Mojisola Adekunle-Obasanjo
Mojisola Adekunle-Obasanjo | |
---|---|
Rayuwa | |
Haihuwa | 10 ga Augusta, 1944 |
ƙasa | Najeriya |
Mutuwa | Lagos,, 4 ga Yuni, 2009 |
Sana'a | |
Sana'a | ɗan siyasa |
Mojisola Adekunle-Obasanjo (An haifeta 10 ga watan Agusta shekarar 1944 - 4 ga watan Yuni,shekarar 2009), mai ritaya ce daga cikin sojojin Najeriya da ta kafa jam'iyyar Gwagwarmayar Talakawa a Najeriya (Masses Movement of Nigeria) a shekarar 1998, daga baya ta yi takarar Shugaban kasa a karkashin jam'iyyar Masses Movement of Nigeria (MMN) a shekarar 2003 . Ta Kuma yi takara a shekarar 2007 inda ta zama yar'takara mace kaɗai acikin waɗanda aka kaɗa wa ƙuri'a a matsayinta na mace ɗaya tilo da za ayi takara a zaɓen shugaban ƙasa na shekarar 2007 .]].[1][2]
Ta kasance tsohuwar matar aure (1991-1998) ta tsohon Shugaban ƙasan Najeriya Olusegun Obasanjo.[3]
Adekunle-Obasanjo ta mutu a ranar Alhamis, 4 ga watan Yuni, shekarar 2009 a gidan 'yarta-Adetokunbo a birnin Ikoyi jihar Legas bayan gajeriyar rashin lafiya.[4][5]
Ta kasance ta bar tana da yara huɗu (4) da jikoki masu yawa.[5]
Aikin siyasa
[gyara sashe | gyara masomin]Mojisola ta yi aiki a matsayin mai aikin gidan Rediyo tare da Sojojin Najeriya saboda mafi yawan ayyukanta kafin ta yi ritaya daga aiki. A shekarar 2003, Manjo Mojisola ya tsaya takarar shugaban ƙasa a zaɓen shugaban ƙasa da na Gubernatorial. Ta samu adadin kuri'u 157,560 wanda ya yi daidai da 0.40% na ƙuri'un da aka amince da su.
Ta kuma yi takara a zaɓen Najeriya na shekarar 2007 kuma an kayar da ita.[6][7][8]
Manazarta
[gyara sashe | gyara masomin]- ↑ James Ezema. "Women in Politics: Challenges, and the Rwandan Example". Newswatch Times. Archived from the original on April 22, 2015. Retrieved April 22, 2015.
- ↑ Celestine Okafor (April 3, 2004). "We'll mobilise the masses, says Moji Obasanjo!". Vanguard media. Archived from the original on July 1, 2019. Retrieved April 22, 2014.
- ↑ Britannica (April 3, 2004). "Biography of Obasanjo!". Britannica website. Retrieved April 22, 2014.
- ↑ Godwin Mbachu (March 5, 2015). "Female Presidential Candidates: How Far can They Go?". Leadership News. Archived from the original on June 11, 2016. Retrieved April 22, 2015.
- ↑ 5.0 5.1 Cite error: Invalid
<ref>
tag; no text was provided for refs namedBiography of Obasanjo Britannica
- ↑ All Africa. "Nigeria: Moji Obasanjo Dies at 65". AllAfrica.
- ↑ Gupta, K.R (2005). Studies in World Affairs, Vol. 1 (1 ed.). India: Atlantic Publishers & Distributors (P) Ltd. p. 116. ISBN 9788126904952.
- ↑ Sahara Reporters. "Major Moji Obasanjo is Dead!-PM News, Lagos". Sahara Reporters. Retrieved 11 March 2019.
Haɗin waje
[gyara sashe | gyara masomin]