0% found this document useful (0 votes)
2K views179 pages

Bafulatana Complete

Copyright
© © All Rights Reserved
We take content rights seriously. If you suspect this is your content, claim it here.
Available Formats
Download as TXT, PDF, TXT or read online on Scribd
0% found this document useful (0 votes)
2K views179 pages

Bafulatana Complete

Copyright
© © All Rights Reserved
We take content rights seriously. If you suspect this is your content, claim it here.
Available Formats
Download as TXT, PDF, TXT or read online on Scribd
You are on page 1/ 179

[3/3, 5:21 PM] Chubado Mohd: ❄️❄️❄️❄️❄️❄️

❄️❄️❄️❄️❄️❄️
🐄🐄🐄🐄
🐄🐄🐄🐄
*_BAFULATANA_*
✨RETURN✨
🐄🐄🐄🐄
🐄🐄🐄🐄
❄️❄️❄️❄️❄️❄️
❄️❄️❄️❄️❄️❄️

*Page - 1*

*WRITING BY :ZM CHUBAƊO*✍️

*WARNING! WARNING!! WARNING!!!*

*_THE BOOK BAFULATANA IS NOT FOR SALE, DUK WANDA YA SIYAR MIKI DASHI TO ƊAM
DAMFARA NE WLLH, HKAA KUMA DUK WANDA YA SIYARMIN DASHI KO YA JUYA MIN SHI TA WATA
FUSKAR BATAREDA SANINA BA ALLAH YA ISA _*

*_Da sunan Allah me Rahama me jinqai salati da ɗaukaka su tabbata ga manzon tsira
Annabin mu Muhammad (S.A.W). Ya ubangiji kayi min katangar qarfe da duk wanda ke
shirin ɗaga min hankali a yanar gizo Ko waneneshi Mace ko Namiji🤲 sannan kayi riqo
da hannuna wajen Rubuta dukkan abinda ze amfani al'umar musulmi gabaɗaya._*

*_wannan littafi ba Sabo bane tsoho ne zan sake faɗaɗa muku shi ta yanda waƴanda
basu karanta ba A baya zasu samu damar karantashi , amma sedai salon zesha banban
dana farko kamar yanda sunan littafin ya canza Salo daga BAFULATANA zuwa BAFULATANA
RETURN. Fatan Ubangiji yasa mu Amfana da darusan dake ciki_*

***

*_GYAMBU ((TARABA STATE))_*

Tafiya suke cikin daji tare da shanunsu wata matashiyar yarinya Ce wadda bazata
wuce shekaru goma sha hudu ba se kuma dattijon dake kusa da ita da alama dai
mahaifin ta ne, cike da damuwa yarinyar ta daga Kanta ta kalli mahaifin Nata
cikeda damuwa tace "wllh Baba nagaji kawai ka tafi Gida idan na huta zan tawo
da shanun ta Ƙare maganar Da damuwa akan fuskarta.

Tunda ta fara magana mahaifin nata Ke kallonta sannan Yayi murmushi yace "to Rabe
Babu damuwa amma fa ki kula sosai Da kanki. a nitse ta amsa da to "Baba.

Shafa kanta yayi sannan ya juya ya Kama hanyar gida Ya barta a Dajin tareda
Dabbobin, yana tafiya Rabe ta nufi wata Ƙatuwar bishiya dake gefanta ta zauna dan
ta huta a nitse ta Ta fara cire Takalmin Robar dake Ƙafarta, tana Gama cirewa ta
Jingina da jikin bishiyar bata jima da kwanciyar ba Wani gajiyayyen bacci ya Samu
nasarar ɗauke ta sabda Tsabar gajiyar dake tareda ita, kallo daya Zakayi mata ka
fahimci tana jin dadin baccin da takeyi.

A hankali iska me daɗi ta fara kadawa Tareda ƙamshin ƙasa wanda hakan ya gauraye a
guri guda ƙamshin ya canza zuwa wani yanayi me daɗin gaske can kuma se aka fara
iska me qarfi wadda itace ta zama sillar farkawar Rabe daga baccin datakeyi a
hankali ta daga Dara-Daran idanunta Sama Tana kallon hadarin daya gauraye sararin
Samaniya ya koma launin baki aiko da sauri ta mike tafara kada shanun tana fadin
su kama hanyar gida cikin harshen fulatanci tayi maganar nan da nan shanun suka
fara tafiya kamar yanda tace musu suna cikin tafiya Yayyafi ya fara sauka a
hankali can kuma se ruwan ya balle kamar da bakin Ƙwarya, A maddin ta nemi
maɓoya se kawai ta dinga tsalle tana murna Ruwan na sauka a jikinta tana dariya,
Haka nan Ruwan yayiwa Rabe dukan tsiya amma itako ko a jikinta wai an tsikari
kakkausa inji 'yana magana lol.

Cike da annashuwa take tafiya tana tsalle tana kuma shiga cikin ruwan da ya taru
a kan hanya Har Ruwan ya ɗauke Kasancewar kayan jikinta na farin Saƙi ne yasa Duk
yayu jajir Sabida jar Ƙasar dake hanya, haka tai ta shiga cikin ruwan dake
kwance bisa hanyar tana bin shanun.

Suka kama hanyar gida, basu jima ba suka iso gida seda ta fara kai shanun cikin
garken su sannan ta Ƙarasa inda bukkokin su suke, da gudun ta ta Ƙarasa bakin
Ƙofar da zata sada ta da Bukkar matar babanta da sallama ta shiga Ɗakin cikin
harshen Fulatanci tace " inna na dawo.

cike da bacin rai tare da tarin tsana take kallonta, cike da masifa tace " Uwar me
zan miki da kike gayamin kin dawo shegiya me mugun hali, Zaki fita ko sena fito
naci ubanki shegiyar yarinya me baƙin jinin tsiya har yanzu kinƙi auruwa sabida
baƙin jininki, uwarki ma a tsiyace ta Ƙare kuma kema a haka zaki Ƙare Tinda kikayo
gadon tsiya. Inna ta ƙare maganar tana hucci kamar macijiya

Tunda ta fara maganar Rabe Ke kallonta cike da rashin fahimta dan harga Allah
bata fahimci abinda Innah Lauren take nufi ba Sam, kullum tana gaya mata haka
amma Sam abin Be taɓa damunta Kamar yau ba, tambaya ɗayace ke mata yawo a cikin
zuciyarta a gameda maganganun inna laure shin meyasa kullum take Maimaita mata
magana ɗaya babu canji? Shin meyasa take yawan tunani akan magar innar a yan
kawanakin nan?

Tana cikin duniyar tunanin datakeyi ne taji Saukar murfin kwano a daman goshinta!

Inna Laure ce ta buga mata tana huci lokaci guda kuma ta suri kwanon dake gabanta
ta
Cike da Mugunta ta jefi Rabe dashi Daidai saitin hancinta aiko nan da nan Jini ya
fara fita a goshin ta Da hancinta, gigicewa ta juya tana nemam hanyar fita daga
bukkar Tana Neman agaji sabida Jinin data gani yana Zuba daga hancinta da goshinta,
sosai ta gigice sabida a Rayuwarta batason ganin jini komai ƙanƙantarsa tsoronsa
take ji. Da gudu ta nufi hanyar garken shanunsu Tana kuka sabida batado Babanta ya
dawo ya gani tabbas bazata taɓa jin daɗin haƙan ba.

Karo taji tayi da mutum cikeda tsoro taja da baya zata fati taji an riƙeta gam,
mahaifinta ne malam moddibo,
Cike da tashin hankali yake firta "innanillahi'wainnah'ilaihirraji'un

Cike da tashin hankali ya Jawota jikinsa tare da kama goshin Yana dubawa da sauri,
hannunta Ya kama suka nufi Ɗakinsa dan yasa mata maganin daze tsayar da zubar
jinin, cikin ikon Allah kuwa jinin ya tsaya amma sedai goshin ya kumbura sosai kuma
Yayi jajzir kasancewarta fara, a hankali take sauke numfashi sabida zafin da gurin
ke mata cikin sanyi murya baban ya fara magana Kamar haka
"Rabi'atu kiyi haƙuri da rayuwa kamar yanda nake gaya miki kullum kuma dik abin
da ze dinga hadaki da Laure ki dinga kauce masa sbda bata da burin daya wuce ta
illatamin ke, sanin kanki ne bani da kowa Daya rage mini a yanzu seke, tunda na
rasa mahaifiyarki nakejin a raina cewar na rasa wani Ɓangare na rayuwata, shikuma
dan Uwana tuna kina jaririya aka nemashi aka rasa seda ga baya aka samu gawarsa a
bakin hanya, A kwai cuwuka sosai a cikin Rayuwata wanda banaso ma na dinga tunasu
sabida yanda zuciyata ke zafi a sanadinsu. A sanadin mutuwar ɗan Uwama muka dena
bin titi da dabbobin mu Har zuwa lokacin da mahaifiyarki ta haifeki, tunda na rasa
iyaye na ban Ƙara samun farin ciki ba seda na auri mahaifiyarki, amma itama daga
baya Allah ya karbe Rayuwarya ta rasu ta barmin ke, tun kina shan nono a haka
kina fara girma ina kula dake
Bayan rasuwar mahaifiyarki da shekara 2 malm iro yazomin da shawarar na Ƙara aure
Kodan sabida ki samu rayuwa me in ganci, cike da damuwa na kalleshi nace " Banƙi
shawararka ba Iro sedai inajin tsoron wace mace zan Aura wadda zata iya riƙemin
Rabe bisa gaskiya da Amana?
Har ga Allah bana so Rabe ta rayu da ciwon maraicin Uwa A Rayuwarta Ko kaɗan. da
kulawa malm Iro ke kallon Aminin nasa
Yayi murmushi yace "indai wannan ne ba wata matsa bace Moddibo zan baka Ƙanwata
Laure ka aura nasan zata riƙeta da Dukkan gaskiyarta fatana kawai ka Amince da
wannan batun Kuma ka kwantar da hankalin ka.

badan zuciyata taso ba na Amince Da maganar Auren laure, koda


malam Iro ya fahimci zuciyata bata gama amincewa da mganar auren ba se ya sake
murmushi a karo na biyu yace "indai Har ka amince ka aureta nikuma nayi maka
alƙawarin zan zama me koyar da Ƴarka Rabe karatun addini Tayanda zata zama daban a
cikin sauran yaran dake maƙotaka da Rugar mu. Ya ƙare maganar cikeda murmushi

Batare da tinanin komai ba na amince zan auri Laure. Ashe abinda ban sani ba shine
sanadin tarwatsewar rayuwar gidana da farin cikin Ƴata ba Auro. Moddibbo ya Ƙare
maganar Yana Kuka

A nitse Rabe ta rarrafo kusa da mahaifin nata ta rugumeshi tana kuka tare da share
mai hawayen dake Sauka a saman kumatunsa da tafin hanunta, seda moddibo Yayi kuka
me isarsa sannan Yayi shiru, cike da kulawa Ya shafi gefan fuskarta yace "kinci
abinci Kuwa? Da sauri ta Ɗaga masa kanta alamar ae kuma a zahirin gaskia bata
ci ba, Ta amsa masa da Ae ne kawai dan hankali n mahaifin nata ya kwanta

Moddibo yay murmushi yace "to maza tashi ki tafi daukar karatun don kar lokaci ya
ƙure miki banda tsayawa wasa kinji Allah, ya albarkaci rayuwar ki Rabe na.
Ta amsa da amin sannan ta tashi ta nufi makarantar Allon malm iro inda take
daukar karatu,

Dik da cewar su fulanin daji ne amma Sam hakan Be zama illa garesu ba Kuma be
hanasu karatun addini Ba, duk cikin sa' oin Rabe babu wacce batayi aure ba se ita
da Ƙawarta Ruƙatu sune kawai suka rage a yaran da basuyi auren ba,
Rabe kyakkyawar yarinya ce kallo Ɗaya zakai mata ka fahimci hakn, tana da manyan
idanu tare da gashin gira me yawa hancinta dogo ne sosai kamar na mahaifin ta
sannan yana da dan fadi kadan, labbanta ma daidaita ne kuma suna da dan tudu kadan
tanada yalwataccen gashin kai ma'ana yana da tsayi sosai Irin na Fulanin Asali kuma
ƴan gado, Rabe doguwa ce Sosai tayanda tsayinta yafi ƙarfin shekarunta, kallo
daya zakayi mata ka fahimci tana da kyau da diri irin na fulanin Usuli, Rabe
miskilace ta ajin Ƙarshe magana ma ba damunta tayi ba Se idan ta zama dole, sedai
Sam hakan baya hanata Gaida mutane

Rabe yarinya ma'abociya fara'a da son karatu hakan ne yasa malm iron ke Ƙaunarta
sosai
Sbda tana gane karatu Cikin sauƙi, koda wasa bata sakewa samarin Rugar tasu
wannan ne yasa suke cewa tana da girman kai , amma a zahiri sam ba haka bane Mutum
ɗaya ne ya nace mata har seda yasa ta fara kulashi sabida baƙin nacinsa Ana kiransa
da Suna BAMANGA shima baɗan Rugarsu bane ɗan Rugar dake maƙotaka da tasu ne, a
nitse ta qarasa makarantar Abin mamaki babu wanda yazo se ita kadai, Ajiye Allon
ta tayi sannan ta dauki tsintsiya ta share gurin Tass ta shimfiɗa tabarman kabar
Dake jingine tahau ta zauna ta fara bitan karatunta dan a ranar zata wanke Allon
ta
Tana cikin karatun ne Ruƙatu ta Ƙara so da sallamar ta amma Rabe bata Amsa ba Har
seda takai aya sannan ta daga kai da murmushi ta ansa mata sallamar,
Ruƙatu tayi dariya tace "sannu sarkin hadda shine ko ki biyo min ko?? To ai gashi
nazo nima kuma nasan dan ki rigani wanke Allo ne yasa kika tawo kika barni to ai
na gane wayon naki
*_((duk wannan maganar cikin harshen fulatanci suke Yinta nayi haka ne dan me
karatu ya fahimci gundarin labarin sbda idan nayi ammafani da harshen fulatanci ba
lallai wani ya fahimci abinda labarin Ya ƙunsa ba))_*
Rabe tayi dariya Tace "Ruƙatu kenan keda zakiyi aure kwanan nan ai kin ma kusa
ki dena zuwa makarantar Gabaɗaya saurin me zakiyi kuma?

Haɗe rai Ruƙatu tayi Sannan tace "to ai se munyi sauka zanyi Auren kuma yau
saura sati biyu mu sauke da ikon Allah.

murmushi Rabe tayi sannan tace "to Allah ya nuna mana sati biyun.

*_Gareku masoyana kuma mabiya littattafaina, idan har salon yayi muku zan gane daga
Yawan comment Ɗinga ga wannan littafi. Ima muku batan Alkhairi tareɗa baku tabbacin
cewar wannan littafi ze zo muku da zarar na kammala littafina me taken KUYARDA
DANI👏_*

Sonso Fisabilillah❤

Sushmah💋

Comment
Nd
Share
[3/3, 5:22 PM] Chubado Mohd: ❄️❄️❄️❄️❄️❄️
❄️❄️❄️❄️❄️❄️
🐄🐄🐄🐄
🐄🐄🐄🐄
*BAFULATANA*
✨RETURN✨
🐄🐄🐄🐄
🐄🐄🐄🐄
❄️❄️❄️❄️❄️❄️
❄️❄️❄️❄️❄️❄️

*_Page: 2-3_*

*_A JIYA NAYI MISTAKE A MADADIN NA NACE GYAMBU ((TARABA STATE)) SENA SAKA GYAMBU
((ADAMAWA STATE)) A FARKON PAGE 1 MANTAWA NAYI CEWAR GYAMBU BA'A CIKIN JIHAR
ADAMAWA TAKE BA A CIKIN JIHAR TARABA TAKE FATAN ZAKU FAHIMCENI MABIYA WANNAN
LITTAFI😊_*

✍️____Da haka suka rufe hirar tasu sakamakon Ƙarasowar malam Iro gurin, cike da
girmamawa suka gadashi ya amsa tare da sakin fuska yace " An gaida Ƙawayen juna
Idan har akaji maganar Rabe to da Ruƙatu ne koda Moddibbo. Malam Iro ya faɗi hakan
yana murmushi

Suma murmushin sukayi Basuce komai ba kansu a sunkuye, Ruƙatu aka fara biyawa
Allonta sannan aka biyawa Rabe Ma nata, suna kammala Karatun ba jimawa sukayiwa
malam Iro sallama kana Suka kama hanyar gidajensu, a hanyar komawar ne sukai
kacibus da Aliko Wanda ze auri Ruƙatu, Tun kafin su ƙaraso inda yake ya kafesu da
idanu kamar ze cinyesu, turo Baki Rabe tayi sannan ta zinguri Ruƙatu tace "da alama
nan gaba wannan maƙale matan naki har makaranta ze dinga binmu idan har ba'a ɗaura
muku igiyar Aure ba. Rabe ta faɗi hakan yayin da take nuna mata Aliko

A nitse suke tafiya har suka ƙaraso inda Alikon ke tsaye cike da fara'a suka gaisa
da Rabe ita kuwa Ruƙatu se Faman boye fiska take a bayan Rabe wai ita Ala dole
kunyarsa takeji,
Basu jima a tsaye ba Rabe tayimai sallama ta nufi gida cike da tinanin Abinda zata
tarar Na daga bala'in Inna Laure, siyasa taita wasa a hanya harta gama cinye
sairan lokacin daya rage mata sannan ta kama hanyar gida sabida tasan mahaifin duk
inda yake a wannan lokacin to ya koma gida, bata dawo gida ba se yamma liƙis
kasancewar suna da nisa da makarantar, cike da fargaba ta Ƙarasa dakin da take
kwana ta kwanta tare da sauke ajiyar zuciya.

A hankali ta firta Kalmar "Alhamdulillah Bisa rashin haɗuwar da basuyi da inna ba,
Sabida har ga Allah batason duk abinda ze ƙara haɗata da inna Laure dan tasan
haduwar Tasu ba alkairi bane, tana cikin wannan tinanin ne taji Antaɓa Labulan
buhun ɗake jikin Ƙofar bukkar ta, da sauri ta mike tsaye A matiƙar tsorace har
jikinta na Rawa sabida yanda tsoron ya tsirga mata Duk a zatonta innah Laure ce ,
da sallama ya shigo Ɗakin Yana kallonta Da mamaki sabida yanda yaga jikinta na
rawa irin haka da gudu ta Ƙarasa gareshi ta rungume shi Gam Lokaci guda ta fashe
Masa da wani irin kuka.

Shiru yayi yana sauraron kukan nata tamkar wadda ke shirin shiɗewa, sosai Yakejin
kukan na taɓa zuciyarsa Sedai beyi yunƙurin hanata ba Donta damu damar yin me
isarta, hannunsa yasa ya share mata hawayen dake zubo mata yace "kiyi haƙuri Rabe
nasan Kinada Cikakkiyar hujjar Da zakiyi kuka sabida rashin dacen da kikayi da
matar uba irin Laure, ki Ƙara haƙuri Insha Allah wata rana se labari kinji ?

Da sauri ta Ɗaga kanta alamar To.

A hankali Moddibbo ya kama kafadunta ya zaunar da ita a bakin katifar ciyawar


dake Ɗakin yace "daga yau nayi miki Alƙawarin Cewar bazaki sake kukan rashin uwa
ba Insha Allahu kinji Rabe? Be jira cewarta ba Ya Nufi ƙofar fita Daga bukkar
zuciyarsa na zafi akan lamarin Laure.

Da sauri ta ɗago tace "baba Don Allah kayi Min Aure ko zan dena ganin innah Laure!

Cike da mamaki moddibbo ya juyo yana kallon Ta yace "Aure kikace Rabe? Ba tare da
tinanin komaiba ta daga Masa kai alamar Ae,
Jikin sa a mace ya tako Har inda take zaune ya dafa Kafaɗunta cike da kulawa yace "
dagaske kike kina son aure Rabi'atou?

Ba tare da fargaba ko shakkaba tace " Ae Baba Ina so Indai zan dena ganin inna. Ta
faɗa tana kallonsa hawaye na zubo mata, harga Allah bata San me ake nufi da
Kalmar Auren ba Kawai tana jinta a bakine Batareda da tasan tarin Abubuwan dake
cikinsa ba kawai ta fada ne dan ta samu sauqi a zuciyarta.

Modibbo yayi murmushi yace "shike nan zan kawo miki mijin da zaki Aura har gida
Tunda dai kince Auren kikeso kinji?

Da sauri ta washe baki cike da yarinta tace "to Babah yaushe zaka kawo Min shi??
Sosai Maganarta ta bawa moddibo dariya Don haka ya kasa cewa komai illa dariyar
dayakeyi kawai, itama murmushin tayi
A hankali ya kama kumatunta yace "nan da 'yana kawanaki kadan zan kawo miki shi
Rabe na. yana kaiwa nan ya Fice daga bukkar ya nufi masallaci,

itama tashi tayi taje tayi alwala tayi sallah sannan ta ta nufi dakin Babanta,
tana shiga Ɗakin ta sameshi a zaune yana Hada magunguna Gargajiya, dayake Abinda
yakeyi kenan bada magani irin na GargajiYa, duk Rugar su shi ake kira idan
rashin lafiya ya samu wani Kuma cikin ikon Allah ana dacewa da maganin Nasa Idan
har ya bayar.
Da sallama ta shiga ta zauna Daga gefansa tayi shiru batare da tace komai ba,
hakan ne ya Bawa moddibbo damar fahimtar yunwa take ji, be ce mata komaiba ya
Ɗakko kwanon dake gefansa ya mika mata da sauri ta karɓa Ta buɗe faifan da ka rufe
kwanon dashi furace da nono nana da nan ta kafa kai tafara sha Batare da ta
sauke kwanon ba, daga yanda take shan furar ne abin ya bawa moddibo mamaki a nan
zuciyar sa ta fara zargin anya kuwa Rabe taci abinci kuwa???

Tabbas ze Iya Ɗaukar komai Da Laure zatayiwa ƴarsa guda ɗaya tak a Duniya amma fa
banda Horon yunwa, a fusace ya tashi ya nufi bukkar Laure ko sallama be mata ba
Sabida yanda Ransa ya Ɓaci ya Hauta da bala'i kan cewa ze jure komai da zatai
masa amma fa Sam banda yiwa gudan jininsa Rabe horon yunwa,
Tunda ya fara masifar Laure ke kallonsa cike da mamaki sabida tunda take da
moddibo be taba Ɗaga mata murya ba balle Har yayi mata faɗa Irin haka, Ashe Dama
haka moddibo yake?? Tabbas ta yarda ransa ya Ɓacci sosai shiyasa bata Tanka masa
ba tunda ya fara fadan, idan Har tace zatayi magana tofa tabbas Zasuyi ɓatacciya
donta lura komai ze Iya faruwa Wanda kuma ba lallai yay mata dadi ba,

Yana gama zazzaga mata Faɗan ja juya yay gaba ya barta da fargabar Faɗansa,
Yana Fita Ɗakinsa ya nufa da sallama ya shiga Ya zauna yay shiru yana kallonta,
har ya fita ya dawo Rabe na zaune a inda ya bar ta Bata tashi ba Har seda ta
shanye Furar tas sannan ta miƙa masa kwanon tace "Baba gashi na Shanye.

Murmushi Ya ƙirƙiro yayi Mata tareda shafa kanta Yace "Allah yayi Miki albarka
Rabe. Tana kallonsa tace "Amin Babana

Hira suka dingayi dashi jefi-jefi tana tayashi tankaɗe maganin dake gabansa har
suka gama sannan ta kwashe ta zuba masa a cikin Boronsa ((jaka)) dayake zuba
magungunan a ciki, sun jima tana yi masa shirmen hirarta har ya gaji yace taje
tayi bacci Dare yayi, nanfa Rabe ta Tubure ita fir Bazata tafi Ba seya rakata Har
ɗakinta, haka kuwa akayi har Ɗakin ta moddibo ya Rakata Be fito ba har seda ta
fara bacci sannan ya tofa mata addu'o'i sannan yay Fita ya Rufe mata ƙofar ɗakin da
ƙofar karan dake gefe.

Wshe gari da zanyi safiya Rabe ta fito cikin shirinta na tafiya kiwo, sanye take
Kayan farin Saƙi irin nasu na fulanin asali Ƙafarta sanye cikin rufaffen takalmi
na roba Yalo shar dashi,
Ɗakin moddibo ta nufa da sallama sannan ta shiga ta zauna Daga Ɗan nesa dashi
Kaɗan yana Karin kumallo,

da fara'a ya dubeta yace " Matso kusa dani mana Rabi'atou na. Cike da fara'a ta
qarasa jikn Baban nata cike da soyayya ta faɗa jikin sa Tana murmushi,
Tare sukayi Karin kumallon Safen dashi bayan sun gama ne suka fito tare Da ita Yana
riƙe da hannunta A waje sukaci karo da Laure tana ƙoƙarin sauke ruwan zafin dake
kan murhu. Hade rai Tayi kamar taga mutuwar ta Sannan ta ɗauke kai daga barin
kallonsu,
A dan tsorace Rabe ta gaisheta, seda ta faki idon moddibo sannan ta watsawa Rabe
wani ɗan iskan kallo Wanda hakan yasa da sauri Rabe ta koma bayan moddibo ta
Ƙanƙameshi.
bece komai ba ya kama hannunta suka fice daga Gidan Ko waiwayen laure beyi ba
Suna fita garken Shanu suka nufa dan su fita kiwo,
A nitse ta kalli Moddibbo tace "Baba yau ni kaɗai zani kiwo Base mun tafi tare ba
kaga se mu raba shanun Gida biyu Keman, kai kayi hanyar gabas nikuma nabi yamma
idan muka dawo se'a ga Shanun waye sukafi Ƙoshi Idan mun dawo ?

Cike da kulawa yace mata to muje sena raba mana, da sauri take binsa cike da
zumudin zata kiwo ita kaɗai,
Basu wani ɓata lokaci ba ya raba Musu shanun gida biyu ya Tisa nasa yay gaba
itama tayi gaba Da nata, seda yay mata kashedin ta kula da kanta sosai kuma kada
tayi nisa sosai Kuma banda bin titi sbda ya tsani bin titi A rayuwarda tunda ya
rasa Ƙaninsa Zakhariya.

Tafiya take Hankalinta a kwance kallo ɗaya zakayi mata ka Fahimci tana cikin farin
ciki mara misaltuwa, Yawo sukaitayi a Dajin Suna karaɗe ko ina, Har suka shafe
kimanin Awanni a cikin Dajin seda suka Ɗauki lokaci Me tsayi sannan Rabe ta lura
Da lokacin zuwa makarantar ta Yayi,
Dole Yasa ta kora shanun suka kama hanyar gida Badan Ranta yaso ba.

koda ta dawo seta fahimci babanta be dawo ba, Saɓanin kullum Lokacin daya saba
dawowar, tambaya ɗayace keyi mata yawo a kwanyar kanta shine "meyasa Har yanzu
Babanta be dawo Gida ba??

Ɓangaren moddibo kuwa Tafiya kawai yake tareda shanun Amma sam hankalinsa naga
ɗiyarsa wadda ya tura daji da shanu batareda ya haɗata da kowa ba, addu'a kawai
yakeyi Allah ya tsare mas ita da ikonsa, daidai kan kwanar daze yanka ya ɗauki
hanyar Ya hangi mutum kwance Ƙasan wata ƙatuwar bishiyar Marke, Be kawo komai a
ransa na harya ƙaraso jikin bishiyar kasancewar ta gefanta ze Ratsa ya kama hanyar
gida Seyayi zaton ko hutawa Mutumin keyi sabida hali na tafiya amma daya Ƙaraso
seyaga sabanin tinanin sa,
Yaro ne matashi sanye Cikin wata Dakakkiyar shadda light blue an masa dinkin
Muhammed se faman yararin tsada da kyau takeyi kansa babu hula An Kafta masa wani
Ƙaton Sara Daga gefan kansa ta hagu, hakama Ƙirjin sa da kuma bayan sa, gefan
cikinsa kuma Alamace na sukar wuƙa babu abinda ke zuba a jikinsa se
jini.

dik da saran dake jikin sa hakan baze hanaka fahimtar kyau Da tsarin Halitta irin
na matashin ba, cikin sauri moddibo ya Ƙarasa kusa dashi ya dago shi Lokaci guda
kuma ya ɗora yatsunsa a saitin Wuyansa dedai babbar jijiyar dake kai saƙo zuwa
ƙwaƙwalwa a nan ne ya fahimci Da sauran numfashi A taredashi, sabida tsabar
Rikicewa yama rasa ta Inda ze fara bashi taimakon gaggawar,, (Emergency treatment )
Can wata dabara ta faɗo masa, nan da nan Moddibo ya Ɗaga matashin da ƙarfin tsiya
Ya Dorashi a bayan Ɗaya daga cikin shanun ya Ɗaure shi Tamau a jikinta ta yanda
baze faɗi ba Sannan ya nufi hanyar gida,
Sun jima Suna tafiya sannan suka Ƙara so gida.

a Ƙofar gida suka hadu da Wadda tun dawowarta taƙi yarda ta shiga gidan ta kafa ta
tsare A waje tana jiran dawowar Modibbo,

Da sauri moddibo yace ta shiga da shanun cikin garke Ta ɗauresu ba tare da ta kula
da mutumin dake ɗaure a bayan saniyar ba tayi gaba, da Ƙar moddibo ya kwanto shi
daga jinkin saniyar Yayi hanyar dakinsa dashi, suna shiga ya kwantar dashi akan
tabar marsa Sannan ya mike ya Ɗakko Boronsa dayake sa magani A ciki ya ajiye Ta
daga gefe Sannan ya Ɗakko wata Ƙarya ya ajiye Wadda ke ɗauke da Ƙaho da kuma Aska
a ciki se wani garin magani da kuma wasu manyam ganye masu kimanin girman tafin
hannu duk a cikin ƙwaryar.
take moddibo ya Ya ɗauki wannan Askar ya shiga yanka rigar dake jikin matashin
"Subahanallah Shine kawai abinda Moddibo Ya iya firtawa Kenan sabida yanda yaga
jini ya taru a gefan Ƙirjinsa Da kuma irin saran Rashin Imanin da akayi masa, da
alama seda aka dake shi sannan aka sareshi Wanda hakan ya bashi tabbacin Kashe
matashin ake ƙoƙarin yi,
A nitse ya dauki Askar ya daidaici gurin da Ɓakin jinin ya taru sannan ya yanka nan
da nan Mataccen jini Daya taru a gurin ya fara fita, a hankali ya shiga goge
mai Jinin har seda ya gama gaba Ɗaya sannan ya shiga samai magani a jikin
raunukan Dake jikinsa.

bayan ya gama sa masa maganin ne ya fito yana kwaɗama Laure kira, jikinta na rawa
ta Ƙaraso tace " gani mlm Lafiya dai ko?

Be kulata ba Yace " maza ki kawo min ruwan zafi Yanzu-yanxu jiki na rawa ta
tashi ta hada wuta ta Dora Masa ruwan zafin......

Sushmah💋
[3/3, 5:22 PM] Chubado Mohd: ❄️❄️❄️❄️❄️❄️
❄️❄️❄️❄️❄️❄️
🐄🐄🐄🐄
🐄🐄🐄🐄
*BAFULATANA*
✨RETURN✨
🐄🐄🐄🐄
🐄🐄🐄🐄
❄️❄️❄️❄️❄️❄️
❄️❄️❄️❄️❄️❄️

*_WRITING BY :CHUBAƊO_*

*_Page:4-5_*

_____✍️Ta ɗan ɗauki lokaci kamin ta kawo ruwan zafin sabida sha'anin itace a
lokacin Damuna a kwai wiyar sha'ani, dakyar ta samu wutar ta kama sannan ta ɗora
Ruwan se faman minta takeyi ba'a jimaba Ruwan ya tafasa,
Wata ƙatuwat ƙwarya ta ɗaukko ta juye masa ruwan zafin a ciki sannan ta ɗauka ta
nufi dakinsa dan ta kai masa ruwan.

Sallama tayi daga bakin ƙofar batareda ta shiga ba sannan yay mata izinin shiga,
Ruwan Ya karɓa ya Ajiye a gefe sannan ya ɗakko wani farin saki ya jefa a cikin
ruwan zafin seda ya fara hucewa sannan ya ɗakko wani garin magani a ɗaure cikin
tsumma ya zuba a cikin ruwan, duk wannan abinda yakeyi ita dai Laure banda
kallon moddibo babu abinda takeyi bakinta a cike fal da tarin tambayoyi amma ta
rasa ta inda zata fara yin Tambayar.

A hanzarce moddibo ke gabatar da komai sabida matashin ya Rasa jini dayawa, Inna
Laure na nan tsaye Rabe ta shigo ɗakin tanabin ko ina da kallon Sannan ta kalli
Moddibo tace Baba wannan shine mijin daka samo min din?

Be kalleta ba yace "A'a sam wannan bashi bane Raɓe amma na tabbata shima ɗin zezo
nan bada jimawa ba.

ya ƙare maganar yana saka yatsansa a saitin inda aka cakawa matsin wuƙa a ciki
donyaji ya yanayin zurfin ciwon yake.
Cike da damuwa ta kali Mahaifin nata tace "Nikam baba inajin tsoron karmu
taimakishi a ƙarshe ya citar damu tunda bamusan waye shi ba. Ta faɗi hakan
tareda leƙa raunin dake jikin matashin

Moddibo be damu da ya bata amsa ba sabda shi gaba daya hankalinsa yana kan wannan
matashin burinsa kawai a wannan lokacin be wuce yaga ya ceci Rayuwarsa ba,
Kamar zatayi kuka tace "baba amma wannan daga ganinsa baƙo ne ko dubi irin kayan
jikinsa Sam ba irin namu bane?

Itadai Laure batace musu ƙala ba Har Rabe ta kama surutunta sannan ta jefo tata
tambayar tace "mlm a ina ka samo wannan yaron? Kai yanzu baka jin tsoron ɗaukko
shi nan gaba yazo ya zame mana masifa?

Moddibo ya kalleya yay shiru sannan yayi murmushi yace "haba Laure meyasa kike
magana irinta yara ne a ina kika taɓa ganin inda taimako ya zama masifa?

shiru tayi masa tana kallonsa ba tare da tace ƙala ba, daya ga bata da niyar magana
seya cigaba da magana nan ya labarta mata komai tin daga Hauwarsa da yaron har
zuwa ɗakko shin da Yayi be ɓoye musu komai ba,
Nan da nan idon Rabe ya fara zubda hawaye dama ya lafiyar kura balle kuma tayi
Zawo.
Ita ko Laure ko a jikinta balle ma har ta tausaya masa dataga abin na neman isarta
seta fice daga ɗakin tana mitar wai moddibo ze jawo musu bala'i daze fi ƙarfinsu.

Shidai be kulata ba sema cigaba da gogewa matashin busashen jinin dake jikinsa da
ruwan maganin daya haɗa,
Cikin muryar kuka Rabe tace "baba!.

ya ɗago yana kallon ta sedai bece mata komai ba, a hankali tace "dame zan Iya
taimaka maka naga yana zubar da jini?

Murmushi Moddibo yayi yace so nake kullum ki dinga yi masa adduar samun lfy
kinji shi kaɗaine taimakon da zakiyimin dani dashi? daga masa kai tayi alamar
gamsuwa sannan ya dubeta yace "maza kije Rugarsu Bamanga ki Samomin ƙayar ɗinki
zanyi amfani da ita yanzun nan.

Da sauri ta juya ta fita daga ɗakin zuciyarta fal tausayin matashin Saurayin wanda
basusan daga wace nahiyar ya fito ba.

Tana zuwa Rugarsu Bamanga Direct ta nufi inda ƙayar take ta fara karyowa harta
cira dayawa sannan ta juyo hanyar gida, koda suka Haɗu da Bamanga ba irin kiran da
beyi mata b Amma ta shareshi tayi hanyar gida, dataga ma yanshirin takura mata seta
sanya gudu dole tasa ya ƙyaleta

Ko Sallama batayi ba ta shiga ɗakin Moddibo ta ta zube masa ƙayar a gabansa tana
nishi tace "baba gashi. Karɓa yayi cikin mintunan da bazasu gaza 5 ba ya fara
haɗa naman gurin da aka soƙeshi da wuƙar yana tsirewa da ƙayar harya gama ɗinke
ciwukan dake jikin matashin sannan yasa magani a gurin, cikin ikon Allah da
hikimarsa kuwa zubar jinin ta tsaya.

Tunda ya fara ɗinkin Rabr ke kuka harya kammala, share mata hawayen yayi da
hannunsa sannan yace ta tashi ta wuce ɗakinta ta kwanta, ba musu ta mike ta tafi
ɗakin kamar yanda yace mata.

A wannan Ranar dai Rabe batayi wani baccin kirki ba.

A kwana a tashi ba wuya a gurin Allah yau matshinnan ya cika sati biyu Cif a
gidansu Rabe amma ba abinda alamar farkawa a taredashi haka kuma babu inda yake
motsi a jikinsa sedai kawai numfashi, tun suna sa ran farkawarsa har suka cire rai
farkawar sa a nan kusa.
Rabe ce kawai take kula dashi itace ke saka masa magani har zuwa kan abinci, kunu
ne kawai ke iya shiga cikinsa sabida yanda haƙoransa suka datse.

Kullum itake zuba masa kunun a baki da ludayi tin baya shiga bakin har yazo yana
shiga kaɗan-kaɗan,
Kallo ɗaya zakayiwa matashin ka fahimci ya rame sosai akan ranar da moddibo yazo
dashi Gidan, tun ranar da aka kawoshi gdan Laure bata ƙara leƙowa dakin ba.

A cewar ta idan masifar ta zo to ta afkawa moddibo shikaɗai da ƴarsa,

Kujifa masu karatu😂

Wasa-wsa Rabe ta shafe kwanaki bata zuwa makaranta Haka kuma ko kiwo bata zuwa,
amma Sam hakan baya damunta sabda Damuwar datasa a ranta, Abinda tasa a ranta
kawai shine taimakon mutum yana daya daga cikin dabi'u masu kyau A Rayuwa. Dole
tasan wata rana zasuci Ribar abinda abinda sukayi na taimakon wannan matashi

Mlm iro yazo yafi a Ƙirga kan Rabe ta dawo makarantar ayi suka da ita amma fir
taki yarda ta koma dan a ganin ta idan ta fita koda Ƙofar gida Ne to waye ze
Kula da wannan bawan Allahn?

Moddibo ne ya shigo Ɗakin hannunsa riƙe da wata saiwa ya mika mata yace " maza
jeki tafasa Min ita ki kawo min kinji.
Da sauri ta karɓa taje ta haɗo Ƙirare ta Kunna wutar ta Dora maganin, ba'a dau
lokaci me tsayiba ruwan ya fara dahuwa tareda saiwar bata sauke ba hae seda Wutar
ta mutu Gaba ɗaya sannan ta juye maganin a qwarya ta kaiwa moddibo, da murmushi
a kan fuskarsa ya karba yana sa mata albarka, seda maganin Ya fara hucewa
moddibo ya dago kan matashin ya shiga zubawa Masa abaki.

dikda cewa ana zubawa wani na zubewa ansamu wani ya shiga cikin nasa, bayan ya
gama ne ya shiga goge masa jiki da sauran maganin, tundaga ranar
Kullum Se'an masa haka har aka shafe Tsahon wata Guda anayi amma still babu wani
ci gaba. Itako Rabe bata da aiki se kuka Ta wani ɓangaren kuma ga Bala'in inna
Laure, nan da nan duk tabi ta rame se hanci da idanu Kamar ba ita ba.

Sosai Abin Hakan ke ƙara Ɗagawa moddibo hankali to amma bashida yanda zeyi illa
kawai yayta addu'a.
Laure CE ta Shigo Ɗakin da sallama ya amsa mata Ba yabo ba fallasa.

A dakile tace " yame jikin? Modibo yace "Da sauƙi Alhamdulillah sannan yayi
murmushi a karo na biyu yace hala fita zakiyi Nenaga kin shigo min ɗaki?

Basarwa tayi kamar batajishi tace "ae Fita zanyi dama ta rasa ta Inda zata fara
tambayar sa cewar zata fita, a takice yace mata"sekin dawo Indan kinje kya gaida
su Iro da Gwaggoji.

Bata amsa Shi ba tayi gaba bayan fitarta Tana sababi.

hamisu Ne Ya shigo gidan hankalinsa a matiƙar tashe yace " don Allah malam modobo
kazo muje ka duba mahaifina wllh jikin nasa ne ya tashi. Hamisu ya faɗi hakan
yana kuka

moddibo be Ɓata lokaciba ya fito suka wuce Gidansu Hamisun, har sun fita ya dawo
yace Rabe ta koma dakinsa sabda maralafiyan,
Da sauri ta mike tare da yi masa Allah Ya kiyaye ta koma dakin ta zauna, zubawa
matashin ido tayi ba tare da tace komai ba Nanda nan hawaye Ya fara wanke mata
Fusaka cikin muryar ta fara magana Kamar haka "wai kai yaushe zaka tashi ne?shin
kasan yanda mukeji a ran mu Duk a gameda kai? Dan Allah ka tashi ko hankalin babana
ze kwanta Na roƙeka!!

Ta jima tana suru tanta kamar wata zararriya sannan tayi shiru ta cigaba da kukanta
fukarta dik tayi Ja idanunta Duk sun kumbura abin ka da farar mace....

Ta jima tana kukan sannan bacci ya dauke ta,


A hankali matashin ya fara motsa hannunsa daƙar ya Iya daga hannun sa ya maidashi
Ƙirjinsa Sabida tsabar Azabar dayakeji a jikinsa,

A hankali ta buɗe idanunta sabida jin da tayi kamar motsi yasa ta bude idanunta
daƙar ta maida kallon ta gareshi, Nan da nan ta miƙe zaune sosai ta Ƙara buɗe
Manyan idanunta sosai Tana mamaki
ya akai hannunsa ya koma Ƙirjinsa? Tambayar da take mata yawo Kenan a zuciyarta.

A nitse ta maida kallonta kan fiskarsa Ta ƙura masa idanu kamar meso gano wank abu
a taredashi, ta jima tana kallon sa kamar bazata dena ba kamar a mafarki taga
yana Ɗan motsa idanun sa, Ƙara zaro idanunta Tayi waje cike da mamaki Ta miƙe
tsaye still idanunta akansa,

A hankali ya fara bude Idanunsa har ya gama buɗesu gaba ɗaya Yana me ƙarewa ɗakin
kallo harya dauke manyan idanunsa a kan fuskar Rabe,
A firgice ya fara Ƙoƙarin tashi yana so yaja Da baya sabida Yanda ya tsorata da
Ganinta.
Ƙara Ya saki sabida wani Irin azababben zafi dayaji a gadon bayan sa Har zuwa
saitin gefan cikinsa na Dama, bashiri ya koma ya kwanta yana maida numfashi, da
sauri Rabe ta sake matsowa kusa dashi sosai sannan ta fara magana cikin harshen
fulatanci take cewa "kayi a hankali sabda jikin ka akwai rauni Sosai!

Tunda ta fara magana yake kallon Yanda take motsa bakinta har ta kai Ƙarshen
maganar. dikda cewa be fahimci abinda take faɗa ba hakan be hanashi Ƙare mata
kallo ba, kyakkyawa ce Sosai ta gaban kwatance don tafi kamada irin larabawan
yankin ƙasar Misira, tana gama maganar ta sakar masa murmushi Wanda seda tasa
gabansa ya faɗi ya ɗauke idonsa da suri daga barin kallonta

mikewa ta fita daga dakin ,


Tana fita dakin ta nufaa ta Ɗakko wani rufaffen kwano Wanda Moddibo ya bata kafin
ya fita sannan ta dawo ta sake zama dab dashi Tana murmushi a karo na biyu sannan
tace Dashi " zaka iya tashi kuwa ?

Kura mata ido yayi cikeda rashin Fahimtar abinda take faɗa. dataga be gane me take
nufi ba setai mai nuni Da hannu alamar ya tashi,
A hankali ya Fara yunƙurin tashi a karo nabiyu amma kuma seya kasa ya Dole yasa ya
koma ya kwanta, alama tayi masa da hannunta kan cewar ya sake ƙoƙartawa Amma kuma
setaga bashida niyar yin hakan.

mikewa tayi sannan ta koma bayan sa Ta fara ƙoƙarin dagoshi,,

cike da mamaki yake kallonta tare da Girmama Ƙarfin hali irin nata, jibeta fa
'yar qarama da ita wai zata Ɗagashi, lallaima yarinya nan Ta gama raina masa
Hankali ya faɗi hakan a zuciyayarsa, ba zato yaji ta cakume shi Da dukkan ƙarfinta
ta fara giji-gijin ɗagashii, Wata uwar Ƙara Ya saki sabda zafin dayaji na ciwon
dake bayan sa, bata damu da ihun dayeke ba har seda ta zaunar dashi,
Daƙar Sannan ta zube ƙasa tana maida numfashi.

Dakyar ya Iya ɗago idon sa da suka fara canza kalah dan azaba ya kalleta lokaci
Ɗaya itama ta dago idonsu ya sarƙe cikin na juna.
gabanta ne ya Yanke ya fadi da sauri tayi Ƙasa da idonta, a nitse Takai
hannunta kan kwanon da ta Ɗakko a daki ta buɗe, fura ce da nono Wadda aka zugawa
uban suga ta Ɗiba ta miƙa msa Bakinsa alamar yasha, sarai ya gane nufinta a
hankali ya fara Ɗago hanunsa amma kuma seya kasa, ya jima yana kallon ludayin
sannan ya maida kallonsa kanta Batareda ya karɓa ba.

Tambayar Dake yaWo s kansa itace "wai shin inane nan?

"Kuma wannan yarinyar wacece ita?

"Waze tambaya ya bashi amsoshin wannan tambayoyi nasa?

Data ga bashi da niyar bude bakin ne seta sake miqa masa ludayin har yana taba lips
dinsa , sa'a sannan ya dawo daga duniyar tinanin daya afka, a nitse ya buɗe bakin
ya fara seeping Furar a hankali, se kuma ya kauda kansa da sauri kamar Wanda ya
tina wani abu,
Daqar ta samu ta lallabashi ya sha sosai.

Bayan ya gama sha ne ta Ɗakko masa maganin sa shima ta bashi yasha , tunda ta Fara
bashi maganin yake mamakin yarinyar
Badan komai ba se yanda take Da zafin nama a komai nata, ƙoƙarinta ya zarta na
shekarunta dubada yanda taketa dawainiya dashi, harga Allah ya jinjinawa jarumtar
ta matiƙa.

tana gama shafa mai maganin ta taimaka masa ya kwanta yana kwanciya moddibo ya
shigo Ɗakin da sallamar da gudu Rabe ta nufeshi ta rungumeshi tana fadin " baba ya
tashi wllh ya tashi,
Kana kallonta zaka fahimci tana cikin Farin ciki ba kaɗan ba.

Tunda ta fara magana moddibo yake kallonta da murmushi yace" to yanzu kuka ya
Ƙare Kenan ko?
Da sauri ta rufe fuskarta da zarazarn hannayenta tana dariya.

Tun shigowar moddibo matashin yake kallon su har zuwa sanda Rabe ta rungumeshi,
se kallon su yake cike da burgewa da alama mahaifin tane ya fada a zuciyar sa,
sabda suna bala'in kama da juna!

Sushmah💋
[3/3, 5:22 PM] Chubado Mohd: ❄️❄️❄️❄️❄️❄️
❄️❄️❄️❄️❄️❄️
🐄🐄🐄🐄
🐄🐄🐄🐄
*BAFULATANA*
✨RETURN✨
🐄🐄🐄🐄
🐄🐄🐄🐄
❄️❄️❄️❄️❄️❄️
❄️❄️❄️❄️❄️❄️

*_Page :6 -7_*

*_WRITING BY: CHUBAƊO_*


____✍️A nitse moddibo ya Ƙarasa kusa da matashin ya sunkuya da murmushi Kwance a
kan fuskarsa yace "sannu da jiki Yaro kashe doguwar jinya.

Cikin harshen fulatanci moddibo Yayi maganar.

ido kawai matashin yake bin moddibo dashi Batareda yasan abinda yake faɗa ba.
Kallon Rabe moddibo yace "da alamafa bayajin abinda muke faɗa. Ya ƙare maganar da
damuwa akan fuskarsa

Itadai batace komai ba ta zuba musu idanu kawai tana kallonsu

Koda ya fahimci matashin baya gane abinda yake faɗa sabida banbanci yare se
dabara ta faɗo Masa ya kalli matashin Cikin kwaɓaɓɓiyar Hausarsa yace "Shannu yaro
ya shikejin ƙarfin jukin naki?

Matashin ya bude baki da nufin ya amsawa moddibo amma sedai muryanshi bata fita
sosai sabda mura data kamashi Yace "Alhamdulillah da sauki.

A nitse moddibo ya fara magana kamar haka


"Yaro nasan zuciyarka a cike take da tambayoyi akan mu, haka
Kuma nasan zakaso kasan meye dalilin zuwanka wannan gurin? To magana Ta gaskia
itace ina Kan hanyar dawo wata daga kiwo ne Allah ya hadani dakai A cikin
mayuyacin hali kana kwance cikin jini !!
Haƙiƙa duk abinda Alla ya hukunta shiyake faruwa shiyasa ma har nabi hanyar dana
Daɗe amma da Allah ya Ƙaddara haɗuwarmu dakai se Gashi ya nufeni da bin hanyar
Duk dan na ceci Rayuwarka.

A lokacin dana tsince ka Ban taɓa zaton zan sameka da sauran numfashi a tareda
kai ba amma Dana tabaka sena fahimci kana numfashi, a haka na ɗakko ka a daji na
kawo nan mukaita kula dakai tareda rauni kan Dake jikin ka har Allah ya amince
mana ka tashi A yanzu.

Nan da nan idon matashin ya kawo ruwa ba komai ne yasa shi hawaye ba se irin
karamcin da moddibo yay masa A Rayuwa tabbas bashida abinda ze iya biyasa dashi,
Yanzu babbar damuwarsa A yanzu Itace be San halin da Mahaifinsa yake ciki ba,
sedai bashida wani zaɓi wanda ya wuce yaci gaba da zama tareda wannan bawan Allahn
kuma ya mant da rayuwarsa ta baya!

Cike da kulawa moddibo ya dafashi yace "kayi haƙuri yaro nasan dole zakayi kewar
gida tareda ƴan uwanka amma ka Ƙara haƙuri jikinka ya Ƙara Ƙwari Inyaso seka Koma
garesu Kaji?

Ɗaga masa kai kawai matashin yayi ba tare da Yace dashi komai ba ya mayarda
idanunsa ya kulle,
Har moddibo ya mike se kuma ya sake sunkuyowa yace da matashin yaro ya sunan ka??

Gabansa ne ya faɗi yayin da yaji tambayar da Modibbo yayi masa amma, nan da nan
wani ɓangare na zuciyarsa yace masa "karka sake ka faɗi cikakken Sunanka dana
mahaifinka idan ba haka ba Mutanan nan Zasu gane gane waye kai cikin sauƙi kuma su
mayar dakai hannun maƙiyanka waƴanda suka jefaka a wannan halim da kake ciki a
yanzu!

Ajiyar zuciya ya sauke me nauyin gaske Still idanunsa a Rufe ba tareda ya buɗesu ba
Yace "Uhm uhnn Sunana Sunana Muhammad Ali.

Ɗan jim kaɗan Moddibo yayi yana kallonsa sannan yayi murmushi yace "Masha Allah
Muhammad ai babban Sunana To Allah ya ƙara lfy.

Duk wannan hiran da suke Rabe na jinsu a nitse ta Ƙaraso kusa da matashin da
murmushi a fiskarta tace "Anya sunan Muhammad ne?

Da sauri ya buɗe manyan idanunsa yana kallonta har seda gabansa ya faɗi sannan ya
ƙaƙalo murmushi a karo na farko yace " Ae Sunana kenan kamar yanda kikaji Muhammad
Ali. Ya faɗa yayin dayake ɓatar da murmushin dake kan fuskarsa a lokaci guda.

Tun daga lokacin da Matashin yayi mata murmushi har zuwa sanda ya gama magana
take kallon sa ,
Ba komai take kallo ba se tsabar kyau Da tsarin halitta irin nasa, bata tabbatar
da shi kyakkyawa bane seda yayi murmushi A iya Tsahon rayuwarta Har zuwa yanzu bata
taɓa ganin mutum irinsa ba,
Mutane dayawa Kan fada Mata cewar tana da kyau amma yau Kam taga Wanda ya fita
kyau da tsarin halitta,

(Nima kaina Danake kwaso muku rahoto seda na dan tsorata da kyawu irin na wannan
matashi lol)

Seda moddibo ya dafata sannan ta dawo daga duniyar tinanin da take,,,


A daburce tace "baba yaushe za'a kuma bashi abinci?
Harga Allah ba abinda tayi niyar fada ba kenan tsabaragen daburcewa ne yasa ta
fadi hakan, sosai moddibo ya fahimci halin data Samu kanta a ciki amma kawai
seyay murmushi ya fita daga Ɗakin.

A hankali A hankali ya Buɗe idanunsa ya ɗago kansa ya kalleta yace ya sunan ki?

A taƙaice tace" Sunana Rabe.


A hankali ya kuma maimaita sunan Yana wani yamutsa fuska yace "what's that does
mean?

Ƙura masa idanu tayi tana kallonsa, hakan yasa ya taɓe baki ƙaɗan Yace" ok lem me
call you with Fulani, I can't even call you with that locally name is it Rabe or
what ever. A taqaice Ya sake kallonta still itama kallonsa take batareda tamasan
abinda yake faɗa yace "You can't thanks for everything Fulani girl. Ya faɗi
hakan yana mayar da idanunsa ya kulle

ta jima tana juya kalmarsa ta ƙarshe a ranta dikda cewa bata San meyake nufi da
ita ba, amma setaji Kalmar tayi mata dadi Kuma ta tsaya mata a Rai. A haka taɓar
ɗakin tana ta juya maganar a Ranta

har yamma
Moddibo Rabe bata ƙara dawowa ɗakin ba Har lokacin shafa masa magani yayi Shida
kansa ya shafa masa maganin, sannan yasa Rabe ta Dora masa ruwan zabi ta kawo masa
tana kawowa tayi waje abinta, moddibo ya tashi ya nufi inda Matashin ke kwance a
hankali ya fara kiran sunan sa,
A nitse ya buɗe idanunsa a fiskar moddibo,
Murmushi Yayi masa sannan yace ka gyara zan goge ma jikin ka , a nitse ya fara
Ƙoƙarin tashi amma kuma seya kasa tashi moddibo ne ya taimaka masa Harya tashi
zaune.

wani farin saki moddibo ya Ƙara Ɗakkowa ya tsoma a cikin ruwan ya fara gasa Masa
jikinsa, dik da cewa jikinsa nayi masa ciwo sosai hakan be hana moddibo gsa masa
Shi yanda ya dace ba,
Yana gamawa ya Ɗakko maganin shafi ya shafa masa sannan ya taimaka masa yayi
alwala, Cikin mintunan da bazasu gaza 5 ba ya shiga rama sallolin da ake Kansa.

ya Dade yana yi dik da cewa besan adadin kwanakin daya Kwashe baya cikin haiyacinsa
ba a Wannan Ƙauyen,

Seda ya Ɗau lokaci me tsayi sannan ya idar, moddibo ne ya tai maka masa ya kwanta
sannan ya Ɗakko wani zanin saki ya lullube shi ba'a Ɗau lokaci Me tsahi ba bacci
yay a won gaba dashi

*****
Ɓan garen Rabe kuwa tunda ta fita bata sake dawowa Ɗakin ba
Sallah ta gabatar sannan ta fito ta gabatar da aiyukan da ta saba na yau da kullum
seda ta gama tsaf sannan ta koma daki da nufin ta gabatar da sallar ishsha'i,
bayan ta idar ta jima tana adduo'inta sannan ta shafa,
Da sauri ta mike ta cire mayafinta ta nufi katifar ciyawarta Dake ɗakin dan ta
kwanta sbda sanyin daya fara busawa,
Kamar daga sama taji an banko mata cikin Ɗakin aiko da sauri ta miƙe sabda sanin
ko wacece ta shigo Ɗin, dan indan da sabo Yaci ace ta Saba da halin Laure.

Masifa fal ranta ta shigo Ɗakin tare da y


Binta da wani wulaƙantaccen kallo tace " to yar gatan gata rere A fito kiyi min
ayki dakike Koƙarin kwanciya Bacci ƴar mowa Wato ga baiwa Ubanki ya ajiye inyi
muku wahala ko ? To wllh baki isa kiyi bacci yanzu ba Har sekin gamamin aiyukan
dake cikin gidan nan.
Bata jira cewarta ba ta fincikota sukayi waje, wasu tarin kwanuka ta gani an
jibge Matasu gefe kuma Ruwane a cikin wata Ƙatuwar fanteka da alama Ruwan ya
Dade a gurin Batun base an fada ma ya dau sanyi ba,,

Kallo daya zaka yiwa kwanukan ka fahimci babu Wani datti ko kadan a jikin su kawai
tsabaragen mugunta ne yasa Laure ta Fito dasu.

Ba musu Rabe ta sunkuya ta fara Ɗauraye kwanukan tanayi jikinta na rawa sabda
sanyi Dake busawa har taci Ƙarfin kwanukan, da laure taga bazata Iya jure sanyi
ba setai shigewarta Ɗakin tabar Rabe a waje tana fama Da sanyi, ta ɗau lokaci me
tsawo Tana ɗauraye kwanukan sannan ta gama ta kife mata su,
ta wuce daki jikinta Se rawar sanyi yakeyi, tana shiga ta kwanta dikda cewa ta
lulluba amma Sam bata dena jin sanyin ba,,

Abu kamar wasa Haqoranta suka fara haduwa da juna Suna fitar da wani sauti na
daban, nana da nan zazzabi me zafi ya rufeta daƙar ta samu bacci ya Ɗauke ta
Ba ita ta farka ba se bayan an idar da sallar asuba, daƙar ta samu tayi alwala ta
gabatar da sallar
Ko data idarma kasa tashi tayi daga inda Tayi sallar sabda wani irin azababben
jirin data keji.

Har gari Yayi haske sosai kowa ya fara harko kin Gabansa amma Rabe bata fito ba.

A Ɓangaran moddibo Sosai Yayi mamakin rashin ganin Giftawar Rabe har wannan lokacin
Bata fitoba, azatonsa ko bacci takeyi shiyasa be wani damu sosai ba,
A nitse ya gama gabatar da komai na karyawa Wanda Matashin zeyi Karin kumallo
dashi, amma
Har ya gama bega idon Rabe ba, se kuma abin ya fara damun moddibo

Ɓangaren Matashin saurayin kuwa tunda ya tashi daga baccin safen da yayi ya afka
duniyar tunanin meyasa Yakeda tarin maƙiya ne a Rayuwarsa? Me yay musu suke son
ganin bayansa a Rayuwa? Me kuma ya tare musu har haka?

Modibbo ne ya Katse masa tunanin dayakeyi ta hanyar shigowarsa ɗakin tareɗa


abincin Sa A hannunsa yace " ya kamata ka tashi kaci abinci kasha maganin ka ko?

Ba musu ya fara Ƙoƙarin tashi dikda cewa ba iyawa zeyi ba,,


Moddibo ya saki murmushi yace" yaro gaskiya kana da Ƙarfin hali sosai ka Ƙara
haƙuri Insha Allah ka kusa fara tashi da kanka.
Tunda moddibo ya fara magana idon Matashin yana kansa se kuma Yayi murmushi yace
"to baba Allah yasa Hakan Sedai bazan gaji da Ƙara jaddada godiya ta a gareka ba
sabda Haƙiƙa ka taimaki rayuwata, Ablokacin dana fitar da ran akan Rayuwar
duniyar gabaɗaya!! Shiru ya ɗanyi sannan ya sake kallon moddibo yace " thank you
for saving my life,,, ya Ƙarashe maganar tare da hawaye

Da sauri moddibo ya dafa kafaɗunsa yace "kada ka damu yaro ni nayi maka dan Allah
ne badan wani ba, dan haka ka dena zubar da hawayenka kaima kamar Ɗa kake a gurina
kuma nayi maka Alƙawarin Cewar zan kula da kai har zuwa ranar da zaka Samu sauƙi
ka koma ga iyayen ka. ya Ƙare maganar da murmushi A kan fuskarsa

Canza fuska matashin yayi a likacin da moddibo yayi masa zancen komawa gida, Sosai
yake jin kalaman moddibo a Saman zuciyar sa harga Allah dattijon ya shiga ransa,
moddibo ne ya share mai hawayen sa sannan ya fara bashi kunun Daya shigo dashi
irin nasu na Fulanin Asali, Sosai Matashun ke jin daɗin kunun dan haka yasha sosai
sannan yace ya Ƙoshi.

Moddibo yayi murmushi yace masha Allah tunda yanzu ka Ƙoshi bari na shafa maka
maganin ka se kuma kasha na shan ko?

Matashin yace "haka ne.


Seda moddibo ya gama shafa mai maganin sannan ya bashi Nashan shima ya shanye. yana
gamawa yace to yaro bari in je inga Rabe ko lafia naga har yanzu bata fito ba.

Matashin yace" hakane kam yakamata a duba agani ko lfya,


Daga haka moddibo yay waje ya nufi Ɗakin Rabe da sallama, tana nan a Inda tai
sallah jikinta se rawa yake da sauri moddibo ya nufeta yana tambayar ta Meya
sameta?

yana taba jikinta yace " subahanallah!!


Rabe meya sameki be jira cewarta ba ya kinkimeta yayi Ɗakinsa da ita banda hawaye
babu abinda ke fita a idonta a haka ya Ƙaraso Ƙakin da ita,
Da sallama ya shigo Ɗakin sannan ya kwantar da Ita.

tunda suka shigo Ɗakin gaban Sa ya faɗi ganin wadda moddibo ya kwantar Daga ɗan
nesa dashi, a rude yake tambayar moddibo abinda ya sameta har yana Ƙoƙarin tashi
daga inda ya ke kwance,
Sosai moddibo ke kallonsa girmama sanin yakamata irin na matashi, cikeda tsantsar
so da Ƙauna Moddibo yace "yaro ka kwantar da hankalin ka ba wani Abu bane zazzabi
ne kawai Kuma zata samu sauƙi da izinin Allah. Ya faɗi hakan yana kallonsa

Har ga Allah moddibo yaji Matashin ya Ƙara kwanta masa a rai musamman dayaga ya
nuna kulawar sa a kan tilon 'yarsa guda daya!

Wai shin wanene wannan matashin ne kuma mene cikaken sunansa?

Sannan kuma meyasa yake fargabar komawa ga iyayensa ?

Menene hujjarsa na ƙin gayawa modɗibo sunansa a lokacin daya tambayeshi Ya gaya
masa wani sunan na daban?
Comment
And
Share

Sushmah💋
[3/3, 5:22 PM] Chubado Mohd: ❄️❄️❄️❄️❄️❄️
❄️❄️❄️❄️❄️❄️
🐄🐄🐄🐄
🐄🐄🐄🐄
*BAFULATANA*
✨RETURN✨
🐄🐄🐄🐄
🐄🐄🐄🐄
❄️❄️❄️❄️❄️❄️
❄️❄️❄️❄️❄️❄️

_Page : 8-9_

*_WRITING BY: CHUBAƊO_*

____✍️Murmushi moddibo yay masa sannan ya juwaya ya ɗakko ƙatuwar Boron sa (jaka)
dayake sa magani a ciki ya ɗaukko wani farin magani ya jiƙashi a wani madaidaicin
kwanon sha, seda ya ɗan ɗauki lokaci sannan ya ɗgota ya fara ƙoƙarin bata,

Ba tayi masa gaddama ba ta karɓa tasha sabda bata ƙin magani kokaɗan.

Duk abinda suke idon sa yana Kansu se kallon su yake a ransa yana mamakin yanda
moddibo yake Iya gane ko wani ƙullin maganin dake cikin jakar, shi'a tsarinsa sam
be yarda da maganin Gargajiya ba sena Asbiti a cewarsa wai a maganin Gargajiya
baya maganin cuta sedai ma ya ƙarawa mutum wata cutar. Amma se gashi a yau maganin
Gargajiya yayi masa ranah fiyeda zatonsa.

shiyasa a rayuwa kada ka raina baiwar da Allah yayiwa wani ko wata komai
ƙanƙantarta idan ba haka ba watara seka samu kanka da a ƙarƙashin Abinda kake
Rainawar kuma yayi maka Rana.

A hankali seyaji abin yana birgeshi sosai lallai ilimin sanin itace shima abune me
zaman kansa bawai kowa ne yake da wannan baiwarba, domin kuwa shima abune me zaman
kansa. Bata jima da shan maganin ba bacci ya ɗauketa ta banda zufa ba abinda
takeyi wanda hakan ya bawa moddibo tabbacin cewar zazzaɓin ya sauka.

Matashin ya kalli moddibo cike da damuwa yace "ya Kamata kayi wani Abu kagafa se
gumi take kodai zamu kaita asibiti ne??

Kallon tsaf modibbo yayi mai da mamaki kwance akan fuskarsa sannan yace "hmmm a
wannan ƙungurmin Dajin kake tinanin Samun Asibiti?

Batare da tunanin komaiba yace "ae mana aiko ba'a


Nan ba ina zaton idan muka fita da ita zuwa cikin gari zamu sami Asibitin dazamu
kaita. Ƙura masa idanu moddibo yayi harya kai ƙarshen maganarsa take yanayinsa
ya canza yace "yaro ka gani nan tunda na tashi da iyayena a nan muke Rayuwa bamu
taɓa tunanin muyi nisa da nan ba tunda muka dawo nan muka yada zango damu da
jama'armu, Asalin mu 'yan jihar Adamawa ne Haifafun NUMAN ne mu ba Asalin cikin
garin Adamawa ba a cikin Daji muke Rayuwa tareda Dabbobin mu, dolece tasa mukabar
Mahaifarmu muka dawo nan Sabida wata Masifa data Afka mana.

Modibbo sauƙe ajiyar zuciya yacigaba da cewa " mu uku kacal iyayenmu suka Haifa,
mu biyu ne maza se kuma Ƙaramar kanwar mu BADDO wadda a halin yanzu bansan inda
take ba Shin tana Raye ne kokuma ta Mutu Allah shikaɗai ne masani!!! Ya faɗa
Hawaye na Sakko masa.

Wani irin kuka ne ya taso masa wanda ya daɗe beyi irin sa ba a wannan lokacin,
koda Wasa Matashin beyi yinƙurin ya dakatar dashi ba sabida ya samu Zuciyarsa tayi
Sanyi

Seda yayi me isarsa sannan ya daidaita nutsuwarsa ya cigaba da cewa " tun daga
Ranar da muka nemi ƙanwata Baddo Muka rasa iyayen mu suka shiga tashin hankali mara
misaltuwa, bayan wanda muka samu kanmu a ciki kafin ɓatanta, wannan dalilin ne yasa
muka tattara ƙwanmu da ƙwar-kwatan mu mukabar NUMAN muka dawo nan da zama sakamakon
ƴan fashin da suka sa mu a gaba ba dare ba Rana, babban takaicin ma shine ba Iya
fashin da suke mana bane matsalar har yaran mu mata ƙanana suke yiwa Fyɗe a gaban
idanun mu ba tareda imani ko tausayi ba.

wannan Shine dalilin dayasa muka bar jaharmu ta asali muka Dawo wannan dajin,
dikkan mu dakake gani duk ƴan uwan juna ne, shiyasa muke zaune lfy lau a nan ɗin
batareda mun leƙa cikin gari ba ko hanyar titi bama bi Tunda ɗan Uwana Zakariya ya
gamuda Haɗarin mota a sanadin tsallaka titi, a lokacin da muka ɗakkoshi ya Rasa
jini sosai shiyasa muka yanke shawarar mukaishi Asibitin, mashin ɗin malm Iro muka
hau mu uku muka nufi Babban Asibitin Gwamnati dake cikin garin gyambu Amma sam
sukaƙi taimaka mana, munaji muna gani a gaban idon mu Zakariya ya Rasa Rayuwarsa
munyi kuka har muka gode Allah sannan muka sake ɗakko gawar muka dawo da ita gida,
tundaga lokacin zuwa Asbiti ya gama ficemin a rai wllh ko sunansa ma banason sabida
mutanan mu na wannan lokacin a cike suke taf da son zuciya gamida Rashin tausayin
talaka.

"sosai jikin matashin yayi da labarin Moddibo wanda yay matiƙar taɓa masa zuciya
sannan yace "A zaman danai dakai na fahimci cewar kai mutum ne na musamman wanda
yakeda shahararriyar baiwar da kaikanka bakasan iyakarta ba, da ace Hukumar lfy
zasu samu labarinka tabbas dasun Amfana dakai ta ɓangare da dama musamman abinda ya
shafi sani akan itacen gargajiya

"Hmmm kaidai ai sha'ani kawai yaro amma lamarin mutanan dake cikin wannan duniyar
sesu,
Wata rana da yamma bana mantawa wasu mutane suka shigo mana Nan da sunan Su
jami'an hukumar lafiya ne, kuma sunzo ne don su kafana mana Sansaninsu a nan sbda
muma mu samu cigaba.

"batareda tunanin komai ba muka karbe su hannu biyu Ashe abinda bamu sani ba shine
cutarmu sukazo suyi, Dayawa a cikin mu kasuwanci shanu mukeyi wanda ya zame mana
tamkar Sana'ar Gado seda suka bari kowa ya dawo daga kasuwancin sa yaxo da
kuɗaɗe masu yawa sannan suka far make mu cikin Dare suka ƙwace komai sannan suka
kashe na kashewa,
Tun daga lokacin bamu ƙara yarda da kowani mahaluki ba, hatta baƙi ma muka dena
karbarsu koda kuwa daga ina suke.

"shiyasa tunda naju ka ambaci sunan Asibiti kaga yanayina ya canza yaro sabida ko
sunan Asibitin banason ji wllh, yanzu zancen danake maka wllh da mutanan Rugar
nan zasu samu labarin zuwanka tabbas da se sun koreka kokuma ma su kashe ka.

A firgice Matashin ya zaro manyan idanunsa yana kallonsa jin kalmarsa ta ƙarshe
wato kisa sannan yace "to Baba meyasa lokacin da abin ya faru Baku nemi tai makon
jami'an tsaro ba ???
Moddibo ya kalleshi yayi murmushi irin na takaici yace " yaro da fari minyi
ƙoƙarin gwada yin hakan amma daga baya se muka gane itama hukumar se a hankali.

Matashin yayi shiru a zuciyarsa yace "Ashe Dama a kwai mutane masu fiskantar
irin wannan rayuwa?? Be taɓa zaton a kwai irinsu moddibo dake Rayuwa a cikin
wannan halin me cikeda ƙunci ba,
Tabbas Allah ne ya Ƙaddara zuwansa wannan gurin dan ya Ƙara Imani a kan rayuwar
duniya,
Haƙiƙa baka sanin Allah yayi maka Wata ni'ima a Rayuwarka har seka ga Wanda be
kaika ba sannan kake sanin Allah yayi maka Gagarumar Ni'ima,
Haka kawai seya samu kansa da jin tausayin su tareda ƙudurtawa kansa cewar insha
Allah seya temakesu da wani jinjinan Abu daze Amfanesu da izinin Allah.

Tunda garin Allah ya waye Laure ta fice daga Gidan sabda bata da wani buri
yanzu a rayuwata daya wuce Rayuwar Rabe bata inganta ba kamar ta Sauram Sa'o'inta,
tafiso tayi Rayuwa a ƙasƙance ta ƙare a tantal baɗeɗe, shiyasa ta ɗorawa zuciyarta
tsanar yarinyar tun batakai haka ba, duk wani buri na laure a yanzu be wuce taga ta
samu haihuwa da Moddibo ba ta hakane kawai zata iya mallake dukiyar sa.

Tabdi kujifa masu karatu!


Dama ance yanzu ba'a maƙiyin nesa , ya Allah ka shiga tsakanin mu da maƙiyan mu
na sarari Dana boye🤲
********

*ZAFAR ENTERPRISES* shararren Companyn dayay fice a ɓangaren kasuwanci a cikin


ƙasashen Duniya guda 12 , waƴanda suka haɗa da America, Germany, Cairo,London da
sauran ƙasashen duniya wanda yake mallaki ga babban Ɗan kasuwar nan Alhaji
Abdulwahab Abdullah, dandazon ƴan Jaridan na hanga a Harabar Babban Companyn nasu
dake Garin abuja banyi ƙasa a gwiwa ba na kutsa ta cikinsu yaja tunga na tsaya don
in samu damar ɗakkowa masu karatu Rahoto.

Wani farin Mutumi ne ya fito wanda baze wuce shekaru Sittin ba a duniya (60years)
Sanye cikin wata dakakkiyar Suite Baƙa wuluk da ita se ɗaukar idanu takeyi, tafiya
kawai yakeyi Fuskarsa a tamke babu Annuri, inda bodyguards ɗinsa majiya ƙarfi
kimanin Mutum biyar suke take masa baya harya ƙaraso ga ƴan jaridar, nan da nan
Sukayi masa caa tamkar ƙudajen da sukai arba da Buhun Sikari abinka da babban mutum
kuma me wahalar gani

Kallo ɗaya zakayi masa ka fahimci irin tashin hankalin dayake ciki duk a sanadin
Ɓatan tilon ɗansa tsahon wata Uku babu wata ƙwaƙƙwarar magana akan yaron, cikeda
Damuwa Dattijon ya sauke glass ɗin dake idanunsa ya fuskanci, wani irin takaici ne
ya ƙara samun muhalli a zuciyarsa sabida besan abinda ƴan jaridar nan suke nema
dashi ba, wannan wace irin masiface ??

A halin dayake ciki a yanzu bayajin zasu iya samun koda kalma ɗaya daga gareshi,
Wata matashiyar yarinya ce ta fito daga Companyn itama sanye da Suite Royal blue
riga da wando, ƙafarta sanye take cikin wani dogon takalmi me tsinin gaske ta sanya
wata irin hula wadda tafi kamada ta mata ƴan ƙwalisa, inda ta rufe idanunta a
cikin wani baƙin glass wanda ya mamaye rabin Fuskarta.

A ƙasaice take takowa harta ƙaraso inda ƴan jaridar suke ta tsaya daga gefan
Dattijon tace "duk wanda keda burin yiwa Mahaifina tambaya toya dunƙuleta a guri
guda ya faɗeta don bamuda lokacin ɓatawa, sannan ta kalli Mahaifin nata tayi
murmushi tace "Abie ya kamata kayi magana dasu koda kaɗan ne.

Cikeda ƙosawa ya dubeta yace "Fadilah I can't say anything about my son at this
moment, please tell them to leave Don Allah ya faɗa yayin da aka buɗe masa mota ya
shiga sukabar harabar gurin zuciyarsa a cike tab da kewar Ɗansa.

*_Thank yo so much my dearest sister's, wllh har zuciyata nakejin dadin comment
ɗinku akan wannan littafin, ngde sosai da qaunarku gareni sonso fisabilillah❤_*

Sushmah💋
[3/3, 5:23 PM] Chubado Mohd: ❄️❄️❄️❄️❄️❄️
❄️❄️❄️❄️❄️❄️
🐄🐄🐄🐄
🐄🐄🐄🐄
*BAFULATANA*
✨RETURN✨
🐄🐄🐄🐄
🐄🐄🐄🐄
❄️❄️❄️❄️❄️❄️
❄️❄️❄️❄️❄️❄️

*_Page : 10 - 11_*

*_Naji qorafin wasu daga cikin masu bin wannan littafin kan cewar typing Error
yanayin yawa, to magana ta gaskiya sedai ince kuyi haquri dani a haka amma maganar
Editing kam bazan iyayi muku shi ba, sabida a kwai abubuwa masu yawa dake gabana a
halin yanzu. Ina muku sonso Fisabilillah duk masu bin wannan lottafi 🥰_*

*_WRITING BY: CHUBAƊO_*

____✍️Sam ba haka Fadilah taso ba taso Ace Abie yayi magana da ƴan jaridar a ƙalla
ta samu Sunanta itama ya ɗagu a duniya kamar na YayantA Muzaffar, tsaki taja lokaci
guda kuma ta faɗa motar dake bayan ta Abie sukabar harabar Companyn

A cikin wata ukun da suka shuɗe na ɓatan MUZAFFAR ABDULWAHAB ABDULLAH THE C.E.O OF
ZAFAR ENTERPRISES, ba ƙaramin girgiza Al'uma abin yayi ba abinka da masu hannu da
shuni duk sanda ka kunna Redio da gidajen talabijin koda yaushe zancen akeyi tareda
yaɗa hotunansa a shafukan sada Zumunta, koda yaushe zancen akeyi tamkar baza'a
dena ba amma still babu wanda yaji labarin sa kokuma wata ƙwaƙƙwarar magana a
kansa.

MAITAMA WUSE II ABUJA

Unguwace data haɗa manyan Ginagine na alfarma hakakuma wadda aka ƙawata da abubuwa
dayawa na jin daɗin Rayuwa a gurin, duk wanda kagani a gurin tofa yaci ya tara
dukiya ne ba kaɗan ba, a haka motocin daƙe ɗauke da tambarin Sunan Alhaji
Abdulwahab Abdullah suka sulalo cikin Unguwar suna masu tsala gudu, a gaban wani
tangamemen gida suka tsaya lokaci guda kuma suka zabga uban horn Get ɗin da kansa
ya wangale kansa sannan suka danna hancinan Motocin zuwa cikin babbar harabar gidan
wadda taji kayayyakin ƙawa na ban mamaki.

Fitowa sukai da Sauri Guards ɗin suna masu Azamar buɗewa me gidan nasu ƙofa ya
fito, Direct ƙofar dazata sadashi da maine Perlour ɗin dake gidan ya nufa still
damuwa kwance akan Fuskarsa, Hajiya Sakinah ce zaune kan ɗaya daga cikin luntsuma-
luntsuman manyan Royal chairs ɗin dake falon hannunta ɗauke da Rumote tana kallon
abinda ke faruwa a duniya, kallo ɗaya zakayi mata ka fahimci tana cikin babban
tashin hankali mara misaltuwa, da hanzari ta miƙe ta nufi me gidan nata idanunta na
shirin kawo ƙwalla tace "Abie har yanzu babu wani labari akan Muzaffar?

Kasa ce mata komai yayi sabida damuwa lokaci guda ya zube akan ɗaya daga cikin
kujerun dake falon yace "har yanzu babu wani labari Sakinah wllh inaji a jikina
tamkar wani babban lamari ya faru da yarona! Kullum bana iya bacci sabida tunanin
Halin dayake ciki, jiya naje mun zauna da IG akan lamarin yace zasu ƙara tsaurara
bin ciki wllh Hajiya Sakina tabbas nima kuna dabda Rasani muddin Ba'aga Muzaffar
ba.. Ya faɗa yana dafe kansa da a lokaci guda sabida wani irin Sara masa da kan
yayi

Ƙwalla ce ta taru a idanun Hajiya Sakinah lokaci guda kuma suka zubo sannan ta zube
a gaban Abie tace "Haba Abie kaifa musulmi ne ya kamata kayi imani akan dukkan
abinda Allah ya aiko maka, muzaffar fa ba ɗanka bane kaikaɗai nima kaina ɗana ne
amma meyasa kakeso ka dinga nuna gazawarka a gabana ne shin baka tunani akan tawa
damuwar ne?

Kasa bata Amsa yayi har Fadilah ta shigo Falon kanta tsaye ta zauna daga gefan Abie
batareda tace dasu ƙala ba. Wata uwar Harara Hajiya Sakinah ta sakarma Fadilah
Sannan tace "waike meyake damun tunaninki ne Fadilah?

"wannan wace irin shiga ce haka sekace ɗiyar Kafurai? Har zuwa wani lokaci zaki
ɗauka a haka kafin kiyiwa kanki faɗa a Rayuwarki?

"kai Momy Don Allah to meye aibun shigar tawa ?

"Uwarki ce aibun ai, nace Uwarki ce aibun Fadilah. Momy ta katseta ta hanyar faɗar
hakan sannan ta ƙara da cewa "bazance komai ba a kanki tunda Allah ma sheda ne akan
irin tarbiyar dana baki, yanzu ke don Allah ko kunya bakiji ba Ace ɗan uwanki
namiji Guda ɗaya tilo yau an nemeshi an rasa tsahon wata huɗu kenan amma ke kina
nan kina yawo a gari da shigar ƴan iska?

"anya kuwa Fadilah Rayuwa zatayu miki a haka kuwa?

Miƙewa Fadilah tayi tana tura baki tabar Falon tana faɗin "aini dama an daɗe da
tsanata a gidan nan kowa yafi fifita Yaya Muzaffar akan kowa da ace nice ma na ɓata
I'm sure of that wllh babu wanda ze damu irin haka daga ke har Abie ɗin. Ta faɗa
tana biga ƙofar glass ɗin dake falon

Da ido kawai iyayen nata suka bita batareda iya furta komai ba.

GYAMBU RUGAR ARƊO

A kwana a tashi ba wuya a gurin Allah yau Matashin ya cika wata Uku cur a Gidan
moddibo cikin ikon Allah ya samu sauqi sosai, a ɗan watannin daya shafe taredasu
yasa har ya canzawa Modibbo matsayi daga wanta ya taimaki Rayuwarsa zuwa muhalli na
Uba, tabbas moddibo mutum ne na musamman wanda ya kamata ya bawa muhali mafi daraja
daga zuciyarsa, sabida Samun irinsu a wannan lokacin abune mawuyaci

A ɗan zaman dayayi dasu ya ƙara ilimi akan zamanta kewar Rayuwar duniya musamman ta
ɓangaren mu'amala da jama'a

Rabe ce ta fito ɗauke da babbar Fanteka zataje ɗebo Ruwa, a zaune ta samu Muhammad
Ali ya zubawa Shanun dake cikin garkensu idanu tamkar me nazari akan wani abu,
harta ƙaraso gurin besan tazo ba hakanne yasa ta ɗauki wani ƙaramin sanda ta jefa
masa.

Miƙewa yayi da Sauri yana kallonta sannan ya Haɗe Rai yace "what's that does mean?
Tsaki yaɗan ja sabida sanin ba gane abida ya faɗa take ba common Hausa ma wani abun
se yayi da gaske sannan take Fahimta balle kuma turanci sannan yace "meye haka ?

Dariya tayi har seda beauty point ɗinta suka lotsa sannan tace "kawai na gwadaka ne
don na gane ko kanada tsoro

Turo baki yayi yana kallonta sannan yayi murmushi yace "ni sam ba matsoraci bane
I'm a hero. Ya faɗa yana ɗaga mata hannayensa duka biyu Sama

Dariya ta sakeyi sannan ta ƙurawa bayan sa idanu batareda tace dashi ƙala ba.
Ɗagowa yayi yana kalonta yace "meye kike kallo haka?

Ɗaga kafaɗunta tayi sannan tace " ba komai kawai Gizo-Gizo nakuma shaquwa na gani a
kan rigarka ta baya.

Ihu ya saka yana tsalle lokaci guda kuma ya faɗo kanta suka faɗi ƙasa still yana
zuba mata ihun likaci guda kuma ya ƙanƙameta yana Rintse idanu.

Tureshi tayi da Sauri lokaci guda kuma ta miƙe tana karkaɗe jikinta ta ɗauki
Fantekarta ta nufi Hanyar Rafi tana me ƙyalkyala masa dariya.

Tsaki yayi lokacin daya kalli gwiwar hannunsa yaga yaji ciwo kaɗan jini na fitowa
kaɗan-kaɗan abinda da Ajebo 😂

Bayanta yabi fuskarsa a ɗaure treda ƙudurtawa kansa cewar seya Rama abinda tayi
masa, a haka har duka ɗebo Ruwan suka ɗauki hanyar komawa gida, tafiya kawai suke
bame cewa wani ƙala a tsakaninsu har suka iso hanyar data raba Rugarsu Rabe da kuma
tasu Bamanga.

Lokaci Guda sukaga an kewayesu, Bamanga ne dashi da jama'arsa ko wanne hannunsa


ɗauke da Sandar gado lol

Ɗaure Fuska Rabe tayi tana kallon Bamanga cikin harshen fulatanci tace "meye haka
zakuzo ku tare mana hanya kamar wasu ƴan Daba?

Kallon Tsaf Bamanga yayi mata Sannan yace "yanzu ke har kinada bakin magana akan na
tareku? Yau kwa nawa kenan ina zuwa gidanku kullum seki ce min in tafi baki da lfy
Ashe wannan Kaɗon shine ciwon dake hanaki fitowa gurina ? Bamanga ya faɗa yana
nuna Matashin dake gefan Rabe a tsaye yana kallon ikon Allah.

A ƙarshe da abin ya isheshi Fantekar Ruwan yasa Hannu a kanta ya ɗauke sannan ya
kalleta yace "if you handle the game with this guy you will meet me at home ya faɗa
yana barin gurin gabaɗaya

Be jima da tafiya ba Rabe tabi bayansa da gudu lokaci guda Su Bamanga suka bita da
idanu baki a Sake.

A iya ɗan wannan lokacin da suka kwashe tare da Rabe za'a iya cewa a kwai shaƙuwa
metarin yawa wadda ta samu gurbin shiga tsakanin SuRabe sedai bazamu fassara
shaƙuwar da sunan syayyah ba, sedai kawai mu kirata da sunan ƴan uwantaka sabida a
tsarin matashin babu batun soyayya a lamarin sa.

Wannan shi bahaushe ke kirada sabo tirken wawa, a haka suka shafe kwanaki a
ƙarƙashin muhali guda ɗaya
Sosai yakejin daɗin Rayuwar gurin sedai har cikin Zuciyarsa yana kewar Mahaifinsa
da mahaifiyarsa, idan tunanin ya isheshi se kawai yabi Rabe su tafi kiwo, sosai
yakejin daɗin hakan har zuciyarsa

******
*BAYAN SATI BIYU*

Washe garin da safe moddibo ya gama haɗa masa komai nasa wanda ya tsinceshi
dashi saɓanin Rigarsa wanda jini ya ɓata da kuma yagewar dake jikinta yasa moddibo
ya jefar tun a washe garin Ranar daya tsince shi, Wata Rigar Farin Saƙi irin tasu
ta Fulani ya Ɗakko masa tareda miƙa masa yace "karɓi ka sanya a jikin ka tare da
wandon shaddar taka na tabbata wata rana a ƙalla idan ka kalli Rigar zaka tuna
damu.

karɓar rigar matashin yayi ya sanya a jikinsa lokaci guda kuma ya maida kallonsa
ga Moddibo, ba ƙaramin kyau Rigar tayi masa ba domin kuwa tsayawa faɗin irin kyan
datayi masa ma ɓata lokaci ne

Bayan ya gama ne moddibo yay gyaran murya irin nasu na dattijawa ya kalli
matashin yace "yaro yau dai gashi ka warke cikin ikon Allah bayan doguwar jinyar
ɗakasha a tareda mu yau gashi har kana shirin tafiya, sedai kuma har yau bamu San
Ainihin kokai waye ba, se nake ganin a yanda mukai sabo dakai ya kamata musan koda
kaɗan ne daga tarihin Rayuwarka ko babu komai m ƙulla zumunci.

Sabida wata rana bamu San a inda zamu sake haduwa da juna ba!

Sosai kalaman moddibo suka taɓashi dan harga Allah yanajin tsohon a Ransa, tabbas
gaskiya ya fada
Ya kamata ya gaya musu ko shi ɗin wanene.

Murmushi yayi sannan yace " sunana Muzaffar Abdulwahab Abdullah the C.e.o of zafar
Enterprises .....!

Sushmah 💋
[3/3, 5:23 PM] Chubado Mohd: ❄️❄️❄️❄️❄️❄️
❄️❄️❄️❄️❄️❄️
🐄🐄🐄🐄
🐄🐄🐄🐄
*BAFULATANA*
✨RETURN✨
🐄🐄🐄🐄
🐄🐄🐄🐄
❄️❄️❄️❄️❄️❄️
❄️❄️❄️❄️❄️❄️

*_Page :12-13_*

*_WRITING BY: CHUBAƊO_*

____✍️"Ni ɗane ga Abdulwahab Abdullah, mu uku kawai Mahaifinmu ya haifa kaf cikinsu
nine babba se Fadilah Sannan zainab, ni kaɗaine Namiji kuma wanda ke jan ragamar
kamfanoninsa dake nan gida Nigeria harma dana ƙasashen waje. Ajiyar zuciya ya sauke
sannan ya ƙara da cewa

"mahaifina Haifaffan Garin kano ne a unguwar Hotoro Su biyu ne kaɗai a gurin


iyayensu dashida ƙanwarsa Asma'u muna kiranta da Mama.

Mahaifinsu Shahararren ɗan kasuwa ne sosai, wanda ya kasance kaf garin na kano ana
matiƙar jidashi a ɓangaren shaharar kasuwanci, ya Rasu yabar duniya a lokacin da
Mahaifina yake dabda kammala karatunsa na Scondry school inda Asma'u kuma take
dabda shiga sas 2, bayan Rasuwar kakana ba jimawa Itama mahaifiyarsu ta bishi
sakamakon Ciwon zuciya, bayan Rasuwar Hajiya da kimanin shekara 2 Mahaifina ya fara
tasowa sosai a ɓangaren Kasuwanci sabida yanda Allah ya sanyawa dukiyar Albarka,
cikin ƙanƙanin lokaci Sunansa ya zarta na Mahaifinsa a fanin shahara a duniya,
bayan Asma'u tayi Aure ne ta buƙaci da A raba musu gado

Sosai Mahaifina ya nuna mata rashin dacewar hakan amma sam taƙi fahimta dole yasa
ya amince da abinda tazo dashi ɗin kuma ya yakai maganar kotun Musulunci dake Kano
aka raba musu gadon, bayan an Raba musu gado dashida Ƙanwarsa Asma'u Itama ta fara
business da kuɗaɗenta sedai bata ɗauki lokaci me tsaho ba jarin nata ya karye,
shiko Mahaifina tamkar ana ƙara ɗagashi haka dukiyar ta dinga haɓaka sedai sam
hakan besa ya canzawa ƙanwar tasa ba yana matiƙar sonta sosai sabida shikaɗaine ya
Rage mata a Rayuwa don haka dole ne ya kyautata mata.

Koda Muzaffar yazo nan a zancensa seya kalli moddibo yace "baba wannan shine
tarihina a taƙaice.

Zuru Moddibo yayi masa yana kallonsa cikeda Rashin Fahimta yace "har yanzu yaro
baka sanar dani abinda nake son ji a tareda kai ba, kana so ka gaya min cewar dama
ba Sunan ka muhammad Ali ba kamar yanda ka gayamin a baya ba?

"Meyasa ka zaɓi hanyar yaudarata bayan nida zuciya ɗaya na zauna dakai?

Jikin Muzaffar ba ƙaramin sanyi yayi ba sannan yace "don Allah ka gafarce ni Baba
karkaga laifin pls, ni mutum ne me mu'amala da mutane kala-kala a hakan kuma wanda
ake farautar Rayuwarsa ta ɓangarori da dama, shin laifi ne don nayi ƙaryadon na
kare kai na?

"a'a yaro sam ba laifi kayi ba indai har ta fuskar tsaron lfyar ka ne, amma ta wata
fuskar tabbas ka cutar da yarda ta a gareka. "aa don Allah baba karkace haka wllh
bada nufi nayi ba amma tabbas nasan nan gaba zaka Fahimceni akan manufata na ɓoye
maka Asalina! Modibbo yay Ajiyar zuciya yace "Shikenan na karɓi Uzirinka sannan
innai maka fatan Alkhairi a Rayuwark ta gaba, sedai kafin ka tafi zan baka wata
babbar gudun mawa wadda nake da tabbacin cewar zata taimakeka da izinin Allah koda
ko wani irin yanayi zaka shiga. Moddibo ya faɗi hakan a lokacin dayake miƙawa
Muzaffar wani jiƙo dake cikin ƙaramin ƙoƙo ya shanye.

Seda ya shanye tass sannan ya kalleshi yace "Baba wannan maganin na menene ?
Moddibo ya kalleshi yace "maganin tsarin jiki ne dana gajeshi a gurin mahaifina
wanda ya gargaɗeni kan cewar kar in badashi ga kowa se wanda naji zuciyata ta
Amince dashi sannan zan iya badashi, har A raina nakejin cewar na yarda dakai
shiyasa ma harna baka wannan dafa'in namu na gado wanda nakeda tabbacin cewar
zakaga amfaninsa a gaba koda kuwa banan kusa bane, nidai nasihata a gareka shine ka
riƙe Gaskiya da kuma amana karka taɓa bari zuciyarka ta ruɗeka ka cutar da wanda
yayarda dakai komai rintsi.

Sosai jikinsa yay sanyi da kalaman Moddibo dan haka ba tareda zato ko tsammani ba
yay jashi jikinsa ya Rungumeshi yanajin wani iri a zuciyarsa wanda ke kamada yanayi
na kewa.
Zare jikinsa yayai daga na muzaffar sannan ya ɗau Boron Maganinsa yayi waje abinsa
ba tareda yace dashi ƙala ba, shima muzaffar ɗin fita yayi waje seda ya ɗauki
lokaci me tsayi sannan ya koma cikin gidan a ciki suka haɗu da Rabe tana ƙoƙarin
shiga ɗakin Moddibo, bin bayanta yayi shima

Yana shiga ya nemi guri ya zauna itama zaman tayi tunda ta zauna take kallon sa
tun be lura ba har ya ya fahimci irin kallon da take masa, amma seya share sabda
yasan indai ya kalleta dena kallon sa zatayi, shi kuma haka kawai yaji baya so ta
dena kallon nasa, haka kawai yaji yana son hakan har cikin Randa.

Ta jima tana aikin kallon sa sannan ya dago idanunsun ya sarƙe cikin na juna kashe
mata ido,
Da sauri tayi ƙasa da idanunta sbda wani irin kwarjini dataga yayi mata bugu da
qarima ga kashe mata idon dayayi.
Abine ya bashi dariya sosai sannan yace" o'o yau na kama Fulani Girl tana satar
kallona da alama she wants to say something oya say it. Ya faɗa yana wani kallonta

Kasa ɗagowa tayi haka kawai setaji tanajin kunyarsa dukda irin damuwar dake Ranta
akan tafiyarsa, kamar me koyon magana haka ta fuɗe baki tace "meyasa zaka tafi
bayan mun saba dakai?

Ɗan jim yayi yana kallon gefanta kaɗan sannan yace "sabida inaso naje namu gidan
nima naga iyayena I'm sure of that Suna nan suna nemana wata ƙilama har abinci basa
ci. Faɗa fuskarsa na sauyawa

"Nasan suma zasu shiga damuwa duk a rashin ganinka da basayi, na tabbata muma irin
damuwar zamu shiga a sanadin sabon da mukayi dakai. Rabe ta faɗi hakan hawaye na
taruwa a manyan fararan idanunta

Kasa ce mata komai yayi hakan yasa ta kalleshi tace "meyasa ka ɓoye mana gaskiyar
sunan ka?

Kallonta yayi yace "sabida lokacinda ya kamata ku sani beyi ba shiyasa.

Kallonsa kawai takeyi a ranta tana mamakin halinsa, yanzun nan ze sake dakai har
kuyi hira amma lokaci guda seya gimtse kamar bashi ba, taɓe baki tayi tace "inaso
nasan sunan naka da bakaso a sani?

A taƙaice yace "Muzaffar Abdulwahab Abdullah.

Kallonsa tayi tareda wara manyan idanunta tace "gaskiya sunanka yanada tsayi sosai
zan iya kiranka da Zafar?

Kallonta kawai yake harta kai ƙarshen maganar sannan ya sauke numfashi yace "As you
wish

Bata sake cewa komai ba tayi shiru wanda hakan ya bashi tabbaci akan cewar bata
cikin yanayi me daɗi

Jikinsa a mace ya kalleta yace"wllh bana so ki dinga sa damuwa a ranki gameda


tafiya ta nace miki idan na tafi zan dawo wani lokacin bazan daɗe ba kodan sabida
ke.
Ya ƙare maganar tare da nuna ta da hannunsa

Sosai maganarsa tayi mata daɗi har hakan yasa ta saki murmushin daya ƙara baiyana
kyawunta sannan tace "na yarda dakai yaya zafar! Nasan bazaka manta dani ba kuma
nima bazan manta dakai ba zafar komai yawan shekarun daza'ayi nan gaba.

Da sauri ya kalleta a ransa yana mamakikn yarinyar, wayonta da maganganunta ya


zarta shekarunta da ace zata samu wayewa a tareda ita tabbas da anyi cikakkiyar ƴar
baiwa a nan wajen iya tsara magana cikin hikima.

A nitse ta kalleshi tace Hamma zafar idan ka tafi zanyi kewarka sosai bazan gaji
da gayamaka cewar na saba dakai ba koda zan maimaita shekarun haihuwata ne ina faɗa
maka, ni kaina bansan dalilin daya sa nake jin zafin tafiyarka a raina ba zafar!

Sosai yake kallon ta tunda ta fara magana sannan yace"ni kaina Ina jinki a
raina Rabi'atu! Ta yanda har nake jin bana so na tafi na barki a nan! Har ga Allah
naji jini na ya hadu dake, bama Iya nanan abin ya tsayaba kinada gurbi a
zuciyata kamar yanda Zainab take da muƙami a cikim Raina!

Kamar daga sama yaji ta jefo masa tambaya tace "wacece Zainab?

Murmushin gefan baki yayi yace "she's my younger sister, inasonta Sosai sabida
tana iya haƙura da komai don tabbatuwar farin cikina, shiyasa nakeji da ida Except
Fadilah.

Taɓe baki tayi sannan ta kauda kanta don harga Allah ba gane maganarsa take sosai
ba, abu ɗaya kawai ta gane shine ƙanwarsa ce.

Murmushi kawai yayi sannan yacigaba da cewa "duk duniyar nan Bayan Abie da Momy
tareda sauran ƙannena babu wanda ya samu kusanci dani se ke! Dan haka kina da
matsayi na musamman a zuciyar Muzaffar Abdulwahab Abdullah.

Yanda ta nutsu tana sauraransa seka rantse tana fahimtar abinda yake faɗa mata , ta
Daɗe tana juya abin a ranta daga ƙarshe data kasa gane manufarsa seta jefa masa
tambayar datasa har seda ya ɗago ya kalleta tace "Hamma zafar dama ana Iya bawa
mutum matsayi a zuciya?

Da sauri ya ɗauke kansa daga barin kallonta sannan yace " a'a ba'ayi kawai dai na
faɗa ne nima. suna cikin maganar Laure ta bankade ƙofar ɗakin tace "to tsinanniya
fito nan kiyi min aiki
Kin shige ɗaki da garjejen namijin da a tsaye yafi ubanki ƙirar ƙarfi da tsayi
kuna lalata, in banda masifa da jaraba irinta yaran zamani inake ina wannan
gabjejen ƙato wanda ko babbar macen kirki ma setaci baƙar wuya a hannunsa Amma dan
rashin kunya se liqe masa kike yi se kace ba BAFULATANA ba !
Shegiya me bin maza karuwan wofi.

sosai abin yayiwa muzaffar zafi a rai dukda bada hausa tayi maganar ba ya fahimci
komai, amma seya danne zuciyar sa yay kamar be gane abinda take faɗa ɗin ba.

Rabe kuwa banda kuka ba abinda takeyi sabida zafin da kalaman inna Laure sukayi
mata a zuciyarta, Sarai tasan abinda bin maza ke nufi dukda ƙarancin shekarun ta.

A hankali ya matasa kusa da ita yana kallonta yace "kiyi haƙuri Rabi'atou insha
Allah wata rana se labari.

Taɓe baki Laure tayi sannan ta karkace ta dinga zuba tijara sannan ta fice ta bar
musu dakin!

Sosai abin ya batawa muzaffar rai dan haka ya kasa cewa komai, cikin tatatausan
lafazi yace " tashi kije ki shirya mutafi kiwo.
Tana jinsa amma setayi kamar bataji me yace ba ta cigaba da kukanta, sosai kukanta
yake taba zuciyarsa amma yayi shiru yana kallonta

Dan kanta ta rarrashi kanta tayi shiru, a haka moddibo yay sallama a ƙofar ɗakin
sannan ya shigo, kokaɗan beyi mamakin ganin su a tare ba sabda hakan sam ba sabon
Abu bane,
Da gudu Rabe ta ta nufi Baban nata ta rungumeshi se kuma ta sake fashewa da wani
sabon kuka. cike da damuwa moddibo ya ɗagota yana kallon fiskarta yace "meya faru
kuma ?
Bata CE komaiba sabda kukan daya ci ƙarfin ta, bataso ta sanar dashi abinda inna
laure tayi mata shiyasa tayi saurin nuna muzaffar da hannunta wanda ke tsaye daga
gefe tace "baba yaya zafar ne yake faɗamin wai zetafi Gidan su ya barmu! ta ƙarashe
mganar tana kuka.

Murmushi moddibo yayi sannan ya dafa Kafadunta yace " haba kekuwa meyasa zakiyi
haka?
Kadafa ki manta ke ɗin ƙanwarsa ce dole wata rana ze sake zuwa kodan ya ganki dan
haka ki dena kuka kinji?
Da sauri ta daga kanta alamar ta yarda da batun Baban nata, dan hka ta share
hawayenta sannan ta koma kusa da muzaffar tace "Hamma Zafar baba yace "zaka dawo
wata rana dan haka bazan sake kuka ba sbda babana baya min ƙarya komai ya fadamin
gaskiya nake daukar sa.

tunda ta fara maganar muzaffar ke kallonta sosai yake nazarin yarinyar gata
karama amma tana da kaifin tunani wannan idan ta kai shekara 20 yazata kasance?
Lallai Rabi'atu tana da wayo kuma yana jinjina irin soyayyah dake tsakanin ta da
mahaifin ta,
Murmushi yayi mata tare da Jan hancinta da hannunsa dikansu sukayi dariya sannan
suka yiwa moddibo Sallanar sesun dawo sannan suka wuce kiwo ita da Muzaffar.

*******
*_MUMBAI BABBAN BIRNIN ƘASAR INDIA_*

ƙarfe 8:00 na dare agogon ƙasar ya buga, wata hamshaƙiyar matace ke Sakkowa daga
saman benan dake cikin wani ƙayataccen falo wanda yafi kamada aljannar duniya
kunnenta ɗauke da wayarta ƙirar Iphone da alama waya takeyi, a hankali take sakkowa
cikin isa da ƙasaita hannunta jere da wasu murɗaɗɗun zobuna na zinare, sanye taƙe
cikin doguwar rigar less ɗan ubansu wanda yaji uban stones a jikinsa a haka harta
iso cikin falon ta zauna. Daga ɓangaren Abie yace "Aisha lallai ya kamata komai
yazo ƙarshe wllh na gaji da zaman nan naki a wata ƙasar ta daban don haka a cikin
satin nan ya kamata ki dawo ƙarsarmu ta haihuwa mu zauna tare a nan cikin iyalai
na.

Ɗaure Fuska Hajiya Aisha tayi sannan tace "ina me baka haƙurin sanar dakai cewar
bazan iya barin ƙasar india in dawo Nigeria ba, ina ganin gara ba baka lokaci ka
samu kayi tunani akan maganata wata ƙila zaka sakko muci gaba da zama kamar da,
amma idan na dawo Nigeria waze cigaba da gudanar da lamari Zafar Enterprises ?

Kasa magana Abie yayi ya katse kiran sabida takaicin ta, wani irin abu yaji yana
taso masa wanda yafi kamada na ɓacin rai sannan ya jefar da wayar a gefanta.

*_ABUJA NIGERIA_*
ɓangaren Abie kuwa daƙar ya iya miƙewa ya nufi toilet donya watsa ruwa ,
gabaɗaya tunaninsa ya tsaya cak babu wani abu dakeyi masa daɗi komai ya fice masa
a rai, a dadafe yayi wankan ya fito cikin mintunan da bazasu gaza goma ba ya gama
shiryawa cikin riga da wando na farar shadda ayi mata ɗinki irin nasu na manyan
masu Hannu da farcen Susa, ba laifi kayan sun masa kyau dik da irin ramar dake kan
fuskarsa da gangar jikinsa, kana kallon sa zaka fahimci baya cikin kwanciyar
hankali a haka ya fito daga part ɗinsa cikin shirin fita, Momy ya samu zaune a
falo se fadilah da Zainab wadda ke zaune kusa da momy duk lamarin Duniya ya
isheta.

Remote Fadilah ta ɗauka tana ƙoƙarin Kunna Ƙatuwa Tv bangon dake falon tamkar ba
Ɗan uwanta ciki ɗaya ake shelar nema ba a kafafen yaɗa labarai da duk wani saƙo da
lungu dake duniya ba

Kallonta kawai Abie keyi zuciyarsa na tafarfasa yace "bazance miki komai ba Fadilah
ma na tabbatarwa da kaina cewar sena shata miki layi da komai nawa sannan zaki
shiga taitayinki. Abie ya faɗi hakan zuciyasa na zafi akan Halaiyar Fadilah

Ficewa yayi daga falon harya fito harabar gidan Guards ɗinsa suka buɗe masa ƙofa
sannan Driver yaja motar sauran suka mara musu baya suka ɗauki hanyar gidan IG

Momy najin fitarsa Wasu zafafan Hawaye suka shiga zubo Mata tana kallon Fadilah

A fisace Zainab ta tashi itama tana kallon Fadilah tace "ban taɓa ganin irin wannan
haukan ba wllh se'a kanki Fadilah, wannan wani irin Rashin imani kike dashi?

Karfa ki manta Yaya ɗan uwa ki ne Uwa ɗaya uba ɗaya amma kuma kike gwada masa
wannan ƙiyayyar ta ba gaira ba dalili? Wllh ban taɓa ganin hka ba se'a Kanki wai
ace mutum yana girma amma yana rasa hankali.. Zainab ta faɗa yayin da take
kallon Fadilah tana huci

Gadan-Gadan Fadilah tai kanta Hannunta ɗauke da Cokali me yatsu lokaci guda kuma
zainab ta Saki ƙara..

.
*_Wllh Biki su Chubaɗo suke daƙyar ma ta iya zama tayi muku wannan page ɗin, fatan
zakuyi min Uziri🥰_*

Comment
Nd
Share

Sushmah💋
[3/3, 5:23 PM] Chubado Mohd: ❄️❄️❄️❄️❄️❄️
❄️❄️❄️❄️❄️❄️
🐄🐄🐄🐄
🐄🐄🐄🐄
*BAFULATANA*
✨RETURN✨
🐄🐄🐄🐄
🐄🐄🐄🐄
❄️❄️❄️❄️❄️❄️
❄️❄️❄️❄️❄️❄️

*_Page :14_*

*_WRITING BY: CHUBAƊO_*

____✍️Miƙewa momy tayi a fusace ta nufi Fadilah da ƙarfin tsiya ta ɓanɓare Zainab
wadda ke kuka ta ɗauke fuskar Fadilah da kyakkyawan mari wanda yasa har seda taga
taurari sannan ta nunata da yatsa tace "don uwarki nan gaba seki san irin Rashin
tarbiyar dazakiyi a gabana, wllh Fadilah na fara tantama a kanki anya kuwa ke
jinina ce?

Ɗagowa Fadilah tayi da jajayen idanunta tana kallon Momy hawaye na zubo mata tace
"Momy yau ni kika mara akan Zainaba?

A fusace tace "na mareki Fadilah wllh muddin kikaci gaba dayin irin wannan rashin
tarbiyar senayi miki abinda yafi haka muni ma.
Momy ta faɗi hakan a fusace sannan taja hannun Zainab suka bar mata falon, sosai
hakan yayiwa Fadilah Zafi a rai lokaci kuda kuma ta kife akan ɗaya daga cikin
kujerun dake falon ta dinga gurzar kuka kamar wadda uwarta ta mutu.

Ɓangaren Dady kuwa Direct office ɗin IG ya nufa, cikeda damuwa ya fuskanceshi yace
"na rasa abinda yake min daɗi a cikin wannan duniyar IG komai ya tsayamin cak har
yanzu babu wata ƙwaƙƙwarar magana akan ɓatan ɗana kullum abu guda kake gayamin
zakuyi bincikd. Dafa kafaɗunsa Dady IG yayi sannan yace "Haba abokina karka
wuce iyaka a maganarka mana, kada ka manta Allah kan jarraba imaninmu ta ɓangarori
dadama wata ƙila ya ɗauke ɗanka yayi nisa dashi daga gareka donya gwada imanin ka
ne. Na tabbata dukk irin son da kakeyiwa Muzaffar da irin nuna damuwarka akansa
Bakai rabin irin damuwar da Annabi Ishaq (A.s) ya shigaba a lokacin da ɗansa Yusuf
(A.s) ya ɓata ba, amma kuma dayay haƙuri da jarrabawar data sameshi na ɓatan
ɗansa wani sakamako ya samu a sanadin haƙurin dayayi?

Sosai jikin Dady yay masifar sanyi a sanadin maganar IG, cikeda jin kunyar kansa ya
ɗaga kai sama yace "ya ubangijina ka gafarta min kuskurena a gareka Bisaga Rauni na
ya Allah, sannan ka baiyana min ɗana a ɗuk inda yake ko a mace ko a raye ya
Arahmurrahimin!

Da Ameen IG y amsa sannan ya dubi abokin nasa yace "insha Allah zamu ganshi da
ikon Allah, sannan zamu ƙara faɗaɗa binkicen mu a jahohi daban daban fatana kawai a
gareka shine ka ƙara haƙuri na ɗan lokaci insha Allah komai zeyi dedai.

Shawarwari IG ya dinga bawa Dady daga bisani kuma sukai sallama da juna.

*_RUGAR ARƊO (Taraba State)_*

Zaune suke cikin Dajin da suka kutsa tareda dabbobinsu Rabe ta kalli muzaffar tace
"ina cikin farin ciki sosai yau. Murmushi yayi sannan yace "meyasa kike farin
cikin? Ya faɗi hakan yana kallonta

Sinkuyar da kanta ƙasa tayi tace "Sabida ka biyoni kiwo a Rana ta ƙarshe wadda
bayan ita banida tabbacin cewar zan sake ganinka, ni'a ganina wannan babbar nasara
ce dana samu a Rayuwata a zamantakewar da mukayi dakai don Allah Hamma Xafar idan
ka koma Gidanku Karka manta Dani!!!!!

Tunda ta fara maganar yake kallonta tareda maida duk wani hankaƙinsa a gareta
sannan yace "a duk irin jerin mutanan da kika fassara Muzaffar a fanin
zamantakewarsa dake to'a irin yanayin zaki sameshi don haka abinda kike fata na
karna manta dake Tabbataccen al'amari ne wanda ke gudana a tsakanina dake
Rabi'atou, kada ki manta cewar kefa ƙanwata ce dole watarana koban dawo sabida
kowa ba zan dawo Sabida ke. Ya faɗa yana kallon tsakiyar ƙwayar idanunta

A haka dai kiwon nasu ya kasance har suka dawo gida, tun'a daren Ranar Rabe bata
sake shigowa ɗakin ba har Garin Allah ya waye muzaffar ya fara shirin tafiya, ko
kaɗan bataso ta haɗu dashi a lokacin tafiyarsa tafi so ta fara koyawa kanta haƙurin
Rashinsa a tareda ita. Da wannan Batun ta samarwa kanta matsaya Tun bayan fitowar
alfijir datayi Sallar Asuba tayi nesa da Gidan har Muzaffar ya kammala shirinsa ya
fito sanye cikin shigar kaya Na farin Saƙi irin na Fulani
Sosai kayan suka karɓi jikinsa tamkar dama can Bafulatanin ne

Har a ransa yaji cewar yanaso ya sake ganinta kafin tafiyarsa amma sam ya kasa
tambayar Moddibo ina take, sam beso Sabonsa da ita har yakai wannan matakin ba
sabida bayaso zuciyarta takaishi wani matsayi na daban wanda ya wuce na ƴan uwan
taka kamar yanda ya ajiyeta a matsayin ƙanwa, shiyasa sam wasu lokutan yake jan
baya da ita a irin alkhairan da mahaifinta yayi masa bayaso shaƙuwarsa da ƴar ya
Rushe wannan dangantakar a tsakaninsu.

A haka suka fito daga ɗakin har bakin ƙofar bukkar Inna Laure Muzaffar ya tsaya
tareda durƙusawa ya kalleta yace "To Inna ni zan wuce gida ina roƙon Allah ya saka
muku da alkhairi bisa taimakon da kukayi min a rayuwa ta, a zaman danayi dake idam
har na taɓayi miki wani abu mara daɗi don Allah ki gafarce ni pls. Ya faɗa yayinda
yake miƙewa daga ƙofar ɗakin ya juya

Taɓe baki Inna laure tayi sannan tace "o'o ɗannan bakamin komai ba, hasalima ni
daɗin tafiyar taka nakeji har Raina sabida bansan tsiyar datake tareda kai ba, nida
zaka temakeni ma wllh idan ka futa daga Rugar nan ka roƙi Allah mantar dakai
hanyar shigowa garin nan gaba ɗaya.

Murmushi kawai yayi sannan yace "insha Allah zanyi Addu'ar amma sedai nace Allah ya
mantar dani ƙofar ɗakinki badai ta Rugar nan gabaɗaya ba. Be jira cewarta ba yayi
gaba abinsa

Har cikin zuciyar Moddibo yaji tafiyar yaron sabida yanda yakejinsa a Ransa, Babur
ɗin malam Iro moddibo ya karɓo Aro sannna ya ɗauki muzaffar a bayan Mashin ɗin suka
Tafi donya kaishi tashar dake cikin Gari.

Har tasha yakaishi sannan ya biya masa kuɗin mota ya juya ze tafi, da sauri
muzaffar ya biyoshi ya Ringumeshi tareda kama Hannunsa yace "Banida isassun
kalmomin dazanyi godiya a gareka Baba amma ina roƙon Allah ya gina maka gida a
gidan Aljanna!!

Zare jikinsa Moddibo yayi daga nasa sannan ya juya da Sauri yana hawaye batareda ya
juyo ba ya kunna mashin ɗin yabar Gurin muzaffar na kallonsa.

Sosai yaji shima zuciyarsa tayi mugun Rauni amma kuma bashida wani zaɓi dole ne ya
koma gida kodan sabida iyayensa da sauran ƴan Uwansa. Yana nan tsaye har motar ta
cika suka kama hanyar Abuja zuciyarsa a cike Fal da kewar Fulanin Dajin.......

*_Naga ƙaunar ku da Soyayyarku akan wannan littafi gamida Addu'o'in alkhairinku


gareni, thank you all for the Support and Comment ubangiji yabar zumunci_*

Comment
And
Share
Sushmah💋
[3/3, 5:23 PM] Chubado Mohd: ❄️❄️❄️❄️❄️❄️
❄️❄️❄️❄️❄️❄️
🐄🐄🐄🐄
🐄🐄🐄🐄
*BAFULATANA*
✨RETURN✨
🐄🐄🐄🐄
🐄🐄🐄🐄
❄️❄️❄️❄️❄️❄️
❄️❄️❄️❄️❄️❄️

*_Page :15_*

_Sisters wllh biki mukeyi shiyasa kuka jini Shiru amma dazaran mun gama to har
sekun gaji dani Aradu.🥰_

*_WRITING BY: CHUBAƊO_*

____✍️Tunda ya shiga motar abu guda biyu ne keyi masa yawo a saman zuciyarsa, na
farko shine ƙwallar daya gani a kwance cikin ƙwayar idon Modɗibo wanda yakeda
tabbacin cewar ƙaunar dayakeyi masa ce sular faruwar hakan, abu na biyu kuma shine
sabon daya bari har ya shiga tsakaninsa da ƙaramar yarinyar da ko'a mafarki be taɓa
zaton ze iya samamata gurbi a cikin zuciyarsa ba domin kuwa shi'a tsarinsa babu
maganar Soyayya a cikinsa, shin yanzu a wani hali zata kasance bayan tafiyarsa?

Ajiyar zuciya ya sauke a karo mara adadi basu suka iso garin Abuja ba se ƙarfe 8pm
na dare, kuɗin da modɗibo ya bashi ya kalla sannan ya tare Taxi yace "Maitama zaka
kaini. Daga haka ya buɗe motar ya shiga ciki suka ɗauki hanyar Maitama, har Suka
isa cikin Maitama Muzaffar na tunanin makomar Yanda Rabe Zata kasance a sanadin
tafiyarsa. Me taxi ɗine ya katseshi ta hanyar cewa "malam mun iso maitama fa a
ina zan ajiye ka?

Shiru yayi kimanin ƴan sakanni sannan ya faɗa mishi inda ze kaishi, a bakin ƙofar
makeken get ɗin gidansu me motar ya faka sannan Muzaffar ya fito tareda miƙa masa
kuɗin motar, yana karɓa yaja motar yayi gaba abinshi a ransa yana mamakin ganganci
irin na wannan Bafulatani

A nitse yake takawa harya kai jikin Get ɗin tareda Sanya babban yatsansa na hannun
damansa a jikin tompprint ɗin dake Jikin Get ɗin take get ɗin ya buɗe yana shiga
gidan ya juyo da sauri kafin Get ɗin ya rufe kansa yace "Nande feri miwarti insha
Allah Rabi'atou!! Mimeɗataye yejutugo beko awanniyam dole watarana Zan dawo
gareki Fulani girl. Ya faɗi hakan yayinda get ɗin ke Rufewa

A nitse yake takawa harya isa tsakiyar farfajiyar gidan tun kafin ya sake ɗaga
ƙafarsa guards ɗin dake tsaron gidan ta ciki suka kewayeshi lokaci gududa kuma suka
wurga masa tamyar shi waye bakinsu a haɗe lokaci guda?

Tsura musu idanu kawai yayi lokaci guda kuma takaicinsu ya cikashi amma still ya
kasa ce musu komai Kuma bebar kallonsu ba. Kayan jikinsa ya kalla lokaci guda kuma
ya maida hannunsa kan lallausar Sumarsa data fara fitowa sosai kuma tayi yawa
sabida Askin da Moddibo yayi masa a lokacin daya tsince shi sakamakon saran dake
kansa a lokacin yayi tareda datse lips ɗinsa da Fararen haƙoransa yace "who the
hell are you to stop me and asking who I'm? Muzaffar ya faɗi hakan yayinda yake
gyara tsaiwarsa irin wadda ya sabayi yayinda yaci nasara a kan dukkan abinda yasa a
gabansa.

Take idanunsu ya firfito wajen yayinda kunnuwansu sukai Arba da Amon muryar
muzaffar me cikeda tsantsar izza gamida yarda dakai zubewa sukai a ƙasa gabaɗayansu
suna masu ban haƙuri a gareshi tareda murnan ganinsa, kallon tsaf yayi musu sannan
ya daɗa gyara tsaiwarsa yace "duk kanku ku miƙe inada saƙon baku, banaso kowa yasan
ina cikin gidannan har zuwa lokacinda zan baina kaina a radin kaina. Yana gama
faɗar hakan ya juya ya fara tafiya

Da sauri ɗaya daga cikin Guards me Suna Selomon yace "but why sir Amma kullumfa se
babban megida ya shiga damuwa wasu lokutan ma har ya zubarda hawayensa duk a
sanadin ɓacrwarka, amma kana ganin hakan baze zama illa ga lafiyarsa ba?

Tsayawa cak yayi batareda ya juyo ba yace "abida na baɗa kenan Selomon kuma duk
wanda ya saɓawa ƙa'idata tabbas ku sani to a bakin akinsa. Ya faɗa yana barin kurin
Direct Side ɗinsa ya nufa tareda murɗa haɗaɗɗen Handile ɗin dake jikin ƙofar wanda
yafi kamada na musamman sannan ya shiga falon

Masha Allah haƙiƙa wannan falo ya gama ƙawatuwa da dukkan ababan ƙyaleƙyale na
Duniya, dukda cewar babu wani tarkace a falon amma komai na ciki Expensive abu ne
hular dake rataye a bayansa ya cire tareda hurgata a saman manyan Royal chairs ɗin
dake falon masu launin Golden da yarfan Ruwan Zinare a jikinsu, maida kallonsa yayi
kan makekiyar flaczima ɗin dake falon wanda take very slim babu wani tudu a tareda
ita, ɗan tsaki yaja kaɗan sannan ya wuce Bedroom ɗinsa

Nan ma faɗar irin haɗuwar ɗakin wllh ɓata lokaci ne a gareni tareda ku masu karatu,
amma hasashen haɗuwar ɗakin C.E.O of xafar ɗin ya rage gareku readers😂 kusan
abinku da matashi me jini a jika kuma ɗan ƙwalisa me citta a hannu dole ne komai
nasa ya zama Very Expensive

Toilet ya nufa Direct ya buɗe shima nan ɗin dai ba'a magana domin kuwa babban guri
ne me zaman kansa wanda ya haɗa da kayan ƙawa na ban mamaki, babban jakuzi ne daga
can gefe se kuma wani falelen abu daga gefe wanda yafi kamada bahon tare ruwa amma
sedai shi yanada girma sosai don mutum ze iya shigewa cikinsa complite

Gefansa kuma wata slim drower ce wadda aka zuba towels farare masu azabar kyau
gamida burgewa, Direct kusa da wannan abun me kamada bahon wankan ya nufa sannan ya
kara hannunsa daga gefan wani Rami dake jikin abin take ruwa ya fara ɓulɓulowa daga
cikin abin, kafin kace me tuni Ruwan ya gama taruwa kuma still ruwan da zafinsa
daidai yin wankan mutum zare rigar dake jikinsa yayi tareda dogon wandon saƙin take
wurɗaɗɗen jikinsa gamida faffaɗan ƙirjinsa suka baiyana, se'a lokacin na fahimci
cewar lallai matashin ma'abocin cikar zati ne gamida haiba duba da irin yanda
zanen 6part ɗin dake cikinsa suka baiyana a fili, cikin bahon ya shiga ya zauna
tareda lumshe manyan idanunsa sabida yamda zafin Ruwan yake ratsa duk wata gaba
dake jikinsa, seda ya shafe kusan 30mnt a haka sannan ya fito tareda danna wani
buttum dake jikin abin take ruwan ya tsiyaye sannan ya shiga jakuxi ɗin yayi wanka
ya ɗauro wani babban towel a jikinsa tareda ratayo wani ƙaramin towel ɗin a kansa

Goge gashin kansa yayi da ƙaramin towel ɗin dake wuyansa sannan ya buɗe Makekiyar
closets ɗinshi dake manne a jikin bangon ɗakin, ɓangaren ƙananan kayanshinya bude
take Sportwears ɗin suka baiyana tareda Sleeping dress ɗinshi wanda gabaɗayansu
suka kasance mallakin Companyn Armany.

Wata lallausar riga blue ya jawo da wandonta ya sanya a jikinsa sannan ya tada
Sallar magrib dake kansa sannan yayi isha gaminda shafa'i da wutiri, seda ya gama
tasbihinsa sannan ya miƙe a matiƙar gajiye yayiwa kansa masuki a kan makeken Royaƙ
bed ɗinsa wanda yayiwa ɗakin ƙawanya, yana kwanciya wani gajiyayyen bacci ya
ɗaukeshi.

Ɓangaren Abie kuwa sosai suka sake dagewa da Addu'o'i akan ɓatan ɗan nasu, Momy ce
zaune bisa Daining ta zubawa abincin da zainab ta zuba mata idanu batareda takai
koda cokali ɗaya bakinta ba, hakama Abie wanda ke gefan momyn cikeda damuwa Zainab
ta kalli iyayen nata tace "Haba Abie don Allah ya kamata kuyi haƙuri da jarrabawar
da Allah ya aiko mana, idan har ku iyayenmu kunasa damuwa a zukatanku irin haka
mukuma idan wani abun ya sameku a sanadin hakan ya kuke tsammanin zamuyi da Rayuwar
mu?

Ajiyar zuciya Abie ya sauke lokaci guda kuma ƙwalla ta samu gurɓi a cikin ƙwayar
idonsa yace "kiyi haƙuri daughter ni kaina abin ne yakeso yafi ƙarfina kaina duk ya
kulle duk a sanadin ɓatan yaron nan taya kike zaton zamu iya kwantar da hankalin mu
?

"Amma Abie ai....

Ƙarar wayar Abie ce data gauraye falon gaba ɗaya yasa Zainab tayi shiru tana kallon
Abie ɗin Ƙurawa wayar idanu yayi yana kallon screen ɗin tareda sunan wanda ke
kiran nashi, abokin kasuwancinsu ne wanda zasu zauna dasu gobe da safe akan harkar
kasuwanci kuma ya tabbata cewar idan mutumin yasan Muzaffar baya nan tabbas zecire
hannun jarinsa dake Companynsu.

Fadilah dake ta bugar abincinta ta ɗago ta kalli Abie tace "ka ɗaga wayar
hankalinka kwance kuyi magana dashi I'm sure of that idan har yayi magana dani baze
sake ambaton Muzaffar ba sedai Fadilah MD ZAFAR ENTERPRISES.

Taɓe baki Zainb tayi sannan tace "Amma dai da alamar cewar Fadilah Abdulwahab
Abdullah zata yaudari kanta ne kawyai wajen haɗa ƙwarewarta data namijin duniya
kuma wanda ya saba cuɗanya da manyan-manyan Turawan da sukai fice a duniya ta
ɓangaren Kasuwanci kuma ya kaisu ƙasa. Zainab ta faɗi hakan yayinda take
ƙyalƙyalewa da dariya

A Fusace Fadilah tayi kanta zainab ta mike da sauri harda gudu ta haura sama ta
shige ɗakinta ta murza masa key tana me ƙara kwashewa Fadilah dake buga mata ƙofar
daki kamar zata ɓalla da dariya

Haka Fadilah ta gama tsaiwarta tana jaraba harta gaji tabar gurin Zainab na dariya

Babu yadda Dady ya iya dole ya ɗaga wayar kuma ya basu tabbacin cewar Hameyd ze
halacci meeting ɗin 11am dot. Kallonsa kawai momy keyi fuskarta ɗauke da mamki
tace "haba Abie don Allah meyasa zakayi alƙawarin da bazaka iya cikawa ba?

Kamar zeyi kuka yace "Toya zanyi dasu fisabilillahi!! Nikam banida wata mafita
wadda tafi hakan. Miƙewa kawai momy tayi tabar gurin Don bata juri wannan batun
ba, a haka lamarin ya kasance shima Dady ya miƙe yabi bayanta

*_Gyambu Taraba State_*

Tun bayan tafiyarsa Rabe ta fara ƙoƙari yaƙida sabonda tayi da muzaffar Amma kuma
sam hakan yafi ƙarfinta dole yasa ta fashe da kuka sabida Rashin sanin mafita a
Rayuwarta, bata taɓa zaton cewar shaƙuwarta dashi takai wannan matakin ba amma kuma
se gashin lamarin ya zarta tunaninta da Fahimtarta, a yanda takejin zuciyarta a
halin yanzu komai ze iya faruwa da ita

A wannan daren tayi kuka kamar Ranta ze fita har seda ta gaji ta godewa Allah, wllh
da ace tasan irin halin da zata shiga kenan a sanadin Sabo da Muzaffar toda bata
bari hakan ta faru da ita ba, A haka ta kaji da kukan har wani wahalallen Bacci yay
Awon gaba da ita bisa ƙaramar katifar ciyawar dake ɗakin.

******

Abuja Nigeria

Washe gari ko Sallah Asuba Muzaffar be samu ba sabida baccin dayasha kansa, a
gaggauce ya tashi yayi Sallar Asuba ko Tasbihi beyi ba ya miƙe ya koma gado ya
kwanta be farka ba har se waje ƙarfe goma na safe, wanka ya shiga ya fito sannan
ya tsaya a gaban wata ƙaramar drower din dake gefan closets ɗinsa. Wali emvlop ya
zaro ya buɗe sannan yana duba Abubuwan dayay missing a sanadin ɓatansa, tsaki
yaɗanja kaɗan lokacin dayaci karoda neeting ɗin daze shiga yau da Mr. Vicram
Aditiya

Take ya maida takardan ya buɗe ƙatuwar closets ɗinsa wadda ke ɗauke da Haɗaɗɗun
korian Suite ɗinsa masu masifar kyau, wata baƙar Suite ya zaro a jikin hanga
ɗinta ya jefata kan makeken gadonsa sannan ya fara shiryawa cikin Sauri, cikin
mintunan da bazasu gaza 10 ba ya kamala shiryawa wayar dake gefan gadonsa ya ɗauka
ya shiga kiran wayar Samuwal Shugaban guards ɗinsa yace "im waiting 4u guys you
should be fast the time is going.

Katse wayar yayi tareda tsayawa a gaban mirior yana gyara lallausar sumar dake
kansa, cikin mintina kaɗan su Samuwal suka iso gidan bayan fitarsu Abie da
Fadilah.

Motocine a jere kimanin guda 12 ƙirar Formatic C300 tun ya fito Suka firfito suna
jiran fitowarsa, a nitse yake takowa gurin cikin takunsa na isa da ƙaisata ya shiga
mota Suka ɗauki hanyar Compayn Zuciyarsa a dake.

Semuc a sauka lfy C.E.O

Sushmah💋
[3/3, 5:23 PM] Chubado Mohd: ❄️❄️❄️❄️❄️❄️
❄️❄️❄️❄️❄️❄️
🐄🐄🐄🐄
🐄🐄🐄🐄
*BAFULATANA*
✨RETURN✨
🐄🐄🐄🐄
🐄🐄🐄🐄
❄️❄️❄️❄️❄️❄️
❄️❄️❄️❄️❄️❄️

*_Page :16_*

*_WRITING BY: CHUBAƊO_*


___✍️Sosai idanunta suka ciko da tarin ƙwalla gamida wani irin karaji ta fara
takowa zuwa gabansa idanunta na tsiyayar kwallah harta iso gabansa ta tsaya, lokaci
guda kuma ta miƙa hannunta na dama zuwaga kyakkyawar fuskarsa tana me sakin kukan
datake dannewa, rungumeshi tayi ƙam a jikinta tana kuka sosai

Jikinsa ne yayi masa bala'in sanyi lokaci guda kuma yaji tausayinta na mamaye duk
wata gaɓa dake jikinsa yace "mom why are you crying like this? Plz mom don Allah
kiyi shiru wllh hakan yana taɓa zuciyata sosai!!!

Zare jikinta tayi daga nasa tana me zubar da hawaye wanda yafi kamada na farin
ciki tace "ina ka shiga tsahon wannan lokacin ka barmu da ciwuka a zukatan mu?

Share mata hawayen yayi da farin hanky ɗin dake hannunsa sannan ya kama hannunta
suka ƙarasa cikin falon ya zaunar da ita Tareda zube ƙafafunsa a ƙasa suna masu
fuskantar juna yace "wannan maganar bata yanzu bace Momy nidai fatana bai wuce ki
dakatar da wannan kukan da kikeyi ba, wllh momy kukanki yana ɗaga min hankali don
Allah kiyi shiru pls.

Ajiyar zuciya Abie ya sauke sannan ya kalleta yace "kiyi haƙuri kibar kukan hakanan
tunda dai damuwar tamu ta yaye gabaɗaya semu godewa Allah. Zainab ce ta shigo falon
fuskarta a haɗe kamar zatayi kuka batareda ta lura da Muzaffar wanda ke zaune bisa
kafet ɗin dayayima falon kawanya ta kalli Abie tace "don Allah Abie kalli abinda Ya
Fadilah tama wayana Don kawai na gaya mata gaskiya. Ta faɗi hakan idanunta na
zubar da ƙwallar takaici

Hannu Abie ya miƙa mata alamar tazo gareshi ba musu kuwa ta nufeshi ta zauna a
gefansa tana sakin wani irin kuka, murmushi Abie yayi sannan yace "ya isa haka
nan indai wayace silar zubar hawayen zainaban Abie to ya zama ɗole a gareni in siya
miki duk wayar da kikeso. " A'a Abie ninan zan Siyawa ƙanwata waya baseka
wahalar da kanka ba tunda har tana dani. Muzaffar ya faɗi hakan yana murmushi

Da wani irin mamaki gamida kaɗuwa Zainab ta kalli Direction ɗin da muzaffar ɗin ke
zaune se faman murmushi yake mata, da gudu ta miƙe daga gefan Abie ta nufi muzaffar
ta rungumeshi tana kukan farin cikin, zareta yayi daga jikinta yana binta da
hararar wasa yace " see you ji yanda kike kuka kaman wata goyon kaka. Bige masa
hannu tayi tana turo baki ta ƙara Hugging nasa sosai. Dariya kawai Abie yayi sannan
ya miƙe yana kallon muzaffar yace "oya tashi muje falona I want to talk to you
about something. Miƙewa yayi da sauri yace "to ranka ya daɗe Alhaji Abie.
Gabaɗayan falon dariya sukayi sannan Abie y kama hannunsa sukabar falon zuwa
harabar gidan ta baya inda makeken Guiding ɗinsu wanda aka ƙawata da abubuwan
rayuwa na jin daɗi kala daban-daban.

*_MUMBAI INDIA_*

Zaune take cikin makeken falonta na alfarma hannunta ɗauke da System wadda ke ajiye
a gefanta idanunta manne da wani farin glass wanda yafi kamada na ƙara ƙarfin gani,
daga yanda ta nutsu tana kallon system ɗin kaɗai zaka fahimci cewar A kwai abinda
takeyi me matiƙar mahimmanci a ciki, wayarta ƙirar Iphone ce ta ɗauki ruri wanda
hakan yasa ta ɗago daradaran idanunta tana kallon wayar, Abie shine sunan daya
baiyana akan screen ɗin wayar

Ɗan murmushi tayi irin na manyan matan da suka fara manyanta sannan ta dakatar da
Abinda takeyi ta fara ƙoƙarin amsa wayar still tana murmushi. Daga ɓangaren Abie
yace "Assalamu'alaikum. Ajiyar zuciya ta sauke kaɗan sannan Hajiya Aisha tace
"wa'alaikumussalam Abie ya gda ya kuma aiki?

Zuciyarsa a dake yace" lfy lau Aisha yakamata fa ki fahimci cewar dukkan abinda na
gaya miki akan dawowarki Nigeria bawai ina wasa bane, banaso ki ƙureni har nayi
miki abinda tun ƙuciyarmu dake banyi miki ba, kullum lamarinki ƙara gaba yakeyi a
duk lokacin danayi miki maganar dawowa Nigeria to wllh kiji ki sani muddin baki bi
Umarni na a wannan lokacin ba wllh bazan sake nanki ba! Inyaso duk abinda kikaga
yafi miki sekiyi. Tun kafin tayi yunƙurin magana Abie ya katse wayar yana huci

Ƙurawa wayar idanu tayi lokaci guda kuma ta Fashe da wani irin kuka, cikeda rashin
sanin mafita seda tayi me isarta sannan ta share hawayenta ta mike batareda ta
kashe System ɗinba ta haura upstairs, toilet ta shiga shiga ta ɗauro Alwala sabida
gabatowar lokacin sallar Zuhur, bata jima a toilet ɗin ba ta fito Direct kan
daddumar dake shimfiɗe a ɗakin daga kusurwarn gadon dake ɗakin ta nufa lokaci guda
kuma ta ɗauki farin dogon hijabinta daketa uban ƙamshi a kan hanger ɗin datake
rataye jakunkunanta ta ɗauka tareda kabbara sallar nata, ta jima kafinta idar nan
ma seda ta shafe awa guda tana addu'o'inta sannan ta shafa. Wayarta ta janyo ta
shiga kiran Muzaffar harta masa 2 miss call amma be ɗagaba dole ta haƙura ta fice
daga ɗakin tana me nanata maganar da Abie ya gama faɗa mata a ƙoƙon zuciyarta, har
cikin ranta takejin cewar ta tsani Nigeria irin tsanarda ko'a mafarki bata taɓa
ganin irinta ba! Shin meyasa Abie yake ƙoƙarin tilasta mata dawowa gamida
barazana akan hakan??

Wani siririn tsaki taja mara sauti sannan taci gaba da gudanar da aiyukanta dake
gabanta amma still zuciyarta babu daɗi.

Wannan shine abinda ya faru a ƙasar india tsakanin Abie da Hajiya Aisha

*_GYAMBU TARABA STATE_*

Zaune take ta haɗe kanta da gwiwa tana aikin daya aureta a ƴan kwanakin nan wato
tunani, moddibo ne ya fito cikin shirin tafiyar kiwo tsayawa yayi daga ɗan nesa da
ita yana kallonta gabaɗaya ta gama ramewa babu abinda ya rage a kan fuskarta se
dogon hanci da idanu, sosai yake tausaya mata dukda cewar ya gama karantar abinda
ke kwance cikin ƙwayar idanunta a matsayinsa na uba gareta dolene ya fahimci
damuwarta koda baze iya tsinana mata komai a kai ba.

A hankali yake ɗaga ƙafafuwansa waƴanda sukayi masa nauyi harya isa gareta ya
durƙusa bisa kan ƙafafunsa gamida kai hannunsa kan fuskarta, dagowa tayi a sanyaye
suka haɗa ido da mahaifin nata lokaci guda kuma ta saki wani irin kuka wanda ya
taso mata a lokacin. Shiru moddibo yayi yana me bubbuga bayanta ba tareda yayi
yunƙurin hanata kukan ba a haka Inna Laure ta fito ta samesu, taɓe baki tayi daga
inda take cikin harshen Fulatanci tace "indai kuka ne wllh yanzu kika fara tunda
kika biyewa kaɗo ya kaiki kuma ya baro, indai kuka to bakimayi komai ba.

A fusace modɗibo ya kalleta zuciyarsa na tafasa yace "Haba Laure!! har zuwa wani
lokaci zaki ɗauka kina ƙara rura wutar gobarar hassadar dakeci a cikin zuciyarki ?
Wllh inaji miki tsoron ranar dazaki girbi abubuwan da kike shikawa da hannunki!

Taɓe baki tayi tana binsa da wani ɗan iskan kallo wanda yafi kamada na rainin
hankali sannan tace "meko zan girba wanda ya wuce alkhairi ? Wllh moddibo bazan
girbi komai ba a gaba se alkhairi. Ta faɗi hakan tana barin gurin

Da ido kawai Moddibo yabita batareda ya iya furta koda kallama guda ba, ajiyar
zuciya ya sauke sannan yace "Ya Allah kayi mana tsari da cutar hassada wadda zata
makantar da ganin mu zuwa wani al'amari na daban.

A halin dayake ciki a yanzu abubuwa dayawane suke addabar zuciyarsa wanda shi kansa
ya rasa ta hanyar daze iya warwaresu face ya miƙa lamarinsa ga Rabbissamawati
wal'ardi!
Hannunta kawai ya kama suka nufi garken shanunsu, shida kansa ya kwance shanun
sannan ya kaɗasu suka tafi kiwo zuciyar ko wannanesu a dagule, saɓanin Fulani girl
wadda soyayyar muzaffar ta gama zagaye duk wata gaɓa ta jini dake cikin jikinta.

********

Al'amarin muzaffar kuwa sosai yake gudanar da abubuwan dake gabansa yama manta da
rayuwar dayayi kimanin tsahon wata uku a wani daji tareda wasu fulani daji masu
karamci, shi kansa be fiye samun lokacin kansa ba har aka shafe wata Shida cur yana
yawo a ƙasashen duniya don bunƙasa hannun jari da kasuwancin mahaifinsa......... A
ɗan wannan tsukun lokacin daga dawowarsa zuwa yanzu baze iya cewa a ga yawan
lokacin daya samu na hutawa a taredashi ba.

Amma lokaci zuwa lokaci yakan tunasu har yayi murmushi, musamman ma Moddibo da
irin karamcin dayayi masa a rayuwa. Haƙiƙa zuciyar ɗan Adam kan ginu da abubuwa
guda biyu na ɗaya shine tuna hacci na biyu kuma hassada, amma me wayo kan iya
magancewa kansa cutar hassada ne ta hanyar cusawa kansa yada da dukkan abinda wani
yafishi dashi komai ƙanƙantarsa, abu mafi mahimmanci kuma shine addu'a tareda qara
himma wajen roƙon Allah akan ya cire maka ciwon hassada komai ƙanƙantarsa a
rayuwarka, wllh idan ka ginu akan hakan babu abinda ze dameka koda ko meneneshi😊

Comment
Nd
Share

Sushmah💋
[3/3, 5:23 PM] Chubado Mohd: ❄️❄️❄️❄️❄️❄️
❄️❄️❄️❄️❄️❄️
🐄🐄🐄🐄
🐄🐄🐄🐄
*BAFULATANA*
✨RETURN✨
🐄🐄🐄🐄
🐄🐄🐄🐄
❄️❄️❄️❄️❄️❄️
❄️❄️❄️❄️❄️❄️

*_Page :17_*

*_WRITING BY: CHUBAƊO_*

: ‫ِبْســــــــــــــــــــــِم َالّلِه الَّرْحمِن الَّرِحيم‬

O Allah, we can't escape our return to You. Forgive our sins and accept our good
deeds. Let our last days be the best of our days, and make our last sentence on
earth be "Kalimatush Shahadah", Ameen
*JUMU'AT MUBARAK TO ALL MUSLIMS UMMAH!!!*

*_O'o naji qorqfinku mabiya wannan littafi har seda na godema Allah 😄 Don haka
qorafinku ya karɓu isha Allah zan cigaba da rubuta muku wannan littafi koda ba
kullum zan dinga baku update ba, motsi yafi laɓewa inji ƴan magana lol. Ngde sosai
da nuna qaunarku a gareni sonso fisabilillah❤️
_*

___✍️Zaune yake cikin hamshaƙin office ɗinshi wanda aka ƙawatashi da abubuwa na
musamman wa ƴanda suke tafiya da zamani idanunsa sanye cikin wani bakin glass
mallakin compayn prada, gabaɗaya ya maida hnkalinsa kan system ɗin dake gabansa
tsaki yaɗan ja kaɗan tareda zare baƙin glass ɗin daya rufe idanunsa dashi donya
tabbatar da abinda idanun nasa suka gane masa, wara manyan idanunsa yayi kaɗan
yana kallon yanayin sababbin tsare-tsaren da aka samu a cikin ɗan tsukun lokacin
daya rasa a cikin Rayuwarsa na ɓatansa, lokaci guda ya miƙe yana wani cizon jan
lips ɗinsa na ƙasa ya nufi office ɗin Accounter Salahudden, duk inda yabi kallonsa
kawai ma'aikatan keyi tareda risinawa suna kwasar gaisuwar a gareshi faɗaɗa
murmushin yaƙen dake kan fuskarsa yayi tareda amsa musu gaisuwar da sakin fuska a
haka har ya isa office ɗin Accounter Salahuddeen ɗin.

Tun kafin ya iso office ɗin Salahudden ke kallonsa ta glass ɗin dake zagaye da ko
ina na office ɗin, Ɗaure fuska Muzaffar yayi sannan ya tura ƙofar ya shiga cikin
takunsa me ɗauke da sirrin kwarjinin dake taredashi, Direct gaban table ɗin dake
jibge da uban files gamida system ɗin dake gaban Salahuɗden ya nufa idanunsa na
cikim nasa.

Da sauri Salahudden ya miƙe yana murmushi yace "Ran C.e.o ya daɗe yau kaine da
kanka a cikin office ɗina aida bakazo da kanka ba ka turo an kira maka ni inyaso ni
sena kawo kaina gareka Allah ya taimakeka.

Taɓe baki Muzaffar yayi yana kallonsa a ransa yana me jinjinawa ƙwarewar Salahudden
a wajen iya kafcen dramar wasan kwaikwayo yace "Accounter a ƙa'idar wannan
Companyn tun kafin haihuwata zuwa yanzu ba'a taɓa fitar da kuɗi komai ƙanƙantarsa
batareda an shigar da hujjar abinda akayi dasu a rubuce ba a matsayin sheda.
meyasa ka fitar da kuɗi kimanin naira million 60 batareda sani na ba ?

Zaro ido Salahuddeen yayi yana kallonsa da manyan idanunsa lokaci guda kuma wani
irin gumi ya shiga keto masa tamkar an sheƙa masa ruwa a daburce yace
"Ammm.....Ae.....dadd..dama..inaso...uuhmm "ka dakatar da wannan dramar da kake
ƙoƙarin shiryawa a gabana Salahuddeen!!!!!. Muzaffar ya katseshi ta hanyar daka
masa wata uwar tsawa cikin ɓacin rai yace "zaka gayamin dalilin fitar kuɗin ne
kokuwa sena sa an Rubuta maka takaddar Sallaman ka daga aiki gaba ɗaya?

Miƙewa Salahudden yayi da sauri ya zagayo inda muzaffar ɗin ke tsaye yace "aa don
Allah C.e.o karkayi min haka na roƙeƙa wllh ba laifina bane fin ƙarfina akayi dole
yasa na taimaka mata muka fitar da kuɗin ba tareda saninka ba, idan har ka koreni
wllh kayiwa rayuwata illa ta ɓangarori da dama pls kayi haƙuri ka yafe min wllh zan
maka bayanin yanda akai komai ya faru!

Kallon sheƙeƙe yakebin Salahudden ɗin dashi lokaci guda kuma yace "wannan
matsalarka ce kiada kuka aikata tare da wanda yafi ƙarfin naka oya tashi ka bani
cikakkun bayanai akan fitar kuɗin da kuma sunan uban wanda yasaka kuka fitar da
kuɗin. Jikinsa na rawa ya juya ya fara neman takardun kasancewar abin be wani daɗe
ba yasa ya binkitosu cikin sauƙi ya miƙa masa, karɓa yayi ya fara dubawa take sunan
Md Fadilah Abdulwahab ya baiyana a jikin takardan ƙuru-ƙuru a matsayin wadda aka
haɗa hannu da ita wajen fitar da kuɗin

Wani shaiɗanin murmushi ne yay escaping red lips ɗinsa ya kalli Accounter yace
"karka taɓa tsammanin cewar zan ƙyaleka ban hukuntaka ba akn abinda kuka aikata
kaida Md ba Salahudden, it possible hukuncin dana yanke mata kaima shi zan zartar
akanka ba tareda na banbanta hakan ba tunda har ka iya biye mata kuka haɗa hannu
wajen gudanar da zanbo cikin Aminci A cikin wannan Company, dole ne ku karɓi
hukunci. Ya faɗi hakan yana wani datse lips ɗinsa da white tooth ɗinsa da
suka ƙara ƙawata kyakkyawar fuskarsa

Juyawa yayi ya fice tareda takardun a hannunsa ranshi a ɓace. Dole ne ya ɗauki
mataki akan Fadilah a wannan karon don baze ci gaba da zuba mata idanu tana aikata
duk abinda taga dama ba becouse this time ta fara wuce iyakarta.

Be dire ko ina ba se Office ɗinshi tareda zuɓe takardun a saman table ɗinsa sannan
ya zauna ya jawo system ɗinshi zuwa gabansa ya fara daddannawa, cikin mintunan da
bazasu gaza 4 ba ya kammala rubuta gajeran saƙon da yake rubutawa tareda turashi
ta wani Email Address sannan ya miƙe ya fice tareda rufe System ɗin. Tun kafin ya
fito saƙon korar Fadilah Abdulwahab Abdullah ya cika Companyn abinka da zamani na
kimiya

Fadilah dake zaune cikin office ɗinta tana gudanar da Aiyukanta ne ta ɗago ta
zubawa wayarta idanu sabida ƙarar saƙon daya shigo mata a wannan lokacin, tsaki
taja me sauti sannan ta jawo wayar ta buɗe saƙon tan akarantawa take idanunta suka
firfito sabida tashin hankalin data samu kanta a ciki, wani irin tuƙuƙin baƙin ciki
ne ya turniƙeta nan take wata sabuwar wutar tsanar muzaffar ta fara kwaranya a
saman zuciyarta. Miƙewa tayi a hasale ta nufi ƙofar fita daga office ɗin tana
huci tamkar zata tashi sama, Direct office ɗin Abie ta nufa ƙwalla kwance a
tsakiyar ƙwayar idanunta

Duk inda ta nufa sedai kaga ana juyawa ana kallonta masu yi mata dariya a ɓoye nayi
masu jajanta mata ma nayi, wannan baƙin cikin ne yasa tana shiga office ɗin Abie ta
fashe da kukan baƙin ciki da takaici a lokacin dataga kujerar zaman Abie ɗin babu
kowa a kai hakanne ya bata tabbacin cewar Ya tafi gida, kife kanta tayi akan
gwiwarta ta shiga gurzar kuka bisa wannan abin kunyar da muzaffar ya jawo mata a
idon mutanan dake ƙasanta.

Zuciya ce ta kwasheta ta fito daga office ɗin har idanunta na Rufewa sabida fishi
da ɓacin Rai ta nufi ƙofar fita daga companyn da wani irin mugun gudu ta ƙarasa
fitowa a lokacin data hangi Muzaffar na ƙoƙarin shiga mota gurds ɗinsa na tsaye
alamar gida Zashi

Kamar ƙiftawar idanu se gata a gabansa lokaci guda kuma ta damƙi wuyan Korean suits
ɗin dake jikinsa ta fara ƙoƙarin fito dashi tana binsa da kallon tsana.

Wani irin ɓacin rai ne ya tasowa Muzaffar lokaci guda ya fito daga motar tareda
watsa mata wasu lafiyayyun maruka a fuskarta, lokaci guda kuma yasa ƙafa tokareta
take tayi baya lu zata faɗi ya riƙeta da sauri yana huci yace "komai yazo ƙarshe
fadilah tunda kikasa yau na dora hannuna a jikinki. Wai shin ke wace irin yarinya
ce? Wllh da ace ba'a gida Momy ta haifeki ba zance sam keba jinin mu bace sabida
baƙin Halinki, karki bari ki kaini bango Fadilah nayi abinda ze janyo wani sabon
al'amarin a tsakanina dake so you have to respect your self.

Ya faɗa yayin da yake tureta daga jikinsa cikin fushi

Kifewa tayi a gurin tana kuka shikuma ya rufe motar suka bar harabar companyn zuwa
gida, ta jima tana kuka a gurin sannan ta miƙe ta nufi motarta ta shiga gurds ɗin
mutum biyu na take mata baya a motarsu suka nufi gida zuciyarta na suya .

Ɓangaren Muzaffar kuwa sosai yakejin haushin kansa da har ya iya ɗaga hannu ya doki
ƙanwarsa wadda suka fito ciki ɗaya sabida wani ƙaramin laifi data aikata masa na
kama masa wuyan riga a cikkn jama'a nan take yaji wani irin tausayinta na
kwaranyowa daga ƙasan zuciyarsa, a haka suka kai gida Ransa duk babu daɗi, Direct
part ɗinsa ya wuce sabida be shirya yin magana da kowa ba sabida yanda Fadilah ta
ɓata masa mood ɗinsa na yau.
Bayan dawowarsa da minti goma sega Fadilah ma ta dawo, buɗe motar tayi ta fita tana
kuka batareda ta jira gurds ɗinta sin buɗe mata ba kamar yanda ta saba ba, cikin
gidan ta nufa da cogalelen takalminta tana kuka a haka ta shiga falon ko Sallama
babu, gabaɗayansu ido suka zuba mata daga Momy har Abie zainab kuwa baki ta saki da
hanci tana kwasar kallo sabida a iya zaman da sukayi tare kafin ta tafi India bata
taɓa ganin Fadilah tana kuka irin haka ba se yau itako meya sameta haka?

Bata kulawa kowa ba ta kwasa da gudu ta nufi Upstairs tana ƙara sautin kukanta
Al'amarin daya ƙara ɗagawa su Abie hankali kenan sukabi bayanta, duk yanda sukaso
su cimma Fadilah abin ya faskara tana shiga ɗakinta ta murza key ta faɗa gado ta
shiga rusa wani sabon kukan baƙin cikin, duk irin rarrashi da ban bakin dasu Abie
keyi kanta buɗe musu ƙofar fur Fadilah taƙi buɗewa dole yasa suka haƙura suka
barta.

*******

*Gyambu Taraba state*

Zuwa yanzu kam moddibo ya gama sarewa da lamarin Rabe sabida yanda yarinyar ta rame
kuma ta fita haiyacinta, bata da aiki se kuka da keɓe kanta daga shiga cikin mutane
wannan al'amarin ne yake ƙara ɗaga masa hankali, ko abincin kirki bata iya ci yau
tunda sanyi safiya take fama da wani irin ciwon ƙirji me matiƙar zafi, buguda ƙari
ga wani irin nauyi da saitin zuciyarta keyi mata.

Kokaɗan bataso ta nuna gazawarta a idon Mahaifinta wadda yanke kallonta a matsayin
sanyin idaniya a gareshi, tasan dolene idan ya fahimci irin halinda take ciki beze
taɓa samun kwanciyar hankali ba shiyasa ta zaɓida ta boye masa lalurarta, kwance
take kan katifar ciyawarta idnunta na kallon saman bukkar dake ɗakin wasu zafafan
hawayene suka shiga zubo mata a lokacin data tuna abinda ya faru a tsakaninta da
Muzaffar ranar da suka tafi kiwo na ƙarshe dashi.

*Flash back*

tunda suka tafi kiwo bashi da aikin daya wuce kallonta haka kawai yaji cewar yana
shi'awar kallon nata dik inda tabi idanunsa na kanta tamkar baze dena kallonta
ba, ita kuwa sabgar gabanta kawai take ba tareda ta lura da irin kallon dayake
binta dashi ba tana ɗagowa a karon farko idanunsu ya sarƙe cikin na juna
A hankali ta buɗe baki tace" Hamma zafar meyasa kake yawan kallona a ƴan kwanakin
nan?

Murmushi yayi sannan yace"sabda zanyi missing naki.

Sosai take kallon sa tace " meye kuma mushin ke nufi?.

Dariyace ta kamashi amma kuma ya danne yace "kalmar tana nufin zanyi kewarki ne to.

Wata irin Dariya ce ta kamata sosai irin wadda bata tabayin kamarta ba a gabansa
ba a Iya zaman da yayi tareda dasu, daƙar ta iya saita kanta ta dena dariyar tana
kallonsa tace "amma Kaɗo ka iya tsiya Aradu.

Tunda ta fara dariyar yake kallonta kamar zeyi kuka yace, meyasa kik dariya irin
haka bakisan yawan dariya yana gusar da imani ba?

Murmushi tayi tace abinda ka faɗa ne ya bani dariya, Aradu senaji Kalmar taban
tamin daban a shikin kaina.

Hade rai yayi yace " to kada ki sake min irin wannan dariyar bana so, kinji yanda
kika tsorata ni kuwa?
Sunkuyar dakai tayi sannan ta riƙe kunnuwanta guda biyun kamar yanda yakeyi mata
idan ya ɓata mata rai kamar zatayi kuka ta tsuguna ƙasa tace "waɗu munyal Hamma
zafar badan ƙara ba!

Dariya ta bashi sosai dan haka yay murmushi tare da Jan kumatunta yace "uhm that's
my Fulani girl shikenan na haƙura amma kaɗan.
Dariya sukayi gaba ɗayansu dukansu, a haka wannan Ranar ta kasance daban a garesu
koma a kirata da Rana ta musamman a gareta.

A zaman datayi dashi kullum ƙara samun kusanci yake da zuciyarta batareda ita
kanta tasan hakan ba, wasu Zafafan hawayene suka shiga zubo mata yayi data farka
daga duniya tunanin data Afka akan matashin ɗan kasuwar mejida kuɗi da ƙwalisa
wanda a gurinta ya kasance tamkar wani mutum na daban wanda take kallo tamkar wani
waliyi a birnin zuciyarta Saɓanin shida ya mance da batun wata fulani girl dake
Rayuwa a wani ƙaramin daji wanda sam be gina masa wani muhali a cikin filin
zuciyasa daze iya tunawa nan kusa ba.

Zuwa yanzu kam ta sare kan cewar Zafar baze taɓa cika alƙawarinsa gareta ba na
cewar ze dawo gareta komai daran daɗewa koda kuwa ba nan kusa bane yau gashi ya
kwarari kusan shekara da tafiya ba tareda ya juyo gareta ba. Burinta a yanzu shine
Allah yasa a duk inda Hamma zafar yake ya kasance a cikin Farin ciki da
ingantacciyar rayuwa koda ace baze ƙara tunata a cikin Rayuwarsa ba har Abada zata
cigaba dayi masa kyakkyawan fata har zuwa ranar da Ranta zebar jikinta.

*Abujah*

Tunda ya dawo ya kasa gudanar da komai sabida ɓacin ran daya dawo dashi daga
office, ajiyar zuciya ya sauke me nauyin gaske sannan ya miƙe ya faɗa toilet donyin
wanka be jima ba ya fito ɗaure da towel ɗaya a ƙungunsa ƙarami kuma bisa wuyansa,
goge jikinsa yayi tsaf batareda ya shafa maiba ya buɗe tafkekiyar drower ɗinsa dake
manne a jikin katafaren bangon dake ɗakin ya fito da wasu ƙananan kaya marasa nauyi
ya sanya a jikinsa, tareda yin cumming lallausar Sumar dake kansa ya fita harabar
gidan.

Da Zainab yaci karo tana mishi murmushi tace "bro Anul Abie da momy ne sukace y
nazo na dubaka ko lfy sunji ka dawo amma bakazo kayi lunch ba. Dafa kafaɗanta yayi
suka fara tafiya tare har suka isa maine falo ɗin Momy suna ɗan taɓa hira sannan
yace "Cutie zee jeki haɗamin ouds pls banson cin komai yau

Da kalli Momy ta bishi wanda yafi kamada na mamaki tace "Son a kwai abinda ke
damunka kenan tunda naji kace Zainab ta haɗa maka ouds meyake damunka?

Ajiyar zuciya ya ɗan sauke kaɗan sannan yaja ɗaya daga cikin kujerun dake zagaye da
daining ɗin yace "Mom ba wani babban al'amari bane fa. Haɗe rai tayi tana kallonsa
da sauri ya janye idinsa ya kalli Abie yace "pls Abie kace mom ta bar yimin irin
wannan kallon don Allah wllh xan faɗa muku komai.

Murmushi abie yayi me cikeda dattako sannan yace "to naji gaya mana meke faruwa.
Ɗan jim yayi sannan ya shiga sanar da Abie kaf abinda ya faru a tsakaninsa da
Fadilah ba tareda ya rage komai ba. Ƙura masa ido mom tayi bakinta a buɗe sabida
tsabar mamaki...........

Sushmah💋
[3/3, 5:35 PM] Chubado Mohd: ❄️❄️❄️❄️❄️❄️
❄️❄️❄️❄️❄️❄️
🐄🐄🐄🐄
🐄🐄🐄🐄
*BAFULATANA*
✨RETURN✨
🐄🐄🐄🐄
🐄🐄🐄🐄
❄️❄️❄️❄️❄️❄️
❄️❄️❄️❄️❄️❄️

*_Page :19_*

*_WRITING BY: CHUBAƊO_*

Not Edited
____✍️nausawa tayi cikin jejin babu abinda takeyi se kuka sabida rabuwar datayi da
mahaifinta, jefa ƙafarta kawai takeyi batareda tasan inda take jefata ba ga dare
daya farayi, babu komai cikin dajin face kukan gyare da kuma na tsintsaye
kasancewarta Bafulatanar Daji hakan besa taji tsoro ba becouse dama a cikin
dabbobin ta tashi kuma take rayuwa so babu wani baƙon Abu a gareta , babbn abinda
zuciyarta ta yarda dashi shine there's nothing can happen to her because her father
prayer is still by her side, da wannan tunanin kawai tke tafe zuciyarta nayi mata
zafi.

Ta sani sarai cewar ita kaɗaice ta ragewa mahaifinta a halin yanzu haka kuma ƙaunar
dayake mata me girma ce, batajin ze iya sadaukar da wannan babbar ƙaunar dayake
mata a banza becouse ruwa baya tsami banza inji ƴan magana. Dole yanada dalilinsa
me ƙarfin gaske da har yasa yashi rabuwa da ita a wannan lokacin. Ƙirjinta ne ya
amsa da sauri lokaci guda kuma ta zuɓe akan gwiwoyinta tareda ɗora hannunta na
dama a saitin zuciyarta, rarrafawa tayi tareda gyara zaman wannna jakar saƙin da
moddibo ya rataya mata a kafaɗarta batareda ta bari jakar ta faɗi ba, a haka ta
jingina bayanta da wata ƙatuwar bishiya tana maida numfashi.

*_ABIJA NIGERIA_*

yau tunda sanyi safiya Muzaffar ya gama shirinsa cikin wata Ash ɗin Korean suits
iya gwiwa kasancewar garin da ɗan sanyi sosai, tsaye yake jikin makeken Dressing
mirror ɗin dake manne jikin bangon ɗakin yana gyara zaman agogon rolex ɗin dake
hannunsa, ƙurawa kansa idanu yayi kamar meson gano wani abu a tattareda kansa,
lumshe idanunsa yayi sannan ya buɗe wanda hakan yayi daidai da saukar idanunsa kan
tabon ciwon da lallausan gashin kansa ya fara rufewa, hanunsa yakai gurin ya janye
lumsasshen gashin kansa yana kallon tabon lokaci guda ya dafe kansa yace "ya
Rabbi!!

Juyawa yayi da sauri ya fita daga bedroom ɗin nasa zuwa falo, koda ya fito falon ma
tsayawa yayi cak becouse ya kasa tuna actual abinda ya fito dashi daga ɗakin,
zibewa yayi akan ɗaya daga cikin haɗaɗɗun royal chairs ɗin sukayiwa falon ƙawanya.

Wayarsa ce ta ɗauki ruri yana dubawa yaga sunan Abie yana yawo akan screen na
wayar, ajiyar zuciya ya sauke meɗan nauyi sannan ya answer call ɗin Abie yace
"son gobe ne fa meeting ɗin daza'a gabatar a India ya kamata ka fara shiri akan
tafiya zuwa gobe da yardan ubangiji lallai ya kamata ace kana guri za'ayi komai
becouse hajiya Aisha she's not feeling fine.

"insha Allah zanyi ƙoƙarin yin hakan Abie and then you should send me her number so
that na kirata na dubata. "Ok son i will send it for you. Abie ya faɗi hakan
yayinda yake katse kiran
Ajiye wayar shima muzaffar yayi haka kawai seya samu kansa dajin wani baƙon yanayi
wanda ya kasa misaltashi, ajiyar zuciya ya sauke a karo na biyu a lokacin da Babban
Amininsa Edress Adam ya faɗo masa a rai, wayar dake gefansa ya zaro lokaci guda
kuma ya fara ƙoƙarin lalibo number ɗin Edrees ɗin tareda kira, harya katse amma
Edress sam be ɗaga ba har seda ya sake kiransa a karo na biyu sannan ya ɗauka
tareda faɗin "shugaban masu kirki WhatsApp?

Tsaki muzaffar yaja kaɗan sannan yace "fine ya kk?. " I'm fine and you? Edrees
ya faɗi hakan yana wani male baki kamar an masa dole. A daƙile muzaffar yace "ban
sani ba ɗan renin sens you but you know what?

Edrees dake zaune a madaidaicin falonsa ɗauke da remot a hannunsa yace " how could
I know bayan bkaa gayamin ba? Kaga malam forget about what I did to you pls
let's talk. Muzaffar ya faɗi hakan yana gyara zamansa akan sofa ɗin dayakd
zaune.

naji and I don't want to talk to you right now because you baka neman mutum se
matsalanka ya taso, don haka yanzu ni kuma banida time ɗinka malm idan ka matsu da
magana dani seka jirani har ranar sazan dawo Abuja becouse I'm not in Abuja yanzu.
Jan numfashi Muzaffar yayi sannan yay murmushi yace "ok ba damuwa nikam gibr zan
wuce india maybe next time. Ya faɗa yana katse kiran da murmushi sosai a saman
face ɗinshi.

zaiynab ce ta shigo falon sanye jikin doguwan riga milk colour ta yafa mayafin bisa
kanta tace "Hayatie kazo inji Mom da alama you have a visitor. Ɗan buɗa
lumsassun idanunsa yayi sosai yace "who? Zainab na dariya tace "uhmmmm i think
is the IG Doughter. Taɓe baki yayi yace "kuma se akace miki wurina tazo ko? Da
sauri Zainab tace "sure becouse tana zuwa kaikaɗai ta tambaya kuma senake gankn
kam......."its ok Qurrah tell her that bana nan na fita kinji. Muzaffar ya katseta
ta hanyar faɗar hakan.

fita zainab tayi tana dariya a maine parlour ɗin ta samu Hajar Abdullah suna ɗan
taɓa hira da Mom tace "yace na gaya miki ki sameshi a part ɗinsa he's to busy for
doing something. Murmushi Hajar tayi wanda ya ƙara mata kyau sannan ta niƙe ta nufi
ɓangaren muzaffar ɗin, a nitse ta murɗa handile na ƙofar falon tareda sallama ta
shiga ciki wanda hakan yayi daidai da miƙewarsa yana buɗe boturan gaban Korean
suits ɗin dake jikinsa, juyowa yayi yana kallon bakin ƙofar take ya tsaya cak yana
kallonta with surprise on his handsome face. Tunanin daya fara zuwa masa kai shine
taya akai yarinyar nan tasan hanyar part ɗinshi?

Takowa ta farayi a hankali harta iso tsakiyar falon da murmushi akan fuskarta tace
" fatan na sameka lfy? Ɗan jim yayi yana kallonta sannan yace "fine and you?

murmushi kawai tayi tace "fine kwana biyu. Ta faɗa tana ƙoƙarin zama da sauri ya
dakatar da ita yace "no base kin zauna ba don fita zanyi inada aiki a office. Ya
faɗi hakan yana sauya yanayin fuskarsa zuwa wani yanayi na daban. Kamar zatayi
kuka tace "muzaffar meye laifina don kawai inason ka? Shin koda so ɗaya ka taɓa
tunani akan cewar yanakeji a gameda kai?

Ajiyar zuciya ta sauke kaɗan yayinda idanunta suka ciko da ƙwalla tace "bazanga
laifinka ba kokaɗan tunda har tsarinka ne a haka na rashin bawa mace damarta
acikin Rayuwarka amma inaso ka tunada Abu guda ɗaya cewar, duk mutumin daya nuna
maka kulawa a rayuwa kuma har ya iya sadaukar da lokacinsa a kanka dukdan ya samu
kusanci dakai tofa wannan mutumin ba abin yarwa bane balle har ka jinginar dashi
kimanin tsahon lokaci ba tareda ka tuna dashi ba.......... All i know is I love you
Zafar Abdulwahab!!!

Ƙirjinsa ne ya buga da ƙarfi a lokacin da kalamanta na ƙarshe suka sauka a cikin


kunnuwansa, lokaci guda ya dafe kansa da hannayensa duka wani irin baƙon yanayi ne
ya samu gurbi da matsuguni a cikin zuciyarsa zama yayi jagwab akan kujera yana
sauke numfashi, A hankali siraran laɓɓansa suka motsa cikin Husky voice ɗinsa yace
"Im so sorry Fulani girl ban kasance me cika alƙawari a gareki ba i'm sorry for
what I did to you my dearest Fulani's girl insha Allah I wll be back for you just
for you soon!!

Ƙura masa ido Hajar tayi tana kallonsa hawaye cike tab da idanunta tace "who is
that Fulani girl pls I want to know something about her who is she? Ajiyar
zuciya ya sauke yana kallonta lokaci guda kuma ya miƙe ya nufi bedroom ɗinsa har ya
buɗe ya shike Hajar nabinsa da kallo tana me tausayin kanta akan son mutumin da
bata taɓa samun kulawa daga gareshiba koda so ɗaya.

*_Thanks for the love and support sisters about this novel BAFULATANA ❤️
_*

comment
nd
share

Sushmah💋
[3/3, 5:35 PM] Chubado Mohd: ❄️❄️❄️❄️❄️❄️
❄️❄️❄️❄️❄️❄️
🐄🐄🐄🐄
🐄🐄🐄🐄
*BAFULATANA*
✨RETURN✨
🐄🐄🐄🐄
🐄🐄🐄🐄
❄️❄️❄️❄️❄️❄️
❄️❄️❄️❄️❄️❄️

*_Page :18_*

*_WRITING BY: CHUBAƊO_*

___✍️Daga irin kallon da momy take masa Abie ya Fahimci irin zallar mamakin dake
kwance a saman fuskarta, a fusace momy ta kalleshi tace "amma kaidai wllh anyi
sakarai tunda har ka barta baka karya mata ƙafafu ba, ni wllh Abie lamarin
yarinyar nan ya fara ɗagamin hankali musamman ma ɗabi'unta, wllh da ace ba'a gida
na haifeta ba tsaf zance canzamin ita akai wannan wace irin jarrabar rayuwace ne?

Dakatar da ita Abie yayi ta hanyar ɗaga mata hannu yace "look malama karki ɓatamin
zuriya ta hanyar jifan ɗiyata da miyagun maganganu a madadin kiyi mata Addu'ah,
karfa ki manta fushin iyaye tareda kalamansu akansu yanada matiƙar kaifi arayuwar
ƴaƴasu don haka karki sake furta komai akanta muddin ba alkhairi bane. Insha Allah
komai zeyi daidai watarana zata canza halinta daga baƙi xuwa maikyau

Jiki a mace mom ta miƙe ta nufi upstairs ɗakin Fadilah ranta amatiƙar ɓace tura
ƙofar tayi tareda tsayawa a bakin ƙofar tana bin kowace kusurwa dake ɗakin da
kallo.
Zaune ta hangeta ta haɗe kai da gwiwa zaune dirshen kan makeken lallausan kafet ɗin
dake ɗakin fuskarta duk ta caɓe da hawaye, ƙarasawa mom tayi tana binta da wani ɗan
iskan kallo wanda yasa hanjin cikin Fadilah motsawa, wani sabon marin mom ta
ɗauketa dashi wanda yasa har seda kanta ya bugu da allon gadon dake ɗakin sannan ta
nunata da yatsa tace " bansan wani irin baƙin haline ke bibiyar zuciyarki ba
fadilah! Ke wace irin maramutunci ce da har zaki saka hannu ki shaƙi wuyan rigar
yayanki wanda ya girme miki fiyeda shekaru biyar? Duk haƙuri irin nasa seda kika
ƙureshi Fadilah harya ɗaga hannu ya mareki why are you Behave like that why
Fadilah?

Kuka kawai takeyi hannunsa still on her own face wadda ta caɓe da ruwan hawaye
gamida majina, mom batabar ɗakin ba seda tayiwa Fadilah tatas sannan ta fito zuwa
downstairs inda tabar su Abie, jikin zainab a mace ta kalli Muzaffar tace "bro I'm
so sorry for Fadilah's action I'm sure she will regret what she did to you soon.
But kafin nan you should forgive her please kar abin ya mata yawa kaji Hayatie.

Murmushin gefan baki ya sakin mata yace "it's OK Qurrah i forgive her since ai
tun kafin ma nazo gida, so karki ɓata bakinki share batun kawai

Dariya tayi shidai Abie cin Abincinsa kawai yake harya gama bece dasu ƙala ba, a
haka kowa ya gama cin Abincin da abinda yake aiyanawa a ransa.

Se yamma liƙis Fadila ta fito daga ɗaki duk fiskarta ta kumbura abinka da ajebo
lol, shima yunwace ta matsa mata shiyasa ma ta fito donta samawa kanta abinda
zataci, Zaynab ta Samu ita kaɗai a falon se kuma Hajara me aikinsu wadda ta ɗan
fara manyanta suna hira, ɗauke kanta tayi kamar bata gansu ba ta nufi khitchine
tana raba ido kozata samu abinda zata zubawa ƴaƴan hanjinta, tsayawa tayi cak
tanabin ko ina da kallo amma bataga wani abu dafaffe ba kwaɗawa Hajara kira ta
shigayi kamar zata tashi gidan, da hanzari Hajara ta iso khitchine ɗin tana faɗin
"Gani ranki shi daɗe me kike so ?

Wani kallon sheƙeƙe ta bita dashi tana wani male baki tace "ki dafanin endomie
yanzu ki kawo min ɗaki, bata jira cewarta ba ta juya tabar khitchine ɗin tana wani
ɗaga kai kamar zata tashi sama harta kama step zainaba tayi Saurin cewa "oh Allah
ya Fadilah Ashe kuma haka abu ya faru babu ɗaɗinji, kaico amma gaskiya na jajanta
miki don daga ganin fuskar nan taki ta maru ba kaɗan b.......... Tun kafin ta rufe
baki Fadilah tayo kanta gadan-gadan tana huci.

Da sauri zaynab ta miƙe tayi waje da gudu tana ihu, da Abie sukaci karo yana
ƙoƙarin shigowa falon kunnensa ɗauke da waya da sauri zaynab tayi bayansa tana
tura baki tace "uhmm Abie kaga ya Fadilah ko?

Takaici ne ya kamashi lokaci guda kuma ya zare wayar daga kunnensa yanabinsu da
kallo batareda yace dasu ƙala ba, suda kansu sukasha jinin jikinsu Jiki a mace
zainab tace "we are sorry Abie baramu ƙara ba.

Raɓawa Abie yayi ta gefansu ya wuce tareda mayar da wayarsa kunnensa yaci gaba da
wayanshi.

*GYAMBU TARABA STATE*

Zuwa yanzu Raɓe ta gama fitar da ran cewar Muzaffar ze dawo gareta kamar yanda ya
alƙawaranta mata hakan, tafi danganta hakan da cewar ya daɗe da mantawa da ita ma,
moddibo ne zaune kan tabarmar kaba yanashan Dawo inna laure ta fito ta zauna daga
gefansa suna ɗan taɓa hira kamar daga sama sukaji Tashin harbin bunduga dabda
bijirowar almuru, da wani irin mugun sauri Rabe dake bakin murhu ta miƙe tana raba
idanu sabida tsabar tashin hankalin data samu kanta a ciki, fuzgar hannunta moddibo
yayi yana suka shige bukkarsa a matiƙar kiɗime wata ƙatuwar Boronsa ya ɗaukko a
rataye ya sakaƙala mata ita a kafaɗarta lokaci guda kuma ya kama kafaɗunta da duka
hannayensa biyu yana kallonta idanunsa cike tab da ƙwalla yace "da alama mafarkin
dana jima inayi dab yake da tabbatuwa Rabi'atou tabbas mafarkin bayin Allah gaskiya
ne mafarkin annabawan Allah kuma wahayi ne, tabbas abinda ubangi ke nuna min ta
hanyar mafarki na shine ke shirin faruwa babu shakka ranar Rabuwata dake yazo
Rabi'atou! Rabuwarmu tazo a cikin yanayin da gabaɗayanmu bazamu so hakan ba sedai
babu yadda muka iya da abinda ubangiji ya tsara mana, banida yadda na iya dole ne
nayi duk me yuwuwa a matsayina na mahaifinki naga cewar kin tsira daga wannan
babbar masifar data tunkaro mu a yau kodan gudun kar tarihi ya maimaita kansa.

"amma baba meyasa se kalmar rabuwace zata fito daga bakinka a lokacin danafi kowa
buƙatarka? Wllh baba tunani na ya gaza kamar yanda shekaruna suka gaza wajen
fahimtar kalmar da kake nanata min ta Rabuwa..... Don Allah baba kada ka bari
bakinka ya sake furta wannan kalmar tabbas zuciyata da gangar jikina bazasu taɓa
iya fahimtar abinda kakeso su fahimta ba Baba!!!!!? Ta faɗi hakan tana wani irin
rushewa da kuka a jikinsa.

Sautin kuwar jama'ar dake rugar kawai kakeji tareda ƙara kusantowar ƙarar harbin
bindigar wajen bukkokinsu, fusgeta Modibbo yayi daga jikinsa lokaci guda kuma ya
daka mata tsawa yace "lallai ya zama wajibi ki saurareni a matsayina na mahaifinki,
idan har Allah ya hukunta cewar zamu sake haɗuwa tabbas zamu haɗu amma kuma idan
Allah ya raba ganawa a tsakanin mu lallai ki kasance me kare martabar mutuncin ki
har zuwa muhalin daya dace, sannan idan ƙaddara ta sake haɗaki da Muzaffar lallai
ki gaya masa cewar idan da hali to ya cika alƙawarin daya ɗaukarmin a kanki, idan
kuma ƙaddara bata haɗaku ba lallai karki kuskura ki ƙara tako ƙafarki cikin Gyambu
har rayuwarki ta ƙare a inda kikaj........! Ya faɗi hakan wani irin kuka yana
taso masa.

Wani irin tausayinta yakeji sedai vayajin cewar ze iya barinta a taredashi a wannan
halin sabida sam baze juri ganin mutuwarta a gaban idanunsa ba, ya sani cewar abu
ne mawuyaci mace ta rayu a inda bata babu wani nata kuma ta rayu ciki salama
kokuma cikin Aminci batareda ta lalace ba, sedai babu yadda ya iya dole hakan shine
mafita a garesu gabaɗaya. Ɗaga hannunsa yayi sama yana kuka yace "ya ubangiji na
ga Amanar daka bani nna ta ƴar dana haifa, ya Rabbissamawati wal'ardi ka kulamin da
ita a duk halinda zata samu kanta a ciki, ya Allah kada ka barta da iyawarta ka Iya
mata da iyawarka ya Allah!

zata sake magana kenan ya dakatar da ita ta hanyar jan hannunta suka fito daga
bukkar yana share hawayensa.

Koda suka fito basu cimma inna laure a tsakar gidan ba hakanne yasa moddibo leƙawa
ɗakinta don ya tabbatar da tana ciki kokuma ta tsere, can ya hangeta ta haye kan
katifar ciyawarta jikinta banda rawa babu abinda yakeyi, takawa yayi da sauri ya
fuzgota tana tirjewa a haka ya janyota suka fito, gabaɗaya babu abinda ke tashi a
rugar face sautin harɓin bindigar da ƴan fashin ke amfani da ita, baka ganin komai
se ƙurar jar ƙasar dake tashi a gurin hakanne ya haifar hargitsewar dabbobinsu,
hatta shanunsu duk sun kwance sun fazama cikin daji a gigice.

Cikin jeji moddibo ya nausa dasu banda gudu babu abinda sukeyi a haka har suka fara
nisa da rugar, fusge hannunta Laure tayi daga cikin na modibbo tace "Sakarni
Moddibo wllh ban ƙara ko taku guda daga nan, kana nufin haka zamubar dukiyarmu da
kuma ƴan uwanmu ɓarayi na kashesu kamar tsintsaye?

Hawaye ne ya zubo masa a lokacin daya tina Wasiyar mahaifinsa na cewar" a duk sanda
masifa ta afka muku modibbo da zarar ka samu nasarar fita daga gurin da masifar ke
faruwa kaida iyalanka koda wasa karka bar ɗayansu ya koma inda abin ke faruwa idan
kuwa har hakan ta faru lallai ɗayanku ze mutu idan kuwa har ba'a mutu ba to zaku
tabka babbar Asara cikin biyu za'ai ɗaya.
Fashewa yayi da kuka ya janyo Rabe yana kuka ya Rungumeta lokaci guda kuma ya zare
jikinsa daga nata yace "lallai kiyi nisa da wannan jihar tamu nisa me tsahon gaske
sannan ki sanya a ranki cewar idan da rabo wata rana zamu sake haɗuwa. Juyawa
yayi da sauri zebi bayan Laure da hanzari ta riƙe hannunsa tana kuka tace "kayimin
alƙawarin cewar zaka jirani har lokacin da ƙaddarar data rabamu zata dawo dani
babana. Zeyi magana ta dakatar dashi tace " nidai kayimin alƙawarin cewar zaka
jirani har lokacin da zan dawo gareka a raye batare da kabari muwa ta riske ka ba.

Gabaɗayansu kuka sukeyi me taɓa zuciyar duk wani me imani, da sauri ya ɗaga mata
kai yace "nayi miki alƙawari ƴata tabbas zan jiraki har zuwa ranar da ƙaddara zata
dawo min dake. Yana faɗin haka ta saki hannunsa tana kuka ta juya ba tareda ta sake
juyowa ba ta nausa cikin jeji batareda sanin inda ta nufa ba.

Zubewa yayi a ƙasa ya fara sharɓar kuka musamman daya tuna alƙawarin daya ɗaukarwa
ɗiyarsa wadda be taɓa gaya mata abinda yake ba gaskiya ba daga bakinsa, se gashi
yau an wayi gari yayi mata alƙwarin da baze iya cika matashi ba.

Ya jima yana kukan sannan ya miƙe yabi bayan laure yana me ƙara jaddada Amanar
Rabi'atou ga ubangijinsa....

*Chai nasha ƙorafi mara adadi dik akan wannan littafi 😂*

*Yasin idan banga ruwan comment ba se bayan sati biyu zaku sake ganina koma na
ajiye alqalamin gabaɗaya Huta roro waken gixo yaqi ƴaƴa *

Comment
Nd
Share

Sushmah💋
[3/3, 5:35 PM] Chubado Mohd: ❄️❄️❄️❄️❄️❄️
❄️❄️❄️❄️❄️❄️
🐄🐄🐄🐄
🐄🐄🐄🐄
*BAFULATANA*
✨RETURN✨
🐄🐄🐄🐄
🐄🐄🐄🐄
❄️❄️❄️❄️❄️❄️
❄️❄️❄️❄️❄️❄️

*_Page :20_*

*_WRITING BY: CHUBAƊO_*

____✍️ Da kallo kawai hajar tabishi tana me tausayin kanta a nan gaba, Allah ne
kawai shedarta akan irin son datakema wannan bawan Allahn tun daga ranar data fara
ganinsa zuciyarta ta amsa, batajin cewar zata jurar rashinsa koda na kimanin ƙwayar
zarra ne.
Share hawayen dake xubo mata tayi sannan ta ƙara gyara zamanta akan kujerar datake
kai, a yau dai kam ta lasarwa kanta takobin cewar bazata taɓa barin falon nan ba
harse taji matsayinta a gurin Muzaffar koda hakan ze zama wani abu me zaman kansa
ne a tsakaninsu. Tambaya ɗaya ce taƙe mata yawo a zuciyarta shine wacece wannan
Fulani girl ɗin da cikamakin Rayuwarta yake Ambaton sunanta haka a gabanta batareda
shakka ba?

A ƙalla ba ƙasaru ba Hajar seda ta shafe Awanni uku chur zaune a falon batareda
uban gaiyar yasan da ita a gurin ba har yayi baccinsa ya tashi kana yayi wanka ya
canza kaya zuwa launin ƙananan , Black jeans with Sky blue T-shirt Sosai kayan ya
karɓi jikinsa tamkar dama danshi akayisu, komai nasa tsaf-tsaf dashi shiyasa yake
classy guy. silifas ya ɗauko a cikin shoe rack ɗinsa me launin baƙi ƙirar
companyn Batozy ya sanya a ƙafarsa, hakanne ya sake fito da ainihin kalar hasken
fatar jikinsa gaba ɗaya, a nitse yake takawa harya fito daga Bedroom ɗin ya
ƙaraso cikin falon tsayawa yayi chak yana kallon hajar wadda ke bacci da mamaki
kwance akan fuskarsa yace "ya salam what kind of lady is this?

Haɗe rai yayi sosai tareda bugawa gefan kujerar firgigit Hajar ta tashi tana
kallonsa, ƙura mata idanu yayi with serious face yace "me kikeyi har yanzu baki
tafi gida ba?

"taya zan tafi bayan har yanzu bansan matsayina a gareka ba? Hajar ta faɗi hakan
idanunta na shirin kawo ƙwalla.

"look hajar ya kamata ace zuwa yanzu kin fahimci manufa ta, ni gabaɗaya yanzu babu
soyayyah a tsarina a zatona ya kamata ace zuwa yanzu kin daɗe da cireni a ranki
tunda na gaya miki abinda ya kamata ace kin gane kokuwa?. Ya faɗi hakan yana
kallon tsakiyar idonta

Kuka Hjaar ta fashe masa dashi al'amarin daya ƙara ɗaga masa hankali kenan, a
rayuwarsa ya tsani kukan mace ballantana kuma ace shine silar yin kukan nata da
sauri yace "its ok hajar pls stop crying yanzu kije gida insha Allah idna na dawo
daga india satin gaba me zuwa zanzo gidanku se muyi magana ok? Da sauri ta ɗaga
masa kai tana share hawayen dake idonta ta miƙe tsaye, kusan a tare suka fito daga
part ɗinsa har suka iso maine falon Momy

Waya suka samu Momy nayi tana ganinsu ta katse kiran tace "bari zamuyi magana zuwa
gobe. Daga hakan ta katse kiran tana binsu da kallo

Sunkuyar dakai hajar tayi cikeda jin kunyar Momyn tace "mom zan wuce gida. Kallon
tsaf mom tayi mata sannan ta ɗaga mata kai tace "kigaida mamanki. Bata ƙra cewa
komai ba ta nufi daining batareda tace da muzaffar ƙala ba, sosai yasha jinin
jikinsa da irin kallon tuhumar da Momy ke binsa dashi yace "mom pls me namiki?

Tsayawa tayi ba tareda ta juyo ba tace "Au tambayata ma kakeyi donka rainani? Me
wannan yarinyar takeyi a part ɗinka har tsahon wannan awannin kuna tare?

Da sauri yace "Mom!!!! Are you suspecting me for doing something with her?

Ba tareda ta kalleshi ba tace "no at all but bari Abie ya dawo dolene a tsayar da
maganar Aurenka koma da wace yarinya ne sabida ni bazan ɗauki iskancin nan a gidana
ba, and let me tell you something muzaffar wllh dole ne kayi Aure idan har baka son
ganin ɓacin raina. Damn sauri yace "mom Aure Kuma? But senake ganin...... "ya
isheni haka nan malam ka wuce kawai ka bani guri.

Jikinsa a mace yabar falon ransa a matiƙar ɓace, yana fita harabar gidan ya nufi
mota ze shiga da sauri Selomon ya nufoshi ze buɗe masa ƙofa ya dakatar dashi yace
"ban key yau ni kaɗai zan fita. Ba mutsu ya miƙa masa keyn ya shiga motar ya buga
mata key ya fuce daga gidan gaba ɗaya, tabas dole ne ya zauna da Abie tun kafin mom
ta rigashi yin hakan yasan dole Abie ze fahimce shi becouse baze masa dole akan
abinda bayaso ba ko kaɗan, tsaki yaɗan ja kaɗan lokacin da Hajar ta faɗo masa a
rai yace "komai ya faru itace silah.

Murmushin mugunta yayi daya tuna zainab, tabbas yasan itace ta haɗa masa komai
tunda ai seda ya gaya mata cewar karta faɗawa hajar yana gida amma kuma seda ta
gaya mata, dole ne ya hukunta ta akan hakan.

*_GYAMBU TARABA STATE_*

Duk yanda Laure ke tsammanin bala'in dake faruwa a garin Ashe abin ya wuce zatonta
da kuma tunaninta, amma sam dukda hakan batayi tunanin komawa da baya ba still
hankalinta na kan dukiyar da moddibo ya jima yana tarawa, bata dire ko ina ba se
ɗakin moddibo nan ta fara birkita ɗakin ɗakin ta ko'ina tana neman jakar saƙin
dayake zuba kuɗaɗensa masu nauyin gaske, gaba ɗaya ta gama burkita ko ina duk
yanda taso ganin jakar amma sam abin ya faskara dole yasa ta dakata da bin ciken
jakar ta tsaya cak tana tunani, tabbas ɗazu da suna gudu taga jakar a bayan Rabe
kenan hakan yana nufin duka kuɗaɗen moddibo ya baiwa ƴarsa ta gudu dasu?

kurma ihu tayi kamar wata mahaukaciya sannan ta fito daga bukkar tana me nadamar
dawowar datayi, lallai dole ne tabi bayan Rabe ta tayi mata shegen duka sannan kum
ata ƙwace jakar inyaso ta shiga duniya daganan ta buɗe sabuwar Rayuwa. Juyawa tayi
da nufin barin gurin kamar daga sama taga manyan ƙarti majiya ƙarfi sun kewayeta ko
wannansa riƙe da bundiga ƙirar Ak47 suna kallonta, nan take hanjin cikinta suka
yamutse.

bata ƙara sarewa ba seda taga su malam Iro duk an ɗaɗɗauresu jini na zuba daga
gefan cikinsa, ananne fa ta ƙara furgicewa kuma ta fashe da kuka moddibo dake zaune
bisa gwiwoyinsa duk an tamkeshi da igiya kansa na zubar da jini ya ɗago idanunsa da
ƙyar jirin jini na ɗibarsa ya zuba mata idanu cikin yanayi irin na fitar haiyaci,
nan take laure ta ɗora hannu bisa kanta ta kurma wani uban ihu.

Ɗaya daga cikin ƴan fashin ne ya ɗaga hannu ya zabga mata wani lafiyayyen mari ne
shiga nan take Laure ta tsuke bakinta tana wani zare idanu, babban cikinsu ne ya
kalli wanda ya mareta yace dashu "kai Sage maza jefamin ita a ɗaki zan ɗan rage
zafi da ita.

Gabanta ne yay masifar faɗu lokaci guda kuma ta zuɓe a ƙasa tana roƙonsu kan cewar
su rufa mata Asiri karsu keta mata haddi, wani marin ya sake watsa mata take gefan
bakinta ya fashe ya fara jini tanaji tana gani wannan ƙaton ya hurgata cikin ɗakin
moddibo ogansu yayi mata fyɗe a gaban idon mutannan dake gurin. Wani irin kuka
laure keyi sabida baƙin cikin data samu kanta a ciki bayan ya samu nutsuwa da itane
ya fito waje yana gyara zaman wandon dake jikinsa ya kalli yaransa yace "idan dame
buƙata a cikinku seya antaya shima yay mata juyen baƙin mansa.

Jiki na rawa Sage yace "oga zan ɗan kwashi romon nima. Dariya suka fashe da ita
sannan Sage ya antaya ciki shima ya huce takaicinsa a kan Inna Laure a taƙaice dai
seda mutum huɗu sukaiwa Inna Laure Fyaɗe tanaji kuma tana gani babu yadda ta iya.

a wannan rana Laure tayi kukan da batasan Adadinsa ba haka kuma tayi dana sani mara
misaltuwa a Rayuwarta , nan take nadamar Rayuwa tayi mata dirar mikiya a lokacinda
komai ya lalace mata.

*_ƁANGAREN RABE KUWA_* Jingina tayi da wannan bishiyar dake gefanta tareda zubawa
Sarautar Allah idanu, wani irin kuka ne ya taso mata a lokacin data tunada halinda
tabar Ahalinta a ciki babban abinda yake ƙara ɗaga mata hankali shine rayuwar da
zatayi a nan gaba tareda mutanan da bata taɓa saninsu ba. Seda tayi kuka me
isarta sannan ta miƙe ta gyara zaman jakar dake kafaɗarta wanda moddibo ya bata
sannan taci gaba da tafiya tana kukan, seda tayi tafiya me nisan gaske sannan ta
fito titi

bin ko ina take da kallo lokaci guda kuma zallar mamaki ya baiyana ƙarara akan
fuskarta, sun kuyawa tayi tana shafa titin da yatsun hannunta a ɗan tsorace da
sauri ta janye hannunta tareɗa ja da baya kaɗan still her eyes on the titin, mamaki
takeyi shin menene wannan abin haka?

a iya Rayuwarta bata taɓa fito titi ba shiyasa ganinsa a yau ya zame mata tamkar
sabon abu ne a gareta, tana nan tsaye taki gaba taki baya kawai ba zato ba
tsammanin wata haɗaɗɗiyar motar ƙirar ford ta sako kai, da wani irin mugun gudu
Rabe ta kwasa tana ihu tayi cikin Dajin sabida ganin motar datayi, gabaɗaya a
zatonta wata halittar ce me matiƙar tsoratarwa

Seda ta tabbatar motar ta wuce sannan ta fito hannunta ƙanƙame da jakar Saƙin nan
dai da Mahaifinta ya bata, kamar me koyar tafiya haka ta dinga taka titin don gani
take a kowani lokaci ze iya ɓurmawa da ita (Allah sarki iyayena fulani😂)

Ruwan sama ne ya kece dole yasa ta nemi wata Bishiyar ta haye samanta ta lafe tayi
shiru, a hankali Ruwan ke sauka a saman kanta yana kwaranyowa ta saman gashinta
zuwa gangar jikinta, lumshe manyan idanunta tayi tareda faɗawa cikin duniyar
tunanin makomar Rayuwarta.......

*_ABUJA NIGERIA_*

Se wajen 8:pm sannan muzaffar ya dawo gida Direct falon Abie ya nufa sedai yana
shiga falon yaga mom a gefan Abie ɗin, gabansa ne ya faɗi amma kuma seya dake yayi
murmushi ya ƙarasa cikin falon da Sallama, da sakin fuska with so much love for
his son Abie yace "come near me my Qurratu ain. Da sauri ya isa gareshi ya zauna
daga ƙasan ƙafafun Abie ɗin tareda kwa tar da kansa a saman ƙafafunsa, murmushi
kawai mom tayi ta ɗauke kanta a lokacin da kiran waya ya shigo mata , kallon Abie
tayi taga hankaƙinsa gabaɗaya yana kan ɗansa hakan yasa tayi murmushi ta niƙe ta
fita tareda kara wayar a kunnenta, sosai hakan yayiwa Muzaffar daɗi don haka ya
miƙe ya koma kan kujeran kusa da Abie tareda kama hannunsa cikin nasa ya damƙesu
guri guda yace "Abie I feel like I'm a lucky son that I have you as a father, Abie
ka cikemin gurbin komai danake buƙata a rayuwata but I don't know why I feel like
I'm miss something in my life Abie, har yanzu kuma na kasa gane menene wannan abin
dana rasa ɗin!!

Murmushi Abie yayi me cikeda dattako sannan yace " so tari a rayuwa mukayi kewar
abubuwa dayawa a cikin Rayuwarmu musamman ma ace waƴanda muke ƙauna. Ƙauna kuma
Abie? Muzaffar ya faɗi hakan cikeda rashin gamsuwa

Murmushi Abie ya sakeyi a karo na biyu yace " amatsayina na Abokinka ba mahaifi ba
ina me baka shawaran cewa ka koma ka saurari zuciyarka yayinda ka keɓance kanka
kaikaɗai to a nan ne zaka fahimci cewar lallai abinda na Sanar dakai gameda
feelings ɗinka to soyayya ce a hakan ma me ƙarfin gaske, from this moment I'm going
to be precious About what I say.

"Abie what are you trying to say wai? Muzaffar ya faɗi hakan yayinda ya ƙara kafe
Abie da dara-daran idanunsa

murmushi Abie ya sakeyi a karona uku sannan yaci gaba da cewa "Think carefully Son.
Whoever it Is, or whatever situation it is that's Love my Son.

wani irin zaro idanu muzaffar yayi tamkar wanda aka gaya masa wani babban tashi
hankali ya kalli Abie tareda sauke Ajiyar zuciya yace "yanzun kam na fahimci abinda
kake nufi Abie but why nakejin sauyi a cikin Rayuwata daga shekarun baya zuwa
yanzun?
nikam tabbas inaji a jikina cewar tamkar a kwai wani Abou me mahimmanci wanda ya
zarta Kalmar so a rayuwata dana rasashi Abie, pls meneɓe shi?

Kallon tsaf Abie kebin muzaffar ɗin dashi sannan ya miƙe yace "naga alamaɗ idan har
na biye maka to zamu shekara dakai a nan batareda ka gaji ta jefomin sinƙi-sinƙin
tambayoyinka ba, oya tashi ka tafi gobe to 6:am insha Allah jirginku ze ɗaga zuwa
india.

Langaɓar dakai muzaffar yayi yace "no Abie nidai vanason tafiya a privet jet ɗin
company nafiso na tafi a nomal jirgi kamar kow....... Kallon da Abie ya watsa masa
ne yasashi haɗiye maganar dayay niyar faɗa. Miƙewa yayi tareda baya Abie side hugg
sannan ya fice daga falon zuwa ɓangaren sa, kasancewar yayi sallar isshansa a inda
yaje yasa ya fara rage kayansa sannan ya faɗa toilet, wanka yayi ya fito tareda
shiryawa cikin lausasan kayan baccinsa yabi lafiyar gado

Washe gari tun sassafe ya tashi ya shirya cikin wata Arniyar Korean suits ƴar gaske
me azabar kyau baƙa wuluk da itase ɗaukar idanu takeyi sannan ya tsaya a gaban
mudubin dake ɗakin ya gyara gashin kansa me laushin gaske da santsi tamkar na
jinsin fararen fata, a wannan lokacin kallo ɗaya zakayi masa ka fahimci cewar yafi
kamata larabawan yankin ƙasar misirah, ni kaina a yau seda na rola muzaffar fiyeda
zaton me karatu domin kuwa ya haɗu iya haɗuwa.

Ƙafarsa sanye take cikin wani dakakken takalmin fata ƙirar Compayn Kang gi boam
dake yanki Korea ta kudu. Da alama komai na muzaffar daga ƙasar akai odarsu

a nitse ya fito daga

Part ɗinsa cikin takunsa na isa da ƙasaita ya nufi falon mom, be sameta a falon ba
se Fadilah dake zaune cikin kayan baccinta me launin kalar milk tana kallin news a
Tv, wuceta yayi ba tareda ya kalleta ba ya haura upstairs Don because he don't have
her time at all ya tsani mutum mara respect ko kaɗan shiyasa ma ya fita sabganta.

Ƙofan ɗakin mom ya ƙwanƙwasa seda ta bashi izinin shiga sannan ya kunna kai cikin
bedroom ɗin da sallama a zaune ya sameta a gefan rantsatsen makeken gadonta tana
jiran ya karaso, gefanta ta nuna masa alamar ya ƙaraso ya zauna ba musu yayi yanda
ta umarceshin

Ɗan jim tayi kaɗan sannan ta dubeshi cikeda damuwa tace "harka shirya kenan se
tafiya? Da kulawa ya kalleta yace "ae mom na gaba zan wuce ɗin Kenan . Gefan
fuskarsa ta ɗan shafa kaɗan sannan tace "Allah ubangiji ya bada sa'a yasa kuma kaje
lafy ka dawo mana lfy. Da amin ya amsa mata sannan ya miƙe yace bye mom.

Harya kai bakin ƙofar fita idanunta na kansa sannan tace " Make sure you don't
have any interest on Hajiya Aisha harka dawo gidannan domin kuwa har yanzu ban gama
yarda da ita ba kaji ko?

Dan jim yayi kaɗan a ransa yana mamakin abinda yasa mom har yanzu batason ya dinga
shiga sabgar Hajiya Aishan, ya daɗe yana lura da cewar duk sanda ze tafi wata ƙasa
mom bata damuwa amma dazaran taji zeje India to daga ranar duk seta sauya kuma ta
shiga damuwa, shin wai meye a tsakaninsu da ita ne Da har yanzu be sani ba????

Comment
Nd
Share
Love you all guys

Sushmah💋
[3/3, 5:36 PM] Chubado Mohd: ❄️❄️❄️❄️❄️❄️
❄️❄️❄️❄️❄️❄️
🐄🐄🐄🐄
🐄🐄🐄🐄
*BAFULATANA*
✨RETURN✨
🐄🐄🐄🐄
🐄🐄🐄🐄
❄️❄️❄️❄️❄️❄️
❄️❄️❄️❄️❄️❄️

Page :21

*_WRITING BY: CHUBAƊO_*

Banyi Editing ba ayi haquri da typing Error

___✍️ Kallonta yake sosai jin taƙi magana ne yasa ya dawo gefan gadon ya zauna
tareda riƙe hannunta cikin nasa yace "mom what is the problem between you and
Ummie?

Wani ɗan iskan kallo Mom tabishi dashi tareda fuzge hannunta daga nasa tace "don't
call her with that name Again in front of me Muzaffar, if you do it again wllh zaka
fuskanci fushina. Shiru yayi a ransa yana girmama irin wannan rashin jituwa dake
tsakaninsu koma menene yana roƙon Allah ya kawo ƙarshensa, miƙewa yayi yana kallon
Agogon dake ɗaure a tsintsiyar hannunsa tareda fadin "ni zan Wuce semunyi waya.
"Allah ya bada sa'a mom ta faɗi hakan tana miƙewa zuwa toilet

Murmushi ya saki me sauti tareda ƙudurtawa kansa cewar koma mene tsakaninsu seya
tonoshi da izinin Allah sannan ya fice daga ɗakin, a Falo sukaci karo da Zainab
wadda ta fito kicin ɗauke da pride Egg with chips a flet becouse ita dawuri takeyin
braekfast except mutanna gidan da se 11 or 12 ma, tsayawa yayi chak yana kallonta
yana murmushi maƙalewa tayi daga inda take tana kallonsa tareda marairaice fuska
tace "Eyyah I'm sorry Hayaty wllh damuna tayi shiyasa na nuna mata part ɗinka.
Still Kallonta yake with smile on his face yace "is ok Qurraty zo mana ƴar ƙanwata.

Da sauri ta maƙe kafanaɗa tace "umm ni bazanzo fa nasan dukana zakayi. "haba ke
kuwa taya zan dakeki kedai zo mana kiji, ya faɗa yana takawa a hankali zuwa inda
take. Da sauri ta Ajiye flet ɗin akan daining ta naɗe riganta ta futa da gudu
zata haura sama shi kuma ya bita, zagaya falon suka dingayi Zaynab na ihu har Abie
ya shigo falon murmushi kawai yayi sannan ya nemi guri ya zauna yace "look malam
zaku makara fa time ɗin tafiyarka ya kusa fa saura 15mnt

Tsayawa Zaynab tayi jin yayanta zeyi tafiya harya zo ya kamata tareda kama kunnenta
na hagu da ƙarfi ya matsa yace "wllh this is the first and last warning dazan miki
akan nunawa wata ƙatuwa hanyar part ɗina. Ƙara zaynab ta saki tana roƙonsa sannan
ya sakin mata kunnen ya kama hannunta suka dawo tsakiyar falon inda Abie ke zaune,
taɓe baki Fadilah tayi tareda ƙara maida hankalinta ga Tv

Murmushi Abie yayi sannan suka gaisa da sanyin idaniyar nasa wato Muzaffar sannan
Zaynab ma ta gaidashi, cikeda soyayya yake amsa mata gaisuwar tareda shafa gefan
fuskarta kamar zatayi kuka tace "Abie wai india yaya ze tafi amma shind ko labari
babu? Nikam Abie inason zuwa india sabida ummie ta iya miyan gyaɗa sosai sannan
kuma tana bawa mutum lokacinta suyi hira fiyeda yanda Mom ke mana, pls Abie don
Allah idan na gama school ka nema min Admition a imperial college of Engineering
dake mumbai kaga kenan zan dunga zama tareda ita har ta koyamin irin salon
girkinta me daɗ....... "Har Abada kuwa wannan ranar bazatazo ba zaynab. And this is
the last warning dazan miki akan Ambaton sunan wannan matar a cikin gidana idan
kuma kika sake to wllh zakiga fushina. Mom ce ta katsewa zainab magana ta hanyar
faɗar hakan cikin ɓacin rai

Daga Abie har Zainab ɗin kallonta kawai sukeyi shiko muzaffar yama kasa cewa komai
sabida inda sabo ya saba ganin wannan abin a gidan tun yana ɗan ƙarami, koda wasa
Mom ta tsani taji ana ambaton sunan Hajiya Aisha a gabanta jitake kamar zuciyarta
zata fashe sabida baƙin ciki musamman idan taji yaranta na kiranta da Ummie

A haka ta ƙaraso falon cikin shigar doguwar rigar shadda an mata ɗinkin Senegal
wanda yaji uban stones se baza ƙyalli yake hannunta ɗauke da wasu murɗaɗɗun zobuna
na zinare, da Alama dai rakiyar bazata ta fito tayiwa ɗan gaban goshin nata.

Kallonta kawai Abie keyi yana mamakin ƙarfin Hali irin nata koda wasa be taɓa zatoɓ
cewa zafin kishinta yakai haka ba, babban abin takaicin ma wai akan Hajiya Aisha
wadda sam ita bata gabanta, Hajiya Aisha irin matan nan ne masu shiga ran mutane
koya kayi mu'amala da ita seka sota, wannan dalilin ne yasa ta samu kaso tamanin
daga soyayyar Abie kuma yakejin cewar itaɗin ta musamman ce a gurinsa. Girgiza kai
kawai yayi ya miƙe yace "oya muje jarya makara.

a haka Ahalin gidan suka fito gabaɗayansu except Fadilah wadda takaici ya isheta
ta koma sama ta buɗe ɗakinta ta haye gado.

Har sun fita Harbar gidan Baba Hajara ta fito ɗauke da wata babbar leda tan me
faɗin "ƙaramin me gida tsaya mana karyi babbar mantuwa na tagomashin danayi mka
tanaɗi. Ta faɗi hakan cikin yanayi na wasa

da sauri muzaffar ya dawo da baya zuwa inda take donya sawaqe mata yanayin tafiyar
sabida fama da ciwon ƙafar datakeyi wasu lokutan, yana son matar sosai sabida yanda
take bashi kulawa tareda nuna masa ƙauna tasha rasa Abubuwa dayawa sabidashi
shiyasa yake kallonta a matsayin kaka a gareshi ba mai aiki ba, wasu lokutan idan
yana kallonta yakanji a ransa cewar ita ɗin tamkar madubice a rayuwarsa shiyasa
tasu tazo ɗaya

Miƙa masa manyan ledodin guda biyu tayi sannan tace "Dambun nama ne nayi maka tun
jiya danaji Abbanka yana faɗar tafiyar india, ɗaya naka ne ɗaya kuma kabawa Hajiya
Aisha sannan kace ina gaisheta gaisuwa me tarin yawa koma ince mara adadi, Dariya
yayi sannan yace "ngde sosai Me ran ƙarfe Allah ya ƙara miki lfyar datafi wadda
kike da ita a yanzu. Kafaɗarsa ta ɗan dafa sannan tace "kaima haka Me gidana Allah
ya kaika lfy ya kuma dawo dakai lfy.

Da Amin ya Amsa mata har bakin mota ta rakashi sannan ta dawo gida a ranta tanajin
kewar Hajiya Aisha na ratsa duk wata gaɓa ta jikinta, itadai kam Allah yasa mata
ƙaunar wannan baiwar Allah tun ranar data fara ganinta har zuwa ranar data bar
ƙasar Nigeria Duk a rashin jituwar da basuyi da Mom, harta shiga cikin gida ta
zauna a ɗakinta batabar tunanin Aisha ba nan take gabanta ya faɗi a lokacin data
tuna wani abu daya faru shekaru Talatin da biyar da suka wuce. Nan take Baba
Hajarah ta mike ta fara zarya tamkar wadda wani babban al'amari ke shirin faruwa da
ita.

Su Abie basu dawo gida ba har seda sukaga tashin jirgin su Muzaffar nan ma kafin ya
shiga jirgi seda Mom tayi masa kashedi kan cewar yayi taka tsan-tsan da duk wani
abu daze kusantashi da Aisha. Sannan suka dawo gida cikeda kewarsa
*_GYAMBU TARABA STATE_*

tana zaune a saman bishiyar a haka bacci ya fara ƙoƙarin ɗaukarta jin kamar zata
faɗo daga bishiyan ne yasa ta farka da sauri tareda kifa cikinta kan reshen
bishiyan tayanda zatafi jin daɗin kwanciyar batareda fargaban faɗowa ba, a haka
wani gajiyayyen bacci ya ɗauketa me cike da tarin muggan mafarkai iri-iri akan
mahaifinta firgigit ta miƙe tana me fashewa da kuka a haka idanunta duk suka
kumbura kuma suka soye da batun bacci, ma'ana yanda taga rana haka taga dare a
wannan ranar sakkowa tayi daga saman bishiyar cikeda ƙwarewa sekace rainon Biri
abunku da rainon daji dole ne a samu ƙsarewa ta wannan fannin, jakarta ta sake
rayayawa sannan ta ɗauki hanya ba tareda tasan inda ta nufa ba.

*_MUMBAI BABBAN BIRNIN ƘASAR INDIA_*

Hajiya Aisha ce tsaye cikin kicin ɗinta na alfarma tana haɗawa ɗan mijin nata
abinci na musamman wanda zata tarbeshi dashi, abinci kala-kala ta haɗa masa na
ƙasashe daban-daban sannan ta fito dakanta ta jeresu a saman katafaren dining ɗin
dake cikin Hamshaƙin falon nata, duk yanda ƴan aikinta sukaso su taimaka mata amma
fir Hajiya Aisha taƙi amincewa da hakan tace subarshi ita da kanta zata girka masa
sabida yanda mijinta keji da ɗan nasa dole ne tayi masa kara sajen kula dashi.

Bayan ta kammala ne ta bada umarnin aje a gyara masa inda ze sauka, cikin mintuna
kaɗan suka kammala gyaran gurin tareda fesheshi da expensive air freshener me
sanyin ƙamshi da daɗi, bayan sun gama da minti goma motocin dake under companynsu
dake mumbai ɗin suka tsaya a ƙofar gidan cikin jerin gwano,, a nitse ya sanyo
ƙafarsa waje wadda ke sanye cikin dakakken baƙin takalmin fatar dake ƙafarsa lokaci
guda ya saki wani hamshaƙin murmushi wanda ya baiyana haibarsa a fili

fitowa Ummie tayi cikin shigar doguwar riga Abayah me launin kalar Maroon wadda
taji uban stones masu ɗaukar idanu, kallo ɗaya zakayi mata ka fahimci cewar ta fara
manyanta don a ƙalla ba ƙasaru ba shekarunta zasu kai 57, tayi lulluɓi da wani
babban mayafi kuma me kauri wanda ya kasance launin Ruwan madara sosai.

Faɗaɗa murmushinta tayi tana faɗin " maraba lale da babban baƙo kuma ɗaga sadaukin
mijina.

Washe baki yayi sosai har seda fararen haƙoransa suka baiyana yace "nagde Ummie
aida kin bari na shigo baki fito ba. Harara ta sakin masa sannan tace "ai shekarun
da yawa muzaffar taya zan iya zama a ciki naji xuwanka? Ai dole ne in fito na
tarɓeka

shiru yayi yana kallonta tareda son gano baƙin halin da mom ke yawan faɗar
tanadashi, shidai kam bazece yasan sharri ta ba tunda har be taɓa yin dogon zama da
ita ba balle har ya fahimci hakan. Kodai a kwai abinda take shirya masa ta bayan
fage ne wanda shi be san dashi ba?????

Thanks 4d love fans🙏

Comment
Nd
Share

Sushmah💋
[3/3, 5:36 PM] Chubado Mohd: ❄️❄️❄️❄️❄️❄️
❄️❄️❄️❄️❄️❄️
🐄🐄🐄🐄
🐄🐄🐄🐄
*BAFULATANA*
✨RETURN✨
🐄🐄🐄🐄
🐄🐄🐄🐄
❄️❄️❄️❄️❄️❄️
❄️❄️❄️❄️❄️❄️

Page :22

*_WRITING BY: CHUBAƊO_*

Banyi Editing ba

___✍️murmushi yayi sannan yace "ngde Ummie kusan a tare suka shiga cikin gidan
wanda aka ƙawata da kayan ƙwa na zamani kuma masu matiƙar tsada, miƙewa yayi Direct
zuwa inda ya saba sauka idan yazo ƙasar harya kai bakin ƙofar part ɗin Ze murɗa
handile ɗin ƙofar Ummie tace " idan kayi wanka ka huta sekazo daining kaci Abinci.

Da to ya Amsa mata yana me ƙara faɗaɗa murmushin dake kan Fuskarsa sannan ya kunna
kai zuwa cikin haɗaɗɗen falon, bedroom ya shige tareda rage kayan dake jikinsa zuwa
singlet with boxer wanda hakan ya baiyana santala-santalan legs ɗinsa, a hankali
yake takawa harya isa cikin ƙayataccen toilet ɗin wanda aka wadashi abubuwan ƙyale-
ƙyale iri-iri, tsayawa yayi cak yana kallon kowace kusurwa dake toilet ɗin bisa ga
mamakinsa komai an sauya masashi daga waƴanda ya sani a baya zusa Sababbi, a nitse
yake takawa cikin takunsa harya isa gaban wani baban Abu wanda yafi kamada bahon
wanka na zamani, ruwa ya tara a cikin ƙaton bahon me ɗan zafi tareda zuba shower
gel ɗin daya saba amfani dashi mallakin Companyn Olay me bala'in ƙamshi take kumfa
ta cika bahon ,

Murmushi yayi me kyau tareda shiga cikin Ruwan ya zauna tareda lumshe manyan
idanunsa zafin ruwan na ratsa duk wata gaba ta jikinsa, sosai yakejin daɗin yanda
zafin ruwan ke Ratsashi ya jima a ciki daga baya ya buɗe ruwan ya wuce sannan ya
tare wani yayi wankan ya fito. Bayan ya fito daga wankan be wani tsaya shafe-shafe
kamar yanda ya sababa ya shirya cikin kayan sport marasa nauyi tareda kabbara
sallar dake kansa, ya jima yana sallar sannan ya idar taredayin Azkar ɗinsa kamar
yanda ya saba a kowace Rana.

Yana miƙewa kiran Abie ya shigo wayanshi daga yanayin ringing ɗin ya Fahimci cewar
Abie ne, zama yayi daga bakin gadon dake ɗakin tareda kara wayar a kunnensa da
sallama yace "Abie ya gida? Ɓangaren Abie yayi murmushi yace "lfy lau Son ya
gajiyan Hanya? Ɗan shagwaɓe fuska yayi sannan yace "uhm wllh Abie a kwaita kagafa
se yanzu na yi wanka tun shigowana ƙasar. Dariya Abie yayi me Sauti sannan yace "ka
kula da kanka sosai I'm sure of you will do your job with full success. Muzaffar
yayi murmushi yace " sure Abie insha Allah.

Mom dake zaune gefan Abie haka kawai seta samu kanta da rashin samun kwanciyar
Hankali tunda muzaffar yayi tafiya, haka nan seta samu kanta da rashin Amintuwa da
tafiya jiki babu ƙwari ta karɓi wayar daga hannun Abie cikin tattausan lafazi tace
"Boy ya dai ina fatan kana lfy? Ɗan shafa gefan fuskarsa yayi kana yace "I'm fine
mom and why your voice was so cool? "I don't know why darling I'm just feel like
something is definitely going to happen to me. Pls take good care of yourself kaji
yaron kirki? Sannan ka kula da makircin Hajiya Aisha ok.

Shiru yayi bece komai ba a haka suka katse wayar Abie na binta da kallon mamaki
yace "why are you behave like that Hajiya Saratu? Meyasa ke bakya ƙaunar kiga an
zauna lfy ne?

Yau kimanin shekaru nawa ana wannan abin ai yaci ace yanzu kun haƙura kuma kun
zubar da komai kodan kwanciyar Hankalina. Cikeda karyewar zuciya mom tace "Abie
bazaka gane komai ba shiyasa kake faɗar hakan, taya matar dta nunawa ɗana tsana tun
yama ɗan ƙarami kayi tsammanin cewar yanzu bazata iya cutarmin dashi ba?

Nifa uwa ce Abie taya bazanyi yaƙi da duk wani me neman cutar min da rayuwar ƴaƴana
ba? Kada ka manta da wacece matarka Aisha kasancewar bata taɓa haihuwaba tunda ta
hafi ɗanta bezo da raiba take ƙoƙarin ganin bayan nawa ɗan har zuwa lokacin daka
ɗauketa tabar ƙasar nan. Wllh nasan she can do anything don ganin ta lalata min
rayuwar Ahalina amma nasan onday one time you will understand what I mean insha
Allah.

Shidai Abie girgiza kai kawai yayi tareda miƙewa ya faɗa toilet tana binsa da
kallo,

*******
Ɓangaren Muzaffar kuwa Ajiye wayar yayi ya fita sabida wani irin juyawa da cikinsa
keyi sabida yunwa yana fita a falo ya samu Ummie tareda wata ƴar aikinta Maryam
kallo ɗaya zakayi mata kasan ƴar Nigeria ce, a ƙalla shekarun Maryam zasu kai 40
tun lokacin da Ummie tabar nigeria Suka taho tare.

da fara'a Ummie ta tarbeshi suka nufi daining ita kuma Maryam ta durƙusa tana
gaisheshi with so much respect, murmushi kawai ya sakin mata sannan ya wuceta ba
tareda ya amsa ba Hajiya Aisha da kanta tayi sarving nashi Abincin wanda keta zuba
uban ƙamshi sannan ta miƙa masa itama ta xauna ta fara zuba nata Abincin wanda keda
banbanci danasa kasancewar tanada ciwon suger

Kusan a tare suka fara cin Abincin har wani lumshe ido Muzaffar keyi sabida Daɗin
Abincin hakan ne yasa yaci sosai har ummie tayi mamakin hakan, dabida a iya sanin
datayi masa bayacin abinci sosai.

bayan sun gama cin Abincin ne Maryam ta miƙe ta kwashe kayan Abincin takaisu kicin
tareda gyara gurin, zama sukai a falon suna ɗan taɓa hira duk akan abinda ya
kawoshi Indian wani tayi murmushi wani kuma ta kalleshi, wayarta ce tayi ƙara hakan
yasa ta maida hankalinta ga wayar tareda karawa a kunnenta Tace "bayi zamuyi magana
yau insha Allah komai ze kammala ba tareda anci lokaci sosai ba. Ta faɗi hakan tana
satar kallon muzaffar wanda ya maida duk hankalinsa akan System ɗinta dake gabansa,

a nitse yake gabatar da komai cikin nutsu ba zato ba tsammani yaji cikinsa yay wani
irin juyawa tareda muɗa masa, dafe cikin yayi da duka hannayensa tareda zube
gwiwowinsa a ƙasa ya saki wata irin ƙara wadda ta firgita Hajiya Aisha da me
aikinta Maryam dake kicin tana wanke kwanikan da akaci abinci dasu, Sakin wayar
Hajiya Aisha tayi tareda nufo kansa gadan-gadan tana raba idanu hanyar kicin ta
kalla ganin babu wanda ya taho yasa ta ɗagoshi tana kallon fuskarsa kimanin 5second
jin tafiyar Mutum daga hanyar kicin ɗin yasa itama ta saki ihun neman taimako. A
gigice maryam ta ƙaraso gurin idanunta duk a waje sabida tashin hankalin tareda
kallon Ummie lokaci guda kuma ta sake maida kallonta ga muzaffar wanda ke fitarda
wata irin farar kumfa daga bakinsa hakanne ya bata tabbacin cewar Guba yaci.

cikeda tashin Hankali maryam ta dora hannu akanta tana faɗin


"innanillahiw'inna'ilaihirraji'un!!!!!!

a gigice maryam ta nufi wayar telho ɗin dake ajiye bisa wani ƙaramin table ta shiga
wayar Babban Asibitin kuɗin dake kusa dasu ko'a samu a ceto Rayuwarsa cikin Sauƙi.
Ummie kuwa ta kasa motsin kirki balle har ta tsinana wanu abin arziƙin a gareshi,
take wani irin gumi ya fara keto mata tareda nadama mara misaltuwa babban abinda
ke ɗaga mata hankali a wannan lokacin shine da wani ido zata kali Abie bisa wannan
abinda data kasance itace silar Faruwarsa?

tabbas duk irin sonda yake mata a wannan lokacin ta tabbata bazata tsira ba daga
hannunsa shida matarsa Saratu ba tunda har tayi poisoning ɗin dansu namiji
tilo........

*GYMBU TARABA STATE*

Da ƙyar Inna Laure kejan numfashi sabida tsabar azabar datakeji ko hannunta ta kasa
ɗagawa balle tasan ran cewar zata iya miƙewa, seda suka gama zuba Rashin imaninsu
sannan suka tattara komai suka tafi dashi tareda ketawa Yara ƙanana haddinsu, a
wannan rana rayuka dayawa sun sosu da baƙin ciki mara misaltuwa haka kuma zuciyoyi
sun baƙanta, a wannan tsukun ne Mahaifin Ruƙatu Babbar Aminiya ga Rabe ya rasa
Rayuwarsa al'amarin daya ƙara ɗaga mata hankali kenan.

sosai malam iro ya zubar da jini sosai har hakan yasa suka fitar da rai da cewar ze
tashi, moddibo kuwa gabaɗaya ya kasa cewa komai duk a sanadin bala'in daya sameshi,
baya iya furta komai se ido kawai dayakebin kowa dashi, miƙewa yayi ya shiga
ɗakinsa da sauri ya kauda kansa sabida ganin irin Rashin imanin da suka aikatawa
Laure komai bushewar zuciyarka dolene ka tausaya mata muddin kanada imani, da sauri
ya isa gareta sabida ganin yanda jini ke zuba daga ƙasanta duk yamda yaso ya
taimaka mata kasawa yayi dole ya zube a gurin ya saki kuka me sauti da ban tausayi,
itama kanta Lauren kuka takeyi tareda tausayawa kanta a irin Rayuwar dazata
fuskanta nan gaba

seda yayi me isarsa sannan ya miƙe ya fita daga ɗakin ya haɗo ƙirare ya kunna wuta
tareda ɗora ƙatuwar tukunya akai, cikin mintunan da bazasu gaza 20 ba ruwan ya
tafasa wata babbar fanteka ya ɗakki ya zuba ruwan a ciki kimanin rabin fantekar
sannan ya ɗauka ya shiga da ita ɗakin ya zuba wani garin magani a ciki take kallar
ruwan ta sauya zuwa launin kore, seda yaɗan sha iska sannan ya kinkimeta ya zaunar
da ita cikin ruwan, wata uwar ƙara ta saki har seda ta bashi tausayi

cikin ikon Allah jinin ya tsaya har taji ɗan dama-dama a jikinta, seda ya gana bata
duk wani taimaki dayake ganin ze iya bata sannan ya fita zuwa waje ya fara duba
sauran jama'a ba tareda ya damu da jinin dake zuba a kansa ba. *_(Allah sarki
modibo haqiqa kyakkyawar zuciyar halitta ce ba kowani mutum ne ke tuna al'uma ba a
lokacin da musiba ta sameshi ba, kowa kansa yake fara ginawa sannan daga baya ya
tuna da al'uma amma shi kuma moddibo yace "al'uma itace farko kafin kansa. Ya Allah
ka cire mana son kai da ƙyashi daga zukatan mu🤲)_*

A hakan seda ya tallafawa kowa sannan ya agazawa kansa daga baya. Baze iya furta
komai ba a irin wannan halin baƙin cikin dayake ciki ba, amma yana roƙon Allah ya
saka musu bisa zalincin da aka aikata musu

******

The fulani girl Tafiya take tana kallon titin kmaar wata me koyan tafiya ba zato ba
tsammani wasu farar mota sol ƙirar formatic C350 Da suka taho cikin jerin gwanonsu
kimanin guda 6 ta gaban tai sama da Ita, take ta zube a saman kwantar jini na
ɓulɓula ta hancinta da kunnuwanta!!!!

A gigice Drivern dake motar ya fito take motocin dake binsa a baya suka tsaya
sabida ganin tsayawarsa, kwance yake cikin motar dake tsakiya yana latsar waya
yaji motocin sun tsaya, dago madaidaitan idanunsa yayi yana kallon drivern dake jan
motar dayake cikin yace "what's wrong?
Cikeda girmamawa matashin Drivern yace "I don't know sir but let me check. Maida
hankalinsa kan wayar yayi batareda ya damu da abinda ke faruwan ba yaji an
ƙwanƙwasa glass ɗin motar dayake ciki, cikeda damuwa Wanda ya ƙwanƙwasa ɗin yace
"im sorry sir hatsari muka samu a sanadin bige wata yarinya.

Da sauri guy ɗin ya ajiye wayar ya fito cikeda tashin hankali, sanye yake ciki wata
dakakkiyar suit's maroon colour dogo ne sosai ma'abocin cikar zati da kuma
kwarjini, sam be kasance cikin jerin maza masu hasken fata ba amma yanada gogewar
fata sosai irinta ƴaƴan masu hannu da shuni.

Gabansa ne ya faɗi a lokacin dayayi arba da jinin dake futa ta hancinta da kuma
kunnenta, a hanzarce ya tsuguna yace "pls be fast let's take her to the hospital.

Babu ɓata lokaci suka sanyata a cikin ɗaya daga cikin motociɓ batareda sunyi
la'ajari da kar jinin ya ɓata musu mota ba suka kwasa da wani mahaukacin gudu suka
nufi wani ƙaramin hospital dake dabda cikin wani ƙaramin ƙauye dake maƙotaka da
dajin. Babban abinda ze bawa me karatu mamaki shine still her hand is on the wannan
jakar da Modibo ya Rataya mata.

Tofa ana wata ga wata 🤔

thanks 4d love guys

comment
nd
share

sushmah💋
[3/3, 5:36 PM] Chubado Mohd: ❄️❄️❄️❄️❄️❄️
❄️❄️❄️❄️❄️❄️
🐄🐄🐄🐄
🐄🐄🐄🐄
*BAFULATANA*
✨RETURN✨
🐄🐄🐄🐄
🐄🐄🐄🐄
❄️❄️❄️❄️❄️❄️
❄️❄️❄️❄️❄️❄️

Page :23

*_WRITING BY: CHUBAƊO_*

____✍️Cikin mintunan da bazasu gaza goma ba likitan dake on duty ya shiga bata
taimakon gaggawa don gudun kar jinin dake fita ta kunnenta ya samu nasarar taɓa
ƙwaƙwalwar ta, dukda cewa Asibitin basuda isassun kayan aiki sunyi bakin ƙoƙarinsu
akanta kuma Cikin ikon Allah suka samu nasarar tsaida zubar jinin cikin sauƙi.
Gabaɗaya haɓkalin matshin a tashe yake dukda cewar mutum neshi me izza Amma sam
bashida kwanciyar hankali yayinda yaga na ƙasa dashi a cikin hali na buƙatar
taimako, likitam na fitowa Direct gurin matashin ya nufa tareda miƙa masa hannu
yace "congrats munyi nasara wajen tsaida zubar jinin sedai tana buƙatar ƙarin jini
sabida tarasa jini dayawa amma yanzu hkaa mun saka mata drip da ace so samu ne ku
miƙata ga babban Asbitin don gudun karta samu matsala a ƙwaƙwalwar ta, Zaro ido
matashin yayi tareda dafe kansa cikeda damuwa yace "oh my God!!!!! Kallonsa ya
mayar ga guards ɗinsa sannan yace " nanda zuwa wani lokaci zamu isa Abuja daga nan?

Kallonsa sukai da kulawa sannan ɗyaa daga cikinsu yace" ranka ya daɗe zamu iya
ɗaukar lokaci me ɗan tsayi kafin mu isa sabida doguwar tafiyace sosai amma zamuyi
iya bakin ƙoƙarinmu don ganin mun isa akan lokaci da yardan Allah. Ajiyar zuciya
ya sauke meɗan nauyi sannan ya biya kuɗin Asbitin tareda bada umarnin a fito da ita
asa a mota zasu wuce, ba musu suka shiga cikin Asbitin suka fito da ita tareda
sanyata a bayan ɗaya daga cikin motar suka kwantar tareda gyara mata zaman drip ɗin
dake saƙale a hannunta sannan sukaja motoci @360

Ba ƙaramin gudu suka dinga zubawa ba cikin ikon Allah kuwa suka shigo garin Abuja
akan lokaci, wani hamshaƙin Asibitin kuɗi suka nufa da ita wanda ke cikin Asokoro
inda Family Dr. Ɗinsu ke aiki me Suna Mujaheed Abdullahi, cikin ƙanƙanin lokaci
suka shiga bata taimakon gaggawa abinka da masu citta a hannu sun juma suna
gudanar da aikinsu a kanta sannan Dr. Mujaheed ɗin ya fito daga ɗakin wata
matashiyar nurs na biye dashi a baya.

Direct inda matashin ke zaune tareda Gurds ɗinsa Dr. Mujaheed ya nufa sannan ya
kalleshi yace "muje office ba musu ya miƙe yabi bayansa seda duka ɗanyi tafi kaɗan
sannan suka isa office ɗin me shegen kyau sannan suka zauna, cikeda damuwa
matashin yace "ya jikin nata Dr.? Murmushi Dr. Mujaheed yayi yace "ka kwantar da
hankalinka Edriss insha Allah komai zeyi daidai, ka godewa Allah ma kun kawota
akan lokaci. Murmushin jin daɗi Edriss Adam yayi tareda faɗin "Alhamdulillah Dr.
Wllh har hankalina ya kwanta.

Magungunan da suke buƙata ya rubuta masa tareda cewa "a halin yanzu tana buƙatar
jini domin kuwa ta rasa jini dayawa, mun binkita mun gani launin jininta me wuyar
samu ne kuma ya kamata a ƙara mata shi da gaggawa idan ba haka ba gaskiya something
can happen to her. Da sauri Edriss yace " no Dr. You can take my own because nau'in
jini na ze iya yiwa kowa

Ƙura masa manyan idanunsa Dr. Mujaheed yayi a zuciyarsa yana mamakin yanda Edriss
ya damu da wannan baiwar Allah, ajiyar zuciya ya sauke sannan yace "who is she to
you Edriss?

Murmushin rainin hankali Edriss yayi yace "ba wannan ba tukun muje ka ɗau jini na.
Ya faɗi hakan yana kallon tsakiyar ƙwayar idon Mujaheed ɗin

Basarwa yayi ya miƙe yace "bani zan ɗau jininka ba Edriss yanzu dai zan turaka inda
za'a ɗauka ɗin, cikin mintunan da bazasu gaza 10 ba akayi komai aka gama se'a
lokacin hankalin Edriss ya kwanta sannan ya wuce gida donya samu ya huta.

INDIA🇮🇳

dakewa Ummie tayi tana binsa da kallo tamkar wadda aka dasata a gurin, gaba ɗaya ji
take komai ya tsaya mata chak har motar Asibitin ta ƙaraso ƙofar gidan still tana
tsaye kan ƙafafunta, Maryam ce ta fita da hanzari tayo musu jagora zuwa cikin gidan
inda muzaffar ɗin ke kwance samɓal babu alamar numfashi a taredashi, kin kimarsa
sukayi suka ɗorashi bisa wani siriri gado sannan suka fito dashi Zuwa cikin motar,
basu jira fitowar wani daga cikin gidan ba sukaja motar sabida ganin irin condition
ɗin mara lfyn se bayan sun fita Hajiya Aisha ta zube bisa doguwar kujerar dake
falon tana maida numfashi

wayar muzaffar dake kusa da System ɗin Ummie ce ta fara ƙara kasa ɗagawa ummie tayi
hakanne yasa maryam ta isa ga wayar jikinta na wani irin rawa ta Amsa ba tareda ta
duba sunan me kiran ba, cikin yanayi na rashin kwanciyar hankali mom tace "boy are
you Ok?

Wani irin fashewa Maryam tayi da kuka nan ta shiga zaiyanawa Mom halinda muzaffar
ɗin ke ciki. Wani irin Zabura mom tayi ta miƙe zaune daga kwancen da take cikin
yanayi na fitar haiyaci tace "ɗan nawa ne yafi guba ??????

Abie wanda ke kwance ne ya miƙe idansa nakan Mom wadda jikinta ke wani irin rawa
sabida tsabar tashin hankali, fashewa tayi da kuka tana danne ƙirjinta dake mata
wani irin suya ta kalli Abie bakinta na rawa tace "kagani ko? Senayi magana sekace
kishi ne ke ƙoƙarin hanani zaman Lfy da Aisha to gashi nan yau ta zubawa ɗana guba
a abinci kuma ya........... Girgizata yayi da wani irin Sauri sabida ganin idanunta
na ƙoƙarin rufewa take mom ta dawo daidai cikin haiyacinta tareda faɗawa jikin Abie
ta saki wani irin kuka me taɓa zuciyar duk wata uwa datasan ma'anar haihuwa. A
daran ranar Abie yayi hayar privet jet zuwa ƙasar India aiko kiran sallar farko
suka himmata sukabar ƙasar.

India 🇮🇳

Hajiya Aisha da ƙyar ta iya miƙewa ta koma ɗakinta tareda zubewa a bakin gadonta
zuciyarta duk a cushe, gabadaya komai ya tsaya mata tayanda takejin cewar dama
hakan bata faru ba do take tayi kuka amma kuma ta kasa yin hakan, dama idan wani
bala'in ya sameka hawayen ma ɗaukewa yake gabaɗaya a haka har gari ya fara haske
still tana zaune batareda ta rintsa ba.

cikin ikon Allah jirginsu Abie ya sauka lfy cikin mintuna kaɗan motocin company
sukazo ɗaukarsu Kasan cewar basu san Asibitin da aka kwantar da Muzaffar ɗin ba
dole yasa suka ɗauki hanyar gidan Hajiya Aisha, gabaɗaya mom ta birkice tamkar wata
zararriya idanunta duk sunbi sun koɗe sabida kukan data gurza, a haka motocin suka
tsaya a bakin ƙofar gidan cikin jerin gwano.

kokaɗan basu jira an buɗe musu ƙofar motar ba kamar yanda suka saba mom ta ɓalle
murfin motar ta diro tana huci, da wani irin sauri ta shiga gidan tana kwaɗawa
Ummie kira a birkice, sautin muryarta ne yasa Hajiya Aisha tasha jinin jikinta kuma
ta fito daga ɗaki jikinta a saluɓe tamkar kazar da ƙwai ya fashe ma

tana fitowa idonsu ya sarƙe cikin na juna a karon farko tun bayan shekara 35, wani
irin wawan Mari mom ta ɗauke Ummie dashi har seda taga taurari tun kafin ta
watsetsake ta ƙara ɗauketa da wani marin, cikin kiɗima Ummie tace "ni kika mara
Saratu?

cikin fusata Mom tace "na mareki Kiyi duk abinda zakiyi, Se yau na sake tabbatar da
cewar ki cikakkiyar shaiɗaniya ce Aisha kuma wllh ki kwana da sanin cewar sena
hukuntaki a bisa laifinki na bawa ɗana guba wllh koda kuwa abinda na mallaka ze
ƙare akan shariya dake!!!!

Abie dake tsaye yana kallonsu ji yayi duk Hajiya Aisha ta sure masa a rai a sanadin
abinda ta aikatawa gudan jininsa namiji tilo tabbas baze ƙyaleta ba a wannan karon
dole ne shari'a tayi aiki akanta, ya juya yana kallon jami'an tsaron dake bayansa
yace "ku tafi da ita!!!

Wani irin zazzafan hawaye ne ya zubo mata daga idanunta ba tareda tayi magana ba
jami'an suka tusata Station abisa yunqurinta na kisan kai..............
Har suka fita da ita bata dena kallon Abie ba lokaci guda kuma ta fashe da wani
irin kuka wanda ita kaɗai tasan ma'anar abinta.

Thanks 4d love fans❤️

comment
nd
share

Sushmah💋
[3/3, 5:36 PM] Chubado Mohd: ❄️❄️❄️❄️❄️❄️
❄️❄️❄️❄️❄️❄️
🐄🐄🐄🐄
🐄🐄🐄🐄
*BAFULATANA*
✨RETURN✨
🐄🐄🐄🐄
🐄🐄🐄🐄
❄️❄️❄️❄️❄️❄️
❄️❄️❄️❄️❄️❄️

*_Page :24_*

*_WRITING BY: CHUBAƊO_*

Banyi Editing ba

_____✍️Har suka fita kuka takeyi sosai jikin Abie ya sanyi dajin sautin kukanta
seda dukda hakan bayajin cewar ze iya ƙyaleta bisa yunƙurinta na kashe masa ɗa.

Tsaki Mom taja tana shirin magana sega maryam ta fito, ƙura mata iɗanu mom tayi a
ranta tana tunanin inda tasan wannan fuskar Katse mata tunani maryam tayi ta hanyar
cewa "Sannunku da zuwa Ranki ya daɗe nice wadda mukai magana dake ta waya ta faɗi
hakan tana matse ƙwallar data zubo mata da gefan zanin Atamfar dake jikinta. Ajiyar
zuciya mom itama hawaye na zubo mata tace "wani Asbiti aka kaimin ɗana ?

"Ghandy Special Hospital ne dake Ƙarshen Layin nan naryam ta faɗin hakan. Cikeda
Masifa mom tace "taya za'ai kukaishi ƙaramin Asibiti a madadin kukaishi na Compay?
Wll......" kinga Saratu pls ki nutsu ki dawo cikin haiyacin ki insha Allah komai
zeyi daidai, Nasan Asbitin farin sani kuma sunada kayan aiki sosai karki manta nan
ba Nigeria bace suna bawa Asbitocinsu dukkan abinda ya dace wanda za'a kula da
marasa lfy dasu cikin ƙwarewa.

Kuka ta fashe masa dashi har suka fita daga gidan zuwa Asibiti bata dena kukan ba,
a nitse Driver ɗin dake tuƙasu ya faka motar a harabar Asibitin inda aka tanada
sabida hakan, Dukda cewar Asbitin ƙarami ne amma yana da kyau gamida tsari fiyeda
zaton me karatu kusan gabaɗaya hankalin mom baya jikinta burinta kawai taga
halinda ɗanta yake ciki.

A haka suka isa reception na Asbitin A nitse Abie ga ƙarasa gurin da wasu nurses ke
zaune da alama sune cashier's na Asbitin, tambayarsu yayi inda aka kwantar da mara
lfyan cikin harshen turanci matashiyar yarinyar tace "faɗi sunan mara lfyn sena
duba maka. Cikin mintuna kaɗan ya gaya mata sunan take ta binciko musu ɗakin da
mara lfyn yake suka nufin ɗakin

A bakin ƙofar ɗakin suka tsaya sabida hanasu shiga da akayi seta ƙofar glass ɗin
dake jikin ɗakin suke hangensa, kwance yake kan gadon Asbitin an saka masa uniform
me launin kalar brown, fuskarsa ɗauke taƙe da oxygen inda bakinsa kuma akai warring
wani dogon five wanda ya taho tundaga cikinsa sabida poison ɗin dayaci, babu abinda
ke motsi a jikinsa se iskar numfashin dake fita ta cikin na'urar oxygen ɗin da aka
saka masa. Se'a lokacin idanun Abie suka sauka akan Rubutun da akai bisa jikin
ƙofar glass ɗin dake jikin ɗakin kamar haka (ICU) intensive care unit. Ajiyar
zuciya ya sauke me ƙarfin gaske a ransa yace "lallai ɗansa yana cikin tsaka me wuya
tunda har aka kawoshi cikin wannan ɗakin to abin bana wasa bane. Wani iri yakeji a
zuciyarsa gameda wannan gagarumin cin Amanar da Hajiya Aisha tayi masa, meyasa zata
aikatawa ɗan daya haifa irin wannan zalincin?

Kuka sosai mom take hakanne yasa Abie ya jawota jikinsa yana bubbuga bayanta, wata
irin tsanar Ummie ce take ƙara ratsa duk wani lungu da saƙo na zuciyarta tareda
ƙudurtawa kanta cewar wllh koda abinda ta mallaka ze ƙare setayi shariya da Hajiya
Aisha tayanda nan gaba koda ɗan dabba bazata sake yunƙurin kashewa ba ballan tana
ɗan mutum.

*******

ƁANGAREN HAJIYA AISHA kuwa station suka hurgata suka kulle gabaɗaya komai ya tsaya
mata cak ta rasa abinda ke mata daɗi a cikin wannan duniyar, bata taɓa zaton haka
daga gurin Abie ba tayi zaton cewar ɗabi'arta data ɗaɗe tana nuwa masa bazata
barshi ya amince da wannan al'amarin daya faru da ita cikin sauƙi ba amma kuma se
gashi shida kansa yasa ƴan sandan wata ƙasa suka kamata har cikin gidanta suka fito
da ita suka kawota wannan gurin mara tsabta. Tabbas tayi data sani a rayuwarta na
sanin Abie da zuriyarsa tun farko, da ace bata sanshi ba da duk hakan bata faruwa.

wani irin kukan baƙin ciki ne ya taso mata tareda data sanin Abinda ta aikata a
Rayuwar ta, babban tashin hankalinta a yanzu shine taya zata iya sanar da iyayenta
da ƴan uwanta halin datake ciki??????

A haka Rayuwa ta dinga tafiyar mata cikin yanayi na rashin jin daɗin Rayuwa gamida
walwala.

NIGERIA 🇳🇬

Edriss ne zaune tareda mom ɗinsa cikin danƙareren falonsu na alfarma wanda ko gidan
shigaban ƙasa se haka, da damuwa kwance akan Handsome face ɗinsa yace "mom nifa
hankalina sam ba'a kwance yake ba wllh inaji a jikina cewar dama banje Taraban nan
ba sam wllh. Ya faɗa kamar zeyi kuka

Da kulawa matar daya kira da mom ta ɗago fararen idanunta ta kalleshi tace "why
are you saying that sweetie? "mom wata yarinya muka bige a hanyar dawowan mu daga
Taraba. Edriss ya faɗi hakan yana kallon tsakiyar idanun mahaifiyar tasa. Be damu
da irin kallon datake binsa dashi ba yaci gaba da cewa" haka kawai naji a raina ina
tausayin yarinyar mom becouse ƙarama ce sosai kuma wllh mom she's pretty.

Sosai mom Edriss ta kaɗu dajin baya nan ɗan nata da ƙyar ta iya cewa " yanzu Edriss
a wannan uban dajin ta ina gida ze kasance balle har a samu yarinya har ku bige da
mota?

a dake ya kalleta yace "no mom ba yarinya bace kamar kowa she's Fulani girl......
Cikeda kaduwa Mom Edriss ta kalleshi tsoro ƙarara akan fuskarta tace "Fulani girl?
Ta faɗa cikin karaji.........

comment
Nd
Share

Sushmah💋
[3/3, 5:36 PM] Chubado Mohd: ❄️❄️❄️❄️❄️❄️
❄️❄️❄️❄️❄️❄️
🐄🐄🐄🐄
🐄🐄🐄🐄
*BAFULATANA*
✨RETURN✨
🐄🐄🐄🐄
🐄🐄🐄🐄
❄️❄️❄️❄️❄️❄️
❄️❄️❄️❄️❄️❄️

Page :25

*_WRITING BY: CHUBAƊO_*

*_All Characters, place, organizations and incident of this Interesting Novel are
fictitious😁, so pls my dearest sisters abinda yake me kyau a ciki to dashi zamuyi
koyi bada akasin hakan ba, Allah ya bamu ikon aiki da darasin dake ciki don isar
mazon Allah✊_*

___✍️ Murmushi yayi har seda fararen haƙoransa suka baiyana sannan yace "mom why
are you looking so surprised?

Ajiyar zuciya mom Edriss ta saki sannan tace "no like that sweetie I'm just feel
like there's definitely something behind the Fulani's girl ɗin ne thats why I look
so shocked. Dariya Edriss yayi yace "pls mom ki manta da wannan maganar babu komai
a tareda ita se alkhairi insha Allah wllh mom tausayin yarinyar nakeji because
she's to young like Sis Zeeyadah. Ya faɗa kamar ze sakin mata kuka

Shiru Mom Edriss tayi tareda maida hankalinta ga makekiyar Tvn bangon dake manne a
cikin falon, miƙewa Edriss yayi tareda faɗin pls mom ki shirya zuwa 4pm insha Allah
semuje Hospital ɗin ki ganta. Ya faɗa yana kallon ƙofar falon sabida motsin dayaji
a gurin

Hajar ce ta shigo cikin Shigar doguwar rigar material Baƙi wuluk wadda tai bala'in
bin jikinta, sosai kayan sukai bala'in karɓar jikinta kasancewarta farar fata
sedai a ɓangare na Addini sam shigar datayi bata dace da koyarwan Addinin mususulci
ba, taɓe baki Edriss yayi yana kallonta yace "hey meye haka kekuma kamar wata ƴar
babyn Roba?

Hararanshi tayi tareda zama a kusa da mom kamar zara shige jikinta tace "uhm ai
dama kai ya Ediyan ɗinan komai sekayi magana baka gani kayi shiru. Ta faɗa tana
ƙunƙuni a ranta kuma tace "baƙauye kawai. Wani shegen kallo ya watsa mata lokaci
guda kuma ya saki muskilin murmushi yace "look at you don Allah tayama za'ai Zafsy
ya soki (muzaffar)? Wllh mom yarinyar nan babu namijin daze sota a haka jibeta fa
sekace ɗiyar mutannan gabashin Ameerica. "gaya mata dai ya Edyan kullum gani take
kamar tafi kowa wayewa sabida Dady ya kaita ƙasar England tayi karatu. Zeyadah
dake sakkowa daga saman sters ta faɗi hakan tana dariya, Zeeyadah ƙanwa ce ga
Edriss uwa ɗaya Uba ɗaya kamar yanda hajar ma ta kasance ƙanwa a gareshi, Edriss
shine babba sannan Hajar se kuma Zeeyadah wadda ta kasance Auta, mahaifinsu Alhaji
Adamu babban ɗan sanda ne wanda a yanzu yake taka matsayin IG a nan ƙasarmu ta
Nigeria, a kwai shaƙuwa sosai a Tsakanin Edriss da Sisters ɗinsa Hajar da kuma
zeeyadah sedai shaƙuwar dake tsakanin Zeeyadah da Edriss ya shallake duk yanda me
karatu ke zato da kuma tsammani, shiyasa take kiransa da Ediyan a madadin Edriss.
Hakan ya samo Asaline da ƙuruciyar Zeeyadah wannan shine mafarin komai.

Itadai Mom Edriss jinsu kawai takeyi amma hankalinta naga wannan yarinyar da ɗanta
ya kira da fulani girl. Haka kawai takejin zuciyarta na rawa gabaɗaya ta rasa
makama babbaɓ burinta shine tayi ido huɗu da wannan yarinyar kota samu nutsuwar
zuciya.

*****

India 🇮🇳

Bayan Abie sunbar Asbitin da muzaffar ɗin ke kwance basu dire ko ina ba se
magarƙamar da aka sanƙame Ummie a ciki, nan take bada ɓata lokaci ba ya nemi da a
tura case ɗin babban ofishin jakadancin Nigeria dake ƙasar indian kasancewarsu ba
ƴan ƙasa ba. Be wani sha wahala ba suka amince da hakan tareda tura case ɗin can
kamar yanda Abie ya buƙata

Muhammad Kareem Ahmad shine wanda case ɗin Ummie bisa yunƙurin kisan muzaffar ya
faɗo hannunsa, gyara zaman farin glashin dake manne a idanunsa yayi tareda gyara
zamansa bisa hamshaƙiyar lallausar kujerar dake cikin katafaren office ɗin sannan
ya dubi Abie yace" ina evidance ɗin da Asibiti suka baku wanda ya tabbatar da cewa
Guba yaron yaci?

Miƙa hannu Abie yayi ya karɓi takardun dake hannun Mom wadda tunda sukabar Asbitin
take kuka ya mikawa Muhammad kareem Ahmad su, ƙurawa takardun idanu yayi yanabin
komai daki-daki cikeda sanin kan aikinsa kimanin wani lokaci me tsayi sannan ya
dubi Abie cikin ido yace

"haƙiƙa wannan al'amarin zan iya cewa a kwai tarin sarƙaƙiya a cikinsa wanda idan
bamu maida hankali ba zamu iya zartar da hukunci ba'a muhallin daya dace ba Alhaji
Abdulwahab, dole ne mu zarfafa buncike har mu gano gaskiyar lamarin nan, a
sakamakon da likitocin Asibitin da yaron yake kwance suka bayar ya nuna cewar gubar
bata daɗe a cikin jikinsa ba ta fita sannan kuma iskar daya shaƙa kafin yaci
abincin ita kanta a gurɓace take don haka dole ne mu ƙara samun cikakken bayani
akan wannan case ɗin na Hajiya Aisha.

A wannan takin ita kaɗaice zata iya fitar damu daga shakku. Ya faɗi hakan yana
kallon wani matashin saurayi yace "kace musu su shigo da me laifin nan zata amsa
min wasu tambayoyi dazanyi mata. Juyawa matashin yayi a hanzarce ya fice cikin ƴan
mintunan da bazasu gaza 2ba aka shigo da hajiya Aisha hannunta ɗaure cikin ankwa
idanunta duk sun jeme sabida kuka, kallo ɗaya zakayi mata ka fahimci cewar bata
cikin nutsuwarta ko kaɗan...

wani irin kallon tsana mom take binta dashi har Ummie n ta zauna a kujerar da aka
nuna mata, tunda ta shiga bata ɗaga kanta ba don batasan da idon da zata kalli Abie
ba
Kallon tsaf Muhammad kareem Ahmad yakebin Ummie dashi cikeda son tabbatar da abinda
yake tunani a kanta dannan yace "Hajiya Aisha shin zaki ya baiyana mana abinda ya
faru a wannan ranar da kika ciyarda ɗan mijinki guba a cikin abinci?

cikeda dakewar zuciya tace "Ae zan iya tunawa ranka ya daɗe, a wannan ranar da
kaina na dafa abincin dazan saukeshi dashi bayan na kammala dafawa na jera a kan
daining ina jiran isowarsa na buɗe kular Abincin danasan yafi so na zuba masa guba
a ciki tayanda zeci ya mut....... Wani irin Kuka ne ya taso mata dole yasa tayi
shiru da maganar ta shiga rusar kuka. Wani irin tuƙuƙin baƙin ciki ne ya tasowa
Abie a lokacin dayake kallonta cike da tsana yace "Muhammad don Allah Zan roƙeka
alfarma a karona farko ina roƙonka don girman Allah ka tura case ɗinnan gida
Nigeria ta yanda za'a hukunta wannan baiwar Allah butulu da tushe.

shiru Muhammad yayi bakajin sautin komai sena kukan Mom, cikin muryar kuka mom tace
don Allah ka taimaka mana Ranka ya daɗe plssssss. Mom taja plss ɗin kamar zata
shiɗe

Kamar bazece komai ba ya kalli Abie yace "naji duk batunku sedai bazamu amince ba
harse munga yanayin jikin yaron, bazeyu ku tafi ba harse ranar da yaron ya dawo
cikin haiyacinsa ta hakane kawai zamu iya tura ƙararku zuwa gida Nigeria Inyaso
sesuku shiga kotu........

Godiya mom ta dingayi masa sannan suka masa sallama itakuma hajiya Aisha aksake
maida ita magarƙama aka kulle.

Ko kaɗan bata dana sani aka abinda ta aikata gani take abinda tayi shine daidai,
dukda cewar a tsare take a hannun hukuma wllh seta koyawa Hajiya saratu hankali
tayanda zata sanyata cikin baƙin ciki fiyeda zato koda kuwa za'a yanke mata
hukuncin kisa ne gabaɗaya. Ta ƙare maganar tana murmushi wanda yafi kamada na
takaici

*_GHANDY HOSPITAL 🏥_*

Dr. Varun ne bisa kan muzaffar hannunsa ɗauke da wata ƙaramar na'ura wadda ya
saitata bisa kan cikinsa, gefansa

*Kuyi haquri don Allah da wannan ban samun time ne, da kuji ni shiru gwara na baku
update koda kaɗan ne. Thanks 4d lover sisters🥰*

comment
Nd
Share

sushmah💋
[3/3, 5:36 PM] Chubado Mohd: ❄️❄️❄️❄️❄️❄️
❄️❄️❄️❄️❄️❄️
🐄🐄🐄🐄
🐄🐄🐄🐄
*BAFULATANA*
✨RETURN✨
🐄🐄🐄🐄
🐄🐄🐄🐄
❄️❄️❄️❄️❄️❄️
❄️❄️❄️❄️❄️❄️

*_Page :26_*

*_DUK ABINDA ALLAH YA BUƊE BABU WANDA YA ISA YA RUFESHI, HAKA KUMA DUK ABINDA ALLAH
YA RUFE BABU WANDA YA ISA YA BUƊESHI. AL'AMARIN ALLAH HAKA YAKE _*

*_Ya ubangiji kayi min tsari da duk wanda ke neman ɗaga min hankali mace ko namiji
a duniyar yanar gizo🤲, ya ubangiji ka gina min katangar ƙarfe a tsakanina dasu
Allah idan ni ban sansu Allah kasansu ya ubangiji kai mana maganinsu don isar
manzon Allah SAW🤲_*

*_Masu cewa chubaɗo tace Karku fasa cewa nace kuyita faɗa daga nan har mahadi ya
baiyana, ku aiki ya kama tunda gabaɗayan ku babu me wuta bare aljanna da sannu kuma
zamu haɗe a madakata✊._*

*_WRITING BY: CHUBAƊO_*

Banyi Editing ba

___✍️Gefansa kuma wata matashiyar yarinya ce riƙe da faranti silver irin wanda
malaman lfy ke amfani dashi, abubuwa ne akan farantin dayawa waƴanda suka danganci
ɓangare irin na ciwon muzaffar ɗin.

Bayan ya gama scanning cikin nasa ne ya gano cewar a kwai inda gubar ta fara yi
masa illa ta ɓangaren liver ɗinsa, nan take ya bada umarnin a turashi zuwa ɗakin
tiyata don a tari matsalar dawuri idan bahaka ba tsab ze iya rasa rayuwarsa, a
gaggauce aka turashi zuwa ɗakin tiyatar cikin mintunan da bazasu gaza 30ba suka
kammala cikin ƙwarewa da kuma yarda dakansu a fagen aikin sannan suka maidashi zuwa
ɗaki na musamman.

A haka rayuwa taita tafi still babu wani canji a tareda muzaffar ɗin

Nigeria🇳🇬

Edriss ne sanye cikin ƙananan kaya black jeans with write T-shirt gashin kansa duk
ya baje harta bayan wuyansa hannunsa ɗauke da mukullin mota ya kalli mom wadda ke
gyara zaman mayafin dake jikinta yace "mom amma dai bada waƴan nan yaran zamu tafi
Hospital ɗin ba? Ya faɗa yana kallon su Hajar da zeeyadah.

Taɓe baki mom tayi tace "why are you asking me Bayan gasu nan duk da bakinsu?
Male baki yayi irin na ajeboters ɗinnan sannan ya fara ƙoƙarin fita daga falon da
sauri Zeeyadah tace "pls ya Edyan don Allah zan biku.

Juyowa yayi yana kallonta kimanin wasu mintoci sannan ya sakin mata murmushi yace
"ok amma da sharaɗi babu yawan surutu kinji ko? Da sauri tayi nodding kanta alamar
ta yarda da sharaɗinsa.

Mom na miƙewa Zeeyadah ma ta miƙe tana gyara rolling ɗin kanta sannan ta kalli
Hajar tace "Aunty ke zaman gida ya kama mukam kinga tafiyar mu. Wata uwar harara
ta watsa mata sannan tace "dama ai sedai ke ɗin tunda kece uwar neman gindin zama
da cusa kai. Hajar ta faɗa tana jan wani uban tsaki

Tun kafin ta ƙara wata magana mom tace "wllh Hajar zakici Uwarki dani a falon nan
tunda ke rashin kunyar taki kullum ƙara yawa takeyi a madadin ta ragu, to wllh nida
kaina zan sauke miki duk abinda yake kanki. Mom ta faɗi hakan yana zuba uban huji
gwalo zeeyadah tayi mata sannan taja hannun mom sukai gaba abinsu.

A harabar gidan suka samu Edyan yana ganinsu ya nufi wata zabgegiyar Renge Rover
ɗinsa baƙa wuluk da ita se faman ɗaukar idanu takeyi da hanzari guards ɗinsa suma
suka fara ƙoƙarin tada motocinsu dole hakan yasa Edyan ya fito ya kallesu yace "no
base kun bini ba zanje ni kaɗai Hospital zanje. Cikeda girmamawa ɗaya daga cikin
guards ɗin yace "amma ranka shi daɗe Me girma IG fa yayi mana kashedi akan barinka
kai kaɗai ka fit........."tunda ni jariri ne ko ? Edyan ya faɗi hakan with so
much angry.

A ladafce suka haɗa baki suna faɗin we are sorry sir. Tsaki yaja sannan ya buɗewa
mom back seat na motar sannan ta shiga ya rufe zeeyadah kuma ta kame a front seat,
harya shiga motar be ce da kowa ƙala ba a haka yaja motar suka fice daga gidan
gabaɗaya Zuwa Asbitin, cikin min tunan da bazasu gaza 15ba suka iso babban
madaidaicin private hospital ɗin wanda aka qawata da kayan qawa iri-iri tamkar ba
Asibiti ba. A notse ya faka motar cikeda ƙwarewa sannan ya fito ya zagayo ya
buɗewa mom side ɗinta ta fito tana murmushi sannan ya rufe motar.

Sakkowa zeeyadah tayi tabi bayansu suka ƙarasa cikin harabar Asibitin, Direct
office ɗin Dr. Mujaheed suka nufa, bayan sun shiga da sallama Edyan ya miƙa masa
hannu suka gaisa sannan suka gaisa da mom da zeeyadah, nan Edyan yake tambayarda
yame jiki?

Ɗan murmushi Dr. Mujaheed yayi sannan yace "jikinta da sauƙi sedai tun jiya data
farka take mana kuka kuma taƙi bari kowa yazo kusa da ita munyi2 taci abinci amma
taƙi sam. Cikeda damuwa Edyan yace "kana nufin har yanzu babu abinda tasa a
cikinta se kuka datakeyi?

Dr. Mujaheed yace "sure.

Da sauri Edyan ya miƙe ya bar office ɗin ya nufi ɗakin da aka kwantar da itan, Da
sallama ɗauke a bakinsa ya tura ƙofar tareda zura gaba ɗayan jikinsa cikin ɗakin
sedai sam be saki ƙofar ba. A nitse yakebin kowace kusurwa na ɗakin da kallo harya
sauke manyan fararan idanunsa akanta, gabaɗaya dukta takure guri guda tareda haɗe
kanta da gwiwarta bakajin sautin komai sena kukanta.

A nitse ya fara takowa cikin takunsa harya ƙaraso bakin gadon bata ɗago ba hakan ne
ya bashi damar ƙare mata kallo tun daga kan yatsun ƙafarta har zuwa kan manyan2
kitso biyun dake kanta ba wanda yaci uban datti gashida mugun tsayi na ban mamaki,
sedai dukda hakan bazaka kasa gane irin kyanda gashin nata yake dashi ba abinka da
Fulanin Usuli.

A hankali ya miƙa hannunsa ya dafa kafaɗunta a wani irin mugun furgice ta ɗago
idanunta duk sun caɓe da hawaye taja baya da sauri tan me ƙara ƙanƙame jikinta
still her eyes is on his handsome face. Cikin harshen Fulatanci ta fara magana
kamar haka " ka matsa kusa dani banson Rayuwa a cikink........ Wani irin kuka ne
ya taso mata dole yasa tayi shiru.

Jikinsa ne yay masifar sanyi dukda besan abinda take faɗi ba don haka ya sake miƙa
hannunsa ze taɓata yace "its OK dear but plz stop crying don Allah kodon sabida
condition ɗinda kike ciki na rashin fly plz Cutie girl. Ya ƙare maganar yana
kallon tsakiyar ƙwayar idanunta

Ƙura masa idanu ita tayi tana kallonta a ranta tana aiyana cewar "komai nasa irin
na hamma zafar har yanda yake magana yana saka wani yare na daban, sedai gashin
kansu da yanayi na ƙirar jikinsu ne sam ba ɗaya ba wannan sam be kai Hamma zafar
hasken fata ba seda shima ba laifi yana da kyau sosai na nunawa sa'a. Haka kawai
taji zuciyarta ta amince dashi kuma ta yarda dashi, batace masa komai ba tasa
hannunta ta janyo takalman robarta dake gefanta ta rungume a ƙirjinta tareda zubawa
flet ɗin abincin da aka ajiye mata tun ɗazu bataci ba idanu.

Murmushi yayi yace "zakici ?

Turo baki tayi batace masa komai ba, ɗakkowa yayi ya miƙa mata flet ɗin yana
murmushi jada baya tayi tana kallonsa alamar ma ita tsoro kwanon Abincin yake
bata, riƙewa yayi a hannunsa sannan ya kalleta yace " ki lura da kyau ki kalleni
babu abinda kwanon abincin zeyi miki ok. Still tana kallonsa sannan ya ɗebi
abincin da cokalin kaɗan yakai bakinsa yaci sannan ya miƙa mata yace "oya eat.

Maƙe masa kafaɗa tayi tana shirin fashe masa da kuka yace " hay look don't cry
please just eat. Taɓe baki tayi tana wani mirza ido. Ganin dayay bata da niyan
karɓa ne yasa ya matsa dabda ita ya fara bata abincin ta cokalin tanaci tana
zubarwa a haka haraya gaba bata ya ajiye flet ɗin yace "barin je na dawo ko?

Da wani irin mugun sauri ta diro daga gadon ta riqe hannunsa gam tana hawaye a haka
su mom da Dr. Suka shigo ɗakin. Bayansa ta koma da sauri tana ɓoyewa alamar
batason mutane sosai

Murmushi mom tayi tana kallonta cikeda so sannan ta maida kallonta ga Edyan tace
"Dr. Ya bada takaddan sallama se kuma drugs daya rubuta kuma suma mun siyo mata
yanzu gida zamu wuce kawai. Murmushi kwai yayi yace "ok mom muje. Ya faɗa yana riƙe
da hannunta

Har sunkai ƙofa ta fizege hannunta ta dawo ta ɗauki wannan jakar da Moddibo ya bata
sannan ta dawo ta riƙe hannunsa suka fita.

Wajen shiga mota ba ƙaramar ɗirama akayi da ita ba ihu ta dinga zuba musu seda
Edyan yay dagaske sannan ta yarda ta shiga suka tafi gida gabaɗaya, duk a tsorace
take kallonsu kawai take itako zeeyadah gabaɗaya tausayin yarinyar ya gama cika
mata zuciya.

India🇮🇳

A kwana a tashi babu wuya a gurin Allah a ɗan wannan tsukun lokacin abubuwa dayawa
sun faru masu daɗi da marasa dadi, a ɓangaren Muzaffar kuwa sosai yake samun sauƙi
dukda irin ɓarnar da poison ɗin yayi masa a ciki, ada sam baya iya zama amma yanzu
kam yana iya zama da kansa harma yayi tafiya koda bame tsaho bace. Sosai hkaan yawa
Su mom da Abie daɗi har hakan ya kasa ɓoyuwa akan fuskokinsu.

Bayan sati biyu da samun lfyar muzaffar Muhammad Karim Ahmad ya tura case ɗinsu
zuwa Nigeria tun kafin su dawo ƙasar aka fara bincike akan case ɗin kasancewar
Ummie ta amsa Laifinta na cewar ita ta bashi gubar da hannunta yasa al'amarin
yazowa masu yanke hukuncin da sauƙi, wahe gari da sassafe jirginsu ya ɗaga zuwa
Nigeria.

Sosai Ummie ta fita daga haiyacinta kamar ba ita ba, tun Doguwan rigar da aka
Kamata da ita sanda abin ya faru har yanzu itace a jikinta idanunta duk sun zurma
sunyi ciki tamkar bana Hajiya Aisha ba mata ƴar ƙwalisa da son kwalliya a haka aka
sake jefata cikin magarƙama aka rufe.

Mom sun koma gida lfy kullum.ƙara tattalin ɗanta takeyi kasancewar Zaynab sun koma
makaranta ne yasa komai yazo Musu da sauƘi, komai nasa mom ce keyi da kanta wasu
lokutan abin har yana bawa Abie mamaki, Baba Hajarah ma ba ƙaramin tashin hankali
ta shiga ba santa tayi arba da Muzaffar gabaɗaya ya rame yayi duhu kamar bashi ba,
kuka ta dingayi itama daga bisani kuma ta haƙura tacigaba dayi masa addu'o'in
Alkhairi da kuma na samun lfy.

Washe gari da safe mom ta kira Baba Hajara tazo ta sameta a falo tareda maryam me
aikin Hajiya Aisha a zaune, da girmamawa Baba Hajara ta gaida Momy sannan ta
sunkuyar da kanta

Mom ta kalleta tace "Hajara ga maryam nan zaku zauna tare kuci gaba da gudanar da
hidimomin gidannan don Allah seku haɗe kanku kuma ku zauna da juna lfy.

Murmushi Baba Hajara tayi tace "to Hajiya insha Allahu. Mom ta kalli maryam tace
"ki ɗauki kayanki ki bita zata nuna miki ma saukinki. Da to Maryma ta amsa sannan
ta miƙe tabi bayan Baba Hajara suka nufi ɓangarensu.

Tunda Abie ya dawo daga india be samu ya zauna ba sabida ciku2 shariyarsu da Ummie,
so yake ayi abin bisa sirri don bayaso kimarsa ta taɓu a idanun al'uma dakuma na
ƴan jarida kasancewarsa babban mutum kuma wanda ƙasa kejidashi. Be wani sha wahala
ba me shariya ya amince da batunsa na mayar da shari'ar tasu ta sirri because this
is the only thing dayake ganin ze iyayiwa ummie a rayuwarta don bayaso ta
wulaƙanta a idon duniya har yanzu yana ƙaunarta a cikin zuciyarsa ƙauna me tarin
yawa bata wasa ba.

Washe gari Ya kama litinin ne kuma a ranar shariyar zata fara, Mom ce ta fito cikin
shigarta na alfarmar a nitse ta gama sakkowa daga sters ɗin sannan ta samu Fadilah
a falo tana kallon news.

Da kulawa mom ta kalleta tace "dota idan kin tashi kije ki duba yayanki sannan kisa
Hajara ta dafa masa abu meɗan ruwa2 wanda zeji daɗin ci seki kai masa kinji ko?

Fadilah tayi musmushi tace "ok mom sekin dawo Abie ya shigo tun ɗazo da alama
keyake jira. Shafa kanta mom tayi tareda sumbatarta sannan ta fice a hanya sukaci
karo da Baba Hajara ta dawo daga rabawa masu gadi da masu yankan flowers abinci.

Cikeda girmamawa suka gaisa sannan tace "to semun dawo Hajara. Da murmushi a akan
fuskar baba hajara tace "hajiya yau kece da fitar sassafe?

Tsayawa mom tayi cak sannan ta juyo da murmushi tace "wllh fitar ta dole ce kotu
zamu kinsan mun shigar da ƙara akan Aisha.

Take gaban Baba Hajara ya buga da ƙarfi tanaji tana gani a haka mom tayi gaba ta
barta zuciyarta na dukan tara2.

Thanks 4d love sisters naga addu'o'inku Allah yabar zumunci👏

Comment
Nd
Share

❄️
Sushmah[3/3, 5:36 PM] Chubado Mohd: ❄️❄️❄️❄️❄️
❄️❄️❄️❄️❄️❄️
🐄🐄🐄🐄
🐄🐄🐄🐄
*BAFULATANA*
✨RETURN✨
🐄🐄🐄🐄
🐄🐄🐄🐄
❄️❄️❄️❄️❄️❄️
❄️❄️❄️❄️❄️❄️

Page :22

*_WRITING BY: CHUBAƊO_*

Banyi Editing ba

___✍️murmushi yayi sannan yace "ngde Ummie kusan a tare suka shiga cikin gidan
wanda aka ƙawata da kayan ƙwa na zamani kuma masu matiƙar tsada, miƙewa yayi Direct
zuwa inda ya saba sauka idan yazo ƙasar harya kai bakin ƙofar part ɗin Ze murɗa
handile ɗin ƙofar Ummie tace " idan kayi wanka ka huta sekazo daining kaci Abinci.

Da to ya Amsa mata yana me ƙara faɗaɗa murmushin dake kan Fuskarsa sannan ya kunna
kai zuwa cikin haɗaɗɗen falon, bedroom ya shige tareda rage kayan dake jikinsa zuwa
singlet with boxer wanda hakan ya baiyana santala-santalan legs ɗinsa, a hankali
yake takawa harya isa cikin ƙayataccen toilet ɗin wanda aka wadashi abubuwan ƙyale-
ƙyale iri-iri, tsayawa yayi cak yana kallon kowace kusurwa dake toilet ɗin bisa ga
mamakinsa komai an sauya masashi daga waƴanda ya sani a baya zusa Sababbi, a nitse
yake takawa cikin takunsa harya isa gaban wani baban Abu wanda yafi kamada bahon
wanka na zamani, ruwa ya tara a cikin ƙaton bahon me ɗan zafi tareda zuba shower
gel ɗin daya saba amfani dashi mallakin Companyn Olay me bala'in ƙamshi take kumfa
ta cika bahon ,

Murmushi yayi me kyau tareda shiga cikin Ruwan ya zauna tareda lumshe manyan
idanunsa zafin ruwan na ratsa duk wata gaba ta jikinsa, sosai yakejin daɗin yanda
zafin ruwan ke Ratsashi ya jima a ciki daga baya ya buɗe ruwan ya wuce sannan ya
tare wani yayi wankan ya fito. Bayan ya fito daga wankan be wani tsaya shafe-shafe
kamar yanda ya sababa ya shirya cikin kayan sport marasa nauyi tareda kabbara
sallar dake kansa, ya jima yana sallar sannan ya idar taredayin Azkar ɗinsa kamar
yanda ya saba a kowace Rana.

Yana miƙewa kiran Abie ya shigo wayanshi daga yanayin ringing ɗin ya Fahimci cewar
Abie ne, zama yayi daga bakin gadon dake ɗakin tareda kara wayar a kunnensa da
sallama yace "Abie ya gida? Ɓangaren Abie yayi murmushi yace "lfy lau Son ya
gajiyan Hanya? Ɗan shagwaɓe fuska yayi sannan yace "uhm wllh Abie a kwaita kagafa
se yanzu na yi wanka tun shigowana ƙasar. Dariya Abie yayi me Sauti sannan yace "ka
kula da kanka sosai I'm sure of you will do your job with full success. Muzaffar
yayi murmushi yace " sure Abie insha Allah.

Mom dake zaune gefan Abie haka kawai seta samu kanta da rashin samun kwanciyar
Hankali tunda muzaffar yayi tafiya, haka nan seta samu kanta da rashin Amintuwa da
tafiya jiki babu ƙwari ta karɓi wayar daga hannun Abie cikin tattausan lafazi tace
"Boy ya dai ina fatan kana lfy? Ɗan shafa gefan fuskarsa yayi kana yace "I'm fine
mom and why your voice was so cool? "I don't know why darling I'm just feel like
something is definitely going to happen to me. Pls take good care of yourself kaji
yaron kirki? Sannan ka kula da makircin Hajiya Aisha ok.

Shiru yayi bece komai ba a haka suka katse wayar Abie na binta da kallon mamaki
yace "why are you behave like that Hajiya Saratu? Meyasa ke bakya ƙaunar kiga an
zauna lfy ne?

Yau kimanin shekaru nawa ana wannan abin ai yaci ace yanzu kun haƙura kuma kun
zubar da komai kodan kwanciyar Hankalina. Cikeda karyewar zuciya mom tace "Abie
bazaka gane komai ba shiyasa kake faɗar hakan, taya matar dta nunawa ɗana tsana tun
yama ɗan ƙarami kayi tsammanin cewar yanzu bazata iya cutarmin dashi ba?

Nifa uwa ce Abie taya bazanyi yaƙi da duk wani me neman cutar min da rayuwar ƴaƴana
ba? Kada ka manta da wacece matarka Aisha kasancewar bata taɓa haihuwaba tunda ta
hafi ɗanta bezo da raiba take ƙoƙarin ganin bayan nawa ɗan har zuwa lokacin daka
ɗauketa tabar ƙasar nan. Wllh nasan she can do anything don ganin ta lalata min
rayuwar Ahalina amma nasan onday one time you will understand what I mean insha
Allah.

Shidai Abie girgiza kai kawai yayi tareda miƙewa ya faɗa toilet tana binsa da
kallo,

*******
Ɓangaren Muzaffar kuwa Ajiye wayar yayi ya fita sabida wani irin juyawa da cikinsa
keyi sabida yunwa yana fita a falo ya samu Ummie tareda wata ƴar aikinta Maryam
kallo ɗaya zakayi mata kasan ƴar Nigeria ce, a ƙalla shekarun Maryam zasu kai 40
tun lokacin da Ummie tabar nigeria Suka taho tare.

da fara'a Ummie ta tarbeshi suka nufi daining ita kuma Maryam ta durƙusa tana
gaisheshi with so much respect, murmushi kawai ya sakin mata sannan ya wuceta ba
tareda ya amsa ba Hajiya Aisha da kanta tayi sarving nashi Abincin wanda keta zuba
uban ƙamshi sannan ta miƙa masa itama ta xauna ta fara zuba nata Abincin wanda keda
banbanci danasa kasancewar tanada ciwon suger

Kusan a tare suka fara cin Abincin har wani lumshe ido Muzaffar keyi sabida Daɗin
Abincin hakan ne yasa yaci sosai har ummie tayi mamakin hakan, dabida a iya sanin
datayi masa bayacin abinci sosai.

bayan sun gama cin Abincin ne Maryam ta miƙe ta kwashe kayan Abincin takaisu kicin
tareda gyara gurin, zama sukai a falon suna ɗan taɓa hira duk akan abinda ya
kawoshi Indian wani tayi murmushi wani kuma ta kalleshi, wayarta ce tayi ƙara hakan
yasa ta maida hankalinta ga wayar tareda karawa a kunnenta Tace "bayi zamuyi magana
yau insha Allah komai ze kammala ba tareda anci lokaci sosai ba. Ta faɗi hakan tana
satar kallon muzaffar wanda ya maida duk hankalinsa akan System ɗinta dake gabansa,

a nitse yake gabatar da komai cikin nutsu ba zato ba tsammani yaji cikinsa yay wani
irin juyawa tareda muɗa masa, dafe cikin yayi da duka hannayensa tareda zube
gwiwowinsa a ƙasa ya saki wata irin ƙara wadda ta firgita Hajiya Aisha da me
aikinta Maryam dake kicin tana wanke kwanikan da akaci abinci dasu, Sakin wayar
Hajiya Aisha tayi tareda nufo kansa gadan-gadan tana raba idanu hanyar kicin ta
kalla ganin babu wanda ya taho yasa ta ɗagoshi tana kallon fuskarsa kimanin 5second
jin tafiyar Mutum daga hanyar kicin ɗin yasa itama ta saki ihun neman taimako. A
gigice maryam ta ƙaraso gurin idanunta duk a waje sabida tashin hankalin tareda
kallon Ummie lokaci guda kuma ta sake maida kallonta ga muzaffar wanda ke fitarda
wata irin farar kumfa daga bakinsa hakanne ya bata tabbacin cewar Guba yaci.

cikeda tashin Hankali maryam ta dora hannu akanta tana faɗin


"innanillahiw'inna'ilaihirraji'un!!!!!!

a gigice maryam ta nufi wayar telho ɗin dake ajiye bisa wani ƙaramin table ta shiga
wayar Babban Asibitin kuɗin dake kusa dasu ko'a samu a ceto Rayuwarsa cikin Sauƙi.

Ummie kuwa ta kasa motsin kirki balle har ta tsinana wanu abin arziƙin a gareshi,
take wani irin gumi ya fara keto mata tareda nadama mara misaltuwa babban abinda
ke ɗaga mata hankali a wannan lokacin shine da wani ido zata kali Abie bisa wannan
abinda data kasance itace silar Faruwarsa?

tabbas duk irin sonda yake mata a wannan lokacin ta tabbata bazata tsira ba daga
hannunsa shida matarsa Saratu ba tunda har tayi poisoning ɗin dansu namiji
tilo........

*GYMBU TARABA STATE*

Da ƙyar Inna Laure kejan numfashi sabida tsabar azabar datakeji ko hannunta ta kasa
ɗagawa balle tasan ran cewar zata iya miƙewa, seda suka gama zuba Rashin imaninsu
sannan suka tattara komai suka tafi dashi tareda ketawa Yara ƙanana haddinsu, a
wannan rana rayuka dayawa sun sosu da baƙin ciki mara misaltuwa haka kuma zuciyoyi
sun baƙanta, a wannan tsukun ne Mahaifin Ruƙatu Babbar Aminiya ga Rabe ya rasa
Rayuwarsa al'amarin daya ƙara ɗaga mata hankali kenan.

sosai malam iro ya zubar da jini sosai har hakan yasa suka fitar da rai da cewar ze
tashi, moddibo kuwa gabaɗaya ya kasa cewa komai duk a sanadin bala'in daya sameshi,
baya iya furta komai se ido kawai dayakebin kowa dashi, miƙewa yayi ya shiga
ɗakinsa da sauri ya kauda kansa sabida ganin irin Rashin imanin da suka aikatawa
Laure komai bushewar zuciyarka dolene ka tausaya mata muddin kanada imani, da sauri
ya isa gareta sabida ganin yanda jini ke zuba daga ƙasanta duk yamda yaso ya
taimaka mata kasawa yayi dole ya zube a gurin ya saki kuka me sauti da ban tausayi,
itama kanta Lauren kuka takeyi tareda tausayawa kanta a irin Rayuwar dazata
fuskanta nan gaba

seda yayi me isarsa sannan ya miƙe ya fita daga ɗakin ya haɗo ƙirare ya kunna wuta
tareda ɗora ƙatuwar tukunya akai, cikin mintunan da bazasu gaza 20 ba ruwan ya
tafasa wata babbar fanteka ya ɗakki ya zuba ruwan a ciki kimanin rabin fantekar
sannan ya ɗauka ya shiga da ita ɗakin ya zuba wani garin magani a ciki take kallar
ruwan ta sauya zuwa launin kore, seda yaɗan sha iska sannan ya kinkimeta ya zaunar
da ita cikin ruwan, wata uwar ƙara ta saki har seda ta bashi tausayi

cikin ikon Allah jinin ya tsaya har taji ɗan dama-dama a jikinta, seda ya gana bata
duk wani taimaki dayake ganin ze iya bata sannan ya fita zuwa waje ya fara duba
sauran jama'a ba tareda ya damu da jinin dake zuba a kansa ba. *_(Allah sarki
modibo haqiqa kyakkyawar zuciyar halitta ce ba kowani mutum ne ke tuna al'uma ba a
lokacin da musiba ta sameshi ba, kowa kansa yake fara ginawa sannan daga baya ya
tuna da al'uma amma shi kuma moddibo yace "al'uma itace farko kafin kansa. Ya Allah
ka cire mana son kai da ƙyashi daga zukatan mu🤲)_*

A hakan seda ya tallafawa kowa sannan ya agazawa kansa daga baya. Baze iya furta
komai ba a irin wannan halin baƙin cikin dayake ciki ba, amma yana roƙon Allah ya
saka musu bisa zalincin da aka aikata musu

******

The fulani girl Tafiya take tana kallon titin kmaar wata me koyan tafiya ba zato ba
tsammani wasu farar mota sol ƙirar formatic C350 Da suka taho cikin jerin gwanonsu
kimanin guda 6 ta gaban tai sama da Ita, take ta zube a saman kwantar jini na
ɓulɓula ta hancinta da kunnuwanta!!!!
A gigice Drivern dake motar ya fito take motocin dake binsa a baya suka tsaya
sabida ganin tsayawarsa, kwance yake cikin motar dake tsakiya yana latsar waya
yaji motocin sun tsaya, dago madaidaitan idanunsa yayi yana kallon drivern dake jan
motar dayake cikin yace "what's wrong?

Cikeda girmamawa matashin Drivern yace "I don't know sir but let me check. Maida
hankalinsa kan wayar yayi batareda ya damu da abinda ke faruwan ba yaji an
ƙwanƙwasa glass ɗin motar dayake ciki, cikeda damuwa Wanda ya ƙwanƙwasa ɗin yace
"im sorry sir hatsari muka samu a sanadin bige wata yarinya.

Da sauri guy ɗin ya ajiye wayar ya fito cikeda tashin hankali, sanye yake ciki wata
dakakkiyar suit's maroon colour dogo ne sosai ma'abocin cikar zati da kuma
kwarjini, sam be kasance cikin jerin maza masu hasken fata ba amma yanada gogewar
fata sosai irinta ƴaƴan masu hannu da shuni.

Gabansa ne ya faɗi a lokacin dayayi arba da jinin dake futa ta hancinta da kuma
kunnenta, a hanzarce ya tsuguna yace "pls be fast let's take her to the hospital.

Babu ɓata lokaci suka sanyata a cikin ɗaya daga cikin motociɓ batareda sunyi
la'ajari da kar jinin ya ɓata musu mota ba suka kwasa da wani mahaukacin gudu suka
nufi wani ƙaramin hospital dake dabda cikin wani ƙaramin ƙauye dake maƙotaka da
dajin. Babban abinda ze bawa me karatu mamaki shine still her hand is on the wannan
jakar da Modibo ya Rataya mata.

Tofa ana wata ga wata 🤔

thanks 4d love guys

comment
nd
share

sushmah💋
[3/3, 5:36 PM] Chubado Mohd: ❄️❄️❄️❄️❄️❄️
❄️❄️❄️❄️❄️❄️
🐄🐄🐄🐄
🐄🐄🐄🐄
*BAFULATANA*
✨RETURN✨
🐄🐄🐄🐄
🐄🐄🐄🐄
❄️❄️❄️❄️❄️❄️
❄️❄️❄️❄️❄️❄️

Page :23

*_WRITING BY: CHUBAƊO_*


____✍️Cikin mintunan da bazasu gaza goma ba likitan dake on duty ya shiga bata
taimakon gaggawa don gudun kar jinin dake fita ta kunnenta ya samu nasarar taɓa
ƙwaƙwalwar ta, dukda cewa Asibitin basuda isassun kayan aiki sunyi bakin ƙoƙarinsu
akanta kuma Cikin ikon Allah suka samu nasarar tsaida zubar jinin cikin sauƙi.

Gabaɗaya haɓkalin matshin a tashe yake dukda cewar mutum neshi me izza Amma sam
bashida kwanciyar hankali yayinda yaga na ƙasa dashi a cikin hali na buƙatar
taimako, likitam na fitowa Direct gurin matashin ya nufa tareda miƙa masa hannu
yace "congrats munyi nasara wajen tsaida zubar jinin sedai tana buƙatar ƙarin jini
sabida tarasa jini dayawa amma yanzu hkaa mun saka mata drip da ace so samu ne ku
miƙata ga babban Asbitin don gudun karta samu matsala a ƙwaƙwalwar ta, Zaro ido
matashin yayi tareda dafe kansa cikeda damuwa yace "oh my God!!!!! Kallonsa ya
mayar ga guards ɗinsa sannan yace " nanda zuwa wani lokaci zamu isa Abuja daga nan?

Kallonsa sukai da kulawa sannan ɗyaa daga cikinsu yace" ranka ya daɗe zamu iya
ɗaukar lokaci me ɗan tsayi kafin mu isa sabida doguwar tafiyace sosai amma zamuyi
iya bakin ƙoƙarinmu don ganin mun isa akan lokaci da yardan Allah. Ajiyar zuciya
ya sauke meɗan nauyi sannan ya biya kuɗin Asbitin tareda bada umarnin a fito da ita
asa a mota zasu wuce, ba musu suka shiga cikin Asbitin suka fito da ita tareda
sanyata a bayan ɗaya daga cikin motar suka kwantar tareda gyara mata zaman drip ɗin
dake saƙale a hannunta sannan sukaja motoci @360

Ba ƙaramin gudu suka dinga zubawa ba cikin ikon Allah kuwa suka shigo garin Abuja
akan lokaci, wani hamshaƙin Asibitin kuɗi suka nufa da ita wanda ke cikin Asokoro
inda Family Dr. Ɗinsu ke aiki me Suna Mujaheed Abdullahi, cikin ƙanƙanin lokaci
suka shiga bata taimakon gaggawa abinka da masu citta a hannu sun juma suna
gudanar da aikinsu a kanta sannan Dr. Mujaheed ɗin ya fito daga ɗakin wata
matashiyar nurs na biye dashi a baya.

Direct inda matashin ke zaune tareda Gurds ɗinsa Dr. Mujaheed ya nufa sannan ya
kalleshi yace "muje office ba musu ya miƙe yabi bayansa seda duka ɗanyi tafi kaɗan
sannan suka isa office ɗin me shegen kyau sannan suka zauna, cikeda damuwa
matashin yace "ya jikin nata Dr.? Murmushi Dr. Mujaheed yayi yace "ka kwantar da
hankalinka Edriss insha Allah komai zeyi daidai, ka godewa Allah ma kun kawota
akan lokaci. Murmushin jin daɗi Edriss Adam yayi tareda faɗin "Alhamdulillah Dr.
Wllh har hankalina ya kwanta.

Magungunan da suke buƙata ya rubuta masa tareda cewa "a halin yanzu tana buƙatar
jini domin kuwa ta rasa jini dayawa, mun binkita mun gani launin jininta me wuyar
samu ne kuma ya kamata a ƙara mata shi da gaggawa idan ba haka ba gaskiya something
can happen to her. Da sauri Edriss yace " no Dr. You can take my own because nau'in
jini na ze iya yiwa kowa

Ƙura masa manyan idanunsa Dr. Mujaheed yayi a zuciyarsa yana mamakin yanda Edriss
ya damu da wannan baiwar Allah, ajiyar zuciya ya sauke sannan yace "who is she to
you Edriss?

Murmushin rainin hankali Edriss yayi yace "ba wannan ba tukun muje ka ɗau jini na.
Ya faɗi hakan yana kallon tsakiyar ƙwayar idon Mujaheed ɗin

Basarwa yayi ya miƙe yace "bani zan ɗau jininka ba Edriss yanzu dai zan turaka inda
za'a ɗauka ɗin, cikin mintunan da bazasu gaza 10 ba akayi komai aka gama se'a
lokacin hankalin Edriss ya kwanta sannan ya wuce gida donya samu ya huta.

INDIA🇮🇳

dakewa Ummie tayi tana binsa da kallo tamkar wadda aka dasata a gurin, gaba ɗaya ji
take komai ya tsaya mata chak har motar Asibitin ta ƙaraso ƙofar gidan still tana
tsaye kan ƙafafunta, Maryam ce ta fita da hanzari tayo musu jagora zuwa cikin gidan
inda muzaffar ɗin ke kwance samɓal babu alamar numfashi a taredashi, kin kimarsa
sukayi suka ɗorashi bisa wani siriri gado sannan suka fito dashi Zuwa cikin motar,
basu jira fitowar wani daga cikin gidan ba sukaja motar sabida ganin irin condition
ɗin mara lfyn se bayan sun fita Hajiya Aisha ta zube bisa doguwar kujerar dake
falon tana maida numfashi

wayar muzaffar dake kusa da System ɗin Ummie ce ta fara ƙara kasa ɗagawa ummie tayi
hakanne yasa maryam ta isa ga wayar jikinta na wani irin rawa ta Amsa ba tareda ta
duba sunan me kiran ba, cikin yanayi na rashin kwanciyar hankali mom tace "boy are
you Ok?

Wani irin fashewa Maryam tayi da kuka nan ta shiga zaiyanawa Mom halinda muzaffar
ɗin ke ciki. Wani irin Zabura mom tayi ta miƙe zaune daga kwancen da take cikin
yanayi na fitar haiyaci tace "ɗan nawa ne yafi guba ??????

Abie wanda ke kwance ne ya miƙe idansa nakan Mom wadda jikinta ke wani irin rawa
sabida tsabar tashin hankali, fashewa tayi da kuka tana danne ƙirjinta dake mata
wani irin suya ta kalli Abie bakinta na rawa tace "kagani ko? Senayi magana sekace
kishi ne ke ƙoƙarin hanani zaman Lfy da Aisha to gashi nan yau ta zubawa ɗana guba
a abinci kuma ya........... Girgizata yayi da wani irin Sauri sabida ganin idanunta
na ƙoƙarin rufewa take mom ta dawo daidai cikin haiyacinta tareda faɗawa jikin Abie
ta saki wani irin kuka me taɓa zuciyar duk wata uwa datasan ma'anar haihuwa. A
daran ranar Abie yayi hayar privet jet zuwa ƙasar India aiko kiran sallar farko
suka himmata sukabar ƙasar.

India 🇮🇳

Hajiya Aisha da ƙyar ta iya miƙewa ta koma ɗakinta tareda zubewa a bakin gadonta
zuciyarta duk a cushe, gabadaya komai ya tsaya mata tayanda takejin cewar dama
hakan bata faru ba do take tayi kuka amma kuma ta kasa yin hakan, dama idan wani
bala'in ya sameka hawayen ma ɗaukewa yake gabaɗaya a haka har gari ya fara haske
still tana zaune batareda ta rintsa ba.

cikin ikon Allah jirginsu Abie ya sauka lfy cikin mintuna kaɗan motocin company
sukazo ɗaukarsu Kasan cewar basu san Asibitin da aka kwantar da Muzaffar ɗin ba
dole yasa suka ɗauki hanyar gidan Hajiya Aisha, gabaɗaya mom ta birkice tamkar wata
zararriya idanunta duk sunbi sun koɗe sabida kukan data gurza, a haka motocin suka
tsaya a bakin ƙofar gidan cikin jerin gwano.

kokaɗan basu jira an buɗe musu ƙofar motar ba kamar yanda suka saba mom ta ɓalle
murfin motar ta diro tana huci, da wani irin sauri ta shiga gidan tana kwaɗawa
Ummie kira a birkice, sautin muryarta ne yasa Hajiya Aisha tasha jinin jikinta kuma
ta fito daga ɗaki jikinta a saluɓe tamkar kazar da ƙwai ya fashe ma

tana fitowa idonsu ya sarƙe cikin na juna a karon farko tun bayan shekara 35, wani
irin wawan Mari mom ta ɗauke Ummie dashi har seda taga taurari tun kafin ta
watsetsake ta ƙara ɗauketa da wani marin, cikin kiɗima Ummie tace "ni kika mara
Saratu?

cikin fusata Mom tace "na mareki Kiyi duk abinda zakiyi, Se yau na sake tabbatar da
cewar ki cikakkiyar shaiɗaniya ce Aisha kuma wllh ki kwana da sanin cewar sena
hukuntaki a bisa laifinki na bawa ɗana guba wllh koda kuwa abinda na mallaka ze
ƙare akan shariya dake!!!!

Abie dake tsaye yana kallonsu ji yayi duk Hajiya Aisha ta sure masa a rai a sanadin
abinda ta aikatawa gudan jininsa namiji tilo tabbas baze ƙyaleta ba a wannan karon
dole ne shari'a tayi aiki akanta, ya juya yana kallon jami'an tsaron dake bayansa
yace "ku tafi da ita!!!

Wani irin zazzafan hawaye ne ya zubo mata daga idanunta ba tareda tayi magana ba
jami'an suka tusata Station abisa yunqurinta na kisan kai..............

Har suka fita da ita bata dena kallon Abie ba lokaci guda kuma ta fashe da wani
irin kuka wanda ita kaɗai tasan ma'anar abinta.

Thanks 4d love fans❤️

comment
nd
share

Sushmah💋
[3/3, 5:36 PM] Chubado Mohd: ❄️❄️❄️❄️❄️❄️
❄️❄️❄️❄️❄️❄️
🐄🐄🐄🐄
🐄🐄🐄🐄
*BAFULATANA*
✨RETURN✨
🐄🐄🐄🐄
🐄🐄🐄🐄
❄️❄️❄️❄️❄️❄️
❄️❄️❄️❄️❄️❄️

*_Page :24_*

*_WRITING BY: CHUBAƊO_*

Banyi Editing ba

_____✍️Har suka fita kuka takeyi sosai jikin Abie ya sanyi dajin sautin kukanta
seda dukda hakan bayajin cewar ze iya ƙyaleta bisa yunƙurinta na kashe masa ɗa.

Tsaki Mom taja tana shirin magana sega maryam ta fito, ƙura mata iɗanu mom tayi a
ranta tana tunanin inda tasan wannan fuskar Katse mata tunani maryam tayi ta hanyar
cewa "Sannunku da zuwa Ranki ya daɗe nice wadda mukai magana dake ta waya ta faɗi
hakan tana matse ƙwallar data zubo mata da gefan zanin Atamfar dake jikinta. Ajiyar
zuciya mom itama hawaye na zubo mata tace "wani Asbiti aka kaimin ɗana ?

"Ghandy Special Hospital ne dake Ƙarshen Layin nan naryam ta faɗin hakan. Cikeda
Masifa mom tace "taya za'ai kukaishi ƙaramin Asibiti a madadin kukaishi na Compay?
Wll......" kinga Saratu pls ki nutsu ki dawo cikin haiyacin ki insha Allah komai
zeyi daidai, Nasan Asbitin farin sani kuma sunada kayan aiki sosai karki manta nan
ba Nigeria bace suna bawa Asbitocinsu dukkan abinda ya dace wanda za'a kula da
marasa lfy dasu cikin ƙwarewa.

Kuka ta fashe masa dashi har suka fita daga gidan zuwa Asibiti bata dena kukan ba,
a nitse Driver ɗin dake tuƙasu ya faka motar a harabar Asibitin inda aka tanada
sabida hakan, Dukda cewar Asbitin ƙarami ne amma yana da kyau gamida tsari fiyeda
zaton me karatu kusan gabaɗaya hankalin mom baya jikinta burinta kawai taga
halinda ɗanta yake ciki.

A haka suka isa reception na Asbitin A nitse Abie ga ƙarasa gurin da wasu nurses ke
zaune da alama sune cashier's na Asbitin, tambayarsu yayi inda aka kwantar da mara
lfyan cikin harshen turanci matashiyar yarinyar tace "faɗi sunan mara lfyn sena
duba maka. Cikin mintuna kaɗan ya gaya mata sunan take ta binciko musu ɗakin da
mara lfyn yake suka nufin ɗakin

A bakin ƙofar ɗakin suka tsaya sabida hanasu shiga da akayi seta ƙofar glass ɗin
dake jikin ɗakin suke hangensa, kwance yake kan gadon Asbitin an saka masa uniform
me launin kalar brown, fuskarsa ɗauke taƙe da oxygen inda bakinsa kuma akai warring
wani dogon five wanda ya taho tundaga cikinsa sabida poison ɗin dayaci, babu abinda
ke motsi a jikinsa se iskar numfashin dake fita ta cikin na'urar oxygen ɗin da aka
saka masa. Se'a lokacin idanun Abie suka sauka akan Rubutun da akai bisa jikin
ƙofar glass ɗin dake jikin ɗakin kamar haka (ICU) intensive care unit. Ajiyar
zuciya ya sauke me ƙarfin gaske a ransa yace "lallai ɗansa yana cikin tsaka me wuya
tunda har aka kawoshi cikin wannan ɗakin to abin bana wasa bane. Wani iri yakeji a
zuciyarsa gameda wannan gagarumin cin Amanar da Hajiya Aisha tayi masa, meyasa zata
aikatawa ɗan daya haifa irin wannan zalincin?

Kuka sosai mom take hakanne yasa Abie ya jawota jikinsa yana bubbuga bayanta, wata
irin tsanar Ummie ce take ƙara ratsa duk wani lungu da saƙo na zuciyarta tareda
ƙudurtawa kanta cewar wllh koda abinda ta mallaka ze ƙare setayi shariya da Hajiya
Aisha tayanda nan gaba koda ɗan dabba bazata sake yunƙurin kashewa ba ballan tana
ɗan mutum.

*******

ƁANGAREN HAJIYA AISHA kuwa station suka hurgata suka kulle gabaɗaya komai ya tsaya
mata cak ta rasa abinda ke mata daɗi a cikin wannan duniyar, bata taɓa zaton haka
daga gurin Abie ba tayi zaton cewar ɗabi'arta data ɗaɗe tana nuwa masa bazata
barshi ya amince da wannan al'amarin daya faru da ita cikin sauƙi ba amma kuma se
gashi shida kansa yasa ƴan sandan wata ƙasa suka kamata har cikin gidanta suka fito
da ita suka kawota wannan gurin mara tsabta. Tabbas tayi data sani a rayuwarta na
sanin Abie da zuriyarsa tun farko, da ace bata sanshi ba da duk hakan bata faruwa.

wani irin kukan baƙin ciki ne ya taso mata tareda data sanin Abinda ta aikata a
Rayuwar ta, babban tashin hankalinta a yanzu shine taya zata iya sanar da iyayenta
da ƴan uwanta halin datake ciki??????

A haka Rayuwa ta dinga tafiyar mata cikin yanayi na rashin jin daɗin Rayuwa gamida
walwala.

NIGERIA 🇳🇬

Edriss ne zaune tareda mom ɗinsa cikin danƙareren falonsu na alfarma wanda ko gidan
shigaban ƙasa se haka, da damuwa kwance akan Handsome face ɗinsa yace "mom nifa
hankalina sam ba'a kwance yake ba wllh inaji a jikina cewar dama banje Taraban nan
ba sam wllh. Ya faɗa kamar zeyi kuka

Da kulawa matar daya kira da mom ta ɗago fararen idanunta ta kalleshi tace "why
are you saying that sweetie? "mom wata yarinya muka bige a hanyar dawowan mu daga
Taraba. Edriss ya faɗi hakan yana kallon tsakiyar idanun mahaifiyar tasa. Be damu
da irin kallon datake binsa dashi ba yaci gaba da cewa" haka kawai naji a raina ina
tausayin yarinyar mom becouse ƙarama ce sosai kuma wllh mom she's pretty.

Sosai mom Edriss ta kaɗu dajin baya nan ɗan nata da ƙyar ta iya cewa " yanzu Edriss
a wannan uban dajin ta ina gida ze kasance balle har a samu yarinya har ku bige da
mota?

a dake ya kalleta yace "no mom ba yarinya bace kamar kowa she's Fulani girl......

Cikeda kaduwa Mom Edriss ta kalleshi tsoro ƙarara akan fuskarta tace "Fulani girl?
Ta faɗa cikin karaji.........

comment
Nd
Share

Sushmah💋
[3/3, 5:36 PM] Chubado Mohd: ❄️❄️❄️❄️❄️❄️
❄️❄️❄️❄️❄️❄️
🐄🐄🐄🐄
🐄🐄🐄🐄
*BAFULATANA*
✨RETURN✨
🐄🐄🐄🐄
🐄🐄🐄🐄
❄️❄️❄️❄️❄️❄️
❄️❄️❄️❄️❄️❄️

Page :25

*_WRITING BY: CHUBAƊO_*

*_All Characters, place, organizations and incident of this Interesting Novel are
fictitious😁, so pls my dearest sisters abinda yake me kyau a ciki to dashi zamuyi
koyi bada akasin hakan ba, Allah ya bamu ikon aiki da darasin dake ciki don isar
mazon Allah✊_*

___✍️ Murmushi yayi har seda fararen haƙoransa suka baiyana sannan yace "mom why
are you looking so surprised?

Ajiyar zuciya mom Edriss ta saki sannan tace "no like that sweetie I'm just feel
like there's definitely something behind the Fulani's girl ɗin ne thats why I look
so shocked. Dariya Edriss yayi yace "pls mom ki manta da wannan maganar babu komai
a tareda ita se alkhairi insha Allah wllh mom tausayin yarinyar nakeji because
she's to young like Sis Zeeyadah. Ya faɗa kamar ze sakin mata kuka

Shiru Mom Edriss tayi tareda maida hankalinta ga makekiyar Tvn bangon dake manne a
cikin falon, miƙewa Edriss yayi tareda faɗin pls mom ki shirya zuwa 4pm insha Allah
semuje Hospital ɗin ki ganta. Ya faɗa yana kallon ƙofar falon sabida motsin dayaji
a gurin

Hajar ce ta shigo cikin Shigar doguwar rigar material Baƙi wuluk wadda tai bala'in
bin jikinta, sosai kayan sukai bala'in karɓar jikinta kasancewarta farar fata
sedai a ɓangare na Addini sam shigar datayi bata dace da koyarwan Addinin mususulci
ba, taɓe baki Edriss yayi yana kallonta yace "hey meye haka kekuma kamar wata ƴar
babyn Roba?

Hararanshi tayi tareda zama a kusa da mom kamar zara shige jikinta tace "uhm ai
dama kai ya Ediyan ɗinan komai sekayi magana baka gani kayi shiru. Ta faɗa tana
ƙunƙuni a ranta kuma tace "baƙauye kawai. Wani shegen kallo ya watsa mata lokaci
guda kuma ya saki muskilin murmushi yace "look at you don Allah tayama za'ai Zafsy
ya soki (muzaffar)? Wllh mom yarinyar nan babu namijin daze sota a haka jibeta fa
sekace ɗiyar mutannan gabashin Ameerica. "gaya mata dai ya Edyan kullum gani take
kamar tafi kowa wayewa sabida Dady ya kaita ƙasar England tayi karatu. Zeyadah
dake sakkowa daga saman sters ta faɗi hakan tana dariya, Zeeyadah ƙanwa ce ga
Edriss uwa ɗaya Uba ɗaya kamar yanda hajar ma ta kasance ƙanwa a gareshi, Edriss
shine babba sannan Hajar se kuma Zeeyadah wadda ta kasance Auta, mahaifinsu Alhaji
Adamu babban ɗan sanda ne wanda a yanzu yake taka matsayin IG a nan ƙasarmu ta
Nigeria, a kwai shaƙuwa sosai a Tsakanin Edriss da Sisters ɗinsa Hajar da kuma
zeeyadah sedai shaƙuwar dake tsakanin Zeeyadah da Edriss ya shallake duk yanda me
karatu ke zato da kuma tsammani, shiyasa take kiransa da Ediyan a madadin Edriss.
Hakan ya samo Asaline da ƙuruciyar Zeeyadah wannan shine mafarin komai.

Itadai Mom Edriss jinsu kawai takeyi amma hankalinta naga wannan yarinyar da ɗanta
ya kira da fulani girl. Haka kawai takejin zuciyarta na rawa gabaɗaya ta rasa
makama babbaɓ burinta shine tayi ido huɗu da wannan yarinyar kota samu nutsuwar
zuciya.

*****

India 🇮🇳

Bayan Abie sunbar Asbitin da muzaffar ɗin ke kwance basu dire ko ina ba se
magarƙamar da aka sanƙame Ummie a ciki, nan take bada ɓata lokaci ba ya nemi da a
tura case ɗin babban ofishin jakadancin Nigeria dake ƙasar indian kasancewarsu ba
ƴan ƙasa ba. Be wani sha wahala ba suka amince da hakan tareda tura case ɗin can
kamar yanda Abie ya buƙata

Muhammad Kareem Ahmad shine wanda case ɗin Ummie bisa yunƙurin kisan muzaffar ya
faɗo hannunsa, gyara zaman farin glashin dake manne a idanunsa yayi tareda gyara
zamansa bisa hamshaƙiyar lallausar kujerar dake cikin katafaren office ɗin sannan
ya dubi Abie yace" ina evidance ɗin da Asibiti suka baku wanda ya tabbatar da cewa
Guba yaron yaci?

Miƙa hannu Abie yayi ya karɓi takardun dake hannun Mom wadda tunda sukabar Asbitin
take kuka ya mikawa Muhammad kareem Ahmad su, ƙurawa takardun idanu yayi yanabin
komai daki-daki cikeda sanin kan aikinsa kimanin wani lokaci me tsayi sannan ya
dubi Abie cikin ido yace

"haƙiƙa wannan al'amarin zan iya cewa a kwai tarin sarƙaƙiya a cikinsa wanda idan
bamu maida hankali ba zamu iya zartar da hukunci ba'a muhallin daya dace ba Alhaji
Abdulwahab, dole ne mu zarfafa buncike har mu gano gaskiyar lamarin nan, a
sakamakon da likitocin Asibitin da yaron yake kwance suka bayar ya nuna cewar gubar
bata daɗe a cikin jikinsa ba ta fita sannan kuma iskar daya shaƙa kafin yaci
abincin ita kanta a gurɓace take don haka dole ne mu ƙara samun cikakken bayani
akan wannan case ɗin na Hajiya Aisha.

A wannan takin ita kaɗaice zata iya fitar damu daga shakku. Ya faɗi hakan yana
kallon wani matashin saurayi yace "kace musu su shigo da me laifin nan zata amsa
min wasu tambayoyi dazanyi mata. Juyawa matashin yayi a hanzarce ya fice cikin ƴan
mintunan da bazasu gaza 2ba aka shigo da hajiya Aisha hannunta ɗaure cikin ankwa
idanunta duk sun jeme sabida kuka, kallo ɗaya zakayi mata ka fahimci cewar bata
cikin nutsuwarta ko kaɗan...

wani irin kallon tsana mom take binta dashi har Ummie n ta zauna a kujerar da aka
nuna mata, tunda ta shiga bata ɗaga kanta ba don batasan da idon da zata kalli Abie
ba

Kallon tsaf Muhammad kareem Ahmad yakebin Ummie dashi cikeda son tabbatar da abinda
yake tunani a kanta dannan yace "Hajiya Aisha shin zaki ya baiyana mana abinda ya
faru a wannan ranar da kika ciyarda ɗan mijinki guba a cikin abinci?

cikeda dakewar zuciya tace "Ae zan iya tunawa ranka ya daɗe, a wannan ranar da
kaina na dafa abincin dazan saukeshi dashi bayan na kammala dafawa na jera a kan
daining ina jiran isowarsa na buɗe kular Abincin danasan yafi so na zuba masa guba
a ciki tayanda zeci ya mut....... Wani irin Kuka ne ya taso mata dole yasa tayi
shiru da maganar ta shiga rusar kuka. Wani irin tuƙuƙin baƙin ciki ne ya tasowa
Abie a lokacin dayake kallonta cike da tsana yace "Muhammad don Allah Zan roƙeka
alfarma a karona farko ina roƙonka don girman Allah ka tura case ɗinnan gida
Nigeria ta yanda za'a hukunta wannan baiwar Allah butulu da tushe.

shiru Muhammad yayi bakajin sautin komai sena kukan Mom, cikin muryar kuka mom tace
don Allah ka taimaka mana Ranka ya daɗe plssssss. Mom taja plss ɗin kamar zata
shiɗe

Kamar bazece komai ba ya kalli Abie yace "naji duk batunku sedai bazamu amince ba
harse munga yanayin jikin yaron, bazeyu ku tafi ba harse ranar da yaron ya dawo
cikin haiyacinsa ta hakane kawai zamu iya tura ƙararku zuwa gida Nigeria Inyaso
sesuku shiga kotu........

Godiya mom ta dingayi masa sannan suka masa sallama itakuma hajiya Aisha aksake
maida ita magarƙama aka kulle.

Ko kaɗan bata dana sani aka abinda ta aikata gani take abinda tayi shine daidai,
dukda cewar a tsare take a hannun hukuma wllh seta koyawa Hajiya saratu hankali
tayanda zata sanyata cikin baƙin ciki fiyeda zato koda kuwa za'a yanke mata
hukuncin kisa ne gabaɗaya. Ta ƙare maganar tana murmushi wanda yafi kamada na
takaici

*_GHANDY HOSPITAL 🏥_*

Dr. Varun ne bisa kan muzaffar hannunsa ɗauke da wata ƙaramar na'ura wadda ya
saitata bisa kan cikinsa, gefansa

*Kuyi haquri don Allah da wannan ban samun time ne, da kuji ni shiru gwara na baku
update koda kaɗan ne. Thanks 4d lover sisters🥰*

comment
Nd
Share

sushmah💋
[3/3, 5:36 PM] Chubado Mohd: ❄️❄️❄️❄️❄️❄️
❄️❄️❄️❄️❄️❄️
🐄🐄🐄🐄
🐄🐄🐄🐄
*BAFULATANA*
✨RETURN✨
🐄🐄🐄🐄
🐄🐄🐄🐄
❄️❄️❄️❄️❄️❄️
❄️❄️❄️❄️❄️❄️

*_Page :26_*

*_DUK ABINDA ALLAH YA BUƊE BABU WANDA YA ISA YA RUFESHI, HAKA KUMA DUK ABINDA ALLAH
YA RUFE BABU WANDA YA ISA YA BUƊESHI. AL'AMARIN ALLAH HAKA YAKE _*

*_Ya ubangiji kayi min tsari da duk wanda ke neman ɗaga min hankali mace ko namiji
a duniyar yanar gizo🤲, ya ubangiji ka gina min katangar ƙarfe a tsakanina dasu
Allah idan ni ban sansu Allah kasansu ya ubangiji kai mana maganinsu don isar
manzon Allah SAW🤲_*

*_Masu cewa chubaɗo tace Karku fasa cewa nace kuyita faɗa daga nan har mahadi ya
baiyana, ku aiki ya kama tunda gabaɗayan ku babu me wuta bare aljanna da sannu kuma
zamu haɗe a madakata✊._*

*_WRITING BY: CHUBAƊO_*

Banyi Editing ba

___✍️Gefansa kuma wata matashiyar yarinya ce riƙe da faranti silver irin wanda
malaman lfy ke amfani dashi, abubuwa ne akan farantin dayawa waƴanda suka danganci
ɓangare irin na ciwon muzaffar ɗin.

Bayan ya gama scanning cikin nasa ne ya gano cewar a kwai inda gubar ta fara yi
masa illa ta ɓangaren liver ɗinsa, nan take ya bada umarnin a turashi zuwa ɗakin
tiyata don a tari matsalar dawuri idan bahaka ba tsab ze iya rasa rayuwarsa, a
gaggauce aka turashi zuwa ɗakin tiyatar cikin mintunan da bazasu gaza 30ba suka
kammala cikin ƙwarewa da kuma yarda dakansu a fagen aikin sannan suka maidashi zuwa
ɗaki na musamman.

A haka rayuwa taita tafi still babu wani canji a tareda muzaffar ɗin

Nigeria🇳🇬

Edriss ne sanye cikin ƙananan kaya black jeans with write T-shirt gashin kansa duk
ya baje harta bayan wuyansa hannunsa ɗauke da mukullin mota ya kalli mom wadda ke
gyara zaman mayafin dake jikinta yace "mom amma dai bada waƴan nan yaran zamu tafi
Hospital ɗin ba? Ya faɗa yana kallon su Hajar da zeeyadah.

Taɓe baki mom tayi tace "why are you asking me Bayan gasu nan duk da bakinsu?
Male baki yayi irin na ajeboters ɗinnan sannan ya fara ƙoƙarin fita daga falon da
sauri Zeeyadah tace "pls ya Edyan don Allah zan biku.

Juyowa yayi yana kallonta kimanin wasu mintoci sannan ya sakin mata murmushi yace
"ok amma da sharaɗi babu yawan surutu kinji ko? Da sauri tayi nodding kanta alamar
ta yarda da sharaɗinsa.

Mom na miƙewa Zeeyadah ma ta miƙe tana gyara rolling ɗin kanta sannan ta kalli
Hajar tace "Aunty ke zaman gida ya kama mukam kinga tafiyar mu. Wata uwar harara
ta watsa mata sannan tace "dama ai sedai ke ɗin tunda kece uwar neman gindin zama
da cusa kai. Hajar ta faɗa tana jan wani uban tsaki

Tun kafin ta ƙara wata magana mom tace "wllh Hajar zakici Uwarki dani a falon nan
tunda ke rashin kunyar taki kullum ƙara yawa takeyi a madadin ta ragu, to wllh nida
kaina zan sauke miki duk abinda yake kanki. Mom ta faɗi hakan yana zuba uban huji
gwalo zeeyadah tayi mata sannan taja hannun mom sukai gaba abinsu.

A harabar gidan suka samu Edyan yana ganinsu ya nufi wata zabgegiyar Renge Rover
ɗinsa baƙa wuluk da ita se faman ɗaukar idanu takeyi da hanzari guards ɗinsa suma
suka fara ƙoƙarin tada motocinsu dole hakan yasa Edyan ya fito ya kallesu yace "no
base kun bini ba zanje ni kaɗai Hospital zanje. Cikeda girmamawa ɗaya daga cikin
guards ɗin yace "amma ranka shi daɗe Me girma IG fa yayi mana kashedi akan barinka
kai kaɗai ka fit........."tunda ni jariri ne ko ? Edyan ya faɗi hakan with so
much angry.

A ladafce suka haɗa baki suna faɗin we are sorry sir. Tsaki yaja sannan ya buɗewa
mom back seat na motar sannan ta shiga ya rufe zeeyadah kuma ta kame a front seat,
harya shiga motar be ce da kowa ƙala ba a haka yaja motar suka fice daga gidan
gabaɗaya Zuwa Asbitin, cikin min tunan da bazasu gaza 15ba suka iso babban
madaidaicin private hospital ɗin wanda aka qawata da kayan qawa iri-iri tamkar ba
Asibiti ba. A notse ya faka motar cikeda ƙwarewa sannan ya fito ya zagayo ya
buɗewa mom side ɗinta ta fito tana murmushi sannan ya rufe motar.

Sakkowa zeeyadah tayi tabi bayansu suka ƙarasa cikin harabar Asibitin, Direct
office ɗin Dr. Mujaheed suka nufa, bayan sun shiga da sallama Edyan ya miƙa masa
hannu suka gaisa sannan suka gaisa da mom da zeeyadah, nan Edyan yake tambayarda
yame jiki?

Ɗan murmushi Dr. Mujaheed yayi sannan yace "jikinta da sauƙi sedai tun jiya data
farka take mana kuka kuma taƙi bari kowa yazo kusa da ita munyi2 taci abinci amma
taƙi sam. Cikeda damuwa Edyan yace "kana nufin har yanzu babu abinda tasa a
cikinta se kuka datakeyi?

Dr. Mujaheed yace "sure.

Da sauri Edyan ya miƙe ya bar office ɗin ya nufi ɗakin da aka kwantar da itan, Da
sallama ɗauke a bakinsa ya tura ƙofar tareda zura gaba ɗayan jikinsa cikin ɗakin
sedai sam be saki ƙofar ba. A nitse yakebin kowace kusurwa na ɗakin da kallo harya
sauke manyan fararan idanunsa akanta, gabaɗaya dukta takure guri guda tareda haɗe
kanta da gwiwarta bakajin sautin komai sena kukanta.

A nitse ya fara takowa cikin takunsa harya ƙaraso bakin gadon bata ɗago ba hakan ne
ya bashi damar ƙare mata kallo tun daga kan yatsun ƙafarta har zuwa kan manyan2
kitso biyun dake kanta ba wanda yaci uban datti gashida mugun tsayi na ban mamaki,
sedai dukda hakan bazaka kasa gane irin kyanda gashin nata yake dashi ba abinka da
Fulanin Usuli.

A hankali ya miƙa hannunsa ya dafa kafaɗunta a wani irin mugun furgice ta ɗago
idanunta duk sun caɓe da hawaye taja baya da sauri tan me ƙara ƙanƙame jikinta
still her eyes is on his handsome face. Cikin harshen Fulatanci ta fara magana
kamar haka " ka matsa kusa dani banson Rayuwa a cikink........ Wani irin kuka ne
ya taso mata dole yasa tayi shiru.

Jikinsa ne yay masifar sanyi dukda besan abinda take faɗi ba don haka ya sake miƙa
hannunsa ze taɓata yace "its OK dear but plz stop crying don Allah kodon sabida
condition ɗinda kike ciki na rashin fly plz Cutie girl. Ya ƙare maganar yana
kallon tsakiyar ƙwayar idanunta

Ƙura masa idanu ita tayi tana kallonta a ranta tana aiyana cewar "komai nasa irin
na hamma zafar har yanda yake magana yana saka wani yare na daban, sedai gashin
kansu da yanayi na ƙirar jikinsu ne sam ba ɗaya ba wannan sam be kai Hamma zafar
hasken fata ba seda shima ba laifi yana da kyau sosai na nunawa sa'a. Haka kawai
taji zuciyarta ta amince dashi kuma ta yarda dashi, batace masa komai ba tasa
hannunta ta janyo takalman robarta dake gefanta ta rungume a ƙirjinta tareda zubawa
flet ɗin abincin da aka ajiye mata tun ɗazu bataci ba idanu.

Murmushi yayi yace "zakici ?

Turo baki tayi batace masa komai ba, ɗakkowa yayi ya miƙa mata flet ɗin yana
murmushi jada baya tayi tana kallonsa alamar ma ita tsoro kwanon Abincin yake
bata, riƙewa yayi a hannunsa sannan ya kalleta yace " ki lura da kyau ki kalleni
babu abinda kwanon abincin zeyi miki ok. Still tana kallonsa sannan ya ɗebi
abincin da cokalin kaɗan yakai bakinsa yaci sannan ya miƙa mata yace "oya eat.

Maƙe masa kafaɗa tayi tana shirin fashe masa da kuka yace " hay look don't cry
please just eat. Taɓe baki tayi tana wani mirza ido. Ganin dayay bata da niyan
karɓa ne yasa ya matsa dabda ita ya fara bata abincin ta cokalin tanaci tana
zubarwa a haka haraya gaba bata ya ajiye flet ɗin yace "barin je na dawo ko?

Da wani irin mugun sauri ta diro daga gadon ta riqe hannunsa gam tana hawaye a haka
su mom da Dr. Suka shigo ɗakin. Bayansa ta koma da sauri tana ɓoyewa alamar
batason mutane sosai

Murmushi mom tayi tana kallonta cikeda so sannan ta maida kallonta ga Edyan tace
"Dr. Ya bada takaddan sallama se kuma drugs daya rubuta kuma suma mun siyo mata
yanzu gida zamu wuce kawai. Murmushi kwai yayi yace "ok mom muje. Ya faɗa yana riƙe
da hannunta

Har sunkai ƙofa ta fizege hannunta ta dawo ta ɗauki wannan jakar da Moddibo ya bata
sannan ta dawo ta riƙe hannunsa suka fita.

Wajen shiga mota ba ƙaramar ɗirama akayi da ita ba ihu ta dinga zuba musu seda
Edyan yay dagaske sannan ta yarda ta shiga suka tafi gida gabaɗaya, duk a tsorace
take kallonsu kawai take itako zeeyadah gabaɗaya tausayin yarinyar ya gama cika
mata zuciya.

India🇮🇳

A kwana a tashi babu wuya a gurin Allah a ɗan wannan tsukun lokacin abubuwa dayawa
sun faru masu daɗi da marasa dadi, a ɓangaren Muzaffar kuwa sosai yake samun sauƙi
dukda irin ɓarnar da poison ɗin yayi masa a ciki, ada sam baya iya zama amma yanzu
kam yana iya zama da kansa harma yayi tafiya koda bame tsaho bace. Sosai hkaan yawa
Su mom da Abie daɗi har hakan ya kasa ɓoyuwa akan fuskokinsu.

Bayan sati biyu da samun lfyar muzaffar Muhammad Karim Ahmad ya tura case ɗinsu
zuwa Nigeria tun kafin su dawo ƙasar aka fara bincike akan case ɗin kasancewar
Ummie ta amsa Laifinta na cewar ita ta bashi gubar da hannunta yasa al'amarin
yazowa masu yanke hukuncin da sauƙi, wahe gari da sassafe jirginsu ya ɗaga zuwa
Nigeria.

Sosai Ummie ta fita daga haiyacinta kamar ba ita ba, tun Doguwan rigar da aka
Kamata da ita sanda abin ya faru har yanzu itace a jikinta idanunta duk sun zurma
sunyi ciki tamkar bana Hajiya Aisha ba mata ƴar ƙwalisa da son kwalliya a haka aka
sake jefata cikin magarƙama aka rufe.
Mom sun koma gida lfy kullum.ƙara tattalin ɗanta takeyi kasancewar Zaynab sun koma
makaranta ne yasa komai yazo Musu da sauƘi, komai nasa mom ce keyi da kanta wasu
lokutan abin har yana bawa Abie mamaki, Baba Hajarah ma ba ƙaramin tashin hankali
ta shiga ba santa tayi arba da Muzaffar gabaɗaya ya rame yayi duhu kamar bashi ba,
kuka ta dingayi itama daga bisani kuma ta haƙura tacigaba dayi masa addu'o'in
Alkhairi da kuma na samun lfy.

Washe gari da safe mom ta kira Baba Hajara tazo ta sameta a falo tareda maryam me
aikin Hajiya Aisha a zaune, da girmamawa Baba Hajara ta gaida Momy sannan ta
sunkuyar da kanta

Mom ta kalleta tace "Hajara ga maryam nan zaku zauna tare kuci gaba da gudanar da
hidimomin gidannan don Allah seku haɗe kanku kuma ku zauna da juna lfy.

Murmushi Baba Hajara tayi tace "to Hajiya insha Allahu. Mom ta kalli maryam tace
"ki ɗauki kayanki ki bita zata nuna miki ma saukinki. Da to Maryma ta amsa sannan
ta miƙe tabi bayan Baba Hajara suka nufi ɓangarensu.

Tunda Abie ya dawo daga india be samu ya zauna ba sabida ciku2 shariyarsu da Ummie,
so yake ayi abin bisa sirri don bayaso kimarsa ta taɓu a idanun al'uma dakuma na
ƴan jarida kasancewarsa babban mutum kuma wanda ƙasa kejidashi. Be wani sha wahala
ba me shariya ya amince da batunsa na mayar da shari'ar tasu ta sirri because this
is the only thing dayake ganin ze iyayiwa ummie a rayuwarta don bayaso ta
wulaƙanta a idon duniya har yanzu yana ƙaunarta a cikin zuciyarsa ƙauna me tarin
yawa bata wasa ba.

Washe gari Ya kama litinin ne kuma a ranar shariyar zata fara, Mom ce ta fito cikin
shigarta na alfarmar a nitse ta gama sakkowa daga sters ɗin sannan ta samu Fadilah
a falo tana kallon news.

Da kulawa mom ta kalleta tace "dota idan kin tashi kije ki duba yayanki sannan kisa
Hajara ta dafa masa abu meɗan ruwa2 wanda zeji daɗin ci seki kai masa kinji ko?

Fadilah tayi musmushi tace "ok mom sekin dawo Abie ya shigo tun ɗazo da alama
keyake jira. Shafa kanta mom tayi tareda sumbatarta sannan ta fice a hanya sukaci
karo da Baba Hajara ta dawo daga rabawa masu gadi da masu yankan flowers abinci.

Cikeda girmamawa suka gaisa sannan tace "to semun dawo Hajara. Da murmushi a akan
fuskar baba hajara tace "hajiya yau kece da fitar sassafe?

Tsayawa mom tayi cak sannan ta juyo da murmushi tace "wllh fitar ta dole ce kotu
zamu kinsan mun shigar da ƙara akan Aisha.

Take gaban Baba Hajara ya buga da ƙarfi tanaji tana gani a haka mom tayi gaba ta
barta zuciyarta na dukan tara2.

Thanks 4d love sisters naga addu'o'inku Allah yabar zumunci👏


Comment
Nd
Share

Sushmah💋
[3/3, 5:36 PM] Chubado Mohd: ❄️❄️❄️❄️❄️❄️
❄️❄️❄️❄️❄️❄️
🐄🐄🐄🐄
🐄🐄🐄🐄
*BAFULATANA*
✨RETURN✨
🐄🐄🐄🐄
🐄🐄🐄🐄
❄️❄️❄️❄️❄️❄️
❄️❄️❄️❄️❄️❄️

*_Page :27_*

*_WRITING BY: CHUBAƊO_*

BANYI EDITING BA

____✍️Wata irin zuface ta shiga yankowa Baba hajara tamkar an kunna fanfo da ƙyar
ta iya ƙarasawa ɗakinsu tana ɗingisawa sabida ƙafar dake ɗan mata ciwo ta zauna
daga gefan katifarta kasancewar ita nata katifan a ƙasa yake sabida yanayin
jikinta, duk sanyin Ac n dake ɗakin nemassa tayi ta rasa sabida tsabar rashin
kwanciyar hankali, maryam ce ta shigo hannunta ɗauke da faranti ta takeshi da
soyayyoyar shinkafa wadda taji uban kayan lambu se baza ƙamshi takeyi, harta zauna
tana kallon baba sabida yanda taganta duk ta fita haiyacinta.

Ajiye Abincin tayi tareda matsowa gareta tace "Baba lfy kuwa nagani haka duk kin
fita haiyacinki?

Hawayen da suka samu zarafin zubo mata Baba ta goge sannan ta kalli maryam tace
"wai nikam meyake shirin faruwa a gidannan ne tsawon shekaru ina cikinsa bantaɓa
cin karoda abinda ya ɗagamin hankali kamar wannan ba, wllh maryamu inajiyewa kaina
tsoron abinda zeje yazo a cikin wannan iyalin danake kallo tamkar nawa!!

Yanzu Hajiya Saratu take sanar dani cewar wai kotu zata tafi da sassafen nan haka
kawai sena samu kaina da rashin kwanciyar hankali duk a dalilin jin hakan.

Sakin baki maryam tayi tana kallon baba harta gama magana sannan tace "Baba karkice
min bakuda labari akan abinda ya faru bayan zuwan ƙaramin megida ƙasar india? To
idan kuwa har Hajiya bata sanar daku ba tabbas kirkinta da kuma sanin yakamatanta
ya wuce duk yanda ake zatonsa.

idan har zan iya tinawa daidai Baba yau shekarata Talatin ina tareda Hajiya Aisha
inai mata aiki tun tana ƙasar nan har Allah ya ɗagata daga nan muka koma India tare
ban taba samunta da wani hali na rashin kirki ba kokuma kyautatawa ba komai
ƙanƙantarsa, haka kuma duk wanda Allah ya haɗata zama dashi tanayin iya ƙoƙarin
wajen kyautata masa koda kuwa maƙiyinta ne shi, Amma abin mamaki se gashi an kama
Hajiya Aisha dumu2 da zubawa ƙaramin megida guba a cikin abincinsa da kuma abin
shansa, ni kaina na girgiza a lokacin da abin ya faru harnake ganin kamar sharri
akayi mata badan ina gurin abin ya faru ba wllh zance ɗora mata kawai akayi Baba.

Amma se gashi ta faɗa da bakinta cewar itace ta zuba masa guba don kawai ta kawo
ƙarshen nunfashinsa wannan shine maƙasudin baiyanar mugun halinta a gaban kowa,
nafi zargin cewar don kawai bata samu haihuwa da Alhaji bane shiyasa ta gammaci
data kashe musu ɗa donta huce haushin wannan zafin. Maryam ta faɗa hawaye na zubo
mata

Shiru Baba tayi tana kallonta haka kawai setaji sam zuciyarta ta kasa yarda da
wannan laifin da ake zargin Hajiya Aisha dashi, wllh ko a gaban uban waye zata iya
shedar ta kan cewar bazata taɓa iya aikata wannan gagarumin laifin ba koda kuwa ga
dabba ne ba mutum ba, a hakan kuma wai muzaffar gaskiya itakam tana tantama akai
koma menene zata zauna da Alhaji tasan se sanar da ita gaskiyar lamarin kuma tasan
ze saurareta tunda uwa ya ɗauketa ba ƴar aikin gidansa ba.

Murmushi Baba Hajara tayi tana kallon maryam tace " wllh maryam kin ban mamaki da
har kika bari zuciyarki ta iya faɗawa cikin zargin matar data shekara Talatin tana
tallafawa Rayuwarki ta ɓangarori da dama batareda ta nuna gajiyawarta ba koda so
ɗaya, nayi mamaki sosai da kika iya yarda da wannan zargin a lokacin da aka
baiyanashi kunnuwanki sukajishi tabbas kinji kunya maryamu. Baba ta faɗi hakan
tana bin maryam da wani irin kallo wanda yasa taji ta muzanta.

Wani irin sanyi jikin maryamu yayi sabida kalaman da baba ta faɗa to amma ya
zatayi dole ne ta faɗi abinda idanunta suka gane mata a wannan rana, don Hajiya
Aisha ta taimka mata a rayuwa hakan baya nufin zata iya zuba idanu ta kalleta a
yayinda tayi yunƙurin kashe ɗan mijin kishiyarta Hajiya Saratu.

a haka hirar tasu ta tashi jikin kowa babu ƙwari, suna nan zaune Fadilah ta shigo
ɗakin kunnenta ɗauke da waya ta kalli Baba tace "mom tace ki dafawa Muzaffar
farfesun kifi da kuma abinci meɗan ruwa2, and then zaki iya haɗa masa da wani abin
meɗan daɗi haka. Ta faɗa tana kallon Baban tana wani yatsin fuska

Murmushi Baba tayi sannan ta miƙe tace "zama be kamani ba miji nacan ciki babu
komai bari inje na sama masa abu meɗan galmi-galmi ya samu ya tauna. Ta faɗa tana
miƙewa da salati ɗauke a bakinta tayi kicin tahau hidimar girkawa muzaffar abinda
zeci.

Bata wani ɗauki lokaci ba ta kallama komai se baza ƙamshi farfesun kifin yakeyi
tamkar ba tsohuwace ta girkashi ba, sosai baba ta ƙware a fagen dafa abinci shiyasa
tai fice a cikin gidan musamman a gurin Muzaffar indai ba ita ta girka abinci ba
to wllh lami ne a gurinsa shiyasa yake sonta sosai.

Da yammaci wajen ƙarfe 5pm Muzaffar dake tafiya a duke sabida yanayin condition ɗin
dayake ciki ya isa katafaren garden ɗinsu wanda aka ƙawata da duk wani abu na jin
daɗin Rayuwa da ɗebe keywa ya zauna akan ɗaya daga cikin fararan kujerun da akayiwa
ado da jajayen duwatsu masu matiƙar sheƙi da ɗaukar ido dake maƙotaka da katafaren
swimming ɗin dake gurin, gefe kuma wasu fulawoyi ne masu fitarda wani irin nau'in
ƙamshi wanda yafi kamada na musamman gamida sanya nutsuwar zuciya.

Miƙe dogayen ƙafafuwansa yayi kan kujerar tareda ɗora zara2 dogayen yatsunsa a
saman ƙirjinsa tareda lumshe tsumammun idanunsa yay shiru yana nazari akan
jarrabawar data sameshi a ƴan kwanakin nan, kokaɗan bayaso a sanadinsa Abie ya rabu
da matar daya daɗe yana tareda ita morethen 35years don kawai tayi yunƙurin
kasheshi, komadai menene a shekarun baya ta wahalta masa a lokacin dayake yaro da
ƙarfin jikinta dakuma bakin aljihunta dole tunda ta aikata hakan tanada wani
ɓoyyayan dalilinta dayasa ta aikata hakan. Wani siririn tsaki yaja a lokacin
daya tuna maganar kotun dazasu sake shiga sati me zuwa wanda daga shine Hajiya
Aisha zata fuskanci hukunci, gyara zaman kansa yayi bisa lallausan hannun kujerar
dayake kai a haka daddaɗan yanayin dake gurin ya fara tasiri a jikin kowace gaɓa ta
jikinsa lokaci guda hakan ya zama tamkar wata ilhama ne dake jan zuciyarsa zuwaga
Fulani girl ɗinsa,

lumshe manyan idanunsa yayi tareda buɗesu lokaci guda akan korayen tsirran da suka
ƙawata gurin ya saki wani kyakkyawan murmushi wanda hakan yasa dimples ɗinsa both
side suka lotsa a tare. A hankali can ƙasan maƙoshinsa yace "i miss you babe I miss
everything about you my poor babe . Ya faɗa yana gyara zaman hannayensa dake zube
saman ƙirjinsa.

wata danƙareriyar jeep ce ƙirar ford ta sulalo cikin harabar gidan Maroon colour
wadda taji uban tinted da gani kasan duk wanda ya kasance mamallakin wannan mota to
la shakka hannunsa ya cuɗi gadon bayansa, a nutse motar tai parking sannan ta ɓalle
murfin motar ta sanyo ƙafarta waje wadda ke cikin wani haɗaɗɗen takalmi baƙi wuluk
me bala'in tsini dashi se walwali yake sabida stones ɗin da akai masa ado dasu masu
matiƙar haske da ɗaukar idanu,

Hajar ce the IG doughter ta sakko cikin wata shainaɗaniyar shiga ta ban mamaki
tamkar wadda zata zaɓen sarauniyar kyau komai na jikinta baƙi ne hakanne ya bawa
hasken fatarta damar baiyana a sarari, sosai doguwar rigar me fasalin fitet gown ta
amshi jikinta tareda matse ta sosai tayanda duk wata halitta ta jikinta ta baiyana,
a yangance take tafiya tana zuba yauƙi tana ƙoƙarin shiga falon gidan sukaci
karoda Baba Hajara wadda ke ɗauke da babban flet a hannunta ta shiryawa ɗan gaban
goshin nata Abinci zata kai masa, da fara'ar da bata kai zuciya ba Hajar tace "let
me help you Old woman. Ba musu ta miƙa mata farantin tana kallonta bakinta a sake,
murmushi ta sakin mata tace "yana ina na kai masa don nasan wannan abincin da
ganinsa na mijin Hajar ne ko tsohuwa?

gyaɗa mata kai tayi tareda nuna mata hanyar garden batareda tayi magana ba don ita
har ga Allah lamarin yarinyar nan yana masifar bata tsoro, "wannan wani irin
lalacewar zamani ne ni Hajara?

Ko a jikin hajar sam bata damu da irin kallon da Tsohuwar kebinta dashi ba tai
hanyar inda ta nuna mata tana wani juya mazaunai a haka ta isa garden ɗin ta
sameshi idanunsa a lumshe, Ajiye flet ɗin tayi sannan ta sunkuya dabda fuskarsa
tana wani bin fuskarsa da kallo kamar zata cinyeshi ɗanye, saukar numfashinta da
nata ne suka haifar da sarƙewar numfashi a tsakaninsu take shauƙinso ya fara fuzgar
Hajar ta fara ƙoƙarin kaiwa jajayen laɓɓansa farmaki hakan yasashi buɗe idanu da
sauri ya saukesu bisa beauty face ɗinta.

jada baya tayi da sauri sabida wani bala'in kwarjini dayayi mata, kallon tsaf yayi
mata kimanin 5second sannan ya miƙe yabar mata gurin yana riƙe da cikinsa, gabaɗaya
ji yake dama ya kwasawa ƴar banza mari kozata fita daga sabgarsa wannan wani irin
bala'i ne haka ?

shidai kam Allah ya jarabce shi da jarababbiyar yarinya wadda idan har beyi da
gaske ba tsaf zata iya jefashi a masifa watarana.

Fashewa da kuka Hajar tayi a gurin sabida takaicin abinda yayi mata amma sabida
naci irin nata haka ta miƙe tabi bayansa still tana kukan...

*_GYAMBU TARABA STATE_*

Tunda wannan mummunan al'amari ya faru da inna laure gabaɗaya duniya ta juya mata
baya duk tabi ta rame ta koɗe kamar ba ita ba, yawan masifar nan ma duk ta dena
kullum bata da aiki se kuka yau kimanin wata guda kenan da faruwar lamarin amma
sam ta kasa mantawa da komai, duk sanda ta tuna ji take tamkar a lokacin abin ke
faruwa da ita haƙika Fyaɗe babbar masiface me zaman kanta kuma duk wadda akayiwa
shi an gama kashe mata rayuwa na har Abada!!!!

yauma kamar kullum Moddibo dake tsaye jikin ƙofar ɗakinta ya ɗaga labulan buhun
yana kallonta kukan takeyi duk yanda yaso ya shareta kasaw yayi dole tasa ya shiga
ɗakin ya zauna daga gefan katifar ciyarwar dake ɗakin ya dubeta ya dinga bata baki
harya samu tayi shiru, sosai ya dinga zuba mata nasiha a kan yarda da ƙaddara da
kuma haƙuri babu abinda take se kuka tareda nadamar bijirewa umarninsa datayi a
baya, tabbas da bata biyewa son zuciyarta ba wata ƙila da yanzu ta tsira da sauran
mutuncinta. Shidai moddibo miƙewa kawai yayi yabar mata ɗakin don tunda abin ya
faru yaji gabaɗaya Laure ta gama sire masa, bayajin ze iya zaman Aure da ita
kokaɗan sedai ze mata alfarma guda ɗaya ya cigaba da zama da ita batareda wani abu
ya gifta a tsakaninsu ba, idan ta amince da hakan to shikenan zeci gabada zama da
ita a haka tunda duk wanda ya rufa Asirin ƴar wani To Allah xe rufa nasa .....
Badan haka ba wllh da tabbas ya gama zama da Laure har Abadah

*_ABUJA_*

Koda suka dawo daga Asbiti basu Samu Hajar a gida ba wannan dalilin yasa sam
batasan da zuwan Rabe gidan ba, Tanacan tana neman soyayyar muzaffar a gidansu

A ɗakin zeeyadah aka sauketa sannan mom tabada Umarnin zeeyadah ta tsefe mata
wannan gashin nata Dayaci uban datti a gyara mata amma fir Rabe taƙi yarda se zuba
ihu takeyi dataga Zeeyada na neman takura mata ne yasa ta fusge jikinta ta koma
gefan Edyan ta zauna tana matsar ƙwalla dole tasa zeeyadah ta ƙyaleta, Dariya Edyan
Yayi sannan ya kalli zeeyadah yace "bani abin tsifa gashin. Ba musu ta miƙa masa ya
kama doguwar jelar Ƙatuwar kalban yana tsefewa A hankali tamkar wanda ke koyon
tsifan, yamutsa fuska ta farayi alamar tanajin zafi zata tashi taga ya haɗe rai
dole yasa ta sunkuyar dakai tana wasa da yatsun hannunta a haka harya gama warware
mata kasancewar guda biyu ne dama Kalban, nan da nan gashin ya baje a gadon
bayanta tareda rufe mata fuskarta daga mom har zeeyadah seda yanayin gashin nata
ya basu mamaki, ranar momce da kanta ta wanke mata gashin tass a toilet ɗin
zeeyadah nan ma ba ƙaramin danbarwa sukasha da ita ba sannan aka gama, Bayan an
gama wankin kan ne mom tayi mata wanka Tas ta wanketa se zuba ihu takeyi Sedai
duk uban ihun datake zubawa be hana mom saɓeta ba, Towel tasa babba ta ɗaura Mata
tareda busar mata da gashin tas wanda ya ƙara wani mugun baƙi da santsi sannan
suka fito mom tace "zeeyada ta bata kayan bacci ta saka .

Doguwar riga ta ɗakko mata me ƙaranin hannu daƙyar ta yarda ta nuna mata tasa amma
sam taƙi yarda a kama gashin dole suka ƙyaleta se uban kuka take zuba musu, tana
fitowa falo ta faɗa jikin Edyan ta fara Wani sabon kukan hular hannun zeeyadah ya
karɓa ya saka mata dukda haka gashin be rufe duka ba se faman sauke ajiyar zuciya
takeyi.

A haka sukai diner Tana manne a jikinsa harta fara bacci sannan ya mike Tareda
zare Jikinsa daga nata zebar falon da sauri itama ta miƙe zata bishi Duk irin
baccin dake idonta tsayawa yayi cak yana kallenta bece komai kawai ya nufi ɗakin
zeeyadah tana biye dashi har suka shige mom da Zeeyadah na kallon ikon Allah.

Zeeyadah data sake baki tana kallonsu ta kalli mom tace "momcy wllh nikam tausayi
take bani bata iya hausa ba gashi kuma ƙaddara ta kutso mata da silar rabuwa da
iyayenta mom, na tabbata yanzu iyayenta hankalinsu A tashe yake sabida ɓatanta.

Shiru mom tayi itama tana kallonta ita kanta tunanin dayake mata yawo kenan a saman
zuciyarta, insha Allahu itakuwa zata taimakawa wannan yarinya har zuwa ranar dazasu
maidata gaban iyayenta don ita harga Allah takejin yarinyar a cikin ranta musumman
idan tana kallonta.

Duna shiga ya nuna mata mata gado yace "hau ki kwanta kasa yi masa musu tayi ta
hau gadon still tana kallonsa Wani bala'in laushi taji wanda bata taɓa jin irinsa
ba a Rayuwarta da wani irin mugun sauri ta saukko tana ihu zata shige jikinsa ya
dakatar da ita. Yana kallon tsakiyar ƙwayar idanunta ya sake ce mata hau ki kwanta
nan ma ba ƙaramar wahala ta bashi ba sannan ta hau ta kwanta, seda ya tabbatar da
bacci ya ɗauketa sannan ya fita daga ɗakin yana murmushi.

Comment
Nd
Share

sushmah💋
[3/3, 5:36 PM] Chubado Mohd: ❄️❄️❄️❄️❄️❄️
❄️❄️❄️❄️❄️❄️
🐄🐄🐄🐄
🐄🐄🐄🐄
*BAFULATANA*
✨RETURN✨
🐄🐄🐄🐄
🐄🐄🐄🐄
❄️❄️❄️❄️❄️❄️
❄️❄️❄️❄️❄️❄️

*_Page :28_*

*_WRITING BY: CHUBAƊO_*

Banyi Editing ba

✍️___inda yabarsu mom da zeeyadah a nan ya dawo ya samesu komawa yay ya zauna
sannan suka kalli juna gabaɗayansu suka fashe da dariya, momce ta kalleshi tace
"wllh Edyan a kwai aiki agaban mu babba ma kuwa becouse yarinyar nan daga ganin ta
da kuma yanayinta cikakkiyar Asalin Bafulatanar Dake Rayuwa a cikin daji ce. Ajiyar
zuciya yaɗan sauke sannan ya kalli mom yace "ni kaina mom na lura da hakan duba da
yanda take yawan janyewa daga mutane tareda nuna tsoronta ƙarara ga wasu abubuwan
tabbas bata taɓa ganinsu ba kuma batasan da dasu ba. Anyway we have to help her
with everything dazata buqata a Rayuwa Especially knowledge.

Ɗaga kai Mom tayi Alamar gamsuwa da maganganunsa tace "but sweetie what about her
parents da kuma danginta? Sam be kamata ace daga ka bige musu yarinya ka ɗakkota
ka daga garinsu ka kawota nan ba Edyan I'm sure of duk inda iyayen yarin nan suke
wllh nasan hankalinsu baze taɓa kwanciya ba, don haka duk yanda za'ayi ka samu idan
ta ƙara samun sauƙi ka mayar musu da yarinya inda haɗarin motar ya faru na tabbata
bazata kasa tuna inda gidansu yake ba.

Kallon mom zeeyadah tayi da sauri idanunta na shirin zubar da hawaye tace "pls mom
let her to stay with us for a long while before she gets to her on parents pls mom,
indai har ba itace da kanta tace zata tafi ba don Allah karki sake cewa ya mayar da
ita pls wllh daga lokacin dana fara kallon ƙwayar idonta na fahimci there's
something behind her mom is either good or bad Allah shikaɗai yasani but pls mom
let her to stay Don Manzon Allah. Ta faɗa tana fashewa da kuka

Gabaɗayansu kallonta suke shi kansa Edyan bayaso yayi jayayya da ita ne amma a
zahiri sam bayaso ya mayar da yarinyar, haka kawai yaji ubangiji yasa masa wani
irin tausayinta wanda shi kansa besan daga ina hakan ke fitowa ba a yanzubashida
burin daya wuci yaga rayuwar yarinyar ta inganta ta yanda bayaso yaga ta rasa wani
abu a cikin Rayuwarta, kowace daƙiƙa idan ya kalleta burukansa akanta ƙara yawa
suke nason ganin tazama kamar kowa. Hajar ce ta shigo falon hannunta ɗauke da
mukullin motanta tana bada step tamkar me koyon tafiya, da kallo mamaki mom tabita
sannan ta maida kallonta ga Agogo tace " ke daga ina kike at this time eh?

Dukansu kafeta sukai da ido suna jiran suji me zatace . Turo baki tayi tareda jan
kujerar daining ɗin tace "gidansu Fadilah naje karɓan wani abou a gurinta and
kum....."abunda ubanki ya Ajiye a gidan kikaje karɓa ko? Mom ta katseta cikin
fishi sannan taci gaba da cewa "waike mara hankalin inace Hajar? Don uwarki an
gaya miki nan ƙasar india ne da mace ke zuwa neman Aure gidansu saurayi?

Murmushi Edyan yayi wanda yake baiyana takaicinsa akan ɗabi'ar ƙanwar tasa yace "ai
ko a indian ma mom namiji shike fara zuwa da danginsa suga yarinyar kafin daga
bisani ta biya sadaki a ɗaura musu Aure, kinga kenan ko'a nan matan indiawan da
addini be ishesu ba sunfi Hajar hankali da kuma mutunta kansu, na rantse da Allah
mom koda ace nine Muzaffar bazan taɓa Auren wannan mahaukaciyar wadda batasan ciwon
kanta ba as uwar ƴaƴana ba. Ya faɗa cikin ɗaga murya alamar ta gama bashi haushi

Ƙus tayi taƙi magana sabida tasan tanayin magana zeci ubanta a falon yasa ta
sunkuyar dakai tana hawaye, itadai zeeyadah kallonta kawai takeyi tana mamakin
wannan ɗabi'ar ta ƴar uwar tata, miƙewa yayi yabar falon zeeyadah ma ta kama
hanyar ɗakinta ya kasance daga mom se ita, hakanne ya bata dama yimata faɗa sosai
sannan ta miƙe ta barta a gurin tana kuka.

******

Ɓangaren muzaffar kuwa sosai yake samun sauƙi don yanzu yana iya miƙewa yayi tafiya
kamar yanda yake da, sedai ramar dake tare dashi komai yanzu bayajin daɗinsa ko
kaɗan musamman idan ya zauna shikaɗai bashida wani aiki wanda ya wuce na tunani,
gabaɗaya duniyar ta fice masa a kai sabida yanda mutannan cikinta suke sam wasunsu
basuda imani sukan iya aikata komai akan abin duniya, abu ɗayane yake masa yawo a
saman zuciyarsa shine meyasa Ummie take ƙoƙarin kasheshi ta hanyar bashi guba a
abincin? Amsar daya gaza samu kenan har yanzu dukda cewar wani ɓangare na
zuciyarsa sunyi mata uziri akan hakan.

Wayarsa dake gefan bedside ce ta ɗauki ruri a kasalance ya miƙa kyakkyawan hannunsa
ma'abocin dogayen yatsu ya ɗakko wayar, murmushi ya sakki a lokacin dayaga sunan
Edriss na yawo a saman makeken screen ɗin wayar, ajiyar zuciya ya sauke sannan ya
ɗaga yana dariya

Taɓe baki Edyan yayi yace "kayi dariya mana wllh zafar baka da kirki amma kasan me
wllh daga yau bazan ƙara neman ka ba tundai ɗan iska ne bakasan zumunci ba.
"muzaffar yay dariya sosai sannan yace "I'm sorry buddy but I'm not in Nigeria
that's why ban kiraka ba, bana gayama zani India wani meeting ba to wllh ban daɗe
da dawowa ba yau sati ɗaya kenan ai. Edyan yace " oopss joma joma guy matsalanka
not mine. Anyway i'm withing the nabourhood If na Gama I will let u know insha
Allah zan shiga gidanku na ganka shugaban marasa kirki.

Dariya Muzaffar yayi yace "wurin wa kazo aria ɗin mu? Taɓe baki Edyan yayi yace "
to see muhammad Fu'ad Almakora. Baye ya katse wayar

Se wajan 3pm Edyan ya ƙaraso gidan Direct part ɗin mom ya nufa da sallama, a falon
ƙasa ya sameta nan ya ƙasara cikeda girmamawa ya gaisheta da sakin fuska ta amsa
tareda faɗin "yasu Mamin ka? Edyan yace "the are fine mom. Cikeda tsokana
takelleshi tace "oh Allah kullum se ƙara girma kuke amma daga kai har abokin naka
an rasa wanda ze ajiye mata ko se faman yawo kuke a gari haka nan to wllh ƙauye
zanje na samomu masu degree faranti. Dariya ya ƙyalƙyale dashi a haka Fadilah ta
sakko falon ta sameshi, a yangance tace "hi beko kalleta ba yace "Hi. Miƙewa
yayi yace "mom barinje gurin wancan tuzurun. Dariya tayi tace "tuzurai dai zakace

Yana shiga falon ya sameshi yanashan cofee nan suka shiga hirar yaushe gamo basu
wani jima tareba kiran zeeyadah ya shigo wayanshi yana ganin kiran yasan a kwai
matsala dan haka ya ɗaga yace " ya akai?. Daga ɓangaren zeeyadah tace " ya Edyan
wllh taƙicin abinci kuma se kuka take wai bata ganka ba. Murmushi yayi yace "ok I'm
coming insha Allah. Zeeyada tace "ok. tareda kashe wayar

Miƙewa yay yace "my guy semunyi waya be jira cewarsa ba ya fice daga falo.

*******

A kwana a tashi ba wuya a gurin Allah yau ta kama litinin wanda yay daidai da sha
huɗu ga watan juneru shekara ta dubu biyu da Ashirin 14/1/2020 wanda yayi daidai
da zartarwar Alƙalin dake jagorantar shariyar Su Abie da Ummie akan yunƙurin kashe
masa ɗanda ya haifa da cikinsa da tayi, kasancewar shariyar ta sirrice yasa babu
wani cikowa a cikin babban falon alƙali Abubakar Najeeb ɗin se maga-takardansa da
kuma masu hurumi na zartawar dake kotu tareda sauran jama'ar Alƙali Abubakar Najeeb
ta ɓangaren aiki, gefan dama kuma Ummie ce hannunta ɗaure cikin sarƙa se kuma
Abie da mom dake ɗan nesa da ita se maryam da kuma muzaffar da Fadilah, a cikinsu
Baba hajara ce kawai babu

Alƙali Ya kalli maryam da aka gabatar masa a matsayin sheda lokacinda Abin ya faru
yace " ya sunanki? Kanta a ƙasa tace "Sunana maryam Alasan me gatari ranka ya
daɗe. Alƙali yace "kina nan lokacin da Aisha ta zubawa ɗan mijinta guba a cikin
abincin data girka masa da hannunta? Da sauri Maryam ta girgiza kai tace "banga
sanda ta zuba ba amma tabbas itace ta girka da kanta kuma ta zuba masa da hannunta,
kusan a tare ma suka fara cin abincin seɗai ita nata ta zuba ganye sosai sabida
tanada ciwon siga. Alƙali ya sake kallon maryam a karona huɗu kimanin ƴan sakanni
yace "kenan itama irin abincin data zuba masan taci kenan ?

Da sauri maryam tace "ae raɓka ya daɗe shi taci hatta lemon dayashama itama shi
tasha, bayan sun gama ne na kwashe kwanukan Abinjin na tafi ina wankewa shine
naji ihunsa lokacin dana tawo daga kicin a tsaye naganta a kansa dukta rikice tama
rasa meya kamata tayi data ganni seta fara zuba ihu. Girgiza kai alƙali yayi
tareda maida kallonsa ga Hajiya Aisha wadda duk tabi ta fita haiyacinta bakinta
dukya bushe sabida rashin cin abinci yace " Aisha kinada ja akan abinda maryam ta
faɗa akanki?

Girgiza masa kai tayi tace " a'a banida abin faɗa akai komai ta faɗa gaskiya ne a
kaina nice na zuba masa guba da hannuna don yaci ya mutum sabida bana ƙaunarsa ko
dedai da ƙwayar zarra Ranka shi daɗe don haka kawai ka yanke min hukunci dedai da
laifina!!! Ta faɗa a lokacin da idonta ya sauka cikin na Abie
Gabaɗayansu seda kalamanta suka girgizasu musamman ma Abie da Muzaffar waƴanda
suka kafera da tsimammun idanunsu sabida tsabar kaɗuwa, wasu zafafan hawaye ne suka
zubowa Abie lokaci guda sabida baƙin cikin kalaman Ummie, meyasa Aisha zatayi masa
haka? Matar dayasi fiyeda ko wace mace a doron ƙasa bayan iyayensa sabida sonda
yake mata har yanzu baya samun bacci sabida tunnain halinda take ciki dukda irin
abinda ta aikatawa gudan jininsa hakan besa yaji cewar ze iya musanya sonda yake
mata da ƙiyayya ba amma yau itace take iya firta wannan kalaman na cewar ta tsani
ɗanda ya haifa a cikin babu ko kara balle kunya? Kawar da kansa gefe Abie yayi
yana me share hawayensa don bayaso iyalansa su fuskanci gazawarsa ta ko ina

Shikam muzaffar sam ya kasa yarda da abinda Ummie ta faɗa don tunda ya shigo falon
suka haɗa ido beta ƙara kallon inda yake ba, so yake ta kalleshi donya gano gaskiya
abinda ke ranta ta silar ƙwayar idonsa Amma kuma sam taƙi bashi wannan damar dole
ya haƙura shima amma still idanunsa nakan matar, mom kuwa farin ciki ne ya cika
zuciyarta ko banza yau Aisha zataga ƙarshenta a sakamakon yunƙurin kashe mata ɗa.

Alƙali yace "abisa shedu da kuma amsa laifinta da mai lefi tayi vatareda tabawa
kotu wahala ba wannan kotu ta yankewa Aisha Abdurrahman hukuncin shekara goma sha
biyar a gidan yari sakamakon yunƙurin kashe Muzaffar Abdulwahab Abdullah datayi.
Alƙali ya faɗi hakan yayinda yake ƙoƙarin buga gudumar tabbatar da hukunci kamar
daga sama sukaji ance "tayaya kuke tsammanin cewa Uwa zata iya kashe ɗanda ta haifa
da cikinta??

Juyowa sukai gabaɗayansu suna kallon babbar ƙofar falon don ganin wanda yayi
maganar........

Comment
Nd
Share

Sushmah💋
[3/3, 5:36 PM] Chubado Mohd: ❄️❄️❄️❄️❄️❄️
❄️❄️❄️❄️❄️❄️
🐄🐄🐄🐄
🐄🐄🐄🐄
*BAFULATANA*
✨RETURN✨
🐄🐄🐄🐄
🐄🐄🐄🐄
❄️❄️❄️❄️❄️❄️
❄️❄️❄️❄️❄️❄️

Page :29

*_WRITING BY: CHUBAƊO_*


___✍️BABA HAJARA ce ta shigo falon tana ɗingisa ƙafarta harta iso tsakiyar falon
idonta nakan Ummi sannan ta nemi guri ta zauna tana sauke numfashi ta kalli alƙalin
tace "kamar yanda kaji n akatse ka a yayinda kake yunƙurin tabka kuskure a cikin
hukuncinka to haka maganar take Ranka ya daɗe, taya kake tsammanin cewa Uwar data
tsuguna ta haifi ɗa da cikinta zata iya kasheshi ta hanyar zuba masa guba a cikin
abincin cinsa kamar yanda binciken ku da hasashenku ya kama Aisha dumu-dumu dashi?

"don girman Allah Baba Hajara karkiyimin haka ki tuna irin girman alƙawarin dake
tsakanina dake cewar zaki riƙemin Amana akan wannan sirrin Baba bamuyi dake zaki
faɗeshi ga kowa ba duk rintsi duk wuya kum......."kiyi gaƙuri Aisha amma kunnuwana
da idanuna bazasu taɓa iya jurar ganin gudan jininki da mahaifinsa suna yi miki
kallon muguwa ba, dole ne yau na baiyana wannan sirrin ga kowa koda kuwa zaki
cigaba dayimin kallon mace mara riƙon amana da kuma rashin martaba alƙawari muddin
zaki fita daga cikin wannan jarrabawar da kike ciki. Baba Hajara ta faɗi hakan
yayinda hawaye ke zubo mata

Alƙaline ya sauke ajiyar zuciya yace "Baba wacece ke? Shin kema kinada alaƙa da
wannan case ɗinne kokuwa?

Da sauri Baba Hajara tace "tabbas ranka ya daɗe inada alaƙa da wannan case ɗin
wanda kuma nake da tabbacin cewar mukullin warware wannan case ɗin ma kusan a
hannuna yake don haka idan ka bani dama yanzu zan warware muku komai a gabanka
inyaso bayan na gama seka yankewa Aisha hukunci kamar yanda ka fara daga farko.
Sosai Ummie ta tsananta kukanta tace "kiyiwa girman Allah karki buɗe wannan sirrin
da muka rufe wanda babu wanda yasanshi dagani seke Baba Hajara, kada ki kasance a
cikin mutane marasa riƙon Amana da alƙawari wllh nina zuba masa guba da hannuna
donyaci ya mutu kuma nayi hakanne sabida ƙiyayyar danake masa, kada ki baiyana
wannan sirrin don baze taɓa canza komai ba Baba Hajara don girman Allah!!!!!
Ummie ta faɗi hakan tana kallon tsakiyar ƙwayar idon Baba Hajara tana kuka.

Wata uwar tsawa Mom ta daka musu tace "kai karku maidamu ƴan iska a nan gurin ku
zaunar damu kuna shirya mana wasan kwaikwayon yaudara da rainin hankali, lallai
Hajara na yarda rikicin tsufa ya fara taɓa ƙwaƙwalwarki shiyasa kike magana irinta
marasa hankali da tunani, ɗan nawa zaki dinga dangantawa da wannan Azzalumar juyar
matar bayan ina numfashi a doron ƙasa?

Shidai muzaffar gabaɗaya ya zama kamar wani mutum-mutumi sabida tsabar ruɗani da
kuma ɗaurewar kai, zuwa yanxu ya fara tunanin cewar wata ƙila mafarki yakeyi ba
zahiri bane yasa wannan abin me kamada tatsuniya yake faruwa a gurin. Shi kansa
Abie binsu kawai yake da kallo daga mom ɗin har Ummie da Baba Hajarar batareda ya
iya firta koda kalma ɗaya ba sabida ruɗani. Bakajin komai se hayaniyar mom dukta
bi ta ƙanƙame muzaffar sekace wata zararriya tana zuba surutai wai babu wanda ya
isa ya rabata da ɗanta wllh hakanne yasa Alƙali ya daka mata tsawa ba shiri ta
tsuke bakinta still tana ƙanƙame da hannun muzaffar tana kuka

Sannan Alƙali ya kalli Baba hajara yace "ci gaba muna sauraronki kafin nan muna
buƙatar jin cikakken sunanki

Ɗan jim tayi sannan tace "Sunana Hajara Ɗanladi kuma ni mutuniyar kano ce ƴar
Asalin Unguwar kabara. Alƙali ya ɗanyi rubuce-rubucensa sannan ya ɗago yace "meye
hujjarki na cewa Aisha bazata iya kashe ɗan mijinta ba?

"hakane ranka ya daɗe kamar yanda na faɗa da farko cewar Aisha baxata iya kashe
muxaffar ba to haka maganar take sabida itaɗin Mahaifiyarsa ce wannan dalilin yasa
na faɗin hakan ranka ya daɗe. Alƙali yace meye hujjarki na cewar muzaffar ɗan
Aisha ne?

Kallon Ummie Dake kuka Baba tayi sannan ta kalli Alƙali tace "tabbas nikeda
cikakkiyar hujjar dazan tabbatar maka da cewar Aisha itace mahaifiyar wannan yaro.
Gaba ɗaya falon suka zuba mata idanu suna kallonta ciki kuwa harda mom wadda itama
take kuka kamar bazata dena ba hannunta damƙe cikin na muzaffar suna sauraron baba
don siji jawabin dazata gabatar.

Baba Hajara ta fara magana kamar haka👇

"Shekaru 35 da suka wuce a shekarar 1985 lokacin ban daɗe da fara aiki a gidan
Alhaji Abdulwahab Abdullah ba, lokacin matarsa Aisha tana Amarya a lokacin bazatafi
shekara 18 a duniya ba
[3/3, 5:36 PM] Chubado Mohd: ❄️❄️❄️❄️❄️❄️
❄️❄️❄️❄️❄️❄️
🐄🐄🐄🐄
🐄🐄🐄🐄
*BAFULATANA*
✨RETURN✨
🐄🐄🐄🐄
🐄🐄🐄🐄
❄️❄️❄️❄️❄️❄️
❄️❄️❄️❄️❄️❄️

*_Page :29 to 30_*

*_WRITING BY: CHUBAƊO_*

Banyi Editing ba kuyi haquri da typing Error pls

___✍️BABA HAJARA ce ta shigo falon tana ɗingisa ƙafarta harta iso tsakiyar falon
idonta nakan Ummi sannan ta nemi guri ta zauna tana sauke numfashi ta kalli alƙalin
tace "kamar yanda kaji n akatse ka a yayinda kake yunƙurin tabka kuskure a cikin
hukuncinka to haka maganar take Ranka ya daɗe, taya kake tsammanin cewa Uwar data
tsuguna ta haifi ɗa da cikinta zata iya kasheshi ta hanyar zuba masa guba a cikin
abincin cinsa kamar yanda binciken ku da hasashenku ya kama Aisha dumu-dumu dashi?

"don girman Allah Baba Hajara karkiyimin haka ki tuna irin girman alƙawarin dake
tsakanina dake cewar zaki riƙemin Amana akan wannan sirrin Baba bamuyi dake zaki
faɗeshi ga kowa ba duk rintsi duk wuya kum......."kiyi gaƙuri Aisha amma kunnuwana
da idanuna bazasu taɓa iya jurar ganin gudan jininki da mahaifinsa suna yi miki
kallon muguwa ba, dole ne yau na baiyana wannan sirrin ga kowa koda kuwa zaki
cigaba dayimin kallon mace mara riƙon amana da kuma rashin martaba alƙawari muddin
zaki fita daga cikin wannan jarrabawar da kike ciki. Baba Hajara ta faɗi hakan
yayinda hawaye ke zubo mata

Alƙaline ya sauke ajiyar zuciya yace "Baba wacece ke? Shin kema kinada alaƙa da
wannan case ɗinne kokuwa?

Da sauri Baba Hajara tace "tabbas ranka ya daɗe inada alaƙa da wannan case ɗin
wanda kuma nake da tabbacin cewar mukullin warware wannan case ɗin ma kusan a
hannuna yake don haka idan ka bani dama yanzu zan warware muku komai a gabanka
inyaso bayan na gama seka yankewa Aisha hukunci kamar yanda ka fara daga farko.
Sosai Ummie ta tsananta kukanta tace "kiyiwa girman Allah karki buɗe wannan sirrin
da muka rufe wanda babu wanda yasanshi dagani seke Baba Hajara, kada ki kasance a
cikin mutane marasa riƙon Amana da alƙawari wllh nina zuba masa guba da hannuna
donyaci ya mutu kuma nayi hakanne sabida ƙiyayyar danake masa, kada ki baiyana
wannan sirrin don baze taɓa canza komai ba Baba Hajara don girman Allah!!!!!
Ummie ta faɗi hakan tana kallon tsakiyar ƙwayar idon Baba Hajara tana kuka.
Wata uwar tsawa Mom ta daka musu tace "kai karku maidamu ƴan iska a nan gurin ku
zaunar damu kuna shirya mana wasan kwaikwayon yaudara da rainin hankali, lallai
Hajara na yarda rikicin tsufa ya fara taɓa ƙwaƙwalwarki shiyasa kike magana irinta
marasa hankali da tunani, ɗan nawa zaki dinga dangantawa da wannan Azzalumar juyar
matar bayan ina numfashi a doron ƙasa?

Shidai muzaffar gabaɗaya ya zama kamar wani mutum-mutumi sabida tsabar ruɗani da
kuma ɗaurewar kai, zuwa yanxu ya fara tunanin cewar wata ƙila mafarki yakeyi ba
zahiri bane yasa wannan abin me kamada tatsuniya yake faruwa a gurin. Shi kansa
Abie binsu kawai yake da kallo daga mom ɗin har Ummie da Baba Hajarar batareda ya
iya firta koda kalma ɗaya ba sabida ruɗani. Bakajin komai se hayaniyar mom dukta
bi ta ƙanƙame muzaffar sekace wata zararriya tana zuba surutai wai babu wanda ya
isa ya rabata da ɗanta wllh hakanne yasa Alƙali ya daka mata tsawa ba shiri ta
tsuke bakinta still tana ƙanƙame da hannun muzaffar tana kuka

Sannan Alƙali ya kalli Baba hajara yace "ci gaba muna sauraronki kafin nan muna
buƙatar jin cikakken sunanki

Ɗan jim tayi sannan tace "Sunana Hajara Ɗanladi kuma ni mutuniyar kano ce ƴar
Asalin Unguwar kabara. Alƙali ya ɗanyi rubuce-rubucensa sannan ya ɗago yace "meye
hujjarki na cewa Aisha bazata iya kashe ɗan mijinta ba?

"hakane ranka ya daɗe kamar yanda na faɗa da farko cewar Aisha baxata iya kashe
muxaffar ba to haka maganar take sabida itaɗin Mahaifiyarsa ce wannan dalilin yasa
na faɗin hakan ranka ya daɗe. Alƙali yace meye hujjarki na cewar muzaffar ɗan
Aisha ne?

Kallon Ummie Dake kuka Baba tayi sannan ta kalli Alƙali tace "tabbas nikeda
cikakkiyar hujjar dazan tabbatar maka da cewar Aisha itace mahaifiyar wannan yaro.
Gaba ɗaya falon suka zuba mata idanu suna kallonta ciki kuwa harda mom wadda itama
take kuka kamar bazata dena ba hannunta damƙe cikin na muzaffar suna sauraron baba
don siji jawabin dazata gabatar.

Baba Hajara ta fara magana kamar haka👇

"Shekaru 35 da suka wuce a shekarar 1985 lokacin ban daɗe da fara aiki a gidan
Alhaji Abdulwahab Abdullah ba, lokacin matarsa Aisha tana Amarya kuma bazatafi
shekaru 18 a duniya ba.

A lokacin Aisha bata da wayon dazata iya gabatar da wasu abubuwan na rayuwar gidan
mijinta da sauransu, wasu lokutan nike nuna mata yanda zatayi wasu abubuwan idaɓ
suka gagareta wannan dalilin yasa muka samu shaƙuwa sosai a tsakanina da ita dukda
cewar ni kawai me aikinta ce amma sam ita batayi min kallon haka kallon uwa ma
takeyi min

Sosai mijinta ke ƙaunarta kuma yake bata kulawa a haka har suka shafe shekara da
shekaru amma shiru Aisha babu labarin ciki a tareda ita, dukda hakan mijinta be
taɓa nuna mata damuwarsa akan hakanba hasali ma itace ke nuna damuwarta akan hakan
har suka shafe shekaru goma da Aure amma shiru babu maganar haihuwa, wannan dalilin
yasa Aisha ta da kanta ta tunkari mijinta Abdulwahab kan cewar lallai seya ƙara
Aure sabida tana iya yuwuwa itace bata haihuwar bashi ba.

A wannan ranar ba ƙaramin saɓani suka samu ba har seda na shiga maganar nai musu
nasiha sosai sannan suka daidaita a tsakaninsu sukaci gaba da zamansu kamar yanda
suka saba, wata ranar litinin Alhaji ya dawo daga Saudiya bayan ya dawo ne yake
sanar da Aisha cewar ya haɗu da wata budurwa a can kuma har cikin ransa yarinyar ta
kwanta masa don hkaa yana son Aurenta.
Dukda cewar maganar ta ɗan taɓata amma sam Aisha bata nuna masa a ba sema farin
ciki data tayashi tareda yi masa fatan alkhairi a cikin Auren nasa dazeyi, sosai
Yayi farin ciki da hakan tareda yiwa Allah godiya daya bashi mace me kima da
girmama buƙatar mijinta kamar Aisha. A wannan daren Aisha tayi kuka kamar ranta ze
fita sedai bata gazaba wajen gayawa Allah matsalarta cikin dare ba kan cewar ya
zaɓa musu abinda yafi zama alkhairi a cikin wannan lamari na auren da mijinta ze
ƙara, lokacin da Aisha ta sameni da zancen sosai na dingayi mata nasiha tareda
ƙara bata haƙuri akan ta ƙara danne zuciyarta insha Allah komai zeyi daidai.

Haka kuwa akayi Aisha tayi haƙuri taci gaba da sabgoginta har lokacin bikin ya
matso kuma akayi lfy batareda wata matsala ta taso ba, haka kuma Aisha bta gajiya
ba wajen bawa mjinta kulawa kamr yanda ta saba ba har Amarya Saratu ta shafe wata
guda cur a cikin gidan ba'a samu wata matsala ta kunno kai ba, seda tafiya tayi
tafiya sannan Saratu Amarya ta fara ɓullo da wasu mugayen halayenta a filli na
makirci, idan Alhaji yana gida seta san yanda tayi ta muzgunawa Aisha don kawai ta
kulata su raba abin faɗa sedai kawai tayi murmushi ta raɓa ta gefanta ta koma
ɗakinta, bayan wata uku da bikin Saratu da Alhaji alamun ciki suka fara baiyana a
jikin Saratu lokacin da ta fahimci ciki ne da ita ba ƙaramin faarin ciki tayi ba
don hka ta fara shimfiɗa fefan iskanci kala-kala shi kuma alhaji yana biye mata,
idan na dafa abinci setace ita sam ba nawa takeso ba girkin Aisha takeso dole haka
Aisha zata fito ta shiga kicin ta girka mata duk abinda takeso batareda ta canza
fuska ba ko kaɗan, idan na yunƙura zan taimaka mata setace na barshi ai abin cigaba
ne yazo musu itada mijinta da abokiyar zaman ta.

Tun daga lokacin Aisha ta zama itace me girkawa Saratu abinci tamkar baiwa ba matar
gida ba amma dukda hakan bata taɓa nuna damuwar ta ba sam

Wata ranar juma'a Aisha ta tashi da zazzaɓi me zafin gaske ranar Alhaji ba ƙaramar
rikicewa yayi ba amma ita saratu ko'a jikinta lokacin da alhaji ya ɗauketa mukaje
Asibiti gwajin farko ya nuna cewar Aisha na ɗauke da ciki kimanin wata 3 ashe duk
wannan uwar wahalar datakeyi nayiwa Saratu girki itama nata cikin na maƙale da ita
a jikinta batareda ta sani ba, murna a gurin alhaji ranar ba'a magana haka itama
Aisha harda ɗan kukanta a haka muka rankayo muka dawo gida fuskokin mu ɗauke da
farin ciki

Lokacin da Saratu ta samu labarin cikin jikin Aisha ba qaramin tashin hankali ta
shiga ba harta kasa ɓoye hakan a fuskarta amma dayake makirace seta nunawa Alhaji
farin cikinta a fili harda kukan ta na farin ciki wanda yafi kamada na munafunci,
amma kuma a zuciyarta ba ƙaramin baƙin ciki taji da hakan ba, har ɗaki tabi Aisha
ta sameta tace "hmmm naji ance kinyi ciki kema shiyasa naga se wani rawar kai kike
kina ƙara shigewa mijin namu ko? To wllh kiji kuma ki sani muddin ina numfashi ni
kuma bazan taɓa barin ɗanda kika haifa ya shaƙi iskar duniya ba Aisha don haka ki
rubuta ki Ajiye wannan!.

Wannan magana ta girgiza Aisha matiƙa tareda dasa mata tsoron saratu tun daga
lokacin ta shiga takatsantsan da duk wani abu daze haɗata da ita, a haka dai
sukaci gaba da rayuwar har naƙudar Saratu ta tashi gashi kuma Alhaji baya gari,
muda Driver ne muka kaita Asibiti Aisha kuma ta zauna a gida gabaɗaya abin duniya
duk ya isheta kasancewar dare ne, Saratu tasha wahala sosai kamar bazata kai
labari ba wannan dalilin ne ya haifar mata da jijjiga bayan ta haifi ƴarta mace
sankaceciya fara tass da ita sedai yarinyar batazo da Rai ba. Sosai na tausayawa
saratu dana tuna irin yanda take sanya rai akan ƴaƴa da kuma irin shirin datayiwa
haihuwar sedai ga abinda Allah ya aiko babu yanda muka iya

washe gari da safe na dawo gida don na duba halin da Aisha take ciki jikina a
masifar sanyaye tofa a nan ne na sameta akan gwiwa itama babu yanda take, tasha
wahala sosai haka kuma nabuga na raya da ita mutafi Asbiti amma fir Aisha taƙi sema
hannuna data rike gam cikin nata idanunta duk sun koɗe bakinta ya bushe ƙamas dashi
cikin yanayi na zafin ciwon naƙuta tace "Baba Hajara Saratu ta Sauka lfy?

Idanuna ne suka ciko da ƙwalla na kalleta nace "Ae ta sauka an samu ɗiya mace Amma
sedai yarinyar batazo da rai ba! Take gaban Aisha ya faɗi lokaci guda kuma
hawaye suka zubo mata na tausayin kanta a lokacin data tuna kalaman saratu a kanta
zatayi magana kenan wani irin nishi ya taso mata cikin ikon Allah itama Allah ta
haifi Sankacecen ɗanta fari tass dashi me kamada ubansa sak tamkar yayi kaki, tofa
a nan ne hankalin Aisha ya ƙara masifar tashi data lurada abinda ta haifa ɗin cikin
jini lokaci guda ta fashe da kuka tare kama hannaye na duka biyun tace "don girman
Allah Baba Hajara zan ƙoƙeki wata alfarma wadda ko bayan raina idan kikayi min ita
bazan taɓa manta alkhairin ki a gareni ba, kin sani na sani muddin saratu ta farka
tasan ɗiyarta batazo da rai ba tabbas bazata barmin ɗana ya rayu cikin sa'ada ba,
Allah ya sani ina matiƙar son ɗana irin son da ban taɓa yiwa wata halitta
kwatankwacinsa ba don hkaa bazan juri ganin wani abu ya sameshi ba, shiyasa na
yanke shawarar musanyawa Saratu abinda ta haifa da ɗana na cikina inyaso ni sena
ɗauki tata tunda dama can batazo da rai ba kinga kenan kota farka nasan zata
ƙaunaci ɗan kishiyarta ƙauna me tarin yawa tayanda bazara taɓa jurar ganin wani abu
mummuna ya sameshi ba, saɓanin in barshi a hannuna ta farka ta ganshi kuma ta
dingayi masa kallon maƙiyi.

Wllh baba Hajara zuciyata bazata iya jurar ganin ɗan dana haifa yana fuskantar wata
rayuwa ta ƙiyayya daga abokiyar zamana ba da hakan ta faru dashi gara na bar mata
shi har abada tayanda zata ɗingayi masa kallon ɗa har ranar da zanbar duniya!!!!!.
Wannan alfarmar kawai nakeso kiyi min Baba Hajarah idan har bakiyi min ba har
Saratu ta farka wani abu ya samu gudan jinina to wllh har abada zanyi dana sani
akan haɗuwata dake.

Kuka na dingayi tareda ɗaga yaron na sanyashi cikin zani kuma na gyarashi tsaf
dashi itama Kuma Aisha na gyarata sannan ta kalleni tace" Baba Hajara kawoshi na
ganshi. Ba nusu na miƙa matashi ta karɓa ta ƙura masa idanu tana kallonsa yaron se
tsotsar hannunsa yake sabida yunwar dayake ji wata irin ƙaunarsa ce take ratsa duk
wata gaba ta jikinta. Ba shiri ta zaro Nono fara bashi tana kuka har yaron ya
ƙoshi sannan ta zare ta miƙa minshi batareda ta kuma kallonsa ba tace kiyi sauri
Baba kikaishi tun kafin mutane su fara taruwa.

A haka na karɓeshi na tafi dashi Asibitin cikin ikon Allah kuwa bansha wahala ba
naje na musanya mata sannan na ɗakko gawar jaririyar na fito da ita ba tareda wani
ya ganni ba na kawowa Aisha sannan na kira Alhaji na sanar dashi cewar matansa sun
haihu Aisha ta haifi mace amma yarinyar batazo da rai ba, Saratu kuma ta haifi ɗa
namiji suna cikin ƙoshin lfy.

Wannan labari sam beyiwa Alhaji daɗi ba amma sam babu yanda ya iya da abinda Allah
ya aiko dole ya karɓa kuma yayi godiya.

Vayan saratu ta samu Lfy an sallamota daga Asibitin ba'ayi taron suna ba Alhaji da
kansa ya bawa Aisha zaɓi kanta zaɓawa ɗansa suna shine ta sanya masa suna muzaffar,
ranar ba ƙaramin bala'i aka kwasa ba seda alhaji yayiwa saratu da gaske sannan ta
shiga taitayinta akan Aisha wannan shine maƙasudin tsanar da Saratu tayiwa Aisha,
a haka aka dinga rayuwa a gidan da daɗi babu daɗi.

Wasu lokutan idan Saratu ta shiga wanka har ɗakinta Aisha ke shika kasancewar tana
jimawa a banɗaki idan tana wanka se Aisha ta ɗauki muzaffar ta bashi nono harse ya
ƙoshi sannan zata ajiyeshi ta fice da sauri. Kasancewar Saratu bata da ruwan nono
me kyau yasa likitansu yace sam karta bashi nono se madara wannan dalilim yasa
Saratu bata taɓa shayar da muzaffar ba.
A haka ta ɓarauniyar hanya Aisha ta dinga shayar da muzaffar har tsahon watanni
biyar batareda Saratu ta sani ba a haka har har Allah ya kawo hatsaniyar data
kaure a tsakanin Aisha da Saratu harta kaisu ga faɗa tofa a washe garin ranar ne
Alhaji yasa aka samowa Aisha me aiki wadda zasu tafi india tareda ita shine aka
samo mata Maryamu, a daren da zasu tafi Aisha tayi kuka kamar ranta ze fita tareda
kamo hannuna tace " Baba Hajara ga Amanar ɗana nan don Allah ki sanya ido akansa
karki barshi yayi duk wasu abubuwan dazasu kawo cikar ga tarbiyarsa sannan kuma abu
na ƙarshe shine ki riƙemin amanar sirrina, a haka suka tafi tare maryamu muna masu
kewar juna.

To Alƙali kaji gaskiyar abinda ya faru kai a radin kanka kana ganin cewar wannan
uwar data daɗe tana begen ɗanta zata iya ɗaukar guba ta zuba masa a cikin abincin
don kawai ta kasheshi??

Gabaɗaya falon shuru ya ɗauka aka rasa wanda zece ƙala.

Sannan Ummie ta fara magana tace"..............

Comment
Nd
Share

Sushmah💋
[3/3, 5:36 PM] Chubado Mohd: ❄️❄️❄️❄️❄️❄️
❄️❄️❄️❄️❄️❄️
🐄🐄🐄🐄
🐄🐄🐄🐄
*BAFULATANA*
✨RETURN✨
🐄🐄🐄🐄
🐄🐄🐄🐄
❄️❄️❄️❄️❄️❄️
❄️❄️❄️❄️❄️❄️

Page :31

*_WRITING BY: CHUBAƊO_*

*_Wannan shafin sadaukarwa ne ga dukkan masoya wannan littafi me taken BAFULATANA


RETURN, waƴanda na sani da waƴanda ma ban sansu ba ina roqon Allah ya Amintar da
zukatanmu zuwa gareshi sonso fisabilillah🥰_*

*_Bafulatana fans group ina gaisheku kyauta batareda kun biya ba ina ganin comment
ɗinku sosai i really appreciate it sonso fisabilillah Kuma🥰_*
___✍️ Na kasance Uwa mara adalci ga ɗanta tunda har na iya aikata hakan ga ɗana
guda ɗaya tillo wanda dagashi har yau Allah be sake bani haiyuwa ba, sedai banyi
hakan don bana ƙaunarsa ba hasali ma nayi hakanne sabida tsananin kaunar danakeyi
masa sakamakon iƙirarin da Saratu tayi min na cewar muddin tana numfashi a doron
ƙasa bazata taɓa bari abinda na haifa ya rayu ba, tunda ta gayamin hakan na rasa
duk wani kwanciyar hankali a rayuwata har zuwa ranar dana Haifi abinda ke cikina, a
wannan ranar ne na yanke hukuncin danake ganin shine mafita a gareni da kuma abinda
na haifa bisa taimakon Baba Hajarah, ko wace Uwa abinda nayi shi zatayi da wannan
damar na sanya Saratu ta Raini ɗanda na haifa da cikina tared duk wata soyayyah
saɓanin mugun nufin datayi niyar aikatawa akansa, na tabbata da ace tasan da hakan
seta cika burinta a kansa kamar yanda ta ƙuɗurta ɗin. Ummie ta faɗi hakan
yayinda take ɗago jajayen idanunta tana kallon Abie dasu.

"Kutumar Uba wllh baku isa ba Aisha daga ke har wannan ƙasurgumar munafuƙar
tsohuwar da bata san darajar shekarunta ba, Na rantse da Allah banga uban daya isa
ya rabani da ɗana ba koda kuwa wayeshi... Mom ta faɗi hakan tana wani irin huci
kamar macijiya, tareda ƙara ƙanƙame hannun muzaffar wanda kw zune kamar an dasashi
sabida tsabar tashin hankali, gaba ɗaya jin maganganunsu yake tamkar almara wani
irin zafi yakeji zuciyarsa nayi masa tareda wani irin baƙin ciki dake taso masa
wanda ya rasa na menene, sosai idanunsa suka kaɗai sukai ja lokaci gud kuma
jijiyoyin jikinsa duk suka mimmiƙe tamkar wanda ke shirin shiga filin dambe

Abie kuwa kallon Ummie kawai yakeyi take wasu irin hawaye masu masifar ɗumi suka
fara zubo masa, lokaci guda kuma nadamar abinda ya aikatawa Ummien ta shiga
kwaranya a duk wani saƙo da lungu na zuciyarsa.

Sabida ɗaurewa da kawunan mutanan dake falon yayi yasa alƙali ya bada umarnin Ummie
da muzaffar da mom suje suyi DNA TEST don a tabbatar da nau'ikan ƙwayar halittar
waye a jikin muzaffar ɗin sannan suzo da sakamakon ranar dazasu sake zama a kotun
sirrin. Sakamakon ɗage wannan zama da akayi ne yasa Abie ya buƙaci da a bashi
belin Ummie daƙyar Alƙalin ya amince sannan ya bada belinta suka wuce gida zuciyar
kowa a dagule kuma babu daɗi.

Tunda suka taho a mota mom ke kuka irin kukan nan me cikeda tashin hankali gamida
tsantsar damuwa, Fadilah kuwa kallonta kawai takeyi tama kasa rarrashinta sabida
tsaɓar mamaki da kuma ɗaurewar kan datake ciki a gameda wannan fitinar data taso
musu a haka jerin motocin suka iso cikin hamshaƙiyar unguwar tasu.

Abie na cikin motar da Ummie take tareda Baba Hajarah bakinsa na Rawa yace "Aisha
me......" don girman Allah ka ƙyaleni Abdul I don't want to talk you please. All I
need now is to rest so leave me alone don girman Allah. Ummie ta faɗi hakan
lokacinda idanunta ke kawo ƙwallah wadda tafi kamada ta zallar baƙin ciki da
takaici.

A nitse motocin suka faka sannan kowa ya sakko, ko kaɗan mom bata tsaya a gurin ba
ta nufi inda Muzaffar ke tsaye ta wani kama hannunsa suka shige cikin gida still
tana kuka kamar wata mahaukaciya, itadai Ummie da ido kawai ta bita har suka shige
sannan ta ɗaga jajayen idanunta tana kallon ɓangarenta a lokacin datake gidan,
hannun Baba hajara ta kama Maryamu tana biyeda ita suka nufi ɓangaren nata dukda
bata da tabbacin a gyare yake sukabar Abie nan a tsaye kamar wanda aka dasashi a
gurin.

Gabaɗaya tunanin duniya ya gama isarsa komai ya dagule masa kamar zeyi kuka ya
zauna dirshan a ƙasan haɗaɗɗen interluks ɗin dake shimfiɗe a ƙasa kamar an bada
hannu aka shiryasu ba sabida tsaruwarsu, gabaɗaya tunanin duniya yay masa yawa
yama rasa mezeyi yaji daɗi a halinda yake ciki yanzu so yake kawai yay kuka amma
sam ya kasayin hakan, ya jima a gurin zaune cikeda Rashin sanin makama da Abinyi
sannan ya miƙe ya isa side ɗinsa ya zuɓe a makeken gadonsa yana tunanin ta yanda ze
shawo kan Aisharsa.

Ɓangarensu Ummie kuwa sosai tayi mamaki da ganin yanda aka ƙawata mata komai na
ɓangaren nata, duk da cewar ta shafe shekaru masu yawa bata ƙasar an canza komai an
zuba mata na zamani masu jaraban kyau gamida tsada komai na cikin falon expensive
abu ne har zuwa bedroom ɗinta, ɗaya ɓangaren ta nunawa su Baba Hajara tace "ku
shiga can ku zauna nan ne ze zama part ɗinku. Tana gama faɗin hakan ta wuce ɗaya
ɗakin ta buɗe sam bata tsaya bin ɗakin da kallo ba ta faɗa toilet don mugun
ƙyanƙyamin kanta takeji ba kaɗan ba.

Ta jima tana wankan sannan ta ɗauro Alwala ta fito ɗaure da wani ƙaton towel wanda
ya saukar mata har idon sawun ƙafarta, gaban mudubi ta zauna tareda zubawa kanta
idanu lokaci guda kuma ta fashe da wani irin kuka har lips ɗinta na rawa sabida
yanda take kukan.

Mom kuwa tunda ta shiga falon bata dire ko inada Muzaffar ba se bedroom ɗinta
zaunar dshi tayi a babban dogon soofer ɗin dake ɗakin tareda zama a ƙasa tana
facing ɗinsa tareda damƙe hannayensa ta fashe da wani irin kuka tace "Na shiga uku
yarona wllh so suke kawai su rabani dakai don sunga banida abinda na mallaka sekai
a duniya tareda sauran ƙannenka, wllh nasan ƙarya Aisha takeyi mana kawai tanaso
ta ɓullo da wani abu ne wanda zesa ta ɓoye laifinta na yunƙurin kashe ka i know
that tun ba yauba cewar Hajara Munafukar tsohuwace so take kawai ta kawo mana
ruɗani, pls boy karka bari maganarsu ta shiga cikin kanka wllh I'm your biological
mother!!!!!. Ta faɗa tana ƙara rushe masa da kuka

Gabaɗaya jinya kawai yake inda gefe guda na zuciyarsa ke cike taf da wani irin
tausayin mom ɗin, jnayota yayi jikinsa ya rungumeta yanaji saukar hawayenta a gadon
bayansa.

*******

Rabe ce zaune a tsakiyar makeken gadon Zeeyadah tana kuka tashi zeeyadah tayi
idanunta fal da bacci tana kallonta kamar zatayi kuka don takaici tace "meye kuma?
Haɗiye kukan Rabe tayi cikin sanyinta tace "Babana!. Daga haka bata sake cewa komai
ba donharga Allah bata da isashshen hausar dazatayi mata bayanin abinda ke damun
nata na mafarkin Mahaifinta datayi harya sata kuka.

dafa kafaɗunta Zeeyadah tayi tace "kiyi haƙuri kinji insha Allah komai zeyi daidai.

Kwanciya sukai har bacci ya sake ɗaukar zeeyadah still Rabe idonta biyu, jikinta a
mace ta miƙe tanabin ko inada kalli musamman ma ƙwan fitilar dake ɗakin wanda kalar
hasken dake jikinsa ya rikiɗe zuwa blue colour daidai na bacci, ta jima tana
kallon ƙwan fitilar sannan ta buɗe ƙofar ɗakin daƙyar ta fito sabida wani irin
masifan ƙishirwa datake ji, a gaban dispenser ɗin dake falon ta tsaya tareda
tsugunawa ta zuba mata idanu tana kallon ruwan dake cikin dogon roban jikin
dispenser ɗin, kama robar tayi da ƙarfin tsiya zata cire tasha ruwan se uban haki
take amma ko gezau roban ruwan beyi ba, fashewa tayi da kuka tana dukan dispenser
ɗun da hannayenta a nitse taji an buɗe ƙofar ɗakin dake bayanta

Da sauri ta juya tana kallon ƙofar da ake ƙoƙarin buɗewar, Hajar ce ta fito tana
zuba uwar hamma da alama itama Ruwan ta fito sha tsayawa tayi cak yayinda idanunta
suka sarƙe cikin na Rabe nan take ta ƙwalla ƙara me matiƙar firgitarwa

Rabe dake tsaye gashin kanta dukya baje a gadon batanta itama ihun ta saki kankace
me tuni mutanan gidan kowa ya fito falon a tsorace jiki na Rawa.
Edyan na ƙarasowa gurin Rabe ta ɓoye a bayansa tana rarraba idanu tana kallon Hajar
wadda ta ƙanƙame mom tana faɗin "waiyyo mom Aljana na gani wllh mom Aljanace. Tsaki
mom ta saki tace "dilla malama ki nutsu ba wata aljana wannan ce fa uhmm. Se kuma
mom tayi shiru sabida sam batasan Sunan dazata kira Raben dashi ba becouse batasan
sunan ta ba har yanzu bata gaya musu ba.

zarota yay daga bayansa yace "look ba abinda zata miki kinji just feel free with
her ok? Ƙura masa idanu tayi tana kallonsa babu ko ƙiftawa hure mata idon yayi da
iskan bakinsa dole yasa ta sunkuyar da kanta bajajjen gashinta ya rufe mata fuska
kamar zatai kuka ta turo baki tace "miyara diyam.

Kafeta sukai gabaki ɗayansu da idanu suna mamakin yanda tayi magana a karon farko
tun zuwanta gidan, wani irin murmushi Edyan ya saki ya kalli mom yace "what did
she say ?

Ajiyar zujiya mom tayi lokaci guda kuma yanayinta ya sauya tace "she said that she
want to drink water. Edyan yace "wow i like Fulani language wllh mom and then
what should we call her as her name mom?

Ɗan jim kaɗan mom tayi tareda faɗin ban saniba Edyan, caraf zeeyada tace "mu dinga
kiranta ihsan yaya. Taɓe baki yayi yace "no let us call her Mulaikha. Ya faɗa yana
kallon tsakiyar ƙwayar idanunta ta cikin dogon gashinta dayayi mata rumfa yace "as
from today your name is Mulaikha kinji?

turo baki tayi alamar bata ma san meyake faɗa ba dariya yayi me sauti tareda janye
gashin dake saman fuskarta baƙi wuluk dashi yace "daga yau sunan ki mulaikha ne
har zuwa ranar dazaki faɗa mana sunan ki na gaskiya kinji? ..... Kamar daga sama
yaji tace "miyara diyam.

cup ya ɗauka ya murɗo mata ruwan a dispenser ɗin sannan ya miƙa mata ta kafa kai ta
fara sha batareda ta sauke ba........

comment
Nd
share

Sushmah💋
[3/3, 5:37 PM] Chubado Mohd: ❄️❄️❄️❄️❄️❄️
❄️❄️❄️❄️❄️❄️
🐄🐄🐄🐄
🐄🐄🐄🐄
*BAFULATANA*
✨RETURN✨
🐄🐄🐄🐄
🐄🐄🐄🐄
❄️❄️❄️❄️❄️❄️
❄️❄️❄️❄️❄️❄️

Page :32

NOT EDITED

*_WRITING BY: CHUBAƊO_*


___✍️ Zeeyadah ya kalla yace "go and bring Ribom for me pls wannan gashin nata
yayi yawa ai duk yabi ya takurata. da sauri zeeyadah ta juya zuwa ɗakinta ta ɗakko
ribom ɗin a cikin nata ta kawo masa

Dogayen hannayensa ya miƙa ya haɗe mata gashin gabaɗaya guri guda ya ɗaure mata se
faman yamutsa fuska take alamar tanajin zafi, tsaki Hajar ta saki ta kalli mom
tace "who is this girl please mom? Dubi fa yanda ta wani zo ta bawa mutane tsoro
da wannan shegen farin fuskan nata kamar aljanah, wllh mom taci sa'a darene yanzun
dasena falla mata mari. Ta faɗa tana shigewa ɗakinta tareda bunko ƙofar da wani
irin ƙarfi sabida haushi

Shiru Edyan yayi yana bin ƙofar ɗakin Hajar ɗin da kallo sannan yay murmushi bece
komai ba ya miƙe yabar falon kama hannunta zeeyada tayi tana kallon fuskarta wadda
wani lumsashshen baƙin gashi yayiwa ado bisa goshinta tace "muje ba musu tabi
bayanta tana murza idanunta da ɗaya hannunta.

Da ido mom tabisu a ranta tanajin wata irin ƙaunar yarinyar gamida tausayinta suna
ratsa duk wata gaba ta jikinta, sosai takejin yarinyar a kusa da zuciyarta wata
ita kanta batasan dalilin hakan ba.

Washe gari da safe Zeeyadah ta shirya cikin Uniform ɗinta milk and cofee colour
ƙafarta sanye cikin wata farar socks da bakin takalmi, ƙura mata idanu Rabe tayi a
ranta tana girmama irin shigar dataga Zeeyadahn tayi turo baki tayi a ranta tace
"kai amma wanna bata da kunya dubeta duk jikinta a waje.

Juyowa zeeyadah tayi suka haɗa ido da sauri Rabe ta sauke kanta ƙasa tana wasa da
dogayen yatsun hannunta, murmushi ta saki sannan ta tako zuwa kusa da ita tace
"Mulaikha why are you looking at me like that uhm? Kina son wani abu ne? .
Zeeyadah ta jera mata tambayoyin a lokaci guda

Ƙara turo mata ɗan ƙaramin bakinta tayi still her eyes on her face batareda tace
komai ba, ajiyar zuciya Zeeyadah ta saki tace "ok barina tafi school sena dawo ta
faɗi hakan tana hugging nata with so much love irin na fisabilillah ɗinnan.

Dagalo tayi tana kallonta harta fice daga ɗakin bata jina da fita ba mom ta shigo
ɗakin da sauri ta ɗago fararen idanunta tana kallon Mom ɗin wadda itama ɗin take
kallonta, sauke idanunta mom tayi da sauri a ranta tanajin cewar tabbas tasan wani
me irin idanun yarinyar but she can't remember, murmushi ta ƙaƙalo ta kalleta cikin
harshen Fulatanci tace mata " taso muje kici abinci ki shiya Edyan idan ya fito ze
kaiki makaranta kema. Ƙurawa mon idanu tayi mamaki kwance akan fuskarta ta buɗe
baki itama cikin Harshen Fulatanci tace "dama kinajin Fulatanci?

Murmushi mom kawai tayi tareda kama hannunta suka fita zuwa falo, Tea me bala'in
kauri mom ta haɗa mata tareda zuba mata soyayyen dankali a gefan flet kaɗan se kuma
pride egg shima a gefe. Wani flet ɗin mom ta jawo ta zuba mata pepe soup ɗin kaza
a ciki wanda yaji uban kayan ƙamshi se baza ƙamshi yakeyi ta tura mata shi gabanta
tace " maza ki cinye ki bani flet ɗin.

Shiru tayi tana bin abincin da kallo wanda a iya Rayuwarta sam bata taɓa cin karoda
irinsa ba se a wannan rana, babban Abinda ya bata mamaki gamida ɗaure mata kai
shine yanda taga kwanon abincin fari tas dashi kamar madubi"kamar zatayi kuka ta
kalli mom cikin harsheta na fulatanci tace "taya mutum zeci abinci a cikin mudubi
irin wannan ? Nikam gaskiya inajin tsoro kar wani abu ya faru dani yayinda nakecin
abincin a cikin kwanon.

Dariya mon tayi tareda shafa tumulin gashin dake kanta tace "karki damu babu abinda
zai faruda ke kedai kawai kici abincin ki. Kwanon ta ɗaga sama tana wani leƙa
ƙasansa se kuma tasa ɗayan hannunta ta shafo ƙasan flet ɗin da pepe soup ɗin ke
ciki ta kai bakinta a tunaninta romon ze fito ta bayan kwanon. A haka Hajar ta
fito daga ɗakinta cikin wata doguwar rigar material me azabar kyau gamida bin jiki,
sosai kayan suka karɓi jikinta abinka da ƴar ƙwalisa. Lol a yangance take
takunta irin na mata masu jida kansu hannunta ɗaukeda wayarta ƙirar Iphone, tun
daga nesa take kallon Rabe tana wani yamutsa fuska harta zo ta bayanta zata Raɓa ta
wuce zuwa inda mom take, wayar hannunta ce ta fara Ringing wanda hakan yazama
tamkar wani abu na daban a kunnuwan Rabe, sosai ta gigice dajin ƙarar wayar take
hannunta ya fara rawa lokaci guda kuma juya bayanta tareda saki flet ɗin dake
hannunta sabida yanda ta tsure take romon naman ya sheƙewa hajar a
jikinta.........

Wata uwar tsawa Hajar ta daka mata wadda tasa gaba daya ta fice daga sauran
nutsuwar data rage mata se kawai ta fashe da kuka, gadan-gadan Hajar ta nufeta
da nufin ta watsa mata wani lafiyayyen mari Mom ta riƙeta gam lokaci guda kuma ta
watsa mata wani lafiyayyen mari wanda seda taga wasu kyawawan taurari nayi mata
yawo a tsakiyar kanta, cikeda ɓacin rai mom tace " Hajar meyake damunki ne ? Anya
kuwa kina cikin haiyacin ki? To don uwarki da kika nufeta me kike shirin yi mata da
kika nufeta gadan-gadan bayan tsorata tan da kikayi?

da sauri mom ta ƙarasa gareta tana faɗin "I'm sorry my baby girl kukan ya isa haka
nan kinji ko? Ta faɗa tana janyota jikinta tareda rungumeta . Kuka kawai Rabe
keyi gabaɗaya duk ta gama ruɗewa

Kallonta Hajar tayi Hawaye na tsiyaya daga cikin idanunta wanda yafi kamada na
takaici sannan ta kalli mom tace "Mom ni kika mara akan wannan bush girl din ko?

Wata uwar harara mom ta watsa mata tace "na mareki don uwarki. Kuma wllh koda
kallon banza kika sakeyi mata wllh sena baki mamaki a cikin gidannan

Barin gurin Hajar tayi da sauri tana dafe da kuncinta tana kuka ta koma ɗakinta
tareda faɗawa kan makeken gadonta ta shiga rera sabon kuka. Da Sallama Edyan ya
shigo falon cikin wata dakakkiyar Maroon Egyptian Suit wadda tabi jikinsa tareda
baiyana tsantsar cikar zatin dayake dashi hannunsa na bisa wuyansa yana gyara zaman
tie ɗin dake wuyansa, fuskarsa babu komai a fuskarsa se wani ƙayataccen murmushi
wanda ya zame masa tamkar ɗabi'a a gareshi, kyawawan pink lips ɗinsa se faman
shaining suk e tamkar ya shafa musu lipstik.

tsayawa yayi chak yana kallonsu bayareda ya samu zarafin ƙarasowa cikin falon ba,
ƙamshin turarensa ne ya karaɗe falon da sauri ta ɗago fuskarta wadda ta caɓe da
hawaye daga jikin mom tana kallonsa, sosai ƙirjinsa ya amsa lokaci guda kuma ta
miƙe ta da gudunta taje ta faɗa jikinsa tana me sakin wank sabon kukan. Janyeta
yayi da sauri daga jikinsa tareda ranƙwafowa daidai tsahonta yace .................

*yau banyi dayawa ba banajin daɗin jikina ne😢*

Comment
Nd
Share

sushmah💋
[3/3, 5:37 PM] Chubado Mohd: ❄️❄️❄️❄️❄️❄️
❄️❄️❄️❄️❄️❄️
🐄🐄🐄🐄
🐄🐄🐄🐄
*BAFULATANA*
✨RETURN✨
🐄🐄🐄🐄
🐄🐄🐄🐄
❄️❄️❄️❄️❄️❄️
❄️❄️❄️❄️❄️❄️

*_WRITING BY :CHUBAƊO_*

*_PAGE: 33_*

*DON ALLAH IDAN KINSAN STICKER ZAKI SAKAMIN AS A COMMENT PLS KI RIQE KAYARKI
BANASO *

____✍️Whats wrong with you dear?. Ya duk ya wani rikice yana kallonta sanin
dayay bazata iya bashi amsa bane yasa ya maida kallonsa ga mom yace "Meya sameta
take kuka haka?

Ajiyar zuciya ta sauke me nauyi sannan tace "ita da Hajar ne wllh. A ƙufule yace
"Hajar kuma mom? nan da nan ransa yay masifar ɓaci take yanayinsa ya sauya lokaci
guda kuma ya maida ita bayansa ya fara takawa da nufin ya tafi ɗakin Hajar ɗin yaji
ta riƙe hannunsa gam, yana juyowa idanunsu suka sarke cikin na juna hawayen dake
maƙale a cikin idanunta ne suka samu nasarar zubowa girgiza masa kai tayi da sauri
Alamar karya je, ba musu ya tsaya chak yayinda ko wace gaba ta jikinsa tayi sanyi.

Mom ya kalla da shanyayyun idanunsa yace "pls mom bring her hijab zamu wuce school
ɗin da ita. Ba musu mom ta juya ɗakinsu ta ɗakko mata Hijab ɗin Zeeyadah Maroon
dogo ta kawo mata tareda sanya mata, sosai Hijab ɗin ya karɓi ta tareda baiyana
ainihin kalar Hasken fatarta hannunta ya kama suka fice daga falon ba tareda ya
lura da noƙewar da takeyi ba alamar ya sakin mata hannu.

Har parking space suka isa a haka yana riƙeda hannunta se faman murza idonta takeyi
da ɗaya hannun alamar tayi kuka sosai Guards ɗinsa dake tsaye curko-curko ta kalla
majiya ƙarfi dasu da sauri ta koma bayansa ta maƙale tana raba idanu, murmushi yayi
tareda fito da ita daga bayansa ɗaya cikin guards ɗin ya taho da sauri ze buɗe masa
ƙofar motar ya dakatar dashi ta hanyar cewa " leave it I will opened for her don't
worry is my duty as from today insha Allah. Edyan ya faɗi hakan yana ƙara faɗaɗa
murmushin sa

Ƙura masa idanu tayi tana kallonsa musamman yanda yake motsa ɗan ƙaramin Cute pink
lips ɗinsa, sosai taji ya burgeta har hakan yasa ta shagala da kallonsa a ranta
tace " Handi mim boni shi kuma haka yake komai nasa me kyau ne. Hure mata idanu
yayi da iskar bakinsa take ta dawo cikin haiyacin tana wani lumshe idanu kamar
mejin bacci sunkuyowa yayi dabda tsayinta yace " why are you looking at me like
that Mulaikha? Ya faɗa yana kallon dogayen zara-zaran gashin idanunta da suka wani
irin mammanne da junansu sabida danshin hawayen daya jiƙasu. Turo ɗan ƙaramin red
lips ɗinta tayi waƴanda suka ɗan fara bushewa Kaɗan ta kalli ƙasa jan hannunta
yayi ya kaita bakin motar ya buɗe mata cikin Huskey voice ɗinsa yace " shiga.

Ba musu ta ɗaga ƙafarta da ƙyar cikin wani silifas me yawan igiyoyi ƙirar companyn
Binci, gabaɗaya ji take kamar babu takalmi a ƙafarta ita babbar damuwarta ma shine
yanda takalmin yake wahalar da ita wajen yin tafiya kamar zatayi kuka ta zauna
hijab ɗin ɗukya takura mata dabida rashin sabo.

Rufe mata ƙofar yayi sannan ya zagayo ta ɗaya ɓangaren ɗaya daga cikin guards ya
buɗe masa motar ya shiga ya zauna daga gefanta sannan motocin suka fice daga gidan
Gabaɗaya, sosai takebin ko ina da kallo a ranta tana mamakin yanayin garin da kuma
tsarinsa gani take kamar tamkar a wata duniyar ta daban take ba wadda take ciki tun
farko ba, jikinta ne ya fara rawa sabida yanayin irin gudun dataga suna tsalawa
yasa ta matsa kusa dashi sosai tareda damƙe hannunsa cikin nata, murmushi yayi
sannan yace "look mulaikha babu abinda ze sameki just relax I'm with you kinji?
Kamar taji abinda yace yasa ta ɗan saki jikinta

Ganin suna shirin ɗaukar hanyar office ɗinsa dake ministry of finance yasa yace "no
banan zamu fara zuwa ba School ɗinsu zeeyadah zamu fara zuwa zayi mata
registration, cikeda girmamawa wanda kejan motar ya amsa da to ranka ya daɗe
cikin mintunan da bazasu gaza 5 ba suka iso bakin get ɗin makekiyar makaranta wadda
akayi rubutu kamar haka *_AL-FALAQ INTERNATIONAL SCHOOL_* central Area. Ciki suka
shiga suka faka sannan ya fito cikin takunsa na isa sa ƙasaita yana gyara zaman
rigar dake jikinsa ya buɗe mata ƙofar ta fito se faman kalle-kalle takeyi ya kama
hannunta suka fara takawa a hankali, yanayin yanda take tafiya yake kalli tamkar
wadda ake koyawa sabida yanda takalmin ƙafarta ke wahalar da ita sunkuyawa tayi
tareda cire takalmin ta ringumesu a ƙirjinta da ɗaya hannun tana jiran su tafi,
kalle-kalle ya fara yana sannan ya dubeta yace "ajiye kisa . Kamar zatayi kuka ta
kafeshi da ido so take tayi masa magana amma bazata iya ba don batasan me zatace
masa ba.

Ganin bata da niyar maganar ne yasa ya karɓi takalmin ya ajiye mata a saitin
ƙafarta yace "oya wear it. Har zata turo masa baki se kuma taga ya harareta ba
shiri ta fasa. Har suka shiga principal office ɗin hannuta na cikin nasa

Nan da nan ya karantawa principal ɗin ƙudirinsa na sanyata a makarantar sosai shima
yayi farin ciki da hakan tareda tambayar sunan ɗalibar, Shiru Edyan yayi yana
tunanin sunan daze sanya mata a matsayin na mahaifinta amma ya rasa samun matsaya
kawai seya kalli principal ɗin yace "her name is Mulaikha Edyan Edriss. Nan take
kuwa akai mata rigista da wannan suna tareda bata Uniform da duk wasu abubuwan da
ɗalibi ke buƙata na makaranta.

Nan take ya biya kuɗin komai sannan yay salama da principal ɗin akan gobe zata fara
zuwa makaranta inda zata kasance a cikin jerin ɗalibai ƴan jss 1

Koda suka bar makarantar office ya wuce da ita sannan ya haɗa mata tea da kansa
daya fahimci tanajin yunwa. Se wajen 4pm ya tashi daga office seda suka biya da
Sahad store dake Garki ya jibgar mata siyayyar kayan sawa wanda duk suka kasance
dogayan riguna donya fahimci sunfi mata daɗin sakawa sannan suka wuce gida.

****

Gidan Alhaji Abdulwahab kuwa wata irin rayuwa akeyi mara daɗi tamkar ba wannan
Ahalin ba wanda suka saba rayuwasu cikin farin ciki da walwala ba, sosai Ummie
take ɗaurewa Abie fuska ko part ɗinta ya shigo sam batabi ta kansa balle har
maganar fatar baki ta haɗasu, wani irin haushinsa takeji tareda ƙunar zuciya idan
ta tunada irin cin fuskar dayayi mata a rayuwa ta hanyar damƙata a hannun hukuma
batareda yayi mata uziri ba ko kaɗan, yauma kamar kullum zaune take a makeken
falonta suna hira da Baba Hajara Abie ya shigo perlourn, sanye take cikin wata
doguwar riga milk colour wadda taji uban stons masu ɗaukar idanu gamida sheƙi,
kallo ɗaya zakayi mata ka fahimci ita ɗin ma'abociyar sanya dogayen riguna ce domin
kuwa sunfi komai yawa a cikin kayanta, tunda ta kalleshi so ɗaya ta ɗauke kai bata
ƙarabi takansa ba waje ya nema ya zauna akan ƴan ubansun royal kujerun da sukayima
parlourn ƙawanya sannan ya dubi Baba hajara yace " don Allah Baba bari nayi magana
da Aishat.

Baba tayi murmushi tace "to ranka ya daɗe ta faɗa tana miƙewa daƙyar sannan ta fara
takawa a hankali tabar perlourn. Tana fita Abie ya miƙe daga inda yake zaune ya
dawo kusa da ita tareda sauke Ajiyar zuciya yace "Aisha kowani ɗan Adam a Rayuwa
ajizi ne kuma ze iya aikata badaidai ba a kowani lokaci, nasan ban kyauta miki ba
ko kaɗan tunda harna kasayin uziri a gareki akan laifinda har yau zuciyata bata
gama gamsuwa da cewar kekika aikata ba! Nasan zaki dinga kallona a matsayin mutum
me son kansa dayawa amma kuma ta wata fuskar koda kece a matsayina abinda nayi shi
zakiyi Aishatou, sannan kuma ni'a tawa wautar ba komai ne yasa na aikata haka ba
face zallar sonda nakeyiwa gudan jina tareda ƙoƙarin ganin nayi masa adalci a
matsayina na uba a gareshi wanda Allah ya damƙamin Amanarsa... "Hmmm Abdul kenan ni
wato ba amana bace a gareka sannan kuma niba iyayene suka haifeni ba tunda har ka
iya ɗaukata ka miƙani ga hannun hukumar daba ta ƙasarmu ba duk a bisa zargin na
ciyar da ɗanka guba, ni'a zatona koda a labari kaji cewar ni Aisha zan iya kashe
koda dabbace wllh zakayi kokwanto a kai tunda har kafi kowa sanin Halaiyata da
ɗabi'una Abdul amma se gashi abin takaici harda kai aka ɗaukeni aka ɗamƙani ga
hukuma suka azabtar dani duk akan laifinda bani na aikat.......... Wani irin kuka
ne yaci ƙarfinta yasa dole tayi shiru ta kasa ƙarasa maganar sabida yanda kukan
baƙin cikin abin ya turniƙeta.

Janyota jikinsa Abie yayi tareda haɗeta da ƙirjinsa yanajin wani irin sonta da kuma
tausayinsa na ratsa matsa kowani lungu da saƙo na zuciyar sa, wani irin nauyinta
da kunyarta yakeji a yanzu musamman idan ya tuna irin ɗumbin halacciɓ da Aishar
tayi masa a rayuwarsa, ta sadaukar da abubuwa dayawa na rayuwarta sabida shi ciki
kuwa harda gudan jinin tilon ɗanta data haifa a duniya kuma duk tayi hakanne
sabidashi a kasalance ya buɗe bakinsa dayayi masa wani irin mugun nauyi yace " Don
girman Allah Aisha kiyafemin abinda na aikata a gareki pls karki bari zuciyarki ta
samamin wani gurbi na ɓacin rai a cikinta don girman Allah!!!!!

Tureshi tayi daga jikinta tana kuka tace "gurbi dai kace ko Abdul toka sani tun
ranar daka miƙani ga hukua zuciyata tayi maka tanadin wani babban masauki zallar
tsanar.......... Da sauri Abie ya yunƙura cikin zafin nama ya haɗe bakinsa da nata
guri ɗaya. Duk yanda Ummie taso ta ƙwace kanta abin gagararta yayi domin kuwa Abie
be mata riƙon wasa ba, nan take dattijon ya shiga sarrafa matarsa cikin salo na
ƙwarewa da bajinta a fagen iya soyayyah gamida tattali ya jefa uwar gidan tasa
Ummie cikin duniyar gajimaren soyayyarsa ganida begensa. Ganin ze wuce gona da iri
ne yasa ta shammaceshi ta fusge jikinta tayi hanyar ɗakinta, yunƙurawa yayi ya bita
tana ƙoƙarin kulle ƙofar ya tura da ƙarfin tsiya ƙofar ta buɗe bayan ya shiga ne
ya murzawa ƙofar key ya janyota jikinsa yana aikin rarrashi, ganin zata bashi
wahala ne yasa ya shiga aikin rarrashin ta wata hanyar daban mesa zuciya ta
zagwanye sabida shauƙin so gamida zallar ƙauna mara algus a cikinta, nan dai Abie
ya sami nasarar sheƙe zuciyar ummie suka faɗa duniyar Ma'aurata.

Sosai Abie ya fahimci yayi kewar matar tasa tsahon lokaci wanda itama Ummien ta
ɓangarenta kusan hakanne a haka dai al'amura suka wakana komai kuma ya tafi daidai
kamar yanda yake fata. A haka dai Ummie ta daure ta kuma yafewa mijin nata don
koda wasa bazata iya fushi ɗashi ba sam.

Ɓangaren Muzaffar kuwa kwance yake a ɓangarensa ko abinci ya kasa ci sabida tsabar
fargabar dayake ciki komai bayajin daɗinsa don hkaa ma be nemi wani abinci ba
sabida halinda yake ciki yafi gaban nan, wayarsa dake gefansa ce ta ɗauki ƙara
harta katse be kalli inda wayar take ba, seda aka sake kira a karo na biyu sannan
ya miƙa hannunsa ya ɗauka tareda karawa a kunnensa batareda ya kalli screen ɗin ba,
Muryar Hajar ya tsinkaya ta doki dodon kunnensa tace "Hi sweetheart. Shiru yayi
sabida rashin sanin makamar abinda zece mata, kamar zata mai kuka tace" sweetheart
are you there? Daƙyar ya Iya buɗe bakinsa cikeda ƙosawa da maganganunta yace
"yeah WhatsApp? Lushe idanunta tayi da sauri sabida wani irin daɗi dataji tace "i
just call you ne dama to ask you ko kana lfy, I feel like something is definitely
wrong with you sweetheart, wllh koda fitar numfashinka ce ta sauya senaji a
jikina..... Ta faɗi hakan idanunta na cikowa taf da kwallah.

Shiru yayi yana sauraron ta maganganunta nayi masa yawo a tsakiyar kansa, yau a
karon farko yaji cewar hajar ta samu wani ɓangare na daban a cikin ransa dukda cewa
hakan ba yana nufin yana sonta bane a'a kawai dai yaji ta bala'in burgeshi ne data
fahimci irin halinda yake ciki a maganarsa. Ajiyar zuciya ya sauke me ƙarfin gaske
yace "I'm fine Hajar is just a headache but Alhamdulillah I'm feeling better now.
Zatayi magana kenan ya katseta ta hanyar cewa" i will call you tomorrow in the
morning Insha'Allah. Ya katse wayar

Washe gari da safe kamar yanda ya mata alƙawari ya kirata suka ɗanyi magana sannan
ya katse wajen 8am suka tafi Asbitin gabaɗayansu don Ayi musu gwajin ƙwayar
halittar da alƙali ya bada Umarni (DNA TEST) tunda suka fita daga gidan ƙirjin
muzaffar ke bugawa da ƙarfi hakama na Mom wadda tun a daren ranar bata rintsa ba
sabida tashin hankali, daga ranar da Alƙali ya ɗage zaman shariyar zuwa yanzu duk
Mom ta gama Ramewa ta fita haiyacinta kamar ba ita ba se dogon hanci wanda ya fito
yay mata ƙwam a tsakiyar fuska. A haka suka isa cikin Babban General Hospital ɗin
dake garin na Abuja don tabbatar da abinda sukazo neman.......

Thanks for d du'ah sisters Rabbi yabar zumunci👏

Comment
Nd
Share

Sushmah💋
[3/3, 5:37 PM] Chubado Mohd: ❄️❄️❄️❄️❄️❄️
❄️❄️❄️❄️❄️❄️
🐄🐄🐄🐄
🐄🐄🐄🐄
*BAFULATANA*
✨RETURN✨
🐄🐄🐄🐄
🐄🐄🐄🐄
❄️❄️❄️❄️❄️❄️
❄️❄️❄️❄️❄️❄️

*_Page:34_*

*_WRITING BY:CHUBAƊO_*

Banyi Editing ba
____✍️Jiki babu ƙwari muzaffar ya sakko daga motar hakama Ummie wadda ta kasance
ita kaɗaice a motar datake babu kowa ciki se drivern dake tuƙa motar, cikin sa'a
kuwa idanunta dana muzaffar suka Sarƙe cikin na juna wanda tunda ya fara mallakar
hankalinsa hakan bata taɓa faruwa a tsakaninsu ba, wani irin Amo da soyayyar uwar
ce kwance a tsakiyar ƙwayar idanun Ummie wanda sam hakan ya gaza ɓoyuwa.

Take jikin muzaffar ya fara barazanar rawa tamkar ana kaɗa masa gangi, wani irin
baƙon yanayi yakeji a cikn jikinsa me wahalar fassarawa a gareshi wanda sam ya
gaza fuskantar ma'anar wannan yanayi dayake ciki ɗin, hannunsa mom ta damƙe cikin
nasa hakanne ya taka mahimmiyar yawa wajen dawo dashi cikin nutsuwarsa.

A hka suka shiga cikin farfajiyar inda ake gudanar da DNA test ɗin jinin mom aka
fara ɗauka sannan aka ɗauki na Ummie da kuma na muzaffar, kasancewar a kwai cigaba
yanzu ba kamar da ba cikin Awa ɗaya akai komai aka gama har fitowar sakamakon
duka, karɓa sukayi sannan suka fita zuwa motocinsu Ba tareda Ummie ta sake kallon
indasu mom da Abie ɗin ke tsaye ba, a yanzu damuwarta ɗayace shine tasan halinda
gudan jininta yake ciki wanda sam yaƙi yarda ya haɗa idanunsa da ita tun bayan
fitowarsu daga lab ɗin.

Motocin suka buɗe kowa ya shiga sannan suka ɗun guma zuwa faɗar alƙali don yake
hukuncin daya dace ba tareda an zalinci koɗaya daga cikinsu ba.

Bayan sun isa Inda za'a yanke hukuncin addu'a alƙali ya fara buɗewa da ita sananna
ya bada umarni ga magatakardansa daya karɓo sakamakon Asibitin dake hannun
security ɗin da aka haɗasu dashi don gudun ruɗani sannan ya kaimasa shi kuma ya
miƙawa likitan dake zaune can daga gefan hannun daman Alƙalin donya tabbatar musu
da abinda sakamakon yazo dashi, karɓa likitan yayi tareda warware takardan cikin
nutsuwa Seda ya kama nazartar takardun sannan ya dubi alƙali cikeda nutsuwa yace "
Sakamokon ƙwayar Halittar farko wanda ke ɗauke da sunan Aisha Muhammad Lamiɗo
wanda binciken ƙwayar halitarta ya nuna cewar lallai tanada kamanceceniyar halittar
jini da wasu nau'ika wanda yay daidai da ƙwayar halittar Muzaffar Abdulwahab
Abdullah saɓanin yanda sakamakon Saratu Ahmadu Bello ya bayar sam babu
kamanceceniyar halitta ta jini kota wani abu a tsakaninta da Muzaffar ɗin.

A zabure mom ta tashi lokaci guda kuma ta zube akan ƙafafunta ta fashe da wani irin
kuka me masifar ban tausayi, daga yanda take kukan kaɗai zaka fahimci cewar tana
cikin gagarumin bala'i mara misaltuwa. Sosai take wani irin kuka kamar zata shiɗe
da wani irin hanzari kamar an mintsineta ta miƙe ta isa gaban Muzaffar ta zauna
tana gunjin kuka tace "shikenan ya tabbata kaiɗin Ba ɗana bane Muzaffar?!! Mom
ta jefo masa tambayar yayinda idanunta ke zubar da hawayen tausayin kanta da kuma
makomarta.

Toshe mata baki muzaffar yayi da sauri idanunsa a cike tab da ƙwalla shima yace
"don't say that Mom. Kema mahaifiyata ce tunda kece kika raineni tun ina cikin
tsuma kuma kikaci gaba da wahala dani tun daga yarinta na har zuwa girma na, duk
wata wahala da uwa keji a lokacinda take rainon ɗanta kinsha dani mom haka kuma
Allah shikaɗai ne masani aka lokutan dana dinga hanaki bacci sabida kukana tun ina
jariri harna mallakin hankalina. A cikin jerin nauyin larurar rainon da duw wata
uwa keyida ɗanta kinyi dani cikina ne kawai baki ɗauka ba tareda ciwon naƙudar
haihuta, don haka wllh kema uwace a gareni mom don Allah karki sake bari bakinki ya
furta cewar keɗin ba mahaifiyata bace!!!!!! Ya faɗa yana sakin wani irin marayan
kuka me matiƙar taɓa zuciya.

Duk ilahirin jama'ar dake falon kuka suke na tausayin Rayukan guda biyu idan ka
cire alƙali tareda muƙarrabansa, ita kanta Ummie kukan take tareda jin wani irin
tausayin abokiyar zaman nata Saratu na ratsa duk wata gaɓa ta jikinta.
Baba Hajara ma kukan takyi saɓanin maryamu da idanunta ke soye tanabin kowa da
kallo.

Bayan lafawar komai ne alƙali ya tabbatar da hukunci cewar Muzaffar ɗan Aisha ne ba
ɗan Saratu ba kamar yanda duniya ta ɗauka, a karon farko a rayiwar Fadilah taji
cewar dama ace Muzaffar yayanta ne kamar yanda take kallonta a shekarun baya lallai
a yau kam ta fahimci wani abou a tareda ɗan uwan nata, ba komai ta fahimta ba illa
zallar ma'anarsa da kuma irin kulawar daya dinga bata don ganin ta zama mutuniyar
kirki wadda zata sanya mahaifansu Alfahari kamar ƙanwarta zainab. Ta daɗe tana
kokwanto akan wasu ɗabi'un nasa dayake nunawa ga duk wanda Allah ya haɗashi zama
ɗashi, mutum ne shi very friendly and social Ashe duk wannan ɗabi'un nasa gado yayi
daga mahaifiyarsa. Wani irin kuka ne ya kufcewa Fadilah tareda dana sanin abubuwan
data dinga aikata masa don kawai taga ta daƙile tauraronsa a idon duniya

Gyaran murya Alƙali yayi tareda gyara glashin dake idanunsa ya kalli Ummie yace "a
lokacin da kika kammala dafa Abincin da kika sauki Muzaffar dashi shin kin matsa
daga kicin ɗin ko daidai da second ɗaya?

Da sauri Ummie ta kalleshi se kuma tayi shiru tareda kallo gefe guda alamar tanason
ta samu damar tunawa cikin sauƙi, da sauri ta kalli Alƙali tace " Ban motsa naje
ko ina ba seda a lokacin danagama kwashe abincin a cikin wormers nasa Maryamu ta
kwashe taje ta jera kulolin akan daining ta faɗa tana kallon Maryamu wadda wani
irin gumi ya fara yanko mata.......

Comment
Nd
Share

Sushmah💋
[3/3, 5:37 PM] Chubado Mohd: ❄️❄️❄️❄️❄️❄️
❄️❄️❄️❄️❄️❄️
🐄🐄🐄🐄
🐄🐄🐄🐄
*BAFULATANA*
✨RETURN✨
🐄🐄🐄🐄
🐄🐄🐄🐄
❄️❄️❄️❄️❄️❄️
❄️❄️❄️❄️❄️❄️

Page :35

*_WRITING BY: CHUBAƊO_*


___Kafeta da ido Alƙali yayi take Maryamu ta ida fita cikin duk wata nutsuwarta can
kuma seta fashe da kuka tana kallon Alƙali tace "Ranka ya daɗe don girman Allah
kaimin Rai karka hukuntani da abinda bazan iya jurewa ba wllh tsautsayi ne yasa na
aikata hakan. Maryamu ta faɗi hakan tana kafeshi ida ƙananun idanunta se kuma can
ta bushe da dariya hartana neman shiɗewa tace "Haka kakeso kaji nace ko Alƙali?

Wani ɗan iskan murmushi ta saki sannan ta tacigaba da cewa"wannan kukan dakaga
inayi bana komai bane face na zalar baƙin ciki da namar cewar haƙata bata cimma ga
ruwa ba tunda har ban samu nasarar dazanga bayan Aisha ba sabida tsabar tsanar
danayi mata, a Rayuwata idan akwai wanda na tsana fiyeda mutuwata to wllh Aisha ce
dukda kasancewarta mutuniyar kirki hakan besa na taɓajin ƙaunarta a raina koɗa
kimanin girman ƙwayar zarra ba. Naso ace na samu nasarar kashe muzaffar kodan a
yankewa Aisha hukuncin Kisa ta hanyar Rataya kokuma a jefata cikin babbar kurkun da
zata haɗu da bala'in dazefi ƙarfinta a ƙarshe harma ya zama ajalinta amma kuma kash
se gashi ta fita cikin sauƙi daga cikin ramin muguntar dana gina mata.

Gabaɗaya falon kallonta akeyi especially Ummie da idanunta suka firfito sabida
tsabar mamakin kalaman na maryamu, wani irin ƙululun abu ne ya taso mata ya tsaya
mata a maƙoshinta sabida yanda yawun bakinta ya ƙafe daƙyar ta iya haɗo kalaman da
suka rage mata akan harshenta tace "Maryamu me nayi miki kekuwa a Rayuwa da har
zakiyi min irin wannan gagarumar tsanar?

Murmushi maryamu ta saki wanda iyakarsa laɓɓanta wanda yafi kamada na zallar tsana
mara tushe balle makama tace "wllh bakiyi min komai ba Aisha Hasalima se alkhairi
da kikayi min a Rayuwa tareda duk wani ma dake kusa dani, kawai dai laifinki ɗayane
a gurina shina na tsaneki kuma bana ƙaunarki wannan kawai shine dalilina kuma
wllh na ƙudurtawa zuciyata cewar muddin ina numfashi a doron ƙasa tofa senaga
bayan.....

Saukar wani lafiyayyen mari Maryamu taji a saman fuskarta wanda yasa ba shiri ta
haɗiye maganar datake faɗa tareda zubawa wanda ya wanke mata fuska da marin, tun
kafin ta ida ƙare mata kallo ta sake ɗauketa da wani hamshaƙin marin wanda yasa
kunnuwanta suka toshe kimanin wasu mintuna sannan ta nunata da yatsa tace "Amma
kedai wannan mata anyi cikakkiyar shaiɗaniya kuma butulu mara tabbas, lallai keta
musammance a cikin jami'ar bada horo ta musamman tareda ƙwarewa a fanin Butulci da
kuma cin amana, koda yake banyi mamaki ba idan akace gabaɗaya shekarun nan naki sun
zama na banza shiyasa tunda idanuna suka sauka a kanki naji cewa har cikin
zuciyata bana ƙaunarki ashe abinda ban saniba shine keɗin gabaɗayanki tamkar
tauraruwa me jela kike wadda ganinki sam ba alkhairi bane.!!! Fadilah ta faɗi
hakan tana wani irin huci kamar zata cinye Maryamu ɗanya.

Itadai mom gabaɗaya bin Maryamu take da kallo yayinda hawayen idanunta suka tsaya
cak lallai yau kam ta yarda da cewar inda ranka kasha kallo a duniya, lallai duk
tsiyarka a doron ƙasa to wllh a kwai mafiyinka a komai walau alkhairi ko sharri
mom bata samu zarafin magana ba Alƙali ta buga gudumar tabbatar da hukuncinsa don
kowa ya nutsu kuma ya bada hankalinsa don sauraron hukuncin daze yakewa maryamun

Alƙali ya nisa yace "bisa dubada hujjoji tareda iƙirarin da maryamu tayi na
yunƙurin kashe muzaffar Abdulwahab Abdullah tareda iƙirarin cewar Setaga bayan
Aisha Muhammad Lamiɗo don haka wannan kotu me alfarma ta yankewa Maryamu hukuncin
life in prison har ƙarshen Rayuwarta kamae yanda hukuncin yazo a cikin littafin
kunɗin tsarin hukuncin mulkin Nigeria. Ya faɗa tareda buga wannan guduma sannan ya
bada umarni da akama Maryamu doka ta fara aiki akanta daga wannan rana

Wani Uban ihu Maryamu ta zunduma tareda fuzgar biron dake gaban aljiun Rugarsa tayi
kan Ummie gadan-gadan har tana haɗa hanya sabida muguwar zuciya, da wani irin
mugun zafin nama Muzaffar ya ture Ummie gefe Tayi baza zata Faɗi Abie ya tareda da
hanzari ta faɗa jikinsa hakanne yayi daidai da saukar biron da Maryamu tai niyar
cakawa Ummie a gefan hannunsa na dama take jini ya ɓalle ya fara zuba, kamata sukai
da ƙarfin tsiya sukai waje da ita inda motar tafiya prison ɗin take cikin muntuna
da bazasu gaza 10 ba sukabar harabar kotun da ita se Babbar Prison ɗin da ake adana
manyan shahararun ƴan ta'adda waƴanda aka yankewa hukuncin kisa dake babban birnin
na taraiya Abuja.

Da hanzari Ummie ta fuzge jikinta daga na Abie ta nufi muzaffar tareda sanya
hannunta ta danne inda jinin ke zuba hawaye na sakko mata, yau a karon farko a
Rayuwarta hannunta ya taɓa jikin Gudan jininta muzaffar tun bayaɓ shekara 35 a
lokacin yana jariri, wani irin Abu ne me kamada nau'i shaƙuwa gamida zallar ƙauna
da soyayyar ɗada Uwarsa tana Ratsa duk wata gaba ta jinin dake gudana a jikinsu,
tabbas a yau ya gamsu da cewar Ummie itace Mahaifiyarsa because he feel something
about her as a mother saɓanin mom dabe taɓa jin irin wannna shauƙin a tareda ita
ba, Ashe dama wannan nutsuwra dake ratsashi a wannan lokacin a sanadin taɓashin da
Ummie tayi shine abinda ya rasa a rayuwarsa tsahon shekara 35?

Janyo Ummie yayi da hanzari ya Rugumeta lokaci guda kuma ya saki kuka tareda
kwantar da kansa a kafaɗunta ya shiga rera sabon kuka tamkar wani ƙaramin yaro,
shafa bayansa kawai Ummie takeyi itama hawaye nayi mata Ambaliya a saman Fuskarta

Gabaɗaya falon ficewa sukai duk girmansa ya kasance daga Muzaffar se Ummie kuka
kawai yakeyi tana shafa bayansa ba tareda ta dakatar dashiba sabida a wannan
lokacin babu abinda yake buƙata sama da hakan da ƙyar ya iya buɗe bakinsa muryarsa
na Cracking yace "Ummie why? Why Ummi....... Gabaɗaya yama kasa magana sabida
tsabar yanda kukan yaci ƙarfinsa, still she's tapping his shoulder hawayenta na
ƙara tsananta zubowa

Ummie ƙara rungume ɗannata tayi cike da so ganida zallar ƙauna,


Seda suka dauki lokaci me tsayi a haka babu Wanda ya samu zarafin magana

Duk abinda ke faruwa a tsakanin Ummie da ɗan nata Fadilah na zaune na kallonsu
itama tana hawaye sabida tsabar yanda suka bala'in bata tausayi it almost 35 years
Rabonda yaji ɗumin jikin mahaifiyarsa, A hankali Fadilah ta sakko ƙasa daidai inda
ƙafafun Muzaffar batareda tayi magana ba ta wani irin fashe da kuka tareda ficewa
daga falon da saurinta, wani irin kunyar Muzaffar takeji bisaga abubuwa na rashin
kunya da ƙiyayyar data dinga nuna masa mara tushe takeji se'a yanzu ta fahimci
cewar Ashe ba tsanarsa tayi ba kawai dai kishi takeyi dashi akan abinda take ganin
nata ne ba nasa ba wanda tafi dan ganta hakan da ƙuruciya gamida wauta, harta kai
ƙofar fita daga falon se kuma ta tsaya Chak lokaci guda kuma ta juyo tana kallonsu
tace " haƙiƙa ina me jajanta muku akan abinda ya Sameku dakai da Ummie yaya
Muzaffar Haka kuma ina me yi maka addu'ar alkhairi a koda yaushe sbda kai ɗin ɗan
uwa na ne guda ɗaya tilo, wanda kaf duniyar nan bamuda kamar ka nasani wata rana
dole Kaine zaka zama uba a garemu gaba ɗaya, tunda Uwata ta haifeni ban taɓa jin
kunya irinta yauba danake tsaye a gabanka nake kuka yaya muzaffar! Yaudai kam na
yarda da maganganunka da kake gayamin kullum cewar idan har ban gyara wasu abubuwan
na Rayuwata ba tabbas wata rana zanyi nadama to yaudai kam da alama wannan ranar
ce tazo min tunda har na fahimci kuskurena tun kafin lokaci ya ƙuremin.

A madadin Mahifiyata dani kaina Don Allah Ina me roƙon ku afuwa dakai da Ummie
akan abinda muka aikata muku don Allah yaya muzaffar ka yafe mana plsss. Ta faɗa
tana zubewa akan gwiwoyinta still tana maganar tana hawaye.

A hankali ta ɗaga jajayen idanunta ta kalli Ummie tace " haƙiƙa kin cika Uwa wadda
ta cancanci da a yaba mata, tunda har kika Iya sadaukar da ɗanki guda ɗaya tilo
dan kawai ki sanya mikinki farin cikin wllh dik inda uwa ta gari Takai to kinkai a
kiraki da wannan suna Ummie, naso ace ina ɗaya daga cikin waƴanda suka fito daga
cikin cikinki tabbas danayi alfahari dake a matsayin Uwa.
Tana kaiwa nan ta miƙe ta fice daga fallon tana me zubar da hawaye
A wannan rana muzaffar kwanan farin ciki Yayi, hakama Ummie da Abie ta ɓangaren Mom
ma kusan hakane ko babu komai yanzu tayi karatun tanutsu da al'amarin Rayuwar
duniya, haka kuma ta fahimci cewar lallai Aisha ta musamman ce tunda a ko ina take
Halaiyarta ta gari itace ke jamata alkhairin Rayuwar duniya.

RUGAR HARDO
GYAMBU TARABA (STATE)

Kwance yake cikin yanayi na Rashin lfy sosai daƙyar yake iya miƙewa ya zauna sabida
nauyin da gefan ƙirjinsa na hagu ne masa, gabaɗaya lips ɗinsa duk sun bushe alamar
baya iya cin abincin kirki balle yasha Ruwan daze hana bakin bushewa

Inna Laure ce ta shigo ɗakin jikinta a matiƙar mace ta zauna daga gefansa hannunta
ɗauke da ƙoƙo ta jiƙo masa magani, kamar zatayi kuka tace " don Allah ka daure ka
tashi ko yayane ka samu kasha tunda idan kasha ɗin ciwon yanayin Sauƙi.

Hawayen dake maƙale cikin ƙwayar idanunsa ne suka samu zarafin Zubowa sannan ya
sanya hannunsa na dama ya danne saitin zuciyarsa yace "taya zan iya Rabuwa da ciwon
tunani gamida na Zuciya bayan Amanar da Allah ya bani bata taredani a Yanzu? Laure
inaji a jikina cewar tamkar mun Rabu kenan nida Rabe har abada kuma bazamu sake
haɗuwa da juna ba

Sedai zan mutu ne da abu guda ɗaya wanda kemin ciwo a Raina Laure, wllh ina matiƙar
jin kunyar kaina dana ɗiyata tunda har na iya turata da hannuna kuma ta tafi
tabarni ba tareda ta juyo koda so ɗaya ba, ina me jiyewa kaina tsoron irin halinda
zata samu kanta a ciki na kaɗaici da kuma sharrin Zaman........ Kuka ne yaci
ƙarfinsa haryasa maganar ta katse ba tareda ya shiryawa hakan ba, wani irin tari
ne ya taso masa me matiƙar wahalar fita wannna dalilin ne ya haifar masa da
sarƙewar numfashi al'amarin daya ƙara gigita Inna Laure kenan . Da ƙyar tarin ya
tsaya sannan moddibo yaci gabada cewa " don Allah zan roƙeki wata alfarma guda ɗaya
a iya zaman da mukayi nidake Laure, koda Ace bayan na mutum Allah ze haɗaki Da
Rabi'atou ki gaya mata cewar ina matiƙar ƙaunarta sannan kuma ta riƙe alƙawarin
data ɗaukar min!!!!

Ɗagoshi tayi da mugun sauri zuciyarta na bugawa da wani irin ƙarfi, hawaye ne suka
shiga zubo mata tamkar an kunna fanfo sabida tsabar tausayin Moddibon bakinta na
Rawa tace "don Allah ka dena faɗar haka malam ai cuta ba mutuwa bace kuma insha
Allah duk inda Rabe take tana cikin hannu na gari da izinin Allah.

Murmushin ƙarfin halli ya sakar mata zeyi magana kenan harshen yaƙi bashi dama,
Idanunsa ne suka fara wani irin ƙafewa lokaci ɗaya kuma numfashinsa ya fara sarƙewa
cikin abonda befi daƙiƙa biyu ba jikinsa ya saki idanunsa kuma suka wani irin
juye...............😭

Thanks 4d love guys i really appreciate it 🥰


Comment
Nd
Share

Sushmah💋
[3/3, 5:37 PM] Chubado Mohd: ❄️❄️❄️❄️❄️❄️
❄️❄️❄️❄️❄️❄️
🐄🐄🐄🐄
🐄🐄🐄🐄
*BAFULATANA*
✨RETURN✨
🐄🐄🐄🐄
🐄🐄🐄🐄
❄️❄️❄️❄️❄️❄️
❄️❄️❄️❄️❄️❄️

Page :36

*_Qaddara macece mara tabbas takan iya canzawa a kowani lokaci, kamar yanda
Qaddararso kan afkawa zukata batareda zato ko tsammani ba😊 ._*

*_WRITING BY: CHUBAƊO_*

NOT EDITED

____✍️Wai irin ihu inna laure ta kurma tareda cakumoshi zuwa jikinta lokaci guda
kuma taci gaba da buga ƙirjinsa da hannunta tana wani irin kuka tamkar ranta zebar
jikinta tace "kayiwa girman Allah kada kayiwa Rayuwarmu haka moddibo, ka tuna irin
girman alƙawarin dake tsakanin ka da ɗiyarka kafin zannan ƙaddara ya samu nasarar
giftawa a tsakanin ku, a yanzu ni kaina idan ka tafi ka barni a irin wannan halin
dana samu kaina a ciki wllh banajin zan iya jurar hakan koda kuwa na kwatankwacin
ƙwayar zarra ne, ko kaɗan bazanso muyi Rabuwa irin wannan dakai ba ba tareda ka
yafemin ba!!!!! Hannunta tasa ta share hawayen daya zubo mata sannan taci gaba da
cewa " na kasance tamkar wata shaiɗaniyar mata a gareka Moddibo, zuciyata da tunani
na basu taɓa zaiyanomin amfaninka a rayuwata ba seyau dakake shirin barina a
lokacin danafi kowa buƙatarka, kasha faɗamin cewar idan har ban canza halayena da
ɗabi'una ba tabbas a kwai Ranar Nadama wadda zatazo min nan bada jimawa ba, naso
Ace wannan ranar batazomin a haka ba seda na wanke laifina a gareka tareda nuna
maka duk wata kulawa da Mace ta gari ya dace ta bawa mijin da Allah ya azutata
dashi amma kash se gashi mutuwa ta gifta a tsakanin mu damu dakai batareda ta bamu
damar yin bankwana ba. Ta faɗi hakan tana ƙara rushewa da wani irin kuka wanda
yafi na farko

ABUJA NIGERIA

Al'amarin gidan Cp (commissioner of police) Kuwa sosai Rayuwar gidan take tafiya
daidai batareda sun bari Cp yasan da batun Bafulatanar dajin dake cikin gidansa a
zaune ba kasancewar be fiye shiga part ɗin Mom ba itace ke zuwa nasa, sosai suke
nuna mata kulawa tamkar sun daɗe da saninta kullum Edyan ke kaita makaranta tareda
gurds ɗinsa sannan ya wuce Office, kullum se sunyi daru da ita sannan zata yarda ta
sauka daga motar idan ya matsa mata seda ta riƙe hannunsa taita kuka, sosai yakejin
kukanta a ransa tamkar ana watsa masa ruwan narkakkiyar Dalma rage tsahonsa yayi
daidai da nata tareda gyara mata zaman hular dake kanta wadda ta baiyana kwantaccen
gashin dake zagaye da kyakkyawar fuskarta yace "look mulaikha kukan ya isa haka nan
baran daɗe ba zanzo ɗaukanki yau kinji?

Maƙemai kafaɗa tayi tana turo baki still hawaye na fita daga cikin fararen idanunta
masu masifar ɗaukar hankali, lumshe idon tayi ta wani buɗesu lokaci guda akan
handsome face ɗinsa ba tareda tace komai ba, jan hancinta yayi tareda kai bakinsa
saitin goshinta yay kissing forehead lumshe idanunta tayi da sauri lokaci guda
kuma taja da baya tana ƙwalalo masa ido hardasa hannu a baki alamar mamaki.

Dari yayi mata tareda ɗaga mata hannu ya shige mota sukabar harabar makarantar
batareda ya juyo ba, still tayi tana kallon motocin har suka fice daga school ɗin
idonta na kallon get ɗin ajiyar zuciya ta sauke sannan ta juya a hankali tana
tafiya hannunta na dama kuma riƙe da goshinta inda Edyan yay kissing a haka harta
kai class ɗinsu tana aikin tunanin abinda Kaɗo Edyan ɗin yayi mata.

Wannan shine abinda ya wakana a tsakanin Edyan da Mulaikha (the fulani girl Rabe)

*****

Zaune mom take a falonta idanunta na kallon sama Zainab ta shigo bayanta ɗauke da
jakarta ta goyo baƙa wuluk da ita wadda tayi mata masifar kyau, duk sallamar
datakeyi Mom bata sani ba seda ta matso kusa da ita ta zauna sannan ta ɗago ta
kalleta tareda ƙaƙalo murmushin dole tace " welcome home my sweetie Qurrah.
Ajiyar zuciya Zainab ta sauke fuskarta ɗauke da damuwa tace "mom meyake damunki
haka naga duk kinyi wani iri? Zainab ta ƙare maganar kamar zatayi kuka.

Dafata mom tayi jikinta a mace tace "karki damu Qurrah ba wani abu bane kawai dai
banajin daɗi ne, maza tashi kije kiyi wanka kicanza kaya kici abinci ki huta
inyaso mayi maganar ok? Ɗaga mata kai zainab tayi tareda faɗin ok . Ta faɗa
yayinda take miƙewa zata bar falon

Tsayawa tayi chak se kuma ta juyo tana murmushi tace "mom banga bro ba but I'm sure
he's not in the office right now so were is he wllh I want to see him nayi missin
ɗinshi badly. Wani irin kuka ne ya tasowa mom amma kuma seta danne tace "yana
part ɗin Aisha . Yarda jakar bayanta Zainab tayi ta dawo kusa da mom tace "mom kina
nufin Ummie ta dawo ? Ɗaga mata kai kawai mom tayi ba tareda tayi magana ba. Da
wani irin mugun gudu zainab ta tashi ta fice daga falon tana Dariya bata dire ko
ina ba se part ɗin Ummie.

Zaune take kan ɗaya daga cikin maka-makan Kujerun alfarmar dake falon Inda kan
Muzaffar ke kwance bisa kafaɗunta suna ɗan taɓa hira, wani irin daɗi yakeji gamida
shauƙin mahaifiya na fuzgarsa gyara zaman kansa yayi sosai a kafaɗun Ummien ta
yanda zejin daɗin kwanciyar yace "Ummie i want to tell you something akan wani abu
dana aikata a Rayuwata, ajiyar zuciya yaɗan sauke sannan yaci gaba da cewa, last 6
months ago na haɗu da wani mutumi a can jihar taraba Ummie a lokacin da bana
haiyacina. Ummie ya taimakeni a Rayuwa sannan ya sadaukar da abubuwa dayawa
sabida ni nan dai ya kwashe komai ya gayawa Ummie abida ya faru ciki kuwa harda
labarin Rabe.

Kallon Ummien yayi kamar ze sakin mata kuka yace " i feel something about her
musamman idan muna tareda ita, a wasu lokutan ma har nakanji zuciyata na zafi idan
na ganta da wani muddin ba mahaifinta bane I don't know ko menene. Shafa kansa
Ummie tayi tana murmushi tace " so tari a rayuwa bama sani ma'anar waƴanda suke
taredamu har semunyi nisa dasu sannan muke sanin ma'anarsu da kuma amfaninsu a
taredamu, yanayin da kakeji akan yarinyar sam ba baƙo bane a idon duniya amma kuma
a tareda kai hakan tamkar wani sabon al'amari ne me zaman kansa. Lallai ziciyarka
ta faɗa cikin wani babban al'amari me zaman kansa wanda zan baka tabbacin cewar ba
komai bane illa soyayya kuma me ƙarfin gaske ba ƙarama ba.

Miƙewa yayi da sauri daga jikinta yana kallon Ummien yace " love dai?? A hakan
kuma ni Ummie?

Murmushi ta sakin masa tace " sosai kuwa tabbas ka faɗa a soyayya me ƙarfin gaske
koda kuwa Ace bakasan hakan ba, ita soyayya kamar iska haka take tana tasowa ne a
lokutan da bamuyi zato ko tsammani ba don haka ina me baka shawarin cewa lallai ka
gaggauta shiryawa don ka cika alƙawarin da Ka ɗaukarwa bayin Allahn nan, sannan abu
mafi mahimmanci shine koda ba sabida soyayyarka da ƴarsu ba lallai ya kamata ka
ziyarcesu kodan kaga halinda suke ciki.

ɗaga kansa yayi alamar gamsuwa da maganar Ummien sannan ya miƙe yace "ummie barinje
masallaci kafin Abie ya dawo. Turo ƙofar falon akai zainab ce ta shigo da gudu
sabida zumuɗi ko sallama batayi ba ta faɗa jikin Ummie tana dariyar farin cikin
ganinta, baki Muzaffar ya saki yana kallonta yace "ke yau kuma ni kika share ko?

dariya tayi tana kallonsa tace "uhm naga Ummie ai bazan kulaka yau ba sabida inason
nasha miyar gyaɗa. Dariya suka saki gabaɗayansu sannan ya fice daga falon. Tunanin
maganar Da ummie ta faɗa masa akan Rabe yana yawo a saman zuciyarsa da kuma
ƙwaƙwalwarsa a haka yayi sallar la'asar ɗin zuciyarsa duk a dagule, koda ya dawo
Masallacin ma part ɗin mom ya nufa dondai kawai ya samu ta rage damuwa akan abinda
ke damunta na rashinsa a matsayin ɗa, yana shiga ta miƙe da sauri ta nufeshi tareda
shafa gefan fuskarsa tace "kacin abinci dai ko?. Hawayen dake maƙale a cikin
ƙwayar idanunta ne suka samu nasarar zubowa, hannayenta ya kama ya damƙe cikin nasa
cikeda damuwa yace "don girman Allah mom kiɗena kuka wllh kukanki yana masifar ɗaga
min hankali Pls.

Janta yayi ya zaunar da ita a saman kujera sannan yay murmushi yace "har yanzu ke
uwatace kuma babu wanda ya isa ya canza hakan koda kuwa Ummie ce da kanta, so pls
ki kwantar da hankalinki don Allah. "Yauwa yaya gara da kazo da kanka tun ɗazu
nake fama da mom taci abinci amma taƙi se faman kuka takeyi. Fadilah ta faɗi hakan
yayinda take sakkowa daga saman stars

zaro manyan idanunsa yayi yace "kina nufin tun tea ɗin safe ne kawai a cikinta?
"sure. Fadilah ta faɗi hakan. Miƙewa yayi da sauri ya isa daining Aria ya biɗe
manyan womers ɗin dake jere ya fara ƙoƙarin zuba mata abincin, white rice ce da
stew wadda taji uban naman kaji a nitse ya kammala zuba mata sannan ya dawo falon
ya zauna daga gefanta ya ɗebo abincin ya fara bata tana karɓa, kallon Fadilah yayi
wadda keta satar kallonsa yace " bring water for me. Juyawa tayi jiki a saluɓe taje
ta ɗakki masa sassanyen bottle water da cup ta kawo masa.

Tsiyaya ruwan yayiɓa cup ɗin ya miƙa mata ta karɓa tasha a haka dai har mom ta
cinye abincin tass sannan ya tattara kwanukan yakai kicin. Hira suka ɗan taɓa da
mom ɗin dukda taƙi yarda ta saki jikinta dashi harya miƙe yabar falon zuwa part
ɗinsa.

koda ya koma part ɗin nasa ma kasa zaune yayi balle tsaye sabida yanda maganar
Ummie take masa yawo a tsakiyar zuciyarsa haka kuma wanu ɓangare na zuciyarsa yake
aiyana masa wani abu a gameda Moddido, miƙewa yayi da sauri ya ɗauki ɗyaa daga
cikin tarin mukullan motar dake zuɓe akan table ɗin glass ɗin dake tsakiyar falon
ya fice da sauri...........
Thanks 4d love sisters 🥰

Shushmah💋
[3/3, 5:37 PM] Chubado Mohd: ❄️❄️❄️❄️❄️❄️
❄️❄️❄️❄️❄️❄️
🐄🐄🐄🐄
🐄🐄🐄🐄
*BAFULATANA*
✨RETURN✨
🐄🐄🐄🐄
🐄🐄🐄🐄
❄️❄️❄️❄️❄️❄️
❄️❄️❄️❄️❄️❄️

Page :37

*_WRITING BY: CHUBAƊO_*

*_I dedicate this special page for all the members of HOME OF QUALITY WRITERS
ASSOCIATION Especially Aglan Nissa ina taya ku murna cika shekara ɗaya tak da
kafuwar qungiyarku, ubangiji ya qara ɗaukaka tareda basirar faɗakar da al'uma
tareda nishaɗantarwa._*

Banyi Editing ba

____✍️Yana fita mota ya ɗauka tareda ɗanna mata key yabar harabar gidan zuciyarsa
na wani irin beating a hankali, wani iri yakeji a jikinsa duk a sakamakon tunanin
moddibo dake bin duk wata gabar jini da curin tsokar dake gudana a cikin jikinsa,
bugu da ƙari kuma wani ɓangare na zuciyar tasa a kasu mafi yawa yafi ta'allaka ne
ga Rabi'atoun sa wadda a yanzu ta gama mamaye duk wata kusurwa dake cikin
zuciyarsa, tabbas kam a yanzu ya gama yarda da cewar ya faɗa a cikin zazzafar
soyayya wadda abu ne mawuyaci ya iya jurar wani abu me girma ta sanadin hakan.

Driving ɗinsa kawai yake very gently but sedai duk wata nutsuwansa sam baya
taredashi jifa-jifa yakan maida wani kaso daga cikin nutsuwarsa a kan titi don
gudun afkuwar wani abu mara daɗi, ɗan sirin tsaki yaja tareda kai hannunsa jikin
redion dake manne a jikin motar ya kunna waƙa mutuniyarsa Selindion cikin waƙarta
me taken I'm yours only you.

Yanayin sanyin muryar mawaƙiyar ne tareda amon dake fita a muryarta ne ya haɗe da
sanyin Ac ɗin dake busa ko ina na motar hakanne yay sanadiyae saukarwa da Muzaffar
wata irin kasala me cikeda tsantsar kewa gamida begen abar Ƙaunarsa, lallai
soyayyar dayake mata zazzafa ce wadda Bayajin ze iya jureta koda kaɗan ne, yanayin
dayake ciki a yanzu baƙone a gareshi domin shiɗin baƙone kuma sabun shiga a lamarin
irin wannan wanda ya dangaci gamaiyar zuciyoyi biyu.
A haka yayta saƙa da warwara harya kai babban filin jirgi na harkar abinda ya
danganci sufuri dake cikin babban birnin taraiya Abuja, be wani ɓata lokaci ba yayi
booking flight from Abuja to Taraba a cikin jerin wanda ze tashi gobe da misalin
ƙarfe 5:am na Asubahi sannan ya kama hanyar komawa gida, koda ya dawo gida da
wani irin ciwon kai ya shigo sabida yawan tunanin daya matsawa kansa dashi duk a
dalilin rashin sabo a kan baƙon al'amarin daya samu kansa a ciki wanda Ummiensa ta
bashi tabbacin cewar ya faɗa a soyayyar Fulani girl ɗinne wanda shi sam beyi
noticing hakan ba ko kadan, Direct part ɗinsa ya nufa yanajin wani irin abu na
nuƙurƙusarsa a cikin ko wace jijiyar jinin dake maƙale a tsokar jikinsa. Zubewa
yayi akan ɗaya daga cikin hamshaƙan kujerun dake falon nasa tareda lumshe manyan
idanunsa da suka fara canza launi sabida ciwon kan dake addabarsa, gyara
kwanciyarsa yayi batareda ya damu da ya cire murɗaɗɗen takalmin fatar dake saƙale
cikin kyakkyawar ƙafarsa ma'abociyar haske gamida limsassun gashi ba, ajiyar
zuciya ya sauke me ƙarfin gaske tareda laso Red lips ɗinsa da suka fara ɗan bushewa
kaɗan.

Dukda irin ciwon da kan nasa keyi sam hakan be hanashi sakin wani ƙayataccen
Murmshi ba wanda yake ɗauke da abubuwa da dama a cikinsa, a hankali ya buɗe bakinsa
cikin Husky voice ɗinsa yace "Am comming for you babe. Ya faɗa tareda datse lips
ɗinsa da fararen haƙoransa

Koda yaje yin diner a babban falon ya tararda gabaɗaya Ahalin gidan suna kallon
ƙofa da alama shigowarsa kawai ake jira, ɗan turo cute red lips ɗinsa yayi gaba
kaɗan batareda yace da kowa ƙalaba yaja kujerar daya saba zama wadda take dab data
Abie ya wani haɗe rai duk dan kar wani ya samu zarafin tambayarsa Daga inda yake
yabarsu suna aikin jiransa. Murmushi kawai Abie yayi tareda girgiza kai A ransa
yace "ɗan Basaja. Sannan ya fara cin abincinsa.

Ummie kuwa kasa cin abincin tayi se faman juya cokalin dake hannunta takeyi, a
zahiri so take ta tambayeshi damuwarsa amma kuma tanajin Nauyin yin hakan a gaban
Saratu ko babu komai ai ta bata dama akan muzaffar ɗin kodan darajar rainonsa datai
mata, wadda ta kafeshi da idanun tun shigowarsa kmaar daga sama ummie ta tsinkayi
muryar mom tana faɗin "son were are you coming from?

Kamar zeyi kuka yaɗan shafi kwantaccen sajen da yaywa fuskar ado baƙi wuluk dashi
se faman shining yake yace "naje hira ne mom.

Zaro ido mom tayi tareda kafeshi da idanunta tace "Hira dai kace ?

Murmushi yayi mara sauti yace "Sure mom. Idan ban fara zuwa hira yanzuba se zuwa
wani lokacin zan fara ? Daƙuwa mom tayi masa tace " lokacin da ka koyi kunya don
gidanku.

Dariya gabaɗaya falon sukayi sannan zainab ta kalleshi tace "yaya Wace me sa'arce
wannan har tasa ka fara sonta ba tareda kayi shawa dani ba?

Wani shegen kallo ya watsa mata batareda yace komai ba, kallonsa Fadilah tayi tana
dariya tace "nasan duk inda wannan budurwan na yaya take kyakkyawa ce sosai
harnaji inaso na ganta wllh. Ta faɗa tana binsa da kallon tsokana

Caraf zainab tayi tace "uhmm nasan dai duk kyanta bata kaini ba don haka dole ne ma
naje musaba da juna kodan nayi mata screning Sosai.

Haɗe rai yayi shi'a dole da gaske yake yace "kedawa zakije har ku saba ɗin da ita?
Ba tareda ta kalleshi ba kurɓi juce ɗin dake gabanta cikin cup ɗin glass tace dakai
mana, nidai pls in zakaje next time zan bika don musan juna da ita Sosai kafin ta
shigo Familyn mu.
Kallon gefan ido yayi mata yace "no base kinje ba batason hayaniya ki bari ba yanzu
ba, nasan idan na kaiki takura mata zakiyi da shegen surutun ki. Ya faɗa yana wani
yatsine fuska sabida ciwon kan dake damunsa

Jifa-jifa yakan juya ya kalli Ummie wadda tunda suka fara hirarsu sedai kawai tayi
murmushi batareda tasa musu baki ba, miƙewa tayi tace "to nikam zan wuce part ɗina
Asuba ta gari. Ummie ta faɗi hakan batareda ta kalli inda Abie ke zaune ba, harta
fara tafiye ta tsinkayi muryar mom a tsakiyar kunnenta kamar haka "pls Aisha ki
tsaya ki tafi da mijinki. Miƙewa Abie yayi yana murmushi cikeda dattako ya kalli
mom yace " aiko baki faɗa ba Saratu nasan alkunya kawai Aisha takeyi miki don haka
barina bi matana. Dariya mom tayi tace "Abie aina fika sanin Aisha macece me
alkunya shiyasa takecin ribar zamada duk wanda Allah ya haɗata dashi.

Bece mata komaiba hakama Ummie data fara tafiya ba tareda ta waigo ba harta fice
daga falon Abie na biyeda ita se faman rawar kai yake mata tamkar wani sabon Ango,
jikinta ya janyota suna tafiyar tare har suka isa part ɗinta suna shiya wani
janyota jikinsa tareda kafeta da lumsassun idanunsa masu matiƙar narka mata zuciya
yace" Aishata ina matiƙar jin kunyarki tun daga lokacin dana ƙuntatawa zuciyarki
ta hanyar miƙaki ga hannun hukuma ba tareda kin aikata laifin komai ba, hasalima
duk abubuwan da kika aikata kinyisu ne domin farin cikina don Allah Aisha ki yafewa
mijinki ko zan samu zuciyata da nutsu daga zargin rashin kyautawar danai miki pls
Aish........." taya kake tsammanin cewa Aisha zata iya ƙullatarka don kawai kayi
mata laifi Abdul?

Ummie ta faɗi hakan tana kallon tsakiyar ƙwayar idanun Abie ɗin wanda shima ɗin ita
yake kallo, murmushi ta sakin masa sannan tacigaba da cewa " Banida wani zaɓi wanda
ya wuce inyi uziri a gareka bisa laifinka tareda kuma nuna maka cewar lallai ɗan
Adam ajizi ne, haka kuma a muhalin da kake kai a matsayinka na Uba koma wanene
abinda kai shizeyi Abdul don haka ka kwantar da Hankalinka daga rana irinta yau
karka sake kallon kanka a matsayin mai lefi a idona Abie.

Shiru Abie yayi still idanunsa na kanta ji yake komai tayi ƙara burgeshi takeyi,
tunda ya Aureta yau kimanin shekaru talatin bata taɓayin jayayya dashi ba komai ya
ɗorata a kai shi takeyi ba tareda ta nuna masa rashin jin daɗinta a kai ba koda
kuwa abin beyi mata daɗi a ranta ba, jikinsa a mace yace "Amma Aish...... Haɗe
bakinta tayi da nasa guri ɗaya cikin wani irin yanayi dake baiyana tsantsar
shauƙinta a gareshi, wata irin wutar ƙaunarsa ce ke ganiyar fizgart tamkar zata
zautar da ita, daga kallon farko a wannan lokacin bazaka iya tantance ma'anar irin
sumbatar da sukewa junansu ba, sabida hakan tamkar wani al'amari ne dayafi faruwa a
tsakanin tsofaffin masoya waƴanda sukai nutsu a Cikin ƙoramar soyayyah Mara
misaltuwa.

Tsaiwar ce ta fara ƙoƙarin gagararsu ba shiri suka zube A ƙasa bisa makeken kafet
ɗin da yaywa falon ƙawanya suna maida numfashi, daga kan Abie har Ummie babu wanda
baiyana alfarma da shauƙin da suke ciki a gameda junansu, kunsan idan gwani ya haɗu
da gwana wajen ƙwarewa a soyayya tofa sedai kawai aja musu ƙofa a barsu su kaɗai😂

Shiyasa nima nai waje naja musu ƙofar falon don al'amarin dattijawan ya zarce
tunanin chubaɗo balle harta iya samun zarafin rubuta muku shi🤧

*_(Jan hankali a gareku matan Aure, wllh soyayya bata taɓa tsufa so karki bari wai
dan kinga kin haifi yara masu yawa kuma sun kawo ƙarfi kice bazaki nunawa mijinki
tattali da ƙauna ba yayinda kuke gudanar da al'amarin sirrin kwanciyar Aure ba, my
dearest sisters wllh namiji komai tsufansa yana masifarson tattali da kuma zazzafar
soyayya musamman yayinda kuka keɓance dagake seshi, kada ki taɓa bari mijinki yaga
gazawarki akan komai ma na zamanta kewa base lallai ta hanyar kwanciya ba, a kwai
hanyoyi dadama wanda zakiyi amfani dasu ki dasawa mijinki tsantsar qaunarki ba
tareda da boka ko malam ba, kunga ɗan kissing ɗinnan da kuke rainawa wllh karkiyi
wasa dashi wajen yi masa su kala-kala, idan ma baki iyaba to ki koya domin wllh a
kwai wani irin ni'imtaccen sirri a cikin sumbatar juna wanda Allah ne da kansa ya
sanya hakan ba tareda mun sani ba ta hanyar ƙawazucin mu, yayida ma'aurata suke
gudanar da kissing a tsakaninsu numfashinsu kan sarƙe dana juna tareda fitar da
wani irin maganaɗisu me haifar da zazzafar soyayya gamida ƙauna me ƙarfin gaske a
tsakaninsu. So pls sisters we have to be very careful akan wannan sirrin karkuyi
sake akai don Allah.)_* kuma bance wata marakunyar budurwar ta gwada ba sabida sam
ba ɗabi'ar arziƙi bace a gareki ki bari wani ƙato yay kissing ɗinki babu aure ba
♀️
, a kwai tarin cututtukan da ake ɗauka ta hanyar kissing ɗin wani ƙaton don haka
wllh ku kiyye.

Washe gari da duku-duku Muzaffar ya fito cikin shirinsa na wata shaiɗaniyar shadda
gizna brown colour se faman baza yararin tsada takeyi gamida kyau anyi masa ɗinkin
Muhammed, hannunsa ɗaure yake cikin rantsatsen agogonsa na rolex me launin kalar
golden wanda ya ƙara haska tsintsiyar hannunsa, dukda cewar kansa a kwai hula sam
be hana fitowar kwantaccen baƙin gashinsa wanda yabi harta tsintsiyar donkin
wuyansa ba, ƙafarsa sanye take cikin wani haɗaɗɗen takalmi meɗan yatsa wanda aka
ƙerashi daga fatar damusa me launin kalar brown da yarfen milk kaɗan a jiki,
wayoyinsa ya ɗauka ya zuba a aljihunsa sannan ya ɗauki Atm card ɗinshi yasa a cikin
wata cute ƙaramar wallet sannan ya fito se baza uban ƙashi yake tamkar wanda aka
tsamo daga ƙoramar ruwan turare gabaɗaya.

Duk wanda ya ganshi a wannan lokacin zeyi zaton sam ba mutumin ƙasar nigeria bane
sabida yafi kamada larabawan yakin ƙasar Misrah (Egypt) shugar dake jikinsa ce
kawai zatasa ka fahimci shiɗin cikakken ɗan Nigeria ne.

Yana fitowa parking lot ya nufa ya faɗa cikin wata hamshaƙiyar Bugati baƙa wuluk
wadda taji uban tinted kamar bala'i ya figeta @360 se babban filin jirgin dake
cikin babban birnin taraiya, yana zuwa befi saura minti biyar jirgin ya tashi ba
don haka a gaggauce ya perkar motar sannan ya fito ƙarfe biyar ɗin Asuba na
bugawa jirginsu ya ɗaga zuba Tarabah State.

Se muce a sauka lfy Muzaffar ✊

Sushmah💋
[3/3, 5:38 PM] Chubado Mohd: ❄️❄️❄️❄️❄️❄️
❄️❄️❄️❄️❄️❄️
🐄🐄🐄🐄
🐄🐄🐄🐄
*BAFULATANA*
✨RETURN✨
🐄🐄🐄🐄
🐄🐄🐄🐄
❄️❄️❄️❄️❄️❄️
❄️❄️❄️❄️❄️❄️
Page :38

*_WRITING BY: CHUBAƊO_*

Banyi Editing ba

____✍️Cikin ikon Allah da himarsa suka iso garin Taraba lfy, sedai tunda ya shigo
cikin garin taraba ƙirjinsa ke wani irin bugawa wanda shi kansa besan dalilin hakan
ba, sedai yafi ta'allaƙa hakan da baƙon yanayin dayake ciki wanda Ummien sa ta
fassara masa shi da suna Soyayya, ajiyar zuciya ya sauke tareda shafa kwantaccen
lallausan baƙin gashin dake zagaye da kyakkyawar Fuskarsa ma'abociyar haiba da kuma
kwarjini

cikin gari ya shiga zuciyarsa a cike fal da tarun abubuwa wanda yasa hakan ya
haifar masa da faɗuwar gaba me tsananin gaske, guri ya nema daga geban wani babban
titi ya zauna tareda dafe saitin zuciyarsa idanunsa a lumshe, ya jima a hakan
sannan ya miƙe ya fara tafiya cikin takunsa na isa da ƙasaita harya isa bakin wani
Babban bakin wanda akayi rubutu kamar haka ZENITH BANK.

kuɗaɗemasu yawan gaske ya cira sannan ya fito ya samu shatar wata ƙaramar motar
dazata kaishi Gyambu ya shiga ciki ya zauna tareda biyan Driver kuɗinsa ya kuma
buƙaci da ya kaishi wani babban super makert ɗin dazeyi siyayyar kayan Abincin,
ɗaga masa kai Driver ɗin yayi cikeda girmamawa sannan yaja motar don cika umarni.

A gaban wani katafaren Super maket suka tsaya ya cikin nutsuwa ya fito jikinsa duk
babu wani guzari ya shiga ciki ya fara labtar kayan abinci tun daga kan buhuhuwan
shinkafa har zuwa kan catons na taliya, seda ya kashe kuɗi sosai ba ɗan kaɗan ba
sannan yaje ya biya kayan aka fito masa dasu zuwa mota, taf aka cika booth na motar
babu masaka tsinke har seda aka zuba wasu kayan a sit ɗin bayan motar sannan suka
kama hanya don gudin karsu ɓata lokaci.

Sunyi tafiya me nisa gaske damkar zasu bar gari sannan suka iso bakin hanyar dazata
kaisu cikin Rugar tasu Moddibo, tsayawa da motar Driver yayi sannan ya dubi
muzaffar yace "Ranka ya daɗe ta ina kake tsammanin zamu iya ratsawa ta cikin wannan
dajin ?

"sannan kuma gurin wa zakace a cikin wannan sunkurun dajin da babu wani bil'adama
dake Rayuwa a cikinsa? A haka dai kayi kamada mutum me kamala kuna wanda
hankalinsa yake taredashi balle ince ko matsalar ƙwaƙwalwa gareka.

Ɗan jim muzaffar yayi kamar bazece komaiba yace "kaga malam ji nake biyanka nayi?
Indai har ba kyauta ka ɗakko ni ba to kayi yadda nace ɗin idan kuma kuɗinne yayi
maka kaɗan seka gayamin na ƙara maka.

Washe baki mutumin yayi sannan ga taka motar suka kutsa cikin dajin, ta tsakiyar
labin fulani suka dinga raɓawa suna samawa kansu hanya har suka iso cikin tsakiyar
rugar, suna faka motar Befi da mintuna kaɗan ba Mazan Garin suka zagaye motar
hannunsu ɗauke da manyan makamai.

Sosai Drivern ya tsorata hakama muzaffar amma kumashi seya dake batareda ya nuna
tsoron dake taredashi ba ya fito yana kallon screen ɗin wayarsa , cikin harshen
fulatanci wanda yafi kamada na zallar ɗan koyo yace "ni baƙon Alkhairi ne a gareku
bana sharri ba, hkaa kuma nazo ne don na gana da Malam moddibo.
Take yanayin fuskarsu ya sauya daga yanayin da suke ciki zuwa na tausayi suka
dubeshi ba tareda sunce dashi ƙala ba suka buɗa masa hanya ya nufi ƙofar karan dake
kewaye da gidan nasu Rabe ya kunna kai ciki, mata ya gani a zazzaune inda su kuma
su malam iro suke ƙoƙarin fitowa da gawar moddibbo dake kwance samɓal cikin makara
an lulluɓeshi da zani, har suka gama fito dashi daga cikin bukkarsa da aka
shiryashi a ciki idanunsa na kansu ba tareda ya motsa ba sabida tsabar tashin
hankalin dayake ciki. Bayan sun fito dashi ne muzaffar ya samu zarafin zubewa akan
ƙafafunsa dirshen a ƙasa ƙirjinsa na wani irin bugawa.

Banda rawa babu abinda bakinsa keyi so yake yayi magana amma kuma ya kasa daƙyar
ya iya ɗaga hannunsa yay nuni da makarar daga inda yake zaune ya buɗe bakinsa
dakyar ya haɗo kalmomin dake maƙale a ƙasan maƙoshinsa yace "why Baffah ? "why are
you doing this to me? "I said why!!!? Muzaffar ya faɗa da wani irin ƙarfi lokaci
guda kuma ya fashe da wani irin kuka kamar mace.

Hakanne ya janyo hankalin jama'ar dake gidan zuwa gareshi gaɓaɗayansu suka kafeshi
da ido suna kallonsa.

Babu wanda yace dashi ƙala sabida sam basu shaidashi ba ciki kuwa harda Inna Laure,
kallonsa kawai takeyi Idanunta na zubar da Hawaye me matiƙar zafi da ciwo tambaya
ɗayace take mata yawo a rai wadda ta rasa amsarta itace shin wanene wannan
Matashin ?

Yanaji yana gani su Malam iro suka Raɓa ta gefansa suka fita da gawar zuwa Waje
donsuyi masa sallah, ya jima a gurin zaune yana kuka har suka kabbar Sallah still
yana zaune ya kasa koda motsin kirki

Shiru yayi ya zubawa ƙofar ɗakinsa idanu nan da nan ya faɗa cikin ƙoramar tunani,
da wani irin mugun sauri ya tashi ya fita da gudu zuwa inda Malam iro ke gabatar da
Sallar gawar yasa hannu ya fin cike zanin da aka rufeshi dasi, cikin ƙanƙanin
lokaci ya saita hannunsa a daidai saitin zuciyarsa yasa hannunsa duka biyun ya fara
dannawa da ƙarfi still idanunsa na zubar da hawaye.

Sallame sallar sukayi da hanzari sukayo kansa suka janyeshi daga jikin gazawa kowa
na tofa albarkacin bakinsa, masuyi masa kallon mahaukaci nayi haka kuma masu magana
ma nayi.

Shidai Drivern da sukazo tare kallonsa kawai yakeyi a ransa yana me tausaya masa,
igiya suka samu me kaurin gaske suka ɗaure muzaffar da ita sannan aka samu akayiwa
moddibo sallar

Bayan sun idar ne suka fara giji-gijin ɗaukar makarar take sukaga jikin moddibon na
wani irin karkarwa, gab aɗayansu jama'ar dake gurin tserewa sukai kowannensu ya
cika wandonsa da iska sabida faruwar wannan abin al'ajabi idan kuka cire Malam iro,
shine kaɗai be iya barin gurin ba ya tsaya cak yanai masa addu'o'i. Shima alfarmar
ilimin Addinin dayake dashi wadatacce ne ya sanyashi tsayawar batareda ya gudu ba,
fuzge jikinsa muzaffar yayi da ƙarfin tsiya tareda nufo gurin da wani mugun gudu,
kallon Driver ɗin da sukazo tare yayi cikin ɗaga murya yace "matso da motar
mukaishi Asbiti.

Dama can drivern ya gama sauke kayan da suka lodo na abinci hakanne ya basu damar
saka moddibon a ciki sannan muzaffar ya shiga baya tareda moddibo shikuma malam Iro
ya zauna a mazaunin gaba shi kuma Drivern yaja motar da gudun gaske suka nufi
cikin garin Gyambu don nema masa taimakon gaggawa daga likitoci.
Comment
Nd
Share

Don't forget to vote on whatpad.

Sushmah 💋
[3/3, 5:38 PM] Chubado Mohd: ❄️❄️❄️❄️❄️❄️
❄️❄️❄️❄️❄️❄️
🐄🐄🐄🐄
🐄🐄🐄🐄
*BAFULATANA*
✨RETURN✨
🐄🐄🐄🐄
🐄🐄🐄🐄
❄️❄️❄️❄️❄️❄️
❄️❄️❄️❄️❄️❄️

Page : 39

*_WRITING BY: CHUBAƊO_*

Banyi Editing ba

____✍️Direct Babban Asibitin dake cikin garin na Gyambu suka wuce dashi cikin ikon
Allah a ɗan ƙanƙanin lokaci manyan liƙitocin dake on duty a ranar suka rufu a
kansa, sun jima suna kokawa da numfashinsa sannan suka samu nasarar daidaituwarsa,
bayan 2hours likitan daya jagoranci lamarin mara lfiyar ya fito sanye da farar
labcord ɗinsa wanda gefanta duk yay stain da jini, wata irin zuface kwance a saman
goshin likitan alamar sun wahala sosai wajan shawa kan matsalar, a nitse yake
takowa cikeda nutsuwa harya ƙaraso inda su Muzaffar da Malam iro ke zaune damuwa
fal a saman fuskokinsa ya tsaya ba tareda ya iya furta musu ko kalma guda ba.

Nurse ɗin dake bayan likitance ta maida kallonta ga Muzaffar tareda kafeshi da
mayun idanunta kamar zata cinyeshi ɗanye, ganin sam basu lura da tsaiwarsu bane a
gurin sabida ruɗun da suke ciki Nurse ɗin tai gyaran murya cikeda gwalangwaso irin
na ƴan duniya tace " Ranka ya daɗe Dr. Na magana.

A hanzarce muzaffar ya ɗago manyan fararen Eye ball ɗinsa ya saukesu kan Likitan
cikeda damuwa yace "Dr. How is he pls?

Ajiyar zujiya Likitan ya sauke tareda nazartar yanayin muzaffar ɗin sannan yay
murmushi yace "is ok dear he is fine Alhamdulillah ya fita daga Haɗari, sannan a
kwai mahimman abubuwan daya kamata mu tattauna dakai akan conditon ɗin mara lfyn,
muje office . Yana gama faɗin hakan yay gaba su kuma suka mara masa baya
A tsayawa yayi a jikin wata ƙofa wadda akayi rubutu da nau'in bakin ink kamar
haka Dr. Fauwaz Qaribullah. Wannan ne ya basu tabbacin cewa lallai nan ɗin shine
office ɗin nasa.

A nitse suka shiga office ɗin gabaɗayansu ciki kuwa harda Dr. Fauwaz ɗin zama yayi
sannan suma suka yauna tareda fuskantarsa alamar a ƙage suke suji bayanin daze musu
ɗin, murmushi yayi kaɗan sannan ya gyara zaman lab courd ɗin dake jikinsa yace "im
sorry to say but gaskiya he is in critical condition abu mafi girma ma shine
zuciyarsa ta riga ta harbu sakamakon wani tdiro daya bito masa a tsakiyar zuciyar
tasa, magana ta gaskiya a yanzu se'an masa Aiki don rabashi da wannan abin cikin
sauri a hakan ma idan anyi babu tabbacin cewar ze tashi. Ya faɗa yana kallon
tsakiyar ƙwayar idanun Muzaffar wanda tashin hankali mara misaltuwa ya baiyana akan
fuskarsa.

Cikeda damuwa kamar ze fashe da kuka yace "pls Dr. Babu wani abu dazaka iya taimaka
mana dashi akan condition ɗin nasa? Ɗan jim kaɗan Dr. Fauwaz yayi yace " munada
hanya gudaɗaya wanda nake ganin a kwai yuwuwar a dace. Da sauri muzaffar yace
"inajinka Dr.

Dr. Yace "ina ganin yanzu zamuyi muku transfer xuwa wani babban Asibiti dake yola
im sure of that Idankunje zaku dace. Dakatar dashi muzaffar yayi ta hanyar cewa no
Dr. Ka bari kawai nidai alfarma ɗaya nakeso kamin shine ka haɗamin manyan likitocin
da sukasan aikinsu wa ƴanda kuma zasu iya taimaka masa kafin zuwa gobe inyaso semu
fita dashi india akan batun aikin yanzu bari nayi waya ai mana booking jirgi semu
wuce Abuja gabaɗaya kafin goben.

Da wannan batun suka samu matsaya, bayan sun fita daga office ɗin Dr. Fauwaz Malam
iro ya kalli Muzaffar yace "yaro taya zan iya yarda dakai kan cewar bazaka cutar da
Moddibo ba idan har ka tafi dashi? Hannunsa muzaffa ya kama cikin nasa yace "a
halin yanzu bazan iya furta maka komai ba Malam amma abinda na sani shine wajibi ne
in biya Baffa alkhairin dayayi min koda kuwa hakan yana nufin gabaɗaya dukiyata
zata ƙare ne, ya taimakeni a lokacin danake buƙatar taimako shin laifine dan nima
nayi yunƙurin ceton tasa Rayuwar alhalin kuma inada damar yin hakan malam?

Da sauri ya ɗaga masa kai alamar aa bakayi laifi ba, kuɗi masu yawa muzaffar ya
zaro ya miƙawa malam yace "don Allah malam ga wannan kuɗin ka kula da duk wata
buƙata ta iyalan Moddibo sannan kayi musu dukkan abinda sukeso, kuma ka shaida musu
cewar insha Allah Baffa ze samu lafiya har ya dawo musu da ƙafafunsa da izinin
Allah, sannan idan ka koma gida ka gayawa Rabi'atou cewar ina gaisheta kuma nan
bada jimawa ba zan dawo gareta . Ya faɗi maganar tareda baiyana zallar soyayyarsa
gareta

kallon tsaf malm Iro yay masa da dukkan alamu besan abinda ke faruwa a cikin
Rayuwar Rabe ba, wata irin zazxafar ƙwallar tausayinsa ce ta zubowa malam iro
lokaci guda kuma ya juya yabar harabar Asibitin, tabbas yanzu kam ya shaida wannan
matashi babu shakka shine wanda ya zauna dasu har kimanin watanni huɗu a taredasu.
Komadai menene yanada yaqinin cewar baze taɓa cutar da Moddibon ba.

tun kafin muzaffar subar gyambu ya ɗaga waya ya kira PA ɗinsa Mubaraq Nuhu yace
yayi masa booking ɗin private jet zuwa ƙasar india, cikeda girmamawa ya amsa masa
tareda katse kiran, kamar yanda ya buƙata hakanne ya kasance gurin Dr. Fauwaz ɗin
shida kansa ya haɗashi da ƙwararrun likitoci tareda mara lafiyan jirginsu ya ɗaga
se birnin taraiya.

koda suka iso a ɗaya daga cikin gidajen ma'aikatansu ya sauki likitocin tareda duk
wani abu dazasu buƙata sabida mara lfyan dukda cewar basa tsammanin faruwar wani
abu mara daɗi a taredashi, shiko daga nan gida ya wuce Direct part ɗinsa ya nufa
ya watsa ruwa sannan ya shiga part ɗin mom ya shaida mata cewar zeyi tafiya zuwa
india, sosai suka dinga zuba masa adɗu'a ba tareda sun damu da tambayarsa dalilin
yin tafiyar tasa ba tunda dama can sunsan yakanje ɗin musamman idan yanada meeting
da abikanan kasuwancinsa, ya ɗan jima a nan suna hira sannan ya miƙe zuwa part ɗin
Ummie da sallama ɗauke a bakinsa ya shiga falon wanda keda zuba uban ƙamshin
turaren wuta, babu kowa a falon se Baba Hajarah wadda ke kallon film ɗin hausa a
tashar Tauraruwa, zama yayi a kusada ita tareda sanya kansa bisa kafaɗunta yace "
Me ran Ƙarfe ya kike?

murmushi tayi tace "ina lfy ƙaramin me gida ya naganka haka nan kamar bakajin
daɗin? Uhmm lfy na ƙalau wllh kawai dai na gaji ne sosai gashi kuma zanje india
gobe insha Allah inada meeting. Jinjina kai tayi tace "to Allah ya kaiku lfy ya
tsare hanya ɗan albarka. Da amin ya amsa mata yace "ummie fa? "Yanzu ta shiga ciki

miƙewa yayi ya nufi bedroom ɗin Ummien , a kwance ya sameta saman doguwar kujerar
dake ɗakin Direct nufarta yayi yay hugging ɗinta tareda faɗin i miss u My. "katse
wayar tayi ta dubeshi tace "ya dai na ganka haka kamar kana cikin damuwa? "no lfy
lau Ummie kawai dai kewanki nake tunanin zanyi sabida gobe zan wuce india inada
meeting da wasu sababbin masu hannun jari a companyn mu.

nan ma Addu'ah tayita mishi kusan a tare sukai Diner sannan ya fice ya koma part
ɗinsa tareda sanya ran cewa insha Allah kafin Abi ya dawo daga kano yabar ƙasar tun
kafin ya ɓaro jirginsa...

A gurguje pls

cikin ikon Allah kuwa washe gari da sassafe jirginsu ya ɗaga zuwa Qasar india.
Semuce A sauka lfy C.E.O

*_ƁANGAREN GIDAN ME GIRMA C.P KUWA_*

Edyan ne zaune bisa makeken ƙayataccen falons wanda aka ƙawata da ababan jin daɗi
na duniya gamida ƙawata guri, kallo ɗaya zakayiwa falon ka fahimci shiɗin bame
yasanson shirgi bane ba, sanye yake da farar T-shirt gamida wando treequater
wanda ya kasance baƙi wuluk dashi, ƙafafunsa zube kan table ɗin glass ɗin dake
ajiye kusa dashi idanunsa a lumshe, turo ƙofar falon tayi tareda ɗan tsayawa kaɗan
tana bin ko ina na falon da kallo hannunta ɗauke da littafin da biro kamar zata
fashe da kuka, a hankali idanunta suka sauka akan Hansome face ɗinsa ma'abociyar
kwarjini gamida Haiba, kafeshi tai da manyan idanunta karona Farko a Rayuwarta
dataji tunanin muzaffar ya faɗo mata a cikin zuciya da kuma gangar jikinta
Gabaɗaya, takure jikinta tayi guri guda lokaci guda kuma taji sanyin Ac ɗin dake
falon yana nema yayiwa duk wata gaɓa dake jikinta illah.

Wani irin daskararren hawayene me cikeda ɗaci gamida Zallar muradi mara misaltuwa
ne ya fara kwaranya a kan kyakkyawar fuskarta, sakin littafin tayi ya faɗi a saman
haɗaɗɗen kafent ɗin daya zagaye falon ta ko' ina tareda sanya hannunta ta ƙanƙame
jikinta gaba ɗaya.

Faɗuwar littafince ta janyo hankalin Edyan zuwa gareta, a hankali ya buɗe limsassun
idanunsa masu cikeda da alamar bacci ya daukesu tar a kanta. Ganin hawayen dake
zuba a saman fuskarta ne yasa ya mike da hanzari ya isa gareta tareda dafa
kafaɗunta duka biyu yace "what's wrong dear? Ya faɗa cikeda zallar nuna damuwarsa
gareta.

Kasa amsa masa tai illa ƙara matse jikinta da ta sakeyi guri guda tamkar wadda aka
jefa a cikin ƙorar ƙanƙara, lumshe idanunsa yayi ya sake buɗesu akan beauty face
ɗinta yace "wllh da kinsan yanda nakeji idan naga hawayenki da bazaki taɓayin
shi'awar ki zubar dasu haka a banza ba, zuciyata da duk wata gabar da jijiyoyin
jinina kebi sukan ɗauki wani irin zafi wanda ya zarce na tafasashiyan dalma a duk
lokacin dana ganki kina kuka, kodan sabida yanda zuciyata ke zafi meyasa koda so
ɗaya ne bazaki hana kanki kuka ba Mulaikha?

Kafeshi tai da manyan idanunta tana me nazari akan maganarsa, daga irin kallon da
take masa kaɗai zaka fahimci cewa sarai ta fahimci inda kalamansa suka dosa, amma
kuma da ace shima ze san irin halinda take ciki a wannan lokaci tabbas dayayi mata
uziri koda kaɗan ne, a irin yanda taƙeji a nata ran idan aka misalta da nasa wllh
tata azabar ta zarce tasa. Wasu sababbin hawaye ne suka shiga sakko mata babu
ƙaƙƙautawa lumshe lumsassun idanunsa Edyan yayi tareda miƙar da ita tsaye lokaci
guda kuma a karo na farko a Rayuwarsa ya janyota jikinsa yay hugging ɗinta with so
much love and caring. Gabaɗayansu wani baƙon yanayi suka samu kansu a ciki me
matiƙar wahalar fassarawa sedai dukda hakan batayi yunƙurin zare jikinta daga nasa
ba sema ƙara fashewa datai da wani sabon kukan wanda ita kanta batasan na menene
ba.

Bubbuga bayanta ya dingayi a hankali ba tareda yayi ƙoƙarin hanata yin kukan ba,
all he know is to let her cry and cry at least she will get some peace of mind
akan abinda takeji dukda cewar be san meyeshi ba because har yanzu didn't tell him
anything about her story shi kuma sam be tambayeta ba, abu ɗaya kawai ya sani shine
a kwai ciwo a cikin Rayuwarta wanda take buƙatar koda so ɗaya ne abarta tai kuka
koda kaɗan ne wata ƙila ciwon dake ranta ze rage raɗaɗi.

Seda tai me isarta sannan tayi shiru a hankali ta zare jikinta daga nasa ta
kalleshi da idanunta da suka rine zuwa launin na wadda tayi kuka tace "bro
Assigment pls.

Hannunta ya kama zuwa tdakiyar falon ya zaunar da ita akan lallausan kafet ɗin yace
"bring the book let me see. Ɗan jim kaɗan tayi sabida yanda turancin nasa yaɗanyiwa
fahimtarta nauri se kuma ta kalleshi tace "Noi?

Dariya ya sakin mata har seda kyawawan white teeth ɗinsa suka baiyana yace "nace
muga littafin naki ?. Turo baki tayi a ranta tace "oh wai maganar ma baza'ayita
yanda mutum ze gane cikin sauƙi ba. Hannunsa yasa yaja siririn dogon hancinta har
seda ta ɗan saki ƙara sannan ya fara nuna mata yanda zatayi tayi ta fitar da answer
ɗin, tunda suka fara taketa faman tura baki ita a dole wai ya takura mata. Bayan
sun gama ne ta tattara book ɗin da biro ɗin ta fice daga falon babu ko thanks.

Dariya kawai yayi a ransa yana ƙarajin yarinyar a ransa sosai, haka kawai yakejin
daɗin zama da ita sabida yanda wasu abubuwan nata ke yawan bashi dariya, duk
daɗewarta a gidan besa ta manta wasu ɗabi'un nata dake nuna ainihin daga ina ta
fito ba, a zahiri idan ka kalleta haka zakayi tsammanin itaɗin wayayyiyar mace ce
Saɓanin idan tayi magana kokuma ta tafko maka wani shirmen nata me cike da zallar
gidadanci, dariyace ta kufce masa daya tuna lokacin daya sameta a zaune dafi'an a
saman daining tayi dare-ɗare tana shafa butter a jikinta. A hankali ya saki wani
ƙaya taccen murmushi tareda Furta " Funny girl. A haka dai rayuwa ta dinga
tafiya a tsakanin su cikeda zallar kulawa gamida nuna mata duk wata soyayya dazata
sa ta manta abinda ke Ranta wanda kullum take aikin mafarkinsa.

Zeeyadah ce zaune a gefan gadonsu Rabe kuma tana kwance ta zubama saman ɗakin idanu
tana aikin tunani, a hankali taji sallamar mom da hanzari ta miƙe tana mata
murmushi alamar ta saba da ita sosai, cikin harshen fulatanci mom tace "dota
bazakizo ki rungumeni ba kodai bakiyi kewata bane 2days? Tun kafin ta rufe
bakinta ta tafi da gudu ta faɗa jikinta tana ɓoye fuskarta a jikin mom ɗin.

Edyan ne ya shigo ɗakin hannunsa ɗauke da wani kwali ya kalleta yace "Mulaikha come
with me I want to show you something special that I Bay it for you I'm sure you
will love it. Da hanzari ta saki mom tabi bayansa ba tareda ta lura da irin kallon
dasu mom ɗin kebinta dashi ba, a falo sukaci karoda Hajar tana ƙoƙarin shigowa
falon da sauri ta ɗaga fararen idanunta tareda washe mata baki tace "welcome beck
sister. Hararanta tayi ba tareda ta kulata ba ta wuce tana jan tsaki

Shidai Edyan sam bebi takan wata Hajar ba ya buɗe kwalin ya fito da wani takalimi
ƙirar toms me masifar kyau gamida tsada, ƙurawa takalmin idanu tayi kinta a buɗe
tamkar taga ktafaren abin al'ajabi, ƙafarta ya jawo ya fara ƙoƙarin saka mata
takalmin tayi saurin janyewa tareda fuzge takalmin daga hannusa tana dariya tace
"wannan ai ba takalmi bane mudubi ne patner. Ta faɗa tana ƙalla idanunta ta cikin
babban ston ɗin dake saman toms ɗin wanda keta baza uban kyalli tamkar ɗanyen
daimond 💎

Baki ya saki yana kallonta kamar ya samu tv wani irin masifan burgeshi yaji tayi
shiyasa ma ya shagala da kallonta, batareda ya shirya fuskanta abinda zeje yazo ba
daga can ƙasan maƙoshinsa yace "I love you Mulaikha i really Love you with all my
heart !!

Dakin baki tayi tareda maida kallonta gareshu ta wani irin kafeshi da wani irin
mayan kallo wanda har seda yaji jikinsa yayi sanyi, ta ɓangarenta kuma haka kawai
taji a ranta cewar kalmar daya faɗa ɗin tayi madifar jan hankalinta becouse ta taɓa
jinta a kwanakin baya da daɗewa, seɗai dukda hakan sam bata san me kalmar take nufi
ba.

Murmushi yayi tareda Sumbatar gefan kumatunta ya fice daga falon ba tareda ya
waiwayo ba, yana dabda fita daga ƙofar falon ya tsinkayi muryarta tace "thank you
partner. Be juyo ba ya fice gabaɗaya

Daki ta koma da kwalin takalmin a hannunta ta tarar da zeeyadah na zaine a bakin


gado tana amsa waya, itadai bataji ƙarshen maganar da zeeyadah keyi ba taji tace "I
love you too dear.

Kafeta tayi da idaninta sannan ta ajiye takalmin a tsakiyar ɗakin ta nufi zeeyadah
tareda ɗora hannunta a daman kafaɗunta tace "pls me wannan kalmar take nufi?
Cikeda rashin fahimta tace "wani kalma kuma Mulaikha?

"i love you ? Ta faɗa with so much courage. Kallonta kawai Zeeyadah tayi da mamaki
kwance a saman fuskarta tace "who told you so mulaikha? Ba tareda ta kalleta ba
tace "pa....... Momce ta shigo ɗakin hakanne yasa bata ƙarasa maganar ba ta nufi
mom da sauri tareda ɗaukan takalmin tana dariya ta nufi mom ɗin dashi tana nuna
mata.......

comment
Nd
Share

Don't forget to vote on whatpad

Sushmah💋
[3/3, 5:38 PM] Chubado Mohd: ❄️❄️❄️❄️❄️❄️
❄️❄️❄️❄️❄️❄️
🐄🐄🐄🐄
🐄🐄🐄🐄
*BAFULATANA*
✨RETURN✨
🐄🐄🐄🐄
🐄🐄🐄🐄
❄️❄️❄️❄️❄️❄️
❄️❄️❄️❄️❄️❄️

Page : 40-41

*_WRITING BY: CHUBAƊO_*

*Duk wata Qaddarar dake ɗauke da zallar soyayya gamida muradi me ƙarfin gaske Kan
zamewa zuciya Kamar gyambo me matiƙar zafi gamida Ciwo musamman Idan Zanan
ƙaddarar rabuwa ya gifta atsakanin masoyan😢.*

*Banyi Editing ba kuyi haquri da typing error*

____✍️Sosai mom ta nuna mata jin daɗinta akan takalmin da Edyan ɗin ya siya mata
musamman dataga yanada Mulaikhan ta nuna jin daɗinta sosai akai, kallonta mom
tayi cikin ido tace " kince mishi kin gode ko Mulaikha?

Murmushi ta sakin ma mom ɗin har seda beauty point ɗinta both side suka lotsa at
the same time, juyawa mom tayi ta kalli zeeyadah tace ki ajiye wayar nan malam kuzo
khitchine zamu shirya abinci na musamman Sabida yau Dadynku xe dawo. Wani uban
tsalle zeeyadah ta buga tareda wirga wayar kan gado tazo ta rungume mom tana murnar
tace "are you serious mom?

Ɗaga mata kai mom tayi tareda faɗin "sure darling. Sannan ta Shafi gefan fuskokinsu
tace "muje ko. Tare suka fita zuwa kicin suka fara gabatar da komai cikin tsari
tareda zumuɗin dawowar mijin nata ita kuma zeeyadah na farin cikin ganin Dawowar
Daddyn nasu, a haka har suka gama girkin cikin nutsuwa da aminci bayan sun gama
girkin a manyan kuloli na gani na faɗa mom ta kwashe abincin sannan ta kalli Rabe
tace "dota kuzo kuje keda Zeeyadah part ɗin Daddy ku gyara sannan ku kwashe womers
ɗin nan ku kai kan daining ɗinsa. Da to suka amsa sannan suka tafi cika umarnin mom
ɗin.

Kamar yanda mom ɗin ta faɗa hakan ne kuwa ya kasance, sosai suka shiga gyaran part
ɗin da dukkan ƙarfinsu tun kafin aci litinin da talata a aikin zeeyadah ta xube
akan kujera tace ta gaji, murmushi Rabe tayi sannan ta ci gaba da aikin ba tareda
ta huta ba seda ta gama tsaf sannan suka fito zeeyada na kuranta ta da irin zafin
naman da mulaikan kedashi, itadai mulaikha murmushi kawai take har suka fice daga
falon sannan suka fita

Se wajen yamma sannan jirginsu Dad ya sauka a babban birnin taraiya Abuja, gabaɗaya
Ahalin na gidan Edyan ya kwasa a mota da kansa ba tareda guards ba suka tafi except
Mulaikha da aka bari a gida don gudun kar dad ya ganta.

Lokacin da sukaje ba ƙaramin farin ciki dad yayi da ganinsu ba sabida yanda yay
masifar kewarsu, shigewa jikinsa Zeeyadah tayi tana dariya tace "dad i miss you
wllh. Murmushinsa ya faɗaɗa sannan ya kalli mom yace "murja banga mamana ba were is
she?

Ɗan jim kaɗan mom tayi don wllh koze kasheta bata san inda Hajar take ba, rabonta
da ita tun safe kafin ta tafi office. Murmushi ta ƙaƙalo masa tace " she's in the
office...

Taɓe baki Edyan yayi a haka har motocin jami'an tsaron suka iso sannan suka
ɗaukeshi tareda yi masa rakiya zuwa gida tareda iyalansa, suna isowa gida aka
wangale musu Get motocin suka dinga danno kai kamar bazasi ƙare ba, dad na fitowa
daga motar idanunsa suka sauka akan Rabe data leƙo ta windon falon sama. Da sauri
ta saki labulan gabanta na faɗuwa.

*NEW DELHI*

Mohad moghandi special Hospital, muzaffar ne zaune bisa wani ƙayataccen ɗaki wanda
aka ƙawata da kayayyakin kula da lfy iri-iri, wani ƙasaitaccen gado na hanga daga
can gefe wanda moddibo ke kai idanunsa a rufe ruf, a tsakanin bakinsa kuma
masuburbuɗar oxygen ce maƙale a fusƙarsa wadda take sauwaqe masa hanyar shaƙar
numfashi cikin sauƙi. Ƙura masa idanu muzaffar yayi yana kallonsa cikeda zallar
tausayinsa yasa hannunsa ya shafi gefan fuskarsa sannan ya fice daga ɗakin da
sauri.

Direct inda aka tanada don biyan kuɗin tiyatar ya nufa batareda ɓata lokaci ba yayi
musu transfer Ɗin naira million 5 ɗin da suka buƙata sannan suka bashi racit
shedar ya biya yabar gurin zuwa ɗakin da yabar modɗibon, cikin mintunan da bazasu
gaza goma ba aka shiga dashi tiyata room ɗin a ƙarƙashin jagrancin Dr. Rahul Gufta
da teams ɗinsa.

Semuce Allah yasa ayi a sa'a Dr. Rahul Gufta.

Ako wani lokaci abubuwa da dama kan sauya manufarsu musamman ga zuciyar dake cike
da zallar muradi gamida begen akan dukkan abunda take mafarkin samu tareda
mallakarsa na har abada, zuwa yanzu baze iya tabbatarwa da kansa irin halin dayake
ciki ba hatta jinin dake gudana a jikin kowace gaba ta jikinsa a gauraye yake da
wani nau'i na musamman tareda sirki irin na zazzafar soyayya mara misaltuwa.

Amsawa ƙirjinsa yayi da sauri lokaci guda kuma wani irin tsoro ya ɗarsu a saman
zuciyarsa , haka kawai seyaji jikinsa yamasa masifar sanyi wanda hakan yasa ya
durƙushe a saman gwiwoyinsa tareda dafe saitin zuciyarsa dake fitarda wani irin
bugu me sauti, iskar dake bakinsa ya furzar da ɗan sauran guzarin daya rage masa a
nitse ya miƙe tareda jan ƙafafunsa da sukai masa wani irin Nauyi harya samu zarafin
ƙarasawa bakin gadon da Moddibo ke kwance, hannunsa ya miƙa ya kamo hannun
moddibon cikin nasa ya ɗamƙe tareda zaman bisa kujerar dake bakin gadon, a hankali
yake iya buɗe bakinsa da nufin yayi masa magana Amma kuma seya kasa sabida yanda
maganar dayake son faɗa ɗin tayi masa nauyi, ajiyar zuciya ya dinga saukewa akai
akai tamkar wanda ta gwabza tsere da ingarman doki maji ƙarfi.

A tabbas a yanzu kam ya ƙara tabbatarwa da kansa cewar shiɗin baƙo ne akan lamari
irin wanda ya samu kansa a ciki, haka kuma da ace yanada yanda zeyi da wannan
muraɗin dake addabar zuciyarsa a kowace daƙiƙa ta Rayuwarsa tabbas daya samawa
kansa mafita a kai, gabansa ne ya faɗi a karo na biyu daya tuna da batun Auren dake
tsakaninta da Bawuro, cikeda zallar tashin hankali ya zare hannunsa daga cikin na
moddibo idanunsa sukai wani irin ja.

Wayarsa ce ta ɗauki ruri, a hankali ya zaro wayar tareɗa zubawa screen ɗin wayan
manyan idanunsa masu ɗaukar hankalin duk wani me kallonsu, sunam Ummie daya gani
yana yawo a saman wayar ne yasa ya ɗaukar ba tareda yayi magana ba.
"Assalamu'alaikum. Ummie ta faɗa muryarta ɗauke da Amon murmushi a cikinta .
Wata nannauyar Ajiyar zuciya Muzaffar ya saki har seda Ummie ta ɗan razana kaɗan,
cikin yanayin damuwa da zallar kulawa Ummie tace "Sweetheart are you alright?

Kamar zeyi kuka yace "Ummie I'm scared I don't want to lose her!!! I feel like
kamar somthing is definitely happen to her Umm..... Kasa ƙarasawa yayi sabida yanda
ƙirjinsa yay masa masifar nauyi kamar ze tsage.

Miƙewa Ummie tayi daga zaunen datake sabida yanda hankalinta yay masifan tashi da
yanayin muzaffar ɗin tace "look son pls relax don Allah ka nutsu karka sawa kanka
damuwa ka kwantar da hankalinka zuwa lokacin dazaka dawo Nigeria insha Allah komai
zeyi daidai, ka sa a ranka cewer babu bind ze faruda it se alkhiri kaji ko?

A hankali yake sauke nufshi kimanin lokaci meɗan tsayi can ƙasan maƙoshinsa yace
"pls Ummie keep pray for me wllh i don't want lose her idan na rasata wani abu ze
iya faruwa dan......."stop saying that son!!!! Are you in your sense? "I don't
want you to say anything like that again kaji na gaya maka indai baso kake nima
wani abin ya faru dani kafin kai ba. Ummie ta faɗi hakan a matiƙar harziƙe

Kamar zeyi kuka yace "I'm sorry ummie baran ƙaraba. Murmushi ta sakin masa har yana
iya jiyo sautinsa tace "that's my darling son Barakhallahu'feekah, ka kula da kanka
kaji ko and don't forget to pray ok? Jikinsa a mace yace "ok Ummie bye.

Katse wayar tayi tareda yin shiru tana nazari akan damuwar gudan jinin nata,
jikinta ne yayi wani irin sanyi data tuna cewar ɗan nata baƙo ne a cikin al'amarikn
daya danganci muradi me haɗe da sirki irin na soyayyah.

Hannu ta ɗaga tace"ya ubangijina ga amanar daka bani nan ta ɗan dana haifa,
amatsayina na uwa kuma me rauni banida ikon dazan iya yaye masa damuwarsa komai
ƙanƙantar ta sekai Ubangijina, ina roƙonka da sunaye ka tsarkaka mafiya kyawu ya
Allah ka sauwaƙe masa samun cikar muradinsa cikin sauƙi ba tareda ya sha wahala
kokuma ya shiga wani hali ba. Ummie Ta faɗi hakan tana share ƙwallar data zubo
mata a saman fuskarta, sallamar Abie ce ta sanyata saurin goge ƙwallar da sauri
sedai dukda hakan seda Abie ɗin ya gani a hanzarce ya ƙaraso kareta damuwa kwance a
saman fuskarsa ya zauna daga gefanta yace "Aisha lfy kike kuka? Meya faru dake da
harya sakaki zubda hawaye irin haka? Abie ya jera mata tambayoyin duk a
lokaci guda.

Dakewa tayi tareda gaiyato jarumta a tareda ita tace "Abdul inajin tsoro kar yaron
mu ya faɗa a cikin ramin soyayyar da balallai ya iya fitowa ba, muzaffar ya faɗa a
soyayyar wata yarinya wadda ta kasance Bafulatana ce sun haɗu ne a can wata ruga
dake cikin jihar taraba sakamakon taimakonsa da mahaifin ta yayi a lokacin dayake
dabda rasa rayuwarsa, nan dai Ummie ta sanar da Abie kaf abinda ke faruwa ba tareda
ta iya ɓoye masa koda kalma ɗaya ba, ƙuri Abie yayi mata yana kallonta tamkar ya
samu Tv harta dasa aya ba tareda ya katseta ba.

Seda ta gama tsaf sannan ya dubeta yace "kina nugin ɓatan da muzaffar yayi tsahon
watanni dama wasu ne suke ƙoƙarin halaka min ɗa ba tareda na sani ba kuma shima be
sanar dani ba? Dafa kafaɗarsa Ummie tayi cikeda rarrashi tace "ka kwantar da
hankalinka Abdul an riga da anyii handling komai ai tunda har Maryama ɗin ta shiga
hannun hukuma.

Shiru yayi yana ƙara juya abin a ransa sannan ya dubeta yace "lallai be kamata mu
gaza wajen samawa ɗanmu cikar muradinsa na Auren yarinyar dayake so ba Aisha, koda
ace a ƙarƙashin ƙasa take bawai a Daji ba ni nan zanje na nema masa Auranta koda
ace gabaɗaya abind na mallaka ze ƙare ne gaba ɗaya, tunda har kikaji ya furta miki
da bakinsa cewar yanasonta I'm very sure he loves her more than our think, becouse
shiɗin mutum ne me matiƙar zurfin ciki akan dukkan lamarinsa tinda har ya kasa
ɓoyewa to lallai abin ba ƙarami bane sedai kawai muyi fatan dawowarsa ƙasar lfy.

Da Amin Ummie ta amsa tana me ƙara jinjina lamarin a ranta.

******

Al'amarin gidansu Edyan kuwa sosai rayuwarsu ke tafiya cikeda jin daɗi gamida
walwala, lokacin da Dady ya dawo daga America yayi mamakin ganin baƙuwar fuskar
dake zaune a gidansa, don haka ya buƙaci da mom ta taro masa taron Ahalin nasa
gabaɗaya don yaji ba'asin komai, bayan sun hallara a babban falon na Dady sosai
Mulaikha (Rabe) ta tsorata da ganin Dadyn kasancewar bata taɓa ganinsa a gidan ba
se yau, ƙanƙame jikinta tayi a jikin mom kamar zata shige jikinta.

A nitse Dady yakai dubansa gareta tareda ajiye News Paper ɗin dake hannunsa sannan
ya kalli mom yace "ina sauraronki meye ma'anar zaman yarinyar nan a gidan nan ?
Tun kafin mom tayi magana Hajar tayi caraf tace "kaima dai Daddy ka faɗa wllh nima
dawowa nayi na sameta a gidan nan, kuma wllh daddy laifin mom ne tun a lokacin da
Ya Edyan yazo da ita gidannan naso su korata inda ta fito amma sukaƙi, wllh ranar
har Marina Mom tayi akan wannan yarinyar da ba'asan Asalinta ta don kawai ita
BAFULATANA CE.

Mari kika ce Mamana? Sure Daddy wllh marina mom tayi akanta don kawai nayi mata
tsawa!

A fusace Daddy ya dubi mom yace "anya kina cikin hankalinki Murjanatu da har zaki
ɗaga hannu ki mari Mamana sabida tayiwa wannan yarinyar tsawa ? Dad ya faɗa
yana nuna Mulaikha dake ƙara ƙanƙame mom jikinta se uban rawa yakeyi.

Dukda cewat batajin abinda suke faɗa sosai sabida ba wani jin hausar take me tsaho
ba ta fahimci cewar lallai Dady akanta yake magana.

Wata uwar tsawa daddy ya dakawa Mulaikhan (Rabe) wadda tasa ta sakin mom da sauri
ta fashe da wani irin kuka tana kallon mom ɗin yace "gashi nayi mata tsawa
Murjanatu nima sekizo ki mareni sabida na ɗagawa ƴar gwal murya. Ya faɗa yana wani
hura hanci kamar zeyi aman wuta sabida fushi.

Sallamar Edyan ce ta katse Dady daga faɗam dayake zubawa mom kamar ya Ari baki, a
rayuwar dady Allah ya jarabceshi dason Hajar tayanda har baya iya yi mata faɗa idan
tayi ba daidai ba don kawai ya sanya mata sunan Mahaifiyarsa wato HAJARAH, Wannan
dalilin yasa hajar takecin karanta babu babbaka

Da wani iri sauri Rabe ta miƙe ta nufi Edyan ta faɗa jikinsa tareda ƙanƙameshi ta
saki wani sabon kukan daya ƙara ɗaga masa hankali, ƙoƙarin rabata da jikinsa ya
farayi amma ina da sauri ta koma bayansa tareda rige gefan rigarsa jikinta na wani
irin rawa kamar mazari.

Daga yanayin fuskokin iyayen nasa ya fahimci akwai abinda ke faruwa, dakewa yayi
yajata tana turjewa har suka isa falon idanunsa nakan mom da idanunta suka sauya
launi sabida ɓacin rai, wllh da ace ba'a gida ta haifi Hajar ba tsaf zatace canza
mata ita akai, bata gama dawowa daga duniyar tunani ba ta tsinkayi muryar daddy
yana faɗin "tunda abin ya zama Rashin mutunci da ɗibar albarka lallai yarinyar nan
tabar min gidana yau ɗin nan base anjima ba tunda har akanta kika sanya hannu kika
marar min yarinya, yanzu ke Murja don Allah ko dukanta Mamana tayi ai kya tayata
bawai kisa hannu ki mareta b..... "haba daddy don Allah why are you saying that?

Baki Cp ya wangale yana kallon ɗan nasa yace " Au tambayata ma kakeyi Edriss?

"no dad kawai dai gani nai kamar ba'a kyautawa yarinyar nan ba idan aka mata haka,
bama wannan ba dad mom fa ita ta haifi hajar bawai Hajar ce ta haifeta ba,
shikenan kuma uwa bata da rights ɗin dazata ɗaga hannu ta mari ƴarta se'an mata
kashedi don kawai abata dama ta raina mutane? Wllh dad ina jiye maka tsoron
ranar daza'a koro maka hajar daga gidan miji sabida baƙin halin da kuma ƙarancin
tarbiyar......... "keep quiet Edriss!!!!!! Dady ya katseshi ta hanyar daka masa
wata uwar tsawa.

"ohh ai gashi nan kai naga tarbiyar a tareda kai, look I don't want to repeat my
word and karka bari raina ya ɓaci maza- maza ka ɗauki yarinyar nan ta barmin gidana
yanzu base anjima ba, idan yaso seka idan zaku iya kaita duk inda kukeso amma ba
nan ba tunda har sabida ita Murja kike iya marin ƴata kaikuma Edriss kake jayayya
dani.... "don girman Allah Dad kayi haƙuri karka yanke hukunci cikin fishi, na
tabbata don baka zauna da ita bane shiyasa kake ganin kamar ita ɗin ba'abar a zauna
da ita bane dad, amma wllh tafi yaya Hajar halaye masu kyau nesa ma ba kusa ba
sannan kuma dad ko kaine kaga abinda yaya Hajar tayiwa baiwar Allahr nan kaida
kanka zaka hukunta tat....... Haɗiye maganar Zeeyadah tayi sabida wani ɗan iskan
kallo da Dad ke binta dashi

Miƙewa yayi a fusace ya kalli Edyan yace "maza ka ɗauketa ta barmin gidana yanzu
base anjima ba, kuma wllh muddin bakayi abinda nace ba seƙaga fushina

Miƙewa Hajar tayi zuciyarta fessss tabi bayan dad, kokaɗanbataji komai ba akan
yanayin data saka mahaifiyarta a ciki ba da ƴan uwanta.

Iya ɓacin rai ran Edyan ya gama ɓaci har wani irin ɗaci yakeji a saman maƙoshinsa,
kasa cewa komai yayi yaja hannunta sukabar falon zuwa part ɗinsa suna shiga Direct
bedroom Ɗinsa ya wuce still yana riƙe da hannunta, zaunar da ita yayi a bakin
gadonsa se faman murza idanunta da suka koma kalar ja takeyi sabida kukan datayi,
miƙewa yayi zuwa gaban drower ɗinsa ya buɗe ya ɗakko wannan jakar saƙin daya
tsinceta da ita sannan ya dawo gabanta ya zauna akan dandiryan ƙasan carpet ɗin
tareda zuba mata manyan tsimammun idanunsa Cikin harshen turanci ya farai mata
magana donya fuskanci zuwa yanzu tafi ganeshi Sosai akan Hausa yce " tunda muka
bugeki da mota naji a raina cewar tabbas akwai wani babban al'amari a tareda
Rayuwarki, haka kuma daga yanayin ƙwayar idanunki na ƙara tabbatarwa da kaina cewar
lallai a kwai ciwo a Rayuwarki wanda kike ɓoyewa har yanzu kin gaza sanar da kowa.
Bazan tilasta ki cewar lallai sekin sanar dani labarin Rayuwarki ba Mulaikha kawai
nidai inaso na taimakeki dukda cewar har ynzu bansan wacece ke ba, a shirye nake na
fuskanci ko wani irin ƙalu bale a rayuwata muddin hakan zesa ki haɗu da iyayenki no
matter what!!!! Ya faɗa tareda ɗora mata jakar Sakin akan ƙafafunta

Jikinta ne yay wani irin sanyi duk a sanadin kalamansa da yay amfani dasu na
ƙarshe, lokaci guda taji wani abu ya tsirga mata a tsakiyar ƙirjinta a gameda Edyan
ɗin a zahirin gaskiya ta daɗe da bashi wani mashahurin matsayi wanda ya zarta na
musamman a cikin zuciyarta tunda Allah ya haɗata dashi a cikin littafin ƙaddarar
ta, daƙyar ta iya tsayar da hawayen dake zubo mata bakinta na wani irin
vibrateting tace " Sunana Rabi'atou Abubakar Moddibo ne, kuma ni haifaffiyar jihar
tarabace, Mahaifina makiyayi ne na taso cikin maraicin Uwa sedai dukda hakan besa
Mahaifina ya gaza nuna min ƙauna daga ɓangare biyu ba, ma'ana ya gama cike duk wani
ɓangare a gareni dazesa na tuna cewar na rasa kulawar Mahaifiyata. Nan dai ta
kwashe komai ta sanar da Edyan har zuwa ranar da ƙaddara rabuwa samu nasarar
giftawa a tsakinin Mahaifinta.

Wani irin kuka ne ya kufce mata don haka ta shiga rerawa kamar bazata dena ba, koda
wasa beyi yunƙurin hanata kukan ba dinya fahimci a wannan lokacin babu abinda ze
sama mata nutsuwa kamar kukan, seda tayi me isarta sannan ya shig ashare mata
hawayen yace " it's OK dear insha Allah I will make sure naga kin koma gaban
mahaifinki lfy ba tareda wani abu ya sameki ba koda hakan yana nufin bazan dawo
namu gidan da numfashi b...... Da sauri ta ɗora hannunta akan pink soft lips ɗinsa
tana hawaye tace "stop saying that partner insha Allah babu abinda ze sameka sai
alkhairi.

Murmushi yayi me sauti wanda ya ƙara baiyana kyawunsa sannan ya miƙe tareda janyo
wata babbar trolly dake ajiye can gefe yazo gabanta ya tsaya yana kallonta ido
cikin ido ba tareda ya iyafurta ko kalma ɗaya ba, itama kallonsa take a karon farko
a rayuwarta dashi Wani irin abu ne ya tsirga musu a lokaci guda da sauri ta ɗauke
idanunta daga kansa ƙirjinta na bugawa da ƙarfin gaske, hannunsa ta tsinkaya a
daidai satin fuskarta alamar tazo su tafi ba musu ta ɗora hannunta ya Bisa
tattausan hannunsa suka fara tafiya. A bakin ƙofar sukai kaciɓus da mom idanunta
duk ya caɓe da hawaye da wani irin mugun sauri ta nufi Rabe ta rungumeta tana ƙara
sautin kukanta.

******

NEW DELHI INDIA

Alhamdulillah anyi aiki cikin nasara da kuma sa'a, sosai jikin moddibo ke ƙara
samun sauƙi tamkar bashi ba har wani irin haske ya ƙara sabida yanda yake samun
kulawa daga masu alhakin akan hakan, sedai har kawo yi wannan lokacin basuyi ido
hudu da Muzaffar ba, a lokacin daya farka yaga fararen fata suna kai kawo a cikin
Asibitin yayi zaton mafarki yakeyi kokuma ƙiyamarsa ce ta tsaya, shiru yayi yanabin
ko wace kusurwa ta ɗakin da kallo har zuwa haɗaɗɗen gadon dayake kwance a kai,
shigowar Dr. Rahul Gufta ne ya ƙara firgita tunaninsa musamman dayaga kyawawan mata
sanye da fararen kaya a jikinsu ya ɗauka Mala'ikun da akace suna zuwa yiwa mutum
tambaya ne a cikin kabarinsa yayinda aka binne shi, da sauri ya rintse idanunsa
yana yana ambatona sunayen ubangiji tareda neman sauƙi wajen amsa tambaya😂

Dubashi Dr. Rahul yayi tareda duban Nurse din dake bayansa yace "ta bashi abinci
sannan yasha magani. Cikeda girmamawa ta amsa da "ok sir. Juyawa yayi yabar ɗakin
yana murmushin ganin tarin cigaban da suka samu a cikin tiyatar zuciyar da sukayiwa
moddibon. Da ido kawai Moddibo kebin nurse ɗin a ransa yace "kodai tashi yayi a
wata duniyar ta daban Batareda ya sani ba? sedai dukda irin abubuwan dayake facing
besa tunaninsa yayi ƙaura daga kan tilon ƴarsa Guda ɗaya ba wato Rabe, a kullum Be
taɓa gazawa dayi mata Addu'ar alkhairi ba kullum addu'arsa shine a duk inda take
ubangiji ya tsare masa ita da tsarewarsa. Wasu lokutan har kuka yakeyi idan abin
ya isheshi

A haka harya kwashe satin biyu cur yana jinya a cikin babban Asibitin dake cikin
Birnin New delhi ɗin ƙarƙashin kulawar Dr. Rahul Guftah sannan yasan wanda ya ɗauki
nauyin aikin nasa wato Muzaffar, lokacin daya sani seda ya zubar da hawaye masu
yawan gaske, da ƙyar muzaffar ya rarrasheshi yayi shiru sannan suka shiga hirar
yaushe gamo.

Cikeda kunya muzaffar ya ɗago manyan idanunsa yana kallon Baffa yace "Baba ya
Rabi'atou take? Lokacin danaje hankalina ya tashi ban samu zarafin haɗuwa da ita
ba. Ya faɗa bakinsa na rawa cikeda tsoron karaya ce masa tayi Aure.

Kafeshi d ido modɗibo yayi take wata sabuwae ƙwalla ta zubo masa cikeda karayar
zuciya ya shiga sanarwa da muzaffar ɗin abinda ya faru. Wata irin zabuwa muzaffar
yayi jikinsa na wani irin rawa kamar mazari , bakinsa na rawa yace "
k...kkkk....kana nufin Matar tawa ce ba'asan inda take ba?

Ya faɗa yanayinsa na ƙara sauyawa kamar wani bugagge

Kallon da moddibo ke masa ne yasashi haɗiye maganar dake maƙale a maƙoshinsa.


Comment
Nd
Share

Don't forget to vote on whatpad 🥰

Sushmah✍️[3/3, 5:38 PM] Chubado Mohd: ❄️❄️❄️❄️❄️❄️


❄️❄️❄️❄️❄️❄️
🐄🐄🐄🐄
🐄🐄🐄🐄
*BAFULATANA*
✨RETURN✨
🐄🐄🐄🐄
🐄🐄🐄🐄
❄️❄️❄️❄️❄️❄️
❄️❄️❄️❄️❄️❄️

Page :42

*_WRITING BY: CHUBAƊO_*

*_Allah yayiwa Mahaifin Mamana Rasuwa a jiya 5/12/2020 ina roqonku arziqi don Allah
ku sanyashi a cikin addu'oinku ubangiji yay masa Rahama tareda sauran musulmai baki
ɗaya Amin😭_*

Banyi Editing ba kuyi haquri👏

____✍️ Daga irin kallon dayake binsa dashi ne yasa moddibo ya fahimci irin zallar
soyayya tareda muradin dake cinsa a zuciyarsa tabbas wannan ƙaunar dake gudana a
jinin muzaffar ba ƙarama bace ta zarta duk wani hasashensa, amma kuma a zahiri
seya basar tamkar be fahimci komai a tareda yanayin nasa ba kokuma inda ya dosa
ba, ya jima yana kallonsa daga bisani kuma ya kauda kansa gefe zuciyarsa na bugawa
da ƙarfin gaske

rintse idanunsa muzaffar yayi da ƙarfi lokaci guda kuma ƙijinsa ya shiga bigawa da
wani irin ƙarfi ji yake tamkar ana janye masa jini da ruwan dake gudana a duk wata
gaɓa ta jikinta, se'a yanzu yakejin cewar tabbas be kyautawa kansa ba da har ya
kasa fahimtar ma'anar abinda ke gudana a cikin ransa seda lokaci ya ƙure masa, dafe
kansa yayi da dika hannayensa biyu tareda zubewa akan wata lallausar kujera dake
gefansa.

Wata irin zuface take keto masa dukkuwa da irin sanyin Ac ɗin dake ɗakin, kallonsa
kawai moddibo keyi a ransa yana mɗe tausaya masa duk a sanadin halinda zuciyar
Muzaffar ɗin ke ciki, tabbas baya buƙatar ƙarin bayani akan irin son da muzaffar
ɗin keyiwa ɗiyarsa domin kuwa duk amsar dayake son tabbatarwa da kanso ƙwayar idon
muzaffar ɗin ta gama nunawa.

Ajiyar zuciya kawai yake saukewa Akai-akai tamkar wanda ya gwabza tsere da
ingarman doki maji ƙarfi, lokaci-lokaci yakan dunƙuƙe hannunsa ya daki ɗaya tafin
hannun nasa dashi, miƙewa yayi da nufiknbarin ɗakin da sauri se kuma ya tsaya cak
ba tareda ya juyo ba yace "tabbas zan sauke nauyin dana ɗaukarwa kaina bawai a
matsayin babban yaya kawai ba Baffa, zanyi hakanne ta wata fuskar daban a matsayin
Jajirtaccen masoyi wanda zuciyarsa ke cike taf da zallar ƙauna me haɗe da sirkin
muradi a cikinta, zan hakanne tareda yaƙinin sauke nauyina a matsayin mijin Aure
ga Rabi'atou!!!!!

Ya faɗu hakan tareda ficewa daga ɗakin cikin wani irin saurin da tunda yake betaɓa
sanin yanadashi ba a Rayuwarsa, da ido kawai Moddibo ya bishi harya ɓacewa ganinsa
a ransa kuma yana jinjina irin girma da tasirin muradin dake gudana a cikin jinin
muzaffar ɗin wanda abu ne mawuyaci zuciyar dake ɗauke da wannan nauyin ta samawa
kanta hutu koda na sakan guda ne.

Tausayinsa ne yay masa dirar mikiya lokaci guda kuma ya sanya hannunsa ya share
hawayen daya zubo masa na tausayin rayuka biyu, ta wani ɓangaren ɗiyarsa dabe san
irin halinda take ciki ba, ta wani ɓangaren kuma tausayin halinda zuciyar muzaffar
ke ciki.

Jinginar da kansa yayi sosai a jikin filo ɗin dake bayansa abubuwa dayawa nayi
masa yawo saman zuciyarsa, sama ya ɗaga idanunsa hawayen dake maƙale cikin ƙwayar
idonsa suka tsananta zuba yace "Ya Haiyyu ya Qaiyyum Allah gani a gareka ina me
miƙa matsalolina gareka tareda sanya yaƙinin cewar kaikadai ne me yaye damuwa kuma
ka maye gurbinta da farin ciki, ya Ubangiji ka yayemin baƙin cikin da zuciyata ke
ciki sannan ka bani mafita akan dukkan lamarina tareda sauran al'umar musulmi
gabaɗaya🤲.

Shirune ya biyo baya kimanin tsahon lokaci bayan ya kammala Addu'ar hakanne ya
bashi damar faɗawa a cikin tunani me zurfin gaske dangane da narkakkiyar sosayayyar
dake kwance a tsakiyar idanun muzaffar, haka kawai yakeji a ransa cewar duk inda
cancantar samun nagartaccen namiji me narkata take to tabbas Muzaffar ɗin yana da
ita, sedai dukda hakan bayajin cewar ze iya damƙa masa hannun ɗiyarsa a matsayin
mata gareshi harse in Bawuro ne dakansa yace ya janye alƙawarin Auren dake
tsakaninsa da ita shine ze iya Bashi Aurenta ba tareda haufi kokaɗan ba. Ajiyar
zuciya ya sauke me nauyin gaske wanda hakan yasa yaji ƙirjinsa saitin gurin da
akayi masa tiyatar nayi masa xafi, a haka Doctor Rahul Guftah ya shigo ya sameshi
nan ma seda suka sake dogon bincike akan gurin da suka yanka ɗin sannan ya bada
umarnin da nurse ɗin dake bayansa ta bashi maganin daya ɗorashi akai bayan ya
tabbatar da cewar babu wata matsala a tareda moddibon sannan ya fita daga ɗakin
yana mamakin Rashin ƙan jikin da moddibo baya dashi, mostly duk wanda akayiwa irin
wannan tiyatar seya shafe kimanin watanni yana jinya kafin ya warke amma kuma shi
befi wata dayi ba amma gurin harya haɗe.

*******

Bayan Muzaffar yabar Asibitin Direct haɗaɗɗen Gidan da Ummie ta zauna ya nufa ba
tareda ya jira Guard ɗinsa sun buɗe masa ƙofa ba ya fito yay cikin gidan idanunsa
sun sauya kala daga farare zuwa nau'in jah, gabaɗaya jininsa tafasa yake sakamakon
wutar muradin dake ruruwa a cikin ko wace gaɓa ta jikinsa, tsayawa yayi cak a
lokacin daya isa tsakiyar kantameman falon dake cikin gidan ƙofar part ɗin Ummie
ya ƙurawa idanu lokaci guda kuma zuciyarsa ta fara masa sanyi, A hankali yake jin
zafinda zuciyarsa ke masa yana yaye takawa ya dingayi a hankali cikin salonsa na
hamshaƙin ƙaƙƙarfan namiji harya isa jikin ƙofar part ɗin Ummien ya murɗa da ɗan
sauran ƙarfin daya rage masa.

A hankali ya shiga madaidaicin palon da aka ƙawatashi da madaidaitan kujeru masu


matiƙar tsari gamida ɗaukar idanu, bin ko ina yake da kallo har idanunsa suka sauka
akan wata System ƙirar Companyn I phone, haka kawai seyaji zuciyarsa ta alaƙantu
akanta ba shiri ya isa ga System ɗin ya ɗauka tareda da zubewa akan lallausan Kafet
ɗin daya mamaye falon ya buɗe System ɗin yana bin pic ɗin dake malale akan icon ɗin
system ɗin wanda yakeda tabbacin cewa Hotonsa ne a lokacin da Abie ya haɗa masa
bikin Birthday ɗin cika shekara goma a duniya. Shafa icon ɗin system ɗin yayi
lokaci guda kuma ya saki wani lallausan murmushi daya ƙara baiyana ainihin
kyawunsa.

Wata folder ya gani A kan icon ɗin an Rubuta QURRATU'AIN a jiki da sauri ya danna
Enter take folɗer ɗin ta buɗe, hotunansa ya dinga gani bila'adadin wasu tun yana
jariri ɗanye goyo wasu kuma ya fara takawa gasunan dai barkatai, wani ɗan rubutu ne
yaja hankalinsa a ƙasan wani hotonsa lokacin daya kammala karatun Degree ɗinsa. Ga
rubutun kamar haka👇

"Ko wace uwa takanyi alfahari da duk wata ingantacciyar rayuwar ɗa ɗanta ya samu,
sedai ni ba kamar ko wace uwa nake fa balle harna na nuna alfaharina a wannan ranar
data zamo ta musamman a gareka Yarona, sedai dukda hakan bazan taɓa gazawaba wajen
faɗa maka cewar ina matiƙar alfahari dakai ba Muzaffar Abdulwahab Abdullah sabida
kaikaɗai ne duniya ta!!!!

Zuciyarsa ce ta karye a lokacin daya gama karanta wannan rubutu da ummien tayi a
hankali wasu siraran hawaye suka shiga sakko masa wani rauna nannen murmushi ne
yayi Escaping cute read lips ɗinsa muryarsa na rawa yace "I'm proud of you to
Ummie to have you as a mother. A haka ya dinga bin pics ɗin yana kallo wasu yayi
dariya wasu kuma yayi kuka a haka yaji zuciyanshi tayi masa sanyi harya manta da
muradin daya shigo dashi a maƙale cikin zuciyansa.

A kwana a tashi ba wuya a gurin Allah yau moddibo ya shafe watanni Uku cur a
Asibitin dake babban birnin na india wato mumbai bayan doguwar jinyar dayayi,
kallo ɗaya zaka masa kaga yanda yay wani irin fresh dashi kaman bashi ba, gashin
kansa ya ƙara fitowa yayi wani irin baƙi se sheƙi yakeyi dukda furfuran dake
tsakiyar kansa be hana fitoda duhun da gashin yayi ba, inda wanda yasanshi a baya
zega moddibo wllh seya rantse wani balaraban yankin ƙasar Misira ne yazo. Yau Ta
kama litinin ce wanda yay daidai da 28/12/ 2019 a yau moddibbo ya karɓi sallama
daga babban Asibitin koyarwan dake Mumbai, sosai hakan ya masa daɗi don haka basu
wani ɓata lokaci ba Muzaffar yasa a fara yi musu booking ɗin privet jet wanda zasu
koma Nigeria.

Bayan ya gama wayar ne kiran Abie ya shigo cikeda so Muzaffar ya ɗaga tareda
marairaicewa kamar Abie ɗin na ganinsa yace "im so sorry for the confusion Abie
nasan zuwa yanzu ka gama ganoni kan cewan ba wani meeting danazoyi India but insha
Allah I will explain everything to you my darling Abie don Allah kada kayi fushi
dani kaji?

Ajiyar zuciya Abie ya saki har seda mom dake gefansa ta kalleshi sannan yace "is ok
son ai Vicram ya sanar dani dukkan abinda kayimik ƙaryan akai but make sure gobe ku
dawo gida tunda an sallameku sannan kuma seka shiya abinda zaka gayawa mon ɗinka
idan ka dawo domin kuwa she's angry with you. Ya faɗa tareda katse wayar.

Dan zaro ido Muzaffar yayi suna haɗa ido da Moddibbo ya sakin masa cute murmushinsa
me ƙara mishi kyau, a daran ranar muzaffar yasa aka kaisu wani haɗaɗɗen super maket
ya narkarwa moddibo siyayya kamar me, har seda ya taka masa birki sannan ya dena
ɓarna da kuɗin wani zoɓe ya gani na zinare wanda ya masifan ɗaukan hankalinsa take
ya isa ga zoben yana kallonsa cikeda birgewa, kallon matar dake gurin yayi yace ta
naɗe masa zoɓen yanaso ze siya sannan ya kuma nuna mata wasu zobunan guda uku suma
duk na zinare ne yace ta naɗe masa su, sannan ya biya kudin duka kayan aka kai
musu mota sukabar harabar gurin.

A daidai danjar dake tsakanin inda super maket ɗin yake ya hangi wani tsohon
ba'indiye yana saida wasu duwatsu masu shegen kyau gamida ɗaukan hankali, a nitse
ya balle murfin motar ya fita ba tareda yace da moddibo ƙala ba ya nufi gurin
mutumin dayaga wasu maza da mata duk sun zagayeshi shima ya tsaya yana kallon wasu
abin hannu da aka haɗasu guri guda da alama na mace ne da kuma namiji.

Yana tsaiwa a gurin dattijon ba'indiyan ya kalleshi cikin harshen turanci yace
"take a look It's an eternal bracelet that will tie the fate of two together
forever, so you have to buy it

Tsohon ya ƙare maganar yana murmushin dake baiyana yaƙininsa gameda wannan
warwaraye guda biyu.

Ɗan buɗa manyan idnunsa muzaffar yayi yace "eternal bracelet?

Tosohon ya ɗaga kai yace "sure if you share this with your lover, even if you to
break up each of you will go round and round until the two of you meet again.

Shiru yayi yana kallonsa kimani mintuna biyu sannan yace a naɗe masa yanaso.
Jikin dattijon har rawa yakeyi Ya naɗe masa ya miƙa masa shikuma ya biyashi kuɗin
ya tafi. A haka suka ƙarasa gida suna ɗan taɓa hira da moddibon

Washe gari suna idarda sallan Asuba kiran Abie ya shigo wayansa , basu jima suna
magana ba ya shaidawa Abie ɗin jirginsu na gabda tashi zuwa Nigeria sannan ya katse
wayan da murmushi kwance a saman handsome face ɗinsa around 6:00am jirginsu ya
muzaffar da malam Moddibo ya ɗaga zuwa ƙasarsu ta aihuwa.

Semuce a sauka lfy C.E.O of zafar ENTERPRISES ✈️

********

Ƙanƙameta Mom tayi jikinta duk a sanyaye a hankali Edyan ya kama hannunta cikin
nasa still Rabi'atou na jikinta yace "mom kin sani sanin kanki muddin Daddy ya
yanke hukunci akan abu no body can change his mind sedai Allah kawai, don haka ki
dena kuka insha Allah yau base anjima ba I will take to her to her parents I will
make sure bata wulaƙanta ba so don't worry mom Allah is with us.

Ajiyar zuciya ta sauke tareda jin gamsuwar cewa ɗanta zeyi abinda ya dace dukda
cewa mijinta be bashi goyon baya akan hakan ba, kasa magana tayi illah zare jikinta
datayi daga na Rabi'atoun ta juya da sauri tabar falon tana sharar ƙwalla.

Ita kanta Rabi'atoun kukan take a haka Edyan yaja hannunta suka fita daga ɗakin
tana waiwayen part ɗin mom ko zataga zeeyadah, da gudu zeeyadah ta fito daga part
ɗin daddy ta nufota tareda rungumeta kusan a tare suka fashe da kuka sabida tsabar
sabon dake tsakaninsu da juna. Seda sukai me isarsu sannan yajata suka isa gaban
motarshi, da hanzari guards ɗinsa suka nufoshi da nufin buɗe masa ƙofa ya dakatar
dasu dole yasa sukaja gefe suna kallonsa, ƙatuwan jakan yasa a buth ɗin motar
sannan ya buɗe gidan gaba ya sakata ya rufe a nitse yake takawa harya kai side ɗin
driver ya buɗe motar yana ƙoƙarin shiga zeeyadah ƙwalla masa kira tace " Ya Edyan
Allah ya kiyaye hanya but make sure you take good care of her pls!!!!. Ta faɗa
tana fashewa da wani sabon kukan.

Ɗaga mata kai yayi lokaci guda kuma ya shiga motar ya mata key sukabar gidan ransa
na mishi zafi, seda sukai tafiya me nisa sannan ya dubeta ciken sanyi murya yace
"zaki iya gane hanyar Gidanku ko?

Ɗaga masa kai tayi muryanta na rawa tace "sure.


Da wani irin mugun gudu ya kwashi motar sika kama hanaya.

((tofa wannan shi ake kirada saɓani me wuyar sani, to se muce a sauka lfy Mulaikhan
Edyan😊))

*******

Cikin ikon Allah da hikimarsa mutanan India suka iso Nigeria lfy, tun kafin
jirginsu ya iso garin na Abuja Abie ya turo Guards ɗin muzaffar ɗin da wasu
danƙara-danƙaran Expensive motaci ƙirar companyn Ford's masu shegan kyau suka iso
suna jiran saukar jirgin.

Jirgijn na sauka seda suka shafe kimanin 15 munites sannan matattakalar jikin
jirgin ta fito, a hankali muzaffar dake sanye cikin wata shaiɗaniyar baƙar suite
wuluk da ita wadda ta mugun karɓan jikinsa kamar dinshi akayita, sosai fuskanshi
tayi wani irin haske sabida ramar dake taredashi, yanayin yanda read lips ɗinsa ya
wani irin tattare kaman ya shafa Janbaki ba ƙaramin kyau hakan ya ƙarama fuskan
nashi ba. Bayansa kuma moddibo ne biye dashi sanye ciki wata farar jallabiya
mallakin companyn Emraty Fara tass da ita, kallo daya zakayi masa kaga zallar
kamalar dayake da ita.

A haka suka Ƙaraso gaban motocin guards suka buɗe musu ƙofa bayan sun zuba kayansu
a booth ɗin motar sannan sukaja motocin cikin jerin gwanonda suka saba gwanin ban
shi'awa.

Tunda suka shiga motar zuciyar moddibo ke cike taf da mamakin matsayi da kuma gata
irin na Muzaffar take yaji zuciyarsa ta amsa duk a lokaci guda.......

Comment
And
Share

Sushmah✍️
[3/3, 5:38 PM] Chubado Mohd: ❄️❄️❄️❄️❄️❄️
❄️❄️❄️❄️❄️❄️
🐄🐄🐄🐄
🐄🐄🐄🐄
*BAFULATANA*
✨RETURN✨
🐄🐄🐄🐄
🐄🐄🐄🐄
❄️❄️❄️❄️❄️❄️
❄️❄️❄️❄️❄️❄️

*_WRITING BY:CHUBAƊO_*

NOT EDITED
____✍️ Cikin nutsuwa motocin ke tafiya har suka samu nasarar isowa cikin Maitama,
duk inda motocin suka sulala Sedai kawai kaga moddibo na baza idanu yana kallon
ƙuduran Allah da kuma hikimarsa, a ransa kuma yana me girmama ƙwarewar maginan da
sukai gine-ginan dake cikin garin a iya tsahon Rayuwarsa yayi yawo sosai tundaga
kansu ƙasar Niger dadai sauransu amma betaɓa cin karoda guri mekyau irin Abuja ba
kodan a daji ya sabayin Rayuwa oho

A haka suka iso ƙofar kantamemen gidan Me kamada aljannar duniya babu abinda ya
ɗaurema Moddibo kai irin ganin yanda Get ɗin ya buɗe kansa da kansa ba tareda kowa
ya taɓashi ba nan take yaji wani irin tsoro ya tsigawa zuciyarsa da gangan jikinsa,
Haka suka kunna kai zuwa cikin gidan kallo ɗaya zakayiwa Muzaffar ka fahimci yana
cikin Farin ciki dukda irin damuwar dake kwance a cikin ransa sam hakan be hanashi
baiyana farin cikin ganin Ahalinsa ba.

Hannun Moddibo ya kama ya riƙe cikin nasa musamman daya Fahimci yanayinsa ya sauya
daga wanda suka baro airport dashi suwa wani, Ajiyar zuciya ya sauke sannan yay
murmushi yace "pls baffa feels free with us don Allah we are all family kasa a
ranka nan ma gidanka kazo. Ya faɗa yana matsa hannun Baffan cikin nashi

Gabaɗaya Ahalin gidan suna farfajiyan gidan suna jiran fitowansu Except Ummie dake
khitchine tana shiyawa ɗan nata girki na musamman don tarbarsa.

A wannan rana babu wanda beyi farin ciki da dawowar muzaffar ɗin ba, bayan sun iso
sun huta ne muzaffar ke sanar da Abie irin karamcin da moddibo yayi masa a lokacin
dayake dabda rasa Rayuwarsa, sosai Abie ya nuna jin daɗinsa tareda sanyawa a ɗauki
modɗibo a kaishi masauki na musamman wanda aka qawata da karan alatu na jin daɗin
rayuwa iri-iri.

Tabbas moddibo ya fahimci cewar muzaffar ba mutum bane gamagari kamar sauran yara
ba, yaro neshi ɗan gata kuma ɗan asali da ga mutane masu tarin ɗukiya a haka ya
kwana ya hantse a cikin wannan aljannar duniyar, sedai dukda hakan zuciyarsa naga
tunanin ƴarsa guda ɗaya tillo wato Rabe.

Moddibo ne zaune qasan Makeken kafet ɗin dake hamshaqin falom yana daure boronsa
(jaka) da alama shirin tafiya gda yake, muzaffar ne ya shigo dakin da murmushi
Kwance a kan Kyakkyawar fiskarsa yace " baba. se kuma yayi shiru da sauri ya qaraso
Cikin falon inda moddibon ke zaune yana ɗaure jakar kayan da suka dawo dashi daga
india, cike da damuwa Ya kalleshi kaman ze sakin masa kuka yace " baba badai har ka
fara shirin tafiya ba?

Murmushi moddibo yayi irin nasu na dattijawan qwarai yace "to yaro me kuma zan
tsaya jira? Tunda Allah ya amince maka ka zama silar ceton Rayuwata me kuma zan
zauna jira wanda ya wuce in koma ga iyalina?

Shiru Muzaffar yayi a ransa yanajin kewar moddibon ta fara addabarsa tun kafin ma
ya tafi, a hankali ya buɗe jajayan laɓɓansa zeyi magana middibo ya rigashi ta
hanyar cewa "zuwa yanzu Nasan Gabaɗaya jama'ar garinmu da kuma iyalina sam basa
cikin kwanciyar hankali duk sabida tunanin irin halinda nake ciki Musamman ma Laure
nasan Setafi kowa damuwa, da Ace ma Rabi'atou na tana tana gida tashin hankalin
dazata shiyaga seyafi na kowa sabida ban taba tafiya me Nisan Irin wannan shafe
watanni bana tareda ita ba, sbda tinanin Irin halinda zata shiga idan bana nan
ɗin, Se gashi kuma yanzu babbar ƙaddarar Rabuwa ta gifta a tsakanin mu ba tareda
mun shiryawa hakan b.......!

Wasu siraran Hawayene suka zubo masa dole ya kasa qarasa maganar yay shiru,
Sunkuyawa muzaffar yayi tareda dafa kafaɗunda cikeda zallan kulawa yace "kayi
haquri baffa amma komai muqaddari ne daga Allah kamar yanda qaddara tayi nasarar
rabaku da ita isha Allah wannan qaddarar ce zata sake zama silar haɗuwarku, jikina
yana bani cewar a duk inda Rabi'atou take sam bata cikin yanayi na rashin daɗi
sabida muddin hawayenta suka zuba to wllh senaji haka a cikin jinin jikina so Dont
worry Baffa insha Allah komai ze wuce.

Kasaƙe Moddibo yayi yana kallonsa a ransa yana girmama lamari irinna muzaffar ɗin,
sam bashida yanayin izzar Da yaran Da iyayensu suka tara musu dukiya suke da ita,
Muzaffar he's a nice person and social komai nasa da sauqi yake ɗaukarsa tamkar ba
magajin attajirin Mamallakin companonin nan Ba Alhaji Abdulwab Abdullah ba.

Kafaɗarsa moddibo ya dafa still yana hawaye yace "Allah ya albarkaci Rayuwarka yaro
haqiqa iyayenka sunyi sa'ar haihuwa da suka haifi ɗa kamar ka.

Murmushi kawai muzaffar yayi ba tareda yace komai ba, ajiyar zuciya yaɗan sauke
sannan yace "da inada ikon hanaka tafiya wllh Baffa danayi hakan amma kum......
"Kada ka Damu yaro ai yanzu mun riga mun zama ahalin juna don haka babu me iya
yanke wannan alaqar.

Kamar muzaffar zeyi kuka yace "yaushe ne tafiyar taka Baffa?

"Gobe da ikon Allah zan kama hanyar gda Tunda Allah ya azitani da lfyar dana daɗe
bani da ita Wanda ta kasance kaine silar samuwarta. ya Qarashe maganar da murmushi
a Kan fiskarsa

Murmushi muzaffar yayi Yace "don Allah baffa ka dena cewa hka nimafa ka ceci tawa
rayuwar don haka nizan gode maka kuma har duniya ta gushe bazan taɓa dena godewa
likitan gargajiya irin Baffa na ba. Ya faɗI hakan yayinda yake faɗaɗa
murmushinsa gareshi.

sosai moddibo yaji Daɗin maganar muzaffar Ɗin , nan dai ya shiga yi masa nasihu
masu Matiqar shiga jiki, sosai
Jikin muzaffar Yayi sanyi sbda nasihun da moddibon yayi masa, a ransa seyaji dama
moddibo ya zauna tare dashi haka kawai dattijon ya gama shiga ransa,
Jiki ba qwari muzaffar ya miqe sbda jin kiran sallar ishsha'i, be cewa moddibo
komaiba ya nufi hanyar fita Daga falon zuciyarsa a matiqar dagule.

Murmushi moddibo ya kuma yi A karona biyi sbda ya fahimci muzaffar Ɗin fishi yayi
sbda yace ze tafi gobe,
Miqewa yayi shima suka nufi masallacin tare, daidai lokacin da Ummie ta loqo ta
windown falon ta Don ganin fitarsu sedai sam bataga fuskokinsu ba se bayan su Data
hanga sannan ta koma taci gaba da jera abinci akan dining.

Koda aka idar Da sallan muzaffar ya Dade yana addu'oinsa sannan suka shafa suka
fito gaba daya,
Dai dai lokacin da Abie ma ya fito, kusan a tare suka jera suna tafe suna hira
anan muzaffar ke shaidawa Dady tafiyar moddibo, sosai Abie ma yaji ba dadi sbda
yanda ya saba dashi a kwana dayan da sukayi a gida kamar sun shekara da sanin
juna, Shi kansa Abie ɗin yana buqatar ace sun samu lokaci da moddibo Donsi tattauna
sosai akan wasu abubuwan na daban waƴanda suka shafi rayuwar Moddibon da kuma
abubuwan dake faruwa a cikin garuruwansu na fasa qwaurin da ƴan bindiga daɗi suke
musu ta hanyar yiwa yaransu qanana fyɗe kuma su qwace musu dukiyoyinsu, kodan
darajar ceton Rayuwar ɗansa tilo dayayi shikuma dalilin wannan ya qudurtama kansa
cewar tabbas seya taimaka musu koda kuwa hakan yana nufin ze rasa wani ɓangare na
dukiyarsa ne gabaɗaya.

Har a cikin Ran Abie yaji cewar yana matiqar qaunar Moddibo sabida Yamada sauri
saboda mutane Kuma ga kirki, gashi da haquri da sanin ya kamata shiyasa yake da
dadin mu'amala Ta kowani fanni,
Indai ya zauna dakai koda na wuni daya ne to Se Zuciyarka ta qaunace shi Koda baka
shiryawa hakan ba Sbda dattijon a kwai shiga rai,
Suna shiga Falon da aka saukeshi Abie Ya kalli moddibo yace" tunda gobe zaka tafi
don Allah Meze hana Kazo Muje bangarena Muci abincin dare tare Dakai?

Shiru moddibo Yayi kamar bazece komai ba sannan ya ɗago yace "ina me baka haquri
akan wannan al'amari dakazo min dashi wllh bazan iya zuwa ba idan naje tamkar ka
takurani ne.

Duk yanda Abie yayi dashi amma sam yaqi amincewa Dole ya haqura badan yaso ba
yayiwa moddibo seda safe, sannan ya wuce bangaren Ummie.

fita Muzaffar yayi dan dakko musu abinci a bangaren Ummien sa , be jima ba ya dawo
dauke da manyan food flasks guda biyu se Zaynab dake Biyeda bayan sa hannunta
dauke da flat da spoons ajiyewa tayi sannan ta koma ta daukko wani Babban flet
Wanda ke dauke da kosilo Wanda yaji Uban qwai da bama ansa wata fara leda an rufe
farantin da ita ta yanda kana Iya ganin abinda ke cikin flet din, da sallama ta
shigo ta ajiye sannan ta gaida moddibo cike da girmamawa. da kulawa ya amsa mata
tareda sakin fuskarsa dukda irin halinda zuciyarsa take ciki na kewar ɗiyarsa,
Jikinsa a mace ya tambayar ta sunan ta murmushi tayi sannan tace "Sunana Zaynab.

Murmushi moddibo yayi sannan yace" Ashe mata tace da kanta. dukansu suka sa dariya
sannan ta miqe tayi musu saida safe ta wuce bangaren su A ranta tana mamakin kyau
da cikar zati irin na moddibo.

Zaune suke kan dining suna cin abinci Abie yake sanar da Ummie Batun tafiyar
moddibo da safe idan Allah ya kaimu, Shiru tayi tana kallon Abie ɗin ba tareda ta
iya furta koda kalma guda ba Lokaci guda kuma yanayinta ya sauya,

A hankali tace" daga zuwansa har ze koma se kace ana korar sa?

Murmushi Abie yayi sannan yace "wllh nima haka nace dashi amma fir yaqi yarda ya
qara kwana ki Kidan sabida batun lfyarsa ma.

Dik wannan hiran da suke itada Abie qarfin hali kawai take Haka kawai setaji wani
iri haka a jikinta sabida mutumin yayi mata abinda bazata taɓa mantawa dashi ba a
Rayuwarta.

Abie ne ya katseta ta hanyar sanar da ita yayi kewarta,


Murmushi Ummie tayi sannan tace " Abou muzaffar kenan sekace wasu yara?

Dariya yayi sannan yace " au yara ne kawai suke da hurumin yin soyayyah?

Bata CE masa komaiba dan ta fahimci Neman magana kawai yakeyi Da ita,
A hankali ta ajiye cokalin dake hannunta ta miqe a taqaice tace seda safe.
Sam beyi qoqarin hanata tafiya ba sbda ya fahimci yanayinta ya canza tunda ya
ambaci Tafiyar moddibbo.
Abinda ya qara daure masa kai shine meyasa Ta canza lokaci guda haka?

A hankali ya rintse idanunsa, sbda baya son abinda ze batawa matar tasa rai Koda
kuwa menene shi, a daddafe ya kammala cin abinci, ya miqe ya nufi bedroom din
shima a zaune ya sameta da alama daga toilet ta fito, kana kallon ta zakasan tana
cikin damuwa, bece mata komai ba ya shiga toilet yayi brush sannan yayi wanka
yafito, beyi mamakin ganin ta ajiye masa jallabiya ba sbda hakan al'adarta ce,
murmushi yayi sannan ya sanya Jallabiyar a jikin sa.

yana gama sawa Ya haye gado abinsa bece mata komaiba yaja bargon Dake gefanta da
nufin ya kwanta, donya qudurtama kansa cewar baze taɓa tambayarta dalilin
sauyawarta ba sabida ita kanta tasan hakan na mugun ɗaga masa hankali shiyasa ma
tayi.

Da kanta ta fahimci Tayiwa megidan nata laifi dan hka ta bude baki tace "don
Allah kayi haquri bani da yanda zanyi ne dolece tasa,
Sanin kanka ne kasan bazan taba mantawa da irin binda wannan baƙon mutumin yayiwa
ɗana ba, sannan kuma taya kake tsammanin zan iya jure ganin halinda ɗanmu yake ciki
a sanadin soyayyar yarinyar da bamuda tabbacin sanin inda take a halin yanzu?

"meyasa bazakayi amfaninda damarka ta mahaifi ka nema masa aurenta ga mahaifinta


kafin ya tafi ba?

"Haba Aisha so nwa kikeso muyi maganar nan ne sabida Allah? Nayi magana da bawan
Allahn nan ya cemiɓ a kwai maganar Auren wani akan yarinyar shikenan kuma sena
matsa masa akai don kawai inada kuɗi kuma inason ɗana?

Kuri tayi masa da ido se kawai ta fashe Masa da kuka.


Sosai Take kukan wanda ita kanta Bazata iya cewa ga dalilin Yin kukan Nata ba.
Ganin abin nata bame qarewa bane yasa me Gidan nata ya Jawota jikinsa yana me
bibbiga bayanta, seda ta tsagaita da kukan sannan ya dafata ya Fara mata nasiha
sosai tareda sake nuna mata mahimmancin yarda da qaddara,
Jikinta ne yayi sanyi sosai a hankali Tasa hannunta tajaa bargon dake gefanta ta
kwanta Bisa jikinsa tana sauke numfashi, seda ya tabbata ta nutsu sannan ya fara
tambayarta Kan cewae me take ganin zeyiwa moddibo idan ze tafi sbda nuna jin dadin
abinda yayiwa dansa Wanda yasan ko duniyar nan yabashi be biyasa ba?

Murmushi Ummie tayi me sauti sannan tace "ka bari tukunna seda safen mayi
maganar.
Bata qara cewa komaiba tayi addu'ointa ta tofa, ba jimawa bacci Me nauyin gaske ya
dauketa.

****
Bangaren su muzaffar kuwa hira suke sosai da moddibo sekace ba dare ba, sun jima
suna hiran sannan moddibo ya tashi ya wuce daki sbda bacci daya ke ji, kuma gashi
fitar wuri yake so yayi,

Murmushi muzaffar yayi tareda Fadin seda safe. A hankali ya tashi ya kashe TV Ɗin
daketa faman aiki sannan ya rage Ac dake falon sannan ya rage wutar falon ya mike
ya nufi bangaren sa, bisa ga mamakin sa seyaga an qara gyara masa Part ɗin nasa ,
ko ba'a fada ba yasan Aikin zaynab ne,
Murmushi yayi sanan yace" Allah sarki my Qurrah
Wanka yayi sannan ya fito daga toilet din sanye da wata farar jallabiya, dik da
cewa shirin bacci yayi amma rigar ba qara min kyau tayi masa ba, a hankali ya
qraso bakin makeken gadon sa qirar Italian ya zauna yayi shiru, kallo daya zaka
yimasa ka fahimci damuwa a fiskarsa,
Wani abin hannun roba dake hannunsa ya taba se kuma ya saki wani tattausan
murmushi, a hankali ya firta "I miss you My darling Fulani girl, I miss everything
about you. murmushi ya sake yi a karo na biyu sannan ya hau gadonsa yaja Lallausan
bargon dake gefansa ya kwanta, ya jima yana nazarinta tareda Tina wasu abubuwan da
suka wakana a tsakaninsa da ita gami da yawan murmushin ta sannan bacci yay a won
gaba dashi.

Kiran sallar farko moddibo ya mike ya shiga toilet yayi Wanka Sabida zamansa a
india yasa ya koyi amfani da banɗakunan zamani, alwala yayi ya kimtsa Sannan ya
fita zuwa
Masallaci, yana shiga masallaci ya gabatar da raka'atanul fijir bayan ya idar ya
dan jima a zaune yana addu'ah sannan aka gabatar da sallar asuba,
Bayan ya fito masallaci suka hadu da muzaffar suka wuce gda suna hirarrakin su,
Ban garan moddibo suka nufa ya tayashi ya hada kayan sa ya daure Su tsaf guri
guda.

seda gari yayi haske sannan Abie ya shigo bangaren dan su gaisa da moddibo, bayan
sun gaisa ne Dady yace masa yazo su gaisa da mahaifiyar muzaffar sannan yayi
breakfast, se su wuce, murmushi moddibo yayi sannan ya CE to babu damuwa idan ka
shiga seka sanar da iyalin Naka shigo war tawa,
Murmushi Abie yayi sannan ya kalli muzaffar yace "ka shigo dashi falon Ummien ka
idan ya kammala Inyaso bayan sun gaisa da ita Ummien seka kira Saratu itama su
gaisa. murmushi Muzaffar yayi ya amsa da to Abie as you wish

Abie na shiga ya sanar da Ummie cewar moddibo ze shigo yayi mata sallama, murmushi
tayi sannan tace gaskia be kamata ya tafi yanzu ba dama ya qara mana kwana 2
murmushi Abie yayi Nandai sukaita hira abinsu.

Mamie tace ina zuwa naji kamar abinda na Dora yana kamawa , kichin ta nifa dan ta
sauke abinda ta Dora,
Tana fita su moddibo da muzaffar suka shigo falon, guri muzaffar ya nuwa moddibo
sannan ya zauna shima Daga gefansa hira suketa dan yi da Abie itama jefi-jefi, a
haka Ummie ta fito ta samesu, ko kadan moddibo be kalli fiskarta ba itama haka ta
qaraso falon fiskarta dauke da murmushi a nitse ta zauna a gefan Abie sannan ta
fara gaida moddibo.

a nitse ya fara amsawa cike da kulawa, Lokaci guda Ummie ta ɗago fararen idanunta
ta saukesu akan mamallakin muryar data doki dodon kunnenta, Wanda har duniya ta
tashi bazata taɓa manta mamallakin wannan muryar ba.

Kallon moddibo take haka shima kallon Nata yake cike da tashin hankali yake nuna
ta da yatsa,
Kasa cewa komai yayi dan haka kawai ya miqe da nufin yabar falon gaba daya,

Da sauri Ummie ta riqe qafafuwansa tana Wani irin kuka me tsima zuciya, cikin kukan
take fadin dan Allah Baffa iya kayi haquri ka yafe min nasan nayi kuskure a
rayuwa ta yanda bazan Iya gyara laifi nab!!!!

Ta qarasa maganar tana kuka sosai.

Cike da rashin fahimta Abie yake kallon su haka ma muzaffar da kansa ya gama
daurewa,
Cike da damuwa Abie yake tambayar Ummie shin tasan moddibo ne Kokuma ya abin yake?

Shin meye hadinta dashi da har take fadin ya yafe mata?

Da qar ta Iya bude baki tace "dan uwa nane shine yayana moddibo da mukaje nema
shekaru a shirin da biyar da suka wuce, to shine wannan ta qara fashewa da kuka,

Qarfin hali moddibo yayi ya fisge qafarsa daga hannunta ya fice daga falon da sauri
yana zubar da hawaye,
Ko kayan sa be Tsaya dauka ba ya fice daga Gidan gaba daya,
Yana fita ya samu Taxi ya shiga batare da ya gaya masa inda ze kaishiba !!
Seda suka fara tafiya Daɗan jimawa sannan me motar yace "mlm INA zan kaika?

A taqaice Moddibo yace " masa tashar mota zaka kaini don Allah Inda zan samu
motar TARABA.

Shiru mai motar yayi a tareda jefa motar kan titin daze kaisu tashar JABI

suna iya ya kwanto kuɗinsa ya miƙa masa yakoyi sa'a cikon mutum ɗaya ake Nema,
Be wani bata lokaci ba ya biya kuɗin motar ya shiga ya zauna still hawaye na zuba
daga cikin idanunsa sabida wani irin suya da zuciyarsa keyi masa.
*****

Tun bayan tafiyar moddibo Ummie take kuka, gaba daya hankalin Abie ya gama tashi
yama rasa me zeyi guri ya samu ya zauna tare da dafe kansa daya ke masa wani irin
nauyi,, falon ne yayi shiru baka jin komai se sautin kukan Ummie, muzaffar ne yayi
qarfin halin cewa Abie sam wannan zaman fa ba shine mafita ba fa,
Kawai tashi zamuyi mubi bayan sa, nasan ze sauraremu inayaso se'a gyara matsalar
Ina ganin hakan zefi da wannan zaman da mukeyi,

cikin kuka Ummie tace "wllh nasan halin sa muzaffar yana da matiqar haquri amma
idan yayi fishi yana da wuyar sha'ani!

A hankali Abie ya sauke ajiyar zuciya sannan yace " abinda muzaffar ya fada shine
daidai ki tashi kije ki wanke fuskarki ki shiya mubi bayansa hakan shine mafita.

haka kuwa akayi a gurguje Mamie ta gama kimtsawa ta fito, koda ta fito bata samu
muzaffar da dady a falon ba , dan haka bata tsaya jiran komaiba ta nufi waje, tana
fita ta hangi muzaffar a parking space yana tsaye a jikin wata Jibgegiyar Jib qirar
ford, da alama fitowarta yake jira, sanye yake cikin wata dakakkiyar shadda milk
colour ammata dinkin Jampa da wando, aikin dake jikin shaddar maroon color ne dan
haka ya sanya hula maroon da ratsin milk a jiki ta kalmin qafarsa me danyasa ne
shima maroon, se agogon Rolex din dake Ɗaure a tsintsiyar hannunsa, sosai yayi
Wani irin masifan kyau Kamar ba wanda ke cikin damuwa ba kayan sunyi matiqar amsar
jikin sa, a hankali Ummie ta qarasa inda yake Tsaye kallo daya zakai mata kasan
tana cikin damuwa mara musaltuwa, amma dik da haka damuwar bata hana futowar
kyawun da Ummie n keda Shiva, S'a yanzu muzaffar ya qare mata kallo ya fahimci irin
mugun kamar da suke da moddibon Banbancinsu kawai Ummie batakaishi hasken fata da
kuma manyan idanu ba.

da sauri dan nata ya matso kusa da ita ya rungumeta Cikin sigan lallashi yace
"don Allah Ummie ki rage damuwa indai baffa ne wllh Nasam ze fahimce ki, nasan shi
yana da sauqin hali a Iya zaman danayi dashi , pls Ummie ki cire Yawan damuwar haka
don Allah!

Batace komaiba se cire jikinta Datayi daga nasa , sannan tayi wani marayen
murmushi me baiyana karayar zuciya da qarfin gwiwa tace "hka dai kace yaro amma ni
nasan da wuya Baffa iya ya yayfemin abinda nayi masa.
Be sake cewa komaiba sbda fitowar Abie dasu Mom daya gani, a nitse suka qaraso
gurin Suma jikinsu a saluɓe murmushi Ummie tayi musu tareda Faɗin " muntashi
lfy ?

Momce ta amsa mata da fara'arta Hakama su Zaynab da Fadilah dake tsaye a bayan
Abie,

Cikeda gimamawa muzaffar Yace "good morning mom. "morning son ka tashi lfy?

Da fara'a kwance a saman fuskarsa yace "im fine mom.

Kallon mom Abie yayi yace "Saratu zamu ɗanyi wata doguwar tafiya pls zuwa anjima
kisa Fadilah Takai baba Hajara Hospital lokacin ganin likitanta yayi. Cikeda
damuwa mom tace "amma dai lfy dai ko Abie?

"no karki damu lfy lau wani uziri ne ya tasomin akan compayn da Aisha take leading
a india to shine zamuje TARABA Akan Maganar.

"to Allah ubangiji ya tsare amma waye zeja motar?

A taqaice Abie yace "muzaffar. Da dauri Zaynab tace "Abie don Allah zan biku
becouse ban taɓa ganin Yaya yayi driving me nisa kamar haka ba. Ba musu Abie ya
amince mata sannan suka shiga mota mom da Fadilah na zuba musu addu'o'i

Comment
Nd
Share

Chubaɗo✍️
[3/3, 5:39 PM] Chubado Mohd: ❄️❄️❄️❄️❄️❄️
❄️❄️❄️❄️❄️❄️
🐄🐄🐄🐄
🐄🐄🐄🐄
*BAFULATANA*
✨RETURN✨
🐄🐄🐄🐄
🐄🐄🐄🐄
❄️❄️❄️❄️❄️❄️
❄️❄️❄️❄️❄️❄️

Page :44

*_WRITING BY: CHUBAƊO_*

Not Edited

___✍️Har bakin motar Mom tazo ta tsaya a daidai saitin inda muzaffar ke zaune
bayansu Ummie da Abie sun shiga motar sun zauna, hannunta ta zura cikin motar tana
shafa kan muzaffar zuwa wuyansa tace "Allah ya kiyaye muku hanyar son, kada ka
manta da addu'a sannan kuma banda gudu mara amfani a titi. Murmushi ya sakin
mara with so much love irin na ɗa da uwarsa yace "sure mom bt pls take good care of
your self. Har ya fara qoqarin tada motan Se kuma ya kalli Fadilah dake tsaye tana
kallonsu yace " MD ki fara shirin zuwa office daga yau sannan kuma don Allah karki
manta da kai Baba Hajara Asbiti don I'm sure ta manta yau zata koma ganin Docter.
Murmushi tayi irin wanda ke baiyana tsantsar farin cikin dake zuciyarta tace
"thank you so much our humble br........

Sam Be jira cewarta ba ya tashi motar suka bar harabar gidan mom na ɗaga musu
hannu tareda Fadilah suka kama hanyar TARABA STATE, cikin nutsuwa muzaffar ke tuka
motar tamkar ba wannan hamshaƙin matashin da ƙarti ke tukawa a mota ba, lokaci-
lokaci yakan ɗaga manyan idanunsa ya kalli Ummie ta mudubin dakw gaban motar gaba
ɗaya duk ta zama wata iri sabida damuwa, wata siririyan ajiyan zuciya sauke a ransa
yana ƙara jinjina buwaya da hikima irinta ubangiji, yanzu banda Allah waya isa yay
wannan?

Ummie ta Rabu da Ahalinta tsahon kimanin shekaru 35 amma se gashi cikin ikon Allah
ɓatansa ya zama sanadiyar haɗuwarta da Yayanta, tabbas komai na ubangiji yanada
iyakansa shiyasa Allah ya jefo musu wannan al'amarin a matsayin zannan ƙaddararsu
gabaɗaya.
******

Se wajen qarfe 10pm na dare sannan su moddibo suka iso cikin garin taraba sannan ya
fara shirin kama hanyar Rugarsu kokaɗan be damuda duhun da garin yayi ba, jefa
ƙafarsa kawai yakeyi tsabar sabida tsabar tanda zuciyarsa ke ke tafasa da baƙin
ciki, gabaɗaya jiyake komai na dawo masa a ƙwaƙwalwarsa tamkar a lokacin abin ke
faruwa, wasu zafaffan hawayene suka zubo masa yasa hannunsa ya share still be dena
tafiya ba, a haka har ya iso cikin Rugar tasu tun kafin ya isa ga ƙofar gidansa
jama'ar garin wasu suka dinga kallonsa kamar sun samu Tv kasancewar yanzu basa
bacci da wuri sabida tsaron lfyarsu,

ko kaɗan be damu da irin kallon da suke binsa dashiba hasalima baƙin cikin dake
ransa ma baze barshi harya damu da irin kallon ɗa suke masan ba, Direct ƙofar
zagayayyen karan daya kewaye ɗakunansu dashi ya nufa ya shige gidan ba tareda ya
iya furtawa jama'an dake biye da bayansa koda kalma guda ba, Bamanga ne yay ƙarfin
juyawa da saurinsa ya nufi gidan malam Iro zuciyarsa fal farin ciki donya shaida
masa cewan Amininsa moddibo fa Allah yayi masa dawowa cikin ƙoshin lfy.

Da sauri malam Iro ya miƙe tsaye lokaci guda kuma ya fara jerawa Allah kirari da
sunayensa mafiya kyau, da murmushin me ɗauke da zallar farin ciki ya Raɓa ta gefan
Bamanga ya fita da sauri zuwa gidan moddibo, ta cikin jama'ar dake tsaye ya raba ya
kutsa kansa tsaye cikin gidan yana me ƙwallawa Moddibo kira with so much love and
caring.

Tsayawa moddibo yay cak yana bin Malam Iro da Kallo batareda ya iya furta ko kalma
guda ba, da sauri malam Iro ya matso gareshi ya Rungumese yana me shafa kwantaccen
vaƙin gaskin kan Abokin nasa hawaye na zubo masa. Shima kansa moddibon kukan yake
sabida murnan ganin abokin nasa da kuma taron jama'an dukda suka taru sabida shi.
Cikin farin ciki malam iro yace "haqiqa Allah mai iko ne akan komai, haka kuma babu
shakka wannan yaro yanada sufa irinta ƴan aljanna wato cika alqawari, kamar yanda
yay mana alqawari akanka gashi kuwa ya cika cikin yardan ubangiji da kuma
amincewansa, tabbas yayi namijin qoqari musman yanda yake ɗaukar nauyin duk wani ci
da sha na iyalinka har zuwa yau da Allah ya nufeka da dawowa garemu, bama iyalinka
kadai ba kaf wannan Rugar babu wanda be amfana da arziqin wannan yaro ba, haqiqa
duk inda wannan yaro ya fito to tabbas iyayensa mutanan kirki ne kuma masu karamci.

Ƙura masa idanu Moddibo yayi babu ko ƙiftawa harya gama magana bece da malam iron
Qala ba, haka kuma shima malm iron sam be damu da yanayin dake kan fuskar moddibon
ba yafi danganta hakan da ƙaton cikin dake jikin Inna laure ne ya haifar da wannan
sauyin a fuskar abokin nasa. Ajiyar zuciya malam iro ya saki a ransa yace "toya
muka iya da lamarin qaddarar da Allah ya hukunta?

Se'a lokacin Moddibo ya lura da Laure dake zaune bisa ƙofar ɗakinsa ta miƙe
ƙafafunta Ga uban Ciki ya fito yayi girma ta tsareshi da manyan idanunta da suka
gama koɗewa sabida kukan daya zama abin yinta koda yaushe.

Wani irin bugawa qirjin Moddibo yayi lokacin dayay arba da wannan tulelen cikin
dake jikin laure, kasa magana yayi illa wani irin ja da idanunsa sukayi lokaci guda
kuma jijiyoyin kansa suka mimmiƙe kamar wanda ke shirin gabza dambe a filin daga,
da ƙyar ya iya tattara kalmomin bakinsa ya firta
"Innanillahiwa'inna'ilaihirraji'un!!!!!

Hakanne yay daidai da tsaiwar wata jibgegiyar baƙar mota jib ƙirar companyn Ford
gabaɗayanta an lulluɓeta da baƙin tinted wanda ya mugun ƙarawa motar kyau da
kwarjini........
Comment
Nd
Share

Thanks 4d love💕 yanzu kam insha Allah babu tsayawa harse mun gaba dukda cewan befi
3 pages or 4 mu gama book ɗin gabaɗaya ba, ammafa idan naga Ruwan comment ne zanyi
hakan 😁

Sushmah ✍️
[3/3, 5:39 PM] Chubado Mohd: ❄️❄️❄️❄️❄️❄️
❄️❄️❄️❄️❄️❄️
🐄🐄🐄🐄
🐄🐄🐄🐄
*BAFULATANA*
✨RETURN✨
🐄🐄🐄🐄
🐄🐄🐄🐄
❄️❄️❄️❄️❄️❄️
❄️❄️❄️❄️❄️❄️

Page :45

*_WRITING BY: CHUBAƊO_*

____✍️Tun daga cikin motar yake kallon yanda jama'ar rugar suke gudu suna neman
maɓoya wasu wasu kuma na tsaye ƙyam hannunsu riqe da sandinansu sunyi shirin kai
duka, ganin da sukai babu wanda ya fito daga cikin motar ne yasa suka qara himma
wajen damqe sandinan dake hannun nasu tamkar kace ket su zura a guje.

juyawa yayi a sanyaye yana kallonta da manyan idanunsa waƴanda suka faraa sauya
launi tun bayan tasowarsu daga Abuja, cikin tattausar muryanshi me ɗauke da amo a
cikinta yace "kin tbbata nan shine garinku mulaikha?

Sunkuyar da Kanta tayi tana wasa da igiyar belt ɗin motar dake daure a jikinta
kamar wadda ya tilasta mata dole setayi maganar tace "Sure.

Kallonta yayi kimanin 4second sannan ya ɗauke fuskarsa ya maida kallonsa waje yana
nazarin mutanan dake tsaye suna jiran fitowar mamallakin motar da wannan uban
daren, hasken ƙwan gaban motar ne ya zame abin kallo wanda shi kuma ta ɓangaren
Edyan hasken shine ya bashi damar qarewa mutanan dake gurin kallo harya karancin
yanayinsu, ba zato ba tsammani ya bude murfin motar ya fito sanye yake da jeans
and Tshirt wanda sukai masifan yi mishi kyau dukda cewar baya cikin yanayi me daɗi
amma sam hakan be hana baiyanar kyansa da kuma kwarjinin dayake dashi ba, ganin
hakan yasa itama ta buɗe murfin motar ta ɓangare ta ta fito idanunta nakan mutanan
dake tsaye suna kallonsu tamkar sun samu Tv, nan take su Bamanga dukai kan Edyan
da nufin su Rufeshi da duka cikin wani irin yanayi me fitar da Amo ta kallesu
cikin tsawa tace "Shin mutumin dayay wa ɗiyarku alkhairi ya taimaketa a lokacin
datake buqatar taimako shine kuke qoqarin illatawa?

Tsayawa sukai cak suna kallonsa ba tareda sun juyo sun dubeta ba, shikuwa Edyan
yana tsaya bisa digadigansan s ayana kallonsu ba tareda ya motsa ba, qraasowa tayi
gurin tana kallonsu ido cikin ido suma ɗin kallonta suke irin kallon nan dayafi
kamada na rashin sanayya.

Se'a lokacin ta tuna da canjin da rayuwarta ta samu a Sanadin Partner ɗinta Edyan
kamar yanda take kiransa tun bayan haɗuwarta dashi. Ba lallau bane mutanan dake
gurin su ganeta ba don haka da sauri ta isa gabansa ta tsaya shi kuma Edyan din na
tsaye qyam a bayanta be motsa ba.

Bamanga ne ya ɗaga sandan hannunsa take ya sauke matashi a saman goshinta kafin
kace me tuni gurin ya fashe ya fara fitarda jini, a gigice tayi baya zata faɗi
sabida wani jirin azaba daya ɗibeta cin zafin nama bamanga ya sake ɗaga sandar da
nufin ya saukewa Edyan Rabe dake qarin faɗuwa ta cikin wani irin mugun zafin nama
da bata taɓa zaton tanadashi ba tayi wuf ta sake shiga gaban Edyan ɗin take sandar
ta sake sauka bisa gefan fuskarta. Cikin ƴar daƙiƙar da bazata wuce 2 ba ta faɗi
ƙasa sumammiya.

Ganin jinin dake fita ta bakinta da kuma goshinta ne ya mugun fusata Edyan dake
tsugune bisa kanta yana ƙwala mata kira cikin wani irin karaji me cikeda nuna
tashin hankali, da ƙarfi yake kiran sunanta tamkar wani zararre ya miƙe kamar
mayunwacin zaki yay kan Bamanga da duka ƙarfinsa ya shiga gabza masa naushi yana
faɗin "how dare you dazaka sa sanda irin wannan ka daki Mulaikha ta?

Bakajin tashin komai se ihun Bamanga wanda ya cika gurin sabida duhun daya farayi,
ihunsa ne ya jawo hankalin Moddibo da malam iro wanda ke tsaye a cikin gidan da
sauri suka fito don ganin abinda ke faruwa, kasancewar hasken fitilar gaban motar a
kunne yake shine ya basu damar ganin abinda ke faruwa a tsakanin Bamanga da Baquwar
fuskar dake gabzar bamangan kamar Allah ya aikoshi.

Da sauri suka nufeshi da nufin su ƙwaci Bamangan a hannun Edyan amma sam hakan ya
farkara, daga can gefe ya tsinkayi muryar Rabe wadda ke Rawa sabida Azabar bugun
datasha a hannun bamanga tace " plz partner stop beating him he's my.....uhm.. He's
mmmmm.... My brother!!!!!

Cak Edyan ya tsaya da dukan kamar wanda aka matsawa remote, a hankali ta miqe tsaye
dukda jirin dake ɗaukarta kamar ance ta juya idanunta suka sauka akan Mahaifinta
Moddibo wanda ke ƙoƙarin ɗaga Bamanga Wanda jini ke fita ta bakinsa, da wani irin
gudu Rabe ta kwasa ta nufi moddibo tana wani irin kuka tana kiran "Babana wayyo
Allah babana is that you!!!!! Faɗawa tayi jikinsa ta saki wani marayan kuka wanda
yasa gabaɗaya mutanan gurin suka dare suna bita da kallo.

Da qyar ta iya tsagaita kukan ta ɗago tana kallonsa cikin ido cikeda shauqin si
irin na ƴa da ubanta tace "haqiqa Babba ka cika alqawarinka gareni sedai ni ban
cika maka wanda nayi maka ba babana! Ko kaɗan A tsakanina dakai tasirin qaddarar
yayi kaɗan ya zama silar rabuwata dak........... Wani irin kuka ne ya sake qwace
mata a karo na biyu.

Gabaɗaya Moddibo kasa motsin kirki yayi illa wasu zafafan hawaye dake masa zarya a
saman kumatunsa, qura mata idanu yayi sannan ya buɗe bakinsa dayayi masa nauyi yace
"so tari a Rayuwa wasu al'amuran sunfi qarfi rai da gangar jiki ya iya musalta
ɗacinsa, shiyasa tasirin zanan qaddara yasha banban da komai a rayuwar ɗan Adam,
haqiqa Allah mabuwayin sarki ne kuma mai jida ganine shi shiyasa ya taqaita min
zafin jarrabar rayuwar danake ciki ba tareda nasha wahala mai tsanani wajen nemanki
ba!!!!
Duk mutanan dake gurin seda suka tausaya musu ciki kuwa harda Edyan wanda ke tsaye
yana fitarda numfashi, ganin abin nasu bana qare bane yasa ya koma mota ya buɗe
wata qaramar box dake sit ɗin baya ya ɗakko wata madaidaiciyar box ya dawo inda
Rabe da moddibo ke rungume da juna suna aikin kuka ya kama hannunta ba tareda ya
lura da irin kallonda mutanan gurin suke masa ba ya zaunar da ita a ƙasa dirshen
sannnan ya buɗe box ɗin ya fito da soft cotton with hydrogen ya fara goge mata
ciwon dake goshinta yana fitarda jini, seda ya gama tsaf sannan yasa mata flasta ya
rufe gurin yana kallon tsakiyar kwayar idanunta with so much love and emotion.
Sauke idanunsa yayi a hankali ya mayar kan box ɗin tareda ɗakko wani ƙaramin magani
wanda aka rubuta pain reliver a jiki ya ɓallo ya miƙa mata yace "let bring the
water for you. Ya faɗa yana miqewa ya koma mota can se gashida bottle water ya
miqa mata ta karɓa tasha maganin tana wani yatsina fuska.

Gabaɗaya mutanna dake gurin kowa kallonsu yakeyi inda wasu daga ciki suke mamakin
rashin kunyar da Edyan, musamman yanda sukaga yana kama mata hannu, basu ida shiga
mamaki ba seda sukaga ya Kama hannunta yana qoqarin miqar da ita tsaye.

Gabaɗayansu zaro idanu sukai suna binta da wani irin kallo se'a lokacin ta lura da
abinda ta aikata ɗin ba shiri ta fusge hannunta daga ruqon da Edyan ɗin ya mata ta
koma kuda moddibo ta tsaya se faman raba idanu take kamar wadda tayiwa sarki qarya.
A haka taron ya watse kowa da abinda yake saqawa a gameda Edyan da Rabe.

Sosai moddibo ya tarbi Edyan kamar ze goyashi sabida yanda Raben ta gaya masa irin
alkhairin dayayi mata a rayuwarta tun bayan haɗuwarta dashi, hakan ba qaramin
dadi yayiwa modɗibo ba harya kasa ɓoye hakan a fili dukda irin tashin hankalin da
zuciyarsa take ciki a gameda halinda ya dawo ya samu Laure a ciki, kasancewar dare
yayi sosai ne yasa Moddibo ya raka Rabe bukkarta ya kunna mata fitilar lagwanin
dake ɗakin sannan ya zaunar da ita bisa katifar ciyawar dake ɗakin ya dubeta yace
"wanene wannan matashin da kuka taho taredashi?

Ajiyar zuciya ta sauke me nauyin gaske a hankali ta maida kallonta qasa ta shiga
korawa mahaifin nata bayani akan Edris da kuma irin kulawa da qaunar daya nuna mata
a rayuwa. Shiru moddibo yayi yana kallonta bece komai ba akan maganar ya dubeta
yace "ki kwanta ki huta zuwa safiya zamuyi nagana. Kwanciya tayi idanunta na kallon
saman ɗakin tayi lamo da ita sannan ya fita tareda kashe mata fitilan lagwanin.

Yana fita ɗakinsa ya nufa inda yabar Edyan don haka ya shimfiɗa masa zanin gadonsa
meɗan haske ya kalleshi yace " Cikin gurɓatcciyar hausarsa yace ka kwanta yaro dare
Yana yi kuma gashi kun kwaso hanya. Yana gama faɗin Haka ya juya jikinsa a
salube ya bar ɗakin yay canta bayan bukkokinsa ya fashe da wani irin
kuka..............

Chubado✍️
[3/3, 5:39 PM] Chubado Mohd: ❄️❄️❄️❄️❄️❄️
❄️❄️❄️❄️❄️❄️
🐄🐄🐄🐄
🐄🐄🐄🐄
*BAFULATANA*
✨RETURN✨
🐄🐄🐄🐄
🐄🐄🐄🐄
❄️❄️❄️❄️❄️❄️
❄️❄️❄️❄️❄️❄️

Page :46

*_WRITING BY: CHUBAƊO_*

Not edited

_____✍️Wani irin kuka yakeyi tamkar ransa ze fita seda ya ɗau lokaci me tsayi
yanayi sannan ya danni zuciyarsa yayi shiru, dafe kansa yayi da duka hannayensa
biyu yana me tausayawa kansa bisa jarrabawar da Allah yayi masa gefe kuma ga
iftila'in daya faɗawa iyalinsa wannan wace irin musiba ce haka ace iyalinka na
ɗauke da cikin da Allah kaɗai yasan ubansa.

Maza sama da uku ace sunwa mace fyɗe at same time wa zaka nuna a matsayin uban
wannan yaro?

Gabansa ne yay wata irin faɗuwa lokaci guda kuma ya dafe saitin zuciyarsa dayaji
tana masa wani irin zafi, miqewa yayi daqyar ya nufi bukkarsa inda Ya sauki Edyan a
ciki ya fara laluben ƴar qaramar jakar da ya shigo gidan da ita wadda ke ɗauke da
magungunansa na Asbiti ya ɓalla ya afa a baka, ya jima zaune sannan ya ɗan samu
relif da ace yabar wannan jakar a gidansu Muzaffar a sanadin Ganin Danejo dayayi da
besan inda ze tsoma ransa ba.

Fita ya sakeyi zuwa bukkar da Laure ke ajiye shirginta ya kwanta acan ya barwa
Edyan ɗakin shi kaɗai donya sake, yanajin fitar moddibo ya miƙe ya zauna tareda
kunna fitilar wayarsa take hasken ya game ko wace kusurwa ta ɗakin, ajiyar zuciya
ya sauke me qarfin gaske sabida wani irin ciwo dayaji haqarqarinsa na dama ya
farayi sabida rashin saboda irin wannan makwancin, ɗan buɗa idanunsa yayi tareda
shafa kwantacciyar sumar gefan fuskarsa sannan ya miqe ya fara zagaya ɗakin yana
tunanin yanda za'ai ya iya baci akan katifar ciyawan dake ɗakin, take yaji
zuciyarsa ta mugun karye wasu siraran hawayen tausayin su moddibo ya fara zubo masa

"Taya za'ai ace mutum ya iya rayuwa a cikin irin wannan Dajin?

Edyan yayiwa kansa wannan tambayar, take wani ɓangare na zuciyarsa yace dashi "ba
gashi nan su suna rayuwa a ciki ba.

Hannunsa yasa na dama ya shafe ƙwallar data zubo masa a hankali ya furta
"Alhamdulillah ya Rabb dakaimin ni'imar da ba kowa kayiwa kamarta ba, na tabbata ka
haɗani da mulaikha ne don kawai a sanadinta nazo naga irin rayuwar da sukeyi Don
kawai na Qara imani akan Rayuwa, ya Allah ka qara mana sutura duniya da lahira don
Alfarman manzon Rahama (S.A.W). A haka Edyan yayta tufka da warwara har bacci ya
fara ɗaukarsa,

Kamae wanda aka mintsina yay firgigit ya tashi sabida wani irin kukan qwaro daya
addabeshi, koya ya rufe idanunsa da nufin yayi bacci seyaji ya kasa sabida qarar
kukan gyaren daya cika ɗakin, wani sirin tsaki ya saki tareda miqewa ya zauna a
saman katifar kamar ze saki kuka sabida takaicin kukan qwaron da kuma rashin sabo
da kwanan irin wannan gurin, duk irin gajiyan dayayi kasa baccin yayi yanda yaga
rana haka yaga dare.
Wannan shine abinda ya faru a Rugar Arɗo.

*******

Ɓangaren su muzaffar kuwa basu shigo cikin Gyambu ba se wajen qarfe 11:00pm na
dare, direct wani babban hotel suka nufa muzaffar yay musu booking ɗakuna guda
biyu Ummie tareda Zainab shi kuma nasu shida Abie

Bayan kowa ya nufi ɗakin baccin nasu ne Muzaffar ya buɗe ƙofar ɗakinsu ya fito zuwa
inda nasu Ummie yake, a zaune ya sameta bisa saman dadduma da Alama sallar ishsha'i
ta gama gabatarwa, tsayawa yayi daga bakin qofar yana kallon yanda damuwa ke
baiyane qarara a saman fuskarta take wani irin tausayinta ya gama cika zuciyarsa,
a salube ya tako zuwa gareta ya zauna daga gefanta tareda kamo hannayenta cikin
nasa yana ɗan mammatsaya cikin sugar rarrashi yace "Ummie nasan yanda kikeji a
ranki sam ba abubane me sauki da mutum ze iya handling dinshi cikin sauqi, bt dukda
hakan ya kamata ace kin qarama kanki qarfin gwiwa akan jarrabawar datazo miki a
rayuwa, don Allah ki ragewa kanki damuwa sabida kar wani abun ya sameki na tabbata
Baffa ze fahimceki kuma delensa ya karɓe yunda keɗin jininsa ce no matter what,
koda ace sular rabuwa bata gifta a tsakaninki dashi ba dole wata sekun rabu tunda
tun ran gini ran zane Allah ya rubuta muku hakan a zannan qaddarar ku.

Ajiyar zuciya muzaffar ya sauke me qarfun gaske sannan yaci gaba da cewa " ummie
qaddara ba abarda ɗan adam zeyi shawara a kanta bace, rubutu ne tun daga mafari
kafin ayi halitta don haka babu yadda muka iya dole tsarin Allah shine a saman
komai indai har baffa ɗan uwanki ne na haqiqa wllh zeyi miki uziri akan dukkan
abinda zaki faɗa masa, don haka ki dena sa damuwa a ranki insha Allah everything is
going to be alright kinji Ummie na?

Muzaffar ya faɗa yana jawota jikinsa yay hugging ɗinta with so much love between
son to his mother.

Kuka Ummie keyi qasa-qasa tareda miqa godiyarta ga Allah daya bata ɗa irin muzaffar
wanda yafi darajar kilo giram 70 na zinare a idanunta.

Ya jima tareda ita sannan ya miqe yay mata sallama zuwa ɗakinsu, bisa ga mamakinsa
a zaune ya samu Abie shima ya kasa rintsawa duk a dalilin damuwar da Aisharsa ke
ciki, zama muzaffar yayi daga gefan abie ba tareda ya kalleshi ba yace " Abie wani
al'amari ne a rayuwar Ummie wanda har yake sanyata zubar hawaye irin haka?

Kallonsa Abie yayi da sauri lokaci guda kuma yay qasa da idanunsa yace "koma menene
zakaji komai da zarar mun isa ga moddibo. Abie na gama faɗin haka ya haye gadon
yaja ɓargo ya rufe jikinsa dukda cewar idanunsa a soye suke babu alamar bacci a
cikinsu.

(o'o see love don Allah, wllh duk duniyar nan babu abinda yafi samun miji na gari
ni'ima da kwanciyar hankali, so pls my dearest sisters wake up and keep praying for
miji na gari, wllh idam kika saki vaki kina bacci cikin dare ba tareda kin miqe kin
roqi miji na gari ba your life is in danger malama, becouse duk duniyar nan babu
abinda yakai samun miji na gari daɗi. ya Allah ka zaɓawa ƴan matan mu da mazajen
mu mata na gari tareda zuriya ɗaiyiba ))

Washe gari tun 7:00am suka haɗa komai nasu suka kama hanyar rugar Arɗo, tun daga
irin jejin da suke ratsawa ta ciki suna tafiya zuciyar Abie ta fara tsinkewa,
babban abinda ya ɗaure masa kai shine taya za'ai ace mutum me rai ya rayu a cikin
wannan qungurmin dajin?

Haka muzaffar ya dinga ratsawa ta cikin labi (hanyar shanu) harya isa cikin rugar,
motar daya hanga a tsaye ce tasa ya qara qaimi don ganin ya isa kusa da motar.
Parking yayi a saitin motar yana qare mata kallo harya fito daga cikin tasu motar,
zaro idanu yayi lokacin da idanunsa sukai tozali da bayan motar da kuma sunan dake
manne a saman lambar motar me ɗauke da harufa guda biyu kamar
haka......................

Comment
Nd
Share

Don't forget to vote on whatpad

Chubaɗo✍️
[3/3, 5:39 PM] Chubado Mohd: ❄️❄️❄️❄️❄️❄️
❄️❄️❄️❄️❄️❄️
🐄🐄🐄🐄
🐄🐄🐄🐄
*BAFULATANA*
✨RETURN✨
🐄🐄🐄🐄
🐄🐄🐄🐄
❄️❄️❄️❄️❄️❄️
❄️❄️❄️❄️❄️❄️

Page :47

*_WRITING BY: CHUBAƊO_*

*_Miɗoyatta himɓe jeɗo tokka'am bomiɗotora Allah barkiɗinamon thnks so much for the
love 👏_*

Yau dai kam Na saka fulatanci a wannan page ɗin sosai sedai ayi haquri dani 😂

BANYI EDITING BA

____✍️Da mamaki kwance saman fuskarsa ya isa jikin motar wanda zuciyarda ta gama
aiyana masa ta Edyan ce, ya jima yana nanata harufan sunan dake saman jikin lambar
motar kamar me koyon karatu, tambayan dake addabarsa a wannan lokacin itace "shin
me Edyan keyi a nan kuma meya kawoshi?

"muje mana ka tsaya kana kallon mata.

Abie ya katse masa tunani wannan hakan yay daidai da fitowar Moddibo da kuma Edyan
daga gidan, da sauri Ummie ta nufi inda moddibon ke tsaye wanda yanayinsa ya mukun
sauyawa daga ganinta cikeɗa ɓacin rai yace "* _ta'awara kumbi'am danejo, miɗa
mimeta milara ma hotoha aburti_* ( karki matso kusa dani Danejo banason na qara
ganinki a rayuwata ki koma inda kika fito) ya faɗa yana nunata da yatsa cikin
ɓacin rai.

Wani irin zubewa Umnue tayi bisa qafafunta tareda haɗa hannayenta duka biyu cikin
harshen fulatanci tace " Hamma useli waɗɗu munyal na'aibiyamma nonnon Allah arti
bindi plss. (don Allah yaya kayi haquri ba laifina bane haka Allah ya rubuta a
qarqashin qaddarar mu).

Cikeda fushi gamida ɓacin rai moddibo ya nunata yace "An'asamte abiya miwaɗa munyal
Danejo? (yanzuke bakiji kunyar kallona kice min nayi haquri ba Daneji?)

Gabaɗaya gurin zuba musu ido akayi ciki kuwa harda Edyan wanda kansa ya mugun gama
ɗaurewa da maganganunsu, daga Abie har Muzaffar babu wanda yay qoqarin dakatar da
wani a tsakaninsu sedai dukansu sunajin zafin zubar hawayen Ummien, musamman
muzaffar da har yanayinsa ya fara canzawa din haka da sauri ya isa inda Ummien ke
zube tana kuka shima ya zube nasa gwiwoyin tareda haɗa hannayensa guri guda alamar
roqo yace "bansan wani laifi Mahaifiyata ta aikata maka ba Baffa amma dukda hakan a
matsayina na ɗa a gareta ina roqa mata alfarmar yafiya a gareka don girman Allah ka
yafe mata ba tareda kayi tunani akan irin girman laifin data aikata maka ba, kada
ka manta baffa komai na rayuwa yana tafiya ne da zannan qaddara kuma idan har
ubangiji ya rubuta hakan to babu shakka se'abin ya tabbata don haka nake roqonka
arziqi don girman Allah ka yafe mata kodan darajarmu nida mahaifina!!!!!!

Muzaffar ya faɗa wasu zafafan hawaye na zubo masa Sabida jinɓzafin zubar hawayen
mahaifiyar tasa dayakejin zubarsu tamkar zubar tafasasshiyan dalma asaman zuciyasa.

Gabaɗaya kallonsu mutanan dake tsaye a qofar gidan sukayi kunsan mutanan mu da
kallo idan sukaga baqon abu lol 😂

Kasa cewa qala modɗibo yayi sabida masifan kunyar muzaffar ɗin dayakeji, badan
darajarsa ba wllh ko kallon ummien bazeyi ba haka kawai yakejin kimar yaron a
idanunsa ta yanda yakejin zai iya sadaukar masa da komai nasa Muddin mallakinsa ne.
Juyawa yayi ya shige gidan ba tareda ya iya sake futa koda kallama guda ba

Matsowa Edyan yayi inda Abie ke tsaye tareda ɗan rissinawa ya gaidashi, da sakin
fuska Abie ya amsa masa tareda dafa kafaɗunsa yace "ai tun jiya nake jarraba number
Cp amma na kasa samunsa.

Edyan yayi murmushi yace "he's fine Abie, be jima da dawowa ba ai. Ya faɗa yana
kallon Ummie wadda ta miqe da sauri tabi bayan moddibo

Qarasawa gurin yayi yana kallon muzaffar wanda shima ɗin ita yake kallo jikinsa a
matiqar mace ya sauke kallonsa ga barin Ummie sannan ya dubi Edyan da mamaki kwance
a kan handsome face ɗinsa yace "meya kawoka nan kuma dude?

Yatsina fuska Edyan yayi yace "i bring my baby to meet with her parents ne thats
why I'm here. Ya faɗa with so much emotion on his face.

Take hanjin cikin muzaffar suka wani irin juya a lokaci guda nan da nan zuciyarsa
ta wani irin buga da qarfi amma kuma seya dake ya saki wani ɗan banzan murmushi
wanda ya ɓoye weakness dinsa yace "waw thats nice dude.

"Kaifa meya kawoku ? Edyan ya faɗi hakan yana tsareshi da manyan idanunsa.

Ɗan jim kaɗan muzaffar yayi kamar bazeyi magana ba ya ɗan saci kallon cikin mota
yaga still zainab na bacci sannan yace "is just a family issues. Taɓe baki Edyan
yayi yace "ok tashi mu shiga ciki
Miqewa yayi daga tsugunnen dayake ya koma mota ya tada zainab sannan suka shiga
cikin gidan gabaɗayansu kowa da abinda yake saqawa a zuciyarsa.

Suna shiga direct ɗakin moddibo sukaiwa kansu masauki dukda cewar moddibon be wani
sake dasu ba amma yayi qoqari sosai wajen danne zuciyarsa akan abinda qanwar tasa
ta aikata masa. Bayan sun zauna ne modɗibo yasa Rabi'atou ta kawo musu
tafasashshen madara da kuma damammiyar dawo wadda taji uban kayan qamshi irin na
Asalin fulani.

Ƙura mata idanu Ummie tayi tana kallonta lokaci guda kuma ta saki wani tattausan
murmushi wanda ya baiyana ainihin kyanta da kuma irin kamar da suke da moddibo.
Itama Rabi'atoun kallonta takeyi sannan ta durqusa ta gaishesu dukda cewar batasan
daga nahiyar da duke ba, kokaɗn hankalinta bekai ga muzaffar wanda ke zaune a
kusada Edyan ba hakan yasa ta miqe ta fara qoqarin fita

Daqyar ya iya bude bakinsa sabida wani masifan kyau dayaga ta qara masa a sanadin
canjin data samu yace "uhm you don't know how to great right?

Tsayawa tayi cak ba tareda ta samu zarafin juyowa ba sabida tsabar ruɗun data shiga
a sakamakon jin muryar mutumin da kullum zuciyarta ke bugawa dason sake jin sautin
muryarsa a rayuwarta, da ɗan sauran qarfin daya rage mata ta tattara ta juyo a
hankali take idanunsu ya sarqe cikin na juna,

Gabaɗayansu zuciyarsu bugawa take kusan duk a lokaci guda haka kuma kowa da abinda
yake saqawa a ransa gameda abokin gamin nasa. Sauke idanunta tayi da sauri kamar
me koyon magana tace "g..ood morning! Sam bata tsaya sauraron respond ɗinsa
ba ta fice daga ɗakin zuciyarta na bugawa.

Ɗakin da bata taɓa zaton zata iya sake shigarsa ba ta nufa sabida tsabar ruɗanin
dake tareda ita, a hankali tasa hannunta ta ɗaga labulan buhun dake jikin bukkar
tareda kunna kai ciki still tayi tana kallon Inna Laure dake zaune dirshen da uban
ciki qafafunta duk sun kumbura.

Wani irin farin ciki ne ya ziyarci zuciyarta take shauqin da murna suka yaye mata
hujabin tsoron lauren data daɗe tanaji ta nufeta da wani irin excitement on her
face ta rungumeta, ko babu komai itama zata haifa mata qanin daze dinga ɗebe mata
kewar kaɗaicin data taso a cikinsa.

Duk yanda taso ta Ta kali fuskar inna Lauren sam abin be yuwu mata ba dole ta
haqura ta fara qoqarin matsa mata qafar yanda zata ɗanji dama-dama

A ɓangaren zuciyar Laure nadamace zallarta dukda cewar bata fito mata da hakan a
fili ba, gabaɗaya kunyar yarinyar takeji musamman idan ta tuna irin zaluncin data
dingai mata a rayuwa ba tareda haqqinta ba, tayi mata alkaba'i me tarin yawa wanda
bakinta baze iya qayadewa ba se gashi tun ba'aje ko ina ba Allah ya mayar matada
mugun nifinta a kanta, hawayene suka zubo mata amma kuma setai saurin sa hannunta
ta goge gudunɓkar Rabi'atoun ta gani.

A haka har aka kwashe lokaci meɗan tsayi suna tare tana matsa mata qafar.

A ɗakin moddibo kuwa shirun ne ya fara gundurar kowa amma banda Ummie wadda ke
zaune jefi-jefi takan ɗaga idanunta ta kalli yayan nata. Abie ne ya katse shirun
ta hanyar cewa "salati goma ga manzon Allah (S.A.W) nan take kowa ya amsa aka
shiga jerawa manzon Rahama salati bayan sun kammala Abie ya ɗaga kansa ya kalli
modɗibo yace "da farko dai ina mai baka haquri bisa abinda ke tsakaninka da Aisha
bawai a matsayin suruki ba a'a ina magana ne a matsayina na Abdulwahab Abdalla kuma
ubaga ɗanda Aisha ta haifa, haqiqa Aisha tayi kuskure musamman data gaza haquri ta
zauna tareda danginta sakamakon iftila'in daya faɗa mata, gabaɗayan mu dagani
harkai babu wanda ze iya misalta irin ciwon da zuciyar Aisha ke ciki tunda
gabadayan maza ne ba mata ba amma kuma dazamu ɗora kanmu a matsayinta na tabbata
hukuncin data zartarwa rayuwarta muma irinsa zamu yanke kokuma akasin hakan, banaso
ka kalli aisha a matsayin mace mara tausayi kokuma adalci sabida sam siffarta ba
haka take.

A iya zaman danai da ita kimnain shekaru talatin da biyar na karanci halaiyarta ta
yanda ko ina naje zan bada labarin wacece ita.

"amma kuma ai hakan be hanata iya guduwa tabar Ahalinta ba duk sabida wani
dalilinta mara tushe!!!!! Moddibo ya faɗi hakan ransa a matiqar ɓace. abie
zeyi magana Moddibo ya kalli su muzaffar da Edyan se kuma zainab dke zaune suna
raba idanu yace "maza ku tashu ku bamu guri zamuyi magana.

Ba musu gabaɗayansu suka miƙe suka fita kamar yanda modɗibon ya buqata sannan ya
dubi Abie yaci gabada cewa "duk na saurari batunka nima yanzu zakaji abinda na
riqa a matsayin hujja dukda cewar ba lallai Danejo ta sanar dakai ba, kamar yanda
ka faɗa a maganganunka na baya tabbas ni kaina mai iya bada shaida fiyeda yanda ka
bayar ne akan Danejo sabida tun batasan kanta ba nake rainonta da hannayena, nasha
haqura da abubuwa da dama a rayuwarta don kawai na inganta Rayuwarta to amma meye
laifina don kawai qaddara ta Fyaɗe ta faɗawa rayuwarta shikenan seta gudu ta barni
ba tareda ta sanar dani inda zataje ba har tsahon shekara 35?

A matsayinka na uba wanda keda ƴaƴa mata ka ɗora maganata akan mizani shin wani
irin hukunci zaka yankewa Aisha a lokaciɓ da qaddara ta sake haɗaka da ita?

Shiru Abie yayi zuciyarsa cikeda zallar tausayin modɗibo he wish to see his sister
kamar yanda modɗibo yaga tasa qanwar wadda tun bayan rasuwar mahaifinsu da aka musu
rabon gado ba jimawa mijinta ya ɗauketa sukabar garin ba tareda ya sanar dashi ba,
tunda suka tafi har yau be qarajin duriyarsu yayi neman harya gaji duk kuɗinsa da
kuma shahararsa har yau babu wani labari akan Balaraba qanwarsa. Nan take Abie ya
fashe da kukan tausayin kansa

Seda yay me isarsa sannan ya ɗaga kai ya kalli moddibo yace "ina roqonka Arziqi ɗon
Allah ka yafe mata wllh da kasan irin wahalar da Aisha tasha akan tunaninka na
tabbata zaka yafe mata ba tareda ka tsaya dogon nazari ba, tundaga lokacin dana
tsinci Aisha a bakin hanya babu numfashi a jikinta har zuwa lokacin dana fara
soyayya da ita har mukai Aure Aisha bata taɓa samun kwanciyar hankalin manta ka ba,
haka kuma munje numan yafi a qirga amma kuma bamu sameku ba se bukkokinku da aka
sakawa wuta suka qone, dukda haka Aisha bata yanke qauna ba kuma bata fasa zuwa
numan ba akan kozata samu labarin inda kuka koma.

A qarshe da abin yayi tsamari ɗaukarta nayi kacokan na maida ita india da zama
kozata rage yawan damuwar dake ranta. A qarshe kuma ina me maka wasilci kan cewar
Allah ma munayi masa laifi kuma ya yafe mana ba tareda ya duba girman laifin da
muka aikata masa ba.....

Hawayen dake idanunsa Moddibo ya share sannan ya kalli ummie dake zaune tanata
gurzar kuka a karon farko tun shigowarta ɗakin yace" na yafe miki Danejo Allah
ubangiji ya yafe mana gabaɗaya 😭

Zabura tayi ta riqe qafafunsa tace "nagode Hamma Allah ya qara girma.

A haka kowannensu zuciyasa ta cika da farin ciki mara misaltuwa, fitowa Abie yay
daga bukkar bisaga mamakinsa muzaffar na kan wani dutse wanda ke facing ɗin ɗakin
moddibon daga ɗan nesa, fara'ar kan fuskar Abie ce ta bashi tabbacin cewar baffan
ya yafewa mahaifiyar tasa. Misalta irin farin cikin da muzaffar ke ciki abu ne da
baze yuwu ba don haka suka rungume juna da Abie shikuma Edyan yanata baza uban
murmushi wanda ke nuna farin cikinsa ga abokin nasa.
Tun'a safiyar ranar labari ya gama karaɗe rugagen dake maqotaka datasu moddibo kan
cewar Danejo da Rabe sun dawo harda ɗanta saurayi ma da kuma mijinta, don haka
akwai taron al'ada wanda za'a habatarwa da Danejo da kuma ɗanta wanda ba'ayi mata
ba tun shekarun baya *_(niko nace kuji bidi'a don Allah 🤣)_*

Kafin kace me jama'a kowa ya fara halarta zuwa bikin Al'adar Auren danejo da kuma
mijinta.

Bayan Azahar aka kawo kayan sakin da Ummie da Abie zasu saka wanda ya kasance
launin blue da yallow a cikin wasu qwarya guda biyu kowada nasa se kuma takalman
roba suma guda biyu da kuma lulluɓi, su muzaffar da Edyan ma sam ba'a barsu a
baya ba sedai su nasu kayan na farin saqi ne kamar na sauran ƴan gaiya, bayan anyi
sallar la'asar ne Bulo handi tazi tasa Ummie ta sanya kayan saqin da aka kawoma
ummien sannan ta umarceta dataje ta taimakwa mai gidan nata ya shirya tunda tasan
yanda ake komai. Ba musu ta fita daga fakin zuwa inda Abie yake

Seda ta tabbatar ta taimaka masa ya gama saka komai na biki al'adar sannan ta ɗakko
cinkon saqaqqiyar igiyar kaban dake gefe ta rataya masa suka fito tare, a waje suka
cimma su muzaffar da edyan da zainab suma sun shiya cikin farin saqin suna jiram
fitowarsu.

Kusan a tare suka nufo inda ake gudanar da shagalin bikin al'adar daga muzaffar har
Edyan seda abin ya nemi ya basu tsoro musamman yanda sukaga an gangama uban itace
uwa naci gefe kuma nawa saniya guda ne a banqare ana gasashi gabaɗaya fuskokin
mutanna dake gurin duk an fenteta da uban farin fenti da yellow irindai kwalliyar
fulanin jeji, har aka kabbara kiran sallar magrib ba'a fara shagalinba har seda
kowa yay sallar magrib tukunna

Sosai abin ya burge zainab don haka ta fito da wayarta tana ɗaukar vedio tun daga
zuwansu Abie har kujerar da suka zauna seda ta dauka a vedion , kafin kace me tuni
shagali ya kankama abin babu kama hannun yaro sannan Rabe suka qaraso gurin itada
ruqatu da kuma Modɗibo, gabaɗyansu tsareta sukai da ido daga muzaffar ɗin har Edyan
ɗin, nan take zuciyar muzaffar ta fara aiyana masa kan cewar yaje gareta.

Yana shirin miqewa Edyan ya rigashi miqewa ya nufeta fuskarsa ɗaukeda wani
hamshaqin murmushi tareda fito da wayarsa ya fara ɗaukarta hotuna tana dariya, yana
zuwa kusa da ita yace "looking so Masha Allah partner. Washe haqora tayi
tace "thank you partner and you too.

Matsawa yayi dab da ita yace "can I snap a picture with you babe?

Why not. Ta faɗa tana gyara tsaiwanta sosai kusa dashi

Duk abinda suke idanun muzaffar na kansu babu abinda zuciyarsa keyi banda tafasa, a
fusace ya miqe daga inda yake zaune ya nufi inda suke ɗaukar hoton har idanunsa
nayi masa sabida ɓacin rai............ Hannunsa yaji an riqe ta baya don haka ya
tsaya chak jikinsa na wani irin rawa yana juyawa yaga zainab ce ba shiri yay
hugging ɗinta still jikinsa na rawa, a tsorace take binsa da kallo Cikeda tsoro ta
zare jikinta daga nasa tace "what's wrong bro? talk to me pls.
Comment
Nd
Share

Dont forget to vote on whatpad.

Chubaɗo
[3/3, 5:40 PM] Chubado Mohd: ❄️❄️❄️❄️❄️❄️
❄️❄️❄️❄️❄️❄️
🐄🐄🐄🐄
🐄🐄🐄🐄
*BAFULATANA*
✨RETURN✨
🐄🐄🐄🐄
🐄🐄🐄🐄
❄️❄️❄️❄️❄️❄️
❄️❄️❄️❄️❄️❄️

Page :48

*_WRITING BY: CHUBAƊO_*

*ɗan tsokaci a gameda masu cewa ya kamata ace muzaffar yasan dalilin dayasa
mahaifiyarsa tabar Rugarsu zuwa wani guri na daban, ina so kuyi aiki da basirar da
Allah ya baku a matsayinku na ƴan Adam masu tunani, inaso ku ɗora kanku a matsayin
da Muzaffar kekai shin ya zakuji idan akace yau wani ɗan fashi ya hauro gidanka
kuma yayiwa mahaifiyarka Fyaɗe? Na tabbata da ace hakan ta faru gara ace ƴan
fashi sun shigo gidan ka sun kashe mahaifiyarka se hankalin ka yafi kwanciya da
ace wani ɗan iskan banza ya ketwa mahaifiyarka alfarmarta, bawai ban karɓi
qorafinku bane a'a kawai dai inaso ku ɗora lamarin a mizanin dedaito da hankali ne👏
*

BANYI EDITING BA

_____✍️A ɗan wannan taqin abubuwa dadama sun faru masu daɗi da kuma marasa daɗi,
lokacin da zuciyarta ta gama tabbatar mata da cewar lallai muzaffar ya tafi a irin
yanayin data gama tabbatarma da kanta cewar baze sake waiwayarta ba se kawai ta
sake fashewa da wani irin kuka wanda it kaɗai tasan ma'anar abinta, haqiqa ita
kanta tasan bata kyauta masa ba musamman data nuna masa halin ko'in kula a lokacin
datasan yana matiqar buqatar hakan, to Amma yata iya bazata iya barin Edyan ba
sabida ya haskaka rayuwarta ta ɓangarori da dama. Don haka kowa yanada
mahaimmancinsa a idanunta da kuma zuciyarta.

*******

Ɓangaren Edyan da abokanan tafiyarsa kowa ya isa gida lfy haka kuma kowa da abinda
zuciyarsa ke tufka masa ta ɓangaren abinda ke wakana a zukatansu, lokacin da
Edyan ya isa gida Direct part ɗinsa ya nufa tareda faɗawa toilet ya sakarwa kansa
ruwa me zafin gaske sabida gajiyar dake taredashi, ya jima a toilet ɗin sannan ya
ɗaura alwala ya fito ɗaure da wani babban towel wanda ya tsaya masa iya
digadigansa, ko mai bai shafa ba ya Buɗe tangamemiyar drower ɗinsa dake manne a
jikin bangon ɗakin ya fara bin side ɗin inda qananan kayansa suke, wata riga mara
nauyi ya ɗakko da wandonta mallakin companyn Pajamas ya saka sannan ya tada sallar
dake kansa, yana idarwa ko tasbihi beyi ba ya miqe ya hau kan makeken gadonsa
sabida wani irin bacci dake muqurqusarsa, cikin mintuna kadan bacci mai nauyi ya
ɗaukeshi.

Al'amarin Muzaffar kuwa tun bayan dawowarsu gabaɗaya zuciyarsa ta gaza samun
nutsuwa sabida tarin damuwar dake kwance a qasan zuciyarsa, duk hada-hadar dayakeyi
daurewa kawai yakeyi yana gabatar da wasu abubuwan don haka yay wata iri Rama wadda
sedata girgiza Mommy, dukda irin damuwar dayake ciki sam be fasa gudanar da
yanayin aikinsa ba don haka nasarori kullum qara samuwa suke a sanadinsa.

Zaune yake a cikin hamshaqin office ɗinsa yana matsa na'urar laptop ɗin dake
gabansa, kallo ɗaya zakayi masa ka fahimci he is doing something important on his
system ɗin. Ahankali take takowa cikin takunta na isa da qasaita harta samu
nasarar tura qofar glass ɗin dake office ɗin, da hanzari sectary ɗinsa ya nufota
yana faɗin "I'm sorry ma'am but my boss said he don't want to see any client
karnabar kowa ya shiga senan da 1 hour. tsayawa Hajar tayi jikinta duk a mace
sabida tasan halinshi sarai muddin ya faɗi abu aka saɓa tofa bashida sauqi ko kaɗan
ta wannan fannin.

Makeken glass ɗin dake manne a fuskarta ta zare tareda ɗaga qafafunta ta nufi gurin
da aka tanada don zaman baqi masu jiran iso idan sunzo, badan ranta yaso ba ta zaro
wayarta tana wani latsawa tamkar babu abinda ke damunta. Tana nan zaune Ta hangi
fadilah cikin shigar wata arniyar baqar suite with street siket se faman walwalin
baqi takeyi, kanta kuma ɗaure cikin rolling irin na mutanna qasar misrah a nitse
take takowa cikeda nutsuwa tamkar ba stubborn Fadilah ɗinnan ba me shigen nuna isa
da kuma wulaqanci ba, Direct office ɗin ta shige hannunta ɗauke da wani file ko
lura da Hajar dake zaune gurin batayi ba.

Ta jima a ciki sannan suka fito taredashi hannunsa bisa kafaɗar Fadeelah ɗin suna
dariya, still tayi tana kallonsu ba tareda sun lura da ita ba fadilah ne ta kalleta
lokaci guda kuma ta zaro ido tace "oh Hajar long time no see ya kk? Ta faɗa
tareda matsawa ga Hajar ɗin wadda ta kafe Muzaffar da wani mayen kallo kamar zata
cinyesa ɗanye, wani irin masifan kyau taga yayi mata a cikin Royal blue ɗin Korean
suit ɗin dake jikinsa wadda tai masifan karɓar jikinsa. A dabuce ta saki murmushi
Ba tareda ta iya furtama Fadilah dake tsaye komai ba.

Kallonsa Fadilah tayi tace "Yaya lemme back to my office I have a client that are
still waiting for me. Ta faɗa tareda barin gurin tana dariyar yanda taga ya wani
sauya fuska duk sabida ganin chiwebegum ɗin nasa kamar yanda take kiran Hajar ɗin
dashi.

Kamar zatayi kuka ta qaraso gurin da yake tsaye ta kafeshi da mayun idanunta tana
kallonshi tace "kayi haquri my ster kawai bazan iya zaman jiranka har zuwa lokacin
da kasawa ranka zakazo gidan mu bane, kwanaki can da daɗewa kace min zakazo gida
muyi magana amma kum......... Kuka ta sakin masa sabida yanda takjin ciwon abin a
ranta.

Ɗan wara manyan idanunta yayi sabida yanda ta mugun bashi mamaki, hannunsa yasa ya
dafe kansa tareda firzar da wani irin iska mai zafi daga bakinsa yace "look Hajar I
don't want any trouble plz oya tashi muje badai rashin zuwa gidanku bane kawai
matsalar ? To muje . Ya faɗa yana nuna mata hanya

Takawa ta farayi tana share hawayen dake sakko mata suka fito farfajiyan companyn,
kallonsa tayi zatayi magana ya dakatar da ita ta hanyar cewa"ki shiga motarki zan
biki a baya banson problem, juyawa tayi da sauri ta shiga motan ta sannan shima ya
shiga nasa guards ɗinsa na take masa baya a haka har suka isa gidansu Hajar Ɗin ya
ɓalle murfin motar dayake ciki ya kalli Solomon yace "ku jirani a nan base kun
shigo ciki ba nan da 5minute zan fito insha Allah.
Be jira cewarsu ba ya tura qofar get ɗin ya shiga cikin gidan, a hankali yake
takawa cikin takunsa na isa da jinkai harya isa maine qofar da zata sadashi da pard
ɗin Mom Edyan ba tareda ya tsaya ga hajar wadda ta ƙwafe a guiding tana jiran ya
qaraso susha hirar love ba.

A nitse ya shiga falon da sallama tareda fara qoqarin zare rufaffan takalmin fatar
dake qafarsa, dakatar dashi Mom tayi ta hanyar cewa bar takalmin ka ka shigo dashi
son. Ta faɗa tareda yalwata murmushin fuskarta

Cikeda kunya ya durqusa har qasa yace "mom ina yini? "lfy lau muzaffar yau
kaine a gidan namu? "ae wllh mom nine dama nazo ne nayi muku godiya bisa ɗawainiyar
da kukayi da Rabi'atou. Haɗe rai mom tayi ta sake kallonsa tace "banda abinka
muzaffar Ai rabi'atou ƴa take a gurina koda ace babu alaqar jini a tsakaninka da
ita, haka kuma bamuyi mata don ka gode mana ba komai mukayi mata wllh munyi mata
shine don Allah badan neman jiran saka mako ba.

Shafa gefan kansa yay cikeɗa da kunya sannan yace "mom Edyan yana nan kuwa? Ba
tareda ta kalleshi ba tayi murmushi tace yana part ɗinsa be jima da dawowa daga
office ba. Zeeyadah ce ta shigo falon hannunta ɗauke da flet wanda ke ɗauke da
fruite a ciki, da sakin fuska gamida girmamawa ta iso falon tana faɗin sannuda zuwa
ya muzaffar yau kaine a gidan namu?

Murmushi yayi mata wanda ya qarawa fuskarsa kyau yace "yeah. Murmushin dake kwance
kan fuskarta ta qara faɗaɗawa tace "your highly welcome.

Miqewa yayi tareda faɗin "thank you dear kafin yama mom sallama ya nufi part ɗin
Aminin nasa Edyan, a hankali yake tafiya zuciyarsa ɗauke da wani al'amari wanda
yakejin masifar nauyinsa tamkar an ɗora masa gingimemen dutse me girman gaske, ko
kadan bayaso mace ta shiga tsakaninsa da Babban Amininsa shiyasa yake qoqarin ganin
ya yaqi al'amarin dake ransa gameda Edyan ɗin, yana matiqar martaɓa Edyan tayanda
yakejin cewar qimarsa takai ya iya sallama masa komene muddin hakan zai sanyashi
farin ciki koda kuwa ace Rabi'atoun ce kuwa.

A hankali ya murɗa babbar qofar dake falon tareda kunna kai ciki, babu kowa a falon
se Tv dake ta faman aiki don haka Direct ya nufi qofar bedroom ɗinsa, da sallama
ɗauke a bakinsa ya tura qofar tareda sauke manyan fararen idanunsa Akan kowace
kusurwa dake cikin ɗakin, sakin qofar yayi ya Still yaci gaba da takawa zuwa cikin
ɗakin harya isa bakin makeken gadon dake ɗakin ya zauna yana me zubawa qofar toilet
ɗin dayaji zubar ruwa idanu.

Seda ya kwashe kimanin 3minute zaune sannan Edyan ya fito sanye cikin farar
jallabiya yana sauke hannun rigar zuwa qasa da alama Alwala yayi, kafeshi da ido
muzaffar yayi batareda yace dashi qala ba, murmushi Edyan yayi tareda qarasowa ga
aminin nasa ya zauna daga gefansa yana me qara yalwata murmushinsa yace "anya kuwa
idanuna daidai suke nuna min kokuwa dai gizo kake min? Idan har zan iya tunawa
daidai rabonda mu haɗu irin haka tun a Gyambu. Ya faɗa yana dafa kafaɗun muzaffar
ɗin wanda ke kallosa har yanzu baice qala ba

Ajiyar zuciya ya sauke me nauyin gaske sannan yace "nazo ne kawai na ganka nima
sabida inaji a jikina cewar Nayi Kewarka Edyan !!! Muzaffar ya faɗi hakan yana
kallon Edyan ɗin yana murmushi shima, amma kuma a ransa yana me tausayawa Edyan ɗin
sabida wata shegiyar rama dayayi wanda yake da tabbacin cewar irin damuwar dake
addabarsa kullum a zuciyarsa irinta ce ke addabar Aminin nasa Shima, take wani irin
tausayinsa yay masa dirar mikiya a ransa.

Seda suka ɗan taɓa hira kimanin tsahon mintuna 5 sannan nuzaffar ya miqe yana
murmushin qarfin hali yace "zan wuce gida zuwa anjima mayi waya ko?
Ajiyar zuciya Edyan ɗin yaɗan sauke sannan yay murmushi cikeda qarfin hali yace
"ok thank you so much for the visit. Kallon tsaf muzaffar yay masa sannan ya dafa
kafaɗunsa lokaci guda kuma ya fice daga ɗakin cikin takunsa harya ɓace idanun
Edyan na kansa a ransa yana me tausaya masa shima.

Koda ya fita direct guiding ɗin ya nufa inda yake da tabbacin cewar Hajar na gurin
tana Aikin jiransa, tunda ya nufo gurin ta kafshi da idnu tamkar zata haɗiyeshi
sabida so harya samu guri ya zauna still tana kallonsa, yana zama ya sarqe
qafafunsa ɗaya kan ɗaya sannan ya dubeta a karon farko a rayuwarsa yace "Hajaaaar!

Wani irin Amsawa qirjinta yayi sabida wannan shine karon farko dataji sunanta a
bakinsa, wani irin farin ciki taji yana ratsa zuciyarta nan take hawayen farin ciki
ya farayi mata zarya, bakinta yana rawa ta fara magana daqyar tace "haqiqa yau
itace rana ta farko a rayuwata wadda tazo min da tarin alkhairai ciki kuwa harda
wannan zaman da mukai da juna dakai a yanzu, wllh Muzaffar zuciyata me rauni ce
indai har akan son da take maka ne na shiryawa dukkan abunda ke shirin yimin
katanga dakai Koda kuwa hakan na nufin Rasa Rayuwata ne gabaɗaya!!! Don Allah ka
fahimci damuwata kada ka hukuntani da abinda bazan iya ɗauka ba plssssss.

Tunda ta fara magana ya kafeta da tsimammun idanunsa waƴanda suka tashi daga launin
farare suka surka da launin ja sabida tausayinta, a hankali ya dubeta tareda sauke
numfashi yace "Haqiqa na tausaya miki Hajar kuma babu shakka kin samu nasarar dasa
tausayinki a zuciya ta, nasani jarrabawar soyayya ba qaramin Abu bane haka kuma
duk mutumin daya samu kansa a ciki abu ne mawuyaci ya iya samun kwanciyar hankali
harse zuwa ranar da ya samu abinda ransa ke muradi, sedai dukda hakan ina me baki
haquri bisa abinda bakina ze furta miki a yanzu wllh hajar a halin yanzu sam ba
relationship bane a gabana I have a lot of abubuwan dake gabana wanda sam bazan
iya haɗasu da soyayyah ba, koda ace ma zanyi soyayya to zuciyata tanada wadda
takeso kuma take Qauna banajin cewar zan iya son wata mace kamar yanda nake sonta!
Wannan dalilin yasa bazan iya amsar soyayyarki ba koda kuwa ace na Rasa daman Auren
wadda zuciyar tawa takeso.

A hankali sautin kukanta ke tashi cikin wani irin yanayi na zallar tausayin kanta
da makomarta tace " sonda nake maka a cikin jinina yake yawo banajin cewar haquri
ze iya wadatar da zuciyata harya sa na iya cireka a raina, amma don Allah shin
zaka iya sanar dani dalilin dayasa bazaka iya karɓan soyayya na ba?

Murmushi ya saki wanda ke baiyana zallar tausayawarsa gareta sam bayaso yay hurting
ɗinta daqyar ya iya buɗe bakinsa yace " sabida baki dace da irin tsarin matar da
zuciyata keso ba Hajar!! addinin mu ya horar damu cewar idan zamuyi aure to mu
zaɓama ƴaƴan mu uwa ta gari bawai kuma ina nufin keɗin ba mace ta gari bace a'a
hajar sam ba haka nake nufi ba, kawai dai bazan iya zamada matar data maida
rayuwarta irinta turawa ba kamar dai yanda kike a yanzu, wllh da ace qanwarki
zeeyadah ce ke sona kamar yanda kike sona tabbas zan iya Aurenta kuma na zauna da
ita badan komai ba kodan sabida kyawawan halayenta......... Yana kaiwa nan ya
miqe idanunta sun sauya kala sabida yanda yake tausaya mata bisa dakon soyayyarsa
data daɗe tanayi tsahon lokaci.

A haka yabar gurin ko waiwayonta beyi ba. Zubewa Hajar tayi a gurin lokaci guda
kuma ta saki wani irin kuka mecin rai gaamida zallar tausayin makomar rayuwarta.

Yana zuwa ya shiga mota Solomon sukaja motar sukabar harabar qofar gidan.

Tun bayan dawowarsu daga Gyambu muzaffar ya tattara lamarinta ya ajiye a gefe
tareda maida dukkan hankalinsa ga aikinsa, sosai yake wata irin rama sabida yanda
abin ke cinsa a rai fiyeda duk zaton mai karatu amma tsabaragen kafiya da taurin
zuciya ya hanashi samarwa zuciyarsa abinda takeso. A haka rayuwa ta dinga tafiyar
masa da daɗi babu daɗi still yaqi koma mata kamar yanda take mafarki a kowace
wayewar garin safiya.

Kamar yanda Ummie ta sanar da Moddibo cewar zata sake dawowa bayan sati ɗaya hakan
kuwa akayi, tun ana washe garin ranar dazata tafi Gyambun ta kammala shirya duk
kayayyakin dazatayi musu tsaraba dashi, zaune take a tsakiyar falonta ta miƙe
ƙafafunta tana duba kayayyakin da Abie ya shigo dasu wanda zatayi musu tsaraba
dashi, Baba Hajara ce ta shigo falon hannunta ɗauke da wani ƙaranin bokitin roba
cike taf da dambun naman kaza, inda ɗaya hannun nata kuma take ɗauke da farantin
silver cike taf da kwaɗon zogale wanda yaji uban quli-quli da tumatur, fuskarta
ɗauke da murmushi ta qaraso inda Ummie ke zaune ta miqa mata farantin zogalen tace
"Ranki ya daɗe ga zogalen an kammala haɗawa.

Da mamaki Ummie ta ɗago tana kallon baban hajaran sannan tace "haba baba don
Allah ? So nawa zan gaya miki cewar ki ɗena ɗorawa kanki hidimata tunda kema kanki
ba lafiyarce ta isheki ba?

Nidai don Allah baba karki sake bawa kanki aiki da sunan zaki wahalta min don
girman Allah. Ummie ta faɗi hakan yayinda take kallon baba hajarar wadda keta
faman murmushi

Cikeda dattako Baba Hajara tace "haba Ranki ya daɗe ai wannan sam ba aiki bane me
wahala da har zaki damu kanki don kawai nayi miki shi, don haka sam ki dena damun
kanki akai ne jikina ya daɗe da warwarewa. Zatayi magana kenan Muzaffar da
Fadilah sika shugo falon bakinsu ɗauke da sallama yana gaba Fadilah na binsa a baya
a haka suka shigo tsakiyar falon idanunsu duk akan farantin dake gaban ummie cikeda
uban zogale wanda aka baɗeshi da quli gamida tumatur me yawan gaske, zama suka
sannan Fadilah ta gaida Ummie tana dariya tace "Ummie muqaddiman naku kukeyi kenan
keda Baba Hajara akan aiki ko?

Da sakin fuska tace kin ganta nan wllh Fadilah kullum senayi fama da ita akan
magana ɗaya dai amma taki ta bari miqewa baba hajara tayi tareda miqawa muzaffar
bokitin dambun naman datayi masa don tasan yana sonsa sosai, faɗaɗa murmushinsa
yayi tareda karɓan bokitin yace "kai lallai matar nan kin iya kula da mijinki yanda
ya kamata. Ya faɗa yana ɗiban dambun yakai bakinsa

Dariya sukai gabaɗaya sannan Ummie ta miqe ta wuce ɗakinta, sun jima suna aiki a
system tareda Fadilah se wajen dabda magrib suka gama aikin tsaɓ sannan kowa ya
koma ɓangarensu.

Washe gari gabaɗayansu Ahalin gidan suka raka Ummie airport ciki kuwa harda Mom da
baba Hajara da kuma zainab, har seda sukaga tashin jirginsu sannan suka koma gida
ita kuma Ummie jirginsu ya nufi birnin na Yola.

******

Gyambu (taraba state)

Jirginsu na sauka wasu lafiyayyun motoci guda uku baqaqe wuluk sukazo ɗaukarta
cikin qanqanin lokaci Ummie ta fito cikin shigar doguwan riga me shegen kyau, take
guards ɗin suka buɗe mata motar dake tsakiya ta shiga ta zauna sannan suka ɗauki
hanyar gyambu.

Sosai moddibo yay farin cikin da zuwan ummien har hakan ya gaza ɓoyuwa a kan
fuskarsa, don haka ya shiga hada-hadan haɗa mata duk wasu abubuwa dayasan tana
masifan sonsu tun tana qarama.
Sosai Ummie kejan Rave a jikinta don haka yarinyar ta ɗan saki jiki da ita ko babu
komai ganinta na rage mata kewar Abin Qaunarta muzaffar. A haka rayuwa ta dinga
tafiya kullum zuciyarta na azabtuwa da kewar zaratan mazajen datai rayuwa dasu kuma
har zuciyarta ta afka a qoramar saboda su.

Sosai ummie kejin daɗin zaman garin hkaa kuma wata irin shaquwa ta musamman na qara
giftawa a tsakanin Moddibo da kuma qanwar tasa, wannan dalilin yasa ta qara
tabbatarwa da kanta cewar maganar bahaushe gaskiya ne dayake cewa "kowa yabar gida
tofa gida ya barshi. Sosai take kula da yanayin cikin laure wanda yay masifar
girma don haka ummie ta dubeta da kulawa tace " Amma laure wannan cikin naki kun
taɓa zuwa Asbiti akan batun awo kuwa? Ni watansa nawa ne ma tukun na?

Jikinta a mace laure ta kalli ummie tace..........

Sushmah ✍️
[3/3, 5:40 PM] Chubado Mohd: ❄️❄️❄️❄️❄️❄️
❄️❄️❄️❄️❄️❄️
🐄🐄🐄🐄
🐄🐄🐄🐄
*BAFULATANA*
✨RETURN✨
🐄🐄🐄🐄
🐄🐄🐄🐄
❄️❄️❄️❄️❄️❄️
❄️❄️❄️❄️❄️❄️

Page :49

*_WRITING BY: CHUBAƊO_*

Banyi Editing ba

____Jikinta a mace tace "ai kinsan yanayin yanda muke rayuwa A nan Danejo don haka
ban fahimci abinda kike kira da wannan sunan ba.

Murmushi kawai Ummie tayi a ranta tana taya ɗan uwan nata samun haihuwa a karona
biyu, addu'arta ɗaya ce Allah yasa Laure ta haifa masa zaratan maza guda Biyu kodan
ƴaƴansu su samu yawaitar ƴan uwa ba kamarsu ba da suka kasance su uku rak a gaban
iyayensu. A haka moddibo ya shigo gidan ya samesu fuskarsa ɗauke da murmushi yaja
ɗaya daga cikin kujerar tsugunon dake gefan ummie ya zauna hannunsa dauke da baƙar
leda meɗan girma kaɗan Gamida qatuwar qwarya wadda aka rufeta faifai.

Da kulawa Ummie ta dubeshi cikin harshen fulatanci tace "sannuda isowa hamma.

Murmushin dake kwance a saman fuskarsa ya qara yalwatawa ya dubeta yace " yauwa
Danejo maza tashi ki ɗakko min ƙwarya kizo mu kasa wannan goron ɗaurin Auren.
Bakinta sake ta dubeshi fuskarta ɗaukeda mamaki tace "Goron ɗaurin Aure kuma Hamma?

Bece mata qala ba illah Ajiye qwaryar dake hannunsa da yayi wadda ke ɗauke da
farin saqi tass a cikinta gamida mayafinsa se kuma takalmin roba guda biyu a gaban
Ummie kana ya sauke ajiyar zuciya yace "Danejo ga kaYan tsaida maganar Auren
Rabi'atou nan iyayen BAMANGA sun kawo yanzunan.

Kafeshi da idanu Ummie tayi gabanta na dukan tara-tara, abu ɗaya ne ke dabaibaye da
zuciyarta shine tausayin Muzaffar wanda tasan ba lallai bane ya iya jure rashin
Rabe a taredashi ba. Amma kuma a zahiri se Ummie tayi murmushin irin na ɓoye
damuwar nan sannan tace "masha Allah ubangiji ya sanya alkhairi ya kumasa ayi damu,
amma Hamma wata nawa kasanya musu kafin Auren?

A taqaice Moddibo yace "sam ba watanni nasaka ba Danejo kwana biyu kawai na saka
jibi-jibin nan zan ɗaura mata Aure. Yana kaiwa nan ya miqe yabar gurin ba
tareda ya damu da irin kallom mamakin da ummie da Inna Laure kebinsa dashi ba yay
gaba abinsa

Rabe dake tsaye jikin ƙofar karan dake jingine da ɗakinta sam batasan sanda ta
sulale akan qafafunta zuciyarta na bugawa da mugun qarfi ba, Allah ya sani sam
bazata iya hana zuciyarta abinda takeso a wannan gabar ba ko kaɗan, sedai tasan
koda giyar wake tasha sam bazata iya bijirewa mahafinta akan muradinsa na Aurar da
ita ga Bamanga ba,

Komai da mafarinsa tasani sanin kanta Bamanga ba shine zaɓin Zuciyarta ba to amma
idan harta bijirewa wannan Auren tamkar ta kunyata mahaifinta ne, Aure ta da
Bamanga tamkar igiyar kabar da aka daɗe ana tufkata ne tunkafin tasan kanta, ma'ana
dai Aurene da iyayensu sukai alqawarin faurawa tun a ranar da aka haifeta don haka
dole ne tayi haquri da Bamanga a matsayin mijinda Qaddara ta zaɓa mata shi.

Daga Ummie har Inna laure babu wanda ya tanka akan lamarin hukuncin da Moddibon ya
zartar, dole tasa suka amince da hukuncinsa dukda cewar a zukatansu sunada ja akan
abinda yake shirin zartarwa akan Raben.

Tun daga Ranar Rabe ta ɗaura da zubar da hawaye gamida tilastawa kanta faɗawa a
qoramar tunanin zaratan mazan da suka shigo rayuwarta a baya, sosai ta rame tayi
wani irin duhu duk a kwana ɗaya kachal tamkar ba ita ba, ko abinci se Ummie ta
matsa mata kana take iya cinsa shima ba wani sosai take cin ba.

Tun'a daran jajiberen Aurenta da Bamanga Rabe ta gama saddaqarwa da kanta cewar
tabbas tayi rashi a rayuwarta irin rashinda bazata taɓa mayarda kamarsa ba, a
hankali take ɗaga qafarta harta iso bakin qofar bukkar da mamie ke kwana,
sunkuyawa tayi kana ta shiga cikin bukkar bakinta ɗauke da sallama, a zaune ta samu
Ummie wadda keshan fura se faman murmushi takeyi da alama video call takeyi itada
su Zainab da kuma Abie. Tana ganin shigowarta Ummie ta kashe wayar tareda maida
hankalinta ga Rabe tace " Dota na Amarya shigo mana kika tsaya kamar kuwa kinsan
yanzu nake shirin nabiki ɗaki akan maganar shirin bikin sekuma gashi kinzo da
kanki, yau insha Allah Adda Maryamu da yafendunki Gwaggoji duk yau zasu iso insha
Allah daga yolah.

Kanta a qasa tayi murmushi kawai ba tareda ta iya furta koda kalma guda ba, ko babu
komai har a ranta ta ɗanji sanyi dajin batun zuwan qanwar Mahaifiyarta da kuma
kakarta wadda ta haifi Mahaufiyarta wadda sike kirada (gwaggoji) ko babu komai
tasan zata ragewa kanta damuwa muddin ta tattauna matsalarta da wani

Kanta a qasa tana wasa da yatsun hannunta tace "Ummie ki bani aron wayarki zan
kirasu mom.
Shiru Ummie tayi a ranta tana mamakin yanda yarinyar kejin nauyinta sannan tayi
murmushi ta miqa mata wayar Ta karɓa tabar ɗakin tanajin wani irin sanyi na ratsa
zuciyarta, tana fita ɗakinta ta koma tareda buɗe qatuwar jakar da Edyan ya lafto
mata uwar siyayya lokacin daze dawo da ita gida tayi lokaci guda kuma ta zaro wani
qaramin card, qurama card ɗin idanu tayi zuciyarta na wani irin racing sannan ta
shiga danna numbers ɗin jikin katin a jikin wayar sannan ta kara a kunnenta tareda
lumshe idanunta tana jiran ya ɗauka.

Can ɓangaren wanda ta kira ɗin zaune yake cikin katafaren ofinshinsa wanda aka
qawata da kayan alatu na morewa rayuwa ya ɗora dogaren santala-santalan qafafunsa
duka biyun a saman table ɗin dake gabansa, a hankali ya ɗaga hannunsa na dama yana
me sassautawa kansa necktie ɗin dake ɗaure a wuyansa.

Qarar wayarsa ce ta katseshi wadda ke ajiye bisa gefansa a nitse yakai hannunsa ya
ɗauka tareda zubawa number dake kiran nasa tsimammun idanunsa kamar baze ɗauka ba
se kuma can ya ɗaga tareda karawa a kunnensa yay shiru ba tareda yace qala ba.

Daga ɓangarenta Ajiyar zuciya ta sauke me qarfin gaske sannan ta buɗe bakinta
wanda yayi mata nauyi tace "yaya Edyan nice mulaikha c.....!!! Se kuma ta fashe
mishi da wani irin kuka wanda yasa ba shiri Edyan ya miƙe tsaye cikin kiɗima gamida
tsagwaron tashin hankali yana faɗin "meya faru dake mulaikha ? Meyasa kike kuka
irin haka?

Edyan ya jefa mata waƴannan tambayoyin duk a lokaci guda, daqyar ta iya buɗe
bakinta tace "don Allah partner kazo I wanted to see you tomorrow plss.........!

Ajiyar zuciya ya sauke sannan ya gyara zamansa kamar tana gabansa yace "look
mulaikha don Allah ki ɗena kuka kinji babe, kin sani banason kukan ki sabida it
really hurts me so please don't cry again OK?

Ɗaga masa kanta tayi kamar yana gabanta lokaci kuda kuma tace "uhm. Murmushi yay
kaɗan sannan yace"not hmmm mulaikha na just promise me cewan bazaki sake kuka irin
haka ba kinji?

Bakinta ta buɗe a hankali tace "i promise!

"yauwa that's my girl bye. Ya faɗa yana me katse kiran ba tareda ya tsaya jin
abinda zatace ba.

Ƙurawa wayar manyan idanunta tayi tana kallon wayar kamar bazata dena ba, tana
riqe da wayar wani sabon kiran ya shigo wayar Ummie da sauri ta ɗauka ta kara a
kunnenta sabida duk a zatonta Edyan ɗinne ya sake kiranta a karona biyu.

Daga ɗaya bangaren zainab tace "Ummie gaskiya ya kamata ki dawo haka nan wllh
sabida bro Qurraty bashida lfy jiya ko office bai samu yaje ba, pls Ummie don Allah
ki dawo koke ze iya sanar dake abinda ke damunsa.

Sakin wayar Rabe tayi sabida tsabar bugawar da zuciyarta dayi da mugun qarfi loƙaci
guda kuma ta sulale qasa jiɓirrrr kamar zubewar gini............
Chubaɗo ✍️
[3/3, 5:40 PM] Chubado Mohd: ❄️❄️❄️❄️❄️❄️
❄️❄️❄️❄️❄️❄️
🐄🐄🐄🐄
🐄🐄🐄🐄
*BAFULATANA*
✨RETURN✨
🐄🐄🐄🐄
🐄🐄🐄🐄
❄️❄️❄️❄️❄️❄️
❄️❄️❄️❄️❄️❄️

Page:50

*_I Dedicate this special page for you SADIYA SIDI SA'ID (SIDIYA the writer of
GIDAN MISBAHU) na rantse da Allah tukuicin Qaunar da kikemin kyautar shafi guda na
littafin dana sadaukar miki yayi kaɗan ya zama tukwici a garki, amma nasan Ɗan
gidan gima shine ke halin girma duk inda akace akazo al'amarin ki na gado ne bana
taka haye ba, na daɗe ina cin karoda mutane daban-daban a rayuwata Amma wllh ban
taɓa karo da wadda ta qaunace ni bisa gaskiya da Amana kamar ke ba. I'm so proud of
you malamar FARSAFA kokuma in kiraki da kwalba uwar Alkhairi Don bazance Uwar
sharri ba 😂_*

*_MASU YIMIN ADDU'AR ALKHAIRI AKAN EXAM ƊIN DANAKE GABATARWA ALLAH UBANGIJI YA SAKA
DA ALKHAIRI KUMA YABAR ZUMUNCI❤️
_*

___✍️Sulalewar datayi zuwa qasa ne ya bawa hannunta damar danna kiran number Zainab
ba tareda tasan tayi hakan ba sabida tsabar tashin han kalin data samu kanta a
ciki, daga ɓangaren zainab murmushin qarfin hali ta saki kana tace "Ummien mu!!

Jin sunan data ambata ne yasa Muzaffar dake kwance bisa cinyar mom ya kaleta da
idanunsa waƴanda suka canza launi sabida halinda zuciyarsa ke ciki ba tareda ya iya
cewa komai ba ya miqa mata hannu alamar ta bashi wayar, ba musu ta zainab ta miqa
masa ya karɓa tareda kara wayar a gefan kunnensa yace " Ummiey na!

Wani irin bugawa Qirjinta yayi da qarfin gaske a lokacin data tsinkayi amon
muryarsa ta doki dodon kunnenta.

Wani irin zaro ido tayi se kawai ta saki wani irin kuka daga qasan maqoshinta
tareda sanya hannunta ɗaya ta rufe bakinta gam dashi, tabbas tasan tayi kewar
muryarsa kwatankwacin yanda zuciyarta ke bugawa a ko wace rama, haqiqa yau ta gama
tabbatarwa da kanta cewar numfashinta gabaɗayan sa yana fita ne da sirkin ɗigon
kewar muzaffar me tsananin gaske a cikinsa, haka kuma batajin cewar zata iya ɗauke
kanta daga barin tunaninsa koda kuwa ace badashi zata rayuwa ba a nan gaba!!!

Ajiyar zuciya muzaffar yaɗan sauke sannan yayi murmushi mara sauti yace "Ummie kada
ki damu wllh ba wani serious ciwo bane kawai rikicin Qurra ne so ki gama abinda
kikeyi a nitse kafin ki dawo. Ya faɗa yana katse kiran ba tareda yaji sautin
kukan nata ba ko kaɗan

Miqewa tayi jikinta a mace ta kaiwa Ummie wayarta sannan ta fito ta koma ɗaki ta
kwanta sabida wani irim juya mata da kanta keyi ta wani ɓangaren kuma ji take kamar
zuciyarta zata faso qirjinta ta fito.
*********

A kwana a tashi babu wuya a gurin Allah kamar yanda moddibo yayi alqawari hakan ne
kuwa ya kasance, don haka tun ana gobe ɗaurin Auren Rabe da Bamanga Edyan da mom
ɗinsa da kuma zeeyadah suka iso garin, tunda suka yanko hanyar Rugar zeeyadah da
Mom suka cika da ɗumbin mamakin yanda jama'ar garin suke Rayuwa ba tareda fargaba
ko tsoro ba, lallai bahaushe yayi gaskiya dayace "Allah ɗaya gari banban. Dukda
kasancewar mom Edyan cikakkiyar Bafulatar yolo hakan be hanata shiga mamakin irin
yanayin dajin da Raben ta fito ba, A haka motarsu ta iso tayi parking a gaban gidan
still suna qara jinjina lamarin a ransu , Suna tsayawa ba jimawa sega motar su
Abie ma ta iso tareda Driver ɗinsa da kuma wasu jibga-jibgan haɗaɗɗun jib baqaqe
wuluk se baza qyallin sabunta suke suna take masa baya, sannan suka fito daga cikin
motocin duk a lokaci guda.

Da sakin fuska gamida girmamawa Edyan ya isa ga Abie tareda rissinawa ya gaisheshi,
fara'ar dake kan fuskar Abie ce ta qaru a lokacin dayaga Edyan ɗin sannan ya amsa
masa da kulawa a haka suka antaya zuwa indasu Ummie ke tsaye suna jiran
qarasowarsu.

Sosai ummie tayi farin ciki da zuwan Matar C.p ɗin don har hakan ya gaza ɓoyuwa a
saman kyakkyawar fuskarta, hugging ɗin zeeyadah Ummie tayi tana Murmushi tace
"bansanki ba Edyan kawai na sani shima don yana zuwa gurina ne duk sanda yaje
india, nan dai sukai murmushi gabaɗayan su sannan suka antaya zuwa cikin gidan inda
bukkokinsu suke.

Sosai Ummie ta taka rawar gani wajen ganin ta cikawa su Mom Edyan da Zeeyadah
gabansu ta kayan qwalan da maqwalashe, kafin kace me tuni har Inna Laure ta dama
musu lafiyayan Fura da kuma nono wanda yaji Uban suga, sosai Zeeyadah ya buɗe
cikinta tasha furar kamar bazata dena ba sabida an jima ba'a gamu ba 😂

Se bayan ta gama cika cikinta ta kalli Ummie tace "Banga Amaryar tamu ba pls where
is she?

Hararar wasa Mom ta jefa mata tace "ja'ira se yanzu zaki tambayeta tunda kinci kin
qoshi ko? "no wllh mom ba haka bane tunda mukazo garin nan take raina kema ai
kinsan hakan. Zeeyadah ta faɗi hakan tana dariya

Edyan ne ya shigo ɗakin ɗauke da sallama hannunsa Rike da babban kwanon sha ya
kalli Ummie yace "Ummie Abie yace ki qra masa Suger a ciki. Ya faɗa yana miqa
mata kwanon yana murmushi

Karɓa tayi itama tana dariyar tace "hmmmmm nikam ban taɓa ganin mutum me son suger
kamar Abie ba ko tsoron shan zaqi bayayi. Ta faɗa tana karɓar kwanon tareda zuba
masa suger ɗin ta miqa masa ya karɓa ya fice daga ɗakin, yana fita zeeyadah ma ta
miqe tabi bayansa da sauri tace "ya Edyan wai ina ne ɗakin mulaikha ne ?

Murmushi ya sakin mata tareda nuna mata bukkar sannan yay gaba abinsa, da sauri
Zeeyadah ta nufi ɗakin cikeda zumuɗin ganin mulaikhanta bakinta ɗauke da sallama
ta shiga

A kwance ta sameta idanunta a lumshi bisa qaramar katifarta, da sauri zeeyadah ta


isa gareta tareda faɗawa jikinta tana dariya, buɗe lumsassun idanunta Rabe tayi
waƴanda sukai mata masifar nauyi akan zeeyada lokaci guda kuma ta miƙe zaune ta
rungumeta, kukan data daɗe tana dannewa ne ya samu nasarar kufce mata don hkaa ta
shiga rerawa a jikin Zeeyadan tamkar dama jira takeyi ta ganta

Ɗan buɗa idanunta Zeeyadah tayi cikeda damuwa ta zarota daga jikinta tana kallon
fuskarta wadda ta jiqe da hawaye tace " meyasa kike kuka irin haka Mulaikha shin
bakya tsoron kanki yazo yanayi miki ciwo? Koma dai wani abin ne yake damunki ne?
Hannunta tasa ta goge fuskarta sannan ta kama hannun zeeyadah tace "ina so naga
Partner yanzu pls!

Wayar hannun zeeyadah ta karɓa da sauri ta shiga kiran Edyan, bugu ɗaya ya ɗauka
tareda faɗin ya akai ? Duk a zatonsa zeeyadah ce

Bakinta na Rawa tace " i wanted to see you plssssssss!

Take qirjinsa ya wani irin buga wanda sam be shiryawa hakan ba, a hankali ya sauke
ajiyar zuciya yace "ok bt where are you nw?

Zan jiraka a bayan gida wurin shanu. Rabe ta faɗi hakan a taqaice

Katse wayar yayi tareda zubawa qasan gurin idanu sannan ya miqe ya fita yabarsu
Abie da moddibo sunata hira abinsu, jikisa a saluɓe haka ya isa gurin ya sameta a
tsaye ta sarqe hannayenta duka biyun a qirjinta tana jiran isowarsa.

Ya jima a tsayen sannan ya buɗe baki yace "kinaso ki faɗamin wani abun ne?
Hawayene suka zubo mata sannan tasa hannunta ta goge ba tareda ta kalleshi ba tace
" inaso na gaya maka abinda ya kamata ace ka sani ne patner, dukda cewar kusancinka
da muzaffar ya wuce akirashi da abota sedai a kira hakan da sunan ƴan'uwantaka,
partner Muzaffar yanada wata budurwa a Rayuwarsa wadda ya jima yana ɓoye abinda ke
ransa tsahon lokaci.

Ɗago idanunsa yayi cikeda matiqar kaɗuwa ya dubeta yace "wannan wace irin magana ce
kikeyi haka Mulaikha?

Ae haka maganar take Partner amm......." toni meyasa kike zaɓi da ki gayamin wannan
wannan maganar bayan kuma shida bakinsa be taɓa gayamin ba?

Hawayen daya zubo mata ta sake gogewa tace " wasu maganganun da wanda yake qaunarka
kawai zaka iyayinsu Yaya Edyan, musamman akan abinda ya shafi rayuwar ka!

Ni kawai abu ɗaya na sani shine wannan Auren daza a ɗaura min a gobe muddin na Bari
akayishi shine kuskure mafi girma da zan aikata a rayuwata, wllh partner banason
shi kaina gaba ɗaya ya gama kullewa banaso na aikata abinda ze taɓa kimar
mahaifina!!!!!!! Ta fadi hakan tana fashewa da wani irin kuka.

Kafeta kawai da idanu Edyan yayi a ranaa kuma yana aiyana wani al'amari wanda shi
kansa bazece ga matsayar daya samu a ransa ba, tabbas yasani har cikin zuciyarsa
yake qaunar Rabe so me tsananin gaske, to waishin ta ina ma ya kamata ya fara ne?

A hankali yake jan qafarsa harya bar kurin ba tareda ya rarrasheta ba, guri ya
samu daga can nesa da gidan ya zauna har yammacin al'muru ya fara ketowa, a
hankali yaji saukar hannun mutum a saman kafaɗunsa don haka ya ɗago da sauri yana
kallon wanda ya dafashin.

Moddibo ne tsaye bisa kansa yana murmushi yace "ai tun ɗazu nake cigiyar ka shine
Abou muzaffar yace min kanata nan wurin. Ya faɗi hakan yana zama daga gefan Edyan
ɗin, shiru ne ya ratsa gurin tsahon lokaci sannan moddibo ya dubeshi yace " na
rigada na gama gane wanda Rabi'atou take Qauna. Da sauri Edyan ya ɗago yana
kallonsa zeyi magana moddibo ya dakatar dashi ta hanyar cewa "Ba yanzu ba tukunna
zan baka damar magana amma fa har sena gama tawa tukunna.

Wanda takeso ɗin na zauna dashi a yanzu dukda cewar shiɗin be taɓa furta abinda ke
zuciyarsa akanta ga kowa ba, dukda cewar yasan hakan kurkurene me girman gaske amma
kuma yake qoqarin ya aikata ɗin, nariga na gama Fahimtar komai Edriss nariga na
gama gane wanda Rabi'atou take Qauna har cikin Ranta,, idan harna Aurar da ita ga
wanda bataso tabbas na cutar da ita mafi girman cutarwa, nasani damace ubangiji ya
bani a yau wadda zan iya gyara kuskuren danake qoqarin tabkawa a baya ta hanyar
turo min kai zuwa nan, koda wasa bazance Bamanga da Rabi'atou basu dace da juna ba
amma to ya muka iya da zannan abinda qaddara tazo mana dashi?

Zuciyata tana gayamin cewar kaine mutumin dayafi dacewa daya mallaki Rabi'atou.
Da sauri Edyan ya kama hannun moddibo lokaci guda kuma ya maida kallonsa ga
fuskarsa yace "aa baba sam be kamata kayi haka ba, kamata yayi ka zauna da
Rabi'atou kaji ra'ayinta akan Aurensu da bamanga muddin ta nuna batason haka toseka
sake bata wata damar a karo na biyu inyaso seta gaya maka waye zaɓin ranta da
bakinta!!

Da hka hirar tasu ta dasa Aya.

Ɓangaren su Mom Edyan da Ummie kuwa sosai suka kacame da hidimar dafe-dafe da kuma
sarrafa wasu abubuwan daza'a gabatar na al'adah, sosai mata suka cika gidan anata
shewa da kuma aikace-aikace kafin kuma gari ya waye a shaida ɗaurin Aure. Bayan
sallar Isha su Abie da Edyan da kuma gurds ɗinsa suka yada zango a farfajiyar qofar
gidan kafin lokacin kwanciya yayi, miƙewa moddibo yayi ya nufi bukkar Rabe da
sallama ɗauke a bakinsa ya ɗaga labulan dake saqale jikin bukkar, zaune suke ita
da zeeyadah tanata faman bata labarin school Rabe nata murmushi a haka ya qasa
shigowa ɗakin, cikeda girmamawa Zeeyadah ta gaisheshi sannan ta miqe a nitse tabar
ɗakin don ko ba'a faɗa mata ba tasan magana zayi da ita wadda take buqatar sirri.

Zeeyadah na fita ya nemi guri ya zauna daga ɗan gefanta kaɗan yana kallonta kimanin
wasu mintuna Sannan yay ajiyar numfashi yace" idan kinada matsala da wannan auren
sam karki ɓoye min kawai ki sanar dani insha Allah zaki sameni a matsayin uba me
adalci a gareki.

Matsowa tayi tareda kwantar da kanta bisa kafaɗunsa tace " aa baba sam banida
matsala da Auren bamanga sabida ya cancanci mallakata tsahon lokaci, don haka kawai
a ɗaura wllh har cikin raina na amince da hakan!!!!

Ta faɗa tana kallonsa tareda qoqarin mayar da kwallar dake qoqarin zubo mata, ko
kaɗan bataso ta nuna gazawarta kodan sabida ta tsirar da kimar mahaifinta a idanun
jama'ar garinsu, badan haka ba tabbas bataga dalilin dazesa tabar zaɓin ranta ta
ɗau wani ba.

Duk yanda moddibo yaso ya gano abinda take ɓoyewa a ranta ta hanyar kallon idanunta
sam ya kasa gano komai dole ya tabbatarwa da kansa cewar lallai har cikin ranta
takeson Auren Bamangan. Ƙarfe tara na dare dedai Kakar Rabe wadda ta haifi
mahaifiyarta sukazo daga Yolah tareda qannen mahaifiyarta guda biyu, sosai sukai
farin cikin da zuwan nasu misamman ma Rabe wadda har hakan ya gaza ɓoyuwa a tareda
ita a haka dai gidan ya dinga kacamewa da abikanan Arziqi tamkar a lokaci za'a
ɗaura mata Auren.

****

Washe gari tunda sanyin safiya jama'ar Rugar Arɗo suka gama hallara a bakin qofar
gidan moddibo wanda aka shimfiɗa manyan tabarmin kaba fa farfajiyar, Abie ne ya
fito sanye cikin wata rantsatsiyar gizna fara fat da ita wadda taji uban aiki irina
manyan masu kuɗin dake matiqar jida kansu, kallo ɗaya zakayiwa Abie ka fahimci
zallar kar da suke da muzaffar tamkar Abie yayi kaki, bayansa kuma moddibo ne shima
sanye cikin wata hamshaqiyar gizna farar tas da ita wadda tabawa kyawunsa damar
fitowa abinka da bafulatanin Asali wanda yay gadon kyau ba taka haye ba lol😂

A haka suka fito suka zazzauna bisa tabarmin inda Jama'ar ke zaune, can na hangi
Oga Edyan ya ɗau harami shima cikin wata shadda irinta mutanam sinigal brown wadda
tayi masifar masa kyau, sedai fuskarsa sam babu yalwar murmushi kamar yanda ya
saba. Nan moddibo ya shiga gaisawa da abokan arziqi har ya kammala amma shiru babu
labarin Isowar iyayen Ango, tun anasa ran isowarsu har mutane suka fara cire rai
da zuwan nasu nafa aka fara tsegumi qana nan maganganu suka fara tashi, can kamar
daga sama aka jiyo muryar Hashimu Maroqi yana faɗin "Sanarwa daga bakin uban Ango
Jauro ibrahimu Bawuro cewar sun janyen batun Auren Ɗansu Bamaga da kuma Rabi'atou
ɗiyaga Moddibo ɗan lamidon Arɗo bisa wani babban dalili da basu baiyana ba, fatan
malam moddibo ze gafarce su.

Take gaban moddibo yay wata irin faɗuwa lokaci guda kuma idanunsa suka ciko da
qwallar baqin ciki, yanzu shikenan Bamanga ya gama yiwa Rayuwar ɗiyarsa illah
sabida a tsarin al'adarsu muddin wata matsala ta gifta a ranar ɗaurin Aurenki har
takai ga an fasa ɗaura auren tofa har Abada bazaki taɓa yin aure ba a haka zaki
zauna har mutuwarki ta riskeki.

Kamar daga sama Ya tsikayi muryar Edyan a saman kunnensa yana faɗin , dama can
Mulaikha ba sa'ar Aurensa bace don haka ka koma ka sanar da qananan mutanen da Suka
turoka cewar a yau base anjima ba za'a shaida ɗaurin Auren Rabi'atou da wanda ya
dace da ita.

Edyan ya faɗi hakan yana me zaro bandir ɗin ƴam dubu-dubu Guda biyu daga aljihunsa
ya ajiye a gaban moddibo yace "Baba ina me nemawa kaina Aurenta idan har zaka bani,
lokaci guda kuma Abie ya matso dabda moddibo yace "ni nan zan zame masa wakili daze
karɓa masa Aurnta, cin qanqanin lokaci moddibo ya ɗago manyan idanunsa yana kallon
Abie cikin wani irin yanayi wanda yafi kamada na zallar kaɗuwa
yace"................

Sushmah ✍️
[3/3, 5:40 PM] Chubado Mohd: ❄️❄️❄️❄️❄️❄️
❄️❄️❄️❄️❄️❄️
🐄🐄🐄🐄
🐄🐄🐄🐄
*BAFULATANA*
✨RETURN✨
🐄🐄🐄🐄
🐄🐄🐄🐄
❄️❄️❄️❄️❄️❄️
❄️❄️❄️❄️❄️❄️

Page :51

*_WRITING BY: CHUBAƊO_*

____✍️"taya hakan zata kasance kuma Abdulwahab? Murmushi abie ya saki irin nasu
na dattijawa yace "karka damu Moddibo sam be kamata mutanan da aka tara sabida
ɗaurin Auren nan a bari su watse haka nan ba, ɗan jim yayi kaɗan sannan ya maida
kallonsa ga Edyan Yay masa murmushi se kuma ya kalli moddibo da malam iro wanda
sukai shiru suna nazarin abin a ransu, cikin mintunan da bazasu gaza 5 ba jama'ar
dake gurin suka shaiɗa ɗaurin Aurn Rabe da wani daban saɓanin Bamanga wanda
iyayensa suka janye Auren sabida wani dalili nasu na daban wanda har yanzu basu
firta ba.
Nan da nan aka shiga raba Goron ɗaurin Aure da kuma manyan alawori masu tsadar
gaske kamar dama an shiryawa abin, zanso team Edyan kuga yanda ango Edris yake
washw baki tamkar wanda akaiwa bisharada gidan Aljanna, a haka taro ya watse kowa
yana sambarka tun a yammacin Ranar iyayen Amarya da kuma gwaggwanninta sukai shiga
kimtsa amarya sabida gabatar da bikin al'ada kamar yanda suka saba, sedai duk
yanda Edyan yaso ya haɗu da ita sam abin ya gagara sabida an riga an keɓanceta za'a
gabatar mata da abinda suke kira da biddom, idan akace biddom ana nufin wankan
amaryar da fulanin daji keyiwar ɗiyarsu ne da zallar madarar shanu gamida wani
sinadari na musamman wanda ya kasance sirrin su ne musamman ta ɓangaren mallakar
miji da kuma inganta rayuwar Aurataiyarsu.

A lokacin dasu Ummie da mom sukaji da wanda aka ɗaura Auren sosai abin ya girgizasu
musamman ma Ummie, ita kuwa mom Edyan sosai hakan yayi mata daɗi tamkar dama abinda
take burin ya kasance ɗin kenan, a haka suka gabatar da bikin al'adar jikin Ummie a
matiqar sanyaye don harga Allah tana matiqar tausayawa muzaffar Ɗinta, to amma yata
iya tunda haka zanan qaddara yazo masa dashi.

A gurguje pls

Bayan an kammala bikin al'adar sosai Zeeyadah ta kaɗu da yanayin da Rabe ke ciki
sabida zallar damuwar dake cinta a ranta, gaba ɗaya duk ta gama ramewa a tsaye amma
sabida tsabar qarfin hali irin nata taqi bari wani yasan halinda zuciyarta take
ciki, babban abinda ke qara ɗaga mata hankali shine ta ina zata fara rayuwar da
Bamanga a matsayin mijin Aurenta? Sabida harga Allah bata san abinda ke
faruwa da lamarin Aurenta ba, Yafendunta Bintu ce ta shigo ɗakin da aka gama
kafata da murmushi akan fuskarta tace " Baddo.

Kuka Rabe ta sakin mata lokaci guda kuma ta faɗa jikinta tana rerawa, kaf cikinsu
babu wanda yay yunqurin hanata kokuma rarrashinta badan komai ba sedan ta samu
peace of mind, seda tai me isarta sannan tasa tafukan hannunta tana share hawayen
kamar ba itace ta gama gurzar kuka a jikin Yafendu Bintu ba, Inna Laure ce ta
shigo ɗakin tana jan qafa da qyar hannunta ɗauke da wata qaramar qwarya wadda akai
mata jiqo na musamman ta miƙawa yafendu Binto tace " maza ki bata ta shanye zuwa
anjima Ammi Ruqatu zata kawo ɗayan se'a jiqa kafin wayewar garin gobe masu ɗaukar
Amarya suzo.

Murmushin Yafendu Bintu tayi tace "Ae lallai Laure kin dage sekin haɗa ƴar nan taki
Allah dai ya saka miki da alkhairi bisa ɗawainiyar da kikayi, Allah kuma ya rabaki
da cikin jikinki lfy.

Kasa magana Inna laure tayi sabida wata qwalla data taso ta kwanta a saman qwayar
idaninta, nan da nan ciwon dake cinta a ranta ya dawo mata sabo fill a lokacin data
tuna cikin su waye a jikinta , da hanzari ta juya ta fice tana me zubarda kwallar
baƙin ciki da nadama.

A haka dai abubuwa suka dunga tafiya masu daɗi da marasa daɗi Har garin Allah ya
waye Kusan a tare su mom suka fara shirin komawa Abuja, gabaɗaya bakin Edyan ya
gaza rufuwa sabidaTarin farin cikin Da yake ciki

Qarfe shidan safe daidai Aka kimtsata cikin wani Blue ɗin saqi wanda yay masifar
karɓar jikinta, gabaɗaya fuskarta an zane mata ita da wani farin fenti gamida
ratsin yallow, kallo ɗaya zakai mata ka tabbatarwa da kanka cewar kaka cikakkiyar
Asalin BAFULATANAR DAJI wadda ta amsa sunanta ƴar fillon gaske babu sirki. Ɗakin
Moddibo aka fara kaita, nan ya shiga yi mata nasiha me ratsa jiki wadda a zuciyarta
takejinta tamkar nasihar bankwana yake mata, sosai take kuka daga cikin mayafin
saqin da aka rufe mata kanta dashi, ba zato ba tsammani ta miqe ta isa ga mahaifin
nata ta rungumeshi tamau tana gurzar kuka kamar bazata dena ba. Daqyar suka
ɓanɓareta suka fita da ita zuwa bukkar inna Laure, nan ma ba qaramin kuka Rabe
tayi ba hakama Ɓangaren Lauren Itama, nan dai laure ta roqi yafiyar mahainiyar
Allah Rabe, duk yanda taso ta miqe ta isa gareta kasawa tayi sabida nauyin cikin
dake jikinta, har gabanta Rabe ta isa ta durqusa daidai yanda zata iya rungumarta
tace "dukda cewar kin raine ni bada soyayya ba wllh kodedai da rana ɗaya bantaɓa
jin cewar na tsaneki ba, komai ya fito daga bakinki akaina idan kika furtashi ban
taɓa sashi a raina ba balle harya dameni sabida nasan komai na duniya yanada limit,
don haka kisa a ranki cewar kema matsayin uwa kike a gareni na yafe Miki har
Abadah!!!!!!

Ta faɗa tana fashewa da kuka.

Gaba ɗaya Laure ta kasa magana sabida kukan datakeyi a haka aka fita da Rabe zuwaga
kakarta wato Mahaifiyar Babar ta, nan ma nasiha sosai Gwaggoji tayi mata me ratsa
jiki akan Rayuwar duniya da kuma mutanan dazatai Rayuwa dasu waƴanda suka kasance a
kwai banbanci me tarin yawa a ɗabi'unsu da kuma irin nata, nan dai Rabe ta Fahimci
Auren waye a kanta.

Ko kaɗan batai baqin ciki dajin wanda ta Aura ba abu ɗaya kawai ta sani shine komai
Muqaddari ne daga Allah, haka kuma ba komai muke so a rayuwa muke samu ba. Duk inda
miji na gari me tattalin matarsa yakai wllh tasan Edyan ya wuce haka shiyasa
bazata taɓa baƙin ciki da Aurensa ba indai har ta cika ƴar Halak kuma wadda tasan
halacci.

Duk irin sabon dake tsakanin moddibo da ɗiyarsa sam hakan besa ya zubar da hawaye
ba don haka har suka fito da Abie idanunsa rass kamar baya kewarta, hannun Abie ya
kama yana kallon tsakiyar idanunsa yace "zan roqeka wata alfarma Alhaji tareda
yaqini da sanya ran cewar zakayi min ita.

Da kulawa Abie ke kallonsa yace "kafi qarfin haka a gurina wllh kawai ka faɗi me
kakeso wllh zanyi maka shi.

Murmushi moddibo yayi wanda ya baiyana dattijantakarsa yace "so nake da zarar kun
isa inda zakuje don Allah karkubar Rabi'atou ta kwana a wani gida wanda bana
mijinta ba.

Da kulawa Abie yace "insha Allah zan cika maka wannan alqawari naka kuma nida kaina
zan kaita har ɗakinta ba tareda na fari an tsaya gabatar da wata bidi'a ba.

A haka ummie ta fito jiki a mace sukai sallama da kowa dake gurin suka shiga
motocinsu, a wannan halin babu abinda Ummie ke tunani kamar gudan jinin ɗanta
Muzaffar wanda tasan wajibi ne ya shiga gagarumin tashin hankali idan har ya samu
wannan labarin marar daɗin ji a kunne.

A haka suka isah Airport, bayan zuwansu da minti 15 jirginsu ya ɗaga zuwa birnin
taraiya, jirginsu na sauka iyalan C.p suka tarar da manyan motoci na jiran
isowarsu, nan dai sukai Sallama da Mom Edyan da Ummie kowa yayta kansa akan cewar
insha Allah qarfe 4pm zasuzo ɗaukar amaryarsu. Sam ba haka Edyan yaso ba yaso ace
yay gabada matarsa amma kuma sam besamu damar hakan ba.

*****

Ɓangaren Muzaffar kuwa tun bayan lafawar da ciwon da kansa ke masa ya koma bakin
aikinsa, duk irn zafinda zuciyarsa keyi sam hakan besa ya baiyanawa Mom da Fadilah
Damuwarsa ba, Baba Hajara ce kawai tasan Halinda yake ciki sabida irin sonda take
masa, dukda kasancewarta me aiki a gidansu shi sam ba'a hakan yake kallonta ba
kallon kakarsa yake mata kuma wadda yake Qauna.

Zaune yake a Office se faman danna system yake amma sam hankalinsa baya taredashi,
haka kawai yakejin gabansa na faɗuwa wanda gabaɗaya ya rasa dalilin hakan, a haka
ya mike jikinsa a mukun mace yabar office ɗin zuwa gida.

Ɓan garen Edyan kuwa yana zuwa gida wani sabon uban wanka ya ɗauka cikin wata
shaiɗaniyar shadda milk colour wadda kera baza uban yararin tsada da maiqo, fakar
idon mom yay ya ɗau motarsa ya nufi gidansu Muzaffar don ganin Amaryarsa sabida
bayajin cewar ze iya jurar har zuwa Lokacin dazasu kawo masa ita.

Parking yayina tsanaki ya sakko yana qawata fuskarsa da wani hamshaqin murmushi, a
nitse ya fara takawa harya isa part ɗin muzaffar don duk a tunaninsa yana ciki, a
katafaren perlourn Aminin nasa yayiwa kansa masauki tareda zaro wayarsa yana
qoqarin kiran muzaffar ɗin.

A nitse gurds ɗinsa suka parker motar ya fito batareda ya tsaya jiran su buɗe masa
ba ya nufi part ɗinsa, duk irin qarar da wayarsa keyi sam bebi takanta ba harya
shiga parlourn

Tsayawa yayi cak yanabinsa da kallo don beyi tsammanin ganinsa ba sam a wannan
lokacin, murmushin qarfin hali ya sakar masa tareda qarasawa gareshi fuskarsa ɗauke
da mamaki yace " uhmmm looking so masha Allah kamar wani sabon ango.
Muzaffar ya faɗi hakan yana wani male baki cikeda tsokana

Dariya Edyan yayi yace "ae mana ai bakayi makuwa ba pls go and take Shower kazo ka
rakani ɗakin matata.

Ɗan buɗe manyan idanunsa muzaffar yayi yace "your not serious. "wllh da gaske
nake inada ɗakin matana zaka rakani an ɗaura min Aurn bazata yau ɗinnan ba tareda
na shiyawa hakan ba amma idan kana tantama akai ka tambayi Abie ze gaya maka.

Ɗan jim kaɗan muzaffar yayi amma dayake yasan Edyan ɗin be taɓayi masa qarya ba
yasa har a ransa ya amince da abinda ya faɗa ɗin. Tilasta masa Edyan Yayi har seda
yay wanka kuma ya buɗe drower ɗinsa ya ɗakko masa wata milk ɗin shadda sak ta
jikinsa ya bashi ya saka sannan ya ɗora hula tareda ɗaura wani shaiɗanin agogon
rolex wanda ya haska tsintsiyar hannunsa, take ya baiyana a Cikakken matashin ɗan
kasuwar nan meji da nairah wati C.e.o of zafar Enterprises

A haka suka fito harabar gidan se baza qamshi suke, yayi mamaki sosai dayajiyo
hayaniya hirar mutanen gidan a ɓangaren Ummie, don haka kai rsaye can suka fara
nufa, da sallama suka shiga falon buskarsa babu yabo babu fallasa, Abie ummie mom
Fadilah Zainab kai harma da baba hajara duk suna zaune a falon except Amaryar Rabe.

Kafesu da idanu gabaɗaya jama'ar dake falon sukayi a nitse suke takowa har suka
shigo falon suka zauna babu wanda yace "dasu qala har sukasha jinin jikinsu,
kallon ummie Muzaffar yayi yace " Ummie sannunku da dawowa ya hanyar?

Murmushi tayi tace "lfy lau son ya jikinta?

Da kulawa ya amsa amma kuma bisa ga mamakinsa babu fara'a kota ɗigo a saman fuskar
mom, kallonsu Baba hajarah tayi tace "Edirisa Ashe kuma ka ɗauka Aure, to ubangiji
ya sanya alkhairi.

Sosa kai Edyan yayi cikeda jin kunya. Muzaffar zeyi magana kenan Abie yace "oya ku
tashi muje, ba musu suka miqe sukabi bayansa.

Parking space direct Abie ya nufa suna biye dashi, wata baqar bugati suka nufa Abie
ya bude bayan motar ya shiga sannan Edyan ma ya shiga muzaffar kuma Ya shiga baya
Divern yaja motar zuwa cikin can saman layinsu kaɗan, tun kafin su isa inda
zasuje abie yay dailing wata number be jima yana magana ba ya katse, a gaban wani
tanfatsetsen gida na gani na faɗa suka tsaya sannan Abie ya matsa wani qaramin
remote take get ɗin ya buɗe suka kunna kai zuwa cikin gidan.

Parking sukai a haɗaɗɗen parking space ɗin dake gurin sannan suka fito gabaɗayansu
amma banda driver ɗin, cikin gidan suka tasarwa kowa da abinda yake saqawa a
cikin ransa daga muzaffar ɗin har Edyan, a haka suka shiga perlourn da sallama
take wani qamshi na musamman ya daki hancinan su, wani irin lumshe idanu sukai duka
su biyun

A gurguje pls

Fadar irin tsara yanayin falon a gareni abu ne mawuyaci, don hkaa kawai kuyi
hasashen haɗuwar gidan da kanku, zama abie yayai lokaci guda kuma ya ɗago yana
kallon muzaffar yace "haqiqa nasan abinda zan sanar dakai a yanzu dole ne ya ɗaga
maka hankali muzaffar , amma kuma idan kayi haquri da irin hukuncin dana zartar a
kanka na tabbata kaima zuriyarka da zaka haifa nan gaba wajibine suma suyi maka
biyayya kamar yanda nakesa ran cewar zakayi min yanzu, na zartar da wani hukunci
akanka wanda nake da tabbacin cewar idan har kayimin biyayya akansa zaka samu
sakamako me girma a gurin Allah. Haka kuma rayuwarka zatai albarka sakamakon
biyayyar dakayi min..

Ɗagowa yay da manyan idanunsa yana kallon Abie wanda shima ɗin shi yake kallo yace
"bt abie wannan wani irin abu ne haka Dayasa kake min wannan dogon jawabin?

"Aure na ɗaura maka muzaffar batareda sanin ka ba Bayan an kammala ɗaura Auren
Edriss!! Abie ya faɗi hakan a taqaice

Gabansa ne yay wani irin faɗuwa a lokacin dayaji abinda Abie ɗin ke faɗa, lokaci
guda kuma yaji kansa ya wani irin sara masa

Ajiyar zuciya Abie ya sauke me ɗan nauyi sannan yace "wannan abinda na zartar a
gareka iko ne dane jin cewar inadashi akanka, haka kuma nan gidan ka ne daga yau
kar in sake ganin qafarka a gidana ba tareda wani babban dalili ba har tsahon sati
guda, Sannan kuma ban amince ka cutar musu da ƴa ba don kawai tana qaunarka wajibi
ne ka kyautata mata sabida ita ɗin amanarka ce, muddin ka zalinceta dedai da ɗigon
qwayar zarra bazan taɓa yafe maka ba.....

Abie ya faɗi hakan yana miƙewa daga inda yake ya kalli Edyan yace "muje in kai maka
matarka kamar yanda nayiwa mahaifinta alqawari. Be jira cewarsa ba yay gaba Edyan
na take masa baya suka bar Muzaffar zaune sabida tsabar tashin hankalin dayake
ciki.

Ya jima a zaune yana tufka da warwara gefe guda kuma ga wani masifar ciwo da kansa
ke masa, miqewa yayi a hankali zuciyarsa na suya ya nufi wani ɓangare dgaa
hannunsa na dama wanda ya tabbatar Da kansa cewar A nan ɗakuna gidan suke, qofofi
ya gani guda biyu duk suna facing juna tsaki yaɗan ja kaɗan don harga Allah beyaso
ya buɗe wanda maiyar yarinyar da aka liqa masa take.

A hankali ya isa ga ɗaya qofar wadda tafi kusa dashi ya kara kunnensa kimanin ƴan
mintuna sannan ya ɗauke da sauri sabida shashsheqar kukan dayaji, tsaki yayi
sannan yabar gurin da sauri zuwa ɗaya ɗakin ya shige abinsa, bin ɗakin ya dingayi
da kallo sannan ya hau buɗe drowers na ɗakin yana bin kayan da aka zuba a ciki da
kallo kamar dama shiya zaɓo abinsa.

Toilet ya shiga ya sakarwa kansa ruwa kimanin tsahon lokaci sannan yay wanka tareda
ɗaura al'awalar sallar isha ya fito ɗaure da towel ba abinda ya shafawa jikinsa a
ranar duk son qyaleqyalensa, wasu kayan Baccu ya ɗakko qirar Pj-mas Ya saka
jikinsa Sannan ya tada sallah abinsa, ya daɗe yana addu'a bayan ya idar sannan ya
miqe ya kashe fitilar data gauraye ɗakin ya haye kan makeken royal bed din dake
ɗakin.

Kamar daga sama ya dinga jin shasheqar Kuka kamar a ɗakin akeyi, duk yanda yaso
yay bacci kasawa yayi sabida sautin kukanta ya gama cika masa ciki da takaicinta.
Agogon dake manne a jikin gadon ya kalla yaga har 12 tayi ne yasa yaja wani uban
tsaki ya miqe a fusace ya nufi ɗakinta, tura qofar yayi lokaci guda kuma ya fara
bin ko wace kusurwa ta ɗakin da kallo har idonsa ya sauka akan dogayen zarazaran
yatsun Qafarta, kwance take kan makeken gadon dake ɗakin ta bawa ƙofar shigowa
ɗakin baya babu abinda take se kuka wanda har hakan ya haifar mata da dashwar
murya, jikinsa ne yay mugun sanyi daya tunada maganar Abie don haka a ɗaqile kamar
an masa dole yace "malama ba kuka zakizo kisani a gaba kinayi min ba, dama tunda
kika Auri irina ai kinsan me kika Aura ki tashi ki shiga toilet kiyo alwala ki
sameni a ɗakina muyi sallah.

Ya faɗa kamar wanda akayima dole, juyawa yayi ya fice seda ta tabbatar da fitarsa
sannan ta miƙe a hankali ta shiga toilet don cika umarninsa, duk irin yanda taji
zafin kalamansa besa taqi bin umarninsa ba ta jima a banɗakin sannan ta fito ta
ɗauki qaton mayafinta da aka kawota dashi me launin Royal blue ta fita zuwa falon
kanta a qasa.

Tsaye ta sameshi saman dadduma ya wani haɗe rai kamar yaga mala'ikan mutuwa, ko
kallonta beyiba ya daidata tsaiwarsa bisa daddaumar ya tada sallarsa, itama
tsayawa tayi a bayansa sannan ta kabbara sallar basu jima ba suka idar a ranta tana
me tausayin makomar ta.

Ya jika yana tasbihinsa ba tareda ya juyo ba harya fara jiyo hammarta alamar
tanajin bacci sannan ya juyo gareta yana wani male baki kamar yaga kashi yace " ki
buɗe fuskarki malama zan miki tambayoyi akan abinda ya shafi addini!

Gabanta ne yay wata irin faduwa a lokacin data tsinkayi Amon muryarsa a cikin dodon
kunnenta, da wani irik mugun sauri ta yaye mayafin saqin dake jikinta hannke yay
daidai da saukar idanunsu cikin na juna!!!!!

Bakinsu na rawa suke kallon juna ba tareda sun samu zarafin iya futa komai ba
Muzaffar ya wani irin fuzgota Ta matso dabdashi, nan da nan jikinsa Ya ɗau rawa
daqyar ya iya buɗar baki yace "m....m....my...fu...fu....fulani girl!!!!!!!!

Comment
Nd
Share

Don't forget to vote on whatpad pls

Sushmah✍️
[3/3, 5:40 PM] Chubado Mohd: ❄️❄️❄️❄️❄️❄️
❄️❄️❄️❄️❄️❄️
🐄🐄🐄🐄
🐄🐄🐄🐄
*BAFULATANA*
✨RETURN✨
🐄🐄🐄🐄
🐄🐄🐄🐄
❄️❄️❄️❄️❄️❄️
❄️❄️❄️❄️❄️❄️

Page:52

Writing by: chubaɗo✍️

🔚🔚🔚🔚🔚🔚🔚🔚🔚🔚🔚🔚

____✍️Kafeshi tayi da manyan idanunta lokaci guda kuma ta faɗa jikinsa tana faɗin "
Alhamdulillahillazi bini'imatihi tatimussalihata se kuma ta saki kukan daya taso
mata. Wani irin farin ciki ne ke kwarara a saman zuciyarta wanda bakinta da gangar
jikinta sunyi kaɗan su iya Expressing ɗin irin mode ɗin datake ciki, a ɓangarensa
shima hakanne don haka ya sake qanqameta cikin faffaɗan qirjinsa wanda yayi mata
masauki dashi.

Zare jikinsa yayi daga nata tareda saita goshinsa Deda danata har hancinsu na gugar
na juna wanda hakan ya haifar musu da Sarqewar numafashi me ɗauke da wani sirrin
magana ɗisu A cikinsa, da hanzari ya zare jikinsa daga nata Ya nufi daddumar da
suka idar da Sallah ya fuskanci gabas donyin sujudu shukur duk a sanadin mallakar
zaɓin ransa dayayi a matsayin matar Aurensa, ya jima a sujjadar sannan ya ɗago
Tareda zuba mata tsimammun idanunsa waƴanda ke cike taf da zallar sonta gamida
zazzafar Qaunar ta.

Rasa inda ze tsoma ransa yayi sabida tsabar Farin cikin dayake ciki, babu abinda
yake maimaitawa a ransa se Alhamdulillah inda wani ɓangare na zuciyarsa ya dinga
sufawa iyayensu Addu'ar alkhairi wadda ta haɗa da yi musu fatan liɗifin duniya da
kuma na lahira. Ɗagowa tayi tana son ta saci kallon handsom face ɗinsa aiko caraf
idanunsu suka sarqe cikin na juna, Kashe mata ido ɗaya yayi da sauri ta sauke
idonta qasa don bazata iya jura ba

mikewa yayi zuwa kitchine Donya sama mata abinda zata sa a cikinta, Bin ko Wace
kusurwa Dake kitchine ɗin ya dingayi da kallo kamar me neman wani abu, wata
qatuwar leda ya gani fara A ajiye bisa kan sink direct ya nufeta ya fara buɗewa
don ganin abinda ke ciki, da wasu manyan daqwalen kaji yaci karo se tiriri Da baza
qamshi sukeyi sunji uban kayan haɗi wanda yafi kamada na musamman, ɗayar ledar kuma
manyan fresh milk ne a ciki Na qatuwar roba guda biyu masu madaidai cin sanyi

Flet ya ɗauka meɗan girma ya saka kazar Guda ɗaya a ciki tareda glass cup guda biyu
se kuma sansanyar fresh milk ɗin itama daga gefen farantin ya fita xuwa falo, a
inda ya barta a nan Ya dawo ya sameta kanta a qasa.

murmushi ya sakin mata cikeda shauqin sonta ya Ajiye flet ɗin tareda janyota
jikinsa cikeda tattali Ganida zazzafar qaunar ta yace "are you hungry?

Nodding kanta kawai tayi sabida wani abu datakeji yana wani irin taso mata a
sakamakon haɗuwar da jikinsu yayi dana juna, a nitse ya zuro ɗaya hannunsa na dama
Ta bayanta ya janye mayafin Saqin dake jikinta wanda yake ganin tamkar yana shiga
rayuwarsa ne ta hanyar zama hijabi a tsakankinsa da kyakkyawar fuskarta da tasa,
Nan take bakin gashinta wanda yaji uban gyara ya baiyana a gareshi se baza wani
tattausan qamshi yakeyi.

Wani irin yanayi ne ya baqunci gaba ɗaya sassan gabobin halittar dake jikinsa take
yanayin ya haifar masa da wata irin gagarumar kasala Wadda ke ɗauke da zallar
muradin, so gently ya fara feeding ɗinta tana ci shima yana ci har suka qoshi
Dukda cewar a takure takejin kanta sabida wasu qananun abubuwan dake gudana a
tsakanin su, kayan da suka gamaci ya tattara sannan ya miqe ya kai Su kitchine ya
dawo ya kama hannunta suka nufi bedroom ɗinsa saɓanin nata

Be dire ko ina da ita ba se Cikin katafaren toilet Ɗinsa ya zaunar da ita bisa
wata qaya taccen wani abu wanda yafi kamada kujera amma kuma A zahiri ba kujerar
bace, sabon expensive maclean ɗin dake saqale ya ɗaukko tareda sabon brush ya
nufota ya fara Nannaɗe mata rigar dake jikinta Don gudun karya jiqa mata jikinta,
take fararan santala-santalan cinyoyinta suka baiyana gareshi ba tareda wani
shamaki ba, zuciyarsa ce ta amsa da qarfin gaske take jinin jikinsa ya fara tafasa
kamar wanda ake jonawa lantarki, a daddafe yay mata brush ɗin cikeda zallar nuna
kulawarsa gareta harya gama mata shima yayi nashi, ko kaɗan bata kawo komai a ranta
gameda shi ba itadai kawai ta miqawa Allah lamarinta ne tunda tasan baze taɓa
cutar da ita ba, tsinkayar muryarsa tayi a tsakiyar kunnenta Cikin wani irin sauti
wanda ya kasance baqo a gareta yana faɗin "do you want to Bath?

Da wani irin sauri ta ɗago tana kallonsa se kuma tayin saurin sauke idanunta Qasa
aa hankali cikin sanyinta tace " no

Kama Hannunta yay suka fice daga toilet ɗin tareda zaunar da ita bisa dogayen laps
ɗinsa , a hankali yake binta da kallo tun daga kan yatsun hannunta har zuwa kan
dukiyar fulaninta, sosai yaji wani irin abu nabin jinin jikinsa lokaci guda kuma
yaji tamkar tana fuzgar zuciyarsa zuwa gareta Ne, Se'a lokacin ya samu zarafin qare
mata kallo sanye take cikin wata haɗaɗɗiyar doguwar riga less fari me Yarfen blue a
jikinsa wanda ya kasance me taushin gaske Sosai rigar ta mugun kmata daga saman
qirjinta gashin kanta gaba ɗaya a waje yake se wani uban light make-up da ummi
tasa akayi mata tun bayan zuwansu garin Me shegen kyau, Gabaɗaya a takure takejin
kanta musamman yanda taji mazaunanta akan Abinsa lakadan ba ajalan ba 😂

nasihar da ummie tayi mata Ɗazu ce ta fara dawo mata cikin kanta tamkar a lokacin
takeyi mata ita, babban abinda yafi komai tsaya mata a rai shine abinda mom Edyan
ta dinga gaya mata Tun a cikin jirgi ne akan zamanta kewar rayuwar Aure da kuma
abinda shi kansa Auren ya qunsa, ta gargaɗeta sosai akan cewar karta taɓa bari
tayiwa mijinta gaddama akan komi koda kuwa tanajin zafin abinda yake gudanarwa a
gareta ne. Lallai ta zama me biyayya a gareshi tareda karɓar duk wata larura tasa

A hankali taji saukar tattausan red lips ɗinsa a saman nata wanda hakan yasa ta
dawo daga duniyar tunanin data afka, wani irin kissing yake mata tamkar ze cinyeta
ɗanya nan da nan kuwa ya fara birkita mata lissafi, bagon yanayin data samu kanta a
ciki ne ya haifar mata da rawar jiki tamkar wadda ake kaɗawa gangin farauta😂😂

Shi kansa Muzaffar ɗin kwatankwacin yanayin datake ciki a wannan yanayin a gareshi
ma hakan take, iya lips ɗinta kawai yake kissing amma ji yake tamkar an tsomashi a
cikin wata qoramar nutsuwa ne don haka gogan naku ya qara qaimi😂

Cikeda qwarewa gamida salonsa dake birkita mata lissafi Yay amfani harya rabata
da rigar dake jikinta zuwa faffaɗan qugunta take dukiyar fulaninta ta baiyana
cikin wata milk Ɗin breziya shara2 Wadda tai masifan mata kyau tamkar dama dan ita
akayi ta, cikin yanayi na fitar haiyaci ya ɓalle wuk ɗin brar tata nan da nan
abubuwan nata suka baiyana ra'ayil aini a gareshi Batareda da wani hijabi a
tsakaninsa dasu ba, yayi mamaki qwarai dayaga irin girman tagomashin alkhairin da
qirjin nata ke ɗauke dashi, koda wasa be taɓa zaton girmansu yakai haka ba a
hankali ya sauke lumsassun idanunsa a fuskarta wadda ta lumshe idanunta tana karɓar
saqwannin nasa cikin sauqi, suking boobs ɗiɓta ya shigayi kamar he's life depends
on it har seda ta fara jinn zafine ta sakin masa kuka sannan ya sarara mata.

A wannan dare dai gabaɗaya muzaffar kasa controlling kansa yayi har seda ya ratsa
ta Tsakiyar Majalisar ɗinkin duniyar BAFULATANAR DAJIN tasa 😂

A wannan dare haukata muzaffar ne kawai Rabe batayi ba, babban abin mamakin ma
shine duk girman dayake dashi Gamida cikar zatinsa tsaf ta iya ɗauke Larurarsa ta
tsahon shekaru 35 kamar ba yarinya Ƴar shekaru 18 ba, Tasha wahala sosai a
hannunsa amma kuma sam bata nuna gajiyawarta a kai ba har seda ya gama samun
nutsuwa da ita, tayi kuka sosi harta godewa Allah tun hawayen na zubo mata harya
kasance hawayen ya dena fitowa sabida Azabar datakeji a qasanta

lokacin da komai ya lafa ne ya dubeta Yaga irin halin daya sanyata a ciki se kawai
ya fashe mata da kuka Yana me qanqameta a saman qirjinsa sabida tsabar tausayinta
dayay masa dirar mikiya, babu abinda yake iya furtasa se kalmar haquri. Albarka ya
dinga sanya mata tareda kaf wani Dangi nata Dake cikin wannan duniya, kuka
takeyi sosai marar sauti sabida tsaɓar Azabar datasha a hannun sadaukin nata sedai
kokaɗan bataji haushinsa ba sema alfahari datake dashi a can qasan zuciyarta.

*******
A gurguje pls sabida qarancin lokaci

A haka rayuwa ta dinga tafiyar musu cikin aminci da kuma Qaunar juna Marar
misaltuwa kullum yana manne da ita kamar ze maida ita ciki sabida so, bayan
faruwar Auren muzaffar da kwana 2 ne suka Shirya shida ita ita zuwa gaida su Abie,
tun da sanyin safiya suka gama shiri wajen qarfe 11am, inda ta shiya cikin wata
baqar jallabiya me yawar stones wadda tayi mugun karɓarta kasancewarta fara sol da
ita. Shigo muzaffar sanye yake cikin wani farin yadi sol dashi wanda yay masa ɗas
a jikinsa a haka suka iso parking space ɗin hannunsu sarqe dana juna.

Buɗe mata qofar motar yayi ta shiga sannan ya zagaya ya shiga driver Sit yaja motar
suka nufi gidansu kasancewar basu da nisa sosai ne gidan suka iso cikin sauqi,
buɗewa get ɗin yayi suka kunna kai ciki ya samu guri yay parking

Koda suka fito hannunta yake qoqarin kamawa amma fir taqi yarda dole tasa ya
qyaleta yay gaba ita kuma tana take masa baya, part ɗin mom suka fara shiga inda
suka sameta itada Fadilah sunacin kwaɗon zogale, washe baki mom tayi ta miqe tsaye
tana faɗin oyoyo my doter.

Durqusawa Rabe tayi cikin gurɓatacciyar hausarta ta fara gaida mom Fadilah kuwa
dariya ta dingayi tana kallon muzaffar cikeda tsokana tace "ooooo yaya ka mallaki
zaɓin ran naka yanzu shikenan no more headaches again ko?

Hararar wasa yayi mata sukasa dariya gabaɗaya, kallon mom yayi yace "wai Ina
Qurraty ne?

Dariya Fadilah tayi tace "young bride zakace tana gidan angonta ai Allah sarki
sisina sarkin rigima. Gabaɗaya kan muzaffar ɗaurewa yayi yana shirin magana kenan
mom ta katseshi tace "oya muje part ɗin Ummie Abie nason ganin mu Gabaɗaya,
ɗunguma sukai zuwa part ɗin Ummie nan suka tarar da Edyan a Nan shida Amaryarsa
sun hallara.

A lokacin da suka shigo falon hannun Edyan a riqe yake cikin nata dukda cewar ita
ɗin wata masifar kunya ce tayi mata dirar mikiya a lokacin da muzaffar Suka shigo
falon shida Fulanin sa, Da sauri ta janye hannunta daga cikin na Edyan ɗin don kar
wani ma ya gansu

Ɗan buɗe manyan idanunsa yayi ya dubesu da zallar mamaki bt still ya kasa magana.
Nan da nan idansu ya sarqe cikin na juna da Zainab wadda Ke zaune a gefan Edyan
tafi uban wani dakakken less yace "Yana ganku a nan kukuma?

Murmushi Edyan ya saki ya dubeshi yace "canji da zanan qaddarar muce Allah ya
rubuta mana ita a guri Ɗaya kamar yanda ya rubuta taku Qaddarar kaida Rabi'atou!

Haqiqa na girgiza sosai a lokacin Dana Gane kana ɓoyemin gaskiyar abinda ke ranka
akan Rabi'atou amma kuma dukda hakan na fahimci irin sonda kake mata Kwance a
tsakiyar kwayar idanunka, Mun zaɓi Muyi maka hakanne ta hanyar cike gurbin daya
rage mana a tsakanin Amintakar mu Nida kai kuma gashi nayi nasarar Yin hakan,
Edyan ya faɗi hakan yana murmushi sannan yaci gaba da cewa

"Duk zaman danai da ita ban taɓa jin cewar ina sonta ba illa kawai tasausayinta
danakeji A raina, shiyasa nayi amfani da wannna damar don na zaburar dakai harka
baiyana abinda ke cinka a rai amma kuma se gashi ka gaza yin hakan.

Sosai jikin Muzaffar yay wani irin sanyi take hawaye ya Cika idanunsa ya juya yana
kallo n mom wadda itama shi take kallo yace "yanzu dama duk abinda ya faru a baya
har zuwa Aurena da aka ɗaura da ita duk kun sani amma kuma kuka gaza sanar dani?

Ya faɗi hakan a lokacin da hawayen dake maqale a manyan idanunsa ya fara zubo masa
da wani irin mugun sauri ya Nufi Edyan ya rungumeshi Yana faɗin "thanthankSo much
friend wllh I can't explain how much you mean to me, ina roqon Allah ya gina maka
gida a gidan aljanna!!

Dariya suka dinga masa har Ummie da Abie dake tsaye a bakin ƙofar perlourn hatta
baba Hajara ma ba'a barta a baya ba har ita aka haɗu a falon Abie ya haɗesu dika
yay musu nasiha me ratsa jiki, tofa a nan ne Muzaffar kejin Auren Edyan da kuma
qanwarsa Zainab sosai yay farin ciki da hakan don yasan waye Aminin nasa.

Sosai Muzaffar yaji daɗin hakan ba kaɗan ba har hakn ya gaza ɓoyuwa a tareda shi,
huggin zainab yayi yace "congratulations Qurraty to have my best friend as your
husband.

Dariya tayi sannan tace "same to you my handsome bro. Se yamma liqis sannan suka
Koma gidajensu gabaɗaya.

A haka dai Rayuwa ta dinga tafiya da daɗi babu daɗi har Lavarin haihuwar inna
laure ya iso musu cewar ta haihu ɗa namiji amma sedai Ɗan bezo da rai ba, kukan
farin ciki laure da moddibo suka dingayi daga bisani kuma suka koma rayuwar daidai
kamar wani abu betaɓa faruwa Mara daɗi a tsakaninsu ba

Sosai zumunci ya qullu A tsakanin zuriyar C. P mahaifin Edyan da kuma zuriyar 'Abie
sakamakon Auren Zainab da kuma Edyan.

Ɓan garen Hajar kuwa tayi kuka kamar ranta ze fita a lokacin data samu labarin
Auren muzaffar a hakan ma wai da wadda tafi tsana a rayuwarta. Tasha wahala sosai
akan sonda take masa har hakan ya kaita ga kwanciya a gadon asibiti , a haka dai ta
dinga rayuwa da tabon sonsa a ranta har Allah ya haɗata da wani bawon Allah me suna
Ibrahim amma ana kiransa da Khalil, babban ɗan kasuwa ne shima a jirgi suka haɗu
dashi har hakan ya kaisu ga Aure ammafa har zuwa wannan lokacin Namiji ɗaya ne a
ranta Shine Muzaffar Abdulwahab Abdullah, Haka kuma har duniya ta tashi bazata taɓa
iya dena sonsa ba!!!!! (Tabbas jarrabawar sosayya sam bata da daɗi, ya Allah ka
rabamu da son maso wani)

A wannan tsukun Allah ya haɗa Fadilah da wani hamshaqin Ɗan kasuwa kuma
mammallakin companyn kansa me Sulah Salahudden sukai Aure, a haka suka dinga
gudanar da rayuwarsu a tare sedai tunda sukai auren shiru ne babu batun qaruwa Ta
haihuwa a tsakaninsu.

****
Soyayyar da rayukan biyu sukeyi wa junansu kullum qara haɓaka take tana Qara naso,
har Allah ya kawo Rabo a tsakaninsu inda Rabe ta haifi zaratan twins Ɗinta maza
masu matiqar kamada ubansu, zaso kuga murna Da farin ciki a gurin Abie da mom abin
har seda ya fara bawa Ummie tsoro, ranar suna yara sukaci sunan Abdulwahab da kuma
Abdulkharim Wato sunan moddibo da kuma na Abie, inda suke kiran Me sunnan Abie
da LAMIƊO, shikuma Ɗayan MODDIBO A sanadin haihuwar wannan yara mutanan rugar Ardo
suka samu ƴancin da bazasu taɓa mantawa ba inda aka sanya musu matakan tsaro ta ko
wani fanni tareda Gina musu wani babban Asibiti da kuma makarantun boko Don suma su
tafi da zamani, sosai yanayin garin ya canza daga yanda yake a baya zuwa Wani Hatta
fasalin gidan MODDIBO A wannan lokacin za'a iya kiransa da gini na musamman kuma
abin kallo A aria ɗin gabaɗaya, A haka rayuwa ta dinga tafiyar musu da cigaba kala2
duk a sanadin Auren Rabe da Kuma Muzaffar ɗinta.

Bayan wasu shekaru

Zuwa yanzu su Lamiɗo da Moddibo sunyi girma sosai don Shekarunsu Ya kai biyar,
kana kallon yaran zasu shiga ranka sabida yanda sukai gadon kyau bugu da qari kuma
gasu ɓul2 dasu.

Kwance suke kan gadonsu lamiɗo muzaffar ya kalƙeta cike da so yace "ma'am nifa na
kasa gane miki A ƴan kwanakin nan wllh jarabarki tayi yaw.......... Bata bari ya
qarasa ba ta haɗe bakinta da nasa tana kissing ɗinshi kamar dama her life defined
on it, duk yanda yaso karya biye mata seda tayi galaba a kansa zare bakinsa yayi
daga nata yace "pls ki bari karfa yaran nan masu ɗan banzan surutu suzo su gan mu
haka nan.

Aiko kamar daga sama sukaji muryar Lamiɗo da Moddibo suna faɗa akan cewar Lamiɗo
ya hana Moddibo shiga ɗakin shi kuma yace dole seya shiga, a haka iyayen nasu suka
iso gurin suna tambayarsu meyake faruwa?

Turo baki Moddibo yayi yace " Mommy bashi ne ba wai bazan shiga ɗakin ba, sassauta
murya muzaffar yayi yace "Lamiɗo meyasa ka hanashi shiga?

Turo baki shima lamiɗon yayi yace "uhm Dady to ai refreshing kuke kaida Mommy
shiyasa na hanashi shiga don karya gank......... Toshe masa baki Rabe tayi se faman
raba idanu take kamar tayiwa sarki qarya, gaba ɗaya ji tayi kamr zata nitse sabida
Kunya gefe kuma mamakin Wayo irin na Lamiɗo Takeyi

Daka musu tsawa tayi tace " oya go to bed kuma wllh idan na sakejin such words na
fita a bakinka irin haka wllh sena dakaku gabaɗayan ku A gidannan !!!!!! Da gudu
yaran sukai ɗakinsu ba tareda sun juyo ba

Kallonta muzaffar yayi yace "aiga irinta nan kin gani, jawoshi tai jikinta tana
wani Narke masa se raba idanu Take tace "pls sweet muje Wllh i need you so badly!
Ba yadda ya iya hkaa ya bita don shima kansa a buqace yake da ita, kullum ya
ziyarce ta ji yake tana qara masa garɗi tamkar ana qara mata ni'ima ne , babban
abinda ke qara masa sonta shine juriyarta Ga lalurarsa da kuma biyayyar ta a
gareshi.

Murmushi ya saki sannna ya firtaA filli yace"Haqiqa mace me wayo ita kaɗai ce take
gane sirrin biyayyah........

*_Tammat bi hamdillah a nan na kawo qarshen wannna littafi me take BAFULATANA


RETURN, Abinda na faɗa daidai Allah ka bani ladansa kuskuren dake ciki kuma Allah
ka gafarta min 🤲_*

*Darasin dake ciki kuma Allah ka bamu ikon aiki dashi Amin🤲*

*_Waƴanda na bawa haushi A sakamakon wannan littafi ku gafarceni kunsan ɗan Adam
tara yake be cika goma ba Duk yanda kaso ka kyautatama mutane wani bazaka taɓa iya
masa ba😊_*

*Semun sake haɗuwa daku a cikin sabon littafina me suna*


👇

*MURADIN RAI*
(Abou Hateem)

Camment
Nd
Share

Don't forget to vote on whatpad

Sushmah✍️

You might also like