Jump to content

Masarautar Mapungubwe

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.

 

Masarautar Mapungubwe

Wuri
Map
 22°11′33″S 29°14′20″E / 22.1925°S 29.2389°E / -22.1925; 29.2389
Bayanan tarihi
Ƙirƙira 1075
Rushewa 1220

Masarautar Mapungubwe (ko Maphungubgwe) (c. 1075–c. 1220) jaha ce ta tsakiya a Afirka ta Kudu wacce take a mahaɗar kogin Shashe da Limpopo, kudu da Great Zimbabwe. An samo sunan daga ko dai TjiKalanga da Tshivenda. Sunan na iya nufin "Tudun Jackals" ko "dutse-tsoffin gine-gine". Masarautar ita ce mataki na farko a ci gaban da zai kai ga kafa daular Zimbabwe a ƙarni na 13, kuma tare da hada-hadar kasuwancin zinari zuwa Rhapta da Kilwa Kisiwani a gabar tekun gabashin [[Afirka. Masarautar Mapungubwe ta ɗau kimanin shekaru 80, kuma a tsawonta yawan mutanen babban birnin ya kai kusan mutane 5000. [1]

yankin Mapungubwe mai alfahari da masarautar shi

Ana iya danganta wannan wurin binciken kayan tarihi ga Masarautar BuKalanga, wacce ta ƙunshi mutanen Kalanga daga arewa maso gabashin Botswana da yamma/tsakiya ta kudancin Zimbabwe, Nambiya ta kudu da kwarin Zambezi, da Vha Venda a arewa maso gabashin Afirka ta Kudu. Tarin kayan tarihi na Mapungubwe da aka samu a wurin binciken kayan tarihi yana cikin gidan kayan tarihi na Mapungubwe a Pretoria.

mutanen yankin Mapungubwe a yakin su

 Mafi girman mazaunai daga abin da aka yiwa laƙabi da al'adun Kopje na damisa ana kiransa da al'adun K2 kuma shine wanda ya gabace shi nan da nan da zuwan Mapungubwe. [2] Mutanen al'adun K2, mai yiwuwa sun samo asali ne daga kakannin Shona da mutanen Kalanga na kudancin Afirka, suna sha'awar yankin Shashi-Limpopo, mai yiwuwa saboda yana ba da damar noman gauraye. [3] Har ila yau yankin ya kasance babbar ƙasar giwaye, inda ya ke samar da hauren giwa mai daraja. Gudanar da cinikin zinari da hauren giwa ya ƙara ƙarfin siyasa na al'adun K2. [4] A shekara ta 1075, yawan mutanen K2 sun zarce yankin kuma suka ƙaura zuwa Tudun Mapungubwe. [5]

  1. Huffman, page 376
  2. Hrbek, page 322
  3. Hrbek, page 323
  4. Hrbek, page 326
  5. Hrbek, page 324