a jikin sa se
wata kasala ta saukar mata.
Shikam Yusuf ƙirjin sa ne ya shiga bugawa da ƙarfi ba tare da yasan dalilin hakan
ba.
Widad ta tattaro nutsuwar ta ta dube shi ta miƙa masa wayar, yasa hannu ya karɓa
yana kallon ta, a hankali tace
"Yanzu misali a ce wannan wayar ranka ce, a ina zaka ɓoye ta?"
Yusuf yayi ajiyar zuciya yace "zan mata kyakkyawan ɓoyewar da babu wanda ze san
inda take se Allah"
"Good haka nake son ka ɓoye wannan wayar tamkar na baka ranka, duk kusancinka da
mutum karka kuskura yasan da wannan wayar a tare da kai, karka yarda da kowa,
wannan wayar tamkar na baka ranka ne!!! ka kula da ita"
A diririce Yusuf yace "Amma me yasa zan kula da ita haka? Ban gane tamkar kin bani
raina ba"
Ɗan taɓe baki tayi ta juya tace "bashi da mahimmanci kaji wannan a yanzu, saboda
sanin hakan a yanzu tamkar sake jefa rayuwar ka cikin hatsari ne, let me tell you
something, don't trust anyone, i repeat myself don't trust anyone, jeka ƙarfe biyar
zan fita yau"
Yusuf ya jinjina kai yace "Amma kuɗin nan da kika bani wallahi sunyi yawa"
Widad tace "You can go, na sallame ka"
Yusuf yace "Amma ban san yadda zanyi da wannan maƙudan kuɗin ba"
Ba tare da ta kula Yusuf ba ta shiga ƙoƙarin rage kayan jikin ta zata shiga wanka,
ba shiri Yusuf ya juya da sauri ya bar ɗakin, yana mamakin wauta irin ta Widad.
*********************************
Alhaji Musa ne zaune a falon sa, 'yarsa Nurat na kujerar dake facing ɗinsa ta
sunkuyar da kai tana wasa da yatsunata.
"Wallahi Nurat na rasa me zan miki in huce, da tuni harkar nan ta kankama, amma
kikayi mana wauta da hauka, idan abun da muke nema ya samu, se kinfini mora"
Murya na rawa da alama tana tsoron mahaifin nata tace
"dan Allah kayi haƙuri, nima wani ne yace ze saceni idan ban nuna masa inda take
ba"
"waye shi ɗin?" ya tambaye ta a ɗan hasale
"Wallahi ban san waye ba, nima bata gayamin waye shi ba"
"Ni zan gano ko waye inyi maganin sa, yanzu dole ki samo wata hanyar abunda zaki yi
ta sake zuwa gidan nan"
Saurin girgiza kai tayi tace "Ai kasan ba zata ƙara yadda dani ba, wallahi kome
zanyi ba zata zo ba"
A fusace yace "tashi ki bar nan, komai a kasa dake se kinyi wauta, ni nasan abunda
zanyi"
****************************
Album guda na hotunan Widad yake dasu a System ɗinsa, ji yake kamar ya janyo
kwanakin da ze koma Nigeria, kallon hotunan ta kawai yake hakan ke ƙara samasa
nishaɗi.
Video call ya kira Mummy, Hajiya Halima na ganinsa tayi murmushi tace "'yan
makaranta, lokaci ya kusa ko?"
Anwar yace "Eh Mummy se missing ɗinku nake, ina su Ramla ne"
"Suna nan gasu a kusa dani"
"shine ba zasuzo mu gaisa ba, dama ba nemana suke ba"
Amal tace "waze kira ka a kwashe masa kuɗi" Haka suka dinga video call suna hira
da 'yan uwan sa, can yace "Mummy wai ina Widad ne? Naji ance tana Nigeria kuma
tunda nake kira bana ganin ta"
Tsaki Mummy tayi tace "Ban sani ba, ita ta haifeka koni? Idan bani kske nema ba
shikenan, kullum baka da zance sena wanne banzar yarinyar?"
"yi haƙuri Mumsy, Yadda mahaifinta ya riƙemu ai senake ganin kamar babu laifi dan
na tambayi inda take"
Ramla tace "Brother dan Allah karka ɓatawa mutane rai, waya ke maganar wannan
mahaukaciyar"
Anwar yace "ni a ganina, Widad rashin me janta a jiki da kuma depression yasa
condition ɗinta ya zama complicated, amma...
Cikin tsawa Hajiya Halima tace " Rufemin baki dan uban ka, kaga ka kiyaye ni ko in
ɓata maka rai, in baka son ɓacin raina karka sake Yimin zancen yarinyar nan, ko dan
kai kana can baka san irin zaman da muke a gidan nan ba"
Ramla tace "ina ze sani, muna nan ta mayar damu kamar bayi, cin kashi kala kala,
ana Wulaƙanta mu muda mahaifiyar mu amma kana neman ta"
Anwar yace "Amma Mummy....
A fusace tace "ke Amal katse min kiran nan, shashashan banza kawai"
Amal ta katse kiran.
Anwar ya turawa Amal message "Amal ɗan turomin lambar Widad"
Ta masa reply da "Taɓɗijan wa kake tunanin ze samu lambar wannan? Duk yadda kake
tunanin abun ya wuce haka, ba ruwan ta damu fa"
Jujjuya message ɗin ya dinga yi, babban abunda yake bashi takaici be wuce duk
lokacin da ya kira Mummy, ya tambayi ina Widad seta balbaleshi da masifa, duk wanda
ya tambaya ya bashi lambar ta kowa se yace bashi da ita, ya rasa meye dalilin
hakan.
Yana wannan tunanin Fahad ya shigo ɗakin da sallama, ya kalli Anwar yace "Man
what's wrong ne? Nayi sallama baka amsa ba"
Ɗan guntun tsaki Anwar yayi yace "Fahad, ni gaba ɗaya na kasa gane kan lamuran nan
dake faruwa, duk lokacin da zamuyi waya da Mummy, idan har zan tambayi Widad se
taita faɗa, babban abunda yake bani mamaki shine, wai ace duk gidanmu babu me
lambar Widad balle ya bani" Fahad yace "Widad Widad Widad, kai dai baka da zance se
wannan Yarinyar, please don't kill yourself mana, Nifa yadda kake bani labarin ta
sam bata Yimin ba, nifa tun tana ƙarama yadda take wannan Share mutanen haushi take
bani, kuma gashi da bakin ka ka gayamin tana da taɓun hankali "
Anwar yace " shut up please, tunda ba zaka bani shawara ba ka ƙyaleni, baka san
yadda nake ji akan ta ba, kai kana soyayya amma kamar baka san meye son ba, Ni anya
ma in baka Ramla zaka iya riƙe ta kuwa? "
Fahad yayi murmushi yace "Anwar kenan, aini Soyayya ta da Ramla tana sona ina
sonta, amma kai banda wahala babu abunda kake yi"
"Kai kaga wahala, ni bangan ta ba, Ni na ƙagu kamar in janyo lokaci in koma gida,
gashi seka rigani komawa Nigeria"
"Allah ya baka lafiya Anwar, dan ga dukkanin alamu ta shafa maka haukan"
Shiru Anwar yayi ya miƙe ya bar ɗakin, dan Fahad ya fara baƙanta masa rai.
Widad tana ta shirin fita, wayarta ta fara ringing, hannu tasa ta ɗau wayar tasa a
kunnen ta, shiru ta ɗanyi tace "Ok, thank you very much, send the address via my
email" ta ajiye wayar tana ci gaba da shiryawa.
Maimakon ta fito seta tsaya ta saman bene tana duba lokaci, Yusuf ta hango ya fito
da Mota yana ta gogewa dukda a wanke take, abun da ta fuskanta da Yusuf mutum ne
meson tsafta sosai, baya son datti sam.
Message ne ya shigo wayar Yusuf ya ɗaga ya duba.
"Ba'a wannan motar zamu fita ba, ka fita waje ka jirani"
Mamaki ne ya kama Yusuf, tabbas Wannan message ɗin daga Widad ne, 'Amma yaushe ta
samu lamba ta?' ya tambayi kansa, basarwa yayi ya mayar da motar, yana fita wajen
gate yaga wata mota, ba dai me tsada bace dan kamar ma ta ɗanji jiki. Guri ya samu
ya tsaya yana jiran fitowar ta.
Seda yayi kusan mintuna talatin kamar ance ya ɗaga kai ya kalli gate, ganin Widad
ne yasa ƙirjin Yusuf bugawa da ƙarfi.
Wani arnen black leg jeans ne a jikin ta, da wata tied pitted blue body hook, tayi
stocking ta saka beilt, ɗan ƙaramin baƙin veil ta ɗaure gashin kanta, dukda ƙasan
gashin nata ya fito. Google glass ne a fuskar ta baƙi, ga takalmi me matuƙar tsini,
se 'yar ƙaramar jakarta, gaba ɗaya bazaka ce idan Widad ta buɗe baki zata yi hausa
ba, duk wani shape da surar jikin ta ya fito.
Tabbas da Yusuf nada damar Mayar da Widad ta canza kaya da tabbas zeyi, dan haka
kurum yaji takaicin fitar Widad a haka.
Ƙarasowa tayi ta miƙawa Yusuf key ba tare da tace komai ba, jiji a sanyaye ya
karɓa, ya buɗe mata motar ta shiga ya rufe ya zaga mazaunin direba ya zauna, gaba
ɗaya ƙamshin turaren da take ya cika motar, ya kalle ta yace"Ina zamu je?" shiru
tayi na ɗan wani lokaci sannan ta miƙa masa wayarta, yasa hannu ya karɓa ya duba.
Adress ɗin inda ze kaita ne, ya ɗago ya kalleta zeyi magana, amma yaga ta ƙara yi
masa kwarjini, dan haka ya bata wayar ta ya kunna motar.
Yana cikin tuƙi wayarsa ta fara ringing, Umman Yusuf ne a jikin screen ɗin wayar,
ya ɗaga wayar yasa a hansfree ya ajiye ta yace "Umman Yusuf"
"Ɗan gidan Umman sa, yau zaka dawo da wuri ne, an kawomin wani kifi tun daga Yobe,
nayi maka farfesu ka dawo da wuri karya huce, ko kuma in cinye abuna"
Duk da ransa a dagule yake wanda ya rasa dalilin hakan, Amma seda ya maze yace
"Umman Yusuf, ai bazaki iya ci baki ajiye min ba, zan siyo gurasa yai akwai dinner
me kyau"
Hirarsa yake yi da maman sa hankali kwance, se shagwaɓa yake yi kamar yaro ƙarami,
Widad kuwa ƙura masa ido tayi ko ƙiftawa ba tayi, dukda ta cikin Glas ɗin idonta
take kallon sa amma yadda yake wayar da Mahaifiyar sa ba ƙaramin birge ta yayi ba.
A ranta tace 'dama suma talakawa suna jin wannan shauƙin da ƙaunar na iyaye, inama
Ammi na tana raye nima in kwanta a jikin ta in ji daɗi'Ba tayi aune ba taji hawayen
da bata shirya zubowarsu ba. Cire glass ɗin fuskarta tayi tana goge hawayen idon
ta, katse wayar Yusuf yayi ya kalleta yace "lafiya dai?""Lafiya cigaba da tuƙinka,
ina so muje gurin nan kafin 5"Ya jinjina kai ya ci gaba da tuƙin, wani katafaren
hotel ne, motocine suke shiga suna fita a ciki, kowa harkar gaban sa yake yi, sedai
mafi akasari kallo ɗaya zakayi wa mafi yawa daga mutanen dake shiga suna fita, ka
gano rashin tarbiyya da ta ido a tattare dasu, musamman matan duba da yanayin irin
shigar dake jikin su.
Yusuf yayi parking yana kallon Widad, ta buɗe motar ta tsaya tana ƙarewa harabar
hotel ɗin kallo.Da sauri Yusuf ya fito daga motar yana kallon ta, ta dubeshi tace
"wait for me here" ta sa kai da nufin shiga cikin hotel ɗin, da yawa mazan dake
gurin nan hankalinsu ya dawo kanta, Widad ta haɗu iya haɗuwa, wani takaici ne ya
kama Yusuf, ace 'yar musulmi ce da wannan shigar a wannan gurɓataccen gurin.Bin
bayanta ya kuma yi da sauri, ta tsaya ta kalle shi tace "I said you should wait me
inside the car, don't let anyone to see you here, don't tarnish your image because
of me"Ta sake juyawa, ba zato cikin zafin nama da zafin rai Yusuf ya riƙo Widad
gaba ɗaya zuciyar su ta buga a tare, Yusuf ya kalli cikin idon ta yace"Guri irin
wannan be dace da mace me daraja kamar ki ba, Mahaifinki babban mutum ne be kamata
aga 'yarsa a irin wannan gurin ba, ke mace ce kuma me daraja bekamata kowane gara
ya dinga kallon surar jikin ki haka ba, think about it"Nutsuwa Widad tayi seda ya
gama tsaf sannan tace "Cikani tun kan in wanka maka mari a gurin nan, kai waye da
zaka gayamin abunda ya dace dani? this is my life style not yours, dalla Cikani
Malam kana ɓatamin lokaci ni"
A hankali Yusuf yace "I am musulm, ina kishin yadda mutane ke ƙare miki kallo a
haka, kalli irin mutanen dake gurin nan, da yawan su karuwai ne fa da mutanen
banza, shigarki bata da maraba da wanda matan gurin nan marasa daraja suka yi"
Cikin isa tace masa "koba maruwanci ba, Nima shi nazo yi, am prostitute karka ƙara
shiga rayuwa ta, na gaya maks"
Ta juya ta shiga Hotel ɗin da sauri, wani baƙin ciki ne ya tokare zuciyar Yusuf, ya
koma mota ya zauna yana tunani a ransa'to wai kai Yusuf banda shisshigi ina ruwanka
da ita ne?'Wata zuciyar ta tambaye shi.
Yana nan zaune a mota kusan mintuna Arba'in, gajiya yayi da zaman motar ya fito ya
zauna akan motar yana ƙurawa hanyar da Widad tabi ido. Ba tsammani ya hangota tana
fitowa, sedai fuskarta ɗauke da hawaye tana ta share hawayen da handkerchief, inda
motar su take ta nufo idanunta jawur, wani ne ya biyo ta yana ƙoƙarin tsaida ita
yayi mata Magana amma bata tsaya ba, tana zuwa ta buɗe motar ta shige. Yusuf ya
zagaya ya shiga ya kunna motar, gaba ɗaya se yaji ya tsargu da yanayin daya ganta,
gaba ɗaya hankalinsa ya tashi "Are you ok?"
"Do you have any conscience with me being ok or not?" ta tambaye shi a hasale
"Yes i have" ya bata amsa, tsaki tayi ta ɗauke kanta tace "drive very fast please"
gudu sosai Yusuf yake amma azalzalarsa take wai ya ƙara gudu, kuma still bata dena
kukan ba, kuka take me fallasa da tsantsar ɓacin rai da damuwa. Guri Yusuf ya samu
yayi parking ya juyo yana kallonta, ba tace komai ba tasa hannu a jakarta ta ɗakko
wayar ta, ta ɗan daddana sannan ta saka a kunnen ta, tayi shiru na wasu 'yan
mintuna sannan tace "Hello Daddy"
Yusuf baya jin me mahaifin Widad ke cewa, cikin kuka tace "please Daddy I want
Flight back to U. K, i regret coming back to Nigeria, please Daddy talk to Bulama
ask him to set up my visa"
Shiru ta ɗanyi sannan tace "Daddy don't take it for granted please, i can't define
what happens today, dan Allah kace ayimin visa in koma"
"Daddy why? Kayi shekaru ba tare da ni ba se yanzu zaka ce baka so inyi nesa da
kai? Karo na biyu ina neman abu kana ƙin Yimin, shikenan Daddy bayan ciwon
Ƙwaƙwalwa am at risk of having cardiac attack" ta saki wayar ƙasa ta cigaba da
kuka.
Yusuf ya cika da mamakin meyasa Widad kuka haka? Akwai buƙatar yasan me taje yi
Hotel.
"malam kayi sauri ka maida ni gida, ka tsaya kana kallo na"
"Bazan iya tuƙin ba muddin zan cigaba da jin kukan ki" yai maganar fuskarsa ɗauke
da damuwa
A hankali ta ɗago idanunta da suka yi jawur, ta saka ana Yusuf tana son gano
gaskiyar abunda ya faɗa
"to meye haɗinka dani da kuka na ze dame ka, just drive ba ruwan ka da kukana, kayi
abunda ke gabanka"
A hankali ya kunna motar, ya bata wuta ya cigaba da tuƙi, sedai gaba ɗaya hankalin
sa baya jikin sa, yana can yana tunani daban daban.
Ihun Widad ne ya dawo dashi hayyacin sa, sannan ya lura da abunda ke shirin faruwa,
duk yadda yayi ƙoƙarin kaucewa motar, seda me motar ya daki tasu.
Dafe kai Yusuf yayi yace "Subhanallah"
A fusace ta kalli Yusuf "Are you out of your sense, see how you ruin my life, kashe
ni kake so kayi? Baka gani ne? Dama so kake ka kasheni, an haɗa baki da kai zaka
kashe ni ko? Dama na sani"
Kafin Yusuf ya bata amsa tuni me waccan motar ya fito yana zazzaga bala'i, an lotsa
masa mota se an biya shi.
Yusuf ya buɗe motar ya fita jiki ba ƙwari, ya kalli mutumin ze kai shekaru Arba'in,
Yusuf yace "Dan Allah kayi haƙuri, birki ne ya ƙwacemin, kuma kaga traffic ta
tsaida hannun ka amma baka tsaya ba, kuma ni na riga na taho da gudu, amma dai kayi
haƙuri"
"Shut up my friend, ni zaka gayawa traffic ta tsaida hannu na? Titin naka ne kai
kaɗai da zaka dinga wannan gudun, banza shashasha kuma wallahi seka biya ni asarar
da kayi min kokuma kaga abunda zan maka"
Tuni mutane suka fara taruwa, suka cika gurin ana ta bawa Mutumin nan haƙuri, dukda
zagin da yakewa Yusuf amma haƙuri yake bashi, amma mutumin nan ya rintse ido yana
zazzaga masifa yana cin zarafin Yusuf, hakimar kuwa ko fitowa ba tayi ba tana mota
a zaune.
Yusuf yace "Amma naga idan laifi ne fa kaine kayi bani ba, Amma se baka haƙuri nake
kana cigaba da cimin mutunci a gaban mutane, shikenan Yimin duk abunda zaka iya ka
huce"
Yusuf dama gashi a cikin damuwa yake, ga shi ze zagin sa mutumin yake, aikuwa nan
da nan temper ɗinsa ta hau zuciyar sa ta shiga tafasa, dan haka se yayi shiru ya
dena cewa komai.
Mutumin ya cigaba da zazzaga masifa "Do you know who I am da zaka dingamin magana
da gadara,? I will show you what am capable of doing, sena nuna maka ni waye, sena
sa an sauke maka wannan rashin ɗa'ar taka mara tarbiyya kawai"
"You are nobody More than stupid Malam, waye kai idan har kai wani ne bazaka tsaya
kana ɗaga murya akan wannan banzan gwangwanin motar taka ba, kayi abunda zaka yi an
bige motar taka, ina son inga kai waye, kuma me zaka iya?"
Gaba ɗaya suka juyo inda Widad ke magana da jajayen idanunta.
Mutumin ya kalli Widad yace "Lallai ka ɗakko karuwa a mota, dole ka ɗagamin murya
danka birgeta, zanyi maganin ku daga kai har ita"Ya ciro wayarsa yana waya.
Yusuf a harzuƙe zeyi magana Widad ta ɗaga masa hannu alamar yayi shiru.Ta ɗakko
wayar ta tayi 'yan taɓe taɓe.
Mutane suka ja gefe suna son ganin ƙarshen dramar, mintuna kaɗan sega motar 'yan
sanda, suka zo suna wuri wuri, mutumin ya nuna musu Yusuf yace "gashi nan shine,
ku kama shi shida wannan koɗaɗiyar Yarinya me kama da sadakar Yalla"
Tuni ɗaya daga ɗan sandan yaje ya cakumo Yusuf, sedai me ɗan sandan ya jiyo bindiga
a jikin Yusuf!!!
Ayshercool07063065680
_*AƘIDA TA*_
PERFECT WRITERS ASSOCIATION
(WE AIN'T PERFECT BUT WE ARE ALWAYS TRYING OUR BEST, TO MOTIVATE AND ENTERTAIN OUR
READERS)
https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/
P. W. A
*Story and written by*
_*AISHA HUMAIRA (Daddy's girl)*_
The experience writer of *ABDUL JALAL** WATA KISSAR.... (SAI MATA) *And now *AƘIDA
TA *
I dedicated this book to my Mum (Malama Nafisat Adam Muhammad) i love you mum
https://www.wattpad.com/user/Ayshercool7724?
utm_source=android&utm_medium=link&utm_campaign=in
ELEGANT ONLINE WRITER'S
PART1 Page 12
Ɗan sandan ya zare ido zeyi magana, Yusuf yayi saurin girgiza masa kai, ya juya ya
kalli Widad yaga hankalinta baya kansu.
A hankali ya zura hannu a aljihun sa ya ɗakko ID card ya nunawa ɗan sandan, washe
baki ɗan sandan yayi yana niyyar sarawa Yusuf, amma Yusuf ya girgiza masa kai yace
"Dan Allah Yallaɓai ku duba lamarin nan, ni bani da laifi a abunda ya faru, kuma na
bashi haƙuri yaƙi haƙura"
Mutumin ya ƙaraso inda su Yusuf suke yace "kaga Ku tafi da shi ajiyata ne, ku
kulle shi har se nazo station ɗin"
Ɗan sandan Ya kalli Yusuf zeyi magana, sega wasu 'yan sandan sunzo, motar da' yan
sandan suka zo ze tabattar maka da manyan wanda mutumin ya kirane, nan na farkon
suka shiga sarawa wanda Widad ta kira.
Widad tace "ina so a duba Accident ɗin nan, idan direba nane yake da laifi, zan
biya shi kuɗin motar sa uku, idan kuma shi yayi laifin ze durƙusa ya bamu haƙuri,
saboda cin zarafi da ɓata mana lokaci da yayi, in kuma yaƙi a tafi da shi, ajiyata
ne a kulle shi se nazo"
Nan fa kallo ya koma sama, nan 'yan sanda suka shiga dube duben su, aka tabattar da
mutumin nan shine ya karya doka, nan fa mutanen gurin suka ɗau sowa.
Widad taje gaban sa tace " if you are somebody you won't say it yourself, don't
ever say you are Somebody when you are nobody, yanzu ka durƙusa ka bawa direba na
haƙuri akan cin zarafin da kayi masa"
"Wallahi baki isa ba keɗin banza, in bawa wannan wulaƙantaccen haƙuri, kin san koni
waye?"
Ɗaya daga 'yan sandan daya kira ne yaja shi gefe yace "kai wallahi wannan' yar
masu ƙasa ce, idan taso zatasa a ɓatar da kai gaba ɗaya wallahi, kayi abunda tace
kota sa a ɗaureka"
"wannan ƙaramar yarinyar 'yar cikina?"
"to karkayi cigaba da taurin kai, wannan' yan sandan data kira muma iyayen gidanmu
ne"
Mutumin ya dawo a ƙule ya kalli Yusuf yace "Yi haƙuri"
"Akan gwiwowinka zaka durƙusa ka bashi haƙuri" cewar Widad
Cikin tsawa wani ɗan sanda yace "ba zakayi bane? Semun tafi da kai?"
A hankali yaja da baya ze durƙusa, Yusuf yayi saurin riƙe shi tare da girgiza kai
ya kalli Widad yace "please Madam ina nema masa Alfarma, kiyi haƙuri dan Allah, ni
zan durƙusa in baki haƙurin a madadinsa"
Dama Widad tasan Yusuf baze taɓa yadda hakan ta faru ba, tayi ne dan nunawa Mutumin
shi ɗin bakomai bane.
"Shikenan tunda ya haƙura, gobe in Allah kaimu, yaje station ɗinka ya karɓi kuɗin
motar sa, na ninka maka masa sau uku, Amma ya kiyaye gaba"
Ta juya ta tafi motar su, Izzar Widad da yadda ta tafi da al'amuran cikin isa da
izza, da bajinta suka birge mutane, aka dinga sowa, anawa mutumin nan dariya. Dare
yayi musu a gurin nan saboda wannan incident ɗin, Yusuf yaja motar cikin nutsuwa
suka tafi.
Amma still lokaci lokaci tana goge Hawaye a fuskarta, suka ci gaba da tafiya Yusuf
na godewa Allah da Widad bata ga bindigar nan ba, tabbas yasan da Asirinsa ya tonu
daya gama kaɗewa, ƙarshen ta seta kulle shi me fitar dashi se Allah.
suna zuwa gida Yusuf yayi horn Isa ya buɗe musu gate, Yusuf ya shiga da motar yayi
parking, har ya gama abunda zeyi ze buɗe motar ya fita, Widad tana zaune ko gezau
ba tayi ba, bata da niyyar fita daga motar. fita yayi ya zagaya ya buɗe mata ƙofar,
yace "Munzo fa" ɗaga kai tayi ta kalle shi, a hankali ta zuro ƙafafunta da take
jin kamar ba'a jikinta suke ba waje ta yunƙuro ta fito, sedai tana fitowa ta tafi
luuu zata faɗi, cikin zafin nama Yusuf zama shamaki da faruwar hakan, ta hanyar
riƙeta ta faɗa a jikinsa. Ƙirjinsa ya dinga bugawa da ƙarfi, saboda jin hakan wani
irin abu daban, Isa me gadi ne ya zaro ido ganin abunda yake faruwa, Yusuf kamar me
raɗa yace "Are you ok?" Jinjina masa kai tayi ta sake ƙoƙarin miƙewa, amma still
jiri ke kuma ɗibarta, tafiya take tana tangaɗi kamar wadda tasha wani abu, Yusuf
yabi bayanta ya mata rakiya har cikin babban falo, hannunsa riƙe da ƙaramar jakarta
da kuma wayar ta.
A babban falon ta zauna tana riƙe kai, hawaye nata zarya a fuskar ta, ƙoƙarin cire
takalmin ƙafarta take, amma abu ya gagara, se kokawa take da takalmin. Yusuf ya
taka inda take ya durƙusa ya kwance igiyar takalmin nata me tsinin tsiya ya cire
mata.
Ta gyara kwanciyar ta sosai ta miƙe ƙafafunta akan doguwar kujerar tare da lumshe
idonta, don bawa hawayen idon nata damar gangarowa.
Yusuf a ransa yace 'Ikon Allah, wannan wane irin kuka ne?'
"ko za'a kira likita ne?"
"Ni lafiya ta ƙalau" ta bashi amsa idonta a rufe.
"Jikinki yana rawafa, kamar zazzaɓi ze kamaki fa"
"to ina ruwan ka? Jikin ka ne ko nawa? Ni kaimin kayana ɗaki ka tafi ka ban guri"
Ɗan girgiza kai Yusuf yayi yaje ya ajiye mata kayan ta ya fito, tana nan inda ya
barta, yasa kai ya fice.
Yana fitowa ƙofar da zata sa dashi da harabar gidan yaji an riƙo rigarsa, waigawa
yayi yaga waye wannan. Amal ce tsaye tana huci, "Amal lafiya kuwa?" "dole kace
lafiya mana? Yusuf daga ina kake kai da Widad?, saboda tsabar abu harda cire mata
takalmi, Yusuf wai kai wani irin mutum ne dan Allah? Me kake aikatawa ne haka
Yusuf? me yasa lallai seka yi abunda zaka birgeta, bayan kullum baka da kima a idon
ta? Sau nawa nake gaya maka kusanci da ita tamkar kusanci da mutuwarka ne? "
Yusuf yace " look Amal niba wani abu nake nema a gurin Widad ba, kuma ba neman
kusanci nake da ita ba, kawai ina tausayinta ne, kuma ina jin daɗin yadda
mahaifinta ke mutuntani"
"kace tausayi Yusuf? Yusuf daga tausayi so yake shiga, ban taɓa ganin mutumin daya
samu damar da ka samu a gurin ta ba, Yusuf a gidan nan ba kowa keda ikon zuwa inda
take ba in bada izinin ta ba, kai kuwa kana iya zuwa gurin ta duk lokacin da kake
so a matsayin ka na direbanta, Yusuf ina kishin ka, Yusuf sonka nake wallahi bazan
zuba ido abubuwa su cigaba da gudana tsakanin ka da Widad a haka ba"
"Amal, Soyayya tsakanina dake ba zata yuwu ba, Mahaifiyarki bata ƙaunar talaka,
kuma ni talaka ne inani ina iya Soyayya dake Amal?Hausawa suka ce ƙwarya tabi
ƙwarya, idan tabi akushi zata fashe"
"dakata Yusuf" Amal ta katse shi, hawaye tuni ya fara sintiri a idon ta, tace
"bazaka iya Soyayya dani ba, amma zaka iya da Widad ko?"
"Amal ni ba Soyayya nake da Widad ba, inani ina son mace kamar ta, ita a kanta bata
yarda da wata soyayya ba, Amal nayi Soyayya a baya, abun da na fuskanta a soyayya
bazan ƙara yadda in sake fuskantar sa ba, ke kanki da kin san wayeni bazaki soni
ba, ba zaki so kasancewa da mutum kamar ni ba, kiyi hakuri "
"ba abunda ya shafeni, what I know is that ba zan zuba ido ka faɗa soyayya da
mahaukaciya mara tarbiyya ba, kuma bari in gaya maka ba zaka taɓa kuɓucemin ba kasa
wannan a ranka"
Tana gama faɗar haka ta juya da sauri ciki tana kuka, jikin Yusuf yayi sanyi a haka
ya ja jiki ya fito.
Masallaci ya wuce yai sallolinsa, sannan ya zauna yana karatun Al'qur'ani mai
girma, ya daɗe yana addu'a sannan ya miƙe ya nufi titi dan samun abun hawa zuwa
gida.
Abunka da unguwar masu kuɗi, tuni unguwar tayi tsit se sanyi bishiyoyi dake kaɗawa,
yana ta tafiya a ƙasa yana tunanin abubuwa da dama, ya baro layin su Widad sosai
inda security suke, ba tsammani se gani yayi ansha gaban sa da mota, tsayawa yayi
cak yaga ikon Allah.
Wasu ƙarti ne suka fito daga motar suka zagaye shi, ɗayan yace "kaine direban 'yar
gidan Alhaji Nasir?" Ba tare da tsoro ko shakka ba Yusuf yace "Eh nine"
"Good labari ya ishemu cewar akwai kusanci tsakanin ka da ita, duk inda zata tare
kuke zuwa, an samu mu ɗakkota kwanaki amma ka hana, bari in gaya maka wani abu,
zamu ƙyaleka ne saboda zakayi mana amfani, zamu ci gaba da bibiyar ka saboda akwai
wani abu da muke so ka karɓo mana a gurin ta" cewar ɗaya daga cikin ƙartin
Yusuf yace "Babu wani kusanci tsakanin mu, aiki nake mata tana biyana, ko meye kuje
ku tambaye ta ta baku mana"
Ɗaya daga cikin sune ya sakarwa Yusuf wani mummunan naushi, da seda jini ya fito
daga bakin sa, a zuciye Yusuf ya ɗago yana kallonsu, babban yace
"Wallahi idan baka kawo mana abun nan ba se mun kasheka, akwai wasu mahimman
abubuwa da muke so ka karɓo mana a gurinta idan kaƙi semun maka yankan rago"
"Bayan yankan ragon se kuma me?" Yusuf ya faɗa babu alamar tsoro
Wani naushin suka ƙara masa a gefen ido,Maimakon Yusuf ya tsorata, ko ya nuna jin
zafin naushin, se yayi murmushi yace
"idan kunmin yankan rago, ku kuma ku zauna a naɗe duniya daku?, babu wani mahaluki
daya isa yasa Yusuf yin wani abu dan son zuciya da zalunci, kuje ku gayawa wanda ya
aiko ku cewar karya kuskura yayi gangancin cin iyakar gonar da ba tasa ba, idan
kuma yaƙi zanwa shukokin feshi in ƙone nawa da nashi, kowa ya rasa, wannan saƙon
Yusuf ne ga uban gidanku ko wayeshi"
Wani naushin suka yi niyyar kai masa amma ya riƙe hannun ɗayan.
"Waye kai? Waye ya gaya maka wanine ya turomu?" cewar ɗaya daga cikin su
"yadda kuka binciko kuka gano nine direban Widad, haka yakamata ku bincika kusan
wayeni, nasani aikoku akayi ku koma ku ƙara tabbatarwa wanda ya aikoku nina ɗauke
Widad lokacin da yasa a sace ta, ni aikina tuƙata a mota dan haka ya kiyayi
yunƙurin cutar dani"
Hausawa sukace 'sarkin yawa yafi sarkin ƙarfi, sun daki Yusuf sosai, yaso yayi
amfani da bindigar sa, amma yin hakan ze rusa masa da yawa daga shirinsa, dan haka
ya fasa ɗaukar bindigar, suka daddake shi, wani yana iya ramawa wani kuma baya
iyawa.
"zamu cigaba da bibiyarka, harse ka bamu abunda muke nema, zaka gane baka da wayo,
Uban taurin kai, Ubangidanmu yafi ƙarfinka"
haka suka barshi a gurin suka tafi.
Da ƙyar Yusuf yaja jikin sa ya hau Napep ya tafi, hancinsa yana ta zubar da jini,
jiri ne yake ta ɗibarsa saboda jinin da yake zubarwa da yawa, da ƙyar yaje gida,
Allah ya temake shi Umma tayi bacci.
ya cire kayan jikinsa yana goge jinin fuskarsa, Aljihun wandonsa ya taɓa yaji wayar
da Widad ta bashi ɗazu.
Hannu yasa ya ɗakko ta yana jujjuya ta "Ka ɓoye ta kamar yadda zaka ɓoye ranka,
wannan wayar tamkar rayuwar ka ce"
Maganar Widad ta dawo masa, kunna wayar yayi, Amma akwai password akai shiru yayi
yana nazarin kamar yaya wayar nan tamkar rayuwar sa take? Ajiye wayar yayi ya shiga
yayi wanka ya fito, nan ya shiga aikin nasa na tunani dan abubuwa da dama sun faru
da suke buƙatar nazari.
"Me Widad taje yi Hotel? Me ta gani ya sata kuka? Waye ya turo mutanen nan? Ko waye
akwai sa hannun wani a gidan su Widad? Amma dagaske Tausayin Widad zesa ya fara
sonta? Me yasa tasa a durƙusa a bashi haƙuri yau? Tabbas zata iya yuwuwa akwai
Alaƙa tsakanin wani a gidansu Widad da mahaifin Nurat"
Ji yayi kansa kamar ze fashe, dan haka ya rintse idon sa yana addu'a da fatan bacci
ya ɗauke shi koze ɗan samu nutsuwa, Amal ta faɗo masa a rai itama, wai ita bilhaƙƙi
son shi take. Wani tunani ya shigayi watanni shida da suka gabata, da yanzu yana
nan da Auren sa, katsam a dalilin irin tasa ƙaddarar aka fasa wannan Aure, bayan
cin zarafi da wulaƙanci daya fuskanta daga iyayen matar daze Aura, bacci dai se
ɓarawo ne ya ɗauke shi.
*******************************
Da safe Yusuf ya tashi da matsanancin zazzabi, kansa har sarawa yake sosai saboda
dukan da yasha jiya, juyi kawai yake akan gadon gaba ɗaya jikin sa ciwo yake masa,
ganin har kusan ƙarfe tara be fito ba yasa Umma leƙawa ɗakin sa, ta tarar da shi
kwance a kan gadon sa, ƙarasawa tayi ta taɓa jikin sa tace "Yusuf lafiya kuwa?
Naga har ƙarfe tara baka fito ba?"
"Bana jin daɗi ne Umma""dan baka jin daɗi seka zo ka kwanta kana juyi, ka tashi ka
watsa ruwa, ka karya seka sha magani""to Umma"Yusuf ya miƙe ya shiga yai wanka,
kayan breakfast ɗin ta kawo masa ɗaki, ta kalle shi tace "Yusuf kamar kumburi nake
gani a gefen idonka da bakin ka"
Yusuf yace "Mun faɗi akan babur ne jiya da daddare"
"Amma ka kasa gayamin? Meye amfanin hakan, haba Yusuf"Yusuf yace "Yi haƙuri Umma,
bana son ɗaga miki hankali ne"
"Amma ina fatan ba wani mummunan ciwo daka ji?" tai maganar cike da damuwa
"Eh banji ciwo me yawa ba"
Da kanta ta zauna tana bashi Abinci a baki, ta ɗakko masa first aid box ɗinsa ya
ɗau magani ya sha, ya koma ya kwanta.
Kwanciyar sa ba daɗewa Abbas ya kira shi, da ƙyar Yusuf ya ɗaga wayar, Abbas yace
"Mutumina kana ina ne? Ina son ganin ka"
"Ina gida bana jin daɗi ne"
"Subhanallah, meya sameka?"
"Zazzabi ne" Yusuf ya bashi amsa
"Shikenan gani nan zuwa"Su kayi sallama
**************************
Hajiya Halima na zaune falon ta tana shan tea, Isa mai gadi yazo yana kwaɗa sallama
a ƙofar falon ta, A fusace tace "wai meye hakane? Lafiya kame do kamin wannan
sallama kamar kana bina bashi?"
"Hajiya nine, Isa ne" "to ya a kayi?" "Hajiya gurin ki nazo" Ta ɗanyi tsaki sannan
tace "shigo" Ya shiga falon ya durƙusa yace "Ina kwana?" "Kai bana son doguwar
gaisuwar nan meke tafe da kai?"
"to Hajiya kin san shi sha'ani na rayuwa kiwon mutum ake ba dabba ba koba haka ba?"
"kai nifa bana son wannan surutam banzae, ka faɗamin kanka tsaye meke tafe da kai"
Isa ya gyara zama yace "game da sabon direban nan ne Yusuf, gaskiya Hajiya akwai
buƙatar kisa ido, jiya yadda na gansu Allah ya nuna min Annabi salallahu alaihi
wassalam, kin san dai irin shigar da take yi, bayan kin fita ita dashi suka fita,
basu dawo ba se ƙarfe tara na dare, bayan sun dawo a gabana da idanun nan nawa" yai
maganar yana gwalo idon nasa ya cigaba da cewa "da idanu na naga suna rungume juna,
Hajiya a saka ido, kina gani idan ba kiranmu akayi ba bamu da damar shigowa kiga
yadda take hantarar mu, Amma shi ba yau ba gobe cikin sintiri yake har cikin ɗakin
kwanan ta, Allah kaɗai yasan me suke yi, gaki da 'yan mata kema kyawawa bekamata
yana gardi baligi ya dinga wucewa yana kalle miki su ba, shiyasa nace bari inzo in
sanar dake abunda ake ciki "
Dire kofin hannun ta tayi, taja wata nannauyar Ajiyar zuciya tace " Hmm naji
maganganun ka, kuma kazo da magana abun dubawa, tashi kaje zan san abunda zanyi "
Isa ya miƙe yana murna yace "shikenan Hajiya na barki lafiya "
Shiru Hajiya Halima tayi tana zake nazartar kalaman Isa megadi, tabbas Widad bata
yadda wani ya Wulaƙanta Yusuf ba, lokacin da ciwon ta ya tashi taƙi yadda da kowa
se Yusuf, idan har dagaske wani abu na faruwa a tsakanin su to tabbas akwai yuwuwar
ta gayawa Yusuf inda abunda suke nema yake.
**************************
Widad kwana tayi da zazzabi da ciwon kai, da ƙyar ta samu tayi bacci.Jikin ta sam
babu ƙwari ta miƙe domin haɗawa magen ta abunda zeci.Widad na matuƙar son dabbobi,
tana tausayin su fiye da yadda take tausayin mutane, akwai shaƙuwa me ƙarfi
tsakaninta da dabbobinta, mussman ma wannan magen nata pita, da kuma karen ta dake
gidan gona, tana jin daɗin kasancewa da su, dan ba ƙaramin ɗebe mata kewa sukeyi
ba.
Ta samu container ta zuba masa madara, ta samo wani ta zuba masa gugguru, ta koma
gefe tana kallon magen, maimakon magen yaci seya koma jikin ta ya kwanta, dan ya
saba idan lokacin cin Abinci yayi, ta zuba masa nasa yana ci itama tana cin nata
**********************************
Abbas ne yayi Sallama ɗakin Yusuf, da ƙyar Yusuf ya iya amsawa, ya miƙe zaune suka
gaisa da Abbas.
"Sannu Yusuf, ko Asibiti za muje in sauke ka"
Yusuf ya girgiza kai yace "A'a na sha magani kawai, ya kake ya aikin?"
"Alhamdilillah, jiya Oga Suleiman yake neman ka, shine kiran da nayi maka, kuma se
kace baka jin daɗi, yanzu yau ba zaka gidan su mutuniyar taka ba?"
Yusuf yace "bazani ba gaskiya, sedai zuwa gobe in Allah ya kaimu idan naji sauƙi"
Abbas yayi ƙasa da murya yace "Ya kuɗin nan waye ya turo dasu kuwa?"
"itace wai Albashi na ne na watanni uku da bata bani ba, nace mata yayi yawa ta
rage taƙi"
"Taɓɗijan kaima Yusuf da wani abu, kamarya ta rage? Malam kawai kaci kuɗi, meye
labari kuma?"
Yusuf ya gaya masa Hotel da suka je, da yadda suka dawo tana kuka, Amma be gaya
masa zancen wayar nan ba data bashi.Nan suka cigaba da tattaunawa zuwa wani lokaci
Abbas yace ze tafi, Naira dubu ɗari Yusuf yayi masa transfer a cikin kuɗin, Abbas
yaita murna yana godiya suka yi sallama.
Amma ƙasan zuciyar Abbas kamar ya fasa ihu'dana san wannan alherin Yusuf zeje ya
dinga samu da tun farko nina karɓi aikin nan, ya samu dubu ɗari biyar amma ya bani
wata shegiyar dubu ɗari, ga danƙareriyar waya ya samu, na tura shi dan ina gudun
wulaƙanci amma yaje yana samo abun Arziki, dole in san yadda zanyi a cire shi daga
kan aika ni maye ni"
'Amma hatsari da kasadar dake cikin aikin fa?' wata zuciyar ta tambaye shi, tsaki
yayi yana ci gaba da surutai.
*******************************Shafa jikin magen take a hankali tana lallaɓashi
yaci Abinci, wayarta ce ta fara ringing, muzurun nan ya kasa a guje yaje ya ɗakko
ta a bakin sa ya kawo mata, shafa kan muzurun tayi tace "thank you Roux"Ta amsa
wayar tasa a kunnen ta"Ranki ya daɗe Bala fa babu lafiya, an ɗauke shi rai a hannun
Allah an kai shi Babban Asibitin cikin gari, dan besan waye a kansa ba"
Miƙewa tayi tsaye tace "what? How comes? Wace irin rashin lafiya ce wannan?"
"Nima ban sani ba gaskiya, Amma an fita da shi daga Asibitin cikin kurkukun gaba
ɗaya"
Bata kashe wayar ba ta miƙe, da sauri ta shiga bedroom ɗinta ta canza kaya, dukda
yanayi na rashin lafiya da take ciki, wayar ta ta koma ta ɗakko ta fara daddanawa
sannan tasa a kunnen ta.
Yusuf yana jin wayarsa tana ringing ya ƙi ɗagawa yasa ta a silent, ya ajiye wayar
ya cigaba da kwanciyar sa.
Jifa tayi da wayar akan kujera ta fice harabar gidan, gurin su Nura ta nufa, tana
zuwa suna gaishe ta amma bata kula suba tace "Ku kiramin driver yanzu" Jiki na
rawa suja shiga kiran Yusuf babu ƙaƙƙautawa, Amma be ɗaga ba.
Ta kalli Nura tace "ɗakko mota da sauri, zaka fita dani"
Cike da washe baki yaje ya ɗakko mota, ta shiga Nura yaja motar suka fita, gaba
ɗaya ji take kamar tayi Amai, dukda a bayan motar ta zauna amma warin hammatar Nura
ya cika motar, se tsaki take yi badan ya zama urgent ta fita ba babu yadda za'ayi
ta yadda wannan ƙazamin ya jata a mota, suna tafe tana masa tsawa gami da
hantararsa, Amma Yusuf ze gane kurensa na ƙin zuwa da yayi yau sannan yaƙi ɗaga
waya.
Prison tasa ya kaita, suna zuwa ta fita ta shiga, kai tsaye ofishin Hisham ta wuce.
Yana ganin ta yai murmushi ya sallami kowa daga office ɗin sannan yace "barka da
zuwa lady boss, Ashe kin dawo Nigeria?"
"Ya aka yi Bala ya kamu da rashin lafiya da har ta kai shi ga kwanciya, seda aka
fita da shi daga gidan nan?"
"Ranki ya daɗe gaskiya dama yana ɗanyin rashin lafiyar a tsai tsaye, Kawai se ɗan
uwansa ya kawo masa ziyara, bayan ya tafi jikin sa ya rikice"
"yanzu kana nufin kace min Ɗan uwansa ne ya kawo masa abunda yaci, jikin sa ya
rikice kenan? Saboda sakaci da rashin sanin aikin ku?"
"A'a ranki ya daɗe kin san?...
"Yimin shiru malam, saura sati ɗaya tal a koma kotu, kawai se inji wannan banzar
maganar mara tushe, shikenan amma kasani idan har rashin lafiyar Bala haɗin baki
ne, duk wanda yake da hannu a ciki shima abunda ya samu bala ze sameshi. "
Ta miƙe a fusace ta fito, Hashim ya biyo ta da sauri amma ta shiga mota da niyyar
ta ta wuce gurin lawyern Daddy, amma ba zata iya jure wannan tsamin da Nura yake
ba, dan haka tace ya nsida ita gida, tana mamakin ƙoƙari irin na Daddy da yake iya
shaƙe wannan warin hammatar, Yusuf kullum tsaf dashi cikin ƙamshi, amma wannan
ƙazamin kamar baya jin yadda yake wari, seda ta bari sun koma gida, sannan tayi wa
Nura ta tas akan ƙazanta da warin da yake yi a gaban sauran ma'aikatam.
Gaba ɗaya ranta a ɓace, ga jikin ta ba ƙwari gashi a ƙule take da Yusuf, tana shiga
babban falo ta tarar da Hajiya Halima, bata kula ta ba tasa kai zata wuce "Widad
ina son Magana dake"
Widad ta tsaya ta juyo ta kalleta ba tare da tace komai ba.
"Widad bekamata ace kina fita lokacin da kike so ki dawo lokacin da kike so ba a
matsayin ki na mace, sannan ki dinga dawowa sanda kika ga dama ba, Alhalin nida
nake zaune tare dake ban san idan kike zuwa ba, Sannan wannan yaron da yake sintiri
gurin ki har ƙuryar ɗakin ki, Sam be dace ba"
"kinga dakata Malama, zamanki nake a cikin gidan nan? Koke kika ajiyeni? In kun
tashi taku yawon gayamin kuke? Kisawa ranki gidan nan tamkar bariki yake, kowa yayi
abunda yaga dama muddin be ƙetare abunda masu gidan suke so ba, karki ƙara shiga
sabgata, kuma kowa zan kawo cikin gidan nan gidanmu ne, kowa ze je har cikin ɗakina
babu ruwanki, kome nake aikatawa karki ƙara shiga, dan ke ba uwa ta bace baki
haifeni ba, baki da ikon ki samun ido, kema abar a sawa ido ce, kisa ido akan 'ya'
yanki kawai, ba ruwan ki dani....
"Widad!!!" Ramlah ta kira sunan Widad da ƙarfi
"Ramla don't ever try to shout at me, a gidan mu kike ba gidan ku ba, dan haka ki
iya bakin ki, tun kan in fusata"
Tana gama maganar ta juya ta tafi part ɗin ta.
"Tirƙashi Mummy dan Allah ki bani dama ko sau ɗaya, inci mutuncin yarinyar nan in
koya mata hankali ko zanji sanyi a zuciyata"
Mummy ta girgiza kai tace "Kina yin haka Ramla kin ɓata komai, rabu da ita lokaci
ne, yana nan zuwa da zata girbi abunda ta shuka"
**********************************
Se wajen la'asar sannan Yusuf ya ɗanji sauƙi ya tashi, ya shirya yaje Asibiti, aka
duba shi aka bashi magunguna. ya dawo gida ya wuce ɗakinsa, wayarsa ya ɗakko ya
duba, yaga missed calls rututu, ko ba'a gaya masa ba yasan Widad ce take neman sa,
bebi ta kansu ba ya ajiye wayar ya cigaba da harkokinsa.
Dayaji ya ɗanji ƙwarin jikin sa, seya shirya tsaf ya tafi hotel ɗin da suka je da
Widad, Manager yaje nema amma be sameshi ba, ya cewa ma'aikatan su bashi lambar
wayar sa, da farko suka ƙi, seda ya nuna musu id card ɗin sa sannan suka bashi,
seda ya zagaya lungu da saƙo na Hotel ɗin, yana sake monitoring mutanen dake shiga
da fice a hotel ɗin sannan ya koma gida.
Washegari da safe dukda ya tashi jikin sa babu daɗi, Amma haka ya shirya ya tafi
gidan su Widad.
Tunda yaje Isa yake masa wani irin kallon banza, yanata habaice habaice Shi dai
Yusuf be kula shi ba, Nura yace
"Wallahi Yusuf yau kana ruwa, bama kusa da kada ba, cikin bakin kada, jiya ta
fusata sosai, dan zata fita seni na kaita saboda baka zo ba"
Murtalah ya kwashe da dariya yace "bayan kun dawo kuma tai maka tatas a gabanmu
ba, saboda ƙazanta kai Nura jiya kaga tijara a tsakar rana, ai idan nine kai ko
maganar ba zan ɗakko yau ba" yai maganar yana dariya
Nura ya haɗe rai yace "Bana son rashin mutunci da Iskanci"
Ganin suna nema suyi faɗa yasa Yusuf yin gaba abunsa ya barsu a gurin, tafiya kawai
yake yi amma jikin sa babu daɗi.
Yana shiga falon ya tarar da Ramadan ɗan gidan Alhaji Bulama da Amal suna hira.
Yusuf yace "barkanku da Safiya"
Bata amsa masa ba se Ramadan ne yace "Yawwa barka dai, bodyguard ɗin gimbiya"
Yusuf ya ɗanyi murmushi ya nufi hanyar Widad.
Bayansa Amal tabi da kallo, taji wasu hawaye na ƙoƙarin zubo mata, ta tsani
kusancin Widad da Yusuf gani take komai ze iya faruwa, wani sashin na zuciyar ta ma
yana gaya mata akwai wata alƙar a tsakaninsu saboda kusancinsu yayi yawa.
Ramadan ya kalleta yace "lafiya kuwa my?"
Girgiza masa kai kawai tayi tace "lafiya ƙalau"
Yusuf ya shiga ya tsaya a bakin ƙofar bedroom ɗin ta sannan yayi sallama kamar
yadda ya saba.
Yayi Sallama kusan uku amma bata amsa ba, haka ya cigaba da tsayuwa a gurin, seda
aka kwashi wani lokaci sannan ta fito, kallon sa tayi daga sama zuwa ƙasa sannan
tace "Sannu ishashshe kaga damar zuwa kenan?"Shiru Yayi ya sunkuyar da kai, ɗakin
ta shige yabi bayanta da sallama
"Meya hanaka zuwa jiya? Kuma kaƙi ɗaga waya?"
"Bani da lafiya ne shiyasa"
"ƙarya kake" ta faɗi kai tsaye ba tare da duba ratar shekarun da Yusuf ɗin ya bata
ba, shiru ya sake yi bece komai ba, ta tako tazo daf dashi tace "for the second
time meya hanaka zuwa jiya?"
"bani da lafiya ne" ya sake bata amsa
"wai me yasa baka kunyar yin ƙarya ne, meyasa? Ban gaya maka bana son ƙarya ba?"
tai maganar tana ƙoƙarin sa idon ta a cikin nasa
Babu zato ya janyota gaba ɗaya tana facing ɗinsa, ya kafe ta da idon sa, nata cikin
nashi ya ƙura mata ido
Ayi sharing please 🙏🙏🙏
Ayshercool07063065680
_*AƘIDATA*_
*AYSHERCOOL*
PART1 Page 13
ELEGANT ONLINE WRITER'S
Ba ƙaramin firgita tayi ba da abunda Yusuf ɗin yayi, sedai riƙon da yayi mata tana
iya jin huci me zafin da jikin sa ke fitarwa, masifa take son yi amma gaba ɗaya
Yusuf yayi mata wani irin kwarjini ta kasa cewa komai se binsa da tayi da manyan
idanunta.
Cike da jarumta Yusuf yace "Meyasa koda yaushe idan nayi abu seki ƙarya tani? A
koda yaushe ina ƙoƙarin gaya miki iya gaskiya ta amma seki ce ƙarya nake, kin san
yadda mutum keji kuwa idan aka ƙarya tashi, it's really hurts, duk abunda nake yi
ba inayi ne dan in samu kusanci dake ba, nasan AƘIDARKI nasan abunda bakya so, ina
ƙoƙarin kiyaye dokokin da kika kafamin ne, dokokin dana sawa hannu amma koda yaushe
burinki kici zarafina"
"Malam cikani ko" ta faɗa tana masa wani irin kallo
Cikata yayi ya koma gefe ya tsaya.
Seda tayi ajiyar zuciya sannan tace
"hmm tunda nake babu wanda ya taɓa Yimin abunda kayi min a yanzu, ina ɗaga maka
ƙafa ne saboda wasu dalilai biyu zuwa uku, dalilai biyu bakomai ne a gurina ba, dan
ba zasu hanani yanke hukuncin dana ga dama akan ka ba, dalili ɗaya ne me ƙarfin da
yazo da ƙaddarar da ni ban isa in canza shi ba koda hakan bemin ba, ba yadda zanyi
da kai dukda har yanzu ina doubting akan wannan dalilin, Anyway zamu fita yanzu
zamu je gidan gona"
"A wace motar?" ya tambayeta a taƙaice
"kowacce ta bashi amsa"
Har ya juya ze fita yaji tace "meya sameka a fuskarka?"
Ya juyo ya kalleta
"kar kayi min ƙarya" ta faɗa kafin ya bata amsa
"Duka ne" ya bata amsa
"Kamar ya ya duka? Suwaye suka dakeka?"
"Nima ban sansu ba"
Ɗan tsayawa tayi tana nazarinsa, yayin da ya ɗauke kai yaƙi kallonta
"Shikenan, muje"
Suka fito falo, yana gaba tana bayan sa, Amal ta bisu da wata uwar harara.
Ramadan yace
"Allah ya temaki 'yar masu gida, Gimbiyar gida a biki a zauna lafiya, a ɓata miki
mutum yai kwanan baƙinciki,' yar gaban goshi sha lelen masu arziki, tun ɗazu nake
zaman jiranki anan, Megida ne ya aiko ni, yace yana son ganinki"
Ta yamutsa fuska tace "Ina da abunyi, da haka ba zani ba"
Ramadan yace "haka zanje in gaya masa"
"Eh haka za kaje ka gaya masa, bazan zo ba, bazan ƙara zuwa inda yake ba"
"shikenan, kunfi kusa keda shi"
Ta juya suka fice ita da Yusuf.
Amal tace "Ramadan, dan Allah yanzu baka jin haushin irin abunda takewa
mahaifinku?"
Ramadan yace "to me zance Amal? Ni meye nawa a ciki? Da mahaifina da mahaifinta
tashi nayi na gansu tare, kuma haka muka tashi muka ga an sangartata se abunda take
so sukeyi, sun ɗauki son duniya sun ɗora mata, ba'a kwaɓarta komai tayi dai dai ne,
meyasa zanji haushi, tunda ba yau ta fara ba, kuma idan tayi baya jin haushi, a
gabana a gaban sa idan bata ga dama ba Bulama take cemasa kanta tsaye, an riga an
barta ta tashi akan wannan AƘIDAR"
"gaskiya ni abun yana damuna, mu kanmu a cikin gidan nan bamu tsira daga wulaƙancin
ta ba, bamu ba har mahaifiyar mu fa"
"kin san wani abu? Ni yanzu babbar damuwa ta itace, Daddy yace Fahad zasu aurawa
ita, Fahad kuma mutum me faɗa baya son raini ni ban san ta yaya za'ayi wannan zaman
auren ba"
Amal tace "ai duk wanda ya kwashi wannan ya kwashi masifa, gata mahaukaciya ga ba
tarbiyya, gaskiya ina tausayin Fahad"
***********************************
Yusuf yayi parking ɗin motar a gidan gona, Widad na fitowa kamar kullum haka
ma'aikatan suka yo caa suna gaishe ta, ɗaga musu hannu tayi ta kalli Wani daga
cikin ma'aikatan, wanda ya tsare Yusuf da tambayoyi wancan karon tace "Ya aiki ya
kuma dabbobi na?"
"lafiya ƙalau ranki ya daɗe, ko za'a ɗakko dokin ne?"
"A'a sedai ina so kayi min rakiya in zaga su"
"to shikenan ranki ya daɗe" haka suka shiga suna zagawa, sosai Widad take jin
nishaɗi idan tana kallon dabbobi, gaba ɗaya mantawa take da damuwar da take ciki,
suna cikin tafiya tace
"Sale naji wata magana, ban sani ba ko kai ka jita, takanas nace bari inzo domin mu
tattauna ta"
Saleh yace "Allah yasa ba wani abun akace nayi ba ranki ya daɗe?"
"idan ka yadda da kanka ba kayi lefi ba meye na tsarguwa? Labari ya isheni cewar
ɗan uwanka bala bashi ds lafiya, naje har prison dan in duba shi, amma akace min an
fita da shi zuwa babban Asibiti dan be san wake kansa ba, ban kai ga zuwa duba shi
ba har sena je naga lawyer na tukuna "
A gigice Sale ya kalle ta yace " ya za'ayi ace yana rashin lafiya, harta kai ga
baya gane mutane? Shekaranjiya fa naje duba shi, na sameshii lafiya ƙalau, taya
haka zata faru? "
"Nima abunda na gaza ganewa kenan, ace beyi rashin lafiya ba se daya rage 'yan
kwanaki a cigaba da shari'a, Babban Albishir ɗin dana zo maka da shi shine, muddin
na tabbatar da sa hannun ka, zaka maye gurbinsa ne"
Saleh ya kalleta da sauri, bata bari yace komai ba, ta juya ta tafi. Turus Saleh
yayi yana nazarin maganganun Widad. Tunda Yusuf ya fara aiki da Widad, a kullum se
yaga abun mamakin daze kulle masa kai.
Ya kunna motar suna shirin tafiya wayar ta ta ɗau ruri, tana kallon screen ɗin
wayar ta ɗan ɓata rai ta tura baki, ɗaga wayar tayi tasa a hansfree "Hello Daddy"
"lovely fushi kike dani ko?"
"A'a"
"Fushi kike mana, Daddynki yace ya aiko a kira masa ke kince ace bazakiyi zo ba,
Baby Why meyasa kike haka?" shiru tayi taƙi cewa komai.
"Yanzu haka munyi waya, ina so kije kiji meze ce miki"
"Daddy nifa yanzu wani gurin zani, Na gaya maka ina cikin damuwa kunƙi saurara ta,
sema kawomin wasu abubuwa da bana buƙata yake, na gaya maka akwai matsala amma
kunƙi saurara ta"
"Ba shawara nake baki ba, Umarni ne kije gurin Bulama yana son ganin ki"
Tura baki tayi ta ajiye wayar tana haɗe rai, Yusuf be nemi shawarar ta ba ya kaita
gidan Bulama, Ranta a ɓace ta buɗe motar ta fita tana tura baki, har tayi gaba ta
tsaya ta juya taga Yusuf yana rufe mota "Malam ni ka hanzarta ba zaman jiranka zan
tsaya yiba"
Yusuf ya biyo bayanta, suna shiga katafaren falon suka tarar da Iman, ƙanwar
Ramadan, Iman tai murmushi tace "Ohhh beb, ashe zaki zo yanzu Ramadan ya dawo"
Hannu kawai ta ɗagawa Iman ta nufi matattakalr bene. Iman tace "Widad, Nurat ta
kirani tace min tun ranar da kika bar gurin birthday ɗinta baki ƙara ɗaga wayarta
ba, i hope ba saɓani kuka samu ba, dukda nasan halinki dai"
Shiru Widad tayi ta tsaya, saboda yadda abubuwa suka yi mata yawa, sam bata cigaba
da bibiyar meyasa meta a gurin birthday ɗin Nurat ba, dan tafi tunanin ko ciwonta
ne ya tashi a gurin, shiyasa ta kasa tuna komai, juyawa tayi tana kallon inda Yusuf
yake, ya ɗauke kai yaƙi kallon ta.
Still ba tace komai ba ta cigaba da tafiya Yusuf na binta.
A babban falon dake saman benen wanda ya kasance na Bulama anan suka tarar da
Bulama shida matarsa.
Yusuf ya gaishe su suka amsa, Widad kam kyam ta tsaya tana ƙare musu kallo, sannan
ta nemi guri ta zauna abunta tana hura hanci, wata uwar harara matar Bulama take wa
Widad.
Bulama yace "lovely ba gaisuwa?"
Tura baki gaba ta sake yi tana ƙunƙuni, Bulama yayi murmushi yace
"Ikon Allah, ƙiri2 'ya na fushi da babanta, har in tura a kiraki kiƙi zuwa ko? Duk
dan nace a miki Aure kike wannan fushin dani haka?"
Cike da tsiwa tace "Eh dan kace ayimin Aure ne, nace maka bana so, bana so, Amma
kaƙi ban sani ba ko kaima da wata manufar a ranka, nace a min Visa in koma inda na
fito shima kace A'a, ba dole inyi fushi ba"
"Widad meyasa baki da kunya ne? Sam baki da ta ido" cewar matar Bulama.
"Ba dake nake magana ba, ina magana da mijin ki ne karki sake shiga harka ta" Widad
tai maganar a fusace
Bulama yayi murmushi yace "Ummu Ramadan excuse us please"
A fusace Matar Bulama ta tashi ta bar ɗakin tana mita, Bulama ya kalli Yusuf yace
"Young man can you excuse us please?" Yusuf yace "ok sir" ya juya ze fita
"ba inda zeje, ko mene faɗi a gaban sa"
"wow daughter kin yarda dashi haka yaji abubuwan da suka shafi rayuwar ki? Lallai
sauƙi yana samuwa"
"ba wani sauƙi daya samu, ina nan a mahaukaciya ta kamar yadda kuka saba faɗa"
"waya isa yace miki mahaukaciya, ba mahaukaciya bace ke Daughter"
"Eh amma kuke kaini gurin likitocin mahaukata"
Alhaji Bulama yace "Daughter a bar wannan maganar, magana ce Maman ki tazo min da
ita"
"ni uwata ta mutu, an kasheta bani da wata uwa, ta haifi dai wanda ta haifa"
Bulama ya girgiza kai yace "What ever dai, ta kawomin ƙorafi akan ki, kina fita
lokacin da bata sani ba, ki koma bata sani ba, kuma kinsan babu tsaro haka kike
yawo ga rayuwar ki a hatsari, kuma tayi koke akan wannan direban naki, bata jin
daɗin yadda direban ki yake sintiri a sashenki, gaki budurwa ga ta da manyan yara
mata, bekamata ya dinga sintiri kuna keɓewa dashi ba, daughter meyasa ba kya
ɗaukarta kamar mahaifiya ne? "
Shiru Widad tayi tana jinjina kai, Yusuf kam gaba ɗaya ji yayi kamar ƙasa ta tsage
ya nutse, dan shi kansa baya jin daɗin yadda yake shiga inda Widad take, yana ganin
rashin dacewar hakan.
Bulama yace " Daughter baki ce komai ba"
"so nake ka gama tukuna"
"Na gama feedback ɗinki nake jira"
Widad ta gyara zama tace "Ka gaya mata wanda ze iya zama a gidanmu a ƙarƙashin
mulkina shikenan, wanda baze iya ba ƙofa a buɗe take ya ƙara gaba, tunda basu da
zuciya dole su zauna su cigaba da zama, yadda ba ruwana dasu to sudena samun ido,
idan zargin da takemin kenan, to ka gaya mata idan maza nake son kawowa bata isa ta
hanani ba, tunda gidan mu ne, sannan ni bani da uwa, Uwata ta bar duniya an
kasheta, bazan ƙara yadda da wani ba, ban yadda da kowa ba kuma bazan yarda da wani
ba, i start loosing trust on you Bulama, bani da uwa an kashe uwata! Karta ƙara
kiran kanta uwata, ni bani da uwa! Bana son kowa ya raɓeni, ban yadda da kowa ba
wannan AƘIDATA ce"
Jikin ta ne ya fara rawa, wasu irin hawaye na zuba daga idon ta, da sauri Yusuf ya
tashi suna rige rige da Bulama zuwa ga Widad, Numfashi take da ƙyar tana kuka,
Yusuf yazo kanta da sauri yace "Are you ok?" jinjina masa kai tayi Bulama jiki a
sanyaye yace "daughter, ban faɗi wannan maganar dan in ɓata miki rai ba, Nayi ne
dan in tunasar dake mahimmancin haƙuri, kuma koba komai matar mahaifinki ce
sannan.. Ɗagawa Bulama hannu tayi ta miƙe ta nufi waje da sauri.
Bata tsaya ba seda taje mota, gaba ɗaya rayuwar Widad abun tausayi ce, tunda Yusuf
yasan ta bata cikakken sati bata zubar da hawaye ba, Amma ina dangin mahaifinta
kona mahaifiyar ta? "
A haka ya kaita gida, yana tuƙi kamar baya so, saboda yadda yake jin kukan ta me
ban tausayi, kamar yadda ta saba indai sukaje guri suka dawo, kame tazo dashi a
motar zata barshi, se Yusuf ya kawo mata. Dan haka yana parking ta buɗe ta fice, ya
ɗakko jakar da Wayar ta ya bita. Sedai yana shiga Falon ya jiyo sautin kukan Widad
cikin gurɓatcciyar hausar ta take faɗa "danme zaki dinga zuwa kina kai ƙarata, bafa
ki haifeni ba, keba uwata ce ba, kin sani meyasa kike shisshigi a al'amura na, idan
baki dena min haka ba zan ɗau mataki mafi muni akanki, ki ƙyaleni inji da abunda
nake ji, ki ƙyaleni inji da ƙunci da baƙin cikin dana ke ciki tsawon shekaru mana,
danme zaki dinga min haka?"
Masifa take sosai kamar zata shaƙe Hajiya Halima, Abun na Widad ya fara wuce gona
da iri.
Yusuf yace "kina hayyacinki kuwa? Meyasa kike haka?, a haife ta haife ki, bekamata
kidinga gaya mata wannan maganganun ba"
Ta juyo kan Yusuf cikin faɗa tace "Bana hayyacina, ni mahaukaciya ce, idan baka
sani ba yau in gaya maka, bani da hankali har ƙasar waje ake kaini ganin likitan
mahaukata, Amma baka san me nakeji a zuciya ta ba, An kashe mamana ban san kowa ba
se ita, aka kashe ta ba wanda ya damu dani se Babana da Bulama, kowa kansa ya sani
babu wanda ya damu da abunda Widad take ciki, kasan me nake ji a raina idan na tuna
lokacin da aka kashe mahaifiyata? Wannan tabin baze bar zuciyata ba, a ƙyaleni inyi
rayuwar da naga dama mana, "
Yusuf yayi ƙasa da murya yace" is alright I feel your pain "
" you don't feel my pain, your mum is still alive but me... Kasa ƙarasawa tayi se
sake fashewa da tayi da kuka, ta tafi part ɗinta da sauri, Yusuf kam kasa bin bayan
ta yayi wannan karon, Hajiya Halima kam ƙamewa tayi ta zubawa sarautar Allah ido.
Yusuf ya juya ze fice Hajiya Halima tace "Ina zaka tsohon munafuki, zuwan ka gidan
nan shiya hargitsa komai, da yarinyar nan duk rashin mutuncinta bata fiye magana
ba, seda kazo kana hure mata kunne, to idan ma wani ne ya turoka to tabbas zanyi
maganin ka, dan da zarar Alhaji ya dawo zansa ya sallameka, matsiyaci banza dana
wofi kawai "
" Niba matsiyaci bane, Amma talaka ne me wadatar zuci, sannan kafin kisa a koreni
da kaina nayi deciding yin resigning, zan bar aikin nan dan nima abunda yake faruwa
ba daɗi yake min ba ko dan tsira da mutuncina, dole in bar aikin nan tunda bana
shiga aljanna bane"
Fitowar Amal yai daidai da maganganun Yusuf da yace ze bar aikin, sakin ƙaramin
plate ɗin hannun ta tayi, tabi bayan sa da sauri tana kiran sunan sa.
" Idan kika bar ƙofar falon nan da sunan bin bayan sa, zan sallamawa duniya ke in
bar masa ke, tunda haka kike so"
Juyowa tayi tana kallon Mummy, ta juya da sauri part ɗinta tana kuka.
************************************
Abbas se juyi yake akan kujera yayi shiru, gaba ɗaya abun alherin da Yusuf ke samu
a hannun Widad ya tsaya masa a zuciya, yaji meyasa yasa aka tura Yusuf aikin shi
beje ba? Yayi gudun kar yaje a dinga masa wulaƙanci yasa aka tura Yusuf, yanzu
gashi kuɗin data bashi Yayi Albashinsa uku, ga gefe ana biyan sa Albashinsa,
Sallamar Sakina ce ta dawo da shi hayyacin sa, ya amsa mata sallamar ta kalle shi
tace "lafiya kuwa Yallaɓai?""lafiya ya bata amsa"
Ta ɗan taɓe baki tace
"dama zuwa nayi in tambaye ka, dan Allah meyasa Yusuf baya zama a office yanzu?
Wane irin aiki ne aka bashi haka?"
Abbas dama a ƙule yake yana neman wanda ze gayawa matsalar sa, dan haka ya zayyane
mata komai, ciki harda Aibata Yusuf, ba ƙaramin mamaki ne ya kamata ba, ganin duk
headquarter nan babu wanda Yusuf yake sakin jiki dashi kamar Abbas, Amma ace Abbas
ne da bakin sa yake faɗar wannan mahanga akan Yusuf, lallai ɗan Adam ba abun yarda
bane.A zahiri ta maze tace "gaskiya kai yakamata ace kana samun wannan sha tara ta
Arziki ba shi ba, yanzu kayi duk yadda zakai kasa a maye gurbin sa da kai, a karɓe
aikin daga hannun sa, idan kana buƙatar taimakona ma zan maka, kasan mu mata akwai
iya makirci"
Abbas ya washe baki yace "ƙwarai kuwa, amma fa nagode sosai Sakina"
************************************
Har Yusuf ya kama hanyar gida, kawai ya ɗakko wayarsa ya kira Manager Hotel ɗin
nan, ai kuwa wayar ta shiga, Yusuf ya tambaye shi idan yana son ganin sa ya zasu
haɗu? Ya gayawa Yusuf inda zasu haɗu a gidan sa, beyi wata wata ba yaje har gidan
nasa.
Da ganin manager Hotel ɗinma kaga ɗan duniya, suka gaisa da Yusuf, Yusuf yace
"dama wata buƙata ce ke tafe dani, ina son ka nunamin mutanen da suka kama ɗaki a
hotel ɗinku, tun daga farkon wannan watan"
Manager yace "Kai Malam, ni na zata ma wata harkar cigaba ka kawo, wannan abun da
kake tambaya sirri ne bama fitar dashi, manyan mutane ke zuwa Hotel ɗinmu, ba
zamuyi exposing ɗinsu ba dan duniya babu yarda"
"ze kasance sirri ne tsakanina da kai, kasa a bani babu wanda ze sani"
"Malam bazan iyaba, ka tashi ka tafi kawai"
"zan baka dubu ɗari biyar, zaka bani akan wannan farashin?"
(Abunda yasa Yusuf baya son nuna shi waye, ma'aikaci ne na sirri, no need asan shi
waye)
Murmushi mutumin yayi yace "yanzu naji batu, Amma tsakani da Allah turoka akayi,
kokuma ma'aikaci ne kai?"
Girgiza kai Yusuf yayi yace
"Dani ma'aikaci ne ko sisi bazan baka ba, sedai inyi amfani da ƙarfin aiki na,
Matata nake zargi ina so in kamata red handed, kuma kona kamata bazan taɓa sako
sunan ku a lamarin ba"
"Shikenan, Amma dan Allah ya zama sirri tsakaninmu"
"in Allah ya yarda babu meji, da gani se kai"
"shikenan muje se a baka"
Yusuf yace "No bana son yawan zuwa gurin bana son a ganni a gurin, ta Email ɗina
nake so ka turamin, zan baka ɗaya bisa huɗu na kuɗin seka turomin zan baka sauran,
bana saɓa Alƙawari dan haka kaima karka saɓa"
Haka ya amince da wannan yarjejeniyar.
*********************************
Saleh ne yake kaiwa yana komowa, Alhaji Bukar ya fito ya sa meshi, ya kalle shi ya
yatsuna fuska yace "lafiya?"
A fusace Saleh yace "dole ka tambaye ni lafiya, me kasa akayiwa ɗan uwana? Ta yaya
zanje in ganshi lafiya ƙalau kawai labari ya isheni wai bashi da lafiya"
Alhaji Bukar yace "dakata! Da ina son ganin bayan ɗan wanka da tun a shekarun baya
gudun karya tona min Asiri da tuni ya bar duniya, zaman kotu daza'a koma bani da
fargaba sam, inada ƙwararrun lawyoyi da na biya su wanda zasu tsayamin, dan haka ba
abunda zesa in yiwa ɗanuwanka wani abu"
"Au haka ma zakece? Wato kai a wanke ka shikuma ya cigaba da zama a prison ko? Ga
wannan mahaukaciyar Yarinyar taje ta sameni, tace muddin wani abu ya samu Bala ni
zan maye gurbin sa, me kake tunani ne wai? Yarinyar nan tana da kuɗi zata iya
aikata duk abunda taso"
Alhaji Bukar ya ɗan daki kafaɗar Saleh yace
"shiyasa nace kazo mu haɗa kai mu raba ta da dukiyar, mu mallaki gundurin dukiyar
da muke ta farauta muga ta tsiya"
Saleh ya make hannun Bukar yace "Niba dukiyar tace a gabana ba, babu irin
kyautatawar da mahaifinta be minba, ni dukiyar sa bata gabana, ni burina a wanke
ɗan uwana a fito da shi daga kurkuku tunda bashi da laifi"
Wata uwar dariya Alhaji Bukar ya saki yace "ubanwa yace maka bashi da laifi?
Lallai har yanzu kanka a kwano yake, ka ƙyaleshi ya girbi abunda ya shuka, kazo a
haɗa kai a nemi Arziki".
Yana gama maganar ya wuce ya bar Saleh a gurin.
************************************
Yusuf yaita safa da Marwa yana duba wayar sa, ba zato Sega abunda ya nema an turo
masa ta Email ɗinsa, message ɗin na shigowa Manager ya kira Yusuf, Yusuf yayi masa
godiya sannan ya tura masa sauran kuɗin, wanda kuɗaɗen da Widad take bashi ne, dan
wani lokacin idan ta bushi iska se yaga alert.
Yusuf ya tura message ɗin cikin System ɗinsa da sauran wayyoyinsa, nan Yafara aiki
akan bayanan da aka turo masa, ba ƙaramin mamaki ne ya kamashi ba ganin mutanen da
suka ka kama ɗakuna a wannan watan zuwa ranar da suka je Hotel ɗin tare da Widad,
wanda ya kama ɗaki ranar da sukaje shida Widad yafi bashi mamaki, Abun tambayar
anan shine 'ya akayi Widad tasan da zuwan mutumin gurin? Me Widad taje yi? Gurinwa
taje?' me ta gani ya sata kuka? 'Yusuf zuciyarsa ɗaya baya jin Widad zata aikata
wani mummunan aiki na alfasha, amma akwai wani ɓoyayyen abu da yakamata ace ya
sani.
Kamar wanda aka mintsina ya miƙe ya shirya, ya duba agogonsa ƙarfe takwas na dare,
haka ya fita ya tari abun hawa ya tafi unguwar su Nurat.
Unguwar tasu shiru, amma haske ko ina da yake rukunin Gidajen masu kuɗi ne, har
ƙofar gidan aka kaishi aka sauke. Ya sauka ya nufin gidan su Nurat, ya tsaya suka
gaisa da megadin, Yusuf yace "Dan Allah gurin Nurat nazo"
Maigadin ya kalle shi yace "tasan da zuwanka ne?"
"A'a, bata sani ba, Amma ka gaya mata tayi baƙo"
Mai gadi ya kira Nurat a waya yasa a hansfreee ya gayamata tayi baƙo.
"Babu wanda zan haɗu dashi yau, dan haka ba zanga kowa ba"
Yusuf yace "kace mata Widad ce ta aiko ni"
Aida jin Widad ce tayo aiken Nurat ta rikice, tace "Kaishi guest room, ina zuwa"
Maigadin yayiwa Yusuf jagora, har wani katafaren Falo, Yusuf ya zauna yana jiran
fitowarta. Ko mintuna goma ba'ayi ba se gata ta fito, ta ƙaraso cikin falon da
hanzari, sedai tana arba da Yusuf ta rikice ta buɗe baki zata yi ihu ta gudu, Cikin
zafin nama Yusuf ya riƙeta tare da toshe mata baki.
"Meye haka kamar kinga wani aljani ko mugu? Kinga fa mutum ne ni"
Fizgewa tayi, ta shiga Ja da baya ta kwaɓe fuska zata yi kuka tace"Nifa wallahi tun
ranar da kuka bar nan, Widad bata ƙara zuwa gidan mu ba"
Gaba ɗaya Nurat ba tafi sa'ar Widad ba, sedai Widad tafi Nurat jiki sannan Izzarta
da jin kanta yake sa ka ganta kamar Babba.
Yusuf yace "Haba Nur, nifa ba wani abu zanyi miki ba kawai tambayoyi zan miki in
tafi"
Girgiza kai ta shiga yi tana kiran sunan Daddy a hankali.
"Daddyn yana nan ne?" ya tambaye ta
Ta girgiza masa kai alamar A'a
"to ki nutsu ki zauna, hira za muyi in tafi"
A hankali ta zauna, tana rarraba ido dan a tsorace take da Yusuf, dan ba zata manta
randa Yusuf ya shaƙeta ba, har yayi barazanar sace taba.
Yusuf yace "Calm down dear, hira zamuyi kawai in tafi"
Ganin taƙi sakin jikin ta yasa Yusuf ya miƙe ya zaro komai na Aljihunsa, dan ya
tabattar mata da babu wani makami a tare dashi.
Ya kalleta yana ɗan nazarin ta sannan yace "ko ki tambaye ni ina Widad ko? Tun
ranar da ta bar nan baki sake neman ta ba"
"Na kirata bata ɗaga wayata ne, nasan bazata sake yarda dani ba"
"Waye yace miki ba zata sake yarda dake ba? She's very simple and kind, but why do
you attempt to kidnapped her?"
Kamar Nurat zatayi kuka tace "bafa laifi na bane, Daddy ne"
Yusuf ya ɗan ƙara matsowa yace "Amma me tayi wa Daddy haka da zesa a saceta?" yai
maganar yana kallon idon Nurat, Yarinya ce dan haka yake binta a sannu cikin hikima
Ɗan shiru tayi sannan tace "Nifa ban sani ba"
"Haba me sunan manya, Haske maganin duhu, baki kama da maƙaryata ba, ni ya akayi ma
kika san Widad har kuke hulɗa bayan bata son mutane?"
"Nifa ba wani hulɗa mukeyi sosai ba, da tun ina ƙarama, gidan su na U. K yana kusa
da namu daga baya suka dawo Nigeria shine... Sekuma tayi shiru tana satar kallon
Yusuf.
"Shine me? "
"Dad ɗina sunyi faɗa da Daddynta akan Siyasa, shikenan abunda nasani, Amma dan
Allah karka gayamata Daddy nane yasa ayi kidnapping ɗinta idan ta sani, zata sa a
kai Daddy na prison ne"
"bazan gaya mata ba, ai kin gayamin gaskiya, amma naga Daddynta ɗan kasuwa ne ba
Siyasa ba me zesa suyi faɗa da Daddynki akan siyasa"
"to ainima bakomai na sani ba, muna yara lokacin Amma tabbas sunyi faɗa ne shine
yake son ya rama akan Widad, amma ni ban san me yake so yayi mata ba"
Yusuf yace "shikenan nagane, gaskiya you are so kind dear, Insha Allah bazan bari
taji ba, Amma dan Allah karki bari a cutar da ita, kinga marainiya ce ita abun
tausayi, ke kina da Mum da Dad ɗinki ita kuma she's orphan"
Jinjina masa kai kawai tayi.
Yusuf yace "Bani wayarki in sami ki lambata, se mudinga gaisawa ni daga yau nayi
ƙawa, ni zan maye miki gurbin ƙawancen ki da Widad"
Kallon sa tayi ta ɗanyi murmushi yadda yake magana ya burgeta, bashi da hayaniya,
ya iya tsara magana daki daki, se yanzu ta gane ranar da yayi mata wannan barazanar
ne ya koma kamar wani mugu amma ba haka yake ba, ta miƙa masa wayar sannan tace
"Amma ni ban sanka a Family ɗinsu ba, waye kai a gurin ta?"
Yusuf yayi murmushi yace"i don't belong to her family, but a very important person
attached to her destiny"
Kallon sa tayi cike da rashin fahimta za tayi magana ya kashe mata ido ɗaya, gaba
ɗaya seta sunkuyar da kai ta kasa maganar, ya daɗe yana daddana wayarta, ita kuma
ta kasa cewa komai. Seda ya gama abunda yake sannan ya miƙo mata wayar yace
"Nagode sosai ƙawata, Allah ya bar zumunci, ni zan koma naji daɗin kasancewa dake
da wannan hirar da mukayi"
Murmushi tayi tareda sunkuyar da kai tace "baka gayamin sunan ka bafa"
"Sunana Abokin Nurat, Just call me Aboki or any name you like, good night Nur"
Ya ƙarasa maganar tare da nufar hanyar fita yana addu'a Allah ya shiga lamarin sa
akan wannan aiki me hatsarin gaske da yake yi, yasa hanyar da ya ɗakko ta zama
mafita ga al'amuran. Yayinda Nurat ta rakashi da ido har ya fice
Nurat tana komawa cikin gida Maman ta tace "Ke lafiya kuwa? Waye wannan yazo kika
daɗe haka?" "Abokina ne yazo muka gaisa" tai maganar cike da basarwa ta shige ɗakin
ta tana tunanin Yusuf.
_*AƘIDA TA*_
PERFECT WRITERS ASSOCIATION
(WE AIN'T PERFECT BUT WE ARE ALWAYS TRYING OUR BEST, TO MOTIVATE AND ENTERTAIN OUR
READERS)
https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/
P. W. A
*Story and written by*
_*AISHA HUMAIRA (Daddy's girl)*_
The experience writer of *ABDUL JALAL** WATA KISSAR.... (SAI MATA) *And now *AƘIDA
TA *
I dedicated this book to my Mum (Malama Nafisat Adam Muhammad) i love you mum
https://www.wattpad.com/user/Ayshercool7724?
utm_source=android&utm_medium=link&utm_campaign=in
PART1 Page 14
ELEGANT ONLINE WRITER'S
Sosai Yusuf yake ƙara samun haske akan lamarin binciken da yake yi, Sam babu
specific lokacin da Widad take bawa Yusuf albashi, duk lokacin da ta bushi Iska
sedai yaga alert ɗin kuɗi, kuma kuɗi masu yawa, sannan be isa yayi magana ba.
Yana ta tattara bayananan daze gabatar a gurin aiki na sakamakon binciken da yake
yi.
Tunda Yusuf ya tafi Nurat take tunanin, ko ta gayawa Mahaifiyarta yadda suka yi da
Yusuf, wata zuciyar ta gargaɗe ta akan hakan.
********************************
Gaba ɗaya Widad ta takura kanta, sam ko Babban falo bata fitowa, tana iya sashin ta
daga ita se magenta, duk da haka Yusuf kullum se yaje koda baze ganta ba kuwa.
Lambar wani abokinsa likita ya dubo a wayarsa ya kirashi, se da ta kusa katsewa
sannan ya ɗauka.
"Yusuf kana da kirki kuwa? Ace ka ɓata ko neman mutane baka yi?"
Yusuf yace "Amma ka tsaya mu fara gaisawa, sarkin ƙorafi"
Nan suka gaisa suka taɓa hirar yaushe rabo, sannan Yusuf yace "dama doctor Hamza
ina da wata 'yar tambaya ne, dukda nasan tambayar da zan maka ba a fannin daka
karanta kenan ba, amma na sanka da shige shige"
Hamza yace "shikenan ina jinka, Allah yasa nasan amsar tambayar taka, in babu amsar
ma se'a nemo"
'Masha Allah, dan Allah Hamza wace irin larurar ƙwaƙwalwa ce take sa mutum ya dinga
gudun mutane? "
Doctor Hamza yace"Anthropophobia kenan, is a mental disorder, masu irin wannan
larurar suna jin tsoron taron mutane, idan abun ya tsananta ma ko ahalinsu basa son
su raɓe su, sedai wasu tsirari daga mutane, basu fiye son taron jama'a ba, ko shiga
cikin mutane basa so"
Yusuf yayi ajiyar zuciya yace "to me yake haddasa ciwon"
Hamza yace "eh to, abun da yake haddassa wannan larurar ga wasu, idan an taɓa cin
amanarsu, mussaman wanda suka yadda da shi, ko kuma wani abu da ya taɓa faruwa dasu
mara daɗi a rayuwarsu, wasu kuma hormones ne suke haddasa musu excessive fear ya
danganta dai, zakaga wataran suna lafiya ƙalau ga wanda ciwon be tsananta a gare su
ba, amma idan ya tashi zaka ga basa son haɗa ido da mutane, basa son suga ana
kallonsu, kosu kasa bacci, ko yawan ciwon kai, bugun zuciyar su ya canza, wasu
numfashinsu har ɗaukewa yake, ko su dinga karkarwa in sunga baƙo, ko wanda basu
yadda dashi ba, ko kuma su dinga wrong perception akan abubuwa, ko su dinga ganin
duk wanda ya raɓesu ze cutar da sune"
"Ok magana, nagode sosai Hamza amma meye maganin ciwon?"
"gaskiya babu wani sahihin maganin ciwon gaskiya, rehabilitation ne a dinga kwantar
musu da hankali tare da ƙoƙarin canza musu tunani daga mummuna zuwa kyakkyawa, dan
wasu in damuwar tayi musu yawa suna fara shaye2, ko dinga wasu tunani wanda ya saɓa
da abunda yake a zahiri, ayi ƙoƙarin samar da wani abu daze dinga ɗebe musu kewa,
koya ɗauke musu hankali daga damuwarsu, in kaga an basu magani mafi akasari sedai a
basu magani akan sauran matsala, kamar bugun zuciyar, ko daidaituwar hormones ɗin
ko makamancin hakan...
Shiru Yusuf yayi yana tunani, meye alaƙar ƙwayar daya gani a ƙasan kofin shayin da
za'a bawa Widad da ciwon nata, Doctor Hamza Yana cikin yiwa Yusuf bayanin ne ya
hango Widad ta fito, tana nufo inda yake zaune, gaba ɗaya fuskarta a haɗe kamar
kullum, yauma shigar tata da ta saba ita tayi, jikin nan a tsuke a cikin ƙananan
kaya.
Da sauri Yusuf yace "shikenan nagode sosai doctor, nagane Allah ya saka da
alkhairi" ya katse wayar
Ya shiga wani tunanin, "to wace irin Allura akewa Widad haka? Amal tace masa ana
mata wata Allura, ga kuma abunda likita yace"
Ta ƙaraso ta kalle shi a yamutse tace "ɗakko mota, zamu airport ne yanzu"
Ya kalle ta yace "me zamuje yi a Airport?"
"ban sani ba" ta bashi amsa
Ƙasa yai da idonsa yayi mata wani irin kallo sannan ya miƙe yai gaba, gaba ɗaya
kasa gane kalar kallon tayi meya ke nufi da haka?
Ya ɗakko mota ya kunna suka fara tafiya, suna tafiya yana satar kallonta yana
tunanin, me zeyi wa Widad wanda ze temaka gurin canza tunanin ta mara kyau zuwa me
kyau, kamar yadda doctor Hamza ya gaya masa.
Yana cikin tunanin wayarsa ta fara ringing, sedai lambar ba suna, kuma yana tsoron
ya ɗaga yaje a cikin abokan aikinsa ne, wani yayi masa kwaɓa, sekuma ya tuna
halinta, yanzu yana ƙin ɗaga wayar zata masa wata fassarar, haka ya basar ya ɗaga
wayar yasa a kunnen sa tare da yin sallama.
Siririyar muryar mace ce ta amsa tace"Aboki ya kake?" se yanzu ya gane muryar
Nurat, murmushi yayi yace "lafiya ƙalau, light ya kike?"Wani murmushi ne ya suɓuce
mata tace "lafiya ƙalau friend, dama cewa nayi bari in kiraka mu gaisa"
"Amma gaskiya kin kyauta Light, ina fatan kina lafiya ba kya cikin kowace irin
damuwa? Kin san damuwa da yawan haɗe rai yana sa mutum ɓacin rai da saurin tsufa,
kuma duk kyansa ya koma kamar wani abun tsoro"
Da sauri Widad ta juyo ta kalle shi, amma ya basar ya cigaba da wayar, yayin da
Nurat tayi murmushi tace "Ni lafiya ƙalau nake, bani da wata damuwa ko matsala ina
Widad?"
"tana gidansu, ko ince kina gaishe ta ne?"
Kamar Yusuf yana ganinta ta girgiza kai tace "Kamanta kace kar in gaya mata muna
abota? Na tambayane kawai dan inji ko tana lafiya"
"Eh kuma fa hakane? Amma yaushe zakizo ki ganta?"
"Ai ban san wane irin kallo za tayi min ba idan nazo gidansu, inajin tsoror"
Tsaki Widad tayi ba tare da ta kalli Yusuf ba tace
"Malam ka isheni, ka cikamin kunne"Murmushi Yusuf yayi yace "light, se anjima Madam
tace na cika mata kunne"
Jiki a sanyaye Nurat tace "Madam kuma? Dama kana da Aurene?"
Yusuf yace "Babba dani kice bani da Aure, ina da Aure mana muna tare da ita ma,
munɗan fita ne, se anjima kar in sake ɓata mata rai"
Wani irin wulaƙantaccen kallo Widad tayi masa, dama yasan a rina "ni kake cewa
matarka? Baka da hankaline, ni ka kalleni ka cemin matarka"
"waye cemiki dake nake ne? Am just kidding idan ba haka nayi mata ba zata ga kamar
na mata wulaƙanci ne, kuma babu daɗi ka Wulaƙanta mutum it hurts a lot, Yusuf baya
Wulaƙanta mutane"
Wani tsakin ta kuma ja ta ɗauke kanta, yayin da shi kuma yayi murmushi, a ransa
yace 'Insha Allah, sena canza miki dukkanin wannan gurɓatattun tunanin naki kafin
in kammala bincike na"
Gurin wani restaurant sukabi, tace masa ya tsaya ai kuwa yayi parking, tana yi tana
duba agogon hannunta, ta buɗe motar ta fita, shima ya fito yabi bayanta.
Cikin restaurant ɗin ta shiga ta samu guri ta zauna, Yusuf be jira unarninta ba
shima yaja kujera ya zauna.
Aka kawo musu menu(jadawalin Abincin da suke available) Ta karɓa tana jujjuya menu
ɗin, ɗan ɓata fuska tayi ta zaɓi Abunda take so,Aka bawa Yusuf ma, ya kalli Menu
ɗin ya girgiza kai yace "Ni ban iya cin irin wannan Abincin ba gaskiya, Umma ta
cika min ciki da ɗumamen tuwo dan haka ni ba abunda zanci"
Kallonsa tayi ta ɗauke kanta, yayin da waiter ɗin tayi murmushi ta karɓi menu ɗin
ta tafi.
Karon Farko da Yusuf yaga Widad tana cin normal Abinci, sam bata damu da Abinci ba,
sedai yaga tana 'yan ciye ciye, ta yaya mutum zeyi lafiya ba tare da cin cikakken
Abincin da ze gina masa jiki ba, ko duk cikin rashin yardar ne oho mata.
Yanzun ma ba wani cin Abincin take ba, ɗan cakala take a jikin spoon, kamar wata
ƙaramar Yarinya kamar me wasa da Abincin tana kaiwa bakin ta .
Yusuf ya ɗan ƙura mata ido yace "Madam are you really Hungry?"
Cigaba da cakalar Abincin ta tayi ba tare da ta kula shi ba.
Ko ɗaya bisa ukun Abincin bata ci ba, ko naman kai bata taɓa ba, ta ture Abincin ta
ɗau tissue tana goge bakin ta, 'Iko se Allah, Abincin naira dubu huɗu akayi wa
wannan cakalar aka barshi, wani yana nan yana fama da Yunwa'
"wai Harkin ƙoshi?"
"wai ina ruwanka dani ne? Ta yaya zan iya cinye wannan Abincin duka?"
"Amma kin san bazaki iya cinyewa ba kika sa aka kawo miki? Akwai dubban marasa
ƙarfi da Abincin naira ɗari ma gagarar su yake a rana, kalli uban Abincin da kika
bari, wataƙila yanzu wannan da kika rage sedai a zubar, ba kyau Wulaƙanta Abinci,
wataran kema ze iya Wulaƙanta ki"
Ko kallonsa ba tayi ba, ta ɗauke kanta tana kallon wani gurin, amma tayi shiru tana
saurarensa, gefe guda kuma ta shiga tunanin maganar sa, dagaske akwai wanda suke
rasa Abincin naira ɗari ya gagare su? To wani irin Abinci ma mutum zeci da naira
ɗari, se a samu mutum yace bashi da naira ɗari?.
Yusuf Yaja plate ɗin Abincin gabansa ya ɗau spoon ya fara cin Abincin da Widad ta
rage.
Kallon Yusuf take, sosai mamaki yake bata shi sam be ɗau komai da zafi ba, Abincin
data rage yake ci, ko dan dai shi talaka ne oho.
Yusuf ba ƙaramin mamaki yake ba yadda take ɗaga masa ƙafa, dan shi kansa yasan wasu
lokutan yana wuce gona da iri, tana ƙyaleshi ne kawai
"ya naga kina kallona ko nayi wani abun ne na rashin yadda?"
Ɗauke idonta tayi daga kallonsa zuwa wani gurin daban.
Yusuf ya ciko spoon yace "Kinga yadda ake cin Abinci a ciko cokali da Abinci, se
mutum ya ƙoshi ba yadda kike yi ba, kamar kina wasan yara, koda yake yarinyar ce
ai"
Ɗago ido tayi ta kalle shi, amma ya cigaba da cin Abincin yaƙi kallonta, lallai
Yusuf ya samu dama a kanta ya fara rainata, tunda harya samu damar gaya mata
maganganun da yaga dama, ita kanta Widad tana mamakin yadda take ƙyale Yusuf, ba
yadda za tayi dashi wata ƙaddara me ƙarfi ta shigo dashi cikin rayuwarta, wanda ko
dan albarkacin hakan yaci ta dinga ɗaga masa.
Seda ya kammala sannan ta ajiye masa ATM ɗinta, ta miƙe ta nufi hanyar fita, Yusuf
kuma ya nufi gurin biyan kuɗin, kafin Widad ta kai ga ƙofar fita wani mutum da
tunda suka shigo yake kallonta yabi bayanta.Yusuf yace "ashe akwai mini Drama yau"
Ya biya kuɗin ya fito, sedai yana fitowa ya tarar tana zazzagawa Mutumin masifa.
"Kalle ka ni zaka biyo kace in baka lambata? Bazan bayar ba shashsasha an gaya maka
kowa sakaraine irin ka?"
"Ni kike cewa sakarai?"
"Na gaya maka ko akwai abunda zaka iya ne?"
Yusuf ya ƙaraso da sauri gurin yace "haba bawan Allah, ya zaka biyo matar Aure kace
kana so?"
Mutumin ya kalli Yusuf yace "Matar Aure kuma? Da wannan shigar tata?"
"koma wace irin shiga ce tayi ina ruwan ka? Haka muka tsara rayuwar Aurenmu, haka
muka ga damar yi, idan har kasan shigar da tayi bata dace ba meye na biyo ta? Kana
gurin nan muka zo tare mu kaci Abinci, danme zaka biyo ta kace kana so?"
Mutumin yace "Amma indai wannan matarka ce gaskiya kayi dacen Auren kyakykyawar
mace, sedai bata da ɗa'a kuma bata san darajar Auren ta ba"
"bakomai a haka nake son a bata, sannan karka kuma gangancin kiran ta da wasu
miyagun kalamai, ka gode Allah da ban ɗau mummunan mataki akanka ba"
Ya juya ya kalli Widad da mamaki ya hana ta magana, A fusace ta juya ta tafi mota
ba tare da tace komai ba
Yusuf ya juya ya koma motar shima yana shiga ya zauna, ya kunna motar suka fara
tafiya, ba tace komai ba se tafasa da zuciyar ta take yi
Ba zato ba tsammani, Widad ta Ƙanƙance ido tace "i thinks you drunk something
abusive today, kasan me ka faɗa kuwa? Which type of Weed did you take today? Wane
irin rashin hankali ka aikata? Meye hakan kake ne dan me zaka dinga danganta kanka
dani a matsayin mijina, kai ko Auren zanyi zan auri talakan mutum kamar Kane?"
Dukda yadda kalaman Widad suka daki zuciyar Sa haka ya daure, yayi parking ɗin
motarsa, ya matsa Kusa da ita ya matsa yace "Abunda kika ci dai shi naci, dukda
baki san meye So ba, ƙarewa ma kince baki yadda dashi ba, amma the magic behind
Love is that, ba ruwan sa da talaka kome kuɗi, sannan wannan abunda nayi shine
kaɗai mafita daze hana kowane kare da biri binki, da kuma ƙarewa surar jikin ki
kallo, please Dress decently to avoid such type of people, dukda ina matsayin me
miki aiki, aikin ma na direba, I have to tell you something, you have an attractive
beauty Widad, stop exposing it anyhow yana taɓa zuciyata a duk lokacin da kika fito
da wannan shigar naga wasu na ƙarewa wannan kyakykyawar halittar kallo, your beauty
suppose to be only for your husband, duk wata mace me tsadace jikinta ma me tsada
ne meyasa zaki dinga bari ana ganin naki?"
Ɗaga ido tayi tana kallon sa, gaba ɗaya Yusuf ya rufe mata baki, ya kulle mata kai,
gaba ɗaya ta nemi izzar da jin kan da zata masa wulaƙanci ta rasa, yau wani irin
kwarjini yayi mata data kasa cewa komai, shi kuma ya samu damar hakan yake ta
abunda yaga dama, a baya zata iya rantsewa baze aikata haka ba, ganin yadda ko
magana baya son yi.
Haka suka cigaba da tafiya kamar kurame, kowa da abunda yake saƙawa a zuciyar sa,
gaba ɗaya tunanin rashin mutuncin da zata yi wa Yusuf take.
Har suka ƙarasa airport bata iya cewa komai ba, parking yayi amma bata buɗe murfin
motar ta fita ba, shima zaman sa yayi yaƙi fita, ya sauke glasan suka cigaba da
zama, lokaci2 ta dinga duba agogon hannun ta.
Buɗe ƙofar tayi ta fita, shima ya buɗe ya fito, Alhaji Nasir ne yake tahowa da
brief case ɗinsa a hannun sa.
Yusuf ya ƙarasa da sauri yana gaida Alhaji Nasir tareda karɓar brief case ɗin
hannun sa. Alhaji Nasir yace "Yayana na kaina, fatan na sameku lafiya ya amana ta?"
Yusuf yay murmushi yace "Alhamdilillah"
Ya kalli Widad yace "my Lovely har yanzu kina fushi da Dad ko?" yai maganar yana
rungume Widad, kamar anmata dole tace "Welcome Daddy"
Alhaji Nasir ya ɗan shafa bayan ta yace"thank you sweetheart" suka ɗunguma zuwa
mota gaba ɗaya, suna tafiya Alhaji Nasir da Yusuf ne kawai ke hira, Amma Widad
tunanin ta ta yaya zata hukunta Yusuf.
Har Yusuf ya gama aikin sa na ranar ya tafi Widad bata samu mafita ba.
***********************************
"Jama'a bafa a bori da sanyin jiki, wannan ce damar da yakamata muyi amfani da ita,
tunda Allah yasa yarinyar nan tana ƙasar nan musan abunda za muyi" cewar Alhaji
Munir
Alhaji Musa yace "Ni idan an samu abun nan falillahil hamd, amma babban burina be
wuce in Wulaƙanta Alhaji Nasir a idon duniya shida ahalinsa ba kamar yadda ya
Wulaƙanta ni ya ɓata min suna"
Alhaji Haruna yace "gaba ɗayanmu buƙatar mu ɗaya ce, kuma kunsan Alhaji Bukar shike
bamu umarnin abunda zamuyi, karmu yadda muyi abunda ze waegaza shirin mu, yanzu
yarinyar taje gidan yari tayi wa Hashim barazana akan indai da hannun sa akan
wannan lamari daya samu Bala to tabbas zata ɗau mataki akansa "
Alhaji Musa yace " Umarnin Alhaji Bukar kawai nake jira, amma akwai yuwuwar shima a
kauda shi, dan komai ze iya faruwa barinsa a doron ƙasa"
Alhaji Haruna ya zame akan kujera yana shafa tumbinsa yace"Ni dai kam da zan samu
yarinyar nan, So nake gaskiya, dan akwai ta da ƙira daidai gwargwado".
Tsaki Alhaji Munir yayi yace "kai ka fiye shirme, ana ta kai wake ta kaya, in in
hutawa kake so, ka fita ƙasashen waje ga mata nan farare yadda kake so, amma yanzu
ka bari idan muka karɓi abunda muke so, muka aika Nasir Daula kiyama, se kayi yadda
kaso"
Wata uwar dariya suka saki hadda shewa.
**********************************
"Bulama tafiya tayi Alhamdilillah, na samu approval na fara business ɗina da China"
"Masha Allah, naji daɗin hakan, Allah yayi jagora"
Baban Widad yace "Ameen ya Allah, sedai ko kun samu saɓani da 'yar taka ne? Tunda
na dawo naga bata walwala ko akwai matsala ne?"
Alhaji Bulama yai murmushi yace "hmm Widad' yata ta kaina, tabbas munyi faɗa, kasan
tunda nace ayi mata Aure take jin haushi na, tazo ta sameni akan wai sena mata Visa
ta koma naƙi, shine take fushi"
Alhaji Nasir ya girgiza kai yace "Nima wancan satin ta kirani tana kuka, akan
lallai sena kiraka nasa an mata visa ta koma, ni kuma gaskiya bazan bari ta koma
ba, idanma zatavkoma se bayan Auren ta da Fahad sa tafi tare"
"hakane, daga lokacin da ta fara tara iyali dole ta dena wannan halayen nata,
sannan mamanta ta kawomin ƙararta akan yadda suke da direban nan, na kirata nayi
mata faɗa, nanma ta sake yin fushi dani"
Alhaji Nasir yai murmushi yace "ina tunanin akwai wani ɓoyayyen al'amari a tattare
da yaron nan, ba ƙaramin daɗi naji ba ganin shine mutum na farko bayan nida kai da
Widad take sakewa dashi"
"Amma karfa muyi sake yazo suyi shaƙuwar da zamu yi da nasani"
"Insha Allah ba zamuyi ba, dan yaron yana da tarbiyya sosai"
"Amma idan soyayya ta shiga tsakanin su fa?"
Alhaji Nasir yace " Yarinyar da bata yadda da soyayya ba, ta ina zasu fara soyayya?
Gaba ɗaya Widad ɗina a birkice take bata da alƙibla"
Bulama yace "Kasan bata da alƙibla ai kuwa ba abun mamaki bane ta fara soyayya da
direban ta, tunda shi so baya sallama".
"to nidai duk abunda ze saka ta farinciki shi nake so, idan ta kawo shi tace tana
so bakomai se in Aura nata shi"
Bulama yace "Allah ya kiyaye mu aura mata direba haba Daula"
"to masu 'ya, ai seka biye mata kuyi tayi"
Sukayi dariya suka shiga hirara duniya.
***********************************Sintiri take a ɗakin ta, tana son gazgata abunda
take ji a zuciyar ta game da Abokin ta. Dagaske na kamu da Son wanda yake daga
ɓangaren maƙiyin mahaifi na, amma ban san alaƙarshi da Widad ba, amma tunda na
gansu tare suna da alaƙa.Shiru tayi tana tuna yadda ya zauna a kusa da ita yana
mata magana, cikin rarrashi danta saki jiki dashi.
Kamar light da yake kiran ta dashi yafi komai yi mata daɗi, Amma dagaske yana da
Aure? Ta tambayi kanta, anya za'a yarda a auramin me mata? Gashi kuma ɗan uwan
Widad.
Dafe kai tayi tace "Subhanallah"
"ke lafiya kuwa? Sintirin me kike tayi haka kamar kinwa sarki ƙarya?"
Juyawa tayi ta kalli inda Maman ta ke tsaye tace "bakomai fa"
"bakomai, a hakan? Gaba ɗaya alamu sun nuna baki da gaskiya sam"
Ta ɗan tura baki tace "wallahi ina da gaskiya"
"shikenan, idan tayi wari maji"
Nurat ta koma kan gadonta ta zauna ta ɗakko wayarta ta shiga kiran layin Yusuf amma
shiru baya shiga, tayi2 harta gaji ta ajiye, tana mamakin ya akayi hakan ta faru?
Shikuwa Yusuf tun ranar data kira shi agaban Widad, yana komawa gida ya cire layin
ya ajiye gaba ɗaya.
**********************************
Oga Suleiman ne zaune akan kujera yana gwadawa Sakina wasu ayyuka a computer, sun
maida hankali sosai kan aikin.
Abbas ne yayi sallama, suka ɗago gaba ɗaya suka dube shi tare da amsa sallamarsa,
Sakina ta gaida Abbas, yayin da Abbas ya ƙamewa Suleman cikin girmamawa.
Suleiman ya bashi damar zama, sannan ya miƙa masa hannu suka gaisa, Suleiman yace
"Abbas kwana biyu banga Yusuf ba fa, ya kamata ace yazo ya gabatar min da sakamakon
binciken da yayi"
Abbas yace "ranka ya daɗe, nima kaina na kasa gane inda yasa gaba, gaba ɗaya kamar
ba aikin yake ba, yaje ya shantake se abun Arziki yake samu a gidan, alherin da
suke masa yasa gaba ɗaya hankalin sa baya kan aikin, da dai da hali a canza shi da
wani kawai"
Suleiman yace "Amma kaika cemin ze iya aikin, da kai nace zan bawa ka nunamin ya
fika haƙuri da juriya"
"Ai Oga sam ban san haka ze faru ba, ban taɓa sanin Yusuf yana da son abun duniya
ba seda ya karɓi aikin nan, ba abunda yake se neman gindin zama a gidan da yake"
Sakina kam sakin baki tayi tana sauraren yadda Abbas ke ɓata Yusuf a gurin ogansu,
wanda hakan ze iya jawowa Yusuf babbar matsala a gurin aikin nasu, Yusuf ya yadda
da Abbas sosai, dan yana masa kallon ɗan uwa bama abokin aiki ba.
Oga Suleiman yace "shikenan, zan duba idan da dama zan kira shi a waya ma, inaga
karɓar aikin zanyi daga hannun sa in bawa wani"
***********************************
Gidan shiru babu kowa, Yusuf yana inda ya saba zama idan yaje gidan su Widad,
Murtalah ne yazo inda Yusuf yake yace "Malam Yusuf kana nan kana hutawa ashe?"
"wallahi kuwa Murtala ya aikin?"
"Alhamdilillah, ai kana fama Yusuf, kullum se kazo ko zakayi aiki ko ba zaka yi ba"
Yusuf yayi murmushi yace "to ya za'ayi tunda na yadda zanyi aikin, ai dole in cika
ƙa'idar aikin"
Murtalah yace "hakane" suna cikin hirar Amal ta fito, ta ƙaraso inda Yusuf ke
zaune, ranta a ɓace tace "kazo ana son ganin ka"
Ba musu ya miƙe yabi bayan ta, suna shiga babban falo har Yusuf zeyi hanyar
ɓangaren Widad, dan yasan be wuce ace ita take kiransa ba, tunda Alhaji Nasir baya
nan.
Amal tace "A'a, ba a nan ake neman ka ba"Ta nuna masa hanyar ɗaya part ɗin dabe
taɓa taka gurin ba, seda ya ɗanyi jimmm ya kalle ta sannan yace "shikenan muje"
Suka rankaya ɓangaren data nuna masa, tana tafe yana binta a bayaWata ƙofa ta buɗe
suka shiga, matsakaicin bedroom ne, me ɗauke da kayan more rayuwa sedai be kai
haɗuwar na gimbiyar gidan ba.
Amal ta juyo ta kalle shi tace "Yusuf Meka ke nufi dani ne?"
Cike da rashin fahimta yace "kamar yaya? Kince ana kirana kuma kin kawo ni nan"
"Yusuf nina nake nemanka ba wani ba, na gaya maka abunda ke raina amma ka maidani
kamar wata banza, Haba Yusuf me yasa baka da tausayi ne? Soyayyar ka nata wahalar
dani amma hankalin ka yana kan waccan banzar mahaukaciyar, har dama ka samu a kanta
wanda zaka rama irin wulaƙancin da take maka, ATM ɗinta kwanansa nawa a gurin ka?
kamata yayi kayi amfani da wannan damar ka azurta kanka, tausayin mara tausayi
asara, asara ne gagaruma ko dai dan Widad tana da kuɗi shiyasa kake Wulaƙanta ni?"
Yusuf be taɓa jin son Amal a ransa ba, ta yaya suna muzanta wadda suke cin Arzikin
gidan su, ina gashi da yake bare? Kuma suna ta jadadda masa yayi wannan gagarumar
sata haka?
"Amal ki fuskance ni, niba na Wulaƙanta mutane, sannan bani na tara musu dukiya ba,
ta yaya zan musu wannan mummunan aiki? Ni ba Ɓarawo bane, dukiyar Widad bata gabana
mutunci da girmamawa ya fiye min wata dukiya komai yawan ta, indai ban rasa ci da
sha ba Alhamdilillah a yadda Allah ya ajiye ni, Widad batamin laifin komai ba, babu
wani abu da tayi min wanda zesa in cutar da ita ko mahaifinta, tsakanina da su in
musu aiki ne su biyani bisa ga yarjejeniyar da na sakawa hannu, Amma Amal tsakani
na dake babu batun Soyayya duba da banbanci da kuma tazarar dake tsakanin mu, ke
'yar masu kuɗi ce, ni kuma talaka ne matsiyaci kamar yadda mutan gidan ku suke
faɗa"
"Yanzu kana nufin ba zaka karɓi Soyayya ta ba Yusuf, ka zaɓi cigaba da wahalar da
zuciya ta, mace me kima kamata ince ina sonka amma ka watsamin ƙasa a ido? To
wallahi baka isa ba, zaɓi biyu ke gareka kodai ka karɓi Soyayya ta, ko kuma in
shirya maka gadar zaren da idan ta rufta da kai har Abada ba zaka sake wani Amfani
ba"
'Kiyi duk abunda ki kiga dama, tabbas da soyayyar gaskiya kike min da baki faɗi
haka ba, tabbas na taɓa Soyayya nasan zafin ta, Amma ba' a dole a soyayya "
Yana gama maganar ya juya ya fice daga ɗakin, biyo bayan sa tayi tana ƙwala masa
kira, Amma yaƙi tsayawa yana buɗe ƙofar part ɗin ze fita yayi tozali da gimbiya
'yar masu gida, Widad ce a tsaye a bakin ƙofar dake facing ɗin wadda ya fito, se
muzurai take idanunta sunyi Ja, tana masa wani irin kallo me wuyar fassara.
Me kuke tunanin ze faru?
(Masha Allah, am speechless wlh, Addu'arku tayi tasiri a gareni ina miƙa muku
godiya, masu tambayar jikin Daddy Alhamdilillah ya warke ras💃💃💃 almost done with
the exams only some part remains, saura fatan Nasara, farinciki yasa nace bari inyi
surprising ɗinku da posting, ina jiran jin comments me fasa waya, idan anyi Comment
yadda nake so gobema akwai posting insha Allah 😍😍😍 ina godiya masoya)
Domin sharhi, gyara, ko shawara feel free to contact me Ayshercool07063065680
_*AƘIDATA*_
PERFECT WRITERS ASSOCIATION
(WE AIN'T PERFECT BUT WE ARE ALWAYS TRYING OUR BEST, TO MOTIVATE AND ENTERTAIN OUR
READERS)
https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/
P. W. A
*Story and written by*
_*AISHA HUMAIRA (Daddy's girl)*_
The experience writer of *ABDUL JALAL** WATA KISSAR.... (SAI MATA) *And now *AƘIDA
TA *
I dedicated this book to my Mum (Malama Nafisat Adam Muhammad) i love you mum
PART1 Page 15
ELEGANT ONLINE WRITER'S
Turus Yusuf yayi ya rasa me yakamata yayi? Me zeyi wanda zesa Widad ta yadda da
shi, Amal ma da ta ƙaraso domin cimma Yusuf, tana ganin Widad itama tayi Turus ta
shiga rarraba ido kamar an sacewa karya 'ya' ya.
Widad tayi wa Yusuf alama da hannu ya biyo ta, ji yake kamar ƙasa ta tsage ya
shige, haka ya bi bayan Widad zuwa part ɗin ta, gaba ɗaya ya saddaƙar yana jiran
jin ruwan masifa daga bakin Widad.
Ta kalle shi tace "nayi list na abubuwa da nake buƙata ne, za kaje ka siyomin, ka
lura da duka abunda na rubuta bana buƙatar product ɗin basu nace ba"
Jiki ba ƙwari ya jinjina mata kai, ta ɗakko paper ta miƙa masa tare da ATM card, a
sanyaye yasa hannu ya ksrɓa, amma harya juya zefita beji tace masa komai akan
ganinsa ya fito daga sashin su Amal ba.
Har ze fita ya tsaya ya juyo ko zata yi magana, amma yaga tana danna wayarta, tana
ɗaga ido suka yi ido huɗu dashi ta kalle shi tace
"Lafiya? Ka tafi mana"
Ya kalle ta yace "bakomai"
Ya juya ya fita yana sake waiwayen Widad ko zata yi magana.
Fahad ne keta shirya kayansa a trolley, Anwar ya kalleshi yace "Fahad ji nake kamar
in bika mu koma Nigeria tare, amma ba yadda zanyi, munzo tare ka rigani kammaluwa"
Fahad yace "Ai kai ba komawa Nigeria ce ta dame ka ba, zuwa kaga wannan yarinyar ne
ya dame ka"
"ƙwarai kuwa faɗi ka ƙara Fahad, ni kaɗai nasan abunda nake ji game da ita, nima
ina nan dawowa ai Insha Allah, inga farincikin zuciya ta"
"Allah yayi maka magani, dan kaibnaga abun naka ka afka da yawa" "kadai bari
kawai, dan Allah Fahad kayi ƙoƙari ka samo min lambar ta idan kaje Nigeria" Yatsuna
fuska Fahad yayi yace "gaskiya ban maka Alƙawari ba, dan tamin rashin mutunci
marinta zanyi" Anwar yayi dariya yace "da kuwa ka ƙare rayuwar ka a prison" "kaini
ka isheni da zancen yarinyar nan haba"
Ƙarshe Fahad ya fice ya barwa Anwar ɗakin, dan ba ƙaramin haushi yake bashi ba idan
yana zancen Widad.
***********************************
"Ana ƙoƙarin a hallaka min ɗan uwana, sannan kuna min barazana da rayuwa ta, gefe
guda ga yarinyar nan itama ta sakoni gaba, anya Alhaji Haruna kunmin adalci kenan?"
Alhaji Haruna yace "Adalci ɗaya za muyi maka Sale, kayi aiki nan na ƙarshe da muke
so, in ba haka ba da kai da ɗanuwanka haka zaku ƙare kuyi biyu babu, tabbas muka
samu abunda muke so zamu fidda ɗan uwanka, sannan baku ba na kusa da kuma seya
azurta"
Saleh ya fesar da iska yace "kamar yaya? Yanzu dai ta tabbata kune kuja bawa ɗan
uwana abunda yasa rashin lafiya ta kama shi, don ku kasheshi karya tona muku asiri"
Alhaji Haruna yayi murmushi yace "zata iya kasan mune, kuma zata iya kasancewa
bamu bane ba, ka sani ko ɗan uwanka ya tona mana Asiri bashi da wata cikakkiyar
hujja a kanmu, kuma muna da ƙarfin da zamu siye Alƙalai da lawyoyi, shari'ar ta
tafi a banza, shi kuma a cigaba da tsaron sa, abu ɗaya ya rage maka, shine ka haɗa
kai damu mu gudanar da wannan aikin tare "
Maimakon Saleh yayi magana, sema tsaki da yayi yai waje yana wani irin huci kamar
kumurci.
***********************************Kafin Yusuf yaje aiken da Widad tayi masa seya
wuce gida ya ɗakko system ɗinsa ya wuce office.
Yana shigowa harabar station ɗin ya tsaya yana gaisawa da mutane, Sakinace ta hango
shi, ta yunƙuro ta fito da sauri ta tare shi, ta kalle shi tace"Sannu da zuwa yau
ka leƙo mu kenan?"
"Yawwa sannu" kawai yasa kai ya wuce, ya nufi office ɗin Abbas, gaba ɗaya dirircewa
tayi ta shiga tunanin ya zata yi ta fahimtar ds Yusuf, irin illar Kasancewar sa da
Abbas.
Yusuf yana zuwa ya miƙawa Abbas hannu suka gaisa, Abbas yace "mutumina gidan daula
sun ɓoye mana kai gaba ɗaya fa"
Yusuf yace "bari kawai Abbas, kullum a cikin zullumi nake, the more nake binciken
the more nake sake gano Wata sarƙaƙiyar, in taƙaice maka ma an fara bina wallahi"
"Kamar ya an fara binka?"
"Wai wani abu ake so in karɓo a hannun Widad, gashi yau na shiga wata cakwakiya a
gidan nan, ina ta jira ta sauken kwandon bala'i amma taƙi kulani, ƙarewa ma aikena
tayi, shine nace tunda na samu chance bari inzo inga oga Suleiman"
Abbas yace "ka gan shi kayi masa me?"
"In fara presenting abunda bincike na ya nuna min mana, akwai buƙatar tsananta
bincike a wasu guraren, amma kaga ai yakamata in gaya masa"
Abbas yace "garajen Meka ke hakane Yusuf? Ka bari ka kammala binciken nan, idan ka
kammala base ka kawo masa ba, Yallaɓan mafa baya nan ana nemansa a headquarter za
suyi meeting, kasan koka bashi cewa zeyi kabi komai a hankali"
"So kake inzo inyi laifi kenan? Ni nafi ganewa in fara presenting ɗin aikin"
Abbas yace "A'a karka damu, kabi komai a hankali"
Yusuf yace "shikenan bari in tashi in tafi, dama nan aikena aka yi"
Abbas yace "Amma Yusuf akwai cigaba a cikin binciken kuwa?"
Yusuf yace "Sosai makuwa, an samu ci gaba, the more nake binciken the more nake
sake cin karo da wasu matsalolin, Amma idan bincikena ya tabbatar da abunda nake
zargi, mutane da yawa a ƙasar nan za suji kunya"
Abbas yace "wai tukuna ma inga abunda kayi kake son ka nuna masan, suwaye za suji
kunyar?"
Yusuf yace "kabari sena kuma dawowa se mu cigaba da zancen yanzu ina sauri tunda
baya nan tafiya zanyi"
Yusuf yaja System ɗinshi yai waje, bayansa Abbas yabi da kallo yana ƙwafa, 'Sena sa
an Ƙwace aikin daga hannun ka tukuna za kayi bayani'
Sakina tana so ta yiwa Yusuf magana, amma sam yaƙi bata fuska, tana ji tana gani ya
fice daga gurin, tunani ta shiga yi, yadda Yusuf ya yadda da Abbas babu lallai kota
gaya masa ya yadda da abunda tace.
Yusuf yaje yayiwa Widad siyayyar data aike shi, ya wuce gida ya gama abunda yake yi
sannan ya koma gidan su Widad.
Har yanzu gabansa faɗuwa yake, ya ɗau kayan ya shiga ya kai mata, sedai da yaje
bata part ɗin nata se maganta akan gado.
Ya ajiye mata kayayyakin, ya ɗaga ƙasan pillow ɗinta ya sa mata ATM Card ɗinta ya
fito.
A falo ya ci karo da maman su Amal, ta masa wani irin mugun kallo tace "kai daga
yau, bana son sake ganin ka shigomin falo ba tare da ka nemi izini ba, na gaji da
wannan sintirin da kakemin, baligi kana ratsawa kana wuce ɗakin ta, baze yuwu ba"
"kiyi haƙuri Hajiya, nima ba da san raina ba, sedai ita Madam bata jiran izinin
kowa kafin ta yanke hukunci, dan haka wannan maganar a tsakanin ku ya kamata ku
tattauna ta"
Har Hajiya Halima ta buɗe baki zata yi magana se kuma tayi shiru, waiwaya wa yayi
yaga Shigowar Widad ce tasa ta yin shiru, bata kula su ba tayi part ɗinta, shima
Yusuf ya silale ya bar falon.
*******************************
"Maman Yara ina cikin farinciki Ɗana ze dawo, yakamata ayi dukkanin wasu shirye
shirye da suka dace domin tarbarsa, yasuhe rabon sa da ƙasar nan? Sannan ya dawo ya
tarar da kyakkyawan Albishir"
Haɗe rai Hajiya Sarah tayi tace "nikuma takaici ne fal raina wallahi"
"Saboda me takaici fal ranki, kamar ba ɗanki me ze dawo ba?"
"Eh ɗana ne, amma abunda kake shirin yi kaima kasan be kamata ba, ta yaya yarona
lafiyayye zaka haɗa shi Aure da mahaukaciyar da bata san girman kowa ba, ga bata da
tarbiyya"
Alhaji Bulama yace "Easy Madam, Sarah shifa ɗa na kowane, bekamata ki cigaba da
aibata Widad ba, itama kamsr 'ya take a gurin mu duba da yadda mahaifinta yayi mana
halacci a rayuwa, muna ƙoƙarin yin abunda zesa ta dawo hayyacin ta ne, kuma kinga
mu munsan larurarta, Fahad ze iya haƙuri ya zauna da ita, saɓanin a bawa wani a
waje Auren ta"
"to kai kaɗai ne yakamata kayi tamakon? Ina sauran mutanen gari? Nidai gaskiya aka
haɗa Auren ɗana da wannan tantiriyar mara mutuncin an cucemu, kai kanka da kake
matsayin uba a gurin ta cin zarafin ka take, inaga ɗanka kuma?"
"Sarah, bazan zaɓawa yarona abunda ze cutar da shi ba, Aure yana gyara mutum,
wuyarta su zauna a guri ɗaya ze iya canza ta"
"A'a canza halin wannan yarinyar banga ta inda ze yuwu ba Sam, kawai ka canza
shawara da tunani"
Tai maganar tare da miƙewa ta bar masa ɗakin
************************************
Yallaɓai Suleiman na dawowa, Abbas ya miƙe ya tafi Office ɗinsa, ya shiga ya gaida
Sulaiman cikin girmamawa irin ta masu ɗamara, se da yayi masa izini sannan ya
zauna, suka sake gaisawa.
Abbas yace "Yallaɓai, lokaci fa na ƙurewa, game da aikin nan daka bawa Yusuf, bana
tunanin abunda aka sashi yake yi, ɗazu yazo gurin nan, na ɗanyi masa tambayoyi akan
aikin, Amma Amsoshin daya bani sam basu gamsheni ba, da alama dukiyar dake gidan da
alherin da suke masa yasa ya bar aikin da 'aka sashi "
" Amma a iya sanina Yusuf mutum ne me hazaƙa, nasan shi da ƙwazo da himma akan
aiki, ba shida kwaɗayi sam"
"Yallaɓai mutum na iya canzawa a kowane lokaci, Yusuf abokina ne, amma ba yadda
zanyi, bana son inci amanar aiki ko' a samu matsala akan harkar aikin mu kimar mu
ta zube a idon duniya, Amma ya kamata kayi wani abu yallaɓai"
Suleiman ya ɗanyi shiru sannan yace "idan kuwa hakane, to tabbas Yusuf ya bani
mama, sedai zan kira shi muyi magana, zan bibiye shi idan har na gano maganar da
kake gayamin gaskiya ne, zan ɗau mataki na musamman akansa"
Abbas yace "Yallaɓai idan har ka kira shi kuyi magana ai zaka ɓata komai, zeyi duk
me yuwuwa ya kare kansa koda kuwa ƙarya ze maka danka yarda da shi, tunda shima
jami'in tsaro ne yasan duk hanyar da zebi ya kare kansa"
Suleman yace "Abbas base ka nunamin aikina ba, Nagode da wannan bayani naka zan
bincika, ka ciji jami'i nagari tunda har kishin aikin ka be hanaka ɓoye laifin
Abokin ka ba"
Abbas ya miƙe ya sarawa Suleiman sannan ya fice.
Koda ya bar Office ɗin Suleiman Office ɗinsa ya koma yana tunani, tunani yake
akanme zeyi wanda zesa gaba ɗaya aikin da Yusuf yayi ya lalace kowa ma ya huta?
************************************
Gaba ɗaya Nurat ta rasa abunda yake mata daɗi, ta shiga damuwa rashin samun wayar
mutumin da ko sunansa bata sani ba, dama Widad ta dena ɗaga wayarta gaba ɗaya, tun
ranar da tazo birthday ɗin ta, abun nan ya faru, ta fara shawarar ko gidan su Widad
zata je don ta tambaye ta wannan wanda suka zo taren. Sedai kuma tayi wani tunani,
aiki ne me matuƙar sauƙi a gurin Widad ta sa aka mata a ɗaure, bata da tabbacin
Abokinta ya gayawa Widad abunda ya faru kokuma A'a, gaba ɗaya ta rasa abunda yake
mata daɗi, komai ya dena mata daɗi se tunanin wannan bawan Allah, me matuƙar kirki,
a farko tayi zaton shima mugu ne lokacin da ya ritsata har yayi mata barazana, amma
yanzu ta gane ba haka abun yake ba, ranar da yazo gidan yanayin yadda ya
mu'analance ta da kyakkyawar ma'amala.
************************************.
Fahad ne da Anwar tsaye a tashar jirgin Sama, Anwar yace "Fahad ina taya ka murnar
kammala karatun ka, Allah ubangiji ya kaika gida lafiya, sena taho nima in next
couple of weeks Insha Allah"
Fahad yayi murmushi yace "to baban Soyayya, kaima ina taya ka murna, tsiran namu
befi sati biyu, ina maka fatan Nasara ɗan uwana seka taho".
Suka rungume juna suna murmushi, sannan Fahad yaja trolley ɗinsa yayi gaba.
"Amal kin san wani abu kuwa? Munyi waya da Yaya Anwar yace min Fahad yau ze dawo
Nigeria, baki ji daɗin da nake ji ba, dan Allah me ya kamata inyi wanda zan sake
kama zuciyar sa, yaji in ba niba se rijiya"
Wani banzan kallo Amal tayi wa Ramlah tace "Ban sani ba, kije kiyi abunda kika ga
ya dace"
Cike da mamaki Ramlah tace "lafiyar ki kuwa? Me yayi zafi daga neman shawara zaki
hayayyaƙomin?"
"dole kice haka mana, da yake matsalarki itace damuwa kawai, ni ina lokacin da nake
cikin tawa damuwar ziga Mummy kikeyi, kuka haɗemin kai kuka dinga hantara ta, har
dena kulani kukayi saboda kawai nace ina son Yusuf, Ashe ke kaɗai kika san So, ni
ban sanshi ba ko? Can ta mulmule miki gara tun wuri kema ki cire shi daga ranki,
dan in kin manta bari in tuna miki, 'yar masu gida akace ze aura kuma kinsan baki
isa kice kina da matsala da hakan ba, danke ba mutum bace a kanta, kuma kinsan baki
isa kiyi takara da ita ba, akan haka ba' aƙi a baki red card daga gidan nan ba, you
better go back to your senses "
Tana gama faɗin haka ta miƙe ta fice daga ɗakin, wani zazzafan gumi ne ya shiga
karyowa Ramla, dan gaba ɗaya ta manta ds batun ance za'a haɗa Auren Widad da Fahad.
Gaba ɗaya kanta ys kulle dan bata san wama yakamata ta tunkara ba, Mummy ba abunda
zata iyayi, shiru tayi tana tunanin meye mafita? "
************************************
Widad ta dudduba Aiken da Yusuf ya kawo mata, ya siyo komai kamar yadda tace, harda
receipt ya kawo mata, tana duddubawa taci karo da wata leda, ɗakko ledar tayi ta
buɗe me zata gani, wasu tsala tsalan Abaya ne kala biyar, kowacce da kalar ta
sunsha stones se ƙyalli sukeyi, ta ɗauka ɗaya bayan ɗaya tana jujjuya su. 'me
wannan gayen yake nufi?' ta tambayi kanta
'harni ze saiwa kaya ya bani? Meya maida ni ko nayi masa kalar saka wannan kayan?'
Tattare kayan tayi ta fito falo a fusace, da watsasu akan kujera, part ɗin su Amal
ta nufa tana huci, babu ko sallama ta banka ɗakin su Amal, gaba ɗaya seda suka
razana, mussman Amal dan a tsorace take tun ranar da Widad ta gansu tare da Yusuf.
Ta kalli Amal tace "Kije bakin gate, ki kiramin wancan sakaran direban yanzun nan"
tana gama maganar ta juya ta fice
Ramalh na ganin a yadda Widad ta shigo tayi magana, tasan akwai matsala dan haka ta
miƙe ta fita dan ganin me ze faru, Jikin Amal na rawa ta miƙe tayi waje kiran
Yusuf.
Koda saƙon Kiran Widad ya riski Yusuf yasan a rina, yasan ze fuskanci wulaƙanci,
Amma ya dake ya shiga cikin gidan.
A falo ya tarar da ita a tsaye, tana wani irin huci, haɗi da sauke numfashi, Tabbas
Widad Yarinya ce ƙarama Amma Allah yayi mata kwarjini na musamman.
Yaje daf da ita ya tsaya ya sunkuyar da kai ba tare da yace komai ba.
"Kalleni nan"
A hankali ya ɗaga idonsa yasa a nata, dukda bugawar da ƙirjin Widad yayi be hanata
cewa "Nayi maka kama da matsiyaciya ko me neman temako?"
Kallon ta yayi bece komai baCikin tsawa tace "magana nake maka"
"temako ana yinsa ga kowa, duba da rayuwar gaba ɗaya taimakon juna mukeyi, dan haka
ba fuska ake gane...
" Shut up!!! "Tai maganar tare da ɗaga masa hannu
"waye kai? Me kake da shi? Me kake taƙama dashi wanda har yasa kake ganin kana da
abunda zaka ɗauka ka bani? Me kake da shi? Ni zaka bawa wannan banzayen Abubuwan na
maka kama da wadda zata saka wannan tarkacen, shara? Ka taɓa ganin na saka irin
wannan kayan? Ko na ce maka ina da buƙatar su? "
Te Ɗebo kayan dake kan kujera ta watsa masa a fuskar sa tace " don't you ever try
to make this mistake again, ka nemi mabuƙata ka basu Widad tafi ƙarfin saka wannan
tsumman"
Idon Yusuf jawur ya ɗago ya kafe ta da ido, ko ƙyaftawa baya yi, dukda hucin da
take hakan be hana ta tsayawa tana kallon sa ba itama.
Ba zato ba tsammani suka ga Daddy ya ƙaraso cikin falon, ya durƙusa ya tsince
rigunan, yazo gaban Yusuf ya kamo hannun Yusuf yasa nasa yace"Yusuf wannan kyautar
ni kayi wa, ba Widad ba, lokacin da zanyi tafiya ka kawo alheri ka bani kace in
ƙara a guzuri, kuma ka nemi da kar in gayawa kowa, yanzu ma ka ɗakko kyauta ka bawa
'yata ɗiya tilo da nafiso, Tunda Allah yayi min Arziki babu wanda ya taɓa ɗaukar
alherin naira biyar ya bani, saboda kowa gani yake ni me wadata ne bana buƙata,
sedai ma kullum a nema a gurina, idan kuwa kaga anmin kyauta to wani abu ake nema a
gurina, Mutum na farko da yayi min kyauta har sau biyu kuma saboda Allah, nagode
sosai Yusuf, nasan kana haƙuri Amma ka ƙara zaka ga ribar sa, Widad ta gode da
wannan kyautar"
Tabbas ba dan Alhaji Nasir ba, ko duniya yake samu a gidan nan baze sake zuwa ba,
da babu abunda ze hana ya miƙa file ɗin aikin a ɗora wani dan ya gaji.
Yusuf bece komai ba, ya jinjinawa Alhaji Nasir kai ya fice, zuciyar sa na ƙuna dan
gaba ɗaya jijiyoyin kansa sun miƙe saboda ɓacin rai.
Alhaji Nasir yayi wa Widad wani irin kallo, ya wuce part ɗinsa da kayan a hannun
sa.Se a lokacin ta sha jinin jikin ta, bin bayan Daddy tayi da sauri zuwa part
ɗinsa.
Ramla tace "Allah ya ƙara, maganin me shishshigi kenan, da haka da haka wataran
zata sallameshi kowa ya huta"
Amal tace "kema kiji da abunda ke damunki mana, aikin banza kawai"
A ɗaki Widad ta riski Mahaifinta, tace "Daddy are you angry?"
Shiru yayi mata yana ƙoƙarin ninke rigunan.
"Daddy am talking to you, why will you be angry? Am I wrong?"
Shiru ya kuma yi bece mata komai ba.
"Daddy magana fa nake maka"
"Me kike so ince miki Widad? Yaron nan yana matuƙar ƙoƙari da haƙurin zama dake,
Amma kalli yadda kike treating ɗinsa, yana miki biyayya yadda ya kamata amma bakya
gani, can you remember when last someone offer you a gift, for the sake of God?
Meye laifin sa dan ya baki wannan kayan, irin wannan rigunan Amminki take sakawa,
sunfi mutunci akan wanda ke kike sakawa, bana son takuramiki saboda yanayin halin
da kike ciki, Amma ba kya tausayin kanki, meye aibu da wanda yake ƙasan ka ya baka
kyauta, dukda muzguna masa da kike da wulaƙanci amma ya miki alheri, meyasa zaki
Wulaƙanta shi, Widad ko baki yadda da abunda na gaya miki kwanaki ba? "
Shiri tayi tana nazarin maganganun Mahaifinta.
"baki ga yadda ya fita ransa a ɓace ba? Baki kyauta ba sam"
"to yanzu ni me kake so inyi?"
"ki karɓi wannan kayan kiyi amfani da su"
"Over my death body, gaskiya Daddy bazan iya saka wannan kayan ba"
Daddy ya jinjina kai yace "As you wish, zanje ganin likita gobe in Allah ya kaimu,
sannan baƙonki yana nan zuwa da weekends ɗin nan"
"Waye baƙona kuma?"
"Fahad, mijin da zaki aura!!!"
Widad ji tayi tamkar Daddy ya watsa mata wuta me matuƙar zafi.
(MASHA ALLAH NA KAMMALA JARRABAWA ALHAMDILILLAH, INA GODIYA DA ADDU'OINKU NAJI DAƊI
NAGODE SOSAI NA GAMA JARRABAWA YAU ALHAMDILILLAH)
Domin gyara sharhi ko shawara feel free to contact me Ayshercool07063065680
_*AƘIDATA*_
PERFECT WRITERS ASSOCIATION
(WE AIN'T PERFECT BUT WE ARE ALWAYS TRYING OUR BEST, TO MOTIVATE AND ENTERTAIN OUR
READERS)
https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/
P. W. A
*Story and written by*
_*AISHA HUMAIRA (Daddy's girl)*_
The experience writer of *ABDUL JALAL** WATA KISSAR.... (SAI MATA) *And now *AƘIDA
TA *
I dedicated this book to my Mum (Malama Nafisat Adam Muhammad) i love you mum
Haƙƙin Mallaka ⚠ : Littafin nan mallaki nane, tun daga sunan labarin zuwa abunda ya
ƙunsa, ban yadda wani ko wata ya sauyamin ko yin Amfani da wani ɓangare na labarin
ba ba tare da izinina ba, Nagode
https://www.wattpad.com/user/Ayshercool7724?
utm_source=android&utm_medium=link&utm_campaign=invitefriends
ELEGANT ONLINE WRITER'S
PART1 Page 16_17
(Ayimin afuwa jiya nayi mistake ɗin pages)
Ko kallon inda Daddy yake bata kuma yiba ta fice ta bar masa ɗakin.
Komawa ɗakinta tayi, tana jin yadda zuciyarta ke wani irin bugu kamar zata fasa
ƙirjinta ta fito 'kenan har yanzu Daddy be janye maganar nan ba? Daddy why?' Tayi
maganar da ƙarfi, tana sauke numfashi a hankali ta zube a ƙasan carfet, gaba ɗaya
kanta ya kulle ta rasa abunyi, tabbas wannan karon Daddy dagaske yake, idan kuwa
har Daddy ya dage a wannan ƙudurin nasa to tabbas zata bijre, koma hakan yayi
sanadiyyar ya rasa ta gaba ɗaya, kuma seta shata babban layi tsakanin ta da Bulama.
Ramla tunani take me zata yi wanda zesa a janye maganar Widad da Fahad, ya za'ayi
mutumin data daɗe tana tararirayar soyayyar sa lokaci ɗaya a wargaza mata komai,
sam hakan bame yuwuwa bane, dole tasan abunyi dan yiwa wannan tufkar hanci.
************************************
Kallo ɗaya zakayi wa iyalan kasan suna cikin farin ciki, gaba ɗaya sun hallara a
katafaren falon gabansu shaƙe da nau'ikan Abinci kala kala, kowanne fuskarsa ɗauke
da farinciki.
Ramadan yace "Wallahi broz Fahad gaba ɗaya kaima ka zama kamar Bature, kaga yadda
skin ɗinka tayi fresh kamar wani jariri"
Alhaji Bulama yace "Wannan Ƙaton ne fatarsa kamar jariri, kai dai Ramadan ka fiye
shiririta"
Hajiya Sarah tace "Haba Daddy, ka kalli yadda ya wani murje yayi ƙalau dashi"
Iman tace "Nikam banga abunda ya canza ba sedai yayi haske ya ƙaro iyayi, ko
hausarma bata fita sosai se kace Widad"
Ɗan ɓata fuska Hajiya Sarah tayi jin an ambaci Widad.
Alhaji Bulama yace "se suje can su cigaba da gwarancinsu"
Sam Fahad be fahimci abunda mahaifinsa yake nufi ba, haka suka ci gaba da ciye
ciyensu suna hira cike da ƙaunar juna.
Yusuf kuwa tunda ya baro falon nan ransa a ɓace kai tsaye gida ya wuce, zuciyar sa
nata faman tafasa, tabbas ƙarshen wulaƙanci yau Widad tayi masa, banda dalilin
aikin sa da kuma mutuncin mahaifinta da baze sake komawa gidan ba.
Nurat bata da aiki se tunanin Yusuf, ko bacci ta kwanta mafarkinsa take, gaba ɗaya
zuciyar ta ta kasa samun nutsuwa, ta kira lambar Yusuf harta gaji, ta koma kiran ta
Widad, amma itama bata tafiya, abun duniya duk ya ishe ta.
Tana zaune tana wannan zaman tunanin mahaifinta ya shigo ɗakin ta, da sauri ta miƙe
daga kwanciyar da take. Ya kalle ta yace "ke meya ke damun ki ne?" Girgiza masa kai
tayi tace "bakomai Daddy" "to naga Maman ki bata nan, gobe in Allah ya kaimu zamuyi
baƙi ki gaya mata, za'ayi mana girki bana son na masu aiki fa"
"To zan gaya mata insha Allah"
"shikenan sena dawo" "Adawo lafiya Daddy" "Allah yasa"
Gaba ɗaya ɓacin rai ya hana Yusuf bacci, kamar shi dukda yasan ba wata uwace da shi
ba amma Widad ta dinga gaya masa wannan baƙaƙen maganganun gaskiya idan ya ƙyaleta
tabbas taci bulus. Tunani ya shiga yi me ze mata wanda ze nuna mata mahimmancin ɗan
Adam. Da ƙyar bacci ya ɗauke shi cike da ɓacin rai.
Da gari ya waye so yayi yaje gurin aiki amma ya fasa, yayi zamansa a gida se bayan
azahar sannan yaje gidan.
Nura da Isa se wani kallon banza suke masa, Yusuf bashi da lokacin su dan haka bebi
ta kansu ba.
Be daɗe da zuwa ba Alhaji Nasir ya fito, yana ganinsa kamar babu abunda ya faru
Yusuf ya miƙe ya nufi inda yake. Cike da girmamawa kamar kullum suka gaisa, Alhaji
Nasir yace "Yusuf kaga yau ma tafiya ta kamani, kar a gaji dani dai ga Amanar tilon
'yata nan, Fahad zezo gurin ta a satin nan Insha Allah, dan Allah a samin ido akan
ta, sannan ka cigaba da haƙuri"
Yusuf yace "Insha Allah, Allah ya kaika lafiya ya dawo da kai lafiya"
"Ameen Yusuf"
Ya shiga mota, Nura yaja suka fita.
Larai me aiki ce ta fito ta samu Yusuf tace "kaje inji 'yar masu gida"
Yusuf yace "Ina zuwa"
Yai zaman sa kamar bashi akace ana kira ba, Isa yace "da alama Yusuf ka raina
Yarinyar nan, badan kaine ba akwai wanda ya isa yayi mata haka ta ƙyaleshi, turowa
fa tayi tana kiran ka, amma ka basar kana shagalinka"
Ko gezau Yusuf beyi ba, balle Ya nuna yasan me Isa yake faɗa.
Isa yace "da kai fa nake magana"
Still be tanka masa ba, Isa yace "eh da alama kaima ta koya maka baƙin halin, kadai
bi a hankali tunda kaima ɗan uwa talaka ne, inka ɗau wannan rayuwar ba inda zata
kaika"
Yusuf be kula shi ba ya miƙe ya bar gurin.
Yusuf na tafiya sega Abbas yazo, Isa na ganin shi ya washe baki yace "Sani dama
kana nan? Kwata kwata wayarka ta dena shiga"
"ina nan wallahi, na koma ƙauye ne, ya kake ya aikin?"
"Alhamdilillah, ya ka baro mutan gidan?"
"Lafiya ƙalau Alhamdilillah, ina Yusuf kuwa?" Isa ya taɓa baki yace "Yana nan
yanzun nan ya shiga cikin gida, gimbiyar masu gida tana kiransa" "Allah sarki, ina
fatan yana aikin sa babu matsala?" "Eh to yana yi, se shishshigi da zaƙewa, yaga ya
samu gurin zama a gurin masu gidan, shine yake ta Wulaƙanta mu gamu gashi amma se
yaga dama ze kula mu"
"Hmm ni kaina wannan baƙin halin nasa yana ƙular dani, dama haka yake se kunyi a
hankali wasu lokutan bashi da kirki sam wallahi".
Yusuf seda ya ɗan tsorata, ganin Widad ta rame daga jiya zuwa yau, idanunta a
kumbure da alama kuka tayi sosai, gaba ɗaya se yaji tausayin ta ya kama shi.
"Gurin Bulama zaka kaini yanzun nan"
Jinjina mata kai yayi, ta miƙa masa jakarta ya karɓa sannan suka fito.
Tunda suka fito Abbas ya ƙura musu ido, se kace mata da miji, tabbas Yusuf ya samu
gindin zama yadda yakamata a gidan nan.
Yusuf na ganin Abbas tun daga nesa ya fara murmushi, suna isowa inda su Abbas suke
kafin Yusuf yayi magana, Widad ta ƙurawa Abbas ido, shikansa Abbas seda yasha jinin
jikin sa.
"Waye wannan?" Widad ta tambayi Isa megadi"
Cikin inda inda Isa yace "Amm... Am. Dama abokina ne, kuma shine wanda ya kawo
Yusuf aiki a gidan nan, ina tunanin ma ɗan uwansa ne"
"Kar in ƙara ganin sa a gidan nan, ko a harabar area nan na sake ganinsa zan ɗau
matakin da ya dace"
Binta sukayi da kallo, inda sabo Yusuf ya saba da wannan halin nata, dan haja
yayiwa Abbas Alama da zasu yi waya.
Abbas ya miƙe cikin mamaki ya bar gidan.
Yusuf dama beyi zaton zata gaya masa dalilin ta na korar Abbas ba, amma abun ya
bashi mamaki, seya barshi a matsayin kawai duk cikin hakinta ne na rashin yarda da
mutane.
Koda suka iso gidan Bulama, kafin su shiga megadi ya sanar dasu cewar Bulama da shi
da iyalansa basa nan sun fita.
Haka Yusuf ya juya akalar motar suka koma gida.
Abbas ba ƙaramin mamaki yayi ba, yaga dai farkon zuwansa gidan daya kawo Yusuf tare
suka je, amma yau ta nuna bata sanshi ba wai kar ya ƙara, zuwa gidan.
Kai tsaye Abbas ya ɗakko wayarsa ya kira layin Saleh.
"Hello Saleh kana ina ne?"
"ina gidan gona bakin aiki, meyafaru?"
"ina son ganinka ne"
"ka bari zanzo in same ka a gidanka, karka zo nan babu security"
"shikenan sekazo"
Yusuf Alla Alla yake ya kai Widad gida ya tafi gurin Abbas.
Seda suka je gida yay parking, Widad ta kalle shi tace "Karka bar gidan nan se
bayan sallar isha'i"
"Saboda me?" ya tambaye ta
Bata bashi Amsa ba ta fice daga motar ta barshi a gurin, ba ƙaramin haushi yaji ba,
yasan dai duk abu ba wani gurin ze kuma kaita ba, Amma tace baze tafi ba, da
niyyarsa yayi tafiyar sa amma se ya fasa, haka ya cigaba da zama har se lokacin da
tace ya tafi.
Saleh ne zaune shida Abbas a wani ɗan madaidaicin falo, Saleh yace"Neman me kake
min ne haka?"
Abbas yace "dole in neme ka ai, Yusuf se alheri yake samu a wannan aikin da yake,
ta sakarmasa kuɗi kawai take sakarmasa, seda nayi dana sanin rashin yin aikin nan
da kaina"
Saleh yai murmushi yace "tabbas Widad akwai kyauta ta ban mamaki, Sedai kasan aikin
da yake a rayuwar sa a hatsari take ko?"
"Nasani amma babban abunda ya ɗauremin kai shine yau naje gidan gurin sa, Amma tana
ganina tace kar in ƙara zuwa ko area gidan"
"zata aikata saboda bata da yadda sam, dan haka bata son baƙuwar fuska, gani take
kowa ma cutar da ita zeyi, yanzu ya ake ciki game da binciken da yake yi, naga
alamar yaron yasan aikin sa, duk yadda kaso ka daki cikin sa ba ze gaya maka komai
ba, na jarraba shi rannan da suka zo tare, Amma naga yana da wayo "
Abbas yace " Hmmm, aiki kam yasan kan aikin sa sosai, dan ina tabbatar maka da yana
aikin yadda ya kamata yana tattara abubuwa masu mahimmanci sedai har yanzu ban san
meye sakamakon binciken nasa ba"
Saleh ya numfasa yace "yanzu abunda nake so da kai shine, ka kawomin rahoton duk
binciken da yayi, ka kawomin file ɗin zan miƙa shi ga wannan mutanen dan su
sakarmin ɗan uwana dan ina zargin su suka yi poisoning ɗinsa yake kwance ba lafiya"
Abbas yace "yana na'aikaci ina ma'aikaci tayaya kake tunanin ze yadda ya bani
kundin binciken sa?"
"wannan ya rage naka kuma Abbas, ni na gama magana kuma ka saka ido ka cigaba da
bibiyar sa dan jin yanayin kusancinsa da ita"
"Shikenan zanyi iya abunda zan iya, Insha Allah zan kawo maka abunda ka buƙata.
Ba ƙaramin haushi Yusuf yaji ba da Widad ta hana shi tafiya da wuri, dan haka se
bayan isha'i sannan ya tafi gida, bayan yaje gida yaci Abinci yana shirin kwanciya
message ya shigo wayarsa
"HAR YANZU MUNA SANE DA KAI, KUMA ZAMU CIGABA DA BIBIYAR KA HAR SEKA BAMU ABUNDA
MUKE SO A HANNUN WIDAD"
Tsaki Yusuf yayai ya ɗanyi shiru yana tunanin wai wani abubne wannan haka da'ake
son karɓa a gurin Widad, da har ake masa barazana haka? Ganin bashi da amsa yasa
yai kwanciyarsa.
************************************"Fahad kasan meyasa na kiraka muyi magana a
daidai wannan lokacin?"
Fahad ya girgiza kai yace "a'a Daddy"
Bulama yace "Yawwa, na yanke wani hukunci ne kafin ka dawo, shine nake so ka baani
aron hankalin ka da kunnuwan ka da kyau ka saurareni"
"To Daddy ina jinka"
"Kasan Widad ai ko? 'yar gidan Alhaji Nasir daula"?
"Eh Daddy nasani"
"Kasan alaƙar dake tsakanina da mahaifinta ko?"
"Nasani Daddy" Fahad ya bashi amsa
"Masha Allah, Kasancewar ka yaro me biyayya shiyasa na yanke wani hukunci wanda
nasan ba zaka bijiremin ba Insha Allah"
"Ina jinka Daddy".
"Kamar yadda kasani, yarinyar nan ta gamu da larurar Ƙwaƙwalwa, ta ɗau wata AƘIDA
da wata irin rayuwa ta nayi, ta zaɓi rayuwar kaɗaici wanda hakan ke barazana ga
lafiyar ƙwaƙwalrwata, shine muka yabke hukuncin yi mata Aure nida mahaifinta, koda
Allah zesa a dace a samo kan hankalin ta"
Fahad yace "to ai Daddy ni banga meye nawa a ciki ba"
"Fahad kai muka yanke shawarar zaka auri Widad"
A razane Fahad ya kalli Mahaifinsa yace "Kamar ya ni Daddy, kawai se in auri
mahaukaciya kaifa kace bata da hankali ta yaya zan Aure ta?"
"ta yadda na gaya maka mana, aiba hauka take tuburan ba se lokaci lokaci yake
tashi, dan haka umarni nake baka ba shawara ba, idan bamu haɗu an temaki yarinyar
nan ba waze aure ta da wannan larurar?"
"Amma Daddy a rasa wanda za'a bawa seni? Ina da wadda nake so meyasa za'amin haka?
Ta yaya za'a yanke min hukuncin yarinyar da zan aura ba tare da izinina ba"
Cikin tsawa Bulama yace "rufemin baki, na gaya maka wannan umarnina ne, kuma dole
kabi gobe in Allah ya kaimu zakaje ku gaisa da ita, kuma wallahi naji wani abu daga
gareka wanda be gamshe ni ba, kasan halina sakarai kawai"
A hasale Fahad ya tashi ya bar falon mahaifinsa, ɗakin mahaifiyarsa ya tafi yana
kumbura fuska.
"lafiya ka shigomin ɗaki ba ko sallama kana ta haɗe rai kamar tsohon raƙumi?"
"Mumsy kina gidan nan, kina raye za'ayi min Auren dole? Kamarni ta yaya za'a
auramin mahaukaciya?"
Ajiyar zuciya tayi tace "Fahad this is out of my control, I did my best to destroy
this matter but is beyond my control, ba yadda banyi da mahaifinka ba amma fafur
yaƙi, ya zanyi sedai kayi haƙuri"
"Au Hakama zaki ce? Wallahi se yarinyar nan tayi dana sanin Aure na, sena mata
wulaƙancin daba'a taɓa yi mata ba se naci mutuncin ta, zata gane kuskurenta"
"Kai Fahad ka shiga hankalin ka, 'yar gidan Daula ce fa, ita zaka ciwa mutuncin?
Amma kasan me ci mata mutunci ke nufi ko?"
"ko' yar gidan bushashace ba Daula ba ba ruwana wallahi"
"shikenan kaje kayi abunda ka ga dama kaida ubanka ba me ɗagamin hankali wallahi"
Fuuuu Fahad ya fice ya bar ɗakin yana tsaki
Da safe Yusuf yanata shiri, dan yau gurin aiki yake son zuwa dole yana son ganin
Yallaɓai Suleiman, Amma message ya shigo wayar sa.
"ka tabattar ƙarfe takwas tayi maka a gidanmu, zakamin aiki yau"
Yana ganin message ɗin yasan daga Widad ne, haushi ne ya kama shi gaba ɗaya bashi
da lokacin kansa sena wannan fitsararriyar yarinyar.
Haka ya shirya a gaggauce ya tafi gidansu Widad, mutan gidan ko tashi daga bacci
basu yi ba, tsabar takura irin ta Widad da son nuna isarra yasa take masa wannan
ikon.
Wani ɗan ƙaramin lambu dake gidan Yusuf ya tafi yai zaman sa, yana kallon shuke
shuke da tsuntsayen dake gurin.
Jin tsayuwar mutum yayi a bayan sa dan haka da sauri ya juyo.Amal ce tsaye a bakin
lambun tana ƙare masa kallo "barka da Safiya Yusuf"
"Yawwa barka" ya faɗa a taƙaice
"Yusuf wai ya naga kana wani baya baya dani? Dan Allah kayi haƙuri da abunda ya
faru, wallahi ina matuƙar kishin ka ne"
"Amal dan Allah kiyi haƙuri, ni bana son abunda zesa ki jamin matsala, ki ƙyaleni
dan Allah"
"Idan kaga na ƙyaleka to tabbas ɗayan mu ruhinsa ya rabu da gangar jikinsa, ni
matsala duk girmanta duk ƙanƙantar ta bana gudun ta, indai akan biyan buƙata tane,
kalleni Yusuf me na rasa? Wace tawaye Allah yayimin da ban kai ka kalleni ka karɓi
soyayya ta ba, kana ganin irin mazan da suke sintiri a gidan nan da sunan suna
sona, Amma na ajiye class ɗina na ajesu a gefe nace kai nake so, me zesa kace baka
sona"
"Saboda bana Soyayya, bata gabana babu ita a tsarina, dan Allah ki ƙyaleni"
"ƙarya kake Yusuf kana Soyayya, koma baka yi zaka fara a kaina bazan taɓa ƙyaleka
ba, zan cigaba da bibiyar ka sena hanaka jin daɗi muddin baka amince da soyayya ta
ba "
"Masoyiyar gaskiya ba zata taɓa faɗar haka ba, ke ba abun yadda bace dan haka bazan
taɓa yadda da wannan shirmen ba"
"Yusuf ko nawa kake so zan mallaka maka, in har zaka yadda ka karɓi soyayya ta"
"Shi son gaskiya tsada ne dashi, kuɗi komai yawan su basa siyansa, dan haka Allah
be baki arziƙin da zaki siyi soyayya a gurin Yusuf ba"
Yana gama maganar ya juya ya fice daga lambun yana mamakin wannan naci irin na
Amal.
************************************Ramla ce kwance hannunta riƙe da waya tana
magana a hankali cikin iyayi
"Abun ƙauna ta, yau kwananka huɗu da dawowa Nigeria, yakamata ace kazo na ganka fa,
Allah badan inajin nauyi ba da tuni ni zanzo inda kake in ganka"
Daga can ɓangaren Fahad yace "Am Sorry beb, ina cikin damuwa ne gidan naku ne gaba
ɗaya bana son zuwa, Ramla wai Daddy ze haɗani Aure da wata mahaukaciya a gidan ku,
Ramlah kamarni za'ayiwa Auren dole? Auren ma da mahaukaciya, kuma Daddy se masifa
yake wai se nazo mun gaisa da ita"
"Fahad nasan maganar nan tun kafin ka dawo, ban gaya maka ba saboda bana son ɓacin
ranka, Amma ina cikin damuwa Fahad you know I love you" tai maganar cikin damuwa
"easy baby, ki kwantar da hankalinki, idan nazo se nayiwa yarinyar nan rashin
mutunci, ni bazan aure ta ba dan ba sonta nake ba, bazan taɓa yadda da Auren nan
ba, naga Daddy ya fara fushi, in anjima zan shigo gidan naku in ganta, Amma ni ke
zanzo gani Beb"
Murmushi tayi tace "Ohh my God, amma naji daɗi Fahad seka zo".
Ta kashe wayar tare da yin wani tsallen murna.
************************************
Se ƙarfe sha ɗaya na safe tayi miƙa, ta farka daga nannauyan baccin da take, ta
sakko daga kan gadonta magen ta yana biye da ita.Corridor ɗin ɗakin ta tabi wanda
ze sada ta da barandar benen, miƙa ta sake yi tana ambaton sunan Allah tare da
shaƙar sassanyar isakar dake kaɗawa, haka nan take jin wai irin nishaɗi da bata san
dalilin jinsa ba, tsyawa tayi tana kallon komai dake harabar gidan.
Yusuf ji yayi kamar ana kallon sa dan haka ya ɗaga kansa sama, ai kuwa karaf
idanunsa suka sauka a cikin nata, alama tayi masa da hannu ya zo, dan haka ya miƙe
ya tafi.
Dukda yana jin haushin abunda tayi masa akan kayan daya bata, amma yau yaga
fuskarta ba yabo ba fallasa haka nan yaji hakan yayi masa daɗi.A ɗakinta ya sameta,
tana tsaye a gaban madubi ta janyo drower mudubin tana ƙoƙarin ɗakko wani abu.
Idan kunnuwan ta ba ƙarya suke gaya mata ba tabbas Yusuf cewa yayi "Good morning
daughter" kamar yadda Daddyn ta yakan faɗa, shiru tayi ta cigaba da duba abunda
take nema tsawon wasu daƙiƙu, sannan ta ɗago ta kalle shi tace "Roux taƙi cin komai
tun jiya, na rasa meke damunta na bata Madara taƙi sha, ka siyo mata ko cabin ne,
in gani in zata ci ban san me yake damunta ba" (wato magenta)
Haushi ne ya kama Yusuf, saboda tsabar wulaƙanci mage ze fita siyowa Abinci.Bece
komai ba ya juya ya fita yana ƙoƙarin ɓoye jin haushin sa.
Yana tafiya ya tuna da Message ɗin da'aka turomasa da daddare dan haka ya samu guri
ya kira Oga Suleiman.
Bayan sun gaisa Yusuf yace "Yallaɓai na so in shigo yau in nuna maka report ɗina
amma abu ya gagara, Wannan rigimammiyar ta kasa ta tsare ban samu na shigo ba"
Suleiman yace "Aikam dan har na fara ƙorafin, yanzu me ake ciki?"
"Yallaɓai akwai abubuwa na ban mamaki a binciken nan, zan turomaka report ɗin ta
Email ɗinka ka duba, Yallaɓai case ɗin akwai sa hannun mutanen dan ban zata ba,
sannan karo na biyu ana min barazana wanda ya ƙara tabattar da tabbas ana bibiyar
yarinyar nan ana son karɓar wani abu a hannunta wanda ni kaina ban san menene ba"
"Masha Allah, har kayi aiki haka Yusuf? Ka turo zan duba in Allah ya yadda inda
yuwuwa zan miƙa report ɗin naka gaba, nasan zaka iya dama bazan can zaka daga kan
aikin ba"
"Yallaɓai da karɓar aikin za kayi?"
"karka damu da wannan, ka turomin zan duba dan daga sama ana tambaya ta ina muka
tsaya a binciken?"
Yusuf yace "Amma Yallaɓai wai wa yasa ayi wannan aikin ne? Waye yace ayi binciken?"
"Yusuf nima ban saniba, daga sama aka bada order ayi wannan aikin"
"Yallaɓai ya kamata kasan gawa zaka bada aikin, dan abun akwai sarƙaƙiya"
"Karka damu Yusuf, komai ze tafi daidai insha Allah, kamar yadda kace ana maka
barazana, duk lokacin da ka buƙaci temako kayi magana, sannan ka kasance cikin
shiri ka dinga yawo da makaminka""Ina lura sosai Yallaɓai, Allah yayi mana jagora
gaba ɗaya"
"Ameen Yusuf Allah ya tsare"
Yusuf seda ya tsaya ya turawa Suleiman aikin sannan ya tafi.
Koda Yusuf ya dawo daga aiken yiwa mage siyayya, ya tarar da uwar ɗakinsa ta fito
daga wanka, pink ɗin rigar wanka ce a jikin ta, ta naɗe gashin kanta da towel shima
pink.
Zare towel ɗin dake kanta tayi, gashin ta ya zuba a kan kafaɗunta, Satar kallon ta
Yusuf yake, tabbas Allah yayi mata halitta mekyau, tana da kyau sosai ga dogon
gashi, Yarinya ce sedai izza da gadara, tana kallon Ya dawo amma taƙi kula shi.
Wani ƙaramin plate ta ɗakko ta miƙawa Yusuf tace "ka sa mata cabin ɗin anan, ga
madara ka haɗa mata dashi"
Yusuf yai shiru yana sauraren ikon Allah, yanaji yana gani aka sashi haɗawa mage
Abinci.
Still dai magen bataci ba se kwanciya da take.
Cike da damuwa Widad ta kalli Yusuf tace "taƙi cin wannan ma, inaga bata da lafiya
idan akwai wani private veterinary se mu kaita" ta faɗa cike da damuwa tana sake
shafa magen, hakan ya ƙara fito da tsantsar yarintar ta.
"waye ze buɗewa wani private veterinary? Babu wani private veterinary dana sani
nidai, yunwa take ji kawai bata ƙoshi ne"
"kamarya? Ina bata Abinci sosai fa"
"Ai kema ba Abinci kike ciba balle magen, kullum abu ɗaya ai dole ta gaji ta dena
ci"
Cikin damuwa tace "to me zan dinga bata?"
"Abinci me nauyi na hausawa, amma kullum daga popcorn se madara ai dole ta mutu" Da
sauri ta kalli Yusuf tana girgiza kai tace "A'a ni bana so ta mutu ina sonta fa"
Gaba ɗaya yau Yusuf cike yake da mamakin yadda take masa magana cikin nutsuwa ba
izza, yasan kuma saboda magen ne, dan ya lura tana tausayin dabbobi fiye da yadda
take tausayin ɗan Adam, tana matuƙar ƙaunar dabbobi Yusuf a ransa yace "ta wani
fannin rayuwar turai ba tayi ba"
"to muke rasa 'yan uwanmu mutane ma balle dabba, idan ta mutu seki ɗakko wata"
"Ni nafison wannan gaskiya, tun ire iren magunan Ammi ne, idan ta mutu zan shiga
damuwa"
Shiru yayi yana kallon Widad data sunkuyar da kanta tana shafa jikin magen, magen
tayi lamo a jikinta, gashin kanta har rufe mata fuska yake, Yusuf yana mamakin
wannan dogon gashin na kan Widad dan har yanzu yana tantama idan nata ne.
A hankali ya matso daf da ita ya shafa jikin magen dake hannun ta yace "Allah ya
bata lafiya, don't worry Madam zata warke Insha Allah"
Widad ta jinjina kai, tare da jin ƙaruwar bugun zuciyar ta kasancewar yadda suke
daf da juna, ta ɗago idonta ta kalle shi tace "da ina so mu fita zanje Saloon, Amma
zan zauna inga yadda jikin nata ze kasance ko zuwa yamma ne semu tafi"
Yusuf ya ɗan ƙura mata ido sannan a hankali yace "As you wish your majesty" ji tayi
tsigar jikin ta tashi, wanda ta rasa dalilin jin hakan, haɗe rai tayi tace "karka
sake ka fita kaje ko'ina idan ba nina baka izini ba, ka zauna zuwa la'asar insha
Allah zamu fita" Murmushi yayi mata tare da ɗan duƙawa cikin girmamawa yace
"Considered it done Gimbiyar Daddy"
Ya yunƙura ze miƙe Amal ta shigo hannun ta ɗauke da waya, turus tayi tana binsu da
kallo, yayin da taji wani abu tundaga ƙafarta zuwa ƙirjinta ya to kare mata wuya.
Da ƙyar ta miƙawa Widad waya tace "gashi Daddy zeyi magana dake" Widad bata kalle
ta ba, bata bata amsa ba ta kalli Yusuf tace "bani wayata akan mirror"Amal bata
kuma cewa komai ba ta juya ta tafi a hasale.
Widad ta karɓi wayar ta kira lambar Daddy, ya ɗaga suka gaisa yace "Lovely meyasa
wayarki bata shiga?"
"Jinyar Roux nake, bata da lafiya"
"To Allah ya bata lafiya, dama munyi waya da Daddynki yau baƙonki zezo"
"waye baƙona?"
"Fahad mana, zezo ya ganki ku gaisa dan Allah Lovely banda wulaƙanci ko makamancin
haka, shima ɗanuwankine Yayan Ramadan ne, yana nan tafe Anjima Insha Allah" Nan da
nan dukkan annurin fuskarta ya ɗauke ta dire wayar tace
"Ina nan ina jiran zuwan sa, yazo ya sami Widad Nasir Daula, yazo yaga mahaukaciyar
da'ake shirin ƙaƙaba masa"
Ayshercool 07063065680
_*AƘIDATA*_
PERFECT WRITERS ASSOCIATION
(WE AIN'T PERFECT BUT WE ARE ALWAYS TRYING OUR BEST, TO MOTIVATE AND ENTERTAIN OUR
READERS)
https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/
*Story and written by*
_*AISHA HUMAIRA (Daddy's girl)*_
The experience writer of *ABDUL JALAL** WATA KISSAR.... (SAI MATA) *And now *AƘIDA
TA *
I dedicated this book to my Mum (Malama Nafisat Adam Muhammad) i love you mum
Haƙƙin Mallaka ⚠ : Littafin nan mallaki nane, tun daga sunan labarin zuwa abunda ya
ƙunsa, ban yadda wani ko wata ya sauyamin ko yin Amfani da wani ɓangare na labarin
ba ba tare da izinina ba, Nagode
https://www.wattpad.com/user/Ayshercool7724?
utm_source=android&utm_medium=link&utm_campaign=invitefriends
ELEGANT ONLINE WRITER'S
PART1 Page 18
Binta da Kallo Yusuf yayi, ganin yadda ta canza lokaci ɗaya annurin fuskarta ya
ɗauke, tabbas akwai drama yau.
"Jeka anjima zamu fita" ta faɗa ba tare da ta kalli Yusuf ba
Miƙewa yayi ya fito daga ɗakin ya nufi hanyar fita, ba zato Amal tasha gabansa
wanda ya tilasta masa tsayawa.
"Yusuf ka fara ƙoƙarin tsallake iyaka, Yusuf meyasa baka tsoron Allah ka dinga nuna
kai na Allah ne amma baka kyautawa rayuwarka, Yusuf kai mugune mara tausayi baka da
tausayi baka tausayina, ko kaɗan soyayyata bata da daraja a idonka, na rasa meye a
tsakaninka da Widad, wallahi akan Son da nake maka banƙi komai ze faru ya faru ba,
wallahi akanka koni ko Widad "
Girgiza kai Yusuf yayi yace " keya dace a nemawa maganin mahaukata ai, nayi iya
ƙoƙarina in ganar dake amma kin kasa ganewa, bana Soyayya bani da ra'ayinki, ba
abunda ya kawoni nan kenan ba, ki ƙyale rayuwar Yusuf ta huta, tun kafin in nuna
miki ainihin kalata na gaya miki"
"Haka kace?"
"Eh haka nace, ko baki da kunne ne?"
"bayan ƙalubalen dake gabanka saboda Kasancewar ka da wannan mahaukaciyar, ka
shirya ƙalubalen da zaka fuskanta daga gareni"
"duk wanda ya dogara da Allah, to ya isar masa"
Yusuf ya bata amsa yasa kai ya fice, ya barta tana mamakin wannan taurin kai irin
na Yusuf.
Bayan Suleiman ya gama nazarin abunda Yusuf ya tura masa, yayi mamakin jajircewa da
kuma ƙoƙarin da yayi, tabbas Yusuf jajirtacce ne me kuma hikima da iya aiki, amma
meye dalilin da yasa Abbas yakeson lallai a ƙwace aiki a bashi? Lallai akwai wata a
ƙasa Abbas yana da fuska biyu.
Yusuf yana nan zaune yana ganin yadda aketa aiken su Murtalah, anata shirye shirye
da alama akwai baƙon da gidan zasu tara yau, shi dai yana guri ɗaya nasa ido.
Ƙarfe biyu na rana Yusuf ya dawo daga masallaci sallar Azahar, wata dalleliyar mota
ta shigo gidan, wani matashi ne ya fito daga motar, jikinsa sanye da ƙananan kaya
kallo ɗaya zaka masa kasan ɗan hutune, ya ɗaga kai ya ƙarewa gidan kallo tsaf, su
Isa mai gadi suna gaisheshi yana ɗaga musu hannu ba tare da ya amsa ba.
Shidai Yusuf be kula shi ba, sema ɗauke kai da yayi kamar bega Matashin ba, ba zato
suka jiyo muryar Ramla ta taho da gudu tana faɗin "Oyoyo my heart beat" Ba kunya
suka rungume juna a gurin.
Fahad yace "I miss you so much Baby"
"I miss you too mine" Fahad yayi kissing ɗinta a forehead yace "kin ƙara kyau my
Ramlat"
"Kyau ai kaine ka ƙara kyau, mutanen Amurka muje daga ciki ko"
Suka shige hannunsu saƙale da juna.
Nura direba yayi tsaki yace "ƙaryar banza burodi a lefe, waisu a dole turawa ba
kunya taje ta rungume ƙasurgumin gaddi tana ce masa Baby tir da wannan hali"
Shidai Yusuf bece musu komai ba suka ci gaba da gulmarsu.
A babban falon dake ɓangaren Hajiya Halima aka sauki Fahad, suka dinga hira yana
basu labarin Anwar shima ya kusa dawowa.
Fahad ya ɗan ɓata fuska yace "Hajiya wai ina Yarinyar take ne? Ance inzo in ganta
karta ƙullamin wani sharrin a gurin father ta jamin magana, danni sam ba'a
kyautamin ba da'akace zan Aureta"
Ɓata rai Ramla tayi ta miƙe ta bar falon, Hajiya Halima tace "Aikuwa dai an gama
da kai, dan yarinya ce ba tarbiyya ga kuma uwa uba hauka"
"wallahi Hajiya na rasa wani irin tunani Daddy yayi haka, da yasa yake son illata
rayuwa ta, nazo ne dai kar'ace banzoba amma sena tabattar da na mata rashin mutunci
yadda ko ganina tayi ba zata nuna ta sanni ba"
Amal ta kalleshi a yatsine, sam Fahad haushi yake bata yana ta wani iyayi shi
lallai ya dawo daga Turai, indai Widad ce ze gane kurensa ne.
Ba kunya Fahad ya miƙe yace "Hajiya bari inje gurin Ramla, naga tayi fushi"
"Shikenan kunfi kusa ai"
A ɗakinta ya sameta tayi kicin kicin da rai, ta haɗe fuska, ya zauna kusa da ita ya
janyota jikinsa yace "haba Baby, meye abun damuwa nifa danke nazo gidan nan, ba
dan wata banza ba meye na ɓata rai, ki tsaya kiga matakin da zan ɗauka yau akanta"
"Fahad inajin tsaro fa, su Daddy suna san Auren nan naku, zasu iya tursasa maka fa"
"waye ya gaya miki? Kamarni aina wuce ajin amin auren dole, calm down Baby" ya faɗa
yana jan hancinta
Murmushi Tayi tace "bari in shirya maka Abinci a dining, na maka girki"
Kafin yayi magana wayarsa ta fara ringing yace "excuse me Daddy ne"
Ya ɗaga wayar yasa a kunnensa yace "hello Daddy"
"Fahad kaje gurin nata kuwa?"
"Amm.. Eh ina gidan amma ban ganta ba"
"to ka tsaya ku gaisa, sannan yarinyar nan ka bita a hankali bata da cikakkiyar
lafiya, kabi a sannu ka kwantar mata da hankali"
Tura baki Fahada yayi yace "Haba Daddy sekace uwata, yarinyar ma ashe mahaukaciya
ce"
"ba zakayi ba kenan?
" Naji zanyi "
" idan naji wani abu na rashin kyautawa daga ɓangarenka sena saɓa maka, shashasha
wanda be san halacci ba, aiko wani kaga ze Wulaƙanta 'yar Nasir Daula kai me tare
matane"Bulama yayiwa Fahad tatas sannan ya kashe wayar
Fahad yace "kar wannan abun ya ɗaga miki hankali kinji babyna, ina tare dake,
nasan matakin da zan ɗauka"
Ta jinjina masa kai suka fito babban falo, Fahad yace "kiramin ita".Ramla ta nufi
part ɗin Widad, a falonta ta tarar da ita tana kwance a ƙasa ta ɗora ƙafafunta akan
kujera, mageneta na kan cikinta a kwance, itakuma tana danna waya.
Ramlah tace "Fahad yazo, yana falo yana jiranki"
Ai kamar da kujerun gurin Ramla ke magana ba da Widad ba, dan ko motsi ba tayi ba.
"Magana fa nake miki"
"And then? Ko bayan hauka kuma inada larurar kurmanta ne? Kinyi magan na jiki kin
cigaba da tsayawa a kaina, ki matsa daga kaina"
"Amma se ki bani amsa ai, tunda keba kurma bace"
Miƙewa Zaune Widad tayi tace barmin falo.
"Amma...
" ki fice nace, ko Bulama ne yazo da kansa be isa ya tursasani in saurare shiba,
kije ki gaya masa ya cigaba da jira idan ze iya daga nan zuwa lokacin da zan fito,
idan baze iyaba ze iya komawa ya tambayi Bulama tsarukana, idan ya shirya ɗauka ya
sake dawowa, fita ki barmin ɗakina"
Buɗe baki Ramla tayi tabi Widad da kallo, wato ita kullum rashin mutuncinta ƙara
ta'azzara yake, ina ita ina zuwa ta Sanarwa da Fahad wannan baƙin saƙo, mussman shi
dabe san kan Gimbiyar ba.
Ramla ta juya ta fice ta koma main falo tace "Baby naje yanzu ta tashi daga bacci
zata shirya ta fito"
Ramla ta zauna a kusa da Fahad suka shiga hirarsu, tun Fahad yana tsammanin fitowar
Widad harya fara ƙulewa.
"Ramlah wai yarinyar nan ba zata fito bane?"
"Fahad baka ga komai ba, indai akan wannan Yarinyar ne, idan ka kuskura ka aureta
taka ta ƙare wallahi"
"zan saita mata zama kuwa, dan nafi ƙarfin wata banza ta Wulaƙanta ni, bari inje
akwai wani friend ɗina a quarters ɗin nan, inaso mu gaisa ina dawowa"
"to ka fara cin Abincin mana"
"karki damu yanzu zanje in dawo"
Ramlah ta rakashi har gaban motarsa, kallo ɗaya Yusuf yayi musu ya ɗauke kai, Fahad
yace "Baby wai waye wannan ne?"
Yai maganar yana nuna Yusuf, yamutsa fuska tayi tace "Direban wannan sakaryar ce"
"yanzu wannan ne direba?"
"direba ne, sedai ya samu gindin zama fiye da duk wani me aiki a gidan nan, shiyasa
har wani jin kansa yake"
"ku kuka ƙyaleshi baku saita masa zama ba"
"ni yanzu ba shine a gabana ba, kaje kayi sauri ka dawo kaci Abinci"
Suka yi sallama Fahad ya tafi, se bayan ƙarfe huɗu Yusuf yaga message ɗin Widad, ya
miƙe ya shiga part ɗinta.
Yau dogon skirt ne a jikinta baƙi, da wata riga me dogon hannu ta ɗora ɗan ƙaramin
veil akanta, tayi kyau sosai kayan sun zauna cif a jikinta sedai ana ganin duk wani
shape na jikinta.
Tunda Yusuf ya shigo ba tayi magana ba, se sabgar gabanta take yi.
"Ya jikin magenki?" ya tambaye ta
Abunda Yusuf ya faɗa ne yasa ta ɗagowa da sauri tace "i think she got better now,
she's able to play"
"Allah ya bata lafiya, na ɗauka mutuwa zata yi ashe da sauran kwananta a gaba"
Harar Yusuf tayi ta ɗau jakarta tayi waje, binta yake a hankali baya sauri yana
tafiya kamsr kazar da ƙwai ya fashewa a ciki , ta juyo ta kalle shi tace "wannan
wace irin tafiya ce kuma?"
"Nifa gaskiya Yunwa nake ji, tun safe ban kuma cin komai ba, kuma kince kar inje ko
ina ban samu na fita naci Abinci ba"
Hararasa tayi tai gaba abunta, suna fitowa falo taga an shaƙe kan dining da Kulolin
Abinci, wani murmushi tayi ta kalli Yusuf tace "jirani anan" Ta juya ta koma part
ɗinta, fitowa tayi hannunta ɗauke da magenta ta nufi dining.
Alama ta yiwa Yusuf da hannu yaje, ya nufi kan haɗaɗɗen dining ɗin da'aka shaƙe da
kayan Abinci.
Tai masa alama da ya zauna, yaja kujera ya zauna tace "buɗe duk abunda kake so a
gurin nan kaci" Kallonta yay yace "Amma ranki ya daɗe, naga kamar baƙo aka
shiryawa teburin
" bana son musu ko jayayya, umarni na baka ba shawararka nake nema ba" ta faɗa
cikin faɗa da bada umarni.
Yusuf ya shiga buɗe Kulolin, Abinci ne kala kala kamar ba'asan zafin nema ba, yasan
duk tsiya wanda aka shiryawa Abincin baze iya cinyewa ba.
Widad ta zuba kifi akan plate ta miƙawa magenta, Taja plate itama ta ɗiba ta zuba,
dama Yusuf yunwa yake ji ga Abinci yayi daɗi nan ya dinga zurawa (samun guri direba
a dining 🤣🤣🤣)
Ramla ce ta fito itada Amal suna magana, me zasu gani Widad da mage ga direbanta
suna cin Abincin da'aka shirya karɓar baƙon Ramla sannan baƙon Widad, Amal tayi
saroro tana kallon Ramla.
A fusace Ramla ta ƙarasa dining ɗin kamarta fashe da kuka tace "Widad wane irin
wulaƙanci ne wannan, ta yaya za'ayiwa baƙo girki ki zauna kina ci naga dai idan
munyi Abinci ba ci kike ba, dan kawai ki muzgunamin kika yi haka? Saboda wulaƙanci
kuma ace harda direbanki saboda tsabar tozarci"
Shidai Yusuf bece komai ba, Widad cikin ko in kula tace "Ramla me direban nan nawa
yayi miki ne haka? Naga kuna takun saƙa sosai dashi, kina yawan manta wani abu
Ramla, duk wanda yake aiki a ƙarƙashina matsayinsa ɗaya da duk wanda yake zaune a
gidan nan ƙarƙashin kulawa ta, dan haka babu laifi dan na bashi Abinci ko?"
Cike da ɓacin rai Ramlah tace "Amma fa baƙo nayiwa, ta yaya zaki min haka? Ina
laifin kice inda saura in zuba masa"
Widad tace "waini wannan baƙon gurina yazo ko gurinki?"
Ras gaban Ramla ya faɗi jin tambayar da Widad tayi mata,"naga alamar gurinmu yazo
nida ke, nasan kina tunanin me zakice masa ne, idan baki da abunda zaki gaya masa
kice kinyi masa girki, 'yar masu gida tayi yadda take so dashi"
Hajiya Halima da ta fito ta riski rigimar tace "Amma Widad baki kyauta ba, ya za'
ayi kidinga nuna direba yafi 'yan gida"
"Ni bana abu dan in kyauta dama, bana abu dan in birge kowa, muddin zan cigaba da
saka doka ana watsi da ita nikuma zan cigaba da ɗaukar matakin daya dace, if i can
recall a falon nan nayi kashedi akan a dinga bawa direbana Abinci, akayi fatali da
dokar aka barshi da yunwa tun safe, nayi abunda ya dace ne, ga ragowa nan mun bari
idan baƙon naki yana buƙata seya ci dan naga ƙirarsa ta mayuntace dama kamar baya
ƙoshi"
Tai maganar tana kallon Ramla, tare da goge hannunta da tissue. Da gudu Ramla ta
bar falon tana kuka, ita kanta Amal ba taji daɗin abunda Widad tayi ba taji haushin
hakan.
Yayi parking ɗin motarsa a harabar gidan ya fito daga motar, yana rufe motar tare
da amsa waya, kamar an ce ya ɗaga kai ya hangota tana fitowa, fara ce sosai fari me
ɗaukar ido, tana da matsakaicin tsayi sannan tana da shape me kyau.
Tabbas idan ba gizo idonsa ke masa ba wannan itace Yarinyar da Anwar yake kallo a
hoto yana nuna masa, kenan itace Widad ɗin daza'a haɗa shi Aure da ita? '
Cigaba da Ƙarasowa Widad tayi, Yusuf na bayanta da jakarta a hannunsa, tana kallon
Fahad suka zo zata wuce shi "Widad Nasir Daula" Fahad ya kira sunanta.
Ta tsaya cak bata juyoba tace "Fahad Bulama"
"Amma kin san gurinki nazo kina kallona zaki wuce ki tafi"
A hankali ta juyo cike da izzarta ta ban mamaki, ta ƙare masa kallo sannan tace
"banyi tsammanin kaine Fahad ɗinba ai, na ambaci sunan ne dan tabattar da kai ɗinne
ko ba kaiba, dan abun da mamaki ace kaine Fahad ɗin, ina jinka faɗi abunda ke tafe
da kai"
Fahad ya jinjina kai yace "tun ɗazu nake gidan nan ina jiranki, meze hana mu shiga
daga ciki mu samu guri mu zauna se muyi magana"
"bani da wannan lokacin, yi maganar ka anan inajinka" ta faɗa tana kallon Idon
Fahad.
Fahad be taɓa zaton haka Widad take ba, ta kai mace har mace sedai tana da girman
kai da izza.
Ya kalli Yusuf yace "Amm ko zaka iya bamu guri, zamuyi magana"
"Ko da Bulama zanyi magana agabansa ake yi, dan haka cigaba da maganar ka" ta faɗa
cikin isa
"Amma kin san Aure zamuyi, meyasa zaki dinga gayamin magana haka ba respect, har ki
dinga kiran sunan mahaifina kai tsaye"
"Anƙi ayi respecting ɗin naka, Babana ma ina faɗar sunansa balle wani Bulama, kai a
tunaninka kai namijin daze tunkareni a matsayin wadda ze aurane?, ɗan sake kallon
kanka mana sannan ka kalli da wadda kake magana kasan niba ajinka bace, haka
Bulaman be gaya maka yadda mukayi da shi bane? Bana soyayya ban yadda da ita ba
kuna ba zanyi Aure ba, ana ƙoƙarin cusamin kaine kawai kuma bani da ra'ayin Auren
namiji irinka, dama ka kai Namiji ne zan iya maleji, amma sam baka da ƙira da zatin
da za'a kalleka a kiraka Namiji balle ace mijin Widad, ka sani koda ace Widad nada
ra'ayin Aure bazan taɓa zaɓarka a matsayin miji ba, banga alamar nagarta da kamala
a tare da kai ba, idan kana da zuciya kaje ka gayawa Babana Bulama baka son haɗin
Auren nan, 'yar tasa bata sonka, in baka da ita kuma kace masa kana son Auren kaga
yadda zamu ƙareta da kai "
Aiba Fahad ba hatta Yusuf jikinsa yayi sanyi da wannan mummunan cin zarafi da'akayi
wa Fahad, koba komai ɗan uwansa ne namiji.
Gaba ɗaya Fahad kasa magana yayi, be taɓa tunanin haka Yarinyar nan take ba, duk
wadda za'ayi sedai ayi amma seya auri Widad, sedai hakan yayi sanadiyyar ɓatawarsa
da Anwar, ze tabbatarwa da Widad shi Namiji ne, Namijin ma irin wanda kowace mace
keda burin samu, be tsaya ba ya shige motarsa ya fice.
Yusuf yana diving ya kalli Widad data cika tayi fam yace "Madam amma kamar abunda
kikayi wa wannan bawan Allah be dace ba, bakya tunanin ya Alhaji zeji idan yaji
labarin abunda kika yi, baki kyauta ba
"Yoseef!!!" karo na farko da Widad ta kira sunansa cike da gargaɗi, koda wasa bata
taɓa attempting kiran sunansa ba, danshi be zaci tasan sunan nasa bama, sannan
yadda ta faɗi sunan nasa yasha banban da yadda ake kiran sunan nasa, dukda Wasu
lokutan hausa bata isheta ba, idan ta faɗi wani abun yasha banban da yadda ake
faɗa.
"karka kusakura in dawo kanka, meyasa kake son shiga rayuwata, ban taɓa ganin
mutumin da nake ɗagawa ƙafa kamar kai ba, shiumrun da nake maka Albarkacin
mahaifina kakeci, kar in ƙara yin abu kace zaka yi challenging ɗina, duk abunda
kaga nayi inada dalili karka ƙara challenging ɗina if not i will teach you a lesson
you never forget "
Tai maganar a matuƙar fusace cike da gargaɗi.
" Allah ya huci zuciyarki, Allah ya baki haƙuri insha Allah ba zan sake ba"
Ya kaita gurin saloon kaman yadda ta buƙata.
Ramlah tayi kuka sosai akan wannan wulaƙanci da Widad tayi mata, seda idanunta
sukayi jawur saboda kuka, ƙanwar bayanta dan kawai suna zaune a gidansu ake musu
wannan wulaƙancin haka. Mummy ta tako tazo gaban gadon Ramla ta zauna ta dafata
tace "Am sorry daughter nasan....
"Mummy dan Allah ki ƙyaleni wallahi wannan karon sena ɗau mataki, haba abun ya isa
haka wace irin rayuwace wannan muke a gidan nan se kace zamanin Bayi, wallahi sena
ɗau matakin daya dace"
"A'a Ramla tynda kikaga na haƙura ban ɗau mataki ba kema haƙuri zakiyi, karki ja
mana Asara goma da Ashirin, kin san taɓa wannan yarinyar dai dai yake da kawo
ƙarshenmu a gidan nan"
"Niba ita zan taɓa ba, wannan sakaran zan nunawa kuskurensa, se yayi dana sanin
zuwa gidan nan, zega abunda zan masa"
******************************
Alhaji Munir, Musa, Haruna se kuma Sale ne zaune a katafaren Falon suna tattaunawa,
kana ganin fuskokinsu zaka san abunda suke tattaunawar yana da matuƙar mahimmanci a
gurinsu.
Nurat ce ta shigo falon bakinta ɗauke da Sallama tana ɗauke da manyan kuloli a
hannunta.
Gaba ɗaya suka bita da ido, kanta a ƙasa ta ƙaraso cikin falon ta durƙusa tana
gaishesu, Amsawa sukayi gaba ɗaya Alhaji Munir yace "wai yanzu Nurat ce ta girma
haka, gaskiya babu zumunci yakamata ace yaran nan suna zumunci suna a tsakaninsu"
Alhaji Haruna yace "gaskiya kam danni banda yanzu ma ban santa ba"
Nan sukayi ta surutunsu, yayin da Saleh yake gefe yaƙi cewa komai, Nurat ta gana
hada hadar kawo musu Abinci ta juya bar falon.
"Wai kai Saleh bazaka saki jiki damu bane? Akwai fa riba a harƙallar nan" cewar
Alhaji Musa
"Niba ribar ce a gabana ba ɗan uwana ne a gabana, yana gadon Asibiti kunsa an bashi
guba ku kuma kuna nan kuna cin Abinci"
Alhaji Haruna yace "to kuka kake so muyi? Wallahi idan asirinmu ya tonu dagamu
harshi sedai wasu bamu ba danme zamu bari ya fallasamu"
"shikenan a rayuwa kenan kowa kansa ya sani"
"ƙwarai kuwa ka bari harƙallar nan ta faɗa, idan ta faɗa ka samu kasanka seka
fiddashi"
Alhaji Musa yace "Wasan yana dab da zuwa ƙarshe indai abunda muka tsara ya tafi
daidai"
Alhaji Haruna yace "ƙwarai kuwa"
Suka maida kai suka cigaba da hirarsu yayin da Saleh gaba ɗaya abun duniya ya
dameshi.
***********************************
Gaba ɗaya a sukwane Fahad ya koma gida, se huci yake kamar wani fusataccen kumurci,
a falo ya tarar da mahaifiyarsa da ƙannensa, yazo ze wuxe fuuu Hajiya Sarah ta miƙe
da sauri tace "lafiya kuwa Fahad?"
Ya daki kujera yace "harni za'a kalla ace ban kai namiji ba? Me take taƙama dashi
ne haka? Ni Fahad Bulama har akwai Yarinyar da zata kalleni taci zarafina, dan
kawai tana da kuɗi, toni na ganta kuma ina sonta sannan zan nuna mata ni cikakken
namiji wanda mata je rububin samu!!! Meta taka da harta ke wannan izgilin da cin
zarafi ga mutane? "
"kuɗi yaro wanda hausawa kance masu gidan rana, tabbas Widad ko ba ran Mahaifinta
tana da kuɗin da zata taka wanda taso, kar ka manta da bazarsu muke rawa Fahad, ina
son saka alkhairi ne da alkhairi shiyasa nake ƙoƙarin haɗaka Aure da ita, karka
kusakura inji kayi mata wani abu wanda ze ɓata ranta kona mahaifinta, bazaka taɓa
gujewa wannan Auren ba"Alhaji Bulama ne tsaye a ƙafar benen dake falon, yana wannan
maganar
" dan tana da kuɗi, kuɗin banza kuɗin wofi, akanta aka fara arziki? Aiko da ance a
gujewa Auren bazan guje masa ba ina sonta tayi min, amma wallahi na aure ta she
must pay for what she did, kai kafin in Aureta ma zan Wulaƙanta ta wulaƙanci mafi
muni wallahi ni za'ayiwa cin zarafi irin wannan bata isa ba Wallahi "
Ya juya ya bar falon a matuƙar fusace
Hajiya Sarah cikin masifa tace " Alhaji seda nace maka bana son wannan haɗin, kawai
ka kaimin yaro ana Wulaƙanta shi daga dawowarsa yaje gurinta zata ci zarafinsa
haka, yarinya babu tarbiyya babu ta ido, na gaji da wannan abu"
"maza ki ziga shi, wallahi duk wanda yayi yunƙurin kawowa auren nan cikas zega
matakin da zan ɗauka, sannan kija masa kunne, wallahi idan yayi yunƙurin yi mata
wani abu ta ɗaureshi wallahi ba zan sa baki a sake shi ba, kinji na gaya miki ku
bar komai a hannuna nasan matakin da zan ɗauka"
Yai maganar tare da barin falon ya koma benensa
Yusuf kam tunda aka masa warning yaja bakinsa ya tsuke har sukaje suka dawo be kuma
cewa komai ba, amma yana jinsa a ƙoshe saboda garar da ya kwasa yau.
Se bayan isha'i ya baro gidansu Widad, yanata sauri ya koma gida
Ba zato kawai yaga an saka masa wuƙa a saitin Ƙirjinsa, tasayawa yayi cak ba tare
da yayi yunƙurin guduwa ba.
Kamar waccan ranar mutanen da suka tareshi ne suka sake tareshi.
"munzone dan mu cigaba da jadadda maka har yanzu muna bibiyarka, muna jiran karɓar
wannan abun daga hannunka muna nan muna cigaba da sa maka ido da duk wani motsinka"
"Wai wani abune wannan kuke son karɓa? Ku gayamin in karɓo in baku ku ƙyaleni"
"An gaya maka bamu da lissafi ne? Ba zamu gaya maka menene ba, amma da zarar ka
samu abun zamu sani, kuma zamu biyoka mu karɓa"
Suka koma cikin motarsu suka tafi, sedai sunyi ganganci dan tuni Yusuf ya ɗauke
lambar motar akansa.
Yau yaci sa'a basu dake shiba suka tafi suka barshi, gida ya tafi yana tunanin meye
wannan abun da'aka damu se an karɓa a gurin Widad.
A haka har ya ƙarasa gida, Seda ya zauna sukayi hira da Ummansa dukda abubuwa sun
cunkushewa ƙwaƙwalwarsa.
Ya gama cin Abinci ya tafi ɗakinsa, dole zeyi tracking ɗin lambar motar nan ya gano
motar waye.
Da ya koma gida Ummansa taita mita akan daren da yake kaiwa a waje, yaita bata
haƙuri yana rarrashinta sannan ya tafi ɗakinsa, ya nutsa a duniyar tunani sosai
wayarsa ta fara ringing. Lambar Sakina ce kamar kar ya ɗaga, sekuma ya ɗaga yasa a
kunnensa tare da sallama.
"Yusuf baka yi bacci ba?"
"Eh banyi ba" ya bata amsa a taƙaice
"dama magana nake so muyi"
"Amma kinsan dare yayi ko?"
"eh nasani, maganar tana da mahimmanci ne a gareka"
Yusuf yace "to ina jinki"
"Yusuf akwai buƙatar ka dinga taka tsantsan da wasu abubuwan, akwai mutanen da suke
nuna suna tare da kai amma a bayan idonka suna cin dunduniyarka, ba kowane mutum ne
aboki na gaskiya ba"
Yusuf yace "nifa bana son irin wannan ƙananan maganganun, ni ina zaune da kowa
lafiya"
"ba ƙananan maganganu bane ba, ka dai yi a hankali sannan karka yadda wani yasan
sakamakon binciken da kake komai kusancinka dashi in ba yallaɓai ba shawara ce
yakamata ka kula"
"Shikenan nagode" Yusuf ya faɗa cike da ƙosawa, shi sam baya san abunda ze haɗa shi
da Sakina baya son mace mara kamin kai sam.
Amma nazarin maganganun ta ya shiga yi, wayarsa ce ta sake ɗaukar ringing har yayi
tsaki ze kashe wayar yaga lambar Alhaji Nasir.
Cikin ladabi ya ɗaga wayar suka gaisa da Baban Widad, Alhaji Nasir yace "Yusuf
meyefaru ɗazu da Fahad yazo gurin Daughter" . Cikin kame kame Yusuf yace "Amm..
Yallaɓai yazo sun gaisa"
"Yusuf karka kareta, ka gayamin gaskiya me tayi masa? Wace irin karɓa tayi masa?"
"da alama dai beyi mata bane, ta ɗan dai nuna masa bata sonsa ne"
"Yusuf karka fara ƙarya saboda ka kare uwar ɗakinka, Bulama ya tabattar min da
wulaƙanci tayiwa Fahad, kuma nasani zata aikata na kiraka ne dan in tabattar,
saboda zan ɗau mataki na ƙarshe daya dace da ita, duk abunda nake dan gyaran
rayuwar ta nake amma ta kasa ganewa, dan haka zan ɗau matakin da bata taɓa zata ba
akanta wanda ze kasance hukunci na ƙarshe da zan yanke akanta "
Domin gyara sharhi ko shawara, feel free to contact meAyshercool 07063065680
_*AƘIDATA*_
PERFECT WRITERS ASSOCIATION
(WE AIN'T PERFECT BUT WE ARE ALWAYS TRYING OUR BEST, TO MOTIVATE AND ENTERTAIN OUR
READERS)
https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/
*Story and written by*
_*AISHA HUMAIRA (Daddy's girl)*_
The experience writer of *ABDUL JALAL** WATA KISSAR.... (SAI MATA) *And now *AƘIDA
TA *
I dedicated this book to my Mum (Malama Nafisat Adam Muhammad) i love you mum
Haƙƙin Mallaka ⚠ : Littafin nan mallaki nane, tun daga sunan labarin zuwa abunda ya
ƙunsa, ban yadda wani ko wata ya sauyamin ko yin Amfani da wani ɓangare na labarin
ba ba tare da izinina ba, Nagode
https://www.wattpad.com/user/Ayshercool7724?
utm_source=android&utm_medium=link&utm_campaign=invitefriends
ELEGANT ONLINE WRITER'S
PART1 Page 19_20
Gaba ɗaya Yusuf ya dirircei yace "Amm... Amma Yallaɓai wani mataki zaka ɗauka haka
akanta, ina fatan ba wanda ze mata tsauri bane?"
"Yusuf kenan, ka damu da al'amarin Widad haka nan naji na yadda da kai, shiyasa har
nake saka a cikin abunda ya shafi rayuwar mu, na yanke shawarar tsayar da ranar
Aurenta a ƙarshen wannan watan zuwa farkon wata me kamawa"
"Amma yallaɓai baka ganin hakan ze sake jefa rayuwarta cikin hatsari, duba da yadda
babu Aure a tsarin Rayuwar ta?"
"Yusuf, Widad fa mutum ce kuma lafiyayyiya tana ƙin Aurene saboda wasu dalilanta da
suke masu rauni a gurina, bana so in mutu in barta cikin kaɗaici, nasan Bulama baze
taɓa barin ɗansa ya Wulaƙanta Widad ba ko bayan raina, dan Allah ka cigaba da
yimana addu'a, Amma insha Allah ko ba taso zan ɗaura mata aure karo na farko a
rayuwata da zan ɓata mata rai, amma ina fatan hakan ya zama alkhairi a gareta,
Insha Allah gobe zuwa jibi zan dawk"
"shikenan Yallaɓai, Allah ya tabattar da alkhairi ya dawo da kai lafiya"
"Ameen Yusufa nagode sosai"
Tunda sukayi Sallama da mahaifin Widad abun duniya ya damu Yusuf, ji yake matakin
da mahaifin Widad ke shirin ɗauka tamkar ƙarasa rugurguza rayuwar uwar ɗakinsa ne
gaba ɗaya, matakin yayi tsauri sosai, haka nan yaji wani irin matsanancin kishi na
taso masa game da Widad ɗin.
Dafe kansa yayi tare da faɗin "Innalillahi wa inna ialaihi raji'un, Allah ka
tsareni da sake faɗawa hatsarin Soyayya, Allah yasa tausayinta kawai nake ji,
tabbas idan na fara son Widad zan shiga matsala fiye da wadda nasha a baya"
Bacci kam se Ɓarawo ne ya kama Yusuf.
Kwana biyu a tsakani Yusuf yana zuwa gidansu Widad amma ba wani aiki da yake yi,
kuma sam baya ganinta.
Abubuwa sun ƙara cakuɗewa Yusuf, tunani kala kala a zuciyarsa amma zuciyarsa tafi
fargaba akan hukuncin da Daddy ya yanke ɗauka akan Widad.
Ya ɗakko wayarsa yana ɗan duddubawa kawai yaga message ya shigo wayarsa, anyiwa
ma'aikata canjin gurin aiki ciki harda Abbas, an maida Abbas aiki a kudancin
Nigeria, abun ya ɗaurewa Yusuf kai sosai, mafi akasari anfi yin wa mutum wannan
canjin aikin ne, kodai dan wani mahimmin bincike, ko ƙarin girma kokuma dan hukunci
ga wani laifi da ya aikata, sedai shi a ganinsa babu ɗaya da Abbas yayi wanda zesa
ayi masa wannan transfer.
Ba shiri Yusuf ya bar gidansu Widad ya tafi gurin aikinsu, kai tsaye ofishin Oga
Suleiman ya wuce, gaje suka gaisa Suleiman yace "Yusuf naga aikin daka turomin,
kayi ƙoƙari sosai Yusuf sannan ina taya ka murna da sabon muƙaminka"
Yusuf cikin rashin fahimta yace "Yallaɓai nida ban fahimci abun nan ba, me Abbas
yayi za'a ɗauke shi daga gurin nan akaishi wata uwa duniya?"
"Nima ban san meyasa hakan ta faru ba, sedai daga sama ne akayi wannan transfer
sannan ka samu ƙarin matsayi"
Yusuf ya dafe kai yace "Yallaɓai babu yadda za'ayi a bar Abbas a gurin nan ne?
Bekamata a raba shi da iyalinsa ba zuwa wata uwa duniya ba, ni dai banji daɗin
hakan ba, zanyi kewar abokina kuma ɗan uwana"
Suleiman ya jinjina sauƙin kai irin na Yusuf yace "ya za'ayi se haƙuri haka
sha'anin aiki yake"
Jiki a sanyaye Yusuf ya baro office ɗin Suleiman ya nufi na Abbas, se sarawa Yusuf
ake ana masa murna amma shi sam hankalinsa yana kan wannan transfer da'akayiwa
Abbas.
Da sallama ya shiga Office ɗin ya tarar da Abbas yana ta tattara kayansa dake
Office ɗin.
"Abbas ya akayi haka? Me yasa akayi maka transfer haka ta gaggawa?"
Abbas yace "nima ban sani ba Yusuf, jiya aka sanar dani kuma akace lallai gobe in
Allah ya kaimu in tafi"
"yanzu babu wani abu da zamu iyayi a fasa wannan transfer ɗin?"
"Yusuf nayi duk ƙoƙarin da zanyi amma abun ya gagara"
Gaba ɗaya Yusuf ya rasa abunda yake masa daɗi, dan har cikin ransa yake jin rabuwa
da Abbas ɗin, dan yana jin Abbas tamkar wani ɗan uwansa.
Wayar Yusuf ce ta fara ringing, ya ɗakkota daga aljihunsa ya ɗaga.
"Yusuf mai gida ya dawo yanzun nan, yace a kiraka"
"Shikenan gani nan zuwa"
Yusuf ya kashe wayar yace "Abbas zanzo gida insha Allah, zan ganka muyi sallama"
Abbas yace "Yusuf na ta yaka murna, an ƙara maka matsayi"
Yusuf yace "Abbas sam bana murna da wannan ƙarin matsayin, ni tafiyarka ce damuwa
ta, bari inje wannan kiran zan nemeka Insha Allah"
Sukayi musabiha, Yusuf ya juya ya fita, Abbas ya raka bayan Yusuf da harara tare da
yin ƙwafa.
Tun daga harabar gidan Yusuf yaga manyan motoci da alama bayan dawowar maigidan
anyi baƙi a gidan.
Kansa tsaye ya nufi cikin gidan, a falon ya tarar da Alhaji Nasir, Bulama, Fahad
Hajiya Halima da iyalanta.
Yusuf ya ƙaraso yana gaishesu, Alhaji Nasir yace "ƙaraso kusa dani Yayana, nace a
kiraka aka cemin ka fita ne"
Yusuf yace "eh naje wani uzuri ne"
Fahad se wani hararar Yusuf yake, shiko Yusuf ya basar kamar be gani ba.
Tsit falon yayi na wani lokaci, Yusuf ya rasa dalilin hakan, yana ɗaga kai yaga
gimbiyar ta fito daga ƙofar part ɗinta, da alamu wannan zaman fitowarta ake jira,
seda ta tsaya ta ƙare musu kallo ɗaya bayan ɗaya sannan ta ƙaraso cikin takunta na
isa, ta samu kujera ɗaya ta zauna ba tare da ta kula kowa ba.
Alhaji Nasir yace "daughter"
"Na'am Daddy"
"waye wannan?" ya nuna mata Bulama
"Alhaji Bulama"
"kin san matsayinsa a gurina?"
"Just a long time business partner to you"
"he is more than that to me, kuma kin sani danme zan baki umarni kiyi fatali dashi?
Duk abunda mukeyi munayi ne dan rayuwarki, danme zaki ciwa Fahad mutunci? A gaban
Yusuf komai ya faru, daughter nasan duk abunda kike yi, ina ƙyale ki ne saboda
nasan halinda kike ciki na maraici, amma kina zarce ƙa'ida wasu lokutan, daughter
farincikin ki muke fata shiyasa muke son aurar dake"
Gaba ɗaya Widad ta ɗauke kai daga kallon Daddynta zuwa wani sashin daban, tanajin
ɓacin ran saboda wannan daƙiƙin talasurun Fahad ɗin yau Daddynta ke mata faɗa, ze
gane bashi da wayo.
"dan haka whether you like it or not, i have took the final decision, ending of
this month zuwa farkon wata na gaba zan ɗaura Auren ki da Fahad"
Zare ido Ramlah tayi, taji zuciyarta kamar zata faɗo.
Fahad ya wani gyara zama ya kalli Alhaji Nasir yace "sannan Daddy gaskiya yakamata
ayi mata magana akan tasan yadda zata dinga gayamin magana, ta tauna ta kafin ta
faɗeta dan sam bata da ɗa'a"
Miƙewa Widad tayi tsaye a fusace tace "Over my death Body Daddy, wallahi da in
auri wannan mara amfanin gara in kashe kaina, kai ka isa ka kalli tsabar idona kace
a koyamin yadda zan magana, waye kai"
"Widad!!!" mahaifinta ya kira sunanta tare da Miƙewa kamar ze kai mata duka. Cikin
zafin nama Yusuf ya miƙe ya shiga tsakanin Widad da mahaifinta ya girgiza kai yace
"Yallaɓai ayi mata afuwa dan Allah, baka saba yi mata magana haka ba karka fara
yanzu karkasa zuciyarta tayi rauni, kowa ya juya mata baya, ka sauraretaba zata
rasa dalilinta na ƙinsa ba"
Alhaji Nasir yace "Amma Yusuf yakamata Widad tayi min haka a gaban mutane ta nuna
ban isa ba?"
Girgiza kai Yusuf yayi yace "ba tayi haka dan Wulaƙanta kaba, ta tashi a
environment ɗin da kowa yana da 'yancin faɗan abunda yake ra' ayinsa, karka ɗau
hakan a matsayin ta Wulaƙanta ka, kayi haƙuri dan Allah kasan bata da lafiya"
Tuni hawaye ya wanke fuskar Widad ta kalli Daddynta karo na farko a rayuwar ta da
yaƙi bin abunda takeso, hannayenta biyu ta haɗa tareda duƙar da kanta alamar neman
afuwa, daga nan ta juya ɗakinta.
Alhaji Nasir ya nemi guri ya zauna, Bulama yace "lamarin daughter se haƙuri, Allah
ya shirya mana"
Hajiya Halima ta gyatsine baki tace "wannan direban ne yake hure mata kunne take
iskancin data ga dama, na rasa wace irin alaƙace tsakaninsu banda haka ana mata
faɗa meye na tsoma baki? Kaima Yallaɓai harda kai da kake saka bare a al'amuran
gidanka" Alhaji Nasir yace "ba ruwan Yusuf, a irin taurin kai na Widad da irin
haƙuri na Yusuf be isa ya hure mata kunne ba, sedai haƙurinsa ne yasa suke tare har
yanzu, dan haka karki ƙara aibata shi ko ɗora masa laifi, kaimu Fahad zan shawo kan
komai insha Allah"
Yusuf ya miƙe yayi musu sallama ya fice suka cigaba da tattaunawa.
Cakwakiyar gidan nan akwai sarƙaƙiya da ban mamaki, yana nan zaune ya dafe kai yayi
shiru Bulama da Fahad suka fito zasu tafi, Bulama ya shiga motarsa direbansa ya ja
suka tafi.
Fahad ya tako zuwa gaban Yusuf ya zauna yana fuskantar Yusuf yace
"kaine direban Widad ko?"
Yusuf yace "Eh nine"
"Naga kamar matsayinka a gidan nan ya wuce matsayinka na zahiri, zan ja maka kunne
ne idan har kana shishshigi da iyayi ka kiyayi Fahad, dan bana barin duk wani abu
daze kawomin cikas, matsiyaci kawai kalli rigar wuyanka wai har kaine zaka shiga
maganar da bata shafeka ba"
Yusuf yayi murmushi ya miƙawa Fahad hannu yace "Assalamu Alaikum warahmatullah"
Fahad ya kalleshi yace "ni zaka miƙowa hannu kace mu gaisa, kasan koni waye?"
"haka Addini na ya koyamin, ban saniba ko zama a cikin turawa yasa ka manta hakan,
rigar wuyana zata iya fin taka daraja in har da gumin halak na sameta, sannan nafi
kowa sanin ko kai waye, ɗan adam ne da'aka samar daga Najasa wanda ƙarshena ni da
kake kira matsiyaci da kai da kake ganin kanka wani ƙarshen mu ɗaya wato turɓaya
kuma Abincin tsutsa, kana fuffukar ban san waye kaiba, kamar ba'a gabana mace ta
keta ka ba ta Wulaƙanta ka, wulaƙanci mafi ƙasƙanci shine yadda ake cusa mata kai
tana cewa bata sonka "
Galala Fahad yayi yana kallon Yusuf, sam be zaci Yusuf ya iya yanka baƙaƙen
magnganu haka ba, Yusuf ya miƙe yace " ka kiyaye gaba, dan idan baki yasan me ze
faɗa be san abunda za'a mayar masa ba, bana shkkar kowa se Mahaliccina, kana
gayamin abunda beminba zan rama, ni yanzu damuwata be wuce yadda a dalilinka aka
samun uwar ɗakina a damuwa ba, damuwarta tafi komai tsayawa a zuciyata"
************************************
"Akan me za'a ayi maka transfer bayan bamu sallami wannan mutanen ba? Waima waye
yayi maka transfer ne haka ba shiri? Aknme za'a ɗauke ka daga garin nan?"
Abbas yayi ajiyar zuciya yace " wallahi ranka ya daɗe ban san yadda hakan ta faru
ba, Suleiman ya cemin daga sama transfer ɗin tazo, abun baƙin ciki aka maye gurbina
dana bari da Yusuf, ni ina kyautata zaton shine yaje yasa akamin transfer dan ya
gaji muƙamina, kuma da yake munafiki ne ya zo yana nuna damuwarsa akan transfer ɗin
da'akayi min"
Saleh ya numfasa yace "Abbas tabbas akwai babbar matsala wannan transfe da'akayi
maka ba tare da samun binciken da Yusuf yayi ba, a ɗan ganin da nayi masa beyi kama
da mugun mutum ba yana da nutsuwa, dan haka bashi da hannu a cikin transfer ɗin
da'akayi maka, ni babban burina in samu binciken da yayi a hannuna in sallami
wancan mutanen kafin su shiga target ɗinsu na biyu kuma na ƙarshe akan Widad, wanda
target ne me hatsarin gaske"
Abbas yace "nifa takaicina shikenan yanzu ba zan samu kuɗaɗen nan ba? Gaskiya na
ƙallafa rai amma karka damu Yallaɓai, dukda zan bar garin nan dole a samu binciken
da Yusuf yayi"
Saleh yace "don't stress yourself i know what to do"
"Amma kana ganin rashin bada file ɗin akan kari zesa kaima ka shiga cikin matsala?"
"babu wata matsala am also planning something, karka damu ni zan tafi duk yadda ake
ciki zamuyi waya"
Daga nan suka yi sallama.
Sam Yusuf ya dena ganin Widad, hakan yasashi shiga damuwa sosai, hakan yaso ya
shafi aikin da yake yi, ya damu sosai yaga halin da take ciki, bashi da hujjar
shiga cikin gidan tunda ba nemansa akayiba.
Mutanen gidan dama ba wanda yake saurarar Yusuf, dan haka haka yake zuwa ya wuni ya
tafi zuciyarsa cike da son sanin halin da take ciki.
Yusuf yana zaune yana tunanin yadda zega Widad dan yasan koba'a gaya masa ba Widad
tana cikin damuwa.
Fitowar Alhaji Nasir dasu Hajiya Halima ne ya dawo da Yusuf daga tunanin da yake
yi, Fuskar Alhaji Nasir akwai damuwa amma ya danne damuwar tasa yana ta fara'a.
Yayiwa Yusuf alama da yazo, Yusuf ya taso yazo, Alhaji Nasir yace "Babban Yaya,
airport za muje zamu ɗakko ɗana Anwar, ya kammala karatun sa"
Yusuf yayi murmushi yace "Masha Allah, shima Yayan uwa ɗakina ne?"
Alhaji Nasir yayi murmushi yace "Yusufa kenan, ai uwaɗakin ka bata da wa ba ƙani,
Amma Anwar ma ɗana ne tunda na riƙe shi"
Yusuf yace "ba da ita zamuje bane? Naga ita bata fito ba?" Yusuf yayi maganar cike
da son sanin halinda Widad take ciki.
"Kasan tana fushi dani ne, ta dena zuwa inda nake ma, na ɗan ƙyaleta ne ta huta,
har seta gane mahimmancin maganata"
Har Yusuf zeyi magana, Hajiya Halima tace "Kaga ka ishemu da surutu, muyi mu tafi
kar jirginsu ya sauka yazo yana faman jira"
Alhaji Nasir yace "Bimin shi a hankali Halima, Yaya nane a girmama shi ko dan
sunan nasa"
Nura yana gefe ji yake kaman ya shaƙe Yusuf, ba'a taɓa ma'aikacin da Alhaji Nasir
ke nunawa soyayya kamae Yusuf ba dukda mutum ne me girmama na ƙasanshi, tsabar abu
yanzu Alhaji Nasir be fiye damuwa da Nura yaja shi a mota ba sedai Yusuf.
Gaban Mota Amal ta shige, yayin da su kuma suka shiga baya, Suna tafe a mota iyalan
suna hira kamar ba abunda ke damunsu, Alhaji Nasir yana dauriya ne kawai, yayin da
Yusuf ko uffan yakasa cewa hankalin sa na kan Widad.
Koda suka je airport sunyi A ƙalla mintuna talatin, sannan wanda suka zo dominsan
jirginsu ya sauka, matashin kamarsa ɗaya sak da Amal, kana kallonsa kasan ɗan
uwansu ne, da gudu sukaje suka rungume shi cike da farinciki, ya ƙaraso gaban
Alhaji Nasir ya durƙusa ya gaishe shi.
Bayan sun gaisa ya kalli Yusuf ya miƙa masa hannu sukayi musabaha, da alama Anwar
shi a nutse yake ba kamar 'yan uwansa ba, daga nan suka nufi hanyar gida, suna tafe
kamar zasu fasa motar da hayaniya da shewa.
Har sukaje gida hirarsu kawai suke, amma alamu sun nuna Alhaji Nasir biye musu
kawai yake, sun Sakkowa sukayi cikin gida yayinda aka bar Yusuf da kwaso akwatunan
Anwar.
Suna shiga falo kawai Yusuf yaga Widad a zaune tana shan ruwan roba, sedai idanunta
a kumbure suke, alamar kodai bata bacci kokuma kuka take yi, gaba ɗaya Yusuf yaji
babu daɗi.
Anwar yace "Masha Allah, little queen ta girma Amma Daddy sha ka fashe ka bata dan
yayi wuri ace tayi wannan girman"
Daddy yayi murmushi yace "gata nan tambaye ta, in da ragiwar sha ka fashe ɗin kaima
ta sammaka"
Ba tsammani Yusuf yaga Widad ta ɗanyi murmushi, yayin da Hajiya Halima ta tsuke
fuska tace "kaga muje ka wataa ruwa ka nemi Abinci"
Anwar yace "bari Mummy in gama ganin lovely ɗin Daddyn ta inji dalilin da yasa ba
tazo taroni ba"
Yai maganar yana ƙarasawa inda Widad take ya zauna, Alhaji Nasir kam part ɗinsa ya
wuce yana murmushi saboda Anwar akwai barkwanci.
Ramla cikin tsawa ta cewa Yusuf "dalla malam ka ajiye kayan na ki fita, uban sa ido
kawai"
"Karki kuma yi masa tsawa, na kuma gayamiki ba zamanki yake ba, idan kika ƙara
hukuncin daze biyo baya ka iya ɓatawa kowa rai" Widad tayi maganar ba tare da
kallon Ramla ba.
Anwar yace "Ramla baki kyauta ba, babu daɗi abunda kikayi fa"
A fusace Mummy tace "dalla tashi ka wuce ciki, ina magana harda neman guri ka
zauna"
Anwar ya miƙe yace "Widad idan na fito zanzo mu gaisa sosai ki bani sirrin wannan
girman naki"
"No need Anwar, yanzu ma mun gaisa yawan shiga harkata ka iya baka matsala da kai
da Ahalinka, ina taya ka murnar kammala karatunka, Allah yasa al'umma su amfana"
Tai maganar tana miƙa masa hannu suka gaisa, from no where Yusuf yaji wani takaici
ya tokare masa zuciya ganin abunda ya faru.
Mummy ta tasa ahalinta suka shige sashinta, aka bar Yusuf da Widad a falon har ya
juya ze fita ya bar falon ya waiwayo, ba zato suka haɗa ido tai saurin ɗauke nata
idon daga nasa, a hankali ya dawo ya kalleta yace "Madam ko baki da lafiya ne?"
Girgiza masa kai tayi tace "jirani a waje gani nan zamu fita" ya jinjina mata kai
ya fita.
Cike da damuwa Anwar yace "Mumsy meyasa bakya son Widad ne? Me tayi mikine haka?"
Ramla tace "yanzu daka dawo idonka ze gane maka ai"
"kar in sake magana ki samun baki, in bahaka ba sena tattakaki na gaya miki"
Ya maida hankalinsa kan Hajiya Halima yace "Rayuwar ta abun tausayi ce, tana
buƙatar kulawa meyw a ciki dan ki haɗemu gaba ɗaya kin nuna mata kamar ke kika
haifeta"
Amal tace "Taɓɗijan lallai baka san yarinyar nan da taurin kai kamar arnan farko
ba, ba mutunci a lamuranta balle tausasawa bata ganin kowa da gashi waye za janyo
ta a jiki?"
"Amla yaushe kika koma hakane? Gaba ɗaya kun zama fitsararru"
"karka ƙara ce musu fitsararru na gaya maka, bazan riƙe yarinyar da zata nemi ta
halakani da baƙinciki ba, bata da tarbiyya sam bata da ɗa'a, shikansa mahaifin nata
bata ƙyaleshi ba, weekends ɗin nan Fahad yazo ganin ta za'a haɗasu Aure da shi da
ubansa ta haɗa ta wanke su da rashin mutunci tsaf, ubanta ya kirata yayi mata faɗa
nan ma ta sake kunyata shi a gaban mutane ta hanyar nuna masa be isa ba"
Cike da ɗimuwa Anwar yace "wait ji nayi kamar kince za'a haɗata Aurw da Fahad,
wani Fahad ɗin wai?"
"Fahad ɗin Bulama mana" ta bashi amsa
A diririce yace "Mummy ta yaya haka zata farune? Ita tace tana sonshi? A zatona ai
Ramla yake so"
Amla tace "Ramla yake so, amma babansa da Babanta sukayi ƙarfa ƙarfa sukace zasu
aura masa ita, tayi masa rashin mutunci amma yace ba gudu ba ja da baya seya aure
ta"
Anwar yace "Impossible wallahi sedai ayi biyu babu, Fahad yafi kowa sanin yadda
nake son yarinyar nan danme zemin haka? Na tabbata da nine bazan masa haka ba,
wallahi indai da raina Fahad be isa ba, sedai zumuncin namu ya watse"
"haka nima indai da raina baka isa ka aureta ba, sedai ka canza wata uwar bani ba,
dan da hankalina ɗana baze auri dangin mahaukata gadon rashin tarbiyya ba"
Bin mahaifiyar tasa yayi da ido, tare da mamakin wannan magana data fito daga
bakinta, be kuma cewa komai ba ya fice cikin hanzari.
Wata katafariyar ma'aikata sukaje, Yusuf yayi mamakin haɗuwa gami da tsaruwar
ma'aikatar kamar ba'a ƙasa Nigeria ba, Widad ta dinga ratsawa Yusuf na binta kamar
inuwa haka suka isa wani makeken Office.
Kai tsaye ba neman izina ta bankaɗa ofishin ta shiga, Bulama ne zaune da ɗansa
Fahad suna dudsuba wasu file, Widad ta kallesu tana huci kamar mayuwanciyar Mesa.
"daughter lafiya kuwa?" Bulama ya tambayeta.
"Dole ka tambayi lafiya mana tunda kayi nasarar cusawa mahaifina ra'ayinka wansa
yake barazana ga ratuwata, be taɓa fushi dani kamar wannan karon ba yana kallon
hawaye akan fuskata amma ya kasa share min hawayen, ya barni tsawon kwanaki ina
fama da ƙuncin zuciya "
Bulama yace " Calm down daughter, wannan fa duk ba abun zafi bane, ke kika kambama
abun kika maida shi babba, meye laifin Fahad dan an Aure shi? Kuma daba'a aure a
haifeki? "
" kai baka ga laifin ɗanka ba ni na gani, bashi da nagartar daze iya zama miji a
gare ni, na tsane shi bana sonsa kuma bazan aure shi ba, sannan ka gaggauta zuwa ka
janye wannan maganar daga gurin mahaifina ya dena fushi dani, fushinsa yana daga
abunda ke jefa zuciyata cikin tashin hankali, be taɓa fushibdanibba se a dalikin
wannan gurguwar shawarar taka, bazanyi aure ba ka janye wannan maganar idan ba haka
ba Wallahi sena baka mamaki daga kai har ɗan naka"
"Ke jahila!" Fahad ya faɗa tare da yunƙurin kai mata mari, ganin yadda take wa
mahaifinsa shouting, sedai ba zato yaji an riƙe hannunsa anyi gefe dashi.
"karka kuskura koda wasa ka kuma yunƙurin ɗaga hannu akanta, koda mafarki kake kaga
hakan zata faru kayi duk me yuwuwa kaga ka farka da baccin dan mummunan mafarkine
balle a gaske, sannan kasan da kalmomin da zakayi amfani gurin yi mata magana"
Yusuf yayi maganar cikin fushi da harzuƙa, wani irin kwarjini Yusuf yayiwa Fahad,
dan a doke tsaf Yusuf ze bazar dashi a gurin.
Bulama yace "ɗan samari kamar kana zaƙewa fa wasu lokutan"
Yusuf ya saki hannun Fahad cikin ladabi yace "bahaka bane ranka ya dade, nayi
ƙoƙarin hana faruwar tsamin alaƙar daze biyo baya idan har Alhaji Nasir yaji ɗanka
ya dakar masa 'ya me"
Bulama yace "koda baka yi hakan ba ni zan ɗau mataki Yusuf, bazan bari hakan ta
faru ba sam"
Widad tace "naso ka bari ya dakeni, in sa a nuna masa shi ba komai bane, in nunawa
duniya da bazata yake rawa, duk wannan fuffukar da yake da sena nuna masa in ba
Widad babu shi, kuma Auren nan dole a fasashi, nazo ne dama dan in muku gargaɗi na
ƙarshe a janye maganar nan kafin rugujewar duk wata alaƙa dake tsakaninka da
mahaifina"
Sosai Fahad ya dinga huci, a gabansa yarinya ƙarama take cim zarafin mahaifinsa.
Bayan fitarsu Widad, Bulama yayi shiru yana tunani, Fahad yace "Daddy wannan wace
irin dabbar yarinya ce me kyan ɗan maciji, bata da tarbiyya bata da ta ido Sam, ta
dubi mutum kamar kai ta dinga gaya masa wannan maganganun, kana kallonta kuma
Daddy"
Bulama yayi ajiyar zuciya yace "daka sake ka daki yarinyar nan da tabbas yanzu
wani zancen ake ba wannan ba, koda wasa karka kuskura kayi gangancin cewar zaka
dake ta, ta wuce yadda kake tunani, tabbas ba dan inajin nauyin Daula ba da se an
fasa Auren nan, dan ina ganin ƙiyayyarka a idonta wanda har hakan yake son ya
shafeni"
Fahad ya daki teburi yace "Nikuma ina sonta a hakan, zan Aure ta koda zata kashe
kanta sena Aureta na wulaƙantata na nuna mata ita bakomai bace zanga wanda ze
Nasara tsakanin ni da ita"
Bulama ya girgiza kai yace "Fahad kenan kai kana tunanin zaka iya Wulaƙanta ta
idan ka Aureta, dole kayi haƙuri da duk abunda zata aikata maka, zamuyi mata aurene
dan samun nutsuwar ta ba dan a muzguna mata ba, shiyasa tun da fari bamu nemi wani
bare sekai"
Gajeren tsaki Fahad yayi yaja kujera ya zauna tare da dafe kansa.
Kallonsa take yana tuƙi fuskarsa ɗauke da ɓacin rai, tunani take a duk lokacin da
yaga wani na shirin cin zarafinta ko ɓata mata rai se yayi duk me yuwa ya hana
faruwar hakan, a duk lokacin da take cikin damuwa zataga damuwa a fuskarsa, wanda
ko ɓata masa rai tayi be fiye nuna damuwa haka ba.Ajiyar zuciya ta sauke seda Yusuf
ya juyo ya kalleta yace "lafiya kuwa?"
Ta jinjina masa kai alamar eh, haka suka koma gida ranta a matuƙar ɓace.
Anwar suka gani a harabar gidan, ya ƙaraso da sauri inda take yace "Widad ina kika
jene? Tun ɗazu nake dubaki a gidan nan ban ganki ba" yai maganar cike da damuwa.
Widad tace "Anwar bana son daga dawowarka ka fara shiga cikin matsalolin gidan
nan, zaka fuskanci fushin mahaifiyarka idan haraka cigaba da shiga harkata, am
sorry amma kayi harkokinka inyi nawa please"
Ze sake yin magana tayi gaba ta shige ta barshi a gurin, ya kalli Yusuf yace "ɗan
uwa dan Allah meke wakana a gidan nan ne? Ni gaba ɗaya abubuwan mamaki suke bani"
Yusuf yace "gaskiya nima ban sani ba, tunda nima banfi watanni huɗu da fara aiki a
gidan nan ba, bakomai nasani ba, sedai damuwa na damunta sakamakon Auren da za'ayi
mata, bata fiye son a shiga harkar ta ba idan tana cikin damuwa shine kawai abunda
nasani"
"dan Allah wai dama maganar Auren nan dagaske ne?"
"Eh gaskene" Yusuf ya bashi amsa
"Impossible" Anwar ya faɗa da ɗan ƙarfi
"Ni Fahad zeyi wa haka? Saboda cin amana da wulaƙanci" Anwar ya girgiza kai ya koma
cikin gida fuskarsa ɗauke da ɓacin rai.
Washegari da safe Yusuf ya shirya ya fita, seda ya fara biyawa gidan Abbas amma ya
tarar baya nan, kamar yaje office amma ya fasa ya wuce gidansu Widad.
"Yusuf gimbiyar masu gida da kanta ta fito nemanka, da alama ka makara fa"
Yusuf yace "wani abune ya ɗan tsareni, bari inje in ganta"
Murtalah yace "tana lambu ita da tsuntsayenta da ƙanwarta wato kyanwarta"
Yusuf yayi murmushi ya nufi lambun, kamar yadda Murtalah ya gaya masa tana lambun
ita da magenta Roux, magana takewa magen nata kamar da mutum take magana tana cewa
"Roux har yanzu Daddy yana fushi dani, gaba ɗaya duniya tamin zafi, ba wanda ya
goyi bayana ko ya tausayawa halin da nake ciki, ba zan iyayiwa Daddy biyayya in
Auri Fahad ba, ji nake kamar zuciyata zata tsaya saboda ɓacin rai, amma dole in san
hujjar da zan gabatarwa Daddy da zesa a fasa Auren nan, am so much disturbed Roux"
Tana maganar tana shafa jikin magen, yayinda magen tayi luf a jikin Widad kamar
tasan me take gaya mata, lokuta da dama Yusuf yana jin Widad tana hira da Mage,
hirar da be taɓa jin tana yi da ɗan adam cikin mutuntawa da nutsuwa haka ba.
Ji tayi kamar ana kallonta ta ɗaga kai suka haɗa ido da Yusuf, ta tsuke fuska tace
"baka iya Sallama bane?"
"Ai idan nayi sallama bakya amsawa" ya bata amsa
"Se yanzu kaga damar zuwa ko?"
"Umma na taya aiki shiyasa banzo da wuri ba"
"shikenan, zamu fita yau ƙarfe tara"
"Amma ai tara ta wuce yanzu, sedai ta gobe in Allah ya kaimu"
"tara na dare" ta bashi amsa
"tara na dare kuma? Ina zamuje haka da daddare? Kuma mu dawo yaushe? "
Ba tare da ta kalli Yusuf ba tace "hmmm akwai ka da ƙwarin gwiwa, ƙarfin hali bin
ƙwaƙwƙwafi da sa ido sekace ɗan Sanda ko wani jami'in sirri, za kayi kyau da Aikin
ɗan sanda ko kuma fannin shari'a"
Wani abune ya tsarga tun daga kan Yusuf har yatsunsa na ƙafa.......
(INA BUƘATAR JIN SHARHINKU FANS, ME KUKE TUNANI NE AKAN WANNAN TURKA TURKA, INGA
COMMENTS ƊINKU KO IN KOMA POSTING DA TSALLAKEN KWANA ƊAYA)
Share and share please domin sharhi, gyara ko shawara Ayshercool 07063065680
_*AƘIDATA*_
PERFECT WRITERS ASSOCIATION
(WE AIN'T PERFECT BUT WE ARE ALWAYS TRYING OUR BEST, TO MOTIVATE AND ENTERTAIN OUR
READERS)
https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/
*Story and written by*
_*AISHA HUMAIRA (Daddy's girl)*_
The experience writer of *ABDUL JALAL** WATA KISSAR.... (SAI MATA) *And now *AƘIDA
TA *
I dedicated this book to my Mum (Malama Nafisat Adam Muhammad) i love you mum
Haƙƙin Mallaka ⚠ : Littafin nan mallaki nane, tun daga sunan labarin zuwa abunda ya
ƙunsa, ban yadda wani ko wata ya sauyamin ko yin Amfani da wani ɓangare na labarin
ba ba tare da izinina ba, Nagode
https://www.wattpad.com/user/Ayshercool7724?
utm_source=android&utm_medium=link&utm_campaign=invitefriends
ELEGANT ONLINE WRITER'S
PART1 Page 20_21
Widad ta cigaba da cewa "da aikin shari'a zakayi zeyi wuya a iya kada kai, yakamata
Alhaji Nasir yayiwa yayansa wani abu, yakamata ya nema maka makaranta ko dai
horarwa akan aikin tsaro kokuma a nema maka aikin shari'a" ta ƙarasa maganar da
wani ɗan guntun murmushi
Yusuf ya daskare ya kasa ko motsa ɗan yatsansa 'Widad ta gano shine kokuwa?'
"Jeka in lokacin yayi kazo mu tafi"
Kasa motsawa Yusuf yayi, ya tasaya yana kallon Widad, ta ɗago ta kalle shi tace "ya
dai naga ka tsaya? Meyafaru?"
Girgiza kai yayi ya juya ze fita, beji takuma cewa komai ba.
Tunani ne ya shiga zarya a zuciyarsa, kodai Widad tasan waye shine? Amma ya tuna da
sharaɗinta bata yafewa wanda yayi mata ƙarya, a rashin yarda nan tata tabbas da
tasan waye shi da tuni tayi maganinsa ta ɗau mataki akansa.A hankali ya furta
"Ubangiji Allah ka shiga lamarina, Allah yasa har in kammala aikin nan yarinyar nan
ba zata ganoni ba"
*****************************
"Amma ni tabbas ba'ayimin Adalci a wannan lamarin ba, nida ɗan uwana ku kusan
halaka shi sannan ace bazan ganshi ba, wannan wane irin zalunci ne"
"zaka iya kiransa da duka abunda kaga dama, amma tabbas ba zaka ganshi ba, zamu ci
gaba da ajiye shi a ɓoyayyen guri har se sakamakon binciken nan yazo hannun mu"
Saleh yace "binciken nan bani na yake yi ba, kun san hukumar da sukeyi meze sa ku
cigaba da azabtar min da ɗan uwa"
"saboda shi kaɗai ne hujjar daze fallasa komai a kotu, kuma yana nan shirin tona
mana Asiri dan haka gara muyi maganinsa"
Cike da damuwa Saleh yace "to ai wanda yake ƙoƙarin samo min sakamakon anyi masa
transfer ya kuke so inyi, ni ko ganinsa inyi shikenan"
Alhaji Musa yace "baja da wannan damar Saleh, kayi abunda muka ce kawai"
A fusace Saleh ya miƙe ya bar gurin zuciyarsa na masa zugi, tabbas su Alhaji Musa
masifa ne a rayuwarsa da ɗan uwansa.
Anwar a cikin ɓacin rai yaje ya samu Fahad a gida, Fahad na ganinsa yace "Ohh God,
Anwar ai namanta gaba ɗaya jiya zaka dawo am so sorry brother"
Jiki a sanyaye Anwar ya kalli Fahad yace "Am disappointed Fahad, dole kace ka manta
jiya zan dawo, yanzu Fahad yarinyar dana daɗe ina mafarkin aura ita zaka aura?"
Ajiyar zuciya Fahad yayi yace "am sorry, nima bani nace ina son ta ba cusa min ita
akayi akace sena Aureta dan anga tana da taɓun hankali"
"Fahad, Widad ba irin matan da za'a cusawa mutum bane, sannan idan har cusa maka
ita akayi saboda taɓin hankali, ni ka barmin ita in aura tunda ni ina son ta"
"nice maka akayi bana sonta? Ko kuma so kake in kalli mahaifina ince zan bijirewa
umarninsa"
Anwar yace "ni bahaka nake nufi ba amma nasani ka sani Baka dace da Widad ba, nasan
halinka gaba da baya"
"kasan halina amma ka barni nake soyayya da ƙanwarka? Ko abun naka son zuciya ne?"
"son zuciya be wuce wanda ake shirin yiwa Widad ba, Ramla tasan dai dai tasan
abunda take yi dan haka idan ta zaɓeka a matsayin miji ita taso hakan, Amma Widad
fa Yarinya ce sannan...
"kaga Anwar ya isheni haka" Fahad yai maganar a tsawace
"Idan har ba so kake abotarmu ta samu matsala ba ka ƙyaleni, ka fita daga batun
Auren nan"
"Idan kuma naƙifa?"
"Komai ze iya faruwa"
Anwar yace "to sonake koman ya fary Fahad, naga baka gane rarrashi zan ɓullo maka
ta inda ya dace"
Fahad yace "Anwar karka kuskura kaje ka faɗi wani mummunan abu a kaina a gurin
mahaifin Widad"
"Fahad dani da kai a ƙarƙashin kulawarsa mukayi karatu, ba abunda be mana na gata a
rayuwa ba, bana jin Widad kanta ta moreshi kamar yadda muka moreshi, idan har aka
lulluɓe kura da fatar Akuya ba muyiwa Alhaji Nasir Adalci ba, kaima kasan baka dace
sa Auren 'yarsa ba"
"Amma Anwar kasan taimakawa zan in Aureta tunda mahaukaciya ce?"
"kabar taimakon naka mana, kaje ka auri Ramlah"
"Amma Anwar meyasa kake fifita Bare akan ƙanwarka? Idan har dagaske kake Ramla
yakamata kace bazan Aura ba"
"Fahad ba goyon bayan bare nake ba, goyon bayan gaskiya nake kuma kaima ka sani"
Yana gama maganar ya fice a fusace cikin sauri.
**********************************Ɓangarren Nurat kam lamarin mahaifinta yana bata
mamaki, gaba ɗaya babu wanda ya gane inda yasa gaba daga ita har mahaifiyarta, ga
ta'amali da wasu irin ƙarti da yakeyi wanda daka gansu zaka san ba mutanen kirki
bane, suyita musu zirga zirga a gida, babu me ikon cewa uffan saboda duk tsoronsa
suke ji.
Gefe guda kam tunanin Abokinta ya cika mata zuciya, zuciyar ta na matuƙar begen ta
ganshi amma abu ya gagara, tasan ko giyar wake tasha bata isa taje gidansu Widad
ba, tunda ta dena ɗaga wayarta tasan akwai wata a ƙasa haɗuwarta sa Widad ze iya
haifar mata da matsala ne kawai.
Ba zata iya ƙirga adadin saƙonni da kuma kiran da tayiwa Yusuf ba, gefe guda kuma
dai zuciyar ta na kwaɗai mata son sanin me mahaifinta ke ƙullawa wanda yasa shi yin
mu'amala da wannan mutanen haka, suke ta musu sintiri a gida.
************************************
Anwar ne ya shiga ɗakin Alhaji Nasir da Sallama, cikin sakin fuska ya amsa masa,
sedai mahaifiyarsa tana tare da Alhaji Nasir ɗin a wannan lokacin, fuskarsa ta nuna
yana cikin damuwa kuma yana son yin magana ne.
Alhaji Nasir yace "shigo mana Anwar"
Anwar ya ƙarasa ya zauna a ƙasan carfet yana sunkuyar da kai, can yace"Daddy, naji
ka yanke wani hukunci, wai dagaske nan da ƙarshen wata zaka aurar da Widad?"
"eh hakane Anwar, halin ƙanwar taka ne se ita, gashi har yanzu ciwon ta yakan
tashi, bekamata ace mamanku ta cigaba da ɗawainiya da ita ba, akwai buƙatar itama
tayi Aure tunda ta girma"
"Amma Daddy kayi bincike akan wanda zaka bawan kuwa?"
Alhaji Nasir yace "bafa wani ne ba, Fahad ne ba wai wani guri aka samo mata mijin
ba, Fahad ne Abokin ka ɗan gidan Bulama"
Irin mugun kallon da mahaifiyarsa ke jifansa dashi ne yasa ya kasa cewa komai yace
"shikenan Daddy, Allah ya Sanya alkhairi ya kaimu lokacin"
Ya tashi gwiwa a saɓule yana kallon mahaifiyarsa ya bar ɗakina.
Alhaji Nasir yace "Halima kaman akwai abunda yake damun Anwar amma ya kasa faɗa"
"ba abunda yake damunsa, naga dai kamar ya ɗan damu ne da batun Auren Widad"
"ko dai yana sonta ne?"
Da sauri tace "A'a kasan halinsa dai da tausayi, da yana son ta ai da tuntuni ya
faɗa"
"hakane, aikam da ban bawa Fahad ba da Anwar zan bawa, dukda gaba ɗayansu 'ya' yana
ne, amma wata kusan ai tafi wata"
"hakane kam, Allah ya wuce mana gaba"
Bayan ta sallami Alhaji Nasir, ta fito ta tafi ɗakin Anwar, yana zaune a bakin gado
ya dafe kai yana tunani, jin motsin shigowarta ne yasa shi ɗagowa ya kalleta,
Hajiya Halima tace"kaga Anwar zuwa nayi in sake yi maka kashedi, wallahi tun wuri
ka fita daga harkar Auren nan, wai ƙanwar uwarkace ita kota ubanka? Ka shiga
hankalin ka na gaya maka"
Fahad yace "Allah ya baki haƙuri, Insha Allah zan kiyaye, amma dai Fahad be dace da
Aurenta ba"
"da anyi magana ka iya bada haƙuri ai, ko waze aurawa ina ruwanka, shi ya haifeta
ba in ya ga dama yaje ya aurawa kare ita mana ina ruwan wani?"
"Amma Mummy ya zakiyi da Ramla da take mutuwar son Fahad?"
"Ai magana ta ƙare tunda Fahad ze auri mahaukaciya, Allah ya bata wanda ya fishi
seta haƙura"
"Amma ba kya tunanin yadda take son shi hakan ya haifar da matsala?"
"Kai rufemin baki, Allah ya tsaremu da matsala ina sake jan kunnenka ka fita daga
sabgar yarinyar nan, in kuma kaƙi ji baka ƙi gani ba"
Anwar ya bita da kallo yayin da ta bar ɗakin, ya girgiza kai tare da sauke ajiyar
zuciya.
Yusuf yana zaune a mota yana ɗan danna wayarsa yana jiran fitowar Widad, be san ta
taho ba kawai yaji ta buɗe motar, da sauri ya ɗago ya kalleta, wato abun nata
kullum ƙara gaba yake, yau shigar tata tafi ta kullum muni, kamar yadda ta saba
gaban mota ta shiga garin zama seda jikinsu ya gogi juna, amma kowannensu ya basar.
Shiru Yusuf yayi bece komai ba, ta ɗakko wayarta ta miƙa masa, ya karɓa ya duba,
kwatancen idan zasuje ne ya sake duba agogon hannunsa ƙarfe tara daidai na dare,
zuba mata idanun yayi yayinda itakuma take kallon wani gurin.Ba zato yaji ta fizge
wayarta daga hannunsa tace
"malam bana son kallo"
"Aikuwa kallo kin gamu dashi muddin da wannan shigar zaki fita" ya bata amsa
"shikenan cigaba da kallona karka fasa, wallahi kasa na makara zuwa inda zanje se
nayi mummunan ɓata maka rai"
Ta faɗa in a very serious tone, haka yaja motar suka fita, gaba ɗaya jikinsa babu
ƙwari yake tuƙin.
Yusuf be tsinke al'amarin ba seda yaga sun iso wani katafaren Club a cikin sabon
garin Kano, kallon Widad yake yaga me zata yi ganin yadda zaratan karuwai da 'yan
iska ke shiga suna fita a gurin.
Yunƙurawa tayi da nufin buɗe ƙofar taji yasa lock, ta kalle shi tace "buɗeni zan
fita"
"kije ina?"
"inda ka aikeni" ta faɗa cikin fushi
Gyara zama yayi ya ɗauke kansa daga kallon ta.
"magana fa nake maka"
"idan har na bari kika shiga wannan gurin a haka, ba yiwa kaina adalci ba kuma
Allah ze kamani da laifin cin Amana"
"Dalla ka rufemin baki, ina ruwanka da nine? Ina ruwanka da rayuwata na gaya maka
kadenamin shishshigi fa bana so, ina kunyar Daddy ne ba dan haka ba da tuni na daɗe
da karta maka rashin mutunci"
Kashingiɗa Yusuf yayi yace "kin daɗe baki yi ba, rashin mutunci wanne ne bakimin
ba, ba wanda ban gani ba, dan haka duk wanda kika yi zan shanye amma ba zaki shiga
gurin nan ba"
A cikin matuƙar hasala tace "ka buɗemin ƙofa Malam, nima karuwanci nazo yi gurin
nan ka ƙyaleni inyi rayuwar da naga dama"
"Aikuwa da ajinki ya zube beb, duk yadda kike yanƙwana gayu kizo nan kiyi karuwanci
ba class, ki canza guri mana"
Wani ƙululun baƙin ciki ne ya tokare zuciyarta, wai ita Widad yau direbanta yake
yanƙwanawa yana raina mata hankali yadda yake so, hakan be taɓa faruwa ba a tarihin
rayuwar ta
"Naji ajin nawa ya zube, malam ka buɗen ƙofa nace"
Ramawa Yusuf yayi kamar yadda takewa mutane, yayi kamar baya jin me take faɗa.
Jikinta har rawa yake saboda masifa tana zazzagawa Yusuf faɗa, a zafafe ta miƙa
hannu zata yi unlocking ɗin motar Yusuf ya riƙeta, a tare suka ji wata irin faɗuwar
gaba, Jikin Yusuf har rawa yake dan besan yadda akayi ya riƙeta ba, yayin da nata
ƙirjin ya dinga bugawa fiye dana Yusuf.
Tattaro Jarumtarsa yayi ya maida ita seat ɗinta, ya saka mata seat belt yaja motar
ya bar gurin.
Widad zata iya cewa tunda take bata taɓa haɗuwa da mutumin daya raina mata hankali
kamar Yusuf ba, dukda yana matuƙar yi mata biyayya tabbas yau ya tsallake iyakarsa,
da yasan me tazo yi a Club ɗin da be mata haka ba, dole ta nuna masa munin kuskuren
daya aikata yau, bata kuma ce masa uffan ba.
Ta naji tana ganin ya maida ita gida, zuciyarta na cigaba da tafasa kamar ta tsaga
ƙirjinta.
Seda suka koma gida sannan yayi parking, ya fito ya buɗe mata ƙofar motar, ta fito
ta tsaya ta saka idonta a nasa tace
"ban taɓa sanin baka da hankali ba se yau, kana tunanin na manta da contract ɗin
daka sawa hannu? Harka samu damae da zaka nunamin ban isaba, saboda jahilci da
rashin tunani irin na talaka, kasan me na jeyi gurin? Har zaka nunamin isa da Izza,
ina ruwanka dani meyasa kake son zaƙewa cikin al'amuran rayuwa ta?, ko dan ina ɗaga
maka ƙafa shiyasa kake ƙoƙarin takani, yau zan nuna maka ka saɓamin doka kuma dole
ka karɓi hukuncin abunda kayi, banza mara amfani ka lalata min komai saboda Jahilci
da son nuna kai wani ne, kamin hauka da wauta ka wargazamin komai saboda ƙaramin
tunaninka, Amfaninka shine kamin aiki in biyaka amma ka zaƙe, dan haka zan nuna
maka kai ba wata tsiyar bane a gurina kuma ka tsallake gona da iri "
Shiru Yusuf tayi seda ta gama sannan ya kakmeta yace " da bani da amfani da Allah
be halicceni ba, babu wata halitta da Allah yayi wadda bata da amfani, tunda bani
da Amfani zan ƙyaleki ki amfani kanki, tabbas da Allah yayi kowa me kuɗi da babu
wanda zeji daɗi, kuma babu wanda ze mori wani, talaka yana da amfani, muma ba laifi
mukayi wa Allah yayi mu a ƙarƙashin ku ba"
Yasa hannu a aljihunsa ya ɗakko key ɗin motar, ya kamo hannunta yace "bani da
Amfani, dan haka ki nemo me Amfani ya cigaba da yi miki aiki, idan harni ɗan halak
ne bazan ƙara miki aiki ba, ga mukullayenki nan talaka mutum ne kuma yana da zuciya
tunda iyayene suka haifemu kamar yadda aka haifeki" . Ya ɗanƙa mata key ɗinta a
hannu, jifa tayi da mukullayen tace "baka isa ba, wallahi yadda kasa hannu a
takardar yarjejeniyar ka fara aikin seka kammala shi, se anje ƙarshe da kai"
"sedai ki nemo me Amfani yayi miki amma bani ba"
cikin gida da sauri, hakan yayi daidai da shigowar motar Anwar.
Tana zuwa ɗaki tayi jifa da kayan hannunta ta shiga sintiri hawaye na bin idonta
tace "shikenan babu wanda ze fahimci halin da nake ciki? Wannan banzan ya ɓata min
shirina ya wargaza komai, me yake tunani ne? Har na bashi damar daze shiga rayuwata
haka ya yanke min hukunci, yanzu ina hukunta shi kuma Daddy ni ze ɗorawa laifi"
Anwar ne ya shigo da sauri ɗakin yace "Widad lafiya kuwa? Meke faruwane?"
Girgiza masa kai tayi tace "bakomai"
"a'a ya bakomai naga kamar kuna cacar baki da direbanki, kuma gashi kina kuka
meyafaru"
Shiru tayi masa ta wuce kan gadonta tayi zamanta.Kusa da ita yaje ya zauna yace
"dawowata naga abubuwa daban daban wanda suka bani mamakiba gidan nan, wanda ban
gane kansu ba, gashi Daddy yace wai Aure ze miki, meyasa zaki Auri Fahad"
Kallon Anwar tayi amma taƙi cewa komai.
"Say something please"Lumshe ido tayi taƙi magana, duk yadda Anwar yayi taƙi magana
haka ya ƙyaleta ya bar ɗakin jiki ba ƙwari.
Yusuf kam har ya koma gida zuciyarsa na tafasa, wai shine mara Amfani a tarihin
rayuwarsa babu irin kalar cin zarafin da ba'ayi masa ba ya jure, Amma yau na Widad
yaji zafinsu sosai.Haka ya ƙarasa gida, Umma ta lura tunda ya dawo baya walwala
sosai dan haka tace "tilo meke faruwane? Naga kamar ranka a ɓace yake"
"bakomai Umma"
"bana son fulatanci fa, ko kana da wanda zaka gayawa damuwar ka bayan ni?"
Girgiza kai yayi yace "Umma na rasa abunyi gaba ɗaya, Anyiwa Abbas transfer,
yarinyar da nake wa aiki mun samu matsala na ajiye aikin, gashi ban sanar da
shugabanni na ba kafin in yanke hukuncin, kuma ba aikin direba kawai nake mata ba
kare lafiyar ta nake, ba ƙaramin hatsari take ciki ba ga mahaifinta wai Aurar da
ita zeyi, Umma abubuwan dayawa nama rasa me zanyi "
"Allah sarki Jarumin ɗana, tun tasaowarka da jarumta na sanka da juriya meze sa ka
karaya a wannan lokacin? Ni kaina ina jin tausayinka amma kasa Allah a lamarin ka
sannan kayi haƙuri da komai, ɗaukaka bata zuwa ana kwance ba zato Aka ƙara maka
matsayi a gurin aiki, jajircewarka ce tasa suka baka, dan haka ka zama Jarumi
Yusufa, nan gaba iyali zaka riƙe kaga zama da mata se kayi haƙuri se Jarumin gaske,
lokuta da dama bama gane Amfanin mutum se bayan ya matsa daga kusa damu"
Kallon Ummansa yayi yace "wani irin iyali kuma?"
"kayi Aure mana kaima ka hayayyafa, nima inga jikokin tilon ɗana"
Girgiza mata kai yayi yace "na yanke ƙauna Umma, kiyi haƙuri mu ƙarasa rayuwar mu
a haka, nima na isheki"
"haba Yusuf, me rai ai baya yanke ƙauna daga rahamar ubangiji, dole kayi Aure
wataran"
"Umma bana son tarihi ya maimaita kansa, bana son abunda ze sake ɗaga mana hankali,
dan haka mu bar wannan maganar seda safe"
Ya miƙe yana tafiya a hankali ya bar ɗakin, Umman Yusuf ta dafe kai tace "Allah ka
kawo mafita da sauyi na alkhairi ga rayuwar wannan bawa naka, Allah ka kawo masa
mafita ka yaye masa damuwarsa"
Yusuf ya kashe wayoyinsa gaba ɗaya, baya fita ko'ina kullum yana gida, Dama bashi
da wasu abokai a unguwar, dan haka baya zuwa ko ina.Umma bata takura masa ba ta
ƙyaleshi.
Widad kam tun daga ranar ko falo ta dena fitowa, Daddy kam dama ba shiga harkarta
yake ba, se bayan tafiyar Yusuf ta gane Amfaninsa ta ɓangarori daban daban, gashi
taga dagaske Yusuf ya dena zuwa gidan kwata kwata.
Haka nan Alhaji Nasir yaji ya damu da son ganin 'yar tasa dan ba ƙaramin missing
ɗinta yake ba, yanzun ma ya danne zuciyarsa ne kawai dan ya samu ta saduda amma
abun ba sauyi.
Part ɗinta ya tafi domin ya ganta, sedai yana zuwa bedroom ɗinta ya tarar ta
rurrufe ko'ina, da sauri ya ƙarasa ya tura ƙofar ɗakin nata, ɗakin duhu ta kashe
fitulun ɗakin, kunna fitilar ɗakin yayi haske ya gauraye ko ina, yana kunna fitila
ta saka ihu ta shige cikin bargo.
Da sauri Daddy ya ƙarasa yace "innalillahi wa inna ialaihi raji'un, Babyna nine fa
Daddy ne ɗago ki ganni"
Dunƙulewa ta sake yi tana karkarwa, a hankali ya ƙarasa ya ɗagota sedai taƙi yadda
su haɗa ido.
Daddy ya girgiza kai yace "ciwon ne ya dawo again? Kalli Yadda kika rame lovely,
subhanallah meke damunki ne haka?"
Ba tace komai ba sedai kwantar da kanta da tayi a jikin Daddyn nata, jikinta kamar
ana girgizata.
Yusuf ya ɗakko tsohon layinsa yasa a waya, sedai yana sakawa yaga saƙonnin Nurat na
shigowa, messages ɗin ya shiga dubawa ɗaya bayan ɗaya sedai yana cikin dubawar
kiran Nurat ya shigo wayar, kamar kar ya ɗaga amma ya ɗaga yace
"Assalamu Alaikum"
Wata nannauyar ajiyar zuciya Nurat tayi tace "Aboki anya duniya da gaskiya, ka
manta dani ko?"
"haba ƙawata, ya zan manta dake light, wayata ce ta lalace shiyasa"
"Allah sarki, duk hankalina ya tashi na zata wani abun ne ya same ka"
"ba abunda ya sameni light fatan kina lafiya"
"Lafiya ƙalau, amma ina son ganinka ne Aboki"
"me zaki bani in kin ganni?"
"magana nake so muyi"
"muyi ta a waya mana light, abubuwa sunmin yawa sosai"
Ajiyar zuciya tayi tace "zefi kyau dai in ganka, mahaifina ne naga yana harka da
wasu irin mutane wanda da ganinsu kaga marasa kirki, ga yawan zuwa gidanmu dasu
Alhaji Musa suke yi, kace idan naji wani abu wanda zesa a cutar da Widad in gaya
maka, amma dai ban san meke faruwa ba"
Gaban Yusuf ne ya faɗi cikin sauri yace "a ina zamu haɗune Nurat?"
"nace ina son ganinka kace ba lokaci, amma da yake nayi maganar Widad shine kace
zaka zo"
"yi haƙuri Light"
Nurat tace "sedai kazo gidanmu, babana yana gari baze yuwu mu haɗu ba"
"shikenan insha Allah, zan san yadda zanyi mu haɗu"
"Aboki baka gayamin sunanka ba fa"
"ƙawa zan gaya miki very soon insha Allah, dan Allah in an samu wani update ɗin ki
sanar dani, sannan akwai ajiyata a wayarki ki kula sosai light"
"Ajiya kuma? Wace irin Ajiya?"
Murmushi Yusuf yayi yace"Light, light tabbas ina da Ajiya a gurinki, dan Allah ki
kula da kanki da kuma wayarki, idaan nazo zan nuna miki ajiyar"
"shikenan Aboki, amma dan Allah ka dena rufe wayarka"
"to shikenan insha Allah"
Tunda Yusuf yaji labarin nan hankalinsa ya tashi, ya shiga tunanin ya Widad take,
ba shiri ya miƙe ya shiga shiryawa. Ya fito tsakar gida, Umma ta kalle shi tace "se
ina kuma?"
"zanje gidansu Widad ne?"
"yau kuma, to Adawo lafiya"
Ya amsa da Allah yasa.
Yana zuwa gidan Isa yace "Yusuf ina ka shigane ka dena zuwa gidan nan kusan kwana
tara, me gida yasa an kiraka a waya shima ya kira amma layinka baya shiga, ka dena
zuwa ba tare da wani dalili ba"
Bece komai ba ya shiga cikin gidan da sauri, yana zuwa ɓangarenta ya nufa ya tarar
bata nan, ya fito babban falo yaga Amal.
"Amal dan Allah ina Widad ne"
Banza tayi masa taƙi ce masa komai Anwar ne ya shigo hannunsa riƙe da leda yana
ganin Yusuf yace "bawan Allah kwana da kwanaki ake nemanka baka zuwa, daga samun
saɓani ka ɗauke ƙafa Uwar ɗakinka na neman rasa ranta.
Ba ƙaramin razana Yusuf yayi ba yace " tana ina? "
Anwar yace " tana ɓangaren Daddy "
Da sauri Yusuf ya nufi sashin na Alhaji Nasir yana shiga ya tarar da Widad a zaune
Daddy yana ta aikin rarrashi tace Abinci amma taƙi se kuka take.
Daddy na ganin Yusuf yace "Alhamdilillah, Yusuf ashe zaka dawo saura ƙiris in fita
nemanka da kaina"
Yusuf seda ya firgita Widad ta zabge gaba ɗaya, ta rame sosai ta ƙara haske
idanunta a kumbure, juyawa tayi gaba ɗaya taƙi kallon inda Yusuf yake.
Yusuf yace "Yallaɓai bata da lafiya ne?"
"ciwonta ne ya tashi, ta fara samun sauƙi naga baka zuwa na tambaya, tace min
rigima kukayi ka dena zuwa, na mata faɗa naga ta sake shiga damuwa ga kuma batun
Auren nan, ta dena cin Abinci ko magana taƙiyi, se kuka munyi magana da wani
abokina a Abuja yace akwai babban likitan Ƙwaƙwalwa a international Hospital yana
zuwa ranar Talata, idan ba zaka damu ba dan Allah ina so ka temakamin ku tafi tare,
na yadda da kai Yusuf nasan ba zaka cutar dani ko 'yata ba, tafiyar tazo daidai da
taronmu na shekara idan banje ba akwai matsala, seku sauka a gidan Abokin nawa kuje
Asibitin daga nan duk abunda kukayi kuka gama ranar Monday jirginta ze ɗaga Zuwa
England, ta koma taje ta ɗan huta, kafin in san me ya kamata inyi, naga tafi samun
nutsuwa a can"
Jiki a sanyaye Yusuf yace " Shikenan an fasa Auren nata?"
"eh munyi magana da Bulama, mun yanke shawarar ɗaga Auren se ta samu sauƙi, idan
babu matsala baka da wani abunda zakayi ban takura ka ba seku tafi"
"Shikenan Yallaɓai zanje in shirya insha Allah, Allah ya bata lafiya ko nan da
birnin Sin ne zanje insha Allah "
"to shikenan masha Allah, nagode sosai Allah yayi Albarka ya jiƙan mahaifa, tafiyar
safe nake son kuyi dan kuje da wuri, jibi in Allah ya kaimu zamu kwana a gidan
gona, da an idar da sallar Asuba seku tafi, nace kubi jirgi tace A'a"
"Ameen ya Allah Bakomai Yallaɓai, zanje in shirya insha Allah"
Yusuf a ransa yace 'dole inje wannan tafiya, duk cikin aikina ne'
Kallon Widad yake amma sam taƙi kallon inda Yusuf yake.
Miƙewa tayi ta bar ɗakin daddyn gaba ɗaya.
Alhaji Nasir yace "Yusuf tabbas nasan kana da haƙuri, shiyasa kuka daɗe tare da
'yata, kana da matuƙar tasiri a rayuwarta ko yanzu ka canza mata abubuwa da dama na
rayuwarta nagode da wannan namijin ƙoƙari da sadaukarwa ga' yata"
"bakomai Yallaɓai Allah yasa a dace, Allah ya bata lafiya"
********************* **************
"Masha Allah, komai yana tafiya yadda muka tsara, komai zezo ƙarshe koda tsiya koda
tsiya tsiya se mun mallaki abunda muke so" cewar Alhaji Munir
Alhaji Musa ya kwashe da dariya yace "tabbas haka maganar ka take, nayiwa yaran
nan jan kunne yadda yakamata baza'a samu matsala ba Saleh yace ze sanar damu duk
wani abu da ake ciki"
Alhaji Munir yace "ƙunrunƙus, yayin da muka ɗauke hankalinsa ta ɓangare ɗaya,
ɓangare ɗaya kuma baze halarci taron kasuwanci ba"
Suka ƙyalƙyale da dariya gaba ɗaya.
(RASHIN SANI......)
Share and share please 🙏 🙏 🙏 🙏
Domin gyara sharhi, ko shawaraAyshercool07063065680
_*AƘIDATA*_
PERFECT WRITERS ASSOCIATION
(WE AIN'T PERFECT BUT WE ARE ALWAYS TRYING OUR BEST, TO MOTIVATE AND ENTERTAIN OUR
READERS)
https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/
*Story and written by*
_*AISHA HUMAIRA (Daddy's girl)*_
The experience writer of *ABDUL JALAL** WATA KISSAR.... (SAI MATA) *And now *AƘIDA
TA *
I dedicated this book to my Mum (Malama Nafisat Adam Muhammad) i love you mum
Haƙƙin Mallaka ⚠ : Littafin nan mallaki nane, tun daga sunan labarin zuwa abunda ya
ƙunsa, ban yadda wani ko wata ya sauyamin ko yin Amfani da wani ɓangare na labarin
ba ba tare da izinina ba, Nagode
https://www.wattpad.com/user/Ayshercool7724?
utm_source=android&utm_medium=link&utm_campaign=invitefriends
ELEGANT ONLINE WRITER'S
PART1 Page 22_23
Yusuf yaso yabi bayan Widad dan ya duba ta, amma yasan halinta tsaf zata
yanƙwanashi, dan haka ya yanke shawarar tafiya kawai.
Office ya wuce kai tsaye, ya tarar da Suleiman yana shirin fita suka gaisa Suleiman
yace "Yusuf akwai wani update ne"?
"Eh yallaɓai gurinka ma nazo"
"shikenan mu koma ciki" suka juya zuwa cikin office ɗin gaba ɗayansu.
Nan Yusuf ya zayyanewa Oga Suleiman komai da yake wakana, akan harkar binciken da
batun tafiyar da za suyi, da abunda Nurat ta sanar dashi.
Suleiman yace "Amma baka ganin mu haɗaka da abokan aiki, suyi muku rakiya a wata
motar gudun samun matsala?"
Yusuf yace "Insha Allah babu wata matsala Oga, kasan a slide mistake yarinyar nan
zata iya ganewa nikuma bana son ta gane komai a yanzu har bincikenmu ya kammala".
"shikenan Yusuf Allah yayi mana jagora, Insha Allah zakayi Nasara ana ta samun
haske akan lamarin, bari ni zan fita ne yanzu zanje headquarter"
"to shikenan Yallaɓai a sauka lafiya"
Bayan tafiyar Suleiman Yusuf ya fito yana shirin tafiya, Suka haɗu da Sakina,
Sakina tace
"Ashe yau ka samu ka shigo, ban samu na maka murnar ƙarin matsayi ba, Allah ya
tayaka riƙo"
Yusuf yace "Ameen nagode"
"sannan ina tayaka murnar rabuwa da mugun aboki wato Abbas"
Cikin mamaki da rashin fahimta yace "kamar yaya?"
"Kamar yadda na gaya maka, Allah ne ya dube ka ya rabaku, a baya nasan koda na faɗa
ba zaka yadda ba, yanzunma ban sa ran ka yadda ba amma wataran zaka ce na gaya
maka, Allah ya bada sa'a ya tayaka riƙo"
Tayi gaba ta bar Yusuf a gurin yayinda ya bita da kallo.
Da Yusuf ya koma gida yayiwa Umma bayanin tafiyar da zasu yi ya raka Widad, da
farko taƙi yadda tace sam bata san zance ba.
Yusuf yace "haba Umma, ya za'ayi nida na ɗau Alƙawarin Yiwa jama'a aiki aikin ya
taso kice baza'ayi ba, bayan ke kike cewa inyi gaskiya a aikina? Kina so in bari a
cutar da ita ne, ba zan iya jure in ga wani mummunan abu ya sameta ba"
"nifa na kasa gane meke wakana tsakaninka da wannan uwar ɗakin, ka damu da ita
dayawa"
"ba wani abu da yake wakana Umman Yusuf, kawai dai mahaifinta na mutuntani ne
sosai"
"shikenan Yusuf, Allah ya bada sa'a zanyi kewarka zakayi kwanaki ba tare da Umma
ba"
Yusuf yace "nikaina ina tunanin hakan, Amma insha Allah ba abunda ze faru kwana
biyar ne kawai tafiyar"
"to Allah ya bada sa'a"
Ya amsa da "Ameen"
Haka nan Umman Yusuf take jin kamar akwai wani abu daze faru dalilin tafiyar nan,
sedai ta kasa gane na daɗine ko akasin hakan.
Rana bata ƙarya sedai uwar ɗiya taji kunya, Yusuf ya shirya jakarsa da kayansa da
ze dinga sawa da ɗan sauran kayan buƙatarsa a traveling bag.
Yaje gaban Ummansa yace "Umma na fito zan tafi, zan kwana a gidan gobe in Allah ya
kaimu da Asuba zamu tafi"
Umma ta riƙo hannun Yusuf tace "ka kula da kanka Yusuf, kai kaɗai ka ragemin,
Allah yayi maka Albarka ya sadaka da dukkan Alkhairi, Allah yayi maganin maƙiyanka
ya karemin kai.."
Kasa ƙarasawa tayi ta fashe da kuka, gaba ɗaya jikin Yusuf yayi sanyi yace "Umma ko
in fasa tafiyar nan?"
Ta girgiza kai da sauri tace "A'a bakomai yi tafiyarka, ban san kayi nesa dani ba
shiyasa naji ba daɗi"
Haka sukayi Sallama ya tafi.
A can gidansu Widad da yaje, yaje ya sameta a ɗakinta tana ta aikin kuka, magenta
se kewayata take itama tana kuka gwanin ban tausayi.
A sanyaye Yusuf yace "waike abun kuka baya miki wahala, kiyi ta azabtar da
rayuwarki, kiyi haƙuri ki dena kuka koma meye yake damun ki Allah yana sane dake"
Sallamar Alhaji Nasir ce ta katse Yusuf daga maganar da yake yi
"Yusuf ka shirya ne?"
"Eh ranka ya daɗe na shirya ni"
"to shikenan ta haɗa nata kayan, bayan la'asar semu tafi can farm house"
Yusuf yace "to shikenan ranka ya daɗe"
Alhaji Nasir yace "daughter ki tashi ki haɗa kayan naki, ya kaiki gidan daddynki
Bulama kuyi sallama"
Cikin kuka Widad tace "bazan ƙara zuwa inda yake ba, baya sona yafi san ɗansa"
Alhaji Nasir yace "Allah ya baki haƙuri tashi ki hada kayan, ko inyiwa Halima
magana tasa a haɗa miki"
"Ni ba wanda ze haɗamin, zanyi da kaina"
Haka Widad taita daru san ranta, Daddy ya dena mata faɗa lallaɓata yake yanzu.
************************************"Daddy wai yanzu shikenan an fasa ɗaura mana
Auren?"
Bulama yace "Eh, an ɗaga dai akwai buƙatar taga likita, har yanzu bata da lafiya"
"Daddy wane irin likita kuma? Naga dai da hankalinta ba hauka take tuburan ba"
"eh mahaifinta ne yacemin akwai buƙatar a barta ta ɗan huta, dan gaba ɗaya tana
nema ta illata kanta, ta damu sosai bata son Auren nan, dan haka ma zata Wuce
England ta huta"
"wace irin maganace wannan, an samin rai kuma ace an fasa?"
Mahaifiyar Fahad dake gefe, tunda suka fara magana ba tace komai ba se yanzu tace
"kai Dalla Allah ya rufa maka Asiri kana nema ka tonawa kanka, Allah ya rabaka da
Auren mara tarbiyya mahaukaciya"
Fahad yace "Ni gaskiya ina sonta a haka, kuma nasan Anwar ne yaje ya kai gulma ta
gurin Alhaji Nasir, shiyasa yace haka, ko yana so ko baya so se anyi auren nan dani
mu zuba mu gani"
Bulama na ƙoƙarin dakatar da Fahad, amma yaƙi tsayawa ya fice.
Yana fita ya ɗau mota ya nufi unguwar su Widad, yana zuwa beyi wata wata ba ya nufi
boys quarters inda Sashin Anwar yake, Anwar yana zaune yana kallon labarai Fahad ya
shigo bako sallama.
Anwar yace "Lafiya zaka shigomin ba sallama?"
"dole ka tambayi lafiya mana, ai ban san haka kake ba, ban san ka iya munafunci ba
se yau, saboda rashin son cigabana shine ka shiga ka fita aka ɗaga Aurena da Widad
bayan ina can inata shiri"
"kamar yaya kenan? Waye ya gaya maka ni na hana aurenku ko nace a ɗaga?"
"Au kai tunaninka wanine ya gayamin, bayan da bakinka kazo ka faɗamin, kayi Nasara
Amma kasani Aure yana nan daram tsakanina da ita kuma se nayi maganinka"
Anwar yace "Yanzu Fahad akan Mace kakemin wannan cin mutuncin? Ina ɗan uwanka kuma
abokinka?"
"na maka ɗin, haifata kayi da ba zan maka ba?"
"Ni bam rufe ido maci mutuncinka ba saboda cin amanar abota na amincewa da Auren
Yarinyar da nake so, se kaine zakamin?"
Fahad yace "Ai ban ma yi maka komai ba, kuma wallahi ko bangon duniya zata zan bita
sena Aure ta"
Anwar ya kashingiɗa a jikin kujera yace "Ashe dai haɗin da'akayi ita za'afi cuta,
saboda naka haukan yafi nata fitowa"
"Anwar ni kake cewa mahaukaci?"
Banza Anwar yayi masa be kuma ce masa komai ba
"zakaga ƙarshen rashin mutunci kuwa"
"Ya ƙare akanka" Anwar ya bashi Amsa
A fusace Fahad ya baro part ɗin Anwar yana huci, yana ƙoƙarin shiga motarsa Ramlah
ta ƙaraso da sauri tana faɗin haba "Fahad yanzu har kazo gidan nan amma ka tafi ba
tare da ka ganni ba"
"Am sorry, zuwan gaggawa ne shiyasa yakike?"
Ramlah tace "gaskiya ban yadda ba, kazo mu shiga ciki"
"A'a Ramlah ina sauri ne, zamu haɗe insha Allah"
Ya shige mota ya bar Ramlah a gurin.
Da Yamma ƙarfe huɗu Yusuf ya shiga gidan, sedai yaga Hajiya Halima na masa wani
irin mugun kallo, wanda be gane dalilin hakan ba, ko kulata beba ya wuce part ɗin
Widad.Tana zaune a gefen gado tana shafa jikin magenta, tayi shiru kana kallonta
zaka san ɗauke take da damuwa.
Yusuf yace "Ya jiki kuma?"
Wata uwar harara ta aika masa ta ɗauke kanta.
Akwatunan ta data shirya manya guda biyu da ƙarama, abun har mamaki ya bawa Yusuf
me zata yi da wannan uban kayan haka oho?
Ya ɗauki trolleys ɗin ɗaya bayan ɗaya ya kaisu Mota.
Alhaji Nasir ya fito cikin shirinsa tsaf, yaje ya fito da Gimbiyar 'yar tasa a falo
yana shirin fitowa Hajiya Halima ta tarar da shi tace "Nifa Alhaji ban gane ba?
Ina zaka ne haka ba bayani, naga har ana fita da akwatuna"
Alhaji Nasir yace "eh zamu ɗan fita ne, ba zamu kwana a gida ba Lovely zataje Abuja
ganin likita daga nan kuma zata wuce UK"
"Amma shine baka gayamin ba se yanzu, sekace kana zaman gaba dani? Ace Widad zata
tafi amma baka gayamin ba"
Wata uwar harara Widad ta aikamata dashi haɗe da tsaki tayi waje abunta, Yusuf ma
be tsaya a gurin ba yabi bayan Widad a hanyar da zasu fita harabar gidan Amal tace
"Allah ya raka taki gona, ma huta na kwana biyu kafin ki dawo, kai kuma ka dawo ka
sameni"
Daga Yusuf har Widad ba wanda ya tanka mata sukayi gaba, kamar kullum gaban motar
ya buɗe mata ta shiga, shima ya zagaya ya shiga suna jiran fitowar Alhaji Nasir.
Kusan mintuna sha biyar sannan ya fito shima ya shiga motar, Anwar ne ya fito ya
ƙaraso da sauri yace "ina zakuje ne haka Daddy?"
Alhaji Nasir yace "zamuje farm house ne, gobe in Allah ya kaimu Yusuf ze raka
Lovely zataje ganin likita Abuja, idan ta gama zata koma England ta huta"
Turus Anwar yayi yana kallon su, jiki a sanyaye yace "Shikenan, A dawo lafiya Allah
ya kiyaye hanya"
Ya juya ze koma BQ, da sauri Widad ta buɗe motar ta kira sunansa, ya tsaya ta
ƙarasa da sauri inda yake ta kalle shi tace "Anwar lafiya kuwa?"
Anwar ya ƙaƙalo murmushi yace "lafiya ƙalau Widad"
"Amma naga mood ɗinka ya canza"
"zanyi missing ɗinki ne"
Ɗan tsayawa tayi tana kallon sa, jiki a sanyaye tace "Anwar haka kurum naji bana
son tafiyar nan, ji nake kamar akwai abunda ze faru a tafiyar nan, dan Allah idan
na tafi ka kularmin da Daddy dan Allah ji nake kamar wani abu ze sameshi idan na
tafi "
Tai maganar hawaye na bin fuskarta.Anwar yace "Widad akwai matsala ne?"
Girgiza masa kai tayi tace "ni dai ka riƙemin Amana dan Allah"
"shikenan karki damu, Insha Allah zan kula dashi, zakije ki dawo ki sameshi lafiya"
Ta jinjina masa kai tayi murmushi tace "Nagode Anwar"
Ta juya ta koma mota, shikam Yusuf wani takaici ne ya ƙule shi yadda taje ta tsaya
tana magana da Anwar.
Yusuf yaja motar suka nufi gidan gona, tunda ma'aikatan suka ga tare da Alhaji
Nasir ne suka dinga tururuwar zuwa kwasar gaisuwa, dan ya daɗe beje gidan gonar ba,
nan ya dinga musu fara'a ya zolayi wannan ya zolayi wancan yana musu kyautar kuɗi.
Saleh ne ya shigo harabar gidan ya ƙaraso gaban Alhaji Nasir yana murmushi yace
"Barka da sauka Alhajin Allah yaushe rabonka damu a gidan nan, sedai muji labarin
kazo gari "
Alhaji Nasir yace "Abubuwa ne sunyi yawa Saleh ya aikin, ya haƙuri damu?"
Saleh yayi murmushi yace "Yallaɓai ai kuke haƙuri damu"
"to Allah ya ƙara mana haƙuri da juna, zan maka transfer ɗin kuɗi aje ayo order
Abinci gaba ɗaya ma'aikatan gidan nan Vip kowa yaci ya ƙoshi"
"Allah ya temakeka Alhaji namu, Allah ya ƙara nisan kwana da Arziki me Amfani"
Alhaji Nasir yace "Ameen Saleh, soja marmari daga nesa"
Saleh yayi murmushi ya fita, yana fita ya samu wani guri ya laɓe ya ɗakko wayarsa
ya daddana yasa a kunnensa
"Oga sunzo, kuma da alama a gidan nan zasu kwana gaba ɗaya"
"shikenan kasa mana ido akansu sosai, sannan ka lura da motar da zasu yi tafiyar a
cikinta kasa tracker dan karsu tafi kafin su Dage suje"
Saleh yace "shikenan as you wish, amma dan Allah karku saɓa Alƙawari"
"karka damu kai dai kayi abunda muka ce"
Alhaji Nasir ya turawa Seh kuɗi, yayo order Abincin ma'aikatan gidan nan kowa yaci
yasha yana walwala, aka kaiwa Alhaji Nasir nasu, Alhaji Nasir ya haɗe nasa da na
Yusuf yace suci tare, ba ƙaramin mamaki abun ya bawa Yusuf ba, ace babban mutum
kamar Alhaji Nasir yace zeci Abinci kwano ɗaya da ma'aikacin 'yarsa lallai be ɗau
duniya da zafi ba.
Widad kam sam bata walwala, Ƙarewa ma ɗaki ta ɗaya ta samu ta shige tayi kwanciyar
ta.
Yusuf kam suka zauna da Alhaji Nasir suna ta hira, kamar ɗa da Uba yana bashi
labarin tafiye tafiyen da yayi da ƙalubalen kasuwanci da kuma nasarorin daya samu.
Can Alhaji Nasir ya nisa yace
"kaga gidan nan shine gidana na asali, ina jin daɗin unguwar nan amma tun bayan
rasuwar mahaifiyar Widad naga bata son zaman gidan, saboda ita na canza gida, nan
kuma aka zuba dabbobi a wani ɓangaren saboda tama son dabbobi"
Yusuf yace "Allah sarki, tabbas naga tana matuƙar son dabbobi kam"
Alhaji Nasir yace "Yusuf dan Allah ka ƙara haƙuri da 'yata, na yaba sosai da
ƙoƙarin ka Allah ya saka maka da Alkhairi, dan Allah idan ta gama ganin likitan,
ranar da zata bar ƙasar nan dan Allah ka tabattar jirgunta ya tashi, da ni naso in
kaita da kaina, amma akwai taron kasuwanci na shekara da nake halarta, idan har ban
halarta ba akwai matsala ga dukiyata, wadda take gauraye data al'umma"
Yusuf yace "dukiyar ka data al'umma kuma?"
Alhaji Nasir yace "Eh mana, akwai hannun jarin mutane a cikin kasuwanci na, wanda
ciki harda masu ƙaramin ƙarfi idan har ban halarci taron nan ba to tabbas dukiyoyin
wasu zasu halaka"
"Amma meyasa dukiyar wasu zasu halaka, dan baka halarci taron ba? '
Alhaji Nasir yayi murmushi yace" karka damu, idan Allah yasa kuka dawo zan gaya
maka yanzu dare ya fara yi "
Yusuf a ransa yace" to ko dai Alhaji Nasir yasan maƙiyansa ne? "
A fili kuma yace "Amma yallaɓai kana ganin za' a samu Nasara idan taga wannan
likitan?"
"To abun duk lalabune a duhu Yusuf, bamu san inda zamu dace ba"
Suna cikin maganar saƙo ya shigo wayar Alhaji Nasir, ya ɗakko wayar ya dubaJikin
Alhaji Nasir ne ya kama rawa, a ɗan gigice yace "Amm.. Ammm Yusuf jeka ka kwanta
dare yayi, saboda ku samu ku fita da wuri gobe in Allah ya kaimu, kabi wannan
varrender akwai ɗaki yana kallonka acan zaka kwanta"
Yana gama faɗin haka ya shige wani ɗaki ya rufe ƙofa, mamaki ne yakama Yusuf ya
miƙe ya nufi inda Alhaji Nasir ya kwatanta masa ya shiga.
Masha Allah, ɗakine tangameme babu abunda babu na jin daɗin rayuwa a ciki, gadon
kansa abun kallo ne kamar ka sace ka gudu, hotunan Widad ne ko ina a ɗakin, Yusuf
ya dinga ƙare musu kallo, idonsa ya sauke akan haɗaɗɗen hoton Widad.
Tayi kyau sosai tayi murmushi cikin wata jar doguwar riga, ta baje gashin kanta
kamar ba ita ba.Ya daɗe yana kallon hotunan dake jikin bango, sannan ya ajiye
jakarsa, yana sake ƙarewa ɗakin kallo.
Ya shiga banɗakin yayi alwala ya dawo yayi nafilfili yayi karatun Al'qur'ani da
addu'oi sannan ya nemi guri ya kwanta.
Wajen ƙarfe biyu na dare cikin bacci Yusuf yaji muryar Alhaji Nasir na rawa yana
kiran sunan Yusuf, a gigice Yusuf ya farka ya tashi zaune.
Alhaji Nasir ya kamo hannun Yusuf yace "taso Yusuf akwai matsala"
"matsalar me Alhaji?"
"Yusuf rayuwar Widad, ni idan tawa ta salwanta bakomai, bana son Widad ta rasa
Ranta"
Cike da mamaki haka Yusuf ya biyo bayan Alhaji Nasir, suka tarar Widad na tsaye a
falo tana kuka, gaba ɗaya Yusuf ya rikice yace
"Alhaji meke faruwa ne"
Jiki na tsuma Alhaji Nasir ya miƙawa Yusuf wayarsa
"RANA BA TA ƘARYA SEDAI UWAR ƊIYA TAJI KUNYA, YAU ZAMU KAWO ƘARSHEN WASAN KURAR DA
MUKE, KODAI KA YADDA KA BAMU ABUNDA MUKE BUƘATA KA HALARCI TARON KASUWANCI, KO KUMA
KA HANAMU KA RASA RANKA DA NA 'YARKA, KOMU KASHE TA AGABANKA MU BAR MAKA MUGUN
TABO, WATAƘILA HAKAN YASA KA BAMU ABUNDA MUKESO"
Yusuf yace "to koma mene ka basu mana, saboda rayuwar ka da tata su tsira"
"Yusuf ni kaina abunda suke so in basu ba nawa bane, nayiwa kaina Alƙawarin bawa
meshi abunsa, dan haka bazan basau ba"
Yusuf yace "to ko ka kira jami'an tsaro"
"A' a Yusuf hakanma matsala ne, dan Allah ka ɗau Widad ku tafi maza ku tafi yanzu"
Fashewa da kuka Widad tayi tace "Ni bazan tafi na barka ba Daddy, bana son wani
abu ya same ka, Daddy bana son tafiya kai kaɗai ka ragemin"
Dattijon yana zubar da hawaye yace
"Widad bana son rayuwarki ta salwanta, nima ke kaɗaice dani, idan suka kama ki
komai ya ɓaci, ki tabbatar kin miƙa amanar nan ga masu ita, karki yards ta salwanta
ko a karon banza wasu su karɓa, maza ku tafi"
Ƙanƙame mahaifinta tayi tana kuka tace "Daddy ba inda zanje, kome ze faru ya faru
muna tare"
Daddy da kansa yaja hannun Widad ya kaita mota, ya kalli Yusuf yace "Allah ya
kiyaye ku Yusufa, na yarda da kai ka kularmin da Amana ta, ka kula da Widad kayi
haƙuri da ita, karku sake ku dawo idan bani na kira ku ba, zaman Widad anan tana
cikin hatsari mutanen nan dagaske suke"
Haka Yusuf ya shiga motar yaja, Widad tana wani irin kuka me ban tausayi.
Su kansu ma'aikatan sunyi mamakin fitar su Yusuf a wannan daren.
Saleh ne ya samu Alhaji Nasir yace "Alhaji lafiya kuwa? Meke faruwane haka?"
Daula yace "Wata 'yar ƙaramae matsala ce, Amma komai ze daidaita insha Allah"
Alhaji Nasir ya koma cikin gidan yana safa da marwa ya rasa abunyi, wayarsa ya
ɗakko ya kira Bulama a waya ya sanar dashi halin da yake ciki.
Yusuf kam a besan inda ze nufa ba a wannan tsohon daren, gaba ɗaya sahu ya ɗauke se
abunda ba'a rasa ba,gudu yake yana ratsa tituna ba tare da yasan inda ze dosa ba.
Befi mintuna talatin ba sega Bulama yazo gidan a sukwane, suka haɗu da Alhaji Nasir
a harabar gidan, Bulama a gigice yace "Daula ina Widad ɗin take yanzu?"
A kiɗime Daddyn Widad yace "na haɗata da direbanta nace su tafi"
"su tafi suje ina?"
'Bulama na rasa yadda zanyi ne, ina tsoron rayuwar Widad ta taɓu, nasan yaron baze
cutar da ita ba"
A fusace Bulama yace "kayi hauka ne Nasiru, kamar ya ka haɗata da direba? Kasan
daga ina yake ko kuma ina ze kaita, memakon ka kira' yan sanda kawai seka haɗata da
direba idan kuma bakinsa ɗaya da mutanen fa"
Girgiza kai Alhaji Nasir yayi yace "bana tunanin haka Bulama kaina ya gana kullewa
ne"
Alhaji Bulama ya ɗau waya ya fara kiran 'yan sanda.
Sosai Yusuf yake gudu akan titi, yayin da Widad ta dunƙule tana aikin kuka, Yusuf
ya kasa cewa komai se tunanin ya zasu tsira, sedai babu zato yaci karo da wata mota
anyi parking ɗinta a tsakiyar titi, wani irin parking na rashin mutunci yanda babu
damar Yusuf ya iya wucewa, ga gefe jeji ne, yayi reverse ze juya kan motar wata
motar tazo ta ƙara rufe bayan tasu Yusuf aka sasu a tsakiya.
Wasu irin ƙarti ne suka fito daga motocin suka kewaye su Motarsu Widad, gaba ɗaya
Widad ta rikice ganin suna tunkaro su, suna zuwa suka buɗe ƙofofin motar, suka sawa
Yusuf bindinga aka suka ce Widad ta fito.
Ko motsi ba tayi ba balle ta ɗaga kai ta kalle su, cikin tsawa ɗaya yace "ba
magana ake miki ba"
Sunkuyar da kai tayi taƙi motsawa, ɗaya yasa hannu ze fizgota aikuwa ta riƙe Yusuf
gam tana kurma ihu
"Yoseef karka bari su tafi dani"
Yusuf ya riƙe hannun ta yace "me mu kayi muku kuke ƙoƙarin cin zarafin mu akan
titi haka"
"zaka rufe mana baki ko semun fasa kanka da bindiga, dalla ku fizgota ta ƙarfin
tsiya suna ɓata mana lokaci"
Ai Widad sekace Mayya ko ƙarfe ta riƙe Yusuf gam, wani gigitaccen mari ɗayan ya
kwaɗawa Widad yana ƙoƙarin janyo ta, sedai ga mamakin Yusuf mutumin yana sauke
hannun sa Widad ta rama marin, dukda a gigice take tace "karka ƙara gangancin
marina, wallahi ka kuma dukana sena rama"
"Ashar ya saki yace lallai wannan yarinyar akwai ƙarfin hali, yau zamuyi maganinki"
Hannu ya kai ze shaƙota, amma Yusuf ya riƙe hannun mutumin yace "karka kuskura ka
sake marinta"
"Idan aka sake marinta me zakayi? Dan Allah oga ka bani dama in fasa kan gayen nan
da bindiga"
Shugabansu yace "babu kisan kai a wannan deal ɗin, ban sani ba ko zuwa gaba"
Suka cigaba da jan Widad, Yusuf yaƙi sakin ta, baya son ya zafafa suyi mata illa
gashi babu makami a jikinsa.
Yace "idan kunga kun tafi da Widad to tabbas kun kasheni ne, amma ba inda zaku da
ita"
Ganin Yusuf na ɓata musu lokaci ga Widad na nema tasa asrinsu ya tonu, bakinta yaƙi
rufuwa sunan Yusuf kawai take kira, haka suka haɗa da Yusuf suka sasu a tasu motar.
Suka ƙulle hannayensu, sukayi daji dasu, ihu Widad ta cigaba dayi, gaba ɗaya ta
manne a jikin Yusuf sosai tana cewa "ni ku ƙyalemu, besan komai akai ba, direba
nane kawai ku ƙyalemu mu tafi"
Yusuf yace "kiyi shiru karsu illataki"
Ai be gama rufe bakinsa ba, suka sa ƙyalle suka rufe musu ido.
Widad tasa haƙoranta ta riƙe rigar Yusuf, duk dan kar su raba ta da Yusuf, se haki
take tana jin yadda zuciyar Yusuf ke bugawa, Yusuf kam ya yabawa jarumtar Widad
yau.
Shikansa Saleh da'aka haɗa baki dashi akayi aikin, ya rikice gaba ɗaya ya shiga
damuwa mussman yadda yaga Alhaji Nasir na zubda Hawaye yana kaiwa yana komowa a
harabar gidan, Alhaji Bulama nata rarrashinsa amma se kuka yake kamar ƙaramin yaro,
zuwan 'yan sanda yayi dai dai da shigowar wani saƙon wayar Alhaji Nasir.
"A ZATONKA KA FIMU WAYO NE, MUN KAMA' YARKA DA DIREBANKA SUNA HANNUNMU, SHAWARA TA
RAGE NAKA, ZAMU CIGABA DA AZABTAR DASU, DAN HAKA SEKA KA ZAƁA KO RANSU KOKUMA
ABUNDA MUKA NEMA A HANNUNKA"
Yana gama karanta saƙon ya yanke jiki ya faɗi a gurin
In an karanta ayi share please🙏 🙏 🙏
Gyara, sharhi ko shawaraAyshercool07063065680
_*AƘIDATA*_
PERFECT WRITERS ASSOCIATION
(WE AIN'T PERFECT BUT WE ARE ALWAYS TRYING OUR BEST, TO MOTIVATE AND ENTERTAIN OUR
READERS)
https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/
*Story and written by*
_*AISHA HUMAIRA (Daddy's girl)*_
The experience writer of *ABDUL JALAL** WATA KISSAR.... (SAI MATA) *And now *AƘIDA
TA *
I dedicated this book to my Mum (Malama Nafisat Adam Muhammad) i love you mum
Haƙƙin Mallaka ⚠ : Littafin nan mallaki nane, tun daga sunan labarin zuwa abunda ya
ƙunsa, ban yadda wani ko wata ya sauyamin ko yin Amfani da wani ɓangare na labarin
ba ba tare da izinina ba, Nagode
https://www.wattpad.com/user/Ayshercool7724?
utm_source=android&utm_medium=link&utm_campaign=invitefriends
ELEGANT ONLINE WRITER'S
PART1 Page 24_25
Gaba ɗaya ma'aikatan gidan su kayo kan Alhaji Nasir, sedai jikinsa kamar babu rai,
'yan sanda suka ƙaraso cikin gidan aka kwashi Alhaji Nasir a daren zuwa Asibiti.
Widad kam gajiya tayi da zaman motar, saboda tafiya suke bata wasa ba cikin wani
irin azababben gudu, jin tafiyar taƙi ƙarewa ne yasa Widad fara mustu mutsu, tun
tana mutsu mutsun har bacci ya kwashe ta, a firgice ta farka ta kurma wani uban ihu
tana kiran "wayyo Allah na Yoseef, karka tafi ka barni"
Yusuf yace "Widad ina nan, muna tare har yanzu Allah ze fitarmu insha Allah, ki
dena shouting karsu miki wani abun"
Me tuƙa motar yace gara dai kaja mata kunnen.
Memakon tayi shiru ta cigaba da ihu tana "ku ƙyalemu mu tafi, yoseef na gaji da
zaman nan hannuna igiyar nan ta dameni, bayana ciwo na gaji bayana ze karye"
Wata hoda su watsawa Widad, wanda hakan yasa ta baccin dole, ba Widad ba har Yusuf
gaba ɗaya bacci ya kwashe su.
Ana kai Alhaji Nasir Asibiti, aka kwantar da shi aka dinga masa allurai da ƙarin
ruwa, ga oxygen ansa masa domin temakawa numfashinsa dake barazanar ɗaukewa.
Likitoci suka duƙufa akansa, suna bashi dukkanin taimakon da zasu iya, ga jininsa
ya hau fiye da kima suna ta ƙoƙari jininsa ya sauka.
Yusuf ne ya fara farkawa jin motar ta tsaya, aka buɗe motar suka kwance musu ido,
mamakine ya kama Yusuf, tun cikin dare suke tafiyar nan amma da'aka kwance musu ido
yaga yanayin garin kamar Azahar ta gota, daji ne sosai ciyayi sun lulluɓe ko ina,
gaba ɗaya Yusuf baya gane inane gabas ko yamma ya kasa gane ta ina suka zo nan
gurin.
Widad kam sam bata hayyacinta, ta farka amma se tangaɗi take haka suka sasu a gaba
zuwa wani gini.
Yusuf yayi mamakin yadda aka shigo cikin wannan uban dajin akayi ginin gida, suka
buɗe gidan suka shiga dasu Yusuf.
Gaba ɗaya gurin kango ne, kuma ga dukkanin alamu an samar dashi ne mussman saboda
wannan aikin, saboda gurin sabon gini ne harda ragowar kayan aikin ginin.
Wani ɗaki suka kai su Widad suka ajiye, akan tsurar tabarma suka kawo musu ruwan
pure water guda biyu suka ajiye musu suka maida ƙofa suka rufesu a ciki.
Yusuf ya ɗau ruwa ɗaya ya fasa ya bawa Widad, aikuwa nan da na ta zuƙeshi da alama
tana jin ƙishirwar sosai, ga ko salla ba suyi ba haka ya zuba mata ruwa tayi
alwala, ɗan ragowar shima yayi ba tare da sun san inane gabas ba haka suka gabatar
da salla.
Shiru Widad tayi, gaba ɗaya jikinta ciwo yake ga wata uwar yunwa da take ji, gashi
har yanzu jikinta babu ƙwari saboda hodar da suka watsa mata.
Ta kalli Yusuf da yayi shiru ya sunkuyar da kai, gaba ɗaya tausayinsa yakamata duk
a dalilin ta wannan masifar ta faɗa masa.
Kifewa tayi a gurin, hakan yasa Yusuf ɗagowa da sauri yana kiran sunan ta, cikin
kasala tace "Yunwa nake ji"
A hankali yace "kiyi haƙuri kinji, Insha Allah zamu bar gurin nan, kuma zaki ci
Abinci"
Ba tace komai ba ta maida kanta ta kwanta, wani irin sanyi na ratsa ta, miƙewa
Yusuf yayi yana zagaye ɗakin harda ban ɗaki sedai an rufe ko ina babu hanyar tsira.
Zagaye ɗakin ya shiga yi yana sake tunanin menene mafita, ya kalli inda Widad ke
kwancw ta takure sosai gwanin ban tausayi.
Haka suka wanzu babu me cewa komai tsawon wasu awanni, suka riƙe alwalarsu in sun
kintaci lokacin salla se suyi.
Alhaji Bulama ya samu ya koma gida, dan Alhaji Nasir ya farfaɗo ya samu bacci, yana
zuwa Matarsa tace "kaikam ina ka tafi haka, na farka na nemeka na rasa na dinga
kiran wayarka kaƙi ɗagawa, duk ka ɗaga mana hankali"
"Daula ne babu lafiya" ya bata amsa
Sekuma jikinta yayi sanyi tace "meya same shi?"
"An sace 'yarsa da direbanta, shi kuma ya yanke jiki ya faɗi"
Dafe ƙirji Hajiya Sarah tayi tace "Kamar ya an sace su sekace kaji? Yaza' ayi ace
'ya kamar ta Alhaji Nasir an saceta, suwaye suka sace ta?"
"Mutanen da suke bibiyar sa ne, ni nafi kyautata zaton harda haɗin bakin direban
nata"
Sarah ta girgiza kai tace "Amma Alhaji wannan yaron sam neyi zubin Azzalumai ba"
"ke bari, duniyar nan babu gaskiya shi mugu ai bashi da kama"
"Hakane, Allah ya fidda su lafiya, amma an sanarwa jami'am tsaro?"
Bulama yace "eh na sanar musu an fara bincike ma"
Gaba ɗaya Hajiya Sarah ta shiga damuwa, dukda yadda take jin haushin Widad, su
Ramadan ma da Iman sin shiga damuwa sosai da jin labarin.
Isa megadi ne ya shigo falon gidan a gigice yana kiran Hajiya. A fusace Hajiya
Halima tace "lafiya kake min wannan kiran kamar wata 'yarka"
"Hajiya babu lafiya fa, muna nan zaune gaho an sace Autar daula da direbanta, shi
kuma Alhaji yana kwance a Asibiti"
"to shine me zaka zo kanamin wannan kiran, aita sace tan mana ai hakane ya dace da
ita, Allah yasa daga na su kashe ta ma kowa ya huta, fita ka ban guri ka koma kan
aikin ka"
Galala Isa ya bita da kallo, "bazaka fita ba sena zo na kwasheka da mari"
Jiki a sanyaye yayi waje yana tunanin, to idan ma bata tausayawa Widad ba saboda
tana musu wulaƙanci to Alhajin fa, wanda duk wani gata da jin daɗi a dalilinsa suka
same shi. Yana wannan tunanin yayi karo da Anwar ba tare da ya sani ba.
Anwar yace " lafiya kuwa? Kana tafe baka ganin gabanka"
A firgice Isa ya labarta masa abunda ke faruwa, wata mummunar faɗuwar gabace ta
kama Anwar yace "garin yaya Isa? Ina Alhajin yake?"
Isa yace "Ance yana Asibiti, amma bam san wane Asibitin bane, sedai a tambayi
Alhaji Bulama"
Anwar yace "shikenan nagode"
Ya nufi cikin gida da hanzari, ya tarar mahaifiyarsa da Ramlah suna ta hirarsu.
Anwar hankali a tashe yace "Mummy kin san meke faruwa kuwa, Daddy yana kwance ba
lafiya sannan an sace little"
Cike da salo da iya rainin hankali Hajiya Halima ta miƙe tayi gigicewar ƙarya tace
"haba dai waye ya gaya maka, bana son wasa fa"
Anwar yace "ba wasa bane Mummy, ki kwantar da hankalinki, zanje gidan su Fahad
inji komai, se inzo muje Asibitin".
"shikenan hanzarta Anwar, innalillahi wa inna ialaihi raji'un Allah yasa ba gaske
bane"
Anwar yace "Mummy ki kwantar da hankalinki, ina dawowa" yayi waje da sauri ko
ganin gabansa ba yayi saboda tashin hankali.
Duhu ya fara yi sosai, ba wanda yasa wani abu a cikinsa tsakanin Widad da Yusuf,
can sukaji hayaniyar mutanen da suka sace su sun shigo, Widad tayi zumbur ta tashi
zaune, suka saka mukulli suka kwance sarƙar da suka kulle ƙofar da ita da kuma
kwaɗon sannan suka shigo.
Manyan torchlight suka kunna suna haske su Yusuf, suka shigo hannunsu ɗauke da
mugayen makamai, da manyan bindigogi.
Babban ya haske Widad da fitila, ta sunkuyar da kai taƙi ɗagowa yace "shegiya
kalleta kamar ta Allah, zamu kawo ƙarshen wannan izzar da gadarar taki uwar taurin
kai"
Yai maganar tare da ajiye mata takeaway a gaban ta, wata bushashiyar shinkafa ce a
ciki sekace ƙanzo gefen shinkafar duk ƙonanniya.
"ki tashi kici Abinci Malama, sedai ba irin na gidan shashsashan ubanki bane daya
sangartaki"
Ƙafarta ta saka tayi Ball da takeaway ɗin shinkafar ta watse a gurin.
Aikuwa ya harzuƙa ya shaƙeta yana faɗin "nan ba gidan ubanki bane da zaki mana
gadara, zakiga yadda zamu lallasa ki sekin sauke wannan izzar taki"
A gigice Yusuf yazo ya riƙe hannun sa yace "dan girman Allah kayi haƙuri ka
ƙyaleta, a galabaice take zata iya mutuwa inka cigaba da shaƙeta"
Yayi jifa da ita ta faɗi jiki ba ƙwari tana kakari, ya kalli Yusuf yace "banza ɗan
shishshigi ga abunda shishshigi yaja maka nan, aka dinga ja maka kunne akanta amma
kaƙi ji, ga shi nan koba komai kaima ka shiga wahala"
Yusuf bece komai ba yayi kan Widad yana ɗagota, da ƙyar take numfashi. Yusuf yace
"Uwar ɗakina, ki dena musu gardama ko so kike su kashe ki a gurin nan?"
Lumshe ido kawai tayi tana sauke numfashi da ƙyar.
Hadda Saleh aka tafi Asibiti gurin Alhaji Nasir, an samu ya farfaɗo har ya zauna
sedai yayi shiru baya magana.
Saleh yace "sannu ranka ya daɗe"
Daula ya jinjina kai, ya kamo hannun Saleh yana ta haki yace "Saleh 'yata, an
sacemin Widad da Yusuf nayi dana sanin saka Yusuf a harkar tafiyar nan, gashi ya
shiga matsala a dalilina"
Saleh yayi shiru sannan yace "kayi haƙuri ka kwantar da hankalinka Alhajin Allah,
babu yadda za' ayi akasa gano inda Widad take, a matsayinka na babban mutum a ƙasar
nan, Insha Allah zasu kuɓuta"
Daula yace "ai ba wai kuɓutar tasu ba, yadda zasu tsira da rayuwar su bayan sun
kuɓutan shi nake tunani"
Saleh yace "karka damu da wannan Yallaɓai, yanzu Addu'ar mu suke buƙata insha
insha Allah zasu kuɓuta"
Bulama ne da matarsa suka shigo ɗakin shida Anwar da su Ramadan, Bulama yace
"sannu ya jikin naka?"
"Alhamdilillah"
"Ubangiji Allah ya ƙara afuwa"
"Ameen" na suka shiga yi masa sannu, Anwar ya ƙarasa kusa dashi yace "Sannu Daddy
Allah ya baka lafiya"
Kasa Amsawa yayi sema share ƙwalla da yayi yace "Anwar an sacemin Widad, an sace
autar daula, ga yaron dabe ji ba be gani ba shima ta ritsa dashi"
Cikin damuwa Anwar yace "ka kwantar da hankalinka Daddy, Insha Allah zasu kuɓuta,
za'a gansu, babansu Fahad yace min an kai report"
Alhaji Nasir yace "Allah yasa su kuɓuta gaba ɗaya yasa karsu cutarmin da su"
Alhaji Bulama yace "ka jika da wani zance, muji da 'yarmu da' aka sace kana wani
kar'a cutar dasu"
Alhaji Daula yace "haba Bulama, ai gara su riƙe Widad su saki Yusuf, yana zamansa
a dalilina da 'yata ya shiga hatsari, in gaya maka gaskiya tsakanin Widad da Yusuf
ba wanda bana so, Allah ya samin ƙaunar yaron a zuciya ta, bazan so ya rasa ransa
ba shima, Allah ya bayyana min su duka ba wanda bana so"
Kuka sosai Alhaji Nasir yake kamar ƙaramin yaro, Anwar ne ya rungume shi a jikinsa,
yana faɗin "yi haƙuri Daddy, duk zasu kuɓuta cikin ƙoshin lafiya, kar lafiyar ka ta
taɓu, kaima muna buƙatarka"
Hajiya Sarah tace "dole Baban Widad yayi kuka kuma gaskiya ya faɗa, yaron nan shima
abun tausayi ne, beji ba be gani ba tsautsayi ya ritsa dashi abun da tausayi"
Alhaji Bulama yace "dama ku mata wani lokacin ba hankali kuka cika ba, dama Allah
yayi haka zata faru dashi, amma mudai mu samu 'yarmu ta kuɓuta"
Hajiya Sarah tace "shi Yusuf ɗin ba uwace ta haife shi ba? Ya zataji idan ta samu
labarin ɓatan ɗanta?"
Ramadan ne yai saurin cewa "Mummy kiyi haƙuri kiyi shiru, duk zasu bayyana insha
Allah, Allah sarki Yusuf ɗin nan yana da kirki wallahi ga haƙuri da yawan murmushi"
Likita ne ya shigo ze duba Alhaji Nasir, dan haka duk aka basu umarnin su fita daga
ɗakin domin a duba shi.
Anwar ya maida su Alhaji Nasir gida, ya shiga part ɗin Fahad, sedai ya tarar da shi
da mace suna shan shisha, Anwar ya girgiza kai dan ya saba ganin Anwar a wannan
halin, mussman da suna ƙasar waje, Anwar yace "Fahad baka san meya faru da Widad
bane da direbanta, ina ta kiranka baka ɗaga ba?"
Fahad ya fesar da hayaƙi yace "Nasani mana"
"Amma ko Daddyn namu ai yakamata kaje ka duba"
Fahad ya kalle shi yace "Daddynku ku suwa? Baza'a dubo shi ɗin ba, ni burina duk
inda ta shiga a nemo min mata ta, dan nasan wannan tsinannen direban ne ya gudu da
ita, kuma sena nuna masa iyakarsa"
Karuwar dake tare da Fahad tace "Baby wai maganar wa kuke yi ne?"
Fahad yace "ba ruwan ki uwar shishshigi, jeki shirya inzo in maida ke gida"
Anwar yace "Fahad se yanzu na sake tabattar da Widad a kan gaskiya take na ƙin
yadda da mutane, yanzu Fahad kasan nida kai iyayenmu basu da ƙarfin kaimu ƙasashen
waje, amma ya ɗauke mu kamar yaransa, ya kaimu ƙasar waje mukayi karatu, dukkaninmu
ba wanda be mallakawa motar hawa ba da gidan kansa, muba komai ba silarsa muka zama
wani abu, kalli yadda muke fantamawa a cikin rigar arzikinsa, albarkacin sunansa
duk inda muka shiga a faɗin ƙasar nan muna da Alfarma, yau shine Iftila'i ze faɗa
masa amma ka nuna halin ko in kula, Anya Fahad kana gayawa kanka gaskiya kuwa "
Fahad yace " A'a sedai idan yanzu zaka fara gayamin gaskiyar "
Yai maganar tareda miƙewa ya shige bedroom ɗinsa, jiki a saɓule Anwar ya baro gidan
Bulama ya koma Asibiti, ya bawa Alhaji Nasir Abinci ya canza masa kaya, sedai yaita
mamakin rashin ganin mahaifiyarsa taje Asibitin gurin mijinta.
Gida ya koma yana tunanin butulci irin na Fahad, a falo ya tarar da Hajiya Halima
tana cin Abinci suna kallon zee world, sedai kamar Amal ce a cikin damuwa.
Anwar yayi sallama suka amsa gaba ɗaya, Anwar yace "Mummy meyasa ba kije Asibiti
ba?"
"bana jin daɗine, bana son inje inga abunda ze sake ɗagamin hankali"
"Amma Mummy ai jikin nasa da sauƙi, kuma yakamata ace ko su Ramla sunje duba shi"
A fusace tace "Ubansu ne da lallai se sunje duba shi, fita ka bani guri dalla"
Buɗe baki yayi yana kallon mahaifiyarsa yana ƙoƙarin tabattar da anya daga bakinta
wannan maganar ke fitowa?
Duhu ya fara yi, sauro ya shiga ambaliya a gurin nan, Yusuf ya zauna se akin yi
mata fifita yake da wani gutsararren kwali, A hankali Yusuf yace "Kidena musu
taurin kai kinji, sannan idan an baki Abincin ki karɓa kici, baze yuwu ki zauna da
yunwa ba"
"ba zanci ba" ta bashi amsa
"kin fi son su cigaba da azabtar dake?"
Shiru tayi masa ba tace komai ba, can ya kuma cewa
"dan Allah ki basu abunda suke nema, dan su ƙyale ki ko a yanzu kin galabaita"
"wallahi ko zasu kasheni bazan basu ba, shiyasa nace tun farko su sake ka ni su
barni anan"
"tayaya zasu sakeni in tafi, alhalin kina gurinsu sedai kome ze faru ya faru muna
tare"
Ajiyar zuciya ta shiga saukewa, tana jin yadda sauro ke shagali akanta, abunda bata
saba ba, bata son yin kuka dan yanzu Yusuf ze ɗaga hankalinsa
Cikinsu babu wanda ya rintsa, har gari ya waye, taimama sukayi sukayi sallar Asuba.
Fuskar Widad duk ta kumbura saboda sanyi da cizon sauro, kuma har a lokacin jikinta
babu ƙwari.
Yusuf yana zaune, yayin da Widad ke kwance akan tabarmar, buɗe ƙofar ɗakin akayi
suka sake shigowa su huɗu.
Suka kalli inda Widad ke kwance, ɗayan ya buga mata tsawa yace
"tashi ko in taka ƙafarki in karya banza"
Gyara kwanciya tayi ta juya musu baya, alamar bata da niyyar tashin, yau Yusuf ya
ƙara tabbatar da azababben taurin kai da Widad ke dashi.
Da sauri Yusuf yazo inda take ya ɗaga ta zaune yace "ya haka ne, so kike yauma su
dake ki"
Wani banzan kallo tayiwa shugabn nasu ta ɗaunke kai tana hura hanci.
Ɗayan yace "shegiya se kyau kamar ita tayi kanta, amma zuciyar ta kamar dutse
shegiya me kama da sadakar yalla"
Babban su yace "zamuyi maganinta kafin tabar gurin nan, da ganin idonta yunwa take
ji, amma saboda taurin kai taƙi cin Abinci, ku ɗakko Abinci ku bata idan taga dama
taci"
Shinkafa da wake ce irin garau garau ɗin nan takan 'yan talla, tayi sanyi ƙalau ga
ba mai sosai, suka dire mata a gabanta, yunƙurawa tayi zata sake fatali da Abincin
Yusuf ya riƙe ta yace "dan Allah ki daure kici, kinga tun shekaranjiya rabonki da
Abinci"
Ta kalli idon Yusuf tace "bazan ci ba"
Ɗayan yace "kai dalla ka ƙyaleta mana, kar taci ubanwa tayiwa, Oga ka fara aiki
kawai"
Rarrashin duniya Widad tayi mursisi taƙi cin Abinci.
Babban cikinsu ya ɗakko wayarsa zeyi kira.
"Nurat ki kaiwa Daddynki tea ɗin nan da baƙinsa, kafin yazo ya ishemu da faɗa"
Nurat ta miƙe ta ɗauki kayan tea ta nufi part ɗin mahaifinta.
Alhaji Munir ya shafa ƙaton cikinsa yace "nifa bakina yaƙi rufuwa ma, nasan dole
abun nan yazo hannunmu a yau base gobe ba, nace a tura masa saƙo, kodai ya bayar ko
mu cigaba da tsare ta"
Alhaji Musa yace "ba kai kaɗai ba ni kaina ina cikin murna, sun kwana a hannu,
Daula yana gadon Asibiti yana ta sharɓar hawaye, mutum se taurin kan tsiya kamar
arnen dutse"
Suka kwashe da dariya, Alhaji Haruna yace "dalla ƙyaleshi, gefe guda baze samu
Halartar taron shekara na kasuwanci ba, da haka zamu sanar da cewa an samu
gagarumar Asara kasuwancin da muke yi, zamu bada fake Account statement, zamu
kwashi rabonmu kafin wancan yazo hannunmu, ai daula ya gama yawo wai shi me
gaskiya"
Suka sake kwashewa da dariya, wayar Alhaji Haruna ce ta fara ringing, ya ɗaga ya sa
musu a hands free, Alhaji Haruna yace "Ya me ake ciki ne?"
"Yallaɓai tunda nake aikin nan, ko a maza ban taɓa ganin mutum me baƙin taurin kai
kamar yarinyar nan ba, kwana biyu kenan taƙi cin Abinci, ruwa kawai take sha, gashi
kamar bata da lafiya kullum tana kwance ko magana seta ga dama take yi"
Alhaji Munir yayi tsaki yace "dalla ku rabu da ita, ku karɓo mana abunda muke
buƙata, sannan ku turawa ubanta saƙo shima koya bamu ko kuma ku kashe ta"
Daga wayar akace "An gama Oga, yadda kukace"
Nurat da taje kai musu shayi jikinta ya shiga ɓari, dan tsaf taji hirar da
mahaifinta suke yi, cikin sanɗa taje ta ajiye farantin kayan shayin, ta ruga da
gudu ɗakinta ta saka hijjabi ta ɗau wayarta ta fice daga gidan.
Babban cikin mutanen wanda suke cewa me Adda ne ya ɗakko wata kujera ya zauna a
gaban Widad ya kalle ta cikin tsawa yace
"ke kalleni nan, ina takaddun nan suke? Ki gayamin cikin ruwan sanyi ko kuma in
kasheki in koma in kashe wancan daƙiƙin uban naki"
Sunkuyar da ka tayi tai shiru, Yusuf yace "Yana miki magana ki gaya masa, su
ƙyaleki ki huta"
Kallon Yusuf tayi da jajayen idonta sannan tace "takaddun da suke nema, akwai masu
shi nayiwa Daddy Alƙawarin miƙasu ga masu shi, kuma na bawa masu shi suna can suna
yawon su a gari, me suke so kuma ince musu"
"ƙarya kike, duk binciken da'akayi sun tabattar da suna wajen ki dan haka ki
gayamana inda suke"
A harzuƙe tace "bazan faɗa ba, nace bazan faɗa ba kayi abunda zaka yi!"
Kan bindiga ɗaya yasa ya buga mata a baki, take jini ya shiga zuba daga bakinta
Yusuf ya gigice ze tashi, suka ɗora masa bindiga aka "kana motsawa zamu fasa kanka
da harsashi"
Widad ta tattaro dukkan yawun bakinta, me ɗauke da jini ta tofawa shugabannin nasu
tace "wallahi ko me zaki sedai kayi, bazan bayar ba ka koma ka gayawa Azsaluman da
suka saku aiki cewar bazan bayar ba, kuma matsorata ne tunda suka gaza fitowa gaba
da gaba su karɓi abunda suke so, kuma ko sun kasheni na kafa musu tarkon da ko
bayan raina se Asirinsu ya tonu, saboda na sansu kuma na tattara duk wata hujja da
yakamata a kansu san......
Bata ƙarasa ba ta kuma jin wani marin a fuskarta, a duk lokacin da suka daki Widad
Yusuf ji yake kamar ƙirjinsa ya tsage dan baƙin ciki, sedai ba yadda ya iya muddin
yayi wani yunƙuri dabe gamshesu ba zasu mata illa, dan ba imani ne dasu ba, ga
Widad bakinta yaƙi mutuwa.
Nurat bata tsaya ko ina ba se gidan su Widad, a waje ta tarar da Anwar ya fito da
mota ze fita, Anwar ne ya ganta dan sam bata lura dashi ba yace "Nurat"
Ɗaga kai tai ta kalle shi sannan tace "Yaya Anwar ashe ka dawo, babu Labari"
Anwar yace "Na dawo, ina zaki haka naga kamar bakya hayyacinki"
Nurat tace "gurin Widad nazo"
Anwar yace "baki san na sace ta ba ita da direbanta?"
Hannu ta ɗora a ka, ta durƙusa a gurin ta fashe da kuka, Anwar ya fito daga motar
yace "Nurat lafiya kuwa?"
Nurat tace "lafiya ƙalau, dan Allah kasan wani ɗan uwanta wanda suke yawo tare?"
Anwar yace "Ai Widad bata da ɗan uwa"
Nurat tacs "Nasani, wannan zaka ga tare suke yawo, ban san sunashi ba ya cemin ɗan
uwanta me shi, wani dogo kamar bafulatani, me yawan murmushi"
Anwar yace "ko Yusuf kike nufi?"
Nurat tace "ban san sunansa ba"
Anwar yace "indai Yusuf ne tare suke yawo kam, kuma tare aka sace su"
Zare ido waje tayi tace "tare aka sace su, na shiga uku ni Nurat, meyasa aka sace
su?"
Anwar yace "shine abunda bamu sani ba, amma 'yan sanda na nan na bincike yanzu
haka zanje Asibiti gurin daddynta ne, daga nan mu koma station"
Nurat tace "zan iya binka in duba shi?"
Anwar yace "meze hana? Muje"
Suka shiga motar suka tafi.
Me Adda ya jinjinawa wannan baƙi taurin kai na Widad, yasa bakin bindiga ya daki
kanta dashi ta kurma wani uban ihu tace "wallahi ba zan faɗa ba, sedai kayi min
duk abunda zakamin"
Ya kuma ɗaga bakin bindiga ze da keta, Yusuf ya miƙe ya riƙe shi gam yace 'Anya
akwai imaniba zuciyar ka, kalli yadda take kururuwa amma ba zaka ƙyaleta ba"
Me adda yasa hannu ya hankaɗa Yusuf amma Yusuf ko gezau beba, ya kalli Yusuf ya
kuma ƙoƙarin hankaɗeshi amma Yusuf ko gezau balle ya kai ƙasa dukda ya kwana biyu
ba Abinci amma hakan besa ya faɗi ba.
Haɗuwa sukayi su huɗu suka kama dukan Yusuf, da manyan sanduna, suka masa jina jina
sannan suka ɗaureshi, tun suna dukansa Widad na ihu harta suma a gurin.
Koda Anwar yaje a Asibiti seya tarar da mahaifiyarsa da su Ramlah a gurin, tayi
masa ƙaryar wai da'aka gayamata abunda ya faru suma tayi seda aka kaita Asibiti
shiyasa bata zoba, shi kuma Daddy ya yarda da abunda ta faɗa.
Anwar tun yana mamakin abubuwan da suke faruwa harya dena.
Nurat ta ƙarasa gaban Gadon Alhaji Nasir tace "Sannu Daddy ya jiki".
Ta faɗa tana sheshesheƙar kuka.
Alhaji Nasir yace "da sauƙi Nurat, ashe kin samu labarin ɓatan ƙawar ki?"
Ta jinjina masa kai alamar eh, yace "to ki cigaba da Addu'a Allah ya bayyana ta,
sannan ki koma gida kar babanki yayi miki faɗa kinzo nan"
Ya kalli Anwar yace "ɗan beauty mayar min da ita gida kaji"
Yai maganar cikin ƙarfin hali cike da zolayar Anwar. Anwar yayi murmushi, tare da
wayancewa ya goge ƙwallar dake idonsa, kallo ɗaya zaka yiwa Alhaji Nasir kasan yana
matuƙar jin jiki.
Tunawa yayi da abunda Widad ta gaya masa daren da abun ze faru, take yaji wasu
hawayen na bin idonsa, duniya Kenan Abun tsoro.
Saleh ya kasa zama, ya kasa tsaye abun duniya ya dames hi, tabbas Alhaji Nasir
mutumin kirki ne ya masa alkhairi daban daban a rayuwar sa, ga Yusuf dabe ji ba be
gani ba shima an ritsa dashi, anya hakki ze barshi kuwa, wannan tunanin ne ya cika
masa zuciya ko Abinci ya kasa ci.
Widad ta buɗe ido a hankali ta kalli inda Yusuf ke kwance, duk jikinsa jini, se
sauke ajiyar zuciya yake, gashi an ɗaure shi tamau da sarƙa.
Ko tashi bata iyayi saboda dukan da take sha, jikin ta ko ina rauni ne, ta janyo
jikinta a hankali tazo inda Yusuf ke kwance kawai ta faɗa kansa tana kuka.
"Yoseef dan Allah ka tashi, dan Allah kayi magana idan kana jina"
A hankali can ƙasan maƙoshinsa ido a lumshe yace "Insha Allah zamu kuɓuta, ki dena
kuka, ina mana Addu'a nasan Daddynki ma yana yi, Ummana ma tana yi mana"
Haka ta cigaba da ƙoƙari ko zata iya kwance Yusuf, amma abu yaci tira.
"Ranka ya daɗe yarinyar nan fa baza tayi magana ba, mun daka mun daka amma kamar
jinjirar jaka saboda taurin kai, mun mata jina jina amma taƙi faɗa se rashin kunya
take yi, gashi kwana huɗun nan Ruwa kawai suke sha, ita muna bata Abinci amma taƙi
ci duk ta galabaita "
Alhaji Haruna yace " A tauna tsakuwa, dan aya taji tsoro kuyi mata azaba wadda
zataji a jikinta"
Me adda yace "An gama ranka ya daɗe"
Ya buɗe ƙofar ɗakin dasu Widad ke ciki, tana zaune a gaban Yusuf ta zuba masa ido
idonta yayi jawur saboda yunwa da wahala, gashin kanta duk ƙasa da abun ciyay,
saboda birgimar da take a gurin, ya sauka a kafaɗarta ya baje kamar mara hankali.
Suka ƙaraso suka kwance Yusuf, da shima yake a mugun galabaice, suna kwance shi
Widad ta kama ƙasan rigarsa tana goge masa jinin jikinsa, me Adda ya fizgota ya
zaunar da ita tana fuskantar sa yace "ke dan uwarki wannan shine karo na ƙarshe da
zan tambayeki, dan mun gaji da wannan sintirn a wannan surƙumin dajin, ina takaddun
nan suke?"
Cikin tsawa tace "ban sani ba! Kuma karka sake zagin uwata dan uwa bata fi uwa ba"
Yadda gashin kanta baƙi kamar na Larabawa ya baje, gaba ɗaya seta burgeshi danƙo
gashin kanta yayi ya miƙar da ita tsaye, tsanani zafi yasa ta fasa ihu, Yusuf ya
yunƙura ze miƙe suka sake buga masa sanda a ƙafa ya faɗi ƙasa.
Ya kai bakinsa na Widad da niyyar ya haɗe bakinsu, tayi masa gware da kanta, dukda
yaji zafi hakan besa ya cikata ba, ya kuma danƙar gashin kanta ze haɗe bakinsu, ta
tattaro ƙarfinta ta daki mararsa da ƙafarta, a gigice yayi jifa da ita, ya ɗakko
ƙaramar pistol ya harbe ta a hannu, tare sukayi ƙara da Yusuf ta zube a gurin jini
na zuba a dantsenta.
Me adda miƙewa tsaye ma kasawa yayi saboda bala'in azabar da yake ji, 'yan uwansa
suka ɗauke shi, suka sake kulle su Widad.
Yusuf ya ƙarasa kan Widad ya ɗagota, a gigice yake magana "Widad sannu, kina
ganina?"
Ta jinjina masa kai dukda idonta na ƙoƙarin lumshewa, jikinta se rawa yaje gumi na
tsatstsafo mata ta ko' ina.
Yusuf ya ɗau ɗan siririn mayafint da tazo dashi ya ɗaure mata damtsen, ya rungomata
jikinsa yana jijjigata yace
"Dan Allah karki tafi ki barni, zamu bar gurin nan insha Allah, zan maida ke gurin
Daddy, dan Allah Widad karki tafi ki bar Yusuf"
Sosai hawaye ke zuba daga idon Yusuf, magana takeson tayi amma ta kasa, se rawa da
bakinta yake yi kawai, ta ɗaga hannu da nufin ta kaishi fuskar Yusuf amma abu ya
gagara hannun ya sauka tun tana ganin Yusuf dishi dishi harta dena ganinsa wuyanta
ya langaɓe.
Rungume ta yayi a jikinsa yana ambaton Allah, yana sheshesheƙar kuma, yayin da
mayafin da ya ɗaure mata hannu dashi ya jiƙe sharkaf da jini.
In an karanta ayi share please, masu neman recent pages dan Allah ku dinga dubawa a
watpad, @ Ayshercool7724.
Domin gyara, sharhi ko shawaraAyshercool07063065680
_*AƘIDATA*_
PERFECT WRITERS ASSOCIATION
(WE AIN'T PERFECT BUT WE ARE ALWAYS TRYING OUR BEST, TO MOTIVATE AND ENTERTAIN OUR
READERS)
https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/
*Story and written by*
_*AISHA HUMAIRA (Daddy's girl)*_
The experience writer of *ABDUL JALAL** WATA KISSAR.... (SAI MATA) *And now *AƘIDA
TA *
I dedicated this book to my Mum (Malama Nafisat Adam Muhammad) i love you mum
Haƙƙin Mallaka ⚠ : Littafin nan mallaki nane, tun daga sunan labarin zuwa abunda ya
ƙunsa, ban yadda wani ko wata ya sauyamin ko yin Amfani da wani ɓangare na labarin
ba ba tare da izinina ba, Nagode
https://www.wattpad.com/user/Ayshercool7724?
utm_source=android&utm_medium=link&utm_campaign=invitefriends
(GAMAYYAR MARUBUTA NA ELEGANT ONLINE WRITER'S, INA GODIYA DA KARRAMANI DA'AKAYI DA
CERTIFICATE NIDA ƘUNGIYATA TA PERFECT WRITERS ASSOCIATION, INA GODIYA DA WANNAN
KARAMCI UBANGIJI ALLAH YA ƘARA HAƊA KAN MARUBUTAN MU AMEEN, INAWA KOWA DA KOWA
FATAN ALKHAIRI, TARE DA FATAN KOWA YAJE GIDA LAIFIN)
ELEGANT ONLINE WRITER'S
PART1 Page 26_27
Gaba ɗaya Widad ko motsi ba tayi, Yusuf ya rungumeta sosai a jikinsa kamar wani ze
ƙwace masa ita, zuciyar ta na bugawa amma numfashinta baya fita sosai, ga cikinta
se ƙara yake saboda yunwa.
Anwar ya kai Nurat gida, suka yi Sallama, ta shige gida jikin ta na rawa ta tafi
ɗakin mahaifiyar ta.
"ke ina kika fita kikaje ban sani ba?"
"Mummy akwai matsala fa"
Cike da rashin fahimta mahaifiyar ta tace "matsalar me?"
"Widad ta ɓata an sace ta"
Dafe ƙirji tayi tace "innalillahi wa inna ialaihi raji'un, waye ya gaya miki?"
"Mummy can naje fa, Daddynta yana Asibiti ma naje na duba shi ma"
Zaro ido tayi tace "ubanwa yace kije? Sekin jawa kanki faɗa a gurin mahaifinki ko?
Tashi maza kije ki cire hijjabin nan ki huta"
Nurat ta kalli mahaifiyar ta tace "Mummy, Daddy ne fa yasa aka sace Widad"
"inji ubanwa? Rufen baki shashasha, in kika sake maganar nan yaji kema zeyi maganin
ki"
"Mummy a matsayinki na uwa, ya zakiji idan ni aka sace, yakamata ki cire tsoro a
ranki ki gayawa babana gaskiya, ranar da hakki ya tashi bashi kaɗai ze kama ba
harmu" Ta ƙare maganar tare da ficewa daga ɗakin gaba ɗaya
Kwata kwata duk bidirin da'ake Fahad beje yaga jikin Alhaji Nasir ba shima kuma
Alhaji Nasir be tambaya ba, yana fama da kansa.
Mussaman Abbas daga inda yake aiki ya kira Umman Yusuf ya sanar da ita ɓatan ɗanta,
dama ta kira wayar Yusuf harta gaji bata shiga. Aikuwa ta kiɗime sosai ta tashi
hankalin ta, ta shirya ta tafi gurin aikin Yusuf.
Ma'aikatan su kansu a kiɗime suke tun bayan da suka samu labarin ɓatan Yusuf,
Suleman yayi duk yadda zeyi a basu damar bincike akam al'amarin amma daga sama aka
hanasu, akace an riga an danƙa case ɗin a hannun wasu jam'ian tsaron.
Sosai Umman Yusuf tasa Abbas a gaba tana zabga kuka "dan Allah ranka ya daɗe ina
ɗana yake? Ku kuka sashi aikin nan ina kuka turamin shi shi kaɗai nake kallo inji
daɗi, Yusuf ne kaɗai dani, dan Allah ku temaka ku nemomin Yusuf ɗina"
Cikin ƙwarin gwiwa Sulaiman yace "ki kwantar da hankalinki Umma, Insha Allah indai
Yusuf ne zamuyi duk me yuwuwa muga mun kuɓutar dashi, an baza jami'an tsaro kuma
ins me tabbatar miki ba abunda zasuyi masa dan bashi suke hari ba, yarinyar da
yakewa aiki suke hari, dan ba suce abasu komai ba, yanzu haka mahaifin yarinyar
yana kwance a asibiti, kuma bashi da magana seta Yusuf"
Suleiman ya dinga kwantar mata da hankali, amma abunka da ɗa d uwa ta saurari
kalaman Suleiman ne kawai, amma bata ga alamar ana neman ɗan nata ba.
Umman Yusuf bacci ya ga gareta, balle cin Abinci banda kuka da Addu'a babu abunda
take yi wa ɗan nata, dan yanzu a duniya idan ta rasa Yusuf ba.
Jikin Alhaji Nasir ƙara rikicewa yake saboda damuwa, Anwar yace wa Mahaifiyarsa
"Mummy ya kamata ayi wani abu akan rashin lafiyar daddy, inze yuwu ayi visa a fita
da shi, kullum jikinsa ƙara rikicewa yake babu sauƙi"
Hajiya Halima tace "ko bangon duniya za'a kai shi idan Allah yayi niyyar karɓar
rayuwarsa ba yadda muka iya, anan ɗinma naga likitocin suna iya ƙoƙarin su, meye
kuma se an kwashi jiki an tafi ƙasar waje dan ɓarnar kuɗi"
"Mummy ɓarnar kuɗi kuma? Koma ɓarnar kuɗin ne naga nasane ai, meye amfaninsu in
baza'a nema masa lafiya ba"
"kaga Anwar ka kiyaye ni, kafini sanin abunda ya dace ne? Fita ka ban guri kafin in
ɓata maka rai, sakarai kawai"
Fitowa yayi gwiwa a saɓule yana tunanin wannan halina Mummynsa.
Gidan Bulama ya tafi, yaje ya tarar yana shirin fita, suka gaisa da Anwar, Anwar
yace "Daddy gurinka nazo"
Bulama yace "gashi ina shirin fita ne, Amma meya faru?"
Anwar yace "Daddy dama cewa nayi meze hana a fita da Daddynmu waje a duba shi
yadda ya kamata a can, naga kullum ciwon nasa gaba yake ba sauƙi"
Alhaji Bulama yace "Anwar kazo da magana me kyau, amma ka sani ko an fitar da
Daula waje in har baze cire damuwa dake ransa ba, babu yadda za'ayi magunguna suyi
masa aiki, haka likitoci suke ta faɗa"
"Amma da dai an jarraba, amma jikinsa yana bani tsoro"
Alhaji Bulama yayi shiru sannan yace "shikenan Anwar, zamu yi maganar da
mahaifiyarka, zanga abunda ya dace ayi"
Anwar yayi masa godiya sannan ya tafi.
Alhaji Haruna ne zaune akan kujera, fuskar nan tasa babu alamar imani ya kalli wani
matashi dake zaune yace
"doctor Sufyan, mun yaba da ƙoƙarin da kuke yi a Asibitinka akan Shahararren
Attajirin da'ake ji dashi a faɗin ƙasar nan wato Alhaji Nasir Daula"
Doctor Sufyan yayi murmushi yace "Nagode ranka ya daɗe"
Alhaji Musa yace "Kasan meyasa muka kiraka?"
Sufyan ya girgiza kai alamar aa'
Alhaji Haruna ya gyara zama yace "Abunda muke so da kai shine, bama son Daula ya
tashi"
Zare ido Sufyan yayi yace "kamar yaya?"
Alhaji Musa yace "Nutsu ka kwantar da hankalinka, ba muna nufin ka kasheshi ba, A'a
bama so ya tashi ya warke ta hanyar dena bashi magungunan da ya dace, kayi duk
abunda zakayi masa wanda ze ƙara kwantar dashi, idan kayi haka akwai lada me tsoka
da zamu baka"
Saleh dake gurin gaba ɗaya ya rikice yace "Amma Yallaɓai ba muyi haka daku ba, idan
kuma ya rasa ransa fa?"
Alhaji Haruna yace "Saleh ka rufewa mutane baki, karka ɓatamin rai"
Ya maida hankalinsa kan doctor Sufyan yace "Yaya zakayi ko bazaka yi ba?"
Doctor Sufyan yace "Nifa na ɗau Alƙawarin bazan cutar da lafiyar kowa ba kafin in
fara aiki, kuma Alhaji Nasir ya yadda dani, na daɗe ina duba shi lokaci ɗaya kuma
se in....
" Kai dakata " Alhaji Musa ya dakawa Sufyan tsawa yace " karka kawo mana maganar
banza malam, idan baka yi ba zamu nemi wani, kwata kwata aikin wata uku muke so
kayi mana, za mu baka Naira miliyan goma, idan yayi maka kaɗan zamu ƙara maka"
Zare ido Sufyan yayi yace "miliyan Goma"
"ƙwarai kuwa, miliyan goma idan kuma kaƙi zamu saka wani amma ka tabattar da kaima
ba zamu ƙyaleka ba"
Cikin hanzari Sufyan yace "zanyi ma, na amince zanyi insha Allah karka damu Alhaji"
Shiru Saleh yayi yana tunani, wato akan kuɗi mutanen yanzu duk alkhairinka sesu
manta, idan baze manta ba dangin Sufyan ɗaiɗaiku ne Daula be kai aikin Hajji ba,
Amma ya amince ze karɓi kuɗi ya cutar da Alhaji Nasir "
Da Sufyan ze tafi dubu ɗari biyar suka bashi wai ya zuba mai a mota.
Saleh yayi shiru abun duniya duk ya dameshi.Su Alhaji Musa kuwa cigaba da ƙulle
ƙullen sharrinsu suka yi.
Wayar Alhaji Haruna ce ta fara ringing, suka tsagaita da dariyar da suke Ya ɗaga
wayar yace
"Yaya me Adda, ya ake ciki ta faɗa maka kuwa?"
"Ina fa ta faɗa se wahalar damu take, ga taurin kai da tsiwar tsiya, sannan ta bada
saƙo a baku"
Alhaji Musa a gigice yace "Kamar ya ta bada saƙo abamu ta sanmu ne?"
Me adda yace "ina nasan mata, cewa tayi mu cewa wanda suka sa a sace ta, ta tattaar
duk wata hujja akan su, ko bayan an kashe ta asirinku ze tonu"
Wani gumine ya shiga tsatsafowa Alhaji Haruna yace "ƙarya take bata sanmu ba, a
gidan uban wa ta sanmu balle ta tattara wata hujja a kanmu, yanzu kana ina ne?"
"ina cikin gari mana, naje Asibiti ne wani yarfi yarinyar nan ta min na kasa ko
miƙewa tsaye, na ɗauka ma na tashi daga aiki"
Alhaji Musa yace "wani sakarci ne zesa ku baro su acan, maza ka koma ku gana mata
Azaba iya Azaba seta faɗi inda takaddun suke, idan ta faɗi inda suke ku kashe su
kawai"
Saleh yace "What akan me za'a kashe ta?"
Alhaji Musa be saurari Saleh ba ya cigaba da wayar sa.
Me Adda yace "gaskiya Oga kisan Yarinya kamar wannan ba kamar kashe sauran mutane
bane, tsaf wannan cinnakun zasuyi ram damu"
Alhji Haruna yace "ba wanda ze kama ku, zancen nan da muke maka gaba ɗaya mun siye
jami'an tsaro ba wani bincike da'ake akan ɓatan nata, dan haka ka gaggauta zuwa
jibi idan bata faɗa ba ka tirsasa ta, ta gaya maka wasu hujjoji take dasu sannan ka
kashe mana su"
Me Adda yace "angama Oga"
Alhaji Haruna ya sharce gumi yace "bala'i, Musa anya ba dagaske yarinyar nan ta
gano mu ba, karfa muje dagaske take"
"Rabu da ita ƙarya take, da dagaske ta sanmu da tuni ta ɗau mataki akanmu, amma
kasan bamu gayawa Munir da Bukar hukuncin da muka yanke ba?"
Alhaji Haruna yace "Suma idan mun gaya musu hukuncin da za susa ayi mata kenan a
kashe ta kawai, karta ja mana masifa"
Alhaji Musa ya kalli Saleh yace "wai kai meye naka na saka baki dan munce a kashe
ta, kabi a sannu fa wallahi kar kasa musa a haɗa da kai, kabi umarnin mu kawai"
Saleh yayi murmushi yace "Tausayin Daula ne ya kamani wallahi, karka damu bazan
baku kunya ba insha Allah dani za'a kammala komai nima in samu rabona"
"daka temaki kanka" cewar Alhaji Haruna, yayin da cikkunansu suka ɗuri ruwa.
Yusuf yana nan zaune rungume da Widad, har duhu yayi gari ya waye, sam be bacci ba
gani yake da yayi bacci Widad zata mutu, dan bugun zuciyar ta da yake ji shike
tabattar masa tana da rai, dan wani lokacin har motsawa take.
A hankali Yusuf ya kwantar da ita, yayi taimama yayi sallar Asuba, shima gaba ɗaya
jikinsa a sake yake babu ƙwari saboda azabar wahala, ga yunwa ga duka ga cizon
sauro ga azabar sanyi dake gurin, amma gaba ɗaya yafi tausayawa Widad, lokaci
lokaci yakan kwance hannun nata, ya goge jinin ya sake ɗaure mata, ga wani irin
zazzafan zazzabi da ko sauka bayayi a jikinta.
A hankali Widad ta buɗe ido, sedai dishi dishi take gani bata gane komai, tana yi
tana lumshe ido haka take kallon Yusuf. Yusuf ya girgiza ta yace "Alhamdilillah,
you are alive" Bata iya amsa masa ba, sedai idonta ya sake rufewa
Yana rungume da ita, yayi shiru yana ta ambaton Allah, babu zato ba tsammani yaji
ana ta sukuwa a saman roofing ɗin ɗakin, Yusuf ya ɗaga kai yana son gane meke
faruwa haka? Cigaba da sukuwa akayi a gurin anata ƙoƙarin ɓare kwanon, can kuma
se'aka dena, yaji anata ƙoƙarin buɗe ƙofar da suke ciki, waze gani Saleh ne ya
shigo cikin ɗakin.
A gigice Yusuf yace "kaine? Da kai aka haɗa baki kenan aka mana haka?"
Saleh yace "baka da lokacin wannan tambayoyin, zuwa nayi na tseratar da ku, ka
adana tambayoyinka, idan kun tsira seka yi su"
Hankalinsa ya kai kan hannun Widad dake sume yama zubar da jini, da sauri ya ƙaraso
yace "meya sameta haka? Harbinta sukayi?"
Yusuf bece masa komai ba, sedai kallon tuhuma da yake ta binsa dashi.
Saleh yace "zaka iya tafiya kuwa?"
Yusuf ya jinjina masa kai alamar eh, "to taso maza"
Yusuf ya yunƙura ya miƙe, amma ƙafafunsa se rawa suke saboda dukan daya sha, ga uwa
uba yunwar da yake ji. Amma cikin jarumta, da sadaukarwa ya miƙe ya goya Widad a
bayansa.
Suka fito daga gidan, Saleh ya maida gidan ya rufe, sannan ya ɓare saman roofing
yayi hanya, sannan yayi musu jagora hannunsa ɗauke da compass dake nuna masa
direction suka nausa cikin daji.
Yusuf ji yake kamar ze kifa, amma haka ya cigaba da tafiya, Saleh ya kalle shi yace
"ko zaka sauketa in ta yaka?"
Yusuf ya girgiza kai yace "A'a karka damu"
Tafiya sukayi bata wasa ba, ƙafar Yusuf ko takalmi babu, ya dinga taka abubuwa
danma ta cikin ciyayi suke kutsawa, haka suka dinga tafiyar cikin sauri, suna bi
takan ciyayi dan kaucewa barin sawunsu yadda za'a gane hanyar da suka bi, daji ne
har daji me sarƙaƙiyar tsiya, da manyan bishiyu.
Sunyi tafiya me nisan gaske sannan suka fito titi, sam Yusuf be san a ina suke
bama, Saleh ya nunawa Yusuf mota yace "ya shiga"
Yusuf yayi turus ya kalli Saleh, a wahalce yace "wannan taimakon ma da kayi mana
mungode, amma bazan hauba, Insha Allah zamu bar gurin nan".
"Yusuf, wallahi suka kamaku kashe ku zasuyi, da inada niyyar cutar daku da bazan
ceceku ba"
Da ƙyar Yusuf ya yadda, ya hau motar, da alama Saleh ya gama shirya komai.
Shima Saleh haka yayi doguwar tafiya dasu a motar, tafiya kamar za'a bar duniya
dazuka kawai suke ratsawa, tituna bakowa se su kaɗai, Shiru ne ya wanzu tsakaninsu
har suka fara fita gari.
Wani ɗan madaidaicin Asibiti suka tarar a hanya, Saleh yayi parking Yasa Yusuf ya
ɗakko Widad suka shiga Asibitin.
Kuɗi Saleh ya ajiyewa likitan, dan haka ba wani dogon bincike suka karɓi Widad,
Amma Yusuf yaƙi zuwa ko'ina, a gabansa aka cirewa Widad bullet, akace se an tafi
neman jini za'a ƙara mata.
Yusuf yace a ɗibi nashi, Saleh yace "baze yuwu a ɗebi naka ba, kaima a galabaice
kake akwai buƙatar a duba ka"
Yusuf ya dage sedai a gwada jininsa in zeyi a ɗiba a sa mata.
Aka duba aka ga Yusuf ze iya bawa Widad jini, saboda rukunin jininsa ake cewa
universal donor wato O-, sedai an samu jinin Yusuf da malaria, likitan yace
"baze yuwu asa mata jinin ba"
Shikuma Yusuf yace be yadda da kowa ba, jininsa za'a saka.
Saleh yace "kaga doctor, koma menene a jinin nasa saka mata, can taƙarke musu dan
zamanmu anan akwai hatsari"
Aka bawa Yusuf Abinci, amma ya kasa ci se ɗan kaɗan saboda hankalinsa na kan Widad,
ana ɗibar Jinin Yusuf jiri ya ɗebe shi ya yanke jiki ya faɗi, haka aka ɗauke shi
aka bashi gado.
Akayi treating ɗin raunkan jikin Yusuf, aka masa allaurai dan samun relief.
Aka sakawa Widad jinin Yusuf, tare da sauran Allurai, Yusuf na farfaɗowa ya fara
tambayar ina Widad.
Likitan yace "wai dan Allah meye alaƙarsa da wannan yarinyar haka?"
Saleh yace "ƙanwarsa ce shiyasa ya damu da ita, 'yan fashi ne suka harbeta akan
hanyar su ta tafiya, ita kaɗai yake da ita shiyasa"
Yusuf ya koma inda Widad take yasa ta a gaba, ya ƙura mata ido ko ƙyaftawa bayayi,
tunda aka cire bullet ɗin nan har yanzu bata farka ba.
A hankali ta buɗe idonta, ta yunƙura zata miƙe Yusuf ya riƙeta yace "bi a hankali
fa jikinki babu ƙwari"
Ta kalli Yusuf tace "A ina muke nan?"
"I think we are save now insha Allah, yanzu zamu koma gida" ya bata amsa
Saleh ya shigo ɗakin yace "waye yace maka zaku koma gida ne"?
Widad ta kalli Saleh ta ƙura masa ido, kamar taga baƙuwar halitta.
Yusuf yace "meyasa ba zamu koma gida ba yanzu?"
"saboda idan kuka koma, da kai da ita da mahafinta duk sesun kasheku"
Yusuf yace "meyasa?"
"Zan gaya maka komai, Amma daga nan mafaka zan baku, inda zaku ɓuya ba zasu san
inda kuke ba na gama shirya komai daga nan tafiya kawai zamuyi"
Saleh ya miƙowa Yusuf wata babbar jarkar youghurt yace "gashi nan kuci nasan ba
wani Abincin kirki a cikinu, sannan ka canza riga ita kuma a sama ta hijjabi"
Yusuf ya karɓi youghurt ɗin ya buɗe ya miƙa mata, amma ta ɗauke kai, Yusuf ya
girgiza youghurt ɗin ya ɗaga kai ya sha, sannan ya sake miƙa mata.
Se a lokacin ta karɓa, ta dinga sha saboda azabar yunwar da take ji, sedai tana
gama sha ta dinga amai saboda kwanakin da tayi babu Abinci a cikinta.
Saleh yace "Yusuf yakamata mu bar gurin nan da gaggawa in kaiku inda zaku fake,
zamanmu anan hatsari ne na gaske"
Yusuf yace "Amma jikinta har yanzu bata da lafiya, ya za'ayi mu tafi a haka?"
Saleh yace "zamu karɓi magungunan da zaku cigaba da Amfani da shi, amma dole mu bar
gurin nan"
Haka likitan ya tattara magungunan Yusuf dana Widad ya basu, suka hau mota Saleh ya
cigaba da nausawa dasu seda suka sake shafe wata tafiyar, Widad kam magungunan data
sha basu saketa ba dan haka duka tafiyar nan bacci take, seda sukazo wata mararraba
sannan Saleh yayi parking, wata tsohuwar motace akori kura ('yar ƙurƙura) gaba ɗaya
ta sha jiki ta fatattake, hatta fentin jikinta ya koɗe duk ta mole, anyi parking
ɗintabakin hanya.
Wani mutum ne ya fito daga a kori kurar, suka gaisa da Saleh, Saleh ya bashi
mukullin motar da suka je da ita, suka kwance lambar motar dake jiki da wata.
Saleh Ya kalli Yusuf yace "Yusuf ku fito wannan motar zamu hau mu ƙarasa"
Yusuf yace "nifa Saleh ban gane wannan abubuwan ba, kodai kaima kana da wani
ƙudurin ne akanmu"
"Yusuf wallahi ba wani abu da nake shiryawa don in cutar daku, sedai ƙoƙarin ceton
rayuwar ku"
Yusuf ya fito hannun sa ɗauke da Widad suka shiga 'yar ƙurƙuran nan, Saleh yaja
motar. (Yau Widad ce a cikin irin wannan motar🙄)
Tashin hankali ba' a samasa rana, duk wannan uwar tafiyar da suka sha Nafila ce
akan wadda suke yi yanzu, wata irin ruɓaɓɓiyar hanya suka bi, banda ƙura babu
abunda yake tashi wata irin lalatacciyar hanyace, duk kwazazzabai da turɓaya ga
uban ramuka, wani ramin in suka shiga da ƙyar suke fita ga ƙurƙuran nan se wani
irin ƙugi injinta yake yi, gashi sun matsu a motar, duk yayin da suka shiga rami
haka suke bige kafaɗu da ƙarfen motar.
Wannan kwaraf kwaraf ɗin ne yasa Widad ta farka, a hankali ta kalli Yusuf tace
"A ina muke?"
Yusuf yace "Sannu ya jikin naki?"
Bata bashi amsa ba ta kuma cewa "A ina muke ne?"
"Mun kuɓuta ne, Saleh ze bamu mafaka"
Ɗan lumshe ido tayi sannan tace "Na gaji jikina ciwo yake, hannuna zafi kaina ze
fashe, Wayyo Allah Daddy na"
Yusuf yace "kiyi haƙuri insha Allah komai ze daidaita, zakiji sauƙi mun taho da
magunguna"
Shiru tayi ta sake kwantar da jikinta a ƙirjin Yusuf, hawaye na bin gefen idonta.
Tun Yusuf yana sa ran tafiyar ta ƙare har yayi shiru ya zubawa sarautar Allah ido.
A hankali Yusuf ya fara ganin gidaje tsilla tsilla a gurin, gine gine na tsurar
ƙasa haka Gidajen suke, wasuma ko katanga babu a haka suke, yayi mamakin wannan
irin ƙasurgumin ƙauye haka da yadda mutane ke rayuwa a cikinsa, suka baro duk bakin
hanya suka shigo wannan surƙuƙin guri sukayi ginin Gidaje.
A hankali suna cigaba da tafiya, yaga ƙauyene sosai me ɗauke da gidaje da mutane a
ciki, sedai sunyi hannun riga da duk wani abun more rayuwa da jin daɗi, kama daga
Makaranta, Asibiti, ko wani abu me kama da borehole tunda suka shiga ƙauyen Yusuf
be ganshi ba.
A ƙofar wani babban gidan ƙasa, an shafawa ƙofar gidan farar ƙasa, alama dai
mamallakin gidan yana riƙe da wata sarauta ne a ƙauyen.
Saleh yace "Yusuf ina zuwa"
Ya sauka daga motar ya shiga cikin gidan, Yusuf yana ta ƙarewa gurin kallo yana
tunanin anya Widad zata iya rayuwa a cikin gurin nan?
A hankali yaji tace "Ka yadda da Saleh, kana da tabbacin shima ba cutar damu
zeba?"
"Ko ban yadda dashi ba, Allah baze bashi damae cutar damu ba, nidai fatana inga
kinji sauƙi gaba ɗaya"
Ajiyar zuciya tayi, tai shiru ba tace komai ba can Saleh ya fito shida wani
dattijon Mutum, kansa ɗauke sa rawani.
Suka ƙaraso gaban akori kurar, dattijon yace "sannu dai ɗan samari"
Yusuf yace yawwa Baba, barka da yamma
"Yawwa barka" mutumin ya kalli Saleh yace "sune wannan?"
"Eh sune wanda na gaya maka, ina son su zauna a gidanka na wani lokaci, kafin komai
ya lafa su koma"
"Amma kana ganin babu wata matsala Saleh, nifa bana son abunda zezo ya ɗagawa
Al'ummar garina hankali, kasan ku mutan binni se a hankali"
Saleh yace "Haba dai, wane irin matsala taimako zakayi, baka ga yadda suke a
galabaice ba, babu wata matsala insha Allah"
"Shikenan, shigo dasu se a kaisu ɗakin daka gyara musun"
Yanzu ma Widad ba zata iya tafiya ba, Yusuf ne ya ɗauke ta zuwa cikin gidan.
Duk da rabi tana hayyacin ta rabi bata hayyacin ta, tana mamakin mutane ne ke
rayuwa a wannan gidan, roofing gidan kansa na Azarane, ta dinga kallon roofing tana
tunanin menene wannan? Yayin da wasu ɗakunan roofing danga ne.
Tunda suka shigo gidan, mutan gidan maza da mata suka fito suka yi cirko cirko
kamar zakaru suna binsu Yusuf da kallo kamar sunga baƙin halitta.
Wani ɗakine a can ƙarshen gidan, Saleh yasa mukulli ya buɗe ƙofar katakon dake
ɗakin ya shiga yacewa Yusuf "bismillah"
Ba lefi ɗakin yana da girma amma ba sosai ba, yana da taga guda ɗaya wadda akayi ta
da katako da kuma langa langa, ɗakin ginin ƙasa ne tsura, sedai anyiwa ƙasan floor,
aka shimfiɗa buhu a ƙasa sannan aka kawo tabarma duk aka shimfiɗa.
Akwai matsaikaciyar katifa a shimfiɗe a ƙasa, da bargo guda biyu se fula guda ɗaya
duk sababbi.
Gefe ga tulu, da wani ƙaramin kwandon kwanuka da 'yan kwanuka a ciki, gefe ga
sababbun bokitai guda biyu, da sabuwar buta.
Akan katifar Yusuf ya kwantar da Widad, da duk inda ya motsa ta ciwo yake mata.
Dattijon yace "wannan bata da lafiya ne haka?"
Saleh yace "Eh bata da lafiya, a hannun masu garkuwa fa na karɓo su, na maka
bayanin komai, dan Allah Baba a kula dasu, duk abunda suke buƙata ayi musu"
"Shikenan, indai nine baka da matsala, ko baka kawo kowa ya zauna a gidan nan ba,
gidan nan na jama'a ne, Allah ya basu lafiya"
Ya juya ya fita, yana kora yaran da suka yi dandazo a ƙofar ɗakin suna leƙen su
Widad.
Idon Yusuf ne ya sauka akan akwatunan Widad data shirya domin tafiyar da zasuyi, da
traveling bag ɗinsa da suka bari a motar da'aka sace su.
Yusuf ya zare ido yace "Nifa Saleh ina buƙatar kamin bayanin abubuwa, ya akayi ka
samu jakunkunan mu na tafiya? Ya akayi kasan idan muke kaje ka tseratar damu?"
Saleh yace "Nasan zakayi mamaki, kuma dole ku tambaya, Amma yanzu ina sauri saboda
zan koma kano kar su gane wani abu a ƙasa su fara zargina, duk yadda aka shirya
sace ku dani akayi shi, Tun bayan sace ku ni kuma na fara shirin yadda zaku tsira,
amma ka sani koda wasa karka kuskura kayi gangancin barin ƙauyen nan in bani na
fita daku ba, dan wallahi suka ganku sekun kasheku"
Yusuf yace "wai tsaya, wai inane nan ma tukuna?"
"Nan wani ƙauye ne a cikin garin Bauchi, Zan dinga zuwa ina duba ku, a waccan jakar
na ajiye muku abubuwan da ba'a rasa ba da zaku buƙata kafin ku saba da irin rayuwar
da suke yi, ga kuma kayanku can dana kawo nan, nan gidan ƙanin kakana ne dan haka
insha Allah baku da wata matsala, idan ma dawo za kaji komai "
Saleh ya fita tsakar gida ya kalli wata dattijuwa yace "Gwaggo dan Allah Amana nan,
a kula da baƙin nan dan manyane duk abunda suke buƙata ayi musu"
Gwaggo tace "Lallai kam, baƙin suna da girma a gurinka, tunda sanadinsu gashi kana
leƙo mu"
Wata mata a tsakar gidan tace "Eh aimu da yake cinyesu zamuyi shiyasa ba'a bamu
amanar baƙin ba se ita"
Saleh yace "Aifa kedai halinki yana nan bazaki canza ba" yayi gaba abunsa, ya tafi
gurin me gari suka sake tattaunawa sannan ya tafi.
Haka Saleh ya tafi ya bar su Yusuf a cikin wannan ƙasurgumin ƙauye.
A hankali Widad tayi juyi, ta ƙarewa ɗakin da take ciki kallo, wai anan zata zauna
ita da suka zo sam bata zaci wai nan mutane ne ke rayuwa a cikin gurin ba se yanzu.
Yusuf yaje yayo Alwala, yazo ya tada salla sedai duk inda yayi se mutanen gidan su
bishi da kallo.
Widad ta cire hijjabin jikinta, jikinta se faman ƙaiƙayi yake mata, Yusuf ya idar
da salla zeyi magana ta riga shi ta hanyar cewa "zanyi wanka"
Ɗan zare ido yayi yace "to shikenan, bari inwa mutan gidan magana"
Ya fito tsakar gidan, yaga wadda Saleh ya kira da Gwaggo ɗazu tana ta aiki a tsakar
gida, yace mata "dan Allah Mama ko zamu samu ruwan ɗumi, mara lafiyar zata yi
wanka, nikuma ko na sanyi ne na samu se inyi Amfani da shi"
Tayi murmushi tace "bakomai, na zuba ruwan tuwon dare dama, bari in ɗibar maka"
Yusuf yace "to nagode"
Ya tafi ɗakin su, ya ɗakko sabon bokiti, aka zuba ruwa aka sirka Yusuf ya koma
ɗakin yace "An haɗa ruwan"
Ta tashi zaune ta fara kiciniyar cire rigar jikinta, sedai hannunta na hagu shine
wanda aka harbeta, na dama kuma yana ciwo saboda duka da wahalar mota.
Yusuf ya juya mata baya da nufin ta kintsa ya kaita banɗakin.
"Zoka tayani cire wannan rigar na kasa cirewa....
(Akwa ƙura fa🚶 🚶 🚶 🚶 🚶)
Share, share and share please 🙏
Domin, gyara sharhi ko shawara Ayshercool 07063065680
_*AƘIDATA*_
PERFECT WRITERS ASSOCIATION
(WE AIN'T PERFECT BUT WE ARE ALWAYS TRYING OUR BEST, TO MOTIVATE AND ENTERTAIN OUR
READERS)
https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/
*Story and written by*
_*AISHA HUMAIRA (Daddy's girl)*_
The experience writer of *ABDUL JALAL** WATA KISSAR.... (SAI MATA) *And now *AƘIDA
TA *
I dedicated this book to my Mum (Malama Nafisat Adam Muhammad) i love you mum
Haƙƙin Mallaka ⚠ : Littafin nan mallaki nane, tun daga sunan labarin zuwa abunda ya
ƙunsa, ban yadda wani ko wata ya sauyamin ko yin Amfani da wani ɓangare na labarin
ba ba tare da izinina ba, Nagode
https://www.wattpad.com/user/Ayshercool7724?
utm_source=android&utm_medium=link&utm_campaign=invitefriends
ELEGANT ONLINE WRITER'S
PART1 Page 28_29
Gaba ɗaya dirircewa Yusuf yayi, se yayi kamar beji me tace ba, ganin yaƙi magana
yasa itama tai shiru ta nemi guri ta kashingiɗa.
Yusuf ya waigo yace "Kin gama kintsawar ne?"
Kawai ya ganta a zaune.
"Ya haka kuma? Se ruwan ya huce?"
"Ban sani ba, ai kana jina ina magana kayi min shiru, nace kazo ka tayani in cire
rigar nan, amma kayi kamar baka jiba"
Ikon Allah bata da lafiyar ma, an tsira da ƙyar bakinta be mutu ba, gashi da ƙyar
take maganar.
Yusuf yace "bari inyiwa mutanen gidan magana, se suzo su cire miki"
"Wallahi babu matar da zata taɓani" tai maganar tana kuka
Seda Yusuf yayi shiru, sannan ya tako a hankali kan katifar da take, ya zagaya
bayanta hannunsa rawa yake ya zuge zip ɗin doguwar rigar tata ƙasa.
Farar fatarta ta bayyana cikin wata baƙar vest, shiru yayi yana kallonta, ta janyo
hijjabi ta mayar ta yunƙura zata miƙe tsaye amma jiri ya kwashe ta.
Yusuf yace "ki dena gaggawa, a halin da kike ciki ɗin nan, idan kika faɗi zaki ji
ciwo fa"
Ya duba ya ɗakko soson wankanta dake cikin Akwatinta, sedai babu sabulu haka ya
riƙota suka fito, Gwaggo na ganin haka ta taho da sauri da nufin ta taya Yusuf,
Amma Widad ta maƙale hannunta, ta manne a jikin Yusuf tabi gwaggo da ido, gwaggo ta
tsaya sororo tana kallonsu.
Yusuf yace "Mama karki damu, kiyi haƙuri haka halinta yake bata da yadda ne"
Matar dake gaban murhu ta juyo ta kallesu tace "yau nake ganin ikon Allah, wannan
gwandamemiyar matar ce take ƙyuya se kace me shan Nono, taɓ amma lamari ya ɓaci,
koda yake wannan kamar ma ba irin tamuce ta nan ƙasar ba"
Widad tabi matar gaban murhun da kallo, haƙoranta yellow shar ga haƙorannata wasu
sunyi goyon kura, gata baƙa sosai ga fuskarta duk tsagu, gashi se ƙara baje hanci
take.
Gwaggo tace "Haba Hari, ina ruwanki da ita irinku ne ke sawa adinga cewa Hausawa
basu da kirki, yanzu da taji abunda kike faɗa ba"
Zatonsu duk Widad bata jin hausa, gwaggo ta kalli Yusuf tace "ga banɗakin can seka
kaita"
Suna zuwa ƙofar banɗakin Widad tayi tiris taƙi gaba taƙi baya. Yusuf yace "muje
mana seki shiga kiyi wankan"
Girgiza masa kai tayi tace "Ni wallahi tsoro nake ji bazan iya shiga ba" sam Widad
gurin be mata kama da banɗaki ba, kamar wani gidan horo haka taga gurin.
"meye abun tsoron, zan jiraki anan gurin kiyi ki fito"
Riƙe shi tayi tsam tana girgiza kai tace "Ni na fasa wankan, bazan shiga nan ba"
Gwaggo tace "ɗan nan ya naga bata shiga ba, lafiya kuwa?"
Yusuf yace "wai tsoro take ji ba zata iya shiga ba"
Gwaggo tace "Allah sarki, ƙasashenku babu irin wannan banɗakin ko? Abun duk se
haƙuri ai, akwai wani ɗaki da babu komai a ciki ta shiga tayi a ciki kawai"
Yusuf yace "mungode Mama"
"A'a bakomai"
Ta nuna musu ɗakin, duk yadda Yusuf ya tsani roƙo, haka ya karya billensa ya
tambayi sabulun wanka, sedai Sabulun da suke wanka da shi irin sabulun nan ne kore
na wanki me ƙarnin tsiya, Yusuf ya miƙawa Widad, tasa hannu ta karɓi sabulun ta
kalli Yusuf kawai yaga Hawaye a idonta.
Tausayinta ya kama shi, amma ya basar kamar bega hawayen idonta ba, haka ta shiga
ɗakin da siminti a ƙasan ɗakin, tayi wankan nan tsigar jikinta na tashi saboda
yadda ruwan in ya zuba a ƙasa yake taɓata, ga tashin zuciya saboda ƙarnin sabulun,
ba shiri ta ajiye sabulun tayi wankan a haja, sedai taji daɗin ruwan zafin sosai "
Ta fito tana kama bango, Yusuf ya riƙeta ya maida ita ɗaki, ya duba Akwatinta ya
ɗakko kaya ya bata, ta saka itama tayi salla.
Saleh beje gida ba se bayan sha biyu na dare, yayi tunanin ko yaje yayi magana da
doctor Safwan amma wata zuciyar ta hana shi, saboda yadda Safwan ya dinga rawar
jiki da yaji batun kuɗi tsaf zeje ya gaya musu, yaje ya sameshi.Gaba ɗaya tunaninsa
ya koma kan yaze ƙwaci Alhaji Nasir a gurin wannan Azzaluman mutanen? Dan ba
ƙaramin shiri suke dashi ba.
Me Adda suka koma inda suka ajiye su Widad, da niyyar ayita ta ƙare, suna zuwa suka
buɗe gidan, suka shiga suka saka mukulli suka buɗe ɗakin suka ga wayam ba kowa a
ciki, a kiɗime ɗayan yace "Me Adda bafa kowa a ɗakin nan"
Ƙarasawa yayi da sauri ya shiga ɗakin shima amma ba kowa a ciki, nan da nan suka
gigice suka shiga lalauben su Widad.
Me Adda yace "Mutanen da ko iya takawa basayi, ta yaya zasu gudu? Duk matakan
tsaron dake gurin nan ina sukabi suka fita?"
Cam ɗaya daga cikinsu ya ɗaga kai ya kalli Roofing ɗakin yace "me Adda kalli ta
nan suka fice" yai maganar yana nuna musu saman roofing ɗakin
Me Adda a gigice yace "ya zama dole mu bazama neman su, amma ta yaya suka samu abu
sukayi hanya har suka fita?"
Ɗaya daga cikinsu yace "Allah ne ya san yadda suka gudu"
Me Adda yace "bamu da lokacin ɓatawa, maza maza mubi sahun su yadda suke a
galabaice ba lallai su iya tafiya me nisa ba" Haka kuwa akayi suka rarraba kansu a
cikin daji.
Saleh yaje duba Alhaji Nasir a Asibiti, ya tarar da Anwar a gurinsa, suka gaisa
yayi masa ya me jiki, ya ɗan dubi Anwar yace"Amma meyasa baza'a fita da Alhaji waje
a nema masa magani ba?"
Anwar yace "Nayi duk me yuwuwa inga an fita da shi, amma Mummy da Alhaji Bulama
sunce nan ma ana kula da shi"
Saleh yace "Abunda za'ayi yanzu shi ne, ka ɗauke shi ka canza masa Asibiti ba tare
da ka sanar dasu ba, ko ba'a fita dashi waje ba a camza masa Asibiti, sedai kawai
suga ka canza maaa Asibiti"
Anwar yace "Amma zasuji babu daɗi idan nayi hakan, suna ganin nanma ana ƙoƙari
akansa amma inyi haka kamar ban kyauta ba"
"Anwar zamanku a Asibitin nan yaci ace jikinsa yana karɓar treatment yadda
yakamata, amma har yanzu babu wani cigaba, mu canza masa wani Asibitin kawai"
Anwar yace "Kana ganin babu matsala idan muka yi hakan?"
"eh babu matsala, Amma karkace ni nace ka canza masa Asibiti"
Anwae yace "shikenan, ka kawo shawara me kyau insha Allah gobe in Allah ya kaimu
da Safe, sedai suzo su tarar na canza masa Asibiti ni kaina rashin samun sauƙin nan
nasa yana bani mamaki"
Doctor Sufyan ne yake ta zagaye acikin Office ɗinsa, yana tunanin me yakamata yayi
akan batun su Alhaji Haruna, yana tuno irin halacci da kirkin Alhaji Daula, idan
aka haɗa kai dashi aka cutar dashi to tabbas mesa Adalci ba, Amma wani mataki
Alhaji Musa zasu ɗauka akansa idan har be abunda sukace ba?.
Fitowa yayi da sauri daga office ɗin nasa ya nufi ɗakin da Alhaji Nasir yake, yana
zuwa shiga suka haɗu da Saleh, suka yi kallon kallo babu wanda ya cewa kowa komai
suka wuce.
Ya shiga ɗakin da Sallama, Anwar ya amsa masa, doctor Sufyan yace "Anwar yame jikin
kuwa?"
"Jiki sedai muce Alhamdilillah, amma doctor na fara karaya da yanayin jikin sa,
babu wani cigaba fa gashi nayiwa su Mummy magana a fita dashi amma sunƙi amincewa,
na rasa dalili"
Sufyan yace "ka kwantar da hankalinka Anwar, treatments ɗin dai da muke masa anan,
shi za suyi masa a can, komai ze tafi dai dai ze warke in Allah ya yarda"
Anwar yace "Shikenan Allah yasa"
Haka Widad ta kwanta akan katifar, Yusuf ya ɗau bargo ɗaya ya koma bakin ƙofa ya
shimfiɗa ya kwanta, shiru Widad ta kasa bacci, tana tunanin wai itace zata kwana a
gurin nan, ga sauro se kururuwa yake mata a kunne, ga zafi ga jikinta da yake ciwo,
ga rashin lafiya tana fama.
Ɓangaren Yusuf ma shiru Yayi yana saƙe saƙe, yana tunanin wani hali Ummansa take
ciki, yasan duk inda take hankalin ta a tashe yake, dan tun tasowarsa be taɓa nesa
da ita ba, wani ɓangare na zuciyar sa yana tunanin Alhaji Nasir yasan tabbas shima
yana cikin damuwa, ko wani haki yake ciki Allah masani, ga zamansa da Widad a ɗaki
ɗaya baze yuwu ba, tunda ba muharramarsa bace, gashi ba ta yadda da kowa se shi, ga
wasu abubuwan se anyi mata saboda bata da lafiya, dole idan Saleh yazo yayi masa
magana asama masa wani ɗakin, dan gudun afkawa tarkon sheɗan.
Yana nan kwancw sauro yana cizonsa, yana masa hada hada aka, ga cinnaka da yake ta
gasa masa cizo a gurin nan, tunani yake Allah yasa kae cinnakan ya ciji Widad.
Katsam ya jiyo sheshsheƙar Widad tana kuka, da yayi kamar ya basar amma ya dinga
jin kukan nata a zuciyar sa, tabbas yakamata a tausaya mata.
Ɗakin baƙiƙirin da duhu, ko tafin hannu ba'a iya gani saboda duhu, haka yaja
jikinsa cikin lalube yaje gefen katifar ta yace "uwa ɗakina kukan me kike?"
Maimakon tayi magana seta sake fashewa da kuka, Yusuf yace "Am sorry, i feel your
pain kiyi haƙuri ki karɓi hakan a matsayin ƙaddarar mu, yakamata ki gode Allah da
yasa muka tsira daga hannun mutanen nan, kuma insha Allah zamu koma gida ki dena
kuka, kiyi bacci zaki ji daɗin jikin ki"
"I can't sleep, sauro ya dameni zafi nake ji, kuma ina tunanin Daddy na"
Tai maganar tana sake fashewa da kuka.
"kiyi hakuri, Insha Allah Daddy yana nan lafiya, komai ze wuce kamar be faru ba, ki
dena kuka kinga baki da lafiya"
Ajiyar zuciya kawai tayi, ta lumshe idinta tana jin yadda zuciyarta ke raɗaɗi.
Da Asuba yayi Alwala yazo ya tada Salla, bacci take dan sam bata samu bacci ba da
daddare, seda ya idar sannan ya tashe ta ya kaita tayi alwala tazo ta tada salla.
Da gari ya fara haske me gari da kansa yayi sallama a ƙofar ɗakin su Yusuf, Yusuf
ya fita ya durƙusa ya gaishe shi.
Ya amsa cikin mutuntawa yace "Ya me jikin kuwa?"
Yusuf yace "Jikinta da sauƙi Alhamdilillah"
"Masha Allah, Allah ya ƙara afuwa ya bata lafiya, karkaji komai ku saki jikinku duk
abunda kuke buƙata kuyi magana insha Allah baze gagara ba"
Yusuf yace "Masha Allah, mungode sosai da wannan karamcin naku"
"Karka damu, ai shi ɗa na kowa ne"
Wajejen ƙarfe tara na Safe aka aiko yaro ya kawowa Su Yusuf Koko me zafi da ɗumamen
tuwo, Yusuf ya karɓa yace sun gode.
Ya kalli Widad dake zaune tayi shiru, gwanin ban tausayi yace "ga Abinci an kawo,
ki daure kici se Kisha magani"
Kallon kwanon tuwon tayi, sannan ta kalli kwanon da'aka zubo kokon, har ɗan gara
kwanon kokon, amma na tuwon dai se a hankali ga warin daddawar nan ji tayi kamar
tayi amai, miyar nan baƙa wuluk ga uban tuwo a ido in ka kalli Tuwon nan kasan ze
azabar tauri.
Ta kalli kokon tana tunanin ta ina zata sha abun sha a cikin kwano, ta kalli Yusuf
tace "janye min wannan baƙin Abincin kar inyi amai"
Kallonta yayi da mamaki, tuwon ne bata sani ba ko kuma tsabar rainin hankali ne? Ta
miƙa hannu ta ɗau kwanon kokon, ta dinga juya kwanon sannan ta kai bakin ta, karɓa
ɗaya tayi ta dire kwanon ta yamutsa fuska kamar zata yi kuka.
Yusuf yace "ya dai?"
"Ba daɗi" ta bashi amsa
"to ai badan daɗi zaki sha ba, kinga nan ba kamar gida bane da zakici abunda kike
so, ki daure kisha"
Banza tayi masa taƙi kallonsa, ya ɗau kwanon ya zuƙi kokon, kokon dawane kuma
gasarar tayi tsami dan ta ɗan fara wari ma, gashi babu ko ɗigon sugar a ciki.
Yusuf yace "kinga babu wani Abincin da zan baki, idan baki sha ba babu wani Abincin
da zaki samu kici, ki daure ki ɗauke numfashi kawai kisha"
Da ƙyar ya lallaɓata ta sha kokon nan shima kaɗan ta sha tace ita ta ƙoshi, sannan
ya bata magungunanta.
Yusuf yace "Inaga yakamata inyi musu magana, idan da hali a bani ɗakin da zan
dinga kwana, kinga be dace mudinga kwana a ɗaki ɗaya nida ke ba, sannan dole kiyi
haƙuri su ɗan dinga temaka miki ko gurin wankan ne da canza kaya, nida nake miki be
dace ba, tunda ba muharrama tace keba"
Da sauri ta kalle shi tace "Nikaɗai zan dinga kwana a ɗakin nan? Ni gaskiya bazan
iya ba"
"to se a samu a yaran gidan wasu su dinga ta yaki kwana"
Ai tuni ta fara kuka tace "Ni wallahi ba wanda nasani a gurin nan ba zaka tafi ka
barni a ɗakin nan ba, kuma wallahi niba zasu dinga taɓani ba, wannan matar me
haƙora tsoro take bani, in ba haka ba kawai ka maida ni gida"
Yusuf ya ƙara kwantar da murya yace "Widad mufa musulmi ne, mun san illar zaman mu
a guri ɗaya, bekamata yadda nake kula dake ba bayan ga 'yan uwanki mata a gidan nan
ba"
"to ni ka maida ni gida mana, kkme ze faru ya faru amma wallahi ba inda zaka tafi
ka barni".
"so kike mu koma gida wani abu ya sameki?
" Idan ba zamu koma gida ba, to bazaka bar ɗakin nan ba, in ba haka ba ni zan tafi
gidan nikaɗai "
"Amma kin san zamana dake a ɗaki ɗaya ya saɓawa shari'ar musulunci?"
Shiru tayi bata ce komai ba, Yusuf yace "kiyi haƙuri, mutan gidan nan suna da kirki
kuma duk mutane ne, babu wanda ze cutar dake, kiyi haƙuri zanje in samu me garin
muyi magana"
Riƙo rigar Yusuf tayi ta fashe da kuka tace "Wallahi bazan dinga zama a ɗakin nan
nikaɗai ba, sedai duk inda zaka in bika"
Shiru yayi yana Kallonta, kuka take sosai har cikin ranta, tabbas yasan halinta da
ƙyanƙyami da rashin yadda, ba zata yadda ta zauna da kowa a ɗaki ɗaya ba in bashi
ba, kuma gashi hakan ya haramta.
Jiki a sanyaye yace "shikenan is ok kidena kuka, idan har kina son mu cigaba da
zama tare a ɗakin nan inyi jinyarki bisa shari'a mafita ɗaya ce, kuma mafitar nasan
me tsaurin gaske ce a gurinki ba lallai ki yadda ba"
Widad ta ɗago idonta tace "Meye mafitar?"
Yusuf yace " Sedai ki amince muyi Aure zuwa lokacin da zaki warke, mu koma gida
semu rabu"
Gaban Widad ne ya faɗi ta tsaya tana masa wani irin kallo
Duk yadda me Adda yake tunanin lamarin ya wuce tunaninsa, dan babu wata alama ko
sheda da zata nuna maka inda su Yusuf sukabi, suka yi sintiri da neman duniya a
dajin nan basu sami su Yusuf ba, me Adda yace "gaskiya ina mamakin guduwar mutanen
nan, tabbas akwai munafiki a cikinmu, wanda ya kuɓutar dasu banda haka yaza'ayi
mutanen da ko tashi basa iyawa ace sun gudu?"
"Oga nima dai nayi wannan tunanin, dan tabbas maganar ka haka take, da saka hannun
wani a kuɓutar tasu"
Me Adda yace "Ni yanzu tunanina yadda zanwa wannan mutanen bayanin sun ɓata, dan
wallahi babu lallai su ƙyalemu"
"To Oga ko muma sanfewa za muyi muyi ta kanmu"
Me Adda yace "ƙwarai kuwa, Amma zamu fara kiransu mu gaya musu su san meya dace
suyi, sannan muma muyi ta kanmu da ba mutunci mutanen nan suka cika ba"
Suleiman shike zuwa ya rarrashi Maman Yusuf, dan ko Abinci bata iya ci, sedai
wataran inzeje yayi mata Nasiha ya sai wani abun ya kai mata.
Yauma bayan Azahar da ya taso daga gurin aiki gidan su Yusuf yaje, yatarar da Umman
Yusuf akan dadduma taci kuka ta ƙoshi, idanunta duk sunyi jawur.
Suka gaisa Suleiman yace "Umma har yanzu baki dena kukan ba? Ki sani wannan carbin
da kike ja kina masa Addu'a yafi wannan kukan da kike yi, dan Allah ki kwantar da
hankalinki, kar wani ciwon ya shige ki"
Umman Yusuf tace "To Suleiman dangana ta zama dole, yau da gawar Yusuf na gani
seta fiyemin kwanciyar hankali akan ɓatansa, ban san a ina yake ba, yaci Abinci?
Yayi wanka? Me yake ciki? Yana samun Abincin da yake so duk ban sani ba, Allah ne
kawai ya barwa kansa sani, dole in shiga damuwa inyi kuka"
Suleiman yace "hakane Umma, amma ki kwantar da hankalinki, muna nan muna bincike
akan mu gano inda Yusuf yake, very soon zakiji labari me daɗi, kuma kisawa
zuciyarki addu'ar nan da kike tana isa ga Yusuf insha Allah muna sa ran jin labari
me daɗi akan Yusuf"
Umman Yusuf tace "Nagode Suleiman, Allah ya saka da alkhairi tunda abun nan ya faru
kai kaɗai kake zuwa inda nake ka rarrashenin, Nagode Allah yayi Albarka"
Suleiman yace "Ameen Umma, kin san mahaifin yarinyar ma yana can a gadon Asibiti,
sedai fatan Allah ya bayyanasu"
Umma ta amsa da Ameen.
Nurat ta kuma satar jiki, mahaifiyarta bata sani ba ta tafi Asibiti duba jikin
Baban Widad, koda taje Anwar kawai ta gani a gurinsa, sedai abun mamaki har yana
zaune yana cin Abinci da kansa.
Nurat tace "Alhamdilillah lafiya ta fara samuwa, ya ƙarfin jiki kuwa Daddy?"
Daula yayi murmushi yace "Alhamdilillah, yau gani a zaune ina cin Abinci ma"
Nurat tace "Alhamdilillah" Ta kalli Anwar tace "Yaya Anwar ina kwana"
Anwar yace "lafiya ƙalau, ya mutan gidan?"
"duk suna lafiya Alhamdilillah, Amma ina su Anty Ramlah ne?"
Ɗan kame kame Anwar ya fara yace "kin san da yake tunda Daddy ya kwanta itama taƙi
lafiya, tana can tana jinya su Amal ke kula da ita"
Nurat tace "Allah sarki, Allah ya sawwake naje in duba ta"
Saleh ne yayi sallama ya shigo, yana ganin Daula a zaune yace "Alhamdilillah
Alhajin Allah, kaine a zaune haka kake cin Abinci?"
Daula yayi murmushi yace "Alhamdilillah, tambayi Anwar da kaina na tashi na zauna,
sedai bana jin daɗin Abincin sam tunanin 'ya' yana nake, ban san a halinda suke
ciki ba"
Saleh yace "Insha Allah suna lafiya, kuma da yardar Allah za'a gansu"
Nurat tayi shiru zuciyarta gaba ɗaya ta tsinke, tausayin Daddyn Widad ya kamata, ji
take tamkar ta gaya masa abunda ke faruwa, Amma idan ta faɗa da wani suna za'a
kirata, kuma meye hujjarta na cewa da hannun mahaifinta a sace Widad tunda ita
kaɗai taji abunda suka faɗa, Mahaifinta yana zaune da nasa iyalin cikin kwanciyar
hankali, amma ya jefa rayuwar wannan iyalan cikin fargaba da damuwa.
Tana cikin tunanin Daddy yace "Nurat, ki koma gida kinji ko, nagode sosai Allah
yayi miki Albarka"
Nurat tace "Ameen Daddy"
Ta miƙe tsaye ta fita, Anwar yabi bayanta suka fita, suna fita harabar ta tsaya ta
kalli Anwar tace "Yaya Anwar wai meyasa baza'a fita da Daddy waje ba, tunda yana da
kuɗin nan ba babu ba? Kana kallon da yadda yake numfashi fa"
Anwar yace "Wallahi Nurat, nayi iya yina amma su Mummy sunƙi Amincewa, wai anan ma
ana kula dashi, Jiya Saleh ya bani shawarar ko Asibiti in canza masa basu sani ba,
sedai kawai suga an canza amma ina tunanin abunda ze biyo ba idan nayi hakan"
Nurat tayi ajiyar zuciya tace "ya batun taron kasuwanci da'ake yi duk ƙarshen
shekara da ma'aikata da 'yan kasuwa kuwa?"
Anwar yace "Ana nan za' ayi jibi insha Allah"
Nurat tace "babu wanda ze wakilci Daddyn Widad kenan?"
"Nurat ana ta lafiyarsa wake ta wani taron kasuwanci"
"Amma idan da kara, tunda shike jagorantar taron ayi wani abu akai, tunda yana
kwance ba lafiya"
"Ayi wani abu kamar me kenan?"
Nurat tace "A ɗaga taron zuwa wani lokacin"
Anwar yace "kina ganin su saura mahalarta taron zasu yarda da haka?"
"Yaya Anwar, ƙaddara bata wuce kan kowa ba, dan haka babu laifi idan munyi wani abu
akai"
Anwar ya gyara tsaiwa yace "to gurin wa zamuje ayi mana wannan Alfarmar?"
Nurat tace "karka damu ina da hanya, duk yadda ake ciki zan kiraka amma wannan
maganar da gani se kai, karka gayawa kowa"
"insha Allah babu wanda zan gayawa, Allah ya saka da alkhairi da wannan taimako da
zakiyi"
"Babu komai yaya, yiwa kaine inda kara ai bekamata ayi taron nan Daddy na kwance
ba"
A ranta kuwa cewa tayi "daka san Abunda ake shirya yi a gurin taron nan, da kaima
ka nemawa Alhaji Daula mafita '
Saleh ya kalli Alhaji Daula yace" Yanzu idan nace maka na san inda Widad take zaka
yadda? "
Daula yayi murmushi yace " daka san inda Widad take da baka ƙyaleni ina fama haka
ba"
Saleh yace "Hakane, jikina yana bani Su Widad sun kuɓuta, sedai kasan su dawo
cikin garin nan hatsari ne?"
Daula yayi shiru yace "Tabbas, dan mutanen nan basu da imani, Allah kaɗai yasan
halin da suke ciki, ina cikin damuwa sosai Saleh"
Saleh yace "Insha Allah nan ba da daɗewa ba zanzo maka da Labari me daɗi a kansu"
"kamar yaya kenan?"
"Kai dai ka kwantar da hankinka Alhajin Allah, kasan retired solder neni, nasan
techniques na abubuwa da dama, dan haka ina daf da gano su"
Riƙo hannun Saleh yayi yace "Dan Allah Saleh dagaske kake? Gaba ɗay....
Farinciki yasa Daula kasa cigaba da magana, sema tari daya sarƙeshi.
Saleh yace" ka kwantar da hankalinka, Amma wannan maganar iyani da kaine, ban yadda
wani yaji ba, ko Bulama karka sake ka gayawa "
" Insha Allah bazan gayawa kowa ba, Nagode Saleh "
Yusuf ya cigaba da kallon Widad da take masa wani irin kallo, zame hannun ta yayi
daga jikin rigarsa yace" Shikenan tunda baki amince ba, na manta baki da babban
maƙiyi kamar Aure, kuma Aure ma kamar Auren maƙasƙancin mutum irin direbanki, bani
da wani zaɓi na zama dake inba Aure mukayi ba, kuma niba abunda ze haɗa ni dake har
mu gama zamanmu anan mu koma gida, tunda baki amince ba shikenan "
Ya ƙarasa maganar tare da miƙewa ya nufi hanyar fita, jiki a sanyaye Widad tace"Na
Amince!"
Share, share and Share please 🙏🙏🙏
Domin gyara sharhi ko shawara Ayshercool 07063065680
_*AƘIDATA*_
PERFECT WRITERS ASSOCIATION
(WE AIN'T PERFECT BUT WE ARE ALWAYS TRYING OUR BEST, TO MOTIVATE AND ENTERTAIN OUR
READERS)
https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/
*Story and written by*
_*AISHA HUMAIRA (Daddy's girl)*_
The experience writer of *ABDUL JALAL** WATA KISSAR.... (SAI MATA) *And now *AƘIDA
TA *
I dedicated this book to my Mum (Malama Nafisat Adam Muhammad) i love you mum
Haƙƙin Mallaka ⚠ : Littafin nan mallaki nane, tun daga sunan labarin zuwa abunda ya
ƙunsa, ban yadda wani ko wata ya sauyamin ko yin Amfani da wani ɓangare na labarin
ba ba tare da izinina ba, Nagode
https://www.wattpad.com/user/Ayshercool7724?
utm_source=android&utm_medium=link&utm_campaign=invitefriends
NOT EDITED
ELEGANT ONLINE WRITER'S
PART1 Page 30_31
Yusuf ya tsaya cak ya waigo ya kalle ta yace "are you serious kin amince?"
Shiru tayi, taƙi ce masa komai, har yanzu izzar tana nan, abune mawuyaci ta
maimaita magana sau biyu, Yusuf yace "Shikenan, idan Saleh yazo zanyi masa magana,
kokuma in samu maigari in masa bayanin komai"
Gyara kwanciyarta tayi tace "kuma ranar da zamu koma gida zaka sakeni,gara kasa
wannan a ranka"
Yusuf yayi murmushi yace "karki damu, nidai fatana ki samu lafiya komai ya lafa mu
koma gida"
Nurat ta koma gida, ta lallaɓa zata silale ta shiga ɓangarenta, "daga ina kike?"
Taji muryar mahaifinta, tsayawa tayi amma takasa cewa komai, cikin tsawa yace "Nace
gidan ubanwa kikaje?"
"Amm.. Ammmm. Dama... Damanaje gidansu ƙawata ne shine....
" shine ubanki, yaushe kika fara fita ke kaɗai babu direba? Daga gidan ubanwa kike?
Zaki gayamin ko sena kwantar dake na yankaki a gurin nan"
Nurat ta faɗa a Shagwaɓe "Nifa ba inda naje"
"Ubanwa ya kaiki duba Daula a Asibiti ubanki ne?"
A razane ta ɗago ta kalleshi, ta shiga rarraba ido.
"ba magana nake miki ba?"
"Daddy waye ya gaya maka naje duba shi?"
"Ubanki ne ya gayamin" Alhaji Musa ya bata amsa
"Kin san a duniya mutumin nan maƙiyinane, shine kika kwashi jiki kika tafi?"
Nurat tace "Daddy, 'yarsa ƙawatace kuma dukda abunda ke tsakaninku tazo gidan nan
birthday na ta bani kyautar mota, yanzu kuma a sace ta mahaifinta a gadon Asibiti
in kasa duba shi"
Kafin ta ƙarasa ya ɗauketa da mari, wanda seda ta dena gani na wani ɗan lokaci.
Da sauri Mahaifiyar Nurat ta fito tana cewa "lafiya kuwa? Me tayi maka ne?"
"dole ki tambayi me tayimin mana, munafuka daga ke har ita, wato da saninki ta fita
taje Asibiti duba Daula, babban maƙiyina ko?"
Mahaifiyar Nurat tace "haba Alhaji kai waye ya gaya maka can taje"
Alhaji musa yace "Rufemin baki kafin in haɗa dake in muku duka, na wuce duk yadda
kuke tunani, duk wani motsinku a waje ina da masu kawomin rahoto, kuma daga yau na
saka doka, kada ki kuskura Nuratu ta sake fita daga cikin gidan nan, ban yadda ta
sake zuwa ko'ina ba, idan kuwa ta sake sena saɓa muku daga ke har ita"
Maman Nurat taji zafin marin da yayiwa 'yarta, dan ba taga laifin da tayi wanda
harta cancanci wannan marin ba.
Taja hannun Nurat zuwa ɗakinta, ta kalleta tace "kema Allah ya ƙara, gobe ma ki
sake, gashi nan ya mareki a banza, kin fiye rawar kai Nurat"
Nurat ta share hawayenta tace "Ni ban san wani tantirin munafikin ne ya gaya masa
naje ba, Amma idan harna cika 'ya ta halak inason mahaifina ya dace da rahamar
Ubangiji, dole in shiga rusa duk wani mummunan ƙudirinsa, ta haka ne kawai zan huce
wannan marin da yayi min"
"kinga karki jawa kanki wani tashin hankalin, ki ɗakko mana magana kin san halinsa
sarai"
"Mummy, wallahi zubawa Mahaifina ido yana abunda yaga dama, alhalin nida ke munsan
ba dai dai yake ba bamu kyauta ba, babu ruwanki a ciki nikaɗai zanyi komai.
" Na sani, amma Nurat ina jiye miki matakin daze ɗauka akanki, idan ya gane abunda
kikeyi "
Nurat tace "ba abunda ze gane, sedai inke zaki gaya masa"
Ta ɗau jakarta ta bar ɗakin, ta nufi nata ɗakin.
Amal ta zama kamar wata me jinya, ta rame sosai dan ko Abinci bata iya ci Sam,
sedai abunda ba'a rasa ba, yanzu ma Mummy ce da Ramlah suke cin Abinci suna
hirarsu, yayin da Amal juya cokali kawai take, ba ta kai ko loma ɗaya bakin ta ba.
Ramlah tace "wai Abincin ne bakyaci, kokuwa? naga se juya spoon kike"
Hajiya Halima tace "na lura da yarinyar nan, kwanakin nan sam bata walwala ta
takure kanta da yawa"
Amal tace "Nifa wallahi ɓatan Yusuf ne ke ɗaga min hankali, wallahi na damu sosai
beji ba be gani ba am sace shi, Allah kaɗai yasan wahalar da yake sha"
Ramlah tace "Ai kece 'yar wahalar, dama abunda yasa kike wannan damuwar kenan?"
Hajiya Halima tace " waini Yusuf ɗin nan ko tare mukayi Naƙudarki ne muka haifeki
ban sani ba? Ubanki ne shi? Ko haifarki yayi idan baki kiyayeni da maganarsa ba
sena fasa miki baki, kije ki kashe kanki saboda wani ɗan iska, Allah yasa su haɗa
dashi su kashe"
Zare ido Amal tayi tace "Mummy a kasheshi kuma?"
"Eh a kashe shi, munafikin yaro na tsani yaron nan wallahi ba ƙaramin daɗi naji ba
da aka sace dashi"
Ramlah tace "wallahi nima naji daɗin hakan, munafuki yaita sunkuyar da kai kamar na
Allah, saboda shi ba irin wulaƙancin da wannan makirar ba tayi mana ba, yanzu da
suka ƙara gaba se hutawarmu muke"
Amal ta dire cokalin ta miƙe ta bar musu dining ɗin.
Mummy tace "Allah ya kawo lokacin da burinmu ze cika, ita kuma tana wani shirme
daban"
Ramlah tace "kedai bari Mummy, nifa harna fara tunanin irin bushshar da zanyi, da
yadda zan fantama in kece raini a cikin manyan yara, wayyo Allah daɗi"
Mummy tace "kedai bari yarinya, ai komai yana tafiya daidai" Suka kwashe da wata
uwar dariya, hakan yayi daidai da shigowar Anwar, hakan yasa suka ja baki sukayi
tsit.
Ganin yadda sam halin da Daula ke ciki baya gaban mahaifiyarsa da 'yan uwansa yasa
ya girgiza kai, tunda Daula ya kwanta a Asibiti bata taɓa kwana a gurinsa ba, se
tafi kwana uku ma bata je ba.
Hajiya Halima tace "Allah sarki yaron kirki, Anwar duk ka rame fa, anya baza' a
nemi me kula da Alhaji a dinga biyansa ba, ba haƙƙinka bane yin jinyarsa, duk kayi
wani iri jinya ba sauƙi fa"
Ya kalli mahaifiyarsa yace "Ciyar damu ɗaukae ɗawainiyar karatunmu da sauran
buƙatunmu da yake haƙƙinsa ne? Me yasa lokacin da yakw ɗawainiyar damu baki ce masa
ba haƙƙinsa bane, babanmu yayi mana ba tunda yana raye?"
Ya ajiye kayan hannunsa yayi waje zuciyar sa na ƙuna, da irin wannan hali na
mahaifiyarsa.
Ramlah taja wani ɗan gajeren tsaki tace " Mummy ya kamata anemo wanda zasu ɓalle
ƙofar ɗakin yarinyar nan, mu ɗibi abunda zamu ɗiba, kuma mu shiga ɗakin ubanta mu
kwashi abunda muka samu kafin wancan manyan suzo"
Hajiya Halima tace "hakane, amma dole muyi komai a hankali naga Anwar yana neman
ya gane halin da'ake ciki nikuma bazan so hakan ba"
Ramlah tace "Ai Mummy ki rabu da Yaya Anwar ɗin nan kawai"
Saleh ne a hukumar 'yan Sanda na farin kaya, ya nemi ganawa da Sulaiman, ai kuwa be
sha wata wahala ba saboda Kasancewar shima ma'aikacin tsarone.
Ya shiga Office ɗin Suleiman suka gaisa, Saleh ya gabatarwa Suleiman kansa sannan
yace "kamar yadda nima jami' in tsaro ne nazo maka da wata mahimmiyar maganane
akan jami'inku da'aka sace tare da 'yar gidan Daula"
Suleiman yace "ya akayi kasan jami' inmu ne? Ba kowa yasan Yusuf ɗan sanda bane"
Saleh yace "ba abun mamaki bane dan na san hakan, Amma yanzu ba wannan ne mafi
a'ala ba, ka tsaya ka saurareni da kyau, na kuɓuttar da Jami'inku tare da 'yar
gidan Daula"
Wani irin kallo Suleiman yayi masa yace "ya akayi kasan inda suke harka kuɓuttar
dasu? Kenan dasa hannunka akan sacesun da' akayi"
Saleh yace "ka dena wannan muzuran, ka tsaya in maka bayani dan baka da ikon da
zaka kamani ko gayawa duniya abunda ya faru, idan kayi haka kayi abakin ranka"
Nan Saleh ya warwarewa Suleiman komai sedai be faɗa masa ƙauyen daya bawa su Widad
mafaka ba, Suleiman yayi matuƙar girgiza da jin labarin da Saleh ya gaya masa,
Saleh yace "a yanzu haka babu wani bincike da akeyi akan ɓatansu, saboda sun siye
jam'ian tsaro gaba ɗaya kuma suna harin rayuwar Daula duk saboda dukiyarsa, na
fuskanci idan nayi wani kyakkyawan yunƙuri a gurin ceton Daula tabbas Asirina ze
tonu, kuma zasu kasheni, kaima na gaya maka dan ka sani, ka samu iyayen Yusuf ka
musu bayani, dan hankalinsu ya kwanta, sannan ka gargaɗesu akan suyi shiru da bakin
su "
Suleiman ya jinjina kai yace ai abunda za'ayi yanzu shine, zan ɗaukeka muje gaban
mahaifiyar Yusuf kayi mata bayani da bakinka dan ta samu nutsuwa"
Saleh yace "kana ganin babu matsala?, bafa nason a ganeni"
Suleiman yace "babu wata matsala insha Allah, hankalin mahaifiyarsa ne yaƙi
kwanciya, ta damu sosai"
Saleh yace "shikenan muje"
Suleiman yayi musu jagora har gidansu Yusuf, ba ƙaramin farinciki tayi ba da jin an
kuɓuttar mata da Yusuf ɗinta, sedai jin an ɓoye shi a ƙauye, ga kuma bata san ranar
dawowarsa ba yasa tace "Allah sarki Yusufa na, koze iya rayuwar ƙauye? Be saba ba
nace ko zaku kaini in ganshi?"
Saleh yace "A'a hakan bame yuwuwa bane, akwai hatsari a cikin hakan, sedai zanyi
recoding ɗin muryarki in kai masa, amma baze yuwu in kaiki inda yake ba"
Umma tace "ynzu dai dan Allah dagaske kake ya tsira baya hannun Azzaluman da suka
sace shi?"
Saleh yace "tabbas basa nan, ya kuɓuta"
Umma tace "Allah kaine abun godiya, ubangiji Allah ya ƙara tsare su"
Widad kuwa wunin ranar nan ji take kamar ba ita ba, wai ita da bakinta ta Amince da
Auren Yusuf, abun da tafi tsana a rayuwar ta yau da bakinta ta amince. Amma da:ace
wannan me korayen haƙoran me kama dana horo tazo ta dinga kwana da ita, ko wannan
yaran nasu masu kallon jaraba, gara tayi maleji ta Auri Yusuf ɗin su dinga kwana
guri ɗaya, tunda duk abu dai shi ta sani.
Widad sam bata iya cin Abincin da ake kawo musu, saboda gaba ɗaya kwanon da'ake
kawo Abincin kansa idan ta kalla be mata ba ba zata ci ba, se taji kamar tayi amai,
Yusuf yayi ta fama da ita ga larura tana fama, ga rashin cin Abinci.
Haka a daddafe suka kwana uku, kullum tana kan katifa, Yusuf yana bakin ƙofa a
ƙasa, idan ta fito tsakar gidan nan to tare da Yusuf ne ze rakata banɗaki, shima
bata shiga banɗakinsu, wannan ɗakin da ba kowa a ciki take wankanta, shima idan
tayi abunda zata yi tun safe bata sake yadda ko fitsari ta sake yi.
Ko sannu bata taɓa haɗata da mutan gidan ba, shiyasa suke zaton ko bata jin hausa
ma, haka suke wuni a ɗaki bata yadda Yusuf ya fita ya barta, tsakaninsa da ita
sedai kallon kallo.
Babban abunda yake ƙara bata haushi be wuce yadda data fito, gaba ɗaya sesu koma
kallonta ba, sekace sunga wasu halittu daban, ita tarasa meye abunda suke kallo.
Yanzu tana ɗan iyayiwa kanta wasu abubuwan, dukda bata gama warkewa ba, bata cin
Abinci sosai, dukda a da ɗinma ba wani ci take ba, Yanzu kam cimar ƙauyen nan ta
sha banban da irin wadda ta saba gani, gaba ɗaya kalar Abincinsu yasha banban da
wanda ta saba gani ko ta saba ci.
Yusuf yana son yayiwa megari bayani, amma yana tsoron irin kallon daze masa kuma
gashi besan me Saleh yace masa ba game dasuA haka suka kwana uku, ranar kwana na
ukun da yamma ba tsammani suka ji salamar Saleh, ba ƙaramin farinciki Yusuf yayi da
zuwan Saleh ba, yayo musu siyayya cikin ledoji.
Saleh suka gaisa da Yusuf, yace "Yusuf ya zaman haƙuri ya me jiki kuma?"
Yusuf yace "Alhamdilillah, me jiki tana samun sauƙi"
Saleh yace "fatan dai komai lafiya, kuna lafiya kuda mutan gidan?"
Yusuf yace "Alhamdilillah komai lafiya ƙalau"
Saleh ya kalli Widad yace "Autar Daula ya jikin naki?"
Banza tayi masa ba tace komai ba, Saleh yace "hmm aike in dan halinki ne ko kashe
ki za'ayi mutum baze ceceki ba, sedai amiki dan Allah dan karamcin mahaifinki, mace
se tsabar girman kai da izzar tsiya, yanzu dai dole ki sauke su ki rungumi ƙaddarar
da tayi kutse cikin rayuwar ki ba tare da kin shirya mata ba, ki sani abunda kika
gayawa wanda sukayi garkuwa da ku, sun Sanarwa da wanda suka sa a sace ku, dan haka
idanma dagaske kin san wanda suka sa a saceku inama baki sani ba kikace kin sani,
sun bada umarnin a kasheku, zuwa yanzu basu san kun kuɓuta ba, da zarar sun farga
kun gudu zasu saka ɗambar nemanku, dan haka idan kin gadama ki haƙura ki zauna anan
na wani ɗan lokaci domin ki tserar da rayuwar ki, in baki ga dama ba kuma kiyi
yadda kike so "
Yadda Widad take a kashingiɗe ko motsi ba tayi ba, balle Saleh yasa ran jin wani
abu daga gareta.
Yusuf ne yace " Ayi dai haƙuri, Insha Allah zata zauna ma, kuma mungode sosai da
taimakon da kayi mana Allah ya saka da alkhairi, ya Yallaɓai kuwa? "
Saleh yace "Yana nan ƙalau, dan ina daf da sanar dashi cewar kun tsira, kasan komai
nima se nayi lissafi nake yinshi, domin ɓadda sahu, jiya munje gidanku na gana da
mahaifiyarka ma"
Da sauri Yusuf ya ɗago ya kalle shi zeyi magana, Amma Saleh ya girgiza masa kai.
Yusuf yace "Amma ya akayi kasan wanda suka sacemu, harka kuɓutar damu?"
Saleh yace "labarin dogone Malam Yusuf, uwa ɗakinka tasa an kama ɗan uwana an tsare
shi tsawon shekaru goma, akan zargin dasa hannunsa akan kisan mahaifiyarta, na haɗa
kai da maƙiyanta domin in rama abunda tayi min, sedai suma maƙiyan nata kansu kawai
suka sani basu da adalci, gefe guda dukda zargin da yake kan ɗan uwana mahaifinta
be fasa kyautatamin ba, yana matuƙar girmamani yana kyautatamin ga kuma kai Yusuf
da babu ruwan ka, shiyasa na ceceku ba dan halinta ba Wallahi "
"I don't judge based on Assumptions, what happens ten years back is still dancing
in my memory, abunda ya faru a wancan lokacin ina jinsa a raina kuma ina ganinsa a
idona tamkar a yanzu yake faruwa, da sa hannun Bala akan abunda ya faru, kuma ko ka
ceceni ko kar ka ceceni hakan baze taɓa canza ƙaddarata ba, nasan wanda suke
bibiyar abun nan tsawon shekaru suna da Alaƙa da wanda suka kashe mahaifiyata,
kallona kawai kuke but am beyond your expectations, idan kaje ka ƙara tabattar musu
ko bayan raina se sun Wulaƙanta se Asirinsu ya tonu wulaƙanta mafi muni a duniya "
Tuni Hawaye ya wanke fuskarta, yadda take maganar zaka san abun yana taɓa mata
zuciya sosai, Yusuf yace"Amm inaga ku bar wannan maganar, it's hurt her feelings
kuma kaga bata da lafiya, dama ina son muyi wata magana da kai ne"
Saleh yace "Ina jinka"
Yusuf yace "kaga zaman da muke da ita a ɗaki ɗaya be halarta ba, tunda ba muharrama
ta bace, kuma kasan ba zata yadda matan gidan nan su kula da ita ba, ga yanayi na
jinya tana ciki, da nace mu raba ɗaki taƙi yadda, amma munyi shawarar zamuyi Aure,
yadda zan iya jinyarta lokacin da Allah ya ƙaddara zamu bar garin nan semu rabu, da
naso in yiwa megari bayani, amma ban san yadda kuka yi da shi ba"
Saleh yace "eh to ni namanta kam banyi tunanin raba muku ɗaki ba, taɓ amma wannan
zaka aura? Allah ya baka haƙuri da juriya, tashi muje gurin me garin, dama Jibi in
Allah ya kaimu Juma'a se'a ɗaura"
Widad dai bata tanka musu ba, suka tashi suka tafi turakar mai gari.
Mai gari na ganinsu tare yace "Masha Allah, Saleh fatan dai ba wata matsala ba
suce, mun musu wani laifin bako?"
Saleh yace "Lafiya ƙalau babu wata matsala, munzo da wata 'yar magana ne"
Maigari yace "Masha Allah"
Saleh yace "Ina son in Allah ya kaimu jibi da rai da lafiya, ka ɗaurawa baƙinka
Aure"
Buɗe baki Maigari yayi yace "dama ba matarsa bace?"
"Eh ba matarsa bace, ƙanwarsa ce hatsarin ya ritsa dasu tare kamar yadda nayi maka
bayani, 'yar uwarsa ce amma da Aure a tsakanin su"
Maigari yace "Shikenan babu laifi, amma hakan baze kawo matsala ba idan suka koma
gida?"
Saleh yace "kaikam Baffa ba dai tsoro ba,' yan uwane fa kuma ba lallai su koma gida
nan kusa, se rigimar da'ake a garinsu ta lafa"
Maigari yace "Shikenan Allah ya kaimu, idan anyi sallar Juma'ar se' a ɗaura"
Saleh yace "yawwa Baffa godiya muke, nima ina nan bazan tafi ba se Allah ya kaimu
juma'ar idan an ɗaura Auren"
Maigari yace "to madalla babu laifi"
Suka fito shida Yusuf, Yusuf yace "nikam me ka cewa Maigari ne a kanmu?"
Saleh yace "kasan mutumin ƙauye, kawai kifeshi nayi, nace masa faɗan ƙabilanci ake
a garinku, kun samu kun tsira da ƙyara akan hanyarku ta guduwa kuma akayi garkuwa
daku, har yanzu garinku babu lafiya"
Yusuf yayi murmushi yace "Allah sarki, yana da kirki da karamci kam,Amma nifa bani
da sadakin da zan bayar"
Saleh yace "karka damu zan bayar, Allah yasa Auren ka yayi silar shiryuwarta daga
wannan baƙin taurin kan da izzar, shegiya me kama da Aljanu"
Yusuf yace "dan Allah kadena zagin ta, bana jin daɗi idan ka zageta, ɗazuma ka sata
kuka"
Saleh ya yamutsa fuska yace "Yusuf ina zaton kana son yarinyar nan ne, in bahaka ba
tun a baya su Nura dama sunce baka ganin laifinta, da'an mata abu sekaji haushi"
Yusuf yayi murmushi yace "Saleh, duk ɗan adam tara yake be cika goma ba, duk
rashin kirkinta akwai halayenta masu kyau, su kansu su Nuran yanzu zasu gane
Amfaninta"
Saleh yace "eh amma rashin kirkinta yafi kirkinta yawa ai"
Yusuf yayi murmushi yace "koma dai yane ni nasan tana da kirki ai, amma dagaske
kaje gidanmu? Ya akayi kasan gidanmu?"
Saleh yayi murmushi yace" Yusuf kenan, har gurin aikinka nasani kai jami'in tsarone
na farin kaya"
Gaban Yusuf ne ya faɗi "ya akayi kasan hakan?"
"saboda ina tare da maƙiyan Daula, binciken da'aka saka ma duk cikin shirinsu ne,
ni naje na shirya komai, ba lallai kasan komai yanzu ba, amma anaso ka gama ka
tattara bayanai akan binciken se akai sama, su kuma su karɓa su basu, duk cikin
ƙoƙarin su na goge duk wata sheda da zesa asan sunawa Daula da 'yarsa zagon ƙasa,
sedai basu san cewar kai aka saka kayi binciken ba, sudai kawai zaman jiran
sakamakon bincikenka suke, basu san kaike binciken ba shi kanaa me gidanka Suleiman
be san hakan ba, sedai akwai wani abokin aikinka da nayi connecting dashi, da
zimmar idan ka gama binciken ya dinga bani wasu bayanai daga abunda kake binciken,
sedai bazan gaya maka waye ba"
Shiru Yusuf yayi gaba ɗaya kansa ya gama kullewa, kenan dama duk wannan wahalar da
yake sha shirine, jiki a sanyaye yace "Widas tasan koni waye?"
Saleh yace "Yadda take shiri haka maƙiyanta sukeyi, sannan da ta san kai waye,
wallahi da yanzu kana prison saboda bata yafewa wanda yayi mata ƙarya koya yaudare
ta, kayi fatan Allah yasa ta fara sonka kafin lokacin da zata san ko waye, wataƙila
ta sassauta maka"
Gaba ɗaya Yusuf yayi shiru ya rasa abunda yake masa daɗi.
Saleh yace "zomu je mu ɗan zazzaga, kaga yanayin yadda ƙauyen yake"
Haka akayi Yusuf yabi Saleh, garin yana da kyau sedai ƙauyen ƙayau ne, babu ababen
more rayuwa sam.
Ramlah tasha kwalliya cikin wasu ƙananan kaya, tayi kyau sosai, tana zaune a falo
tana kaɗa ƙafa, aka kirata a waya, tana ganin me kiran ta miƙe tsaye, ta ɗau
ƙaramin gyalenta ta yafa tace "Mummy yazo bari inje"
Hajiya Halima tace "shikenan sekin dawo"
Amal tace "wallahi Ramlah baki da aji, daga zuwansa harkin miƙe kina rawar ƙafa
zaki fita da nice da yanzu kina nan kinamin surutu, wani banza dashi gwalagwaji se
shegiyar ƙarya da iyayi"
Ramlah a fusace "Mummy kinga kiyiwa Amal magana ba ruwanta dani"
Mummy tace "Amal kar in ƙara jin bakinki a gurin nan"
Amal ta kwaɓe fuska tace "eh ai tuni na gane, kin fi son Ramlah akaina, damuwar ta
ce kawai damuwa ni kuma baki damu dani ba, shikenan"
Ta miƙe fuuuu ta bar falon, Ramlah tayi waje abunta, a harabar gidan taga Fahad
sanye da ƙananan kaya da tabarau yana tsaye a jikin motarsa, ta ƙarasa gurinsa tana
wani yauƙi, tana ƙarasawa inda yake ya rungume ta, ba kunya ba tsoron Allah suka
fara kissing ɗin juna a gaban ma'aikatan dake gurin, Fahad ya zame bakinsa a
hankali yace "you look so cute Baby"
Ramlah tace "Really, you look good too baka ga yadda kayi kyau ba"
Ya riƙo ƙugunta yace "mu tafi ko"
"Ke Ramlah!" muryar Anwar ce cikin fushi yace "meye haka? Baki da hankali ne?
Malama wuce ki koma gida"
Fahad yace "kamar ya ta koma gida, meyasa kake hakane Anwar"
A tsawace Anwar yace "zaki koma ko sena ɓaɓallaki a gurin nan, ballagaza kawai"
Da sauri Ramlah ta jiya da gudu cikin gida.
Anwar ya kalli Fahad yace "Fahad kayi Asara wallahi, ita waccan da kake iƙrarin
zaka aura baka samu ba, shine ka dawo zaka lallaɓa ka lalata ƙanwata, meyasa baka
da imani Fahad, kana da 'yar uwa mace fa, baka tsoron ayimata abunda kake wa'
ya'yan wasu, ya zakaji idan wani yayiwa Iman abunda kake yi "
Be rufe baki ba ya jiyo muryar Hajiya Halima tana masifa" Anwar meye haka, yaushe
ka zama haka? Ya zasu fita da yarinya zaka ce ba zata ba, tunda wannan shashashar
ta ɓata ai ita ze Aura, me zesa ka kore ta haka akeyi? "
Anwar kamar zeyi kuka yace" Mummy ke uwace, kamata yayi kisa ido sosai akan Yaran
nan, yanzu ya dace Ramlah tabi saurayi da yammacin nan, kalli suturar dake jikinta
fa"
"rufemin baki ko in gaggaura maka mari, ke wuce ku tafi"
Anwar yana kallo Ramlah ta shige motar Fahad, yayin da Fahad ke masa wani irin
kallo na ya kaga lamarin.
Anwar dama Asibiti zashi gurin Alhaji Nasir, dan haka be sake cewa komai ba ya juya
ya tafi.
Nura yace "Bala'i ana shegiya a gidan Nasir Daula, duk iskanci shigar banza da
izzar Gimbiyar Daula ban taɓa ganin ta aikata makamancin abunda wannan kwazgwamar
tayi a gaban mu ba"
Isa me gadi yace "kaidai bari Nura, ai iskanci guri yake samu, kai da Yarinyar nan
tana nan waya isa ya shigo gidan nan ya aikata wannan baɗalar, kuma wallahi kayan
basu yiwa wannan shegiyar Ramlan kyau ba, wanka ai se Gimbiyar gidan nan, kaga kaya
cas a jikinta kamar ita tayi kanta"
Nura yace "kai dai bari Malam Isa, ni se yanzu nake ganin Amfaninta a gidan nan,
duk wulaƙancinta idan tana nan se an bamu Abinci sau uku a rana munci mun ƙoshi a
gidan nan, amma kalli yanzu sau ɗaya ma ba'a bamu"
Isa yace "kai ba wannan ba, nifa ban gane kan wannan matar ba, kofa Asibiti basa
zuwa, Anwar ɗin nan ne kawai yake zuwa yana kula dashi su kuwa ko a jikinsu"
Nufa yace "Hmm kai dai bar kowane munafuki inda ka ganshi, kallon mutan gidan nan
kawai nake yi"
A kayan da Saleh ya kawowa su Yusuf, hadda kayan sawa ya kawowa Yusuf, dan Widad
Akwatinan ta akawai kayan sawa, ya kawo musu man shafawa da sabulun wanka, dasu
Omo, ya siyo musu sabon risho, da fitila sekuma kwalin batir, saboda garin ba Wuta.
Rana bata ƙarya sedai uwar ɗiya taji kunya, Ranar Juma'a bayan an idar da sallar
juma'a aka ɗaura Auren Yusuf da Widad akan sadaki naira dubu goma sha biyar, shi
kansa inda masallacin juma'ar nasu yake se anyi wata uwar tafiya daga nan inda su
Yusuf suke kafin aje, ga shi duk ya lalace ya fatattake.
Nurat ce zaune a ɗakinta da system akan cinyarta, a hankali ta zare earpiece ɗin
kunnenta tace "Alhamdilillah, done with this chapter"
Ta ɗakko wayarta ta kira Anwar, tayi sa'a ya ɗaga, ko gaisawa ba suyi ba tace
"Alhamdilillah Yaya Anwar, na turo maka lamabar wani Bature, abokin cinikayyar
baban Widad ne sosai, tare dashi za'ayi zaman taron kasuwancin, dan sune kusan
wanda suke shirya taron kasuwancin, na san shi lokacin da nayi makaranta a England,
muna zuwa gidansa tare da Widad, nayi masa bayani, Amma dukda haka nace zan bashi
lambarka kuyi magana "
Jiki a sanyaye, tunda acikin damuwa yake yace " Madalla, Allah yasaka miki da
Alkhairi Nurat, abokan kasuwancinsa da yakamata suyi wannan ƙoƙarin babu wanda yayi
tunanin yin hakan, kowa harkar gabansa kawai yake, kamar ba wanda ya damu da halin
da yake ciki"
Nurat tace "Hakane dama Yaya Anwar, kasan wani ya gayawa mahaifina naje duba Baban
Widad, yanzu ya hanani fita kwata2"
Anwar yace "haba dai? Waye ya gaya masa?"
"Nima ban sani ba, amma insha Allah karka damu, zamu cigaba da communicating ta
waya, ya jikin nasa kuwa?"
Anwar yace "to Alhamdilillah za'ace, yau dai naga jikin nasa ya tashi, dan se NG
tube aka samasa tanan na bashi Abinci yau"
Nurat tace "Allah yasaka maka da alheri Yaya Anwar"
Anwar yace "Nurat kome nayiwa Alhaji Nasir Daula ai kaina nayiwa, karki damu Allah
yayi mana jagora"
Ta amsa da Ameen.Sukayi sallama tace "Alhamdilillah, saura kuma kuɓutar da Yusuf,
Allah ka bani ikon kuɓutar dashi" tunani ta shigayi, ta yaya zata san inda su
Yusuf suke balle ta kuɓutar dasu?
Yusuf, da Saleh se megari da samarin 'ya' yansa suka shigo gidan, hannunsu ɗauke da
goro dabino da alawa, uwargidan megari wadda suke cewa gwaggo tace "Malam ya dai na
ganku da kayan ɗaurin Aure haka? Bikinwa akeyi?"
Megari yace "baƙin 'ya' yanmu aka ɗaurawa Aure yau, ga naku kayan Ɗaurin Auren nan
ayi musu addu'a"
Harira wadda itace matarsa ta tsakiya tace "Taɓɗijan kwaɗo, auda ba matarsa bace
suke kwana ɗaki ɗaya? Aikin gama ya gama ai, me kuma za'a ɗaurawa Aure?"
Megari yace "ina ruwanki? Meye naki a ciki? Ke bakinki baya taɓa faɗar alkhairi"
Saleh yace "ke Hari ki iya bakinki akan mutanen nan, bana son rigima fa kin san
halina, uwar gulma kawai"Dama sun saba faɗa basa jituwa da Saleh sam
Gwaggo tace "daka gayamana da wuri, aida mun ɗanyi girki mun gayawa maƙwabta"
Saleh yace "gwaggona 'yar Aljanna, karki damu hakanma mungode, Allah yasaka miki da
alkhairinsa"
Daga nan Yusuf da Saleh suka wuce ɗakin Widad, tana sanye da hijjabi da alama salla
ta idar, tana zaune a gefen katifa suka shigo ɗakin, Yusuf ya ƙaraso gabanta ya
ajiye mata goro da alawar ɗaurin Auren, ya miƙa mata sadakinta yace "uwaɗakina ga
Sadakinki nan, an ɗaura Auren"
Ta ɗaga kai ta ɗan tsurawa Yusuf ido, sekuma ta sunkuyar da kai tana zubda hawaye,
Yusuf yace "me kuma ya faru?"Girgiza masa kai tayi alamar bakomai, yace "ga
sadakinki nan, ki karɓa na kine"
"ka barsu a gurinka ni ba'abunda zanyi dashi"
"Ai haƙƙinki ne, mallakin kine"
"Nikuma nace ka riƙe" tai maganar a ɗan hasale
"Ai hakan baze yuwu bane, amma ki dena kuka kinji, bana son yawan kukan da kike,
nidai tunda na sanki kusan kullum cikin kuka kike, dan Allah kiyi hakuri ki
sassautawa zuciyarki, wallahi ba ƙaramin damuwa nake shiga ba idan naga kina kukan
nan"
Saleh yace "dalla in bazata karɓa ba, ka sai mata ɗan Akuya da kuɗin, idan na tafi
ka zauna kayi ta rarrashin nata, kazo muje zanyi magana dakai, ina son in tafi
kafin mutanen nan su farga"
Alhaji Musa ne a tsaye, hannunsa ɗauke da waya yace "wai kaji abunda naji kuwa, wai
an ɗaga taron kasuwanci na kamfanunnukan Daula saboda bashi da lafiya"
Wanda yake wayar dashi yace "Naji, ƙarewa ma ni message aka turomin"
Alhaji Musa yace "to wani matsiyacin ne ya shirya hakan? Waye da wannan aikin,
ya'akayi ma turawan nan suka san da bashi da lafiya?"
"Nima ban sani ba, nayi iya bincike na ban gane wanda ya gaya musu ba, amma dole
muyi wani abu akai, idan wannan damar ta wuce mu, kuma bamu samu abun hannun 'yarsa
ba to tabbas zamu tafka gagarumar asara"
Alhaji Musa yace "Shikenan, dole muyi meeting yau ƙarfe biyu na dare, zan sanar
dasu Alhaji Haruna"
Ya kashe wayar yana cigaba da masifa, wayar ta sace ta sake fara ringing, a fusace
ya ɗaga yace "meye waye?"
"Me Adda ne"
"Yawwa me ake cikine me Adda? Ta faɗa ɗin ko kuwa? Kaga idan bata faɗa ba, kusa
flier ku dinga cire mata yatsu ɗaya bayan ɗaya har seta faɗa"
Me Adda yace "ka tsaya ka saurareni da kyau, yau kwana biyar kenan sun gudu da inda
muka ajiye su, mun zaga ko'ina a dajin nam bamu samesu ba shine ma yanke shawarar
in sanar da kai"
"what!!!"
(Mutanen Zamfara masu an yanke mana Network, da masu Anty cool daga farko, dan
Allah idan kuna da manhajar Wattpad, idan kukayi searching ɗin littafin AƘIDATA
kokuma Ayshercool7724 zaku sameshi tun daga farko har inda na tsaya, kuna bani aiki
yaseen 🙄🙄🙄 duba ga yadda ake ta yaɗa cewar what's app ze dena aiki dukda bani da
tabbas, ga link ɗin group ɗina na telegram nan meso se yayi joining
https://t.me/joinchat/SYIfEaoQo_JlNDM0 ina godiya da ƙaunar ku masoya 😍😍😍)
Domin gyara, sharhi ko shawaraAyshercool07063065680
_*AƘIDATA*_
PERFECT WRITERS ASSOCIATION
(WE AIN'T PERFECT BUT WE ARE ALWAYS TRYING OUR BEST, TO MOTIVATE AND ENTERTAIN OUR
READERS)
https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/
*Story and written by*
_*AISHA HUMAIRA (Daddy's girl)*_
The experience writer of *ABDUL JALAL** WATA KISSAR.... (SAI MATA) *And now *AƘIDA
TA *
I dedicated this book to my Mum (Malama Nafisat Adam Muhammad) i love you mum
Haƙƙin Mallaka ⚠ : Littafin nan mallaki nane, tun daga sunan labarin zuwa abunda ya
ƙunsa, ban yadda wani ko wata ya sauyamin ko yin Amfani da wani ɓangare na labarin
ba ba tare da izinina ba, Nagode
https://www.wattpad.com/user/Ayshercool7724?
utm_source=android&utm_medium=link&utm_campaign=invitefriends
NOT EDITED
ELEGANT ONLINE WRITER'S
PART1 Page 32_33
Alhaji Musa yace "Me Adda, ina irin wannan wasan da kaine? Wace irin maganar banza
kake faɗa haka?"
Me Adda yace "ba maganar banza bace, roofing kwano suka buɗe suka gudu"
"Roofing kwanon ne ba kuyi da kyauba kokuwa?"
"wallahi munyi komai yadda yakamata, ni babban abunda ya bani mamaki be wuce yadda
ko iya miƙewa tsaye ba sayi saboda wahala, amma suka iya tserewa, ni yanz....
Alhaji Musa ya katse shi ta hanyar cewa " kaga dalla rufemin baki, na yadda da
ƙarewarka a wannan fannin shiyasa na baka aikin nan, amma ka kunyatani, shekara
nawa kayi kana aikata irin wannan Aikin? Miyagun ayyuka mawa ka aikata kana Nasara,
amma se yanzu wannan ɗan ƙaramin aikin ka bari har suka gudu saboda hauka, wallahi
tun wuri ka nemo su na gaya maka"
Ya ajiye wayar tare da yin jifa da ita yana dafe kai, jinjina kai yayi yace "Akwai
babbar matsala"
Ramlah ce kwance akan gadon Hotel, se bacci take yi kamar matacciya, ta lulluɓe
jikinta da blanket, Fahad na gefenta yana ta busa shisha. Seda yasha me isarsa
sannan ya duba agogon hannunsa, ya miƙe zaune dagashi se gajeren wando, yaye
blanket ɗin da Ramlah ke ciki yayi ya ɗagota zaune, ko sutura babu a jikinta, busa
mata hayaƙi yayi a fuska, a hankali ta motsa ta fara tari, buɗe idanunta tayi wanda
sukayi mata matuƙar nauyi ta kalle shi.
Fahad yayi wani murmushi irin na 'yan bariki yace "baccin ya isa haka, yakamata mu
koma gida, kafin yaynki ya fara masifa"
Miƙa tayi ta sake kwanciya a jikinsa tace "ƙarfe nawa ne?"
"Ƙarfe takwas na safe" ya bata amsa, ba shiri ta watsakke tare da zaro ido tace
"takwas na safe, na shiga uku Fahad, wacw irin ƙwaya ka bani haka? Me zan cewa
Mummy?"
Murmushi yayi yace "matsoraciya kawai, ashe iskancin naki na ƙarya ne, karki damu
baby zance mata a gidanmu kika kwana kawai"
Tayi ajiyar zuciya tace "kuma kasan Mummy tana yarda da maganar ka sosai, har naji
daɗi wallahi I love you Fahad"
"Love you too baby"
"Fahad tunda Widad ta ɓata zaka Aureni?"
Ya sake rungumeta yace "idan ban Aureki ba wa zan aura? Itama na yadda da Aurenta
ne dan in Aureta in Wulaƙanta ta, Allah ya temake ta wannan abu ya faru, amma a
duniya in bake ba wace macece ta dace da Fahad?"
Murmushi tayi tama jin daɗin kalamansa ma yaudara suna ratsa ta.
Saleh ya kamo hannun Yusuf suka fito waje, Saleh yace
" Samun mutum managarci me Amana kamarka abune me matuƙar wahala Yusuf, ka cika
mutum nagari abun a jinjina masa, iyakar sadaukarwa kayi ta, ina fatan wannan Auren
anyi shi kenan har gaban Abada, duk macen da ta auri namiji irinka yakamata ta gode
Allah, nasan kayi haƙuri a baya dan haka ina fatan ka ƙara haƙuri, Widad yarinya ce
me tsiwa da girman kai amma zakaji daɗin zama da ita, saboda tana sa sauƙin kai ga
wanda ya gane kanta, dan wani lokacin gane kanta se a hankali, nasan zata baka
wahala kafin ta saba da zaman garin nan, amma kayi haƙuri a hankali zata saba, babu
wanda ta sani a yanzu daga Allah se kai, ka riƙe Amana Yusuf babu tabbacin ku koma
gida Widad ta tarar da mahaifinta a raye! "
Wata irin mummunar faɗuwar gaba Yusuf yaji, yace " Innalillahi wa inna ialaihi
raji'un, me kake Nufi? "
"tunda kuka ɓata Daula yake gadon Asibiti, kullum zancensa 'ya' yana wani hali suke
ciki? An ɗaga taron da suke burin ayi suyi amfani da sunan Daula su damfari
biliyoyin kuɗi, yanzu idan suka farga kun gudu akwai gagarumar matsala, maganar da
nake maka matarsa ba ita take jinyarsa ba, tana can tana shagalinta, babban ɗanta
Anwar shike ta sintirin jinyarsa, sannan an bawa likitansa maƙudan kuɗi sunce yayi
duk me yuwuwa kar Daula ya warke, Nayi duk ƙoƙarin da zanyi a rabashi da Asibitin
amma ba hali, muddin nayi wani babban yunƙuri komai ze lalace "
Yusuf ya dafe kai ya shiga jera salati, "Rananar da'aka ɗaukeku ni naje na janye
Motar da kuke ciki daga titi na maida ita, aka cire lamabr motar, shiyasa na samu
wayoyinku da kuma wannan Akwatunan naku, amma bazan baku wayoyin ba, dan nasan
tabbas za'a iya tracking ɗin inda kuke, zan kawo maka ƙaramar waya da sim wadda
zamu dinga communicating da kai, mahaifiyarka na gaisheka tana ta samaka Albarka "
Yusuf kasa magana yayi se zuciyarsa daketa faman tafasa, suka nufi turakar megari
Saleh yace " Baffa zan koma yau, na bawa ila kuɗi da kayan aiki, zezo yayi musu
banɗaki, wallahi nan da kwana uku idan beyi ba, yasan halina, na bashi isassun kuɗi
wallahi na dawo beyi ba koya cinye kuɗin sena karya shi, kaja masa kunne" Megari
yace "Subhanallah zeyima Insha Allah, ɗakin nan da bakomai shi za'a gyara ba wani
abu, ai kaine ka sashi zeyi insha Allah" Saleh yayiwa Megari sallama, Yusuf ya
ɗanyiwa Saleh rakiya sannan ya koma. Gaba ɗaya kamar an zarewa Yusuf laka jin
maganganun da Saleh ya gaya masa, ji yake tamkar mahaifinsa ne a wannan haɗarin,
wani irin tausayin Widad ya kama shi.
Ya shiga gidan yana takawa da ƙyar, gwaggo ce tace "Malam Yusufa Allah ya Sanya
Alkhairi ya baku zaman lafiya, yasa anyi kenan kasan lamarin Aure se anyi haƙuri
Allah ya baku zaman lafiya"
Yusuf ya ƙaƙaro murmushi yace "Ameen ya Allah nagode sosai"
Gwaggo tace "sedai akwai ɗan bikin Al'ada da mukeyi anan in akayi Aure, yakamata
mu gayyaci mutane mu ɗanyi mu tayaku murna"
Yusuf yace "Allah sarki Mama, base kin wahal da kanki ba, kinga ita Amaryar ma bata
cikakkiyar lafiya kuma har yanzu a tsorace take, baki ga ko magana bata sonyi ba,
Addu'ar ku da kulawar da kuke bamuma mungode sosai"
Gwaggo tace "shikenan Allah ya bata lafiya"
Yusuf yace "Ameen"
Jiki babu ƙwari ya ƙarasa ɗakin nasu, kayan ɗaurin Auren suna nan a inda suke, da
kuɗin sadakin nata, tana zaune ta haɗe kai da gwiwa se rusar uban kuka take.
Dole Widad tayi kuka, rayuwar ta cike take da ƙaddara daban daban, a hankali ya
ƙaraso bakin katifar ya zauna, sam bataji zuwansa ba seji tayi ya taɓa ta, a ɗan
razane ta ɗago ta kalleshi, ganin Yusuf ne yasa ta maida kanta kan gwiwarta ta
cigaba da kukanta.
Yusuf yasa hannu ya ɗagota yana kallon yadda farar fatarta ta koma ja saboda kuka
da wahala. Girgiza mata kai yayi amma yakasa ce mata komai, dan bema san ta'ina ze
fara ba, Widad ta cancanci tayi kuka.
A hankali tasa hannu ta ture nasa hannun ta kwanta, tare da ɗora hannunta akan
fuskarta tana ci gaba da kukan, A hankali take furta "Ya Allah, aslihli sha'ani
kullahu, wala takilni ila Nafsi, ɗarfatu ainun"
(wuya koda magani ba daɗi, ashe Widad ta iya Addu'a haka 🙄)
Yusuf ya zauna ya zuba mata ido wai a hakama bata san halin da mahaifinta ke cikiba
kenan, inaga inta sani.
Yarone yayi Sallama ɗakinsu Yusuf, Yusuf ya amsa, yaron yace "Wai gashi inji
gwaggo"
Yusuf ya karɓi ƙwaryar da'aka rufeya da faifai, yace "Masha Allah, kace mata
mungode"
Yaron yace to ya fita, Yusuf ya ajiye Ƙwaryar yayi shiru yana kallon Widad da
jikinta har rawa yake saboda tsabar kuka.
Yusuf yayi shiru, abubuwa suka cinkushe masa kai, nan da nan kansa ya fara sarawa,
ya jingina da jikin bango ya rasa abunda yake masa daɗi.
A hankali Widad ta buɗe idonta, ta kalli inda Yusuf ke zaune yayi shiru, jijiyoyin
kansa duk sun tashi, ga idonsa yayi ja kallo ɗaya zaka masa kasan a cikin damuwa
yake.
Ta miƙe zaune a hankali, yai saurin juyowa yana kallonta, ta goge hawayenta tace
"me'aka kawo? Yunwa nakeji"
Yusuf yace "ban san me'aka kawo ba bari im duba"
Ya ɗakko ƙwaryar ya duba, fura da Nono ne aka dama, tace "bani cokali a can gurin"
Ya duba ya ɗakko mata, ya bata. Sosai take jin yunwa ta ɗiba ta kai bakinta, ajiye
cokalin tayi a gefe ta kafa kai ta dinga sha, tasha ya kai rabi sannan ta ajiye, ta
koma gefe ta zauna tana lumshe ido.
Yusuf yace "kin ƙoshi ne?" ta jinjina masa kai ba tare da ta buɗe idonta ba, yasa
hannu ya ɗau wadda ta rage ya fara sha, an zuba zuma a cikin furar shiyasa tasha da
yawa.
Gaba ɗaya Yusuf tausayi yake bata, beji ba be gani ba ƙaddara ta haɗasj se wahala
suke sha tare, duk abunda za'a kawo na Abinci indai zata iya ci, se taci ta rage
sannan zeci, kuma seya tabattar ta ƙoshi sannan ko yaya ta rage shima yaci.
Kallonsa take yadda ya duƙa yana shan furar, wadda ba isarsa za tayi ba, ta lura
shidai a rayuwarsa be ɗau komai da zafi ba, irin mutanen nan ne da duk yadda rayuwa
tazo zasu karɓeta a haka.
Yusuf ji yayi kamar tana kallonsa, ya ɗago kai ba tayi zato ba suka haɗa ido, tao
saurin ɗauke nata idon.
Jiki a sanyaye yace "har yanzu dai kukan baki dena ba? Yakamata ace zuwa yanzu kin
sawa zuciyarki haƙuri, kukan nan bashi da amfani, kina ƙaramin damuwa akan wadda
nake ciki ne"
"Ni nace ka damu dani ne? Don't try to comfort me when ever am crying, kaji da
damuwarka kaima"
Yusuf yace "tun daga lokacin da kika fara kuka saboda damuwa zuwa yanzu, maganin me
kuka yayi miki? Kuka baya maganin damuwa wasu lokutan sema dai ya ƙara maka ƙuncin
zuciya, ina tare da ke a guri ɗaya ta yaya zan zuba miki ido kiyi ta kuka, kina
wahalar da kanki da yawa "
" kowa yaji da kansa malam ka dena damun kanka akaina"
Yusuf yace "Ai bazan iya bane, in dai kina kuka nikuma zuciyata rauni take"
Tsaki tayi tace "Se kai tayi ai"
Yusuf murmushi yayi bece komai ba.
Can tace "yanzu kaga death contract ɗin da nake gaya maka muddin zakayi aiki dani
ko? Meyasa baka yi tunani akai ba kasa hannu, dukda na gaya maka haka? "
Yusuf yace "saboda shi bawa baya taɓa tsallake ƙaddararsa, Allah ya ƙaddara se haka
ta faru"
Shiru tayi ta shiga duniyar tunani, tana cikin tunanin ne bacci ya kwasheta daga
nan inda take zaune, ta lanƙwashe wuyanta.
Yusuf ya miƙe yaje da nufin ya gyara mata kwanciya saboda wuyanta, ashe baccin nata
ba nisa yayi ba, ta buɗe idonta ta kalle shi, haɗe rai tayi tace "meye haka?"
"yi haƙuri, gani nai kin lanƙwasa wuyanki, kar yayi miki ciwo kuma bana son in
tasheki"
"to ina ruwanka inma yayi min ciwon? Dalla cikani kuma karka ƙara taɓani na gaya
maka"
(Nikam nace Mamaki 😂 jimin mara kunya, sekace yau aka fara)
Murmushi yayi yace "shikenan Allah ya huci zuciyarki"
Ta kwanta tareda juya masa baya, Yusuf ya ƙura mata ido tare da yin murmushi a
ransa yace 'insha Allah sena maye gurbin wannan damuwar taki da farinciki'
Yusuf ji yake kamar bashi ba, wai shine ya Auri Widad, yasan badan ƙaddara ta
Ubangiji ba, kamar shi a yadda yake ya Auri mace irin Widad kyakkyawa 'yar me kuɗi
haka, sedai wani iko na ubangiji.
Haka nan yake fatan Allah yasa su kasance tare har Abada, Allah yasa idan ta gano
waye shi karta guje shi.
Misalin ƙarfe biyu da rabi na dare, Nurat taji motsi a harabar gidansu, ta leƙa ta
taga ta hango mahaifinta ya fita shida direbansa, tunani ta shiga yi ina mahaifinta
zeje a wannan daren haka? Tashi tayi ta tafi ɗakinsa, ta murɗa ƙofar a hankali ta
shiga, ƙarƙashin gadonsa taje ta ɗakko wayarta da ta ajiye ta kunna recording.
Tayi saving ta fito daga ɗakin ta koma nata ɗakin, anan taji wayar da yayi da batun
kuɓutar su Widad, da sauri ta miƙe tsaye tana Alhamdilillah, ta dinga kunna
recording ɗin tana sake saurara, hankalinta ya koma son sanin me zasu tattauna a
meeting ɗin da zasuyi a wannan tsakiyar dare kamar wasu matsafa.
Babban falon Hotel ne suke zaune, sunyi jugum jugum kamar masu jiran tsammani kallo
ɗaya zaka musu kasan suna cikin damuwa. Alhaji Haruna yace "jama'a ayi magana,
abubuwa da sun taho kamar abun arziki, amma yanzu komai taɓarɓarwa yake, ta yaya
za'ace sun gudu se kace a film, ko wata tatsuniya.
Alhaji Munir yace "nima abun ya ɗauremin kai, ga kuma wannan samu da rashi da muka
gani, muna shirya abu amma wai an fasa taron, wannan shegun turawan ne suka ce a
ɗaga, na rasa wani baƙin munafukin ne ya gaya musu ba, nifa kaina gaba ɗaya ya
kulle"
Alhaji Musa yace "babu yadda za'ayi ace su kasa jim rashin lafiyarsa ko kun manta
shahararsa ne? Dole zasuji ai"
Wayar hannun Alhaji Musace ta fara ringing, ya fito da ita ya ɗaga .
"ban samu halartar zaman da kuke a daren yauba, hakanma duk yana cikin shirina ne,
yakamata ku maida hankali gurin gane cewar wani yana muku zagon ƙasa, akwai na
jikinku wanda yasan siriinku shine yake ta dagula muku lissafi, ku maida hankali
gurin gano waye, sannan kusam duk yadda zakuyi ku kama wanda sukayi garkuwa da 'yar
gidan Daula ku kashe su, in bahaka ba akwai gagarumar matsala, sannan ko a mace ko
a raye ku tabattar an kama yaran nan an kashesu" yana gama maganar ya kashe
wayarsa.
Nan fa suka sake shiga wani ruɗanin, tabbas inba wanda yake cikinsu ba babu ta
yadda za' ayi Su Widad su iya tsira daga inda aka ɓoyesu.
Alhaji Haruna yace "to kun daiji abunda Alhaji Bukar yace, yanzu abunda za'ayi
shine, kusa a binciko mana wanda aka bawa bincike hukumar jam'ian tsaro, ayi karɓo
mana sakamakon binciken, hakan ze ƙara haska mana wani abun"
Alhaji Munir yace "wannan kuma aikin Saleh ne, shi'aka ɗorawa wannan ragamar"
Alhaji Musa yace "Na kira shi sam labarsa bata shiga, inaga zan tura ɗan aike a
kiramin shi da safe"
Haka suka gama tattaunawa suka tashi ba tare da cimma wata ƙwaƙwarar matsaya ba.
Da safe Hajiya Halima nata safa da marwa, layin Ramlah sam baya shiga, ƙarfe goma
na safe sega Ramlah ta dawo, Hajiya Halima tace "daga ina kike?"
Kafin tayi magana Fahad ya shigo, Yace 'Mummy barka da safiya, mun miki laifi ko?
Wallahi bayan mun dawo daga cinema ne naga kwana biyu ba taje gidanmu ba, kawai
muka zarce can, daga nan kuma mumsy tace seta kwana tunda bata zumunci "
Hajiya Halima tace " Aida ta kira ta gayamin, hankalina ya tashi ince kaddai kuma
an sace mana ku"
Ramlah tace "haba Mummy wani irin sacewa kuma, ai an san wanda ake sata, ina tare
da Fahad waye yavisa ya saceni"
Sukayi dariya gaba ɗaya, Fahad ya kashe mata ido, sukayi Sallama ya tafi.
Ramlah na zuwa ɗakinta ta jefar da jakarta ta kife akan gado ta cigaba da bacci,
saboda har yanzu ƙwayar da ta sha bata saketa ba, kuma ga rashin sabo dama, dan
bata taɓa shan kayan maye ba.
Yusuf bayan ya dawo daga sallar Asuba, har ya kwanta ya tashi, ya duba shimfiɗar
Widad yaga bata nan, zumbur ya miƙe zaune a gigice yana waige waige, miƙewa yayi ya
fito tsakar gidan bakowa, saboda yanayin garin da sanyi kuma gari be gama waye ba,
leƙe leƙe ya shiga yi yana nemanta, can ya hangota daga wani ɗan lungu tana tsaye
tana leƙa wata taga se murmushi take, hannunta riƙe da brush da toothpaste, kan nan
ko ɗan kwali babu, gashinta ko taza babu ta naɗeshi da ribbon ya kwanta a bayanta.
A hankali ya ƙarasa inda take cike da son sanin me takewa wannan murmushi haka?
Jin mutum tayi a tsaye a bayanta, ta juyo a ɗan razane, Yusuf ta gani a tsaye a daf
da ita.
"meye haka?"
Yusuf yace "gani nayi kina tsaye kina murmushi, shiyasa nace bari inga abunda ya
saki nishaɗi haka? Sannan gari akwai sanyi fa, kalli kanki babu ɗan kwali kar mura
ta kamaki, sannan kayan jikinki maza na shiga na fita a gidan nan, kar gari yayi
haske suzo su sameki a haka, su kansu matan gidan zasu ga hakan wani iri saboda ya
saɓawa Al'adunsu"
"Wai kai meyasa ka fiye shishshigi da takura ne?"
"ba shishshigi da takura bane, kinga yanzu kina da Aure fa"
"kaga wannan Auren fa dashi da babu duk ɗaya, karka ƙara sawa ranka wani Aure
mukayi"
Yusuf ya ɗanyi murmushi, cike da basar da zancen yace "kin tsorata nifa, harna
kwanta na duba ban ganki ba, shiru shiru kuma naga baki shigo ɗaki ba"
"hmm kayi zaton zan gudune? In gudu inje ina? Ko kana zaton zan gudu da wannan
Auren naka a kaina? Idan kaga na gudu ko na bar ƙauyen nan to tabbas ka sakeni ne"
Yusuf yace "idan kuma ban sake kin bafa?"
Juyowa tayi ta saka idonta a nasa tace "me kace?"
Girgiza mata kai yayi alamar bakomai, ta harareshi tace "ban guri in wuce"
Seda ta tafi ya Leƙa me take kallo, ɗakin zomaye ne, an kunna musu aci balbal an
rataye ta, se guje guje suke suna haƙa ƙasa, da wasanninsu shine abunda yasa ta
nishaɗi ta tsaya take kallonsu.
Yusuf ya koma ya kwanta bacci ya ɗauke shi, ita kuwa Widad data gama brush ɗin
komawa tayi ta cigaba da kallon zomaye, seda ta gaji sannan ta koma ɗaki.
Yusuf yayi juyi ya buɗe idonsa a hankali, ya sauke su akan Widad, ta gyara
shimfiɗarta sa kanta, ta sauke Akwatunanta tana ta gyara kayan ciki, ta ware masu
datti ta tattare Akwatunan ta canza musu guri, duk Yusuf yana kallonta, Widas sam
bata son ƙazanta, tana da matuƙar son tsafta a rayuwarta.
Yusuf ya tashi ya kwashe kayan shimfiɗarasa ya ninke, bata kula shi ba sabgoginta
kawai take, Yusuf yayi mamakin danganar da Widad tayi, dukda har yanzu bata saba da
abubuwa da yawa ba.
"wai babu inda za'a samu inji wanki ne? Ina son a wanke min wannan kayan ne"
Yusuf yace "Ai baki da wani injin wankin daya wuceni, in kin haɗa se in ɗiba inje
in wanko su"
Widad tace "kaine zaka wankemin kayan?"
Yusuf yace "eh mana, ko kinga alamar injin wanki a garin nan, tunda muka zo kin
taɓa ganin wuta?"
"to gasu nan na haɗa, kaje kace a bani ruwan wanka"
Yusuf ya girgiza kai yace "to"
Ya miƙe ya ɗau bokiti ya fita, Widad ta buɗe Akwatinta ta ɗakko towel ta ɗaura, ta
saka hijjabi ta biyo bayansa yadda ana haɗa ruwan se ta shiga tayi wanka.
Mutan gidan sunata hada Hadar yadda za'a haɗa karin kumallo, ga dukkan alamu yau
mutuniyar Widas ce da girki, wato Harira.
Yusuf ya durƙusa ya gaishesu, cikin jin nauyi kafin yayi magana Gwaggo tace
"Yusufa na ganka da bokiti, ruwan wankan za'a zuba mata?"
Yusuf yace "eh Mama"
Tace "kawo in zuba maka anan, ya jikin nata kuwa"
Yusuf yace "jiki Alhamdilillah"
Tace "Madalla, nikam ya sunan nata ne? Bamu san sunanta ba"
Yusuf yayi murmushi yace "Sunanta Widad"
Hari dake gaban murhu ta juyo da sauri tace
"Bala'i, wannan wane irin sunane? Hudas ko wudas sekace kayan citta da masoro wane
irin sunane wannan"
Tsakin Widad ne yasa Yusuf juyawa, yadda ta tamke fuskane ya tabattar maaa sa taji
abunda Hari tace, Yusuf kamar yayi dariya Amma ya basar kar suyi faɗa a gaban
mutane.
Gwaggo tace "kaga 'yar halak, ana zancenta se gata, sedai ni wannan sunan nata na
Larabawa bazan iya faɗa ba, Amarya ya jikin naki?"
Widad a ranta tace "wai Amarya Taɓɗijan"
Yusuf yace "Ana miki ya jiki?"
"Naji sauƙi"
Galala Hari ta bita da kallo tace "Ashe bahaushiya ce, wallahi ganinta nake kamar
bata jin hausa, yo aini harna fara tunanin ko kurma ce, ashe tana magana sannu
Amarya wudas, ashe kina magana Allah sarki, ya jiki?"
Sake yamutsa fuska Widad tayi, 'ita dai wannan matar bata gajiya da magana, kodai
bata san yadda haƙoranta suke bane take buɗesu tana surutu haka, bar wani kore kore
ne a jikinsu, ga maganar tsiya da take dashi"
Widad bata kulata ba, aka haɗa mata ruwanta, Yusuf ya kaimata inda take wanka.
Aka haɗa Yusuf da yaro ya rakashi rafin da matasan garin suke haɗuwa suyi wanki.
Amlace ta shiga ɗakin Ramlah, ta dinga bubbuga mata filo, da ƙyar Ramlah ta tashi a
fusace tace "Meye haka Amal?"
Amal tace "Anya lafiyar ki kuwa? Ƙarfe biyi fa, amma har yanzu bacci kike,
yakamata ki tashi haka ai"
Miƙewa tayi zaune tana miƙa tare da duba agogo, dagaske biyu na rana, haka ta miƙe
ta tafi banɗaki tayi wanka sannan ta ɗanji ƙarfin jikinta.
Koda Saleh ya dawo kano, be biya ko'ima ba Asibiti ya fara zuwa duba jikin Alhaji
Nasir, amma yanayin jikin nasa se godiyar Allah, Nurses suka gaya masa Anwar yaje
masallaci.
Saleh ya zauna a kusa da Alhaji Nasir, wanda idanunsa ke lumshe yake numfashi da
temakon Na'urar dakw bashi iskar Oxygen, ya riƙo hannunsa da suka yi sanyi ƙalau,
cike da tausayawa ya kai bakinsa daidai kunnensa yace "Allah ya baka lafiya
Yallaɓai, 'ya' yanka sun kuɓuta daga hannun miyagun nan, yanzu haka suna wasu ƙauye
na basu mafaka, saboda tseratar da Rayuwarsu, Yusuf yayi ƙoƙari matuƙa ya kula da
Amanarka, yana kula da gimbiyarka sosai, Amma munyi maka wani laifi da ban san ya
zaka ɗauki abunba, Na wuce gaba Yusuf ya Auri 'yarka, dan kasan bata yadda da kowa
seshi, kuma baze yuwu ya cigaba da kula da ita ba, tunda ba muharramarsa bace"
Dukda Alhaji Nasir ba iya magana zeba, da alama yana jin abunda Saleh yake faɗa,
ƙara riƙe hannun Saleh yayi gam sannan yayi masa murmushi.
Saleh yace "Amma karka kuskura ka gayawa kowa, kayi shiru da bakinka"
Anwar ne ya shigo bakinsa ɗauke da Sallama, yana ganin Saleh yayi murmushi yace
"Saleh sannu da zuwa, naje Sallane"
Saleh yace "bakomai Anwar, ya me jiki?"
Shiru Anwar yayi, ƙwalla na taruwa a idonsa yace
"Saleh na rasa wane irin abokai Allah ya bawa bawan Allah nan, sam hankalinsu baya
kansa, amma lokacin da yake da lafiya sune kan gaba gurin nuna masa ƙauna, Amma
dubi yanzu, look at how he's suffering alone, ba wanda ya bani mamaki kamar
mahaifiyata"
Anwar ya ƙarasa maganar, jijiyoyin kansa na tashi idonsa yayi ja, Alhaji Nasir ne
yayiwa Anwar Alamar yaje da hannunsa.
Anwar ya ƙarasa gaban gadon Alhaji Nasir ya zauna.
Alhaji Nasir ya kamo hannun Anwar, sannan ya miƙa hannunsa ɗaya yana shafa kan
Anwar tareda yi masa murmushi a hankali yace "Nagode, Nagode"
Kawai Anwar ya rungume Daula ya fashe da kuka, shima Daula hawayene suka fara bin
gefen idonsa, da ba ƙaramin mamaki ya shiga ba, ganin yadda gaba ɗaya mutanensa da
suke tare dashi suka watse suka barshi, ciki harda matarsa da take morarsa.
Yusuf yaje ya tarar da matasa da magidanta a gurin wankin nan, wasu na wanki wasu
na wanka a ruwan, in an koro dabbobi suma suzo su sha ruwan, amma a haka yaga wasu
na ɗiba na tafiya dashi abun ya bashi mamaki, dama a gurin salla megari ya gabatar
dashi, dan haka wasu daga cikinsu sun sanshi. Duk rashin son mutane irin na Yusuf
ya ɗan sake dasu, suka dinga hira suma bashi labari akan yanayin garin nasu. Abun
ya dinga bawa Yusuf mamaki, suna rayuwa cike da son juna mutanen ƙauyen, sedai abun
mamaki ɗan majaillisar dake wakiltar yankin kakannisa 'yan garinne, amma abun
mamaki sukace lokacin da yake campaign har falafalan wuta aka samu su, ya gina musu
borehole guda ɗaya can wajen gidan kakaninsa shima se anyi tafiya me nisan gaske
borehole ɗin yake, yace idan suka zaɓe shi yaci ze janyo musu wutar lantarki,
tundaga wannan campaign da yazo tsawon shekara uku basu sake ganinsa ba, ko gidan
kakannin nasa baya zuwa ziyara gaba ɗaya ya koma Abuja. Haka Yusuf suka cigaba da
hira shikuma yana wankinsa, seda ya gama suka bushe ya ninko kayan tsaf, sannan
suka taho sa wani maƙocin gidan megari zuwa gida.
Yana zuwa gida ya tarar da Widad a ƙofar ɗakinsu a zaune, zaman dirshen a ƙasa
fuskarta tayi jawur saboda kuka, Yusuf ya razana ko ciwonta ne ya tashi. Gwaggo na
ganinsa tace "yawwa Yusufa, wallahi muna tsakar gida muna aiki muka jiyo ihunta, ta
fito da gudu mukaje kanta, juyin duniya taƙi magana tayi zamanta a nan gurin, munce
ta bar ranar ta shiga ko ɗakina ta zauna taƙi.
Yusuf ya ƙarasa inda take ya ajiye bokitin hannunsa me ɗauke da ninkakkun kayansu
yace "lafiya kuwa? Meyasameki haka?"
Cikin harshen turanci tace masa, "wasu ƙwarine suka yi ta cizona, sekuma naga
spider manya guda biyu a ɗakin, dana fito nan ma ƙwarin suka cigaba da cizona"
Girgiza kai yayi yace "shikenan tunda na dawo tashi mu shiga ɗaki, kalli a yadda
kike kin zauna a tsakar gida kowa yana kallonki a haka, kuma kinga kin tayarwa da
mutanen gidan hankali"
"wallahi bazan shiga ba se an cire wannan spider ni bana sonshi, bana son ganinsa
it's irritating me, looks at my body"
Se yanzu ya lura da yadda kafofin gashinta suka buɗe, jikinta yayi wani irin
burɗin_ burɗin, fuskarta ma tayi ja saboda cizon sauro.
Hari tace "Allah dai yasa ba wani abun mukayi mata ba, dan naga alamar makirace,
tun ɗazu muke fama taƙi magana, Amma tana ganin mijinta ta fara magana hadda
karairaya"
Widad ta ɗaga kai ta ƙurawa Hari ido, yayin da gwaggo taji haushin abunda Harin
tayi.
Yusuf kam ba ƙaramin dariya Hari ke bashi ba idan ta kunna Widad, yasan Widad tana
mata kawaici ne kafin ta ɗan sake.
Yace "ba wani abun kukayi mata ba, wai wani abune ya cijeta amma, bakomai yanzu zan
shiga in duba"
Yusuf ya shiga ya duba bega gizo2 ba, sedai cinnaku dake yawo a ɗakin, da alama su
suka cijeta. Yasa tsintsiya ya shashsharesu tsaf, sannan yace ta dawo ɗakin.
Yusuf "Yace meye ya cijekin?"
Guri ta zauna ta janye rigar jikinta, ta nuna masa cinyarta, fara tas fiye da
fuskarta, sedai tayi ja saboda cizon cinnaka, banda wanda ya gasa mata a hannu.
Yusuf yace "Sannu bari in tambayi gwaggo inda zaitun ta bani ki shafa" Zumɓura
baki tayi tace "ni banyi wanka ba"
Haka ya karɓo ruwa tayi wanka, sannan ta dawo ɗakin, ya bata guri ta sa kaya, ya
ɗakko zaitun ta zauna ya shafa mata a na hannun, ya fara shafa mata a ƙafarta ne a
hankali, haka kurum taji jikinta wani iri, kawai seji yayi ta doke hannunsa tace
"meye haka?"
"Me kuma nayi miki?"
"ban sani ba" ta bashi amsa tare da miƙewa, ɗan sunkuyar da kai yayi yana murmushi.
Daga Asibitin gurin Alhaji Musa Saleh ya wuce, yaje ya sames hi a office ɗinsa.
Saleh yace "Ranka ya daɗe kwana biyu bani da lafiya, ko ƙofar ɗaki bana iya
fitowa, shiyasa kwana biyu bana zuwa"
Alhaji Haruna yace "Akwai damuwa fa, ko Kasan me Adda ya cemin yarinyar nan sun
gudu"
A razane Saleh yace "wace irin maganar banzace wannan? Kamarya sun gudu?"
"Nima dai abunda na gani kenan, gaba ɗaya sun mayar mana da aiki baya, yanzu Bukar
yace ko a raye ko'a mace anemosu a kashesu kar Asirinmu ya tonu, sannan kaje ka
bincika mana wa'aka bawa aikin binciken nan a cikin jam'ian tsaro?"
Saleh yace "Amma fa wani hanzari ba gudu ba, ina kyautata zaton me Adda yana sane
ya sake su, wataƙila tace zata bashi kuɗine koma ta ninka masa abunda kuka bashi,
shine ya sake su, in bahaka ba ta yaya zasu iya tserewa? Kokuma a cikinku ne wani
ya zagaya ya haɗa baki dashi, idan an karɓo abun a gaya masa shikaɗai ba"
Shiru Alhaji Haruna yayi yace "Biri yayi kama da mutum, kuma fa Saleh kayi magana,
tabbas dan nasan zata iya, kuma babu Abunda me Adda baze iya akan kuɗi ba"
Jinjina mara adadi ga ɗumbin masoya littafin AƘIDATA, niba abunda zance muku se
godiya Allah ya bar ƙauna, ga dogon page nan, nima inga dogon sharhi, ga link ɗin
telegram nan a ƙasa
https://t.me/joinchat/SYIfEaoQo_JlNDM0
Share, share and share please 🙏 🙏 🙏 Domin gyara sharhi, ko shawara Ayshercool
07063065680
_*AƘIDATA*_
PERFECT WRITERS ASSOCIATION
(WE AIN'T PERFECT BUT WE ARE ALWAYS TRYING OUR BEST, TO MOTIVATE AND ENTERTAIN OUR
READERS)
https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/
*Story and written by*
_*AISHA HUMAIRA _(Daddy's girl)*_
The experience writer of *ABDUL JALAL** WATA KISSAR.... (SAI MATA) *And now *AƘIDA
TA *
I dedicated this book to my Mum (Malama Nafisat Adam Muhammad) i love you mum
Haƙƙin Mallaka ⚠ : Littafin nan mallaki nane, tun daga sunan labarin zuwa abunda ya
ƙunsa, ban yadda wani ko wata ya sauyamin ko yin Amfani da wani ɓangare na labarin
ba ba tare da izinina ba, Nagode
https://www.wattpad.com/user/Ayshercool7724?
utm_source=android&utm_medium=link&utm_campaign=invitefriends
NOT EDITED
ELEGANT ONLINE WRITER'S
PART1 Page 34_35
Saleh ya cigaba da ziga Alhaji Haruna, akan lallai yayi bincike, dan zata iya
yuwuwa abokan harƙallaesa ne wani yasa a karɓo masa abun hannun Widad, shiyasa me
Adda yace masa sun gudu.
Alhaji Haruna yace "Nagode sosai Saleh, Insha Allah zanyi tunani akai"
Saleh yace "bakomai yallaɓai, bari in ɗanje gida in huta, kasan bana jin daɗin
jikin nan nawa"
Alhaji Haruna yace "shikenan Allah ya sawwake"
Saleh ya tashi ya tafi
Sakina ce fuskarta ɗauke sa damuwa ta shiga ofishin Suleiman, Suleiman yace "Sakina
lafiya kuwa?"
Sakina tace "Yallaɓai akwai damuwa, yau sati biyu sa sace Yusuf amma har yanzu babu
wani kyakkyawan rahoto, da yake nuna ana bincike akan lamarin nan, anya anyi adalci
kuwa duba da yadda Yusuf yake bada gudunmuwa akan harkar tsaro, amma ace shi wannan
iftila'in ya faɗa masa amma babu wani yunƙuri da'ake gurin ceto shi, idan ya rasa
ransa fa? " ta ƙarasa maganar kamar zata yi kuka.
Suleiman yace "look Sakina, kiyi wani tunani kodan Albarkacin 'yar babban attajirin
da' aka sace su tare, yaci ace an maida hankali akan nemansu, amma har yanzu shiru,
shikansa Daulan yana gadon Asibiti a kwance, na kai ƙorafi akan abari muma mu
gudanar da namu binciken, amma daga sama aka bani umarnin cewar ba'a samu ba, ana
gudanar da bincike akan al'amarin, babu wani abu da zamu iya banda muyi musu Addu'a
"
Sakina tace " shikenan Yallaɓai, ubangiji Allah ya kuɓutar dasu lafiya, bari in
koma kan aikina"
"Shikenan Sakina, Allah ya taimaka"
Sakina na tafiya, telephone ɗin gaban Suleiman ta fara ringing, ya sa hannu ya
ɗaga, jin muryar wanda ya kira shin yasa shi miƙewa tsaye cikin girmamawa yana amsa
wayar.
"A cikin ma'aikatanka wa'aka saka akan binciken masu bibiyar Alhaji Nasir Daula?"
Suleiman yace "Yallaɓai Yusuf ne, wanda aka ƙarawa matsayi kwanan nan"
"A gaggauta kammala binciken nan, a miƙo bayanan binciken nan headquarter"
Suleiman yace "Ok Sir"
Yusuf ya kalli Widad da tayi kicin kicin da fuska yace "ga kayan nan na wankesu,
sun bushe ma gaba ɗaya"
Tasa hannu ta ciro kayan daga bokiti, taga kayan a haɗe dana Yusuf, kwashe nata
tayi ta zube masa nasa a gurin, Yusuf yasa hannu ya kwashe ya zuba a jakarsa.
Ya kalleta yace "kinci Abinci kuwa?"
"ni banci wani Abinci ba, kaga fa abunda aka kawo"
Kwano ta miƙa masa, yasa hannu ya buɗe dafaffiyar masarace a ciki da ɓawonta da
komai, Yusuf yace "to me yasa baki ciba?"
"ta ina zanci ? Kawai se in kama cin masara, ni ban taɓa ganin anci masara ba,
nidai kawai nasan Abinci akeyi da ita, amma ba'aci"
Yusuf yace "ikon Allah, wannan wace irin hausa ce? Waye ya gaya miki ba'a cin
masara"
Ya zauna ya ɓare masarar tsaf, ya ɗaurayeta, yace "nasan kece baki taɓa ciba, amma
ana cin masara dafaffiya ko gasashiya, ci kiji"
Ɗauke kai tayi taƙi karɓa, Yusuf kuwa yasa masara a gaba ya fara ci, zuba masa ido
tayi tana kallon ikon Allah, yana nufin itama haka zata ɗau masarar ta dinga wannan
kokawar haka sekace wata saniya.
Plate ya ɗakko ya shiga ɓanɓarowa yana tara mata a plate yace "gashi na ciro miki
ɗauki kici"
Ba kunya tasa hannu ta fara tsinta tana kaiwa bakinta, dan bilhaƙƙi ita bata taɓa
ganin ana cin masara a haka ba, amma kuma tabbas da daɗi, ya dinga cirowa yana tara
mata tana tsinta tana ci, kamar wata 'yar yaye, cikin ikon Allah a haka kuma ta
ƙoshi.
Shiru tayi ta tuna lokacin da sukaje restaurant cin Abinci, Yusuf yake gayamata
Naira ɗarin cin Abinci tana gagarar wasu, take ganin kamar ƙarya yake, se gashi
yanzu ta gani da idonta, da wanine ya bata labarin ana dafa masara aci a matsayin
Abinci zata ce ƙaryane dan bata taɓa gani ba.
Can Yusuf yace "inda ƙwaron ya cijeki ya dena zafin?"
Ta gyaɗa masa kai alamar eh, yace "hannun da'aka harbe ki fa?"
"yayi sauƙi, ina iya motsa hannun sosai, sedai idan ma bige ne nake jin zafin"
Yusuf yace "masha Allah, Allah ya ƙara miki ingantacciyar lafiya"
Shiru tayi kamar ba taji ba, Yusuf yace "Addu'ar ma bakya so?"
Shiru tayi masa tana sake ƙarewa roofing ɗin ɗakin kallo, tana son gane dame akayi
shi.
Yusuf yace "me kike kallone?"
Widad tace "kai subhanallah, wallahi ka dameni da surutu haba, sekace waccan matar
me haƙora"
Yusuf yace "to shikenan na dena gimbiyata"
Ɗagowa tayi ta masa wani irin kallo, ba shiri ya miƙe yayi waje ya bar mata ɗakin
yana murmushi.
Wasa2 Ramlah ta ganewa shaye2, bata salla se wajen ƙarfe takwas na safe, da ta idar
zata ɗakko Coca-Cola tasha, seta kai ƙarfe biyun rana tana bacci.
Yanzuma Amal ce ta shiga ɗakin Ramlah, ta tarar da ita tana girgiza jarkar Coca-
Cola.
Amal tace "Ramlah, wai me yake damunki ne haka? Wane irin coc ne kike sha ba yau
ba gobe ga shegen bacci kamae kin haɗiyi kasa"
Ramlah ta kalleta tace "kina da matsala da hakanne?"
"ba wai batun ina da matsala da hakan bane, sedai cewa kina ganganci da rayuwar ki,
baccin da kike ya wuce ƙa'ida, kuma wannan coc da kike sha yayi yawa sosai, nifa na
fara zargin wani abu kike sha a cikin coc ɗin nan"
"Ke Amal! Ki kiyayeni, dalla wuce ki barmin ɗaki, ina ruwanki dani idanma wani abun
nake sha?"
Amal tace "shawara ce nake baki, amma
" wallahi Amal in baki barmin ɗaki ba sena miki rashin mutunci, Dalla ƙara gaba
kije kiji da kanki"
Amal tace "shikenan Kije ki ƙarata" ta fito daga ɗakin.
Yanzu kusan kullum se Ramlah ta fita, ko tare da Fahad ko ita kaɗai, kuma Hajiya
Halima bata taɓa yi mata magana akan hakan ba.
Anwar kam ya tattara yasa musu ido, ya maida hankali akan kula da Alhaji Nasir,
kwata kwata ya dena shiga sabgarsu ma.
Abubuwa suka fara cakuɗewa su Alhaji Musa, suka kuma hayar wasu 'yan ta' addan
domin a nemo musu su Me Adda, yayin da Alhaji Haruna ya keta tunani akan maganar
da Saleh ya gaya masa game da tserewar Su Yusuf.
Meeting suke akai akai akan yadda zasu ɓullowa al'amarin,Alhaji Munir yace "tabbas
idan har yaran nan suka kuɓuta suka dawo Asirinmu ze iya tonuwa"
Alhaji Musa yace "yakamata ku kwantar da hankalinku, babu yadda za'ayi Asirinmu ya
tonu, yanzu naga Likitan nan yana aikin da muka sashi, dan yanzu baya gane waye
akansa sam"
Alhaji Haruna yace "hakane Daula ya zama abun tausayi, talakawan da yake fafutuka
akansu, an hana kowa zuwa inda yake, manyan ƙasar nan ma kowa yayi watsi da
lamarinsa, yanzu haka nasa Jam'ian tsaro su hana kowa shiga inda yake, se ɗan matar
nan tasa, shi kuma wannan soko ne, ba abunda yake ganewa, shekaranjiya wasu baƙin
turawa sunzo duba shi, amma an hana su ganinsa ance yana ƙarƙashin kulawar likita
baza'a ganshi ba"
Alhaji Musa yace "Good hakanma yayi, a hana kowa zuwa inda yake muyi yadda muke so,
Amma Nifa har yanzu ina mamaki akan guduwar yaran nan, kuma da suka kuɓuta aida
zasu dawo a gari a gansu, amma har yanzu babu wanda yaji ɗuriyarsu"
Alhaji Munir yace "ni kaina abunda yake ɗauremin kai kenan, zuwa yanzu ai yaci ace
anji labarin sun dawo, amma babu wanda yaji hakan"
Alhaji Musa yace "shiyasa nake tunanin akwai wata a ƙasa ruwa baya tsami banza,
akwai munafiki a cikin mu"
Alhaji Haruna yace "kamarya? Kana nufin a tsakaninmu munafikin yake kokuwa?"
Alhaji Munir yace "kunga ya isa haka, nima nayi zargin haka amma babu lallai da
munafuki a tsakaninmu, sedai a wanda suke mana aiki tabbas, kokuma akwai wani a
gefe daya ke farautar abunda muke nema"
Alhj Haruna yace "ba abunda baze iya faruwa ba, Amma kar mu ɗora komai akan zargi
semun tabattar"
Kamar yadda Saleh ya bada umarni, aka ginawa Widad nata banɗakin, akwai wata
ƙatuwar rijiya a gidan ruwan sam bashi da kyau, haka nan ake amfani dashi a gidan,
ko kuma mutum yayi tafiyayyiya yaje rafi ya Ɗebo.
Yusuf kuwa tafiya yake me nisa, yaje ya ɗebo ruwa a wannan borehole guda ɗaya tal
ta garin, yazo gida ya tafasa idan ya huce seya zuba a randarsu suke amfani da shi
a matsayin na sha.
Har yanzu Widad bata saba da kowa a gidan ba, ba ruwanta dasu sedai in sun haɗu a
tsakar gida suka mata sannu ta amsa, amma bata shiga sabgar Hari sam, saboda Hari
baƙar magana take gaya mata.
Yanzu ma tana tsugune tana brush da yamma, yaran Hari suka kewaye Widad suna
kallonta, mussman dogon gashinta dake ɗaukar ido, gata ba ma'abociyar saka kallabi
ba, abun haushi hadda 'yan matan gidan da suka tasa, se kallonta suke ita ta rasa
se yaushe zasu saba da ganinta su dena mata wannan kallon haka?.
Widad tace "kai me kuke kallone, haba bana son kallon nan da kuke min, did i look
like a beast?"
Hari tace "yo sunga abunda basu saba gani ba, kin fito tiɓitiɓi da wasu irin kaya
ai dole su kalleki ni wallahi da ban zaci ma musulma ce ke kina jin hausa ba"
Widad tace "eh ba musulma bace ni, gunki nake bautawa yana ɗaki idan kina so ki
ganshi"
Sam hari bata zaci Widad tana da baki hadda baƙar magana ba.
Gwaggo tace "Amarya ƙyaleta kiyi haƙuri"
Sannan ta kalli Hari tace "haba Hari, kin fiye magana wallahi duk haƙurin yarinyar
nan kinsa ta fara tanka miki"
Hari tace "yo Yaya yara sunga abunda basu saba gani ba ba dole su kalla ba"
Yusuf yana ta tunanin wace sana'ar ze ɗan fara, saboda ya saukewa mutan gidan
ɗawainiyar da'ake dasu, ga Widad bakomai take ciba duk ta rame, ya dawo daga sallar
Azahar ya tarar an kawowa Widad gujjiya, tanaci hadda ɓawon, Yusuf yace "mekike ci
ne?"
Ta ɗan taɓe baki tace "na manta sunanshi, amma inaga wake ne wannan maman ce ta
bani"
Yusuf ya kwashe da dariya, ta haɗe rai tana kallonsa, yace "haba Madam, wannan ne
waken? Kuma da ɓawo kike ci bari kiga"
Ya zauna yana ɓarewa yana bata, ita tunda take bata san wata gujjiya ba, da taci a
baki se taji kamar wake, ta zata ma wake ne yazo a haka.
Tun Yusuf yana mamakin bata san abubuwa da yawa ba, har ya dena mussman duba da
yanayin rayuwarta, ita ba sakewa take da mutane ba, kuma mafi yawa a waje tayi
rayuwarta, dan haka yake mata uzuri a wasu abubuwan.
Yusuf yace "Ina son in fara zuwa kasuwar garin nan, inga me zan fara siyarwa saboda
mu ragewa mutanen gidan nan ɗawainiyar da suke damu"
"dama akwai kasuwa a dajin nan?"
"daji kuma?"
"Eh mana" ta bashi amsa
Yusuf yace "eh akwai kasuwa amma se anyi tafiya me nisa sosai, nayi magana da
megari ya haɗani da yaronsa tare zamuje kasuwar gobe in Allah ya kaimu inga yanayin
abubuwan"
Tace "Shikenan" tana ci gaba da cin gujjiyarta, seda ta gama ta kalle shi tace
"Wanka"
Yusuf yace "to" ya haɗa mata ruwa sannan ya fita sallar la'asar
A gurin salla Yusuf yaga abun mamaki, akwai ƙaramin gurin da suke jam'in salla,
akwai ƙarancin ilimi ga mutan ƙauyen, liman ya makara wani yaja salla a raka'ar
ƙarshe liman yazo, raka'ar ƙarshe kawai ya samu, itama an ɗago daga ruku'u, da'aka
idar Yusuf yana jira yaga liman ya tashi ya kawo wadda be samu ba amma yaga liman
yayi ƙyam yaja gefe yana laziminsa.
Yusuf ya dinga kallonsa ko ze tashi ya canza sallane, amma yaga aka jima liman ya
shafa addu'a ya miƙe ya gaisa da mutane ya ƙara gaba.
Yusuf yayi shiru a ransa yace "wannan mutumin dabe san hukuncin salla ba, shine
kuma yake jan salla? Tabbas akwai matsala babba, mutanen garin nan suna buƙatar
ilimin Addini, ya barwa ransa cewa zeyi wa megari magana, yaga ta inda ze iya basu
gudunmuwa.
Ya shiga cikin gida ya shiga ɗakinsu da sallama, Widad ta fito daga wankan tana
shafa mai, ba tare da ta kalle shi ba ta amsa ƙasa ƙasa, ta cigaba da abunda take.
Kusa da ita yaje ya zauna yana kallonta, duk cikin salon son yasa ta kula shi, dan
idan har bashi yayi mata magana ba in zasu kwana idan ba wani abu take buƙata ba,
ba zata kula shi ba.
Tana jin yadda ya zauna daf da ita ya ƙureta da ido, kamar tasan maganar yake so
tayi, taƙi magana.
Cike da fargaba dan yasan ze sha masifa, amma ya maze ya kai hannunsa gashin kanta
yace
"wannan gashin yaushe rabonsa da a taje shi? Insha Allah idan na fara zuwa kasuwa
indai naga comb zan siyo, in taje shi da kaina"
Bige hannunsa tayi tace "wai kai meye haka? Me yasa kake son taɓani ne? Na gaya
maka bana son karka ƙara taɓani na gaya maka, in ba haka ba duk abunda nayi maka
kai ka siya, haba sekace baka da zuciya, ko baka gane magana"
Shiru yayi kawai yana kallonta yadda take ta masa masifa, shi yaga tana magana ma
se yaji daɗi a ransa, dan yaga ta rage yawan kukan da take yi.
Ga mamakinta murmushi yayi maimakon taga yaji haushi.
"kawo man in tayaki shafawa" yai maganar yana ɗaukar robar man, ƙwacewa tayi tace
"bana so na gama"
Yusuf yace"Shikenan bari in baki guri kisa kaya"
"inma baka bani gurin ba baze hanani sa kayana ba"
Yayi murmushi ya miƙe cike da jin daɗin yasa ta magana, bayansa tabi kallo yana
fita ta ajiye abunda ke hannunta ta shiga goge hawayen da ita kaɗai tasan
dalilinsu.
Doctor Sufyan yana Office ɗinsa, yana jiran lokaci yayi ze shiga tiyata, wayarsa
yaji ta fara ringin, ya tsaya ya ɗaga tareda yin sallama.
"Sufyan ne?"
"Eh nine"
"ina son ka kasa kunne ka saurareni dakyau, dukda nasan baka san dawa kake magana
ba, hakan ya faru ne sakamakon sanin wanda kake maganar dashi a gurinka bashi da
amfani, ina son ka saurareni da kyau kaji abunda zan gaya maka, kana jina ko?"
Sufyan yace "ina jinka"
"kamar yadda aka baka kwangilar sake kwantar da Daula, aka baka miliyoyin kuɗi akan
karya warke, kuma kayi dan tuni wani percentage ya shiga hannunka, to nima aiki
nake son kayi min, niba kwantar da Daula nake so kayi ba, kawar da Daula nake son
kayi!!!"
Miƙewa doctor Sufyan yayi tsaye ya shiga waige waige karya je wani yaji abunda ake
faɗa masa a waya, cikin rawar murya yace "amm.. Ban gane me kake fada ba fa"
"ƙarya ka keyi ka gane, kuma kaji me nace tunda ka iya karɓar kuɗi kake bashi wrong
treatment, to zaka iya karɓar kuɗi ka kasheshi, likita ne kai babu me zarginka,
tunda kowa yasan condition ɗinsa yayi worse, bazance ga abunda zan bi yaka ba,
sedai da kanka nakeso ka yanke abunda zan bi yaka "
Wani wahallalen gumine ya dinga ratsowa Sufyan, gumi yake ji har tsakanin
cinyoyinsa, yace " Amma kisan Alhaji Daula hatsari ne, dole se anyi bincike akan
gawar sa, don a tabattar da abunda ya kashe shi, idan aka ganoni fa, ina da iyali
da ƙananan yara nasan kasheni za'ayi, Daula babban Attajiri ne"
"meye marabar abunda kake masa yanzu da wanda nace kayi masa, sanin kanka ne wrong
treatment ɗinma ze iya kasheshi, baka da damar cewa ba zakayi ba, saboda na maka
tarko ta ko'ina, ina da duk yadda akayi ka karɓi kuɗi kake bashi wrong treatment,
duk wata hujja daza'a kamaka ina dashi, idan kuma naga dama zan saka ɗauke ɗaya
daga 'ya' yan naka ko kayi ko kuma ransa ya salwanta, zaɓi ya rage naka, sannan
idan kaga dama ka gayawa wani"
Ƙit aka katse kiran, gaba ɗaya doctor Sufyan yaji kamar an zare masa laka, jikinsa
se rawa yake ya duba wayarsa yaga anyi hiding ɗin lambar, dan ko unknown number be
fito ba, duk sanyin Ac dake office ɗin shi gumi yake, kamar wanda ya tuƙa tuwon
gidan biki a tsakae rana.
Yau da wuri Yusuf ya shirya, dan zebi ɗan megari kasuwa, ɗan megarin shima matashi
ne be kai Yusuf ba, a bayan gidan megari nasa gidan yake, da matarsa da 'ya' yansa
shida.
Har Yusuf ya gama shirinsa, aka kawo musu Abincin safe Widad bacci take, a hankali
ya ƙarasa gaban katifarta ya janye bargon jikinta, bacci take hankalinta kwance, se
yarintarta ta sake fitowa ta ƙara kyau a idon Yusuf, yayi shiru yana kallonta.
A hankali ya ɗan daki pillow ɗin da take kai, amma bata motsa ba, ya sake taɓa
pillow amma still bata motsa ba, hannu yasa ya ɗan daddaki nata hannun, kamar me
tashin ƙaramin yaro, juyi tayi amma taƙi buɗe ido.
"Widad" karo na farko a rayuwarta data ji ya kira sunanta, taji zuciyar ta ta buga
da ƙarfi, ta buɗe ido ta kalle shi
Yace "ga breakfast an kawo karya huce, kuma inason zan fita ni"
"shine zaka wani durƙuso kaina haka? Kamar zaka shige cikina"
"ke komai nayi miki lefi ne? To sorry tashi karya huce kinji gimbiyar..
Kallonsa take taji meze ƙarasa, maimakon ya ƙarasa se yayi murmushi yace "tashi
kije kiyi brush, muci Abinci "
Ta miƙe ta ɗau brush tayi waje, Yusuf ya gyara mata shimfiɗa, ya gyara ɗakin.
Widad ta fita tsakar gida, gwaggo tace "Amarya ina kwana"
Widad tace "lafiya ƙalau"
Gwaggo tace "Alhamdilillah ya ƙarfin jiki?"
"Naji sauƙi"
Gwaggo tace "to madalla"
Hari ta ƙurowa Widad ido tana so tayi magana, Widad tace
"idan baki dena kallona ba, sena saka butar hannuna na ɓallo miki wannan haƙorin
da yake leƙowa idan kina magana"
Hari tace "ke hudas kike ko wudas, yau dai ban kulaki ba balle ace na shiga
harkarki"
Widad ta Harareta ta wuce banɗakinta.
Data fito ta manta da batun Yusuf dake jiranta, ta tsaya gurin da take leƙen
zomaye.
Seda tayi me isarta, sannan ta koma ɗaki. seda taga Yusuf sannan ta tuna ashe ita
yake jira suci Abinci, yace "naga kin daɗe?"
Kai tsaye tace "kallon zomaye nayi" , ta ajiye kayan brush ɗinta, tazo ta zauna ta
buɗe kwanon farko, dakakken ƙuli ƙuli ne a ciki, ta rufe ta buɗe ɗayan dafaffen
dankalin hausa ne a ciki da ɓawonsa da komai manya guda uku.
Ta kalli Yusuf tace "meye wannan?"
"Dankali" ya bata amsa
"kuma a haka? Ta yaya za'aci"
Yusuf yace "ga mahaɗin nan ƙuliƙuli a wannan kwanon"
Widad tace "ta yaya za'aci wannan abun ba tea?"
Yusuf yace "seki kora da ruwa" yai maganar tare da fara ɓare dankalin.
ta zuba masa ido, ya ɓare tsaf ya yayyanka shi a kwano, ya ɗebo ruwa ya ajiye mata
yace "bismillah"
Tsayawa tayi tana kallonsa kamar wata sokuwa, ya ɗakko ɗaya ya dangwala da ƙuli
ƙuli ya kai bakinta, ɗauke kanta tayi tasa hannu ta karɓa tasa a bakinta.
Ba zata ce babu daɗi ba, sedai gurin haɗiyewa ne daƙyar take yi, dan kasa haɗiyewa
tayi seda ta haɗa da ruwa.
Dan haka shima ba taci dayawa ba tace ita bazata iya cin wannan abun ba, shaƙe mata
wuya yake.
Yusuf ne yaci sauran, sannan yayi mata sallama ya tafi.
Sufyan abun duniya ya dameshi, ya rasa inda ze saka ransa, ba ƙaramin hatsari bane
kashe shahararren mutum kamar Daula, amma kowa se saka rayuwarsa yake a hatsari
saboda suna taƙamar suna da kuɗi, shiba abun ya kaisu gurin 'yan sanda ba, shi ze
kwana a ciki.
Gaba ɗaya daren nan yakasa bacci, sedai juyi dafa da Asuba aka kuma sake kiransa,
bashi da zaɓin daya wuce ya amsa wayar.
"baka da isasheshen lokacin ɓatawa gurin aiwatar sa wannan aikin, kana da yau zuwa
gobe in Allah ya kaimu ne kawai, idan baka yi ba ni zan aikata maka abunda nace"
Aka katse layin, Doctor Sufyan yayi jifa da wayar ya dafe kai, matarsa ta lura da
yana cikin damuwa ta tambaye shi ko lafiya, yace mata babu komai.
Widad bata taɓa shiga damuwa ba, tsawon lokacin data ɗauka tana rayuwar kaɗaici a
rayuwarta se wannan karon, tunda Yusuf ya fita be dawo ba taji gaba ɗaya duniyar ta
mata faɗi, gashi ita bata saba da kowa ba se shi, seta ji ta wani iri kamar ita
kaɗaice a duniyar, koba komai ganin motsinsa yana rage mata damuwa.
Yau wuni guda tana ɗaki, ba wanda yake shigowa inda take, saboda bata da fuskar
daza'ayi mata hakan, bayan tayi sallar la'asar yunwa ta isheta ta fito tsakar gida.
Gwaggo tace "Amarya lafiya dai ko?"
Widad tace "Naga har yanzu Yusuf be dawo ba kuma ni yunwa nakeji"
Gwaggo tace "Allah sarki, yau Harice da girki bata aiko miki da Abinci ba kenan"
Widad tace "kota aiko ba zanci ba, dan ƙazama ce"
Hari dake salla a tsakar gida ko sallamewa ba tayi ba tace "jar'uba kekam anyi mara
albarka, nice ƙazamar?"
"Eh kece ƙazama, kalli zanin jikinki kalli faratanki, hijjabin jikinki ma me datti
ne, sekiyi abu ki bani inci, an gaya miki komai nake ci?"
Wato Widad sam ta dena ragawa Hari, gwaggo tayi murmushi tace "Yanzu to me zakici?
Widad tayi shiru ba tace komai ba, gwaggo tace "Akwai Furar megari dana dama, bari
in ɗebar miki"
Widad tace "Nagode"
Hari tace "Furar malam ɗin zaki ɗiba ki bata? Lallai Yaya akwaiki da neman gindin
zama"
Widad tace "Eh ita za'a ban, ba zanci Abincinki ba"
Gwaggo dai ba tace komai ba, ta ɗebowa Widad fura a kofin silba ta bata, ta samu
guri ta zauna tana sha.
Furar tayi zaƙi zau da zumar da'aka zuba a ciki, tana cikin shan furar can seta
miƙe tsaye, gwaggo tace "kin ƙoshi ne?"
Widad tace "A'a Yusuf na ragewa"
Hari tace "Ohh ni jikar Hama, ji wata fitsara take cewa ta ragewa mijinta abu"
Wasu matane suka shigo su Uku, ɗaya 'yar babba biyu kuma 'yan mata da sallama suka
shigo, Hari tace "Ahh marabanku da dawowa, wai an sha suna"
Ɗayace ta kalli Widad tace "Hari wace wannan?"
Hari tace "wasu baƙine mukayi"
Ɗayar tace "kalleta kamar balarabiya"
Widad bata tanka musu ba ta koma ɗakinta.
Sukam bajewa sukayi a tsakar gida, ɗayar itama matar megari ce hansai, se 'yan
matan Hindu da Hanne, suma' ya'yansa ne sunje wani ƙauyene, inda 'yar megari take
Aure ta haihu.
Se bayan la'asar Yusuf ya dawo gida, kallo ɗaya zakayi masa kasan a gajiye yake, ya
gaisa da mutanen gidan ya shiga ɗakinsu.
Ba sannu da zuwa bakomai Widad tace "Shine kaƙi dawowa se yanzu?"
Yusuf yace yanzun ma tun ɗazu na taho, akwai nisane sosai.
Ya ajiye kayan hannunsa, yaje yayi wanka, a ɗaki yayi salla saboda gajiya ya nemi
guri ya kwanta yayi shiru.
Widad tace "to ni dai gaskiya ka dinga dawowa da wuri, kawai seka tafi ka barni
nikaɗai, gaba ɗaya nagaji"
Yusuf ya kalleta yace "Aikin me kikayi kika gaji?"
"Aikin zama ba abunda nake, ba kowa a ɗakin nan seni kaɗai"
"Amma ai da mutane a gidan, seki fita kuyi hira"
"Ni gaskiya dana fita wannan me haƙoran take min rashin mutunci, nikuma ramawa
nake"
Yusuf yace "Kidinga ƙyaleta, kinga babbace ba sa'arki bace ta girmeki"
"da alama ka manta Widad Nasir Daula ce ko?"
Yusuf yace "ya za'ayi na manta nina isa? Yau ba'a kawo komai bane yunwa nake ji"
Widad ta taɓe baki tace "wannan ƙazamarce tayi girki, ni kuma nace ba zamu ciba,
shine Mama ta bani furar mijinta"
Buɗe baki Yusuf yayi yace "ba dai ce mata kikayi ƙazama a gabanta ba?"
"idan na gaya mata zata cinye nine?"
Yusuf ya dafe kai, ita Widad a rayuwar ta bata san kara ko alkunya ba sam.
Ta ɗakko kofin furar nan tace "gashi nasha na rage maka"
Yusuf yace "dagaske ragemin kikayi?"
"is there anything special, dan na rage maka?"
Yusuf yace a"a a ransa kuma yace "lallai kin damu dani"
Yusuf yace "Naje kasuwa, naga abubuwa ana saye da siyarwa ba laifi, ɗan megari ze
aran kuɗi, inga me zan fara siyarwa, ranar daba kasuwa kuma naje wani gurin inga me
zanyi"
"to duk meye na wannan wahalar?, naga dai barin gurin nan zamuyi"
"A'a yakamata in koma ciyar dake da kaina, da duk buƙatunki be kamata mucigaba da
ɗora musu ɗawainiya ba, nauyinki a kaina yake yanzu"
Kallonsa tayi tace "don't bother yourself, wannan fa ba Aure neba"
"meye inba Aure ba?"
Tace "Shiri mana"
Yace "Ba ruwan Allah da shiri, kuma koda shirin ne aini yakamata in kula da Gimbiya
ta"
"karka ƙara cemin gimbiyarka"
Yusuf yayi murmushi yace "Lokacin da muna gida gimbiyar Daddy ce, yanzu kuma da
muke nan ba wanda kika sani seni, dan haka gimbiyata ce"
Tsaki tayi ta miƙe daga inda take zaune, Yusuf yace "Komai naki me kyau ne Widad"
Ko Kallonsa ba tayi ba tayi masa shiru, yace "ga Alƙawarin da nayi miki, na samo
comb da ƙyar a kasuwa, yaushe zamu gyara gashin namu?"
Ficewa tayi daga ɗakin ta barshi, shi kuma ya dinga murmushi ganin takaici ya hana
ta magana, Yusuf yace da haka da haka gimbiya"
Sufyan fa hankalinsa gaba ɗaya ya gama tashi, ya hanga yaga bashi da wata mafita
data rage masa banda ya aikata abunda akace, ya haɗa allurai a cikin syringe ya
zauna ya zuba musu ido, gabansa nata dukan biyar biyar, kiransa akayi a waya,
hannun narawa ya ɗauka
"Ka shirya aiwatar da aikinne ko kuwa?"
Cikin jan numfashi Sufyan yace "Eh na shirya"
"shikenan, ina jiran sakamako a yau, ka duba wayarka zakaga Alert ɗin kuɗi"Sufyan
bece komai ba ya ajiye wayar yana yakice gumi.
Zuwa yanzu Widad ta fara dangana, ta ɗan fara sabawa da halin data tsinci kanta a
ciki, Cikin dare Widad tana bacci tayi juyi, hasken farin wata ya hasake ɗakin, ta
hangi Yusuf a zaune akan shimfiɗarsa yayi tagumi,Da alama tunani yake.
A ranta tace 'Ashe shima yana damuwa, amma ya dinga basarwa yace nize hanani kuka'
"wai tunanin mekake?"
Firgigit ya dawo hayyacinsa, yace "idonki biyune?"
"A'a mafarki nake na maka magana"
Yusuf yace "hmm ba tunani nake bafa, cinnaka ne ya cijeni na kasa bacci"
"yaushe ka fara ƙarya?"
"dagaske nake" yai maganar tare da miƙewa ya fita waje, Alwala yaje ya ɗauro yazo
ya tada salla, Widad kam baccinta ta koma.
Yusuf yana cikin sallar ne yaji A gigice Widad tace "Innalillahi wa inna ialaihi
raji'un, wayyo Allah Daddyna"
Ta miƙe da gudu tayi hanyar waje
(Up Up masoya littafin AƘIDATA, Comments ɗinku na matukar ƙayatar dani, shike bani
ƙwarin gwiwa nayin posting, Allah ya bar ƙauna 😍 😍 😍)
Share, share and share please 🙏 🙏 🙏Domin gyara, sharhi ko shawara Ayshercool
07063065680
_*AƘIDATA*_
PERFECT WRITERS ASSOCIATION
(WE AIN'T PERFECT BUT WE ARE ALWAYS TRYING OUR BEST, TO MOTIVATE AND ENTERTAIN OUR
READERS)
https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/
*Story and written by*
_*AISHA HUMAIRA _(Daddy's girl)*_
The experience writer of *ABDUL JALAL** WATA KISSAR.... (SAI MATA) *And now *AƘIDA
TA *
I dedicated this book to my Mum (Malama Nafisat Adam Muhammad) i love you mum
Haƙƙin Mallaka ⚠ : Littafin nan mallaki nane, tun daga sunan labarin zuwa abunda ya
ƙunsa, ban yadda wani ko wata ya sauyamin ko yin Amfani da wani ɓangare na labarin
ba ba tare da izinina ba, Nagode
https://www.wattpad.com/user/Ayshercool7724?
utm_source=android&utm_medium=link&utm_campaign=invitefriends
NOT EDITED
ELEGANT ONLINE WRITER'S
PART1 Page 36_37
Riƙeta gam Yusuf yayi, yayin da ta cigaba da fizge fizge tana kuka, a hankali Yusuf
ya zame ya zauna da ita a jikinsa, ya toshe mata baki, saboda dare ne nan da nan
sautinta ze iya cika ko'ina.
Yusuf yace "Widad, ki nutsu mana darene yanzu karkisa hankalin mutane ya dawo
kanmu, mafarki kikayi fa"
Girgiza masa kai ta shiga yi, cikin kuka tace "is not just a dream, wani abu na
shirin faruwa da Daddyna, ka ƙyaleni inje in ganshi, wani abu ze sameshi"
"yanzu idan kika tafi ina zaki? Daddy Addu'ar mu yake buƙata, tun ɗazu nan salla
nake ina mana addu'a muda iyayen mu, Insha Allah babu wanda ze iya cutar dasu, kuma
Saleh ya cemin ya gaya masa muna nan tare, kidena kuka"
Girgiza kai take tana kuka tace "Daddy na, shikaɗai ya ragemin bani da kowa, bana
son in rasa Daddyna, idan na rasa Daddy babu sauran me ƙaunata sedai dukiyar daze
bari, wayyo Allah Daddyna, ya Allah secure my Dad, Allah yasa in koma in tarad da
kai a raye"
Gaban Yusuf ne ya faɗi, ya tuna abunda Saleh ya gaya masa game da mahaifin Widad.
Kuka take sosai jikinta har rawa yake, ga wani irin gumi daya rufe ta, ɗora
hannunsa yayi a saman ƙirjinta, se bugawa zuciyarta take da ƙarfin gaske.
Yusuf ya shiga karanta mata dukkan Addu'ar da tazo bakinsa, a hankali zuciyarta ta
rage bugawa da sauri da sauri, can kuma bacci ya ɗauketa, ta shiga sauke Ajiyar
zuciya.
Yusuf ya miƙe a hankali da ita, ya kaita kan katifarta ya rufe ta da bargo, ya koma
ya sake alwala ya cigaba da sallar sa.
Alhaji Musane keta sintiri a cikin ɗakinsa, se safa da marwa yake ya kai gwauro ya
kai mari, ya rasa abunda yake masa daɗi, sosai maganganun Saleh sunyi tasiri a
zuciyarsa, sosai zargi ya ɗarsu a ransa cewar a cikinsu akwai wanda ya zame yake
shirin cin amanarsu, kamar yadda ya zame a baya yaso ya haɗa kai shida Alhaji
Bukar. A fili ya furta dole "inyi wani abu akai"
Juyowa yayi yaga Nurat a tsaye a ƙofar ɗakinsa da tray ɗauke da kayan marmari a
ciki, a fusace yace "dan uwarki laɓe kika koma Yimin ko?"
Cikin dakewa tace "meyasa zan maka laɓe kuma Daddy, tun ɗazu nake sallama amma baka
amsa ba"
"Kuma shine seki tsaya ki laɓe?"
"Daddy bafa laɓewa nayi ba"
"zoki ajiye kayan nan ki fita ki ban guri"
Nurat taje ta ajiye masa tray ɗin ta fita, gaba ɗaya Nurat ta lura mahaifinta a
kamar a ruɗe yake, akwai abunda yake damunsa, zata so sanin abunda yake damunsa,
dan wataƙila yana da alaƙa da harƙallar da suke ƙullawa akan Alhaji Nasir da
iyalansa.
Bayan sallar Asuba yau a masallaci, Yusuf ne ya tsaya ya ɗanyi wa mutanen ƙauyen
Nasiha akan neman ilimin Addini, ta hanyar janyo musu ayoyi da hadisan manzon Allah
salallahu alaihi wassalam, be fito yace musu basu da ilimi ba, amma a cikin bayanin
da yake musu ya kawo musu misalin yadda mutum ze kawo raka'oin daya rasa idan yazo
bin jam'i, nan suka dinga gano irin tafka tafka da kwaɓar da suke yi.
Wani mutum yace "gaskiya Malam Yusufa munji daɗin wannan bayanin naka, danni harga
Allah na ƙaru da abubuwa da dama, danni wallahi na zata idan mutum yayi alwala in
yayi tusa indai ba tayi ƙara ba to bata karye ba"
Na kusa dashi yace "Nikuma wallahi na zata ko sujjada ka samu in ana salla shikenan
ka samu salla, dan Allah yakamata ka cigaba da yi mana wannan bayanin idan anyi
sallar Asuba ko kuma da daddare mudinga taruwa anan kana ƙara fahimtar damu
abubuwa"
Megari yace "hakane kam, Yusufa idan bamu takura maka ba, muna buƙatar hakan"
Yusuf yace "Ai babu batun takura ranka ya daɗe, mafi alkairin mutane shine wanda
yasan ilimi kuma ya sanar dashi"
Seda gari yayi haske tukuna suka watse, suna mamakin kurakuran da suke aikatawa a
sha'anin addininsu.
Yana shiga gidan yayi karo da wata budurwa tana koro dabbobi daga turke zasu fita
kiwo, tana ganin Yusuf tayi turus tana kallonsa, har Yusuf ze wuce tace masa "Ina
kwana"
Yusuf yace "Yawwa lafiya ƙalau sannunki"
Yai gaba abunsa, ƙura masa ido tayi harya wuce ya shige ɗakinsu, anan ta tabattar
da cewa shine mijin wannan farar matar me gashi.
Da sauri ta koma ɗakinsu, tana kiran "Hindu, Hindu"
Hindu dake sharar ɗaki tace "lafiya kikemin wannan kiran?"
Hanne tace "kinga mijin wannan farar matar nan ta jiya kuwa?"
"me yayi?" hindu ta tambaya
"innalillahi, wallahi ban taɓa ganin namiji me kyau kamarsa ba"
Hindu tace "har Lamiɗon rigarsu gwaggo?"
Hanne tace "wallahi harshi, taɓ bakiga kyau ba masha Allah, ban taɓa ganin namiji
me kyansa ba"
Hindu tace "bakiga matarsa bama, fara me kyau"
Hanne tace "dalla wannan da gani bata da mutunci, kinga kallon da tayi mana jiya
kamar taga kashi, da gani bata da mutunci"
Hindu tace "ke Hanne karkice haka, aikinga bata sanmu ba"
Hanne tace "ke dallacan Allah yasa in kuma ganinsa"
Yusuf ya shiga ɗaki ya tarar da Widad a zaune, ya kalleta yace "ina kwana?"
Kallonsa tayi kawai ba tace komai ba, Yusuf yace "Munyi magana da ɗan megari na
bashi kuɗi, zeje cikin gari ze siyo miki kayan tea da sauran abun buƙata"
Ita dai ba tace komai ba, sema lumshe idanunta da tayi.
"wai meke damunki ne kuma?"
"Bakomai"
"zakiyi wanka ne? Ina son zan fita"
Tace "kaje kawai, zanyi komai da kaina"
Yusuf yace "Aini tsoron fitarma nakeji, jiya da daddare ki tsoratani sosai, kar in
fitane kema kice zaki tafi"
Shiru tayi masa ta ƙara rufe idonta, "Widad" ya kira sunanta, a ɗan hasale tace
"meye ne?"
"Inaga bari in haƙura da fitar nan, bari inje inyiwa abokin tafiyar tawa magana se
in dawo"
"Nifa ban hanaka tafiya ba, ba inda zani jiyanma na tsorata ne mafarkin da nayi"
Yusuf yace "dagaske idan na fita bazaki tafi ki barni ba"?
Ɗagowa tayi tana kallon cikin ƙwayar idonsa, ta jinjina masa kai alamar eh, yayi
murmushi yace
"to bari inje in wanke mana kwanuka, in wanke miki banɗaki se in tafi, sena dawo,
in a kawo abun karyawa kiyi breakfast ɗinki kawai, base kin ragemin ba"
Yai maganar tare da miƙewa ya fice, ya kwashi kwanukan ya zuba ruwa, Hanne ce ta
hango Yusuf da kwanuka, ta taho da sauri tace "kawo in wanke maka"
Yusuf yace "A'a bakomai nagode, yanzu zan wanke in gama"
"dan Allah ka kawo, ai be kamata kayi wanke wanke da kanka ba, idan Baffa ya gani
ma ze iyayi mana faɗa"
Yusuf yace "kema 'yarsa ce ne?"
Hanne tace "eh nima' yarsa ce nida Hindu, muje wani ƙauyene suna, se jiya muka
dawo"
Yusuf yace "Allah sarki, Allah yayiwa rayuwar ku Albarka"
Cike da jin daɗi Hanne tace "Ameen" ta karɓi kwanukan, yace "in kin gama, seki
kai mata ɗakin"
Hanne tace "to" tana mamakin ace yana da mata amma shize wanke wanke, Yusuf ya
janyo ruwa a rijiya ya wanke banɗakinsu, yayi wanka ya fice.
Hanne ta gama wanke wanke, ta tafi ƙofar ɗakinsu Widad, ta tsaya tana sallama, ƙasa
ƙasa Hanne ta shiga ɗakin ta cewa Widad "ga kwanuka inji mijinki"
"Ajiye anan"Hanne ta ajiye, ta juya ta fita tana mamakin wannan irin nuna isa na
Widad.
Anwar ya gayarawa Daula jikinsa, ya canza masa kaya ya bashi Abinci da sirinji, ta
cikin robar dake hancin Daula, ya gyara ɗakin ya tattara kayansa marasa kyau ya
fita ze bayar akai gida su Nura su wanke.
Sufyan ne ya tinkari ɗakin da Alhaji Nasir yake, gaban sa se faɗuwa yake, ji yake
kamar kowa kallonsa yake a baranda ya haɗu da Anwar, suka gaisa da Anwar, doctor
Sufyan yace "ina zaka haka Anwar? Kasan bama san ana barinsa shi kaɗai"
Anwar yace "yanzu zan koma, kayan nan na fito dashi zan kaiwa direba ya kai gida a
wanke"
Sufyan yace "to masha Allah, ga wasu magunguna na rubuta, idan ka kai kayan wankin
seka biya pharmacy ka siyo"
Suna nan tsaye aka fito da wani mutum ya mutu an turo shi a gado za'a fita dashi.
Anwar yace "doctor, dan Allah nasan lafiyar Alhaji ba a hannunka take ba tana
hannun Allah, dan Allah ka ƙara ƙoƙari, bawan Allah nan kullum jikinsa ƙara
rikicewa yake"
Sufyan ya dafa kafaɗar Anwar yace "karka damu Anwar, kamar yadda ka faɗa sauƙi na
Allah ne, Amma muna fatan Allah ya bawa Daula lafiya"
Anwar yace "shikenan nagode, bari inje"
Anwar yayi gaba, Sufyan ya tsaya a gurin yayi shiru, sannan yayi gaba jikinsa gaba
ɗaya babu ƙwari, a haka ya taka har yaje ƙofar ɗakin da Daula yake, yasa hannu ya
murɗa ƙofar ya shiga, sedai me yana shiga yaga wayam ba kowa akan gadon, ya ƙarasa
gaban gadon da sauri ya yaye bargon kai, ba Daula babu alamarsa, ya buɗe banɗaki ya
duba nan ma kowa, ya duba bayan ƙofa zuwa ƙarƙashin gado, amma be ganshi ba ƙarewa
har fridge ya buɗe amma bega alamar Daula ba.
Cire gilashin dake idonsa yayi yana zazzare ido, yana waige waige kamar Ɓarawo
Fitowa yayi da sauri daga ɗakin, aikuwa yayi karo da Anwar, Anwar yace "doctor
Sufyan ya dai? Naganka a haka? Na kawo maganin"
Doctor Sufyan yace "Amm... Mmm.. Nace ina Mara lafiyar ne?"
Anwar yace "kamarya? Yana ciki mana"
Sufyan yace "Baya nan na duba ko ina ban ganshi ba"
Anwar yace "kamar yaya? Ya za'ayi in fita barshi, daga zuwa siyo magani kace baka
gasnhi ba? Sekace wata eiga, mutumin da komai sena masa ta yaya ze iya fita?"
Sufyan yace "Nima abunda ya bani mamaki kenan, na duba ko'ina ban ganshi ba, har
banɗaki na duba baya nan"
Kallon tuhuma Anwar yayiwa Sufyan yace "Amma gaskiya ni ina tantama, babu wanda ya
shiga ɗakin bayan fita ta sekai"
Sufyan yace "Wallahi ban tarar dashi a ɗakin nan ba kaji na rantse"
Anwar ya ɗaga waya ya kira 'yan sanda, ya kira ya sanar da Bulama abunda ake ciki.
Widad ta gaji da zaman ɗaki, ta fito tsakar gida ƙarƙashin bishiya ta zauna, yaron
gurin hansai ne da baze wuce shekaru uku ba, yake ta kallon Widad yana leƙa gashin
kanta, murmushi Widad tayi tace "Naga kana son gashin nan, zo in baka ka taɓa"
Tsayawa yaron yayi yana murmushi, a hankali ya ƙaraso inda Widad take, ta riƙe
hannunsa ta ɗora akan gashinta, nan yaron ya shiga wasa da gashin nata yana dariya.
Hansai data fito taga abunda yake faruwa, tunda suka dawo suka tarar dasu Widad, ko
sannu bata taɓa haɗasu ba, ko murmurewa bata taɓa ganin tayi ba, Hausawa sukace me
ɗa wawa se taji daɗin yadda Widad take wasa da ɗan nata.
Hindu data fito tsakar gidanma, tana ganin haka ta ƙaraso tace "kai Sani sakar mata
gashi mana, ya takura miki ko?"
Widad tace "A'a nibe takura min ba, naga yana son kamawa ne shiyasa nace yazo ya
taɓa"
Hindu tace "Abunka daba'a saba ganiba shiyasa yazo ya saki gaba"
Widad tayi murmushi har haƙoranta suka fito tace "gashin ne ba'a saba gani ba,
bayan duk kanku ba'a aske yake ba"
Hindu tace "to ai ganin gashi me yawan naki dai basu saba gani ba, kuma dan Allah
ke 'yar ƙasar nan ce?"
Hansai dake ƙoƙarin haɗa wuta tace "wallahi nima abunda ke bani mamaki kenan, dan
Allah' yar ƙasar nan ce ke?"
Widad tace "taɓ 'yar ƙasar nan ceni mana, banyi kama da Hausawa bane"
Hindu tace "gaskiya ko bahaushiya ce ke, to sedai ko ruwa biyu"
Widad tace "ruwa biyu kamar yaya?"
Hansai tace "kamar ace mamanki bahaushiya mahaifinki wani yaren, ko mahaifinki
bahaushe mamanki wata yaren"
Widad ta ɗanyi jim sannan ta murmusa tace "dukkansu Hausawa ne, mazauna Kano"
Hindu tace "kano, dan Allah a kano kike?"
Widad tace "kin taɓa zuwa ne?"
"Ni waze kaini kano? Muna dai jin labarin kano, ance garin yana da kyau sosai, kuma
mutanen kano suna da kirki"
Widad tace "Insha Allah wataran zaki kano, ba laifi kam kano tana da kyau, nikam ya
sunanki ne"
Hindu tace "sunana Hindu"
Widad tace "Masha Allah, Hindatu"
Gwaggo ce ta fito hannunta ɗauke da ƙwarya da rariya tace "Amarya yau hira ake
haka? Badan da kaina naga kina surutu ba, da zance bake bace"
Widad tace "Wallahi gwaggo bani da surutu, amma ina magana sosai ai"
Hanne kuwa dake bakin rijiya tana wanke wanke ko kulasu ba tayi ba.
Itakuwa Hari fitowa tayi da gero, ta zuba a turmi ta fara daka tana habaice
habaicenta, basu kulata ba suka cigaba da hira.
Gwaggo tace "Ai Amarya mutum rahama ne, ko yaya idan kina ɗan fitowa ana hira zaki
rage kaɗaici, amma ace ke mijinki kawai kika sani"
Widad tace "Mama kenan, to ai shikaɗai ɗin kawai na sani, kawo in tayaki tankaɗawa"
Gwaggo tace "A'a kar in takura miki"
Widad tace "ni baki takuramin ba"
Ta ɗaga kai ta kalli Hari tace "dan Allah malama kiyi ɗaya, ko dakan kokuma waƙe
waƙen haba dan Allah, da wanne za muji ƙarar daka ko kuma na wannan hayaniyar da
kike yi"
Hari tace "Allah ya haɗani da Baƙar Jaraba ni Hari jikar Hama, na kulaki ne ko
tsabar jan bala'i ne? Wallahi ki fita a sabgata, tun kafin in miki wulaƙanci"
Widad ta sunkuyar da kai tana dariya, dama abunda take so kenan, ta zungurota taita
masifa, dan ita yanzu ta maida Hari comedy.
Widad ta karɓi tankaɗe kamar abun Arziki, ta riƙe rariyar da hannu ɗaya, ta ɗaga
hannun sama tana girgiza rariyar, garin kuwa se kama gabansa yake, dan haka iska ta
dinga kwashe shi, gwaggo kuma takasa yi mata magana saboda kawaici.
Yusuf ne yayi sallama hannunsa ɗauke da ledar viva, hango Widad yayi tayi buɗu buɗu
a cikin gari, gashi a ƙarƙashin bishiya take tankaɗen, iska duk ta kwashe garin.
Hanne na ganinsa ta wani fara mutsu mutsu da gyare2, tace "sannu da zuwa" Yusuf be
kula da ita baDa sauri ya ƙarasa inda Widad take yace 'Subhanallah Widad waye ya
saki wannan aikin "
Gwaggo tace "seda nace base tayi ba, tace in bata tayi"
Yusuf yace "wa yace ki bata, Mama bata iya bafa, kalli yadda tayi miki Asarar gari"
Murmushi gwaggo tayi, ta ɗauke kai daga kallonsu.
Widad tace "Na iya, ba gashi inayi ba, kai komai nayi seka gwalemin"
Yusuf yace "Ni na isa kiyi abu in gwale, amma kalli yadda kika ɓata gurin"
"Ni dai ka ƙyaleni in cigaba da aikina"
Yace "Naji, amma kawo in nuna miki yadda akeyi"
"A'a ni naga yadda akeyi ai, shine nima nake gwadawa"
Gwaggo kam gaba ɗaya kunya suka bata, dan haka ta miƙe ta bar musu gurin gaba ɗaya.
Yusuf yayi ƙasa da murya yace "dan Allah kiyi haƙuri ki kawo, wallahi baki iya ba
kawaici kawai tayi miki, amma wannan aika aika kike mata"
Sakar masa rariyar tayi, ya shiga gwada mata yadda ake yi, kawai ta kwashe da
dariya, ya kalle ta yace "lafiya kuwa?"
"A'a gani nayi ka iya sosai"
Ba ƙaramin kyau tayi ba dariyar da tayi, karon farko da tayi fara'a haka sosai ya
gani.
Kawai ya shagala da kallonta, ya ɗanyi murmushi ya cigaba da nuna mata yadda akeyi.
Hanne kuwa ji tayi ta tsani Widad gaba ɗaya, ko ganinta bata son yi ganin Yadda
Yusuf ke wani ƙure Widad da ido se taji kamar tayi kuka.
Megari ne yayi sallama ya shigo, yace "Malam Yusuf ka dawo kenan?"
Yusuf yace "eh Baba na dawo" Megari yana jin daɗin yadda Yusuf yake girmamashi
Yace "ya kasuwar kuwa?"
Yusuf yace "Alhamdilillah, naje harna dawo"
Megari yace "to masha Allah"
Widad kam ko kallon Megari ba tayi ba, balle tace masa wani abu, Megari ya ƙaraso
inda take yace "wannan 'ya tawa akwai miskilanci, tunda ba zata kula baban nata ba,
toga tsaraba na kawo mata, Allah ya ƙara ƙarfin jiki"
Ya ajiye mata dabino rabin kwano a gabanta, Yusuf yace "Mungode sosai Baba, Allah
yasaka da alkhairi"
Megari yace "A' a bakomai Yusufa, Allah ne ya haɗa mu zama tare, kuma naji harga
Allah kun kwantamin, Allah yayi muku Albarka"
Yusuf yace "Ameen"
Yusuf ya ɗau ledae daya shigo da ita, da wadda Megari ya bawa Widad, ya shige gaba
Widad na binsa a baya, gwaggo tace "Amarya karɓi kayan hannun nasa mana"
Widad tace "Ai ze iya ɗauka, ni yamin nauyi"
Gwaggo ta jinjinawa gaɓunta irinta Widad, akwai buƙatar a zaunar da ita ayi mata
takara akan zama da miji.
Suna shiga ɗaki Yusuf yace "yanzu uwaɗakina abaki abu amma ki kasa cewa kin gode,
baze ji daɗi ba fa"
Maimakon tayi magana, sema sosa kai data hauyi tana wasa da gashin kanta ta wuce
inda katifarta take, Yusuf ya bita da ido, wato se yanzu yake ganin tsabar
yarintar Widad, wato a da ɗinma tsabar izzarta da jin kaine yake sa ka ganta kamar
wata babba amma kwanan nan wautar da Widad keyi wasu lokutan, suke ƙara fito da
yarintar ta, sedai har yanzu wannan izzar da jin kan basu barta ba.
Yusuf yace yakamata kidinga gaida Megari, kinga yana mana ƙoƙari shima kinji
gimbiyata.Aikuwa nan da nan ta haɗa rai , Yusuf yace "meye kuma na haɗe ran?"
"Ai kafini sanin abunda ka faɗa, kuma kasan bana so"
Hindu ce tayi sallama a ɗakin nasu Yusuf ya amsa, ta shigo da kwano ta durƙusa ta
gaida Yusuf, Yusuf ya amsa mata, tace "Amarya gashi inji Gwaggo"
Widad tace "to Nagode"
Hindu ta juya ta fita, Widad ta buɗe kaanon tace "yau kuma meye wannan?"
Yusuf ya karɓa ya duba yace "kwaɗon rama ne"
Ta kalle shi tace "meke nan?"
Yusuf yace "kici kiji mana"
Tashi tayi taje ta wanke hannu tazo ta zauna, ta ɗiba takai bakinta, yatsine fuska
tayi tana taunawa da ƙyar, kamar tayi kuka tace"Wai su mutanen nan basa girka
abunda akeci ne?"
Yusuf kamar ya tintsire da dariya yace "wannan me ake dashi in ba ciba"
"to naji tsami, ga gishiri da kamar sugar"
Yusuf yace "kyaji dashi, nidai bari inje inyi salla" ya miƙe ya fita.
Abu kamar wasa, sa 'yan sanda suka tashi suka kama Anwar da Doctor Sufyan, wai za'
ayi bincike a kansu akan ɓatan Alhaji Nasir Daula, aka kama wasu daga ma'aikatan
Asibitin sannan aka rufe Asibitin. Tun ana ɓoye ɓoye har abu ya fara bayyana cewar
wai Alhaji Nasir Daula ya ɓata a Asibiti.
Hankalin Hajiya Halima ya tashi, jin an kama mata ɗa an kai shi police station,
gidan Bulama ta shirya ta tafi bagazan bagazan ta ɗau mota ta fice.
Tana fita Isa yace "Matsiyaciyar mata, da yake ɗanta aka kama kalli yadda ta fita
afujajan, amma mijinta na kwance a Asibiti ko a jikinta, ni ɗanne ma yake bani
tausayi da nace Allah yasa baza'a sake shi ba"
Murtalah yace "ai Matsiyaciya ɗaya kenan, kalli yadda ta saida fiye da rabin
motocin gidan nan, kalli Yadda tabi ta rage mana albashi dan Azzaluma ce, Allah
sarki Yusuf da uwaɗakinsa, ko a wane hali suke oho?"
Nura yace "Ai wallahi se yanzu nake ganin ranar yarinyar nan, duk wulaƙancinta
haƙƙinmu baya ciwo koda megida baya nan, ubangiji Allah ya bayyana Alhaji Daula"
Isa yace "Ameen dai abubuwa se faruwa suke kamar almara wai anemi mutum a gadon
Asibiti a rasa, Allah ya kyauta"
Suka haɗa baki sukace "Ameen"
Yusuf ya dawo daga salla, yaga kwanon rama a rufe, yace "kaddai baki ci ba"?
Dabinonta take ci tace "ni bazan iya cin wannan Abunba"
Yana duba kwanon yaga ta tattare ƙuli ƙulin, da tumatir da Albasar da gurjin dake
kai ta cinye abunta, ta bar gayan ramar duk ta lashe ƙulin jiki.
Murmushi yayi bece komai ba, ya ci ramar nan a haka, se jikinta yayi sanyi taga
bata kyauta ba.
"Gimbiyata, ga wake nan na siyo mana a kasuwa yau da yamma za'a kawo kayan tea
harda bredi"
Da sauri ta kalle shi tace "dan Allah dagaske hadda bredi?"
"ya zan miki ƙarya, inje ki hukunta ni, dagaske nake"
"Yau zanci bredi"
Yusuf yace "hadda shayi makuwa, bari inje in watsa ruwa na gaji sosai"
Widad tace "to, ba zaka ci dabinon ba?"
"bari in wanka tukuna"
Ya tashi ya ɗau bokiti ya fita, seda taga ta kassara dabinon nan, ta masa cin ƙoshi
sannan ta ajiyewa Yusuf sauran.
Ta miƙe ta tattare ƙwallyen ta tafi taje ta zubar, gwaggo na ganin Widad tace
"Amarya zo kinji yarinyar kirki"
Widad ta ƙarasa inda take, gwaggo tace "Amarya, daga yanzu idan mijinki ya dawo in
yazo da kaya duk abunda kike ki tashi ki karɓi kayan hannunsa kinji?"
Widad a ranta tace 'wai nan duk zatonsu wani Auren kirki mukayi?'
A fili tace "To Mama zan dinga yi, amma gaskiya banda kaya me nauyi"
Gwaggo tayi murmushi tace "dama bance dame nauyi ba, amma ki dinga kula dashi
sosai, ko so kike yayi miki amarya?"
Widad dariya kawai tayi tace "Mama kenan, to in yayi meye a ciki, nidai fatana mu
koma gida"
Gwaggo tace "hakane amma yakamata kidinga nuna kishi akansa, zeji daɗi ko Auren
dolene kukayi?"
Ganin kamar Widad bata son zancen ne, yasa Widad tace "jeki abunki ɗiyata"
Widad ta juya ta tafi ɗaki, tana zuwa ta tarar Yusuf ya fito daga wankan, yana
tsaye da gajeren wando a jikinsa yana goge ruwan wankan jikinsa, wasu irin dogayen
gashi ne a jikin Yusuf, taga yayi mata wani irin girma da kwarjini.
A ɗan gigice tace "Yoseef meye haka?"
Da sauri ya waigo ya kalleta yace "meyafaru?"
"meyasa zaka shigomin ɗaki a haka? Kalleka fa tsirara"
Yusuf ya kalli kansa yace "Niba tsirara nake ba"
"to meye haka, naga a can banɗakin kake sa kayanka"
Yusuf yace "Ramawa nakeyi, Allah ya bani haƙuri in dai a haka tsirara nake, toke
ban san a ya kike yawo ba"
Tsaki tayi ta shige can lungun ɗaki, ta juya masa baya ya juyo ya kalleta, yayi
murmushi ya gama tsane jikinsa, ya zura riga, ya ɗakko man shafawa yazo kusa da ita
yace
"dan Allah ki tayani shafawa a bayana mana"
"Allah ya kiyaye, ni ka tashi daga kusa dani" ƙememe taƙi kallonsa.
Yusuf yace "kalli kiga"
Rintse ido ta sake yi tace "ni bazan Kalleka ba, seka sa kaya wallahi ko inyi ihu
da ƙarfi"
"Aina saka kayan"
A hankali ta buɗe idonta tana kallonsa, Wani irin kallo yake mata, wanda ta kasa
gane ma'anar kallon da yake mata.
Zamewa yayi ya kwanta akan cinyarta, yace "Wash na gaji bayana ciwo yake kamar zan
ɓalle"
Itadai kamar Yusuf ya ɗaureta yau, ta kasa magana sam balle ta motsa, hannunta ya
kama yana ta murzawa a hankali, har bacci ya ɗaukeshi.
Har yanzu hannunsa yana cikin nata, Ƙura masa ido Widad tayi, gaba ɗaya Yusuf
tausayi yake bata mussman idan ta tuna beji ba be gani ba tsautsayi ya ritsa dashi,
se wahala yake faman sha, kuma be taɓa nuna mata ya gaza ba.
Riƙe hannunsa ta sake yi, ta toshe bakinta tana kuka, hawayen tausayinsu ya kamata.
Yusuf da bacci ya ɗauke shi, ya buɗe idonsa jin saukar hawayenta a fuskarsa, a
gigice ya miƙe zaune yace "subhanallah meyafaru? Nine me nayi miki"?
Bata iya bashi amsa ba se kuka data cigaba dayi, Yusuf yace
"yi haƙuri na ɗagaki, tunda bakyaso bazan sake kwanciya a jikinki ba, yi haƙuri"
Ta lura baya son yaga tana kuka, dan haka ta basar dan karya gane acikin damuwa
take yasa tace "Kuma idan muka koma gida sena gayawa Daddy taɓani ka dingayi"
Yusuf yace "Yi haƙuri bazan sake ba, goge hawayenki bazan sake ba insha Allah, bari
in sauka ma daga kan katifar"
"A'a ka kwanta anan, amma idan ka sake taɓani se nayi kuka, kuma Daddy zan gayawa
idan muka koma gida"
"To shikenan naji"
Ya kwanta ya juya mata baya, murmushi ta dingayi ta miƙe ta tsallake shi tayi waje.
Alhaji Munir yace "Impossible, ta yaya Alhaji Nasir ze ɓata a gadon Asibiti, sekace
ɓatan rigar sawa"
Alhaji Haruna yace "Abun da mamaki, a yadda yake dai be isa ya gudu da ƙafafunsa ba
akwai wata a ƙasa"
Alhaji Munir yace "tabbas akwai lauje cikin naɗi, inma dai akwai wanda yake gefe
yake mana manaƙisa, amma kowaye idan muka tono shi abun baze masa da daɗi ba"
Babu ko sallama Hajiya Halima ta shiga Falon Hajiya Sarah, a fusace ta kalli Sarah
tace "ina megidan nan yake?"
Hajiya Sarah tace "lafiya kuwa, maman Anwar?"
"bani da lokacin baki wannan amsar, kije ki gaya masa ina son ganinsa"
Bulama yace "Ai gani nan ina kusa"
Hajiya Halima ta kalleshi tace "da sanin ka aka kama min ɗana?"
Bulama yace "haka labari yazomin an kama shi"
"to ba labari bane ba, an kama min ɗana, to wallahi baze yuwu ba, daga abun Arziki
seya koma na tsiya, daga yayi jinyarsa an sace shi a Asibiti se'a kamamin yaro
akanme?"
Bulama yace "yanzu sace mijin naki be dameki ba?"
"Dalla karka gayamin maganar banza ko ka rainamin hankali mana, kai sace shin
damunka yayi?"
"Yaya za'a sacemin Aminina ɗan uwana, sannan kizo kina tayarmin da hankali akan an
kama ɗanki? Ki bar doka tayi aikinta, in sunga bashi da laifi zasu sake shi"
"dokar banza dokar wofi, ni zaka gayawa doka, doka nawa kayi amfani da kuɗi kayi
fatali da ita a ƙasar nan? Ina son kayi Amfani da wannan damar taka da ikon kayi
fatali da wannan dokar kasa a sakarmin ɗana, in bahaka ba you know what am capable
of doing"
Godiya me tarin yawa Fans ina godiya 😍 😍 😍 😍 😍 😍
Domin gyara, sharhi ko shawara Ayshercool 07063065680
_*AƘIDATA*_
PERFECT WRITERS ASSOCIATION
(WE AIN'T PERFECT BUT WE ARE ALWAYS TRYING OUR BEST, TO MOTIVATE AND ENTERTAIN OUR
READERS)
https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/
*Story and written by*
_*AISHA HUMAIRA _(Daddy's girl)*_
The experience writer of *ABDUL JALAL** WATA KISSAR.... (SAI MATA) *And now *AƘIDA
TA *
I dedicated this book to my Mum (Malama Nafisat Adam Muhammad) i love you mum
Haƙƙin Mallaka ⚠ : Littafin nan mallaki nane, tun daga sunan labarin zuwa abunda ya
ƙunsa, ban yadda wani ko wata ya sauyamin ko yin Amfani da wani ɓangare na labarin
ba ba tare da izinina ba, Nagode
https://www.wattpad.com/user/Ayshercool7724?
utm_source=android&utm_medium=link&utm_campaign=invitefriends
NOT EDITED
ELEGANT ONLINE WRITER'S
PART1 Page 38_39
Shi kansa Saleh abun ya ɗaure masa kai, ta yaya za'a je har Asibiti a sace mara
lafiya, kuma bayan da jam'ian tsaro a cikin Asibitin da suke tsaron lafiyarsa, koda
yake ba abun mamaki bane a haɗa baki dasu a sace shin, saboda da yawa mutanen yanzu
suna iya yin komai saboda kuɗi.
Maman Nurat ce ta shigo ɗakinta, ta tarar da Nurat tana kan system tana danne
danne, ta ɗago ta kalli Mahaifiyarta tace "Mummy lafiya kuwa?"
Mummy tace "Mhmm, wani labari naji"
Nurat tace "labarin me?"
"wai an nemi Alhaji Daula an rasa a Asibiti, yanzu haka an kama Shugaban Asibitin
doctor Sufyan da kuma Anwar"
Zare farin glashin idonta Nurat tayi tace "What are serious Mum?"
"did I ever lie to you?"
Cikin kaɗuwa Nurat ta girgiza kai tace "Na shiga uku da wannan masifa, daga wannan
se wannan ana ƙoƙarin a kashe wannan amma se waccan ta faru, an sace masa 'ya har
yanzu ba wanda yasan inda suke, yana kwance yana fama da jinya an bishi gadon
Asibiti an sace shi, innalillahi wa inna ialaihi raji'un, Mummy me Anwar yayi aka
kama shi to? "
Mummy tace " ina zan sani, ance dai har dashi a cikin suspect "
Nurat tace" idan harda sa hannun Yaya Anwar a ɓatan baban Widad, to tabbas beyi
hakan dan cutar dashi ba, akwai dalili yakamata in ganshi "
Zare ido Mummy tayi tace " kiga wa? Ba dani ba Wallahi idan kika sake kika fita
duk abunda yayi miki ke kika siya, na gaya miki babu ruwanki ki koma gefe ki taya
su da Addu'a yafi "
Shiru Nurat tayi bata kuma cewa komai ba, Mummy ta gama mitarta ta tashi ta fita,
ita kuwa Nurat ta shiga tunanin yadda zata yi ta fita.
Yanzu duk lokacin da aka idar da sallar Asuba, se Yusuf ya tsaya sunyi karatu a
masallaci, aikuwa gasu da son karatun babu girman kai a lamarin su, dan haka yake
jin daɗin koyar dasu, kuma ya basu damar yi masa tambayoyi, wasu tambayoyin idan
kajisu sam bazaka ce musulmi ne ba, saboda tsagwaron Jahilci, Yusuf baya kyararsu
ko hantararsu, haka yake amsa musu. Akwai wanda yake tambayar Yusuf bayan an watse
daga gurin karatun, wai shi ya zata in mutum ya kwanta da iyalinsa ba'a wanka se
ranar Juma'a, Yusuf yayi masa bayani dalla dalla, kuma ya ƙudurce babu batun kunya,
shine maudu'in daze musu gobe in Allah ya kai rai a gurin karatu "
Ya koma gida ya tarar da hakimar tanata kwasar baccinta, ya nemi guri shima ya ɗan
kwanta, nannauyan bacci ne ya ɗauke shi, can cikin baccin nasa ya jiyo ihun Widad a
tsakar gida, aikuwa a gigice ya tashi ya fita, wata kazar harice Widad tazo wucewa
ta zata 'ya' yanta zata taɓa mata, dan haka ta fara bin Widad tana kai baki zata
cije ta, shine take ta wannan ihun tana zagaye, ita kuma kazar na cigaba da binta.
Hari na kallonta, ta dinga tintsira dariya, a gigice Yusuf ya fito, yazo da
sauri ya kori kazar ya kalli Widad yace "haba my queen, gaskiya kin ban kunya kaza
ce fa kawai "
Widad tace "to ba cizona take son tayi ba, kuma wlh idan ta sake bina sena kamata
na tura ta a cikin wutar can ta ƙone kowa ya huta"
Hari tace "kan bala'i, kazar tawa zaki saka a murhu? Aikuwa dana miki rashin
mutunci kuma wallahi da sekin biyani"
Yusuf yace "yi haƙuri bama iyawa zata yi ba, tana faɗane kawai yanzun ma tanawa
kazar ihu, ta ina zata iya kamawa balle tasa a murhu?"
Widad tai farat tace "to sena buga mata wannan icen ta mutu, ko in Takata da ƙafata
harta mutu, garama kija mata kunne"
"Kazar zan jawa kunne ko kuma wa?"
"Eh ita kazar"
"ta yaya zanjawa kaza kunne? Ko nima kazarce?"
Widad tace "to waya sani"
Gwaggo dake banɗaki kam dariyarta ta sha, dan yanzu sun saba kusan kullum da
rigimar Widad da Hari suke karyawa.
Yusuf da wanine yace masa Widad ta iya neman magana cewa ze ƙaryane, amma yanzu
yake ganin zahiri da ikon Allah, haka yaita bawa Hari haƙuri sannan yasa Widad a
gaba zuwa ɗaki.
Ya ƙura mata ido sannan yace "da wanine ya cemin kin iya rikici haka cewa zanyi an
miki ƙarya, amma gashi da idona ina ganin ikon Allah, kullum sekin nemi magana"
"da da bana yi ancemin mahaukaciya bana son mutane, yanzu kuma kace na fiye rigima"
Yusuf yace "yi haƙuri, amma adinga ragewa kinji queen, waini ya'akayi kika sake da
mutan gidan nan, abun ya bani mamaki fa"
"Basu san ni wace ba, dan haka bana tunanin zasu cutar dani, dukda suma bawai yarda
dasu nayi ba, amma inajin daɗin yadda suke kyautata min ne"
Yusuf yace "to nifa, an yarda dani?"
Kallon up and down Tayi masa tace "tukuna dai"
"shikenan ni na yadda dake ai, zoki zauna kusa dani muyi hira"
"Baza'ayi hirar ba, idan nazo kusa da kai taɓani zakayi"
Dariya Yusuf yayi, yace "taɓakinne bakya so inyi?"
"Eh bana so, kai kuma sekace dole seka taɓani"
"ba laifina bane, laifin zuciyata ne Gimbiyata"
"kai ka sani kai da zuciyar taka"
Tai maganar tare da kwanciya ta koma bacci, a hankali Yusuf ya dawo kusa da ita ya
kwanta, tana yunƙurin juyi akan katifarta taji mutum, ta leƙo kanta daga bargo taga
Yusuf.
"wai dan Allah meyasa kake min hakane, tasarmin daga kan katifa"
"Niba taɓaki zanyi ba, ina son inyi bacci ne zuwa ƙarfe goma in fita, Amma cinnaku
se cizona suke wuyana ciwo yake saboda kwanciyar ƙasa, haba uwa ɗakina, atemaka a
tausayamin mana"
Tura baki tayi tace "to matsa ni in fita tsakar gida in baka guri seka kwanta"
Zaro ido yayi yace "haka kawai inje ki fita ki jawomin magana, ki fita neman
rigima, a'a yi zamanki anan"
"toni gaskiya bazan kwanta a kusa da kai ba"
Banza yayi mata ya gyara kwanciyarsa, tare da lumshe ido, yunƙurawa tayi zata fice
ya fizgota ya zaunar da ita yace "yi haƙuri, bari in tashi in bar miki katifar,
base kin fita kin janyomin magana ba, har mamaki nake yadda kika koyo rigima"
"nifa ba magana zan ɗakko ba, ni kawai zomaye zan kalla"
"Idan kika tsokani Baba Hari, ba zan baki bredin ba"
"aikuwa kuka zanyi in ka hanani" ta miƙe tayi waje abunta.
Hankalin Hajiya Halima ya kasa kwanciya sam, saboda rufe mata ɗa da'akayi, Amal ma
duk abun ya dametta, suna ta zaryar station amma abu ya gagara, Yanzu ma Amal ce ta
tafi ɗakin Ramlah, ta tarar da ita a zaune tana waya, da Fahad. Amal ta samu guri
ta zauna, ta jira ta kammala sannan ta kalli Amal tace "lafiya kuwa? Kin shigomin
ɗaki kin sani a gaba kina ta kallona"
Amal tace "Ramlah waike baki damu bane dan Allah, kwanan Yayanmu Uku a hannun 'yan
sanda, Mummy se zarya take anƙi sakinsa, amma kin shigo ɗaki wayarki kawai kike"
"to Amal haukacewa kike so kiga nayi ko yaya? Shima Allah ya ƙara masa waishi ga me
mutunci ya zauna yana jiyyar uban da ya tsinta a rana, kinga hakan ze zamo masa
darasi gobe baya ƙara taimakao ba"
Amal tace "bekamata ki faɗi haka ba Ramlah? Ta wani fannin in aka duba abunda Yaya
yayi beyi laifi ba, ko so kike duniya ta farga da halin da'ake ciki? Ace bashi da
lafiya amma babu wanda ya damu a cikinmu? Ni wallahi abun ya fara damuna koba komai
Yaya Anwar ɗan uwanmu ne"
Ramlah tayi ajiyar zuciya tace "kuma fa hakane, ni kaina ta wani fannin inajin ba
daɗi rufe shin da'akayi, amma me zan iya akai wanda Mummy ta kasa"?
Amal tace "Fahad zakiyiwa magana, dan Mummy taje har gidansu ta gayawa mahaifinsa
amma yaƙi ɗaukar abun da mahimmanci, ke tunda kuna ɗasawa dashi kisa yayiwa
mahaifinsa magana yasa baki a saki Yayanmu"
Ramlah tace "Anya kuwa? Fahad fa akwai lafiyar kafiya mussman yanzu da suke takun
saƙa da yaya"
Amal ta taɓe baki tace "ashema ba son naki yake ba tsakani da Allah tunda ze iya
barinki cikin damuwa, Allah wadaran wannan soyayyar"
"Amal ni kike cewa Allah wadaran?"
"Na faɗa Allah ya wadaranta, dama wannan banzan Fahad ɗin me fuskar jakai kansa
kawai ya sani, in ba soyayyar ƙarya ba, yayiwa mahaifinsa magana yasa baki a saki
ɗan uwanmu mana, naga shima dai ɗan uwansa ne"
Ramlah tace "Aikuwa Amal i will prove you wrong, zan nuna miki soyayyar mu ta
gaskiya ce"
Amal tace "in gani ƙas, ancewa kare ana biki a gidansu, ƙaryar banza burodi a lefe,
ina amfanin soyayyar da baka da alfarma a gun wanda kake so"
Ta tashi ta bar mata ɗakin, tana ci gaba da mita da tsaki.
Nurat ta shirya cikin doguwar riga, tayi rolling ta ɗau wayarta da jakarta ta fito,
ta leƙa ɗakin mamanta taga tana bacci, ta taho cikim sanɗa ta fito harabar gidan,
da sauri sauri ta tafi bakin gate tace "zoka buɗemin ƙofa zan fita"
Me gadi ya kalleta yace "ina zaki?"
"ka aikeni ne? Ka buɗemin zan fita"
Ya ɗan sosa kai yace "Madam, me gidan nan yace kar in kuskura in sake bari ki fita,
muddin bashi ya bada umarnin hakan ba"
A ɗan hasale tace "ka buɗemin ba nisa zanyi ba, yanzu zan dawo"
Girgiza mata kai yayi yace "dan Allah kiyi haƙuri, wallahi zan fuskanci fushinsa
muddin na bari kika fita"
Juya tayi cikin gida, jiki ba ƙwari tana tunanin meye mafita, can wani abu ya faɗo
mata, ta miƙe ta fito tace masa "kazo Mummy na kiranka"
Ya miƙe ya biyo bayan Nurat, yana gaba tana binsa a baya, yana shiga falonsu cikin
sanɗa ta dawo baya a hankali, tayi waje tana zuwa tasa mukulli ta buɗe gate ɗin
tayi waje abunta.
Gidansu Widad ta tafi, tana zuwa tayi sa'a ta tarar da Amal a babban falo tana
karyawa, Amal na ganinta ta buɗe baki tace "Nurat yau kece a gidanmu haka? Abun
mamaki"
Nurat tayi murmushi tace "meye na mamakin kuma?"
Amal tace "ni dai nasan koda zaki zo gidan nan saboda Widad zaki zo, kuma duk garin
nan ba wanda be san anyi kidnapping ɗinsu ba, kuma dai amma baban ku besan kinzo
ba"
Nurat tayi murmushi tace "tabbas nasan an sace Widad da ɗan uwanta, sedai...
Amal tace " ɗan uwanta kuma? Direbanta dai"
Nurat tace "direba kuma kamar yaya direba?"
Amal tace "kamar yadda na gaya miki, ita da Yusuf ne aka ɗauke su, Yusuf kuma
direbanta ne"
Nurat tayi shiru, sannan tace "Amma meye alaƙar dake tsakaninta da Yusuf?"
Amal tace "Allah kaɗai yasani, Wallahi Nurat ina cikin matuƙar damuwa ɓatn nan
nasu, mussman Yusuf idan nace zan nuna damuwar da nake ciki ma babu me saurarata a
gidan nan, Amma duk rashin yardar Widad ta yadda da Yusuf fiye da tunaninki"
"Amma Amal mezesa matashi kamar Yusuf ya ɓige da aikin direba a gidan masu kuɗi?"
Amal tace "bake ba ni kaina ina wannan tambayar, amma kin san da wani aikin
gwamnatin gara aiki a gida kamar wannan, dan ba Widad ba hatta me gidan nan ya
yadda dashi sosai, Amma a yadda Yusuf ya haɗu kam, bekamata ace aikin direba yake
ba, nayi masa zancen ya nemi wani aikin, amma yaƙi yarda, yafi ƙaunar kasancewa a
ƙarƙashin wannan uwar izzar, tana hantararsa tana komai amma baya ganin laifinta"
Shiru Nurat tayi kamar ba zata ce komai ba, can tayi ajiyar zuciya tace "Amal ya
batun Yaya Anwar kuwa?"
Amal tace "hamm, yana can Mummy tana ta fama anƙi sakinsa, wai har yanzu bincike
ake akai"
Nurat tace "wani station ɗinne?"
"Suna state CID shida Likitan"
Nurat tace "Allah ya fidda shi lafiya, Insha Allah zanje in ganshi"
Amal tace "kai amma kuwa mungode sosai Nurat"
Nurat tace "bakomai Amal, se anjima"
Yusuf yayi baccinsa ya tashi, ya buɗe jakarsa ya ɗakko kayan tea daya bada sautu
aka kawo masa, ya ɗora tea Widad tana tsakar gida suna hira da Hindu, da hansai.
Yayinda Hanne se wani gyatsine fuska take yi, bata kallon ko inda Widad take, Widad
data fita bata taɓa nuna tasan da halittar Hanne ba, abun da Hanne bata sani ba
shine, mutanen da suka damu da itama ba kowa take iya shiga sabgarsa ba, balle
wanda ya nuna be damu da ita ba.
Yusuf ne ya fito tsakar gida, yaje ɗakin megari suka sake gaisawa ya zauna suka
shiga hira.
Widad na zaune kusa da gwaggo, tana dama koko tana kallon yadda take yi, Widad tace
"Mama haɗa kokon nan ma ashe ba wahala, na iya haɗa custard shima zan iya wannan"
Hansai tace "meye kuma kostan?"
Widad tace "wani abune shima sha ake, kamar haka ake dama shi amma suna da ɗan
banbanci da wannan, Ai zaki ban watarna nima inyi ko?"
"taɓ za'a sha kwaɓa kuwa, yadda kike a sangarcen nan ba uwar da kika iya, mijinki
na fama wallahi, ba uwar da kika iya se zance"
Widad ta ɗaga ido ta kalli Hari tace "Mijinki ne yake fama da ƙazantarki ba nawa
ba, kuma karki ƙara cemin sangartacciya"
Gwaggo tace "yi haƙuri Amarya, ƙyaleta"
Gwaggo ta fara rabon koko, ana zuba na kofin megari Widad tasa hannu ta ɗauka tace
"wannan nake so, wannan kofin yafi kyau"
Gwaggo ta ɗanyi shiru, Hansai tace "Amarya kofin megari nefa"
Widad ta tura baki tace "toni ina son kofin, wannan nake so"
Gwaggo tace "Hindu, jeki ki duba ƙasan gadona a cikin kwanukan Hanne ki ɗakkon
sabon kofi irina Malam"
Hanne tace "kai gwaggo kofin Auren nawa za'a ɗakko?"
Gwaggo tace "eh kema ba Allah ne ya baki ba, a sai miki wani"
Haka aka ɗakko sabon kofin silva, se ƙyalli yake da murfinsa aka zubawa Widad koko
a ciki, Hanne ta dinga mita tana kumbura baki, ai Widad bata nuna tasan da zaman
Hanne a gurin ba.
Hanne na tsaka da masifar ne sega Yusuf ya fito daga ɗakin megari, ai nan da nan
Hanne ta nutsu ta fara murmushi, Yusuf ya harari Widad dan yaji duk abunda ya faru,
ita kuwa tayi kamar bata ganshi ba.
Hanne ta durƙusa ta gaida Yusuf, Yusuf ya ɗan saki fuska ya amsa mata, yazo ya
durƙusa ya gaida su gwaggo, duk faɗan da Hari keyi da Widad, tana matuƙar girmama
Yusuf, dan suna ɗasawa dashi.
Hanne tace "yau ba wanke wanke ne ka kawo ayi?"
Yusuf ya kalli inda Widad take, yaga ko a jikin ta, jujjuya kofin kokonta kawai
take.
Yusuf yace "A'a babu na wanke tun Asuba.
Gwaggo tace "kaine kake wanke wanken? "
Yusuf yayi murmushi yace "A'a Mama, wani lokacin ina rage mata aikine kawai"
Gwaggo ta kalli Widad tace "Anya Ɗiyata?"
Widad tace "Mena yi? Shine yake cewa zeyi fa, kuma idan nace zanyi se yace ban iya
ba"
Hanne tace "ka dinga barinsu, da safe se in haɗa in wanke, tunda bata iya ba"
Hansai tace "ikon Allah, toke Hanne dole ne sekin wanke musu kwanukan?"
Widad tace "Yoseef kaga sabon kofinmu, Mama ta bamu"
Yusuf yace "Ahh mama mungode sosai Allah yasaka da alkhairi"
Ya kalli Widad yace "let's go and have a breakfast"
Ta miƙe tayi gaba, suna zuwa ɗaki yace "sannu kinji"
Cikin rashin fahimta tace "aikin me nayi kakemin sannu?"
"yanzu memakon kice in sai miki kofin kina so, kawai seki sa rigima ke se'an baki?"
"ko zaka Ƙwace ka mayar ne?"
Yusuf yace "A'a ni bance ba, na dafa shayi ne kuma gashi kin karɓo koko"
Da sauri tace "dan Allah dagaske?"
Bece mata komai ba, ya wuce ya sauke tukunyar tea ɗin, ya buɗe jakarsa ya ɗakko
kayan tea ɗin ya haɗa mata shayi yasa mata madara, tana zaune tana kallonsa, ya
ɗauka ya kai ya ɗanɗana yaji in beyi zafi da yawa ba sannan ya bata.
Ta kalle shi tace "meye kuma seka sha zaka bani?"
"Na duba ne inji in beyi zafi da yawa ba karki ƙone baki"
"to shine zaka sa baki a jikin kofin, toni gaskiya da cokali zan sha tunda kasa
baki, ko in canza kofi"
Tsayawa yayi yana kallonta, taje ta ɗakko wani kofin ta juye a ciki, ta ɗau bredin
ta gutsura ta koma gefe.
Karon farko da taga fuskar Yusuf ta canza saboda abunda tayi, ta nuna ƙarara tana
ƙyamarsa kenan.
Tana kallon yadda ya ɗan ɓata fuska, ya kasa sakin jiki yaci Abincin ma, amma ta
basar ta cigaba da cin bredinta, da a gidane ba yadda za'ayi taci bredi babu
mahaɗi, amma yanzu se tura shi take kuma tana jin daɗinsa a haka.
Ƙarshe Yusuf miƙewa yayi yaje yayo wanka, yazo ya fara shirin fita sedai yaƙi cewa
uffan, be sake kula ta ba shirinsa kawai yake.
Widad ta matsa inda yake tace "wai naga ka wani yi shiru, lafiya dai?"
Girgiza mata kai yayi, ya cigaba da shirinsa "Amma naji kayi shiru haka? Nasan baka
saba zama haka kayi tsit ba"
Still shiru ya kuma yi mata, yana gyara kayansa dake cikin jakar matafiya.
Ɗagowar da zeyi taga idonsa yayi jawur, gaba ɗaya se jikin ta yayi sanyi.
"dan Allah meye ya same ka?"
Raɓata yayi ze wuce ta sha gabansa tana kallonsa.
Ze kuma kaucewa ta kuma shan gabansa, ba tayi tsammani ba Yusuf ya janyota ya haɗe
bakinsa da nata.
Mutsu Mutsu ta dingayi tana ƙoƙarin ƙwacewa, amma ta kasa ko ƙwaƙwaran motsi,
saboda yafi ƙarfinta nesa ba kusa ba.
A hankali ya cika ta, tayi baya da sauri tana rarraba ido, tare da sauke numfashi.
Tofar da yawun bakin ta ta dingayi, tana goge bakinta tana kuka.
Yusuf ya ƙaraso inda take, amma ta shiga ja da baya, riƙota yayi ya ƙura mata ido,
take yayi mata wani irin kwarjini.
Cikin sanyin jiki Yusuf yace "Widad da zuciya zatamin adalci to da ban iya jure duk
wulaƙancin da kikemin a baya ba, saboda Yusuf baya Jura wulaƙanci dan shima mutum
ne kamar kowa, sedai kash zuciya ta ta fara son abunda tasan yayi mata nisa har
abada, wanda be dace da ita ba, zuciyata ta saɓa Alƙawarin da mukayi da ita nayin
ban kwana da soyayya har Abada, hakan shine kawai mafita ga irin rayuwar da Yusuf
ya tsinci kansa a ciki, Amma ko warkewa banba daga cikin zugi da raɗaɗin da
zuciyata ke ciki ba, ƙaddara ta haɗani dake, kuma zuciyata ta shiga begen ki, Auren
nan da mukayi har cikin zuciyata nake som Auren nan, sedai nasan dole wataran zamu
rabu saboda bamu gina Auren akan tirbar soyayya ba, dan Allah Widad ni bance sekin
soni ba, saboda nasan hakan baya cikin tsarin rayuwar ki, kuma tamkar ƙasƙancine a
gareki Auren mutumin dabe kaiki a komai ba, nasan yanzu ma kutsen ƙaddara ne ya
haɗamu zama inuwa ɗaya dake, ko baki soni ba dan Allah kidena nunamin ƙyama kinji
Gimbiya, yi haƙuri na saki kuka" yai maganar yana ƙoƙarin goge mata hawaye
Fizgewa tayi tace "Dalla ni cikani in wuce, the must useless word i hate in my life
Love, kaima ka shiga sahun imagination da shirme kenan, ban guri ni zan wuce"
Ta ture shi tayi gaba abunta, ta ɗakko brush da toothpaste ta tafi sake wanke baki,
duk dan Yusuf yayi kissing ɗinta.
Jiki a sanyaye ya ƙarasa shiryawa, ya fito ze fita ko kallon inda yake ba tayi ba,
ganin ba kowa a tsakar gidan se Hanne yasa yazo gabanta yace "Zan tafi"
"Jirani inzo in zama mota seka hau ka tafi"
Ya girgiza kai yace "nasan kina jin haushina, kiyi haƙuri"
Banza tayi masa ta cigaba da abunda take, Hanne tace "Adawo lafiya Allah ya tsare"
Yusuf yayi murmushi yace "Allah yasa nagode"
Har yayi gaba ya waigo ya kalle ta, suka haɗa ido ya ɗan lumshe ido yace "I love
you My queen"
Wata uwar harara tayi masa ta miƙe ta bar tsakar gidan.
Nurat tana zaune a reception, da ƙyar aka bari taga Anwar, fuskarsa duk ta ɗaga
yayi wani iri, a gigice tace "Yaya Anwar me kayi aka kama ka haka?"
Anwar yace "wallahi Nurat ban saniba, wai ana tuhumata da haɗin bakina akan sace
Daddy, kuma wallahi ban san komai ba, na gyara masa jiki na bashi abinci, likita
yace inje in karɓo wani magani, ina komawa se cemin yayi wai ya shiga ɗakin amma be
ganshi ba"
Nurat tace "kamar yaya, ta yaya za'a sace mutum a Asibiti mutumin dako motsin kirki
baya iyayi"
Anwar yace "wallahi bam sani ba Nurat, ni yanzu ba kamanin da'akayine damuwa ta
ba, sanin inda Alhaji Nasir yake shine babbar damuwa ta, ba shi da lafiya waye ya
sace shi? Waze kula dashi? Waze bashi magani na rasa wacce irin masifa ce tasa ake
bibiyarsa haka"
Shiru Nurat tayi tana zancen zuci 'Anya kuwa babu sa hannun mahaifina a sace
Alhaji Nasir?'
Ta ɗago ta kalli Anwar tace "Yaya Anwar baka yi laifi ba dan baka banga dalilin da
zesa a kama ka ba, dan haka ka kwantar da hankalinka, akwai wani cousin brother
ɗina, barrister Abdallah zan masa magana ya shiga cikin case ɗin"
Anwar yace "bakya ganin akwai matsala? Kar a sashi a matsala fa, sunce in suka gama
bincike za'a sakeni"
"babu wata matsala insha Allah, ka kwantar da hankalinka, Insha Allah zak bar gurin
nan"
Anwar yace "Nagode sosai Ƙanwata, Allah yasaka miki da alkhairi"
Nurat tace "you deserve it dear" ta ɗau jakarta tayi waje.
Ramlah ce zaune a motar Fahad, ta murtuke fuska yana ta surutu amma tayi shiru,
kallonta yayi yace "beb, ya inata magana amma kinyi shiru, lafiya kuwa?"
"Fahad yanzu ace brother na yana ɗaure, amma koka jajantamin talk less of kace zaka
kai masa ziyara"
Fahad yace "ni inje state CID no i can't tarnish my image"
"Amma fa kaima ɗan uwanka nae"
"Yeah really, you are right dear but zuwa gurin nan se masu manyan crimes da manyan
terrors, kuma kinga daddy na sanannen mutum ne, ace anga mutum kamar ni a irin
wannan gurin is not fair at all, it will tarnish our family image"
Ramlah tace 'but your dad can bale him out, so you don't care about my feelings,
ɗan uwana yana rufe kaikuma abunda ya dameka daban ko? "
"Ai na miki bayani, ban san me kike so ayi ba kuma"
"ina son ka saka baki, Daddynka yayi magana a sake shi"
"Amma Ramlah kin san ba abune me sauƙi yin hakan ba ko, yaynki an haɗa baki dashi
an sace Daula, me zesa Daddy yasa baki"
A fusace Ramlah tace "shut up Fahad, ta yaya Anwar ze hakan, tare kukayi school
room ɗinku ɗaya, you know what he can do and what he cannot do, dan haka ina jiran
kaje kayi magana da mahaifinka a fito da shi, that's the only way you can prove to
me that you loves me"
Tana gama maganar tayi waje ta bar motar, ɗan taɓe baki yayi ya kunna motarsa yayi
tafiyarsa.
Yau da Yusuf ya dawo a ɗaki ya tarar da widad, kamar tana cikin damuwa ya kalle ta
yace "Na dawo"
Jinjina masa kai kawai tayi, amma ta kasa magana, se ya zata tun abunda ya faru da
safe ne yasa take jin haushinsa.
"Meke damun kine? Ko har yanzu fushin kike dani?"
A kasale tace "Bakomai fa"
Haka ya fita yaje yayi wanka ya dawo ya sameta a inda ya barta, yau dambun tsaki
Hansai ta girka ta aiko musu, amma taƙi sakin jiki taci, ya kaɗa ya raya amma tace
lafiyarta ƙalau, sedai ya lura buni buni seta tafi toilet ta dawo.
"Gimbiya ko cikin kine ya ɓaci?"
Girgiza masa kai tayi tare da kwanciya, haka taita yi har washegari gaba ɗaya kamar
bata da sukuni, kuma taƙi gaya masa abunda yake damun ta, haka ya fita ya barta ya
ɗauka dai fushi kawai take, Da Azahar ya dawo sedai ya tarar da tun Abincin safe
bata kuma cin komai ba.
Yaje gabanta ya durƙusa yana ƙare mata kallo yace "dan Allah idan fushi kike dani
kiyi haƙuri, kin sani a damuwa fa"
"Nifa ba fushi nake ba, ka ƙyaleni kawai"
"baki da lafiya ne?"
"lafiya ta ƙalau"
"but you look so much restless"
Shiru tayi bata ce uffan ba, ya miƙe yana duba kwanuka yaga abunda aka kawao, se
yaga tana ta dube duben abun shimfiɗar dake kan katifarta.
Yana zuwa ya ɗagata cak daga kan katifar, meze gani jini ne a jikin ta, ya ɓata
mata jiki da katifar.
A gigice yace "Subhanallah, Widad meya same ki haka?"
Take ta fashe da kuka tace "Period yazo min tun jiya bani da pad"
Cike da damuwa yace "shikenan is ok, kwantar da hankalinki"
Yasa hannu ya naɗe bedsheets ɗin, ya ɗora ruwa yayi ɗumi ya haɗa mata ruwa, ya
rakata banɗaki, ya dawo ya haɗa abun shimfiɗar da kayan data cire ya zubasu a
bokiti.
Tayi wankan ta fito ta dawo ɗakin, har yanzu bata dena kuka ba, Yusuf yace "jeki
zauna bari inje gurin Mama inga inda wani taimako da zata bamu"
"Idan na zauna ɓata gurin zanyi"
Yusuf yace "bakomai zauna, idan ya ɓaci zan gyara"
Ya zaunar da ita ya fita da sauri.
Yana fita tsakar gida Hanne ta kalle shi tayi murmushi tace "kana buƙatar wani
abune?"
Yusuf yace "gwaggo zaki kira min dan Allah"
Tace "to"
Ta tashi ta shiga ɗakin gwaggo, gwaggo ta fito ta kalli Yusuf tace "lafiya dai
malam Yusuf?"
Cike da kunya, Yusuf yayi mata bayani, Gwaggo tace "to mudai yaranmu da tsimmane
suke amfani, ban sani ba ko zata iya amfani da shi"
Yusuf yace "bakomai Gwaggo, zata iya insha Allah"
Gwaggo ta shiga ɗaki ta ɗakko sabon turmin Atamfa, da sabuwar reza, da ƙyar Gwaggo
ta iya shiga ɗakin nasu saboda kunya.
Widad na zaune da towel se vest a jikinta, Gwaggo tace "Sannu Amarya ya jiki?"
Widad tace "lafiya ƙalau"
Tasa reza ta yanka Sabuwar Atamfa ta gwadawa Widad yadda zata yi.
Widad tayi shiru taƙi cewa uffan, Yusuf yace "Mama nagode sosai da taimakonki,
Allah ya saka da alkhairi"
Gwaggo tace "bakomai Malam Yusufa"
Gwaggo ta fita, tana fita Hari tace "Yaya wai Wudas ɗince bata da lafiya?"
Gwaggo tace "Eh"
"meya same ta?"
Gwaggo bata amsa mata ba, Hanne tace "waini Gwaggo meye na yanka sabuwar Atamfarki,
wallahi kin fiye zaƙewa akan wannan fitsararriyar"
Gwaggo a fusace tace "wallahi kika kuma magana sena kwaɗa miki mari, ina kallon ki
duk abunda kike yi, ɗa na kowa ne, meye dan na yanka Atamfa? Abum duniya fararre
ƙararre"
Haushi Hanne taji, dan da wuya kaga Gwaggo tana faɗa se an ɓata mata rai sosai,
Amma yau akan wannan koɗaɗɗiyar tana ta mata masifa.
Yusuf ya kalli Widad yace "gimbiyata nasan baki saba amfani da irin wannan ba, amma
kiyi haƙuri gidanmu babu mata nikaɗai ne shiyasa nima ban san kan wannan abubuwan
ba, da tuntuni nasa an nemo miki abunda zaki yi amfani dashi"
Da ƙyar Yusuf ya lallaɓata ta saka ƙyallen nan, sam she's not comfortable with this
thing, gaba ɗaya ta takure kanta, Yusuf yana kallonta ta kwanta ta zauna gaba ɗaya
ta kasa zama.
Ya kwashi kayan data ɓata yaje ya wanke su tsaf, taga ya dawo ɗaki yana goge hannu
ta kalleshi tace "wai me kayi?"
"kayanki na wanke"
"Kayan jinin?"
"Eh mana, nasan idan na bar miki ba zaki iya wankewa ba"
Shiru tayi ta bishi da kallo, tuno abunda ya faru da safe tayi, yadda tay masa
wulaƙanci amma har ya manta yana tarairayarta, yasa hannu a kayanta na jini ya
wanke.
Ganin da yayi ta kasa zaune ta kasa tsaye yace "Gimbiyata meya ke damunki yanzu?"
"ƙafafuna ne kamar ba nawa ba, babu daɗi marata ma ciwo takemin"
Yazo ya zauna a kusa da ita, ya kamo ƙafafunta ya ɗora akan cinyarsa yana matsa
mata a hankali, lumshe ido ta dinga yi.
Ta ɗauke ƙafafunta daga kan cinyarsa, ta ɗora kanta sannan ta miƙa masa hannunta,
tana masa nuni daya ja mata yatsun, haka Yusuf ya riƙe yatsun ta yana matsawa a
hankali, babu daɗewa kuwa bacci yayi gaba da ita.
Seda Nurat ta tinkaro komawa gida sannan gabanta ya shiga faɗuwa, dan se yanzu ma
ta tuna taɓargazar da tayi.
Kanta tsaye tana ta Addu'a ta fara buga gate ɗin, me gadi yazo ya buɗe mata bece
mata uffan ba, ta shiga cikin gidan, sedai me a harabar gidan idonta ya sauka a
cikin na mahaifinta yana zaune yana kallonta.
SANARWA! SANARWA!! SANARWA!!!
(Ina ma'abota karatun littafin AƘIDATA, a fari nace zan bada littafin kyauta ba
tare da ko sisi ba, amin Afuwa wani dalili zesa zan saida book2 and 3,dukda nima ba
hakan naso ba, gaba ɗaya kyauta nayi niyya bada littafina, Amma dalilin me ƙarfi
zesa in saida ƙarashen in na gama book1 ina fatan zaku fahimceni)
Domin gyara, sharhi ko shawara Ayshercool 07063065680
_*AƘIDATA*_
PERFECT WRITERS ASSOCIATION
(WE AIN'T PERFECT BUT WE ARE ALWAYS TRYING OUR BEST, TO MOTIVATE AND ENTERTAIN OUR
READERS)
https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/
*Story and written by*
_*AISHA HUMAIRA _(Daddy's girl)*_
The experience writer of *ABDUL JALAL** WATA KISSAR.... (SAI MATA) *And now *AƘIDA
TA *
I dedicated this book to my Mum (Malama Nafisat Adam Muhammad) i love you mum
Haƙƙin Mallaka ⚠ : Littafin nan mallaki nane, tun daga sunan labarin zuwa abunda ya
ƙunsa, ban yadda wani ko wata ya sauyamin ko yin Amfani da wani ɓangare na labarin
ba ba tare da izinina ba, Nagode
https://www.wattpad.com/user/Ayshercool7724?
utm_source=android&utm_medium=link&utm_campaign=invitefriends
NOT EDITED
ELEGANT ONLINE WRITER'S
PART1 Page 40_41
Gaban Nurat ne ya shiga bugawa da sauri da sauri, ta shiga zazzare ido be kula ta
ba bece mata komai ba, tazo ta tsaya tana kallon sa, taga harta wuce bece mata
uffan ba.
Ta shiga ɗaki ta nemi guri ta zauna, tayi shiru tana tunanin yadda zata samu Anwar
ya kuɓuta, babu zato taji an murɗa ƙofar ɗakin nata.
Mahaifinta ne ya shigo yana rarraba ido, gadan gadan yayo kanta yana faɗin "gidan
ubanwa kika je?"
Miƙewa tayi a gigice ta shiga ja da baya tana faɗin "babu inda naje Daddy"
"ƙarya kike munafuka, harni zan saka doka ki sa ƙafa kiyi fatali da ita? Uwarki ta
ɗaure miki gindin kiyi rashin mutunci ko? Ni da Daula waye ya haifeki?"
"Daddy niba gurinsa na je ba, Ai an ɗauke shi daga Asibiti"
Sekuma yayi sak, "Ubanwa waye ya gaya miki?"
"wallahi Daddy a gari naji"
"to gidan ubanwa kikaje? Zaki gayamin ko sena yanka ki a gidan nan?"
Girgiza kai take, takasa magana ya cakumo wuyanta yana zazzare ido, kakari ta dinga
yi tana kuka tace "Wallahi Daddy ba inda naje, kawai gajiya nayi da zaman gidan na
fita, dan Allah kayi haƙuri"
"se naci ubanki yadda idan na sake saka doka ba zaki takamin ba"
Cikin kuka Nurat tace "Wayyo Allah Mummy, ki temakeni karya kasheni"
Maimakon ya saketa sake shaƙeta yayi, yana kuma zaro mata ido kamar tsohon maye.
Kakarin Nurat ne yasa mahaifiyar ta, ta sallame salar da take, a guje ta rugo ɗakin
Nurat, ta tarar ya shaƙe Nurat kamar ya kama sa'ansa ko kuma wani shahararren
Ɓarawo.
"Kayi haukane, ka cikamin 'yata ita kaɗai ce dani, kana gani duk yaranmu mutuwa
suke, ita kaɗai Allah ya barmin ka ƙyalemin' yata"
Juyowa yayi a fusace ya mangare mahaifiyar Nurat yace "itama ɗin gara in aikata
inda waɗancn suka tafi, muddin zata dinga takemin doka, tasan a duniya bani da
maƙiyi sama da Daula, danme zata dinga zuwa inda yake, akan me?"
Yai maganar tare da wurgi da Nurat, wadda tuni ta fara fita a hayyacinta, dan daya
jefar da ita ko motsi ba tayi, se kokawa take da numfashi.
Da sauri Maman Nurat ta nufi kan Nurat, yayin da Alhaji Musa ya cigaba da banbami,
ta ɗago Nurat sedai bata numfashi.
Cikin kuka tace "wallahi idan ka kashe min 'ya se nayi shari'a da kai, Kai kanka
kawai ka sani, buƙata in ba ta kaba baka damu da kowa ba"
A fusace yace "Maza karki fasa yin shari'a dani, idan na kashe ta na kashe banza,
duk son da nakewa mutum muddin ze bujiremin to zega ba dai dai ba tabbas"
Banza tayi masa, Taje ta buɗe fridge ta ɗakko ruwa me sanyi ta shiga shafawa Nurat,
a hankali ta dinga sauke Numfashi, tana buɗe ido ta fashe da kuka tace "Mummy anya
Daddy ne ya haife ni? Kalli yadda yayi yunƙurin kasheni me nayi masa haka?"
"kema da halinki Nurat, kin fiye taurin kai, na hana ki wannan abun da kike amma
kin kasa ganewa, gashi ze kashe ki a banza"
Shiru Nurat tayi, tabbas tunda mahaifinta yake yunƙurin kashe ta akan taje inda
Daula yake, to tabbas wani mummunan abu yake aikatawa, kuma na abunda baze iya
aikatawa akan kowa ba.Lumshe idon ta tayi tana jin yadda ƙirjinta yayi nauyi, wani
irin baƙinciki ya mamaye zuciyarta.
Shikuwa Alhaji Musa yana komawa ɗaki ya shiga sintiri, kamar yadda ya zame masa
jiki a 'yan kwanakin nan, ba shi da nutsuwa sam, musamman da' aka ce su Widad sun
gudu daga inda aka sace su, gashi sunsa a nemo su a ko'ina suke amma abu ya gagara.
Gashi yanzu wata maganar rainin hankali da ta taso, wai an sace Daula akan gadon
Asibiti, 'Anya ba wani rainin hankalim su Alhaji Haruna suke shiryawa ba?'
A hankali Widad ta buɗe ido daga baccin da yayi awon gaba da ita, taga Yusuf ya
jingina da jikin bango ya lumshe idanunsa, hannunsa ɗaya yana wasa da gashin kanta,
a hankali tayi miƙa tare da hamma, da sauri ya buɗe ido yana jera mata sannu.
Ba tace komai ba se jinjina masa kai da take.
Miƙewa tayi zaune, se kuma yaga ta yamutsa fuska.
Kallon ta yayi da sauri yace "lafiya dai?"
Ɗan tura baki tayi tace "am not confortable at all, ji nake kaman am stain"
Yusuf yace "kiyi haƙuri insha Allah, zan san yadda zanyi a samo miki wancan da kike
amfani da shi"
Widad tace "baza a samu wanda nake amfani da shi ba, sedai a siyomin kowanne ne,
bana son wannan abun da nake using dashi yanzu, is so much irritating"
Yusuf yace "Shikenan, Insha Allah zan san abunyi"
"Sannan kuma..." se kuma tayi shiru
"sannan kuma me?" Yusuf ya tambaya
"Nasan baza'a samu shaving cream ko powder ba, a siyomin shaver please"
Cike da son ya kunnata Yusuf yace "shaver kuma, me zakiyi da shaver?"
"Abunda kake yi da ita" ta bashi amsa cike da tsiwa
Yayi murmushi yace "Aini gemuna nake askewa da ita"
Ta kalle shi ta ɗan tsuke baki tace "Nima nawa gemun zan aske"
Aikuwa Yusuf ya kwashe da dariya, sosai yadda tayi magana da abunda ta faɗa ɗin ya
bashi dariya, kallonsa take yi yadda dariyar tayi masa kyau.
"wallahi idan ka ƙware ba ruwana"
Tai maganar tana shirin Miƙewa, ya kalleta yace "Ina zaki?"
"tsakar gida nake son fita"
"Amma kin manta halin da kike ciki ne?"
"To zama zan tayi ina kallonka, ni na gaji da kwanciyar ma, zan kula sosai"
Yusuf yace "Aini bana gajiya da kallon kyakkyawar fuskar nan taki, muyi zamanmu a
ɗaki nima na iya hirar se in miki, kuma baki ci Abinci ba, ko kin manta?"
'ƙyale Abincin nan, ni idan ina period bana son Abinci sosai "
Yusuf yace " dama can haka kike, ina lura dake tarkace kawai kike ci ba Abinci ba,
so nake ki ƙara Ƙiba ki daure kici ko kaɗan ne mana"
"Ni gaskiya, ba irin wannan nake so ba"
"wanne kike so" ya faɗa cike da kulawa.
Ɗan tsura masa ido tayi, sannan tace "Bari dai inci kaɗan"
Ya ɗakko kwanon dambun ya ajiye mata, tasa cokali ta fara ci, dambun tsaki ne amma
yaji gyaɗa da zogale yayi daɗi Sosai.
Widad tace "tunda nazo ƙauyen nan, ban taɓa cin Abinci me daɗin wannan ba"
Yusuf yayi murmushi yace "harda bredin jiya?"
Widad tace "hmm dan dai kar kaji haushi ne, amma gaskiya bredin nan ya daɗe a
ajiye, se marmashewa yake ba daɗi"
Yusuf yace "dagaske ba kya son inji haushi?"
Ɗan kallonsa tayi tace "No i mean banyi niyyar magana ba lokacin shine kawai, ka
ɗakko spoon muci Abinci mana"
Yusuf ya girgiza kai yace "A'a kici kawai, idan kin rage se inci"
Widad tace "meyasa? Ai ze ishemu"
Yusuf yace "bana son in samiki yawuna a jiki, naga bakya son hakan"
Ɗan tura baki tayi, cikin ƙunƙuni tace "na nawa kuma, ƙarewa ma ai Yawun naka ka
samun a bakina jiya"
Yusuf yace "ai bazan manta wannan moment ɗinba, nayi kissing ɗin gimbiyata the most
memorable moment in my life"
Widad tace "tabbas kam, ka kafa tarihi, kayi abunda wani mahaluki be taɓa gangancin
gwadawa ba, kayi min abunda ban taɓa zaton wani zemin in ƙyaleshi ba, hmm ban san
meyasa kake min abubuwa son ranka ba, ƙyaleka kawai nake"
"Are you sure babu wanda ya taɓa kissing ɗinki seni?"
Watsa dambu tayi a bakinta, ta ja wasu seconds sannan tace "Idan an taɓayi kana
tunanin zanji tsoron ka ne? Ban taɓa shan yawun Ƙato ba se a kanka, kuma bashi ka
ɗauka, tunda kasa na haɗiye yawunka"
Murmushi Yusuf yayi yace "Yaushe ne ranar biyan bashin?"
Banza tayi masa taƙi ko kallon inda yake, can Yusuf yace "Amma meyasa kike zuwa
Clubs da kuma Hotel?"
Jin tambayar tayi a bazata, take taji tana kokawa da dambun dake bakinta, gaba ɗaya
Mood ɗinta ya canza a hankali tace
"ai tun a lokacin na gaya maka me nake zuwa yi, na gaya maka ni karuwa ce kamar
yadda matan gurin suke"
Haɗe rai Yusuf yayi yace "Kamar yadda bakya son ƙarya, na tabbata kema bakya aikata
ta se bisa kuskure, meyasa zaki gayamin haka? Ko kina son zuciya ta ta buga ne?".
"Tunda baka yarda ba shikenan, amma kasan dai bazan zauna ina rantse maka dan ka
yarda dani bako?"
Ta ajiye spoon ɗin Abincin ta je ta sha ruwa, tayi waje abunta ta bar Yusuf a gurin
a zaune.
Roƙon Allah ya shiga yi akan Allah yasa abunda Widad ta faɗa ƙaryane, dan ba
ƙaramin kishi yaji ba, kuma yasan halin ta ko meye zata yi ƙoƙarin gaya maka
gaskiya, ko ta maka daɗi ko akasin hakan'
Tana fitowa Gwaggo tace "Amarya kin ware kenan?"
Widad tace "eh Alhamdilillah"
"Masha Allah, haka nake son ji"
Hari tace "Wai meya same ki ne?"
Widad tace "Kaji Baba Harin nan, sekace kin damu dani, bayan ko gani kika yi zan
mutu murna zaki yi, to ciwon yara nake bana tsofaffi ba dan haka base kinji ba"
Aikuwa a fusace Hari tace "karki ƙara cemin tsohuwa, ta ina nayi miki kama da
tsohuwa? Da ƙuruciyata dudu shekarun nawa ba zasu gaza Ashirin da shida ba, amma
kike kiramin tsufa"
Ai gaba ɗaya wanda ke tsakar gidan ba wanda be dariya ba, Widad tace "A'a kin manta
a zanin goyo kike ma ƙarewar yarinta, harfa jikokine dake amma kice shekarar ki
Ashirin da shida, shekarar ki biyar akamiki Aure kenan"
Hari tace "koma yane dai, niba tsohuwa bace ba ehee, dan jina nake garas kamar 'yar
shekara goma sha shida"
Widad tayi dariya tace "dama zaki dinga gayune, za kiga yadda zaki koma yarinya
sharaf, amma indai baki dena ƙazanta ba, to tabbas wataran za' a kalle ki ace
shekararki sittin da 'yan kai"
Hari tayi kicin kicin da Fuska, dan Widad ta fara kaita bango, idan ta cigaba da
biye mata to tabbas za suyi ba daɗi, dan haka tayiwa Widad banza.
Widad ta ƙarasa inda Hindu ke tsinke zogale ta zauna tace "Hindatu, ya ki keyi?
bari in tayaki"
Hindu Ta gwadawa Widad yadda ake tsintar zogale, ta zauna suna yi tare.
Can Widad tace "Hindu, wai kuma idan kuna period bakwa amfani da pad ne? Se tsimma"
Hindu tace "meye kuma firiyios?"
Widad tace "A'a ba kije makaranta bane? Me yasa Common things idan na faɗa, seki ce
baki sani ba?"
Hindu tace "bari Amarya wallahi muna son karatun nan, amma ba yadda muka iya ne,
kinga inda muke zuwa makarantar furamarai can wani ƙauye ne, kusan ƙauyuka biyar
duk ita muke zuwa, to guri ba kusa ba nisa kafin kaje duk anyi wani abu baka nan,
lokacin damuna kuwa bama samun zuwa, sannan akayi ruwan Sama me ƙarfi ya kwashe
kwanon da'aka rufa azuzuwa, ai kuwa akace mu dena zuwa se an gyara, dan haka tun
aji huɗu furamarai nidai na dena zuwa har yanzu "
Widad tayi shiru, ita ko a tatsuniya bata taɓa jin wannan al'amarin ba, ace a
Nigeria akwai 'yan ƙasa wanda basa samun ilimi, ina wakilansu? Meye amfanin
shugabannin da suka zaɓa suka wakilta dan suyi musu aiki? Ace ƙauyuka huɗu su
dogara da primary ɗaya, kuma shima se sun sha baƙar wahala kafin suje, dole abun ya
fita daga ransu'
Widad tace "gaskiya banji daɗi ba Hindu, ai Ilimi shine mutum, tabbas da'a bakin
wani naji cewa zanyi ƙarya ne labarine kawai"
Hindu tace "aikuwa gashi a zahiri kinji, shiyasa duk muka haƙura wasu suka kama
talla har zuwa lokacin da mace zata samu miji tayi Aure, dama idan kana karatun
wasu kallon ɗan iska suke maka, muka koma zuwa ta Allo ta Allonma gata nan dai
nidai na samu nayi izu biyar na haddace itama munyi yawa, babu wata kulawa yadda
yakamata, dan anan wajejenmu makarantar Allo ɗaya ce"
Widad ta jinjina kai tace" to sauran litattaafai fa, kamar Ahlari, fiqhu hadisan
manzon Allah salallahu alaihi wassalam, suma ana koya muku? "
Hindu tace" Taɓɗijan, Al'qur'ani kawai ake koya mana a makarantar Allo, kuma shima
mun dena zuwa, se Baffanmu ne dai da yana koya mana Alhadisin Auwwalu, shima yace
mana Babansa ne ya koya masa, kuma ma yanzu duk mun manta tunda shekarun da yawa "
Widad kawai tayi tagumi tana sauraren Hindu, tana jin kwamacalar da ko a Film bata
taɓa ganin irinta ba, yanzu dama da irin wannan mutanen suna rayuwa a haka, amma
ake samun mutanen da suke wawashe dukiyar al'umma, a 'ya' yan sanatoci akwai wanda
tasan ana biya musu ku&in makaranta na secondary naira milyan uku, duk term miliyan
ɗaya, iya 'yan tsirarin' ya'yansa, amma ga dubunnai zaune a gida babu arabi babu
boko, irin wannan ne idan suka faɗa harkar ta'addanci basa imani sam.
Hindu ta kalli Widad tace "ya naga kinyi shiru ne?"
Widad tace "Mhmm bakomai"
Hindu tace "Yawwa, dan Allah meye Firiyas ɗin da kika ce?"
Widad tace "Period nace, ina nufin jinin Al'ada"
Hindu tace "Auho ai ban gane ba, seki cemin baƙon wata, ai mu da tsumma mukeyi, mu
yayyanka tsumma semu dinga amfani dashi, duk wanda muka cire se mu wanke mu ninke"
Widad ta kalleta da sauri tace "ku wanke me?"
"tsimmar mana, idan ɗan kamfan mutum ɗaya ma haka ze haɗa duk ya wanke, ya ɗan jira
ya bushe seya sake mayarwa"
Dafe kai Widad tayi, tayi shiru ta shiga duniyar tunani, ta tuna yadda take
fantamawa a cikin kuɗi, babu abunda ta nema ta rasa a rayuwar ta, Kama daga Abinci,
sutura abun hawa gurin kwana, har wasu kuɗi ne da ita na musamman wanda take kula
da dabbobinta kawai, tayi kyautar mota, tayi kyautar gida ta bada kuɗi kamar aikin
banza, ashe akwai bayin Allahn da sun fidda rai da samun wani jin daɗi.
Hindu tace "Amarya, Allah yasa ba wani abun na miki ba, naga kin ɓata rai?"
Widad tace "bakomai Hindu, mu cigaba da aikin kawai"
Widad bata iya tsinkar zogalen ba, dan haka wani yanayi wani kuma harda kararen
jiki take zubawa, Hindu bata damu idan Widad ta zuba a haka se tabi tana gyarawa.
Hanne ce ta taho a fusace tasa hannu ta ɗauke robar da suke tara zogalen tace
"Aikin banza, ke Hindu kin san ba abunda ta iya kawai kin ɗauki abu kin bata kinsa
se ɓatawa mutane take, tana mayar mana da aiki baya kin zauna se surutan shirme ki
keyi, da yanzu an wanke an ɗora amma duk ta ɓata mana"
Hindu tace "Haba Hanne, to ba a hankali zata iya ba, kuma ai tayani take tana yi
ina gyarawa, meye a ciki dan munyi tare"
Tsaki Hanne Tayi, tai gaba da robar zogalen, Widad ko ɗaga kai ba tayi ba balle ta
kalli Hanne, tayi shiru ba tace komai ba.
Cikin damuwa Hindu tace "dan Allah Amarya kiyi haƙuri, ni ban san meyasa take
wannan abubuwan ba"
Widad tayi murmushi tace "Ni banyi fushi ba ai, bakomai"
Saleh ya ɗau waya ya kira Abbas, sedai har tayi ringing ta katse be ɗaga ba, tana
katsewar ne Abbas ya biyo kiran, Saleh ya ɗaga tare da yin Sallama Abbas ya amsa,
Saleh yace"Malam Abbas, kayi gaba ko waiwaye baka yi, kana da labarin an sace
amininka kuwa tare da 'yar gidan Daula?"
Abbas yace "ƙwarai kuwa na sani, dan nine ma na gayawa mahaifiyarsa"
Saleh yace "Wani tunani kayi akai kuwa?"
"wani tunani zanyi kuwa, maganinsa kenan ai, shegen shishshiginsa da rawar kai yaja
masa, ni Allah ne ya dube ni, dani naso in maye gurbinsa da dani za'a ɗauke, Amma
kuwa an karɓi files ɗin daga hannunsa?"
Shiru Saleh yayi sannan yace "basu karɓa ba tukuna, ni suke jira, har yanzu basu
san cewar Yusuf ne jami'in tsaron ba, zancen da nake maka yanzu haka Yusuf sun
tsere daga inda aka ɓoye su"
Abbas yace "haba dai, garin yaya akayi suka tsere? Kai Yusuf fa ba ƙaramin
hatsabibi bane ba"
Saleh yace "babu wanda ya sani, kuma har suka gudu ba'a samu karɓar abun nan daga
hannun yarinyar ba, yanzu maganar da nake maka, shi kansa Daulan an ɗauke shi a
gadon Asibiti, babu wanda yasan inda yake"
"Innalillahi wa inna ialaihi raji'un, garin yaya, yanzu shikenan munyi biyu babu,
nifa ba wanda yake tuntuɓata yanzu tunda akamin transfer"
Saleh yace "karka damu, ina son ka saurareni da kyau, duk abunda ake ciki zan dinga
sanar da kai, karka kusakura wani daga cikin su yayi yunƙurin haɗa kai da kai, dan
yanzu gaba ɗaya kawunansu a rarrabe yake, duk wanda ya tuntuɓeka koya tambayeka
wani abu game da wanda aka bawa binciken nan kace baka sani ba"
Abbas yace "to aini basu sanni ba, kai suka sani me zesa su nemeni?"
"Abbas mutane ne masu wayo matuƙa, yanzu haka a manyanka na gurin aiki wani ze iya
bugun cikinka ya tambayeka wani abu, karka kuskura ka gaya wani, wani abu akan
harkar nan, na gaya maka kansu ya rarrabu, wasu zasu iya zamewa suyi harkar nan
babu mu, bayan wahalar da mukayi "
Abbas yace " bakomai na fahimce ka, Insha Allah babu wanda zeji wata magana daga
bakina, dama kai ka jawoni cikin harkar "
Saleh yace " Good nagode "
Sukayi Sallama, Saleh ya jinjina kai yanzu ya sake jinjinawa Widad, lallai bata da
laifi naƙin yadda da mutane, ƙir ƙiri Abbas na jikin Yusuf ne, amma saboda kuɗi
yake masa zagon ƙasa, tabbas mutum abun tsoro ne, kuma da alama Abbas Soko ne, dan
haka yi masa wayo ba wani abu bane me wahala.
Saleh yana son sake komawa gurinsu Widad, dan haka yana ta ɗanyi musu siyayya.
Alhaji Musa ne ya kira shi a waya yace 'lallai yana son ganinsa a guest house
ɗinsa'
Haka Saleh ya bar abunda yake yi ya tafi gidan Alhaji Musa.
Yaje ya tarar dashi a lambun dake gidan, suka gaisa Alhaji Musa yace "Saleh ina
cikin damuwa fa"
"wace irin damuwa kuma ranka ya daɗe?"
"Na fuskanci Nurat tana ƙoƙarin fara yin shisshigi ga al'amuran Daula, gashi yanzu
ina ɗari ɗari da su Haruna, ina tsoron Ayi Amfani da ita a cutar da ita koni, yanzu
babban abunda ya sake bani mamaki be wuce yadda Daula yayi ɓatan dabo ba, ko kusa
ko alama an rasa inda yake, zargina yana ƙara tabatta akan ana min maƙarƙashiya,
kodai su Alhaji Haruna suke cuta ta suke al'amuran su suka ɗai, kokuma akwai wani a
gefe daya ke harin abunda muke hari, ko kuma yasan siriinmu yake son temakawa
Daula"
Saleh yayi ajiyar zuciya yace "banƙi ta taka ba, Amma ko waye wannan tabbas na
jikin ku ne, amma abun da mamaki ace an nemi Daula ko sama ko ƙasa an rasa sekace
wata takadda"
"Shine abunda ya ɗauremin kai ai, ni yanzu gefe zan koma in nemawa kaina mafita,
idan abun nan ya samu shikenan, in be samu ba shikenan, suma har yanzu da suka gudu
babu wanda ya sake jin ɗuriyarsu, dan haka ni inaga tunda babu wanda yasan inda
Daula yake, zan fito takarar Senate ne kawai "
Da sauri Saleh ya kalle shi yace " Amma ta yaya kake tunanin mutane zasu yarda su
zaɓeka? Bayan Daula ya riga ya ɓata siyasarka a idon duniya? "
Alhaji Musa yace " shiyasa nima na ƙuduri aniyar kota wane hali, sena Wulaƙanta
Daula a idon duniya, sannan malamai zan shiga a rufemin bakin jama'a, akwai yarana
da suke aiki a wasu daga kamfanunukan Daula, zamu haɗa kai dasu mu karkatar da wasu
kuɗaɗe inyi amfani da su, niba kuɗin Daula ne sjka dameni ba, yadda zan Wulaƙanta
shi in ɗaiɗaita shine ya dameni, amma ko yanzu na rage raɗaɗin dake zuciyata, kuma
zan cigaba da bibiyarsa se naga babu inda ya rage wanda ze jingina yaji daɗi,
sannan in dawo kan su Alhaji Munir"
Yadda Alhaji Musa ke maganar babu alamun tausayi ko imani a tare da shi, har
zuciyarsa yake faɗar wannan maganganun. Saleh ya ɓoye duk mamakinsa, ya dinga ziga
Alhaji Musa, Alhaji Musa ya kawo kuɗi ya bawa Saleh, Saleh a ransa yace "ka bada
kuɗin da zanyiwa maƙiyan ka siyayya, kuma nima zancigaba da bibiyarku, ɗaya bayan
ɗaya sena ɗau fansar cin amanata da kuka yi, da saɓa Yarjejeniyar da muka yi daku"
Widad gaba ɗaya hirar da suka yi da Hindu ta tsaye mata a zuciya, ta tuna yadda
haka siddan se ɗan kasuwa yayiwa ɗan siyasa kyauta motar miliyoyi, ko biliyoyin
nairori, Amma al'ummar su suna tagayyara, da yunwa da rashin kyakkyawan mahalli.
Yusuf yaga gaba ɗaya Widad tayi wani iri, seta zauna tayi shiru tana tunani, dukda
shima zuciyarsa ba daɗi, Amma sam baya son ganinta a damuwa dan haka yace "Ran
gimbiyata ya daɗe meke damunki ne?"
Jiki a sanyaye tace "Abubuwa da yawa"
Yusuf yace "Kamar me? Ko har yanzu fushin kike dani"?
Jiki a matukar sanyaye ta bashi labarin hirar da suka yi da Hindu, daga ƙarshe tace
"tabbas ƙaddarar data sameni na zuwa ƙauyen nan, ishara ce Allah ya nunamin, na
rayu cikin gata wanda nake ganin babu wani abu da zan iya nema in rasa a rayuwata,
ranar da kace min akwai mutanen da Naira ɗari take gagararsu, gani nake kawai ka
faɗane dan ka rainamin hankali saboda a lokacin, abun da ke cikin asusun bankina ya
ninka ɗari sau ɗari, bani da wata damuwa ko matsala, Amma ace a rayuwa akwai tarin
'ya' ya mata da suke zaune ba ilimi? Akwai tarin mutanen da suke rayuwa da
gurɓataccen ruwan sha? Akwai tarin yara manyan gobe da rayuwarsu ta lalace saboda
rashin gurin samun ilimi, Yoseef yaran masu kuɗi na Almubazzaranci da dukiya, da
yawanmu bamu san yadda aka tara kuɗin ba... Kasa ƙarasawa tayi gaba ɗaya jikinta
yayi sanyi, wani irin ɓacin rai ke taso mata, yadda ake ɓarnar kuɗi gurin bukukuwan
birthday dana Aure, da makamantan su.
Yusuf ya taso daga inda yake, yazo ya samu guri ya zauna kusa da ita yace "Widad
baki ga komai ba, a yanzu haka a cikin ni'ima muke, a gidan megari muke a zaune,
kuma gidansa da rufin Asiri, ya kike tunanin gidajen sauran talakawa da suke garin
nan? Wanima abunda zasu cin ma babu, Widad talauci gaskiya ne, shiyasa Wulaƙanta
mutane bashi da kyau "
Widad tace" tabbas wulaƙanta mutane bashi da kyau, nasan mutane dayawa sunamin
kallon mace me izza da Wulaƙanta mutane, sedai...
Se kuma tayi shiru, Yusuf yace "sedai me?"
"Bakomai" ta bashi amsa tare da basar da zancen.
Da Asuba bayan Yusuf ya dawo daga sallar Asuba yazo ya tattara kwanuka zeje ya
wanke, Widad tace "ka bari zan wanke"
Yusuf yace "No ki huta kawai, bari in wanke ai ba yawa kwanukan"
Widad tace "ce maka akayi ban iya wanke wanken bane?"
"Ni na isa ince gimbiya bata iya wanke wanke ba?"
Widad tace "gashi nan kuwa ka faɗa"
"A'a ni ban faɗa ba, taso muje muyi tare"
Widad ta tashi tabi Yusuf suka je suka wanke kwanukan tare, ta tattare duk kwanukan
wanke wanken da'akayi fatali dasu na Abincin dare a tsakar gidan, ta haɗesu a guri
ɗaya, Yusuf yasa tsintsiya duk girman tsakar gidan yana sharewa, Widad ta dinga
kallon ikon Allah, yadda Yusuf yake sarrafa tsintsiya kamar mace.
Widad tace "dan Allah dagaske kai ka ɗaine a gidanku?"
Yusuf yace "Eh nikaɗai ne Mamana ta haifa, ni nake mata aikin gida, shara,
wanke_wanke hadda girki duk ta koyamin ni nake yi, idan ta tafi unguwa kafin ta
dawo nayi komai"
Widad tace "shiyasa ka iya aiki sosai, nima nasan da tare na girma da Ammi na da
duk na iya aiki, da baza'a dinga kallon ban iya komaiba"
Yusuf yazo kusa da ita ya tsaya, ya kalleta yace "karki damu gimbiyata, Insha Allah
muna tare zaki iya komai kafin mu koma gida"
Widad ta kalle shi tace "dagaske har girki zaka koyamin? Nafa iya girki amma ba
sosai ba"
Hannu yasa ya ɗago haɓarta yace "zaki iya komai insha Allah, duk zan koya miki,
amma bana son taurin kai, dan nasan halinki"
"Nice me taurin kai?"
Yusuf yace "eh kina dashi amma kaɗan"
Murmushi Widad tayi tace "Ni dai in zaka koyamin zanyi duk abunda kake so"
Yusuf yace "dagaske?"
Widad ta jinjina masa kai, ya matso daf da ita yace "to shikenan, Yimin kiss a
goshina ma ba'a baki ba, se in koya miki kunna risho yau"
Tureshi tayi tace "Baza'ai wannan ɗinba"
Matseta yayi a jikin bishiyar ya riƙota, cikin sigar magiya yace "please Gimbiyata,
ko sau ɗaya ki nuna kin damu dani please"
Cikin tsiwa tace "to Jaririne kai? Ko goya ka zanyi?"
Kwantar da kansa yayi a kafaɗarta yace "to goyanin mana, ko daga nan zuwa ɗakine"
"Eh ba shakka, ba kunya wai in goya ka, sakeni ko in cijeka yanzun nan"
Hanne ce ta fito daga ɗakinsu, tana fitowa idonta ya sauka akan Yusuf da Widad dake
tsaye a jikin bishiyar ceɗiya dake tsakar gidan, kamar zasu shige jikin juna.
Da ƙyar ta haɗiye wani irin mugun yawu a wuyan ta, ta koma cikin ɗakinsu tana fesar
da numfashin baƙin ciki.
Hindu ce ta Kalle ta tace "Hanne lafiya kuwa?"
Hanne tace "wallahi Hindu na tsani matar Yusuf, ji nake kamar in shaƙeta"
Cike da mamaki Hindu ta kalle ta tace "kamar yaya kin tsane ta?"
Hanne tace "Hindu dan Allah kina ganin Yusuf ze iya Aurena?"
Wani mugun kallo Hindu tayi mata tace "Anya kina kallon kanki a mudubi kuwa? Kina
ganin mace jawur, kalle ki kice kina son mijinta, matar nan fa tana miki kawaici
akan Mijinta, kiyi ta mata wulaƙanci amma tana ƙyale ki, karki kuskura Gwaggo taji
wannan maganar da kike"
Hanne tace "ba zaki gane ba Hindu, wallahi Yusuf ɗin nan yana da kirki sosai, ita
ba abunda ta iya se rashin kunya, gata bata da tarbiyya sam gata a wani taɓare, ga
tsbar iskanci da rainin hankali, komai se tace bata sani ba"
Hindu tace "A'a wallahi tana da kirki, niba abunda tamin da zan zageta, kije kiyi
ke kaɗai, Allah ya yaye miki wahala, dan tabbas yana da wannan matar babu abunda ze
dake"
Yau kam Widad ta ɗan rage yiwa Widad rashin kunya, dan tare suka ci Abinci saboda
tana son ya dinga koya mata aikin gida, dan tana jin zafin gorin da'ake mata, wai
bata iya komai ba.
Bayan sallar la'asar Widad ta fito daga ɗakinsu, dama gyara ɗakin baya mata wahala
da gyara gado duk wannan ta iya.
Hari ta hanga a inuwar bishiya tana saƙa mafici, Widad ta ɗakko kujera ta zauna a
kusa da ita tace "Uwata ta kaina"
Hari ta harareta tace "Allah ya kiyaye in haifi 'ya irin ki, na haifi fitinanniya
kamarki ai se ince ko sa kamun hannu akayi"
Murmushi Widad tayi tace "ba wannan ba, ɗan koyamin wannan abun da kike yi mana,
idan na iya se in dinga ta yaki"
"Lallai nasan ba iyawa zakiyi ba"
Widad tace "Allah zan iya"
Hari tace "Keɗin ce zaki iya, taɓ"
Widad tace "ni zaki wulaƙanta dan zaki koyamin abu? Shikenan"
Hansai tace "Amarya ba wahala, nima na iya zan koya miki"
Widad tace "Yawwa ummu Sani, thank you very much, May Allah subhanahu wata'ala
bless and unite your Family"
Hari tace "kekam wudas akwaiki da tsirfa, meye hakan kuma kika faɗa? Ke ba zaki iya
magana ba sekinyi yaren Yahudawa, kiyi ta zagin mutane"
Widad tace "aini kona rasa abun zagi, bazan zageki ba"
Hindu tace "Nidai dan Allah amarya ki koyamin turanci, ina son inga na iya"
Widad tace "Shikenan, zan koya miki insha Allah, amma nima zaki dinga koyamin
abunda ban iya ba"
Hindu tace "duk abunda kika ce zan koya miki"
Gwaggo na gefe tana jinsu, tana murmushi, sam Widad bata da girman kai idan bata
iya abuba, zata yi ta magiya a koya mata.
Da Yamma aka kawo manyan Ayaba daga gonar megari, aka raba aka bawa kowa, Widad se
murna take dan tana son Ayaba, ajiyewa taje tayi a ɗaki tace, se Yusuf yazo zasu
raba.
Yau Yusuf se gefin magariba ya dawo gidan, ya gaji sosai. Tunda ya samu ya watsa
ruwa ya dawo ɗaki ya kwanta, salla ma a gida yayi.
Widad tace "Yoseef ga Banana, an bamu daga gonar megari aka cirota, nace in ka dawo
semu raba dan idan na fara ci, bazan iya rage maka ba"
Murmushi yayi yace "bani guda ɗaya kawai ta isa, kici Abunki"
Ta ɗan ɓata fuska tace "saboda me bakaci? In ajiye maka abu kace ba zaka ci ba"
"i don't have appetite, that's why"
Ta kalle shi tace "kamar yaya?"
Rungume ta yayi a jikinsa, ya kwantar da kansa a kafaɗarta yayi shiru.
Widad ta kalle shi da sauri tace "Subhanallah, ai baka da lafiya jikinka yayi zafi
sosai fa"
Yusuf yace "karki damu zan warke insha Allah"
Yana nan rungume da ita, yana ta juya kansa a jikin ta, tana jin yadda jikinsa yake
tsuma jikinsa na ƙara ɗaukar zafi.
Widad cike da damuwa tace "Yoseef jikinka zafi yake sake ɗauka fa"
Kasa magana yayi, sosai jikinsa yake rawa, da sauri ta miƙe ta ɗakko bargo ta rufa
masa.
Haƙoransa se karkarwa sukeyi, ta ɗebo ruwa ta duba kayan ta, ta ɗakko wata vest
ɗinta, ta shiga shafa masa ruwa a jikinsa, amma kamar tana ƙara rura masa wuta,
jifa tayi da abunda take jiƙa masa jikin ta rungume shi ta fashe da kuka.
Share, share and share please 🙏 🙏
(insha Allah ranar 20th ga wata zan fara posting ɗin book 2&3, befi saura page biyu
ba in kammala book 1, nagode ga wanda suka fahimceni, wanda suka zageni ma nagode,
wanda suka shirya siya zasu iya tuntuɓata ta wannan lambar 07063065680 nagode
ƙwarai dagaske, a nunamin ƙauna ta hanyar siyan littafin akan farashi me rahusa,
Akwai garaɓasa ga mutum biyar ɗin farko da suka fara siya, cakwakiya da warwara
suna book 2&3 don't missed it guys sena jiku"
Domin gyara sharhi, ko shawara Ayshercool 07063065680
_*AƘIDATA*_
PERFECT WRITERS ASSOCIATION
(WE AIN'T PERFECT BUT WE ARE ALWAYS TRYING OUR BEST, TO MOTIVATE AND ENTERTAIN OUR
READERS)
https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/
*Story and written by*
_*AISHA HUMAIRA _(Daddy's girl)*_
The experience writer of *ABDUL JALAL** WATA KISSAR.... (SAI MATA) *And now *AƘIDA
TA *
I dedicated this book to my Mum (Malama Nafisat Adam Muhammad) i love you mum
Haƙƙin Mallaka ⚠ : Littafin nan mallaki nane, tun daga sunan labarin zuwa abunda ya
ƙunsa, ban yadda wani ko wata ya sauyamin ko yin Amfani da wani ɓangare na labarin
ba ba tare da izinina ba, Nagode
https://www.wattpad.com/user/Ayshercool7724?
utm_source=android&utm_medium=link&utm_campaign=invitefriends
NOT EDITED (BANYI EDITING BA)
ELEGANT ONLINE WRITER'S
PART1 Page 42_43
Sosai Widad ke rusa kuka, Yusuf kasa magana yayi sedai ya ƙanƙameta a jikimsa, yana
dukan bayanta da sigar rarrashi.
Can ta miƙe cikin hanzari ta fito waje, tana ta goge Hawaye ta samu Gwaggo tace
"Mama Yoseef bashi da lafiya"
A gigice Gwaggo tace "Subhanallah, meya sameshi?"
Maimakon Widad tayi magana seta fashe da kuka, Hanne da take wanke wanke take ta
dire kwanukan ta miƙe tsaye.
Gwaggo tace "Yi shiru, muje muga jikin nasa"
Hansai ma da Hari gaba ɗaya jikinsu yayi sanyi, ɗaki gwaggo tabi Widad ta tarar da
Yusuf yana ta karkarwa a cikin bargo.
Gwaggo tace "Subhanallah, sannu Yusufa Allah ya baka lafiya"
Be iya magana ba se jinjina mata kai da yayi, Hari tace "Yaya meya abunyi yanzu,
ga Malam baya nan yaje taronsu na masu sarauta"
Hansai tace "ina sauran saiwoyin nan, a jiƙa a bashi mana, kan malam yazo asan
abunda yakamata ayi"
Widad ta koma kusa da Yusuf, tana ci gaba da share Hawaye, Hansai tace "Kidena kuka
in Allah ya yadda ze samu lafiya"
Hanne ce ta shigo ɗakin itama, ta leƙa taga yadda Yusuf ke rawar jiki, gaba ɗaya se
taji jikin ta yayi sanyi, a ranta tace 'dama wannan kinibabbiyar zazzaɓim ya kama'
Suka dinga rarrashin Widad, yayin da Yusuf ko iya ɗaga kansa ba yayi, Hansai ce ta
kawo wasu jiƙe jiƙe wai a bawa Yusuf, Widad ta kalli kwanon ta girgiza kai, cikin
kuka tace "A'a wannan abubuwan suna da hatsari ga lafiya, nidai a kai shi Asibiti
kawai"
Hari tace "Asibiti, ai kuwa ya mutu ba'a jeba, dan daga nan kafin aje Asibiti har
mutum ya mutu akai gawarsa ba'a isa ba"
Sake rushewa Widad tayi da kuka tace "In Allah ya yadda baze mutu ba, semun koma
gida tare, dan Allah Yoseef kaji sauƙi"
Gwaggo tace "Hari kina da matsala wallahi, wace irin magana ce haka ba tsari,
kalli yadda kika sake tayar mata da hankali fa"
Hari tace "Wallahi Yaya ni bada wani abu na faɗa ba, misali dai na bata, amma Wudas
kiyi haƙuri, Insha Allah ze warke amma Asibiti kam kafin aje shi sedai idan
amalanke za'a samo a ɗorashi, a fita can wajen gari sannan...
Hansai tace" haba Hari, ana rarrashin ta kina ƙara Sakata kuka, Amarya karki damu
insha Allah za'a kai shi Asibiti bari Malam yazo "
Widad ta riƙe hannun Yusuf tana ci gaba da kuka, Hanne tace " Sannu Allah ya baka
lafiya "
Har magariba sannan megari ya dawo, ya tarar da zancen rashin lafiyar Yusuf, megari
yace " me aka bashi na magani? "
Hansai tace " Na jiƙo tazargade nace a bashi, matarsa tace baza'a bashi ba sedai
akai shi Asibiti"
Megari yace "Kin san mutan birni, basu fiye amfani da irin wannan magunguna namu
ba, Amma yadda za'a kai Yusuf Asibiti nake ji, kafin Aje ya ƙara galabaita, dan
miƙaƙiyar tafiya ce ta gaske"
Widad tace "Yanzu duk garin nan babu Asibiti, ko chemist babu?"
Hindu tace "kamis ɗayane a garin nan, shima a cikin kasuwar yamma da gari yaje,
ba'a buɗeshi se ranar kasuwa"
Dafe kai Widad tayi tana faɗin "Innalillahi wa inna ialaihi raji'un, wane irin
abune haka, gari kamar wannan me ɗauke da al'umma suna rayuwa a ciki, ace babu
gurin shan magani, Yasalam sannu Yoseef Allah ya baka lafiya"
Bece komai ba, se riƙe hannayenta da yayi, da hannu yayi mata nuni da zeyi alwala,
Gwaggo ta bada ruwan ɗumi, Widad ta sirka masa, se a ɗaki yayi alwalar dan ko
tsakar gida baya iya fita, saboda azabar sanyin da yake ji.
A zaune Yusuf yayi salla, Widad idanunta har sunyi jawur saboda kukan da tayi, ta
kalle shi tace "me zaka ci? Kaga tun safe baka ci Abinci ba"
Girgiza mata kai yayi, alamar baya son komai "
Ya nemi guri ze sake kwanciya, Widad tace " kwanciyar nan zata ƙara kashe maka
jikine, ka bari gobe in Allah ya kaimu duk yadda za'ayi za'a san yadda za'a kaika
Asibiti kaji, sannu Allah ya baka lafiya "
Ta ƙarasa maganar idonta fal hawaye.
Murmushi Yusuf yayi, ya kai hannunsa dake rawa fuskarta ya goge mata hawaye tare da
girgiza mata kai, alamar ta dena kuka.
Haka Widad ta raba dare ba tare da tayi bacci ba, data motsa sedai tayi ta shafa
masa ruwa, amma jikinsa kamar wuta.
Tun tana yi da ƙarfinta, har bacci ya mamaye idonta ta kife a gurin tana bacci, a
haka ya janyo ta jikinsa, yana kaɗe mata sauro yayin da ya kasa bacci saboda azabar
ciwon gaɓoɓi da zafin zazzabi.
Da Asuba Widad ta farka, tana buɗe ido tace "Yoseef"
Da Mm ya amsa mata.
"baka yi bacci bane?"
"Nayi ya faɗa a hankali"
"ya jikin naka?"
"Naji sauƙi, samomin ruwan Alwala"
Ta miƙe ta fita waje, ta kawo masa ruwa yayi alwala yayi sallar Asuba.
Gwaggo tayo kunu ta aikowa da Yusuf, kasa sha yayi saboda yana jin jiki, amma
saboda kukan da Widad take, ya karɓa ya sha kaɗan, haka nan ya amayar da shi gaba
ɗaya, nan fa abun duniya ya ishi Widad, ta kasa cin Abinci se kuka.
Megari ya tashi ɗansa, yace "yaje can gaban su, ya aro babur azo a tafi da Yusuf
Asibiti"
Har wajen ƙarfe sha ɗaya Widad tana tare da Yusuf, ko tsakar gidan ta kasa fita, ta
kama yatsunsa tana ja masa a hankali kamar yadda yake mata, sam taƙi cin komai.
Wajen sha biyu na rana Saleh yazo gidan, zuwan Saleh ba ƙaramin daɗi yayi mata ba,
Megari yace "Alhamdilillah, kazo a dai dai, dama Yusuf yana kwance babu lafiya na
aika azo ds babur a kai shi Asibiti, tun jiya ko magana baya iyayi"
A gigice Saleh ya tafi ɗakin su Widad, Hindu da Hanne dasu Gwaggo suka bishi dan a
yanke shawarar ƙarshe game da rashin lafiyar nasa, Saleh yayi Sallama Widad ta
amsa, ya shiga ɗakin ya tarar da Yusuf ya ɗora kansa akan cinyar Widad, idanunta
sunyi ja har sun fara kumbura.
Seda Saleh ya ɗanyi turus dan tabattar da abunda yake gani, wanda ko a wasan
kwaikwayo akace Widad zata yi hakan baze yadda ba.
Ya ƙarasa cikin ɗakin, ya kalli Widad yace "meyasa me shi haka?"
Tsuke Fuska tayi sannan tace "zazzabi yake"
Ya kalli Yusuf yace "Sannu Yusuf, bari inje wannan sedai ko mota a samu, ba zaka
iya hawan babur ba, se inzo akaika Asibiti"
Yusuf be iya cewa komai ba, se jinjina masa kai da yayi, tun a hannun wanda suka
sace su Widad ta jinjinawa jarumta irin ta Yusuf, tunda harta kai ga baya magana to
tabbas ta tabbatar yana jin jiki ƙwarai.
Saleh yace "Ranki ya daɗe bari inje a duba motar ko, se a zo a tafi dashi"
Cikin isa da take nunawa ma'aikatanta tace "ina fatan kaga halin da yake ciki, dan
haka bana buƙatar ɓata lokaci, duk inda abun hawa yake a nemo azo a kai shi
Asibiti, kar ya sake galabaita"
Mamaki ne ya kama su, Yadda Widad take wa Saleh magana cikin isa da gadara, dukda
irin taimakon da yayi musu, ga kuma tarin tazarar shekaru da ya bata, amma take
masa wannan isar haka, se suka ga ta canza kamar ba Widad ɗin dake magana sanyi
sanyi ba.
Saleh ya ɗago ya ɗan ƙurawa Widad ido na wani ɗan lokaci.
Cikin tsawa tace "Kamar na gaya maka bana son ɓata lokaci, ka tsaya kana kallona,
he's condition is getting worse, ko nawa za'a kashe ayi a nema masa lafiya" tai
maganar tana wani sauke wahalallen numfashi.
Cikin harshen turanci Saleh yace "You are under my care now, why are you still
shouting at me like this, so you are still rude up to now"
"My name remains Widad Nasir, Nothing will make me change, No matter what you did
to help me, my policies remains constant, nothing has change"
Cikin rawar sanyi Yusuf ya shiga girgizawa Widad kai alamar tayi shiru.
Sudai mutan gida se binsu su kayi da ido.
Hanne ce taja wani uban tsaki tace "Aikin banza, ace mutum baya ganin girman kowa,
se tsabar wulaƙanci da rashin ta ido"
Da sauri Saleh yace "Ke dawa kike? Idan kika kuma gangancin yin wannan mummunan
furicin akanta duk abunda ya biyo baya ke kika siya, ko dan kin ganta zaune a
gidanku, kin sam wace ita?"
Gwaggo tace "ayi haƙuri dai, naji tsayuwar Babur a waje, ina ga Ila ne ya dawo,
maza jeka ku samo akori kura a kai shi Asibiti"
Haka akayi, Saleh yaje suka hau babur suka tafi nemo akori kura.
Sosai Fahad ya fara missing ɗin Ramlah, dan ba ƙaramin hutawa yake da ita ba, itama
a ɓangarenta tana missing ɗinsa, amma tana so ta tabattar da idan dagaske yana
sonta, kamar yadda Amal ta goranta mata.
Fahad ya ɗau waya ya kira Ramlah, tana ganin kiransa babu ko jan aji ta ɗauka da
rawar jiki "Hello Baby, shine kika watsar dani ko?"
"ba watsar da kai nayi ba, kaine ka watsar dani ka kasa Yimin abunda na tambayeka"
"Ramlah ki gane, baƙi nayi ba fa, kin san halin Daddy, ko zancen baya so na ɗakko
masa, yaƙi saurarata sam gashi bani da lafiya se tunaninki nake, kuma nasan damuwa
ce tamin yawa"
"dan Allah dagaske baka da lafiya? Ai ban sani ba, ohhh Sorry please i understand
you, nasan kana son za kayi iya ƙoƙarin ka, bakomai hakanma nagode sosai my love"
Yayi ajiyar zuciya yace "Never mind baby, yanzu ya za'ayi ne? Inzo mu ɗan fitane
yau ɗin?"
"Ni gaskiya a'a"
Ya ƙara marairaicewa yace "please na, ko so kike ace kizo ga gawata?"
"No bazata kaimu ga haka ba, kazo anjima mu fita, kasan bana son dsmuwarka my one"
"wow that's my only Ramlah, na ɗauka nikaɗai nake sonki na damu dake ai, shikenan
dan Allah ki ƙure a daka, kiyi kwalliyar nan wadda ke narkamin zuciya"
"shikenan karka damu, sekazo"
Sukayi Sallama Fahad yace "akanme zanso a sako wani Anwar, yazo ya hanani rawar
gaban hantsi, ai gara ayi ta tsare shi a can kowa ma ya huta.
Wasa2 labari ya karaɗe gari, an nemi Daula an rasa, abu kamar wasa kusan sati biyu
amma babu ko wanda yaji ɗuriyarsa, Alhaji Munir ne da Alhaji Haruna zaune a office,
sunyi jugum jugum.
Alhaji Munir yace "Nifa gaba ɗaya abubuwan nan suna nema su kwaɓe, wai kamar almara
har yanzu babu ɗuriyar Daula, babu ta wannan shegiyar 'yar tasa me baƙin taurin kai
kamar ubanta, kuma gashi an ɗaga taron kasuwanci komai ya watse, nifa gaba ɗaya na
fara karaya"
Alhaji Haruna yace "wace irin karaya kuma? Ai ba gudu ba ja da baya a wannan
harkar, mun ɓata shekaru da dama akan wannan sabgar, kawai kuma semu sare yanzu,
a'a baze yuwu ba, ni yanzu na fara tunanin anya ba wanine yake mana maƙarƙashiya
ba?"
"Hmm bari kawai, ni kaina nayi tunanin hakan, an tuhumi doctor Sufyan har yanzu
yace be san komai akan ɓatan Daula ba, ga ɗan gidan Hajiya Halima shima da yake
kula da Daula, an tsare shi amma yace besan komai ba, wannan wane irin lamarine
haka?"
Alhaji Haruna yace " Wani abun haushin ma, Halima se shiga take tana fita a sakar
mata ɗanta, tana neman ta tona mana Asiri "
Alhaji Munir yace " Ai duk wata sabga daza'a saka mata a ciki, to tabbas za'a sha
takaici, tun farko nace kar a saka matar nan amma aka ƙi bin shawarata, gashi nan
komai se kwaɓewa yake"
"Haba Munir, kai badan da temakonta ba ai da wata nasarar bamu sameta ba, ta bamu
gudunmuwa sosai, sedai yanzu tana neman ta ɓata rawarta da tsalle"
Alhaji Munir yace "Kai ba wannan bama, kasan se siyar da manyan motocin Daula, tana
ta holansuba ɓoye tana siyarwa, da wasu ƙananan kadarorinsa a ɓoye"
Zaro ido Alhaji Haruna yayi yace "bangane ba, kai waye ya gaya maka?"
"Al'amarin duniya baya ɓuya fa, nima labari naji kuma kana ganin mun fita wayo ne,
kar take kallonmu matar nan mugun wayo ne da ita fa, tsohuwar 'yar duniya ce"
Shiru Alhaji Haruna yayi yace "Amma wannan ta cika muguwa, rabu da ita in tasan
wata ai bata san wata ba, zamuyi magana da Musa, su tattauna da Bukar, muga yadda
zamuyi maganinta"
Se wajen la' asar sannan Saleh suka zo da Mota, sedai akori kuran ta ɗanfi wadda
aka kawo su ƙauyen a ciki, da ƙyar Yusuf ya miƙe Saleh ya riƙe shi, yana takawa a
hankali.
Widad ta zuro Hijjabi tace binsu zata yi, Aikuwa Seleh yace "A'a base kinje ba,
nida Ila da Megari za muje mu kai shi"
Ai nan da nan tasha gabansu ta tsaya ta kalli Seleh tace "wai kai a tunaninka har
nayi yaddar da zaka ɗauke shi ka tafi da shi, bayan ban san inda zaka kai shi ba,
baze yuwu ba duk inda za'aje sedai aje dani"
Saleh yace "look, idan ina da nufin cutar daku, to da yanzu ba wannan zancen ake
ba, ni bani da niyyar cutar ku, Asibiti zamu kai shi"
Megari yace "ki kwantar da hankalinki, Insha Allah babu abunda ze sameshi"
Kunyar Megari da Gwaggo ne yasa Widad fasa binsu, ta kalli Yusuf tace "Allah ya
baka lafiya Yoseef, Allah ya kula da kai kamar yadda kake kula dani"
Ɗagowa Yusuf yayi ya kalle ta, ya sakar mata murmushi suka yi waje.
Wajen ƙarfe Biyar na yamma, Anwar yazo gidansu Ramlah, ya kirata a waya ta fifo,
har tazo falo suka haɗu da Amal, Amal ta kalli Ramlah tace "se ina?"
"zan fita ne" Ramlah ta bata amsa.
Amal ta jinjina kai tace "A dai dinga kula Ramlah, a dinga abunda ƙuda zebi, wannan
gabtalin da kike ba yau ba gobe, ze ɓata miki suna ne"
"Ke dalla sauraramin, bana son shisshigi na gaya miki, ina ruwanki dsni ne? Kinfa
fara isata na gaya miki"
Ta sa kai ta fice daga falon cike ɓacin rai.
Kai tsaye taje ta shige motar Fahad suka fita, Nura yace "Allah wadaran wannan
shegiyar Ramlah me kama da balbela"
Isa yace "bari, iskancin da take mana a gidan nan ko Gimbiyar Daula ba tayi shiba,
kullum suna titi ita da wannan me kai kamar tumatir ɗin"
Murtalah yace "Ai har gara ma Amal da Anwar, Amma da matar gidan nan da Ramlah
Allah ya tsine musu Albarka"
Isa yace "Ameen ya Allah, kalli duk manyan motocin dake gidan nan tabi ta siyar,
kamar dasu tazo se facaka suke da kuɗi, Kai ta wani fannin yanzu bana ganin laifin
'yar masu gida da take musu rashin mutunci"
Murtalah yace "dama Hausawa sunce,' kada Allah ya kawo ranar yabo' duk rashin
mutuncin da take Yusuf se yayi ta kare ta, se yanzu nake ganin gaskiyar zancensa da
yace bata yiwa mutum wulaƙanci seya yi mata laifi"
Nura yace "Mhmm Ai kawai Allah yasaka mana, amma gidan nan ana abubuwa sedai fatan
Allah ya kyauta"
Duk inda Hajiya Sarah tasan zata buga ta buga, amma anƙi sakin Anwar, gaba ɗaya ta
rasa inda zata tsoma ranta, Anbi an toshe duk wata hanya da zata saka a samu belin
Anwar.
Yanzu ma haka ta dawo fakan fakan kamar korarriya, a mugun guje ta shigo da mota
gidan.
Tana shiga ta fara kiran "Ramlah! Ramlah! Ke Amal kuna inane?"
Amal ta fito tace "Mummy Ramlah fa bata nan"
"gidan ubanwa taje?"
Amal tace "sun fita ita da Fahad"
"zanci ubanta ita da Fahad ɗin kuwa, ai tunda ubansa ya watsa min ƙasa a ido, to
tabbas zan masa rashin mutunci, zan nuna masa wacece Halima idan ya manta"
Amal tace "Mummy ɗan uwan naki?"
"Eh shi ɗin, tunda bani da kima a idon sa, nima zan nuna masa bashi da ita a nawa
idon"
Amal tace "Mummy a bi dai komai a hankali, kar azo ayi aika aika"
Hajiya Halima tace "dalla rabu dani, ze gane ni ya taɓa, ai ɗa befi ɗa ba, yasani
yaron nan besan inda aka kaai mutumin nan ba, amma se cemin yake wai in ƙyale doka
tayi aikinta, na zagi dokar shi doka nawa yayi fatali da a rayuwar sa, zega tsiya"
Tai part ɗinta tana cigaba da banbami, kamar wadda ke shirin Zarewa.
Saleh da Yusuf da ɗan megari suka tafi kai Yusuf Asibiti, aka bar Widad da mutan
gida tana ta faman yi musu kuka.
Gwaggo da Hindu ne suka iya zaman rarrashin Widad.
Hari tace wai ke Wudas daga miji na zazzaɓi seki zauna kita mana kuka, memakon ki
masa Addu'a "
Ko kallon Hari ba tayi ba, ta miƙe ta tafi ɗakinsu tayi kwanciyarta tana cigaba da
kuka.
Nurat suka dinga communicatinga da cousin ɗinta akan yadda za'ayi belin Anwar.
Yanzu ma tana kwance akan gadonta hannunta ɗauke da waya, tace" Brother ya ake ciki
ne? Yakamata a gaggauta fitar da Anwar bashi da laifin komai fa"
"Nurat, kince bakyason asan muna ƙoƙarin belinsa, dan haka nake taka tsantsan,
sedai abunda na gano shine tsare Anwar da akayi da manufa akayi shi, idan muka
matsa tabbas za'a gano ke kikasa ayi belinamsa, tunda an san alaƙar dake tsakanin
mu"
Cikin karaya Nurat tace "yanzu Brother babu abunda zaka iyayimin, Anwar be cancanci
ya zauna a gurin nan ba"
Yace "Nurat, lawyan mahaifiyarsa ma yana ta ƙoƙari, amma har yanzu sun hana
belinshi bansan meye abunyi ba, amma meyasa kika damu ya fita bayan kin san munin
Alaƙar dake tsakanin mahaifinki da Daula?"
"Brother, idan akazo batun gaskiya da adalci ba'a kawo maganar alaƙa, an cutar da
Anwar fiye da yadda kake zato, shikaɗai ne akan lamarin rashin lafiyar Alhaji
Nasir, amma kalli abunda ya biyo baya, kodai an masa hakane dan a tozarta shi, ko
kuma wanda ya sace shine yake son wanke kansa ta hanyar sawa a kama Anwar "
Barrister yace "Amma abun da mamaki ta yaya za'a iya sace mutum Attajiri kamar
wannan a gadon Asibiti, kuma babu wani ƙwaƙwaran bayani, abun da mamaki fa"
Nurat tace "Brother, dan Allah idan kana da dama ina son kazo in ganka, ina son mu
tattauna wani zance da kai dan Allah"
Barrister yace "Fara gayamin mana"
"A'a Brother, nidai so nake ina ganka, akwai magana ne a bakina"
"shikenan karki damu, Insha Allah idan ma samu lokaci zanzo insha Allah"
"Yawwa brother nagode sosai"
Ta kashe wayarta ta ajiye, shiru tayi abubuwa da dama suna damun zuciyarta, har
yanzu bata ji alamar labarin inda su Yusuf suke ba, har yanzu bata sake jin wani
magana game dasu ba, ta shiga tuna hirar da suka yi da Amal akan alaƙar Widad da
Yusuf, ji tayi tana gumi dukda sanyin AC dake ɗakin nata, amma ta shiga haɗa gumi,
miƙewa tayi ta tafi toilet da niyyar ta watsa ruwa ta rage damuwa.
Har bayan magariba babu labarin dawowar su Yusuf, nan fa Widad ta sake gigicewa, ta
shiga sintir a gidan nan tana "Allah ka duba Yoseef ka bashi lafiya, Allah ka
bashi lafiya ba danni ba"
Gaba ɗaya tausayin ta ya hana Gwaggo nutsuwa, se aikin rarrashin Widad take, ita
kuwa Hari harta ƙule saboda ganin abun na Widad take kama harda shagwaɓa dan taga
ana lallaɓata, kawai dan mutum yana zazzaɓi ta cikawa mutane gida da ihu.
Dukda Hanne itama tana cikin damuwar rashin lafiyar Yusuf, amma ji take kamar ta
make Widad, gaba ɗaya ta hana mutane sukuni, se wani kuka take se kace wadda akace
ya mutu.
Gwaggo ta zauna tasa Widad a gaba taci Abinci, amma ta gagara ci, Gwaggo tace
"Amarya kiyi haƙuri, kici Abinci kinji, ki cigaba dayi masa Addu'a"
Cikin kuka Widad tace "Mama idan wani abu ya samu Yoseef sanadina ne, ba danni ba
ba dan yasanni ba da duk baze shiga wannan halin ba"
Gwaggo tace "A'a kiyi haƙuri, Allah ne ya ɗora masa, kuma ze yaye masa"
Har dare basu dawo ba, ba Saleh ba dalilinsa, hankalin Widad ya sake tashi, yanzu
take sake ganin Amfanin Yusuf a tare da ita, dare yayi tace bazata iya zama a ɗakin
ita kaɗai ba, Gwaggo tace taje ɗakinta ta kwana, amma Widad fafur taƙi, ƙarshe
Hindu ce tabi Widad ɗakinsu ta tayata kwana.
Har yanzu hankalin Umman Yusuf yaƙi kwanciya, rashin Yusuf a tare da ita ba ƙaramin
abu bane a gurinta, sam rayuwa kawai take ba dan tana jin daɗin rayuwar ba, Yusuf
shine ɗanta ɗaya tilo, yau a sanadin aikinsa yayi nesa da ita, bata san inda yake
ba, gashi a hukumance babu wanda yace mata komai, se Suleiman da yake sintirin zuwa
ganinta yana kwantar mata da hankali.
Wataran a ɗakin Yusuf ɗin take kwana, taita kuka gwanin ban tausayi, tana matuƙar
ɗan nata rabuwarta da shi ji take kamar ta rasa komai na rayuwarta.
Bacci kam Widad ba tayi shi ba, Hindu tun tana rarrashin ta harta gaji tayi bacci,
Widad kam kwana tayi tana Addu'a, Allah ya bawa Yusuf lafiya.
Se washegari sannan Ila da suka tafi kai Yusuf Asibiti tare yazo gidan, Widad na
ganin shi a gigice tace "Ina Yoseef ɗin? Yana ina?"
Ila yace "ki kwantar da hankalinki, kwantar dashi akai, can cikin garin Bauchi muka
kai shi, ya ɗan samu sauƙi Amma yaji jiki fa, kafin muje har Suma ya dinga yi a
mota, amma ya farfaɗo, baza'a sallameshi yau ba"
Hanne dake gefe tace "Alhamdilillah" Gaba ɗaya suka juya suna kallonta, banda
Widad da tace "dan Allah dagaske kake ya tashi?"
Ila yace "kwarankwatsa dagaske nake, dan yace in gaidaki, Saleh na baro a gurinsa"
Se a lokacin Widad ta ɗanji hankalin ta ya ɗan kwanta, harta samu tayi wanka,
megari ma yayi ta mata Nasiha akan wannan kukan data dingayi.
Ramla kam a kusan buge ta dawo gidan nan, Hajiya Halima bata ga dawowarta ba, Amal
ce taga wucewarta kamar tana tangaɗi, binta tayi da sauri ɗakinta, ta tarar tayi
cilli da jakarta da takalmanta ta zube akan carfet tana bacci, Amal tace
"Innalillahi wa inna ialaihi raji'un, Ramla me zan gani haka, meya same ki?"
Ramla kasa magana tayi se ɗaga hannu da take, cikin maye tace "ke.. Keee.. Nace ina
ruwank.... Ki dani neeeee.. Ki fita nace"
"Ramla, shaye2 kika fara ne?"
Shiru Ramla tayi mata, ta cigaba da baccinta.
Gaba ɗaya hantar cikin Amal ya kaɗa, tabbas Ramla shaye2 take, dan maye take yi, ta
tuna yadda take bacci ba ƙaƙƙautawa, da tayi kamar taje ta gayawa mahaifiyarsu, se
kuma ta tuna dama a ƙule take da Fahad da mahaifinsa, muddin ta gayamata za'ayi
ɓatacciya ne.
Kwanan Yusuf uku a Asibiti, gaba ɗaya Widad ta rame, idanunta duk sun kumbura,
jama'ar ƙauyen duk sun san rashin lafiyar Yusuf, dan shike jansu Sallar Asuba da
magariba zuwa isha'iyanzu, kuma ga karatu da yake koya musu suna jin daɗinsa.
Widad ta zuba ido, taga ta ina Za'a dawo mata da Yusuf, dan Ila ya gaya musu ranar
za'a sallameshi.
Gwaggo tasa akayi Abinci, aka dama Fura saboda Yusuf.
Ila ya shigo gidan da Sallama yace "ku kintsa, mun dawo maƙota sun baibaye mota
zasu shigo da shi"
Da ƙyar Gwaggo ta janye Widad zuwa ɗakinta, saboda maza zasu shigo, dukda damuwar
da Widad ke ciki be hana Widad kallon Ɗakin Gwaggo ba, yasha jeren samiru da
fanteku, ga gadonta na ƙarfe me rumfa da mudubi, ginin tsurar ƙasane ɗakin amma
yayiwa Widad kyau nesa ba kusa ba, ga ƙwarya da'akayi wa itama nata jeren, ƙwaryar
ta sha zane mekyau, ga wasu a cikin ragaya, Widad bata taɓa ganin irinsu ba"
Idan ba gizo kunnuwanta suka yi mata ba, to tabbas a cikin muryar mazan da suka yi
Sallama hadda Yusuf. Zumbur ta miƙe tsaye, Gwaggo tace "aikuwa ga muryar ɗana nan,
Alhamdilillah lafiya ta samu"
Kasa jurewa Widad tayi, kawai se gani Gwaggo tayi Widad tayi waje, kai tsaye ta
nufi ɗakinsu, ga mutane maza a ciki, wasu na ƙoƙarin fitowa, haka ta kutsa ta
shiga, ta hango Yusuf yana zaune yana murmushi, sedai yayi rama sosai, yayi haske.
Da gudu ta ƙarasa ta rungume shi, ta kasa magana kawai ta fashe da kuka.
Ɗaya bayan ɗaya suka zame suka bar ɗakin, yau suka ga taɓara, ba kunya bakomai ba
kara tazo ta rungume Yusuf a gabansu.
Suna fita Yusuf ya ha&a hannayensa ya rungumeta shima yace "Queen kin rame, duk
kinyi wani iri"
Maimakon ta bashi amsa se sake kwanciya da tayi a jikinsa tace "Ya jiki ka warke?"
" Na warke amma ina ganin yadda kika rame naji zata dawo"
Hanne ce tayi sallama da kayan Abinci a hannunta, sedai me taga Yusuf da Widad
rungume da juna, take taji jikinta ya hau rawa, bata taɓa ganin hakan a zahiri ba,
sannan ga wani kishi daya taso mata, take ta saki kwanon dake hannunta.
(Gobe insha Allah, zan kammala book 1,Ashirin ga wata insha Allah zan fara book
2&3, tuni an fara biyan kuɗin, kuma zaku iya hanzarta biya ta wannan hanyar dake
ƙasa "
Normal group duka littafi biyun ₦300Idan kuma ɗaya zaki siya ₦200
VIP ₦ 500
Inkuma sena gama zaki sai complete document ₦700
Account NumberAisha Adam 0009450228Ja'iz Bank
Ko katin MTN banda VTU please A turo evidence of payment ta 07063065680
Duk Wanda ya biya yayi min magana ta what's app number ɗina inyi adding ɗinsa a
group ɗin Nagode
Domin gyara sharhi ko shawaraAyshercool
_*AƘIDATA*_
PERFECT WRITERS ASSOCIATION
(WE AIN'T PERFECT BUT WE ARE ALWAYS TRYING OUR BEST, TO MOTIVATE AND ENTERTAIN OUR
READERS)
https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/
*Story and written by*
_*AISHA HUMAIRA _(Daddy's girl)*_
The experience writer of *ABDUL JALAL** WATA KISSAR.... (SAI MATA) *And now *AƘIDA
TA *
I dedicated this book to my Mum (Malama Nafisat Adam Muhammad) i love you mum
Haƙƙin Mallaka ⚠ : Littafin nan mallaki nane, tun daga sunan labarin zuwa abunda ya
ƙunsa, ban yadda wani ko wata ya sauyamin ko yin Amfani da wani ɓangare na labarin
ba ba tare da izinina ba, Nagode
https://www.wattpad.com/user/Ayshercool7724?
utm_source=android&utm_medium=link&utm_campaign=invitefriends
NOT EDITED (BANYI EDITING BA)
ELEGANT ONLINE WRITER'S
PART1 Page 44_45
Yusuf ne yayi saurin ɗagowa ya kalli Hanne, Yusuf yace "Subhanallah, garin yaya
kika ɓarar da Abinci?"
Widad kam ko motsawa ba tayi ba balle ta tashi daga jikin Yusuf. Cikin rawar jiki
Hanne tace "Tuntuɓe nayi shine ya zube, bari in samo in kwashe"Ta juya ta fita da
sauri, tana fita tsakar gida Gwaggo ta kalleta tace "ke meye haka, ba dai Abincin
da nace ki kaiwa mara lafiyan kika zubar ba?"
Cikin inda inda tace "Amm.. Mm... Tuntuɓe nayi shine ya zube"
A fusace Gwaggo tace "kekam kamar mara hankali wani lokacin, kije ki kai Abinci
kawai seki zubar dan shirme"
Hanne ba tace komai ba ta tafi ta ɗau tsintsiya da abun kwashe shara ta tafi gyara
inda ta ɓata musu, cike da zullumin me zata je ta sake tararwa.
Gwaggo tace "Hindu tashi ki duba sauran kunu a ɗakina ki kai musu ba'a bar mara
lafiya da Yunwa ba"
Sukam Maƙota da suka rako Yusuf ne suka dinga jinjina rashin ta ido irin na Widad,
a gabansu ba kunya taje ta rungume mijinta.
Wani da'ake kira da Lado me Jakai yace "to ai kunsan su ba namu ne na nan ba,
jama'ar birni ne baku ga matar tasa bama kamar balarabiya, su sun saba irin wannan
bakomai ne ba"
Ɗayan da'ake cewa Liti yace "Aradu amma ai kunya wani abuce, tunda nasan duk abu
Hausawa ne"
Lado yace "ku kuga haka, su a gurinsu ba wani abun bane ba"
Liti yace "Sumi sumi dashi haka, Amma ta rungume shi ya wani basar abunsa, memakon
ma ya ɗanyi mata tsawa ya hanata"
Wani me shekaru a cikin su yace "Kai waye ya gaya maka suna hantarar matansu,
lallaɓasu suke yi, ni wallahi birgeni ma suka yi"
Kwashewa sukayi da Dariya gaba ɗayansu, harda ƙyaƙyacewa.
Hindu tayi Sallama, da kofin kunu tace "gashi inji Gwaggo, tace dan Allah kuyi
haƙuri Hanne ta zubar da Abincin"
Yusuf yace "bakomai Hindatu hakanma mungode"
Hindu tace "Amarya yau za'a ci Abinci, tunda me gidan ya dawo"
Yusuf yace "Ai naga alama bata cin Abinci ta rame sosai"
Hindu tace "bata ci, Gwaggo taita fama da ita sedai tayi ta kuka, ko bacci bata
iyayi"
Widad ta yatsine baki tace "Akanme zanƙi bacci, in kasa cin Abinci toni ƙiba ma
nayi, ci nake in ƙoshi"
Hindu tayi dariya tace "bari a kirawo Gwaggo a tambaye ta"
Sukayi dariya, Hindu tayi waje, Yusuf ya kalli Widad yace "bani kunun insha dan
inajin Yunwa"
Widad ta miƙe ta ɗakko kofin kunu, tazo ta zauna tana bawa Yusuf, Saleh ne yayi
Sallama ya shigo ɗakinsu.
Kallon Widad yayi yai murmushi yace "Allah me iko, Allah ba yadda be iyaba, wai
Gimbiyar Daula ce ke bawa direbanta Abinci a baki, abun da mamaki"
Banza tayi masa ta cigaba da bawa Yusuf kunu, Yusuf yace "Saleh ƙaraso ka zauna
mana"
Saleh yace "to bari in ƙaraso, ina fatan hankalinki ya kwanta ban gudu dashi ba,
gashi na dawo miki da shi, kuma Alhamdilillah jikinsa yayi kyau"
Shiru ta kuma yi bata ce komai ba, Yusuf yace "Ana magana fa"
Widad tace "me zance?"
Saleh yace "base kince komai ba kam, Malaria me ƙarfi da typhoid ne suka kama
Yusuf, sannan ulcer na damunsa, ga rashin sabo da wasu abubuwa da yake yi, wanda be
saba ba, dan haka shine damuwa gajiya da pressure ga kuma zazzaɓi gaba ɗaya suka
dameshi, amma Alhamdilillah mun samu an ceto miki shi, yasamu sauƙi Alhamdilillah,
na samo Net guda ɗaya, yace min ba guri ɗaya muke kwana ba, dan haka ga guda biyu
nan ke ɗaya shi ɗaya, likita yace 'ya dena zama da yunwa, ya dena barin sauro yana
cizonsa, sannan a kula ya shanye magungunansa"
Widad tace "Aishi zaka gayawa bani ba, tunda ze iya kula da kansa ko"
Mamkine ya kama Saleh, ya tuna yadda ta dinga kuka ranar da zasu tafi da Yusuf,
amma yanzu tana faɗar wata magana daban, shi kansa Yusuf beji daɗin hakan ba, amma
ya basar.
Saleh yace "koma dai menene, Zan zauna zuwa jibi in Allah ya kaimu zan koma, nayi
muku siyayya wajen gobe in Allah ya kaimu za'a kawo muku"
Yusuf yace "Mungode sosai da ɗawainiyar da kake mana, Allah ya saka da alkhairi,
Allah ya biya ka"
Saleh yace "Ameen"
Ita kuwa madigar, miƙewa tayi tai waje abunta, ba tare da ta sake tanka musu ba.
Amal na kwance akan gadonta tayi shiru sosai take tunani, tayi zurfi sosai a
tunani, Mummy ta shigo ɗaki Amal ta tarar a kwance tayi shiru tana ta tunani"
Mummy tace "ke meye haka? Tunanin me kike yi? "
Amal ta ɗan tura baki tace "lafiya ƙalau Mummy"
"Amma kika zauna kika yi shiru haka? Kina ƙarama dake kike tunani haka"
"Mummy ina ɗan zancen zuci ne kawai"
"to idan waccan uwar baccin ta tashi ki gaya mata zan fita, ni na rasa gane kan
wannan baccin banzan dat take yi sekace wata kasa"
Ita dai Amal bata gayawa Mummy abunda Ramlan keyi ba.
Bayan fitar Mummy kwanciya Amal ta sake yi tana cigaba da tunani, kuma ba tunanin
kowa take ba face Yusuf, tun tana dannewa yanzu abu yavfara gagara, bata iya ɓoyewa
sam, Bata iya cin Abinci ba tayi zaton ƙaunar Yusuf haka tayi mat wannan mugun
kamun ba, gaba ɗaya yanzu haushin samarin ta take ji, gani take duk cikinsu Yusuf
yafi su komai dukda Kasancewarsa talaka, amma ya haɗu gashi nutsatse babu Hayaniya
a tare da shi, ji tagi inama a sako Yusuf a riƙe Widad, dama itake hana ta rawar
gaban hantsi, dan ta rasa wace irin Alaƙace ke tsakanin su, Widad bata da yadda
kamar me, bata yadda kowa ya raɓe ta ba, amma ta yadda da Yusuf ya shiga jikinta
sosai da sosai, Yusuf yasan abubuwan dasu da suke zaune da ita basu sani ba.
"Ke Amal! Tun ɗazu nake miki magana amma se kace wata kurma, kinmin shiru"
Firgigit Amal ta kalli Ramlah, tayi ajiyar zuciya tace "Meye nayi min ihu kuma?"
"na dole inyi miki ihu ba, tun ɗazu nake kanki ina magana amma kinyi shiru"
Amal ta miƙe zaune ta kalli Ramlah tace "ban san kin shigo abane, dana san kin
shigo ai zanyi responding"
"Wai nikam wane irin tunani haka kike yi?"
"Ramlah tunanin komai ma inayi, Abubuwa da yawa sun dameni, Amma Ramlah jiya fa
maye kike kika dawo"
"Maye kuma?"
"Eh mana, wallahi jiya a buge kika dawo gidan nan, Mummy kuma a ƙule take dake,
fitar da kikayi da Fahad"
Ramlah ta ɗan ɓata rai tace "ba wani maye da nake, na gaji ne kawai, sannan me
Fahad ɗin kuma yayi?"
Amal tace "Eh to, kin san sunyi faɗa da ɗan uwanta akan belin Yaya Anwar, shiyasa"
"to kuma shine seya shafi Fahad, laifin meyayi? Kuma shima bakiga yadda yake ƙoƙari
akan lamarin ba, amma kin san halin babansu da kafiya"
Amal tace "wani tabacci kike da shi na yana ƙoƙarin nan, nifa kallon Fahad ɗin nan
kawai nake, bakin maƙaryata ne dashi"
Ramlah tace "zaki fara ko? Karki kusakura kici masa mutunci"
Amal tace "ke niba wannan ba, nifa naji tana cewa za'ayi uwar watsi idan ba'a fito
mata da Yaya Anwar ba, karta yi wani abu daza'a zo ana da nasani daga baya"
Ramlah tace "kuma fa hakane, kin san bata iya fushi ba, bari inje ɗakinta in
sameta"
Amal tace "to ai ta fita"
"ta tafi ina?"
"Nima ban sani ba, ni dai tacemin zata fita"
Ramlah tace "Shikenan, bari inje kitchen in samu ɗan abunda zanci, da yamma zanje
gurin wani birthday na 'yar gidan IG na ƙasa, na tura a ɗakkomin wata sabuwar motar
megidan nan daga kamfani, da ita zanje, kin san gurine na manyan yara fa"
Amal tace "Mhmm yakamata kam"
"waini meke damunki ne Amal, bakya walwala fa"
"Ramlah wace walwala zanyi? Yaya Anwar a rufe, hankalin Mummy yaƙi kwanciya, ga uwa
uba wallahi Ramlah Ji nake kamar inyi me saboda rashin Yusuf, na shiga damuwa
wallahi ko bacci na kwanta yanzu mafarkinsa nake yi, na rasa inda zan saka raina,
tun ina iya dannewa yanzu na kasa "
Wani uban dogon tsaki Ramlah taja tace " Aikin banza, shine zaki kashe kanki saboda
wannan jakin"
"Karki sake kiransa da Jaki, Inda wanda za'a kira Jaki to tabbas Fahad ne, dan
kunnuwansa ma irin na jakaine ga ƙaryar tsiya".
Haka abun nasa ya koma faɗa, ƙarshe sukayi baran Baran.
Widad ta fita tsakar gida, ta ƙarasa inda Gwaggo take tana murmushi, Hari tace "ohh
ni Harira, se wangale baki kike miji ya dawo, kin ware"
Widad tace "Toke ya kika gani? A garin nan banda Allah se shi na sani, idan
lafiyarsa ta taɓu akwai damuwa sosai"
Gwaggo tace "ƙyaleta Amarya, zolayarki take"
Widad tace "Mama, dan Allah abun nan na ɗakinki sunmin kyau sosai"
Gwaggo tace "me fa?"
Widad tace "kwanukan nan da kika shirya a ɗakinki, sunyi kyau sosai fa"
Gwaggo tayi murmushi tace "Widad kenan, kayan Su Samira da fanteka kenan, mu dasu
mukeyin adon ɗaki"
Widad tace "Masha Allah, gaskiya sunmin kyau sosai Mama"
Can ta hango bulugari, a gefen Gwaggo zata kaɗa miya.
Widad tace "ya sunan wannan Mama? Wanda kike juya miya dashi"
Gwaggo tace "Bulugari kenan, dashi muke kaɗa miya"
"Mama wannan tunkunyar naganta baƙa sosai"
Gwaggo tayi murmushi tace "wannan itace Talle Amarya, tukunya ce ta ƙasa, muna
girki a cikinta, miya tafi zaƙi da daɗi Sosai"
Widad tayi murmushi tace "taɓ Mama duk ban san wannan abubuwan ba, ban taɓa ganinsu
ba"
Gwaggo tace "hakane dama, tunda ba kuyi rayuwar karkara ba ba lallai ki sansu ba,
bari inje ɗaki in ɗakko abun kaɗi"
Gwaggo ta tashi ta tafi, tana tafiya Hanne tayi tsaki tace "Aikin banza mutum ya
zauna yaita ƙarya, mtseww aikin banza dana wofi, wai bata san bulugari da fanteka
ba"
Widad ko waigawa ba tayi ba, tai shiru abunta, Hari tace "wato Wudas kinfi jin
tsoron Hanne, ta gayamiki duk abunda data ga dama, kiyi ƙus amma da nice da tuni
kim hayayyaƙomin"
Wani irin kallo Widad tayi wa Hari, nan take cikin Hari ya kaɗa, ganin wani irin
kallo da Widad tayi mata, se taga kamar ta canza gaba ɗaya daga kamaninta, ba shiri
Hari taja bakinta ta tsuke.
Saleh ya kalli Yusuf yace "Sannu Yusuf, gaskiya kana fama, yanzu haka kuke zaune?
Tana maka wannan gadarar da jin kan, bayan taimakonta kake"
Yusuf yayi murmushi yace "lafiya ƙalau muke zaune da ita, duk wannan abubuwan bata
Yimin, ƙalau muke zaune Alhamdilillah"
Saleh yace "kaga nifa bana son wannan kawaicin naka, kalli yadda take wani bintsire
bintsire, tana cin magani, na zata tuni ta dena wannan halin nata?"
Yusuf yace "Kai da ita ta baka amsar wannan tambayar, Amma nan ma shigo ka tarar
tana bani Abinci ai"
Saleh yace "kuma fa hakane, lallai kai ɗan baiwa ne kuma na musamman Yusuf, wannan
yarinyar me Azabar taurin kai, amma take kula da kai haka, ta yadda ka shiga
jikimta gaskiya abun da mamaki, kayi namijin ƙoƙari fa"
Yusuf yayi murmushi yace "Haka lamarin ubangiji yake, yanzu ya jikin mahaifinta?"
Saleh yayi shiru da alama jikinsa yayi sanyi yace "labari mara daɗi Yusuf, yanzu
ma badan ka tambaya ba bazan gaya maka ba"
A rikice Yusuf yace "Subhanallah, meyafaru kuma?"
Saleh ya gyara zama ya waiga yaji babu motsin kowa sannan ya waigo ya kalli Yusuf
yace "An sace Daula akan gadon Asibiti"
Dafe ƙirji Yusuf yayi yace "Innalillahi wa inna ialaihi raji'un, kamar yaya?"
Saleh yace "kaima dai ka tambaya, abun kamar almara, Kasan tunda yake rashin lafiya
Anwar ne kawai yake sintirin jinyarsa, matarsa da sauran yaran ba ruwansu dashi,
daga ya ɗan fito daga ɗakin, ya koma aka nemi Daula aka rasa, yanzu haka an kama
Anwar da me Asibitin ana tuhumarsu, yau sati uku kenan sun tsare "
Dafe kai Yusuf yayi ya shiga murza goshi, wannan wane irin bala'i ne? Duk yadda
yake zaton lamarin ya wuce tunaninsa, wane irin tashin hankali ne haka?
Saleh yace " ka kwantar da hankslinka fa, ban gaya maka dan ka ɗaga hankalinka ba,
sedai ka tayata da Addu'a, sannan karka bari ta sani"
Yusuf yace "kuma ana bincike akan lamarin, ba'a gano inda yake ba?"
Saleh yace "kai dai ayi sha'ani, har yanzu babu Labari"
"Amma naji kamar kace kasan suwaye ke wannan abubuwan"
Saleh yayi murmushi yace "kaifa jami'in tsarone, kuma kai aka bawa wannan aikin na
binciken, zuwa yanzu ai nasan ka samu haske akan binciken da kayi"
Yusuf yace "kamar yaya kenan?"
"Kana nufin baka gane me nake nufi ba? Ai shikenan mu bar zancen, kar tazo ta same
mu muna maganar"
Yusuf yace "Ya Ummana kuwa Saleh?"
"tana nan lafiya, Suleiman yana kula maka da ita"
"Amma Saleh, Akwai wani abokin aikina Abbas, babban Abokina nane, yana Ibadan akan
aiki, ko Suleiman yayi maka maganrsa, nasan idan yasan ina nan Abbas ze shiga
damuwa ina da tabbacim se yazo nan"
Ƙura masa ido Saleh yayi, ya ɗanyi shiru sannan yace "gaskiya ba muyi maganar wani
da shi ba, kai dai kunci gaba da haƙuri, komai ze wuce kamar ba'ayi ba Insha Allah"
Yusuf yace "Allah yasa"
Saleh yace "bari in ɗan fita waje, in zaga gari"
Yusuf yace "bari in bika bana son zaman gidan ne, gara in fita in ɗan tattaka"
Saleh yace "kar kasa matarka tamin tijara fa"
Yusuf yai murmushi yace "bakomai"
Suka fito shida Yusuf, Can Saleh ya hango Widad a kusa da Gwaggo suna hira, Widad
ta maida hankalinta sosai akan Abunda Gwaggon take yi.
Saleh yace "iko se Allah, da a mafarki aka haskomin wannan abun ze faru, zance
sharrin mafarki ne"
Widad ta ɗaga ido ta hango Yusuf, ya fito da alama fita za suyi, Widad tace "ya
dai, naga ka fito, ina zaka haka?"
"You leave alone in the room, am so boring, Saleh is going out, so i feel like to
follow him"
Widad tace "gaskiya ban yadda ba, ka koma ka huta in kuma ka faɗi fa?".
"Bazan faɗi ba insha Allah, ina son in ga gari ne kawai"
Widad tace "Shikenan, kar kayi nisa dai"
"As you wish your majesty"
Saleh jinjina kai kawai yayi, yayin da Yusuf yake jin wani irin matsanancin
tausayinta, ko ya zataji idan taji labarin mahaifinta ya ɓata shima?.
Haka yabi Saleh suka fice.
A harabar gidan su Nurat kuwa, Nurat ce zaune a ɗaya daga fararen kujerun dake
harabar gidan, ita da Barrister Khalil cousin ɗinta, teburin gabansu ɗauke da lemu
ka da kuma kofunan glass.
Barrister Khalil yace "kince kina son ganina, gashi nazo amma kin kasa cemin komai"
"Brother, aini sam ban san ta ina zan fara maka bama, na rasa me ya kamata ince
maka"
"Ki nutsu, ki gayamin komai a hankali, an fahimceki Insha Allah"
Ta ɗanyi ajiyar zuciya sannan tace "brother, game da maganar da mukayi da kaine na
belin Anwar" Se kuma tayi shiru.
Khalil yace "Mhmm ina jinki, gayamin ke nake sauraro"
"Barrister, kai ɗan uwana ne, kona ɓoyewa kowa wani abun, kai bazan ɓoye maka ba,
amma ina son maganar ta tsaya iya nida kai, ko Kasan akwai hannun mahaifina a cikin
abubuwan da suke faruwa da Alhaji Daula?"
A hankali Khalil ya zare glashin fuskarsa, ya kalle ta yace " kamar yaya? Ban gane
me kike nufi ba"
'Nasan abun ze baka mamaki, amma kasan Alhaji Daula me silar ɓacin siyasar
Mahaifina? "
"Eh na sani, nasan da wannan"
"Mahaifina yayi alwashin ko ze mutu se ya rama abunda Alhaji Daula yayi masa, ya
haɗa kai da wasu manyan abokan kasuwancin Alhaji Daula, suna ƙoƙarin ganin bayansa,
zancen da nake maka, da saninsa aka sace 'yar gidan Daula da direbanta"
Hankici ya ɗakko a aljihunsa ya share gumin fuskarsa yace "wani tabbaci kike dashi,
akan wannan maganar da kike yi"
"Brother, nikaɗai ce sheda, se Mummy amma kasan halin Mummy da tsoro, ba zata taɓa
bamu goyon baya ba, yanzun kaima ma gaya maka ne, saboda yadda abun ke cin
zuciyata, na rasa wa zan gayawa inji daɗi a raina"
Khalil yayi shiru sannan yace "am sorry to say, Nurat mahaifinki gaba ɗayansa
zuciyarsa babu Allah a cikinta, yanzu muddin ya gano mum sam me yake yi to tabbas
ze ɗau mataki a kanmj, nasan shi ba tun yanzu ba"
"Nasani brother, nikaina tunda naje na duba Daula a Asibiti ya samun takunkumi, ya
hanani fita, rannan dana fita baka ga yadda ya shaƙeni ba kamar ze kasheni"
Khalil ya jinjina kai yace "yanzu Addu'a zamu ci gaba dayi, mahaifinki yana da
goyon bayan manya sosai, dan haka babu wanda ze tsaya ya ɗau mataki, sedai muyi ta
addu'a"
Nurat tace "hakane Brother, but am so much disturbed wallahi"
"Kakri damu, ki kwantar da hankalinki, Dukda haka zan duba inga me zan iyayi akai"
"Shikenan nagode sosai brother, Allah ya ƙara ɗaukaka"
"Ameen ya Allah karki damu kinji, ki kwantar da hankalinki, komai zezo da sauƙi"
Haka sukka cigaba da tattaunawa.
"Alhaji Musa wai yanzu duk kuna kallo haka ɗana ze cigaba da zama a prison? Ba
zakuyi komai akai ba? Na gaji da yawon da kukemin da hankali fa"
Alhaji Musa yace "Ni yanzu me kike son inyine? Nifa bani na sa aka kama ɗanki ba,
me kike so inyi?"
"Idan ba ku kuka sa aka kamashi ba, amma kuna da ƙarfin da zaku sa a sakarmin shi
aiko? Wane irin abune haka, se zarya nake a tsakanin ku, amma kowa da kalar rainin
hankalin daze mun"
"Kinga saurara, ni babu abunda zan iyayi akan wannan al'amarin, wannan babban case
ne da yake buƙatar bincike, idan bashi da laifi zasu sake shi fa"
Hajiya Halima tace "Shikenan nagode sosai da abunda kukayi min, wato na gama yi
muku amfani, zaku watsamin ƙasa a ido, zaku ga abunda zanyi"
Ta juya fuuu tayi waje kamar zata tashi sama, tana tafe tana banbami, ofishin
Bulama ta tafi, ta tarar yana shirin fita, ya kalle ta yace "Halima lafiya kuwa?"
"karka ƙara tambaya ta ko lafiya, lafiyar kenan kana nan hankalinka kwance, ni kuma
nawa a tashe ko baccin kirki bana samu, na zama kamar mahaukaciya, ɗana yana can a
tsare, kun nunamin halin ko in kula, kun nuna baku damu da halin da nake ciki ba"
Bulama yace "Nikam Halima kina bani mamaki, ɗanki fa ɗana ne, nima nawa hankalin
ba'a kwance yake ba, muna iya ƙoƙarin mu, amma abunda ake gayamana shine, ana
zargin da sa hannun Anwar a wannan abu daya faru, kuma duniya ta kasa kunne taji
wani mataki za'a ɗauka, me kike tsammani idan aka ji da sa hannuna aka saki Anwar?
"
" Kaga sauraramin dan Allah, bana son maganar banza data wofi, na sani ka sani
Anwar baze iya aikata laifin da ake tuhumarsa ba"
"A'a karki shedeshi, ba'a shedar ɗa a zamanin nan"
"Bulama, na gama magana da kai, zanje inyi abunda ya dace kawai"
Bulama yace "abunda ya dace kamar yaya?"
"Ka zuba ido zaka gani, bar ganin kai ɗan uwanane zan iya yin komai akan ɗana, na
gaya maka"
Bulama yace "hmm kibi a sannu dai, kin san ido ya fara dawowa kanki yadda kike
wadaƙa da wasu daga cikin kadarorin mijinki? Mutane sun san me kike aikatawa, ki
sani tsalle ɗaya ke kai mutum rijiya, amma se yayi dubu be fito ba"
Tsaki tayi, ta ɗau mukullin motarta tace "wannan kuma kai ta shafa bani ba, nasan
abunda nakeyi"
Tai waje abunta, tana fita Bulama ya ɗau waya, ya danna yasa a kunnensa yayi shiru,
can kuma yace "Yawwa kana jina da kyau, ina son ku ƙara tsananta tsaro da sa ido
akan yaron nan Anwar, under no circumstances zaku bada belinsa, ku matsa se ya faɗi
inda Daula yake, dan uwarsa ba abunda ba zata iya ba"
Daga cam ɓangaren yace "Ok sir an gama Insha Allah"
Bayan barin Hajiya Halima Office ɗin Alhaji Musa, su Alhaji Haruna suka dira, dukda
haushinsu da Musa yake ji, amma ya maze ya sakar musu fuska yace "kun san yanzun
nan wannan mahaukaciyar ta bar gurin nan"
Alhaji Haruna yace "wa kenan?"
"Hajiya Halima mana, tazo nan tana ta banbami, wai munƙi saka baki a sakar mata ɗa"
Alhaji Munir yace "ƙyale wannan mahaukaciyar, ni wata shawara nazo mana da ita"
Suka tattara masa hankalinsu, suna saurarensa "Abunda nake gani shine, mu samu
lauyoyin Daula, mu siye su, su saka hannu su fitar mana da wasu daga kadororinsa, a
sasu a kasuwa a karya su, sannan ayi takaddun ƙarya, muce muna binsa zunzurtun
bashi"
Alhaji Haruna yace "kayi magana mekyau, sedai abunda ka manta shine, lawayoyinsa
basu san kan dukiyarsa kamar yadda wannan koɗaɗiyar 'yar ta sani ba, ta san komai
tasan inda komai yake"
Alhaji Munir yace "to tunda yanzu ba ita babu ubanta aise muyi yadda zamuyi mu
kwashi rabonmu, ko so kuke se wannan mahaukaciyar matar tasa ta ƙarar da komai ita
da' ya'yanta? A ɓoye fa se saida kadarorinsa sukeyi, haka zamu zauna mu zuba ido."
Alhaji Musa ya nisa yace "duk naji ta bakin ku, kuma kowa yazo da magana me kyau,
zamu jarraba lawyoyin suma, danni yanzu kuɗin tsayawa takara nake nema"
Kallonsa sukayi gaba ɗaya sukace "kamar ya tsayawa takara?"
"kamar yadda na gaya muku, bazan zauna bani ga tsuntsu bani da tarko ba"
Alhaji Haruna yace "hala ka manta da baƙin fentin da kake da shi, a dalilin Daula?"
"ina fa na manta, sedai a ƙasar nan indai kana da kuɗi ba abunda baze yuwu ba"
"Amma baka ganin hakan, ya saɓa da Yarjejeniyar mu, idan kayi haka kamar ka zame
daga cikinmu ne, kuma me zaka cewa Bukar?"
"Bukar ubanane, ko haifata yayi? Ba gudu ba ja da baya, ina tare da ku amma tabbas
zanyi takara"
Gaba ɗaya Yusuf ya fara jin kunyar mutanen da yake ja salla, musamman idan ya tuna
abunda Widad tayi a gaban su, tunda su hakan kamar baƙon al'amarine a gare su, haka
nan ya ɗan dinga basarwa, sukayi sallar magariba da isha'i suna ta sake duba shi.
Widad jin shiru Yusuf be shigo ba, yasa ta fito tsakar gida ta samu wani ɗan gidan
Hansai tace masa "kaga ɗan jeka waje ka cewa Yoseef in jini nace, baze dawo ba se
sauron ya sake cizonsa yazo ya kwantamin?"
Gwaggo dake alwala tace "A'a kul kaje ka faɗi haka, kace tace 'dan Allah ya shigo
gida, kar sauro ya kuma cizonsa'"
Widad tace "to ai kusan abunda na faɗa kika maimaita"
Gwaggo tace "A'a ke naki umarni da kashedi kika yi, aishi miji abun lallaɓawane da
tattalawa, ki kalli yadda kika damu da bashi da lafiya, ki dinga masa magana da
girmamawa kinji Amarya, yana da kirki mijinki, kema ki dinga tausasa harshen ki a
kansa"
Widad tace "To Hajiya Mama"
Gwaggo tace "ni a Hajiya, to me rai baya fidda rai da rahama, amma abun da wuya"
"Insha Allah indai da rai da rabo, zaki je saudi Arabia in dai Allah be ɗau rayuwar
wani daga cikin mu ba, idan muka koma gida lafiya zaki je ƙasa me tsarki"
Tsaki Hanne tayi tace "san a sani, ji wata ƙarya kuma da son nuna iyawa, karma kisa
rai ana gayamiki gaibu"
"Ke! Ki kiyayeni, dake muke taɗin, ina ruwan ki Hanne ki kiyayeni fa"
Widad ta juya kawai ta koma ɗaki, ta ɗakko ƙaramar fitilarsu ta kunna, batirin ma
ya fara sanyi.
Ta zauna tayi shiru tana tunani, sallamar Yusuf ce tasa ta ɗago ta amsa masa, yaje
kusa da ita ya zauna, daya kalleta se tausayinta ya kama shi yace "gani naji ance
kina nemana"
"shine tun la'asar kaƙi dawowa, se sauro ya kuma cizonka ko?"
"Ai na warke, Alhamdilillah" "dan ka warke shine se kaje, ka kuma kwaso wani
zazzaɓin, kazo ka ɗagamin hankali"
"Insha Allah na warware ai, ance jinina ma yayi ƙasa, dole in dinga cin ganyayyaki"
"Sannu kaji jiki ai"
"Gaskiya muje ki dawomin da jinina dana baki"
"wai jininsa, jinin naka ma duk malaria ya ƙara samun zazzaɓi, zan biya ka jinin ka
harda riba ma"
Dariya Yusuf yayi yace "ni iya nawa nake so, bana son naki danni bana son jinin me
taurin kai"
"kai kai, nice me taurin kai? Zaka ga taurin kai'
Kwanciya yayi a kafaɗarta yace " dan Allah a sake rungumeni mana, i need your body
warm "
Ture shi tayi tace 'kaje kaji ɗumin bargo mana"
Cikin kwantar da kai yace "A' a ni gaskiya naki nake so, ai naga yau ke kika
rungumeni, idan muka koma gida sena gayawa Ummana, nima ince kina rungumeni"
Widad tace "ai kai ka fara bani ba, ka koyamin abunda ban iya ba"
Dariya Yusuf yayi yace "nayi mamakin yadda kika damu da rashin lafiya ta My queen"
"A cikin AƘIDATA babu butulci, bana manta alkhairi, bazan taɓa manta wahalar daka
sha saboda rayuwa ta ba, idan na nuna halin ko in kula ga kafiyarka to tabbas banwa
kaina adalci ba, dukda ana faɗin bani da kirki, banj da mutunci amma bana manta
alkhairi"
Yusuf yace "waye yace miki baki da kirki, kina da kirki uwaɗakina"
"Hmm yoseef kenan, ka dena kareni danka burgeni, amma nasan bani da kirki kamar
yadda da yawa mutane ke faɗa"
"ba kareki nake dan na burgeki ba, ina faɗa miki gaskiya ne kawai, amma kince bakya
manta alkhairi, amma meyasa bakwa jituwa da Saleh, dukda irin taimakonmi da yayi?"
"saboda bana yafiya ga mutane ma'abota fuska biyu, da fari mahaifina ya yarda da
shi da ɗam uwansa, amma ya koma ɓangaren maƙiyanmu, yanzu ya kuma dawowa ɓangaren
mu, wani tabbaci muke dashi na muma baze sake juya mana baya ba? Duk yardar da
nayiwa mutum, duk girman Alkhairin da yayumin, muddin yaci amanata koya min ƙarya
to tabbas ze shafe dukkan alkhairansa a idona, bana yafewa mayaudari da maƙaryaci
ko me fuska biyu, wannan itace AƘIDATA!!!
TOFA! Alhamdilillah nan na kawo ƙarshen kashi na ɗaya a littafin AƘIDATA,
Ɗanɗano daga Littafi na biyu
(idanunta sunyi jawur, kamar wadda aka zubawa barkono saboda kuka, ta sunkuyaf da
kanta ta shafi ciknta, cikin zubda hawaye tace "wace amsa zan bawa abunda yake
cikina, idan har ya girma ya samu labarin mahaifiyarsa taje kotu ta bada sheda akan
mahaifinsa an kai shi prison, kaicona haɗuwa ta da Yusuf ta zame masa babbar
ƙaddara a rayuwarsa, ya sadaukar da rayuwarsa don in ganta tawa, amma maƙiyana sun
na ƙoƙarin cin galaba akanmu, abun da basu sani ba shine...............)
Karku bari a baku labari, saƙar labarin mukayi a na farko, tufaka da warwarar gami
da cakwakiyar suna littafi na biyu dana uku, anan gwaramar take
SHINE MEYE LABARIN YUSUF? MEYE LABARIN WIDAD? WAYE MAMALLAKIN ABUNDA AKE NEMA A
HANNUN WIDAD? MEYE ABUNDA AKE NEMAN? WAYE YA SACE DAULA? SHIN ZASU BARO ƘAUYEN NAN?
ZASU KOMA GIDA DA WANNAN AUREN? YA ZATA KAYA TSAKANIN WANNAN MANYAN ALHAZAI? YA
WIDAD ZATA YI IDAN TA GANE YUSUF JAMI'IN TSARO NE YA MATA ƘARYA?
Akwai cakwakiya me tarin yawa karku bari a baku labari, ga masu buƙatar siya
Normal group duka littafi biyun ₦300Idan kuma ɗaya zaki siya ₦200
VIP ₦ 500
Inkuma sena gama zaki sai complete document ₦700
Account NumberAisha Adam 0009450228Ja'iz Bank
Ko katin MTN banda VTU please A turo evidence of payment ta 07063065680
Zan fara posting ɗin littafi na biyu dana uku, ranar 20 ga watan October
Masu neman complete zasu sameshi ranar biyar ga watan November insha Allah
Domin gyara, sharhi ko shawaraAyshercool. 07063065680
Nagode da ƙaunar da kuka nunamin
: LITTAFIN KUƊI NE, BA DANNI BA DAN ALLAH KI SIYA KAFIN KI KARANTA BA DANNI BA DAN
ALLAH.
LITTAFI NA ƊAYA KYAUTA NE, WANNAN NA KUƊI NE
NORMAL GROUP
₦300
VIP ₦500
A TURA TA WANNAN ACCOUNT ƊIN 0009450228
AISHA ADAM
JA'IZ BANK
46_47
shiru Yusuf yayi yana kallon Widad, yayin da yaji gaba ɗaya hantar cikinsa ta kaɗa
jin abunda Widad ɗin ta faɗa, ta kalleshi tace
"Ya naji kayi shiru ne? Akwai matsala ne?"
girgiza mata kai yayi yace
"A'a babu komai" Widad tace
Kasa motsawa yayi daga inda yake, balle ya aikata ɗaya daga cikin abunda tace, sake
kallonsa tayi tace "wai ko dai jikin ne?"
" to ai gani nai duk ka wani koma so silent, shiyasa nayi zaton ko jikin ne, ka
tashi zan kwanta "
Yusuf ya miƙe, ya bata guri ta gyara shimfiɗar ta ta kwanta, yayin da ya koma gefe
yayi jugum kamar wanda aka gayawa saƙon mutuwa.
A ƙoƙarinsa na kaucewa zargi daga Widad, ya miƙe ya ɗakko Abincin da niyyar ya fara
ci, Amma gaba ɗaya ya ya kasa, tunani burjik a zuciyar sa, ga labarin da Saleh ya
gaya masa, ga kuma itama abunda ta faɗa masa yanzu, ashe dai da daru a gaba, ko
wane irin hukunci zata yi masa idan ta gano shi jami'in sirrine? Gashi zuciyarsa ta
riga ta gama kamuwa da tsananin ƙaunar Widad, yana matuƙar jin sonta a ransa, a
yanzu haka dama yana ɗar ɗar, saboda yasan bashi da tabbacin idan suka koma gida
Widad ta cigaba da zama da Auren sa, dukda a yanzu yana ƙoƙarinya jarraba Widad
yaga ko tana son shi, a ƙaddara ma ta yadda da Auren, su cigaba da zama tare, waye
yasan Aure suka yi, Saleh ne kawai sheda ta yaya zasu fuskanci mutane suyi musu
bayanin wannan rikita rikita?.
Nan da nan wani irin gumi ya shiga tsasttsafowa Yusuf, lallai akwai ƙura a gaba,
kasa cin Abincin yayi, dama gashi bakinsa babu ɗanɗano saboda zazzaɓi, dan haka ya
ajiye Abincin a gefe ya nemi guri ya kwanta, sedai kamar yadda beyi tsammani ba,
bacci ya ƙauracewa idonsa se tunani, yanzu meye mafita? Ta ina ze tunkari Widad
yayi mata bayanin waye shi, dan kamata yayi ace shi ya gaya mata ba wani ba.
Haka nan jiki a sanyaye ya cigaba da tunani, ya daɗe a zaune ba tare da ya kwanta
ba, yana ta saƙawa yana warwarewa.
Da sauri ya dawo daga tunanin da yake yace "Babu komai karki damu"
"Nasani dole zakayi tunanin gida, nasan baka jin daɗin zaman garin nan, ko baka
faɗa ba zaman garin nan ba daɗi, Amma ni ta wani ɓangaren rahama ne a gare ni, bana
fargaba ko tashin hankali saboda maƙiyana, ina matuƙar jin daɗin karamcin da
mutanen gidan nan suke min, dukda yadda zaman garin ke bani wahala, amma karamcin
su da goyon bayanka na ƙara bani ƙwarin gwiwa, tabbas duk wani motsi da zanyi ina
tunanin Daddy, ina tunanin wani hali yake ciki, me yake yi? Nasan ina ransa, sedai
ina masa Addu'a zuwa lokacin da Allah ze kawo ƙarshen wannan abun in koma gida,
kaima kayi haƙuri nasan duk nice silar shigar ka wannan halin"
Ta ƙarasa maganar cikin damuwa. Yusuf yace "bana dana sanin kasancewa ta dake anan,
saboda karamcin mahaifinki da yadda da yayi dani beci ace na bar 'yarsa ɗaya tilo
ta shiga wani hali in kasa temaka mata ba, sedai dole inyi kewar Ummana, bata da
kowa seni, mahaifina ya rasu, gata marainiya ni kaɗai ne a kusa da ita muke rayuwar
mu tare, Allah kaɗai yasan irin damuwar da take ciki, dan tunda na tashi ban taɓa
nesa da ita ba, nasan tana cikin damuwa "
Yusuf yace "hakane kam, naga kin sake dasu sosai kamar bake ba, kamar ba kece me
wannan AƘIDAR ta ƙin mutane ba, me yiwa mutane kallon miyagu ba"
"Hmm ina da dalilin yin hakan, ka kwanta dare ya fara yi, kaga baka da lafiya akwai
buƙatar ka samu isashen bacci"
Yusuf yace "ni gaskiya daɗin sunan nake ji, My Queen, My life, I love you so much
My dearest Queen"
Tsaki tayi, ta canza position ɗin da take kwance ta toshe kunne ta, wai danma karta
cigaba da jin meze ce"
Yusuf yayi murmushi, ya kwanta sedai fa bacci yaƙi yuwuwa, saboda saƙawa da
warwarewa da yayi tayi, akan ya sanar da Widad gaskiya waye shi, kokuma karya gaya
mata?
"Barrister Hafiz, kuyi duba a cikin lamarin nan da kyau, ku tsananta tunani kafin
yanke hukunci, akwai gwagwaɓar riba da zaku samu idan akayi wannan harƙallar daku,
zaku samu alheri fiye da tunaninku, zaku samu arziƙin da baku samu a harkar aiki
bama"
Barrister Hafiz ya gyara zama yace "Abunda nake so ku fahimta anan shine, wannan
aikin fa hatsari ne dashi, mu sa hannu a siyar da kadarorin Daula, karkuyi mamaki
akwai masu bibiyar al'amuran dukiyarsa bamu sani ba, idan abu yazo ya tonu sunanmu
ze ɓaci, kuma mu rasa aikin mu, sannan mu fuskanci fushin hukuma"
Alhaji Musa yace "Barrister, sha'anin ƙasar nan tamu yanzu kowa mafita yake nemawa
kansa, da kayi ƙaramin laifi a kaika prison a banza, gara kayi gagarumi wanda zaka
samu mafita a al'amuranka, kuɗi zaka samu manya ba ƙanana ba, wanda baku taɓa zaton
samu ba, kuma a yanzu waye yasan inda Daula yake? Idan abubuwan nan suka samu zaku
iya barin ƙasar ma gaba ɗaya, dan haka ku san dabarun da zakuyi, kuyi mana wata
takarda da zata nuna yayi holan wasu daga kadarorinsa, a bisa farashi me sauƙi ".
Ya kice gumi Barrister Hafiz yayi yace" Yallaɓai akwai buƙatar a ɗan bamu lokaci,
zamuyi shawara tukuna "
"Shikenan, amma bama buƙatar a ɓata dogon lokaci, muna sauraren ku"
Hajiya Sarah ce zaune gefen Bulama, yana shan tea yana karanta jarida, tace
"Yallaɓai, dan Allah ka tausayawa Hajiya Halima, kasa baki a sakar mata ɗanta, gaba
ɗaya ta kasa nutsuwa, hankalin ta gaba ɗaya baya jikinta saboda damuwa"
Bulama ya nisa yace "banƙi ta taki ba, amma baki fini son Halima ba, da ina da
yadda zanyi da zanyi ƙoƙari in saka a fitar da shi, amma wannan case ɗin ba ƙarami
bane, idan na matsa sunana ze iya ɓaci"
"Hakane amma ya kamata kayi wani abu, koda ta ɓangaren kwantar mata da hankali ne,
Allah kaɗai yasan halin da take ciki, ba ƙaramin abu bane uwa ta iya jure ɗanta a
wani yanayi, idan ka bincika babu lallai ko Abincin kirki tana iya ci"
"Eh to banƙi zancen ki ba, amma Halima mace ce me taurin kai da rashin haƙuri,
maimakon tayi haƙuri a bi komai a hankali, amma se azalzala ta take, irin wannan
lamarin a hankali ake binsa, amma ita ta fiye garaje, case ɗin nan ba ƙaramin case
bane ba, karki manta Daula ne fa aka nema aka rasa, kuma shine yake kula dashi,
gaba ɗaya ana saurarar hukuma aji me zasu ce, Amma insha Allah ze fita "
Hajiya Sarah tace " shikenan, Allah yasa amma tana cikin damuwa sosai, Allah ya
fitar dashi, dan yaron kirki ne sosai "
Bacci be ɗauki Yusuf ba se wajen Asuba, dan haka da Asuba kasa tashi yayi, Widad ce
ta fara tashi taje tayi alwala, ta dawo amma be tashi ba.
Hannu tasa tana ɗan dukan ƙafarsa tace " ka tashi ka makara fa yau "
"Eh mana duba gurin kiga, har yayi ja fa, kin zage ƙarfinki kina ta faman dukana"
Dagewa tayi ta ƙara masa wani dukan tace "wannan kuma se kace na karya ka ko?"
Yusuf yace "kai, tabbas idan na riƙe ki se na rama, zan rama wannan dukan da kika
yi min" yai maganar tare da miƙewa ya fita waje domin yin alwala yazo yayi sallar
Asuba.
Da gari ya ƙara haske, Gwaggo ta aiko musu da koko da ƙosai, Widad ta zauna ta
dinga tsintar ƙosan ta naci, tace bata shan kokon, shikam Yusuf yaji daɗin yadda ta
fara sakewa, yanzu tana iya cin Abincin su, dukda a yanzun ma bakomai take iya
ciba, amma tana iya cin wasu abubuwan, yanzu wanke wanke ma, ita take abunta ta
wanke banɗaki, wataran kuma Hindu ce ke mata.
"nifa ba son wannan kokon nake ba, wataran ji nake kamar zanyi amai idan na sha"
Yusuf yace "Allah yasa Baba Hari ta jiki, Kisha faɗa da baƙar magana"
Dariya Widad tayi tace "Aikuwa dai, ai gaba ɗaya matar nan comedy ce, komai ta gani
se tayi magana, wani abun ina sane nake yi, amma bata ganewa taita faɗa"
Yusuf yace "Hmm Allah ya shiryeki to, aini ban san haka kika iya neman magana ba,
ganin cewar a baya ko maganar ma bakya son yi, idan anga fara'arki to da magenki ne
roux ko kuma Daddy"
"Allah sarki, harka tunamin da sister roux ɗina, nasan tana missing ɗina, maybe ma
yanzu sun barta ta mutu saboda yunwa, nasan bame kulamin da ita, nima haushina suke
ji balle magena"
Yusuf yace "Eyya Sorry, Insha Allah bata mutu ba zamu koma ki tarar da ita tana
nan"
"Hmm is very hard gaskiya, am missing Home Yoseef, ina tunanin dabbobina gaba ɗaya
nasan suna missing ɗina"
"wai me yasa kikafi son dabbobinki akan mutane, kina ƙaunar dabbobi sosai"
Widad tayi ajiyar zuciya tace "labarin yana da tsayi sosai, Amma tabbas dabbobi sun
fiyemin mutane, except in some circumstances, duk abu indai dabba ta shaƙu da kai,
ba zata yadda a haɗa kai da ita a cutar da kai ba, amma dan adam fa yana iya manta
dukkan alkhairinka a hada kai dashi a cuceka, shiyasa na zabi rayuwata a cikin
dabbobi”
Yusuf yace “hakane maganarki amma sedai ba duka aka zama daya ba, Amma na Allah ai
basa karewa sannan ba yadda zaai ace mutum yayi rayuwa ba mutane"
Widad tace "kai ka ga haka, nikam nayi, kuma yafi kwanciyar hankali"
Yusuf yace "Ai ba ƙaramin mamaki nayi ba, ranar dana ga kina sukuwa akan doki"
Widad tayi murmushi tace "i miss that Moment, ko a England ina wasan polo, ina son
tseren dokuna sosai"
Daga nan be kuma cewa komai ba ya maida kai yayi shiru yana da cin abincin a
hankali, widad ta kalleshi tace kamar
" akwai Magana abakinka da kake so ka gayamin,naga jiya tun jiya kana ta yawan
kallona"
Yusuf yace aini kullum cikin kallonki nake, babu wani abu da nake son gayamiki
"shikenan tunda kace haka,amma gara inda akwai ka gaggauta gayamin, bazan takuraka
seka gayamun ba amma nasan akwai abunda yake damunka”
“ba ido nake samka ba, yanayinka ne ya nuna min, amma shikenan ba ina kokarin matsa
maka bane, ko son sanin me kake ciki ba, ni bari in tashi in fita in dan sha iska”
Yususf ya kalleta yace “bana son kifita ki barni,ina jin daɗin hirar nan da muke”
Yamutsa fuska tayi tace "ni kuma na gaji da zaman dakin, dan haka waje zan fita”
Yusuf yace “shikenan tunda haka kike so,your wish is mine my queen”
“ka ji dashi dai, inka gama karka manta da shan maganinka" daga nan tai waje abunta
Alhaji Haruna ne shida Alhaji Munir suke cigaba da tattaunawa akan al amuransu.
Alhaji Munir yace "‘anya baka ganin ayi kokari a sakarwa matar nan danta, da yasan
inda Daula yake iya azabar da aka gana masa ya isa ya fadi inda yake, amma tunda be
faɗa ba to tabbas besan inda yake ba, gashi ana batun tafiya kotu, karfa matar nan
ta tona mana asiri”
Alhaji Haruna yace “ka kwantar da hankalin ka, hakan ma duk shirine, idan sun tafi
kotu, za a dauke hankalin mutane daga wasu abubuwan, da zarar hankali ya dauke ya
karkata can, mukuma semu cigaba da barnar mu, kafin a farga mun kwashi abunda muka
kwasa koda wancan abubuwan basu samu ba”
“banƙi ta taka ba, amma ka gane wani abu guda daya, mudinga yi muna ankarewa da
abunda ze biyo baya, yanzun idan aka shiga kotun nan slide mistake ze iya sakawa
asrinmu ya tonu, sannan maganar da muke har yanzu fa babu wanda yasan inda yaran
nan suka shiga, tunda suka gudu har yanzu shiru babu labarinsu, babu labarin inda
suka tafi, kuma har yanzu basu dawo garin nan ba, gaba daya a tsorace nake, kuma
yakamta ace zuwa yanzu shi wannan yaran da muka sa su sace su me adda yake kowa?,
yakamata ace basa raye bekamata abarsu suci bulus ba,suma fa hatsarine as garemu”
Alhaji Haruna yayi murmushi yace “Alhaji Munir ikon Allah, kaikam wasu lokutan
akwaika da tsoro, munefa masu kasar nan, ko yaya muka ga wani abu na shirin kawo
mana tangarda zamuyi maganinsa, mukeda hukumar tsaro kudi da masu mulki, kai a
tunnainka har akwai wani wanda ze kawo mana tarnaki ne? ka sha kuruminka, komai a
tsare yake, shekara nawa mukayi ana tafiyar nan, ba tare da an samu mtsala ba?
Karka manta Alhaji Bukar ma fa namune, kadai mubi komai sannu”
Alhaji Munir yace “ duk nasan da wanan, amma abunda nake so ka sani shine,wannan
mahaukaciyar matar fa zata iya komai idan taji za a kaimata danta prison,bafa zata
zuba mana ido tana kallo danta ya tafi prison ba”
“shikenan, amma nifa kwanan nan na fuskanci wasu halaye da Musa yake yi, sam na
kasa gane kansa fa”
“ba kai kadai ba, nima kallonsa kawai nake, kar ace na fiye matsawa ne ko neman
rigima shiyasa kawai nake kyleshi”
Alhaji Munir yace “Banda shi mahaukaci ne, wai takara ze fito, ubanwa ze zabeshi
bayan bakin tabon da Daula ya goga masa, ai mutane ba mahaukata bane”
“aikam babu alamar hnakli, gara yaje mutane su cinye ɗan abunda ya tara ɗin ai, se
sun talauta shi sannan yazo ya fadi zaben, mutum se taurin kan tsiya, baya ɗaukar
shawara sam, indai 'yan siysa ne zasu ziga shine, su cinye komai idan ya fadi su
gudu su barshi”
Alhaji Musa yace “:ai shiyasa ban damu da in bashi shawara ba gara yaje suma suci
rabon su, daga baya yayi hankali ai”
“shikenan,semunyi waya”
Daga na sukayi sallama.
Ganin wucewar Hajiya Halima ne yasa Ramlah bin bayanta zuwa dakinta, tana zuwa tace
“Mummylafiya kuwa?”
Zama hajiya Halima tayi tace “ina fa lafiya, wai kotu za akai Anwar kotu fa Ranlah”
“sun hana , sunce ba zasu bada belinsa ba, kuma wadan nan banzayen sunki suyimin
komai akai, sun barni se wahala nake nikadai, nikadai na haifeshi nikadai nake
wahala ta, dan san abunda ze biyo baya kenan da ban barin Anwar yaje yana wannan
wahalar ba, idan yaso ba zagi ba ko tsinewa ce duniiya sumun baze dameni ba,amma
ina kallo akaimin da na prison baze yuwu ba, niba abun in tona asiri ba, nima zan
kwana a ciki, da sedai ayi duk wadda za ayi”
Ramla tace ” mummy kiyi hakuri, ki kwantar da hankalinki, idan kika fallasa ba iya
asirinsu ba hatta namu muma ze tonu ne, dan haka kiyi hakuri mubi a hankali”
“wani irin mubi a hankali komai yana lalacewa, in zuba ido akaimin ɗana prison sam
baze yuwu ba wallahi, ana shiga kotu nasan prion ne zasuce zasu kaimin shi”
Tunda widad ta fice tsakar gida bata sake komawa ɗaki ba, tana maƙale da Gwaggo da
Hindu tana koyo aikin gida, yayinda gefe guda sunayi suna faɗa da Hari, yayinda
Hanne keta jifanta da bakaken maganganu, wani abun Widad ta gane wani ba zata gane
ba, dan wata hussar ina tayi tsauri bata ganewa sam, ita dai tafi maida hankali
akan ta koyi aikin,Gwaggo bata hantarar ta idan tayi ba daidai ba seta gyara mata
cikin ruwan sanyi.
Saleh ne ya shigo gidan, ya tarar Widad zatayi tatar gasara, tanata kokowa da abun
tatar Gwaggo tana gyara mata, gashi ta maida duk hankalinta so take ta koya, gwanin
ban dariya da tausayi.
Da sallama Saleh ya shiga dakinsu Widad, ya tarar da Yusuf a zaune yayi shiru yayi
zurfi a duniyar tunani, Yusuf ya dago ya amsa.
Yusuf yayi dariya yace “danma baka ga yadda take tankaɗe ba, bakaga asarar garin da
tayiwa Gwaggo ba, ai Gwaggo ba karamin mutunci take man aba, se fatan Allah ya
sakamata da alkairi”
Saleh yace “ai abunma da takaici ace yarinya kamar wanna bata iya aikin gida
ba,abun da kunya ai”
Saleh yace “waye ze koya mata, ta dinga hantarar mutum tana masa wulakanci”
Sale yai murmushi yace “masu mata manya,to Allah ya bada hakuri, na manta ne, Allah
yasa in an tashi komawa a tafiwa da Daula jika”
Shiru Yusuf yayi bece komai ba yana tunani, Saleh yace “lafiya kuwa?”
Yusuf yace “Saleh akwai matsala ina cikn damuwa sosai, har yanzu bata san waye
niba, bana son taji a wani gurin tayimin kallon makaryaci, yanzu ban san ta in zan
faraba bansa n ya zata kalli abunba, zata iyayimin bore ina tsoron darunta”
Saleh yace “hakane amma ai kai namijine, kuma zuwa yanzu duk ta rage wasu abubuwan
ai, ba lallai ta maka wulakanci tunda yanzu ba wanda ta sani se kai”
“Saleh anya ba ka manta wacece Widad ba? Jiya ta gama jadaddamin bata yafiya ga
wanda yayi mata karya ko yaci amanarta”
Saleh yace "ƙwarai na san wacece ita, yadda ta gaya maka hakane bata yafiya ga
wanda yayi mata ƙarya ko yaci amanarta, duk yadda suke da shi kuwa, amma ai kai
akwai alaƙa me matuƙar ƙarfi a tsakaninku, zata iya ɗaga maka ƙafa kuma kamata yayi
ace kai da kanka ka gaya mata, karka bari taji a waje, idan kuwa ka kuskura ta samu
labari a gurin wani akwai matsala, dan bata ƙi ka tafi prison ba kaima, tace an
haɗa baki da kai za'a cuce ta, abun da nake ganin dai yafi shine ka sanar da ita
kawai, hakan zefi "
"tabbas nasan bata yafiya ga wanda yaci amanarta, nikam Saleh me kayi mata wanda
yasa ta kasa duba alkhairin ka se laifukanka? "
Saleh yayi murmushi yace " labari ne me tsawo Yusuf, kuma gaya maka labarin tamkar
ƙara wani laifin ne akan laifi, amma ka bari idan tayi niyya zata iya gaya maka
komai, nidai shawarata da kai, tun kuna nan ka gayamata waye kai"
Yusuf yaja ajiyar zuciya yace " Inajin tsoro Saleh, harga Allah ni fa ina son Widad
ne tsakani da Allah, yanzu idan na gaya mata zata iya ƙina, a yanzu mu tana ƙasa
tana dabo ne, dan itafa bata yadda akwai so ba, dan haka bani da tabbacin tana
sona, kuma inzo in gaya mata wannan magana, abun ze lalace gaba ɗaya ne fa"
Saleh yace "haba namijin duniya, ai kai kana da jarumrtar da ka cancanci a sara
maka, haka nan duka butulcin me butulci dole ya sarawa namijin ƙoƙarin da kayi akan
Widad, ni kaina na fuskanci sonta kake, amma dole zata ɗaga maka ƙafa dan baka
cancanci ta wulaƙanta ka ba, be cancanci ta manta da alkhairin da kayi maka ba,
dukda yarinyar wata irin muguwar bahaguwa ce, amma kayi ƙoƙari kafin ku bar garin
nan tasan abunda ake ciki "
Yusuf ya dafe kai yace " Subhanallah, ban san ta ina zan fara ba Saleh, ina tsoron
abunda ze biyo baya, ni kome zata yi baze dameni ba, ni fargaba ta karta rabu dani
ko tayi min wata mummunar fahimta "
" Yusuf kenan, da alama wannan ne karonka na farko na shiga soyayya ko?"
Yusuf ya girgiza kai yace " Na taɓa soyayya Saleh, har na sawa kaina bazan sake
soyayya ba, katsam Widad ta shigo cikin rayuwata ba tare da na warke daga wancan
ciwon dake zuciyata ba, kuma har nake jin cewa a yanzu inawa Widad son da banyi wa
waccan yarinyar ba"
Saleh yace "lallai kana cikin Jarrabawa Yusuf, ina maka fatan Alkhairi tare da
fatan Allah ya fitar da kai"
Sallamar Widad ce a ɗakin ta katsesu, suka amsa mata gaba ɗaya, fuskarta duk
bushashiyar gasara, kanta babu ɗankwali goshinta duk gumi.
Ta kalli Yusuf tace "ka zauna kana ta surutu, baka san lokacin salla yayi bane, har
an fara aikowa ana tuna maka, kaje kaja salla"
Yusuf yace "aini yanzu gaba ɗaya kunyar mutanen nake ji".
Yusuf yace "tunda kika rungume ni a gabansu, indai suka ganni se inga suna wani
sunkuyar da kai"
Ɗan guntun tsaki Widad tayi tace "to dana rungumeka a gaban su is it an
abomination? Saɓo nayi kome?"
"to ai su basu saba ganin irin haka ba, is against their norms"
Widad tace "to su suka sani, ni wanka zanje inyi, kaje kayi sallar"
Yusuf yace "to bari inje in dawo in rama dukan da kika yi min da Asuba"
"ina nan ina jiranka kuwa, kasan dai na fika ƙarfi yanzu, kai sauro ya zuƙe maka
ƙarfi".
"dole kice haka mana, tunda na baki jinina, dole kiyi ƙarfi ai"
Ta kalle shi tace "ji wata magana, jinin naka ma da bashi da kyau, duk ba wasu
sinadarai a cikinsa, shine duk ka dameni da ka bani jini, to zan biya ka abunka"
Tana zaune tana shafa man zaitun a jikinta Yusuf ya dawo, ta bawa ƙofa baya, farar
fatarta se ƙyalli take da ɗaukar ido, ga baƙin gashinta ya kwanta sosai a bayan ta,
ƙasansa ya jiƙe da ruwan wanka, ba taji dawowar Yusuf ba se jinsa tayi zaune a kusa
da ita, numfashinsa na sauka a jikinta.
Da sauri ta ɗago ta kalle shi tace "meye haka? Ya zaka zo ba ko sallama, ka zauna
kana shinshinani"
Seda tasa Yusuf yayi dariyar dabe shirya yinta ba, yace "niba shinshinaki nake ba,
se kace wani kare"
Beyi magana ba, ya kalli hannun ta data tsiyayo zaitun, ya zura nasa hannun akan
nata, zaitun ɗin wani duk ya zube, ya shiga shafa mata a jikinta.
Ji tayi tsaigar jikinta na tashi, ɗan yamutse fuska tayi tace "Yoseef bana so, ka
bari in shafa da kaina"
Tsaki tayi ta ɗan ɗaga murya tace "nace maka bana so" tai maganar tana ƙoƙarin
miƙewa, Amma Yusuf ya riƙeta ya hanata tashi, a hankali yace "yi haƙuri Widad,
magana nake so muyi" yai maganar yana sauke numfashi.
Littafin kuɗi ne, kuyi magana ta wannan lambar domin siyan littafin
Nagode
07063065680
11/14/21, 6:09 PM - Ummee Musa: 48_49
Haɗe rai tayi tace "dan za muyi magana shine zaka dinga yimin wannan abun haka, ni
bana so gaskiya karka sake yimin"
Maimakon yayi magana Shiru yayi ya sake ƙanƙameta sosai a jikinsa, ya kwantar da
kansa a jikinta, ita kuwa mutsu mustu kawai take, so take taga ta ƙwace daga
jikinsa, amma abu ya gagara, ya riƙeta sosai ga ƙarfinsu ba ɗaya ba.
A hasale Widad tace "Wai dan Allah Yoseef meye hakane?, ka cikani towel ɗin jikina
ze kwance fa? Nace maka bana so ka cikani dan Allah, wallahi gaba ɗaya ka canza
hali, kwanan nan sekai tayi min wasu abubuwa wanda bana so, kuma kana sane"
A hankali ya cika ta, ya kwanta akan katifar yayi shiru tare da lumshe idonsa.
Se kuma ta juya tana kallonsa tace "meye kuma?" ba tare da ya buɗe idonsa ba ya
girgiza mata kai.
Gabansa ne ya faɗi, yaga be kyautu yayi mata wannan zancen a wannan gaɓar ba data
ɗau zafi, dan haka ya buɗe idonsa ya ɗan tsare ta da ido yace dama ba wata magana
bace, ina son in sake gayamiki Ina sonki Widad "
Ha ɗe rai tayi tace " kaga tasarmin daga kan katifa ta, tunda ba zaka dena wannan
shirmen ba, kuma daga yau in ka san wannan shiritar zaka gayamin, karka sake cewa
zakayi magana dani na gaya maka, dan bazan saurareka ba"
Yusuf yace "Maganar tawace shiririta? Queen ba shirita bace i mean it, kalmar so ba
abun wasa bane ko imagination ba, please my Queen ki yarda ina sonki mana"
Banza tayi masa, ta ɗakko kayanta tana ƙoƙarin sakawa, ya juya mata baya don ta sa
kayanta.
tayi ƙasa da muryarta cikin ƙunƙuni tace 'kaji da shi dai, kai ta mun wasu abubuwa
amma idan zansa kaya seka wani juya, wai kai gaka na Allah, inma baka juya ba niba
abunda ya dameni sa ka yana zanyi'
Bece mata komai ba se dai murmushi da yayi, se data gama sa kayan, ta yunƙura zata
miƙe ya sake riƙeta, a fusace tayi niyyar yi masa rashin mutunci, amma ya rungumota
ta kasa cewa komai jin ya haɗe bakin su.
Gaba ɗaya Yusuf yafi ƙarfinta, ta kasa gane kansa kwata kwata, kwanan nan se wasu
ɗabi'u yake mata wanda bata gane kansu, tana ji tana gani seda yayi me isarsa
sannan ya cika ta, ba zata iya ƙwace kanta ba.
Yana cikata bata kuma kallonsa ba, ba tace komai ba rai a matuƙar ɓace tayi waje,
kallo ɗaya zaka yiwa fuskar ta kasan a fusace take, ta fita tsakar gida rana ta
take, kowa yana ɗaki ta fita ta samu guri a ƙasan bishiya tayi zamanta.
Hakanan Yusuf ya dinga jin be kyauta ba abunda yayi, amma ya zeyi shima bayin kansa
bane, mutum ne shima kuma me cikakkiyar lafiya, shi kansa yanzu ya fara ɗar ɗar na
zama da Widad a guri ɗaya, komai ze iya faruwa.
Barrister Khalil kam tunda yakoma gida yake tunanin hirar da sukayi da Nurat game
da mahaifinta, tabbas mahaifin Nurat ba karamin hatsabibi bane ,ze iya aikata komai
muddin burinsa ze cika ,amma yayi mamakin yadda Nurat tace masa da saka hannunsa a
sace Daula da akayi,abun da mamaki matuka, nan ya shiga nazarin ta ina yakamata
yayi wani abu? Amm muddin ya kuskura Alhaji Musa yasan yana wani yunkuri,ko kuma ya
gane ya san wani abu akan abunda yake aiktawa,to tabbas ba abunda ze hanashi daukar
mataki akansa,dan bashi da Imani sam.
Barrister Hafiz ma tunda ya koma gida yake tunanin batun da aka bijiro masa da shi
akan dukiyar Daula,tabbas kudi abun sone,amma meze biyo baya idan suka amince akayi
wann aika aika? Idan sukayi aikin nan tabbas zasu samu kudi,amma hatsarin dake
cikin hakan shine abun dubawa, watakila idan shi nya amince ba lallai sauran
lawyoyin su yadd ba,amm tabbas yana son kudi shima.
Ya yanke shawarar zefara tuntubarsu daya bayan daya yaji opinion din sauran akan
lamarin abunda suka yanke shikenan.
Ya tashi ya dau mukullin motarsa ya fice.
Anwar kuwa gaba daya yayi baki,ya rame saboda zaman gurin nan babu sauki sam, ga
sauro ga rahsin kula, ga azabar wahala da ake gana musu akan lallai se sun fadi
inda Daula yake, amsar sa dai dayace be san inda yake ba.
Yana zaune a inda suke ajiye yayi shiru yana tunani,s hi babban abunda yake damunsa
shine waye ya sace Daula? Wanda ya sace shin yana iya kula dashi?maganinsa ma ko
ana kula dashi a bashi oho? Yayi zurfi a duniyar tunani yaji an kira sunansa, a
hankali ya daga kai, dan sandan yace
Anwar ya taso ya taho a hankali yana jan kafa,yabiyo bayan dan sandan.
wanda aka nuna masan akace shine me nemansa sam be sanshi ba, dan ko ganinsa be
taɓayi ba.
Mutumin ya kalli Anwar yace “ naji ance ranar sha biyar ga wata za a kaiku kotu
ko?”
Dukda ban gabatar maka da kaina ba baka san koni waye ba,nima turoni akayi
gurinka,kuma ancemin babu bukatar seka san waye ya turoni, yanzua abunda nake so
nbda kai shine ina son ka gayamin tsakani da Allah meka sani game da batan Alhaji
Nasir”
Anwar ya gaya masa iya abunda ya sani,Mutumin yace "shikenan karka damu ka kwantar
da hankalinka,insha Allah komai zezo da sauki”
Mutumin yace “sannan kuma, bana bukatar kowa yasan nazo gurinka ciki harda
mahaifiyarka’
Widad na zaune a gindin bishiya, tana tunanin abunda ya shiga tsakaninta da Yusuf,
tai shiru sosai tana tunani, tama rasa me yakamata tayi, haushi zataji kome?, Ganin
Widad zaune ita kaɗai a gindin bishiya yasa Hindu tazo ta Zauna a gurin Widad, tace
"Amarya me kike anan ke ka ɗai haka?"
Murmushi Widad tayi tace "to ta ina zamu fara, bansan a inda kika tsaya a turancin
ba"
Nan Widad ta shiga koya Mata daga ƙananan abubuwa wanda zata iya riƙewa.
Yusuf ya fito ze tafi Sallar la'asar, ya ya kalli su Widad yace "karatu ake ne?"
Widad bata amsa ba, Hindu ce tace "eh wallahi turanci ake koyamin"
Yusuf ya ƙaraso ya zauna a kusa da ita yace "Shine kike cin Abincin babu ko
gayyata? Bari inzo muci tare, kin san cin Abinci tsakanin ma'aurata yana ƙara
danƙon soyayya, nikuma ina son Soyayyarmu ta wuce ɗanƙo ta zama kamar ƙarfe"
Ya wanke hannu yazo yasa hannu suna cin Abincin, amma Widad taƙi ce masa komai.
Se yanzu Yusuf ya fuskanci fushi take dashi.
Yusuf yayi ƙasa da muryarsa yace "My Queen me nayi miki ne? Se magana nake am kin
basar dani, bana jin daɗin hakan fa"
Yusuf yace "Abunda nayi miki a ɗaki ne yasa kike fushi dani ni ko?"
Cire hannunta tayi daga Abincin, taje ta wanko hannunta ta dawo tai zamanta, shiru
yayi yana sake binta da kallo.
Ta ƙara wani rausayar da kai tana murmushi, ta ƙaraso inda yake zaune kusa da Widad
a kan tabarma, tace "bari in ɗauke kwanon, naga kamar ka gama cin Abincin"
Bece mata komai ba, taje ta ɗauke kwanon ta kai gurin wanke wanke, ta kawo masa
ruwa a buta tace "ga wannan ka wanke hannu"
Ta jinjina masa kai tana murmushi, Widad ko kallon inda suke ba tayi ba, ta cigaba
da kaɗa ƙafarta.
Tana jin yadda Hanne keta wata kwarkwasa, Hindu dake banɗaki ji take kamar ta fito
ta shaƙe Hanne, ta wani ɓangaren kuma tana ganin baiken Widad, data zuba mata ido
ta ƙyaleta.
Yusuf ya tashi ya tafi ɗakin su, Hindu na fitowa daga banɗaki a fusace tace
"Hanne gaskiya abunda kike bakya kyautawa, ya zaki dinga shigewa mijin mace a
gabanta, dan kawai kinga tana ɗaga miki ƙafa, haba Hanne dan Allah ki dimga tunani
mana"
Hanne tace "ba zanyi tunanin ba ɗin, ina ruwanki dani? Tunda ita ba zata iya kula
dashi ba ai shikenan, mace ba abunda ta iya se girman kai, sam bata da tarbiyya,
bata san darajar miji ba"
Widad ta miƙe zata koma ɗaki, sedai babu zato Hanne taji Widad ta shaƙeta da rigar
jikin ta, seda idanunta suka yo waje dan azaba, cikin zare ido da ɗaga murya Widad
tace
"Am tired, ban taɓa ɗagawa wani mahaluki ƙafar dana ɗaga miki ba, ina ƙyaleki ne
saboda Karamcin iyayenki a gare ni, kin san wacece ni? Babu ruwana da alaƙar dake
tsakaninki da Yoseef, amma karki sake sakani a irin wannan haukan naki, banda
ƙaddara ko a mafarki aka ce ni Widad zan zauna a wannan ƙasƙantaccen gurin zance
ƙaryane, saboda kawai ina zaune a cikin wannan jar ƙasar shine zaki dinga gayamin
baƙaƙen maganganu? Kin san wace ni, idan kin san wace Widad ko hanya muka haɗa
sekin kauce, banda dalilin ƙaddara babu abunda ze haɗanj da daƙiƙiyar baƙauyiya
kamarki, hanyar dana sa ƙafata na wuce ma baki isa ki biyo ta ba"
Hanne se kakari takeyi, Su Hari sukazo da gudu amma suka kasa ƙwatar Hanne a hannun
Widad, fitowar Yusuf ne yayi daidai da shigowar Saleh, da sauri Yusuf ya ƙarasa
inda dramar ke faruwa, idanun Widad sunyi jawur, fuskarta sharkaf hawaye tana
masifa.
Yusuf ya ƙarasa yasa hannu ya cire hannun Widad daga wuyan Hanne, Hanne ta shiƙi
iskar 'yanci, ta koma gefe tana ta haki tana zare ido, kamar an karɓeta daga hannun
zaki.
Saleh yace "Wallahi da ta kasheki ta kashe banza, dan babu wanda ya isa ya ɗaukarr
miki mataki, kin san wacece kuwa? Kin san' yar waye ita? Ko dan kawai kin ganta a
cikin gidan nan a zaune, ina lura da yadda kike mata wasu abubuwan tana ƙyaleki,
tunda kika ga nima tana mun abunda taga dama ina ƙyaleta to tabbas kin san ba a
banza ba, ƙaddara ce ta kawota zama daku, amma ke a gidan su ko me goge mata
takalmi baza'a ɗauke ki ba"
Gwaggo tana jin duk dramar da'ake yi, amma tai shiru a ɗaki bata ko fito tsakar
gidan ba, saboda tasan abunda ke faruwa, tasan yadda Hanne ne ke wuce gona da iri a
wasu lokutan.
Shikan sa Yusuf yasan ba ƙaramin ɗaga ƙafa Widad kewa Hanne ba, a yadda Widad keda
izza bata ɗauka raini, amma take sharewa idan ta mata wani abun, lallai haƙurinta
ne ya ƙare.
Suka shiga ɗaki, Widad se kuka take jikinta na tsuma, ga gumi data haɗa.
Yusuf ya shiga share mata hawayen fuskarta tare da faɗin "is ok, kiyi haƙuri nasan
kina haƙuri, Amma ki ƙara insha Allah mun kusa mu koma gida"
Kamar wadda aka mintsina, ta miƙe daga jikinsa a fusace tace "dalla ma ni ƙyaleni,
ba kaine kake mata dariya ba, yasa ta rainani takemin wani kallo na daban ba, harni
wannan baƙauyiyar yarinyar zata kalla ta dinga zagina? Tunda kana mata dariya dole
ta Kalleni ta dinga cewa ban iya kula da miji ba se ita, ai seka Aure ta tazo ta
kula da kai, wallahi ta kuma yimin abunda bemin ba, sena ɗau mataki mafi muni a
kanta, zan nuna mata wacece Widad "
From no where Yusuf yaji wani farinciki yana ratsa shi, Widad ta fara kishinsa
kenan? Murmushi yayi yace
" Ohh yasalam, shikenan tabbas nayi laifi, dukda badan ina mata murmushi ba, da
tabbas ba zata rainamin 'ya ƙwalisar mata ta ba, amma ayi haƙuri zan kiyaye insha
Allah, na dena mata dariya amma ayi min afuwa".
"Ayi haƙuri dai, kar ayi aika aika, ki dena kuka share hawayen ki maza, mijinki
baze sake kallonta yayi mata dariya ba"
Shiru tayi masa ta cigaba da ajiyar zuciya. Yusuf a ransa yace 'insha Allah ko
baki son meye so ba zaki sanshi a kaina, kuma ina fatan ki furta da bakinki kina
son Yusuf, muje zuwa dai'
Shikam Saleh a tsakar gida ya cigaba da zazzaga musu masifa, akan abubuwan da Hanne
ke yiwa Widad, sun sha mamaki jin yace ko za'a tattara kaf ƙauyen da kadarorin da
mutanen ƙauyen suka mallaka ba zasu sai gidan mahaifin Widad ɗaya wanda take rayuwa
a ciki ba.
Hindu ta yadda da maganar Saleh, saboda sam Widad ba tayi kalar wahala ba.
Ita kuwa Hanne jinsa kawai take badan ta yadda ba, shaƙar da Widad tayi mata tafi
komai bata mamaki da ɗaga mata hankali.
Ramlah ce ta shiga falo, ta tarar da Amal a kwance tana kallo, amma hankalin ta sam
baya kan tv tunani kawai takeyi, a ɗan gigice tace "Amal wai kinji Anwar kotu za'a
kaisu next week"
"Dama ana kai mutum kotu, koda ba'a tabattar da laifin da ake tuhumarsa ba?"
Ramah tace "ya za'ayi in sani? Nifa hankalina ya tashi, ashe abun nayi ne"
Amal tace "mun shiga uku Ramla, da ƙyar in aka shiga kotu kiga ba'a kai shi prison
ba, yanzu meye abunyi?"
"wallahi nima ban sani ba, gaba ɗaya kaina ya gama kullewa, Ga Mummy ta damu sosai,
ko Abinci ma ba ta ci fa"
"Subhanallah, Allah sarki Yaya Anwar, yanzu fa da sunje koti se ace se prison"
Ramlah tace "wallahi nima abunda nake tunani kenan Amal, Allah sarki bawan Allah"
Har dare Widad taƙi walwala, ko kula Yusuf ta ƙiyi, yau ko harar da suke a tsakar
gida dasu Hansai bata zauna ba, ta gyara shimfiɗar ta zata kwanta, Yusuf yaje kusa
da ita yace
"My Queen dan Allah kidena fushi dani, nasan yau gaba ɗaya ranki a ɓace yake, na
farko na sake gangancin sumbatarki, ga kuma wancan laifin shima da kika ce nayi,
dan Allah kiyi haƙuri bazan iya jure ganinki cikin ɓacin rai ba"
"Amma inaga dole mu koma kan shawarata ta farko, na yakamata mu raba ɗaki, kinga ni
ba waliyyi bane mutum ne kamar kowa, idan muna tare a guri ɗaya akwai matsala, ina
gudun wani abu yazo ya faru, kinga na fara gazawa gurin riƙe Alƙawarin yarjejeniyar
dake tsakaninmu"
"wallahi bazan kwana a ɗakin nan nikaɗai ba, duk inda zaka je sena bika"
"to idan na kuma kissing ɗinki kika haɗemin rai se nayi abunda yafi haka, kina bani
ciwon kai Widad, komai nayi laifi ne a gurinki, ki dinga sassauta min mana, a dinga
jin tausayina"
Kwanciya tayi ta juya masa baya, shima kuwa ya kwanta a bayanta, banza tayi masa
taƙi magana, ta lumshe ido da nufin tayi bacci, a kunnenta ya dinga raɗa mata
"I love you My Queen, ina sonki Widad, and I mean it from the bottom of my heart, i
love you"
Cike da ƙosawa Widad tace "Naji amma dan Allah ka ƙyaleni inyi bacci"
"kaika santa"
Ana ta shirye shirye za'a kai su Anwar kotu domin fara sauraren ƙararsu, akan
tuhumarsu da'ake da haɗa baki gurin sace Daula, Anwar ya duƙufa sosai da Addu'oi
babu dare babu rana.
Yana zaune da safe wani ɗan sanda yazo ya buɗeshi, aka tasa ƙeyarsa zuwa wani guri,
wannan mutumin dai daya zo ya kuma gani, aka bawa Anwar kayansa da aka karɓa.
Mutumin ya miƙawa Anwar hannu suka gaisa yace "masha Allah, you are free now malam
Anwar, muje in ajiyeka a gida"
Cikin mamaki Anwar ya kalle shi yace "i am free as how? An game bani da laifi
kenan?"
Kamar soko haka Anwar yabi mutumin, kuma ya kasa tambayar sa waye shi, ya kai shi
restaurant yaci Abinci sannan ya wuce ya kai shi har ƙofar gida.
Mutumin ya kalli Anwar yace "Anwar ina maka fatan Alkhairi, ina maka murnar fitowa
da kayi da kuma tsallake tarkon azzalumai, seka kula Allah ya kiyaye gaba"
Anwar yace "sedai ni tunda kake zuwa gurina ban gane ka ba"
Mutumin yace "nasan baka sanni ba, kuma bazaka ganeni ba, sedai nima aikoni akayi
ba'a bani umarnin sanar da kai wayeni ba, babu buƙatar hakan Daula yana tare da
ubangida na, shiyasa aka ɗauke shi a Asibiti, yana gurinsa dan haka ka kwantar da
hankalinka"
A firgice Anwar yace "dan Allah waye uban gidan naka? Daula bashi da lafiya, yana
buƙatar kulawar likita"
"ɗan samari kai dai ba Ruwanka, koma a wani hali yake ciki tunda dai kai ka fita,
maza jeka zan tafi"
Jiki a sanyaye Anwar ya sauka, yana bin motar da kallo kamar wani soko, har motar
ta bara layin.
Gate ɗin gjdansu ya nufa, ya ƙwanƙwasa ƙofar gate ɗin, Isa ne yazo ua buɗe ƙaramar
ƙofar, yana ganin Anwar ya shiga mutstsuka ido ko gizo yake masa, Isa yace
Buɗe masa ƙofar yayi ya shigo, Isa yace "Yallaɓai an sakoka kenan?"
Anwar yace "Alhamdilillah Isa an sakoni" nan ma'aikatan suka dinga murna suna taya
shi farinciki.
Cikin gidan ya ƙarasa, yana shiga ya tarar babu kowa a falo, ɗakin mahaifiyarsa ya
nufa, yasa hannu ya murɗa ƙofar ɗakin yayi Sallama, da sauri ta waigo dan mamar
Muryar Anwar taji, aikuwa ba kama bane shi ɗinne, ai da hanzari ta miƙe, ta nufe
shi da sauri
Rungume ta yayi yace "Mummy ki bari in huta se in gaya miki, duk kin rame Mummy na"
Kuka ta saka tace "ba dole ba Anwar, baka nan na rasa me kemin daɗi, nasan zaman
gurin nan sam ba daɗi yake maka ba, nayi zarya harna gaji anƙi a sakeka, ko Abinci
bana iya ci, bana baccin kirki"
Suna nan zaune sega su Amal, dan ta manta ma bata sanar dasu dawowar Anwar ba, nan
suka dinga murna suna farinciki da dawowar Anwar, aka shiga yi masa girki, yai
wanka ya huta dan ko ina na jikinsa tsami yake masa saboda wahala.
Anwar yace "wallahi Mummy ikon Allah kawai, ina zaune akace in fito, wani mutum ya
ɗakkoni a motarsa yace bani da laifin komai, ya kawoni har gida ya tafi"
Ɗan yatsine fuska tayi tace "meye haka sekace wata almara?"
"ikon Allah ko wane mutumi ne wannan oho? Ta be gaya maka waye shi ba?"
"nayi nayi ya gayamin, amma yaƙi sam, be gayamin ko waye shi ba"
Amal tace "Mummy koma dai waye, tunda Allah yasa an sako mana shi ai shikenan, mu
dama fatanmu ka dawo gida"
Mummy tace "Amma da mamaki, ina mamakin waye haka? Dan na san ba'a cikin waɗan cam
tsinannun bane marasa imani"
Da sauri ta wayence tace "A'a karka damu, 'yan sanda nake nufi, ba irin zaryar da
banyi ba amma suka ƙi bani belinka"
"Allah sarki, ai Abincin su suke karewa suma Mummy, bekamata ki tsine musu ba"
Mummy tace "hakane kam, na dena tsinemusu tunda nidai ɗana ya fito"
Yau Widad har takwas na safe bata tashi ba, tunda tayi sallar Asuba, Yusuf yaje kan
shimfiɗarta ya riƙe hannunta a nasa yana ɗan matsawa yace "My heart, ki tashi
baccin ya isa haka, ki tashi kici Abinci"
Motsawa tayi a hankali tayi juyi tace "kaci Abincinka, ni bacci nake ji"
"A'a ni gaskiya bazan iya cin Abincin babu ke ba, ki tashi please"
Shiru tayi ta sake lumshe ido, "zanyi miki abunda bakya so yanzun nan fa"
Murmushi tayi tace "banyi brush ba dai" ta ƙarasa tana dariya, Yusuf yace "aini
bana ƙyamar ki, kece kike ƙyamata komai naki ni so nake"
Ya duba inda take ajiyewa, ya ɗakko ya bata, tana zaune akan katifar bata tashi ba,
Yusuf yace "ya dai? Ko sena ɗauke kine?"
Jinjina masa kai tayi alamar eh, aikuwa ya ƙaraso ya ɗauketa cak, dariya take tace
"ajiyeni tun kan Baba Hari tamin ba'a ko ace na aikata wani babbam zunubi a koreni
daga garin nan"
Tayi waje, taje tai brush ta dawo suka fara cin ɗumamen tuwo.
Yusuf kallonta yake, da alama tana cikin nishaɗi, yanzu ne lokacin da ya dace ya
gaya mata abunda yake son gaya mata, yai shiru yana saƙe saƙen yadda ze ɓullo da
zancen yaji tace
"Me kake son gayamin ne da yake razanaka har yanzu ka kasa gayamin? Ka gayamin
kawai ina saurarenka"
Littafin kuɗi, dan Allah a biya kafin a karanta badanniba dan girman Allah
A tuntuɓeni ta wannan lambar
07063065680
11/14/21, 6:09 PM - Ummee Musa: 50_51
NA KUƊI NE, BOOK 1 NE FREE, DAN ALLAH A BIYA KAFIN A KARANTA BA DANNI BA DAN
ALLAH 🙏🙏🙏
gaba ɗaya Yusuf ya ɗan ruɗe yace "ba wani abu da nake son gayamiki ba fa, kece kike
ganin kamar ina son in faɗi wani abu ne"
Murmushi tayi tace "Hmm Yoseef kenan, a ɗan zaman da nayi da kai daga lokacin da ka
fara min aiki, na fuskanci halayenka da yawa, koba haka ba ina iya karantar abunda
ke ran mutum ta hanyar fuskarsa, bana son ƙarya, karka ji wani abu, babu abunda zan
maka, se abunda Allah yayi nufin ya faru da kai"
Yusuf yace "dama ina son in gaya miki yau nake son na cigaba da fitane, ina son in
sai mana wasu abubuwan na buƙatunmu, wasu abubuwan duk sun ƙare"
Widad tace "Yaushe ka warke da har zaka fara zancen fita? Se kaje ka kuma haɗuwa da
wata rashin lafiyar ko? toni babu ruwana, tunda dai ban takura maka nace seka
saimin abunda baka dashi ba, ka ƙyaleni komai aka bani zanci, in wanda zan iya cine
se inci, in bazan iya ciba kuma se in haƙura kawai"
Sosai ta bawa Yusuf tausayi jin abunda ta faɗa, Yusuf yace " duk da haka Yakamata
ace nima ina taɓuka wani abun da kaina, in sauke haƙƙinki da yake kaina, in sai
miki abubuwan da kike buƙata koba duka ba"
"Shikenan, amma nidai bance kayi abunda zaka cutu ba koka wahala ba, ka kula da
lafiyarka"
Yusuf ya gama shirinsa tsaf ze fita, Saleh ya shigo gidan ya kalli Yusuf yace "Ahh
Yusuf ina zuwa haka? '
Saleh yace " Haba Yusuf, kasan fa baka da lafiya sosai "
Yusuf yace " shima zaman guri ɗayan babu daɗi Saleh "
Harice take a tsugune tana ta tattara ƙwan da kazarta tayi zata bayar akai kasuwa,
Yusuf yace " Baba Hari, wannan ƙwan na siyarwa ne?"
Yusuf yace "Masha Allah, inba damuwa a zuba na kaji biyar na zabi biyar, a kaiwa
Queen idan na dawo insha Allah zan bada kuɗin"
"Awo sekace min Wudas, amma kun ai bazan gane ba idan kace haka"
Saleh yace "Hari baki abun magana, Queen yace ba kun ba, yana nufin sarauniya"
Hari tace "dan dai kaine, kuma ina jin kunyar ka, amma da ita zata siya bazan sayar
mata da ƙwan nan ba"
Saleh yace "kedai kinji kunya, ki rasa da wadda zaki dinga faɗa se wannan
Yarinyar"
Dariya suka yi, Saleh ya dinga mamaki, dama Widad ta iya magana haka hadda tsokana?
Hari tace tunda Yusuf ne ze sai ƙwan, ya biya kuɗin biyar, ta bashi biyar kyauta,
amma bata yarda ya bawa Widad wanda ta bashi ba.
Widad tace "Hari dama kina ɗan dafa ƙwan nan kici, dase kinfi haka ƙiba da kyau, ke
kullum cikin neman kuɗi kamar zakiyi ƙwace, kuma na rasa inda kike kai kuɗin"
Hararta Hari tayi taƙi ta kulata, aka ɗakko kwano za'a sakwa Widad ƙwai, Widad tace
"kuma idan kika samun ƙanana bana so, manya za'a bani dan nima ƙatuwa ce"
Haka Widad tasaka Hari a gaba, tana ta zolayarta ita kuwa Hari tunda Widad ta shaƙe
Hanne take ɗan shakkarta.
Widad tace "ba zaka soyamin ƙwan ba zaka tafi?" tai maganar kamar wata ƙaramar
yarinya tana sa hannu a gashin kanta.
Gwaggo ta sunkuyar da kai tana jin taɓara, Yusuf yace "ki bari in dawo"
Yusuf yace "Shikenan Muje in soyamiki, amma nasan ba iya ci zaki yi yanzu ba, dan
yanzu kika gama cin Abinci"
Widad ta cunkusa baki tace "Ni gaskiya Mama nasa nake so, naga kin fi son Yoseef
dani, ni kowa baya sona"
Gwaggo tace "nina isa ince bana sonki, waceni niko nake sonkj, amma ina nema masa
Alfarma, a ɗaga masa ƙafa tunda fita zeyi"
Widad tace "shikenan Allah ya temake ka, jeka seka dawo" tai maganar tare da kashe
masa ido ɗaya.
Hari tace "A'uzubullahi wannan Yarinyar idan ka zauna a inda take seta karya maka
alwala"
Dariya Yusuf yayi sukayi waje shida Saleh, Saleh yace "Salute to you Yusuf, babu
wanda ya isa ya biyaka namijin ƙoƙarin nan da kake, kalli yarinyar da take rayuwa
kamar wata halitta daban, me gudun jama'a da son rayuwar kaɗaici, amma ita ta sake
a ƙauye haka take rayuwarta, cikin farin ciki fjye da wanda take a gidansu da yake
da tarin arziki "
" Saleh, ai dama kuɗi dukiya ba sune kwanciyar hankali ba, farinciki zama cikin
wanda suka damu da kai shine farinciki, mutanen wannan zamanin muke ganin in kana
da kuɗi kana da komai, ka wuce baƙin ciki "
Saleh yace" tabbas hakane maganarka Yusuf, da fa tsakaninta da mutane kallon banza
da hantara, amma yanzu kalli yadda ta sake da Gwaggo ta maida ta kamar wata
kakarta"
Yusuf yace "sosai makuwa, akwai shaƙuwa a tsakaninsu, Gwaggo nada sauƙin kai, kuma
tana janta a jiki, bata hantararta idan tayi mata wauta ko wani abu, shiyasa itama
take sonta"
Yusuf yace "ina doubting akan wannan ciwon da take dashi, ina da question mark
akai, amma lokaci nake jira"
"Alhaji Musa, kaji wata maganar banza wai an saki Yaron nan Anwar"?
Alhaji Musa yace "haka nima labari ya isheni, ni kaina abun ya ɗauremjn kai Munir,
wane mara mutuncin ne haka, waye yayi wannan karambanin?"
Alhajj Munir yace "munyi waya da Bukar, yace ze bincika nima nasa a bincikamin amma
har yanzu babu wani labari, an rasa waye yasa a sake shi, wai daga sama aka bada
umarni"
Alhaji Musa yace "waye a saman ya bada umarni damu bamu sani ba? Ta yaya ana
tuhumarsa da wannan babban laifin za'a sake shi, idan kuwa hakane to tabbas muna da
abokan Adawa wanda suke mana zagon ƙasa akan lamarin nan"
Alhaji Haruna da tun ɗazu bece uffan ba ya nisa yace "ni kaina gaba ɗaya ya kulle,
na rasa abunyi semun toshe nan se can ya buɗe, na rasa wane banzan ne yayi wannan
aikin"
Alhaji Musa yace "tabbas akwai lauje cikin naɗi, yanzu abunda ze faru shine, zamu
saurari Bukar muji me zece, lallai a binciki wanda yayi wannaan aika aikar, sannan
a tabattar an kama yaron nan an maida shi"
"haka ma za'ayi, wannan shine abunda ya dace, akama shi harse an ga Daula"
Anwar yana zaune yana cin Abinci yace "Mumsy kin san wani abu kuwa?"
"wato bawa baya taɓa gane Allah subhanahu wata'ala yayi masa ni'ima, se yayinda
wannan ni'imar ta gushe, kinga ko 'yancin kayi yawonka ɗin nan inda kaga dama, ba
ƙaramar ni' ima bace, zama guri ɗaya bala'ine Mum, ga rashin gurin kwanciya me
kyau, ba Abinci me kyau, wai danma nine fa wasu haka suke tagayyara a cikin gurin
nan "
Hajiya Halima tace " Aini duk zance ya ƙare, tunda Allah ya fito min da kak, Se
fatan Allah ya kiyaye gaba"
Anwar yace "Ameen Mummy, ni yanzu fatana ubangiji Allah ya bayyana Daddy, yasa
yana hannu nagari, dan na tsorata da abubuwan da suke faruwa"
Mummy tace "kai kam wannan dashi ya haife ka da an shiga uku, kai har yanzu baka
shiga hankalinka ba, ba kaga masifar daka shiga saboda temako ba, still kai
tunaninsa ka keyi"
. "Mummy ba zan taɓa iya dena tunaninsa ba, saboda gudunmuwarsa a rayuwar mu"
Wayar Anwar ce ta shiga ringing, ya ajiye spoon ɗin da yake cin Abincin ya ɗaga
wayar yasa a kunnensa.
Lambar Bulama ce, bayan sun gaisa Bulama yace "Anwar ashe ka fito?"
"to Alhamdilillah, Allah ya kiyaye gaba inba damuwa ina son ganinka anan gida,
zamuyi magana"
"Mummy meyasa?"
"saboda haka naga dama, akanme zece kaje bayan ba irin sintirim da ba ba akan yasa
baki a sake ka yaƙi"
Anwar yace "haba Mummy, kidinga yiwa mutane uzuri mana, a baya kinsha neman Alfarma
yayi miki, dan wannan karon be miki ba be kamata ki manta baya ba, kiyi haƙuri i je
i ji meze ce"
"shikenan tunda kace haka, amma ba dan haka ba Wallahi da bazaka ba"
Da yamma Hindu tayi kwalliya itada su Hanne da ƙannensu zeuje biki, Widad na ganin
Hindu tace "Masha Allah, you look so beautiful Hindatu, kina da kyau masha Allah"
Hindu tace "Rufani ki saya Amarya, ai daga kanku kyau ya ƙare, kina ganina baƙa
kirin ina wani kyau yake?"
Widad tace "waye yace miki baki da kyau? Ke nima fa ba wata kyakkyawa bace, dan
dai ina da haske ne, amma baki ganki ba, kinyi kyau Allah ya baki miji nagari ɗan
birni"
"hmm Amarya kenan, ni da ban taɓa zuwa birni ba, banyi boko ba ta ina ɗan birni ze
ganni ya aura"
Widad tace "da ina da Yaya namiji zance ya aure ki Hindu, kina da kirki kaman Mama,
wai ina zakune?"
Widad tace "laaa shine babu gayyata, ku jirani zan biku, dama ban taɓa fita waje
ba"
Hindu tace "to ai Amarya baki da kaya irin Atamfa, duk kayanki ba irin namu bane,
idan muka je seki zama abin kallo, kuma dama gaki ba kalarmu ba"
Gwaggo tace "A'a amarya bekamata ki fita ba, baki tambayi mijinki ba, se da yaddar
sa sannan zaki fita"
"dukda haka, kuda kukayi ilimi ma Amarya, ai kunfi mu sanin hukuncin hakan"
Hak Widad tana ji tana gani aka tafi biki aka barta a gidan.
Bata ji daɗin hanatan da Gwaggo tayi ba, sedai bata son yi mata musune.
Daf da la'asar Yusuf ya dawo, ya taho da kayan da Saleh ya bayar a siyo musu, seda
Gwaggo ta kalli Widad sannan ta tashi, ta taya shi kai kayan ɗaki.
Ya fito ya ɗauki buta yana alwala, yace "Mama yau naga gidan shiru, ina mutan gidan
ne?"
Gwaggo tace "sun tafi biki, tace zata bisu nace karta je seta tambayeka, shine
taƙi kulani"
Yusuf yayi dariya yace "babbar magana, faɗa tsakanin 'ya da uwa yau"
Widad tace "tunda nazo fa ban taɓa fita ba, kullum ina gida"
Gwaggo tace "ɗiyar albarka a dinga saya masa sunan mana, idan daga ke se shine seki
faɗa, amma a gaban mutane mu nan abun kunyane mace ta dinga faɗan sunan mijinta kai
tsaye"
Gwaggo tace "ki dai samo wani sunan mi dinga gaya masa, kafin Allah ya baku rabo,
in kin haihu seki dinga cewa baban wane ko wance"
Haɗa ido sukayi da Yusuf, ga mamakinsa se yaga ta kwashe da dariya tace "taɓ sedai
inya Auri Hanne ta haifa masa, amma ni babu wannan Kalamin, ai Yayana ne kai ko
Yoseef?"
Tai maganar cikin sigar zolaya, tayi gaba ta bar tsakar gidan, Gwaggo ta zata
kishine yake damunta, saboda tasan yadda basa shiri da Hanne, shi kuwa Yusuf, a
wata cakwalkwalin cakwakiyar tunani ta kuma sashi, duk jikinsa yayi sanyi.
Bayan yayi sallar la'asar ya koma gida, ya tarar da Widad tana gyaran Akwati, ya
kalleta yace "Queen waye yace miki zan Auri Hanne? Idan kuma Gwaggo ba taji daɗin
abunda kika faɗa bafa?"
"Ai naga ita Hanne kaman she's having the same feelings on you, she also believes
in love"
"to waye yasan muku? Ranar da zamu koma gida, idan ka sake ni base ka Aure ta ba,
ka tafi da sabuwar Amaryarka ba"
Tsaki Yusuf yayi, saboda yaji haushi sosai, ya miƙe ya bar ɗakin, bin bayansa Widad
tayi da kallo, ta taɓe baki ta cigaba da aiki ta.
Tunda ya fita be dawo gida ba se bayan sallar isha'i, sannan yaƙi kulata kwata
kwata, dukda taji ba daɗin dena kulatan da yayi da yawan tsokanar ta da yake, yaji
ba daɗi amma ta maze ta basar dashi itama, haka kowa ya kwanta be kula kowa ba.
Da Asuba ma da yayi salla, suka zauna zaman karatu seda gari ya fara haske sannan
ya taho gidan, tun bayan da aka idar da sallar Asuba kafin a fara karatu, Saleh ya
janyo Yusuf waje yace "Nifa zan koma, sammako zanyi in tafi tunda kaji sauƙi" .
Yusuf ya ɗanyi shiru sannan ya girgiza kai yace "A'a amma zan gayamata insha
Allah"
Saleh yace "gara ka gaya mata, tayi duk borin da zata yi ta gama a nan, sedai Kayi
haƙuri, ina son insha Allah idan na koma zanje in gaida Ummanka, in gaya mata kana
cikin ƙoshin lafiya"
Yusuf yayi murmushi yace "ka gaya mata ina lafiya, kuma ina kewarta, sannan ta
kwantar da hankalinta"
Saleh yace "zan gaya mata insha Allah, sena sake dawowa"
Widad kam wanke wanke suke ita da Hindu, Hindu tace "Amarya ban taɓa tsammanin kin
iya faɗa haka ba, ashe kina sane kike ƙyale Hanne se kace bakya kishin mijinki"
Buɗe baki Hindu tayi tace "baki san meye kishi ba?"
Widad ta jinjina mata kai tace "ni ban san wani kishi ba, banajin komai ina dai ji
ana faɗa amma ban san me ake jiba"
"Lallai Amarya abun mamakin ki da yawa yake, se kace wadda akayiwa Auren dole?
Zakice ba kya kishinsa, Amma dai ai kina sonshi ko?"
Taɓe baki Widad tayi tace "Nifa ban san me ake ji ba a son nan, nifa kawai gani
nake wannan son shirme ne, babu wani so mutanene kawai ke abunsu"
Dariya Hindu tayi tace "Yanzu dai bakya son Yusuf ɗin kenan?"
"To base na yadda akwai son sannan zan iya banbance idan ina sonshi ko bana sonshi
ba?"
Hindu tace "ina mamakin kalar taki rayuwar Amarya, gaba ɗaya abubuwan ki wani
lokacin sun saɓa da na sauran mutane, anya gidan ku akwai mutane kuwa?"
Widad tayi dariya tace "eh mana, akwai mutane, sedai nikaɗai nake rayuwata"
"Amma meyasa kika dinga kuka, kika kasa cin Abinci da mijinki bashi da lafiya?"
Ɗan shiru Widad tayi tace "Saboda idan Yoseef ya mutu, nima tamkar matacciya nake,
ban san kowa anan ba se Allah se shi, sannan ya sha wahala sosai sabodani, yana
shiga damuwa idan bani da lafiya ko ina cikin damuwa, shiyasa naji rashin lafiyarsa
har cikin raina, kuma kinga ni bani da wa ko ƙani, Mamana ta rasu ina Yarinya
Babana kawai nasani, Yanzu Yusuf shine yaya na, shine ƙanina shine ɗan uwana, shine
komai nawa anan"
Hindu tace "Allah sarki Amarya, kin bani tausayi wallahi, amma Saleh yace mana ɗan
uwanki ne Yusuf"
Widad tace "ɗan uwana ne mana, Allah ne ya bawa Babana shi, ya zama garkuwa a
gareni, Hindu kina da kirki sosai naga garin nan kun ɗau Aure da mahimmanci sosai,
Allah ba yadda be iya ba, na dage ba zanyi Aure a rayuwa ta ba, babu Aure a gabana
saboda wani ƙuduri da nake dashi a raina, babu zato ƙaddara tasa na Auri Yusuf, ina
yiwa mazanmu na Hausawa kallon wanda basu san darajar Aure ba, gaba ɗaya ina yiwa
Aure kallon rayuwar muzgunawa, Amma ina miki fatan ki Auri Namji kamar Yoseef, idan
akace akwai mutum me haƙuri kamarsa zance ƙaryane, Amma yana da haƙuri sosai, nasan
yana haƙuri dani, ni gaba ɗaya tausayinsa nake ji Hindu saboda.....
Ta kasa ƙare maganar se Hawaye dake bin idonta, Yusuf yana tsaye a soro yana jin
duk hirar da sukeyi, a hankali Yusuf yayi gyaran murya tare da yin sallama.
Yusuf yace "ƙyaleta, idan bata tashi ba, zan ɗauketa ne cak in kaita"
Hindu ta sunkuyar da kai, dan abun nasu Yusuf wani lokacin basa jin kunya.
Murmushi Yusuf yayi, ta zauna ta zuba masa ido, ya fasa ƙwan ya kaɗa yasa gishiri,
dan su nan babu Seasoning.
"taɓ gaskiya kaji daɗi, ina Baban ka, baka maganarsa kullum se Ummanka kake faɗa"
"Ameen"
Ya miƙo mata ƙwan a plate, ya dafa mata tea ya haɗa mata, Widad tace "Allah sarki
rayuwa, yau ni nake murna zan ci ƙwai, alhalin har kamfanine dani da'ake fitar da
ƙwai har wajen Nigeria"
Yusuf yace "haka lamarin ubangiji yake, sedai dama da bredi se yafi daɗi"
"hakan ma nagode, zama da kai ka koyamin ci kuma da ni ba haka nake ba"
"Eh mana, so nake idan muka koma gida kar aga rama a tare da ke"
"Aikuwa ba zance kaci dole ba, cikinka ni ci zan in ƙoshi, kaita jin ƙamshinsa"
Tai murmushi tace "Gwaggo tana koyamin ai, zakayi mamakin yadda zan iya girki, inyi
girki me daɗin da baka taɓa cin irinsa ba"
Ta cigaba da cin Abincinta, ƙura mata ido yayi yaga yadda take nishaɗi, tana cin
Abincinta cikin nishaɗi, tunani yake ko ya gayamata yanzu? Tunda tana cikin
nishaɗi, to idan kuma ya ɓata mata nishaɗin da take fa?.
Ba tare da ta kalli Yusuf ba tace "gayamin abunda kake son gayamin ka dena kallona
kar in ƙware"
Jin maganar tata yayi a bazata, dan be zaci tana kallonsa ba, kuma yaji muryarta ta
a asalin Widad ɗinta me cike da izza da jin kai.
" bana son ƙarya, kuma bana son wasa da hankali Yoseef, ina jinka ka gayamin abunda
kake son faɗa "
Gaban Yusuf ya faɗi, yace " dan Allah ina son ki fahimceni dama... "
"ni mutum ce kamarka, ban isa inyi maka abunda Allah be maka ba, sedai kome bakinka
ze furta, karka kuskura kayi min ƙarya"
"to ai ƙaryar ma nayi miki Widad, shiyasa nake fargabar ta ina zan fara miki
maganar ban san yanda zaki fahimci abun ba"
Wani irin sheɗanin kallo ta ɗago idonta tayi masa, me cike da tarin tuhuma, da
gargaɗi gami da kashedi.
LITTAFIN KUƊI NE, DAN ALLAH KI SIYA KAFIN KI KARANTA, BA DANNI BA DA GIRMAN ALLAH.
A TUNTUƁENI TA WANNAN LAMBAR
07063065680
11/14/21, 6:09 PM - Ummee Musa: 52_53
LITTAFIN KUƊI NE, DAN ALLAH KI SIYA KAFIN KI KARANTA BA DANNI BA DAN ALLAH
07063065680
Gaba ɗaya Yusuf ya shiga taradaddi, gumi ya tsasttsafo masa a goshi, saboda irin
kallon da take masa, dan tun a nan yaga alamar rashin nasara.
Ɗauke idonta tayi daga kallonsa tace "ina jinka" tai maganar tana zuƙar tea ɗinta,
Yusuf yace
"Da farko zan fara da baki haƙuri dan Allah... "
Katseshi tayi ta hanyar cewa "bana son wani ban haƙuri, ka tafi kai tsaye kawai ina
jinka"
Cikin damuwa yace "dole in baki haƙuri, saboda a karon farko da ƙarya na fara miki,
tun a zuwana akan ƙarya nazo miki, saboda nima ban san ya akai hakan ta faru ba,
saboda" Se kuma yayi shiru.
Ba tare da ta kalle shi ba tace
"to tunda ka kasa gayamin ni bari in gaya maka abunda kake son faɗa ɗin ka kasa, na
farko kai jam'in ɗan sanda ne na sirri ko ba haka ba?"
Ƙuuuu cikin Yusuf ya kaɗa, ya kalle ta a razane, ta ci gaba da cin Abincinta tace
"cigaba na fara maka, ƙarasa ina jinka, saura me kuma?"
Kasa magana yayi, ya dinga binta da kallo cike da ban al'ajabi, kamar yaga wata
halitta daban.
"yanzun ma zaka cigaba ne ko in cigaba da gaya maka"? Tai maganar tana kallonsa
Cikin isa da taƙama tace "An turo ka ne a matsayin jami'in sirri, da sunan wai ka
bani kariya ko?"
Buɗe baki Yusuf yayi yana kallonta, amma ya kasa cewa komai dama tasan waye shi?
Wani irin yawu Yusuf ya haɗiye da ƙyar, kai da ka ganshi kaga mara gaskiya, yadda
yake ta gumi kuma ya kasa cewa komai.
"tunda ka kasa magana bari in ƙarasa maka, bayan bani kariya da kake, kuma kana yin
bincike akan maƙiyan mahaifina, da wanda suke bibiya ta, ka maida hankali sosai
akan aikinka, sannan kana taka tsan tsan dan kar in san ko kai waye"
Ta ɗanyi shiru tana nazarinsa sannan tace "Sannu Yoseef amma meyasa kasa hannu
akan contract ɗina, bayan na gaya maka bana yafewa maƙaryaci?, saboda tsabar taurin
kai, son aiki da rashin nuna gazawa ka saka hannu, dukda baka san wane irin hukunci
zan ɗauka akanka ba idan na ganoka, idan ban manta ba a lokacin nace if you know
you are here to spy don't sign the contract, but you feel like to sign it, saboda
ba zaka iya komawa Office ba tare da kayi aikin da'aka turoka ba right? Yoseef
meyasa kayimin ƙarya? "
Jiki a sanyaye Yusuf yace " ai kin bawa kanki wannan amsar Widad, bazan iya komawa
ince ba zanyi aikin ba, saboda Alƙawari nayi kafin in fara aiki zan kare rayuka da
dukiyoyin jama'a, kuma tunda na fara aikin, dagaske har cikin zuciyata naji ina son
in baki kariya, musamman ranar da mukaje gurin birthday Nurat akayi yunƙurin
saceki, tun anan na fara karaya, na ƙara tabattarwa lallai rayuwarki a hatsari
take, dan haka nayi ɗamarar baki kariya iya iyawata, amma dan Allah ya akayi kika
san wannan abubuwan haka?"
Ta ɗan jinjina kai tace " lallai biri yayi kama da mutum, ranar ba yadda banyi da
kai ka gayamin meyafaru ba, amma kaƙi ka gayamin, nima nasan nayi ganganci a wannan
ranar, na zuwa gidan Alhaji Musa, sedai ina ƙoƙarin cire kaina a cikin rigimarsa da
mahaifina, shine dalilina na zuwa gidans, amma shima ka ɓoyemin baka gayamin
meyafaru ba ranar, meyasa? "
Yusuf yace " saboda muddin na gaya miki zakiyi yunƙurin ɗaukar mataki ne, da kinyi
yinƙurin yin haka nikuma Asiri naa ze iya tonuwa, kuma zaki ɓata komai ne, Amma dan
Allah ya akayi kika sani? "
Cikin isa tace "Lallai ka raina Wacece Widad da kuma AƘIDARTA, in dai nice har
yanzu bakaga komai ba, Tunda kazo gidanmu, jikina ya bani akwai something different
with you, either good or bad, na kasa nutsuwa, na dinga ɓullo da abubuwa daban
daban amma na kasa gane komai na cutarwa a tare da kai, ranar da 'yan sanda suka
kama ka da bindiga, ni na fara ganin bindigar a jikinka kafin mu fita daga gida,
kazo shiga mota ka ɗaga rigarka naga bindigar, nai shiru ban nuna na gani ba, dan
ina son sanin da wacce kazo, sannan inga wani hukunci ne ya dace da kai, bayan mun
fita a ranar aka kamaka da bindiga ka bawa 'yan sanda id card, sukayi ƙoƙarin
saluting ɗinka amma ka hanasu, tun daga nan nabi diddigi da ƙwaƙƙwafinka na gane
waye kai, har headquarter ɗinku naje aka bincikomin waye kai, sedai abu ɗaya ne ban
gano ba har yanzu, waye yasa a baka aikin nan?!"
Yusuf yayi ajiyar zuciya, cikin damuwa yace " Nima ban sani ba, da bani za'a bawa
aikin ba, amma abokin aikina yace a bani na fishi haƙuri, ban san waye ya bada
aikinba nima"
Widad tace "Abokin aikinka Sani me zuwa gurin Isa megadi ko? Wato Abbas"
"Ni na saka aka ɗauke shi daga kano, aka kai shi kudancin Nigeria saboda ban yadda
dashi ba, yayi ruwan Azzalumai da yawa"
Yusuf yace "Dama kece kika saka aka ɗauke shi? Ba mugu bane aminina ne, bani da
aboki sama dashi"
"Yana ɗaya daga abunda yake cutar da mutane, shine saurin yadda, waye ya gaya maka
duk memaka dariya sonka yake yi? Kayi kuskure ni bemin ba, shiyasa nasa aka rabashi
da garin nan, sannan ina cike da son sanin waye ya bada wannan aikin"
Yusuf kam rasa bakin magana yayi, se kallonta kawai da yake yi.
Widad tace "shikenan" ta miƙe tsaye ta ɗau kwanukanta, yaji taja sumar kansa tace
"matsoraci kawai, ashe haka kake da tsoro, i wish kaga idonka yadda suka sauya,
kaine mutum na farko da na yafewa wanda yai min laifi mafi muni, saboda kaima
hanyar da akabi aka baka aikin dan a cutar da kaine"
"Bazan faɗa ba, ban yadda da kai ba" tai waje abunta tana dariya.
Mamaki ya cika Yusuf tatil, yanzu dama kallon biri yake mata take masa na Ayaba,
tasan waye shi tsawon lokacin nan, be taɓa zaton zata gane ba yadda ya dinga taka
tsan tsan, lallai Widad ba ƙaramin wayone da ita ba, amma kuma yana da tarin
tambayoyi daze mata, amma taƙi bashi damar yin hakan.
Anwar ne ya shigo falon mahaifiyarsa yace "Mummy zanje kiran da Babansu Fahad yake
min ne"
"Saboda haka naga dama" ta bashi amsa, ta ɗau wayarta ta kira Amal tace tazo.
Amal tace to, Hajiya Halima ta kalle shi tace "jeka mota ka jira ta"
Anwar ya fita kamar yadda aka bashi umarni, Amal ta shirya ta koma ɗakin
mahaifiyarta, tace "Mummy gani na shirya"
"Yawwa ki buɗe kunnenki ki jini, wannan yayan naku wani lokacin sakaraine, ba
hankali ya cika ba, ina son ki saka min ido akansa, duk abunda ya faru ko abunda
Bulama yace idan kun dawo ki gayamin"
Suna zuwa gidan Bulama, Ramadan da Iman suka shiga murna Ramadan yace "Sannu
Anwar, barka da Arziki Allah ya kiyaye gaba ya bayyana Daddy"
Nan suka tsaya suna hira, Hajiya Sarah ta fito daga ɓangaren ta, itama tana ganin
Anwar ta faɗaɗa murmushinta tace "Anwar, sannu Anwar ashe ka fito da yau naso inzo
har gida in maka jaje, Amma naji alamun hawan jinina ya tashi, shiyasa na fasa
fitar"
Amal tayi murmushi tace " Mummy kenan tana lafiya "
Bulama ne ya sakko daga kan benensa, bayan ya sakko Anwar cikin girmamawa ya rusina
yace " barka da Yamma Daddy "
Ya kalli Anwar yace "barka da Arziki Anwar, ba irin sintiri da shiga ficen da
ba'ayi ba akan aga an samu ka kuɓuta amma Allah be nufa ba, amma ya akayi suka
sakoka ne suka bar Sufyan?"
Anwar yace "to nima dai wani mutum ne yazo ya taho dani, bemin wani gamshashen
bayani akai ba, ya cemin shima wanine ya turoshi"
"Allah sarki, haka lamarin ubangiji yake ai, kaga mu ba yadda bamuyi ba amma abu ya
gagara, mahaifiyarka ta ɗaga hankalinta ta dinga ganin kamar bama wani ƙoƙari akai,
se gashi Allah yayi an sako ka, to ubangiji Allah ya kiyaye gaba"
"Ameen ya Allah Daddy, Daddy nace to har yanzu babu wani labari akan ɓatan Daddy,
har yanzu ba'a san inda yake ba?"
Bulama cikin damuwa yace "Anwar da akwai wani labari ai da kaji, babu wani labari
har yanzu, binciken ake amma kamar ba'ayi"
"ubangiji Allah ya bayyana shi, ni fatana Allah yasa yana hannu nagari, tunda bashi
da lafiya"
Hajiya Sarah tace "sha'anin ƙasarmu ai se Addu'a, banda haka ace an sace mutum
kamar Alhaji Daula, abun da mamaki kuma har yanzu ko a jita jita babu wanda yaji
inda yake, bawan Allah nan ba lafiya ba, yana fama da kansa ga tashin hankalin an
sace masa 'ya, Amma a bishi har gadon Asibiti a sace, ga' yar tasa har yanzu babu
wanda yasan inda take, abun akwai ban tausayi, Daula yana ganin Jarrabawa "
Bulama yace " tabbas, yana ganin jarrabawa, na rasa wani irin abune wannan ita
kanta Widad wata na biyu zuwa uku kenan da ɓatan tal, amma babu labarin inda take,
ni abun har tsoro yake bani"
Anwar yace "gaskiya ne, abun da tsoro kam, kamar Widad tasan meze faru ranar da
zasu tafi farm house, tana kuka tacemin ga Amanar Daddy nan in kula dashi, nace
mata zanyi iya ƙoƙarina, Amma ga abunda ya faru, i don't even know how to explain
this incident to her when she's back "
Ramadan dake gefe yace " Allah sarki, karka damu ai duk wanda yaji abunda ya faru
yasan ƙaddara ce, Amma ni wani lokacin har mamakin Widad nake, yarinyar nan 'yar
baiwace akwai ta da kai"
Anwar yace "sosai makuwa, ina fatan Allah ya bayyana mana su gaba ɗaya"
A harabar gidan suka haɗu da Fahad, Fahad yana ganinsa cike da borin kumya ya
rungume Anwar yana faɗin "Ohh God, so you are free now, Alhamdilillah na ta yaka
murna, Allah ya kiyaye gaba, nace zanje in duba ka akace ba'a bari a ganku"
Anwar yace "Haba kamar kai kaje inda nake ace bazaka ganni ba, da kazo da zamu iya
haɗuwa ai"
Fahad yace "kasan bana son disgracing, and those people are good in that, but da
naji ance court za'a kaiku ya akayi ka fito?"
Tsaki tayi tai masa wani irin kallon banza, ta buɗe mota ta shige.
Anwar ya girgiza kai yace "Fahad bari inje, akwai inda nake son zuwa daga nan".
Anwar yayi murmushin yaƙe yace "Fahad kenan, za suji insha Allah"
Suna cikin tafiya Anwar yace "wai Amal meyasa kuke yawan faɗa da Fahad ne? Banji
daɗin abun kikayi masa ba, ya yanki ne fa"
Amal ta kwaɓe baki tace "nifa wallahi Yaya Anwar na tsani Fahad ɗin nan, nifa tun
asali bemin ba, mugun maƙaryaci ne munafuki duk yadda kuke dashi ya kasa zuwa ya
jajanta maka abunda ya same ka"
Anwar yace "to meye a ciki? Koma menene ba gashi Allah ya fito dani ba, idan kace
zaka dinga biye wa mutane ranka ne kawai ze ta ɓaci"
Amal tace "taɓ ai kai zuciyar ka daban Yaya, ba kowa ze iya wannan abun naka ba"
Da suka je gida a waje yayi parking, ya kalli Amal yace "sauka ki shiga gida, ina
son zani wani guri ne"
Ba musu ta sauka daga motar ta shige gida, shi kuma Anwar ya tafi.
Shiru shiru Yusuf be fito daga ɗaki ba, har Widad taje tayi wanke wanke ta dawo
yana zaune a inda ta barshi, ta kalle shi tace "wai yau bazaka fitan bane?"
"to ai naga ko wanka ba kayi ba, ko har yanzu tunanin kake ne?"
Ɗan murmushin yaƙe yayi, yana sake mamakin Widad, ya miƙe yaje yayi wanka ya
shirya, yana yi yana kallonta yaga ko zata canza masa, amma yaga babu wata alama ta
damuwa a tare da ita.
"zan tafi"
"Wai naga se wani sunkuyar da kai kake, kana komai a sanyaye meyafaru ne"
A hankali Widad tana ta koyon abubuwa, dan yanzu ta fara iya saƙa mafici da Hindu
ke koya mata, tana gane abubuwa duk aikin da zasuyi seta shiga cikin su tana
ƙoƙari.
Yanzu indai Widad zasu gaisa da Hindu da turanci suke yi, Hindu na da matuƙar
ƙoƙarin riƙe abubuwa, gashi ta sawa zuciyar ta zata iya, tana son karatun sosai,
Widad ta koya mata na boko sannan tana mata bayani akan litattafan addini, sega
Hindu ta iya gaisuwa da turanci, tasan sunan abubuwa, Widad tana yawan yi mata
magana da turanci dan wasu lokutan hausar ma wahala take mata, dan haka Hindu take
kama wasu abubuwan.
Nan fa Hindu ta fara birge wasu daga cikin ƙawayenta, suke cewa itama ta koya musu.
Hindu suna ɗaki tana yiwa Gwaggo tsifa tace "Gwaggo, kinga laraban gidan me
tabarma, da su Ishalle ne wai suma suke son a dinga koya musu karatu, nace zan
tambayi Amarya amma nauyinta nake ji, kar taga kamar na takura mata"
Gwaggo tace "kunfi kusa keda ita ai, Amma na lura kamar bata son mutane fa, kina
ganin ko baƙi akayi ɗaki take komawa bata son mutane, amma ki tambaye ta idan zata
dinga yi muku taren"
Hindu tace "to shikenan zan tambayeta insha Allah, Amma nikam Gwaggo Amarya ba
ƙaramin mamaki take bani ba, wai bata son meye kishi ba, kuma wai ita gani take
Soyayya ƙaryace da ɓata lokaci, na tambayeta to bata son mijin nata? Wai wallahi
itama bata sani ba ko tana sonshi ko bata sonshi "
Gwaggo tayi murmushi tace " Amarya 'yata ta kaina, yarinyar kam tabbas yarinta ce
ke damunta, kuma kinga karta kamar shagwaɓaɓiya ce, bata san abubuwa da dama na
rayuwa ba, shi kansa zaman Auren da alama bata san meye ba, Amma insha Allah ina
son in zauna da ita, in dinga yi mata nasiha, naga tana jin faɗa, dan Hindu ina jin
takaicin Abunda Hanne ke aikatawa a gidan nan, yadda take shigewa Yaron nan, dan
ina daf da kai ƙararta gurin mahaifinku"
Hindu tace "A'a Gwaggo dan Allah kiyi hakuri, idan kika gaya masa ze ɓata mata rai
sosai, ni mamakin da ta ke bani da kuɗin Aurenta a ka fa, amma take haka, ki dai
cigaba da ja mata kunne zata dena"
Har Yusuf ya dawo a cikin damuwa yake, saboda ya fuskanci kwata kwata gane kan
Widad se Allah, yanzu zaku zauna lafiya ana jimawa ta canza gaba ɗaya.
Widad bata san ya dawo ba, ta fito daga wanka tana zuwa ta tarar da Yusuf ya kwanta
a ƙasa, ya lumshe ido.
Widad tace "ya dai harka dawo ne? Ya naga ka kwanta haka a ƙasa, ko jikinne?"
Ya buɗe idonsa ya kalleta yace "Eh na dawo, na gajine sosai bayana da ƙafafuna ciwo
suke min"
Ajiye bokitin tayi ta zauna kusa dashi tace "me kaje kayi a wajen bayanka yake ciwo
sekace tsoho?"
'meye kuma Faskare? " ta tambaye shi, kallonta yayi yace " Faskaren ne baki sani
ba? "
" Wallahi ban sani ba, kaima kana ganin wani abun idam nace ban sani ba ƙarya nake
ko? "
" A' a ni bance ƙarya kike ba, nasan baki sani bane, kuma daɗina dake idan baki
sani ba kina tambaya"
Widad tace "to ai ba wani abu bane, idan mutum be sani ba gara ya tambaya, ka tashi
kaci Abinci seka yi wanka mana"
"Ai sunan naki ne bana son faɗa, kuma Daddy ma Gimbiya yake ce miki, ko in koma ce
miki lovely kamar yadda yake faɗa?"
Dundu tayi masa tace "A'a Widad zaka dinga cemin, niba lovely kowa bace ta Daddy
ce"
Yusuf yace "so kike Gwaggo tayi min faɗa? Tace ina faɗar sunan ki"?
Dariya Widad tayi tace "Hajiya Mama manya, tace in dena kiran sunan ka fa ko?"
"Eh amma baki dena ba kuma, ga sunan nawa ma baki iya faɗa ba, ana Yusuf kina
Yoseef amma fa suman yana min daɗi in kin faɗa"
Murmushi tayi tana danna masa baya tace "shikenan zan dinga cewa Yayana, kamar
yadda Daddy yake ce maka"
Yusuf yace "A'a nifa mijinki ne ba Yayan ki ba, call me with romantic names mana,
haba ke kuwa"
Shiru tayi masa, a hankali ya juyo daga ruf da cikin da yayi yace "Nagode sosai My
wife, Allah yasa ki a Aljanna, naji daɗin tausar nan kamar karki dena, dama kin iya
kula da miji haka?"
"A'a zomaye na iya kulawa da, ai koma meye kaika koyamin, idan bani da lafiya
kayimin ina jin daɗi, shiyasa nayi maka"
Shiru ya ɗanyi sannan yace "Widad, meyasa kika ƙyaleni dukda girman laifin da nayi
miki, baki hukunta ni ba?"
Widad tace "Saboda Widad ba azzaluma bace, babu zalunci a AƘIDATA, duk wanda na
kasa yafewa abunda yayi min to tabbas girman laifinsa ya wuce tunani, ya wuce
laifin da zan iya yafewane"
"tabbas laifinka ya kai girman a hukunta ka, sedai kash akwai wani dalili me ƙarfin
gaske daze hana ka karɓi hukunci, akwai wata ƙaddara da ta ratsa, ita ce zata hana
ka karɓi hukunci, sannan idan nace zan hukunta ka Yoseef banwa kaina adalci ba, dan
ka bani kariya ka bawa rayuwata kariya sosai, Allah ma muna masa laifi ya yafe mana
ai, matsoraci kaga gumin da ka dingayi ɗazu kamar ba kaine Jarumin ɗan sanda ba me
gwagwarmaya kamar yadda aka bani labari, amma se gashi ina baka tsoro"
"Wudas babu Jarumi a soyayya, ba hukuncin da za kimin ne damuwata ba, kice zaki
rabu dani shine damuwata"
"A ina?"
"da wani sunan ka kirani?"
"kaima ko? Zanyi maganinka da kai da Harin da kuke ɓatamin suna, ni ba haka aka
samin ba"
"niba ruwana, ɗanawa kawai nayi ai, kuma sunan naki ne na Larabawa, ba kowa ze iya
faɗa ba"
"Yoseef ina missing ɗin Daddy sosai, zuciya ta na kwaɗayin in ganshi, i missed a
lot from him, ina kewar babana, dashi na rayu na buɗi ido, amma yanzu muna duniya
ɗaya amma munyiwa juna nisan gaske, a dalilin wasu tsirarin mutane da suka saka
rayuwarmu a gaba "
Hawaye ne ya fara bin idonta, janyota jikinsa yayi ya shiga share mata hawayen
cikin tausayawa yace " tabbas yin nesa da wanda muke so ba abune me sauƙi ba, kin
ganni nima ban taɓa nisa da mahaifiyata haka ba, amma mu ɗau wannan a matsayin wata
ƙaddara ta darasin rayuwa, kiyi hakuri insha Allah zamu koma kiga Daddy, nasan
zaman ƙauyen nan tamakar zaman prison ne a gurinki amma ki daure mu cinye
jarrabawar mu"
Ajiyar zuciya ta sauke, ta sake kwanciya a jikinsa tace "zamana a ƙauyen nan baya
damuna, na ɗau hakan tamkar wani darasine na rayuwa, Allah ya na nunamin ishara, na
koyi abubuwa da dama na rayuwa wanda bam sansu ba da, kuma a nan ina zaune
hankalina a kwance babu tashin hankali, babu fargabar komai saɓanin a gida, ga
dukiyar ga komai hankalina kullum a tashe ina tunanin ta inda maƙiya zasu farmin,
nidai tun taso wata rayuwata a cikin ƙaddara take, ina fatan Allah ya kawomin
ƙarshen abun nan haka, ya kawo kwanciyar hankali a gareni da mahaifina"
Tai maganar tana ci gaba da zubar da hawaye, sosai tausayinta ke ratsa ilahirin
jikin Yusuf, ya dinga shfa gashin kanta cikin sigar rarrashi zuwa gefen fuskarta,
yana tunanin anya duk ƙaddarar da Widad ta tashi a ciki takai a misalta ta dashi
wadda ya tashi a cikinta?......
LITTAFIN KUƊI NE, DAN ALLAH KI SIYA KAFIN KI KARANTA BA DANNI BA DAN ALLAH
NA ƊAYA KYAUTA NE, WANNAN NA SIYARWA NE
₦300 TA WANNAN ACCOUNT ƊIN
0009450228
JA'IZ BANK
AISHA ADAM
A TURA SHEDAR BIYA TA WANNAN LAMBAR
07063065680
11/14/21, 6:09 PM - Ummee Musa: 54_55
LITTAFIN KUƊI NE, DAN ALLAH KI SIYA KAFIN KI KARANTA BA DANNI BA DAN ALLAH, LITTAFI
NA ƊAYA KYAUTA NE WANNAN NA SIYARWA NE
NORMAL GROUP ₦300
VIP ₦500 NE KITURA TA WANNAN ACCOUNT ƊIN
0009450228
JA'IZ BANK
AISHA ADAM
SE A TURA SHEDAR BIYA TA WANNAN LAMBAR
07063065680
Shiri ne ya wanzu a tsakaninsu, na wani ɗan lokaci, har bacci yayi awon gaba da
Widad, Yusuf ya ƙurawa fuskarta ido, yana jin wani abu na fizgarsa game da ita,
wani irin sonta na ƙara ratsa ilahirin jikinsa.
Wai yau Widad ce kwance a hannunsa, har take masa kuka yana rarrashinta, kamar ba
itace wannan me tsawa da muzuran ba, ya kwaɗaitu da son jin meyafaru da ita a
rayuwa, meyafaru a rayuwarta haka? Amma yasan idan ya takura seya sani, to tsaf ze
rusa duk wata alaƙa da yadda da take tsakaninsu
Anwar kuwa gidan su Nurat ya tafi, seda yaje ƙofar gidansu sannan ya ɗakko wayarsa
ya kirata, tana kwance tana kallon TV sedai idonta ce kawai akan tv, yayinda
zuciyar ta tana can tana fama da tunani, se da wayar ta katse ya kuma kira sannan
ta faraga, tasa hannu ta ɗaga wayar sedai tayi mamakin ganin sunan wanda yake kan
wayar, Sunan Anwar ne a jiki.
Cikin farin ciki Nurat tace "innalillahi, i don't even know what to say, I pray
that am not dreaming"
Anwar yayi murmushi yace "you are not dreaming dear, ina harabar gidanku"
Mayafin doguwar rigar jikinta ta ɗauka ta yafa, ta ruga da gudu tayi waje, aikuwa
tana zuwa ta tarar da Anwar zaune a cikin mota, da sauri ta ƙarasa gaban motar,
tana ganin Anwar ɗinne kuwa kawai ta tsaya tana murmushi a lokaci ɗaya hawayen
tausayinsa da farinciki ya shiga bin fuskarta.
Ya rame sosai, se dogon hanci da manyan idanunsa da suka sake yin zuru zuru, ga
duhu da yaya, koba a gaya maka ba akasan inda yaje babu komai se zunzurutun wahala.
"Yaya Anwar dole inyi kuka, baka ji ba baka gani ba daga abun alkhairi aka kama ka,
kaje kasha wahala ba yadda banyi ba a ɓoye a samu a sakeka amma abu ya gagara,
ƙarewa ma akace kotu za'a kaika na shiga damuwa sosai hankalina ya tashi, se gashi
Allah yasa ka fito Alhamdilillah, ban taɓa zaton zaka fito ba"
Anwar yayi murmushi yace "hakane, amma yanzu dena kukan mana"
Murmushi tayi tace "ƙyaleni na farinciki ne, taso muje Mummy ma na ciki seku
gaisa, amma dan Allah karka nuna muna wani abu tarene, kawai dai ka nuna ka biyo a
gaisa ne please"
Ya miƙe ya bita zuwa cikin gidan, a falo ya zauna yayin da Nurat ta shiga ɗakin
mahaifiyarta "Mummy kizo ga Anwar yazo ku gaisa"
Mummy tace "Allah sarki, yaron kirki ashe an sake shi, bari gani nan bari inzo
mugaisa"
Ta sako mayafi ta fito, Anwar ya risina ya gaishe ta tace "Anwar ashe an sako ka?
To Ubangiji Allah ya tsare gaba"
Nurat ta jashi suka koma harabar gidan, ta kalle shi tace "Yaya Anwar, ya akayi ka
fito ne?"
Ya ɗanyi ajiyar zuciya yace "kowa tambayar da yake min kenan, wallahi ban sam waye
ya fito dani ba, ban san mutumin ba, na tambaye shi waye shi, yace wai ba'a bashi
damar ya sanar dani waye shi ba, amma kin san wani abu?"
Anwar ya ɗan ƙara ƙasa da muryarsa yace "ya cemin Daddy yana gurinsu, shiyasa ma
suka sa aka sakeni, amma ban san dalilin da yasa suka sa aka sakeni aka bar Doctor
Sufyan ba"
Zaro ido tayi tace "yana gurinsu kuma? To suwaye su? Meyasa suka ɗauke shi?"
"Nima be bani amsa ba Nurat, abun da ya cemin kawai kenan, wallahi gaba ɗaya a
cikin damuwa nake, babu Widad babu Daddynta, gashi ranar daza'a ɗauketa kamar tasan
abunda ze faru tacemin Anwar ga Amanar Daddy na nan ka kulamin dashi"
Cikin damuwa Nurat tace "kayi haƙuri Yaya Anwar, Allah ya gani kayi iya ƙoƙarinka,
amma ƙaddara fa ta riga fata, babu yadda muka iya, sedai muyi ta musu Addu'a Allah
yasa suna hannu nagari"
Anwar yace "Ameen, Amma abun da damuwa ace mace kamar Widad a hannun wanda ba'a san
ko suwaye ba, akwai tashin hankali sosai Nurat, kin san ku mata kusa a cikin
hatsari kuke, daɗina ɗaya tana tare da Yusuf, amma dukda haka abun ba daɗi, mussman
shi ƙaddara ta faɗa masa beji ba be gani ba"
Nurat ta ɗanyi shiru tace "hakane kam, ni kaina ina tausayin Yusuf Anwar, amma dan
Allah dagaske direban Widad ne?"
Ɗan girgiza kai tayi tace "yana da kirki sosai, kuma da alama ta yadda dashi sosai,
na zata ɗan uwantane"
"Nima na gani, kuma yana ƙoƙari sosai akanta, yana mata biyayya ne sosai, kuma yana
da haƙuri shiyasa suke shiri wasu lokutan"
Nurat tace "hakane kam, amma kuwa anje gidan su Yusuf ɗin, 'yan uwansa sun san
halin da yake ciki?"
"Aini kinga ban daɗe da dawowa ba, wasu abubuwan duk ban san me ake ciki ba, ban
san daga ina yake zuwa ba, sedai zan bincika inji ubangiji Allah ya bayyana mana su
gaba ɗaya, amma ina cikin damuwa sosai Nurat, tun Widad na ƙarama nake sonta, ban
taɓa furtawa ba, saboda sanin halinta, katsan bayan na dawo naji ance Fahad ɗan
gidan Alhaji Bulama zata aura, naita ƙoƙarin in cireta daga raina, sedai ashe ita
gaba ɗaya bata da babban maƙiyi a duniyar nan sama da Aure, tana yiwa Aure wani
bahagon kallo ne, har a yanzu haka na kasa cireta daga raina, ina jin sonta a
zuciyata, ko bacci bana iyayi yadda yakamata, gashi ban san inda take ba gashi na
kasa riƙe amanar data barmin"
Wani irin tausayin Anwar ne ya kamata, a ranta tace 'ashe kaima kana cikin damuwar
da nake ta soyayya'
A zahiri kuma tace "na tausaya maka Yaya Anwar, ka sawa ranka wannan ɗin Jarrabawa
ce, ubangiji Allah yasa mu cinye jarrabawar nan, kasha Lemom mana"
Girgiza mata kai yayi yace "A'a tafiya zanyi nagode sosai Nurat"
Ɓata rai tayi tace "gaskiya idan baka sha ba bazan ji daɗi ba, sekace na baka wani
guba, ko kaima Widad ɗinne?"
Mahaifin Nurat ne ya dawo suna tsaka da hira, ya shigo da motarsa gidan yayi
parking, ya fito daga motar yazo ze raɓa su ya wuce, Anwar yace "barka da Rana
Yallaɓai"
Ɗan tsayawa yayi ya kalli Anwar yace "wa nake gani haka kamar Anwar?"
"to yayi kyau haka ake so ai, har yanzu kuma babu wani labari akan ɓatan Daula ko?"
Alhaji Musa yace "gaskiya ne, ai dama bekamata a tsare wanda bashi da laifi ba,
hakan ba daidai bane, kuma lawyoyin naku ne suka fitar da kai?"
"A'a su hana su belina akayi, daga baya ma in sunzo hana su ganina ake, wani mutum
ne yazo aka fitar dani"
Duk a aikin gida da Widad ke koya bata taɓa attempting zuwa gaban murhu ba, saboda
bata son hayaƙi sam, ko menene tana daga gefe.
Tana zaune a ƙarƙashin bishiya tana gyaran wake, Hindu tace "Amarya dan Allah
ƙawayena ne suke so suma a dinga koya musu karatu, in basu dameki ba, in baza'a
takura miki ba"
Widad ta ɗanyi shiru sannan tace "shikenan tunda ta hanyar ki ne, aini ban isa ince
a'a ba, su samo abun rubutu da littafi se mucigaba insha Allah"
Gwaggo tace "Amarya idan da takura fa karkiyi kara, kice musu a'a kawai su haƙura"
"A'a Mama babu takura, bana son mutane ne dai su fiye zuwa inda nake, amma ai
bakomai shi ilimin 'ya mace ai abun sone, koba komai zasu amfani al' ummar da suke
ciki, suzo zan koya musu Insha Allah"
Gwaggo tace "to Allah ya saka miki da Alkhairi, mu zuwanki garin nan alkhairi ne
ai a wajenmu"
Widad tai murmushi tace "bakomai Mama, nima haɗuwata daku alkhairi ne ai".
Hindu tace "lallai su Indo zasuji daɗi, bari inyi sharar nan inje in gaya musu"
Hari tace "wudas dan Allah nima gasu abu na nan a haɗamin dasu dan Allah"
Hararta Widad tayi tace "baza'a koya musu ba ɗin, yaren yahudawan zan koya musu?"
Hari ta wangale baki tace "haba Wudas, dan Allah kiyi haƙuri ki koya musu"
Hari bata kuma yin magana ba, tayi shiru ganin yadda Widad ta haɗe rai, Hanne ce ta
fito tana wani yatsine fuska tana harare harare, Hindu ta kalle ta tace "Hanne ke
zakiyi wanke wanke fa yau, kin bari ƙudaje se bin kwanukan suke"
Hanne ta galla mata harara tace "bazan ba, inda can ke kike sani inyi, banza uwar
shisshigi da sa ido"
Hindu tace "ke kika sani, haka za'a miki auren kije kina ƙazanta, ki bar kwanuka
ƙudaje nabi"
"Eh naji gara ni inada mashinshini ma, kefa ba uban wanda yake zuwa gjrinki, aba
kamar mujiya aikin banza kawai"
Shiru Hindu tayi tana goge Hawaye, Gwaggo ce ta janyo Hanne ta dinga kifa mata mari
a zuciye.
Widad tace "wai Auren nan dolene? Meye dan mutum bashi da saurayi? Saurayin banza
dana wofi, Auren dole ne, itama wannan banzar mata hankali se kace ba sister ɗinki
ba, kuna uwa ɗaya kina cin zarafinta"
Hansai tace "ba uwarsu ɗaya ba, Hindu ita kaɗai babarta ta haifa ta rasu, Gwaggo
ce ta Riƙeta"
Widad tayi mamaki sosai, dan yadda Gwaggo ke son Hindu seka zata ita ta haife ta.
Widad ta ƙarasa inda Hindu ke tsugune tana kuka, Widad taje ta rugumo Hindu ta
dinga rarrashinta tace "kiyi haƙuri kinji Hindu, Allah has a better plan for you
kinji Hindu, kiyi haƙuri ki ƙyalesu, ai Aurem ba dole bane"
Gwaggo seda tayiwa Hanne tatas da zagi, ta tsitsstinka mata mari, tazo ta kama
hannun Hindu tace "dan Allah kiyi haƙuri kinji Hinduna, muna nan insha Allah miji
nagari zezo miki insha Allah"
Ita dai Hindu ba tace komai ba, se goge hawayenta da yake faman yi, tana jin zafin
Gorin da akan mata na cewa bata da saurayi, Widad ma abun ba ƙaramin baƙantawa
Widad rai yayi ba, dan bata son taga abunda ze taɓa mata Hindu, Allah ya haɗa
jininsu sosai.
Widad ta kalli Hari tace "kekam abunda kika yi baki kyauta ba Hari, ke kanki aka
bibiya sadakarki aka bawa megari ba dan kina da wani abu da namiji ze kalla ya
aureki ba, dan ba kyau kika fi Hindu ba, yakamata ki dinga jan girmanki kema kin
haifi mata"
Gaba ɗaya ƙarashen wunin nan haka Hindu tayi shi ba walwala, hakan ya shafi
Walwalar Widad itama, seta kasa sakewa sukayi jugum jugum.
Nurat suka gama hirarsu da Anwar, tai masa rakiya har mota ya tafi, sannan ta dawo,
tana shiga falo ta tarar da mahaifinta a tsaye yana huci, ya kalleta yace "dan
ubanki meya haɗaki da wannan yaron?"
"ina ruwana koma uban waye? Ke yanzu shikenan ban isa in gayamiki kiji ba? Meye
haɗinki dashi nace?"
Mahaifiyar Nurat ce ta fito da sauri tace "dan Allah ka saurarawa yarinyar nan,
wucewa yazo yi ya tsaya suka gaisa meye abun ɗaga hankali kuma? '
" ke dama ke kike goya mata baya take karyamin doka, ni anya ma kuwa wannan' yata
ce"
Cikin mamaki tace "Meka ke nufi da anya kuwa 'yarka ce? Zargina kake kome? Kokuma
dan kana abu zata kake kowama haka yake?"
"to kace ƙaryane mana? Ni zaka kalla kace anya 'yarka ce?"
Aikuwa cike da zuciya yayi kan mahaifiyar Nurat, sedai cikin gaggawa Nurat ta shiga
tsakani tana kuka, aikuwa yasa hannu ya shaƙota yayi wurgi gefe ɗaya, bisa
tsautsayi tai gware da center table, take ta zube a gurin jini ya shiga zuba a
goshinta kamar an buɗe famfo, take suka yi kanta da gudu, sedai ko motsi ba tayi.
Mahaifiyarta ce ta ɗagota a gigice tana kiran sunanta, Alhaji Musa yasa hannu yana
ƙoƙarin karɓar Nurat a hannunta amma ta riƙeta gama taƙi sakarmasa ita, cikin kuka
tace "ka ƙyalemin 'yata, ai dama kace ba' yarka bace, tunda ka kashemin ita se
hankalinka ya kwanta"
Be saurareta ba ya suri Nurat da sauri yayi waje da ita jini yana zuba a goshinta.
Amal kuwa bayan ta shiga gida, Hajiya Halima tace "ina Anwar ɗin?"
"Nifa bana son yawan yawon nan da yake tafiya, se wani abun ya sameshi tukuna ko?
Ze dawo ya sameni ne, ina jinki meyafaru da kukaje gurin Bulama"
Amal tace "ba wani abu bane, dama kawai tambayarsa yayi ya akayi yayi free? Se kuma
jaje da yayi masa"
Hajiya Halima tayi tsaki tace "Aikin banza, dana san hakane wallahi ba zashi ba,
mutumin banza kawai"
Amal tai murmushi tace "in an jima zamuga kun jone ai, ba'a shiga faɗanku"
Widad bata wani iya rarrashi ba, dan haka ta kasa saka Hindu farinciki, haka kurum
idan ta tuna Gorin da'akayiwa Hindu se taji ta ƙara tsanar Hanne, sam Hanne bata
ɗakko halin Gwaggo ba, Gwaggo mace ce me kirki da kawaici, ba zaka taɓa cewa ba ita
ta haifi Hindu ba, saboda yadda take nunawa kamar tafi son Hindu ma aka Hanne kai
kace gaba ɗaya ita ta haife su, bautar da Hindu take wa Gwaggo Hanne ba tayi, ga
shegen som jikin tsiya, shiyasa basa shiri da Gwaggo.
Gwaggo se jan Hindu take da hira, amma taƙi sakin jiki, saboda gaba ɗaya ranta a
ɓace yake, haka suka haƙura suka ƙyaleta, sedai hakan ba ƙaramin damun Widad yayi
ba.
Yau shiru shiru Yusuf be dawo ba, gashi tun la'asar hadari yake haɗuwa a garin, se
cida ake me ƙarfin gaske, kowa ya shige ɗaki ga iska da'ake yi, gaba ɗaya hankalin
Widad yaƙi kwanciya, Yusuf be dawo ba ga hadari se cida yake, ga wani irin tsoro da
ya baibayeta, lungun kan katifa ta koma tayi shiru tana ta addu'a a ranta.
Har magariba Yusuf be dawo ba, daga bakin ƙofar ɗakinsu tayi alwala, ta rufe ƙofar
ta dawo tayi salla, se wata irin walƙiya ake.
Ana idar da la'asar aka kece da ruwan sama kamar da bakin ƙwarya, babu Yusuf babu
labarinsa, hakan ba ƙaramin ɗagawa Widad hankali yayi ba, be taɓa yin haka ba se
yau.
Tun Widad na tsumayin dawowar Yusuf harta fara cire rai, ga tsoro da ya bai baye
ta, take ta fashe da kuka, ta dinga kuka kamar wata ƙaramar yarinya, ga tsoro ga
gefe guda tana tunanin ko wani abu ya samu Yusuf ne.
Har wajen ƙarfe goma da rabi na dare, gashi babu alamar za'a tsagaita da ruwan nan,
ta dunƙule guri ɗaya tana kuka, ji take tamkar ɗakin nan ze ruso a kanta, dan in
akayi cida ji take tamkar ɗakin yana vibrating.
Babu zato ba tsammani taga An turo ƙofar ɗakin, Yusuf ne ya shigo ya jiƙe sharkaf
da ruwa se ɗiga yake, jikinsa yana rawar sanyi.
Tana ganinsa maimakon ta tausayawa a halin daya dawo, kawai ta fashe da kuka ta
haushi da faɗa
"Ina kaje ka tsaya, kalli agogo ƙarfe nawa? Kawai ka kama ka ɗagamin hankali ga
tsoro inaji, ka fita kaje kayi zamanka baka damu da halin da zan shiga ba, wannan
wane irin abu ne haka?"
Aikuwa Yusuf ya ƙule, akanta yaje yasha wannan uwar baƙar wahalar, ga ruwan sama
yayi masa duka, bata tausaya masa ba se masifa da ta haushi da ita daga shigowarsa,
aikuwa ya ajiye kayan hannunsa, yasa hannu a aljihunsa ya ɗakko wata leda ya jefo
mata, ya juya ya shiga kokawar canza kayan jikinsa.
Ledar ta ɗauka, taji an nannaɗe leda cikin leda, ga ɗumi a jikin Ledar, se ƙarnin
kifi da yake tashi a jiki.
Yadda ya haɗe rai ne yai mata banza yasa ta gane haushi yaji, ya canza kayan
jikinsa ya ɗau abun shimfiɗarsa ya shimfiɗa a bakin ƙofa inda yake kwanciya, ga
babu abun rufa ga iska da feshin ruwa a gurin.
Gaba ɗaya taji tausayinsa ya kamata, ta ƙarasa kan bargon da yake kwana ta zauna
tace
"ka taso mu kwanta akan shimfiɗata, kaga nan ruwa yana jiƙaka"
Banza yayi mata, yaƙi ko motsawa daga inda yake, balle tasa ran ze kulata.
"Yoseef magana fa nake maka" still dai bece komai ba yayi mata banza.
Ta Kai hannunta ta shiga ɗan girgiza shi tana faɗin "dan Allah ka tashi, muje mu
kwanta nan akwai sanyi"
A ɗan kausashe yace "malama ki ƙyaleni, tunda bakya tausayina komai nayi abun faɗa
ne a gurinki, bana taɓa yi miki abu ki yaba, sedai ki ɓata mini rai, maimakon ki
tambayi ya akayi na daɗe haka meya sameni kawai kin hauni da masifa, ni matsa ki
ban guri ki dena taɓani"
"ina ruwanki idan nayi, ai ba damuwa kika yi dani ba, ki rabu dani kawai"
Taga dai alamar Yusuf bashi da niyyar tashi, dan haka kawai tayi kwanciyarta a
bayansa, sosai ruwa yake feshi yana jiƙasu.
Yusuf yace "ke ki tashi daga gurin nan, wannan ruwan da yake taɓaki ze iya saki
mura ko zazzaɓi"
"gara ya samu tare, tunda bazaka tashi ba" tai maganar tana sake maƙalƙaleshi ta
baya, Yusuf jiya yi yana nema ya dena fushin da yake, ya maze ya kunna fitilar
torchlight ya haskata yace "malama ki cikani kije ki kwanta"
Noƙe masa kafaɗa tayi, Yusuf yace "Shikenan naji, tashi muje mu kwanta a taki
shimfiɗar"
Tana jin haka ta miƙe suka nufi katifar, ta gyara musu ita Yusuf ya zauna yace
"miƙomin ledar nan" ta juya zata ɗakko akayi wata walƙiya data haske ɗakin gaba
ɗaya.
Gaba ɗaya ta afko kan Yusuf, ta riƙe shi gam jikinta yana tsuma, ta runtse ido
sosai tana ajiyar zuciya.
Aikuwa akayi wata tsawa me ƙarfin gaske, ruwa ya sake ɓallewa, haska fuskarta yayi
yaga yadda jikinta yake tsuma tayi wiƙi wiƙi da ido kamar Agola a rabon gado, yai
dariya yace "wai baki iya addu'a bane, se tsoro da kuka?"
Tashi tayi daga jikinsa tana cuna baki gaba, ta miƙo masa ledar kifine a ciki, ya
kalle ta yace "wani guri aka kwatantamin, nace bari inje in siyo miki kifi, gurin
da nisa ga babu abun hawa a kusa, nayi tafiyar ƙafa sosai, shiyasa kiga na daɗe fa"
Shiru tayi tana kallonsa kamar taga wani sabon abu, ya buɗe ledar kifin, manya
manyan gashashiyar tarwaɗa ce da karfashe.
Ya zauna ya dinga cire ƙayar ya ɗakko ya kai bakinta, tasa hannu zata karɓa ya
girgiza mata kai yace "karki ɓata hannunki da ƙarni"
Haka ya dinga bata tana ci, can kawai yaga tana hawaye, ya kalleta yace "meyafaru
kuma? Yanzu kuma me nayi miki"
Girgiza masa kai tayi alamar bakomai.
"Haba Queen, meye abun kukan kuma? Kukan ki yana ɗagamin hankali sosai, dan Allah
kidena kinji, bakomai is my responsibility to make you happy Baby"
Shiru tayi tana ci gaba da share hawaye, seda ta ƙoshi sannan Yusuf yaje ya wanke
hannunsa, ya dawo ya tarar da ita a zaune.
A hankali ta zame jikinta ta kwanta tayi shiru, kamar wadda ruwa ya cinye, shima ya
kwanta sedai ko mintuna biyar ba'ayi ba aka sake ƙyallo walƙiya, aikuwa ta kuma
cakumo Yusuf kamar jikinsa ya tsage ta shige.
Shima Yusuf ya rungumeta gam a jikinsa, yana wasa da saman gashinta data ɗaure da
ribbon.
A hankali ya kai hannunsa kan ribbon ɗin, saitin kunneta yace "in cire?"
"inka cire min seka gyaramin"
Murmushi yayi, ya zare ribbon ɗin dogon Gashin kanta ya baje akan katifar.
Yusuf ya dinga wasa da gashin, yana ɗaga shi yana wasa dashi, can Widad tace
"Yoseef wai dan Allah Aure dolene? Sannan meyasa ake Aure ne?"
LITTAFIN KUƊI NE, DAN ALLAH KI SIYA KAFIN KI KARANTA BA DANNI BA DAN ALLAH, LITTAFI
NA ƊAYA KYAUTA NE WANNAN NA SIYARWA NE
NORMAL GROUP ₦300
VIP ₦500 NE KITURA TA WANNAN ACCOUNT ƊIN
0009450228
JA'IZ BANK
AISHA ADAM
SE A TURA SHEDAR BIYA TA WANNAN LAMBAR
07063065680
11/14/21, 6:09 PM - Ummee Musa: LITTAFIN KUƊI NE, DAN ALLAH KI SIYA KAFIN KI
KARANTA BA DANNI BA DAN ALLAH, LITTAFI NA ƊAYA KYAUTA NE WANNAN NA SIYARWA NE
NORMAL GROUP ₦300
VIP ₦500 NE KITURA TA WANNAN ACCOUNT ƊIN
0009450228
JA'IZ BANK
AISHA ADAM
SE A TURA SHEDAR BIYA TA WANNAN LAMBAR
07063065680
56_57
"Kaima wannan wane irin sunane, ni dan Allah ka dinga faɗar sunana"
"Allah ka ƙara gayamin kaima sena samo wani sunan na sama ka mara daɗi"
Dariya yayi yace "ke baki san ina matuƙar jin nauyin faɗar sunan nan bane? Yanamin
nauyi a bakina, bana iya faɗar sunanki fa"
"to ai tambayar ta kice tazo a wata iri, nama rasa me zance miki"
A waje daka ke koyarwa in sun tambayeka wace amsa kake basu? "
" ƙureni zakiyi kenan? "
Yusuf yaja ajiyar zuciya yace "Aure ba farilla bane, amma yana da fa'ida tunda
Allah ya halatta yinsa, idan kika duba akwai tarin hadisan manzon Allah salallahu
alaihi wassalam da suke magana akan Aure, sannan akwai ayoyi a cikin Al'qur'ani da
suke magana akan Aure, akwai wani Hadisin Annabi salallahu alaihi wassalam yace
'kuyi aure ku hayayyafa domin inyi alfahari daku ranar Alƙiyama, kinga anan yana
daga amfanin Aure samun zuriya, yin aure ka haifi' ya'ya nagari babban Alkhairi ne
shima duba ga hadisin manzon Allah salallahu alaihi wassalam da yace 'idan bawa ya
rasu dukkanin ayyukansa suna tsayawa banda abubuwa guda huɗu, wanda ya mutu yana me
imani da Allah, da sadaƙatul jariya sadaka me gudana, kamar gina rijiya makarantar
islamiyya da sauransu, ko wanda ya sanar da wani ilimi wanda ko bayan ya mutu ske
amfani da shi, da kuma ɗa nagari, kinga anan yana daga cikin amfanin Aure kayi shi
ka samu ɗa nagari ka mutu ya dinga maka addu'a, duk ayyukan bawa suna tsayawa idan
ya mutu, amma in kayi Aure Allah ya baka ɗa nagari, yana maka addu'a, kinga babbar
ribace wannan, ko yayi wani aiki da ladan ze dinga iskeka. Akwai hadisin manzon
Allah salallahu alaihi wassalam da yake cewa 'ya ku taron samari, wanda ya samu iko
a cikinku to yayi Aure, idan kuma bashi da halin yin Aure to yayi Azumi, kinga
Aure yana da amfani domin shi katanga ne daga aikata zina, yana sanya nutsuwa a
zukatan wanda suka yi shi, akwai tarin hadisan manzon Allah salallahu alaihi da
ayoyi da suka yi magana akan Aure, dan haka Aure yana da mahimmanci sosai your
majesty"
Ajiyar zuciya Widad tayi tace "idan mutum be Aure ba ya aikata laifi?"
"A'a, kamar yadda na gayamiki Aure ba farilla bane, dan haka babu laifi ga wanda
beyi ba muddin ze kiyaye iyakokin ubangiji ya tsare kansa daga aikata dukkan wani
nau'i na Zina, sedai darajar wanda yake da Aure da wanda bashi da shi ba ɗaya bane,
mussman mace duk abunda tayi na aiki kona ibada a cikin gidan Aurenta tana da lada,
hakama namiji duba da gaba ɗaya shikansa Auren ibada ne, akwai wanda sam Aure be
halatta suyi shiba, misali wanda bashi da abunda ze iya riƙe Auren, ko yake da wata
nakasa da baze iya sauke haƙƙin iyalinsa na Aure ba wanda ze zamana da cutarwa a
ciki"
Se kuma yai shiru, be kuma cewa komai ba, Widad ta sake gyara kwanciyarta a jikinsa
tace "to amma a haka akewa mutum wani kallo dan mutum be Aure ba, yau anyi abunda
ya ɓatamin rai, yau na fara ganin anawa mutum rashin mutunci akan ba shi da
saurayi, baka ga Abunda aka yi wa Hindu ba, abun ya bani haushi sosai ya bani
mamaki"
Yusuf yace "To ai cikar mutuncin mutum shine Aure Habibty, kece kike masa wani
kallo na daban"
"to tunda dai Auren ba dole bane, ai bekamata a dinga takurawa mutum ba, yanzu by
mistake idan tayi Auren wani abu daba a so ya faru still ita za'a ɗorawa laifi,
gaba ɗaya yau wani iri ta wuni tayi kuka sosai"
Widad tace "Wallahi kuwa, ina sonta har raina tana da kirki"
Yusuf yace "Ashe kin san meye son, nine kawai bakya so"
"Nifa ban san irin son da kai kake faɗa ba, amma ina jin Hindu kamar 'yar uwata,
inaji dama gidanmu ɗaya ace ina da sister nima, nifa da zasu yadda idan zamu koma
gida in tafi da ita"
Yusuf yace "Ai kina dasu, gasu Amal nan da Ramlah suma sisters ɗinki ne, amma kike
musu wulaƙanci"
Widad tace "Wallahi na tsanesu, tsana mafi tsanani da ban taɓa yiwa wata halitta
ba, kuma ina nan idan na koma gida se sun bar mana gida, dan ba gidan ubansu bane"
"Subhanallah meyasa?"
Shiru tayi masa taƙi magana, tana jin yadda yake ta jera numfashi, kamar wani mara
gaskiya, zuciyarsa na harbawa da sauri da sauri, ga ruwan sama da yake ƙara zuba
kamar da bakin ƙwarya.
A ɗan shagwaɓe Widad tace "Yoseef am scared, kuma sanyi nake ji"
Yusuf yace "calm down, muna tare ba abunda ze faru insha Allah, keep praying"
Ta jinjina masa kai, a hankali Yusuf ya shiga kiran sunanta, tana jinsa amma taƙi
amsawa, sema wata kasala da take saukar mata.
Tana jin abunda Yusuf yake yi, amma ta kasa ko motsi, duk yadda Yusuf yaso tattara
nutsuwarsa ya guje faruwar wani abu a tsakaninsa da Widad abu ya gagara.
Ba dan ruwan saman da'ake ta kwararawa ba kamar da bakin ƙwarya, da babu abunda ze
hana mutanen ƙauyen da kewaye sanin abunda ya faru a tsakaninsu, saboda yadda Widad
ta dinga kuka da neman temako, rakin tsiya da kuma Shagwaɓa.
Tun tana kukan har tayi shiru, muryarta ta dena fita sosai.
Seda Yusuf ya dawo hayyacinsa dafe kansa cike da dana sani, da tuhumar kansa akan
wani ganganci ne ya ɗebe shi ya aikata hakan?
Widad se ajiyar zuciya take, tana kuka ƙasa ƙasa, gaba ɗaya Yusuf ya bata tsoro
kuma ya bata mamaki.
Gaba ɗaya jikin Yusuf yayi sanyi ya kasa magana, ya rasa mema zece mata.
A hankali yaja rigarsa ya saka, ya miƙe ya ɗau bokiti da tukunya ya fita tsakar
gida, a cikin wannan ruwan da ake ya tafi rumfar da'ake girki, ya dinga tona cikin
murhun, ya tattara gawayi da ƙyar ya tashi garwashi, ya ɗora ruwa.
Haka ya zauna ya dinga fama, seda ruwan nan yayi zafi sosai ya haɗa mata, ya kai
banɗaki ya ajiye.
Shi kansa jikinsa a matuƙar mace yake, ya koma ɗakin ya shiga ya tarar da ita a
inda ya barta a kwance tana kuka, Ya durƙusa ya ɗagota ya samata hijjabi, a hankali
yace "tashi muje ga ruwan wanka can na kai miki"
Bata kula shi ba ta miƙe tsaye, ta dafa bango sedai tana zuwa bakin ƙofa ta tsaya,
saboda tsoro ga tsigar jikinta dake tashi, saboda wani irin sanyi da take ji, gashi
gaba ɗaya tsakar gidan ya jagwale.
Kawai ji tayi yayi sama da ita, ya kaita banɗaki ya ajiye mata fitila, ya koma can
tsallaken wajen rumfa ya tsaya.
Ta daɗe sannan ta buɗe ƙofar banɗakin, Yusuf yaje ya ɗauke ta ya maida ita ɗaki,
shi be tsaya wani dafa ruwa ba, saboda garwashin duk ya mutu, a haka ya ɗebi ruwan
da sanyi da komai yaje yayi wanka.
Wani private hospital aka kai Nurat, nan da nan suka karɓeta a emergency, likitoci
suka shiga ƙoƙarin ceto ran Nurat, ta hanyar tsaida jinin dake ta zuba a goshinta.
Da ƙyar jinin nan ya tsaya, aka nan naɗe mata goshinta da bandeji, goshin ya
kumbura suntum har gefen idonta saboda buguwar da tayi.
Likita ne ya fito ya samesu a reception, suka yo kansa gaba ɗaya suna jero masa
tambayoyi.
"ku kwantar da hankalinku, raunine kawai ta samu, Allah ya rufa asiri be shafi
idonta ba, amma idan ta farfaɗo akwai gwaje gwajen da zamuyi muga inda yuwuwar ayi
mata hoton Ƙwaƙwalwa, dan naga jini yana fita daga hancinta, karmu je ko akwai
internal injury "
Mahaifiyar Nurat tace " Na shiga uku, hoton Ƙwaƙwalwa kuma likita? Ba dai haukacewa
tayi ba? "
Tsaki Alhaji Musa yayi yace " kaga dan Allah ƙyaleta, na fahimce ka idan ta farfaɗo
ɗin in akwai buƙatar hakan se ayi hoton, ni dai fatana Allah ya bata lafiya"
"dole kace a rabu dani mana, tunda ka kusa kashemin 'ya, kuma yanzu kana wani nuna
kamar ka damu da ita"
"ban sani ba, kuma wallahi duk abunda ya samu' yata kaine"
Likita yace "haba dan Allah yallaɓai, da girmanku da komai, hakan be dace ba ai,
akwai marasa lafiya a kwance, kamata yayi kuyi ta lafiyar 'yarku ba faɗa ba"
Wayar Alhaji Musa ce ta shiga ringing, ya ɗanyi gefe ya ɗakko wayar yasa a kunnensa
yace "Hello ina ji"
Alhaji Musa yace "eh Home Accident ne, ta faɗi ne ta bige but is not that
complicated"
"Ok to shikenan, Allah ya ƙara afuwa, zamu shigo mu duba ta insha Allah"
Nurse ɗin tace "eh zaku iya shiga ku ganta, bacci take"
Nurat tana kwance tana bacci, ga drip an sa mata suka ƙarasa gaban gadon Nurat,
mahaifiyar ta ta zauna a gefen gadon ta kamo hannun Nurat, jikinta ya ɗau zafi
sosai Amma baccinta take ta sha.
A hankali Nurat ta buɗe ido, ta kalli inda Mummynta take, a hankali ta kai hannu
tta shaf goshinta inda aka nannaɗe da bandeji, ta kalli Mummynta tace "Mummy me aka
samin a goshina?"
Alhaji Musa yace "Am sorry kinji Babyna, is just a little bit mistake, kema ki
dinga jin magana ki dena taurin kai"
Widad se farkawa tayi ta nemi Yusuf ta rasa a ɗakin, tayi tunanin ko ya tsaya
sallar Asuba ne yayi karatu, gaba ɗaya jikinta ciwo yake, ta lallaɓa taje tayi
sallar Asuba.
Ta koma kan katifarta ta kwanta, kanta se ciwo yake da duk ilahirin jikinta ciwo
yake mata, ba ƙaramin mamaki Yusuf ya bata ba jiya, bacci ne ya sake yin awon gaba
da ita.
Har sha ɗaya na safe bata ga Yusuf ba ba taga alamarsa ba, ta tashi ta lallaɓa ta
gyara ɗakinta, ta ɗau bokiti taje ta karɓi ruwa tayi wanka.
Ta koma ta ɗau kofi ta fita tana takawa a hankali, saboda yadda tsakar gidan ya
jagwalgwale sakamakon mamakon ruwan saman da'akayi jiya da daddare, tsigar jikinta
se tashi take saboda ƙyanƙyami, ga ƙarnin ruwa daya kwanta.
Ƙofar ɗakin gwaggo taje tayi sallama, Gwaggo ta amsa mata, ta nemi izini sannan ta
shiga.
Gwaggo tace "Amarya, yanzu nake sa ran in aiki Hindu ince ta dubamin me, yau shiru
ban ganki ba ko dan anyi ruwan sama ne"
Widad tace "bana jin daɗi ne, in akwai Abinci ki bani yunwa nake ji"
Da yake yau ba Gwaggo ce da girki ba, yanzu se ranar girkin Gwaggo ake basu Abinci,
dan Widad bata cin Abincin kowa se nata, in dai ba ita tayi girki ba baza taci ba,
sedai Yusuf ya girka mata wani abun.
Gwaggo tace "Amarya bani nayi girki ba yau, amma ina da garin kunu an karɓomin
jiya daga gurin niƙa, bari in dama miki"
Ta nemi guri ta zauna tana sake ƙarewa ɗakin Gwaggo kallo, wand ke matuƙar birgeta,
sedai sam abunda ya faru tsakaninta da Yusuf jiua ya kasa barin zuciyar ta.
Hindu tayi murmushi tace "Amarya dama kin tashi? Na zata har yanzu bacci kike ai"
Widad tayi murmushi tace "A'a yazan ta bacci har I yanzu, na tashi tun ɗazu ai"
"gani nayi kinyi wani iri, idonki kamar kinyi kuka, kuma kamar me zazzaɓi"
Hanne ta bankaɗo ɗakin ta shigo, babu ko sallama ta kalli Widad da Hindu taja wani
uban tsaki, ta ƙarasa ciki basu kulata ba Hindu ta cigaba da jerawa Widad sannu.
Gwaggo ta kawowa Widad kunu, Widad tayi ta godiya ta tashi ta koma ɗakinta.
Dama ba'a batun sugar acikin kunun da suke sha ko kuma koko, a haka suke sha itama
kuma ta saba a haka take sha.
Kunun nan da ta sha har la'asar, bata sake cin komai ba, se Dafaffiyar gyaɗar da
Hindu ta bata.
Shikam Yusuf nauyin Widad ne ya hana shi dawowa, be san da wani ido ze kalleta ba,
besan da wani kalaman ze amfani gurin kare kansa ba, tabbas yasan yayi aika aika a
daren jiya, wadda shima be yi shirin afkuwar al'amarin ba, besan ta ina ze fara
haɗa ido da ita ba, besan wani mataki zata ɗauka a kansa ba.
Haka nan ya tunkaro gidan yana tunanin, gabansa yana faɗuwa se Addu'a yake.
Yai sallama ya tsaya suka gaisa dasu Hari, yai sallama a ƙofar ɗakin Gwaggo ma suka
gaisa, da yake yau tun Asuba be dawo ba.
Da harta buɗe baki za tayi masa tsiwa, kawai ta tuna abunda ya faru jiya da daddare
a tsakaninsu, ba shiri ta tsuke bakinta kawai tasa kuka.
Dama Yusuf yasan a rina, ya ƙarasa inda take, yasa hannu ze kama hannayenta amma ta
janye hannunta.
Yusuf ya ɗan ƙura mata ido, ji ba ƙwari ya fara magana yace "Widad ban san ta ina
yakamata in fara ba, bani da kalaman da zanyi Amfani dasu wajen baki haƙuri, gaba
ɗaya na rasa me yakamata inyi, ina me baki haƙuri sannan na shirya karɓar duk irin
hukuncin da kika shirya Yimin" yai maganar fuskarsa na fallasar da tsantsar damuwa
dake kwance a zuciyarsa.
Cikin kuka tace "shine ka tafi ka barni tun safe, bayan kasan...." ta ɗanyi shiru
sannan ta ɗora "bayan kasan abunda kayi min, bani da lafiya tun Asuba baka sake
dawowa ba, ga yunwa nake ji, Se gurin Gwaggo naje ta bani kokon tsamiya" ta ƙarasa
maganar cikin kuka.
Seda Yusuf yaji kamar yayi dariya, amma ya dake yace "subhanallah, am very sorry,
na manta ne kuma ina jin nauyinki sakamakon abunda ya faru jiya, dan Allah kiyi
haƙuri, i don't even know how it happens"
Widad a ranta tace 'jimin ɗan rainin hankali, wai he don't even know how it
happens, se kace yana maye yayi abunda yayi'
Haɗe rai ta sake yi ta cigaba da kukanta, tace "Kuma seka sake ni"
Yusuf yace "Naji amma ba yanzu ba se mun koma gida, for now am very sorry please,
am not able to fulfill my promises to you, dan Allah kiyi hakuri Widad"
Banza tayi masa taƙi cewa komai, da haushinsa take ji kama sosai he takes away her
pride, sannan yasa ƙafa yayi tafiyarsa tun safe ya barta, bata shirya faruwar haka
ba sam a rayuwarta, babu Aure a gabanta, amma Yusuf ya ɓata mata komai yanzu.
Hannu ya kai ze taɓa ta, aikuwa ta zabura ta miƙe zaune da sauri tana faɗin "wayyo
Allah Daddy"
Yusuf a rikice yace "yi haƙuri ba wani abun zan kuma yi miki ba"
"Kuma sena gayawa Daddy idan muka koma gida, idan kayi min hakane dan karka sakeni,
let me tell you, we must go separated, you must divorce me na gaya maka"
Yusuf yace "Widad trust me, is not intentionally shiyasa nake iya ƙoƙarina akan in
kiyaye, but am human being, am not super natural"
"you said i should trust you how? After you know this is arranged marriage, but you
took away my pride, how can I trust you Bayan Kamin ƙarya a baya, bazan taɓa
trusting ɗinka ba"
Gaba ɗaya Yusuf ya rikice, ya rasa abunda yake masa daɗi, ya dafe kai yana kallon
yadda take kuka, tausayinsa ne ya kamata, tace "Nifa Yunwa nake ji, kokon tsamiya
kawai na sha tun safe"
Yana cikin gaganiyar ɗora girki taga kamar yana ɗingishi ne, bata kula ba ta share
shi.
Ya dawo ya ɗakko leda ya ɗakko mata pad guda goma sha biyu, da Maclean sabo da su
man shafawa yace "Kinga na siyo miki pad ɗin, kuma naga Maclean ɗinmu ya kusa
ƙarewa na ɗanyi mana siyayya"
Tasa hannu ta karɓa tace "Nagode sosai Allah yasaka da alkhairi" yaji daɗin
godiyar da tayi masa tace "amma zan bawa Hindu, itama ta dinga amfani da pad
instead of cloth"
"Kawo in wanke maka, kar ayi sallama a ga kana wanke shinkafa da kanka, bayan kana
da Aure kuma akwai mata a gidan"
Yusuf yace "karki damu Hannatu, ai shinkafar kaɗance zan iya wankewa"
Hanne ta ƙaraso tana faɗin gaskiya a'a, nidai bani nan in wanke maka.
Widad ta gani tsaya a bakin ƙofar ɗakinta, tana watso mata wani mugun kallo, take
Hanne ta tuno da shaƙar data sha, nan da nan cikinta ya kaɗa ta tsaya tayi sororo,
Yusuf ya ɗaga kai ya waiga, yaga ashe Widad ta gani, bata ce musu komai ba ta shige
ɗakin, tana jiran Yusuf ya shigo ta zazzage masa.
Ita mamaki ma take yi, yadda ta kasa zagewa ta ƙare masa saboda abunda ya shiga
tsakaninsu, tunda ya shiga ɗakin take binsa da kallo.
"Malam daga yanzu idan zakayi kule kulenka ka bari seka sakeni tukuna na gaya maka"
Kallonta Yusuf yayi yace "Dagaske har ranki so kike ki rabu dani?"
Kallonsa tayi tace "to da tare aka halicce mu? Ko kuma ka manta bisa yarjejeniya
mukayi Aure ne haba? Nifa bani nace ka fara sona ba, dan baka gara tun wuri kasan
abunyi"
Shiru yayi ya cigaba da tunani, har ya kammala girkin ya sauke, ya ɗora mai akan
wuta ya soya, sedai bisa tsautsayi saboda tunani mai ya zubar masa a hannu.
Da sauri ta juyo taga abunda yake faruwa, ai nan da nan ta ƙarasa gabansa tana
faɗin "Subhanallah, yoseef garin Yaya? Me kake tunani haka? Kalli yadda ka ƙone
hannu, innalillahi"
Ta riƙe hannun nasa, ta sa rigarta tan goge masa inda man ya zuba a hannun sa,
karaf idonta ya sauka akan ƙafar wandonsa, kamar jinine a jiki, ta kai hannu ta
janye wandkn, rauni me yaji a gurin, kamar an saka ƙarfe anja gurin.
"wannan karki damu, dama zanje cikin garine in siya miki pad ɗin nan, to kin san
hanya bata da kyau, shine muka faɗi a babur, amma karki damu zan warke Insha Allah"
Kallonsa tayi, wani irin tausayins ya game zuciyar ta, hawaye sharkaf a fuskar ta
tace
"This is serious, ya isa haka, yakamata mu koma gida kome ze faru ya gara faru, ba
zamu cigaba da zama a nan lafiyarka na taɓuwa saboda ni ba"
Yusuf yayi murmushi cikin jarumta yace "wannan ai ba ciwo bane me girma, zan warke
very soon insha Allah, ki kwantar da hankalinki"
Cikin kuka ta shiga girgiza kai tace 'No, Yoseef se mun bar garin nan haka, wahalar
da kake sha saboda ni ta isa haka, is enough ba dangin iya ba na baba se wahala
kake saboda ni? Idan har lafiyarka ta cigaba da taɓuwa bazan yafewa kaina ba, gida
zamu koma ba zamu ci gaba da zama anan ba kome ze faru ya faru"
LITTAFIN KUƊI NE, DAN ALLAH KI SIYA KAFIN KI KARANTA BA DANNI BA DAN ALLAH, LITTAFI
NA ƊAYA KYAUTA NE WANNAN NA SIYARWA NE
NORMAL GROUP ₦300
VIP ₦500 NE KITURA TA WANNAN ACCOUNT ƊIN
0009450228
JA'IZ BANK
AISHA ADAM
SE A TURA SHEDAR BIYA TA WANNAN LAMBAR
07063065680
11/14/21, 6:09 PM - Ummee Musa: LITTAFIN KUƊI NE, DAN ALLAH KI SIYA KAFIN KI
KARANTA BA DANNI BA DAN ALLAH, LITTAFI NA ƊAYA KYAUTA NE WANNAN NA SIYARWA NE
NORMAL GROUP ₦300
VIP ₦500 NE KITURA TA WANNAN ACCOUNT ƊIN
0009450228
JA'IZ BANK
AISHA ADAM
SE A TURA SHEDAR BIYA TA WANNAN LAMBAR
07063065680
58 _59
Ɗan ƙura mata ido Yusuf yayi yace "haba Widad, ya zaki ce mu koma gida a wannan
yanayin? Komai ze iya faruwa fa"
"Koma meye yafarun, amma be kamata ratuwarka ta cigaba da cutuwa saboda ni ba,
kalli ƙaddara daga wannan se wannan yakamata inyi maka adalci bekamata in nuna son
kaina da yawa ba"
Yusuf ya shiga share mata hawaye yace "Karki sake cewa ba dangin iya babu na baba
tsakanina dake, koba komai koda mun rabu kin taɓa zama wani ɓangare na tarihin
rayuwata wanda baze taɓa gogewa ba, dan haka kome nayi a yanzu domin farincikin ki
bakomai domin kuwa haƙƙina ne inyi miki, a gurin Allah babu wani abu like arranged
marriage, duk abunda abunda ze sameni saboda kare rayuwarki baze dameni ba, saboda
mahimmancin da kike dashi a gurina, kidena kuka zan warke insha Allah "
Girgiza kai ta shigayi, tana son yin magana amma ta kasa dan haka kawai ta faɗa
jikinsa ta cigaba da kuka.
Yusuf a ransa yace 'alamu sun bayyana ƙarara Widad tana sona, sedai ita bata san
hakan ba'
'Amma idan harka bari Widad ta fara sonka kayi mata adalci kuwa? Kayi mata ƙarya a
karo na biyu, anya ƙaddarorin rayuwarku zasu haɗu a guri guda?' wata zuciyar ta
shiga gargaɗinsa.
Jiki a sanyaye yake dukan bayanta cikin sigar rarrashi yace "ni ban gaji dake ba,
kuma duk abunda yake faruwa dani baze taɓa sawa in juya miki baya ba, saboda Amana
ce na karɓa a gurin mahaifinki, kuma Allah ya jarabci zuciyata da sonki, babu yadda
zanyi ƙaddrata kenan"
A hankali ta tashi daga jikinsa, ta ɗan zuba masa ido, shi kuwa Yusuf me yake ji
haka game da ita da baya iya ganin laifinta, kuma yake tarar dukkan ƙalubalen daze
taso?.
"Naje chemist, na sai magani ciwon bayamin zafi ai, bari nayi alwala inje waje inja
salla"
" ba wani amma, kawai kayi salla a gida, kar kaje ka fama raunin nan"
Da ƙyar ta yadda yaje yayi salla ya dawo, tazo ta zauna ta saka masa man zaitun a
gurin, ta nayi tana jera masa sannu.
Da kanta ta gyara masa shimfiɗarsa, ya kwanta, tana sake kallon yadda ciwon ya
ɗanyi zurfi.
Tai maganar tana shafa sumar kansa, yai murmushi yace "Ameen ya Allah nagode
sosai"
"meye wani ka gode?" kawai se ya shagala da kallonta, ta kalle shi tace "naga kana
kallona, idan ka sake kayi abunda bana so koka tsokaneni ko, zaka ga yadda zanyi da
kai"
"Masoyiyya, meyasa da muna gida kika cemin ke Karuwa ce? Alhalin ba haka bane?"
"meye maraba ta da karuwa a wannan lokacin? A shigar da nayi, da kuma inda naje
harka ɓatami rai ranar, Daka san me najeyi da bakamin haka a wannan ranar ba"
"Nifa tun a wannan lokacin ina matuƙar kishinki ne, tun a lokacin nake sonki
shiyasa nake nuna kishina a fili, Abubuwa da yawa suna ɗauremin kai a wancan
lokacin ina buƙatar warawara daga gareki"
"Yoseef kenan, kaine mutum na farko da ya shigo rayuwata a hagunce kuma ya zama
garkuwa a gareni, ya samu damar da da ɗunbin mutane basu samu ba, kayi nasarar
canza wasu daga cikin tunanina, sedai har yanzu baka bani labarin sakamakon
bincikenka da kayi ba akan maƙiyana"
Yusuf yai murmushi yace "Naƙi na gaya mikin, nima ban yadda dake ba"
Dariya Widad tayi, harda kai masa dukan wasa a ƙirjinsa tace "nice baka yadda dani
ba? Ai nima daliline yasa hakan, koka manta niɗin mahaukaciya ce? Haukana ne yasa
bana yadda da mutane, kai kuma kaga kana da hankali"
Yusuf yace "Nifa gaskiya inada question mark akan wannan ciwon naki, meya hana
ciwon tashi anan?"
Kasancewar a duhu suke, yasa se shseshsheƙar kukan Widad yaji, cikin sauri yace
"Am sorry, i don't mean to hurt you, ban san ze ɓata miki rai ba tambayar yi
haƙuri" yai maganar da sigar rarrashi, yana shafa bayanta.
Yauma Allah ne ya kiyaye, dan tana jin Yusuf ya fara zarce ƙa'ida ta narka masa
cizo, ba shiri ya cikata ta miƙe ta koma kan shimfiɗar ta, tayi shiruu kamar ruwa
ya cinye ta.
Kwanan Nurat uku a Asibiti, anata zuwa duba ta, Allah ya temake ta da akayi hoton
ƙwaƙwalwar, babu wata matsala a cikin kanta dan haka aka sallameta daga Asibitin.
Suleiman ne zaune a gaban wani mutum a office, da gani mutumin babbansa ne a gurin
aiki, mutumin ya kalli suleiman yace "Nagaji da gafara sk ko ƙaho ban gani ba, har
yanzu babu wani bayani akan Assignment ɗin nan da muka bayar"
"yallaɓai wanda muka bawa aikin, shine direban 'yar gidan Alhaji Nasir kuma tare
aka sace su"
Suleiman ya gyara zama yace "ƙwarai yallaɓai, Yusuf jam'in mune, yaje da saunan
aikin direba amma shine wanda muka tura muka saka aiki, kuma yanzu haka tare aka
sace su ita dashi"
Jinjina kai mutumin yayi yace "Amma babu wani abu daya fara gabatarwa na sakamakon
binciken da yayi?"
"gaskiya Yallaɓai babu, dan a satin da nayi masa magana ya cemin zezo office yayi
bayani, a satin aka sace su"
Susu huɗune zaune a wani matsakaicin falon Hotel, Alhaji Bukar yace "wata maganar
banza da naji, wai yaron nan da'aka sacesu tare shine jami'in tsaron da aka tura
yayi wannan binciken"
Alhaji Musa yace "Innalillahi wa inna ialaihi raji'un, shikenan na kaɗe har ganyena
inda wannan yaron da suke yawo tare ne"
"Ranar da Nurat take birthday sukazo, lokacin da nayi attempting a sacemin ita,
shiya ritsa Nurat da bindiga ta gaya masa inda Yar Daula take"
Alhaji Munir yace "ji wata maganar banza, to me yasa tun a lokacin baka faɗa ba se
yanzu"
"to ta yaya zan in sani, na tambayi Nurat tacemin itama bata san waye ba, se yanzu
da akayi zancen nan sannan na gane"
Alhaji Haruna yace "gaskiya malam ka kwafsa mana, kayi mana gyɗa a gurin nan,
maimakon tun a lokacin kasa ayi bincike a gano maka shi, aji dalilin da yasa ya
hana a sace yarinyar, wataƙila ma da tun a lokacin munsan waye shi"
Alhaji Bukar yace "ku dakata, kuskure ne dai an riga anyi shi, sedai a kiyaye gaba
kuma a sake shiri, babban abunda ya ɗagamin hankali shine, bai bada komai na shedar
binciken da yake yi ba, babu wanda yasan meye sakamakon binciken nasa, amma tabbas
tunda ya gano kayi yunƙurin saceta, nasan ze maida hankali da yin bincike akanka"
Zufa Alhaji Musa ya shiga sharewa yace "yanzu meye abunyi? Hankalina fa ya fara
tashi, gashi babu wanda yasan inda suke"
Alhaji Munir yace "kaine a ruwa ai, tunda kikayi shirme da sakaci"
"Mune a ruwa dai, idan Asirina ya tonu ai naku ma gaba ɗaya ya tonu"
Alhaji Haruna yace "dan Allah kuyi shiru mu nemo mafita, aikin gama ya gama ba
yanzu ya kamata a nemi mafita ba, abun da ya kamata mu yi yanzu shine neman mafita"
Alhaji Bukar yace "yanzu magana ta farko dai shine, mu matsa lamba musan inda
Daula yake, ɓatan Daula ma fa wani babban giɓine kuma hatsari a garemu, ga 'yarsa
itama bamu san a inda take ba yanzu, ga wannan yaron da wannan maganar ta taso
yanzu"
Alhaji Munir yace "Sannan wanda ya sa aka saki Yaron gurin Halima shima ba ƙaramar
barazana bane a gare mu, dan bamu san waye ba, kuma banu san manufarsa ba"
Alhaji Musa yace "Aini nafi kowa shiga matsala, a hanzarta a nemo mafita gaskiya"
Alhaji Bukar yace "ku kwantar da hankinku, zan san abunyi insha Allah, nasan yadda
zanyi da al'amarin"
Bukar yace "when I come out with the final decision I will let you know, Musa ka
kwanta da hankalinka, ba abunda ze faru zanwa tufkar hanci"
Haɗe rai tayi tace "Kai harkuna da bakin da zaka wani kirani kana ya Yara? Bayan
rashin mutuncin da kukayi min akan belin Anwar?"
Alhaji Haruna yace "ke, ki bar wannan maganar akwai matsala ne fa"
"Matsala ta ƙaremu ku acan tsakaninku banda ni, karka sake sani a cikin matsalarku
tunda kowa kansa ya sani"
"Yaron nan Yusuf yake ko Yunusa, ashe jam'in sirrine, shine wanda yake binciken"
Mummy tace "kai ɗan tsaya mana, Wai Yusuf direban Widad?"
"Oho nima ban sani ba, wanda dai aka sacesu tare, ashe shine yaron da yake binciken
nan, muna ganin munyi dabara ashe da kanmu muka burmawa kanmu wuƙa, yaron nan shine
yake gudanar da binciken"
"Innalillahi wa inna ialaihi raji'un, na shiga uku Haruna dan Allah yaron nan
dagaske ɗan sanda ne?"
"ƙwarai kuwa, ɗan sanda ne ma farin kaya, kuma shike gudanar da binciken nan"
"Shikenan, wallahi idan ya dawo garin nan tabbas na kaɗe, an karɓi bayanin binciken
kuwa?"
"ba'a karɓa ba dan ba'a samu ba, amma Alhaji Bukar yace mu saurare shi, ze faɗa
mana abunda za'ayi"
Hajiya Halima tace "ni dai dan girman Allah ku gaggauta samo mafita, wallahi akwai
matsala" tai maganar tare da ajiye wayar tana faɗin na shiga uku.
"Yara akwai damuwa fa, wai ashe munafukin yaron nan ɗan sanda ne?"
"Wai Yusuf?"
Ramlah tace "ta yaya ya zama ɗan sanda? Mummy ke waye ya gaya miki?"
Ramlah tace "No wonder, sam wannan beyi kalar wanda za'ace yana cikin wahala ba, ko
kuma rashin ilimi, ashe munafukine shiyasa na tsane shi, shege Azzalumi"
Amal tace "shiyasa wani lokacin nake hanaki yi masa wasu abubuwan Mummy, ki saki
baki kiyi ta sakin maganganu anyhow, gashi abunda ya faru ai"
Ramlah tace "dan Allah kiyiwa mutane shiru, yanzu mafita za'a nema ko surutan
zaki cigaba dayi?"
Amal tace "ko anemi mafita ko kar anemi mafita aikin gama ai ya gama, sedai a
kiyayi gaba"
Hajiya Halima tana jinsu tayi shiru, gaba ɗaya ta shiga tunani yadda take sakin
magana yadda taga dama, ashe kallonsu kawai yake"
Mummy tace "Nima ban sani ba, amma Bukar yace mu saurare shi, ze samo mafita"
"to Ubangiji Allah yasa mafitar me ɓullewa ce, amma nikaina abun ya tsoratani"
Ramlah tace "ki kwantar da hankalinki Mummy, Insha Allah bakomai, dan ni kaina a
tsure nake, kin san na taɓa zuwa nace ya samomin Password ɗin Widad, Amma tunda
Alhaji Bukar yace akwai mafita, to tabbas akwaita, ki kwantar da hankalinki"
Mummy ta jinjina kai, Anwar ne yai sallama a ɗakin, ya kalli fuskokinsu yace "Ya
dai na ganku kunyi jugum jugum, akwai matsala ne?"
A fusace Mummy tace 'Kai fita ka barmin ɗaki, uban bin ƙwaƙwƙwafi, ance maka
bakomai amma ka dage "
" Allah ya baki haƙuri " daga nan yai waje abunsa.
Da Asuba tayi Yusuf ya dawo daga gurin karatu, lokacin gari yayi haske ya ɗumama
musu shinkafa sukaci da safe.
Ya miƙe ze fara shirin fita, ta kalle shi tace " naga kana shiri, ina zakane? "
"Meyasa?"
"Se kaje wani abun ya kuma faruwa? Ka bari ƙafar ta warke kana ɗingisawa da ƙyar
kana maganar zaka fita"
" ba wani kawai, idan kace seka fita kana tafiya, nima zan ɗauki hijjabina in tafi
"
Widad ta tsaya tana waige waige, tace "tana ina robar take?"
Gwaggo tayi murmushi tace "ruwan ɗorawa nace, gata can a gefen randa"
Hari tace "na shiga uku da wannan lamari, waike komai baki sani ba? Kwarankwatsa
ko a birni an san waɗan nan abubuwan, amma kiyi ta rainawa mutane hankali"
Kamar basuji me tace ba, Gwaggo tace "Saran itace shine Faskare"
Widad ta ɗanyi shiru, sannan ta jinjina kai, ta kuma cewa "Gwaggo wai meyasa naga
ruwanku seya dinga yin kala, ni wanda Yoseef yake ɗebo mana yafi wannan kyau sosai"
Widad ta toshe baki tana dariya, tace "yi haƙuri na manta ne, wanda mijina yake
ɗebowa"
Gwaggo ta girgiza kai tace "Inda Yusufa yake ɗebo muku ruwane, ba giri ɗaya da
namu ba, shi birtsatse yake zuwa ya ɗebo muku, kuma tafiyar da yake a ƙasa kafin
yaje gurin ta ɓaci, da nisa sosai ita kaɗai ce burtsatse a garin nan"
"Nasan dai famfo, amma ban san meye tuƙa tuƙa ba"
Shikan sa Yusuf da yake ɗaki yana jiyosu, seda yace "Allah yasa kar Gwaggo ta gaji
da wannan tambayoyin na Widad.
Allah yasa aka zuba mata ruwan ɗumi ta tafi wankanta.
Bayan ta fito daga wankanne tana shiga ɗaki, ta tarar Yusuf ya tattara kayansu na
wanki ya ɗaure a guri ɗaya.
"Can wani gurine bakin ruwa, nake wankin, jira nake in ƙarasa yi miki girkin rana
in tafi in wanko kayan"
"No kiyi zamanki a gida inje in dawo, gurin ba kowa kuma bakin ruwane"
"gaskiya ban yadda ba, tunda muka zo garin nam ban taɓa fita ba, gaskiya ka tafi
dani, nima base in koyi yadda akeyi ba im dinga yi mana"
"bana so Kisha wahala ne, ki bari inje inyi indai fitane, zam fita dake mu zaga
gari"
Ya fuskanci haushi taji, dan haka ya ƙarasa inda take yace "Meyasa kike da saurin
Fushi ne Masoyiyya, shikenan zamuje tare, kinsan bana son ɓacin ranki"
Tura baki tayi taƙi magana, ya juyota ta fuskance shi yace "smile mana habibty"
"In kina tura bakin nan i just feel like to kiss you"
Ɗago ido tayi da sauri cikin Shagwaɓa tace "kaga ka bari bana so"
Yadda tayi maganar ne ta bashi dariya, yace "shikenan, ina bim bashi se anmin
murmushin nan. To ko in ta yaki sa kayan?"
Da sauri tace "A'a bana so wallahi" tai maganar tsoro ƙarara a idonta.
Murmushi yayi, ya juya ya cigaba da haɗa kayan, seda ya kammala yayi musu girki,
sannan yai waje.
Ta tsaya ta saka hijjabinta, da silifas ɗinta ɗan madina ta fito, Hindu taga Widad
ta sha hijjabi, dan bata saba gani ba idan ba salla Widad zata yi ba sunyi hannun
riga da hijnabi, Hindu tace "Amarya ina zuwa haka?"
"Fita zamuyi nida Yoseef, naga kamar Gwaggo wanka take inta fito ki gayamata"
Hindu tace "shikenan zan gaya mata insha Allah, sekun dawo yau zanyi wunin
kaɗaici"
Widad tace "Allah sarki Hindu, nima zanyi kewarki, semun dawo"
Widad tayi hanyar fita, sedai tana zuwa ta tarar an zubawa Manyan ragunan megari
harawa a hanyar fita wajen, gasu da manya manyan ƙaho a murɗe, sun kai su goma sha,
suna ture ture suna cin Abinci.
Ƙura musu Ido Widad tayi, tana tunanin ta ina zata wuce.
Jin shiru Widad bata fito ba yasa Yusuf dawowa yaga ko lafiya.
Ya tarar da ita a tsaye tana kallon raguna, Yusuf yace "Madam ke nake jira fa, kim
tsaya kallon raguna"
"Tsoron mekuma?"
Yusuf ya girgiza kai yace "yanzu ragunan ne yasa kika tsaya kika kasa fitowa? Duk
soyayyarki da dabbobin kuma yanzu tsoronsu kike ji?"
"To wai so kake, su dakeni da wannan ƙahon suji min ciwo, ko ance maka ni 'yar
sanda ce?"
Ya ratso cikin ragunan ze kama hannunta su wuce, amma taƙi wai sedai ya koresu ta
wuce, amma bazata shiga ta tsakaninsu ba.
Cak ya ɗagata ya ratsa ya wuce, sannan ya ajiyeta, hakan yayi dai dai da fitowar
Hari taga abunda ya faru, ai take ta fara salati
"la'ilahaillalahu, yau nake ganin gardiyar lukutar baɗala a tsakar rana, wane irin
abune haka goɗoɗo ba fasali bakomai?"
Seda Yusuf ya ƙunshe baki yana dariya, Widad har tayi shirin ramawa, ya janyo
hannunta sukayi waje.
"Alhaji Haruna, nayi muku duk iya ƙoƙarin da zanyi muku, duk ayyukam da kuka sani
nayi muku, yakamata ku zama masu cika Alƙawari fa"
"Kai Saleh wai baka san a halinda muke ciki bane? Wai ashe yaron da aka sace 'yar
gidan Daula dashi, wai ashe ɗan sanda ne"
Hantar cikin Saleh ta kaɗa amma ya basar yace "kamar ya ɗan sanda, direba dai"
"to ɗan sanda ne, anyi bincike an tabattar mana da jami'in tsarone ma farin kaya"
Saleh yace "lallai biri yayi kama da mutum, amma yaya aka yi haka ta kasance?"
"Kai zamu tambaya, tunda kai muka wakilta a wannan ɓangaren"
Saleh yace "to ai nima ban san komai ba, ban san shi aka saka ba sam, amma gaskiya
ya iya yaudara, shine yazo a matsayin direba"
Alhaji Haruna yace "to gashi nan dai, kuma bincike ya tabattar kamar maye yake
akan aikin sa, idan ya saka case a gaba se yaga bayansa, kuma bimcike ya nuna ya
fara gano Alhaji Musa, sannan Hajiya Halima tayi ɓarin zance a gabansa"
Alhaji Haruna yace "abunyi kam a yanzu babu, Alhaji Bukar yace mu saurare shi, ze
nemo mana mafita"
Saleh yace "lallai abubuwa sun fara lalacewa, ya zama dole a hanzarta samo mafita,
tun kafin su dawo garin nan in bahaka labari fa ze canza"
Haruna yace "gaskiya ne maganar ka, muna nan dai muna sauraren Bukar"
Saleh yace "Amma ya maganar ɗan uwana kuwa? Naga bakwa wani abu akan Alƙawarinmu
fa"
"kai dalla ana ta kai wake ta kaya? Muna ruwa tsundum muna tsakiyar masifa kana
maganar wani mutum da a yanzu bashi da wani amfani"
"Alhaji Haruna, ɗan uwan nawane bashi da Amfani, dama haka mukayi daku?"
"to ba dole ince bashi da amfani ba, tunda a yanzu ba ta tashi muke ba, muna
tsakiyar masifa kana wani zance daban, ni kaga tafiyata, ina da appointment ƙarfe
biyu da rabi"
Ya tashi ya bar masa falon, Saleh ya jinjina kai yace "lallai ashe kuwa an yanka,
kuma zata tashi"
Suna tafe suna hira, tana yaba kyan garin dukda rashin ababan more rayuwar dake
ƙauyen.
Widad ta kalli Yusuf tace "ya naga kana ɗingisawa ne, ko in goyaka ne?"
Yusuf yay murmushi yace "wai zaki goyani, kamar ba kece kika kasa wuce raguna ba
ɗazu"
"wane ni ince wani abu ya samu Gimbiyata, ai bam san idan zan sa raina ba"
Suka cigaba da tafiya, Widad tana ta tambaye tambaye, wata tambayar idan tayi
sekace wannan tsabar rainin hankali ne, nan ko harga Allah abubuwa da yawa bata
sani ba, can tace "Allah sarki, wai se gani a ruɓabiyar motar ice aka kawoni garin
nan, Allah sarki rayuwa"
"Mhmm Ameen, amma naji jiki ranar, ji nayi kamar zan bar duniya ba dan da kai ba da
ban san meze faru dani ba, Nasan idan muka koma gida kana da tukuici a gurin Daddy,
ka kula da amanarsa"
Yusuf yayi murmushi yace "ni bana buƙatar komai a gurin Daddy a matsayin tukuici
se abu ɗaya"
LITTAFIN KUƊI NE, DAN ALLAH KI SIYA KAFIN KI KARANTA BA DANNI BA DAN ALLAH, LITTAFI
NA ƊAYA KYAUTA NE WANNAN NA SIYARWA NE
NORMAL GROUP ₦300
VIP ₦500 NE KITURA TA WANNAN ACCOUNT ƊIN
0009450228
JA'IZ BANK
AISHA ADAM
SE A TURA SHEDAR BIYA TA WANNAN LAMBAR
07063065680
11/14/21, 6:09 PM - Ummee Musa: LITTAFIN KUƊI NE, DAN ALLAH KI SIYA KAFIN KI
KARANTA BA DANNI BA DAN ALLAH, LITTAFI NA ƊAYA KYAUTA NE WANNAN NA SIYARWA NE
NORMAL GROUP ₦300
VIP ₦500 NE KITURA TA WANNAN ACCOUNT ƊIN
0009450228
JA'IZ BANK
AISHA ADAM
SE A TURA SHEDAR BIYA TA WANNAN LAMBAR
07063065680
60_61
Kallonsa ta ɗanyi tace "ina fatan Allah ya rabaka da son abunda ba zaka samu ba,
na gaya maka babu Aure a tsarin rayuwata, bazan ji daɗi ba ace wani abu ya sameka
saboda ni ba, amma ina fatan zumuncinmu ya ɗore nida kai"
Yusuf yayi Ajiyar zuciya yace "naga jarrabawa daban daban a rayuwata, ciki harda
Jarrabawa a kan Soyayya, sam bani da sa'a a wannan ɓangaren, dukda tarin gargaɗi da
kashedin da kikemin akan Sonki da nake, nakasa jin zan iya dena sonki, a kowane
lokaci ina sake jin sonki a raina"
Shiru tayi suka cigaba da tafiya, ba tare da sun sake cewa komai ba.
Yusuf yayi murmushin yaƙe yace "waye yace miki nagaji ne? Ko ance miki nima ragone
irinki?"
"Nice ma raguwar?"
Dariya tayi tace "kaikam baka mantuwa ko? Saura mu koma gida kace ga abunda nayi
ka jamin raini"
"Ni na isa in faɗi abunda Gimbiya tayi, ai wannan sirrine kuma tarihi ne me matuƙar
girman gaske daze zauna a zukatanmu nida ke"
Widad tai murmushi tace "gaskiya ne, wannan rayuwar ba zata taɓa gogewa a zuciyata
ba"
Yusuf yace "dukda ragoncin nan naki, akwai inda na jinjina miki Gimbiya, ban taɓa
tunanin samun jarumar mace kamarki ba, yadda kika sa hannu kika rama dukan da
kidnappers ɗin nan sukayi miki, na jinjina miki ta wannan fannin"
Murmushi tayi tace "hakan ya samo asaline tun daga ƙuruciya ta, Allah Sarki, Allah
ya jiƙan Ammi na da Baban Yoseef"
"Ni na isa imce bana so, Ameen ya Allah, ubangiji Allah yayi musu Rahama"
"Ameen"
Sunyi tafiya me nisa sannan suka iso rafin, ba kowa a gurin, gurin shiru se kukan
tsintsaye, da kaɗawar bishiyu.
Widad tace "Wow masha Allah, ɗan uwa gurin nan yayi kyau sosai"
"enjoy yourself"
Yusuf ya shiga aikin yi musu wanki, yayin da Widad keta kalle Kallen tsuntsaye.
"Ai da alama kina da rashin ji, ba wanda ze gane hakan se wanda yake zaune dake"
"Wanda yake zaune da ni ɗin ma ba kowa ne ze gane hakan ba, kaima ban san yadda
akayi na sake da kai haka ba, haka kurum naji kamar in yadda da kai"
Cigaba tayi da wasanninta a gurin, tayi nan tayi can ta Leƙa nan ta leƙa can, Yusuf
yana ta wanki har ya kammala, yai shanya ya zura ƙafafinsa a cikin ruwan, kusa da
Yusuf tazo zauna itama ta zura ƙafafunta a ruwan tana kallonsa.
"Ban taɓa sanin a duniya akwai mutane nagari kamarka ba, da ina yiwa talakawa
kallon mayun kuɗi, maciya amana, amma gaba ɗaya you proves me wrong"
Yusuf yace "dama bekamata ka yankewa mutane hukunci da laifin tsirari daga cikinsu
ba, duk lalacewar zamani akwai na kirki"
Widad tace "Aikama nagani, dan yadda nake treating ɗinka a gida ban taɓa zaton
zaka iya taimakona ba, nayi mamakin ganin hawaye a idonka lokacin da ni kaina na
yanke tsammani da cigaba da rayuwa"
"Habibty, a wannan lokacin da kin mutu ban san ya zanyi ba, Nagode Allah da ya
nunamin na Aure ki, dukda ba kya sona"
Shiru tayi ba tace komai ba, can Yusuf yace "Widad, yanzu idan na mutu zaki damu?"
"To wannan wace irin tambaya ce mara amfani, kawai muna hira ka kama wannan zancen
ni bana so"
Ɗagota Yusuf yayi ya kalli idonta, ƙwallace kwance a idonta, se wani tura baki
take, murmushi yayi ya maida ita jikinsa ya kwantar da ita, ya shiga shafa bayanta.
Yusuf yace "Yaushe na zama ɗan uwane, naji kin canza min suna'
" Gwaggo ta hanani faɗar sunan ka, kuma kaga ni bani da ɗan uwa, se gaka ka bani
jini, kaga mun zama 'yan uwa tunda an samun jininka, mun zama' yan uwa kenan"
Dariya Yusuf yayi yace "wannan philosophy ɗinfa,? Lallai kam shikenan nima nayi
ƙanwa tunda bani da ƙanwa mace"
Ta gyara kwanciyarta a jikinsa tace "Yoseef, idan muka koma gida zaka dawo gidanmu
ka zauna kaida ummanka?"
"Dan Allah ka dawo gidanmu, nasan bazaka cigaba da tuƙani a mota ba, nasan maybe ma
in koma ƙasar waje, amma dan Allah ka dawo gidanmu kaji"
Girgiza mata kai yayi yace "so kike Mamansu Amal ta dinga wulaƙanta Ummana? Kuma
zaman me zanzo inyi a gidanku, bayan bamu da wata alaƙa, kafin nan fa mun rabu"
"Dan mun rabu shine zaka ce bazaka dawo gidanmu ba, sannan idan na koma gida dole
ta bar mana gida"
"Saboda wani dalili me girman gaske, amma yanzu ba wannan maganar muke ba, dan
Allah idan mun koma gida ka dawo gidanmu da zama,"
"Nida bakya sona, me zan zo gidanku inyi? Idan dai har ina ganinki zan cigaba da
sonki ne, kuma ni bakya sona"
"Nifa ba tsanarka nayi ba, kawai ni bana son soyayya ne, ban santa ba kuma ban iya
ba, dan bata birgeni, ƙarya ce da tarin damuwa a cikinta, amma ni bana son ko mun
koma gida kayi nesa dani, na saba da kai sosai, kana iya haƙuri da dukkanin
halayena, kuma kai garkuwa ne a gareni, dan Allah Yoseef ka yadda kaji ɗan uwa"
Yusuf kam murmushi yayi, a ransa yace 'sarkin taurin kai, kina sona amma kina
garani'
A fili ya maze yace "Idan muka koma gidanku ace munje kwaɗayi, ni nafison in zauna
a gidanmu nida Ummana"
"dan Allah, ba wanda zece muku haka, Dan Allah Yoseef kaji"
Wani abune ya dinga fizgar Yusuf game da Widad, yana jin wani irin farinciki a tare
da shi, abunda bata son dai yayi mata, sedai wannan karon bata hana shi ba, sema
biye masa da tayi.
A hankali ya cire bakinsa daga nata ya riƙe hannunta yace "ina sonki Habibty"
Kawai ya tsaya ya zuba mata ido, a hankali tace "yakamata muje muci Abinci"
Yusuf ya cikata, suka miƙe ya shimfiɗa musu abu suka zauna, ya buɗe shinkafa da
wake, da manja ya ɗakko tumatir da gurji ya yayyanka, ya juya suka fara ci.
"Gani nayi kina loma fiye da tawa, zaki cinye Abincin ki barni"
Ya dinga jin farinciki, ganin yadda Widad ɗinsa ke nishaɗi tana fara'a, saɓanin
Widad ɗin daya sani a baya, me shegen haɗe ran tsiya da koke koke, mara afuwa da
tausayi.
Juyawa yayi gefensa ya tsinko wata 'yar ciwa, ya miƙo mata yana cewa
"If you ask me to be your king, i will turn around and said, you mean to tell me
that I can have you when ever I want, i can tell you that I love you when you love
me too, no more waiting for ever our love...
Kwashewa da dariya Widad tayi tace " Ai ba haka ake waƙar ba, kuma flower ake
bayarwa, amma ni ka bani ciyawa sekace wata Akuya"
Yusuf yayi murmushi yace "A yanzu bani da wani abu da zan baki ai, shiyasa na baki
wannan instead of flower"
Saleh ne a gigice ya shiga babban Ofishin dake cikin harabar gurin, Suleiman ne
zaune yana danna system ɗinsa, Saleh ya shigo da sallama.
Suleiman ya ɗago tare da yin murmushi yace "Masha Allah, yau kaine a ofishin nawa?
Kwana biyu"
Saleh ya miƙa masa hannu suka gaisa, yace "Suleiman ya aikin naku?"
Saleh yace "lafiya ƙalau, yana gaisheku ina sa ran zuwa gurin mahaifiyarsa, im
sake kwantar mata da hankali tare da tabattar mata yana cikin ƙoshin lafiya"
Suleiman ya gyara zama yace "hakane, hakam abune me kyau nima da week ends ɗin
nan, naje gidan sedai har yanzu ta kasa kwantar da hankali ta, akwai buƙatar ka
ɗakko mata muryarsa, kokuma ka haɗasu a waya su gaisa"
Saleh yace "No baze yuwu ba, ai bama zuwa garin nan da waya, kai mutanen nan fa
sun shallake tunanin ka, nima ina lura da duka abunda nake yi, bana shiga da waya,
haka nake zuwa in fito"
"to ubangiji Allah ya kuɓutar dasu, ina mamakin yadda abubuwan suke tafiya, kullum
sake taɓarɓarewa sukeyi"
"mutanen nan sun gano waye Yusuf, kuma suna shirin ɗaukar mataki akan hakan?"
Saleh yace "niba wannan ba, babban abunda ya dameni shine, rashin sanin wani irin
mataki zasu ɗauka akansa, gashi kuma yana can yana cikin zulumi akan ta yaya ze
sanar da Widad gaskiyar waye shi, kasanta bata afuwa bata yafiya ga duka wanda yayi
mata ƙarya, muddin suka dawo garin nan sannan ta gane waye shi akwai matsala "
Suleiman yace '" dukda gargaɗina da tayimin, amma bari in gaya maka yadda akayi
tasan waye shi, wataran da yamma na kammala abunda nake zan bar office ɗin nan,
kawai sega wata mota ta shigo gurin nan a guje, kamar zata tashi sama,
ma' aikatanmu sukayi kanta don son ganin wane mara ɗa'ar ne haka? Ko a jikin me
tuƙin, Ta buɗe motar ta fito, wata matashiyar budurwa ce jikinta sanye da abaya, ta
saka face mask, sannan ta rufe fuskarta da glass.
Kai tsaye inda nake ta shiga tunkarowa, da ma'aikatanmu sunyi kanta zasu hanata
ƙarasowa, nace su barta ta ƙaraso.
Ko kallonsu batayi ba tazo inda nake ta tsaya ta kalleni tace "kaine Suleiman?"
tace "sunana Widad Nasir Daula, nazo me zan maka wasu tambayoyi, kuma idan ka
amsamin ba dai dai ba, ka shirya karɓar abunda ze biyo baya, bana sassauci ga
mutane maƙaryata, waye Yusuf?"
Suleiman yace "Yusuf jami'inmun ne, ɗan sanda ne na farin kaya" Suleiman ya bata
amsa
"danme zaku turoshi? Me yasa kuka turoshi,? wato an haɗa kai daku a cuceni"
Cikin isa da izza tace "akan me? Sannan kuma waye ya bada umarnin hakan? Ko kuma
ni nace ina buƙatar hakanne? An haɗa kai daku za'a cutar dani, in ba hakaba meyasa
Yusuf yasa hannu akan takardar zeyi aiki dani, dukda na gaya masa hakan tamkar saka
hannu akan kwangilar mutuwarsane? Na kama Yusuf da bindiga"
Tun anan Suleiman ya jinjinawa Yusuf, ya yabawa ƙoƙarin sa na jure zama tare da yin
aiki da Widad, saboda yadda take magana cike da izza da isa.
Suleiman yace " kamar yadda na gaya miki, Yusuf jajirtaccen ɗan sandane, kuma ba
abun mamaki bane samun ɗan sanda da bindiga, sannan Yusuf baza'a taɓa bashi aiki ya
dawo dashi yace ya karaya ko baze iyaba, amma sam bashi da laifi, kuma da farko
bashi mukayi niyyar bawa aikinba, abokin aikinsane yace a bashi saboda jajircewarsa
da haƙurinsa"
Ajiyar zuciya Widad tayi tana huci, inda Allah ya temaki Sulaiman gaskiyar data
buƙata ita yake gaya mata, ta kalle shi tace "Ina buƙatar sanin waye yasa a dinga
bin diddigi na?"
Suleiman yace "kamar yadda na gaya miki ne, ban saniba nima umarni aka bani daga
sama, ban san komai akai ba"
Widad tace "shikenan, ni zanje in bincika da kaina, amma zan maka gargaɗi da jan
kunne, Yusuf be san na ganshi da bindiga ba, kada ka kuskura Yusuf yasan nasan waye
shi, idan har ka gaya masa nasan waye shi zan gane, and you know what am capable of
doing"
Suleiman yace "karki damu, Insha Allah baze sani ba, bazan gaya masa ba"
Tace "and Mark you, bana son kowa yasan da nice nazo gurin nan, and zan cigaba da
bibiyarka, duk lokacin da Yusuf yayi misbehaving ko wani abu na yunƙurin cin amana
ta, to dasa hannunka a ciki"
Suleiman yace "ina me tabattar miki da babu abunda zeyi na cin amanarki"
Ta miƙe a gadarance, ta maida face mask ɗinta, ta saka glass ɗinta ta fito, sedai
tana fitowa Abbas ya kawo kai yana shigowa, ta tsaya ta ƙura masa ido, harya shige
wani office, sam Abbas be lura da kallon da take masa ba, ba tace komai ba tayi
gaba da sauri ta hau motarta ta bar gurin.
Bayan wasu 'yan kwanaki da yin hakan, Widad ta kira Suleiman tace tana son ya
gayamata full name na Abbas da rank ɗinsa, amma Suleiman yace hakan ya saɓa da ƙa'
idar aikinsu, sedai ta gaya masa meyasa take neman hakan, bata kuma bi takansa ba
bayan kwana uku, aka kawo transfer later na Abbas aka maye gurbinsa da Yusuf.
Saleh ya jinjina kai yace "wato duk inda mutum yake tunanin hatsabibancin yarinyar
nan ta wuce haka, yana cam yana ta zullumi akan yadda ze gayamata, ashe tuni ta
sani"
Sulaiman yace "tabbas tasan waye Yusuf, kallonsa kawai take sannan kamar yadda
naimata Alƙawari ban gaya masa ba"
Saleh yace "Allah sarki, ni gaba ɗaya tausayi yake bani wallahi, bejiba be gani ba
yana ta ɗawainiya da yarinyar ta bata san kimar mutane ba, duk naga ta rage wannan
zafin kan nata, ta kwantar da mai tana rayuwa a ƙauyen da babu wuta, babu ruwa babu
abubuwan more rayuwa, abun gaanin ban tausayi"
Suleiman yace "Allah sarki Yusuf, samun mutum me irin zuciyarsa se an tona, ina
masa fatan ubangiji Allah ya kuɓutaf dashi, daga sharrin Azzaluman nan"
Saleh yace "Ameen ya Allah, amma tabbas Yusuf yana cikin jarrabawa, dan ina tunanin
matakin da zasu ɗauka akansa, basu da imani sam"
Suleiman yace "Allah ya fisu kam, amma indai batun sadaukarwa ne, to tabbas Yusuf
yayita"
Se bayan la'asar, lokacin kayansu sun bushe sannan Yusuf ya tattaresu ya ninke,
suka kamo hanyar gida, suna tafe suna hira gwanin ban sha'awa, Widad nata takura
masa da tambayoyi dan duk abunda ta gani bata sani ba seta tambaya.
Suna zuwa gida Gwaggo tai murmushi tace "Amarya yau gidan nan ba daɗi ba kya nan,
duk naji ba daɗi"
Widad tai murmushi tace "nima haka naji ba daɗi yau Mama"
Hindu tace "wallahi kuwa Gwaggo, gaba ɗaya yau gidan se a hankali ba daɗi da bakya
nan"
Hari tace "Nikam naji daɗi, bakin mutane shiru yau ba neman magana"
'
Widad tace "in mutane na magana ki dena saka baki, danke ba mutum bace"
Gwaggo tace "Amarya yau wake muka dafa, ban sani ba ko zaki iyaci, dan haka na
dama miki kunu gashi can da zafinsa"
Widad tace "wayyo Allah Mamana ta kaina, nagode sosai Allah yasaka da alkhairi,
wakenma duk zan iyaci nagode sosai Mama"
Seda tayi me isarta sannan ta koma ɗakin, Yusuf tun yana mamakin halin Widad har ya
dena, ta kwaso kwanukan wanke wanke tayi, gaba ɗaya yau wani irin nishaɗi take ji,
taji daɗin fitar da suka yi sosai, wani irin farinciki ya dinga ratsata.
Ta karɓo musu Abincin gurin Gwaggo, suka zauna suka ci, bayan sun gama ne ta ɗanyi
shiru sannan tace "Naji daɗin fitar nan sosai Yoseef, ban taɓa tunanin ana samun
farinciki haka ba koda babu dukiya"
Yusuf yace "aishi farinciki da jin daɗi base ka tara dukiya ba, indai zakayi
tawakkali da yadda Allah ya ajiyeka, zakayi rayuwarka cikin farin ciki da jin daɗi,
kuma har kafi me Dukiya walwala ma".
Widad tace "ƙwarai kuwa yau na gani, rabon da inyi farinciki haka tun Ammi na nada
rai, shekara goma baya kenan"
Yusuf yace "kina nufin duk tsawon wannan shekarun, bakya farinciki?"
"tun bayan rasuwar Ammi, ban kuma samun farinciki haka ba, babu club ɗin da bana
zuwa a waje, dan inyi nishaɗi, nice club ɗim wrestling stadiums na ball da sauran
wasanni, amma babu sauyi, na kanji nishaɗi ne kawai idan nai wasan doki, kona
kasance da dabbobi kuma idan ina Tare da Alhaji Nasir Daula "
'yar Wulaƙanci yau kuma saunan baban nata take faɗa gatsal"
Ta cigaba da cewa "nasan Daddy zeyi murna sosai, idan ya ganni cikin walwala haka,
danya fidda ran faruwar hakan a rayuwata" ta ƙarasa maganar muryarta na rawa alamun
zata yi kuka.
Rungumota Yusuf yayi yace "haba Jarumata, kuma Gimbiya ta, karkiyi kuka please
kiyi haƙuri kinji babyna, nifa jarumtar nan taki burgeni take yi, dan haka idan
muka koma gida, zan saki a aikin ɗan sanda kema"
Kwashewa tayi da dariya, tace 'kai dai kaje kaita aikin ɗan sandan, nikam a kai
kasuwa "
" Zaki iya kama' yan fashi fa da ɓarayi da wannan dakakkiyar zuciyar taki Baby"
Yusuf yace "am just kidding, idan wanda suka kashe mahaifiyarki ne, Insha Allah ni
zan ɗau nauyin yin wannan binciken"
Girgiza masa kai tayi tace "this the most dangerous case, don't take the risk of
it, ni suke bibiya suke son ganin bayana, dan haka koni ko su, karka sa kanka a
ciki, a yanzu ma kalli yadda kake wahala"
Yusuf yace "Amma suwaye suka kashe ta, kuma meyasa? '
Yusuf yace "i have to know even a little bit of your life"
"bazan faɗa ba, ban yadda da kai ba" tai maganar tana dariya.
Yusuf yace "ai yadda ta ƙare, tunda muka zama abu ɗaya, har muka kasance a inuwa
ɗaya"
"Inuwar Aure mana Baby na, kuma gashi.... Sekuma yayi shiru
Widad tace " Kuma gashi me? Ƙarasa mana, kai ko kunyata na baka ji ko? Allah ya
shiryeka, ni cikani"
Ƙara rungumeta yayi yana murmushi yace "Kunyarwa zanji? Mutum da matarsa"
"Matar ƙauye ba, dan iya nan ne, kafin mu koma gida zamu rabu'
Murmushi kawai Yusuf yayi bece mata komai ba, a hankali yace " ki gayamin mana "
" wai mai meyasa ka damu se kaji tarihin rayuwata? Ko nima binciken ake a kaina? "
Yusuf ya kwanta, ta kalle shi tace "kuma wallahi idan kamin wani abu, se munyi
faɗa na gaya maka"
"Bansani ba"
LITTAFIN KUƊI NE, DAN ALLAH KI SIYA KAFIN KI KARANTA BA DANNI BA DAN ALLAH, LITTAFI
NA ƊAYA KYAUTA NE WANNAN NA SIYARWA NE
NORMAL GROUP ₦300
VIP ₦500 NE KITURA TA WANNAN ACCOUNT ƊIN
0009450228
JA'IZ BANK
AISHA ADAM
SE A TURA SHEDAR BIYA TA WANNAN LAMBAR
07063065680
11/14/21, 6:09 PM - Ummee Musa: LITTAFIN KUƊI NE, DAN ALLAH KI SIYA KAFIN KI
KARANTA BA DANNI BA DAN ALLAH, LITTAFI NA ƊAYA KYAUTA NE WANNAN NA SIYARWA NE
NORMAL GROUP ₦300
VIP ₦500 NE KITURA TA WANNAN ACCOUNT ƊIN
0009450228
JA'IZ BANK
AISHA ADAM
SE A TURA SHEDAR BIYA TA WANNAN LAMBAR
07063065680
60_61
Kallonsa ta ɗanyi tace "ina fatan Allah ya rabaka da son abunda ba zaka samu ba,
na gaya maka babu Aure a tsarin rayuwata, bazan ji daɗi ba ace wani abu ya sameka
saboda ni ba, amma ina fatan zumuncinmu ya ɗore nida kai"
Yusuf yayi Ajiyar zuciya yace "naga jarrabawa daban daban a rayuwata, ciki harda
Jarrabawa a kan Soyayya, sam bani da sa'a a wannan ɓangaren, dukda tarin gargaɗi da
kashedin da kikemin akan Sonki da nake, nakasa jin zan iya dena sonki, a kowane
lokaci ina sake jin sonki a raina"
Shiru tayi suka cigaba da tafiya, ba tare da sun sake cewa komai ba.
Yusuf yayi murmushin yaƙe yace "waye yace miki nagaji ne? Ko ance miki nima ragone
irinki?"
"Nice ma raguwar?"
Dariya tayi tace "kaikam baka mantuwa ko? Saura mu koma gida kace ga abunda nayi
ka jamin raini"
"Ni na isa in faɗi abunda Gimbiya tayi, ai wannan sirrine kuma tarihi ne me matuƙar
girman gaske daze zauna a zukatanmu nida ke"
Widad tai murmushi tace "gaskiya ne, wannan rayuwar ba zata taɓa gogewa a zuciyata
ba"
Yusuf yace "dukda ragoncin nan naki, akwai inda na jinjina miki Gimbiya, ban taɓa
tunanin samun jarumar mace kamarki ba, yadda kika sa hannu kika rama dukan da
kidnappers ɗin nan sukayi miki, na jinjina miki ta wannan fannin"
Murmushi tayi tace "hakan ya samo asaline tun daga ƙuruciya ta, Allah Sarki, Allah
ya jiƙan Ammi na da Baban Yoseef"
"Ni na isa imce bana so, Ameen ya Allah, ubangiji Allah yayi musu Rahama"
"Ameen"
Sunyi tafiya me nisa sannan suka iso rafin, ba kowa a gurin, gurin shiru se kukan
tsintsaye, da kaɗawar bishiyu.
Widad tace "Wow masha Allah, ɗan uwa gurin nan yayi kyau sosai"
"enjoy yourself"
Yusuf ya shiga aikin yi musu wanki, yayin da Widad keta kalle Kallen tsuntsaye.
"Ɗan uwa da ruwan nan yana da kyau sosai, da swimming zanyi"
"Ai da alama kina da rashin ji, ba wanda ze gane hakan se wanda yake zaune dake"
"Wanda yake zaune da ni ɗin ma ba kowa ne ze gane hakan ba, kaima ban san yadda
akayi na sake da kai haka ba, haka kurum naji kamar in yadda da kai"
Cigaba tayi da wasanninta a gurin, tayi nan tayi can ta Leƙa nan ta leƙa can, Yusuf
yana ta wanki har ya kammala, yai shanya ya zura ƙafafinsa a cikin ruwan, kusa da
Yusuf tazo zauna itama ta zura ƙafafunta a ruwan tana kallonsa.
"Ban taɓa sanin a duniya akwai mutane nagari kamarka ba, da ina yiwa talakawa
kallon mayun kuɗi, maciya amana, amma gaba ɗaya you proves me wrong"
Yusuf yace "dama bekamata ka yankewa mutane hukunci da laifin tsirari daga cikinsu
ba, duk lalacewar zamani akwai na kirki"
Widad tace "Aikama nagani, dan yadda nake treating ɗinka a gida ban taɓa zaton
zaka iya taimakona ba, nayi mamakin ganin hawaye a idonka lokacin da ni kaina na
yanke tsammani da cigaba da rayuwa"
"Habibty, a wannan lokacin da kin mutu ban san ya zanyi ba, Nagode Allah da ya
nunamin na Aure ki, dukda ba kya sona"
Shiru tayi ba tace komai ba, can Yusuf yace "Widad, yanzu idan na mutu zaki damu?"
"To wannan wace irin tambaya ce mara amfani, kawai muna hira ka kama wannan zancen
ni bana so"
Ɗagota Yusuf yayi ya kalli idonta, ƙwallace kwance a idonta, se wani tura baki
take, murmushi yayi ya maida ita jikinsa ya kwantar da ita, ya shiga shafa bayanta.
Ɗagowa tayi ta kalle shi tace "Ɗan uwa"
Yusuf yace "Yaushe na zama ɗan uwane, naji kin canza min suna'
" Gwaggo ta hanani faɗar sunan ka, kuma kaga ni bani da ɗan uwa, se gaka ka bani
jini, kaga mun zama 'yan uwa tunda an samun jininka, mun zama' yan uwa kenan"
Dariya Yusuf yayi yace "wannan philosophy ɗinfa,? Lallai kam shikenan nima nayi
ƙanwa tunda bani da ƙanwa mace"
Ta gyara kwanciyarta a jikinsa tace "Yoseef, idan muka koma gida zaka dawo gidanmu
ka zauna kaida ummanka?"
"Dan Allah ka dawo gidanmu, nasan bazaka cigaba da tuƙani a mota ba, nasan maybe ma
in koma ƙasar waje, amma dan Allah ka dawo gidanmu kaji"
Girgiza mata kai yayi yace "so kike Mamansu Amal ta dinga wulaƙanta Ummana? Kuma
zaman me zanzo inyi a gidanku, bayan bamu da wata alaƙa, kafin nan fa mun rabu"
"Dan mun rabu shine zaka ce bazaka dawo gidanmu ba, sannan idan na koma gida dole
ta bar mana gida"
"Saboda wani dalili me girman gaske, amma yanzu ba wannan maganar muke ba, dan
Allah idan mun koma gida ka dawo gidanmu da zama,"
"Nida bakya sona, me zan zo gidanku inyi? Idan dai har ina ganinki zan cigaba da
sonki ne, kuma ni bakya sona"
"Nifa ba tsanarka nayi ba, kawai ni bana son soyayya ne, ban santa ba kuma ban iya
ba, dan bata birgeni, ƙarya ce da tarin damuwa a cikinta, amma ni bana son ko mun
koma gida kayi nesa dani, na saba da kai sosai, kana iya haƙuri da dukkanin
halayena, kuma kai garkuwa ne a gareni, dan Allah Yoseef ka yadda kaji ɗan uwa"
Yusuf kam murmushi yayi, a ransa yace 'sarkin taurin kai, kina sona amma kina
garani'
A fili ya maze yace "Idan muka koma gidanku ace munje kwaɗayi, ni nafison in zauna
a gidanmu nida Ummana"
"dan Allah, ba wanda zece muku haka, Dan Allah Yoseef kaji"
Wani abune ya dinga fizgar Yusuf game da Widad, yana jin wani irin farinciki a tare
da shi, abunda bata son dai yayi mata, sedai wannan karon bata hana shi ba, sema
biye masa da tayi.
A hankali ya cire bakinsa daga nata ya riƙe hannunta yace "ina sonki Habibty"
Kawai ya tsaya ya zuba mata ido, a hankali tace "yakamata muje muci Abinci"
Yusuf ya cikata, suka miƙe ya shimfiɗa musu abu suka zauna, ya buɗe shinkafa da
wake, da manja ya ɗakko tumatir da gurji ya yayyanka, ya juya suka fara ci.
Suna ci yana kallon Widad, ta kwantar da hankalinta, ta rugumi ƙaddarar rayuwarta,
da farkom zuwansu ne se yayi fama kafin taci Abincin, amma yanzu hankali kwance ta
dinga cin Abincinta.
"Gani nayi kina loma fiye da tawa, zaki cinye Abincin ki barni"
Ya dinga jin farinciki, ganin yadda Widad ɗinsa ke nishaɗi tana fara'a, saɓanin
Widad ɗin daya sani a baya, me shegen haɗe ran tsiya da koke koke, mara afuwa da
tausayi.
Juyawa yayi gefensa ya tsinko wata 'yar ciwa, ya miƙo mata yana cewa
"If you ask me to be your king, i will turn around and said, you mean to tell me
that I can have you when ever I want, i can tell you that I love you when you love
me too, no more waiting for ever our love...
Kwashewa da dariya Widad tayi tace " Ai ba haka ake waƙar ba, kuma flower ake
bayarwa, amma ni ka bani ciyawa sekace wata Akuya"
Yusuf yayi murmushi yace "A yanzu bani da wani abu da zan baki ai, shiyasa na baki
wannan instead of flower"
Saleh ne a gigice ya shiga babban Ofishin dake cikin harabar gurin, Suleiman ne
zaune yana danna system ɗinsa, Saleh ya shigo da sallama.
Suleiman ya ɗago tare da yin murmushi yace "Masha Allah, yau kaine a ofishin nawa?
Kwana biyu"
Saleh ya miƙa masa hannu suka gaisa, yace "Suleiman ya aikin naku?"
Saleh yace "lafiya ƙalau, yana gaisheku ina sa ran zuwa gurin mahaifiyarsa, im
sake kwantar mata da hankali tare da tabattar mata yana cikin ƙoshin lafiya"
Suleiman ya gyara zama yace "hakane, hakam abune me kyau nima da week ends ɗin
nan, naje gidan sedai har yanzu ta kasa kwantar da hankali ta, akwai buƙatar ka
ɗakko mata muryarsa, kokuma ka haɗasu a waya su gaisa"
Saleh yace "No baze yuwu ba, ai bama zuwa garin nan da waya, kai mutanen nan fa
sun shallake tunanin ka, nima ina lura da duka abunda nake yi, bana shiga da waya,
haka nake zuwa in fito"
"to ubangiji Allah ya kuɓutar dasu, ina mamakin yadda abubuwan suke tafiya, kullum
sake taɓarɓarewa sukeyi"
"mutanen nan sun gano waye Yusuf, kuma suna shirin ɗaukar mataki akan hakan?"
Suleiman yace "ya akayi suka sani?"
Saleh yace "niba wannan ba, babban abunda ya dameni shine, rashin sanin wani irin
mataki zasu ɗauka akansa, gashi kuma yana can yana cikin zulumi akan ta yaya ze
sanar da Widad gaskiyar waye shi, kasanta bata afuwa bata yafiya ga duka wanda yayi
mata ƙarya, muddin suka dawo garin nan sannan ta gane waye shi akwai matsala "
Suleiman yace '" dukda gargaɗina da tayimin, amma bari in gaya maka yadda akayi
tasan waye shi, wataran da yamma na kammala abunda nake zan bar office ɗin nan,
kawai sega wata mota ta shigo gurin nan a guje, kamar zata tashi sama,
ma' aikatanmu sukayi kanta don son ganin wane mara ɗa'ar ne haka? Ko a jikin me
tuƙin, Ta buɗe motar ta fito, wata matashiyar budurwa ce jikinta sanye da abaya, ta
saka face mask, sannan ta rufe fuskarta da glass.
Kai tsaye inda nake ta shiga tunkarowa, da ma'aikatanmu sunyi kanta zasu hanata
ƙarasowa, nace su barta ta ƙaraso.
Ko kallonsu batayi ba tazo inda nake ta tsaya ta kalleni tace "kaine Suleiman?"
tace "sunana Widad Nasir Daula, nazo me zan maka wasu tambayoyi, kuma idan ka
amsamin ba dai dai ba, ka shirya karɓar abunda ze biyo baya, bana sassauci ga
mutane maƙaryata, waye Yusuf?"
Suleiman yace "Yusuf jami'inmun ne, ɗan sanda ne na farin kaya" Suleiman ya bata
amsa
"danme zaku turoshi? Me yasa kuka turoshi,? wato an haɗa kai daku a cuceni"
Cikin isa da izza tace "akan me? Sannan kuma waye ya bada umarnin hakan? Ko kuma
ni nace ina buƙatar hakanne? An haɗa kai daku za'a cutar dani, in ba hakaba meyasa
Yusuf yasa hannu akan takardar zeyi aiki dani, dukda na gaya masa hakan tamkar saka
hannu akan kwangilar mutuwarsane? Na kama Yusuf da bindiga"
Tun anan Suleiman ya jinjinawa Yusuf, ya yabawa ƙoƙarin sa na jure zama tare da yin
aiki da Widad, saboda yadda take magana cike da izza da isa.
Suleiman yace " kamar yadda na gaya miki, Yusuf jajirtaccen ɗan sandane, kuma ba
abun mamaki bane samun ɗan sanda da bindiga, sannan Yusuf baza'a taɓa bashi aiki ya
dawo dashi yace ya karaya ko baze iyaba, amma sam bashi da laifi, kuma da farko
bashi mukayi niyyar bawa aikinba, abokin aikinsane yace a bashi saboda jajircewarsa
da haƙurinsa"
Ajiyar zuciya Widad tayi tana huci, inda Allah ya temaki Sulaiman gaskiyar data
buƙata ita yake gaya mata, ta kalle shi tace "Ina buƙatar sanin waye yasa a dinga
bin diddigi na?"
Suleiman yace "kamar yadda na gaya miki ne, ban saniba nima umarni aka bani daga
sama, ban san komai akai ba"
Widad tace "shikenan, ni zanje in bincika da kaina, amma zan maka gargaɗi da jan
kunne, Yusuf be san na ganshi da bindiga ba, kada ka kuskura Yusuf yasan nasan waye
shi, idan har ka gaya masa nasan waye shi zan gane, and you know what am capable of
doing"
Suleiman yace "karki damu, Insha Allah baze sani ba, bazan gaya masa ba"
Tace "and Mark you, bana son kowa yasan da nice nazo gurin nan, and zan cigaba da
bibiyarka, duk lokacin da Yusuf yayi misbehaving ko wani abu na yunƙurin cin amana
ta, to dasa hannunka a ciki"
Suleiman yace "ina me tabattar miki da babu abunda zeyi na cin amanarki"
Ta miƙe a gadarance, ta maida face mask ɗinta, ta saka glass ɗinta ta fito, sedai
tana fitowa Abbas ya kawo kai yana shigowa, ta tsaya ta ƙura masa ido, harya shige
wani office, sam Abbas be lura da kallon da take masa ba, ba tace komai ba tayi
gaba da sauri ta hau motarta ta bar gurin.
Bayan wasu 'yan kwanaki da yin hakan, Widad ta kira Suleiman tace tana son ya
gayamata full name na Abbas da rank ɗinsa, amma Suleiman yace hakan ya saɓa da ƙa'
idar aikinsu, sedai ta gaya masa meyasa take neman hakan, bata kuma bi takansa ba
bayan kwana uku, aka kawo transfer later na Abbas aka maye gurbinsa da Yusuf.
Saleh ya jinjina kai yace "wato duk inda mutum yake tunanin hatsabibancin yarinyar
nan ta wuce haka, yana cam yana ta zullumi akan yadda ze gayamata, ashe tuni ta
sani"
Sulaiman yace "tabbas tasan waye Yusuf, kallonsa kawai take sannan kamar yadda
naimata Alƙawari ban gaya masa ba"
Saleh yace "Allah sarki, ni gaba ɗaya tausayi yake bani wallahi, bejiba be gani ba
yana ta ɗawainiya da yarinyar ta bata san kimar mutane ba, duk naga ta rage wannan
zafin kan nata, ta kwantar da mai tana rayuwa a ƙauyen da babu wuta, babu ruwa babu
abubuwan more rayuwa, abun gaanin ban tausayi"
Suleiman yace "Allah sarki Yusuf, samun mutum me irin zuciyarsa se an tona, ina
masa fatan ubangiji Allah ya kuɓutaf dashi, daga sharrin Azzaluman nan"
Saleh yace "Ameen ya Allah, amma tabbas Yusuf yana cikin jarrabawa, dan ina tunanin
matakin da zasu ɗauka akansa, basu da imani sam"
Suleiman yace "Allah ya fisu kam, amma indai batun sadaukarwa ne, to tabbas Yusuf
yayita"
Haka suka cigaba da tattaunawa a tsakanin su.
Se bayan la'asar, lokacin kayansu sun bushe sannan Yusuf ya tattaresu ya ninke,
suka kamo hanyar gida, suna tafe suna hira gwanin ban sha'awa, Widad nata takura
masa da tambayoyi dan duk abunda ta gani bata sani ba seta tambaya.
Suna zuwa gida Gwaggo tai murmushi tace "Amarya yau gidan nan ba daɗi ba kya nan,
duk naji ba daɗi"
Widad tai murmushi tace "nima haka naji ba daɗi yau Mama"
Hindu tace "wallahi kuwa Gwaggo, gaba ɗaya yau gidan se a hankali ba daɗi da bakya
nan"
Hari tace "Nikam naji daɗi, bakin mutane shiru yau ba neman magana"
'
Widad tace "in mutane na magana ki dena saka baki, danke ba mutum bace"
Gwaggo tace "Amarya yau wake muka dafa, ban sani ba ko zaki iyaci, dan haka na
dama miki kunu gashi can da zafinsa"
Widad tace "wayyo Allah Mamana ta kaina, nagode sosai Allah yasaka da alkhairi,
wakenma duk zan iyaci nagode sosai Mama"
Hari tana ta ƙulla gyaɗarta ta siyarwa, Widad tazo ta cika hannu ta zuba a hijjabi
tayi ɗaki, Hari ta buɗe baki tace "Wudas yaseen sekin biyani kuɗin gyaɗar nan"
Seda tayi me isarta sannan ta koma ɗakin, Yusuf tun yana mamakin halin Widad har ya
dena, ta kwaso kwanukan wanke wanke tayi, gaba ɗaya yau wani irin nishaɗi take ji,
taji daɗin fitar da suka yi sosai, wani irin farinciki ya dinga ratsata.
Ta karɓo musu Abincin gurin Gwaggo, suka zauna suka ci, bayan sun gama ne ta ɗanyi
shiru sannan tace "Naji daɗin fitar nan sosai Yoseef, ban taɓa tunanin ana samun
farinciki haka ba koda babu dukiya"
Yusuf yace "aishi farinciki da jin daɗi base ka tara dukiya ba, indai zakayi
tawakkali da yadda Allah ya ajiyeka, zakayi rayuwarka cikin farin ciki da jin daɗi,
kuma har kafi me Dukiya walwala ma".
Widad tace "ƙwarai kuwa yau na gani, rabon da inyi farinciki haka tun Ammi na nada
rai, shekara goma baya kenan"
Yusuf yace "kina nufin duk tsawon wannan shekarun, bakya farinciki?"
"tun bayan rasuwar Ammi, ban kuma samun farinciki haka ba, babu club ɗin da bana
zuwa a waje, dan inyi nishaɗi, nice club ɗim wrestling stadiums na ball da sauran
wasanni, amma babu sauyi, na kanji nishaɗi ne kawai idan nai wasan doki, kona
kasance da dabbobi kuma idan ina Tare da Alhaji Nasir Daula "
'yar Wulaƙanci yau kuma saunan baban nata take faɗa gatsal"
Ta cigaba da cewa "nasan Daddy zeyi murna sosai, idan ya ganni cikin walwala haka,
danya fidda ran faruwar hakan a rayuwata" ta ƙarasa maganar muryarta na rawa alamun
zata yi kuka.
Rungumota Yusuf yayi yace "haba Jarumata, kuma Gimbiya ta, karkiyi kuka please
kiyi haƙuri kinji babyna, nifa jarumtar nan taki burgeni take yi, dan haka idan
muka koma gida, zan saki a aikin ɗan sanda kema"
Kwashewa tayi da dariya, tace 'kai dai kaje kaita aikin ɗan sandan, nikam a kai
kasuwa "
" Zaki iya kama' yan fashi fa da ɓarayi da wannan dakakkiyar zuciyar taki Baby"
Yusuf yace "am just kidding, idan wanda suka kashe mahaifiyarki ne, Insha Allah ni
zan ɗau nauyin yin wannan binciken"
Girgiza masa kai tayi tace "this the most dangerous case, don't take the risk of
it, ni suke bibiya suke son ganin bayana, dan haka koni ko su, karka sa kanka a
ciki, a yanzu ma kalli yadda kake wahala"
Yusuf yace "Amma suwaye suka kashe ta, kuma meyasa? '
Yusuf yace "i have to know even a little bit of your life"
"bazan faɗa ba, ban yadda da kai ba" tai maganar tana dariya.
Yusuf yace "ai yadda ta ƙare, tunda muka zama abu ɗaya, har muka kasance a inuwa
ɗaya"
"Inuwar Aure mana Baby na, kuma gashi.... Sekuma yayi shiru
Widad tace " Kuma gashi me? Ƙarasa mana, kai ko kunyata na baka ji ko? Allah ya
shiryeka, ni cikani"
Ƙara rungumeta yayi yana murmushi yace "Kunyarwa zanji? Mutum da matarsa"
"Matar ƙauye ba, dan iya nan ne, kafin mu koma gida zamu rabu'
Murmushi kawai Yusuf yayi bece mata komai ba, a hankali yace " ki gayamin mana "
" wai mai meyasa ka damu se kaji tarihin rayuwata? Ko nima binciken ake a kaina? "
Yusuf ya kwanta, ta kalle shi tace "kuma wallahi idan kamin wani abu, se munyi
faɗa na gaya maka"
Yusuf yace "idan nai miki me?"
"Bansani ba"
LITTAFIN KUƊI NE, DAN ALLAH KI SIYA KAFIN KI KARANTA BA DANNI BA DAN ALLAH, LITTAFI
NA ƊAYA KYAUTA NE WANNAN NA SIYARWA NE
NORMAL GROUP ₦300
VIP ₦500 NE KITURA TA WANNAN ACCOUNT ƊIN
0009450228
JA'IZ BANK
AISHA ADAM
SE A TURA SHEDAR BIYA TA WANNAN LAMBAR
07063065680
11/14/21, 6:09 PM - Ummee Musa: LITTAFIN KUƊI NE, DAN ALLAH KI SIYA KAFIN KI
KARANTA BA DANNI BA DAN ALLAH, LITTAFI NA ƊAYA KYAUTA NE WANNAN NA SIYARWA NE
NORMAL GROUP ₦300
VIP ₦500 NE KITURA TA WANNAN ACCOUNT ƊIN
0009450228
JA'IZ BANK
AISHA ADAM
SE A TURA SHEDAR BIYA TA WANNAN LAMBAR
07063065680
60_61
Mahaifin Widad Alhaji Nasir haifaffen garin Kano ne, su biyu Allah ya bawa
iyayensu, Shida Yayansa me suna Yusuf.
Yusuf shine babba sannan Nasir, kusan shekaru takwas Yusuf ya bawa Nasir, Nasir da
Yusuf suna da matukar haƙuri da biyayya, dan har Yusuf yafi Nasir haƙuri, Yusuf
yana matuƙar ƙaunar ƙaninsa, tun suna yara duk wata hidimar Nasir Yusuf ne yake
yinta.
Mahaifiyar su Marainiya ce, bata da wani cikakken gata, mahaifinsu Nasir kuma,
shikaɗai mahaifiyarsa ta haifa, sauran duk uba ɗaya suke, hakan yasa take fuskantar
ƙalubale daga ɓangaren dangin miji, tsangwamar da suke masa ta shafeta.
Ko a unguwa ana jinjina tarbiyyar Su Nasir, saboda suna da matuƙar nutsuwa, ko
tarin abokan nam basu dasu, tare suke komai nasu, kansu a matuƙar haɗe yake, Nasir
yana girmama Yusuf a matsayinsa na wansa, shi kuma Yusuf yana matuƙar ƙaunar Nasir
da tausayinsa a matsayinsa na ƙaninsa, hakan ne yasa duk inda me sunan Yusuf yake
Alhaji Nasir Daula yake girmama shi sosai.
Lokacin da suka fara tasowa, Nasir ya fara yin abokai, saboda yafi yayansa baki
da son mutane, mahaifinsu yana da rufin Asiri daidai gwargwado basu nemi komai sun
rasa ba.
Sun fara kawo ƙarfi Allah ya karɓi rayuwar mahaifinsu, sunji mutuwar nan sosai, sun
daɗe suma alhinin mutuwar nan, da ran mahaifinnasu dama dangimsa ba damuwa sukayi
da su ba, balle yanzu ya bar duniya, dan haka suka sake yin watsi dasu, suka ci
gaba da faɗi tashi suda mahaifiyarsu.
A wannan ƙadamin wasu mutane suka tare a kusa da gidansu Nasir, sedai mutanen ba
masu ƙarfi bane ba, Nasir yana matuƙar tausayin Yaran gidan, saboda rashin gata, a
haka ya janyo ɗaya daga cikin 'yan gidan ya zama abokinsa, Yaron sunan kakanshi ne
dashi, shine ake masa inkiya da irin inkiyar kakan nasa wato Bulama, kullum tare
suke cin Abinci da Bulama, suje yawon balla tare da sauransu.
Sedai halayar Bulama da Nasir tasha bamban, Bulama baya shakkar iyayensa, ga mugun
rashin ji da yake fama, dan haka Yusuf ya tsani Bulama, yayi yayi ya raba Nasir da
Bulama abu ya gagara.
Yusuf yana jami'a, Nasir yana babbar sakandire Allah ya karɓi rayuwar mahaifiyarsu,
Sunyi kuka sosai, saboda ita kaɗai ta rage musu, wadda suke kalla suji daɗi, saboda
dangin mahaifinsu dasu da babu duk ɗaya, ga mahaifiyarsu itama ba wani gata ne da
ita ba, dan haka koda aka share makoki babu wanda yabi ta kansu, cewar dangin
mahaifinsu ai su ɗin mazane zasu iya kula da kansu, base am ɗau ɗawainiyar su ba.
Nan Nasir ya ƙullaci dangin mahaifinsu, dama harda sakacinsu yayi sanadiyyar
rasuwar mahaifiyarsu, tana rashin lafiya sun yi sintiri gidan ƙanin mahaifinsu ya
basu kuɗi su kaita Asibiti amma ya hana, suka dinga 'yan uwan uban akan su temaka
musu amma suka ƙi.
Haka suka tattara ɗan abun hannunsu, suka kaita Asibiti aka rubuta musu Allurara
dubu saba' in, suna cikin taradaddim yadda zasu samu kuɗin rai yayi halimsa.
Tunda Allah yayi mata rasuwa, Nasir be ƙara takawa inda dangin mahaifinsu suke ba,
haka Yusuf ya cigaba da buga buga da faɗi tashi, ya sai musu Abinci ya biya musu
kuɗin makaranta, amma duk da haka Nasir be rabu da Bulama ba kuma be dena tamaka
masa ba.
A haka da ƙyar Yusuf ya kammala karatunsa, ya dinga faɗi tashi neman sana'a, ya
samu aikin banki da ƙyar ta hannun wani ɗan siyasa.
Cikin ikon Allah, Allah ya rufa masa Asiri har yayi Aure, dukda Nasir ya kawo
ƙarfin daze fita ya nema, amma Yusuf be fasa ɗawainiya dashi ba, hatta sabulun daze
wanka Yusuf seya siya ya bashi, akayi sa'a Nasir yana ɗasawa da matar Yayansa
sosai, saboda bashi da ƙyuya, duk aikin data sashi yi mata yake, dukda kasancewarsa
ya zama saurayi, wasu lokutan har zama suke suyi hira tare, ko suyi shawara.
Ɗan zuwan da suke gidan, haka Bulama yake mata 'yan sace sace, haka take shiru
saboda Nasir, Yayan Nasir ya sha dunƙule kuɗi masu kauri ya bawa Nasir da nufin
yayi sana' a, amma se Bualama ya ziga shi, su kewaye kuɗin suyi bushasha, aita
kashewa 'yan matan Bulama, su sai kaya su sai kayan Ball ayi shagali kuɗi su ƙare,
da Yusuf yaga abunda yake faruwa seya koma yake kafawa Nasir sana' a, nan ma Bulama
ya bishi su ragargaje komai.
A hankali Nasir ya fara yiwa kansa faɗa, yaga asarar da yakewa Yayansa tayi yawa,
gashi be taɓa nuna masa ya gaji ba, sedai yayi fushi yace baze sake bashi jari ba
se yayi hankali.
Ya koma ya sameshi yace ya bashi jari, in Allah ya yarda ze alkinta, Amma Yusuf
yace baze bashi suje su haɗu da sakarkarun abokansa su cinye ba se yayi hankali,
haka yaita sintiri amma ya hana shi.
Da yaga hakan yaƙi seya koma ta gurin matar Yusuf wato Nadiya, watarana yaje ya
sameta a falo, bayan sun gaisa yace "Anty taimako nake nema fa"
Tace "temakon mefa?"
"Anty Yaya ya hanani Jari, nayi nayi amma yace se nayi hankali, dan Allah kisa
baki, nasam yadda yake sonki da kince a bani ta zauna"
Nadiya tayi murmushi tace "ai kai lamarin naka ne se a hankali, se an baka kaje ku
kewaye ku cinye kai da abokai, kamar baka da wayo"
"Nidai dan Allah kisa baki ya bani, Allah bazan ɓafnatar ba zan tattala"
Nadiya tace "shikenan, rashin sana'a ga matashi bata da daɗi, bari ya shigo gidan
inga ya za'ayi"
Nasir yace "Yawwa Antyna ta kaina, Allah yasaka da alkhairi, ya kawo 'yan biyu sau
biyu" (da yake tunda akayi auren bata samu rabo ba"
Tai murmushi ta ce "Ameen ya Allah Nasir, Allah yasa ya baka jarin nan, daga nan ka
zama babbn done"
"Ameen Anty, bari in ɗau carbi inta masa lazimi kafin ya dawo"
Tai dariya tace "idan ma be baka ba, ina sa ran a kawomin kuɗin gonata, se in baka"
Suna cikin hirar ne sega Yusuf ya dawo, Yusuf yace " Ashe kana nan, na biya ta can
gidan in baka takalmin dana siyo maka amma baka nan"
Nadiya tace "ka zauna kaci Abinci tukuna, idan kaci se in gaya maka saƙon nasa"
Haka akayi, tare ma sukaci Abincin shida Nasir, bayan sun kammala Yusuf yace "to
Uwargida, ina jinki tunda naga kun haɗa kai, nasan wataƙila wani abu akeso na bayar
ko inyi"
Dariya suka yi, Nadiya tace "Yawwa ranka ya daɗe, kaga yanzu kamar Nasir ai
bekamata ace seka sai masa takalmin sawa ba, kamata yayi ace duk wannan abubuwan
shiyakewa kansa, dan haka yazo neman alfarma dan Allah a temaka masa da jari"
Yusuf yace "An hanashin baza'a bayar ba, in kuma bashi yake shida wancam yaron mara
kunya su haɗu su cinye, gara ko meye yazo in sai masa, idan ya ƙara hankali se in
bashi jarin"
Nasir yace "dan Allah Yaya, Allah nayi hankali zan tattala"
Yusuf yace "Anƙi ɗin, ai tun rannan nace bazan sake baka ba"
Nadiya tace "A dai yi haƙuri ranka ya daɗe, Insha Allah baze sake ba"
Yusuf yace "to naji, tunda haɗe mun kai zakuyi, naji zan bashi jari, amma rance zan
bashi"
"shikenan tunda bakwa so, ai bazan sake bashi kuɗi yaje yaci a banza ba, tunda
besan zafinsu ba"
Nasir yace "Anty na yadda, Insha Allah zan dawo masa dasj, nidai a bani jarin"
Nadiya tace "dan Allah kace ya dawo maka da rabi, ya riƙe rabi mana"
Yusuf yace "Nifa in bakwaso kuɗina sun huta, nasan abunda zanyi dasu"
Yusuf yace "waini wace sana'ar ma zakiyi ne? Kuma nawa kake buƙata?"
Nasir yace "Yaya sarƙoƙi nake son in dinga siyarwa, zan kama shago a kasuwa sannan
in zuba kayan, ance dubu ɗari biyar zasu isheni".
Zaro ido Yusuf yayi yace "dubu dari biyar? Kana da hankali kuwa?"
Nadiya tace "kana dasu fa, kafi ƙarfinsu dan Allah ka bashi"
"Gaskiya bazan bashi ba, zan dai bashi ɗari uku yaje ya nemi sauran, ɗari ukunma
bashi"
Nadiya tace "Nasir karka damu, idan aka kawomin kuɗina, kazo in baka sauran, inaji
a jikina wannan sana'ar ds zaka fara itace silar arzikinka, ka zama hamshaƙin
Attajiri, wanda ze tara Daula ta ban mamaki"
Nasir ya washe baki yace "Allah yasa Antyna ta kaina, da duk sati sena kaiki
Makka, shi kuwa yaya se shekara shekara zan dinga kai shi"
Yusuf yace "kar Allah yasa ka kainin, bana insha Allah zan tafi ai, kuma kema ban
yadda ki bashi kuɗi kyauta ba, rance zaki bashi kuma tare zamu je da kaina a kama
shagon"
Har zata yi magana, ya dakatar da ita, ya hanta magana, Nasir yaita godiya sannan
ya tafi.
Bayan tafiyar sa Yusuf yace "Nadiya, ina jin daɗin yadda kike nunawa ɗan uwana
ƙauna kamar ɗan uwanki, ni kaina ina tunanin wace sana'a zan sama mishi, saboda
nasan bayan raina babu wanda ze iya ɗawainiya dashi kamar yadda nakeyi, ba ƙinsa
nake da nace rance na bashi ba, hakan ne zesa ya maida ya tattala abunda aka bashi
"
Nadiya tace " Shikenan tunda haka kace, Amma kana min kyautatawar dako nawa nakwa
'yan uwanka alheri dashi ban faɗi ba, amma tunda kace haka shikenan "
Bayan kwana bakwai, aka tattara kuɗi akaje aka kamawa Nasir shago, aka zuba kayan
sarƙoƙi kala kala, Nasir ya maida kai sosai a tafi da shagon nan, duk yadda Bulama
yaso a kassara shagon Nasir yaƙi, sedai wataran Bulama yazo ya taya shi zama koya
yayi masa shara, shi kuma ya biya shi, amma a hakan Bulama yana taɓa ƙuruciyar ɓera
wato sata.
Allah yasawa kasuwancin nasa albarka, nan da nan kasuwanci ya kankama, idan kuɗi
suna nema su yanke masa idan ya zaga gurin Matar yayansa seta ƙara masa kuɗi, a
hankali ya dinga sabawa da mutane, idan yaji labarin wani kasuwancin seya ɗibi kuɗi
ya jarraba, shine ya buga nan ya buga can.
Wataran aci riba, wata ran a faɗi, Yusuf yana yi yana monitoring ɗin ƙanin nasa,
idan ya tambayeshi yaushe zan dawo maka da kuɗin se yace 'ba yanzu ba, idan lokacin
karɓa yayi zan karɓa'
Haka ya dinga faɗi tashi, da Nadiya ta ganshi seta fara tsokanarsa da seka gina
Daula me ban mammaki babban don, a haka abokansa da maƙota suka fara kiransa da
Daula kawai.
Ana nan wani hamshaƙin attajiri a kusa da gidan Yusuf, yaje ya auro wata balarabiya
'yar maroco, akayi shagali sosai' yan uwanta na can maroco suka zo Nigeria, akayi
shagalin biki sosai.
Bayan wani lokaci balarabiyar nan ta haihu, aka kawo mata wata Yarinya a cikin
danginta, ta zauna tare da ita saboda ta dinga tayata raino, kafin jaririn yayi
ƙwari.
Nasir ya kan shiga gidan mutumin, da yake akwai babban ɗan mutumin me suna Ahmad a
gidan, suna gaisawa sosai da Nasir, shi ya bashi shawarar fara sana'ar kayan
sarƙoƙi na mata, dan haka Nasir yana shiga gidan sosai, dan ya saba da ita Amaryar
wannan mutumin Islam wato balarabiyar maroco.
Duk lokacin da Nasir ya shiga gidan sukan haɗu da wannan balarabiyar Yarinyar me
suna Huda 'yar uwar Islam , yana ɗan jin larabci dan haka sukan gaisa, kokuma suyi
magana da turanci.
Huda bata da saurin sabo, amma ta saba da Nasir, ko fita ba tayi amma Saboda Nasir
har gidan Yusuf take shiga nemansa idan taga bata ganshi ba, saboda Nasir yana da
barkwanci, gashi ya iya hira dan haka yakan ɗebe mata kewa sosai.
A hankali mutuncinsu ya rikiɗe zuwa Soyayya, sun shaƙu da juna sosai, da farko
lokacin da tazo Nigeria cewa tayi ba zata fi sati biyu ba zata koma ƙasarsu, Islam
na ta fama da ita ta zauna amma fafur taƙi, amma saboda Nasir se gashi ta shafe
watanni uku ba tare da ta koma maroco ba.
Ya zamana Nasir ya dena karɓar Abinci a gidan yayansa Yusuf, saboda Huda zata ajiye
masa idan an dafa a gidansu, idan yaje ta kawo masa su zauna yana ci suna hira.
Kasancewar Nasir mutumin kirki ne daga shi har yayansa, yasa duk mutanen unguwa sun
sanshi, kuma shi wannan Attajiri mijin islam yasan Nasir sosai, kuma yasan yana
zuwa gidansa, shi ya fara tsokanarsa yana cewa
"Nifa Malam Nasiru ban gane wannan mutuncin haka tsakaninka da Huda ba, ko kaima
marocon zaka ne?"
Tun suna ɓoye ɓoye harta bayyana ga mutane, Nasir da Huda soyayya sukeyi, wasu
lokutan idan aka aiketa shiyake rakata, saboda wani abun bata sanshi da hausa ba,
kyautar sarƙoƙi kuwa da yake bata babu adadi.
Wataran haka zata shiga gidan Yayan Nasir, gurin Nadiya ta wuni a gurinta suna
hira, a haka har take sedai sam Allah be haɗa jinin Huda da Bulama ba, da tana
ɓoyewa, harta kasa ɓoyewar take gayawa Nasir ita bata san ganinsa da wannan
Bulaman.
Nasir yace "Hudallahi Bulama abokina ne, kuma ɗan uwanane ban san me yasa bakwa
shiri ba"
Huda tace "Nifa ba hanaku hulɗa nayi ba, amma idan zakazo gidan nan ka dena zuwa
dashi, yaita faman kallona, ni kuma bana so"
Nasir yace "ki kwantar da hankalinki, ba abunda ze miki, dan dai kallo ai ba cinye
ki zeba"
Maimakon Huda tayi magana, se tayi shiru idonta ya cika da ƙwalla, Islam tace
"kuka kuma? Me yasa ki kuka?"
Islam tace "meyasa, keda da ƙyar aka lallaɓoki kika yadda kika zauna"
Huda ta share hawayenta tace "bana son in koma saboda... Sekuma tayi shiru
Huda ta jinjina mata kai, Islam tace " Amma Huda kin san bazasu yadda su aura miki
shiba? Kin san irin tashin da mukayi a gidanmu, nima dan Alhaji yana da kuɗi ne
suka yadda suka Auramin shi, amma kinga Nasir bashi da kuɗin daze iya biya ya
Aureki, kuma a can ga Habibullah sun masa Alƙawarin bashi Aurenki"
Cikin kuka Huda tace "ni bana son Habib, Nasir nake so, dan Allah Ukty kisa baki,
wallahi ina son Nasir sosai"
Islam tace "kidena kuka ukty, Insha Allah zan tayaki da Addu'a amma nasan ko zaki
Auri Nasir zaki sha wuya"
Daga maroco musamman aka taso ƙanin mahaifin su Huda yazo ya tafi da ita, tayi kuka
sosai saboda zata rabu da Nasir, shi kansa Nasir ya shiga damuwa sosai, ranar da
zasuyi Sallama Huda ta dinga kuka, Nasir kamar ze hauka.
Dan bayan sun rabu ɗaki ya koma yaje yaita nasa kukan shima, tunda Huda ta koma ya
dena zuwa gidan wansa ko karɓar Abinci, ya zamana kasuwa ma ba kullum yake zuwa ba,
sedai wataran Bulama yaje ya buɗe shagon ya zauna yayi wadaƙarsa san ransa da kuɗi.
Mussaman Yusuf ya aika aka kira masa Nasir, Yusuf yace "Wato Nasir saboda wannan
yarinyar kake nema ka kashe kanka ko? Ko Abinci ka dena zuwa ci, kai yanzu ko Auren
ne ina kaga kuɗin da zaka iya auran balarabiyar yarinyar nan? Shikansa maƙocin nawa
bakaji kuɗin da ya kashe gurin auro yarta ba, me muke dashi Nasir? Kayi haƙuri ka
cigaba da walwalarka, nan gaba Insha Allah ni zan maka Auren ma da kaina, a samo
maka 'yar baƙa me kyau ka Aura ko ƙanina"
Zumɓura baki Nasir yayi, ya haɗe rai ƙwalla ta taru a idonsa. Nadiya tace "Shifa
farar fatar nan yake so da dogon gashi ko Nasir?"
Girgiza kai Nasir yayi yace "Ni wallahi kawai sonta nake, ni bana son wata inba
Huda ba"
Haushi ne ya kama Yusuf, da ze masa Masifa, amma ganin Nasir yana kuka yasan lallai
ya kamu da yawa.
Se ya koma rarrashinsa, dayi masa Nasiha da ƙyar da rarrashi da Addu'a sannan Nasir
ya cigaba da zuwa shagonsa, badan ya cire Huda daga ransa ba.
Ɓangaren Huda ma tunda ta koma maroco suka kasa gane kanta, bata walwala Sam,
sannan taƙi saurarar wanda akeso a Aura matan, sam baya gabanta kullum cikin
tunanin Nasir take da barkwancinsa, gashi lokacin waya bata yawaita a hannun mutane
ba, balle ta dinga kiransa suna magana.
Aka fara shirye shiryen bikin Huda da Habib, amma Huda sam bata saurarensa se aikin
kuka, gaba ɗaya tabi ta rame suka kasa gane kanta.
Islam ta shirya taje ganin gida, domin ayi shirye shiryen biki da ita, sedai me
ganin 'yar uwatta ya razana ta gaba ɗaya ta rame, bata walwala se kuka.
Gashi iyayensu sun rasu, a hannun wan mahaifinsu suke, shi kuma mutum ne me azabar
tsauri kuma kaifi ɗayane baya magana biyu, dan duk wannan botsarewar da Huda take
akan Auren Habib be dameshi ba sam, shirin Aurar da ita kawai yake.
Seda Islam taje ta gaya masa aiga Halinda Huda take ciki, akwai wanda take so a
Nigeria.
Nan yai tsalle ya dire yace baze taɓa yuwuwa ba, in dai yana nan a raye ba zata
Auri wani ba idan ba Habib ba.
Da jin wannan batu hankalin Huda ya ƙara tashi, duk 'ya' yan wan mahaifinsu ba
wanda yakewa Auren dole, sesu, yanzun ma yana son ya aurawa Habib Huda ne saboda
yana da kuɗi kuma yana ci.
Mijin Islam har maroco yaje, akan maganar Huda dan Islam tana ta kuka ganin tilon
ƙanwarta na neman rasa ranta saboda baƙin cikin auren dole daza'ayi mata.
Alhaji Abubakar yasa baki akan su ƙyale Huda da Auren nan, ko basu Aurawa Nasir ba
su ƙyaleta tunda bata son Auren amma suka ƙi, har yayi barazanar ze ɗauke Huda kuma
ze haɗa wan mahaifinsu da hukuma akan abunda yake yunƙurin yi.
Ɓangaren Nasir ma, tunda yaji halin da Huda take ciki ya shiga matsananciyar
damuwa, har kwanciya yayi a Asibiti, damuwa tayi masa yawa gashi kullum ƙara son
Huda yake a cikin zuciyarsa, tun Yusuf yana jin haushin ƙanin nasa har ya dawo yana
tausaya masa, saboda ya lura kamar jarabta ce wannan Soyayyar tasa da Huda.
Hatta dangin su Huda da 'yan uwa suma suka sako Wan mahaifin Su Huda a gaba akan ya
aura mata wanda takeso taje can ta ƙarata, indai mazan ƙabilar hausawa ne da
ƙafarta zata dawo, itama Yayarta dan tana Auren me kuɗi ne, shiyasa ya iya riƙeta,
itama babu tabbacin baza' a sakota nan kusa ba, dama me kuɗi itama ta samo da ɗan
sauƙi amma ta ɗakko talaka, kota aureshi Auren ba inda zashi, ita dai Huda tace
taji ta gani taje ƙasar Hausawa ta zauna dasu ita ba taga wani aibunsu ba, duk
miyagun halayen da ake faɗa bata gani ba, kuma suna zaune da iyalansu lafiya.
Ganin baki yayi yawa yasa wan mahaifinta yace "da kuɗin Auren Huda, da kayan Aure
da sadaki da komai da komai ya yanke dirham dubu ɗari takwas"
Yusuf yana gida, akazo ana sallama dashi, ya fito dan ganin me sallamar hana zuwa
yaga mijin Islam ne wato Alhaji Abubakar, ya fito suka gaisa da juna, Alhaji
Abubakar yace "wato dama magana ce nake tafe da ita akan ɗan uwanka Nasir, naje
maroco ƙasar su matata, yarinyar nan Huda tama cikin matsanancin hali, ɗan uwan
mahaifinta ma shirin yi mata Auren dole, mun kai ruwa rana sosai dashi, dan haka
yace idan Nasir ya shirya nan da sati biyu ya kai kuɗin Aure, komai da komai dirham
dubu ɗari takwas "
Alhaji Abubakar ya ɗanyi shiru sannan yace " Naira miliyan uku da dubu ɗari shida
kenan a kuɗinmu na nan"
Shiru Yusuf yayi, ya yakice gumi sannan yace "innalillahi wa inna ialaihi raji'un,
to zamuje muyi shawara inga inda yadda zamuyi, amma bamu da shi a ɗaka balle a
waje, ni kaina yadda gaba ɗaya Nasir ya sukurkuce abun yana damuna, amma bakomai
nagode sosai da ƙoƙarinka nagode"
Alhaji Abubakar yace "karka damu, ai ɗa na kowane kuma Nasir yaron kirkine
ubangiji Allah ya yassare muku"
Sukayi Sallama ya tafi, jiki a sanyaye Yusuf ya shiga cikin gida, gaba ɗaya kamar
an zare masa laka, Nadiya ta kalle shi tace "ranka ya daɗe lafiya kuwa?"
Ya samu guri ya zauna yace "Nadiya akwai matsala, baban Yarinyar nan Huda yace nan
da sati biyu mu kai miliyan uku da dubu ɗari shida sannan a bashi ita, nikuma kin
san bani ds ita, gashi ina tsoron wani ciwo ya kama min Nasir, gaba ɗaya yasa kansa
a damuwa, duka abunda zan tsawatarwa Nasir ince ya bari yaƙi hanuwa to tabbas
wannan jarrabawa ce a gareshi, Nadiya na rasa abunyi ina zan samu wannan kuɗin
haka? "
Nadiya tace " yanzu meye abunyi, nikaina na fuskanci idan ba'a ɗau matakin daya
dace ba, akwai yuwuwar ya faɗa mawuyacin hali "
Yusuf yace " shine abunda nake tsoro, bazan iya fitowa in nunawa Nasir gazawa taba
gurin sama masa abunda yakeso ba, kinga kwanan nan kuɗin hannuna na tatike aka buɗe
masa shago, idan aka saki shagon aka karɓi kuɗin idan yayi aure dame ze Riƙeta? "
Nadiya tace "ai kama bar batun a saki shagon nan, muyi tunanin wata mafitar"
Yusuf yace "bazan gaya masa halin da ake ciki ba, inaga zan rubutawa bankinmu su
bani aron kuɗin, idan yaso a dinga cirewa a albashina, akai musu kamar yadda Nasir
ne kaɗai ɗan uwana itama Islam Huda ce kaɗai 'yar uwatta, idan muka temakesu kinga
mun ceci rayuka biyu kenan, amma kiyi shiru da bakinki karki gaya masa Nadiya "
Nadiya tace " Insha Allah bazan gaya masa ba, amma asaka gidana na cikin gari a
kasuwa, idan aka siyar semu ragewa banki kuɗinsu ko? "
Yusuf yace" A'a Nadiya, ɗawainiyar da kike da Yusuf aita isa haka, ki bari kawai '
Nadiya ta haɗe rai tace "to ainima Nasir ɗan uwanane, tunda muna zaune da kai kana
kula dani, meyasa zan bar ɗan uwanka cikin damuwa?"
Yusuf yace "Shikenan, ki bari in dawo se mucigaba da maganar, bari inje inyi sallar
isha' i in dawo"
Yai maganar yana miƙewa, sedai yana fitowa ya ci karo da Nasir a tsaye a ƙofar
ɗakin......
LITTAFIN KUƊI NE, DAN ALLAH KI SIYA KAFIN KI KARANTA BA DANNI BA DAN ALLAH, LITTAFI
NA ƊAYA KYAUTA NE WANNAN NA SIYARWA NE
NORMAL GROUP ₦300
VIP ₦500 NE KITURA TA WANNAN ACCOUNT ƊIN
0009450228
JA'IZ BANK
AISHA ADAM
SE A TURA SHEDAR BIYA TA WANNAN LAMBAR
07063065680
11/14/21, 6:09 PM - Ummee Musa: LITTAFIN KUƊI NE, DAN ALLAH KI SIYA KAFIN KI
KARANTA BA DANNI BA DAN ALLAH, LITTAFI NA ƊAYA KYAUTA NE WANNAN NA SIYARWA NE
NORMAL GROUP ₦300
VIP ₦500 NE KITURA TA WANNAN ACCOUNT ƊIN
0009450228
JA'IZ BANK
AISHA ADAM
SE A TURA SHEDAR BIYA TA WANNAN LAMBAR
07063065680
64_65
Nasir yace "Yayana, tun ɗazu nake gurin nan naji duk hirar da kuke da Anty, sedai
bazan bari ka cigaba da wahalar da kanka saboda niba, akwai buƙatar kaima ka gina
rayuwar ka data iyalinka ni dai ka ƙyaleni kawai, na haƙura da Huda"
Yusuf yace "ba shawararka nake nema ba, a gurin Allah nake nema, fita ka bani guri"
"Yayana, ka saurareni na haƙura da zancen Huda wallahi, bazan sake zancenta bama"
Yusuf be saurari Nasir ba yai waje abunsa, Nasir ya ƙarasa shiga ya tarar da Nadiya
a zaune ya nemi guri ya zauna yace "Anty dan Allah kisa baki, kar Yaya ya ciwo
bashi saboda ni, ki gaya masa na haƙura da zancen Hudan nan"
"ba batun in zuba ido bane rayuwarku da cutu saboda ni, dan Allah Anty ki gaya masa
na haƙura da Huda"
Nasir yace "haba Bulama, ya zakace haka, kasan yadda nake son Huda kuwa?"
Bulama yace "eh mana, kai banda abun soyayya meya haɗo biri da gada dama, ina kai
ina Auren balarabiya ko dan kaga kana juya kuɗi a hannunka, malam ka nemi wata me
ɗan rangwamen gata in auren kake so kayi"
Nasir yace "ni bama wannan ba Bulama, kasan Yaya Nasir wai bashi ze ciyo a kai
kuɗin Auren Huda, sun yanaka mana kuɗi kusan million huɗu"
"Eh mana, sunce zasu bani, amma baffanta yace kuɗin Auren million huɗu, na rasa
yadda zanyi ne, ga Yayana wai ze ciyo bashi akai kuɗin auren"
"bashi kuma? Kawai ka bari idan ya karɓo bashin, kazo muje 'yan mata se wadda kake
so, mezesa ka wahalar da kanka akan wannan balarabiyar, hasken fatane fa kawai da
gashin'
Nasir yace " A'a gaskiya ni Huda nake sl, kuma bazan ma bari ya karɓo bashin nan ba
gaskiya"
Bulama yace "kai meyasa baka da wayo, wallahi garin nan akwa tsula tsulan 'yan
mata, duk abunda kake so zasuyi maka indai da uwar kuɗin ka"
Tsaki Nasir yayi, ya tashi ya bar gurin saboda kunna shi da Bulama yayi.
Be zame ko ina ba se gidan Alhaji Abubakar, ya samu Ahmad ɗan gidan Alhaji
Abubakar, suka zauna suka gaisa Ahmad yace "Angon Huda ya akayine? Naga baka
walwala sam"
"Ahmad ina zanyi wata walwala? An yanka min sadaki fiye da tunani, gashi gaba ɗaya
jarin da ribar da nake juyawa basu fi million ɗaya ba, ga Yaya Yusuf duk ya damu,
har yana batun ze karɓi loan, gaba ɗaya na damu nina ma haƙura gaba ɗaya, amma yaƙi
saurarata"
Ahmad yace "Nasir, ita kanta Huda tana buƙatar taimako, idan ka aureta zata samu
sassauci, Allah baze hanaka yadda zakayi ba, Insha Allah, in dai matarka ce seka
Aureta"
Nasir yace "Ni dai na haƙura na fidda rai, nasan ina matuƙar son Huda, amma bani
da halin Aurenta"
"Ka dena faɗar haka, Insha Allah za'a samo kuɗin nan, kuma zaka auri Huda"
Yusuf ya dinga faɗuwa yana tashi, ya fasa karɓar bashin banki saboda haramcin
hakan, Amma ya saida abubuwansa ya tattara kuɗin hannunsa da ƙyar sukayi million
ɗaya da rabi, Ahmad ya bawa Nasir gudunmuwar dubu ɗari biyu, shima ya tattara ɗan
abunda yake dashi, amma kuɗi ko million biyu basu yi ba, saura kwana uku kwanakin
su cika, Alhaji Abubakar yazo ya samu Yayan Nasir yace "Malam Yusuf ya ake ciki
ne? Kun haɗa kuɗin kuwa?"
Yusuf yace "wallahi kuɗin nan basu kai ba, muna ta faɗi tashine, dan Allah inda
hali a basu haƙuri su ɗan ƙaramana lokaci, dan Allah karsu bawa wani, Insha Allah
zamu cika a samu Nasir ya aureta"
Ajiyar zuciya Alhaji Abubakar yayi yace "nikam wani irin so kakewa Nasir haka?"
Yusuf yayi murmushi yace "Nasir ne kaɗai ya ragemin, kuma kaga yarone ƙarami ba
wani babba bane, kuma maraya ne, yana buƙatar a jashi a jiki, kuma iyayenmu sun
mana wasiyya sosai akan muso juna, inyi haƙuri dashi in kula dashi, kaga dole in
kula da marayana"
Alhaji Abubakar yace "Masha Allah, gaskiya na daɗe banga managarcin mutum kamarka
ba Yusuf, Allah ya biyaka, kawo abunda ya samun, inje musu dashi inga ya zamuyi"
Yusuf ya dinga murna, kamar Alhaji Abubakar yace an bawa ƙaninsa Hudan, yaje ya
kawo masa kuɗin, ya duba ya ƙirga su sannan yace "zanje can marocon, zanga yadda
zamuyi, amma da ina da 'ya ko ƙanwa gaskiya dana baka, dan na yaba da amanarka da
haƙuri da ɗan uwanka'
Yusuf yayi murmushi yace " rufamin Asiri kar Uwargida ta jimu, kasa ta haɗemin rai
yau"
Sam Nasir be san me ake ciki ba, Yusuf yana ta cigaba da fafutuka, yana haɗawa da
Addu'a.
Tafiyar Alhaji Abubakar da kwana biyar, ya dawo yai sallama da Yusuf ya sanar masa
da an basu Huda.
Yusuf yai godiya kamar ze duƙawa Alhaji Abubakar, har seda yasa Alhaji Abubakar
yaji kunya.
Shikam Nasir ya dawo daga kasuwa, yayi sallar isha'i yaje yayi kwanciyarsa, ko
abinci be nema ba, babu abunda yake banda begen Huda.
Nasir be gane me yayansa yake nufi ba, yayi zaton zolayarsa kawai yake.
Yusuf yace "gobe in Allah ya kaimu, masu aiki zasuzo suyi gyare gyare a gidan nan,
ka tattare kayanka ka koma shagon gidana"
Yusuf yace "Rufamin Asiri, inani ina ƙara Aure, Nadiyata ta isheni matar rufin
Asiri, 'yar aljanna insha Allah, har ƙiyama muna tare da ita"
"Hudanka mana"
" Sun baka, nan da sati biyu insha Allah za' a ɗaura Aure"
Ai ba shiri Nasir ya rungume Yusuf ya fashe da kuka yace "Yayana, wallahi na rasa
me zance ma gaba ɗaya, yadda kake ƙoƙarin farantamin rai, Allah ya sadaka da
Annabin rahama, yasaka a aljanna ma ɗaukakiya"
Yusuf yace 'Ameen ya Allah, tare da kai ƙanina, farincikin ka shine nawa, nima
nasan idan nine a halin da kake ciki, ba zaka zuba ido ba, ina me maka nasiha daka
kula musu da' ya, ko bayan ba raina ka tuna gwagwarmayar da muka sha kafin ka
sameta, ka nunawa duniya mazan hausawa Jarumai ne, kuma sun iya riƙe mace su bata
kulawa "
Nasir yace " karka damu Yayana, Insha Allah zanyi iya ƙoƙarina inga na riƙe Huda
da Amana"
Haka Yusuf ya ci gaba da yi masa nasiha, da jan kunne akan sha'anin Aure.
Nan da nan magana ta cika unguwa Nasir ze auri Huda, wani abun takaici dangin
mahaifinsu sukace bada yawunsu ba, ba zasu yi jagora aje a Aurowa Nasir balarabiya
ba, babu hannunsu a ciki, abun nan ya ƙara tsayawa Nasir a rai, ƙiri ƙiri se bare
ne yayi jagorancin karɓa masa Auren wato Alhaji Abubakar.
Haka suka tafi maroco, da Alhaji Abubakar, da ɗansa Ahmad, da Yusuf da Nasir da
wasu Abokan Alhaji Abubakar suka tafi maroco, Nasir yaso a tafi da Bulama, amma
Yusuf ya hana yace ba zasu je da shi ba.
Huda ji take kamar ba itaba, lokacin da aka faɗa mata kuɗin da aka yankewa Nasir ta
fidda rai da Aurensa, saboda tasan bashi da wannan kuɗin, ta fidda rai gaba ɗaya ta
haƙura, se rashin lafiya take tana rama, babu zato babu tsammani yayarta Islam tazo
mata da zancen ai megidanta ya zo da kuɗin Auren Nasir daga Nigeria, Alhaji
Abubakar ne ya cika kuɗin, amma babu wanda ya gayawa hakan.
Baffansu Huda be taɓa tsammanin za'a iya biyan kuɗin nan ba, duba da yadda aka gaya
masa Nasir marayane, kuma bashi da ƙarfi, ganin haka yasa yace tunda ta dage se
bahaushe, bahaushen ma talaka ta dage ita da 'yar uwarta to suje, gasu nan ga
bahaushe, kuma ya cire hannunsa daga kansu, kome ze faru ta nemi' yar uwatta da
mijinta da suka dage akan se anyi wannan Auren, karsu ƙara nemansa.
Huda ta wani fannin tayi farinciki, yayinda gefe ɗaya kuma hankalinta a tashe, jin
cewar jigon da suke tunƙaho da shi yace bashi basu.
Alhaji Abubakar kuma yace yaji ya gani, shi har Abada Aure albarkarsa ake nema ba
wai tarin dukiya ba, idan da rabo a gaba Nasir zeyi Arziki, kuma in dai Huda ce
kome ze faru ze riƙeta, balle babu abunda ze faru se alkhairi.
Shikuma Habib yace se an biya shi duk abunda ya kashewa Huda, alhalin duk abunda
Ake bayarwar ba bata akeyi ba, wanima bata san an bayar ɗinba.
Da kuɗin Auren gurin Nasir, aka tattara abunda ya samu aka biya Habib.
Kamar wasa ranar wata juma'a, bayan sallar juma'a, a masallacin Kairaouine, suka
ɗanyi shagalinsu a can, da suka tashi dawowa Nigeria, Alhaji Abubakar ya kasa ya
tsare ya karɓi sadakin Huda a hannun ƙanin mahaifinta, sauran 'yan uwa ma suka
tattara mata sha tara ta arziki, wani aka bata wani kuma aka ƙwace, suka taho da
Amarya Nigeria.
'yan unguwar su Nasir, suka haɗa kuɗi suka shirya musu walima, wani ya bada hall,
wani ya bada buhun shinkafa, gaba ɗaya kai baka ce Auren maraya ne ba, abokansu
suka dinga basu gudunmuwar kuɗi wasu kaya, saboda duk wanda yasan Nasir da Yusuf
yasan iyayensu, yasan mutane ne masu karamci da biyayya.
A lokacin maƙoci yana ganin ya isa da ɗan maƙocinsa, ana zaune lafiya kamar 'yan
uwa dan haka Nasir yayi mamakin yadda bare sukayi musu wannan karar amma dangin
mahaifinsu suja kasa yi musu.
Duk Wanda yaji yadda akayi auren yasan kawai rabone, dama Allah ya rubuta Huda
rabon Nasir ce.
Huda ta tare a gidanta, musamman Yusuf yasa Nasir a gaba sukaje gaban Alhaji
Abubakar sukayi masa godiya dashi da Islma amaryarsa.
Nasir baze taɓa manta alherin Ahmad da mahaifinsa ba, da sauran abokansa, amma
Bulama babu abunda yayi masa, sema wadaƙa da sata daya dingayiwa Nasir a shago,
ganin hankalinsa ya koma kan Auren da zeyi.
Sam Bulama beso Nasir ya auri zuƙeƙiyar balarabiyar yarinya ba, kullum suna tare,
amma gaba ɗaya Nasir ya fishi sa'a a rayuwa.
Kuɗaɗen da Nasir ya samu na gudunmuwa, da wanda aka bawa Yusuf ya ɗau abunda ze
ɗauka ya bawa Nasir sauran, ya sake zuba dukiyar a harkar kasuwancinsa, duk inda
yaji wata harkar samu seya ɗebi kuɗi ya tafi ya jarabba, duk lokacin da yayiwa
Yusuf zancen be bashi kuɗin daya ara masa, se yace ya ajiye masa ba yanzu ba, dan
gani yake idan ya karɓa hakan ze iya shafar kasuwancin ƙanin nasa, yana nan zaune
da matarsa lafiya, yana sonta tana son shi, Arziki se bunƙasa yake a hankali.
Ya ɗaukewa Yusuf ɗawainiyar siyan kayan Abincin gidansa, ya nuna masa baya so amma
be bari ba.
Huda ta ɗau kuɗinta na sadaki da abubuwan data samo a can ƙasarsu, ta bawa Nasir
tace ya haɗa, da tayi ta ajiyar kuɗin babu abunda zata yi dasu gara ya dinga juya
su, ya karɓa ya haɗa yana juyawa, a hankali ya dinga janyo abokansa cikin harkar
kasuwancin da yake yi, wasu suzo zuciyarsu ɗaya wasu kuma suzo da niyyar mugunta.
Allah maji roƙon bawa, katsam Nadiya matar Yusuf ta samu juna biyu bayan shafe
shekaru uku da Aure, Nasir kamar ya zuba ruwa a ƙasa ya sha, danma yafi yayansa
farinciki da wannan rabo, kullum zancensa Anty Nadiya idan kin haihu ni zanyi kaza.
Tun kafin bikin Nasir ta samu cikin, sam Nasir be saniba saboda yana cikin gararin
soyayya, Nadiya ta girni Huda, amma suna mutunci sosai suna ƙaunar juna, Duk inda
Ahmad yaji harkar kasuwanci da samu seya janyo Nasir, shikuma Nasir seya janyo
Bulama, wani abun Bulama ya ɓata lamarin.
A hankali Abu ya bunƙasa, sanadiyyar Ahmad Nasir ya fara fita ƙasashen ƙetare, yana
shigo da kayan ado na mata da turarruka, Ahmad ya koya masa yadda ake siyan Hannun
Jari a manyan kamfanunnuka.
Nan da nan Kuɗi suka fara zaunawa Nasir, duk kasuwancin daya shiga seya samu
alheri, shine nan shine can.
Ba ƙaramin daɗi Yusuf yaji ba, ganin dukda ƙarancin shekaru na Nasir amma ya fara
nutsuwa, dan a lokacin befi shekaru Ashirin da uku ba yayi Auren, a wannan lokacin
Auren wuri ba wani abu bane, indai yaro yana da sana'a.
Bulama ya tsani alaƙar Ahmad da Nasir sam, da yana zuwa gidan Nasir, amma fafur
Huda ta nuna bata son ya dinga zuwar mata gida.
Kafin Nasir yaje Saudiyya Yayansa ya fara biyawa yaje Umara, Yusuf yace Nasir ya
fara zuwa amma yaƙi yace shi yakeso ya tafi.
Ba ƙaramin daɗi da farinciki Yusuf yayi ba, dan badan a wancan lokacin ya haɗa
kuɗin Auren Nasir ba, da tuni yaje, aikuwa yayi farinciki sosai.
Bayan dawowar Yusuf daga Saudiyya, lokacin Wata huɗu da Aurensu Nasir, matar Yusuf
Nadiya ta haihu, Nasir kamar shi akayiwa haihuwar nan dan murna, kayan jariri kaf
dana me jego shiya siya, hatta abun hakika shine yayi.
Tunda akayi haihuwar nan, Huda take zuwa gidan mejegon nan, tana addu'ar itama
ubangiji Allah ya bata nata, dan tana matuƙar son yara.
Kwana bakwai da haihuwa akayi suna, yaron yaci sunan Mahaifinsu Nasir wato Umar
faruk, ganin Nasir ya fara ajiye abun arziki yasa, da sunan Umar dangin Mahaifinsu
suka zo suna.
Anci an sha dai dai gwargwado anyi shagalin sunan daba'a taɓa makamancinsa a
unguwar nan ba, nan Sunan Daula ya sake bin Nasir sosai, Suna nunawa junansu ƙauna
da sadaukarwa a tsakanin shi da ɗan uwansa.
Gaba ɗaya kusan Wuni Huda take yi a gidan Nadiya, ko taje gurin yayarta Islam taita
musu raino saboda son yara da take yi.
Kasuwancin Daula fa ya faɗaɗa, abun har mamaki yake bawa mutane, babban abunda yasa
mutane ke ƙara son Nasir shine hannunsa a sake yake, bashi da rowa sam, ga jan
yaransu da yake akan harkar sana'a, dukda cutar da suke masa wasu lokutan.
Yusuf yana yawan yi masa faɗa akan watsi da yayi da 'yan uwan mahaifinsa, hakan be
kamata ba, dan ko gaishe su baya zuwa yi.
Nadiya na fama da raino, ba damar zuwa Saudiyya, Nasir ya biyawa kansa da Huda suje
suyi Umara, lokacin nan Ahmad ma zashi, ana i gobe zasu tafi, suka je gidan Yayansa
Yusuf suyi musu sallama.
Suka zauna suka dinga hira kamar bazasu rabu ba, suka dinga tuna lokacin
ƙuruciyarsu da gwagwarmayar da suka yi ta rayuwa, da kuma wahalar maraici.
Har Huda ta dinga kuka, Yusuf yace "haba Huda, ai lokacin ya wuce ba gashi yanzu
se labari ba?"
Nadiya tace "itafa Huda ko a labari bata son taji abunda ze taɓa wannan mijin
nata, jinsa take kamar ranta, dan haka ku dena ma wannan labarim"
Huda ta ƙunshe kanta tana dariya, Nasir yace "Anty ya kika gani, kema fa haka
kike son Yayana, laifi ne dan ta so mijin ta, wallahi my Huda kidena jin kunyar
Anty Nadiya, naga ta fara damun ki"
Huda ita dai sedai tayi murmushi, Yusuf yace "ɗanuwa babu abunda zan cewa Allah se
godiya, kamar yadda Antynka take fata gashi ka bunƙasa kamar wasa, Allah ya ƙara
yalwata maka Arzikinka, Allah yasa ku yi ibada karɓaɓiya, ya dawo daku lafiya,
sannan yakamata kayi haƙuri ka manta da abunda dangin mahaifinmu sukayi mana, komai
ya wuce suma ka dinga kyautata musu "
Nasir yace " Taɓɗijan, wallahi nida su har abada, bazan manta cin zarafi da
wulaƙancin da suka yi mana a rayuwa ba"
Yusuf yace 'A' a Nasir, abun da haƙuri be bayar ba, rashin sa baze bayar ba, ka
maida komai ba komai ba, se kaga Allah ya daɗa buɗa maka, sannan ina gargaɗinka
akan wannan yaron Bulama yake kowa? Ban yarda ka barshi akan kayanka ba, ko harkar
kasuwancinka ba, dan bashi da kirki "
Nasir yace " Nikam na rasa me Bulama yayi muku kuka tsane shi, ni tausayi yake bani
kaga shima marayane, kuma basu da ƙarfi "
Yusuf yace " banƙi kayi taimako ba, amma ya kamata kasan irin taimakon da zaka
dingayi, Ka kiyayi yaron nan"
Nasir yace "to babbn Yaya magajin babanmu, Antyna ta kaina insha Allah baɗi in
Allah ya kaimu lokacin aikin hajji, seki barmin babana kema kije ki sauke farali"
Nasir yace "Ameen, ban cika Alƙawari ba, ke nace zan fara kaiwa amma na kai Yaya,
nayi son kai ko?"
Nadiya tace "ai duk wanda ya kyautatawa Mijina ni yayiwa, nan duniya in ana son
farincikina to a kyautatawa mijin marainiya"
Nasir yace "imra'ati kinji ko? Tana tsokanarki kin fiye sona, amma ji abunda take
cewa"
Sukayi dariya, Nasir yace "Yayana, wai yaushe zan dawo muku da kuɗinku ne? Kasan
fa yanzu Alhamdilillah, zan iya biyanku hadda riba"
Yusuf yayi dariya yace "Naji, Alhamdilillah haka nake fata, ka ci gaba da juya
mana, lokacin karɓar yana nan zuwa, mesu ze karɓa"
Nasir yace "waye me su ɗin dazs karɓ?"
Yusuf yace "kai Baba suda sarki zance, kuje dare ya fara yi, kuje kuyi sallama dasu
Antyn Huda, nima jibi in Allah ya kaimu nida su Nadiya zamu tafi Abuja, zamuje wani
taro zan wakilci bankinmu, inaga daga nan idan na dawo zasu bani allowances ɗina na
siyan gida da mota"
Nasir yace "masha Allah, Allah ya tabattar Yayana, Huda bani babana sanyin
idaniyata, in sake ganinsa in sumbaci fararen kumatunsa"
Huda ta miƙa masa Faruk, ya karɓi jaririn ya rungume shi, yana sumbatar fuskarsa.
Yusuf yace "gaskiya Nasir kana ƙaunar wannan ɗan naka, Maman Faruk sekinyi dagaske
karsu ƙwace mana ɗa shida matarsa"
Haka suka wanzu suna zolayar juna, suna hira tare sukaci Abincin dare kamar karsu
rabu, suka shiga gurin Islam sukayi mata sallama itama, nan mu sun daɗe a can, daga
ƙarshe Yusuf da Nadiya seda suka kusa rakasu gida sannan suka juya suka koma.
Washegari Alhaji Abubakar ya aiko da babbar mota, aka ɗauki su Nasir da Huda da
matarsa, su Yusuf sukayi musu rakiya har airport, canma seda suka tsaya hira kaman
karsu rabu, sannan suka tafi.
Satinsu uku a can sannan suka dawo gida Nigeria, sedai dawowar tasu suka tarar da
abu mafi muni a tarihin rayuwarsu, wannan rana ta zamewa Huda da Nasir rana mafi
muni da a tashin hankali, tashin hankalin da bazasu taɓa mantawa da shi ba a
tarihin rayuwarsu, ranar tazo musu da wani al'amari me taɓa zuciya da girgiza ruhi,
basu kaɗai ba hatta Ahmad ɗan gidan Alhaji Abubakar wannan rana tazo masa da baƙin
tarihin da baze taɓa goguwa a zuciyarsa ba
LITTAFIN KUƊI NE, DAN ALLAH KI SIYA KAFIN KI KARANTA BA DANNI BA DAN ALLAH, LITTAFI
NA ƊAYA KYAUTA NE WANNAN NA SIYARWA NE
NORMAL GROUP ₦300
VIP ₦500 NE KITURA TA WANNAN ACCOUNT ƊIN
0009450228
JA'IZ BANK
AISHA ADAM
SE A TURA SHEDAR BIYA TA WANNAN LAMBAR
07063065680
11/14/21, 6:09 PM - Ummee Musa: LITTAFIN KUƊI NE, DAN ALLAH KI SIYA KAFIN KI
KARANTA BA DANNI BA DAN ALLAH, LITTAFI NA ƊAYA KYAUTA NE WANNAN NA SIYARWA NE
NORMAL GROUP ₦300
VIP ₦500 NE KITURA TA WANNAN ACCOUNT ƊIN
0009450228
JA'IZ BANK
AISHA ADAM
SE A TURA SHEDAR BIYA TA WANNAN LAMBAR
07063065680
66_67
Mummunan labari, Islam 'yar uwar Huda, ta bawa me aikinta guga, yana cikin yi, me
gidan ya dawo ya aike shi, koda me gugan ya dawo se ya tattare kayan gugar yace da
safe ya ƙarasa, ashe ya manta be kashe dutsen gugar ba, cikin tsautsayi cikin dare
dutsen ya ɗau zafi wuta ta fara ci, babu wanda ya farga, har wutar ta shiga gidan
Yusuf Yayan Nasir, gobara ce ta tashi sosai, daga gidan Alhaji Abubakar, har gidan
Yusuf babu wanda aka iya ceta, gaba ɗaya.
tsautsayin wutar nan ya ritsa dasu, suka ƙone ƙurmus a cikin wannan gobarar, 'yan
unguwar sun kaɗu sun shiga cikin tashin hankali da wannan ifyila'i ya faru, se
yayyafa musu ruwa akayi aka rufesu dan babu ta inda za' a iya sallatarsu.
Nasir ya kaɗu da samun wannan mummunan tashin hankali, dan bashi ba hatta Huda se
kwasarsu akayi zuwa Asibiti, dan babu wanda yake cikin hayyacinsa.
Dukda Ahmad ma ya kaɗu ya shiga cikin tashin hankali, da labarin daya tarar na
rasuwar mahaifinsa, dama shi mahaifiyarsa itace Uwargidan Alhaji Abubakar, kuma ta
rasu yana da wasu matan amma ba a wannan gidan suke ba, da ya Auro Islam ne ya
sakata a wannan gidan, ya dawo da Ahmad gidan, shima ya kaɗu ya shiga cikin tashin
hankali, shine babba a gurin mahaifinsa gashi yana ji dashi, dukda ya sha wahalar
matan uba, amma Auren Islam yasa ya samu sassauci, dan ita sam babu ruwan ta, dukda
wannan masifar tashin hankali da yake ciki, amma ya tausayawa Nasir da Huda, dan
duk wanda wannan mutuwar zata taɓa a bayansu yake.
Seda Nasir ya kwana biyar besan inda kansa yake ba, numfashi ma baya iyayi seda
taimakon Oxygen, ita kuwa Huda tunda ta farka bata magana, sedai hawaye yaita bin
fuskarta, ko Abinci bata iyaci balle magana, fuskarta ta kumbura tai jawur, ga
rashin 'yar uwatta, ga ɗan uwan mijinta da matarsa, ga babu mijin' yar uwatta, ga
mijinta a kwance shima rai a hannun Allah.
Likitoci suka rufu akansa, suna monitoring ɗin bugun zuciyarsa, salati kawai yake
yana faɗin " Yayana, ɗan uwana, shi kaɗai ne ya ragemin, Anty Nadiya da ɗansu duk
babu, innalillahi wa inna ialaihi raji'un "
Wani liktane yace " haba ɗan uwa kamar ba musulmi ba, kayi haƙuri kayi tawwakali,
idan kaji ƙaddarar wani seka rufe baki, kayi haƙuri mu samu mu ceci rayuwar ka, an
san mutuwa da ciwo amma kayi haƙuri "
Nasir yace " likita, ɗan uwana ya mutu, da zan tafi umara ya muka dinga hira, ashe
wasiyya ce, nayi rashi likita, banji rasuwar iyayena kamar yadda naji mutuwar Yusuf
da Nadiya ba, har ɗan namu ma na rasa, innalillahi wa inna ialaihi raji'un wayyo
Allah yayana"
Likitan ya dafa kafaɗarsa yace "Allah yasan da kai, kayi haƙuri, Allah shike da
rayuwar kowane bawa, ka kwantar da hankalinka, matarka mafa tana can munata ƙoƙari
akanta, karta rasa hankalin ta, idan taganka a mawiyacin hali to jikinta ze rikice"
Jinina kai Nasir ya shigayi yana "Allah sarki Hudana, Huda munyi rashi, mun rasa
'yan uwa dagani harke, Allah ka zama gatan mu, Allah kayiwa bayinka Rahama"
Likitan yace "A' a ka bari za'a kawo ta, har nan inda kake bama son ka dinga
wahalar da jikinka"
A wannan kwanaki biyar ɗin Huda tayi ɓari, amma saboda halin da suke ciki ba'a
sanar musu ba, dukda alhini da Ahmad ke ciki, amma a haka yake ta sintiri a
Asibitin, wata ƙawar mahaifiyar su Nasir ce take sintirin jinyar Huda, yayin da
Ahmad ke kula da Nasir, 'yan unguwa nata zuwa yi musu jaje da kuma duba su.
Duk Wanda yaga halin da suke ciki, sya tausaya musu, gaba ɗaya sun rame mussman
Huda abun yafi mata yawa, yanzu ta rasa kowa da komai nata, se Allah da kuma
mijinta Nasir, shima gashi a kwance se yadda Allah yayi dashi, ga ɗan uwan
mahaifinsu ya sallamasu, dan bezo Nigeria gurin ta'aziyya ba, kuma labarin gobarar
ya iskeshi, yace suje can su ƙarata ba abunda yayi masa zafi.
Nasir ya takura akan yana son ganin Huda, a haka aka turo Huda a wheel chair tazo
duba Nasir.
Tana ganinsa a zaune ta ɗanji sanyi a ranta, ganin nasa jikin da sauƙi, ana
ƙarasawa da ita suka rungume juna suna kuka, Kuka me tsuma zuciya, a hankali Huda
tace "zaujee, mun rasasu gaba ɗaya babu wanda yayi rai a cikin su '
Nasir yace " Na sani Huda, babu yadda muka iya se mu rungumi ƙaddararmu, sukuma mu
cigaba da yi musu Addu'a "
Nan suka dinga kuka, aka rasa me rarrashin wani, Ahmad ne ya shigo ya tarar dasu a
wannan yanayi, suna ta kuka.
Ahmad yaja kujera ya zauna, ya dubi su Nasir cike da rauni da karaya shima ya fara
magana yace " Nasir, dama itafa duniya munzone tamkar matafiya, dole wataran mu
barta, sannan dukkan ɗan Adam dole ne Allah ya jarrabe shi, Allah baya barin mumini
babu jarrabawa, dan haka nida ku mu rungumi ƙaddrara mu, mu yi tawwakali mu barwa
Allah komai, shi ze bamu mafita, su kuma da muka rasa muyi musu Addu'a "
Ahmad ya ƙarasa maganar, ƙwalla na zuba daga idanunsa, amma ya cigaba da tausarsu
yanayi musu Nasiha.
Seda suka shafe sati biyu a Asibiti, saboda jikin Nasir, dan zuciyarsa ta taɓu
saboda damuwa, haka likitoci suka gindaya masa sharuɗa da magunguna, sannan aka
sanar dashi ɓarin da Huda tayi, sam da gashi har ita basu san da cikin ba, dan koda
zasu tafi umara da aka yi gwaji babu, yanzu kuma an tabattar masa da cikin watansa
uku ma, Ba laifi Bulama ma yayi zaryar Asibitin nan sosai, saboda Nasir, dan dukda
rashin jituwar da yake da Yayan Nasir ya tausaya masa wannan rashin da suka yi
lokaci ɗaya, shima ya dinga rarrashin Nasir, akan ya kwantar da hankalinsa ya
rungumi ƙaddara.
A haka aka sallamesu suka koma gida, sedai babu me iya rarrashin wani a cikinsu,
idan abun ya taɓosu se su wuni kuka ita dashi, dama ga Nasir da raguwar zuciya, su
wuni cikin damuwa babu me ko iya cin Abincin, saboda dukkaninsu mutuwar tana dukan
su.
Kusan watanni Uku, da mutuwar har ɗan gara Nasir ya fara jarumta yanzu, amma Huda
kam babu wannan batun, musamman gari ya waye da ta saba ta tafi gidan Nadiya, ko
Yayarta Islam taje taita musu rainon 'ya' ya kasancewar tana matuƙar som yara, amma
lokaci ɗaya Allah ya karɓe su gaba ɗaya.
Yanzu Nasir na iya zaman rarrashin ta, yaita bata baki yana tausarata, yace "Huda,
ni dake Allah ne gatanmu, shiya haliccemu gaba ɗaya, kuma yafi mu sonsu daya
karɓesu, ni dake dole muyi kukan maraici, nasan zakiyi tunanin ya rayuwarki zata
kasance a nan gaba? Huda a duniya bayan iyayena ina jin maganar Yayana fiye da
tunaninki, kuma nima nasam abunda ya dace, nasan gwagwarmayar da akayi kafin in
Aureki, dan haka ko sau ɗaya karki sawa zuciyarki Nasir ze juya miki baya, nida ke
yanzu gaba ɗaya muna cikin maraici gaba da baya, dan haka mu rungumi ƙaddararmu mu
rayu tare, mu jure duk wani ƙalubale mu kasance a tare har zuwa namu wa'adin, in
dai ta ɓangare nane, Insha Allah bazaki zubda hawaye ba"
Huda tayi ajiyar zuciya tace "Zaujee, nima nasan abune mawuyaci in fuskanci
ƙalubale ko juya baya daga gareka, ina da kyakkyawan yaƙini akanka, amma dole in
koka, munyi rashin da ba zamu mayar da wannan gurbin ba, kamar yadda ka faɗa insha
Allah, duk tsanani zan jure duk wata ƙaddara in rayu da kai, bani da kowa se Allah
sekuma kai"
Nasir yace "Insha Allah, bazan baki kunya ba Huda, nasan halaccin da kikamin a
rayuwa, dan haka insha Allah zan kasance dake, zan kasance me baki kariya, kuma zan
zame miki mijin marainiya insha Allah"
Shikuma Nasir likkafa se ƙara cigaba take, gaba ɗaya ya zama busy man, yawo ƙasa
ƙasa kasuwanci kala kala, duk ba wanda ba yayi.
Shine saida kayan sarƙoƙi, motoci, kayan masarufi, ga shaguna da yake dasu a
kasuwa, na siye da siyarwa, hannun jari dayake siya a manyan kamfanunnuka.
Nan da nan ya zama kamar bashi ba, gashi dai matashi amma ya tara kuɗi.
Nasir ya ɗauki Huda sukaje ƙasarsu can Maroco, amma baffanta yayi musu wulaƙanci,
Kasancewar besan Nasir ya fara arziki ba, yayi musu fata fata yace yadda aka cinye
'yar uwatta itama haka za' a cinyeta, haka suka dawo Nigeria da ɓacin rai.
Ganin Huda ta kasa samun nutsuwa har yanzu, ga tarin damuwa data sa a ranta, hakan
yasa ya ɗauketa ya tafi da ita ƙasashen waje, can Dubai inda yafi harkokinsa, ya
koma makaranta a can, sedai tun bayan ɓarin nan Huda bata sake samun ciki ba,
kullum cikin addu'a take ubangiji Allah ya bata rabo itama.
Ya zamana Huda tana Dubai, kowani abun zezo yi Nigeria, ita tana can duk dan ya
samu ta rage damuwa.
Seda suka shekara takwas da Aure bata sake yin ko ɓari ba, abun duniya duk ya
addabeta, shikam ko a jikinsa, dukda yana addu'a sosai a ransa a bun yana damunsa,
amma sam baya nuna mata, ta takura masa sukaje Asibiti akayi musu gwaje gwaje, amma
akace lafiyarsu ƙalau.
Se a shekara ta tara Allah yasa Huda ta samu ciki, aikuwa Nasir yayi murna babu
adadi, nan suka shiga rainon cikin nan da tattalinsa, gefe guda kuma ya zama
matashin ɗan kasuwa na farko, wanda sunansa yake zagawa a cikin Nigeria, a hankali
yasan manyan 'yan siyasa da attajirai, saboda har harkar kwangila yake yi, nan
dangin mahifinsa suka shiga ƙoƙarin nuna ai ɗansu ne, amma fafur yaƙi yadda su raɓe
shi, a cikin dangi can suka haɗu da wani Musa, sun ɗan haɗa alaƙa amma ba irin ta
sosai ɗin nan ba, ɗan unguwarsu ne dai, ya dinga shisshigewa Nasir, tun Nasir na
basar dashi, har ya fara sakewa dashi.
Musa ya nuna sha'awarsa ga harkar siyasa, Nasir ya haɗashi da manyan 'yan siyasa,
ya goyi bayansa akan harkar siyasar, nan da nan mutane suka karɓi Musa, a dalilin
Nasir, kasancewar Nasir mutum ne na mutane, mutane na ƙaunarshi saboda hannunsa a
sake yake, ga shaharar da yayi ganin Nasir ne ya talatta Musa da kansa, hakan yasa
mutane suka karɓe shi hannu biyu biyu.
Bulama kam basa jituwa da Ahmad, dan haka ya dinga shiga yana fita danya raba Ahmad
da Daula, gashi kusan duk wani harkar kasuwanci Ahmad ne yake jan Daula, dan tun
yana ƙarami Mahaifinsa ɗan kasuwane, dan haka yasan sirrin kasuwanci sosai, Ahmad
yana yawan ankarar da Daula akan ya kiyayi Bulama, amma se Nasir yace ai Bulama ya
zamani na zama shi, rabuwarmu abune me wahalar gaske.
Bulama ya kunno musu wata rigima akan harkar kasuwancin da suke, ya shiga ya fita
seda yasa Daula da Ahmad sukayi baran baran suka rabu, ya zamana shine ma gaban
Nasir.
Watan cikin Huda tara cif ta haifo sankaceciyar jariryarta mace, Daula ya rasa
inda zesa ransa dan murna, sedai haihuwar ta fama musu mutuwar mutanen da suka taka
mahimmiyar rawa a rayuwar su, yau gashi kamar yadda Nadiya ke fata, Nasir ya amsa
sunan Daula, ga rabo sun samu, amma babu ɗaya a mutanen nan daze taya su farinciki.
Haihuwar jaririyar nan tasa sun zubda hawaye, har damuwa taso ta maye gurbin
farincikin da suke ciki, wani abun mamaki jaririyar nan ta ɗakko kamanin Islam
Yayar Huda, dukda Huda da Islam suna kama sosai, amma kamanin Jaririyar nan sunfi
karkata ga Islam.
Huda tana zaune rungume da jaririyar nan tace "Duk wanda yake ƙaunata, ya ƙaunaci
jaririyar nan, duk wanda yaƙi jaririyar nan to tabbas ni yaƙi, a duniya yanzu banda
Allah, se mijina da wannan 'yar, su kaɗai Allah ya mallakamin, inajin son' yar nan
a raina, kamar yadda nake son mahaifinta, Allah yasa ta zamo me jinƙi da tausayi
kamar mahaifinta "
Nasir ya rungume Huda da jaririyarsu yace" tabbas nima duk me sona, to ya ƙaunaci
Huda da jaririyar nan, Allah yasa mun ƙara yawa, ya azurtamu ta samun ƙaruwa, yanzu
wani suna kike ganin zamu saka mata? Ko mu mayaf da Sunan Anty Islam '
Girgiza masa kai Huda tayi tace "A' a idan ka mayar min da sunan Islam, bazan iya
tsawatar mata ba, kamaninta ɗaya da Islam zan dinga ganin kamad itace, haka idan ka
samun sunan Anty Nadiya, nan ma bazan iya tsawatar mata ba, saboda ina girmama Anty
Nadiya, tambarin mutjwarsu baze taɓa barin zuciya ta ba, gara mu sa kamata wani
sunan daban, mu sama ta Widad, wato soyayya da Abota, na zaɓi sunan ne saboda yana
da kyakkyawar ma'ana, Ina sonta kuma itace babbar ƙawata"
Haka akayi gagarumin shagalin suna, a Nigeria, nan dangin mahaifin su Nasir suka
dinga rige rigen zuwa, saboda Arziki ya samu, Bulama ya taya Nasir murnar haihuwar
Widad sosai, duk da saɓanin da suka samu da Ahmad, seda yazo yayiwa Nasir barka, ya
bawa Widad kyaututtuka, Bulama ne ya saiwa Widad Haikika, yayi Ƙaton Akwati da
kayan jarirai, haka nan yaji yana ƙaunar yarinyar, sanadin abunda yayiwa Widad,
yasa mafi yawa na ƙiyayyar da Huda ke masa ta ragu, dan taji haushin rabuwar Nasir
da Ahmad, abunka da abun masu Arziki da neman gurin zama, nan masu kuɗi suka dinga
bajinta suna gwangwaje jaririyar nan da manyan kyautuka, dan kawai su birge Daula,
ko ace wane ya bada kaza.
Kafin su koma Dubai, kusan kullum se Bulama da matarsa sunzo, dan ya ɗauki Widad,
ko kuka take ya dinga rarrashinta kenan, Yana matuƙar son yarinyar.
Kwanansu Arba'in Nasir ya ɗauke Huda suka koma, Bulama ma albarkacin Nasir ya fara
kama ƙasa, nan da nan ya shiga aure Auren mata, ya auri wannan ya saki, ya Auri
waccan ya kora, tun Nasir yana masa faɗa harya ƙyaleshi.
Kadarorin da Aka tarawa Widad na suna, Daula ya haɗa ya siyar bisa shawarar Huda,
suka haɗa kuɗi suka buɗe kamfanin sarrafa ƙarafa, manyan mutane har daga ƙasashen
ƙetare suka zuba hannayen jarinsu cikin kasuwancin, nan fa Sunan Daula ya ƙara
shahara, ya zama babban attajiri, me sana'a goma maganin me gasa.
Widad ta fara wayo a hankali tana girma, ta isa shiga makaranta se Daula ya koma
England, saboda mafi akasari yanzu yafi ta'amalli dasu akan harkar kasuwancin
motoci, aka saka Widad a makaranta, Huda kuma ta dage da koyar da ita na Addini,
dukda akwai wani ustaz dayake koyar da yaran musulmai a ƙasar.
Sedai gaba ɗaya rayuwar Widad da girmanta, ya sha ban ban dana sauran yara, sun
raba gari da duk wasu ɗabi'u na yara, duk inda yaro yake an sanshi da son kallon
fina finan cartoon, kona dabbobi amma banda Widad, idan za tayi kallon film, daga
wrestling, se film wanda ake yaƙe yaƙe ko harbe harben bindiga, kokuma fina finan
horo na ban tsoro, kona harkar fashi, suke birgeta, sam bata kallon wani film ɗin
Indiya ko soyayya da tausayi, basa gabanta, Huda taita fada tana mita, amma Nasir
se yace ta ƙyaleta, nan gaba zata dena.
Huda taita mita tace "yarinya kamar ba mutum ba, ke duk abunda mutane suke yi ko
suke so, ke kunyi hannun riga dashi?"
Widad tana da miskilanci, bata magana seta ga dama, idan har kaji ta zage tana
surutu, kodai da mahaifintane ko kuma Bulama ne ya kawo musu ziyara, bata wasa da
'yan uwanta yara, sedai taita gwada tsalle tsalle, da harbin bindiga da take gani a
film, shine wasanta sosai abun yake damun Huda, Nasir yace tayi haƙuri irin tata
ƙuruciyar kenan.
Widad tafi sakewa Da Babanta akan Amminta wato Huda, Huda tana da zafi sosai akan
tarbiyyar Widad, yayinda Babanta duk abunda takeso shi yake so, amma duk da haka
akwai soyayya da shaƙuwa a tsakanin Widad da Amminta, babban abunda yake haɗasu
shine rashin son mutanen Widad da kuma wannan kallon da take yi.
Widad ko ƙawayen kirki bata da su, saboda rashin son maganar ta, sedai tana ji da
magenta, tana nuna musu soyayya, sune abokan wasanta, dasu take hirarta.
Tun bayan haihuwar Widad me abun mamaki, Huda bata sake samun haihuwa ba, tana ta
Addu'a tana fatan ubangiji Allah yasa ta kuma samun rabo.
A wannan lokacin shaharar Daula ta wuce iya Nigeria, da taimakon Allah Daula ya
goyawa Musa baya da maƙudan kuɗaɗe, ya tsaya takara a wata jam'iyar siyayasa a
wannan lokacin, a dalilin son da mutane suke wa Nasir Daula suka zaɓi Musa.
Tunda Musa yaci zaɓe nan ya ɓarke da bushasha, bashi da aiki se gantalin ƙasashen
duniya, ya manta da al'ummar da suka zaɓeshi, da irin Alƙwarirukan daya ɗaukarwa
mutane, Ya kai 'yarsa Nurat makaranta a ƙasar waje, inda Widad take karatu, Nurat
tana matuƙar son Widad, Kasancewar Widad ce bahaushiya' yar uwatta a makarantar,
duk sauran yaran turawa ne, tun Widad bata damuwa da Nurat harta fara kulata, a
hankali suka fara sabawa suna shaƙuwa da juna.
Widad sam tun haihuwarta, rayuwarta tafi a ƙasar waje, idan sunzo Nigeria to hutu
sukazo ko kuma ziyara, gashi Huda ba wani Hausa takeji ba, tama jin Husa amma ba
sosai ba, dan haka wasu abubuwan duk Widad bata sansu ba.
Nasir ya haɗa kai da wasu 'yan china, suka buɗe wata katafariyar ma' aikatar harkar
kwangila, na gine ginen tituna, da shigo da kayan gini, ya jawo matasa sosai cikin
harkar, bayan wancan kamfanin ƙarafa da yake dasu, da sauran manyan kadarorinsa na
mamaki, dan har rijiyar mai Daula ya mallaka, kullum Arziƙinsa gaba yake, baya
baya, gashi ba wani babba ba a a wannan lokacin, amma ya tara Arziki da shahara.
Shekarun Widad bakwai a duniya, har Huda sun fidda ran samun wani ɗan, kawai ta
tashi da matsanancin ciwon ciki, tayi zaton ɓacin cikine kawai, amma ta wuni a
kwance, hakan yasa Daula ya ɗauketa zuwa Asibiti, a nan aka tabattar masa da tama
ɗauke da juna biyu.
Daula ya rasa inda zesa kansa dan farinciki, sunyi murna sosai da samun wannan
cikin, nan ya ƙara ririta Huda fiye da yadda yake yi a baya.
Da tayi motsi se yace "me unborn ɗina yake sone, har Widad ta fara kishi tace
"Daddy, wai yanzu kafin son unborn ɗin nan ne dani?"
"wane ni, ga gimbiyata ince nafison wani dake, ai you are my forever Queen, babu
wanda ze rusamin fadarki, kiyi yadda kike so Gimbiyar Daula'
Ire iren wannan kirarin, da soyayyar da mahaifinta ke mata suke fasa mata kai,
Widad bata taɓa kukan babu ba, bata san ta nemi abu ta rasa shi ba, haka ta taso
cikin zunzurutun jin daɗi da dukiya ta ban mamaki.
Tun Widad tana ƙarama take bada kyauta, idan Daula ya ga dama, se yace "Ran
Gimbiyata ya daɗe, ga wane me kike so a bashi?"
Duk abunda ta faɗa ta zauna, se an bawa mutum, Huda taita mita tama ya fiye
sangarta Widad, shi kuma ya kance idan banyiwa Widad abunda takeso ba se yaushe?
Idan na mutu bata mori dukiyar mahaifinta bafa?"
Ya sai kadarori da sunayen Widad, kadarorin daya siya da sunanta basu da adadi,
Widad komai yi mata akeyi, suna da nanny.
A hankali Huda taga idan ta biyewa Daula, to Widad zata tashi a sangarce, dan haka
take ɗan koya mata waus abubuwan, kamar gyaran ɗakin data kwanta, ɗauke kwanon
Abinci, da shara daidai wadda zata iya.
Katsam bayan tenure Musa ta farko, yana ƙoƙarin ya koma, labarin irin almundahanar
da Musa yayi ta iske Daula, abun yayi masa ciwo, ya goyawa macuci baya ya jagoranci
al'umma, amma ƙarshe ya zalunce su, Daula da kansa ya kai Musa EFCC yace su tuhume
shi, a bincike shi ya fito da haƙƙin mutane.
Abun ya bawa mutane mamaki, ganin shiya kawo Musa Siyasa, amma da kansa ya kaishi
gurin hukuma, sannan yace bashi bashi, kuma duk hukuncin daya dace ayi masa.
Gaba ɗaya siyasar Musa, da mutuncinsa ya zube a idon mutane, dama farin jinin
saboda Daula ne, mutane suka juya masa baya.
Ƙarshe da kyar ya sha a hannun EFCC, dan seda aka kaishi prison a ƙasƙance, aka
ƙwace wasu daga kadarorin da ya mallaka, a wannan lokacin abubuwa basu taɓarɓare
kamar yanzu ba, da ƙyara wasu daga 'yan siyasa suka dinga shiga suna fita, seda
Musa yayi watanni shida a prison, sannan aka sako shi da kyar, shima se da aka
ƙwace masa passport, dan gwamnatin lokacin ba tasu bace.
Wannan dalilin yasa Musa ƙulattar Daula, ya manta duk alkhairin da Daula yayi masa,
ya manta yadda ya tsamoshi daga ƙangin talauci da shaye2, yayi aniyar rama abunda
Daula yayi masa kota halin ƙaƙa, yayi Alƙawarin tozarta shi da wulaƙa ta shi, kamar
yadda yayi masa, yayi alwashin ɗanɗanawa Daula baƙin ciki mafi muni a rayuwarsa,
tunda ya ɓata masa suma ya lalata masa siyasarsa.....
LITTAFIN KUƊI NE, DAN ALLAH KI SIYA KAFIN KI KARANTA BA DANNI BA DAN ALLAH, LITTAFI
NA ƊAYA KYAUTA NE WANNAN NA SIYARWA NE
NORMAL GROUP ₦300
VIP ₦500 NE KITURA TA WANNAN ACCOUNT ƊIN
0009450228
JA'IZ BANK
AISHA ADAM
SE A TURA SHEDAR BIYA TA WANNAN LAMBAR
07063065680
11/14/21, 6:09 PM - Ummee Musa: .LITTAFIN KUƊI NE, DAN ALLAH KI SIYA KAFIN KI
KARANTA BA DANNI BA DAN ALLAH, LITTAFI NA ƊAYA KYAUTA NE WANNAN NA SIYARWA NE
NORMAL GROUP ₦300
VIP ₦500 NE KITURA TA WANNAN ACCOUNT ƊIN
0009450228
JA'IZ BANK
AISHA ADAM
SE A TURA SHEDAR BIYA TA WANNAN LAMBAR
07063065680
68_69
Cikin Huda ya ci gaba da girma, yayin da gefe ɗaya Daula ya fara tara maƙiya da
mahassada, danshi duk abunda zeyi be yadda da cuta ko ha'inci ba, komai nasa
tsakani da Allah yake yinsa, ga gefe guda mutanen daya ƙwacewa kasuwar wasu
abubuwan, suma suka sako shi gaba suna jin haushinsa.
Wata gidan Talabijin yayi hira da Daula, akan yadda akayi ya fara kasuwanci,
nasarorin daya samu da kuma ƙalubale, duk ya dinga bada amsa, gashi duk hirar da
za'ayi dashi se yayi zancen Yayansa Yusuf, se yayi musu addu'a, duk inda me Suna
Yusuf yake Nasir kamar ze duƙa masa saboda girmamawa, komai ƙanƙantar Yaro indai
yana da wannan sunan, to tabbas yana da ƙima a idon Nasir.
Babban abunda ya daɗa ja masa baƙin jini shine, yadda yakewa al'umma hidima, yake
facaka da dukiyarsa gurin hidimtawa al'umma da addini, wanda sauran abikan
kasuwancinsa basa yi, hakan yasa ya ƙara samun masoya ta kowane fanni.
A cikin hirar da'ake dashine ya bayyanawa 'yan jarida cewar, shifa ainihin kuɗin
daya fara kasuwanci dasu bashi aka bashi, kuma be biya bashin ba, ya sanar dasu
cewa wanda ya bashi bashin ya gaya masa me kuɗin yana nam zuwa ya karɓi wannan
kuɗi, dan haka gundarin dukiyar da yake juyawa yana samun riba akwai me ita, kuma
duk sanda lokaci yayi indai me dukiyar ya bayyana to tabbas shi keda kaso bakwai
cikin goma na dukiyar daya mallaka, ya ƙara da cewa a hirar nan da suke, tuni ya
ware wannan dukiyar guri guda, ko bayan ransa duk wanda yasa hannu akan wasiyyar
daya bari da takaddun dukiyar daya ware, to tabbas wannan dukiya tasace, ko waye
yasa hannu akai tasa ce "
Wannan hira da Daula yayi ba ƙaramin cecekuce ta janyo ba a cikin al'umma, wasu
suna jinjinawa amanarsa, wasu suna ganin wautarsa suna inama zasuga inda tajaddun
suke su saka hannu su karɓe kuɗaɗen, wanda suke da hannun jari a kamfanunnukansa
suka shiga zullumi, akwai dukiyarsu a cikin kuɗaɗen Daula, kuma muddin ya janye
daga kasuwancin to tabbas zasu talauce, dan haka suka shiga tunanin nemawa kansu
mafita.
Katsam akayiwa Huda scanning, aka tabattaf da cewa tana ɗauke da ɗa namijine a
cikin ta, ana gayawa Daula ya zube yayi sujjadar godiya ga Allah, bakinsa yaƙi
rufuwa, farincikinsa yakasa ɓuya.
Sunyi murna sosai da wannan kyauta da Allah yayi musu, Kasancewar Daula ya daɗe
yana kuma neman haihuwa yasa shi, ya shiga gayawa abokansa ai Madam ta samu rabo,
kuma anyi scanning ance zata haifi namiji, zatonsa duk masuyi masa dariyar nan
masoyansa ne, zasu taya shi farinciki, ashe abunda be sani ba ta ciki na cikine
kawai, dan gaba ɗaya ba ƙaunarsa suke ba, dukda da yawa su, Daula shine silar
Arziƙinsu.
Watarana suna zaune suna hira da abokansa, suke bugun cikinsa Haruna yace "Yanzu
kai Daula, gashi ga abunda kace akan cewa akwai me kaso bakwai na dukiyarka, yanzu
idan ba'a samu wanda yasa hannun bafa? Sannan meyasa me dukiyar baze zo ya karɓa
ba"
Daula yace "me kuɗin, yayana ne da matarsa da Allah yayi musu rasuwa, kuma shi ya
gayamin akwai wanda ze karɓi wannan kuɗin, dan haka nayi a rubuce ko bayan raina
idan mesu bezoba, a rabawa al'umma su, ko kuma a gina abunda al'umma zasu amfana"
Nasir yace "eh mana, haka shine yakamata ai, har wasiyya nayi yadda na kasafta
dukiyar"
"to yanzu a ina suke, balle mesu ɗin yasa hannu ya karɓa?"
Daula yace "idan har me dukiyar nan yazo, no matter how hard seya karɓi abarsa,
babu wanda yasan inda suke, se Allah seni, nayi bayanin komai a video wasiyyar dana
bari, na danƙashi a hannun 'yata Widad"
Daula yai murmushi yace "wannan Yarinyar, yadda kanta yake lissafi naka bayayi, a
hakan tayi min alƙawarin zata adana wasiyyata kamar yadda zata adana Ranta daza ta
ganshi"
Haka sukayi ta bugun cikin Daula, wani abun ya gaya musu, wani abun ya waske shi
duk a ganinsa an zama ɗaya, har yake labarta musu ai matarsa namiji zata haifa.
Cikin Huda yana da watanni bakwai, ta dage tace ita seta koma Nigeria a can take
son ta haihu, Daula ya kaɗa ya raya tace ita Nigeria takeson ta koma, yanzu zaman
nan ya isheta.
Haka Daula ya tattara ya dawo Nigeria, dama akwai katafaren gidansa me girman
gaske, inda suke sauka idan sunzo, akwai ma'aikata a gidan saboda girmansa, dukda
babu kowa a gidan akwai megadin gidan Bala, Sojane shiyake kula da shuke shuke da
sauran al'amauran gidan idan basa nan, gidane har gida katafaren gaske me matuƙar
girma da yalwa.
Suka koma Nigeria suka sauka a wannan gidan, lokacin da cikin Huda ya shiga watanni
takwas tafiya ta kama Nasir ta gaggawa, Huda haka nan taji bata son ya tafi, ta
dinga masa Shagwaɓa harda kuka ita karya tafi.
Widad ganin Mamanta na kuka, hadda shagwaɓa yasa tace "da nice da yanzu Ammi kin
koreni kince na fiye takura, shine kikewa Daddy kuka ko? Daddy ka ƙyale Ammi
shagwaɓabiya"
Nasir yayi murmushi yace "my princess gayamata dai, kalli tana kuka kaman baby"
Widad suka haɗu ita da Babanta suka dinga tsokanar Huda suna dariya, akwai
kyakkyawar fahimta da ƙaunar juna a tsakaninsu, haka yaita rarrashin Huda, harta
haƙura ta ƙyaleshi ya tafi, ita dama tsoromta bata son ya tafi daga ita se Widad a
gida ga tsohon ciki.
Kwana biyu da tafiyar Daula, cikin dare sun tsaka da bacci, Widad ta tashi ta shiga
kiran "Ammi, Ammi ki tashi"
Widad ta jinjina mata kai, Huda tace "Widad kin fiye rigima, ko tausayin halin da
nake ciki bakya yi, tashi muje in haɗa miki"
Haka ta kama hannun Widad zuwa kitchen, ta haɗa mata Frisco ta samata madara ta
bata, Widad ta zauna tana sha, yayin da Huda keta hamma saboda bacci.
Widad ta kalli Amminta tace "Ammina kije ki kwanta, idan na gama nima zanzo in
kwanta"
Tafiyar Ammin ɗaki ba daɗewa, Widad taji kamar ana taɓa gate ɗin gidansu, ga Ƙaton
karensu yanata zabga haushi, a zatonta ko Daddynta ne ya dawo a daren nan, dan haka
ta taka kujera, ta hau kan drower ɗin kitchen, ta leƙa Window, da yake gurin a
saman bene ne, hakan ya bata damar ganin abunda ke faruwa a ƙasa harabar gidan.
Ƙaton police dog ɗin nasu yake ta haushi yana zagaye, a harabar gidan, Bala soja ya
kama karen ya maida shi ɗakinsa ya rufe, sannan yaje ya zare sakatar dake gate ɗin.
Wasu mutane ne suka shigo cikin gidan, sun kai su biyar fuskarsu ɗauke da mask
baƙi, baka gane fuskokin su, ga manyan bindugu a hannunsu.
Tunani Widad tayi, a irin fina finan da take kallo, idan akaga mutane da irin
wannan shigar musamman cikin dare, to they are dangerous, tana nan akan drower taga
Bala yayi musu jagora har ƙofar da zata sadaka da cikin gidan.
Ya buɗe musu ƙofar suka shiga, Widad ta sakko daga kan drower a hankali, ta leƙa ta
ɗaya window, tana gani suka shigo babban falon ƙasan benen, suka shiga haurowa
saman benen, komawa tayi ta ɓuya suka buɗe ƙofar ɗakin da Huda take ciki suka
shiga.
Suna shiga Widad ta fito daga kitchen ɗin, tana tafiya a hankali tazo ta window
dake corridor ta tsaya ta Leƙa window a hankali, cikin sanɗa take komai.
Tana gani ɗaya ya kunna fitila, haske ya gauraye ɗakin, Huda ta buɗe ido tana
salati, nan da nan ɗayan ya janyo pillow ya danneta, ta dinga mutsu mutsu tana
fizge fizge, Kasancewar ƙaramar rigar bacci ce a jikinta, kana iya ganin yadda
cikin dake jikinta ya dunƙule guri ɗaya.
Widad tana tsaye tana kallonsu, ta toshe bakinta da hannunta, tana ta gumi jikinta
yana tsuma, ƙafafunta se rawa suke, tun Huda na iya mutsu mutsu da ƙoƙarin ƙwacewa,
ɗaya ya zaga ya hau kan gadon ya riƙe hannayenta, tun tana motsa ƙafafunta, har rai
yayi halinsa ta dena motsi.
Widad na zuwa nan kawai ta rirriƙe Yusuf ta fashe da wani irin kuka me matuƙar ban
tausayi, ba Widad ba shi kansa Yusuf seda jikinsa yai sanyi, labarin ya ratsashi
sosai, tun daga rayuwar iyayenta zuwa kanta a cikin ƙaddara take, rungumeta Yusuf
yayi yana shafa bayanta da sigar rarrashi, amma ya kasa magana sam se Ajiyar
zuciya.
Ganin Widad bata da niyyar sassauta kukan da take yasa Yusuf ya fara magana, cike
da rauni da tausayawa yace "Am very sorry dear, ubangiji Allah jiƙansu gaba ɗaya,
take heart Widad, Allah ya jiƙan Ammi"
"Yoseef, my Mum was killed before my eyes, a gaban idona aka kashemin ita, bayan an
san bani da gata se Allah se ita da Daddy na, amma without fear, she was killed
mercilessly, ga tsohon ciki, how can I forget this in my life, how?"
Jikinta har tsuma yake saboda kukan da take, ga wani irin numfashi da take jerawa,
Yusuf yace " tabbas an cutar da ahlinku, cutarwa mafi muni Widad, amma kiyi haƙuri
ki miƙa lamarinki ga Allah, dama Allah yayi a lokacin mahaifiyarki zata rasu, bawa
baya wuce lokacinsa"
Widad tace "na sani, da Ammi mutuwar Allah tayi, bazan cigaba da damuwa tsawon
wannan lokacin ba, nasan lokacinta ne yayi, amma aka kasheta da tsohon ciki laifin
meta yi? Me tayi musu zasu kashemin ita Yoseef?" ta maganar muryarta na sarƙewa.
Seda Yusuf ya zubda hawayen tausayin Widad, ya shiga share mata hawayenta yana, "
kiyi haƙuri, mucigaba da yi musu Addu'a, kidena wannan kukan, Allah yayi mata
rahama, take heart "
Shaƙuwa Widad ta dingayi, numfashinta yana sama yana ƙasa, gigicewa Yusuf yayi ya
shiga kiran sunanta, tana jinsa amma bata iya magana hannunsa ya ɗora akan
ƙirjinta ya shiga karanta mata duk abunda yazo bakinsa, na ayoyin alƙur'ani.
A hankali ta dinga sauke ajiyar zuciya, ta dena shaƙuwar, Yusuf yace mata sannu,
jinjina masa kai kawai tayi.
Yace "dare yayi sosai yanzu, ma cigaba wani lokacin, ki kwanta ki huta"
Ta jinjina masa kai, ya gyara mata pillow ya kwantar da ita ze miƙe, ta riƙe
hannunsa, ya kalleta yace "ya dai?"
"Akwai hadari a garin, akwai yuwuwar ayi ruwan sama, ka kwanta anan kawai".
"Eh bakomai ka kwanta, i need a shoulder to cry on, ka kwana a kusa dani"
Har yanzun dai kuka Widad take yi, ya kwanta ya ɗora kanta a Ƙirjinsa, ya dinga
sauke ajiyar zuciya, tana cigaba da zubar da hawaye.
Yusuf yaja wata doguwar ajiyar zuciya yace "Gimbiya kina son ki karyamin zuciya ne
in cigaba da kukan nima?"
Girgiza masa kai tayi, yace "kinga har shaƙuwa kikeyi, kin kusa shiɗewa ɗazu
saboda kuka, kiyi haƙuri dan Allah ki dena haka ya isa, yi shiru muyi musu addu'a"
Widad tace "karka damu da shiɗewar da nayi, bayan ciwon hauka inada ciwon zuciya
kamar Daddy na, dan haka ba wani abu bane, nasan idan kwana na ya ƙare zanbi Ammi
na ne"
"Widad bakya tausayina ko? Baki damu da ki dinga gayamin zaki mutu ki barni ba ko?
Babu ruwanki da halin da zan shiga idan kika mutu kika barni bako?"
Ɗago kanta tayi tana kallon Yusuf, dukda a cikin duhu suke amma ta kai hannunta
fuskarsa taji ɗumin hawaye a fuskarsa.
Murmushi tayi tace " Ragon maza kawai, ɗan sanda yana kuka, se kace ba jarumi ba,
ni meyasa ka damu dani haka baka son in mutu in barka? Dukda tarin rashin kirki na
a gareka"
Tai maganar cike da son bagarar da wancan zancen da suke.
Mirginata yayi ya koma kanta, a hankali ya kai fuskarsa kunnenta yana mata numfashi
a kunne sannan yace "saboda ni bana ganin laifinki, kuma ni bana riƙo ina sonki
sosai, kuma ba kince ni ɗan uwanki bane?, kuma seki tafi ki bar ɗanuwa haka akeyi?
Bakya tunanin halin da ɗan uwa ze shiga? Anya kina 'yan uwantakar dani kuwa?"
Murmushi tayi tace "wani lokacin inayi, wani lokacin kuma ba nayi"
Tai maganar tana dariya, ta rungume Yusuf tace "dare yayi sosai, muyi shiru haka
mu kwanta"
Yusuf ya sake gyara kwanciyarsa a jikinta, yayi shiru wani irin matsanancin
tausayin ta yana ratsa ransa, daga ita har mahaifinta kowannen su yaga ƙaddarar
rayuwa daban daban.
Alhaji Musa yana zaune yana karyawa da safe a falonsa, wayarsa ta fara ringing,
ɗaukar wayarsa yayi ya tafi bedroom, ya rufe ɗakin ya saka key sannan ya ɗaga
wayar.
"Ka kasa kunne yau, zakaji matakin dana ɗauka akan Yaron nan, dan haka ka kwantar
da hankalinka babu abunda ze faru"
Ajiyar zuciya Musa yayi yace "Alhamdilillah, Insha Allah zan saurara inji wani
irin mataki ka ɗauka akan lamarin, amma to batun Daula fa? Har yanzu fa babu wani
labari a game da shi, ya muke ciki a wannan ɓangaren?"
"Karka damu, shima ina nan ina tunanin mafita, sannan wannan Likitan shima masa a
kau dashi, dan amfaninsa ya ƙare"
Bukar yace "Eh shi, na bada umarnin da ya dace akansa shima, dan haka kowa ya
kwantar da hankalinsa"
Daga nan ya kashe wayarsa, yana jin wani sanyi a ransa, dan da ba ƙaramin ɗurar
ruwa cikinsa yayi ba.
Nura direba ne a cikin lambun Widad yana ta gyarawa, yana cire ciyayin ciki yana
gyara flowers ɗin tare da sharewa, yace "Allah sarki, lambun nan kansa yayi babban
rashi, da meshi tana nan babu yadda za'ayi a barshi a haka, kai rayuwa ba tabbas"
Kukan mage ya dingaji a tsakanin flowers, har ya tsorata ze ruga da gudu, sekuma
yayi ta maza ya dake, leƙawa ya shigayi a hankali, yana duba ciyayin.
Roux ce magen Widad a kwance, gaba ɗaya tayi wani iri abun tsoro, da ƙatuwace magen
nan, gata da kyau gwanin ban sha'awa da yake bata Nigeria bace, amma yanzu kamar an
jiƙata a ruwan zafi, gaba ɗaya gashin jikinta yayi wani iri, gashi duk ya zube ta
koma wata iri abun tsoro.
Nura yasa hannu ya ɗakkota, ya nufi bakin gate da ita, yana zuwa ya ajiye ta, Isa
ya kalleshi ya yamutsa fuska yace "meye wannan haka?"
Nura yace "kaima dai ka faɗa, ai maraici yakama magen nan, abun tausayi"
Isa yace "wannan matsiyatan basu kula da mutum bama balle wata mage, duk halin nan
da ake ciki na rashin me gidan nan da' yarsa ko a jikin su, sabgarsu kawai suke har
gara ma Anwar ɗin nan, shikam akwai kirki sosai"
Nura yace "bari Isa, Allah abun tsoro duniya abun tsoro, kalli da yadda gidan nan
kullum cikin shige da ficen mutane ake, amma yanzu tsit kake ji"
Murtalah yace "kai dai bari, bari in jarraba bawa magem nan Abinci ko zata ci"
Isa yace "kaga fa baka da abunda zaka bata, dan Wani Abincin da fake ci kai kanka
baka taɓa ciba, ka ƙyaleta kawai ta ƙarasa ta hutawa rayuwarta"
Murtalah yace "A'a ba'ayi haka ba, Yanzu a dalilin taimakon dabbar nan se kaga
Allah nima yaji ƙaina, kuma dame ita tana nan kasan bata yarda abar wani da yunwa a
gidan nan ba, dan haka zan jarraba bata Abinci ko zata ci"
Isa yace "ai se kai tayi ɗan wahala, ga hanyoyin neman lada nan ba adadi, amma ka
tsaya wahalar da kanka akan abar data kusa mutuwa"
Murtalah be kuma kula shi ba, yaje ya siyo biscuit katako, da madara 'yar talatin
yazo ya haɗa ya bata, ai nan da nan magen nam ta lamushe, saboda azabar Yunwa da
take ji, abunka da dabba da sabo, tana jin ƙwarin jikinta ta koma ɗakin Widad, tana
kuka ta hau kan gadonta ta sauka, ta fito falonta zuwa babban falo.
Ramlah tace "wai dama wannan shegiyar halittar tana raye bata mutu ba?"
"ke nifa duk wani abu daya shafi waccan banzar ba sonsa nake ba, tunda Allah yasa
ta bar gidan nan mukayi 'yanci, muke warwasawa son ranmu, babu tsawa balle hantara,
shiyasa bana son ganin duk wani abu daya shafeta balle raina ya ɓaci"
Amal tace "dukda haka dai karki huce akan magen nan danni tausayinta nake ji, itama
magen wata kinibabbiya kamar uwarɗakinta, bata zuwa ko ina se tare da ita, ai gashi
yanzu tana wahala"
Ramlah tace "tunda uwaɗakin nata bata nan, ai itama seta ƙara mai"
Da ƙyar Yusuf ya iya tashi sallar Asuba saboda daɗewar da suka yi basu yi bacci ba
jiya, hadari yana ta cida, da akama ruwan sama za'ayi.
Ya tashi Widad sannan yaje yayi alwala ya fita salla, sedai harya dawo bata tashi
ba, hannunsa yaje ya wanke yazo yana shafa mata ruwan a fuskarta.
A hankali tayi miƙa, ta koma ta kuma lumshe idonta, ɗagota yayi daga kwanciyar gaba
ɗaya ya ɗan ƙura mata ido sannan yace "wai wani darem za'a kuma yi miki ne?"
Kasa buɗe idon tayi saboda baccin da take ji, hannayenta ya shiga matsawa yace
"kalli gari ya wayefa, buɗe idonki ki gani"
. A hankali ta buɗe idonta, tabbas gari ya fara hasks duhun Asuba ya yaye, ta kalle
shi tace "meyasa baka tasheni ba"?
"na tasheki baki tashi bane" a hankali ta zauna sosai, sannan ta miƙe taje tayi
alwala tazo ta tada salla, Yusuf yana gefe yana cigaba da lazumi, ya kwaɗaitu da
son jin ƙarshen labarin Widad, sedai yasan halinta da rikicin tsiya, idan bata ga
dama ba haka zatai ta ja masa rai ba zata gaya masa ba, idan ya takura ta se yaji
kuma suyi faɗa.
Data idar da sallar ta fara lazimi ta kife a gurin, yana kallonta da alama bacci ne
sosai a kanta, ya tashi a hankali ya ɗagata ya maida ita kan katifar, still yana
jin tausayinta yana ratsa ruhinsa da ganganr jikinsa.
Ya kwanta a bayanta cike da fargabar kar ta tashi ta kama masifa, tunda ba ita tace
ya kwanta ba, sedai ta ɗanyi juyi taji shi a bayanta, a hankali ta juyo tana
fuskantarsa, ba tare da ta buɗe idonta ba, ta zura hannunta ta rungumeshi, ta
kwantar da kanta a jikinsa, a haka bacci ya sake yin awon gaba dasu.
Har shaɗaya da rabi na Safe basu farka ba, Hari sunata aikace aikacen su a tsakar
gida, ta kalli Gwaggo tace "Yaya, har yanzu fa Wudas basu fito ba, lafiya kuwa?"
Gwaggo tace "lafiya ƙalau insha Allah, ai da Asuba shi yaja salla, dan haka lafiya
ƙalau"
Hansai tace "A'a haba Yaya Hari, abu na mata da miji ina ruwanki? Ba suyi niyyar
fitowa yanzu bane"
Widad ce ta fara farkawa, ta buɗe idonta taga yadda rana tayi, a hankali ta bar
jikin Yusuf ta tashi zaune, garin ta tashin ne shima ya farka, ya kalli garin yadda
rana ta buɗe, yace "Subhanallah, rana tayi ma"
Widad tace "Aikam dai, kasan bamuyi bacci da wuri ba, shiyasa"
Yusuf yace "hakane, gashi ko breakfast bakiyi ba, bari in tashi idan akwai Abinci a
gurin Gwaggo shikenan, in babu se inzo in dafa"
Widad tace "karka damu ni bana jin Yunwa, wanka nake son inyi amma ina son Ka
temakamin in wanke kaina, gani nake kamar baha fita yana damuna sosai saboda babu
gyara"
Yusuf yace "to aini ban san yadda ake yi ba, ban san yadda ake wanke gashi ba"
Yusuf yayi murmushi yace "wannan ai me sauƙi ne, dan bana gajiya da taɓawa, amma
wankewa ni ban san yadda ake yi ba"
"Yau zaka koya kuwa, zan karɓo ruwa a gurin Gwaggo seka tayani mu wanke"
Yusuf yace "wait, waima a ina zamu wanke kan? Ba dai banɗaki ba"
"Koma a inane" ta bashi amsa
Yusuf yace "kawai se aga mun shiga banɗaki tare? No banda wannan, sannan da kunya
aga na taƙarƙare ina tayaki wankin kai a tsakar gida, ki bari seda daddare, muje
toilet mu wanke gashin, yadda ba wanda ze ganmu"
Hararar Yusuf tayi tace "ni yanzu nake so, idan aka wanke kafin dare ya sha iska,
in aka wanke daddarw na kwanta ai wari zeyi tunda babu shampoo"
Yusuf yace "ni ya zanyi, kawai aga mun shiga banɗaki tare? Da kunya fa"
"Au wai nan kunya kake ji, amma ai baka jin kunyata tunda..
Suleiman ne tafe yana driving a motarsa, yana sauraren radio yana jiran ƙarfe huɗu
ta cika ya saurari labaran yamma, kanin labaran ne suka ɗauki hankalinsa, hakan
yasa shi maida hankali don jin cikakkun labaran.
Labarin farko da aka sanarne ya ɗau hankalinsa, ya kaɗashi matuƙa ya tayar masa da
hankali, be gama tsinkewa da lamarin ba, seda ya ƙarasa traffic ta tsaida hannun da
yake, wani yaro yazo ya tsaya a window motarsa yana masa tallan jarida, shafin
farko ya kalla yaji gabansa yayi mummunar faɗuwa.
LITTAFIN KUƊI NE, DAN ALLAH KI SIYA KAFIN KI KARANTA BA DANNI BA DAN ALLAH, LITTAFI
NA ƊAYA KYAUTA NE WANNAN NA SIYARWA NE
NORMAL GROUP ₦300
VIP ₦500 NE KITURA TA WANNAN ACCOUNT ƊIN
0009450228
JA'IZ BANK
AISHA ADAM
SE A TURA SHEDAR BIYA TA WANNAN LAMBAR
07063065680
MASU FITARMIN DA LITTAFI KUMA, IN DAI DAI KUKE KUN SANI IDAN AKASIN HAKANE MA KUN
SANI
11/14/21, 6:09 PM - Ummee Musa: LITTAFIN KUƊI NE, DAN ALLAH KI SIYA KAFIN KI
KARANTA BA DANNI BA DAN ALLAH, LITTAFI NA ƊAYA KYAUTA NE WANNAN NA SIYARWA NE
NORMAL GROUP ₦300
VIP ₦500 NE KITURA TA WANNAN ACCOUNT ƊIN
0009450228
JA'IZ BANK
AISHA ADAM
SE A TURA SHEDAR BIYA TA WANNAN LAMBAR
07063065680
70_71
Da rawar jiki Suleiman ya sayi jaridar nan yayi parking a gefen titi, hoton Yusuf
ne a bangon jaridar an rubuta wanted, ya buɗe cikin jaridar ya shiga duba shafin da
labarin yake, wai 'yan sanda sun fitar da sakamakon binciken da suka yi akan ɓatan
'yar gidan Daula, bincike ya tabattar musu da direban Widad Nasir Daula wanda aka
sani da Yusuf, shine ya sace Widad yayi garkuwa da ita, ba sace su akayi tare ba,
dan haka jam'ian tsaro suna nan suna binciken inda suke, sannan duk wanda ya gano
inda suke ya faɗa akwai kyauta me tsoka.
Gaba ɗaya jikin Sulaiman yayi sanyi, akanme za'a fitar da wannan sakamakon
binciken? Meye dalili? Cikin hanzari ya juya sitiyarin motarsa zuwa wani gurin,
tuƙin kawai yake amma hankalinsa sam baya kan abunda yake yi, Allah ne ya kaishi
inda yake son zuwa.
Harabar headquarter 'yan sanda yaje yayi parking ɗin motarsa, ya fita da sauri daga
cikin motar, yana shiga harabar gurin ƙananan' yan sanda sunata sara masa, cikin
gaggawa ya nufi wani office, ya buɗe ya shiga suka gaisa da ma mallakin Office ɗin,
Suleiman ya zauna ya miƙa masa jaridar hannunsa sannan yace "SP waye ya fitar da
sakamakon wannan binciken haka? Har aka sanar da 'yan jarida?"
SP yace "kamar yaya kenan? Sakamakon binciken da akayi kenan, kuma aka bada umarni
mu sanar"
Suleiman yace "haba SP, wannan yaron fa jami' inmu ne, ta yaya kake tunanin ze iya
aikata wannan mummunan aikin haka, sam ba haka abun ya faru ba, ta yaya za'ace
Yusuf ne yayi garkuwa da 'yar gidan Daula? Ta yaya?"
"Kaga karka zo ka ɗagamin hankali mana, nima umarni aka bani inyi wannan Sanarwar
kuma nayi, meye nawa a ciki?"
"An gabatar maka da sakamakon binciken da akayi kafin kayi wannan Sanarwar, wannan
fa tamkar ɓatawa hukumar' yan sanda sunane, ta yaya wasu tsirarin mutane zasu sa ku
saɓa dokar aikinmu saboda biyan buƙatarsu?"
SP ya kalli Suleiman yace "ya akayi kasan wasu tsirarin mutane ne suka sa ayi
hakan?"
Nan da nan Suleiman ya dawo hayyacinsa ya daidaita nutsuwarsa yace "to koma dai a
cikinmu ne mukayi hakan ai munsan mun saɓa dokar aiki, yaron nan abokin aikinmu ne,
jajirtaccen ma'aikaci ne mara ƙyuya, ga gaskiya a harkar aikinsa, ya dace ayi masa
haka, zan iya rantse maka ko a wasa Yusuf baze aikata haka ba"
SP yace "wannan kuma kai ta shafa bani ba, kai kake zaune dashi kasan halinsa, ni
babu ruwana sakamakon da aka gabatarmin shi zan bayyanawa al'umma, dan haka in baka
da abunyi zaka iya bani guri, ina da baƙi"
Cike da baƙin ciki da ɓacin rai, Suleiman ya baro office ɗin nan, gaba ɗaya
tausayin Yusuf da mamaki suka cika zuciyarsa, tabbas idan akayiwa Yusuf haka an
zalunce shi, kuma an zubar da kimar aikin ɗan sanda a idon duniya.
Saleh ne yayi jifa da jaridar hannunsa yace "Impossible, Alhaji Musa anya kanaso
mu gama da duniya lafiya kuwa? Ta yaya za'ace anyi masa wannan ƙazafin haka? Abun
yayi yawa, yakamata mudinga yi muna jin tsoron Allah"
Alhaji Musa yace "kai dakata! Meyasa ba zamu nemawa kanmu mafita ba? Ina ruwanmu
da koma wani hali ze shiga, ai ba ƙarya akayi masa ba, in ba hakaba meyasa da suka
gudu basu dawo ba, waye yasan inda suke? Dan haka shiya saceta yayi garkuwa da ita,
kuma ya koma yayi garkuwa da mahaifinta, ai mafita muke nemawa kanmu, ɗan sanda
nefa, yanzu idan ya dawo asirinmu ne ze tonu, dan haka gara da mukayi masa haka,
idan kuma baka cikinmu ne zaka iya ƙarawa gaba"
Saleh yayi shiru cike da takaici da baƙin ciki, ya rasa mema yakamata yayi, idan
aka yi haka an cutar da rayuwar Yusuf ba kaɗan ba, rasa abunyi yayi kawai ya juya
ya fice a matuƙar fusace.
Hari tana ta fifitar Wuta, ta kuma kallon ƙofar ɗakinsu Widad tace "taɓ amma
wannan abu yayi yawa haka, ai kome suke yaci ace sun fito haka, sha biyun rana fa
wane irin abune haka?"
Banza Gwaggo tayi da ita, yayin da Hansai tace "ke kuma sa idonki yayi yawa, ina
ruwanki da koma me suke yi ina ruwanki? Kedai bakya rasa abun faɗa shiyasa duk tabi
ta raina ki"
"to naga abun magana bazan magana ba? Ai abun da damu ace garin Allah ya waye, har
wannan lokaci suna ƙule a ɗaka, idan wani abun ya samesu fa"
Widad ce ta fito hannunta ɗauke da bokiti, ta ƙaraso inda Gwaggo take ta gaisheta,
tace "A temakamin da ruwa, ina so da ɗan yawa zan wanke gashina ne"
Gwaggo ta karɓi bokitin, taje rumfar da suke girki ta Ɗebo mata ruwan, Yusuf a
kunyace ya fito suka gaisa da mutanen gidan, yaje ya Ɗebo ruwa a rijiya ya sirka ya
kai banɗaki.
Widad ta ɗakko abun wanka, tazo ta shige banɗaki, Yusuf ya rasa yadda zeyi ya bita
toilet ɗin nan saboda kunya, leƙowa tayi tace "Yoseef ka shigo mana, kose ruwan
yayi sanyi?"
Hari ta tsaya tana kallon ikon Allah, haka Yusuf ya shiga banɗakin nan, ta cire
hijjabin jikinta daga ita se towel, ta cire ribbon ɗinta, ta zauna akan kujera, Nan
Yusuf ya shiga tayata wanke gashin nan me matuƙar tsawo da yawa.
Hansai kam burgeta sukayi, yayin da Hari ta taɓe baki tace "ni tunda uwata ta
haifeni ban taɓa ganin baɗalar da nake gani a gurin bayin Allah nan ba"
Hansai tace "taɓ wallahi nikam birgeni sukeyi, yanzu kai anan ka isa miji ya wani
ta yaka wanke kai, yadda yake ɗawainiya da ita ba ƙaramin birgeni yake ba"
Hari tace "mhmm, ai ko sharar ɗaki baki isa miji anan ya tayaki ba, balle wani
wanke kai, ai maza suna birni, mu nan se godiyar Allah kawai"
Yusuf dai bega wani datti da kan Widad yayi ba, ta dai damune kawai ta wanke kan
nata, tunda ta saba wanke shi akai akai.
Seda ta gama ya bata guri tayi wanka, duk ya jiƙa kayansa da ruwa, Widad tayi
wankanta ta kammala sannan ta fito, Towel ɗin nan kawai ta ɗauro ta fito, gashin
nan ya baje a bayanta se ɗigar da ruwa yake.
Ai gaba ɗaya sukabi Widad da kallo, tubarkallah Allah yayi mata kyau da halitta me
ɗaukar hankali, ta kama ƙasan gashinta tana yarfewa, ga towel ɗin iyakacinsa
gwiwarta, fatarta se sheƙi take.
Hanne tabi Widad da kallo, tana tunanin me zata yi mata ta huce wannan baƙincikin,
Widad kamar da gayya take juya jikinta har ta shiga ɗakinsu.
Hindu ta lura da irin kallon da Hanne ke yiwa Widad, dan haka tace "Masha Allah,
Allah me halitta duk mutumin da yake da mace kamar Amarya, wallahi babu me kama da
bayan tukunyar daze kalla balle yayi sha" War Aurenta, kamar ita tayi kanta masha
Allah "
Yusuf ya kalli Widad yace " Masoyiyya ba dai a haka kika fito ba? "
"Anya kin san irin kyawun halittar da Allah yayi miki, koda ba maza baki abun gudu
ne, dan Allah karki kuma fita a haka"
Yusuf yace "maganar tawa ce bata da amfani ko? Shine kike sharewa"
Hindu tayi sallama ƙofar ɗakinsu, ta kawo musu Abinci, Yusuf ne yaje ya karɓo ya
dawo ya zauna, Widad bata da niyyar saka kaya, a haka take zaune abunta, Yusuf kam
se ƙureta yake da ido, gaba ɗaya ya rasa sukuni har suka kammala cin Abincin idonsa
a kanta.
Ɗakko zaitun tayi ta miƙa masa, ta koma ta zauna tana cin jiƙaƙiyar aya da Hindu ta
koya mata ci.
Yana shafa mata man yanajin fatarta kamar ze ji mata rauni idan beyi a hankali ba,
Yusuf yace "me kike cine haka?"
Tace "Hindu ce ta bani, ina son wannan abubuwan da Aya, da wata baƙar aba
mulmulmulalliya, da yama sunanta wani abu baƙa cikinsa ja ƙanana me ɗan tsami
tsami"
Yusuf ya jinjina kai yace sannu bagwariya, ɗinya da tsamiyar biri dai ko? "
Haka ya kammala shafa mata mai, se sheƙi fatar take saboda man zaitun daya shafa
mata, yaje ya buɗe Akwatinta ya ɗakko mata kaya, Ya kalleta yace " bari in samiki
"
Yusuf yace "Meyasa ba kyaso? Ai tunda na shafa miki mai saura sa kaya kuma"
Labari ya game gari a game da Yusuf, Nurat tana kwance tana kallon labaran dare a
TV aka nuno zancen Yusuf, ta kaɗu matuƙa da ganin labarin da gudu ta tafi ɗakin
mahaifiyarta tana ƙwala mata kira.
"Ta yaya zanga abunda kika gani? Ina nan kina can"
"Mummy an buga fastocin Yusuf, wai he is wanted shine yayi garkuwa da Widad sannan
yayi da mahaifinta"
Tace "Allah sarki, dama duk abun nan shine ya sacesu aketeta nemansu?"
Nurat kamar ta fashe da kuka tace "Mummy, ki gane me nake nufi mana, wannan abun
duk shirin su Daddy ne, Daddy ne suke ƙulla wannan abubuwan, Yusuf bashi da laifin
komai fa"
Da sauri Mahaifiyarta ta riƙota, ta rufe mata baki tana waige waige, a fusace ta
kalli Nurat tace "waike yaushe zakiyi hankali ne? Kina kallo kwanan nan ya kusa
halakaki, shine kike wannan maganar, maza ki bari ya jiki idan ya ƙarasaki
shikenan"
Cire hannun Mahaifiyarta tayi daga bakin ta ta kalle ta tace "haba Mummy, yanzu
shikenan mu zuba ido babu wani abu da zamuyi, wallahi Umma Yusuf baze sace Widad
ba, ina yaga yadda ze iya sace Daula a gadon Asibiti, shikenan idan baka da kuɗi
baka da gata a garin nan?"
"to dan ubanki kije kiyi tayi, ina gargaɗinkibakan shiga wannan sabgar tasa, akan
ya hana ki fita kawai ya kusa aikaki lahira, amma se sake cusa kanki kike kina bin
diddiginsa, ki cigaba karki fasa, inya kasheki ya kashe banza dukda shiya haifeki,
kinfi kowa sanin takun saƙar dake tsakaninsa da Daula, kuma kin san alwashin da
yayi, ki cigaba da sa kanki a lamuransa, inkin ƙiji ba zaki ƙi gani ba"
"Amma Mummy......"
A fusace tace "Amma me? Kije kiyi dan ubanki karki fasa, fita ki barmin ɗaki"
Jiki a sanyaye ta fito daga ɗakin, tana jin wani irin jiri yana kwasarta, tana
fitowa falo taci karo da mahaifinta, yana shirin fita, suka haɗa ido ya ganta kamar
wata mara gaskiya, tana tafiya a hankali, ya kalle ta yace "ke lafiya kuwa?"
Ba tace masa komai ba, se binsa da tayi da ido.
Yace "jeki ki kiramin mahaifiyar ki" ko kallon inda yake ba tayi ba, ta shige
ɗakinta ta kulle ƙofa, ta faɗa kan gadonta ta fashe da kuka.
Mamaki ne ya kama Alhaji Musa, ya nufi ɗakin Maman Nurat, yaje ya tarar da ita tana
gyara kan mudubinta, ya kalleta yace "to uwar masifa, hala wani abun kikayiwa
yarinyar nan, na ganta a waje na mata magana taƙi kulani"
Wata uwar harara maman Nurat tayi masa tace "masifa harna kaika, daka kusa
hallakata saboda tsabar masifarka da son zuciya, niba wani abun nayi mata ba,
halayenka ne suke baƙanta mata zuciya"
Tace "Ahh gaba ɗaya ka canza mana, kana treating ɗinta kamar ba kai ka haifeta ba,
dole ranta ya dinga ɓaci"
A fusace yace "ƙarya kike munafuka, kece kike zigata, idan ba haka ba ya za'ai in
haifi 'ya sannan kikama kawomin ƙabali da ba' adi, babu yadda za'ayi 'yata ta dinga
min wannan halin na taurin kai, in bake kike zigata ba"
Ta Harare shi tace "au har kamanta tantama kakeyi akan ko kai ka haifeta? Ai baka
da tabbacin kaika haifeta ko ba kai ka haifeta ba"
"Malama karki gayamin maganar banza, Nurat' ya tace nina haifeta, kuma ina son
abata"
Tsaki tayi ta miƙe tace "ƙaryar banza kawai, ji wata fuffuka kake 'yarka ce, bayan
da hannunka ka kusa kasheta"
Banza tayi masa ta shige banɗakinta, ta rufe ƙofa ta barshi a gurin a tsaye.
Juyawa yayi ya fito daga ɗakin, ya kuma kallon ƙofar Nurat, still a rufe take bata
buɗe ba, girgiza kai kawai yayi ya fice abunsa.
Ita kuwa Nurat tana cikin ɗakin, se rusa uban kuka take, tana jinjina zalunci irin
na Mahaifinta, sun haɗa kai sun sace 'yar Daula tare da Yusuf, kuma ya koma sunsa
ace shine yayi garkuwa da mahaifinta, tuna tana iya kukan hawaye na zuba, har tayi
shiru se ajiyar zuciya da take yi.
Da Yamma Widad suna zaune dasu Hindu, kowacce da littafinta tana koya musu karatu,
cikin ikon Allah da yake sunsa kansu, suna fahimtar karatun sosai, duk me tambaya
ta bashi damar ya tambaye ta, dukda idan tare da su Indo take koyawa Hindu karatu
bata wani sakar musu fuska, amma a hakan girmamata sukeyi sosai, saboda bata
hantararsu sam, bayan sun kammala karatun ne kuma ta shiga yi musu bayani akan
tsafta da mahimmancinta, ta shiga ɗakinta ta ɗakko musu pad a cikin wadda Yusuf ya
siyo mata, ta bawa kowa ɗaya, tayi musu bayanin yadda ake amfani da ita, da kuma
yadda zasu dinga kula da kansu lokacin al'ada, kunya suka dingaji suna wani sinne
kai, hakan seda ya kusa bawa Widad dariya, dan sam ba taga abun jin kunya a bayanin
nata ba, suka karɓa suka dinga yi mata godiya, suna nan zaune suna bitar karatun da
tayi musu, ita kuma tana ta faman saƙar mafici da Hindu ta koya mata.
Yusuf ne yayi Sallama, suka amsa gaba ɗaya suna gaishe shi, hannunsa ɗauke da
ledoji, Widad ta kalle shi ta basar tana zumɓura baki, Gwaggo ta harareta, ta gane
kallon da Gwaggon take mata, taje ta karɓi kayan hannun Yusuf ne, aikuwa ta tura
baki tace "mhmm Mama kayanfa da nauyi, kuma ze iya kaiwa ɗakin"
Dariya ta bawa su Indo, dan yadda take haɗe rai tana koya musu karatu, bazaka ce
tana dariya ba, Gwaggo tace "haba yarinyar kirki, aikin ladane fa duk abunda kika
masa yaji daɗi lada zaki samu, ko ba kyason ladan ne?"
"Ina so mana"
Widad ta miƙe ta ƙarasa inda Yusuf yake yana kallonta, tana zuwa ta karɓi leda ɗaya
tana harararsa, Yusuf yace "to mara kunya, ni kike harara ko?"
Gwaggo tace "Allah ya huci zuciyarki, tuba muke, kai kuma haka akeyi, ka samu za'a
karɓi kayan naka shine za kace mata mara kunya?"
Yusuf yayi dariya suka wuce ɗaki, Hari tace "wallahi Wudas ɗin nan ba ƙaramar
taɓararriya bace, gaba ɗayanta gaɓuwa ce"
Me gari kam yana ɗaki yana jin dramarsu, koda ya fito ya kalli Gwaggo yace "Allah
ya saka miki da Alkhairi Hasana, kina ƙoƙari da wannan 'yar taki"
Sukayi dariya, ya koma kan ɗaliban Widad yana cewa "masha Allah, kuna gane karatun
dai ko?"
Ya kalli inda Hanne take zaune, yace "ke ina naki littafin?"
Me gari yace "saboda me banda ita? Ke meyasa ba zaki koya ba? '
"ba kyason ƙaniyarki, kije ki samu Ila, ki gaya masa nace idan yaje kasuwa ya taho
miki da kayan rubutu kema, idan na kuma zuwa na tarar ana karatu bake senaci
mutuncinki"
Kallon me gari tayi, ta yaya ma zata fara zama wannan mara mutuncin, 'yar
wulaƙancin ta koyar da ita? Shiru tayi masa taƙi kula shi, dan ba zata taɓa zama
wannan banzar ta koya mata karatu ba.
Gaba ɗaya Anwar a rikice ya shigo babban falon gidan, ya tarar da Amal da Hajiya
Halima na shirin fita, yayin da Ramlah ke zaune tana zuba Coca-Cola a kofi tana sha
a hankali.
"A'a ni kasan ba wani shiri nake da radio ba, dama da Daula yana nan ne, shine
sarkin labarai da radio saboda kasuwanci"
Anwar ya girgiza kai yace "Mummy, na rasa mema zance miki, yanzun nan naji a
labarai, wai hukumar 'yan sanda sun fitar da sakamakon binciken ɓatan Widad"
Cikin Hajiya Halima yayi wata ƙara, ta dake tace "me sukace, ni sam banji labarai
ba, am ganta ne?"
"Mummy wai ana zargin Yusuf ne yayi garkuwa da ita, ya nemi maƙudan kuɗaɗe da aka
hana shi, shine yayi garkuwa da Daddy"
Wani sanyi ne ya ratsa Hajiya Halima, dan ba ƙaramin daɗi labarin yayi mata ba,
amma ta nuna kaɗuwarta a fili tace "to yanzu ya ake ciki? An kama shi ne?"
"Mummy ba'a kama shi ba, amma ance duk inda aka ganshi ko a mace ko a raye a kamo
shi, Amma ni sam banji na yadda da wannan labarin ba Mummy, ya za'ayi Yusuf ya iya
aikata haka? Yusuf baze wannan abunba, dukda ban daɗe tare da shiba, amma beyi
siffar miyagu ba, ni ban yadda da wannan labarin ba"
"to kar Allah yasa ka yadda mana, ubankane shi, ai a rayuwar nan kai dai kaga mutum
kawai, yana ta shisshigi a gurin me gidan nan da Widad, ashe macuci ne Azzalumi, ai
ba'a gane mugu a fuska tunda kaji an faɗi haka to tabbas ya aikata ne"
Anwar ya girgiza kai yace "gaskiya bazan taɓa yadda ba Mummy, dan yadda akayi aka
sace Alhaji Nasir ba ƙaramin me hikima ne ya shirya faruwar hakan ba, kuma shida
aka sace su ta yaya harya iya dawowa ya sace mahaifin Widad, nifa ina da shakku
akan wannan sakamakon fa"
Ramlah ta taɓe baki tace "ni dama wannan da ganinsa ya saba aikata laifi, kuma
zata iya yuwuwa da wasu ya haɗa kai bashi kaɗai yayi ba, tunda ɗansanda ne yasan
duk wasu hanyoyi na aikata laifi, kuma ba abun mamaki bane dan yayi garkuwa da ita,
tunda yasan da yawa daga sirrikanta, har ATM ɗinta tama bashi, ba inda be sani ba a
ɗakinta, duk wani gantali da zata tare suke zuwa, Allah kaɗai yasan iya abunda suke
yi kaga kuwa ba abun mamaki bane dan ya sace ta"
"ƙarya kikeyi Ramlah!!! Nasani kin sani Wallahi Yusuf baze taɓa iya sace Widad ba,
a gaskiya abun nan ya isa haka, haba dan Allah shikenan a dinga rayuwa babu tausayi
ba imani, mutum beji ba be gani ba a ɗora masa wannan masifar, kun san hkuncin duk
wanda aka kama da laifin garkuwa da mutane kuwa? "
A fusace Hajiya Halima tace " Ke Amal rufemin baki, ya isheki haka, koma meye
hukuncin ina ruwan wani tunda harya iya aikata laifi mummuna irin wannan, yaje ayi
masa duk hukuncin daya dace dashi, ina ruwan wani can ta Matse masa"
Ƙurawa mahaifiyarta ido tayi na wani ɗan lokaci, kawai tayi ƙwafa ta juya da gudu
ta koma ɓangaren su tana kuka.
Kame kame Hajiya Halims ta shigayi "Amm gaskiya Amal yarinyar nan bata da hankali,
tunda ta ƙyalla ido akan yaron nan ta fara sonshi shikenan ta susuce, bata taɓa
yadda ace ga abunda yayi, yaro sekace iblishi, duk yabi ya saye zuciyar mutane da
halin kirki amma yana zagayewa yana cutar da mutane, me siffar munafukai.
Wani irin kallo Anwar yabi mahaifiyarsa dashi, kallon data kasan tantance kallon
meya ke mata, cam yace "koma meye dai, shi Allah ya haramtawa kansa zalunci sannan
hmya haramtashi a tsakanin mu, dan haka yana kallon komai, Mummy be halatta
kidinga saurin yanke hukunci akan abubuwa ba, baki da tabbas akan shiya aikata
dagaske ko kuma bashi bane, amma kin zauna kina ta tsine masa kin aibata shi, nan
akamin ƙazafi aka ɗaureni kika kasa samun sukuni sam, bakya tunanin shima uwace ta
haife shi? Bakya tunanin wani hali take ciki itama a yanzu, kefa uwace Mummy, duk
abunda zakiyi you need to have that feeling as a mother, saboda kema kin haifa,
kuma kome ka shuka duk daɗewa zeyi tsuro ka girbi abunka da hannunka....
LITTAFIN KUƊI NE, DAN ALLAH KI SIYA KAFIN KI KARANTA BA DANNI BA DAN ALLAH, LITTAFI
NA ƊAYA KYAUTA NE WANNAN NA SIYARWA NE
NORMAL GROUP ₦300
VIP ₦500 NE KITURA TA WANNAN ACCOUNT ƊIN
0009450228
JA'IZ BANK
AISHA ADAM
SE A TURA SHEDAR BIYA TA WANNAN LAMBAR
07063065680
MASU FITARMIN DA LITTAFI KUJI TSORON ALLAH, AMANACE TSAKANIN NI DAKU, IDAN KUKA
FITAR BAKUMIN ADALCI BA
11/14/21, 6:09 PM - Ummee Musa: LITTAFIN KUƊI NE, DAN ALLAH KI SIYA KAFIN KI
KARANTA BA DANNI BA DAN ALLAH, LITTAFI NA ƊAYA KYAUTA NE WANNAN NA SIYARWA NE
NORMAL GROUP ₦300
VIP ₦500 NE KITURA TA WANNAN ACCOUNT ƊIN
0009450228
JA'IZ BANK
AISHA ADAM
SE A TURA SHEDAR BIYA TA WANNAN LAMBAR
07063065680
72_73
Saroro Hajiya Halima tayi tana kallon Anwar, har yayi ya gama ya juya ya bar ɗakin.
Hajiya Halima tace "ke me yaron nan yake nufi ne? Naji yana wasu maganganu, kamar
jurwaye me kama da wanka"
Taɓe baki Ramlah tayi tace "dan Allah ƙyaleshi Mummy, kin sanshi da sanyin haki da
kuma tausayi, shi gaba ɗaya kamar bake kika haife shi ba saboda sakalancinsa, kawai
dai surutu ne irin nasa, manta da shi kawai"
Hajiya Halima tayi ajiyar zuciya tace "Saura waccan makirar, bari inje inci
ubanta, tana nema ta tonamin Asiri, 'yar banza mara mutunci"
Ramlah tace "A' a Mummy karki kuskura, kin san haukan Son Guy ɗin nan da take, kina
matsawa ba taƙi ta ɓata komai ba, ki bita a sannu".
Tai ƙwafa tace "yarinya se kace yayi mata Asiri, duk zancen da za'ayi akan yaron
nan seta kawo cikas, dani take zancen dan ƙaniyarta"
"ki daibi a hankali Mummy, dan ba taƙi ta zama rival ɗinki ba, kin san halin Amal
sarai"
"Aikuwa da nayi maganinta, ina uwatta ta zama rival ɗina, amma nikam ba ƙaramin
daɗi matakin nan yayi min ba, gaskiya mutanen nan basu da dama, kinga tunda akayi
wannan sanarwar da an gano shi shikenan, a yanke masa hukunci kowama ya huta"
Ramlah tace "hakane, sedai ita uwar gayyar wani mataki zaku ɗauka akanta, dan bana
tunanin zata bari a rufe shi, ƙaddara ma an rufesh ta yaya za'a karɓi abun
hannunta, dan ba ƙaramar gaddamamiya bace"
"Allah masani, su suka san yadda za suyi da ita, nidai fatana ayi abani kasona
kawai".. Suka kawashe da dariya kamar wasu ƙawaye.
Widad kam suna shiga ɗakin ta ajiye ledar data karɓa a hannunsa, ya zagaya gefenta
ya ajiye na hannunsa ya kalleta yace
"Sannu da gida rigimammiya, tunda baki iya cewa miji sannu da zuwa ba, se tura baki
kika iya"
Kallonsa tayi ba tace komai ba ta sake tura baki, ta nemi guri ta zauna, Yusuf yace
"kin gama da ɗaliban naki ne? Naga kin zauna"
Tace "eh mun gama, na basu assignment ma, sannan nifa na bada kyautar pad ɗin nan,
na basu suma su dinga amfani da su, zan baka kuɗi ka siyo musu brush da toothpaste,
da shaver they need a lot counseling on personal hygiene, naga abubuwan nasu duk se
a hankali"
Yusuf yayi murmushi yace "kaga malama ta gari me son ɗalibanta, naji daɗin hakan
da kika yi dan kin temake su sosai kam, Allah ya baki lada amma a ina kika samu
kuɗi?"
Widad tace "kuɗin sadakina mana, kuma yanzu na iya wannan maficin, Hindu kuma zata
koyamin saƙa ksya, Mama tace idan nayi aka siyar na tara kuɗina, nikuma nace mata
zomaye zan siya nima in dinga ganinsu"
Murmushi kawai Yusuf yayi, Widad akwaita da Wauta wasu lokutan, yace "Sannu sarkin
son dabbobi, gashi nan Na auno mana shinkafa, na siyo mana kifi da gurji da albasa,
zaki ci Abinci me daɗi yau, bari inzo in tsince shinkafar kafin magariba tayi"
Widad tace "tsakuwa kuma? A cikin Abincin ake ganin tsakuwa kuma a ci?waye yake
zubawa"
Yusuf yayi murmushi yace "Eh mana, ke kinma samu me tsakuwar, idan na gaya miki a
inda nake samo me tsakuwar zakiyi mamakin nisan gurin, ko kinga gidan nan ana dafa
shinkafa dukda a haka wai gidan megarine?"
Shiru tayi, tabbas tunda sukazo bata taɓa ganin an dafa shinkafa ba, babban abunda
suka fi ci shine, dankali, rogo, kunu, se kayan rama, zogale da sauran kayan
gargajiya.
Amma abun ya ɗaurewa Widad kai, wai tsakuwa a cikin Abinci, ta kalli Yusuf jiki a
saɓule tace "Sannu da ƙoƙari, Allah ya saka maka da alheri, na tambayi Mama meye
faskare, ta gayamin dama ina son in gaya maka, yakamata Kadena wannan aikin, kaga
jikinka be saba ba"
Yusuf yai murmushi yace "eh jikina yafi saba wa da tuƙa motocinki manya masu AC,
sanyi na ratsani ƙamshin turarenki ya hanani sukuni, shauƙin soyayyarki yaita
ɗibata, gefe kuma anamin tsiwa ana dakamin tsawa, i miss that moment fa"
Dariya ya bata tace "hakama zakace?"
Yace "eh mana, sedai duk da haka nauyin ciyar dake a wuyana yake, dan haka zan iya
kowane aikine muddin be saɓa dokar addini ba dan in ciyar dake, bani da hujjar da
zan tsaya gaban Allah in faɗa na kasa ciyar da ke alhalin inada rai da lafiya, dan
haka karki damu kinji beb" yai maganar yana kashe mata ido ɗaya.
Ta ƙara tabattarwa da kanta da lallai Yusuf na daban ne, shi dai akwai sanyin hali,
ta tuna labarin da Daddynta yake bata akan Yayansa, hakan yana nuna duk masu sunan
haka suke kenan.
Suka gama ci, ya ɗakko rake a leda, yace mata "ga tsaraba na kawo miki, ko shima
baki sanshi ba"
Ta kalli raken ta harareshi tace "sugar cane ɗinne ban sani ba, amma bazan iya sha
a haka ba, yayi min gjrma a baki"
Yusuf yace "toni ba abun in dinga gutsuro miki ina baki ba, kar in sa yawu kiƙi
sha"
Hararasa tayi tace "yawu kuma na nawa, sedai kuma kar a ƙara, ka koyamin ƙazanta
kawai"
"wallahi ban iyaba, dan ban taɓayi ba, kaika fara Yimin"
"Kiss mana" Yusuf yayi dariya sosai, ba ruwanta wasu lokutan sosai yake ganin
ƙuruciya da kuma wautar Widad.
Murmushi yayi, ya samo wuƙa ya dinga sara mata raken ƙanana, tana ɗauka tana sha,
seda suka gama shan rakensu tare, sunayi suna hira,
Yusuf yace "gaba ɗaya kayan ƙwalamar nan na gargajiya sunfi lafiya da inganta jikin
ɗan adam, saɓanin artificial ones ɗin nan, suyi ta haddasa ciwo kala kala"
Widad tace "aikam dai suna da daɗi Sosai, dan bana missing chocolates da ice cream
yanzu tunda ina cin waɗan nan"
Suka cigaba da hira, ba tare da sun yi faɗan da suka saba ba, bayan sun kammala
Yusuf ya gyara gurin, yaje yayi wanka sannan itama ta ɗau bokiti taje ta karɓi
ruwan wanka, Hari taita mita wai zuwa yanzu yaci ace Widad tana wanka da ruwan
sanyi, amma dan gajeren fi'ili kullum se an bata ruwan ɗumi.
Widad bata saurareta ba ta tafi wankanta, bayan ta fito ta shiga ɗaki, ta ajiye
bokitin ta nufi shimfiɗar ta domin sa kaya, tana hasakawa da fitila taga Yusuf
kwance akan katifarta, daga shi se gajeren wando, ya lumshe ido da alama bacci nema
ya ɗauke shi, da farko seda ta firgita ganin sankacecen mutum dogo kwance a gurin,
daga baya kuma taga Yusuf ne.
Ƙafarsa ta haska taga ciwon da yaji yana warkewa a hankali, sannan ta hasak
jikinsa, tun daga kansa har fuskarsa zuwa ƙirjinsa da ƙafafunsa, lulkuɓe suje da
dogayen gashi.
Inda akwatinta suke a gefen Yusuf ne, gashi ya kwanta a gurin, kuma bata son ta
tasheshi dan da alama a gajiye yake, ta zarwle hijjabin jikin ta ta shanya saboda a
jiƙe yake da ruwan wanka, tazo ta zauna kusa da Yusuf tana son ta ɗakko Akwatin,
amma se taga kamar ze tashi, ta ɗan ƙura masa ido, duk ya rame se dogon hancinsa da
yake tsaye kyam, ga ƙasumba data fara fito masa wadda da bashi da ita (kasancwarsa
jam'in tsaro, basa tara gemu) .
A hankali hannunta yana rawa, ta kai hannunta kan sajensa, wanda yake a kwance
kamar na Fulani, a hankali ta dinga shafa gashin ta gangaro har ƙirjinsa inda
gashin yafi yawa, ta dinga wasa da gashin a hankali, tana yi tana zancen zuci,
yunƙurawa tayi zata ɗauke hannunta taji ya riƙe hannunta, zaro ido tayi a firgice
tace "dama idonka biyu?"
Gaba ɗaya ya janyo ta jikinsa, ya kwantar da ita akan katifar, yace "me kike yi ne
tun ɗazu? Duk abunda kike ina jinki fa"
Haɗe rai tayi tace "ɗagani Malam, wai baka san kana da nauyi bane?"
"jika wai se taɓaka nake, me zan taɓa wannan gashin daka tara duk abun ƙyama ma,
abun amai shine ɗin zan taɓa, ni cikani in sa kaya, kar towel ɗina ya cire"
Dariya yayi, ya haska fuskarta da fitila yace "meye abun ƙyamar? Gashin jikin
nawane abun ƙyama ko kume me?"
Rufe idonta tayi tana tura baki, ya kama hannuta ya ɗora akan Ƙirjinsa, yace "da
abun ƙyamane dabe burgeki kin taɓa ba"
Tace "meye abun burgewa anan, sakarmin hannuna ko in tsige gashin nan ɗaya bayan
ɗaya"
"Sarkin daɗin baki, da zakayi politics se an zaɓeka saboda wannan daɗin bakin naka"
A kunnenta yace "ko banyi politics ba, dama ban iyaba amma ina fatan ki zaɓeni a
matsayin abokin rayuwarki Weeeedaat, ina sonki masoyiyya ta, na taɓa soyayya a baya
amma yanzu nake gane a baya shirme nayi, yanzu ne nake Soyayya, saboda ban san
takamaimai a ina nake jin sonki a cikin zuciya ta ba"
Shiru tayi ta ƙanƙame Yusuf tana saurare kalaman da yake gayamata, sedai tun ba'aje
ko ina ba, al'amarin ya fara canza salo zuwa wani abu daban, da fari kamar Widad
zata dake daga baya kuma tace bata san zance ba, ta tubure masa gaba ɗaya, but
Yusuf he shows her the superiority of a Man.
Tashi tayi zaune, ta janyo bargo ta rufe jikinta, tana neman towel ɗinta, yana daga
kwance ya kai hannu ze taɓa ta Amma ta bige hnnunsa, tana ta faman zumɓura baki,
zaune ya tashi shima zeyi magana, amma ta fashe da kuka.
yace "Am sorry please, dan Allah kiyi haƙuri, is not intentionally kuskurene mun
riga munyi shi sedai.. "
Katseshi tayi ta hanyar cewa "eh dama is not intentionally mana, tunda maye kake,
kullum haka kake cemin is wasn't intentionally kuma bayan kana sane, kuma karka
sake cewa munyi kuskure kayi dai"
Yusuf yace "jimin mara kunya, amma ina kwance kika zo inda nake ai"
"kazo inda nake dai, waye yace kazo ka kwantamin akan katifata?"
"Amma dana kwanta akan katifarki, shine akace ki zauna kina taɓani?"
Rasa me zata ce tayi, kawai ta fashe da kuka Yusuf ya lura kukan Shagwaɓa ne kawai
takeji, amma yace "shikenan am sorry, ya isa haka kukan, ba zata sake faruwa ba,
semu kiyaye gaba"
Ƙwacewa tayi daga jikinsa tace "ka kiyaye gaba dai, kawai nayi wanka na zan
kwanta, kawai ka ɓatamin"
Ta cigaba da ƙunƙuninta, ta miƙe ta sake zura hijjabi tayi waje, yayin da Yusuf ya
koma ya kwanta yana murmushi, dan shi wasu lokutan wannan rigimar tata birge shi
take.
Taje bakin rumfar da ake girki ta tsaya daga baya, Hari tayi daren Abinci tana ta
tankaɗe zata tuƙa tuwo, Widad tace "a zubamun ruwa zan wanka"
Ta ɗago ta kalli Widad tace "sannu Agwagwa, ko kuma ince tarwaɗa sarkin wanka, ba
ɗazu Yaya ta zuba miki ruwan kikayi wanka ba?"
"waike sau nawa kike wanka a rana ne? Ke ko ɗan tsallaken nan bakya yi, kullum se
kinyi wanka, ni a rana ma bansan sau nawa kike wankan ba, kuma yanzu ko Awa biyu
ba'ayi da wankan naki ba kin kuma ɗakko bokiti kin dawo"
Widad tace "Allah ya kiyaye inyi fashin wanka, an gayamiki kowa irinki ne? Kawai
mutum ya zauna be wanka ba har ya kwana ya tashi, ni ki zubamin dan Allah"
Hari tace "ko dame kike yawo bazan baki ruwan nan ba, wannan wane irin wanka ne
sekace me iskokai?"
"Zaki zubamin ruwan ko sena gayamiki abunda yasa zan kuma wankan?"
"Ina ruwana da abunda yasa zaki sake wanka, keta shafa mace sekace wata kifi kullum
cikin ta'annati da ruwa, ba dare ba rana, haba ni matsa ki bani guri"
"Hari za'aji kanmu dake a daren nan fa, kin fiye samun ido da shisshigi gaskiya,
zuciya ta na gaya min in faɗi wani abu"
Hari tace "aike in mutum ya biye miki yana tsaye ze bar musulunci seya sake wankan
shiga musulunci"
Widad ta nemi guri ta zauna a tsakar gidan, Hari ta tashi taje ɗaki ɗakko abu,
dukda Widad bata san hayaƙi haka ta toshe hanci, taje gaban murhun ta ɗebi ruwanta
ta ƙara gaba.
Hari na fitowa taga Widad ta kwashe ruwa fiye da rabi, nan ta tsaya ta dinga
zazzaga masifa, Widad ta fito ko takanta bata bi ba tai wucewarta ɗakinsu.
Gwaggo ce taita bawa Hari haƙuri, saboda yadda ta wage maƙogoro tana ta zazzaga
bala'i a daren nan, kuma Widad ta shareta tana ta surutu.
Wani daddaɗan bacci ne yayi awon gaba da Yusuf, dan duk neman maganar data fita
tayi be sani ba, kallonsa tayi taga baccinsa ma yake yi.
"Tasarmin daga kan katifa, zan saka kaya in kwanta" tai maganar tana dukan filon da
yake kai, a hankali ya motsa, ba tare da yace komai ba ya miƙe ya bata guri, shima
ya fita dan yin wankan, ba tare da yasan me Widad ɗin taje ta aikata ba.
Umman Yusuf tana zaune tana lazimi, ta kunna radio, dan gaba ɗaya ji take duniyar
ta mata faɗi saboda rashin Yusuf a gidan, ba ta jin daɗin komai, ji take ta rasa
wani sashi me girma, Tana ta laziminta hankalinta ya ɗauke, jin an ambaci cikakken
Sunan Yusuf a radio yasa ta dawo daga tunanin da take yi, ta maida hankalinta kan
radion ta ɗakkota ta ƙaro sautin.
Rahoton da aka faɗane na bincike ya tabattar da Yusuf ne yai garkuwa da Widad dan
ya karɓi kuɗin fansa yasa tayi jifa da radion a gigice, jikinta ya hau rawa, take
ta fashe da kuka tana girgiza kai, cikin kuka tace
"baze yuwu ba, Yusuf ɗina ba haka yake ba, ni ɗana baze taɓa aikata wannan mummunan
aikin ba, innalillahi wa inna ialaihi raji'un, wayyo Allah ɗana, wayyo Yusuf aikin
ɗan sand be maka rana ba, wannan aiki da kayi yayi silar rushewar farincikinmh, yau
nayi baƙinciki fiye da wanda muka rayu a ciki ni da kai, wayyo Allah ɗana, Allah ka
kuɓutarmin da Yusuf "
Sosai take kuka, kamar zata shiɗe haka tayi zaman daɓaro tana ta rusa uban kuka
babu me rarrashinta, gwanin ban tausayi.
Amal idanunta har sun kumbura saboda kukan da tayi, Hajiya Halima ta shigo ɗakin ta
tarar da ita tace " Haba Autan Mummy, kukan ne har yanzu baki dena ba, haba Amal
ɗina"
Tai maganar tana rungume Amal a jikinta, ta cigaba da cewa "haba Amal, meye abun
kuka, dan Allah ki cire yaron nan daga ranki, kinfi son Asirin Mummy ya tonu a idon
duniya? Kin san bani kaɗai ba har ku ta shafa, duk fafatukar nan da nake danku nake
yi"
Amal tace "Mummy, nasani amma abun yayi yawane, haba Mummy ki duba lamarin nan fa
ki gani, Abunda akayiwa Yusuf yayi yawa Mummy"
Hajiya Halima tace "ke bafa sharri akayi masa ba, tunda akace ya gudu daga hannun
wancan mutanen meyasa basu dawo ba? Kina ta kuka akansa, shi kuma ba kya gabansa
sam, kina kallon yadda ya dinga yanƙwanaki, yana wulaƙantaki shida waccan
fitsararriyar mara mutuncin, suka dinga wulaƙantaki bama ke kaɗaiba harni ba kunya
ba tsoron Allah suka dinga cin mutuncinmu, dan haka meye a ciki dan suma an musu?
Ki dena kukan nan kinji, ki share hawayenki, danku nake wannan faɗi tashin, ki dena
kuka kina ɗagamin hankali kinji"
Haka nan Yusuf yaji jikinsa yayi sanyi, kamar wani abu yana faruwa, jiki a sanyaye
yaje yayi wanka ya dawo ɗaki, Hari tana ganin ya shiga banɗaki da bokiti tace
Babban abun takaicin, Hari ba a hankali take magana ba, Yusuf ji yayi kamar karya
fito daga banɗakin nan saboda nauyin maganganun Hari, a matuƙar kunyace ya fito ya
wuce ɗakinsu, Widad ta lura kamar jikin Yusuf a sanyaye yake, kamar wani abu yana
damunsa.
Ya amsa da "Na'am"
"Dan Allah ka gayamin abunda yake damunka, zaka sani a damuwa fa"
Yaji daɗi a ransa, da yaga ta damu da damuwarsa, "kece kike ganin wani abu yana
damuna, ni lafiya ƙalau nake"
Harya juya ze tafi inda yake kwanciya, yaji ta riƙe rigarsa, tsayawa yayi ya juyo
yaga ta zuba masa ido.
"Yoseef, ba yau nafara ganinka ba, ina gane fushinka ko damuwa, just recently kake
walawala, suddenly kuma mood ɗinka ya canza, me nayi maka?"
"Ni ba abunda kikamin banda bani joy da happiness i ever expected to get"
Yai maganar yana jan hancinta, "kana son ka koma gida ko? Nima na damu mu koma
dukda ina jin daɗin zaman gurin yanzu, amma ina kewar Daddy sosai"
Gyara zamansa yayi yace "Dole ne muyi kewar iyayenmu da masoya Widad, kasancewar
ƙaddararki na kamanceceniya da tawa, sedai sun sha banban, Akwai dalilin da yasa
Allah ya haɗamu a nan, se mucigaba da haƙuri muga hukuncin da Allah zeyi, amma ni
ba abunda kika yi min kinji masoyiyya, ni farinciki kika bani ma, wanda baze taɓa
gogewa a zuciyata ba, I love you so much Baby "
Yai maganar yana rungumeta, ba tace komai ba se murmushi da tayi, Yusuf yana daga
cikin mutanen da bazata manta dasu ba a rayuwarta, dan Ya canza mata gurɓataccen
tunaninta, yayi sadaukarwar da bata taɓa tunanin wani zeyi akanta ba, yana haƙuri
da dukkan halinta me kyau ko akasin haka.
Ya nisa yace "bari in baki guri ki kwanta, nasan lokacin baccinki yayi"
Dukda a cikin duhu ne, amma ta niƙe kafaɗa tace "mu kwana anan tare mana"
Murmushi yayi yai ƙasa da muryarsa dai dai kunnenta yace "haka kawai inje wani abu
yafaru, kiyi ta haɗemin rai kina hararata, yanzu ma ban san yadda akayi ba naga an
ƙyaleni, dukda haka ban fidda ran da safe inga an ɗauremin fuska ba"
Yusuf ya gyara kwanciyarsa yace "as you wish your majesty, ni dama haka nakeso,
saboda hakan yana ƙara danƙon soyayya a tsakanin ma'aurata"
Bata kula shi ba, sedai sake shigewa da tayi jikinsa sosai tana lumshe ido.
"shhh, lokacin bacci yayi kayi bacci kawai, bana son in ƙara maka damuwa"
Haka suka wanzu a haka, bacci ya ɗauke Widad yayin da Yusuf ya kasa samun nutsuwa,
yana sake ji a jikinsa akwai wani abu mara daɗi dake faruwa a wani guri, wanda
hakan ya shafeshi ko kuma ya shafi Widad.
LITTAFIN KUƊI NE, DAN ALLAH KI SIYA KAFIN KI KARANTA BA DANNI BA DAN ALLAH, LITTAFI
NA ƊAYA KYAUTA NE WANNAN NA SIYARWA NE
NORMAL GROUP ₦300
VIP ₦500 NE KITURA TA WANNAN ACCOUNT ƊIN
0009450228
JA'IZ BANK
AISHA ADAM
SE A TURA SHEDAR BIYA TA WANNAN LAMBAR
07063065680
IDAN KUMA KIN SIYA AMANACE KARKI FITARMIN DAN ALLAH 🙏🙏🙏
11/14/21, 6:09 PM - Ummee Musa: LITTAFIN KUƊI NE, DAN ALLAH KI SIYA KAFIN KI
KARANTA BA DANNI BA DAN ALLAH, LITTAFI NA ƊAYA KYAUTA NE WANNAN NA SIYARWA NE
NORMAL GROUP ₦300
VIP ₦500 NE KITURA TA WANNAN ACCOUNT ƊIN
0009450228
JA'IZ BANK
AISHA ADAM
SE A TURA SHEDAR BIYA TA WANNAN LAMBAR
07063065680
IDAN KUMA KIN SIYA AMANACE KARKI FITARMIN DAN ALLAH 🙏🙏🙏
74_75
Yadda Uman Yusuf taga rana haka taga dare, gaba ɗaya ta rasa wanda zata kira ta
gayawa halin da take ciki, unguwarsu kuwa tuni labari ya cikata, akan ga abunda
Yusuf ya aikata, beji ba be gani ba an ɗaura masa mugun sharri, wasu suna ƙaryene,
wasu suna ba'a shedar mutum.
Mata suka dinga shiga da nufin suyi mata jaje, hadda wanda tun ɓatan Yusuf basu yi
mata jaje ba, se yanzu da wannan labarin ya fasu.
Saleh ne a office ɗin Suleiman, ya kai gwauro ya kai mari, ya kalli Suleiman yace
"ni gaba ɗaya kaina ya rufe ruf, na rasa me yakamata inyi, gaba ɗaya mutanen nan
sun shammaceni, banyi zaton ta nan zasu ɓullo ba, duk yadda nake tunanin zaluncinsu
sun wuce nan, na rasa mema zanyi ko me zance"
Suleiman dake zaune akan kujera yai shiru, ya nisa ya ɗago daga jinginar da yayi
yace "ni kaina bansan me zan iyayi ba, naje na samu Sp amma yaƙi saurarata, wai
sakamakon da aka bashi shiya sanar, nabi duk nayi ƙoƙarin da zan iya, na tuntuɓi
masu ruwa da tsaki akan abun, amma kowa ya nunamin ba ruwansa, ma'aikatan gidan nan
gaba ɗaya hankalin mu a tashe yake, kuma nasan muddin mukayi wani yunƙuri, to muma
baza'a barmu ba, zasu ɗau mataki akanmu ne, amma yanzu meye abunyi? "
Saleh yace " Abunyi be wuce inje in ƙara tabattar da na toshe duk wata kafa, wadda
zata sa a gane inda suke ba, sannan in ja masa kunne da wannan uwar taurin kan
yarinyar, akan duk tsanani karsu sake su bar gurin nan, idan har bani ne naje nace
su baro gurin ba"
Suleiman yace "gaskiya, ka gaggauta zuwa ka same su kam, sannan ni gaba ɗaya kunyar
mahaifiyar Yusuf nake ji, ban san me zance mata akan wannan al'amarin ba, ni nake
bata ƙwarin gwiwa akan ɓatan nan nasa, akazo kazo da labarin sun kuɓuta, amma still
hankakinta a tashe yake, ban san ya zata yi ba idan ta samu wannan Mummunan labarin
"
Saleh yace " dole zata damu sosai, Amma haka nan za'ayi ƙoƙari a kwantar mata da
hankali, dan barinta haka babu me rareshinta shima wata babbar matsala ne"
Suleiman yace "hakane, ubangiji Allah ya shiga lamarin bayinsa, bari in tashi
insha Allah zanje in gaisheta, a sake bata haƙuri da kwantar mata da hankali"
Daren Yau kusan kwana su Alhaji Haruna sukayi suna meeting, sunyi farincikin da jin
mafitar da Bukar ya samo musu, dan ba suyi zaton irin wannan mafitar ze kawo musu
ba, dan haka yanzu kallo ze koma ga sauraren 'yan sanda aga ta inda zasu fara kamo
Yusuf.
Alhaji Musa yace "yanzu idan aka gano su, yaya zamuyi da wannan shu' umar yarinyar
me jarababben taurin kan bala'i"
Alhaji Munir yace "kai dai bari, yau shekaru kusan goma muna bibiyar abun nan,
amma 'yar masu baƙin halin yarinyar nan ta hana, ba abun mu kashe ta ba kuma muzo
muyi biyu babu"
Alhaji Haruna yace "idan muka kashe ta ai kuma zamu tashi a tutar babu ne gaba
ɗaya, ya zamana duk wannan wahalar ta tashi a banza, ai yadda naji Bukar yace, shi
wannan ɗan sandan yaron da an kamosu shi zamu fara kawarwa, saboda Kasancewar sa
tare da ita matsala ne a gare mu, idan aka kauda shi, itakuma tunda babu wanda
yasan inda ubanta yake, zamuyi poisoning ɗinta ne, a fita da ita waje neman lafiya,
idan yaso kodai ta faɗi inda suke kokuma a aikata"
Alhaji Munir yace "Amma fa kun san rashin sanin inda Daula yake, itama wata babbar
barazana ce me zaman kanta, muna ruwa fa idan Daula ya bayyana bamu samu abun nan
ba, yakamata ace mun san inda yake a hallaka shi tunda wuri"
Alhaji Musa yace "Ai ana nan kan bincike, an duƙufa sosai gurin gano inda yake,
kuma akwai alamun nasara, sannan idan aka gano shi kasheshi kawai za'ayi, karma a
ɓata lokaci, tunda dama an bada sanarwar duk wannan yaron shine yayi garkuwa dasu"
Alhaji Haruna yace "nifa a gurin nan kamar anyi wauta, in ba hakaba ta yaya za'ace
waishi ne ya sace Daula, duk tsaron dake Asibitin nan"
Alhaji Musa yace "nima da nayi wannan tunanin, amma Bukar yace ya san abunda yasa
yayi hakan, ni wai ya maganar wannan yaron da muka yi magana, Barrister Hafiz, har
yanzu bece mana komai game da abunda suka yanke ba"
Alhaji Munir yace "Aishine, yau kusan sati biyu amma babu wani feedback, idan ba
zasuyi ba kawai muje mu haɗo kai da banki, mu kunno wata wutar"
"Ahh ayi takkaddun boge mana, ace ana bin kasuwancinsa wasu mahaukatan kuɗi mana,
idan yaso se muyi agreement da bankin, mu basu wani percentage"
Alhaji Musa yace "amma fa kasan Daula baya cin bashin banki?"
Munir yace "Nida kai muka san wannan, sauran mutane basu sani ba, dan haka muyi
tunani akai, idan can baze samu ba se mubi nan, kasan na san Ambassador Auwal
Inuwa, kuma kunsan suna da banki, komai zezo da sauƙi"
Haka suka cigaba da ƙulla tsiyatakunsu, kala kala babu ko tsoron Allah a ransu.
Nurat a wuni ɗaya amma gaba ɗaya ta zube ta rame saboda zunzurutun damuwa da
tunani, tana tunanin irin hukuncin da za'ayiwa Yusuf idan har aka gabatar da shi a
gaban kotu, tana tunanin wannan zalunci ace an sace mutum, kuma a koma da baya a
ɗora masa laifin da hukuncunsa daze iya sanadiyyar ɓata feature ɗinsa, tunani ta
shiga yi, me za tayi wanda zesa ta samu abunda zata taimaki Yusuf dashi idan
buƙatar hakan ta taso?
Ta ɗakko wayarta ta kira Anwar, sedai wayarsa bata shiga sam, ta kuma jarraba layin
Khalil amma shima se ace mata busy, ƙarshe dai se haƙura tayi ta ajiye wayar ta
maida kai ta kwanta.
Yanzu ɗaliban Widad in sunzo, suke mata wanke wanke da shara, dukda ta nuna bata so
amma sesu dage se sunyi, suna matuƙar sonta, dukda bata da fuska amma tana jansu a
jiki tana koya musu abubuwa da dama.
Yau Habi ce ta taho mata da soyayyiyar gyɗa me ɓawo, kusan kwano guda tace babarta
ce ta kawo mata, Widad tace "Aini dan Allah nake koyar daku, ba dan ku bani wani
abuba, ina dai roƙonku ku dingamin addu'a, amma ni base kun biyani ba, kuma duk
wanda yake sha'awar koyar wani abu, ko abunda nake koya muku ƙofata a buɗe yake
yazo ya koya"
Gwaggo tace "Amarya ba kyau maida hannun kyauta, ai basu isa sun biyaki abunda
kike koyar dasu ba, jin daɗin abunda kike musu ne yasa suka baki, ki karɓa kawai"
Habi tace "yawwa Gwaggo, wallahi ba zamu biyata ba kam, amma dan Allah malama ki
karɓa"
Da ƙyar dan Gwaggo tasa baki sannan ta karɓa, bayan tafiyar su Gwaggo ta cigaba
dayi mata nasiha, na cewar zasu ga kamar wulaƙanci ne yasa bata karɓar abu idan sun
bata.
Tafiyarsu keda Wuya kuma, megari ya shigo, yanzu Widad tana sakin jiki ta
gaisheshi, harma wasu lokutan ya dinga tsokanar ta, ya shigo yara suka biyoshi da
manyan ƙwarya, ɗaya an shaƙeta da ƙwan zabo, ɗaya kuma Nono ne a ciki, megari yasa
Hindu ta kira Widad, ta fito suka gaisa yace "Nasan Malam Yusuf be dawo ba, ga
wannan inji ɗalibansa suka ce a bashi"
Abun ya bawa Widad mamaki, mutanen ƙauyen nan sudai suna girmama malamai, kuma suna
da rige rigen son suga sun kyautatawa mutane, saɓanin irin rayuwar da ake a birni,
mutum yana ganin ɗanuwansa a matsala amma ya share, koma a haɗa kai dashi a cutar
da mutum.
Widad ta karɓi kayan tace "to Baba, Yoseef ya gode sosai zan gaya masa idan ya
dawo"
Megari yayi murmushi yace "bagwariyar 'yata, Yusuf ake cewa ba Yoseefa ba"
Widad tayi murmushi tace "na kasa gyarawa, kuma shima ai yafison in ce masa Yoseef
ɗin, kona fara cewa Yusuf se in manta"
Megari yace "Ahh masha Allah, tunda me gidan da kansa haka yakeso gara a kira shi
da hakan"
Widad ta ɗau kayan zuwa ɗakinsu, Hari tace "wai me gida duk kayan nasu ne gaba
ɗaya mu kuma fa?"
Yace "ke dai Allah ya shiryeki, nan har siyar da ƙwan zabo kike a gidan nan dana
kaji, baki taɓa dafawa kin bawa kowa ɗaya a gidan nan ba, a gabanki dai na faɗa
nace ɗalibai da yake koyar damu a masallaci sune sukace a bashi, zalamammiya kawai"
Ya wuce ɗakinsa yana cigaba da mita, Widad taje ta samu guri a ɗakinta ta ɗauki
gyaɗar da aka bata tana ci, Yusuf ya dawo ya tarar da ita.
Raba gyaɗar take biyu da bakinta, idan ta fito shikenan, idan bata fito ba ta haɗa
da ɓawaonta ta cinye kayarta.
Seda Yusuf yaci dariya sannan ya nuna mata yadda ake ci, tace "ga wannan kayan,
Megari ya bani yace a baka inji ɗaliban ka"
Yusuf ya kalli yawan Nonon nan da ƙwan zabi aƙall zeyi guda hamsin, yanzu ma a
hanya wani ya tareshi ya bashi Albasa.
Yusuf ya jinjina kai yace "Ni wallahi kunyar karɓar kayan nan nakeji Widad, nifa
saboda Allah nake koyar dasu"
Widad tace "nima kaga duk yawan gyaɗar nan haka suka bani, nace bazan karɓa ba Mama
taitamin faɗa"
Widad ta Harare shi tace "ai sedai ka maida wannan albasar, amma baza'a maida
wannan ƙwan da madarar nan ba"
Yusuf yayi murmushi yace "wai yau uwa ɗakina aka bawa kyauta ta karɓa, har take
baza'a mayar ba, saɓanin da kana bata abu zata ce ka rainata, ko zaka cutar da ita"
Widad ta ɗan ja ajiyar zuciya tace "baka manta faɗanmu akan kayan daka bani ba ko?"
Yusuf yaje yayi musu godiya da karamcin nan da suka yi masa, suka ce yafi ƙarfin
haka a gurinsu, tunda yake koya musu karatu ai ya gama musu komai.
Yusuf haka ya karkasa kayan nan, yayi rabonsu a cikin gidan nan, Widad kam taji
daɗin ƙwan nan da Nono, dan Abinci ma seta ga dama take ci.
A hankali ɗaliban Widad suka ƙara yawa, harda ƙana nan yara, ta koya musu na boko
ta koya musu na Addini.
Yauma wajen ƙarfe biyar na Yamma, tana ƙoƙarin sallamar ɗalibanta ƙananan yara,
sega Saleh yazo, Kallo ɗaya Widad tayi masa ta ɗauke kanta, jin Sallamar wasu ne
yasa ta sake ɗaga kai ta kalle su, Saleh ne shida wani mutum, da wata mace da
manyan Akwatunan su.
Mutan gidan ne suka ruɗe da shewa ganin mutanen da suka shigo tare da Saleh, da
alama dai sun san mutanen, Maida kai Widad tayi ta cigaba da abunda take.
Matar ba zata wuce shekaru Ashirin ba, ta kalli Widad tace "Gwaggo ina muka samu
balarabiya ne?"
Wadda suka kira da Jamila tun shigowarta, yara suka karɓi jaririyar bayan ta, ta
kalli Widad tace "Sannunki" kallonta kawai Widad tayi tai shiru.
Hari tace "iya shege ne, tana ji sarai kulaki ne da ba zata yi ba, haka take
wannan wulaƙancin"
Yanzu ma kallon Saleh tayi ta ɗauke kai, yai murmushi yace "Ina Yusuf ɗin yake
ne?"
Ai kamar da yana magana da dutse, wanda suka shigo tare da Saleh yace "to wannan
da alama 'yar Mulki ce dai"
Ƙarshe da Widad taga zasu takura mata gaba ɗaya seta bar musu tsakargidan ma, ta
koma ɗaki.
Baƙin nan suka shiga ɗakin Gwaggo, suka ajijiye kayansu, mutan gidan sunata
farincikin ganin Jamila, da mijinta da kuma jaririyarsu.
Saleh da mijin Jamila wato Sunusi, suka shiga turakar megari, bayan ya sallami
baƙinsa ya shigo ya tarar dasu, megari yayi murmushi yace "Soja marmari daga nesa,
ya akayi kuka haɗu?"
Saleh yace "A tasha na gano su sunzo hutu, muka hawo akorikurar shu'aibu tare ya
kawomu gida"
Sunusi yace "duk muna lafiya, gamu munzo muyi muku hutu"
"eh babu laifi, amma Nasan kun kwasarwa yarinyar nan iskar hanya, dan ko Arba'in
basu rufa ba"
Sunusi yace "Baffa ya za'ayi, ta matsa ita dai tazo gida, kasan can inda muke babu
hausawa sosai, zaman se a hankali gaba ɗaya"
Megari yace "hakane, Allah yayi mana jagora gaba ɗaya, Saleh ya ka baro binni, da
mutan kanon Dabo?"
"kowa lafiya ƙalau, na shigo ma ban tarar da Yusuf ba, se ita matar tasa, nayi
magana kuma ta shareni"
Megari yace "Malam Yusufa be dawo ba ai, aini tunda nake ban taɓa ganin Yarinya
meji da isa kamarta ba, akwai mulki kam, ni kaina na daɗe bata saba dani ba, ko
gaisheni ba tayi, ba ruwanta da kowa daga mijinta se Hassana (Gwaggo), se a hankali
kuma ta fara sabawa dasu Hindu, se daga baya kuma na gane ɗabi'arta ce rashin yadda
da saurin sabo, amma tana da kirki sosai "
Saleh yace " Ai Baffa baka ga komai ba, in dai mulki da ji da kaine, ba abunda ka
gani, yanzu ai ta sakko ta saki jiki daku sosai, Amma ai bata da yadda sam"
Sunusi yace "to meyasa, nima daga zuwana na gani, Jamila na mata magana tayi banza
da ita, kaima kayi mata ta share"
Saleh yace "idan na gaya maka wacece ita, seka riƙe baki abar maganar kawai"
"Haba wane mutum, aini zuwansu garina Alkhairi ne wallahi, basu takurani ba sam,
sedai ina tunanin kana ganin babu wata matsala zamansu anan ɗin, nifa matsala ce
bana so"
Saleh ya nisa yace "babu wata matsala Insha Allah Baffa, amma zamansu anan shine
tsira da rayuwarsu, zuwa wani ɗan lokaci insha Allah zasu bar nan, ni dai fatana a
cigaba da haƙuri dasu"
"Saleh aini zuwansu nan alkhairi ne, baka tarar da yara gidan nan ba? Da Asuba ko
magariba shi Yusuf ya koyar da karatun Addini, gashi da ladabi, ba hantara ba cin
mutunci yake gyaramana kwaɓar da mukeyi, da Yamma kuma ita ke koyar da yaranmu
darussan boko, da Addini, kasan mu babu makarantu haka na muke zaune da jahilci se
ɗan abunda ba'a rasa ba"
"daka shigo ba kaga yara da 'yan mata a gidan nan ba, dukda gidan nan na mutane ne
amma karatu take koya musu"
Se daf da magariba sannan Yusuf ya dawo, Yusuf be tarar da Saleh ba dan haka ya
gaisa da su Hari ya wuce ɗaki, yana zuwa ya tarar da gimbiyar ta cika tayi fam,
kallo ɗaya yayi mata yace "Subhanallah, me kuma ya faru? Ko nine na miki wani
abu?"
Girgiza masa kai tayi tace "A'a, Saleh ne yazo na ganshi shi da wasu, na kasa
yadda hankalina yaƙi kwanciya, ban san suwaye ba"
"To shine zaki ɗaga hankalin ki haka? Ki bari muji ta bakinsa mana"
"A'a, nifa bana son irin wannan abun, ko dai musan suwaye, ko kuma wallahi bazan
kuma kwana a garin nan ba, komai dare sena bar garin nan"
Yusuf yace "yi haƙuri ki kwantar da hankalinki, zan masa magana idan mun haɗu a
gurin salla"
Bata son tayarwa da Yusuf hankali, shiyasa ta ƙyaleshi, kamar yadda ya zata sun
haɗu da Saleh a masallaci, bayan sun idar da salla, suka gaisa Yusuf yace "kwana
biyu, yau kusan watanka guda rabonka damu"
Saleh yace "wallahi kuwa, abubuwa ne sun ɗanmin yawa, ai ɗazu naga gimbiyar taka,
na mata magana juyin duniya taƙi kulani, a gaban mutane"
Yusuf ya ɗanyi murmushi yace "kasan dama kuna takun saƙa da ita, kuma ta ganka da
baƙi bata san kosu waye ba, dole ba zata kulaka ba"
Yace "hakane, amma duk da haka yakamata ko gaisawa muyi, ina gaisheta amma ko kallo
ban isheta ba"
'hmmm Yusuf kenan, in dai wannan ce babu ranar gyarawa, baƙin da take magana kuma
ba wasu bane, mata da miji ne, namijin shima ɗan megarine, matar ma kusan haka, ya
tashi da' yan fitintunu ne baya ji, ga yawon tsiya se a shafe watanni uku huɗu, ba
a ganshi ba, shine na ɗauke shi na kai shi makarantar horar da sojoji, to beyi
karatun boko ba, dan haka kurtu ne yana barrack suna gadin gidan wani babban hafsin
soja, shine yayi Aure ya tafi da matar, yanzuma ya samu hutun ƙarshen shekara ne,
ga matar ta haihu shine muka haɗu a tasha sunzo gida, suyi hutunsu a nan amma banda
haka babu wani abu, amma kai ɗan sanda ne ai, zaka iya bincikawa"
Yusuf yace "A'a babu buƙatar hakan, gara ta sanine ai, kasan bata da yadda"
"Hakane, amma ayi haƙuri dai, yanzu meye labari? Ya ake ciki a gida?"
Saleh ya ɗanyi shiru sannan yace "Yusuf labari ba daɗi kama, sedai fatan ubangiji
Allah ya shiga lamarin"
"Saleh, dan Allah kamin bayani gwari gwari mana, ban gane labari babu daɗi ba, aani
abune ya samu Ummana? Ko mahaifin Widad? Ko kuma wata matsalarce ka gayamin mana"
Saleh yace "kwantar da hankalinka babu ɗaya, mahaifin Widad dai kamar yadda ka
sani, har yanzun babu wanda yasan inda yake se Allah, ana ta bincike amma shiru, ko
yana hannunsu, ko yana wani gurin Allah ne mafi sanin wannan, sannan mahaifiyarka
tana lafiya, mun rabu da Suleiman akan zeje ya gaishe ta ma, sedai....... " Se
kuma yayi shiru.
" Se kuma me? Dan Allah ka gayamin kana ɗagamin hankali fa"
"Yusuf jin meke faruwa bashi da wani amfani a gareka, abun da nake so da kai shine,
kayi taka tsantsan gurin zuwa cin kasuwar nan da kake yi, sannan ka ƙara tsananta
Addu'a, kuyi haƙuri kunci gaba da zama anan, dan sun saka a nemoku duk inda kuke"
Yusuf ya dafe kai yace "Innalillahi wa inna ialaihi raji'un, yanzu meye abunyi?
Zuwa yaushe ne zamanmu ze ƙare anan, kar mu takurawa mutan gidan, sannan kuma
cigaban zamana da Widad a inuwar Aure shima matsala ne babba, babu wanda yasan
batun Aure mukayi se kai"
Saleh yace "batun takura, baku takura musu ba, dan munyi magana da megari, sannan
Aurenku aini na san anyi, ina da sheda, kawai Allah yasa ku kawai Daula jika"
"Saleh, why are you not serious about this issue? Bafa abun wasa bane, wani irin
kallo mahaifinta zemin, wani suna ze kirani dashi idan har muka koma gida da ɗa?"
"Ahh kallon siriki ze maka mana, karka damu Daula ba baƙon zafi bane, idan har
'yarsa tana ƙaunarka, kaje ka tabattar da irin son da take maka tukuna, nidai
fatana iya wuya, idan bani nazo nace kubar gurin nan ba, kuyi zamanku anan, ka koma
maza karta fara zargin wani abu "
Har Yusuf ya shiga cikin gidan jikinsa a mace yake, gaba ɗaya ya easa meye yake
masa daɗi, Saleh ya sake dagula masa lissafi, yanzu idan aka gano inda suke shida
Widad meye sunansa? Idan ya kasance Widad ta samu juna biyu meye makomar yaron,
sannan yayi mata adalci makuwa, idan har ya bari suka haɗa zuriya da ita, bayan
bata san shi waye ba, ba tasan mecece tasa ƙaddarar ba balle yaji hukuncin da zata
ɗauka akansa? Baya tunanin ɗorewar Alaƙa a tsakaninsu muddin taji waye shi, ba ita
ba hatta mahaifinta baze farinciki ya zamo siriki a gareshi ba.
LITTAFIN KUƊI NE, DAN ALLAH KI SIYA KAFIN KI KARANTA BA DANNI BA DAN ALLAH, LITTAFI
NA ƊAYA KYAUTA NE WANNAN NA SIYARWA NE
NORMAL GROUP ₦300
VIP ₦500 NE KITURA TA WANNAN ACCOUNT ƊIN
0009450228
JA'IZ BANK
AISHA ADAM
SE A TURA SHEDAR BIYA TA WANNAN LAMBAR
07063065680
IDAN KUMA KIN SIYA AMANACE KARKI FITARMIN DAN ALLAH 🙏🙏🙏
11/14/21, 6:09 PM - Ummee Musa: LITTAFIN KUƊI NE, DAN ALLAH KI SIYA KAFIN KI
KARANTA BA DANNI BA DAN ALLAH, LITTAFI NA ƊAYA KYAUTA NE WANNAN NA SIYARWA NE
NORMAL GROUP ₦300
VIP ₦500 NE KITURA TA WANNAN ACCOUNT ƊIN
0009450228
JA'IZ BANK
AISHA ADAM
SE A TURA SHEDAR BIYA TA WANNAN LAMBAR
07063065680
IDAN KUMA KIN SIYA AMANACE KARKI FITARMIN DAN ALLAH 🙏🙏🙏
76_77
A haka Yusuf ya ƙarasa ɗakinsu, yana zuwa ya zauna yayi shiru ya zurafafa a cikin
tunani.
"Meya gaya maka haka, wanda ya jefa ka cikin wannan dogon tunanin?" yaji muryar
Widad.
"Har yanzu fa ban canza daga Widad ɗin daka sani ba, bana son ƙarya bana son ɓoye
ɓoye, ka gayamin tun kafin kaima in saka a Jerin wanda nake zargi"
"zargin zaku haɗa kai ku cutar dani, in ba haka ba, meye na ɓoyemin wasu abubuwan
da dole nasan sun shafi rayuwata?"
Yusuf ya kalle ta yace "har yanzu kina tunanin zan iya kasancewa cikin masu cutar
dake?"
"Yoseef, zuciya bata da ƙashi ya kamata kamin uzuri, musamman a irin rayuwar da na
tsinci kaina, amma ya kamata in dinga sanin al'amuran da suka shafeni"
"Ba wani abu bane, dama ya gayamin muƙara haƙuri da zama anan ne, saboda ana can
ana nemanmu, maƙiyanki sun baza komar anemomu, tunda tuni labarin guduwarmu ya
iskesu, sannan baƙon da suka zo tare, shima ɗan uwansane, soja ne sunzo hutune
shida matarsa, shikenan "
Ba tayi magana ba, se riƙe gashin kanta da tayi, sekuma ta shiga jan numfashi tana
zazzare ido, ta dunƙule hannunta, tana girgiza kai.
A Rikice Yusuf yace " Subhanallah, lafiyar ki kuwa Widad? Meyafaru? "
Girgiza kai take hawaye na zuba daga idonta tace " almost ten years, good ten years
ana cutar dani, bani kaɗaiba har wanda ya raɓeni, yana ɗaya daga abunda ya nesanta
ni daga mutane, bana son rayuwar wani ta shiga matsala saboda ni, amma ƙaddara ta
haɗa rayuwarka da tawa kana ta faman wahala, an cutar dani an kassara lafiyata, an
cigaba da bin diddigina ana son ganin bayana saboda abun duniya, kuma aka jefa
ƙiyayyata a zukatan jama'a suka koma gefe suna zagin AƘIDATA, Insha Allah bazan
mutu ba sena ga bayan maƙiyana, ko kuma mu yi mutuwar kasko nida su, i can't
tolerate it anymore "
Tai maganar tana jifa da kayan gurin, sannan ta yunƙura zata miƙe, Yusuf ya riƙeta
gama, fizge fizge ta dingayi tana kai masa duka tana nema ta ƙwace daga hannunsa,
ya riƙeta sosai yana mata addu'a, surutai take sosai cikin ɗaga murya, idan Yusuf
yasa hannu ya toshe mata baki, se taita kai masa duka, idan ya riƙe hannunta kuma
seta hau surutai, yana gudun hankalin mutane ya dawo kansu, dan sam baya son wani
yasan tana da larurar taɓin hankali, dan haka kawai ya haɗe bakinsa da nata.
Tun tana mimmiƙewa tana son ta ƙwace, harta gaji jikinta yayi sanyi, Numfashi take
saukewa a hankali, hawaye na bin gefen idonta, seda yaga ta dena fizge fizgen
sannan ya cire bakinsa daga nata, ta lumshe idonta kamar me bacci, Yusuf ya
rungumeta yana cigaba da karanta mata duka Addu'ar da tazo bakinsa.
Widad ya kira sunanta, ɗaga masa hannu tayi alamar ya ƙyaleta, sun daɗe a haka
sannan ta tashi zaune, Yusuf ya kalleta yace "Sannu"
Jinjina masa kai kawai tayi ta sunkuyar da kai, ya riƙe hannayenta yace "dan Allah
kidena saka damuwa a ranki, kinga hakan yana shafar lafiyarki"
"bazan iya dena damuwa ba, saboda an diga an gama kassara rayuwata, bana jin zan
samu nutsuwa har se ranar da na gamsu, na ɗau fansar abunda akayimin"
"Rayuwa ba zata tafi a haka ba, lafiyar ki abun dubawa ce, kalli yadda lokaci ɗaya
kika fita hayyacinki fa"
"Ai dama ba lafiyar ce dani ba, dan haka ba wani abu dan na ƙarasa a haka"
Kawai ta rufe bakinta da hannunta tana kuka, Yusuf ya shiga share mata hawayenta,
yana cewa "ke lafiyayyiya ce, kuma ina miki fatan samun lafiya me ɗorewa"
Tai murmushi me ciwo tace "wai in warke daga haukan? Ko ciwon zuciya?"
Yusuf ya ɗanyi shiru sannan yace "nifa akwai ranar da naga an saka miki wata ƙwaya
a cikin tea, amma baki sha ba, shiyasa nake da question mark akan wannan ciwon
naki"
Seda tayi shiru na wasu lokuta, sannan ta gyara zamanta tace "Bayan an kashe
Ammina, ɗaya daga cikin wannan mutanen, ya ɗakko wayarsa ya fara waya, yayi wayarsa
ya gama sannan ya kalli sauran yace, ku cajemin gidan nan, akwai wata yarinya, ku
kawomin ita nan, Widad na tsaye tana jinsu, bata ko motsa daga inda take ba, suka
fito suka shiga bincike gidan nan, amma basu ga Widad ba, suka dawo sukace "mun
caje ko ina a gidan nan bamu ga yarinyar nan ba"
Yace "ta yaya za kuce baku ganta ba, bayan tana cikin gidan nan?"
Suka haɗu har dashi suna dubawa, sun wuce ta inda Widad take yafi sau uku, amma
Allah besa sun ganta ba.
Suka sauka ƙasa falo, babban ya sake kiran waya, ya sanar da wani cewar sun duba
kaf basu ga Widad ba, kawai Widad ji tayi yace " An gama Oga.... "
Bata iya jin cikakken sunan daya faɗa ba, kamar taji dai dai kamar kuma ba daidai
ba.
Babban yace "kai mu tafi, Oga yace yasan yadda zeyi da ita, mu ɓace kafin a gane
munzo"
Haka suka rankaya suka fita, cikin sanɗa Widad ta sakko daga kan benen, ta sakko
falo taje ta leƙa taga, taga sunyi maganganu da Bala, sannan ya buɗe musu ƙofa suka
fita.
Widad ta juya ta koma kan bene, ta koma ɗakin da Amminta take cikin sauri, tana
zuwa ta tarar da ita a yadda ta batta.
Widad ta shiga jijjigata tana kiran "Ammi ki tashi mutanen sun tafi, baki ji ciwo
bako?"
Ganin Ammin nata bata motasa ba yasa tace "Ammina bacci kikayi ne? Ko kuma sanyi
kike ji?"
Nanma bata samu amsa ba, dan haka ta ɗakko bargo ta lulluɓeta, itama ta shiga
bargon ta rungume Ammin nata, daga nan bacci yayi awon gaba da ita.
Dukda Kasancewarta yarinya ƙarama, amma da Asuba Amminta ke tashinta salla, Asuba
tayi Widad ta tashi taje tayi salla, Amma Amminta bata motsa ba, ta sake zuwa ta
kwanta a jikin gawar ta koma bacci, har kusan ƙarfe tara na safe Widad ta farka, ta
shiga girgiza gawar Ammin tana "Ammi ki tashi bakiyi salla ba, kuma yunwa nake ji,
Ammina ki tashi ina jin yunwa, Ammi Abinci" haka Widad ta cigaba da hayyata irin
tasu ta yara, ba tare da tasan Ammin mutuwa tayi ba.
Tana nan zaune, ta gaji ta shiga wasa da gashin kan Ammin nata, tana mata surutu ba
tare da tasan mutuwa tayi ba.
Tana nan zaune Bala ya buɗe ɗakin ya shigo, ya kalli Widad yace "ke a ina kika
kwana?"
Kallonsa Widad tayi ta ɗauke kai, ya kalli Gawar Huda dake kwance a gurin, ya juya
ya fita.
Wajen ƙarfe sha ɗaya sega Bulama da wasu abokan kasuwancin Daula, suka shigo har
ɗakin, Bulama ya kalli Huda ya shiga rangaɗa salati, ya kalli Bala yace " kuma ba
rashin lafiya ce ta kamata cikin dare ba?"
Bala yace "nima ban sani ba, gani nai shiru banji motsinsu ba, shine na shiga
dubawa, nazo na tarar da gawa da yarinya"
Bulama yayi ajiyar zuciya yace "Allah me iko, Allah yayi mata rahama amma abun da
mamaki, munyi waya da Daula, lafiya ya tafi ya barsu, amma a wayi gari ta rasu,
Allah kenan, yanzu dai a kira motar Asibiti aje da gawar a dubata a Asibiti, ita
kuma daughter a tafi da ita gidana, zuwa muga yadda hali zeyi"
Widad ta dinga bin Bala da ido, tamkar bata taɓa ganinsa ba, duk inda ya motsa seta
bishi da ido.
Aka ɗauketa aka tafi da ita gidan Bulama, aka tafi da gawar Huda Asibiti.
Tunda aka kai Widad gidan Bulama, ba tace uffan ba se kallonsu da take kamar baƙin
halitta, aka bata Abinci harta fara ci, ta ture ta shiga kuka tana kiran Ammina.
Gaba ɗaya tausayinta, ya kama Hajiya Sarah, ta dinga rarrashin Widad amma fafur
Widad taƙi yin shiru, Fahad yace "kai wannan wace irin jarabbabiyar yarinya ce,
banza kawai ana ta magana ana rarrashin ta se wani iskanci take yi, shegiya kai me
kama da Aljanu"
Fahad be rufe baki ba, Widad ta ɗauki wani kofin glass ta jefa masa, gaba ɗaya ta
basu mamaki, suka juyo suna kallonta, kofin ya sameshi a ƙafa ya faɗi ya fashe,
sannan kuma ta koma gefe tana kallonsa tana huci, kanta yayo ze maketa a zuciye,
Hajiya Sarah ta tareshi tace
Fizgewa yayi ze daketa, amma Widad ta shammaceshi, ta kafa masa haƙora a hannu, da
ƙyar aka ɓanɓareta dan seda gurin ya fashe.
Fahad ya dinga ihu yana "na shiga uku Mayya, 'yar gidan mayu zata shanye min jini"
Tun daga lokacin, ko hanya basa haɗawa da Widad, dan tunda ya zageta ta tsane shi,
a wunin ranar nan gaba ɗaya suka rasa yadda za suyi da Widad, suka kasa gane kanta
dan bata jin rarrashi, bata sanshi ba ga kafirin taurin kan masifa, taƙi cin Abinci
taƙi saurarar kowa, da Hajiya Sarah ta gaji ta kira Bulama ta gaya masa, shi kuma
yace ayiwa direbansa magana Fahad ya rako su Asibitin, dan Daula ya iso.
Fahad yace "Allah ya kiyaye in raka Mayya, wannan a binciki danginsu mayune,
shegiya kawai"
Ƙarshe direba ne ya kai Widad Asibiti, bata tsaya jiran direban ba, ta shiga cikin
Asibitin tana leƙe leƙe, ta buɗa wannan ƙofar ta buɗe waccan.
A saman bene ta buɗe wani ɗaki, taga su Bulama da Bala a ciki da wasu mutane, se
Mahaifinta durƙushe a gaban gado an rufe gawa, yana rusar uban kuka kamar ƙaramin
yaro, Widad ta tsaya tayi sak tana binsu da kallo, Daula na ɗaga ido yaga Widad ya
sake fashewa da kuka, ya miƙowa Widad hannu, jiki a sanyaye ta ƙarasa ta faɗa
jikinsa, cikin kuka Daula yace "Lovely daughter, mun rasa Amminki, ta tafi ta
barmu"
Daula ya buɗe mata fuskar Huda, kamar kace mata tashi ta miƙe zaune.
Zumbur Widad ta miƙe tsaye, tana kallon mahaifinta, idan bata manta ba ko a film da
take kallo, when someone is dead, you won't see him again, that's mean her Ammi has
gone, she won't see her again.
Wata irin ƙara tayi tana tirje tirje, ƙarshe se ɗaukarta akayi aka kaita pediatric,
aka mata allurai, se bayan an kai Huda nakwancinta sannan Widad ta farka.
Amma tunda ta farka ba ummm ba umm, idonta a buɗe amma sam bata magana, bayan an
dawo daga kai Huda, Daula se kuka yake yana sharɓe hawaye, Asibiti ya wuce gurin
Widad ya tarar ta farka, su Bulama dai yana biye dashi dasu Bala, ya zauna ya
rungume Widad a jikinsa, yana kuka yayin da Widad ta tsaida idonta akan Bala
megadi, bata ko ƙyaftawa.
Daula yace "i don't actually know daughter, likitoci sunce ta samu cardiac failure
ne"
"How?"
Mamaki ya cika su yadda take magana, sekace wata babba, kuma she's very serious
about what she says "
Alhaji Munir yace " ranka ya daɗe, yakamata fa muje gida, mutane na jiranka.
Haka suka tafi da gida, Daula na cigaba da kuka wiwi, Bulama da sauran mutane suka
raka shi gida, har an kafa manyan rumfuna, manyan mutane gaba ɗaya sun hallara,
anata miƙo gaisuwa.
Daula na rungume da Widad a jikinsa, Widad gani take kamar ƙaryane wai Ammi ta
mutu.
Seda ta kwana biyu cirr ko gyangyaɗi ba tayi ba, hakan ya firgita Daula kar wani
abu ya sameta, ya fara tunanin ko Asibiti ze maida ita, dan seta wuni ba tace uffan
ba, sedai lokaci lokaci ta fashe da kuka.
Ranar uku, gidan nan ya cika da ɗan Adam, babu masaka tsinke Kasancewar ita kanta
Huda mutuniyar kirki ce ga kyauta.
Ana zauna a nayiwa Daula gaisuwa, ta dubi wani babban ɗan sanda, ta tashi daga
jikin Daula ta tafi gaban ɗan sandan ta zauna, ta kalle shi tace "Are you a
police?"
Widad tace " idan na tambayeka, will you do your best to help me? "
Mamaki ya kama mutanen gurin, yadda take zaro magana haka, daki daki kamar babbar
mace.
Widad ta ɗagawa mahaifinta hannu, alamar ya ƙyaleta, ta kalli cikin idon ɗan sandan
tace "you promise to help me, tambayar da zan maka itace, idan aka rufe fuskar
mutum da pillow ze mutu?"
"misali, Daddy ya doramin pillow fuskata, inta motsi amma yaƙi ɗagani, kawai se
misali Bala megadi ya dawo ya riƙemin ƙafa, in dena motsi, to zan iya mutuwa"
Yace "yes of course dear, it's a murder attack, kisan kai kenan a ina kikaga anyi?"
"Yanzu misali, idan na gaya maka a inda na gani, wani mataki zaka ɗauka?"
Gaba ɗaya rumfar tayi shiru, ana sauraren Widad, Ɗan sandan yace "zamuyi abunda
doka tace akai, idan har muka kama mutum da laifi, zamu kashi kotu a yanke masa
hukunci"
"Arrest Bala! And the doctor that confirms that my Mum is dead, as a result of
cardiac attack" ta faɗa kai tsaye
"Why" ya tambaye ta
Cikin ƙara tace "Bala yasan suwaye suka kashe Ammina, kasheta akayi fa, i use to
watch in movies, she was killed not dead as a result of cardiac attack, Ka kama
Bala ko in kasheshi, he's responsible for the murder, na ganshi shine ya buɗe wa
wasu ƙofa, suka rufe ammina da pillow, Arrest him i said "!
Gaba ɗaya Widad ta hargitsa gurin, ihu take sosai tana nema ta fita daga
hayyacinta, se kurma ihu take tana akama Bala.
Alhaji Haruna yace" ya za'a biyewa yarinya ƙarama tana wa mutane shirme, watakila
alhinin mutuwane ko mafarki tayi "
Daula ya fashe da kuka yace " Widad mutum ce, kuma yarinya ƙarama, amma idan kaga
tayi maka ƙarya ajizanci ne irin na ɗan Adam, dan haka Arrest him, ayi bincike akai
"
Yai maganar yana kuka, aikuwa Bala yana ihu haka aka buga masa ankwa akayi gaba
dashi, nan wasu suka dinga jinjinawa kaifin basira irin na Widad da ƙarfin hali,
yayin da wasubsuke ganin be kamata a kama Bala ba, tunda shirmen yarane.
Nan fa 'yan sanda kuma suka shiga bincike akan Bala, Widad ta fayyace musu yadda
abun ya faru, Alhaji Haruna yace "Nasir, bekamata a biyewa yarinya ƙarama ba, ta
faɗi magana sannan a yadda"
Daula yace "Tunda Widad ta faɗi haka ba ƙarya take ba, bata taɓa haka ba, kuma
akwai ƙamshin gaskiya a lamarin nan, dan haka se abunda hukuma tace, dan nikaina
bana ja da ikon Allah, amma tabbas mutuwar Huda, abar a bincika ce, lafiya muka
rabu da ita, ba ta da wani ciwo, ace in dawo in tarar ta rasu, Allah na tuba "
Kawai ya fashe da kuka, Bulama yace " Nasir, kayi haƙuri nasan irin mahimmancin
Huda a rayuwarka, amma karkayi abunda zaka dawo kana dana sani, kar azo aji kunya "
Widad na kan kujera, tana wasa da yatsunta, tunda suke maganar su bata saka baki
ba, se yanzu tace "Daddy, ko nima na mutu kar ka bari a ƙyale Bala, seya faɗi wanda
suka kashe Ammina, idan ba hakaba zan faɗa maka ko suwaye"
Zaro ido sukayi, suka juyo da kallonsu kanta, Daula yace "Baby na, dagaske kin san
suwaye? Ya akayi kika sani? Gayamin suwaye, meyafaru?"
"Daddy nima ban san suwaye ba, amma nasan mutum ɗaya, naji sun faɗi sunan wani
mutum, amma zanyi tunani in tuna, na manta sunan, amma zan tuna idan be faɗa ba zan
faɗa"
Bulama yace "Daula anya yarinyar nan bata samu matsala a ƙwaƙwalwarta ba? Ji wata
irin magana da take fa, Anya baza'a kaita Asibiti ba"
Alhaji Haruna yace "gaskiya kam, nima naga kamar alamun haka a tare da ita"
"Niba mahaukaciya bace, karku sake cemin mahaukaciya, ni nasan abunda nake, wasune
suka danne Ammina da pillow, ni ina da hankali"
Daula ya rungumeta yace "Sorry my lovely, nima na sani lafiyarki ƙalau ai"
Wasa wasa Widad gaba ɗaya walwalarta ta ɗauke, ta dena walwala ta dena fara'a, ko
Abinci bata iya ci saboda kewa dake damunta, wasu lokutan seta wuni akan gadon nan
da aka kashe Ammi, ko haka kurum taje ta buɗe wardrobe ɗin Ammin, ta watso kayan
Ammin duka ta zauna a cikin kayan tana rusa uban kuka, haka Daula zezo ya na
rarrashinta, wani lokacin kuma ya zauna ya tayata kukan.
Sosai Widad kaɗaici yake damunta, dama gata bame son mutane ba, Babu wani dangi da
suke dasu da suke zuwa gurin su, dan haka Widad abun ya ƙara nata yawa, haka kurum
wani lokacin da daddare seta hau firgita tana cewa "Daddy gasu nan, ka tashi kaima
karsu kasheka" ko taita ihu tana ƙoƙarin fita da gudu, se Daula ya riƙeta gam.
Sosai ta dena magana, sedai ta kan zauna taita kallon magunan Ammi da take kiwo, da
zomaye da tsuntsaye, da yake Huda mace ce me son dabbobi, sosai take kula dasu tana
ciyar dasu, idan Widad tana kallonsu, se taga kamar Amminta tana nan, zata zo ta
basu Abinci, haka zata zauna tana musu magana
"Kuma kunyi missing Ammina ko? An kashe ta, amma zata zo ta baku Abinci"
Bulama yace "Daula, nifa na fara jin tsoro da sha'anin yarinyar nan, karfa muna
zaune ta haukace, gaba ɗaya ta canza lokaci ɗaya, ta zama wata iri"
Daula yace "nima na gani, abun yana damuna, na rasa ya zanyi bana son in rasa
ɗiyata, kota rasa hankalinta, gashi kullum cikin kashedi takemin akan, lallai kar
in bari a saki Bala, sannan idan be faɗi waye ba ita zata faɗa, nayi nayi ta faɗa
taƙi gayamin, yanzu fa ko Abincin kirki bata ci, se koke koke"
Bulama yace "yanzu ajiyar da ka bata na dukiyar nan, baka tsoron ta samun taɓin
Ƙwaƙwalwa, ayi asarar maƙudan kuɗaɗen nan?"
Daula yace "duk me wannan dukiyar, in dai ta sace ko waye, kuma ko a ina yaje,
seya karɓi kayarsa dan haka wannan ba abun damuwa bane, ni abunda ya dameni yanzu,
shine lafiyar ta"
Bulama yace "karka damu, akwai wani likitan ƙwaƙwalwa da Alhaji Munir ya sani, zan
masa magana ya turoshi yazo ya duba ta"
Haka akayi, washegari Bulama yazo da Likitan nan da Alhaji Munir, Widad na ganinsa
ta miƙe da gudu ta maƙalƙale Daula, juyin duniya ta sunkuyar da kanta taƙi
kallonsu.
Suka gaisa da Daula, Daula yace "lovely ga likita ze dubaki, ki gaishe shi"
Ƙara sunkuyar da kai tayi, taƙi kallonsu, likitan yace "Baby zomu gaisa mana,
tambayarki zanyi"
Juyin duniya Widad taƙi magana, duk tambayoyin da suke mata taƙi amsawa, likitan
nan ya kaɗa ya raya, amma tayi mursisi kamar yana magana da itace.
Daula yasa hannu ya janyo ta daga bayansa data shige, ta sunkuyar da kai kamar
sabuwar bokanya.
Ya ɗorata akan cinyarsa yace "Babyna lookup" ta ɗago ta kalli mahaifinta idonta
fal hawaye.
Yace "ba cutar dake za suyi ba, tambayarki za'ayi lafiyarki nake son a dubamin,
kinji Gimbiyar Daddynta"
"Daddy, idan Bala be faɗi wanda suka kashe Ammina ba, zan faɗi sunan da mutanen
suka faɗa idan na tuna, ina kallonsu Bala ne ya rufe Alba Dog, ya buɗe musu ƙofa,
shiya rako su har kan bene, ina kitchen ina kallonsu, har akace su nemoni a gidan
nan"
Bulama yace "ikon Allah, kalli abunda ake tambayarta daban, abun da take faɗa
daban"
Daula ya dafe kai yace "Innalillahi wa inna ialaihi raji'un, Allah ka rufamin
Asiri kar Abunda ya ragemin ya kufcemin, Allah ka bawa 'yata lafiya".
Kawai ya fashe da kuka, yana ƙanƙame Widad a ƙirjinsa, aikuwa ta kwanta a jikinsa,
tana ajiyar zuciya.
Likitan da suke kira da Hamisu yace "Alhaji ina me sake yi maka ta' aziyyar rashin
matarka, sannan kayi haƙuri ka dena kukan nan, ka bani haɗin kai ka amsa tambayoyin
da zan maka, saboda alamu sun nuna Ƙwaƙwalwarta ta fara taɓuwa, tana iya bacci, ya
yanayin cin Abincin ta?"
Daula yayi masa bayanin duk abunda Widad take yi, nan aka tabattar masa depression
ne yake damunta.
"zan mata wata allura guda ɗaya, idan akayi mata insha Allah zata samu sauƙi, za'a
samu ƙwaƙwalwarta ta dinga karɓar abunda ake so "
Widad tana zaune, aka haɗa allura aka zuƙa, tana kwance jikin Daula, likitan ya
ɗaga hannunta, daidai dantsanta yayi mata allurar, sedai me ko mintuna biyar ba'ayi
ba.........
LITTAFIN KUƊI NE, DAN ALLAH KI SIYA KAFIN KI KARANTA BA DANNI BA DAN ALLAH, LITTAFI
NA ƊAYA KYAUTA NE WANNAN NA SIYARWA NE
NORMAL GROUP ₦300
VIP ₦500 NE KITURA TA WANNAN ACCOUNT ƊIN
0009450228
JA'IZ BANK
AISHA ADAM
SE A TURA SHEDAR BIYA TA WANNAN LAMBAR
07063065680
IDAN KUMA KIN SIYA AMANACE KARKI FITARMIN DAN ALLAH 🙏🙏🙏
11/14/21, 6:09 PM - Ummee Musa: LITTAFIN KUƊI NE, DAN ALLAH KI SIYA KAFIN KI
KARANTA BA DANNI BA DAN ALLAH, LITTAFI NA ƊAYA KYAUTA NE WANNAN NA SIYARWA NE
NORMAL GROUP ₦300
VIP ₦500 NE KITURA TA WANNAN ACCOUNT ƊIN
0009450228
JA'IZ BANK
AISHA ADAM
SE A TURA SHEDAR BIYA TA WANNAN LAMBAR
07063065680
IDAN KUMA KIN SIYA AMANACE KARKI FITARMIN DAN ALLAH 🙏🙏🙏
78_79
Take Widad taji duniyar tana juya mata, taga abubuwan dake ƙasa sun koma sama, na
sama sun dawo ƙasa, ta kasa gane inda kanta yake, ta dinga jin kamar ta tashi ta
zura da gudu, ta riƙe kanta gam, kafin can ta kurma wani uba ihu ta miƙe tsaye tana
zazzare idi.
Daula a gigice ya riƙeta yace "Subhanallah, doctor meke faruwa ne? Kaga abunda
take fa, meya sameta ne? Innalillahi wa inna ialaihi raji'un"
Likitan yace "wannan shike tabbatar da ta samu taɓin hankali ne, badan haka ba da
babu abunda allurar za tayi mata, dole a cigaba da kula da ita, idan ba hakaba kuma
zata zama tuburan, amma zan sake mata wata allaurar zata samu relief tayi bacci"
Widad tana ta gunji, tana fizge fizge haka aka kuma yi mata Allura, wadda seda ta
ƙara birkitata ga baki ɗaya, ya zamana bata gane a duniya take ko a ina? Ga mutane
tana kallonsu, amma bata gane meke faruwa, a haka har wani irin galabaitaccen bacci
ya ɗauketa a wahalce.
Seda bacci ya ɗauketa sannan hankalin Daula ya kwanta, ya kalli likitan yace "yanzu
doctor, wannan baccin shine samun relief ɗinta? Sannan kuma ya batun yadda za'a
cigaba da kula da ita"
Doctor Hamisu yace "Eh shine samun sauƙinta, tunda kace baccin ma bata yinsa sosai,
dan haka karka damu, ko yaushe zata kai tana wannan baccin babu wata matsala ba
abun damuwa bane"
Daula ya jinjina kai yace "shikenan, ubangiji Allah ya bata lafiya ya tashi
kafaɗunta, Allah ya baki lafiya daughter na"
Alhaji Munir yace "to tunda hakane baka ganin a cikin taɓin hankalin ne yasa tace
kashe mahaifiyarta akayi? Tasa aka kama Bala? Kuma ma ai tayi ƙanƙanta ace ta bada
irin wannan shedar an yarda an karɓa"
Daula ya haɗe rai yace "bana yadda in zalunci kowa a rayuwa ta, ina taka tsantsan
da duk abunda zan aikata da zesa in ɓatawa wani, ko in zalunci wani dukda tarin
dukiyar da nake da ita, amma a wannan karon nima zan ɗana izza da amfani da ƙarfin
dukiya da Allah ya bani, in dai hakan ze samarwa da 'yata farinciki, bari in gaya
maka wani abu, ko nawane zan kashe a cigaba da tsare Bala, har se ya faɗi abunda
yasani game da kisan matata, uwar' yata"
Bulama yace "Daula karfa soyayyar 'yarka yasa ka aikata abunda zakazo kana
danasani, abi komai a sannu har a gano bakin zaren, kaga yarinyar nan ga abunda aka
ce yana damunta, ga kuma ita abunda take faɗa, kar ƙaunar da kake mata yasa ka ɓata
sunanka a idon duniya"
Daula ya kalli Widad dake kwance a jikinsa, ya shafi gashin kanta yace "bata taɓa
aikata wani abu makamancin haka ba, 'yata ba irin sauran yara bace, Ƙwaƙwalwarta na
aiki fiye da shekarunta, tunaninta ya zarta tunani irin na yara, a baya Huda na
ɓacin ran irin halayen Widad, tana jin haushin irin kallace kallacen da take yi,
sedai me bayan ran Huda wannan hali na Widad yayi rana, saboda ni abunda likita ya
faɗa daban abunda kuma ya faru daban, abun da baku sani ba shine, har kitchen inda
ta hau kan drower, har garin hawa abunda take ci ya zuba a ƙasa, seda ta nunawa
'yan sanda, kuma ta nuna musu ta ƙofar da Bala ya shiga da mutanen nan, an auna
gurin anga zanen yatsunsa a jiki, dan haka bana tantama abunda ta faɗi gaskiya ne"
Munir yace "Amma, baka ganin lokacin da ya shigo duba sune ya kama ƙofar ya shigo,
har hoton yatsunsa ya fito"
"Wannan kuma aikin hukuma ne, su zasu tabattar da gaskiyar abunda ya faru, amma
wannan karon nima zan ɗana, zanyi Amfani da ƙarfin dukiyata, da kuma alfarma da
sanayya da nake da ita a faɗin ƙasar nan, se an nemo wanda suka kashe matata, kuma
wallahi ko Arziƙina ze ƙare se na tabattar da anbi mana haƙƙinmu"
Likitan yace "Amma ranka ya daɗe kabi komai a sannu yafi, alamu sun nuna yarinyar
ka tun tana ƙarama take da larurar Ƙwaƙwalwa, amma baka ɗau mataki ba"
Daula yace "ni lafiyar 'yata ƙalau, babu abunda ya samu Ƙwaƙwalwarta a wancan
lokacin, Allah dai ya bata kaifin basira fiye da shekarunta" yana gama maganar ya
miƙe, ya saɓa Widad a kafaɗarsa ya tafi ɗakinsa da ita, yaje ya kwantar da ita, ya
koma gefenta ya kwanta ya ƙura mata ido yana jin tausayinta na ratsashi, Widad ta
rasa mahaifiya da ƙananan shekaru, yasan rayuwar maraici, yasan yadda take,
musamman ga 'ya mace tafi shan wahala, take hawaye suka shiga zarya a fuskarsa
yace "insha Allah zanyi iyayina, ba zakiyi kukan maraici ba Widad"
Wasa wasa tunda aka yiwa Widad Allurar nan bata sake farkawa ba, haka ta dinga
wannan baccin kamar wata matacciya, abun ya ɗagawa Daula hankali sosai, Amma likita
yace masa bakomai samun relief ɗinta kenan.
Seda Widad tayi kwana biyu cir tana wannan baccin, ko motsi ba tayi rana ta biyu da
yamma sannan ta farka, tunda ta fara baccin nan Daula baya matsawa ko nan da can,
yana kusa da ita, har Allah yasa ta farka.
Koda ta farka ta farka da wata irin matsananciyar yunwa, amma ta kasa cewa tana jin
yunwa, maganar duniya Daula yayi amma taƙi bashi amsa, sedai ta bishi da ido.
Ya haɗo Abinci yazo ya zauna yana bata, tana ci tana kallonsa kamar taga sabon abu
a tare da shi, yana cikin cin aka zo aka sanar dashi yayi baƙi yace ayi musu iso
nan inda yake baze iya tashi ya bar Widad ba.
Aka musu iso suka shiga har inda Daula yake, sedai Widad na ganinsu se taga kamar
wannan mutanen da suka kashe Amminta, seta dinga ganinsu da wannan mask ɗin a
fuskarsu, abunda ya faru da Amminta ya shiga dawo mata fes a idonta, taga kamar a
lokacin abun ke shirin faruwa, aikuwa ta kurma ihu me razanarwa, haka yasa mutanen
suka tsaya suna zuba mata ido, ta riƙe Daula gam tana ihu, ta rintse idanunta
alamar bata son ganin kowa gaba ɗaya.
Ƙarshe mutanen nan se barin ɗakin nan sukayi gaba ɗaya, suka koma babban falo suka
jira shi, abu kamar wasa sosai Widad take gudun mutane bata son kowa a inda take
inba Daddynta ko Bulama ba.
Watarana tana zaune a ɗakin Daddynta, tana wasa da magen Amminta data bari, Alhaji
Daula yana son ya ɗan fita, amma yana tunanin yadda zeyi da Widad.
Widad da a rana bata fi tayi magana sau a ƙirga ba amma tace "Daddy kaje inda kake
son zuwa, ba inda zani"
"A'a lovely, ina tsoron barinki anan ke kaɗai, abubuwa sun fara bani tsoro, ina
zaton zan sa a ƙara security"
"Eh lovely, Amma a binciken 'yan sanda, security na kan babban titi sunga wucewar
mota tsakar darw ta shigo hanyarmu, sedai wai sunyi zaton gurina ko wani suka zo,
saboda kin san mukanyi meeting cikin dare, amma har yanzu anata bincike"
Widad ta jinjina kai tace "Daddy kaje kawai, ina nan ba inda zani"
Daula yace "nayi murna daughter, yau kina magana sosai da kanki".
Tayi murmushi, Daula ya shirya ya fita.
Bayan fitarsa Widad ta fito ta dinga zagaye gidan, kamar bata saba ganin gidan ba.
Kamar gaske ta fara dawowa daidai, amma dukda haka bata son mutane sam, daga
Daddynta bata son kowa ya raɓeta, balle a yimata wani abun, haka Daula yake yawo da
ita gurin taro ko harkokin kasuwanci, kamar yadda uwa ke yawo da ɗanta, sam ko
makaranta bata zuwa saboda rashin son mutane, indai ba'a gida ba ko tana tare da
Daddynta bata zama a ko ina.
Wataran zeje taron kasuwanci Africa ta kudu, nanma ya ɗauki Widad ya tafi da ita,
ranar da suka dawo kusan ƙarfe ɗaya na dare, direbansa yaje ya ɗakkosu daga airport
suna tafe suna hira, kawai aka tare motar tasu.
Widad na ganin mutanen da suka taresu ta gigice, yanayin jikinsu sak wanda suka
kashe Ammi, gasu da mask a fuskarsu.
Widad ba zata taɓa mantawa da wannan muryar ba, tabbas sune wanda sukaje har gida
suka danne Umminta da pillow, nan da nan jikin Widad ya ɗau rawa, amma ta dake taƙi
nuna alamar Hakan.
Suka bubbuɗe murfin motar, Daula ya rungume Widad a jikinsa yana ta nanata
Hasbunalahi wani'imal wakil, suka fizgo direban Daula ƙasa suka saita masa bindiga.
Ɗaya daga cikinsu Wanda Widad bazata manta dashi ba, shine wanda taji yana wayar
nan ranar da suka kasje mahaifiyarta, har ya ambaci sunan wani mutum, ya kalli
Daula yace "Nasiru Daula, haƙiƙa ina me tabattar maka da zaka bi matarka inda ta
tafi idan har ka mana gardama, tambaya ɗaya zan maka kuma amsa nake so ta kai
tsaye, ina wannan takaddun da wasiyyar da kayi na cewar akwai wanda yake da kashi
bakwai bisa goma na dukiyarka suna ina?"
Cikin tsawa yace " kai, karka min wata taƙama da jin kai, babu wani amfani da
taurin kai ko tsaurinka ze maka a nan, zan iya fasa maka kaibda harsashen nan"
Ko gezau beba balle susa ran ze basu amsa, yunƙurwa sukayi zasu danƙo Daula daga
cikin motar, Amma Widad ta buɗe hannayenta ta tare mahaifinta.
Daula yace "lovely, ki bari kar suyi miki wani abun kinji, karsu illatamin ke"
"Am not afraid of anyone, abunda suke nema yana gurina, karsu ƙara yi maka tsawa"
Kallonta suka shigayi, dudu ba zata fi shekaru takwas ba, amma kalli yadda take
magana kamar ba yarinya ba.
Hannu babban cikinsu ya saka ze fizgo Widad, amma Daula ya riƙita gam suna janta,
shi kuma ya riƙeta gam.
Daula yace "idan kuka kasheta kun kasheni, kuma kun rasa abunda kuke nema, kuma
koda kun barmu a raye shima duk ɗaya zaku rasa abunda kuke nema, dan wallahi kome
zakuyi da kaina bazan baku amana ba, bazan baku kayan da ba nawa ba, sedai idan
Widad ɗince ta yarda ta baku bani da matsala da duk wanda ta ɗauka ta bawa"
Zuro hannu ya kuma yi ze danƙo Widad, sedai a wannan karon bisa sa'a, Widad ta nuna
musu ita mahaukaciya ce, dan kukan kura tayi ta datse yatsan mutumin nan a bakinta,
ta kafa masa haƙora kamar yadda ta yiwa Fahad.
Abun mamaki sega Ƙaton da yake ɗauke da bindiga yana kurma ihu, yasa kan bindiga ya
daki kan Widad, wanda hakan yasa ta ƙwala ihu ta sake shi, sega jini na zuba ta
hancinta ta sume a gurin, ganin Asirinsu na ƙoƙarin tonuwa yasa suka cika
wandunansu da iska suka ɓace daga gurin.
Daula gaba ɗaya ya rikice, ƙarshe direban ne yayi dabarar wucewa dasu Asibiti, aka
kai Widad emergency gaba ɗaya Daula ya rasa abunda yake masa daɗi, matsala daga
wannan se wancan be maganin wannan ba waccan ta kunno kai.
Yai shiru ya dafe kansa ya zubawa Widad ido, wadda ke kwance ruwa na shiga jikinta,
ya kifa kai akan gadon da take yai kuka yai kuka, harya gaji yayi shiru, cikin dare
Widad ta farka tayi juyi taji kanta yayi mata nauyi, ta juya taga mahaifinta ya
kifa kansa a kan gadonta, ya riƙe hannayenta, da alamu yana cikin matsananciyar
damuwa, a hankali tayi juyi ta rungumo kan Daddynta ta kwantar da kanta a kan nasa,
a haka bacci ya ɗauketa.
Wayewar gari labari ya cika gari, ga abunda ya sami Daula da 'yarsa nanma akayi ta
tururwar zuwa Asibiti dubata.
Daula ya tafi masallaci salla sega wasu mutane sun shigo ɗakin nata, wai sunzo
dubata, ta dinga binsu da kallo, suka zazzauna, kallo ɗaya ta gane wanda ya buga
mata bindiga jiya, wanda suka kashe Amminta ne, bata taɓa ganin fuskarsa ba se yau,
bata ƙara tabattarwa ba seda ta kalli inda ta gasa masa cizo jiya, a hankali yace
Shiru tayi ba tace masa komai ba, yazo gaban gadonta ya durƙusa sannan kalleta
yace "Baby girl, tambayarki zanyi kinji ko? Ina abubuwan da Dad ɗinki ya baki
ajiya, su nake son ki gayamin inda suke kinji, nima bazan gayawa kowa ba"
Widad ta tsare shi da manya manyan idanunta tana masa wani irin kallo, daya kasa
gane na menene?
Still ba amsa, ya ɗakko wata ƙaramar wuƙa yace "idan baki gayamin ba, zan
gutsutsura naman jikinki da wuƙar nan, in dafa in cinye, gayamin nace"
Ya ɗauka Widad irin yaran dazewa barazana ne, amsar data bashi shine "idan ka
kasheni bakomai, nasan dai Daddy zeyi kuka, amma nasan wanda ya kashemin Ammina"
tai maganar tana kallonsa
A fusace yace "ina ruwana da wanda ya kashe ta? Kema kashe ki zanyi in kashe
babanki idan baki faɗan ba"
Maimakon ta bashi amsa, se tace "Na rubutawa DSP wasiƙa, zan gayamasa wanda ya
kashe Ammina, yayimin Alƙawarin ze gano suwaye"
"Ke dan ubanki ba wannan muke tambayarki ba, ina kayan nan suke?"
Widad bata nuna ta ganesu ba, ta sake kallon hannunsa tabbas shine babu ko tantama,
ga inda ta cijeshi jiya a tsintsiyar hannu, abun da ya faru ranar da aka yi kisan
ya sake dawo mata ranta, gani tayi ya miƙe ya ɗakko handkerchief a aljihunsa ze
saka mata a hanci, nan experience ɗinta na kallace kallacen films ya dawo mata,
bata san ya akayi ba ta fasa ihu, ta ɗakko kwalbar malt zata buga masa, ai kafin
tayi wani yunƙuri, sun bar ɗakin nata da sauri, nan ta cigaba da kurma ihu tana
jifa da kwalabe a ɗakin.
Da gudu Daula dasu Bulama, da ɗan sandan Da Widad ta saka ya kama Bala, suka ƙaraso
ɗakin, dama suna kan hanyar zuwa ɗakinne, Daula yayiwa ɗansandan waya, yayi masa
bayani, shine ya taho Asibitin.
Tayi watsi da kwalabe tana kuka, Daula jiki a sanyaye ya karaya, tabbas hauka ya
tabatta akan Widad, ta haukace.
Daula yana da matuƙar raunin zuciya, dan haka kuka baya bashi wahala, haka ze zauna
idan damuwa tayi masa yawa yaita abunsa.
Yazo kan gadon nata ya zauna, aikuwa nan da nan ta rungume shi, tana ta sauke
numfashi kamar wadda tayi dambe.
Ɗansandan yace "Alhaji, wannan harin da aka kai muku jiya, ya tabattar da maganar
Widad, kashe matarka akayi muma munata tattara abunda bincike ya nuna mana, Insha
Allah kamar yadda nayi Alƙawari, se naga abunda ya turewa buzu naɗi"
Babu tunanin komai, Daula ya amince, Bulama ya saɓa Widad a kafaɗarsa, suka fito
sedai tasa tafukan hannayenta ta rufe idonta, saboda bata san haske kuma bata son
koda wasa ta sake ganin mutanen nan.
Asibitin doctor Hamisu suka wuce, ya karɓesu hannu bibiyu, ya sake ɗurkawa Widad
allurai wanda suka sake rikita ta gaba ɗaya, sannan ya ɗirka mata allurar bacci.
Gaba ɗaya seda inspector ya kamu da matsanancin tausyin Widad, yarinya ƙarama amma
rayuwarta a garari haka, ya kalli Daula yace
"ranka ya daɗe, yakamata ace an sake tsananta matakan tsaro, a hanyar gidanka
saboda kariya ga lafiyarka da kuma ta 'yarka, ina jin tausayin yarinyar nan, kuma
nayi mata Alƙawari insha Allah bazan mutu ba zan cika mata, tacemin zata yi magana
dani rannan, tace maganar tana da mahimmanci sosai, dan haka insha Allah zan sake
zuwa, in duba ta sannan inji maganar da zata yi min"
Daula yace "Nagode DSP da wannan ɗawainiya da kake, Allah yasaka maka da alheri"
"Karka damu, aikina ne yin hakan ai, Allah ya bawa Baby lafiya"
Kwana biyu da tafiyar DSP, lokacin Widad ta farfaɗo, a lokacin aka sanar da rasuwar
Wannan DAP Na 'yan sanda da yake faɗi tashi akan case ɗin, ranar da ya bar gurin
Widad, akayi masa kiran gaggawa Lagos, akan hanyarsa sukayi artabu da' yan fashi
aka kashe shi.
Daula ya kaɗu matuƙar gaske da jin wannan labarin, ya shiga damuwa haka kurum
zuciyarsa ke raya masa, ba haka abun ya faru ba, yanzu kenan duk me niyyar
taumakonsu se anga bayansa?
Wannan karonma farkawar Widad yazo da sabon salo, bayan rashin magana ma, sam bata
son haske sedai a rurrufe ko ina, ko yaya haske yake bata sonsa komai sedai tayi a
ɗaki.
Ta ƙara shiga damuwa da taji labarin mutuwar DSP, dukda ba magana take son yi ba
amma tayi kuka sosai.
Tace "Daddy"
"Daddy dan Allah, ko duk kuɗinmu zasu ƙare, karka bari a saki Bala megadi"
"Insha Allah Baby, bazan bari ba amma na fara damuwa, gashi baki da lafiya, gashi
an fara kashs duk masu niyyar temakonmu"
Ta kalli Daula tace "idan an kashe masu taimakon mu, Allah ze temake mu, idan kaje
gaisuwa kayiwa iyalinsa alheri, ka basu haƙuri"
Gaba ɗaya Daula ya ajiye batun harkar kasuwanci a gefe, ya tattara hankalinsa akan
lafiyar 'yarsa.
Suna zaune da Bulama a falon gidansa, Bulama yace "Daula, zamanka fa da Widad a
gidan nan baze yuwu ba, zuwa yanzu ya kamata kayi Aure kodan ka samu me ta yaka
kula da ita, ga harkokinka suna nema su tsaya, ni da zaka yadda dana ɗauketa,
saboda ina son Yarinyar nan"
Daula yace "nasan kana son 'yata Bulama, sedai koms za' ace sedai ace, zan cigaba
da kula da ita, ina nema mata lafiya, yanzu abunda ya dameni ina son in samo
malamai suzo su raba gadon Huda"
Bulama yace "wane irin gado kuma? Naga dama idan wani abu take dashi kaika bata,
tunda ta mutu ai ya zama naka"
Daula ya girgiza kai yace "A'a, akwai kuɗaɗenta masu yawa da bani lokacin da mukayi
Aure, ina son a ware natane a cikin dukiyata, idan aka ware zan mallakwa Widad su"
"Kamar yaya? Da can ka ware kashi bakwai, yanzu kuma Allah kaɗai yasan kashi nawa
zaka kuma warewa, Widad ɗin da take yarinya me zata yi da dukiya? Kuma yanzu idan
duk ka kwashe kuɗaɗen nan, kasan adadin mutanen da zasu durƙushe kuwa? Mutane
dayawa da Allah suka dogara, amma suna daga kwamce suke Arziki saboda kasiwancinka"
"Nasani Bulama, amma hakan baya nufin zan janye kuɗaɗen ne, zan cigaba da juyasu,
amma zan canza suna na dana 'yata akan abunda yake mallakinta, kuma insha Allah
idan naga maganin da ake mata anan beyi ba, zamu dan gana da ƙasashen waje ne
kawai"
Widad fa ba zuwa makaranta, kullum se a gida banda zabure zabure da ihun da take yi
cikin dare, ga ƙin mutane dan a tsorace take da mutanen nan kar su sake dawowa su
cutar da su.
Sedai a hakan an cigaba da yiwa Daula barazana iri iri ta waya, ace za'a kasheshi
ko za'a sace Widad idan be faɗi inda takaddun nan suke ba, tun yana zarya hukumar
'yan sanda harya haƙura gaba ɗaya.
Bulama ya saka Daula a gaba da yayi Aure, dan ba mutuncinsa bane babban mutum
kamarshk ace bashi da Aure kuma yana zaune da gashi se ƙaramar yarinya a gida ba.
Daula yace "sam baze Aure ba, yazan babu me maye gurbin Huda"
Bulama yace "idan balarabiya kake so, kana da kuɗin da zaka je kowani ƙasa ka auro
mace, wadda kake so"
Daula ya kan ce masa "ba balarabiya nake so ba, nagarta nake nema irin ta Huda"
Bulama ya matsa, ya dage ya takurawa Daula, Daula yace "nifa ka ƙyaleni, lafiyar
'yata ta fiyemin wani Aure"
Amma Bulama ya cigaba da matsawa, gefe guda kuma anata bankawa Widad allurai da
ƙwayoyi da suke birkita mata lissafi, ƙiri ƙiri ta dena zancen zata faɗi wanda ya
kashe Amminta, gaba ɗaya aka tsaya da zancen ma, a haka aka daddafa aka fara
shari'a da Bala, anan Daula yayi amfani da tasirin dukiya, shari'a taƙi gaba taƙi
baya aka tsare Bala, da rundunar sojoji sunso kawowa Bala ɗauki, Kasancewar nasu
ne, sedai Daula yai amfani da kuɗinsa, hakan yaƙi tasiri.
Ganin Daula bashi da niyyar yin Auren nan, gaba ɗaya ya tattara hankakinsa akan
'yarsa yasa Bulama da kansa nemawa Daula matar daze Aura, sedai me.......
LITTAFIN KUƊI NE, DAN ALLAH KI SIYA KAFIN KI KARANTA BA DANNI BA DAN ALLAH, LITTAFI
NA ƊAYA KYAUTA NE WANNAN NA SIYARWA NE
NORMAL GROUP ₦300
VIP ₦500 NE KITURA TA WANNAN ACCOUNT ƊIN
0009450228
JA'IZ BANK
AISHA ADAM
SE A TURA SHEDAR BIYA TA WANNAN LAMBAR
07063065680
IDAN KUMA KIN SIYA AMANACE KARKI FITARMIN DAN ALLAH 🙏🙏🙏
11/14/21, 6:09 PM - Ummee Musa: LITTAFIN KUƊI NE, DAN ALLAH KI SIYA KAFIN KI
KARANTA BA DANNI BA DAN ALLAH, LITTAFI NA ƊAYA KYAUTA NE WANNAN NA SIYARWA NE
NORMAL GROUP ₦300
VIP ₦500 NE KITURA TA WANNAN ACCOUNT ƊIN
0009450228
JA'IZ BANK
AISHA ADAM
SE A TURA SHEDAR BIYA TA WANNAN LAMBAR
07063065680
IDAN KUMA KIN SIYA AMANACE KARKI FITARMIN DAN ALLAH 🙏🙏🙏
80_81
Daula yace "Yarinyar nan itace uwata, itace Ubana itace komaina a yanzu, dan haka
duk hukuncin data yanke shikenan"
Bulama yaji kamar yayiwa Daula dukan tsiya ya huce, haka ya ci gaba da cusa masa
matar nan, 'yar uwace a gurin Bulama matar, sun rabu da mijinta tana da yara Uku,
mijin idan ya shura takalmansa se yayi wattanni ba'asan inda yake ba, ga ba Abinci
ya barta da yar taita wahala shine aka raba auren.
Daula fafur yaƙi maganar sam, Ita kam Gimbiyar wato Widad ana cigaba da sake
birkita mata tunani, ta hanyar ƙwayoyi da kuma allurai, gaba ɗaya ta koma wata
iriya abun tausayi, wani lokacin idan ta rasa me yake damunta sedai tayi ta kuka,
takasa banbance a aace duniyar take.
Wani lokacin haka kurum tana zaune, sedai taji ana mata ihu ko ana kuruwa a cikin
kunnuwanta, ko taga duniya tana juyawa, ko kuma taji kamar ana buɗe ƙofa za'a shigo
kawai se zuciyarta ta bata mutanen nan ne zasu shigo.
Abun duniya ya ishi Daula, ga surutun mutane ya fara masa yawa akan yakamata yayi
Aure, bekamata ya cigaba da zama haka ba.
Bulama yace "kaga Daula, tun wuri ya kamata ka nemawa kanka mafita, kai ba dan
Allah yasa kana da nasibi akan harkar kasuwanci ba, da tuni kasuwancinka yazo
ƙarshe gaba ɗaya, kuma kaɗaici ze iya sawa Widad ta ƙara shiga wani hali, babu
yadda za'ayi rayuwar yarinya ƙarama ta yuwu ba tare da mace me kulawa da ita ba,
kai a yanzu taurin kai ba naka bane, kaje ka samu kayi Auren nan ko hankalinka yafi
kwanciya "
Daula yace " Bulama ba naƙi inyi Auren nan neba, bana son in Auri wadda zata zo
takasa jure zama dani, wadda zata ƙarasa kassarani, yanzu duk macen da zan aura,
zata aureni ne dan dukiyata, matata ta fari kuwa ta Aureni tun banda komai, shiyasa
nake jin tsoron hakan, ko in Auri mace ta haihu dani in kasa daidaita adalci a
tsakanin 'ya' yan, dan bazan taɓa kamanta ƙaunar abunda Huda ta bari da wani ba,
Allah sarki Huda ba ita ba abunda yake cikinta, Allah ya jiƙanki Huda ya saka miki
kissan gillar da akayi miki"
Bulama ya dafa kafaɗarsa yace "Nasir, Kayi haƙuri, zan samo maka mace me hankali,
kaga Haliman nan muyuniyar kirkice 'yar uwatace, mijin tane ta Aura Azzalumi,
ƙarshe aka raba Auren, nayi imani da Allah zata zauna da kai lafiya, harta kula da
Yarinyar nan tunda kaƙi bani ita, da naso ka bani ita kafin kayi Auren se in dawo
maka da ita, amma kace kafi son ka kula da ita, tunda hakane gara ka lallaɓa kayi
Aure, amma zaman da kake haka be dace sam, kuma kaima ka sani"
Haka Bulama yaita lallaɓa Daula, harya yadda zeje su gaisa da ita matar.
Duk da rashin lafiya na Widad, haka ya shiryata suka tafi tare, gidan da Halima
take duk a kwararraɓe ba gyara, aka masa iso sitting room ɗin gidan, tunda sukaje
Widad take kallon gidan, ita bata taɓa ganin gida a haka ba, gashi ɗan ƙarami gashi
wani irin.
Halima taitawa Widad magana amma taƙi kulata, Alhaji Nasir yace "Halima kinga
'yata Widad, kuma bata da cikakkiyar lafiya tun rasuwar mahaifiyarta ta samu
matsalar Ƙwaƙwalwa, bata yadda da kowa ban saniba ko zaki iya zama da ita, danni da
banyi niyyar yin Aure ba, amma saboda Bulama ya matsa, kuma ke' yar uwarsa ce yasa
nace to shikenan na amince, amma ya kikace? "
Halima tace " insha Allah zan iya zama da ita in kula da ita, tunda kaga nima ina
da yara, in Allah ya yarda baze gagara ba"
Daula yace "Masha Allah, idan ba zaki damu ba, mahaifin yaran baze ce komai ba,
zaki iya tarewa tare dasu, mu zauna gaba ɗaya"
Nan ta rusuna tace "Masha Allah, nagode sosai Allah yasaka da alkhairi Alhaji"
Yarane sukayi sallama, suka amsa musu gaba ɗaya, su ukune bini in bika, sanye da
uniform ɗin makarantar gwamnati, kowannensu hannusa ɗauke da jakar nan ta da wadda
ake cewa Baba nagode, takalmansu Sandal wanda ake cewa ganda, duk sun tsufa sun
cinye, sun tsitsinke.
Yaran Biyu mata ne ɗaya namiji, suka gaida Daula, ya amsa musu cikin fara'a, Widad
ta dinga kallonsu ɗaya bayan ɗaya, tana kallon suturar jikinsu, duk wani iri haka
take ganinsu.
Namijin ne wanda aƙalla ze kai shekaru goma sha huɗu yace "Mama, wannan wacece?"
Yai maganar yana nuna Widad, Halima tace "to sarkin surutu, aje a cire Uniform".
Haɗe rai Widad ta ƙarayi ta kwanta a jikin Daula, Daula yace "ai bata da lafiya ne
Yaya Anwar"
Anwar yace "Allah ya bata lafiya, ina da sweet bari in baki kina so?"
Yai maganar yana zura hannu a jakar makarantar sa, ya miƙo mata alewa 'yar uku
biyar guda biyu, ga mamakin Daula yaga tasa hannu ta karɓa tace "thank you"
Nan Daula ya shiga murmushi, abunka dame ɗa, nan ya fara jin insha Allah a hankali
Widad zata ware, ta saki jiki dasu idan ya Auri Halima, Sukam yaran matan kallon
Widad kawai sukeyi, kyakkyawa da ita, ga gashi dan kanta ko ɗankwali babu, tana
sanye da riga da skirt kamar 'yar turawa, tana kwance a jikin Babanta ta buɗe
alawar nan tasa a bakinta, ta buɗe ɗaya tasawa Daula a baki gwanin ban sha' awa.
Suka tashi tafiya Daula ya babbasu kuɗi, babu ko kara suka karɓe, sedai fafur Anwar
yaƙi karɓa yace tunda an bawa Su Amal da mamansu baze karɓa ba, juyin duniya yace
a'a, Widad ta zura hannu a aljihun mahaifinta ta ɗakko kuɗi taje ta miƙawa Anwar
kuma ta tsatstsareshi da ido.
Daula yace "Good, kuma ba'a maida kyautar Gimbiya, ni idan na baka kaƙi karɓa, ita
ba'a maida mata da abu idan ta bayar"
Nan Daula yaji daɗin ƙauna da karamcin da sukayi musu, dan haka ya amince da Auren
Halima, amma yace baze zauna a wannan gidan ba canza gida zeyi.
Ya sanar da Bulama sun amince, haka Bulama ya wuce gaba Daula ya auri Halima,
sannan yace ta taho da 'ya' yanta ze riƙe mata.
Suka tare a sabon gidan Daula, sedai fa wannan rashin yaddar na Widad yana nan, sam
basa gabanta bata damu dasu ba, har gara Anwar shima wani lokacin take ɗan yadda
dashi, amma Ramlah da Amal kam bata ɗaukesu wasu mutane bama.
Part ɗinta daban a cikin gidan, dan karma wani ya takura mata.
Halima kam tana Auren Daula nan da nan 'ya' yanta suka koma ce mata Mummy daga
Mama, nan da nan sukayi shar, Daula ya sauya musu makaranta zuwa ta 'ya' yan masu
kuɗi, ha ajiye musu direba da yake kaisu yana dawo dasu, komai shar dasu nan da nan
suka fara canzawa, sedai babban abunda yake tsayewa Halima shine, Daula ya fifita
'yarsa akanta, ko magana tayi idan Widad ta rusheta ta zauna a gurin Daula, idan
wani abu kake so a hannun Daula muddin Widad ta amince ka samu, wani lokacin ma
itace zata baka, dan haka ta ɗorawa Widad karan tsana.
Ƙwayoyi da Alluran da akewa Widad sunyi tasiri a jikinta, ya zamana ko ba abata ba,
haka kurum zata fara wannan fizge fizgen da iface ifacen, idan har Daula baya nan
haka zata yi ta faman wannan kuruwar, suna jinta babu me kawo mata agaji, haka wasu
lokutan zata jiyawa kanta rauni, ta gama ihun harta gaji ta faɗi, Anwar ne kawai
idan yana nan yake iya taimakonta, Abinci idan anyi se anga dama za'a bata, ita
kuma baza tace a bata ba, amma a gaban Daula Suyita nan nan da ita suna bata kulawa
da nuna mata soyayya, baya kaso komai a ransa saboda halin ko in kular da take wa
su Halima, saboda yana tunanin yanayin ciwon nata ne.
Tun daga nan Widad ta ƙara tsinkewa da lamarin mutanen nan, suyita nuna mata kulawa
a gaban mahaifinta, amma daga ita sesu suyi ta zaginta, suna ce mata mahaukaciya.
Hakan yasa ta ƙara zame jikinta daga garesu, sam bata iya fitowa tayi karo dasu,
babban abunda ya ɗaure mata kai, be wuce yadda taga mutumin da taji an ambaci
sunansa ranar da aka kashe Amminta, yazo gidanba a lokacin Daddynta baya gari, abun
ya ɗaure mata kai sosai, ya daɗe a gidan sannan ya tafi, kafin ya tafi zuciya ta
dinga azalzalar Widad taje tai masa wani abu daze illatashi, amma ta gagara aikata
komai.
Jikintane ya fara tsuma, ta dinga tuna abunda ya faru, nan ta faɗi tana wannan ihun
da take yi idan abun ya motsa, suna jiyo kururuwar Widad amma kota kanta basu biba,
haka ta dinga gurnani ita kaɗai.
Anwar ya tafi ɓangarenta, yaje ya tarar da ita a zube a ƙasa a falonta, gaba ɗaya
bata hayyacinta, a gigice Anwar ya fito falo yace "Mummy, Widad fa ba lafiya, tana
sume a ɗakinta"
Halima ta lura da yadda Anwar yake nan nan da Widad, taga alamun bazata samu goyon
bayansa ba, dan haka ta maze sukaje kan Widad, ya kwantar da ita akan kujera, aka
kira likita, yace akaita can Asibitinsa, nan fa ya kuma ɗura mata wannan allura me
kama da ta doki, wadda ke gigita Widad.
Cikin tangaɗin wahalarwa da allurar ke mata, bata gane komai ga idonta a buɗe amma
sam bata cikin hankalinta, Wannan mutumin da aka ambaci sunansa ne yazo kanta, ya
ƙura mata ido sannan yace
"Ke ki gayamin inda kayan nan suke, takaddun nan da ubanki ya baki ayce akwai mesu,
suna ina?"
Kallonsa Widad take, bata gane gaskene abun yake faruwa ko kuma mafarkin ne, ta kai
idonta gefe taga Halima a zaune a gurin, lumshe idonta tayi taƙi magana.
Cikin tsawa yace " zakiyi magana ko sena miki azaba, irin wadda ba'a taɓa miki
makamanciyarta ba"?
Ko gezau ba tayi ba daga inda take, ta lumshe idonta tamkar bacci ya ɗauketa
Halima tace "bafa a hayyacinta take ba"
Mutumin yace "Aikuwa zata dawwama a haka muddin ba zata faɗa ba, semun kashe Uban
nata, an dinga ɗirka mata allurar nan kenan, da ƙwayoyi seta zama mahaukaciya
tuburan ta girma tana yawo tsirara tana bin bola saboda rashin gata"
Widad najinsa, wani irin ƙuna ranta ya shiga yi, yasa an kashe mata mahaifiya, kuma
yazo kanta yana gayamata maganar banza, sam takasa gane ko mafarki take ko a zahiri
abun ya faru, ganin haka yasa hawaye ya fara bin gefen idonta, ta tabattar da ta
haukace.
Can bayan wasu awanni, taji an taɓata ai wani kukan kura tayi dan a zatonta wannan
mutumin ne, ta kai masa wata irin mahaukaciyar shaƙa tana zazzare ido, sedai kuma
se taga ashe mahaifinta ne, da farko fuskar wancan ta gani, daga baya kuma taga
ashe Daddynta ne, ba ƙaramin tsorata Daula yayi ba, tunda har Widad ta fara ƙoƙarin
shaƙeshi to tabbas hauka ya tabatta, a hankali ta ajiye hannunta ta kwanta a jikin
Daddynta.
Ko mintuna biyu ba'ayi ba kuma se bacci, amma cikin baccin banda mafarke mafarke ba
abunda take yi, seta dinga ganin mafarkan kamar gaske, dan haka seta ƙwala ihu.
Sosai fa Daula ya shiga damuwa, Doctor Hamisu yace "Ranka ya daɗe, kaga ana
treatment ɗin nan but her body is not responding to the treatment, dan haka she
needs to be admitted to psychiatric Hospital, yadda za'afi kula da ita"
Hawaye ne ya ƙwacewa Daula yace "Over my death body, in ɗau 'yata da hannuna in kai
psychiatric, bazan iya ba, zan cigaba da kula da ita, idan yaso a cigaba da mata
treatment"
Bayan ta ɗan farfaɗo, ya ɗau' yarsa yayi gida, kwana biyu ta ɗanji sauƙi amma
lokaci lokaci takan yi ihun nan na dare.
Daula yana zaune da Halima da yaranta a falo suna hira, harda yaranta da jansu yake
kamar 'ya' yansa, Widad ta fito tana taku ɗai ɗai tana kallonsu, Babban abunda ya
ƙular da Halima be wuce yadda Daula ya miƙe tsaye ba domin tarar Widad, sekace yaga
wa shugabarsa, gata gwansamemiya da ita, kusan shekara tara amma haka yake ɗorata a
cinya kokuma ya goya ta a bayansa, ta zauna a cinyar Daula tace
"Daddy, tunda babu me dubamin wanda ya kashe Ammina, ina son gidan nan da Ammi ta
rasu ka siyomin su zomo, su mage da duk domestic Animals, ka haɗa dana Ammi in
dinga ganinsu"
Daula yace "considered it done your majesty, yadda kike so haka za'ayi, kwanan nan
ina son in buɗe miki Account mu dinga tara ribarmu ta kasuwanci nida ke"
Murmushi kawai Widad tayi ba tace komai ba, se can tace "Daddy wai na dena zuwa
makaranta ne?"
Daula yace "ina so ki warke ne tukuna, bana son a kaiki makaranta ki cigaba da
rashin lafiya"
Widad tace "Daddy bana son zaman gidan nan kwata kwata"
Cikin Halima ya ɗuri ruwa, ta zata Widad zata tona mata Asiri, amma se tace "idan
ina nan ina tunanin Ammine sosai"
"Babyna, shiyasa muka taso daga wancan gidan fa, saboda ki dena ganin abunda ze
ɗaga miki hankali"
"Nan ma akwai wanda yake ɗagamin hankali, kuma ni makaranta nakeso in koma, ka
maidani gidanmu na England seka kaini boarding school"
"No Daddy, kaga nan kullum kana cikin damuwa saboda ni, ni kuma ina tsorata sosai
anan, dan Allah ka kaini can bana son zaman nan, please Daddy"
Anwar yace "banji Daɗi ba, bazan ji daɗi ba idan kika tafi Widad"
Widad ɗin dako fara'ar kirki ba tayi amma tai murmushi, dan Anwar yana nuna mata
tausayi, ko Daddy baya nan idan shi yana nan suna sassauta mata, Widad tace "ko
zaka bini ne, mu tafi tare?"
Anwar yace "Ƙwarai kuwa, daga nan har birnin sin, idan zaki dani zan biki"
Murmushi tayi tace "aini makarantar mahaukata za'a kaini, kai kuma kana da hankali
ai"
Sosai Anwar yaji tausayinta yace "Ai zakiji sauƙi insha Allah, zaki warke ki dena
cewa kanki mahaukaciya"
Halima da tun ɗazu ba tace uffan ba, dan wani mugun haushinsu take ji, da gashi har
'yar tasa.
Kwana biyu da yin wannan maganar, cikin dare suna bacci aka kuma shigowa gidan,
dukda tarin security dake layin gidan, still dai wannan takaddu suka sake biyowa,
aka rufe ɓangaren Halima da' ya'yanta suka shiga na Daula suka tarar dashi yana
bacci, Widad na bayansa tana bacci itama.
Haka suka tashesu, Amma saboda gaddama da taurin kai irin na Daula daga shi har
Widad suka ƙi magana, a gabansa suka dinga solata suna bugawa da ƙasa dan tayi
magana amma taƙi, ba abunda Daula ze iya saboda kashedin da suka yi masa na zasu
kashe Widad idan yayi wani yunƙuri.
Wani daga cikinsu yakama kumatun Widad, da suke ɓulɓul jajawur saboda hutu, yasa
Ƙaton hannunsa ya matse da ƙarfi seda tayi wani uban zillo dan azaba ta saki
fitsari, amma taƙi magana se kace wata itace.
Ƙarshe haka suka yi jifa da ita a galabaice, suka zuba mata ido, tana kallon Daula
yana kallonta yana hawaye itama tana yi.
Ɗayan yace "Wallahi ban taɓa ganin halitta me taurin kan mutumin nan da 'ya' yansa
ba, ba dan ba abamu umarnin kisa ba, da wallahi sena musu kisan wulaƙanci mafi
azabtarwa"
Ƙarshe haka suka haƙura suka tafi, Widad ta shiga tunanin ya akayi aka kuma shigowa
gidan duk da tarin security ɗin nan?
Ɓangaren Daula ma yanzu ya amince dole Widad ta bar ƙasar nan dan tseratar da
rayuwarta, kusan kullum cikin turo masa saƙo ake akan idan be bayarba za'a kashe
shi, ko a sace 'yarsa, tun yana damuwa harya fara sabawa.
Ya nemi shawarar Bulama, Bulama ya goya masa baya akan ya fita da Widad ƙasar waje,
hakan tamkar tseratar da ita ne.
Haka kuwa akayi, Daula ya nemawa Widad makaranta a makarantar masu fama da larura
ta musamman a ƙasar England, Anwar kamar yayi kuka, Widad tace tana son ya rakata
makarantar, karon farko da Anwar ya hau jirgi.
Cikin harshen larabci Widad tace "ni ba uwata bace, uwata ta mutu bani da uwa a
yanzu, kuma ni mahaukaciyace, babu wanda zeso ya zama maman mahaukaci"
Daddy yai shiru yana kallonta, bece komai ba suka tafi airport, da ita da Daddynta,
da Bulama da Anwar suka tafi, tana tunanin irin zaman da Daddynta zeyi da wannan
matar me fuska biyu, dan ko a yanzu ta lura da tana wulaƙanta mata mahaifi wani
lokacin, kuma baya iyayi mata magana.
Haka aka kai Widad wannan makaranta, aka danƙata a hannun likitocin can ƙasar,
Daula yana kuka itama tana kuka suka rabu.
Tun a hanya kewar Widad ta damu Daula, Anwar ne yaita bashi haƙuri, dan Bulama ya
gaji da rarrashin Daula.
Haka ya dawo gida zuciyarsa fal tunanin Tilon 'yarsa, yanzu bashi da kowa se Allah
se' yar nan, yana mata son da shi kansa be san kansa ba, dan duk ƙaunar da yakewa
mahaifiyarta ta koma kanta.
Kamar yadda Widad ta buƙata, wannan Ƙaton gidan nasu na farko, haka ya zuba
dabbobin nan a gidan nan, dukda Widad ɗin bata nan.
Kullum cikin hirarta yake da begenta, abun fa ba sauƙi, dan ba'a fasa masa barazana
ba iri iri, ta waya akan dukiyar nan, ƙarshe ya ware kason Widad a dukiyarsa, itama
yasa mata a kasuwanci aka cigaba da juyawa, haka rayuwa ta cigaba da tafiya.
Da Anwar yayi candy, Daula ya ɗauke shi dashi da Fahad ya kaisu ƙasashen waje yayi
sponsoring ɗin karatunsu, da komai da komai.
Amal da Ramlah kuwa manyan makaratun yaran masu kuɗi suke yi, ya mallakawa Halima
kadarori da dama, taje Saudiyya ita da yaranta, duk ƙasar da suke so sunje, an kai
waninta ma, amma gaba ɗaya bata gani ba, wannan dukiyar ce take hari itama, ga
baƙinciki da kishin da take da Widad da Huda wadda ta riga ta rasu, jin maƙudan
kuɗin da suke Asusun Widad kawai ba ƙaramin firgita ta sukayi ba.
Saleh kuwa bayan an kama Bala ɗanuwansa, maƙiyan Daula sukayi amfani da shi suka sa
aka kai shi gidan Daula yin aiki, dan ya zame musu CID, suka cusa masa aƙidar
lallai yaɗau fansar abunda akayiwa ɗan uwansa Bala.
Haka Widad ta cigaba da rayuwa, a cikin mahaukata iri iri, ana cigaba da bata
kulawa a can, komai yi musu akeyi, Daula na yawan zuwa ganinta, dan wasu lokutan
har gidansa na can yake tafiya da ita, suyi kwanaki su sha hira sannan in ze tafi
ya maida ita, lokaci lokaci Bulama ma yakan kai mata ziyara, a bayan gidansu gidan
Alhaji Musa yake, dan haka sukan haɗu da juna.
Lokacin da zata shiga high school (secondary school) tace lallai se an cire ta daga
makarantar mahaukata, dan ita ta warke, da yake Daula baya son ɓacin ranta haka ya
cireta, da yake dama Asibiti ne haɗe da makarantar masu buƙata ta musamman.
Daula ya taho da Hajiya Halima da yaranta, amma a ranar seda jikin Widad ya kusa
motsawa, ta birkice masa sosai, tace "kodai su bar mata gidan nan, ko ita ta bar
musu"
Daula yace "daughter, Mummy cefa kuma dan su ganki suka zo"
'Daddy karka ƙara ce mata Mummy na, kuma ina neman alfarmarka, idan har ina England
karsu ƙara sa ƙafa a ƙasar nan, nan gidan Ammi ne da ita muka rayu a cikinsa, dan
haka bana buƙatarsu anan "
Aikuwa jikin Daula yana rawa, aka maida su Hajiya Halima Hotel, abun nan ya
baƙantawa Hajiya Halima rai fiye da tunani.
Tun daga nan suka fara takun saƙa, duk isa da hura hancin da Halima take yi se
Widad tayi abunda zata nuna mata bata isa ba.
Widad ta shiga high school, itama boarding ce, amma bata mahaukata ba.
Daga ƙasar da take idan taso se tayo waya, ta bada umarni a Nigeria kuma abunda
tace shi za'ayi, duk azabar bin malaman Halima, amma ta kasa raba Daula da Widad.
Wataran Widad tazo hutu Nigeria....
LITTAFIN KUƊI NE, DAN ALLAH KI SIYA KAFIN KI KARANTA BA DANNI BA DAN ALLAH, LITTAFI
NA ƊAYA KYAUTA NE WANNAN NA SIYARWA NE
NORMAL GROUP ₦300
VIP ₦500 NE KITURA TA WANNAN ACCOUNT ƊIN
0009450228
JA'IZ BANK
AISHA ADAM
SE A TURA SHEDAR BIYA TA WANNAN LAMBAR
07063065680
IDAN KUMA KIN SIYA AMANACE KARKI FITARMIN DAN ALLAH 🙏🙏🙏
11/14/21, 6:09 PM - Ummee Musa: .LITTAFIN KUƊI NE, DAN ALLAH KI SIYA KAFIN KI
KARANTA BA DANNI BA DAN ALLAH, LITTAFI NA ƊAYA KYAUTA NE WANNAN NA SIYARWA NE
NORMAL GROUP ₦300
VIP ₦500 NE KITURA TA WANNAN ACCOUNT ƊIN
0009450228
JA'IZ BANK
AISHA ADAM
SE A TURA SHEDAR BIYA TA WANNAN LAMBAR
07063065680
IDAN KUMA KIN SIYA AMANACE KARKI FITARMIN DAN ALLAH 🙏🙏🙏
82_83
Lokacin da tazo Nigeria, maƙerin budurci ya fara ƙera Widad, ta fara zama budurwa
me ji da kyau, zamanta a Turai sam bata san saka wata Atamfa ko makamancin kayan
al'ada ba, da Amminta na da rai ma mafi yawan rayuwar su tana Turaine, dan haka
sedai a saka mata blouse, yanzu kuma babu ran mahaifiyarta, gashi a tsakiyar turawa
take, dan haka duk shigar da taga dama yi take ba wanda ya damu, Daula ya ɗaukar
mata Nanny, idan anyi hutu tana gidansu na can, ita da Nannynta wata 'yar Nigeria
ce amma bayerabiya, sedai a dafa taci, hatta gadonta da zata kwanta ta tashi sedai
a gyara mata, saboda haka bata iya komai ba.
Itama Nannyn Widad ba wani yadda take da ita ba, gani take duk wanda ta yadda dashi
ze iya cutar ta, ba abunda Widad ta iya na aiki, duk wani abu yi mata ake, ba wata
wahala data sani a rayuwar ta, komai ta nema akwai available, kuɗi ko nawa take
buƙata akwai shi available.
Widad tazo Nigeria, Daula ya dinga murna dan kusan shekararta Biyar bata taka
Nigeria ba, sedai tunda ta dawo babu ragayya ko sassauci tsakaninta dasu Amal da
babarsu, sam basa gabanta idan tana rayuwa a part ɗinta mantawa take dasu, Daula ya
dinga zagayawa da ita guraren kasuwancin sa, da wanda yasa aka buɗe mata, taje har
tsohon gidansu data sa aka maida shi na gona, gurin yayi mata kyau, tasa aka gyara
mata wasu abubuwan aka canza mata wasu, ta cewa mahaifinta wato Daula tana son a
siya mata dokuna biyu irin na wasan polo a saka mata a gidan, sannan aka kawo wani
kare nasu, wanda yake a ƙasar waje, tasa aka kawo shi gidan aka ajiye.
Cikin hira Daula yake gayawa Hajiya Halima batun siyan doki, yace
"kinga rigima irin ta 'yarki ko? Saboda rigima wai dokin polo takeso a siyo a
samata a wancan gidan namu, nasa ayo mata order su"
Dama Hajiya Halima tayi tayi su koma wancan gidan, dan yafi haɗuwa da girma amma
Widad tace baza"a koma ba, ƙarshe ma tasa aka zuba mata kiwon dabbobi a ciki, wani
ɓangaren gida sosai, wani ɓangaren gidan gona.
Hajiya Halima tace "Yanzu kai Alhaji saboda ka rasa abunda zakayi da kuɗi, seka sai
wannan dokunan? Suna fa da tsada, kuma me zata yi da wasu dokuna tana mace"
Daula yace "Ai babu itace damuwa, amma tunda akwai za'a sai mata, ian son abunda
takeso, kin san ba wata lafiya ce sa ita ba, shiyasa nake son yi mata abunda
takeso, kodan ta samu farinciki, na rasa me zanyi wanda ze dinga ɗebe mata kewa,
yasa ta sake da kowa"
Widad data kawo kai zata shigo falon Daddy taji wannan maganar da suka yi, da yadda
Halima take kushe a sai mata abunda takeso, Widad ta maze ta shiga falon ta kalli
Daula tace
"Weldone Dad"
"Fine Daddy"
Widad tace "No but Daddy, i see over twelve cars in the parking space, what are
they used for?"
Daula yayi murmushi yace "na gidane, wanda muke hawa, ni nawa biyune kawai sauran
na mamanki ne da Yayyaenki, tunda kinzo kema se ki sai wanda kike so"
Widad ta haɗe rai cikin hura hanci tace "Niba uwata bace, bani da uwa dan haka bata
haifeni ba, , and na saka a kwashe motocin a kaimin su farmhouse a ajiye, na barwa
kowa mota ɗaya yayi amfani da ita ta isa, kai kuma an bar maka naka my king" ta
ƙarasa maganar tana murmushi.
Daula yace "to babu laifi, godiya muke gimbiyar Daula, yadda kikace ai haka za'ayi"
Tayi wa Hajiya Halima wani kallon tsana na baki isa ba sannan ta fice, tana fita
Halima zata fara complain, amma Daula ya dakatar da ita yace "itama dukiyarta ce,
duk yadda tayi daidai ne"
Halima taji kamar ta samo abu ta kashe Widad dan baƙin ciki, tun daga Nan fa suka
dinga takun saƙa da Widad da matar babanta, bata ganin mutuncinsu sam, sannan bata
yadda da kowa ba, sakamakon duk wanda suke cutar da Mahaifinta Yaran talakawane
daya janyo a jikinsa sukayi Arziki sanadinsa, wanda ya yarda dasu sune suke cutar
dashi.
A wannan zuwan ma, seda akai kaiwa Widad Mummunan Hari, akaso a sace ta amma Allah
ya kuɓutar da ita, daga nan ta tattara komatsanta ta koma England ta cigaba da zuwa
makaranta.
Daula ya bubuɗe guraren kasuwanci da kuɗinta, ciki hadda manyan gidajen gona,
shagunan kasuwa da sauransu, dan haka Widad ma ta kasance 'yace me arziki a ƙashin
kanta.
Gaba ɗaya a rayuwarta batayi zaman shekara shida a Nigeria ba, shiyasa abubuwa da
dama ita bata sansu ba, ko in anyi take mamaki.
Wannan hali da ta tsinci kanta a ciki a rayuwarta yasa, ta yanke ƙauna da samun
mutanen kirki, wanda ze zauna da kai a halin akwai ko babu, kuma ta yadda cewa duk
talaka ze iyayin komai akan kuɗi, ta yadda idan har ka amince da mutum ya shiga
jikinka, shine na farko daze fara cutar ka, ta lura mutane da yawa suna nuna mata
kulawa ita da mahaifinta ne saboda wannan dukiyar da suke da ita, da babu wannan
dukiyar da ba zasu dinga mutuntasu haka ba, dan haka itakuma take taka duk wanda
taso.
Tun data bar Nigeria a wannan lokacin bata kuma dawowa ba, seda ta cika shekaru
goma sha takwas, bayan shekara huɗu kenan, lokacin ta zama cikakkiyar budurwa,
yanayin tsarin rayuwarta duk na turawa ne, dukda hali na rashin sakewa da mutane da
take dashi, amma tana zuwa gurin shaƙatawa da buɗe ido.
Bayan gama high school ɗinta tace a Nigeria zata zo tayi karatun Jami'a, saboda
kawai ta ƙallafa ran seta ta gano suwaye kuma suke da sa hannu akan kisan
mahaifiyarta, suke cigaba da bibiyarta da mahaifinta akan dukiyar nan? Kuma tana
son nunawa Hajiya Halima iyakarta saboda zaƙewar da take tayi yawa, da yadda take
juya Daula yadda take so.
A wannan dawowartata ne aka kawo mata kusan direbobi uku, amma da sun fara aiki se
taga kamar an haɗa baki dasu zasu cutar da ita, dan laifi ƙalilan seta kori mutum,
bata ragayya bata sassauci bata afuwa ga ƙarya ko yaudara.
Dukda wannan tsawon shekaru, Magungunan nan basu dena aiki a jikin Widad ba,
sakamakon ƙarfinsu ne da pressure da suke bawa jikinta yasa ta kamu da ciwon
zuciya, ko kuma haka nan jikinta ya rikice ta fara wannan tsoron.
Widad ta ɗanyi shiru sannan tace "Nasan akwai abubuwa da nayi da kake buƙatar
sanin dalilina na yinsu, akwai ranar da mukaje Hotel nace maka ni karuwa ce, naje
wannan Hotel ɗinne, dan ganewa idona wani abu kuma na gani, wasu mutane ne da nake
zargi da sa hannunsu, na gansu tare da matar Daddy, da alama sunyi meeting ne, kuma
nasan akan Daddy ne, munje Club tare ranar harka hanani shiga, naje ne domin in
kama Fahad red handed ta yadda maganar Aure tsakanina da shi zata rushe, haka nan
tun zuwanka naji wani sashi na zuciyata nason Amincewa da kai, dukda wani ɓangaren
yana gargaɗina, nace bari in jarrabaka tukuna, duk inda zanje nake tafiya da kai,
sannan na maka umarnin cewa ban yadda kayi magana da kowa ba duk inda zamuje,
saboda ina tsoron a haɗa baki da kai, watarana kana zaune a gidanmu inda ka saba
zama, ina kan varrendar na saman bene, kawai na hango Amal taje inda kake, ka taso
kuka taho tare, na fito falo inga meze faru, za kayo hanyar part ɗina, se tace maka
ai bana nan ina part ɗinsu, ka bita zuwa ɓangaren su, ni kuma na bi bayanku, nasan
zakayi mamaki daka fito ka ganni a tsaye a gurin amma ban ce maka komai ba, haka
kurum na fara sakewa da kai bayan na gano waye kai, ganin bibiyata da ake ya fara
yawa yasa na ƙara jarrabaka, na baka ATM ɗina, ka tafi dashi tsawon sati biyu, a
gaban mutanen gidanmu, wanda nasan dole su bibiyeka a kai, amma ga mamakina bayan
sati biyu, se gashi ka dawomin da shi, ba tare da ko ƙwandala ta ɓata ba, kuma yana
daga abunda ya ƙara nesantani da mutane shine, duk wanda ya raɓeni shima cikin
matsala yake shiga, an dinga bibiyarsa kenan dan a samu wannan takaddun, shiyasa
nake sake yin baya baya da kowa, sedai kai ka riga ka shigo rayuwata gaba ɗaya, ban
iya kareka da shiga hatsarin da nake ciki ba, seda aka ritsa da kai, sannan
ƙiyayyata ga Aure kuma ya samo asaline ga yadda naga Bulama ya maida Aure da saki
tamkar shan ruwa, nakan bibiyi shafukan sada zumunta na kanga irin complains akan
Aure, kuma ga mahaifina yayi Aure, Amma matarsa sam baya gabanta abunda yake
hannunsa shi takeso, se nake ganin muddin nayi Aure tamkar na shiga matsala ne,
kuma komai ze iya faruwa dank, kuma a yadda nake jina bazan zauna ƙarƙashin wani
yayi amfani da ikonsa a kaina ya wulaƙantani ba, shine abunda ya faru har zuwa
ɗaukemu sa akayi tare, Yoseef wannan shine ƙarshen labarina dana mahaifina, kaga
laifina akan AƘIDATA? Ban cancanci in guji mutane ba? Ko kuma rayuwar kaɗaici zata
zama laifi idan har nayi hakan ne dan kaucewa tarayya da azzalumai masu biyu?
Mutane dayawa basu san meyafaru dani ba, abu ɗaya kullum suke kallo shine AƘIDATA "
Shiru Yusuf yayi, yasa hannayensa biyu ya dafe kansa, Widad tasa hannu ta janye
nasa, tace " Kana jina kuwa?"
Wata irin ajiyar zuciya yaja, wadda seda Widad ta ɗan razana, ta ɗau fitila ta
haskashi, sedai taga Hawaye a Fuskar Yusuf, jijiyon kansa duk sun ɗaga ya ƙara wani
kwarjini, ga ja da idanunsa sukayi, saboda labarin Widad ya kaɗashi matuƙar gaske,
gaba ɗayanta abun tausayi ce, taga jalala da iftila'i me ban tausayi, a kashe maka
mahaifiya a haukata maka tunani, sannan a cigaba da bibiyar rayuwarka da barazana
da tsoratarwa iri iri.
"Shiyasa na dinga ja maka rai fa akan baka labarin nan, kalli yadda ka ɗaga
hankalinka hadda kuka, dan Allah kabari Yoseef, ni yanzu na fara mantawa da wasu
abubuwan saboda sadaukarwarka a gareni, baka yi sallar isha'i bama, gashi yauma
munyi dare, kayi salla kaci Abincinka seka kwanta "
Bece mata komai ba ya miƙe, sosai yake jin tausayin Widad, gaba ɗaya labarin nan ya
tsaye masa a ransa, Widad ta koma kan shimfiɗarta, sannan ta fara zubda nata
hawayen dan bata son ta sake ɗaga masa hankali, tana kallonsa sau biyu yana sake
sallame salla, yayi ya idar nan ma ya daɗe sosai akan sallayar sannan ya tashi, be
ko kula Abincin ba, shimfiɗar ma beyi ba a ƙasa yaje ya kwanta a rigingine.
Nanfa Ƙwaƙwalwarsa ta shiga kaiwa tana komowa akan abubuwa da dama, da irin
binciken da yayi, lokaci lokaci idan ya tuna labarin Widad se yaja tsaki, dan ya
rasa a inda yakamata ya ajiye wannan tsagwaron zalunci haka.
Ƙarshe ma tashi yayi zaune ya sake dafe kansa, sedai Duk abun nan Widad tana
kallonsa, tana tunanin yanzu akwai wanda zeji labarin abunda ya sameta ya tausaya
mata haka, harya shiga wannan irin damuwar? Dukda tarin wulaƙanci da isa data dinga
nuna masa, amma ya dake ya shanye har yake jin tausayinta haka, bayan ɗawainiyar da
yayi da ita, da ƙoƙarin kareta daya dingayi, lokacin da akazo sace ta ba dashi
sukayi niyyar ɗauka ba, ya dage ba zasu tafi da ita ba, shine suka haɗa dashi, ga
wahala da azaba da ya sha gurin kuɓutarsu, gashi har yanzu a kan shan wahala yake,
a rayuwar da tayi idan akace mata akwai mutum me irin zuciyar Yusuf a zamanin nan
to tabbas za tace ƙaryane, ita kam me zata yiwa Yoseef, ta saka masa tasan ko duk
abunda ta mallaka zata bashi bata isa ta biya shi ba.
A hankali ta tashi ta tafi inda yake zaune ya rafka tagumi, ta janye hannun tace
"wai bazaka kwanta bane? Kuma ina shimfiɗar kake zaune a ƙasa haka?"
"ko Abinci ma fa baka ciba, ga yunwa ga rashin bacci? Gaskiya ban yadda ba"
Yusuf yace "kije ki kwanta kawai, ni bana jin bacci"
"A'a, kije ki kwanta kinji nasan zaki bacci idan kika kwanta"
Tai murmushin ƙarfin hali tace "baka san jikinka yafi katifar nan daɗin bacci ba,
kwanta se in kwanta"
Haka Yusuf ya kwanta, ita kuma ta kwanta a jikinsa, tasa hannu ta zare ribbon ɗin
kanta, ta kamo hannunsa ta ɗora a kan gashin ta, a hankali ya rungumeta da hannu
ɗaya, yasa hannu ɗaya yana wasa da gashin nata.
Tana jin yadda zuciyarsa ke lugude da ƙarfin gaske, ya zamana ma taji kamar baya
numfashi daidai, dukda a duhu ne amma Widad ta gane har yanzu Yusuf kuka yake, yana
da matuƙar dauriya da juriya, amma wannan karon ya kasa jurewar, saboda jin Widad
yake tamkar wani sashine na tsoka a zuciyarsa, haka kurum yake jin kamar shi
akayiwa laifin ma ba ita ba.
Ƙanƙame Yusuf tayi ta fashe da kuka, Cikin jan numfashi Yusuf yace "Widad lafiya,
kukan me kike kuma?"
"Dan Allah Yoseef kamanta da labarin nan da na gaya maka, karkasa shi a ranka dan
Allah, kar wani abu ya same ka ji yadda kake numfashi fa"
Sosai ya sake rungumeta yace "Never mind dear, ba abunda ze sameni insha Allah,
ina tunanin meye mafita ne kawai, a shirye nake da in baki gudunmuwa kota wani
ɓangare dan tina Asirin wanda suke aikata muku wannan zalunci haka, amma kafin nan
nasan koba duka ba kin san wasu daga cikin mutanen nan, meyasa kika ƙyalesu baki
tona musu Asiri ba? "
" Yossef yadda nake shiri akansu haka suke yi a kaina, sun fini iya mugunta da
zalunci, na haskawa mahaifina wasu daga cikin su, hakan yasa ya yanke hulɗar
kasuwanci da wasunsu, sannan wace hujja nake dashi daze tabattar da abunda nake
zarginsu? Bani da sheda se Allah"
Cikin raɗa Yusuf yaje dai dai kunnenta yace "meyasa kika ƙyale Bulama, bayan ko a
binciken da nake, ina sanya babbar alamar tambaya a gareshi, dan sam ban yadda da
shiba, amma naga kina masa kallon uba, kuma ni shine babban suspect ɗina"
"Saboda bashi nake hari ba, Bukar nake hari, na barwa zuciyata insha Allah koni ko
shi, ko kuma muyi mutuwar kasko dashi, Insha Allah se Bukar yaje ƙiyama da tabon da
zan masa, ya azabtar da rayuwata, yaso kassarani da mahaifina yamin zalunci mafi
muni, wannan abunda akayi mana nasan da sa hannunsa, da Bukar da Baban Nurat sesun
wulaƙanta a rayuwa, sun cutar dani Yoseef " tai maganar tana fashewa da kuka,
rarrashinta ya dingayi sannan yace
"Waye kuma Bukar? Banji kin faɗe shi a labarin da kika bani ba"
Ta gyara kwanciyarta sannan tace "Bukar! Bukar! Alhaji Bukar! Tabbas ban faɗeshi a
labarin da na baka ba, saboda labarin ma wani sashe na baka, na ɓoye maka wani, na
kuma canza inda faɗa maka bashi da amfani, saboda jin wani sashin na labarina a
gareka tamkar tarwatsa shirin sa nake ne, amma ina fatan ubangiji, Allah ya maida
mu gida lafiya, zan baka sauran ɓangaren dana cire maka a labarin, dan se mun koma
gida jin ɓangaren zeyi amfani, har in cika dukkan burikana, sannan a lokacin zan
baka labarin waye Bukar "
Yusuf yace " Shikenan, ubangiji Allah ya kawo lokacin da zamu koma, Insha Allah se
inda ƙarfina ya ƙare Widad, zan baki goyon baya ɗari bisa ɗari mu shiga kowane irin
ƙalubale dan cikar burinki"
Haka suka kwana a ƙasa shida ita, a gurin nan ga sanyi cikin dare amma basu iya
tashi daga gurin ba, saboda damuwar da zukatansu suke ciki.
Umman Yusuf se fama take da hawan jini saboda damuwa da tunani, ga rashin cin
Abinci da bata iya ci balle bacci, gaba ɗaya ta rame tayi wani iri saboda tunanin
halin da ɗanta Yusuf ke ciki, ga kuma wannan labari daya cika gari, ita dai tasan
ɗanta ba mutumin banza bane, dan tasan tabbas wannan zance ƙaryace akayi masa.
Tana nan kwance bayan la'asar a inda tayi salla, tana jan carbi tana ta kai kukanta
ga Allah akan Allah ya kuɓutar mata da ɗanta, yasa yana cikin ƙoshin lafiya.
Sallama Suleiman yayi, taja jiki da ƙyar ta tashi zaune da ƙyar ta amsa masa, ya
tsorata ganin halin da take ciki, a ɗan firgice Suleiman yace "Umma meyasameki
haka?"
Take ta fashe da kuka tace "baka ga Sanarwar da akayi a kafafen yaɗa labarai bane?
Wai Yusufana ake nema ido rufe wai ya sace 'ya, haɗuwar Ɗana da wannan alhali ba
alheri bane, tunda ya fara aiki da yarinyar nan walwalarsa ta ragu kullum cikin
tunani yake, kullum cikin damuwa yake banda sintirin fita da wuri baze dawo ba se
dare amma ƙarshe abunda za'a sakamana da shi kenan, bakomai akwai Allah, Allah ya
bimana haƙƙinmu"
Suleiman yace "Umma kiyi haƙuri, yanzun ma abunda ya kawoni kenan, amma yanzu zan
fara kaiki Asibiti tukuna, a duba ki kamar baki da lafiya"
Umman Yusuf tace "Ni ba inda zani, lafiya ta ƙalau ɗana nake tunani kawai, shiyasa
ake ganin kamar bani da lafiya"
Da ƙyar Suleiman ya lallaɓata ta yadda ya kaita Asibiti, sukaje akayi mata gwaje
gwaje, akace hawan jinine ga ulcer, aka rubuta mata magunguna sannan ya ɗauketa
zuwa gida.
Suna tafe tana share hawaye, bayan ya kaita gida yace "Umma ki kula da
magungunanki, kidinga shansu akan lokaci, sannan shi lamari irin wannan Addu'ar ku
muke nema, idan harda Addu'ar ku, babu wani abu daze same mu insha Allah, Yusuf
Addu'ar ki yake nema kiyi haƙuri, komai ze daidaita insha Allah"
"Amma Suleiman, kana ganin yau watanni huɗu kenan, ban saka Yusuf a idona ba, baya
nan ban san idan yake ba katsam kuma inga wannan al'amari haka, kuma naji labarin
Abokinsa Abbas yazo, amma ko jaje bezo yamin ba"
Suleiman yace "ki kwantar hankalinki Umma, Abbas baze dawo miki da Yusuf ba, ki
manta dashi, Insha Allah muna nan muna ƙoƙari akai, sannan insha Allah zan kawo
miki kayan Abinci dana buƙata, amma kisa haƙuri a ranki"
Umma tace "shikenan, nagode sosai Allah yasaka da alkhairi, Allah yayi maka albarka
ya raba ka da duniya lafiya"
Aka cigaba da yamaɗiɗi da zancen Yusuf, akan ya sace Widad ya gudu da ita,
fastocinsa suka cigaba da yawo, dayake in Allah yasa kana zaman lafiya da kowa,
baka rasa masoya, wanda suka san Yusuf suka san halinsa suka dinga ƙaryatawa, suna
taya shi da Addu'a.
Ramlah na kwance akan gadon ɗakin Hotel, Fahad yana tsaye yana taje kansa a gaban
mudubi, Ramlah tace "Fahad, lokaci fa yana ƙurewa, zuwa yanzu yakamata ace an fara
maganar aurenmu, amma naga kamar baka damu ba ko zancem baka yi"
Fahad cikin salonsa na yaudara yace "Beb kin fiye garaje fa, mubi komai a hankali
mana, nida nake so ayi classic wedding, so nake bikinmu ya zama the expensive
wedding of the year, wasu kuɗi nake jira a hannun Dad, shiyasa amma kiyi haƙuri,
soon za'ayi komai insha Allah"
Ta ɗan kwaɓe baki tace "Allah yasa, danni ina ma tantama akanka, kar inje Widad
ta dawo kaƙi Aurena kace se ita, dan haka kayi min wancan karon"
"No karki damu, ai abunda yaaa nace zan Aureta, saboda in karɓo mana kuɗaɗen
hannunta ne, in rabata da komai im azabtar da ita, sannan in sake ta, that's my
plan, but unfortunately it's fails, ni yanzu wannan jakin daya gudu da ita, Allah
yasa karya karɓe abun ya barmu "
Ramlah tace 'kamar kuwa ka sani, dan wallahi zata iya bashi, can you imagine ATM
ɗinta yayi over 1 week a gurinsa, naje masa mu haɗa kai a samu wani abu amma fafur
yaƙi, munafuki se gashi yayi awon gaba da ita"
Fahad yace "suje su ƙarata, ai tunda ba' a san inda Dad ɗinta yake ba, zan cigaba
da kawo masu siyan kadarorim nan, a rage wani abun"
Ramlah tace "hakane kam, nidai so nake ayi muyi Auren nan, kaga sau biyu ina
abortion fa"
"Aini kasan abun planning ɗin nan, suna da nasu matsalolin, ɗan bani tablet biyu in
saka a coc, i want doze up"
Ya miƙo mata magani, ta zuba a lemo ta girgiza tasha, sannan ta kwanta bacci.
Ya kalleta a ransa yace "baki da hankali, uban waye ze Aureki ashe ma bani da
hankali, zanta lallaɓaki ina morewa, gefe guda kuma in cigaba da damfararku"
Yauma Yusuf se a ɗaki sukayi salla, dan bacci be ɗauke shi ba, se daf da Asuba.
Bayan sunyi salla, suka koma suka kwanta bacci, sedai shi Yusuf baccin ya gagareshi
sam, a cikin tunanin ma ya raaa wanne zeyi, se kusa ƙarfe goma sannan ya kwantar da
Widad ya tashi ya shiga gyaran ɗaki, ya shaee ɗakin ya haɗo kwanukan wanke wanke ya
fito tsakar gida.
Da Hanne yayi karo tana shara, tana ganinsa ta zuba masa ido tana murmushi, Yusuf
yace mata "Ina kwana"
Tasa hannu ta karɓa, Yusuf ya koma ɗaki ya dafawa Widad ruwan wanka, sannan yaje ze
tasheta.
Zama yayi ya zuba mata ido, yana jin ƙaunarta da wani irin tausayinta yana ratsa ko
ina na jikinsa
Numfashin da yake mata a fuskane yasa ta buɗe ido tana kallonsa, har yanzu idon
Yusuf ja, ga alamun damuwa nan ƙarara a fuskarsa.
Miƙa tayi tana ɗan lumshe ido, Yusuf se binta da kallo yake.
Ajiyar zuciya tayi, ta shafi sajensa a hankali tace "naji ɗagani in cire kaya inje
inyi wanka"
Maimakon ya ɗaga ta seya sake gyara kwanciya a jikinta, yana kuma nanata mata "ina
sonki Matata, ina sonki Widad"
Gaba ɗaya taji wata kasala na saukar mata, batayi magana ba sedai tasa hannu ta
rungumeshi itama.
84_85
Yusuf ya ɗago da sauri, yayin da jikin Hanne ya ɗau rawa, ba tare da tace uffan ba
ta ajiye kwanukan da ta wanke, jikinta na rawa ta fice waje, yayin da wani abu
kamar dutse yazo ya daskare mata a ƙirjinta, tana tafe amma kamar ta kifa, danko
gabanta bata gani, maimakon taji haushin Yusuf, se wani tuƙuƙin tsanar Widad da
taji a ranta, kamar ta janyo ta ta shaƙe haka take ji.
Widad kuwa tsaki tayi, ta haɗe rai tace "kaga malam ɗagani mana"
Yusuf yace "to nikuma meye laifina da zaki wani haɗemin rai haka?"
Ta ƙara haɗe rai tace "kaika sani dan Allah nika ɗagani, ina da abunyi fa"
Ta katse shi ta hanyar cewa" dan Allah malam ka ɗagani nace, bana son jin komai
daga bakinka, kuma karka ƙara bawa wata 'yar ƙauye kwanukana ta wanke min na gaya
maka, in bahaka ba nika ajiyemin abuna zan wanke, idan kuwa ta sake wanken kwanuka
na, wallahi sena zuba su gaba ɗaya a wannan rijiyar ta gidan nan, kuma idan na kuma
ganinta a ɗakina duk abunda nayi mata ita ta janyowa kanta na gaya maka "
Yusuf ya ƙura mata ido, yana kallon yadda take masifa fuskarta na bayyanar da
matsanancin kishin dake zuciyarta, amma yanzu daze ce tana sonshi seta fara masa
iyayi, tana ita bata san so ba, kawai dai danya temake ta ne.
Ta ture shi daga jikinta, ta miƙe tana kumbure kumbure ta cire kayanta ta tafi
wanka.
Bayan fitarta ya miƙe, ya gyara mata shimfiɗarta, Gwaggo ta aiko musu da Abun karin
kumallo.
Koda Widad ta fita tsakar gida, tana kallon mugun Kallon da Hanne ke mata, banda
Widad na ganin darajar Gwaggo, da ba abunda ze hana tayiwa Hanne rashin mutunci me
wuyar mantawa, amma ta ƙyaleta taje tayi wankanta.
Data dawo ɗakima Yusuf yana ta ƙoƙarin rarrashinta, amma ta basar dashi taƙi kula
shi, ta barshi yaita ɓaɓatunsa shikaɗai, ta ɗakko kaya zata saka yazo ya karɓi
kayan daga hannunta, amma tasa hannu fizge abunta, sosai kishi me zafi ya bayyana a
fuskarta, Yusuf yace bari yayi amfani da wannan damar gurin jarraba Widad, bari
yaga idan dagaske kishinsa take ko kuwa?.
Ya koma gefe ya zuba mata ido, tasa kayanta, ta koma gefe tana shafa mai tai kicin
kicin da fuskarta, kamar ba itace suke tare ɗazu ba cikin farin ciki.
Yusuf yace "Allah sarki rayuwa, Ohh koya Amal ɗina tayi da taji an sace mata ni,
Amal ta gama matowa a sona, she really loves me, ga Nurat ma light, ga fara'a ga
kirki she also loves me, itama ban san ya zataji ba, ga Sakina abokiyar aikina,
abunda ya hana in bawa Sakina fuska shine shigar matsatsun kaya, da yawan kule
kulen maza, se gashi Allah yasa na Auri me sa matsatsun kayan, ga tsiwa gashi sam
bata sona, taita bani wahala, gashi ina matuƙar sonta, kissing ɗinta in nayi ta
dingamin faɗa kenan tanamin tsiwa, laifi koni nayi ko bani nayi ba taita fushi
dani, bata tausayina sam, nikaɗai nake sonta, Nasan da Nurat na Aura dana huta, zan
sha soyayya dan akwaita da tausayi da sanyin hali, sannan masha Allah, gata da lips
masu kyau, nasan ita ba zata dinga ƙyamata ba, ko kissing ɗinta na....
Aibe ƙarasa ba yaji saukar ludayin roba a ƙeyarsa, seda ya razana ya kalli inda
Widad take, kawai ta fashe da kuka harda hawaye.
Yusuf yace "Ke lafiya Mena yi miki kuma? Kinƙi kulani nazo ina hirata kuma seki
jefe ni, sekin jimin rauni tukuna, mu koma gida 'yan matan nawa duk su gujeni?ko
kuma su kasa ganeni?"
Aikuwa ta ƙara sautin kukan nata sosai, harda sheshsehseƙa, wani guntun murmushi
yayi a ransa yace' yarinya kin faller '
Amma a zahiri seya miƙe, yazo inda take yace " Widad, meyasa ki kuka ne? Kowani
abun nayi miki ne?"
Yusuf yace "to meyasa kika jefeni da ludayi? Baki san naji zafi ba?"
"Ni bana son zancen da kake ne, raina ɓaci yake ni karka ƙaramin zancen wata a
gabana, bana so am feeling bad, ni gaba ɗaya ma zuciyata haushi nake ji"
Yusuf ji yayi kamar ya ƙyalƙyale da dariya, amma yasan yana yin hakan, sabuwar
rigima zata saka masa, dan haka yace
"Ohhh shikenan ya isa haka, am very sorry bazan sake ba, dena kukan kinji abar
sona, na dena insha Allah dena kukan haka kinji gimbiyar"
Widad ta ture hannusa cikin zumɓira baki tace "ni rabu dani, tunda ka sani kuka"
"Yi haƙuri I don't mean to hurt you Baby, ban zaci ranki ze ɓaci ba, kinga se binki
nake ina magana amma kika shareni, se da ki kaji nafara lissafin 'yan matama sannan
kika hau kuka"
Yusuf yace "Oho nima ban sani ba, aike zan tambaya" Yusuf ya bata amsa ɗan taɓa
baki tayi ta ɗanyi tsaki sannan tace
Yusuf yace "A' a naje gidansu dai, bayan mahaifinta yayi yunƙurin sawa a sace ki,
ita na ritsa da bindiga ta gayamin inda kike, bayan nan na koma gidansu, dan inyi
mata wasu tambayoyi, da farko ta tsorata daga baya kuma ta saki jiki, muka dinga
hira a haka na samu abunda nake son ji daga gare ta, har mukayi exchange na lamba,
akwai ranar da muka fita dake, nakw waya nace ina tare da matata ne, ai da ita muke
waya, sedai daga baya na fuskanci Nurat ta kamu da sona ne "
"To waike meye naki na tambaya ne? Bayan kince bakya sona, ina ruwanki ki ƙyaleni
in samo mesona, wanda bazata gujeni ba kota dinga min tsiwa ba"
Ɗan guntun tsaki tayi, tare da jin haushin kanta ko meye na damuwa ma oho, ta janyo
kwanon Abinci ta buɗe, kofin an zuba kunun tsamiya, kwanon kuma wainar gero ce an
barbaɗeta da ƙuli ƙuli, Widad tace "wannan wane irin Abinci ne kuma, shima wani
baƙi dashi??"
Tace "Meye kuma wainar gero, mutanen nan suna son yin Abinci baƙi" tai maganar
Tare da saka hannu ta fara yashe ƙulin kai tana lashewa, Yusuf ya kalle ta yace
"bismillahi, kwaɗayayyiya zaki cinye ƙuli ƙulin ki barmin gaya ko? Dama kin saba"
Hararsa tayi ta cigaba da lasar ƙuli ƙulinta, Yusuf yace "baze fa yuwu ba, se saka
yawu kike a jiki, idan muka koma gida sena gayawa Daddy yadda kike bani wahala, duk
na rame kekuma ƙibarki kawai kikeyi"
Duk da a fusace take amma murmushi ya suɓucemata tace 'kamar kasan akanka Daddy ze
iya zaneni ma inaga, dan yana matuƙar sonka sosai"
Yusuf yace "sosai makuwa, ai bazan manta alkhairinsa a gareni ba, kuma koba komai
ko bama tare, yana da matsayi a gurina saboda na taɓa Auren 'yarsa, dan haka
inajinsa kamar mahaifina mussman yadda yake girmamani"
Widad ta jinjina kai, har cikin ranta taji daɗin yadda Yusuf yace yana son
mahaifinta harya ya beshi haka.
wainar geron nan ba ƙaramin daɗi tayiwa Widad ba, ta saki jiki taci sosai, sed suka
gama faɗansu da Yusuf sannan ya fita.
Widad ta fito tsakar gida, amma bata ga Hindu ba, ta kalli Hansai tace "wai ina
Hinduna ne yau ban ganta ba fa"?
"Hindunki a ina?" Hari ta faɗa tana yatsune fuska.
Banza Widad tayi mata, ta kafe Hansai da ido tana jiran amsar tambayarta, Hansai
tace "Zazzaɓi take yi, tana ɗakin Gwaggo a kwance"
Widad ta tafi ɗakin Gwaggo, ta tsaya a bakin ƙofa tayi sallama, Aka amsa ta nemi
izinin shiga, sannan ta shiga.
Jamila na zaune a gefe tana shayar da jaririyarta, yayin da Hanne keta ƙoƙarin
gyara ɗakin Gwaggo, Gwaggo kuma tana ta rarrashin Hindu taci Abinci amma taƙi.
Widad ta kalli Jamila ta ɗauke kai, tazo ta nemi guri ta zauna a gaban Gwaggo tace
"Mama, meyasa ba'a gayamin Hindu ba lafiya ba?"
Gwaggo tace "ahh haba, ya za'ai a takura miki, amma yanzu ai gashi da kika fito
kinji"
Jamila taji haushin sharetan da Widad tayi a karo na biyu, kuma tana ji tana mata
magana.
Hindu tayi murmushi tana gyɗa kai, yayin da Hanne se cika take tana batsewa, tana
faman jan tsaki kamar wadda akayiwa wani abu, dan data tuna a yadda ta gansu itada
Yusuf se taji kamar ta fashe da kuka.
Widad ta kai Hannu ta taɓa Hindu, jikinta zafi sosai Widad tace "Gwaggo, baza'a
kaita Asibiti ba? A kaita a duba ta mana"
Gwaggo tace "hmm Amarya kenan, da kinsan azabar tazarar dake tsakaninmu da Asibiti
da baki ce a kaita ba, bamu da Asibiti a garin nan, ƙauye uku zuwa huɗune
tsakaninmu da Asibitin shaka tafi, yanzu kafin a kaita ma wani wahalar ne, duk seta
galabaita"
Widad ta girgiza kai tace "ni wallahi ina mamakin yadda za'ace mutane suna rayuwa
babu Asibiti a guri, ai wannan se mutum ya rasa ransa ma ba'a bashi wani agaji ba,
haba dan Allah to yanzu ba abunda za'a bata"?
"A'a na ɗan jiƙa kayan magungunanmu na gargajiya, na ɗan bata shima kuma tayi
amansa"
Widad tace "Mama nifa bana son wannan kayan jiƙe jiƙen, su ba ƙa'ida ne dashi ba
kawai sha akeyi, kuma kayan ciki basa san wannan jiƙe jiƙen, yanzu se wani abun ya
taɓu, bari Yoseef ya dawo, in da sauran nasa magungunan se a bata"
Bayan Widad ta gama duba Hindu, ta tashi ta fita, Gwaggo ma ta fito tsakar gida,
Jamila tace "wai nikam wacece wannan? Tana ji ana mata magana amma tana wani jin
kanta tana share mutane"
Hanne tayi tsaki tace "bar shegiya, haka take wannan wulaƙancin dan tama ganinta a
koɗe kamar an wanke karas, taita wa mutane wani iskancin banza da taƙama, se tsabar
rashin kunya da rashin tarbiyya, ko magana bata iyaba ga ƙaryar masifa, komai seta
dinga nuna bata sanshi ba, saboda gogewa mutane hadda "
Hindu dukda jin jikin da take, ba zata iya jure jin ana cin zarafin Widad ba, Hindu
taja tsaki tace " Wallahi Jamila ba bata da mutunci bane, ni baki ga yadda tamin
ba, bata da wata matsala, sedai bata sakin jiki da mutane, seta daɗe tukuna, bata
fiye son mutane bane, amma Hanne san zuciya ne yasa kike cewa bata da mutunci"
A fusace Hanne tace "dalla malama yiwa mutane shiru, aikin banza uwar shisshigi
se wani naniƙe mata kike kina cusa kai ba kwarjini, aikin banza dana wofi kawai"
Jamila tace "ya isa haka, ke Hanne abun faɗa baya miki wuya yaseen, har yanzu kina
nan da tijararki baki dena ba"
Hanne ta riƙe ƙugu tana harare harae tace "ƙwarai kuwa, wallahi anamin nake ramawa
ehee, babu 'yar masu baƙin jinin da zan saurarawa"
Shiru Hindu tayi, jin Hanne na ƙoƙarin fara ci mata fuska, Jamila tace "Hanne meye
hakane? Nace ya isafa"
Hanne ta zumɓura baki tai waje, yinin yau Widad kanta bata da sakewa, ji take kamar
itama bata da lafiya, Hindu tana matuƙar birgeta saboda biyayyarta da haƙurinta,
shiyasa idan bata nan ko bata walwala Widad ma take shiga damuwa.
Saleh kam kwana biyu yayi ya koma kano, yaje ya tarar abubuwa nata sake rikicewa,
dan ya fara karaya ya zubawa sarautar Allah ido, saboda tarakun da'aka kafawa
Yusuf, ubangiji Allah ne kaɗai ze iya fidda shi, dan babu imani babu tsoron Allah
ko tausayi a tare da su Alhaji Musa.
Saleh yana gidan da yake zaune, yaji ana buga ƙofa yana zuwa ya buɗe yaga Abbas,
Saleh yayi murmushi yace "Ahh saukar yaushe haka? Shigo daga ciki mana"
Abbas yabi bayan Saleh suka shiga, har falon Saleh, Abbas yace "ai yau sati na
guda a garin nan, nazo in ɗan huta ba inda nake zuwa shiyasa baka ganni ba se yau"
Saleh yace "wai ni kuwa nace ya ake ciki ne? Har yanzu babu wani labari ne? Tun
tafiyata banji wani motsi ba har yanzu ba'a samu komai bane?"
Saleh yace "haryanzu ba wani abu fa, ana ta fama ne abun duk se a hankali, shi can
ya gudu ba'a san inda suke ba, shima kuma an sace shi, shi Daula babu wanda yasan
inda yake haryanzu, anata fama ne"
Abbas yace "Ai naga sanarwar da aka yi akan Yusuf ne ya sace Ita 'yar Daula, hakan
yayi ai hakan shine zesa hankalin mutane ya ɗauke daga yin zargi, se a koma
sauraren ta inda za' a gano su, ni babban abunda yake damuna ma kar muje ta bashi
takaddun mu muna nan, dan wallahi ba kaga alherin da take masa ba"
Saleh kallon Abbas kawai yake harya kai aya, sannan ya numfasa yace "insha Allah,
babu abunda ze faru, kota bashi takaddun babu yadda zeyi dasu, su Munir su suka san
kan dukiyar, su suka san yadda za'ayi lamarin ya wakana, karka damu komai ze tafi
daidai, sedai kamar yadda na gaya maka kansu suma a rarrabe yake yanzu haka, karka
yadda wani ɓangare yazo ya nemi wani abu a gurinka, ka yadda ka bayar, karmu ɗau
side mu zama a tsakiya, tunda bamu san ɓangaren da zasu yi nasara ba"
Abbas yace "dan wannan, ai karka damu tuntuni kamin wannan kashedin, kuma naji na
ɗauka, dan haka ka kwantar da hankalinka, sedai muna biue dasu, zuwa lokacin daza'a
samu ɗin"
Daga baya kuma suka yi Sallama, Abbas ya shig motarsa sega kiran Suleiman, ya ɗaga
yana faɗin "Allah ya temaki Oga, barka da yamma"
"Alhamdilillah Oga"
"Good, naji ance ka shigo garin nan, inba damuwa ina son mu haɗu gobe in Allah ya
kaimu"
Abbas ya ɗanyi Jim sannan yace "shikenan Oga, yadda kace kaman da ƙarfe nawa?"
Yana kashe wayar, Saleh yaja tsaki yace "Aikin banza munafukan banza, da kai aka
haɗa baki aka canzamin gurin aiki, aka maida Yusuf kan kujerata, aiga abunda ya
sameshi nan, Allah ya ƙara masa saura kaima"
Nurat ta rame tayi duhu, gaba ɗaya bata jin daɗin komai, tun mahaifiyarta tana
rarrashinta harta haƙura, ita zatonta halayen mahaifinta ne suka sa tashi ga wani
hali, bata san me yake damunta ba, ko Abincin kirki bata iyaci, ga wunin ɗaki data
tsira, seta wuni cur bata fito ko falo ba tana ɗaki, Abinci in an kaimata ba zata
ciba, sedai idan Mahaifiyar tace ta shiga ta sata a gaba shine zata ɗanci kaɗan,
fuskar nan tayi fayau bakoma se dogon hancinta da idanuwa saboda damuwa.
Shikuwa mahaifinta sabgar gabansa kawai yake, yana ta faɗi tashi yana kashe
kuɗi gurin malamai da 'yan tsibbu, da gurin manyan' yan siyasa domin ya samu ya
koma takarar ɗan majalissa da Daula ya tsaya masa yayi, gefe guda kuma sunata
cigaba da ƙulle ƙullen yadda ko sun rasa wanccan kuɗin, su samu wani kason ta
ɓarauniyar hanya.
Yanzumu shiryawa yayi tsaf, ya tafi gidan Barrister Hafiz da kansa, domin jin inda
maganarsu ta kwana akan batun ayi takaddar boge, ayi gwanjon wasu daga kadarorin
Daula.
Barrister Hafiz ya karɓi Alhaj Musa hannu biyu, ya masa iso har falo aka gabatar
masa da Kayan ciye2, Alhaj Musa ya ture farantin fruit ɗin yace "kafin wannan, dama
zuwa nayi inji inda maganar da mukayi ta kwana? Yau kimanin wata guda kenan da yin
maganarmu, amma shiru ba amo ba labari bakace mana komai ba, bamu san a ina aka
kwana ba"
Barrister Hafiz ya ɗanyi shiru sannan yace "Yallaɓai kamar yadda a wancan lokacin
muka rabu akan cewar, zan tattauna da sauran abokan aikin da muka kasance lawyoyin
Alhaji Nasir Daula, na bisu ɗaya bayan ɗaya kowa naji ra'ayinsa, na zaɓe wanda nake
ganin zasu iya yadda ayi harkar nan dasu, sedai me nazarin da mukayi, da binciken
da muka sake yi shine, duk wata kadara da Daula ze siya muna sani, ko ince wasu
daga kadarorin daze siya, a gabanmu akeyi da komai da komai, sedai fa takaddun
Kadarorinsa babu ɗaya daga cikinmu daya san inda yake ajiye takaddunsa, dukda
kasancewar mu lawyoyinsa, 'yar nan tasa dai ita kaɗai ce tasan inda kayansa suke,
bakomai muka saniba, munyi tunanin yin takaddar boge kamar yadda kuka ce sedai babu
wanda ze iya kwafar sa hannun sa, wataƙila se wannan yarinyar tasa"
Alhaji Musa yai shiru sannan yace, "shikenan ba damuwa, zamuje a bincika dole za'a
samu wanda ze iya kwafa, nagode sosai idan akwai buƙatar sake nemanka, zaka jimu
nan gaba nagode"
Nurat ce zaune a bakin gadonta tana ta sharɓe hawaye, wanda ya zamar mata jiki a
'yan kwanakin nan, tayi zurfi sosai a tunani, taji sallama a hankali ta ɗaga kai
domin ganin me sallamar barrister Khalil ne, bayansa kuma mahaifiyarta ce, Amsa
masa tayi cikin sanyin jiki.
A ɗan razane ya kalleta yace "Subhanallah Anty Sauda dama haka Nurat ta koma?"
"to gata nan dai, shiyasa na kiraka ai, ban sani ba kokai idan kayi mata faɗa taji"
Khalil yace "sistona, meke damunki haka kinga yadda kika rame kuwa?"
Shiru Nurat tayi ba tace komai ba, Khalil yace "gayamin meke faruwa ne?"
Ɗaga kai tayi ta kalli mahaifiyarta ta sunkuyar da kai, Khalil yace "Anty Sauda
bamu guri muyi magana"
Ba musu ta juya ta fice ta basu guri, Khalil ya rufe ƙofae, sannan ya ɗakko kujerar
gaban dressing mirror ɗinta ya ajiye ya zauna, ya kalleta yace "Nurat, tsakanina
dake kin san babu ɓoye ɓoye ko? Bama ɓoyewa juna komai ki gayamin meke faruwa, kin
san bazan fallasa sirrinki ba, sirrinki nawane ki gayamin koda taimakon da zan
iyayi miki"
Aikuwa ta sake fashewa da kuka, seda tayi me isarta sannan tace "Brother meyasa
wayarka bata shiga, na kira layinka babu adadi amma taƙi shiga?"
Khalil yace "wayar aka sa emin a gurin ɗaurin Aure, se yau naje nayi swapping ɗin
layin, amma meyasa baki kira ko Mama ba muyi magana?"
Nurat ta goge hawayenta tace "bana son kowa yasan meke faruwa ne, bana son wani
yaji shiyasa ban kira kowa ba".
ɗakko wayarta tayi, ta buɗe labaran da ake yaɗawa akan ɓatan Widad, labarin me
ɗauke da hoton Yusuf.
Khalil ya kalli wayar yace "eh naga labarin yana ta zaga gari"
Nurat tace "Allah ya jarrabeni da son wannan bawan Allah brother, kuma wannan shine
wanda Daddy na yasaka a gaba, wallahi brother ina tabattar maka da dasa hannun
Daddy na aka sacesu, kuma yanzu anyi sanarwa wai shi ya sace Daula da 'yarsa,
wallahi baze aikata haka ba brother, dan Allah ka temakeni ka temaki Yusuf "
Khalil yace " yi shiru dena kukan, tsaya yanzu kin zaɓi soyayyarki akan
mahaifinki"?
"Brother ba soyayya na zaɓa ba, gaskiya na zaɓa na fifita, na gaya maka komai fa a
baya, koka manta?"
Khalil yace "ya za'ayi in manta, ban manta ba kuma indai abunda kika faɗa hakane,
to tabbas mahaifinki bashi da imani, yanzu me kike ganin za'ayi? Tukuna ma waishi
wannan ɗin waye? "
Nurat tace "Sonake a ɓoye, ka bincika waye Yusuf da kuma inda yake, sannan ina son
a ɓoye ka cigaba da bin diddigin mahaifina ko zaka samu wani bayanin, wanda ze
wanke Yusuf"
Khalil yace "kin haɗani da aiki me hatsarin gaske, amma indai hakan ze sama miki
farinciki to zanyi insha Allah"
Ai bata san lokacin da ta faɗa jikin Khalil tana masa godiya ba, kallonta yake yi
yana tunani a ransa yace "insha Allah, zan sadaukar da tawa soyayyar dan ganin kin
samu taki Nurat"
Zuwa yamma Hindu ta ɗanji sauƙin jikinta, dan harta fito tsakar gidama, Widad tana
ta murna, Jamila na jikin ɗakin Hansai, tana wasa da jaririyarta, Widad ta ƙura
mata ido kamar tace ta bata jaririyar ta ɗauka, dan ita dai da wayonta bata taɓa
ɗaukar jariri ba.
Yusuf yayi Sallama ya shigo, sedai abunda ya ganine yasa ya rikice cikin ɗaga murya
yace "Subhanallah......
LITTAFIN KUƊI NE, DAN ALLAH KI SIYA KAFIN KI KARANTA BA DANNI BA DAN ALLAH, LITTAFI
NA ƊAYA KYAUTA NE WANNAN NA SIYARWA NE
NORMAL GROUP ₦300
VIP ₦500 NE KITURA TA WANNAN ACCOUNT ƊIN
0009450228
JA'IZ BANK
AISHA ADAM
SE A TURA SHEDAR BIYA TA WANNAN LAMBAR
07063065680
IDAN KUMA KIN SIYA AMANACE KARKI FITARMIN DAN ALLAH 🙏🙏🙏
11/14/21, 6:09 PM - Ummee Musa: LITTAFIN KUƊI NE, DAN ALLAH KI SIYA KAFIN KI
KARANTA BA DANNI BA DAN ALLAH, LITTAFI NA ƊAYA KYAUTA NE WANNAN NA SIYARWA NE
NORMAL GROUP ₦300
VIP ₦500 NE KITURA TA WANNAN ACCOUNT ƊIN
0009450228
JA'IZ BANK
AISHA ADAM
SE A TURA SHEDAR BIYA TA WANNAN LAMBAR
07063065680
IDAN KUMA KIN SIYA AMANACE KARKI FITARMIN DAN ALLAH 🙏🙏🙏
86_87
Wato bakomai Yusuf ya gani ba, illa Widad bata taɓa kula Jamila ba, amma taji tana
son taje ta ɗau jaririyar nan dako arba'in ba tayi ba, gashi baya tunanin ta taɓa
ɗaukar jaririn, Jamila na ƙoƙarin bata 'yar, idan ba'ayi wasa ba tsaf Widad inta
ɗauki 'yar nan zata iya jimata rauni saboda yanayin ɗaukar da take shirin yiwa
jaririyar.
Yusuf ya ƙaraso da sauri yace "karki bata, bata iya ɗauka ba karta jiwa Babyn ciwo"
Widad ta juyo ta kalleshi, aikuwa ta haɗe rai sosai tace "kamar yaya ban iya ɗauka
ba?"
Yusuf yace "eh baki iya ɗauka ba, sekin jima ta ciwo tukuna?"
"wai kai komai ban iya ba, ba a haka zan koya ba, ni gaskiya kabari a bani in
ɗauka" tai maganar tana ƙoƙarin cicciɓar ƙafafuwan jaririyar"
Yusuf yace "yi haƙuri tsaya kiga yadda za'ayi, bari in ɗauka ni se in baki"
Yusuf ya karɓi jaririyar, dake ta bacci, yayin da Jamila kuma rigimar Yusuf da
Widad suka burgeta matuƙa suka bata dariya.
Yana tafe tana biye dashi har ɗakinsu, suna zuwa ta zauna tace "to zauna ka bani"
Yusuf ya zauna ya nuna mata yadda zata yi da hannunta, sannan ya ɗora mata
Jaririyar a hannu, jaririyar dai baƙace sedai fes da ita, an mata wanka an samata
riga me kyau, rigar nata ƙamshin miski, da alama Jamila tana da tsafta.
Widad ta ƙurawa Jaririyar ido, ta dinga jin ina ma tatace, ace wannan 'yarta ce, a
ranta tace "da ina zan sa kaina dan daɗi'
Yusuf yace "ikon Allah, ina wannan yarinyar tasan wani wasa? Jaririya cefa dan
Allah ki ƙyaleta tayi baccinta, idan kika tasheta kuma kuka za taitayi, mamanta ta
karɓeta daga hannunki"
Widad tace "to bazan tashe ta ba, amma sonake ta buɗe idonta"
"to na ƙyaleta"
Widad ta cigaba da kallonta, tana ta sake ayyana ina ma ace wannan 'yarta ce.
Yusuf yana canza kaya, yana yi yana kallon Widad, dan karya ɗauke ido Widad tayi
wani abu daze cutar da jaririyar, Widad ta nutsu sosai danko ƙwaƙwƙwaran motsin
kirki ba tayi, ta riƙe jaririyar sosai.
Widad tace ' Yoseef ka samin ita a bayana, irin yadda akeyi ɗin nan"
Yusuf yace "yau naga ta kaina ni Yusuf, Allah ya haɗani da rigimammiyar mace, keda
kike koyon ɗaukar jaririyar ma yanzu, shine zaki wani ce a goya miki ita? Zan
ƙwaceta in kaiwa mamanta, ki cigaba damin rikici"
Zumɓura masa baki tayi, tana sake gyara zamanta, ya ɗakko Abincinsa ya zauna ya
fara ci, Amma Widad ta hau kici kicin ɗaga jaririyar nan wai zata saka a kafaɗarta,
Yusuf ya miƙe da sauri yaje ya karɓe yarinyar nan, danma jaririyar me haƙuri ce, ba
tayi kuka ba se buɗe ido da tayi tana miƙa.
Yusuf ya fito tsakar gida yace "Mama ungo Jaririyar nan, bawa mamanta ita tun kan
Widad tayi aika aika"
Widad kamar zata yi kuka ta biyoshi da sauri tace "Mama dan Allah ki bani, kawaifa
dan nace ina son inga ta buɗe ido, shine se cewa yake ban iya ɗauka ba"
Yusuf yace "karki bata, wai sena goya mata ita, ko ɗaukar jaririyar bata iya ba ta
ina za'ayi goyo?"
Jamila dai banda dariya ba abunda take yi, Widad tayi kicin kicin ita a dole anyi
mata laifi.
Megari dake ɗakin Hansai yana jinsu ya fito yana cewa "haba Malam Yusufa, yama
za'ayi kace bata iya ɗaukar jariri ba, Rabu dashi yarinyar kirki Allah ya baki naki
kema"
Hari tace "jimin mara kunya, kikace Ameen a gaban mutane, kai Wudas baki da kunya
Al'qur'an"
"baza'aji kunyar ba ɗin, meye abun kunya kuma dan nace Ameen"
Jamila taji daɗin yadda dukda Widad bata kula ta amma ta nuna tana son 'yarta.
Bayan sun koma ɗaki Yusuf ya kalleta yace "Sannu uwar rikici"
Yusuf kamar yayi dariya, haka ya dinga dariyarsa ƙasa ƙasa yana cin Abincinsa, har
akayi sallar magariba bata kula Yusuf.
Ta fito tsakar gida zata yi alwala, taga Gwaggo tana aikinta a tsakar gida, Widad
tace "Mama wai nan garin ba'a samun Irish potato ne?"
Tace "dankali"
Gwaggo tace "Auho, ai da kiyiwa Yusuf magana, ko kuma Ila idan sunje kasuwa su
samo miki"
Widad tace "bafa wannan ba Mama, dankalin nan 'yan ƙanana, ba masu zaƙin ba su nake
sha' awa fa"
Gwaggo tace "taɓ aikuwa yana ɗan wahala, dan se anje can birni ake samu"
Gwaggo kawai tayi murmushi, ana ɗan sayewa kar a faɗa kai tsaye amma ita ta faɗa,
Gwaggo ta ƙyaleta ta cigaba da aikinta, Widad taje tayi sallarta, ta zauna akan
dadduma tayi shiru, kawai taji har cikin ranta tana son ta samu ciki, ace yau gata
ɗauke da ɗanta na kanta a jikin ta, idan ta haihu ta samu ɗa da zata dinga gani
tana jin daɗi.
Tana zaune tana ta karanta wasiƙar jaki, Yusuf yayi sallama tana jinsa tai masa
banza, ta miƙe ta fara shirin kwanciya.
Seda ya bari ta kwanta sannan ya tafi rarrashi, tana jinsa ya hawo katifar yana
lalubenta amma ta shareshi.
"Kina jina amma kika shareni ko Queen, laifin me nayi miki ne?"
Cikin Shagwaɓa tace "to ba kaine komai nayi kake cewa ban iya ba"
"To kin iya ɗinne? Matar ƙauye kawai sarkin rigima"
"Eh naji na yadda, ni mijin ƙauyene kuma mijin matar ƙauye, karki damu zan siyo
miki teddy ki dinga wasa dashi, shima kamar baby ne seki koyi goyon a jiki"
"bawani nan teddy daban, teddy mutum ne? Toni mutum nake so"
Yusuf yace "Eh tunda baki da mutum, seki rainon teddy da haka zaki koyi rainon
jaririn gaske"
Sosai Widad ke bawa Yusuf dariya wasu lokutan, Yace "idan mutum yana yaro idan
yayi wasa da dolls 'yar tsana, yana iya raino koba jariri a gidansu, amma ke baki
iya ba '
Widad tace" waye ya gaya maka da ina yarinya ina wani wasa ni? Nifa kamar boss nake
da ina yarinya, ba ruwana da wani wasa irin na yara"
A haka suna taɓa hirarsu har bacci yayi awon gaba dasu gaba ɗaya.
Da gari ya waye, Widad tana fitowa taga Hindu na tattare tsakar gida tana shara,
Widad tace "Hindu kin warke ne kike aiki?"
Hindu tace "jikina da sauƙi Amarya, gani nayi tsakar gidan yayi wani iri, duk
ganyen bishiya ya faɗo, shiyasa nace bari in gyara kafin a firfito"
"Kai Hindu, kina fama da kanki ki bari a share mana gaskiya bari"
Widad ta ƙwace tsintsiyar ta hana Hindu sharar, ta gama abunda zata yi ita ta
share, sannan ɗakinta koma ɗakinta tayi kwanciyarta.
Wajejen takwas da rabi Widad ta farka, ta hangi Yusuf a zaune da gashi se gajeren
wando yana buɗe kwanon Abinci, da alama har yayi wanka ma, dan jikinsa se ƙyallin
mai yake.
Ƙura masa ido tayi tana kallonsa, sam Yusuf bashi da makusa gashi da ƙira me kyau,
gashi shikansa me kyau ne, ga kuma uwa uba zuciya me kyau.
Tasowa tayi tazo inda yake ta zauna, ta kwanta a jikinsa hannunta kuma tana shafa
gadon bayansa.
Maimakon tayi magana sema wani sake lafewa da tayi a jikinsa, tana sake shafa
bayansa.
Yusuf yayi murmushi ya cigaba da abunda yake, can yace "in kin gama shafanin seki
ɗagani zanci Abinci, tunda naga kamar ke bakya jin yunwa"
Yanzunma shirun ta kuma yi, ta cigaba da abunda take, janyota yayi gaba ɗaya ya
ɗorata akan cinyarsa, yana ƙaremata kallo yace "ƙalau kuwa? Ko yau da son jiki kika
farkane?"
Murmushi tayi masa, ta kwanta sosai a jikin nasa, tana ƙare masa kallo tun daga
fuskarsa har ƙirjinsa, ta kai hannu tana wasa da gashin nasa.
Buge hannunta yayi yace "mara kunya nan kika gama cewa abun ƙyamane, amma indai
kika gani sekin taɓa"
Murguɗa baki tayi tace "ai idan baka yi wasa ba, da fork zan maka shaving, duk in
cire shi"
Yai murmushi yana cigaba da cin Abincin sa, still kallon Yusuf take yadda yake
komai a nutse, Yusuf yace "Malama karfa ki cijeni"
Bata san lokacin da dariya ta ƙwace mata ba, tace "aikuwa dan kasan na saba ba, da
an takurani idan naga bani da mafita, se cizo kuma haƙorana dafi garesu, duk abunda
na kama sena fasa shi, shiyasa Fahad ɗin Bulama yake cemin Mayya, tunda na huda shi
da haƙorana"
Jiki a sanyaye Yusuf yace "yanzu idan muka rabu, muka koma gida Fahad zaki aura
ko?"
Da sauri tace "Allah ya kiyaye, wallahi ko maza sun ƙare bazan auri wannan ba,
mashayin giyane fa, ga neman mata kai zaka so in Auri wannan?"
Yusuf ya girgiza mata kai, ya ɗan tsura mata ido yace "I can't imagine my life
without you Widad, ko mu koma idan zaki Auri wani bazan iya jurewa ba, ban san ya
zanyi ba"
"waye yace maka zanyi Aureni? Ni ba zanyi Aure ba, bani Abincin nima inci, amma a
baki zaka bani yau" tai maganar cike da son da basar da wancan zancen da suke yi.
Haka ya dinga bata Abincin tana karɓa, kamar 'yar yaye suka gama sannan yayi shirin
fita, yau da kanta har soro ta raka shi, ta tsaya ta kalle shi tace "bana son ka
fita Yoseef, kamar kazo mu koma ɗaki"
"Kawai inta kallonka, kana bani nishaɗi, da jokes ɗinka da halayenka masu kyau"
Yai murmushi yace "nima idan na fita, duk damuwa nake in dawo, saboda inzo inga
abar sona, am missing you fa idan na fita".
Yusuf yace "yanzu abunda za'ayi shine, Yimin wani abu da in na fita har in dawo
bazan manta ba"
Yusuf yace "just kiss me here 'yai maganar yana nuna mata kumatunsa na dama.
Ganin tsakar gidan ba kowa yasa Widad, ta rungume Yusuf ta fara kissing ɗinsa a
baki, he was so much surprise da abunda Widad ɗin tayi, dan haka yasa hannu biyu ya
rungumeta yana murmushi.
Hari ta bankaɗo labule zata fito daga ɗaki, hannunta da kofin da' aka karya, kawai
tai gamo da Yusuf da Widad a bakin zaure, Yusuf ya bawa Hari baya dan haka be ganta
ba sam, Widad kuwa ta ganta, amma tana sane ta basar ta ƙara maƙalƙale Yusuf ta
cigaba da abunda take.
Da gudu Hari ta koma ɗaki, ta bankaɗo labule ta rufo ƙofa, Widad ta zame bakinta ta
hau dariya, Yusuf yace "ya dai?"
Yusuf yace "rana me matuƙar tarihi a gurina, ba iya yau zan cigaba da tunanin ki ba
har abada zanyi tunanin ki My Queen"
Ya riƙo ƙugunta yana kallon ƙwayar idonta, Widad tace "Idan ma makara baka fita da
wuri baf ba ruwana"
"Aiko ke kike da ruwa, dan ke kika hanani fita, ɗan ƙara min kiss ɗin mana kona 10
seconda ne"
Tureshi ta shiga yi tana dariya, tim suka ji an saki kwano, Hanne ta taho da
fantekarta cike da Albasa, tayi karo dasu Yusuf, take taji ganinta ya ɗauke ta saki
fantekar albasar, Yusuf yace "Subhanallah garin yaya kika zubar? '
Yai maganar yana sakin Widad, ya yunƙura da nufin ya durƙusa ya tayata tsince
albasar, amma Widad ta riƙe shi ta tsatstsare shi da ido tace " meye naka a ciki?
Ko kai ka zubar mata? "
Yusuf yace "A' a amma kinga mu muka tsoratata ta zubar da albasar, yakamata a
tayata kwashewa"
Wani mugun kallo tayi wa Yusuf, taja tsaki ta koma cikin gida, Yusuf ya durƙusa ya
taya Hanne suka tsince Albasar, yace "ki dinga kula sosai, ki dena yawan tsorata
kinji?"
Ta ɗau fantekarta tai waje, tana kuka tana tunanin me zata yiwa Widad yadda zata
ɗan ɗana mata taji abunda take ji.
Alhaji Musane yace "Nifa gaba ɗaya na fara gajiya da wannan wahalar, daga wannan
se wannan abu sekace jaraba? Abu yaƙi ci yaƙi cinyewa, shi ya ɓace ɓat kamar kuɗi
an neme shi an rasa, shima wannan ɓangaren yarinyar har yanzu babu wanda ya ganosu,
suma lawyoyin nasa sun kawowa mutane wasu surutansu na banza "
Alhaji Haruna yace "haba Alhaji Musa, ni ban taɓa ganin ka karaya ba akan abu se
yau, duk abunda aka fiye shan wuya akansa za'a samu ne, yanzu mafita yakamata mu
nema amma dole mu kassara Daula, mu kassara wannan dukiyar dayake taƙama da ita"
Alhaji Musa yace "to meye mafitar, nagaji wallahi haba, ni zuwa zanyi in maida
hankali akan harkar takarata kawai"
Alhaji Munir yace "kaga dan Allah Kadena mana zancen wata takara please, zancen
takararka kai kaɗai ta shafa, mu muyi abunda ya dame mu kawai, Alhaji Haruna meye
mafita"
"na saka a duba mana, wanda ze iya kwafar mana saka hannun Daula, sannan kafin a
samu me saka hannun ayi fafutuka a bincika mana bankin nan, shima mu gwada muji ta
ina zamu dace"
Alhaji Musa yace "to ai shikenan, Allah yasa mu dace, amma ni na fara gajiya
wallahi, gashi shima wancan banzan yaron har yanzu ba'a gano shi ba, nifa sonake a
kamashi kafin su shigo garin nan"
Haruna yace "karka damu, ai matakan da muka saka baze tsallake tarkonmu ba, ka
kwantar da hankalinka komai ze tafi dai dai"
Alhaji Musa yace "shikenan Allah yasa hakan, ynzu a duba mana me iya kwafar signing
ɗin nan"
Gidan Alhaji Daula kuwa, Hajiya Halima se shagalinsu suke da dukiya suna facaka, A
ɓoye Ramlah take satar wasu abubuwan ba tare da mahaifiyarta ta sani ba ta kaiwa
Fahad ya sayar ya kawo mata abunda yaga dama, sannan kuma su raba abunda ya kawo
mata ɗin, Amal kam gaba ɗaya a cikin damuwa taje, dukda irin romon bakan da
Mahaifiyar su take mata, akan cewar ai bakomai dan an kama Yusuf, amma hankalinta
yaƙi kwanciya, sam bata da nutsuwa sosai take jin Yusuf a ranta, take tausayin
halin da ze shiga idan aka kamashi da laifin ya sace Widad.
Anwar kam kasuwarsa ya koma zuwa, sam baya zaman gidan nan saboda irin takaicin da
yake ƙunsa a cikin gidan, a kan idonsa yana ji yana gani haka Fahad yake zuwa ya
ɗauki Ramlah a mota su fita, kuma mahaifiyarsu na gani bazata ce komai ba, shikansa
ya fara lura da sauyin ɗabi'a na Ramlah, ya fara zargin ko ta fara shaye shayey,
amma yasan da yayi magana mahaifiyarsu zata ƙarhata shi ƙarshe ma su ƙareta babu
daɗi dan haka ya zuba musu ido.
Ma'aikatan gidan kuwa, su Isa se yanzu suka gane zaman Widad a gidan nan Rahama ne
a garesu, saboda tsagwaron wulaƙanci da cin mutunci da suke fuskanta daga gurin
Hajiya Halima da 'ya' yanta, zagi da cin zarafi gami da wulaƙanci ba irin wanda
ba'a musu, Albashinsu kuma duk Hajiya Halima tabi zaftare musu, shima se sufi wata
ba'a basu ba, zaman haƙuri kawai sukeyi a gidan nan, duk inda suka zauna banda
tsinewa Hajiya Halima da 'ya' yanta babu abunda sukeyi, suna shiwa Widad da Alhaji
Nasir Albarka, saboda kaɓakin arzikin da suke basu shida 'yarsa se yanzu suke ganin
duk izzar Widad a cikin gata suke, dan gashi a yanzu an maidasu kamar bayi a gidan
haka suke zaune.
Saleh ma yana ji yana gani, a gidan gonar nan haka Hajiya Halima ke zuwa ta ɗau
abunda takeso ta fito dashi daga gidan ta siyar, ba yadda ya iya dan idan ya zaƙe
su Alhaji Musa zasu iya gano shi, balli ya tashi dan haka se dai ya zura ido.
Hanne bayan ta dawo daga kai albasarta kuwa, ɓangaren Jamila ta wuce taje tayi jifa
da fantekar albasar, Jamila tace "ke lafiya kuwa, ke da yayanki yana nan kikazo
kika mana jifa da kwanon nan da yaci ƙaniyarki ai"
Hanne tayi tsaki tace "wallahi Jamila na tsani wannan koɗaɗiyyar bayahudiyar, na
rasa me zan mata in huce"
Jamila tace "wai meye tsakanin kune? Me tayi miki haka kuke takun saƙa"
"Wai ba damar magana ta haɗani da mijin ta, seta hau gayan magana, kokuma seta
ganni se ta hau wani rungumeshi"
Jamila tace "ikon Allah, toke meye naki a ciki, ba mijin ta bane ba?"
"to dan mijin ta ne seta dinga min haka? Naga dai namiji na maya huɗune, shikenan
kuma baza'a kula shi ba?"
Jamila tace "Auho, yanzu na gane inda kika dosa, to tun wuri ki kiyayi kanki, ina
ruwanki da mijin ta? Ke ke inake ina wannan bawan Allah, yana da wannan mace kamar
ita tayi kanta, ki taba kanki da wahala ki lallaɓa da wanda aka sa miki rana"
Ji tayi wani mugun haushi ya kuma kamata, ta ja tsaki ta ɗau fantekarta tayi waje.
Saboda tsabar takaici Widad kam a ɗaki ta wuni, tunda ta fito ta gaida Gwaggo ta
koma ɗakinsu, dan ta riga ta gama kawowa iya wuya akan abunda yake faruwa, so take
tayiwa Hannne abunda idan ta taho suka haɗu seta canza hanya, ace yarinya 'yar
ƙauye kamar wannan ta dinga shigar mata hanci, wata zuciyar tace ' me zakiytsaya
tankawa waccan kucakar, shi Yusuf ɗin zaki yiwa' haka ta wuni tana ƙunci da ɓacin
rai, Abincin rana ma ta fara ci ta kasa ta ajiye, ta nemi guri ta kwanta.
Koda Yusuf ya dawo gida da yamma, yama manta da abunda ya faru da Safe, ya dawo ya
tarar se cika take tana bastewa, Yusuf yace "Babyna wai meya farune kike wani
haɗemin rai?"
Shiru tayi masa ko inda yake taƙi kallo, ƙarshema ta miƙe zata fice, Yusuf yay Wuf
ya riƙota yace "haba gimbiyata, me nayi miki ne, bana jin daɗin irin wannan
hukuncin da kikemin, ki hukunta ni ban san laifina ba"
Ƙwacewa tayi tace "ka ƙyaleni, ka koma gurin waccan 'yar ƙauyen daƙiƙiya ka Aureta,
kuma kazo ka sakeni na gaya maka, nika ƙyaleni ita kaje ka aureta ka rabu dani,
tunda itace mace"
Wai yau yake ganin kishi gangariyarsa, dan shaf ya manta da wani abu ya faru yau da
safe, ashe abun yana ranta tun safen nan.
"Widad meye ya kawo wannan maganar kuma, ni nace miki ina son watane, ni ban
gayamiki haka ba, meyasa kikemin hakane,? Haba Widad ki dinga jin tausayina inje in
dawo a wahale, kekuma ki ƙaramin pressure"
Tsaki tayi, tai waje zata bar ɗakin, ya biyota yana cewa "naji na karɓi laifina,
kiyi haƙuri dan Allah '
Gwaggo ta kawo kai zata fito daga banɗaki, taga suna rigima seta koma bata fito ba.
Widad ta samu kujera ta zauna kawai ta fashe da kuka, tama rasa kukan me take yi
ne.
Yusuf kuma ya koma ɗaki, ya rasa abunda ma zeyi.
Gwaggo ta kamo hannunta ta janyota zuwa ɗakinta, ta zaunar da ita akan gado.
Jamila na nan zaune a ɗakin, da yake da ta gama aikin da zata yi a ɓangarenta nan
take tahowa.
Gwaggo ta kalleta tace "Amarya, meyasa kike haka? Meyafaru ne ba wai sa miki ido
nake ba, na kawo kai naga kina rigima da mijinki, yana baki haƙuri, ba wai ina son
jin lallai meya haɗaku bane, a'a yakamata ki gyara mu'amalar Aurenki 'yata, ki samu
namiji ya damu dake haka, ga mijinki yaron kirki me haƙuri, amma ki dinga masa
haka, anya kuwa namiji ya miki laifi ya baki haƙuri amma kiƙi saurararsa ba' a haka
'yata"
Jamila dake zaune tace "Taɓɗijan lallai ke' yar gata ce, har ana baki haƙuri,
lallai kinyi dace ai wani namijim shi ze miki laifi, kuma ya dinga fushi sekin
bashi haƙuri, ai kekam kinyi dace"
Nan suka dinga yiwa Widad faɗa, suna mata nasiha akan yadda ake kula da miji,
Gwaggo tace "Amarya mahaifiyarki na da rai kuwa?"
Widad ta girgiza kai alamar a'a, "mariƙiyarki bata gayamiki yadda rayuwa take ne?"
Widad tayi shiru ba tace komai ba, nan suka zage suna mata nasiha, se kuma jikin ta
yayi sanyi, tabbas Yusuf yana matuƙar haƙuri da ita, sekuma taji sam bata kyauta ba
abunda tayi.
Jamila ta tashi ta goya 'yarta tace' zomu je ɗakina kiji wani abu".......
LITTAFIN KUƊI NE, DAN ALLAH KI SIYA KAFIN KI KARANTA BA DANNI BA DAN ALLAH, LITTAFI
NA ƊAYA KYAUTA NE WANNAN NA SIYARWA NE
NORMAL GROUP ₦300
VIP ₦500 NE KITURA TA WANNAN ACCOUNT ƊIN
0009450228
JA'IZ BANK
AISHA ADAM
SE A TURA SHEDAR BIYA TA WANNAN LAMBAR
07063065680
IDAN KUMA KIN SIYA AMANACE KARKI FITARMIN DAN ALLAH 🙏🙏🙏
11/14/21, 6:09 PM - Ummee Musa: LITTAFIN KUƊI NE, DAN ALLAH KI SIYA KAFIN KI
KARANTA BA DANNI BA DAN ALLAH, LITTAFI NA ƊAYA KYAUTA NE WANNAN NA SIYARWA NE
NORMAL GROUP ₦300
VIP ₦500 NE KITURA TA WANNAN ACCOUNT ƊIN
0009450228
JA'IZ BANK
AISHA ADAM
SE A TURA SHEDAR BIYA TA WANNAN LAMBAR
07063065680
IDAN KUMA KIN SIYA AMANACE KARKI FITARMIN DAN ALLAH 🙏🙏🙏
88_89
Widad ta tashi tabi Jamila, suka zaga ɓangaren Jamila, ta buɗe ɗakinta tayi mata
iso, suka shiga sannan ta kalli Widad tace
"dukda naga baki da sakin jiki da mutane, amma naji ina son in temakeki, kinga nima
da a ƙauyen nan nake, da mijina ya aureni muka tafi can barikin sojoji, to a can
nima naga abubuwa, duk banyi karatun boko ba, amma na bazama na fara nema, naga
yadda mata ke kula da mijk, naga a mugun ƙauye nake bansan komai ba, a tashin da
mukayi a garin nan komai iyayen mu basa iya gayamana, mussman da ya shafi ɓangaren
Aure ba abunda suke iya gayamana, saboda kunya amma ita rayuwar Aure faɗine da ita,
amma a ɗan zaman da nayi zuwan nan nawa na fuskanci abubuwa da dama, ta wasu
ɓangaren kina ƙoƙari, amma ta wani ɓangaren kina da rauni, mijinki yana da kyau
yana da kirki masha Allah, idan har kikayi sake 'yan matan ƙauyen nan zasu cigaba
da bibiyar sane, kiyi ƙoƙari ki riƙeshi sosai saboda mijinki zinare ne, samunsa a
cikin maza akwai wahala
Dan haka shi namiji idan yana ta taka, baka wannan dogon jan ajin, ai daya miki
laifi idan ya baki haƙuri kawai a wuce gurin, idan ba haka ba ze fara tunanin ko
bakya sonshi ne, ya fara leƙe leƙen wasu matan, idan da ba yayi to zaki koya masa
da kanki
Sannan wasu lokutan kina gsyamasa baƙar magana, kuma hakan be kamata ba tunda mijin
kine, ba kowace magana zaki dinga gaya maaa yadda kike so ba, a koda yaushe mune
ƙasa dasu dan haka dole mi bisu, dukda ban san dalilin zamanku a garin nan ba, amm
gaki sam babu abunda ya haɗa kalarki da ƙauyen nan, dan baki kama da wadda take a
wahala ba, amma ke yanzu dake kaɗai aka bari ki kula da kanki a ƙauyen nan zaki
iya? Babu lallai ki iya saboda haka kodan yadda yake tsaye yana kula dake, yake iya
ƙoƙarinsa akanki ya cancanci ki girmamashi saboda haka.
Nasan ko ban faɗa miki ba abubuwan da Hanne take kinsan son mijinki take yi, dan
haka seki kula sosai bar ganin kima da wannan kyan surar, yanzu se hankalinsa ya
ɗauke idan kika gaza sauke haƙƙoƙinsa dake kanki.
Ki kula ki tsare haƙƙinsa, sannan rayuwar Aure duk ta haƙurice, babu yadda za'ayi
ace kullum shi ze dinga baki haƙuri, tun yana ta taki zeyi watsi dake wataran, mata
na rububin irin mijinki, dan haka dan Allah ki dinga haƙuri dashi, karki ƙara yi
masa abunda Gwaggo ta gani ɗazu.
Dan Allah ki kwantar da hankalinki ki kula da mijinki, duk abunda baki gane ba ki
tambayeni zan gayamiki, dan ita Gwaggo bakomai zata gayamiki ba saboda kunya"
Nan ta cigaba gayawa Widad abubuwa da dama akan sabgar Aure, wanda Widad sam bata
sani ba, nan ta dinga koya mata kissa da dabarun zama da miji, wanda ita Widad sam
bata taɓa sanin su bama, dan ita rayuwar Auren bata gabanta balle tasan meya ƙunsa.
Abun ya dinga bawa Widad mamaki, lallai wanda ya rasa uwa yayi kuka, ita banda
yanzu ma wasu abubuwan bata sansu ba game da Auren, lallai Yusuf yana haƙuri, wata
zuciyar ta ta tace 'amma ai Auren bogine bana gaske ba meye na damuwa da ɗaga
hankali?'
Wata zuciyar kuma tace 'dukda hakan dai, ai yakamata ko yaya ki kyautata masa, ko
bakomai ya cancanci hakan daga gareki, karki zama me butulci mana.
Duk da Jamila ba wata babba bace, amma ta gayawa Widad abubuwa da dama da yakamata
ace ta sani, game da rayuwar Aure, wanda yanayin zamansu da Yusuf ita bata saniba.
Widad tayi mata godiya, sannan suka dawo ɓangaren su Gwaggo, koda ta koma Yusuf ya
fita bayanan, dan haka ta shiga shagalinta.
Hari na ganin Widad a tsakar gida tace "Mhmm yau ninaga abunda yafi ƙarfina yafi
ƙarfin idanuna, wai nikam dama Yaya nace mutane ma na wa junansu ɗura kamar yadda
tsuntsaye keyi?"
Gwaggo tace "to ikon Allah, nima ban sani ba gaskiya dan ban taɓa jiba ko gani, se
yanzu a bakinki"
Hari tace "hmmm, ai ina ganin tsiyataku kala daban daban, wani abunma idan na gani
na dinga Tuba kenan kar inje in fita daga musulunci ban sani ba, banda jaraba ace
mutum yasa bakinsa a cikin na ɗan uwansa, saboda tsabar ƙazanta, yo nidai nasam
tsuntsaye ne kawai ke yin haka, amma se gashi mutane ma nayi, kai ina ganin masifa
ƙuru ƙuru"
Widad ta ƙura mata ido, Ba shiri Hari taja bakinta ta tsuke, tun kan Widad ta
gayamata baƙar magana itama.
Widad a ranta tace "ke wannan haƙoran naki, gaftara gaftara koraye wane mijin ze
sha'awar sa bakinsa a naki? '
Yusuf ya dawo amma yayi watsi da Widad, yaƙi shiga sabgarta ya cigaba da harkokin
gabansa, sam yaƙi kula ta, gaba ɗaya se taji babu daɗi, ta kuma rasa yadda zata yi
ya kula ta.
Yusuf ya samu guri yai kwanciyarsa, ba tare da ya tsokane ta ba yau, koya mata
hira, ko yazo inda take ya share ta kamar shikaɗaine a ɗakin.
Bacci ma ya nemi ya gagareta, gashi 'yan kwanakin nan ta fara sabawa da kwanciya a
jikinsa, amma yaƙi kulata yau, gaba ɗaya taji garin ya mata zafi.
Da safe ma farkawa tayi taga yayi ficewarsa, ta rasa abunda yake mata daɗi haka nan
jiki a sanyaye take komai, tayi wanka ta karya.
Hindu ta tsiri yin Faten tsaki, Widad tace suyi a kan risho ɗinta, suka gyara
yakuwa tare da kabewa, anan Jamila ta sake lura shikansa aikin Widad bata iya ba,
danma ba tun farkon zuwanta taga kwaɓar da Widad take ba.
Akayi fate aka gama, suka zuba suka fara sha, Widad da ƙyar tai spoon biyu tace
"ni gaskiya wannan abun ba daɗi, tayar min da zuciya ma yake, ga tsami ga gishiri
ni na kasa gane ma meye taste ɗin Abincin"
Jamila ta dinga tsokanar Widad, wai kodai cikine kuma baya son faten, ita dai Widad
har yanzu bata sake da Jamila ba, amma taji daɗin bayanan da tayi mata.
Kuma babban abunda yake burgeta da Jamila, kullum jaririyarta tsaf da ita, kuma
idan taje ɗauka bata hanata, tana bata ta ɗauka.
Jamila tace "kinga abunda nake gayamiki ko? Allah yasa ba budurwa yayi ba wadda
zata dinga tarairayarsa ba"
Zare ido Widad tayi ta harari Jamila tace "shi ya isa ma?"
Jamila tayi murmushi tace "ai shikenan, cikin hira ta cigaba da ganar da Widad wasu
al'amuran, dukda wani lokacin in anyi gabas se tayi yamma.
Da yamma taga su Gwaggo suna ta shirye shirye, Widad tace" Mama ina zuku ne kuke ta
shiri haka? "
Gwaggo tace " bikine zamu wani ƙauye a gabanmu, Yayar Baffa ce zata yi Auren 'ya"
Gwaggo tace "to ki tambayi Yusuf tukuna, danmu kwana uku zamuyi"
"to ai bazece komai ba, dan Allah nidai zan biku zanje nima in haɗa kayana"
"Amarya, babu yadda za'ayi muyi tafiya dake, ba tare da kin nemi izininsa ba, idan
ya bari bakomai semu tafi'
Wani wahalallaen bacci ne Nurat take yinsa bayan sallar Azahar, wayarta dake ƙasan
pillow ta fara vibrating, a ɗan razane ta farka, tasa hannu a ƙasan pillowa ta
ɗakko wayar, ta amsa sannan ta saka a kunnenta "Hello Brother"
Ta miƙe zaune da sauri tace "No karka zo dan Allah, Daddy yana gida yanzu ze iya
fara zargin wani abu, kuma kasan ya hanani fita, amma me ake ciki?"
Khalil yace "Aikin da kika bani na fara, amma ko kin san cewa Yusuf ɗin nan ɗan
sanda ne?"
"Kamar yaya? Wai dama dagaske ne shi ɗan sanda ne? Naji a labarai na zata ƙaryane
ai"
Khalil yace "to gaske ne, ɗan sanda ne na farin kaya, yayi basaja yaje a matsayin
direba, kuma yayi garkuwa da yarinyar"
"Kahlil saboda wanke Yusuf yasa na sakoka a cikin wannan lamarin, dan Allah karka
ƙara danganta Yusuf da wannan mugun aikin, baze taɓa aikata haka ba na tabatta"
Khalil yace "shikenan naji, karkiyi kuka, ai ina kan yin bincike ne, ban tabattar
ba, abun da ake ciki zan miki magana, amma banda kuka kinji ƙanwata"
Widad da wuri ta sallami ɗalibanta yau, dan wasa wasa da yammar nan cika tsakar
gidan Megari akeyi, an samo musu alli da allo na rubutu, sannan kowa da littafinsa
da abun rubutu, babban abunda yake burge Widad be wuce yadda suke girmamata ba,
suna girmama malami a ƙauyen nan, kuma a hankali tana jansu a jiki yanzu, musamman
'yan ƙananan yaran nan, da sunzo kwanukanta ɗakinta har tsakar gidan duk se subi su
gyara, saboda tsabar girmamawa.
Widad nata ɗokin Yusuf ya dawo ta tambaye shi, dan harta manta sunyi faɗa, seda ya
dawo taga ba fuska, Yusuf be taɓa mata kwarjinin da yayi mata yau ba, sam ta kasa
masa magana sedai kallonsa kawai da take yi.
Koda yayi alwala ya fita sallar magariba, se bayan isha'i sosai sannan ya dawo, ya
ɗau Abincinsa ya fara ci, ta zuba masa ido amma ta kasa magana, can dai taita maza
tace
"Yoseef dama, su Mama ne zasu je biki, shine tace in tambayeka idan zaka barni in
bisu, inje inga yadda akeyi"
Banza Yusuf yayi mata, kamar beji me tace ba, "Yoseef magana fa nake maka"
Jin maganar tayi wani banbarakwai ba tsari, wai tayi abunda taga dama.
"Meye na tambayata kuma ne? Nace kiyi abunda kika ga dama, ai damani baki ɗaukeni
miji ba, na kan manta in wuce gona da iri wasu lokutan, waini game mata, na kan
manta ashe nifa direba ne, iyakaci in miki aiki ki biyani, dan haka idan harni
mininki ne, to ban yadda kije ba, sedai nasan ba lallai ki yadda da hukunci na,
saboda ban kai a kirani mijinki ba, ban isa komai a gurin kiba, dan haka kiyi
abunda kike so, zama ko zuwa ya rage naki"
Yana gama maganar ya tashi ya bar mata ɗakin, wani malolon takaicine ya tokare mata
zuciya, dama Wai Yusuf ya iya fushi haka?
Har washegari be kumabi takanta ba, tana ji tana gani su Gwaggo suka shirya yaransu
da manyansu suka tafi aka barsu a gida, Jamila na ɓangaren ta nata bisu ba, se
abokiyar kishin Widad wato Hanne bata bisu tace bata da lafiya ita bazata ba dan
haka tana gida itama.
Da daddare Yusuf ya idar da sallar isha'i yana lazimi, Widad a hankali tace
"Yoseef" ta kira sunansa kusan sau uku, amma yayi shiru, can tace
"Yuzarsef"
Da sauri ya ɗaga ido ya kalleta jin sunan data faɗa, dukda be amsa ba amma taga
damuwarsa ta ƙaru, ya kifa goshinsa akan gwiwar ƙafafuwansa daya ɗage.
Sanye da zumbulelen hijjabinta tazo, tasa hannu ta ɗago fuskarsa tace "wani laifin
na kuma yi maka dan na kiraka da Yuzarsef?"
Girgiza mata kai yayi, alamar a'a yana ƙoƙarin maida kansa.
Ta sa hannu biyu ta tallafi fuskarsa tace "Yoseef, me nayi maka ne? Dan Allah kayi
haƙuri"
Yusuf yace "aini baki min komai ba, sedai yau ina son in san saki nawa kike so in
miki?"
Yace "kin manta abunda kika gayamin ne? Ina son in koyawa kaina rayuwa ko babu ke
ne, kusan koyaushe kina maganar in sakeki, duk ƙoƙarina bakya gani, bakya
tausayamin ya zanyi? Gara idan muka rabu inda wani ɗakin duk rashin kyansa a bani,
in lallaɓa in fara koyawa kaina zama ko babu ke"
Aikuwa ta fashe da kuka tace "nifa ban san nayi ba, ban san meyasa nake jin haushi
idan naga wata ta raɓeka ba, tun jiya nake maka magana, amma kana shareni, se
kulaka nake amma kaƙi ko kallona, na tambayeka abu ka hanani, kuma banyi ba, amma
ka kama min faɗa, you want turn on me ko, shikenan"
Ta juya zata tashi ya Riƙeta, yace "babu wani dalili da zesa in juya miki baya,
sedai nine kin kasamin adalci, bakya iyayi min adalci a wasu lokutan, kiyi ta bani
wahala saboda kinga ina sonki ko?"
Share hawaye tayi, ba tare da tace komai ba, Yusuf yace "yanzu me kikeson ayi?"
"shikenan za'ayi yadda kike so, amma da bakinki nake son ki faɗi saki nawa kike
so?"
Shiru tayi batayi magana ba, sema sunkuyar da kanta da tayi tana kallon wani gurin
daban.
Ɗison hawayen ta ya gani yana ɗigowa a ƙasa, taƙi ɗaga kanta kuma taƙi magana.
Ta miƙe sum sum ta tafi katifarta ta kwanta, tai shiru tana tunani, wai yanzu
dagaske Yusuf yake sakinta zeyi, se taji gabanta ya faɗi, 'to meye dan ya sakeki,
dama ai akan haka kuke' wani sashe na zuciyarta ya gayamata.
'Amma dukda haka nayi sabo dashi, sabo me ƙarfin gaske, yanzu idan ya rabu dani ya
zanyi? Zan koma irin rayuwar kaɗaici na ta baya kenan?'
Kawai ta sake fashewa da kuka, yana jinta amma yai shiru kamar be san tana yiba, se
can dare bayan ya idar da sallar dare, yayi addu'oin da zeyi sannan ya tao a
hankali ya hau kan katifar ya rungume ta a jikinsa, lokacin har riga tayi bacci,
wannan fushin da yayi da ita na kwana biyu shikansa yaji a jikinsa, dan ba ƙaramin
kewarta yayi ba, a jininsa yake jin soyayyar Widad na ratsashi, shi dai yana
matuƙar sonta.
Kamar yadda Suleiman ya buƙata, Abbas yaje office ɗinsa, seda ya ɗan jira ya
sallami baƙi sannan ya ganshi.
Bayan sun gaisa ne Suleiman yace "Abbas ashe ka shigo garin nan babu Labari, sekace
wanda akayi zaman gaba aika leƙo a gaisa '
Abbas ya ɗan sosa kai yace " Ai Yallaɓai abubuwan ne dama duk se a hankali, kuma
ni ɗanje ziyare ziyare ne, shiyasa amma dama can nayi niyyar in ɓullo a gaisa ai,
da amana bazan watsar daku ba"
Suleiman yace "madalla ai haka ake so, nace ka kuwa ji abunda ya faru da Yusuf?"
Abbas yace "naji yallaɓai, abun ya bani mamaki, mutum a fuska mumini amma zuciyarsa
ba Allah, saboda son zuciya kawai daga aiki seka yi garkuwa da 'yar mutane, gaskiya
bewa kansa adalci ba, Yusuf ya bada mamaki"
Suleiman yai ƙuri da ido yana sauraren Abbas, se da ya gama sannan yayi ajiyar
zuciya yace "to ai koma menene Allah baya bacci, kuma muna bayan ɗan uwanmu, Insha
Allah, sannan bama saka ran Yusuf ze aikata abunda ake tuhhmarsa dashi sam, yanzu
ni babban abunda yaaa na kiraka shine, kaga kaine babban Abokinsa, mahaifiyarsa
tana cikin damuwa ƙwarai, naje gurinta take cemin taji ance kaje amma ba kaje ka
mata jajen abunda ya samu Yusuf ba, dan Allah ka daure ka zagaya kayi mata jaje ko
ka ɗebe mata kewar ɗanta"
Abbas yace "shikenan, dan dai wannan insha Allah daga nan ma zanje, Allah sarki
insha Allah zan biya in gaisheta"
Abbas na fitowa yace "Aikin banza, ina ruwana uwatace ita, taje duk abunda ze
sameta ya sameta, nan aka canza gurin aiki aka bawa ɗanta muƙamina, ba abunda tace
se yanzu wani in mata jaje baza'ayi ba ɗin, Allah ya ƙara '
Harze wuce ya hangi Sakina ta taho da files a hannunta, yana ganinta ya fara
murmushi yace "budurwar kidnapper, ashe abunda ya faru kenan? Saurayinki yaje ya
sace' yar masu kuɗi gaskiya kuna ruwa"
Sakina tace "haba Abbas, yazaka maida abun abun wasa? Wannan maganar be dace a jita
daga bakinka ba a matsayinsa na Abokinka, kuma abokin aikin mu, kuma kasan baze
aikata hakan ba"
"ke dalla ware, waye yace miki baze aikata ba? Mutum nefa shi, waye baya son kuɗi a
rayuwar nan? Kedai Allah ya kyauta kawai ya tona masa Asiri, dama ya daɗe yana naɗe
kura da fatar Akuya ne"
Sakina ta dinga bin Abbas da kallon mamaki, wai babban abokine yake faɗar maganganu
akan Abokinsa haka, lallai duniyar nan ba abun yadda bace.
Da Asuba Yusuf ya tashi Widad tayi salla, taji daɗi yau ya kulata ya tasheta tayi
salla, bayan ta idar ta koma baccin nata na ƙa'ida.
Yusuf yayi komai, har sharar tsakar gida, Hanne a ɓangaren Jamila ta kwana, da safe
ta dawo ɓangaren su dan taga Yusuf, aikuwa ta tarar dashi yana shara.
Duk yadda Hanne taso ko hira su ɗanyi da Yusuf yaƙi yadda, saboda ya gane Lagon
Widad yanzu, kishi ne da ita matuƙa, dan haka ya fara ƙoƙarin kiyayewa.
Sam Hanne bata ji daɗin yadda Yusuf yayi mata yau ba.
Ya koma ya ɗora girki a ɗaki, yana yi ya kalli inda Widad ke kwance na bacci, yana
zuwa beyi wata wata ba ya ɗagata sama yai waje da ita tsakar gida.
Buɗe baki tayi zata yi ihu, ya rufe mata baki yace "ke nine fa" sannan tai shiru
tana ajiyar zuciya tace 'shine zaka tsoratani kuma?'
"Yaushe kika zama matsoraciya ne? Kedai kiyi bacci kiyi bacci, ko gajiya bakya yi?
Karɓi brush ɗinki ki wanke baki, muje ki tayani girki"
Yai maganar yana matsa mata toothpaste, "Yayan Daddy ka dena fushin dani ne?"
Yusuf yace "kona haƙura anjima ma, sekin sake abunda zanyi fushi dake"
Ba tace komai ba ta fara wanke bakinta, suka gama suka koma ɗaki, can Widad tace
"Yoseed, meyasa da nace maka Yuzarsef naga ka shiga damuwa jiya?"
Yace "karki damu ba wani abu bane, kin tunamin da babana ne"
LITTAFIN KUƊI NE, DAN ALLAH KI SIYA KAFIN KI KARANTA BA DANNI BA DAN ALLAH, LITTAFI
NA ƊAYA KYAUTA NE WANNAN NA SIYARWA NE
NORMAL GROUP ₦300
VIP ₦500 NE KITURA TA WANNAN ACCOUNT ƊIN
0009450228
JA'IZ BANK
AISHA ADAM
SE A TURA SHEDAR BIYA TA WANNAN LAMBAR
07063065680
11/14/21, 6:09 PM - Ummee Musa: LITTAFIN KUƊI NE, DAN ALLAH KI SIYA KAFIN KI
KARANTA BA DANNI BA DAN ALLAH, LITTAFI NA ƊAYA KYAUTA NE WANNAN NA SIYARWA NE
NORMAL GROUP ₦300
VIP ₦500 NE KITURA TA WANNAN ACCOUNT ƊIN
0009450228
JA'IZ BANK
AISHA ADAM
SE A TURA SHEDAR BIYA TA WANNAN LAMBAR
07063065680
IDAN KUMA KIN SIYA AMANACE KARKI FITARMIN DAN ALLAH 🙏🙏🙏
90_91
Saroro tayi tana kallonsa ta kasa gane me yake nufi da wannan kallon da yake mata,
tace
"ya dai naga kamar ka ɓata rai? Ko na sake faɗan wani abun na dai dai ba"
Yusuf yace "A'a ba ɓata rai nayi ba, karki damu zo kici Abincin ki, nasan kina jin
yunwa yanzu, dan rana tayi baki karya ba"
Ya zuba mata Abincin, Haka taci Abincin tana lura da yadda Yusuf duk yayi wani iri,
kamar wani abu yana ɗan damunsa, amma babu alamar ze faɗa mata meke damun nasa.
Anwar ya shirya yaje gidansu Fahad, domin yana son ganin Bulama suyi magana, sedai
be sami Fahad a gida ba, dama ba gurinsa yaje ba dan haka be kula ba ya nemi idan
Bulama yana nan a masa iso, Ramadan yayi masa iso zuwa gurin Bulama, Bulama na
ganinsa yayi murmushi yace "Anwar, anya in kulaka kwana biyu baka leƙowa mu gaisa"
Anwar yayi murmushi yace "tuba nake, abubuwa ne suka ɗanyi yawa wlh, Daddy ya aiki
ya gida? Naji amce zaka Umarah shiyasa nace bari inzo in sameka"
"Alhamdilillah Anwar, eh insha Allah sati ma gaba zan tafi da yardar Allah, ya
gidan naku ya babarta ka da ƙannenka?"
"Masha Allah, nice to hear that haka akeso ai, naji kana son ganina meyafaru ne?"
Anwar yace "Amm Daddy, dama nazo ne akan inji wai har yanzu babu wani labari game
da ɓatan Mariƙinmune? Har yanzu babu shi babu Widad gashi lokaci yana ta ƙara ja,
amma shiru babu wani labari akai"
Bulama ya gyara zama sannan yace "Ahh mekuma kake sonji Anwar, bayan wanda yake ta
yawo a gari? Widad garin jajibe jajibenta duk wayo da ƙin mutanenta, amma ta yayimo
tsiya, wani koɗaɗɗen yaro me kama da sadakar yalla nan, direbanta ta ɗauki duk wata
ragamar yaddarta ta bashi, ko gidan nan tazo duk sirrin magana sedai muyi a
gabansa, ko nan da cam ba zata je ba seda shi, duk maganar da zamuyi sedai a
gabansa, dan haka duk yadda take kaffa kaffa yasan wasu daga cikin sirrinta, gashi
ƙarshe 'yan sanda bincikensu ya tabattar musu da cewar, shine yayi garkuwa da ita,
ya nemi kuɗin fansa a gurin mahaifinta, dabe samu ba shine yabi Asibitin ya sace
mahaifinta, yanzu dai' yan sanda suna nan suna binciken inda zasu gansu, amma shiru
babu Labari, sedai a cigaba da Addu'a sannan mu cigaba da sauraren abunda zasu ce,
amma abun da ɗaure kai fa sosai"
Anwar yace "nifa Daddy har yanzu ban yadda da wannan sakamakon binciken ba da aka
bayyana, babu yadda za'ayi ace shine ya saceta, Daddy kasanta da wayon tsiya, babu
yadda za' ayi tana sane ta bari yasan sirrinta, sedai idan akwai wata manufa da
take dashi a kanta, sannan daga rundunar 'yan sandan nan a farko an sanar da sace
su akayi, har an siyar da motar da aka sace su a ciki an ganta a kasuwa, ba' a
kumabi takan zancem ba, basu bincika ya akai motar taje kasuwa ba, kuma azo a sake
sanar da cewa wai shine ya saceta, it doesn't make sense, kuma bayan haka ace ya
kuma zuwa ya sace mahaifinta, sam beyi kama da criminals ba, ni gaba ɗaya banji
ƙamshin gaskiya a lamarin nan ba, akwai wata a ƙasa dai"
Bulama yace "eh to, kaima maganarka abun dubawace, amma ka sani mutum yana iya
canzawa a kowane lokaci, kuma ze iya yuwuwa shine ya saida motar, tunda yasan
siriikanta dan yasan abunda ban sani ba ni game da ita, sannan kuma duk abunka da
ƙwaƙwƙwafinka kasan dai ba zaka gwadawa 'yan sanda aikinsu ba, tunda suka faɗi haka
kasan abunda bincikensu ya nuna musu kenan, ba zasu yi ƙarya ba haka kurum, kabar
mutum akan aikinsa kawai"
Anwar kamar ze kuka yace "Amma Daddy babu abunda' yan sanda ba zasu iyayi akan kuɗi
ba kaima ka sani, idan wasu ba zasu yi ba, wasu zasuyi tunda suma mutane ne, dan
haka ba abun mamaki bane suma 'yan sanda suyi komai akan kuɗi ba, dan haka yakamata
ta ɓangarenka ma, kasa a sake bincikawa a tabattar da in dagaske binciken nasu haka
yake, kasan Alhaji Nasir da' yarsa suna da maƙiya, komai fa ze iya faruwa, zata iya
yuwuwa su suke wannan abubuwan haka"
Bulama yayi dariya irin tasu ta tsofaffin manya yace "Yaro yarone dai, Amma kaima
kace wani abu me mahimmanci fa, shikenan Anwar tunda haka kace, Insha Allah zanga
ƙoƙarin da zanyi ta ɓangarena, tabbas Daula yana da maƙiya kam, kuma komai ze iya
faruwa, zanga abunda zan iya, Allah ya wuce mana gaba"
Kasancewar gidan babu kowa yasa Yusuf baya fita ko ina, dan baze iya fita ya barta
a gida ba ita kaɗai, yasan ba zata zauna bama, suna zaune tama ta saƙa mafici Ya
ɗan kalleta yace "Widad"
Ta ɗago ta kalleshi Tace "Na'am"
Yace "Me kike tunani game da wannan baƙin, ɗan megari da matarsa, bakya ganin
Asirinmu ze iya tonuwa zamanmu dasu? Kar muje a samu matsala fa"
Widad ta ajiye abun hannunta jiki a sanyaye tace "To aini gaba ɗaya kaina ya kulle
Yoseef, na rasa meye abunyi wallahi, kawai ni yanzu na fawallawa Allah lamarinsa,
duk yadda yayi damu shikenan, ni dai babban fatana in cika burina kafin in mutu,
nasan ko asirinmu ya tonu, ko be tonu ba dole ɗayanmu zeyi nasara, komu ko maƙiya,
dan haka na miƙawa Allah lamarina, Allah ya kiyaye mu gaba ɗaya, amma nima nayi
irin wannan tunanin naka, amma ba yadda na iya, in mun bar nan ina zamu?"
Yusuf yayi ajiyar zuciya yace "da farko ina ɗan jin shakku a raina ne, amma Saleh
ya tabattar min da babu komai, ba abunda ze faru yasan matakan daya ɗauka, sedai
ina fatan Allah yasa hakan, Allah ya kiyayemu da kiyayewarsa"
Tace "Ameen ya Allah, Amma Yoseef nifa har yanzu baka taɓa gayamin meka gano a naka
binciken ba, da kayi a lokacin muna gida"
Yusuf ya ɗanyi murmushi yace "Anƙi a faɗa ɗin, kema ai jamin rai kika dingayi,
kika ƙi gayamin tarihinki"
Yusuf yace "to shagwaɓaɓiya karkimin kuka dai, bincike daga cikin gidanku na fara
yi, sedai nayi mamakin ƙiyayyar da matar mahaifin ki ke miki, da farko nayi zaton
tana yi ne saboda halayenki, da abunda kikeyi na wulaƙanta ta da 'ya' yanta, sedai
daga baya na gane son zuciyarta ne abunda take, akwai ranar da kika rufe ƙofa kika
ƙi buɗewa, nasa Amal ta kawo miki tea, sedai kika zubar da tea ɗin, nayi mamakin
ganin ƙwaya a ƙasan kofin shayin"
Tace "samunsu nayi a falo, suna tattauna yadda zata damfari Daddy kuɗi, kasan na
kanyi kwanaki a part ɗina ban fito ba, shine suka sakankance suna hirarsu, basu yi
tsammani ba kawai suka ganni a ƙofar falo, shine suka shiga kame kame, bance musu
komai ba, na fita dama fita zamuyi da kai ranar, bayan mun dawo cikin dare ina
bacci, da yake ban rufe ƙofar ɗakina ba, kawai seji nayi cikin bacci ana lalabun
hannuna, nayi yinƙuri zan ƙwaci hannuna kawai akayi min Allura, irin Allurar da'ake
min a baya a birkita ni, take na fara dena gane abubuwa sosai, ban san wanda yayi
min allurar ba, amma a haka bayan ya fita na tashi ina tangaɗi na rufe ƙofata, tun
daga nan ban sake sanin abunda ke faruwa ba, se bayan dawowar Daddy, shiyasa a
rayuwa na tsani matar nan Yoseef, na tsaneta fiye da yadda kake tunani, ji nake
kamar in shaƙeta seta mutu"
"a'a karki kuma cewa zaki kashe mutum, sannan kika sani ko Daddy yana son matarsa?
Ki barwa Allah zakiga sakayyar daze miki, amma banda ambaton kisa"
"Rabu dani bazaka gane ba Wallahi, dama muna komawa Seta barmana gida, sannan Aure
zan nemawa Daddy da kaina, sannan ko banyi kisa ba idona idon Bukar a zahiri seya
tafi lahira da tabom da zanyi masa"
"Kibi komai a hankali Widad, Insha Allah komai zamu bishi a hankali, kuma zamuyi
nasara da yardar Allah, Amma karki yinƙurim ɗaukar doka a hannu, dukda bansan waye
Bukar ɗinba, kuma bansan meya yi miki ba, amma karkiyi ganganci, muyi komai a
dokance"
Ta girgiza kai tace "bazaka gane me nake jiba a Yoseef, idan ban kashe mutumin nan
ba kona masa illar da zan nakasta shi ba, to zan mutu ne" tai maganar tana kwanciya
a jikinsa.
Yasa hannu ya rungumeta a jikinsa, shiru ya wanzu a tsakanin su.
Yusuf idan suka gaji da zaman ɗaki sesu dawo tsakar gida, suyi shimfiɗa suyi zaman
su, sannan gaba ɗaya Yusuf ya shiga kiyaye abunda yasan zai ɓata mata rai.
Lokaci lokaci takan shiga ɓangaren Jamila, dan ta ɗau jaririyarta, dan har goya
mata ita take yanzu, idan ta goyamata ita ta zauna guri ɗaya ta nutsu sosai kamar
am goyawa yaro, Jamila tace "Widad waike bakya saka Atamfa ne,? Kullum se ƙananan
kaya, baki san yawan saka abu ɗaya yana gundurar mijinki ba?zeso yaga kin canza ai"
Widad tace "nifa ban iya saka wata atmfa ba, tun taso wata ni bana saka wata
Atamfa fa ko makamancin haka"
Jamila tace "Eh naga alama nima, amma Aikuwa yakamata mu bawa mijinki mamaki, ina
da sabuwar atamfa na haihuwar Yusra da aka bani na barka, zan kai a ɗinka miki"
Widad tace "A'a karfa Yoseef yaji haushi, ko yace ban gaya masa ba"
Jamila tace "baze ce komai ba, zeyi mamaki ya ganki acikin Atamfa, karki damu ba
abunda zece zeyi murna shima, kim san maza nason a basu mamaki, amma ina fatan kun
shirya da shi"?
Widad tace "eh mun shirya, tun jiya amma da ƙyar yayi fushi dani sosai"
Jamila tayi murmushi tace "Yawwa tawan, karki ƙara bari ya kwana yana fushi dake
kinji ko, sannan ke zakiyi dabarun daze dena daɗewa yana fushi dake"
Widad tace "to ni ya zanyi?, yana daɗewa beyi ba, amma idan yayi fushi da ƙyar
yake sauka fa"
Tace "to kidena yin abunda ze sashi fushin mana, kuma Kinga yadda kike da kyan nan
masha Allah, gaki da manyan idanu masu ɗaukar hankali masha Allah, ki dena kallonsa
kamar yadda kike kallon sauran mutane, ki nuna masa Wata kissar sai mata (wanda be
karanta littafin wata kissar sai mata ba na Ammar da Mufeeda, ya garzaya ya nemi
nashi, akwai darasi a ciki 😍 da Nishaɗantarwa)
Idan zaki masa magana, ki dinga kashe masa ido, ko ɗan shanye idanunki kamar kina
maye, dama na ganki masha Allah, shagwaɓaɓiya ce duk kidinga masa, ko yayi fushinma
da kansa ze sakko, saboda karya yi missing wannan kallon"
Widad kawai ta kwashe da dariya, "Au dariya ma na baki? Aiko ki gwada zaki bani
labari, ki dinga zuwar masa da abubuwan da bakya masa a baya, hakan zesa ya ƙara
sonki, kin san mazan ne seda lallaɓawa, amma dukda haka suna mana ƙoƙari kuma suna
haƙuri damu, sedai duk Allah ya bamu haƙurin zama da juna"
Hanne ce ta shigo, ta dinga jiyo dariyar Widad da Jamila, ta ƙaraso ta ɗaga labule,
taga Widad a zaune da goyon 'ya suna hira da Jamila, ai shigowar da ba tayi ba
kenan ta koma, tana tsaki.
Sunusi ne mijin Jamila ya dawo, dan haka Widad ta bawa Jamila' yarta ta fice, dama
ba gaisawa suke ba da Widad, dan haka ne kulata ba bata kula shi ba ta fito ta tafi
ɓangarensu, ta tarar Yusuf ya shimfiɗa tabarma a tsakar gida yayi ruf da ciki, yana
karanta azkar.
Yace "ya hakane? sekin karyamin baya ne? So kike ki maidani gurgu?"
Yace "to naji ɗagani, dan kin ƙara nauyi, matar ƙauye kawai kina ƙauye amma ƙiba
kike"
"kaima Mijin ƙauye, kuma bazan tashi ba, idan ka takuramin kuma ka sha cizo ba"
Yusuf yace "hmm aikin taɓa cizona fa, akwai tabon a jikina"
Yasa hannu ya janyota daga bayansa, ya kwantar da ita a jikin bango yana kallonta,
sannan yace
"Ranar da kika kusa taramin jama'ar garin nan, kalli inda kika cijeni, banda duka
dana sha a gurinki"
Tura baki tayi tace "Eh anyi ɗin ba kaine ka... Se tai shiru
Yusuf ma dariya yayi ya juya yayi rigingine, ta kwanta a ƙirjinsa tace "Yayan
Daddy, a rayuwa yadda da farinciki sune gaba gurin sada mutum da walwala, kalleni a
garin da babu wauti, ba ruwa, ba waya, ba system, ba motoci babu duk wani abu na
more rayuwa, amma gashi kai kaɗai kana bani farincikin da duk wannan abubuwan dana
rayu dasu basu bani ba, dukda na sha wahala kafin sabawa da wasu abubuwan a garin
nan, amma bayan na saba sena gane ita rayuwa a bace me sauƙi, yadda ka ɗauketa haka
take zuwar maka Nagode sosai Ɗan uwana, kayi rawar gani a rayuwar Yarinyar da baka
haɗa komai da ita ba"
Rungumeta yayi yace "ina fatan kasancewa dake har ƙarshen rayuwa ta Widad, dukda
bani da tabaccin ina da mahalli a zuciyarki, kuma ban san yadda al'umma zasu karɓi
Auren nan namu ba, amma nidai nasan ina sonki Widad, ban san yadda hali zeyi ba a
nan gaba, ko dai mu kasance tare, kokuma mu rabu, amma ni dai nasan ina sonki,
Dukda soyayya ta ta baya, banji naso wata kamarki ba, I love you Widad "
Ƙanƙame Yusuf tayi, tana jin wani irin shauƙi yana ɗibarta, a koda yaushe ta kanji
farinciki idan yana tare da ita, koda suna gida yana a matsayin direbanta, ko tana
cikin ɓacin rai idan taga yazo se taji damuwarta ta ragu, tana jinsa sosai a ranta
amma ta kasa danganta hakan da Soyayya, a duk lokacin da taji damuwa ta mata yawa,
tana haɗa ƙirjinta da nasa zataji bugun zuciyarta na daidaituwa, da zarar ya fara
rarrashinta ta kan manta ɗinbin damuwarta, tayi wani irin sabo na bazata da Yusuf,
wanda har take jin ya zata kasance idan ta koma gida, Yusuf ya nesanta ida?.
"Saboda Halima zata bar mana gida, da kaina zan samowa Daddy mata ya aura, zaka
dawo gidanmu ko?"
"Nima ban san dalili ba, sedai ina jin a jikina, rasa ka a rayuwata babban giɓine,
kuma tamkar rasa garkuwa ne a gareni"
"Nima rashinki a gareni babban giɓine, saboda na kamu da makauniyar soyayya cikin
bazata, amma ban saniba ko zaki iya cigaba da zama dani idan kika san wani abu game
da rayuwata"
"Ni dai koma meye, dan Allah ka zauna a gidanmu idan mun koma kaji"
Ta maganar cikin Shagwaɓa tana kallonsa, "Babyna wannan wane irin kallone haka
kikemin? You look so cute da kika juya idonki"
Kamar ƙaramar yarinya ta kuma cewa "dan Allah kec zaka dawo mana"
Ji suke tamkar suka ɗaine a duniyar, Kasancewar gidan ba kowa dan haka hankali
kwance suke soyayyarsu a tsakar gida, basu san Hanne tana ɗaki tana jiyo dariyarsu
ba, dan har leƙsensu take ta taga tana share hawaye.
Anwar yayi tunanin bari ya tsaya a gidansu Nurat su gaisa, kwana biyu kota waya
basa haɗuwa dan bama hawa yake social media ba sosai balle su gaisa, sannan su
jajantawa juna abubuwan da suke wakana, sedai a bakin gate megadi ya tareshi yace
"wa kake nema ne?"
Megadin yace "baka da labarin abunda ya sameta wancan zuwan naka ne? Mahaifinta
seda ya kusa halakata, ni ban san hali irin na mutumin nan ba, dan haka yun wuri
kabar gurin nan tun kafin kaja mata wata wahalar"
Mamakine ya cika Anwar sosai da jin abunda megadin yace, amma yace "Shikenan,
nagode sosai, dan Allah ka gayamata nazo mu gaisa ne kawai, kace ina gaishe ta
sosai, sannan idan ta samu lokaci ta taɓani a waya se in kirata"
Megadin yace "Shikenan, zan gayamata wannan karka damu kanka dan dai saƙo"
Anwar ya cika da mamakin me zesa a hukunta Nurat dan yaje gurinta, alhalin
mahaifinta be nuna masa komai ba har gaisawa sukayi dashi, amma ace an hukunta ta
kuma bata gaya masa ga abunda ya faru ba.
Haka yakama hanyar gida, yanata zancen zuci, yana danja a tsaye yana ta tunani a
ransa kamar ance ya ɗaga kansa, ya hango Ramlah a farajiyar wata plaza, da Fahad da
wasu maza suna ta shan shisha, kayan jikinta sun Matseta sosai kamar ba 'yar
musulmi ba, abun ya ɗaure masa kai ya sake mustsustuke idonsa ya kalli gurin, babu
ko tantama itace, ya dafe kai yace "innalillahi wa inna ialaihi raji'un, Mummy kina
me Ramlah ta lalace haka? Kalli yadda ta koma"
Motarsa ya fizga a guje yai gida, zuciyarsa na wani irin tafasa kamar ta tsaga
ƙirjinsa ta fito dan baƙin ciki.
Sedi yana zuwa gidan, ita kanta Mummyn bata nan gidan babu kowa se masu aiki.
Ya zauna a falo yana jin zafi akan sakaci irin na mahaifiyarsu, kuma da yayi magana
taji haushinsa, amma yau kome ze faru seya ɗau mataki akan Ramlah.
Tun la'asar yaga Ramlah, amma har bayan isha'i babu wanda ya dawo gidan, yana nan
zaune Yaji ƙararar mota ya leƙa, ya hango Ramla ta fito da ƙyar take iya buɗe
idoma, saboda azabar buguwar da tayi, amma a haka ta tuƙo mota zuwa gida.
Ta riƙo takalmanta a hannu da jakarta, tana tafe tana gware da bango harta shigo
falon.
Cikin maye tace "Ni.. Ni...... Ni....... Fa na inda naje, kawai naje cin... Cin
Abinci ne a w. Wa. Wani restaurants that's all"
Kwaɗamata mari yayi, wanda seda ta dawo hayyacinta na 'yan sakanni, ya zare beilt
ya dinga dukanta yana ƙwallo da ita, seda yayi mata kaca kaca ya tabattar ta daku
sannan
yace "kaiconki Ramlah, kin biyewa wannan ɗan iskan kina lalacewa, dama Aurenki zeyi
da sauƙi wataƙila ya shiryu a sanadin ki, amma kawai kin biye masa kin ɓata
rayuwarki a banza a wofi kaiconki Ramlah, yanzu kin riga kin ɓata rayuwarki, ke ba
aurenki zeyi ba kuma babu wani mutumin kirki daze yadda ya haɗa zuriya dake, tunda
kika zaɓi rayuwar shaye shaye da lalacewa"
Hajiya Halima ce ta buɗe ƙofar falon, ta shigo ita da Amal, sedai tayi tozali da
Ramlah a baje a gurin fuskarta duk a kumbure, saboda dukan da ta sha, gashi a
hakanma maye take yi.
Cikin ɓacin rai Anwar yace "Mummy ɗazu a danja, na hangeta a harabar wata plaza
suna shna shishsa ita da maza, da wannan sakaran Fahad ɗin mara tarbiyya, kuma ta
dawo gidan nan tana maye"
"Kuma shine zaka mata wannan dukan, idan ka kashe ta kuma fa kalli yadda ka daketa,
idan kaji mata rauni kace baka san yadda akayi ba?"
"Mummy, amma yanzu laifin Ramlah bekai a hukunta ta ba? Shaye2 tana mace, kallifa a
hakan ma maye take yi, bata san meke faruwa ba, kuma amma a haka kike cewa meyasa
na daketa?"
"Rufemin baki ko in tsinkeka da mari, baiwar ubankace ita da zaka mata wannan
dukan? Kai duk laifin da kake yi haka nake kamaka in jibga kamar jaki? Ka ɓatawa
yarinya halittun fuska, kuma kana cemin maye take, haka ake mayen zafin duka dai
yasa take surutai, dalla wuce ka bani guri babban banza kawai "
A fusace tace "fitarmin daga falo tun ban rama mata abunda kayi mata ba, ɗan banza
me baƙin hali kamar ubansa, yadda halinka yake haka na matsiyacin ubanku yake,
baƙin hali dai akwai shi hadda na masifa da jaraba ka gado shi a gurinsa, fice ka
bani guri me zuciyar banza data wofi "
Anwar yasha mamakin zagi da cin zarafin da mahaifiyarsu tayi masa, alhalin ga
gaskiya tana gani ƙurƙuru, amma ta rintse ido ta masa wannan mummunan cin fuska
haka.
Hajiya Halima ta ƙarasa gaban Ramlah tana ɗagota tace " Sannu Ramlah, Allah ya
haɗaku da jarababbem ɗan uwa yana nema yaga bayanki, ni na rasa wannan mummunaan
hali daya kwaso a gurin ubanku, Amal kawomin ruwan sanyi a fridge in shafa mata ko
zata farka daga suman da tayi, da wannan surutan da take yi"
Amal tace "Mummy, maganar gaskiya fa Yaya Anwar yana da gaskiya, Ramlah fa maye
take yi, kuma ba yau ta fara shan kayan maye ba"
"Kamar yadda na gaya miki mana, wallahi tana shaye2 ne, wannan cocacolan da take
sha, syrup take juyewa a ciki ta sha abunta, shine zakiga tana ta faman bacci, nayi
mata magana amma kin san halinta baji take ba, wannan Fahad ɗin kuma shine silar
komai"
"Ke Rufemin baki, idan har dagaske ne tana shaye2 da tuni na sani, ko kuma wani
abune yake damunta yasa tayi shaye2, amma idan ta tashi zamuyi magana, sannan daga
nan kar in sake jin maganar nan kinji na gayamiki"
Da daddare Yusuf yana kusa da Widad akan katifarta suna bacci tare, wani mummunan
mafarki Widad tayi, suna tafiya ita da Yusuf a wani guri me kyau, suna sanye da
kaya masu kyau sosai, yana riƙe da hannunta yana mata hira tana ta dariya, shima
fuskarsa ɗauke da murmushi.
Babu zato wata mata ta ɓullo a fusace, ta riƙe hannun Yusuf tana jansa, Widad ta
fashe da kuka ta riƙe Yusuf gam tana
"dan Allah Yoseef karka tafi ka barni, dan Allah ki ƙyalemin shi nawane ba naki
bane, na fiki buƙatarsa, nafi ki kusanci dashi, dan Allah kiji tausayina ki barmin
shi, dan Yoseef karka barni"
Yusuf kuma ya fara ƙoƙarin bin matar nan su tafi, yana kallon Widad fuskarsa ɗauke
da damuwa, da alama shima yafi son zama a gurin Widad.
Hannunsa ya fara zamewa daga na Widad, ta fara dena ganin fuskar Yusuf se dishi
dishi.
A firgice ta farka daga baccin tana haki, tana ambaton sunan Allah, a gigice ta
ɗakko fitila tana haska inda Yusuf yake sedai me......
LITTAFIN KUƊI NE, DAN ALLAH KI SIYA KAFIN KI KARANTA BA DANNI BA DAN ALLAH, LITTAFI
NA ƊAYA KYAUTA NE WANNAN NA SIYARWA NE
NORMAL GROUP ₦300
VIP ₦500 NE KITURA TA WANNAN ACCOUNT ƊIN
0009450228
JA'IZ BANK
AISHA ADAM
SE A TURA SHEDAR BIYA TA WANNAN LAMBAR
07063065680
IDAN KUMA KIN SIYA AMANACE KARKI FITARMIN DAN ALLAH 🙏🙏🙏
11/15/21, 4:52 PM - Buhainat: LITTAFIN KUƊI NE, DAN ALLAH KI SIYA KAFIN KI KARANTA
BA DANNI BA DAN ALLAH, LITTAFI NA ƊAYA KYAUTA NE WANNAN NA SIYARWA NE
NORMAL GROUP ₦300
VIP ₦500 NE KITURA TA WANNAN ACCOUNT ƊIN
0009450228
JA'IZ BANK
AISHA ADAM
SE A TURA SHEDAR BIYA TA WANNAN LAMBAR
07063065680
IDAN KUMA KIN SIYA AMANACE KARKI FITARMIN DAN ALLAH 🙏🙏🙏
94_95
Haska inda Yusuf ke kwance tayi tana sauke numfashi, gani tayi ya haɗa gumi yana
bacci, daga shi se dogon wando da alama zafine ya isheshi, shine ya cire rigar ya
kwanta haka, ta hasakashi sosai taga kamar baya numfashi, ta kai hannunta da sauri
Ƙirjinsa saitin zuciyarsa, taji zuciyarsa tana bugawa a hankali, bacci yake yi
sosai sedai yayi gumi sharkaf a jikinsa.
Tashi tayi a hankali ta tafi ta lalubo mafici, tazo ta zauna ta ɗaga kansa ta ɗora
a kan cinyarta, ta shiga yi masa fifita, tana goge hawayen da bata san dalilinsu
ba, tama jin yadda ƙirjinta ke cigaba da bugawa saboda mafarkin nan da tayi, tana
kuma godewa Allah da yasa ba gaske bane mafarki ne.
Yusuf ne yayi ƙoƙarin yin juyi, yaji shi a jikin mutum, ya kai hannu ya tattaɓata,
ga ƙaramar fitilarsu ta kunna wadda haskenta yayi ƙasa sosai saboda rashin batir.
Ta jinjina masa kai alamar eh, "to meyasa kawai zaki katse baccinki ki tashi kina
min fifita?"
Tace "kasa bacci nayi, kuma naga kayi gumi dayawa, ka kwanta kawai ka cigaba da
baccinka"
Yai murmushi yace "Allah sarki my Widad, nagode sosai Allah yayi miki albarka,
amma Kasancewar ina mijinki kina mata ta bashi ke nufin, in cutar dake ba dare
lokaci ne da Allah ya bawa bayinsa, dan su huta ko suyi ibada, amma in hanaki naki
baccin dan nawa no baze yuwu ba, kece yakamata in miki fifita kiyi bacci saboda
nasan wata ƙila zafine ya hanaki baccin, kuma nine gaba dake akwai buƙatar in
tausaya miki "
Girgiza masa kai ta kuma yi tace " A'a kabari, kwanta kayi bacci kawai "
Tashi zaune yayi, ya karɓe maficin hannunta sannan ya kwantar da ita, yana mata
fifita yace " wai na ganki some how looking disturbed, menene meya hanaki bacci ne
matar? "
Murmushi yayi yace "Ohh My God, ya ilahil alamina Widad dreams are not true,
mafarkine fa kawai meye na ɗaga hankalinki, ba gani a tare da ke ba, dena kuka haba
babyna"
Kukan ta sake fashewa dashi tace "i don't want to lose you, Ina tsoron ya zama
gaske mafarkin, sometimes our dreams come true, ina jin tsoro sosai, and am still
having palpitation, ina jin kamar ze faru ne a gaske"
Yusuf yace "No my dear, kawai dai kin tsorata ne, kuma zuciyar ki ta fara jin
abunda Yusuf yake ji game dake, amma in dai nine bazan gujeki ba ko in juya miki
baya, sedai in daga ɓangaren ki a samu akasi, amma nikam nasan ina son matata"
Yai maganar yana saka hancinsa a wuyanta, shiru ta ɗanyi tana ƙara so ta tabbatarwa
da zuciyarta kalaman Yoseef ɗin, na mafarkine kawai baze zama gaskiya ba, amma
dagaske kenan Ta kamu da soyayya?
Tana cikin tunanin taji Yusuf yace "Wife, ina kika samu wannan turaren ne, tun
rana yake tashi a jikinki, ina ta ƙoƙarin riƙe kaina, tauraren nan yayi daɗi a
jikinki sosai"
Cikin cuna baki irin na wanda ya gama kuka tace "Jamila ce tabani"
Ta gyɗa masa kai, yace "good, ki tambayeta kuɗin turaren nan, zan bayar a ƙara
mana"
"Dayawa fa ta bani, wai itama maƙociyarta ce a barrack ɗim da take ta bata dayawa
da ta haihu, shine nima ta zubamin kuma da yawa fa ta bani"
Cikin nishaɗi yace "dukda haka i suppose to pay for it, naji daɗi Sosai, bazan
manta kyautar turaren da kika bani ba, kyauta ta farko da kika bani, kyauta daga
hannun masoyiyya, amma sedai naji kamar wari nake shiyasa kika bani turare"
Duk da a damuwa take, amma seda tayi dariya tace "taɓ duk wannan gayun naka, dukda
basajar da kake yi amma abunda ya fara birgeni da kai ashine tsaftarka, dan wasu
dan suna irin wannan aikin se suyita ƙazanta, su a dole se sun nuna talaucinsu,
abun da yasa na baka turaren nan, duk lokacin da naji turare na tashi a jikinka, se
naji wata kasala ta kamani, ko laifi kayi min seka rage ƙarfin fushin da nake ɗauke
dashi, shiyasa nace bari in canza maka turare ko zan dena jin hakan, wataƙila daga
turaren naka ne "
Yace "bakomai, just forget, ni dai ki bari kawai in shaƙi wannan ƙamshin me daɗin
gaske"
Shiru tayi tana saurarensa ba tare da ta sake cewa uffan ba, aikuwa Yusuf ya wuce
makaɗi da rawa, yau dai be sha cizo ba🤭🤭, sema wani farinciki mara misaltuwa da
suka tsinci kansu a ciki.
A hankali a kunnenta yace "God bless you my Wife, thank you very much"
Ƙin magana tayi, sema lafewa data sake yi a jikinsa, yace "tashi in ɗora mana
ruwa, naga akwai sauran kalanzir ko?"
Widad tace "eh akwai, amma shekaranjiya Hindu tayi girki a kai, idan babu se muyi
dana sanyi"
"No akanme? Haka kurum in baki ruwan sanyi kiyi wanka inje ki shiɗemin, abunda baki
saba ba, bakomai zan dafa mana, inma babu naje in tada murhu yanzun nan"
"Eh mana, meye a ciki, muna cikin baccin mu kin tasheni kin janyo mana aiki"
Akayi sa'a da kalanzir ɗin, ya fito da rishon tsakar gida ya ɗora musu ruwa, saboda
yanayi na zafi kae ɗakin ya ƙara ɗaukar zafi, kafin ruwan yayi zafi, Yusuf ya ɗakko
musu gashashiyar gujjiya suka zauna suka kama cin abarsu suna hira a wannan daren,
se kace aljanu.
Jin ana ɓuruntu, yasa Hanne ta miƙe cikin tsoro ta leƙa taga dan ganin meke faruwa,
ta hangesu zaune a cikin farin wata, suna ciue ciyensu suna hira.
Ta jinjina kai tace "lallai wannan kinyi dacen miji, yana sakar mata fuska sosai
saɓanin mazan garin nan, wanima murmushi baze iyayiwa mace na wai karta raina shi.
Ƙarshe ma tare sukayi wankansu, Yusuf jinsa yake kamar wani sabon mutum, wani irin
farinciki ya mamaye zuciyarsa, sedai duk da ɓangaren Widad ma hakan take, amma ta
kasa manta mafarkin da tayi akan Yusuf, haka kurum abun ya tsaye mata a rai.
Anwar gaba ɗaya abunda ya faru yau a gidansu ya tsaye masa a rai, muraran
mahaifiyarsu ta tabattar maaa da tafi ƙaunar Ramlah akansa, kuma bata son ace ga
laifin da tayi, balle a saka rana zata mata hukunci, ransa ya ɓaci sosai dan haka
ya fara tunanin, wane mataki yakamata ya ɗauka, dan janye jikinsa daga harkokin
gidanma gaba ɗaya?.
Yana kwance yana tunanin meye mafita, yaji wayarsa tana ringing, da kamar baze ɗaga
ba amma ya janyo wayar ya ɗaga.
Jin muryar Nurat ce tayi masa sallama yasa ya ɗan saki ransa ya amsa, Nurat tace
"Yaya Anwar, ɗazu kazo baka samu ganina ba"
Anwar yace 'eh, nazo mu gaisa amma megadi yacemin zan ja miki matsala, wancan zuwan
da nayi ma na jamiki matsala amma baki gayamin ba"
Ajiyar zuciya Nurat tayi tace "hmm kai dai bari kawai Yaya Anwar, abunne duk se a
hankali, na kasa gane kan mahaifina gaba ɗaya, ya hanani fita zuwa ko ina, sannan
ya hana kowa yazo inda nake, na kasa gane manufarsa, sam ban gane inda ya dosa ba"
Anwar yace "Amma kuma lokacin da yazo ya samemu tare be nunamin komai ba"
"Ai haka yake yi, baya taɓa nunawa a gaban mutane, amma bayan tafiyar ka har dukana
yayi"
"Subhanallah, kiyi haƙuri wallahi ban zan zuwana ze kawo miki matsala a gurin
mahaifinki ba"
Nurat tace "bakomai karka damu Yaya Anwar, ba laifinka bane, sannan kayi haƙuri
rashin haɗuwar da mukayi"
"A'a bakomai Nurat, ina fatan ubangiji Allah ya daidaita tsakanin ku, dama biyowa
nayi mu gaisa, wallahi nima kusan a cikin damuwa nake Nurat"
"Subhanallah, meyafaru?"
"Wallahi Nurat abubuwan nan da suke faruwa gaba ɗaya na rasa abunyi ma, jiya Ramlah
a buge ta dawo tayi mankas da ƙwaya, amma ƙiri ƙiri dan na hukuntata Mummy ta
fituttuke tace ƙaryane, taita faman Yimin faɗa, ban san meyasa take haka ba, abu in
dak Ramlah ce bazata taɓa ganin laifinta ba, ƙarara take nuna banbanci a
tsakaninmu"
Nurat tace "se haƙuri ai, lamarin iyayen nan namu sedai addu'a, ni gashi nikaɗaice
a gurin iyayena, amma wasu lokutan idan Daddy yayi min wani abun, se inga kamsr
bashi ya haifeni ba, yaita treating ɗina a hagunce, abun yana damuna sosai"
Anwar yace "kin san kowane bawa da irin tasa jarabbawar, kowa akwai ta ɓangaren da
Allah yake jarabtarsa, sedai fatan Allah ya bamu ikon cin jarrabawa"
Ajiyar zuciya tayi tace "News kam baza'a rasa ba, amma kasan wai Yusuf ɗan sanda
ne ashe?"
'Eh nasani, amma da farko nima ban saniba, se daga bayan nan, da aka fitar da
wannan Sanarwar"
"To ni dai abunda nake gani, wata maƙarƙashiyar ce aka shirya domin ɓatawa Yusuf
suna, turoshi akayi domin bincike akan maƙiyan Daula, amma kuma daga baya ake nema
a ɗora masa sharri, ni yadda naji ma sunce wai babu wanda ya turoshi aiki gidan"
Nurat tayi ajiyar zuciya tace "Yaya Anwar, wannan abubuwan duk shirine akayi shi
domin a ci mutuncin Yusuf, kuma shiryayiya ce aka shirya wannan lamarin, ni ban san
yadda za'ayi Yusuf ya ƙuɓuta ba, yana cikin matsala"
Anwar yace "hakane, nima naje na samu Alhaji Bulama, tunda yana da alfarma a ƙasar
nan, ayi bincike yadda yakamata"
Nurat tace "Yaya Anwar, tayasu da Addu'a shine abunda yakamata, amma harkar ƙasar
nan se godiyar Allah, gashi haryanzu babu labarin Mahaifin Widad"
Anwar yace "wallahi kuwa, to Allah ya wuce mana gaba, Allah ya kawo mafita gaba
ɗaya"
Washegari da safe, Widad ta riga Yusuf tashi, yau da kanta ta dafa ruwa tayi wanka,
ta gyara tsakar gidan nan fes tayi wanke wanke, ta zuba shinkafa ta fara tsincewa,
ta tsince shinkafar nan iya yadda zata iya, amma Yusuf be tashi daga bacci ba,
Taje inda yake kwance ta zauna ya gama ƙare masa kallo, sannan ta shiga tashinsa
kamar zata tashi jariri.
A hankali ya buɗe ido, yanayi yana lumshewa alamar bacci be isheshi ba tace "wai
yau da Yunwa zaka barni?"
Murmushi yayi ya sake lumshe idonsa, cikin Shagwaɓa tace "tashi Yunwa nakeji fa"
"Haba dai?"
Ya miƙe ya duba ta share ko ina, tayi wanka har shinkafa ta gyara ta wanke,
murmushi yayi yace "Alhamdilillah, mutuniyar ta fara zama mace"
"Dama ni namijice?"
"A:a ni bance ba, amma mace ai seda aikin gida, kice zamuyi surprising Daddy '
lokaci lokaci Widad se taji gabanta ya faɗi, amma ta dake da dinga ɓoyewa, dan
karya gane tana cikin damuwa.
Widad tace "Yoseef ina kewar su Mama sosai da Hindu, mutum rahama ne"
" A' a ni ba haka nace ba, na saba ganinsu ne, ina ganin mostinsu da giftawarsu,
amma kwana biyun nan shiru bana ganinsu"
Yusuf yace "yanzu kin gane amfanin mutum a rayuwar ɗan adam kenan? Babu yadda
za'ayi mutum yayi rayuwa shi kaɗai babu mutane kuma yace hakan yafi daɗi"
'hakane, dan ina gudun a cutar dani ne, shiyasa nake gudun mutane, amma yanzu nasan
wannan mutanen da muke tare dasu bazasu cutar dani ba, shiyasa nake kewarsu"
"hakane, naga taku tazo ɗaya dasu sosai, Amma naji anjima zasu dawo ai ko?"
Ta amsa da Ameen.
Anwar sosai yake tunanin samawa kansa mafita, akan lamarin gidansu dan duk se yaji
zaman gidan baya kansa ya fita a ransa.
Shiga yayi gidan da nufin gaida mahaifiyar su da safe kamar yadda ya saba, sedai ta
window ɗin ɗakinta yaji suna magana ita da Ramlah, seya tsaya be ƙarasa ba.
"Ramlah wannan rayuwar da kika ɗauka ba inda zata kai miki, ki kiyayi kanki da
shaye shaye nan, kinga na gwale 'yan uwanki jiya amma tabbas maye kikeyi, dan dai
inajin daɗin shawara dake ne da fushi zanyi dake"
"Shikenan, ai dama nasan zaki dena, nace ya kukayi da Fahad ɗinne, ina fatan dai
baze tona mana asiri ko gurin babansa ba"?
' Haba Mummy, shiya fara ma tunda abun nan harda shi ake ƙaruwa "
"Yawwa haka nake son ji, yanzu wannan manyan filayen nasa nake so in sa a kasuwa na
GRA, dan haka kiyi masa magana, kamar yadda akayiwa Gidajen layout ɗin nan takadda,
suma wannan ayi musu takaddu mu siyar, ke ni ko miliyan sha biyar biyar, a siye su"
Ramlah ta ɗan zaro ido tace "Mummy million sha biyar kima, a filayen miliyan kusan
arba'in ɗin za" a siya a haka? "
" Eh to seme? Da gumunmu muka tara? Nifa sonake ayi yadda za'ayi mu ɗan tara daga
nan mu san nayi, dan haka ki masa magana, ke har gidan nan ma sena siyar dashi, ai
in sun san wata basu san wata ba"
"hakane Mummy, amma gaskiya baza'a siyar da filayen nan a haka ba se an ƙafa, in ba
haka ba mume zamu ci?"
"to koma dai yane, kiyi masa magana ayo takaddun daga nan musasu a kasuwa"
"Shikenan zamuyi waya dashi, kokuma inaga anjima ma zezo, se muyi maganar gaba
ɗaya"
Hajiya Halima tace "ainaji daɗin harkar nan da yaron nan, motocin nan na farmhouse
ma ai duk shi yayi mana hanya aka siyar dasu, banda sauran abubuwa, aini wannan
lamarin ma gaba ta kaimu"
Anwar ji yayi kamar ƙasa ta buɗe ya nutse a ciki, dama kadarorin Daula mahaifiyar
sa ke siyarwa yana wadaƙa da kuɗin? Lallai ɗan Adam butulu ne, idan ya tambayeta
ina motocin gidan se tace tasa an kaisu Farm House, dama abunda take yi kenan?
Innalillahi wa inna ialaihi raji'un'
Jiki a sanyaye yaje ya ɗau motarsa ya tafi gidan gonar Alhaji Daula wanda aka riga
aka mallakawa Widad, yaje da niyyar zagaye yake ya biya dan yaga gidan, ya tarar
fiye da rabin motocin nan idan ya tambaya se ace Hajiya ta turo a ɗauka, hatta
dabbobin Widad tana ta musu ɗuki ɗai ɗai, dan akwai da yawa wanda bana ƙasar nan ba
a ciki, dan haka ana siyansu da tsada.
Abun ya bawa Anwar mamaki, ya tuna irin gwagwarmaya da ɗawainiya da Daula yayi
dasu, amma mahaifiyar su ta rasa dame zata saka masa se wannan zalunci da tsantsar
butulci, lallai ɗan Adam butulu.
Da ƙyar ya kai kansa gida, saboda azabar ɓacin ran da yake ciki, ta haɗa kai da
'ya' yanta suna ta wadaƙa da dukiyar marainiya data mahaifinta, se yanzu yake jin
Widad bata da laifi da suke iƙrarin tana Wulaƙantasu.
Da yamma Widad taita zuba ido a hanya taga ta ina su Gwaggo zasu dawo, se bayan
ƙarfe biyar se gasu sunyi sallama sun dawo, Widad ta dinga murna, tace "Sannunku
da zuwa na zaci ma kum fasa dawowa yau"
Gwaggo tace "aiko kowa be dawo hau ba dole in dawo saboda ke, muna can amma
hankalina yana nan"
Widad tace "Hindu 'yan biki, a huta azo a bani labarin abunda ya faru"
Hindu tace "ni wallahi muna gurin biki, hankalina yana kan makaranta"
"to aini tunda kuka tafi, nace a bari sekun dawo a cigaba'
Suka baje a tsakar gida, Yusuf ya fito yayi musu sannu da zuwa sannan ya fita.
Saboda ɗaurin Aure, megari ma yaje gurin bikin, da shi da Sunusi Kasancewar Yayar
megari ce ta aurar da 'ya, nan ma Yusuf ya shiga yayi musu sannu da zuwa, daga nan
megari yaja shi da hira suka shantake a gurin.
Gwaggo ta baje kayan biki da suka zo dasu, ƙulli daban tayiwa Widad na kayan gara
kuma fal da yawa, kayan zaƙin nan.
Gasu wainar masa da ƙuli, Widad tana son kayan zaƙi dama, ta zauna ta cicci abunta
tana lashe baki.
Ana idar da sallar magariba ta tura yaro ya kira mata Yusuf a waje, Yusuf ya shigo
gidan ya shiga ɗaki ya sameta yace
Ta miƙe ta ɗakko masa kayan da Gwaggo ta bata, Yusuf yace "masha Allah, 'yar gatan
Gwaggo wannan duk namu ne?"
"Eh mana shiyasa nace kazo kaci naka, gashi nan kaci iya cinka, ni na tafi tsakar
gida"
Tana gama maganar ta miƙe ta fita.
Yusuf ya zauna yana cin kayan gara, Widad tayi waje, Hindu tana ta bata labarin
yadda bikin ya gudana, Hanne kuwa se cika take tana batsewa, ba wanda yabi ta kanta
suka ƙyaleta da ƙuncin ran da take yi.
Bayan Yusuf ya gama ya fito tsakar gida yana alwala, Widad tace "Mama waiya mutum
ze gane idan yana da cikine?"
Jamila tace "karki damu, ni zan gaya miki in munfi haka yawa"
Widad tace "koma yane, ni dai dan Allah Mama ki dingamin Addu'a, Allah yasa in samu
ciki"
Hari tace "Ai himma kawai zaki ƙara, idan kika shiga ɗaki tun magariba, se wata
magaribar"
Sam Widad bata gane me Hari ke nufi ba, Yusuf shi kunya cema duk ta kama shi, ya
tashi ya fice waje.
Widad ta tashi ta bita, Jamila tace "Widad nace miki irin wannan tambayoyin, ni
zaki dinga yiwa ba Gwaggo ba, kunyace dasu, kinga baki taɓa haihuwa ba balle ace
kin san alamomin, dan haka ba lallai alamomin da zan gaya miki su zamana ciki bane,
amma mafi akasari dai cikinne ke sawa, Alamomin da zaki gane kina da ciki sun haɗa
da, ɗaukewar Jinin al'ada, zazzaɓi, ciwon kai, jiri, Mamanki zasu danyi miki nauyi,
koma su dinga zafi, yawan tashin zuciya, koma amai, yawan san ki kasance da mijinki
a shimfiɗar Aure, ko jin haushin hakan, yawan som cin wani abu ko ƙin wani kalar
Abincin, da sauransu amma alamomin ba lallai kiji su duka ba"
Jamila tace "Ɗaukewar Al'ada, ko kuma laulayi idan cikin me laulayi ne"
Jamila tace "abubuwan duk da nake gayamiki, kina ganewa kuma kina aikatawa dai ko?"
Suka cigaba da hirarsu, tana ci gaba dayi mata lectures akan Rayuwar Aure.
Da daddare Yusuf ya dawo Widad tayi masa sannu da zuwa, ya lura da ta canza akan
abubuwa da dama, wanda da a baya ba tayi.
Ba zato Yusuf yaji Widad tace "Yayan Daddy dan Allah meye maganin mata?"
Widad tayi shiru ba tace komai ba, kawai taga Yusuf ya kwashe da dariya yace
"lallai yarinya kina ruwa"
Gaba ɗaya bata gane me Yusuf yake nufi ba, taga ya ɗauki kayan shimfiɗarsa yayi
wajen kwanan sa.
" Naga ka ɗauki kayan shimfiɗarka, yau bazaka kwana a gurina ba?'
Kamar zata yi kuka tace "Amma naga yaushe rabon daka kwana anan gurin, kawai se yau
zaka wani ce a can zaka kwanta?'"
Kamar Yusuf zeyi dariya ya maze yace "A'a ni gaskiya sha'awar kwanan kam bargona
nake, kowa ya kwanta a inda ya saba kwana"
Kawai ta zauna tana kuka, Yusuf ya sha dariya sosai, dan Widad ta iya gaɓunta wasu
lokutan, seda yaga dagaske take sannan ya koma inda suke kwana yana mata dariya.
Da gari ya waye, idan Widad ta tuna abunda tayi jiya kawai se wani irin haushi
yakamata taita tsaki, Yusuf yace "uwar kwaɗayi, gobema kije a kuma baki abunda baki
sani ba kici"
Yusuf yaita dariya yace "A'a gaskiya ki ƙara, ni zan bada kuɗi ma ki ƙara"
Ya dinga mata dariya, taga idan ta biyewa dariyar da Yusuf ke mata se tayi kuka,
dan haka ta biye masa suka dinga dariyar tare.
Cam tace "Yoseef, dan Allah ka dinga min addu'a, Allah yasa in samu ciki, haihuwa
nake so nayi nima"
Maimakon yayi magana, kawai seya janye ta daga jikinsa ya bar mata ɗakin.
Mamaki ne ya cika Widad ta bishi da kallo, tana tunanin me yake nufi da wannan
abunda yake yi, duk lokacin da tayi zancen tana son samu ciki, seya canza mata meye
Nufinsa nayin haka?......
LITTAFIN KUƊI NE, DAN ALLAH KI SIYA KAFIN KI KARANTA BA DANNI BA DAN ALLAH, LITTAFI
NA ƊAYA KYAUTA NE WANNAN NA SIYARWA NE
NORMAL GROUP ₦300
VIP ₦500 NE KITURA TA WANNAN ACCOUNT ƊIN
0009450228
JA'IZ BANK
AISHA ADAM
SE A TURA SHEDAR BIYA TA WANNAN LAMBAR
07063065680
IDAN KUMA KIN SIYA AMANACE KARKI FITARMIN DAN ALLAH 🙏🙏🙏
11/15/21, 4:52 PM - Buhainat: LITTAFIN KUƊI NE, DAN ALLAH KI SIYA KAFIN KI KARANTA
BA DANNI BA DAN ALLAH, LITTAFI NA ƊAYA KYAUTA NE WANNAN NA SIYARWA NE
NORMAL GROUP ₦300
VIP ₦500 NE KITURA TA WANNAN ACCOUNT ƊIN
0009450228
JA'IZ BANK
AISHA ADAM
SE A TURA SHEDAR BIYA TA WANNAN LAMBAR
07063065680
IDAN KUMA KIN SIYA AMANACE KARKI FITARMIN DAN ALLAH 🙏🙏🙏
96_97
Widad taje ta samu guri tayi zamanta a tsakar gida tana kuka, saboda tayi mamakin
abunda Yusuf yayi, idan wanine yace ze mata haka tabbas zata ƙaryata, amma se gashi
Yusuf ke ƙyamar haihuwa ko meye dalilinsa oho, to koma dai wani daliline ai bashi
da ƙarfin da zesa ace yana gudun haihuwa haka, idanma tunanin sa yadda zasu yi idan
sun koma gida, ai suna da hujjar da zata nuna aure sukayi ba zaman kansu ba, kuma
tasan Daddy zeyi farinciki da hakan, abun da yake ta buri yaga 'ya' yan Widad a
rayuwarsa.
Kusan kwana biyu babu Anwar, an kai har gurin 'yan sanda amma babu Labari.
Hajiya Halima ta tafi gurin Alhaji Munir, yana ganinta ya ɗan ɓata rai yace "to
uwar matsala, ke duk inda aka ganki ba alkhairi se tarin matsala da damuwa"
Haɗe rai tayi sosai tace "nice ma kake gayawa haka? Dole kace ganina ba alkhairi
bane, kuma ai ganin naku ba alkhairi bane ba, malam ɗana ya ɓata Anwar, tun jiya
ban san inda yake ba, idan wata ƙulla ƙullar kuka haɗa, kowani makircin to kufito
min da ɗana, dan babu ruwansa a harƙallar da mukeyi "
Alhaji Munir yace " to akama ɗanki ayi masa me? Har akwai abunda za'ayi aji tsoron
gayamiki ne? Kije can kineme shi, idanma a cikin namu ne toni dai bada yawuna ba,
dan ban san anyi ba, sedai ko Musa kowani amma ni ban san komai ba kam"
"to bari kaji in gaya maka, idan ma ka sani ka rainamin hankali wallahi duk abunda
nayi maka kai ka ja, dan wallahi sena saka mutum dana sani da cizon yatsa"
Alhaji Munir ya taɓe baki yace "a banza ƙiba a kunne, ƙarewa 'yar gidan Daulama duk
zare idonta da hura hanci shekaru kusan Goma sha biyu ta kasa gano mu balle ta ɗau
mataki, se wata ke zakizo min da wannan ƙaramar barazanar taki dan ki firgitani,
kije kiyi duk abunda zakiyi karki fasa, tunda naga alama daga ke har Musa kun fara
hauka"
"Shikenan, zakaga hauka ganin idonka, wallahi idan da saka hannunku kika sacemin
yaro wallahi se kunyi danasani, zan nuna muku masifa da kaidin mace, shima Musan
zanje in kasa masa warning, tun wuri ka kiyaye ni, ku fita daga idona kallon ku
kawai nake yi"
Ta juya a fusace ta koma inda motarta take, Alhaji Munir ya bita da ido, yayi tsaki
ya koma ciki yana jinjina hauka da rashin hankali na mata.
Daga nan gurin Alhaji Musa taje a Office ɗinsa na neman zaɓe, nan ma suka fafata,
sukayiwa juna kaca kaca shi da ita, sannan ta bar gurin rai a ɓace.
Murtalane yake gyarawa Anwar ɗakinsa wasu lokutan, wani lokacin kuma da kansa yake
gyara abunsa dan shi babu ruwansa, be ɗau duniyar da zafi ba sam kamar yadda
mahaifiyarsa da' yan uwansa suka ɗauka, Nura ya shiga yana gyara ɗakin Anwar, yaga
takadda a ƙarƙashin fulon Anwar ya ɗakko tajadar ya buɗe yakaranta ta tsaf sannan
ya ɗauka ya nufi cikin gidan.
Suna zazzaune a falo sunyi jugum jugum, suna jimami da tunanin inda za'a ga Anwar
Murtalah yayi sallama.
Suna kallonsa amma ba wanda ya amsa masa, a fusace Hajiya Halima tace "dalla
malami meyene, kamar baka san a halin da muke ciki ba, kazo ka samu a gaba da
sallama, meyene jarababbu kawai?"
Murtalah yaji haushin abunda Hajiya Halima tayi masa, koda yake imda sabo sun saba,
hantara da Wulakan da cin mutunci, sun saba ganinsa dan abunda wanda ya ɗaukesu
aikin baya musuma yanzu yi musu ake sedai haƙuri, amma ya dake yace "Dama ba wani
abu bane, ina gyara ɗakin Anwar ne na tsinci takadda a ƙarƙashin fulonsa, shine
nace bari in kawo miki"
Tasa hannu ta karɓi takaddar sannan tace "to ai seka tafi ko? Ko a gabanka zan duba
kaga reaction ɗina, aji daɗin gulma, munafukai kawai 'yan sa ido"
Sum sum Murtalah ya fice yana ƙunƙuni, a ransa yace "Ubangiji Allah ya kawo mana
ƙarshenku, jarababbiya dake da wannan matsiyatan' ya'yan naki masu kama da jakuna,
da bakinsu kaman na yaran hankaka'
Nurane yaji Murtala na zage zage da tsine tsine, yace " kai kuma kai dawa? "
Murtalah yace "nida wannan balamar matar mana, daga zuwa na tsinci takadda a ɗakin
ɗanta naje kaimata, ta kama zagina tana cemin munafuki, ni dana san hakane ma da
wallahi ban kai mata takaddar ba, inga ta tsiya"
Nura yace "kaima meya kaika? Jiya Daga Isa ya ɗanyi mata tunanin albashi, ta zage
shi tsaf taci masa mutunci, hadda wai tunda ba gidan ubanmu bane, wanda ya gaji
yaga baze iya ba ƙofa a bude take ya ƙara gaba, kajifa se kace ita nata gidan
ubanne, ko daga gidansu tayi gammo tazo dashi, aimu tsakanin mu da wannan matar
sedai Allah ya isa wallahi "
Murtalah yace " Allah ya isa me 'yanci makuwa wallahi, dan koni na mata ba adadi
banza tana tafiya a karkace, ita ba ɗa' a 'ya' ya babu tarbiyya, se kayan ɗuwawu
kamar zata kai kayan tusa birni"
Sosai Nura ya dinga dariya yace "Wallahi idan ta jika seka bar gidan nan, kaima ka
sani yaseen, amma fa ka iya ba'a da cin mutunci"
Murtalah yace "to takorenin mana, ai yanzu gidan Daula sunan ne kawai, amma babu
komai a ciki duk a bushe muke, saboda wannan iblishiyar matar, kana gani yanzu duk
tarin jama'ar dake zuwa gidan nan yanzu babu kowa saboda baƙin halinta, wannan da a
aljanu tazo ba shakka se ace itace babar sheɗan"
Nura yai dariya kamar cikinsa zs ciwo, ganin yadda Murtalah ya harzuƙa sosai se
bala'i yake yana zage zage da rashin mutunci da gani kasan an kai shi maƙurar
bangone.
Nura yace "malam kar dai kayi saɓo, a gidan ubanwa ka taɓa jin ance sheɗam yana da
uwa, hattara dai"
"Bari Nura rainane ya ɓaci wallahi, Allah yasaka mana wallahi, Allah ya nuna mana
ranar da dubunta zata cika a tarkatata a koreta da wannan iblisan 'ya' yan nata"
Nura yace "Ameen dai, manyan iblisai makuwa, dan wannan babbar me soyayyen ido
shaye2 take yanzu, saura ƙiris shekaranjiya tabi ta kan ƙafar Isa da tayoyin mota,
Allah ya temake shi yai saurin matsawa kuma ta fito daga motar, ta zage iyayi da
kakaninsa tsaf sannan tabar gurin nan tana maye "
Murtalah yace " haka zasu ƙare, saura kuma hauka da tamɓele, tunda haƙƙin mutane
suka san susa a gaba suci babu imani babu tausayi "
Hajiya Halima kuwa tana buɗe takaddar, taci karo da rubutun Anwar kamar haka
" *_Asslam Alaikum warahmatullah zuwa ga mahaifiyata, nasan lokacin da zaki riski
saƙona nayi nisa da gida, nisam da bana tunanin zan iya waiwayar gida a kwanan nan,
na bar gidane saboda faɗar ma'aiki salallahu alaihi wassalam, babu biyayya ga abun
halitta gurin saɓawa Mahalicci, dan haka bazan iya jure cigaba da zama daku ba ana
aiakta abunda be kamata ba, nasan idan nayi Yunƙurin yi miki nasiha ba zaki
saurareni ba, kin zaɓi lalacewar 'yarki saboda tana miki hanya gurin tara dukiyar
Haram, kin fifita akanmu wanda kema kin san hakan ba dai dai bane, kuma kina ɗauki
ɗai ɗai ga kayan mutumin daya yayi sanadiyar fitarmu daga masifar talauci zuwa
arziki, kin haɗa kai da maƙiyansa ana cutar dashi, nayi dana sani nayi kuka da
bincike na ya tabattar min da dake aka haɗa baki komai yake gudana tsakaninsa da
maƙiyansa, kaicon wannan butulci naki Mummy, ni bazan iya cigaba da zama daku ba
dan haka na bar muku gidan, dama bana ubana bane ba, ina miki fatan Alkhairi dake
da ƙannena a duk inda kuke, Allah ya sadamu da alkhairi, ɗanki me ƙaunarki har
kullum ANWAR *_
Jikintane ya hau tsuma tana rarraba ido, yayin da wani irin gumi from no where ya
shiga tsatsafo mata, ta dinga rarraba ido kamar shege a rabon gado.
Miƙo mata tayi, domin idinta ya gane mata, Ramlah ta karɓa ta shiga karantowa a
fili, tana zuwa ƙarshe ta yarda takaddar tace "shikenan munshiga uku Mummy,
wallahi tonon asirinmu yazo, dan abune me sauƙi a gurin Anwar ya tona mana Asiri,
kin san halinsa Mummy, yau munshiga uku, wayyo wallahi har cikina ya fara ciwo"
Amal tace "wannan shi ake kira tashin hankali wanda ba'a samasa rana, ina muka
kama tunda wannan me iƙrarin ustazancin ya san abunda ake ciki"
Hajiya Halima ta goge fuskarta tace "ni tunanina a gidan ubanwa yasan wannan
maganar? Waye ya gaya masa? Tsawon shekaru goma sha ɗaya ana abun nan a sirrance
cikin rufin Asiri, waye ya tina min wannan Asirin haka ni Halima?"
Ramlah tace "Mummy ba wannan tunanin ya kamata kiyi ba, tunanin meye mafita
yakamata ayai, tunda sanin inda ya samu labarin bashi da amfani"
Hajiya Halima tace "toni ta ina zan fara ne? Ta ina yakamata infara neman mafitar?
Na farko ban san inda ya tafi ba, kuma tabbas abune mawuyaci ya iya ɓoye abun nan
yakasa gayawa wani, ke ni gaba ɗaya na rasa abunyi wallahi, kuma ɗazun nan naje
mukayi kaca kaca dasu Alhaji Munir, da Alhaji Musa na zata su suka sace shi, ni
wallahi da iya tafiyar yayi da sauƙi, amma sanin wannan abubuwan yafi komai masifar
ɗagamin hankali, kar Anwar ya tona min Asiri in lalace a bakin duniya"
Ramlah tace "aida iya lalacewa a bakin duniya ne da sauƙi Mummy, idan Asiri ya
tonufa se komai ya watse ya lalace manya manya abubuwa ne zasu tonu, wanda baki isa
kici bulus ba"
Cikin tashin hankali Hajiya Halima tace "Au nikaɗai ma banda ku?"
Ramlah tace "Mummy koda mu koba mu, ai laifinki yafi namu yawa, duk abunda mukayi
kece kika samu a hanya, yanzu mafita ɗaya ce, kije ki samu su su Alhaji Harunan, ku
sake sasantawa dama kun saba faɗa ku shirya ai, kuje ku sasanta kunemi mafita, dan
wallahi Asirin ki ya tonu nasu ya tonu dan se mun faɗi komai "
" Kai Amma wannan yaro akwai shege me baƙin hali, kamar duk fafatukar nan ba danku
nakeyi ba? "
Amal tace " Mummy amma kin san halinsa, dama da kuɗin nan sun samu ban san yadda
za'ayi dashi ba, dan kema kanki kin san baze cisu ba"
Halima ta zauna kawai murza goshi take yi, saboda tashin hankali da damuwa.
Widad fafur taƙi Yusuf, zaman ɗakinma ta ƙiyi, ya dafa Abinci da safe amma taƙici,
ƙarshe ma ta koma ɗakin Gwaggo, ta hau gadon Gwaggo tayi kwanciyar ta, Yusuf ya
rasa ta ina ze fara yiwa Widad bayani, ta ina ze fara nuna mata yana mata son da
baze taɓa juya mata baya akan wani abu da takeso ba muddin be saɓawa ubangiji ba?
Yana da dalilinsa me ƙarfi ya zeyi tagane gaba ɗaya ta fututtuke taƙi saurarensa.
Gwaggo ta fuskanci kamar sun kuma samun saɓani tsakanin ta da Yusuf, amma bata son
taita mata shisshigi, dan haka ta ƙyaleta, dan gaba ɗaya walwalarta ta ragu, kusan
ko san magana ma ba tayi, ko kayi maganar ma bata san abunda kake faɗa ba tana
tunani.
Dan mamaki yakasa barin zuciyarta wai Yusuf ne yake gudun ta haihu dashi, ita iya
tunaninta babu wani dalili daze sa yayi hakan sedai son zuciyarsa kawai.
Da daddare ya dawo tana kallonsa, bata kulashi ba dan ko sallamarsa ƙin Amsawa
tayi, ta barmasa ɗakin gaba ɗaya ta koma tsakar gida inda aka baje tabarma ana
hira.
Haka ya fito kamar maraya, yayi alwala ya tafi salla, ya dawo shiru shiru taƙi
komawa ɗakin, har kusan ƙarfe goma na dare, ya fito yazo inda take dayake duk hirar
nan ma da ake yi, ita ba wani magana take ba, sedai in anyi abun dariya ta ɗanyi
murmushi, sam hankalinta baya kan hirar ta fitone kawai dan karma Yusuf yayi mata
magana.
Tana jikin bango, babu haske a inda take zaune, yazo ya zauna a kusa da ita yayi
ƙasa da muryarsa yace "My love, dan Allah kizo muje ɗaki mana, kin barni kamar
maraya kin dawo nan kin zauna, dan Allah kiyi haƙuri kizo mu koma mana, kina da
miji amma kizo zaman hira"
"Yoseef bana son sake jin kalamn nan naka na yaudara, wanda naji a bayama sun isa
Allah ya amfana, kaje da can ai ba tare muke hirar ba"
"bakaji bane in sake maimaitawa, kalaman yaudara da kake yaudara ta dasu na fara
amince maka zaka butulcemin mana"
"Yi haƙuri dan Allah karki ɗaga murya mana, zomu je ɗaki muyi magana"
Yusuf ya sake marairaicewa yace "nasan haushina kikeji, a ƙule kike dani amma
please and please am very sorry, kiyi haƙuri mu koma ɗaki"
Ƙarshe ma juya masa baya tayi, alamar idan ya gama ze iya tashi yayi gaba.
Abun duniya ya ishi Yusuf, haka ya tashi ya tafi ɗaki, jiki a sanyaye, ya dinga
tunanin dama tun farko data fara zancen cikin, ba haka ya ɓullo mata ba, gashi ta
birkice gaba ɗaya, tama ƙi saurararsa.
SE kusan sha ɗaya da rabi, dabar hirara nan ta watse, kowa ya tashi ya tafi
makwancinsa, Widad ma ɗakinsu ta nufa, sedai tana zuwa ta tarar da Yusuf a zaune be
kwanta ba.
Tazo ta tsallake shi ta shige abunta, tana ƙoƙarin canza kaya, Yusuf yace "Widad,
akwai buƙatar ko sau ɗaya ki bani dama, in kare kaina yana da kyau kiji ta bakina
kafin yanke hukunci"
"baka da ta cewa fa, ai labarin zuciya a tambayi fuska babu wani abu da zaka
gayamin, fuskarka ta bayyana abunda ke cikin zuciyar ka, dan haka ka ƙyaleni kawai,
bana san sake jin komai kawai ka rabu dani, kuma ɗane idan Allah ya bani kace ba
naka bans, ni ima so kuma bana buƙatar taimakonka a rainon ɗana, da can baka san
cikin ze shiga ba kake mu'amala dani, ko in an tashi bani ciki shawara za'ayi da
kai? "
" Nace dai kiyi haƙuri please, zan gayamiki dalilina dan Allah, amma kiyi haƙuri ki
dena wannan fushin"
"kaga idan ka takurani wallahi zan fita ina kwana a waje, ka ƙyaleni"
Ya dinga binta da kallo harta kwanta abunta taja bargo ta rufe kanta.
Amal ce zaune tayi tagumi jugum, kamar an musu mutuwa tace "Mummy, yanzu idan kinje
gurinsu Alhaji Haruna me zaki ce musu? Kuma ta ina za'a fara binciken inda ya
tafi?"
Hajiya Halima tace " sanin gaibu se Allah Amal, zanje dai inga yadda zamuyi dasu
ne kawai"
Ramlah tace "to yanzu idan aka ganshi Meza kiyi masa?"
Hajiya Halima tace "ubansa zanci da farko, sannan ince masa duk abunda aka
gayamasa ƙaryane"
"Mummy, Yaya Anwar fa isa almost 30 years, he is not kid, tayaya zaki gayamasa haka
ya yadda, idan kuma ba gaya masa akayi ba wani abu ya gani fa?"
"Waike Amal bakinki baya faɗar alheri se sharrine, to rufen baki tunda bazaki faɗi
abun alkhairi ba"
Ramlah tace "bahaka bane Mummy, yanzu idan kika je neman mafita gurinsu Alhaji
Haruna, kina ganin suna ganin Asirinsu ze tonu idan suka ganshi zasu ƙyaleshi
hakane? Karfa ki manta har yanzu babu wanda yake sa tabbas na Bala yana raye a
kurkuku, saboda sun tsoron Asirinsu ya tonu ana cewa sunsa an kashe shi, kuma sun
cigaba da aiki da Saleb, ba tare da yasan sun kashe ɗan uwansa ba, those people are
evil, they are very dangerous fa"
"Na shiga uku ni Halima, yanzu ya zanyi wallahi duk cikinku ina sonku, babu wanda
zan iya zuba ido inga ya cutu in haƙura, duk ni na haifeku ina ƙaunar ku"
Amal tace "mun sani Mummy, kiyi haƙuri ki kwantar da hankalinki a nemo mafita mana"
Isa megadi na zaune a bakin gate, riƙe da 'yar radionsa, yana ta fama ya kama
stationsa amma se wani ɓurari take saboda rashin batur, ya dire radion yana zage
zage da Tsinewa Hajiya Halima, ganin kuɗin batirin radio ma ya ga gareshi.
Jiya yi ana bugun gate ɗin da ƙarfi kamar za' a karya ƙofar, shi dai beji horn ɗin
mota ba, dan baka ya miƙe a fusace yana bala'i yana masife yana cewa "wani jakin me
wannan yake mana wannan bugun se kace gidan ubansa, kokuma wani ɗan fashi, mutum se
kace gidan uabansa, ko yaya kuka buga anaji, muma za'a buɗe amma komai se mutane
sun yi hauka, aikin banza iyayen maula kawai"
Haka ya ci gaba da surfa masifa, sannan ya buɗe gate ɗin, wani mutum ya gani a
tsaye, da wani koɗaɗɗen yadinsa shara shara, hularsa ma tayi baƙi ƙirin saboda
dauɗa wani zaburarre dashi kamar korarre, Isa ya ƙare masa kallo yace "mutane ba
dai Jaraba ba, baka san an sace me gidan ba, dama shine yake baku, wannan
mastiyaciyar me hannun jarirar ba'a ɓanɓararta jeka Allah ya baka haƙuri, an dema
sadaka a gidan nan"
Mutumin yace "ba Sadaka nazo nema ba, gurin Halima nazo"
"au gatsal kake faɗar sunantaa? Allah yasa ta jika, tukuna ma a danginta ban taɓa
ganin mutum kamarka yazo ba, daga ina ko kwatance akayi maka?"
"ba kwatance akayimin ba, kaje kace mata tayi baƙo, ita tasan waye"
Isa yace "shikenan, shigo daga ciki seka zauna akan benci, amma in turoka akayi a
baka aikima, babu guri dan muma ba biyanmu take ba, mace ce hannu kamar kuturwa,
tasan a bata amma bata san ta bayar ba"
Haka Isa ya cigaba da soki burutsunsa, yaje ya sanar da Hajiya Halima zuwan baƙon
nan, amma ƙarshe seda ya fito da baƙin ciki da dana sanin zuwa sanar da saƙon nan.
Har kusan awa guda bata fito ba, Muratalah ne yaji tausayinsa ya bashi ruwa, dan da
gani muyumin ya jigata kafin yazo, ita shaf tama manta da wani baƙo da akace tayi,
ta shiryo tsaf abunta zata fita, har an ɗakko mata mota, Nura yace "Hajiya baƙonki
fa"
A fusace ta juya zata yi masifa "wai wane jarababbem ne haka aka dameni dashi"
Tana waiwayawa ta zare ido ta dafe ƙirji tace "Na shiga uku, Shu'aibu!!!"
Abun duniya ya dami Yusuf, baccinma ya gagar ɗaukarsa, jin shiri yasa ya zata ko
Widad tayi bacci, kwana biyu kenan basu kwanta manne da juna ba, duk yaji babu
daɗi, a hankali ya lalaɓa yaje bayanta ya kwanta ya shiga bargon nata, ya rungumeta
a jikinsa.
"Malam meye hakane? Ka lallaɓone kazo ka samu abunda kake so in anjima nace Allah
ya bani ciki ka haɗe rai"?
Yusuf ya girgiza mata kai yace "Aa', ɗumin jikinki nake son ji, dan Allah kimin
afuwa Widad, ki saurareni please"
"Dan Allah nima ka ƙyaleni, wallahi bana son jin komai daga bakinka, lallaɓani
zakayi in yarda da kai, in anjima kuma ka juyan baga"
"babu juya baya tsakanina dakw Widad, ina son ki fahimceni ne kawai, bari in baki
labarin wani yaro"
Miƙewa take ƙoƙarin yi, tace "bana son ji, ka riƙe abunka"
"Dan Allah ki tsaya kiji, yana da mahimmanci sannan akwai darasin rayuwa a ciki"
Ganin bata da niyyar saurararsa yasa ya janyota jikinsa, ya rungumeta gam sosai
yana ajiyar zuciya, a hankali taji ɓacin ran nata na raguwa, dan haka ta kwanta
tayi shiru tana sauraren bugun zuciyarsa.
Yusuf ya nisa sannan yace "Labarin yaron nan zaki ji daɗinsa sosai, bari in
gayamiki abunda ya samu yaron.....
Mun kusa ƙarƙare part 2, idan part 2 kawai kika siya karki sake ayi 3 babu ke.
LITTAFIN KUƊI NE, DAN ALLAH KI SIYA KAFIN KI KARANTA BA DANNI BA DAN ALLAH, LITTAFI
NA ƊAYA KYAUTA NE WANNAN NA SIYARWA NE
NORMAL GROUP ₦300
VIP ₦500 NE KITURA TA WANNAN ACCOUNT ƊIN
0009450228
JA'IZ BANK
AISHA ADAM
SE A TURA SHEDAR BIYA TA WANNAN LAMBAR
07063065680
IDAN KUMA KIN SIYA AMANACE KARKI FITARMIN DAN ALLAH 🙏🙏🙏
11/15/21, 4:53 PM - Buhainat: LITTAFIN KUƊI NE, DAN ALLAH KI SIYA KAFIN KI KARANTA
BA DANNI BA DAN ALLAH, LITTAFI NA ƊAYA KYAUTA NE WANNAN NA SIYARWA NE
NORMAL GROUP ₦300
VIP ₦500 NE KITURA TA WANNAN ACCOUNT ƊIN
0009450228
JA'IZ BANK
AISHA ADAM
SE A TURA SHEDAR BIYA TA WANNAN LAMBAR
07063065680
IDAN KUMA KIN SIYA AMANACE KARKI FITARMIN DAN ALLAH 🙏🙏🙏
98_99
"Akwai wani Mutum me suna Bashir, shida matarsa me suna Jidda, wadda sukayi Auren
soyayya, kusan shekara uku babu haihuwa, kin san yanayin ƙasar Hausa, abun ya kan
zama abun damuwa koma gori ga matar da bata haihuwa.
Aka dinga ziga mutumin nan akan yaƙara Aure tunda bata haihuwa amma yaƙi, gashi
babban ɗan Sanda yana matuƙar son matar nan tasa, yana da rufin Asirinsa dai dai
gwargwado, matar nan tasa tana matuƙar kyautata masa shida 'yan uwansa dukda yadda
suka tsaneta suka sata gaba, suna ganin komai ya samu akanta yake ƙarewa, gata da
yawan larura Kasancewar tana da Athma, kuma genotype ɗinta AS ne, dan haka kusan
kullum cikin rashin lafiya take da zaryar Asibiti, shi kuma yana jin tausayinta
saboda mahaifiyarta bata raye, ga mahaifinta bashi da cikakkiyar lafiya shima.
Idan ciwonta ya tashi, shine yake ayyukan gidan, ko kuma yayi zaman jinyarta a gida
ko a Asibiti, duk wata kulawa daya dace ya bata yana bata, katsam Allah ya bata
ciki ba zato ba tsammani, ya dinga murna shida ita, sedai cikin beje ko ina ba ya
zube saboda yawan rashin lafiya.
Bashir mutum ne me tawakkali dan haka be taɓa gazawa ba, baya nuna mata ya ƙosa da
rashin lafiyar da take yawan yi, ya kance a tausayi irin na mata da son da matarsa
Jidda ke masa, idan shine yake a halin yawan larurar nan bazata guje shi ba, to shi
meze sa ya gujeta, bayan ba ita tayi wa kanta ba, Allah ne ya jarabceta.
Bashir Ya zama abun kwatance a dangi, mijin tace nusari da ire iren wannan miyagun
sunayen haka suke kiransa, wai ya ƙare a gindin mace seta talautashi tukuna ta
tsiyata shi, kullum cikin ciwo gashi bata da wata mamora tunda ba haihuwa take yi
ba, ya zamana saboda irin wannan cin mutunci da ake mata ko shiga tarurrukan biki
ko suna ko makamancin haka ya hanata, saboda muddin zasu haɗu da 'yan uwansa gorin
nan ne se anyi shi.
Idan suka fuskanci baya gari, haka zasuje har gida su zazzaga mata rashin mutunci
iri iri, su ɗauki abunda suka ga dama, suce ai kayan ɗan uwansune, banda tayi Asiri
ta mallake shi, ta yaya ze dinga bata abubuwa bayan juyace ba haihuwa take ba, se
aikin larura dasa ɗanuwansu zaryar Asibiti, duk ta tsiya tashi saboda yawan rashin
lafiyar da take yi, yayi da lafiyarsa yayi da aljihunsa, dan hatta jini idan ta
buƙata shike bata.
Ita kuma ba sawa ba fitarwa, haka zasuyi abunda suka ga dama idan sun tafi ta sha
kukanta, kamar yadda suka saba baya gari sukaje suka mata cin kashi yadda suke so,
ya dawo ya tarar da ita tasha kuka, ya tambaye ta meyasa meta? Tace masa ai
bakomai, seda taga ze ɗau zafi sannan ta gaya masa, shi yayi mamaki, be taɓa sanin
har gida suke biyota suyi mata ba, aikuwa yaje yayi musu tatas, kuma yace musu mutu
ka raba shi da matarsa, tana da matsayi me girman gaske a zuciyar sa, dan haka
komai tayi bata laifi a gurinsa, yace larura da lafiya duk na Allah ne, me lafiya
na ina komawa mara ita, mara ita ya samu, babu wanda yake sa kuɗinsa dan ya sai
cuta, sedai Allah yana jarrabar komai, dan haka ya yadda rashin haihuwar Jidda, da
rashin lafiyar ta jarabtace Allah ya jarrabesu dan ya gwada imaninsu.
Nan ma dangi suka kuma kwaroroto, suna yamaɗiɗi dashi, waiya fifita matarsa akan
danginsa, abun takaicin hadda maza ake wannan sakarcin, ba abunda yake ƙona masa
rai irin hadda ƙannensa da suke uwa ɗaya uba ɗaya suke ƙin abunda yake so, ya
tabattar a zuciyar tausayi da imani na mahaifiyarsu, da tana da rai duk bazata bari
ayi masa haka ba, shikam Bashir ya musu banza dasu da surutun da suke yi, yayi
kamar besan sunayi ba.
Daga baya ma ya koma, indai zeyi tafiya ta 'yan kwanaki wani garin harkar aiki, da
ita yake tafiya suje su dawo, dan karma wani daga danginsa su bita gida su ɗaga
mata hankali Wataran tafiya ta kama shi, yace ta shirya su tafi Tare, haka kuwa
akayi suka tafi tare, seda sukayi wata guda sannan suka shirya dawowa Kano, sedai
dare yafa yi musu a hanya, Bashir yace 'Jidda, dole idan muka shiga gari mu samu
Hotel mu kwana, kin san ƙasar nan ba security "
Jidda tace " dama abunda nake son in gaya maka kenan, dan a tsorace nake "
" to sarkin tsoro, karki damu muna samun guri zamu tsagaita da tafiyar "
Da yake daga kudu suke, wani dajin idan sukabi, sesu shafe tafiyar awa guda basu ga
ko giftawar me keke ba, balle abun hawa.
Daga nesa suka dinga hango hayaƙi, gaba ɗaya Jidda ta tsurw tace "Anya bazamu juya
ba? Nifa tsoro nakeji hayaƙin meye wancan?" '
"idan mun juya mu koma ina? Aiba inda zamu se naga meke faruwa a gurin"
Jidda ta cigaba da salati, dan tunda yasa kansa seya ƙarasa, saboda Bashir Jarumi
ne sosai, bashi da tsoro.
Suna suka ga wata motace tayi hatsari a gurin, sun daki bishiya motar ta kama da
wuta, ma'aurata ne a ciki sun kasa buɗe murfin motar su fita, se matar ta daki
glass ɗin motar da yayi saura be ƙarasa rugurgujewa ba, ya fashe, tana ta ihu Wuta
na cin jikinta tana Yusuf ɗana, ɗana Yusuf ta jefo jariri daga Widow, hannun ta duk
ya ƙone se salati take, da alama shi mijin nata dama tuni ya mutu.
Ta wurgo jaririm ta wannan tagar, sedai jikinsa lafiya ƙalau beji ciwo ba, amma
gefen wuyansa ya yanke, saboda glass ɗin motar daya fashe, yaron yasha hayaƙin
gobara, baya numfashi sosai ga jini na zuba a wuyansa, Jidda tai Wuf ta ɗauki
kyakkyawan jaririn a towel, se ƙamshim turare da ƙaurin hayaƙi yake yi, suna ji
suna gani haka Wuta ta ƙone motar da iyayen wannan jariri yake.
Jidda tai kuka tai kuka, tunda take bata taɓa ganin bala'i da tashin hankali irin
wannan ba, Bashir ya rarrasheta, suka shiga mota ya dinga tsala gudu, har suka fita
gari suka sami Asibiti suka shiga, kasancewarsa ɗan sanda id card kawai ya nuna
akayi admiting ɗin jaririn.
Bashir ya ɗakko waya daga aljihunsa, Jidda tace "wa zaka kira?"
Bashir yace "zanyi wayane, in gayawa abokan aikina incident ɗin ɗaya faru, azo a
san yadda za'ayi muyi mus handing ove jaririn mutafi gida"
Girgiza kai ta shigayi tace "dan Allah Yaya Bashir ina son yarom nan ka barmin
shi, karma ka gayawa 'yan sanda mun samu yaro, kabarmin ina so tunda ban taɓa
haihuwa ba"
"Yaya Bashir, komai nasu fa ya ƙone, ta ina za' a fara neman dangin nasa, dan Allah
ka barmin inajin ƙauna da tausayin Yaron nan a raina, dan Allah ka bsr maganar nan,
zan raini yaron nan in dai kamin izinin hakan, dan Allah"
Bashir yayi shiru, ganin yadda take kuka, bilhaƙƙi son ɗan nan take dagaske, yasa
yace "shikenan is ok, Allah ya tayaki riƙo maman Yusuf, Allah ya raya mana Yusuf
bisa tafarki madaidaici, ya bashi haƙuri da juriya irin na me sunan"
Nan ta dinga murna, ta rungume Bashir tana zuba masa godiya da Addu'a, ita da
Bashir sukaje yayo siyayyar kayan jarirai kala kala, da duk abunda zasu buƙata,
seda suka kwana uku a Asibitin daba'a garinsu ba, dan jaririn ya samu sauƙi.
Bashir kuma yayi waya, akaje aka kwashe gawarwakin nan a inda aka yi hatsarin.
A kwana ukun nan madara take haɗawa ta bashi, Jaririn sam bashi da rigima, harta
ɗan fara damuwa ko jikin nasa ne be gama warwarewa ba, daga baya kuma ta fuskanci
haka halinsa yake, bashi da rigima sam, bayan an sallamosu suka kamo hanyar gida,
amma tun a hanya ta fara tunanin me zata cewa dangin mijinta idan suka ganta da ɗa?
Bashir ya lura da yadda tayi shiru, yace "Maman Yusuf, ya kuma naga damuwa a
fuskarki?"
Ta ɗan yi ajiyar zuciya tace "Yaya Bashir, ina fargabar amsar da zamu bawa mutane,
idan suka ganni da jariri, mussman su Yaya Asma'u"
Bashir yace "ba dai kina son ɗanki ba?" ta jinjina masa kai alamar eh.
"to karka damu da abunda mutane zasu faɗa, kisa a ranki ba rainon kariri kawai
zakiyi ba, harda na ƙalubale ki manta da wani ƙalubake da abunda mutane zasu faɗa,
mu rungumi jaririnmu, Allah ne ya bamu"
Yace "meze hana, muda muke nema Allah ya bamu, ai ina son duk abunda kike so, ina
son Yusuf nima bari kiga mu koma gida, hakika zan kuma yanka masa, muyi shagalin
suna dan Jaririn naki befi watanni biyu ba, gashi me kyau masha Allah kamar ke"
Jidda tayi murmushi tace 'mijina ɗan Aljanna, Allah ya baka abunda kake nema
duniya da lahira "
Bayan la' asar suka isa gida, bayan sun yi salla sun huta, ta dafa ruwa ta yiwa
jaririnta wanka, ta canza masa kaya, ta goya abunta tana jin ƙaunarsa a ranta.
Bashir da kansa ya sai cingam, ya dinga aikawa mutane cewar za suyi taron sunan
jariri, mutane suka dinga mamaki dan su dai basu san tana da ciki ba.
Nan 'yan uwansa sukazo domin ganin ba' asi, aikuwa suka tarar da ita da Jariri.
Wani Yayansa ya sashi a gaba da tambayoyi, akan sun san matarsa ba haihuwa take ba,
ina suka samo ɗa Bashir yaƙi gayamusu, suka haɗashi da wani ƙanin babarsu, ya kira
shi ya tambayeshi,
Bashir yace "gidan marayu sukaje suka ɗakko yaro, jaririn iyayensa ne suka yi
hatsari suka mutu, kuma ba'a san daga inda suke ba, shine sukaje gidan suka karɓo
shi.
Nan ma 'yan uwa suka samu nayi, wai ya biyewa matarsa sunje gidan marayu sun ɗakko
shege, babu wani iyayen yaron sun mutu, duk yaran dake gidan shegune.
Jidda ta dinga kuka tana ɗanta ba shege bane, Bashir yaita rarrashinta, ya gayyaci
mutane akayi sunan Yusuf, akayi shagali sosai aka watse.
Jidda ta rungumi jaririmta da mijinta, sedai wani abun mamaki da iko na ubangiji,
tunda Allah yasa suka fara rainon ɗan nan, Jidda ta dena wannan rashin lafiyar da
take yawan yi, ta warke sarai ta dena kwanciyar Asibiti, idan ba an faɗa maka ba
bazaka ce tayi fama da jinya ba a baya, sosai suke rainon Yusuf, bazaka taɓa cewa
ba ɗansu bane, idan har kana son farincikin Jidda da Bashir to kaso ɗansu Yusuf.
Sedai fa dangin mijinta suka kuma sata a gaba, suka tsani yaron nan ƙarara suke
nuna masa ƙyama, suke ce masa shege, Sedai Jidda tayi kuka, ita dai tasan Yusuf ba
shege bane da iyayensa, amma haka take sharesu ta cigaba da kulawa da shi ita da
mijinta Bashir.
Jidda ta kauda kai daga duk wani ƙalubale da take fuskanta, akan rainon Yusuf ta
kowane ɓangare, Bashir yana iya ƙoƙrinsa akan Yusuf, daya isa shiga makaranta ya
sashi a makarantar kuɗi, wanda a wannan lokacin se 'ya' yan wane da wani ake kaiwa
private school, amma yasa shi a private school, yasa shi a makarantar islamiyya, ga
tahfeez sannan aka ɗaukar masa malamin lesson, idan Bashir na gari shike kai Yusuf
makaranta ya ɗakko shi, idan baya nan kuma Jidda ke kaishi, Yusuf ya taso cikin
gata da kulawa, yayin da gefe guda dangin babansa suka sake ɗora masa karan tsana
shida iyayensa, mussman Jidda waita asirce musu ɗan uwa tasa sun ɗakko shege yana
masa bauta, ya taɓe a gindinta dana wannan shegen yaron.
Babban abun mamakin be wuce yadda suma yana wahalta musu dai dai gwargwado yadda ze
iya amma basa gani.
Yusuf ya tashi da tarbiyya da ilimin addini dana zamani, gashi da matuƙar haƙuri,
da wuya kaga yayi fushi, be fiye shiga faɗace faɗacen yara ba, karatunsa ya fiye
masa komai.
A tsakanin maƙwabta ma ana samun hassada da ƙyashi, ganin kaf tsukinsu babu me
gatan Yusuf, komai ana masa sam bashi da wata damuwa, hakan yasa maƙwabta suma suka
fara jin haushinsa, abun wasa duk tsadarsa zakaga Yusuf dashi, shi kaɗai amma keken
hawa uku ne dashi na hawa, shekararsa takwas a duniya, amma har system yake da ita
saboda karatun Al'qur'ani da sauran litattafan addini dana zamani, dan haka
Ƙwaƙwalwar Yusuf na kawo wuta sosai.
Nanma maƙota suka fara jin haushinsa, saboda wannan gata da tarairaya a cewarsu
dama gashi shege kuma ana ƙara sangarta shi, Yusuf tunda ƙuruciyarsa yake jin
kalmar shegen nandm daga bakin mutane, besan ma'anar kalmar ba, amma yasan kalmace
me muni, da wasu lokutan maƙotan ko yaransu kan gaya masa, ko kuma dangin Abbansa,
Yusuf yana da matuƙar haƙuri da kawaici, ko wasa ya fito cikin yara idan yaga
za'ayi faɗa ko rigima, seya bar gurin ya koma gida, wasu lokutan har haushin
haƙurinsa Bashir ya kanji, yaita masa faɗa ya dena yadda yara suna masa rashin
mutunci yana ƙyalesu, se yace ai malaminsu yace "Allah yace yana son bayinsa masu
haƙuri"
Katsam ranar suka yi faɗa da wani yaron maƙwabcinsu, akan kayan wasan Yusuf ɗin,
yaron ya dinga zaginsa, uwar ɗan ta fito ta shigarwa Ɗanta, Yusuf ya juya ze koma
gida, yaron ya biyo shi ya dake shi, Jidda ta fito jin Hayaniya, Jidda tace "Maman
Salim bekamata ki dinga shiga faɗan yara ba, ɗa na kowane kamata yayi ki haɗasu ki
musu nasiha, in da kara ɗana da ɗanki ai duk naki ne, idan zaman tsakani da Allah
akeyi, Yusuf da Salim duk namune'
" Ke saurara karki ƙara haɗa ɗan sunna da shege, tsintacciyar mage wadda bata mage,
akan me? Kedai da kika ɗakkoshi kikaga zaki iya se kije kiyi, kekaɗai ne ɗanki amma
ni wannan yaron ba ɗana bane"
Nan da nan ran Jidda ya ɓaci, kawai ta durƙusa a gurin fashe da kuka, da yake ita
bata da baki sosai, Yusuf yazo ya rungumeta yai shiru yana sake juya kalmar shege a
ransa.
Salim ya ɗau dutse da nufin ya jefi Yusuf, amma ya samu Jidda a gadon baya, karo na
farko da Yusuf ya harziƙa, beyi wata wata ba yai sama da Salim ya sake shi a kwata.
Nan babar Yusuf ta gigice ta biyo Yusuf zata daka, dai dai lokacin motar Bashir ta
shigo layin, take yayi parking ya fito yace "ke lafiya zaki dakarmin ɗa? Ke kuma
Umman Yusuf meya sameki haka kike kuka?"
Aikuwa ba tayi nauyin baki ba ta gaya masa komai, nan ya fara sirfa bala'i, yace
"na lura mutanen nan bakwasan zaman lafiya, wallahi duk wanda ya kuma kiran ɗana da
shege sena ɗaure mutum, kai kuma Yusuf duk yaran da ya kuma gayamaka haka, ko ya
dakeka baka zanemin shi ba, ni zan zaneka da kaina, ba babarka zaka dinga shigarwa
faɗa ba, duk wanda yayi maka ka masa duka ka lallasan mon yaro, in yaso akawomin
ƙararaka zan bada haƙuri "
Tun daga nan Yara suka ɗan saurarawa Yusuf, saboda babansa mutum ne me raha da
barkwanci amma be iya fushi ba da tashin hankali, Yusuf ya cigaba da tasowa, tun be
gane kalmar da ake gaya masa ba harya gane ma'anarta, baze manta ranar wata Juma'a
ba, wadda itace ranar da ya gane mariƙansa basu suja haife shi ba, ya ɗauka ana
gayamasa shegene kawai dan a zageshi, amma ya gane basu suka haife shiba.
Ƙanwar Bashir, me suna Balaraba ta haihu, saboda gudun magana yasa Jidda ta shirya,
ta shirya ɗanta tsaf dasu, kai kace wata matar hamshaƙin attajirice, saboda Bashir
baya wasa gurin kula da gidansa, daga ci har sha da sutura, baya wasa gurin basu,
shiyasa kullum iyalinsa suke tsaf dasu.
Suka shirya tun safe Bashir ya tafi kaisu gidan suna, a ƙofar gidan yayi parking ya
kalli Jidda yace "kin san Allah, ba dan kin matsa ba da bazakuzo sunan nan ba, ke
kin damu Yusuf yasan 'yan uwana, saboda halin Rayuwa ni kuma nasan babu wani amfani
da hakan zeyi, dan haka idan kimga ba hali ki samu abun hawa kukoma gida, idan
kinga zasuyi muku cin mutunci ki kirani a waya ko ku koma gida kinji ko? "
Jidda ta jinjina kai, Bashir yace "ki kularmin da kanki da Yarona, ya kalli Yusuf
yace " My boy, zaka shiga cikin yara, bance ka saurarawa duk wanda ya taɓamin kai
ba kaji ko? "
Yusuf yayi murmushi ya sunkuyar da kai, Bashir ya sumbaci goshinsa, sannan suka
shiga gidan, suna shiga basu samu wata karɓar arziki ba, sema bimta da aka dingayi
da kallo a nayiwa zanin jikinta kuɗi, da kayan jikin Yusuf.
Suka dinga zage zagen su, suna faɗar baƙaƙen maganganu, Jidda ta tashi da nufin ta
taya su aiki, suka dinga caccakarta kamar zasu cinye ta ɗanya, suna mata gori suna
zaginta.
Ta tashi ta koma gefe, ta ɗau Yusuf ta ɗora akan cinyarta, tana share hawaye, Yusuf
ya kwanta a jikinta yayi lamo yana jin yadda take kuka, har kusan ƙarfe ɗaya ana ta
rabon Abinci, amma aka hanata ita da Yusuf, ga lokacin da shabiyu na rana tayi,
take bawa Yusuf abinci, se can wata mata daga maƙotan Balaraba ce ta kawo musu
Abinci, dambun shinkafa aka kawo musu, sedai Yusuf baya cin dambu, se Jidda ta aiki
wani yaro tace
"Dan Allah jeka gurin da ake rabon Abinci, kace a baka waina zan bawa yarone, in
basu baka ba kazo ka karɓi kuɗi ka siyomin wani abun in bashi"
Yaron yana zuwa yace a bashi waina, wata ta kalle shi tace "waye yace a baka"?
Ya nuno Umman Yusuf yace "gata can, ita ce tace a bata zata bawa yaronta, wai baya
cin dambu"
Asma'u tace "iyeee ina abun yake inji Mayya, saboda samun guri har wani zaɓen
Abinci yaron yake yi, lallai abunda mamaki samun guri, dama ɗan uwanmu ne ya haife
shi da sauƙi, amma kin sashi a gaba anje gidan marayu an ɗakko shege se wahala yake
akanku, ke gaki juya shi gashi shege ba dangin iya babu na baba an samu guri se
iskanci ake, kina ci kina ƙiba kina narka kashi, gefe shegen daba'a san asalinsa ba
ma yana cin nasa rabon, kin kanainaye mana ɗan uwa kin hanashi yayi mana komai "
Balaraba tace " wai lafiya kike wannan kwarmaton haka? "
" inafa lafiya, za'amin iyayi da feleƙe wai wannan shegen yaron sun samun an basu
Abinci, hadda turowa wai a canza masa bayacin dambu, saboda samun guri wai Abincin
ma seya zaɓa, dan ubanka da a gidan Marayun ka taso, naga uban da zakawa sanaben
baka cin kaza, kai kaza kake ci"
Jidda ta toshe baki ta fashe da kuka, a nan Yusuf ya fara fuskantar ashe ba Babansa
ne ya haifeshi ba, idan be manta ba a makarantar su sun taɓa zuwa gidan marayu,
akace musu wanda iyayensu suka yadda sune, kokuma wanda iyayen suka rasu, wato
kenan shima yadda shi akayi, ko iyayensa na asali sun mutu.
Jidda ta tashi, ta kama hannun Yusuf ta baro gidan nan, kafin ta fito ma shaddarta
milk ta sha aiki, suka watsa mata dagwalon kayan miya, haka suka tafi tana tafe a
hanya tana kuka,
Yusuf yace "Umman Yusuf kiyi haƙuri, kidena kuka Allah yana son masu haƙuri, haka
ya sayyadina yake gayamin"
Amma ta kasa dena kukan nan, ta rasa wani abu tayiwa dangin Bashir suka tsaneta
haka, banda hauka ina laifin Yusuf a wannan al'amarin? Me yayi musu? Shida yake
yaro ƙarami, take tayi wani tunani ita yanzu daba cikakkiyar lafiya ba, idan ta
mutu waye ze kular mata dashi, ita dai Allah ya jarrabeta da son Yaron nan, tasan
babu matar da zata kulamata da ɗanta tsakani da Allah haka.
"ɗan Babansa, meyafaru ne? You look somehow disturbed, meyafaru ne gayamin"
Yusuf yace "am ko Abba, ba abunda yake damuna, munje gurin suna amma ba'ani Babyn
na ɗauka ba"
Bashir yace "Subhanallah, to shikenan rabu dasu, da kaina zan kaika a baka ka ɗauka
tunda kana so"
Yusuf yace "to Abba nagode, nima Allah yasa Ummana ta haifi Baby, in dinga kular
mata da ita ina goya ta"
Bashir yace "Ameen ya Allah yarona, waini idan ka girma me kake son ka zama ne?"
"Wow that's good my Boy, Allah ya bani rai da lafiya inga burinka ya cika Yusufana,
kenan baza'abi sahun Abba ba a kare dukiya da rayukan al'umma ba?"
"Ina so Daddy, amma bana son in dinga cin hanci, ustaz ya cemin ba kyau"
Bashir yayi murmushi yace "babu aikin daba'a cin hanci Mu Son, nima na gashi
police bane, kaga ina irin wannan?"
"To ko duk 'yan sanda zasu lalace, amma kai ka tsaya kai da fata akan gaskiya idan
wasu basu yi nasara ba, wasu zasu samu sassauci a sanadin ka, dan haka' yan sanda
ba 'yan rashawa bane kaji Masoyina"
Jidda tace "Abba, ko kunya ba kaji kake cewa ɗan fari masoyinka ko? Allah yasa
tsofaffi su jika, kasha zazzaga"
Bashir yace "sedai suyi su gaji, amma ina son masoyin nan nawa, inajinsa a
zuciyata, idan na kalle shi ina samun farinciki da nutsuwa, nasan ko bayan raina
akwai amfanin da zewa al'umma, ɗan waliyin Allah me halin sufaye"
Jidda tace "ina ganin ikon Allah, kabari a faɗa mana kawai kasa shi a gaba kana ta
koɗashi, Taso muje in maka addu'a in kwantar da kai"
Bashir yace "ke yanzu me kike inba shagwaɓashi ba, baccin ma sekin kaishi,
ƙyalemin yarona ya gama jin ɗumina tukuna"
Yusuf yace "Abbana ɗan aljanna, ina sonka da kai da Umman Yusuf, Allah yasa ku a
Aljanna"
Suka cigaba da hirarsu cikin so da ƙaunar juna, can Yusuf yayi shiru yana tunani,
Bashir yace "ɗan waliyin Allah, me kake tunani ne? Kowani abun akayi maka da kuka
fita, gayamin ko waye inci ƙaniyarsa"
LITTAFIN KUƊI NE, DAN ALLAH KI SIYA KAFIN KI KARANTA BA DANNI BA DAN ALLAH, LITTAFI
NA ƊAYA KYAUTA NE WANNAN NA SIYARWA NE
NORMAL GROUP ₦300
VIP ₦500 NE KITURA TA WANNAN ACCOUNT ƊIN
0009450228
JA'IZ BANK
AISHA ADAM
SE A TURA SHEDAR BIYA TA WANNAN LAMBAR
07063065680
IDAN KUMA KIN SIYA AMANACE KARKI FITARMIN DAN ALLAH 🙏🙏🙏
(Albishir ga masoya, ma'abota bibiyar litattaafaina, dama ta samu zaku fara samun
litattaafaina na audio, akan YouTube channel ɗina me suna Cool Arewa TV
https://youtube.com/channel/UCD5vnvA5laU8ti4LLz2_QEg
Kuyi liking sannan ku danna subscribe, domin fara samun litattaafaina na audio,
nagode sosai da ƙaunar ku gareni"
11/15/21, 4:53 PM - Buhainat: LITTAFIN KUƊI NE, DAN ALLAH KI SIYA KAFIN KI KARANTA
BA DANNI BA DAN ALLAH, LITTAFI NA ƊAYA KYAUTA NE WANNAN NA SIYARWA NE
NORMAL GROUP ₦300
VIP ₦500 NE KITURA TA WANNAN ACCOUNT ƊIN
0009450228
JA'IZ BANK
AISHA ADAM
SE A TURA SHEDAR BIYA TA WANNAN LAMBAR
07063065680
IDAN KUMA KIN SIYA AMANACE KARKI FITARMIN DAN ALLAH 🙏🙏🙏
(Albishir ga masoya, ma'abota bibiyar litattaafaina, dama ta samu zaku fara samun
litattaafaina na audio, akan YouTube channel ɗina me suna Cool Arewa TV
https://youtube.com/channel/UCD5vnvA5laU8ti4LLz2_QEg
Kuyi liking sannan ku danna subscribe, domin fara samun litattaafaina na audio,
nagode sosai da ƙaunar ku gareni"
100_101
Tsit sukayi gaba ɗaya suka shiga kallon kallo ita da Bashir, Bashir yace
"Yusuf, waye yace maka a gidan marayu kake? Wani mara hankalin me ya faɗi haka?"
Yusuf yace "Yaya Asma'au naji tana faɗa, Mamansu Amira, kuma rannan dana tambaya
ance mana a makaranta wanda suke gidan marayu basu da iyaye, tsintarsu akayi an
jefar dasu"
Bashir a fusace yace "ƙarya take yi kaji ko, ba wani gidan marayu da aka ɗakkoka,
ƙarya take nina haifeka"
Jidda tace "Abba ya zakace masa ƙarya take, babba ce fa ba haka yakamata ka faɗa
ba, tunda yarone bekamata kace masa babba kamar wannan tana ƙaryaba, ka gaya masa
wani abun dai"
Bashir yace "idan bance ƙarya take ba me zance? Ko so kike a sawa ɗana wani tunani
na daban a zuciyarsa, nina haifi ɗana duk wadda ta kuma gayamaka haka kace Nine nan
babanka, in ba haka su gayamaka gidan marayun dana ɗakko ka, kuma duk wanda ya kuma
gayamaka haka kazo ka sameni ka gayamin, kaga yadda zan da mutum"
Ran Bashir ya ɓaci sosai ya dinga faɗa yana mita, dan ba ƙaramin jin haushi yayi
ba, abun yana damunsa yadda ake aibata masa yaro, yaron da yake jin sonsa a cikin
jikinsa
Bashir yace "Ke yanzu a gabanki ake gayawa ɗana haka, amma ba kice komai ba, kuma
ni baki gayamin ba balle in ɗau mataki, ɗana me haƙuri da hazaƙa amma a fara cusa
masa tunani da ƙuruciyarsa, bazan lamunta ba Wallahi tabbas duk wanda ya kuma
wannan gangancin zanyi maganinsa"
Ya tashi Fuuu ya ɗau Yusuf, ya kai shi ɗakinsa ya kwantar da shi, ya zauna yaita
masa addu'a yana shafa kansa me ɗauke da tarin suma me kyau, har bacci ya kwashi
Yusuf, dukda zuciyarsa na cike da zullumi da tunani iri a kan maganganun da mutane
ke gayamasa.
Haka Rayuwa ta cigaba da gudana, Yusuf yana cikin gata da jin daɗi dai dai ɗan
talaka me rufin Asiri, Yusuf akwai tsanani biyayya da haƙuri, gashi tun yana yaro
yana da ilimi sosai, gashi mahaddacin Al'qur'ani ne.
Bashir ɗan Sanda ne nagari, mutane sukance masa cinnaka ba ka san na gida ba, ko
suce masa murmushin talaka, saboda gaskiya da riƙon Amanarsa, komarli kuɗinka da
Arzikinka baze saurara maka ba idan baka da gaskiya, sannan umarni in dai na san
zuciya ne, ba daga sama ba koda gurin uban waye baze karɓi umarnin san zuciya ba,
aikinsa kawai yake bilhaƙƙi, ba son zuciya da cin Amanar ƙasa,shiyasa talakawa ke
masa addu'a suke ƙaunarsa.
Shekarar Yusuf tara a duniya, Babansa Bashir akayi masa kiran gaggawa yayi tafiya
Lagos a hanya 'yan fashi suka kashe shi, shi da uban gidansa.
Umman Yusuf da Yusuf sunji mutuwar nan, sun kaɗu dajin mutuwar nan, sunyi kuka,
sunyi kuka dan sunsan sunyi rashin babban bangon jingina, Bashir mutum ne nagari,
dukda ɗan takun saƙar dake tsakaninsa da maƙotansa akan Yusuf, amma sunji
mutuwarsa, mutum ne me barkwanci da raha, ga kyauta da girmama mutane, mafi akasari
in kaga anyi faɗa dashi to haƙƙin wani za'a take, shi be fiye daɗa akan kansa dan
an masa wani abuba, sedai in an taɓa Yusuf ko Jidda, ko an danne haƙƙin wani, dan
haka da talakawa masoyansa, da iyalansa da jama'ar unguwa sunji mutuwarsa sosai,
hatta su kansu rundunar tsaron sun san sunyi rashin ma'aikaci.
Bayan an gama zaman makoki maƙota suka farayi da Jidda, wai saga yadda zata yi, ta
miƙe ƙafa komai sedai miji yayi mata, hatta slifas na tsakar gida Bashir be yadda
ta siya ba shiyake siyan komai, yanzu tunda ya mutu a ga yadda zata yi, gata ga
yaron da ba'a san wace tayi cikin shege ta yar ba, sukaje suka ɗakko, yanzu ai taje
ta maida ɗan da suka ɗakko ai.
Jidda bata da matemaki se Allah, rayuwa ta fara musu zafi, saboda bata da hanyar
samun kuɗi, ta fara tunanin sana'ar da zata yi danta samu suci Abinci, kar ɗanta
yasha wahalar rayuwa.
Manyan 'yan sanda suka shiga yi mata romon baka, akan cewar zasu shiga su fita a
samu haƙƙinsa ya fita, duk da jajircewar Bashir da wahalar da yayiwa Ƙasa, babu
wanda ya kuma bi ta kan iyalansa, haka Umman Yusuf ta shiga faɗi tashin yadda zata
yi domin ganin basu tagayyara ba, amma abun mamakin, komai ta kasa na siyarwa se
maƙotanta suƙi siya, ko kuma su karɓe bashi su barta, sunaji suna gani haka ta cire
Yusuf daga makarantar kuɗi ta maida shi ta gwamnati, dama ya gama primary secondary
ze shiga, wasu lokutan har Abinci ma se tayi fama sannan suke iyaci, mutanen da
Bashir ya dinga tallafawa babu wanda ya kuma bi takansu, dama ba'a batun danginsa
tunda ba ƙaunarsu suke ba, haka Umman Yusuf ta samu Nanny a wata makaranta da ƙyar,
ta kaɗa ta raya su ɗauketa aiki, tana da diploma amma suka ƙi, waisu masu degree
suke ɗauka, sedai su bata Nanny, haka ta karɓi aikin Nanny take yi, tana zama ta
zubda hawaye idan ta tuna Bashir, wata wahalar duk bata santa ba se daga baya, dama
'yan uwanta duk kusan matane, kuma uba ɗaya suke ba uwa ɗaya ba, kuma mahaifim nasu
ya rasu, gashi dama suma duk fama suke da kansu, talakawa suke Aure, dama ita suke
raɓa su samu wani abun, shima suna yi suna mata hassadar tana auren me rufin Asiri,
tunda aka gama zaman makoki babu wanda ya sake ya waiwayarta.
A hakan ana wannan faman, amma Umman Yusuf bata yadda Yusuf ya fita da mummunar
kama ba, ko yayi mummunar cima ba, ta yadda ta zauna da yunwa, Yusuf yaci.
Ga aikin Nanny ɗin nan babu wata riba, se zunzurutun wahala, ga wulaƙanci daga
malamai, yaran da iyayen su dukda wannan ƙoƙarin da take yi ba'a gani.
Yusuf idan yaga tayi shiru se yace "Ummana kiyi haƙuri kinji, nima bana son wannan
aikin da kikeyi, nima zan duba sana'ar da zan iya in dinga temaka miki, ki bar
wannan aikin"
Umman Yusuf tace "A'a ban yadda ba, yarone kai ƙarami kamata yayi ka maida hankali
akan karatunka, idan kasan daɗin kuɗi bazaka maida hankali ba"
Fafur ta hana shi neman kuɗi, idan bashi da littafi yana son ya siya baze tambayeta
ba, sedai ɗan ashirin ɗin motar da take bashi, da kuɗin break ɗinsa haka ze tafiyar
ƙafa, dan ya rage ya siya, karya tambayeta yasan bata dashi, dubu goman da'ake bata
na aikin bata zuwa ko ina.
Watarana Ummansa ta tashi babu lafiya, kusan sati biyu ba taje makaranta ba, gashi
babu kuɗin magani, ko zuwa Asibiti tana ta fama da Asma, dan haka bata sani ba
Yusuf yaje gidan Yayan Bashir, Ɗanlami yaje ya gaya masa amma yayi masa kaca kaca
ya kore shi, yace baze taimaka musu ba, bayan zagi da cin mutunci da yayiwa Yusuf
da gorin aishi ba ɗan ɗanuwansu bane, tun daga nan Yusuf ya ƙuduri aniyar kome ze
samesu, baze ƙara neman taimako a gurin wani ba.
Haka Yusuf ya samu guri a hanya ya zauna yayi kuka, yayi kuka yai me isarsa sannan
ya koma gida haka ya zuba ido, Jidda tasha jiki ta rame tayi wani iri, tana ɗanji
sauƙi ta koma makaranta suka bata dubu huɗu, suka ce sun koreta, dukda sun san bata
da lafiya, haka suka koma gida suka tsuguna, Umman Yusuf ta rasa inda zata saka
ranta, ga larura ga babu ta musu katutu, kuɗin da aka bata dubu huɗun nan baze sai
musu ishashsen Abinci ba, balle ta sai magani, maƙota babu me taimakonta dako
ƙwayar hatsi, sedai in ta fito aita mata habaici ana yada mata magana.
Abunda bata taɓayi ba, ta shiga ɗibar zannunwanta tana siyarwa, dan a lokacin Yusuf
kansa bashi da lafiya, dauriya kawai yake yi, tun yana daurewa harta koma ta kwanta
babu lafiya, shima ya kwanta ba lafiya, dan komai se tayi masa saboda zafin ciwo.
Haka ta kwashi flasanta da Bashir ne mafi akasari yake sauya mata, ta kai kasuwa
akayi musu sayen wulaƙanci, ta karɓo kuɗin ta ɗau Yusuf zuwa Asibiti, suna zuwa aka
basu gado, Ulcer ta masa mummunan kamu, ga typhoid da malaria, ita bata ta kanta ta
lafiyar Yusuf take, Bill ɗinsu kusan dubu goma sha huɗu dukda Asibitin gwamnati ne,
haka ta zare ta biya, taje pharmacy ta karɓo magani zata koma ward, 'yan sanda suka
kawo wasu sunyi accident.
Yace "Ai na sanki, ai tare mukayi aiki da Bashir, baki ganeni ba? Isyaku ne fa,
amma yana ganki haka, baki da lafiya ne?"
Tace "A' a Ɗanmu ne ba lafiya, na kawo shi nan aka bamu gado, an kaantar dashi"
Mutumin yace "A'a, naga da kamar private Hospital kuke zuwa? Ya zaki kawo yaranku
nan gurin? Ke kanki kamar baki da lafiya fa"
Haɗe rai tayi, dan mutumin nan ya fara isarta tace "lafiyata ƙalau ni"
Yace "yi haƙuri, naga kamar kin fara hasala, amma ai naga kuɗinsa ya fito wata biyu
baya, amma ya zan ganku haka, kuma kuɗin nasa dayawa"
"Kina nufin baki sani ba? To 'yan uwansa da wasu' yan sanda sun haɗa kai sun karɓi
kuɗinsu, ai na zata an baku naku?"
Da gudu ta wuce ɗakin da Yusuf yake kwance, tana kuka yanzu kuɗin mijinta sun fito
amma sun karɓa sun cinye, tasan babu yadda za'ayi ko ficika su bata, ga tarin
wahala da suke ciki, amma ba imani suka hanata kowani kasone a ciki, haka taje ta
zaunatayi kuka kamar ba gobe.
Kwanansu takwas a Asibiti aka sallami Yusuf suka koma gida, ta ƙarasa jinyarsa a
gida ya koma makaranta, tayi tayi makarantar nan da take Nanny su maida ta bakin
aikinta amma suka ƙi, haka ta haƙura duk yadda ta kai ga danne zuciyarta, seda
tayiwa dangin mijinta Allah ya isa, akan haƙƙin mijinta da suka danne suka cinye
sukaɗai.
A ɓoye wani maƙocin su yaga yadda taketa wahala, yai mata hanya gurin wani ɗan
siyasa a temaka mata, amma mutumin nan ya nuna mata halin bunsurai, dan haka bata
kuma zuwa ba, itace wankau, itace aikatau na biki kona taro, Yusuf yana Sss1 aka
tafi da shi Quiz Abuja na akan harkar lissafi, aikuwa Yusuf yazo na ɗaya aka bashi
kyautar dubu ɗari biyar, malamansu suma suka cicciri nasu dana babu gaira ba
dalili, ƙarshe dubu ɗari biyu aka bashi.
Umma tayi murna da samun kuɗin nan, Yusuf yace "Umma duk an kwashe fiye da rabin
kuɗin, kinga da mun samu da yawa, dubu ɗari biyar fa aka bani"
Umma tace "Yusuf ina lefi, da ina muka samu wannan ɗinma? Ai Alhamdilillah mai dai
Allah yayi maka albarka, ya ƙara hasken makaranta ya jiƙan Abbanka'
Yusuf yace " Ameen Umma, ga kuɗin nan, wace sana'a kike ganin zamu fara ne? "
Umma tace " Yusuf ka maida hankali a karatunka, sannan kuɗin nan ka ɗau abunda zaka
ɗauka, semu yi tunanin abunyi"
"haba Umma, na girma fa ki bari in fara sana'a mana, kuma ni ba abunda zan ɗauka a
kuɗin nan, muyi tunanin abunyi"
"A'a Yusuf, dole ka sai sutura, zan shiga kasuwa in samo maka yaduka, da takalama,
dako ɗan agogone, ka fara zama saurayi, ina kallo kayanka duk sun mutu, ba yadda
zanyi ne kawai"
Yusuf yace "Umma karkice zaki kashemin kuɗi dayawa, ina sa ran zamu kuma zuwa wani
competition ɗin, kema ki sai wani abu a ciki, nace ko injin markaɗe zamu siya, se a
ajiye shi a ƙofar gida idan na dawo in dinga zama"
Aikuwa Umma ta yadda da shawarar Yusuf, suka ajiye kuɗi basu taɓa ba tukuna, suna
shirin siyan injin markaɗe.
Yusuf ya dawo daga makaranta sukaje kasuwa suja siyo inji, akazo aka saita komai
suka sai kayan Abinci da sauran buƙatu.
Da safe idan Yusuf ya tafi makaranta, Ummace take markaɗen a cikin gida, idan ya
dawo ya fito dashi waje yayi zuwa magariba, se maƙota suka fara surtu wai ana cika
musu kunne, bayan a ƙarshen kayanma akwai babbn gurin niƙa, da suke wuni guda niƙa,
amma suka zo sukace wai suna takura musu da ƙarar inji.
Duk shiru na Yusuf ya dinga faɗa, yace "wallahi babu wanda ya isa ya hanamu sana'a,
me kuke so muyi ƙasa zamu ci kome, yanzu da wani fitinannen na zama sekunfi kowa
tsinemin, ba irin wahalar da bamu shaba, kuma mun kafa sana'a kuce semun ɗauke baze
yuwuwa ba"
Maƙwabcinsu Na jikin gidansu yace "kai dalla har kana da bakin magana, banza
tsintacce wanda ba'asan asalinsa ba, karuwa tayi ciki ta haife ta yar, an tsintoka
an rufa maka Asiri, amma kazo kanawa mutane Iskanci a gari"
Maganar nan tayiwa Yusuf ciwo, yaji haushin maganar nan, yaji kamar ya soka masa
mashi a zuciyarsa, amma ya dake yace "idanma hakan akayi, inma ba hakan bane, ba a
kaina aka fara ba, kuma ba kaina za'a ƙare ba"
Umma dake cikin gida, tazo ta janye hannun Yusuf tana kuka suka koma cikin gida
tace "Yusuf mi haƙura da markaɗen nan kawai, bazan iya jure ana cimim zarafinka
ba, bazan iya ba"
Ya goge mata hawaye yace "Umma idan mun dena Meza muci, kidena damuwa ni baya
damuna, saboda nasan bani da wasu iyaye inba Ummana ba, da Abbana Allah ya jiƙansa,
ki rabu dasu kawai, komai lokacine wataran in ance suyi min ba zasuyi ba"
Haka yaita rarrashinta yana bata haƙuri, washegari ya tafi makaranta, bayan ya dawo
tun daga soro ya fara jiyo kukan ummansa tana "da ikon Allah se Allah yasakamin
abunda kukayi min, yadda kukayi nufin tozartani Allah yasakamin, wallahi ɗanlami da
kai da Ballo da 'yan uwanka bazan yafe muku zaluncin da kukamin ba, wallahi Allah
ya isa"
Yusuf ya shigavda sauri, yaje ya sameta a dirƙushe tana kuka, ga su Yaya ɗanlami da
wasu mutane.
Yusuf yace "Umman Yusuf, lafiya kuwa me suke mana a gida? Me kuma mukayi musu?"
Yaya Bello yace "kai dalla tafi can banza, meye naka a ciki wani wai me muke muku
a gida, inane gidan naku meye haɗakinka da Bashir,? Ɗan tsintuwane fa kawai amma ko
taku baka dashi a abunda ya bari, seka bazama neman karuwar da ta haifeka ta
yasarka ta nuna maka ubanka"
Cikin kuka Umma tace "Wallahi karka ƙara shegantamin ɗa, Yusuf ba karuwa ce ta
haife shi ba, ɗana ne, kuma ɗan sunnane duk Wanda ya kuma shegantashi ban yafe ba"
Yusuf bece komai ba, yaje ya durƙusa ya ɗago Umman dake kuka yace "Umma meyafaru
ne wai?"
"Yusuf kaga, bayan sunje sun karɓe haƙƙin Babanka sun cinye, babu wanda ya waiwaye
mu, sun saida gidan da muke ciki, an bamu notice, wai bazasu bamu gadon komai na
Bashir ba, Yusuf an mana adalci kenan? Yanzu sun kyauta kenan? Yusuf ynzu kana
ganin da Bashir ne a raye ze musu haka? "
Yusuf ya rumgumeta ganin yadda jikinta har rawa yake tana kuka, gata ba cikakkiyar
lafiya ba yace "Ummana kiyi haƙuri, ai Allah baya bacci ni idan bani da gadonsa
aike matarsa ce yakamata su baki"
"Yusuf gidan nanfa nawane nida kai, har rubutu Bashir yayi ya bari kafin ya rasu,
kuma Bello ya sani amma shine suka saida gidan, idan na tashi daga nan mu koma ina?
Me nake dashi idan na bar nan?"
Ɗanlami yace "koma gidan ubanwa zaki ki tafi, ai dama ba gidan ubanki baane, seki
koma gidan ƙasar da ubanki ya mutu ya bari, shi kuma ya koma gidan ajiye shegu da
kuka ɗakko shi"
"Haba Umman Yusuf, aishi Allah baya bacci, kuma Allah na kowane baya barin zalunci,
menene gida idan sunyi haka dansu wulaƙantamu Allah baze basu dama ba, ki kwantar
da hankalinki mun rasa Abba ma, kuma dangana mukayi mukai haƙuri, dan haka gida
ɗazune, in da rai da lafiya insha Allah sena gina miki gida na ban mamaki, gidan a
wanke hannu kafin a taɓa "
Yai maganar yana goge mata hawayen fuskarta, yana murmushi dukda Shima fuskarsa
sharkaf take da hawaye.
Murmushi tayi na ƙarfin hali tace " na dena Yusuf, na barwa Allah nasam baze
wulaƙantamu ba"
Saboda keta haddi da cin mutunci, tana zaune wai za'a wuce da masu siuen gida har
ɗakin baccinta a duba, Yusuf ya miƙe ya tare ƙofar yace "dul abunda zakumin zan
iya jurewa, amma wallahi duk garin nan babu mecin mutuncin uwata in ƙyaleshi, ɗakin
baccinta gurin sirrinta ne, dan haka babu me shiga, jibi in Allah ya kaimu zamu
tashi mu bar muku gidan, ba zamuyi shari'a daku ba, amma Allah ya biwa Ummana
haƙƙinta"
Bello yace "kaikuma kai a wa? Gayyar tsiya arna a idi? Kama je kayi shari'ar damu
mana, dalla gafara nan a duba ɗaki sirrin banza sirrin wofi"
"Wallahi taku ɗaya ka ƙara daga inda kake, kai yunƙurin shiga ɗakin nan idan na
ɗaga ka se nayi jifa da kai ta katangar nan wallahi"
Tabbas yadda ƙirar jikin Yusuf take, dukda ba wani girma yayi ba tsaf ze iya
aikatawa, haka suka haƙura suka tafi suka ƙyalesu.
Umman Yusuf ta cigaba tana cewa "Yusuf Allah yasaka mana, kana gani ana cewa an
kashe Abbanka, aka dawo da motarsa suka ɗauka suka siyar, banyi magana ba, kuɗinsa
suka fito suka wuce gaba suka karɓe suka cinye, se a bakin jama'a naji labarin
kuɗin sun fito, duk 'yan kadarorin daya bari sun siyar, kuma suna kallon wahalar da
nake yi, babu tausayi babu imani a tare da su, ya suke so muyi da ranmu Yusuf, sun
cutar damu"
Tai maganar cikin kuka da sheshsheƙa, Yusuf yace "Umma kidena kukan nan, zanje a
samo me siyan injin markaɗen nan, da ɗan cinikin da mukayi mu samu gida ko ƙaramine
mu kama"
Jinjina masa kai kawai tayi, tana share Hawaye, Yusuf yace "Umma wao ya akayi kika
san haƙƙin Abba ya fito sun cinye?"
Ta share hawayenta, ta gayamasa yadda suka yi da ɗan sandan nan, Yusuf yace "Umma
tunda ya gayamiki haka, kuma beyi ƙoƙarin taimakonmu ba to tabbas dashi aka ci
kuɗin nan, dan babu yadda za'ayi ba'aci kuɗi dashi ba yasan anyi, abunda nakeso
dake shine kiyi haƙuri, Allah baya bacci, ki bar batun kaisu ƙara, mu barwa Allah,
Insha Allah Ummana wataran zaki yi dariya zamuji daɗi, kidena kuka Umman Yusuf "
Yusuf kai inji kasuwa ya siyar, sedai babu wata daraja, saboda anga a Matse suke,
suka har haɗa suka bada rabin kuɗin gida, suka wani ƙaramin gida haya, suka koma
ciki suka zauna.
Yusuf ya kusa shiga aji shida ma sakandire, dan haka yasan dole za'a buƙaci kuɗi a
hannun su, kuma yasan Umman bata dashi, ga kuɗin hannunsu babu, ɗan Abincin da suka
koma gida dashi babu, ga babu jarin sana'a, kuma kuɗin haya rabi suka bayar .
Yazamana Yusuf ya fara tunanin mafita, ana idar da sallar Asuba, yake zuwa ya karɓi
hayar kura yayi ga ruwa, ya tattara abunda ya samu, ya dawo gida ya saimusu abun
karyawa, Umma ta matsa se taji inda ya samo kuɗi, yayi mata bayani aiko se kuka
tace "Allah ya jiƙan Bashir, da yana raye nasan babu yadda za'ayi ya bar abun
ƙaunarsa yayi wannan wahalar, Kayi haƙuri Yusuf nakasa baka kulawar data dace"
"Haba Ummana, aini na wuce lokacin da zaki nemo ki bani, sedai in nema in baki, dan
Allah kidena kukan nan, kidena wannan tunanin please"
Haka rayuwa ta cigaba da ja, Yusuf sana'a iri iri, yayi wannan yayi waccan komai
ƙasƙancinta kuwa, harya ɗan tarawa Ummansa jarin saida man ƙuli da manja a cikin
gida, a haka suka tara cikon kuɗin haya, suka biya suka ɗan samu sassauci gurin
samun Abincin da zasu ci.
Dayake da suka tashi ba nisa sukayi da unguwar tasu ba, dan haka wani lokacin idan
ya turo kurar ruwa, yakan haɗu da maƙotansu na da, se yaji suna "Ohh rayuwa juyi
juyi, wai yau ɗangata ke tura kurar ruwa, dama shiya dace dashi tunda dai ba'a
gatan aka haife shi ba"
Yusuf baya tankawa, shi dai babban burinsa asirinsu ya rufu shi da Ummansa.
Allah ya temake shi yaci qualifying, dan haka kuɗin Neco kawai ya biya, da na Jamb
dayake Asusu sukayi shida Umman, suke jefa abunda ya samu saboda hidimar karatunsa.
Yusuf ya zana jarrabawa gaba ɗaya, Waec, Neco, da kuma Jamb, dayake Allah maji
roƙon bawane, kuma kullum cikin yi masa addu'a Umma take, Se Allah yasa ya tsallake
gaba ɗaya jarabbawarsa, ya samj maki me kayu da ake nema, dan haka har admission ya
samu a jami'a, sedai fannin daya ɗauka na medicine, kuɗinsa ya kai kusan naira dubu
sittin ta wannan lokacin, wadda kuma kuɗi ce masu yawa a wannan zamanin, Nanfa
murnar Umma ta koma ciki, ina zata samu wannan kuɗin? Me take dashi wanda zata yi
ta cika burin ɗanta? Burin da dashi Abbansa ya rasu, Yusuf yayi karatu ya amfani
al'umma......
LITTAFIN KUƊI NE, DAN ALLAH KI SIYA KAFIN KI KARANTA BA DANNI BA DAN ALLAH, LITTAFI
NA ƊAYA KYAUTA NE WANNAN NA SIYARWA NE
NORMAL GROUP ₦300
VIP ₦500 NE KITURA TA WANNAN ACCOUNT ƊIN
0009450228
JA'IZ BANK
AISHA ADAM
SE A TURA SHEDAR BIYA TA WANNAN LAMBAR
07063065680
IDAN KUMA KIN SIYA AMANACE KARKI FITARMIN DAN ALLAH 🙏🙏🙏
(Albishir ga masoya, ma'abota bibiyar litattaafaina, dama ta samu zaku fara samun
litattaafaina na audio, akan YouTube channel ɗina me suna Cool Arewa TV
https://youtube.com/channel/UCD5vnvA5laU8ti4LLz2_QEg
Kuyi liking sannan ku danna subscribe, domin fara samun litattaafaina na audio,
nagode sosai da ƙaunar ku gareni"
11/15/21, 4:53 PM - Buhainat: LITTAFIN KUƊI NE, DAN ALLAH KI SIYA KAFIN KI KARANTA
BA DANNI BA DAN ALLAH, LITTAFI NA ƊAYA KYAUTA NE WANNAN NA SIYARWA NE
NORMAL GROUP ₦300
VIP ₦500 NE KITURA TA WANNAN ACCOUNT ƊIN
0009450228
JA'IZ BANK
AISHA ADAM
SE A TURA SHEDAR BIYA TA WANNAN LAMBAR
07063065680
IDAN KUMA KIN SIYA AMANACE KARKI FITARMIN DAN ALLAH 🙏🙏🙏
(Albishir ga masoya, ma'abota bibiyar litattaafaina, dama ta samu zaku fara samun
litattaafaina na audio, akan YouTube channel ɗina me suna Cool Arewa TV
https://youtube.com/channel/UCD5vnvA5laU8ti4LLz2_QEg
Kuyi liking sannan ku danna subscribe, domin fara samun litattaafaina na audio,
nagode sosai da ƙaunar ku gareni"
102_103
Abu ya zamana ga ƙoshi ga kwanan Yunwa, ga bikin zuwa babu zanin ɗaurawa, course me
wahalar samu gashi Allah yabawa Yusuf amma babu hanyar yinsa.
Yusuf kam ya fidda rao, dukda ƙaunar karatun da yake a ransa, amma babu yadda iya,
tunda yasan basu dashi.
Allah sarki, Jidda ta damu kanta, tasan ba lallai ya kuma samun wannan damar ba,
yana son karatun sosai, idan be samu ba tasan abun ze dameshi, amma baze nuna mata
ba, ta duƙufa addu'a, ta nayi tana rarrashin Yusuf akan idan karatun nan be samuba,
su barwa Allah, Allah ya kawo masu mafita.
Sam Yusuf baya nuna mata da ya damu lallai se yayi karatun, 'yan unguwa suma ganin
yadda suke fama da rayuwarsu, amma babu me tallafarsu se Allah.
katsam aka kira shi a waya akace gwamnati ta bashi scholarship, an fidda gwarazan
shekara na makarantun kimiyya da fasaha, kuma Sunan Yusuf ya fito ya samu.
Shi Yusuf jin abun ya dingayi kamar almara, banda iko na ubangiji wa zeyi wannan
hukuncin haka? Umma kamar ta zuba ruwa a ƙaaa ta sha dan farinciki, tayi murna ta
godewa Allah, babu zato babu tsammani dama tazo musu ba tare da wata wahala ba.
Akayi shirye shiryen komai ya fara karatu, sedai wannan karatun karatune me wahalar
gaske, ba karatun ne matsalar Yusuf ba sedai kuɗin transport, na handout
excursions, practicals, field trips, kullum cikikn kawo kawo ake, gashi baya samun
damar yin 'yan sana' oinsa saboda zaman makaranta.
Dama a unguwa babu ruwansa da kowa, ko abokai bashi da su saboda gudun gori da
wulaƙancin mutane, Amma dukda haka be tsira ba, aita surutu waiya fiue girman kai,
daba'a san wayeshi bane shine ze dinga jawa mutane aji, yana wani hura hanci, shi
dai shirune nasa, baya tofa komai baaa gaban sa.
Karatu abu fa ya fara gagara, da ƙyar Yusuf ke iya karatun nan, saboda babu, Yusuf
gashi ƙwaro na gaske saboda haddar Al'qur'ani babu karatun dake bashi wahala.
Shekararsa biyu yana karatun, akayi zaɓe aka canza gwamnati, ba tausayi ba ragayya
ga yaran talakawa gwamnati tace babu kuɗi, bazata iya cigaba da biyawa yaran da aka
bawa scholarship kuɗin makaranta ba, wanda yake da hali ya ɗau nauyin kansa.
Yusuf yanaji yana gani ya ajiye karatun medicine ya dawo gida ya zauna, Umma seda
tayi kuka, shiko Yusuf akwai dakiya yaita bata haƙuri yace "Umma da bamu san zan
fara karatun bama, Allah ya bani dama, yanzu kuma ya ƙwace damarsa, mu ɗauka a
ranmu Allah yayi mana wani tanadine wanda yafi wannan karki damu Ummana"
Ita babbr damuwarta kar karatun ya fita daga ransa, yazo ko an samu damar ya ƙiyi
takasa cika masa burinsa.
Nanma 'yan unguwa suka ɗau surutu, dan Ya dena zuwa makaranta, baƙaƙen maganganu
habaici da zunɗe haka yake ganinsu kala kala, Yusuf ya kan rufe kansa a ɗaki da
daddare yayi kuka, yayi kuka har ya gaji ya bawa kansa haƙuri, tun tasowarsa yake
fuskantar ƙubalen cin zarafin wai shi bashi da iyaye, a gidan marasa iyaye aka
tsinto shi,har yanzu yi ake ba'a fasa ba.
Yusuf ya dawo zaman gida, ya shiga neman yadda zasuyi su rufawa kansu asiri shida
Ummansa, a haka wani mutum anan maƙotansu, dan sun ɗanfi wanda suka baro mutunci,
ya samowa Yusuf Form na polytechnic, Yusuf yaji daɗi Sosai dan shi yanzu duk abunda
yazo masa a rayuwa karɓarsa yake, bashi da wani zaɓi wanda ya wuce hakan, ya sake
jamb ya cike Civil engineering a nan polytechnic, aikuwa ya samu ya fara zuwa,
cikin ikon Allah sana'ar Ummansa ta mai ta kafu ta karɓu, ana siya sosai, ta nemawa
Yusuf gurin koyon sana'a a gurin masu furniture, shima seda ta biya kusan dubu
hamsin sannan aka karɓeshi.
Kullum idan ya dawo daga makaranta, se yaje gurin koyon aiki, idan ya tashi ya
shiga kasuwa yaga meze samu yayi, saboda baya san ɗorawa Ummansa wahala, sam Yusuf
bashi da hutu, a haka ya kammala poly, Umma tace baze tsaya ba, ya nemi Form na D.
E ya tafi, shi gaba ɗaya jikinsa ya fara sanyi da harkar karatun nan, ta bashi kuɗi
yaje ya karɓo form yayi applying, aikuwa by luck ya samu suka bashi level 2 a
university, haka nan yau akwai gobe babu haka rayuwa ta dinga tafiya, a wahalce da
ƙyar Yusuf ya kammala karatun nan, aka zo maganar tafiya service, Umma taji bazata
iya jure Yusuf ya bar gari ya batta ba.
Haka akayi cuku cuku, Yusuf yayi service ɗinsa a kano, bayan an kammala yazo babu
aikin yi, sedai kame kame, ga inda yake koyar aikin kafintan Wasu yarabawa ne, masu
muguntar tsiya, ganin yana da saurin ganewa yasa suke masa mugunta, gurin koyarwar.
Zaman haka ba aiki ba sana'a ya ishi Yusuf, sedai 'yan bige bige, amma a hakan idan
Ummansa taji tana da kuɗi a jikinta, haka take siya masa kaya masu tsada na sawa,
shiyasa bazaka ce suna fama da rayuwa ba.
Rannan yana zaune yana duba wayarsa, yaga wani posting, mutane nata tofa albarkacin
bakinsu akan harkar tsaro, sedai babban abunda ya bashi mamaki, be wuce yadda mafi
yawa sharhin da akayi, ƙorafine akan jami'an tsaro, seya tuna hirar da suka taɓa yi
da Abbansa kafin ya rasu, ya tuna yadda akayi aka haɗa kai aka cinye haƙƙin
ummansa, tabbas kamar yadda Abbansa ya faɗa, koda mutum ɗayane yake nagari a cikin
'yan sanda, ko yaya wani ze amfanu dashi, dan haka se yaji yana sh' awar yayi
applying shima.
"Kamar yaya Yusuf? Bana son rasaka kamar yadda na rasa Abbanka, dan Allah kabar
maganar nan"
"Umma, idan baki amince ba shikenan, amma Umma bakya tunanin da akwai wani
tsayayyen ɗan sanda me gaskiya a gurin da an tsaya mana gurin karɓo haƙƙinki, Umma
kin san mutane nawane ke shiga garari sakamakon rashin aiki yadda yakamata da wasu
maciya amana sukeyi a ƙasar nan? Umma in dai zamu dinga ƙyamar aikin mu dingawa
'yan sanda kuɗin goro to tabbas za' aita cutar mutane, duk abu ba'a rasa na Allah,
sedai idan suka yi ƙaranci zalunci ne yake yawaita, Umma idan kika bibiya akwai
mata irin irinki wanda aka zalunta, kuma za'a cigaba da yi idan har ba'a ɗau mataki
me kyau ba, ina son yin aikin ɗan sanda ne saboda in temaki al'umma, ima son zama
ɗan sanda dan in ɗora daga inda mahaifina ya tsaya, dan Allah Umma ki amince, amma
in bakya so na haƙura "
Jikinta ne yayi sanyi, ta ɗanyi shiru taga tabbas maganganun Yusuf haka suke, kuma
tana da yaƙinin cewa Yusuf mutum ne nagari, abune mawuyaci a haɗa kai dashi a cuci
wani.
Ta numfasa sannan tace " Shikenan Yusuf, na amince ubangiji Allah yayi maka jagora,
ya goyi bayanka ya kareka a duk inda kake, Allah ya wuce maka gaba a al'amuranka,
ina fatan zaka zama mutum nagari me gaskiya da riƙon Amana, Allah yasa a sanadiyar
ƙudirinka ya zamana an share hawayen wanda aka zalunta, kayi gaskiya da adalci
Yusuf "
Yusuf yayi murmushin jin daɗi da farinciki, yace " Insha Allah Ummana, in Allah ya
yadda ba zanyi wani abu wanda ya saɓawa Alƙawarin da mukayi dake ba, Addu'ar ki
nake buƙata, Allah ya kauda zuciyata daga aikata duk wani abu da ze saɓawa Allah "
Umma tace "Addu'a ai kullum cikinta nake Yusuf, ina fatan Allah ya tsare, amma bana
son ka sha wahala, training ɗin nan nasufa da wuya, karka je su baka wanda bazaka
iya ba, Abbanka yana bani labarin wahalar abun nan"
"Haba Umma, sekace wani ragon maza, kin ganina santalelen ƙato dani, se in goya
maza goma in gudu dasu a bayan nan nawa"
Umma tai dariya tace "eh lallai, ba shakka naga alama kam"
Nanma Allah ya temake shi ya samu makarantar horar da 'yan sanda, Yusuf yasha
wahala ya fuskanci ƙalubale daban daban, a haka harya kammala makarantar nan,
sukayi passing out, Allah ya temake shi ya fita da babban rank, sakamakon yayi
karatu yana da degree.
Yusuf ya kama aiki, sedai Umma kullum cikin nasiha take, na akan yaji tsoron Allah
akan wannan aiki daya fara, cikin ikon Allah yana fara samun salary yazo ya zubewa
Umma kuɗin yace "Umman Yusuf, Insha Allah inaji a jikina lokacin da zamu samu
sassauci yazo, ga wahalarmu ta wannan watan, na karɓo salary"
Umma tace "Alhamdilillah, dama komai yayi farko zeyi ƙarshe ai, Allah yayi albarka
amma ka ɗau kuɗinka, ni duk abunda ka sanmun karɓa zanyi ince Allah yayi albarka"
"Haba Umman Yusuf, wannan nakine halak malak, na bar miki, ba abunda zanyi dasu ni
duk abunda kika sanmun a ciki shikenan nagode, ki fara more wahalar da muka sha
Umma"
Kawai seta fashe da kuka, Yusuf ya rikice gaba ɗaya yace "subhanallah, Umma laifi
nayi mikine? Yi haƙuri dan Allah, ban san zan ɓata miki rai ba"
Ta girgiza kai cikin kuka tace "Tun kana ƙarami Yusuf, naso inyi duk me yuwuwa dan
ganin baka gane bamu muka haifeka ba, amma hakan ya gagara, duk yadda muka kai ga
ɓoyewa nida Abbanka abu ya gagara, bakin mutane yakasa yin shiru, suka dinga
wulaƙantamin kai da maganganu marasa daɗin gaske masu muni, har seda suka saka
kasan bani na haifeka ba, amma haka kake min biyayya kamarni na haifeka, A baya
nayi kukan Gorin rashin haihuwa, an goran tamin nayi kuka nayi kuka, amma tunda
Allah ya bani kai, na dena wannan kukan, nasan ba lallai ɗan dana haifa yayi min
biyayyar da kake mun ba Yusuf " ta ƙarasa maganar cikin kuka, Yusuf yaji ta fama
masa ciwon dake raɗaɗi a cikin zuciyar sa, yaji kamar ya fashe da kuka, sedai be
taɓa gangancin zubda hawayen rashin sanin suwaye iyayensa a gaban Jidda ba, dan
idan yayi haka ya zama butulu abun Allah wadai, ya tattara nutsuwarsa ya dake, ya
riƙe hannunta yace "wayema yace ba Yusuf ba ɗan Ummansa bane, samun uwa kamar
Umman Yusuf me sadaukarwa da juriya a wannan lokacin se anyi tonawar gaske, Wa
Yusuf zeso in be so Ummansa ba, waze wa Biyayya idan bebi Ummansa ba, Ummana ina
neman Aljannata, duk me neman Aljannarsa Annabi salallahu alaihi wassalam yace yabi
Allah da ma'aiki sannan yabi uwa, shiyasa nake bin tawa mahaifiyar domin neman
albarka da samun wannan Aljannah, shiyasa nake bin Ummana nasan babi da abun
biyanta ladan shayarwarta da ɗawainiyarta, Allah ya haɗamu a Aljanna gaba ɗaya,
amma wannan kuɗin na Umman Yusuf ne halak malak, da Yusuf da abunda Yusuf ya
mallaka duk na Ummane"
Ta rungume Yusuf ta fashe da kuka, a hankali Yusuf ya lumshe ido yana zubar da nasa
hawayen ƙasa ƙasa, dan karta ji yana kuka, ta goge hawayenta tace "Yusuf indai
nice, nagode sosai Allah yayi Albarka, amma ka ɗauki kuɗinka, kaje kayi buƙatunka
gabanka, sedai ka ɗan sai mana Abinci"
Yusuf yace "Umma, nifa kuɗin nan bazan ciba, ki sanmun na mota zuwa gurin aiki
kawai"
Yusuf yace "ni na isa inyi Jayayya dake, tunda kin rasa abunyi dasu bari in baki
shawarar yadda za'a kashe, ki rabasu biyu, rabi ki ban abunda zakimin, ki riƙe
sauran, rabin idan mun samu kuɗi mudinga ƙarawa a kai, mu nemi fili a wata unguwar,
mu fara gini, gara mu koma gidan kanmu "
Umma tace " na daɗe ina wannan tunanin Yusuf, yana da kyau ko fili mu siya, sedai
bazan karɓe maka kuɗi duka ba, nasan kana da buƙatu kaima "
"Umma ni zan baki abu kiƙi karɓa ko? Allah ya jiƙan masoyina, nasan da shine baze
min haka ba"
Umma tace "shikenan, naji Allah yayi albarka, Allah ya kareka daga sharrin maƙiya"
Shigar Yusuf aikin ɗan sanda na farin kaya, nan da nan sunansa aka fara saninsa,
musamman jin laƙabin sunan mahaifinsa, Yusuf Bashir Maitama, Yusuf akwai ƙwazo akan
harkar aiki, baya wasa ba ruwansa da cin hanci ko rashawa shidai aikinsa kawai.
Bayan ya fara aikine ya gano irin cakwakiya da maguɗin dake cikin aikin, da irin
tuggu da maƙrƙashiya dake aikin, ga me laifi ƙiri ƙiri kana gani amma saboda yana
da wane ko yasan wane, se ace a ƙyaleshi, amma idan aka kamo ɗan malam wane ƙarshe
'yan sanda suna iya ajalinsa, ko ka samu case ka fara aiki a kai, daga sama se a
turaka wani gurin a karɓe aikin, ko a ƙirƙiri laifi a ɗorawa wani dan a samu wani
abu a hannun sa, da ire iren wannan ha' incin, A haka Yusuf yai tunanin yadda
rasuwar mahaifinsa ta kasance, a nan ya gane tabbas set up ne mutuwar mahaifinsa da
ubangidansa, sedai bashi da evidence dan in be manta ba, suna kan wani case ne, aka
kira shi shida ubangidansa can Lagos, daga tafiyarsu se gawarsu, Yusuf baya son
ɗagawa ummansa hankali dan haka be gayamata bata ba, ya bar zancen.
Yusuf ya dage da aikin ginin gidansu, dukda muguntar da'ake masa a gurin koyon
aiki, a haka ya iya aikin kafinta, ya kama shago ya zuba yara suke masa aikin yana
biyansu.
Duk yadda aka so asa Yusuf a harkar cin hanci amma yaƙi, aka dinga cewa shima
tsinannen kafiya da taurin kaine dashi kamar ubansa marigayi, ko talauci ze
kasheshi baya karɓar kuɗin rashawa.
Yusuf ya kammal ginin gidansu, da kansa yayi furnitures ya zuba a gidan, kamar
gidan wata amarya, gidan yayi kyau hatta kayan sawa seda ya canzawa ummansa kafin
su koma gida, ya zuba kayan Abinci rana ɗaya yaje ya ɗakkota ya kawo ta gidan nan,
umma sarkin kuka seda tayi kukan nata data saba, yaita rarrashinta, suka kwaso
sauran kayan buƙatunsu suka dawo sabon gida, Yusuf ya sai Babur lifan me kyau.
Alhamdilillah rayuwa ta fara yi musu sauƙi, Daidai gwargwado suna hutawa, ga salary
ɗinsa ga gurin furnitures, ya hana Umma sana'ar komai, data motsa se yace "Umman
Yusuf me kike so, Ummana me za'ayi miki?"
Sam bata da damuwar komai, dama gata ba wani girma tayi ba dan lokacin da Suka
tsinci Yusuf ba tafi sha bakwai ba, dan da ƙuruciyarta sosai akayi mata Aure, bayan
mutuwar Bashir wasu sun nuna suna sha'awar Auren ta, amma taƙi Aure saboda rayuwar
Yusuf, tasan ba lallai a riƙe mata ba.
Babban abunda yake damun Umma da Yusuf shine ko abokan kirki bashi dasu, gashi
kamar mace wani lokacin kullum yana naniƙe da ita, da girmansa da komai amma idan
zata unguwa, seya bita, ya jirata a waje itakuma ta shiga, ko zata wuni yana gurin
a zaune, idan kasuwa ce haka zasu tafi tare, haka idan Asibiti ne, idan ya dawo
daga makaranta, idan ba masallaci ba baze je waje ya ɗanyi hira da abokai ba, tayi
faɗan harta gaji amma yaƙi denawa, abun da Ummansa bata gane ba shine, shi hana
gudun magana ne, ko ace anyi rigima yana gurin ko kuma wani abu ya haɗashi da wani
ayi masa gori.
Yanzu gashi ya kammala karatu, ga aikin yi gashi ya zama cikakken namiji amma ko
budurwa bata taɓa jin Yusuf yayi ba, to mutumin da bashi da abokai mazama balle
wata budurwa, ko a gurin aiki abokinsa ɗaya da yake biyo shi gida shine Abbas,
banda wannan Yusuf bashi da wasu Abokai.
Rannan yayi musu Abincin dare, ya zubi suna ci Umma tace "Wai nikam Yusuf, kai ko
budurwa baka da ita ne, sa'aninka sun fara Aure, amma kai ko zancen budurwa baka
yi, ko dai nice ake ɓoyewa"
Ya ɗan tura baki yace "Umma ni me zanyi da wata budurwa kuma, ni bani da wata
budurwa"
"Saboda me baka da budurwa? Se kace ba namiji ba, haka zancigaba da zama da kai
gunsumeme ba Aure, sedai duk inda zani kana biye dani? Ai lokaci yayi da zaka nemi
iyali kaima"
"Iyeee, kai kodai baka da lafiya ne? Idan bahaka ba, amma kace baka so in ƙyaleka,
idan baka da lafiya ne ka gayamin in san abunyi, amma ta yaya za ka ce baka son
Aure?"
Ya gane inda Umman ta dosa amma yace "Umma wane irin rashin lafiya, niba zazzaɓi
ba ba wani ciwo ba, kina ganina rasam danu, kawai ni matan ne se a hankali, bana
son wadda zata zo ta damemu"
"Ai ina maka addu'a, kuma nasan Allah ya amsa, Insha Allah mace tagari zaka samo
mana, amma dai gaskiya anemomin sirika, ko kuma ni in nemo"
Yusuf ya miƙe tsam yace "Hajiya Umma kenan, me abun mamaki Allah ya ƙaro mana
Arziki in biyamiki Makka, ni nayi nan seda safe"
"Au zancen ne baka so shine ka gudu ko? Zakazo ka sameni kuwa dan ƙaniyar ka,
jikoki nake son gani, na ƙagu ka ƙara gaba yara nake son gani "
Yusuf yayi waje yana dariya yace "Hajiya Umma, tawa ta kaina.
Wataran ya dawo a babur ɗinsa, ze wuce gida yaji ance " Sannu da zuwa "
Ya waiga yaga wata matashiyar budurwa ce, shi dai yasan yana ganinta a nan
unguwarsu, amma besan daga inda take ba, kuma ba abunda yake haɗashi da ita, dan
haka be kawo dashi take ba yai gaba abunsa.
Aikuwa yaji haushin ƙin kulatan da yayi, haka ta wuce ta tafi nata Aiken.
Da safe ya fito ze sai bredi, suka kuma haɗuwa da ita, tace masa ina kwana, ya
waiga ya kuma kallonta tace "nace ina kwana"
Ya zamana kusan kullum in dai ze fita kokuma ya dawo seya ganta, kuma seta kula
shi, shi harta fara bashi haushi ma.
Wataran Asmar Umma ta tashi ga zazzafan zazzabi, Yusuf ya kaita Asibiti aka rubuto
mata ruwa da allurai, aka sama ta wasu a can ya taho da sauran gida.
Da daddare za'ayi mata allura, yaje chemist ɗin bakin titi, yaje ya gayawa me
chemist ɗin ko zezo yayi mata allurar a gida seya biya shi
Me chemist yace "karka damu, kaje zan turo ƙanwata tayi mata"
Yusuf ya koma gida yana jira, yai girki ya tattara kwanukan yana wankewa, tayi
sallama, ya miƙe kalleta aikuwa ya haɗe rai yace "ke lafiya?"
Taya fari da ido tace "ba gurinka nazo ba kake wani haɗemin rai, ina mara lafiyar
tamu?"
Yusuf ya harareta yace "wace mara lafiyar? Malama ƙara gaba ba nan bane"
"Kamar yaya, Yaya Sani ya cemin inzo zan mata allura fa"
Yusuf a ransa yace "ji wani iyayi, wai Ummanta ummana dai ni kaɗai"
Yai mata jagora gurin Ummansa, Yadda ta dinga lallaɓa Umman ne, yaji daɗi Sosai,
bayan ta gama yace 'nawa ne? "
Ta Harare shi tace "in mutum yayiwa mamansa abu seya biya? Ummana Allah ya ƙara
sauƙi"
Umma tayi murmushi tace "nagode sosai' yata, Allah yasaka da alkhairi"
Yusuf ya tsaya sororo yana kallonta tace "kaje ka cigaba da wanke wankenka mana,
Umma seda Safe Allah ya ƙara sauƙi, likita ya rubuta a samiki ruwa, safe da yamma
na kwana biyu, zanzo in samiki insha Allah"
Umma tace "to shikenan nagode Allah yayi albarka, amma baki gayamasa nawane kuɗin
ba ya biya"
Yarinyar tace "Abunda ze biya shine, yaje ya ƙarasa wanke wankensa, yai miki shara
ya siyo miki duk abunda kike so kici, kiji ƙwarin jikin ki"
Umma tace "to shikenan kana dai ji ko?"
Yusuf kawai ya sosa kai, Yarinyar tace "dan Allah ka fitar dani bakin hanyar nan
taku, lungunku da duhu ina jin tsoro"
Ya kalli Umma ya kalli yarinyar, ta kashe masa ido ɗaya tayi gaba.....
LITTAFIN KUƊI NE, DAN ALLAH KI SIYA KAFIN KI KARANTA BA DANNI BA DAN ALLAH, LITTAFI
NA ƊAYA KYAUTA NE WANNAN NA SIYARWA NE
NORMAL GROUP ₦300
VIP ₦500 NE KITURA TA WANNAN ACCOUNT ƊIN
0009450228
JA'IZ BANK
AISHA ADAM
SE A TURA SHEDAR BIYA TA WANNAN LAMBAR
07063065680
IDAN KUMA KIN SIYA AMANACE KARKI FITARMIN DAN ALLAH 🙏🙏🙏
(Albishir ga masoya, ma'abota bibiyar litattaafaina, dama ta samu zaku fara samun
litattaafaina na audio, akan YouTube channel ɗina me suna Cool Arewa TV
https://youtube.com/channel/UCD5vnvA5laU8ti4LLz2_QEg
Kuyi liking sannan ku danna subscribe, domin fara samun litattaafaina na audio,
nagode sosai da ƙaunar ku gareni"
11/15/21, 4:53 PM - Buhainat: LITTAFIN KUƊI NE, DAN ALLAH KI SIYA KAFIN KI KARANTA
BA DANNI BA DAN ALLAH, LITTAFI NA ƊAYA KYAUTA NE WANNAN NA SIYARWA NE
NORMAL GROUP ₦300
VIP ₦500 NE KITURA TA WANNAN ACCOUNT ƊIN
0009450228
JA'IZ BANK
AISHA ADAM
SE A TURA SHEDAR BIYA TA WANNAN LAMBAR
07063065680
IDAN KUMA KIN SIYA AMANACE KARKI FITARMIN DAN ALLAH 🙏🙏🙏
(Albishir ga masoya, ma'abota bibiyar litattaafaina, dama ta samu zaku fara samun
litattaafaina na audio, akan YouTube channel ɗina me suna Cool Arewa TV
https://youtube.com/channel/UCD5vnvA5laU8ti4LLz2_QEg
Kuyi liking sannan ku danna subscribe, domin fara samun litattaafaina na audio,
nagode sosai da ƙaunar ku gareni"
104_105
Yusuf ya bita da kallo yana hararta, Umma tace "eh yakamata, Yusuf rakata hanya
kaga dare ya fara yi, ni baki gayamin sunanki bama gashi zaki tafi"
Badan Yusuf yaso ba ya biyota suka fito, Salma tace "wai kai baka amsa gaisuwa
ne?"
Salma tace "A'a kace dai nice baka amsa gaisuwa ta, da safe idan na ganka koda
yamma idan na gaisheka seka wani basar kamar baka ji ba, kuma fa kana jina"
Banza yai mata suka cigaba da tafiya, "au kana ji ina maka magana shine kamin
shiru, ga mara hankali ko?"
"Shikenan kar Allah yasa ka kulani ɗin, kuma ma bana son rakiyar"
Ya juya ya koma gidansu, Salma tace "lallai ka cika ɗan rainin hankali, dani kake
zancen"
Washegari da Safe yakasance weekends ne ba aiki, dan haka bayan ya dawo daga salla,
ya duba Umma yaga jikin nata da sauƙi, yakoma ɗaki ya baje ya dinga bacci, saboda
baya samun hutu sosai, yana tara gajiya matuƙa.
Se kusan ƙarfe goma na safe ya tashi da sauri, dan ya manta shaf zeyi girki, ya
tafi ɗakin Umma da sauri ya shiga da sallama ya tarar da Umma a zaune da ruwa a
hannuta, Yusuf yace "Ummana dan Allah kiyi haƙuri, bacci ne ya ɗaukeni me nauyi,
ashe har an samiki ruwan ban sani ba ne, bari inje in ɗora ko tea ne inje in siyo
bredi"
Salma ce tayi sallama ɗakin, hannunta ɗauke da plate da kofi, Yusuf yana zaune a
falon Umma, daga shi se gajeren wando da vest, dan haka kyakkyawar surar jikinsa ta
bayyana, namijin gaske me tsabar kwarjini da kamala.
Yana ganin Salama ya miƙe yace " ke meye haka zaki shigowa mutane babu sallama,
baki tsaya an baki iziniba kika shigo?"
Umma tace "A'a ai tun ɗazu tana gidan nan, ita taimin shara da aikace aikace ma"
Ya kalli Salma da ta tsatstsareshi da ido yace "to waye ya sata, Da kin bari Umma
idan na tashi ai zanyi, ke Malama ajiye kwanukan nan ki tafi angode, zan kaiwa
yayanki kuɗinki ya ajiye miki"
Hararrasa Salma tayi harda murguɗa baki, Umma tace "jimin yaro da faɗan ba gaira
ba dalili, daga taimako ita meta yi maka?"
"To Umma data gama aida seta tafi, amma kalli yadda ta ganni a haka ba kaya, kuma
ta wani tsareni da ido"
Umma tace "to ubanwaye yace ka fito a hakan, ƙyaleshi kinji yau ban san dame ya
tashi ba, naga yau rigima yake ji"
Haka aka ƙarashe kwanakin nan a haka, kullum tazo se sunyi faɗa da Yusuf, in dai
tazo seta yiwa Umma 'yan aikace aikace kafin ta tafi, ko su zauna su sha hira ita
da Umma, Salma tana da kyau dai dai gwargwado, gata' yar kwalliya da iya ƙwalisa,
tana da hasken fata da matskaicin tsawo, sannan tana da ƙirar jiki me kyau, ta
yadda ko tafiya take tana ɗaukar hankali.
Mazan unguwar nan dana wajen umguwar da yawa suna rushing a kanta, amma bata da
lokacin su, ba matasan samari ba har manyan masu kuɗi suna nuna tayinsu amma basu
isheta kallo ba, Saboda mace ce me class, a mazan ma ba kowa ke iya tunkarar ta ba,
saboda duk girmanka idan kamata abunda beyi mata ba, zata keta kane yadda take so
kuma ko a gaban waye, Tayi school of Nursing, tayi midwife tana ji da kanta sosai.
A bakin yayyyanta taji suna hirar Yusuf wataran da daddare, ɗayan yace "Habu
gaskiya gayen nan da yaja salla da Asuba dama ya zasu bashi limanci, jar uba kaji
ƙira'a kamar a Misra"
Habu yace "bari Usman, ni kaina da yaja sallar nan kamar kar ya dena karatun nan,
ai rashin zuwan liman da wuri yau munga 'yan Islamiyya, anya wannan a ƙasar nan yai
ilimin Addini?"
Usman yace "waya san masa, gaskiya ya iya karatu inaga zanje muyi bonding kona samu
hasken makaranta"
"A gidan uwarwa zaka samu hasken makarantar? Bayan ko sauka Al'qur'ani ba muyi da
kaiba ka fece neman kuɗi"
Habu yace "eh naji, aiba sharaɗine se mutum yayi sauka za'ayi abota dashi ba"
"To bari in gayamaka, kaga duk wannan ilimin nasa shegen girman kaine dashi, baha
kula kowa, iyakaci in ze wuce yai muku sallama, ban da haka ko aboki bashi da shi a
unguwar nan, inda gayen ya ban haushi kenan, dan kana da ilimi ubanwa zakayiwa
girman kai, kai ba wani shahararraen attajiri ba, ba basarake ba amma kace bazaka
kula mutane ba"
Habu yace "Aikuwa ilimin baze masa amfani ba, dan girman kai rawanin tsiyane, ni
harnaji ya bani haushi wallahi '
Salma tace " Kukam Allah ya shirye ku, kawai kun zauna kuna tayi da bawan Allah
kamar kun rasa abunyi "
Usman yace " ke abun da haushi fa, mutum be fika da uban komai ba amma ya dinga
hura maka hanci, baze dingawa mutane magana ba, ai dole ayi dashi"
Salma tace "to ka sani ko haka nature ɗinsa take, maybe jan ajinsa yake yi".
Habu yace "Nature ɗin banza da wofi, kuma jan ajin me sekace mace, jan aji ai se
mata, kana namiji ubanwa zaka jawa wani aji, yana gaddi ina gaddi za'a jamin aji,
wallahi mutum be isa ba"
"Nikam nafison irin haka, inga mutum gentle, yafi ma wata macen jan aji amma ace
duk inda mutum ya zauna dan yana namiji ya dinga sakin baki haba, ai abun ba tsari"
Habu yace "wannan yarinyar kinci kai tabbas baki da hankali, namiji in ba ɗan daudu
ba meye na wani jan aji"
Haka suka cigaba da wannan jayayya a tsakaninsu, ya zamana kusan kullum se anyi
zancen Yusuf, saboda ko minti biyar liman ya ƙara bezo ba, se kaji ana Malam Yusuf
a jamu salla, saboda kawai suji ƙira'arsa me daɗin sauraro.
Zuciyar Salma ta kwaɗaitu da san ganin Yusuf, saboda yadda take jin ana maganar sa,
wataran da yamma taje karɓar kuɗi a chemist ɗin Usman, Yusuf yaje siyawa Umma
Inhaler, tunda ya shiga daga tafiyarsa ma taga yadda yake taku cikin nutsuwa, yayi
sallama suka amsa sannan ya gaishesu, ƙamshin turarensa ya gauraye shagon, Salma ta
shagala da kallonsa, wanda shi sam be san ta nayi ba, ya karɓi abunda ze siya yai
waje.
Yana fita Salma tace "Masha Allah, Yaya wannan ma a unguwar nan yakene? Kaga mutum
nutsatse, ga ƙamshin turare, wanda seka gifta maza goma ba kaji ba, se warin
hamnata mussman irinsu Yaya Habu"
Usman yace "Allah yasa yaji abunda kikace ya casaki san ransa, shegiya uwar leƙe
leƙe, duk tarin samarinki amma kuma kina yaba wani"
Tace "kai Yayana, wallahi ko kai da kake namiji kasan gayen nan ya haɗu, kaga da
yai murmushi, wasu dimples suka lotsa wayyo Allah na, gaskiya me kyau ne, kuma me
ajine"
Usman yace "dalla wuce can, haka zaki ƙare ƙarshe mummuna zaki aura"
"A ina?"
"wannan wanda ya fita ɗin mana, in dai a unguwar nan yake, ina ciki"
. Usman yace "aikuwa zakiyo waje daga cikin da kika shiga, dan girman kaine dashi
kamar ƙaruna"
Salma tace "haba dai? Wayyo Allah na gaskiya ya haɗu, bashi da makusa, ga kyau ga
ilimi ga nutsuwa ga tsafta, gaskiya yamin"
"to 'yar wahala, wata wahalar ta ganki kenan, dan wannan banga ta inda ze kulaki
ba, dukda wannan koɗaɗiyar fatar taki"
"to fatar tawa ma hassada ake mata, to Allah ya shiryeka, ni na tafi ka tayani
addu'a kawai"
Ta juya ta fita da sauri, tun daga ranar ta gano gidansu Yusuf, take daidaitar
lokacin fitarsa da dawowarsa, idan ta ganshi se tayi masa magana, farko da yake ƙin
amsa gaisuwarta tayi zaton zancensu Habu haka yaje yana da girman kai, seda taje
gidansu sawa Ummansa Ruwa taga yadda yake aikin gida, ga shagwaɓa kamar mace, ga
tsananin biyayya ga mahaifiyarsa, anan ta gane mutane da yawa basu fahimce shi ba,
bashi da son shiga mutane ne, amma mutum ne simple.
Tun daga nan Salma ta liƙe masa, idan ta ganshi seta masa magana kota tsikane shi,
wataran sedai ya harareta yai tafiyarsa, ta maida gidansu Yusuf gidan zuwanta, ko
tayo girki ta kawowa Umma, ko tazo nan gidan ta tayata aiki.
Sabo ne ƙarfi ya shiga tsakanin Umma da Salma, tana jin daɗin yadda take girmamata
take tayata wasu ayyukan, dukda Yusuf haushin Salma yake ji amma a hankali, saboda
soyayyar da take nunawa Ummansa da mutuntawa yasa, yake ɗan saurara mata kuma har
cikin ransa yake jin daɗin kulawar da take nunawa mahaifiyarsa.
Wataran Salma taje gidansu Yusuf wajen ƙarfe sha ɗaya na Safe, ta tarar da babur
ɗinsa be fita ba, ta shiga cikin gidan ta tarar da Umma a tsakar gida hannunta da
mayafi, Salma tace "Umma ina zuwa haka? Kuma Yaya Yusuf be fita bane? naga babur
ɗinsa"
Umma tace "dama chemist ɗin yayanki zanje, kwanan sa kusan biyar yana zazzaɓi sama
sama, nayi nayi yaje Asibiti yaƙi yau jikin nasa rau da zazzaɓi ko gurin aiki ya
kasa fita, shine nace bari in kira yayanki, ya duba shi idan akwai abunda ze iyayi
masa to, in kuma babu mutafi Asibiti, yana jin jiki, kin san shi da dauriya da
taurin kai, yauma dan yaji uwar barine ya kasa fita gurin aiki"
Salma tace "Ina Yaya Yusuf ɗin yake? Nima zan iya duba shi ai"
Umma na maganar aka kirata a waya, ta tsaya ɗagawa Salma ta shiga ɗakin nasa da
Sallama, ɗakin tas dashi kama r na mace, komai fes fes se ƙamshin turaren wuta da
drumer ke tashi, gwanin ban sha'awa.
Ta hango Yusuf kwance akan gado, ya lulluɓa da bargo, a hankali ta ƙarasa gaban
gadon nasa, tasa hannu ta janye bargon tace "to shagwaɓaɓɓe, kazo ka kwanta kaƙi
zuwa Asibiti, ka tayarwa da Umma hankali"
A hankali ya buɗe idonsa ya kalli Salma, cikin ƙarfin hali yace "malama fitarmin
daga ɗaki"
"bazan fita ba ɗin, meke damunka ummance tace inzo in duba inga me ya kamata ayi
maka"
Lumshe ido yayi yaƙi magana, Umma tazo tace "Salma yaya? Za'a iya duba shi a gida"
Salma tace "eh, za'a iya, zanje in karɓo ruwa da allurai in masa, amma ya rage
kayan jikinsa, ki shashshafa masa ruwa ina zuwa"
Haka akayi Salma ta sassaka masa ruwa, da allurai sannan Yusuf ya samu kansa.
Washegari da safe da ta dawo, ta tarar da abokan aikinsa sunzo duba shi, babu wanda
yasan Yusuf ɗan sanda ne a unguwar dan haka Salma tayi zaton 'yan uwansa ne suka zo
duba shi, ta taho masa da Abinci daga gida.
Salma tace "No karki damu, zeci in kun tafi da kaina zan bashi ko Yayana"
Sunkuyar da kai yayi yai mata shiru, yayin da Abbas suka shiga tsokanarsa, Sakina
kuwa ta dinga harar Salma, ta dinga cika tana batsewa, saboda gaba ɗaya Haushi
Salma ta bata.
Bayan ya warke ya koma gurin aiki, sedai Sakina ma ta fito da manufarta na soyayyar
ta ga Yusuf, sedai Yusuf ya nuna mata sam shi babu wannan, babu maganar soyayya a
tsakaninsa da ita.
Salma kuma ya maida ita kamar Ƙanwarsa, dan wataran shike ɗakkota ma daga inda take
attachment, kusan duk ta kori samarinta saboda Yusuf, se sukai sha ɗayan dare suna
waya, amma sam shi Yusuf ba wai dan yana sonta ba, dan ya ɗauketa ƙanwa ne kuma
takan bashi shawarwari masu kyau.
Ita kanta Umma ita duk a zatonta soyayya ce tsakanin su, tana ta jin daɗi tana
murna Yusuf zeyi dacen mata, dan Salma akwai kirki sosai.
Wataran Umma ta sai wata doguwar riga me kyau, ta saiwa Salma ta bawa Yusuf tace
shi ze kai mata rigar.
Haka Yusuf ya karɓi riga ya kai a matsayin shine ya siya, Salma ta dinga murna tana
masa godiya, har ze tafi tace "Yayana nawa nikaɗai"
Yusuf yace "what? Aure kuma Salma? Ai babu batun aure a tsakanin mu, ni ƙanwa na
ɗaukeki fa"
"Yusuf, ƙanwa kuma? Yanzu duk abunda ke tsakaninmu ba soyayya bace? Yusuf na kori
kowa a samarina, babanmu ya tambayeni, nace ni kai na tsayar yace in sallami
masoyana, amma ka cemin babu soyayya a tsakanin mu?"
Yusuf yace "Salma, banyi hakan da cutar dake ba, amma dan Allah kiyi haƙuri, ni
gaskiya ban shirya yin aure ba"
Ai bata jira me zece ba ta shige gida da gudu tana kuka, Yusuf ya dinga mamakin son
da take masa.
Kwana biyu Umma taga kwana biyu ba taga Salma ba, tacewa Yusuf "kaga kwana biyu
banga 'yata ba, ko zaka je anjima ka jimin ko lafiya?"
Nan Yusuf ya warwarewa Umma komai, aikuwa ta sameshi ta inda ta shiga bata nan take
fita ba, "haba Yusuf, dan wulaƙanci yanzu duk sintiri da ɗawainiyar da yarinyar
nan take damu, kace kai bakama san sonka take ba? Ni ina nan na saki baki zan samu
Kayi Aure amma ka cemin kai bakama son sonka take ba? Idan ba sonka take ba ubanka
take yi? Wani irin mutum ne kai Yusuf? Haba Yusuf haka rayuwa zata yi? Ba zakayi
Aure ba haka zamuyi ta zama a cikin gidan nan, kamalar mutum ai aure, amma kai in
anyi gabas seka yi yamma, duk abunda mutane ke gani daidai kai Ba haka yake a
gurinka ba? Haka rayuwa zata tafi a haka? Wallahi in baka yi wasa ba haƙƙinta ze
kama ka "
Ganin ran Ummansa ya ɓaci, yasa ya shiga damuwa ya dinga bata haƙuri, tace idan
yana son ta haƙura yaje ya rarrashi Salma sannan ya amince zw Aure ta, tunanin
Farko daya fara zuwa zuciyarsa shine waye ze tsaya masa yayi Auren? Amma gudun
ɓacin ranta yai shiru.
Yaje gidansu Salma ya tarar bata da lafiya duk tayi wani iri saboda damuwa, Yusuf
ya dinga rarrashinta, ya tabattar mata da ya amince da batun Auren, Salma ta dinga
murna, take taji tama warke daga ciwon.
Suka shiga soyayya shida Salma, shi dai tausayinta da yake ji yafi yawa, dan baze
ce ga takamaimai feelings ɗin da yake dashi akan Salma ba, Sone da tausayi, ko kuma
tausayin ne kawai.
Nan aka shiga gulma a unguwa, wai Yusuf daga zuwansa yasa Salma ta kori kowa yana
juyata yadda yaga dama, ya maida ita 'yar aikin babarsa, kullum cikin sintiri take
a gidansu, saboda Salma yasa ya fara kula yayyenta a hankali sukuma suke jansa
cikin jama' ar unguwa dan seka zauna dashi zaka gane bashi da wani girman kai.
Wataran suna sitting room ɗinsu Salma suna hira ita da Yusuf, ta sha ado se zabga
ƙamshi take, suna ta taɗi ya miƙe ze tafi aka ɗauke wuta, aikuwa ta rungume shi
tana kukan Shagwaɓa wai ita tsoron duhu take.
Yusuf yace "Salma ki cikani, kar wani yazo ya ganmu, amana mummunar fassara"
"Ni tsoro nakeji, tai maganar cikin Shagwaɓa tana sake kwanciya a jikinsa, ga wani
ƙamshin turare da take yi, take jikin Yusuf ya fara tsuma, karo na farko daya
rungumi mace a jikinsa, ya dinga jin wani irin yanayi yana bijiro masa, sheɗan na
ƙoƙarin yi musu lalata, nan da nan yasa hannu ya raba Salma da jikinsa yai waje da
saurin gaske.
Ko daya koma gida, ya sauya kaya ya kwanta ya kasa manta abunda ya faru, gaba ɗaya
bacci ya ƙauracewa idonsa, tunani iri iri, a nan ya ƙara yadda da tabbas ya kai
munzalin da lallai yana buƙatar mace a tare da shi, sedai waye ze tsaya masa, tunda
harkar Aure dole seda uba, ko wakilansa.
Azumi ya gabato Yusuf yayi wa Salma siyayyar kayan Azumi, dana salla, Umma ba
ruwanta da duk abunda ze siya ya kaiwa Salma, sema dai ta dinga yakamata ka ƙara
kaza.
Ya haɗa sha tara ta arziki ya kaiwa Salma, Salma ta dinga murna tana godiya, Yusuf
yana kashe mata kuɗi sosai.
Bayan kwana biyu mahaifinta yasa aka kira masa Yusuf, yace ya turo magabatansa ayi
maganar Aure, tunda dai sun fuskanci juna, wahalar da yake ta isa haka.
Sedai Yusuf ya koma gida cike da zullumi a zuciyarsa, waze turo? Wa yake dashi
banda Allah da Ummansa?
Bayan ya koma gida daya gayamata tayi murna, sedai itama kanta seda jikinta yayi
sanyi, amma ta dake tace masa shikenan bakomai, Insha Allah za'a tura a tambayar
masa, Yusuf be cikata da tambaya ba ya ƙyaleta.
Umma ta shirya ta tafi gurin Yaya ɗan lami, ta gayamasa cewar dan Allah Yusuf ya
samu yarinyar daze Aura ne, tana so ba dan ita ba su wuce masa gaba su tambayar
masa Aure, Yaya ɗanlami yace mata ai ba matsala, bakomai dan dai wannan, zasuyi
zasuje su tambayar masa Aure.
Umma ta dawo gida tana ta murna tana farinciki, Yusuf ze Aure ze zama cikakken
mutum shima kamar kowa.
Wataran ya dawo da yamma, daga gurin harkar furnitures ɗinsa, yazo ya tarar da
cincirindon mutane a ƙofar gidansu, se gabansa ya faɗi ya zaci wani abune ya samu
Ummansa, dan haka a guje ya ƙarasa cikin gidan yana ture mutane, yaje ya tarar da
ita a zaune tana kuka, ga kayan daya saiwa Salma na Azumi dana salla, a baje a
gabanta wasu mata suna cewa
"gayyar tsiya ashe bashi da uba, ya lallaɓo ze aurar mana 'ya, to Allah ya rufamana
Asiri, seku koma gidan marasa iyaye inda aka ɗakkoshi, a ɗakko masa mata a can ba
dai' yarmu ba, banda mutanen nan na kirki ne sunje sun gayamana, da haka zamu bawa
mara uba 'ya, ai kema kin san bakiyiwa kanki adalci ba"
Yusuf ransa ya ɓaci, dan yau an masa tozarci mafi muni, dama abunda yake ta gudu
kenan Umma takasa ganewa, maimakon a dawo masa da kayansa salin alin, shine seda
aka tara wannan gayyar mutane sannan za' aci zarafinsa haka, kuma ma dan baƙin ciki
akazo akasa mahaifiyarsa a gaba da cin mutunci kuma aka cika gidan kamar wanda
sukai sata ko maita, cikin tsananin ɓacin rai da juriya, Yusuf ya kalli Matan yace
"mun muku laifi, Allah ya baku haƙuri, tunda kun gama abunda zakuyi, zaku iya fita"
"Ai dole kace haka mana, tunda ka lallaɓo zakayi cuta, yarinya da samarinta na
arziki amma zaka cuceta, yarinya 'yar dangi kyakkyawar gaske"
"Wallahi idan kika kuma gayamin maganar banza sena wanka miki mari, get out from
here"
Yadda yayi maganar a fusace ne yasa jikinsu na rawa, sukayi waje dasu da gayyar
mutanen da suka cika gidan, anata ƙananan maganganu, wai ashe duk girman kan nasa
ma bashi da uba, yana taƙama da wannan kyan nasa yana hura hanci, ashe ma shegene.
Yusuf be cewa Umma komai ba, ya tattare kayan yaje ya ajiye, ya wuce ɗakinsa ya
kwanta, zuciyarsa na masa wani irin raɗaɗi mara misaltuwa.
Umma tasan ba kowa ne yaje ya gaya musu wannan maganar ba face su ɗanlami, tayi
danasanin zuwa ta samesu akan su wucewa Yusuf gaba akan harkar Aure, yanzu shikenan
baza'a auri ɗanta ba saboda wannan dalilin? Dukda tarin nagarta dayake da ita.
Tun daga ranar ko hanyar gidansu Salma ,Yusuf be ƙara biba, ba damar ya fita ko
yazo wucewa se yaji ana yada masa da maganganu marasa daɗi, ya goge lambar Salma,
da duk wani abu daya shafeta.
Sedai hakan ya zame masa tamkar wani ciwo a ransa, Yana kewarta saboda sun shaƙu
sosai.
Wataran ya fito ze fita aiki ya ganta a ƙofar gidansu, ya ɗauke kai ze wuce amma ta
sha gabansa tace "Gurinka nazo"
"Yusuf, ni kaina banji daɗin abunda akayi maka saboda ni ba, ban san haka abun yake
ba, amma abun yafi ƙarfina ba yadda na iya, dan Allah kayi haƙuri, kuma ka bawa
Umma haƙuri, ga katin ɗaurin Aurena nan, ina buƙatar addu'arka, kuma ina fatan
ubangiji Allah ya baka wadda ta fini, komai da komai nagode da lokacin ka Yusuf "
Ta zira masa katin ɗaurin Auren a gaban babur ɗinsa, ta juya tana share hawaye,
shiba katin Aurenta nema ya dameshi ba, kukan da take ne ya bashi tausayi.
Gaba ɗaya ya rufe babin Salma a rayuwarsa, ya koma rayuwarsa sedai mikin nan baze
taɓa barin zuciyarsa ba.
Yusuf yayi ajiyar zuciya sannan yace "ko wata biyu ba'ayi ba da abunda ya faru, aka
bani aikin nan akanki, da farko nace ba zanyi ba, amma Abbas ya takurani, saboda
wai ina da haƙuri, sedai ranar farko dana fara tozali dake, dukda isarki da
izzarki, duk da jan aji da wulaƙancinki, se da naji zuciyata tayi bugun da bata
taɓayin irinsa ba, ga kwarjininki yasa na kasa haɗa ido dake, ban shirya ba banyi
tsammani ba na shiga kokawa da zuciyata akan Sonki da take, na nemi 'yar talakawa
ma ban samu ba, saboda rashin asalina, ina ga ' ya kamarki, me Asali me dukiya
gashi uwa uba naje a matsayin direba, se akanki na tabattar da Biyayya ce da
shaƙuwa tasa na karɓi Salma a wancan lokacin, Amma wannan karon zuciyata ce da
kanta ta zaɓi abunda take so, Widad bani da tabbas idan Dagaske Umma take na cewar,
hatsari iyayena sukayi aka jefoni ta taga, nasan zata iya gayamin hakan dan
hankalina ya kwanta, amma zance mafi yawa shine a gidan marayu aka ɗakkoni, Yanzu
zaki yadda ki haɗa zuriya da mutum irina? Ki haihu dani alhalin bani da dangi se
Allah se Ummana? Ni ba ina gudun haihuwa bane, nima ina fatan ganin jinina a
duniya, amma kinji dalilina Auren nan kansa da mukayi a cikin zullumi nake Widad,
ni dai nasan ina sonki amma bani da asalin da za'a nuna, nasan Ko Daddynki baze
amince ba Widad, tuntuni nake zullumin gayamiki wannan labarin nawa, zaki zauna
dani a haka?, ina sonki Widad, akanki na fara jin shauƙin soyayya, naji zan iya duk
wata sadaukarwa saboda ke, dan Allah kar rashin iyayena yasa ki gujeni, ina sonki
Widad ni kaina ina mamakin son da nake miki"
Ya ƙarasa maganar yana kuka, shaɓe shaɓe da hawaye kamar mace, Widad ta ƙanƙameshi
itama tana kukan, ta rungumeshi kamar jariri a ƙirjinta, ta dinga shafa sumar kansa
tana
Kamar ta ƙara tunzura Yusuf, kuka yake sosai harda sheshsheƙa, da alama abun yana
cin zuciyarsa.
Tana kuka take cewa "Yoseef dan Allah kayi haƙuri, ka dena kukan nan haka please"
Ya girgiza mata kai yace "ki ƙyaleni inyi inji sassauci a zuciyata Widad, ban taɓa
yiwa wani kukan rayuwar da nayi ko na tashi a ciki ba seke, i need a shoulder to
cry on, ƙyaleni inyi matata"
Widad ta rungumeshi tana kuka, tana tausayawa irin rayuwar da suka yi, dan daga ita
har Yusuf kowa yaga rayuwa, kowa da irin ƙaddarar daya fuskanta a raguwarsa, amma
na Yusuf ya ratsata sosai, ya bata tausayi matuƙa, ya wahala a rayuwarsa.
"zan rayu da kai a duk ya kake, zan karɓi kowane ƙalubale daze taso saboda kai, ina
son Aurena Yoseef, ina son zama da kai, ba ruwana da waye kai, nagartar ka da
gaskiyar ka sun wadatar dani, stop crying my Husband, nima ai kana gani ba dangin
ne dani ba, daga Allah se Babana, duk dangin babu, dan haka ina so mu zama ɗaya mu
samar da family nida kai, ka dena kuka mijina "
TAMMAT BI HAMDILLAH, NA KAMMALA KASHI NA BIYU ZAN SHIGA NA UKU, WANDA SHINE NA
ƘARSHE DA YARDAR ALLAH
LITTAFIN KUƊI NE, DAN ALLAH KI SIYA KAFIN KI KARANTA BA DANNI BA DAN ALLAH, LITTAFI
NA ƊAYA KYAUTA NE WANNAN NA SIYARWA NE
NORMAL GROUP ₦300
VIP ₦500 NE KITURA TA WANNAN ACCOUNT ƊIN
0009450228
JA'IZ BANK
AISHA ADAM
SE A TURA SHEDAR BIYA TA WANNAN LAMBAR
07063065680
IDAN KUMA KIN SIYA AMANACE KARKI FITARMIN DAN ALLAH 🙏🙏🙏
(Albishir ga masoya, ma'abota bibiyar litattaafaina, dama ta samu zaku fara samun
litattaafaina na audio, akan YouTube channel ɗina me suna Cool Arewa TV
https://youtube.com/channel/UCD5vnvA5laU8ti4LLz2_QEg
Kuyi liking sannan ku danna subscribe, domin fara samun litattaafaina na audio,
nagode sosai da ƙaunar ku gareni"
11/15/21, 4:53 PM - Buhainat: LITTAFIN KUƊI NE, DAN ALLAH KI SIYA KAFIN KI KARANTA
BA DANNI BA DAN ALLAH, LITTAFI NA ƊAYA KYAUTA NE WANNAN NA SIYARWA NE
NORMAL GROUP ₦300
VIP ₦500 NE KITURA TA WANNAN ACCOUNT ƊIN
0009450228
JA'IZ BANK
AISHA ADAM
SE A TURA SHEDAR BIYA TA WANNAN LAMBAR
07063065680
IDAN KUMA KIN SIYA AMANACE KARKI FITARMIN DAN ALLAH 🙏🙏🙏
(Albishir ga masoya, ma'abota bibiyar litattaafaina, dama ta samu zaku fara samun
litattaafaina na audio, akan YouTube channel ɗina me suna Cool Arewa TV
https://youtube.com/channel/UCD5vnvA5laU8ti4LLz2_QEg
Kuyi liking sannan ku danna subscribe, domin fara samun litattaafaina na audio,
nagode sosai da ƙaunar ku gareni"
106_107
"Yoseef dan Allah Kadena kukan nan, zaka ɗagamin hankali, ya isa haka please kar
kanka yayi ciwo kaji"
"Hmm, my wife tsawon shekaru talatin da biyu, abu yana damuna a zuciya, ban samu
nayi kuka yadda nake so ba, dan haka dan Allah ki barni inyi, kin ƙyaleni nika ɗai
nasan what i go through, na shiga damuwa da baƙin ciki daban daban a rayuwata, i
suppose to cry ko zan rage "
"No Yoseef, kace Alhamdilillah daya barka da ranka da lafiyarka, kuma insha Allah
daɗi yana tafe, dan bayan duk wata wuya se daɗi da yardar Allah, ka dena kuka kaji
Ɗan uwana, we are now family ai ko?"
Ajiyar zuciya ya dinga saukewa, yace "Widad dagaske zaki cigaba da zama dani, koda
mun koma gida?"
Widad tace "dagaske nake, Insha Allah mutu ka raba nida kai, kaine dai dai da
rayuwata Yoseef, a yanzu kasanni fiye da yadda kowa ya sanni, ciki harda mahaifina,
kasan abunda nake so kasan wanda bana so, you are such an amazing guy, kuma ni
labarinka da naji, bazan iya rabuwa da kai ba, ƙaddarorinmu suna kamanceceniya da
juna, dan haka zamanmu zeyi dai dai da yanayin rayuwar mu, zan zauna da kai Yoseef,
ba ruwana da a inda aka samo ka ko makamancin haka, kuma insha Allah bazaka sake
zubda hawaye saboda haka ba, ka dena kuka kaji Mijina "
Tai maganar tana share masa hawaye, itakuma tana zubda hawayen, Yusuf ya ɗago kansa
yana share mata hawayen fuskarta itama yace " Am sorry Baby, na saki kuka ko? Yi
haƙuri yau nayi ragwanci a gaban matata, zata rainani"
Ya ƙarasa maganar yana murmushin yaƙe, "kwanta muyi bacci, dare yayi kar gobe in
Allah ya kaimu a barni da yunwa"
Yai murmushi tare da kwanciya a jikin ta, tasa hannayenta ta zagaye bayansa dashi,
tana shafa sumar kansa da hannunta ɗaya, Yusuf yana ta jan ajiyar zuciya, ta shiga
ɗan duddukan bayansa alamar rarrashi.
Wani irin kallo Hajiya Halima ta shiga yiwa mutumin, Mutumin yace "kina mamakin
ganinane? Ai bekamata kiyi mamaki ba, butulu mara Alƙawari"
Ramlah ce ta fito ita da Amal, Ramlah tace "Mummy ya har yanzun baki tafi ba? What
are you still doing their?"
Suka ƙaraso inda take tsaye ita da mutumin nan, Amal ta buɗe baki tare da dafe
ƙirji, Ramlah tace "Mummy wannan kuma wanene? Barar ce baza'a bari kifi ta ayimiki
ba, se an biyoki har nan, mutane sun fiye zalama kamar zasuyi ƙwace dan azabar son
kuɗi"
Amal tace "kai Ramlah, babanmu ne fa, baki gane shi bane?"
Ramlah tace "What? Wannan ɗin kalle shi wani buguzun buguzun dashi kamar korarre"
Ramlah tace "Taɓɗijan, God forbid in nuna wannan ince shine ubana, alhalin ina
bearing da Sunan Nasir Daula, sannan wannan yazo yace wai shi ne babanmu, Allah ya
kiyaye wallahi wannan ko riƙon jakata bazan ɗauke shi ba, ni ubana ya mutu da
daɗewa, sedai babansu Anwar"
Ta juya ta shige gidan tana ci gaba da maganganu, mutumin ya kalleta yace "Halima
haka mukayi dake? Saboda son zuciya irin naki haka kika mayar min da 'ya' ya,
yarinyata ta kalleni tana gayamin wannan maganganun, dama haka mukayi dake?"
Hajiya Halima tace "kaga, dan Allah karka ɗagamin murya a gaban ma'aikatana, kazo
mu shiga daga ciki ayi duk wacce za'ayi mana"
Ya bita suka shiga cikin falo, Amal ta tafi gurin Ramlah ta buɗe ƙofar ɗakin nata
ta shiga, ta sameta tana zaune tana danna waya, Amal tace
"Ramlah bekamata kiyiwa mahaifinmu haka ba, ai duk lalacewarsa shine ya haifemu"
Ramlah tace "wait, wai dan Allah dagaske wannan bagidajen shine mahaifinmu?"
"Ramlah ki gyara maganarki fa, wallahi babanmu ne ya zaki manta fuskarsa, wallahi
babanmu ne"
"gaskiya sedai Babanku, kalli mutum a koɗe kamar baya cin Abinci, kalli suturar
jikinsa yazo yace shi babanmu ne, gaskiya niba ubana bane, ai abun kunyane mu nuna
wannan muce ubanmu ne, bayan duniya tasan da sunan Daula muke amfani, ai kawai
babanmu ya mutu, amma wannan ai be kai mutum ba balle ace masa uba"
Amal tace "ikon Allah, wallahi Ramlah kina sane, babu yadda za'ayi kice kin manta
kamanin mahaifinmu, dukda tunda muka bar gurinsa bamu kuma zuwa ba"
Ramlah tace "ke ina sane wallahi, na gane shi sarai, amma ni karan kaina kunya
nakeji in kalle shi ince mahaifina ne, haba mutum a tsiyace kamar matafiyin da
guzuri ya ƙare masa, kuma ya tsaya ze fara kora bayani a gaban wannan gidadawan,
salon su raina mutane"
Shu'aibu ya kalleta yace "dama ina zan waye, mara mutunci dama haka mukayi dake?
Nace haka mukayi dake? Akan yarjejeniya mukayi komai, amma da yake ke butulu ce,
kinzo kin samu jin daɗi kin watsar dani, kinyi watsi da Yarjejeniyar da mukayi,
shine nazo in miki tuni, ki cika Alƙawari sannan ki bani 'ya' yana"
"wane 'ya' yan naka, malam karma ka ɗakko wannan maganar, dan ba zata yuwu ba, me
ka sani na 'ya' yan naka, seda na gama wahalar? Lokacin mora yayi sannan kace in
baka no, baze yuwu ba"
Shu'aibu yace "kin san Allah Halima, sekin bani 'ya' yana gaba ɗayansu bazan bar
ko guda ba, kuma sekin cika Alƙawarin da mukayi daku"
Tsaki tayi tace "bani account number ɗinka, zan baka dubu ɗari biyar, ka tafi ka
bani guri dan Allah"
"Ni zaki kalla ki bawa dubu ɗari biyar, ki riƙe kayarki amma ki saurari abunda ze
biyo baya"
"Kaga dan Allah karmuje ga haka, ka zauna muyi magana, Alƙawari da mukayi fa har
yanzu wannan kuɗi basu samu ba, ya kake so inyi ne"
Shu'aibu yace "ƙarya kike, shakrar ki nawa a gidan nan, kima nufin duk zamanki a
gidan nan baki samu komai ba, aiko duk jikina kunne ne bazan yadda ba Wallahi"
"Wai kai baka san 'yarsa itace ta hana ruwa gudu ba,? dan Allah karka ɗagamin
hankali ka bani account number, zan samaka million ɗaya"
Shu' aibu yace "ashema bani da hankali, kusan shekara goma sha, ko ficika bata
shiga hannuna ba kice zaki ban million ɗaya, baki nemi sulhu ba tabbas, kuma abunda
ze biyo baya baze miki daɗi ba na gaya miki"
Hajiya Halima tace "kaga shua'aibu bazaka zo ka ɗagamin hankali ba Wallahi, yanzu
ma daka zo a wani zullumin bala'in nake, ko dai ka haƙura da abunda zan baka kokuma
ka haƙura, dan ban san ya kake so inyi ba, yarinyar daza'a karɓi dukiyar a hannuta
ba'a san inda take ba, shi kansa me gidan ba'asan a inda yake ba, komai yana nema
ya jagwalgwale min, kuma kazo kana gayamin maganar banza, dan Allah ka sauraramin"
"Naji zan saurara miki, amma nima ki saurari abunda ze biyo baya, kin sanni kin sam
abunda zan iya aikatawa, wallahi nima zan baki mamaki, zan ƙara miki matsala akan
wadda kike ciki, sannan ki gayawa 'ya' yana ina nan zuwa in ɗauke abuna"
"ka ɗauki wa? Can kaje ka nemi 'ya' yanka, karka ƙara ce mana 'ya' yanka, can ka
nemi 'ya' yanka malam" Ramlah da ta fito daga part ɗinta take faɗa.
Shu'aibu yai murmushi yace "Allah sarki yaro yarone, Halima na fuskanci wannan
yarinyar halina ta ɗakko, Rawar kanta da zafin kanta kamarni, amma ki gargaɗeta in
ba haka ba, abunda ze biyo baya ke dasu baze muku daɗi ba Wallahi"
Mummy tace "ke Ramalh, wannan fa mahaifinku ne, kidena gayamasa maganar da kika ga
dama kinji ko?"
"wallahi karki ƙara haɗani dashi, can ya nemi yaransa ba dai niba, uwar meya
maganta mana a rayuwar daze zo yana wani mu 'ya' yansa ne, dan Allah mu yayi ya
wuce ya bamu guri, kidena ssaurarensa ki fita a samo mafita akan ɓatan Anwar, idan
ba hakaba kika biyewa wannan koɗaɗɗen mutumin, komai ze iya faruwa, Anwar ze iya
tona miki asiri idan wannan be tona miki ba"
Zaro ido shu'aibu yayi yace "Anwar ɗin ne ya ɓata? Halima dagaske ne abunda
nakeji?"
A fhaace tace "Eh gaske ne shu'aibu, duk akan a samu kuɗin nan, Anwar ya gudu ya
bar gidan nan, se me ina nikaɗai naita ɗawainiya dasu ina ruwanka dasu, dan Allah
ka barni inji da kaina"
"zan barki kiji da kanki, zan tafi a yanzu bazan kuma dawowa ba se a lokacin daya
dace, ko kuma in cigaba dayi miki aike, zan baki account number na, ina buƙata kuɗi
naira million hamsin, nan da kwana bakwai idan baki turamin wallahi, wallahi abunda
ze biyo baya baze miki daɗi ba"
Ramlah tace "ai se kazo ka ƙwata ai, tunda kai ka tara mata"
Aikuwa ya shammaci Ramlah ya wanketa da mari, jikinsa na rawa kamar wanda aka
kaɗawa gangi yace "da uwarki nake magana, ba dake ba ko ita lokacin da tana
hannuna idan ina magana tana magana, tasan me yake biyo baya, idan kin manta dan
lokacin kina ƙarama gara in tuna miki, Halima ki gargaɗeta ki gaya mata abunda zan
iya, idan na kuma zuwa gidan nan, taimin tsinin baki sena yagalgalata a gurin nan,
kuma nan ba gidana bane, zanzo in ɗauke ku, lokaci yayi da zan mori abunda na haifa
nima"
Ramlah ta zabura zata yi magana, amma Hajiya Halima ta dakatar da ita, ta hanata,
shi kuma ya juya ya fice yana huci yana sauke numfashi.
Tunda garin Allah ya waye, Widad take nan nan da Yusuf, se wani lallaɓashi take
tana tarairayarsa, daya tashi da safe, idanunsa sunyi ja sosai sun ɗan kumbura,
saboda kukan da yayi jiya, da ta kalli Yusuf se taji kamar ta fashe da kuka, idan
ta tuna labarin daya bata, da irin wahalar da ya sha shida mariƙiyarsa, sun sha
wahalar rayuwa sosai.
Ta ɗakko kunu, ta dinga ɗebowa tana bashi a baki, Yusuf yace "yau kuma nina koma
jaririn? Se wani lallaɓani kike?"
"ba dole in lallaɓaka ba, nima kana lallaɓani ai, ko baka sone?"
Ta dinga bashi Abinci a baki, yana ci yana lumshe ido, dan dauriya kawai yake, har
yanzu zuciyarsa babu daɗi, gaba ɗaya a cunkushe ransa yake, amma ya daure yana
murmushi dan kar ya ɗaga mata hankali.
Ta ɗago ido taga ya ƙura mata ido yana kallonta, ta miƙa masa kofin kunun bakinsa,
kawai taga idonsa ya cika da ƙwalla, tasan dauriya yake kawai, amma ransa babu
daɗi.
Kawai ya lumshe idonsa ya bawa hawayen daya taru a idonsa damar gangarowa, ɗaya
bayan ɗaya suna zarya a fuskarsa, yasa hannayensa biyu ya tallefe fuskarsa, hawaye
na cigaba da bin fuskartasa.
Itama hawayen ne ya shiga zubo mata, tasa hannu ta janye masa hannayen daya rufe
fuskarsa, ta janyo kansa jikinta, tana son rarrashinsa amma tama rasa me zata ce
masa, aikuwa ya kwanta sosai a jikinsa, yana kuka hadda sheshsheƙa, kai kace wani
ɗan yaye ne.
"Haba Yoseef, habe Yoseef is ok please, kana son wani ciwon ya kama min kaine? Idan
ciwo ya shige ka ya zanyi, baka son kaga Lokacin da zamuyi building namu family
ɗin, Allah yayi maka gata daya baka rai da lafiya Yusuf, Insha Allah zan share maka
hawayen ka a rayuwa, bazan ƙara bari a maka gori ba, komai ya wuce ai, ya zama
tarihi tunda ba shiri duk da kowanne mu ya fidda ran samun abokin rayuwa amma Allah
ya haɗamu ya ƙaddara aurenmu, ba tare da mun shirya ba, tabbas ƙaddararmu tana
kamanceceniya da juna, ni wallahi jinake dama ni na samu uwar riƙo kamar ummanka,
Yoseef kana kallo ni ga gatan ga komai, amma inaji ina gani aka maidani
mahaukaciyar ƙarfi da yaji, aka haɗani da larurar Ƙwaƙwalwa da zuciya, ga rashin
kwanciyar hankali, ina so kamanta da wannan abun kamar be faru ba, kodai tunanin
Salman kake ne? "
Duk da kuka yake, seda ya ɗan murmusa sannan ya girgiza kai yace " inda ke babu
macen da Yusuf ze tuna"
Yai maganar yana kallonta, tai murmushi tace " na zauna da kai a ɗakin ƙasa, duk
abunda ka banj na karɓa naci, kuma muke rayuwar mu a haka, ina ne zaka kaini bazan
bika ba, amma gaskiya ni bana son aikin nan naka"
Ta ɗanyi shiru sannan tace "Yoseef, DSP Bashir shine Abbanka da aka kashe saboda
case ɗin Ammina fa"
Yusuf yace "tun lokacin ina miki aiki, na nake bincike akan statement ɗin kashe
mahaifina da akace 'yan fashi sunyi, inata tunanin abun, kina bani labarin ki
Nagano musababbin kisan Abba, kuma na gane dalilin da yasa da najewa Umma da batun
aiki a gidanku, take cemin bata so, dukda bamu taɓa hirar da ita ba"
"Yoseef Kayi haƙuri kaji, ka dena koke koken nan hak, kana karyamin zuciyata sosai,
ka dena kuka kaji ɗan gidan Umma"
"Nima ban sani ba, amma ina fatan Allah ha haɗani da wani, wanda yake yana da alaƙa
da iyayena, ko 'yan uwana komai talaucinsa ina son in samu in ga wani daga dangina,
koa yake is not possible, tunda babu wanda ya sanni a dangin nawa, kuma nima ba
wanda na sani "
Widad tace " bazaka dena kukan ba kenan? Ba gani ba, ba nace maka zamu haɗa namu
family ɗin ba, mu haifi yara ga Daddy, ga Umma gamu da 'ya' yan da zamu haifa, ba
Family ya haɗu ba kenan?"
Yusuf yace " bazaki gane ba Baby, anyway nagode sosai da kulawarki, banjin wani
bayan Ummana ya taɓa min rarrashin daya shigeni kamar wanda kikamin, ban taɓa zama
nayi makamancin hirar nan da wani ba, duk alaƙata dashi kuwa, ko Umma bama wannan
hirara da ita, balle wani saboda kar in ɗaga mata hankali, taga hawayena dan kar
taga kamar ta gaza da kula dani ne, dan nasan tabbas idan na saɓamata Allah baze
barni ba, ta shayar dani ta bani duk wata kulawa ta uwa da ɗa, kece kawai nayi
wannan hirar dake, shiyasa I express all how I feel in my heart, kuma naji daɗin
gayamikin da nayi, naji na rage kaso mafi yawa na damuwata thank you sweet heart"
"Allah sarki mijina, kayi haƙuri kaji, tamu jarabatar kenan, amma ko abokinka Abbas
baka taɓa yiwa zancen ba?"
Yusuf ya girgiza kai yace "A'a ban taɓa yi masa ba, amma me yasa kika tambaya?"
Widad tace "saboda na tsane shi, gaba ɗaya siffar munafukai ce dashi haushi yake
bani, shiyasa nasa aka rabaka dashi, aka maida shi nesa da gurin aikinka"
"Amma Widad meyasa? Abokinane fa ya bani gudunmuwa sosai fa a harkar aiki da sauran
mu'amalar rayuwa"
Widad tace "Oho nidai na tsane shi, kuma wallahi idan ya kuma raɓarka sena
ɗaureshi"
"Z" ta bashi amsa tare da ƙura masa ido, alamar bata son zancen.
"Yanzu za kamin Addu'ar in samu Babyn, kokuwa har yanzu baka son in haihu da kai"
Ya girgiza kai yace "Ai magana ta ƙare, tunda har kika amince dani dukda kinji
labarina, Allah yabamu masu albarka Babyn Yoseef"
Washe baki tayi tana murmushi, ta rasa mema zata yi dan murna, kawai ta rungume
Yusuf ta haɗe bakinsa da nata tana kissing ɗinsa, Yusuf ya rungumeta shima yana
kissing ɗinta suna murmushi, daga nan kuma aka shiga wani bigire daban .....
(Nikuma na fece 🚶 🚶 🚶)
Bayan fitar shu'aibu Halima a fusace ta hau Ramlah da faɗa
"Ramlah kinyi haukane? Koba komai mutumin nan mahaifin kune? Kin san hatsarin
dayake dashi kuwa? Ko dan kuna ƙanana na bar gidansa baku san irin halayensa ba,
shu'aibu da kike ganinsa bashi da imani, bashi da tausayi tsohon ɗan dabane
gawurtacce makuwa kuma matsafi, idan kika zaƙe wallahi ze iya kauda ke, dan akan
rigimar gonar gado har ɗanuwansa uwa ɗaya uba ɗaya ya kashe, dan haka ki kiyayi
wannan tsinannen bakin naki, wanda besan yakamata ba kina zaƙewa dayawa, tynda kika
ga ina binsa sannu sannu, nasan hatsarin dayake da shine, idan kinƙi ji bakyaƙi
gani ba, idan kin gadama ki gyara idan bahaka ba, matakin daze ɗauka baze mana daɗi
ba dagani harku"
"Ke rufemin baki, bana son cika baki kin san shi rashin jin da yayi"
Ramlah tace "shi ta shafa bani ba, but he must pay for what he did"
Hajiya Halima ta girgiza kai tace "Amal ɗakko mayafinki, kizo ki rakani gurin
Alhaji Haruna, zan kira shi a waya yanzu, idan yana nan muje mu sameshi ayi maganin
wannan matsalolin"
Gidan Alhaji Haruna sukaje, aka musu iso part ɗinsa, yana zaune yana kallon labarai
a tashar Al Jazeera.
Suka samu guri suka zauna, tunda suka shigo yake bin Amal da kallo, kamar tsohon
maye.
Hajiya Halima tace "nikam duk a bar wannan maganar, yaron wajena daya ɓata ba sace
shi akayi ba, guduwa yayi daga gida, kuma baun takaicin shine, ya gano abubuwan da
nake aikatawa, dan hara takadda ya bari"
Alhaji Haruna yace "Halima kina me haka ta faru? Garin yaya yasani, wannan yaron
naki me kama da ustazai kin san ze iya tona mana asiri fa"
Halima tace "hmm wallahi ban san yadda akayi ya sani ba, shekara Goma ina ƙumbiya
ƙumbiya muna wannan harƙallar tare, amma be sani ba, ban san wane munafikin ne ya
gaya masa ba, kuma ma ba wannan ba ɗazu fa uban 'ya' yana yazo"
"Shu'aibu mana, koka manta bisa yarjejeniya da aka yi dashi ya sakeni, kuma tunda
muka rabu, ba'a cika masa Alƙawarin ba, dan haka yazo yana barazanar karɓe yaransa,
kuma wai sena tura masa wasu maƙudan kuɗaɗe koya tona mana Asiri"
Alhaji Haruna yace "toki tura masa kuɗin mana, ko kin fi son asirin naki ya tonu?"
Hajiya Halima tace "wace irin maganace wannan, kafa san hatsarin da mutumin nan
yake dashi fa"
Alhaji Haruna yace "lallai akwai matsala gagaruma makuwa, amma yanzu abunda za'ayi
ki saurareni, zamuyi magana dasu, yadda aka yanke zan miki magana"
Hajiya Halima tace "to shikenan, amma dan Allah kuyi maganar da wuri"
Yace "shikenan, karki damu wannan ma yarinyar kice ne? Naga harta fi yayarta kyau"
Hajiya Halima tace "eh itace 'yar auta ta ai, daga Ramlah se ita"
"Masha Allah, yaran naki masu kyau, sunfi kama da yayarta, Anwar ne ban san
kamannin wa yayi ba"
Hajiya Halima tace "kamanin Ubansa yayi, wasu lokutan kuma dani yake kama"
Alhaji Haruna yace "A' a baya kama da shu'aibu sam, kamarsa daban shima"
Amal ta miƙe tana haɗe rai, saboda kallon da Alhaji Haruna yake mata.
Tana fita Hajiya Halima tace "Anwar fa ubansa daban shima, dana rabu da mijina na
fari akwai cikinsa ko wata ɗaya beba na auri shu'aibu, na haifeshi a gidansa amma
ba shine ubansa ba"
"kaga a bar maganar nan kawai, ba wanda na taɓa gayawa se kai duk yadda kukayi se
muyi waya"
Ta miƙe ta fito, ya biyo bayanta yana sake bin Amal da kallo, kamar wani maye.
Saleh yayi 'yar siyayyar daya saba yi, ya shirya domin kaiwa su Widad ziyara, ya
tafi tasha da nufin ya hau mota, da yake tafiyar dare yake yi in dai zeje garin
dasu Widad suke, ya zuba kayansa a motar haya, ya zaga banɗakin tasha domin ya kama
ruwa, yana fitowa yaji an shaƙa masa wani abu anyi sama dashi, daga nan be sake
sanin inda kansa yake ba se......
LITTAFIN KUƊI NE, DAN ALLAH KI SIYA KAFIN KI KARANTA BA DANNI BA DAN ALLAH, LITTAFI
NA ƊAYA KYAUTA NE WANNAN NA SIYARWA NE
NORMAL GROUP ₦300
VIP ₦500 NE KITURA TA WANNAN ACCOUNT ƊIN
0009450228
JA'IZ BANK
AISHA ADAM
SE A TURA SHEDAR BIYA TA WANNAN LAMBAR
07063065680
IDAN KUMA KIN SIYA AMANACE KARKI FITARMIN DAN ALLAH 🙏🙏🙏
(Albishir ga masoya, ma'abota bibiyar litattaafaina, dama ta samu zaku fara samun
litattaafaina na audio, akan YouTube channel ɗina me suna Cool Arewa TV
https://youtube.com/channel/UCD5vnvA5laU8ti4LLz2_QEg
Kuyi liking sannan ku danna subscribe, domin fara samun litattaafaina na audio,
nagode sosai da ƙaunar ku gareni"
(Albishir ga masoya, ma'abota bibiyar litattaafaina, dama ta samu zaku fara samun
litattaafaina na audio, akan YouTube channel ɗina me suna Cool Arewa TV
https://youtube.com/channel/UCD5vnvA5laU8ti4LLz2_QEg
Kuyi liking sannan ku danna subscribe, domin fara samun litattaafaina na audio,
nagode sosai da ƙaunar ku gareni"
104_105
Saleh dai ne ce komai ba, yana jin yadda ake tafiya dashi a mota 'yan sanda, a
galabaice yake dan haka be san inda suke tafiya ba, harabar police station akayi
parking, aka fito da Saleh, yana tangaɗi haka aka tankaɗa shi cikin cell aka ƙulle.
Duk da yamma ce amma sauro har ya fara shagali a gurin nan, ga zafi a gurin kamar
oven, haka Saleh ya baje a ƙasa ƙirjinsa da cikinsa na masa ciwo kamar zasu tsage,
saboda duk daya sha da katako.
Yana jin wani ɗan sanda yayi sallama, sauram suka dinga sara masa, ɗaya daga 'yan
sandan da suka ɗakko Saleh yace "Oga gashi nan a cell, munje mun ɗakko shi"
"Kai baka san me zaka rubuta ba, ku rubuta bayani akan an same shi da laifin haɗa
kai da Yusuf, sun sace 'yar gidan Nasir Daula, sun ɓoye su, ka dai rubuta abunda
yakamata"
Ɗan sandan ya sara masa yace "ok sir, za' ayi yadda kace"
"Yawwa that's very good, and a matsa shi yadda yakamata ya faɗi abunda ake nema a
gurinsa"
Yace "good"
Nurat tai ajiyar zuciya tace "bad news brother, Daddy ya dage akan cewar wai sena
tafi imperial U. K Inyi karatau a can, me Daddy yake nufi dani ne?"
"Calm down dear, make your statement clear please, kamar yaya imperial Collage, ke
kaɗai zaki koma UK ɗin kiyi karatu, wanda kika yi a baya be isa ba"
"Nima shi na gani brother, shifa yayi min alƙawarin zanyi school a Nigeria, a
Nigeria zanyi high institution, Amma kawai yazomin da wannan maganar, da alama yana
zargina ne da fara bin diddiginsa, ni kuma gaskiya i won't tolerate it dear,
gaskiya zan bijire"
Khalil yace "subhanallah, Nurat don't say that again, haba Nurat na sanki da
biyayya da haƙuri, me zesa ki fara faɗar haka kuma? Haba Sister na"
Kuka Nurat ta fashe dashi tace "Broz Khalil, iya biyayya da haƙuri kasan nayi,
nayiwa Daddy biyayya yadda yakamata, nayi ƙoƙarin kasancewa a cikin 'ya' ya nagari
masu haƙuri, tun taso wata fa kullum cikin tsangwama da kyarar mahaifiyata yake,
amma ban taɓa kulashi akan hakan ba, Brother babu ɗan daze dinga ganin mutuncin duk
mutumin daze dinga cin zarafin mahaifiyarsa, komai kusanci da soyayyar dake
tsakaninsu kuwa, amma na share na ɗauke kai, nake masa biyayya, ni da mahaifiyata
mun masa biyayya, amma baya gani Khalil, baya gani kullum cikin zagi da cin zarafin
mu yake, har gara ni yana ɗagamin ƙafa, akan mahaifiyata lokaci yayi da zan nuna
masa nima 'yar halak ce, zan nuna masa ni ma' yace, wallahi bazan sake masa biyayya
ba nagaji Khalil "
Khalil yace " Calm down, calm down my dear, i feel your pain Baby, kiyi haƙuri dan
Allah, nasan me kike ji a zuciyarki, amma dan Allah karki bijirewa mahaifinki,
hakan ba halinki bane ba"
"Yanzu na koya, kuma shine ya koyamin, kuma zega canji tabbas, na masa biyayya har
akan abunda be dace ba, haka kake so in cigaba da binsa yana jan rayuwata data
mahaifiyata a ƙasa?"
Cikin kuka tace "Khalil, Daddy da farko ni yasa in hilaci Widad, aka sumar da ita
za'a sace ta, Yusuf ya ceceta, wani abunma baze faɗu ba ni kawai ka ƙyaleni, idan
kuma ya dage sena bar ƙasar nan wallahi sena kawo masa ɗan shege ya raina a cikin
gidansa na rantse da Allah "
" Innalillahi wa inna ialaihi raji'un, Nurat kin san me kike faɗa kuwa? Ko kin fara
shaye2 ne ban sani ba"
Ta ƙara sautin kukan ta tace "idan ma ban fara ba ina daf da farawa, dan wallahi ya
takuramin zan bar masa gidansa in shiga duniya, ko in tafi England inyi irin
rayuwar da yake ganin gara inyi irinta da ya kasa cinma nasa burin"
Khalil ya kwantar da muryarsa yace "kina jina Nurat, am sorry kinji, nasan a irin
matsala da damuwar da kike ciki, amma kin san zukata nawa ne zasu shiga garari idan
kika lalace? Mummynki da kike wannan damuwar saboda ita, ya kike gank idan taga
tilon 'yarta ta faɗa mummunar rayuwa? Ya kike tunanin shi masoyin naki ze kalle ki
idan kika koma mutuniyar banza? Family duk zasu shiga damuwa idan suka ji labarin
yarinyar da suke so, suke ji da ita ta shiga wata rayuwa daban, dan Allah kiyi
haƙuri ki bar wannan maganar "
" Brother idan na bar wannan maganar wacce zanyi? Am tired wallahi na gaji dayi
masa biyayya, Khalil abun ba sauƙi fa, dama mutumin kirki ne da sauƙi"
"Nasani Nurat, ki kwantar da hankalinki kinji, Insha Allah zan shigo gidan naku,
zanzo muyi magana amma ki dena kukan nan please, kuma karki sake faɗin wannan
maganar kinji Light" gabata ne ya faɗi jin yace mata Light, sunan da Yusuf ke
gayamata, ajiyar zuciya tayi tayi jifa da wayar, tana ci gaba da rushewa da kuka.
A hankali hannun Amal yana warkewa, an kwance mata bandejin kanta ma, se hannun da
haryanzu akayi hangin ɗinsa a wuyanta, yanzzhma ta fito daga wanka tana tsaye a
gaban madubi, daga ita se towel kanta a tsefe, ta baje gashin kanta, ba laifi
gashinta yana da tsawo, ga hannuta sagale a wuyanta, ga goshinta inda yayi tabon
ciwon da Alhaji Haruna yaji mata, ta dinga ƙarewa kanta kallo a mudubi.
A hankali tace "dubeni, mace har mace, bani da makusa sedai an gurguntamin rayuwa,
an rabani da mutuncina saboda zalunci, kuma ya biyoni da wasu tarkacen banza saboda
ya rainamin hankali, bayan tabo na sarari da yayi min, ya barmin na zuciya me
matuƙar ɗaci da baze goge ba, me zanyiwa mutumin nan in huxe, wace irin illa zan
masa daze dasa masa baƙin ciki a rayuwar sa ne? Me zanyi ne Amal kiyi tunani
ƙwaƙwalwarki bata ja Sam "
Ta dafe kanta ta fashe da kuka, tana tuna yadda ya suka dinga kokawa, da muguntar
da yayi mata yacinma burinsa, zubewa tayi a gurin tana wani irin kuka, me tsuma
zuciya
" Duk laifinki ne Mummy, laifin kine, nace ba zani ba kika ce se naje, Mummy why? "
Jikinta har rawa yake saboda kuka, dukda daga wanka ta fito amma ta haɗa gumi, ga
hawaye ga majina se shesheƙa take.
Ramlah ta shigo ɗakin, ta tarar da ita a zaune a ƙasa, idonta yai ja tana kuka.
Ramlah ta ƙaraso da sauri tace " ke Amal lafiya kuwa? Meye haka? Meye ya same ki"
"Bakomai"
Tsaki Amal Tayi tace "excuse me please, dan Allah ki bani guri, ina son kaɗaicine"
"Na miki kama da Widad ne, balle kice na haukace? Kawai ki fita ki bani guri"
"Amma Amal"
"Dan Allah ki fita ki ƙyaleni, kad in haɗiyi zuciya in mutu, dan Allah ki fita!"
Tai maganar cikin kuka, Ramlah na fita taje ta dstse ƙofarta ta kwanta akan gadonta
ta cigaba da rera kukanta, tana jin Ramlah ta kira Mummy, suka dinga buga ƙofar
amma tayi musu banza kamar ba taji ba.
Bukar ya kira Alhaji Haruna, Ya ɗaga wayar suka gaisa, Bukar yace "kunyi waya da
Musa ne?"
Alhaji Haruna yace "A'a gaskiya, na kwana biyu bamuyi waya ba"
Alhaji Bukar yace "ok, na zaci kunyi wayane, haryanzu be ce mana komai ba akan
batun wanda ze saka mana hannun, kuma yace mu saurareshi zuwa Laraba, anjima zamuyi
meeting kota zoom ne, sannan ya batun takaddar da aka ce wannan yaron ya bari? Ka
karɓo mana ɗinne kokuwa?"
Alhaji Haruna yace "eh na karɓo, naje har gidan da kaina naje na karɓo takaddar"
Alhaji Bukar yace "good, kasan duk wata sheda da zesa a ganemu, dole mu ɓatar da
ita kar wani ya samu, dan haka ka kawomin takaddar nan"
Yace "shikenan, Insha Allah zan kawo maka ita, sannan zan sanar dasu batun meeting
ɗin nan da kace"
Alhaji Bukar ya ajiye wayar, ya miƙe ya bar ɗakin dayake, dan ya manta da ya karɓi
tajaddar yazo da ita nan gidan ko kuma a can ya barta gurin da ta bashi?.
Hindu tana tsakar gida, suna ta aiki a tsakar gida, Hanne tana gefe tana gyaran
wake zasuyi alala.
Hari tace "sannu da aiki Hanne, Allah ya kaimu bikinki mu kira masu kiɗan ƙwarya
muyi ta juyi a gidan nan"
Hanne ta taɓe baki, dan ita sama gaba ɗaya haushin Auren nan ma take ji, dan Yanzu
haushin mijin da zata aura takeji, dan gani take bashi da komai idan ta kalli
Yusuf, ita dai tana son Yusuf sosai, tana jin ina ma ya aure ta, da tafi kowacce
mace dace a ƙauyen nan, da yana ɗan kulata amma yanzu ya dena, saboda wannan
koɗaɗɗiyar matar tasa me kama da Yahudawa.
Hindu tace "Allah dai ya kaimu bikin nan ds rai da lafiya, ban san wane irin
shagali zanyi ba, nima sena gyagije nayi shagali, idan kika tattara kika tafi in
gaje gurin kwanciyar ki da nawa, Abinci ma zan haɗe nawa da naki ne, dama yanzu ba
ƙoshi nake ba" Hindu Tayi maganar cikin sigar wasa da zolaya.
Amma Hanne ta karkace ta kyaɓe baki, ta kalli Hindu tace "aifa dama ina zaki ƙoshi
tunda mayya na gidan? Ai gara in tattara in bar miki gidan ki cigaba da haɗa
kafaɗunki dana iyayen mu, tunda dai ke kinfi kowa baƙin jini, babu wanda yake sonki
balle kisa ran zakiyi aure ki bar gidan nan, ai se kiyi ta zaman gidan ki ƙare ki
tsufa a gida, mujiyar garin nan, shikenan mutum ba zuciya balle ya samo wanda ze
rufa masa Asiri ".
Ai tuni idon Hindu ya ciko da hawaye, ita har ga Allah wasa tayi wa Hanne, amma
harta fara yan kamata baƙaƙen maganganu da cin zarafi, Hanne na ɗagowa suka yi ido
huɗu da Yusuf, da alama duk yaji abunda ta faɗa, sekuma ta shiga kame kame, dan
wata irin kunyace ta kamata, bece komai ba ya sa kai ya fice, dan be fiye son shiga
sabgar iyalan gidan ba.
Yana fita Widad ta fito tsakar gidan nan, taga yadda Hindu ta nutsu tayi shiru, ido
duk ya tara hawaye saboda zafin maganganun Hanne.
Widad tace "ke Hindu, wai ita wannan banzar 'yar uwar taƙi haifarki tayi? Haifarki
Tayi da zata dinga gaya miki magana kina jinta? Wai wane ɗan matsiyatan zata aura a
garin nan da har take miki wannan gorin haka? Wanda zata aura ɗin ma ya kai a kira
shi namiji da take miki gori a kansa "?
Hanne tana hura hanci, cike da ƙauyanci da jahilci tace " Wallahi, tallahi nafi
ƙarfin auren matsiyaci, niba matsiyaci zan aura ba"
"wallahi kika bari nazo inda kike, na shaƙeki se na jefa ki a rijiyar nan, saboda
me zaki takurawa yarinya dan bata magana, dan kinga tana da haƙuri, wallahi ki
kiyayeni akan ɓata mata rai"
Wata irin zuciya ce ta kwashi Widad, sedai Hindu tai saurin riƙeta tace "A'a
Amarya yi haƙuri ƙyaleta kawai"
Widad ta harzuƙa matuƙar gaske, ji take tamkar ta jefa Hanne a rijiya, mussman idan
ta tuna yadda take juya manyan attajirai masu ji da kansu, amma wata kucakar 'yar
ƙauye na gayamata magana, ƙwafa kawai tayi tace "ba alfahari ba amma Wallahi da
kin san wacece Widad, da baki isa ki yadda in haɗa ido dake ba, dan wallahi ko masu
gyaran gadon baccina sun fiki kyan gani, ki zuba ido zakiga mijin da Hindu zata
aura, Jahila kawai"
Ta wuce ɗakinta tana huci, duk wannan budurin Gwaggo da Hari basa nan akayi shi,
amma abun yana damun Widad taji an taɓa Hindu, setaji kamar ita aka taɓa, danma ita
Hindun ce shashasha take tsayawa ana mata wulaƙanci.
Amal kam wani tunani tayi a ranta, dan haka ta miƙe da ɗan sauri, ta fita falo,
Mummy ta kalleta tace "kinga damar buɗewa yanzu?"
Amal tace "Mummy Ramlah ta kasa fahimta tane, wani lokacin idan ina cikin jin
zafin ciwo, bana son kowa a inda nake, nafison kaɗaici amma se a takuramin, kun
kasa ganewa"
Tace "da sauƙi, Mummy dan Allah aramin wayarki zan transfer ɗin kuɗi, ni banki sun
hanani wai ba network"
Ba musu ta miƙawa Amal wayar, Amal ta karɓa ta koma gefe, ta tura lambar Alhaji
Haruna wayarta, ta bata wayar tace "Mummy, ga wayar nagode"
Ta koam ɗakinta, tana zuwa ta kulle ƙofa ta zauna akam gadonta ta kira Alhaji
Haruna.
Lokacin yana tsaka da bulayin neman takadda, ya ɗaga suka gaisa dashi, sannan tace
"Naga saƙonka, amma meyasa kwana biyu ba kazo ka dubani ba"
Se ynzu ya ɗau muryar ta, yai murmushi yace "nima naji saƙonki, ance bayan mota
zakizo karɓar gids ma"
"zuciya ta, ta fara rayamin kawai idan na warke zan bazama in nemi arziki, in more
ƙuruciya ta, idan ka shirya nima a shirye naake zan dawo gareka, tunda aikim gama
ya gama tunda fari"
Yai wata shegiyar dariya sannan yace "ni zaki yaudara, ko har kin manta abunda kika
gayamin a Asibiti, kaina yana ja sosai dan haka abune mawuyaci kiyi galaba a kaina,
tabbas naji daɗin kasancewa dake sedai bazan sake amincewa dake ba, tunda kikayi
wannan fueucin, ki sake shawara kinji 'yan mata, idan da gaske kike ki bazama ki
kama wasu alhazan, nikam na gama muma na biya tunda na bada motar miliyoyi"
Bata sanma yadda akayi ta ajiye wayar ba, tana jera ajiyar zuciya kamar wadda tai
gudu, duk yadda take tunanin abun ya wuce tunaninta, ashema matan suna suka tara,
ba kowaccece ke iya kaidin ba, shi kansa shirya makircin ba abune me sauƙi ba, tai
sharkaf da gumi tana sake tunanin wata hanyar.
Yusuf na dawowa Widad ta manta da damuwar da take ciki, sedai duk da hakan seda ya
gane, yace "Maman Baby, ya akayi ne naga kamar ranki a ɗan ɓace yake"
Tace "A'a ni ba abunda akayi min, Ina ɗan tunani akan Hindu ne, ina ma Megari ze
bani ita idan mun koma gida"
Yusuf yace "gaskiya abune me wahala, ya ɗau 'ya ya bamu alhalin bamu da wata
dangantaka a tsakaninmu"
Ta jinjina kai tace "hakane, Gaskiya nifa na damu Saleh yazo ayi wacce za' ayi, na
fara gajiya hankalina yayi gida sosai fa"
Yusuf yace "ki kwantar da hankalinki, nima shi nake jira yazo, muji abunda yakamata
ayi"
Yace "Ameen"
A gurin 'yan sandan ma babu sassauci, baƙar wahala Saleh yake sha, dan yana
kyautata zaton an masa illa saboda duka, dan a nan ɗinma' yan sanda ke sa kulki,
suyi ta dukansa izaya daban daban wai lallai seya faɗi inda su Yusuf suke, ga
rashin Abinci gashi ko Najasa ne sedai yayi a nan, nan da nan Saleh ya fita daga
hayyacinsa, ya canza kamanni fuska duk ta kumbura, ko ina rauni me yake zubda jini,
sun doddoke masa ƙafafuwa da ƙyar yake iya miƙewa.
Da Safe Yusuf yana kwance akan cinyar Widad, ta samu comb se jagwalgwala masa sumar
kansa take yi, shi kuma yana lumshe ido, can yace "gaskiya ki ƙyalemin gashina
mana, haba se izaya kikemin a kaina"
"To aini na gaji se jagwalgwala min suma ake, ga zafi banda ma tsabar rigima irin
taki ta ina za'a kitsa sumata?"
Yace "shikenan, Allah sarki ni, gaskiya idan na kuma jin zafi sena rama, sena aske
wannan gashin naki da akewa mutane iyayi dashi"
Tai murmushi tace "daka temakeni, dan ba dan babu kyau ba sena rage shi, kuma idan
ka aske ai kanka kayiwa, kaine kake wasa dashi ai"
Ta sunkuyar da kai cikin matuƙar jin kunya, Widad tace "sarkin kunya, idan na aura
miki ɗan birnin haka zaki dingayi masa?"
Hindu ta juya da sauri tana murmushi, ta bar ɗakin, Widad tace "Yuzarsef, wallahi
da ina da Yaya, ko wani ɗan uwa da babu abunda ze hana in roƙi ya auri Hindu, she's
very kind and innocent"
Yusuf yaga abun na Widad ba na ƙarewa bane, dan haka ya tashi daga cinyarta yace
"ke nagaji, kaina se zafi yake duk kin jagwalgwala min suma"
"ni kayiwa haka ko? In ƙara ganin ka taɓamin gashi ni da kaine, kuma ma insha Allah
ta mace zan haifa, saboda in dinga mata kitso ta zama ƙawata kuma"
Yusuf yace "sannu sarkin shirirta, da shirme, ga tsabar ƙuruciya mutum baze gane
hakan ba, se ya zauna dake, to ni bame yiwa 'yata kitso balle a jagwalgwala mata
kai, idan kin haifi namiji nakine, mace kuma ta wace"
"A' a ban yadda ba, gaba ɗaya nawane, bayan kace baka son Baby"
Yusuf yace "Nina ce miki bana so? So kai amma ki bari ki samu cikin tukuna, sekimin
iyayi da tsari"
Yace "zan miki ƙarya ne? Kin manta shekarata biyu ina medicine, baki da komai
madam"
Ta kwaɓe fuska kamar zata yi kuka tace "insha Allah ina da shi"
Yusuf yace "idan na dawo da daddare, kwaɗon gurji da zogale zan mana, zaki ci?"
Widad tace "Sosai ma, ranar Gwaggo tayi naci da daɗi Sosai"
Duk iya dubawar da Saleh zeyi, yayi amma ya rasa takaddar nan, ya duba ya duba amma
takadda tace ɗaukeni inda ka'a ajiyeni, gashi yacewa Bukar ya karɓo takaddar nan.
Ya koma guest House ɗinsa, inda suka dinga kokawa da Amal, ya dinga duba takaddar
nan, yai tsai gana dubawa ya birkita komai, ya hango ta a ƙasan gado.
Hamdala yayi, ya durƙusa ya ɗakko takaddar, yana ajiyar zuciya ya buɗe takaddar,
sedai me ba takaddar bace form ne na koyon kwalliya na Amal, tsaki yayi yai jifa da
takaddar yana tunanin ina yasa waccan takadda data bashi, amma kuma lokacin da ta
bashi takaddar ai be buɗa ba, balle yasan me ta bashi, hankalinsa na kan yai mata
akuyanci kawai, ya birkita ko ina amma babu wata takaddar se wannan, nan take gumi
ya shiga tsasttsafo masa.
Widad taita jiran Yusuf ya dawo, dan se nishaɗi take ji ze kawo gurji yayi musu
kwaɗo, bayan ya dawo da kayan gurjin da yamma, ta zauna ta cire ɓawon tsaf, ta
gyara zogalen suka ɗora zogalen akan wuta, suna zaune suna hira a ƙofar ɗakinsu
suna aikin su, hankali kwance yayin da zamantakewarsu kan burge wasu daga mutanen
gidan.
Ya gama suka haɗa Kwaɗon nan a roba, Suka bawa wanda zasu bawa, Widad se haɗiyar
yawu take, ta zauna zata saka hannu ta fara ci Yusuf yace "tsaya waye yace ki fara
ci, salon ki fini loma ki fini ci ko?"
Ai ba ta saurareshi ba, danji take kamar hanjinta ze fito idan bata ci ba, jiki na
rawa ta sa hannu ta fara cin Abunta, Yusuf yana kallonta yana nazarinta, tunda ta
fara ci bata saurareshi ba seda taji ta ƙoshi tukuna, ta miƙe taje ta wanke
hannunta ta sha ruwa ta dawo ɗaki sannan tace " Yawwa ina jinka, mema kace ɗazu?"
"Yawwa mijin acici, kai dai ubangiji Allah yayi maka albarka, ya saka maka da
alheri nagode sosai"
Kawai ta kwashe da dariya tace "ba ruwana cin abuna zanyi ehe"
Tace "What? Wai Yoseef meye haka? Kawai ba damar inyi magana seka canza mata
ma'ana"
Tai maganar tana kai masa duka, ya kwanta yana dariya yasa pillow yana karewa.
"Eh naji bakomai, a haka 'yan mata suke rububina, saboda munina a haka suke sona"
Widad tace "Wallahi idan muka koma gida, duk wadda tayi gangancin raɓarka zata ga
matakin da zan ɗauka wallahi"
Yace "haka akeyi, shikenan duk suna kallo se kice baza'a kulani ba, bayan kin
sanni da farinjini, cewa fa kika yi in Auri Hanne"
Tsaki tayi zata tashi, ya fizgota jikinsa, yasa fitila ya haske mata fuska.
Da sauri tace "No, i don't mean you should divorce me, ka cikani i mean"
Yai murmushi yace "nima na sani ai, ni dake ai mutu ka raba Babayna me kama da
teddy"
Tace "Yoseef me yake damunka ne yau? Duk ka takuramin nice kuma me kama da teddy?"
"Eh ramawa nayi, ko kin manta haka kika cemin cartoon jiya"
Yai maganar yana dariya, itama dariyar ce ta kamata, ta buɗe baki kamar zata cije
shi, amma ta fara kissing ɗinsa.
Kamar ranar suka fara kasancewa da juna, sunyi nishaɗi mara misaltuwa, sun
farantawa junansu rai sosai, kowanne yana sake jin ɗan uwansa a ransa.
Haka suka wayi gari cikin farin ciki, sedai dukda wannan farincikin Yusuf se fama
yake da fargaba, ya rasa dalilin hakan.
Yana ta shiri ze fita, yaji kamar harbin bindiga, gabansa ya faɗi yace "Lovely,
kamar harbi fa nake ji"
Widad tace "A'a ko dai tunanin gurin aiki kake, amma wane irin harbin bindiga ana
zaune ƙalau? Bari inyi walha, idan na idar seka tafi"
Ta juya ta tada salla, tayi raka'ar farko zata yi ta biyu suka ji Hayaniya, aka
sake harba bindiga a ƙofar gidan mutane nata guje guje.
Daga tsakar gida suka ji ana "duk wanda ya motsa, zamu fasa kansa da bindiga, kowa
ya tsaya a inda yake"
Gaba ɗaya jikinsu se tsuma yake, Hari ta samu wani lungu a bayan randa ta shige, se
zare ido take saboda tsoro.
Nan da nan sega jiniyar motar' yan sanda ta ƙaraso
Da gudu Widad ta fito tsakar gidan, amma taga 'yan sanda tare da Saleh hannunsa duk
ankwa a cikin mawuyacin hali.
Widad tace "ban sani ba, bazan faɗi inda yaken ba"
Hari daga inda ta laɓe tace "Wudas ki dena magana karsu kashe ki fa"
Yusuf ya fito daga ɗakinsu, jikinsa sanye da jallabiya, ya ƙarasa gabansu ya miƙa
musu hannunsa cikin surrender
.
Widad ta fashe da kuka tace "No! This is impossible, me yayi muku? Laifin me yayi
mijinane fa, ku cire masa wannan cuff ɗin"
Su kai mata banza suka tasa ƙeyar Yusuf, itama suka sata a gaba ihu take tana
kururuwa akan su sake shi amma sukayi burus da ita.
Aka sashi a bayan motar 'yan sanda, idonsa yayi ja ya kasa magana, se kallonta da
yake gaba ɗaya ta birkice se ihu take tana kuka, muryarta harta fara dashewa.
"Ina sonka, Yusuf ina sonka, I love you Yusuf, dan Allah ku sakarmin mijina, beyi
laifi ba, beyi laifin komai ba"
Yusuf ya ƙura mata ido, ya lumshe idonsa a hankali, yayin da Widad ke zubda wani
irin hawaye tana kuka, me sauti.
Aka sakata a motar gida seinna, shikuma a bayan motar 'yan sanda gashi ga Saleh,
kowanne hannu da sarƙa!!!
LITTAFIN KUƊI NE, DAN ALLAH KI SIYA KAFIN KI KARANTA BA DANNI BA DAN ALLAH, LITTAFI
NA ƊAYA KYAUTA NE WANNAN NA SIYARWA NE
NORMAL GROUP ₦300
VIP ₦500 NE KITURA TA WANNAN ACCOUNT ƊIN
0009450228
JA'IZ BANK
AISHA ADAM
SE A TURA SHEDAR BIYA TA WANNAN LAMBAR
07063065680
IDAN KUMA KIN SIYA AMANACE KARKI FITARMIN DAN ALLAH 🙏🙏🙏
(Albishir ga masoya, ma'abota bibiyar litattaafaina, dama ta samu zaku fara samun
litattaafaina na audio, akan YouTube channel ɗina me suna Cool Arewa TV
https://youtube.com/channel/UCD5vnvA5laU8ti4LLz2_QEg
Kuyi liking sannan ku danna subscribe, domin fara samun litattaafaina na audio,
nagode sosai da ƙaunar ku gareni"
11/17/21, 5:35 PM - Buhainat: LITTAFIN KUƊI NE, DAN ALLAH KI SIYA KAFIN KI KARANTA
BA DANNI BA DAN ALLAH, LITTAFI NA ƊAYA KYAUTA NE WANNAN NA SIYARWA NE
NORMAL GROUP ₦300
VIP ₦500 NE KITURA TA WANNAN ACCOUNT ƊIN
0009450228
JA'IZ BANK
AISHA ADAM
SE A TURA SHEDAR BIYA TA WANNAN LAMBAR
07063065680
(Albishir ga masoya, ma'abota bibiyar litattaafaina, dama ta samu zaku fara samun
litattaafaina na audio, akan YouTube channel ɗina me suna Cool Arewa TV
https://youtube.com/channel/UCD5vnvA5laU8ti4LLz2_QEg
Kuyi liking sannan ku danna subscribe, domin fara samun litattaafaina na audio,
nagode sosai da ƙaunar ku gareni"
106_107
Sosai Widad ta cigaba da gunjin kuka, yayin da mutanen ƙauyen suka fito suka yi
duru duru suna kallo, ɗaliban Widad se kuka suke, haka Hindu gaba ɗaya ta birkice
banda kuka ba abunda take yi, ba Hindu ba kawai hatta Megari, da su Hari hankalinsu
ya tashi sosai, ga Sunusi mijin Jamila baya nan akazo aka kama su Widad.
Ana tafe a hanya amma bakin Widad yaƙi mutuwa, kuka kawai take akan a sakar mata
mijin ta, tun Yusuf yana iya juyo muryarta da kukanta, har muryar tata ta dashe ba
ajin me take faɗa sosai, haka sukaita tafiya har suka fito daga wannan kwazazzaban,
da ramukan dake hanyar garin, suka hau kan kwalta ɗoɗar suka kama hanyar Kano.
Alhaji Haruna fa ya haɗa uban gumi, saboda ya tabattar da babu wannan takadda,
takaddar form ɗin koyon kwalliya ta bashi, ba shiri ya ɗau wayarsa ya kirata da
lambar da ta kirashi ɗazu, tana ganin kiran nasa Amal ta tashi da sauri, ta duba
har zata ɗaga kawai ta fasa, ta ajiye wayar yai mata kira yafi Ashirin, ƙarshema ta
saka wayar a silent tai kwanciyarta.
Yai wujiga wujiga, saboda takaddar nan saboda yasan Bukar ba kyau, gashi ya riga
yace aiya karɓo, tunda takaddar zata iya zama sheda a kansu, wannan wasiƙar zata
nuna akwai halin rashin gaskiya da mahaifiyar Anwar take aikatawa wanda yasa ya bar
gida, idan tuhuma tayi tuhuma kuma za'a gano su.
Ya tura mata saƙo kusan kala shida amma babu reply, can dai ta ɗau wayar ta duba
saƙon daya turo, magiya yake mata akan dan Allah ta ɗaga wayarsa, mahimmiyar magana
yake son suyi.
Tana cikin karantawa kuwa ya kuma kira, seda taja aji sannan ta ɗaga, yai ajiyar
zuciya yace "habba kyakkyawa, tun ɗazu naake kiran waya, amma anyi biris dani?"
"A'a kwantar da hankalinki, ai duk abun bana zafi bame ko ɗaga hankali, magana
zamuyi"
Yace "Yawwa, dama cewa nayi wannan takaddar da kika kawomin, kinyi mistake ba
wasiƙar kika bani ba, form ɗinki ne na koyon kwalliya, kinyi mistake gurin bani"
"A'a dama ba wani abu bane ba, cewa nai zanzo in karɓa in an jima, saboda takaddar
tana da mahimmanci sosai"
"Karka sake ka soma zuwa inda nake, bazan bayarba ka riƙe wadda na baka a matsayin
ta"
Alhaji Haruna yai gyaran murya yace "haba beautiful Baby, ai abun duk bekamata ya
kaimu ga haka ba, meye na ɗaukar zafi haka? Ai abun bana zafi bane ba, ki gayamin
me kike so ayi yanzu in karɓi takaddar nan? Ko nawane zan baki"
Amal ta janyo Jakarta, wadda yace tayi accident da ita, ta duba amma itama taga
babu takaddar a ciki, amma tai ajiyar zuciya tace "nima nazo maka da buƙata ta,
amma kaƙi amincewa, dan haka kowa ha riƙe buƙatarsa, bazan bayarba gara asirin kowa
ma ya tonu a huta"
Yace "dan Allah kar muyi haka dake, ki bani takaddar nan na riga na cewa Bukar na
karɓo takardar yace in kai masa, kuma yanzu inzo ince bahaka ba, baze sauraramin
ba"
Amal tace "Ai gara karya saurara makan, kamar yadda nima baka sauraramin ba, kuma
baka karɓi buƙata ta ba"
Am tace "A'a ai kuma mun wuce wannan maganar yanzu, zan baka takadda bisa sharuɗa,
yanzu abu na farko zan gaya maka Account Number ɗina, ina son inji wasu kuɗi masu
nauyi, domin inci kaji in warke da wuri daga raunin daka min"
Ta kashe wayarta, lumshe ido tare da faɗin "Alhamdilillah, cikin sauƙi Allah ya
kawomin hanyar da zan rama cin zarafin da kayi min, tabbas inaga yadda takkadar nan
nayi, dan babu ita a jakata, amma a haka zan maka rashin mutunci in rama"
Alert ne ya shigo wayarta, ta ɗaga ta duba 500k ne, ta jinjina kai tace yanzu aka
fara wasan
Seda yayi mata kira biyar, sannan ta ɗaga a fusace tace "wai meye ne?"
Ta katse kiran tare da kashe wayarta gaba ɗaya, ta kulle ɗakinta da key, tai
kwanciyarta.
Tunda suka taho Yusuf bece uffan ba, yai shiru yana saƙawa yana kwancewa a
zuciyarsa, tabbas duk sunan da za'a kira shi dashi, ko a tuhume shi dashi, bashi da
abunda ze kare kansa dashi, tabbas shi dai tunda ya tashi a rayuwarsa a siraɗin
ƙaddara yake, daga wannan ya faɗa waccan, daga waccan ya faɗo wannan, haka ya
sunkuyar da kansa yana ta tsabihi ga Allah, akan ya sauƙaƙa masa wannan lamarin.
Sun shigowa cikin garin kano, akayi hanyar babbar headquarter hukumar 'yan sanda
dake garin kano, motarsu Widad kuma tayi wani gurin, ai tana ganin haka ta kuma
fashewa da ihu, tana bori tana kuka tana "ina zaku kaishi? Ina zaku kaimin
mijina? Beyi laifin komai ba, babu abunda yayi muku, ku ƙyalemin mijina wayyo Allah
na Yoseef duk nice sila, saboda ni ka shiga wannan tashin hankalin, Dan Allah ka
yafemin Yoseef, Allah ka fitar da mijina daga sharrin Azzaluman nan, Allah ga
bawanka ka fitarmin da mijina"
Ta ƙarasa maganar, tana wani irin kuka me taɓa zuciya babu wanda ya kula ta a cikin
'yan sandan suka cigaba da tafiya.
Wani ofishin' yan sandan aka tafi da ita, suka fito da ita daga mota zuwa gurin
'yan sanda, idanunta sun kumbura sunyi ja saboda kuka.
Wani ɗan sanda yace "gata yallaɓai, yanzu muka shigo gari, shi an wuce dashi
headquarter, ita kuma gata"
Ɗan sandan ya kalleta yace "Good, Madam congratulations, you are now free, mun
cetoki daga hannun wanda sukayi garkuwa dake"
"Niba garkuwa yayi dani ba, wanda sukayi garkuwa dani daban, Yoseef ceto na yayi,
shine ya temakeni beyi garkuwa dani ba, ka gaya musu suje su sakarmin mijina"
Ɗan sandan yace "koma dai ya akayi, wannan ku ta shafa ke dashi, muba abunda ya
dame mu, zamu rubuta sannan mu sanar da duniya cewar, munyi namijin ƙoƙari gurin
bincike mun gano wanda yayi garkuwa da Widad Nasir Daula, kuma ba wani bane face
direbanta, wanda ya kasance ɗansanda, yaje gidansu yai basaja dan yayi garkuwa da
ita, nasan hakan ze sake ɗaga darajar rundunar mu a ga namijin ƙoƙarin da muke, ba
dare ba rana gurin kare rayuka da kuma dukiyoyin al'umma "
Ta faɗa cikin ƙaraji, tace " idan har ina raye ina numfashi, ko komai nawa ze ƙare
se Yusuf ya fita, babu wanda ze cutarmin dashi, baku isa ba azzalumai ma cuta,
lokacin da aka yi garkuwa damu muna buƙatar taimakk, babu wanda ya taimakemu na
kusa rasa rayuwa ta, se yanzu da yayi komai ya gama, Allah yasa ya kare rayuwata,
shine za'a masa sharri wallahi bazan lamunta ba, he's my Husband "
Ɗan sandan nan yace " ku ɗaukemin wannan mahaukaciyar daga gabana, a tafi da ita
Asibiti a duba lafiyarta, sannan ku kiramin Ubanta Bulama tunda babu wanda yasan
inda wancan yake "
Widad bata gane meyake nufi ba ta cigaba da kukanta, haka suka kawo Ambulance dan
iya makirci, aka sheƙa mata wani abu ta sume a gurin, aka kira 'yan jaridu suka
cika gurin, aka ɗauki Widad aka saka ta a motar Agajin gaggawa wato Ambulance suka
tafi da ita.
Jaridu kuwa da sassafe shafin farko, hotunan Yusuf ne da Saleh, musamman na Yusuf
ɗaure a cikin sarƙa ya sunkuyar da kai, gefe ga hoton Widad da aka ɗauka an fito da
ita daga ofishin 'yan sanda an sata a ambulance, daka kunna gidan radio, labarai ko
talabijin babu abunda zaka fara ji se
"Me dokar bacci ya ɓige da gyangyɗi, kuma ƙarshen tika tiki tik inji hausawa A
yaune jami' am tasaro sukayi nasarar cafke jami'in ɗan sandan nan na farin kaya
wato Yusuf Bashir Maitama, wanda yayi garkuwa da 'yar gidan fitaccen me Arziki nan
a gida da wajen Nigeria wato Nasir Daula,' yan sandan sunyi nasarar gano shi ya
sace ta tare da ɓoyeta a wani ƙasurgumin ƙauye dake garin Bauchi, 'yan sandan sun
ceto Widad Nasir Daula, wadda ke cikin mawuyacin hali, da zauwansu basu yi wata
wata ba aka kira motar Asibiti aka tafi da ita domin duba lafiyarta, zamu ci gaba
da bibiya da kasa kunne domin jin wani mataki hukuma zata ɗauka akan wannan ɗan
sanda, wanda ake tunanin har shi Nasir Daula ɗin shine yai garkuwa dashi, mu dai
anan se muce Allah ya kyauta, yai mana tsari da irin wannan jam'ian tsaro a cikin
al'ummar mu"
Nan fa gari ya ɗau ɗumi, aka dinga cece kuce, wasu na Allah wadai suna Tsinewa
Yusuf, yayin da wasu ke a bari a ga abunda bincike zeyi tukuna.
Widad kam bata sake sanin inda kanta yake ba, inda har a gadon Asibiti aka bita aka
dinga ɗaukar hotunan ta, ga fuskarta tayi ja saboda kuka, da gajiyar tafiyar hanya,
amma aka dinga ɗauka ana watsawa duniya wai tana cikin mawuyacin hali, hannunta
ɗauke da drip.
Alhaji Haruna ya kasa zaune ya kasa tsaye, ba a taɓa raina masa hankali kamar yadda
akayi yau ba, ya kira layin Hajiya Halima, Ramlah na zaune a falo wayar ta fara
ringing, Mummy tana ciki tana amsa wata wayar dan haka ta ɗaga wayar tasa a
kunnenta tace "Hello"
"Dan Allah idan Amal tana kusa ɗan bata wayar muyi magana"
Ta miƙe ta tafi ɗakin Amal, amma ɗakin a rufe harta kashe fitila ma "
Ramlah tace " gaskiya tayi bacci, dan ta rufe ɗakinta ma ta kashe fitila"
Yace "Yasalam"
Ya kashe wayar yace "Amma dai Allah ya Tsinewa yarinyar nan, kaga min shegiyar
yarinya mara albarka" ya ciji yatsa yai ƙwafa yace "dani kike zancen wallahi, kema
sema wulaƙantaki,"
Amal ta ɗau wayarta ta tura masa saƙo tace "ka cigaba da kiran Mummy, kana cewa
kana son Magana dani, wallahi idan baka yi wasa ba sena gayamata abunda kayi min,
kuma kasan halinta sarai, kasan buyaginta zata maka abunda kai kanka zaka kasa gane
kansa, dan haka muddin ba zaka cika sharaɗina ba, wallahi ba zan baka ba na gaya
maka, kuma ni wannan kuɗin sunmin kaɗan, nima a account dina ina da wanda suka
fisu"
Ta kashe wayarta ta sake kwanciya, ya duba message ɗin, yaja wata ajiyar zuciya
yana cije leɓe, totally ta riga ta gama raina masa hankali, yama rasa me zeyi ko me
zece.
Yana nan tsaye yana tunanin mafita kiran wayar Bukar ya shigo wayarsa, ya ɗaga jiki
na tsuma, yace "Hello"
"Haruna, yau muna da zama na gaggawa, cikin dare dan haka duk ku tattaru"
"banda ita, sannan kazo min da wannan takaddar, zamuyi magana a kai itama"
Daga nan ya kashe wayar, Alhaji Haruna ya yakice gumi, yana huci Amal ta masa
rashin mutunci, dan kawai abu ya shiga tsakaninsu se tayi masa haka?.
Mutan ƙauyen da Widad suka zauna suka dinga taradaddi, kowa da abunda yake faɗa
wasu suna dama megari yayi wauta, wataƙila dama can 'yan fashi ne ko wasu masu
laifin ne, amma daga zuwansu ya karɓesu, be san daga inda suke ba.
Hindu kam kuka, kamar wadda aka kama uwarta, ita kanta Hari gaba ɗaya jikinta a
sanyaye yake, wunin ranar gidan daga masu koke koke, se masu salallami, Hanne kuwa
ko a jikinta.
Koda Sunusi ya dawo, Jamika ta gaya masa abunda ya faru, dan haka yace dole gobe
insha Allah ya tafi kank, yaje yaji ba'asin abunda ya faru.
Jamila tace "dan Allah karkaje, kar kaima a kama ka, dan na san da kana nan
wataƙila da kai zasu haɗa"
Sunusi yace "da nayi musu me? Kince an kama Saleh, kuma Saleh shiya kawo su nan,
meyasa aka kama shi, dole zanje inji"
Daddare megari ya tara iyalansa yace "to wannan bayin Allah dai, ni dai a ɗan
zaman da mukayi dasu, ban tunanin mutane ne marasa gaskiya, ko makamancin haka,
zamanmu da su ma mu alkhairi ya zame mana a garin nan, dan haka dan Allah ina
roƙonku da kuyi haƙuri ku dena kuka, kukan ya isa haka, Hasana nasanki da son 'ya'
ya kuma zamanmu dasu jin shaƙu dasu sosai, dan Allah kidena kuka kiyi musu Addu'a,
Hindu Baffa kema kukan ya isa haka, muyi musu Addu'a, Allah ya basu mafita sannan
Hari a samo makulli a rufe musu ɗakinsu, kar wanda ya sake shiga tunda da kayansu a
ciki "
Hari ta tashi ta shiga ɗakinta ta samo mukulli, tana ƙoƙarin rufewa taga bokitinsu
a tsakar gida, ta tafi ta ɗakko bokitin, kawai ta fashe da kuka tace " Allah sarki
Wudas, da yanzu muna faɗa akan ruwan zafin da zata yi wanka, tace sena bata na bawa
mijin ta, ban taɓa ganin abun tausayi kamar yau ba, yadda ta rikice tana kuka,
Allah sarki Allah ya fitar dasu"
A kaita bata haƙuri, aka kulle ɗakinsu aka bawa Megari mukullin, ya kai ɗakinsa ya
ɓoye.
Yusuf yana kwance a cikin cell, an raba masa cell shida Saleh, sauro yana ta masa
buduri a ka, yai rigingine yana tunanin ya Umma zataji idan wannan mummunan labari
ya isheta?.
Aka buɗe ƙofar cell ɗin, wasu 'yan sanda suka shigo su biyu, ya tashi zaune yana
kallon su.
Ɗaya ya kalleshi yace "munafuki, kalleshi kamar na Allah, amma ƙasurgumin Azzalumi
ne, kai garkuwa da' ya ka koma kayi da Ubanta, saboda kai Azzalumi ne, kuma a haka
wai kai ɗansanda ne"
Yusuf yai shiru be ko ɗaga kai ba, ɗayan yace "rabu dashi corporal Sani, zuwa gobe
in Allah ya kaimu semun sauya halittun fuskarsa, kafin 'yan jarida suzo, a buga shi
a nunawa duniya shi, azzalumin banza dana wofi kawai"
Yusuf dai yai shiru bece komai ba, suka gama zage zagensu suka fita, suka sake rufe
shi, tun Abincin safe Yusuf be kuma cin komai ba, ga doguwar tafiyar da suka yi,
amma sam baya jin yunwa tunanin makaomarsa kawai yake a wannan hali da yake ciki.
Nurat na kwance cikin dare, taji Mahaifinta yana waya ƙasa ƙasa, ya fito daga
ɗakinsa da alama dai fita zeyi, ta kalli agogo ƙarfe biyu da rabi na dare, ta buɗe
ƙofar ɗakin ta fito falo, aikuwa yana fitowa ya ganta a falo, ya ɗan haɗe rai yace
"ke me kike yi a falo a wannan tsohon daren haka?"
Ta nufi hanyar kitchen, tana tunanin ina zashi a wannan tsohon daren, ta fito ta
tarar da shi a falon a tsaye, yace "kinsha ruwan?"
Harta juya ta tafi, ta waigo taga yana tsaye yana kallon ta, tace "Amma naga kamar
fita zakayi, ina zaka yanzu dare yayi sosai"
"Yaushe na fara wasa dake? Ko kuma kika zama uwata da zaki dinga tuhuma ta haka?"
"hmm Daddy kenan, ai kaine kake abun tuhumar, wani irin abune wannan da ba'ayi ido
ma ganin ido ba se yanzu a tsakiyar dare haka hmmm Allah dai ya kyauta?"
Ta buɗe ɗakinta ta shige, ta barshi tsaye yana binta da kallo, yarinyar da idan ta
ganshi jikinta ke rawa, itace take gaya masa magama haka, tabbas uwarta ce ke
zigata kuma zeyi maganinsu gaba ɗaya.
Kamar yadda suka saba haɗuwa yauma sun hallara gabaɗayansu, suna zazzaune a ɗakin
Hotel ɗin da ya zamana babu ma me kama shi sesu.
Alhaji Bukar yace "ku duk baku sani ba, dukda yadda da labarin ya yaɗu a daren nan?
To ina nufin Yaron nan Yusuf, direbanta wanda aka yi garkuwa dasu tare"
Alhaji Bukar yace "An kamosu a wani ƙauye a Bauchi, inda Saleh ya basu mafaka,
yanzu haka yana hannun 'yan sanda, za' a tattare duk wata sheda da ta kamata daga
nam za'a kaishi kotu, zamu saki kuɗi ayi masa shari'a da hukuncin daya dace da shi,
saboda babu wanda ya ta:a kawo mana cikas da tangarɗa a harkar nan kamar shi, kunga
daga nan babu wanda ya isa yace mune muka sa akayi garkuwa dasu"
Alhaji Munir yace "good, wannan abu yayi kyawuuu sosai, kuma ya tafi yadda ake so,
dan haka semu hanzarta, mu kuma samu hanyar da zamu ɓalli namu kason tun kan Daula
ya bayyana, dan shi har yanzu bamu san fa inda yake ba, kar muje wasu su rigamu
karɓa abun nan fa"
Bukar yace "na toshe duk wata hanya da zata saka wani ya mallaki abun nan bamu ba,
sannan dole nasa a matsa yaron nan, idan ma abun yana hannunsa ya faɗi inda suke"
Alhaji Musa yace "kai amma abu yayi kyau wallahi, komai ya tafi yadda yakamata"
Alhaji Bukar yace "Haruna ina takaddar da wancan yaron ya bari, ɗan gurin Halima?
Shima nasa a nemo shi, duk inda aka ganshi kawai a kawar dashi, bama san duk wani
abu da zesa a samu sheda a kanmu"
Alhaji Haruna yai tsilli tsilli da ido yace "Amm.. Mm.. Wallahi an ɗan samu
akasine, na rasa inda takaddar ta faɗa amma ina ta ƙoƙarin dubawa"
Yace "Ayimin afuwa dan Allah, Insha Allah za'a nemota in kawo"
Alhaji Bukar yace "shikenan, nan da kwana bakwai, na baka isashen lokaci, nan kusa
nake so a fara shari'ar yaron nan, ba da nisa ba, kuma ina son a rufe duk wata
hujja da zata bayyana mu"
Alhaji Haruna yace "insha Allah, zan kawo takaddar nan ba da jimawa ba"
Widad ce ke ƙoƙarin farkawa, se jujjuya wuyanta take tana kuka cikin bacci, "Wayyo
Allah na, yuzarsef yunwa nake ji, zuciya ta ciwo take, Yoseef dan Allah, dan Allah
ka dawo please! Ta farka a gigice tana kiran Yoseef! Yoseef kana inane?"
Bulama ne da Matarsa Hajiya Sarah a gigice suka yi kanta gaba ɗaya, Bulama yace
"Sannu daughter, sannu ki kwantar da hankalinki, kin ganni a tare da ke, ga Maman
Iman ma, an kuɓutar dake ki kwantar da hankalinki"
"Ni bazan kwantar da hankalina ba, ina mijina yake? Ina Yoseef kace su sakarmin
shi, ni ba saceni yayi ba, wallahi idan basu sake shi ba mutuwa zanyi, laifina ne,
duk saboda ya ceceni haka ta faru dashi, beyi laifi ba, tun farko seda na gaya masa
death contract ne amma ya amince, kaga abunda nake nufi Yoseef, dan Allah ku
ƙyaleshi idan wani abu ya sameshi bazan yafewa kaina ba, dan Allah ka cewa Bukar na
dawo, ni yazo ya kamani yasa a sakarmin mijina dan Allah "
Tai maganar wasu irin hawaye na ambaliya daga idonta, idanun da suka rine zuwa
kalar ja jawur suka kumbure.
Bulama yace "toni ina na san wani Bukar, balle in nemo miki shi? Ke kaɗai kika
sanshi, ni ban san a inda yake ba"
Kafin ya rufe baki...
(Albishir ga masoya, ma'abota bibiyar litattaafaina, dama ta samu zaku fara samun
litattaafaina na audio, akan YouTube channel ɗina me suna Cool Arewa TV
https://youtube.com/channel/UCD5vnvA5laU8ti4LLz2_QEg
Kuyi liking sannan ku danna subscribe, domin fara samun litattaafaina na audio,
nagode sosai da ƙaunar ku gareni"
108_109
Kafin ya rufe baki ta cire drip ɗin hannunta tayi jifa dashi tace "ni na sanshi,
kuma zan nemo shi insha Allah, dole a sakarmin Yoseef ɗina"
Hajiya Sarah tace "haba Widad, baji da lafiya fa, drip ne a jikinki, ya zaki cire
ki yar?"
"ni lafiyata ƙalau, ba abunda yake damuna se son inga an sakarmin mijina"
Hajiya Sarah tace "wane irin aure ba tare da izinin magamabatnki ba? Anya ba ciwon
nakine ya tashi ba?"
"Karka ƙara dangantani da hauka, na gaya maka in bahaka ba zan maka haaukan ganin
idonka"
Ta diro daga kan gadon zata yi waje, aka Riƙeta da ƙyar tana fizge fizge seta ƙwace
ta fita.
Da Alhaji Musa ya koma gida a harabar gidan ya tarar da Nurat a zaune yai parking
ya fito ze wuce ta kalle shi ta dauke kai, ya kalleta yace "can't you greet your
Dad?"
Yace "why"
"saboda yadda kake treating ɗina kamar ba 'yarka ba" ta ƙarasa maganar tana tashi
ta bar gurin ya bita da kallo.
Harta shiga ɗaki taji ta gaji da zaman, ga Khalil yace zezo amma shiru bezo ba,
fitowa tayi daga ɗakinta ta haɗo tea, ta dawo falo ta zauna ta kunna TV ta nayi
tana ɗan shan tea ɗinta a hankali.
Ta tarar har angama title ɗin news ɗin an fara labaran, sedai ana fara gabatar da
labarin su Yusuf jikinta ya hau shaking, gabanta ya shiga dukan uku uku, ai ba'a
gama labaran ba ta saki kofin tea ɗin dake hannunta, da ibu zata saka amma ta toshe
bakinta, ta shiga ɗakinta da sauri ta kulle ƙofa, zubewa tayi a gurin ta shiga
rusar kuka kamar wadda babanta ya mutu, ta dinga kuka tabbas babu ko tantama wannan
ƙulle ƙullen mahaifinta ne, wataƙila shine ma dalilin kwanansa a waje jiya, wannan
labarin sam babu ƙamshin gaskiya a cikinsa, ta yaya za'ayi garkuwa da mutane kuma
an gano su ace Yusuf ne ya saceta baze yuwu ba.
Ta ɗakko wayarta ta shige toilet, ta nemo lambar Khalil, tana kuka Khalil ya ɗaga,
yana ɗagawa ta fashe da kuka yace 'Nurat lafiya kuwa, meyafaru ne? "
"Amma meyasa baka gayamin ba? Kaga abunda ya faru kaga abunda akace Yusuf yayi ko?"
Khalil yace "nagani, bana son in ɗaga miki hankaline, amma tun jiya da daddare na
gani, gefw guda kuma Anwar ɗan gidan Hajiya Halima shima ba'asan inda yake ba, duk
na ɓoye ne, dan gudun tayar miki da hankali"
Nurat ta share hawayenta tace "Yaya Khalil, ka dena min ɓoye ɓoye, lokaci yayi da
zaka temakeni, Khalil mahaifina azzalumi ne wallahi, jiya be kwana a gida ba, nasan
saboda wannan dalilin ne, Wallahi idan ba'ayi wani abu a kai ba, rayuwar Yusuf zata
shiga garari"
"Nasani Nurat, but am doing my best kinji, bari kinga yanzu zan shigo gidan naku
kafin in wuce office"
Nurat tace "No karkazo, ka san shi da zargi, zefara zargin wani abune dan Allah
karka zo ka bari kawai, mu dinga communicating ta waya ya isa, bana son ya gane
komai"
Khalil yace "shikenan, naji ki kwantar da hankalinki, komai zezo da sauƙi zancigaba
da bibiya inga yadda zata kaya"
Ta jinjina kai ta ajiye wayar, tana ci gaba da jujjuya kai tana tausayawa Yusuf.
Ma'aikatan gidan Alhaji Daula suka rikice jin kabarin abunda ya faru da Yusuf, sun
kadu matuƙar gaske dukda wasun su suna jin haushinsa amma a zaman da suka yi dashi
sun sanshi da sanyin hali, basa tunanin ze aikata wannan aiki haka.
Ɓangaren Suleiman makuwa ya kaɗu Matuƙa da jin wannan labarin, hankalinsa ya tashi
sosai ya tafi headquarter da kansa dan ganin Yusuf, amma fafur aka hanashi ganinsa,
dukda shima babban jami'ine amma a kace baze ganshi ba, ana kan gudanar da bincike
akansu ne.
Yusuf kam yaci duka da kulki a hannun kuratan 'yan sanda, yama rasa dukan me suke
masa? Me suke yai musu su ƙyaleshi, ya daku iya dakuwa ƙafafunsa da bayansa ya gaya
masa saboda duka, yana nan gurin a duƙe wani ɗan sanda ya shigo aka ajiye ɗan
sandan kujera ya zauna, ya sallami kowa daga gurin, ya ɗan ƙurawa Yusuf ido sannan
yace "Malam Yusuf"
"Ina so karka bamu wahala, kuma karka bawa kanka wahala, yana da kyau ka amsa
laifinka tun a nan dan muyi gaggawar kaika kotu a yanke maka hukuncin daya dace,
sannan abu na gaba shine, Widad ta baka bayanin inda dukiyar da mahaifinata ya ware
take?"
Ɗago kai Yusuf yayi, ya kalli ɗan sandan, se yanzu ya ƙara tabattar da cewa wannan
abun set up ne kawai, an shirya wulaƙant shi ne kawai.
Cikin shouting ɗan sandan yace" ba magana nake maka ba? Ta gaya maka ko kuwa, ka
sauƙaƙawa kanka ka gayamin suna ina? "
Cikin dakiya da juriya irin na Yusuf, ya sake gyra zamansa ya ƙi kallon ɗan sandan,
ai kuwa ɗan sandan nan ya harzuƙa, yasa aka kawo masa kulki, ya ding bugawa Yusuf,
Yusuf ya dinga juyi a gurin saboda azabar wahala dayake sha, dan dukan kulkin nan
ba ƙaramin shigarsa yake ba, amma sukayi sukayi, Yusuf yaƙi cewa uffan.
Widad kam aka hana 'yan jarida ganinta, aka gama bata magunguna da gwaje gwaje,
Bulama ya ɗauketa zuwa gidan sa, Widad sam bata iya ma magana yanzu, haka aka tafi
da ita gidan Bulama.
Likitoci suka bada rahoton, wai ta samu raunuka a jikinta, kuma ta galabaita saboda
rashin Abinci da azabtarwar da ta sha hannun Yusuf da yayi garkuwa da ita.
Bulama ya tafi da ita gidansa, sedai banda sharar hawaye babu abunda take yi,
ƙarshe ma maganar ta gagara, aka bata ɗaki, suna shiga ɗakin ta zube a ƙasa tana
maida numfashi, saboda nauyin da taji ƙirjinta yayi mata, ta kalli Bulama tace
"meyasa ka kawoni nan?"
"Nan ba gidanmu bane, ina Daddy yake tunda nazo ban ganshi ba, yana ina?"
Hajiya Sarah ta kalli Bulama, shima ya kalleta yace "Amm daughter kin gane, ki
kwantar da hankalinki kinji, Daddyn ki yana nan lafiya, kuma yana nan zuwa insha
Allah, kedai ki kwantar da hankalinki kawai saboda lafiyarki"
Widad tace "ni babu abunda ya sameni, ka gayamin ina mahaifina yake? Ina Daddy na"
Hajiya Sarah tace "Kaga, Ka gayamata gaskiya kawai, tunda har Allah yasa an gano
ta bashi da wani amfani a cigaba da yi mata ɓoye ɓoye, dan haka kawai ka fito ka
faɗa mata gaskiya"
Bulama yace "Sarah meyasa kike hakane? Kina ganin halin da take ciki amma kina wani
zance daban meyasa kike hakane?"
Hajiya Sarah tace "dan meyasa ba zanyi haka ba, ka gayamata gaskiya mana da wuri,
kasan halinta sarai ba baka sani ba, idan ta sani daga baya duk seta ɗaga mana
hankali gaba ɗaya gidan nan, ni a yanzu hakama a tsorace nake, kafi kowa sanin
halinta"
Bulama yace "koma meye halin nata ba haƙuri zakiyi ba, da 'yar kice haka zaki ce?
Kiyi haƙuri mana muga yadda hali zeyi"
Sunata jayayya a tsakanin su, Widad ta zame jiki ta zauna a gurin, tai musu shiru
ta lumshe idonta tana jin sautin yadda zuciyarta ke bugawa da sauri sauri kamar
zata tsaga ƙirjinta ta fito.
Bulama ya durƙuso gabanta yace "ki kwantar da hanlinki kinji daughter, babu wata
matsala Daddynki yana nan lafiya, zezo inda kike, amma sekin kwantar da hankalinki,
kin san baki da cikakkiyar lafiya, mubi komai a sannu"
"saboda me? Meyasa zakice a sake shi, mutumin da yayi garkuwa dake, aka samoki da
ƙyar a wani ƙungurmin ƙauye, sannan kice a sake shi, baki duba abunda yayi miki
bane?"
"Yoseef beyi garkuwa dani ba sam, anyi garkuwa damune ni da shi, ba wahalar da beyi
ba saboda in tsira da rayuwata, meyasa yanzu za'ace shine ya saceni? Anyi masa
adalci kenan kasa a sake shi please, dan Allah a saki Yoseef bashi da laifin komai
fa" ta ƙarasa maganar tana kuka.
Bulama yace "Ni yanzu ta yaya zan fara sakawa a sake shi? 'yan sanda sun fitar da
rahoto akan abunda ya faru kawai ace nasa a sake shi, bafa a ko ina ake alfarma ba,
yanzu gaba ɗaya case na hannun hukuma, babu abunda zan iya ni"
"Shikenan tunda babu abunda zaka iya, ni zanyi ko zan ƙarar da dukiyar Daula sena
fitar da Yoseef, saboda ni ba butulu bace ba, Yoseef yayi min halacci"
Ta miƙe ta kwanta a gurin, tana ta kera gwaron numfashi, wani na bin wani.
Suleiman gidan su Yusuf ya tafi, yana zuwa ya tarar da Umman Yusuf a kwance, an
kewaye ta ana yayyafa mata ruwa, sam bata san inda kanta yake ba, ga Asmarta ta
tashi tana jan numfashi da ƙyar, an sheƙa mata inhaler amma a banza.
Suleiman yace "Subhanallah, ya ba'a kaita Asibiti ba? Meye ya faru da ita haka?"
Wata maƙociyarsu tace "wallahi yau da Asuba bayan ta idar da sallar Asuba, ya
kunna radio taji ance an kama ɗanta Yusuf, shikenan muka jiyo kukanta, muna shigowa
harta fara fita daga hayyacinta, numfashi yaƙi tsayawa a ƙirjinta.
Suleiman yace" da ba seku kaita Asibiti ba, koda kuwa na gwamnati ne ba, zata iya
rasa ranta fa a haka, maza ku ɗakkota ga mota can, a sata a ciki mu tafi Asibiti "
Haka kuwa akayi, aka sa Umman Yusuf a mota, da wasu maƙotanta suka Tafi Kaita
Asibiti.
Suna zuwa aka karɓeta a emergency, aka shiga da ita, likitoci sukayi gwaje gwajen
da zasuyi suka ga jininta ya hau fiye da kima, dama tana zuwa shan magani ana duba
jinin, tun lokacin da Yusuf ya ɓata ta haɗu da hawan jini.
Yanzu jinin ya hau fiye da kima, ga Asma ta tashi saboda kukan da take yi, gaba
ɗaya bata a hayyacinta, a nata ƙoƙarin ganin jinin ya sauka amma abu ya gagara,
ƙarshe seda aka haɗa mata da oxygen, da allurai da drip, Suleiman duk ya biya
charges ɗin.
Da Safe Amal bata tashi ba se wajen sha ɗaya na safe, ta tashi daga bacci ta tashi
da wata irin yunwa, ta tashi ta shiga toilet tayi wanka, ta canza kayan jikinta
daga na bacci, har zata fita tace "bari dai in kunna wayata, inga me wannan jakin
kuma ya kuma turowa" ta zauna ta kunna wayarta, ta buɗe data messages nata shigowa,
amma babu na Alhaji Haruna, ta taɓe baki ta tashi zata fita, sega kiran wayarsa ya
shigo wayarta.
"ba rana ba wata, muddin ba zaka cika sharuɗan dana sama ka ba"
"Waike ynzu 500k ne suka miki kaɗan? Haba ke kuwa dan Allah"
Amal tace "kaga sauraramin, meye wani 500k,duk kuɗin da kake sata na haram kakeci,
seni zaka rainawa hankali, wallahi bazan baka takaddar nan a 500k ba"
Aikuwa ya fusata yace "ke wai wace irin yarinya ce, kwana bakwai fa kawai aka bani
in kai takaddar nan, ya zakice bazaki bank ba haka akeyi?"
"Kai bari kaji in gaya maka wani abu, wallahi idan baka yi wasa ba sena sa takaddar
nan ta zama hujja akanku gaba ɗaya"
"Eh har ita, duk zaka ja muku ne, bari in maka magana ta ƙarshe, wallahi bazan baka
takaddar nan ba har se ka bani kuɗin da zaka fanshi budurcina da ka karɓa ta ƙarfi"
"ai kace min ka ga kaidi iri iri na mata a bariki, to zan nuna maka nawa na
dabanne, zan kawo ƙarshen bunsurancinka, wallahi ko inje in haɗa maka masifa da
tashin hankali a gurin Alhaji Bukar ɗin, baka san kalar nawa kaidin ba zan gwada
maka Akuya kawai"
Ai kasa magana yayi, se bin wayar yayi da kallo, lallai yarinyar nan bata da
mutunci sam.
Ta ajiye wayar tace za kaga tsiya ganin idonka, tai tsaki ta saka wayar a caji ta
fito falo, Dariyar Mummy taji da Ramlah, Ramlah tace "dara taci gida, sunzo hannu
Alhamdilillah, naji ance a ƙungurmin ƙauye aka gano su, koya akayi ta iya zaman
wannan ƙauyen oho"
Mummy tace "su suka sani, ni dai tunda an kamo su na fara jin ƙamshin samun kuɗin
nan"
Ramlah tace "Ance yana can hannun 'yan sanda ido ya raina fata, tun jiya ya fara
cin ƙaniyarsa a hannunsu, ai gara yaji jiki, kafin a shiga kotu ya raina kansa"
Mummy tace "eh Bulama ya cemin idan aka gama bincike kotu za' a kaishi, dan haka ni
yanzu ba ta tashi nake ba, ta Anwar nakeyi har yanzu shiru, tunda Amal ta kai musu
takaddar basu sake cemin komai ba"
Ramlah tace "zasuyi miki magana ne, bari mu kunna TV mu sake ganin idon munafukin
nan, dan ban manta lokacin da ake wulaƙantamu ana cin zarafin mu saboda shi ba"
Ajiyar zuciya Amal tayi, wanda yasa suka juya gaba ɗaya suka kalleta, wucewa tayi
kitchen dan Samarwa kanta abunda zata ci.
Mummy tace "Auta ya jiki?"
Ta kalli Mummy ta ɗauke kai, ta wuce kitchen, ta fito daga kitchen tazo ta zauna
tace "Mummy, hira naji kuna yi kamar an kama Yusuf ko?"
Ramlah tai farat tace "Eh an kama shi, seme ne kuma? Ko zaki fara wa mutane
shirmen naki ne?"
Amal ta girgiza kai tace "No akanme? Ina Ita Widad ɗin take?"
Amal ta jinjina kai, ta tashi ta tafi ɗakimta, tana jinjina kai, da sauri ta ɗauki
wayarta ta shiga social media, aikuwa taga yadda labarin ya cika social media,
yadda aka haɗa ƙarya da gaskiya.
Ta ajiye wayar tayi shiru tana tunani, kasa shan tea ɗin nan tayi, se tunani daya
dabai baye zuciyarta, gaba ɗaya tausayin Yusuf ya mamaye zuciyarta, tama jin
tsohuwar soyayyar sa na taso mata.
"ya maganar shirye shiryen tafiyarki ne, you should preparing for it fa, lokaci
yana gabatowa"
"Daddy na gaya maka ni bana son tafiyar nan, ni ba inda zanje a gida Nigeria zanyi
karatun"
"ba zakiyi a nan ɗin ba, ƙasar nan zaki bari, waike yaushe muka fara sainsa dake
ne? Ni zance ga yadda za'ayi amma ki bijiremin? To baki isa ba nina haifeki bake
kika haifeni ba"
Ya dinga banbamin bala'insa, yayi ya gama tsaf bata sake cewa komai ba, seda ya
gama tukuna sannan ta miƙe ta bar masa ɗakinsa, tana zuwa ɗakinta tace 'wallahi ba
inda zanje, bazan bar ƙasar nan ana wannan halin ba, se naga abunda ya turewa buzu
naɗi"
Yusuf kam ya daku a gurin jami' an tsaro, akan lallai seya amsa shine ya sace
Widad, amma Yusuf ƙemem yaƙi magana, dama shi Saleh ba'a maganarsa saboda ya
galabaita fiye da Yusuf ko magana baya iyayi, bama shi da lafiya.
Juyin duniya Yusuf ya amsa shine ya sace Widad yaƙi, yaƙi ko ɗaga kansa ma balle
yayi magana.
Mutumin da yake jibgarsa yace "ga 'yan jarida cam suka cika harabar gidan nan, zamu
basu lokaci suyi magana da kai, ka furta kaine ka sace yarinyar nan koka samj
sassauci, idan kuma kaƙi to haka zamu ci gaba da casaka a gurin nan, gara ka nemawa
kanka mafita, ka amsa kai ka sace ta"
Yusuf dai beyi magana ba, aka taso ƙeyarsa a gaba aka saka masa handcuffs hannu da
ƙafa, aka fito da shi harabar headquarter na 'yan sanda, fuskarsa duk ta kumbur
saboda duka.
' yan jarida sun cika gurin nan, suka kewaye Yusuf da abun magana, kowa yana yanko
masa tambaya, wasu ta gaske wasu ta cin mutunci, amma Yusuf yai shiru, sukayi
sukayi har suka gaji, har ya juya za'a maida shi ya tsaya ya waigo, ya kalli' yan
jaridar nan yace "Bani na sace ta ba"
Kawai ya juya, ds ƙyar 'yan sanda suka dakatar da' yan jaridar nan aka mayar da
Yusuf inda aka ɗakko shi.
Nurat gaba ɗaya ta tayarwa da Khalil hankali akan maganar Yusuf, ga koke koken da
take akan batun komawarta karatu, tana ta saƙawa da warwar akan ta gudu ta bar
gidan gaba ɗaya, amma sedai tasan idan tayi hakan ba zata sake daraja a idon mutane
ba.
Alhaji Haruna duk ya shiga damuwa da tashin hankali, akan takaddar nan da Amal keta
rainamasa hankali akan ta, ya shiga part ɗin Amaryarsa ya tarar da ita ta ƙurawa TV
ido cike da damuwa, ya zauna kusa da ita yace "Baby kallo ake ne?"
Ta ɗan ɓata fuska tace "ina kallon wani abune daya tsayamin a zuciya, wannan bawan
Allah da aka kama akan 'yar gidan Daula ya tsayemin, i can't imagine ze aikata wani
abu makamancin haka, ƙarya ce kawai akayi masa"
Yace "ke ya akayi kika san ƙarya akayi masa? Wannan shine abunda ya dace dashi,
kuma zamu tsaya kai da fata se an hukunta shi anyi maganin irinsa a cikin al'umma"
Ta kalle shi tace "Nasan Yusuf, fiye da yadda kake tunani, inaga mahaufiyarsa ce
kawai zata fini sanin waye shi, wallahi wannan maganar ƙarya ake masa, mutumin da
yake kamar waliyyi dan haƙuri, wannan maganar ƙaryane wallahi"
Alhaji Haruna yace "Salma meye haɗinki dashi da kike wannan zaƙewar, meye haka
kike yi akansa, kuma a gabana?"
Ta Harare shi tace "Yusuf unguwar mu ɗaya, kuma tsohon saurayi nane, wanda aka
hanani Aurensa aka ƙaƙabamin kai"
Kawai ya kwashe da dariya yace "lallai baki da hankali, aikuwa kina ji kina gani
ze tafi prison Salmata, sedai haƙuri"
Ya tashi ya barta a gurin, tausayin Yusuf ya kamata, tasan Yusuf baze taɓa aikata
abunda akace yayi ba.
Widad tana zaune kamad wata mahaukaciya, tun jiya da safe rabonta da Abinci, tana
jin yadda zuciyarta take bugawa ba daidai ba, tai shiru tunani da tausayin Yusuf ne
yake ta ratsa zuciyarta.
Iman ta shigowa da Widad da Abinci tace "ga Abinci, ki daure kici dan Allah"
Iman tace to, befi mintuna biyar da fitarta ba sega Bulama ya shigo ɗakin, yana
shigowa ya kalleta yace "innalillahi wa inna ialaihi raji'un, Widad har yanzu
bakya cin Abincin, subhanallah ko mota za'a ɗakko mu tafi Asibiti ne?"
Cikin tsawa tace "ka dena amsamin tambayata da tambaya, ina Yoseef yake?"
Ta miƙe tsaye tace "har yanzu baka yi komai a kai ba ko? Ni ka maidani gidan mu
gurin Daddy na, shiyasan ranar da Yusuf yayi masa, baze bari ya cutu ba akan laifin
da beyi ba"
"Karka ƙara cewa in kwantar da hankalina, ina Alhaji Nasir Daula yake? Ina babana
Daddyna nake maka magana, yana ina? Ta yaya za'ace tun jiya har yanzu babu shi babu
dalilinsa bezo inda nake ba"?
Tai maganar a jere bako haɗiyar yawu, tare da ɗaga murya sosai.
Ai be rufe baki ba tasa ƙafa tai ball da kayan breakfast ɗin, ta riƙe gaban rigar
Bulama tace "ka gayamin gaskiya, ina Daula yake? Idan an kashemin shine ka
gayamin, yana ina? Ina yake ina Daddyna?!"
Jin Hayaniya yasa tuni mutan gidan suka fara taruwa a ɗakin, Hajiya Sarah tace
"babanki Nasir Daula, tun bayan ɓatanki ya kwanta rashin lafiya, aka bishi har
gadon Asibiti aka sace shi, har yau babu wanda yasan inda yake"
A hankali Widad ta saki rigar Bulama, tana kallon Hajiya Sarah "Annn. An sace
Daddyn Widad a gadon Asibiti, this serious, Daddyn how comes? Ta yaya za'a sace shi
ba wanda ya sani, shikenan na rasa Yoseef ɗina, Daddyna ma ace ba'a ganshi ba,
Noooooo! This impossible!!!
Ayi subscribing YouTube channel ɗina dan Allah, me suna Cool Arewa TV
11/21/21, 7:45 AM - Buhainat: LITTAFIN KUƊI NE, DAN ALLAH KI SIYA KAFIN KI KARANTA
BA DANNI BA DAN ALLAH, LITTAFI NA ƊAYA KYAUTA NE WANNAN NA SIYARWA NE
NORMAL GROUP ₦300
VIP ₦500 NE KITURA TA WANNAN ACCOUNT ƊIN
0009450228
JA'IZ BANK
AISHA ADAM
SE A TURA SHEDAR BIYA TA WANNAN LAMBAR
07063065680
IDAN KUMA KIN SIYA AMANACE KARKI FITARMIN DAN ALLAH 🙏🙏🙏
(Albishir ga masoya, ma'abota bibiyar litattaafaina, dama ta samu zaku fara samun
litattaafaina na audio, akan YouTube channel ɗina me suna Cool Arewa TV
https://youtube.com/channel/UCD5vnvA5laU8ti4LLz2_QEg
Kuyi liking sannan ku danna subscribe, domin fara samun litattaafaina na audio,
nagode sosai da ƙaunar ku gareni"
LITTAFIN KUƊI NE, DAN ALLAH KI SIYA KAFIN KI KARANTA BA DANNI BA DAN ALLAH, LITTAFI
NA ƊAYA KYAUTA NE WANNAN NA SIYARWA NE
NORMAL GROUP ₦300
VIP ₦500 NE KITURA TA WANNAN ACCOUNT ƊIN
0009450228
JA'IZ BANK
AISHA ADAM
SE A TURA SHEDAR BIYA TA WANNAN LAMBAR
07063065680
(Albishir ga masoya, ma'abota bibiyar litattaafaina, dama ta samu zaku fara samun
litattaafaina na audio, akan YouTube channel ɗina me suna Cool Arewa TV
https://youtube.com/channel/UCD5vnvA5laU8ti4LLz2_QEg
Kuyi liking sannan ku danna subscribe, domin fara samun litattaafaina na audio,
nagode sosai da ƙaunar ku gareni"
110_111
Me Adda ya kawowa mutumin kujera ya zauna, ya kalli Saleh yace "ka dena mamaki
mana, ai bekamata kayi mamaki ba, a zatonka kai kaɗaine me wayo, ko kuma kafi kowa
wayo? Kifi na ganinka me jar koma, kallonka kawai nakeyi"
Saleh yace "hmm Bukar kenan, kaima kuka karya Alƙawari balle ni, haka mukayi daku?
Ashe kun kashe min ɗan uwana, banma sani ba balle kua bamu gawar muyi masa sitira,
dama haka akeyi, kunyi amfani dani ne dan cinma burinku?"
"ƙwarai kuwa, muna amfani da kaine dan cinma burinmu, kai bari in gayamaka wani
abu, ku duka wanda nake aikin harƙallar nam daku, ina amfani da kune dan cinma
burina nikaɗai, na ɗaukeku karnukan farauta tane kawai "
Me Adda ya yunƙura ze kaiwa Saleh duka amma Bukar ya hana shi yace "ƙyaleshi, ai
baaka ga komai a cikin ƙudrina da AƘIDATA ba, kuma dama tuntuni kowannen ku nayi
masa tanadin makomarsa idan deal ɗinmu ya kammala, sedai kai kayi gaggawa gurin
riskar taka makomar, tunda ka yaudareni kaci amanata zaka riski makomarka a nan
kusa, ina Widad take? "
Saleh yai masa wani irin mugun kallo yace "ni ka bawa ajiyarsu kokuwa? Kaje ka
tambayi wanda aka sa su sacesu gasu nan a gabanka"
'bana son in wahalar da kai kafin ka mutu Saleh, ko dan irin wahalar da kayimin,
amma gaddama da taurin kai zesa in maka uƙuba wadda zata yi ajalinka, Saleh kaine
ka bawa Widad da direbanta mafaka, kasan inda suke kaine ka kuɓutar dasu, dan haka
karka wahalar dani, ko ka wahalar da kanka kafin ka mutu, ka gayamin ina ka kaisu"?
"Ni bani na ɗauke su ba, ban san inda suke ba, dan haka karka ƙara tambaya ta na
gaya maka"
Bukar yace "Shikenan, tunda baka san rarrashi ba, bari a biyo maka ta inda ya
dace, Me Addda ku gasamim shi tsawon kwana uku, muga iya juriyarsa a mtsayinsa na
kurtun soja"
Daga nan Bukar ya tashi ya fita daga ɗakin suka rufa masa baya.
Amal tana ta sauri taje ta kai takaddun nan, daga nan ta kai wadda aka bata ta
kaiwa Alhaji Haruna, yamma ta fara yi sosai kuma bata son Mummy ta kama faɗan nata
akan bataje aiken da tayi mata da wuri ba, dan haka a harabar gidan gurin shiga
mota ta ƙarasa saka takaddun a jakarta, da wasiƙar gurin Anwar, da takaddar form
ɗinta, ta buɗe mota ta shiga ta fice.
Unguwar da guest House ɗin Alhaji Haruna take shiru babu mutane a unguwar, duk se
kangwaye da sababbin gidaje, bata kawo komai a ranta ba tace bari taje ta fara kai
masa tasa takaddar, daga nan kuma seta je gurin nata kai takaddar.
Tana zuwa megadi ya buɗe mata gate ta shiga, tace "yana nan kuwa?"
Ta fito daga motar ta shiga, ta murɗa ƙofar falon tare da yin sallama, sedai babu
kowa a falon, ta nemi guri tayi zamanta a falon, shiru shiru babu wanda ya fito, ta
tashi ta koma gurin megadi tace "Anya kuwa yana nan? Naje nayi sallama amma shiru
ba'a amsa ba"
Megadi yace "ai be fiye zama a falon ba, ki shiga yana ciki"
Tace "Cikin ina? Kaga ungo bari in baka takaddar ka ajiye masa"
Megadin yace "rufani ki saya, ai be yadda in karɓi kowane saƙo ba idan bashi yace
ba, ki buɗe ƙofar dake cikin falon wasu falukan ne a ciki fa"
Ya rakata, yana gaba tana bin bayansa, suka dinga ratsa faluka, sukaje wata ƙofa
yace "yawwa a nan yake ganin baƙi, ki shiga ki bashi"
"kazo dai mi shiga tare, danni bazan iya maida kaina waje ba, wannan gida duk
lunguna kamar gidan matsafa"
Ta buɗe ɗakin ta shiga da sallama ashe bedroom ne, ya amsa mata yana zaune akan
gado yana danna system, yana ganinta ya faɗaɗa murmushinsa yace "Ashe kinzo, ai
tun ɗazu nake jiranki" yai maganar yana binta da kallo.
Haɗe rai tayi tace "eh nazo, ina falo ne ga takaddar tace akawo maka"
A fusace ta kalle shi tace "meye haka kuma? Dalla malam sakeni"
Yace "haba Baby, gaki kamar wayayyiya amma kina wani kidahumanci, ki kwantar da
hankalinki karki ji komai kinji"
Yai murmushi yace "to idan kinyi ihu kina tunanin akwai wanda ze kawo miki ɗauki
ne? Ba wani abu fa rainane ya biya kawai, ki kwantar da hankalinki kici Arziki ki
barshi"
Kici kicin ƙwacewa ta shiga yi amma ya riƙeta gama, yana wani lashe baki kamar kare
yace "'yar uwarki ta fiki wayewa, ke kamar ba' yar birni ba"
Ya fara ƙoƙarin rabata da kayan jikinta, sosai Amal take ihu tana ƙwacewa, tana
rirriƙe jikinta tana kururuwa, amma tsohon najadun nan ko a jikinsa, burinsa kawai
ya cimma burinsa, Amal ta dunƙule hannu ta dinga kai masa naushi kota ko ina, wani
naushi data kai masa a ido a gigice ya sake ta, yaja da baya, ta durƙusa tana
ƙoƙarin mayar da kayanta, kuma taso mata yayi haiƙan yana kuma riƙeta, sosai kokawa
ta ka came a tsakanin su, ya hankaɗata ƙasa ta faɗi akan hannunta, ta kurma wani
uban ihu, saboda azababben zafin da taji ya ratsa hannunta, haka ta kuma yunƙurawa
ta miƙe sedai ta kasa ɗaga hannun nata, ganin zata hana shi rawar gaban hantsi, be
tausayawa halin da take ciki ba, ya shammaceta ya buga mata kwalba a goshi, ta kuma
kurma ihu ta baje a gurin a sume.
Yusuf seda ya kwana biyu sannan ya iya cigaba da fita, sedai wata irin shaƙuwa da
kusanci ne ke ƙara shiga tsakaninsa da Widad, wata irin kulawa take bashi ta
musamman wadda bata masa a baya, ga Jamila dake ƙara sata a hanya yadda zata dinga
kula da mijin ta, gefe guda kuma ta tara ɗalibai sosai, idan yamma tayi cika gidan
megari ake yara da manya tana koyar dasu ilimin addini dana zamani.
Yau Widad ta haɗa kayanta dana Yusuf ta wanke su tsaf, gwanin ban sha'awa.
Yusuf ya dawo a gajiye, yana dawowa ya tarar da Widad harta dafa ruwan wanka ta
ajiye masa.
Yusuf yayi murmushi yace "Waini wannan kulawar da ake bani fa, nifa abun yana
mamaki, an maida ni wani ɗan gata meye sirrin ne?"
Widad tai masa fari da ido tace "tukuici kawai zaka bayar, if you really
appreciate"
Ba tace masa koma ba se murmushi da tayi, tana sake kashe masa ido, Yusuf yace "Ohh
my God, wannan kallon da kikemin se in rasa ina zan sa kaina, gaba ɗaya narkamin
zuciyata yake Baby"
Widad tai dariya tace "shagwaɓaɓɓe kawai, ji yadda yake magana kamar wani Baby"
"zan mana, dayawa ma zanci sosai tunda Baby ce zata bani a baki"
Yai murmushi ya fice daga ɗakin, yaje yayo wanka ya dawo ɗakin, sedai ya tarar bata
ɗakin tana tsakar gida, yana zuwa yaga babu kayansa, ya duba Akwatin Widad yaga
kayansa a wanke, ya ɗadɗaga ya haska yagansu a wanke fes, mamkine ya kama shi, ya
fito ya ƙwala mata kira, ta taso taje Yusuf yace
"My Wife, gani nayi kamar an wanke min kaya, ya haka?"
"Amma waye ya wanke min? Nidai nasan baki iya wanki ba, ni nake mana to yaya akayi
aka wanke su?"
"Shikenan kuma a haka zan zauna ban iya komai ba,? To in gaya maka na iya aiki
sosai yanzu, nice nan na wanke mana su ɗazu"
Yusuf yace "abun mamaki, yanzu ke kika wanke mana kayan nan duka? Ina mamaki fa"
"Ni na isa ince basu fita ba, sun fita fes, amma baki saba ba karki sake wankewa,
zan wanke mana da kaina kinji matar Yusuf"
Yace "bafa na son gaddama, kawai ka bari nagode Allah yayi albarka, amma ni zan
dinga wanke mana kinji beautyna"
"A'a ai kai ba bawana bane, dan haka nima yakamata in dinga ƙoƙartawa, tunda ina
iyawa ai bakomai kai ba murna zakayi ba ina koya ba"
Yusuf yace "naji amma ki bari mu dingayi tare, kinji Babyn Yusuf"
"Yawwa Babyna I love you" yai maganar yana kissing din goshinta, bata bashi amsa ba
se murmushi da tayi, tana lumshe ido, babban abunda yake bawa Yusuf mamaki da ita
be wuce yadda idan har yace yana sonta, sedai tayi murmushi amma ita ta kasa
gayamasa hakan, har yanzu yakasa gane haƙiƙanin abunda yake ranta, sedai yana ganin
kishinsa da tausayinsa muraran a idonta, sedai tausayi da kishi suna cikin alama na
soyayya.
Widad tace "zauna inzo in baka abincin, naga kwana biyu ba kaci kana ƙoshi, bana
son mu koma gida a ganka a rame, bazanji daɗi ba, aga nayi ƙiba mijina kuma a rame
ba'"
Yusuf yace "inyee kaga masu miji, kamar ba mutum ne yake cewa shi be yadda da Aure
ba, baze aura ya zauna a ƙarƙashin wani ba, kawai se naji mutum yana cewa ina son
Aurena Yoseef, Zan zauna da kai a yadda kake, ya akayi mutum ya canza ra'ayi ne
haka da sauri?"
Yusuf yayi dariya yace "gayamin meyasa kike son Aurennaki ne? Gayamin mana"
Widad tace "nima ban san yadda akayi haka ba, a baya ina da dalilin da yasa nace
bazan yi aure ba, amma yanzu na samu mijin marainiya, wanda yake lallaɓani ban yaɓa
zaton akwai miji irinsa ba, ka bani farinciki mara misaltuwa, shiyasa nake jin
kamar bazan iya bari kayi nesa dani ba, shiyasa nake son Aurena "
Yusuf yayi murmushi yace "Mutum ma ya faɗi gaskiya ma, se wani kauce kauce kike,
zama ki faɗi gaskiya ne ai"
Widad ta buɗe baki tace "ba ruwana, Allah ya shiryeka, a haka kaman salihi amma
mutum yaita sakin magana"
"Kyaji dashi dai, ni dai azo a bani Abincina inci yunwa nakeji"
Ta zauna tana bawa Yusuf Abincin sa a baki, suna hirarsu cikin nishaɗi da jin
daɗi.
Amal kawai farakwa tayi ta ganta akan gadon Asibiti, taga kanta nannaɗe da bandeji,
hannunta ma data faɗi akai haka, mamkine ya kamata ta juya ta ganta a ɗakin Asibiti
a kwance, ga wani irin raɗaɗi da yake ratsata daga tsakanin ƙafafunta.
Shiru tayi taga Mummy ta shigo ɗakin hannunta da ledar magani, ta ƙaraso da sauri
tana Autana sannu, ya jikin naki ne?"
Mummy tace "hatsari kika yi mana Baby, ina zaune a gida Alhaji Haruna yayi min waya
yacemin bayan kin kai masa takaddar, kika samu hatsari a titin unguwarsu"
Wani uban ihu ta saki, da tuno abunda ya faru tsakaninta da Alhaji Haruna, ya mata
fyaɗe kenan, kuma yake gayawa mahaifiyarta hatsari tayi.
Ta fashe da kuka, tana jujjuya kanta, wani irin baƙin ciki ne da takaici ya mamaye
mata zuciya.
Mummy tace " Haba Amal, kiyi haƙuri dan Allah, ai abun be tsawwala ba Autana,
karaya kika samu a hannu se kwalba daya fasa miki goshi, Ai Alhaji Haruna yayi mana
mutunci, shiya kawoki Asibitin nan"
Kawai Amal ta dinga kuka, ji tayi kamar ta shaƙe mahaifiyarta jin maganar da take,
ya cuceta ya kassara rayuwarta, ya raba ta da mutuncinta, kuma ya kawota Asibiti
yace hatsari tayi, ji tayi kamar zuciyarta ta tsaga ƙirjinta ta fito saboda azabar
baƙinciki da takaici, tama rasa me zata yi, kawai ta fasa ihu ta fizge ruwan dake
jikinta tayi jifa dashi, ta dinga wani uban ihu, da ƙyar aka kira likitoci, aka
daddanneta akayi mata allurar bacci.
Mummy ta kalli likitan cike da damuwa tace "Doctor, wai dan Allah meyasa meta ne?
Naga kamar ta haukace"
Likitan yace "A'a ba haukacewa tayi ba, stress ne da damuwa suka ɗan dameta amma
insha Allah komai zezo da sauƙi, zamu sake mata hoton hannun, idan hali yayi a
goben ma insha Allah zamu iyayi mata aikin, tunda Alhaji Haruna ya gama biyan
komai, dama anan yake da family file "
Bayan sallar isha'i Yusuf ya shigo, ya tarar da Widad a kwance ta kunna fitila,
tana ta saƙa maficinta daga nan inda take kwance, yai sallama ta amsa, yana zuwa ya
kwanta a kanta.
Cikin Shagwaɓa tace "wayyo Allah na, Yuzarsef meye haka? Kana fa da nauyi seka
danne min kan Babyna"
Yusuf yace "wainine nake da nauyi, ina wani Baby yake anan?"
Tace 'ba a nan mana" tai maganar tana nuna masa cikinta.
Yusuf yasa hannu ya danna cikin nata yace "Malama bakomai anan hanji, waye yace
miki a nan ɗa yake zama"
"wayyo Allah na, Yoseef yau cinzali kake ji, dan Allah ka dena danna min cikina,
kar kasa in haifi ɗa da lotsatsen ƙeya mana"
Yace "Madam wannan cikin naki bakomai a ciki, inma akwai be zama mutum ba, amma
duk kin ishi mutane, ke wannan idan cikin ya samu na shigesu, da langwai da
Shagwaɓa"
Widad ta tura baki tace "Yuzarsef, da nace zan sakawa jaririna sunanka, amma na
fasa tunda kana adawa da baybn nan nawa"
"Iyee, ba kara ba kunya Baby, Allah ya shiryeki wallahi za'aga uwa mara kunya
gaskiya"
Yusuf yace "iko se Allah, wai yanzu ke kin haƙiƙance ɗane a cikinki? Kwana nawa
kika ƙara baki period ba?, ina shekaranjiya kika cemin mararki na ciwo baki period
ɗinba?"
"Ai bezo ba tukuna, kwana biyar ya ƙara fa, Insha Allah ina da ciki"
Yusuf yace "mara kunya kawai" yai maganar tare da danna gefen mararta ɗaya, wani
irin ihu tayi haɗi da zillo, se hawaye, Yusuf ya bita da kallo yana nazarinta.
Yusuf yace "yi haƙuri, am sorry kinji babyna, yi haƙuri bazan sake ba insha Allah,
abu nake son ji"
"Ni ƙyaleni, kawai se cin zalina kake, kuma bazan kwana da kai ba a katifata ba,
tunda haka ka koma"
"Ke kin isa ki koreni daga kan katifar nan, ina nan tare zamu kwana semun samo
Babyn Baby"
"Ni na samu Babyna in gaya maka, kuma sena rama abunda kayi min, ni wanka zanje
inyi"
Yusuf yace "ina nan ina jiranki, kije kiyi wankan kizo kimin tausa inyi bacci"
"bazan ba" tai maganar tana hararasa, sannan ta miƙe ta fice daga ɗakin tana
murmushi.
Haka suka kwana tare abunsu, cike da soyayya da ƙaunar juna, tana sake jin Yusuf a
zuciyarta, bata jin zata iya rabuwa dashi.
Saleh kam iya azaba ya shata, su ciko bokiti su danna kansa a ciki, seya suma,
banda wutar lantarki da suka dinga jona masa, ga ba Abinci babu ruwan sha, ya
galabaita fiye da tunani, banda duka da suke masa da katakwaye, sun masa laga laga
gaba ɗaya Saleh ya zama abun tausayi, ya galabaita ya lalace saboda azaba, suyita
buga masa itace a ciki, kai da ƙirjinsa, ya dinga fidda jini ta baki da hancinsa,
gaba ɗaya ya suma baya hayyacinsa a haka se da aka kwana uku, sannan suka yi waya
suka sanar da Bukar, yace musu yana nan tafe zezo gidan da ake ajiye da Saleh yaji
idan yayi laushi zuwa yanzu.
"Alhaji Bukar, kana sane da cewar mahaifinmu yazo har gidanmu ya saka hannu ya
mareni?"
"Eh, naji na samu labarin zuwansa, amma ni sam ban san da zancen ya dakeki ba"
Ramlah tace "to ya saka hannu ya dakeni, bayan tsawon shekaru be san cina shana ko
suturata ba, an gayamin cewar hatsabibine, dan haka sonake in nuna masa ya haifi
wadda ta fishi hatsabiban ci"
Alhaji Bukar yace "Anya zakifi mahaifinku hatsabibanci kuwa? Amma me kike so ayi
masa?"
"Sonake a nemo shi duk inda yake, a sauke masa hannun da ya mareni dashi"
"Naga dai shima ba mutumin kirki bane, koda bama tare dashi, labarin aika aikar
dayayi duk na sani, dan haka rama cuta ga macuci ibadane, zan kawo ƙarshen iya
shegensa, a sauke masa hannu nake buƙata"
Alhaju Bukar yace "kin samu yarinya, kije kin kwantar da hankalinki, za'ayi abunda
ya dace, yadda kike so haka za'ayi ai".
Koda Amal ta sake farkawa ta ganta a Asibiti ta tabattar ba mafarki take ba, ta
sake fashewa da kuka, ta tuna yadda suka yi da Alhaji Haruna, shikenan Ya kassara
mata rayuwa, ya cuce ta, ya gama da ita, tinƙahon kowace mace shine budurcinta amma
a banza wani tsohon najadu dabba ya kassara mata rayuwa, ya tarwatsa mata rayuwa ya
cuceta, wasu irin zafafan Hawaye suka shiga yi mata sintiri a fuskar ta, tana
tunanin me zata yiwa Alhaji Haruna ta huce, me zata yi masa wanda zesa ta huce, ita
gaba ɗaya Yusuf ta tanadar wa kanta, saboda babu komai a zuciyar ta inba shiba,
dole tayi wani abu wanda zaya rama abunda Alhaji Haruna yayi mata.
Ramlah ta kalleta tace "Amal wai wannan wani irin kukane haka? Ki saurarawa kanki
mana, Allah ya taƙaita miki wahala baki mutu ba, kuma hannun be cire gaba ɗaya ba,
amma se kuka kikeyi, ki kwantar da hankalinki dan Allah kiyi haƙuri.
Mummy da ta idar da salla tace " tayani gaya mata dai Ko zataji, tunda abun nan ya
faru take kuka, na rasa kukan ubanme take haka? Ni kin kai masa takadda makuwa
kafin abun ya faru?"
Banza tayi mata, ta ɗauke kanta ta cigaba da kukanta, Alhaji Haruna ne yai sallama,
ya buɗe ƙofar ɗakin ya shigo, hannunsa ɗauke da manyan ledoji, ya shigo suka gaisa
da Mummy, yace " Ya jikin Auta kuwa? "
Mummy tace "Jiki da sauƙi, sedai se kuka take, taƙi yin shiru, kuma ga abun be
tsawwala da yawa ba, karayace kuma ance yau za'a mata ɗori"
Lallai mutumin nan ya cika gardin ɗan iska, ya mata wannan aika aika, sannan yazo
wai yazo dubata, shiru tayi taƙi magana.
Hajiya Halima tace "Amal ba magana ake miki ba kika yi shiru? '
Alhaji Haruna yace "Halima ku ɗan bamu guri dan Allah, zan mata magana"
Ba musu suka fice, sedai kallo Ramlah ta dinga binsa dashi na tuhuma.
Yace "Haba Baby, daga abu ya faru shikenan seki ɗaga hankalinki, haba Baby Amal,
kiyi haƙuri kinji ai is not that painful, zaki warke kuma karayar nan is just an
accident, zaki warke insha Allah, amma kidena kukan haka kinji"
Ji tayi kamar ya kunna wuta a zuciyarta, tabbas ds da makami seta kasheshi kome
za'ayi mata ayi, ga mahaifiyarta sam batayi hankalin gane abunda ya faru ba.
Ganin tayi shiru, yasa ya janyo ya jikinsa yana faɗin "you make my day jiya, na
daɗe ban samu mace kamarki ba, ki kwantar da hankalinki mucigaba da rayuwar mu babu
wanda ze gane kinji"
Amal tai shiru, taƙi buɗe ido zuciyarta ta dinga tafasa, ganin tayi shiru batayi
magana ba, yasa seda yayi shagalinsa sannan ya dunƙulo bandir ɗin kuɗi ya zube
mata.
Seda yaje bakin ƙofa ze fita tace "idan ba'a gaɓa gwada maka kaidin mace ba, ka
fara ƙirgawa daga yau zaka fara gani, wallahi Haruna sena maka abunda bazaka manta
ba har abada, sena maka Baƙin tabon da yafi wanda kayi min, wallahi sena ƙulla maka
makirin da duniya basu isa su kwance maka ba, zaka gane baka da wayo daga maina
bazaka sake gwada akuyanci akan wata 'ya ba, ka saurareni....'
.
LITTAFIN KUƊI NE, DAN ALLAH KI SIYA KAFIN KI KARANTA BA DANNI BA DAN ALLAH, LITTAFI
NA ƊAYA KYAUTA NE WANNAN NA SIYARWA NE
NORMAL GROUP ₦300
VIP ₦500 NE KITURA TA WANNAN ACCOUNT ƊIN
0009450228
JA'IZ BANK
AISHA ADAM
SE A TURA SHEDAR BIYA TA WANNAN LAMBAR
07063065680
IDAN KUMA KIN SIYA AMANACE KARKI FITARMIN DAN ALLAH 🙏🙏🙏
(Albishir ga masoya, ma'abota bibiyar litattaafaina, dama ta samu zaku fara samun
litattaafaina na audio, akan YouTube channel ɗina me suna Cool Arewa TV
https://youtube.com/channel/UCD5vnvA5laU8ti4LLz2_QEg
Kuyi liking sannan ku danna subscribe, domin fara samun litattaafaina na audio,
nagode sosai da ƙaunar ku gareni"
11/21/21, 7:45 AM - Buhainat: LITTAFIN KUƊI NE, DAN ALLAH KI SIYA KAFIN KI KARANTA
BA DANNI BA DAN ALLAH, LITTAFI NA ƊAYA KYAUTA NE WANNAN NA SIYARWA NE
NORMAL GROUP ₦300
VIP ₦500 NE KITURA TA WANNAN ACCOUNT ƊIN
0009450228
JA'IZ BANK
AISHA ADAM
SE A TURA SHEDAR BIYA TA WANNAN LAMBAR
07063065680
IDAN KUMA KIN SIYA AMANACE KARKI FITARMIN DAN ALLAH 🙏🙏🙏
(Albishir ga masoya, ma'abota bibiyar litattaafaina, dama ta samu zaku fara samun
litattaafaina na audio, akan YouTube channel ɗina me suna Cool Arewa TV
https://youtube.com/channel/UCD5vnvA5laU8ti4LLz2_QEg
Kuyi liking sannan ku danna subscribe, domin fara samun litattaafaina na audio,
nagode sosai da ƙaunar ku gareni"
112_113
Alhaji Haruna yai murmushi irin na tsofaffin 'yan duniya sannan yace
"hmm Yaro man kaza, wato shi dai yaro yarone kam, ke a gwagwarmayar da nayi, babu
kalar karuwar da ban gani ba, babu kalar barazana da kaidin matan da ban gani ba,
nayi Aure Aure, nayi biye biye ba irin matan da ban gani ba, dan haka' yar ƙaramar
barazanar ki bazata tsoratani ba, you better calm yourself down, ba'a kanki aka
fara ba kuma ba'a kanki za'a ƙare ba, karki ƙarawa kanki ciwo akan ciwo, ki kwantar
da hankalinki ki more ƙuruciyarki ki tara abun duniya"
Wani gululun baƙin ciki ne yazo ya tokare maƙogwaron Amal, wanda yasa ta jan
numfashi da kyar, ta rasa me zata yiwa Alhaji Haruna wanda zesa taji ta rage azabar
da zuciyarta ke mata, ga karaya data samu ga rauni a kanta, ga uwa uba fyaɗe da
yayi mata, kuma yazo ya tsaya yana gayamata maganar banza, ta lumshe idonta wasu
irin hawaye na takaici da baƙin ciki suna bin gefen idonta.
Tana jinsa ya buɗe ƙofar yai waje abunsa hankalinsa kwance wani nishaɗi yana
ratsashi, dan ba abunda yake ji na damuwa ko tashin hankali a tare da shi dangane
da abunda ya aikata.
Kusan mintuna ashirin da fitarsa, Ramlah tai sallama ta dawo ɗakin, ta janyo kujera
ta zauna a gaban gadon Amal, Amal tace "Ina Mummy ne?"
Amal ta jinjina kai, tana sake jin wani irin zafi a hannuta da ƙasanta, ta ɗan
rintse ido tana girgiza kai, an mata illar da bazai taɓa gyaruwa ba ta gyara
kwanciyarta tana ajiyar zuciya
.
Ramlah ta kalleta tace "Amal meye tsakanin ki da wannan mutumin ne, naga fa kamar
akwai damuwa a tare da ke? Meyafaru ne"
Girgiza mata kai tayi tace "bakomai"
Ramlah tace "ki gayamin gaskiya, ko akwai taimakon da zan iyayi miki, naga kamar
akwai wani ɓoyaayyen al'amari a tsakaninku ke da shi, naji yana yiwa Mummy wasu
maganganu ne marasa kan gafo, wai ai shi ya gani yana so, wai idan zata bashi ke
yana so, ni ina tunanin ma wannan hatsarin da akace kinyi, gaba ɗaya na kasa yadda
abun kamar wani shirin film ko tatsuniya fa"
Amal taji kamar ta gayawa Ramlah gaskiya, se taga yin hakan tamkar tonawa kanta
asiri ne, kuma idan harta nemi taimakon wani, to bata cika mace ba, yakamata ta
nunawa Haruna tsantsar kaidi da makirci irin na 'ya mace.
Amal ta dake tace "Idan ma yana nufin sona yake, gaskiya ni bazan auri tsoho
kamarshi ba, amma in dai zan fizgi rabona a jikinsa ai shikenan, zan iya biye masa
nima in tatsi arziki som raina, Amma dan Allah ki temakamin da ruwan zafi mana, zan
gasa jikina, dan duk ciwo yake min"
Ramlah ta jinjina kai, taje samo mata ruwa me zafi ta rakata banɗaki, da ƙyar ta
iya kintsa jikinta, saboda karayar hannunta, ga ciwo da kanta keyi, haka ta tsaya
tai kuka me isarta a toilet sannan ta fito.
Saleh ya jigata sosai, Alhaji Bukar yaje yaga halin da Saleh yake ciki seda ya ɗan
tsorata, dan kar Saleh ya mutu, dan muddin Saleh ya mutu shikenan, abubuwa sun
lalace, dan haka yasa aka kira likitansa, ya duba shi yai masa allaurai ya samasa
ruwa, da ƙyar Saleh ya farfaɗo koda ya farfaɗo ruwan leda ɗayane se garau garau na
shinkafa da aka kawo masa, mutumin daya kwana uku babu abinci, amma ya faraka a
bashi bushshsiyar shinkafa da wake, abunka da me jin yunwa ya kama Abincin nan ya
dinga turawa, sedai ba'aje ko ina ba yaji kamar yana cin duwatsu ne, dan haka ya
dinga aman abincin nan, Saleh ya galabaita sosy, dan kwanakin nan gaba ɗaya a ɗaure
yake a igiya kamar rago, dan haka kowace gaɓa tasa ciwo take masa, ga shedar igiya
ta fito raɗa raɗa a jikinsa duk fatarsa tayi jajawur, ga ciwon ƙirji saboda dukan
da yake sha da katako kamar Ɓarawo.
Bukar ya kalli Saleh yace "wuya koda magani ba daɗi, ina fatan zuwa yanzu ka
ɗanɗana kuɗarka kuma zaka bani haɗin kai, ka gayamin abunda na buƙata, ko kuma in
sa a ninka maka wannan azabtarwar da ake maka.
Shiru Saleh yayi beyi magana ba, se suka numfashi dayake na wahala, yayi zuru zuri
dashi kamar wanda yayi amai da gudawa, maganar duniya Amma Saleh yaƙi cewa uffan.
Me Adda yace "wai ba zakayi magana ba, semun ƙarasa sauke maka allon ƙirjinka?"
Bukar yace "saurara tukuna, wannan idan aka yi ƙwaƙwaran yunƙuri ze iya mutuwa,
kuma idan ya mutu ze jamin gagarumar asarane a yanzu haka, dan haka ƙyaleshi
tukuna, zuwa anjima idan be faɗa ba, a kamashi kusamin kansa a ƙasa, ƙafafunsa a
sama a samo ruwan zafi ku saɓulemin fatarsa dashi, ku barshi anan gurin "
Saleh yabi Bukar da kallo, yana jinjina mugunta da zalunci irin na Bukar, haka
Alhaji Bukar ya fice ya barshi a hannun su me Adda yayi tafiyarsa.
Akayiwa Amal aiki a hannunta, aiki yayi kyau an ɗorata, mutane nata tururwar zuwa
dubata a Asibiti, kullum a can Hajiya Halima take kwana, kwana uku da yin ɗorin
likita ya sallameta, yace su dinga zuwa duk bayan sati biyu ana dubawa harya gama
warkewa gaba ɗaya.
Aka basu magunguna da sauran abun buƙata suka tafi gida, ma'aikatan gidan su Nura
su Murtalah duk suka shiga suka dubata, suna fitowa Nura yace "Allah ya ƙara,
Allah yasa karta warke da wuri hannunma ya ruɓe, jakar matar nan da yake 'yarta ce
ta samu matsala, ji yadda ta dinga zarya a Asibiti, amma lokacin da megida yana
kwance a Asibiti, sefa ta ga dama take zuwa, ɗantane kawai yaita wahalar jinya,
shiba ubansa ba ba komai ba"
Isa yace "karkiya wa Amal wannan muguwar addu'ar, da dai waccan me ƙaton bakin ce
Ramlah, ai gara Amal sau dubu da Ramla, dukda itama Amal ɗin ta iya rashin mutunci"
Murtalah dake gefe yace "hakane kam, Allah sarki, Allah ne kaɗai yasan inda megida
yake, kaga kaman ma sum rufe babinsa, basa neman inda yake Yusuf kawai suke nema"
Nura yace "Allah sarki, wallahi tsayinsa nakeji, koba komai ba ruwansa wallahi"
Isa yace "kai dai bari, aiko ni da nake jin haushinsa da addua nake masa yanzu, na
dinga duba yadda wasu abubuwan suk dinga faruwa amma baya magana, nan ze zauna in
ta gayamasa baƙaƙen magana amma ko kallo bam isheshi ba, ima dana sanin wasu
abubuwan da nayi masa wallahi "
Nura yace " nima inayi, amma ka fini zaƙewa sosai, kaga nifa da ace wani ne wallahi
ko dagaske sace yarinyar nan yayi, wallahi sena hana a kama shi, yasha wahalrta
sosai wallahi, ta gara shi san ranta "
Isa yace " Ai wannan akwai sa'a, duk garawar da take masa basu rabu ba, ya dinga
mata biyayya, nifa wallahi ban yadda shiya sace ta ba, makirci ne kawai "
"Nan Hajiya ta kirani falonta tace min, duk yadda zanyi inyi in nemo mata inda
adireshin gidansu Yusuf yake, nayi nayi ya gayamin yaƙi, in ba makirci na Meza tayi
da adireshin sa, kuma kun san wani abu, babu ma'aikacin da ake ɗagawa ƙafa a gidan
nan kamarsa saboda 'yar masu gida"
Murtalah yace "ƙwarai kuwa, dan ba ƙaramin ci musu mutunci take ba saboda shi, amma
dagaske an saka nemo inda yake?"
Isa yace "wallahi dagaske nake, sedai sam kamar yasan an sani fafur yaƙi gayamin,
shegen wayone dashi kamar dila"
Nura yace "ba ɗan sanda bane, kai ka isa ka masa wayo nan da nan, ai kaima kasan
baka isa ba"
"Au kai a labaran da aka sanar ba gani bane, to ɗan sandan farin kaya ne, aikin
bincike yake a gidan nan"
Murtalah yace "to an barka a baya, baka san kanun Labaran ba kam, ɗan sanda ne ai
shiyasa hankalin mutan gidan ya sake tashi"
Isa yace "tir ƙashi, amma wannan anyi munafuki, shine be taɓa gayamana ba, muka
zauma dashi muyi ta sakin baki"
Nura yace "to mutan gidan ma basu sani ba, balle kai ance maka jami'in sirrine
kawai seya zo ya fara gayamaka ai shi ɗansanda ne? Saboda be san aikinsa ba kobe
san ciwon kansa ba? Kai dai Isa naga ranar sa zaka waye"
Ramlah ta shigo ɗakin tace "Amal kizo ga matan Alhaji Harun nan sunzo dubaki"
Kallon Ramlah tayi kamar bata gane me tace ba, Ramlah tace "ko bakiji bane?"
Amal tace "Ai abunne naji wani iri, sun sanni ne daza suzo dubani?
Ramlah tace "oho muku, sun san Mummy ai, idan ke basu sanki ba"
"haka kawai, bazan zo ba, ki koma ki san abunda zaki gaya musu"
Tai maganar tare da kwanciya, Ramlah ta ɗan taɓe baki ta juya ta fice.
Amal ta sake jinjina rashin kunya, da iskanci irin na Alhaji Haruna, saboda ya
gawurta har matansa ya turo su dubata, to suce mata me? Ji tayi kamar taje ta tona
masa Asiri a gurinsu, amma meye shedarta? Taja tsaki tai shiru tana ci gaba da
tunani.
Kamar wadda aka mintsina ta miƙe da sauri, dan seda ta kusa fama hannunta, ta tako
a hankali ta fito, a hanya suka haɗu da Mummy, dan Ramlah ta gaya mata saƙon Amal,
Mummy tace "da meyasa kikace bazaki fito ba?"
Amal tace "gaba ɗaya jikina ciwo yake, bana son hayaniya ne, sedai kuma naga babu
daɗi, shiyasa nace kawai bari inzo mu gaisa"
Suka fito gaba ɗaya falon, uwargidansace se Amaryarsa wadda take yarinya sosai,
Amal ta ƙaraso suka gaisa, sukayi mata ya jiki, Amal ta amsa tana binsu da kallo
ɗaya bayan ɗaya.
Da zasu tafi uwargidan tace "ga mukullin mota yace a baki, gata can yace a baki
tunda taki ta lalace, Allah ya ƙara sauƙi"
Amal tai murmushin takaici tace "Amma fa nagode sosai, ai masa godiya ace masa
naji daɗin motar nan fa, sannan ina nan tafe karɓar mukullin gida kuma"
Basu kawo komai ba, tunda ce musu yayi 'yace a gurinsa tunda sun san Hajiya Halima,
Amal ta karɓi lambar wayarsu, tace sa dinga gaisawa.
Nurat tana zaune suna hira da Mummynta, ta gwada layin Anwar harta gaji amma shiru
bata shiga, tun abun baya damunta har ya fara damunta, ta kalli mahaifiyarta tace
"Mummy fita nake son yi fa"
"Kije ina?"
"Mummy duk inda ta kama, tunda aka samin doka yau kwana nawa ban fita ko ina ba,
gashi ina buƙatar in ɗan fita ɗin in rage zafi, kullum ina cikin gida kamar wata
mara gaskiya"
Mummy tace "nidai babu duwana, duk abunda kika jawa ka ki shikenan ba ruwana, kin
san yadda kuka ƙareta dashi wancan karon dai"
"Mummy gidan Daula nake son zuwa, ina sin jin ko lafiya, layin Yaya Anwar baya
shiga fa Sam"
"Mummy ba haka bane, ai gaida me gaishe ka ko baze amsa ba, amma tunda hakane, bari
in jida zuwan bdk Khalil, idan yazo ya biya ya dubamin ko lafiya"
"Ke wani Khalil ɗin, baki san ranar da yazo ya tarar dashi ba kirana yayi yana
masifa ba, wai zaryar me Khalil yake masa a cikin gida ba? Wai in dakatar da shi da
zuwa ba"
Nurat tace "to Mummy ke kuma baki ce masa komai ba, sannan me Khalil yayi masa?"
"Oho kin san halinsa na rashin gaskiya ai, shi duk wani motsi seya zata bin
diddiginsa ake, shiyasa kullum bashi da nutsuwa ai, shima dole zanyi masa waya, ya
rage yawan sintir a gidan nan, ya bari se an kwana biyu yazo"
Nurat ta dafe kai tace "Ohh my God, ba dai gudun tinon Asiri yake ba, Insha Allah
ya gamu da shi kenan, in Allah ya yadda se asirinsa ya tonu"
"Ke rufemin baki, kar yazo ya tarar dske kina wannan maganaganun, ya zata wani abun
muke shiryawa"
A fusace Nurat ta miƙe ta e "to ya zata iɗn mana Mummy, na gajiya walilahi, am
tired"
Ta juya ta bar falon ranta a ɓace, zuciyarta na wani irin tafasa tana tururi.
Yusuf na zaune yana zaune, Widad na kwance akan cin yarsa, yana ta wasa da gashin
kanta, tana masa hira sedai gaba ɗaya hankalinsa baya kanta, ya tafi can duniyar
tunani, ƙirjinsa nata bugawa haka kurum, yaka sa gank dalikin bugawar ƙirjin nasa,
"Yoseef" ta kira sunansa, da sauri ya dawo hayyacinsa yace "Na'am"
Ta gyara kwanciyarta tace "Yuzarsef, kwana biyu Saleh bezo na, nifa hankalina yayi
gida, gaba ɗaya na ɗan fara damuwa tunda yake zuwa be taɓa cemin komai akan
mahaifina ba, zuciyata na son ganin mahaifina, ina yawan mafarkinsa ina son jin
abunda ke faruwa gaskiya"
Seda gaban Yusuf ya faɗi, dan Saleh ha tabbatar masa babu wani sahihin kabadi har
yanzu akan ɓatan mahaifinta, gashi ita bata sani bama, ya dake yace "tabbas nima
ina ta fama da kokwanto a raina, ina son sanin meke faruwa a gida, gashi naga kwana
biyu Saleh bezo ba"
Tace "hakane, dukda ni ba shiga sabgarsa nake ba, amma dole zan tambaye shi ya
Daddyna yake, in dai lafiya ƙalau ne, baze jure tsawon wannan lokacin be gannj ba,
dase yazo har nan kota halin yayane, amma tunda naji shiru something is going wrong
somewhere, gidanmu nake son komawa "
" Insha Allah nothing is wrong anywhere, komai yana tafiya dai dai, am yakamata mu
koma gida haka kam"
Yace "Ameen, but Baby ta yaya zamu tabattarwa da al'umma Aurenmu, meye shedarmu?"
Yace "hakane Allah sheda ne, amma baze yuwu mu gayawa mutane haka ba, dole mu nuna
shedar aure mukayi, tunda au can babu wansa yasan hakan"
Widad tace "karka damu, Saleh ya sani, ga al'ummar garin nan da muka zauna tare
dasu, suma sun isa sheda ai"
Tace "Ameen"
Alhaji Musa yana zaune a ɗakinsa yana cin Abinci, ya ɗau waya ya kira Nurat yace
yana son ganinta a ɗakinsa, Mamanta ta kalle shi tace "lafiya kuwa? Ina fatan dai
ba wani laifin tayi maka ba?"
"ina ruwanki ne? Nida 'yata bazan kirata ba, ki zuba ido kawai"
Tace "Ai gara in dingayi ina bin ba' asai, saboda naga kai abun naka se a hankali
gaba ɗaya"
Nurat tayi sallama ta shigo da dogon hijjabinta a jikinta, yace "Bacci kike ne?"
Ta jinjina masa kai yace "yawwa 'yar gidan Daddy, dama ba wani abune yasa na kiraki
ba, zan sanar dake jn the next couple of weeks zaki koma Karatu"
Yace "can inda kika baro mana abroad, na nema miki imperial College London, kije
kiyi business administration ɗin da kike so a can"
Girgiza masa kai tayi tace "Amma Daddy ai ba haka mukayi da kaiba, ka tambayeni
nace maka ni a Nigeria nake son in cigaba, ka amincemin kuma yanzu kace ba haka ba"
Yace "look Nurat, ina nema miki sauƙi ne da kuma safe environment, inda zakije kiyi
karatun ki cikin nutsuwa da kwanciyar hankali"
Tace "Nan ma akwai nutsuwa da kwanciyar hankali ai, ni dai kawai ka ƙyaleni a nan,
bana son zuwa"
Aikuwa ya harzuƙa yace "ke, nine zance ga yadda za'ayi kice ke ba hakaba? Waye ya
haifi wani tsakanin nida ke?"
Nurat tace "kai ka haifeni, amma kaima ka cika Alƙawari mana Daddy, baka gudun
yadda tarbiyyata zata kasance, ni ina can ku kuna nan ni gaskiya bazanje ba"
Ya kalli Maman Nurat dake gefe tana jinsu yace "wato ke kike ziga yarinyar nan
take rashin mutuncin da taga dama ko? Idan ba hakaba ya za'ayi ina magana tana
magana?"
"Malam babu ruwana ni, 'yarka ce yau da gobe ai tafi ƙarfin wasa, ka fiye son kanka
da yawa, shiyasa tun yarinyar nan na maka biyayya harta zo ta dena yi maka saboda
son zuciyarka, kuma nima gaskiya ban yadda inyi nesa da ita ba, tunda mun baro
ƙasar ma meye kuma ita za' a maida ita"
Alhaji Musa yace "lallai ba shakka, na ƙara tabattar da cewa ke kike ziga yarinyar
nan, in faɗa ki faɗa tana gani ai dole itama ta fara, to bari kijin in gayamiki
tafiya daram, seta tafi dole ta bar ƙasar nan taje inda na nema mata karatu"
Nurat ta fashe da kuka tace "ni gaskiya bazani ba, kuma idan aka takura sena je,
wallahi barin gidan nan zanyi, dama naga yanzu ba'a ƙauna ta, tunda har yunƙurin
rabani da rayuwata akayi" tai maganar tana ficewa daga falon, tana ji yana ƙwala
mata kira amma tai banza dashi tai tafiyarta ko waigowa ba tayi ba.
Yusuf yana kwance har wajen shaɗayan safe, idonsa a lumshe yayi rigingine yana jin
yadda gabansa ke cigaba da faɗuwa akai akai, Widad ta shigo ɗakin ta fito daga
wanka tace "Yoseef, wai ba zaka tashi bane haryanzu shaɗayan rana, seka sa Hari
tazo tana gayamin magana ko? Ina jinta shekaranjiya wai na fiye jaraba goma na
safiya ina rufe ƙofa saboda shegen sa ido irin nata"
Yusuf ya kwashe da dariya yace "Ai gaskiya ta faɗa ba ƙarya ba, hakane abunda ta
faɗa waike dole sekin samo Baby ba"
Widad ta buɗe baki tace "lallai Yoseef sannu, hakama zakace ko? Kaifa kace in rufe
ƙofa sanyi kake ji, shine zakamin sharri"?
"dole ki rasa mana, kuma yau bazan kwana akan katifarki ba, a ƙasa zan kwana"
"A'a dai karkizo kina min kuka, wai kai Yoseef meye haka? Dan Allah kazo ka kwanta"
yai maganar yana kwaikwayon muryarta.
Yai murmushi ya maida idonsa ya lumshe, ta ɗan ƙura masa ido, ya ɗan faɗa sedai
masha Allah Yusuf ba dai kyau ba.
"Ba wani kyau a nan gurin, wannan zanƙalelen hancin kaman cartoon"
Tazo tasa hannu ta matse masa hanci, Yusuf yace "ko ki sakarmin hanci, ko kuma
yanzu in ɓaro ɗan dake cikin ki"
Yai dariya yace " Yarinya baki da komai a wannan cikin naki "
Tai maganar tana tura baki, yayin da ya bita da kallo yana jin sonta na ƙara
ninkuwa a zuciyarsa, idan ya tuna lokacin da take garashi da izza da rashin
mutunci, ga gefe guda azabtuwa da soyayyarta daya dingayi ba tare da ta sani ba,
idan akace masa akwai rana da zata zo su kasance a haka baze yadda ba, amma shine
zaune da ita a ƙarƙashin inuwa ɗaya ta Aure, suke zaune ba tare da ya ɗaga masa
hankali ba, wani farinciki ne ke ratsa zuciyarsa, tabbas da Widad ta rayu da masoya
na gaskiya, mussman tare da mahaifiyar ta ba zata yi wannan izzar da jin kai ba,
sedai rashin masoya, da kuma tsantstsar zalunci da butulci da aka gwada mata yasa
tayi wa mutane gaba ɗaya kuɗin goro mussman talakawa.
Saleh gaba ɗaya ya sadaƙar, jira yake kawai suzo su fara gana masa azabar da Bukar
yayi umarni, sedai basu yi masa komai ba sedai ɗaɗɗaureshi da suka kuma yi.
Yana zaune a inda yake aka buɗe ƙofar ɗakin da yake kwance a ciki, ya ɗaga kai seya
ga 'yan sanda sun shigo, tare da Alhaji Bukar, ya nuna musu shi yace "gashi nan, ku
tuhume shi yasan inda suke, kuyi masa duk wata izaya da duk wani abubda zesa ya
faɗi gaskiya, karku saurara masa dan Allah"
Ɗaya ɗan sandan yace "karka wani damu, zamuyi abunda ya dace" suka kwancewa Saleh
wannan igiyoyin suka ɗauke shi suka sashi a mota suka tafi dashi.
LITTAFIN KUƊI NE, DAN ALLAH KI SIYA KAFIN KI KARANTA BA DANNI BA DAN ALLAH, LITTAFI
NA ƊAYA KYAUTA NE WANNAN NA SIYARWA NE
NORMAL GROUP ₦300
VIP ₦500 NE KITURA TA WANNAN ACCOUNT ƊIN
0009450228
JA'IZ BANK
AISHA ADAM
SE A TURA SHEDAR BIYA TA WANNAN LAMBAR
07063065680
IDAN KUMA KIN SIYA AMANACE KARKI FITARMIN DAN ALLAH 🙏🙏🙏
(Albishir ga masoya, ma'abota bibiyar litattaafaina, dama ta samu zaku fara samun
litattaafaina na audio, akan YouTube channel ɗina me suna Cool Arewa TV
https://youtube.com/channel/UCD5vnvA5laU8ti4LLz2_QEg
Kuyi liking sannan ku danna subscribe, domin fara samun litattaafaina na audio,
nagode sosai da ƙaunar ku gareni"
11/21/21, 7:45 AM - Buhainat: LITTAFIN KUƊI NE, DAN ALLAH KI SIYA KAFIN KI KARANTA
BA DANNI BA DAN ALLAH, LITTAFI NA ƊAYA KYAUTA NE WANNAN NA SIYARWA NE
NORMAL GROUP ₦300
VIP ₦500 NE KITURA TA WANNAN ACCOUNT ƊIN
0009450228
JA'IZ BANK
AISHA ADAM
SE A TURA SHEDAR BIYA TA WANNAN LAMBAR
07063065680
IDAN KUMA KIN SIYA AMANACE KARKI FITARMIN DAN ALLAH 🙏🙏🙏
(Albishir ga masoya, ma'abota bibiyar litattaafaina, dama ta samu zaku fara samun
litattaafaina na audio, akan YouTube channel ɗina me suna Cool Arewa TV
https://youtube.com/channel/UCD5vnvA5laU8ti4LLz2_QEg
Kuyi liking sannan ku danna subscribe, domin fara samun litattaafaina na audio,
nagode sosai da ƙaunar ku gareni"
114_115
Saleh dai ne ce komai ba, yana jin yadda ake tafiya dashi a mota 'yan sanda, a
galabaice yake dan haka be san inda suke tafiya ba, harabar police station akayi
parking, aka fito da Saleh, yana tangaɗi haka aka tankaɗa shi cikin cell aka ƙulle.
Duk da yamma ce amma sauro har ya fara shagali a gurin nan, ga zafi a gurin kamar
oven, haka Saleh ya baje a ƙasa ƙirjinsa da cikinsa na masa ciwo kamar zasu tsage,
saboda duk daya sha da katako.
Yana jin wani ɗan sanda yayi sallama, sauram suka dinga sara masa, ɗaya daga 'yan
sandan da suka ɗakko Saleh yace "Oga gashi nan a cell, munje mun ɗakko shi"
"Kai baka san me zaka rubuta ba, ku rubuta bayani akan an same shi da laifin haɗa
kai da Yusuf, sun sace 'yar gidan Nasir Daula, sun ɓoye su, ka dai rubuta abunda
yakamata"
Ɗan sandan ya sara masa yace "ok sir, za' ayi yadda kace"
"Yawwa that's very good, and a matsa shi yadda yakamata ya faɗi abunda ake nema a
gurinsa"
Yace "good"
Hankalin Nurat ya tashi sosai, ganin cewar dagaske mahaifinta yake ze raba ta da
ƙasar, itama tayi ɗamarar wannan karon zata bijire masa, kome ze faru se taga ƙwal
uwar daka, se taga ƙarshen abunda mahaifinta yake yi, dan barin mutum irinsa suna
cigaba da abunda suke so a doron ƙasa hatsari ne ga al'umma, wataran za'a iya wayar
gari mutanen kirki su ƙare, ta ɗau wayarta ta kira Khalil, Khalil ya ɗaga yace
Nurat tai ajiyar zuciya tace "bad news brother, Daddy ya dage akan cewar wai sena
tafi imperial U. K Inyi karatau a can, me Daddy yake nufi dani ne?"
"Calm down dear, make your statement clear please, kamar yaya imperial Collage, ke
kaɗai zaki koma UK ɗin kiyi karatu, wanda kika yi a baya be isa ba"
"Nima shi na gani brother, shifa yayi min alƙawarin zanyi school a Nigeria, a
Nigeria zanyi high institution, Amma kawai yazomin da wannan maganar, da alama yana
zargina ne da fara bin diddiginsa, ni kuma gaskiya i won't tolerate it dear,
gaskiya zan bijire"
Khalil yace "subhanallah, Nurat don't say that again, haba Nurat na sanki da
biyayya da haƙuri, me zesa ki fara faɗar haka kuma? Haba Sister na"
Kuka Nurat ta fashe dashi tace "Broz Khalil, iya biyayya da haƙuri kasan nayi,
nayiwa Daddy biyayya yadda yakamata, nayi ƙoƙarin kasancewa a cikin 'ya' ya nagari
masu haƙuri, tun taso wata fa kullum cikin tsangwama da kyarar mahaifiyata yake,
amma ban taɓa kulashi akan hakan ba, Brother babu ɗan daze dinga ganin mutuncin duk
mutumin daze dinga cin zarafin mahaifiyarsa, komai kusanci da soyayyar dake
tsakaninsu kuwa, amma na share na ɗauke kai, nake masa biyayya, ni da mahaifiyata
mun masa biyayya, amma baya gani Khalil, baya gani kullum cikin zagi da cin zarafin
mu yake, har gara ni yana ɗagamin ƙafa, akan mahaifiyata lokaci yayi da zan nuna
masa nima 'yar halak ce, zan nuna masa ni ma' yace, wallahi bazan sake masa biyayya
ba nagaji Khalil "
Khalil yace " Calm down, calm down my dear, i feel your pain Baby, kiyi haƙuri dan
Allah, nasan me kike ji a zuciyarki, amma dan Allah karki bijirewa mahaifinki,
hakan ba halinki bane ba"
"Yanzu na koya, kuma shine ya koyamin, kuma zega canji tabbas, na masa biyayya har
akan abunda be dace ba, haka kake so in cigaba da binsa yana jan rayuwata data
mahaifiyata a ƙasa?"
Cikin kuka tace "Khalil, Daddy da farko ni yasa in hilaci Widad, aka sumar da ita
za'a sace ta, Yusuf ya ceceta, wani abunma baze faɗu ba ni kawai ka ƙyaleni, idan
kuma ya dage sena bar ƙasar nan wallahi sena kawo masa ɗan shege ya raina a cikin
gidansa na rantse da Allah "
" Innalillahi wa inna ialaihi raji'un, Nurat kin san me kike faɗa kuwa? Ko kin fara
shaye2 ne ban sani ba"
Ta ƙara sautin kukan ta tace "idan ma ban fara ba ina daf da farawa, dan wallahi ya
takuramin zan bar masa gidansa in shiga duniya, ko in tafi England inyi irin
rayuwar da yake ganin gara inyi irinta da ya kasa cinma nasa burin"
Khalil ya kwantar da muryarsa yace "kina jina Nurat, am sorry kinji, nasan a irin
matsala da damuwar da kike ciki, amma kin san zukata nawa ne zasu shiga garari idan
kika lalace? Mummynki da kike wannan damuwar saboda ita, ya kike gank idan taga
tilon 'yarta ta faɗa mummunar rayuwa? Ya kike tunanin shi masoyin naki ze kalle ki
idan kika koma mutuniyar banza? Family duk zasu shiga damuwa idan suka ji labarin
yarinyar da suke so, suke ji da ita ta shiga wata rayuwa daban, dan Allah kiyi
haƙuri ki bar wannan maganar "
" Brother idan na bar wannan maganar wacce zanyi? Am tired wallahi na gaji dayi
masa biyayya, Khalil abun ba sauƙi fa, dama mutumin kirki ne da sauƙi"
"Nasani Nurat, ki kwantar da hankalinki kinji, Insha Allah zan shigo gidan naku,
zanzo muyi magana amma ki dena kukan nan please, kuma karki sake faɗin wannan
maganar kinji Light" gabata ne ya faɗi jin yace mata Light, sunan da Yusuf ke
gayamata, ajiyar zuciya tayi tayi jifa da wayar, tana ci gaba da rushewa da kuka.
A hankali hannun Amal yana warkewa, an kwance mata bandejin kanta ma, se hannun da
haryanzu akayi hangin ɗinsa a wuyanta, yanzzhma ta fito daga wanka tana tsaye a
gaban madubi, daga ita se towel kanta a tsefe, ta baje gashin kanta, ba laifi
gashinta yana da tsawo, ga hannuta sagale a wuyanta, ga goshinta inda yayi tabon
ciwon da Alhaji Haruna yaji mata, ta dinga ƙarewa kanta kallo a mudubi.
A hankali tace "dubeni, mace har mace, bani da makusa sedai an gurguntamin rayuwa,
an rabani da mutuncina saboda zalunci, kuma ya biyoni da wasu tarkacen banza saboda
ya rainamin hankali, bayan tabo na sarari da yayi min, ya barmin na zuciya me
matuƙar ɗaci da baze goge ba, me zanyiwa mutumin nan in huxe, wace irin illa zan
masa daze dasa masa baƙin ciki a rayuwar sa ne? Me zanyi ne Amal kiyi tunani
ƙwaƙwalwarki bata ja Sam "
Ta dafe kanta ta fashe da kuka, tana tuna yadda ya suka dinga kokawa, da muguntar
da yayi mata yacinma burinsa, zubewa tayi a gurin tana wani irin kuka, me tsuma
zuciya
" Duk laifinki ne Mummy, laifin kine, nace ba zani ba kika ce se naje, Mummy why? "
Jikinta har rawa yake saboda kuka, dukda daga wanka ta fito amma ta haɗa gumi, ga
hawaye ga majina se shesheƙa take.
Ramlah ta shigo ɗakin, ta tarar da ita a zaune a ƙasa, idonta yai ja tana kuka.
Ramlah ta ƙaraso da sauri tace " ke Amal lafiya kuwa? Meye haka? Meye ya same ki"
"Bakomai"
Tsaki Amal Tayi tace "excuse me please, dan Allah ki bani guri, ina son kaɗaicine"
"Na miki kama da Widad ne, balle kice na haukace? Kawai ki fita ki bani guri"
"Amma Amal"
"Dan Allah ki fita ki ƙyaleni, kad in haɗiyi zuciya in mutu, dan Allah ki fita!"
Tai maganar cikin kuka, Ramlah na fita taje ta dstse ƙofarta ta kwanta akan gadonta
ta cigaba da rera kukanta, tana jin Ramlah ta kira Mummy, suka dinga buga ƙofar
amma tayi musu banza kamar ba taji ba.
Bukar ya kira Alhaji Haruna, Ya ɗaga wayar suka gaisa, Bukar yace "kunyi waya da
Musa ne?"
Alhaji Haruna yace "A'a gaskiya, na kwana biyu bamuyi waya ba"
Alhaji Bukar yace "ok, na zaci kunyi wayane, haryanzu be ce mana komai ba akan
batun wanda ze saka mana hannun, kuma yace mu saurareshi zuwa Laraba, anjima zamuyi
meeting kota zoom ne, sannan ya batun takaddar da aka ce wannan yaron ya bari? Ka
karɓo mana ɗinne kokuwa?"
Alhaji Haruna yace "eh na karɓo, naje har gidan da kaina naje na karɓo takaddar"
Alhaji Bukar yace "good, kasan duk wata sheda da zesa a ganemu, dole mu ɓatar da
ita kar wani ya samu, dan haka ka kawomin takaddar nan"
Yace "shikenan, Insha Allah zan kawo maka ita, sannan zan sanar dasu batun meeting
ɗin nan da kace"
Alhaji Bukar ya ajiye wayar, ya miƙe ya bar ɗakin dayake, dan ya manta da ya karɓi
tajaddar yazo da ita nan gidan ko kuma a can ya barta gurin da ta bashi?.
Hindu tana tsakar gida, suna ta aiki a tsakar gida, Hanne tana gefe tana gyaran
wake zasuyi alala.
Hari tace "sannu da aiki Hanne, Allah ya kaimu bikinki mu kira masu kiɗan ƙwarya
muyi ta juyi a gidan nan"
Hanne ta taɓe baki, dan ita sama gaba ɗaya haushin Auren nan ma take ji, dan Yanzu
haushin mijin da zata aura takeji, dan gani take bashi da komai idan ta kalli
Yusuf, ita dai tana son Yusuf sosai, tana jin ina ma ya aure ta, da tafi kowacce
mace dace a ƙauyen nan, da yana ɗan kulata amma yanzu ya dena, saboda wannan
koɗaɗɗiyar matar tasa me kama da Yahudawa.
Hindu tace "Allah dai ya kaimu bikin nan ds rai da lafiya, ban san wane irin
shagali zanyi ba, nima sena gyagije nayi shagali, idan kika tattara kika tafi in
gaje gurin kwanciyar ki da nawa, Abinci ma zan haɗe nawa da naki ne, dama yanzu ba
ƙoshi nake ba" Hindu Tayi maganar cikin sigar wasa da zolaya.
Amma Hanne ta karkace ta kyaɓe baki, ta kalli Hindu tace "aifa dama ina zaki ƙoshi
tunda mayya na gidan? Ai gara in tattara in bar miki gidan ki cigaba da haɗa
kafaɗunki dana iyayen mu, tunda dai ke kinfi kowa baƙin jini, babu wanda yake sonki
balle kisa ran zakiyi aure ki bar gidan nan, ai se kiyi ta zaman gidan ki ƙare ki
tsufa a gida, mujiyar garin nan, shikenan mutum ba zuciya balle ya samo wanda ze
rufa masa Asiri ".
Ai tuni idon Hindu ya ciko da hawaye, ita har ga Allah wasa tayi wa Hanne, amma
harta fara yan kamata baƙaƙen maganganu da cin zarafi, Hanne na ɗagowa suka yi ido
huɗu da Yusuf, da alama duk yaji abunda ta faɗa, sekuma ta shiga kame kame, dan
wata irin kunyace ta kamata, bece komai ba ya sa kai ya fice, dan be fiye son shiga
sabgar iyalan gidan ba.
Yana fita Widad ta fito tsakar gidan nan, taga yadda Hindu ta nutsu tayi shiru, ido
duk ya tara hawaye saboda zafin maganganun Hanne.
Widad tace "ke Hindu, wai ita wannan banzar 'yar uwar taƙi haifarki tayi? Haifarki
Tayi da zata dinga gaya miki magana kina jinta? Wai wane ɗan matsiyatan zata aura a
garin nan da har take miki wannan gorin haka? Wanda zata aura ɗin ma ya kai a kira
shi namiji da take miki gori a kansa "?
Hanne tana hura hanci, cike da ƙauyanci da jahilci tace " Wallahi, tallahi nafi
ƙarfin auren matsiyaci, niba matsiyaci zan aura ba"
"wallahi kika bari nazo inda kike, na shaƙeki se na jefa ki a rijiyar nan, saboda
me zaki takurawa yarinya dan bata magana, dan kinga tana da haƙuri, wallahi ki
kiyayeni akan ɓata mata rai"
Wata irin zuciya ce ta kwashi Widad, sedai Hindu tai saurin riƙeta tace "A'a
Amarya yi haƙuri ƙyaleta kawai"
Widad ta harzuƙa matuƙar gaske, ji take tamkar ta jefa Hanne a rijiya, mussman idan
ta tuna yadda take juya manyan attajirai masu ji da kansu, amma wata kucakar 'yar
ƙauye na gayamata magana, ƙwafa kawai tayi tace "ba alfahari ba amma Wallahi da
kin san wacece Widad, da baki isa ki yadda in haɗa ido dake ba, dan wallahi ko masu
gyaran gadon baccina sun fiki kyan gani, ki zuba ido zakiga mijin da Hindu zata
aura, Jahila kawai"
Ta wuce ɗakinta tana huci, duk wannan budurin Gwaggo da Hari basa nan akayi shi,
amma abun yana damun Widad taji an taɓa Hindu, setaji kamar ita aka taɓa, danma ita
Hindun ce shashasha take tsayawa ana mata wulaƙanci.
Amal kam wani tunani tayi a ranta, dan haka ta miƙe da ɗan sauri, ta fita falo,
Mummy ta kalleta tace "kinga damar buɗewa yanzu?"
Amal tace "Mummy Ramlah ta kasa fahimta tane, wani lokacin idan ina cikin jin
zafin ciwo, bana son kowa a inda nake, nafison kaɗaici amma se a takuramin, kun
kasa ganewa"
Tace "da sauƙi, Mummy dan Allah aramin wayarki zan transfer ɗin kuɗi, ni banki sun
hanani wai ba network"
Ba musu ta miƙawa Amal wayar, Amal ta karɓa ta koma gefe, ta tura lambar Alhaji
Haruna wayarta, ta bata wayar tace "Mummy, ga wayar nagode"
Ta koam ɗakinta, tana zuwa ta kulle ƙofa ta zauna akam gadonta ta kira Alhaji
Haruna.
Lokacin yana tsaka da bulayin neman takadda, ya ɗaga suka gaisa dashi, sannan tace
"Naga saƙonka, amma meyasa kwana biyu ba kazo ka dubani ba"
Se ynzu ya ɗau muryar ta, yai murmushi yace "nima naji saƙonki, ance bayan mota
zakizo karɓar gids ma"
"zuciya ta, ta fara rayamin kawai idan na warke zan bazama in nemi arziki, in more
ƙuruciya ta, idan ka shirya nima a shirye naake zan dawo gareka, tunda aikim gama
ya gama tunda fari"
Yai wata shegiyar dariya sannan yace "ni zaki yaudara, ko har kin manta abunda kika
gayamin a Asibiti, kaina yana ja sosai dan haka abune mawuyaci kiyi galaba a kaina,
tabbas naji daɗin kasancewa dake sedai bazan sake amincewa dake ba, tunda kikayi
wannan fueucin, ki sake shawara kinji 'yan mata, idan da gaske kike ki bazama ki
kama wasu alhazan, nikam na gama muma na biya tunda na bada motar miliyoyi"
Bata sanma yadda akayi ta ajiye wayar ba, tana jera ajiyar zuciya kamar wadda tai
gudu, duk yadda take tunanin abun ya wuce tunaninta, ashema matan suna suka tara,
ba kowaccece ke iya kaidin ba, shi kansa shirya makircin ba abune me sauƙi ba, tai
sharkaf da gumi tana sake tunanin wata hanyar.
Yusuf na dawowa Widad ta manta da damuwar da take ciki, sedai duk da hakan seda ya
gane, yace "Maman Baby, ya akayi ne naga kamar ranki a ɗan ɓace yake"
Tace "A'a ni ba abunda akayi min, Ina ɗan tunani akan Hindu ne, ina ma Megari ze
bani ita idan mun koma gida"
Yusuf yace "gaskiya abune me wahala, ya ɗau 'ya ya bamu alhalin bamu da wata
dangantaka a tsakaninmu"
Ta jinjina kai tace "hakane, Gaskiya nifa na damu Saleh yazo ayi wacce za' ayi, na
fara gajiya hankalina yayi gida sosai fa"
Yusuf yace "ki kwantar da hankalinki, nima shi nake jira yazo, muji abunda yakamata
ayi"
A gurin 'yan sandan ma babu sassauci, baƙar wahala Saleh yake sha, dan yana
kyautata zaton an masa illa saboda duka, dan a nan ɗinma' yan sanda ke sa kulki,
suyi ta dukansa izaya daban daban wai lallai seya faɗi inda su Yusuf suke, ga
rashin Abinci gashi ko Najasa ne sedai yayi a nan, nan da nan Saleh ya fita daga
hayyacinsa, ya canza kamanni fuska duk ta kumbura, ko ina rauni me yake zubda jini,
sun doddoke masa ƙafafuwa da ƙyar yake iya miƙewa.
Da Safe Yusuf yana kwance akan cinyar Widad, ta samu comb se jagwalgwala masa sumar
kansa take yi, shi kuma yana lumshe ido, can yace "gaskiya ki ƙyalemin gashina
mana, haba se izaya kikemin a kaina"
"To aini na gaji se jagwalgwala min suma ake, ga zafi banda ma tsabar rigima irin
taki ta ina za'a kitsa sumata?"
Yace "shikenan, Allah sarki ni, gaskiya idan na kuma jin zafi sena rama, sena aske
wannan gashin naki da akewa mutane iyayi dashi"
Tai murmushi tace "daka temakeni, dan ba dan babu kyau ba sena rage shi, kuma idan
ka aske ai kanka kayiwa, kaine kake wasa dashi ai"
Hindu Tayi sallama kawo musu Abincin Safe, akayi mata izinin shiga tana shiga ta
tarar da Yusuf kwance akan cinyar Widad.
Ta sunkuyar da kai cikin matuƙar jin kunya, Widad tace "sarkin kunya, idan na aura
miki ɗan birnin haka zaki dingayi masa?"
Hindu ta juya da sauri tana murmushi, ta bar ɗakin, Widad tace "Yuzarsef, wallahi
da ina da Yaya, ko wani ɗan uwa da babu abunda ze hana in roƙi ya auri Hindu, she's
very kind and innocent"
Yusuf yaga abun na Widad ba na ƙarewa bane, dan haka ya tashi daga cinyarta yace
"ke nagaji, kaina se zafi yake duk kin jagwalgwala min suma"
"ni kayiwa haka ko? In ƙara ganin ka taɓamin gashi ni da kaine, kuma ma insha Allah
ta mace zan haifa, saboda in dinga mata kitso ta zama ƙawata kuma"
Yusuf yace "sannu sarkin shirirta, da shirme, ga tsabar ƙuruciya mutum baze gane
hakan ba, se ya zauna dake, to ni bame yiwa 'yata kitso balle a jagwalgwala mata
kai, idan kin haifi namiji nakine, mace kuma ta wace"
"A' a ban yadda ba, gaba ɗaya nawane, bayan kace baka son Baby"
Yusuf yace "Nina ce miki bana so? So kai amma ki bari ki samu cikin tukuna, sekimin
iyayi da tsari"
Ta kwaɓe fuska kamar zata yi kuka tace "insha Allah ina da shi"
Yusuf yace "idan na dawo da daddare, kwaɗon gurji da zogale zan mana, zaki ci?"
Widad tace "Sosai ma, ranar Gwaggo tayi naci da daɗi Sosai"
Duk iya dubawar da Saleh zeyi, yayi amma ya rasa takaddar nan, ya duba ya duba amma
takadda tace ɗaukeni inda ka'a ajiyeni, gashi yacewa Bukar ya karɓo takaddar nan.
Ya koma guest House ɗinsa, inda suka dinga kokawa da Amal, ya dinga duba takaddar
nan, yai tsai gana dubawa ya birkita komai, ya hango ta a ƙasan gado.
Hamdala yayi, ya durƙusa ya ɗakko takaddar, yana ajiyar zuciya ya buɗe takaddar,
sedai me ba takaddar bace form ne na koyon kwalliya na Amal, tsaki yayi yai jifa da
takaddar yana tunanin ina yasa waccan takadda data bashi, amma kuma lokacin da ta
bashi takaddar ai be buɗa ba, balle yasan me ta bashi, hankalinsa na kan yai mata
akuyanci kawai, ya birkita ko ina amma babu wata takaddar se wannan, nan take gumi
ya shiga tsasttsafo masa.
Widad taita jiran Yusuf ya dawo, dan se nishaɗi take ji ze kawo gurji yayi musu
kwaɗo, bayan ya dawo da kayan gurjin da yamma, ta zauna ta cire ɓawon tsaf, ta
gyara zogalen suka ɗora zogalen akan wuta, suna zaune suna hira a ƙofar ɗakinsu
suna aikin su, hankali kwance yayin da zamantakewarsu kan burge wasu daga mutanen
gidan.
Ya gama suka haɗa Kwaɗon nan a roba, Suka bawa wanda zasu bawa, Widad se haɗiyar
yawu take, ta zauna zata saka hannu ta fara ci Yusuf yace "tsaya waye yace ki fara
ci, salon ki fini loma ki fini ci ko?"
Ai ba ta saurareshi ba, danji take kamar hanjinta ze fito idan bata ci ba, jiki na
rawa ta sa hannu ta fara cin Abunta, Yusuf yana kallonta yana nazarinta, tunda ta
fara ci bata saurareshi ba seda taji ta ƙoshi tukuna, ta miƙe taje ta wanke
hannunta ta sha ruwa ta dawo ɗaki sannan tace " Yawwa ina jinka, mema kace ɗazu?"
"Yawwa mijin acici, kai dai ubangiji Allah yayi maka albarka, ya saka maka da
alheri nagode sosai"
Kawai ta kwashe da dariya tace "ba ruwana cin abuna zanyi ehe"
Tace "What? Wai Yoseef meye haka? Kawai ba damar inyi magana seka canza mata
ma'ana"
Tai maganar tana kai masa duka, ya kwanta yana dariya yasa pillow yana karewa.
"Eh naji bakomai, a haka 'yan mata suke rububina, saboda munina a haka suke sona"
Widad tace "Wallahi idan muka koma gida, duk wadda tayi gangancin raɓarka zata ga
matakin da zan ɗauka wallahi"
Yace "haka akeyi, shikenan duk suna kallo se kice baza'a kulani ba, bayan kin
sanni da farinjini, cewa fa kika yi in Auri Hanne"
Tsaki tayi zata tashi, ya fizgota jikinsa, yasa fitila ya haske mata fuska.
Yusuf yai ƙasa da murya yace "An taɓa gayamiki ke kyakkyawa ce kuwa My wife?"
Da sauri tace "No, i don't mean you should divorce me, ka cikani i mean"
Yai murmushi yace "nima na sani ai, ni dake ai mutu ka raba Babayna me kama da
teddy"
Tace "Yoseef me yake damunka ne yau? Duk ka takuramin nice kuma me kama da teddy?"
"Eh ramawa nayi, ko kin manta haka kika cemin cartoon jiya"
Yai maganar yana dariya, itama dariyar ce ta kamata, ta buɗe baki kamar zata cije
shi, amma ta fara kissing ɗinsa.
Kamar ranar suka fara kasancewa da juna, sunyi nishaɗi mara misaltuwa, sun
farantawa junansu rai sosai, kowanne yana sake jin ɗan uwansa a ransa.
Haka suka wayi gari cikin farin ciki, sedai dukda wannan farincikin Yusuf se fama
yake da fargaba, ya rasa dalilin hakan.
Yana ta shiri ze fita, yaji kamar harbin bindiga, gabansa ya faɗi yace "Lovely,
kamar harbi fa nake ji"
Widad tace "A'a ko dai tunanin gurin aiki kake, amma wane irin harbin bindiga ana
zaune ƙalau? Bari inyi walha, idan na idar seka tafi"
Ta juya ta tada salla, tayi raka'ar farko zata yi ta biyu suka ji Hayaniya, aka
sake harba bindiga a ƙofar gidan mutane nata guje guje.
Yusuf yace "Innalillahi wa inna ialaihi raji'un"
Daga tsakar gida suka ji ana "duk wanda ya motsa, zamu fasa kansa da bindiga, kowa
ya tsaya a inda yake"
Gaba ɗaya jikinsu se tsuma yake, Hari ta samu wani lungu a bayan randa ta shige, se
zare ido take saboda tsoro.
Nan da nan sega jiniyar motar' yan sanda ta ƙaraso
Da gudu Widad ta fito tsakar gidan, amma taga 'yan sanda tare da Saleh hannunsa duk
ankwa a cikin mawuyacin hali.
Widad tace "ban sani ba, bazan faɗi inda yaken ba"
Hari daga inda ta laɓe tace "Wudas ki dena magana karsu kashe ki fa"
Yusuf ya fito daga ɗakinsu, jikinsa sanye da jallabiya, ya ƙarasa gabansu ya miƙa
musu hannunsa cikin surrender
.
Widad ta fashe da kuka tace "No! This is impossible, me yayi muku? Laifin me yayi
mijinane fa, ku cire masa wannan cuff ɗin"
Su kai mata banza suka tasa ƙeyar Yusuf, itama suka sata a gaba ihu take tana
kururuwa akan su sake shi amma sukayi burus da ita.
Aka sashi a bayan motar 'yan sanda, idonsa yayi ja ya kasa magana, se kallonta da
yake gaba ɗaya ta birkice se ihu take tana kuka, muryarta harta fara dashewa.
"Ina sonka, Yusuf ina sonka, I love you Yusuf, dan Allah ku sakarmin mijina, beyi
laifi ba, beyi laifin komai ba"
Yusuf ya ƙura mata ido, ya lumshe idonsa a hankali, yayin da Widad ke zubda wani
irin hawaye tana kuka, me sauti.
Aka sakata a motar gida seinna, shikuma a bayan motar 'yan sanda gashi ga Saleh,
kowanne hannu da sarƙa!!!
LITTAFIN KUƊI NE, DAN ALLAH KI SIYA KAFIN KI KARANTA BA DANNI BA DAN ALLAH, LITTAFI
NA ƊAYA KYAUTA NE WANNAN NA SIYARWA NE
NORMAL GROUP ₦300
VIP ₦500 NE KITURA TA WANNAN ACCOUNT ƊIN
0009450228
JA'IZ BANK
AISHA ADAM
SE A TURA SHEDAR BIYA TA WANNAN LAMBAR
07063065680
IDAN KUMA KIN SIYA AMANACE KARKI FITARMIN DAN ALLAH 🙏🙏🙏
(Albishir ga masoya, ma'abota bibiyar litattaafaina, dama ta samu zaku fara samun
litattaafaina na audio, akan YouTube channel ɗina me suna Cool Arewa TV
https://youtube.com/channel/UCD5vnvA5laU8ti4LLz2_QEg
Kuyi liking sannan ku danna subscribe, domin fara samun litattaafaina na audio,
nagode sosai da ƙaunar ku gareni"
11/22/21, 4:49 PM - Buhainat: LITTAFIN KUƊI NE, DAN ALLAH KI SIYA KAFIN KI KARANTA
BA DANNI BA DAN ALLAH, LITTAFI NA ƊAYA KYAUTA NE WANNAN NA SIYARWA NE
NORMAL GROUP ₦300
VIP ₦500 NE KITURA TA WANNAN ACCOUNT ƊIN
0009450228
JA'IZ BANK
AISHA ADAM
SE A TURA SHEDAR BIYA TA WANNAN LAMBAR
07063065680
(Albishir ga masoya, ma'abota bibiyar litattaafaina, dama ta samu zaku fara samun
litattaafaina na audio, akan YouTube channel ɗina me suna Cool Arewa TV
https://youtube.com/channel/UCD5vnvA5laU8ti4LLz2_QEg
Kuyi liking sannan ku danna subscribe, domin fara samun litattaafaina na audio,
nagode sosai da ƙaunar ku gareni"
116_117
Sosai Widad ta cigaba da gunjin kuka, yayin da mutanen ƙauyen suka fito suka yi
duru duru suna kallo, ɗaliban Widad se kuka suke, haka Hindu gaba ɗaya ta birkice
banda kuka ba abunda take yi, ba Hindu ba kawai hatta Megari, da su Hari hankalinsu
ya tashi sosai, ga Sunusi mijin Jamila baya nan akazo aka kama su Widad.
Ana tafe a hanya amma bakin Widad yaƙi mutuwa, kuka kawai take akan a sakar mata
mijin ta, tun Yusuf yana iya juyo muryarta da kukanta, har muryar tata ta dashe ba
ajin me take faɗa sosai, haka sukaita tafiya har suka fito daga wannan kwazazzaban,
da ramukan dake hanyar garin, suka hau kan kwalta ɗoɗar suka kama hanyar Kano.
Alhaji Haruna fa ya haɗa uban gumi, saboda ya tabattar da babu wannan takadda,
takaddar form ɗin koyon kwalliya ta bashi, ba shiri ya ɗau wayarsa ya kirata da
lambar da ta kirashi ɗazu, tana ganin kiran nasa Amal ta tashi da sauri, ta duba
har zata ɗaga kawai ta fasa, ta ajiye wayar yai mata kira yafi Ashirin, ƙarshema ta
saka wayar a silent tai kwanciyarta.
Yai wujiga wujiga, saboda takaddar nan saboda yasan Bukar ba kyau, gashi ya riga
yace aiya karɓo, tunda takaddar zata iya zama sheda a kansu, wannan wasiƙar zata
nuna akwai halin rashin gaskiya da mahaifiyar Anwar take aikatawa wanda yasa ya bar
gida, idan tuhuma tayi tuhuma kuma za'a gano su.
Ya tura mata saƙo kusan kala shida amma babu reply, can dai ta ɗau wayar ta duba
saƙon daya turo, magiya yake mata akan dan Allah ta ɗaga wayarsa, mahimmiyar magana
yake son suyi.
Tana cikin karantawa kuwa ya kuma kira, seda taja aji sannan ta ɗaga, yai ajiyar
zuciya yace "habba kyakkyawa, tun ɗazu naake kiran waya, amma anyi biris dani?"
"A'a kwantar da hankalinki, ai duk abun bana zafi bame ko ɗaga hankali, magana
zamuyi"
Yace "Yawwa, dama cewa nayi wannan takaddar da kika kawomin, kinyi mistake ba
wasiƙar kika bani ba, form ɗinki ne na koyon kwalliya, kinyi mistake gurin bani"
"A'a dama ba wani abu bane ba, cewa nai zanzo in karɓa in an jima, saboda takaddar
tana da mahimmanci sosai"
"Karka sake ka soma zuwa inda nake, bazan bayarba ka riƙe wadda na baka a matsayin
ta"
Alhaji Haruna yai gyaran murya yace "haba beautiful Baby, ai abun duk bekamata ya
kaimu ga haka ba, meye na ɗaukar zafi haka? Ai abun bana zafi bane ba, ki gayamin
me kike so ayi yanzu in karɓi takaddar nan? Ko nawane zan baki"
Amal ta janyo Jakarta, wadda yace tayi accident da ita, ta duba amma itama taga
babu takaddar a ciki, amma tai ajiyar zuciya tace "nima nazo maka da buƙata ta,
amma kaƙi amincewa, dan haka kowa ha riƙe buƙatarsa, bazan bayarba gara asirin kowa
ma ya tonu a huta"
Yace "dan Allah kar muyi haka dake, ki bani takaddar nan na riga na cewa Bukar na
karɓo takardar yace in kai masa, kuma yanzu inzo ince bahaka ba, baze sauraramin
ba"
Amal tace "Ai gara karya saurara makan, kamar yadda nima baka sauraramin ba, kuma
baka karɓi buƙata ta ba"
Am tace "A'a ai kuma mun wuce wannan maganar yanzu, zan baka takadda bisa sharuɗa,
yanzu abu na farko zan gaya maka Account Number ɗina, ina son inji wasu kuɗi masu
nauyi, domin inci kaji in warke da wuri daga raunin daka min"
Ta kashe wayarta, lumshe ido tare da faɗin "Alhamdilillah, cikin sauƙi Allah ya
kawomin hanyar da zan rama cin zarafin da kayi min, tabbas inaga yadda takkadar nan
nayi, dan babu ita a jakata, amma a haka zan maka rashin mutunci in rama"
Alert ne ya shigo wayarta, ta ɗaga ta duba 500k ne, ta jinjina kai tace yanzu aka
fara wasan
Seda yayi mata kira biyar, sannan ta ɗaga a fusace tace "wai meye ne?"
Tunda suka taho Yusuf bece uffan ba, yai shiru yana saƙawa yana kwancewa a
zuciyarsa, tabbas duk sunan da za'a kira shi dashi, ko a tuhume shi dashi, bashi da
abunda ze kare kansa dashi, tabbas shi dai tunda ya tashi a rayuwarsa a siraɗin
ƙaddara yake, daga wannan ya faɗa waccan, daga waccan ya faɗo wannan, haka ya
sunkuyar da kansa yana ta tsabihi ga Allah, akan ya sauƙaƙa masa wannan lamarin.
Sun shigowa cikin garin kano, akayi hanyar babbar headquarter hukumar 'yan sanda
dake garin kano, motarsu Widad kuma tayi wani gurin, ai tana ganin haka ta kuma
fashewa da ihu, tana bori tana kuka tana "ina zaku kaishi? Ina zaku kaimin
mijina? Beyi laifin komai ba, babu abunda yayi muku, ku ƙyalemin mijina wayyo Allah
na Yoseef duk nice sila, saboda ni ka shiga wannan tashin hankalin, Dan Allah ka
yafemin Yoseef, Allah ka fitar da mijina daga sharrin Azzaluman nan, Allah ga
bawanka ka fitarmin da mijina"
Ta ƙarasa maganar, tana wani irin kuka me taɓa zuciya babu wanda ya kula ta a cikin
'yan sandan suka cigaba da tafiya.
Wani ofishin' yan sandan aka tafi da ita, suka fito da ita daga mota zuwa gurin
'yan sanda, idanunta sun kumbura sunyi ja saboda kuka.
Wani ɗan sanda yace "gata yallaɓai, yanzu muka shigo gari, shi an wuce dashi
headquarter, ita kuma gata"
Ɗan sandan ya kalleta yace "Good, Madam congratulations, you are now free, mun
cetoki daga hannun wanda sukayi garkuwa dake"
"Niba garkuwa yayi dani ba, wanda sukayi garkuwa dani daban, Yoseef ceto na yayi,
shine ya temakeni beyi garkuwa dani ba, ka gaya musu suje su sakarmin mijina"
Ɗan sandan yace "koma dai ya akayi, wannan ku ta shafa ke dashi, muba abunda ya
dame mu, zamu rubuta sannan mu sanar da duniya cewar, munyi namijin ƙoƙari gurin
bincike mun gano wanda yayi garkuwa da Widad Nasir Daula, kuma ba wani bane face
direbanta, wanda ya kasance ɗansanda, yaje gidansu yai basaja dan yayi garkuwa da
ita, nasan hakan ze sake ɗaga darajar rundunar mu a ga namijin ƙoƙarin da muke, ba
dare ba rana gurin kare rayuka da kuma dukiyoyin al'umma "
Ta faɗa cikin ƙaraji, tace " idan har ina raye ina numfashi, ko komai nawa ze ƙare
se Yusuf ya fita, babu wanda ze cutarmin dashi, baku isa ba azzalumai ma cuta,
lokacin da aka yi garkuwa damu muna buƙatar taimakk, babu wanda ya taimakemu na
kusa rasa rayuwa ta, se yanzu da yayi komai ya gama, Allah yasa ya kare rayuwata,
shine za'a masa sharri wallahi bazan lamunta ba, he's my Husband "
Ɗan sandan nan yace " ku ɗaukemin wannan mahaukaciyar daga gabana, a tafi da ita
Asibiti a duba lafiyarta, sannan ku kiramin Ubanta Bulama tunda babu wanda yasan
inda wancan yake "
Widad bata gane meyake nufi ba ta cigaba da kukanta, haka suka kawo Ambulance dan
iya makirci, aka sheƙa mata wani abu ta sume a gurin, aka kira 'yan jaridu suka
cika gurin, aka ɗauki Widad aka saka ta a motar Agajin gaggawa wato Ambulance suka
tafi da ita.
Jaridu kuwa da sassafe shafin farko, hotunan Yusuf ne da Saleh, musamman na Yusuf
ɗaure a cikin sarƙa ya sunkuyar da kai, gefe ga hoton Widad da aka ɗauka an fito da
ita daga ofishin 'yan sanda an sata a ambulance, daka kunna gidan radio, labarai ko
talabijin babu abunda zaka fara ji se
"Me dokar bacci ya ɓige da gyangyɗi, kuma ƙarshen tika tiki tik inji hausawa A
yaune jami' am tasaro sukayi nasarar cafke jami'in ɗan sandan nan na farin kaya
wato Yusuf Bashir Maitama, wanda yayi garkuwa da 'yar gidan fitaccen me Arziki nan
a gida da wajen Nigeria wato Nasir Daula,' yan sandan sunyi nasarar gano shi ya
sace ta tare da ɓoyeta a wani ƙasurgumin ƙauye dake garin Bauchi, 'yan sandan sun
ceto Widad Nasir Daula, wadda ke cikin mawuyacin hali, da zauwansu basu yi wata
wata ba aka kira motar Asibiti aka tafi da ita domin duba lafiyarta, zamu ci gaba
da bibiya da kasa kunne domin jin wani mataki hukuma zata ɗauka akan wannan ɗan
sanda, wanda ake tunanin har shi Nasir Daula ɗin shine yai garkuwa dashi, mu dai
anan se muce Allah ya kyauta, yai mana tsari da irin wannan jam'ian tsaro a cikin
al'ummar mu"
Nan fa gari ya ɗau ɗumi, aka dinga cece kuce, wasu na Allah wadai suna Tsinewa
Yusuf, yayin da wasu ke a bari a ga abunda bincike zeyi tukuna.
Widad kam bata sake sanin inda kanta yake ba, inda har a gadon Asibiti aka bita aka
dinga ɗaukar hotunan ta, ga fuskarta tayi ja saboda kuka, da gajiyar tafiyar hanya,
amma aka dinga ɗauka ana watsawa duniya wai tana cikin mawuyacin hali, hannunta
ɗauke da drip.
Alhaji Haruna ya kasa zaune ya kasa tsaye, ba a taɓa raina masa hankali kamar yadda
akayi yau ba, ya kira layin Hajiya Halima, Ramlah na zaune a falo wayar ta fara
ringing, Mummy tana ciki tana amsa wata wayar dan haka ta ɗaga wayar tasa a
kunnenta tace "Hello"
"Dan Allah idan Amal tana kusa ɗan bata wayar muyi magana"
Ta miƙe ta tafi ɗakin Amal, amma ɗakin a rufe harta kashe fitila ma "
Ramlah tace " gaskiya tayi bacci, dan ta rufe ɗakinta ma ta kashe fitila"
Yace "Yasalam"
Ya kashe wayar yace "Amma dai Allah ya Tsinewa yarinyar nan, kaga min shegiyar
yarinya mara albarka" ya ciji yatsa yai ƙwafa yace "dani kike zancen wallahi, kema
sema wulaƙantaki,"
Amal ta ɗau wayarta ta tura masa saƙo tace "ka cigaba da kiran Mummy, kana cewa
kana son Magana dani, wallahi idan baka yi wasa ba sena gayamata abunda kayi min,
kuma kasan halinta sarai, kasan buyaginta zata maka abunda kai kanka zaka kasa gane
kansa, dan haka muddin ba zaka cika sharaɗina ba, wallahi ba zan baka ba na gaya
maka, kuma ni wannan kuɗin sunmin kaɗan, nima a account dina ina da wanda suka
fisu"
Ta kashe wayarta ta sake kwanciya, ya duba message ɗin, yaja wata ajiyar zuciya
yana cije leɓe, totally ta riga ta gama raina masa hankali, yama rasa me zeyi ko me
zece.
Yana nan tsaye yana tunanin mafita kiran wayar Bukar ya shigo wayarsa, ya ɗaga jiki
na tsuma, yace "Hello"
"Haruna, yau muna da zama na gaggawa, cikin dare dan haka duk ku tattaru"
"banda ita, sannan kazo min da wannan takaddar, zamuyi magana a kai itama"
Daga nan ya kashe wayar, Alhaji Haruna ya yakice gumi, yana huci Amal ta masa
rashin mutunci, dan kawai abu ya shiga tsakaninsu se tayi masa haka?.
Mutan ƙauyen da Widad suka zauna suka dinga taradaddi, kowa da abunda yake faɗa
wasu suna dama megari yayi wauta, wataƙila dama can 'yan fashi ne ko wasu masu
laifin ne, amma daga zuwansu ya karɓesu, be san daga inda suke ba.
Hindu kam kuka, kamar wadda aka kama uwarta, ita kanta Hari gaba ɗaya jikinta a
sanyaye yake, wunin ranar gidan daga masu koke koke, se masu salallami, Hanne kuwa
ko a jikinta.
Koda Sunusi ya dawo, Jamika ta gaya masa abunda ya faru, dan haka yace dole gobe
insha Allah ya tafi kank, yaje yaji ba'asin abunda ya faru.
Jamila tace "dan Allah karkaje, kar kaima a kama ka, dan na san da kana nan
wataƙila da kai zasu haɗa"
Sunusi yace "da nayi musu me? Kince an kama Saleh, kuma Saleh shiya kawo su nan,
meyasa aka kama shi, dole zanje inji"
Daddare megari ya tara iyalansa yace "to wannan bayin Allah dai, ni dai a ɗan
zaman da mukayi dasu, ban tunanin mutane ne marasa gaskiya, ko makamancin haka,
zamanmu da su ma mu alkhairi ya zame mana a garin nan, dan haka dan Allah ina
roƙonku da kuyi haƙuri ku dena kuka, kukan ya isa haka, Hasana nasanki da son 'ya'
ya kuma zamanmu dasu jin shaƙu dasu sosai, dan Allah kidena kuka kiyi musu Addu'a,
Hindu Baffa kema kukan ya isa haka, muyi musu Addu'a, Allah ya basu mafita sannan
Hari a samo makulli a rufe musu ɗakinsu, kar wanda ya sake shiga tunda da kayansu a
ciki "
Hari ta tashi ta shiga ɗakinta ta samo mukulli, tana ƙoƙarin rufewa taga bokitinsu
a tsakar gida, ta tafi ta ɗakko bokitin, kawai ta fashe da kuka tace " Allah sarki
Wudas, da yanzu muna faɗa akan ruwan zafin da zata yi wanka, tace sena bata na bawa
mijin ta, ban taɓa ganin abun tausayi kamar yau ba, yadda ta rikice tana kuka,
Allah sarki Allah ya fitar dasu"
A kaita bata haƙuri, aka kulle ɗakinsu aka bawa Megari mukullin, ya kai ɗakinsa ya
ɓoye.
Yusuf yana kwance a cikin cell, an raba masa cell shida Saleh, sauro yana ta masa
buduri a ka, yai rigingine yana tunanin ya Umma zataji idan wannan mummunan labari
ya isheta?.
Aka buɗe ƙofar cell ɗin, wasu 'yan sanda suka shigo su biyu, ya tashi zaune yana
kallon su.
Ɗaya ya kalleshi yace "munafuki, kalleshi kamar na Allah, amma ƙasurgumin Azzalumi
ne, kai garkuwa da' ya ka koma kayi da Ubanta, saboda kai Azzalumi ne, kuma a haka
wai kai ɗansanda ne"
Yusuf yai shiru be ko ɗaga kai ba, ɗayan yace "rabu dashi corporal Sani, zuwa gobe
in Allah ya kaimu semun sauya halittun fuskarsa, kafin 'yan jarida suzo, a buga shi
a nunawa duniya shi, azzalumin banza dana wofi kawai"
Yusuf dai yai shiru bece komai ba, suka gama zage zagensu suka fita, suka sake rufe
shi, tun Abincin safe Yusuf be kuma cin komai ba, ga doguwar tafiyar da suka yi,
amma sam baya jin yunwa tunanin makaomarsa kawai yake a wannan hali da yake ciki.
Nurat na kwance cikin dare, taji Mahaifinta yana waya ƙasa ƙasa, ya fito daga
ɗakinsa da alama dai fita zeyi, ta kalli agogo ƙarfe biyu da rabi na dare, ta buɗe
ƙofar ɗakin ta fito falo, aikuwa yana fitowa ya ganta a falo, ya ɗan haɗe rai yace
"ke me kike yi a falo a wannan tsohon daren haka?"
Ta nufi hanyar kitchen, tana tunanin ina zashi a wannan tsohon daren, ta fito ta
tarar da shi a falon a tsaye, yace "kinsha ruwan?"
Harta juya ta tafi, ta waigo taga yana tsaye yana kallon ta, tace "Amma naga kamar
fita zakayi, ina zaka yanzu dare yayi sosai"
"Yaushe na fara wasa dake? Ko kuma kika zama uwata da zaki dinga tuhuma ta haka?"
"hmm Daddy kenan, ai kaine kake abun tuhumar, wani irin abune wannan da ba'ayi ido
ma ganin ido ba se yanzu a tsakiyar dare haka hmmm Allah dai ya kyauta?"
Ta buɗe ɗakinta ta shige, ta barshi tsaye yana binta da kallo, yarinyar da idan ta
ganshi jikinta ke rawa, itace take gaya masa magama haka, tabbas uwarta ce ke
zigata kuma zeyi maganinsu gaba ɗaya.
Kamar yadda suka saba haɗuwa yauma sun hallara gabaɗayansu, suna zazzaune a ɗakin
Hotel ɗin da ya zamana babu ma me kama shi sesu.
Alhaji Bukar yace "ku duk baku sani ba, dukda yadda da labarin ya yaɗu a daren nan?
To ina nufin Yaron nan Yusuf, direbanta wanda aka yi garkuwa dasu tare"
Alhaji Bukar yace "An kamosu a wani ƙauye a Bauchi, inda Saleh ya basu mafaka,
yanzu haka yana hannun 'yan sanda, za' a tattare duk wata sheda da ta kamata daga
nam za'a kaishi kotu, zamu saki kuɗi ayi masa shari'a da hukuncin daya dace da shi,
saboda babu wanda ya ta:a kawo mana cikas da tangarɗa a harkar nan kamar shi, kunga
daga nan babu wanda ya isa yace mune muka sa akayi garkuwa dasu"
Alhaji Munir yace "good, wannan abu yayi kyawuuu sosai, kuma ya tafi yadda ake so,
dan haka semu hanzarta, mu kuma samu hanyar da zamu ɓalli namu kason tun kan Daula
ya bayyana, dan shi har yanzu bamu san fa inda yake ba, kar muje wasu su rigamu
karɓa abun nan fa"
Bukar yace "na toshe duk wata hanya da zata saka wani ya mallaki abun nan bamu ba,
sannan dole nasa a matsa yaron nan, idan ma abun yana hannunsa ya faɗi inda suke"
Alhaji Musa yace "kai amma abu yayi kyau wallahi, komai ya tafi yadda yakamata"
Alhaji Bukar yace "Haruna ina takaddar da wancan yaron ya bari, ɗan gurin Halima?
Shima nasa a nemo shi, duk inda aka ganshi kawai a kawar dashi, bama san duk wani
abu da zesa a samu sheda a kanmu"
Alhaji Haruna yai tsilli tsilli da ido yace "Amm.. Mm.. Wallahi an ɗan samu
akasine, na rasa inda takaddar ta faɗa amma ina ta ƙoƙarin dubawa"
Yace "Ayimin afuwa dan Allah, Insha Allah za'a nemota in kawo"
Alhaji Bukar yace "shikenan, nan da kwana bakwai, na baka isashen lokaci, nan kusa
nake so a fara shari'ar yaron nan, ba da nisa ba, kuma ina son a rufe duk wata
hujja da zata bayyana mu"
Alhaji Haruna yace "insha Allah, zan kawo takaddar nan ba da jimawa ba"
Widad ce ke ƙoƙarin farkawa, se jujjuya wuyanta take tana kuka cikin bacci, "Wayyo
Allah na, yuzarsef yunwa nake ji, zuciya ta ciwo take, Yoseef dan Allah, dan Allah
ka dawo please! Ta farka a gigice tana kiran Yoseef! Yoseef kana inane?"
Bulama ne da Matarsa Hajiya Sarah a gigice suka yi kanta gaba ɗaya, Bulama yace
"Sannu daughter, sannu ki kwantar da hankalinki, kin ganni a tare da ke, ga Maman
Iman ma, an kuɓutar dake ki kwantar da hankalinki"
"Ni bazan kwantar da hankalina ba, ina mijina yake? Ina Yoseef kace su sakarmin
shi, ni ba saceni yayi ba, wallahi idan basu sake shi ba mutuwa zanyi, laifina ne,
duk saboda ya ceceni haka ta faru dashi, beyi laifi ba, tun farko seda na gaya masa
death contract ne amma ya amince, kaga abunda nake nufi Yoseef, dan Allah ku
ƙyaleshi idan wani abu ya sameshi bazan yafewa kaina ba, dan Allah ka cewa Bukar na
dawo, ni yazo ya kamani yasa a sakarmin mijina dan Allah "
Tai maganar wasu irin hawaye na ambaliya daga idonta, idanun da suka rine zuwa
kalar ja jawur suka kumbure.
Bulama yace "toni ina na san wani Bukar, balle in nemo miki shi? Ke kaɗai kika
sanshi, ni ban san a inda yake ba"
(Albishir ga masoya, ma'abota bibiyar litattaafaina, dama ta samu zaku fara samun
litattaafaina na audio, akan YouTube channel ɗina me suna Cool Arewa TV
https://youtube.com/channel/UCD5vnvA5laU8ti4LLz2_QEg
Kuyi liking sannan ku danna subscribe, domin fara samun litattaafaina na audio,
nagode sosai da ƙaunar ku gareni"
118_119
Alhaji Haruna kam juyi yayi ya farka ya ganshi kwance a gurin daya sha lemon nan,
shi dai yasan da magariba Amal tazo, amma yanzu yaga kamar yammace, nan da nan ya
tashi da sauri yana dube dube, ya kalli agogo yaga ƙarfe biyar na yamma, ya duba
yaga wayarsa a gefensa a kashe, me yarinyar nan tayi masa haka? Ko kuma meye ya
faru da shine?
Yai yai ya tuna wani abu amma ya kasa, ya gagara tuna komai daga inda ya sha lemon
nan baya iya tuna komai, ya tashi ya fito falonsa amma komai yana nan yadda yake,
babu abunda ya canza.
Duk ya lalleƙa babu wani canji daya gani, amma ya akayi yayi wannan baccin haka?
Ya tambayi kansa, tabbas wannan yarinyar ce tayi masa wani abu, sedai ya kasa gane
meyafaru dashi.
Sunusi duk yadda yake tunanin lamarin ya wuce nan, dan daya zo Kano ya samu labarin
inda su Saleh suke tsare, sedai tun daga bakin gate wani yace masa tun wuri yayi
takansa, karma a san daga imda yazo ko kuma shi wanene a gurin Saleh, idan ba haka
ba tabbas shima kamshi zasuyi su rufe har dashi.
Haka Sale ya koma babu wani daddaɗan labari, su kuma su megari suna can suna jiran
sa yazo ya gaya musu yabake ciki, sedai yanayin fuskarsa kawai ya nuna musu babu
nasara.
Me gari yace "Sunusi, kayi mana bayani, da kaje kanon menene ya faru? Ya kukayi
dasu?kaga su Yusuf ɗin da Saleh fatan suna lafiya?" megari ya jero masa tambayoyin.
Sunusi yace "Baffa, lamarin nan fa ya wuce inda kake tunani fa, duk abun ba yadda
muke tunani bane, ita wannan yarinyar daka gani, matar wannan Yusuf ɗin Wato Widad,
'yar gidan Alhaji Nasir Daula ce, wai ance Yusuf ɗin ne suka haɗa kai da Saleh
sukayi garkuwa da ita, dan su karɓi kuɗin fansa, shine sukazo suka ɓoyeta a garin
nan"
Hansai tace " wai Daula dai shahararren attajirin nan da ake labarinsa? Wanda ake
yawan faɗansa ɗin nan"
Gwaggo tace 'biri yayi kama da mutum, kwata kwata yarinyar nan ba kalar wahala
bace, yanayin yadda take rayuwarta da yadda bata iya wasu abubuwan ba ze tabattar
maka da bata tashi cikin wahala ba, sedai gaskiya bazan taɓa yadda wai satota
sukayi ba, nan fa suka zo da ita babu lafiya Yusuf ne ya goyota a bayan sa, bata
yadda da kowa seshi farkon zuwa su, kuma da satota yayi da tabbas tayi yunƙurin
guduwa wataran "
Hari tace " Akwai dai wani abu a ƙasa, amma yadda take ji da Yusuf ɗin nan ƙaryane
a ce satota yayi, komai shi, kullum tana liƙe dashi, sannan ace satota yayi gaskiya
ban yadda ba sam "
Sunusi yace " to kai Baffa da baka san daga inda suke ba, ka karɓe su?"
Megari yace " Saleh ne ya kawomin su, yace garinsu faɗa akeyi, babu kwanciyar
hankali an kashe iyayensu, shida ita 'yan uwane, amma ba ciki ɗaya ba, na wuce gaba
aka ɗaura musu Aure saboda dai ai baka ƙi taimakon mutum ba, amma ni dai gaskiya
ban yadda ace wai satota sukayi ba, dan lokacin da suka zo gidan nan, shi kamsa
Yusuf ɗin kamar a galabaice yake bashi da lafiya, zaka ce daga gurin da ake yaƙi
suke '
Hindu tace "kuma da kaje babu wanda ka gani a cikinsu, daga Amarya har mijin
nata?"
Sunusi yace "ke, case ɗinfa babba ne, yafi gaban yadda kike tunani, kedai kiyi ta
addu'a kawai"
Hindu tace "Allah sarki' yar uwata, gaskiya na tausaya mata, ashe 'yar gidan
attajirai ce amma tazo tai rayuwa a wannan ƙauyen namu? Kuma taita binmu tana
lallaɓamu mu koya mata abu, kuma da alama mijinta kawai ake nema, da akazo kamasu
tambayarta suke yana ina"
Aka buɗe ƙofar ɗakin da Widad ke ciki aka shigo, ko ba'a faɗa ba tasan waye ya
shigo ɗakin, dan haka ko ɗaga kai batayi ta kalleshi ba, ta maida hankalinta ga
wani gurin, ya ƙaraso ya zauna a gabanta yana ƙare mata kallo, still bata motsa ba
balle ta ɗaga kanta ta kalleshi.
"koki kalli inda nake, ko karki kalla yin biyayya ga dukkanin umarnina ya zame miki
dole a yanzu, tunda shine last option ɗinki, tunda kika riga kika gano waye Bukar,
zan gwada miki aikinsa a aikace, ranar Litinin za'a kai wancan sakaram da kike
iƙrarin mijinki ns kotu, kuma na ɗau dukkan wasu matakai dana san zasuyi amfani
sena tura shi gidan yari ya ƙare rayuwarsa a can, babanki kuwa koma ina ya tafi ya
tafi kenan, har Abada har gaba da Abada baze dawo ba, dama burina kenan in ɗaiɗai
ta farincikin sa"
Widad dai bata motsa ba balle tayi magana, tai shiru ta cigaba da kallon waje ɗaya.
Ya cigaba da cewa "ki temaki kanki tun baki makara ba, ki bani takaddun da ubanki
ya ware, yace wai dukiyar akwai me ita, duk wanda yasa hannu akan takaddun nasane
suna ina?"
"Idan ubaka ne ya tara masa seka sa in baka, bazan bayar ba nayu Alƙawarin me ita
zan bawa, kuma na riga na miƙasu ga masu ita"
"Na gaya maka ɗin, tsakanin wuta da aljanna wacce kake da ita, balle ka sani? An
faɗa maka ɗin kayi abunda zakayi karka fasa"
"Ina binki sannu sannu ne, saboda har yanzu akwai ɓurɓushin imani a raina,
mahaifinki yamin ranar dabe yiwa wani a rayuwa ba, sannan dukiyar ki ce dalilin
tsayawar kasuwancina da ƙafafunsa shiyasa nake son in kamanta miki adalci, ina
takaddun suke? Ki gayamin cikin ruwan sanyi tun ban saɓa miki ba, kokuma na gwada
miki"
"Idan kana so ka kashe ni hankalinka ya kwanta, kuma zalunci indai nakane wanne ne
ban gani ba, ai babu irin wanda baka gwadamin ba, ko zaka gutststura naman jikina,
bazan baka ba"
ai kuwa ya kifa mata mari, abun da ba'a taɓa yi mata ba a rayuwar ta, dan seda
bakinta ya fashe.
"Wallahi ko kina so, koba kya so sekin bani kuma ba kimin wannan raunin a banza ba
se na ɗau mataki a kanki"
"bazan bayarba, Amana ce kuma na danƙata a hannun masu ita suna rayuwarsu, me kake
so inyi maka? Ko me zance maka?"
"ƙarya ki keyi, baki danƙata a hannun kowa ba, ki gayamin ina suke" yai maganar
cikin tsawa.
Banza tayi masa, taƙi magana ta shiga goge jinin da bakinta yake yi, ai kuwa taji
saukar tio a jikinta, tunda Widad take ba'a taɓa dukanta da abu me zafim wannan ba,
bayan wanda aka mata da bakin bindiga, ta banƙare ta ƙwala ihu, take fatar jikinta
ta tashi tai jawur kamar an ƙonata.
Tana zubar da hawaye tana girgiza kai, ji take kamar an saka mata wuta a bayanta,
saboda azabar bala'i, ya sake zage ƙarfinsa ya shiga zuba mata, tun tana iya ihu
harta kasa, se nishi da take yi yasa ƙafarsa da babu ciwon yai ball da ita, ai
dukan da yayi mata be mata ciwo ba, kamar yadda yai ball da ita da ƙafarsa, ya
ƙaraso inda take yana huci yace
Aikuwa haka ya buɗe baki ya ƙwala ihu shima, dan har jini gurin ya fara, ta janyo
wuƙar nan da ta ji masa ciwo da ita akan taga, tace "wallahi idan baka fita daga
gurin nan ba kashe ka zanyi, sena kashe ka wallahi '
Tuna yadda ya sha yanka da wuƙa ne wancan lokacin yasa shi fita da sauri yana
faɗin " dawowata ta biyu bazata miki daɗi ba, zaya kasance dawowa me muni a gare
ki "
Ya fita hannun sa riƙe da cinyarsa, tana masa wani irin zugi, har yanzu Widad ba
tayi laushi ba, halinta be canza ba na baƙar zuciya da taurin kai na jaraba, gashi
dukda dukan databsha da rashin lafiyar da take ciki, be hana ta fama masa ciwon nan
ba, dan gashi har ya fara tstatsafo da jini, ta fama masa yai ƙwafa ya fita yana
tunanin yadda zewa Widad izaya irin wadda ba'a taɓa yi mata ba, wadda zata
tirsasata yin abunda yake so.
Ita kuwa Widad zama tayi tana kuka, saboda azabar raɗaɗin da jikinta ke mata saboda
dukan da ta sha da tio, jikinta duk yayi tsami, tai kuka tai kuka harta fara tari
daga nan kuma se Amai, gashi ba komai a cikin nata, dan baka ta dinga yunƙuri amma
babu abunda yake fita, se miyau ga ɗaci da maƙogwaronta yake, se kuma ta shiga aman
jini, haka ta dinga kakarin aman nan gwanin ban tausayi, abun da bata saba ba ya
sameta, taji ba abunda take so banda ta samu ƙanƙara ta matsa lemon tsami ta sha
ba.
Tan nan ta kwanta akan tiles, tana jin yadda sanyin ke ratsata, jikinta kuma yana
ɗaukar zafi.
A hankali aka turo ƙofar ɗakin nata, ta tashi zumbur dan zatonta Bulama ne, wannan
me aikince ta shigo cikin sanɗa, taga Widad a mawiyacin hali, dan tana jiyo
kakarinta tun ɗazu.
Widad zata yi magana tai sauri ta girgiza mata kai, cikin ƙasa da murya tace
"karki ɗaga murya mana, kinga Alhaji Bukar yace kar a kuma baki Abinci se sau ɗaya
a rana, ya gindaya mugayen sharuɗa akanki, ni kuma ina jin tausayinki zan ɗan
temaka mikine, ga Abinci na kawo miki kici"
Widad tace "bana ci, ki bani ruwa me sanyi sosai, ki bani in sha"
"A'a, kici Abinci mana, cikinki bakomai ga jikinki ya ɗau zafi sosai ki daure"
Ta tirsasa Widad yaci Abincin kaɗan, ta bata ruwan sanyi kamar yadda ta buƙata,
sannan tai mata sallama ta fita.
Widad ta koma kan tiles ɗin nan tayi kwanciyarta, fatar jikinta duk jini ya kwanta
akan fatar ta, ta lumshe idonta ga sanyin A. C gana tiles haka tai kwanciyar ta
abunta.
Umma jikinta sauƙi an sallameta daga Asibiti, sedai jikin nata ya kasa ƙwari,
saboda tsabar damuwa da tashin hankali da take ciki, ta rame sosai tayi zuru zuru
duk ta fita daga hayyacinta, bata iya cin Abinci sam sedai abunda ba'a rasa ba,
kullum tana cikin Addu'a ne, dan da kanta taje ganin Yusuf amma aka hanata ganinsa,
haka ta dawo gwiwa a saɓule.
Tana zaune ta idar da sallar la'asar, tana lazimi idonta duk yayi ja saboda rashin
bacci, sallama taji anyi ta amsa sedai kafin ta bada izinin shigowa Suka shigo
ɗakin gaba ɗaya, ta ɗaga kai ta kallesu tace "Sannunku da zuwa Anty Asma'u"
"A'a riƙe sannu da zuwanki, zuwa mukayi muyi kallo sannan mu jajanta, yau dai kinga
maganar da muke tayi tun shekarun baya, tsintacciyar mage bata mage, yau dai shege
ya ɗakko miki magana, dama ina shege zeyi wani abun arziki, kina ta wahala kika
saka ɗan uwanmu yaita wahala daku, ke juya shi kuma shege yau dak gashi ƙarshen
Alawa ƙasa, ya zama gagarumin ɗan ta'adda ya sace 'ya yaje yai mata fyaɗe yana
neman kuɗin fansa, Allah wadaran naka ya lalace "
Balaraba tace " Ameen dai Anty, alhakinmu ne ya kama su, da tasa ɗan uwanmu ya
dinga wahala dasu, yana wulaƙantamu yau gashi kina kuka da idonki, kuka kam yanzu
kika farashi, saura ke se sunzo sun haɗa ke dashi tukuna, tunda idan ya samo tare
kuke ci"
Suka dinga zazzage mata rashin mutunci iri iri, ta inda suka shiha ba ta nan suke
fita ba, Umma ba tace musu komai ba ta sunkuyar da kai kawai, ta cigaba da jan
carbinta na tare da ta kulasu ba.
Suka yi suka gama san ransu, sannan suka tafi Umma ta girgiza kai kawai, tana share
hawaye.
Khalil yace "Nurat, ban samu ganin Widad ba, bata gidan Alhaji Bulama ance wai bata
da lafiya an kaita Asibiti, amma ɗan nasa be gayamin ina take ba, wai shima be sani
ba, nace masa zan kuma komawa inji abunda ake ciki"
Nurat tace "Innalillahi wa inna ialaihi raji'un, Yaya Khalil an kusa shiga kotu fa,
Allah yasa dai a gano ta, na damu sosai dan Allah ka koma da wuri kaji"
"Shikenan insha Allah, karki damu zan koma inga yadda zamu yi dashi"
Alhaji Haruna ya kira layin Amal ba adadi amma taƙi shiga, ya rasa me yarinyar nan
tayi masa ranar da tazo, ta barshi a yashe, yana ta tunanin ne kiran Alhaji Musa ya
shigo wayarsa ji a sanyaye ya ɗaga.
Alhaji Musa yace "Haruna ina ka shiga ne? An kira layin ka ba adadi amma taƙi
shiga, gashi baka bawa Bukar takaddar nan ba gashi za'a shiga kotu, kasan fa idan
wani ya ɗau takaddar nan tsaf zamu shiga matsala, har saƙo aka turo maka na zamuyi
taro amma baka ɗaga ba"
Alhaji Musa yace "ban yadda ba, akwai wani abu a ƙasa, ka gayamin ko menene mana?
Kasan halin Bukar wallahi ze iyayi maka Akuya kasani sarai"
Alhaji Haruna yace "a bar zancen kawai, zanzo in same ka zamuyi magana"
"oho masa dai, wallahi tayi masa sheda da wuƙa, ta yanke shiba fuskarsa da
cinyarsa, kai baka ga yadda ya sha ɗinki ba, gaba ɗaya halittun fuskarsa sun sauya"
Alhaji Haruna yace "innalillahi wa inna ialaihi raji'un, Taɓɗijan dara taci gida
kenan, to wani mataki ya ɗauka"
Alhaji Musa yace "eh to, yace tunda ga riga ta gano shi yasan yadda ze da ita,
sedai kawai idan mun haɗu da kai tukuna, mayi magana mu tattauna maganar bazata yi
ta waya ba, zan shiga meeting ne yanzu"
Ramadan ne yai sallama ya shiga falon mahaifinsa, yana zaune yana kallon labarai,
Ramadan yace "Daddy barka da hutawa"
Bulama yace "Yawwa barka, sannunka wai ni ina ɗan uwanka Fahad ne, yaushe rabon da
in sashi a idona"
Ramadan yace "Daddy kasan halinsa fa, wallahi yau kwanansa huɗu baya gidan nan,
nima ban san inda yake ba, babu wanda yayiwa sallama, dama hana yin haka fa, yakan
kwana biyu ma baya gidan nan"
Ramadan yace "Yawwa Daddy, nace a wane Asibitin Widad take ne, Nurat ta aiko a
gayamata imsa take, tana son ganin tane kasan ƙawarta ce"
Bulama yai shiru yana nazarim Ramadan sannan yace "wata aiko?"
"Wani ne, nima ban sanshi ba, wai ko Khalil ne kowaye, ya cemin ɗan uwanta ne shi,
yana so zeyi magana da Widad ne, Nurat na son sanin halin da take ciki"
"Daddy saboda me? Aikowa yasan tana hannunka, yakamata ka faɗi Asibitin da take,
saboda masu dubiya sannan wataƙila 'yan sanda zasu samu wani rahoton daga gareta"
"Kai Ramadan ka kiyaayeni, ka fiye shisshigin tsiya wallahi, to ban saniba tunda
nace maka tana Asibiti amma kama cigaba damin tambaya"
"Allah ya baka haƙuri, amma Daddy wannan yakan fa dake fuskarka da ƙafarka? Tun
shekaranjiya nake son in tambayeka amma se inga kana bacci, na tambayi Mummy tace
itama bata sani ba"
Bulama yace "Accident ne na samu, tashi ka bani guri tafi maza ka bani guri in
huta"
Haka ya fatattaki Ramadan, ya kulle ƙofarsa ya ɗakko wayarsa ya kira Alhaji Musa,
ya ɗaga yace "Allah ya temaki Bukar Bulama"
Alhaji Bulama yace "Musa kasan da ana shirin samun ɓaraka daga gidanka kuwa?"
Alhaji Musa yace "ɗan yayar Babar Nurat ne, cousins ne shida ita"
"Shine ta turoshi gidana wai azo agane mata ya Widad take? Wai aga halin da take
ciki, da sanin ka akayi haka?"
Alhaji Musa yace "innalillahi wa inna ialaihi raji'un, wallahi ban sani ba saboda
haka fa na kirsheta a gida, ko nan da cam bata zuwa, na hanata zuwa ko ina Sam, ban
san yadda akayi tayi hakan ba, amma ka ƙyaleta zanyi maganin ta, zan ƙwace
wayoyinta sannan in turata ƙasar waje, bakomai zan ɗau mataki a kai, hakan bazata
sake faruwa ba"
"gara dai kayiwa tufkar hanci tun kafin inyi abunda yakamata da kaina, karka ƙara
turomin wani yazo yana neman Widad, ka jawa 'yarka kunne"
"Insha Allah, hakan bazata sake faruwa ba, zanyi abunda ya dace base ka ɗau mataki
da kanka ba"
Bulama yace "da dai yafi"
Litinin, tushen aiki kotu ta cika maƙil, domin ji da ganin yadda shari'a zata
kaya, musamman shari'ar da mutane suke cike da sonji da ganin yadda zata kaya, wato
shari'ar Yusuf Bashir Maitama, ɗaga jajirtaccen ɗansanda wato Bashir Maitama.
Umma ya halarci zaman kotun nan, dan shine kaɗai hanyar da zata ga Ɗanta Yusuf,
'ya' yan Bulama su Alhaji Munir, da Hajiya Halima da 'ya' yanta duk sun halarra a
kotun.
Umma tana nan zune tana waige waige aka shigo da Yusuf, hannunsa ɗauke da sarƙa,
'yan sanda sun taso shi a gaba, yadda yake jan ƙafa da ƙyara da yadda jaabiyarsa
tai baƙiƙirin saboda datti, ga fuskarsa duk a kumbure, kai da gani base an faɗa ba
kasan Yusuf a wahala yake, Umma ta ƙunshe fuskarta a mayafinta ta fashe da kuka.
Haka akaje aka tsayar da Yusuf, 'yan sanda suka kewaye inda yake, Yusuf ya ɗaga kai
yaga yadda kotu ta cika maƙil, masu masa kallon banza nayu, masu na tausayi suna
yi, idonsa ya sauka akan ummansa wadda idonta yayi fururu saboda kuka, ya sunkuyar
da kansa yana danne hawayen dake shirin zubo masa Allah kaɗai yasan me Umma takeji
a rantava yanzu haka.
Aka karantowa Yusuf ƙunshin tuhumar da ake masa, amma Yusuf ya musanta yace "shi
bashi ya sace Widad ba"
Me shari'a Justice Abdallah A dutse yace "duba da yadda lawayan gwamnati ya nemi
a basu dama domin kawo shedunsu, wannan kotu ta ɗage sauraran wannan ƙara zuwa goma
ga wata me kamawa, sannan wannan kotu tayi umarni da akai wanda ake zargi gidan
gyaran hali zuwa lokacin da za'a sake wannan zama"
Haka aka tashi a shria'r yau, aka taho da Yusuf za'a sashi a motar 'yan sanda,' yan
jarida sukayi dandazo amma aka hansu magana da shi, Umma ta taho da gudu Suleiman
ma cikin hanzari ya nufi inda su Yusuf suke, Umma tana kuka tana "dan Allah ku
barni in ganshi ko sau ɗayane, ɗana ne watana kusan biyar rabona dashi, ganinsa
kawai zanyi Suleiman dan Allah kace su bari in ganshi"
Suleiman yace "Dan girman Allah ku bar baiwar Allah nan taga ɗanta, ko sau ɗayane
uwace kunsan ba zata iya jurewa ba, dan Allah ku bari ta ganshi"
"Ba a bamu wannan damar ba, seta bari idan mun kaishi prison taje can idan sun
batta seta ganshi"
Ayshercool
07063065680
11/23/21, 8:06 AM - Buhainat: LITTAFIN KUƊI NE, DAN ALLAH KI SIYA KAFIN KI KARANTA
BA DANNI BA DAN ALLAH, LITTAFI NA ƊAYA KYAUTA NE WANNAN NA SIYARWA NE
NORMAL GROUP ₦300
VIP ₦500 NE KITURA TA WANNAN ACCOUNT ƊIN
0009450228
JA'IZ BANK
AISHA ADAM
SE A TURA SHEDAR BIYA TA WANNAN LAMBAR
07063065680
(Albishir ga masoya, ma'abota bibiyar litattaafaina, dama ta samu zaku fara samun
litattaafaina na audio, akan YouTube channel ɗina me suna Cool Arewa TV
https://youtube.com/channel/UCD5vnvA5laU8ti4LLz2_QEg
Kuyi liking sannan ku danna subscribe, domin fara samun litattaafaina na audio,
nagode sosai da ƙaunar ku gareni"
130_131
Haka aka ja mota aka tafi da Yusuf, umma tana ta zabga kuka, Yusuf ma ya sunkuyar
da kansa yana kuka a cikin motar nan, shiba kaishi gidan yarin bane damuwarsa,
kukan da Ummansa take shine ya tsaya masa a ransa.
Dan abun takaici, 'yan jarida sukazo suka kangawa Umman Abubuwan magana sun antaya
mata tambayoyi, Suleiman ya janyeta suka hau mota suka tafi, ba tare da tace uffan
ba, amma a haka suka naɗi muryarta tana kuka tana ambaton Allah dan suji daɗin
yayatawa a duniya.
Haka aka watse a zaman kotu, kowa da abunda yake faɗa, wasu su faɗi alkhairi wasu
kuma su faɗi som zuciyarsu.
Aka wuce da Yusuf gidan gyaran hali, aka bashi kayan fursunoni, aka shigar da
bayanan sa, sannan aka kaishi ɗakin daze zauna, mutane masu laifi sunyi su sittin a
ɗaki ɗaya, ga rashin isashshen vantilation, ga cunkoso ga tsamin dauɗa da wasu suke
yi, gaba ɗaya abun se godiyar Allah haka akaje aka gwamutsa Yusuf a cikinsu.
Bayan an tashi daga zaman kotune, Bulama yabi Justice Abdullah gidansa, aka masa
iso ya shiga, yana ganinsa A dutse ya faɗaɗa murmushinsa yace "kaine da kanka haka
baa aike ba?"
Bulama yace "Ai saƙonne, yafi da cewa in isar dashi da kaine ba aike ba"
"To Aini dutse banyi zaton haka ba, muda muke da shedu tuni mun tanada, na gaskiya
dana boge amma kace wai ka ɗage sauraren ƙarara, ina laifin a fara gabatar da
shedun, nifa da wuri nake son ayita ta ƙare fa, ayi a yanke masa hukunci in rufe
babainsa, saboda in dai yana nan ze hanani rawar gaban hantsi, dan gaba ɗayansa
matsalane a gare ni wallahi "
A dutse yayi murmushi sannan yace " hmmm Bukar Bulama, ai ita shari'a saɓanin
hankkalice, bar ganin ka saye ni ka saye lawyoyi da hukunar 'yan sanda, karka manta
akwai ƙungiyoyi masu zaman kansu, na kare haƙƙin ɗan Adam, akwai lawyoyi masu zaman
kansu, dukda wasu abubuwa da akayi da suke fito da laifin shi yaron ƙarara, amma
duk da haka zasu saka ido akan shari'ar, za' a samu wanda zasu bibiyi shari'ar, dan
haka muje a sannu, ina sane nayi hakan komai a sannu akeyinsa cikin hikima da
ƙwarewa irin ta aiki "
Bulama yace " Aini gaba ɗaya hankalina baze kwanta ba muddin ba a gama shari'ar nan
ba, yaron nan fa ba ƙaramin bincike yayi akaina ba, kuma bana son Daula ya bayyana
ba'a gama shari'ar nan ba"
"Calm down mana, waini haryanzu babu labarinsa, babu wanda yasan inda yake ne?
Abunfa da mamaki"
"to waye ya sani, anneme shi am rasa kamar wani kuɗi, duk iya bincike na saka anyi
amma babu labarinsa, ni dai kayi kayi ayi gaggawa a ƙarƙarw shari'ar nan da wuri,
ka yanke masa hukunci, kuma hukunima me tsanani wanda ze ƙare a prison"
Justice Abdullah yai murmushi yace "Bukar Bulama, ai komai akan doka akeyinsa,
dukda munawa dokar karen tsaye wasu lokutan, saboda irinku da mukewa alfarma, amma
karka damu insha Allah zanyi duk yadda zanyi in ƙarƙare shari'ar nan, ba da daɗewa
ba yanzu se Allah ya kaimu bayan sati uku zamu sake zama "
"Gara dai ayi a sake zaman, dan Allah karka zake jan lokaci dayawa, bazan iya jira
ba, sonake a ƙare komai"
"Shikenan, kaje ka kwantar da hankalinka, nan kusa zan ƙarƙare shari'ar hankalinka
ya kwanta"
A dutse yace "Amma, wai ya akayi kaji wannan raunin haka? Gaba ɗaya kamaninka sun
sauya kayi wani iri, fuskarka ko ina ɗinki"
Bulama ya miƙe yace "karka damu da wannan, ƙyaleni kawai daga nan wani guri zanje,
ina nan ina sauraren yadda zata kaya"
Nurat! Nurat!! Alhaji Musa ya shigo yana ƙwalawa Nurat kira, ta fito falo tace
"Gani"
"Ba magana nake miki ba? Ubanwaye yace ki aika wai a dubo miki ita babarkice ita
meye haɗinki da ita?"
Nurat ta girgiza kai tace "A'a Daddy nifa ba da wani abu na aika ba, kawai naga
ƙawata ce kuma ga abunda ya sameta, ni kuma ka hanani figa, shine nace aje a
dubamin"
"Ƙawarki ɗin banza da ta wofi, kuma wallahi ki kiyayeni da wannan yaron Khalil,
idan kika bari na sake ganinsa a gidan nan sena ci mutumcinsa, sannan kije ki kwaso
min wayoyinki ki kawomin su nan, kuma ko kina so ko bakya so sati me zuwa zaki bar
ƙasar nan "
Mahaifiyar Nurta ta fito tana cewa," Kwanan nsm bam san meyasa kake wannan abubuwan
haka ba, meye laifi dan kawai tace aje a duba mata ya take? "
" Idan ina magana kika ƙara sakamin baki wallahi sena ci mutuncinki, na gayamiki
kin sani sarai abunda ke tsakanina da uban yarinyar, amma take shisshige mata"
"Amma larura ai tafi ƙarfim wasa, abun jaje ya samu mutum kace baza'a jajanta masa
ba?"
Yace "eh baza'a jajanta ɗin ba, wuce kije ki kawomin wayoyinki, daga yau har ranar
da zaki bar ƙasar nan, bake ba fita ko ina, kuma kar wani ya sake yazomin gida,
ɗakkomin wayoyinki gabaɗaya, har System ɗinki"
Nurat ta shiga ɗakinta, ta ɗauki wayarta ta ɓoye, ta ɗakko sauran ya kai masa, ya
karɓi wayoyin da system ɗin yace "ina ɗaya wayar taki take"?
Yai maganar yana kallon ta, Nurat tace "Na bawa Khalil ya kaimin gurin gyara"
"to ki gaya masa maza maza ya kawota, ki aika direba maza ya karɓomin wayar nan,
maza fice daga nan ki bani guri"
Nurat ta wuce ɗakinta, tana tunanin meye abunyi, koda tsiya koda tsiya tsiya dai
bazata bar ƙasar nan ba, se taga abunda ya turewa buzu naɗi"
Wasa wasa fa fiye da wata guda babu Anwar babu labarinsa, duk neman dazaa'yi anyi
amma ba'a samu Anwar ba, hankalin Hajiya Halima gaba ɗaya a tashe yake, da tana iya
basarwa amma yanzu ta kasa jurewa, ga Shu'aibu ya sata gaba yana ta tatsarta kota
ko ina, ta zauna tayi shiru a falo ta rasa abunda yake mata daɗi.
Sallamar Alhaji Haruna ce tasa ta ɗaga kai ta kalle shi, mamakine yakamata ganinsa
da tai kamar korarre, tace "lafiya kuwa?"
Hajiya Halima tace "to meye yasa kake nemanta? Wani abun tayi makane ko kuwa?"
Amal tace "gani nan, lafiya kake nemana haka? Ko kuma naci ban biys bane?"
Hajiya Halima tace "nifa gaba ɗaya kaina ya kulle, kumin bayanin abunda yake
faruwa"
Amal tace "Mummy, ki kwantar da hankalinki babu wani abu fa, Alhaji muje farfajiya
muyi magana"
Amal ta janye shi zuwa farfajiyar gidan ta kalle shi tace "lallai kaci ksi, baka da
hankali da nasani nz tona maka Asirin abunda kayimin a gabanta, tunda kanka baya js
yadda yakamata"
"ba wani abu na aikata maka ba, illa na saka maye na ɗauki wayarka na bayar anyi
abunda yakamata na turi kuɗi daga Account ɗinka, na raba kuɗin gida biyu na ɗau
rabi, shine fansar budurcina daka ɗauka, kuma bari in gaya maka wani abu, akwai
mahimmin saƙo da na ajiye na rarrabawa mutane, wallahi duk abunda ya sameni kaine,
seka ƙara wannan akan kaidim mata da kace mim ba wanda baka sani ba, wawa kawai
kuma wallahi ka kuma zuwa gidan nan duk abunda nayi maka kaika siya da kuɗinka ba
wani ya sai maka ba, kuma a taƙaice takadda dai babu ita dan nima ban san inda take
ba"
Ta ƙarasa maganar tana masa wani irin mugun kallo, ta shigevta barshi a gurin kaman
gunkin mutanen farko.
Har ta shiga zata wuce ɗakinta, Hajiya Halima ta kira sunanta "Amal"
"Babu komai"
Yace "yana so nane, nikuma nace bana sonshi, ya takuramin nikuma na zage shi, shine
zezo ya ɗagamin hankali"
"to dan ba kya sonsa meye na zagin masa kuma? Ai bekamata ki zage shi ba"
"to Mummy ni kalarsa ce? Ko da ƙuriciyata zan Auri wannan dattijon mutumin ne? Ai
uba na ɗauke shi, amma tunda bega hakan ba shine nai masa abunda ya dace dashi"
"koma dai meye karki kuma zaginsa, dan ya haifeki kuma koba komaiakwai mutunci, da
alaƙa tsakanina dashi"
"karki ji komai Mummy, hakan bazata sake faruwa ba" ta wuce ɗakinta.
Bulama ya fito ze fita, yaga motar Fahad a harabar gidan, dan haka ya fasa fitar ya
nufi BQ inda suke, a falo ya tarar da Fahad, yana ƙoƙarin kunna TV, ya kalli Fahad
yace "kai daga ina kake? Na samu labarin seka kwanaki baka gidan nan, gidan ubanwa
kake zuwa haka?"
Fahad ya sosa kai yace "Daddy gurin abokaina nake zuwa, shiyasa"
"wasu irin abokaine zakaje ka kwana huɗu a gurin su? Kai baku da gidane?"
"muna dashi"
Fahad yai shiru, Bulama yace "Shikenan ka kiyaye idan na sake ji sena hukunta ka
na gaya maka"
Fahad yace 'to, amma Dad what's wrong with you in your face, naga ɗinki a fuskarka"
"Da ka damu dani ai da baka fita ba, kaje kayi kwanaki haka ba, ban sani ba"
Wata yarinya ce ta fito da Towel ɗaure a ƙirjinta daga bedroom ɗin Fahad, Fahad ya
shiga zazzare ido, Bulama yace what, mezam gani haka? Fahad wacece wannan? "
Fahad ya sunkuyara da kai yana sosa kai," ba magana nake maka ba? Wacece wannan ɗin
me take a nan ".
" wallahi ka bani kunya Fahad, neman mata? Akanme kuma a cikin gida na dan asara"
Fahad yace "wallahi Daddy ni Aure nakeso, kuma har yanzu kaƙi ka auramin Widad
shiyasa, ni gaskiya shiyasa kawai nake bi ta ɓarauniyar hanya"
Bulama ya dinga masa bala'i, ya kori karuwar nan, ya taho cikin gida yana zazzaga
bala'i, "Sarah, kina gidan nan amma yaron nan yake neman mata, kai Ramadan ga
ɗakinka ga nasa, amma yake kawo mata gidan nan baka taɓa faɗa ba?"
Ramadan yace "ai Daddy kafi sonsa, kuma kona faɗa ba yadda zakayi ba Shiyasa"
"Nika ke gayawa haka Ramadan?ke Sarah kina kallo amma baki ɗau mataki ba, ko ki
gayamin ba?"
"Barewa bata gudu, ɗanta yai rarrafe" shine amsar kawai data bashi, ya tsaya
sororo yana kallonta.
Nurat taje ta ɗauki wayarta, ta ɓoye ta shiga tunanin yadda zata bawa Khalil wayar
nan, ba tare da mahaifinta ya sani ba, tunda an hanata fita, kuma Mahaifiyarta na
ja maata kunne sosai akan shisshigi akan lamarin mahaifinta.
A hankali ta lallaɓa ta sato wayar Mum ɗinta, ta dawo ɗakinta ta kira Khalil, yana
ɗagawa tace "Brother a gurguje, dan Allah karka sake zuwa gidan Bulama neman
Widad, akwai wata ƙulallaiya a ƙasa, akwai wani abu ds suke ƙullawa shi da Daddy
na, ya gaya masa kaje gidansa neman Widad, amma Daddy yazo yana ta faman min faɗa,
ya ksrɓs wayoyina saura ɗaya kawai, ya za'ayi kazo ka karɓa? "
" Nima na fuskanci akwai wani abu a ƙasa a tsakanin mahaifinki da Bulaman nan, ina
da wani plan ne a ƙasa, amma karki damu zanzo in karɓi wayar "
" karka soma zuwa Brother, akwai matsala, zan san yadda zanyi idan ina so muyi
magana zan kiraka a wayar Mum, se anjima "
"ina ruwanka da cikinta? Nayi wani planning akanta, yanzu haka tama gidana na can
hanyar ƙuyukan nan ma bayan gari, in da nake noman albasa, wannan gidan can na
kaita na ajiye, kuma ko tana so ko bata so, za'a zubar da cikin nan ka Aureta, amma
wannan da kake kawowa aiba mata bsne, idan aka kamanta su da ita "
Fahad ya washe baki yace " to Daddy nagode sosai, wallahi idan na Aureta sema rama
dukan da tayi min, bazan manta marin nan ba"
Bulama yace "kai dai ka bari, aure kamar anyi an gama ne ai"
Widad duk ta ƙare saboda larura da rashin kula, gashi cikin nan ya sakata gaba da
Amai komai taci baya zama in dai ba Ruwan sanyin nan ba da lemon tsami, a ɓoye take
zuwa ta turasasa Widad taci Abinci, sam bata kwanan kan katifar nan sedai kan
tiles, duk ƙibarta seda ta ƙare ta rame sosai, duk tayi wani iri.
Yauma meaikin me suna Sabuwa tazo tana bata ƙosai da kunu, tana ci ds kyar, can
Widad tace "Dan Allah ina labarin mijina kuwa? An fara shari'arsa ko?"
Sabuwa tace "gaskiya an fara, dan har Alƙali ya kaishi prison se bayan sati uku
za'a cigaba da shari'ar"
Widad ta girgiza kai cikin ƙunar zuciya tace "Allah sarki mijina, Allah ya kawo
maka mafita ta inda baka zata ba, babu abunda zan iya yi a kai, Allah ya fitarmin
da kai Yoseef"
Sabuwa tace "Addu'ar dai da kike masa ita yakamata ki cigaba amma ba wannan kukan
ba"
Widad dai nata shiru ba tace komai ba, dan tayi nisa bata jin kira, can tace "zan
kwanta, ina son inyi bacci"
Ko ina da haske, ga wasu ƙarti ne ke sintiri a harabar gidan, babu hanyar guduwa,
gashi dama hanyar gurin gaba ɗaya babu gidaje, se kangwaye da gonaki, da manya
manyan filaye fetal a gurin, dan haka babu hanyar guduwa.
Ta koma kan katifar nan, ta kwanta wani irin ƙaunar Yusuf da tausayinsa na ratsa
jinin jikinta, ga wani irin mugun kewarsa da take yi, tana buƙatarsa a kusa da ita,
ta tabattar da yana kusa da ita yasan da cikin nan, zata sha kulawa sosai.
Ta ƙanƙame filon nan a ƙirjinta, tana hawaye, a hankali tace "i miss you Yoseef,
ina kewarka sosai, Allah yasa abunda ya faru karyasa ka dena sona, ina sonka Yoseef
ka yafemin please, dalilina ka shiga wannan halin Yoseef, ina sonka Yoseef dan
Allah ka dawo gare ni" a hankali take furta maganar tana zubar da hawaye.
Kwana uku da kai Yusuf prison Umma ta damu ta ɗaga hankalinta, akan lallai seta je
ta ganshi, dan haka Suleiman yaje har gida ya ɗakko ta suka tafi gidan yarin tare.
Kasancewar Suleman ɗansanda ne yasa har gurin shugabn gandirobobi na gidan suka
shiga, suka gaisa Suleiman yace "wannan mahaifiyar Yusuf ce, da aka kawo gidan
nan, dan Allah munzo a bamu dama dan Allah muganshi"
Shugaban gandirobobin yace "a gaskiya ba'a bamu wannan damar ba, daga sama akace
karmu bar kowa ya kawo masa ziyara"
Suleiman yace "saboda shi ba mutum bane? Ko kuma ba ɗan ƙasa bane ba? Haba dan
Allah, wallahi kwata kwata babu adalci a shria'r da za'ayiwa Yusuf, dan Allah ka
dubi girman Allah ka bari mu ganshi"
Umma cikin kuka tace "dan Allah dan Annabi ɗan nan kabari in ganshi, kusan watanni
biyar zuwa shida, tynda akayi garkuwa dashi, ban sashiba idona ba ka temakamin"
"Wannan ce mahaifiyarsa?"
Yace "kaman ba ita ta haife shi ba, kamar yayarsa, anyway gaskiya na lura da
yanayinsa, tunda aka kawo mana shi gidan nan, ba sawa ba fitarwa, ko magana ba
ruwansa da kowa, bashi da Hayaniya sam hakan yasa na fara tausayinsa, kuma nake jin
ina shakku akan laifin da akace yayi, sedai baya iya cin Abincin gidan nan kunsan
yanayin yadda Abincin namu yake, kuma gashi ance ba'a yadda kowa yazo gurinsa ba,
nayi nayi inyi interview dashi amma yaƙi magana Sam "
Sulaiman yace " ai ba lallai yai maka ba, kaima Allah ya saka maka da alkhairi,
shima abokin aikinmune ɗan sanda sakamakon wannan abunda ya faru, naji an sanar da
an kore shi daga aikin, amma ita gaskiya ai zata yi halinta, nidai fatana ka mana
wannan alfarmar dan Allah, ka bari mu ganshi"
Suna nan zaune yai umarnin, aje azo da Yusuf suka cigaba da tattaunawa da
gandiroban nan.
Aka shigo da Yusuf sanye da kayan prison, yana jan ƙafarsa da ƙyar da alama ƙafar
ciwo take masa, da Gudu Umma ta tashi taje ta rungume shi tana kuka, Yusuf yasa
hannayensa ya rungumeta shima, hawaye na gangarowa daga idonsa.
Tana so tayi masa magana amma takasa, se kuka da take Yusuf ya share nasa hawayen
sannan ya ɗago Umman ya kalleta ya ƙaƙalo murmushi yace "Umman Yusuf, baki da
lafiya ne? Kinyi baƙi kin rame sosai"
Girgiza kai take tace "Yusuf ka ganka kuwa? Gaba ɗaya ka fita hayyacinka kamsr ba
kai ba, fuskarka duk ciwo Yusuf garin yaya haka ta faru?"
Yusuf bece komai ba, se cigaba da share mata hawaye da yayi, ya samu guri ya zauna,
suka gaisa da Suleiman, Suleiman yace "nayi iya ƙoƙarin da zanyi, akan a barni inzo
inda kake amma abu ya gagara, se yanzu da aka mana alfarma"
Yusuf yace "Aini bani data cewa, na barwa Allah shine ze fidda ni"
Suleiman yace "waini ina Saleh nema, Saleh yasan komai fa"
Yusuf yace "Anyiwa Saleh illafa saboda duka, inaga wani abu ya taɓu a cikin sa,
yana kwance a Asibiti"
Umma tace "Yusuf wai ya akayi haka ta faru ne? Ya akayi aka kamaka kaida ita? Ance
kai kayi garkuwa da ita harda fyaɗe, garin Yaya Yusuf"
"Kasan bazan taɓa yadda ba ai, ina son jin dahir ne"
"Umma, na shiga wannan halin ne dan kawai na temki Widad, ita kaɗai zata iya bada
sheda akan abunda ya faru, se kuma Saleh, kinga bansan ma inda Widad ɗin take ba"
Yusuf yai ajiyar zuciya, Umma tace "wai ya akayi aka kamaka da ita a ƙauye? Garin
yaya Yusuf?"
Suleiman ya bawa Yusuf siyayar da suka yi masa, suka tafi yakasa waigawa ya kuma
kallon Umma saboda yasan kuka take.
Bayan tafiyar su Umma, wannan gandiroban yasa aka canzawa Yusuf ɗaki, zuwa me mutum
Ashirin, yana nsn kwance yana tunanin rayuwa, mussman Widad ya damu da yaji Widad
wai tana hannun Bulama, shifa tun farkon saninta da yayi ya tsani Bulama, mussman
da yayi bincike a kansa, sosai yake kewar matarsa, yana son sanin halin da take
ciki, yana missing ɗinta sosai, kawai Fahad ya faɗo masa a rai, take yaji gabansa
ya faɗi ya miƙe tsaye da sauri.
Cikin dare bacci da ƙyar ya ɗauki Widad, baccin beje ko ina b taji an motsa ƙofar
ɗakin da take kwance, a hankali an buɗe ƙofar.
(Albishir ga masoya, ma'abota bibiyar litattaafaina, dama ta samu zaku fara samun
litattaafaina na audio, akan YouTube channel ɗina me suna Cool Arewa TV
https://youtube.com/channel/UCD5vnvA5laU8ti4LLz2_QEg
Kuyi liking sannan ku danna subscribe, domin fara samun litattaafaina na audio,
nagode sosai da ƙaunar ku gareni"
132_133
Widad ta buɗe idonta a hankali, tana son ganin waye wannan ya shigo mata haka a
wannan daren, Kasancewar ɗakin da duhu shi baya ganinta se ita ke ganinsa, ya ɗakko
ƙaramar wayarsa ya kunna ya haskata, tana kwance ta lumshe ido kamar me bacci, ya
tako ya ƙaraso a hankali inda take, ya ƙara hasketa da fitila ya kai hannu a
hankali ze taɓata ta miƙe zaune da sauri.
Tace "waye wannan? Ɗan dena haskani mana, waye wannan zaka shigomin ɗaki babu izini
ko baka san ni matar Aure bace"?
"Aurenki na banza dana wofi, nazo in rama marin da kikamin ne, yadda gobe in ance
ki kuma yiwa wani abunda kikamin, bazaki ba"
Se yanzu ta ɗau muryarsa, Fahad ne ba wani ba dan haka tai zumbur ta miƙe tsaye,
shima kuwa ya miƙe, ya kai hannu ya riƙota ze gwada mata ƙarfi, sedai tarihi ya
maimaita kansa, kamar yadda ta taɓayi masa shekarun baya, ta saka masa haƙora a
hannunsa, wata irin azaba yaji ta ratsa shi tun daga yatsunsa har kansa, ya danƙi
kanta yai jifa da ita a ƙasa, ai kuwa kanta ya gwaru da bango, hancinta ya fashe,
ta saki wani marayan kuka, saboda zafi da taji, ya kuma yo kanta amma cikin sauri
da zafin nama, ta tashi tai waje da gudu tana ihu, sedai duk wannan ihun da take
babu wanda yayi yunƙurin kawo mata ɗauki, nan suka shiga guje guje dashi, Allah ya
bata sa'a ta samu wani ƙarfe ta buga masa ya gigice, ta koma ɗakinta da sauri ta
rufe ƙofa, gigicewar da yayi tasa yakasa komai ya shiga tangaɗi a gurin, duk ta
bashi wahala sosai.
Ta shige banɗakin dake ɗakin ta rufe, ta dinga rusa kuka, gaba ɗaya ta rasa mema
zata yi? Ta ding kuka me sauti.
Haka nan Yusuf ya dinga jin faɗuwar gaba a wannan daren, yakasa bacci sam, ƙirjinsa
ya dinga bugawa da sauri, yakasa zaune ya kasa tsaye kawai yake jin kamar wani abu
yana faruwa da Widad ɗin, ya dinga addu'a a haka har gari ya waye ba tare da ya
rintsa ba.
Alhaji Haruna ya rasa me zeyi wa Amal ya huce, kuɗin data kwasa a account ɗinsa ba
ƙananan kuɗaɗe bane, ya rasa meze mata wanda ze huce.
Yana zaune yana wannan tunanin Salma ta shigo ɗakinsa a fusace, ya ɗaga kai ya
kalleta yace "lafiya kuwa?"
"dole ka tambayeni lafiya mana, munafuki macuci, to bari kaji in gaya maka, barin
gidanka zanyi bazan zauna ba da kai ba Wallahi, dama can ba sonka nake ba aka
ƙaƙabamin kai"
"Ni se wasu maganganu kike wanda ban gane inda kika dosa ba, kimin bayani yadda zan
gane mana"
Jefo masa wayarta tayi, ya ɗauka ya duba, message ne aka turo mata da wata baƙuwar
lamba "Ki saka ido akan mijinki, in bahaka ba watarn ze shafa muku ciwo, dan yana
ta'amalli da mata a guest house ɗinsa, idan kin musa ina da sheda, zan iya turomiki
idan kina da buƙata"
Wani gumine ya fara tstatsafo masa, ya dake yace "wannan wane irin shirme ne za'a
turomiki ki yadda, kawai a turomiki magana ki yadda, wataƙila ma bake za'a turowa
ba"
"ɗan saurara karka rainamin hankali mana, idan ƙarya ake maka saƙon ya rasa wayar
waze faɗo se tawa? Kuma yawan fitar cikin dare da kake wataran bako sallama ina
kake zuwa?"
"harkar banza dai, wans irin aiakine baza'ayi shi da rana ido na ganin ido ba se a
takatainin dare, wallahi kaji tsoron Allah, kome kake aikatawa Allah yana kallonka,
kuma wallahi idan na tabattar da abunda naake zargi seka sakeni wallahi, kuma sena
tona maka Asiri a idon duniya, bani wayata ni"
Ta saka hannu ta ɗauke wayarta, tai waje ranta a matuƙar ɓace, ya dafe jansa kallai
wanna kafon ya ɗebo ruwan dafa kansa, ga ya haɗu da mskira 'yar damfara.
Kiran Bukar ne ya shigo wayarasa, jiki na rawa ya ɗaga suka gaisa yace "Haruna na
gaji da wannan zagaye zagaye da raini hankamin da kakemin, ka fito ka gayamin
gaskiya mske faruwa, ina takaddar nan take? Idan kuma wata manufar ce da kai kuma
seka ajiye agurinka"
Alhaji Haruna yace "Babu yadda za'ayi takaddar nana tana gurina inƙi kawowa, wata
'yara matsala aka samune, kuma ba da daɗewa ba zan warwarwta a ɗan ƙara ɗagamin
ƙafa"
"Bana alfarma a karo biyu, daga ta farko bana ta biyu, Amma ka sani daga wannan
shikenan, idan wani ya samu takaddar nan Asirinmu ya tonu, ze zama hujja akanmu,
gara idan ɓataraa kayi ka nemota tun wuri, idan kuma ɓoyewa kayi kaje ka cigaba da
ajiyar ta karka fito da ita "
Ya kashe wayar, Alhaji Haruna ya rasa abunda zeyi, aka kuma kiransa da ovt number,
kamar kar ya ɗaga amma ya ɗaga," ɗan duba what's app ɗinka akwai saƙo"
Be ɗauki muryara waye ba, amma dai muraya mr mace ce, ya kunna data ya shiga what's
app ɗinsa, messages suka gama shigowa sannan ya shiga dubawa.
Video ɗin tsiraicinsa ne da wata wadda besan kowacce ba a guest house ɗinsa, daga
ƙasa aka rubuta "dukda wannan abubuwan da na maka banji na fanshi mutuncina daka
keta ba, wallahi idan baka biniba sannu ba sena yaɗawa duniya, kuma yanzu a haka
akwai video ɗin nan a wayar mutum huɗu, isan har wani abu ya faru dani zasu watsa a
duniya"
Ko ba'a gayamasa ba yasan message ɗin Amal ne, yace "Innalillahi wa inna ialaihi
raji'un, be taɓa gamuwa da masifa a rayuwar sa irin wannan ba, ya ɗebo ruwan dafa
kansa over.
Widad kam seda gari ya waye yayi haske sannan tai alwala ta fito tayi sallar Asuba,
ta dinga kai kukanta ga Allah, kuka kama dama ya zame mata jiki, dan inda sabo ta
riga ta gama sabawa.
Tana cikin kukan ne Sabuwa ta shigo mata da abun karyawa, Widad ta kalleta tace
"yanzu dan Allah jiya baki ji ihuna ba cikin dare?"
Sabuwa tace "idan nace vamji ba nayi ƙarya, sedai kona fito ba abunda zan iya yi
miki, saboda Kinsan nima aiki aka ɗaukeni inyi, idan na shiga hurumin da ba nawa
ba, zasu kasheni ne, seda akamin wannan sharaɗin sannan na fara aikin kula dake ɗin
nan"
"Saboda me?"
Widad tana nan zaune sega Bulama ya shigo ɗakinta, shida wasu ƙarti su biyu, aka
kawo masa kujera aka ajiye, ya hau kai ya zauna ya kalli Widad yace "karo na
ƙarshe, ki gayamin inda takaddun nan suke"
Widad ta kalle shi tace "gargaɗi na farko kuma na ƙarshe, ka jawa ɗanka kunne,
idan ya sake zuwa inda nake, wallahi sena kasheshi har lahira"
"ina miki magana kina gayamin wani shirme daban? Ki kasheshi ɗin karki fasa, ina
takaddu suke su nake tambayar ki"
Bulama yace "zan azabtar dake, azaba irin wadda ba'a taɓa yi miki ba, ina suke?"
"Duk Azabarka a duniya ne kawai, kuma babu wanda yake da ikon yin azaba se Allah,
na gaya maka na bawa masu dukiyar nan dukiyarsu, ka ƙyaleni ka rabu da rayuwata
haka"
Bece mata uffan ba, taga na jona wani abu a jikin socket, an miƙawa Bulama ya karɓi
abun yayo kanta gadan gadan, bata motsaba ta tsaya tana kallonsa, kawai ya jona
mata abun a hannunta, ji tayi kamar ba a duniya take ba, ta rasa meke mata daɗi
gaba ɗaya ta fita hayyacinta.
Girgiza kai ta dingayi tana kuka, amma taƙi magana, yasa ƙafa ya take yatsunta yana
murzawa ciki mugunta, amma dayake Indai taurin kaine Widad ta iya shi taƙi magana.
Ba azabtarwar da basu mata ba amma taƙi faɗa, haka suka gaji Bulama ji yake kamar
yasa wuƙa ya yanka ta, amma yaga idan ya kashe ta beyi Achieving komai ba, haka
suka tashi suka fita, suka barta a galabaice.
sedai fitar sa babu daɗewa wani irin ciwon kai ya kama Widad, ko iya gani ba tayi
sosai, ga ƙirjinfa daya riƙe gam, nan ta kwanta tun tana kwnace, harta fara juyi
ya zamana bata iya ganin komai, se dishi dishi daga baya kuma ta dena gani gaba
ɗaya.
Daga nana bata sake farkawa ba se a gadon Asibiti, taji anayiwa Bulama bayanin
zuciyartace ta kumbura kuma ga jininta ya hau, Ba tausayi ba imani Bualama yayiwa
doctor Hamisu umarnin ya cire ɗan cikin Widad koda tsiya ne.
Ta buɗe idonta fes a kansu, amma hakan besa Bulama yai shiru ba, ya bada umarnin a
cire cikin.
Haka doctor Hamisu yaje ya ɗakko allurai, yazo ya haɗasu yayi mata duk tana
kallonsa, sedai ta kasa motsa koda ɗan yatsanta ne, gaba ɗaya tama rasa inane yake
mata ciwo, haka ya kwance cannula yai mata wata allura, sannan yasa wata a ruwa, ya
gama ya fice tana kallonsa.
Sosai Yusuf yake jinsa a damuwa, hankalinsa yaƙi kwanciya sam, yake jin jikinsa ba
daɗi, tunanin Widad ya cika masa zuciya.
"To wai kai Haruna ya akayi ka bari haka ta farune? Ta yaya yarinya ƙarama zata
dinga wasa da hankalinka haka?"
Alhaji Haruna yace "kai dai bari kawai Alhaji Musa, wallahi nikaina ban san abun ze
kai haka ba, ganin irin kuɗaɗen dana bata, ni nama rasa abunyi wallahi, babban abun
tsorona shine video na data ɗauka, karta saki a duniya mutuncina ya zube"
Alhaji Musa yace "rabu da ita, duka barazanar banzace ba zata saki ba ƙarya take"
"Ya zakace ƙarya take? Bayan har Salma ta turawa message a kaina?"
"ni nace maka ka ƙyaleta ai, to ka ƙyaleta ba zata iya yaɗawa ba, sannan batun
takadda ka gayawa Bulama gaskiya kawai, ai da tun farko ka faɗa masa ma da tuni an
wuce gurin, ƙilma yai maka maganinta"
Bacci ne ya ɗauki Widad me nauyi, sedai wani irin gigitaccen ciwon mara yasa ta
farka babu shiri, ji tayi wani irin ciwo yana ratsata, tun daga mararta zuwa
bayanta da ƙafafuwanta, wani irin ƙarfine yazo mata, ta zabura ta fizge cannula,
aikuwa take jini ya shiga zuba daga inda ta cire cannulan.
Ta faɗo daga kan gadon, Nurses ne suka shigo da sauri, suka ga yadda Widad ta faɗo
ƙasa, ta riƙe mararta hawaye na zuba daga idonta, alamar tana jin jiki, ɗayar ta
kalli ɗaya tace "Sister, ki kira likita da sauri yazo ya dubata"
Tace "shikenan bari inje"
Tana zuwa ta sami doctor Hamisu a Office tace "doctor, patient ɗin Alhaji Bulama ta
Amenity she's unconscious fa, harta faɗo daga kan gadon"
"Ku kaita labor room kuyi mata abunda yakamata, Abortion ne cikin jikintane ze
faɗi"
"doctor, amma naga kaman ba case ɗin Abotion aka kawota ba, cardiac failure ne, da
hypertension kawai, ya za'ayi within a minutes ace kuma Abotion yai occurring"
"Are you going to teach me my job? Wace makarantar kika yi ne, baki san cardiac
failure na uwar ze iya shafar abunda ke cikinta bane? Get out from here kije kuyi
abunda nace"
Jiki a saluɓe Nurse ɗin ta fita daga Office ɗin ta koma ɗakin Widad, ta tarar da
ɗaya Nurse ɗin rungume da Widad tana mata sannu.
"Sister ina doctor ɗin?"
"naje yamin wulaƙanci, wai mukai ta labor room abortion ne, muyi mata abunda
yakamata, shikenan babu wani taimako da za'a bata se a bari cikin ya fita?"
Widad kam banda aikin gumi babu abunda take yi, fuskar nan tayi jawur saboda azabar
wahala, haka taita wannan wahalar tana addu'a tana ambaton Allah, tana roƙon Allah
ya bar mata cikin nan.
Ɗayar taje ta samo wata allura a pharmacy tayi wa Widad, cikin ikon Allah se bacci
ya ɗauketa, can sega doctor Hamisu ya shigo yana cewa "Yaya? Cikin ya fita dai ko?"
Nurse ɗin tace "Eh ya faɗi, mun gyarata ne ta samu hutu, amma babu wani wanda suka
zo tare da ita ne?"
"Ba ruwan ku da wannan, tunda mun samu ya faɗi Alhamdilillah, a bata medication
ɗinta na dare"
Bayan fitarsa ɗaya ta kalli ɗayar tace "Sister Habiba, kijimin ikon Allah, ni anya
ba doctor ne yai mata wani abuba akan cikin nan ba kuwa?"
Sister Habiba tace "ya za'ayi in sani, amma nima ina zargin hakan wallahi, Allah
sarki tana murƙusus amma fatanta Allah ya bar mata cikin ta, Insha Allah be zube
ba, ko akanme ze damu cikinta ya zube oho"
"Hmm kedai bari, shida wannan Bulaman dama basu fiye ƙulla abun Arziki ba, naga
shiya kawota kika bibiya karuwarsa ce, ko kuma dai cutarta sukayi suke so su rabata
da cikin, kin san ɗan Bulaman Fahad ya saba kawo mata nan a cire musu ciki"
Sister Safiyya tace "ai kedai bar masu kuɗin nan kawai, Allah dai ya shirya naga
ta samu bacci, gashi babu kowa a gurinta, balle idan ta farka a bata Abinci"
Sister Habiba tace "ai kamar yadda kika faɗa ɗinne, kika bibiya dai ba ta hanyar
Allah aka samu cikin ba, shine suke son su zubar mata ta ƙarfin tsiya"
Baiwar Allah, ita Widad sam bata san meke faruwa ba, wani galabaitaccen baccine ya
ɗauketa, wanda fal yake da mafarkin Yusuf cike da bege da shauƙin son ganinsa, se
kuma mafarkin daddy da take yi.
Ɓangaren Ramlah kuwa, taga kwata kwata kusan Fahad yayi dumping ɗinta aside, kwata
kwata baya ta tata yanzu, dan haka ta shirya da kanta ta tafi Hotel ɗin da yake
zuwa, tana zuwa kuwa ta sameshi da wata mace a ɗakin, Ranta ya ɓaci matuƙa ta dube
shi tace "Lallai Fahad, ka cika tantirin butulalle, a wani postion ka ajiyeni ma
tukuna?"
Fahad yai murmushi yace "postion ɗinki dai na farko, a nan ns ajiye ki, me kike
tunani"
"dalla saurara, karka gayamin maganar banza mana, ban gane postion ɗina na farko
ba, ina maganar Auren mu da kai?"
Fahad ya kwashe da dariya yace "haba tawan, meye muma na ɗaga jijiyoyin wuya haka?
Maganar Aure tana nan mana, ki bari idan na Auri Widad kema se inzo daga baya in
Aure ki"
Ta kalle shi tace "Fahad, yau wace irin giya ka Shane haka? Data gaya maka ƙarya
wadda harta saka ka kalli idona kake gayamin maganar banza da iska?"
"irin wadda na saba sha ce dai, sedai ban sani ba ko nasha expired ne"
"Lallai Fahad kana wasa, baka san abunda ka aikata me ze haifar ba ko? Ds kyau
wallahi ka ɗebo ruwan dafa janka in dai Ramlah ce, zakaga tsiya"
Ta juya buguzun buguzun tai waje, bata zame ko 'ina ba se ofishin Bulama, tana zuwa
ta tarar yana aiki a Office, sedai tayi mamaki ganin ɗinki haka a fuskarsa, koda
yake ba wannan yakawo ta ba.
Ya ɗago ya dubeta yace "Ramlah lafiya kuwa? Ya kika shigomin Office haka?"
"Maganar da mukayi akan wannan mutumin, da yake iƙrarim shi mahaifin mu ne, kace
zaka ɗau mataki akansa, amma har yanzu bani da tabbas na ka ɗauka kokuwa?"
"Banda abunki Ramlah, nima fa ban san takamaimai inda yake zaune ba, ta yaya zan
ɗaukar miki matakin? Nasa aje inda nasan shi, amma baya nan baya zama a guri ɗaya
sam"
Tai tsaki sannan tace "waima ni wane irin hatsari ne dashi haka, wanda yasa Mummy
ke tsoronsa?"
Bulama yace "wannan tambayar ai ita zakiyiwa bani ba, kije ki tambaye ta zata
gayamiki komai"
Tai ajiyar zuciya, tare da jinjina kai tace "idan kai baka ɗau mataki ba, nika
gayamin inda yake in ɗau matakin daya dace dashi mana"
"Haba Ramlah, kema kin san da nasan inda mutumin man yake aida da kaina zam ɗauksr
miki mataki akansa"
Kallon Bulama kawai take, ba wai dan ta gamsu da abunda yake faɗa ba, ta suri
jakarta tai waje tana ƙwafa.
Fafur Nurat ta dena fitowa ko falo, saboda karma su haɗu da mahaifinata yai mata
zancen komawa ƙasar waje.
Dayake yau Weekend ne sam be fita ba, yana gida amma still bega gilmawar Nurat ba,
ya tafi ɗakin matarsa ya tarar tana kwance tana chatting, yace "wai ina yarinyar
nan ne? Wunin yau banga gilamawarta ba"
Ta tashi zaune tace "tana ɗakinta mana, kasan halimta wasu lokutan bata san shiga
mutane, tafi son zaman kaɗaici a ɗakinta, balle kuma ka ƙwace wayoyin ta"
"Ina fatan dai tana nan tana shirin tafiya?"
"kamar yadda nake gayamaka mana, kai ds ita kukayi magana, dan haka babu ruwana ka
tambaye ta idan tana shirin da kanka"
Ya jinina kai, kwanan nan yaga zam iyalin nasa sun dena tsoronsa kamar yadda suke
tskronsa a baya, ya rasa dalili.
Yana shiga ɗakin Nurat, ya tarar tana tilawar Al'qur'ani mai girma, ya jira ta kai
aya ta ɗago ta kalle shi, dan taga magana yake son suyi.
Yace "dama zuwa nayi in ji ko kina shirin tafiyar nan kuwa? Jirginku ze tashi jibi
in Allah ya kaimu fa"
Nurat ta miƙe taje ta ajiye Al'qur'anin ta sannan tace "nifa ba inda zanje Daddy,
tsawon shekaru ina maka biyayya, dukda yi maka biyayya umarnin Allah ne, amma nima
kayimin adalci mana, wallahi idan na tafi karatun nan bashi zanyi ba, rayuwata
kawai zanyi"
"wallahi Daddy kace sena tafi guduwa zanyi daga gidan nan, ni bana son tafiyar"
Ya ƙura mata ido na wasu mintuna, sannan yai ƙwafa ya tashi ya fita.
Widad tana gadon Asibitin nan, ko iya miƙesa ba tayi, amma a haka aka sakata a
wheel chair, Aka kaita mota aka maida ita wannan gidan da ake ɓoye ta.
Haka aka maida Ita, yau s bsta wannan maganin gobe a ɗurma mata wannan Allurar,
haka take ta fama ga ciwo yaƙici yaƙi cinyewa, banda izayar da Bulama ke mata akan
ta bada takaddun nan.
Kwanci tashi asarar rai, Yusuf ya cika sati uku cif a gidan yari, rana ta zagayo
aka koma dashi kotu domin ci gaban shari'arsa.....
IDAN KIN SAI LITTAFIN NAN KE KAƊAI KIKA SIYA, KUMA AMANACE TSAKANINA DAKU, IDAN
KUKA FITAR BAKUMIN ADALCI BA, TUNDA BAMUYI DAKU ZAKU FITARMIN BA.
AYSHERCOOL
07063065680
11/23/21, 10:26 PM - Buhainat: LITTAFIN KUƊI NE, DAN ALLAH KI SIYA KAFIN KI KARANTA
BA DANNI BA DAN ALLAH, LITTAFI NA ƊAYA KYAUTA NE WANNAN NA SIYARWA NE
NORMAL GROUP ₦300
VIP ₦500 NE KITURA TA WANNAN ACCOUNT ƊIN
0009450228
JA'IZ BANK
AISHA ADAM
SE A TURA SHEDAR BIYA TA WANNAN LAMBAR
07063065680
(Albishir ga masoya, ma'abota bibiyar litattaafaina, dama ta samu zaku fara samun
litattaafaina na audio, akan YouTube channel ɗina me suna Cool Arewa TV
https://youtube.com/channel/UCD5vnvA5laU8ti4LLz2_QEg
Kuyi liking sannan ku danna subscribe, domin fara samun litattaafaina na audio,
nagode sosai da ƙaunar ku gareni"
134_135
Yauma kotun a cike take maƙil da ɗan Adam, 'yan jarida kota ko' ina, ga 'yan sanda
da sauran mutane domin sauraren cigaban ƙararar, seda akayi kusan shari'a uku
sannan aka gabatar da ƙarar Yusuf, Barrister Sadik ya fito ya sake gabatar da kansa
a gaban kotu, sannan yace ze fara gabatar da shedun su akan Yusuf.
Barrister Sadik yace "zan fara gabatarwa da kotu shedarmu ta farko akan cewar
Yusuf shine yayi garkuwa da 'yar gidan Alhaji Nasir Daula"
Nan Barrister ya kira wani mutum, mutumin ya fito ya tsaya ya fuskanci kotu,
Barrister ya taka gaban sa yace "ko zaka iya faɗawa kotu sunanka?"
Sada yace "Eh nasan shi, sunanshi Yusuf, yana kawomin gyaran motoci"
"Eh ganina dashi na ƙarshe shine, ranar daya kawomin wata mota yace in siya, nace
masa gaskiya ni bana siyan mota sedai zan haɗashi da masu saida mota, bayan na
haɗashi dasu se aka kawon lambar motar da na kawo maka, wadda ta kasance lambar
motocin gidan Daula ne "
Aikuwa aka kawo lambar mota aka nuna a kotu, wannan lambar ita ce lambar dake jikin
motar da Yusuf suka fita aka sace su a cikinta, tunda Yusuf yake be taɓa ganin
wannan mutumin ba me suna Sada, amma yau an samoshi an masa sharri.
Barrister Khalil yace "Sheda na gaba da zan gabatarwa da wannan kotu shine wanda
ake zargin tare suka haɗa kai da Yusuf suka sace 'yar gidan Nasir Daula wato Saleh"
Aka shigo da Saleh, yana takawa da kyar wanda gaba ɗaya ya fita a hayyacinsa, kallo
ɗaya zakayi masa kasan bashi da lafiya aka rakitoshi.
Akaje aka tsaida Saleh, Barrister Sadik yace "Malam Saleh, ko zaka iya gayamana
waye kai a gidan Daula?"
Cikin murya ƙasa ƙasa yace "Ni tsohon sojane, kuma hadimi a katafaren gidan Daula"
"Shine direban 'yar gidan Daula, shi yake kaita duk inda zata je"
Barrister Sadik yace "ya akayi kuka haɗa baki kuka sace ta, harka basu mafaka?"
Saleh ya kalli Yusuf, ya sunkuyar da kai yace "Bayan Yusuf yayi duk shirin daze,
ya nemi da ina nema masa inda ze zauna ya ɓuya, ba tare da an gano inda suke ba,
yayi Alƙawarin ze bani kuɗi, ni kuma na yadda na amince, daya sato ta na gaya masa
inda zamu haɗu, shine na kaisu wannan ƙauyen daga baya ya je ya saida motar, muka
raba kuɗin "
Yusuf ya ƙurawa Saleh ido, amma Saleh ya kasa ɗaga kai ya kalli Yusuf, ya sunkuyar
da kai yai shiru, yakasa kallon Yusuf, shima Yusuf bashi da zaɓin daya wuce ya
sunkuyar da nasa kan, Umma se kuka take tana mamakin, ya za'ayi ace ɗantane yai
wannan abubuwan haka? "
Barrister Khalil yace 'idan kotu ta bani dama, zan gayyato Malam Audi, wanda shine
Saleh ya nemo ya ɗauki Yusuf da' yar gidan Daula, a ƙurƙurarsa zuwa cikin ƙauyen da
akayi garkuwa da ita"
Malam Audi ya fito shima, Barrister Khalil yai masa tambayoyin duk daya dace yai
masa, shima ya bada amsa, kamar yadda aka buƙata.
Barrister Khalil, ya kira doctor Mustapha wanda shine Likitan daya duba Widad
lokacin da aka harbeta, shima ya fito ya tsaya ya bayyana sunansa a gaban kotu.
Barrister Sadik yace "Doctor Almustapha, kaine Likitan daya karɓi 'yar gidan
Daula, lokacin da Wannan bayin Allah suka kaita Asibitinka ha akayi?"
Doctor Mustapha yace "eh hakane, Wataran da safs ina aiki, suka shigo cikin
Asibiti na, ɗauke da wata matashiyar budurwa wadda take a galabaice, jini nata zuba
daga jikinta, suka shiga da ita Office ɗina, sukace patient suka kawo in duba musu,
nace musu bazan karɓi case ɗinba, saboda harbine a hannunta, amma Saleh ya ciro
bindiga yace idan banba ze kasheni, haka na cire mata bullet daga jikinta, ko gama
watstsakewa ba tayi ba suka ɗauketa suka gudu"
Justice Abdullah A dutse yace "wanda ake ƙara ko kana da abunda zaka ce?"
Yusuf ya girgiza kansa alamar A'a, ya juya ga Barrister Sadik yace "muna
saurarenka Barrister"
Barrister Sadik yace "ya me girma me shari'a, wannan sune ƙwararan shedunmu da
zamu gabatarwa wannan kotu, sannan in Allah ya yarda a zaman kotu na gaba zamu
ƙarasa kawo shedunmu da tarin hujjojunmu, wanda zasu tabattar da wanda ake zargi
shine ya sace 'yar gidan Alhaji Daula"
A dutse yace "duba da yadda barrister ya gabatarwa da kotu shedunsa, kuma aka
tambayi wanda ake ƙara be musa ba, da kuma yadda Barrister ya nema, wannan kotu
tayi umarni da' a maida wanda ake zargi gidan gyaran hali, zuwa sha biyar ga wata
me kamawa"
Yusuf ko ɗaga kai baya yi, saboda bashi da idon daze kalli al'umma dashi mussman
masoyansa, wani abun idan ba'ayi ba anyi wank, ga tarin hujjoji da shedu da aka
gabatar, shi kuma gashi ba masanin fannin shari'a ba, to idan ya musa ma yace me?
Bashi da zaɓin daya wuce ya amsa, haka aka kuma zura shi a motar gidan yari, ba'a
bari 'yan jarida sunyi magana da shi ba, kowa wani yayi magana da shi ba aka tafi
da shi.
Koda Nurat taga yadda kanun shari'ar ya gudana yau gaba ɗaya ta ɗimauce, ta rasa
inda zata saka ranta yanzu shikenan babu wanda ze tsayawa Yusuf kenan? Dukda wannan
shedun da aka gabatar har yanzu zuciyarta bata saduda ba, tana jin sharri ne kawai
akewa Yusuf ɗin.
Ta fita taje ɗakin Mummynta, ta tarar tana salla, ta ɗauki wayarta akan gado tai
waje, bata tsaya ko ina ba se ɗakinta, ta shiga ga kulle ƙofa ta ciki ta kira
Khalil.
"Khalil kana gani an gabatar da shedun ƙarya akan Yusuf, shikenan haka za'a bari a
kulle shi, ba zaka iya komai ba?"
Khalil yace "Nurat, abun ya wuce tunanin ki, ke yarinya ce kuma kina gida a zaune
baki san meke wakana ba, wallahi ana nan ana barazana ga duk wanda yai yunƙurin
shiga shari'ar nan da nufin kare Yusuf, kedai ki cigaba da Addu'a, Allah zeyi
ikonsa, kuma..
Ai bata jira meze ƙarasa faɗa ba, ta ajiye wayar tai shiru ta dafe kai, ta rasa
abunyi dan yanzu kukanma bata iyawa, gaba ɗaya taji kamar jiri na kamata, ta buɗe
ƙofa ta fito tana dafa bango, sedai tama zuwa falo kawai ta faɗi a gurin, hakan yai
dai dai da shigowar Alhaji Musa, ya ƙaraso kanta da sauri yana kiran sunanta, sedai
bata san meke cewa ba.
Ya ɗakko ruwa me sanyi yana shafa mata, a hankali ta dinga sauke numfashi, Mummynta
ta fito falo kawai ta tarar da Alhaji Musa rungumen da Nurat yana shafa mata ruwa.
Yace "Nurat"
Yace "meke damun ki ne haka? Ina shigowa naga kin faɗi, meke damun ki?"
"Kyace fa bakomai? Gata nan ko Abincin kirki bataci, na rasa meke damunta, bayan
tea ko biscuit, bayan nan bata cin komai, haka yake wuni duk tabi ta ƙare ta bushe"
Ya kalleta cikin kulawa yace "meke damunki ne Nurat, meyasa bakya cin Abinci? Duk
kin rame"
Ta jinjina masa kai, yace "zanyi shawara, fitinarki da rawar kanki ce tai yawa,
shiyasa nake son turaki can, zanyi shawara amma kidena ƙin cin Abinci"
Ya ƙura masa ido, yana sonta dukda halinsa dayake ita 'yarsa ce yana sonta, amma
meyasa ze jefa rayuwar' ya'yan wasu cikin damuwa? Adalci kenan hakan? "
Hawaye ya shiga gangarowa gefen idonta, ya dinga share mata yana ya isa haka, tashi
muje ki kwanta ki huta anjima zan kira likita yazo ya dubamin ke.
Ya kama hannunta, ya kaita ɗakin ta ta kwanta, sannan ya fito ya rufe mata ɗakin.
Yauma Widad na zaune, ta ari wayar sabuwa ta duba yadda shari'ar ta kasance, sedai
babu wata hanyar mafita ko nasara akan lamarin, babu wata hanya da zata bi ta
temaki Yusuf, gashi bata da tabbacin da wace manufar wannan matar ke nuna mata
kulawa da tausayi, saboda Bulama makirine, babu abunda baze iya ba, haka ta bata
wayarta ta, ta koma ta kwanta, tare da lumshe idonta.
Har yanzu tana jin alamun cikin ta na nan, dan babu abunda ya sauya na daga abunda
takeji, na laulayi shikuma Doctor Hamisu ya tabattarwa da Bulama cikin Widad ya
fita, gaba ɗaya ta koɗe kamar ba Widad 'yar ƙwalisan mam ba, matashiyar' yar
hamshaƙin attajiri, 'yar gayu me cin zamaninta ba, duk tayi wani iri, ga tashin
hankali da tunani ha pressure ciki, abunda bata saba ba bata san yadda yake ba, ga
kuma sauran ciwukan da suke damunta, banda uban duka da take sha a hannun Bulama,
da sauran mugunta da yake mata.
Yusuf yana zaune a gidan yari, akace yazo yayi baƙi, shi dai yasan an dena barin
kowa yazo inda yake, Umma ma sau ɗaya aka bari ta ganshi, ko saƙo aka kawo masa ba
bashi ake ba, haka yake zamansa a wahale, Yusuf ɗan gayu daya saba da tsafta,
rayuwar gidan nan ba ƙaramin wahala take masa ba.
Aka fito da shi zuwa ofishin gandirobobi, yaga wannan ɗan sandan me kula da sashin
manyan laifuka, daya zauna a sashensa lokacin da yana hannun 'yan sanda, wanda ya
dinga azabtar dashi, Yusuf na ganinsa ya sake haɗe rai ya ƙaraso ya zauna.
Ya kalli Yusuf yai murmushi yace "haba Yusuf, ba faɗa meya kawo gaba kuma? Meye na
haɗe rai dan ka ganni, ashe an fara shari'arka?"
Yusuf yai masa banza yaƙi magana, yace "shikenan, tunda bazakamin magana ba, na
fuskanci kai dai halinka ne a haka, miskilanci da taurin kai, zamanka a hannunmu be
sa ka canza ba, kai dai haka Allah yayi ka kenan?"
"mekazo yi gurina? Bayan an hana kowa yazo gurina kai meyasa aka barka kazo gurina,
me zan maka?"
Yasa hannu a aljihunsa, ya ɗakko biro da farar takadda a cikin wani file, ya miƙawa
Yusuf yace "ɗan Yimin signing ɗinka a nan in gani"
Yusuf ya kalli takaddar ya kalli ɗan sandan yace "na menene wannan?"
"Ni kake cewa bazaka saka ba, kai idanma tinƙahonka kaima ɗan sandane, aiko a aiki
na girmeka, haka a shekaru ni zaka gwadawa taurin Kai?"
Yusuf yace "eh bazan saka hannunbau, bazan saka hannu akan abunda ban san meye ba"
Aikuwa ɗan sandan ya kashe Yusuf da mari, Yusuf kuma ya rama, kafin kace kwabo
gandirobobin nan sunyo kan Yusuf da duka, kota ina suka haɗu suka masa lilis, ko
motsi baya iyayi, sannan aka sureshi aka maida shi, a galabice.
Ɗaurarrun gidan dayawa sun sanshi, baya magana ba ruwansa da kowa, kamun kansa yasa
suke girmama shi, musamman da suka jiya ana masa laƙabi da maitama, akace musu ɗan
gidan marigayi Bashir maitama ne, su suka karɓeshi, suna mamakin wane laifin yayi
aka kama shi aka dake shi haka? Suka samo ruwan zafi a kitchen aka dinga gasa masa
inda ha farfashe a jikinsa.
Duk takurar da akayiwa Yusuf akan ya gwada yin signing ɗinsa, su sake gwadawa dana
Bulama su gani ƙi yayi, aka ƙara tsananta masa a gidan kurkun nan, hantara cin
mutunci zagi, ayyuka ma wahala amma Yusuf yaƙi sakawa fafur, danma wani abun
fursunoni sukan shigar masa saboda suna ganin salihancinsa da haƙurinsa be kamata a
dinga cuzguna masa ba. Ranaku gudu suke, lokaci na ƙara sauri, kamar ƙyaftawar ido,
lokacin komawar Yusuf kotu yayi, suka sake shiga kotu domin cigaban shari'arsa.
A wannan karon kuma Barrister Saminune ya fito dan gabatar da shedu da hujjoji akan
Yusuf.
Barrister Saminu ya gabatar da kansa, sannan yace "kamar yadda wanda aka yi ƙara
yayi da'awa a hannun 'yan sanda cewar a hukumance aka bashi umarnin yayi aiki a
gidan Daula, domin bawa' yarsa kariya, sedai a iya binciken 'yan sanda babu wanda
ya sashi wannan aikin, sannan hukumar' yan sanda tayi Allah wadai da abunda yayi
sun sallameshi daga aikinsa gaba ɗaya, kuma abokin aikinsa me suna Abbas Habib,
wanda wanda ake ƙara yace shine shedarsa akan an sashi aiki a gidan Daula, ya
tabattarwa da kotu cewa, Babu wanda yasaka Yusuf wannan aiki, Yusuf ƙarya yake masa
dan haka Yusuf yayi basaja ne a gidan Daula, yaje da suffar mutanen kirki danya
sace 'yarsa "
Babu abunda ya bawa Yusuf mamaki se jin sunan Abbas, da kuma abunda akace yace a
game dashi, ya jinjina kai ya tuna yadda Widad take nuna tsanarta ga Abbas, ashe
Abbas ze iya yi masa haka? Sekuma yai tunanin Amma Suleiman yana kotun nan, kenan
shima baze iya taimakonsa ba? Yusuf yai shiru kawai yana sauraren ikon Allah.
Babban Abun mamaki, harda su Ramlah aka kira a matsayin wanda zasu bada sheda akan
Yusuf ne ya sace Widad.
Barrister Saminu ya kalli Ramlah yace "ko zaki iya shedawa kotu wacece ke?"
"ko zaki shedawa kotu abunda kika sani game da Yusuf, alaƙar dake tsakaninsa da
Widad yarinyar daya sace?"
Ramlah tace "eh to, lokacin da aka kawo shi zeyi aikin direba, da bata aminta dadhi
ba ita Widad, saboda halinta na rashin yadda, ganin mahaifinta ya yadda dashi,
shiyasa itama ta haƙura da hakan ta yadda dashi a matsayin direban nata, Daya ke
mukan ɗan gaisa da shi, wataran yake tambayata wai dan Allah nasan Password ɗin
Widad na banki, dayake daga baya ta ɗan yadda dashi har ɗakinta yana shiga, nace
masa me zeyi da password ɗinta na banki, se yace min bakomai tambayata kawai yayi,
se nace masa nima ban sani ba, to haka dai Widad ta kan yi complaining akan ana
mata sace sace bayan babu wanda yake shiga ɗakinta seshi, har wataran sukayi
sa'insa ta kusa korarsa, mahaifinta ya hanata, sedai ba daɗewa wannan lamarin ya
faru aka neme ta aka rasa "
Barrister yace " Shikenan, mungode Malama Ramlah zaki iya komawa kije ki zauna "
Yusuf yabi Ramlah da ido, har taje ta zauna, me shari'a yace " ko wanda ake ƙara,
yana da abun cewa? "
Yusuf ya girgiza kai, ya maida kai ya sunkuya, Umma ta tashi da sauri ta fice daga
kotun, tana kuka.
Barrister Saminu yace "idan wannan kotu ta bani dama, zan sake gabatar da sheda
akan wanda ake zargi"
Wani ma'aikacine daga gidan gonar Daula ya fito, aka gabatar da shi a matsayin
Iliya.
Barrister Saminu yace "ranar da abun ya faru, ance kana nan da daddare kana aiki a
gidan meyafaru?"
Iliya yace "eh to, a ranar sunzo gidan dashi da Ita, da Alhaji Nasir Daula, cikin
dare suka fito shida ita kamar ze nuna mata wani abu a wajen mota, kawai ya buɗe
motar ya dannata ta ƙarfi, lokacin ina saman benen dake kusa da inda suke, kafin in
sakko wasu mutane sun ɓullo daga gurin fulawoyi a laɓe, da alama dama suna laɓe ne
gidan a ɓoye suka buɗe masa gate, Jin motsi yasa Daula ya fito a guje, yace lafiya?
Se Saleh yace ai wasu mutane ne suka shigo suka fita da Widad, shine Daula ya faɗi
a gurin "
Suleiman ya sunkuyar da kai kawai, dan kowa yaji yadda ake gudanar da wannan
shari'a, tsantsar son zuciya ne kawai da rashin imani, wata irin bahaguwar shari'a
ake ba fasali babu komai, kuma duk wanda ya bada sheda babu wani bin diddigi a masa
tambayoyi dan tabattar da abunda yake faɗa, kawai se a karɓi wannan shedar.
Barrister Saminu yace "idan kotu ta bani dama, zan gabatar da sheda ta ƙarshe
wadda itace me ɗungurungum, wadda zata tabattar da Wanda ake zargi shine yai
garkuwa da 'yar gidan Alhaji Nasir Daula.
Yusuf ya ƙura ido yaga waye ze shigo, me ze gani Widad ce aka shigo da ita, tayi
haske amma da gani kasan hasken cutane, ta rame tayi wani iri, duk wanda yasan ta a
baya, idan ya ganta baze ganeta ba se mutum yayi dagaske, saboda tsabar rama da
fita hayyacinta da tayi.
Yusuf yabi Widad da ido, yadda ta koma yana tunani daban daban a ranta.
Akaje aka tsaida Widad, amma ta gaza kallon Yusuf, yayin da Yusuf ya kafe ta da
idanuwa, Barrister Khalil yace "ko zaki iya bayyanawa kotu wacece ke?"
"Widad Nasir Daula" ta bashi amsa, ba tare da ta kalle shi ba, ya nuna mata Yusuf
yace "kin san wannan?"
Ya nuna mata Yusuf, ta jinjina masa kai, waye shi? Meye alaƙarki dashi? "
Bata kalli inda Yusuf yake ba tace "da farko direbana ne, yayi aiki tare dani a
gidanmu"
"Lokacin da yayi aiki dake, kin san cewar ɗan sanda ne?"
Ta girgiza kai, "Ana zargin shine ya sace ki, yai garkuwa dake, me zakice akan
haka?"
"Eh Yusuf yayi garkuwa dani, na zauna a hannunsa tsawon watanni biyar, sedai babu
wani abu na cutawarwa ko tsoratarwa da yayimin"
"Ya isa haka Malama Widad, zaki iya tafiya"
Barrister Khalil ya katseta, ganin hawaye ya cika idonta tana neman ta saki layi,
aka fito da ita zasu tafi, se a lokacin ta ɗaga kai ta kalli Yusuf, taga yadda yake
binta da kallon da bata gane na menene ba? Hawayene ke shirin gangarowa a idonta,
ta girgiza masa kai, ta fita daga cikin kotun.
Tana fitowa tai karo da Umman Yusuf, cikin kuka Umma tace "Wallahi keda Allah,
Allah ya sakawa ɗana, wallahi Allah ze bi mana haƙƙinmu, saboda rayuwarki ta ɗana
ta kassara, a sanadiyarki aka kashemin miji, yanzu gashi sanadinki za'a kullemin
ɗa, bayan danke duk ya shiga wannan halin, Allah yana kallonki fa, kiji tsoron
Allah "
Umma na zubda hawaye, Widad na zubda hawaye, tana son tayi magana amma ta gimtse
maganarta saboda abunda hakan ka iya haifarwa, ta shige mota ba tare da ta cewa da
Umma Uffan ba.
Alƙali ya sanya sati biyu, domin yanke hukunci na ƙarshe akan Yusuf, kotu ta watse
ana Yusuf bashi da sauran mafita, tunda ita da bakinta ta tabattar da ya sace ta.
Gaba ɗaya hope ɗin Yusuf ya ƙare, tunda Widad ta tabattar da hakan ba shakka bashi
da mafita sam.
Abun duniya ya ishi Widad, aka maida ita inda ake tsareta a gidan Bulama, ta ɗora
hannu a kanta tana wani irin kuka, jikinta har rawa yake, zuwa yanzu tana jin yadda
abunda ke cikinta yake ɗan motsawa kaɗan kaɗan.
Bulama ya shigo ɗakin da Widad take, yana kallonta ya kwashe da dariya yace "ban
taɓa tunanin zaki so wani abu a rayuwarki bayan mahaifinki, kamar wannan shashashan
Yaron ba, kamar ma kinfi sonshi akan Daula, sedai na ƙarar da soyayyar a nan, na
saka mata aya, tunda gidan yari za'a kaishi"
Widad ta kalli Bukar tace "Kayi kuskure, kai Yusuf gidan yari baze taɓa kawo
ƙarshen soyayyar da nake masa ba, dukda kai ba mutum ne me cika Alƙawari ba, nasan
ba lallai ka cika Alƙawarin da kamin akan Yusuf ba, ni dai fatana kamar yadda
mukayi da kai kar kuyi sanadiyyar rayuwarsa dan Allah "
Tai maganar tana kuka a gaban Bulama, yai dariya yace " wannan kaɗai be isa in bar
yaron nam a raye ba, harse kin gayamin inda kayan nan suke "
Widad ta kalle shi tace " A zatonka kafini wayo da dabara ne, to bari in gaya maka
abunda baka sani ba tsayin shekaru, Daula ba dukiyar ya ɗauka ya danƙamin ba, ya
naɗi video akan yadda takaddun suke, da yadda dukiyar take da kuma a inda take, ni
kuma dana tashi na bawa Amintacce na ya ajiyemin, nasan ko bayan raina, idan ya
gano ajiyar dana bashi ze danƙa amana ga masu ita "
Tai maganar tana tsura masa ido, nata cikin nasa.
" Gurin masoyina mana, da kake so ya ƙare rayuwarsa a prison, seka bari ranar daya
fito seya baka "
Ya wanketa da mari da wannan Ƙaton hannun nasa, idan ya mareta har wani jirine yake
kwasarta, amma ta dake tace "idan ka kasheni, ka kashe dukiyar da kake nema, ka
huta, shedar tana gurinsa, mabuɗin yana gurina, dan haka dabara ta rage game shiga
rijiya"
IDAN KIN SIYA AMANACE, IDAN KIKA FITAR KUMA KINCI AMANA!!!
Ayshercool
07063065680
11/24/21, 10:26 AM - Buhainat: LITTAFIN KUƊI NE, DAN ALLAH KI SIYA KAFIN KI KARANTA
BA DANNI BA DAN ALLAH, LITTAFI NA ƊAYA KYAUTA NE WANNAN NA SIYARWA NE
NORMAL GROUP ₦300
VIP ₦500 NE KITURA TA WANNAN ACCOUNT ƊIN
0009450228
JA'IZ BANK
AISHA ADAM
SE A TURA SHEDAR BIYA TA WANNAN LAMBAR
07063065680
(Albishir ga masoya, ma'abota bibiyar litattaafaina, dama ta samu zaku fara samun
litattaafaina na audio, akan YouTube channel ɗina me suna Cool Arewa TV
https://youtube.com/channel/UCD5vnvA5laU8ti4LLz2_QEg
Kuyi liking sannan ku danna subscribe, domin fara samun litattaafaina na audio,
nagode sosai da ƙaunar ku gareni"
136_137
Widad tai kuka har hawayen suka gagara zuba se ƙunar rai da take, tana jin abunda
ke cikinta yana motsawa kaɗan kaɗan, ta tuna yadda Yusuf ya dinga binta da kallo,
kana ganinsa kasan a tsatsanr wahala yake, fuskarsa duk tabo da raunuka na ciwo.
idanunta sukayi jawur, kamar wadda aka zubawa barkono saboda kuka, ta sunkuyar da
kanta ta shafi cikin ta, da take jin motsinsa kaɗan kaɗan a can ƙasar mararta,
cikin zubda hawaye tace "wace amsa zan bawa abunda yake cikina, idan har ya girma
ya samu labarin mahaifiyarsa taje kotu ta bada sheda akan mahaifinsa an kai shi
prison? Shedarma ta ƙarya, nasan duniya zata zageni ga duka wanda yasan ainihin
abunda ya faru, sedai ba yadda na iya, nayi hakanne da ceton rayuwarsa, kaicona
haɗuwa ta da Yusuf ta zame masa babbar ƙaddara a rayuwarsa, ya sadaukar da
rayuwarsa don inganta tawa, amma maƙiyana suna ƙoƙarin cin galaba akanmu, abun da
basu sani ba shine, tun ran gini tun ran zane, ita gaskiya duk daren daɗewa zata yi
halinta"
Yusuf kam ya sha mamaki da Widad taje ta bada sheda a kotu, akan cewar saceta yayi
sedai yanayin daya gantabya tabattar masa akwai lauje cikin naɗi, akwai abunda yake
damunta, da gani duk inda take ba'a kwanciyar hankali take ba, amma duk da haka ya
zaci zuwanta kotu ze zama sassauci a gareshi, sedai zuwanta kotu ya zama ƙarin
tsanani a gareshi, yanzu kam ya haƙura yasan idan ba ikon Allah ba, bashi da wata
hanyar kuɓuta sam.
Alhaji Haruna kwana biyu ya samu sauƙi, Amal ta dena bibiyar sa, sedai ba ƙaramar
kassarawa tayi masa ba, kwashe masa kuɗin Account da tayi, gashi ba damar kai
rahoto yaje ya ɗaure kansa da kansa, gashi gaba ɗaya yanzu wanda zs nemi shawarar
tasu hankinsu na kan wannan shari'a da'ake fafatawa.
Bulama gaba ɗaya yakasa nutsuwa, dukda wannan shirin da wannan shirin da yake yi,
slide mistake Asirinsa ze iya tonuwa, kuma yasan koda tsiya, koda Arziki Yusuf baze
bada abun nan ba, yayi signing ma a tabattar wannan signing ɗin nasane, me shige
dana Daula amma yaƙi, babu irin dukan da baa'yi masa a gidan yarin nan ba amma
fafur Yusuf yaƙi sakawa, wane ma tabbaci yake dashi akan cewar Recording ɗin yana
gurin Yusuf, dan rainin hankali ba wani abun wahala bane a gurin Widad, zata iya
raina masa hankali tace yana gurin Yusuf amma baya gurin nasa, nan ya dinga takura
Ƙwaƙwalwarsa, akan lallai seya gano mafita.
Umma kuwa tun daga ranar da Widad ta bada wannan shedar taji ta tsane ta, bata
sonta duk wannan halin wahalar sanadiyyarta ya shiga amma taje ta bada shedar zirr,
gashi a maganar da Yusuf yai mata ranar da sukaje ganinsa a prison ya gayamata wai
Widad ɗin matarsa ce, ko ta yaya oho? Umma gaba ɗaya tunaninta ya tsaya, bata da
yadda zata yi wanda zata temaki Yusuf dashi.
Ta kira Suleman tace "dan Allah idan baya komai yaje tana son ganinsa"
Bayan awa ɗaya da rabi, sega Suleiman yazo suka gaisa sannan tace "Suleiman,
nagode sosai Allah yasaka da alkhairi da ƙoƙarin da kake ta min, amma ina neman
wata alfarma ne a gurinka"
Tace "dama cewa nayi, ko zaka samo me siyan gidan nan, ai masa kuɗi a siyar, a
saida Babur ɗin Yusuf, da gurin furnitures ɗinsa, a ɗauki lawyer me zaman kansa
yaje kotu ya tsayawa Yusuf , ko Allah zesa a dace"
Suleiman yace "Umma da hakan ze yuwu, da tuni nayi wallahi base an siyar da gidan
nan ba, har Office akamin aike daga sama, akace muddin nace zan saka kaina a cikin
case ɗin nan, to tabbas zan rasa aikina, kuma nima za'ace dani aka haɗa baki,
sannan a hanya aka kuma tsareni, akace idan nai involving kaina a case ɗin nan, to
za'a kasheni da iyalina, kuma irin wannan barazana akewa duk wanda yai yunƙurin
taimakon Yusuf, shiyasa kikaga an kasa komai a kai, bakiga inaji ina gani akace wai
ba hukumar 'yan sanda ce ta bashi aiki ba, bayan kuma nasan ƙaryane ba, da hannuna
na bawa Yusuf aikin nan, amma ina yunƙurin yin wani abu, komai ze kwaɓe "
Umma tai ajiyar zuciya tace" babu wanda ya bani mamaki irin Abbas, har gida yake
zuwa ya ɗaukeshi su tafi gidansu yarinyar nan, amma saboda rashin imani, yace wai
be san zancen ba"
Suleiman yace "kiyi haƙuri, ki dena kuka haka, dama ai si mutane kullum ƙara koya
maka hankali suke, amma ina tabattar miki Yusuf baze zauna a gidan yari ba, gaskiya
zata yi halin ta"
Nurat kam kamar ta ɗora hannu aka tai ihu, ta rasa abunda yake mata daɗi, wai ace
Widad ya bada wannan shedar aka Yusuf, dukda irin yaddar da tayi dashi, tabbas da
Yusuf yana neman wani abu a gurin Widad dabe dinga bata kariya ba, yanzu shikenan
saboda shedar Widad, ta tabatta Yusuf yayi abunda ake zarginsa dashi, kamar wadda
mintsina, ta tashi da sauri don taje ta sato wayar Mummy tai waya, sedai tana
fitowa falo ta tarar daddynta yana kallon labarai, 'yan jarida na bayyana abunda ya
faru a kotu, Alhaji Musa yace "Maman Nurat, kinga shari'ar yaron nan ko? Dama na
faɗa miki, irinsa ba abun tausayi bane, gashi nan ita kanta yarinyar ta tabattar da
abunda ake zarginsa dashi, bari in kira Bulama"
Ya ɗakko wayarsa ya kira Bulama, "Allah ya baka yawan rai, ai yau naga yadda
shari'ar nan ta kasance, komai ya tafi daidai, kayi ƙoƙari gaskiya, haka ake son
Amini, gashi baya nan amma ka tsaya tsayin daka akan sha'anin iyalinsa, gaskiya
kayi namijin ƙoƙari, Allah dai yasaka da alkhairi"
Nurat bata iya jin abunda ake cewa daga ɗaya ɓangaren, amma tana ganin yadda
Daddynta ke ƙyaƙyata dariyar mugunta a waya.
A hankali ta juya ta koma ɗakinta, tana hawaye tace "Allah sarki Yusuf, ya za'ayi
in fita in gayawa duniya cewar ba kai kayi garkuwa da Widad ba, da saka hannun
mahaifina a sace su Yusuf? Ta yaya? Tabbas idan aka rufe Yusuf ba'a masa adalci ba,
definitely tasan akwai yadda akayi har suka kuɓuta aka kamasu a ƙauye, amma Yusuf
baze garkuwa da Widad ba, ta zauna tai shiru tana tunani, bata san ta ina zata fara
temakawa Yusuf ba, amma tabbas ƙarshen zalunci an masa.
Ramlah ce tsaye akan Fahad tana zazzaga masa masifa, "Wallahi Amal baka isa ba,
tun wuri ka maida hankalinka, nafi ƙarfin ka wulaƙantani, wato ka gama dani ka kama
wasu, to baka isa ba tun wuri kaje ka turo azo ayi maganar Auren nan"
Fahad yai wata irin dariya sannan yace "Ramlah kenan, waye yake yaudarar wani
tsakanin nida ke, dama a rashin wannan yarinyar ne, tuntuni tun ina ƙasar waje kin
san ita zan aura, kuma gata ta dawo, dan haka me kike so inyi miki kuma? Kawai ki
rungumi sorry, in kin samu wani wanda zaku daidaita se ku haɗe, dukda dai bance ke
mummuna bacd but gaskiya ga balarabiya ina kallo bazan aureki ba, sorry kawai "
" Ni kake kallo kake gayawa haka? Lallai baka san Ramlah ba, kai ƙaramin ɗan isaka
ne, wallahi baka isa ba, zaka ga abunda zan maka "
Fahad ya busa hayaƙin shisha sama sannan yai murmushi yace " Hmm keme baki san waye
Fahad ba, karki bari ki gane waye Fahad tabbas "
"Na gayamiki ɗin, dama haka bariki ta gada, kuma ki shiga hankalinki tunda wuri,
tun ban saɓa miki ba"
Ramlah ta kalleshi tai ƙwafa, tai waje a matuƙar fusace, tana fitowa tai karo da
Hajiya Sarah ta fito zata fita, mamaki yakamata ganin Ramlah daga part ɗin Fahad,
ta tsaya Ramlah ta ƙaraso, tana ƙoƙarin buɗe motarta, Hajiya Sarah tace "Ramlah,
lafiya kuwa? Me kika je yi ɗakin Fahad? Ina fatan lafiya?"
Ramlah ta kalleta tace "ba lafiya ba, kuma wallahi ki gayawa ɗanki ya saurari
abunda ze biyo baya"
Hajiya Sarah tace "lafiya kuwa? Meya haɗaki da Fahad ɗinne? Me yayi miki ne?"
"Ki tambaye shi, shi yasan me yayi, kuma ya jira sakamakon abunda yayi min"
Ta bankaɗa ƙofar motarta ta shige ta jata a guje, mamakine ya cika Hajiya Sarah, ta
shiga part ɗin Fahad, tana zuwa ta tarar yana shan shisha ta kalle shi tace
"Fahad, wato har yanzu baka dena shaye shayen banzan nan bako, kana kawo mana matan
banza har cikin gidan nan, kasa ubanka yazo ya kamani da faɗa da masifa, wallahi
kaji tsoron Allah, ita kuma Ramlah meye ya haɗaka da ita?"
"Mum dan Allah ki bar wannan maganar, kawai wasu suratanta ne na banza, marasa
tushe balle makama, tazo ta nawa mutane Hayaniya a ka"
"wane irin Hayaniya ce? Gayamin kasan halin uwatta sarai, daga ita har yaranta ba
mutunci suka cika ba, har gara Anwar ma, amma wannan me soyayyen idon, idan ka sake
wani abu mara daɗi ya haɗaku dasu, wallahi duk abunda suka maka kai ka janyowa
kanka, kaje ka ƙarata kai da uwarsu, idan yaso ubanka yasan yadda zeyi dasu, tunda
'yan uwansa ne, na gaya maka, tunda wannan rayuwar ka zaɓawa kanka Fahad, gaka nam
ga duniyar kaje kayi Allah ya temaka "
Ba ce mata komai ba, ta fito ta baro ɗakin nasa, zuciyarta sam babu daɗi, ace
yaronta na farine ke irin wannan mummunar rayuwa haka, ranat baya mata daɗi Sam.
Amal ta rasa yadda zata yi da uban kuɗin data damfari Alhaji Haruna, gashi sam
Mummy bata san abunda ya faru da ita ba, balle tasan da wannan uban kuɗin data
damfari Alhaji Haruna, sedai Amal ta kasa gane abunda yake damunta, gaba ɗaya yanzu
kullum cikin ciwo take, nan ciwo can ciwo, abun ya fara damunta, ta yanke shawarar
zata je ganin likita zata je taji meye yake damunta haka.
Ramlah kuwa data bar gidan Bulama kamfaninsa ta tafi, yana tsaka da aiki yana
shirin shiga meeting se gata, babu sallama babu komai ta tsaya ta tstsareshi da
ido.
"Ke lafiya kuwa? Ni na rasa waye yafi hanki tsakanin ke da babarki, ya zaki zo ki
tsaya a kaina haka kina ƙaremin kallo babu ko sallama"
"kaga suararamin kawai, tsason shekaru kana juya mahaifiyarmu, muna abunda kake
so, wancan satin har kotu kasa naje na bada sheda akan wannan sharia'r, to nazo da
buƙatata guda ɗaya tam, da nake so kamin"
"wace irin buƙatace haka? Bayan seda aka baki wani percentage kema, kuma idan
kuɗin nan suka samu hadda ke za'a ci"
"Niba kuɗi zaka bani ba, shekaruna sun na ina zaune a gida na gama karatu bana
aimin fari, balle na baƙi, kuma ɗanka Fahad ya taɓa min Alƙawarin Aure, dan haka
tunda wuri azo ayi maganar da za'ayi a wuce gurin"
"Nifa ban gane maganar da kike ba"
"Kamar yaya baka gane me nake nufi ba? Wane yaren nakeyi maka? Ɗanka Fahad ya
Aureni"
"Haba Ramlah, wacs irin kwaɗon magana ce wannan haka mara daɗin ji? Baki san Widad
ze aura ba?"
"ban saniba, kuma matsalar kuce ba ta Ramlah ba, kawai ayi maganar da za'ayi"
Bulama yace "ni kike wa magana a haka? Ƙwarai kuwa waye kai a gudina da bazan maka
magana a haka ba, ina ƙarewa 'yar gidan Daula shekaru ta kwashe tana maka
wulaƙancin data ga dama, balle kuma ni da kake wa kallon biri ina maka ta ayaba,
kawai kayi abunda ya dace, ko kuma komai ya faru "
Bulama yace " Ramlah, ban san meyasa kike haka ba? Kema kin san aurenki da Fahad ba
abune me yuwuwa ba ko? "
" Aurena da Fahad, ba abune me yuwuwa ba, ka gayamin shima ya gayamin, nagode nima
ku jira matakin da zan iya ɗauka "
Ta bar office ɗin Bulama, zuciyarta na ƙuna da raɗaɗin abunda sukayi mata, Amal na
zaune a falo tana kallo, cikinta ss ciwo yake mata, ga wani irin ciwon baya da take
fama dashi, gashi lokaci lokaci inda ta karye yana motsa mata.
Ramlah tana parking ta fito, ta buga ƙofar motar da ƙarfin gaske, tai ciki fuuuuu,
kamar guguwa, Nura yace "Allah dai ya kwashe ma wannan baiwa Albarka, da ita da
duk wanda suka je kotu suka bada shedar ƙarya akan Yusuf"
Murtalah yace "bari Nura, wallahi abun ya bani mamaki sosai, Amma nan aka zo aka
taramu aka mana kashedi akan duk wanda yai wani yunƙuri, ze fallasa wani abu se an
kasheshi, wayaga ta bakin magana, amma da tabbas nima sena bada sheda"
Isa yace "dan Allah Murtalah kaje ka bada shedar nan a saki Yusuf, wallahi
zaluntarsa kawai ake yi"
Nura yace "Allah sarki duniya, kalli Isa wai kaine ke cewa ayi abunda za'a temaki
Yusuf, abun da mamaki"
Isa yace "bari Nura, wallahi duk baƙin cikin mutum da iya ƙiyayyarsa, idan dai har
mutum ya zauna da wannan bawan Allah, wallahi idan kaji za'a masa haka dole ka
tausaya masa, kalli duk irin abunda muka dinga masa baya tanka mana, se azabar
miskilancin tsiya a cikinsa kamar Uwarɗakinsa"
Sukace A'a
"Wai ashe Sani me yankan farce shima ɗan sanda ne, shine fa ya haɗani da Yusuf yace
ɗan uwansa ne, dana gayamasa ana neman direba, amma naji wannan lawyern yace wai
Abbas be san zancen ba, Amma duniya babu gaskiya, tabbas yanzu nake ganin gimbiyar
Daula bata da laifi na ƙin mutane, ka yadda da mutum ya cuce ka a banza, yanzu duk
wanda suke jikin Daula suna morarsa sune suke zalintarsa, kalli matar gidan nan ko
sau ɗaya ba taje kotun nan ba"
Murtalah yace "iko se Allah, wallahi Isa da zamu samu dama ko iya wannan shedun
muka riƙa, aka shiga kotu dasu zasu temakawa Yusuf, amma wallahi ina jin tsoro,
kuma wallahi dani akan matar gidan nan zan bada shedata"
Nura yace "kai ita ta dameka, a samu a Yusuf ya kuɓuta, wallahi dukda nima inajin
haushinsa yadda ƙirƙiri ya samu fada fiye damu a gidan nan, musamman ni daya nemi
ya ƙwacemin aiki na, Amma gaskiya Yusuf baze aikata haka ba, kalli fa ko magana
ake, idan aka sakota ko aka zageta seya haɗe rai yana ɓata fuska yana kare ta,
wallahi da yayi niyyar sace ta da tuni ya saceta, akwai dai yadda akayi "
Ramlah kuwa tana shiga falo, Amal ta kira sunanta, Ramlah ta waigo a fusace tace "
lafiya kuwa? "
" Ashe kema kim bada sheda a kotu akan Yusuf "?
" Yakamata kiyiwa kanki adalci Ramlah, a bar bawan Allah nan da wahalar da aka jefa
shi a ciki, bakya ganin saboda Alhakinsa ne muma namu ɗan uwan yana nan kwana da
kwanaki ba'a ganshi ba, ga mahaifiyarmu se fama take da marurar hawan jini saboda
damuwane da ɓacin rai? "
'Ke dalla sauraramin, an bada shedad kiyi abunda zakiyi, da aga Anwar da kar a
ganshi be dameni ba, abunda yake gabana shi zanyi, kuma karki ƙara yimin wannan
maganar"
Tana zuwa ta jefar da Jakarta akan gado, ta buɗe wardrobe ɗinta ta ɗakko kwalaben
syrup, kawai ta kafa kai ta kama tittilawa cikin ta, Hakan yai dai dai da buɗe
ƙofar ɗakin da Hajiya Halima tayi, ta tarar Ramlah ya shanye kwalaben syrup ta faɗi
a gurin, cikin fitar hayyaci.
"Na shiga uku, Ramlah me zan gani haka? Ramlah dama dagaske shaye2 kike? Me yasa
zaki cuci kanki"
Sam Ramlah bata san me ake ba, tuni ta fara maye ta lula gajimare.
"Amal kinga, shaye2 Ramlah take yi, meke damunta haka zata faɗa wannan mummunar
hanyar haka?"
Amal ta ɗan taɓe baki, tare da naɗe hannunta tace "Allah ya jiƙan Yaya Anwar, ba
dan ya mutu ba, nan ya hukunta ta ya gayamiki ga abunda take yi, amma baki yadda
ba, tuntuni take shaye shayenta, kuma wannan Fahad ɗinne ya koyamata, amma ba yau
ta fara ba"
Hajiya Halima tace "Na shiga uku ni Halima, wannan wace irin masifa ce haka,
Ramlah dama baki dena wannan halin ba, Kisha kwalba huɗu a cikin ki?"
Kamar koda yaushe, yauma zaune suke suna tattaunawa, Bukar yai gyaran murya yace
'ga samu ga rashi, labaran kala biyune, masu daɗi da kuma akasin hakan, wannan
yaron munyi magana da A dutse, ya tabbatar min a zama na gaba ze ƙarƙare shari'ar
yaron nan, sedai wani hanzari ba gudu ba, ita wannan yarinyar da yake ita uwar
Daula ce a jarabar taurin kai, taƙi bayar da abun nan, ba irin azabtarwar da banyi
mata ba, amma taƙi ƙarshe ma se cewa tayi ai "Recording ɗin inda dukiyar take Daula
yayi, ya bata itama bata san inda dukiyar take ba, kuma wai recoding ɗin yana
hannun Wannan yaron Yusuf"
Alhaji Musa yace "kawai aje kurkuku ta ƙarfin tsiya ace ya bayar"
Bukar yace "Mhmm, baku san azabar taurin kan mutanen nan ba, ya saka hannu kawai
mugani a tabattar idan wannan signing ɗin nasa ne, me kama dana Daula, amma wallahi
fafur yaƙi, shima an azabtar dashi kamar kamar me a gidan yarin nan amma yaƙi, na
rasa abunyi"
Alhaji Haruna yace "a sake azabtar dashi mana, ya faɗi inda recording ɗin yake, ko
kuma aje a ɗauke mahaifiyarsa, ai naga tana zuwa kotun"
Bukar yace "ai abun ya wuce tunaninku, idan mukayi wani yunƙuri zamu iya barin
ɓarakar da za'a ganomu, komai a sannu ake samun sa, zan cigaba da bibiyar yadda
za'ayi a samu"
Suka gama tattaaunawa suka watse, dama a office ɗin Bukar sukayi meeting ɗin.
Bayan fitowarsu Alhaji Haruna yacewa Alhaji Musa "Waini anya ba raina mana hankali
Bujar keyi ba, yarinyar nan tana hannunsa fa, babu wanda yasan inda take, ta yaya
za'ace ko yaya bata gaya masa wanj abun ba, nifa kamar mutumin nan raina mana
hankali yake"
Alhaji Musa yace "kai dai bari kawai, kallonsa kawai nake yi, gaba ɗaya kuɗaɗenmu
sun tafi akan wannan harkar, amma Har yanzu babu wata riba"
"ba gara kaiba akaina, ni kamanta wannan yarinyar ta damfareni, rabin kuɗin account
ɗina ta kwashe fa"
"kasa a sato maka ita, kaci ubanta ta mayar maka da kuɗinka, ni yanzu kallon Bukar
kawai nake idan be wasa ba, zan ɓallo ruwa...
LITTAFIN KUƊI NE, IDAN KIN SIYA AMANANE, IDAN KIKA FITARMIN KINCI AMANA, KIMIN
ADALCI KIYIWA KANKI
AYSHERCOOL
07063065680
11/29/21, 8:55 AM - Buhainat: LITTAFIN KUƊI NE, DAN ALLAH KI SIYA KAFIN KI KARANTA
BA DANNI BA DAN ALLAH, LITTAFI NA ƊAYA KYAUTA NE WANNAN NA SIYARWA NE
NORMAL GROUP ₦300
VIP ₦500 NE KITURA TA WANNAN ACCOUNT ƊIN
0009450228
JA'IZ BANK
AISHA ADAM
SE A TURA SHEDAR BIYA TA WANNAN LAMBAR
07063065680
(Albishir ga masoya, ma'abota bibiyar litattaafaina, dama ta samu zaku fara samun
litattaafaina na audio, akan YouTube channel ɗina me suna Cool Arewa TV
https://youtube.com/channel/UCD5vnvA5laU8ti4LLz2_QEg
Kuyi liking sannan ku danna subscribe, domin fara samun litattaafaina na audio,
nagode sosai da ƙaunar ku gareni"
138_139
"Eh zan ɓallo ruwa mana, muddin naga za'a cuceni, zan tads husuma ne, daga fara
harƙallar nan zuwa yanzu zunzurutun kuɗi nawa muka kashe? Haka abun yayi yawa,
mutumin nan ba imani ne dashi ba, ze iyayin komai dan haka gara mu saka ido yadda
yakamata"
Ramlah har gari ya waye, tana tangaɗi bata san me takeyi ba zabo maye, kwalba huɗu
ta shanye babu sirki da komai, tayiwa kanta caji na sosai, yayin da Hajiya Halima
ta dinga kuka, ganin yadda shaye2 ya ratsa Ramlah haka, ga ɓatan Anwar yana cin
zuciyarta, gashi duk 'yan kuɗaɗen data tara Shu' aibu ya karɓesu, ta rasa inda zata
saka kanta.
Amal kam bata tasu takeyi ba, gaba ɗaya bata jin daɗin jikinta, ta rasa takamaimai
meke damunta, tana zaune tana danna wayarta taga wani business, wanda idan kayi
investing kuɗinka, zasu nunnuku a lokaci kaɗan, nan da nan ta gyara zama tana sake
duba yadda bayanin abun yake, ta shiga link ɗin group ɗin da aka bayar, taga yadda
mutane keta comments wai sun sak kuɗinsu an riɓanya musu an basu.
Nan wani tunani yazo mata, dan wannan maƙudan kuɗin da suke account ɗinta bata san
ya zata yi dasu ba, dan haka ta jarraba saka naira dubu hamsin, bayan awannin biyar
aka turo mata dubu ɗari da biyu, abun ya bata mamaki, nan ta dinga murna akan ta
samu sana'a daga kwance zata dinga samun kuɗi.
Widad se kaffakaffa take da Cikinta, kar Bulama ya gane cikin nan yana nan be fita
ba, dan ya fara ɗagawa sosai tana jin motsinsa, wasu lokutan yaji yana motsi sosai,
wani lokacin kuma yayi dankam motsinma se kaɗan kaɗan, mussman idan bata da lafiya,
duk lokacin da taji ya daɗe be motsa ba se tai taɓa cikin tana addu'a Allah yasa ba
wani abunne ya sami abunda take ɗauke dashi ɗin ba.
Cuta kuwa kullum a cikinta take, gashi babu me gayamata yi kaza bar kaza, ita dai
Sabuwa ta kan tirsasata ne taci Abinci, amma babu magani ga kwanciyar ƙasa da take,
da shan abu me sanyi duk se tabi ta kukkumbura, babu hanyar zuwa Asibiti, ga Fahad
dayake yawan kawo mata farmaki wasu lokutan, dan haka baccinma ba iya shi take
cikin kwanciyar hankali ba, sedai tana yi tama farkawa, gani take da nannauyan
bacci ya ɗauketa Fahad ze shigo yai mata wani abun.
Haka rayuwar Widad ke tafiya a wannan gurin da take, gashi dai yafi ɗakinta na
ƙauye nesa ba kusa ba, amma ɗakinta na ƙauye ya fiye mata daɗi da kwanciyar hankali
akan wannan ɗakin da take ciki haka a cike da wannan damuwar da tashin hanaklin.
Se wajen laa'sar sannan Ramlah ta dawo hayyacinta, daga wannan muguwar buguwar da
tayi, taje tayi wanka ta canza kaya, ta nemi abunda zata saka a cikinta, ba tare da
ta kula kowa ba, Hajiya Halima ce ta bita ɗakinta, ta sameta tana ƙoƙarin fara cin
Abinci.
Ta ƙare mata kallo sannan tace "Ramlah, wannan rayuwar ita kika zaɓawa kanki ko?
Rayuwar shaye2, Ramlah kwalba huuɗ fa kika shanye a cikinmi, ke ko tsoron lafiyarki
bakya yi, bakya tausayin halin da nake ciki ko? Ban san inda ɗan uwanku yake ba, ga
wannan uban naku yana ta min barazana akan ze tonamin Asiri, amma a haka kike ƙara
gayyato mana wata matsalar, meyasa haka Ramlah? "
" Dan Allah Mummy ki ƙyaleni injibds abunda ya dameni, ni Fahad ze kalla yace baze
Aureni ba, bayan tuntuni yasan zaman jiran sa nakeyi, amma zemin haka"
"to yanzu dan yace naze aureki ba shine zaki kashe kanki? Shine zaki sha wannan
maganin haka? Haba Ramlah shikaɗai me namiji ko shine autan maza, kina gani kuɗaɗen
hannuna duka babu sun ƙare, shine yake kawo mana wanda suke siyan kadarorin nan fa
a ɓoye, ki lallaɓashi ku rabu lafiya mu samu mu sake wawurarar abunda ya samu mu
siyar, idan muka siyar seki ƙyaleshi, Allah ya baki wani ki aura"
"Mummy, ni gaba ɗaya ma nakasa gane kan maganganun nan da kikeyi fa, kamar yaya
babu kuɗi a hannunki, ina duk kuɗaɗen da kika saida filayen nan? Duk suna ina, kuma
ga wannan kuɗaɗen da ake saka rai na gurin Bulama daze samo a hannunta suma basu
samu ba, abun yazo da rainin hankali fa"
"wai bana gayamiki ubanku ke tamin barazana ba, kin sam maƙudan kuɗaɗen daya karɓa
kuwa hannu na?"
Ramlah tace "wai wannan jakin da yazo harya mareni kike nufi?"
"Ramlah idan shu'aibu ya tinamin Asiri na kaɗe, dan na gama yawo, mutumin nan
hatsabibin gaske ne, baku da wayo lokacin da muka rabu ai"
"Lallai Mummy, wallahi dana san hakane baza'a bashi ko kobo ba, sedai yaje ya tina
karya fasa, yanzu shikenan mun tashi a tutar babu? Duk wannan baƙar wahalar da
mukayi? Yana gefe kika dinga tura masa kuɗi, baze yuwu ba Wallahi"
"bazs yuwu ba kamar yaya? Ai tuni ya yuwu, bashi kuɗin nam sune rufin asirinmu,
kuma karki kuskura kice zakiyi wani abu, kinji ma gayamiki sannan Ramlaj ki shiga
hankalin ki, akan wannan mummunar ɗabi'ar, babu inda zata kaiki shaye2 ba abunyi
bame, kuma ba cinyewa bane "
'mhmm Mummy kenan, yadda raina yake a ɓace idan har ba caji nayiwa kaina ba bana
jin daɗi, kawai ki ƙyaleni idan kuma kina buƙatar in dema shaye2 to tabbas Fahad ya
aureni, idan bahaka ba bakiga komai ba har yanzu"
"Ai gaskiya na gayamiki ba wani abu bz, idan harya Aureni shikenan an wuce gurin
saɓanin haka kuma, komai ma zaki iya gani"
Ta ƙarasa magana, tare da fara cin Abimcinta, bata sake bi ta kan mahaifiyarta dake
kallomta da mamaki ba.
Jiki a saɓule Hajiya Halima ta tashi ta fita ta bar ɗakin Ramlah, ranta sam babu
daɗi, wai yanzu Ramlah ce a wannan mummunar hanyar.
Alhaji Musa sosai yake jin zuciyarsa tana ɗarsa masa wani abiua ransa, yana zargin
Bulama kawai ƙoƙarin kifesu yake yi, yana can yana zare zaren, dan haka dole zeyi
wani abu a akai, ta ƙarƙashin ƙasa ze bincika ya hani ko Bulama na karɓar wani abu
basi sani ba.
Yauma akazo akace ana son ganin Yusuf, ya zata ma ko Ummace ko Suleiman wani ya
kawo masa ziyara, sedai still wannan ɗan sandan ya gani, se wasu gandirobobi, aka
saka Yusuf a wani tsukakkaken ɗaki, da gashi sesu a ciki, aka zaunar da Yusuf ɗan
sandan ya kalleshi yace "Hmm Nasan kayi mamaki, ganin yarinyar daka ceta ta juya
maka baya taje kotu ta bada sheda akanka ko? Dama haka mata suke basu da tabbas,
gashi tana can tana hutawa, ranar da za'a yanke maka hukunci, a satin za'a ɗaura
mata Aure da Fahad Bukar Bulama.
"Au kana mamakine? Ƙwarai Ɗan gidan Bukar Bulama, wato Fahad, yanzu haka ta aiko
mune gurinka, akam cewar akwai ajiyar wani recording data baka, ka gaya mana inda
recorder ɗin take, zamu je mu ɗauka '
Hankalin Yusuf sam baya kan Ɗan sandan, sedai nanata Bukar Bulama day keyi a
zuciyarsa, wato abu biyune ya haɗar masa, ga mamakin Jin an Ambaci Bulama da Bukar,
to kenam shine Bukar ɗin da Widad take magana kokuwa? Idan shine ya akayi gake
zaune a hannun sa? Idan ya cutar da ita fa? Sannan wani irin azababben kishi ya
taso masa, dagaske Widad ɗinsa ce zata Auri Fahad?
'to idan bata aure shi ba me kake so tayi? Kaida rayuwarka zata ƙare a kurkuku,
kuma taje har kotu ta bada sheda akan ka' wata zuciyar ta tunasar dashi, amma dukda
wannan abun ya kasa jin tsanar Widad a ransa, shi wani irin tausayinta ne yake kama
shi ma, kuma gefe guda zuciyarsa ma cigaba da begen sake kasancewa da ita.
"Kai Malam magana nake maka fa!"
Ɗan sandam yai maganar cikin tsawa, Yusuf be razana ba ya kalleshi yace "ita Widad
ɗince tace maka ta bani wani abu ajiya?"
"zan maka ƙaryane?"
Yusuf yace "to meze hana kayi ƙarya, tunda mutum ne kai ba mala'ika ba, kamar yadda
tace muku ta bani ajiya, tazo da kanta ta Karɓa, ta gayamin lokacin data bani,
sannan ta karɓa"
Ɗan sandan yai ƙasa da murya yace "ka bani tunda wuri, ko kuma a ran mahaifiyarka"
Yusuf yace "Ran mahaifiyata yana hannun Allah, babu wanda ze iyayi mata abunda
Allah be rubuta ze sameta ba, Magana ɗayace, ni bata bani komai ba, idan kuma ta
bani ku kawota ta gayamin lokacin data bani ajiyar recording ɗin"
Ɗan sandan nan ya jinjinawa azababben baƙin taurin kai irin na Yusuf, ya kalli
gandirobobi yace "ku tambayeshi"
Yusuf be motsa daga inda yake ba, suka dinga buga masa kulki kota ina, sedai yana
ƙoƙarin karewa, babu wata gaɓa ta jikinsa da bata masa ciwo saboda azabar dukan da
yake sha a kowane lokaci.
Suka farfasa masa jikinsa, banda targaɗe dake yatsunsa saboda duka.
Yusuf yace "ni bata bani komai ba na gaya maka, karka ƙara tambaya ta"
Ya ɗaga hannu ze wanke Yusuf da mari, Amma jarumin ya riƙe hannunsa yace "karka
kuskura ka mareni, kuyita dukana har lokacin da zaku ga na dena numfashi, tunda
haka kuke so, amma karka kuskura ka sake ɗaga hannu kace zaka mareni"
Suka kum sashi gaba da duka, seda suka ga baya motsi, sannan hankalinsu ya kwanta,
suka tafi suka barshi a gurin.
Widad na zaune kawai taji gabanta ya faɗi, hakan yasa kawai ta fashe da kuka, domin
ta fuskanci kamar idan Yusuf yana cikin mawuyacin hali se taji wannan faɗuwar
gaban, ai kuwa ta hau aikin kuka, tayi ta gaji ta haƙura, ta cigaba da yi masa
addu'a, tans tuno irin haƙurin daya dingayi da ita, ga rarrashinta da yake yawan
yi, da yadda ta koyi abubuwa da dama a sanadin zama dashi Yusuf mutum ne, wani irin
shauƙin soyayarsa ne ke taso mata, ta rintse ido ko zata samu sassauci a zuciyarta,
tana jin inama tana buɗe idonta ta ganata a kusa da Yusuf, lallai so ba ƙarya ne
ba.
"Allah ya fitomin da kai Yoseef, ka dawo muyi rayuwa tare, mu rainin cikin nan tare
da kai, nasan da muna tare zan samu kulawarka" tai maganar tana hawaye.
Can kuma tayi wani tunani a ranta, wani irin kallo Yusuf zeyi mata idan Allah yasa
ya fito, bayan taje ta tsaya a gaban mutane ta tabattar da Yusuf saceta yayi.
Cikin kuka tace "wayyo Allah na, Yoseef kayi haƙuri ba laifina bane, nayi hakan ne
dan in ceci rayuwarka, karsu kashemin kai, ban manta halaccinka a gareni ba Yoseef,
ba yadda zanyi ne"
Sabuwace ta shigo da sauri tana faɗin "lafiya kike kuwa? Kinga ki dinga ramgwatawa
kanki wannan kukan da kike yi haka, naji ance kina da ciwon zuciya gashi ba ganin
likita ake kaiki ba, karki kashe kanki a banza mana"
"Ni ki ƙyaleni inyi kukana, baki san abunda yake damuna ba, ki rabu dani dan Allah
ki ƙyaleni"
Sabuwa tace "A'a Allah ya baki haƙuri, na ƙyeki yi abunki som ranki"
Bulama yace "yi addu'arki da kyau, ai ina kusa ba nisa nayi ba, duk abunda zaki
faɗa ki faɗa"
"me Yoseef yayi maka? Meye laifin da yayi maka da kake azabtar dashi haka, kake
neman cutar da rayuwar sa Kasashi a garari?"
Bulama yace "saboda ya raɓeku, ni kuma duk wanda ze raɓeku, in dai ba dani ze haɗa
kai ba in mallaki abunda nakeso to tabbas bashi da wani amfani, shiyasa nake kawar
da du wani makusanta a gareku, ko wanda ke shirin sama muku farinciki, kum ɗaukake
shi da matsayi me girma, dukda baki yadda da mutane amma naga ya zama wani abun
yadda a gareki, nasa an jarabbashi koze aminta damu, ya karɓo abun hannunki ya
bamu, sena fuskanci shima irinki ne, me taurin kan tsiya, kuma ya dasa hasashensa
da bincikensa a kaina, Allah yasa na farga da suri, da yanzu ya kassarani, dan haka
dole in koya masa darasi "
Widad ta ƙure shi da ido tace" Shikenan, ayi dai mu gani, na yadda da rayuwata da
Yoseef da Babana jarrabawa ce Allah yake mana, kuma ina fatan muyi nasara, Allah ya
nunamin ranar da zata zo ka wulaƙanta, ka tozarta a idon duniya "
Bukar yace " daha baya kenan, bayan ns mallaki wannan dukiyar, sannan Wannan uban
masu koɗaɗɗen idon, yaƙi bada recording ɗin, yace shi baki bashi komai ba, dan haka
a wannan karonma dole ki san yadda zaki yi, kodai ya bayar kodai yaita shan wahala
harya mutu a kurkuku, kamar Yadda nasa a ka kashe Bala a gidan yari "
Widad tai murmushi tace " Yoseef be san na bashi ajiyar nan ba, dan haka Kadena
yaudarar kanka da tunanin ko zaka samu abun nan cikin sauƙi "
Bukama ya ƙure ta ido, ta ɗauke kanta daga kallon inda yake, yama rasa me ze mata
saboda tsabar wasa da hankali da raina masa hankali da take yi.
" zaki fanshe ta ne idan kika bada abunda ake nema, dan haka ki zaɓa ko ki bani
abunda na nema, ko kuma a bakin ranta"
"Abunda ka nema yana hannun Yoseef, kuma shima besan meye na bashi ba, sedai ka
kaini gurinsa in karɓa maka, amma karka cutar da ita dan Allah"
"Se kuma kiyi, ba dai taken ki rainin hankali da iya wasa ba, to zaki gane kurenki"
Widad ta bishi da kallo harya fice, ta kwanta a nan inda take, ta lumshe idonta
tana tunani.
Mutane nata sauraren lokaci yayi, suji yadda za'a ƙarƙare shari'ar Yusuf, kullum
Gidajen radio da dandalin sada zumunta zancen kawai ake yi, kowa yana tofa
albarkacin bakinsa, wani ya tofa na alkhairi wani kuma ya tofa akasin haka.
Suleiman yaje kaiwa Umma ziyara shida matarsa Surayya, sedai kallo ɗaya zakayi mata
kasan bayan damuwa harda rashin lafiya take fama.
Surayyah ce ta fara cewa "Umma kodai jikinne ya motsa? Naga kinyi wani iri"
Umma tace "A'a Suleiman, ɗawainiyar nan tayi yawa, lafiyata ƙalau ai"
Suleiman yace "wace irin ɗawainiya kuma Umma, ai in dai da amana nine yakamata in
kula dake, Umma ban san haka abun nan ze kasance ba, Abbas ne yace a bawa Yusuf
aikin nam ze iya, na goyi bayan hakan na bashi aikin, dana san haka zata faru da
ban bashi ba, kuma ace wannan abu ya faru dashi, in kasa kulawa da mahaifiyarsa, ai
da banyi wa kaina adalci ba, ni dai ina baki haƙuri Umma"
Umma tace "haba Suleiman, ai duk wani mumina dole ya yadda da ƙaddara, ba kai ka
kama Yusuf ba, kuma ba kai kasa aka kamashi ba, ƙaddararsa ce a haka, duk imani da
girma irin na Annabawan Allah, seda ya jarrabesu to waye Yusuf da Allah baze
jarrabeshi ba, nasani Allah yana jarrabar bayinsa ne wanda yake so, dan haka inawa
Yarona Addu'a, Allah ya bashi mafita ta idan bamu zata ba, sedai babu wanda ya bani
mamaki kamar Abbas, ba ƙaramin mamaki ya bani ba, irin yadda yake nunawa Yusuf
soyayya, Yusuf bashi da abokin daya wuce shi, da kansa yazo ya ɗau Yusuf ya kai shi
gidansu yarinyar nan, amma yace be san zancen ba"
Suleiman yace "Umma kiyi haƙuri, ki dena tunawa kawai, mu barwa Allah mucigaba da
Addu'a"
Umma tace "Addu'a kam, na duƙufa ina nan inayi, kuma na saka anata saukar
Al'qur'ani, na miƙawa Allah ya isar mana"
Surayyah tace "insha Allah, addu'arki bazata faɗi ƙasa ba Umma, amma Umma akwai
Abinci a gidan nan?"
Umma tace "Aa', sedai in yanzu za'a girka miki, kina jin yunwa ne?"
Surayyah tace "hakan ya nuna bakya cin Abinci Umma, ƙarfe biyu yaci ace ai anyi
girkin rana"
Surayyah tace "ai ramar taki tayi yawa, dama munyi magana da Abban Nihal ne, muna
so ki koma gidanmu zuwa muga yadda hali zeyi"
Umma tace "A'a, hakanma nagode ku barni a nan, bazan ɗora muku wahala ba"
Surayyah tace "Umma ba wahala bace bafa, kinga kaɗaici yana damunki sosai, ga
rashin cin Abinci, ga larurar rashin lafiya kina tare da ita"
Umma ta dage ba zata bar gidan nan ba, Suka dinga mata magiya sukace bazat wuce
sati ɗaya ba, so suke jikinta ya warware.
Da ƙyar Umma ta yarda, Surayyah ta haɗa mata kayan ta, suka tafi da ita gidan
Suleiman.
Yusuf duk iya azabtarwar daya sha, basu samu abunda suke so ba, ƙarshe ma Yusuf ya
koma kurman ƙarfi da yaji, juyin duniya baya magana, itama Widad bata da maraba da
'yar prison ɗin itama, tayi wujuga wujuga itama, kamar korarriya ga Duka ga
azabtarwa da take sha a hannun Bulama, duk ta fita hayyacinta.
Nurat ma bata da kwanciyar hankali, se fama take da damuwa da tunani, sedai ta rufe
ɗakinta tasha kuka, gashi yanzu ta dena samun magana Da Khalil sam.
Haka gidan Hajiya Halima ya rincaɓe, Ramlah shaye2 ba kama hannun yaro, bata ganin
kimar Mahaifiyarsu sam, yayin da Amal kuma gaba ɗaya haushinsu takeji, dan haka tai
dumping ɗinsu gaba ɗaya a side, ta dena shiga sabgar su, ta kama wayarta take shiga
wata caca a online da kuɗin data damfari Alhaji Haruna, sabgar ta kawai take ta
dena shiga harkar mamanta da 'yar uwatta, idan taga Mummya zata dameta da koke koke
ma, ko zancen Ramlah, se tai waje ta bar musu gidan, ko kuma ta shige ɗaki ta rufe
taita danna wayarta, saboda tun kan Ramlah tai nisa da shaye2 Anwar yaso ɗaukar
mataki akan lamarin, amma ta nuna bata so taci masa mutunci, dan haka na meye zata
takura kanta akansu yanzu?.
Rana bata ƙarya sedai uwar ɗiya taji kunya, yau kotu tafi kullum cika, da mutane
daban daban, duk ana jiran jin yadda zata kaya a wannan shari'ar, yadda aka rirriƙo
Yusuf aka shigo da shi cikin sarƙa, yana jan ƙafa da ƙyar, saboda wahala.
Aka kammala wasu shari'ar da take kafinta su Yusuf, sannan akazo kan Tasu Yusuf.
Justice Abdullah A Dutse ya gama rubuce rubucensa sannan yace "duba da yadda muka
fara wannan shari'ar, da irin shedu da hujjoji a gaban wannan kotu, kuma wanda ake
ƙara ya gaza musanta abunda ake tuhumarsa dashi, an samu wanda ake zargi da laifin
yin garkuwa da mutum, duba sashi na 273 na kundin penal court, wannan kotu ta yanke
wa wanda ake ƙara hukuncin shekaru goma a gidan yari, ba tare da zaɓin tara ba,
sekuma laifi na biyu da ake tuhumarsa dashi shine laifin fyaɗe ga ita wadda akai
garkuwa da ita, duba da sashin manyan laifuka, ƙarƙashin sashe na 221 wannan kotu
ta yanke wa wanda ake zargi hukuncin shekaru goma sha huɗu a gidan yari, tare da
aiki me tsanani, sekuma laifi na gaba laifin sata da siyar da abunda ba mallakinsa
ba, saida motar ita wannan yarinya wadda kuɗinta yayi naira miliyan talatin, wannan
kotu ta yanke masa hukuncin shekaru bakwai a gidan yari, da tarar Naira million
biyar, wanda ake ƙara idan hukuncin nan be masa ba, yana da damar ɗaukaka ƙara nan
da kwanaki talatin masu zuwa "
Alƙali ya buga gudumarsa ta kotu, aka sake taso Yusuf a gaba, sarƙa hannu da ƙafa
akayo waje dashi, kamar kullum duk yadda 'yan jarida suka so jin ta bakinsa, yaƙi
cewa uffan.
Suleiman kuwa dama hana Umman Yusuf yayi zuwa ganin shari'ar gaba ɗaya.
Ramlah kuwa ta sake bin Fahad ɗakin Hotel, tana ta zazzaga masa bala' i akan lallai
seya aure ta, Fahad yace "asje ke ƙwayar da kike sha, hauka ta saka miki ban sani
ba, ko matan duniya sun ƙare bazan aure ki ba, kin zama second hand, kije ki samu
wani ajawon daze iya rufamiki asiri".
Cikin ɓacin rai tace "ita wadda kake harin, itama ba second hand ɗin bace?"
'ai gara ita dake, koba komai ko second hand ce ai akwai kyau, dujda kema ba munine
dake ba, amma ai kowa yana son canji, kuma itama da manufa zan aure ta "
" wallahi baka isa ba, kayi kaɗan Fahad, zan gwada maka Rashin mutunci, jaki macuci
kawai wallahi bazan yafe maka ba"
"Ai babarki ce macuciya, itace babbar macuciya, kuma ina baki shawarar kije Asibiti
a tabattar da lafiyarki, saboda akwai matsala a lafiya ta"
Ayshercool
07063065680
11/29/21, 8:55 AM - Buhainat: LITTAFIN KUƊI NE, DAN ALLAH KI SIYA KAFIN KI KARANTA
BA DANNI BA DAN ALLAH, LITTAFI NA ƊAYA KYAUTA NE WANNAN NA SIYARWA NE
NORMAL GROUP ₦300
VIP ₦500 NE KITURA TA WANNAN ACCOUNT ƊIN
0009450228
JA'IZ BANK
AISHA ADAM
SE A TURA SHEDAR BIYA TA WANNAN LAMBAR
07063065680
(Albishir ga masoya, ma'abota bibiyar litattaafaina, dama ta samu zaku fara samun
litattaafaina na audio, akan YouTube channel ɗina me suna Cool Arewa TV
https://youtube.com/channel/UCD5vnvA5laU8ti4LLz2_QEg
Kuyi liking sannan ku danna subscribe, domin fara samun litattaafaina na audio,
nagode sosai da ƙaunar ku gareni"
140_141
Seda Ramlah tai dariya me isarta, yayimda Fahad ya bita da kallon mamaki irin
dariyar da take ƙyaƙyatawa, tace "Fahad ai duk yadda kake tunanina na wuce nan in
gaya maka, shiyasa nake ta binka Allah ma'aiki ka aureni, ban nuna maka nasan kana
ɗauke da cutar HiV ba harka samin ba, nake ta lallaɓaka amma baka gane ba, to na
ɗau matakin daya dace, dan haka zan maka Albishir, Danni agurin Albishir ne, ina me
farincikin sanar da kai cewa Ubanka Bulama ma yana ɗauke da wannan ƙwayar cuta "
" Kurma ne kai? Ko yaren da nayi magana dashi ne baka ji, nace ubanka mahaifi wato
Bulama, shima yana da cutar, na saka masa dan haka seka hanzarta kaje kasa shi ya
fara shan magani akan lokaci, tun kan ciwon ya huda shi sosai, sannan yama da kyau
ka binciki babarkama, ko itama ta rabauat seku duƙufa shan magani, kaga rabajau
daku idan wannan ya manta lokacin sham magani yayi, se wannan ya tuna muku "
Kamar Fahad ze fashe da kuka yace" kina nufin, Dad ɗina yana ɗauke da wannan cutar
ne? "
" Amma wace irin tinkiyace ke Ramlah, yanzu sekiyi mu'amala dani ki koma kiyi da
mahaifina saboda mugun abu? "
Ramlah tace " duk cikin iya takune, da farko shiya fara ɓatamin rayuwa, na rufa
masa Asiri, har na fara sonka, tun a wancan lokacin ya fara take taken baya goyon
bayan soyayyar, kaima kazo ka nemeni na bada ksi bori ya hau ina zaton zaka Aureni,
amma kaƙi kuma na kasa rabuwa da kai, duk da yadda Anwar ya dinga nusar dani, kawai
naga magani a jakarka, na tambayeka na mene kace min na gyaran jiki ne, nai nai ka
bani ka hanani, shine nai snapping nace a samomin maganin, aka gayamin na meye,
nayi kuka na shiga damuwa amma nakasa gayawa mowa damuwata, na cigaba da shaye2
daka koyamin dan ragewa kaina tension, naga babu hanyar da zanbi in huce takaicin
nan daka ƙunsami , seta hanyar sanyawa Ubanka wannan ciwon, se duk muyi jinyar
tare, nake ta binka ka aureni kana rainamin hankali kana ganin ka cuceni, kuma ina
me tabattar maka da cewa dukda kamilewa irin ta ƙaninka Ramadan, shima zan iya
bashi nasa rabon, dan haka seka san abunyi tun dare be maka ba ".
Ta ƙarasa maganar tana hararasa, ta bar ɗakin.
Ya dafe kai ya zauna yana faɗin" Innalillahi wa inna ialaihi raji'un, Allah ya isa
tsakanina dake, kin cuceni, ba kowa aka cuta ba se Mother, tana gefe ta kawamme
kanta ta riƙe Aurenta an kwasa mata masifa, Daddy why? "
(dama ita zina haka take, idan ka yi da ɗan wani za'ai da naka, idan ba ayi da naka
ba in one way or another, dole se wannan illar zinar ya shafi wani naka, zina bata
da wata riba sam, ga zunubi, ga cuta ga ɗaukar alhakin wanda basuji ba basu gani
ba, Allah ya shirya al'ummar musulmi baki ɗaya)
Fahad ya cigaba da kuka yana tunanin, ta yaya ze fara gayawa Mummy abunda ya faru,
wama ze tunkara da wannan Mummunan labari haka?
Babu wanda aka cuta sama da Mummyn mu, dama har yanzu Daddy yana biye biyen mata?
Innalillahi wa inna ialaihi raji'un.
"Ramlah kin cuceni, tsakanina dake Allah ya isa kawai ban yafe ba Wallahi, wayyo
Allah na, ban taɓa dana sanin irin rayuwar da nayi ba se yau, ubangiji Allah yasa
Mummy bata ɗauka ba, saboda abun kunya da Allah wadai, ace inbi yarinya mahaifina
ma yayi, wace irin rayuwa ce haka? Ta yaya zan tun kari Mummy in sanar da ita ta
binciki lafiyarta?
Fahad ya zauna zaman dirshan a ƙasa yana kuka, sekace ɗan yaye kuka harda majina,
ya rasa inda ze saka kansa dan baƙin ciki da takaici, yau a dalilinsa za'a sakawa
mahaifiyarsa wannan larura, koma an riga an saka mata, yanzu ta yaya ze tun kare ta
da wannan maganar?
Seda aka watse daga kotu sannan Bulama yabi Justice A duste chamber, A dutse yai
murmushi yace "ya kaga shari'ar tamu? Naga tunda muka fa fara shari'ar baka zuwa"
Bulama yace "ya za'ayi inzo, sannan shari'a tayi dan yi, shekaru talatin ai kan nan
komai yayi dai dai , amma abunda ya bani mamaki shine meyasa zaka ce wai yana da
damar daze ɗaukaka ƙara, ɗaukaka ƙarar na mene kuma? Tunda ka yanke hukunci, meye
kuma na wani ze iya ɗaukaka ƙara kuma? "
" Bulama kenan, har yanzu baka san meye shari'a ba, babu yadda za'ayi aiwa mutum
hukunci a irin kotunanmu sannan ka hanashi ɗaukaka ƙara idan hukuncin be masa ba,
ba'ai haka ba haka ƙa'idar aikin take ba, nan da kwanaki talatin yana da damar daze
je ya ɗaukaka ƙara "
Bulama ya ɗanyi ƙaramin tsaki yace " to yanzu meye abunyi? "
" Eh to, iyakaci kuyi ƙoƙarin toshe duk wata dama da zata saka ya ɗaukaka ƙararar,
idan kuma ya ɗaukaka ƙararar, to se ka faɗi ka tashi suma ka siye su "
Bulama yai tsaki yace " Aini daya ɗaukaka ƙarar da kar ya ɗaukaka idan na samu
abunda nakeso, can ta matse musu, ni yanzu zanje in maida hankali in samu abunda
nake so "
Bulama kai tsaye gidan da Widad take ya nufa, yana zuwa ya tarar da ita a zaune
cikin zumbulelen hijjabinta, ta ƙara zabgewa, duk babu ƙibar nan, Widad lazumi
kawai take a zuciyarta, dan tasan yaune ranar daza'a yankewa Yusuf hukunci a kotu,
sedai zuwa yanzu bata san wani hukuncin za'a yanke masa ba.
Bulama yazo ya sakata a gaba yana ƙare mata kallo, shikansa yaga yadda duk ta rame
ta fita hayyacinta, mutum baya ce ita ce Widad Nasir Daula ba.
Tunda ya shigo bata motsa ba, balle ta ɗaga kai ta kalle shi, ta zuba guri ɗaya ido
ko motsi ba tayi.
"Ina fatan kinji hukuncin da aka yankewa wannan sakaran xa kike iƙrarin mijinki ne?
Koda yake ba lallai ki sani ba, amma shekarun babu yawa, shekaru talatin da ɗaya
ne, se tarar miliyan biyar, sakamakon kama shi da laifin garkuwa da mutum, laifin
fyaɗe da kuma sata, ina fatan yanzu kin san me Bulama ze iya aikatawa? Koda yake
tun ba yau ba kin san irin abunda nake iya aikatawa idan ina buƙatar abu"
Widad bata motsa ba bata kalle shi ba, tai shiru abunta tana cigabs da ƙurawa guri
ɗaya ido.
"Yanzu kin shirya gayamin inda abubuwan nan suke ko sena je nasa an kashe Uwar
Yusuf"?
A hankali ta ɗaga kai ta dube shi, tace "kai a tunanin ka zan bar mijina ya shekara
talatin da ɗaya a gidan yarine? Lallai baka da hankali, kuma ga dukkanin alamu ka
manta wacece Widad ko? Zan baka mamaki kuwa, Yoseef baze zaman gidan yari ba, kuma
bazaka samu abunda kake so ba"
Widad tace "meye ban gani ba Bukar, zalunci da mugunta wanne ne bakamana ba? Kasa
aka kashe mahaifiyata, kasa aka haukatani, kai kutungwila ka aurawa mahaifina matar
da ta dinga azabtar da shi tsawon lokaci, yana bauta ita da 'ya' yanta amma suna
azabtar dashi, hakan be isheka ba kasa aka dinga kaimin farmaki dan a kasheni akan
dukiyar nan, banda message na razanarwa da tashin hankali da kake turomana, ƙiri
ƙiri ka rabani da ƙasata ta haihuwa saboda mugun zaluncinka, kasa nayi rayuwa kamar
matacciya, babu me raɓata ka jefa tsoron mutane a zuciyata, kasa aka dinga
farautata kamar dabbar daji, Allah ya kawo Yoseef na fara samun sassauci, nan ma
akasa akayi garkuwa damu, muka kuɓuta ya dinga wahala dani, amma a ƙarshe kalli
sanadin zaluncinka abunda aka masa, nida abun a kaina ya ƙare da sauƙi, shi meye
nasa a cikin lamarin nan? Wallahi wata shari'ar se a lahira shi kaɗai ze sakamin
wannan zalunci da kamin "
Bulama ya ƙyaƙyace da dariya yace " ke yanzu da duk kin san ni nake shirya wannan
abubuwan amma kika ƙyaleni nake cin karena ba babbaka? Lallai kin iya wauta, meyasa
kika ƙyaleni kikemin kallon uba bayan kin san ni maƙiyinki ne "
Widad tace " talala na maka, tun ranar da aka kashe mahaifiyata aka ambaci sunanka,
bazan taɓa manatawa ba, sedai na ƙyaleka ne saboda muddin nai wani yunƙuri zaka
kashe min mahaifi, shiyasa na ƙyeleka, amma a yanzu inaji a jikina kana daf da yin
faɗuwar baƙar tasa"
"Hmm, lallai yarinya dole a sarawa ƙoƙarinki, da iya takunki tun kina ƙarama kanki
yake kawo wuta sosai, kin iya lissafi sosai, Amma ki sani ni tsohon hannune a
duniyanci, tunda hukuncin da akayiwa mijinki be zama izina a gareki ba, zan sa a
kamo min uwarsa, inzo in yankata a gabanki tunda ke taurin kai baze barki ki ƙwaci
kanki ba"
Wani mugun kallo tayi masa, ya tashi ya fita daga ɗakin nata, bayan tafiyarsa
Sabuwa ta shigo ɗakin Widad tana dube dube tace "dan Allah ban yarda memory ɗina a
ɗakin nan ba, tun jiya nake nemansa ban ganshi ba sam"
Widad tace "nima ban ganshi ba gaskiya, dan Allah Al'ada ne yazomin, tunda aka
ciremin cikin nan ban ƙarayi ba se yanzu, dan Allah ki aramin dubu ɗaya, in rubuta
miki irin wadda nakeso ki kai kowane shago a baki, idan Allah ya fitar dani zan bi
yaki"
Sabuwa tace "to shikenan" taje ta samo biro da takadda ta bawa Widad ta raba
takaddar biyu, Widad tai rubutu akan kowacce takaddar, da yake Sabuwa bata iya
karatu ba, Widad ta rubuta ta bata ta ɗakko wata leda tace "dan Allah karki gayawa
kowa na aike ki, ki kai shago kice a bani abunda na rubuta a jiki, ki haɗa musu da
wannan ledar ki basu"
Mum Nurat taga sam bata ga gilmawar 'yarta ba, dan haka ta tafi ɗakin Nurat ɗin,
tana zuwa ta tarar tayi wujuga wujuga saboda kuka, se rusa uban kuka take kamar
ubanta ya mutu.
A ɗan gigice tace "ke lafiya kuwa? Meye ya faru dake haka? Me akayi miki ne?"
Maimakon ta bata amsa, sema sake rushewa da kukada tayi, "ke bana son sakarci fa,
menene haka? Meya sameki kike rusa wannan uban kukan haka?"
"To idanma na gani me zanyi, ko kuma me zance? Allah ya bayyana gaskiya kawai, amma
shine zakizo kina wannan uban kukan haka? Ai koni na mutu iyakar wannan kukan
kenan"
"Mummy wai meyasa kike basarwa ne, baki san menene yake wakana ba? Kin san fa komai
Mummy? Daga gidan nan fa ake shirya maƙarƙashiya fa kin sani fa"
Da sauri Mummy ta ƙarasa, ta tishe mata baki tace "dan ubanki yana cikin gidan nan,
so kike ya jiyo yazo yai miki wani abun?"
Nurat ta fizge tace "Haba Mummy, meyasa zamu ɗauke ido akan gaskiya Mummy? Wallahi
ranar lahira muma harda mu a cikin wannan zaluncin da akayi, Mummy da saka hannun
Daddy fa aka sace su Widad, Mummy da kunnena fa naji shi"
Maman Nurat na juyawa taga Alhaji Musa a ƙofar ɗakin, yana kallon su.
Nurat taƙi yin shiru tace "gaskiya Mummy idan mukayi shiru bamu da adalci, wallahi
da saka hannun Daddy akan abunda ya faru, kuma kema kin sani, Wallahi da Daddy ake
shirya komai, Mummy ya zakiji idan ɗankibaka yankewa hukuncin shekaru talatin da
ɗaya a gidan yari? Kefa uwa ce Umma, bakya tunanin me mahaifiyarsa zataji a ranta a
yanzu haka? Ancd shikaɗaine ɗanta amma an yanke masa hukuncin shekaru talatin da
ɗaya a gidan yari "
Cikin tsawa Mummy tace " dan ubanki bazaki min shiru ba, seya miki wani abun
tukuna? "
Nurat tace" Mummy nifa gaskiya nake faɗa, kuma ni zanje in bayar da shedar abunda
ya faru, mahaifina yasan komai fa"
Alhaji Musa ya tako a hankali, yana zuwa bece komai ba ya danƙi hannun Nurat ya
fara jan ta, a gigice Mummy tace "ya haka? Ina zaka kaimin 'yata? Ina zaka kaita?
Karka cutarmin da ita dan Allah, ita kaɗaice' yata karka cutar da ita na gaya maka"
Be tankamata ba, ya dinga jan Nurat, Nurat tana faɗin "Daddy kaji tsoron Allah, a
wannan shekarun naka me kakae nema a duniya haka, wanda zesa kasa hannu a zalunci
wani, da Alhaji Nasir kake da matsala bada 'yarsa ko wanda beji ba be gani ba, dan
Allah Daddy ku ƙyale Daula ya huta, da kunnena naji kana magana kune kuka saka aka
sace Widad da direbanta, kuma yanzu kun sauya maganar kuna gabi aka kaishi kotu aka
yanke masa hukunci akan abunda bejiba be gani ba"
Yana jan Nurat, tana biye dashi yayin da mahaifiyarta ke binsu tana masa magiya,
wani ɗaki yaja Nurat can bayan ɗakinsa a ƙarshen bene, ya jefa ta ciki yasa mukulli
ya kulle ta, ya juya ze tafi, Maman Nurat ta sha gabansa tace "meyasa zaka
kullemin yarinya a wannan ɗakin ita kaɗai? Me yasa haka? Dan Allah ka buɗe mata
ƙofar nan ta fito, karta cutu dan Allah"
Alhaji Musa yace "wallahi bazan buɗe ta ba, ashe kune manyan maƙiyanaba gidan nan?
Dole ta bar ƙasar nan ko tana so ko bata so, kuma kema daga yau, bake ba fita ko
ina, kuma duk sena karɓe wayoyin ki, munafukar banza da ta wofi"
"Niba munafuka bace, karka ƙara kirana da munafuka, halin rashin gaskiya 'yarka ce
ta fara gano kana yi, dan haka babu laifina a cikin wannan batun? Dan Allah ka
buɗemin' yata dan Allah ka barta ta fito, wallahi bazan bari tayi komai ba, dan
Allah kayi haƙuri "
Tsaki yayi, ya raɓa ze wuce ta, amma ta sha gabansa tana kuka akan ya buɗe Nurat,
aikuwa ya Tureta ze wuce bisa ga tsautsayi ta gangaro daga kan benen nan, ta ƙwala
ihu da ƙarfin gaske, tun daga ƙafar farko har ƙasa, da sauri ya bita sedai kan ya
ƙaraso tuni ta ƙarasa, ta faɗa da fuska aikuwa tuni jini ya wanke gurin, jikinsa
yana rawa yazo ya ɗagota, fuskarta ta wanke tsaf da jini, gashi ko motsi ba tayi,
akan idon me gadinsa ta faɗo daga kan benen.
Nurat ta jiyo ihun mahaifiyarta, amma bata san meyafaru ba, dan haka hankakinta ya
tashi, ta shiga dukan ƙofar ɗakin da ƙarfin gaske tans kuka, tana kiran sunan
Mummy.
Aka ɗauki Maman Nurat, zuwa Asibiti cikin gaggawa, ana zuwa aka karɓeta a Asibitin,
da gaggawa aka shiga da ita emergency.
Sabuwa ta dawo gidan da Widad take, ta shiga gurin Widad tace "Nifa naje na kai
musu, amma basu bani komai ba, sun karɓi takardar sun karanta, sun bani wata
takardar, sun karɓi ledar sunce in tafi kawai, hadda tambayata wai waye ya aikoni?"
Widad tayi murmushi tace "inaga basu da ita ne, bani takardar da suka baki"
Ta miƙawa Widad takardar da suka bata, ta karɓa ta karanta, tai ajiyar zuciya tace
"nagode sosai Sabuwa, sunce basu da irin wadda nake so, se Allah ya kaimu jibi kije
ki karɓa"
"no karki damu, zan iya maleji zuwa lokacin da zasu kawo ɗin, bana iya amfani da
kowacce se ita ne"
Sabuwa tace "to shikenan, Allah sarki ashe cikin ya fita dagaske?"
Fahad fa ya rasa inda zesa kansa, da yaga mamansa, se yaji tausayinta ya kama shi,
se yaji ƙwalla ta tarar masa, maimakon yaji haushin kansa, haushin mahaifinsa ya
dinga ji, dan dabe nemi mata ba da babu abunda zesa mahaifiyarsa ta samu, gashi ya
rasa ta inda ze mata wannan baƙin bayanin mara daɗin ji.
Gidansu Amal ma gidan sam babu daɗi, idan Ramlah taga dama a falo, haka take zuwa
ta kama shan shisharta, kota kunna sigari tana busawa, ta baje kayan coadine ɗinta
taita yiwa kanta caji, Hajiya Halima yanzu kam tsaro Ramlah take bata, sam bata
iyayi mata magana, tana kallon ta, tana yi amma bazata iya cenata bari ba, Amal
kuwa dama tuni ta fita daga harkar su.
Hajiya Halima na ɗakinta, ko izininta bata tambaya ba ta fice ta tafi Asibiti dan a
dubata, sedai ta razana da sakamako ya fito aka tabattar mata da tana ɗauke da juna
biyu, ta shiga ɗimuwa da tashin hankali, tun a Asibitin ta lalubi lambar Alhaji
Haruna ta sanar masa da tana ɗauke da juna biyu, kuma ko yasan yadda zeyi da ita ko
kuma tayiwa duniya Albishir da tana ɗauke da cikinsa.
Abubuwa fa suka rincaɓe sosai, Wata Nurse inyamuda ta jata gefe tace mata tasan
inda zata kaita a zubar da cikin, in dai bata son cikin, ba musu ko tunanin komai
Amal ta amince da a zubar da cikin.
Yusuf yana cikin fursunoni, yana zaund shiru kamar yadda ya saba zama, akace yayi
baƙi ya kalli gandiroban ya ɗauke kai kamar beji ba, "Malam da kaifa neka"
gandiroban yai maganar a ɗan hasale"
'me zanje inyi? An riga an yanke min hukunci, burinku ya cika kuda iyayen gidanku,
me kuke nema a gurina kuma? Ko waye bazani ba"
Da jin haka Yusuf ya miƙe da sauri, se kuma yaji bashi da karsashin tunkararta ya
kalleta, dan yasan abune mawuyaci sukuma rayuwa da Ummansa kamar da.
Yusuf yabi bayan gandiroban jiki a saɓule, yana dogara ƙarafarsa da kyar saboda
ciwo da take masa.
Yana zuwa yaga wasu mutane a zazzaune, wanda be sansu ba sam, aka bashi guri ya
zauna yana ƙare musu kallo.
Ɗayan ya kalle shi yace "sannu Malam Yusuf, sunana Barrister Hafiz wannan abokan
aikinane" yai maganar yana miƙawa Yusuf hannu.
Amma Yusuf ya ƙeƙashe ƙasa yaƙi bashi hannu, ya kalle shi yace "me kuke nema a
gurina? Bayan shari'a tazo ƙarshe an yankemin hukunci, me yayi saura kuma me kuke
so inyu muku"
Hafiz jiya yi kamar yayi kuka shima, ya maze yace "haba Yusuf, ai ka tsaya kaji
meke tafe damu ai, Barrister miƙo takaddar nan"
Barristern dake gefensa ya ɗakko takadda ya miƙawa Hafiz, Hafiz ya karɓa ya miƙa
masa yace "ga saƙo inji matarka"
Jikin Yusuf na tsuma ya karɓi takaddar yana buɗewa yaga rubutun Widad "
_Bani da abunda zan iyayi maka a halin da nake ciki I love you My Yoseef, but I
will do my best to see what I can do for you, please pray for me, is either we
should meet again or the time you will be free i pass away_
AYSHERCOOL
07063065680
11/30/21, 8:20 AM - Buhainat: LITTAFIN KUƊI NE, DAN ALLAH KI SIYA KAFIN KI KARANTA
BA DANNI BA DAN ALLAH, LITTAFI NA ƊAYA KYAUTA NE WANNAN NA SIYARWA NE
NORMAL GROUP ₦300
VIP ₦500 NE KITURA TA WANNAN ACCOUNT ƊIN
0009450228
JA'IZ BANK
AISHA ADAM
SE A TURA SHEDAR BIYA TA WANNAN LAMBAR
07063065680
(Albishir ga masoya, ma'abota bibiyar litattaafaina, dama ta samu zaku fara samun
litattaafaina na audio, akan YouTube channel ɗina me suna Cool Arewa TV
https://youtube.com/channel/UCD5vnvA5laU8ti4LLz2_QEg
Kuyi liking sannan ku danna subscribe, domin fara samun litattaafaina na audio,
nagode sosai da ƙaunar ku gareni"
_(INNALILLAHI WA INNA IALAIHI RAJI'UN ina amfani da wannan damar gurin miƙa saƙon
ta'aziyya ga Ɗaukacin zuriyar Hajiya Aisha Muhammad (Baba) bisa babban rashi da
mukayi na rasuwar ta ina fatan ubangiji Allah ya jiƙan ta yai mata rahama, ya kai
haske kabarainta, ubangiji Allah ya duba zuriyar da ta bari, ya bata ladan
ɗawainiya da iyalI da tayi tsawon ranta, ubangiji Allah ya jiƙan kafatanin wanda
suka rigamu gidan gaskiya Musulmi, idan tamu tazo Allah yasa mu cika da kyau da
imani_)
IN THE MEMORY OF LATE HAJIYA AISHA MUHAMMAD, I DEDICATED THIS PAGE TO LATE HAJIYA
AISHA MUHAMMAD (BABA) MAY ALLAH SUBHANAHU WATA'ALA, GRANT HER JANNATUL FIRDAUSI
AMEEN _
Ina ma'abota son gyaran jikinsu yau ga maman sayeed collection tazo muku d
gangariyar maganin gyaran breast (nono)
Maganinmu yayi fice gurin gyaran nono kikai amfani d maganinmu cikin 1week
zakiga result maganinmu yana ciko d nono suyi bul² nono ko yakai silifas y mushewa
kikai amfani dashi zakiga canji
Maganinmu Bashi d side effect mun hadashi d tsirrai d saiwoyi kala² domin Y'an
uwa mata
Muna kano muna tura maganinmu ko wane state d yardar Allah meso yakira wannan
number 08120337219
Chat 08063114606
144_145
Ai zumbur ta miƙe zaune tace "ban gane a kasheshi ba? Anwar ɗin nawa za'a kashe? Me
yayi masa haka?"
Alhaji Musa yace "ke nifa tuni na dawo daga rakiyar mutumin nan, Azzalumi ne kawai,
kansa ya sani bashi da imani sam, ni kaina yanzu haka muna Asibiti nida su Nurat,
amma gaba ɗaya ko yamin jaje se masifa da tashin hankali da yake min, shiyasa na
kwashi kuɗina na saka a siyasa, in samu su bani takara in huta da wannan mulkin
mallakar da yake mana, ga uwar dukiyarmu da muke narkawa amma har ynzu babu wani
bayani "
Hajiya Halima ta fashe da kuka tace " ni Bulama zeyi wa haka? Anwar kamar ɗa yake a
gurinsa amma shine zece a kashemin shi? Baze yuwu ba kuwa "
Ta ajiye wayar, ta miƙe ta shiga ɗakinta ta zura doguwar riga, kusan ƙarfe goma
saura na dare, amma tayi waje ta ɗau mota ta fita ta tafi gidan Bulama a daren.
Shikuma Bulama yana zaune yana ta nazari akan yadda ze ɓullowa al'amura da suke
neman damalmale masa, ya dinga kiran layin su Me Adda amma shiru babu Labari, waya
taƙi shiga sam.
Masu gadi kansu sunyi mamakin ganinta a wannan daren, kamar wata mahaukaciya ko
gabanta bata gani sosai saboda tashin hankali, kai tsaye ya shiga falon dake ƙasa
tana bala'i "Ina Bulama yake? Ina Bulaman?"
Iman ce zaune a falon tana kallon zee world tace "Mummy lafiya kuwa?"
"ban sani ba, ina uban naku yake tsohon macuci azzalumi?"
Iman ta kalleta da mamaki jin irin furcin da take akan mahaifinsu wanda ya kasance
ɗan uwa a gareta, Iman tace "Mummy ya riga ya hau sama, inaga ma ya kwanta fa"
Ai bata tsaya jiran me Imana zata kuma ce mata ba ta haura saman da kanta, ba zato
ba tsammani ya ɗaga kai yaci karo da Hajiya Halima a tsaye a kansa.
Ya kalleta yace "Halima, lafiya kuwa zaki zo a daren nan? Bakya jira ayi miki iso
kawai ki hauromin ɗaki haka?"
"Dalla rufemin baki, me zaka gayamin har wani iso zan jira ayimin, munafuki
azzalumin banza dana wofi, tsawon shekaru ina maka aiki, kana sani duk abunda kaga
dama ina maka, dan ka cinma burinka ba tare da na nuna gazawata ba, shine halin
naka na baƙin kumurci zaka gwadamin, shine kayi umarni da idan anga Anwar a
kasheshi, ɗan nawa za'a kashe? Wallahi baka da imani ba kada Alƙawari tun wuri ka
dakatar da wannan maganar idan ba haka ba Wallahi ran ɗana baze tafi a banza ba"
Zazzaro ido Bulama yayi ya dinga ƙifta mata ido akan tayi shiru, amma tace "bazan
shirun ba, wallahi babu inda zani se an dawo min da ɗana"
"Halima wai wace irin magana kike hakane? Kamar yaya nace idan anga Anwar a
kasheshi? Me Anwar yayi min wanda zesa ince a kashe shi, ni da na kaiwa jam'ian
tsaro maganar dan ayi bincike akansa a gano inda yake ya zakice nace a kasheshi?
Wani munafukin ne ke neman haɗani da 'yar uwata?"
" Kaga bana son kame kame da ƙaryar banza, wanda ya gayamin baze maka ƙarya ba,
macucin banza da na wofi kuma wallahi idan ɗana ya mutu you must pay for it,
wallahi aka kashemin Anwar seka fanshi ransa, nima kasan halina ka san abunda zan
iya aikatawa "
Gaba ɗaya Bulama ya dirirce ya rasa abunyi, ya shiga tsuma yana fatan Allah yasa
wani beji abunda ta faɗa ba.
Ya biyo bayanta ya leƙa, yaga ba kowa a falon ƙasa dukda ɗakin a rufe yake babu
wanda ze iya jiyo me sukayi, ya koma bedroom ɗinsa ya tarar da Hajiya Sarah tana ta
baccinta hankali kwance, yai ajiyar zuciya tare da tunanin bata jiba, amma ya zauna
yai shiru akan gadon yana tunani, tabbas babu wanda ze gayawa Halima wannan maganar
idan ba Alhaji Musa ba, tabbas dole yayi maganin Alhaji Musa.
Cikinsa ne ya murɗa ya tashi ya tafi banɗaki, kusan kwana huɗu kenan yana fama da
gudawa taƙi tsayawa, dan haka ya sa ransa idan ya gama da wannan matter ɗin zeja
yaga likita.
Yusuf se sake juya takaddar nan yake, yana tunanin wani hali Widad ɗin ke ciki,
tabbas yasan da tana da dama bazata barshi a gurin nan ba, dole akwai wani abu da
yake gudana a ɓoye, idan ya kalli sentence ɗinta na ƙarshe na ba lallai su sake
haɗuwa ba se yaji gabansa ya faɗi, lallai ko a ina take tana cikin mawuyacin hali,
"Allah ya ƙara haɗa fuskokinmu my wife, Allah yasa kina hannu na gari, i love you
too" yai maganar a hankali tare da lumshe idonsa.
Rayuwar da suka yi tare a ƙauye ta dinga dawo masa, koba komai zamansa da ita ba
ƙaramin farinciki ya samu ba, zamansu a ƙauye yasa Ƙwaƙwalwarsa da zuciyarsa ta
samu hutu na wani ɗan lokaci, ya daɗe beji cin zarafi da gorin rashin iyaye daga
mutane ba, sedai matukar kewar Ummansa da yayi, be sake zaton ze samu wadda zata
aureshi ba saboda rashin nasaba ba, sedai cikin hukuncin Allah ya auri yarinyar da
zuciyarsa ta mato a sonta, dukda nisa da ratar dake tsakanin su, yarinyar da manyan
wanda suka isa ma basa gabanta, soyayyar ma bata yadda da ita ba, amma Allah ya
ƙaddara Aurensu, har suka yi zama cikin farin ciki, ya dinga tuna irin Shagwaɓarta
wauta da yarinta wasu lokutan, ya tuna lokacin da take koyar tankaɗe, da sanda take
wa Abincin garin kallon banza, da yadda ta dage ita seta samu ciki, da irin kallon
da take masa idan ya tsokane ta.
A hankali ya sake lumshe ido yana murmushi, sekuma ya tuna yadda ta shiga damuwa
daya bata labarinsa, da yadda ta dinga kururuwa tana kuka tana gaya masa tana sonsa
lokacin da aka kama shi a garin, da yadda taje kotu ta bada sheda akansa, ga
shekarun da aka yanke masa a gidan yari, ga abunda ta rubuta masa kawai se yaji ya
karaya hawaye ya shiga bin gefen idonsa, baya tunanin ze sake wata rayuwa me daɗi a
nan gaba, mussman kasancewa da Widad a inuwar Aure.
Da ƙyar likitoci suka samu Nurat ta dawo hayyacinta ta samu bacci, aka sa mata
ruwa, sedai harta farfaɗo ɗin numfashinta da vital signs ɗinta suka daidaita bata
gane mutane sosai, saboda ta galabaita an samu dai bacci ya ɗauketa cike da fatan
idan ta tashi zata iya dawowa hayyacinta gaba ɗaya, mahaifiyarta kuwa gaba ɗaya har
yanzu ba'a gano kanta ba, tana kwance ne kawai, numfashi ne kawai a ƙijinta, banda
haka babu abunda yake aiki a jikinta, sam bata san abunda ke faruwa ba, shi kansa
numfashin nata da ƙyar take yinsa wasu lokutan, saboda ta zubar da jini sosai, kuma
ana kyautata zaton ta samu rauni a cikin kanta, sakamakon buguwa da tayi, likitoci
sun rubuta mata hoton Ƙwaƙwalwa dan tabattar da abunda yake damunta.
Abu kamar wasa, jini yaƙi tsayawa Amal, se aikin zaryar banɗaki take, jini se zuba
yake babu ƙaƙƙautawa, ta rarrafa ta haɗa Abinci tana ci kota samu sauƙin wannan
wahalar haka, zuciyarta tana ƙuna akan yadda Alhaji Haruna ya cuce ta, Hajiya
Halima ta fito falon ta zauna ta dafe kai ta kalli Amal tace
"wai kuwa lafiyarki ƙalau kuwa? Gaba ɗaya kin wani ɗashe kinyi fari ƙal, kamar baki
da jini a jiki, ko baki da lafiya ne?"
Hajiya Halima tai ajiyar zuciya tace "Amal kin kuwa san abunda Bulama yaimin?"
"wai an gano inda Anwar yake, amma yace wai a kasheshi saboda karya tona Asiri"
"Naje har gidansa jiya da daddare, na ƙare masa tatas, nace wallahi aka kashe min
ɗana seya fanshi ransa da nasa ran kona 'ya' yansa"
Amal tabi mahaifiyarsu da kallo, wani irin baƙin ciki ya turnuƙeta, duk
mahaifiyarsu ta ɗaiɗaita rayuwarsu da kanta, kowa yana karɓar nasa kason ɗaya bayan
ɗaya.
Ramlah ce ta fito tana tangaɗi, tana magana cike da maye ta tsaya a tsakiyar falon
tace "Wai ni.... Waini Fahad baze Aureni bane... Bazaki ce ya aureni ba ko? Wa..
W.. Wallahi kuwa bazan dena shaye2 ba tunda ya lalatani, ku.... Kuma... Kumaaa ai
shikenan tunda nasan Na sakawa Bulama cutar tunda shima ya sakamin... Wallahi idan
baka Aureni ba sena sakawa Wannan yaron Ramadan ma, idan yaso kow... Ko..... Kowama
ya samu ni za'ayiwa hauka? Ya.. Ya ɗauka bani da wayo hmm baka san Rmalha bane"
kawai ta faɗi a gurin tana juyi tana ci gaba da sambatu marasa kan gado sam.
Hajiya Halima ta kalleta tace "Ramlah wai wace cutar kike magana akai ne? Wace irin
cuta?"
Ramlah bata san me take ba, juyi kawai take yi tana wasu surutan irin na marasa kan
gado, Amal kam tasan babu mamaki idan akace Fahad yana ɗauke da wannan cutar me
karya garkuwar jiki, amma sedai dagaske Ramlah take tana mu'amala da Bulama ma
kenan, gaban Amal ne ya faɗi kardai ace itama tana da wannan cutar, miƙewa tayi da
sauri zata tafi ɗakinta, Hajiya Halima tace "Amal ina zaki? Kina jin maganar da
gake faɗa? Ko dai duk a cikin maye take ne?"
Amal tace "tunda ki kaji ta faɗa a maye, to ko ba'a mayen bama ya faru, sedai fatan
Allah ya kyauta"
Amal ta tafi ɗakinta, dan itama fama take da kanta, wannan azabar ciwon marar da
zubar jinin sun isheta haka.
Anty Saddiƙa ƙanwar Maman Nurat itace a gurin Nurat, itakuma maman Nurat ba'a barin
kowa ya shiga inda take in ba likitoci ba, saboda tana ƙarƙashin kulawa ta
musamman, Anty Saddiƙa taje salla Khalil na zaune a gurin Nurat, ai kuwa ta farka
ta zaci zata ganta a ɗakin Dad ɗinta ya kulle ta, sedai tana buɗe ido tai arba da
wani gurin daban, ta yunƙura zata tashi zaune, Khalil ya taho da sauri ya riƙeta
yace "yi haƙuri, ki kwanta kinji, karki gaggawa jikinki babu ƙwari"
Ya ɗakko ruwam roba, ya buɗe ya bata ta sha, har ze gyara mata kwanciyarta ta
kwanta, ta riƙe shi gam tana kallonsa, tana ƙoƙarin tuna meyafaru ihun Mummynta ta
tuna, nan da nan ta razana tace masa "Mummy, Khalil Mummy na tana ina?"
"A'a ban yadda ba, naji ihunta fa ranar, ban san meye ya sameta ba, tunda Daddy ya
kulleni ban sake ganinta ba, waini ya akayi ma nazo nan ne?"
Nan ta kwashe duk abunda ya faru ta gaya masa, yai shiru yana nazarin maganganun
Nurat, cikin kuka tace "ina Mummy take? Dan Allah ka kaini in ganta dan Allah"
Khalil yace "ki kwantar da hankalinki, likitoci na can na kula da ita, idan ta
farka zata zo ki ganta"
"Bakomai, ta faɗi ne kawai saboda Dad ɗinki ya rufeki, bari Anty Saddiƙa tazo ta
temaka miki kiyi wanka"
Bayan Saddiƙa ta shigone, Khalil ya tashi ya fita, a reception yaje ya samu Alhaji
Musa a zaune, dan idan yazo Asibitin ya duba su Nurat nan yake dawowa ya zauna, dan
gaba ɗaya haushinsa suke ji.
Ya zauna kusa da Alhaji Musa ya kalle shi yace "garin yaya ƙanwar mahaifiyata ta
faɗo daga bene?"
Alhaji Musa yace "wace irin magana ce wannan? Ba a gabanka nayi wannan bayanin
ba?"
Khalil ya kalle shi yace "to ya akayi ka kulle Nurat? Laifin me tayi maka"
Yai maganar yana ƙoƙarin miƙewa tsaye, amma Khalil ya tareshi yace "na tambayeka
kana ƙoƙarin tashi ina zaka?"
Yace "wai ita Nurat ɗince tace maka kulleta nayi?"
Khalil yace "labari na samu, daga majiya me ƙarfin gaske, dan haka nake tambayarka
garin yaya ka kulleta"
"ba rashin kunya bane, gaskiya ce dama ina da ayar tambaya akanka, wallahi muddin
na ganoka da wani abu ba dai dai ba, naga wani abun kayiwa ƙanwar mahaifiyata ta
faɗo daga bene, wallahi se nayi shari'a da kai, yanzun ma ba ƙyaleka zan ba, dan ba
ƙaramin haushinka nakeji ba"
Alhaji Musa zeyi magana, amma Khalil ya dakatar dashi yace "ba abunda zaka gayamin,
bana buƙatar jin komai daga gareka, amma tabbas ina nan ina bincike akanka, kuma
wallahi ina daf da tsayawa a kotu a gaban alƙali da kai"
Ya miƙe ya bar gurin, Alhaji Musa ya bi shi da kallo, yana tunanin me Khalil yake
nufine?
Bayan Ramlah ta tashi daga mayen da take ne, Hajiya Halima tazo ta sata a gaba tana
tambayarta "Ramlah wata magana naji kina yi ɗazu cikin maye, wai Fahad yasa miki
cuta, kekuma kin sakawa Bulama, wacce magana ce haka?"
Ramlah tace "Eh to, dukda kince a maye nayi maganar kamar yadda kiji maganar haka
take, Bulama shiya fara lalatamin rayuwa ta, na kamu da son ɗansa wanda hakan yasa
na biye masa, sedai Bulama yaƙi goyon bayan ya aureni, yake ta cusa masa 'yar Daula
ya aura saboda ya cika burinsa, soyayyar da nakewa ɗansa tasa na dinga biye masa ya
koyamin shaye2, ya koyamin rayuwar banza nida shi ba abunda bama yi, nace ya Aureni
amma yaƙi, kuma na gano yana da cuta me karya garkuwar jiki, dan haka na ƙuduri
aniyar ramawa na komawa mahaifinsa, kuma da yake ɗan Akuyane ya karɓeni, ba tare da
yasan ina mu'amala da ɗansa ba, dan haka shima ya kwasa, zuwa yanzu nasan uwarsa ma
ta ɗauka, hakan yasa na ɗan rage abunda ke zuciyata gara muyi jinyar tare hadda
ubansa"
Hajiya Halima ta ɗora hannu a ka tace "yanzu Ramlah abunda kikayi kenan? Ramlah
gaba ɗaya kika biyewa namiji kika barbaɗar da rayuwarki da mutuncinki? Kin kyautawa
kanki kenan?"
Ramlah tace "Mummy, bafa laifina bane wannan lamarin, duk wanda yazo neman Aurena
se ki nunamin ai shi ba sa'an aurena bane, ina gidan Attajiri kamar Daula bekamata
in Auri wane ba, ƙarewa ɗan uwanki ya biyoni ya lalata, na kamu da son ɗansa amma
yai biris dani, kuma akan idinki nake fita ai, kin taɓa tuhumata ina muke zuwa nida
Fahad idan mun fita? Me yasa? saboda idonki ya rufe ke burinki ya kawo miki masu
siyan kadarori ki tara kuɗi, don't blame me for this please "
Ta tashi tai tafiyar ta ɗaki ta bar mata falon, Hajiya Halima ta dafe kai ta fashe
da kuka, Bulama ya riga ya gama cutarta a rayuwa, ba ta san mema za tace a game da
shi ba, ya lalata mata rayuwar 'ya, kuma wai yanzu Ramlah na ɗuke da cuta me karya
garkuwar jiki, wanda ta samune a sanadin ɗansa, kuma ya dawo yace a kashe mata ɗa,
ta rushe da kuka harda sheshsheƙa, gaba ɗaya komai ya rikice mata, tama rasa meye
abunyi, wannan wace irin masiface haka take bibiyar ta? Daga wannan se waccan gaba
ɗaya 'ya' yanta sun barbaɗe, haka ta dinga gunjin kuka ita ɗaya a falo, Amal ta
ƙarawa ƙofar ɗakinta key, dan bata son tashin hankali.
Da safe Fahad ya shiga cikin gida, domin gaida iyayensa, sedai yan zaune a falon
Iman nata masa surutu amma sam hankalinsa baya kanta, yayi zurfi a tunani can ya
ɗago kai yace "ke wai ina Mummy ne?"
Ji yayi kamar ta watsa masa wuta, ta ina ze fara gayamata hakinda ake ciki? Koma ya
gayamata ai yasan aikin gama ya riga ya gana zuwa yanzu.
Yana nan zaune Sega Bulama yana Sakkowa, hannunsa ɗauke da jakarsa, Mummy sanye da
doguwar rigar baccinta, ta riƙo masa wayarsa suna hira, Fahad yaji kamar yaje ya
make Bulama saboda tsabar baƙin ciki da takaici, ga wani irin tausayin mahaifiyarsa
ya kama shi.
Hajiya Sarah ta kalli Fahad tace "yau Allah ya nufe ka da shigowa cikin gidan
kenan? Yaushe rabonka da shigowa"
Bulama yace "wai gidan ubanwa kake shigewa ne? Ko haryanzu yawon kake baka kwana a
gida?" ga mamakinsa seya ga Fahad ya maka masa wata uwar harara, abun da be taɓa yi
masa ba, ya kalli mahaifiyarsa yace "Mummy ina kwana?"
Kallonsa sukayi gaba ɗaya, Hajiya Sarah tace "Fahad, daga kan kayan shaye2 naka ka
taso ka shigomin falo ko? Shine har kake gayawa mahaifinka wannan maganar?"
Alhaji Bukar yace "ƙyaleshi, ina daf da maganinsa akan wannan mummunar ɗabi'a ta
shaye2, dank yake zancen, ban agogona zan fita ina da ayyuka da yawa a Office "
Yasa hannu ya karɓi agogonsa, yai waje bayan fitarsa Hajiya Sarah ta kalli Fahad
tace " Fahad, meyasa ka gayawa mahaifinka wannan maganar haka? Kai lalacewar taka
harta kai kayiaa mahaifinka haka? Me yayi maka? "
" Bakomai amma ka faɗa masa wannan maganar? Abunda kayi ya dace kenan?"
"to meyasa kayi, salon mutane suji suce ni nake saku a turbar banza, na ku
Wulaƙanta mahaifinku?"
"Nifa Mummy bakomai, kema da kin san me yayi da baki faɗi wannan maganar ba, kawai
dai Allah ya kyauta"
Ya mike a fusace ya baf falon, tabi bayansa da kallo, Iman tace "Mummy"
"Na'am"
"wai kuwa idonki biyu, jiya da Maman su Amal tazo gidan nan?"
"subhanallah, Allah yasa ba'a akan Ramlah tazo ba, saboda kin san halin ɗan uwanku
sarai, ina kyautata zaton akwai alaƙar banza a tsakanin sa da Ramlah"
. "Mummy ya akayi kika sani?"
"last week na ganta ta fito daga sashinsa, na tambaye ta amma bata gayamin komai
ba, sema baƙar magana da tayi min"
Iman tace "Umma kiyi ta haƙuri, Yaya Fahad se Addu'a gaba ɗaya zamansa a ƙasar waje
ba abunda yasa masa se koyar mugayen halaye"
Hajiya Sarah tace "idan da zaman ƙasar waje dai to harda halinsa, meyasa shi Anwar
be lalace ba se shi? Bani da abunyi se dai yi masa addu'a, baya jin faɗa baya jin
rarrashi, babu wanda banyi ba, amma duk baya ɗauka"
"Mhmm Iman kenan, yaushene watarn ɗin? Mutum ya girma amma kullum ba hankali, Allah
ya kyauta dai kawai".
Yanzu ma Bulama yana zaune a Office, kiran wayar Me Adda kawai yaje amma taƙi
shiga, yai shiru can wayar ta fara ringing, cikin hanzari ya ɗauka ya zata me Adda
ne, sedai yaga baƙuwar lambace, ya ɗaga yai sallama
(Albishir ga masoya, ma'abota bibiyar litattaafaina, dama ta samu zaku fara samun
litattaafaina na audio, akan YouTube channel ɗina me suna Cool Arewa TV
https://youtube.com/channel/UCD5vnvA5laU8ti4LLz2_QEg
Kuyi liking sannan ku danna subscribe, domin fara samun litattaafaina na audio,
nagode sosai da ƙaunar ku gareni"
_(INNALILLAHI WA INNA IALAIHI RAJI'UN ina amfani da wannan damar gurin miƙa saƙon
ta'aziyya ga Ɗaukacin zuriyar Hajiya Aisha Muhammad (Baba) bisa babban rashi da
mukayi na rasuwar ta ina fatan ubangiji Allah ya jiƙan ta yai mata rahama, ya kai
haske kabarainta, ubangiji Allah ya duba zuriyar da ta bari, ya bata ladan
ɗawainiya da iyalI da tayi tsawon ranta, ubangiji Allah ya jiƙan kafatanin wanda
suka rigamu gidan gaskiya Musulmi, idan tamu tazo Allah yasa mu cika da kyau da
imani_)
IN THE MEMORY OF LATE HAJIYA AISHA MUHAMMAD, I DEDICATED THIS PAGE TO LATE HAJIYA
AISHA MUHAMMAD (BABA) MAY ALLAH SUBHANAHU WATA'ALA, GRANT HER JANNATUL FIRDAUSI
AMEEN _
142_143
Yusuf ya dinga jujjuya takardar nan, ya kalli Barrister Hafiz yace "Ya akayi ta
rubuta takadda a bani?"
Barrister Hafiz ya matso daf da Yusuf, ya shiga yi masa magana ƙasa ƙasa (ni kaina
da nake ɗakko rahoton banji me yace masa ba)
Yusuf ya sunkuyar da kai yana sauraren Hafiz, Hafiz ya gama gaya masa abunda ze
gaya masa, Yusuf ya dinga jinjina kai, Hafiz yace "ka sairaremu nan da wani ɗan
lokaci, mungode sosai"
Sukayi musabiha da Yusuf, suka miƙe suk tafi, Yusuf kuma aka maida shi inda yake,
hannunsa ɗauke da takaddar da'akace Widad ce ta bayar a bashi, yaje ya samu guri ya
zauna yana jujjuya takaddar da'aka bashi yana sake karantawa.
A hankali ya furta "Allah yasa kina lafiya Widad, koba wane hali kike Allah ya
kuɓutar dake, ya sake ƙaddara saduwarmu dake"
Widad tana nan a tunanin Allah yasa saƙonta ya isa inda ta aika shi, dan zuwa yanzu
ta sare da zata bar gurin nan, dan bata ga hanyar barin gidan nan ba, Amma Allah
yasa kafin ta mutu Yusuf ya yafe mata, karta mutu yama ɗauke da pain ɗin bada
shedar ƙarya da tayi akansa.
Da ta lumshe ido se hawaye, wani na bin wani, tana tunanin anya zata samu sassauci
game da wannan halin ni 'yasu da take ciki? Ita dai fatan ta Allah ya haɗa ta da
Yusuf ta nemi afuwarsa.
Ganin Widad dagaske ba zata bashi inda dukiyar take ba, tana ta faman raina masa
hankali, ya ƙudurce tabbas ze ɗakko mahaifiyar Yusuf yayi garkuwa da ita, ko ta
bashi, ko kuma ya illata ta a gabanta, tunda ya fuskanci bata son duk wani abu daze
saka Yusuf da ahalinsa su shiga damuwa.
Dan haka ya ɗakko wayarsa, ya kira me Adda "Allah ya temaki Oga, in ba kai waza mu
duƙawa muci?"
Bulama yace "kai kana inane? Kana cikin garin nan ne?"
"A'a, na ɗan baza yin wata harƙalla, duk cikin iya taku da ɓoyewa masu saka na
mujiya"
"ina son ganinka a yau ba se gobe ba, a cikin daren yau nake so kaje ka ɗakkomin
tsohuwar wancan sakaram yaron"
Me Adda yace "sa hankalinka a inuwa, turo adreshinta, zamuyi ram da ita mu kawo
maka"
Bulama yace "Good, zan turo maka adreshin, a daren yau nake son a gama komai, ku
ɗakkota ka kawomin ita"
Likitoci suka yi iya abunda zasu iya akan Mahaifiyar Nurat, amma babu wani cigaba,
ta gaza farfaɗowa gashi jini yaƙi tsayawa, numfashi kawai take amma sam zuciyarta
bata harbawa yadda yakamata, tuni danginta da 'yan uwanta suka cika Asibitin,
Alhaji Musa yayi mamakin yadda akayi suka ji, bayan shi dai be kira kowa ya gaya
masa ba.
Nan suka shiga tambayar ba'asi, akan yadda akayi' yar uwarsu ta faɗo daga kan bene?
Alhaji Musa yace "Wallahi ta fito ne daga ɗaƙi, zata sakko daga kan bene kawai ta
zamo ta gangaro, dama tun safe take cemin tana jiri, nace mata ko Asibiti zamuje
tace in bari seda yamma, ina ga harda jirine ma ya ɗebe ta yasa ta faɗo"
Barrister Khalil kallon Alhaji Musa kawai yake, ji yake tamkar ya danƙo wiyansa ya
rufe shi da duka, dan sam beji ya gamsu da maganar da ya faɗa ba.
Amal ta shirya tsaf, dan taje a zubar mata da ciji ba tare da mahaifiyarta ta san
halin da take ciki ba, gaba ɗaya ta tattara ta zuba musu ido, dan itama fama take
da kanta, ko gani bata iyayi sosai sedai dususu saboda tsabar ɓacin rai da damuwa
da yake ta'azzara mata hawan jini, gaba ɗaya ta koma kamar wata zararriya, yauma ta
tashi tana ta fama da kanta, jiri da ciwon kai jininta ya hau, tana kwance a falo
tana fama da kanta, Amal tazo zata fice.
Amal tace "tana ɗakinta, inaga yauma tayi shaye2 tana can tana bacci"
. Hajiya Halima tai ajiyar zuciya, tace "kekuma ina zaki? Naga kamar fita zakiyi"
"Amma kina kallon yadda nake fama, ina kwance ina fama da kaina, amma zaki saka kai
ki fice ki barni a haka?"
Amal tace "Mummy, na matsu in fitane ina da wani uzuri na gaggawa, ba daɗewa zanyi
ba, ga Ramlah can kuma tana nan ai, ba daɗewa zanyi ba"
Tai maganar tana tafiya, a haka harta bar falon ta fice abunta.
Tana zaune a mota ta kira Alhaji Haruna, ya ɗaga ba tare da yasan wanda ya kira shi
ba, "na gaya maka ina ɗauke da juna biyu, Amma kaƙi ɗaukar kowane mataki ko? To ka
saurareni wallahi zan tona maka Asiri, duniya taji abunda ka aikata"
"wai ke ni dan Allah ya kike son inyi ne? Har yanzu baki fanshe bane? Me kike so
inyi miki?"
'haka ma zaka ce? To shikenan, ciki dai nakane, kai kayi shi, wallahi ba zanyi abun
kunya ni kaɗai ba, na gaya maka'
Suka yi waya da wannan Nurse ɗin, wadda tace zata taimaka mata ta zubar da cikin
nan, ta gaya mata a dai dai inda zasu haɗu.
Aikuwa tana zuwa suka haɗu, ta ɗau Nurse ɗin a motarta, ta fara nunawa Amal hanyar
zuwa Gurin, Amal tace "nifa gaskiya tsoro nakeji, wallahi ji nake kamar wani abu ze
faru"
Nurse ɗin tace "haba ke kuwa, amma dai wannan ne karon farko da zakiyi abortion
ko?"
Amal ta jinjina kai alamar eh, Nurse ɗin tace "karki damu mana, ai ke naki cikinma
ƙaramine, nan da nan za'a cire shi babu wani tashin hankali, ɗan pain ɗin kaɗanne,
ke ciki koya kai 9 months Doctor Hamisu ze jajjageshi ya cire shi tsaf, dan haka ki
kwantar da hankalinki, komai ze tafi normal"
Sukaje Asibitin, Nurse ɗin ta jata har office ɗin doctor Hamisu, suka tarar yana
aiki a system, Nurse ɗin ta gaisheshi tace "Doctor, ga customer fa cikine take son
a cire mata"
Amal tace "nima ban sani ba, amma naji da akamin test ance watansa ɗaya be cika
biyu ba"
Doctor Hamisu yace "ai wannan ba abun damuwa bane ba, za'a cire shi ba wata wahala,
an gayamiki kuɗin aikin?"
Amal tace "eh nima ina ganin kamar na sanka fa, kamar likitan dake duba Widad
shekarun baya"
Amal ta ɗan ɓata fuska tace "wallahi wanine yamin Akuya, daga zuwa kai masa saƙo,
shiyasa nake son inyi acire kafin ta gane"
"ba matsala, karki damu kinji yanzu za'a cireshi insha Allah, Nurse maza kaita
ɗakin da ake aiki ta kwanta ta jirani".
Aka kai Amal ɗakin, ta kwanta tana jiransa, gabatan se faɗuwa yake, tana tunanin
kar wani abu ya faru, bayan an cire cikin "
Tana nan kwance, yazo ya ɗaura mata ruwa, ya bata wani magani ta sha, ko mintuna
goma ba'ayi ba da saka mata ruwan, da bata maganin ta fara wani irin ciwon mara
kamar zata mutu, ta dinga murƙususu, kafin kace meye wannan tuni jini ya fara
malala daga jikinta, bayanta kamar ze ɓalle da ƙugunta, ta dinga antayar da jini,
Nurse ɗin nan ta dinga temaka mata, yazo ya sake mata wasu allauran, yace
"Sister, maza idan ta ɗan huta ki kaita gida ta samu rest, jinin ze tsaya insha
Allah"
Haka kuwa akayi, Ta kai Amal har gida, Amal ta shiga da motar, a dudduƙe ta tafi
ɗakinta ba tare da kowa ya ganta ba, taje ta baje akan gadonta, dan wani irin sanyi
take ji da jiri a lokaci ɗaya.
Duk yadda Suleiman yaso ɓoyewa Umma yadda shari'ar Yusuf ta kaya seda taji a radio,
kasancewarta mace ms son jin radio, da farko zamanta a gidan tare da Surayyah ta
ɗanji daɗi, dan koba komai motsin mutum rahama ne, tana ɗebe mata kewa ita da yaran
ta, kuma ta kan sakata a gaba lallai se taci Abinci, ta sha magani amma tunda taji
hukuncin da akayiwa Yusuf ta kasa zaune ta kasa tsaye, se kuka nan da nan jikinta
ya nemi ya rikice saboda tashin hankali da damuwa.
Suleiman yaje ya sameta a ɗakin da take, yace "Umma, babu yadda za'ayi Yusuf yayi
wannan shekarun haka a gidan yari, ai kowa yaga irin shari'ar da akai, ana nan ana
wani ƙoƙari, sedai cikin sirri ake komai, ki kwantar da hankalinki, nina gayamiki
da yardar ubangiji se Yusuf ya kuɓuta, amma kidena wannan kukan haka da damuwa dan
Allah "
Umma tace " Haba Suleiman, kaifa ka cemin duk wanda yai yunƙurin taimakonsa
barazana ake masa, taya ya za'a samu wanda zasu taimaka masa alhalin kowa yana
kallon yadda akai shari'ar, kuma babu wani taimako da aka masa? Ni na karaya kawai,
haka Allah ya ƙaddara masa rayuwarsa, ƙaddara babi babi, daga wannan se waccan "
tai maganar tana kuka me taɓa zuciya.
Sulaiman yace" Umma, kece fa kike bani misali da Annabawan Allah, da irin jarabtar
da Allah yayi masa, dan haka mu ɗauka jarrabawar sa ce a haka, kuma Allah yasa
sanadin ɗaukakarsa ne yazo a haka, duk yadda Allah ya kai ga jarabtar bawansa, se
kinga ta wani ɓangaren Allah ya masa wata ni'ima wadda ba kowa yayi wa ba, ki
kwantar da hankinki Umma, shirye shirye sunyi nisa ta ƙarƙashin ƙasa, kuma insha
Allah zamu bawa maƙiya kunya "
"Addu'a ina nan ina yi, Allah yayi maka albarka da kai da iyalanka, ubangiji Allah
ya jiƙan magabatanka ya rahamshesu, ubangiji Allah ya raya maka zuriyar ka akan
tafarki madaidaici, yasa su zamo masu jin ƙai kamar kai, Matarka Allah yayi mata
albarka ya sake haɗa kanku, tunda abun nan ya samu ɗana kake tsaye a kaina, kana
bani gudunmuwa iyayinka, kaine dana ganka nake jin daɗi, nake jin daɗin yadda kake
tausata nagode nagode "
Suleiman yace " bakomai umman Yusuf, karki damu duk yiwa kaine, ni ban rayu da
mahaiyata ba, marayane ni tun ina yaro ƙarami, ina jinjina soyayyar uwa ga ɗanta,
shiyasa nasan kina cikin damuwa rashin Yusuf da dole kina buƙatar a tausasa miki,
ga Ɗanki mutum ne nagari kamili, wani abu da Yusuf ya taɓa yimin da bazan manta ba,
lokacin mahaifina yana ciwon ajali sunje duba shi, baya iya cin Abinci sam, Yusuf
ya kai masa dafaffen ƙwai da kayan marmari, naje siyo masa magani Yusuf ya zauna
yana bashi ƙwan nan a baki, bayan ya gama bashi Baba yayi amai, ya ɓatawa Yusuf
jiki, kayansa masu kyau a jikinsa suka ɓaci, amma be nuna damuwarsa ba ya ɗaga shi
ya gyara masa jiki, kullum aka tashi daga gurin aiki se yaje ya duba mahaifina, har
suyi hira, alhalin ni a lokacin ko kulani bayayi sosai, dukda ina shugabansa a
gurin aiki, duk ranar da beje ba Baba ya dinga tambayar ina yaron nan me fararen
idanuwa kuwa? Ranar da Baba ze bar duniya seda yayi masa addu'a sosai, bazan manta
ba, naji daɗin yadda ya nuna damuwa akan mahaifina fiye da tunani, dukda wannan
abun alkhairi da yayi min ba fiye shiga sabgata ba sedai in sha'anin aiki ya
haɗamu, hakan ya tabattar min halinsa ne a haka, halin taimako da tausayi ga
mutane, shiyasa bazan taɓa bari inga wani mummunan abu ya samu iyayen Yusuf ba"
Umma tai ajiyar zuciya tace "Kaga ni be taɓamin wannan hirar ba"
Suleiman yace "Ai Umma wannan ɗan naki halinsa se shi, miskiline ajin farko sedai
akwai tausayi da jin ƙai, ni dai fatana kiyi haƙuri ki kwantar da hankalinki"
(Wato shi alkhairi a rayuwa, idan har zaka aikata shi ko bayan ranka waninka ze
mora, Kayi ƙoƙari kayi abunda mutane zasu dinga tunaka da alkhairin ka, ba da mugun
aiki ba)
Kamar yadda Bulama yai umarni, cikin dare su me Adda suka bazama gidansu Yusuf,
inda suke kyautata zaton Umman Yusuf tana nan.
Amal har dare yayi tana fama da matsanancin ciwon mara kamar zata yi hauka, gashi
ta kasa cin komai, se uban amai da take faman yi, ga jini se zuba yake yaƙi tsayawa
ita kaɗai a ɗaki babu wanda yasan halin da take ciki sam.
Gaba ɗaya babu wanda hankalinsa ya kai kan cewar Nurat bata nan se bayan kwana
ɗaya, tai ihun tayi bugun ƙofar babu wanda ya ji balle ya buɗe ta, gashi bata san
halin da mahaifiyarta ke ciki ba, sakamakon taji ihutmnta amma bata da tabbas ɗin
abunda ya faru da ita.
Khalil ne ya kalli Alhaji Musa yace "wai ina Nurat ne? Tunda mu kazo Asibitin nan
ban ganta ba fa"
Cikin inda inda Alhaji Musa yace "Amm da yake itama bata da lafiyar ne, ban san ya
nata jikin ba, bana son hankalin ta ya tashi ne, bari inje gidan in taho da ita"
Maman Khalil tace "kai Khalil, wai nan a kotu muke ne? Jimin ja'irin yaro ka tasa
mutum a gaba da tambayoyi".
Khalil yace "Allah ya bada haƙuri, muje semu taho nida Nurat ɗin kai seka huta
kawai".
Maman Khalil tace "kuje tare mana, ai bakomai se su taho taho shida ita"
Khalil ya saka Alhaji Musa a gaba, da wani irin kallo wanda ya kasa tantance na
menene.
Haka suka tafi kowa a motar Alhaji Musa, koda sukaje gidan Alhaji Musa yace "bari
in kirata tana saman bene"
Khalil yace "shikenan babu laifi, bari in jira a nan" ya zauna a falo.
Alhaji Musa ya hau sama da sauri, danshi gaba ɗaya ya manta daya kulle Nurat a
ɗaki, yana zuwa ya buɗe ya tarar da ita a baje a sume a ɗakin, a gigice ya ƙarasa
yana kiran sunanta amma bata motsi, da sauri ya ɗakkota ya sakko daga benen,
hannunsa riƙe da ita.
Itama a emergency ɗin aka karɓeta, aka rufu akanta don ceto rayuwarta itama,
rufetan da yayi dama bata karya ba, ga kuka ga damuwa ga tashin hankalin da ta
shiga jin ihun mahaifiyarta, hakan yasa ta shiga tashin hankali, garin kuka tai
shaƙuwa numfashinta ya sarƙe ta faɗi, ga yunwa dan haka abun ya tarar mata, daya
buɗe ɗakinma ya ɗakkota numfashinta iya ƙirjinta ne kawai, babu inda yake motsi a
jikinta.
Alhaji Musa ya koma reception ya zauna ya dafe kai, yana tunanin wannan wace irin
masifa ce haka kashi kashi? Ze kashe iyalansa ɗaya bayan ɗaya da kansa, da hannunsa
duk a dalilin aikin banza, dalilin neman kare a Karofi, Bulama nata musu gafara sa
amma babu ƙaho tsayin shekaru.
Bulama yana ta jiran yaji su me Adda sun bashi feedback akan aikin daya sa kasu,
amma shiru ba suyi magana ba, ya kira layin me Adda babu adadi amma tun tana shiga
ta dawo bata shiga, sema ace masa line busy, daga ƙarshema aka kashe wayar gaba
ɗaya.
Alhaji Musa yana nan zaune, aka kira shi a waya aka sanar masa da an gano inda
Anwar yake, yayiwa Bulama magana, akan me yakamata ayi? An kira wayarsa bata shiga
se ace busy.
Kamar ya share ya basar, amma dai ya kira Bulama, Bulama ya ɗaga yace "ya naji
muryarka a hakane? Baka da lafiya ne?"
"Wallahi abubuwa sun damalmalemin gaba ɗaya, bisa tsautsayi daga zan ture Maman
Nurat daga bene in sakko, bisa tsautsayi ta faɗo kwananta biyu a Asibiti har yanzu
bata hayyacinta, na rufe Nurat a ɗaki saboda ta gano halin da ake ciki, ta gano da
saka hannuna a abunda ke faruwa a gidan Daula, itama gata can a emergency bata san
wake kanta ba, gaba ɗaya na rasa abunyi ma"
Maimakon Bulama ya tausayawa Alhaji Musa halin da yake ciki, seya haushi da faɗa
"wai kai wand irin mutum ne haka Musa? Ya za'ayi kabari yarinyar ka ta gano?
Gaskiya baze yuwu ba sam, wancan karon dana maka magana ashe baka ɗau mataki ba? To
dole kasan yadda zakayi tun wuri dole a ɗau matakin daya dace akanta, bazs yuwu ta
tona mana Asiri ba"
Ran Alhaji Musa yai matuƙar ɓaci da jin Kalaman Bulama, bs tausaya masa halin
dayake ciki ba, amma ya haushi da faɗa, dan haka a hasale yace "kaga ya isa naji,
ance in gaya maka an gano inda Anwar yake, ɗan gidan Hajiya Halima"
"Aina riga na gama bada umarni, a kasheshi kawai dan baze yuwu a ƙyaleshi ba"
Alhaji Musa yace "seka kirasu ka gaya musu, ni yanzu ina cikin wata matsalar ne"
Yana gama faɗin hakan ya katse kiran, tunani ya fara yi, Hajiya Halima tana da
Alaƙa da Bulama 'ya' yanta kamar nasane, amma yace a kashe ɗanta dan kar Asirinsa
ya tonu, dan haka babu shakka idan ya gama da Anwar kan Nurat ze dawo.
Ai nan da nan ya ɗau wayarsa ya kira Hajiya Halima, ta ɗaga wayar da ƙyar alamar
tana jin jiki, tai sallama a hankali
Alhaji Musa yace "malama idan zaki ware muryar ki ki ware, an gano inda ɗanki yake
Anwar, amma Bulama yace A kasheshi dan karya tona masa Asiri....
AYSHERCOOL
07063065680
12/7/21, 11:04 PM - Buhainat: LITTAFIN KUƊI NE, DAN ALLAH KI SIYA KAFIN KI KARANTA
BA DANNI BA DAN ALLAH, LITTAFI NA ƊAYA KYAUTA NE WANNAN NA SIYARWA NE
NORMAL GROUP ₦300
VIP ₦500 NE KITURA TA WANNAN ACCOUNT ƊIN
0009450228
JA'IZ BANK
AISHA ADAM
SE A TURA SHEDAR BIYA TA WANNAN LAMBAR
07063065680
(Albishir ga masoya, ma'abota bibiyar litattaafaina, dama ta samu zaku fara samun
litattaafaina na audio, akan YouTube channel ɗina me suna Cool Arewa TV
https://youtube.com/channel/UCD5vnvA5laU8ti4LLz2_QEg
Kuyi liking sannan ku danna subscribe, domin fara samun litattaafaina na audio,
nagode sosai da ƙaunar ku gareni"
_(INNALILLAHI WA INNA IALAIHI RAJI'UN ina amfani da wannan damar gurin miƙa saƙon
ta'aziyya ga Ɗaukacin zuriyar Hajiya Aisha Muhammad (Baba) bisa babban rashi da
mukayi na rasuwar ta ina fatan ubangiji Allah ya jiƙan ta yai mata rahama, ya kai
haske kabarainta, ubangiji Allah ya duba zuriyar da ta bari, ya bata ladan
ɗawainiya da iyalI da tayi tsawon ranta, ubangiji Allah ya jiƙan kafatanin wanda
suka rigamu gidan gaskiya Musulmi, idan tamu tazo Allah yasa mu cika da kyau da
imani_)
IN THE MEMORY OF LATE HAJIYA AISHA MUHAMMAD, I DEDICATED THIS PAGE TO LATE HAJIYA
AISHA MUHAMMAD (BABA) MAY ALLAH SUBHANAHU WATA'ALA, GRANT HER JANNATUL FIRDAUSI
AMEEN _
Ina ma'abota son gyaran jikinsu yau ga maman sayeed collection tazo muku d
gangariyar maganin gyaran breast (nono)
Maganinmu yayi fice gurin gyaran nono kikai amfani d maganinmu cikin 1week
zakiga result maganinmu yana ciko d nono suyi bul² nono ko yakai silifas y mushewa
kikai amfani dashi zakiga canji
Maganinmu Bashi d side effect mun hadashi d tsirrai d saiwoyi kala² domin Y'an
uwa mata
Muna kano muna tura maganinmu ko wane state d yardar Allah meso yakira wannan
number 08120337219
Chat 08063114606
144_145
Ai zumbur ta miƙe zaune tace "ban gane a kasheshi ba? Anwar ɗin nawa za'a kashe? Me
yayi masa haka?"
Alhaji Musa yace "ke nifa tuni na dawo daga rakiyar mutumin nan, Azzalumi ne kawai,
kansa ya sani bashi da imani sam, ni kaina yanzu haka muna Asibiti nida su Nurat,
amma gaba ɗaya ko yamin jaje se masifa da tashin hankali da yake min, shiyasa na
kwashi kuɗina na saka a siyasa, in samu su bani takara in huta da wannan mulkin
mallakar da yake mana, ga uwar dukiyarmu da muke narkawa amma har ynzu babu wani
bayani "
Hajiya Halima ta fashe da kuka tace " ni Bulama zeyi wa haka? Anwar kamar ɗa yake a
gurinsa amma shine zece a kashemin shi? Baze yuwu ba kuwa "
Ta ajiye wayar, ta miƙe ta shiga ɗakinta ta zura doguwar riga, kusan ƙarfe goma
saura na dare, amma tayi waje ta ɗau mota ta fita ta tafi gidan Bulama a daren.
Shikuma Bulama yana zaune yana ta nazari akan yadda ze ɓullowa al'amura da suke
neman damalmale masa, ya dinga kiran layin su Me Adda amma shiru babu Labari, waya
taƙi shiga sam.
Masu gadi kansu sunyi mamakin ganinta a wannan daren, kamar wata mahaukaciya ko
gabanta bata gani sosai saboda tashin hankali, kai tsaye ya shiga falon dake ƙasa
tana bala'i "Ina Bulama yake? Ina Bulaman?"
Iman ce zaune a falon tana kallon zee world tace "Mummy lafiya kuwa?"
"ban sani ba, ina uban naku yake tsohon macuci azzalumi?"
Iman ta kalleta da mamaki jin irin furcin da take akan mahaifinsu wanda ya kasance
ɗan uwa a gareta, Iman tace "Mummy ya riga ya hau sama, inaga ma ya kwanta fa"
Ai bata tsaya jiran me Imana zata kuma ce mata ba ta haura saman da kanta, ba zato
ba tsammani ya ɗaga kai yaci karo da Hajiya Halima a tsaye a kansa.
Ya kalleta yace "Halima, lafiya kuwa zaki zo a daren nan? Bakya jira ayi miki iso
kawai ki hauromin ɗaki haka?"
"Dalla rufemin baki, me zaka gayamin har wani iso zan jira ayimin, munafuki
azzalumin banza dana wofi, tsawon shekaru ina maka aiki, kana sani duk abunda kaga
dama ina maka, dan ka cinma burinka ba tare da na nuna gazawata ba, shine halin
naka na baƙin kumurci zaka gwadamin, shine kayi umarni da idan anga Anwar a
kasheshi, ɗan nawa za'a kashe? Wallahi baka da imani ba kada Alƙawari tun wuri ka
dakatar da wannan maganar idan ba haka ba Wallahi ran ɗana baze tafi a banza ba"
Zazzaro ido Bulama yayi ya dinga ƙifta mata ido akan tayi shiru, amma tace "bazan
shirun ba, wallahi babu inda zani se an dawo min da ɗana"
"Halima wai wace irin magana kike hakane? Kamar yaya nace idan anga Anwar a
kasheshi? Me Anwar yayi min wanda zesa ince a kashe shi, ni da na kaiwa jam'ian
tsaro maganar dan ayi bincike akansa a gano inda yake ya zakice nace a kasheshi?
Wani munafukin ne ke neman haɗani da 'yar uwata?"
" Kaga bana son kame kame da ƙaryar banza, wanda ya gayamin baze maka ƙarya ba,
macucin banza da na wofi kuma wallahi idan ɗana ya mutu you must pay for it,
wallahi aka kashemin Anwar seka fanshi ransa, nima kasan halina ka san abunda zan
iya aikatawa "
Gaba ɗaya Bulama ya dirirce ya rasa abunyi, ya shiga tsuma yana fatan Allah yasa
wani beji abunda ta faɗa ba.
Ya biyo bayanta ya leƙa, yaga ba kowa a falon ƙasa dukda ɗakin a rufe yake babu
wanda ze iya jiyo me sukayi, ya koma bedroom ɗinsa ya tarar da Hajiya Sarah tana ta
baccinta hankali kwance, yai ajiyar zuciya tare da tunanin bata jiba, amma ya zauna
yai shiru akan gadon yana tunani, tabbas babu wanda ze gayawa Halima wannan maganar
idan ba Alhaji Musa ba, tabbas dole yayi maganin Alhaji Musa.
Cikinsa ne ya murɗa ya tashi ya tafi banɗaki, kusan kwana huɗu kenan yana fama da
gudawa taƙi tsayawa, dan haka ya sa ransa idan ya gama da wannan matter ɗin zeja
yaga likita.
Yusuf se sake juya takaddar nan yake, yana tunanin wani hali Widad ɗin ke ciki,
tabbas yasan da tana da dama bazata barshi a gurin nan ba, dole akwai wani abu da
yake gudana a ɓoye, idan ya kalli sentence ɗinta na ƙarshe na ba lallai su sake
haɗuwa ba se yaji gabansa ya faɗi, lallai ko a ina take tana cikin mawuyacin hali,
"Allah ya ƙara haɗa fuskokinmu my wife, Allah yasa kina hannu na gari, i love you
too" yai maganar a hankali tare da lumshe idonsa.
Rayuwar da suka yi tare a ƙauye ta dinga dawo masa, koba komai zamansa da ita ba
ƙaramin farinciki ya samu ba, zamansu a ƙauye yasa Ƙwaƙwalwarsa da zuciyarsa ta
samu hutu na wani ɗan lokaci, ya daɗe beji cin zarafi da gorin rashin iyaye daga
mutane ba, sedai matukar kewar Ummansa da yayi, be sake zaton ze samu wadda zata
aureshi ba saboda rashin nasaba ba, sedai cikin hukuncin Allah ya auri yarinyar da
zuciyarsa ta mato a sonta, dukda nisa da ratar dake tsakanin su, yarinyar da manyan
wanda suka isa ma basa gabanta, soyayyar ma bata yadda da ita ba, amma Allah ya
ƙaddara Aurensu, har suka yi zama cikin farin ciki, ya dinga tuna irin Shagwaɓarta
wauta da yarinta wasu lokutan, ya tuna lokacin da take koyar tankaɗe, da sanda take
wa Abincin garin kallon banza, da yadda ta dage ita seta samu ciki, da irin kallon
da take masa idan ya tsokane ta.
A hankali ya sake lumshe ido yana murmushi, sekuma ya tuna yadda ta shiga damuwa
daya bata labarinsa, da yadda ta dinga kururuwa tana kuka tana gaya masa tana sonsa
lokacin da aka kama shi a garin, da yadda taje kotu ta bada sheda akansa, ga
shekarun da aka yanke masa a gidan yari, ga abunda ta rubuta masa kawai se yaji ya
karaya hawaye ya shiga bin gefen idonsa, baya tunanin ze sake wata rayuwa me daɗi a
nan gaba, mussman kasancewa da Widad a inuwar Aure.
Da ƙyar likitoci suka samu Nurat ta dawo hayyacinta ta samu bacci, aka sa mata
ruwa, sedai harta farfaɗo ɗin numfashinta da vital signs ɗinta suka daidaita bata
gane mutane sosai, saboda ta galabaita an samu dai bacci ya ɗauketa cike da fatan
idan ta tashi zata iya dawowa hayyacinta gaba ɗaya, mahaifiyarta kuwa gaba ɗaya har
yanzu ba'a gano kanta ba, tana kwance ne kawai, numfashi ne kawai a ƙijinta, banda
haka babu abunda yake aiki a jikinta, sam bata san abunda ke faruwa ba, shi kansa
numfashin nata da ƙyar take yinsa wasu lokutan, saboda ta zubar da jini sosai, kuma
ana kyautata zaton ta samu rauni a cikin kanta, sakamakon buguwa da tayi, likitoci
sun rubuta mata hoton Ƙwaƙwalwa dan tabattar da abunda yake damunta.
Abu kamar wasa, jini yaƙi tsayawa Amal, se aikin zaryar banɗaki take, jini se zuba
yake babu ƙaƙƙautawa, ta rarrafa ta haɗa Abinci tana ci kota samu sauƙin wannan
wahalar haka, zuciyarta tana ƙuna akan yadda Alhaji Haruna ya cuce ta, Hajiya
Halima ta fito falon ta zauna ta dafe kai ta kalli Amal tace
"wai kuwa lafiyarki ƙalau kuwa? Gaba ɗaya kin wani ɗashe kinyi fari ƙal, kamar baki
da jini a jiki, ko baki da lafiya ne?"
Hajiya Halima tai ajiyar zuciya tace "Amal kin kuwa san abunda Bulama yaimin?"
"wai an gano inda Anwar yake, amma yace wai a kasheshi saboda karya tona Asiri"
"Naje har gidansa jiya da daddare, na ƙare masa tatas, nace wallahi aka kashe min
ɗana seya fanshi ransa da nasa ran kona 'ya' yansa"
Amal tabi mahaifiyarsu da kallo, wani irin baƙin ciki ya turnuƙeta, duk
mahaifiyarsu ta ɗaiɗaita rayuwarsu da kanta, kowa yana karɓar nasa kason ɗaya bayan
ɗaya.
Ramlah ce ta fito tana tangaɗi, tana magana cike da maye ta tsaya a tsakiyar falon
tace "Wai ni.... Waini Fahad baze Aureni bane... Bazaki ce ya aureni ba ko? Wa..
W.. Wallahi kuwa bazan dena shaye2 ba tunda ya lalatani, ku.... Kuma... Kumaaa ai
shikenan tunda nasan Na sakawa Bulama cutar tunda shima ya sakamin... Wallahi idan
baka Aureni ba sena sakawa Wannan yaron Ramadan ma, idan yaso kow... Ko..... Kowama
ya samu ni za'ayiwa hauka? Ya.. Ya ɗauka bani da wayo hmm baka san Rmalha bane"
kawai ta faɗi a gurin tana juyi tana ci gaba da sambatu marasa kan gado sam.
Hajiya Halima ta kalleta tace "Ramlah wai wace cutar kike magana akai ne? Wace irin
cuta?"
Ramlah bata san me take ba, juyi kawai take yi tana wasu surutan irin na marasa kan
gado, Amal kam tasan babu mamaki idan akace Fahad yana ɗauke da wannan cutar me
karya garkuwar jiki, amma sedai dagaske Ramlah take tana mu'amala da Bulama ma
kenan, gaban Amal ne ya faɗi kardai ace itama tana da wannan cutar, miƙewa tayi da
sauri zata tafi ɗakinta, Hajiya Halima tace "Amal ina zaki? Kina jin maganar da
gake faɗa? Ko dai duk a cikin maye take ne?"
Amal tace "tunda ki kaji ta faɗa a maye, to ko ba'a mayen bama ya faru, sedai fatan
Allah ya kyauta"
Amal ta tafi ɗakinta, dan itama fama take da kanta, wannan azabar ciwon marar da
zubar jinin sun isheta haka.
Anty Saddiƙa ƙanwar Maman Nurat itace a gurin Nurat, itakuma maman Nurat ba'a barin
kowa ya shiga inda take in ba likitoci ba, saboda tana ƙarƙashin kulawa ta
musamman, Anty Saddiƙa taje salla Khalil na zaune a gurin Nurat, ai kuwa ta farka
ta zaci zata ganta a ɗakin Dad ɗinta ya kulle ta, sedai tana buɗe ido tai arba da
wani gurin daban, ta yunƙura zata tashi zaune, Khalil ya taho da sauri ya riƙeta
yace "yi haƙuri, ki kwanta kinji, karki gaggawa jikinki babu ƙwari"
Ya ɗakko ruwam roba, ya buɗe ya bata ta sha, har ze gyara mata kwanciyarta ta
kwanta, ta riƙe shi gam tana kallonsa, tana ƙoƙarin tuna meyafaru ihun Mummynta ta
tuna, nan da nan ta razana tace masa "Mummy, Khalil Mummy na tana ina?"
Nan ta kwashe duk abunda ya faru ta gaya masa, yai shiru yana nazarin maganganun
Nurat, cikin kuka tace "ina Mummy take? Dan Allah ka kaini in ganta dan Allah"
Khalil yace "ki kwantar da hankalinki, likitoci na can na kula da ita, idan ta
farka zata zo ki ganta"
"Bakomai, ta faɗi ne kawai saboda Dad ɗinki ya rufeki, bari Anty Saddiƙa tazo ta
temaka miki kiyi wanka"
Bayan Saddiƙa ta shigone, Khalil ya tashi ya fita, a reception yaje ya samu Alhaji
Musa a zaune, dan idan yazo Asibitin ya duba su Nurat nan yake dawowa ya zauna, dan
gaba ɗaya haushinsa suke ji.
Ya zauna kusa da Alhaji Musa ya kalle shi yace "garin yaya ƙanwar mahaifiyata ta
faɗo daga bene?"
Alhaji Musa yace "wace irin magana ce wannan? Ba a gabanka nayi wannan bayanin
ba?"
Khalil ya kalle shi yace "to ya akayi ka kulle Nurat? Laifin me tayi maka"
Yai maganar yana ƙoƙarin miƙewa tsaye, amma Khalil ya tareshi yace "na tambayeka
kana ƙoƙarin tashi ina zaka?"
Khalil yace "labari na samu, daga majiya me ƙarfin gaske, dan haka nake tambayarka
garin yaya ka kulleta"
"ba rashin kunya bane, gaskiya ce dama ina da ayar tambaya akanka, wallahi muddin
na ganoka da wani abu ba dai dai ba, naga wani abun kayiwa ƙanwar mahaifiyata ta
faɗo daga bene, wallahi se nayi shari'a da kai, yanzun ma ba ƙyaleka zan ba, dan ba
ƙaramin haushinka nakeji ba"
Alhaji Musa zeyi magana, amma Khalil ya dakatar dashi yace "ba abunda zaka gayamin,
bana buƙatar jin komai daga gareka, amma tabbas ina nan ina bincike akanka, kuma
wallahi ina daf da tsayawa a kotu a gaban alƙali da kai"
Ya miƙe ya bar gurin, Alhaji Musa ya bi shi da kallo, yana tunanin me Khalil yake
nufine?
Bayan Ramlah ta tashi daga mayen da take ne, Hajiya Halima tazo ta sata a gaba tana
tambayarta "Ramlah wata magana naji kina yi ɗazu cikin maye, wai Fahad yasa miki
cuta, kekuma kin sakawa Bulama, wacce magana ce haka?"
Ramlah tace "Eh to, dukda kince a maye nayi maganar kamar yadda kiji maganar haka
take, Bulama shiya fara lalatamin rayuwa ta, na kamu da son ɗansa wanda hakan yasa
na biye masa, sedai Bulama yaƙi goyon bayan ya aureni, yake ta cusa masa 'yar Daula
ya aura saboda ya cika burinsa, soyayyar da nakewa ɗansa tasa na dinga biye masa ya
koyamin shaye2, ya koyamin rayuwar banza nida shi ba abunda bama yi, nace ya Aureni
amma yaƙi, kuma na gano yana da cuta me karya garkuwar jiki, dan haka na ƙuduri
aniyar ramawa na komawa mahaifinsa, kuma da yake ɗan Akuyane ya karɓeni, ba tare da
yasan ina mu'amala da ɗansa ba, dan haka shima ya kwasa, zuwa yanzu nasan uwarsa ma
ta ɗauka, hakan yasa na ɗan rage abunda ke zuciyata gara muyi jinyar tare hadda
ubansa"
Hajiya Halima ta ɗora hannu a ka tace "yanzu Ramlah abunda kikayi kenan? Ramlah
gaba ɗaya kika biyewa namiji kika barbaɗar da rayuwarki da mutuncinki? Kin kyautawa
kanki kenan?"
Ramlah tace "Mummy, bafa laifina bane wannan lamarin, duk wanda yazo neman Aurena
se ki nunamin ai shi ba sa'an aurena bane, ina gidan Attajiri kamar Daula bekamata
in Auri wane ba, ƙarewa ɗan uwanki ya biyoni ya lalata, na kamu da son ɗansa amma
yai biris dani, kuma akan idinki nake fita ai, kin taɓa tuhumata ina muke zuwa nida
Fahad idan mun fita? Me yasa? saboda idonki ya rufe ke burinki ya kawo miki masu
siyan kadarori ki tara kuɗi, don't blame me for this please "
Ta tashi tai tafiyar ta ɗaki ta bar mata falon, Hajiya Halima ta dafe kai ta fashe
da kuka, Bulama ya riga ya gama cutarta a rayuwa, ba ta san mema za tace a game da
shi ba, ya lalata mata rayuwar 'ya, kuma wai yanzu Ramlah na ɗuke da cuta me karya
garkuwar jiki, wanda ta samune a sanadin ɗansa, kuma ya dawo yace a kashe mata ɗa,
ta rushe da kuka harda sheshsheƙa, gaba ɗaya komai ya rikice mata, tama rasa meye
abunyi, wannan wace irin masiface haka take bibiyar ta? Daga wannan se waccan gaba
ɗaya 'ya' yanta sun barbaɗe, haka ta dinga gunjin kuka ita ɗaya a falo, Amal ta
ƙarawa ƙofar ɗakinta key, dan bata son tashin hankali.
Da safe Fahad ya shiga cikin gida, domin gaida iyayensa, sedai yan zaune a falon
Iman nata masa surutu amma sam hankalinsa baya kanta, yayi zurfi a tunani can ya
ɗago kai yace "ke wai ina Mummy ne?"
Ji yayi kamar ta watsa masa wuta, ta ina ze fara gayamata hakinda ake ciki? Koma ya
gayamata ai yasan aikin gama ya riga ya gana zuwa yanzu.
Yana nan zaune Sega Bulama yana Sakkowa, hannunsa ɗauke da jakarsa, Mummy sanye da
doguwar rigar baccinta, ta riƙo masa wayarsa suna hira, Fahad yaji kamar yaje ya
make Bulama saboda tsabar baƙin ciki da takaici, ga wani irin tausayin mahaifiyarsa
ya kama shi.
Hajiya Sarah ta kalli Fahad tace "yau Allah ya nufe ka da shigowa cikin gidan
kenan? Yaushe rabonka da shigowa"
Bulama yace "wai gidan ubanwa kake shigewa ne? Ko haryanzu yawon kake baka kwana a
gida?" ga mamakinsa seya ga Fahad ya maka masa wata uwar harara, abun da be taɓa yi
masa ba, ya kalli mahaifiyarsa yace "Mummy ina kwana?"
Kallonsa sukayi gaba ɗaya, Hajiya Sarah tace "Fahad, daga kan kayan shaye2 naka ka
taso ka shigomin falo ko? Shine har kake gayawa mahaifinka wannan maganar?"
Alhaji Bukar yace "ƙyaleshi, ina daf da maganinsa akan wannan mummunar ɗabi'a ta
shaye2, dank yake zancen, ban agogona zan fita ina da ayyuka da yawa a Office "
Yasa hannu ya karɓi agogonsa, yai waje bayan fitarsa Hajiya Sarah ta kalli Fahad
tace " Fahad, meyasa ka gayawa mahaifinka wannan maganar haka? Kai lalacewar taka
harta kai kayiaa mahaifinka haka? Me yayi maka? "
" Bakomai amma ka faɗa masa wannan maganar? Abunda kayi ya dace kenan?"
"to meyasa kayi, salon mutane suji suce ni nake saku a turbar banza, na ku
Wulaƙanta mahaifinku?"
"Nifa Mummy bakomai, kema da kin san me yayi da baki faɗi wannan maganar ba, kawai
dai Allah ya kyauta"
Ya mike a fusace ya baf falon, tabi bayansa da kallo, Iman tace "Mummy"
"Na'am"
"wai kuwa idonki biyu, jiya da Maman su Amal tazo gidan nan?"
Iman tace "wallahi tazo, bayan ƙarfe goma se bala'i take tana neman Daddy"
"subhanallah, Allah yasa ba'a akan Ramlah tazo ba, saboda kin san halin ɗan uwanku
sarai, ina kyautata zaton akwai alaƙar banza a tsakanin sa da Ramlah"
. "Mummy ya akayi kika sani?"
"last week na ganta ta fito daga sashinsa, na tambaye ta amma bata gayamin komai
ba, sema baƙar magana da tayi min"
Iman tace "Umma kiyi ta haƙuri, Yaya Fahad se Addu'a gaba ɗaya zamansa a ƙasar waje
ba abunda yasa masa se koyar mugayen halaye"
Hajiya Sarah tace "idan da zaman ƙasar waje dai to harda halinsa, meyasa shi Anwar
be lalace ba se shi? Bani da abunyi se dai yi masa addu'a, baya jin faɗa baya jin
rarrashi, babu wanda banyi ba, amma duk baya ɗauka"
"Mhmm Iman kenan, yaushene watarn ɗin? Mutum ya girma amma kullum ba hankali, Allah
ya kyauta dai kawai".
Yanzu ma Bulama yana zaune a Office, kiran wayar Me Adda kawai yaje amma taƙi
shiga, yai shiru can wayar ta fara ringing, cikin hanzari ya ɗauka ya zata me Adda
ne, sedai yaga baƙuwar lambace, ya ɗaga yai sallama
(Albishir ga masoya, ma'abota bibiyar litattaafaina, dama ta samu zaku fara samun
litattaafaina na audio, akan YouTube channel ɗina me suna Cool Arewa TV
https://youtube.com/channel/UCD5vnvA5laU8ti4LLz2_QEg
Kuyi liking sannan ku danna subscribe, domin fara samun litattaafaina na audio,
nagode sosai da ƙaunar ku gareni"
_(INNALILLAHI WA INNA IALAIHI RAJI'UN ina amfani da wannan damar gurin miƙa saƙon
ta'aziyya ga Ɗaukacin zuriyar Hajiya Aisha Muhammad (Baba) bisa babban rashi da
mukayi na rasuwar ta ina fatan ubangiji Allah ya jiƙan ta yai mata rahama, ya kai
haske kabarainta, ubangiji Allah ya duba zuriyar da ta bari, ya bata ladan
ɗawainiya da iyalI da tayi tsawon ranta, ubangiji Allah ya jiƙan kafatanin wanda
suka rigamu gidan gaskiya Musulmi, idan tamu tazo Allah yasa mu cika da kyau da
imani_)
IN THE MEMORY OF LATE HAJIYA AISHA MUHAMMAD, I DEDICATED THIS PAGE TO LATE HAJIYA
AISHA MUHAMMAD (BABA) MAY ALLAH SUBHANAHU WATA'ALA, GRANT HER JANNATUL FIRDAUSI
AMEEN _
146_147
Cikin Bulama yai wata irin ƙara yace "A dutse garin yaya haka ta faru? Ina tarin
kuɗin dana baka kaida lawyoyi, ya za'amin haka?"
'Aini kuɗin daka bani, nayi aikin daya dace da su, na rufe yaron nam amma doka ta
bashi damar ɗaukaka ƙara, kuma ya ɗaukaka ni yanzu shawara ɗaya zan baka, karka
sake a gane kana da hannu cikin wannan badaƙala dake faruwa, idan da hali ma ka
halarci zaman kotu da za'ayi, karka bari wani ya gane da saka hannunka"
Bulama yace "Innalillahi wa inna ialaihi raji'un, ko dai ƙasar zan bari gaba ɗaya
ne? '
" baza' a gane da saka hannunka ba, tunda manyan ƙasar nan da 'aya siyasa dama
jam'ian tsaro suna tare da kai, karkaji komai I will give you the necessary support
i can, ka kwantar da hankalinka fa"
Bulama kawai ya ajiye wayar, ya dafe kansa Fahad ne ya bankaɗo office ɗin kamar
wanda aka jefo, Bulama ya ɗaga kai ya kalleshi, ya mayar ya sunkuyar, Fahad ya
ƙaraso gabansa ya tsaya yace "wallahi Daddy ka bani kunya, ka zubar mana da mutunci
a idom duniya, ka cucemu ka zaluncemu kuma se Allah ya sakawa Mummy"
Kasa vane inda maganganun Fahad ɗin suka dosa yayi, dan haka yace "kai me kame
faɗane haka? Meye hakan?"
"dole ka tambayeni mana, dama Daddy kana alaƙar banza tsakaninka da Ramlah?"
"kai wace irin maganar banzace wannan? Ƙwayar taka bata sakeka a gidan ba shine ka
biyoni har nan za kamin hauka? Wacece kuma Ramlah"
Cikin shouting Fahad yace "niba hauka nake ba, dagaske nake, akwai haramtacciyar
alaƙa a tsakaninka da Fahad, kuma Asirinka ya tonu"
"wane banzan ne ya gaya maka wannan maganar banzar, mara tushe balle makama? Waye
wannan waima wace Ramlah kake nufi ne?"
"Ramlah dai, 'yar gidan Hajiya Halima kumabita ta gayamin, da bakinta ta gayamin"
A fusace Bulama yace "zaka fitarmin daga Office ko sena ci ubanka na tattaka ka,
dama akan tsini nake, saboda mahaukaci ne kai kamar ni, ni zan nemi wannan
yarinyar? Inyi uwarme da ita? Fitarmin daga Office kobin saka security su casamin
kai, kai ko kunya bakajiba, ina ubanka ka tunkareni da wannan maganar ba kai ba
ma'ana, kai data gayamaka meyasa baka yi bincike a kai ba? Kawai ta gayamaka
maganar banza ka hau kai ka yadda, fitarmin daga Office shashasha kawai "
Sekuma Jikin Fahad yai sanyi, dan ƙarya batawa Ramlab wahala, a ransa ya dinga
fatan Allah yasa ƙarya takeyi, yana fita Bulama ya share gumi ya zauna yace
" Jimin tsinanniyar yarinya, ni zata kwaɓawa aiki haka? Waini garin yaya abubuwa
suke ta cakuɗewa ne babu mafita sam a cikin lamuran, daga wannan se wancan? Kai
baze yuwu ba da sake gaskiya"
Mahaifiyar Nurat fa babu sauƙi a lamarin nata, dan a kwanaki ukun nan ko yatsan
ƙafarta bata motsa ba, yadda take a kwance a haka take, sedai a juya ta nan a
juyata can, babu wani cigaba kuma a wannan kwanaki ukun still, lokaci lokaci jini
na fita ta hancinta da bakinta.
Nurat ta ɗaga hankalinta akan san sanin Halinda mahaifiyarat ke ciki, amma se
dai ace mata tana ƙarƙashin kulawa ta musamman ta likitoci, dan haka bazata ganta
ba, Bata da aiki se kuka, danta fara zargin ko ta mutune ake ɓoye mata, Khalil neke
aikin rarrashi kullum cikin rarrashinta yake akan ta kwantar da hankalinta, Mum
ɗinta zata tashi zata warke da yardar Allah.
Sam bata son ganin mahaifinta yazo inda take, data ganshi se taji ranta babu daɗi,
mussman idan ta tuna irin muguntarsa da zalumcinsa, da rashin afuwarsa.
Bulama mussman ya shirya ya tafi gidan Justice A dutse da yamma, lokacin yasan ya
dawo daga gurin aiki.
Bulama yace "Nifa A dutse na kasa gane bayanin ka, ji naifa kace wai harda wannan
barrister me shegen bakin tsiya za'ayi shari'ar nan, yanzu meye abunyi kenan?"
A dutse yace "eh to, kaga dai ko ana hauka kasan A Adam baze karɓi bribe ba, ni
dai shawarata da kai shine karka yi wani Yunƙuri da zesa a ganoka, dan ba kaiba
harni zamu shiga cikin matsala, saboda irin shari'ar da nayi, musamman idan aka
gano na karɓi cin hanci daga hannuka, abun baze mana kyau ba"
Bulama ya dafe kai yace "yanzu shikenan, babu wata mafita kenan?"
Bulama yace "to shikenan, dan Allah idan da wani information ka dinga sanar dani"
A Dutse yace "Insha Allah, kar kaji komai, ba zasu yi Nasara ba"
Fahad kuwa yana zuwa gida, ya ɗau waya ya kira Ramlah, yana kira ta ɗaga.
Aikuwa tana ɗagawa yace "munafukar banza da ta wofi, ashe ƙarya kikewa Mahaifina
zaki haɗani faɗa da ubana, mara mutunci ƙaramar karuwa"
"Lallai Fahad, Bulama ya maida kai gaula, gashi ka ka raineni ka bani training a
harkar karuwanci, amma kuma na shallake tunanink, dan na kai inda baka kaiba, to
idan uban naka ya isa, ya kirani a waya a gabanka yace ƙaryane abunda na faɗa mana,
ko kuma yaje a binciki lafiyarsa ko yazo har gida ya sameni yace ƙarya nayi mana,
ai baka isa ka cuceni a banza ba, gidanku ma kun ƙara yawa masu ciwon, seku dage da
shan magani tare "
Ta katse kiran wayar gaba ɗaya, Fahad ya jinjina kai tabbas tunda ta dage babu ko
shakka mahaifinsa ya aikata abin da Ramlah ta faɗa, kuma da wuya idan ba'a sameshi
da cita me karya garkuwar jiki ba, dan tunda ya iya neman Ramlah to yana biye biyen
mata.
A hankali ya furta wayyo Allah Mummyna, ya nufi gida da sauri, yana zuwa ya tarar
da mahaifiyarsu Hajiya Sarah ta shirya ta sha gayu zata fita, dama gata mace me
iyayi da son kwalliya.
Fahad yai murmushin ƙarfin hali yace" kyau kikamin Mummy "
Jiki a sanyaye Fahad ya tafi part ɗinsa, yana zuwa ɗakinsa ya zube akan akan
gadonsa yana rusa kuka kamar ransa ze fita "wayyo Allah na, kaicona da irin wannan
rayuwar da nayi, a sanadina rayuwar mahaifiyata zata shiga garari, Daddy bakamana
Adalci ba, wayyo Allah kaicona"
Jin hargowar kukan Fahad ne yasa Ramadan farkawa daga bacccin da yake yi, ya fito
daga ɗakinsa ya shiga ɗakin Fahad, ya tarar da shi a zaune zaman dirshen yana ta
gursheƙen kuka.
"Amma kake wannan kukan? Idan ba mutuwa akayi ba meyafaru? Kukan kane fa ya tasheni
daga bacci"
Fahad ya share hawayensa yace "Ramadan Daddy be mana adalci ba, wai ashe Daddy
yana da mummunar alaƙa tsakaninsa da Ramlah"
Ramadan yace "subhanallah, wai kana nufin da Daddynmu take mummunar mu'amala"
Fahad yace "ba wai bane Ramadan, gaskiya ne ita ta gayamin da bakinta"
Ramadan yace "innalillahi wa inna ialaihi raji'un, meyasa Daddy ze mana haka? Fahad
abunda kake aikatawa ga 'ya' yan wasu ne muma yazo mana har cikin gida, kai kayi
Daddy yayi alhalin muna da uwa muna da ƙanwa mace wannan abun dame yai kama?"
Fahad yace "wallahi Ramadan nayi nadama, nadamar da bata da amfani sam, a yanzu
haka maganar da nake maka da ƙyar idan Daddy bashi da cuta me karya garkuwar jiki,
saboda Ramlah ta tabattar min tana da ita"
Fahad a ransa yace "Ramadan idan na gaya maka ni na sakawa Ramlah ciwo ta sakawa
mahaifina ban san wani kallo zakamin ba"
Ramadan ya zauna yana share hawaye, tare da baƙincikin abunda mahaifinsu ya aikata,
tausayin mahaifiyarsu ya mamayeshi, ya kalli ɗan uwansa yace "yanzu Fahad yaya
zamuyi mu gayawa Mummy wannan maganar? Itama taje a binciki lafiyarta tunda wuri?"
Fahad yace "Ramadan abunda nake ta tunani kenan, na rasa abunyi gaba ɗaya, ban san
ta inda zan ɓullowa wannan maganar ba, da ƙyar idan Mummy bata ɗauka ba, dan babu
wanda yasan tun yaushe yake tare da ita, suke mu'amala"
Ramadan ya dafe kansa, ya dinga jujjuya kansa cike da ƙunar rai, ya fice jiki a
sanyaye daga ɗakin Fahad, zuciyarsa na masa wani irin zugi da takaici, gami da
tausayin mahaifiyarsu.
Shirye shirye sukayi nisa, akan ɗaukaka ƙarar Yusuf, manyan lawyoyi da masu kare
haƙƙin ɗan Adam suka shiga lamarin, suna ta tattar hujjoji da shedu wanda suma zasu
gabatar, a sake sharia'r Yusuf.
Yayinda Widad ke zaune a inda take ɓoye, inda Bulama yake ɓoye da ita, take
communicating da mutane a waje, ta hanyar Sabuwa me aiki, taita aikenta da takadda
ba tare da Sabuwa tasan ma'anar hakan ba, ga cikinta ya ɗan ɗaga sosai ya fito, dan
sosai yake motsi yanzu, sedai duk lokacin da cikin ya shiga wani watan, se wata
matsala ta taso, kodai yawan amai, ko ciwon kai, ko rashin son Abinci, haka Widad
keta wahala tana ƙumbiya ƙumbiya da cikin a hijjabi kar wani ya gani, ga Bulama ya
shafe kwanaki bezo ba, tunda yayi mata barazanar kama mahaifiyar Yusuf bata sake
ganinsa ba.
Bulama kuma yaga canji a tattare da yaransa, abun da ya bashi mamaki be wuce yadda
Ramadan ɗin dayake nutsatse yabi sahun Fahad ba, sam basa gaisheshi ko kallon inda
yake basayi, balle ya saka ran wani abu na kirki ya shiga tsakaninsu dashi, suka
dena shiga cikin gidan ma sam.
Bulama yace "Sarah, kin lura da yadda yaran nan suka canza gaba ɗaya a gidan nan?
Na rasa me nayi musu, sam basa shiga harkata sun dena ko gaishesni, ko wani abun
sukace nayi musune?"
Hajiya Sarah tace "ni dai bani da masaniya akan komai, ni Ramadan yafi bani
mamaki ma, nasan ba haka yake ba, amma ban san yadda akayi shima ya ɗauki wannan
mummunan halin ba, amma dan Allah kayi haƙuri, zanyi magana dasu insha Allah"
Daga nan ya kintsa ya fita, bayan fitarsa Hajiya Sarah taje har BQ ta samesu,
'Fahad, wani abu nake gani wanda na kasa gane kansa, meye dalikinku na dena kula
mahaifinku ne?'
"ƙarya kuke yi, akwai dalili idan ba haka ba, meye na wannan shareshin da kuke yi?"
Ramadan zeyi magana, Fahad ya girgiza masa kai yace "Mummy, kin san daddy da yawan
faɗa, komai ya gani se yayi magana, se yayi mita da faɗa, shiyasa muke ɗan janyewa
kawai"
Tace "Ai ba yanayi ne dan ya takuda muku ba, dole idan kukayi ba daidai ba a
tsawatar muku, dan haka bana son wannan abun da kuke, a gyara dan ya fara zargin
koni nake saku kuke masa haka"
Fahad yace "Ramadan, ba'akowane irin yanayi ake gayawa mutum magana ba, ka bari
zamu gayamata '
" Aikuwa bashi da amfani ko mun gaya mata, nasan aikin gama ya gama, ya riga ya
cutar da ita "
Jini fa yaƙi tsayawa Amal, gaba ɗaya ta ɗashe tayi fari, ta kira doctor Hamisu a
waya, ya rubuta mata magani, taje ta siya amma idan ta sha wuni take a kwance tana
jiri, gaba ɗaya tayi wani iri, tambayar duniya taƙi gayawa Hajiya Halima abunda ke
faruwa.
Tana kwance ta lallaɓa, zataje Asibitin da aka cire mata cikin ganin Likitan, se
taga message nata shigowa wayarta, tana dubawa me zata gani? Kuɗinta na Account ake
ta kwashewa, ta tashi a gigice sedai ba wani abu data iyayi an kwashe kuɗin nan
tsaf, sakamakon wani website data shiga, akace ta saka BVN Number ɗinta, kuma ta
saka akayi amfani da shi aka kwashe kuɗin nata.
Ta fito falo a gigice tana kuka, Hajiya Halima tace "ke lafiya kuwa?"
"Wani website ne, na shiga na saka BVN ina ga ta nan aka kwashemin kuiɗn, gashi
nayi investing kusan million biyar a wani business shima an kwashe ma shiga uku"
Hajiya Halima tace "million goma kuma? A kna kika samu million goma?"
Sekuma ta dawo hayyacinta, ta shiag inda inda, cikin tsawa Hajiya Halima tace
"magana nake miki, a ina kika samu million goma?"
Tai shiru tana tura baki, "zakiyi magana ne? Ko kuma sena tashi na tattaka ki?"
Ramlah ta buɗe baki, Hajiya Halima ta miƙe tsaye "ya miki fyaɗe kamar yaya?"
Nan Amal ya kwashe komai ta gayamata, har jinin da take ta zubarwa tunda aka cire
cikin.
Nan da nan jikin Hajiya Halima ya ɗau rawa, ta kasa magana ma gaba ɗaya, ta dinga
bin Amal da Ramlah da kallo.
Tunda mutane suka ji batun Yusuf zeyi appeal, suke ta ɗokin sake zaman ganin
shari'ar nan, ranar da za'a fara sauraren ƙarar kotu ta cika maƙil, musamman jin
labarin a ƙarƙashin jagorancin gogaggaun Matasan lawyoyi dodannin Azzalumai za'ayi
shari'ar, kotu tayi maƙil assurance ɗin da Bulama ya samu a gurin Justice A dutse,
da kuma su Barrister Sadik yasa ya je kotun da ƙwarin gwiwarsa, sedai duk da haka
bashi da wani karsashi, saboda Alƙalin koyun bashi da wasa, balle ka tunkareshi da
wata maganar cin hanci Justice Muhammad Mustapha.
Shikansa Yusuf yayi mamakin ganin, manyan lawyoyin da sukazo dan tsaya masa, da
yawa a radio yake jin sunayen su, sekuma a dandalin sada zumunta, amma yau gashi
gasu wai zasu tsaya masa, a iya saninsa ba kowa ke iya ɗaukarsu shari'a ba, saboda
lawyoyine masu tsadar gasme, kuma basa tsayawa shari'ar Azzalumai, to ta yaya akai
shi suke son tsaya masa? Bayan ta bayyana ƙarara shi me laifine?.
Barrister Adam A Adam ya fito gaban alƙali ya gabatar da kansa a gaban alƙali,
sannan ya kalli kotu yace "sunana Barrister Adam A Adam, ni lawyer ne me zaman
kansa, ina daga cikin tawagar lawyoyin da zasu tsayawa wanda ake ƙara, don bashi
kariya, a tare dani akwai hujjoji da shedu da zasu tabattarwa da alƙali cewar wanda
ake tuhuma, be aijata ɗaya daga laifukan da ake zarginsa dasu ba, idan kotu ta bani
dama ina buƙatar ganin Sada, wanda yace Yusuf ya kai masa mota ya siya "
Sada ya fito yana rarraba ido, dan kallo ɗaya zakayiwa Barrister Adam A Adam kasan
babu wasa a tare da shi, sannan abune mawuyaci a kada shi a shari'a, saboda
gogaggen lawyer ne, kuma ɗan gwagwarmaya.
Barrister ya kalli Sada yace " ko zaka iya gayawa kotu sunanka, da abunda ka sani
akan wanda ake zargi?"
Sada ya maimaita abunda ya faɗa a kotun baya, Barrister Adam yace "wow, ko zaka
iya gayawa kotu wame irin motoci Yusuf ke kai maka gyara daga gidan Daula?"
Barrister yace "wace irin mota ce Yusuf ya kai maka ta gidan Daula ka siya?"
"wow, kasan irin wannan motocin se gidan attajirai irinsu daula kam, amma ya akayi
ka siyi motar da kuɗinta ya haura naira million talatin a matsayinka na bakanike?"
Objection ya me shari'a cewar Barrister Sadik, " Barrister Adam yana ƙoƙarin jefa
tsoro da razani a zuciyar sheda, kuma ai shi arziki sirrine, dan mutum yana ƙaramar
sana'a shikenan baze mallaki dukiya ba? "
Justice Mustapha yace "tambayoyin da Barrister Adam yakewa Sheda, zam basu kauce
ba dan haka wannan ƙorafin be karɓu ba, cigaba da aikinka"
"Amma meyasa kuka sai motar, bayan kun san Yusuf bashi da arzikin daze mallaki
wannan motar?"
"Amm, ai, ai dama bece min satota yayi ba, kawai yace in siya nace masa bana siyan
mota, na haɗashi da me siya na zata ko bashi motar Alhaji Nasir yayi, kasamcewarsa
mutum me kyauta"
Barrister Adam yace "hakane, ina neman alfarma da kotu ta bani dama dan gabatar da
wata ƙwaƙwarar sheda da zata tabattar da abunda Sada ya faɗa ba gaskiya bane"
Aka bawa Adam dama, aka shigo da Nura, aka tsayar da Nura a gurin Tsayuwa,
Barrister Adam yace "ko zaka gayawa kotu sunanka"
"Kasan wannan" aka nuna masa Yusuf, Nura ya jinjina kai alamar eh, "wannan fa?" aka
nuna masa Sada, Nura yace "A'a"
"toko zaka iya shedawa Kotu, abun da ka sani game da abunda ake tuhumar Yusuf
dashi?"
Nura yace "kamar yadda na faɗa sunana Nura, kuma nine direban Alhaji Nasir Daula,
kafin zuwan Yusuf ya fifita Yusuf sama da kowane ma'aikaci a gidan, na shekara a
ƙalla tara ina aiki a gidansa, a haƙiƙanin gaskiya idan mota ta lalace a gidan
Alhaji Nasir, Har gida ake zuwa a gyara ta, kuma Yusuf baya kai gyaran mota iya
abunda nasan yanayi, shine tuƙa 'yaf gidan Alhaji Nasir Daula, sekuma shikansa
Alhaj Daulan wasu lokutan, kuma idan mota ta lalace ma ba' a fiye barinta a gidan
ba, gyara ta ake a bayar da ita, dan haka gaskiya ni ban san wannan bawan Allah ba,
kuma a gidan Alhaji Nasir Daula, babu irin motocin daya faɗa, manyan motoci na
alfarma su ake hawa a gidan Alhaji Nasir"
Barrister Adam yace "Malam Nura muna godiya, ban sani ba ko Sada yana da abun
faɗa?"
Sada ya soma inda inda, yana kallon inda Su Bulama suke, akace ko su Barrister
Sadik suna da abun faɗa? Sukace babu.
Barrister Adam yace "sheda ta gaba da zan gabatarwa da kotu itace, shedar da aka
bawa Yusuf a hukumance, daga hukumar 'yan sanda, na cewar yaje gidan Alhaji Daula
yai bincike sannan ya bawa' yarsa kariya a ɓoye, a matsayinsa na ɗan sandan farin
kaya, wanda hukumar ta musanta hakan, Amma akwai takadda da aka samu, wadda da saka
hannun hukumar da stamp ɗinta, wanda babu wanda ya isa ya samu wannan stamp ɗin,
idan har ba daga ofishin manyan cikin jam'ian tsaron ba " Barrister Adam ya fito
da takadda aka karɓa ka miƙawa alƙali, shi dai Yusuf yana tsaye, yana tunanin waye
ya masa wannan ƙoƙarin haka?"
"dan haka muna neman jin cikakken bayani daga bakin 'yan sanda, idan har bata
hannunsu wannan takadda ta fito ba, ta yaya akayi stamp ɗinsu ya fito a takaddar,
idan kuma da saninsu yaje yin aikin, meyasa suka musanta sune suka bashi aikin?"
AYSHERCOOL
07063065680
12/7/21, 11:04 PM - Buhainat: LITTAFIN KUƊI NE, DAN ALLAH KI SIYA KAFIN KI KARANTA
BA DANNI BA DAN ALLAH, LITTAFI NA ƊAYA KYAUTA NE WANNAN NA SIYARWA NE
NORMAL GROUP ₦300
VIP ₦500 NE KITURA TA WANNAN ACCOUNT ƊIN
0009450228
JA'IZ BANK
AISHA ADAM
SE A TURA SHEDAR BIYA TA WANNAN LAMBAR
07063065680
(Albishir ga masoya, ma'abota bibiyar litattaafaina, dama ta samu zaku fara samun
litattaafaina na audio, akan YouTube channel ɗina me suna Cool Arewa TV
https://youtube.com/channel/UCD5vnvA5laU8ti4LLz2_QEg
Kuyi liking sannan ku danna subscribe, domin fara samun litattaafaina na audio,
nagode sosai da ƙaunar ku gareni"
_(INNALILLAHI WA INNA IALAIHI RAJI'UN ina amfani da wannan damar gurin miƙa saƙon
ta'aziyya ga Ɗaukacin zuriyar Hajiya Aisha Muhammad (Baba) bisa babban rashi da
mukayi na rasuwar ta ina fatan ubangiji Allah ya jiƙan ta yai mata rahama, ya kai
haske kabarainta, ubangiji Allah ya duba zuriyar da ta bari, ya bata ladan
ɗawainiya da iyalI da tayi tsawon ranta, ubangiji Allah ya jiƙan kafatanin wanda
suka rigamu gidan gaskiya Musulmi, idan tamu tazo Allah yasa mu cika da kyau da
imani_)
IN THE MEMORY OF LATE HAJIYA AISHA MUHAMMAD, I DEDICATED THIS PAGE TO LATE HAJIYA
AISHA MUHAMMAD (BABA) MAY ALLAH SUBHANAHU WATA'ALA, GRANT HER JANNATUL FIRDAUSI
AMEEN _
150_151
Zare ido Bulama yayi jin an ambace shi haka, abun da be taɓa kawowa ba, yaga dai
duk shedun da aka gabatar babu wanda yai wata magana da ta shafe shi, amma yaji an
ambaci sunansa.
Ya tsaya yana zazzare ido, ya miƙe cikin fargaba ya fito ya tsaya a inda ake
tsayawa, Barrister Khalil yace
"Alhaji Bukar Bulama, duniya tasan kaine babban abokin mahaifin Widad, wato Alhaji
Nasir Daula, ko zaka iya gayamana abunda kasani game da ɓatanta?"
Bulama yace "Eh to, kafin ɓatan nata dai, kamar yadda ka faɗa ni ubane a gurinta,
dukda rashin yaddarta ga mutane akwai kyakkyawar alaƙa tsakani na da ita, Daula da
'yarsa sun bada amanna sosai ga wannan bawan Allah, sun yadda dashi sosai.
Har nake ja masa kunne akan yayi taka tsan tsan, da wannan yaron saboda be kamata
ace yana shishigemasa haka ba, saboda duniya babu gaskiya, wata rana ina bacci
cikin dare, sega wayar Daula ina ɗagawa a gigice yake gayamin ai Widad direbanta ya
gudu da ita, a daren na tafi gidan gonarsa, yake gayamin ya kira Yusuf akan ze kai
Widad Abuja, yana son ya kwana a nan gidan gonar dan suyi tafiyar Asuba suje da
wuri, amma cikin dare Yusuf ya sace ta ya gudu da ita"
Barrister Khalil yace "duk ina ma'aikatan gidan, da har ya gudu da ita a mota babu
wanda ya sani?"
Khalil yace "Kasancewar ka Uba ga wannan yarinya, bayan an gano inda take, an
karɓota daga hannun masu garkuwa, an kaita Asibiti an gama mata dukkanin wasu gwaje
gwaje da yakamata, tana hannunka a zaune kenan?"
Bulama ya bada amsa, Khalil yace "tana gurinka, amma ba'a gidanka da kake zaune da
iyalinka ba?"
Bulama yace "Eh, tana wani gidan daban sakamakon rashin jituwa dake tsakaninta da
ɗana Fahad, da kuma ta samu hutu"
"Amma me yakawo rashin jituwa tsakaninsu, dukda cewar kusan uba kake a gurinsu
duka"?
Bulama ya rasa yadda zeyi da tambayoyin Khalil, yace "Eh, nima ban san dalili ba,
amma basa jituwa '
Khalil yace "bekamata ace baka sani ba kuwa, sannan duk wanda yasan Alhaji Bukar
Bulama a baya bashi da wannan tabon ɗinki a fuskarsa haka? Ko ya akayi ya samu
wannan tabon? "
Barrister Saminu yai suka akan abunda Khalil yake yi, amma Justice Mustapha yaƙi
saurarrasa, yace Khalil ya cigaba.
"meya haɗaka da' yan daba kana babban mutum har suka maka wannan yankan a fuska
haka?"
Bulama yace 'kuɗi suka nemi in basu ban bayar ba, shine suka yankeni a fuska da
cinya ta "
' A'a"
Bulama kawai yai shiru, yama rasa meze cewa Khalil, saboda yadda ya titsiyeshi da
tambayoyi, tabbas da tun a shari'ar farko irin wannan shari' ar akayiwa Yusuf, da
baze je prison ba, Umma dake zaune na kallon shari'ar banda tasbihi da hamdala ba
abunda take yi a ranta.
Barrister Khalil yace "bayan kai akwai wanda Yasan inda gidan daka ajiye Widad
Nasir Daula yake?"
Yace "Eh"
'ka bawa' yan jarida damar ganawa da ita? Ko kuma jam'ian tsaro sun san inda
take? , ko kuma meyasa iya kaida 'ya' yanka ne suka san inda take, alhalin ana kan
shari'a, dole za'a so bincike se anji wani abun ta bakin ta, ka kaita ka ɓoye ta,
ka tirsasata ta bada shedar ƙarya a kotu, kai yunƙurin cutar da ita, tai maka rauni
da wuƙa, Bulama kaike da alhakin daukkanin abunda ke faruwa a gidan Alhaji Nasir
daula, saboda babu wanda yasan sirrinsa sama da kai"
"Objection yame shari'a, wani irin abu Barrister Khalil yakeyi haka? Yana ƙoƙarin
liƙa laifi ga wanda be jiba be gani ba, ba tare da wata hujja ko sheda ba, yana ta
ƙoƙarin ƙirƙirar labari da hanyar da ze jingina laifi akan wanda bashi da laifi"
cewar barrister Sadik.
Khalil ya saka hannu a aljihunsa ya ɗakko wata waya, yazo gaban Yusuf ya nuna masa
wayar yace "ko za ka iya tuna wannan wayar?".
"wayar waye?"
Khalil yace "meyasa baka gabatar da wannan wayar a matsayin shedarka ba lokacin da
ake maka sharia' ar farko?"
Yusuf yace "saboda an hanani duk wata dama da zan kare kaina"
Khalil yace "ina son ka karɓi wannan wayar, kayiwa kotu bayanin abunda ke ciki"
Yusuf shi gaba ɗaya ya manta ma da batun wayar Nurat, ko ya akayi Khalil ya gano da
wani abu a wayar harya ksrɓota oho, saboda Yusuf besan akwai alaƙa a tsakanin Nurat
da Khalil ba.
sannan na taɓa kai Widad wani hotel, na jirata a waje, ta shiga ta fito tana kuka,
bayan mun koma gida, na maida ita naji lallai ina son sanin me taje yi a Hotel ɗin
nan, bayan na koma na kasa gane komai, sena nemi manager nace ina buƙatar ya bani
record na wanda suka kama ɗaki a hotel ɗinsu, mun kai ruwa rana kafin ya bani, dan
seda na biya shi, aka bani Jerin record na wanda suka kama ɗaki na kusan watanni
huɗu, a nan naga Alhaji Bulama yafi kowa kama ɗaki, dan yakan kama na wata guda,
kuma da na ƙara bincike sena gano suna yawan zama dashi Alhaji Bulama, da Alhaji
Musa, da Alhaji Munir da kuma matar Alhaji Nasir Daula, yanayin yadda Widad ke
matuƙar tsoron mutane da kuma nima yadda akace za'a dinga bibiyata, yasa naji cewar
lallai ya kamata inyiwa binciken da nake kyakkyawan ɓoyo, bayan na system ɗina na
wayata, da wanda nake haɗa report a takadda, dan haka na yanke shawarar zuwa gidan
Alhaji Musa, Na samu Nurat, na samu bayanai daga bakinta na yadda rashin jituwar
mahaifinta da Alhaji Nasir ya samo Asali.
nai amfani da wannan damar, na karɓi wayarta na buɗe wani website nai hiding ɗinsa,
na tura mata duk wani sakamakon binciken da nayi, sannan nai linking ɗinsa da
wayata duka lokacin dana tura wani abu website ɗin ze shiga wayarta, kuma ze zauna
akan wayata, nasan babu wanda zeyi tunanin da wani abu a wayarta, ko da na rasa na
gurina"
Aiba Khalil ba hatta jama'ar kotun, sun jinjinawa Yusuf wannan basira tasa, Khalil
yace "Amma ya akayi kai garkuwa da 'yar Alhaji Nasir Daula?"
Yusuf yace "banyi garkuwa da itaba, Alhaji Nasir ya nemi da inje gidan gonarsa in
kwana, zan kai Widad Abuja dan ganin wani likitan Ƙwaƙwalwa, cikin dare aka turo
masa saƙo a wayarsa, ina kwance ina bacci yazo tasoni nida Widad, ya nunamin saƙon
yace maza maza in ɗau Widad mu bar gidan, na tsaya ina tambayarsa ina zamuje, yace
maza maza in bar gidan da Widad, saboda saƙon da aka tura masa ana barazana ne ga
kodai ya bada abunda akeso, ko kuma a hallaka 'yarsa, nace masa mu kira' yan sanda
amma yace aa', in kula da Widad, na ɗauketa muka fita ba tare da nasan inda zamuba,
munyi tafiya me nisa ga dare, kawai aka zagaye motarmu, da Widad kawai suka so su
ɗauka, ta riƙeni tana kuka na hana su tafi da ita, shune suka haɗa dani, kwananmu
biyar a hannunsu, Saleh ɗaya daga cikin ma'aikatan gidan gonar Alhaji Nasir, yaje
ya kuɓutar damu, an harbi Widad a hannu ya kaimu Asibiti, aka cire mata bullet,
sannan ya bamu mafaka a wannan ƙauyen, ya cemin idan har muka dawo za'a hallaka
Widad dani kaina, dan haka mu zauna zuwa lokacin da komai ze lafa, amma bani na
sace ta ba"
Barrister Saminu ya mike yace "meyasa baku shigar da ƙara ga hukumar 'yan sanda
ba? Ka cigaba da zama da ita a inda babu wanda yasani tsawon lokaci?"
Yusuf zeyi magana Barrister Khalil yace "zan gabatarwa da kotu, wata shedar wadda
take nuna wanda ake zargi bashi da laifi a zaman kotu na gaba"
Nan kotu ta hargitse da Hayaniya, kowa yana tofa albarkacin bakinsa, Alƙali ya buga
gudumarsa, akayi shiru, yai rubuce rubuce sannan yace
Duba da yadda lawyoyi suka gabatar da shedu da hujjoji, wannan kotu me albarka zata
ɗage cigaban wannan sharia'r zuwa nan da sati biyu masu zuwa, dan yin zama na
ƙarshe da yanke hukuncin daya dace akan wannan shari'a, sannan kotu tana umarni da
hukumar 'yan sanda su binciki Alhaji Bulama da tawagarsa"
Kotu ta ɗau hargowa da sowa, 'yan sanda suka tafi da Yusuf gidan yari, Umma ta
kalli Suleiman tace " Suleiman ya haka? Naga za' a maida shi"
Suleiman yace "ki kwantar da hankalinki, kin san shari'a komai a hankali a binsa ki
kwantar da hankalinki"
Hajiya Halima ganin ba'a kama da ita ba, yasa ta silale tai gida, zuciyarta cike da
fargaba da kuma tsoro, tana tunanin meye mafitarta ta ƙarshe? Tasan tunda Bulama
yaje hannu itama tata ta ƙare, sedai tana zuwa gidan ta tarar da gate ɗin gidan
hanhai a buɗe, ga motar 'yansanda, ga mutane sun cika gidan, kamar ta juya ta gudu,
amma ta fasa ta ƙarasa, tana zuwa me zata gani, an rufe mutum da zani alamar ya
mutu, Ramlah se uban kuka take, ga Amal a sume a gefe ana ta mata fifita, jiki na
rawa ta ƙarasa gaban gawar, tasa hannu ta yaye zanin, Innalillahi wa inna ialaihi
raji'un!!!
Gawar Anwar ce ɗanta, gawar se zubar da jini take, idonsa a rufe kamar me bacci,
kamar kace tashi ya tashi a nutsensa yake, amma ya mutu.
Ta ɗora hannu a ka tana kurma ihu "Wayyo Allah na shiga uku ni Halima, Bulama ka
cuceni ka tarwatsa rayuwata, Allah ya isa tsakanina da kai Bulama, Bulama seda kasa
aka kashemin Anwar? Nayi dana sanin saninka, da farko ka rabani da gidan uban
Anwar, na Auri Shu'aibu shima ka kashemin Auren, ka haɗa kai da Shu'aibu kuka kashe
matarsa ya sakeni dan Daula ya aureni, duk biyayyar da na maka, amma ka kashemin
ɗana Me ƙaunata da gayamin gaskiya, wayyo Allah Anwar ɗina, wayyo Anwar ka tashi
dan Allah, na shiga uku "
Tana wannan ihun, tana maganganun nan ana mata video, ita dai Ramlah kasa cewa
komai tayi, se bin mahaifiyarsu da ido, ga Amal wadda babu tabaccin tana da rai
itama, dan abun yazo mata akan gaɓa, dama ta gama galabaita babu jini a jikinta,
kuma ga wannan mutuwar ta Anwar, ƙarseh wannan kururwar da Hajiya Halima keyi, se
rufeta akayi a ɗaki akayiwa Anwar sutura.
Khalil kuwa yana ta rawar jiki yaje ya bawa Nurat labarin yadda shari'a ta kaya,
akwai alamun nasara akan shari'ar Yusuf sedai yana zuwa gida ya tarar da
fuskaokinsu wani iri, Nurat a zube a ƙasa ana ta fama numfashinta ya tsaya.
"Allah yayiwa mahaifiyar Nurat rasuwa, yanzun nan an tafi ɗakko gawarta daga
Asibiti" Anty Saddiƙa tai maganar tana kuka.
Haka itama akayi mata sutura aka sallaceta, aka kaita makwancinta na gaskiya, Nurat
kam tasha kuka kamar ranta ze fita, gaba ɗaya ta birkice an kasa gane kanta ma gaba
ɗaya, se da aka samo likita yai mata alluarar bacci dan ta samu relief.
Amal kuwa har aka kai Anwar bata dawo hayyacinta ba, gawar Anwar ya tara mutane
sosai kasancewarsa mutum ne na mutane, ga sauƙin kai da girmama jama'a.
Fahad ya kaɗu da jin labarin an kama mahaifinsa, da kuma harƙallar da suka ƙulla da
shi da Hajiya Halima, suka dinga siyar da dukiyarsa ba bisa ƙa'ida ba, ga mutuwar
Anwar data dake shi, ya kaɗu matuƙa da jin Anwar ya mutu, ya lallaɓa komtsan sa ya
ɗau mota ya gudu.
Haka Bulama ya kasance a hannun 'yan sanda shima, Aka kama Alhaji Musa, shi laifuka
biyuma aka kama shi dasu, ga laifin hankaɗo matarsa daga bene, gana wanda suka
aikata da Bulama.
Tunda Amal ta farka ta farka ba a daidai ba, tunda ta buɗe idonta bata magana kwata
kwata, sedai taita bin mutane da kallo, kamar bata sansu ba, Hajiya Halima kuwa
kamar wadda ta shekara a daji, tai wujiga wujiga ko tayi shiru idan aka jima se
surutai, taita tonawa kansu Asiri ita da su Bulama, itama ƙarshe ana cikin makoki
'yan sanda suka zo suka yi gaba da ita.
Nurat tana cikin tashin hankali, na rashin mahaifiyarta, ga kama mahaifinta anyi da
wannan manya manyan laifuka haka, dukda tarin abunda yai mata na laifuka, amma ya
haifeta, gaba ɗaya ta rame tai wani iri, ga labarin mutuwar Anwar ya risketa,
mutuwar ta girgiza ta ƙwarai, ba zata manta halacci da kara irin na Anwar ba, Anwar
mutum ne nagari me haƙuri da nagarta gaske.
Bulama a hannun Hukumar 'yasanda ɓangaren SWAT aka danƙasu, domin tuhumarsu, dama
kuwa masu fushi da fushin wani, dan haka ba'a ragawa su Bulama ba sam, kamar yadda
suke sawa a azabtar da wasu, haka suma suka shiga hannu aka dinga azabtar dasu.
Ana wannan halin, a haka sati biyu ta cika, aka koma kotu ranar da aka koma kotu
kallo ɗaya zakayiwa Khalil kasan yana cikin alhini sosai.
Kamar kullum an cika kotun nan maƙil, haka aka shigo dasu Bulama, wujiga wujiga.
Khalil ya fito gaban kotu, ya gabatar da shedarsa da suke dashi akan Bulama.
Babban abunda ya bawa Yusuf mamaki, be wuce yadda yaga Sunusi ya shigo ba, ya buɗe
baki yana kallon Sunusi.
Sunusi yazo ya tsaya, Khalil ya masa umarni ya gabatar da kansa, Sunusi ya gabatar
da kansa sannan yace "tabbas wanda ake zargi bashi da laifi, Saleh ɗan uwanane,
kuma akwai Bala Yayansa, Saleh ya haɗa kai da Alhaji Bulama da niyyar ya ɗau fansa
akan Alhaji Daula na sakawa da 'yarsa tayi aka tsare ɗanuwansa, dan tana zargin da
hannunsa a kashe mahaifinta, sedai Bulama ya gaza cika Alƙawarin da yaiwa Saleh ma
ze saka a saki ɗan uwansa, su ɗau fansa akan Daula, ganin haka yasa ya koma
taimakon' yar gidan Daula, ya kuɓitar dasu daga hannun masu garkuwar, sannan ya
kaisu ƙauyenmu gurin mahaaifina, saboda muddin suka dawo za'a kashe yarinyar, kuma
shima Saleh ze shiga matsala, lokacin da sukaje ƙauyen bata yadda da kowa se Yusuf,
ga jikinta duk rauni se anyi jinyarta, shi kuma yace ita ba muharramarsa bace, babu
yadda zeyi jinyarta wannan dalilin ne yasa Saleh ya shige gaba aka ɗaura musu Aure
bisa amincewarta, shedar da aka saka ya bayar a kotu shedar ƙarya ce, tursasashi
akayi kuma aka masa rauni a cikinsa saboda duka, akace za'a kasheshi in be bada
shedar ba, shine aka kawo shi kotu ya faɗi wannan shedar, sannan lokacin da suke
ƙauye ya gayamin idan har aka kama Yusuf za'a kasheshi dashi da Widad baki ɗaya,
tunda Daula ma ba'asan inda yake ba, nace masa ya gayawa 'yan sanda, amma yace a"a
akwai haɗaka me ƙarfin gaske tsakanin Alhaji Bulama da Hukumomin tsaro, dan haka
yana da ɗaurin gindi, idan ya faɗa tamkar ya sake jefasu a garari ne"
Nan kotu ta ɗau salallami, Barrister Khalil yace " Alhaji Bukar Bulama, kaine mutum
na farko da Alhaji Nasir ya kira bayan an sace 'yarsa, ya akayi wanda suke turo
masa saƙo suka san inda suka tafi idan ba kai ka gaya musu ba? "
Bulama yace " ni.. Ni bani bane ba, ya za' ayi in saka a sace yarinyar da takemin
kallon uba? "
Khalil yace " Akwai sheda, ina son kotu ta bani dama, in gabatar da sheda ta ta
ƙarshe wanda zata tabattar da Alhaji Bulama shike da alhakin dukkan wannan abubuwan
da suke faruwa, yasa akayi garkuwa da 'yar Amininsa, kuma yake bibiyar yadda ze
mallake dukiyar Aminin nasa"
Aka bashi dama, wa Bulama ze gani? Su me Adda aka jero a layi, akaje aka tsaidasu,
nan da nan Bulama ya sadaƙar yasan ƙarshensa yazo.
Khalil yace " tsawon wane lokaci ka ɗauka kana masa aiki? "
Me Adda yace " gaskiya an daɗe, muna masa aiki yana biyan mu, yana bamu kuɗi sosai,
a haƙiƙanin gaskiya mune mukayi garkuwa dasu, 'yan sanda sun tambayemu kuma mun
faɗa musu gaskiya"
Barrister Khalil yace "Ya me girma me shari'a, duba da tarin hujjoji da shedu da
kuma sakamakon' yan sanda, da muka gabatarwa wannan kotu, muna neman wannan kotu me
albarka ta wanke wanda ake ƙara daga wannan tuhuma da 'ake masa
Justice Mustapha Yace " duba ga yadda shari'a ta kasance, da tarin hujjoji da shedu
da aka gabatar, wannan kotu da dogon Nazari da duba ga kudin shari'a wannan kotu ta
wanke wanda ake zargi, wato Yusuf Bashir Maitama, sannan wannan kotu me albarka
tayi umarni da hukumar 'yan sanda su kama Alhaji Bukar Bulama, da muƙarabbansa don
zurafafa bincike a sake gurfanar dasu, sannan hukumar' yan sanda zata biya wanda
ake ƙara Wato Yusuf Naira million goma, sakamakon ɓata masa suna, da tauye masa
haƙƙinsa a matsayinsa na ɗan ƙasa dukda dama da kundin tsarin mulki ya bashi,
sannan kotu tana umarni a maida shi bakin aikin sa "
Yusuf yana jin haka ya fashe da Kuka, ya zube a gurin yana sujudu shukur ga
ubangiji subhanahu wata'ala, kuka sosai kamar wani ƙaramin yaro, Umma ta taho da
gudu, ta rungume shi itama tana zubar da hawaye, tawagar 'yan sanda suka rako Yusuf
wajen kotu, yayin da akayi Ram da Bulama da Alhaji Haruna dake gurin, sannan aka
bazama nemo sauran.
Yusuf na fitowa jama'a suka baibaiyeshi, sedai ya kasa magana se hawaye, Suleiman
ya rungume Yusuf yana faɗin "barka da Arziki abokin aiki, barka da Arziki Yusuf"
Yusuf ya rungume Sulaiman shima, sedai ba bakin magana se hawaye dake fita daga
idonsa, tawagar lawyoyin nan suka zo gaban Yusuf suka dinga miƙa masa hannu suna
gaisawa, Cikin kuka Yusuf yake faɗin "Nagode, Nagode, Nagode" yana maganar yana
kuka dan yama rasa meze ce musu.
Umma ta rirriƙe Yusuf, kamar za'a sake ƙwace mata shi, itama kuka kawai take yi.
Khalil yace "yau na sauke babban nauyin dana ɗauka, na Alƙawari ga Nurat, da nace
zanyi iyayina inga ka kuɓuta"
Khalil ya jinjina kai, yace "Eh Nurat, sannan Yakamata a wuce dashi Asibiti, a
duba lafiyarsa.
Bulama kuwa aka fito da shi, da Alhaji Haruna, dasu Musa a ƙasƙance, mutane nata
tsine musu, 'yan jarida suka sa kasu a gaba, amma sukaƙi magana sam, suka duƙufar
da kai kamar munafukai.
Bisa rakiyar' yan sanda, aka tafi da Yusuf Asibiti.
Yusuf kuwa ya galabaita, dan admitting ɗinsa akayi, yana buƙatar agajin gaggawa,
saboda tarin raunuka dake jikinsa, gashi ya kasa dena kukan da yake yi, Suleiman
cewa yake "Yusuf, kukan nan ya isa haka, ka godewa Allah, dan shine ya dubi halin
da kake ciki ya fitar mana da kai, amma mun shiga cikin damuwa muma lokacin da ka
shiga mawuyacin hali"
Cikin kuka Yusuf yace "Yallaɓai, yanzu kenan harda Abbas aka haɗa kai dan cutar
dani? Yace be san da an bani aikin nan ba? Abbas fa? Aminina Abbas fa?"
Suleiman yace "koma dai menene, ba gashi kai ka kuɓuta ba, kuma nasan shima dole
kotu ta neme shi ai"
Suleiman yace "Ina Barrister Khalil? Lawyern daya dinga magana daga ƙarshe"
"Ai ɗan uwan Nurat ne, kuma itace ta tsaya kai da fata akan ganin an kuɓutar da
Yusuf, Mahaifiyarta ce ta rasu, kuma mahaifintane ya turo uwar daga kan bene, dan
ta masa magana ya kulle Nurat ɗin, ashe duk saboda shari'ar kane akan ta dage ayi
maka adalci, ya gano ta san sirrinsa shine yai dalilin rasuwar mahaifiyarta"
Umma ta dafe ƙirji tace "subhanallah" , Yusuf ya girgiza kai hawaye na bin idonsa
yace
"Allah sarki Nurat, Allah ya jiƙan Mummynki, nayi silar shigarki matsala kema Allah
sarki Nurat"
(INA JIRAN TUKUCINA NA WANNAN OAGE ƊIN, TUNDA AN SAKAR MUKU YUSUF 😎😂😂)
Ayshercool
07063065680
12/7/21, 11:04 PM - Buhainat: LITTAFIN KUƊI NE, DAN ALLAH KI SIYA KAFIN KI KARANTA
BA DANNI BA DAN ALLAH, LITTAFI NA ƊAYA KYAUTA NE WANNAN NA SIYARWA NE
NORMAL GROUP ₦300
VIP ₦500 NE KITURA TA WANNAN ACCOUNT ƊIN
0009450228
JA'IZ BANK
AISHA ADAM
SE A TURA SHEDAR BIYA TA WANNAN LAMBAR
07063065680
(Albishir ga masoya, ma'abota bibiyar litattaafaina, dama ta samu zaku fara samun
litattaafaina na audio, akan YouTube channel ɗina me suna Cool Arewa TV
https://youtube.com/channel/UCD5vnvA5laU8ti4LLz2_QEg
Kuyi liking sannan ku danna subscribe, domin fara samun litattaafaina na audio,
nagode sosai da ƙaunar ku gareni"
_(INNALILLAHI WA INNA IALAIHI RAJI'UN ina amfani da wannan damar gurin miƙa saƙon
ta'aziyya ga Ɗaukacin zuriyar Hajiya Aisha Muhammad (Baba) bisa babban rashi da
mukayi na rasuwar ta ina fatan ubangiji Allah ya jiƙan ta yai mata rahama, ya kai
haske kabarainta, ubangiji Allah ya duba zuriyar da ta bari, ya bata ladan
ɗawainiya da iyalI da tayi tsawon ranta, ubangiji Allah ya jiƙan kafatanin wanda
suka rigamu gidan gaskiya Musulmi, idan tamu tazo Allah yasa mu cika da kyau da
imani_)
IN THE MEMORY OF LATE HAJIYA AISHA MUHAMMAD, I DEDICATED THIS PAGE TO LATE HAJIYA
AISHA MUHAMMAD (BABA) MAY ALLAH SUBHANAHU WATA'ALA, GRANT HER JANNATUL FIRDAUSI
AMEEN _
148_149
Gaba ɗaya Bulama bega alamar Nasara a tattare da wannan shari'ar ba, wata zuciyar
ta dinga rayamasa kawai yaje ya kashe Widad ya huta, wani sashin ya gargaɗeshi akan
aikata hakan.
Haka ya koma gida jikinsa a sanyaye, babu alamar Nasara sam, yana zuwa ya tarar da
Hajiya Sarah da Ramadan suna hira a falo, sedai da yayi sallama maimakon Ramadan ya
amsa sema tsaki daya ja, suka kalleshi gaba ɗaya tace "Ramadan, are you out of
your sense? Mahaifin naka kakewa haka? Ina yabo ka salla zaka kasa alwala?"
Nan da nan Ramadan ya shiga hawaye, "Mummy nayi dana sanin kasamcewarsa mahaifina
wallahi, baki san halin mutumin nan ba mugune azzalumi macuci"
Buɗe baki sukayi suna kallon Ramadan, Yace "Mummy ina abun kunya ina abunda Daddy
ya aikata? Saboda tsabar abun kunya wai 'yar' yar uwarsa, wadda take kamar a
gareshi yake bi, Mummy Ramlah fa kuma ta tabattarwa da Fahad tana ɗauke da cuta me
garkuwar jiki"
Gab ɗaya suka kalleshi a razane, Bulama yace "waye ya gaya maka wannan maganar
banzar?"
"Karka ƙara kiran ta da maganar banza, dan ba ƙarya akayi maka ba, ko basu sani ba
dama yau nayi niyyar zuwa in fayyace musu komai, ɗanka Fahad shine ya shafamin
wannan ciwon, ni kuma nai alwashin shafa maka, dan haka ka bimciki lafiyarka, daga
kai har matarka, daga yau kaida ɗanka seku shiga taitayinku ku kiyayi yaran mutane"
Kuka Hajiya Sarah ke ƙoƙarin yi, amma ta kasa ta dinga binsu da kallo, yayinda
Ramadan ya daskare dan mamaki, Bulama yace "wallahi ƙarya kikemin, ni ban aikata
haka ba, wallahi ƙaryane"
Ramlah tace "wannan kuma ya rage naka Bulama, nayi hakane dama dan tarwatsa kan
iyalinka kamar yadda a sanadinka duk mun ɗaiɗaice babu wanda be abun kunya ba, gara
a raba ai, ace kowama yayi"
Ta kalli Hajiya Sarah tace "Hajiya Sarah kece abar tausayi, Kasancewar kin zauna
da baƙin kumurci tsayin shekaru baki san waye ba, ki gaggauta bincika lafiyarki,
idan baki kamu ba shikenan, idan kuma kin kamu se ince Allah ya bamu lafiya baki
ɗaya"
Ta juya ta bar musu falonsj, ta fics tana fita kuwa Hajiya Sarah ta yanke jiki ta
faɗi cike da ɗimuwa Ramadan da Bulama sukayi kanta, sedai Ramadan yace "karka sake
ka taɓamin uwa, Kuma insha Allah zaka ga sakamakonka tun a nan duniya, macuci mara
imani kawai"
Ramadan ya shiga kiciniyar ɗagota, Fahad kuwa yana ta bayan ɗakin, yana laɓe yaji
komai ya zame ƙasa ya zauna yana kuka, tabbas Ramlah ta rusa musu farinciki gaba
ɗaya, farinciki na har Abada makuwa, ya shiga tunanin me zeyi wanda ze fanshe
wannan cin mutunci da tayi musu?.
Hajiya Halima ma gidan Alhaji Haruna ta tafi, bayan jin irin katoɓarar da yayi mata
akan Amal, taje ta sameshi shida Salma da uwargidansa a falo, da gani wata matsalar
ce na family issues suke solving, taje musu afujajan kamar wadda tayi gobara a ka,
tana zuwa ba sallama ba gaisuwa bakomai ta haushi da bala'i.
"Wallahi Haruna ka bani mamaki, nayi mamakin abunda ka aikatamin, ashe fyaɗe kayiwa
Amal? Daga aikota ta kawo maka takadda dan baƙin zalunci, wallahi baka isa ba
zakaga matakin da zan ɗauka akanka"
Uwargidansa ta bisu da ido, dan ita bata da wani baki sosai, Salma kuwa tace "ba
shakka, biri yayi kama da mutum, shiyasa yarinyar nan ta dinga bibiyar ka? Tana
turon saƙonni da ɓoyayyiyar lamba ashe dagaske ne abuika aikata? Ko kunya ba kaji
ba gaka da yara mata, amma kayiwa wata fyaɗe?"
Cikin inda inda Alhaji Haruna yace "Ni, Ni wallahi ƙarya takemin ita ta kawo kanta"
Salma tace "kai ko kunya bakaji ba kake cewa ifa ga kawo maka kanta? Allah wadaran
halinka nayi dana sanin Aurenk, Wallahi da in Auenka gara ace Yusuf ɗina na Aura
dukda rashin asalinsa, dan nasan baze taɓa wannan akuyancin ba"
Hajiya Halima tace "Haruna ka bani kunya, ka bani mamaki ka cutar min da yarinya,
gaba ɗaya kun kassaramin rayuwata data yarana, wancan ya ɓata kunce a kasheshi,
wannan kai ka lalata ta, waccan kuma Bulama ya lalata ta ɗansa ma yayi, sun saka
mata HIV, na rasa dame ma zan kiraku, kun cuceni kai da Bulama dukda kasancewarsa
ɗan uwana Allah ya isa wallahi "
Tai maganar tana kuka, Alhaji Haruna ya saki tumbi yana kallonta, duk damfara da
satar da 'yarta tayi masa bata gani ba se shi zata kalli abunda yayi mata.
Ya kalleta sama da ƙasa yace "Malama ki fita ki barmin gidana, kije can ku ƙarata,
ita bata gayamiki abunda tayimin ba, se wanda nai mata, kije kiyi duk abunda
zakiyi, kinzo kin ɗagamin hankali a cikin iyalina"
Hajiya Sarah ta kalleshi tace "ni kakewa haka? Ni kake kora daga gidanka? Kamin
wannan mummunan abu sannan ka Kalleni kace in bar maka gida?"
fice daga gidan, zuciyarta na ƙuna gaba ɗaya yaranta sun lalace gaba ɗaya.
Salma taje gabansa ta tsaya tace "wallahi banga amfanin zama da fasiƙin mutum
irinka ba, dan haka ka sakeni malam"
Alhaji Haruna yace "Ai Aurena dake har abada tunda iyayenki kwaɗayayyune, sunga
kuɗi sun auramin ke wallahi bazan sakeki ba dan ina sonki"
"karka sake ka zagarmin iyaye, kuma wallahi seka sakeni tunda ba tare aka haifemu
ba, macuci me abun kunya kawai"
Ya tureta yai wucewarsa yace "kanki ake ji, wadda taga zata zauna shikenan, wadda
bzata iya ba ta ƙara gaba, amma saki kam babu shi"
Cikin kuka Salma tace "wallahi ƙarya kake seka sakeni, wallahi bazan cigaba da zama
sa fasiƙi ba"
Uwargidan kam bata iya magana, sedai kuka dayake irin ta da ɗin nan ce, tun auren
ƙuruciya gashi babu wani isashen ilimi a tare da ita.
Lamarin mahaifiyar Nurat fa sam babu sauƙi a lamarin, dan sati guda kenan babu wani
cigaba, gaba ɗaya Nurat ta ɗaga hankalinta akan halinda mahaifiyarta ke ciki, jin
mahaifintane yai sanadiyar faɗowar mahaifiyarta daga bene yasa taji gaba ɗaya ya
fita daga ranta, ko san ganinsa ma batayi, gashi idan yazo Asibiti dubata 'yan
uwanta suyi ta haɗe masa rai, ko sabgarsa basa shiga, Nurat kam an sallameta tuni
amma taƙi barin Asibitin, idan tana buƙatar wani abuma gidan su Khalil take tafiya,
gidan yayar mahaifiyarata kenan.
Ramadan kam Asibiti ya kai mahaifiyarsu, ya kira Iman dake makaranta suka zauna a
gurinta dan kula da ita, dan ta samu shock ne a wannan lokacin.
Bulama kuwa bayan tafiyar Ramlah ya bita har gida, yana zuwa lokacin Hajiya Halima
ta dawo da baƙincikin gidan Alhaji Haruna, yazo yana wani muzurai yace "Ina Ramlah
take?"
Hajiya Halima ta kalleshi tace 'ban sani na, azzalumi ma cuci burinka ya cika,
gaba ɗaya yaran sun watse Bukar saboda muguntarka da rashin imani"
"Na gayamiki ɗin, ai ba ƙarya nayi miki ba, mugun son Abun duniyarkine ya janyo
miki da kwaɗayi"
"Lallai Bulama ka cika butulu azzalumi, to wallahi zan taka bakin faranti komai ya
watse"
"kar Allah yasa ki fasa takawar, kije kiyi duk abunda zakiyi, ai idan ta tashi
watsewa tare zata watse mana, kuma ki sani idona idon Ramlah sena saka an kashe ta"
Ramlah ta fito daga sashensu tana tauna cingan, kallo ɗaya za kamata kasan 'yar
wisi ce, ta kalli Bulama tace "kai ka isa kasa a kasheni, ai base kunyi barazanar
taka bakim faranti ba, kuji da abunda ke tunakaroku, Asirinku na daf da tonuwa a
kotu, a nan yakamata ku maida kai mussman ma kai, ba wai zaka kasheni ba, dan ni na
diha na kasheka da ranka tuni"
Ta ƙarasa maganar tana ɗura ruwan roba a cikinta, ta juya ta wuce dining dan cin
Abinci, Hajiya Halima ji take tamkar tayi hauka, komai ya dagule mata, ta rasa meke
mata daɗi.
Bulama ya fita da sacacciyar gwiwa jiki ba ƙwari, yanzu duk wannan barazanar da
kwarinin dayake ana tsoronsa duk babu.
Tunda Ramadan ya ɗau mahaifiyarsa daga gidan basu sake komawa ba, har Allah yasa ta
farfaɗo, aka ɗibi jininta aka gwada amma ba'aga ƙwayar cutar ba, akace bayan
watanni uku zasu dawo sake yi, se kuka take tana tunanin wans irin lamarine wannan,
ɗa ya nemi mace ta bashi kanta, kuma ta koma tabi mahaifinsa saboda Taɓarɓarewar
ƙarshen zamani.
Daga Asibiti kai tsaye, Adamawa Ramadan ya tafi da Mummyn, saboda can ne ainihin
garinsu.
Bulama yaje Asibiti aka ɗibi jininsa, da niyyar yasan a wani mataki yake, yana da
cutar ko babu? Amma yakasa tsayawa a gaya masa sakamakon saboda fargaba ya gudu.
Haka abubuwa suka cigaba da damalmalewa azzalumai, basu fargaba lokacin komawa kotu
yayi, ga kawunansu a rarrabe, kowa yana kallon kowa a banza, ga yadda suka dinga
zaluntar junansu.
Yau kuma Barrister Hafiz ne ya fito ya gabatar da kansa, tunda Bulama ya ga
Barrister Hafiz cikinsa ya ɗuri ruwa ya zuba ido yaga meze faru.
Barrister Hafiz ya fito ya gabatar da kansa, yace "Sunana Barrister Hafiz, lawyer
me zaman kansa, ina ɗaya daga cikin lawyoyi gidan Alhaji Nasir Daula, kuma ina ɗaya
daga cikin lawyoyin da zasu bawa wanda ake ƙara kariya, kimanin shekaru goma sha
biyu baya, tun bayan da ayyana cewar kaso bakwai na dukiyarsa akwai me ita, yasa
aka dinga bibiyarsa da 'yarsa akan lallai a karɓi wannan dukiya, har kawo ga kashe
matarsa da akayi, wanda ba' a ƙarabi ta kan case ɗinba tsawon shekaru, a tare dani
akwai shedu da hujjoji da zasu tabattarwa da kotu wanda ake ƙara bashi da hannu
gurin yin garkuwa da 'yar gidan Alhaji Nasir Daula, ko kuma shi Daula kansa "
Ya ƙarasa inda Yusuf yake tsaye, ya kalli Yusuf yace " Malam Yusuf, ko zaka iya
gayamana yadda akayi ka fara aiki a gidan Alhaji Nasir Daula? "
Yusuf ya ɗanyi shiru yana kallon Barrister Hafiz, Barrister Hafiz ya jinjina masa
kai alamar ƙwarin gwiwa.
Yusuf yace "Abokin aikina Abbas, shine yazo ya sameni da maganar ga aikin da ake
so inyi, shugabanmu yace a bani umarnin yin wannan bincike, da farko naƙi amsawa,
daga baya naga tunda aikinane bazan iya cewa a'a ba, tunda ni na ɗau alƙawarin
aiki, Abbas shine ya kaini gidan Alhaji Nasir Daula da kansa, yana zuwar musu gidan
a matsayin Sani me yankan farce, kuma yana mutunci dame gadin gidan "
"Bayan an kaini gurin 'yar gidan Daula, tace min sena saka hannu akan wata takadda
kafin in fara aiki da ita, na karɓa na saka, tace min saka hannun da nayi tamkar na
saka hannu a contract ɗin mutuwana ne, da farko naji tsoro se ban nuna ba saboda
tunda aiki najeyi, bazan janye ba saboda abunda ta faɗa "
Barrister Hafiz ya jinjina kai yace " ko Isa megadi yana gurin nan? "
Isa megadi ya miƙe, aka masa umarni daya fito, ai kuwa ya fito yazo ya tsaya.
Barrister ya kalle shi yace " me zaki iya cewa akan abunda Yusuf ya faɗa "
Isa megadi yace" tabbas lokacin da ake neman direban da ze dinga jan 'yar Alhaji
Daula a mota, Sani me yankan farce, wanda se da aka fara shari'a naji sunansa Abbas
kuma ɗan sandane, shine ya kawo Yusuf gidan nan, kuma daya kawo shi me gidan yana
matuƙar ƙaunarsa saboda haƙurinsa, kuma duk rashin yaddarta ita uwarɗakin nasa tana
yadda dashi sosai"
Kafin Barrister Hafiz ya kuma gabatar da sheda, Barrister Sadik yace yana da
tambayoyin da zewa Yusuf, Alƙali ya bashi dama, yaje gaban Yusuf ya tsaya yace
"Kamar yadda ka bayyanawa kotu cewa, 'yar gidan Nasir Daula tace maka aiki da ita
tamkar signing ne akan contract ɗin mutuwarka, meyasa ka amince kayi aiki da ita,
ko duk cikin shirinka ne na saceta"?
"Objection ya megirma me shari'a, Barrister yana ƙoƙarin saka wanda ake zargi yayi
confessing ne ko kuma tambayarsa yake?"
Alƙali ya buga guduma yace "Order, Barrister Sadik cigaba da tambayoyinka"
Yusuf yace "Ni ɗan sanda ne, kuma dama rayuwar ɗan sanda na tsakanin rayuwa da
mutuwane dan kare rayuwa da dukiyar wasu, shiyasa ban razana na janye ba, saboda
aiki nake"
Barrister Sadik yace "kace bincike kaje yi gidan Alhaji Nasir da kuma bawa 'yarsa
kariya, wane irin bincike?"
"Kamar yadda Barrister ya faɗa ɗazu, ana kai musu farmaki, saboda dukiyar da yace
batasa bace, an bani aikinne dan gano suwaye da kuma bawa Widad kariya"
Barrister Sadik yaga idan ya cigaba da tambayoyin nan, tabbas Yusuf ze ɓallo ruwa,
dan haka ya koma ya zauna.
Barrister Khalil ne ya shigo cikin kotun da hanzari, fuskarsa babu annuri idonsa
jajawur, ya tsaya yace "ina me neman afuwar kotu, na gaza halartar kotu da wuri,
hakan ya biyo bayan neman wata sheda da bata zo hannunmu akan lokaci ba, sunana
Barrister Ibrahim Khalil, lawyer me zaman kansa ina cikin tawagar lawyoyi dake bawa
wanda ake tuhuma kariya, idan kotu ta bani dama, zan fara gabatar da shedu da
hujjoji, amma kafin nan ina son yiwa wanda ake ƙara tambayoyi"
Aka bawa Khalil dama, Khalil yaje gaban Yusuf ya kalleshi, dukda Yusuf a wahale
yake amma hakan be hana Khalil ganin kyau da Yusuf yake dashi ba, yace "Malam
Yusuf, kamar yadda kayi iƙrarin bincike kaje yi gidan Alhaji Nasir Daula, kotu zata
so ta san wane sakamako ka samu na binciken? Sannan ina kudin binciken da kayi?"
Yusuf ya ɗaga ido yai ido huɗu da Hajiya Halima, ya kalli inda Bulama ke zaune, ya
ɗauke kai yace "An karɓi kundin binciken, lokacin da aka kamoni ina hannun 'yan
sanda, sannan a bincikema na farko, akwai yunƙuri da akayi na sace' yar gidan
Daula, a gidan wani tsohon ɗan majalisa da taje taya 'yarsa murnar zagayowar
haihuwarta"
"Matar Alhaji Nasir, tana da wani ɓoyayyen nufi akan Widad, suna bata maganin gusar
da hankali, sannan suna da wani nufi akan dukiyar Alhaji Nasir, dan akwai babbar
'yarta data taɓa cemin in bata password ɗin Banki na' yar Alhaji Nasir"
Barrister Saminu ya mike yace "Objections sir, wannan tambayoyin da Barrister kewa
wanda ake ƙara, basu da tushe balle makama kame kame ne kawai sukeyi, dan haka ina
Roƙon wannan kotu me Alfarma, da tayi watsi da wannan magana da wanda ake ƙara yake
faɗa"
Cikin zafi Khalil yace "ina da tabacci da ƙwararan shedu akan abunda wanda ake
ƙara gaskiya yake faɗa, idan kotu ta bani dama ina son ganin Hajiya Halima, matar
Alhaji Nasir Daula, don gabatar mata da wasu tambayoyi"
Aka bashi dama, Hajiya Halima ta fito, gaba ɗaya ta tsoste tsufanta ya fito jikinta
se rawa take yi, bayan ta tsaya Barrister Khalil ya nemi ta gabatar da kanta, ta
gabatar da kanta a gaban kotu, Khalil yaje gabanta ya ɗakko wata takadda a
aljihunsa, ya ajiye a gabanta yace "kin san rubutun waye wannan?"
Jikinta ne ya hau rawa, wasiƙar da Anwar ya bari ce, ta kalli Khalil a razane ta
girgiza kai tace "A'a ban sani ba"
Ta jinjina kai alamar eh, Khalil ya juya ya kira Murtalah, Murtalah ya fito ya
tsaya, Khalil yace "kotu na buƙatar ka gabatar da kanka, sannan ka faɗi abunda ka
sani"
Murtalah yace "Sunana Murtalah, kuma ɗaya daga masu aiki a gidan Alhaji Nasir
Daula, wata ɗaya zuwa biyu baya, naje ɗakin Anwar zan gyara masa, na ga ya bar
wannan takaddar, na ɗauka na karanta na kaiwa mahaifiyarsa ba tare da na nuna mata
na karanta ba, bayan na kai mata da yamma 'yarta Amal tazo zata fita tana ga sauri,
bata sani ba seta yarda takaddar, nikuma na tsinta, kamar yadda ya rubuta a
takaddar, tun daga wannan lokacin ba' a ƙara ganin inda yake ba ya bar gidan gaba
ɗaya "
Yaje ya dudduba cikin takaddunsa ya ɗakko wani littafi, ya dawo gaban Hajiya Halima
ya miƙa mata littafin yace "wannan kamar littafin ɗanki me Anwar, na Jami'a ko?"
Ta karɓa ta duba, ta jinjina kai, Khalil yace "ki dubamin ko akwai bambanci
tsakanin rubutun cikin wannan littafin dana takaddar gabanki?"
Take ƙafafunta suka hau rawa, taji tana numfashi sama sama, ta tsaya tana rarraba
ido.
Alƙali ya karɓi takadda da littafi, Khalil ya kalli Hajiya Halima yace " wane irin
rashin gaskiya ne haka ɗanki yake tuhumarki dashi? Wanda yasa har ya bar gida?"
Barrister Khalil yace "ina neman wannan kotu ta bani dama, domin yiwa Babban Amini
ga Alhaji Nasir wasu tambayoyi wato Alhaji Bukar Bulama!!!"
Ayshercool
07063065680
12/7/21, 11:04 PM - Buhainat: LITTAFIN KUƊI NE, DAN ALLAH KI SIYA KAFIN KI KARANTA
BA DANNI BA DAN ALLAH, LITTAFI NA ƊAYA KYAUTA NE WANNAN NA SIYARWA NE
NORMAL GROUP ₦300
VIP ₦500 NE KITURA TA WANNAN ACCOUNT ƊIN
0009450228
JA'IZ BANK
AISHA ADAM
SE A TURA SHEDAR BIYA TA WANNAN LAMBAR
07063065680
(Albishir ga masoya, ma'abota bibiyar litattaafaina, dama ta samu zaku fara samun
litattaafaina na audio, akan YouTube channel ɗina me suna Cool Arewa TV
https://youtube.com/channel/UCD5vnvA5laU8ti4LLz2_QEg
Kuyi liking sannan ku danna subscribe, domin fara samun litattaafaina na audio,
nagode sosai da ƙaunar ku gareni"
152_153
Suleiman yace "Yusuf ka kwantar da hankalinka, dama Allah ya ƙaddara hakan seta
faru, ta wannan dalili naka, mudai fatanmu Allah ya baka lafiya ka warware"
Suleiman yace "bakomai Yusuf, Allah dai ya baka lafiya ya ƙara wanke mana kai daga
sharrin maƙiya"
Yusuf yace "Ameen ya Allah, to su lawyoyin da suka tsayamin sun sanni ne? Meyasa
suka tsaya min, kuma meyasa basu taimakeni da farko ba?"
"Yusuf, lokacin da ake maka shari'a ta farko, su Bulama sunyi mamaya ga wannan
shari'a fiye da tunaninka, ta ƙarƙashin ƙasa aka bi aka dinga samo shedun nan fa, a
yadda Khalil yake gayamin, Nurat ce ta takurashi akan lallai ya tsaya a fitar da
kai, saboda tasan wasu daga abubuwan da mahaifinta ke aikatawa, to yazo dai ya
kawomin ziyara, muka tattauna na gaya masa abunda nasani daga abunda Saleh yake
zuwa yana gayamin, yayi duk binciken su daya dace na tallafa masa da abunda nasani,
to su dai sauran lawyoyin bansan yadda akai ya samosu ba, nidai ya sanarmin zasu
ɗaukaka ƙara, shikenan se ranar shari'a nima na gansu "
Yusuf ya jinjina kai yace " Alhamdilillah, Allah nagode maka "
Suleiman yace" An gode Allah kam, ka kwantar da hankalinka, komai ze wuce insha
Allah "
Umma tace " dan Allah ka kwantar da hankalinka, sannan kai shiru da wannan surutun
ka samu isashen bacci "
Har Yusuf yayi shiru, ya kuma cewa " Yallaɓai ya Widad fa? A wani hali take ciki? "
Yusuf yace " cewa nayi a wani hali Widad take ciki? "
A fusace Umma tace " waya san mata, baka da zuciya Yusuf, yarinyar tazo ta bada
sheda akanka, bayan a dalilinta ka shiga halin da kake ciki, amma kana wani maganar
tana ina, in sake jin kayi maganarta sena saɓa maka"
Yusuf yai shiru, Amma yana tunanin shiya kuɓuta, to matarsa fa?.
Widad kuwa tuni 'yan sanda sukaje suka ɗakko ta a gidan nan bayan an kama Bulama
yaji matsa ya faɗi inda take, tana zaune a ɗakin da take, taji ana guje guje, ba
inda ta iya motsawa daga inda take zaune, Sega' yan sanda sun shigo, suka ɗakko ta
suka tafi da ita Asibiti, tayi baƙi duk ta kukkumbura, haka suka ɗakkota a
gakabaice ga babu isashen Abinci da kulawa.
'yan sanda suka kama har wannan Sabuwar, wadda take kuka da Widad a gidan.
Da aka kaita Asibiti ma, a emergency aka ajiye ta, saboda ciwon zuciya da jininta
daya hau fiye da kima, ga dislocation data samu a hannunta saboda ball da Bulama
yake da ita.
Likitoci sun fara tunanin ko a cire mata cikin, saboda kar yai sanadiyyar rasa
ranta, Amma Widad a wahal ce tace "likita, dan Allah ka barmin cikina, gara in
mutu dashi a jikina, dan Allah a bawa Yoseef haƙuri, na bada sheda ne dan in ceci
rayuwarsa, amma nasan ya bani gudunmuwa, dan Allah ya yafemin, nagode Allah tunda
ya kuɓuta"
Haka taita surutai, seda aka mata Allura sannan bacci ya ɗauketa, ta ɗau tsawon
lokaci tana wannan baccin, kafin ta farka sedai ga mamakin su, bayan ta farko
jininta ya sauka ba kamar da ba, suna yi suna monitoring ɗin yanayin jikinta, da
kuma probability na surviving ɗinta da wannan cikin.
Sedai babu kowa a gurin Widad, musamman mace wadda zata dinga kula da ita,
Nurses ne suke mata komai, nan ta sake kukan rashin dangi, da tana da dangi da an
samu me kula da ita.
Ramlah gaba ɗaya itama a zabure take, mutuwar Anwar ta da keta, bata taɓa zaton
dagaske Bulama yasaka a kashe Anwar ba, gashi 'yan sanda suna kama mahaifiyarsu, ga
Amal ita bame hankali ba ita ba mara hankali ba, haka suke zaune gaba ɗaya rayuwa
ta juya musu baya.
Seda Yusuf ya kwan tara a Asibiti, ana masa screening daban daban dan tabattar da
ingancin lafiyarsa, Yusuf ya ɗan murmure sakamakon Abinci da kulawa da yake samu,
kullum se an dafo Abinci daga gidan Suleiman an kawowa Yusuf, ya ɗan farfaɗo sedai
uwar rama da yayi.
Aka sallameshi daga Asibiti, tare da magunguna zuwa gida, tunda suka koma gida 'yan
jaje ke sintirin zuwa gidan nan, wasu dan suyi jaje wasu dan suyi kallo, sedai
Yusuf ko tsakar gida baya fitowa saboda baya san Hayaniya.
Abokan Aikinsa suka yi tawaga guda sukazo duba Yusuf, seda wasu suka yi kukan
farinciki, dukda miskilancin Yusuf, amma akwai kirki da girmama mutane, duk wanda
ya ganshi se yayi mamakin ramar da yayi.
Ɓangare guda kuma, hankalin Yusuf yana kan ta ina zega Widad, a wani hali take
ciki?
Seda Widad tai sati biyu a Asibiti, cikin ikon Allah ta murmure, jininta ya sauka
amma an kafa mata sharaɗin idan ta tashi haihuwa ta taho Asibiti, saboda tana cikin
hatsari karta ce zata haihu a gida, dama tunda aka kai Widad Asibitin kullum 'yan
sanda cikin patrol suke a Asibitin, har zuwa sallamarta da akayi.
Da aka sallameta ma headquarter na' yan sanda aka tafi da ita, domin amsa wasu
tambayoyi da za'a mata, gaba ɗaya saboda yadda akayi shari'ar Yusuf da yadda
abubuwa suka wakana, an sauya manyan shugabbani dake riƙe da manyan muƙamai a
hukumar, duk an canza wanda Bulama ya siye da wasu.
Widad ta faɗi yadda komai ya faru, tun daga kan kisan mahaifiyarta, da irin
Abubuwan da Bulama ya dingayi, ba tare da yasan tasan shine Bukar ba, har sace ta
da akayi tare da Yusuf, ta nuna musu inda aka harbeta a hannu, da yadda Yusuf ya
dinga wahala da ita, ƙarshe seda aka kamo doctor Hamisu wanda yake mata allurar
hauka, da sauran wanda suke da hannu a miyagun laifukan ta'addanci da aka dinga
aikatawa Daula da iyslinsa, Shima Saleh can aka samoshi a wani Asibitin gwamnati
babu kulawa, saboda garin dukan daya dinga sha ya samu rauni a hantarsa.
Widad bata da gurin wanda zata ta zauna, Akace a kaita gidan gwamnati fa zauna,
kafin Allah ya bayyana mahaifinta, tace ita gidan gonar nan zata je ta zauna, akace
baze yuwu ta zauna ita kaɗai ba, Amma Widad ta dage ita babu gidan wanda zata ta
zauna, aka ajiye jami'an tsaro a layi da kuma cikin gidan dan tsaron lafiyarta aka
barta ta zauna ɗi .
Widad Ta dinga tunanin ya akayi Yusuf be nemeta ba, dukda yayi free yanzu, sedai
tayi tunani babu lallai Yusuf ya sake karɓarta, bayan ta gaza taimakonsa a lokacin
da yake buƙatar hakan.
Gaba ɗaya gidan ya canza, babu manyan dawakan nan nata, da wasu daga dabbobinta duk
babu su, haka manyan motocin dake gidan duk babu, an kwakwance wasu abubuwan masu
mahimmanci daga gidan, taga gidan ya mata faɗi, babu Daddy babu kowa a tare da ita
yanzu.
Ta zauna tai shiru tana tunani, ta fito harabar gidan tana zagaye, ma'aikatan se
zuwa suke suna mata fadanci, suna mata jaje tare da barka da Arziki, ta kira wani
daga cikin ma'aikatan gidan Imrana, yazo gabanta ya durƙusa tace "naga gaba ɗaya
gidan nan ya canza, ina wasu daga cikin dabbobina da motocin duk da suke cikin
gidan nan?"
Imrana yace "ranki ya daɗe, Hajiya ce take turowa a ɗiba a fita dasu, kuma bamu da
ta cewa"
Haka ta dinga zaga gidan, tana tuna abubuwa da suke shuɗe, da abubuwan da suka faru
daren da akayi garkuwa dasu, ta shiga ɗakin data kwanta a ranar, tana dube dube,
can ta hango wayarta guda ɗaya a ƙasan gado, Da daddy yazo ya azalzaleta ta tashi
ta fito wayar ta faɗa ƙasan gado, ta ɗau waya ɗaya ta fita, waya ɗayan da yanzu
bata san a inda take ba, ta ɗakko wayar ta ganta a kashe, ta jona a jikin caji
aikuwa ta kama.
Ta jona wayar ta koma ta zauna, a hankali tace "Yoseef am missing you, i have no
one, help me to relay on you, ka yafeni ka dawo gare ni mana"
Ta yanke shawarar komawa tayi zamanta ita kaɗai, ta cigaba da Addu'a Allah ya
bayyana mata mahaifinta, kota rage wata damuwar, amma da kunya a gareta ta tinkari
Yusuf a yanzu.
Gaba ɗaya damuwa da kaɗaici suka baibayeta, ta fito ta ɗau mota zata fita ɗaya daga
cikin 'yan sandan dame gadinta yazo yace "ranki ya daɗe, ina zakije ne haka?"
Yace "ranki ya daɗe har yanzu kina ƙarƙashin kulawar' yan sanda ne, idan kika fita
ke kaɗai hakan ze iya zame mana laifi a sama"
Widad tace "shikenan, dan kuna gadina bazan fita ba? Da can wake kula dani idan ba
Allah ba? Ina kuna garin nan da saninku aka siye wasu daga cikinku akaci zarafin
mijina, aka sacemu babu wanda yai yunƙurin kawo mana ɗauki, se yanzu zaka zo kana
gayamin zancen banza? Ban fidda ran a sake dawowa a haɗa baki daku a cuceni ba"
Ɗan sandan yace " Allah ya temakeki, kiyi haƙuri kin san duk yadda kaso ga kamanta
gaskiya, se an baka umarnin aimata wani abun daga sama kafin kayi, amma dan Allah
kiyi haƙuri karki fita ke kaɗai, dan Allah ki rufamana Asiri, za'a iya ladabatar
damu idan mukayi sakaci wani abun ya same ki, har yanzu kina ƙarƙashin kulawar
jami'an tsaro ne"
Ta jefa masa key ɗin mota tace "kaini gidanmu, inda muke zaune"
Ɗan sandan ya ɗauki key ɗin, yana mamakin wannan izza ta Widad, ta shiga bayan mota
ta zauna, ta tuna idan Yusuf ze fita da ita, a gaban mota take zama, suna tafe
wataran tana zazzaga masa masifa, ko kuma yana wani abun da ze bata haushi suyita
faɗa.
Ta lumshe idonta tana jin yadda sonsa ke ƙara ratsa ilahirin gaɓoɓin jikinta, se
yanzu ta yadda so babbar cutane, bata taɓa tunanin haka yake ba, bata zaci tayi
sabo da Yusuf haka ba, tana jin ya zama wani ɓangare na rayuwarta gaba ɗaya, kobe
nemeta ba doke ita ta nemeshi.
Suna zuwa ƙofar gidan, tace ya tsaya yayi horn, yai horn aikuwa Isa yaeƙo yaga
waye, kawai ya hangi Widad a bayan motar, aikuwa ya gigice ya tafi da gudu ze buɗe
Gate, ya dawo ya kuma komawa ya rasa mema zeyi.
Widad ta sauke gkass ɗin motarta tai masa nuni da yazo, ya taho da sauri jiki na
ɓari yazo ya durƙusa yana faɗin "Allah ya temakeki, Allah ya tsare ki sharrin
maƙiya" kawai ya fashe da kuka ya kasa cigaba da maganar.
"ranki ya daɗe dole inyi kuka, tunda kika tafi babu ke babu Yallaɓai, gaba ɗaya
gidan annurinsa ya ɗauke, muka shiga mummunan yanayi, katsam kuma se gashi kun dawo
amma ba'a yadda akeso ba, a wani yanayi na daban abubuwa sun faru marasa daɗi ranki
ya daɗe Alhamdilillah tunda dai kin dawo kuma kin kuɓuta "
Widad tace " Isa dukda mugayen halayena da kuke faɗa, dama zaku iya shiga damuwa
dan na bar gida? "
Isa yace " A'a a'aha, ai ranki ya daɗe Hausawa sukace kada Allah ya kawo ranar
yabo, amma wallahi zamanki a gidan nan ba ƙaramin haske bane, mungode Allah"
Isa ya zabura da sauri hadda gudu, ya shiga gidan yana ƙwalawa Su Nura kira.
Aikuwa gaba ɗaya suka rankayo suka biyo shi, suna zuwa suka ga Widad bakinsu yaƙi
rufuwa, suka zube a gabanta suna surutai kowa da abunda yake faɗa.
Haka nan Widad taji ƙwalla ta rasa ta mecece? Tai murmushi tace "Nagode Allah,
tunda duk kun tsallake tarko da sharri na Bulama, naji daɗi Sosai da gudunmuwar da
kuka bayar a kotu, gurin kuɓutar da mijina, nagode muku sosai Allah yasaka da
alkhairi"
Abun mamaki wai yau Widad na hira da maa'ikatan gidansu, matar da ko murmushinta
ba'a gani idan ba na mugunta ba, ko tana gaban mahaifinta ba.
Widad tace "IKone na Allah kawai, naji daɗi Sosai da kuka temaka da sheda a kotu"
Murtalah yace "Ai bakomai ranki ya daɗe, Yusuf mutum ne ya cancanci a temaka masa,
tunda na tsinci takaddar nan na rasa ina zan kaita, saboda barazana da akewa duk
wanda yai yunƙurin temakawa Yusuf, katsam sega lawyern Yallaɓai, ya gayyacemu
gidansa a ɓoye yai tattaunawar sirri damu, a nan na bada wannan takaddar "
Widad ta jinjina kai tace " Masha Allah, ina godiya sosai da gudunmuwar ka, kuma
insha Allah kuna da tukuici akan wannan gudunmuwar da kuka bamu "
Nura yace " Allah ya temakeki, wai yanzu dama duk abubuwan nan Alhaji Bulama ke
shirya su, tabbas banga laifinki ba na ƙin mutane da kike, amma abun ya bamu mamaki
sosai "
Widad tai murmushin takaici, har bata son yuna irin azabar da suka sha, tace " ya
ake cikine? Me gidan namu yake ciki dan bazan shiga ba"
Nura yace "ranki ya daɗe, gida babu daɗi dan ya watse gaba ɗaya, bayan ɓatanku,
Yallaɓai ya faɗi yai wata rashin lafiya, babu me zuwa gurinsa ko kula dashi se
Anwar, shine yake masa komai yake jinyarsa, da aka sace Yallaɓai a gadon Asibiti ma
aka kama shi, akace da saka hannunsa ya sha wahala sosai, Amma ya kula da Yallaɓai
"
Jiki a sanyaye Widad tace " Allah sarki Anwar, yana gidan ne yanzu haka? "
Isa yace " ranki ya daɗe, Amma kin san an kama Hajiya ko? "
Yace" to dama ya bar gida ai tuntuni, takaddar daya bari ai ita Murtalah ya tsinta,
ranar da aka yi zaman ƙarshe a kotu, muna nan 'yan sanda suka zo a motoci suna ta
jini ya, na buɗe musu gate sukazo suka shimfiɗe Anwar, an gano shi a wani gida yake
rayuwarsa yana kasuwanci a can cikin Jos, aka kawo shi an kasheshi ta hanyar caka
masa makami a gefen cikinsa, sedai babu wanda yasan wanda ya kasheshi, amma a ranar
kukan da Hajiya Halima take kamar dasa hannun shi Bulaman dai a kisan"
Ai tuni hawaye ya wanke mata fuska, ta dinga jujjuya kai tana maimaita innalillahi
wa inna ialaihi raji'un, Ya Allah, Yaya Anwar ubangiji Allah ya jiƙanka, naso na
sameka a raye in maka godiya riƙemin amana da kai, amma zan dawwama yi maka Addu'ar
samun salama a kabarinka, kana daga cikin mutanen da bazan manta dasu ba a
rayuwata, Allah ya yafe maka Yaya Anwar"
Kuka yaci ƙarfin Widad, yayin da suma duka jikinsu yayi sanyi sukaji mutuwar tamkar
yanzu akayi ta.
Widad cikin kuka tace "Murtalah ka sameni a farm House gobe in Allah ya kaimu da
yamma, nagode muku Allah yasaka da alkhairi nagode sosai"
Ta kasa ko rufe ƙofar motar, se kuka da take yi, Isa ya rufe mata ƙofar motar, ɗan
sandan nan ya ja suka tafi, suna tafe tana kuka, dan Mutuwar Anwar ta da keta fiye
da tunani.
Yusuf ya ɗan warware, Suleiman ya kwashe su a mota domin sujewa Nurat gaisuwa, da
yake an kwana biyu da rasuwar mutane duk sun watse se tsilla tsilla.
Kahlil yai musu iso har wani katafaren falo, aka kira Nurat, Nurat ta fito cikin
Ƙaton hijjabi, tana ganin Yusuf ta kasa magana se hawaye haɗe da murmushi daya
ƙwace mata.
Ta durƙusa har ƙasa ta gaida Umman Yusuf, Yusuf yace "Nurat ya ƙarin haƙuri kuma?"
Nan duk sukayi mata gaisuwa, Umma tace "dama munzo muyi miki gaisuwa ne, kuma
zamuyi zuwa na mussman muyi miki godiya '
Yusuf yace " Nurat, ban san me zance miki ba, wanda ze nuna irin tarin godiyar
dake bakina ba, a sanadiyata ga abubuwa marasa daɗi sun faru dake, Nurat dan Allah
kiyi haƙuri, ban san mema zance ba"
Khalil yace "karka damu Yusuf, dama haka Allah ya ƙaddara seya faru, ba kaine sila
ba, Allah ya riga ya rubuta hakan dama, sedai kam tabbas tayi faɗi tashi a kanka
sosai, tun daga ɓatanku har wannan lokacin"
Umma tace "mungode, mungode Allah ya saka miki da alkhairi, Allah yayi miki
Albarka ya jiƙan mahaifiyarki"
Nurat ta dinga jinjina kai, tana tuno Mummynta, ta kalli Yusuf tace "Kasan kuwa an
kashe Yaya Anwar?"
Ta goge Hawaye tace "Bayan ɓatanku, Daddyn Widad faɗuwa yayi, ya fara rashin
lafiya babu kowa a gurinsa babu me zuwa gurinsa , Anwar ne kawai yake gurinsa, ya
dinga jinyarsa tsawon lokaci, bayan wani lokaci aka sace Daddyn Widad a Asibiti,
aka kama Anwar ya daɗe a tsare ya sha wahala sosai kafin ya kuɓuta, to kwanan nan
dai Brother ya cemin ai Ya bar letter a gida, ya bar gidan gaba ɗaya ba'asan inda
yake ba, ranar da aka gama shari'arka akace an kashe shi kuma ana zargin Bulama ne
yasaka "
. Umma ta dafe kai tana faɗin innalillahi wa inna ialaihi raji'un, yayin da Nurat
ta sake fashewa da kuka.
Khalil yace "se haƙuri, da kuma mu taya su da Addu'a, Wannan me aikin gidan ne
Murtalah, ya tsinto takaddar, ban san ya'akayi yai kyan kai ya kaiwa Barrister
Hafiz ba, dan abun zamana yayi duk wanda yai wani yinƙuri na temakawa a gano
gaskiyar lamarin, se an bishi da mummunar barazana, mutumin nan maƙurane gurin
zalunci"
Umma tai shiru tana hawaye, tana jinjinawa zaluncin Bukar, musamman Da taji wai
ashe Anwar ɗane a gurinsa.
Nurat ta kira Yayar mahaifiyarta suka gaisa da Umma, sun daɗe suna hira suna
jajantawa juna, yayin da Suleiman da Khalil ke hira.
Nurat tai shiru a gefe, tana kuka Yusuf yai ƙasa da muryarsa cike da tausayinta
yace "Light am very sorry, kiyi haƙuri da ƙaddarar data same ki a sanadina dan
Allah"
'Nifa ba kaine silar faruwar haka a gareni ba, dama Allah ya ƙaddaramin haka zata
faru dani ne "
" Bazaki dinga kallona da abunda ya faru ba, koki zargi saboda ni haka ta sameki
ba? "
Ta jinjina masa kai alamar eh, Yusuf yace " Nagode sosai, Allah ya jiƙan Mummy ".
Nurat tace " Ameen, naji ance an kaika Asibiti ya jiki kuma? "
Yusuf yace "A'a ni yakamata in sake dawowa in dubaki in sake miki ta'aziyya, Allah
ya baki haƙurin jure rashin Mahaifiyarki"
Ta jinjina masa kai tana kuka, gaba ɗaya tausayinta ya kama shi sosai, ya cigaba da
rarrashinta, Umma ta fito ta tarar dasu tace "mu tafi ne ka taho kokuwa?"
Ya miƙe Nurat ta rakosu har bakin mota, Yusuf yana ta sake bata haƙuri yana mata
gaisuwa.
Suna tafe a motar, Yusuf yayi shiru yana tausayin Nurat, ga mutuwar Anwar data
gigita shi, ga yana son ganin Widad.
Can yaji Umma tace "gaskiya Yarinyar nan tana da nutsuwa da tarbiyya, na yaba da
hankalinta gashi ta bani tausayi Yusuf, nikam ko zaka nemi Aurenta idan zasu baka?"
AYSHERCOOL
07063065680
12/7/21, 11:04 PM - Buhainat: LITTAFIN KUƊI NE, DAN ALLAH KI SIYA KAFIN KI KARANTA
BA DANNI BA DAN ALLAH, LITTAFI NA ƊAYA KYAUTA NE WANNAN NA SIYARWA NE
NORMAL GROUP ₦300
VIP ₦500 NE KITURA TA WANNAN ACCOUNT ƊIN
0009450228
JA'IZ BANK
AISHA ADAM
SE A TURA SHEDAR BIYA TA WANNAN LAMBAR
07063065680
(Albishir ga masoya, ma'abota bibiyar litattaafaina, dama ta samu zaku fara samun
litattaafaina na audio, akan YouTube channel ɗina me suna Cool Arewa TV
https://youtube.com/channel/UCD5vnvA5laU8ti4LLz2_QEg
Kuyi liking sannan ku danna subscribe, domin fara samun litattaafaina na audio,
nagode sosai da ƙaunar ku gareni"
154_155
Gaban Yusuf yai mummunar faɗuwa jin abunda Umma tace, ya kalli Ummansa ta Mirror,
amma yai shiru yaƙi cewa komai sema ɗauke kansa da yayi yana kallon waje.
Ƙin magana yayi, dan bayama son zancen, Umma tace "Suleiman, dan Allah baka yaba
da hankalin Nurat ba? Yarinyar tana da nutsuwa da kuma kirki sosai"
Suleiman yace "tabbas hakane Umma, ni kaina na yaba da nutsuwar ta, kuma da alama
dai Yusuf akwai dalilin da yasa ta dage ta temake ka"
Umma tace "jimin yaro da wulaƙanci, ana masa magana yayi shiru, kamar ba dashi ake
ba"
Yusuf yace "Umma me zance ne? Nifa ina da Aure ya zanyi da Widad kuma?"
"Karka ƙaramin zancen wannan yarinyar, wadda bata san halcci ba bata san abun
alkhairi ba, kai ko zuciya baka da ita, duk wannan abunda ya sameka sanadinka baze
zame maka darasi ba Yusuf, irin wahalar da ka sha, ba kai kaɗai ba harni kaina da
sauran mutane, amma kake ƙara nanata wai kana da Aure, toni ban san da wannan Auren
ba, ba wani Aure da kake da shi, ni dai ga yarinyar da ta kwantamin"
Yusuf yace "Umma, Widad bazata bada sheda haka kurum ba, akwai wani dal.....
" Rufemin baki, bana son jin zancen yarinyar nan gaba ɗaya, na gaya maka "
Yusuf yai shiru, ya maida idonsa wajen window, yana tunanin yaze da Umma akan
Widad, gashi yana son ya haɗu da ita yana son su gana, amma Umma tana nema ta ɓata
komai, kuma yaga alamar idan ya matsa, ze ɓata mata rai, shi kuma babban abunda
baya so kenan, ɓacin ranta.
Haka Umma da Suleiman suka cigaba da hira har sukaje gida, ba tare da Yusuf ya tofa
ta bakinsa ba, yai shiru dan bema san me suke cewa ba.
Suna zuwa gida Yusuf yaiwa Suleiman sallama ya shige gida abunsa, Umma kuma seda
tayi sallama da Suleiman sannan ta shiga gida.
Widad kam sosai take jin mutuwar Anwar, ji take kamar mutuwar Anwar wani babban
giɓine a gareta, dukda ba ɗan uwanta ne na jini ba, amma Anwar zuciyarsa ba irin ta
mahaifiyarsa bace ba.
Tai kuka, tai kuka ƙarshe taje tai alwala ta tada salla mussman dan taiwa wanda ta
rasa addu'a, ƙarshe ta ɗaga hannu zata yi Addu'a, ta kasa roƙar komai kawai ta
fashe da kuka, "Allah ka yafemin laifukana, Allah na tuba ka yafeni, Ba Ammina, ba
Daddyna, Ba Yaya Anwar, wanda nake sa ran zeji ƙaina maƙiya sun sa na masa abunda
bazan sake kima a idonsa ba, ban san dangin mahaifina ba ban san na mahaifiyata ba,
bani da wanda zan kalla a rayuwata inji sanyi, babu me raɓata babu wanda zan raɓa,
Allah ka kawomin ɗauki "
Ta ƙarasa maganar tana rirriƙe gado da gefenta tana wani irin kuka me raunata
zuciya, idanunta sukayi jawur ta fita hayyacin ta, ta rasa abunda yake mata daɗi,
gashi har yanzu da tsoron mutane a ranta, tana jin tsoron raɓar wani, bata san
meza'a kuma yi mata na cutarwa ba, ta fara tunanin ko ƙauye zata koma gurin Gwaggo?
Wata zuciya tace "suwaye a gareki? Suba danginki ba, wane karɓa zasuyi miki bayan
suna zaune an tayar musu da hankali, hadda 'yan sanda ta yaya zasu sake karɓarki?
Idanma zasu karɓekin kin san hanyar da za' abi aje a garin? '
Lumshe idinta tayi, hawaye na zuba daga idonta, tana jin yadda take sauke numfashi
da ƙyar, alamun zuciyarta bata aiki yadda yakamata.
Ta takure a jikin bango, ta haɗa kai da gwiwarta, tana ci gaba da kuka, sanyin AC
dake ratsata taji sanyin da take ji yayi mata yawa, nan da nan jikinta ya ɗau rawa,
ta dinga rawar sanyi, kanta na wani irin sarawa amma ta kasa motsawa daga inda
takey, ƙarshe ma ta haka ta kwanta a gurin, tana jin cikinta na motsawa, ta tuna
Yusuf be san da cikin bama, ta shafa cikin a hankali tana tausayawa abunda ke cikin
nata.
Amal ta ɗan farfaɗo, sedai befi tayi magana kaɗan a rana ba, bata magana sam seda
ƙyar, gaba ɗaya ta ɗashe ta bushe saboda azabar bleeding da tayi, ga fargaba da
tashin hankali da take ciki na kama Mummynsu, ga mutuwar Anwar da damfarar ta kuɗin
nan da akayi, gashi har yanzu raɗaɗin fyaɗen da Alhaji Haruna ya mata yakasa barin
Ƙwaƙwalwarta, dan haka abun ya mata yawa, ta samu depression, Ramlah ce ke kula da
Ita take jinyarta, taga abun nata bana ƙare bane, ta ɗauketa ta kaita Asibiti.
Likita ya dubata, ya rubuta musu teses, ta kaita lap akayimata, suka kaiwa Likitan,
ya karɓa ya duba ya kalli Amal yace "ƙanwata, gayamin tsakaninki da Allah ƙanwata
meyasameki kike bleeding haka?"
Ramlah tace "doctor, bamu da wannan lokacin yanzu ma baka san da yadda na kawota
ba, kawai ai mata abunda ya dace"
"Amma kun san illar dake tattare da ayiwa mace fyaɗe aja baki ayi shiru ba tare da
ɗaukaf mataki ba, ba hujja bace a ɓoye irin wannan lamarin dan gudun jin kunyar
mutane, ki tsaya ki ƙwaci haƙƙinki shine yakamata, yanzu yaushe abun ya faru? Kuma
da ya faru an kaita Asibiti an mata gwaje gwaje ne? "
Ramlah tace " dan Allah ke dena wannan tambayoyin, kawai ka rubuta mata magani a
wuce gurin "
Ya ɗan taɓe baki yace " Any way, tunda haka kuka zaɓa zan miki bayanin sakamakon
gwaje gwajen da mukayi, wannan abortion ɗin da tayi, an mata amfani da pills me
ƙarfi wanda yafi ƙarfinta sosai, musamman duba da yanayin rukunin jininta, hakan ya
samar da gagarumin rauni a mahaifarta, wanda yasa take ta zubar da jini, mahaifarta
tayi raunin xa abune mawuyaci ta sake ɗaukar ciki, sedai idan an kaita India anyi
mata aiki, akwai wani ƙwararren gynecologist dayake aikin, sannan a shawarce yana
da kyau a dinga kaita tana ganin Likitan Ƙwaƙwalwa, saboda wannan depression ɗin ze
iya zame mata hauka tuburan, duba da yadda matakin depression ɗin nata yayi worst "
Ramlah tace " Innalillahi wa inna ialaihi raji'un, yanzu nawane kuɗin aikin zeci?
"
Ya kashingiɗa a kan kujerarsa yace " idan kun shirya kumin magana, baya cin fiye da
naira miliyan uku haka, ko yanzu idan a shirye kuke, za'a iya booking na jirgi ku
tafi"
Ramlah ta dafe kai, dan babu inda zata samo wannan kuɗaɗen, komai ya ƙare musu,
basu da komai yanzu a kangon gidan kawai suke, gashi taji labarin Widad na Farm
House dan haka a tsorace take, kar Widad tazo ta fatattake su koma tace a kamasu.
Ramlah tace "thank you very much doctor, when we are ready, we will let you know"
Ramlah ta kama hannun Widad, suka fito suka hau motar da ta rage musu zuwa gida,
haka suka koma Ramlah ta saka Amal a gaba tana kallonta, yanzu ita kaɗai ta rage
mata, ba Mummy, ba Anwar, ita kanta bata da tabbacin zata tsira, har gara Amal ita
ba lallai a sameta da wani laifi ba, gashi itama Amal ɗin ta zama shiri shiri,
Ramlah ta rasa abunyi, taje ta ɗakko kayan shaye2 ta ɗurawa cikinta, seda taji tayi
dam sannan ta baje tana bacci a gurin.
Kamar yadda Widad tace wa Murtalah tana son ganinsa, haka akayi yaje gidan gona dan
ya sameta, amma 'yan sandan da suke gadinta suka hanashi shiga, seda sukaje suka
sameta suka gayamata zuwansa, sannan tace a barshi ya shigo tasan da zuwansa.
Har falon ya shiga ya zauna, ta fito cikin dogon hijjabinta, Murtalah a ransa yace
"iko se Allah, wai yanzu Widad uwar tsiwa, gadara ganioda izza itace a haka? Itace
yanzu take komai sanyi sanyi, harda shigar zumbulelen hijjabi haka, lallai tayi
darasi na rayuwa a makarantar duny, me cike da ƙalubale da tarin matsaloli, ya ga
yadda ta sake ramewa, se kumburi a fuskarta, duk ƙibar nan babu da da aukinta, amma
yanzu kamar sillen kara haka ta koma.
Ta ƙaraso ta zauna akan ɗaya daga cikin kujerun falon, gaba ɗaya a takude take
saboda zazzaɓine ma a jikinta, ga jira dake kwasarta dan tun safe tea ne kawai a
cikinta se biscuit, bata da appetite na cin komai sam..
Widad tace "masha Allah, na kiraka ne nan dan muyi magana, zan saka wani aiki ne,
amma kafin nan bani labari, wane hali gidan mahaifina ke ciki?"
Murtalah yace "eh to, kamar dai yadda kika sani, an kama matar gidan saboda da
haɗin bakinta Alhaji Bulama yake gudanar da wasu abubuwan, ita kuma Amal mamar
hankalinta ya gushe, tunda aka kawo gawar Anwar, aka kama mahaifiyarsu ta faɗi
shikenan, ko magana bata son yi, kamar dai ta samu matsala a Ƙwaƙwalwarta ne, ita
kuma babbar dama tun bayan ɓacewarki take bin wannan ɗan gidan Bulaman, to a yadda
muke ganin abubuwa na gudana ma dai, shaye2 take yi dan wataran mankas haka take
dawo mana gidan nan, yanzu dai su biyune kawai a gidan ba kowa "
Widad ta jinjina kai tace " Allah sarki, Allah me yadda yaso, anyi ƙoƙarin
ƙaƙabamin hauka tuburan ga haauka ya fara bibiyar 'ya' yanta, an haɗa kai an
kashemin mahaifiyata, se gashi itama an sa an kashe ɗanta, shi kuma wancan ya kashe
matarsa da hannunsa, haƙƙinmu baze taɓa barinsu jin daɗin duniya ba"
Widad tai maganar tana share hawaye, Murtalah yace "ayi haƙuri ranki ya daɗe, ai
an gode Allah an auna Arziki sosai, Amma dama ita tasa aka kashe mahaifiyarki?"
"karka shiga hurumin da ba naka ba, ka tsaya iya matsayinka, ina son in dinga sanin
duk wani motsinsu, da duk wani abu dayake kaiwa yana komowa a gidan ka dinga
sanarmin, tashi ka tafi"
Murtalah ya miƙe yana godiya, harze fita tace "ya batun salary ɗinku? Ana biyanku
kuwa?"
Yace "ranki ya daɗe, ai se muyi wata biyu kafin a bamu albashin ma, kuma duk anbi
an rarrage mana albashin"
"Kuyi lissafin abunda kuke bi na bashi, zan biya ku ruɓinsu biyu insha Allah"
Murtalah ya zube a gurin yana "Allah ya temakeki, Allah ya baki yawan rai yasa
kifi ƙarfin maƙiyanki"
Tace "ina son saka ka aikine, kaje ka bincikamin inane gidansu, ina son in dinga
sanin duk wani moves ɗinsa ne, ina son dinga sanin halin dayake ciki"
Yace "to ranki ya daɗe, zan ƙoƙari in gano gidan nasu, amma kin san bani da damar
da zan bari gidan nan, in koma unguwarsu saboda a nan aka ajiyeni inyi aiki"
"karka damu, akwai tukuici me kyau, sannan babu wanda ze zargeka akan hakan, zan
baka kariya ince nine na saka aikin"
"baka da matsala"
Yusuf jikinsa yayi kyau sosai, ya farfaɗo daga wannan uban baƙin da yayi kamar
bashi ba, saboda samun sassauci da yayi daga ƙangin zaman gidan kurkuku, sedai Umma
na cigaba da damunsa akan lallai yaje ya nemi Auren Nurat, yace "Umma, kina cewa
inje in nemi Auren Nurat, idan fa na nemi Aurenta dole za'azo bincike wataran, bana
son abunda ya faru dani akan Salma ya sake faruwa, ga kuma abunda ya faru da
iyayenta saboda ni, ina jin tsoro Umma, amma kinga Widad tasan koni wayey, tasan
Halinda nake ciki amma muka zauna tare a haka, ba tare da ta nuna ƙyamarta a gareni
ba"
Umma tace "kaga sauraramin, Itama Nurat ɗin zata iya aurenka ai, yarinyar bata da
matsala kuma banga alamar wulaƙanci a tare da danginsu ba, nifa wannan Widad ɗince
bana so, abun da ya samemu saboda ita bazan taɓa mantawa ba, duk wannan baƙar
azabar ka shata ne saboda ita fa, amma baka gani "
Yusuf yace " Umma, Widad abun tausayi ce, baki san abunda ya faru da ita bane, ni
kaina nasa....
Umma ta katseshi ta hanyar cewa "ban san abunda ya faru da ita ba, kuma bana
buƙatar in sani, tun wuri ka kiyayeni akan wannan yarinyar, ita 'yar masu kuɗice ka
barta taje, taimakon daka mata Allah ya amfana, kaima ka rungumi talaucinka, kuma
idan ka sake ka taka kaje inda take zakaga yadda zanyi da kai, kalli dukda kayi
free ai yakamata ko dubaka tazo tayi amma ba ita babu dalilinta"
Yusuf ya rasa yazewa Umma ta fuskance shi, Yasan dole Umma zataji babu daɗi saboda
yadda take ƙaunarsa, amma Widad taje ta bada wannan shedar, amma taƙi bari ya
gayamata abunda yake faruwa, wanda ita bata sani ba.
Babban abunda ya bawa Umma mamaki, be wuce yadda Yusuf ya ɓata rai ba, duk laifin
da zeyi tai masa faɗa baya fushi, amma ƙarara a fusakrsa wannan karon, ya nuna beji
daɗin hukuncin data yanke ba, ta dinga binsa da kallo, yai shiru bece komai ba.
Ramadan yaji takaici jin labarin mahaifinsi ne ya dinga shirya duk wata manaƙisa
akan Daula, dukda tarin alkhairansa a gareshi, babban abunda ya daɗaɗa masa rai
kuma shine ba' a samu mahaifiyarsu da cutar HIV ba, amma yana ta sake zullumi akan
ance su koma bayan watanni uku a sake yi.
Ramadan yace "Umma, yanzu shikenan Daddy ya lalata rayuwarsa, mu kuma ya bar mana
abh mafi muni da abun kunya, ban taɓa jin labarin mutum me butulci kamar mahaifinmu
ba"
Hajiya Sarah tace "bari kawai Ramadan, ni kaina nayi haƙuri da shi tsawo shekaru
na masa biyayya iyayi na, amma ban taɓa zaton yanawa Daula zagon ƙasa haka ba,
dukda wasu lokutan inajin haushin Widad, amma tabbas mahaifinku ya zalunceta,
zalunci me muni ina fatan Allah yasa bani da wannan cutar, shi kuma yaje can
yaƙarata, ya girbi abunda ya shuka '
Iman tace "waini Mummy, Yaya Fahad baze zo ya duba ki bane? Tunda muka taho Adamawa
be neme mu ba, kuma a waya ba wanda ya kira fa"
Hajiya Sarah tace "ƙyaleshi kawai, ki rabu da shi, aini Na zubawa sarautar Allah
ido kawai, nasan zaluncin da mahaifinku ya aikata muma se hakkin ya shafemu"
Ramadan yace "karkice haka Mummy, ai Allah baya kama wani da laifin wani, dan haka
kiyi hakuri Allah ya yafe mana kurakuranmu"
Ramlah ta farka daga uban baccin da take n shaye2 da tayi, lokaci ya ƙure tana
wannan baccin, amma still damuwar dake tattare da ita bata sake ta ba, ji tayi ma
kamar an ƙara mata wata damuwarne, akan wadda take ciki.
Ta miƙe a hankali amma bata ga Amal ba, tayi zaton ko tana ɗakinta ne, ta tafi
ɗakin nata, ta duba amma nan ma bata ciki sam, ta sakko ta fito harabar gidan ta
tarar masu aiki suna wa Amal fifita.
Isa yace "wuƙa ta ɗakko ta fito da ita, tana yunƙurin kashe kanta, da ƙyar muka
ƙwace wuƙar, shine ta faɗi ta suma"
Ramlah ta ƙarasa ta ɗago Amal tace "why Amal Why? Why will you attempt to kill
yourself, why do you attempt to murder yourself? Haba Amal"
Ta kalli Nura tace ya kawo mata ruwa, ya kawo ruwa aka dinga shafawa Amal ɗin, can
taja ajiyar zuciya ta buɗe ido, Ramlah tace "Amal meyasa zaki yunƙurin kashe
kanki? Komai yai zafi maganinsa Allah"
Cikin kuka Amal tace "Mummy, Mummy na, Yaya Anwar, dan a kainin inga Mummy i love
hery, she's my Mum, dan Allah kice ayi haƙuri bazata sake ba, ina son in ganta"
Ramlah ta rungumeta tana rarrashinta, tace "kiyi haƙy, za'a kaiki ki ganta insha
Allah, amma karki ƙara yunƙurin kashe kanki, kinji ko?"
Amal ta jinjina mata, ta kama hannunta zuwa cikin gidan, yayin da masu aikknysuka
shiga gulmarsu.
Gabaɗaya walwalar Yusuf ta ɗauke, ko Abinci baya iya ci, idan ya kwanta tunanin
Widad kawai yake yi, yana son ya ganta sosai, Amma Umma taƙi.
Ya zauna yai shiru a tsakar gida, Umma ta fito da gyalenta a hannu tace "Yusuf
bari zan ɗan shiga kasuwa, ba daɗeaayzan ba yanzu zan dawo"
Widad tana zaune ta tasa 'ya' yan itatuwa a gabanta, ta kasa ci ta zuba musu ido,
tana kallonsu kamar ranar ta fara ganinsu, kamar an tsunkuleta ta tashi da hanzari,
tai waje ta samu ɗaya daga 'yan sanda dake bata tsaro, ta tambayeshi ina wannan ɗan
sandan da suka fita tare, yace mata "Ai ya tafi aikin da kika sashi ranki ya daɗe"
Ba musu, ya kira shi a waya, aikuwa ya ɗaga ya miƙa mata wayar, Widad tace "ka
gano min gidan nasu?"
Yace "eh na gano, naje na tambayi abokan aikina da suka kaishi Asibiti"
Yace an gama ranki ya daɗe, aikuwa ya tura mata, ta karɓa ta duba ta shiga cikin
gidan da sauri, taje ta shirya tsaf ta fito, bata sairari kowa ba, ta buɗe wata
mota ta shiga, 'yan sandan suka taho kanta suna tambayar ina zata?
Babu wanda ta saurara a cikin su, ta fafari motar tana wani irin mahaukacin horn,
wanda ya tilastawa masu gadin buɗe mata, saboda gudun ɓacin ranta, tai waje da
motar a guje.
Nan da nan' yan sandan suka ɗau mota suka rufa mata baya.
Yusuf yana nan zaune, ya gaji da zaman tsakar gidan, ya tashi ya koma ɗaki, Sallama
yaji a tsakar gida, ya amsa Sallamar daga ɗaki yace "Umman bata nan"
Haushine ya kama Yusuf, shi ga abunda ya dameshi amma baƙuwa zata addabeshi, ya
fito ransa a ɓace kawai yaci karo da Nurat, tai masa murmushi, gaba ɗaya ya ɗan
ruɗe yace "dama kece?"
"Ni na isa ince ki koma, ɗazu Umma ta fita nasan zuwa yanzu tana hanya, shigo
bismillah"
Yusuf ya bata gurin zama a falo, shikuma ya fita waje, yana fita suka gaisa da
Khalil, Yusuf yace "shigo daga ciki mana, ka tsaya a waje"
Khalil yace "A'a bazan shiga ba, Naga ta gaji da zaman kaɗaicine damuwa tana
damunta, nace bari mu fito tazo ta dubaka ta gaida Umman kota samu relief"
Jiki a sanyaye Yusuf yace "Barrister ina matuƙar jin tausayin Nurat, ga kunyarta
nakeji gani nake duk nine sanadin shigarta matsala"
"ka dena faɗar haka Yusuf, ai duk mumini dole ze yadda da ƙaddara me kyau ko mara
kyau"
Yusuf yace "hakane, shigo mana"
Khalil yace "zan shigo, bari inje in ga abokina a nan ƙasan layin ku"
Nurat tana zaune a guri ɗaya, tai shiru Yusuf ya shigo ta ɗaga kai ta kalle shi
tana wannan murmushin nata daya zama nature ɗinta.
Yusuf mabya mayar mata da murmushin, yaje ya ɗakko mata ruwa a fridge da lemo ya
kawo mata, yace " Sannu da zuwa light, ga ruwa Kisha umma tana daf da shigowa"
Shiru tai tana sunkuyar da kai yace "ikon Allah, kunyata kuma kike ji? Ko kuma ba
kya shan irin wannan?"
Ta girgiza masa kai tana murmushi yace "idan Umma ta dawo kuwa sekin sha, Umma
ba'a zuwa gidanta a ƙi karɓar abunda ta bawa mutum"
Can Yusuf yace "light, wai nikam dan Allah ya akayi kika san da abunda na ajiye a
wayarki?"
Cikin sanyin muryarta tace "ai ka taɓa cemin kayi ajiya a wayata, amma baka
gayamin meye ba, lokacin da aka kama ka sena gayawa brother, harda ajiyar da kace
kayi a wayar, shine yace in bashi wayar, ya dinga bincike a kai, daga nan ya kaiwa
wani Abokinsa, ban san yadda akayi suka gano ba "
Yusuf yace " Aini bani da bakin da zan miki godiya Nurat, Allah jiƙan Mummy, Allah
yasaka da alkhairi "
Can kuma tace " dan Allah dagaske kana da Aure? "
" Kai ka taɓa gayamin, da na kiraka a waya, ka cemin kana tare da matarka "
Yusuf yace " A lokacin tsokanar ki nakeyi, bani da Aure amma a yanzu ina da Aure,
Widad mata tace "
Ƙirjin Nurat ya buga da wani irin ƙarfi, take annurin fuskarta ya ɗauke gaba ɗaya.
Yusuf yace " ya dai? Ko kina sona ne, kamar kishi fa nake gani a fuskarki"
Ta ɗago manyan idanunta farare ƙal, ta sauke akan Yusuf, take taji ta karaya gaba
ɗaya ƙwalla na neman cika mata ido.
"Yoseef!!!"
Yaji an kira sunansa, kuma babu me ambatar sunansa a haka idan ba gimbiyar Daula
ba.
AMANA! AMANA! AMANACE!!!
LITTAFIN KUƊI NE.
AYSHERCOOL
07063065680
12/7/21, 11:04 PM - Buhainat: LITTAFIN KUƊI NE, DAN ALLAH KI SIYA KAFIN KI KARANTA
BA DANNI BA DAN ALLAH, LITTAFI NA ƊAYA KYAUTA NE WANNAN NA SIYARWA NE
NORMAL GROUP ₦300
VIP ₦500 NE KITURA TA WANNAN ACCOUNT ƊIN
0009450228
JA'IZ BANK
AISHA ADAM
SE A TURA SHEDAR BIYA TA WANNAN LAMBAR
07063065680
(Albishir ga masoya, ma'abota bibiyar litattaafaina, dama ta samu zaku fara samun
litattaafaina na audio, akan YouTube channel ɗina me suna Cool Arewa TV
https://youtube.com/channel/UCD5vnvA5laU8ti4LLz2_QEg
Kuyi liking sannan ku danna subscribe, domin fara samun litattaafaina na audio,
nagode sosai da ƙaunar ku gareni"
156_157
Yusuf da Nurat duk suka ɗaga kai suna kallon inda Widad ke tsaye a bakin ƙofa, seda
ƙirjin Yusuf ya buga da ƙarfi ganinta a tsaye, fuskarta babu Annuri sam, dan kwata
kwata be taɓa zatan ganinta ba a wannan lokacin, ba Yusuf kawai ba hatta Nurat seda
hanjin cikinta ya kaɗa, ta shiga fargaba saboda yadda Widad ɗin tai kicin kicin da
rai.
Fargaba ce lulluɓe a fuskar Nurat, jikinta se tsuma yake kamar taga zakanya.
Yusuf ya ɗakko ruwan roba, ya buɗe ya zuba a cup ya miƙawa Nurat, amma Nurat ta
kasa karɓa se kallon Widad kawai da take yi, Widad ɗin dake tsaye tana huci.
Nurat tace "Amm.. Am naga kamar gurinka tazo bari in baku guri"
Yusuf yace "yi zaman ki kawai, idan wani abunne ya kawota ta faɗa a nan ina jinta"
Widad ta kalli Yusuf, taiwa Nurat wani mugun kallo, ai ba shiri Nurat ta miƙe, a
ɗarare ta raɓa ta jikin Widad ta fice daga ɗakin, tana fargabar kar Widad ɗin tayi
mata wani abun
Yusuf ya yunƙura daga kan kujerar da yake, ze bar mata ɗakin amma ta sha gabansa ta
kalle shi tace "Yoseef, Anya kamin adalci kuwa? Na cancanci haka daga gareka? Bani
da kowa se Allah, ba uwa, ba uwa, ba dangi ba kowa kasan bani da kowa se Allah, se
kuma kai da nake sa rai, amma kamin haka? Yoseef tunda Allah yasa ka kuɓuta baka
nemi inda nake ba, ina ta faman wahala da rayuwata babu me temakona se Allah, bani
da wani jigo da zan jingina dashi inji farinciki, kawai se inzo in ganka da wata,
bayan kasan zuciyata bazata iya jure hakan ba" tai maganar idonta taf ƙwalla.
Yusuf yace "ni bance ba kimin adalci ba seke zaki gayamin haka? Duk tarin wahalar
dana sha saboda ke, amma kika kalli duniya kika bada shedar ƙarya a kaina Widad,
baki tausayawa halin dana shiga ba, seni zakiwa kallon ban kyauta miki ba?"
"Yoseef, a tunanina ko kowa be fahimceni ba kai zaka fahimceni, na gaya maka komai,
kasan komai game dani fiye da kowa, na baka dukkanin yarda wanda har hakan yasa na
gaya maka waceceni, da abunda ya faru da rayuwata, kasan bazan taɓa yin haka dan in
tozarta ka ba, dukda na ɓoye maka waye Bukar, ba nayi hakan ne dan komai ba se dan
tseratar da rayuwarka, da kuɓutar da kai daga sharrinsu, na ɓoye maka Bukar shine
Bulama saboda na bar hakan a zuciyata har ranar da zan kama shi red handed, sedai
ƙaddara ta riga fata, amma shikenan tunda baka buƙata ta yanzu a rayuwarka, zan
rungumi ƙaddara da irin rayuwar da Allah ya ƙaddara zanyi, amma kafin nan "
Ta saka hannu ta cire dogin hijjabin jikinta, wanda ya kasance har ƙasa, ta cire
doguwar rigar abayar dake jikinta, ya rage daga ita se gajeran wando, da kuma half
vest.
Tozalin da Yusuf yayi da cikin dake jikin Widad ne yasa shi ya ɗan rikice, tabbas
idonsa ba gizo yake masa ba, cikine a jikin Widad gashi nan yayi girma sosai ya
fito.
Ta ƙaraso gabansa ta kama hannunsa, ta ɗora a kan cikin nata tace "dan Allah
Yoseef, koka watsar dani karka watsar da ɗanka, yau idan na mutu bashi da kowa se
kai, dan Allah karka bari yayi irin rayuwar dani ko kai mukayi, Yoseef ka
tausayamin ko dan ɗanka da nake ɗauke dashi.
Yusuf ya kalli Widad ya kalli cikin jikinta yace "You are pregnant Widad"
Ta jinjina masa kai, Yusuf yai murmushi yace "'yar baiwa, ashe Allah ya amsa
Addu'ar ki, ya baki abunda kike nema, hankalinki ya kwanta" yai maganar cikin farin
ciki fuskarsa ɗauke da murmushi.
Ya rungumeta a jikinsa hawaye na zuba daga idonsa, Widad ta rirriƙeshi itama tana
kukan tana faɗin "We miss you Daddy me and your unborn, munyi missing ɗinka sosai,
we really suffered, banyi zaton zan sake ganinka ba, bam zaci zanyi rai zuwa wannan
lokacin ba"
Ta ƙarasa maganar tana sake fashewa da kuka, Yusuf ya sake manneta a jikinsa shima
yana zubar da hawaye yace "i miss you too Babyna, i miss you my Queen, I love you"
Sosai suke kuka daga shi har ita kamsr ƙananan yara, ya sake ɗagota ya kalli cikin
nata, ya rungumota jikinsa ya haɗe bakinsu yana kissing ɗinta, hawayen tausayawa
kansu na zuba a idonsa, yayin da itama kukan take.
Ya cire bakinsa daga nata, yana share mata hawaye ya kalleta yace "ɗan sake
maimaita min abunda kikace yanzu mana"
Murmushi tai ta miƙa hannunta itama fuskarsa, tana share masa hawaye "tace me kake
so in sake faɗa?"
"kin san koda ina prison, kalmomin nan da kika dinga faɗamin ranar da aka kamani
sun tsaya a zuciyata sosai my wife"
Fashewa ta sake yi da kuka tace "dan Allah Yoseef ka dena tunamin kayi zaman
prison please, zuciyata zata tarwatse, am sorry Yoseef duk sanadina ne ka shiga
mummunan yanayi"
Yusuf yace "ni dai a sake cewa ana sona please" yai maganar a Shagwaɓe.
"Nima ban sani ba ai, Yoseef dan Allah ka dawo gareni, akwai maganganu dayawa da
nakeso muyi, kuma kaga nikaɗai nake rayuwa ina farmhouse, kalli jikina duk ya
kumbura, Yoseef zuciyata ciwo take, likitoci sunce idan nazo haihuwa ko dai muyi
surviving, ko mu mutu gaba ɗaya ko ɗaya ya mutu ya bar ɗaya"
"Shhhhh hakan baze faru ba insha Allah, zaki haihu lafiya, kinga a yanzu haka ina
ta fama da Umma saboda ke, kin san a rayuwa Umma bata son abunda ze taɓani, dan
haka abune mawuyaci ta fuskanceni, saboda tana cikin kotu kika bada sheda a kaina,
dan haka sena fara shawo kanta tukuna"
"Dan Allah kayi mata bayani Yoseef, nasan kaika fahimceni kasan komai fa"
"Na sani my wife, kiyi haƙuri, zanyi ƙoƙari inzo har farmhouse ɗin in ganki, yanzu
maida rigarki in rakaki mota, nasan Umma na daf da shigowa"
Ai gaba ɗaya sun manga da batun Nurat, dan Widad ta manta ma da taga Nurat tare da
Yusuf.
Yusuf yai dariya yace "lallai kinyi baki, mara kunya kawai"
Widad tace "Allah sarki Hari mutuniyata, ina jin bayin Allah nan sosai a raina,
ina kewarsu mussman Hinduna da Gwaggo, in komai ya daidaita zamuje insha Allah"
Yusuf yace "kin san kuwa wannan Sunusin, mijin Jamila yaje ya bada sheda a kotu?"
Widad tai ajiyar zuciya tace "shiyasa nace maka ina son mu haɗu, ina da magana da
kai sosai"
Yusuf yace "Malama karki sa mu saki layi, matso in saka miki rigarki"
Murmushi tai masa ta ƙara matsowa daf dashi, sedai yaga abu kamar kwanciyar bulala
yai duhu akan fatarta, wajen damtsenta.
"Baby meye wannan?"
Shiru yai yana nazarinta, idonsa ya kuma sauka akan gefen fuskarta, nan ma wani
tabon ne a gurin, ya sake kallonta zeyi magana tace "waiya kake ƙaremin kallo
hakane kamar yauka fara ganina? Bani rigata in saka tunda kallona zakai ba samin
ba"
Yusuf ya riƙe rigar yace "bazan taɓa gajiya da kallonki ba" yai maganar yana sake
janyota jikinsa, yana sa fuskarsa a wuyanta.
Haka ya saka mata rigar, ta ɗau hijjabin zata saka, ya dakatar da ita ya ɗaga rigar
jikinta, ya sake kallon cikim nata, ya sumbaci cikin ta yace "I love you my
unborn, karka waharmin da Mum ɗinka kaji Babyna, i love both of you"
Widad ta dinga masa dariya, wai yana surutu shi kaɗai, kamar zasu cinye juna, ko
sababbin masoya.
Nurat kam tana fita daga ɗakin, waje tayi amma bata ga Khalila ba, se motocin 'yan
sanda dake gurin, dan haka ta koma tsakar gidan, can nesa da ɗakin da su Yusuf
suke, ta zauna akan kujerar tsakar gida.
Sedai tana jiyo dariyar su, ta sunkuyar da kanta a tsakanin cinyoyinta, tai shiru
tana tunani, tana son Yusuf so na haƙiƙa, tana sonshi saboda Allah, amma tasan
tunda ya auri Widad abune me wahala ya saurareta, kuma ga dukkan Alamu Widad ma
tana matuƙar sonshi itama, dan haka Yusuf babu lallai ya saurare ta.
A hankali ta fara hawaye, tana gogewa a hankali, tana addu'a a zuciyarta "Allah ka
yaye min son Yusuf, Allah ka zaɓamin abunda yafi Alkhairi a rayuwa ta"
Jin abun nasu bana ƙare bane, yasa ta sake miƙewa ta fita waje, tana fitavtarar da
Khalil ya dawo, ya kalleta yace "Ta Yusuf harkin fito ne? Ai bamu gaisa da Umman
ba"
Tai maganar hawaye na ƙoƙarin tona asirin dake zuciyarta, a ɗan dirirce yace "ko
wani abun Yusuf ɗin yayi mkki?"
Ta girgiza masa kai ta buɗe mota ta shige, cike da mamaki Khalil ya bita da kallo.
Umma ceta shigo layin hannunta ɗauke da ledoji, sedai ganin motar 'yan sanda a
ƙofar gidan yasa gabanta ya faɗi, ta dinga nanata innalillahi wa inna ialaihi
raji'un, hankalinta ya ɗan kwanta data hangi Khalil.
Ta ƙaraso inda Khalil ke tsaye, tace "Khalil lafiya kuwa? Naga motar' yan Sanda?"
Khalil yace "lafiya ƙalau Umma, sunce min wani aiki sukeyi, Nurat na kawo ku gaisa
kuma bakya nanma ashe"
Umma tace "Ai da kun shiga Yusuf yana nan ai"
Umma tace "A'a ban yadda ba, Nuratu fitowa zaki mu shiga mu gaisa"
Umma tace "a'a, ai ga Khalil nan Tare kuke kuma ga mota fito maza"
Nurat bata son tayi sanadin da zata gusar da farincikin dake zuciyar masoyinta,
amma babu yadda ta iya, Umma ta haifeta bekamata ta bijirewa umarninta ba.
Nurat ta fito daga motar, tabi bayan Umma suka shiga gidan, sedai suna shiga suka
tarar Yusuf da Widad sun fito, yana riƙe da ƙugun Widad suna murmushi cike da
kulawa da juna.
Suna yin tozali da Umma, Yusuf ya saki Widad da sauri, ita kanta seda Widad ta
tsorata ganin kallon da Umman take musu.
Umma ta kalli Widad tace "kinzo ki sake kulle shin ne kokuwa? Ko prison ɗin kike
son ya koma?"
Umma tace "ya kikayi shiru baki bani amsa ba? Kinzo ki sake maida shi prison ne,
bayan duk wahalar da ya sha saboda ke, ki kaje kotu kika bada sheda akansa, banda
Allah yasa wannan yarinyar Nurat da ɗan uwanta sunyi masa ƙoƙari suma da yanzu
shekaru talatin zeyi a kurkuku "
Widad ta ɗaga ido ta jefi Nurat dake bayan Umma da wani matsiyacin kallo, wanda
yasa Nurat jin kayan cikinta kamar sun koma bayan ta, a hankali ta silale ta fice
ba tare da Umma ta lura ba.
Umma ta kalli Yusuf tace " kai kuma na dawo kanka, mara zuciya kai har abunda yai
saura tsakaninka da wannan yarinyar, saboda rashin zuciya tana mace amma ta biyoka
har gida? Idan na ƙara ganinta a gidan nan duk abunda nayi mata ita siya, yakamata
ma hukuma tai mana tsakani da ita, tunda Allah yasa dai an gane baka da laifi meye
kuma na cigaba da bibiyarka, kowa se yayi hanyarsa Allah ya bada lada "
Yusuf yace 'Umma dan Allah kiyi haƙuri, Widad aurenta nayi mata tace, amma..
Umma ta katse shi tace " kai kasan wannan, ni ban san da haka ba, iya sanin da nayi
baka da wata mata, Ni Nuratu nake fatan ka Aura, dan se tafi wannan yarinyar sauƙin
kai "
Widad ji tayi zuciyarta ta buga da ƙargi, tankar Umma ta soka mata mashi, take taji
ta tsani Nurat, dama ga abunda mahaifinta yai mata, gashi kuma yanzu tana bibiyar
mijinta, hawaye ya fara zarya a fuskar Widad, a hankali ta sanya takalmanta tai
waje.
Yusuf kamar ya ɗora hannu a ka ya kurma ihu haka yake ji, baya son kukan Widad yana
matuƙar ƙaunarta, amma Umma na son datse igiyar farincikin dake tsakanin su.
Umma ta kalle shi tace "wato da Nuratun tazo gidan nan wulaƙanci kai mata saboda
wannan yarinyar ko? Farar fatarta na ɗaukar maka ido kana nema ka gayamin magana
saboda ita ko Yusuf?"
Yusuf ya girgiza kai, Umma tace "duk abun kaga nayi bazanyi dan in citar da kai
ba, wannan yarinyar idan ta ƙara raɓarka za'a iya samun matsala, ka manta da ita
kawai ka nemi wannan yarinyar Nurat, dan se tafi waccan tausayi, kuma dama kaga
Auren naku mutane na shakku a kai, tunda ba kowane yasan da wani kunyi Aure ba,
kayi haƙuri ka rabu da yarinyar nan, Allah ya zaɓa maka mafi Alkhairi kaji yaron
kirki, bana son abunda ze sake ɗaga mana hankali tashin hankalin da muka shiga ma
ubangiji Allah ya yaye mana ya kiyaye gaba, Allah yabaka mace tagari mafi Alkhairi
a rayuwar ka "
Ta miƙa masa wata ƙatuwar leda tace " yawwa ga wannan, yadine guda uku masu kyau da
shadda biyu, idan anyi sallar magariba dare yayi ka kaiwa magaji ya ɗinka maka, ga
takalma nan ma, hadda sabon agogo na siyo maka, ka ƙara akan kayanka, sonake nan
kusa ka koma gurin aikinka"
Ya juya ya shiga ɗakinsa, yana zuwa ya ajiye kayan ya zauna ya dafe kansa yace "ua
zanyi da umarnin Ummana, matar da ta dimga ɗawainiya dani tun a zanin goyo harna
zama mutum, bani da uwar data fita, sannan ya zanyi da matatat wadda a yanzu haka
nauyin kula da ita a kaina yake, haba Umma ki fuskanceni mana"
Nurat kuwa har sukaje gida, bata ce komai ba, juyin duniya Khalil yai yai ta gaya
masa abunda ke faruwa amma fafur taƙi, suna zuwa gida ta shige ɗakinta ta rufe ƙofa
ta shiga aikin kuka, tana jin yadda soyayyar Yusuf ke ƙafa tsuma mata zuciya, tana
shiga dukkan wani sashe na jikinta, amma tasan ssamun Yusuf idan ba wani iko na
Allah ba, abune da baze taɓa yuwuwa ba, ya riga ya mata nisa tunda ya zama miji ga
Widad, ko ba'a gayamata ba Tasan Widad bazata zauna da kishiya ba, kishiyarma ita
wadda mahaifinta ke da Mummunan tabo a gurin Widad ɗin.
Khalil duk ya shiga damuwa ganin Halin da Nurat ke ciki, a nan falo mahaifiyarsa
ta fito ta sameshi tace "Khalil har kun dawo ne? Ina Autar tawa take ne?"
Khalil yace "Ta shiga ɗakinta"
Tace "yaya, da kuka fitan ta ɗam saki jikinta kuwa? Na fuskanci har yanzu Nurat
tana cikin damuwa da alhini, bana son rashin walwalrata, gashi ni bani da 'ya mace
balle ta samu' yar uwa, ni kuma ba son yawan hira take dani ba, na rasa ya zanyi,
Abbanku ma ya faramin magana akan rashin walwalarta wai kowani abu nake mata? Nace
masa ya za'ayi in takuramata tana 'yar ƙanwata? "
Khalil yai ajiyar zuciya yace " Mama akwai abunda yake damunta, kuma baze rasa
nasaba da halin data tsinci kanta a ciki ba, dole se an bita a hankali "
Mama tace " to shikenan, naga kai taku tazo ɗaya sosai, dan Allah ka dinga kwantar
mata da hankali, kana rarrashinta"
"to Mama Insha Allah, bari in shiga inyi alwala magariba tayi '
Ya tashi ya baf falon, uana jin inama ze iya ɗaukewa Nurat damuwar da take ciki.
Widad kam tasha kuka data koma gida, taji ta tsani Nurat bata ƙaunarta sam, ta
barwa ranta sedai ayi duk wadda za' ayi, amma bazata bari Yusuf ya auri Nurat ba.
Yusuf ya fita yai sallar magariba ya kai ɗinkin kayansa, ya dawo yana daf da shiga
gida wani yai masa sallama, ya tsaya ya amsa suka gaisa.
Murmushi yayi cikin rawar jiki ya kunna wayar, ya duba yaga lamba ɗayace a ciki,
maimakon ya kirata da wayar, seya kwafa a ƙaramar wayar dake hannunsa ya kirata.
Tana kwance akan gado, tayi rigingine wayar ta fara ringing, ai da sauri ta ɗakko
wayar ta ɗaga.
"Hello My Queen"
"Shikenan, ya kake?"
Yace "Widad dan Allah kiyi haƙuri da abunda ya faru yau kin san"
"I understand, just forget sonake kawai muyi hira da kai, inji daɗi a raina,
kaɗaici ya dameni ko Abinci bana iyaci Yoseef, ga bani da lafiya I need you Yoseef,
i need your help"
Jiki a sanyaye Yusuf yace 'ki kwantar da hankalinki my wife, Insha Allah inaji a
jikina komai ya kusa zuwa ƙarshe insha Allah, kiyi haƙuri karki cutarmin da kanki
da Babyna, ki dinga cin Abinci please, karki mana illa "
" toni ya zanyi inci, babu me rarrashina ya bani a baki? Gashi bana samin irin
Abincin da nake so, Yoseef dan Allah ka bawa Umma haƙuri ka dawo gare ni please "
" karki damu, Umma zata soki tana da sauƙin kai sosai, Insha Allah zam sam abunyi,
amma dan Allah kici Abinci kinji Wudas ɗina "
Yusuf yai dariya yace " ba haka Hari take ce miki ba? "
" to kai ita ne? Kasan meze faru kashe wayar, zanje inyi wanka video call nake son
muyi in ganka "
Ko takan Abincin dare Yusuf bebi ba, Widad ta sake kiransa video call, ta saki
dogon gashin nan nata, tana shafa mai.
"Allah ne yayi cikin nan baze fita ba, amma allurar zubar da ciki Bulama yasa
ayimin"
"cikin nawa aka so zubarwa?"
"Eh mana, sun kusa kasheni fa, akwai labari idan mun haɗu fa"
Yusuf yace "Allah sarki babyna, mun sha wuya sosai, ko da kikazo kotu kallo ɗaya
nai miki na gane ba'a kwanciyar hankali kike ba"
Widad tace "bar wannan zancen kawai, kar ka ɓatamin rai ka rusa mana farinciki"
Yai murmushi yace "to shikenan, kina min ƙwalele da gashin nan fa"
Tai murmushi tana masa gwalo ta waya, tace "ziro hannu ka taɓa mana"
"Inama in rufe idona in buɗe in ganni a kusa dake, in tayaki shafa man nan"
"Harka tunamin lokacin da muna ƙauye, gaskiya Yoseef kana da haƙuri kayi haƙuri
dani sosai, shiyasa ka taka wani gagarumin matsayi a zuciyata my love"
Har tagama shirin kwanciya, ta kwanga video call suke, ba tare da sun sam dare yayi
ba.
Ƙarfe biyu da rabi lokacin ne Umma take sallar dare, ta fita alwala ta dinga jin
maganar Yusuf ƙasa ƙasa, ta leƙa tagarsa ta hangoshi akan gadonsa ya tasa screen
ɗin waya a gaba yana murmushi.
"Ki kwantar da hankalinki, Insha Allah zuwa jibi zanzo in ganki masoyiyata"
"Allah ya kawo ka lafiya, zaman kaɗaici ya isheni Yoseef, babu kowa a kusa dani fa"
"Ai mace miki zanzo insha Allah, inzo in ganki inji labarin da kike son gayamin,
inji yadda akayi kika samu wannan tabon haka a jikin ki, ki kwanta kiyi bacci dare
yayi fa"
Tace "ok come closer, hug me and kiss me, then we sleep together"
Yusuf yai murmushi yace "nayi missing ɗinki Widad, yai kissing ɗin screen ɗin
wayar yana lumshe ido, ƙarshe ya kashe wayar ya ajiye, ya rungume pillow sosai a
jikinsa yana lumshe ido.
Da safe Yusuf ya tashi yana ta nishaɗi kamar bashi ba, Umma tana kallonsa amma ba
tace masa komai ba.
Ranar da yayiwa Widad alƙawarin ze je yana ta kallon agogo, yana zaune Umma ta
sashi a gaba yaci Abinci, ya gama ci wayarsa ta fara ringing, sedai ba suna amma
yaƙi ɗagawa, Umma tana kallonsa.
Ba haka yaso ba, amma haka nan ya haƙura, ya ɗakko pillow ya kwanta a ɗakin Umman.
Aikuwa babu daɗewa bacci ya ɗaukeshi, saboda dama dare yake rabawa yana soyayya.
Umma ta ɗakko mafici tana masa fifita, Kasancewar an ɗauke wuta gashi ya fara gumi.
Sedai tun ba'aje ko'ina ba Yusuf ya fara surutan bacci.
"My Wife, kiyi murmushi mana yarinya fushi baya miki kyau fa"
Umma ta juya tana kallonsa, iya saninta dashi tun yana yaro ƙarami, baya surutan
bacci, amma yau da ranar Allah yana bacci yana surutu akan wata.
"Baby ki dena kuka, bana so fa, kinga baki da lafiya, kuma Gwaggo yau zata kawo
mana kunun tsamiya, ai zaki sha ko?"
Suleiman ne yai sallama a gidan, Umma ta amsa masa, ya shigo ya zauna yana faɗin
"Lallai ɗan gata, yana bacci Umma na masa fifita, tashi c
Yai maganar yana taɓa Yusuf, Umma tace " ze tashi kuwa, yana mafarkin soyayya "
Suleiman ya daddaki Yusuf, Yusuf ya buɗe ido a hankali, ya tashi zaune yace
"Yallaɓai dama kaine?"
Umma tace "gidansu Nurat zaka je, Munyi waya da Khalil bata da lafiya!!!"
Wayat Yusuf ta shiga ringing, ya kalli wayar lambar Widad ce, tana can tana jiransa
AYSHERCOOL
07063065680
12/7/21, 11:04 PM - Buhainat: LITTAFIN KUƊI NE, DAN ALLAH KI SIYA KAFIN KI KARANTA
BA DANNI BA DAN ALLAH, LITTAFI NA ƊAYA KYAUTA NE WANNAN NA SIYARWA NE
NORMAL GROUP ₦300
VIP ₦500 NE KITURA TA WANNAN ACCOUNT ƊIN
0009450228
JA'IZ BANK
AISHA ADAM
SE A TURA SHEDAR BIYA TA WANNAN LAMBAR
07063065680
(Albishir ga masoya, ma'abota bibiyar litattaafaina, dama ta samu zaku fara samun
litattaafaina na audio, akan YouTube channel ɗina me suna Cool Arewa TV
https://youtube.com/channel/UCD5vnvA5laU8ti4LLz2_QEg
Kuyi liking sannan ku danna subscribe, domin fara samun litattaafaina na audio,
nagode sosai da ƙaunar ku gareni"
158_159
Yusuf ya girgiza kai, Umma tace "to tashi maza, jeka kintsa kazo ku tafi"
Jikin Yusuf babu daɗi, ransa sam ba daɗi yaje yai wanka ya shirya ya fito.
Umma tace "Suleiman, dan Allah ga Shi nan, ka tabattar yaje dan Allah ga kuɗi ku
sai mata ko kayan marmari ne, aje a duba ta, gaida mai gaisheka ko baze amsa ba"
Suleiman ya fito ya shiga motar suka tafi, Umma ta maida Suleiman kamar ɗanta Yaya
a gurin Yusuf, dan shima tana masa hidima shida iyalinsa, tunda yaita faɗi tashi
akan case ɗin Yusuf.
Yusuf be kula Suleiman ba, gaba ɗaya ransa a ɓace yake, ya ɗakko wayarsa ya kira
Widad, tana ɗagwa ta fara mita "Haba Yoseef, inata kiran wayarka kaƙi ɗagawa, na
shirya ina ta jiranka fa"
Tai maganar cikin Shagwaɓa.
Yusuf yace "Am sorry, wata fitace ta gaggawa ta kama ni, amma idan na kammala zanzo
insha Allah, ki kwantar da hankalin ki kinji my Wife"
"To shikenan, zanje ƙauye in Hari tayi girki ta zubo in kawo miki"
Ya maida wayarsa ya ajiye, Suleiman yace "Yusuf zaka karya maganar Ummanka kaje
inda Widad take kenan?"
Yusuf yace "yallaɓi, yakamata ka fahimceni Widad fa ita kaɗai take zaune a gidan
nan, babu kowa kuma ina tare da Aurenta, duk haƙƙoƙinta suna kaina, Umma taƙi bani
dama in mata bayani, bayan haka Widad tana buƙatar kulawa, duk ta kumbura saboda
ciwon zuciya da hawan jini, kuma.. Kuma tana ɗauke da tsohon ciki fa" Yusuf ya
ƙarasa magaanar cike da jin kunya da kuma damuwa.
Suleiman yace "hakane, yakamata ace Umma ta fuskance ka, amma tanaa gudun abunda ze
sake kawo barazana ga rayuwarka ne, amma kabi a hankali, zata fahimta Insha Allah"
Yusuf yace "Allah yasa, amma ni batun Auren nam da Umma ta bijiro dashi, dan Allah
Yallaɓi kasa baki, idan har nace zan Auri Nurat Widad zata rabu dani, kuma ina
matuƙar son mata ta"
"Shikenan nagane halinda kake ciki, amma Nurat ma abun tausayi ce"
Yusuf yace "Nasani, badan kishi irin na Widad ba da zan iya auren Nurat, saboda
tana sona sannan bata da wani aibu, sema nine nake da aibun da za'a gujeni saboda
shi"
Koda dukaje Khalil baya gida, megadi yaje ya sanar da zuwansu, aka musu iso.
Sedai Suleiman yace baze shiga ba sedai Yusuf yaje, haka kuwa akayi aka masa jagora
har falon da aka saukesu wancan zuwa.
Yayar maman Nurat ce ta fara zuwa, Yusuf ya gaisheta cikin girmamawa, sannan ta
koma ta turo masa Nurat.
Yusuf yana nan zaune yana sake kallon wayarsa, yana addu'a Allah yasa kar Widad
tayi fushi, yaji ƙamshin turaren Nurat, ya ɗaga kai ya kalli Nurat, duk ta rame
kallo ɗaya zaka mata kasan bata da lafiya, a hankali take tafiya tana ɗan lumshe
ido irin na marasa lafiya, ta ƙaraso ta zauna a kan carfet.
Yusuf ya dawo kujerar da Nurat ke zaune a ƙasa, ya kalleta yace "Light Dama baki
da lafiya?"
Yusuf yace "lafiya ƙalau, ya jiki ɗazu Umma ke gayamin ban sani bane"
"Amma kin daɗe kina rashin lafiyar nan, meke damunki haka?"
Kasa magana tayi, se hawaye da suka shiga zarya a fuskarta, ba tare da ta shirya
zubarsu ba, dan tayi duk me yuwuwa ganin basu zuba ba, amma abun ya gagara.
Yusuf ya sakko daga kan kujerar, ya zauna a kan carfet ɗin yana kallonta, a hankali
yace "Nurat, dan Allah kiyi magana mana, meyafaru?"
Shiru tayi ta ɗauke kai daga kallon inda yake, dan data kalle shi sonshi ƙara
shigarta yake, da kuma kishinsa.
Ta ɗago idanunta ta kalleshi na wani ɗan lokaci, ta sunkuyar da kanta tana wasa da
yatsunta, a hankali tace "Nagode sosai kazo ka dubani, nagode ka gaida Umma"
Ta yunƙura ta miƙe zata tafi, cikin zafin nama Yusuf ya miƙe ya riƙo hannunta, ta
juyo tana fuskantarsa, ta kalli inda ya riƙe hannunta ta kalli Fuskarsa taji tamkar
ta rungumeshi tayi kuka, ita dai a rayuwarta maza dayawa sun nuna suna sonta, amma
bata taɓa jin ƙauna da soyayyar wani a ranta kamar Yusuf ba, zata iya cewa akansa
ta fara Soyayya.
Yusuf yace "Nurat bana so in zama butulu, bana son zama ɗaya daga cikin masu
butulci, ki gayamin me kike so? Meke saki kuka haka?"
Cikin sassanyar muryarta, me cike da karaya tace "bazan samu abunda nake so ɗin ba
ai, dan haka babu buƙatar cigaba da ɓata lokaci gurin faɗa"
"Yusuf kai nake so, kaine Yusuf, ban taɓa so ba se akanka, ban san haka ake ji ba,
sedai nasan bazan sameka ba, kamin nisa na har abada, nasan ko a mafarki Widad
bazata yadda ka auri wata bayan ita ba, bayan haka ta fini komai, sannan ga abunda
ke tsakaninta da mahaifina, ina ganin ƙiyayyata ƙarara a idonta, ga kuma bazan so
ka dinga samun saɓani da mahaifiyarka saboda ni ba, dan haka ina muku fatan
Alkhairi a rayuwar Aurenku me cike da alkhairi, Allah ya ƙara tsareku daga sharrin
maƙiya, da mahassada nagode sosai Yusuf "
Gaba ɗaya jikinsa yai sanyi, sosai ta bawa Yusuf tausayi, tabbas Nurat ta cancanci
a tausaya mata, da tausayi halin da take ciki a yanzu, amma yasan ko wace kalar
wiwi yake sha, baze haɗa Widad da wata ba, saboda yasan azabar kishi irin na Widad,
Nurat ta zare hannunta daga nasa ta koma ciki da sauri.
Jiki ba ƙwari Yusuf ya fito daga falon, ya nufi waje, Suleiman ya kalleshi yace
"lafiya kuwa?"
"meyafaru"?
Suleiman yace "Au kaida baka san son naka take ba?"
Yusuf ya dafe kai yace "Yallaɓai, dan Allah kamin alfarma ka kaini in ga Widad,
dan Allah bazan daɗe ba insha Allah"
Yusuf yai masa kwatance suka tafi, a bakin gate wani ɗan sanda ya taresu yace "ya
akayi?"
Ɗan sandan yai murmushi yace "Ohhh ashe megidane, ai tun ɗazu take jiranka"
Aka buɗe musu gate, Suleiman ya shiga da motar yana mamakin haɗuwa da tsaruwa gami
da girman gidan.
Yai parking Yusuf ya fito daga motar, yace "Yallaɓai zo mu shiga mana"
Suleiman yace "Gurin budurwa ma ban bika ba se gurin matarka, a'a ina nan"
Yusuf kawai yai murmushi ya girgiza kai, ya shiga ya dinga duba falukan dake gidan,
Kasancewar ya kirata bata ɗaga ba, can ya hangota a wani falo, tana zaune akan 3
seater, ta haɗe rai sosai, sanye take da dogon wando, da 'yar riga ƙarama, ta gyara
gashin kanta ta saka ribbon saki ƙarshensa a bayan ta, hakan ya bawa cikinta
damar fitowa sosai, abun mamaki ta saka jambaki da kwalli a idonta, abun da Yusuf
be taɓa gani ba, sedai ta haɗe rai.
Yusuf ya ƙaraso inda take yana murmushi yace "farar mace alkyabbar mata, why are
you sad? Ba gani nazo ba"
Ta ɗaga kai ta kalle shi, ta mayar ta sunkuyar da kanta tana danna wayarta.
Yusuf ya ƙaraso ya zauna kusa da ita yace "bazaki ɗago in ƙare miki kallo ba?"
Matsawa tayi daga kusa dashi, ya kalleta cike da mamaki yace "lafiya kuwa?"
Maimakon yai mata magana, seya ƙura mata ido, ta saka idonta a nasa tace " Yoseef
gurin Nurat kaje "
" tunda ka cemin zaka wani guri, zuciyata ta kasa samun nutsuwa, naji a jikina
gurinta zaka je, kuma kana shigowa naji kana ƙamshin turarenta, Yoseef wallahi
gurinta kaje"
Yusuf yace "lallai zuciyarki tana tare dani, dan ba tayi miki ƙarya ba, tabbas
naje gurin Nurat bisa ga Umarnin Umma, naje na duba Nurat bata da lafiya, Widad,
Nurat bata cancanci wulaƙanci ko banzatarwata ba, dukda abunda mahaifinta yayi,
amma ta taka mshimmiyar rawa a gurin kuɓutata, kalli ta rasa mahaifiyarta,
mahaifinta ya tafi prison, kuma a yau take gayamin tana sona, be cancanci in
wulaƙatanta ba"
Tai maganar tana tsststare shi da ido, Yusuf yace "ni bahaka nske nufi ba, itama
tasan hakan bame yuwuwa bane, amma yakamata itama a dubata, a tausaya mata, ta rasa
kowa Widad ko ban Aureta ba bata cancanci wulaƙanci ba, ta temakeni kuma kin.....
Cikin faɗa Widad ta dakatar da shi, ta hanyar cewa " ni ka cikamin kunne da ta
temakeka, ni wulaƙanta ka nayi? Ko kana zaton Nurat tana da abunda zata ja da Bukar
Bulama ne? Kasan waye Bulama kuwa? Aiko mahaifinta da suke tare da Bulama, wallahi
bashi da ƙarfin ja da shi, yana da arziki kuma goyon bayan manyan mutane a duniya
ba ƙasa ba kawai, Yoseef Bukar yamin barazana ko inje kotu in bada sheda ko ya
kashe Ummanka, ko kasan ba Nurat ce tai sanadin kuɓitarka ba Allah ne ya kuɓutar da
kai, amma se da na bada kadarorina na miliyoyin nairori, aka siye mutanen Da Bulama
ya siye, nasa aka ninka musu abunda ya basu, na ɗaukar maka babban lawyer wanda
shine ya tsara komai? "
Ta ɗanyi shiru sannan ta kalli Yusuf, daya zuba mata ido tace "inda Bulama ya kaini
ya ɓoye, akwai wata mata da take kula dani a gidan, wayarta nake karɓa inyi
browsing inga yadda shari'arka ke gudana, katsam ta bar wayar a hannuna, ta tafi
aikace aikacenta, ni kuma nayi recording a wayar, na cire memory card ɗin bata sani
ba, na bata wayarta, na rubuta takadda na bata na nannaɗe memory card ɗin a leda, a
cikin takadda, nace ta aramin dubu ɗaya taje ta samu shagon masu saida abubuwa ta
basu, na bata ina addu'a Allah yasa saƙona yaje inda na tura shi.
Nayi rubutu ne, nace 'zuwa ga wannan takaddar taje gareshi, dan Allah ina neman
Alfarma, ina son duk yadda za' ayi ledar dana aiko da ita, da abunda ke cikin
ledar, a kaiwa Barrister Hafiz Mubi, ace masa inji Widad, sannan a karɓi dubu ɗayan
hannun matar a bawa wanda ze kai yayi kuɗin mota, itakuma ace maya babu abunda na
aikota ta saimin.
Shine aka karɓi saƙon, akace mata babu aiken da na mata, ta dawo ba tare da tasan
mena aiketa ba.
Barrister Hafiz, ɗahane daga cikin lawyoyin Daddy, saƙon ya isheshi ya duba, shima
na rubuta masa wasiƙa, nace ya duba cikin memory card ɗin, akwai saƙo ya duba.
A cikin audio na gaya masa yadda ze saida wasu daga kadarorina, ya ɗaukar maka
lawyer, Kasancewarsa abokin Khalil ɗan uwan Nurat, a nan ya samu dama shima suka
haɗu da wasu lawyoyin aka tsaya maka a shari'ar, badan kuɗin da na saki ba, da har
yanzu ba'a ƙare shari'ar a haka ba, da kotu bazata wanke ka ba, harse an kammala
shari'a dasu Bulama, sedai a bada belinka, amma daka motsa sekace Nurat ta maka
halacci, kaje ka ƙarat kai da ita, kaje ka Auri Nurat"
Ta ƙarasa maganar tana kuka, ta tashi zata tafi, Yusuf ya riƙeta gam ya zuba mata
idanunsa, taƙi kallonsa ta cigaba da kukanta, tana ƙoƙarin ƙwace hannunta daga
nasa.
"Kinji nace miki zan auri Nurat ne?"
"kina so in saɓawa Umma, dukda tarin alkhairinta a gareni saboda ke? Idan nayi haka
na kyauta? Kina ganin raguwar auren namu zata yi albarka ne?"
Yusuf yace "ki bani lokaci, ina son in daidiata komai ne, amma sekin dena wannan
koke koken, da tayarmin da hankalin sonake mubi komai a sannu, kinga ni duk ban san
wannan ba se yanzu da kika gayamin, kiyi haƙuri kinji"
"Nika ƙyaleni inyi dan haushinka nake ji" tai maganar tana basarwa
Bata goge hawayen ba, ta kwanta a jikinsa tana sake tura baki gaba, kamar yarinya
ƙarama.
Ya shafa gashin kanta yace "dama haka kike sona? Bani da bakin yi miki godiya,
nagode sosai Babyna, Allah ya bani abunda zan mayar miki da kadarorinki bazan so
ace kin rasa wani abu da kika mallaka saboda ni ba"
Widad tace "Dukiya ɗazu ce, ni kai ne a gabana Yoseef, bana kallon dukiya ni kai
nake kallo kawai, zuciyata kai kawai take kallo, ni kai nake so fa, ni banyi dan
ka biyani ba, ni tukucin zuciyarka nakeso kawai"
Ya rungumeta sosai a jikinsa yace "is ok my love, ki dena kuka na fahimce ki, in
dai zuciyata ce kin samu I love you my wife"
Ta maƙalƙaleshi tana lumshe ido, tana shaƙar ƙamshin turarensa daya kashe mata jiki
sosai.
Yusuf ya shafa gashin kanta yace "kinyi kyau sosai masoyiyata, kamar in sace ki in
gudu haka nakeji"
Widad tace "dan Allah mijina ka fahimtar da Umma, mu samu ta yadda mu rayu tare,
Yoseef na yadda in rasa komai nawa in kasance da kai har abada, you are my world
and happiness Yoseef"
Yusuf kasa magana yayi, se ajiyar zuciya da yake tayi, saboda yadda jikinsa ya mutu
gaba ɗaya, ya dinga sauke ajiyar zuciya, can yace "My love ya babyna yake? Fatan
baya wahalar min dake dai?"
Ta tura baki tace "gaskiya yana bani wahala, yaita kicking cikina, ko ya hanani cin
Abinci"
"ki kwantar da hankalinki, lokacine ze dena insha Allah, zan masa faɗa ya dena
wahalar min da babyna, ke dashi duk ina sonku sosai"
Widad ta tashi daga jikin Yusuf, ta kalli cikinta tana murmushi tace "kaji dai
Abunda Dad ɗinka yace ko? Ka dena takuramin"
Yusuf ya ƙura mata ido sosai, ta ɗago ta kalle shi tace "lafiya kuwa? Wannan
kallon fa? Ga fruit can a dining tashi muje ka bani abaki, nima in baka"
" I want to kiss you, lips ɗinki sunyi kyau sosai da kika sa jambaki "
Murmushi kawai tayi ta ɗauke kai daga kallonsa, a hankali ya sunkuyo da fuskarsa
dai dai tata yana mata wani irin kallo me wuyar fassara, a hankali yake mata
numfashi a fuska, Widad kamar an sassaƙata ta kasa ko motsi daga inda take zaune,
tana jin saukar numfashinsa a fuskar ta.
Rungumeta yayi yana kissing ɗinta, to show her how he misses her, and she responds
to his message to show him that she also miss him, wayar Yusuf data fara ringing ce
ta dakatar dashi daga abunda yake yunƙurin yi.
Sunan Umma ya gani akan screen ɗinsa, yaiwa Widad alama da tayi shiru, ya daidaita
nutsuwar sa ya ɗaga wayar yace "hello Umman Yusuf"
"Umma ai ta koma cikin gida, kin ganni a harabar gidansu, yanzu zamu taho da
Yallaɓai"
Umma tace "to shikenan, ka hanzarta ka dawo, bana son ka dinga nisa sosai"
Ya kashe wayar yasa a aljihunsa, ya kalli Widad dake kwance, ta ɗauke daga kallonsa
yace "sweetheart am sorry, kiyi haƙuri zan tafi kar Umma ta gane nazo gurinki
kinji"
Ya share mata hawayen fuskarta, ya sunkuya ya sumbaci goshinta, sannan ya bar falon
cikin hanzari.
Suleiman na ganinsa yace "kai haka mukayi da kai, daga zuwa ka ganta seka shige
kayi zamanka kana soyayya ka shanyani, har Umma ta kirani a waya, na mata ƙarya ai
muna tare a gidansu Nurat"
Yusuf yace "muje kawai, nima ta kirani karta gane naje gurin Widad"
Tunda suka tafi Yusuf hankalinsa baya jikinsa, ya baro shi can a tare da matarsa,
gashi yayi mamakin jin itace tayi me yuwuwa, da dukiyarta dan ganin shiya kuɓuta
daga halin daya shiga.
Tunani kawai yake yi, Suleiman ya fuskanci hakan, dan haka yaita masa nasiha yana
kwantar masa da hankali, amma sam Yusuf baya gane me Suleiman ke cewa.
A waje Suleiman ya ajiye Yusuf, shi kuma ya tafi, Yusuf ya shiga cikin gidan.
Ya shiga tare da sallama, Umma ta amsa masa tace "Yusuf kun daɗe fa, ya jikin
Nuratun"?
Umma tace "to Allah ya ƙara afuwa, amma ya na ganka wani iri? Akwai matsala ne?"
Umma tace "shikenan, ana daf da shiga sallar magariba, kai alwala ka tafi
masallaci"
Dan kar Umma ta gane yana cikin damuwa, yasa yaje ya ɗauki Abincin dare yaci, Umma
nata masa hira amma baya ganewa, se amsa mata yake da ummmm.
Ya tashi ya tafi ɗakinsa, yana zuwa beyi wata wata ba ya ɗakko waya ya kira
Widad, sedai muryarta ƙasa ƙasa kamar bata da lafiya.
"hirar da zata fi kowacce a gurina, itace ganinka a kusa dani, amma kamin nisa, ina
ji ina gani ba yadda na iya, dukda son da nake maka"
Nan Yusuf ya kwantar da murya ya shiga aikin rarrashi, harta saki jikinta dashi, ta
dena fushin suka koma soyayya, yauma seda suka sha soyayyar su, seda dare yayi
sosai sannan suka kwanta bacci cike da begen junansu.
Umma tana monitoring ɗin Yusuf, ya dena zaman tsakar gida ko kuma hira da ita,
kullum yana ɗaki riƙe da waya, da tayi zancen Nurat seya dinga basarwa, saboda haka
ta zuba masa ido, sedai ta toshe duk wata hanya daze fita yaje yaga Widad, dan bata
son ya kuma raɓar Widad yaja musu matsala.
Sosai fa Suke kewar juna shida matarsa, gashi baze iya bijirewa Umma ba, yana
matuƙar tausayin Widad sosai, dan yadda suka yi waya yau ya gane bata da lafiya
tana jin jiki sosai, ga babu hanyar fita, dan idan harze fita se Umma ta tambayi
ina zashi.
Da Yamma Umma ta hanshi zaune yayi jugum, yayi shiru kamar wanda akayiwa mutuwa.
Ta kalle shi tace "Yusuf zo kaje ka siyo kayan miya, zanyi girki naga yamma tayi"
Yace "to"
Ta bashi kuɗi ta lissafa masa abunda ze siyo mata, sannan ta bashi dubu biyu tace
"ga wannan ka riƙe a hannunka, kafin ka koma gurin aikin"
Umma tana ta aikinta a tsakar gida, taji anyi sallama, ta amsa tare da waigowa
wanda ta gani ne yasata sakin tsintsiyar hannuta ta saki baki, tana kallonsa..
IDAN KIKA FITAR BADA IZININA BA, ALLAH YANA KALLONKI, KUMA KINCI AMANA
AYSHERCOOL
07063065680
12/7/21, 11:04 PM - Buhainat: LITTAFIN KUƊI NE, DAN ALLAH KI SIYA KAFIN KI KARANTA
BA DANNI BA DAN ALLAH, LITTAFI NA ƊAYA KYAUTA NE WANNAN NA SIYARWA NE
NORMAL GROUP ₦300
VIP ₦500 NE KITURA TA WANNAN ACCOUNT ƊIN
0009450228
JA'IZ BANK
AISHA ADAM
SE A TURA SHEDAR BIYA TA WANNAN LAMBAR
07063065680
(Albishir ga masoya, ma'abota bibiyar litattaafaina, dama ta samu zaku fara samun
litattaafaina na audio, akan YouTube channel ɗina me suna Cool Arewa TV
https://youtube.com/channel/UCD5vnvA5laU8ti4LLz2_QEg
Kuyi liking sannan ku danna subscribe, domin fara samun litattaafaina na audio,
nagode sosai da ƙaunar ku gareni"
160_161
Umma ta bi mutumin da kallo kamar taga baƙuwar halitta, mutumin yace "Madam a bamu
guri mu zauna mana, an tsaya ana bina da ido"
Jin yace a basu gurin zamane yasa Umma leƙa bayansa, taga mutumin tare da Widad a
bayansa, take Umma ta ɗan tsuke rai.
Mutumin yace "Jidda wannan kallon fa? Ki bamu gurin zama mana"
Umma tai musu jagora zuwa falonta, taje fridge ta kawo musu ruwa da lemo, Widad
tace "Umma ina wuni"
Umma ta amsa sama sama, Mutumin yace "Jidda dama rai kanga rai? Rabona dake tun
kina budurwa, ban sake sanin inda kike ba, se kwanan nan naji ashe Bashir Maitama
ne mijinki, Allah ya jiƙansa da Rahama"
Umma tace "Ameen ya Allah, kwana ba adadi Alhaji Ahmad, dan yanzu sedai ince
Alhaji ka ƙara ƙiba, kamar ba kaiba kamaninka sun canza saboda kuɗi sun zauna"
Alhaji Ahmad yace "bari Jidda, abubuwa duk se godiyar Allah kawai"
Widad ta jinjina kai, Ya kalli Umma yace "dama kece sirikar tamu kike wahalar min
da 'ya?"
Alhaji Ahmad yace "to a al' adar Hausawa dai, namiji ke zuwa biko, to hula taja
ɗankwali, munzo muyi bikone, dan Allah a temake mu a bamu mijin mu mana, ayi mana
afuwa"
Umma tace "wai ya akayi ta zama 'yarka kuma? Kuma ni gaskiya ina tsoron abunda ze
biyo bayane, ni inajin tsoron ɗana ya sake shiga matsala gaskiya"
Alhaji Ahmad yace "labarin dogone, amma dan Allah ayi haƙuri a bamu mijinmu, zamuyi
miki bayanin komai, amma waini ina sirikin nawa yake nema? A nunamin shi in ganshi,
inga ya yake a yanƙwanamu akansa haka?"
Umma tace "A'a ba wani na musamman bane, kawai ni bana son ɗana ya sake shiga
matsala saboda itane, ya wahala fiye da tunaninka, duk saboda ita, wahalar da akayi
a baya Allah ya amfana"
Yusuf ne yayi sallama, hannunsa ɗauke da ledar aiken da Umma tayi masa, ya shigo
falon cikin nutsuwa da sallama, sedai yana ganin Widad a zaune gabansa ya faɗi, ya
ɗan tsaya yana kallonta, ta sunkuyar da kanta tana wasa da yatsun hannunta.
Yusuf ya durƙusa ya gaida Alhaji Ahmad, Alhaji Ahmad ya amsa yana ƙarewa Yusuf
kallo, yace "iko se Allah, lallai dole a mana jan aji akan wannan zuƙeƙen
matashin, Widad banga laifinki ba da kikabi kika ɗaga hankalinki akan mijinki, dan
an ganshi kyakkyawa shine ake wani jamana Aji"
Yusuf ya ɗanyi murmushi, yana son sanin waye wannan mutumin da suka zo tare da
Widad?
Yusuf ya maida kallonsa ga Widad, ya ɗan kashe mata ido, amma ta haɗe rai tana
ƙoƙarin maida ƙwallar idonta, girgiza mata kai Yusuf yayi, ya ɗakko handkerchief
ɗinsa, ya faki idon Umma, ya miƙawa Widad, Alhaji Ahmad suna magana da Umma, amma
hankalinsa yana kansu Yusuf.
Yusuf ya miƙe ze bar falon, Widad tabi Yusuf da kallo, kamar zata cinye shi.
Alhaji Ahmad ya kalleta yace "Widad ɗan bamu guri, maza tashi ki bishi, ai tunda
Allah yasa munzo se Jidda ta bamu mijinmu, an dena wahalar min da 'ya dan anga yana
da kyau, nasan dai' yata tafi shi kyau"
Umma tayi murmushi, Widad kam cikin hanzari ba kara ba kunya, ta miƙe yabi bayan
Yusuf, yayin da Umma ta jinjina rashin ta ido irin na Widad "
Suna fita Yusuf ya janyota gefe yace " sweetheart, waye wannan mutumin ne? "
"Nifa ban sanshi ba, ya cemin yasan Ummane, nazo mu bada haƙuri"
Yai murmushi yace "shikenan naji, zomuje ɗakina muyi hira kafin su gama maganar"
Widad ta zaro ido tace "haka kurum, Umma tace bani da kunya, ni a nan zan zauna"
Ya shimfiɗa musu dadduma, suka zauna hirarsu suke kawai kamar babu abunda yake
damunsu, Umma ta fito ita da Alhaji Ahmad, Alhaji Ahmad yace "Widad taso mutafi, se
Allah ya kaimu weekends ɗin"
Widad ta tsaya tana kallonsa, kamar bata gane me yake faɗa ba.
Alhaji Ahmad yace "iko se Allah, kiyi haƙuri kizo mutafi, idan Allah ya kaimu
Weekend zamuyi tafiyar nan, kuma ina lallaɓa sirikata mu, dan haka kiyi haƙuri za'a
baki mijinki"
Widad tace "dan Allah ni ka ƙyaleni a nan, wallahi bana son zaman gidan nan nika
ɗai, damuwa damuna take, dan Allah ka barni a nan zuwa weekends ɗin mu tafi ta nan
gaba ɗaya"
Alhaji Ahmad yace "Ikon Allah to sirkarmu kinji abunda tace, bakomai ta zauna ɗin a
nan, zuwa Allah ya kaimu weekends ɗin?"
Umma tace "toni me zance, in dai gidane gashi nan ta zauna, sedai mu bamu da
Arziki ba lallai muna da abubuwan da take buƙata ba"
Yusuf a ransa yace "Umma da kin san a ƙungurmin ƙauyen da muka zauna, da baki faɗi
haka ba"
Alhaji Ahmad yace "toke yanzu gashi baki ɗakko kayanki ba, a haka zaki zauna ɗin?"
Alhaji Ahmad yace "ina ganin ƙauna, ikon Allah dan Allah Jidda ayi haƙuri idan
muka dawo daga tafiya Yusuf ya koma ɗakinsa"
Seda Umma tayi dariya, jin abunda Alhaji Ahmad ya faɗa, gaba ɗaya suka raka shi har
bakin mota ya tafi, sedai tafiyarsa babu wuya aka girke 'yan sanda a bakin layin su
Yusuf dan basu tsaro.
Mutanen layin sunata gulma dan sunga an kawo' yan sanda layin, wataƙila Yusuf aka
kuma zuwa kamawa, tunda yai wannan laifin unguwarsu bata rabo da 'yan sanda.
Yusuf yana son ya keɓe da Widad suyi hira sosai, amma kunyar Umma yake ji sosai,
Umma kam basar dasu tayi kamar bata san da zamansu ba, sabgogin gabanta kawai take
yi.
Bayan sallar magariba Yusuf ya dawo daga masallaci, Widad tace "Yoseef nayi waya
gida, Nura zezo da mota muje farm House mu ɗakko kayan.
Ba daɗewa sega Nura direban Daddy ya ƙaraso, Yusuf yaje ya samu Umma yace " Umma
zan raka Widad ta ɗakko kayan ta "
Sam Yusuf baya jin daɗin yadda Umman keyi, duk se yaji ya damu ya tsargu sosai,
baya jin daɗin hakan sam.
Widad ta saka takalmanta tayi waje, Yusuf yabi bayan ta, suna zuwa Nura ya buɗe
mota ya fito yana, jinjinawa Yusuf hadda duƙawa yana "Allah ya temaki me gida,
Allah ya tsare gabanka da bayanka mijin Hajiya Widad, siriki ga Alhaji Nasir Daula"
Yusuf yai murmushi yace "Nura karka bani kunya mana dan Allah, ni nayi laifi ma,
tunda aka sakeni, ban samu nazo mun gaisa na muku godiya ba, saboda bana son sake
zuwa gidan nan ne, amma ina godiya Nura"
Yai maganar yana miƙawa Nura hannu su gaisa, Nura ya zare ido yace "wane talaka
haɗa hannu da kai yanzu? Ai sedai ai muku gaisuwa irin taku ta manya"
Yusuf yace "dan Allah Nura ka bari, bazanji daɗin haka ba, ka barni a Yusuf direba
na kawai"
Widad tace "aikuwa naga wanda ze kiramin miji da direba, yaga yadda zanyi dashi,
koda yake ni kaɗai zan dinga ce masa direbana"
Sukayi dariya gaba ɗaya, Widad ta ɗakko ƙaramar jakarta, ta ɗebo kuɗi ta miƙawa
Nura tace "gashi nan, ka hau mota ka koma gida, bawa Direbana mukullin, zamuje
yawo tare"
Yusuf yai murmushi yace "Yarinya ki cigaba da cemin direba, idan na kaiki bazan
dawo dake ba"
"kai ka isa"? Tai maganar tana kaimasa dukan wasa a ƙirjinsa, Yusuf ya karɓi
mukullin motar suka shiga suka tafi.
Nura kuma yai ram da kuɗin da Widad ta bashi, dan kuɗin yafi ƙarfin dubu Ashirin,
yana tafe yana mamakin yadda Widad ta canza gaba ɗaya, ga kuma ga dukkan alamu ba
ƙaramin so takewa Yusuf ba.
Haka ya isa gida yana wannan mamakin da tunani, Isa yace "ha na ganka kao kaɗai?
Ina motar da kuma gimbiyar Daula?"
Nura yace "barni inyi mamaki Isa, gaskiya gimbiyar Daula ta canza, kaga wasa da
dariya?"
Isa yace "Inama me? Kana ganin baƙar azabar da ya sha, kafin ya kuɓuta, ni mamakin
da nake ya akayi sukayi auren ne?"
Nura yace "kanaji ana gayamaka, Saleh ne ya kuɓutara dasu, ya kaisu wani ƙauye aka
ɓoyesu, kasan ta bata da yadda sam, taƙi yadda da kowa seshi, kuma ance lokacin
bata da lafiya sosai, tace bame kula da ita seshi, shine fa sukayi Aure a can, daga
nan kuma abu ya zame masa silar Arziki, dan nasan yanzu ita da abunda ta mallaka
yana da iko dasu, dama ka santa ga kyauta, gaskiya ze warwasa, inama inama nima ace
in samu dama haka ko bata kai kamar tasa ba"
Isa yace " babu wanda yafi bani mamaki, se Alhaji Bulama ubangiji Allah yayi mana
tsari da azzalumai kamarsa, yanzu duk yada yake da Daula, da soyayyar da yake
nunawa Daula, ashe azzalumi ne mufuki, na ƙaryane zagon ƙasa yake masa, gaskiya mun
shiga haƙƙin Widad na ganin aibunta, ashe tana da dalili akan ƙin mutane, ji wannan
asara fisabilillahi "
Nura yace " bari kawai Isa, duniya babu gaskiya, mutane mun lalace se fatan
shiriya, amma tabbas gaba ɗaya mutanen nan sunyi tarayya a cikin ƙaddarorinsu,
Alhaji Daula, 'yarsa da kuma Yusuf daya shiga rayuwarsu daga baya, sedai fatan
Allah yasa bakin wahalrsu kenan, kuma Allah ya bayyana Alhaji Daula "
Yusuf da Widad kuwa, seda suka sha yawonsu a gari, sannan ya kaita suka ɗakko
kayanta suka dawo gida.
Ɗakin Umma ya kai akwatin kayan nata ya ajiye, ita dai UMMA bata tanka musu ba,
tana ganin Yadda suke rawar kai akan junansu, da nan nan da juna cike da tsantsar
kulawa da soyayya.
Yusuf ya ɗakko flask ɗinAbinci ya kawo, tuwon Alkama ne miyar kuɓewa Umma dafa,
Yusuf yana zubawa Widad kamar zata shiga cikin kwanon, saboda yadda yawunta ya
tsinke.
"Yoseef dan Allah ka zuba da sauri mana, kana yi a hankali fa, kuma ni sonake inci"
Tai maganar a ɗan Shagwaɓe, Yusuf ya kalli Umma, amma yaga hankalinta baya kansu,
kuma tana jin taɓarar da Widad ɗin keyi.
Yusuf a hankali yace "bazanyi saurin ba"
Ta harari Yusuf tana tura baki, ya zuba mata tuwon nan, miyar ta sha kifi, ya samat
man shanu, yadda Widad ta duƙa tana zuba tuwon nan yafi komai bawa Yusuf mamaki, ci
take kawai ko magana ba tayi.
Widad tace "wallahi ban ƙoshi ba, rabona da Abinci inci cikakken Abinci cikin
kwanciyar hankali, tun ranar da muka baro ƙauyen nan, bana samun Abinci inci, ga
Abincin yayi daɗi Sosai"
Yusuf yace "ikon Allah, yanzu ke tunda kike gurin Bulaman bakya cin Abinci?"
Widad tai murmushi me ciwo tace "Yoseef, bana son tuna abunda ya riga ya wuce, ban
zaci zan kuɓuta ba, na sha wahala fiye da tunaninka, banda duka da baƙar azabtarwa
ba abunda nake sha a hannunsa, ga ɗansa kuma Fahad, daya dinga nema yaci zarafina,
bana samun abunda nake so inci, komai bayamin daɗi, shiyasa na masa wannan tabon da
wuƙa a fuskarsa, ko zan rage raɗaɗin abunda yayi min"
Gaba ɗaya jikin Widad yai sanyi tace "ƙaramin tuwon nan, yunwa nakeji ban ƙoshi
ba"
Ya sake zuba mata, ta dinga cin abunta, ba wata kunya ko kara seda taji tayi ƙyat
babu sauran gurin zubawa sannan ta haƙura, ta tashi taje fridge ta samo ruwa me
sanyin gaske, ta zauna ta sha abunta ta wanko hannunta tazo ta zauna tana hutawa.
Abincin data cine ya fara taso mata, tai shiru ta kasa magana, Yusuf ya zuba abunda
ta rage yana ci.
Cikin hanzari Widad ta tashi ta fita, ta dinga amai, seda ta amayar da duk abunda
taci, Yusuf yabi bayan ta da sauri.
Tayi amai sosai, Yusuf ya temaka mata, ta gyara jikinta ta kuskure bakinta.
Umma ta fito daga ɗaki tace "garin yaya take amai haka? Ko bata da lafiya ne?"
Widad taje ta canza kayanta, zuwa na bacci ta sake burma ƙaton hijjabinta, ta nemi
guri ta kwanta a ƙasan carfet.
Umma ta shigo ɗakin ta ga Widad a kwance a ƙasa tace "tashi ki hau kan gadon mana"
Widad tace "A'a Umma, bana jin daɗin kwanciyar kan katifa, bayana ciwo yake
nafison kwanan ƙasa"
Umma tace "shikenan"
Widad dukda basar da ita da Umma take, amma taji daɗin ganin yadda Umman, ta nuna
mata kulawa.
Umma taje ɗakin Yusuf tace "bani bargonka guda ɗaya, a shimfiɗa nata tace bata son
kwanciyar kan gado"
Yusuf yace "yawwa Umma, naji ana cewa za" ayi tafiya da weekend, amma ina za'aje
ne? "
" ban sani ba, meya hana ka tambayi matarka? Bani bargo ni"
Nurat kam gaba ɗaya damuwa ta addabeta sosai da sosai, bata jin daɗin zaman gidan
gaba ɗaya, gashi ta saka duk mutan gidan a damuwa, ganin yadda taƙi sakin jikinta,
Nurat tai tunani taga damuwa bazata maganta mata abunda ke damunta ba, ta tashi ta
fito falon gidan.
Ba kowa a gidan, duk ma'aikata ne sun tafi gurin aiki, ƙannen Khalil kuma duk suna
kudancin Nigeria suna karatu.
Nurat ta gyara ko'ina na gidan, tayi girki yaje tai wanka ta dawo falo tana kallo,
duk a ƙoƙarin ta na kauda damuwar dake ranta.
Wajen ƙarfe biyu Khalil ya dawo gida, ganin Nurat a falo tana kallo yasa yaji daɗi,
ba kamar da ba da kullum tana ɗaki, ya ƙaraso yana mata murmushi yace "Sisyna,
masha Allah, wannan kyau haka"
Tai murmushi taje ta karɓo kayan hannunsa, tana masa sannu da zuwa tana masa
murmushin nan nata me ɗaukar hankali.
Yaji inama ace matarsa ce.
Nurat tace "Sannu da zuwa, kaje kai wanka kazo yau nina yi girki kaci Abinci"
Nurat tai murmushi, taje ta kai masa kayan ɗakinsa, dake kusa da falon.
Bayan yayi wanka yai salla, ya fito ya zauna a falo yana jiranta, ta shigo da
sallama hannunta ɗauke da kulolin Abinci, ta tarar da Khalil ya zubawa wayarsa ido.
Nurat tace "inyee, da alama wannan matashin barrister ya shiga soyayya, hoton wa
ake kallo haka?"
Ya ɗago ya kalleta yace "kalleki, wai hoton wa nake kallo, niwa zan kalla"
"Nifa dama baka taɓa nunamin budurwarka ba, gaskiya yakamata kayi aure haka, haba
seka zama tuzuru tukuna, dan kaga Mama ta shagwaɓaka ne, da Abincin ta, ta koraka
bakin gate a maka ɗaki, sannan a dena baka abinci zakayi aure"
Khalil yace "kice azabtar dani za'ayi kenan? Hmm ni tsoron matan yanzu nake Nurat,
soyayyar gaskiya tana wahala, shiyasa ni ban taɓa budurwa ba"
Nurat tace "No akwai soyayyar gaskiya mana, kai dai kawai kace tsoron 'yan mata
kake yi, you can't toast a lady"
Tai maganar tana dariya, Khalil ya girgiza kai yace "Eh naji ɗin, yanzu dai in kin
matsu inyi Aure ki samo min budurwa, sannan ki dinga rakani zance"
Nurat tai murmushi, seda fararen haƙoranta suka bayyana tace "ba budurwar da zata
aureka kuwa a haka, in dai sena raka ka zance"
Ta zuba masa Abinci, yanaci yana kallonta, yana jin kamar ya gayamata yana Sonta,
sedai yasan zuciyarta tana tare da Yusuf.
Da Safe Widad ta tashi, Umma tana bacci ta tafi ɗakin Yusuf, yana kwance yayi ɗai
ɗai akan gado, yana baccinsa.
Ta kalli ɗakinsa, ɗakin tsaf dashi, kamar ɗakin wata matar ga Mirror, da gado
wardrobe komai tsaf dashi.
Ta ƙarasa kan gadon nasa, ta zauna ta ƙura masa ido, Wani murmushi take ganin yadda
yake baccinsa hankali kwance, kamar wani jariri ya ɗan ciko daga ramar da yayi,
sedai shima jikinsa duk tabon duka daya sha a prison.
Hannu ta kai tana shafa gefen fuskarsa, tai ƙasa sa muryarta tace "Hubbyna ka
tashi muna jin yunwa fa"
A hankali ya buɗe ido ya kalleta yace "ke kin fiye takura, haba Babyna wace irin
yunwa ƙarfe shida na safe?"
Cikin shagwaɓa tace "ni dagaske yunwa nakeji, ka tashi yunwa nakeji"
Yusuf ya noƙe kafaɗa, yana ɗora kansa akan cinyarta yana lumshe ido.
"Wallahi idan baka tashi ba, zan zauna se Umma tazo ta gamu a nan tare"
Widad ta dinga dariya, har sunje bakin ƙofa, ya juyo ya kalleta ya rungumota
jikinsa yai kissing ɗinta yace "good morning"
"Alhamdilillah, ya babyna?"
Suka feraye dankalin hausa tare, suka dafa tea, suka shiga suya Tare, hirarsu kawai
suke kamar suka ɗaine a gidan.
Umma kuwa tuni motsinsu ya tashe ta, amma bata fito ba karta takurasu, suka gama
sukayi wanke wanke suka gyara komai tsaf.
Widad na shiga ɗakin ta tarar Umma ta tashi, Widad tace "Umma ina kwana"
Duk yadda Umma take basar da Widad, Widad bata nuna mata taji haushi ba sam, tana
girmamata sosai, sedai bata iya kara ta ɓoye soyayyarta ga Yusuf ko a gaban Umma ne
Wajen ƙarfe goma na safe, ciwon ciki ya kama Widad, tun tana mazewa seds Umma ta
gane.
Lokacin Umma ta aiki Yusuf, baya gidan amma ganin Yadda Widad ke murƙusus yasa Umma
ta kira shi a waya.
Da hanzari ya dawo gida, ya tarar Da Widad ta durƙusa tana kuka, se numfashi take
da ƙyar.
Ɗan dirircewa Yusuf yayi, dan Umma bata san da ciki a jikin Widad ba, saboda kullum
cikin zumbulelen hijjabi take.
Umma ta tashi, taje ta ɗaga Widad daga jikin Yusuf, ta kwantar da ita akan pillow,
tace "naga da mota a hannun ka, jeka ɗakko kazo a kaita Asibiti ko ɓarine"
Widad ta haɗa gumi sosai Umma tace "kiyi ta ambaton Allah, kidena kuka"
Widad ta kwanta rigingine, tana jujjuya kai, hakan ya bawa cikin nata damar fitowa
sosai, Umma tayi mamakin ganin cikn nan, kenan dama da cikin aka kamosu?
Widad ta girgiza kai tace "beyi wata shida ba, Allah yasa ba zubewa zeyi ba"
Yusuf dai haka ya ɗakko mota, suka sa Widad a ciki zuwa Asibiti.
Ta sha wahala sosai, seda suka wuni a Asibiti, likita ya tabattar musu da cewa
allurar zubar da ciki da aka dinga mata ce take bata wahala haka.
Widad tace "Bulama, shine yasa aka dingayi min tunda akace masa ina da ciki, Amma
dai cikin yana nan ko likita? Bana son in rasa shi dan Allah"
Likitan yace "ki kwantar da hankalinki, bakomai cikinki yana nan lafiya"
Haka nan Umma taji Widad tana bata tausayi sosai, mussman da taji tace allurar
zubar da ciki aka dinga mata.
Bulama yasha matsa sosai, dan gaba ɗaya ya fita hayyacinsa, a hankali yake ta faɗar
da wanda yake haɗa baki ana cutar Daula, ga HIV ta fara nunawa a jikinsa, gudawa
yake ba ƙaƙƙautawa, ga zazzaɓi me zafin gaske da yake fama.
Ya kalli 'yan sandan dayake hannunsu yace "Ranka ya daɗe, yakamata fa ace an
barni naga lawayerna, dan har yanzu ba' a tabattar da laifin da ake zargina dashi
ba"
Ɗan sandan yace "ka makara, dan baka da wannan damar kaima, kamar yadda ka siye
wasu daga cikin hukumomin tsaro akayi maka yadda kake so a wancan karon, to yanzu
an siyesu, ninkin yadda ka siyesu, kuma anace kar a sake a baka duk wata dama ko
kwatankwacin ƙofar Allura ce, dan haka karka yi zaton zakayi free, kaida 'yanci har
abada daga kai har muƙarrabanka!!!
AYSHERCOOL
07063065680
12/9/21, 2:40 PM - Buhainat: LITTAFIN KUƊI NE, DAN ALLAH KI SIYA KAFIN KI KARANTA
BA DANNI BA DAN ALLAH, LITTAFI NA ƊAYA KYAUTA NE WANNAN NA SIYARWA NE
NORMAL GROUP ₦300
VIP ₦500 NE KITURA TA WANNAN ACCOUNT ƊIN
0009450228
JA'IZ BANK
AISHA ADAM
SE A TURA SHEDAR BIYA TA WANNAN LAMBAR
07063065680
(Albishir ga masoya, ma'abota bibiyar litattaafaina, dama ta samu zaku fara samun
litattaafaina na audio, akan YouTube channel ɗina me suna Cool Arewa TV
https://youtube.com/channel/UCD5vnvA5laU8ti4LLz2_QEg
Kuyi liking sannan ku danna subscribe, domin fara samun litattaafaina na audio,
nagode sosai da ƙaunar ku gareni"
166__167
Gaba ɗaya a razane suka kalli Bulama, ya cigaba da cewa "bayan ya kashe Huda,
shine ya ambaci sunana har Widad taji, da niyyata har ita a kashe, bayan ya kasheta
ne, a gurin zaman makoki Widad ta tonawa Bala asiri a gaban Wannan ɗan sandan,
shima na faɗi na tashi na saka aka kashe shi!"
Yusuf ya rintse ido, yana jin kamar Bulama yana rura wuta a zuciyarsa.
Bulama ya cigaba da cewa," daga nan na lallaɓ Saleh, akan ya saki Halima, akwai
kaso me tsoka daze samu idan harya sake ta ta aureka, dama ba iya kula dasu yake
ba, dan haka ya amince dan yaji batun kuɗi, ya sake ta ko idda batayi ba, na dinga
tura ta a gurinka, har seda ka amince da Aurenta, ka kuma ɗauki ɗawainiyar yaranta,
ta aureka dan ta dinga tatsar mana kuɗi a gurinka.
Da kuma saka ido, domin mu samu ta karɓo mana wannan dukiyar daga hannunka, na saka
aka dingayi wa 'yarka Allurar mahaaukata, saboda kar ta tona min Asiri, kuma inyi
amfani da damar idan ta haukace ko Allah zesa in samu inda dumiyar nan taje, amma a
banza, na dinga tura maka saƙonni kala kala, na razanarwa akan dukiyar nan, na
dinga farmakar ka kaida' yarka da barazanar kisan kai, sannan duk wanda yai
yunƙurin raɓarku koku raɓeshi, se shime in farmake shi, na taka rawar gani akan
AƘIDAR 'yarka, dana ga hakan bzata yuwu ba, na koma ma baka shawarar ka aurar da
ita ga ɗana Fahad, hakan zesa ta canza halaye, amma a zuciyata ina son ta auri
Fahad ne dan idan bamu samu waccan dukiyarba, mu gane zunzurutun dukiyar da ka
malllaka mata, duk wani meeting da yadda za'a karɓi dukiyarka da matarka mukeyi,
watarnma se cikin dare a hotel haka muke meetings ɗin, bazan ɓoye maka ba Daula,
tunda komai yazo ƙarshe wallahi ban taɓa sonka ba, na tsaneka ko ganinka nayi cikin
walwala se inji kamar in kasheka in huta, kafini komai bana appreciating duk wani
goodness ɗinka, burina kawai inga bayanka hankalina ya kwanta, saboda ganinka a
raye ma bana ƙaunar yi "
Daula ya sunkuyar da kai, hawaye na bin idonsa, Alhaji Ahmad yace" kaiconka Bulama,
kayi asara Nasir da dukiyarsa, da ƙarfinsa haka ya dinga maka wahala kai da
iyalinka, ka kawo wasu ma cin arziki, kuma ya musu, amma ƙarshe ga inda ciwon
hassada ya kawoka, to ina maka Albishir dukiyar da kake hari, ga me ita nan"
Ya nuna Yusuf, sannan ya ci gaba da cewa "dukiyarsa ce, shine ɗan Yusuf yayan
Nasir, wanda kasa rai akan lallai seka karɓi dukiyar, ka azabtar dashi da ahalinsa
saboda abun duniya, yadda kazo a banza haka zaka koma a wofi, sannan duk wata
kadara indai ta Nasir ce, zamu karɓeta har gidan da kake ciki da motoci, da
kamfanin daya ɗora kka akai ka maida shi naka, sannan kema Halima da kika dinga
siyar da kadarorinsa, bayan wanda kika ci a baya, da wanda kika dinga sata, duk
wanda kika siyarwa da wani abu ya sai aikin banza, zasu iya yin shari'a daku ku
biyasu dukiyarsu, sannan bisa ga adalci na Nasir, yace "ze baku duk wata dama a
shari'a, baze amfani da dukiya ba ai muku hukuncin daya dace daku akan kisan kai na
matarsa, da kuma garkuwa da kuka yi masa da yaransa"
Widad fuskarta sharkaf hawaye tace "Nikuma zanyi Amfani da ƙarfin dukiya, ayi masa
irin shari'ar da yai amfani da kuɗi akayiwa mijina, kaiconka Bulama daga kai har
'yar uwarka da sauran mutanen da suka zaluncemu, kuda Allah"
Ana cikin haka aka tankaɗo Abbas ma, Ya kalli Yusuf, Yusuf ya kalle shi, Abbas ya
fashe da kuka yana faɗin "dan Allah Yusuf ka yafemin, na biyewa Zuciya da son abun
duniya na aka haɗa kai dani aka cutar da kai, dan Allah Yusuf ka yafemin"
Yusuf ko kallonsa beyi ba, yai waje da sauri, yana tuna shima irin yadda ya amince
da Abbas, be taɓa aboki kamarsa ba, amma yai masa wannan muguntar.
Su Alhaji Ahmad ma sukayi waje, daga gurin, su Alhaji Musa suna ta salalami dan sun
san tasu ta ƙare, ga jikin girma dama kuɗine yasa ba'a gane tsufan nasu sosai,
yanzu kuwa kam se cituttukane ke kunno musu kai kala kala.
Wani ɗan sanda ya biyo bayansu Daula yana musu bayani "To yallaɓai har yanzu muna
nan munata tattara bayanai, da bincike akan wannan baƙin azzalumi da duk wanda ya
haɗa kai dasu, kama daga yadda suka haɗa baki da megadinka, wani Bala zuwa yadda
yasa aka kashe shi a gidan yari, da duk wani wanda yake da hannu muna ta kama
mutane ɗaya bayan ɗaya, kuma ba da daɗewa ba zamu gurfanar dasu a gaban kotu insha
Allah "
Alhaji Ahmad yace " Masha Allah, yayi kyau sosai wannan shine wanda aka bawa aikin
dana bayar, Bulama sukayi amfani da wannan damar wajen cinma burinsu"
Alhaji Ahmad yace "Aini koda bama tare da Daula, ina bibiyar al'amarunsa, kuma
haka nan nake zargin Bulama zata iya kasancewa da hannunsa a masu yiwa Daula
barazana, dan tuni ns gane dukiyarsa yakewa, sedai a lokacin son Bulama ya rufewa
Daula ido, baya ganewa, ina jin duk labarin yadda kike bakya sakewa da mutane, da
larurar taɓin hankali da kuma bibiyarki da ake akan wannan dukiyar, ni kuma na saka
ayi bincike akan me bibiyar taku, sannan a baki tsaro ba tare dake ko mahaifinki
wani ya sani ba, sedai ban san yadda akayi Bulama yasan an bada wannan aikin ba,
har ya shiga ƙoƙarin karɓar file ɗin idan an gama binciken, dan ɓatar da duk wata
hujja da zata saka a gane shi "
Widad ta sauke ajiyar zuciya tace " kowa yayi nagari kansa, a duniya babu abunda za
ayiwa Bulama wanda zesa mu huce takaicin abunda yai mana, sedai ai masa hukuncin
daya dace duniya sauran a barshi se a lahira "
Haka suka shiga mota suka tafi gida, suna jinjinawa azabara zalunci da baƙar
mugunta na Bulama, tunda ya kashe ɗan 'yar uwarsa waye baze kashe ba, duk saboda
abun duniya.
Da suka koma gida, fuskonkinsu kawai Umma ta kalla tasan wani abun takaicin suka
kuma zuwa suka jiyo, a gurin' yan sanda shiyasa tun farko tace bazata bisu ba.
Umma tai musu sannu da zuwa, Daula ya wuce ɗakin hutawarsa, saboda yana buƙatar ya
ɗan huta yayi tunani.
Widad ma ta janye mijinta, zuwa wani ɗakin daban, Alhaji Ahmad ya zauna a kujerar
dake kusa da ta Umma yace "Hajiya Jidda"
"Dole ace miki Hajiya mana, tunda kika riƙe ɗan Daula, kika riƙe babban attajiri
haka"
Umma tace 'mhmm, ni tsoro nake ma kar yace ze ƙwacemin ɗana, bana son sunana ya
canza daga Umman Yusuf, dan bana tunanin ko da Allah ya bani haihuwa, zanso ɗan nan
kamar yadda nake son Yusuf'
'tabbas nima nagani, kuma Wallahi Daula ua jinjinawa ƙoƙarin ki, yace idan ya kalli
abunda Bulama ya masa, se yace "Anya kuwa akwai ragowar mutanen kirki a duniya?
Idan ya duba irin riƙo da wahalar da kika sha da Yusuf se yace duk lalacewar zamani
akwai na Allah, wallahi kin ciri tuta Jidda, kuma abunda kikayi Jihadi ne, riƙon
maraya da zuciya ɗaya tamkar ɗan da kika haifa "
Jidda tace " gashi nan ina morarsa, wataƙila da ban riƙe Yusuf ba haka tsufa ze
riskeni babu me jin ƙaina, 'yan uwana bama su ƙarfi bane, hasalima a gurina suke
nema, bani da wanda muke uwa ɗaya uba ɗaya sedai' yan uba, amma Yusuf ya riƙeni
Uwa, yanamin biyayya fiye da yadda kake zato, ƙare magana ko ɗan dana haifa banajin
zemin biyayyar da Yusuf yayi min, koda ban taɓa haihuwa ba, amma ni riƙon Yusuf
yamin rana, ko be zama komai ba, tausayinsa da jin ƙansa ya gamamin komai "
Alhaji Ahmad yace" hakane, tabbas yana da haƙuri da biyayya, kuma bayan wannan
dukiyar dai Allah yayi tasa ce, da ba lallai ya iya jure wannan tsananin da wahlar
ba, amma da yake tasace kuma Jininsa ne Daula, kinga ya jure duk gwagwarmaya, an
gaisheki Jidda kin cika Uwa tagari "
Jidda tai murmushi tace 'Nikam Ahmad, ina naka iyalin ne?"
"gani nayi tunda mu kazo banga ka koma gidanka ba, ko ka yi zancen su ba"
Yai murmushi yace "iyali suna nan a kano, da ina nan zaune tare dasu ne a nan
Abuja, tace ita dai tafison zaman kano, shine suka koma suka barni sedai in dinga
zuwar musu"
Yace "ameen ya Allah, Jidda nayi mamaki har yanzu kina nan da kyanki baki canza ba
gs gayu"
"wallahi baki tsufa ba, kalleki fa ras dske, amma meyasa baki sake aure ba bayan
mijinki ya rasu?"
Umma tai ajiyar zuciya tace "saboda ina son in kula da yarona, idan na auri wani
waze yadda ya riƙemin shi, mussman da bani na haife shi ba, shiyasa na zaɓi in
zauna ba Aure in riƙeshi"
Alhaji Ahmad yace "to amma ai yanzu ya girma, shima me riƙe wasu ne mussman wannan
sitira da Allah yayi masa yanzu, saboda haka yakamata kiyi aure ai"
Umma tace "tsofaitsofai dani se in kama yin wani aure, a'a ai na girma Aure mun
barwa yara"
Alhaji Ahmad yace "ba wani nan, ni dai ina zawarci har yanzu, ina so"
Umma ta kalli Alhaji Ahmad tace "dan Allah ka dena wannan zamcen haka, haba Ahmad"
"kinga dole inyi wannan zancen, haba Jidda me zesa ki haramtawa kanki Abunda Allah
ya halatta, haka zaki cigaba da zama babu Aure kenan?"
Alhaji Ahmad yace "No, gaskiya bazaki zauna haka ba, kawai ki tsaya mu sasanta"
Umma ta miƙe tace "kai dai bazaka canza hali ba, ka girma kana abun yara"
Yai murmushi yace "Au hakama zakice? Aini bazaki girman a idona ba, tunda.. Bari
dai in shiru"
Widad tace "haba my Fluid of life, wai baka murna da kasancewat ƙanwa a gareka ne?
Naga baka walwala sam duk kana cikin damuwa"
Yusuf yai murmushin ƙarfin hali yace "yama za'ayi ince bana farinciki da Kasancewar
ki ƙanwata, na daɗe ina miki so mai tsanani da takurawa ruhi, se yanzu na tabattar
da ashe son ne ya haɗemin dana 'yan uwantaka, tsabar farinciki ne yasa na rasa ta
ina zan nuna tsantsan farinciki danake ciki, ashe tun tuni da' yar uwata nake tare,
shiyasa nake jin zan iya yin komai ko in bada komai nawa, gurin baki kariya koda
kuwa raina ne, nayi farinciki da haka, kuma gefe guda ina jimanta irin wahalar da
muka sha, da mamakin cin amanar yadda na mutanen wannan zamani, dukda abunda
akayimin be kai na Daddy ba, Amma Widad ko a tatsuniya akacemin Abbas zemin haka
bazan yadda ba, ashe haɗa baki akayi dashi akamin gadar zare, yazo ya lallaɓani aka
bani aiki, shi yayi dan cutar dani, ashe hakan Silar taradda farinciki nane, kai
Widad mutane abun tsorone, banga laifin AƘIDARKI ba baby, kaso mutum dan Allah
shikuma bashi da maƙiyi kamarka"
Ya ƙarasa maganar muryarsa na rawa, alamun karaya Widad ta rungume Yusuf tana shafa
sumar kansa ta sigar rarrashi tace "tabbas haɗuwarmu da wasu mutanen a rayuwarmu
darasi yake bamu, da mutane sunyiwa AƘIDATA mummunara fahimta, amma ba haka kurum
nake abubuwan da nake ba a baya, dukda daga baya na gane a AƘIDATA akwai wadda bata
kamaceni ba, amma a hankali duniya ta ladabtar dani ns gane rayuwa sosai, sannan
nayi farinciki na kasancewarka ɗaya daga ahalina managarcin mutum me matuƙar
kamala, ina sonka Yusuf "
Yusuf ya kalleta dukda gefen idonsa hawayene ke zuba, amma yai murmushi har seda
haƙoransa suka fito yace " waye ya koya miki yadda ake faɗar sunana? In kikace
Yoseef yafimin daɗi, saboda nasan ba wanda yake faɗar sunana a haka se Gimbiyar
Yusuf "
Widad tai murmushi tana sake rungume Yusuf a jikinta, Widad tace "Alhaji Yoseef
Nasir Daula, seka dena bearing wancan sunan, tunda har gida akazo ama kashedi akan
ka dena amfani da sunan saboda tsabar jaraba irin ta mutanen nan"
Yusuf yace "am sorry to say, Baby bazan iya dena amfani da sunan Bashir maitama ba,
saboda shina saniba ubana, shina buɗe ido dashi yana ɗawainiya dani"
Yace "Amma ni gaskiya, wannan kuɗin da ake shirin bani, nifa ban san yadda zanyi
dasu ba"
Yusuf yai shiru yana zancen zuci, Widad tace "mu bar maganar nan, zamuje ƙauye a
satin nan yaushe zamu tare ne, nina gaji gaskiya"
"to mara kunya, kije ki tambayi Daddy, wace tarewa kike nema, banda wannan tarewar
na cikinki"
Sosai Yusuf ya bata dariya tace "ai shikenan, bama semun wani tare ba, ɗaki ɗaya
zamu koma kwana, ai akwai ɗakuna dayawa a gidan nan"
Yusuf yace "Allah ya baki haƙuri, kiyi haƙuri mu koma kano kinji ƙanwata"
Tai murmushi tace "naji, tashi muci Abinci ko?"
Nuray kama tunda ta gano Khalil sonta yake, take jin tausayinsa, be taɓa gayamata
ba, amma idan tana tuna kyautatawarsa, da kulawarsa a gareta, tabbas idan ba so
babu abunda ze kawo hakan.
Tana kitchen tana aikace aikace tana tunanin yai sallama ya shigo, ta amsa masa
tana binsa da kallo.
Tai murmushi tace "kwaɗayi nake ji, ma rasa me zanci na tsiri yin cake"
Ya ɗauka yana ci yana faɗin, "kai Komai naki na dabanne, ban taɓa cin Abinci me
daɗin wannan ba fa, Allah ya bani mace tagari wadda ta iya girki kamarki"
Nurat ta kasa ce masa komai se kallonsa kawai da take yi, jiki a sanyaye yace
"lafiya kuwa?"
"to ai gani nai kamar jikinka ba ƙwari fa, ko akwai matsala ne?"
Ta girgiza masa kai alamar aa' "ko Yusuf ɗinne dai ya kuma yi miki wani abu?"
"Khalil, Ka sani an tabattar da Widad matarsa ce, aure sukayi Dan harda tsohon ciki
ma, kasan a ynzu na shiga sahun maƙiyan Widad, nasan bata ƙaunata yanzu haka, Yusuf
yana son matarsa sosai cigaba da musu shisshigi a rayuwar su ze iya basu matsala,
musamman da Ummansa da take son lallai ya aureni, Yusuf mutum ne me nagarta da
haƙuri ba dan Widad ba ze iya aurena, amma ga laifin da mahaifina yai musu, ga
Widad nasan dukda a baya bata soyayya amma yanzu na fuskanci akan Yusuf ba abunda
bazata iya ba, gara in ƙyalesu bana som zama silar rasa farincikin kowa a rayuwa,
ina wa Widad murnar samin nagartaccen abokin rayuwa, nima Allah ya bani miji nagari
wanda ze soni, me kyawawan halaye kamar Yusuf "
Ta ƙarasa maganar, tana zubar da hawaye sosai, Khalil ya ƙarasa gabanat, wani irin
matsanancin tausayinta ya kama shi, he feels her pain, yasan yadda raɗaɗin son maso
wani yake, Nurat ta so Yusuf sosai yana zuwa inda take tsaye, ta faɗa jikinsa tana
kuka, ya rungumeta a jikinsa yana rarrashinta, da alama abun yana cim zuciyarta
bata samu damar yin kukan bane ba.
"kiyi haƙuri, Allah ze miki musaya mafi Alkhairi, kin san da yawa a rayuwa, mu
kanso abunda ba alkhairi bane a rayuwarmu, Allah ya zaɓa miki mafi Alkhairi
Ƙanwata"
Ta dinga jinjina masa kai, amma ta kasa magana, saitin kunneta yace "koda kuwa
nine, idan Allah ya musanya miki kina so?"
Tashi tayi daga jikinsa ta goge hawauenta tace "cake ɗina ze ƙone, bani guri in
duba"
Tai maganar tana basar da abunda yace kamar bata ji ba, ya dinga bimta da kallo
yana tunanin she didn't accept his proposals.
Su Widad sun shirya tsaf, domin zuwa ƙauye, Widad se murna take, Amma daga baya se
jikinta yai sanyi tace "Daddy, wai ina Saleh ne? Zamuje garin su gurin 'yan uwansa,
me zamuce musu idan suka tambayemu shi?"
Daula yace "ai kema kin san Daula baya manta alkhairi, Saleh yayi sintiri a
Asibiti saboda ni, kuma shiyafara gayamin kuna hannunsa, sannan kunyi Aure, saboda
alkhairin da yayi muku nakejin zan iya yafe masa, na karɓeshi a hannun 'yan sanda,
an kai shi Egypt saboda anma rauni da duka a hantarsa, za' a masa aiki "
Daula yace "Eh, saboda dukansa da aka dingayi a ciki ya samu matsala"
Widad tace "Allah ya bashi lafiya, amma yayi ɗawainiya damu sosai"
Yusuf ne ya fito Umma da Alhaji Ahmad suna bayansa, seda suka fara shirin shiga
motar sannan Yusuf yace "nifa Umma har yanzu banji yadda akayi kika san Alhaji
Ahmad ba?"
Daula yai murmushi yace "Budurwarsa ce ta farko tun zamanin ƙuruciya, a gidansu
akaga be shirya ba Abbanka ya aureta ya barshi'
Kunya ta kama Umma, kamar ta nitse a ƙasa dan kunya, Widad da Yusuf suka shiga
yimata dariya.
Alhaji Ahmad yace" kuma har yanzu ina so ba, amma tace min se ɗanta ya yadda, dan
haka Yusuf nidai ina so har yanzu "
Suka shiga mota suka ɗau hanyar garin Bauchi, bisa rakiyar 'yan sanda.
Tun su Alhaji Daula suna sa ran ƙarewar tafiyar, har suka zuba ido nausawa kawai
ake cikin ƙauyuka, sannan aka bar kan titi aka saki hanya aka nausa wani surƙuƙin
ƙaiye, tun daga nan Daula yake tasibihi, da mamakin azabar surƙuƙin gurin nan.
Nanam sukayi tafiya me nisa akan burji, babu kwalta ba zaka taɓa cewa zaka tarar da
gida ba, se sama da ƙasa sukeyi danma a manyan motoci suke, amma hakan be hanasu
jin jiki ba, idan aka shiga wani ramin, se Yusuf ya riƙe Widad gam saboda kar
abunda ke cikinta ya wahala, a haka suka ƙaraso ƙauyen nan.
Suka fir fito yayinda 'yan garin sukayi dandazo suna kallon motocin, yayin da wasu
suke gudu saboda ganin motar' yan sanda.
Daula ya kalli ƙauyen, ya sake kallo yace "yanzu Baby, a nan kuka rayu?"
Ita kanta Umma daba wani kuɗine da itaba, tunani take ta yadda zata yi rayuwa a
wannan ƙauyen.
Widad ta raɗawa Yusuf a kunne "Allah sarki, yau zanje inga ɗakin amarcinmu"
Tuni labari yajewa megari, ga wasu nan sunzo a jibga jibgan motoci irin na masi
sace mutane, da 'yan sanda, ya fito a ruɗe, dan baya son abunda ze tayarwa da
mutanensa hankali.
Sam be gane Yusuf ba balle Widad, Yusuf ya ƙarasa gaban sa ya zube yana gaisheshi,
seda ya tsurawa Yusuf ido sannan ya gane shi, yace "innalillahi, Malam Yusuf
kaine? Dama zan sake ganinka Yusufa?"
Widad ta ƙaraso itama tana gaida megari, yace "Allahu Akbar, Amarya 'yar gwaggonta"
Ta shiga da sallama, Hindu na zaune tana tankaɗen garin dawa, taji wani irin
ƙamshin turare ya gaauraye gidan, ta ɗaga kai zata amsa sallama tayi tozali da
Widad, aiba shiri tayi wani uban tsalle tai fatali da ƙwaryar garin, tai gurin
Widad tace "Allah yasa ba mafarki nake ba?"
Suka rungume juna suna kuka, Gwaggo ta fito da sauri jin kamar muryar Widad, aikuwa
itace ba wata ba, nan gida ya hargitse da murna da koke koke, Widad tace "ina
aminiyata abikiyar faɗana Hari"
Hansai tace "taje barka bayan layi ita da Hanne, amma yanzu zasu shigo"
Tana gama rufe bakinta, sega Hari da gudu kamar ƙaramar yarinya "wayyo Allah na,
jama'a dagaske Wudas ce? Wai Wudas ce tazo garin nan?"
Widad ta rungume Hari, Hari ta shiga kuka tace "ban taɓa zaton na saba dake haka
ba, seda kuka bar garin nan"
Umma tai sallama itama ta shigo, nan aka shimfiɗa musu tabarma, suka karɓsu hannu
bibbiyu Widad tace "Mama ga Wannan itace Umma mamanmu nida Yoseef"
Hari tace "kamar yaya kenan? Ya za'ayi ku zama uwa ɗaya? '
Widad tace " zaki fara ko? Tunda na gayamiki ki barshi a haka mana"
Hari tace "naji an barshi a hakan"
Hanne tai sallama ta shigo, ta kalli inda Widad take, ta ganta a balarabiyarta,
fatarta ta sake ja tayi kyau sosai, Kallo ɗaya Widad tayi mata ta ɗauke kai daga
kanta.
Tuni aka fara kiciniyar ɗora girki, Widad tace base an ɗora komai ba, sunabda
abinci a mota, amma ita dai idan an gama tuwo a bata zata ci.
Aka karɓo mukulli aka buɗe ɗakinsu da suka zauna, Widad cikin hawaye tace Allah
sarki ɗakin mijina, wayyo rayuwa, a lokacin da nake shan baƙar azaba a hannun
Bulama ji nake tamkar in dawo ƙauyen nan da zama in huta"
Ita kanta Umma tayi mamakin yadda suka rayu a gurin nan, megari yayiwa Su Daddy
jagora har ɗakinsu Widad, nan suka tsaya suma suna mamaki.
Hindu har ƙasa ta durƙusa ta gaishesu, Yusuf yace "Hindu amma dake zamu tafi kano
ko?"
Yace "Ameen"
Daddy ya kalli ɗakin nan nasu yace "yanzu Widad ce ta rayu a ɗakin nan? Allah me
yadda yaso sannu Yusuf nasan ka sha gwagwarmaya"
Yusuf sedai yai murmushi.
Hari yazo kusa da Widad ta zauna tace "abun mamaki, Wudas da ciki ana shan taɓara
nasan"
Widad tace "ko in kira miki Yusuf ki tambaye shi idan ina taɓarar ko ba nayi?"
Hari ta shiga halin nata na ɓare ɓaren zance, aka shiga shigo da kayan Abinci gidan
nan kamar ba gobe, wanima basu san meye ba.
Nan jikinsu ya hau rawa, suka tabattar da lallai Widad 'yaf ga tace gaba da baya.
"A' a wallahi ba tshoho bane, gashi me kyau wallahi yana kama da mijinki sosai,
dake dashi da Yusuf duk kuna kama, irin idanunku ɗaya sak"
A razane Hindu ta kalleta tace "Kamar yaya, ta yaya babanki ze auri 'yar ƙauye
kamarni, gashi babban mutum"
"Hindu ki dena duba wannan, dan Allah ki aure shi, nasan zaki kulamin dashi dan
Allah Hindu ki auri babana"
Jikin Hindu ya hau rawa, zata yi magana amma Widad tace "yi shiru, karkice komai
ina zuwa, kuma karki gayawa kowa wannan maganar"
Widad taje ɗakinsu, inda su Daddy ke zazzaune tace "Daddy, i want to talk to you"
Ba musu ya miƙe ya biyo bayan ta, ta ja shi can waje a wani soro tace "Daddy nifa
nayi maka mata a garin nan"
"Daddy, matar Aure dai nayi maka, dan Allah karka bani kunya kaji Daddy"
Yace "shikenan"
Ta shiga cikin gidan da sauri, ta tarar da Hindu a inda ta barta, jikinta a sanyaye
tace "saka hijjabinki kizo muje"
Hindu ta saka hijjabi, ta biyo bayan Widad, ta mata jagora zuwa inda Daddy yake
zaune, gaba ɗaya yaiwa Hindu wani irin kwarjini, da bata taɓa gani a gurin wani ba.
Suka ƙarasa Widad tace "Daddy, ga amaryar da nayi maka, ina fatan bazaka ƙi karɓa
ba"
Daddy ya kalli Hindj, yarinya ce ƙarama, yace "Amma daughter, naganta yarinya ce
sosai fa, kamar zaki girme mata ma"
Cikin harshen larabci Widad tace "Daddy aiba haramun bane, wallahi yarinyace tagari
me nutsuwa, zakayi alfahari da ita"
Yace "to ita kin tabatta tana sona? Karki ƙwareta dan son kai kinga na girma
dayawa"
"Daddy Hindu bazata ƙika bafa" tai magana kamar zata yi kuka.
"masha Allah, Hindu kinji rigimar da wannan matar ta tattago, ban miki tsufa ba?"
Hindu ta kasa cewa komai, se jikinta dake ta tsuma, tana rarraba ido.
Widad tace "Daddy ai mun gama magana da ita, yanzu megari zakayi wa magana, kaga se
a bada kuɗin aure ma kafin mutafi.
AMANACE!!!
Ayshercool
07063065680
12/10/21, 1:36 AM - Buhainat: LITTAFIN KUƊI NE, DAN ALLAH KI SIYA KAFIN KI KARANTA
BA DANNI BA DAN ALLAH, LITTAFI NA ƊAYA KYAUTA NE WANNAN NA SIYARWA NE
NORMAL GROUP ₦300
VIP ₦500 NE KITURA TA WANNAN ACCOUNT ƊIN
0009450228
JA'IZ BANK
AISHA ADAM
SE A TURA SHEDAR BIYA TA WANNAN LAMBAR
07063065680
(Albishir ga masoya, ma'abota bibiyar litattaafaina, dama ta samu zaku fara samun
litattaafaina na audio, akan YouTube channel ɗina me suna Cool Arewa TV
https://youtube.com/channel/UCD5vnvA5laU8ti4LLz2_QEg
Kuyi liking sannan ku danna subscribe, domin fara samun litattaafaina na audio,
nagode sosai da ƙaunar ku gareni"
168_169
Daula yace 'Widad mubi komai a sannu, ki bari muji ta bakinta, karki mata dole
mana, kuma maganar aure ai ba' a gaggawa "
Widad tace " Daddy, nasan irin zaɓen da na maka ne, ni dai ka amince kawai please "
Daula ya lura da yadda jikin Hindu keta tsuma, ko idonta bata iya ɗagawa ta kalle
shi, ta sunkuyar da kai tanata cimimiyewa a hijjabinta.
Daula yace " Hindatu, tashi ki koma gida, Widad zata sa ki auri tsoho "
Cikin hanzari Hindu ta miƙe, ta shige cikin gida tana haɗa hanya, Daula ya kalli
Widad yace "Widad, wannan haɗin naki beyi ba, kowa zega kamar an ƙwareta ne, tayi
yarinta dayawa kuma kinga ba ita tace miki tana sona ba, gashi ni na riga na fidda
rai da Aure"
Widad tace "Daddy, na zauna a garin nan na zauna dasu, nasan halin yarinyar nan,
Daddy karka duba ƙauyanci ko ƙuruciyarta, ni dai tukuicin dazakamin shine ka Auri
Hindu, sannan akawo musu cigaba a garin nan, shine zaka biyani ɗawainiyar sa sukayi
damu, dan Allah Daddyna "
Da ƙyar ya lallaɓa Widad ta tafi, ta koma gurin Alhaji Ahmad da Yusuf ta dinga musu
magiya akan lallai su saka baki, Daddynta ya auri Hindu, Alhaji Ahmad yace "to muyi
musaay, kice mijinki ya bani ummansa nima"
Widad tai dariya tace "ka samu, nidai fatana Daddy ya amince da Auren Hindu,
sonake kafin mutafi ya bada kuɗin Aurenta"
Umma tace "Widad, ba'a gaggawa a harkar Aure, karki takuramasa ko ita yarinyar ki
takura ta fa"
Yusuf yace "Umma Hindu bata da matsala, and she deserves to marry a descent person
like him, idan harya yarda ya aureta ze sha biyayya"
Widad tace "Yoseef, dan Allah zomuje ka gayawa Megari, bana son Daddy yayi missing
wannan opportunity ɗin"
Daula yai shiru yana tunanin maganar da Widad tazo masa da ita, yadda yaga suna nan
nan da su Widad, da yadda suka sake dasu, suma hira ama wasa ana dariya, da yadda
mutane keta shiga suna fita a gidan, ya tabattar masa da cewa sun riƙe su Yusuf da
Amana, dan haka duk wanda ya shigo gidan seya fita da kuɗi ko Abinci, Daula ya
dinga basu kyautar kuɗi da Abinci, da wannan ya shigo se Widad tace Daddy ga wane a
bashi kaza, ko kuma ai masa kyautar kaza.
Widad sun sha hira da Gwaggo, seda aka tuƙa tuwon nan taci, suna ta faɗa ita Hari,
Hari tace "Ohh ni Hari, wai Wudas ce sa ciki, ranar haihuwa akwai kallo"
Umma sunyi hira sosai da Gwaggo, ta dinga bata labarin yanayin zaman da suka yi
dasu Yusuf a gidan, Hanne kam ta kasa yadda ace wannan ne mahaifin Widad, iya
motocin da suka cika ƙofar gidansu ma 'yan rakiya kawai abun kallone, banda rakiyar
motar' yan sanda, wai ashe dagaske dai Daula ne baban Widad, lallai yaci sunansa
Daula.
Ɗaliban Widad suka dinga zarya suma, suma zuwa gaishe ta da ɗaliban Yusuf,
magidantan da yai ta koyarwa, sedai dukda wannan tarin kaɓakin kayan Abincin da aka
rarrabawa 'yan ƙauyen, wannan yazo ya bawa Widad kyautar kuka, wannan ya kawo
tsintsiya, wannan ya kawo Nono, ƙwan zabi zuma, haka suka dinga kawo musu wai suyi
tsaraba, Daddy yai farinciki da karamcin mutanen garin, da yadda suka riƙe'
ya'yansa suka zauna lafiya, gefe guda kuma ya tausaya musu yadda suke rayuwa ba
makaranta, ba wutar lantarki ba kwalta bare Asibiti.
Kafin su bar garin, Daddy ya sanar da me gari cewa za'azo a gina musu makaranta ta
boko da islamiyya a saka gwamnati ta kawo musu malamai, Widad kuma tace zata gina
musu Asibiti, a kawo musu ma'aikatan lafiya, Daddy yace "Alhaji Yusuf baka yi
magana ba"
Yusuf yai murmushi yace "Aini tunda aka musu makaranta da Asibiti, an gama min
komai, fatana kuma ai musu boreholes na ruwan sha, saboda babu ruwa a garin nan, a
saka gwamnati ta samar musu da wutar lantarki, saboda Asibiti baze yuwu babu wuta
ba.
Nan jama'ar suka dinga murna suna Allah ya Sanya alkhairi, suna saka musu albarka.
Hindu kam ta ƙuke a ɗaki, tana tunanin abunda Widad ke shirin yi, banda abun Widad
ina ita ina wannan hamshaƙin attajiri, ɗan gayu me ilimi ga kyau da dukiya, ita
kuwa ga ƙauyanci da rashin wayewa, amma ta dage seta aure shi, ita gani take kawai
ze aureta ne saboda 'yarsa, amma tabbas ba sa' ar Aurensa bace.
Gaban Hindu ya faɗi, kenan dagaske dai ta tabatta Widad za tayiwa Babanta Auren
dole da' yar ƙauye?
Hanne kuwa gigicewa tayi, dan a ganinta tafi Hindu komai, dan meyasa ba'ace itaba
se wata Hindu, Hindun daba wani kyaune da ita ba ga baƙin jimi, amma ace zata auri
attajiri haka.
Da zasu tafi Widad ji tayi kamar karsu tafi, dan sosai takejin kewa da ƙaunar
mutanen garin, saboda karamcinsu da girmamawa, Ta shiga ɗakin Gwaggo ta sami Hindu
a ƙarshen gado tayi shiru tana tunani.
Widad tace "Hindu, karki ɗaga hankalin ki, babana bashi da matsala ko damuwa,
mutumin kirki ne zaku zauna lafiya ƙalau dashi, sannan an saka wata biyu, saboda
kafin ɗaurin Aure a kawo muku cigaba garin nan, saboda manyan mutane ne zasu garin
nan, munyi magana za'a aiko da mota tun saura sati biyu biki a ɗauke ki a kaimin ke
can kano, mu fara shirye shirye "
Hindu kawai jinjina mata kai tayi, daga nan suka yi sallama suka tafi, a hanya
sunata jinjina karamci da mutuntawa na wannan al'ummar gari.
Gaba ɗaya ƙauyen nan ya ɗauka, Daula ze auri Hindu, ga kuma kaɓakin arzikin da aka
sauke musj, sunata rawa da murna ga alƙawarurrukan da aka musu na kawo musu cigaba
a garin.
Su Widad kuwa garin kanon dabo suka wuce kai tsaye, suka sauka a farmhouse, Bayan
sun huta Alhaji Ahmad ya wuce gidansa, Umma tace ba zata zauna a nan gidan ba,
gidanta zata tafi, shi kuma Yusuf nauyi yake ji, koba komai Daddy sirikinsa ne, ace
suna gida ɗaya su kwana ɗaki ɗaya da Widad, haka ya basar Widad kuma ta dage se
Umma ta kwana a gidan ba zata tafi can gidanta ba, da ƙyar Umma ta yadda ta amince.
Wasa2 Seda suka kwana biyu da dawowa, amma suna farmhouse tare da Umma, kullum se
Alhaji Ahmad yazo, Umma ta takura akan cewa lallai seta bar gidan, dan ita gaba
ɗaya jinta take a takure.
Daddy yace zasu rakata gida, kafin nan ze kaisu gidan daya saiwa su Yusuf, kuma
ranar nan da sati biyu Yusuf ze tafi Lagos, inda babban kamfanin shige da ficen
ƙarafa yake, wanda yake mallakinsane, shi dai Yusuf jin abun yake banbarakwai,
kamar bashi ba.
Koda suka fita seda suka fara zuwa ainihin gidansu da suke zaune, suna zuwa
ma'aikatan nan suka dinga rige rige zuwa gurin Daula, ganin ya bayyana ashe yana
raye, sedai gidan kamar kango, ba shige da ficen mutane, ba manyan motocim dake
harabar gidan, abun duk se a hankali.
Nan su Murtalah, Nura da sauran ma'aikatan gidan suka dinga tururuwar zuwa gaban
Daula, masu kuka nayi masu murna nayi, ai nan da nan labarin bayyanar Daula ya
karaɗa gari, da jaridu Widad kam cikin gidan ta wuce, tana ganin gidan ya koma
kamar wani kango.
Nura yace "to yanzu dai, 'yan sanda sunzo sun kama Ramlah jiya, se Amal ce kawai a
cikin gidan"
Daddy ya jinjina kai, ya shiga cikin gidan, yana shiga ya tarar Widad ta wuce
ɗakinta, Amal tana zaune a falon tana ta kuka kamar an mata mutuwa, ta rame sosai
kamar wadda aka zuƙewa jini, tayi baƙi sosai duk ta canza kamanni gwanin ban
tausayi.
Maimakon Daddy yaji haushinta sema wani tausayinta daya kama shi, kafin yai magana
Widad ta fito, Umma tace "Yusuf wannan kuma wacece?"
Yusuf yace "Umma wannan itace Amal, 'yar matar gidan nan ce"
Widad ta kalli Amal tace "Malama You have to leave this house, within some
minutes, azzalumai kawai marasa tsoron Allah, masu butulci"
Amal ta shiga girgiza kai tana cigaba da kuka, dan idan ta fita bata san ina zata
ba, dan bayan mamansu ta auri Daula, a dangima ba kowa take gani da gashi ba, yanzu
idan ta fita ina zata?
Ya ƙarasa gaban Amal ya durƙusa, yace "Amal ɗin Daddy, baki da lafiya ne? Kikayi
wannan ramar haka?"
Amal cikin kuka tace "Dan Allah kuyi haƙuri, kuyafemin, dan Allah, dan Allah kuyi
haƙuri"
Tai maganar tana haɗa hannayenta alamar neman afuwa 🙏
"Daddy, waiya kake wani lallaɓatane? Do you want give them another chance to finish
us?"
Daddy ya girgiza mata kai, ya sake kallon Amal yace "yanzu meke damunki kika rame
haka?"
Nan ta gaya musu yadda akayi mata fyaɗe, Alhaji Haruna ya keta mata mutunci da
abunda likita yace, a maganartata zaka fuskanci ta samu taɓin hankali.
Yusuf kansa seda tausayinta ya kama shi, duk rashin mutuncinsu, Amal ta ɗanfi
sauƙin kai, dama Ramlah tafi zaƙewa da wulaƙanci.
Daddy yace "ki kwantar da hankalinki, nasan yanzu dole zaki shiga damuwa sosai,
saboda gaba ɗaya 'yan uwanki da iyayenki suna hannu, ina fatan ze zame miki izina
akan abunda ya faru, ban miki Alƙawarin saka baki akan taimakon mahaifiyarki da
yayarki ba, saboda sun cutar dani a rayuwa, amma daga nan ko zuwa wace ƙasane, daga
naira ɗaya zuwa miliyoyi, zan kashe a nema miki lafiya, kidena kuka kiyi musu fatan
Allah ya shiryesu, sannan ki dimga musu Addu'a "
Aikuwa a hasale Widad tace " Daddy, why? Me yasa zakayi wannan hukuncin, dukda
tarin laifukan da suka aikata mana? "
Yusuf ma cikin tsawa yace " Widad, Daddy kikewa magana fa, talk to him with respect
"
" Haba Yoseef, a gabanka akace Mahaifimsu aka saka ya kashe min Ammina, yanzu meze
sa Daddy ya temake ta? Bayan yadda suka so ganin bayana, da ganin ma zama
mahaukaciya tuburan?"
Daula yace "Widad, ɗan halak baya manta alkhairi, ko bakomai ɗan uwanta yamin
wahala, yayi ɗawainiya dani a Asibiti, yamin biyayya, kuma itama ba laifi tana
girmamani, albarkacin Anwar nakeso Amal taci, ba ita tayi miki laifin ba, dan haka
kiyi haƙuri, kiyi haƙuri ba danni ba dan Allah "
Daga gidan suka wuce inda nan ne gidan da Daddy yace nasu Yusuf ne, a unguwar
lamiɗo crescent, gida ne hargida ya haɗu ya tsaru iya tsaruwa, kamar ba'a Nigeria
ba, Widad nata murna yayinda Yusuf ke jinjina abun, waishine da wannan gidan haka?
Amma Babban abunda Widad bata ji daɗinsa ba, be wuce yadda Daddy yace " wai anyi
bookin ɗin jirgi shida Yusuf a ranar zasu tafi lagos da yamma, dan canne inda
kamfanin Yusuf yake, zeje a nuna masa abubuwa tun yanzu, Widad taji haushi sosai,
dan harga Allah tana kewar mijinta sosai, kusan watanni shida ana neman na bakwai
basa tare, amma haryanzu sun kasa samun dama su kasance tare, shikansa Yusuf mazewa
yake dan yana da kunya sosai amma yana kewar matarsa sosai, Widad ce dai wani
lokacin se a hankali bata fiye jin kunya sosai ba, duna da yanayin rayuwarta.
Amal kuwa a ranar Daula yasa aka ɗauketa aka kaita Asibiti, dan a dubata a ga idan
aikin ze yuwu a nan Nigeria.
Haka Widad tana ji tana gani, da yamma su Yusuf suka tafi Lagos, ta koma gidan Umma
tai zamanta, kwana ɗaya da tafiyarsu Lagos, Daula yai hira a kafafen watsa labarai
a can Lagos, ya sake bayyana kansa, ya bayyana dukiya ta Yusuf ce, da irin wahala
da azabtarwar da Bulama yayi masa, ƙarshe yai jan hankali da nasiha me ratsa jiki,
akan mutane su lura da suwaye masoyansu na gaskiya.
Umma da Widad basu san anyi hirar ba, se gani sukai mutane na zuwa gidan, wai sunzo
yiwa Umma murna,ashe Yusuf ɗan Daula ne, babu kunya ciki hardasu Yaya ɗanllami masu
yi masa gori, Sunga Arziki ya sameshi, Widad ta dinga mamaki wato a rayuwa idan
kaga ana nan nan da kai, wata damace Allah ya baka, ko kuma kuɗine da kai.
Garin su Hindu kuwa, tuni aka kai kayan aiki dan cika alƙawarin da Daddy ya ɗauka,
da yake akwai kuɗi, nan da nan aka fara aiki, kuma yace a ɗau leburori a garin dan
su samu wani abu suma, gefe guda sunata shiri suma murna akan Hindu zata Auri
Daula, yayin da ita Hindu gaba ɗaya yake mata kwarjini, take tunanin taya zatai
zaman aure dashi, mutumin daya girmeta nesa ba kusa ba, yama haifeta? "
Nurat kam ta riga ta haƙura da batun Yusuf, tayi murna sosai jin labarin ashe yana
da alƙa da Widad, itama in akabi nasaba ɗan uwantane.
Ta samu Khalil a falo tace masa" brother, kaga wani iko na Allah ko? Duk wannan
wahalar ashe dai ɗan uwan Widad ne Yusuf, kuma akan dukiyarsa aketa wannan abun "
Khalil yace " hakane kam, Allah babu yadda be iya ba, Sakamakon haƙuri da juriya ga
abunda Allah yayi masa, haƙuri me tadda rabo, kema Allah ya baki miji nagari wanda
yake sonki"
Ta jinjina masa kai tana murmushi, "yanzu kin yarda kima sona zaki aureni Nur?"
Ta jinjina masa kai alamar eh, murmushi ya shiga yi yana faɗin Alhamdilillah,
Alhaji na dawowa zan sanar masa "
" kar inje wani yayi min ba daidai ba, gara in hanzarta inyi wuf dake"
Wasa wasa, seda Yusuf sukayi Sati biyu sannan suka dawo Kano, kuma da suka dawo
ɗinma seda Daula yaje har gidansu Nurat domin yi mata ta'aziyyar mahaifiyarta,
abunda bata taɓa zaton Daula zeyi ba, tana ganinsa ta tsaya tana mamaki.
"Alhamdilillah Daddy"
Nanma Yusuf ya sake yi mata gaisuwa, Daula yace "Nurat, idan akabi nasaba ina da
alaƙa ta jini da mahaifinki, dan haka ki ɗaukeni Uba, duk abunda ya taso miki kike
buƙatarsa, ki nemeni ko menene insha Allah, zanyi iya ƙoƙarina imga na miki, am
your father now, kinji Nurat"
Seda Daula ya tsaya suka gaisa da mariƙin nata, sannan suka tafi.
Yallaɓai Suleiman kansa, seda ya samu tagomashin katafaren gida, da kuma kuɗi masu
yawa a gurin Yusuf, saboda irin jajircewa da taimakon da yayi masa.
Kwanansu Uku da dawowa suka tare shida Widad a sabon gidansu, ya samu rakiyar
abokan aikinsa gidan, Kasancewar bashi da wasu abokan kirki, Widad kamar tayi
tsalle dan murna da farinciki.
Bayan kowa ya watse, gajiya duk ta damu Yusuf, saboda hada hada da mutane, dan har
walima akayi na tariyar a event center, Daddy ya gayyato manyan abokansa, Yusuf duk
ya gaji dan be saba da hada hadar mutane haka ba, ya shiga yai wanka, lokacin tuni
Widad ta shiga ɗaya ɗakim tayi nata wankan, dan itama a gajiue take sosai, ta fito
cikin riga da wando na bacci masu jikin bargo pink, ta kashe fitilar ɗakin ta bar
dump side lamp, ta ƙaraso inda Yusuf ke zaune yana taje sumar kansa, Yusuf yace
"malama ce miki akayi na gama kika kashemin fitila?"
Tace "kai ba mace na amma se ƙaƙale, da mace ne Allah kaɗai yasan me zakayi"
Widad tace "kuma mayukana zaka dimga shafawa, na bleaching ne dai ba ruwana in ka
zama fari"
Yusuf yai dariya yace "dan dai bleaching ai ba damuwa ranki ya daɗe, ince mata
tace takemin"
Sukayi dariya tare, ta ƙaraso ta rumgumeshi ta bayansa, tana numfashi a hankali,
kwararar hawayenta yaji a Ƙirjinsa da sauri yace "lafiya kuwa Widad?"
Kasa magana tayi, ta cigaba da kukan, ya janyota gabansa yana sake tambayarta, amma
sema ƙara saugin kukan da tayi, yace "haba Babyna, mena yi miki kuma? Kodai
shagwaɓarce?"
Still bata amsa masa ba, dan haka ya jata zuwa kan katafaren gadon su, ƙato ya
zaunar da ita sannan ya zauna yace "gayamin, menene? Ko laifi nayi miki"
Rumgumeshi tayi tana kuka take faɗin "thank you very much Yoseef, thank you very
much for your love, caring the sacrifice and all you have done for me, you change
my life Yoseef, i love you"
"I love you too my wife, you also done a lot of things for me, bani da bakin godiya
se dai zuciyata taki ce mata ta"
Haka suka cigaba da gayawa jinansu kalamai masu daɗi, masu cike da nuna kewar juna,
daga nan kuma suka wula wani gurin.
🚶 🚶 🚶 🚶
Ji suke tankar lokacin suka yi aure, dan a wannan lokacin suke cin nasu amarcin a
nutse, ba inda Yusuf yake fita, kullum yana gida tare da Widad, yana bata kulawa ta
musamman.
Alhaji Ahmad ma ya nemi Auren Umman Yusuf, akasaka lokacin daidai lokacin bikin
Daula, ayi biki gaba ɗaya
Rana bata ƙarya sedai uwar ɗiya taji kunya, tun saura sati biyu biki, Widad taje
ƙauye ta ɗakko Hindu daga ƙauye zuwa kano domin shirin biki sosai, motar da aka
kawo Hindu Tint glass ne da ita, dan haka bata samu damar ƙarewa garin kallo ba,
seda suka shiga gidan Widad, data fito daga motar cak ta tsaya tana ƙarewa harabar
gidan kawai kallo.
Widad ce ta fito tana murmushi ta ƙaraso tana faɗin "oyoyo amaryar mu, sannu da
zuwa Anty Hindu"
Widad taja Hindu zuwa cikin gidan, yayin da Hindu ta kasa magana saboda tsantsar
mamaki, ace a duniya akwai irin wannan gidan lallai jin daɗi yana birni, suna shiga
falon Widad taji wani irin sanyi ya ratsata wanda babu shi a waje, tun Hindu na
mamaki harta zubawa sarautar Allah ido, dan abun ya shallake hankalinta.
Widad ta dinga koyamata yadda ake amfani da wasu abubuwan, ta dinga kaita gurin
gyaran jiki kafin lokacin biki.
Hindu tayi shar da ita, tayi kyau sosai sedai tana jin kunyar Widad sosai, saura
kwana huɗu biki sannan Widad ta kira Daddynta a waya tace masa yazo ga amaryarsa a
gidan ta.
Ba musu kuwa sega Daddyn a gidan, Hindu na jinjina rashin girman kai na mutumin
nan, yana da matukar sauƙin kai da sanyin hali, dukda kuɗin da yake dashi, da kuma
shekarunsa.
Yana zaune a falo, Hindu suka fito ita da Widad tayi kyau sosai, Widad tana ja da
kyar saboda nauyin cikinta, Widad tace "Daddy ga amaryarka nan, bari in kawo muku
abin sha" ta juya ta koma ciki.
Ƙafar Hindu na rawa ta ƙarasa gaban Dula, ta tsuguna tace "ina wuni"
Daddy yace "lafiya ƙalau Hindatu, ya baƙunta? Ina fatan dai Widad bata takuramiki?"
Hindu ta girgiza kai alamar a'a, yace "to in dai tana matsa miki, ki gayamin nida
ita ne" yai maganar yana murmushi ƙarshe shikaɗai yai taɗin ya gama bata iya cewa
komai, saboda kunya da kwarjinin sa.
Lokacin biki Aka aika da motoci ƙauyen su Hindu, aka kwaso su zuwa birni dan bikin
'yarsu, a tsohon gidansu Widad aka sauke su, sedai Hari tafi kowa rikicewa da ganin
gidan nan, tun daga gate motocin dake harabar gidan suka rikita ta, suka shiga
katafaren falon gidan, Hari ta rasa a ina zata zauna, tace "ohh ni Hari, yanzu
wannan ko' a aljanna ka samu wannan ai ka more"
Hansai tace "ke Hari, ance talaka a gidan aljanna shine gidansa kamar girman
duniya, kike cewa ki samu kamar wannan"
"Ke bari Hansai, ke kina tunanin kin aikata abin da da zaki samu wannan ne? Ai ni
indai irin wannan ne yaseen ya isheni, kai jama'a kun lura da wani abun mamaki
kuwa? Waje lafiya ƙalau amma ɗakin nan hunturu Aradu, sanyi ake sosai a cikin ɗaki
ikon Allah"
Widad tasa aka dinga sauke musu Abinci, Abinci kala kala Gwaggo tace "Amarya wai
ina 'yar tawa ne?"
Gwaggo tai murmushi, Widad tace "zasu taho tare da Daddy, da kuma Umma"
Gida ya ɗau harama, aka kawo Hindu, suka dinga zuba guɗa, gaba ɗaya Hindu ta canza
a sati biyun nan, tayi kyau sosai kamar ba ita ba.
Aka dinga ɗorawa ana sauke musu Abinci, aka ɗakko masu aiki da an ɓata guri su
gyara, Da Yamma aka ɗauki Hindu aka tafi reception, na Daddy da abokansa da kuma
Ahmad, dama umma cewa tayi ba zata ba.
Hanne kam ji take kamar tayi kuka, tafi Hindu kyau da haske amma zata auri wannan
haɗaɗɗen mutum a birni, amma ita zata auri ɗan ƙauye, tunda suka zo Widad ko kallon
inda Hanne take ba tayi balle tayi mata magana.
Washegari juma'a, aka ɗaura Auren Umma, da kuma na Hindu da Daula, anyi shagali
sosai a gidan nan, dukda ba wani gagarumin taro suka yi ba, amma anci an sha sosai
kowa yasan anyi biki, akaita yiwa Hindu Nasiha, akam haƙuri da tsoron Allah, Widad
tace Gwaggo, da Hari suzo a raka Hindu gidan ta "
Hari tace" au wai dama nan ba'a gidanta muke ba? "
" Gidan Amaryar za'a sauke ku? Sannu Hajiya Hari me taɓargaza"
Haka suka cigaba da faɗansu da suka saba ita da Hari, Farm House aka sake gyarawa,
aka canza furnitures wanda ya tattaka gidan da aka sauki su Hari, Hari se salati
take da salallami wai "Nidai Hindu, idan ana neman 'yar wanke wanke dan Allah
zanyi"
Tun Widad na biyewa ƙauyancin Hari harta ƙyaleta, saboda abun nata bana ƙare bane.
Bayan sun rakata, sun mata addu'a Gwaggo tace "to Hindu, mu daga nan gobe in Allah
ya kaimu zamu wuce gida, ki zauna lafiya da mijinki da kowa ma, nasan dai baki da
matsala amma dai ayi haƙuri"
Hindu ta rirriƙe Gwaggo tana kuka, da ƙyar ta cikata suka tafi, suna tafiya tsoro
ya cika Hindu, saboda ita girman gidan ma abun tsorone, gashi tana jiyo kukan
dabbobi kaɗan kaɗan a falon, tana cikin zare idone sega Daula ya shigo da
abokansa.
Ta cukuikuye a cikin lifaya taƙi ɗago kanta balle ta kalli wanima, nan suka musu
fatan Alkhairi sannan suka tafi.
Ayshercool
07063065680
12/22/21, 11:07 PM - Buhainat: LITTAFIN KUƊI NE, DAN ALLAH KI SIYA KAFIN KI KARANTA
BA DANNI BA DAN ALLAH, LITTAFI NA ƊAYA KYAUTA NE WANNAN NA SIYARWA NE
NORMAL GROUP ₦300
VIP ₦500 NE KITURA TA WANNAN ACCOUNT ƊIN
0009450228
JA'IZ BANK
AISHA ADAM
SE A TURA SHEDAR BIYA TA WANNAN LAMBAR
07063065680
(Albishir ga masoya, ma'abota bibiyar litattaafaina, dama ta samu zaku fara samun
litattaafaina na audio, akan YouTube channel ɗina me suna Cool Arewa TV
https://youtube.com/channel/UCD5vnvA5laU8ti4LLz2_QEg
Kuyi liking sannan ku danna subscribe, domin fara samun litattaafaina na audio,
nagode sosai da ƙaunar ku gareni"
170
Ta ɗago a hankali ta kalleshi, sannan ta miƙe tana waige waige, ya miƙe yai gaba
tana binsa a baya, wani gurin seta tsaya kallo, seta ɗago taga ya tsaya jiranta
setai maza ta taho, ya dinga ratsawa da ita faluka, wai nan duk dan zaman mutum
ɗaya akayi shi, suka zo ƙafar bene ya fara hawa tana binsa, sedai ta zame ta faɗi,
saboda matattakalr benen kanta wata iri take ganinta, ga ƙananan fitilu a jiki,
gata kamar ta glass ta tsaya kallo shine ta faɗi, a ɗan gigice ya waigo yna faɗin
"subhanallah, garin yaya? Kodai ɗaukarki zanyi ne?"
Ta miƙa masa hannu, ya riƙe hannunsa kamar bana namiji ba saboda laushi.
Haka suka ƙarasa saman bene, cikin katafaren falonsa, ji tayi sanyin data keji ya
ƙaru, hartana nema ta fara rawar sanyi, yaje ya rage AC suka shiga bedroom, ai a
jikin ƙofa ta tsaya tana kallon ikon Allah, lallai gaskiyar Saleh, da yace ko za'a
saida duk kadarar da 'yan ƙauyensu suka mallaka baza su siyi ko da motar hawan
Widad ba, balle wannan uban gidaje haka.
Ya bata gurin zama, ta zauna already kaji da kayan shaye2 suna ɗakin da plate da
komai, amma juyin duniya Hindu taƙi ci, ba yadda beyi da ita ba, amma taƙi ci, se
ƙyaleta yayi, sukayi alwala sukayi salla, bisa ga koyi ga sunnar ma'aiki salallahu
alaihi wassalam, tare da yin addu'oi, ya miƙe yace mata ga gado cam taje ta kwanta,
shi kansa gadon abun kallo ne, lallai Su Widad sun tara abun duniya.
Shima da ƙyar ta hau ta kwanta, ta dunƙule a guri ɗaya, ya ɗakko ƙaton bargo ya
lulluɓa mata, ya cire babbar rigarsa taga ya sake tada salla, sannan hankalinta ya
kwanta ta shiga baccin ta.
"tsoro nakeji"
Yai murmushi yace "aiba abunda ze sameki, ki rage yawan tsoro dan wataran ke kaɗai
zaki kwana a gidan nan, ki kwanta kiyi addu'a, ba abin da ze sameki"
Sedai a yau ɗinne dai Hindu ta zama cikakkiyar matar aure, dukda tsoro da razanin
data tsinci kanta a ciki.
Su Hari kuwa haka suka koma ƙauye, suna zuzuta haɗuwar gidajen da suka je, Abinci
kam wannan duk azabar cin mugunta da suka yi seda suka barshi, akayi musu rakiya da
sha tara ta arziki, yayin da ayyukan da ake musu sunyi nisa sosai, dan har an kai
musu wutar lantarki ma.
Washegari Widad ta aika direba da Abinci ya kai gidansu, sedai ita amaryar ce taƙi
sakin jiki sam, lokaci lokaci se Daula ya kalleta yayi murmushi, yarinya ce sosai
sedai akwai kunya sosai.
Yace "ga Abinci Widad ta aiko, kizo kici ko in kirata in gayamata kinƙi cin komai"
Ta sakko ta zauna, ya zuba abincin a plate, ya haɗa mata da tea ya bata, sedai
kunyar ci take a gabansa, ta ɗan dinga cakala, ya karɓi plate ɗin, ya ɗebo a spoon
ya kai bakin ta, kunya takeji sosai, ta sunkuyar da kai yace "haka zamuyi dake? In
gayamata kina gaddama ko?"
Abun har mamaki yake bata, babban mutum haka amma ya zauna yana lallaɓata, seda
taci ta ƙoshi ya jata zuwa wani ɗaki ya nuna mata kayan lefenta.
Umman Yusuf, kwana uku da ɗaurin Aure ta tare a babban birnin tarayya, Widad taso
zuwa sedai tana daf da shiga watan haihuwarta, dan haka akace ta haƙura.
Bulama kuma tuni aka shiga zaman kotu, aka dinga shari'a ana warware duk wata
ƙulalliya da makirci daya aikata, laifukan nasa da yawa danshi ƙarshe se hukuncin
rai da rai aka masa, sauran kuma daga me shekaru Ashirin da wani abu seme talatin,
Hajiya Halima kuma shekaru Ashirin da takwas itama, Ramlah kuwa hauka ta dingayi
tuburan saboda azabar shaye2, ƙarshe se gidan mahaukata aka maida ita.
Bulama kuma ya dinga larura, ciwo bayan na ƙanjamau ya din rashin lafiya, aka kai
shi Asibitin gidan yari ashe cancer ce ta kama masa hanji zuwa duburarsa, ga kotu
dukata ƙwace kadsrorinsa ta mayarwa da Daula, bashi da komai ba shi da kuɗin daza'a
masa aiki, ƙarshe haka gurin bayan gidansa ya dinga tsutsa, ga wani irin wari
yanayi, shima Fahad ya samu shekaru sha biyu a gidan yari, gashi ga ubansa Alhaji
Musa kuwa shima rai da rai ne hukuncinsa, saboda hadda laifin kashe matarsa, ga
sugar ya fito masa a ƙafa, shima ƙafa ta dinga ruɓewa kamar bata ɗan Adam ba.
A hankali Hindu take ɗan sakin jiki da Daula, babban abunda yake burgeshi da ita
shine, tsananin biyayya kamar zata shige cikinsa, ko magana yake mata kanta a ƙasa,
wanda rabonsa da samun farinciki tunda Huda ta rasu.
Satinta biyu yasa ta a makaranta, ya ɗaukar mata me zuwa gida yai mata lesson, na
ilimin addini dana zamani, kuma gata da saurin ganewa.
Yanzuma yana zaune ta ɗora kanta akan cinyar sa, yana nuna mata hotunan maman Widad
daya ɗauka a wayarsa, Hindu ta zuba musu ido tace "masha Allah, tana da kyau sosai
gata kamarta ɗaya da Widad"
Sam bata nuna masa kishi ba, sema addu'a data dinga yi mata.
Daula ya bata wani littafin turanci, yace ta karanta yaji, aikuwa ta dinga karanta
masa, gashi makarantar da yasa ta, malaman su turawa ne, tana yi yana tafa mata
yana murmushi.
Jin sallamar su Widad a falon, yasa cikin hanzari ta tashi daga kan cinyar Daula,
tana neman ɗankwali, wai kar Widad taga kamar ta raina shi.
Widad tai murmushi tace "kekam Allah ya shiryeki, ni idan nice ba kunyarki zanji
ba, mijin nakima da yake tsoho"
Hindu ta duƙunƙune fuska tana jin kunya.
Yusuf dai sedai ya kallesu yayi murmushi, sun daɗe a gidan se bayan goma sannan
suka tafi gida.
A satin Saleh ya dawo, an masa aiki ya warke tsaf dashi, yayi murna da jin Daula ya
Auri Hindu, shima an masa halacci sosai, sannan Daula ya canza masa aiki, aka maida
shi Lagos.
Amal ma a nan Nigeria aka mata aiki, sedai taji sauƙi sosai anata ƙoƙari karta rasa
hankalinta, likitan da yayi mata aiki ya nuna yana sonta ze Aure ta, Daula be ɓoye
masa ba ya gaya masa komai game da Amal yace "Amma itama 'ya tace, idan kasan zaka
aure ta ka wulaƙantata ka ƙyalemin' yata"
Daula ya shige gaba ya karɓi kuɗin Aurenta, sedai ita tana Asibiti har yanzu.
Wataran da Safe, Hindu ta tashi daga bacci, sega kiran Widad, ta ɗaga wayar tana
cewa "Maman biyu kin haihune?"
Widad tace "kedai bari, ina nan ina ja, ima wannan dattijon yake? Zanyi magana da
shi"
Widad ta dinga dariya tace" lallai Hindu, Allah ya baki haƙuri yana ina? "
"idan ya tashi kice masa, zan tafi Asibiti na fara jin ciwo, yayi min addu'a zanje
inji abunda zasu ce, zan iya haihuwa ko kuma aikin za'ayi"
Jikiua sanyaye Hindu tace "insha Allah zaki haihu lafiya, ki kwantar da hankalinki"
Hindu ta ajiye wayar tai shiru, Daula ya tashi zaune yana cewa matar dattijo ha
dai.?
Kallonsa tai tayi murmushi tace "lafiya, Widad ce tace zata Asibiti a duba, idan
zata iya haihuwa ko kuma aiki za' a mata"
Da sauri ya karɓi wayar, ya sake kira Yusuf ya ɗaga yace "Daddy mina Asibiti, daga
zuwanmu suka riƙe ta sukace haihuwa zata yi"
Ya gayamasa, aikuwa anan da nan suka shirya shida Hindu suka tafi Asibitin.
Ansha daru da Widad kafin ta haihu, Allah ya temake ta ta haihu da kanta, sedai
Yusuf ya sha kira sosai da Daddy.
Aka fito aka miƙo musu, santalelen jariri me kama da Yusuf sak, Daula ya karɓi
Jaririn yana faɗin masha Allah, Alhamdilillah.
Nan ya shiga bige bigen waya, yana sanar da haihuwar ta Widad, nan da nan aka cika
Asibitin 'yan barka, se bayan awanni huɗu sannan aka sallameta, suka tafi gida.
Daddy ya rasa inda ze saka ransa da murna, a ranar Umma ta dawo kano, Umma kamar
ita akayiwa haihuwar, ta dinga murna tana farinciki ta ɗau jika.
Saura kwana biyu Suna su Hari suka zo daga ƙauye, da abun arzikinsu, megari yabada
raguna biyu manya yace a yankawa jaririn nan, Yusuf yai masa huɗuba da Muhammad
Bashir sunan mariƙinsa, anyi shagali sosai a sunan nan, jariri ya samu kyaututtuka
daban daban daga gurin mutane.
Ana zaune a falon Widad, bayan an dawo daga event ɗin da akayi sunan, ba zato ba
tsammani Widad tace "wai yaushe ne bikin Hanne"
Hari tace "to ai mijin natane har ynzu be shirya ba, lega yake tafiya neman kuɗi,
amma dai abun dai duk se a hankali ba wata Ƙwaƙwaƙwarar sana'a da yake yi"
Widad tace "aiga 'yar uwatta nan Hindu, ta tambayar mata mijinta a sama masa abunyi
shima"
Hindu ta kalli Widad, dan ita harga Allah bata iya tambayar Daula komai, to mema
zata tambayeshi bayan komai ya ajiye mata.
Hindu tayi fuska ba tace komai ba, da daddare Daddy da kansa yaje ya ɗakko Hindu,
bayan sunje gida har sun kwanta yace "Hindatu Widad tacemin zakiyi magana dani ko?"
Hindu ta girgiza kai tace "A'a"
"Bafa nice ba, cewa tai wai ince maka a samawa wanda ze auri Hanne aiki"
Yai murmushi yace 'ta gayamin, ina son ji daga bakinki ne, daga yau kome kike
buƙata kowa kike so ayiwa alfarma ki faɗa kanki tsaye zan masa, ance ya iya tuƙin
mota, zamu bashi jan manyan motocinmu, sannan zan basu gida a nan garin, itama ta
dawo ta zauna a nan ta shiga makaranta "
Hindu harda kukan murna, ta durƙusa har ƙasa tana masa godiya, ya girgiza kai yace"
meye abun damuwa haka kuma? Karki damu kinji"
Haka rayuwa ta cigaba da tafiya, lokaci ɗaya akayi bikin Nurat da kuma Amal, kuma
duk Daulane yayi musu walicci, da kayan ɗaki da manyan kyautuka ga kowaccensu.
Muhammad Bashir wanda suke cewa Aryan yayi wayo, kusan koda yaushe Daula ya kan je
gidan Widad saboda Aryan, yana matuƙar ƙaunar Yaron.
Wataran da daddare Daula ya shigo yace "Hindatu, kisa hijjabinki zamuje muyiwa su
Widad sallama, gobe in Allah ya kaimu zamuje Abuja, daga nan zamuje Dubai ki rakani
taron kasuwanci"
Hindu tace "sekaje dani taron kasuwanci har wata ƙasar, abokanka za suyi maka
dariya ka auri 'yar ƙauye"
"Ni matata ba' yar ƙauye bace, kuma ba inda zanji shakkar shiga da ita, in nunata
ince wannan matata ce, saboda ina sonta a haka"
A daren suka tafi gidansu Widad, Hindu ta kama Aryan ta rungume tana ta masa wasa,
Widad ta karɓi Aryan ta bawa Daddy, taja Hindu ɗakinta, ta bata wata riga tace ta
gwada, Hindu ta cire hijjabinta ta gwada rigar, abun da Widad ke son gani, kuma ta
gani ciki ne a jikin Hindu.
Widad tai kamar bata gani ba, ta bata kyautar riga, a ranta tace "shine Daddy bemin
Albishir ba.
Widad tana jin daɗin yadda mahaifinta ya samu nutsuwa, Dan ita kanta ta lura da
yadda Daddy ya samu nutsuwa, da biyayya da take masa, daga ita har Daddy sunyi tsaf
dasu sunyi ƙiba, watan Aryan biyar Widad tabi Yusuf Lagos, ya kama harkar
kasuwancinsa sosai.
Watannin cikin Hindu tara ta haihu, amma seda aka mata CS aka cire yaron daga
cikinta, saboda yai girma da yawa, kwana biyu tana labor, sannan aka mata cs ɗin
aka cire yaron.
Widad kamar ta zuba ruwa a ƙasa ta sha dan murna, an yi mata ƙani, yaron kamarsa
ɗaya da Yusuf sak, kamar shiya haife shi, kuma kusan duk kamaninsu ɗayane dai da
Daula.
Daula be taɓa saka ran ze sake haihuwa ba, lokacin da aka gayamasa Hindu na da ciki
ma, shiru yayi da bakinsa yaita Addu'a, da cikin ya fara girma kuma ya dena zuwa ko
ina da ita, saboda kar itama ayi mata yadda akayiwa Huda, se yanzu data haihu
sannan kowa yaji, an taya Daula murna sosai, da kyautar da Allah ya bashi na ɗa
namiji.
Widad anyi ƙani, ga kuma ɗa da miji, murna ba kama hannun yaro, se bayan sati biyu
akayi gagarumin shagalin suna, a garin kano, har Nurat da 'yan gidsnsu sunje barka,
sedai Widad sam bata shiga sabgar Nurat sosai, seda Daddy ya zauna ya sata a gaba,
yaita mata faɗa da Nasiha, sannan take ɗan sakin jiki da ita kaɗan.
Duniya ta dawo sabuwa ga wannan ahali, suka dinga tara zuriya, dukda Daddy ya
manyanta amma seda Hindu ta haifi yara huɗu dashi, Widad ma ya haifawa Yusuf yara
uku.
Bulama kuwa bayan shekara shida a haka ya mutu a gidan yari, yana wannan tsutsar da
zubar da ruwan, babu wanda yake iya zuwa inda yake saboda wari da ɗoyi, haka aka
yasar dashi a gadon Asibiti, harya mutu babu wata cikakkiyar kulawa haka ya mutu a
wulaƙance.
Lokaci lokaci Amal ta kanje ta kaiwa mahaifiyarta ziyara a gidan yari, sannan tana
zuwa gidan masu rangwamen hankali, Ramlah ta zama mahaukaciya tuburan, se an
ɗaɗɗaureta haka zatai ta ihu tana fizgar gashin kanta, idan bayan gidane a nan za
tayi, komai a gurin take yi, ta zama mahaukaciya tuburan, abun da Hajiya Halima
taso Widad tayi, shine ya faru a kanta.
Duk wanda ya zamana da sa hannunsa a badaƙalar da Bulama yayi, seda aka masa
hukunci daidai da shi, daya mutu ma ds ƙyar aka samu masu masa jana'iza, sedai kowa
yana toshe hanci saboda yadda jikinsa ya dinga ruɓewa tun yana raye, ga kowa baya
faɗan alkhairi akansa, sedai sharrinsa da Allah wadaran.
Daula baya ƙasar lokacin daya samu labarin rasuwar Bulama, amma seda ya zubda
hawaye jin irin mutuwar da Abokin nasa yayi, tabbas da yana Nigeria dashi za'a
sallaci Bulama, ya dinga kuka yana "Allah ya jiƙanka Abubakar, Allah ya maka rahama
ya yafe maka, yasa jinyar da kayi kaffara ce, ni dai na yafe maka abubuwan da
kamin, Allah ya yafe maka"
Seda Widad taji haushin yadda Daddy ya damu saboda mutuwar Bulama.
Daula a haka ya dinga sawa ana kai kayan Abinci gidan yari, da gidan mahaukata,
Arziki ya cigaba da bunƙasa, Hindu ta zama hamshaƙiyar mace itama, Daula ya ɗau
nauyinta taita karatu na addini dana zamani.
Umma dai Allah be bata haihuwa ba, amma bata sa hakan a ranta, saboda tana da Yusuf
ga sirikata ta ɗaiketa uwa, ga yara sun haifa suna da jikoki, gashi tana zaune da
mijinta da matarsa lafiya, yaransa suna matuƙar girmama ta.
Yusuf ma suka samu kyakkyawar rayuwa, suna zaune abunsu a garin Lagos da yaransu,
ƙauyen su Hindu kuwa, banda wanda yasan ƙauyen ƙayaune a baya ba zakace shine a
yanzu ba, saboda cigaban da suka samu ta kowane fanni, bazasu taɓa mantawa dasu
Widad ba, saboda a sanadinsu ne Allah yasa suka samu wannan cigaban wanda basu samu
ba a baya.
TAMMAT BI HAMDILLAH
9/12/2021
ALHAMDILILLAH ALA KULLI HALIN, ALLAH YA NUFA NA KAMMALA WANNAN LITTAFIN NA AƘIDATA,
INA FATAN DARUSSAN DAKE CIKI ALLAH YA BAMU LADA, AKASIN HAKA UBANGIJI ALLAH YA YAFE
MANA BAKI ƊAYA.
A TARA NAN GABA KAƊAN DOMIN JIM LITTAFIN DA ZANZO MUKU DASHI, AKWAI LITATTAAFAI
JINGIM A TASKAR COOL, WASU NA KUƊI WASU NA KYAUTA, INA FATAN DUK WANDA NAZO MUKU
DASHI, ZAKU KARƁA HANNU BIYU, NAGODE SOSAI DA KULAWARKU DA KUMA ƘAUNARKU A GARENI
SANNAN INA SON JIN RA'AYOYINKU AKAN WANNAN LABARIN DA KUKA KARANTA
AYSHERCOOL
07063065680