Mazhab
Mazhab | |
---|---|
school of thought (en) | |
Bayanai | |
Ƙaramin ɓangare na | Fiƙihu |
Bangare na | Shari'a |
Amfani | bauta a musulunci |
Addini | Musulunci da Sufiyya |
Muhimmin darasi | Sunnah da Ahkam (en) |
Commemorates (en) | al-Hakam (en) da al-Adl (en) |
Ma'aikaci | ummah (en) |
Alaƙanta da | al-milla (en) da ad-dīn (en) |
Mazhab, Madhhab ko Mazhaba مذهب,itace hanyar karantarwa ko tafarkin da Malaman farko na addinin musulunci suka koyar kamar yadda suka koya daga Sahabban Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata agare shi, ko ta hannun tabi'ai wadanda kuma suka koya daga Sahabbai, yarda da inganci da sahihancin karatunsu wadanda duk asalinsu daga Manzon Allah,har zuwa Sahabbansa har ya iso zuwa ga Malamai,shiyasa duk al'ummar musulmai tun a waccan lokaci har izuwa yau aka yarda da suzama tafarkoki na bi da Gina addinin musulunci dasu,[1] Akwai Mazhaba Hudu (4) wadanda ko wanne kabi to anasaran in Allah ya yarda cewar kabi Manzon Allah ne, kamar yadda Manzon Allah yace kubi Abubakar, da Umar da Uthman bin Affan da Aliyu domin sune Halifofi shiryaryu, Ashe kowane daga cikin manyan Sahabban nan kabi to kamar kabi Manzon Allah ne Dan yayi umurni a bi su, haka suma Mazhaba, Misali Mazhabar, Imamu Malik wato Malikyya, Imam Malik yayi karatu a hannun jikan Sayyidina Aliyu Dan Alhasan wato Ja'afar, shi kuma Ja'afar yayi karatu a wurin sahabin Manzon Allah wato Abdullahi Dan Umar Wanda Manzon Allah yakecewa idan akwai wani mutum dayake bin sunnah ta to Abdullahi dan Umar ne.. Haka dukkanin sauran Malaman Mazhaban idan ka duba zakaga duk suna da sila daga sahabbai, sahabbai kuma daga Manzon Allah tsira da aminci sun tabbata agare shi. Cikakkun Mazhaba Hudu da ake dasu sune;
- Mazhabar Hanafiyya, malami Imam Abu Hanifah
- Mazhabar Malikiyya, malami Malik Ibn Anas
- Mazhabar Shafi'iyya, malami Imam Imam Al-Shafi'i
- Mazhabar Hanbaliya, malami Imam Ahmad Ibn Hanbal.[2]
Dukkanin mazhabobin nan sune musulman duniya ke amfani dasu, kasashe daban daban su dauka Mazhabar malamin da yarayu a garinsu ko kuma karantarwarsa da daliban sa sunfi yawa a garin ko nahiyar da suke ciki.
Hotuna
[gyara sashe | gyara masomin]-
Mihrab (marking the direction of the Kaaba in Mecca) - Madrasa of Sultan al-Zahir Barquq
-
Mosque-Madrassa of Sultan Hassan - Cairo
-
Mambobin fitattun mutanen Tunisiya.
Manazarta
[gyara sashe | gyara masomin]- ↑ Hussin, Iza (2014). "Sunni Schools of Jurisprudence". In Emad El-Din Shahin (ed.). The Oxford Encyclopedia of Islam and Politics. Oxford University Press. doi:10.1093/acref:oiso/9780199739356.001.0001. ISBN 9780199739356.
- ↑ Rabb, Intisar A. (2009). "Fiqh". In John L. Esposito (ed.). The Oxford Encyclopedia of the Islamic World. Oxford: Oxford University Press. doi:10.1093/acref/9780195305135.001.0001. ISBN 9780195305135.