0% found this document useful (0 votes)
3K views34 pages

Subul Da Baka Part 3-1

Hajarah
Copyright
© © All Rights Reserved
We take content rights seriously. If you suspect this is your content, claim it here.
Available Formats
Download as TXT, PDF, TXT or read online on Scribd
0% found this document useful (0 votes)
3K views34 pages

Subul Da Baka Part 3-1

Hajarah
Copyright
© © All Rights Reserved
We take content rights seriously. If you suspect this is your content, claim it here.
Available Formats
Download as TXT, PDF, TXT or read online on Scribd
You are on page 1/ 34

Subul da Baka 3 page 1

Posted by ANaM Dorayi on 05:11 PM, 21-May-15


Under: Subul da Baka
Inna ta yunkura ta shiga daki suku ma suka yi
hanyar waje,Ashe zaman tabarma ne nake ga
bai mata ba.A firgice ya shigo babu ko
sallama yana fadin inalillahi wa inailaihi
raji'un daga ni har inna maka mike tsaye cikin
firgici inna take tambayarsa lafiya ibrahim? Sai
kawai ya durkushe kasa idanun sa jawur inna
ya aka yi haka! cikin rashin fahimtar inda ya
dosa tace da akayi me yace inna waye kuma
hameed.yarima ne hameed meya faru mutuwa
yayi? A'a da ransa shine mijinki yanzu an
daura muku aure,inna ta dafe kirji wa! Tirkashi
inalillahi wa inailahiraji'un Nayi saurin
karasawa kusa da ibrahim na
rushe da kuka ina fadin ka rufamin asiri kaje
kace kaine zabina zan iya jure ko wace wahala
amma banda ta gimbiya da mahaifin yarima
wayyo ni humaira na shiga uku ! Ke bana san
shashanci da hauka ina ma yazo kasar yaushe
yasan abinda ke faruwa. Wannan abun yi Allah
ne saboda haka na
fawwala masa komai Allah yasa haka shi ya fi
alkairi a gare mu baki daya ya mike tsaye
yafita muna zaune muka jiyo sallama wa
yarima zai shigo kanshin turarensa ne yafara
yimin sallama.
Daga kurya nake cikin duhu,shi kuma ya zauna
daidai inda aka ajiye fitila na qura masa
ido,ya qara haske da qiba,yayi kyau har yau
kasaitar nan tasa na nan,sai faman basarwa
yake yi,yana 'yar yamutse fuska. takaici ya
qara kama ni na harareshi,nan ma SARAUTAR
zai nuna? Cikin girmamawa ya gaida inna. tun
kafin yayi magana inna ta jero masa
tambayoyi."Haba yarima? don me zaka yanke
hukunci ba tare da shawararmu ba? talauci
haukane? yarinyar nan marainiya ce meyasa
zaka nemar mata tashin hankali fiye da
kwanciyarsa? ya zatayi da mahifinka? humaira
na iya kishi da Gimbiya?" Ya dago kai
fuskarsa a washe yace"Inna ku kwantar da
hankalinku,wallahi. billahi ba ni da niyyar cuta
ko yaudararku maganar mahaifina yanzu haka
yana kwance rai a hannun Allah kuma ina da
yaqinin insha Allahu zanyi amfani da wannan
damar mu daidaita dashi,tunda har yana
ganin ya hore ni da yin biyayya gareshi,kuma
na aikata hakan zan lallabashi ya yafemin,ya
janye maganar ko bayan ransa." Yanzu haka
ana zargin 'yan uwana ne suka jefa shi cikin
wannan halin,domin su gaji sarauta. akwai
rikici da muke ciki inna,amma hakan bazai
taba shafar Humaira ba da iznin Allah. Kafin
inje ga maganar zamanta da Fareeda
(Gimbiya),ina son ki sani cewa,mahaifan
Humaira suna son ganin cewar sun
wulakantaku ko ince suna son ganin kun
wulakanta. dalili kuwa,nayi bincike sosai a
kansu. yanzu haka da muka je maganar
neman aure,ban nuna musu vewar ni din dan
sarauta bane,asali ma na kasance mai
qasqantar da kaina tare da nuna ni din talaka
ne mai neman taimako matuka. Sunyi SUBUL
DA BAKA mai tarin yawa a cikin jawabansu a
inda suke nuni da lallai basu son Humaira ta
fi 'ya'yansu wadatar dace da miji mai rufin
asiri. Maganar Ibrahim shima nayi bincike a
kansa
lallai mutumin kwarai ne kuma ya fito daga
gidan manya masu mutunci. Matsalar matarsa
inda ake nuni da cewar,tafi karfinsa fiye da
tunanin kowa,yana tare da muguwar mata
wacce tana iya yin ko wane irin ta'addanci,da
mugun abu akan duk abin da ta ga zai kawo
mata cikas a rayuwa. Wannan dalilin ya qara
tsorata ni,ga shi na ji hirarsu da Amira. Kuma
da alama kamar Ibrahim din shi ne wanda
yake tsayayye a gareta. Nazo don Allah mu
warware matsalar wallahi har ga Allah banzo
da niyyar auren Humaira ba,amma sai ta qi
saurarena wanda ya nuna min tamkar rike ta
ke dani a zuciyarta,tana ganin kamar nine sila
ta duk matsalarta. Mahaifiyatace ta bani
shawarar nazo wurin magabatanta na kawo
kaina,ba tare da mun san cewar za'ayi
maganar daurin aure ba. Munyi haka da
niyyar daga baya sai ta sami wani ta aura ni
kuma na janye. Saboda haka kada muyiwa
Allah
shishshigi,hakan ya rubuta sai muyi fatan ya
zamo alkhairi agaremu inna. Kada hankalinku
ya tashi,ni ke cikin rikici,amma duk da haka
bana cikin rudani. Na farko yadda zan shawo
kan Maimartaba. Na biyu rudanin da muke
ciki da 'yan uwana. Na uku ya zanyi da
rigimar Gimbiya idan ta sani,bazan sanar da
ita ba sai na sasanta da mahaifina,in ba haka
ba tabbas zata raba mu har abada!" Na
runtse ido cikin radadi ina hango rayuwar da
zan shiga saboda na tabbatar auren Yarima
ba hutu bane a wurina. "Maganar zamansu
da Gimbiya ba matsala bane,domin ni ke iko
da gidana duka qarqashina suke,wallahi inna
ba zan taba amincewa da takura,zalunci ko
tashin hankali a gidana ba." Ya tsagaita da
bayanin nasa kamar yadda dakin ya dauki
shiru. Na kalli inna,sai naga tana zubar da
kwalla. Hankalina ya qara tashi. Ya muskuta
da fadin"Inna kuyi hakuri don Allah,gobe a
bada mata hudu zuwa shida wadanda zamu
tafi da su,domin su ga gidana hankalinki ya
kwanta. Idan kuma zaki bi ke ma to mu tafi da
ke..." "Kai bana son sakarci!" Sai naga yayi
'yar dariyar nan tasa ta qasaita. Ya mike
tsaye"Inna ayi ta hakuri,sai mun zo su shirya
gobe da wuri za mu wuce,wajen karfe takwas
zuwa tara domin mu isa da wuri,kada muyi
dare."
Tafiya muke yi, amman idanuna na gefen titi,
Sumayya da Aisha sai faman tsalle suke yi.
Motar su yarima ke gaba tamu na biye dasu,
Babban abinda ke damun zuciyata shine, idan
mun isa wace tarba za,ayi mana? Ya za a
karbi wannan al'amari? Ina tsoran tashin
hankalin Gimbiya, musamman idan mukayi
tozali da ita ga cewar na aure Yarima a
matsayina na na BAIWARTA. Munyi tafiya mai
nisan gaske inda ake dauke hanya muka kutsa
cikin daji, nan ma munyi tafiya mai dan nisa
wanda su baba har sunfara korafi sannan
muka isa wani gidan gona katton gaske. Acikin
gidan gonar ma sai da mukayi tafiya
mai nisan gaske kafin ya tssaya gaban wani
tankamemen gida, Goggo Huraira matar Baba
imrana kadai ta biyo daga bangaren babana,
itama ganin kwaf yakawo ta. Mata hudu muka
tarar gidan, babu abinda babu na more
rayuwa a gidan, aka kaini wani daki mai
dauke da gado kawai sai mudubinsa, ga kuma
wata kofa a rufe wacce nake kyautata zatton
bandaki ne. Abinci aka dinga shigowa dashi
kala kala cikin wasu manyan kololi, Goggo
huraira ta dinga raba idano tana yaken dayafi
kuka ciwo. Hannu baka hannu kwarya suka
ringayi abinka
da sabon shiga ga farfesun kaji dana kifi, suna
gamawa wasu maza suka shigo da katon
gasasshen rago bisa wani dogon tebir, Goggo
Huraira tazare ido, bayan fitar su, takalli su
inna karsum wai wane ne wannan yaron?
YARIMA!!! Nabata amsa takara fiddo ido tace
amma ku munafukai ne, shine baku fada tun
wuri ba? Su goggo suka kalleta a mamakance
kamar zasuyi wani abu sai sukayi shiru, da
dare yarima yashigo yace ko akwai abinda
ake bukata? Suka ce a a, dare yamika, gari
yayi tsit babu abinda akeji sai minsharin su
goggo ciki yacika da kayan dadi, nikuwa nayi
lamo ina tinanin yadda wannan aure nawa zai
kasance.
Washegari aka hado kalaci mai rai da lafiya,
abin takaici Gogggo ta cika ledoji wai za ta yi
guzuri su masu Inna ganin kayan kamar banza
sai da suka diba. Karfe goma yarima yace su
fito ga wanda zai mayar dasu. A falo muka
tarar da shi zaune Goggo ta wangale baki
tana fadin dan nan mun fa gode kaji. Yayi yi
murmushi yace babu komai. Ya mika wa
kowacce bandir din naira dubu dubu yace su
yi ysaraba a hanya sannan ya dora da fadin.
Akwai buhunhhunan shinkafa, masara, gero,
dawa, sukari, gishiri, kwalin taliya, kuskus,
mahamisa, sha'iy, madara. Akwai kuma
maggi, jarkokin mai kowacce ta dauki biyu
biyu sauran a kai wa Inna kafin muzo, sakon
kudinta na ba direba idan kun isa shi zai ba
kowace kayanta. Mun gode. Su Sumayya ma
suka durkusa saboda kayan da ya basu.
Washegari aka hado kalaci mai rai da lafiya,
abin takaici Gogggo ta cika ledoji wai za ta yi
guzuri su masu Inna ganin kayan kamar banza
sai da suka diba. Karfe goma yarima yace su
fito ga wanda zai mayar dasu. A falo muka
tarar da shi zaune Goggo ta wangale baki
tana fadin dan nan mun fa gode kaji. Yayi yi
murmushi yace babu komai. Ya mika wa
kowacce bandir din naira dubu dubu yace su
yi ysaraba a hanya sannan ya dora da fadin.
Akwai buhunhhunan shinkafa, masara, gero,
dawa, sukari, gishiri, kwalin taliya, kuskus,
mahamisa, sha'iy, madara. Akwai kuma
maggi, jarkokin mai kowacce ta dauki biyu
biyu sauran a kai wa Inna kafin muzo, sakon
kudinta na ba direba idan kun isa shi zai ba
kowace kayanta. Mun gode. Su Sumayya ma
suka durkusa saboda kayan da ya basu.
Gaba daya jikinsu ya dauki rawa suka zube
suna faman godiya. Ni kuma da yake nasan
wannan kadan ne daga cikin aikin yarima abin
bai zamo mini sabo ba kamar su. Na fashe da
kuka lokacin da na ga cewar, motarsu ta bada
wuta zasu tafi. Goggo ta leko kai daga tagar
motar tace. "To yar banza mai kashin tsiya
kukan me kuma kike yi? Wanna aljannar
duniya da Allah ya kawo ki har kina da bakin
kuka, marar mutunci ko zaki yiwa Allah
butulci ne ya rabo ki daga tsiya. Hannuna naji
an kama mun yi baya. Da sauri na kalle shi,
Yarima ne fuskarsa a daure da alamar
maganganun sunyi masa zafi. Ni kuwa banji
komai ba saboda na saba da wadanda ma
suka fi wadannan. Bisa kujera muka zauna
yanayin zaman yasa nayi wata irin kunya ta
kama ni. Na yunkura zan mike ya dawo dani
na fada saman jikinsa na rasa inda zan sanya
kaina don tsananin kunya. Ya rike hannuna
duka biyun tare da tsare ni
da wannan mayen kallon nasa mai narkar da
duk illahirin jikina. Inason furta ya sake ni
amma na kasa sai faman motsa baki nake yi
kalmomin sun gaza fita. Yayi yar dariya yace
Ba fa zan sake ki ba sai kince I Love You
Naku Tabdijan! Ashe zamu shekara a haka kenan!
Na fada a raina. Wai mai yasa kike mun rowar
maganarki Humaira? Ko don kin ga tana kara
kayata zuciyata ne? Na rufe idanuna ko ya za
a yi in san haka? Baza kiyi min magana ba?
To bari na cije bakin da ke yi min rowar
sai...... Nayi saurin bude idona. Yayi
murmushi yace Matsoraciya goge wadannan
hawayen muyi magana. Nayi saurin kallonsa
alamar ya sake ni. Ya
kashe min ido daya. Ki goge da jikina mana?
Bansan lokacin dana balla masa harara ba, ya
kyalkyace da dariya. Wannan irin horo? Ya
sake ni, amma yayi saurin sanya hannusa
yana goge min fuska. Hankalinka ya kwanta
yau hannunka ya taba fuskata. Na fada a zuci.
Na yunkura zan tashi ya dakatar dani. Tsaya
gimbiya, ai yau sarautar hannunki ta ke. Ya
mike tare da zama kasa daidai kafafuna.
Wallahi bani son irin wannan abunda yarima
keyi mini. Na kara daure fuska tamaubabu
alamar fara'a ko kadan. Ya kwantar da murya
a nutse yace. Humaira kina da tsoro?
Tambayar tasa tazo mini a hagunce kamar ya
fahimce ni, sai yace. Ma'ana kina iya kwana
gidan nan ke daya? Nayi saurin daga masa kai
alamar iyawa.
Tsakaninki fa da Allah kina iya? Bana son ki
kwari kanki idan baki iyawa na samo maki yar
kwana. Ina iyawa, na fada da kyar. Abinci fa
kin iya dafawa ko a kwao mai koya miki?
Kamar zance na iya amma kuma wata zuciyar
ta gargade ni dana ce a kawo., saboda
yanayin abincinsu da namu lallai akwai
bambanci mai girman tazara. Na ce Aa. Ya
kalle ni da fadin. Ban gane ba? A kawo na
fada a hankali. Da kyau ya fada yana
murmushi. Kina son mai share share ko za ki
iya da kanki? Allah sarki Inna ita mai lalura
yanzu wa zaiyi mata share sharen? Na girgiza
kai, zanyi da kaina. Lokacin idonuwana suka
ciko da kwalla. Ya matso kusa dani, kiyi
hakuri. Yarima ya ishe ki da tambayoyi, ke
kuma ba kyason tambaya ko? Na dai yi shiru
kawai. Wadda zata koya miki abinci ita zata
nuna miki komai na gidan nan. Koda wasa
karki nuna mata ke matatace. A firgice na
kalle shi. Ya kawar da fuska yace Zan sanar
da ita ke matar abokina ce Haka sauran
wadanda ke nan shiyyar saboda gudun
matsala kafin Allah yasa mu daidaita da
maimartaba. Wayyo ni Humaira na shiga uku!
Kwallan da nake kokarin mayarwa suka fito
day bayan daya. Kiyi hakuri Humaira, wallahi
duk saboda kwanciyar hankalinki zanyi haka
Kada ki damu Allah na bayan mai gaskiya
kinji ? Yau zan wuce mu tafi da maimartaba
Eygpt idan an dace muyi kwana hudu zuwa
biyar Idan kuma an sami akasin haka to sai
yadda Allah yayi.
Take kwalla suka karu ni kuma haka Allah ya
tsaro min tawa rayuwar?? Ya kalle ni, Don
Allah Humaira kada ki sanya wa kanki
damuwa kinji? Da na dawo zamu je Kano ki
gano su Inna kiyi kokari ki kwantar da
hankalinki yadda za su ga cewar ba ki cikin
matsala. Kuma insha Allah idan komai ya
daidaita ina son dawo dasu kusa damu
Saboda Inna na bukatar kulawa. Naji wani
sanyi a raina tare da goge kwallan da ke
fuskata Ya miko mini sabuwar waya yana
cewa Akwai lambata da ta Inna a ciki Kada ki
saka lambar kowa sai da izinina kinji? Nace to
Wayarsa tayi kara ya dauka Hello!..........ok
Ina kan hanya gani nan isowa Ya dawo da
dubansa gare ni Ya shiga wani daki kusan
mintuna hudu Ya fito rike da wata leda Ina
kallonsa ya bude wata dirowa ua dauko wani
dan kwali karami ya gama yar diminiyar sa ya
fita. Na kwanta dabas kan kujera. Allah gamu
gare ka Har kusan karfe daya ina nan zaune.
Kofa naji
ana kwankwasawa na leka sai ga wata
katuwar mata tsaye. Na bude mata sai fara'a
take yi. Yanayin gaisuwar da muka yi da
yadda ta ke magana na gane cewar ba
cikakkiyar ba hausa bace. Tace nice wace zan
koya miki abunci. Ta fada tana mai fata'a
sosai. Nima cikin sakin fuska nace mata. Ba
matsala. Na kawao mata lemu a firij din da ke
falon mai sanyi da ruwa Sanana na kalle ta
Don Allah ki bani mintuna kadan zan yi sallah.
Ta risina cikin girmamawa har mammaki ya
kama ni. Tace As u said Madam no problem
Toh ai kinji fa ni fa bana son turanci yayi yawa
a magan Ko kuma ayi shi cikin sauri domin
karatun nawa yanayinsa akwai da rauni.
Lokacin dana fito nayi mamakin ganinta dana
yi a bakin wata kofa. Tayi hanzarin karasowa
kusa da ni. Yauwa madam muje. Na bi
bayanta sai na ga ashe kicin dinne To ya akayi
ta sani?? Ban sami damar samu amsa ba Ta
katse ni da cewa Yallabai kwana biyar ya
bamu Saboda haka ki dauko biro da takarda
ki ringa rubutawa Saboda gaba rana daya kina
iya mantawa da wani abun Na kalle ta sosai
nace Bani da biro gashi ni bakuwa ce a gidan
Tayi murmushi tace Ayya bari na baki Ni ina
dasu.
Nafisa A. Mamawa
Tabude jaka ta fiddo wani dan book da biro
tamiko min, A kullum zamu ringayin abubuwa
uku zuwa hudu, ko fin haka idan akwai time,
tabude wani katon firij dake kicin din, shakare
yake da kayan lambu da naman kaji dana
dabbobi, wani kuryar daki dake kicin din
shima cike yake da kayan abinci na
buhunhuna dana kwalaye, ga doya, dankali,
kwai, da sauran tarkacen, ta debo dankali
tace hajiya zan ringa yimiki bayani kina rubuta
wa, nikuma inayi a aikace kina gani, na ce to.
GIMA POTATOES ABUBUWAN DA AKE
BUKATA, dankalin turawa, tattasai, Attarugu,
Tumatur, albasa, gishiri, curry, thyme, karas,
pies, green beans, green pepper, alayyahu,
kwai. A fere dankalin turawa kar a yanka, a
barshi haka da girmansa sai ki daka tattasai,
attarugu, tumatur da albasa, kisoya sai kisa
ruwa kizuba dankalin, kisa su maggi, gishiri,
curry, da thyme, ki yanka kayan lambumki irin
carrot, pies, green beans, green pepper,
alayyahu. Sannan ki fasa kwai kamar biyar ko
fin haka kisama masa curry da albasa da
maggi kisoya shi. Kiduba dankalin inya dauko
Dahuwa sai kijuye soyayyen kwan da sauran
kayan lambun.
Banda alayyahu, shi ki samasa ruwan zafi ki
tsane shi, saiki sa namanki ko kifi ko kibarshi
haka, kibar kayan lambun suyi laushi ruwan
kuma yayi kauri, sai kisa albasa da alayyahu
kirage wuta, tayi dariya tace yanzu zakiji shi a
bakinki, a time din data gama yawuna har
tsinkewa yakeyi domin yunwa nakeji nakuma
na cika flet na kuma gefe, gaskiya yayi dadi
wannan gima potatoes din, tayi dariya tace to
kidai rage wuri ga abinci na biyu mai suna,
KABBANI RUS RICE, abinda ake bukata
nama, albasa, maggi, kayan lambu,
tafarnuwa, Cinamon, Cadamon, mint,
Attarugu, Yogot, basmati rice, ki yanka nama
kanana sai ki tafasa, kidan soyashi sama
sama, kiraba shi biyu, kidauko basmati rice ko
kuma wadda kike amfani da ita kidafata
ruwan naman sama sama sai ki yanka karas,
garlic, pies, albasa, ki hada su guri daya, sai
ki daka attaruhu banda tattasai kisoya kizuba
su karas, nama, garlic, maggi, da dai sauran
su, ga wanda bai shan yaji ana iya amfani da
tattasai zalla cinamon, cadamon, mint, sai ki
zuba yogot cokali uku ko hudu, in kina son
zaki dayawa, idan kuma bakiso sai ki zuba
kadan, to your taste. Idan kin gaggauraya sai
ki juje guntun ruwan
silale a ciki idan yatafasa sai ki sa albasa
kirufe ta, kirage wutar har ya tsose yadahu,
zaki iya mata sos din albasa da garlic da
attarugu ko sos din tumatir kawai ko kici
haka. Idan kikayi wannan sai ki sami
mangwaro tunda gaki gidansa akwai manya
manya nan sai bare bayan saiki yanyanka shi
kicire kwallon, sai kizuba tsokar mangwaron
atukunya kisa citta, kanunfari, kuzuba ruwa
kidora a wuta yadahu sosai yafara fashewa sai
ki burge shi kikara ruwa kitace kisa sugar da
fulawa kisa firij.
Ta koya mata abinci da dama( na tsalake ne
saboda nasan dayawanku kun iya
musamman...inma da wadanda basu iyaba
bazasu wauce abokanainaba su kuma insunaso
sai suyimin magana prvt loz).
Bayan ta koya mata komai. Tayi mata rakiya
har bakin kofa, nace Don Allah kiyi hakuri bai
bar min komai ba....gurin is not clear. Tayi
dariya tace wallahi ya biya ni har da doriya, ni
ke da godiya Madam. Naji dadin samunki mai
far'a da son jama'a wallahi domin hausawa
na cewa shimfidar fuska tafi ta tabarma. Sorry
not clear.Amma gobe kizo da wuri don Allah
Na fada ina murmushi. Insha Allah da wuri
zan zo yau ma akasi aka samu Na gode sai
goben. Nace Allah ya nuna mana lafiya. A
kujera na bar wayata na dauko ina latsawa na
ga an kira har sau goma sha uku (13 missed
calls). Na fido ido, ina dubawa na ga Hameed
wato Yarima. Na zauna tare da kura wa wayar
idanu saboda a gaskiya bana iya kiransa. Na
latso lambar Inna, bugu daya ta shiga. Tayi
sallama murya a washe. Wa ke magana? Inna
Humaira ce. Sai naji tayi yar dariya. Humaira
kuna lafiya? Kalau Inna, su Aisha su iso lafiya?
Tace lafiya lau, ya suka barku? Nace kalau. To
Allah yayi muku albarka Kiyi mana godiya mai
tarin yawa wurin yarima don Allah. Ya kira ni
dazun yace zasu yi tafiya , don haka ki kula da
kanki, ki kuma kular masa da gida Allah yayi
muku albarka. Nace Ameen. Mun dade muna
hira inda na lura Inna kamar ba cikin
damuwa, sannan muka yi sallam hankalina ya
kwanta. Kamar abin jira, kiransa ya kara
shigowa. Gabana ya fadi ba wai kiran ke bani
so ba, a'a tambayoyi na tsana a rayuwata. Na
kara wayar a kunne tare da fadin. Assalamu
alaikum. Ya amsa cikin zakuwa tare da ci
gaba da fadin. Ina kika shiga ne tun dazun ina
ta kira shiru, ni duk kin tada min hankali.
"Kicin" na bashi amsa. Me ki ka yi a kicin da
zai dauke ki wannan lokacin Humaira? Kinsan
kuwa yadda kika sa min damuwa? " koyan
abinci". Na kara fada. Yayi ajiyar zuciya tare
da waji murmushi mai fidda sauti.
To idan za a tafi kicin ba a tafiya da waya ne?
Haushi ya kama ni, wai shi ba ya magana kai
tsaye sai ya hada da tambaya? Kin ji? Ya
bukata. Na ce, na mantata ne kan kujera. Yayi
yar dariya, yace Don Allah ni da a ringa
makale wata ko'ina za ki shiga kada ki dora
min hawan jini, Ko ba a sin kiran nawa ne?
Aifa, na fada a zuci. Kinji ba kya son na kira
ne? Nayi masa shiru. Yanzu me da me kika
koya?? Allah ka raba wannan bawa da
tamabay, na fada a zuci. Yayi kasa da murya
Don Allah ki fada min irin abin d kika koaya.
Ai suna da yawa. Nace da shi. Suna da yawa
har guda nawa kika iya? Duka na iya, ai basu
da wuya. To ji ma koya kin. Wai ina marar
lafiya ka tsaya kana faman tsokana? Wallahi
duk tunanina a zuci nayi wannan maganar, sai
kawai na ji ya tuntsire da dariya. Ga shi nan
kusa da ni, ko na bashi ne?? Nayi shiru,
gabana yana faduwa. Hajiya Humaira
Gimbiya, wannan kasaitar taki ke kara ruda ni
wallahi, Toh ko milk and coconut balls din ne
a koya mun. Wai ko Yarima yana dubiya ne?
Nayi murmushi na ce. Hmmmm Yace meye
humm? Gashi zamu yi tafiyar dare ballantana
na taya ki hirar dare. Ba komai. Na fada da
sauri. Ke a wurinki yake ba komai, ni kuwa
akwai wani abu.... ga su nan sun fito za mu
tafi, kar ki kashe wayarki fa. Na ce to. Sai na
kira. Ya fada. Allah ya kiyaye hanya, Allah ya
bashi lafiya.
Cikin jindadi yace, Ameen. Ban jira ya kara
magana ba na latse wayar. Na kalli wayar ko
me ya sa yake yi min wannan surutun alhalin
ba haka yake wa sauran mutane ba? Ban
fama tunanin ba na ji karam! Ina dubawa na
fa sako. Ina rokonki da ki ringa sakin jiki
muna magana ko a wayar ne tunda a fili kin
kasa. Ina cikin wani hali Humaira na rashin
sukuni da kwanciyar hankali, ga matsalar
ciwon maimartaba, ga ta Fareeda. Sannan ga
ta jama'a, wurinki kadai nake jin zan samu
kwanciyar hankali, ba komai zai haifar da
hakan ba sai kin yi responding da duk wata
magana da zan yi miki, don Allah ki saki jiki
da ni ina rokonki. Murmushi kawai nayi. Ga
tsayuwar kicin ' yan share sharen da na yi da
magriba, don haka gajiya ta taso mini, ina
gama wanka waje karfe tara na kwanta ban
kara sannin abin da ake yi ba sai da na bude
ido na fa karfe shidda da kwata na safe. Na
hanzarta yin alwala na gabatar da sallah
Sannan na koma kan gado na kwanta kafin na
kara hutawa zuwa billowar rana. Da wuri
kamar yadda tayi min alkawari ta zo, don tare
da ita muka yi kalaci. Kamar yarda Yarima ya
umurce ta cewa kwana biyar, to hakan akayi,
amma fa na koya abubuwa domin sai dana
cika littafina mai farka arba'in. Kwana biyu
kenan ba mu yi waya da Yarima ba, kuma na
kasa nemansa. Sai na dauko kamar zan kira
sai kuma na fasa. Zaune nake ina gyaran
kumbar hannuna naji motoci sun shigo, na
mike tare da lekawa ta taga ba hango
zungura zunguran motoci nan na sarauta
masu kofofi hudu. Budewar farko na hango
Yarima ya yi saurin fitowa daga nan na ga an
kamo maimartaba sun nufi babbab gida dake
bayan inda nake. Gabana ya fadi, na dafe kirji
tare da koma kan kujera nayi laggwab. Har
bayan isha'i ban ga Yarima ya shigo ba, nan
jikina ya kara mutuwa. Haka na kwanta ba
don bacci ba, Can wajen karfe sha daya naji
motsin mukulli ana bude kofa. Na runtse
idona kamar mai bacci. Kamshin turarensa ya
fara ziyarata kafin na ji ya shigo Na kara yin
lami. Ya gama yan hidindimunsa duk cikin
dakin ko wanka a nan yayi, sannnan naji yana
kokarin hawa kan gadon inda nake. Na tamke
idona. Ya hawo tare da yaye bargo dana
lullube Shirun da na ji ya yi ya bani tabbacin
kallona yake yi. Na tsargu saura kadan na
bude idona sai kawai na yu saurin juyawa
kamar cikin bacci ai sai naji ya janyo ni jikinsa
tare da maida bargo ya rufe mu. Ai sai na
fara kokarin zame jikina Ya kuwa rike ni
tamau!
Ya karkato bakinsa daidai kunnena yana
magana a hankali. Ke ni ne ki kwanta ban yi
niyyar tadaki ba. Amma sai da na zame jikina.
Mene ne haka Humaira? Kina fa wahalar da ni
da yawa Kin yi min rowar muryarki kwana da
yawa Kuma yanzu sai ki hana ni jin dumin
jikinki? Kin ji? Da ke fa nake magana? To me
zance masa dan Allag? Ba ki magana? Ya
tashi zaune. Wallahi ko ki matso konkuwa na
hau kanki. Ba shiri na matsa. Yayi yar dariya.
Matsoraciya duk kya gama Yan kauce kaucen
naki ki dawo hanya......mun dawo me zan
samu na sannu da zuwa? Ya rada min a
kunne, na ji wani yarr!! Kamar na shakare shi
duk na takura Wannan salon kuma ya dawo
da shi? Lallai bone ta ci ni kuwa. Ba fa zan
lamunci shirun nan ba wallahi. Humaira na
gaji da wahalar nan Ko ba kiji ina magana
ba? Ya jikin Baba?? Na fada kamar mai koyon
magana. Da sauki yana nan gidan ma zai huta
na wani lokaci Don haka kada ki sake ki nuna
ina da alaka da ke. Gabana ya fadi ras! Lallai
akwai babbar matsala. Yanzu me zan samu?
Me fa! Duk tunanina a zuci na yi Sai da na ji
yace Me fa ? Hmmmm. Yayi shiru sai na ga
kamar ban kyauta ba Na daure na ce. Ka fadi
me kake so sai in girka maka Bana burin
abinci ya kwana Kuma ban san yau zaka dawo
ba. Ni ba abinci nake so ba. Ban san lokacin
dana ce To me kake so Ya dan kara kasa da
murya kamar wani zai ji Ko dan kiss Ko motsi
ban kara yi ba Kin ji? Zan samu? Humaira da
ke nake Wallahi da Yarima zai gane da ya
daina yi min wadannan tambayoyi nasa. Shi
ne kika kyale ni? Kin ji? Na kara kulewa sai
kace bakinsa aka yi kalmar kinji Don girman
Allah ki taimaka mini Wallahi na kawo wa
raina. Ya kusa bani ma dariya har da magiya.
To tunda kin yi min bukulu juyo ki fuakance ni
Ko hakan ma ba zan samu ba? Na dai yi masa
shiru. Kinji? Wai don Allah kai ba ka san ina
jin kunyarka ba?? Na fada kamar shirin yin
kuka. Sai kawai naji ya kyalkyace da dariya. Ni
ban sani ba. Ashe kunya ta ake ji? Wannan
kunyar bata yi min adalci ba wallahi. Juyo na
rage miki ita Don na lura ke ma ta takura ki
Kin san Allah sai kin zaba Ko ki juyo ko kuma
kiss.
Sai me? Bakinsa naji ya hada da nawa Zan
kwace yayi min wani riko. Na rasa inda zan sa
raina don kunya. Ya dauki mintuna kusan
talatin har jikina yayi lakwas. Yana zame
bakinsa na yi saurin cusa kaina jikinsa kamar
in bude kasa in shige abin da dama ya ke so
kenan Ya kara gyara ni tare da rufe mu da
bargo. Sama sama na fara jin nufashinsa
alamar ya sami barci, amma da na motsa sai
ya yi firgigi tare da matse ni. A haka har na
hakura ni ma ban san kokacin da barawon ya
sace ni ba. Ko da na farka ban ganshi ba,
lokacin bakwai har ta wuce. Ban yi mamakin
wannan muguwar makara fa na yi ba, na
hanzarta gabatar da sallah ban tsaya gyaran
dakin ba na fada kicin. Na soya dankali,
sannan na dafa tsokar nama da albasa da
kayan kamshi, sannan na jajjaga tattasai da
dan tumatir tare da albasa duk na ajiye gefe,
na dauko albasa ba yankata faken falen
sannan na daka wannan dafaffiyar tsokar. Na
zuba mai a tukunya na kawo yankakkar
albasar nan na zuba cikin man ta dauka
dahuwa sannan na zuba cijin man ta dauko
dahuwa sannan na zuba jajjagena da
dakakken nama na ci gaba da motsawa kafin
na dauko baked beans shi ma na zuba ciki
tare da kabeji dana yanka, sannan na zuba su
maggi da sauran kayan kanshi. Wannan itace
miyar cin dankali. Bayan na gama na soya
kwai, sannan na hada kunun kuskus. Madara
na zuba a tukunya kofi daya ta gari da ruwa
rabin kofi suka tafaso sannan na zuba kuskus
tare da kara dan ruwa na bar shi ya dahu
lugub ba sanya maburki na burke ba juye a
kwano na kawo flavour mai kamshin madara
na zuba da madarar ruwa peak sai sukari. Na
hada wadannan kaya na shirya wasu a tire na
rufe da dan kyalle na rufe abinci, gyalena
navdauka tare da fita wajen gidan Cikin sa'a
sai ga wani zai wuce na kira shi muka gaisa
yana min kallon rashin sani ban damu ba
nace. Don Allah ka taimaka ka kai wa
maimartaba kace daga gidan abokin Yarima.
Yana ji na ambaci Yarima ya fara kyarma tare
da karba cikin hanzari yayi gaba. Ni kuma na
kima ciki don hada wa yArima nasa. Sannan
na shiga gyaran gidan da yan share share
cikin yan mintuna kamshin freshner da
turaren
wuta ya gauraye ko'ina. Na fada bandaki na yi
wanka, abin mamaki ina fitowa na tarar an
ajiye min wata doguwar riga mai dankaren
kyau. Motsin kwanukan da na ji a falo ya ba ni
tabbacin shi ne ya shigo. Nayi saurin
shiryawa, amma kunya ta hana ni fita, yadda
riga ta kame ni kam kamar daman an auna da
jikina na kalli kaina na kara kallo. Kai duniya
komai na son gyara. Ni kaina na yaba da kyan
da nayi. Ganin lokaci zai kure har sha daya na
niyyar yi yasa na daure nafito, saboda
gabatar da abincin rana. Zaune yake yana
faman latsa waya na dan karasa nesa da shi
kaina kasa ban yarda mun hada idi ba nace
Barka da sfiya, ya karfin jikin maimartaba?
Gaisuwar tayi masa dadi a yadda na fahimta,
yace. Alhamdulillahi da sauki wallahi, na je
ma gida amso masa karin kumallo ne. Ina
dawowa na tarar har ya gama cin wani abinci
ta baiinsa mai dadin gaske, wai an kawao
masa daga gidan abokina shi ne nakr neman
wannan dan iskan in ji ko shi Abdul amma ba
wanda na samu. Shiru na yi tare da mijewa na
kwashe kayan, ga mamaki ya cinye komai. Ya
kalle ni yana murmushi. Kr ni fa na lashe
abincin, kin dai ci naki ki?
Nayi yar dariya, Eh Dariya na baki? Ya fada
cikin wata irin siga mai nuna matsanancin
farin ciki. Ni dai na yi gaba abina in
murmushi. Abin da na fara yi shine gyara kaza
na wanke na jajjaga dan tarugu da albasa
sannan na daka thyme da citta da tafarnuwa
na hade wuri guda na kawi mai na zuba ciki,
sannan na zuba maggi da gishiri na motse na
shafe kazar nan da su ciki da waje, na saka
gefe na dauko albasa davtumatir na yanka
fyalen fyalen, na yanka kabeji kanana na ajiye
gefe. Na dauki kazar na sa a oven tare da
timing mintuna arba'in da biyar. Na wanke
shinkafa da ma na dora ruwan zafi sun tafasa
na zuba, sannan na barta ta dan dahu, sannan
na sauke na wanke na tsane. Na yanka wani
kabeji, karas, kokumba, koren wake da peas
na tafasa hanta na yankata kanana da yar
albasa. Na zuba mai a tukunya kadan yana yin
zafi na juye vegetables dina da hanta sannan
na zuba zuwa kadan na kawo shinkafar na
zuba tare da motsawa, ruwan suka hau kanta
kadan yadda zan ida dafata na rufe. Ina cikin
gyara kayan miya Yarima ya shigo ya sha
uban ado da irin kayansu na sarauta nan da
nan jikina ya dauki rawa na kasa ci gaba da
yankawa. Ya matso tare da shishige min. Me
kike dafawa haka gida ya rikice da kamshi??
Zaka fara ko? Na fada a zuci, amma a fili na
ce Abinci. Zan sami kamar na mutum hudu
zuwa biyar? Insha Allah. Na bashi amsa. Ya
rungume ni very good my princess. Zamu zo
around 2:30 mu ci , kaya na nan su za ki canja
kinji? Nace To. Duk na kagara ya tafi. Ya kai
hancinsa a wuyana. Inason wannan turaren
very sexy. Na dai yi shiru saboda na riga na yi
mutuwar tsaye, ko me ye sexy kuma? Na
tambayi kaina. Gobe dani za ayi girkin nan
gaskiya, yau ma don am busy shi ya sa. Ya
sake ni, sai mun zo cin abincin. Yana fita na
saki wata ajiyar zuciya jikina gaba daya ya
bige da kamshi turarensa. Da hanzari na kara
gyara wasu kajin uku tunda wankewa ce
kawai, akwai a firij na yi musu hadin ta farkon
na kunna dayan oven din nasa su a ciki. Daidai
shinkafar ta dahu na kwashe a katuwar kula
kafin na gama na san ina zan zuzzuba. Muna
da lemuka kala kala don haka ban wahalar da
kaina wajen hada wani juice ba gani har biyu
da mintuna biyar. Na sami babban kwando
na zuba abinci na shirya wa maimaryaba
komai na ajiye gefe, sannan na je na shirya
wa su Yarima nasu a fako a kan table abin
mamaki naji ana buga kofa.
Na san ba Yarima ba ne sabida yana da
makulli, na hanzarta isa sai na ga wani dogari
da kwanonina, na bude ya durkusa.
Maimartaba ya ce a yi godiya sosai. Na ce
yauwa tsaya ka tafi da wannan. Na hanzarta
na dauko lemuka kansa na sanya masa kusan
kala takwas. Na kwashi nawa na yi daki na
tarar ya ajiye min wata danyar shaddda galila
ta sha aiki sosai, na yo alwala na saka,
sannan na fara gabatar da sallah. Ina
kabbarawa na ji motsin shigowarsu, wani
dadi ya baibaye ni. Ya leko Au sallah kike yi?
Ya fice. Koda na gama naci gaba da cin
abincina a tsanake tunda su ma na ji suna cin
nasu ne. Na gama nayi lamo ina jin hirarsu
sai faman santi suke yi, sunabyi wa Yarima
sharri. Wai da man don ya kwashi girki yasa
ya haukace kaina. Na yafa gyalena na leka
muka gaisa, za su fara tsokanata nayi saurim
komawa ciki. Muryar wani na ji yana cewa,
shege ina ka samo wannan shuwa arab din?
Dole Gimbiya ta haulace bala'in nan alkur'an
yarinyar tsoro ta bani......amma da ita zaka
tafi jibi ko? Dadi ya ziyarce ni, ashe tafiya zai
yi jibi? Ni dama gobe ko yau ne. Baka jin
maganar Yarimaan saboda kasaita da jan
girma wannan mutumin akwai isa. Yaushe ne
ta ke haihuwa Gimbiyar? Ciki gare ta ashe?
Na fada a bayyanr. Suka dai gama hirarsu ina
ji suna amarya mun gode amma na yi shiru.
Tunanina da shi aka fita sai kawai na ga
mutum ya shigo alkyabba a hannu. Ya miko
min. Ungo ki kai min daki. Na mike na isa tare
da mika hannu sai kawai naji mutum ya
rungume ni. Haba irin wannan delicious ai sai
da tukwicin hug. Wallahi kwakwalwarki na ja,
na san ko ita malamar taki da ta koya miki
girkin yanzu ba zata hada kanta da ke ba.
God bless u my princesss. Ya sake ni, zan je
na amso wa maimartaba abinci, Umma har ta
kai ga yi min waya. Nace to kawai. Har ya
juya ya dawo Zo ki yi min rakiya. Ya fizgo ni
muna zuwa bakin kofa ya mamayeni ya kai
bakinsa ga nawa, sannan ya saki ji tare da yi
min gwalo, sai kawai abin ya bani dariya
sosai. Shi ma da dariyar ya bar gidan, na
gaya shiga wani farin ciki mara misaltuwa,
Yarima Hameed kenan. Karfe shidda na
marece naji ana kwankwasa kofa, na hanzarta
tare da tambayar waye? Yace kwanoni ne aka
kawo na abinci. Na hanzarta budewa da man
da hijabi a jikina. Kamar jiya ya risina.
Maimartaba yace, ayi masa godiya mai tarin
yawa, Allah ya albarkace ku ya azurtaku, ya
rufa muku asiru duniya da lahira. Nayi
murmushi cike da jin dadin wadannan
addu'oin nace. Amin ya rabbi. Na karbi kayan
ina shirin juyawa gida, sai ga Yarima kamar
daga sama. Gabana ya fadi jikina yayi sanyi,
ya kalli dan sakon da tuni ya zube kasa yana.
Allah ya taimaki Yarima! Ya daure fuska, ya ya
dai? Na maido wa matar abokinka kwanoni
ne, kuma maimartaba na dada godiya, Allah
ya bar aminci. Tashi ka tafi. Ya fada a
hanzarce. Ni kuma nayi ciki da sauri. Ya biyo
ni har kicin. Dama Humaira ke ce ke aikawa
da abincin da maimartaba ke faman yabawa?
Ke ce matar abokina da yake faman fada wa
duk wanda ya ziyarce shi? Waye ya baki
wannan shawarar? "ba kya tsoron hakan xai iya
janyo a yi
saurin fahimtar tsakaninmu 2nda kin nemi
wannan kusancin har an san da ke? Kin ji?".
Ba tare da na kalle shi ba, na ce. "ka yi
haquri". Ya matso kusa dani "ba laifi na ce kin
yi ba, shin kina ganin ba wata matsala ko ba
kiyi 2nani ba kafin ki yanke hukunci?" a qagare
na ce da shi "ba wata matsala in sha Allah".
"kin tabbata?" "eh". Na fada ina shirin gifta
shi na fita. Ya janyo ni jikinsa. "Allah ya yi miki
albarka humaira". Bai qara fita ba, ya ce muje
na taya shi harhada kayansa, sai wajen 9
muka gama, saboda mun yi sallar magariba
da isha'i sannan tambayoyi da yawan
maganarsa suka ringa bata mana lokaci. "wai
humaira don Allah sai yaushe xaki saki jikinki
da nawa?" murmushi kawai na yi "kin san
shawarar da na ke yi yanxu?". Na
ce "a'a". Ya ce "so nake yi idan na dawo na
san yadda xan maida ki makaranta, ko ba ki
so?". Na fadada murmushin kusan xuwa 'yar
dariya "wallahi ina so saboda ma 2ranci". Ya
kalle ni sosai "2ranci kuma?". "eh wallahi, ina
son iya 2ranci sosai". Ya qyalqyale da dariya
"to ko london xan kai ki qasar 2rawan?". Cikin
'yar dariya na ce "da ko ka kyauta". Wasa-
wasa hira ta barke tsakaninmu, nan da nan ya
fahimci lallai ina son ilimi 2nda ga shi ina hira
da shi cikin sakin jiki, abin da ba taba ba. Da
yake hirar ta yi min dadi ban damu da yadda
muka kwanta gado 1 ba, muna ci gaba da
hirar har sai da na lura da irin shige min da
ya yi tare da yadda salon maganarsa ke...
sauyawa nan da nan tsoro da kunya
suka kama ni, amma ina lokacin da na farga
na makaro, 2ni yarima ya kasa sarrafa kansa,
yana faman salo... Ya rasa ta inda xai billo
min nayi shiru, ni kaina na san kukan ba wai
na ciwo ba ne, tsabar kunya ce ya sa na kasa
tsaida shi, saboda ina 2nanin ta inda xan
tashi, ga shi a dakin ya kasa ya tsare. "don
Allah humaira ki yi haquri". Kalmar da yake ta
nanatawa kenan 2n tashinsa. Ganin ba wani
sauyi sai kawai ya dauke ni cak xuwa bandaki
ya hada min ruwan dumi da komai sannan ya
fito. Na sami damar dago kaina daga qasa ina
raba idanu kamar wacce ta yi qarya. Na ma
ba kaina dariya na samu na yi wanka amma
fitowar ta gagareni. Sai na jiyo motsinsa can
bayan daki, ai ko na yi hanxarin fitowa. Ga
mamakina ya gyara dakin tsaf! Ya sauya xanin
gado sai qamshi ke tashi. Ta taga na
hango shi yana shanya xanin gadon da ya
kware, wato wankewa ya yi. Ina cikin saka
kaya ya shigo, ai ko na yi cikin wardrope din
sai kawai na ji yana dariya. "xan je gurin
maimartaba, ki hada abincin da ni don sai
xuwa jibi xan wuce, na fasa tafia yau". Gabana
ya fadi, ni kam na so ya tafi yau din kamar
yadda ya tsara. Kamar kullum na hada abinci
kala-kala, na shirya masa nasa na aika wa
maimartaba sauran. Na sallame shi sallah
kenan na ji shigowarsa da baqi. Har suka
gama ban fita ba, shi ma bai shigo ba, da
suka tashi kuma suka fita tare. Ina xaune falo
ya dawo da qa2war leda. "sorry humaira,
kadaici ya dame ki ko?". Ya qaraso inda nake.
"wallahi 2n fitarmu ina kasuwa don samo miki
abin kore kadaici". Yana maganar yana
bude ledar tare da fiddo littatafan hausa da
fina-finan hausa sabbi, masu kyau. Dadi ya
kama ni, da ma in taba kara2n hausa ko a
gida, musamman littattafan jamila ibrahim
kankia, naja'atu haruna 'najnoor nasimat', da
kuma na xainab dahiru wauwo 'xeedee'. Ya
miqo min littattafan kusan guda 20, a sama
wani sabon littafin mu2niyar ne, wato xeedee
wai shi 'INA XA MU JE?' daga jin sunan littafin
nasan dole ya yi dadi. Na yi murmushi "na
gode qwarai". "ga kuma hausa films xo in
koya miki hada kayan kallon yadda xa ki ringa
sauyawa daga DVD xuwa satelite wataqila ba
xa ki iya gane connection din ba duk da a
hade suke ko da remote sai ki sauya". Nace
"to". Tare da matsawa cikin doki da murna,
saboda gaskiya xaman kadaici ya ishe ni kam.
"abin ma ba wuya".
Na fada ina yar dariya. Ya yi murmushi. Gare
ki mai saurin fahimta ba...... Akwai sairan
abinci? Wallahi yunwa nake ji. Eh na dafa
wancan babu na ga ba ku rage komai ba.
Yauwa bari na watsa ruwa, hada min kafin na
fito Na shirya masa hadadden farfesun 'yan
ciki da fried taliya, sai kemon kuskus mai
madara da kwakwa a ciki. Ya kwashi girkin
nan da kyau, da ma kadan na yi daidai ni da
shi, ya cinye nasa duka. Na yi yar dariya tare
da kallon empty kwanonin da farantin, sai ya
kyalkyace da dariya. Me kike son cewa? Na
kwashe kawai na wuce kicin. Ya ci gaba da
cewa. Ko fiddo maganarki yarinya, so kike
kice ina da ci ko? Kin manta garinku kenan
lokacin da kike ba ji abinci halan? Daren ranar
mun yi hira da kallon wani fim na Hausa mai
ban dariya na dan Ibro. Washegari kuwa
tunda ya fita da safe sai yamma ya dawo, sai
ga shi da uwar tsaraba kayan daddawa,
kuka,kubewa sauran tarkace wai in ji Inna. Na
yi ta murna, tamkar Inna ce gabana. Goma na
safen washegari ya bar gari da alkawarin bai
wuce sati daya ko biyu. Nanji dadin tafiyarsa
saboda na sami damar sakewa in yi karatun
littattafan da ya sawo mini da fina finai.
Maimartaba ya bada kayan itatuwa kwando
kwando aka kawo tare da dumbin godiyar
dawainiyar da ake da shi. Kullum idan Yarima
bai kirani sau hudu biyar ba, ya kira ni sau
uku karanci. Kamar daga sama ranar wata
asabar, sai ga mahaifiyarsa da wasu barorinta
guda biyu. Na ji dadin zuwanta sosai, saboda
itace wadda ta fara kawo m8n ziyara daga
bangarensa. Na zubo mata abonci dankayan
makulashe, abin mamaki ta ci komai tana yi
tana mini nasihar na rike mijina, kuma na
dage da addu'a. Da za ta tafi na zubo mata
dambun naman kaji cikin wata katuwar
samira, sannan na kunso mata snack na ba
daya daga cikin barorin na ce ta rike mata. Ta
dinga yi min addu'a sannan ta tafi. Kwanan
Yarima goma da tafiya ya yo mini waya ga shi
nan zai hau jirgi yau zai dawo. Nan da nan na
fara shirye shiryen tarbarsa. Ga mamakina har
kusan karfe biyun dare ban yi bacci ba ina
sauraron zuwansa, amma shiru! Na kira
wayarsa sau wajen uku a kashe, hankalina yayi
matukar tashi. Baccin da ban sami yinsa ba
kenan har garin Allah ya waye.
Da safen ma har kusan karfe sha biyu ba wani
labari. Haka na ci gaba da aiki kamar wadda
kwai ya fashewa a ciki. Ina cikin harhada
kayan abincin maimartaba na jiyo alamun
budewar kofa, da hanzari na fito. Ya shigo a
hargitse kamar ba shi ba, gabana ya fadi,
kada dai ace maimartaba ya rasu? Ya kamo
hannuna idanunsa jawur, muka zauna bisa
kujera. Humaira tare muka zo da Zarina,
kuma yau maimartaba zai koma fada. Na saki
ajiyar zuciya a hankali. To mene ne abin
damuwar a nan? Na fada a zuci. Ya karkace
kai kamar mai shirin yin kuka, ya ci gaba da
cewa. A dalilin kyautatawarki da abin da kike
aika masa tun zuwansa yanzu haka ya ce zai
zo a yi miki godiya, kuma har da Zarina yanzu
haka... Na dafe kirji tare da zaro ido ina
shirin yin magana muka jiyo bugun kofa. Da
sauri ya mike tare da lekawa, ya dawo da
gudu. Wallahi su ne! Take na ce Innalillahi
wa'inna ilaihi raji'un, Allahumma laa sahlan
illa maa ja'aktahu salan, wa'anta tij'alik hazna
iza'shi'ta sahlan. Na je na bude ina kara
karanta adduo'in neman sauki a kan duk wani
tsanani a zuciyata. Su Umma ne a gaba kafin
wasu dattawan mata gudu biyu, sannan shi
maimartaba wasu manyan mutane hudu na
bin bayansa. Sannan dogarawa, a bakin kofa
dogarawan suka tsaya. Rakube nake jikin
oofa, ban da kyarma babu abin da nake yi
kaina kas. Kutumar uba! Aka biga wannan zagi
da karfi, a firgicr na dago kaina. Ganin
Gimbiya na yi kusa da ni da alama ita ce
karshe wajen shigowa. Munafuka! Algunguma!!
Kowa yayi cirko cirko tare da kura mata ido,
amma ban da Umma da ta sami kujera ta yi
zamanta. Da ma ke ce matar abokin Yarima
yar iska? Makircin da kuka hada ke nan ke da
uwarki? To wallahi ba ku isa ba, ina Yarima?
Na rantse da Allah yau sai ya sake ki..... Ke
wai lafiyarki kalau kuwa Zarina? Duk wannan
cin zarafin da kike wa yar mutane na mene
ne? Shin ko kin san dalillin zuwanmu wurinta
kuwa? Cikin dattawan matan nan daya ta
katse ta da fadin haka. Ta hankado keyata na yi
taga taga zan fadi,
kawai na ga mutum ya tare ni na fada jikinsa.
Da sauri na kalle shi sai kawai muka ga
maimartaba ya zauna a duke. Ganina jikin
Yarima ya kara harzuka Gimbiya, ta fara
zubda ruwan rashin mutunci ba tare da ta yi
la'akari da wadanda ke wurin ba, tana fada
wa dattawan kobji wace ce, saboda suna da
masaniya kan maimartaba ya haramta aurena
da Yarima ko bayan ransa. Sau biyu tana
kawo harin za ta dake ni yana tarewa, ni kuwa
banda kuka babu abin da nake yi, saboda
tashin hankali. Ni ba na Gimbiyar ya fi
damuna ba, irin hukuncin da maimartaba zai
yanke a kaina kawai na ke ji. Wuri ya
harmutse, fada tsakanin Yarima da Gimbiya
su kuma dattawan wasu na goyon bayan
Gimbiya su kuma dattawan wasu na goyon
bayan Gimbiya, wasu na nuna cewa ba ta
kyauta ba ta yi rashin kunya sosai, tunda ta
aibanta Yarima gaban iyayensa. Duk wannan
hargitsin su Momy da Maimartaba ba su ce
komai ba Ganin abin ya ki ci ya ki cinyewa yasa
maimartaba daka musu wata irin tsawa da
kowa da ya yi mamaki. Nan da nan kowa ya
na'abba. Wannan ai hauka ne! Ya fada,
sannan ya ci gaba da cewa. Ba ku da
bambanci da dabbobi, musamman kai. Ya
nuna Yarima. Gabana ya yi wani mummunan
faduwa, ya kira dansa DABBA ni kuma mai
zan koma. A matsayinka na namiji yausha
zaka biye wa mace musamman lokacin da
kishi ya turniki zuciyarta? To kowa ya zauna
zan yi magana biyu zuwa uku, amma kafin nan
zan fara da abin da ya kawo mu. Ya kalli
Yarima, Ya sunanta? Kansa duke ya ce,
Humaira. Humaira zo daga nan. Ya nuna min
kusa da shi daga kasa, tsoro ya kama ni
saboda na san kaina kawai zai sare da adda
shi ne sakamakona.
Ina kyarma na karasa har lokacin kukan nake.
Godiyar da na zo yi miki ba zan fasa ba. Na
gode, Allah ya yi miki albarka. Wane ne
mijinki kuma?.saboda har da wannan
tambayar na zo yi miki, domin kullum Yarima
ce min yake yi matar abokinsa. Wayyo duniya!
Wayyo Iñna! Wani sab9n kuka ya zo na ji
kamar na zura a guje. Ko ba kya iya magana?
Na ce wane ne mijinki? Wane ne fa banda
Yarima. Gimbiya ta fada a hasale daga inda ta
ke zaune. Cikin tsananin bacin rai maimartaba
ya kalle ta.. Kada ki yarda na gane ba ki da
da'a domin za mu bata, batawa mai tsanani.
Ta zumburi baki ta kauda kai tana gunguni,
abinda ya ba wa kowa mamaki. Ya kalle ni,
Humaira ko zan san wane ne mijinki?
Na dukar da kai ina wani irin kuka, da kyar na
iya furta. YARIMA NE! Amma don Allah ka yi
hakuri, wallahi ba laifina ba ne, ni ma ba da
son.......Dakata! Bari kukan kada ki sarke.
Yanayin yadda ya fadi maganar cikin tausayi
ya sa ni da Yarima saurin kallon juna. Ya mike
tsaye, sai kowa ma ya mike, ni ma dole na
mike saboda an bar ni ni kadai a zaune.
Sakamakon abin arzikin da kika yi kin na yafe
wa Yarima, kuma na aminta da aurenku ko
lahira wani yana cin arzikin wani, to shi ma ya
ci arzikinki, domin tunda ya yi auren farko ban
taba shan riwan gidansa ba sai a nan. Sai ka
tattara matanka ka hada su wuri guda, shi zai
hada kan iyalanka. Yana fadar haka ya yi
hanyar waje, saura kuma suka mara masa
baya.
Wani yayan Yarima ya banko mini harara
wacce ta sa dole na yi kasa da kaina. Karaf! A
kan idon Yarima, ashe hankalinsa na gurinmu
da ma. Gimbiya ta fara zazzaga masifa, tana
fadar maganganu har tana ikirarin plan ne aka
shirya da ma don a ci mutuncinta. Yan baya
suka ji abin da ta ke fada, amma shi
maimartaba tuni ya fice, har ya kai a mota. Ta
yunkura tare da shako wuyana ta makare ni
jikin bango, Yarima ya taso lokacin har ta
kwada min abin fulawa ta fasa min goshi. Da
kyara ya kwace ni tana faman dukana da
harbi, ni kuwa sai kuka nake. Hayaniyarta ta
dawo da su Momy, da kyar suka fidda Zarina
gidan tana ta hauka. Jikina sai rawa yake yi
saboda tsoro duk na firgice sai bari nake. Da
kansa ya wanke min jinin ya sa auduga ya
daure da bandeji.
Wayarsa ta fara kara ya dauka tun bayan da
ya yi sallama, ban da kalmar TO babu abinda
yake fada har ya ajiye. Ya kalle ni asanyaye.
Maimartaba ne ya ce kar k8 sake ki kara
kwana nan gidan, na maida ki can gidana inda
Zarina ta ke ku..... Wallahi Kano zan tafi, ba ni
kara kwana nan garin, ban iya masifar
Gimbiya ko kadan nan din ma kana ganin ga
manya ba ta j8 kunyar raunata ni ba, ina ga
nan ware daga ni sai ita? Aure ne na yi na
Allah, amma ba zan kuma ba. Idan ita ba ta
da hankali ke ma....... Kwarai ni ma haukan
nake a kan komawa gidanka kam, kai auren
gaba daya ke bana yi, ko dole ne? Na fashe
da kuka. Da ma tun farko ni wannan masifar
nake gudy wallahu. Ya langwabe kai. Allah ya
baki hakuri.
Na hayyako masa. Eh da man duk wanda ka ji
ana ba hakuri ai an gama cutarsa. Haba
Humaira 8na hankalin ki ne yau? Daga turu na
fito karewar hauka. Na mike ina faman hada
kaya a jaka. Ya karaso murya a raunane ya ce.
Don Allah ki yi hakuri, mu gode wa Allah da
matsalar ta tsaya gurin Zarina kadai, kin ga
alherinki ne ya sanya mahaifina ya yafe mini
kan rashin bin maganarsa, shu ya sa aka ce
YADA ALHERI BAYA ka tsince shi gaba.
Wallahi.na tabbatar da lallai ya ji dadi sosai a
kan abinda kika aikata, domin ni ina tunanin
fushi da wulakanci wanda zan fuskanta a
lokacin da ya gano abin da nake boyewa, don
ko mahaifiyata ba za ta tsira ba. Shi ya sa na
nace wa aurenki don na san ke alheri ce a
wurina. Wallahi ba ki ji yadda hankalina ya
kwanta ba..... Dole ka sami kwanciyar hankali
mana, ni tunda ka ti silar tada nawa.

Xaharaddeen Shomar
Whatsapp 08168575100

Subul da baka 3 page 2


Posted by ANaM Dorayi on 05:17 PM, 21-May-15
Under: Subul da Baka
Ya yi murmushi,
"ya xa a yi na yi silar tada hankalinki?" "ban
sani ba". Na fada lokacin da nake qoqarin
rufe jakar. "Allah ya ba ki haquri, kin ga
maimartaba ya yaba hankalinki kada ki yi
abinda xai sanya ke ma ki fita ransa kamar
xarina". "dole kuwa in yi, domin na tsira da
raina da lafiata.. A gabanka ta fasa min jiki, to
ina ga ba ka nan?". "nima ai bayan idonta
gashi kina mini tsiwa mai ya hana ki rama? Ko
kin san xarina ta gane kin tsorata da ita? To
wallahi ni ba xan tare miki fada ba, domin
akwai lokacin da dole ba na nan kinga kuwa
dole ta ringa ba ki wahala, amma idan ta ga
cewar ke din ba ki tsoronta, to lallai xa ta
shafa miki lafia, don Xarina ba ta fi qarfinki ba ni
a ganina.
Abin mamaki kishiya...". "ka ga malam ni ba
fitina na xo yi ba...". "nima bana son ki yi
fitinar, amma ya kamata ki amsar wa kanki
'yanci, ki nuna ke ma fa MATA ce ba baiwa
ba. Maganar gida kuma wallahi babu inda xa
ki tafi yau a gidana xa ki kwana ke da
axara'ilunki xarina ta qarasa ki". Na fashe da
kuka, sai kawai ya shige bandaki. ***** *****
*****Tashin hankali ba a sa masa rana,
kwana 2 da komawata gidan aka kawo mini
dattawa guda 2 wadanda xa su ringa tayani
aiki, sabanin gimbiya da nata yara-yara ne
majiya qarfi, kuma aqalla xa su kai su 9 ko 10.
Qaton gida ne da babban 'gate' sannan
kowace bangarenta guda. Yau xan amshi girki
don haka magariba na
yi na fara kimtse-kimtse, 2n 6:pm na sallami
su dagwayye ana gama sallar isha ya shigo.
Na kawo masa abinci ya kalleni. "yo ina en
aikin?". Ba tare da na yarda mun hada ido ba
na ce, "sun tafi sashensu na sallame su".
Murmushi ya yi, "to dauko abincin mu tafi
sashena". Gabana ya fadi, amma ban yarda ya
fahimta ba. A falonshi muka xauna mai tattare
da kayan more rayuwa, kujerun kansu sun ishi
mu2m kallo, ban iya tsayuwa fasalta falon
amma ina iya cewa komai ya ji na more
rayuwa, hmmm! Jin dadi sabo na fada a xuci.
(kun ji mu2niyarku an kile an fara 2nanin jin
dadi). Allah sarki su inna qwalla suka kwanta
suka kwanta a idona da na tuno inda na baro
su. Na duqa xan fara xuba masa abincin
kenan naji an ingijeni nayi baya- baya na fada
qasa da qarfi, kafin na yi wani motsi ta biyo
ni da qafa tana harbi, a rude ya taso tare
da ture ta wuri guda ita ma. "ke wace irin
dabba marar 2nani ce fareeda?". "wallahi
wannan munafukar sai na hallakata a
gidannan, don uban...". fas! fas!! tasst!!! ya
wanka mata kyawawan mari guda 3 a jere.
"kar ki dauke ni sakarai, shashasha mana, ke
me ya sa kike da fitina da rashin son xaman
lafia ne? ko don kin ga ina tausaya miki
saboda abinda ke jikinki?". ta harxuqo masa
kamar ta rama marin da ya yi mata. "mene
kai din in ba sakarai shashashan ba?". ya
qara wanka mata wani marin guda 2 qwarara,
ya juya xai dauko kebul (cable) ta ko dauki
wani abin fulawa ta kwada min a goshi. "bari
in kashe ta don ubanta in ga abin da xa ka
yi".
Tana qoqarin qara rusa min shi ya riqe da
sauri. 2ni jini ya balle yana son dauko
tsumma yana tsoron kada ta qara min wani
dukan. Ya fige ta ya 2ra waje kafin ya rufe
qofa ta banko da qarfi. Ganin idan ya biye
mata ni kuma xan rasa jini da yawa ya sanya
shi qyale ta, ya nufo gurina da sauri. Cak! Ya
dauke ni xuwa bandaki sai kyarma nake ina
kuka, tsoro da fargaba sun fi yawa a gabana.
Muka fito, ya janyo wani akwati sai ga kayan
dressing ya ci gaba da gyarawa. Ta xo kanmu,
"aikin banxa aikin wofi, an asirce ka, an
magance ka er talakaka ke wa wannan
kyarmar kuma don ubanki yau na ga yadda xa
ki kwana dakinnan. Na rantse da Allah ko
gawarki ba a yi mata wanka nan dakin domin
ba na hada daki da ke, banxa talaka". Ya
kalleta a wulaqance saboda yau da fareeda
ba ta da ciki, da Allah kadai ya san illar da
xai mata, ya ce "ga ki nan talaka wacce ba
gaji arxiki ba, maimartaba da ya tilasta ya sa
na aure ki Yau saboda munanan dabi'unki na
tsiya
yana dana sanin aurena da ke, 'yar talakar da
ki ke qyama ki ka raina kuma a yau ita ake
alfahari da ita a matsayin suruka". Bai rufe
baki ba ta hargitso masa qa2war talabijin da
ke manne a bango, ta fado bisa sauran
tarkacen kallon da abubuwar glass ji kake
ratsatsatsa!!! Ya dauki waya kamar mahaukaci.
"hello sahabi kana ina? Don Allah idan kana
iya fitowa yi sauri ka xo gidana yanxu". Ni
kam ina can rakube jikin bango kaina kamar
ya bare, ga wata masassara da ta taso mini,
ko tashin hankali ne ya hana ya yi min allura,
ko ya bani magani? Oho! Shi ya fada ita ta
fada, da ya matsa kusa da ita ta nuno shi da
kwalbar glass ya
rasa inda xai billowa tashin hankalin, iyakar
qarshe ya kai. Sallamar sahabi ya sa duk suka
yi shiru daga ita har shi din "Subhanallahi,
innalillahi, Hameed mene haka ya faru? "mtsew!
Shigo idanunka su gane maka
barna da asarar da yarinyar nan tayi min, duk
goshin er mutane, marainiyar Allah...".
"shegiya dai! Domin mun dade da sanin
shegiya ce ba ubanta ya mutu ba..." "haba
gimbiya don...". "yi min shiru munafuki, ina ce
da kai aka hada baki duk abin da aka qulla.
Ni xa a yi wa makirci? ayi wa plan? xa a
qirqira dafa abinci ana kaiwa sarki don
munafunci, wallahi yau sai dai ayi wacce xa a
yi". "Me fa xa a yi bayan na shirge ki kamar
jaka, don ba xan tausaya miki ba 2nda na ga
abin naki ya wuce 2nani...". "haba yarima har
sau nawa xan fada maka ka daina biye wa
mace?". "ka san Allah na dauka wa raina sai
dai yau na kwana prison, amma lallai gab na
ke da na lalata rayuwar wannan...". In taqaice
muku, haka muka kwana a tsaye ana abu guda
1, ko sallar asuba sai da yarima ya fara yo wa
sannan sahabi ya tafi gudun kada ta qara ji
min wani raunin. Suka dauke ni muka bar
gidan, amma sai da yarima ya tare ta sannan
sahabi ya fidda ni dakin, saboda yunquran da
take yi sai ta caka min gilashi a ciki. Iyakar
firgita da kaduwa nayi, 2n ina kuka har na
koma xare idanu, ni kadai na fige kamar
wacce tayi ciwon shekara. Gidan sahabi muka
je, na yi wanka na yi sallah, na nemi ciwon kai
da masassara na rasa, har qara kan da ya yi
min wani jummm! Allah ka raba bawa da
tashin hankali da fitina. Da qyar na sha rabin
kofin tea shi ma don Hafsat ta matsa min
matar sahabi. Ina kwallonta tana goge qwalla,
ta tausaya min. Xuwa can wajen 12 sai ga su
sun dawo. Ban san me suka tattauna ba, tayi
juyin duniya ta fita na qi fita, saboda sam
bana son ganin yarima, don a ganina shine
musabbabin haddasa min wannan fitinar, 2n
farko da bai dawo rayuwata ba kamar yadda
muka haqura da juna da farko, da hakan ba
ta faru a gare ni ba. Ganin ba ni da niyyar fita ya
sa ta ce, ya
shigo dakinta ya same ni. Baqin cikin
shigowarsa ya sanya ni kuka. Ya yi shiru kusan
mintuna aqalla 8-10, kafin ya fara magana
cikin sarqewar numfashi. "kiyi haquri humaira,
na san cewa ke ba mai son magana ba ce,
ballantana tashin hankali irin wannan, amma
komai ya xo qarshe, mai martaba ya amince
da na raba muku gida. Yanxu haka har ya
bamu wani a lowcost cikin estate din da ya yi.
Don haka ya sa kika ga mun dade sai da
muka kammala komai, yanxu haka ana can
ana sauran gyare- gyaren da ba a qarasa
ba". Ke dai da ke kara2 idan na tanka kin
tanka, ya matso kusa da ni, "ko sai xuwa dare
idan kin qara hutawa nan? Na ga can din ma
ba hayaniya, sannan babu aikin da xa ki yi,
saboda su malama dagwayye na can 2n
daxun". Ko motsi ban yi ba. Ya matso tare da
xama bakin gadon.
.....Farko da kuma kullum lallai tana kan
hanya, 2nda a duk lokacin da muka hadu sai
ta nemi xubda jinina. Ka sallame ni na tafi
gida don girman Allah, bana sha'awar xama
da kai ko da da qwayar xarra ne, domin
wannan fitinar somin tabi ce yanxu aka tsoma
hannu, ma2qar ina tare da kai". "kar ki so
kanki mana humaira! Yanxu wannan baraxanar
ce xa ta sanya ki bijire min? Ki iya 2na cewa,
so da qaunar da nake yi miki ya sa na take
dokar mahaifina na aure ki saboda Allah, na
xabe ki fiye da tsinuwar mahaifina da
fushinsa. Duk wannan baraxanar fareeda ta
sami qwarin gwiwa ne daga wurinki, don ta
fahimci kin kamu da matsanancin tsoronta.
Ina qara fada miki, ki tashi tsaye ki qwatar wa
kanki 'yanci, na tabbatar fareeda ba ta fi
qarfinki ba, kawai kin sa wa ranki tsoro ne. Ga
babban takaici ni din da take yi domin ni,
saboda ta fahimci irin son da nake
yi miki baki nuna damuwa a gare ni ba,
babu wata kulawa. Ki nutsu ki kwantar da
hankalinki ke ma ki nuna mata lallai ke ma
mace ce, saboda duk wannan haukan da cin
mu2ncinta ni ba xan sake ta ba domin
al'adata ba ce sakin mace, duk da ba ni
sonta, kuma ba xan sake ta ba ballantana ga
dana ko diyata da ke jikinta". Ya miqe "xan
jira ki a waje ki kimtsa mu tafi". Yana fita na
koma na kwanta wajen mintuna 5 sai ga
hafsat ta shigo, salati ta kama yi tana tafa
hannaye. "kai jama'a, wai humaira kwanciya ki
kayi? To wallahi tashi ki bi mijinki". Na miqe
ganin ta dauki abin da xafi. Ta biyo tana fadin
"wallahi ba ki da wayo yadda kika dace da
mai qaunarki haka, duk wannan fitinar bai
girgixa shi ba, amma kike ja baya da shi?
Wallahi da ni ce wani sabon salon shafin
soyayyar xan bude, kuma sai a gaban gimbiya
xan nuna don ta ji haushi". Nayi mata banxa
saboda na fahimci bata
gane irin salon masifar gimbiya ba. Xaune
yake cikin motarsa anaconda sahabi na tsaye
jikin taga ban san abinda suke tattaunawa ba.
Yana ajiye ni ya juya wai xai je gida, umma na
son ganinsa. Kai daure har lokacin da bandeji
a goshina, su dagwayye suka tarbe ni suna
masu jajantawa, tausayina fal a fuskarsu. Nayi
murmushi lokacin da na sami kujera na xauna.
"ashe duk kuna jin wannan fitinar?". "qwarai
kuwa ranki ya dade, wannan tashin hankalin ai
babu dadi yau kam na kusa da ita ya shiga 3
saboda yarinyar nan ba ta da kirki ko alama,
rashin ragowa a ba ya da dadi a rayuwa".
"hmmm" kawai na ce. Wayata ce ta dauki
kuka, nayi saurin dubawa don idan yarima ne
wallahi ba xan dauka ba. Sunan inna na gani,
wani irin dadi na ji har cikin raina, na kalli
dagwayye.
"ina ne dakina?". Ta nuna min da hannu.
"ga shi can". Na miqe tare da daga wayar
saboda bana son maganar gabansu duk da
sun santa. "Assalamu alaikum, inna kashe in
bugo miki kar a cinye miki kudi". "a'a barshi
ina da isassun kudi, yarima ya turo min kati
sosai, da ma wancan bai ko yi rabi ba... Duk
kuna lafia ko?" "da sauqi dai inna". Na fada a
hankali cikin muryar damuwa. Hankali tashe
ta ce "me ya faru ne? Ko mahaifin nasa ya
gano matsalar ne?". "a'a inna ko daya, shi
mun daidaita". Na fada mata duk yadda aka
yi "to me aka yi yanxu kuma?". "gimbiya ce
inna wallahi bana iya masifar wannan matar".
"haquri xakiyi, watarana sai labari". "inna ita
fa har gabansa yi min take yi, ga shi tana
iqirarin sai ta hallaka ni".
"duk kishi ne babu abinda xata yi miki
wanda Allah bai miki ba". Kamar in yi kuka,
wai me yasa inna ba ta ganewa kullum idan
ina kwatanta mata, ga shi ba na son fada
mata raunin da ta ji min kada hankalinta har
asmarta ta taso. "xata daina kiyi haquri dama
xama ya qunshi haka ga masu sabon aure,
kuma na hore ki da kai qararta ma2qar
abinda ya faru tsakaninku bayanan. Yana fada
miki baya sonta a baki, wallahi ba ki san
xuciyarsa ba musamman yanxu da take dauke
da ajiyarsa, duk yadda yake sonki yake kuma
dokinki da kin kai masa qorafin matarsa xai ji
kin fara sure masa. Ko 2nkararsa kika yi da
muhimmiyar magana ba xai wani baki
kyakkyawar kulawa ba, domin xai yi 2nanin
qorafinta xa ki kawo masa. Rayuwar aure
humaira haquri ake yi, kowace mace baki san
irin xaman da take yi ba nata abokan xaman,
amma tayi xamanta...
Haka ki rike sirrin mijinki kuma ki kyautata
zamantakewar zamanki da mijinki.munanan
lafia kalau muke kuma muna cikin kwanciyar
hankali dajin dadi alhmdllh kiyita godewa
Allah ga mansura can yar uwarki mijin
dukanta yake watanni nawa da aure amnan hr
ya saketa saki 3 wanda Allah ya
haramta..yarima ne tsaye bakin kofa ya
kuramin ido cikib tuhuma na da dauke
fuska..Allah ya kyauta inna zan kiyayae insha
Allah inyi yadda kikace..yawwa toh Allah yayi
miki Albarka ki dage da addu'a kada yi sanya
da ibadarki,nace toh a gaushe da mutanan
gidan nace zasuji a gaida su sumayya..ke kika
buga mata ko ita ta bugo miki ya tambayeni
lokacin da na ajiye wayar idonsa kyam a kaina
wallahi na tsani kallo, na fada a zuciya
amma a fili sai nace ita ce ta kira ni, wai me?
kokwanto na me ni da uwata? ni ma ai uwata
ce ko? na zaro ido ashe ba a zuciya nayi
maganar ba,na lura ta yi masa zafi sai na hau
kame- kame yayi saurin tarata cikin kunar rai
"don me zaki fada mata rikicin da ake ciki,ko
duk salon rashin kwanciyar hankalinta ne kike
bukata?
rainin hankali duk duniya akwai wanda ya
kaini tattalin kwanciyar hankalin inna. "mst"
ya buga tsaki wallahi humaira kina da matsala
yasa kai ya fice rai a bace mamaki ya kamani
ni na bishi da ido. kamar abin jira wayata ta
kara kuka nayi saurin ridota na ga sunan
amira a hanzarce na daga domin ina da
bukatar nemanta ni kaina. hello kira ni don
allah kiran gwandala daya ce ba kudi
tuni ta mutu alamar kwandala dayar data
ambata an cinye ta babu bata lokaci na kira
ta. kaji manya ta yarima bada kanki a sare.
nayi murmushi nace ke ni bana son iya shege
da man wallahi ni ma ina da niyar kiranki a
yau dinnan. dan allah? nima tun dazu nake
neman ki bata shiga ba daman na fada maki
an sanya rana nan da wata shida bikin yayi.
a'a toh allah ya sanya alkhairi ya kuma nuna
mana lokacin lafiya. safwan kuma ya sami
addmission saudi arabia zai cigaba da karatu
yace shi da nigeria har a bada . nace allah
sarki, amira baki tambayata ya zamana ba ?
nayi mata tambayar dan na kau da wanchan
zancen. hmm ai ko ranar juma'ar nan da abin
ya tuko ni har zan kira ki sai na ga cewa ke fa
har yau baki ce min komai ba toh ni
kuma binciken me zanyi? nayi murmushi,
hmmm ke dai bari na kwashe duk labarin kaf
na fada mata sanna na cigaba da cewa "wai
amma duk wanna fitinar ni yarima yake gani
da laifi shin amira ina ni in fada da gimbiya
lillahi warasuluhu? "tabdi" ta fada da karfi.
nace maccen da kemin wannan illar har
yaushe zan biye mata ranar da ta kunso wuka
ta luma min fa? lallai kam ta kara fada "yanzu
haka fushi yake yi da ni,wai na ki sakin jikina
da shi yana ganina da wani gaggarumin
laifi."ikon allah ta fada tana kara jinjina
maganar. "ba ma kisan ina cikin matsala ba
sai na fada maki cewa ,yanzu ya gama min
fadan don me zan sanar wa inna,kuma wallahi
amira ni ban ma fada mata gimbiya ta ji min
rauni ba shine yayi fushi ya fita, kiji faa? "ke
kam bone ta ciki humaira. wallahi
kuwa na fada a marairaice. to iya gimbiya ta
san inda ka maida ke ni yanzu? ni ban sani ba
amma kema kin tabbata komai daren dadewa
sai ta gano ni matukar ba baruwa nayi da
yarima ba. ta ja dogon tsaki tace " ke wallahi
bnaza ce saboda wata banza sai ki rabu da
mijinki maimkaunar ki haka humaira? wannan
furuncin naki fa zai sanya matsala ta afku
tsakaninki da yarima. wai inna ta baki labarin
yadda ya mayar da gidan ku? gabana ya fadi
nace " kamar ya fa? tace "wai baki sani ba?
ko daya ni dai na rabe da kullum mukan yi
waya da inna sai ta ce kada na gaji da yiwa
yarima godia" "lallai to wallahi kin san gidan
honorable? na hanga nace kwarai, saboda duk
shiyyar unguwarmu babu gidan daya kama
kafar gidan honorable nura nasimat." to ko
kofar gidan ku be kai ba a yanzu wurin kyau
da tsari ke yan aikin inna biyu fa da me mata
abinci da me mata shara da goge goge. "
tsakanin ki da allah amira"? " na rantse da
allah ta fada tana yar dariya. shiyasa nace
maki wlh ki daina wannan furucin , yarima
baya taba iya rabuwa da ke. da yayi maki
fada yanzu har yai fushi ai da sai kiyi tunanin
cewa inna fa mahaifiyarki ce amma ya nuna
damuma fiye da taki, ke bama abin
alfaharinki ne ma kina in a wanna zamanin
akeyin fito na fito da surakai? to wallahi ki
gaggauta zuwa ki bada hakuri sannan kada
matsalar gimbiya ta sanya kiyi watsi da
masoyinki, baraka ta shiga a sami rauni
wannann shine babban burinta. nayi kasa da
murya " amira nagode allah ya bar zumunci".
Amin amin, na gode sai munyi magna. na
dafe kaina tsananin tausayin yarinma ya
mamaye zuciyata kmr kaina zai bare. a
hankali na mike ,rabi na goge wasu zannuwan
gado nace "ina yarima ne ko ya fita?" "A'a
yana dakin chan" ta nuna min da hannu na bi
sirdaden da ta nuna na sa hannu na murda
gaa mamakina naji ta bude. na shiga sai na
ga tankamemen falo ne daa yaji kayan gayu
irin na zamani. na hango kofa daga yamma
alama nan dakin yake na hanzarta isa tare da
budewa. jin an bude kofar yasa shi dagowa
da sauri na lura da idanunsa sun yi ja matuka,
shi dai kam bacin rai na haddasa masa jan
idanun, na fada a zuci saboda yadda na san
idanunsa farare tar har wasu ruwa kake gani
kwance saboda haske. ganin nice sai kawai ya
maida kansa ya
kifa kamar yadda yake kwance ruf da
ciki.tausayinsa ya kamani ,naji kamar na dago
shi na rumgume a yadda naji sonsa ya karu a
raina. sai dai miskilancina bazai barni aikata
hakan ba, na zauna bakin gadon gab da
kafafuwansa ko motsawa bai yi ba. na rasa
inda zan fara, toh me zan ce masa? daraba ta
fado min. "amma yarima wannan kwanciyar
ce fa aka haramta saboda ta yan wuta ce
babu kyau yin ta" a hankali ya juya amma sai
ya bani baya ya kalli can. raina ya bani fushi
yake yi." allah ya baka hakuri" na fada a
hankali. bai dai ce komai ba bai kuma motsa
ba, nan da nan kunya ta baibaye ni naji duk
na tsani kaina. na tuna irin dizgi da wulakanci
sa da gimbiya ta sha, ba shi da wuyar dizgi ai
sai na raina kaina. Na yunkura zan tashi gwiwa
sake ina
nadamar kawo kaina, sai kawai naji an ruko ni
ta baya."ina zaki je kuma? haka ake lallashin
maigida idan yayi fushi?" na sunkuyar da
kaina, ya buga tsaki "ni di wanna kunyar
wallahi tana kwarata....zo na koya maki yadda
ake bawa maigida hakuri" ya shiga yimin
cakullulo tun ina zillewa har na hau kyalkyata
dariya sai kawai ya kura min ido, nayi saurin
rufe idona shi kuma ya kai bakinsa ga nawa
nan da nan yaren ya sauya.******** Cikin
kwana uku ya bude min ido ya koya min son
sa da tarairayarsa muka bude sabon shafin
soyayya.na yi nadamar rashin sakin jikina da
nayi tun farko na gane cewa lallai ba karamin
so yarima ke min ba, ban da shagwaba babu
abinda yake zuba min , duk yadda na wasance
dole wani abun idan yayi min shi sai naji kunya,
shi kuwa banda
zagi babu abinda yake yiwa kunya, wai kunya
na kwarar sa (mata a rike kunya domin ita ce
adon mace, wallahi duk yadda kuka dade da
miji ki rika nuna kina jin kunyar sa wasu
lokutan musamman lokacin da kuke kebe
kudai yana karawa mace martaba da kima a
idonsa). Kullum cikin zabga karya yakeyi a
asibiti cewar yayi tafiya ne maimartaba ya
aike shi. Washe gari ya kama zai koma gidan
gimbiya kamr kar ya tafi nice me kwarin
gwiwar bashi magana, da kyar ta tafi wajan
karfe biyar na yamma. kullum yana zuwa da
safe mu gaisa da marece kuma ya dawo yi
min sai da safe, ina lura dashi sam
walwalarsa ta sauya amma sai kawai na share
na san shi da mutuniyar ne ni dai allah ya min
alamnashara. Rnar da zai dawo ina ta shiri
sai ga shi ya shigo da sauri ina zaune bisa
kujerar gaban madubi. Humaira am sorry kano
zanje yanzu aka
aiko maimartaba baban gimbiya bashi da
lafya har zaa fidda shi waje shine zan kai su
umma suyi masa allah ya kiyaye hanya yanzu
haka gasu chan suna jira na. nan da nan halin
namu ya motsa wato KISHI wani kallo na fara
jefan sa da shi tukun kafin nace "duk gidan ku
a rasa direba sai kai?" abin mamaki sai naga
kamr ransa ya baci. "haba humaira ina laifi
dana ma zo yi maki bankwana da kiji cewar
na tafi ba?" yanzu haka na fada maki ga su
maimartaba can a waje suna jira na idan ba
ke ba wazan wa haka?" ai naga kana ta faman
kyarma ne zaka gdan surukai" kema haka ake
kyarma idan zaa gidan naki.... maganar ta
maqale daga karshe alamr SUBUL DA BAKA
yayi. in shirin maida masa sai kawai ya fice,
wani gululu ya taso min. Banyi barcin kirki ba
ranar, kagara nake
ya dawo na amayar masa ta cikina. haka
abinci ko ruwa na kasa sha. har yarima ya is
aya wulalantani abinda kawai nake nanatawa
araina kenan. kwance nake daki naji shigowar
sa na mike tsaye tare da rike kugu yana
shigowa ko rufe kofa beyi ba na hau masifa
daman ance me shiru-shiru be iya fada ba.
"da zaka fada min magana kan wata banza na
taba aiken ka zo?" ko kuwa na taba aiken ka
wajan uwata....." haba humaira wai maganar
bata wuce ba?" toh kiyi hakuri ni da wasa na
fada."eh din ai da wasan daren ake fadawa
wawa magana. "duk naji kiyi hakuri dan allah
wai dole sai ka zuna da ni ne?nace bana yi ko
dole ne? ya kyakyale da dariya dama na lura
sai gumtseta yake yi. Raina ya kara baci wato
ya maida ni mahaukaciya sai naga ya fara
rawa yana waka 'ashe ana kishina ana kauna ta,
a'a lallai yarima taka-taka' Ban san lokacin da
nima na kyalkyale da dariya ba,saboda ko
waye sai ya dara idan yaga yadda yarima ya
dage yana kwasar rwa. ya daina rawar tare
da daure fuskar nan irin ta shagwaba. "gaskia
ni dai a cigaba da fadan bana so a daina " ni
dai na cigaba da murmushi, yana matso yana
yar dariya "muguwa na gane ki ashe haka nan
ake wani basar wa kaunar yarima tayi katutu
a rai?" nayi murmushi "eh din an ji" ya
rungumo ni "me aka ajiye min?" ina shirin
bashi amsa wayar sa tayi kara ya zura hannu,
sai naga ya sake ni da sauri ya latsa tare da
sanya handsfree yayi kasa da murya "Allah ya
taimake ka" "zancen banza zancen wofi, yanzu
nake
jin labarin ka raba gida, wannan ai shirme ne
lallai ka hanzarta hade matanka waje guda tun
kafin raina ya baci,yaushe zaka iya adalci
matukar basa tare? anya kai jarumi ne yrima?
ba ka iya daidaita matanka?oh allah wadarai
a yau nake so ka maida wacce ka ware maza-
maza. yana gama fadin haka ya kshe wayar.
Gwaram! na koma na zauna tare da dafe
kaina . ya kalle ni "kiyi hakuri sai ki tashi mu
tafi kar abin yazo da bacin ran sarki" Wayyo
ni humaira Wayyo Allah na. Tunda muka fito
gbana yake faduwa ni na tabbatar idan aka
auna jinina a yanzu ya kai dari biyu da wani
abu. har muka isa ina rike da kaina shi dai bai
ce komai ba. Komai yana yadda na barshi su
rabi suka shigo min da akwatuna na. Nayi
tsaye sai zare ido nake ina kyarma ya shigo
da sauri. haba humaira duk kin bi kin tada
hankalin kan waccen yar iskar. Bai rufe baki
ba sai gata "Don ubanki har kina neman raba
ni da shi bayan kin samu kin shigo?" Bata rufe
baki ba ya wnka mata mari uku a jere,sannan
ya kwale belt ya fara tsula mata ta duke kawai
tana kuka tana faman karewa. Na rike shi
"dan allah ka kyale ta,wayyo ni humaira" na
fada ina kuka. bai saurare ni ba na janye shi
baya ta sami halin mikewa tsaye ta nuno ni da
yatsa "wallahi sai na rama kanki shegiya" zai
kara damko ta tayi waje da gudu. tana fita
yaranta suka boye saboda duk sunji abinda ya
auku. ya kalle ni a fusace "Haka zaki yi mata
duk ranar da ta kara zuwa miki ida yar iska"
ni dai a sukurkurce na kwana,washe gari ya
fita da wuri saboda zai je tiyata. na kulle kaina a
daki har kusan karfe
daya saura sai da yunwa taci karfina sannan
na fito. "Rabi dan Allah kawo min tea" tace
"to" tare da juyawa. ni bana sha'awar wani
yayi min aiki amma babu yadda na iya
saboda masifar gimbiya. Ganinta nayi kamr
an jeho ta, nayi saurin mikewa tsaye ban
ankaraba ta rufe ni matsiyacin duka na dinga
kokarin rugawa amma ta babbake ta hani ni
wucewa. Tun ina motsawa har jikina yayi
tsami ni dinga rizgar kuka. Sai da ta barni
kwance tukun ta fita. Rabi ta shigo dauke da
tire duk jikinsu yayi sanyi "Sannu ranki shi
dase,sannu!" Dagwayye ta fada lokacin da ta
ke kokain daga ni ta maida bisa gado. Rabi ta
kalle ni "Wallahi sai kin tashi tsaye gidan nan
lallai gimbiya kwararki za ta ci gaba da yi dan
bata fi karfin ki
bakawai kin sawa ranki tsoro ne" Shiru kawai
nayi masu, fuskata tayi jawur saoda duka ga
shi gefe daya ya kumbura . Na samu na kurba
ruwan tea din sannan na sallame su. karfe
udu
yarima ya dawo hankalinshi yayi mugun tashi.
"Himaira lafiya me ya same ki haka? na
langwabar da kaina sai kuka. "Badai fareeda
bace ko?" me tayi maki?" nan ta shigo"?Duk
ya kidime ya rude, nayi saurin girgiza kai
"Faduwa nayi a bandaki silbi ya kwasheni...."
Subhanallahi, Rabi,Rabi!! ya daga murya kamr
ba shi ba sai gata da gudu "Don me zaku rika
wanke toilet ba ku gogewa? maza je ki tsane
duk wata lema da ke ciki". sumi-sumi ta
wuce. "kin sha magani?" na girgiza kawai
saboda jikina ya gama yin tsami. wannan
fitina har ina? cikin wata tara amma be hana
gimbiya tashin hankali ba. Da Allah ya tashi
taimako na sai gashi washe gari ta haihuwa
da karfe uku na rana. A yadda su Rabi ke fada
min tunda aka ce mata mace ce take kuka har
suka bar asibiti. Nayi murmushi saboda ni
farin cikina na samu sauki.Abin karin tashin
hankali sarki yace a bar yarinya ba ai an kaita
fada ba. ni dai ina bangarena, wanda ya shigo
maraba wanda be shigo ba bana neman sa.
Hidima aka yi sosai an sha shagali ni ma ba'a
barni a baya ba, ko leke ban leka bangaran
gimbiya ba. yarinya taci sunan Fadimatu
Zahra'u.
*** ***** ******
Maryam yar uwar yarima ce, jininmu sai
ya hade da ita kwarai dan a daki na ma take
kwana ita da wasu yan tawagarta. Bayan suna
da kwana biyu na aiki rabi gurun su umma ta
kai masu abinci, ita kuma dagwayye na baya
tana wanki, sai ka gimbiya a harzuke. "Toh
munafuka an fada mana kina tsalle kina murna
an haifa mace,to dan ubanki matsiyaciya ke ko
haihuwar ma baza kiyi ba" Na zaro ido cikin
tsoro da mamaki nace "Wa? Ni? Wallahi
billahi karya....Ban rufe baki ba naji saukar
wani lafiyayyen mari. "Ni zan maki karya
shegiya?" na dafe kunci. "Wallahi ban ce
ba,haba ya zaayi?" ta kai min harbi a cinya
har sai da na tsugunna. "Dan allah gimbiya
kiyi min rai.wannan masifa ta ishe ni, wai ya
kike son na yi ne? Me zan miki ki kyale ni?" Ta
harzuko min "Ina son ki kyale yarima
ki fita rayuwarsa ko kuma wallahi na kashe ki
na kashe banza" Na rushe da kuka. "Yace bai
sakina,bai kyale ni..." "Daure ki akayi da baza
ki tafiba makira?" na baki kwana hudu idan ba
ki bar gidan nan ba wallahi sai dai uwari ta
sake haifo wata mayya kawai". Tana fadar
haka ta fice. "Dole na bar gidan nan" na fada
a sarari tare da shiga daki ina laluben waya.
Ban ga laifin gimbiya ba saboda gaskia ta
fada,ba'a daure ni ba, gidan nan dole in
kama gabana kwana lafiya yafi. Na dauki waya
na latso number Amira, bugu daya ta
shiga,ringin biyu ta dauka."Ta yarima ba da
kanki a sare" kirarin da take min kenan a
kullum da ta dauki wayata,ko da kuwa ita ce
ta kirani ina cewa hello zata fadi haka.
"Hmm" Na fada kawai.
tace ya akayi mutuniyar, hmmm humaiki kimin
magana na sani... AMeera guwa xanyi, saboda
me?? Nakwashe duk yadda mukayi da gimbiya
nasar daita, kinga tunda har tabani zabi gara
kawai... Ta kunduma wani zagi lalle humaira
agaisheki, wallahi yau nakara tabbatarwa
cewa saunace ke, haka zaki zauna tana
cutarki, lallai ki kwatarwa kanki yanci tunda
wuri, nayi mata me?? Nafada ahankali,
kiwanka mata mari kuma ki tabbatar mata
kindaina jin tsoronta.. Hmmmmm.... Nafada
kawai, au bazaki iyaba kenan?? TO wallahi
karki kara kirana akan matsalaki. Idan azaba
ta isheki seki nemawa kanki mafita ameera ina
gudun kada aga zakewata kituna
matsayina da tushena kada naje na debowa
kaina masifar dazatafi karfina. Fada zakiyi ne?
Nace fada zakiyine? Bata hudo miki dazuwa
miki idan yarima baya nan ba? To kidaki
shrgiya kuma kiyi shiru muga idan zata fada.
Nasaki ajiyan zuciya, to ameera nagode. Zan
jarava, nayi agumi, wannan jarabar dayawa
take. Atunanina taga banida halin fitane yasa
takara dawowa, wannan karan ma tsautsayi
nafito kenan bawa dagwaye zanin gado, tana
shigowa tamaida kofar baya ta rufe, gabana
yafadi, na fella da gudu zan fita ta kofar baya
tarigani isowa tana kokarin kullewa, kafin in
ankara, ta shako wuyana, tana neman
makogwarona, har ga allah bani niyyar fada
da gimbiya amma danaga tana neman
rabanida raina, bansan sanda na wancajar
daita ba abinka dame hakuri
nayi zuru!! inna kawai nake tunawa idan
gimbiya bata tashiba, nafashe da kuka
nashiga uku! ashe surabi da yaran gimbiya
suna tsaye kaina bansani ba seda naji daya
tace..hakanan zaki tada hankalinki dimin ko
kotu akaje bakda lefi, saboda taddaki tayi har
gidanki, nayi saurin daga kai. Wallahi
nibansan naiya fada haka ba hasalima
nibanida abokin fada aduniya. HAba gimbiya
munsani aim duka danaji banbarakwai sena
daure nace gashi yanxu tajanyomin batacciya,
ina fadin haka wayata tafara kuka inadubawa
naga yarima, bugun zuciyata ta karu batare
dabace kimai ba nakara akunne na hello
humaira.. Hum nafada,, kina gidane,
huum nafada ahankali. Lafiyarki kalau koh ko
akwai abinda farida tamiki? Babu nace
atakaice, kin tabbata? Um. To me kika wa
mata tayi irin wannab dogon sumar? Sena
fashe da kuka ina fadin tsautsayine wlh, itace
ta hayemin da fitina taki ta kyakeni, bace
mata vanason fada tunda namata alkawarin
zan barmata kai kamar yadda ta gargadeni,
mtschw, sekuma ya ajiye wayar. Haba ranki
yadade dan me zaki tada hankalinki tunda
kunfara kwatarwa kanki yanci, walh kidage kiyi
maganin gimbiya, aikinmayi kokari. Sannan
duk abinda kikewa yarima na kyautatawa karki
fa, dole ki
rashi ki kwatan wa kanki yanci, Allah ne
yabaki babu me kwace miki, mutunciki yasuya
miki duk wannan darajar. Shiru kawai nayi ina
saurarinsu idan wannan takai aya se wannan
ta cabe. Karfe 4 yashigo da kasaitarsa, ina
falo yashigo duk nayi firi firi. Kallo 1 yamin
yakawar dakai. BAn ruwa insha yafada
batareda ya kara kallona ba. Ina bashi
yahada da hannayena yajanyoni jikinsa. Wai
lafiyarki haka, duk kin wani firgice, meya
hadaki da farida amma babason kuka yafada
saboda ya lura idanuna sun cika da kwalla.
Batareda na boye masa komaiba na zayyana
masa jomai daga farko har karshe, yaja
dogon tsaki, aidama seda kowa yayi zaton
haka. Musamman da sahabi yabada shaidar
nan ya kwashe tashi yasa ran maimartaba ya
baci yayi min fadan da babu
gaira, wai bani adalcine shiyasa, har yau
yakasa gane rashin tarbiyyar yarinyar ne, har
yana barazanar babu wacce zan rabu da ita
cikinku. Dle indaidaita kuzauna lfy, bansan
lokacinda nace tabdi ina!! Yayi dariya, kina
ganin dawuya ko, nasunkuyar da kai, ai ina
hango matsalar ne. Kuma wlh me sauki ce,
kinsan meye saukin? Na girgiza ka, kece zaki
bi min daita, Allah yaga zuciyata ba nayi miki
haka bane da niyyar ina tsoronki kema,
nandai baa kano bane balle in nuna miki
karfin mulkin sarauta, ita ma a karkashin wata
masaraurar take dole tayi
biyayya. Nace to. Bani abinci inci, zankoma
asibiti. Seda nabari yagama sannan nace ko
inzo muje nima indubota. Yayi murumshi, ai
harta dawo bazakije ba, kuma ina gargadinki
da wannan tausayin kiboye shi koda tadawo
kada ki nuna mata dan zata kara samun wata
barakar. Amma idan kika shareta lalle zata
fara tsorata da alamuranki. Shiru kawai nayi
ina mamakin irin wannan zuga ta yarimam shi
baze kashe wuta ba sedai ya rura? Nifa anawa
tunanin kenan, kullum sauraron dawowarta
nake, sgikuma innatanbayeshi yaushe zata
dawo seyace min tana can dai, nama amira
waya danneman shawarta ga mamakina duk
magabar dayace irinta yarima. Haka na
santawa sarautar Allah ido ina sauraron
dawowarta. kwana2 natashi banajin dadin
jikina raina yata
baci zuciyata tana zafi, tun bandsmu ba har
abin yafara bani tsoro, inyita neman fada
dashi amma baya yarda yabiyemin, ina zune
afalo naji hayaniyar dawowar gimbiya, banji
faduwar gaba ba kamar baya, shuru bata
shigo gidana ba kamar yadda nayi tsammani
har kwana 4. Ranar jumaa yakama agidanta
yake bayan yadawo masallaci yakawo min
huduba wadda yake tagomin daita duk sati.
Lokacinda yashigo ina wanka seda yajira
nafito sannan. Ashe tayi zargin wani abu,
bayan yafita nakoma daki ina gyaran wadrobe
kawai naga mata, waike dan ubanki me kike
nufi ne? Dane kike takama banza talaka?
Bansan lokacinda nacire dankwalina nadaure
kugu na daura hannu duka2
abinda kike nufi nima shinake nufi kema dan
ubanki, tazaro ido cikin mamaki, nikike zagi?
Anzageki koda abinda kike ganin zaki iya? To
bari infada miki bani tsoronki, ko kifitarmin
gida koyauma kiy kwana asibiti, koki bakunci
lahira don lallai cikin 2 nan se anyi 1. Sakarai
wadda batasan abinda takeyi ba, ke baki
zauna lfy ba baki bar wani yazauna lfy ba, a
sarautar da kike takama dashi raini da rashin
tarbiya ne salon mulkin naku? Ke ko kunya
bakiji, agaban baroron dakike mulka mijinki
ke dizgaki saboda dakikacinki har dukanki
yakeyi amma kinkasa yiwa kanki karatun
tanutsu? Ni diyar talakawan dakika raina gashi
nazo nakwace fadarki awurin iyayen mijinki
dakike taka suna sonki? Kingani riba 2 goma
da ashirin, dan haka kirika addua Allah maji
rokon bayinsa ne. Nizaki fadawa Allah??
anfada miki farida ko da yadda zakiyi dani
ne? Na matsa kusa daita, ina jiranki! Ta
girgiza kai, lallai zaki raina kanki ta juya tafita.
Na fincikota ta baya kedin banza aisedai ji
raina kanki a gidan nan, kuma daga yau zaki
gane shirun da nakeyi a baya ba tsoro bane,
zaman lfy ne nake neman amma tunda
kinkasa ganewa shege kafasa. Sakar min riga
tafada tana hararata. Na ingizata baya tareda
rufe kofa ta. Nadafe kirhi, oh waini yauke
zazzagawa gumbiya masifa tayi shiru? Lalle
yau na gano abinda amira da yarima ke nufi,
ban fada masa yadda mukayi daita ba danko
nuna masa tazo gdan banyi ba. Da marece
muna kwance kan gado abinka da lahadi na
langabe ina shagwaba.
nidai yau sonake muje baya musha iska,
zaune yatashi zumbur me? Namaimata ya
watsa hannu ok lets go. Cikin raina nace aikaji
shi komai turanci idan zaa kashe ni ban iya
fassara abinda yake nufi, amma dai nafahimci
abinda yake nufi, na umarci abimu dakayan
marmari, ni nariga nabashi abaki musamman
dana lura tagan gimbiya abude. Shikuwa yana
mamaki amma isa da miskilanci yahana ya
nuna min. Yana gamawa nace to yagoyani yayi
yawo dani cikin lambu, zauyi gardama nafara
dira dira ina shagwaba irin na yara idan akaki
musu abu. DUK ya rude ya diririce koda ya
sureni yayi zagaye 2 dani se yayi cikin gda da
gudu, ALlah yatemakeni su rabi duk suna
sashensu. SEya kasance duk ranar aikin a
lambu muke wuni gashi bayan dakin Gimbiya ne
duk abinda yake faruwa tana ji wannan abu
yana
kona mata zuciya.
Da wani yammaci ne su Rabi suka kawo min
'Yar
gidan Gimbiya raino in ji Yarima dan na saba da
'yar shi, naji tsoron karba ma saboda kada wani
abu ya faru a zarge ni, su Rabi suka ce dani
dawani abu yafaru muzamu zama shaida
agareki. jn haka yasa na mi,a hannu na
amsheta, tun daga ranar kullum se ankawo
min ita nima haka nake aikowa daita idan har
tayi kuka ban taba yarda naje gidanta ba.
ranar da yarima yacemin zeyi tafiya be fada
mun inda zeje ba ranar baa kawo hauwau ba
na tura rabi wurin yar aikowan karta bari
gimbiya taganta taji ko lfy? DUK naji babu
dadi musamman daaka kwana 2 ana na 3 ne
ina dakin yarima ina gyarawa dayake ranar
zan amshi girki, senaji ana kwankwasa kofa,
atunanina cikinsu rabine senace shigo mana
menene. Ahankali tabude kofan gavana yafadi
yau kuma dame tazo
don Allah kifita ke bakijin komai kullum
masifa ke kawoji gidana amatsayinki na
babba?? Ta girgiza kai senaga kwalla sharr
duk se jikina yayi sanyi. AHAnkali tafara
magana, zuwa nayi inbaki hakuri akan abibda
yafaru abaya sannan inmiki bankwana domin
nafahimci lalle yarima kaunatace bayayi.
Tunkafin na aureshi nake shan wahalarsa
gashi har yau ban taba jin wani dadi daga
gareshi ... Kai dena fadan haka halinki shiya
janyo miki wannar tsanar kuma laifinki ne, tun
farko kinfahimci baya sonki kamar yadda ake
tilasta aurenki gareshi, memajon kidage da
biyayya da kyawawan dabiu se kika nuna ke
YAR SARAUTA ce alhalin shima haka gaba da
baya yanzu haka dazaki gyara halinki yarima
me saukin kaine
aidakyarne, domin nitunda ya aureki be
karayin kwanciyar aure dani ba, setayi shiru
da alamun SUBUL DA BAKA tayi seta bani
tausayi saboda yadda duk ta sukurkurce akan
nadamar datayi, setaci haba dacewa rashin
iya zancena da yadda nake magana cikin
gadara yasa yarima yakara tsanata iyayena
danake samun sauki awurinsu sun tsanenu,
kedin danakeyiwa kinkai karshe. Seta fashe da
kuka hakika shaidan ya rivace ni laananne,
Allag shiyasa shiyasa na yanke shawarar
hakura da yarima dan baze taba sona ba.
Injiwa? Nafada, walh inda dagaske kinyi
nadama gumbiya yarima ze kaunaceki, nikuma
zanyafe miki duniya da lahira nima kiyafe min,
tashare hawaye, ga mamakina sebaga ra tashi
ta tayani gyaran dakin, dakanki kikeyi ina
masu aikin??
nayi murmushi aini da dakin mijina da
abincinsa bame tayani, nike gyarawa nayi
masa girki da kaina. DAgas? Nace Allah. Lalle
zan dunga zuwa daukan course. SAi magariva
takoma gidanta. Kamar inva yarima lbr sebati
shiru dan ze iya gwasalebi koya karya mata
tsari. Washe gari wajen 11 segata da hauwau
muna falo muna karin kumallo. Kida tashigo
setayi turus shikuma ya daure fuska. Alanar
sarautar ta motsa, nati kamar ban lura dasu
ba namike ina yar dariya oyoyo hauwau.
Nakarbeta tamiko min ita dama ita nakawi
miki. Tajuya zata kima sena kamo hannunta Ai
tunda kinzo sai munyi karin
kumallon zaki tafi. Da alama taji dadin hakan
saboda batayi gardama ba shi kuwa wani irin
kallo yake yi mana cikin tuhuma da zargi. "Ya
akayi, mene ne haka?" Cikin zolaya na
kalleshi. "Yo mun shirya da Yayata..." "Mtsss"
kawai ya buga tsaki tare da mikewa zai bar
wurin. Na sha gabansa "haba Yarima, mutum
yayi laifi har ya gane ya tuba amma..." "Kin
tabbatar da gaske take, ko sharrin wannan ce
kika manta?" Kafin na kara magana ta zube
kasa tana rokonsa har da kuka, ni ma sai na
kama kukan saboda tausayi. Kai rayuwa abin
tsoro ce, Allah ka sa mu dace, amin! Ganin
munyi masa rubdugu yasa yace, "shikenan
komai ya wuce". Yana fadar haka yayi
ficewarsa babu wacce ya tsaya ya lallasa. kusan
kwana uku bai dayaye ba, sai
da na ringa lallashin sa da ban magana,
sannan yake zama muna hira saboda ko
girkinta ne kullum da marece tana gidana, har
hakan ya zame mana tamkar zaman majalisa.
Maimartaba kuwa har kyaututtuka ya aiko
mana da su. Da muka tashi zuwa kano tare
mukaje da ita har gida ta roki Inna gafara.
Zama ya koma mana gwanin dadi, ashe duk
neman fadan da nakeyi ciki gareni, mukaje
Yarima yayi min scanning sai ga namiji,
kullum addu'a ta Allah ya sauke ni lafiya.
TAMMAT BI HAMDULILLAHI. nanmuka kawo
karshen littafin subul da haka 1,2&3 amadadin
Zainab dahiru wauwo
( zeedee)***naku ANaM Dorayi kemuku fat an
alkhairi saimunhadu a Novel nagaba

Zaharaddeen Shomar
Whatsapp 08168575100

You might also like