Kura A Rumbu CMPLT
Kura A Rumbu CMPLT
*(Based on true life event, some parts are fictional to spice up the story)*
*Wattpad @MaryamahMrsAm*
*Ban yarda wani ko wata ya juya mun labari ta kowacce siga ba tare da izini na ba*
*Kuɗin karatu yana wakiltar mutum ɗaya ne, kiji tsoron Allah karki ɗauki hakkina ta hanyar fitar mun da
littafi*
*1840175439*
*Access bank*
Zaku ce ya akayi haka 😭 na fiku takaici da baƙin ciki rasa rubutun nan a karo na biyu 😭 in shiga in duba
folder tace dubani in da kika ajiye. Komai ya goge wlh. Bazance dan me ba domin bansan hikimar
ubangiji cikin al'amarin ba. A kullum ina addu'ar Allah ya bani ikon rubuta alkhairi. Idan da rabo zan sake
rubuta WASU MATAN amma abun da ciwo kayi rubutu ya goge.
Ban cika baki ba amma se kunce gara da akayi haka. It was meant to come in the next 1 year or more
ashe yanzu Allah ya nufa. Asha karatu lafiya.
*PAGE 1*
"Malam idan kaje ƊAN ALJANNAH zan sauka" na faɗa ina nunowa me Adaidaitan da muke ciki saitin in
da ze ajiye ni, bayan daya gama daidaita parking na sauka ba tareda na kalli Hansa'u data kalli ɗaya
ɓangaren ba nace
"Da ace kuturwa Allah yayi ni se inji haushi dan kince ba zaki tayani aiki ba, dake ko babu ke bazan rasa
wanda zasu rufamun asiri ba" na faɗa ina miƙawa me Adaidaita ɗari biyar. Bata tankamun ba na juya ba
tareda na amsa tambayar da me mashin ɗin yake mun ba akan iya kuɗi na ze ɗauka ko na mu biyun na
shige kantin. Na rigada na rubuta list ɗin abubuwan da zan siya dan haka kai tsaye na shiga ɗauka cikin
abinda be wuce minti sha biyar ba na gama dan ma na tarar da layi gurin biyan kuɗi. Wani Adaidaitan na
tare ya ƙarasa dani kofar Nasarawa gidan Anty Labiba. Munir na ƙofar gida da abokinsa ina hango su naji
raina ya sake ɓaci dan nasan ƙarshe yanzu Anty Labiba se ta tado da zancen da bana so amma ganin ya
riga da ya ganni in na ce mu juya ma ze ga ai saboda shi ne yasa nacewa me Adaidaitan ya faka na sauka
ina cin magani na biyashi kuɗin sa.
"Barka da zuwa Hajiya Halima" Abokin nasa wanda seda na sauka na gane Yahuza ne ya faɗa yana mun
murmushi, na ɗauke kai sama ciki ciki nace "yawwa". Kafin na miƙawa me Adaidaita kuɗin sa Munir daya
iso kusada dani ya rigani, ɗari biyar ya bashi sannan ya duƙa ya shiga ɗaukar ledojin siyayyar dana zube a
ƙasa. Murmushin sa me kyau yayi kafin yace
"Ashe kece zaki zo shiyasa na kasa tafiya". Na wuce cikin gidan ba tare da na tankashi ba ina ji ya biyo
bayana. Anty Labiba na zaune kan tudun gurin wanke wanke tana cire hancin kayan miya ta ɗago tana
amsa sallamar mu.
"Aa, Munir. Ashe baku tafi ba?" Ta faɗa tana tsame hannunta daga abinda takeyi, a ƙasa ya aje kayan
yana cewa
"Eh wlh, haka nan fa muka tsaya ashe rabon na ganta ne yasa" ya faɗa yana nuna ni. Na tura baki gaba
ina wucewa falon Antyn ina jiyo ta tana cewa
"Billahillazi dai Munir se in ce baka da zuciya, yanzu saboda Allah ba zaka bar yarinyar nan ga mata nan
fululu a gari masu sonka kamar suyi me ba? Wlh idan nice kai inuwar Halima bazan sake kallo ba balle
har maganar arziƙi ta haɗa mu".
"Ba zaki gane ba Anty" se tayi saurin tare shi tace "dama ta ina zan gane? To dai tun wuri gara kawa
kanka faɗa ka nemi wata dan nan kusa banga Halima nada rabon gane wautar data tafka ko in ce take
shirin tafkawa ba. Ita tayi asara wlh samun saurayi nagartacce kamarka me abinyi a zamanin nan" .
"Bari na wuce, adai cigaba da taya mu da addu'a a kuma sake tayani rarrashinta Anty" ya faɗa jin zata
ɓaro wani zancen sannan ya juya ya fita nan kuwa Anty Labiba ta dasa mitar da bata gajiya dayi tunda na
watsa mata ƙasa a ido nace bana son ƙanin mijinta kuma ɗan ɗakinta. Seda na jiyo ƙarar tashin mota
alamar sun tafi kafin na aje mayafina na, kujera na aje kusada inda ya zube mun kayan na shiga gaida
Anty Labiba ta wani amsa mun a ɗage ni se ta bani dariya ma irin wannan ɗaukar dumar magaji da nishi.
Shikenan kuma se akace dan ya mata dole nima ya mun in so shi? Kowa fa da ra'ayinsa a rayuwar nan, ni
da wanda nake so shima rashin zuciya yasa har ya bari maganar ta fito bayan tun ni dashi daya furta mun
na sanar masa ina da wanda nake so ba kuma na ra'ayinsa.
Kayan na shiga fito dasu daga leda Anty Labiba ta kalleni tace
"Ban gaya miki karki sake zuwa gidan nan kice zaki wa wancan santolon cima zaunen abinci ba?" Nan da
nan na haɗa rai nayi kicin kicin bata damu ba taci gaba da cewa
"Tsabar rashin sanin ciwon kai, mazan arziƙi na wahaltawa yammatansu amma shi mace ce take wahalta
masa yana kwance ba cas ba as gaki yar wahala ki ringa dafa abinci ki kai masa ba godi bare na gode
balle a baki tukuici to ba'a gidan ba dan gas ɗina bana gomnati bane kije can gidanku kiyi". Kan ince wani
abu Uncle Sale ya fito daga falo yana cewa
"Meye haka Labiba?" Kitchen ɗin ta dake tsakar gida ta shige ba tareda ta amsa masa ba na gaishe shi ya
amsa yana tambayata su Anty kafin ya bita kitchen ɗin ni kuma na wuce falo ɗauko wayata dan na
manta ban tambayi Bilal abincin me miya yake so ko kuma jallof ba.
Sau biya na kirshi be amsa ba hakan yasa na barshi na tafi akan nayi masa jollop ɗin kawai tunda na siyo
kaza harda cabbage da zanyi coslow. Seda na jira Anty Labiba ta gama miyarta ta fita daga kitchen ɗin
kafin na shiga nawa aikin, nasan magana Uncle Sale ya mata shiyasa ta barni dukda haka shiga goma fita
goma seta mun habaicin ni yar wahala ce ina wa wani can ƙaton banza girki, tsakani da Allah ta ina mijin
da zan aura ya zama ƙaton banza? Laifi ne idan na dafa abinci na basa?
Ana kiran la'asar na kammala komai, cikin sababbin kulolinta na shirya abincin dama na gyara ƙaramin
falonta na saka turaren wuta na kulle, ban bari ta lura ba na shige da kulolin da plates na sake kullo
ɗakin kafin na koma ɗakin su Amir na shiga wanka. Ina tsaka da shiryawa ta shigo tana cewa
"Guda ɗaya ce fa Anty" na faɗa zuge zip ɗin skit ɗina, ta ballamun harara tace
"Ko ɗan tsako ne wlh se na ci, ban muƙullin falo na" sena yi waje da sauri ina cewa
"Amma tsakani da Allah dai an san abun nan na mutum ɗaya ne kuma za'a sa masa rani, bafa shi da
lafiya banda ma bani da kuɗi me kaza ɗaya zata masa ma" na wuce falon tareda maido ƙofa dan karta
biyo no taga kulolinta ta dasa mun sabuwar tijara. Fukafukai na ɗakko mata da ƙundu na zubo mata
albasa da koren tattasan da nayi garnishing pepper chicken ɗin dasu ina ajiyewa kuwa ta fara auna mun
zagi wai mayya na maida ita ko me? A karo na biyu Uncle Sale daya dawo daga sallah ya sake ceto na,
sanin yau weekend yana gidan ma yasa har nayi karambanin zuwa badan haka ba gara in zauna a
gidanmu ƙarshe dai nayi raba daidain duk abinda na dafa dasu Mu'azzam amma babu wanda ze zageni
ya mun gori.
Ƙarfe biyar Bilal ya kirani akan ya iso yana waje, na sake gyara fuska ta na ƙara turare kafin na fita bayan
na gayawa Anty Labiba zuwan nasa ta zage ni ta zage shi sannan ta shige ɗaki. A jikin sabon mashin ɗin
daya ce mun ya siya Lifan na tarar dashi, yasha kwalliya da wata shadda ruwan ƙasa datayi matuƙar
karɓar kalar fatarsa me ɗan duhu. Sabon askin da yayi ya ƙara fito da tsantsar kyansa ga gemun dake
ƙara matar dani a soyayyar sa se na ringa jin kamar na tafi da gudu na rungume sa ko zanji sauƙin
raɗaɗin da sonsa yake haifar mun cikin zuciyata. Cikin taku ɗaɗɗaya na isa inda yake ina murmushi
kamar yanda shima yake doka mun murmushi. Cikin ƙasa da murya kamar me tsoron wani yaji abinda
zan faɗa nace
"Barka da zuwa yarimana", ya saki murmushin jin daɗi tareda gyara tsayuwarsa kafin yace
"Kaina yana ƙasa kawai naji wani haske ya dalle mun ido, na ɗago da mamakin wace fitila ce aka kunna
haka domin dai rana tayi nisa da nan gurin balle nace kaifinta ne ya haska ni seda na kalla naga ashe
kece. Kyanki da annurin fuskarki kullum ƙaruwa suke Halims, anya bazan fara saka baƙin glass ba kafin
ƙyallin fuskarki ya makantar dani?"
Wata dariya nayi kaina ya fasu, irin kalaman nan na Bilal su suke ƙara saka naji duk duniya bani da
sauran buri daya wuce na kasance matar sa idan hakan kuwa ta tabbata nasan na kere sa'a, ni da baƙin
ciki har abada domin ko babu abinci irin wannan maganganun nasa sun isa su ƙosar dani.
"Wane irin wasa? Kina raina irin baiwar da ubangiji ya miki ko? Baki san hasken idanunki kaɗai sun
wadaci a zauna a cikin ɗaki ba tareda an kunna fitila ba?" Ya sake faɗa yana mun kallon dake kashe mun
jiki, sena juya ina cewa
"Ni dai barni haka muje ciki kaida baka jin daɗi ka tsaya kana ta surutu"
"Au, surutu ma nakeyi ko? Shikenan bari na koma inda na fito tunda yabonki da nakeyi sututun banza ne
a gurinki" Ya faɗa yana ɓata fuska kamar ransa ya ɓaci nan da nan hankali na ya ɗaga na juya da sauri ina
cewa
"Haba mana ya zaka ce haka? Nifa ina magana ne akan baka jin daɗi kana gajiyar mun da ƙafafunka da
tsayuwa amma kaima kasan bana taɓa gajiyawa da sauraron kalamanka. Ni a duniya ma bayan karatun
alƙur'ani akawai wani sauti da nake mararin sauraro ne bayan muryarka?"
"A ina zan aje mashin ɗina, ko da yake ma baki ko lura dashi ba balle ki tayani murna"
"Wlh Yarima murnar ganinka da daɗin kalamanka suka sa kai kaɗai nake ji da gani a gabana. Mashin yayi
kyau, Allah yasa lafiya ta kashe Allah kuma ya tsare ka daga sharrin ƙarfe da titi" ya amsa mun da
"Amin Halims". Seda na buɗe masa get ya shiga da mashin ɗin kafin muka jera zuwa cikin gidan tabbas
nida Bilal haɗin nan da bature yake cewa *MADE FOR EACH OTHER*. Ko magulmata dan suke ganin
bamu dace da juna ba suna faɗar haka ne ta wasu fuskokin da a ganinsu muka banbanta bawai a
zahirance ba domin duk wanda ya kalle mu seya ce mun dace da juna, daga kuma sanda na haɗu dashi
na yardarwa zuciyata tare aka halitto ruhikanmu babu kuma wani al'amari da ze raba mu face mutuwa.
"Amma gyaran gida su Anty Labiba sukayi?" Seda na miƙa masa kofin dana cika da ruwan lemon exotic
me sanyi ya karɓa kafin nace
"Eh mana, gidan gefensu ne suka fitar da rabin filinsu shine ya siya yayi ƙari. Wannan falon ma ai sabon
gini ne ka manta da babu shi"
"Lallai Alhaji Sale bayajin garin nan, a yanda ake kukan babu shi har ya samu rarar gyaran gida ba shakka
ƙasar a hannunsu take" ya faɗa bayan daya shanye lemon. Shiru na masa dan nasan yanzu ze fara
surutansa da basu nake son ji ba, ilai kuwa yace
"Yanzu me gida kamar wannan be ishe shi ba har ƙari yayo ni ɗan akurkin nawa ma tunda na kai linta na
gagara cigaba, koda yake su yan oil and gas dama ai arziƙin ƙasar a hannunsu yake. Da ace muma za'a
buɗa mana mu ɗan samu se kiga a wata shida na warware har na fara aje tumbi fa".
Da "uhm" na amsa shi na sauka na fara zuba masa soyayyar jallop ɗin basmati da taji gurzajjen karas da
albasa na ɗora masa ƙirjin kaza in da yafi so da haɗin coslow daya ji kwai da madara da. Tun kafin na
gama zubawa ya sakko kan carpet ya zauna yana cewa
"Kin san fa tunda kika ce zaki mun girki ko karyawar kirki banyi ba yau ciki na empty yake" nayi
murmushi na aje masa plate ɗin ina cewa
"Ai da dai ka ci wani abun ko ba yawa bafa na so ka ringa barin mun cikin ka da yunwa ka sani"
"Ai na ɗauka da safe zaki abincin ne shiyasa da naga har goma tayi baki kirani bane ma nasha Tea" ya
faɗa yana kai lomar farko bakinsa. Yanda ya lumshe ido yana tauna abincin kana gani kasan daɗin ya kai
masa ko ina, seda yayi loma uku kafin ya kalle ni yace
"Wato Halims bana zaton a duniyar nan akwai macen data kaiki iya sarrafa abinci, wai carkwai
maɗagwai. Badan kar inyi saɓo ba se in ce wannan abinci ko hurul'ayni ta dafa ai se haka".
Kaina ya sake fasuwa, na zuba masa zoɓo roba ɗaya ne na sata a fridge ɗin Anty Labiba yana cin abincin
yana santi seda yafi rabi kafin yace na sakko muci na girgiza masa kai ina murmushi naci gaba da kallonsa
yana zuba loma, yanda yake cin abincin ya kamata ace ya bani haushi irin yanda yake cika baki kamar
wanda be taɓa ci ba amma kuma dake zuciyar cike take da so da begensa burge ni yakeyi ina ganin so da
shaƙuwar dake tsakaninmu tasa baya kunyata yake iya cin abinci a gabana. Tas ya tada abincin da iri na
mu huɗu ma ba lallai mu iya cinyewa ba, shi kansa ina mamakin sa dukda nasan maza suna da cin abinci
amma na Bilal kam daban ne kodan yana ƙwallo ne?
Mun daɗe muna hira yana kashe ni da kalaman dake ƙara mun sonsa da ƙaguwar na zamto tasa, ina so
ma sako maza zancen tunin da Abba yace na masa akan turo magabatansa a saka ranar auren mu kusan
wata uku kenan shiru bece komai ba, yanda yake ta sako mun ƙorafin har yanzu wata shida kenan daya
samu aiki wai ba'a fara biyansu albashi ba. Sati uku baya sukaje Abuja akayi capturing nasu IPPIS sun
saka ran samun albashi a watan da aka shiga sedai shiru har anci kwana goma babu labari. Wannan
dalilin yasa nake masa uzuri tunda koda ace an saka ranar bashi da ƙwaƙwƙwarar hanyar da ze tara
kuɗin da ze ƙarasa gininsa har azo maganar lefe da sauran hidimar aure. Samuwar aikin dama da ita
muka dogara to gashi kuma har yanzu ba'a samu yanda ake so ba amma kuma dukda haka kamar yanda
Abba yace suzo a saka rana ko da shekara biyu suka ce lokaci ne da an kirashi ze zo yafi ace ayi ta tafiya
haka babu cigaba. Tun muna ND 2 aka kawo kuɗin aure gashi yanzu satuttuka suka rage da mu gama
HND.
Duk ƙawayena da muka fara karatu tare wasu sunyi aure harda yayayensu waɗanda basuyi ba da yawa
da sa ranarsu da zarar mun ƙarasa karatu se waɗanda Allah be kawo musu mazan ba, a ciki kuma zan iya
cewa nice kaɗai na fara karatu ina da tsayayyen saurayi dan tun ina SS3 muka haɗu da Bilal lokacin daya
zo NYSC makarantar mu gashi ana lissafin shekaru kusan biyar kenan yanzu.
"Halims" ya kira sunana hakan ya ankarar dani zurfin da nayi a tunani. Na sakar masa murmushi ina
gyara mayafin kaina daya zame yace
Kai na girgiza masa ina murmushi nace "babu komai, ina sauraronka"
"Me na faɗa daga ƙarshe to idan dai kina jina?" Ya tambayeni, na sakeyin murmushi nace
"Canka kikayi kawai saboda kinsan harshena baya gajiya da furta abinda yake cikin zuciyata. I love you
whole heartedly Halims, wlh duk sanda nazo gurinki Allah kaɗai yasan yanda name yaƙi da zuciyata
amma ji nake kamar karmu rabu, na masu na kasance tare dake a matsayin matata ta sunna".
Ƙasa nayi da kaina ina murmushi cikin jin kunyar kalamansa, ya matso kusa dani yana cewa
"Dagaske nake Halims, kinga rashin lafiyar nan da nayi duk magungunan da nasha ba wani aiki suka mun
ba ina kwance se ince inama kina kusa dani nasan dakin shayar dani maganin dake tattare dake zan
warke"
Zumbur na miƙe daga kusa dashi ina ɓata fuska cike da shagwaɓa kamar zanyi kuka ya fashe da dariya
yace
"Ni dai bana so" na faɗa ya miƙe yana cewa "Na bari My Halims, bazan sake ba. Amma da gaske a matse
nake da son kasancewa dake. Ki tayani da addu'a akwai abinda nake jira da zarar ya tabbata za'ayi komai
shikenan ki zama tawa ki dena mun ƙwalele kina hanani bacci da dare" ganin na nufi ƙofa yasa ya shiga
dariya yana cewa
"Haba mana nace miki na dena ai yanzun ma baki nane ya suɓuce. Magriba tayi kizo muyi selfie na samu
na rage zafi kar na tafi ina mafarkin kwalliyar nan taki". Dakyar na tsaya ya ɗauke mu selfie a wayarsa
sannan yayi mun ni kaɗai, har munje bakin kofa yace
"Ban ma san me zanci ba da daddare ba wlh. Wai tuwon Anty Murja tayi bayan tasan bana so ga kuma
baki na babu daɗi". A raina nayi murmushi nace "dama jira nake naji zakayi magana ko kuwa" a fili kuma
nace
"Afuwan, ganinka ne duk ya rikitani. Bari nayi maka packaging sauran se kaci idan ka koma"
"Haba dai, su Amir ba zasu ci ba? " Ya faɗa kamar gaske. Sena wuce shi kawai a raina ina gulmar halinsa.
Ko pure water na bashi seya tafi da sauran balle abinci shine zece wani su Amir ba zasu ci ba. A fararen
robobi na juye masa sauran abincin da banda wanda na ɗanɗana da ina girkin ban sake jinsa a baki na
ba. Roba uku na masa ɗaya shinkafa ɗaya kaza se coslow a ɗayar lemon ma na juye masa a gorar Faro na
haɗe masa komai cikin ledar dana ɗakko.
"Wannan halin naki yake tabbatar mun zaki kula da cikina idan mukayi aure, Allah dai yayi miki albarka
ya barmu tare my Halims" ya faɗa sanda ya karɓi ledar. Muka jera yana mun surutu, seda na buɗe masa
get ya fita da mashin na rufe kafin na fita na same shi ya ɗaure ledar yanda abin ciki ba zasu zube ba
kafin ya hau mashin ɗin yana kallona yace
"Da yanzu zaki wuce gida se mu tafi na ɗana ki". Tunda yazo nake raya in masa magana akan da canza
mashin ɗin da yayi dama gini ya cigaba ko yayi amfani kuɗin ya haɗa kayan saka ranar tunda dai tsohon
nasan babu abinda yayi ai amma gudun kar yaga na shiga rayuwarsa yasa nayi shiru se nace
"To bari kawai nayiwa Anty Labiba sallama se mu tafi dama na gaji gashi kuma gobe ina da practical
exam ina so nayi karatu" na juya cikin gidan.
Toshe kunne kawai nayi na haɗa kayana na gudu na bar mata wanke wanke ina tana faɗin zan sake zuwa
ne na tafi, faɗan mu ba wani jimawa yake ba da kanta ma zata nemo ni musamman yanzu da yara zasuyi
hutun makaranta ga tsohon ciki tana dashi dole ta nemo me tayata da kayaniyar yaran. Na ɗane
tsuntsun soyayya ya lula damu muna tafe yana mun surutan da ba wani ji nake sosai ba saboda iska har
muka isa sabon titi gidan mu. A bakin gate ya tsaya na sauka ya kalli ginin benen da ake ɗora mana da
har an fara fenti yace
"Ashe aikin nan yayi nisa haka, wato mu talakawa ne muke jin garin nan masu kuɗi sha'aninku kawai
kikeyi". Fuska ta ba yabo ba fallasa ban dai ce masa komai ba ya shiga laluben aljihu, harga Allah na saka
ran tunda yace mun ya siyi mashin idan ya tashi zuwa ko 5k ce ze bani shiyasa ma banji komai ba na
kashe kuɗin transport ɗina na sati da Abba ya bani nayi masa abinci ko be biyani duka ba a ƙalla zan rage
wani abun musamman da yake ta koɗa daɗin abincin yana faɗin na cancanci tukuici ganin yana laluben
Aljihun yasa nayi ɗan murmushi ina jira se naga ya zaro wayarsa ya buɗe kafin ya juyo yana cewa
"Bari in sake miki hoto wlh kin mun kyau yau ɗin nan irin sosai fa My Halims.
Takaici ya kamani amma haka na gyara ya shiga ɗauka na hoton seda aka kira sallah kafin yamun sallama
ya burga mashin ɗinsa ya tafi na juya jiki ba ƙwari na shiga gida a raina ina ayyana ƙila se jibi da yace ze
zo ko kuma ya mun transfer.
*(Based on true life event, some parts are fictional to spice up the story)*
*LABARI/RUBUTAWA MARYAM FAROUK (UMMU-MAHEER)*
*Wattpad @MaryamahMrsAm*
*Ban yarda wani ko wata ya juya mun labari ta kowacce siga ba tare da izini na ba*
*Kuɗin karatu yana wakiltar mutum ɗaya ne, kiji tsoron Allah karki ɗauki hakkina ta hanyar fitar mun da
littafi.*
*KURA A RUMBU littafin kuɗi ne, a biya naira 800, biya a asusun*
*1840175439*
*Access bank*
*PAGE 2*
Washe gari daƙyar na yakice bacci nayi shirin makaranta, ina gama karatu Bilal ya kirani har gurin ƙarfe
ɗaya muna hira kafin ya barni na kwanta dama ga gajiyar dana kwaso a makaranta jiyan na ɗora data
girki sannan dana dawo gidan ma ban zauna ba na tarar anyi fenti a ɗakina gaba ɗaya an hargitsamun
kaya seda na gyara su sannan na kwanta. Shaf na manta da munyi faɗa da Hansa'u jiya na zauna jiran
zuwanta har ƙarfe tara seda na kirata sau biyu bata amsa ba wanda nasan ba halin ta bane da wuya na
kirata a waya bata amsa ba sedai irin haka idan munyi faɗa. A fili nace
"Lallai, wai ita ta ɗauki abun har zuci ashe. Ni da ya kamata nayi fushi ta zagar mun Habibi banyi ba se
ita? To ai shikenan" na ɗauki jakata da Lab coat na fito falo na tarar da Mama tana ware atamfofi. Sau
biyu ina ce mata zan tafi tana mun Allah ya tsare hanya. Ɗari biyar ce a jakata, zata kaini ta dawo dani
amma bani da canjin da zanci wani abu kuma yau ɗin wuni zamuyi se ƙarfe huɗu zuwa biyar zamu taso.
Ganin na tsaya yasa ta tambayeni lafiya? Na shiga sosa kai, tsaki kawai Mama tayi ta buɗe POS ɗin ta
dake gefe ta zaro dubu ɗaya ta miƙa mun tana cewa
"Banda shegen iyayinki me yasa baki zo kin masa abincin a nan ba?" Karɓa nayi tareda mata godiya na
fita. Ina son Mama, bata zafafawa a lamuranta. Nasan ba wani son zancen aure na da Bilal take ba
musamman yanda duk yan uwanta suke sukar abun amma tunda nida Abba muna son ita ma ta karɓa
tana mana addu'a.
Seda muka fito break kafin muka tsaya da Hansa'u nace mata "wai saboda maganar jiya yasa baki biyo
mun ba yau kuma na kiraki baki amsa ba?"
"In biyo miki kuma? Ina ce kikayi kowa tasa ta fishsheki babu kr babu ni akan Bilal iyayenki ne kawai na
zaki bari ba. To tunda ni ba iyayenki bace ai gara na tattara tsumman rayuwata na baki guri tunda baki
na baze iya shiru ba har idan naga abinda ba daidai ba se nayi magana" Hansa'u ta bani amsa, sena
rungumeta ina cewa
"Haba ƙawata ki barni in kama wa? Ai kin san dai tsakani na dake ya wuce ƙawance kema yar uwata ce
kina cikin waɗanda bazan rabu dasu ba ai" ta mun banza, dake nasan nice da laifi dukda naji haushin
abinda ta faɗa akan Bilal amma kuma nima abinda na mata ya shallake wanda tamun hakan tasa na
ringa bata haƙuri harta sakko muka tafi siyo fanke da lemo. Bayan mun zauna nace mata
"Amma tsakani da Hansy dole a ringa jin kanmu har idan zaki ringa taɓa mun Yarima. Ya kamata ki ringa
mun kara, ko baki son Bilal darajar ƙaunar dake tsakani na dashi ai yaci ki mun kara. Bana so ki dena
zaginsa a gabana idan ma zaki zage shi kiyi can a inda bazanji ba dan nima bazan miki kara ba sena rama
masa"
"Ai shikenan, ni dai bazan zauna tare dake ina kallo kina ƙoƙarin jefa kanki a halaka kuma nayi shiru na
barki ba dole in faɗa miki gaskiya ko ki ɗauka ko karki ɗauka ruwanki" ta bani amsa, a hasale nace
"Auren Bilal ɗin ne kike kira da halaka Hansa'u? Wai me kike nufi da Bilal ne? Ki gaya mun me yake
aikatawa da har kike kiran aurensa da jefa kai a halaka wane mugun hali yake dashi da ban sani ba?" Na
ƙarasa ina miƙewa tsaye. Watsa hannu tayi tace
"Kin fini sanin halakar da nake nufi sedai idan kin so ne zakiwa maganata mummunar fassara. Akwai
halakar duniya data wuce mace tayi rashin dacen mijin aure? Bilal be dace dake ba, kiso ko karki so sena
faɗa ke kike sonsa amma shi ba sonki yake ba idan ma kuma yana sonki to akwai dalilinsa na hakan
amma ba zaki fahimci abinda nake faɗa miki yanzu ba ba kuma na miki fatan kiyi nadamar kin jij
maganar masu sonki a sanda komai ya lalace miki. Tun wuri ga maza fululu masu ƙaunar ki dagaske ki
nemi mijin aure a cikinsu ina mai tabbatar miki har ba Allah ya ƙaddara ba Bilal ya samu wadda ta fiki
sedai kiji wani zancen wlh" ta ƙarasa tana bari na a gurin. A maimakon sulhu se gashi mun sake tafka
wani faɗan dan da aka tashi ban tafi ba seda na sameta na sake zazzaga mata rashin mutunchi na faɗa
mata nasan baƙin ciki take mun ba wani abu da saboda na samu me so na zamuyi auren soyayya da
ƙuruciyarmu ba irinta ba da zata auri tsoho sa'an Babanta shine take mun baƙin ciki. Kwaɗayin daya
kaita ta amsa zata auri tsoho shi zesa ta haɗiyi baƙin cikinta ta kalle mu ni da Habibi na musha soyayya. A
bakin titi na cimmata suna jiran Adaidaita da ƙawayenmu biyu Zainab da Hussaina duk yan unguwar mu
ne tare muke tafiya dama. Hansa'u ta ringa kuka ko a jikina su biyun ma da suka shigar mata nayi musu
tatas nayi tafiyata na barsu raina fes domin ba wanda ya isa ya taɓa Bilal na barshi, dama ta kama kanta
ta fita a sabgata dashi se mu cigaba da lallaɓa zumunchin mu amma ta soka kanta a inda ba'a gayyaceta
ba.
Dana koma gida tsaf na kwashe labari na bawa Bilal daya kirani, ga mamakina se yace wai ban kyauta ba
me yasa zan mata haka ai kamata yayi naji uzurinta domin yanda muke da ita kowa yasan ba zata cutar
dani ba
"Kenan ka yarda kana da mugun halin da har zata ringa faɗar irin Maganganun nan akanka?" Na
tambayeshi, se yace
"No Halims ba haka bane. Abinda nake nufi da se ki mata uzuri ki bita a hankali kiji menene hujjojinta
amma yanzu abinda kika mata gaskiya baki kyauta ba ai tsakaninku ya zarce haka gaskiya banji daɗi ba"
ya ringa mun faɗa har naji haushi ma na kashe wayar.
Kwana biyu da suka biyo baya banje makaranta ba mun samu interval kafin mu fara theory parts na
jarabawa. Tun a washe gari da Mama taga har yamma bance zanje gidansu Hansa'u ba ita kuma bata ga
tazo ba ta tambayeni ko lafiya se kawai nace mata jiya da muka taho gadon ƙaya ta wuce gidan yayarsu.
A washe garin ranar da rana Abba ya dawo daga Enugu sunje wani aiki da magriba bayan ya dawo daga
masallaci ina ɗakina na idar da sallah na jiyo yana ƙwala mun kira, Abba bashi da faɗa daga sautin
muryarsa na san akwai wani abu abinda ya fara zuwar mun ko zancen Bilal ze mun tunda yace kafin ya
dawo musan abinda muke ciki.
Ina fita naga Hansa'u a zaune, a raina nace lallai ma, ƙarata ta kawo ko me? Haka na samu guri na zauna
nan kuwa Abba ya haɗa mu duk mu biyun ya mana kaca kaca kowa ya bata laifinta. A yanda yace tun da
la'asar daya fita aka bashi labarin wai munyi faɗa a makaranta a raina na ringa tsinewa munafukai nasan
kuma baze wuce Nasir ko Musan gidan inji ba sune yan unguwar mu kuma a gabansu mukayi faɗan
shine ashe sunzo unguwa suna yawo damu, Abba ya mana kaca kaca yace kuma mu bawa juna haƙuri
kuma idan ya sake jin irin haka ba faɗa ba seya haɗa mana harda duka mun san kuma ze aikata. Yana da
sanyi da wasa da dariya amma fa kaifi ɗaya ne muddin yace zeyi abu zeyi dan haka muka masa alƙawarin
haka ba zata sake faruwa ba. Washe gari kuwa da mukaje makaranta komai ya wuce, dukda dai Hansa'u
na lura bata gama hucewa ba amma ni na sake gaba ɗaya ina ta janta har daga ƙarshe ta huce muka
cigaba da sabgoginmu.
Ranar Asabar Bilal yace ze zo, tun haɗuwar mu a gidan Anty Labiba be samu ya dawo ba se waya mukeyi,
sun sake komawa Abuja ance wannan watan in sha Allah albashinsu ze fara shiga harma za'a biya su na
baya da basu samu ba. Naji daɗi sosai ko ba komai maganar aurenmu zata taso masu ganin ba aure na
zeyi ba zasuji kunya. Allah ya sani ina son Bilal tamkar rai, yanayinsa da halayyar sa sun min a irin mijin
da nake fatan aure na kuma faɗa na ƙara ciki wuya ko daɗi zan zauna dashi domin shi nake so ba wani
abu ba duk wanda suke zuwa masu abin hannun da ake ganin sunfi dacewa dani ni basu gaba na shi ɗin
shi nake so kuma ina ji a jikina gaba se mun zama abinda ba'ayi zato ba duk masu gulma se sunji kunya.
Kamar ko yaushe nayi masa snacks samosa da cake se dambun nama da Anty Hasiya ƙanwar Abbanmu
ta kawo masa na ɗibar masa. Tsayin fara soyayyar mu Allah keda kullum amma duk sanda Bilal ze zo
sena masa abinci ko wani abun taɓawa da zan bashi. Tun Mama na biye mun harta fita sabgata a
cewarta abin nawa bana ƙare bane, harta kai shi ze faɗa mun abinda yake so ko in tambaye shi babu ko
sisinsa haka zanyi yazo ya cinye har ya tafi da saura balle kuma da azumi gidanmu yake shan ruwa idan
be zoba zan aika masa dashi haka in sallah tayi zan haɗa sha tara ta arziƙi a kaiwa Hajja mahaifiyarsa
sannan in haɗa masa wanda zasu zo da abokanansa suci se an samu me mutunchin gaske ne cikinsu ze
iya ɗaukar wani abu yace mun ga tukuici amma hakan ni sam baya damuna domin dan Allah nake masa
kuma arziƙin so da ƙauna.
Seda a gama jere masa snacks ɗin da kunun aya me sanyi kafin na zauna muka gaisa muna kashe juna da
murmushin ƙauna. Na cika masa kofi da kunun ayar yasha ya gode Allah yana kallona yace
"Wato Halims, bansan kalar murnar da zanyi ba ranar da aka ƙwala shelar ɗaurin aure na dake, ina ga se
na hau kan hasumiyar masallaci tsabar murna" na ƙyalƙyale da dariya nace
"Ka dai rufa mana asiri kar ace ango ya karye a garin murnar aurensa" yace
"Allah Halims baki san yanda nake jinki a raina bane kedai kawai Allah ya kaimu ranar da zan nuna miki
komai a aikace ba surutun da kike ɗauka wasa ba".
Na sadda kai ƙasa ina murmushi kawai ba tareda na ce masa komai ba, ya fara cin samosa yana mun hira
can yace "Albishirinki Halims" na ɗago na kalle shi tareda cewa
"Albashin mu ya fara shiga, an turo mana na wata uku jiya". Sosai naji farin cikin albishirin ɗin nada na
gyara zama ina cewa "kai alhamdulillah naji daɗi sosai Allah yasa albarka" ya amsa da
"Amin" yana cigaba da cin kayan gabansa. Hira muka cigaba ina jira naji ya sako zancen aiko sa rana
tunda salary ya fara shiga amma shiru hakan yasa nace masa
"Dama ko jiya Abba yake sake mun magana nace in sha Allah idan kazo zan gaya maka, to ashe ma jira ya
ƙare tunda abinda muke tsammani ya iso".
Seya shafa kansa yace
"Eh wlh, ai Baba Malam ma yace kawunku na Galadanci ya masa magana akan akwai bikin da za'ayi acan
gidan kakanninku so samu suna so a haɗa"
"Ina ga su ɗin ne, yace wai wata shida suke so a saka wancan ɗin". Ɓata fuska nayi nace "har wata
shida?" Seya kalleni yana cewa
"Kaɗan ko dai yawa?" Na faɗa ina ɓoye fuskata. Na zata ze tsokaneni akan abinda na faɗa se naji yayi
shiru dana ɗaga kai na kalleshi se naga yayi shiru yana kallon center table ɗin dake aje. Da yar damuwa
nace
"Babu komai, kawai ina tunanin yanda al'amura zasu kasance ne. Idan son samu ne ma ni nan da wata
uku ma a kawoki gida na sedai uzururrukan da suke gabana bana tunanin a shekara ɗaya ma zan iya
kammala su" ya faɗa kamar zeyi mun kuka.
"Kin san nauyin da suke kaina Halims. Yanzu fa ba tareda anyi shawara dani ba aka saka bikinsu
Fauziyyah yanzu haka a yanda akayi sa ranar saura wata biyu da sati uku bikin. Daƙyar fa na lallaɓa Baba
Malam ɗin aka maida sa ranar wata shida a lissafi na idan akayi nata kinga na sallameta sannan na koma
kan ginina na ƙarasa se azo ayi sa ranar mu idan na samu yanda nake so ma wata ɗaya ko biyu za'a saka
shikenan".
Kallonsa kawai na ringayi na kasa cewa komai, ban ma gane kan lissafin da yake ba. An saka auren
ƙanwar sa wata shida se anyi nata sannan azo a fara maganar namu a ƙalla dai shekara ɗaya zuwa da
rabi yake sake nemowa akan shekara biyar ɗin da muka kwashe. Karo na farko da Bilal yayi wani abu da
naji haushinsa har raina amma bance komai ba na sunkuyar da kai kawai ina jinsa yana cewa
"Kin san na gaya miki harda gadonta na haɗa nayi sponsoring karatu na in ba dan haka ba waye ze ɗora
mun wahalar aurenta ace se na mata kayan ɗaki dole?"
"Zaka mata mana tunda ai bata da wani yayan da ze mata bayan kai. Kaine makwafin mahaifinta a
yanzu" na faɗa murya a ciki, se yace
"Haka ne idan ina dashi zan mata amma a halin da nake ciki yanzu nima ai ban tsaya da ƙafata ba ga
kuma tawa wahalar a gabana. Se yanzu nake dana sani lokacin da Alhaji Lawan yace muyi musanye na
bashi kango na ya bani wani gida complete dana karɓa canjin nayi wani abu dasu ƙila da tuni yanzu mun
haifi Nur da Nurain ko?" Ya ƙarasa da sigar tambaya. Ɗan murmushi kawai nayi yaci gaba da surutan da
duk uzururrukan sa da basa ƙarewa ne kullum yana so yayi kaza da kaza kafin ayi waye da waye jin yanda
nake amsa masa maganganun yasa yace mun
"Ko kin fara jin bacci ne naji kina amsawa daƙyar?" Se kawai nace masa eh". Yayi murmushi yace
"Karki damu Halims, in sha Allahu komi ya kusa zuwa ƙarshe kinji jinkirin kuma ze zama alkhairi".
Murmushi kawai nayi na miƙe ganin shima ya miƙe tsaye, muna tafe yana cigaba da surutansa ina binsa
da toh har muka je get. Seya juya ya kalleni yana murmushi yace
"Duk yanayinki ya canza mana ko akwai wani abu da baki gaya mun ba?" Ya ƙarasa yana jingina da ƙofa
tareda langwaɓe kai yayi kalar dake sake wujijji gani cikin soyayyarsa. Sena sauke kaina ƙasa dan ma
karya yaudare ni. Ya cigaba da cewa
"Kici gaba da yi mun addu'a kinji in sha Allah zan baki mamaki"
"Toh, Allah yasa" Na bashi amsa. Yaso ya sake jan hirar amma na bashi uzurin kaina namun ciwo ya tafi.
Seda na tattare sauran snacks ɗin na kai kitchen kafin na samu Mama a falo suna kallo dasu Imam. Gefe
na samu na zauna ina ɓata fuska sau ɗaya Mama ta tambayeni meya faru nace babu bata sake cemun
komai ba.
Wayata dana saka caji ta shiga ƙara daga ringing tone ɗin na gane shine hakan yasa na zareta na wuce
ɗaki. Sama sama na ringa amsa masa maganganun da duk kame kame yake can yace mun
"Seda naje aje mashin na shafa naji babu komai nace yau Halims tayi mantuwa"
"Baki packaging mun sauran snacks ɗina ba, sannan abincin ma an manta dashi". Dariya da mamaki ya
bani lokaci ɗaya amma se kawai na bishi da cewa
"Ko na aiko a karɓa dan kin san da zan fita ma cewa Hajja nayi kar a ajiye mun abinci" ya sake faɗa, ban
san lokacin da nace masa
Mamaki sosai ya kamani, wato dama abinci ya biyo baya lallaima Bilal.
Mun saba a ƙalla koda yazo zance idan ya tafi kafin kwanciya bacci se munyi doguwar waya har se na
fara bacci haka da Asuba shi ze tashe ni amma yau har na gama shirin tafiya makaranta banji wayarsa ba.
Dake ban saba ba duk se abin ya dame ni na manta ma da fushin da na farayi hankali na ya sake tashi
dana kira layinsa naji a kashe. Gaba ɗaya wunin ranar sururu nayi shi kowa ya ganni seya tambayi ko
bani da lafiya ne haka dana dawo ƙarshe kawai nacewa Mama kaina ke ciwo na shige ɗaki naci gaba da
kiran wayar Bilal amma har sannan ƙarfe biyar a kashe. Hansa'u na kira dan dama bata shiga makaranta
ba ita bayan mun gaisa nace mata tazo dan Allah idan bata komai,
"Wlh lalle aka samun na ɗauka kema zaki zo ai ko kin fasa" ta bani amsa. Shaf na manta gobe za'a fara
bikin Zainab dake tunda mukayi faɗa da Hansa'u ta ara ta yafa ni kuma da muka shirya banma bi takanta
ba tunda tun asali dama ai shishshigi yasa ta shigarwa ƙawata faɗa bayan munfi kusa. Ko ankon dan dai
mun rigada mun siya ne amma da bazan ba.
"Kina ina?" Na tambayeta ta bani amsa da tana gidansu Ummi me lalle se kawai na zura hijabi na Mama
na mitar lallen se yamma sakaliya zan tafi me yasa bazan bari se da safe ba tunda bazani makaranta ba
nace mata ai baƙi za'a mun ba ja ba. Naji daɗi da na samu Hansa'un ita kaɗai sauran duk an cire musu
sun tafi kangon da za'ayi Hennah party, tas na kwashe yanda mukayi dashi jiya na gaya mata ta gama
saurarona tayi shiru nace
"To me zance Halima? Ni da kika ce in cire baki na daga sabgarki da Bilal yanzu kuma in ce wani abu ki
canza mun ma'ana?" Ta bani amsa. Se nayi tsaki nace
"Ke matsalarki ruƙo wlh ba komai ya rigada ya wuce ba kuma? Dan Allah ki bani shawara me ya kamata
nayi? Wlh ji nake kamar nayi ta kurma ihu wlh ko abinci wlh daƙyar na iya shan tea ji nake komai ya
tsaya mun"
"Lallai kinyi nisa to Allah ya taro ki" ta faɗa tana cire lallen hannunta. Zanyi magana wayata tayi ƙara,
seda na sauke wawiyar ajiyar zuciya kafin na tashi daga kusa da ita inaji tana cewa
"Ai dama kin ƙarasa zubar da ajin ya taka wlh, ai dai Halima kin bada mata Allah ya yafe miki kawai".
Gefe can na koma na amsa, shiru nayi ina jinsa yayi sallama seda ya maimaita sau biyu kafin na amsa.
"Ina kika tafi?" Ya tambayeni kamar wani Babana. Na tura baki nace
"Gidan lalle"
"Ya miki kyau, to gani a ƙofar gida ya za'ayi yunwa nakeji na taso daga aiki naje gida kawai naga wai tuwo
Hajja tayi da miyar kuka fa" ya faɗa. Sena rasa me zance masa ma, wato saboda anyi abinda baya ci a
gidansu shiyasa ma ya kirani da haka nan ne baze kira ba yake nufi ko me?
"Hello" ya faɗa jin nayi shiru sena sauke ajiyar zuciya nace
"Ina zuwa toh" na miƙe ban ko cewa Hansa'u na tafi ba na wuce gida. Yana jingine jikin lifan ɗin sa
kamar kullum cikin gayu irin na yan birni idan ka ganshi da yanayin shigarsa zaka ce ɗan wani hamshaƙin
mai kuɗi ne. Wuce shi nayi na gida, ta ƙofar kitchen ta baya na shiga. Muma tuwon mukayi amma da
lafiyayyar miyar ɗanyar kuɓewa data ji naman rago. Seda na ɗumama miyar kafin na zuba a flask na ƙulla
manshanu a leda da yajin daddawa sannan na shirya komai cikin basket me murfi na haɗa masa da
kwalin exotic ɗaya da robar ruwa. Ina zuge basket ɗin Mama ta shigo kitchen ɗin, kallo ɗaya tamun ta
girgiza kai kawai ta fita nima sum sum na fice kamar wadda aka kama tayi sata, koda yake satar ma nayi
ai.
Tabbacin abinda ya kawo sa kenan ina miƙa masa basket ɗin ya ɗora a gaban mashin ɗin ya hau ba
tareda yace mun komai ba ya amsa key ya bar gurin, tsabar mamaki da al'ajabi kawai na bishi da kallo se
naji zuciyata ta karye banma sani ba ashe hawaye sun ɓalle mun seda na fara ganin dishi dishi kafin na
ankara.
*(Based on true life event, some parts are fictional to spice up the story)*
*Wattpad @MaryamahMrsAm*
*Ban yarda wani ko wata ya juya mun labari ta kowacce siga ba tare da izini na ba*
*Kuɗin karatu yana wakiltar mutum ɗaya ne, kiji tsoron Allah karki ɗauki hakkina ta hanyar fitar mun da
littafi*
*KURA A RUMBU littafin kuɗi ne, a biya naira 800, biya a asusun*
*1840175439*
*Access bank*
*PAGE 3*
Ranar ina idar da sallar isha'i nayi bacci saboda ɓacin rai seda na farka da asuba sannan naga missed calls
ɗin Bilal guda biyu ya kirani tun ƙarfe tara na dare. Duk yanda nake cike da haushin abinda yamun jiya
amma haka nan zuciyar dake sonsa ta angiza ni nabi kiran nasa. Murya ƙasa ƙasa muka gaisa ya shaida
mun yana masallaci idanya fita ze kirani. Ko yasan ina fushi dashi ne se gashi bayan ya fito masallacin ya
kira mun daɗe muna hirar soyayya nan da nan kuma na ware daga fushin na manta da komai. Har Mama
seda ta lura da sauyina kan yanda na kwanta jiya na tashi cikin walwala wunin ranar kuwa haka nayi shi
ga farin cikin gobe juma'a zamu kammala jarabawa. Safiyar Juma'a tun ƙarfe shida na shirya cikin rigar
da mukayi ta graduation. Nayi kyau matuƙa ina kallon kaina a mirror a raina ina yarda da maganar Bilal
da yake yawan faɗin ni kyakykyawa ce dukda ba wai ina da irin shahararren kyau ɗin nan bane na fitar
hayyaci komai nawa ya dace da zubin halittata I'm just too cute.
Nayi mamakin tarar da Bilal a ƙofar gidanmu ba dan dama yana kaini makaranta idan yana da lokaci
amma dake munyi magana na tambayeshi ko zeje mun sign out yace aa shiyasa nayi mamaki dana
ganshi jingine jikin mashin ɗinsa yana ta buga mun murmushi. Ina ganin Hansa'u sun taho da Zainab
Amarya data rufe fuska da niƙan yau zamuyi final exam kuma yau ne kamun bikinta gobe ɗaurin aure na
ɗane Lifan ina ɗaga musu hannu muka wuce. Bilal be tafi ba seda muka fito, shi ya fara mun signing a
farar rigata ta sign out muka sha hotuna sannan ya tafi muka cigaba da budurinmu har zuwa ƙarfe sha
biyu kafin muka wuce gida.
Jakata kawai na aje na ɗauki yan abubuwan da zanyi amfani dasu nayiwa Mama sallama muka wuce
gidan kwalliya dan ma mun kama layi dama ƙawar mu ce me kwalliyar. Kusan mu bakwai mukaje, seda
mukayi sallar azahar muka ci awara kafin aka farayi dake mutum biyu ne kafin karfe huɗu ya rage ni da
Hansa'u kawai. Muna zaune saurayin Baby Isma'il ya kirata a lokacin ita akeyiwa kwalliyar dan haka ta
saka wayar a speaker. Na taɓe baki jin muryar saurayin da take mana kuri dashi, daga muryarsa na
hasaso garan ƙauye ne. Uzuri ta bashi akan ana mata make up ne yace
"Zakije kwalliya amma baki gaya mun ba?" Se ta bashi amsa da "kayi haƙuri, munyi magana jiya ai na
gaya maka yau kamun Zainab ko ka manta"
"Anyi haka, yanzu a ina kuke kwalliyar na gani ko zan samu zuwa na kaiki gurin bikin?" Ya tambayeta ta
gaya masa daga nan sukayi sallama bayan yace ze sako mata kuɗin kwalliyar yanzu. Suna aje wayar ko
minti biyu ba'a yi ba wayarta tayi ƙara alamar shigar saƙo, Zulaiha dake ɗaukar hoto da wayar tayi ihu
tana nuna tace
"Duk kunci albarka ci zan biya muku harda amarya" dama kwalliyar tamu 2k ce ta amarya dubu biyar
gaba ɗaya in akayi total kuɗin ya kama dubu goma sha uku kenan suka shiga mata godiya ban da ni da
seda Hansa'u ta taɓa ni kafin nace nagode.
Ko a jiki na, ba rainawa nayi ba ko hassada nake mata Aa kawai tunda mukayi faɗa da Hansa'u suka bi
bayanta shikenan nima naja baya dasu, badan itan bama yanke alaƙa zanyi dasu dan duk wanda ya nuna
baya so na da Bilal babu ni babu shi balle kuma naga suna wani fariya akan su samarinsu masu kuɗi ko
da zamu taho daga makaranta saurayin Zulaihan ne ya dawo damu tana ta wani kauɗi bayan idan da
naga damar kula samari saboda abin hannunsu kaf cikinsu babu wadda ta isa ta goga kafaɗa dani ko a
yanzu alhamdulillah babu abinda Abbana be tsare mun ba shiyasa wani abun hannun samari baya
burgeni su suka dogara dashi da har suke kula mutanen da kana gani kasan badan so bane ba. Niko Allah
ya rufa mun asiri na samu me sona ina sonsa zamu mori ƙuruciyarmu tare.
Tsaf muka gama kwalliyar mu, munyi kyau sosai aka mana hotuna kafin muka fita inda motar da ango ya
turo ta ɗauki amarya ke jira. Saurayin Baby ya iso dan haka ta shiga motarsa Zulaiha ma saurayinta ne
yazo ɗaukar ta se ni da Hansa'u ne muka shiga motar amarya muka tafi. Bayan an sauke mu kowacce
seda saurayinta ya bata kuɗin da zatayi liƙi dashi har Hansa'u muna hanya da Alhaji Bala ya kirata seda
yayo mata transfer kuɗi masu nauyi kan tayi kwalliya da liƙi haka akayi kamu aka tashi suna ta wanke
amarya ni dai dana liƙa abinda na tanada dama na koma gefe na zauna seda aka tashi zamu tafi gida
kafin har raina naji babu daɗi ganin still kowacce saurayinta ne ze maida gida suna ta zuzutun kwalliyar
su. Kira uku nawa Bilal yace mun ze zo amma gashi har aka tashi shiru dana sake kiransa ma naji wayar a
kashe. Wannan ya ɓata mun rai ban ko tsaya jira a gama watsewa ba nabi yan unguwar mu a Adaidaita
muka tafi.
A ƙofar gida na tarar da Bilal tareda abokinsa Nura, duk da naji haushin ƙin zuwan da yayi gurin bikin
amma ganin dana masa se naji zuciyata tayi sanyi. Light blue ɗin shadda ya saka data dace da atamfar
ankon da mukayi me ruwan dark blue da ratsin fari da light blue ɗin. Na isa inda suke Ina haɗe fuska a
son na nuna masa ɓacin raina amma na kasa musamman da Nura ya fara zolayarmu wai munyi too
match dama mun haɗa baki ne amma gamu nan tamkar ranar auran mu. Haka na lalace a tsaye yana
tsarani har seda Abba ya dawo kafin na wuce ciki su kuma suka tafi bayan sun gaisa dashi.
Ina tsaka da sallar magriba da isha'i da suka haɗe mun Amirah ta shiga ɗakin tana faɗin nazo inji Abba.
Bayan na shafa addu'a na fita falo, Abba ma zaune yana kallon labaran ƙarfe tara. Seda aka tafi hutun
rabin lokaci kafin ya juya kaina yana murmushi yace
"Hali dubu" haka yake tsokanata. Sunan babbar yayarsa ne kuma mafi soyuwa a gare shi cikin yan
uwansa. Kwanana uku a duniya ta rasu seya haɗa soyayyar ta data kasancewata yar da ya fara samu duk
yake mun.
Murmushi nayi kaina yana ƙasa na gaishe shi yana amsa yana tambayata biki kafin ya ɗora da cewa
"Yaya Salahu ya gaya mun sunyi magana da kawun Bilal yace ze kirashi duk yanda ake ciki ɗazu yake sake
ce mun kimanin sati biyu kenan har yanzu beji daga gare su ba". Sena rasa abinda zance masa, ina ji yaci
gaba da cewa
"Ɗazun har zan tsaya nayi masa magana da kaina se kuma sai nace bari na fara jin ta bakinki ko dai
saƙon be iske shi ne". Daƙyar nace
"Eh Abba ya gaya masa. Dama maganar albashinsa da be fara samu bace ta dakatar dashi" se Abba yace
"Aa, har yanzu dama wannan matsalar bata kau ba? Na zata dana haɗashi da Malam Mansur yace mun
an gyara komai tun last two or three months kenan da mukayi maganar.
"Eh Abba an gyara amma salaryn ne wai se wannan watan sannan suka sa masa na wata uku" na faɗa
masa iya abinda na sani, se yayi shiru kafin yace
"Ikon Allah, to barka tunda an gyata ɗin. Yanzu ina kuka tsaya kenan a maganar?"
"Yace zuwa ƙarshen watan nan zasu zo" na faɗa ya amsa mun da
"Toh Allah ya nuna mana. Yaya Salahu ya damu, kin san fa babu sanda zamu haɗu ba tareda yayi mun
mitar ƙin aurar dake ba. Kullum se yace ga Bishira nan da yaya biyu bayan rana ɗaya aka haife ku"
"To ita Abba ai muna gama secondary aka mata aure bata cigaba da karatu ba" na faɗa cikin shagwaɓa
yayi dariya yace
"Haka ne amma dai da kema anyi miki ta tatan da yanzu kin fara tara mana masu samu bari bari a gidan
nan ai". Sena rufe fuska ta da hijabi ina cewa
"Haba Abba ni yar yarinya dani ai dama ban isa aure ba har yanzu"
"Baki isa aure ba amma kin iya dafawa gardi abinci" Mu'azzam daya shigo falon ya faɗa, na galla masa
harara ina cewa
"Se dai in ce ya dena tsokanarki amma babu batun na miki tsakani da ɗan uwanki" Abban ya faɗa nace
"Gaskiya ce bakya so kuma se an faɗa, har gulmarki ake a unguwa da anga yara da kula za'a ce daga
gidan nan ne" Mu'azzam ɗin ya sake faɗa kafin nace wani abu Abba yace
"Ciyar da mabuƙata ba. Kai kake bin bayanta Alhaji shiyasa kullum take sake shiga daji maimakon ta
dawo hanya" Umma data fito daga ɗakinta ta faɗa sena miƙe na sulalae ɗaki na barsu inaji Abban na
kareni yana faɗin ai ba laifi bane idan na bashi da babu ai ba za'a masa ba.
Washe gari akayi ɗaurin auran Zainab a ranar kuma muka rakata gidanta mw kyau acan sabuwar gandu.
Mijinta matashin ɗan kasuwa ne yayi ƙoƙari sosai a gininsa iyayenta ma sunyi namijin ƙoƙari gurin yi
mata kaya da suka sake ƙawata gidan muka fito munata santi da yiwa juna shaƙiyancin wacece next. Duk
su uku da ranar su ni kaɗai ce amma dukda haka a jikina inajin sena rigasu amarcewa domin dai nasu
samarin a yanda suke ko yau akace a fito ayi aure kowanne yana da abin yin auren amma sun tsaya suna
jan lokaci har da Hansa'u da zataje a ta huɗu.
Kusan sati uku da suka biyo baya ina ta juya yanda zan sake ma Bilal magana ganin bamu daɗe dayi ba
kuma ha uzurin daya bani se naji dama Abban ya amsa maganar da kansa kawai dan harga Allah yanzu
dana gama makaranta bana komai hankalina ya fara komawa akan nima nayi aure na tafi nawa gidan.
Safiyar litinin Anty Labiba ta haihu, ina bacci Mama ta tashe ni wai zamuje asibiti daga can kuma bayan
an sallameta muka wuce gida Mama tace in zauna mata kwana biyu, ban so ba amma babu yanda na iya
haka na tafi gida na haɗo kayan da zanyi amfani dasu na kira Bilal ya mayar dani.
Seda nayi mata sati biyu, dake morata takeyi bata damu da zaryar da Bilal ya ringayi ba kullum se yaje
anan zeci abincin dare ko kuma yazo da yamma idan ya taso daga aiki mu ɗanyi hira ya karɓi abinci ya
tafi, duk zuwan da yakeyi kuma sau ɗaya ya samu ya shiga ya yiwa Anty Labiba barka dan kusan duk
sanda zezo tana da baƙi yan barka dake ta kwana biyu bata haihu ba tsakanin Amir da Inayah shekara
ɗaya da rabi ita kuma ta bawa Sadis shekara biyu tun nan kuma seda ta shekara bakwai yanzu ta haifi
Amina takwarar Mama. Ba ƙaramar kunya naji ba sanda Bilal ya gama zamansa a falon Antyn ya tafi ba
tareda ya bada ko sisin kwabo da sunan barka ba. Dama tun kafin suna dana ke masa hirar me ya kamata
mu siya na takwarar da akawa Mama ya fara kawo zancen wata yazo ƙarshe har yanzu ba'a fara salary, a
zato na ze bada wani abu amma se gashi ya tashi ko asi dukda uban naman suna da abincin da na jibga
masa har yan gidansu seda suka ci.
Kwananta goma sha shida da haihuwa na koma gida saboda wata ƙanwar Mijinta bazawara data zo daga
zaria, sena fake da zanje na maida kaya na na ɗebo wasu daga nan na fece ba komai ya saka hakan ba
kuma illah Munir dake neman takura rayuwata yana kuma haɗa ni faɗa da Bilal. Ranar talata na koma
gida Bilal baya gari yaje Jos mijin ƙanwar Hajjan su ne ya rasu babban mutum ne sosai shine duk suka
tafi. Ranar alhamis zasu dawo tunda suka tafi kullum mukayi waya kwana uku kacal amma ya ringa mitar
yayi missing Kano yayi missing abincin Kano ze kace wanda ya tafi wata ƙasar ta daban. Ran da ze dawo
tun safe na tashi da shirin yi masa girki, na yi da ɗan yawa tunda duka tare da Hajja da yayyensa mata
biyu da ƙaninsa ɗaya suka tafi se matar wansa nasna kuma duka a gidan Hajjan zasu sauka kan kowa ta
tafi gidansu. Ina aikin Mama namun tsiyar da sakani tayi se nayi ƙorafin abincin yayi yawa amma dake na
Bilal ne na zage inayi sedai kawai nayi murmushi har na gama na shirya komai nayi wanka a Adaidaita na
ɗauki Amirah muka tafi gidan bayan munyi waya ya gaya mun sun dawo.
Ba wannan ne zuwa na na farko gidansu Bilal ba, badan ma Mama ta kafta mun warning ba da haka nan
ko faɗa mukayi na kirashi a waya be amsa ba zan zari jiki in tafi, tun Hansa'u na rakani har ta dena
yanzun ko nasan ko giyar wake nasha bazan cw tazo muje ba shiyasa ma naja Amirah ko Maman ce mata
nayi Aliyu me Adaidaita zan bawa ya kai musu ni kuma zan wuce gidan kitso badan ba nasan ba zata bari
in kai abincin da kaina ba. A kuyance muka gaisa da yan gidan nasu suna ta nan nan dani kamar su
goyani ban wani jima ba nayi musu sallama muka fita se da muka fito waje kafin naga Bilal dan sanda
muka je ance yana ɗakinsa yana wanka. Se naga kamar ya rame a kwana ukun da ban ganshi ba, ya
jingina jikin bango yana kashe ni da kallon so yace
"Oh da ka ɗauka da wasa nakeyi? Ai na gaya maka zanzo nawa Hajja gaisuwa dama" na bashi amsa seta
miƙe tsaye sosai yana cewa
"Kin san ruwan tea kaɗai nasha muka kamo hanya, ina kwanukan kuma na ganki ke kaɗai?"
"Cikin gida kuma? Abincin nawa kika kai mun cikin gida Halims? Maimakon ki buga mun ƙofa ki ajiye a
nan kafin ki shiga?"
Se naji abun wani iri amma na kanne nace
"To banda abinka dama abincin ai ba kai kaɗai nayiwa ba kuma yana da yawa zasu ɗiba nasu su rage
maka"
"Ragowar wasu zanci kenan?" Ya faɗa kamar a fusace, se kuma yayi shiru na tsaida idona akansa ina
karantar yanayin fuskarsa, se kuma yayi murmushi yace
"To an gode My Halims Allah ya bada lada. Bari na shiga ciki muyi sallama da Yaya Zubaida nasan yanzu
zata wuce se nazo na raka ku". Gefe muka tsaya kusan minti biyar ya fito kamar ransa a ɓace, Adaidaita
ya tare mana muka shiga ganin ya tsaya be shiga ba yasa na kalle shi nace
"Zanzo kawai anjima, yanzu zanje gidan gidan Muslim ne naga ko zan samu abinda zanci dan yunwa
nake ji sosai wlh". Da mamaki nace
"Sun cinye, kin san duk bamu wani tsaya munci abinci ba muka taho shiyasa dama da a gurina kika ajiye
na ɗiba nawa se na kai musu sauran".
Harga Allah seda naji wata kunta ta kamani amma kuma yunwar da yace yanaji ita ce a gabana yanzu
dan haka nace
"Amma basu kyauta ba, to ko muje gida se na dafa maka ko indomie ce. Matar Muslim dake fama da
kanta babu lallai ai tayi girki ma". Seda yayi jimm kafin yace
"Amma ba zaki wahala ba? Kin gama wannan girkin ki sake yin wani?"
"Dafa maka abinda zaka ci kake kira da wahala?" Na faɗa ina langwaɓar da kaina ina kallonsa. Me
Adaidaitan ya kalla kafin yace
"Shikenan nan, kuje bari na canza kaya se na taho" ya ciro ɗari biyar daga aljihunsa ya bawa me
Adaidaitan, seda ya karɓi canji kafin ya koma cikin gidan mu kuma muka wuce. Kallona kawai Mama tayi
sanda nake gaya mata zan sake dafawa Bilal abinci wancan da aka kai musu ya ƙare,
"Wato gidansu kika je? Ke wace irin yarinya ce mara jin magana anya Halima kina son ki siyawa kanki
ƙima da mutunchi a idon dangin Bilal kuwa? Banda ke sakarya ce a ina kika taɓa ganin mace na zirgilli
irin haka akan namiji?" Mama ta faɗa cikin ɓacin rai, nayi ƙasa da kaina kawai na kasa ce mata komai ta
cigaba da bambamin faɗa kafin ta wuce ɗaki, seda ta kullo ƙofa sannan na wuce kitchen jiki na rawa na
ɗora masa Indomin. Kaji biyu na saka a abincin da na musu ɗazu, dubu biyar Abba ya bani yace nayi
cefane harda lemo katan ɗaya da ruwa shima katan na siya musu. Seda na duba freezer babu sauran
nam se kifi, Bilal baya son kifi dan haka kawai na daga masa ita da karas da kabeji na soya masa ƙwai
guda huɗu. A falon Abba na shirya komai, seda na fita tsakar gida zan wanke kayan da nayi amfani dasu
dan famfon cikin kitchen ɗin ya lalace se na gashi tsugunne gaban Abba suna magana.
Ban sam me suka tattauna ba na koma ciki bayan ya shigo seda ya cinye indomin tas yasha lemo kafin ya
kalleni yana murmushi yace
"Dole ai, ka sha tafiya ga yunwa kuma ai kayi ƙoƙari ma" na faɗa ina murmushi se yace
"Yanzu Abba yake mun magana. Ai ma zata ma kin gaya masa abinda na sanar dake se yace mun wai kin
ce masa ƙarshen wata za'a zo gashi watan ya mutu wani ya kama shima harya ƙare shiru me yasa zaki
masa ƙarya?"
Kallonsa nayi jin abinda ya faɗa wai nayiwa Abba ƙarya, bance masa komai ba na maida kaina ƙasa ina
jan zaren mayafin jikina ina jinsa yana cewa
"Kin kasa fahimtar abinda nake gaya miki Halima. Bawai bana son azo maganar saka ranar nan bane aa
ina duba abubuwan da suke gabana daya kamata na kammala kafin ace an fara maganar aure. Yanzu
idan akayi sa rana kowa ze tada hankalinsa ne da son jin yaushe za'ayi biki, da zarar an ɗan samu akasi
an ɗaga daga sanda aka faɗa se kiji maganganu su kansu iyaye zakiga sun ɗauka kamar mutum ya shigo
da shiririta cikin abun. Ni yanzu babban abinda yafi tsayamun shine na kammala gini na kin san kuma dai
gini abu ne me buƙatar tana di da lokaci dan ko da kuɗin a zube kin san aikin gaggawa baya ƙarko"
"Haka ne" na faɗa ina kallonsa ƙwaƙwalwata na son bawa maganganun sa ajin daya dace dasu. Yaci gaba
da cewa
"Kin san ina da taste, akwai plan ɗin dana tsarowa gini na da idan yanzu nace na katse ko na canza da
wani abu daban baze bada yanda ake so ba. Kinga ginin nan shi kaɗai ne nake so ace na kammala duk
wata sauran hidima za'ayi abinda ya samu ne na sani lefe ma zaki iya yafe mun ko My Halims tunda
dama ke ai kullum cikin sababbin sutura kike ko waɗannan na jikinki ma ai ban taɓa ganinki dasu ba" ya
ƙarasa yana wata dariyar data ƙular dani, kafin nace wani abu ya tareni yana cewa
"Wannan bayanin nake so kiyiwa Abba nasan zw fahimce ni tunda ina da hujja me ƙarfi ko shi Baba
Salahun idan aka fahimtar dashi ze gane".
"To amma Bilal me ze hana ka kama haya mana ko da na shekara ɗaya ne pending ka ƙarasa ginin naka?
Na faɗa bayan dana gama jin nasa uzurin, seya wani kalleni kamar wadda na faɗa masa mugun abu yace
"Haya? In kama haya fa kike cewa Halims? Yanzu ke ba zakiji kunya ace gidan haya aka kaiki ba?"
"Wace irin kunya kuma Bilal mutane nawa suke rayuwa a gidan haya? Ita kanta hayar ai se wanda ya isa
ne ma yake da hali ze kama naga wasu sedai su nemi a basu aro" na bashi amsa ina ɓata fuska seya
girgiza kai yace
"No Halims wace irin haya ana zaune ƙalau se kace matsiyaci. Mu gama zagin abokananmu saboda
rashin zuciya sun kasa mallakar gidan kansu se kuma kawai nima na ƙare a haya bayan Allah ya rufa mun
asiri ina da yanda zanyi"
"Oh ashe ma kana da yanda zakayin niyya ce kawai bakayi ba ko kuma nace auren nawa baka shiryawa
ba. Da kuma zaka ce tsiya ce take sakawa ayi haya har kana zaginsu wasu da hakan shi muhalli tamkar
rabon haihuwa da silar mutuwa Allah ke saukar dasu don yanda kaso da faruwar su ko kauce musu baka
da wayo baka da dabara akai kuma idan Allah yaso ya nuna maka iyakarka seya jarabce ka kaima duk
arziƙin ka ya hanaka mallakar gidan kan naka. Mutane nawa keda rufin asiri amma har suka mutu suka
ƙare rayuwar su a gidan haya? Ka fito fili kawai ka faɗa mun abinda yake ranka game dani domin na fara
gajiya da uzurin ka da basa ƙarewa kullum da wanda zaka zo dashi to kawai ka faɗa mun matsayar
maganar mun, idan yi yi idan bari bari kawai nagaji da sa banga ƙaho ba Bilal" na faɗa ina miƙewa tsaye.
*(Based on true life event, some parts are fictional to spice up the story)*
*Wattpad @MaryamahMrsAm*
*Ban yarda wani ko wata ya juya mun labari ta kowacce siga ba tare da izini na ba*
*Kuɗin karatu yana wakiltar mutum ɗaya ne, kiji tsoron Allah karki ɗauki hakkina ta hanyar fitar mun da
littafi*
*KURA A RUMBU littafin kuɗi ne, a biya naira 800, biya a asusun*
*1840175439*
*Access bank*
*PAGE 4*
Ban yarda da gaske Bilal yake da yace ze turo saka rana ba se ranar Juma'a da Baba Salahu yazo gidan
mu bayan sun gama maganar da za suyi da Abba yasa aka kirani. Seda muka gaisa kafin cikin tsare gida
kasancewar sa me ɗan zafi ya kalle ni yace
"Ranar lahadi idan Allah ya kaimu iyayen yaron da yake neman ki suka ce zasu zo saka rana, ina fatan da
sanin ki?".
Duk se na duburburce, abun yazo mun a ba zata domin banyi tsammanin faruwar hakan ba. Waccen
ranar birkice masa nayi dagaske, duk yanda ya so ya lallaɓa ni naƙi biyuwa ƙarshe na kore shi nace karya
sake zuwa in da nake tun da ba aure ya shirya yi ba na gaji. Haka ya tafi yana waige na kuma na kashe
wayata, dukda se da nayi kuka tamkar raina ze fita zuciya ta ringa ingizani dana kira shi amma dake har
raina na shirya motsawa in tabbatar da matsayina a gurin Bilal tilas na jure.
Zuwan sa uku bayan nan bana fita na kuma yi blocking ɗin sa a wayar Mama tun da ya kira sau ɗaya, sati
ɗaya kenan yau daidai se gashi Baba Salahun ya zo mun da labari mafi daɗi a kunnuwana.
Sun kunyar da kai nayi ina murmushin dana kasa hana kai na, Abba dai kallo na kawai yake yana
murmushin shi ma, seda Baba Salahu ya sake maimaita mun tambayar kafin cikin jin kunya nace
"To madalla, dama abinda nake so na tabbatar kenan da yardar ki kafin su zo saboda kin san ni bana
ɗaukar shaƙiyanci irin naku na yaran yanzu. Se anyi magana ta manya daga baya kuzo da wasa shi yasa
kafin manema su zo se na tabbatar da amincewar yarinya yan da zan ci ƙaniyar duk wadda ta dawo zata
kawo mun iya shege. To Allah ya sanya alkhairi ciki yasa zamu ga lokaci". A zuciya ta na amsa da "Amin"
Abba ya amsa a fili daga nan ya sallame ni na fice. Tsabar murna ban san lokacin dana daka tsalle na
rungume Mu'azzam da mu ka ci karo da shi ze shiga falon ba, ya ture ni yana cewa
"Alhamdulillah Allah lokaci yayi na kusa zama matar Bilal" na faɗa cikin maɗaukakiyar murna kafin na
zube a gurin nayi sujjadar godiya.
Mu'azzam ya zabga tsaki yace
"Se kace wadda zata auri wani Bilal ɗin farko, rabon shan wuya yasa kika kafe yarinya amma dai Allah ya
bada sa'a". Kan na amsa shi na jiyo Abba na cewa
"Kai Ibrahim wace irin magana ce wannan?" Sena fake shi na zabga masa mari a ƙeya kafin na kwasa da
gudu nayi ɗakin Mama ina cewa
"Ɗan baƙin ciki se dai ya haɗiyi zuciya ya mutu". Bama ga muciji da Mu'azzam kasancewar mu sakwanni
ga kuma banbancin hallaya. Yana da zafi ji yake ma kamar shine sama dani ko dan ya kere ni a girma ni
kuma gani da son girma ina so yanda yake ƙanina dole ya bini kamar yanda nake juya Imam da Amirah
na uku data huɗun mu.
Mama na zaune tana lazumi na faɗa jikinta ina ci gaba da ihun murna, se da ta ture ni kafin tace
"Mama ki tayani murna jibi Bilal ze turo a saka mana rana" seta saki baki kawai tana kallona ni da kaina
na fahimci wauta da rashin kunyar da nayi se kuma na miƙe na fice daga ɗakin da sauri ina dariya ina jin
ta tana cewa
Seda nayi rawa nayi juyi akan gado kafin na dire na ɗauki wayata, tun da na kashe ta ban sake bi ta kanta
ba. Na kunna kafin ta gama booting ta kawo ji na ringayi kamar na damfarata da ƙasa ko zata fi sauri ina
danna lambobin Bilal naji sallamar Hansa'u a falo se na fita da gudu, Mama da suke gaisawa ta kalle ni
tace
Baki na kamar gonar auduga na rungume Hansa'u Mama ta girgiza kai kawai ta shige kitchen ta barmu.
"Albishirinki ƙawata" na faɗa ta amsa da goro, nayi fari da ido kafin na shaida mata jibi za a yi sa rana ta
da Bilal. Tayi jumm da farko kafin kuma ta saki murmushin da na tabbatar be kai har ƙasan ranta ba tace
"Na tayaki murna ƙawata, Allah ya tabbatar da alkhairi ya nuna mana lokaci"
"Amin Hansy, amin" na faɗa ina sake laluben lambar Bilal. Muryar Abba da Baba Salahu da na jiyo suna
fitowa daga can falon tasa na miƙe ina ce mata
"Muje ɗaki". Ta ringa kallo na kawai na kira Bilal, se da wayar ta kasu katsewa kafin ya amsa murya ba
amo sosai.
"Ba ni da lafiya Halims, kewarki zata hallaka ni" ya faɗa kamar irin wanda yake gargadar mutuwa bayan
dana tambaye shi me ya faru naji muryarsa a ƙasa. Take hankali na ya tashi, na miƙe daga zaunen da
nake ina cewa
"Me ya same ka? Tun yaushe? Shine baka gaya mun ba?"
"Ta ina zan same ki bayan kin kashe wayarki kin yi blocking ɗi na a wayar Mama sannan zuwana uku duk
baki bari na ganki ba?, ni dai ki yafe mun kawai idan na mutu dan yan da nake ji kamar bazan tashi ba"
ya sake faɗa yana sakin numfashi ban san lokacin dana fashe da kuka ina cewa
"Haba dan Allah kar ka mun haka, kana ina yanzu? Kaje asibiti ko kana gida?"
"Ina gida Halims bazan je asibiti ba tun da na fahimci rayuwa ta ki ke nema gara kawai na sauƙaƙa miki in
bar miki duniyar se ki fi jin daɗi kamar yanda kika ce na fita daga rayuwar ki". Ban tsaya sake jin abin da
ze faɗa ba na kashe wayar na figi jaka ta dake kan gado nayi ƙofa, Hansa'u ta biyo ni tana tambaya ta
lafiya amma ban tsaya ba na nufi get se kawai ta biyo ni. Se da muka hau adaidaita kafin cikin kukan da
nake na gaya mata Bilal ne bashi da lafiya. Bata iya riƙe kanta ba ta zabga tsaki tace
"Bilal bashi da lafiya Halima shine kika riki ce haka kina kuka?"
"Ban gane na riki ce ba? In ce miki mijin da zan aura bashi da lafiya har ki tambayi ba a sin rikicewa ta ko
kuka?" Na hayayyaƙo mata. Se ta sake yin tsaki tace
"Wlh ƙarya yake, yanzun nan daga gidansu Maryam Abdullahi nake har gaisawa mukayi yana ƙofar
gidansu suna hira da Abokanan sa".
Nayi mata banza ina ci gaba da share hawaye tun da ba son sa take ba ai dama komai ma daya shafe shi
zata ce ƙarya ne. Ban ko tsaya karɓar canjin adaidaitan ba na wuce ƙofar ɗakin sa na shiga bubbugawa.
Abubakar ƙaninsa ya fito daga cikin gida gani na yasa ya tsaya.
"Yaya Bilal ɗin ne bashi da lafiya?" Ya tambayeni cikin mamaki bayan dana tambaye shi ina Bilal. Se na
ciro wayata na shiga kiran layin sa, Nasiru ne ya amsa yace suna asibiti jikin nasa ne ya riki ce"
"Subhanallahi, babu jimawa fa Yaya Nasirun ya kira shi duk muna tare a cikin gida bari na shiga na
gayawa Hajja se nazo muje asibitin" Abubakar ya faɗa yana komawa cikin gida.
Nasan kara kawai Hansa'u ta mun ta bini asibitin, na ringa rusa kuka ganin Bilal kwance da robar ƙarin
ruwa a ido na se naga ya rame yayi baƙi Abubakar da Hajjansu nata jimamin to me ya same shi tun da su
dai lafiya lau ya fita daga gida se Nasiru ne yace musu dama kwana biyu yana masa ƙorafin ciwon kai da
ƙirji shine suna zaune suna hira wai kawai suma. A asibitin na wuni sur har sallar isha'i se da Abba suka
zo tare da su Mu'azzam kafin na bishi muka tafi gida Hansa'u dama ko minti goma bata yi ba da mukaje
tace mun zata wuce. A hanya Abba yake ce mun wai typhoid da malaria ne suka kwantar dashi lokaci
ɗaya kamar yanda likitan daya tambaya ya faɗa masa. Nayi shiru a raina na raya ƙila basa so a faɗi
ainihin abinda yake damunsa ne dan ni likitan ce mun yayi zuciyar sa ce ta kumbura, wai dama yana da
matsalar zuciya amma duk tsayin zaman mu shine ya ɓoye bai taɓa gaya mun.
Na share hawayen daya gangaro mun ta gefen ido na sanadin tunanin wai Bilal na da matsalar zuciya da
nayi. In da na sani ina zan masa boren da nayi waccen ranar har in share sati ba tare da na amsa wayar
sa ko na bari mun haɗu ba. Ko kallon in da nake Mama bata yi ba da muka koma gidan, ban iya bacci da
kyau ba cikin dare duk motsi na hankali na yana kan Bilal ga wayarsa dama tun ina can Nasiru ya kashe a
dafe na kai safiya tun farar asuba kuwa na shiga kitchen na fara haɗa masa kunun gyaɗa da alala na haɗa
masa da farfesun kayan ciki. Saboda kar Mama tayi faɗa na duka gida nayi kan bakwai na gama na shirya
wanda zan kai masa na ware na gida sannan na wuce wanka a gurguje. Ina fitowa naji Mama na faɗa
"Saboda jiya ban ce mata komai ba shine yau zata ɗibar mun kaya tayi girki ba tare da ta sanar mun ba
to babu in da za'a kai abuncin nan" na jiyo tana faɗa. Nayi saurin zura doguwar riga ba tare da na shafa
komai a jiki na ba na saka hijabi na fita. Daga ne sa na gaishe ta ta galla mun harara tana cewa
"Yanzu Amina ba zan ce magana ta wuce ki barta haka ba se kin sake tadawa?" Abba ya katse ta, se ta
juya kansa tace
"Dama ai kai baka ganin rashin dacewar duk abinda takeyi a gidan nan. Yanzu mutunchi ne ace ta tafi ta
tare a asibiti tun hantsi ina ga da baku je ba ma a can tayi niyyar ta kwana ko? Sannan yanzu kaga uban
abincin da tayi zata kai musu kan ta aka fara soyayya ko kuwa da zata ringa abu kamar mara cikakken
saiti. Badai namiji bane, ka bishi a sannu ma ya ka ƙare balle ka nuna masa ba zaka rayu idan babu shi
ba"
"Ni da kika nuna mun ba zaki rayu idan babu ni ba nayi miki butulci ne Amina da har zaki fara kafa hujja
da halin Maza?" Abba ya faɗa, tuni na sulale nayi kitchen jin maganar na neman canza salo. Na bi ta
ƙofar baya na fice ina zagayowa muka ci karo da Mama ta kuwa falla mun marin da da wayo na bazan iya
tuna sanda ta dake ni ba.
"Har idan na isa dake Halima umarni nake miki ba shawara ba ki fita daga sabgar yaron nan, ban yarda
ba kuma ban amince da cigaban tarayyarki dashi ba" Mama ta faɗa cikin fushin da ban san tana da shi
ba. Hankalina ya tashi matuƙa, na aje kwandon hannuna na fashe da kuka ina cewa
"Ba abin da ya mun amma ina kallo bazan bari ki tura kanki a rami ba. In sha Allahu idan ma da
ƙulumboto ya nemi soyayyar ki zan ci gaba da kaiwa Allah kuka na ya warware komai ya raba ki dashi. Na
gaji, wannan wane irin bala'i ne? Bilal se kace na billahillazi bakya ji bakya gani akansa? To ba dani ba ko
kina so ko bakya so dole ki barshi tun da ba hauka akeyi ba".
Kuka na fasa harda kururuwa Abba ya fito cikin ɓacin rai yace
"Baki ji ba kenan?"
Ta wuce ciki ba tare da ta amsa masa ba tana jaddada mun wallahi na fita se na sha mamakinta yau.
"Dan Allah Abba ka bata haƙuri na faɗa ina kama ƙafarsa, seya ɗago ni yana cewa
"Ya isa, ki koma ciki tunda tace karki fita bari na taso Ibrahim se yaje ya kai musu abincin". Yanda kasan
wadda aka wa mutuwa haka na shiga ɗaki na ringa kuka akan hanani komawa dubo masoyi na da akayi.
Wuni sur ban fito daga ɗaki ba ko abinci ban iya kaiwa baki na ba seda mukayi waya da Bilal ya gaya mun
an sallame shi se lokacin na tsagaitawa kaina har na fita na nemi shayi na sha.
"Ba wasa nakeyi ba bana son auren nan Alhaji kwata kwata abin yaƙi kwanta mun a rai. Wlh ba ƙaramar
murna nayi ba da ya ɗauke ƙafarsa ya dena zuwa itama naga ta fita a batunsa, ni da ka sani da suka ce
zasu zo kawai ku ce musu an mata miji tun da dama tun asali ai ba kuɗi suka kawo ba magana kawai
akayi" Hajiya Amina ta faɗa bayan da suka zauna da Alhaji Aminu yayi mata magana akan rashin
dacewar abin da tayi a ganinsa.
"Me yasa zaki ringa faɗar haka Amina? Ban taɓa zaton zaki shiga layin waɗanda basa son haɗi tsakanin
Halima da yaron nan Bilal ba. A duk sanda na kalle su rayuwarsu ta kan tuna mun a yanda muka fara
tamu tarayyar" se tayi saurin katse shi tace
"Wane banbanci? Irin son da kika nuna mun? Wace irin sadaukarwa ce baki mun ba Amina? A sanda na
nemi auren ki ban ko kama ƙafar Bilal rufin asiri ba. Bana manta ƙanin da yan gidanku suka mun me riga
ɗaya. Kin ciyar dani, kin tufatar dani kin kuma zauna dani cikin halin matsi har muka kawo yau menene
banbanci cikin abinda yake faruwa a rayuwar Halima yanzu?" Alhaji Aminu ya faɗa cikin kwantar da
murya.
Hawayen da suka tarar mata a ido ne suka fara sauka, ta saka gefen hijabinta ta share tana cewa
"Ko da na so ka na so ka ne a matsayin ka na Aminu kai ma ka so ni a Amina. Babu son rai ko so. zuciya a
tarayyar mu. Baka dashi amma kowa ya shaida kai me zuciya ne kuma kana kan tafarkin nema. Baka taɓa
roƙo na nayi maka abu ba kuma na sani a duk sanda na maka abu kana karɓa ne saboda ka faranta mun
kuma a duk sanda Allah ya baka dama ka kan kwatanta kyautata mun kaina daidai yanda zaka iya.
Mahaifi na ya faɗa mun ya baka aure na saboda ya yarda da kai ya kuma yarda da nagartarka ya kuma
san akwai da babu ba zaka wulaƙanta masa ni ba saboda ya yarda tsakani da Allah kake so na. Wace
madogara kake da ita da har ka yarda zaka bawa wancan yaron auren yarka?
Ban ce baya son ta ba amma son da take yi masa ya kere wanda yake mata nesa ba kusa ba, kai namiji
ne. Be zama lallai ka hango illar dake tattare da irin wannan tarayyar ba. Bance a duk in da son mace yafi
yawa yana kasan cewa matsala ba amma muna amfani da abinda yafi faruwa musamman a irin al'umar
da muke ciki yanzu. Yanzu ka kalli abubuwan da Halima takeyi, akan Bilal bata ji bata gani ba kuma ta
shakkar ɓatawa da kowa. Har ta kai yanzu bata shakkar ɓacin rai na akan duk abinda ze faranta ran Bilal.
Tun be aure ta ba take haka ina ga kuma sun zauna me kake tunanin zata zama? Ni dai gaskiya ina jiye
mata tsoro domin zuciyata ta kasa nutsuwa akan al'amarin nan mafi sauƙi a haƙura mu cigaba dayi mata
addu'a Allah ya fito mata da wanda ya fishi alkhairi".
Shiru Alhaji Aminu yayi kawai, sam ya kasa ganin abinda take kira da matsala cikin al'amarin Halima da
Bilal. A iya binciken sa ba'a samu yaron da wani halin banza ko shashanci ba. An san asalinsa, yana da
sana'a ga yarinya tana son sa to me ake nema? Sau tari shi ma ya kanga kamar Haliman ta zurma da
yawa amma yanayin ta ne a haka tun tana yar yarinya ta kan tsananta son abu, ko cikin kayan wasan ta
ta kan tattala tare da kulawa da wanda ta fi so bata taɓa fitar dashi idan suna wasa ta sa'anninta shiyasa
yakan mata uzuri akan abubuwa da yawa nata haryar kenan ta bayyar da soyayya. Cikin nutsuwa ya
ringa kwantarwa da matar tasa da hankali tare da nunar mata da babu komai. Kamar yanda yasan tana
wa yaranta addu'a karta gaza, taci gaba da yiwa Halima in sha Allahu duk ma hasashen da wasu sukeyi
baze yi tasiri ba.
"Yanzu haka nan da wace hujja zamu ce zamu hana shi aurenta? Go be fa suka ce zasu zo saka rana naga
da ƙorafin ki ya tsaya wasa ba aure zeyi ba yanzu kuma ya yunƙuro se ki zo da wata magana daban
Amina ban fa san ki da haka ba na kuma san ba kowa yake zugeki ba illah Labiba kuma zan kirata. Ita dai
tunda Halima taƙi ƙanin Alhaji Saleh shikenan ta tsangwami zancen auren ta Bilal" Abban ya faɗa. Seta
girgiza kai tace
"Babu ruwan Labiba wlh, kuma ko da taƙi al'amarin tana da hujjoji da ababen dubawa ne ai kuma son da
takewa Halima yasa har take adawa da abinda take ganin ze iya zaka matsala a rayuwarta dan dai ka sani
ko ni da na haifi Halima dan dai soyayyar uwa da abin cikin ta daban ce amma bazan ce nafi Labiba
ƙaunar Halima a zahiri ba" Mama ta faɗa. Se yayi murmushi yace
"Bana in kari da ƙaunar dake tsakanin Labiba da Halima wani haɗi ne daga ubangiji wannan na kuma san
duk abinda zatayi akanta zatayi ne don ganin rayuwarta ta in ganta. Ƙaramar uwa da yarta, ai babu me
shiga tsakaninsu dan idan aka juyo ta wani fannin muna nan za ta iya baki kunya kuma ta juya tabi bayan
yarta. Ni dai abin da zan ci gaba da faɗa miki shine ki ci gaba da yi mata addu'a kawai in sha Allahu e
mun ce gara da akayi ba kuma zamuyi nadamar wannan tarayyar ba" da maganganun daya danneta
kenan harta sakko tabi ta tasa taci gaba da addu'ar da dama kullum cikinta take.
A daren ta kira Anty Labiba ta gaya mata zancen zuwa sa ranar a take kuma tace a cireta ciki bata cike da
iskancin Bilal da Halima. Tun dai taji ta gani ai shikenan mai Allah ya tabbatar da alkhairi. Dariya kawai
Maman tayi ta kira Yayarta Hajiya Rumana kawai tace zata yiwa Matar Yayansu Lawan Anty Laure
magana tun da taga ta fara harkar snacks na biki, duk da ba'a gidan zasu zo saka ranar ba amma zatayi
abin tukuici akai can gidan Baba Salahun.
Washe gari lahadi ƙarfe huɗu na rana Kawunnan Bilal biyu da Aminin mahaifinsa ɗaya suka je saka ranar
auren mu gidan Baba Salahu. Kusan a kowanne ɓangare ana al'ada, wasu su kan yi tsohuwar da aka saba
akai akwati da kayan sa rana. Wanda suka zamanantar da abun kuma kuɗi suke badawa waɗan su kuma
a sanda aka kai kuɗin aure ake haɗawa da na sa ranar ko kuma a haɗo kayan tare da lefe to su dai su
Bilal bamu san wanne zasuyi a ciki ba, dama sanda akayi tambaya basu bada komai ba Abba yace baya
buƙatar wani kuɗin na gani ina so ko na aure yanzun ma haka nan suka zo da saka rana shekara ɗaya se
dai Baba Salahu yayi tsallen albarka yace basu san zance ba.
Watanni shida shine abin da suka yanke zasu aurar da yar su, bayan duk dogon zaman jiran sa da aka sha
har idan suna ganin hakan ya musu gajarta to fa suyi haƙuri kawai domin a cikin dangi akwai wanda
dama suka ci burin haɗa ta dashi. Aminin mahaifin Bilal ne yace ba za'a yi haka kuma tabbas kam iya
lokaci an basu domin be manta ba an tafi shekara ta uku kenan da sukayi tambayar auren kuma shi
kansa be san ranar har ta shekara suka shiryo ba da tun kan su zo dama ze gaya musu yayi yawa
musamman dama ga bikin ƙanwar Bilal ɗin da za'a yi duk lissafin sa tare zasu haɗe. Haka dai aka rabu,
duk sauƙin kai da rashin ɗaukar duniya da zafi irin na Baba Salahun bayan sun tafi se da ya kira Abba yayi
masa mitar mutanen fa ko goro basu zo dashi ba balle wani abu na al'ada. Abban yace babu komai.
Irin murnar dana shiga bayan da na samu labarin a watanni shida masu zuwa zan zama mallakin Bilal ba
me faɗuwa bace. Har party na haɗa, cikin sa'a washe garin ranar tayi daidai da ranar zagayowar
haihuwata dama dan haka na roƙi Mama da muke hi hi yanzu akan zanje gidan Anty Labiba. Bata hanani
ba, dama na gayawa Hansa'u da su Baby zamu je gidan zoo ranar birthday na Baby na bawa kuɗi ta yi
mana kayan taɓawa na siyi cake da a jiki aka rubuta mun Happy engagement Mrs Bilal to be ban sanar
ma Bilal ɗin bama se da na samu na bar gida haka ko suka je shi da abokanansa biyu muka sha hotuna
muka ci snacks muka yanka cake bamu ji ma ba na wuce gidan Anty Labiba dan kar zance ya tashi tace
ban je ba. Na dai sha zagi a gunta amma ban damu ba, tace kayan gado yan goron dutse zasu mun duk
tarin da Mama takeyi a saboda aure na ba zata bari ta ɓarna tar da kuɗin ta ba har kayan kitchen da take
siya da wanda itama ta siya mun Amirah zasu ajiyewa nace duk naji.
Shikenan rayuwa ta dawo mun sabuwa, soyayya da shaƙuwar mu da Bilal se abin da ya sake gaba. Na
samu ƙatuwar takadda na zana calender ta wata shida kullum da safe na tashi zan soke ranar ki nake yi
tamkar na janyo lokaci ni dai buri na da fata na kawai na zama matar Bilal.
Wata Juma'a sati biyu kenan da yin sa ranar mu watanni biyar da sati biyu kuma a cikin kwanakin da
suka rage ma aurena da Bilal kamar ko yaushe munyi waya yace mun ze zo gurin ƙarfe biyu kuma se ya
kirani yace na faɗawa Mama idan ya zo ɗin zamu ɗan je wata unguwa. Na ringa juya maganar, ba sabon
abu bane fitar mu taren amma tun bayan da akayi sa ranar mu Mama ta zaunar dani tana mun faɗa da
wasu maganganu in rage rawar kai karna kuskura ganin an saka mana rana da Bilal na ɗauki halin da bani
dashi a da. Ko zuwa yayi yanzu se tace mu zauna a falonta muyi hira ko a compound a maimakon falon
Abba da muka saba zama kamar kuma kaɗan take jira dani abu ƙarami zanyi ta fara mun faɗa shi yasa
duk na rasa ta yanda zan ce mata zamu fita tare.
Ina tsaka da tunanin Amirah dake gidan Anty Labiba taje hutu tayi sallama, naji daɗin zuwan nata sosai,
tare suke da Inaya da Amir wai Babansu Amir ɗin ne ya kawo su. Seda na fita na gaishe shi yana ta
tsokanata wai amarya bayan ya tafi na cewa Mama zanje gidansu Hansa'u in karɓo atamfar ankon Baby
an kawo mana tana can daga nan zamu kai ɗinki. Da Inayah muka tafi Amirah tace ba zata raka ni ba,
seda nawa Bilal text na gaya masa ina gidansu Hansa'u cikin sa'a bata nan wai ta tafi wankin kai bayan
tare mukayi zamuje shine bata kira ni ba. Zama nayi muka ɗan yi hira da Ummansu kafin muka tafi bayan
da Bilal ya kirani akan yazo.
Page ɗaya ya rage free, ina fatan kin aika 800 ɗin ki kuɗin karatu 💃🏼💃🏼💃🏼
*1840175439*
*Access bank*
*Maryam Farouk*
[12/14/2024, 12:03 AM] Hauwa Galadima: *KURA A RUMBU*
*(Based on true life event, some parts are fictional to spice up the story)*
*Wattpad @MaryamahMrsAm*
*Ban yarda wani ko wata ya juya mun labari ta kowacce siga ba tare da izini na ba*
*Kuɗin karatu yana wakiltar mutum ɗaya ne, kiji tsoron Allah karki ɗauki hakkina ta hanyar fitar mun da
littafi*
*KURA A RUMBU littafin kuɗi ne, a biya naira 800, biya a asusun*
*1840175439*
*Access bank*
*PAGE 5*
A motar Nasir na ganshi, ya kame a ciki yanda kasan tasa. A raina nace kuɗi dai ze yi wa Bilal kyau dan
kalarsu aka masa. Yanayin surarsa da irin kayan da yake sakawa ba zaka kalli gidansu kace daga nan ya
fito ba. Yana son gayu, sau tari na kan raya a raina nan yake kashe kuɗin sa gurin siyan sutura da takalma
haɗi da agogo masu tsada duk abin da samari sa'anninsa suke yayi zaka ganshi dashi hakan kuma yana
burge ni duk da ba wadata ce dashi ba amma ba yanda za'a yi ka ganshi ka raina shi.
A gaban motar nima na kame Inayah ta shiga baya muka tafi muna hirar mu gwanin sha'awa, ban
tambaye shi in da zamu je ba shima be gaya mun ba har muka isa Goron dutse cikin GRA dake bayan
matatar ruwa (WRECA). Na ringa kallon unguwar, a iya sani na banda kowa a gurin shima kuma bamu
taɓa hirar wani nasu a nan ɗin ba, cikin wani da ke jere da gidaje hagu da dama muka shiga, gidaje uku
ne ba kammalallu ba a ciki ɗaya ma kamar da mutane a ciki benen sama ne ba'a ƙarasa ba se fili da aka
zagaye da alama ba'a fara gina shi ba. A ƙofar kangon dake ƙarshe layin ya tsaye dake layin baya ɓullewa,
ya kashe motar muka fita na cigaba da kallon gurin ganin ya nufi kofar shiga gidan ya buɗe da muƙulli
yasa muka bi bayansa se dai ban shiga ba na tsaya a waje ina kallon cikin gidan.
"Ya kuka tsaya a waje? Ku shigo mana" ya fada bayan daya juya ya ganmu a tsaye. Se da na ɗan yi jumm
ina kallon cikin gidan kafin nayi bismillah na shiga. Tsakar gidan bashi da girma sosai amma ze iya cin
mota ɗaya ko ma biyu. Duk da ginin ba'a kammala shi ba amma yana yin tsarin yayi kyau. Akwai babbar
ƙofa dake tsakiya tana kallon get, se kuma daga gefe can akwai wata ƙofar ƙarama. Ya buɗe babbar kofar
ya shiga muka bishi, a cikin falon da ba'a yiwa fulasta ba ya tsaya yana kallona yace
"Barka da zuwa gidan Bilal". Se na saki murmushi, wato nan ne gidan da yake gina mana. Ya nuna
bangon hagu in da ƙofa take yace
"Bedrooms ne guda biyu kowanne da toilet, suna da girma nasan zasu ci kowanne irin saitin gado". Seya
matsa ya buɗe kofar dake bangon gabas yana cewa
"Nan kuma kitchen ne da store", waccen ƙofar ta waje kuma ɗaki ne da falo a ciki Master room kenan
ina tunanin ko a faso da ƙofa ta nan" ya nuna mun ɗan corridor dake gefe yace
"Saboda sauƙaƙa miki zirga zirga tsakanin nan da can ko dan yanayi na ruwa da sanyi". Ni dai murmushi
kawai nake kamar wata sokuwa. Ya buɗe ɗakunan muka leƙa har cikin toilets ɗin kamar yan da ya faɗa
suna da girma sosai kam zasu ɗauki kaya har a samu gurin shimfiɗa carpet me ɗan girma. Har can part
ɗin da yace nasa se da muka shiga, a nan naga ya aje buhunhunan sumunti da sauran kwanon da akayi
rufi dukda saman gota ce se kayan toilet da sink na kitchen.Tsakar gida muka koma ya nuna mun ɗan
filin dake kusa da part ɗin yace
"Da nan gurin Hajja tace se ayi ɗaki tun da ga banɗaki a tsakar gida dama ko da zamuyi baƙi maza masu
kwana"
"Uhm" kawai na ce a raina ina lissafa ɗan abinda nake ganin ya rage a aikin ginin. Fulastar ciki ce dan an
yi ta waje da ɗakuna guda biyu nawa, falo ne da kitchen suka rage se can ɓangaren sa.
"Yau kin ga gidanki" ya faɗa bayan da muka zauna a mota. Nayi murmushi nace "guri yayi kyau sosai
Allah ya sa rai aka yi wa"
"Amin My Halims ai se ma an gama aiki an gwagwaje gurin da kaya yan kamfani kyansa ze sake fitowa"
ya bani amsa na amsa masa da
"Haka ne, to Allah ya nuna mana lokaci". Shirun minti biyar ya gifta tsakaninmu ya ci gaba da tuƙi ni
kuma na tsunduma tunanin abinda ya rage a aikin gidan yanzu wanda a gani na saura ne kawai tun da an
yi me wuyar kammala ginin da rufi. Ni duk da yake ta zancen gini na zata irin ko linta be kai ba ashe ma
ƙarashe ne kawai.
"Yanzu kin ga abin da nake gaya miki na akwai sauran shiri a gaba na ko?" Ya katse mun shirun, se na
kalle shi. Ya ci gaba da cewa
"Ban siyi ko kwali ɗaya na Tiles ba. Ga gilasan winduna kin ga boggler kawai aka saka. Ban da ƙarashen
fulasta sannan azo uwa uba wiring ɗin wuta da ruwa ga fenti dasu pop aikin fa ba ƙarami bane Halima".
"Haka ne" ya bani amsa daga nan be sake cewa komai ba har muka je unguwar mu. A hanya muka sauka
ya wuce ina ɗaga masa hannu, se da na sake komawa gidansu Hansa'u cikin sa'a na tarar ta dawo nan
muka zauna na shiga labarta mata yanda gida na yake.
"Lallai Halima ba kunya kika bishi ganin gida ko?" Ta faɗa se na harare ta nace
"Ji banza wai kunya. Kawai naje naga gidan ne wani abu da zan ji kunya lallai ma". Seda Mama ta kira ni
kafin muka fito ta rakani rabin hanya. Sau biyu cikin zirgilli na ina kusan gaya wa Mama zancen munje
ganin gidan se Allah ya cece ni na canza maganar da wata. Abin na mintsili na, nayi kamar na gayawa
Anty Labiba se dai nasan yanda take a cike dani tsaf zata haɗa ni da Mama se kawai na kama kaina na
bar murna ta a ciki na. Bilal dai da ake ganin be kai ba gashi nan cikin hukuncin ubangiji ze yi abinda
kowa se yayi mamaki ga dai gida nan na nunawa sa'a da nasan iya kar masu ƙaryar kuɗin dai suyi kamar
shi ko wanda be kai shi ba kuma a unguwar yan gayu da na tabbatar ƙasa tana tsada a gurin.
Shi ma a yanda yace filin na gadon sa ne ya adana gashi kuwa ya masa rana babu yanda masu gidajen
kusa dashi da ma na nesa basuyi akan ya bar musu ba har musanyan ginannen gida aka bashi da cikon
kuɗi duk yaƙi a cewar sa baze maida kamar sa ba kuma unguwar ta masa da irin tsarin rayuwar da yake
so ya gudanar da iyalansa.
Watanni uku suka shuɗe cikin wata shida na ranar auren mu data rage har sannan kuma daga ɓangare
biyu nawa dana Bilal ba zan ce ga wani shiri da aka fara na biki ba. A gidanmu dai nasan Abba ya yiwa
Mama magana akan abin da ya kamata ayi tace masa suna kan lissafi ne idan ta gama haɗa komai zata
sanar masa ban sake jin sun tada maganar ba. Ina da abubuwan da nake so a mun daga kan zaɓin kayan
ɗaki zuwa sauran kayan amfani se dai ban ga fuskar da zan sakowa Mama maganar ba. Anty Labiba ko
yanzu ban ma isa na doshe ta da wannan zancen ba tun da ƙiris take jira dama ta samu nayi mun. A haka
a ka fara azumi, na ƙudurce a raina har aka sallace ban ga an motsa ba to fa zanyi magana se dai ace nayi
rashin kunya.
A ɓangaren Bilal ma dai shiru ne, nayi zaton yanda nake cike da ɗoki shima hakan ce zata kasance dashi
amma sam ba haka ba. Kullum yazo bashi da zance se na gini, ya rasa ya ze yi, kaza ya ƙara tsada se ya
kashe kaza akan yin abu kaza kuma shi bashi dasu ko waya ya kira ko na kira shi zancen kenan har na
fara gundura da jin sa daya fara akwai se in bashi uzurin zan yi wani abu na kashe wayar. Ban sake shan
mamaki ba se wata rana daya zo bayan shan ruwa yake nuna mun ci gaban aikin da akayi a wayar sa se
na ga babu banbanci da wancan zuwan da mukayi, fulasta kaɗai aka ƙarasa se wiring ɗin ruwa da yace
anyi.
Rai na ya so su, tun ku san sati ɗaya kenan Hansa'u take ta mun magana akan ya kamata mu fitar da
anko in gaya wa Bilal ya bani kuɗi muje kasuwa. Nasan haka akeyi to amma tausayin sa da nake ji da
yanda kullum yake ƙorafin gini ya hana shi sakat yasa nace bazan tambaye shi ba ƙarshe se Abba na
tambaya da Mama ta ji ma tace ba yanzu ba in bari se bayan ƙaramar sallah tunda bikin ze kama bayan
babbar sallah ne da kwana goma a lissafi. Ni ina ta tunanin ƙila ma an kusa gama fenti ashe shi tafiyar
hawainiya ma yake yiwa aikin. Kasa daurewa nayi nace masa
"Yanzu tsahon lokacin nan ashe babu abin da aka ci gaba a ginin nan? Yau fa sauran kwana casa'in da
biyar ace ba'a ma ɗakko hanyar kammala gini ba balle a fara sauran hidimomin biki?" Se ya kalle ni yace
"Wace irin magana kike yi haka Halima? Ashe ma baki yaba abinda nake yi ba kin san tsadar kayan gini
kuwa a wannan zamanin? Karfa ki manta Halima ni nake yiwa kaina komai ba wani bane yake tallafa
mun sannan hidimar nan ba iya tawa bace ba sanin kanki ne ga auren Naja ni zan mata kayan ɗaki bayan
kuma albashi na kin san ba wata hanya ce dani ta samun kuɗi ba". Nayi shiru saboda na hango gaskiya a
cikin tasa maganar shima, ba shi da matallafi se Allah ga kuma hidimar ƙanwar sa kamar yanda yace ita
ma abar dubace.
"Shi yasa tun farko na guji a saka mun rana ba tare da na gama shiri na tsaf ba, kuma da aka je ma ni
shakara ɗaya nace aka tashi aka sa wata shida bayan an san ba lallai na shirya a wannan lokacin ba" ya
sake faɗa kamar cikin fushi. Se na kalle shi na ce
"Ni babu abinda nake nufi kawai raina beji daɗin yan da kika raina ƙoƙari na bane har kina cewa wai duk
tsahon lokaci babu abin da nayi".
Shiru kawai nayi ina kallon sa na rasa ma abin da zan ce har ya gama yayi shiru dan kansa. Haka dai ba
daɗi muka yi sallama ya tafi, ko abincin da nayi niyyar bashi ban ɗauko ba shima kuma be tambaya ba,
da asuba ma be kira ni ba har gari ya waye gurin ƙarfe goma se kuma duk naji na damu. Nasan dai ba
wata magana na gaya masa da ya kamata ace ta masa zafi ba amma hakan nan na danne zuciya ta
albarka cin son da nake masa na kira shi.
"Raina ya ɓaci Halims, ya za ayi duk fafutukar da nakeyi akan naga nayi komai cikin rufin asiri amma kina
rai nawa? Ke baki ga girman gidan bane ba kiga irin tsarin da aka ɗakko ba?" Ya faɗa bayan dana gama
ban baki. Nace
"Gaba ɗaya ka juyawa magana ta manufa ne amma ni ban raina ƙoƙarin ka ba kawai a nawa tunanin dai
zuwa yanzu ko za'a ce da sauran aiki to ƙarashe irin wanda ma be zama dole ba. Kuma ni da zan baka
wata shawara kaji, me ze hana ka mayar da hankali kawai ka gyara iya ɓangaren da zan zauna a ciki? Tun
da dai mu biyu ne kawai a cikin gidan ko da ace ka gyara can ɗin ma ba lallai ace za'a yi amfani dashi
yanzu ba. Kawai ka barshi ka tsayar da hankalin ka a guri ɗaya ina ganin ze fi".
"Ba zaki gane ba. Ki kwantar da hankalin ki za ayi komai kafin lokacin, naga alamar kin fini matsuwa fa
Halims to ki cigaba da daurewa saura ƙiris ba zaki maimaita azumi a gida ba". Na rufe fuska kamar ina
gaban sa nace
"Surutun kawai, zaki yi baya ni ne duk ranar da kika shiga hannu yarinya" ya sake faɗa se nayi saurin
datse wayar jin yana neman sakin layi da azumi a bakin mu. Shikenan muka shirya aka ci gaba da azumi
kwanci tashi har satin sallah ya kama.
Shakara biyar muna tare da Bilal be taɓa mun toshi ba har ga Allah wannan sallar na tsammaci ze yi tun
da dai yanzu ai kusan na zama tasa za'a ce se dai shiru kake ji har sallah ta rage yan kwanaki babu wani
labari. Ranar da ya rage kwana uku idi bayan an sha ruwa yazo kamar ko yaushe ina shirin zuwa gidan
Anty Labiba zan kai mata saƙo daga nan na karɓo mana ɗinku nan mu ni da Mama. Tare da Bilal muka
tafi, bamu jima ba muka dawo tun a hanya yake ce mun wai
"Iye yar gatan Abba da Mama. Yanzu duk ledojin nan kayan sallar ki ne, ni ina nan ko rigar da zan saka
naje idi bani da ita. Takaici yasa na masa banza har ya sauke ni a ƙofar gida, na shiga na aje kayan sannan
na fito mu kan ɗan taɓa hira kafin yayi haramar tafiya, dubu uku ya bani yace gashi nan nayi kitso da
lalle.
"Na bawa Hashir sautun abaya, na ɗauka ze dawo lafin sallah se jiya yake ce mun wai jirginsu washe
garin sallah ne kiyi haƙuri da wannan" ya faɗa bayan daya bani dubu ukun. Gashi dai ba wasu kuɗin azo a
gani ya bani ba, a yanda nake tsaye ma ina da ninkinsu a jikina amma se naji daɗin kyautar tamkar
wanda ya bani miliyan uku. Na ringa murmushi ina cewa na gode shi kuma ya basar wai akan 3k ai ba
haka yaso ba in yi haƙuri da hakan kawai. Dana shiga gida haka na tarar da Mama ina dariya na bata
kuɗin ta kalle ni ta kalle su da taji daga in da suka fito ina ga takaici ne ya saka ta dariya kawai tace ya
kyauta. Washe gari tun da wuri na tafi gidan lalle kafin azahar an gama mun da daddare kuma naje gidan
su Hansa'u ta yarfa mun kitso a nan naga abin arziƙin da Alhaji Bala ya kawo mata na toshi akwati guda
harda kit kamar lefen bazawara ba abin da babu ciki tun azumi na tsakiya dama ya zo gaisuwar azumi
nan ma ya kai musu sha tara ta arziƙi naji mata daɗi amma ba wai abun ya burge ni ba dan ni dai wlh da
dai na auri dattijo kamar Alhaji Balan saboda kuɗi gara in ƙare a talauci tare da wanda nake so.
Ranar idi haka na shaƙe kuloli saiti biyu da abinci, ɗaya na Bilal ɗaya na Hajjan su na bawa Aliyu ne
Adaidaita ya kai musu Mama dai kamar yanda tace taga ikon Allah amma tunda me kawo abincin yace
babu ruwanta a bar ni nayi yanda naso sadaka ce dole ta kama bakinta tun da dama ni nasha wahalar
girka miya, wai na da tuwo kuma matar dake mana duk sallah ce ta zo tayi. Da yamma Bilal yazo,
mutumin da yace beyi ɗinkin sallah ba se gashi da sabuwar kwalliya ba wadda ya turo mun hotunan idi
da ita ba. Daya tashi tafiya nan ma a karon farko ya bani rafar yan naira goma sabbi yace na bawa Imam
da Amirah barka da sallah Mama kuma na gaya mata jibi zasu zo gaishe ta da abokanansa.
An ci sallah an cinye watan shawwal ya mutu har an shiga zulƙida ya raba a taƙaice ce dai ƙasa da
kwanaki sittin a lissafin kwanakin ranar auren mu. Gidan Baba Salahu su Sauda da za ayi bikinmu tare
suna ta shiru tu ni sun fitar da anko, sau ɗaya na yiwa Bilal zancen ina so zan fitar da ankon yace mun ya
kamata kam na bashi tazarar sati ɗaya na ga ko ze mun wani abu amma naji shiru se kawai na share shi
nayi amfani da kuɗin da Abba ya bani muka siyo Atamfa kala biyu, ɗaya ta kamu ɗaya ta yinin biki
saboda rashin ta ido da na nuna masa se ce wa yayi
A lokacin a wasa na ɗauki zancen mukayi dariya kawai ina ce masa "wannan ai hurumin ka ne, idan za
kayi ko ana go be ranar ne ba zamu kasa samar da abin da yammata za suyi amfani dashi ba tun da kasan
shi ankon dinner dama ba da yawa ake yin sa ba" ya ce
"Shi kenan Allah ya kai mu lokacin na gaya miki har idan da hali babu abin da ba za ayi ba Halims ki na
raina soyayyar da naki miki".
Ranar Alhamis aka aiko wa Mama daga gidan Baba Salahu akan ranar Asabar za a kawo lefen Sauda, ni
se da naji aiken na tuna da batun wani abu a aure wai shi lefe. Ko da wasa bamu taɓa zancen da Bilal ba,
be mun maganar ba ni ma ban masa ba ni hankali na duk ya tattare akan ya kammala gini shi yasa ma na
manta da wani batun lefe ƙila. Bayan yaron ya tafi Mu'azzam yake ce mun
"Ke kuma se yaushe za a kawo naki lefen? Ni wai Mama bikin nan yana nan kuwa dan ban ga ana wani
shiri irin za a aurar da yar fari ba ko dama duk bula ce da ake nuna an fi son ta akan mu?"
"Bana son sakarci Mu'azzam wane irin magana ne zaka ce an fi son ta akan ku?" Mama ta kwaɓe shi se
ya ce
"To yanzu dai ya maganar bikin akwai ko babu in san shiri na?" Wai se na ji Mama ta ce masa
"Ga ta nan ai se ka tambaye ta ni ma ban sani ba". Tsabar dariyar shaƙiyanci se da ya faɗo daga kan
kujerar da yake zaune ya ce
"Ai ko dai se dai a tambaye ta, kullum fa ina laɓe wa naji hirar da suke wlh Mama ki tashi tsaye da addu'a
lamarin Halima fa kamar akwai saka hannu"
"Wai Mu'azzam me yasa bakin ka bashi da saiti ne?" Mama ta sake faɗa yace
"To wlh ita take forcing maganar auren nan mutumin nan kullum yazo uzurin safe daban na rana daban
ina ji jiya yana ce mata wai ya siyi interlocks an je ɗakkowa motar tayi accident duk sun farfashe kiji fa
wata jahilar ƙarya ko a gidan uwar wa ma yake ginin oho dan dai ban ga in da aka nuna a unguwar su aka
ce na sa ne ba"
"Tashi ka bani guri Mama" ta kore shi ya fita yana surutansa se da ya maido ƙofar falon ya rufe kafin
Mama ta kalle ni tace
"Saura kwana nawa ya rage biki ne Halima?"
"Kwana hamsin da uku Mama" na bata amsa kai tsaye, ta girgiza kai tace
"Madallah, kwana hamsin da uku amma shiru babu wani motsi daga gidansu yaron nan shi be ce komai
ba iyayensa ma basu ce komai ba ko kuma kun ɗaga ranar ne bamu sani ba?"
"Ai suna ta ci gaba da shiri ne Mama mu ne anan har yanzu ba'a fara komai ba" na faɗa kai na a ƙasa.
Tayi murmushin daya fi kama da yaƙe tace
"Haka ne, to Allah ya nuna mana lokacin da rai da lafiya. Ki shirya kayan ki cikin satin nan zaki koma
gidan Labiba kafin lokacin bikin". Baki na tunzura gaba nace
"Gaskiya ni Mama ki barni nayi zama na a nan kin san dai Anty Labiba yanzu ta canza ba wani so na
takeyi sosai ba". Banza ta mun, ta wuce ɗaki ina mita amma kuma dana zauna nayi tunani nan na gano
ƙila gyaran amare za a fara mun shi yasa tace na koma can dan na san Mama da kunya hali na ne ma
yake sakata magana in ba dan haka ba ba wani shiga sabgata take yi sosai ba. Nan da nan na fara haɗa
kaya da yamma nace mata zan tafi tace Aa na bari se gobe haka ko akayi washe gari da azahar nayi ƙaura
zuwa gidan Anty Labiba.
"Ni kam Halima ko kin ce masa kin yafe lefe ne babu labari? Sannan na zata zuwa yanzu ai ze ce azo a ga
gida ko saboda musan irin tana din da zamuyi" Anty Labiba dake kallo na ta faɗa. Ina danna waya ta na
ce
"Ban san san da zasu kawo ba Anty, gida kuma akwai sauran aikin da ba'a ƙarasa bane shiyasa amma
nasan da zarar an gama ze yi magana aje a gani gidan ai ba wani wahalar jere zeyi ba" nan na shiga
wassafa mata yanda tsarin gidan yake. Tayi shiru kawai tana kallo na kafin tace
"Kin je kin gani kenan" na kalle ta jin kamar ta rafko ni se na wayan ce nace
"Haba dai. A waya dai kullum idan yazo yake nuna mun duk abin da a ka yi". Tayi shiru kamar ba zata ce
komai ba har na fidda ran zata sake magana kafin naji tana cewa
Aje wayata nayi na fuskan ce ta dakyau nace "Me kuma ya faru Anty?"
"Babu abin da da ya faru Halima. Ima tunatar dake ne abin da ya kamata ace a shekarun ki kin fahimta
amma naga kamar baki sani ba ko kuma kin manta. Shin na tambaye ki Halima, tun da kike ki taɓa ɗaga
hannu kin roƙi ubangiji zaɓi cikin tarayyar ki da Bilal kuwa? Kin taɓa yin istikhara kin nemi aga jin ubangiji
cikin al'amarin ku?"
Shiru nayi ina kallon ta lokaci ɗaya kuma jiki na yayi sanyi tiɓis. Tayi murmushin tace
"Ban ce bakya addu'a ba ce miki nayi akan lamarinki da Bilal kina neman zaɓin Allah eh ko a'a shikenan
amsar, ko da yake idan ma kina yi ba zaki taɓa fahimtar abin da ake haska miki ba saboda kin ri gada kin
sakawa zuciyar ki shi ɗin shine alkhairin naki".
"Wallahi Anty ina addu'a, kullum nayi sallah se nace idan da alkhairi cikin tarayya ta dashi Allah ya
tabbatar mana" na faɗa tamkar zan saka mata kuka se tace
"Na yarda. Halima, lokuta da yawa mukan take gaskiya cikin sani mu kai kan mu ga halaka. Muna runtse
ido daga gaskiyar da take gabanmu mu ringa hangen gabanta ko bayanta sannan idan an samu aka si
muyi kuka muce ƙaddara ce. Tabbas rayuwar mu gaba ɗaya tsararren al'amari ne amma dukkan musulmi
ya yarda da tasirin addu'a mun kuma yarda addu'a tana sauya mummunar ƙaddara zuwa kyakykyawa ko
kuma ta sassauta muninta.
Ki sani ko da ace kina addu'a muddin a zuciyar ki akwai abin da kika rigada kika ƙudurce shi ne matsayar
ki ai ba zaki ma Allah wayo ba. Idan abun Alkhairi ne lafiya lau ubangiji da zuciya yake amfani se ya baki,
idan ma ba alkhairi bane tun da har a ranki baki yarda ubangiji ne me bayar wa kuma ya hana ba kika
saka wani ƙulli se Allah ya barki da iyawarki, ba zan yi katsalandan cikin al'amarin aure ba domin sirri ne
amma zan sake gaya miki ki nemi zaɓin Allah da zuciya ɗaya Halima. Allah ya sani ban ji a jiki na tarayyar
ki da Bilal alkhairi bace be kuma nuna wasu alamomi da zasu ƙaryata tunanin mu akan sa ba. Kiyi amfani
da ɗan lokacin daya rage miki Halima kiyi tunani kuma kiyi addu'a, kar ki bari so ya rufe miki ido ki kai
kanki in da zaki ƙare rayuwarki kina nadama. Cutuwarki bake kaɗai zata shafa ba har da mu dan Allah
Halima ki yiwa kan ki gata tun da sauran lokaci ki haƙura da yaron nan. Barin Bilal ba fitar numfashi daga
gangar jikin ki bane, kin rayu kafin wanzuwar sa yanzu ma idan ki ka barshi babu abin da ze same me ki
se alkhairi Halima. Amma shawara ce ban miki dole ba" Anty Labiba ta ƙarasa maganar muryar ta tana
karyewa se ta miƙe tana share hawaye ta shige ɗaki, haka take tana da saurin karaya abu kaɗai ke fito da
raunin ta. Na bita da kallo har ta shige ɗaki ta maido da ƙofa kafin na lumshe idanuwa na ina tariyo
maganganunta ina kuma fassara su tare da aje kowacce a muhallin daya daveyda ita.
Shin kun hango sarewa a lamarin Halima kuwa? Zata yarda ta bar Bilal kamar yanda makusantan ta suke
fata?
Me nene haƙiƙanin matsayin Halima a gurin Bilal? Shin ya ɗauke ta tamkar yanda ta ɗauke shi ko kuwa
dai hasashen da ake mata akan sa gaskiya ne?
Allah shi yasan karatun bebe, haka kuma Allah shi kaɗai yasan gaskiyar dake zuciyar Bilal dan gane da
Halima, shin So ne da gaske ko kuwa akwai wata boyayyar manufa da be bayyana?
Ana zaton wuta a maƙera, Bilal fa ze iya bawa maraɗa kunya cikin tafiyar nan ku dai ku kasance tare da
alƙalami na domin warwarewar duk wani zato da zargi da yake yawo tsakanin zukatanku.
Domin cigaba da karanta littafin KURA A RUMBU wanda ze zo a manhajar TELEGRAM da Whatsapp(only
when subscribers reach 100) ki aika naira 800 kuɗin karatu mallakin mutum ƊAYA zuwa asusun
1840175439
Babu nadama cikin tafiyar nan da yardar Allah. Zamu ilimantu, mu nishaɗantu sannan mu ɗan sha takaici
kaɗan.
Albishir, kiyi joining FANS GROUP na KUNGIYAR MARUBUTA MATA ZALLAH domin samun garaɓasar
karanta ƙarin pages uku Free 💃🏼💃🏼💃🏼💃🏼
(Based on true life event, some parts are fictional to spice up the story)
LABARI/RUBUTAWA MARYAM FAROUK (UMMU-MAHEER)
07061838488
Arewabooks
@Maryamfarouk01
Wattpad
@MaryamahMrsAm
TikTok
@Maryamfarouk_Ummu-mahir Novels
Ban yarda wani ko wata ya juya mun labari ta kowacce siga ba tare da izini na ba. Kuɗin karatu yana
wakiltar mutum ɗaya ne, ki ji tsoron Allah karki ɗauki hakkina ta hanyar fitar mun da littafi
KURA A RUMBU littafin kuɗi ne, a biya naira 800, biya a asusun
1840175439
Access bank
Page 6
Duk nazarin na ban hango abin da take ganin na rashin dai dai ba. Rashin yi mun kyauta ne aibun sa ko
kuwa rashin kammala ginin da be yi ba da kuma zancen lefe? A cikin ukun sune abin da nake ganin Anty
Labiban take emphasizing se dai ni a ganin ta wannan ai ba komai bane ba. Bilal nake so ba abun
hannunsa ba. Iya kar ƙoƙari yana yi gurin ganin ya kammala in da ze ajiye ni kuma ba a ɗaura auren nan
an ga be yi mun lefe ba balle su ce wani abu. Ni duk wani lefe da wasu bidi'o'i basa gabana duk da dai ba
zan ce bana so ba amma tunda nasan wanda zan aura bashi da ƙarfin yi shi yasa ban sawa raina ba sanin
kuma masu shirya mun a gida ba yin al'amarin suke yi ba shi yasa kwata kwata ban sa a ka ba. Ko ankon
yammata na kamu dana fitar saboda naji Mama da Aminyarta Hajiya Rakiya suna maganar ne shiyasa
har na saka ran Maman za tayi taro.
Ban cewa Anty Labiba komai ba itama kuma ganin na ci gaba da sabgogina ba tare da na ce mata komai
ba yasa ta fahimci amsar ke nan ina kan bakana ba gudu ba ja da baya. Allah ya gani tayi bakin ƙoƙarinta
gurin haska mun tun da kuma na runtse ido abin da ya rage kawai su bini da addu'a ne, Allah ya saɓa
tunanin su akan Bilal ɗin. Shikenan ta aje komai ta shiga yi mun gyara irin wanda ya dace da budurwa
kuma yar gata kama ta.
Biki nata matsowa, tun da na koma gidan Anty Labiba sau ɗaya Bilal yazo a waje kuma muka tsaya yace
sauri yake yi be zauna ba tun ranar kuma se dai muyi waya. Idan na masa ƙorafi yace aikin gini ne da
sauran shirye shirye suke hana shi zuwa har ya rage saura kwana ashirin da biyar ranar Hansa'u tazo ta
sakani gaba akan dole na kira Bilal ya basu kuɗin sallamar yammata ko kuma ita ta kira shi da kanta. Kira
biyu na masa be amsa ba se ya mun text akan suna seminar ne ze kira ni. Se na mayarasa da text ɗin
akan Hansa'u ce take so za suyi magana ina jiran sa. Har aka yi sallar isha'i muna zaman jiran kiran sa ko
ya zo amma shiru daga ƙarshe ta tafi bayan da mukayi faɗa dan tace yana sane yaƙi zuwa ni kuma na
kafe akan be gama abin da yake yi bane. Ko minti biyar bata yi da tafiya ba kuwa se gashi ya kira ni. Se da
na gayawa Anty Labiba kafin na fita, ya ringa kallo na yana yaba kyan da nayi.
"Amarya kin sha ƙamshi. Kin ga yanda walwalinki yake haske ido kuwa Halims menene sirrin?"
Murmushi kawai nayi na wuce ciki ya bi bayana ya na cigaba da zugani. Se da na aje masa ruwa da lemo
yana ta bin duk motsi na da ido kamar ze cinye ni ɗanya, har na zauna ya kalle ni yana shafa cikin sa yace
"Yanzu fa muka gama ko gida ban je ba na taho dan nasan kina jira na". Se da na kalle shi sama da ƙasa,
ƙananan kaya ne a jikinsa baƙin wandon da army green ɗin riga short sleeve. Sumar kan sa ta ɗan taru
haka gashin fuskar sa da alama ya kwana biyu be yi aski ba ga ƙamshin turaren sa ya baibaye ko ina ni
dai be yi mun kala da wanda ya wuni a gurin aiki ba. Cikin gida na wuce dan na fahimci maganar tasa
yunwa yake ji. Se da yaci ya ƙoshi ina kallon sa ya sha ruwa kafin ya washe baki yace
"Kin san Allah, ni fa idan bake kika bani abinci ba sam se dai kawai naci amma bana ƙoshi". Nayi
murmushi kawai se ya sake cewa
"To Hansa'un? Babbar Aminiyar mu Allah dai yasa ba tayi fushi ba"
"Ai ta tafi gida ma" na bashi amsa a gajarce, se ya fito da ido yace
"Haba dai? Ai na ɗauka ta dawo nan da zama itama har se an gama biki shi yasa ko da naga nayi magriba
ban gama ba ban damu ba tun da kuna tare".
"Ka ji ka da wata magana fa, bikin saura kwana 25 shi ne zata dawo nan da zama tun yanzu?" Na bashi
amsa ina kallon sa se yace
"Au haka fa, kin san saboda zumuɗi gani nake kamar sati biyu ne ya rage"
"Ban ga alama ba" na bashi amsa kai tsaye se yayi shiru yana kallo na. Haɗe fuska nayi na ci gaba da
cewa
"Dama zuwa tayi akan maganar shirin biki da abun da za muyi na yammata shi ne tace na kira mata kai
ka sallame su".
"Hajiya Hansa'u kenan iyayen rigima, wace sallamar yammata kuma se kace wasu yara ko yammatan
ƙauye?" ya faɗa yana wata dariya me kama da ta rainin hankali. Se kawai na tsaya ina kallon sa jin abin
da yace wai kamar yara ko yammatan ƙauye, me yake nufi kenan?
"Kin yi shiru kina kallo na" ya faɗa yana kawo hannunsa fuskata na goce nace
"Ban fahimci abin da kake cewa bane, a ƙauye ne ake bada sallamar ƙawaye?"
"Ni dai gaskiya rabon da naji an bayar da wani kuɗin yammata tun san da Abdulhadi yayi aure da muka
je can garin ƙawayen amaryar nan suka sa mu gaba wai se mun basu kuɗin party" ya faɗa. Se kawai nayi
shiru ina jin sa yana ta zuga zance shi kaɗai ni kuma ina danna wayata. Sallamar Anty Labiba ce ta katse
shi. Ya zamo daga kan kujera kamar gaske ya shiga gaishe ta ta amsa fuska ba yabo ba fallasa kafin ta
fara magana
"Dama na tambaye ta zancen gida dan muna so mu ga guri saboda musan awon labule da sauran
abubuwan da zamu mata se take cewa bata sani ba, ga lokaci yana ta matsowa bama so a shiga hidimar
biki bamu sallami gidan amarya ba".
Kamar in toshewa Anty Labiba baki haka na ringa ji sanda take maganar, na kalli Bilal yana ta mutsu
mutsu kamar wani mara gaskiya se naga kamar harda zufa yake yi duk kuwa da garin babu zafi. Anty
Labiba tayi shiru tana kallon sa bayan ta gama magana tana jiran jin amsar sa amma be ce komai ba se
satar kallo na da yake yi ni kuma na sadda kaina ƙasa se ta miƙe ta kalle ni tace
"Duk yanda kuka yi ina jiran ki" ta fice ta bamu guri. Gani nayi yanayin fuskar sa ya canza, zuciya ta ta
tsinke amma na dake na saurara naji ze ce wani abu dangane da maganar data masa amma naji shiru se
ma kallon agogo da yayi ya ɗauki muƙullin sa daya ajiye kan center table ya kalle ni yace
"Dare ya fara yi Halims bari nazo na wuce ko?" Ya faɗa yana miƙewa tsaye. Mamaki yasa kawai na bishi
da kallo na kasa cewa komai. Yayi murmushi yace
"Babu rakiya? Ko baki gaji da kallo na bane na zauna?" Cikin ɗari ɗari nace
"Baka ce komai ba akan abin da Anty Labiba ta faɗa". Murmushi ya sake yi mun yace
"Na ji mana Halims, cewa tayi ai duk yanda mukayi ki gaya mata. Na zata duk abin da ake ciki kin sani me
yasa baki gaya musu ba da har zaki bari yanzu ta titsiye ni? Me kike nu fi kenan Halima? So kike a ga
gazawa ta ko me? To yanzu ai se hankalin ki ya kwanta tun da kin tozarta ni" ya faɗa sautin sa a ƙasa se
dai yanayin kalaman da kuma yanda ya kira ni da Halima kai tsaye mai makon Halims yasa na fahimci
ransa a ɓace yake.
"Yanzu kuma me nayi? Wace irin magana kake yi haka dan Allah meye abin tozarci a nan?" Na faɗa ina
marmar da ido, gaba yayi yana cewa "Na gaji sosai bacci kawai nake so nayi zamuyi magana daga baya
kawai"
Yanda kasan ya ɗaure mun baki haka na tashi na masa rakiya zuwa ƙofar falon ya tafi, ɗaki na wuce na
kwanta bayan na kwashe kayan da yayi amfani dasu. Anty Labiba bata ce mun komai ba kamar yanda ni
ma ban ce mata ba, haka Hansa'u data ki rani da safe kan ya mukayi nace zan kira ta shikenan bata sake
tada maganar ba tun ranar kuma Bilal be zo ba a waya ma sau ɗaya ze kira ni da safe ko da yamma da
mun gaisa ze kashe ko da na ɗakko magana ze bani uzurin yana abu shi kenan se washe gari kuma ze
sake kira. A haka muka shafe kwana goma, idan ka ganni baka buƙatar a ce maka bani da nutsuwa
saboda yanda jiki na ya nuna. Dama ba wani auki ne dani ba, ba tsahon kirki kuma bani da kiɓa, ɗan
gyaran da Anty Labiba take mun da kunun alkama da madarar da dake ɗura mun suka sa na fara kumari
yanzu kuma bani cikin nutsuwa ko abincin ma se naji yunwa na neman kayar dani nake ci ita kuma ta
saka mun ido bata ce mun yi bata ce mun bari. Randa aka kwana takwas da zuwan Bilal ne ma da ta
ganni na zauna na zubawa guri ɗaya ido ina tunani shine har ta mun magana tace
"A banza zaki kashe kanki Halima mu zaki yiwa asara tun da dai gashi ƙiri ƙiri ya nuna miki baya yi idan
kina da hankali ya kamata ki cire shi daga ranki. Dama yau nake niyyar in tambaye ki in gayawa Mama
yanda akayi saboda kar su cigaba da shirin biki a banza ko kuwa dai in kama kaina kar in shiga abin da
babu ruwana?"
"Ya yake so nayi Anty? Me zanyi Bilal ya gane irin son da nake masa?" Na faɗa cikin matsanan cin kukan
dake fitowa tun daga ƙasan raina. Na yarda son Bilal jarabawa tace babu kuma wanda ze fahimci yanda
nake ji har shi kansa kuwa. Kamar zata share ni ta wuce se kuma ta zagayo ya zauna gefe na tare da jana
jikin ta nan kuwa na sake samun sararin yin kuka yanda nake so. Cikin tausasawa ta shiga yi mun magana
tana cewa
"Halima har se ya buɗe baki yace baze aure ki ba kafin ki fahimci kurman baƙin da yake miki? Halima ko
a littafin hausa kin taɓa jin labarin neman aure irin naki? Aure fa za a yi na yar mutum ba wai yar tsana
ba amma ace ƙasa da wata ɗaya ba ango ba dangin sa ba babu wani ɓangare da suka nuna murna ko
zumuɗin su akan abin da ze faru a ina kika taɓa ganin an yi haka?
Ki ture duk wasu al'adu ace ba dole bane basu yi ba amma Halima muhalli yana cikin sharuɗan da se sun
samu kafin aure ya ƙullu, a ina ze ajiye ki? Ko kuwa dama lasisi yake nema a gidan ku zaki ci gaba da
zama bayan an ɗaura muku auren ko yaya? Yau idan haya ze kama biki ƙasa da sati uku yaci ace ya samu
har ya nuna guri an san me za a saka miki. Kwana nawa ina miki magana akan ki tuntuɓe shi? Yanzu da
na masa magana da kaina gashi ya nuna miki zahirin da kika kasa ganewa ko kuma da be fito miki a
mutum ba ba auren ki yaron nan ze yi ba ki godewa Allah da be samu galabar lalata miki rayuwa ba ki
haƙura ki barwa Allah zaɓi Halima".
"Bilal yana so na kuma aure na zeyi Anty. Ta yaya za ayi ya turo iyayen sa a saka mana rana har idan ba
aure zeyi ba? Kuma zancen gida na gaya miki gini yake be ƙarasa ba ni muna magana ya kuma tabbatar
mun kafin ranar biki ze gama komai gajen haƙuri kawai kika yi kika masa magana gashi yanzu kin saka
ransa ya ɓaci, yaƙi ya zo a waya ma sau ɗaya yake kira na kuma bata ko bari muyi doguwar magana ze
kashe idan ma har ya ce ya fasa ɗin ai ke ce kika jawo ba wai a karan kansa yayi ra'ayi ba" na faɗa cikin
kuka. Yanda tayi shiru tana kallo na ta tabbatar neman hanya mafi sauƙi da zata huce takaici ma takeyi ta
rasa, se na miƙe ina cewa
"Ni gidan mu kawai zan tafi, dama ai so kike yi ya fasa aure na shiyasa idan ba haka ba ai ina ji har Mama
se da tace ki rabu damu ai ni ce zan aure shi tun da naji na gani kowa nasa ido ne" na wuce ɗakin da
nake ina ci gaba da kuka haɗi da zazzaga mata rashin kunya. Kaya na na shiga haɗa wa a akwati waya ta
dake jikin caji tayi ƙara jin ringing ɗin Bilal yasa na saki kayan hannu na na wuce gurin wayar da sauri na
ɗaga.
Kamar ko da yaushe a kwanakin nan muryarsa cikin sanyi ya amsa gaisuwar da nayi masa kafin yace
"Ba abinda nake yi, wani abu kake buƙata nayi maka? Ko abinci kake so?" Na faɗa cikin zaƙuwa. Ina jin sa
ya sauke ajiyar zuciya kafin yace
"Ina so na ganki ne, akwai maganar da nake so mu tattauna me muhimmanci idan babu damuwa"
"Wace irin damuwa kuma? Yanzu zaka zo ko se da daddare?" Na amsa shi, se yayi ɗan jimm kafin yace
"Ke zaki zo ki same ni idan zaki iya amma". Shiru nayi na kusan minti ɗaya ina juya maganar a raina, abin
da Anty Labiba ta faɗa mun yanzu akan na godewa Allah da be lalata mun rayuwa ba ya faɗo mun a rai
se nayi saurin korar maganar daga raina ina bawa kaina tabbacin Bilal ba ze taɓa yaudara ta ba ba kuma
wannan niyyar ta kawo shi guri na ba.
"Karki takura kanki idan ba zaki iya ba babu damuwa dama magana ce akan abinda ya shafe mu mu biyu
da nake ganin ya kamata mu tattauna amma zamu iya barin ta kawai idan baki da lokaci" ya katse mun
shirun da nayi. Ban san sanda harshe na ya furta
"Ina shagon Sani" ya bani amsa. Se na sauke ajiyar zuciya jin ba wani guri daban ya ce na same shi ba har
na tsinewa shaiɗan ɗin daya fara kawo mun wasi wasi akan Bilal ɗin. Aje wayar nayi na shiga toilet da
sauri na canza pad ɗin jiki na tare da wanke fuskata na fito na canza kaya. Dogon Hijab na saka da niƙab
saboda munafukan unguwan mu. Dana fito ban tarar da Anty Labiba a falo ba se Amir ne ya tare ni yana
tambayata me ya samu Momy ya shiga ɗakin ta ya tarar da ita tana kuka nace masa ban sani ba sauri
nakeyi kuma ana jira na ne yaje ya bata haƙuri.
A bayan gidan mu Chemist ɗin Abokin sa Sani yake, haka na ringa gyara niƙab ɗin fuskata harda canza
tafiya dan kar a gane ni ce, na tarar da shi da Bilal zaune suna hira. Kallo ɗaya na masa na hango ramar
da yayi idanunsa sun sake fitowa haka dogon hancin sa ya ƙara tsayi hatta da lips ɗin sa se naga sun
bushe sun ƙara jaa alamar yana cikin damuwa ko bashi da lafiya. A taƙaice muka gaisa da Sani kafin ya
fita ya bamu guri. Na sauke kaina ƙasa saboda yanda Bilal ya kafe ni da nasa idon da nake jin sun ƙara
kaifi yau, sama da minti biyar muna zaune kafin a hankali ya fara magana yace
"Kiyi haƙuri Halims be kamata ace na ɗauki fushi akan abin da ya faru ba. Bayan na dawo gida na nutsu
na gane kun fini gaskiya se dai ina cikin wani yanayi da ni kaɗai na san wane hali nake ciki duk kuma
wanda zan yiwa bayani be zama lallai ya fuskan ce ni ba". Kallon sa nayi jin yayi shiru se yayi murmushi
ya ci gaba da cewa
"Tun farko shiyasa ban so aka saka bikin nan wata shida ba kuma kema na gaya miki, dalilin da ya saka
bana ɓoye miki komai da nake ciki kenan Halims saboya tunani na duk abin da ya taso za kiyi mun uzuri"
se na ɗaga kai na kalle shi yayi saurin cewa
"Ban ce baki mun ba, wlh na sani kin yi ƙoƙari. Kin mun abin da ba kowacce mace ba kuma na yaba and i
will for ever be grateful for that Halima. Ke ɗin kin nunawa duniya true love still exist, se dai har yanzu
ban kai ba Halima. Nayi tunanin a wata shidan nan zan iya yin ƙoƙarin ganin ban baki kunya ba amma se
yanzu na fahimci wautar da nayi gashi kuma lokaci ya ƙure mun balle na juya da baya".
Gaba na ya yanke ya faɗi baki ja har yana rawa na kalle shi nace
"Ban gane ba, what are you trying to tell me Bilal what do you mean by lokaci ya ƙure balle ka juya
baya?"
"Relax Halima ba wani abu nake nufi ba" ya faɗa yana kama hannu na, se na fizge ina kallon sa se dai na
kasa ci gaba da magana saboda yanda zuciya ta take wani irin bugu kamar zata huda ƙirjina ta fito.
Wayar sa ya ciro daga aljihun sa yayi danne danne kafin ya miƙa mun, hannuna na rawa na karɓa na kalli
screen ɗin. Video gidan daya kai ni a matsayin nasa wanda zamu zauna a ciki ne yake playing, seda na
kalla daga farko har ƙarshe kafin na kalle shi muka haɗa ido dan shima ni yake kallo se ya karɓi wayar ya
mayar da ita aljihunsa kafin ya haɗe hannu biyu ya dafe haɓarsa ya furzar da iska daga bakin sa kafin
yace
"Bayan da aka saka ranar auren mu munyi magana da Baba Liman ya kuma kira gidan su yaron da ze auri
Fadila akan suyi haƙuri a ƙara ranar auren su zuwa wata goma amma suka ƙi yarda akan in dai ba wata
shidan da suka yanke ba se dai a mayar musu da kuɗin su kawai ya haƙura ya fasa auren ta. Na gaya miki
Halima ni zan yi mata komai na aure, babu abin da baki sani ba a kaina tun da mahaifin mu ya rasu duk
wata ragama ta yan ɗakin mu ta dawo kaina. Yayyenmu tun da muka samu saɓani dasu lokacin rabon
gado shike nan suka zare hannun su daga komai daya shafe mu ko sanda nace babu damuwa a bar
zancen auren mu a wata shidan na ɗauka su Yaya Alhaji ze yiwa Fadila kayan ɗaki ne se da kuma biki ya
taho da Hajja tayi musu magana suka ce ai an raba gado an bawa kowa nasa dan haka ba abin da zasu
mana.."
"Bilal ka faɗa mun kai tsaye me kake nufi ko me kake so ayi yanzu dan Allah tun baka janyo zuciya ta ta
buga ba" na katse dogon sharhin daya ɗakko wanda babu abin da nake fahimta a ciki. Shiru yayi ina
kallon yan da abin wuyan sa ke sama da ƙasa alamar magana na cikin sa ya kasa furtata kafin ya sake riƙe
hannaye na biyu duk yanda naso na ƙwace be bani dama ba haka ya kafe idon sa cikin nawa yana murza
zoben dake hannu na yace
"Ina son ki Halima bana fatan na rasa ki amma a yanzu bani da halin auren ki".
"Dagaske Bilal dama yaudara ta kake yi ba aure na zaka yi ba?" Na faɗa cikin karyewar sauti. Se ya ƙara
ƙarfin ruƙon da yayiwa hannaye na yace
"Allah shine shaida ina son ki Halima dai dai da rana ɗaya ban taɓa niyyar yaudarar ki ba"
"Amma da bakin ka yanzu kace ba zaka iya aure na ba, me yasa tun farko baka faɗa mun ba se da ka bari
auren mu ya rage sati biyu?" Na faɗa ina fashe wa da kuka.
"Nayi zaton zan iya Halima, na ɗauka zan samu yanda nake so kafin lokacin amma hakan yaci tura. Ta
yaya kike zaton iyayenki zasu bani ke bayan ba ni da ko muhallin da zan ajiye ki?" Ya faɗa tamkar shi ma
ze fashe da kukan. Kamar zan shiɗe nace
"Shi kuma wannan gidan fa? Ko dama ba naka bane ƙarya kayi mun kace na ka ne?"
"Gida na ne Halima amma wannan shi da kango ai basu da maraba ta yaya mutum ze shiga ya zauna a
gurin da ko daɓe babu? Ki aje maganar wannan gidan a gefe kawai dan dashi da babu banbancin su
kaɗan ne. Da ace ina da sararin da zan kama miki haya ma da wlh bazan damu ba amam bani dashi, a
yanzu bani da wasu kuɗi a tare dani se wanda za a siyawa Fadila kujera su kansu basu gama haɗuwa ba
dama sadakin ta ne na cika kuma na ranci wani abu ciki dashi na ƙarasa aikin fulasta ai kin gani sanda
muka je iya waje ne da fulasta ba ayi a waje ba ko? Zaɓi biyu ne kaɗai ya rage mana Halima, ko dai a
ɗaga auren mu wanda bana zaton iyayenki zasu amince tun da har sun ambata dama akwai wanda suke
so su haɗa ki dashi a familyn ku kenan se dai na haƙura dake tun da bani da halin auren ki shikenan
rayuwa ta tazo ƙarshe ban san wace alƙibla zan kalla ba idan babu ke a tare da ni".
*(Based on true life event, some parts are fictional to spice up the story)*
*Ban yarda wani ko wata ya juya mun labari ta kowacce siga ba tare da izini na ba*
*Kuɗin karatu yana wakiltar mutum ɗaya ne, kiji tsoron Allah karki ɗauki hakkina ta hanyar fitar mun da
littafi*
*KURA A RUMBU littafin kuɗi ne, a biya naira 800, biya a asusun*
*1840175439*
*Access bank*
*PAGE 7*
Page 7
Na fi minti goma tsaye a ƙofar gidan mu ni ban shiga ba kuma ban bar gurin ba. Maganganun da mu kayi
da Bilal ne suke mun amsa kuwwa a kunnuwa na da ƙwaƙwalwata bana kin ko wanne sauti dake zagaye
dani banda muryar sa.
"Ba ni da kuɗin da zan ƙarasa gini Halima, ba kuma ni da sararin da zan kama haya a yanzu. Abu biyu ya
rage, ko dai iyayen ki su ɗaga auren mu ko kuma mu haƙura gaba ɗaya, ƙila a gaba idan muna da rabon
kasancewa tare se muyi aure. Ina son ki Halima amma bani da halin mallakar ki a yanzu" kalaman ƙarshe
daya gaya mun kenan. Bana ko gani sosai na shiga bubbuga ƙofa, se da na buga sau uku kafin aka buɗe.
Musa ne, jikan Goggo Habi Ƙanwar Mahaifin Mamanmu. Ɗan ta ɗaya Baba Sulaiman kuma shine
mahaifin Musan accident suka yi dashi da matar sa duk suka rasu. A Birnin gwari take da zama dama naji
Anty Labiba tana faɗar tace tun biki na saura sati biyu zata zo ashe har ta zo ɗin kuwa.
Kallo na ya tsaya yi saboda niƙab ɗin dake fuska na raɓe shi na wuce ina haɗa hanya, motar Abba da na
gani a ajiye yasa na gane yana gida dan haka kai tsaye na wuce falon sa. Tare da Aminin sa Baba Hashim
na same su suna magana daga kuma yana yin fuskokin su na fahimci ko ma me suke tattauna ba magana
me daɗi bace. A tare suka amsa sallama ta suna kallo na, ka ƙarasa gaban Abba, tamkar wadda tazo isar
da saƙon rasuwa haka na fashe da kuka irin me gigitar nan har jiki na yana jijjiga. Abba ya miƙe hankali
tashe ya ruƙo ni yana cewa
"Lafiya Halima? Me ya samu su Labibar?" Haka Baba Hashimu ma cikin kaɗuwa suka ringa tambaya ta
me nene amma na ƙi cewa komai har se da nayi kuka iya kar yi na se da naga Baba Hashimu ya nufi ƙofa
yana cewa
"Ba se ka kira ta ba". Se da na sake kwashe kusan minti biyar ina kokawa da kukan dake taho mun da
zarar na buɗe baki kafin daƙyar na iya cewa
"Me ya same shi?" Abban ya tambaye ni. Ina kuka tamkar raina ze fita na tsara musu duk yanda mukayi
da Bilal da abin da ya gaya mun ban rage komai ba. Su kayi shiru kamar ruwa ya cinye su banda sautin
kuka na da ƙarar fanka baka jin komai har kusan minti goma da alama duk su biyun bakin su ya mutu sun
rasa abin da zasu faɗa ne. Daƙyar Baba Hashimu ya katse shirun yace mun
"Ki bar kukan haka Halima kiyi shiru muyi magana". Se da na sake shafe wasu mintunan kafin na iya
tsagaitawa da kukan, yace
"Zaman nan da muka yi zancen ki muke yi Halima. Mahaifinki ya kira ni yana cike da damuwa akan
lamarin auran ki. Yau saura kwana goma sha huɗu amma babu wata magana me ƙarfi daga gidan maza
su basu zo akan suna sane da lokaci ba kuma basu ce wani abu dangane da shirun da suka yi ba. Yanzu
Alhaji Salahu muke ji yazo mu ji ta bakin sa akan abin da ya kama muyi se kuma gashi kin zo da wannan
maganar. Ina ganin ai ba abin kuka da tayar da hankali bane ba, dama kullum cikin yi muku addu'a muke
akan Allah ya zaɓa muku mazaje na gari. Irin haka babu daɗi, amma sha'anin aure da ace ayi azo ana
dana sani daga baya gara a haƙura se kiga ubangiji ya musanya miki da wanda ya fishi zama alkhairi a
gare ki".
Kukan dana sake fashewa dashi se ka rantse da Allah irin marin nan na shammata ya zabga mun, ko da
yake ai gara ya dake ni naji zafin a kan fata ta da ciwon da yake neman haifar wa zuciya ta. Na rabu da
Bilal fa yake cewa. Daga shi har Abban Kallo na suka ringa yi cikin mamaki za a ko ace ɗimuwa tamkar dai
basu fahimci dalilin sabon kukan dana dasa ba. Ban ji nauyin Baba Hashim ba domin dama Abba babu
batun jin kunya tsakani na dashi nace
"Wallahi ina son sa Abba, idan na rasa Bilal ban san ya zanyi da rayuwa ta ba ni dai a nemi wata mafitar
amma kar ma a fara cewa in rabu dashi" na haɗe kai na da kujera na ci gaba da rera kuka. Baba Hashim
ya ringa salati yana tafa hannu Abba dai yayi shiru ya tallafe haɓar sa da hannu biyu yana kallo na. A
haka Baba Salahu ya shigo ya same mu, a taƙaice Baba Hashim ya yi masa bayanin abin da nazo musu
dashi yayi shiru kawai yana jimanta abun a ransa yana kallo na, jin kukan nawa bana ƙare bane yasa ya
fara magana cikin lallashi yana cewa
"Yi shiru Halimatu kwantar da hankalin ki babu wanda ze raba ku amma ki fara amsa mun tambayar nan
tsakani da Allah kar ki mun ƙarya ni kuma zan yi iya ƙoƙari na ganin na samar miki muradin ki". Na
tsagaita kukan ina share hawaye haɗi da face maji na da hijabi na, shiry ya ɗan yi cikin jin nauyin
maganar da take bakin sa kafin daƙyar ya iya cewa
"Halimatu, kar kiji nauyi ko kunyar mu ki gaya mun tsakanin ki da Allah wani abu na rashin dacewa ya
taɓa shiga tsakanin ki da Bilal ne?"
Da sauri Abba ya kalle shi se Baba Hashim ya masa alama da ido akan kar yace komai ni kuwa a yanayin
da nake ciki ban ma ji tambayar tasa a wani daban ba kai tsaye na ce masa
"Wallahi Baba Bilal ba ɗan iska bane ni yake so tsakani da Allah ba wai wani abu nawa ba. Ni ko hannu
be taɓa riƙewa da gangan ba aure na yake so kawai ba wani abu ba".
"Alhamdulillah" suka haɗa baki su ukun suka faɗa Abba har seda ya gyara zama ya koma cikin kujera ya
kwanta haɗi da rufe idanun sa. Nasiha Baba Hashim da Baba Salahu suka shiga yi mun se dai jin su kawai
nakeyi badan ina ɗauka ba, sanyin da naji da duk su biyun suke jaddada na kwantar da hankali na babu
abin da ze faru zasu kira Bilal suyi magana dashi. Dana fito daga falon nasan in na shiga gurin Mama
ƙarshe raina ne ze sake ɓaci se kawai na maida niƙab ɗina na fice na tafi gidan su Hansa'u.
Hajiya Amina na zaune ta zabga tagumi tana sauraron Goggo Habi dake zuba tijara, tun yammacin jiya
data sauka gidan ta ce a fito mata da kayan lefe ta gani aka ce babu shi kenan ta dasa tijara in tayi ta gaji
ta huta an jima ta ci gaba, yanzu ma zuwan Inna Salamatu Yayar su Alhaji Aminu ta biyu yasa aka sake
maido da zancen sabo.
"Ni tun da uwata ta haife ni ban taɓa jin labari ko ganin neman aure irin wannan ba, ni fa tun ga ni na da
yaron sau ɗaya ban ga miji a nan ba yana yawo da wata shegiyar suma kamar zakaran da yake tashen
balaga na ɗauka shiritar yarinta tasa ta biye masa da zarar ta samu nutsatstse me hankali zata rabu dashi
ashe abu dai bana ƙare bane. Ban da ma sakaci irin naku na iyayen yanzu ke Amina kina ina har kika bari
har tayi sabo da wannan lalata mogal ɗin?
Irin waɗannan samarin dama kowa yasan basu aje ba basu bawa kowa ajiya ba se dai suyi wanka su
ringa yawo kwararo kwararo duk in da suka ga yarinya me ɗan gwaɓi gwaɓi su shiga jikin ta su hanata
kula mazan arziƙi daga ƙarshe su gudu su barta, in kuma Allah ya ƙaddara an yi aure ayi ta tsallen tsiya
ana jeka ka dawo akan me?
Tun da suka ce zasu zo neman auren me yasa baku dakatar dasu ba ku ce kun wa yar ku miji se yanzu
zaki zauna kina tagumi da maganganun banza da ba zasu miki amfani ba to wlh tun wuri ki tashi tsaye ki
ƙwato yar ki tun ba a kai ki an baro ba, ke Salamatu da zaki ce aure saura sati biyu mutane zasu yi surutu
idan aka fasa in yar ta shiga garari uban waye ze taimaka musu balle a guji maganar da zasu yi? Allah ya
tsinewa duk wanda be yi surutu ba, dama ai mugun hali irin na mutanen yau yasa suka yi shiru kaf
maƙwaftan ku ace an rasa wanda ze bugi ƙirji ya faɗawa Aminun gaskiya idan duk su yan uwansa maza
yan ubanci yasa sun yi shiru suna kallo yar sa zata shiga gararin rayuwa su sauran da za a haɗa auren su
tare idan da haka nasu maneman suka shuka rashin arziƙi ai ba zasu ja baki su kulle ba se shi za a masa
mugunta a bar shi son ya ya rufe masa ido to ba a isa ba se kuma naga uban da ze ƙulla auran nan"
Goggo Habi ta faɗa.
Mama dai juya kai kawai take yi ta kasa cewa komai, tun da Anty Labiba ta kira ta ta gaya mata ta yiwa
Bilal magana da kanta be ce komai ba daga nan ta ƙarasa cire ranta akan al'amarin auren sa da Halima ta
kuma godewa Allah daya sa matsalar ta ɓullo daga gurin sa ko hakan ze sa Halima ta hankalta ta Kuma
haƙura se dai ko da ta yiwa Abban zancen cewa yayi kar ayi saurin yanke hukunci a jira aji ta bakin su tun
da akwai sauran lokaci.
"Amma Hajiya na ke ganin abi komai a sannu ya fi, shi lamarin aure sirri ne ba'a san abin da Allah ya
ɓoye ba be kamata ace muyi katsalandan a ciki ba. Aure nawa akayi a cikin irin haka daga baya kuma se
kiga Allah ya warware komai ya wuce kamar be faru ba balle yaron nan ba wai zauna gari banza bane
yanda kike tuna ni. Da aikin sa, a gwamnatin tarayya yake aiki bama state ba kin ga ko ai yana da
albashin da ze riƙe aure mace biyu ma ba ɗaya ba, shi shirin aure kowa ya sani Allah ke yi ba mutum ba
duk kuɗin ka duk tana din ka se kiga abu ya zo maka ba a yanda kayi tsammani ba musamman ace aure
ya taso ga gini abin duk se a hankali fatan mu dai Allah yasa haɗin ya zama alkhairi duk wani ƙyale ƙyale
da bidi'a ba shi ne ba".
"Lallai Salamatu dole ki ce haka, tone tone babu kyau amma da se in ce ai ba zaki ga aibun abun ba tun
da irin auren da aka miki kenan da Mijin ki na Farko Haladu me kifi har yamma tayi za'a tafi kaiki ɗakin da
aka bashi aro a cikin gidansu ba'a kwashe hatsin da aka ajiye a ciki ba. Haka muka raka ki aka ajiye ki a
ɗakin uwar sa, ina kwananki uku Allah jiƙan rai Halima taje ta ɗakko ki aka kashe auren irin haka kike so a
maimaita to ba da mu ba wallahi ba a taɓa ba ba kuma za a fara akan Halima ba"
"Haba Goggo dan Allah ki de na faɗar haka" Mama ta faɗa se ta juya kan ta kafin tayi magana Abba da
Baba Salahu suka yi sallama hakan yasa tayi shiru. Sama sama ta amsa gaisuwar da suka mata dan tun
jiyan tace komai daya faru laifin Abba ne shi kuma Baba Salahu ta ce yan ubanci yasa yaƙi gayawa Abban
gaskiya. A tsanake Abba ya sanar musu da abin da Halima ta gaya musu ya rufe da cewa
"Da nasan ze zo da wannan maganar da ban fara rabon katin ɗaurin auren nan jiya ba. Gashi jar
abokanai na na wasu garuruwan duk jiya na aika musu dan kar ya zama a ƙurarren lokaci har an fara turo
mun da gudumma yanzu se dai na maida musu na bawa kowa haƙuri kenan".
"Aa wace irin magana kake yi haka ai ba cewa yayi ya fasa ba uzurin sa ya bayar be kammala gini ba,
abun duk me sauƙi ne kiran sa ya kamata ayi aji ta bakin sa ko a kira su waliyyan nasa, idan lokacin ne
baze ishe shi ba se a ɗaura auren a bar biki zuwa sanda ze kammala se su tare idan kuma haya ze nema
duk ba wani abu bane suyi zaman su wata rana se kaga komai ya wuce kamar ba ayi ba" Inna Salamatu
ta faɗa se Goggo Habi ta miƙe tana cewa
"Da ba cikin ku dayayda Aminu ba se in ce kema hassada kike masa Salamatu ko da yake dama ai duniyar
nan ta lala ce kai dai kayi ta kanka kawai to in ga dan bantan uban da ze zauna dashi ko iyayen nasa
maza azo a haɗa duk tsiyar da suka kawo a maida musu yanzun nan ba se an jima ba gara da akayi haka
Allah ya haɗa kowa da rabon sa ma alkhairi kan ta farau fasa aure ko a kanta za'a ƙare balle ace? Maza
Amina taso muje ki tattaro komai da kika san ya kawo gidan nan a fitar dashi".
Mama ta sauke tagumin data zabga tun da Abba ya fara maganar tace
"Mantawa nayi, to bari in ɗauko hijabi na ke Salamatu ki tashi ki raka ni can gidan nasu muje mu zage su
dan ba zamu bar su haka ba ladan ɓatawa jikata lokaci da yayi dan uban sa" Goggo Habi ta sake faɗa, se
Abba yayi saurin cewa
"Duk abin be kai na haka ba Goggo ayi haƙuri" ta musu banza ta shige ɗaki. Daga ciki ta ƙwalawa Mama
kira ta tashi ta tafi. Bayan barin su gurin Inna Salamatu ta kalli Abba tace
"Kada ka biyewa zancen Habiba kasan ta da rikici tun zamanin ƙuruciya balle yanzu da girma ya cimmata,
maganar yaron nan uzuri ne babba yazo dashi tun da dai muhalli a aure yana gaba da komai. A gani na
kar a biyewa shaiɗan ace za'a fasa auren nan akan wannan, arziƙi da babu duk daga Allah ne nan duk
daga babun muka taso gashi yanzu ubangiji ya bawa kowa bakin rabon sa. Ni dai shawarata Aminu ku
kira iyayen yaron nan kuji ta bakin su, in har ba su suka ce a bar maganar auren nan gaba ɗaya ba karku
bari ace daga gefen ku matsala ta ɓullo ba".
"Amma Yaya maganar gaskiya fa lamarin nan abin dubawa ne. Yau da ace yaron nan ya nuna iya ƙoƙarin
sa a sabgar nan za'a fi samun ƙwarin guiwar kyautata masa zato amma fa ki duba tun da aka fara
maganar nan wane yunƙuri yayi ko iyayen sa suka yi, ko sadaka za'a basu auren yarinyar nan ai yaci su
nuna yabawa amma yau har saura kwana goma sha huɗu ba kira ba aike kuma jiya fa ko jiya naga katin
auren ƙanwar sa Alhaji Malam ya raba a kasuwa kuma sunan ta ita kaɗai aka buga ban da nasa" Baba
Salahu ya faɗa, Abba dai be ce komai ba ya harɗe hannu biyu yana sauraron yan uwan nasa. Shi kaɗai
yasan yana yin da yake ciki a zuciyar sa ga irin kukan da Halima takeyi gaba ɗaya komai ya dagule masa.
Sallama Baba Salahu ya musu yace Abba suyi magana da Mama, duk abin da suka yanke ya sanar masa,
bayan fitarsa Inna Salamatu tace su je can falon sa suyi magana saboda Goggo, bayan sun nutsu tace
masa
"Kar ka bari shaiɗan ya shiga zuciyarka kamar yanda ya samu guri a zukatan sauran. Ba se na tuna maka
ba ka fini sanin a yanayin daka auri uwar yarin yar nan ba, idan ban manta ba se da ɗaurin auren ku ya
rage saura kwana uku kafin nayi ɗaukar adashi na baka ka biya kuɗin hayar gidan da kuka fara zama. A
shekara goma na farkon auran ku se da kuka zauna a gida bakwai, da daɗi babu haka Amina tayi haƙuri
da kai daicdai da rana ɗaya bata gaza ba har Allah ya yanke ya kawo ku in da kuke yau, yanzu idan ba
wanda ya sani ba wa za'a faɗawa irin wahalar da kuka sha a rayuwa ya yarda? Baka zaton gwaji ne
ubangiji yake yi maka yaga ta yanda zaka godewa ni'imar da yayi maka. A sanda Amina ta aure ka dai dai
da kayan sakawar ka irgaggu ne Aminu amma yanzu fa? Ko cewa kayi ba zaka maimaita kaya ba kana da
sararin da kullum zaka saka sabo.
Yanda Allah yayi maka bakayi zato ba wata rana shima zeyi masa, a aure nagartar ma'auri ita ce abu ta
farko da ake dubawa. Yaron nan bashi da laifi an san shi an san iyayen sa ubansa mutumin kirki ne har ya
faɗi ya mutu ban taɓa jin an ce ga wani halin sa mara kyau ba badan ma mutuwa me tonon asiri ba ta
yaya za'ayi ace kamar ɗan Alhaji Mansur ya rasa muhallin da ze shiga ya zauna da iyalansa? Kasan sanda
ya rasu basu tasa sosai ba yan uwansu suka hau kan komai suka bar musu abin da suka ga dama shi da
ƙannen sa da suke ciki ɗaya, yayyen sa na sama uku duk mata ne shi ɗin dai shi ya tashi yake ta fafutuka
da nemo abin da ze rufawa uwarsa da yan uwansa asiri yanda ka gan ka ɗin nan hake yake me zumunchi
abin sa na yan uwan sa ne har irin wannan Mijin ne za'a ce ba za'a bashi aure ba?
Karka kuskura ka biyewa mutane dan idan abun kuka ya same ka dariya zasu maka idan na farin ciki
kuma yazo se sun san yanda suka yi suka ture ko shi Salahun da yake wannan maganar naga Maryam
haka ya aurar da ita ba lefen yanzu ka gaya mun duk cikin yayan dangi wa cece take jin daɗi a gidan aure
kamarta? Ka ci gaba da addu'a kawai ka barwa Allah komai shi yasan sirrin daya lulluɓe a cikin auran nan
dama kuma duk wani abun alkhairi ai baya samuwa ta daɗi mu ci gaba da addu'a kawai tun da dai
yarinya tana son sa babu abin da za'a fasa in Allah ya yarda za'a yi komai arziƙin kenan, ubangiji ya hore
maka ka kira shi kaji, idan har aikin gidan nasa ba me yawa bane da za'a iya ƙarasa wa a masa in ma
kuma baze gamu ba a nemi haya ko ka basu gida su zauna arziƙin kenan amma zancen a fasa aure be
taso ba sharrin da za'a bibiye mu dashi kaɗai ma se ka rasa in da zaka tsoma ranka to ina dalili tun da dai
Allah be hana yanda za'ayi ba" maganganun da Inna Salamatu ta faɗa masa kenan da suka bar shi cikin
kogin tuna ni zuciyar sa ta kasu biyu.
*******************
Se yamma lis na koma gidan Anty Labiba, ko da naje gidan su Hansa'u dama ban gaya mata komai ba
data tambaye ni me ya same ni fuskata ta kumbura se kawai nace mata kuka nayi yan uwan Abba ne
suka zo yi mun nasihar aure ta ringa tsokana ta daga nan muka ɗan taɓa zancen biki ƙawayen mu nata
ƙorafin ba'a gani na naƙi nazo a fara shirye shirye nace mata gobe tazo muyi maganar a gidan Anty
Labiba kawai. Ban iya runtsawa ba cikin dare, Bilal be kira ni ba na kira shi kuma wayar sa a kashe ga
Abba ma nayi zaton yanda baya son damuwata kafin wucewar yinin ranar ze aiwatar da abinda ya
kamata ya share mun hawaye na se dai har dare shiru wannan ya ɗaga mun hankali na ringa tunanin ko
dai su Baba Salahu sun zuge shi ne tun da naga alamar daga shi har Baba Hashim ɗin ba son auren suke
ba wannan tunanin ya ninka tashin hankali na tsabar damuwa har ji na ringayi numfashi na yana
sarƙewa, rabuwa ta da Bilal is the last thing i could ever imagine in my life. Ina son Bilal irin wanda ban
san adadin sa ba ba kuma na fatan ace wani abu ya shiga tsaka ni na dashi.
Washe gari da wani irin ciwon kai na farka bana ko iya buɗe ido na da kyau ga ciki na daya ɗauki ciwo
shima dan rabo na da abinci tun na safiyar jiya haka na wuni na kwana. Daƙyar na iya fita kitchen ina
dafa bango na haɗa shayi, a ƙasan kitchen ɗin na zauna na shanye kafin na jingina jikin bango ma rufe
ido na ina jin kaina na bugawa kamar me. Anty Labiba ta shiga, kallo ɗaya ta mun ta wuce yin abin da ya
kai ta kitchen ɗin se da ta gama zaryar fitar musu da abin karyawa ganin har sannan ban motsa ba kafin
tace mun
"Ki tashi ki mun wanke wanke yau wadda zata miki gyaran jiki zata fara zuwa, kalli yanda kikayi firkai
firkai dake a banza zaki kashe kanki saboda wani banza da be san mutunchin ki ba". Se da ta maimaita
sau biyu ban amsa ba a fusa ce tayo kaina tasa ƙafa ta haure ni, ina jin duk abun da take faɗa se dai bani
da ƙarfin amsa mata a zaunen da nake jiki na ya saki gaba ɗaya duniyar ma juyawa takeyi a ido na.
Haurin da ta mun yasa na zame daga bangon dana jingina na sulale a ƙasa ganin haka yasa ta fasa ihu
babu shiri daga nan kuma ban sake tuna komai ba kawai na farka na ganni a gadon Asibiti Bilal na zaune
a gefe na.
[12/22/2024, 9:09 PM] Hauwa Galadima: *KURA A RUMBU*
*(Based on true life event, some parts are fictional to spice up the story)*
*Wattpad @MaryamahMrsAm*
*Ban yarda wani ko wata ya juya mun labari ta kowacce siga ba tare da izini na ba*
*Kuɗin karatu yana wakiltar mutum ɗaya ne, kiji tsoron Allah karki ɗauki hakkina ta hanyar fitar mun da
littafi*
*KURA A RUMBU littafin kuɗi ne, a biya naira 800, biya a asusun*
*1840175439*
*Access bank*
*PAGE 8*
"Sannu Halims, kin tashi" Bilal ya faɗa yana nufo ni se dai shigowar Anty Labiba ɗakin ta katse masa
hanzari se ya ja gefe yana shafa kansa ita kuma ta balla masa harara kafin ta nufo ni ta kamani ganin ina
ƙoƙarin tashi zaune.
"Sannu" ta faɗa tana gyara mun ɗankwali na daya zame. Bilal ne ya fita ya kira wo likita suka dawo ɗakin
tare da Abba. Bin su kawai nakeyi da kallo har likitan ya gama dubani yace babu komai jiki na ya dai dai
ta amma a barni na sake hutawa. Abba yayi mana sallama akan ze je wani guri Bilal na rakuɓe a bango
kamar wani maraya a idon sa na hango tarin damuwa wadda nasan tana da nasaba da halin da nake ciki
se dai wanzuwar Anty Labiba tsakanin mu tasa ya kasa yin motsi me ƙarfi balle yayi mun magana.
Ita ta kai ni toilet da nace mata ina jin fitsari se kawai taci na daure nayi wanka gaba ɗaya ko zan ji daɗin
jiki na. Tana cuɗa mun baya na tambaye ta me ya same ni? Kuma tun yaushe nake asibitin? Ta mun
banza bata amsa ba har muka gama ta ruƙo ni se kuma ta dakata tace na jira ta fita, ina jiyo muryar ta ta
cewa Bilal ya bamu guri, se da ta rufo ƙofa kafin ta dawo ta fito dani cikin kaya na da na gani a ƙaramar
jaka na shirya, bana jin ciwon komai ban da kaina da yayi mun nauyi se jiki na da babu ƙwari dan haka a
zaune nayi sallolin da Anty Labiban tace sun same ni a kwance. Ina idarwa ta miƙa mun cup data haɗa
tea na girgiza mata kai ina cewa
"Bana jin yunwa Anty". Se ta mayar ta ajiye akan drawer ta nemi guri ta zauna tare da ciro wayar ta daga
aljihun rigar ta ta shiga dannawa. Kusan minti goma muka yi shiru, so nake yi na tambaye ta ko Bilal ya
tafi ne amma yanda ta tsare gida yasa na ji shakkar yi mata magana da dai naji bazan iya jurewa ba se
kawai nayi shahada cikin murya ta data ƙara laushi nace
"Ki kiyaye ni Halima, ni zaki tambaya Bilal ya tafi ko yana nan ajiyar sa kika bani ko yaya akayi?. Badai
bakya tausayin kanki ba da kananun shekarun ki zaki jawa kanki ciwo saboda namiji. Se ki zuba ruwa a
ƙasa kisha zaki auri Bilal autan maza. Badai namiji kika ɗaukaka har kike neman halaka kanki saboda shi
ba Halima? Allah ya bada sa'a" se ta miƙe fuuu tayi waje tana ci gaba da maganganu.
Da kallo na rakata har ta fice ina jin babu daɗi a raina. Na rasa wace irin ƙiyayya Anty Labiba take yiwa
Bilal. Ban san me ya tsare mata da bata iya ɓoye tsanar da tayi masa a zahiri ba.
A can waje kuwa cike da damuwa Bilal yake zauna, yana so ya koma cikin ɗakin yaga halin da Halima
take ciki amma rashin ganin fuska a gurin Anty Labiba yasa yake zaune a gurin. Da daren jiya Mu'azzam
ya kira shi ya sanar masa da Halima bata da lafiya an kwantar da ita a asibiti a yanda yace tana ta kiran
sunan sa ne shine Abban su yace a kira shi yazo. Sanda yaje ɗin ya tarar da ita anyi mata allurar bacci a
hirar su ya tsinci wani abu a dalilin rashin lafiyar tata. Duk se yaji ya tsani kansa, yasan Halima tana son
sa shima kuma yana son ta amma kuma ya rasa yanda ze yi dole ya fito ya gaya mata gaskiya. Be yi zaton
zata saka abun haka a ranta har ya kwantar da ita ba se dai da ya ci gaba da jan ta yana ɓoye mata har se
an kai gaɓar da gaskiya zata fito da kanta a ganin sa gara ta sani su taru su nemawa kansu mafita.
Ganin kusan minti talatin shiru Anty Labiba bata leƙo ta kira shi ba ya fara tunanin ko bacci Haliman ta
koma dan yana da yaƙinin ido biyu ba zata gaza neman sa ba tun da tasan yana gurin, tashi yayi yana
ƙarfafawa kansa guiwa akan ko me Anty Labiba zata faɗa se ya koma ɗakin, yana kai hannu ze buɗe
ƙofar ta fito, kallo me kama da harara ta masa haɗi da yin tsaki ta raɓa shi ta wuce se yaji ransa ya ɓaci.
Ta girme shi kuma ƙanwar mahaifiyar Halima ce amma kuma hakan ba shi yake nufin zata ringa
wulaƙanta shi kamar wani wanda yazo mata maula ba. Shi badan Halima ba me ma ze haɗa shi da ita har
ta ringa wulaƙanta shi haka?
Fuska babu walwala ya shiga ɗakin, na ɗaga kai da sauri jin an buɗe ƙofa muka haɗa ido ban san sanda
na miƙe ina sakin murmushi ba ya nufo ni shima yana murmushi yace
"Sau ke gani na nayi ƙasa ina wasa da gefen hijabi na ba tare da nace masa komai ba, ganin sa ya bani
nutsuwar zuciya ya kuma tabbatar mun yana tare dani ma'ana ya janye waɗan can kalaman marasa daɗi
daya faɗa mun jiya wai mu haƙura da juna.
"Ki zauna kar ƙafafun ki su gaji" ya faɗa yana kallo na se na ƙarasa na zauna akan gado har sannan
murmushi be bar kan fuskata ba, ya matso da kujera kusa da ni ya zauna yana leƙa fuskata yace
Harar wasa na masa ba tare da nace komai ba, ya sake gyara kijerar da yake a kai ya langwaɓar da kai
yana kallo na yace
"Ko da nace mu haƙura ƙarya nake yi ni da kaina nasan bazan iya jure rashin ki a tare da ni ba. Tun da
kika tafi ni kaina dauriya ce kawai irin ta maza ta sa ba'a kawo ni an kwantar a gadon Asibiti ba mutuwa
ce kaɗai zata iya raba ni dake Halims amma muddin ina raye dole zan nemo mafita, ki taya ni da addu'a
Allah ya hore mun na fita kunyar ki kafin ranar auren mu albarkacin wannan son da kike mun bazan baki
kunya ba".
Bude ƙofar da aka yi ya saka yaja baya daga gare ni muka kalli ƙofar a tare, Abba ne ya shigo tare da
Uncle Mudassir Autan su Mamanmu. Cikin jin kunya Bilal ya miƙe daga kujerar da yake zaune yana musu
sannu da zuwa, fuskar Abba babu yabo babu fallasa ya nufo in da nake se Uncle Mudassir ne ya amsa
masa kafin shima ya matso yana mun murmushi na gaishe su ya shiga tambayar jiki na sannan ya ɗauki
folder dake kan bedside ya shiga dubawa dake shima likita ne.
"Dr yace zuwa yamma zasu sallame ki tun da babu wani abu ko akwai in da yake yi miki ciwo ne
yanzun?" Abba ya tambaye ni, se na shafa ciki na da naji yayi ƙara alamar ina da buƙatar cin wani abu na
girgiza masa kai a hankali nace
"Allah ya ƙara afuwa, ki huta. Su Goggo Habiba suna hanya ni na hana Mu'azzam ma ya kawo ta tun da
safe saboda an ce a barki ki huta yanzun ma ta tayar da rigima ne tun da kuma sallamar ki za'ayi shi yasa
nace su zo ɗin kawai" Abba ya sake faɗa. Nayi rau rau nace
"Goggo Habiba kuma? To Mama fa?" Be bani amsa ba ya juya kan Bilal da tun shigowar su yayi shiru
kamar ruwa ya cinye shi yace
"Ina ganin zaka iya tafiya ko" se ya kalle ni kafin ya shafa kai haɗi da rusunawa yace
"To Abba, Allah ya bata lafiya yasa kaffara ne" Abba da Uncle Mudassir suka amsa da amin se ya nufi
ƙofa yana waige na.
"Idan ka samu sarari yau ko gobe kazo ina son ganin ka" Abba ya faɗa Bilal na dab da fita, take na karanci
razanar da Bilal yayi se kuma ya waske yana murmushi yace
"To Abba idan ma yanzu kake son ganin nawa se na jira ka a waje"
"Ka same ni a filin sukuwa ƙarfe huɗu zuwa biyar na yamma" Abban ya bashi amsa daga nan ya fita
bayan ya sake musu sallama zuciyar sa fal zullumin ganin me Abban Halima yake so yayi masa?
Se da akayi sallar magriba muka bar asibiti saboda wata allura da aka yi mun ƙarfe shida. Na lumshe ido
na ina ci gaba da sauraron faɗan da Goggo Habi take yi, tun da taje asibitin bakin ta be huta ba har
yanzun da muke hanyar komawa gida zagi kalar wanda ta manta ne kawai bata mun ba har tana cewa in
da ita ce Labiba bari na zatayi na mutu kawai tun da turbar da na zaɓar wa kaina kenan to saboda Allah
ni na ɗorawa kaina son Bilal ake nufi ko me? Allah da kansa ya ce shi yake sanya ƙauna a zukatan
mutane, menene laifi na sabo da nayi so domin Allah? Zuciya ce kowa da irin tasa, wani yana ɗaukar
abubuwa da sauƙi in da wani yake zafafawa babu kuma wanda za'a ce baya kan daidai.
Naji daɗi kuma ban ji ba da naga mun wuce gidanmu ba gidan Anty Labiba ba. Allah ya gani haushin ta
nake ji saboda ita ce silar komai da bata uzzurawa Bilal da tambaya ba ai da komi ba lalace haka ba
rashin jin daɗin komawa gida kuma da naji nasan surutun Goggo Habi tsaf ze iya haifar mun da wani
sabon ciwon se dai ba ta tata nake ba tun da nasan bata da ikon sakawa ko hanawa a cikin lamarin aure
na, kakata ce ta ɓangaren uwa ba uba ba balle naji tsoron zata iya tilasta Abba yayi abin da suke so.
Abin da ya saka jiki na yin sanyi yanda ko kallon banza ban ishi Mama ba balle na arziƙi, haka nan na
shige ɗaki na jiki babu ƙwari ina jin babu daɗi. Mama da ko ciwon kai nake yi se ta damu bata samun
nutsuwa har se taga na warke ita ce zan kwana a asibiti ba taje ta duba ni ba sannan in dawo gida tayi
kamar bata san da wanzuwata ba? Ko da yake ba laifin kowa bane se na Anty Labiba ita take zugata, se
kace ita wani ya mata dole a sanda ta kawo nata mijin da ni ban ma gama tantance yaren sa ba har yau,
su ba yarabawa ba ba igala ba haka nan kuma ta aure shi suke zaune shekara goma ba wanda yace mata
saboda me se ni zata saka a bakin duniya ta cusawa kowa tsanar wanda nake so.
Da daddare gurin ƙarfe sha ɗaya yunwa ta matsa mun dole na katse wayar da muke yi da Bilal na fito
neman abin da zan ci. Tun ƙarfe tara muke waya, yau ɗin ya dawo asalin Bilal ɗina me so na da tattalin
farin ciki na. Zumuɗin da nake jini nin ban ga yana yi akan auran mu ba se gashi yau ya tashi gaba ɗaya
ya rikita ni da tsadaddun kalaman soyayya irin waɗan da kunnuwa suke da muradin sauraro a ko da
yaushe. Rabon da muyi hira ta nutsuwa kuma me daɗi irin haka tun ba'a saka ranar auren mu ba. Kamar
yanda ya ce mun wani alkhairi ne ya sakko mana ba zato na tsammani yana zaune kawai wani tsohon
abokin Baban sa ya kira shi yake cewa ya samu labarin zeyi aure, a taƙaice dai ya saka yayi masa list na
duk wani abu daya rage masa cikin harkar auran yace ze ɗauki nauyi zancen da akeyi har ya turo masa
kuɗaɗe ya ce a fara aikin kafin sauran su iso. Ya ce mun
"Halims Allah na son mu kasance tare, a sanda na sare nake ganin ba zan iya ba se ya turo mun da agaji
ta in da ban yi tsammani ba. Ke alkhairi ce a rayuwa ta ina roƙon Allah ya bani ikon kyautata miki
kwatankwacin yanda kika kawo haske cikin rayuwa ta".
Saboda murna har rawa se da nayi duk da ba wai na gama jin ƙwarin jiki na bane ba, na ringa kwararawa
ko ma wanene wanda ya kawo mana wannan ɗaukin addu'a. Bamu kashe wayar ba se da naji zuciya ta
ta fara tashi dalilin yunwa ga kuma surutun da muke ta yi ba dan Bilal ya so ba muka rabu akan da zarar
na ci abincin na yi masa ko flashing ne.
Abba da Mama na tarar zaune a falo, gaba na ya faɗi ganin hawaye akan fuskar Mama Abba kuma yana
durƙushe gaban ta da alama haƙuri yake bata, na matsa kusa dasu da sauri ido na na kawo ruwa na fara
tambayar me ya faru?
"Babu komai Halima, wai tunanin zakiyi aure ki bar mu ne duk ya fara sanyayar mana jiki shi ne take
kuka" Abba ya faɗa kamar me yin magana da yarinya yar shekara biyar ko ƙasa da haka. Fashewa nayi da
kuka na zauna gaban Mama nace
"Me yasa zan yi kuka saboda ke Halima? Bana fatan ubangiji ya nuna mun ranar da fushin wani daga
cikin ku ze taɓa zuciya ta har yasa in zubar muku da hawaye ina neman tsari da hakan. Hawayen
tausayin nake yi bana baƙin ciki ba" Mama ta faɗa se Abba yace
"Haba Amina ban san sands kika zama me nace akan magana guda ɗaya ba, shi ba zaki yarda da ƙaddara
ki bar komai a hannun Allah ba?"
Kafin tayi magana nayi saurin kama hannun ta ina kuka nace
"Dama na san saboda ni ne, dan Allah Mama kiyi haƙuri, ki yi mun addu'a ki kuma sakawa al'amari na da
Bilal albarka nasan ubangiji baze kunyata ku ba. Addu'ar ku zata kasance hasken da ze kore mana
kowanne duhu. Kuma ki dena damuwa Mama yanzun nan Bilal ya kira ni ya gaya mun wani abokin
Baban sa ya bashi kuɗi yace ya ƙarasa gini, babu abin da ba ze yi ba da yardar Allah Mama ki kwantar da
hankalin ki babu wanda zeyi mana dariya kamar yanda suke sauraro".
"Allah na bar amanar Halima a hannun ka. Kada ka bari wauta da makauniyar soyayya su jagoranci
al'amuran ta a gidan auren ta"
"Amin, yanzu ki kayi magana Amina. In sha Allahu se mun ce gara da aka yi" Abba ya sake faɗa.
A sanyaye na tura shayin dana haɗo zuciya ta duk babu daɗi. Ban zaci rashin son da Mama take yi wa
aure na da Bilal ze saka har ta zubda hawaye ba. Se na ringa jin kamar banyi daidai ba da tun farko naƙi
bin ta tata amma kuma ban hango laifi na akan bin son raina da nayi ba. A cikin labarin ta na samu tawa
ƙarfin guiwar. A kullum ta kan karanta mana irin rayuwar da sukayi da Abba, wuyar da suka ci tare har
zuwa yanzu da daɗi yazo shima suke shan sa tare.
Tun ina ƙarama na tashi da sha'awar irin rayuwar da iyaye na suke gudanar wa ta tsantsar soyayya da
tattalin juna har zuwa kanmu yaran da suka haifa.
Mahaifiya ta Amina Sa'id haifaffiyar unguwar Yakasai ce yayin da Abba yake haifaffen Galadanci. Tamkar
banbancin dare da rana haka suka sha banban gurin asali, Mahaifin Mama attajiri ne kuma basarake
wanda a zamanin sa sunansa yayi amsa kuwwa a ƙwaryar birnin kano da kewaye. Allah ya bashi tarin
dukiya wadda ya ƙare rayuwar sa yana hidimtawa iyalansa da al'ummar dake zagaye dashi. Mamana ita
ce ya ta huɗu cikin jerin yaran sa bakwai daya haifa da matar sa ta aure guda ɗaya Hajiya Saude. Namiji
ne babban su Alhaji Lawan se me bi masa Hajiya Rumana sannan Mama Fauziyya se Amina mamana
kenan, Baba Faisal ya rasu shekaru biyar baya, Baba Mudassir se Anty Labiba data kasance autar su.
Abbana ya fito daga babban gida me yawan ahali domin matan mahaifin su huɗu, a jerin yaya shine na
goma sha uku a gidan gaba ɗaya a ɗakinsu kuma shine na huɗu kuma namiji tilo. Gidan su gida ne irin na
bani babu, Mahaifin su Malam Ibrahim talaka ne domin har ya mutu be bar musu komai ba ban da gidan
gandu. Duk da bashi dashi kuɗi amma yayi ƙoƙari sosai akan tarbiyyar yaransa. Ya saka su makarantar
addini duk kuma wanda kaga yayi karatun boko a gidan to shi ya saka kansa ba Malam Ibrahim ba.
Abbana shine namiji na farko daya fara karatun boko a gidan domin sauran da sun tasa sukayi sauka a
makaranta shikenan se su shiga kasuwa, da dama ta fara zuwa se aure su fara tara Iyali wannan yasa
jikokin gidan muke da bala'in yawa wasu idan ka kalli shekarun su dana iyayen su se kaga kamar basu
suka haife su ire ire na mun shiga layin sa'annin yayan jikoki ne saboda iyayen mu da basu yi aure da
wuri ba.
A BUK Abba ya haɗu da Mama, lokacin yana level 2 Business administration ita kuma tana level 1. Daga
mutunchi kasancewar sa me ƙoƙarin gaske ya kan koya musu karatukan da suka shige musu duhu a
hankali mutunchin nasu ya rikiɗe zuwa soyayya wanda ita Maman ce ta fara nuna sha'awar hakan.
Daƙyar Abba ya amince, badan ba tayi masa ba ko kuma baya son ta se dan ganin tazarar dake tsakanin
sa da ita. Ya kan ce mata
"Akwai banbanci me girma tsakani na dake Amina. Ni ba sa'an auren ki bane, ƙima ta bata kai ta ko da
direban da yake kawo ki makaranta ba ki rufa mun asiri ki barni na kammala karatuna lafiya domin shine
madogara ta idan wani abu ya faru na rasa wannan damar ban san ina zan kama ba". Bata sare ba taci
gaba da bibiyar sa da kuma ubangiji ya ƙadarta akwai rabon aure a tsakanin su se gashi sun yi har an
haife mu a kullum bakin Abba baya gajiyawa da nanata halin karamcin da ahalin Mama suka gwada
masa.
"Sun ƙauna ce ni a sanda bani da komai, sun aminta dani suka bani guda daga mafi soyuwar ahalin su
idan har ban saka musu ta hanyar faranta ran Amina har bakin raina ba da wanne ido zan tsaya gaban
Allah na maida amar da mahaifin ta ya bani?" Abin da yake yawan faɗa kenan. Mama ta manta asalinta
da rayuwar jin daɗin da ta taso a ciki ta rungumu mijin ta da sabuwar rayuwar da ta zaɓawa kanta. Sun
kwana basu ci ba, wata rana su ci sau ɗaya ko sau biyu an tashe su daga gidajen haya ba adadi amma
duk ta jure bata sare ba haka nan dai dai da rana ɗaya bata taɓa tilasta masa karɓan tayin taimakon da
yan uwanta suke masa ba kamar yanda yace mata zai nemi halal ya ciyar da ita alfarma ɗaya kawai yake
nema a gare ta shine karta raina yana ji jikin sa wata rana ze mayar da ita inuwar data saba da ita gashi
kuwa Allah ya amsa bayan wani lokaci.
A sanda Mama take da ciki na Anty Labiba ta dawo gidan mu da zama, tun tana zuwa ta kama mata
ayyuka ta tafi har ya zama ta dawo gidan gaba ɗaya bayan an haife ni saboda yanda take so na. Da ita
aka sha gwagwarmaya ba kuma ta bar gidan mu har se da lokacin auren ta yayi shi yasa Abba ya kan ce
Labiba ce babbar yar sa ba ni ba domin tun tana da shekaru goma a duniya take hannun sa har ya aurar
da ita itama kuma kallon uba take masa b wai mijin yayarta ba.
Na gyara kwanciya ta ina sake nutsawa cikin tunanin dana tafi, irin wannan rayuwar nake so na gina, mu
sha wahala tare da miji na ta yanda a duk sanda Allah yayi mana arziƙi baze manta halacci na ba. Ban
yarda da irin auren da mutanen yanzu suke rububin yi ba na ready made, baki san yanda namiji yasha
wahalar sa ya tara abinda yake dashi ba kin ganshi a me wadata kin aura daga ƙarshe ya ringa goranta
miki cewa arziƙin sa kika hanga idan kuma me mata ne nan ma se ya fifita matar sa da suka sha wahala
tare har a ringa kiran ki da yar tayin cin arziƙi shine abin da ban yarda dashi ba. Matar da aka sha wahala
da ita tafi mutunchi tafi ƙima a gurin miki har ma da duk waɗanda suke zagaye dashi, haka ko da ya auro
wata daga baya itan ce dai zata zama a sama haka nan yayanta se sun banbanta da wanda uwarsu ta zo
rana tsaka.
Daga yana yin da naga gidan mu washe gari na gamsu dagaske an fara shirin biki. Masu aikin kayan zaƙi
na gara ne suka fara baje kolin su haka nan yan uwa da ƙawayen Mama sun fara zuwa suna tsara yanda
biki ze kasance hatta Goggo Habi da taga babu sarki se Allah ta saki musamman da aka aiko da yamma
cewa ranar asabar da zata kama saura sati ɗaya ɗaurin aure za'a kawo lefe na wannan ya wanke mata
zuciya tun da dama tace abin da idan ta tuna yake baƙanta mata rai yanda za'a ɗauki santaleliyar
budurwa kamata a bayar sadaka ashe da iskanci ne yasa yaƙi yin abin da ya kamata yanzu da yaga ana
nema a ƙwace masa goruba daga hannu ai ya motsa a tunanin ta kamar yanda Abba ya gaya mata sun
kira waliyyan sa ne sun ce musu sun fasa shine suka bayar da haƙuri akan wani al'amari ne ya janye
shirun da sukayi amma yanzu komai ya yaye.
A cikin sati ɗaya aka gama aikin gidan Bilal, gida ya fito yayi kyau masha Allah tamkar na wani hamshaƙin
me kuɗi. Ranar alhamis su Anty Labiba suka je suka ga gidan a lokacin ana fenti kowa ya dawo yana
santin gida amma saboda rashin tsoron Allah irin nata da dai ba zata taɓa son Bilal ba se cewa tayi ita
bata yarda gidan sa bane, idan kuma har yana da halin yin gini irin wannan to kuwa ba ƙaramin rainawa
Halima hankali yayi ba. Ni kaina da naga video gidan se da nayi mamakin yanda finishing ya sake fito da
ainihin kyau da tsarin gurin, har ƙofofi naga an canza a sanda muka je na ƙarfe ne har so nayi na masa
magana akan me ze haka a saka dai na zamani amma na kasa ze gashi an canza saman ma da da yace
ceiling ze yi bashi da sararin yin pop yanzu se gashi anyi ga tiles me kama da marbles an malale ko ina
haka kitchen yasha cabinet irin yanda nake mafarki.
A maimakon Asabar da suka fara ambata zasu kawo lefe ranar da aka je ganin gida suka bada uzurin se
ranar Alhamis me zuwa ranar da zamuyi kamu kenan saboda akwai yan uwan Bilal ɗin da zasu zo daga
guri me nisa be kamata a taso su kawo lefe ranar asabar ba kuma ace za'a fara biki ranar alhamis gara
kawai a haɗe ayi komai lokaci ɗaya, babu wani abu da muke jira na amfani a cikin lefen dan haka aka ce
musu babu komai a cikin satin kuma aka yi mun jere na yar gata. Ɗakuna na biyu na part ɗina da ɗaya na
part ɗin Bilal duk se da Abba ya saka mun gado ga kujeru suma saiti biyu. Yanda Anty Labiba ta zage
darje ni da kayan kitchen ya bani mamaki ita da tace duk abinda suka siya Amirah da Inayah zasu aje ma,
babu ce akwai ba'a saka mun a gida na ba. Saboda tsabar zumuɗi irin na Bilal tun ranar da aka fara jere
ya koma kwana a gidan, haka ze ishe ni da tura hotuna da videos, Halims kin ga kaza da aka saka mana?
Kin ga gadonki kuwa? Waya mutu waze tashi se da ya zama har bana so ya kira ni saboda gaba ɗaya
zancen gida ya kwance masa kai.
Rana bata ƙarya aka ce sedai uwar ɗiya taji kunya, tun ranar talata muka fara shagalin bikin aure na da
Bilal wanda aka fara da Ball da abokanan sa suka shirya masa. Washe gari laraba mukayi ƙauyawa day a
gidan Anty Labiba ranar Alhamis kuma Mama tayi mother's eve. Wannan ranar tana cikin ranakun da
bazan manta dasu a tarihin rayuwata da Bilal ba. Munyi kyau na bugawa a shafin farko na jarida dangina
sun nuna mun gata har na ringa ƙaryata cewar da kowa yake baya farin ciki da auran mu. Ana kiran sallar
magriba aka tashi kai tsaye kuma muka fara wucewa gidan mu in da za'ayi mun kamu kafin mu koma
gidan Anty Labiba in da ni da ƙawaye na muke kwana.
Ƙarfe tara yan uwan Bilal suka iso lokacin har ƙawayen Mama da wasu daga cikin yan uwa da suka zauna
jiran karɓar lefe da kamu sun gaji sun tafi se tsirari suka rage, ina tsakiyar ƙawaye na a ɗaki na ana hira
suna tsokana ta babu kunya ina maida musu martanin duk abin da suka faɗa.
Anty Labiba ta shiga ɗakin ta kalle ni kawai ta fashe da wata dariyar da kana gani kasan ta zallar mugunta
ce, muka ringa kallon ta se da tayi me isarta har tana riƙe ciki kafin ta kalle ni tace
"Ke dai Halima kin haɗu da yan bura'uba matsiyata. Ni dai da wannan kayan takaicin salin alin gara yace
a yafe masa kawai ya ƙarasa ɗaukar ki a sadaka yanda aka faro da dai wannan kayan zubar da
mutunchin, Ko da yake Allah ya ƙara ranar baƙin naci kenan, yammata ku taso ga lefe can an kawo" ta
juya ta fita tana cigaba da dariya ta barni da fassarar maganganunta. Gaba ɗaya suka fice suka tafi kallon
lefe aka bar ni ni kaɗai, Hansa'u ce ta fara dawowa a sanyaye ta zauna a kusa dani tayi tagumi ba tare da
tace komai ba.
"Amma Bilal be kyauta ba Halima, tsakani da Allah da wannan shaddar daya ɗinka da designer takalmin
daya saka da uban liƙin daya ringa miki ba gara ya haɗa kuɗin ya siyi akwati ko me guda biyu da kit
bane? Ke ko aro ne ai gara ya yiwo da wannan rashin mutunchin wlh"
"Ban gane ba? Me lefen yayi?" Na sake tambayar ta, se da ta zabga tsaki kafin tace
"A ledoji suka kawo, wlh tallahi in da yasan wannan abun tsiyar zasuyi gara ma ta bakin Anty Labibar ya
ce ayi haƙuri kawai idan yaso ya aje miki kayan acan gidan idan kin je kya ɗinka abin ki. Harka duk da
tsiya da ƙaranta, Allah ka raba mu da irin wannan abun kunyar".
Ta shi nayi na yafa mayafi na Hansa'u na tambaya ta ina zanje na mata banza, buɗe ƙofa nayi na tsaya,
daga in da nake ina hango ledojin kantin El-samad dana Alpen stores zube a tsakira falo ga muryar Anty
Labiba a sama tana tijara wani abu ya taso ya tsaya mun a wuya ban san sanda na juya da baya na faɗa
kan gado na fashe da kukan takaici irin wanda ban taɓa ji ba akan Bilal.
"Karki damu Halims zan baki mamaki. Yanda kuka gwangwaje ni da kayan ɗaki masu kyau bake ba kowa
se yayi mamakin lefen da nayi miki ke dai ki kwantar da hankalin ki kawai" maganar daya gaya mun
kenan ɗazu da muke dawowa daga gurin kamu ashe irin mamakin daya shirya mun kenan.
1840175439
Access bank
07061838488
Nagode
*(Based on true life event, some parts are fictional to spice up the story)*
*Wattpad @MaryamahMrsAm*
*Ban yarda wani ko wata ya juya mun labari ta kowacce siga ba tare da izini na ba*
*Kuɗin karatu yana wakiltar mutum ɗaya ne, kiji tsoron Allah karki ɗauki hakkina ta hanyar fitar mun da
littafi*
*KURA A RUMBU littafin kuɗi ne, a biya naira 800, biya a asusun*
*1840175439*
*Access bank*
Ina ji wayata na ƙara na san kuma Bilal ne amma naƙi amsawa, Allah ya sani har raina naji haushin anin
da ya mun. Wane irin tozarci ne lefe a leda? Idan bashi da kuɗin akwati ya ara mana ko kuma ya bar
lefen gaba ɗaya tun da ni dama ban saka rai da zeyi mun ba. Shine kuma saboda rainin hankali har yana
cewa ze bani mamaki da irin lefen da ze mun aiko ga mamaki nan ya bar mun abin faɗa a cikin dangi da
unguwa. Kusan minti talatin ina kuka ina jiyo hayaniya sama sama daga falo, Anty Labiba ce ta tasa
dangin Bilal da rashin arziƙi ita da Anty Ummi ƙanwar su Abba. Da alama kuma manyan dake gurin abin
da yake ransu kenan shiyasa basu tsawatar musu ba basu dai saka baki ba dan kar ace sun taru sun zaka
ɗaya.
Ko a ƙauye ban taɓa jin an kai lefe a leda ba ai wlh gara ku zubo su kwalla ko fanteka kunyi gargajiya
akan dai wannan nuna tsiyar" Anty Labiba ta faɗa cikin jin haushi. Su kansu kayan ba wai wasu na arziƙi
bane, Atamfofi ne guda bakwai da lace biyu se shadda biyu da material ɗaya se kuma dogayen riguna
kala huɗu da mayafai huɗu haka jaka da takalma duk saiti hurhuɗu. Tsiyar zubo su a leda ce ta rinjayi ta
kayan, ko da yake iya ƙarfin sa yayi ba'a kushe masa ba. Tankawa da yayar Bilal tayi yasa abin ya sake
tsamari aka shiga faɗi in faɗa kamar dai za'a kaure da faɗa se da Baba Abubakar ƙanin su Abba ya shigo
gidan ya tsawatar musu. Dake Abban ma yana gida tare da su Baba Salahu take ya kira shi a waya suka
zo Baba Salahu ya ringa faɗa akan me yasa su Anty Labiba za suyi haka su dai yan kawo lefe guiwa babu
ƙwari suka miƙe. Baba Salamatu da neman ayi ta cewa Mama Fauziyya ina kayan snacks da aka musu da
tukuici? Nan fa baga dangin Maman ba ba ga nata yan uwan ba suka hayayyaƙo mata baiwar Allah har
hawaye se da tayi ƙarshe ma tace ba zata kwana gidan ba tafiya zatayi ba za'a ƙarasa biki da ita ba
daƙyar aka bata haƙuri ta zauna.
Ƙarfe goma da rabi bayan na gama shan kuka na na ƙoshi ina kwance Hansa'u tace mun in zo in ji Abba
ya kira na, na zumbula hijab fuska a kumbure muka fita se naga ta nufi hanyar waje na kalle ta kafin nayi
magana tace
"Suna ƙofar dasu Baban Galadanci". Ban yarda ba amma na bita, ina saka ƙafata a waje muka haɗa ido
da Bilal na juya da sauri kafin na ida komawa ciki ya riƙe hijabi na yana cewa
Tsaye nayi na kasa ci gaba da tafiya amma ban juya na kalle shi ba, se ya zagayo yana fuskanta ta tamkar
ze durƙusa mun yace
"Na fiki baƙin ciki da takaicin abin da yan uwana suka aikata mun domin ba ke suka wulaƙan ta ba ni suka
yi wa, ga Nasir ne shine shaida, dubu hamsin na nawa Yaya Saratu su siyo akwati amma suka aikata
wannan abun amma babu komai kowa yayi me kyau dan kan sa" ya ƙarasa kamar ze yi kuka. Se kuma
naji tausayin sa ya tsurga mun, dama zuciya ta tana ta raya mun babu sanin sa amma na danne yazun
kuma da yake gaba na se naji na yarda dashi amma duk da haka ban nuna ba cikin dake wa nace
"Dama ai kace zaka shayar dani mamaki ga shi kuwa ka bar mun abun faɗa a cikin dangi da ƙawaye ka ja
mun abun gori har jikokinmu" na rufe ido da hijabi na na fara kuka take hankalin sa ya sake tashi. Ya
ringa rantse rantse har yana durƙusawa ya riƙe ƙafafuna ganin zan bar gurin.
Murna fal zuciyata, se da na wana shi iya yanda naji ya mun kafin cikin shagwaɓa nace na haƙura.
"Nagode Halims kuma alƙawari, ba dai akwatin lefe bane? To ki biyo ni bashi in sha Allahu zan biyaki da
dozen ma ran da kika haifar mun Bilal junior ko little Halims" se na rufe ido na cikin kunya jin Nasir na
cewa
"Daga gobe ne ai zamu fara irgen lokaci" ganin zasu fara shaƙiyancin yasa Hansa'u da takaici ya hanata
cewa komai tun tsaiwar mu tace dare yayi mu shiga gida. Haka muka raba dare muna waya da Bilal yana
faɗa mun irin murnar da yake ciki da yanda ya tsara goben mu zata kasan ce. Na ringa juyi a gado ina jin
kamar goben tayi mun nisa.
Washe gari aka tashi da shirin ɗaurin aure, yini da kai amarya duka a ranar za'ayi. Da wuri muka koma
gidan su Hansa'u ni da ƙawaye na da muka kwana tare har sanda muka fita kuma ledojin lefe ma na zube
a falo na dai ji Goggo Habi na cewa Anty Labiba a kwashe waɗannan kayan tsiyar kafin mutane su fara
shigowa a samu na yayatawa a gari. Sanarwar ɗauruwar aure a tsakanina da Bilal yana cikin abubuwa
ma fiya daɗi da kunnuwa na suka taɓa sauraro tsayin rayuwa ta. Tsabar farin ciki bayan da nayi
sujudushshukur se kawai na zauna na fashe da kukan murna. Ƙarfe biyar muka tafi Galadanci in da aka
haɗa mu da sauran cousins ɗina biyu iyayenmu maza suka mana nasiha daga can kuma bayan magriba
aka ɗauki kowa zuwa gidan mijinta.
Kwata kwata na kasa yarda wai yau nice na zama matar Bilal? Da su Anty Labiba zasu tafi ta riƙe hannu
na tana cewa
"Buri ya cika kin zama matar Bilal Halima, se kiyi haƙuri domin yanzu wata rayuwa ta daban zaku shiga
ba wacce kuka saba da ita a waje ba. Yanzu ne za kuyi zaman gaskiya da gskiya halin kowa ya fito, zaki
iya tarar da Bilal a yanda kika tsammaci samun sa koma fiye da haka ki na kuma iya tarar da akasin
hasashen ki ma'ana yazo miki da wasu halaye na daban da basu kika sani a tare dashi ba. Fatan mu
yanda kika masa halacci ya maida miki, kiyi haƙuri da duk abin da zaki ji ko ki gani duk wani gidan aure da
kike gani da kalar ƙalubalen sa haƙurin da ma'aurata suke yi shi yake lulluɓe komai kiga tamkar ba'a
saɓawa. Mace ita take mayar da gidan ta dausayi ko ta mayar dashi filin yaƙi. Yanda kika ɗora mijin ki
haka ze miƙe. Idan kin tafi dashi ta laluma zakiji daɗin sa in kika koya masa hargagi da masifa har tsufa
hara ze ringa miki dan haka ki koyi ta yanda zaki ringa bayyana fushi idan ranki ya ɓaci. Ina miki nasiha da
kiyi koyi da halin Mama, na tabba har kike riƙi halayanta na gari badai a kawo ƙarar ki ba. Ina sake
maimaita miki da kiyi haƙuri Halima, kiyi haƙuri kiyi haƙuri ki ƙara da haƙuri Sadiyayye. Yanzu ba zaki
gane haƙurin me nake nanata miki ba. Allah ya albarkaci rayuwar auren ki, Allah ya mallaka miki Bilal ya
hane shi da yi miki butulci irin na maza" se ta fashe da kuka muka rungume juna daƙyar aka raba mu
suka tafi ya rage saura ni da ƙawaye na.
Dubu hamsin abokanan Bilal suka bada kuɗin siyan baki ga ruwa da lemo katan katan da kayan shayi, a
cikin kuɗin Hansa'u ta cire dubu goma ta saka mun a jakata, itama se da muka sha kuka kafin muka rabu
ya rage daga ni se Habibi na cikin gidan mu. Faɗar irin tarairayar dana samu a gurin Bilal ɓata baki ne,
tamkar ƙwai haka ya ringa riritani yana shayar dani madarar soyayya har ya samu nasarar maida ni
cikakkiyar mace jikin mu ya ƙara sa zama abu ɗaya kamar yanda zukatan mu suka daɗe a tare. Washe
gari haka ya wuni tare dani duk da yan uwanmu da suka fara zuwa tun safe da nashi dangin be fita ba se
da yamma tayi aka zo kawo gara sannan ya fita ana idar da sallar isha'i kuwa ya dawo.
Haka rayuwa ta fara miƙawa, tsakanina da Bilal a kullum so da shaƙuwar mu ƙara karfi yakeyi. A sati
guda da auren mu ina jin da ace wani kuskure ya gifta har ya zamana ban auri Bilal ba da bazan taɓa
yafewa kaina ba. Bilal ƙarshe ne gurin iya tattalin mace, ya iya soyayya. Irin soyayyar nan me tsayawa a
rai da kake wuni cikin shauƙi da tunani ita Bilal yake gwada mun. Se da muka kwashi sati biyu ban da
sallah babu abin da yake fitar dashi daga gida tun da komai muna dashi babu ce kaɗai ba'a sako mun a
cikin garata ba har da soyayyen nama da dafaffen kayan miya da ɗanye se dai idan zan yi girki kawai na
ɗiba. Baƙi yan ganin ɗaki ma sun haƙura saboda yanda baya kunyar idon kowa haka ze zauna a cikin su
ko kuma ya riƙe ni a ɗaki se dai su gaji da jira su tafi. Dake dama dangin sa ne masu zaryar ni nawa tun
da aka kawo gara babu wanda ya sake zuwa se ranar dana yi kwana biyar ne Gwaggo Habi tazo mun
sallama zata koma Birnin gwari.
Ranar da muka yi sati biyu tun safe ya ce mun zamu fita. Na ringa murna dan ji nake kamar na shekara a
guri ɗaya, na ɗauka ma da wuri zamu fitan dan haka kafin azahar na gama girki na shirya se yace mun se
da yamma. Tsaf muka shirya, tsakanin ni dashi se ka rasa tantance wanda auren yafi karɓa. Munyi kyau
jikin mu ya murje muna ta ƙyallin amarci abun mu. Muna tsaye a bakin titi muna jiran abin hawa ya kalle
ni yana murmushi yace
"Kin ga da ace Abba ya sako miki mota a kayan gara hankali kwance zamu fita muna yangar mu a titi".
Murmushi kawai nayi ba tare da nace masa komai ba, gidansu muka fara zuwa tamkar zasu cinye ni
saboda ƙauna. A can mukayi sallar Magriba kafin muka wuce gidan mu Hajja nata mu tsaya mu ci tuwon
dare yaƙi, a cikin dubu goman da Hansa'u ta cire mun na bata dubu biyar ta ringa murna kuwa. Har goma
muna gidan mu saboda Abba be dawo da wuri ba. Na lura da yanda Mama take ta bi na da kallo kamar
na canza mata, se da muka shiga ɗaki take tambaya ta komai lafiya dai nace mata ƙalau.
"Haka ake so aji, Allah ya baku zaman lafiya ya kaɗe fitina. Da go be su Imam suke cewa zasu zo amma
tun da kun zo yau se su bari se wani sati" na mairairaice nace
"Haba Mama zuwan mu daban nasu daban ai, dama goben ya ce zeje wani ɗaurin aure jigawa nasan
kuma zeyi yamma kinga sa tayani hira". Da zamu tafi Mama ta haɗa mun su kuka daddawa da kuɓewa
wanda dama tace se daga baya za'a kawo harda dambun nama da kilishi. Abba ne ya ce Mu'azzam ya
kaimu tun da dare yayi, naso ace mun biya gidan Anty Labiba amma tun kafin mu fita daga gida da na
yiwa Bilal maganar cewa yayi ba yau ba, da muka fito kuma dare yayi shiyasa kawai na haƙura se wani
lokacin. Da yake mun ci abinci wanka kawai mukayi muka kwanta rungume da juna kamar ko yaushe.
Washe gari da wuri ya shirya saboda ɗaurin abokinsa da yace tare sukayi karatun university. Khalil na da
kirki sosai, tun daga Maiduguri ya zo mun biki kin ga ai ba naƙi zuwar masa ba nan dai da Jigawa" ya
faɗa. Ina gyara masa zaman hularsa nace
"Ai kam dai ka kyauta, ba dan yanda kake ta nanata amincin ki dashi ba bazan yar da ka tafi wani guri yini
guda ba tare da ni ba". Se da yaja hanci na ni kuma na shagwaɓe fuska kamar zanyi kuka se ya
rungumeni yana cewa
"You have no idea on how much I'm going to miss you sugar, na faɗa miki kawai dan Khalil ne badan
haka ba yau Sunday dai ɗaurin aure ko a ciki garin Kano ne se dai a mun haƙuri". Nema mukayi mu lalace
a tsaye da soyayya se da wanda zasu tafi ya kira shi kafin ya sake ni duk ya kashe mun ya saka mun
shauƙin son kasancewa tare dashi.
Se da na raka shi get ina masa addu'oi kafin na koma cikin gida, minti uku tsakani wayata ta shiga ƙara na
amsa ganin shine yace
"Babe kin san guy ɗin nan wai motar sa babu mai se yanzu yake faɗa mun?" Nace
"Toh, Allah ma ya sa kun sani da wuri ai ba se da kuka hau hanya in da babu gidan man ba".
"Haka ne, amma yayi yawa ai, me yasa tun tuni be faɗa ba kawai yace mana za'a tafi a motar sa? Ai se
yace dama zamu haɗa kuɗin mai kinga da se musan da lissafin sa" Ya sake faɗa. Se nayi murmushi nace
"To yanzu dear kwata kwata nawa ne zeyi muku full tank da kake wannan mitar, ka bad kuɗin a saka
man ku tafi mana kaga fa lolaci yana ta ja kar ku makara kuma"
"Ni fa 2k kawai na fita da ita shima saboda ba'a son tafiya babu kuɗi. Kuma ATM ɗina jiya na manta shi
hannun Abubakar dana bashi ya ciro kuɗi, amma bari mu dawo na gani na san bazan rasa yan canji dana
bari a gida ba" daga nan ya kashe wayar. Tunanin kar su sake ɓata lokaci yasa kawai na cire dubu biyar
cikin kuɗin da Abba ya bani jiya na riƙe a hannu na, ina jin tsayuwar mota na yafa mayafi na na fita muka
ci karo a bakin get na miƙa mishi ina murmushi se ya karɓa tare da pecking goshi na ya juya yana ɗaga
mun hannu.
Dake su Imam da Amirah harda Inayah d Amir ɗin Anty Labiba sun zo tare muka wuni muna ta sabgogi
se la'asar Mu'azzam ya zo ya ɗauke su, na basu kilishin da na taho dashi jiya daga gida su kaiwa Anty
Labiba tun da nasan tana so kuma Mu'azzam yace su ze fara saukewa a gida bayan sun tafi na hau
gyaran gida kafin wani lokaci na gama komi nayi wanka, ina da miya dan haka couscous zan dafawa Bilal
idan sun dawo.
Dab da sallar isha'i ya shigo gida, se da na haɗa masa ruwan wanka na fitar masa da duk abin da ze yi
amfani dashi kafin na barshi a ɗaki na koma kitchen na ƙarasa haɗa abinci. Har da fruit salad nayi dan
nasan shi daga zarar an ci abincin dare ze fara mitar bakin sa na masa motsi yana so yaci wani abu kuma
ya gaji da cin kayan gara. Mun cin abincin yana mun hirar yanda ɗaurin aure ya kasance, ashe mota ce ta
lalace musu a hanya shiyasa ma sukayi dare. Bayan mun gama na kwashe koma na kai kitchen sannan na
dawo na zauna akan cinyarsa ina jan gashin gemun sa, ya ɗora kan sa a kan ciki na yana cewa
"Har yanzu baki fara jin komai a nan bane?" Dariya nayi na ture shi ina cewa
"Ki dai zauna wasa yarinya ni nasan na daɗe da yin aika aika". Haka muka ringa hira cikin nishaɗi haɗi da
wasannin soyayya. Ƙarfe goma yace mun na kawo masa wani abun ya ɗan taɓa bakin sa na masa motsi,
se na ɗakko fruit salad ɗin da na sakawa madarar gari da condensed gashi yayi sanyi gwanin daɗi na
haɗo da ruwa.
"Ai ko ɗazu na bawa su Inayah su kaiwa Anty Labiba na san ta da son kilishi" na bashi amsa, se naga ya
dakata da abin da yakeyi ya wani kalle ni fuskar sa kamar da fushi yace
"Kilishin kika bayar? Da izinin wa? Wato ita gata sarkin son cin kilishi ni kuma da bansan daɗi ba shiyasa
zaki ɗauke mun abu ki bayar na tare da nayi miki izini ba".
Mamaki maganganun sa suka bani, kilishin da a gidan mu aka bani dan nayi kyautar sa shine ze fara tada
jijiyar wuya yana faɗar maganganu akai? Kai tsaye nace masa
"Yanzu saboda na bawa ƙanwar Mamana abu shine kake wannan faɗan? Kuma fa kilishin nan naga daga
gidan mu na taho dashi, nawa ne meye laifi idan nayi kyaitar sa ga wanda naso?"
"Ni kike faɗawa haka Halima? Ni kike yiwa gori akan kilishi?" Ya faɗa yana miƙewa tsaye.
"Karka canza mun magana ni ba gori na maka ba kawai na tunatar da kai ne kuma ba da wata manufa
nayi magana ta ba".
Ikon Allah, ƙaramar magana ta zama babba. Daga dai zancen kilishi kamar dai dama Bilal yana neman
hanyar da ze tijara ni ne se gashi ya samu nan ya ringa fisaji yana rashin mutunchi da faɗar maganganu
tamkar ba Bilal ɗina ba. Har yana cewa wai dama tun da muka yi aure ya lura na ke masa wani gani gani,
duk abin da zan bashi se in bashi kaɗan, ko kuma idan ya ɗakko da kansa in ringa kallon sa wato taƙama
ta daga gidan mu aka kawo shiyasa to daga yau baze sake cin komai daga abinda ya fito daga gidan mu
ba balle na goranta masa, maganganu dai marasa daɗi marasa ma'ana ya zubar mun da fruit salad ɗin
akan carpet yayi wucewar sa ɗaki yana ci gaba da tijara.
Kuka na zauna ina yi, ni banga abin laifi duk a cikin wannan abun ba, idan ma beji daɗin abin da nayi ba a
zato na ai ba ta haka ya kamata ya nuna mun ba se muyi magana cikin lumana amma ya za'ayi ya fara
faɗa har yana cewa baze sake cin abinda aka kawo daga gidan mu ba. Na zata daya shiga ɗakin ze fito ya
lallashe ni tun da ya barni ina kuka amma har agogo ya buga ƙarfe sha biyu ina zaune ban sani ba, na
share fuska ta na tashi a raina ina tuna nasihohin da Mama tayi mun akwai in da take cewa
"Karki kuskura kiyi kyauta da abun mijin ki ko da ƙwayar zarra ba tare da izinin sa ba, sata ce, har kuma
be yafe miki ba Allah se ya kama ki" 'Amma kuma wannan ai ni aka bawa' na raya a zuciyata, 'ko da yake
tunda an kawo gidan ina ganin ya zamu namu kenan ni dashi' wata zuciyar ta tunasar dani.
A hankali na tura ƙofar ɗakin da ya shiga, akan gado na hango shi yayi ɗai ɗai yana bacci abun sa, wani
abu ya tsaya mun a rai. Wato ko a jikin sa bacci ma kwanta yana yi. Sabbin hawaye ne suka ɓalle mun,
hakan nan na canza kaya na kwanta kusa dashi ina cigaba da ɗauke hawayen daya ƙi tsaya mun dan
banyi zaton Bilal ze fara mun haka ba. Da asuba be tashe ni ba kamar yanda muka saba yayi ficewar sa
masallaci daya dawo kuma ɗayan ɗakin ya shiga ya kwanta. Ban farka ba se kusan bakwai na safe saboda
rashin kwantawa da wuri ga kuma ciwon kan da kuka da damuwar dana kwana dasu suka saka mun.
Nayi mamakin ganin rana tarwai kuma babu Bilal a gefe na, haka dai na watsa ruwa nayi sallah bayan na
gama addu'oi na na fita ganin baya falo se nayi tunanin to ko fita yayi?
Yan ayyukan da zanyi na fara na sake gyara falo na saka turare kafin na wuce kitchen na shiga fere doya.
Har na gama haɗa abin karyawa be shigo ba, ɗaki na koma na ɗakko wayata na shiga kiran sa ga mamaki
na se na jiyo ƙarar wayar daga ɗayan ɗaki na. Katsewa nayi na nufi ɗakin, na murɗa handle ɗin ƙofa naji
shi a rufe da key, mamaki ya sake cika ni, a hankali na shiga ƙwanƙwasawa, nafi minti biyar a tsaye ina
buga ƙofar amma ko motsi ban ji ba balle na saka ran ze buɗe mun.
*(Based on true life event, some parts are fictional to spice up the story)*
*Wattpad @MaryamahMrsAm*
*Ban yarda wani ko wata ya juya mun labari ta kowacce siga ba tare da izini na ba*
*Kuɗin karatu yana wakiltar mutum ɗaya ne, kiji tsoron Allah karki ɗauki hakkina ta hanyar fitar mun da
littafi*
*KURA A RUMBU littafin kuɗi ne, a biya naira 800, biya a asusun*
*1840175439*
*Access bank*
*PAGE 10*
Ɗaki na koma dan bazan iya karyawa ni kaɗai ba na fara sabawa tun da mukayi aure da Bilal bamu taɓa
raba kwano ba, yanzu bama na jin cin abincin raina duk babu daɗi. Tun ina sauraron jin ya buɗe ƙofa ya
fito har bacci ya kwashe ni a kishingiɗen da nake. Ban farka ba se da naji ana ƙwala kiran sallar azahar,
nasha mamakin irin baccin da nayi. Se da sake watsa ruwa saboda jiki na da naji duk ya ɗaure sannan
nayi alwala na fito ina jina fayau ciki na a rarake. Sallar na farayi sannan na gyara fuskata na saka kaya
dukda yanda nake jin yunwa dan Anty Labiba ta hora ni da kasancewa tsaf tsaf ko da yaushe. Daga
yanayin falon na gane ya fito yayi abinda ze yi. Dana duba kan dining kwano kaɗai na tarar an cinye doya
dana soya tas ga kuma cups biyu da aka sha tea, kwashe kwanukan na farayi na kai kitchen sannan na
dafa indomie naci ina mamakin me yayi zafi haka ne da Bilal yake wannan abun?
Ranar haka na wuni ni kaɗai a gida, se da yamma ne ma maƙwafta na mutum huɗu suka shigo mun, biyu
gidan su ɗaya matar wa da ƙani ne Hafsa Maman Salim da Amina ita amarya ce tsiran mu sati biyu kamar
yanda suka ce gidansu shine a farkon layi se Zubaida Maman Yusuf da gidan ta ke kallon nawa da kuma
Bintu ita ce muke katanga ɗaya. Har gab da kiran magriba muna ta hira kafin suka yi mun sallama suka
tafi na rakasu na dawo na gyara gurin da muka ɓata. Zuwan su ya rage mun kewa ya kuma ɗauke mun
hakankali daga damuwar in da Bilal ya tafi yini guda na kuma kira wayar sa sedai tayi ta ƙara baze amsa
ba daga ƙarshe ma ya kashe ta gaba ɗaya.
Har nayi sallar isha'i babu shi babu dalilin sa, zuwa sannan hankali na ya tashi na fara tunanin ba lafiya
ba. Ƙarfe tara na kira Mama ina kuka na gaya mata tun safe Bilal ya fita ina ta kiran sa kuma baya
amsawa daga ƙarshe ma wayar a kashe take.
"To ban da shirme kuma kukan na menene? Ai lafiya ce take ɓuya. Ki kira Nasir ko wani cikin abokanan
sa na gurin aiki kiji ko suna tare tun da hankalin ki be kwanta ba. Amma babu komai ma nasan tun da
kina gida ma ai yana haka ku wuni ba kuyi magana ba se daga baya ya baki uzuri" abin da Mama ta faɗa
kenan amma hakan be sa naji hankali na ya kwanta ba tun da ni dai tun da mukayi aure ko ƙofar gida ze
fita se ya gaya mun. Layin ƙanin sa Abubakar na kira se dai shima na tarar a kashe wannan ya sake
dugunzuma hankali na kawai na zauna na fashe da kuka na rashin madafa. Motsin buɗe ƙofa ya farkar
dani firgigit daga baccin daya sure ni ba tare da na sani ba ina tsaka da kuka. Dishi dishi nake kallon sa ya
tsaya shima yana kallo na kafin ya fara takowa cikin falon se na miƙe da sauri na nufe shi, tsayawa yayi
na faɗa jikin sa tare da fashe wa da kuka ina cewa
"Ina ka tafi? Hankali na ya tashi ina ta kiran wayarka baka amsawa me yasa kayi mun haka?"
A dake cikin yanayin da banyi zato ba bayan ya janye ni daga jikin sa ya kalle ni yace
"Kin aike ni ne balle ki bi ba'asin in da na tsaya?"
Se na bishi da ido kawai na kasa cewa komai, ya yi tsaki tare da zagaye ni ya wuce ciki.
Kamar wata wawiya haka na rakashi da ido har ya shige cikin ɗaki tare da banko ƙofa. Tamkar wacce
ƙwai ya fashewa a ciki haka naja ƙafafu na da suka yi sanyi na zauna kan kujera haɗi da zabga tagumi. So
nake na tunano ta in da na kuskurewa Bilal, me nayi masa da yayi zafi haka? Ina nan zaune ya sake
fitowa fuu ya shige kitchen ina jiyo shi yana birkita kwanuka kafin ya sake fitowa da kofin shayi a hannun
sa se dublan a plate. Nan cikin falon ya zauna bayan daya kunna Tv ya shiga shan shayin sa, yanda yayi
tamkar be san da wanzuwata a gurin ba yasa na fashe da kuka sosai har da shashsheƙa se gani nayi ya
miƙe tsaye da kofin shayin sa da alama gurin ze bar mun. Bazan iya jurewa ba, ina buƙatar nasan
takamaiman dalilin fushin da yake yi dani se na miƙe da sauri na isa gaban sa na durƙusa tare da riƙe
ƙafar sa ina ci gaba da kukan nace
"Ka faɗa mun me nayi maka kake mun irin wannan horon Bilal?"
"Baki ma san me kika mun ba kenan?" Ya faɗa yana ɗage kai sama a ƙoƙarin hana tausayi na yin tasiri a
zuciyar sa. Girgiza kai nayi ina ci gaba da kukan nace
"Wlh ban sani ba, ka taimaka ka gaya mun me na maka bazan iya cigaba da jure fushin ka irin haka ba"
"Shikenan tun da baki san me kika mun ba Halima, duk ranar da kika tuna se muyi maganar" ya faɗa
yana janye ƙafar sa ya wuce cikin ɗaki se dai be kulle ƙofar ba a buɗe ya barta. Zuciya ta na raya mun na
rabu dashi da kansa ze zo in da nake idan ya gama fushin amma zuciyar dake cike da so da begensa ta
rinjaye ni haka na sake bin sa ɗaki ina kuka ina roƙon ya gaya mun abin da na masa amma se da mula
dan kansa kafin ya maido mun da zancen kilishi"
"Kayi haƙuri, ban kawo hakan ze ɓata maka rai ba amma zan kiyaye haka ba zata sake faruwa ba a gaba"
na faɗa ina goge hawaye. Duk da haka be wani sake mun koma yanda muke gaba ɗaya ba se da aka
kwana biyu ranar laraba ya fita da yamma babu jimawa Mu'azzam ya zo ya kawo mun manya manyan
kaji guda goma in ji Abba da ƙwai shima crate goma dake ya buɗe gidab gona ana kiwon kaji da kifi
yanzun an fitar da layers ne da suka dena ƙwai shine aka kawo mun rabo na. Tuwo nayi niyyar yi ganin
kajin yasa na fasa na haɗa lafiyayyen farfe su irin wanda Bilal ke so na kwaɓa fulawa na gasa bread dan
na lura yanzu abin laifi baya yiwa Bilal yawa tsaf idan na kira shi nace ya taho mana da bred ɗin se ya
maida abin na rigima.
Se da akayi sallar isha'i kafin suka shigo gidan shi da Abubakar da Halifa ɗan Babbar yayarsu Anty Na'ima.
Can falon sa ya buɗe musu suka shiga na kai musu ruwa da lemo ganin ya fito da laptop ɗin sa yasa na
fahimci wani abun zasu yi ba yanzu zasu tafi ba dan haka na ɗora musu jallof ɗin taliya na saka musu
kazar a ciki, na sauke kenan na jiyo maganar su a tsakar gida alamun sun fito zasu wuce hakan yasa na
leƙa da sauri na sanar musu ga abinci na sauke ina kuma zasu tafi?
"Da kin barshi Anty sauri mukeyi" Abubakar ɗin ya faɗa, zanyi magana Bilal ya rigani yace
"Ku wuce kawai kasan na cewa Nasir ya jira ka kai masa flash ɗin nan kar ku ɓata masa lokaci"
"Haba dai duk saurin da sukeyi ai sa jira dai su ci abincin, idan kuma ba zaku ci anan ba bari in juye muku
to se ku tafi dashi kawai" na tare shi. Naga irin kallon daya mun amma ban kawo komai ba na koma
kitchen, falon suka shigo suma suka zauna Bilal ya bini kitchen, yana tsaye a kaina na juye musu taliyar
gaba ɗaya a kula tun da dama su na dafawa na saka a kwando na haɗa musu da ruwan gora da lemo
yana nan tsaye a kitchen ɗin na fita na basu mukayi sallama suka tafi. Bana zaton sun kulle mana ƙofa
Bilal ya hau ni da faɗa tamkar ze doke ni, akan me yace su tafi zan ce su tsaya in zuba musu abinci?
Mamaki ya sa na kasa ce masa komai, waccen ranar yayi faɗa dan na yiwa yar uwata kyauta yau kuma
yana yi saboda nayiwa nasa dangin menene matsalar Bilal ne? Ban san ya akayi ba kuma ya rage
banbamin da yakeyi yana cewa
"Bana so, karki sake mun irin haka a gaban yara salon suce ban isa da ke ba kin raina ni in ba haka ba ya
za ayi na baki umarni ki take kiyi wanda ranki ya raya miki? Yanzu da kika juye musu abincin duka ni
wanne zanci"
"Allah ya baka haƙuri" na faɗa a sanyaye kafin na shige kitchen na barshi. Na zata ze shige ɗaki ya kulle
irin na waccen ranar se kuma na tarar dashi a zaune yana kallo, se da na gama jera abubuwan da zamuyi
amfani dasu akan dining kafin nayi masa magana ya taso. Sosai yaci naman nayi mamakin da ban ji ya
tambaye ni daga in da aka samo su ba tun da yasan bamu da sauran naman kaza a gidan se wanda yake
cikin miya. Kafin mu kwanta se da ya sake ci ya kuma jaddada mun in aje masa sauran a fridge karya
nema gobe nace masa na bawa wani.
A haka muka cinye satin, zaman mu ya koma kamar da har ma ya zarce da daɗi da farin ciki. Cikin abin da
yasa nake ƙara son Bilal mutum ne shi da baya son jikin sa, ina kwance zeyi shara yayi mopping wani
lokacin har girki yake ɗora mun, ranar daya ga ina haɗe kayana da sukayi datti kafin na samu wanda ze yi
mun wanki kamar wasa yace na fita dasu tsakar gida, na yi tunanin almajiri ze nemo na fitar na ci gaba
da gyaran ɗaki na se kawai ganin sa nayi ta window yana shanya kayan ashe da kansa ya wanke mun.
Wannan yasa na ke ƙara son sa saboda ya bani mamakin na same shi yanda ma banyi zato ba. Abu ɗaya
yake bani tsoro da halayyar sa yanda yake birkicewa lokaci ɗaya akan ɗan ƙaramin abu da be taka kara
ya karya ba, wani lokacin ya sakko da wuri wani lokacin ko se naji na tsani kaina na tsani dalilin daya sa
na zaɓi rayuwa dashi kafin ya sakko idan komai ya wuce kuma se ya zama kamar wani saɓani be taɓa
shiga tsakanin mu ba.
A haka muka ci sati huɗu da aure se lokacin kuma hutun daya ɗauka ya ƙare ya koma bakin aiki, da safe
idan ze fita har kuka nake yi saboda sabon da nayi na kasancewa tare dashi a ko da yaushe bana taɓa
samun nutsuwa se naga ƙarfe huɗu tayi lokacin shigowar sa gida yayi. Bahaushe yace yau da gobe bata
bar komai ba, a hankali cefanen mu ya fara ja baya. Ɗan yun kayan miya ne suka fara ƙarewa ya rage
albasa kawai nake da, da yake ina da dafaffu a freezer markaɗe da jajjage se banyi azancin sanar dashi
ba. Ranar wata asabar yana gida, da rana yace na dafa mana shinkafa da wake jollof nayi amfani da
bushashshen kifi. A plate ɗaya na zuba mana, har mun fara ci yace na ɗakko masa yaji wai abincin yayi
masa salam da yawa dake da manja nayi. Dukda ya saka yajin ya ce beyi masa yanda yake so a bakin sa
ba dan haka ya tashi ya tafi kitchen da kansa, se da ya ƙwala mun kira naje yake tambaya ta ya yaga
babu kayan miya?
"Sun ƙare ai, saboda ina da markaɗe a ajiye shiyasa ma ban gaya maka" na bashi amsa. Bece mun komai
ba muka koma muka ƙarasa cin abincin kafin ya shirya yace mun ze ɗan fita amma ba jimawa zeyi ba.
"Dan Allah na shirya mu tafi tare" na shiga yi masa magiya amma kamar kullum ya ce Aa. Tun waccen
ranar da muka je gidan su da namu ko ƙofar gida ban sake fita ba ba kalar magiya da nacin da ban masa
ba amma yaƙi. Kafin muyi aure idan aka ce mun Bilal Bilal zeyi kulle zan ƙaryata se gashi a take takensa
na ga hakan. Da nayi masa ƙorafin duk sauran yan uwana da akayi mana aure tare sun je sun gaida
iyayen mu ce mun yayi al'ada ce ba addini ba ni ba zani ba, abin da yasa na haƙura da na yiwa Mama
mita tace na haƙura ai dama yayi wuri wata ɗaya ace na fara yawo. Ni yanzu gidan Anty Labiba na damu
da naje, tun ranar da aka kawo gara bata dawo ba, a waya ma sau biyu ta kira ni akan wani saƙo da tace
za'a kawo mun se bayan an kawo ɗin ta sake kira tayi mun bayanin yanda zanyi dashi. Ko a chat idan ba
ni nayi mata magana ba bata kulani, nasan fushi takeyi dani shi yasa kuma nake so naje gida na bata
haƙuri mu sasanta dan bazan iya jure fushin nata ba.
Ba yanda na iya tun da yace Aa haka na koma ciki na zauna rai na duk babu daɗi se dai kamar yanda yace
be jima ba ya dawo da cefane harda irish potatoe da doya tun da yaga su ma saura kaɗan. Se da na aje
komai in da ya dace kafin na koma gurin sa. Washe gari kamar kullum da wuri na gama haɗa abin
karyawa na soya dankali da ƙwai se ruwan tea, har na gama komai Bilal na ɗaki be fito ba, ganinya kusa
makara yasa na haɗa masa shayi dan ya huce kafin yazo sha na wuce ɗaki gurin sa. Seda na taimaka
masa ya ƙarasa shiryawa kafin muka fito tare ina masa daru akan yayi kyau da yawa ina tsoron kar
yammata su yi ta kallar mun shi a waje. Fusarsa washe da fara'a da alamu yana jin daɗin yanda nake
kambama shi a ko da yaushe ina zuzuta kwalliyar sa. Se da na ja masa kujera ya zauna kafin 1na buɗe
bowl ɗin dana zuba dankalin na janyo plate zan zuba masa,
"Meye wannan Halima?" Ya faɗa da ƙarfi har se da na razana. Jiki na ya ɗauki rawa na saki fork ɗin
hannuna tare da dafe ƙirji na dake harbawa ina ambaton innalillahi wa'inna ilahi raji'un a fili tare da baza
ido ko zan ga abin da ya saka shi wannan razanar haka amma iya hange na banga komai akan dining ɗin
ko kewayen in da muke ba.
"Banga komai ba Bilal" na faɗa cikin rawar murya dan dagaske na tsorata. Cikin ɓacin ran daya nuna har
kan fuskar sa ya nuna bowl ɗin dankalin yana cewa
"Wannan uban dankalin da kika soya waye ze cinye shi? Almubazzaranci zaki fara ko Halima saboda baki
san zafin kuɗi ba baki san yanda ake neman su ba? Yanzu cikin mu mu biyu ne zaki soya wannan abun?
Ko da yake baki da asara shi yasa, se ki zauna kici" daga haka ya miƙe ya saɓa jakarsa ya nufi ƙofa yana ci
gaba da banbami. Ƙarar da ƙofa tayi bayan daya bugota ya dawo dani daga suman wucin gadin da
mamakin Bilal ya sakani yi. Na sauke ajiyar zuciya me ƙarfi tare da jan kujera na zauna saboda ji nayi
ƙafafu na sun yi sanyi kamar ba zasu iya cigaba da ɗauka ta ba. Se na rasa ma tunanin me zanyi, akan
dankali dai Bilal yake kirana almubazza?
Buhu ɗayan da muka cinye a sati biyar be saka ya danganta ni da almubazzaranci ba se yanzu saboda na
soya daga cikin kwano ɗayan daya siyo da kuɗin sa? Dankalin da yake cewa baya gajiya da cin sa, se muci
da safe mu ci da rana da dare ma mu ci, Allah ke da kullum duk safiya har idan ya rigani shiga kitchen
dankali ze feraye ko nayi marmarin doya idan ba shi yaga dama yaci ba se yace sedai kowa yaci abin da
yake so amma shine yake mun tijara akan sa yau?
Ina nan zaune kusan awa guda gaba ɗaya kaina ya kulle har na rasa kalar tunanin da zanyi. Bugun get da
kuma wayata da ta ɗauki ƙara yasa na tattara hankali na guri ɗaya ganin Hansa'u ke kiran yasa na miƙe
dan nasan itan ce take buga ƙofa tun da mun yi magana tun jiya ta gaya mun yau zata zo ta kawo mun
atamfa da kace ɗin ankon bikin ta da aka saka nan da sati shida. Fara'ar dole na ƙirƙira na ɗorawa
fuskata bayan na buɗe musu ƙofa suka shigo tana mun mitar sun daɗe suna bugu kuma dan wulaƙanci
tana kira ban amsa ba. Bana yanayin da zan ja magana se kawai nayi murmushi muka shiga falo. Ƙanwar
ta Abida ce ta wuce kan dining kai tsaye tana cewa
"Ni wlh yunwa nakeji Anty Halima ban karya ba ta taso ni me kuka rage?" Bata ma jira na bata amsa ba
ta dirar wa dankalin Bilal, Hansa'u zata hau ta da faɗa na hanata, ina lura da yanda take kallo na nasan
baze wuce ta karanci damuwa tattare dani bane tun da kuma ban ce mata ba itama ba tayi karambanin
tambayata komai ba, basu jima ba suka wuce bayan ta bar mun atamfa ɗaya da lace ɗin na zata ma wuni
zatayi tace mun Aa yau take so duk wanda zata kaima ankon gida ta gama dasu. Abida bata daddara ba
ta sake ɗaukko kwalin exotic a fridge tasha ta tafi da sauran, yana cikin lemon da Bilal yafi so kuma shi
kaɗai ya rage kwali ɗayan ina kallon ta amma bazan iya cewa ta ajiye ba domin rowa ba hali na bace ba
kuma zan koyeta a gidan aure ba sannan Abida na ɗauke ta ne kamar Amirah ƙanwa ta babu yanda za
ayi na hanata wani abu da nake dashi.
Saboda yanda muka rabu da Bilal yasa na cire komai daga raina na yi masa girkin daya fi so kafin ya dawo
na sake gyara gida na baza turare nima nayi wanka na cancaɗa kwalliya na kame a falo ina jiransa. Rai a
haɗe sallama a ciki ya shigo falon, nayi kamar ban lura da yanayin sa ba na nufe shi ina masa sannu da
zuwa. Be tare ni yanda muka saba ba be kuma gwasale ni yanda nayi zato ba se ya miƙo mun jakar
hannun sa na karɓa ina murmushi tare da yi masa sannu da zuwa, yanda ya amsa ya sosa mun rai har
naji idanuna suna neman su kawo ruwa amma na dake. Kitchen ya wuce na bishi da kallo kafin na wuce
ɗaki na aje masa jakar sannan na shiga banɗaki na tara masa ruwan wanka. Ina ciro masa kayan da ze
saka ya shigo ɗakin, kamar daga sama naji yace
"Kuma kika cinye dankalin duka". Na saci kallon sa shi ɗin ma ni yake kallo se nayi gefe da kai na nace
"Idan an barshi ai lalacewa zeyi". Ƙwafa naji yayi kafin ya shige banɗakin kamar ze tashi sama, ni se ma
ya bani dariya. Abincin ma sama sama yaci ya ture ya shige kitchen, kamar ɗazu da safe ya sake kwazara
mun kira saura ƙiris na ƙware da abincin baki na na maida shi cikin plate ɗin na tashi da sauri.
"Dan girman Allah Bilal ka dena mu irin wannan kiran bana so" na faɗa tamkar zan fashe masa da kuka
ganin sa a tsaye jikin fridge, ya kalle ni kafin ya buɗe fridge ɗin yana nuna ciki yace
"Nayi baƙi sun shanye" na bashi amsa kai tsaye. Yanda ya yi mici mici da ido yana kallona se ka rantse
iyayen sa na zaga.
"Shi lemon nawa kike gaya mun kin yi baƙi sun shanye?" Ya faɗa yana nuna kansa, Allah ya sani na fara
zuwa bango. Wane irin abu ne daga dankali se kuma lemo se kace ana fatara ko tsiya?
"Baƙi nayi suka zo da yara ni ban ma sani ba muna falo suka shigo suka ɗauka kaga kuma babu yanda za
ayi nace su mayar tun da dai abin nan munfi ƙarfin sa ba fatara akeyi ba" na bashi amsa ba tare dana
kalle shi ba. Seda ya kwashi sakanni yana kallo na kafin yace
*(Based on true life event, some parts are fictional to spice up the story)*
*Wattpad @MaryamahMrsAm*
*Ban yarda wani ko wata ya juya mun labari ta kowacce siga ba tare da izini na ba*
*Kuɗin karatu yana wakiltar mutum ɗaya ne, kiji tsoron Allah karki ɗauki hakkina ta hanyar fitar mun da
littafi*
*KURA A RUMBU littafin kuɗi ne, a biya naira 800, biya a asusun*
*1840175439*
*Access bank*
*PAGE 11*
Daƙyar na koma cikin falo na zauna ina jin kaina yana saramun. Me yasa Bilal yake haka? Kullum ace
abinci ne ze ringa haɗa mu rigima?
Ina nan zaune ya fito daga ɗaki yanayin shigar sa na gane nisa ze yi. Ko kallo na be yi ba ya fice sabbin
hawaye suka ɓalle mu. Zuciya ta tana raya mun na barshi naga iya gudun ruwan sa amma gangar jiki na
taƙi bani haɗin kai, bazan ce ga sanda na miƙe na bi bayan sa ina kiran sunan sa ba amma ko a jikin sa ya
yi ficewar sa daga gidan ya bar ni a tsaye ina hawaye. Se da nayi kuka me isa ta, har na danna layin Anty
Labiba zan kai mata kuka na se dai nauyi da kunya suka sa na katse kiran, Ina kallo kuma ta biyo baya
amma na kasa ɗagawa.
Har aka kira sallar magriba be dawo ba, bayan na idar da sallah ina zaune wani tunani ya faɗo mun.
Mu'azzam na kira, bayan mun gaisa na tambaye shi yana ina ne?
"Ina kusa da gidan ki, da zan shigo ma amma bani kaɗai bane kar nayo miki gayya kuma baki san da
zuwan mu ba" ya faɗa. Se na marairaice nace
" Saƙon me? Na gaya miki fa ina unguwar ba wai daga gida zan fito ba" ya faɗa se nayi saurin cewa
"Ai a kanti zaka siyo mun abun, lemo ne ba wani abu ba ka siyo mun Exotic carton ɗaya idan kazo se na
baka kuɗin".
"Ke yanzu duk uban lemukan da aka kawo miki da gara har kun shanye shi ko mutane kika yi ta rabarwa?
To se dai ki aiki mijin ki babu wani lemo da zan kawo miki" ya faɗa yana niyyar katse kiran na san halin sa
tunda ya fara hakan da wuya ze kawo mun ɗin amma idan yaƙi ban san kuma ta hanyar da zan bi mu
shirya da Bilal a gajeran lokaci ba dan haka nace
"Haba ɗan uwana, ina da lemo kala kala shi ɗin ne dai ya ƙare kuma shi nake iya sha yanzu". Shiru yayi
har nayi zaton ma ya kashe wayar kafin naji yace
Jin na samu mafita hankali na ya kwanta se na tashi na shiga tattare kayan abincin dana aje masa na
maida kitchen tun da baze ci ba. Ba'a ɗauki minti ashirin ba Mu'azzam yazo, carton biyu ya siyo mun be
ko zauna ba muka gaisa daga tsaye yace ana jiransa ne. Ɗaki na tafi na ɗakko masa kuɗin amma yaƙi
karɓa.
"Lallai ƙani na an fara hankali" na tsokane shi, se yayi murmushi kawai yana kallon fuska ta dana lura
tunda ya zo yake kallo na yace
"Me ya same ki naga idon ki sunyi jaa kuma sun kumbura fuskar ki ma haka?" Se naji kamar ya fama mun
abin da yake damu na nan da nan ido na ya kawo ƙwalla se dai ban bari sun taru ba na ƙaƙalo murmushi
nace
"Se ki gaya masa ya siyo miki maganin malaria tun da kina barin ƙofa a buɗe dama dole sauro zasu shigo
miki" ya faɗa yana fita. Na bi bayansa, se da muka je get ya sake kallo na yace
"Halima fuskar ki ta nuna kina da damuwa" kawai jin ɗumin hawaye nayi akan fuska ta ba tare da nasan
saukar su ba. Ya gyara tsayuwa yana kallo na yace
"Duk da ke kika siyawa kanki amma ba zan baki shawarar ki shanye baƙin ciki a son kar ayi miki dariya
ba. Idan kika ji ba zaki iya ba ki tafi tun lokaci be ƙure miki ba" daga haka ya fice ya barni tsaye a gurin ina
kuka mara sauti. Se da gabana ya faɗi da naga kiran Mama bayan tafiyar Mu'azzam babu jimawa.
Tunanin ko ya faɗa mata wani abu na shiga yi, to amma me ze ce mata?
Se da ta mun kira biyu kafin na amsa a sanyaye muka gaisa ta tambaye ni jiki na ce da sauƙi.
"Karki kuskura ki tasa kayan zaƙi kice zaki ringa sha, Mu'azzam ya gaya mun kin ce ya siyo miki lemo to ki
tattara su ki aje in ba haka ba wuya zaki kirawa kanki tun yanzu" ta faɗa. Se naji dariya ta kamani, wato
in da lissafin ta ya tafi kenan ciki ne dani amma dan a rabu lafiya se kawai na bita da toh. Bamu jima ba
mukayi sallama tana sake jaddadamun na kiyayi kayan zaƙi ni dai da toh kawai na ringa bin ta. Maganar
da mukayi da Mama tasa na danu sauƙi cikin zuciyata se kawai nayi shafa'i da wutri nayi kwanciya ta.
Ban sanda Bilal ya dawo gidan ba na dai farka cikin dare na ganshi a baya na. Da safe tamkar bamu samu
saɓani jiya ba lafiya lau ya tashi yana jana kamar yanda muka saba ni ce ma nake ɗararewa. Ban yi gigin
taɓa masa dankali ba na ɗumama sauran abincin da be ci ba jiya muka karya dashi, da ze fita yace mun
na shirya idan ya dawo zamu fita wannan tasa na ware nima. Gidajen yayyen sa mata muka zagaya
waɗan da suke ciki ɗaya da wanda suka haɗa uba. Har unguwar su Anty Labiba muka je amma ƙememe
yaƙi yarda mu shiga wai takanas zamu shiryo muje ba ratse ba. Dake dai mun shirya ya sakko daga fushin
ban matsala ba kar ya sake birkice mun tun da dai yayi alƙawarin zamu je da weekend na wuni shikenan.
Haka rayuwa taci gaba da miƙawa a lissafi aure na da Bilal yana cikin wata na biyar kenan a kuma cikin
wannan lokacin nayi karatu game da zamantakewa ta dashi ta rannoni biyu. A bangare ɗaya na tabbatar
da cewa Bilal yana so na domin irin kulawa da tattalin da yake bani na san cewa ba duka haka maza suke
ba. Yana da sauƙin kai sosai a halayya sannan ya ɗauke ni matsayin ƙawa be hakan ne yake ƙarawa
zamanmu armashi.
Idan har yana gida tare muke duka ayyukan gida. Kasancewar sa me tsafta sam baya shiri da ƙazanta be
kuma so jikin sa ba, da sassafe kafin ya fita aiki ze share mun tsakar gida ya wanke haka da falo na nasa
ze share yayi mopping ni kuma naji da gyaran ɗaku na da girki idan ya wuni a gida kuwa hatta sharar
ɗakunan shi zeyi ya gyara ko ina tsaf ya kunna turare dan idan yayi gyaran nafi ganin gurin yayi yanda
nake so saboda babu algus, kullum ze yi shara tofa se ya ɗaga kujeru ya share ƙasan su haka duk wani
abu dake ajiye se ya ɗaga ya goge har mamaki nake yi yanda sam abin be dame shi ba kamar ma hakan
na samar masa da jin daɗi dan cike da walwala yake ayyukansa wankin toilet dama ko na wanke na ɗakin
sa cewa ya keyi be fita ba ze zauna ya sake wankewa tas yanda yake so haka wankin kaya har undies
yake wanke mun wani lokacin muyi tare ina masa ɗauraya wani lokacin yace ban iya ba na barshi se dai
na zauna daga gefe ina masa hira waɗannan halayyar tasa take sake ƙara mun son sa da ƙaunar sa a
zuciya nake kuma ganin ɗaya ɓangaren na halayensa da bana jin daɗin su a matsayin ajizanci irin na ɗan
adam domin kuwa babu wani mutum da yake cikakke dole ka kasance da halayen abin so da kuma
wanda ba kowa yake so ba.
Daga cikin abin da ke yawan janyo saɓani tsakani na Bilal shine ƙorafi. Ko dan yana yawan zama a kusa
da ni ne tun da idan ya fita aiki ya dawo idan ba sallah ba ba in da yake zuwa in kuma ranakun hutu ne
yana gida, ba ƙaramin abu bane yake fitar dashi ko ya fita ma baya jimawa ze dawo dan haka ko yaushe
muna tare dan haka duk abinda zanyi akan idon sa ne kuskure kaɗan kuma zan yi yayi ta mita yana ƙorafi
kenan. Abin da be kai ya kawo ba se ya zama na magana a gurin sa.
Sannan na lura Bilal yana da son ya zama duk wani abu da zanyi ya zama da sanin sa. Sannan mutum ne
me tattali da son abin sa. Har idan ina so na ga fushin sa to fa na taɓa abun sa ba tare da izinin sa ba tun
da kuma na fahimci hakan nake kiyayewa shikenan nayi maganin fitinarsa. A watanni biyar ɗin nan bani
da wata matsala idan aka cire rashin fita da Bilal baya bari na a sanda naso se kuma rashin walwala ta
kuɗi a hannu na. Ina samun kuɗi dan kusan duk sanda zanje gida Abba se ya bani ko ya tura mun a
account a cewar sa kar na ringa damun miji na da bani bani, Saboda gudun fitinar Bilal ko ƙorafi akan
kayan sa bana saurar komai daga gare shi duk abin da nake so cikin kuɗi na nakeyi har shima nayi masa
na kuma yiwa yan uwansa.
Abin sa na sake lura dashi yana jin daɗin shi na hidimta masa amma baya so nayi wa wani dan har idan
wani ya zo mana nayi masa kyauta a gabansa ko beyi magana ba a fuskar sa ina karantar rashin jin daɗi
abun na damuna da na gaji nayi masa magana akan hakan se yace wai abin da nakeyi ze janyo masa raini
a gurin masu zuwa gidan mu shi megida ya kamata ace idan ma kyautar ce yayi ba wai ni ba, saboda a
zauna lafiya se ya zama idan yana nan mukayi baƙi idan kuɗi ne zan bashi nace ya basu idan kuma wani
abun amfani ne zance gashi in ji shi shikenan na samu lafiya da wannan ma.
Tuni result ɗin mu ya fito har wasu daga cikin mu sunyi nisa a service, labarin da naji akan an yi ƙarin
kuɗin da ake biyan yan bautar ƙasa ya sa na himmatu nima. Hansa'u na tambaya kuɗin da ake kashewa
na clearance kafin a karɓi result dan tuni ta karɓi nata harta fara service a Abuja in da tayi aure, gaba
ɗaya kuɗin ya kama dubu goma sha biyu da ɗari biyar. Se da na lissafa abin da nake dashi kwata kwata
dubu biyar da dari bakwai yayi mun saura cikin dubu goman da Abba ya bani shekaran jiya da mukaje. A
ciki na bawa Bilal yayo mana refilling gas ina tsaka da girki jiya ya ƙare, nasan ba'ayi albashi ba da
daddare kuma naji kwaɗayin tsire nan ma na bashi ya siyo mana na dubu ɗaya na dafa mana indomie
muka ci.
Mayar da kuɗin nayi ina jiran ya dawo naji yanda zamuyi tun da yɗauka wa gobe nasan zasu iya samun
albashi. Se da muka ci abinci kafin na sako masa zancen an yi ƙarin allawee.
"Na zata ma na gaya miki, se naji ina ma yanzu ne zanyi service nima" ya faɗa se na yi dariya nace
"Haba kun riga kun ci rabon ku yanzu mune zamu shana. Ina ganin ranar monday se na shiga makaranta
Hansa'u tace zan iya yin komai a rana ɗaya kuma nan da wani satin za'a buɗe registration na Batch B
kaga dai dai kenan".
Na ɗauka maganar da nayi masa zata sa ya fahimci abin da nake nufi duk da be tambaye ni nawa ne abin
da za'a buƙata ba se na barshi akan se ranar tayi tukunna. Cikin daren salaryn sa ya shigo lokacin wayar
tana kusa da ni shi kuma ya shiga kitchen ɗauko abu daya fito kuma ya ɗauki wayar be ce mun komai ba
nima ban damu ba. Monday ta kama hutun ranar ma'aikata dan haka babu aiki se washe gari talata a
daren na sake tuna masa da washe gari fa zan je makaranta yace Allah ya nuna mana. Washe garin da
wuri na shirya, baze fita ba kamar yanda yace suna wani field work ne se ƙarfe sha biyu ze fita zuwa in da
yake yin research. Se da nayi masa girkin rana saboda daga makaranta gida nake so na wuce kafin na
ƙarasa shiryawa. Ina saka Hijabi na ya shigo ɗakin, ya kalle ni ba yabo ba fallasa nima ina kallon sa nace
"Na gama" yau ce rana ta farko da zan fara fita ni kaɗai a tsayin auren mu. Duk in da zanje tare muke fita
ko muje tare ko kuma mu rabu a hanya amma ban taɓa kulle gida na fita ni kaɗai ba.
"Amma fa kar kiyi dare, ina tunanin Hafiz abokin aiki na zasu zo da matar sa yau ki dawo da wuri saboda
ki tanadi abin da zaki tarbe su dashi" ya faɗa. Na ɗaura niƙab a fuskata ina cewa
"In sha Allah bazan daɗe ba". Gefen gado ya zauna ni kuma na gyara tsayuwa jikin chest of drawers ina
jiran ya sallemi ni ganin yana ƙoƙarin kwanciya yasa na ce masa
"Na miki a dawo lafiya ai, ko na zo na rakaki titi ne ba sabanba zaki fita ke kaɗai yau?" Ya faɗa yana
murmushi. Se na ɗage niƙab ɗin ina kallon sa nace
"Eh da ka rakani ɗin ma zanji daɗi amma bana so na wahalar da kai ga rana ta fara tsayawa sallame ni
kawai na tafi".
Aljihun rigar sa ya shiga lalubawa ya zaro kuɗaɗe da nake zaton zasu iya kaiwa 20k ko su fi a ciki ya zari
1k ya miƙa mun yana cewa
"Nagode" na faɗa ina karɓa. Jimm nayi a tsaye ganin ya gyara kwanciya har da jan bargo zuwa cikin sa
yasa na ɗauki jakata kawai na fita. Na fi minti goma zaune a falo ina tunanin in da zan lalubo kuɗin na
rasa. Ina jin kunyar na tambayi Abba duk da shi yace duk abin da nake so in gaya masa amma kuma ai
nima ina da hankali na san dai dai da aka sin haka. Ganin ina ɓata lokaci yasa kawai na tafi. Gidan mu na
fara zuwa, ganin motar Anty Labiba a waje yasa naji kamar na juya amma na daure na shiga.
Su uku na tarar, Mama, Anty Labiba se Anty Fauziyyah.
"Ta Bilal ki ce shigar ninja kuma kika koma" Anty Labiba ta faɗa, nayi murmushi kawai na samu guri na
zauna na shiga gaishe su. Anty Fauziyyah tace
"Tun da aka kaiki bamu dawo ba kema baki leƙo mu ba. Muna ta saka rana zuwan be yuwu ba kar ayi
mana kiran dole ko bamu shirya ba".
"Ai bake kaɗai ba jiya Mami ma take ce mun yaushe zamu je nace idan ta shirya tayi tafiyarta kawai to se
ku haɗa hanya". Jin zata fara abin da tafi iyawa yasa na tashi na shige ɗakin Mama. Ganin wayarta na
kusa da ita yasa na tura mata text, har na ƙosa da jira sannan ta shigo ɗakin tana cewa
"Wane salon iskanci ne kuma haka? Su Labiban ne suka zama baƙin ki yau da zaki wani mun text kina son
magana dani?"
"Kin san halin ta Mama yanzu se ta taso da wata maganar ta daban ni kuma sauri nake yi" na faɗa ina
marairaicewa. Faɗa mata abinda ya kawo ni nayi, ta riƙe haɓa tana kallona kafin ta juya ta fita ba tare da
tace mun komai ba ina kiranta amma bata tsaya. Yanda Anty Labiba ta ƙwala mun kira yasa na gane
handsfree Mama ta mun, kamar zan fasa kuka na fita. Allah ya cece ni kafin ta fara mun tijara Anty
Fauziyyah ta dakatar da ita ta buɗe jakarta ta ciro rafar yan ɗari biyu sababbi ta miƙa mun tana cewa
Ban san ya suka ƙare ba ni dai tun da buƙata ta biya nayi tafiya ta. Ƙarfe uku na gama abin da ya kaini, a
hanyar komawa gida na siyi doya dan ina marmarinta tun kusan wata biyu Kenan kuma be siyo ba dana
masa magana yace wai taja baya tsada take yi ni kuma yanzu ban ma ga tsadar tata ba. Almajirin Maman
Yusuf na bawa ya siyo mun hanta da albasa, se da nayi sallar magriba kafin na ɗora doyar dana rigada na
fere ta tafasa na soya da ƙwai a gefe kuma nayi sauce ɗin hanta taji albasa sosai da kayan ƙamshi. Ina
jere abincin Bilal ya shigo, sauri sauri ya wuce wanka yace mun sun yi waya da Abokin nasa har sun taho
ma suna hanya. Sabon transfer ne aka maido shi Kano daga Enugu, naga jinin su ya haɗu da Bilal sosai
dan rana ku ɗai ɗai ne baze yi zancen Hafiz ba.
Se da na buɗe fridge zan fitar da lemo da ruwan da zan basu naga ashe ruwan gora ya ƙare dama carton
biyu ne na siyo dan tun da na garata ya ƙare daga lemon har ruwan se dai idan naje gida na ɗauko ko na
siya da kuɗi na pure water ya dawo siya lemo dai ze siyo pieces biyu uku idan yayi marmari in na masa
maganar a siyo koda zakuyi baƙin kunya se ganin sa nayi da kwalin Tiara da poster clark, se kawai na
saka aka kawo mun zoɓo baki na alaikum nake yi da yawa ina ajiyewa shima shi yake shanye wa.Jug na
ɗauraye na zuba pure water kawai.
Daga Hafiz ɗin har matar sa kana ganin su kasan yan gayu ne da suka jiƙu da kuɗi. Matar me suna Suhaila
zata girme mun sosai daƙyar idan bata haura shekara talatin ba se dai dake irin jiki na ne da ita ga kuma
gayu in ka kalle ta se ka ɗauka bata fi sa'a ta ba. Tana da fara'a sosai da ganin ta zata yi son mutane haka
shima mijin. Tare muka zauna gaba ɗaya a dining muka ci abinci, ina ta satar kallonta ina sabon course
ɗin kukayda miji. Yanda kasan ƙaramin yaro haka take kula da duk laumar mijin nata har zuwa ya tauna
abincin ya haɗiye, se da yayi rabin nasa sannan ta mayar da hankali ta fara cin nata abincin a raina ina
tunanin ni gwana ce a tattalin miji ashe babu in da na kai gwanaye na gaba na dole masa naga shima
yana nan nan da ita kamar ya goya ta dan da suka shigo jakarta ma a hannun sa take motsi kaɗan kuma
za'a ce mata "are you ok?"
A falo muka bar mazan na jata ɗaki na, yanda muka ringa hira se ka zata mun shekara da sanin juna tana
ta bani labarin Enugu, ita da Mijin nata duk yan Kaduna ne watan su uku kenan da aure yanzu. Har gurin
goma suna gidan. Muka yo exchanging number ina ta jin daɗi dan in ka cire matar Nasir da dama tun
kafin aure na da Bilal mun san juna ita ce matar abokin sa da zamu fara zumunchi yanzu. Da zasu tafi na
rasa me zan bata, ina da ingantattun kayan gyara da Anty Labiba take aiko mun da su duk da bata son
Bilal amma bata wasa da gyara masa ni, nayi tunanin ko na ɗibar wa Suhaila se kuma na fasa dan ban
san ko tana amfani dasu ba tun da ina yawan jin yan gayu na condemning magungunan mata duk da dai
nawa guarantee ne da aka sararrafa da ilimi se kawai na ɗibar mata turarukan wutar da take ta yabon
ƙamshin su. Sababbi ne na siye su gurin wata ƙawar Maman Salin maƙwafciya ta. Turarukan badai
ƙamshi da kama guri ba, na ɗakin da take ta zuzutun ƙamshin sa ya mata daɗi bama kunnawa nayi ba a
jiye kawai suke amma idan ka shiga se ka zata a lokacin ake ƙonawa. (08033950747 in dai turaren wuta
kike nema me daɗin ƙamshi da kama waje karki wuce BISHAQLINKS).
Dubu ashirin na yan ɗari biyar sababbi Hafiz ɗin ya ajiye mun, nayi nayi ya ɗauke kuɗin sa har matar sa
na bawa amma tace aa kyauta ya mun tukuicin girki idan ban karɓa ai ba zasu ji daɗi ba se dai idan
rainawa nayi hakan ya sa nayi masa godiya ina ganin Bilal nata kallo na na aje kuɗin kan center table
muka raka su muna dawowa ya kwashe su yana cewa
"Kai kuma baka san fulako ba so kake kawai an bani kuɗi nayi zuruf na amshe ai se ka mun faɗa ma" na
faɗa ina dariya. Na ɗauka wasa yake da ya ɗauki kuɗin ze ajiye mun daga baya shiyasa ban damu ba. Sati
biyu da suka biyo baya aka fara registration na NYSC.
Se da naje Cafe suka ce mun se na kawo certificate of marriage da appointment letter ko ID card na miji
na da kuma shaidar canjin suna in dai ina so a bar ni a garin da nake kuma kar nayi zaman camp. Tilas na
haƙura da yi a ranar na koma gida, Bilal baya nan sun tafi Katsina gaisuwa acan zasu kwana dan haka na
kira shi na gaya masa yace na bari idan ya dawo se muyi magana. Washe gari suka dawo, be tada zancen
ba se ni ce na masa magana ya ce mun ze tambayi in da akeyin certificate of marriage ɗin da change of
name. Tun ina sauraron naji ya ce an yi ko ga yanda ake ciki har aka kwana uku shiru be ce mun komai
ba, da na sake masa magana ma da ɓacin rai yace mun ai yana sane shima jira yake yi wanda ya bawa
yayi ya ce masa an gama tun da dai ba da kansa ze yi mun ba ai dole na jira. Ganin ransa ya ɓaci yasa na
bar maganar, har ya rage saura kwana biyu a rufe registration be sake ce mun komai ba tun da na tuna
masa wancan ranar dama ya fara wasu attitudes se kawai na rabu dashi da yamma ranar nace masa zan
je gida be kuma hanani ba na tafi.
Cikin sa'a na tarar da Uncle Mudassir ƙanin Mama a gidan, ina faɗa musu abin da ya faru ya hau faɗa
yana cewa da uban me na zauna yi ga waɗan da muka gama karatun tare har sun ci ƙarfin service ɗin su?
Tare muka je dashi aka mun registration ɗin as single, ya karɓi details ɗin yace ze bawa wani abokin sa
dake aiki a NYSC ɗin ayi mun ƙoƙari a barni a Kano. Yanda Bilal be ce mun ba nima na masa shiru se sa
aka kwana uku muna zaune da dare yana danna waya ya kalle ni yace
"Wai ashe an rufe registration din NYSC, amma ɗan iskan mutumin nan be kyauta mun ba dole naje naci
uwarsa gobe. Kullum na kira shi ya ce mun yau gobe gashi har an rufe beyi abun nan ba" ya wani
fututtuke kamar gaske. Kallon sa kawai nayi na maida kai naci gaba da danna wayata.
Sosai naji zafin ko in kular daya gwada mun tun akan zuwa karɓan result da kuma zancen service ɗin nan
yanzu. Se na tuna da wata magana da ya taɓa faɗa a gaba na tun ina diploma, lokacin da Nasir ze auri
matar sa tana karatu yace ze ci gaba da ɗaukar nauyin ta. A gaba na yake cewa Nasir ɗin bashi da
hankali.
"Kai ka sakata a makarantar balle ka ci gaba da ɗaukar nauyin karatun ta? Ai wlh nan da ka ganni idan
iyayen yarinya sun ga zasu bani auren ta tana karatu to su san duk lalurar ta tasu ce ko kuɗin fensir ba
za'a ɗora mun ba tun da ba ni na sakata a makarantar ba". A lokacin kwata kwata ban nazarci maganar
sa ba a rashin hankali na ma gani nayi daidai ne tun da ina jin Abba na yawan cewa ko ze mun aure se na
gama makaranta dan babu dalilin da ze saka ka ɗorawa miji hidimar da bashi yayi niyyar kansa ya saka
maka yar a makarantar ba. Tuna wannan abun yasa naji raina ya sake ɓaci kawai na tashi na bar masa
gurin nayi kwanciya ta a ɗaki be kuma damu ba balle ya biyo ni yaji ba'a si dan dama ni ce nake kasa
zaune na kasa tsaye idan ransa ya ɓaci shi kuwa ko a jikin sa duk fushin da zanyi se dai ya jira na gama
hawa na sakko.
An yi posting cikin rashin sa'a aka cilla ni Bauchi, uzurin da abokin Uncle Mudassir ya bashi na cewa state
of origin ɗina Kano ce kuma banyi registration da wuri ba dan haka list ɗin yan Kano ya cika da daga
wata jahar ne ma ya iya cucu cuku a jefani amma yanzun ma babu damuwa registration kawai zan je nayi
se a mun relocation. Sanda ya kira yana mun wannan baya nin duk se na rikice na rasa ta in da zan fara.
Kwana biyu da suka wuce Bilal ya tsare ni da masifar akan me naje nayi registration a matsayin mara
aure kuma ba da umarnin sa ba? Yayi rantsuwa akan muddin aka kai ni wata jahar se dai nasan yanda ze
yi amma har idan da yawun sa ne ba zan je ba tun da na raina shi na fara yankewa kaina hukunci ba tare
da sanin sa ba. Yanzu haka bama magana, tsaka ni na dashi kallon banza ko abinci na baya ci in ya fita
tun safe se nayi bacci yake dawowa ɗazu har Hajjan su ce ta kira bin ba'asin me ya faru? Bata kuma tsaya
taji uzuri ma ba ta ringa surfamun faɗa wai dama taji ƙishin ƙishin ɗin na raina shi bana jin maganar sa to
wlh na shiga hankali na kuma taka a sannu idan ta juyo kai na ba zan ji da daɗi ba.
Maganganun ta suka kulle mun kai na kasa gane in da ta dosa, ni ce na raina Bilal? Kuma waye yake kai
mata tsogumin? Matar da sa albarka ne tsakanin mu idan naje ko yayanta suka zo ko mukayi waya bakin
ta baya gajiyawa da gode mun da yi mun addu'a ita ce zata kira tana mun wasu maganganu da ban ma
gane kan su ba. Ina cikin wannan jimamin kiran Uncle Mudassir ya same ni, kai na ya sake kullewa na
rasa ina zan kama. Haƙura zanyi da service ɗin nabi yanda Bilal ke so ko kuwa na barshi na bi son rai na?
Ina buƙatar me bani shawara.
*(Based on true life event, some parts are fictional to spice up the story)*
*Wattpad @MaryamahMrsAm*
*Ban yarda wani ko wata ya juya mun labari ta kowacce siga ba tare da izini na ba*
*Kuɗin karatu yana wakiltar mutum ɗaya ne, kiji tsoron Allah karki ɗauki hakkina ta hanyar fitar mun da
littafi*
*KURA A RUMBU littafin kuɗi ne, a biya naira 800, biya a asusun*
*1840175439*
*Access bank*
*Page 12*
"Idan har izini na kike nema ban yarda ba, ko da yake ai kin saba yin gaban kanki. Kiyi duk yanda kika so
Halima lokacin ki ne dama kika samu". Abinda Bilal ya gaya mun kenan bayan dana same shi akan
maganar posting ɗina zuwa garin Bauchi. Duk yanda kuma naso da ya zauna muyi magana ta fahimta
yaƙi, ƙarshe ma barin mun part ɗin yayi gaba ɗaya ya tafi can part ɗin sa da falon kaɗai muke amfani
dashi ina jin sa a daren ya gyara ɗakin tun da dama da hado da komai a ciki ya dawo ya ɗauki bedsheets
da bargo ya koma can.
Kwanan mu uku bana sanin fitar sa bana sanin dawowar sa. Hankali na ya tashi matuƙa, har ƙasan raina
ina jin na masa laifi kuma ya cancanci yayi fushi tunda matar sa nake ya kamata ace duk wani abu daya
shafe ni yana da masaniya a ciki musamman irin wannan abun da tilas nake da buƙatar sahalewar sa.
'Amma kuma na bashi damar sa', zuciya ta ke raya mun. Daga ƙarshe dai ɓangaren da yake ganin abin da
nayi ba daidai bane ya rinjayi wanda yake ganin ina kan daidai. Ranar laraba daya kama washe gari
Alhamis za'a fara shiga Camp da sassafe Uncle Mudassir ya kira ni. Bayan mun gaisa yake ce mun
"Tun jiya naso na kira ki, ina ganin idan da hali ki shirya kawai ki tafi yau tun da gobe za'a buɗe camp ɗin.
Kin ga idan kika kwana can zaki fi fita da wuri kije ki gama abin da zakiyi a goben ba tare da cunkoso yayi
yawa ba jibi kiyi juyowar ki".
Shiru nayi, se da naji yana ta hello hello kafin na sauke ajiyar zuciya nace
"Dama tun da na gaya masa zancen tafiyar ne yake ta fushi, kuma yace in har da yawun sa ne be amince
ba" na ƙarasa muryata na rawa. Se yayi shiru kusan minti ɗaya kafin ya ce mun
"Shikenan, kiyi yanda kika ga ya miki Halima" be ko saurari abin da zan sake faɗa ba ya kashe wayar sa.
Duk se na sake shiga ruɗani. Na ɗauka shi da yake namiji ze fahimce ni ya kuma ƙarfafa mun da nabi
umarnin miji na amma daga amsar sa na gane ransa ne ya ɓaci har ya rasa amsar bani shi yasa ya kashe
wayar. Na zabga tagumi gaba ɗaya ma ƙwaƙwalwa ta ta cushe na kasa tuna ni. Na sauke tagumin jin
wayata ta ɗauki ƙara na ɗago ta daga cinyata, Abba ne yake kira se naji wani rauni ya saukar mun nan da
nan hawaye ya tarar mun a ido.
Cikin ƙoƙarin danne kukan dake son ƙwace mun na gaishe shi ya amsa sannan yace
"Mudassir ya kira ni yanzu, wani abu kika yiwa Bilal ɗin da har ya yanke miki wannan hukuncin?" Se
kawai na fashe masa da kuka. Be hana ni ba nayi me isa ta har naji na samu ƙwarin guiwar yin magana
sannan nace
"Ban masa komai ba wlh Abba. Kawai dai tun da aka buɗe registration ɗin da naje suka ce se na kawo
marriage certificate da sauran takardu na shaidar ina da aure na gaya masa yace ze je ayi, har aka kusa
rufewa beyi ba da na sake masa magana shine ya fara faɗa wai na dame shi ranar na zo mukayi magana
da Mama Uncle Mudassir yana nan shine yace kawai muje nayi ai ba za'a tsaya jiran sa ba. Ina ga
wannan ne yasa yayi fushi ya kuma ƙi tsayawa muyi magana ma balle ya fahimce ni, ni kawai na haƙura
Abba tun da dai be yarda ba" na ƙarasa ina sake fashewa da kuka.
"Toh Abba ya zanyi? Yace be yarda ba kuma ai ba zan tafi ba tare da izinin sa ba" na faɗa cikin kuka, se
Abba yace
"Haka ne, toh Allah ya taimaka ya kawo sauƙi cikin al'amarin. Se a ci gaba da haƙuri Allah yayi miki
albarka" daga nan ya kashe wayar sa. Kuka sosai na sha bayan mun gama wayar har se da naji kaina ya
fara ciwo kafin na rarrashi kaina nayi shiru.
A can gida kuwa bayan da Abba ya aje waya cikin ɓacin rai Mama dake sauraron duk maganganun su
tace
"To me kike so na faɗa bayan wannan Amina? Tace mijin ta be yi mata izini ba, so kike yi nace ta take
maganar sa ta fito ko yaya? Idan aka yi haka ai ba da shi muka ja ba umarnin Allah muka take. Tun da ita
bata da dabarar da zata lallaɓa shi ta kuma haƙura ba shikenan ba duk wanda ze so mata tayi service ɗin
ta haɗa takardun ta guri ɗaya ai ba kamar ita da tayi karatun ba, ki bar maganar nan kawai. Ai ba cewa
akayi daga wannan karon shikenan an gama ba. Akwai wani lokacin sanda ya amince mata se tayi amma
yanzun a barshi kawai" Abban ya bata amsa ƙarara kuma fuskar sa da muryar sa sun nuna ransa be masa
daɗi ba shima da hukuncin da Haliman ta yanke. Tashi Mama tayi daga gurin kawai saboda ranta dake
suya idan ta zauna ƙarshe zata sauke fushin ne akan Abban. Tana shiga ɗakin ta ta kira Anty Labiba ta
gaya mata.
"Dan girman Allah Mama ki barta. Ai bata sako kowa a ciki ba bata nemi shawarar ki ba. Tun da dai haka
taga ya fi mata se mu rakata da addu'a Allah ya bata sa'a amma kar ki wani ɓata ranki akan wannan
abun" Anty Labiban ta faɗa mata.
Ina ji ina gani na haƙura da tafiya service duk a son farantawa Bilal. Ranar Juma'a la'asar ina zaune jigum
ni kaɗai a falo na kunna tv, ido na ne kawai akanta amma sam bana fahimtar abin da ake yi a ciki. Na
zata da Bilal yaga ban tafi ba ze fahimci na haƙura ne na bi umarnin sa ya sakko mu fahimci juna amma
sam banga haka ba, babu abin da ya canza se ma ƙaruwa da yayi dan tun shekaran jiyan cefanen mu ya
ƙare tas be siyo ba be kuma aje mun kuɗin da zan siyo ba ban ma ganshi ba balle na gaya masa shi kuma
kusan sati guda Kenan dama baya cin abinci na dan haka baze ma san menene akwai da wanda babu ba.
Kwana ukun da nayi jere ina cin mai da yaji har ulcer ta ta fara motsawa, ina so na fita na yi aike ina
tsoron sake yin wani lefin.
Ana kiran sallar Magriba Bilal y shigo, rabon da na saka shi a ido na kwana huɗu kenan yau. Na bishi da
ido kamar wadda taga sabuwar halitta, kamar ko yaushe yasha kwalliyar Juma'a cikin shadda se tashin
ƙamshi yake. A kan kujerar dake kallon wadda nake kai ya zauna, na sauke ido na ƙasa ina sakin ajiyar
zuciya jin idanun sa a kaina. Minti kusan biyu ganin yana zaune har sannan kafin na tattaro yamun baki
na na jiƙa maƙoshina daƙyar na furta
"Sannu da zuwa".
"Yawwa sannunki da gida" ya amsa mun, se na ɗaga kai na kalle shi jin muryar sa a sake sak ba fushi ba
ɓacin rai. Hannu ya miƙa mun alamar naje gare shi, ban motsa ba se hawaye da suka ɓalle mun kamar an
kunna famfo. Shi ya taso ya dawo in da nake ya ɗaga ni tare da rungume ni nan na samu dama na ringa
kuka kamar wadda aka aikowa da mutuwar iyaye. Shiga sallah da akayi yasa na janye shi kuma ya wuce
ciki da sauri ya yo alwala.
Be buɗe baki ya bani haƙuri akan abin da ya faru ko ƙauracewa gidan tsayin sati ɗaya da yayi ba amma
ya nuna mun a aikace. Ya ringa tattali na yana ji da ni kafin kace me na manta da duk fushin sa dake
zuciyata muka cigaba da zamanmu kamar wani abu be faru ba. A haka muka sake cinye watanni biyu
wanda ya kama wata takwas kenan da auren mu. Shirye shiryen azumi ya kankama dan ana lissafin saura
kwanaki biyar ko shida a fara azumin watan ramadan. A tsayin tashi na na saba a gidan mu muddin aka
ce azumi ya gabato da wata ɗaya muke fara shirye shirye. Mama tana fitar da kayan kitchen ɗin ta a
wanke komai ta ware waɗan da zata ci gaba da amfani dasu sauran a bayar sannan ta zuba sababbi
wanda nasan Abba ne yake bayar da kuɗin. Kafin a ɗauki azumi kusan abin da baze ajiyu bane kaɗai ba'a
siya a gidan mu a ajiye haka batun kayan sallah wani lokacin kafin a ɗauki azumi an gama mana ɗinki.
Tun da watan sha'aban ya kama nake yiwa Bilal zancen shirin azumi se ya ce mun se kace wani sabon
abu kamar bamu taɓa yin azumi ba shirin me za'ayi? Dake muna da kayan abinci, buhun shinkafar
dafawa uku aka mun ta gara data tuwo biyu, haka dangin su taliya zuwa mai komai uku har carton ɗin
maggi da gishiri ban da ma dangin Bilal dake yawan zuwa dan dai cikin mutum biyu zamu iya fiye da
shekara ma ƙila be fara siyan abinci ba. Duk kuwa sanda wani ze zo na dafa abinci na bayar ko be yi
magana ba se naga ɓacin rai a kan fuskar sa, na rasa irin wannan hali da Bilal ya tsira akan abinci.
Sanda na buɗe buhu na biyu haka ya ringa bala'i wai na ɓarnatar da buhun shinkafa a wata shida a haka
ma wai dan ba ita ake ci kullum ba da kenan a wata ɗaya zata ƙare. Yanzun shinkafa buhu ɗaya ta rage
mana da saura kaɗan a buhun da be ida ƙarewa ba, ina so cikin azumi ko ba kullum ba na ringa dafa
abinci ana yin sadaka amma ban san ko Bilal ze amince ba.
Na rigada nayi list na duk abinda zan iya buƙata da azumi se wanda ba a rasa ba jira kawai nakeyi ayi
albashi na bashi ya siyo mana. Ranar alhamis aka fara yin albashi, a kunne na naji yana waya da wani ɗan
gurin aikin su ya gaya masa sun samu ƙarin albashi. Har raina nayi murna saboda ina tunanin ƙarin da
suka samu ze saka mu ƙara samun walwala tunda kusan cefanen gidansu a kansa yake dukda yayyen sa
mata biyu suna auren masu wadata kuma ba laifi suna hidimtawa mahaifiyar su haka ƙanin sa Abubakar
matashi ne me zuciya sosai amma kullum Hajja cikin kiran sa ya bata kaza ya kawo musu kaza abu kaza
ya ƙare take be kuma gajiyawa ze ɗauka ya kai mata hakan yasa nake ɗauke kai ga yanayin yanda yake
tafiyar da namu cefanen na ke kuma yin abin da naji ina so in har ina da kuɗi a hannu na. To Abban da
yake bani kuɗin tun zancen NYSC na shima na fuskanci chanji a gurin sa, da wuya in je gida na tashi tafiya
ya bani ƙasa da dubu biyar kuma se yace na ɗauki duk abin da nake da buƙata a gidan tun lokacin kuwa
yanzu idan naje dubu biyu uku har dubu ɗaya bani yake yace na hau mota. Kasancewar na saba da ɗan
riƙe kuɗi a hannu na yanzu kuma me banin ya fara janye mun tallafi yasa duk nake ji na a takure.
Ban bashi list ɗin da nayi a ranar alhamis ɗin ba se na bari washe gari juma'a gurin ƙarfe goma bayan ya
gama shiryawa ze fita sannan na ɗakko masa takardar. Kwata kwata abubuwan dana lissafa a ciki basu
haura na dubu goma sha biyar ba zuwa ashirin wanda kuma ina da yaƙinin zasu kaimu har bayan sallah
da nisa ma. Ina murmushi cikin raina ina yaba zati da haiba irin ta Bilal. Kullum ƙara kyau da kwarjini
yake a idanu na musamman da yayi yar kiɓa jikin sa ya cike ya zama cikakken magidanci yanzu, kullum ya
fita cike nake da zullumin kar mata su bibiyar mun shi. Amma na yarda dashi na kuma san bashi da
kwashe kwashe.
Jin yana mun sallama yasa na miƙa masa takardar ya karɓa yana juyata.
"List ne na abubuwan da zamu buƙata kaga yau za'a fara duba wata" na faɗa ganin yana kallona da sigar
neman ƙarin bayani. Se ya buɗe takardar ya shiga bitar abubuwan dana rubuta
"Ke yanzu ana ta abinda za a ci a ƙoshi lissafin ƙwai da dankali dasu doya kike har da plantain?" Ya faɗa
yana kallo na bayan daya ninke takardar. Murmushi na saka dan na ɗauki maganar tasa ne a sigar wasa
nayi far da ido nace
"Eh mana, kasan a gida na saba da su nake karya azumi. Idan aka sha ruwa ban ci dankali ko doya ba ji
nake kamar ma ba azumi na kai ba. Dan ma lokaci ya ƙure ne dama so nayi ka bada kuɗin na bawa Anty
Labiba su daga Jos ake kawo musu har can gida ma duk ita ake bawa ta siyo mana"
"Yayi kyau" na rakashi ina masa a dawo lafiya. Ni ban san wai ashe maganar dana faɗa tayi zafi ba, fitar
sa babu daɗewa se ga Mu'azzam Abba ya aiko shi ya kawo mun gero da wake da sugar irin wanda yake
rabon azumi harda madarar ruwa katan ɗaya da dankali cikin ƙaramin buhu. Sosai naji daɗin kayan,
shikenan tun da ina da mai se na ringayin kunu da ƙosai ko ba yawa a bayar sadaka. A store na gyara
komai na ajiye ina jiran Bilal ya dawo na gaya masa, ranar be shigo ba se ƙarfe tara ya dai kira ni sanda
akayi sanarwar an ga wata yace tuwo zanyi abincin dare dashi yake so yayi sahur. A kwanakin in har ba
yana gida ba daƙyar nake wuce isha'i ban fara bacci ba sedai idan ya dawo ya tashe ni, yau ɗin ma ina
idar da sallah na kwanta a gurin bacci me daɗin gaske ya kwashe ni da bani na tashi farkawa ba se ƙarfe
uku da wasu mintoci na dare shima fitsari ne ya matse ni.
Akan gado na hangi Bilal yayi ɗai ɗai yana bacci abun sa ni kuma ina ƙasa kan abin sallah. Se da nayo
fitsarin kafin na fita falo jin ciki na kamar anyi yawa yunwa ta taso mun lokaci ɗaya. Ban gane kai ba se
da na tashi da malmalar tuwo biyu tukun na ji dama dama. Se sannan na lura da kayan daya zube
tsakiyar carpet, na kunna fitila me haske na shiga buɗe su. Har da nama da kifi da alama a ƙanƙara aka
ciro su dan sun narke duk ruwan su malale mun a kan carpet ga kayan miya suma ciki akwai marasa
kyau. Banji daɗi ba sam da abin da ya mun, jiya fa na shimfiɗa carpet ɗin bayan an dawo dashi daga
wanki gashi me haske shine ze aje mun kaya akai su ɓata ga ƙarnin kifi da nama ni ban ma ce masa ya
siyo mun kifi ba yama sani bana son ɗanyan kifi in dai ba cat fish ba ina da bushashshe da yawa dashi
nake duk abin da naji ina so na kifi.
Ina mita ina kwashe kayan, duk abinda na lissafa masa ya siyo ɗin banda ƙwai. Naman na fara gyarawa
na saka a freezer na juye kayan miya a kwandon su da sauran kayan tea da spices komai na ajiye sannan
na juya kan kifin. Ina buɗe shi naji amai ya yunƙuro mun, kafin na janye shi gefe daga cikin sink ɗin aman
ya ƙwace haka na ringa sheƙashi akan kifin kamar zan amayar da yan hanji, yanda ƙarnin yake dukan
hanci na haka zuciyata take sake hautsinawa aman na sake taho mun. Se da nayi dabarar toshe hanci na
da ɗankwalin kaina kafin na samu sassauci. Daƙyar ba samu ƙatuwar leda na tattare kifin daya sha
wankan amai a ciki na sake zura shi cikin wata ledar, se da na masa leda uku sannan na ajiye a ƙasa na
kwance robar morning fresh na zazzage cikin sink ɗin na ringa wanke gurin, ban ji kitchen ɗin ya mun
dama dama ba se da na zazzage robar hypo daya siyo cikin kayan idan haka siddan ne yaci ace warin
hypon kansa ya hau mun kai amma daɗin sa na ji na ware hanci na ringa shaƙa har seda ya maye gurbin
ƙarnin dake yawo cikin hunhu na sannan na fara komawa cikin hayyaci na sosai.
A sharar baya naje na jefa ledar kifin sannan na dawo na sake gyara kitchen ɗin, seda naji an fara kiraye
kirayen sallah sannan na fita na naɗe carpet shima dan ma kunna burner turaren wuta tun da na kwashe
kayan dama. Ina kici kicin ɗaga carpet Bilal ya fito ɗaga ɗaki, kallo ɗaya na masa na maida kai na ɗaga
carpet ɗin daƙyar ina nishi dan yana da girma da kuma nauyi. Be kula ni ba shima ya wuce kitchen, daga
ciki ya ƙwala mun kira. Seda na zumɓuri baki kafin na amsa na bi bayansa. Yana tsaye gaban sink ya
toshe hanci da hannun sa ya nuna mun robar hypo data morning fresh yace
"Meye haka?"
"Abu na wanke" na bashi amsa ba tare da na kalle shi ba. Ga mamaki se ji nayi yace
"Baki da hankali Halima? Robar hypo ɗin kika ƙarar data abin wanke wanke kiji yanda warin ya cika ko
ina yana neman bugar da mutane, me ma kika wanke?"
"Ni fa ban ce ka siyo da kifi ba gashi nan ƙarnin sa duk ya hautsina mun ya saka ni amai" na ƙarasa ina
toshe baki na dan sunan kifin dana faɗa yasa naji kamar lokacin nake shaƙar ƙarnin sa. Ji nayi dagaske
amai na taho mun dan haka na ture shi daga jikin sink na shiga kwararawa. Yana tsaye har na gama na
wanke fuskata na jingina da cabinet ina mayar da numfashi. Kamar ma abun be dame shi ba ba sannu
balle yaji ba'asin aman kawai ya matsa gaban gas ya buɗe tukunyar miya, se ya juyo ya kalle ni yana
nuna mun tukunyar yace
"Ina naman cikin miyar nan?"
"Na cinye" na bashi amsa ina barin kitchen ɗin dan aman da na sake yi duk ya taso mun da wasu ciwuka
da ban gane musu ba. Ƙafafu na kamar ana sare su ji nake kamar zan faɗi. "Naya yanka biyar ɗin kika
cinye ke kaɗai saboda ke kika siya?" Ya faɗa yana sakin murfin tukunyar, ta gefen ido na kalle shi cikin
ƙunƙuni nace
"Ni dai kar ka fasa mun murfin tukunya" na ƙarasa ina ficewa daga kitchen ɗin. Ina kwanciya kan kujera
ya iso kaina yana huci kamar wani kumurci yace
"Ni ba abin da nace dan Allah ka ƙyale ni naji da kaina" na faɗa ina riƙe ciki na da ya fara murɗa mun.
Tsaye yayi yana kallo na ina murƙususu dan ciwo sosai ciki na ya tayar mun tun ina kan kujera se da na
sauka ƙasa na durƙushe, ganin yanda nake juya kai ina kiran sunan Allah yasa ya rage tsayi yana
tambayar menene, ban iya ce masa komai ba se ciki na dana nuna masa. Ɗaki ya wuce ina jin sa yana
cewa
"Kin ci rabon ki da ba naki ba ai dole kiyi ciwon ciki" hawayen azaba haɗi da takaici suka zubo mun lokaci
ɗaya. Saboda na ci nama shine ze zama sanadin ciwon ciki se kace wadda ta ci na sata ko Allah ya isa?
Farin magani ya dawo dashi a hannun sa ya durƙusa gaba na ya buɗe bayan ya jijjiga ya tsiyaya mun a
murfi. Cikin ikon Allah ina shan maganin ciwon ya fara lafamun, a nan ƙasan tiles ɗin bacci ya kwashe ni,
ban san ya Bilal ya ƙare da sahur ba ni dai na farka naga ga gari ya waye tangarau. Se da na watsa ruwa
nayi sallah ina ji na duk ba yanda na saba ba. Jiki na ba ƙarfi sam ga marata dake murɗa lokaci lokaci se
na kawo ko period ne yake shirin zuwar mun. Dana shiga wanka ma se da nayi amai dan haka na haƙura
da zancen azumin ranar kawai. Har na shirya na sake fitowa falon banji motsin Bilal ba hakan yasa na fita
na leƙa part ɗin sa, ta window falo na hango shi yana bacci akan kujera se na koma cikin gida kawai. Ina
jin yunwa amma sam bana jin cin komai, a haka na ja Carpet ɗin dana naɗe na fita dashi na share wajen
nayi mopping sannan na kwanta ina jin duniyar na hautsina mun.
Bilal be fito ba se gurin sha biyu saura lokacin har na gama murƙususun ciwo har ya sake ni na miƙe na
shiga kitchen ina tafasa indomie da dafaffen ƙwai. Ina tsaye jikin cabinet ina jiran indomin ta ƙarasa na
sauke ya shiga kitchen ɗin, muka haɗa ido se naga kamar harara ta yayi kafin ya mayar da idon sa kan
bowl ɗin dana saka ƙwai biyun dana dafa ina jira su huce na ɓare. Gaban deep freezer ya wuce ya buɗe
ya shiga ɗaga kayan ciki ni dai na wuce na kashe gas ganin indomin ta mun yanda nake so. A fusace ya
ɗago ya kalle ni yace
"Ina kifin dana siyo jiya?"
Nayi kamar banji ba ina ɓare ƙwai na se da ya maimaita da lafazin daya fi na farko kauri kafin na dakata
na juya gaba ɗaya ina kallon sa nace
"Na zuba shi a sink zan wanke ƙarnin sa ya tayar mun da zuciya kafin na kar ga matsawa amai ya ƙwace
kuma babu yanda za ayi ya ciyu shi yasa na zubar dashi"
"Kika zubar saboda kin yi hauka ko me? Ce miki nayi sato shi nayi ko a ƙasa na tsunto da zaki yi amai akai
ki zubar saboda baki san zafin kuɗi ba Halima?" Ya faɗa fuskar sa na amayar da fushin dake cikin zuciyar
sa. Yaci gaba da cewa
"Tsabar baki da mutunchi baki san darajar kuɗi ba shine zakiyi amai akan abin da za a ci kuma ba kunya
ba tsoron Allah kike gaya mun kin zubar kifin dubu biyun kina zuba mun a shara, to wlh idan kin saba
ɓarnatar da abinci a gidan ku saboda sangarta ba a ce miki komai ni a nan ba zan ɗauka ba dan ba sato
kuɗin nake ba da gumi na nake neman su. Kin haramta kifi kin zubar sannan kin mun asarar hypo roba
guda da abun wanke wanke to wlh bazan ɗauka ba ki kuma kwana da sanin se kinyi nadamar abin da
kika yi" ya ja tsaki kamar ze katse harshen sa kafin ya buga murfin freezer ya wuce ni yana cewa
"Aikin banza kawai mace babu abinda ta sani se taci ta kwanta ta ɓarnatar maka da abinci".
*(Based on true life event, some parts are fictional to spice up the story)*
*Wattpad @MaryamahMrsAm*
*Ban yarda wani ko wata ya juya mun labari ta kowacce siga ba tare da izini na ba*
*Kuɗin karatu yana wakiltar mutum ɗaya ne, kiji tsoron Allah karki ɗauki hakkina ta hanyar fitar mun da
littafi*
*KURA A RUMBU littafin kuɗi ne, a biya naira 800, biya a asusun*
*1840175439*
*Access bank*
*Page 13*
Kasaƙe nayi ina kallon sa har ya fice daga kitchen ɗin lokaci ɗaya jiki na yayi sanyi lanƙwas kamar an
watsa mun ruwan sanyi. A hankali na ajiye bowl ɗin hannu na na dafe drawer baya na da hannu biyu jin
jiri na neman ɗiba ta. "Sam wannan ba Bilal bane, ba halin sa bane akwai wani abu da yake damun sa
tabbas" abin da na furta a fili kenan cikin son ƙarfafawa kaina guiwa da kuma bawa kaina tabbacin ba
cikin sani Bilal yayi mun wannan tozarcin ba. Nafi minti biyar kafin na tattara ƙarfin daya rage mun na bi
bayansa zuciyata na ƙarfafa ni da naje naji me ya same shi? A bakin ƙofar ɗakin na ci burki na kasa shiga
saboda yanda zuciya ta take bugawa fat fat. Ba zan iya jurewa ya sake gaya mun wasu maganganun ba
zuciya ta zata iya bugawa amma kuma ina da buƙatar sanin me yake damun sa? Waye ya tunzuro shi
haka ko ma im ce wasu shaiɗanu ne suka shafe shi?.
Ina kama hannun ƙofar aka buɗe daga ciki, mukayi ido huɗu ya jefe ni da kallon da na kasa mantawa
kafin ya ja tsaki kamar ze ture ni ya fice, daga in da nake na jiyo yanda ya buga ƙofar get. A nan gurin na
sulale na zura kaina cikin cinyoyi na se dai hawaye ko ɗis be zubo mun ba zuciyata ce kaɗai take suya
wani abu me ɗaci da maƙaƙi na yawo cikin maƙoshi na. Nafi minti ashirin a zaune a gurin kamar ma ba a
duniyar nake ba, kalaman Bilal na mun amsa kuwwa tamkar a lokacin yake faɗa mun su. Jin ana kiran
wayata a karo na uku yasa na yunƙura daƙyar na tashi, Mama ce take kira na, na san har idan na amsa
tilas zata fahimci halin da nake ciki hakan yasa na mayar da wayar na ajiye na kwanta akan kujera.
A nan na wuni sur sallah kaɗai ke tayar dani gaba ɗaya ji nayi duniyar tayi mun duhu komai ya haɗe mun
na kuma rasa ta ina zan fara gyarota, wa zan kira na faɗa masa matsala ta? Ban san me yasa sam naji na
kasa kiran Anty Labiba ba dukda ita ta fara zuwar mun se kuma Hansa'u amma duk su biyu dana tuna
basa son Bilal se naji be kamata na kai kuka na kan abin da ya shafe su gurin sa ba daga ƙarshe na yanke
shawarar na shanye ɓacin raina ni kaɗai tun da dama cikin nasihohin da aka mun an jaddada mun
muhimmancin riƙe sirrin gidan aure na.
Rashin cin abinci da ɓacin ran da nake ciki suka haifar mun da ciwon kai da ciwon ciki me tsanani. Shida
saura Bilal ya dawo, sama sama nake jiyo muryar sa da alama waya yakeyi yana ta raha amma dana ɗaga
kai bayan daya turo ƙofa ya shigo gani nayi ya haɗe rai tamkar be taɓa dariya a rayuwar sa ba. Tsayuwa
yayi a kaina yana kallo na, nayi kamar bacci nakeyi ina jin sa ya saki tsaki kafin ya wuce yana ƙunƙuni se
na bishi da kallo hawaye na gangarowa ta gefen ido na, kitchen ya shige, daga can naji ya fara kiran suna
na ban amsa ba se gyara kwanciya da nayi na bada baya ina goge hawayen da suka ɓalle mun.
"Wato baki ma ɗora mun abin shan ruwa ba ko? Na lura nema na kike yi da fiti na Halima. Iya asarar da
kika mun bata ishe ki ha yanzu kuma hora ni kike so kiyi da yunwa ko? shikenan kiyi yanda kika so" ya
faɗa ni dai ban juyo ba ya wuce ɗaki be ɗauki lokaci ba ya fito ya sake shiga kitchen ina jin sa yana haɗa
tukwane yana gwarawa ƙarar tana shigar mun har tsakiyar kai. Ina kwance a gurin aka kira sallah na
yunƙura na tashi da ƙyar ina dafe da kaina ga ciki na daya fara yamutsawa dalilin ƙamshin suyar ƙwai
daya fara tasowa daga kitchen ɗin.
A hankali na kalli Bilal ya fito daga kitchen da plate me ɗauke da ƙwai da cup ɗin shayi. Kan center table
ya ajiye su ya wuce cikin ɗaki, ganin ƙwan da ƙamshin daya sake kusanto ni ya hautsina mun zuciya. Da
ƙarfin da ban san in da na same shi ba na miƙe muka ci karo a bakin ƙofa yana shirin fitowa ni kuma zan
shiga ganin yanda na tafi zan kifa ya ruƙoni kafin na ƙwace aman da nake dannewa ya fi ƙarfi na na shiga
kwarara masa a jiki. Irin kallon da yake mun kaɗai naji gara ya rufe ni da masifa ko ya doke ni yafi
wannan kallon. A ƙasa na kwanta ina juyi cikin aman saboda wani irin yanayi da nake ji da bazan iya
fasaltawa ba. Bansan ko imani ne ya shige shi tausayi na ya kama shi ba ya tsugunna dukda kallon da
yake mun wanda daga baya na fahimci na ƙyamar ƙazantar aman da nayi ne be bar fuskar sa ba ya shiga
kiran sunana yana tambayata menene. Da hannu na nuna masa kaina da ciki na, tashi yayi ya cire rigar
jikin sa ya ajiye a gurin sannan ya ɗauke ni, se da ya ɗauraye mun jiki da ruwan ɗumin da nake jin kamar
ruwan dalma yake watsamun take zazzaɓi ya rufe ni.
Yana tsaki kamar ze katse harshen sa ya gyara gurin aman tsaf ya goge ya fesa room freshener sannan ya
ɗauraye kayan sa da nawa da suka ɓaci kafin ya gama bacci ya kwashe ni ban zan ya ya ƙare ba se cikin
dare na farka yunwa na neman yin ajali na. A kan center table na samu sauran jallop ɗin shinkafa daya ci
ya rage na cinye na haɗa da sauran wacce na gani a tukunya sannan na fara gane kaina. Ƙarfe uku da
kwata lokacin, a falo nayi sallar magriba da isha'i da banyi ba ina lazumi Bilal ya fito daga ɗaya ɗakin.
Kallo ɗaya ya mun ya wuce kitchen, zuciya ta ta shigan bugawa ina jira na ji ya fara masifar abincin da
naci amma naji shiru se gashi ya fito da cup da ruwan zafi ya haɗa tea a kan dining ya zauna yasha da
ƙaton bread ɗin sa bayan ya gama ya koma ɗaki ya canzo kayan jikin sa ba tare da yayi mun magana ba
ya tayar da sallah nan kusa da in da nake.
Ina zaune gurin ya dawo daga sallar asuba, kan kujera ya kwanta ya harɗe hannunsa biyu bayan kansa
yana kallon sama, na shafa addu'a na gyara zama ina kallon sa kamar me tsoro na shiga gaishe shi. Nayi
mamakin yanda ya amsa ba yabo ba fallasa har ya tambaye ni jiki na na sanar masa babu abunda yake
damu na a lokacin.
"Naga dankali da doya da wasu kaya a ɗakin can" ya faɗa bayan daya tashi zaune, kaina na ƙasa na ce
"Shine baki faɗa mun ba?" Ya faɗa cikin sautin daya fi na farko taushi. Se na ɗaga kai na kalle shi
maganganun daya yaɓa mun jiya suka shiga dawo mun take ido na ya ciko da hawaye na sadda kaina
ƙasa ba tare da nace komai ba.
"Zan kwanta, idan ƙarfe bakwai tayi ban farka ba ki tashe ni" ya faɗa yana komawa cikin kujerar ya
kwanta. Hakan da yayi ya nuna mun ya huce daga fushin jiyan, amma ni kuma cin mutunchin da ya mun
fa? Shikenan a ganin sa komai ya wuce?
"Amma Bilal abinda ka mun jiya kana ganin ka kyauta?" Na faɗa murya ta na karyewa. Se ya tashi zaune
yana kallo na yace
"Kin sani bana son dawo da abinda ya wuce karki ɓata mun rai Halima" daga haka ya miƙe ya shige ɗaki
ya barni a zaune na rakashi da ido. Duk yanda naso na ƙarfafi kaina na nunawa Bilal jin zafin abin da ya
mun na kasa, ganin ya sakko kawai se na lallashi zuciyata nima na haƙura. A haka azumi ya fara ja har an
kai na goma. Daƙyar nayi guda huɗu saboda yanda lafiya tayi mun ƙaranci. Ciwon mara da ciwon kai
suke damuna ga amai ba dama na shaƙi ƙamshin abinci ko banyi aman ba nayi ta kakari kenan. Munje
chemist da Bilal suka rubutamun magungunan malaria harda allura ta kwana uku an mun amma banji
sauƙi ba. Ganin lokacin al'ada ta ya wuce yasa na fara zargin ko ciki ne dani.
Ranar da aka kai azumi na goma tun yamma dama yace mun idan an sha ruwa zamu je gidan su mu
gaishe su haka yasa dana tashi yin abin shan ruwa nayi da ɗan yawa zan ɗibar wa Hajjansu. A raina na
raya se yayi magana dan kullum ne se yayi mitar ina dafa abinci yana yin yawa da zarar yaga kwanuka ze
fara buɗe buɗe yana mitar duk cikin mu zamu cinye wannan a hakan ma ba wani abin kirki nakeyi ba
saboda bana jin daɗi baya wuce abu biyu me dan sauƙin saraffawa na buɗa baki se kuma abinci da za'a
sake ci da kuma lokacin sahur amma haka ze yi ta surutun nayi da yawa kuma a hakan ze cinye tas har ya
ringa cewa beyi sahur me kyau ba. Dama ƙiri ƙiri ya hanani yin kunu da ƙosai na sadakar da nayi niyya
wai da me zanji?
A kwando na jera kwanukan abincin dana zuba, ina jin kamar zazzaɓi ze rufe ni amma na daure, a sabon
mashin ɗin daya buɗe shekaran jiya muka fita. Tun lokacin biki yace mun ya siyar da mashin ɗin sa se
yanzu ya sake siyan wani. Muna tafe muna hira gwanin sha'awa har muka isa gidan a raina nayi gulmar
yanda bece komai ba daya ga basket ɗin abincin,
kamar Hajiyar su zata goya ni haka ta ringa nan nan da ni. Taji daɗin abincin dana kai mata, ina zaune ta
soya mun ƙosai tace tasan da yawan mutane sun fi son ƙosai da an sauke daga mai shiyasa da yace zamu
zo ta ajiye ƙullin. Sosai kuwa naci ƙosan da kunun tsakiya a nan take gaya mun ai geron da waken ma
daga gidan mu aka kawo musu harda buhun shinkafa dana sugar da pastar mangyaɗa. Se gurin goma
saura muka bar gidan, a hanya naga gurin gasa tsire tun daga nesa naji raina ya biya dan haka nace masa
dan Allah ya tsaya ya mu siya ba musu kuwa ya tsaya ya siya muka wuce gida.
A haka aka ƙara azumi biyar, tun washe garin da muka je gidan su nake jira naji yace na shirya muje
gaida nawa iyayen amma shiru. Har Mama se da ta gaji ta mun magana akan yaushe zamu zo? Na ce
mata bani da lafiya ne amma zamu zo, Allah sarki uwa washe garin da mukayi maganar kuwa se ga Imam
da Amira da Nabila yar ƙanwar Abbanmu Anty Surayya da tazo hutu gidan Mama tace su zo su dubani.
Ran da aka kai azumi na sha biyar ɗin tun asuba na masa zancen se yaushe zamu je gidan mu ne?
"Akwai abin da nake jira ne kin ga ai ba daɗi muje musu hannu haka babu wata tsaraba" amsar daya
bani kenan. Se nace masa
"Yanzu ita Hajja ba haka muka je muka gaishe ta ba bamu kai mata komai ba suma gaisuwa ce ai ba wani
abu aka ce dole se an kawo ba". Kamar baze yarda ba har na fitar da rai kuma bayan la'asar ina ƙoƙarin
ɗora abin shan ruwa yace na shirya kawai ya kaini gidan. Sosai naji daɗi, da muka je be shiga ba ya ce
mun se ya dawo ɗauka ta tukunna yanzu sauri yake ana jiran sa a wani guri. Mama na kitchen da Nabila
suna aiki ta ringa kallo na da mamaki na rungumeta cikin jin daɗin ganin ta dan rabo na da gidan tun
zuwan da nayi akan registration ɗin NYSC. Abba kansa se da ya tsokane ni yace dama gobe suke shirin
zuwa ban haƙuri ace azumi har ya raba basu ga ido na ba gara suzo suji wane laifi sukayi haka.
"Haka ne, amma muga juna ɗin ma ai da daɗi ko Halimatu? Ko da yake ke fa tunda kika samu Bilal
shikenan kika manta da kowa" Abban ya sake tsokanota se kawai na tashi na koma ɗaki dan duk se naji
ban kyauta ba na kuma ƙudire a raina zan gyara hakan ba zata sake faruwa ba. Cikin farin ciki nasha ruwa
da yan uwana, can ƙasan raina ina tunanin ko Bilal ya ci abinci? Ko dame ya karya azumin sa oho? Ana
idar da sallar asham Mu'azzam yace mun
"Ga matsolon mijinki can a waje". Na galla masa harara kawai ba tare da nace komai ba. Tare suka shigo
da Abba, a can falon ya zauna bayan sun gaisa da Mama na shiga kitchen na haɗa masa abinci na bawa
Amirah ta kai masa, se da ya gama kafin mukayi sallama muka tafi kunya duk ta dabaibayeni jin Mama ta
fahimci ina da ciki har tana tambayata wata nawa ne nace mata ban sani ba tun da bamu je asibiti ba pt
test kawai nayi naga positive dan ko Bilal ma ban gayawa ba.
"Ya dai kamata kije gidan Labiba tunda kalar naki hankalin be nuna miki ba har yanzu" Mama ta faɗa
sanda ta rako ni bakin ƙofa. Tunda nayi aure ko sau ɗaya banje gidan Anty Labiba ba ita ma kuma tun
washe garin da aka kaini bata sake komawa ba wata tara kenan muna waya muna chat. Har ga Allah
kawai ina jin kunyar abin da na mata akan zancen aure na da Bilal ne, duk da ko a fuska bata nuna mun
komai ba amma nasan Anty Labibar da na sani babu yanda za'a yi nayi aure ta ɗauki wata tara bata tako
gida na ba har idan ba da wani abu data riƙe a ranta ba ni kuma bana son naje ta tayar da maganar
shiyasa kawai nake gudun zuwa gidan nata. Kuma muna haɗuwa a gida yaranta ma kusan duk sanda su
Amira zasuje mun tare su ke zuwa dasu.
Amsawa Mama nayi da zanje in sha Allah na wuce tana sake jaddada mun na tabbata naje asibiti bata
son sakarci. Washe gari nayiwa Bilal zancen zanje gidan Anty Labiba, be musa yanda ya saba ba yace duk
sanda na shirya na je, take na kirata wayarta a kashe ina hawa whatsapp na ganta online dan haka na ce
mata gobe zanzo in Allah ya kaimu. Amsar data bani
"Bana nan" na ringa juya maganar, bata ma tambayi ƙarfe nawa zanzo ba ko wani abu kawai tace bata
nan. Da take cewa in har na auri Bilal zata yanke zumunta dani ashe dagaske take kenan? Take shaiɗan
ya shiga mun famfo, na watsa hannye a fili nace
"Kin huta ai. Bilal dai da bakya ƙaunar gani na dashi shi ɗin Allah ya zaɓa mun muyi rayuwa tare se
haƙuri". Shikenan naci gaba da sabgogina. Ganin har an kai azumi na ashirin da uku Bilal be bani ko
ƙyalle da sunan na siyi kayan sallah ba na cire rai da zeyi mun ban kuma tambaye shi ba saboda hidimar
daya zo masa katsahan ƙanwar sa da akayi bikin mu tare ta haihu haihuwar kuma tazo mata da matsala
ƙarshe se CS aka mata mijin dake bashi da mutunchi tunda ta kwana ta wuni tana labor washe garin ya
tattaro ta ya kawo ta gida su suka yi duk wata ɗawainiyar asibiti har aka ciro mata babyn kwana uku
kenan ko zuwa ganin su beyi ba. Bilal ne ya biya kuɗin aikin yayyen sa mata kuma suka haɗa mata kayan
barka da sauran abubuwan buƙata da suka tashi suka yiwa yaron huɗu ba da sunan Babban Yayansu da
suke uba ɗaya shine ya bada ragon da aka yanka masa.
Cikin kuɗin da Abba ya tura mun tun washe garin da naje gida na siyi lace guda biyu na haɗa da atamfofi
biyu cikin na lefe da ban taɓa komai a ciki ba na bada ɗinki. Na san Mama bata san ya bani kuɗin ba dan
haka ni ma ban mata zancen ba, da sauran kuɗin nayi sauran buƙatun da nake dasu ciki harda zuwa
asibiti na buɗe file na anti natal dan da na yiwa Bilal magana ina so naje asibiti cewa yayi me zanje yi
bayan ga magunguna nan an bani kuma na samu sauƙi tun da a zahiri babu abinda yake damu na banda
amai se zazzaɓin dare gari na waye wa kuma zan shiga sabgogi na idan naji garau nayi azumi idan naji
bazan iya ba na sauke. Saboda ina so nayi masa ba zata akan cikin se kawai nace masa ulcer se ta tasar
mun ya siyo mun Omeprazole da gestid a chemist yace na ringa sha.
Cikin ikon Allah azumi ya ƙare anyi sanarwar ganin watan sallah ya tsaya, kasancewar sallah ta ta farko a
gidan aure yasa naji ina sha'awar nayi abincin sallah nima yanda naga anayi. Dake tunda Fadila ta haihu
Bilal suke ta zirga zirga tsakanin gida da asibiti wata ran se tara yake dawowa yau ɗin ma yana gida aka
kira shi jikin yaron ya rikice dake da jundice aka haife shi shine ya fita suka mayar dashi asibiti. Har
mamaki nakeyi yanda ya damu sosai da lafiyar ƙanwar tasa ba kuma ya ƙyashin kashe kuɗi, da na
tambaye shi ina mijin ta da suke ta ɗawainiya da ita haka ma cewa yayi shi ba ta mijinta su keyi yanzu ba
dan idan ta mutu su suke da asara ba mijin ba jira sukeyi ma a ƙare azumi suyi ƙarar sa ya saketa ba zata
koma ba. Ban tsawwala da jin dalili ba nace Allah ya rufa asiri kawai muka bar zancen.
Dake muna da kaji da jan nama ba'a fi kwana uku daya siyo su ba kajin guda huɗu ne manya manya se
naman shima da ɗan auki se na ɗibi kaji uku na samu yaro ya yiwo mun cefanen miyar taushe na jiƙa
farar shinkafa akan zanyi waina da sinasir. Tun daren na haɗa miyar ya rage ganye kawai zan zuba na
saka ta a freezer na kwaɓa meat pie shima na haɗa na deɓi kaɗan na soyawa Bilal na saka sauran a
fridge. Ina da samosa da spring rolls dama nace se na haɗa da safen na soya su tare. Na gaji lilis se goma
saura na gama gyaran gida da wanke wanken abubuwan dana ɓata dan har zoɓo na haɗa, ina wanka
Bilal ya dawo daga ganin fuskar sa na san babu lafiya nan yake sanar mun ɗan Fadila ne ya rasu. Na taya
su jimami har nace zan kira ta lokacin yace na bari se da safe, haka nan muka kwana yanda Bilal ya damu
kamar ɗan cikin sa ya rasa. Na ringa ayyana yanda zeyi farin ciki idan ya san ya kusa samun nasa ɗan
shima.
Washe garin da wuri ya shirya dan zasuyi jana'izar yaron kafin lokacin sallar idi. Nima kafin ƙarfe tara na
gama abincin sallah na, na zuba na gidanmu harda na Anty Labiba na ware na gidan su Bilal sannan na
fitar da na maƙwafta. Sayyadi almajirin Maman Yusuf na bawa kuɗin Adaidaita ya kai na gidan mu dan ya
san gidan ina aiken sa, se gurin sha ɗaya Bilal ya dawo tare da abokanan sa su uku. A falon sa na aje
musu abinci suka ci se da akayi azahar suka tafi yace mun na shrya daya dawo daga sallah zamu tafi can
gidan. Tsaf naci kwalliya da ɗaya daga cikin laces ɗin dana ɗinka. Yaron cikin jikina yasa fatata ta goge
nayi shar dani ga yar kiɓar dana ƙara ta sake fito da albarkatun jikina. Hijab daya dace da kayan na saka
dan kar suce suna zaman makoki ni kuma nayo kwalliya. Yana shigowa ya ɗaga ni ya rungumeni, se da
yayi kissing goshi na ya haɗe hanci na da nasa yana kallon cikin ido na yace
"Kin san me yasa name ƙara sonki kullum?" Na girgiza masa kai alamar aa, se ya maida kaina ƙirjin sa
yace
"Baki taɓa bani kunya ba. Duk sanda zan cika baki akanki se kin aikata fiye da yanda na kwarzantaki.
Kasada kawai nayi da su Mansur suka ce zasu biyo ni suci girkin amarya. Nasan ba muyi zancen za kiyi
abincin sallah ba amma sanin da nayi tunani na dana Halims a tare suke tafiya banyi shakku akan zaki
fitar dani kunya ba se gashi harda snacks. Ke dai Allah yayi miki albarka ya barmu tare kinji my Halims"
ya ƙarasa yana brushing lips ɗin sa akan nawa. Na ringa murmushi kamar wawuya jin ya yaba abinda
nayi. Se da muka ɓata lokaci a nahiyar soyayya dan se da ta kaimu da canza wanka kafin mukayi sallar
la'asar mukayi sabon shirin fita. Cewa yayi cikin sa ya zazzage wai dama ba wani abin kirki yaci ba duk su
suka cinye. Na sako masa sinasir guda ɗaya yana ci yace
"Wato yarinyar nan kuɗi ne dake, kikayi ɗinki sallah Allah sarki ni da tsohon kaya naje idi ga kuma
daƙwalen kaji kin zuba mana a miya ai se ki bani barka da sallah kuma na samu na zuba mai a mashin".
Se da nayi far da ido kafin nace
"Ka so tsokana dai kawai da kayan da kajin naga duk kai ka siya, ni sarrafa su kawai nayi". Be sake
magana ba daga yanda naga fuskar sa ta canza lokaci ɗaya kuma nasha jinin jiki na se dai duk son na
hakaito me ze kawo ɓacin ran sa lokaci ɗaya haka na rasa se kawai na kama kaina nayi shiru nima. Sanda
muka isa gidan su lokacin Abubakar ya dawo shima ya sauke kwanukan abincin da na bashi ya yiwo
musu gaba dashi,
"Duka kajin kika dafa kenan?" Ya faɗa a saitin kunne na daidai sanda Hajja ta buɗe flask ɗin miya.
*(Based on true life event, some parts are fictional to spice up the story)*
*Wattpad @MaryamahMrsAm*
*Ban yarda wani ko wata ya juya mun labari ta kowacce siga ba tare da izini na ba*
*Kuɗin karatu yana wakiltar mutum ɗaya ne, kiji tsoron Allah karki ɗauki hakkina ta hanyar fitar mun da
littafi*
*KURA A RUMBU littafin kuɗi ne, a biya naira 800, biya a asusun*
*1840175439*
*Access bank*
*PAGE 14*
Afuwan kun jini shiru. Wadanda suke cikin comment section group na bayar da uzuri.
A ɗarare na ƙarasa yinin cike da taraddadin yanda zamu kwashe da Bilal idan mun koma gida. Se da akayi
magriba ya turo mun text a waya in fito mu tafi. Jikina ya sake yin sanyi, haka nayi sallama da Hajja da
sauran yan gidan su tana ta mun godiyar abin arziƙi da tace an kawo musu daga gidan mu cikin azumi ga
kuma turmin atamfa dana kai mata dama yanzu kuma na kaiwa mejegon itama Atamfa da wani lace
cikin ɗinkunan biki da aka mun sakawata ɗaya ranar naje gidan dashi tace ya mata kyau ni na manta ma
da munyi maganar se bayan data haihun ta roƙe ni in bata tayi fitar suna dashi.
Tare da Nasir na same su tsaye jikin motar Nasir ɗin, muka gaisa a mutunche Bilal ya shiga mzaunin gaba
hakan yasa na fahimci Nasir ɗin ne ze sauke mu gida. A hanya suna ta hira da zarar Nasir ya sako ni se
naji Bilal ya ɗauke wuta gane hakan yasa ko da Nasir ɗin ya sake tsomani cikin maganar nayi kamar ban ji
shi ba. Ni kaɗai na sauka ya miƙa mun muƙulli ba tare da ya kalle ni ba na wuce ciki ina tunanin ina kuma
zasu je kuma har se yaushe ze dawo amma babu fuskar da zan iya tambayar sa. Be shigo gidan ba se
goma da kwata, ina zaune a falo naji tsayuwar mashin ɗin sa, ban motsa ba nasan cikin biyu ko dai ya
buga ko ya kirani a waya tun da be fita da key ba ilai ko se ga kiran sa a maimakon yanda na saba daya
kira in tashi naje na buɗe Get ɗin tunda nasan kiran na menene se kawai na amsa wayar.
Da murya kamar me bacci nayi sallama, ina jin sa yaja tsaki kafin yace
"Zo ki buɗe" daga nan ya katse wayar. Se da na koma ɗaki na ƙara turare kamar me fita zance sannan na
saka hijab na fita. Ban san na ƙarawa kaina laifi ba, ina buɗe ƙofar ƙiris ya rage ya ture ni da tayar mashin
ɗin ya shigo ciki, se da na kulle ƙofar na bi bayansa yana kafe mashin ɗin ya juyo kamar ze rufe ni da
duka yana cewa
"Tsabar kin mayar dani ɗan iska na kiraki amma kiyi zamanki se yanzu kika ga damar zuwa ki buɗe kofar
ko?"
Kallon sa kawai nayi takamaimai ni ban fahimci dalilin wannan hasalar tasa ba. Fuuu ya wuce ɗakin sa,
har na bi shi se kuma na juya na shige falo ina ƙarfafa kaina akan bazan bi ta kansa ba tun da dai ba wani
abu na masa ba. Sinasir ɗin dana ɗumama na saka masa guda ɗaya da yar miya a bowl na haɗa da tea
dana rigada na dafa masa na ɗora komai a try harda ruwa na wuce ɗakin nasa. Ban same shi a falo ba, se
na aje kayan na wuce cikin ɗakin ƙarar saukar ruwa da kayan daya cire dake kan gado yasa na gane
wanka yake yi dan haka na koma falon na zauna. Kusan minti goma ya fito ya shirya cikin jallabiyya yana
ta zuba ƙamshi. Bilal ba dai tsafta da gayu ba, komai sanyi ko ruwa baze kwanta ba tare da yayi wanka
ba. Na kan tuna Anty Labiba da take cewa duk buge ne gayun nasa waya sani ma ko tsaka tsami yakeyi
ya fesa turare gashi dana zauna dashi na tabbatar da tsaftar tasa ta gaske ce in dai ɓangaren tsafta ne na
sarawa Bilal abinda kuma yake ƙarawa abin armashi bashi da son jiki. Yanda baya son ƙazanta baya taɓa
bari in da yake wani abu ya kasance da datti ba kuma ya jiran wani ya masa da ya ga guri be masa yanda
yake so ba ze tashi ya gyara.
Kamar ma be lura da ni ba ya zauna kan kujera yana wani cin magani, nayi murmushi na matsa in da na
ajiye kayan abincin ina cewa
"Ga abinci". Ban damu da shirun da yayi ba dan idan ba ze ci ba nasan ze ce Aa, na buɗe miyar na tura
masa try ɗin gaban sa, kwanon miyar ya ɗauka ya kalla kafin ya watsa mun wani kallo yana cewa
"Pieces biyu ya rage na saka maka ɗaya na aje ɗaya zan ci da safe" na bashi amsa ina tsiyaya masa shayi
a kofi. Ko da ban ɗaga kai na kalle shi ba jiki na ya bani kallo na yake yi ko ma na ce harara ta. Ina jin sa
yayi ƙwafa, se lokacin na ɗaga kai na kalle shi duk kuma yanda naso da in share kar na tanka masa na
kasa, tsautsayi yasa na furta
"Ko in ɗakko maka ne naji kaja ƙwafa karma naci nayi amai tunda ba'a bani ba".
Ban san Bilal ya ƙware a iya sharri ba se da ya dire kwanon miyar hannun sa ya miƙe tsaye yana nuna
kansa yace
Ban san sanda na miƙe ba nima na dafe ƙirji tare da fito da idanu nace
"Ni kika cewa maye ko? Zaki san ni kika alaƙanta da maita Halima". Gaba ɗaya se hankali na ya
dugunzuma, babu alamar cewa wasa yakeyi akan fuskar sa ko furucin sa duk ma ba wannan ba tsakani
da Allah a yaushe na alaƙan ta shi da maita? Idan ma kuma nayi hakan ai ya sani wasa ne be kamata ace
ya fusata ba balle ma kuma duk yanda nake wasa da koma wane akwai irin kalaman da bana taɓa
kuskuren furta su.
Bin bayan sa nayi, yana kwance kan gado ya daga kansa da hannayen sa biyu yana kallon ceiling na shiga
da ƙaramar sallama kamar mara gaskiya. Daga bakin gadon na tsugunna kaina a ƙasa na rasa me zance
masa. In dai ba dama da wani abu a ran Bilal ba be kamata ace ɗan ƙaramin abu haka ya kawo yamutsi a
cikin daren nan ba. Murya ba amo na kira sunan sa, be amsa ba na sake maimaitawa har sau uku still
yayi banza da ni se kawai na kife kaina a kan gadon na fashe da kukan ƙarya, Anty Labiba tana gaya mun
da yawan maza basa son kuka kuma yana daga cikin abin da yafi saurin karya lagon su yawancin maza
basa iya jure ganin matar su tana kuka ko da kuwa ace na rashin gaskiya ne. Na rigada nasan ni nawa
kukan bashi da tasiri a gurin Bilal gwaji kawai na sakeyi ko Allah ze saka yau hakan yayi tasiri ilai kuwa se
ji nayi ya ja tsaki me ƙarfi da har se da na dakata daga dramar da nakeyi, ina kallon sa ya fice daga ɗakin
da bargo a hannun sa ya barni a durƙushe ban san lokacin da kukan gaske ya ƙwace mun ba.
Wace irin rayuwa ce haka ace abinda be taka kara ya karya bane ze ringa zama na tashin hankali a gurin
Bilal? Sannan wannan halin ko in kular da yake gwada mun idan yana cikin fushi ban taɓa hasashen
fuskantar sa daga gurin sa ba. Baya cikin alƙawarin daya ɗaukar mun. Ya gaya mun gidan sa ze zame mun
dausayi ne na farin ciki ba akasin haka ba, shikenan nan da laifi na da ba nawa ba se dai shi yayi fushi na
bishi da rarrashi ni baze taɓa dubana ya fahimci tawa damuwar ya kwantar mun da hankali ba?"
Ban san tsawon lokacin dana ɗauka ina kukan ba har bacci ya kwashe ni a gurin. Mun yi dashi akan
washe garin gidan mu zan tafi na wuni dan haka ko da na tashi naga be sauka daga fushin sa ba ban
damu sosai ba tun da gidan zan bari naje in da zan samu farin ciki na gabatar da shagalin sallah ta cikin
nutsuwa. Ni kam idin farko a gidan Habibi ya zo mun da mishkila. Ruwan shayi kawai na tun da akwai
sauran sinasir muna kuma d bread. A yanda yake a 360 ɗin nan nasan idan na dafa wani abun zamu sake
haurawa ne ban ma kuma ji sha'awar cin komai ɗin ba dan haka kafin ƙarfe goma na gama shiri na tsaf.
Ban zaci ze ci abin karin dana ajiye masa ba se da na fito naga ya cinye harda sauran kazar dana ɗumama
na aje masa da wadda beci ba jiyan da wadda na aje wa kaina, na tattare kwanukan na ɗauraye, a waya
na kira shi bayan dana duba babu mashin ɗin sa, se da na masa missed calls uku be amsa ba na huɗun na
shiga yayi rejecting se ga text message ya biyo baya yana tambayata menene baze iya amsa waya a in da
yake ba?
Sanar masa nayi da na shirya zan tafi gida ya maido mun amsa da
"Ban yarda ba". Na nanata karan ta rubutun yafi sau uku kafin na ajiye wayar lokaci ɗaya hawaye ya cika
mun ido. Idan nace zan kira Mama a waya na gaya mata na fasa zuwa nasan kukan da nake dannewa ze
fi ƙarfi na dan haka na tura mata da text kawai ina ƙoƙarin kashe wayata dan karma ta kirani kuwa se ga
kiran Abba dole na amsa bayan mun gaisa yake tambaya me yasa bazan zo ba? Se da ma toshe baki na
dan kar kuka ya ƙwace mun kafin na sharara musu ƙaryar ciki na ne ya kama ciwo. Murya cike da alhini
ya shiga tambayar me ya same ni? Munje asibiti toh? Nace masa nasha magani kawai se ya bawa Mama
wayar dake nayi mata ƙorafin ciwon mara da nake yawan yi se tace mun na kwanta na huta ƙila aikin da
nayi jiya ne na jijjiga jiki na idan kuma ciwon ya wuce misali to mu tafi asibi kawai nace mata irin wanda
na sabayi ne kuma nasha maganin da aka bani. Suka ringa jera mun sannu, har mun kashe waya ta sake
kira tace ga Amirah nan zasu zo su taya ni zama toh ko da zan buƙaci wani abu.
Sosai nayi kuka, sallah guda yayi mun wannan rashin mutunchin ya hanani zuwa gidan mu bayan duk sun
saka ran zan je. Gurin sha biyu su Amirah suka zo, Mu'azzam ne ya kawo su amma be shigo ba ya wuce.
Mama ta haɗo su da abinci shinkafa da tuwo se miya stew da Amirah tace yanzu Maman tayi mun ga
soyayyen nama na sa da na kaji tuli harda zoɓo da kunun aya Abba kuma ya basu dubu goma a envelope
su kawo mun barka da sallah. Ban san sanda na fashe da kuka ba. Ranar wunin ɗaki nayi se dai bini bini
Amirah ta leƙa ta tambaye ni ko akwai abin da nake so? Da Abubakar ƙanin Bilal suka zo ma ce mata nayi
kawai ta zuba musu abinci tace musu bacci nake yi. Dab da magriba Mu'azzam yazo ɗaukar su har
sannan kuma banga idon Bilal ba. Bayan na rakasu na dawo na kwanta a falo sun gyara mun ko ina har
abincin da zamu ci da daren ta zuba a kuloli ta ajiye sauran kuma nace su bawa almajirai abin da ze ajiyu
kuma ta saka mun a fridge. Ina kwance wayata tayi ƙara, na zata Bilal ne se da na ɗaga ta naga Anty
Labiba ce.
Yau ɗin har gidan ta naso naje, ina jin muryar ta bayan dana amsa wayar kawai kuka ya ƙwace mun. Tayi
shiru kusan minti biyar ina mata kukan kafin tace mun
"Menene?"
Zuciya ta tana raya mun na gaya mata abin da nake ta dakon sa a zuciya ta ni kaɗai se dai ɗaya ɓangaren
na gargaɗi na da kar nayi hakan. Zata mun dariya tace dama se da ta faɗa be zama lallai ma ta fahimci
damuwata har ra bani mafita ba kawai zata fassara abun ne da hasashen ta na farko akan Bilal, wannan
tunanin yasa na fasa faɗa mata ainihin abin da nayi niyya kawai nace mata bani da lafiya ne.
"Kuma saboda baki sa lafiya se ki ringa irin wannan kukan Halima? Baki san shi kansa kukan bashi da
kyau ga me ciki ba so kike ki saka abin da yake cikin ki a damuwa shima? Bana son sakarci, ya kamata dai
yanzu ace kin girma tunda nan da ɗan lokaci uwa kike shirin zama kina wa yar rashin lafiya kuka yanzu
idan ranar haihuwa tazo kuma se yaya kenan?" Ta faɗa. Se na tsagaita da kukan taci gaba da cewa
"Yanzu da su Amir suka dawo yace mun baki da lafiya, toh kun je asibiti dai ko?"
"Eh mun je ba wani abu bane dama marata ce kawai take ciwo kuma nasha magani ta rage" na bata
amsa, se ta ɗan yi shiru kamar bata yarda ba kafin tace
"Shikenan Allah ya ƙara lafiya. Ki ringa kula da kanki duk abin da kika san ze jigata ki kar kiyi, na ma yiwa
Mama magana tuntuni ko za'a sama miki me aiki tace a bari tunda baki nema ba amma ya kamata
gaskiya saboda ba laifi aikin gidan naki da ɗan yawa kuma yanzu hutu kike buƙata musamman tunda
cikin yazo miki da ciwon mara".
"Aa fa yau ne kawai shima nasan saboda aikin da nayi jiya ne amma ba wani abu nake yi da yawa ba duk
su shara da mopping shi yakeyi da kansa" na faɗa dan na taɓa yiwa Bilal zancen yar aiki yace baya so,
yanzu idan ta kawo ta ya koreta sabuwar gaba ce zata ƙullu tsakanin su. Shiru ta sake yi kafin tace
"Shikenan, Allah y sauwaƙe ya bata lafiya me amfani" daga haka mukayi sallama. Jin an fara kiran sallah
yasa na koma ɗaki nayi, se da na idar da isha'i na sake fitowa har sannan kuma Bilal be dawo ba. Ina
tsaka da cin abincin dana saka kaɗan naji ana buga get. Bilal ya fita da key dan haka nasan bashi bane,
nayi mamakin ganin Anty Labiba da Uncle Saleh bayan dana buɗe ƙofar, ban san sanda na rungume ta
ina dariya ba. Rabon ta da gidan tun ranar da aka kawo mun gara, Uncle Saleh be shiga ba a wajen muka
gaisa yace ze je ya dawo muka shiga tare da Anty. Na rasa me ma zan bata, har ga Allah naji daɗin zuwan
ta over ma. Ganin ina ta kwaso ruwa da lemo na kinkimo kular abinci yasa ta dakatar dani tana cewa
"Ke bafa zama zanyi ba. Nan bayan ku zamu je gaisuwa gidan wani abokin sa maman sa ta rasu a UK
suke to sunyi waya yace yazo Kano amma gobe ze wuce Abuja shine muka taho yanzu fa se da muka
kuje kuma ashe shi kaɗai ne yazo banda matar sa, naga zasu ɓata lokaci da hira shine fa nace ya kawo ni
nan na dubaki kafin su gama mu wuce, su Halima matar Bilal, irin wannan mulmul da kika yi lallai Bilal ya
iya kiwo" ta ƙarasa tana kallo na. Na rufe fuska cikin jin kunya ina cewa
"A shekarar kaɗan ne babu ai, haɗuwa tayi wuya se dai mu gamu a hanya nan kuma ai ba wani ganin ki
nakeyi sosai ba kamar yanzu ko?" Ta faɗa, nasan magana ta gaya mun dan haka nayi murmushi kawai na
shiga tambayar ta su Inayah.
"Dama suna gidan Mama ɗazu shine su Amirah basu taho da su ba?" Na faɗa, se tace
"Aa, se gobe zamu je. Amir ne kawai yaje su je kallon hawa tare da su Mu'azzam". Hira muka shiga yi
gwanin daɗi, har tara da rabi sannan Uncle Saleh ya kirata yace gashi nan ya taho. Se sannan ta tambaye
ni Bilal, tambayar da nake ta addu'ar kar Allah ya buɗi bakinta ta mun dan ban san me zan ce mata ba
sanin tun kafin muyi aure da Bilal duk wanda ya sanshi ze bada shaidar baya yawon dare. Duk in da akayi
sallar isha'i ya shiga gida in dai ba guri na ze je ba.
Ce mata nayi yana can gidan su ai be jima da fita ba suka zo, kallon da ta mun yasa na fahimci bata kama
zancen ba. Ta ƙare mun kallo tace
"Wannan kayan ma tun na kwalliyar safe ne da kikayi baki sake wasu ba". Zan kwaso rantsuwa ta
dakatar dani tace
"Idan kika zauna shashanci kanki zakiwa sagegeduwa. Ba yanzu zaki takaicin barin sa ya koyi yawon dare
ba se nan gaba dan haka tun lokaci be ƙure miki ba ki gyara. Duk irin hirar da zeje yayi a wajen ki tanade
ta ki ringa yi masa a gida ya fiye miki alkhairi idan ba haka ba ke kika sani kina zaune can wasu zasu ringa
cusa masa wasu ra'ayoyi na banza a lalata miki miji".
Tunani maganar ta ta jefa ni, anya babu saka hannun abokai cikin baƙin halayen Bilal da nake cin karo
dasu? Waya sani kam ko a yawon da yake tafiya ake yo masa wasu karatu na banza suna gurbata masa
tunani dan dai ni shaida ce ba haka Bilal ɗin dana sani yake ba tabbas. Buɗe ƙofar da akayi ya dawo dani
daga tunanin da na tafi. Muka haɗa ido da Bilal ya galla mun harara ba tare da yayi ko da sallama ba ya
wuce kitchen yana sakin ƙaramin tsaki. Se da naji ina ma da damar da ƙasa zata tsage na shige ciki na
ɓuya ko kuma ace abin da ya farun yanzu mafarki ne zan tashi naga zuwan Anty Labiba be faru ba.
Kamar me ciwon wuya daƙyar na waiga na kalli Anty Labiba dake danna wayarta se ka rantse bata ji
shigowar Bilal ɗin ba. Nayi ƙasa da kai kamar munafuka ina jan yatsun hannu na, daga kitchen ɗin ya
ƙwalo mun kira. Ƙafafu na sun yi sanyin da bazan iya miƙewa ba, sake kiran yayi se lokacin Anty Labiba ta
ɗaga kai ta kalle ni tace
Ina zaton baƙuwar muryar da yaji se gashi ya fito kamar an jefo shi, yayi turus a bakin ƙofa yana raba ido
kafin yayi ƙasa da kai yana shafa ƙeya kamar mara gaskiya lokaci ɗaya ya lalubo murmushi ya ɗora a
fuskar sa ya nufo in da muke yana cewa
"Mun same mu lafiya? Ya sallah?" Ta faɗa tana miƙewa saboda wayar ta data ɗauki ƙarar shigowar kira.
Bata amsa gaisuwar da ya shiga yi mata ba ta nufi ƙofa tana ce mun
"Allah ya ƙara sauƙi Halima na wuce se da safe" ta fice daga falon. Kamar kazar da ƙwai ya fashewa a ciki
haka na bi bayan ta. Yanzu Allah kaɗai yasan tunanin da zata yi kuma. Dubu goma Uncle Saleh ya bani
barka da sallah, Anty Labiba dai tunda ta zauna a motar ko kallo na bata sake yi ba yaja suka tafi.
A kan kujera na tarar da Bilal ya dafe kai da hannu biyu yana jin motsi na ya miƙe fuska ba yabo ba
fallasa yana kallo na yace
*(Based on true life event, some parts are fictional to spice up the story)*
*Wattpad @MaryamahMrsAm*
*Ban yarda wani ko wata ya juya mun labari ta kowacce siga ba tare da izini na ba*
*Kuɗin karatu yana wakiltar mutum ɗaya ne, kiji tsoron Allah karki ɗauki hakkina ta hanyar fitar mun da
littafi*
*KURA A RUMBU littafin kuɗi ne, a biya naira 800, biya a asusun*
*1840175439*
*Access bank*
*PAGE 15*
Ban tanka masa ba na shiga tattare kayan dake ajiye dana gama kuma na wuce ɗakina na kwanta, nayi
mamakin ganin ya biyo ni, nayi lamo a kan gado ina sauraren sa har ya gama uzure uzurensa na bacci
kafin ya kwanta a baya na tare da jana jikin sa yana cewa
"Nasan ba bacci kike yi ba juyo na baki barka da sallah" nayi masa banza duk yanda yake ya mutsani da
son se na biye masa na dake daya gaji ya sake ni ina jin sa yana tsaki har baccin gaske ya ɗauke ni.
Washe gari nayi zaton ze cigaba da fushin amma naga akasin haka dan tun asuba daya tashi be zauna ba
seda ya share gidan tas yayi mopping ya wanke banɗakuna harda na tsakar gida.
Ina kwance a falo kan carpet in da nayi sallah ya shigo bayan ya gama gyara tsakar gidan, zazzaɓi ne a jiki
na sosai, na lulluɓe har kaina ga iskar hadari dake kaɗawa tasa har karkarwar sanyi nake yi. Sama sama
nake jin sa yana kiran suna na, jin ban amsa ba yasa ya ƙaraso in da nake ya duƙa yana kirana tare da ɗan
bubbuga gefen pillow da nake kwance.
"Dame zaki karya?" Ya tambaye ni, nayi shiru dan baki na yayi mun nauyi kuma kusancin da mukayi
ƙamshin turaren sa dake bugun hanci na duk se ya sake hautsinamun kai baki na har ya fara tara yawu
alamar amai na son taso mun. Miƙewa yayi yana cewa
"Shikenan ai, tun jiya nake binki kina mun wulaƙanci. Fitina kike nema ni kuma ba zakiyi da ni ba" ya
shige kitchen. Se maganar sa ta ma bani dariya, wai yana bina ina masa wulaƙanci Bilal kenan me abin
mamaki. Ƙarfe tara na farka daga baccin da ban san sanda ya ɗauke ni ba, zazzaɓin ya saukar mun dan
haka na miƙe ina kallon falon dake ta tashin ƙamshin turaren wuta da roomfreshener. Zancen gaskiya iya
gyaran gidan Bilal ba duk mace ba. Haka nan idan ya bushi iska har canza jeren kujeru ya keyi. Se da nayi
wanka nayi kwalliya cikin sababbin ɗinkin sallar da nayi kafin na shiga kitchen neman abinci. Doya ya
dafa da sauce ɗin ƙwai. Dake akwai wuta se nayi microwaving na haɗa baƙin shayi na dawo falo na
zauna kan carpet na shiga karyawa. Bilal ya shigo falon da sallama, kan kujerar dake kallo na ya zauna
yana murmushi yace
"Ranki ya daɗe an tashi kenan". Kallon sa nayi ba yabo ba fallasa na gaishe shi. Surutu ya fara mun ina
bin sa da eh da aa har na ƙare cin abincin na yunƙura zan maida kwanon kitchen ya karɓa se gashi ya
dawo harda ruwa me sanyi ya ajiye mun.
"Yanzu Hajja ta kira ni kin ji kuma wai taron suna suke so suyi, na zata tun da aka wuce satin ga kuma
daga ita har yaron ba wata lafiya ta ishe su ba ai se su haƙura ko?" Ya faɗa yana kallo na. Na gyara
kwanciya ta nace
"Eh, dama Fadilan tace mun zatayi taron suna ai, kuma haihuwar fari ai ya kamata tayi dama kuma
yawanci in dai C's ne se sati biyu akeyin taro ba ranar kwana bakwai ba"
"Amma dai ƙarawa mutane ɗawainiya ne, baki ga jiya nayi dare ba? Wai fa ɗan iskan mijin nan nata se
jiya sannan suka zo da yayyen sa biyu wai bada haƙuri suka kawo wasu shegun kayan su a leda wai na
barka. Wlh badan Hajja tace nayi shiru ba niyya nayi nace su tafi da tsiyar su tunda da basu kawo ba ɗin
ma babu abin da aka fasa yi mata da ɗan nasu har suna cewa a musu lissafin abin da aka kashe na asibiti
zasu biya kamar gaske" ya sake faɗa. Tun da ya fara maganar na zuba masa ido ina kallon sa, so nake
nace masa kawo kaya a leda ai ba kansu aka fara ba ƙarewar kayan barka naga har lefe sun kai a leda me
yasa dan an musu yanzu abin ze yi musu zafi amma na kasa faɗa saboda nasan ƙarshe ze iya juyawa
maganar manufa yace na masa gori ko wani abu se kawai na datse zancen da cewa
"Wallahi kawai in na tuna zumunchin da Fadila ta mun shiyasa nake tsaye akan sabgoginta. Yarinyar nan
bata ji ƙyashin bani rabon ta na gado nayi sabgogin karatu ba shiyasa ko miliyan nawa zan samu a
rayuwa ta nima ba zan ji takaicin kashe mata ba dan ta mun abinda kowa be mun ba cikin yan uwana"
Bilal ya sake faɗa, a raina na raya
"Ashe dai kasan me maka" yawan zancen Fadila da irin yanda ya ɗaukaki halaccin da ta masa yasa a
kullum nake kyautata masa zaton baze taɓa wofantar dani ko ya manta tawa sadaukarwar a rayuwar sa
ba kamar yanda da yawa suke tunanin ze bani kunya.
"Kinga a duniya bayan Hajja, ke da Fadila kune mata biyu da suke da ƙima da daraja a ido na. Har gaban
abada ba zan manta hallacin ku ba a kullum kuma ina roƙon Allah daya hore mun abin da zan kamanta
muku dan nasan bazan biya ku ba" ya sake faɗa yana matso ni jikin sa. Kaina ya fasu, ban san sanda na
fara murmushi ba kamar gaula. Ban taɓa wa Bilal wani abu da fatan ya biya ni wata rana ba. Komai ina
masa ne saboda son sa da nakeyi tsakani da Allah amma bazanyi ƙarya ba ina jin matuƙar daɗi a duk
sanda ya nuna mun jin daɗin sa kan wani abu da nake masa irin wannan tunasarwar kuma tana sakawa
na cire kokonton dake damun zuciya ta na Bilal ya canza daga bigiren dana san shi saboda sababbin
ɗabi'un da yake gwada mun a yanzu.
Tuni na watsar da ƙudurin motsa kambu na nuna masa ɓacin raina akan rikicin gangan ɗin da yake mun
na biye masa muka shiga filin baje kolin ƙauna. Bayan la'asar ina kwance a falo zazzaɓi na namen dawo
mun, Bilal ya shigo daga masallaci gani na a kwance yace
"Gaskiya ba yau ba, jiya fa cewa Mama nayi bani da lafiya shiyasa muka fasa zuwa kaga ma ƙaryar da
nayi ciwon gaske na neman kwantar dani". Zama yayi a gefe na ya ɗora hannun sa a wuya na yace
"Jikin ki yayi zafi, dubaki Anty Labiba tazo yi jiya kenan? Dama nayi mamakin ganin ta haka kawai ita da
tun da mukayi aure bata taɓa zuwa ba"
"Allah ne be kawo dalilin zuwan bane ba" na faɗa ina gyara zamana. Ya ɗan ɓata fuska yace
"Ba wani nan nine bata so kika aura ba shiyasa ba zata zo gida na ba" se nayi saurin katse shi da cewa
"Ya zanyi nace bana son ƙanwar mahaifiyar ki? Kawai bana jin daɗin yanda bata mun kara ƙarara take
nuna bata ra'ayin kasancewar mu tare tun ina neman auren ki. Sannan nasan har yanzu bata yada
makamanta ba, zuga ki zata cigaba dayi idan kika je gidan".
"Lallai Bilal, ita kuma Anty Labiba saboda bata da abinyi se ta zauna tana zugani. To ta zugani na kashe
aure na ko me? Ribar me zata ci?"
"Ita kuwa zata ci riba tun da wannan soloɓiyon ƙanin mijin nata na sonki kinga burin ta se ya cika ki aure
shi" ya faɗa yana wani zare ido. Kallon sa kawai nayi na koma na kwanta dan maganar ta fara hawar mun
kai. Beyi shiru ba yaci gaba da cewa
"Yanzu Allah kaɗai yasan me zata je ta faɗa jiya, tun da na gaishe ta naga bata amsa ba nasan ta ƙudurce
wani abun ne a ranta". Jin na masa banza ban tanka yasa ya miƙe yana cewa
"Ni bari na tafi toh dan na kira Nasir nace ya shirya ze raka ni mu gaida su Mama zuwa gobe idan kinga
zaki iya daga gidan sunan se kije".
Ban amsa ba na da naji shiru ma na zata ya fita duk da banji motsin buɗe ƙofa ba,
"Halims" ya kira ni, na juya ba tare da na amsa ba. Irin kallon daya yaudare ni dashi nayi kaca kaca a
ƙaunar sa ya watso mun kafin ya tsugunna gaba na ya ruƙo hannu na yace
"Ta me?" Na faɗa a ƙasan maƙoshi saboda kallon da yake mun duk yasa naji wani iri se yace
"Kin san rigimar Hajja, wai dubu hamsin take nema a hannu na daga yanzu zuwa dare ni kuma wlh
account ɗina kaf babu dubu ashirin ma balle ashirin. Gurin Nasir kaɗai nake iya zuwa rancen kuɗi shima
kuma cikin buƙatar su yake. Nace mata bani da kuɗi amma bata yarda ba har tana cewa wai bayarwa ne
kawai bazanyi ba bata ko dubi kuɗin dana kashe na aikin Fadila ba amma dan nace bani da dubu ashirin
take nema tayi fushi"ya ƙarasa kamar zeyi kuka dan har idon sa ya canza.
Har raina naji tausayin sa, na karanci halin Hajjan su maganar Allah mace ce me son abin duniya kuma
bata da uzuri akan babu tafi so a duk sanda a buƙaci abu kawai ayi kusan yana daga abun da yasa nake
ɗagawa Bilal ƙafa dan nasan yana da nauyin daya fi samun sa akansa.
"Ki agaza mun ki samo mun aron dubu hamsin zuwa ƙarshen wata ayi albashi, akwai ma kuɗin da na
rantawa Abubakar satin da za'a shiga ze fitar da kajin sa idan ya bani se ki mayar musu" ya sake faɗa
yana matsa hannu na. Kallon sa nayi nace
"Haba Halims mutane da yawa mana ga yan uwanki ga ƙawayen ki ko gurin Hansa'u ai ba zaki rasa" se na
harare shi nace
"Kuma kawai se na tafi cikin yan uwana ko ƙawaye neman rancen kuɗi kaga ma se a samu nayi dani ace
wahala nake sha a gidan ka har na fara yawon neman rance". Se yayi shiru kamar me nazari kafin yace
"Kuma haka ne. Wlh kaina ya kulle sam na rasa mafita shi yasa ma wannan tunanin be zo mun ba. Ni
kaina akwai gurin waɗan da idan na tambaya zan samu amma kin san bana son raini ba kowa ne ze
fahimci buƙatar matsuwa ta saka ka neman taimako ba se a samu abin gulmar ka a unguwa. Barshi
kawai bari naje na bata abin da nake dashi idan yaso su Yaya Amina sa cika mata sauran tun da dama su
suka ƙirƙiro bidi'ar yin sunan ba wani ba" ya ƙarasa yana miƙewa tsaye.
Kamar wani maraya ya fara tafiya yana waige na, na koma na kwanta ina danne zuciya ta kar tausayin sa
yayi tasiri ya sakani yin abinda banyi niyya na amma ina na kasa. Har ya kai bakin ƙofa na tashi zaune na
kira sunan sa, tsayawa yayi. Na yamutsa fuska. Dubu goman da Abba ya bayar aka kawo mun sa wadda
Uncle Saleh ya bani jiya har ga Allah na gama lissafin me zanyi dasu wasu kayan jarirai irin na turkey
Hansa'u ta turo mun har na zaɓi waɗanda nake ao jira nakeyi na fita na samu wanda zan bawa kuɗin ya
tura mun a account na aika mata ga wata lalukar ta faɗo musu dukda a zahiri abin be shafe ni ba amma
bazan so ran miji na ya ɓaci akan abin da nake da halin fitar dashi ba. Ba dai zan tambayi kowa ba amma
zan masa komai da abinda nake dashi.
Ina dafe kai na shiga ɗaki na fito da rafar sababbin yan ɗari da yan hamsin biyu na haɗa na miƙa masa,
karɓa yayi yana kallo na da sigar neman ƙarin baya ni. Na yamutsa fuska nace
"Jiya Abba ya aiko mun da barka da sallah wannan kuma Uncle Saleh ne ya bani, kayi maneji dasu dan
gaskiya ni babu wanda zan iya tambaya wasu kuɗi yanzu"
"Allah sarki My Halims da kin barsu ma kawai zanje nace mata ban samu ba faɗa ne kawai zata tayi
amma dole ta haƙura tun da dai bazanyi sata na basu ba" ya faɗa yana dawo mun da kuɗin. Ban karɓa ba
na juya na zauna ina cewa
"Allah ya maida miki da dubun su Halims, bari naje ba daɗewa ma zanyi ba zan dawo naji ba'asin
wannan ƙyallin goshin da faɗin kwankwason da kika ƙara kwana biyu. Yana yinki dai kamar akwai wani
abu da kike ɓoye mun" ya faɗa yana kashe mun ido ɗaya. Murmushi nayi tare da zamewa na kwanta ina
ɗaga masa hannu. Yana fita bacci ya kwashe ni ban farka ba kuma se da aka fara kiraye kirayen sallar
magriba. A kan center table naga leda da mangwaro harda yalo fari da kore a ciki se farar takarda a
ninke na buɗe ta 'i might be late, amma karkiyi bacci ki jira ni please' abin da aka rubuta kenan.
Murmushi na saki wani daɗi ya ratsani dan nasan daren yau kam ze zama na daban ne, kasala da
zazzaɓin da nake ji ma duk se na neme su na rasa na tashi ina idar da sallah na shiga shiri dukda bansan
da me ze zo ba.
Washe gari cikin annashuwa da farin ciki muka fita, gidan mu ya sauke ni, a cike na tarar da gidan su
Anty Labiba da sauran ƙannen Mama da suka zo yinin sallah dan tun bayan da mahaifiyar su ta rasu
kasancewar Mama Fauziyya da take babbar su ba'a nan suke zaune ba se Mama ta ƙwace girma ya zama
duk wani haɗuwar su a nan gidan mu sukeyi. Se yamma lis muka leƙa gidan su Bilal suna dukda ni tun
azahar na zabara zan tafi Anty Mimi cousin ɗin su Mama kuma matar Uncle Mudassir ce ta hanani. A
bakin get muka ci karo zata shigo ni kuma zan fita ana yayyafi dan anyi ruwa be ƙarasa ɗaukewa ba tun
farko ma saukar ruwan ce ta hanani tafiya dan niyyata kamar sha ɗaya haka na tafi tunda tara bata
ƙarasa bama ya kaini gida naga kuma da naje zanje ɗin babu wanda yace Aa Anty Labiba cewa ma tayi ya
kamata ai dana haƙura ma da zuwa gidan yau na tafi can tunda muna da suna wai ashe baƙar magana ta
faɗa mun.
"Karki kuskura ki ɗauki wannan salon gaba ya dame ki, ba'a ce kar kiyi sabga da dangin mijin ki ba amma
komai ya zama da iyaka babu cusa kai babu wulaƙanci biki suna ba zancen ki tafi tun wurwuri ki zauna
gara ki shiga a marmarce a gama ki kama gabanki da kina da yara ne ma wannan tun safe kya iya turasu
su shiga cikin yan uwansu idan yaso kya je daga baya amma gari ko gama tsanewa beyi ba kin zari mayafi
zaki tafi kyaje ki rasa gurin zama yanda baki da aikin nan se kwanciya".
Ɗaki na shige jin sun mun caa ashe wai duk shiru kawai sukayi kowa da magana a bakin ta. Ni dai na kasa
nutsuwa gani nake ban kyauta ba ace ana sunan ƙanwar miji na a matsayi na na matar wanta da suka
ɗaki ɗaya nasan yanzu duk faccaloli na wanda mazajen su suka haɗa uba da su Bilal ai sunje se ni kaɗai
ce bazanje da wuri ba. Haushin dalilin daya sa ban fara tsayawa acan ba naji yanda kasan wadda tayi laifi
haka na kasa tsaye na kasa zaune daga ƙarshe ban wa kowa sallama ba na bi ta ƙofar kitchen na fice
surutu ne dai zasuyi su gama kuma duk da zasu ce kar naje naga kowa idan sabgar dangin mijin ta ya
tashi sune a gaba har ma su gayya ce mu shine ne za'a koya mun na wulaƙan ta nawa na kuma kashe
wayata dan karma su kira ni.
Aiko abin da na guda ina zuwa yan gidan su Bilal suka mun caaa wai se yanzu harda Hajjan kuwa da yan
uwanta, abin takaici gurin zama me kyau ma na rada duk da gidan ba'a cike yake ba iya su ne yan ɗakin
su se yan uwan Hajjan da yayan su ko waɗan da suke uba ɗayan mutum ɗaya na gani Farisa sauran sun
ce ruwa ya hana su fito. Haka na ringa raɓe raɓe daga wannan bangon zuwa wancan ga babu fuska hatta
mejegon wani gani gani naga ta mun ba abun na koma gida ba na tarar da surutan su Anty Labiba a
daddafe na jira akayi la'asar suma ban musu sallama ba na kama hanyar gida na.
Daga yanayin yanda Bilal ya shigo gidan na gane ba lafiya ba, be dai ce mun komai ba har na dafa masa
Indomin daya buƙata. Ina shafa mai bayan na fito daga wanka ya shigo ɗakin ya zauna kan bedside
drawer yana kallo na yace
Se naji gaba na ya faɗi dukda cikin sanyi yayi maganar, a hankali ni ma nace
"Kasan anyi ruwa ga zazzaɓi kuma a jiki na se da akayi sallar azahar ruwan ya tsaya sannan na tafi". Kai
ya gyaɗa kawai jin yayi shiru se na cigaba da shiri na ina satar kallon sa, har na kammala na shimfiɗa
sallaya zanyi shafa'i da wutri ya sake cewa
"Eh ni kaɗai na tafi, sun ce na jira mu tafi naga lokaci na ƙurewa shine na tafi"
"Hajja tayi zaton tare zaku je da su Mama ai ta zaunar da mutane akan su gaisa kuma basu je ba shine
wai taji babu daɗi" ya sake faɗa. Yanayin yanda yake maganar se naga kamar yana so yayi faɗa ne se dai
kuma rashin hujja ko dalilin yin faɗan yasa yake fadar maganganun a sanyaye. Ban bashi amsa ba na
tayar da sallaha ta dan jikina duk ciwo yake mun dan ma nayi wanka, washe gari da la'asar salaliya kuwa
se ga Farisa dake akwai ƙanwar mijinta bayan layin mu itama ta haihu yau ne sunan shine ta ratso.
"Ai in gaya miki jiya karki so kiga tijarar da Hajja ta dasa a gida mara dalili. Bafa ayi girki ba banda na safe
har se sanda kika zo ɗin nan fa kikaga ana kiciniyar ɗorawa ga guri ya jiƙe ni dai ana kiran sallar magriba
na tafi lokacin abinci ya sauka jama'a dai sunyi wunin yunwa a gidan suna".
Farisa data gama kora zoɓo me sanyi ta faɗa. Ƙanwar Bilal ce da suke una ɗaya ita kaɗai mamanta ta
haifa a gidan dan haka ta zama bakin ganga bata ɓangaren su Bilal ɗin bata gefen yan ɗaya ɗakin. Tana
da kirki matsalar ta na lura ta fiya gulma da tsegumi ta ɗakko zancen wancan ta kai can aikin ta kenan.
Tun aure na da Bilal take so mu ƙulla mu'amala da na fara sake mata dana fuskanci halin ta se na janye
ko a whatsapp ta mun magana se na ja kwanaki ban amsa ba dukda haka bata haƙura duk sanda tazo
gidan ƙanwar mijin ta dana fahimci suna shiri se ta ratso ko ita ƙanwar mijin nata ma taso ta haɗa mu
zuwan ta uku ban je mata ko sau ɗaya ba dake me hankali ce se ta janye ta rabu da ni.
"Ban da son zuciya dai irin na Babar mu, ashe ke ake ta jira zaku kawo abinci, kin san haihuwar ƙarshe da
Ummi tayi bikin ku saura sati biyu Anty Murya Amaryar Yaya Khamis ce ta ɗauki nauyin abincin da aka ci
a gidan sunan nan se kinga abu, shine suka saka rai kema zaku musu haka. Se gashi da kika tashi zuwa
sungup ance ko abin barka baki bayar ba. Ni dai nace ko ita Ummin da kuɗin Yayanta aka mata ba wai a
aljihun ta ita Anty Murjar ta zare tayi ba wlh. Haka dai aka watsa taro yan fadar Hajja marasa tsoron
Allah sun tafi dake a baki har ana cewa arziƙi beyi rana ba wai ana wa Yaya Bilal murna ua samo yar
masu hannu da shuni ashe duk ƙaryar banza ce babu abin".
*(Based on true life event, some parts are fictional to spice up the story)*
*Wattpad @MaryamahMrsAm*
*Kuɗin karatu yana wakiltar mutum ɗaya ne, kiji tsoron Allah karki ɗauki hakkina ta hanyar fitar mun da
littafi*
*KURA A RUMBU littafin kuɗi ne, a biya naira 800, biya a asusun*
*1840175439*
*Access bank*
*PAGE 16*
*Nayi kuskuren rubutu a page 13, ajizanci ne, abinda ke raina daban abinda alƙalamina ya rubuta daban.
Ina fatan zaku mun uzuri*
Na ringa juya zancen Farisa a raina bayan ta tafi har sanda Bilal ya dawo sau biyu ina buɗe baki da niyyar
tambayar sa gaskiyar abin da ta faɗa mun se na kasa daga ƙarshe na tattara zancen na watsar har ina
ganin baike na dana yarda da maganar tata har na saka a raina. Ta ya ma haka zata yuwu? Kawai dai
haɗa guri ne irin na Farisa amma kuma idan tayi ƙarya ta ƙulla abu mara daɗi tsakani na da dangin Bilal
ribar me zata ci?
Ganin ba ni da wani takamaiman wanda zan tambaya na ji gargar ɗin maganar yasa na barta a bata faru
ba naci gaba da sabgogina.
An gama bikin sallah ta wuce ta bar wawa da bashi kamar yanda hausawa suke faɗa, ranar data kama
kwana bakwai dai dai da yin sallah tun da safe Bilal yace mun zamu fita da yamma. Yanda yake ta zirgilli
da rawar ƙafa akan fitar yasa na ringa mamakin in da zamuje dan be gaya mun ba. Ana la'asar ya shiga
azazzalata da na shirya mu tafi ni kuma gaba ɗaya naji jiki na ya mun nauyi, ina ta so na koma asibiti ma
amma shauni da shiririta ya hanani. Haka dai na ƙoƙarta na shirya, atamfa na saka Holland riga da zani
dan kayana sun fara matse ni da alama dai cikin kiɓa ze saka ni, ina tsaka da ɗaura ɗankwali na ya shiga
ɗakin yanda kasan me shirin tafiya dinner haka ya sha kwalliya da sabuwar shadda cream color se ƙyalli
take yi.
Kallon sa na ringa yi kamar yanda shima yake kallona hanci a ɗage kafin cikin faɗa faɗa yace
"Meye Halims? Wane irin kaya ne wannan kika saka kamar wadda zata je cin kasuwar ƙauye?"
Kallon kaina nayi sama da ƙasa ko zan ga abinda yayi kama da shirin tafiya ƙauye a jiki na amma ban gani
ba dan haka na mayar da kallona kan sa nace
Ba amsa ni ba ya wuce gaban wardrobe ɗina ya buɗe ya shiga birkito kayan ciki yana cewa
"Malama ki cire wannan kin san in da zamuje da zakiyi wannan shigar salon ki zubar mun da mutunchi?
Hannu na harɗe kawai a ƙirji ina kallon ikon Allah. Lace ɗin da nayi kwalliyar kamun bikin mu ya janyo
daga ƙasan kaya ya ware shi kafin ya watsa kan gado ya buɗe in da mayafai na suke yana cewa
"Wannan zaki saka". Se ma ya bani dariya, na matsa gefen gado ina cewa
"Siyar da ke zanyi, malama ki yi abin da nace kawai kar ki ɓata rai da lokaci" ya faɗa yana aje mayafin
daya ɗakko kan kayan. Se na ɗaga rigar nace
"Kasan dai yanzu wannan kayan baze shige ni ba, ka faɗa mun in da zamu je se na duba wanda zasu dace
da fitar na saka"
"Walima zamu je" ya bani amsa a daƙile". Har na buɗe baki zan sake tambayar sa tame? Koma waye ya
gayyace mu se dai yanda ya haɗe girar sama data ƙasa yasa na kama kaina na shiga lalubo wasu kayan
tunda ya kushe atamar dana saka.
A motar Nasir daya karɓo muka fita, se da muka fara tsayawa a kantin Baby dream. A mota ya bar ni ya
shiga bayan wasu mintuna ya fito hannu biyu riƙe da ledoji shaƙe da kayan jarirai ya ajiye su a back sit.
Mamaki fal rai na baki na cike da magana amma babu fuska dole na haɗiye na zubawa sarautar Allah ido.
Can cikin nasarawa gra ya kaimu wani gida. Daga get ɗin farko ma zuwa cikin gidan tafiya ce ta misali,
yanda ya gaisa da masu gadin get ɗin na gane akwai sanayya a tsakanin su amma dukda haka a tsorace
na ringa kalle kalle har muka isa in da ake ajiye motoci.
Kamar mara gaskiya na ringa bin bayan sa har muka isa entrance ɗin gidan ya dannan door bell, mun
kusa minti bakwai a tsaye kafin aka zo aka buɗe, yanda kasan gidan su haka Bilal ya ringa jefa ƙafa ni
kuma ina bin sa a baya, se da muka zauna kan wasu kujeru masu azabar kyau da laushi kafin na fahimci
gidan Abokin sa Hafiz muka dalilin hoton su shida matar sa dake kafe jikin bango. A raina na raya ashe
dai ba ƙarya Bilal yake ba idan yana santin irin arziƙin da Hafiz ɗin suke dashi, na ayyana yana da kuɗi
haka ko me ya kaishi aikin gomnati kuma bama wani shahararre ba irin su CBN ko Oil ko porth authority
naga can aka fi samun yayan manyan ƙasar a ciki.
Tun zuwan da suka mana ni na manta ma da babin su har idan ba shi ya ɗakko zancen su ba, matar ma
da mukayi exchanging number sau ɗaya ta taɓa kirana tace sisters ɗin ta sun ji ƙamshin turaren wutar
dana bata suna so na haɗa ta da me siyarwar (08033950747, kina neman turaren wuta me asalin ƙamshi
da kama guri wanda duk wanda ya shaƙa seya tambayi in da kika samo shi? Ki tuntuɓe ta) shikenan
bamu sake magana ba. Da ina ɗan ganin ta a whatsapp daga baya kuma na dena ganin ta ma na zata
yanda ta sake dani sanda suka zo zamu yi doguwar mu'amala kamar yanda Bilal yake fata toh kuma
hakan bata kasance ba.
Se da mukayi jiran kusan wasu minti goman har seda Bilal ya kira maigidan a waya kafin suka fito yana
saɓe da baby tana bin sa a baya. Na ringa hasaso sanda suka je mana ni dai bangan ta da ciki ba ko kuma
lura ne banyi ba oho dai gashi nan ta haihu. Farat farat kamar karon farko muka gaisa, tace mun
"Baki da kirki Halima, na rasa number ki ke kuma ko sau ɗaya baki ce kinji ni shiru bari ki taɓo ni kiji ya
nake ba ko dai zumunchin ne bakya so muyi?"
"Ai itama wayar ta ta lalace ne, tuntuni kuma tace na karɓo mata number gurin yallaɓai se in manta"
Hafiz yace
"Kai dai kace zaka kare ta kawai amma zuwan ka nawa gidan nan kuna haɗuwa ai ko ka manta ya kamata
ace idan ka ganta ko sau ɗaya ka tuna saƙon da aka baka". Ni dai sakin baki da hanci kawai nayi ina
kallon Bilal jin wannan gingimemiyar ƙarya daya shirga an kuma kama shi. Na sha mamakin jin wai yana
zuwa gidan ashe, lallai se a bar Bilal. Ashe shi yasa ba'a ko tambaye mu daga ina ba aka bar mu muka
shigo, ko me yake zuwa yi se Allah.
Mita Suhaila taci gaba dayi ni dai na bita da ban haƙuri ina riƙe da kyakykyawan babyn ta me suna
Muhammad Sani sunan babanta suna kiran sa Na'im. Duk tarin kayan ciye ciyen da aka cika mu dasu
ruwa kaɗai na iya sha a ciki, se da muka shiga ɗakin ta ta dame ni da se na faɗi abin da nake ra'ayi an
mun tunda ta lura ba ni kaɗai bace baze yuwu na zo gidan banci komai ba. Dankali nace a soya mun dan
na kwana biyu ban ci ba tun azumi. Se bayan sallar Isha'i muka tafi gida shaƙe da kayan arziƙi harda
naman suna kusan cikin ƙaramin bokiti a haka ma tace wai ya ƙare ne haihuwar kusan kwana talatin ni
dai nace an gaida masu kuɗi ko raguna nawa suka yanka se Allah ko kuma dan basu da yan uwa da yawa
a Kano ne tunda mu na gidan su Bilal ma ko hanji ban gani ba cewa akayi mutane sunyi yawa akan
naman ya ƙare dama kuma dabbar ƙarama ce batayi auki ba.
"Ki san a Egypt ta haihu se ranar idi suka dawo yace baya so azo ayi ta jagwalgwala masa yaro shiya sa
suka yi zaman su se da ya ɗan yi ƙwari. Yan gidan su can a Kaduna sukayi suna na zata ma da suka dawo
gida zata wuce wai su basa haka ashe ba'a zuwa wankan gida" Bilal ya faɗa bayan da muka hau titi. Na
gyaɗa kai tare da cewa
"Allah sarki, zuwa wankan gida dama ai ra'ayi ne kuma ma yanzu duk an dena ai kowa a gidan ta take
zama tayi jegon ta"
"Wanda suka de na dai sun dena mu kuwa a dangin mu kwana sittin ma akeyi ba arba'in ba" ya sake
faɗa, se da juya na kalleshi da mamaki nace
"Wato kwana sittin ma? Kai yanzu idan na haihu se ka yarda na tafi gida nayi har kwana sittin bana tare
da kai?"
"Nasan dai zan azabtu da missing ɗin ki amma ya zanyi da abin da al'ada ta gindaya. Kwana sittin ɗin ma
fa bayan an haihu ne wannan lissafin naga matan su Yaya Suleiman da haihuwar fari da cikin su ya shiga
wata tara suke tafiya gida. Kinga kamar Anty Mariya da take ba yar gari ba ina ga se da tayi wata uku ma
ita sannan ta dawo ai to ke tun da a kusa kike da kafin haihuwar zuwa bayan haihuwar se kije kiyi arba'in
biyu kawai, wai ma wata nawa ne cikin yanzu?" Ya ƙarasa yana ɗora hannun sa akan cikina.
Al'ajabi da mamaki suka sa na kasa cewa komai se bin sa da ido dana ringayi ya kuma yi mirsisi abin sa
yaci gaba da tuƙi yana soko mun wata hirar. Mamakin nawa biyu ya kasu, na farko wai ashe ma ya
tabbatar ina da ciki amma ko da wasa ban ga wata murna ko zumuɗi a tattare dashi ba sannan kuma
yanzu lissafi yake idan na tashi haihuwa gidan mu zan yafi nayi arba'in har biyu wato lallai bani da wani
muhimmanci a gurin Bilal. Ji nayi raina ya ɓaci take hawaye ya fara cika mun ido, jin nayi shiru bana
amsa hirar da yakeyi yasa ya kamo hannu na yana cewa
"Bacci kika yi ne ina ta magana kinyi shiru?" Aiko kamar ina jira se hawaye shaaa suka ɓalle mun,
"subhanallahi Halima me kuma ya faru?" Ya faɗa yana gangarewa gefen titi. Haɗe kai nayi da guiwa na
shiga rera kuka kamar wadda aka daka.
A karon farko tun auren mu naga rikicewar gaske tattare da Bilal akan ɓacin raina. Fita yayi ya zagayo ta
in da nake na durƙusa kamar zeyi kukan shima yana roƙon na gaya masa mene ne. Se da nayi me isata
kafin nace
"Yanzu saboda baka farin ciki da kyautar da Allah yayi mana shi yasa ko a fuska baka nuna mun ka sani
ba, ni kaɗai nake shirme na kai ko a jikin ka" na sake fashewa da kuka. Se ya dafa kai kafin ya miƙe yana
murmushi ya koma mazaunin sa.
"Na lura so kike kiyi surprising ɗina shiyasa nake acting along kar na ɓata miki shiri amma da na san ranki
ze ɓaci akan haka da tun sanda na gane nayi magana. Kuma Allah ba wani daɗewa akayi ba, ranar da
kika ce na siyo miki mangwaro ne shine nayi suspecting kuma dama na lura ba kiyi period da azumi ba.
Nasan akwai shirin da kike yi da ya sa baki gaya mun ba kar nayi magana kuma na lalata miki" yayi
maganar ta sigar da ko ba gaskiya ya faɗa ba dole na yarda da abin da yace. Har kaza ya siya mun ƙatuwa
da yoghurt me sanyi, da muka isa gida kuwa a hannu ya ɗauke ni har da yi mun rawa wai dan na yarda
yana murna da ƙaruwar da muka samu.
Baki san yanda nake son yara bane Halims, ko da kika ga ina yi kamar ban damu ba tun da mukayi aure
bana so na ringa magana ne hankalin ki ya tashi bayan kuma bamu zamu bawa kanmu haihuwar ba
amma ban taɓa zaton zamu tsallake watan farko na auren mu baki ɗauki ciki ba ke baki ga irin ƙoƙarin da
nake yi ba?" Ya faɗa yana kashe mun ido. Da hannu biyu na rufe fuskata ina murmushi, daren ya shiga
cikin dararen farin ciki na a gidan Bilal, washe gari da yamma muka je asibiti, an sake mun scanning cikin
har yayi wata uku yana shirin shiga na huɗu, a hanya bayan mun fito daga asibitin yake cemun
"Naga da file ɗin ki na gida kikayi amfani, kuma na san kai tsaye daga account ɗin Abba ake cire kuɗin
magani babu matsala?"
"Ka jika da wata magana kuma wace irin matsala? Duk yan gidan mu kasan asibitin da muke zuwa kenan
nasan idan ma na canza wani ƙarshe hakan ne ze zama laifi shiyasa ban ma yi maka maganar kuɗin
asibiti ba ko wani abu, da har ma na buɗe file a wannan asibitin na gaban mu dan can na fara zuwa ma
kuma da naga dai nan ɗin ya fi sun kuma fi ma'aikata da kayan aiki shiyasa ban koma can ɗin ba" na
bashi amsa.
Da dare se ga kiran Mama, tun da na jiyo muryar Anty Labiba a background dama nasan wani abun ta
ƙulla ilai kuwa bayan mun gaisa Mama tace
"Ɗazu an turowa da Abban ku bill na kuɗin antinatal shine na kira naji shi uban cikin ne yace ba ze ɗauki
nauyin sa ba ko kuwa kalar naki sanin ya kamatan ne yasa zaki ɗorawa Abbanki haƙƙin da ba nasa ba?"
Nayi shiru na kasa ce mata komai, bata damu ba taci gaba da cewa
"To baze biya ba, idan kina so kici gaba da awo a nan ki gayawa mijin ki ya yankar muku kati idan kuma
yana da wani gurin da yake ganin yafi masa ki koma can tunda kin san dai tsare tsaren su da cin kuɗi kar
ki kuskura ki ɗora masa abin da kika san baze iya ba" bata ma jira na amsa ba ta mun sallama ta kashe
wayar ta. Ni dai kacokam na ɗora laifi kan Anty Labiba nasan ita ta zugata dan dai Abba baze ce baze
biya mun kuɗin asibiti ba ita ma Maman a ra'ayin kanta ba zata hana ba se dai idan mazuga irin su Anty
Labiba da Mu'azzam sun shiga lamarin. Rasa ta in da zan farawa Bilal magana nayi, batun ya biya mun
kuɗin awo a wannan asibitin ma be taso ba dan tsakani da Allah a matsayin da yake kai yanzu services
ɗin su sun masa tsada dama dai ace bashi da hidimar kowa ne se tawa da abin da zamu haifa balle ma
nasan Bilal a yanda baya maraba da duk harkar kashe kuɗi bana zaton ko yana da sararin ma ze biya dan
da an fara maganar asibiti dama ze ce shi yafi gane aje Aminu Kano ko Murtala sun fi manayan likitoci da
kayan aiki privet ɗin nan duk kame kame ne.
Ganin a sati huɗun da aka ɗibar mun na komawa awo saura kwana biyar yasa nayi ƙundumbalar tarar sa
safiyar wata asabar na faɗa masa Abba yace ya kamata mu buɗe file namu na kanmu ba naci gaba da
amfani da na gidan mu ba. Bece komai ba amma fuskar sa kaɗai na kalla na gane sam hakan be masa ba,
ranar litinin kuwa be fita aiki ba yace ma shirya muje asibiti a buɗe file ɗin, na ɗauka ma zamuje na nan
unguwar dana fara zuwa tun farko ina kuma shakkar na masa maganar dan tun ranar asabar ɗin ya shiga
ɗaure fuska be dai tafi hutun kulani daya saba idan munyi faɗa ba amma dai magana ma se wadda ta
zama dole ce zeyi mun ba sakin fuska ba walwalar da muka saba.
Asibitin Murtala muka je, dama tun da naga mun ɗauki hanya jiki na ya bani amma ban ce komai ba,
dake akwai wata cousin sister su dake aiki a gurin se gashi nan da nan an mun komai har an bani ranar
zuwa awo muka juya gida. Gidan su ya sauke ni yace se da yamma zezo mu tafi, tun sunan Fadila zuwana
biyu suma a tsaitsaye tare muke zuwa mu tafi tare se yau ne ze ajiye ni ya tafi tun kuma daga yanda
Hajja ta amsa mun gaisuwa nasha jinin jiki na shi yasa yana tafiya na shige ɗakin da Fadila da har sannan
bata koma gidan ta ba take na zauna a can. Na fito alwalar sallar azahar na tarar da Hajjan da Mama
Usaina ƙanwar ta suna zaune a falo suna hira, ban san asalin zancen da sukeyi ba amma yanda suka
canza magana da gani na se naji kakaryda gayya sukayi dan naji.
"Allah na tuba a zamanin nan lafiyar ɗan ka ma ace se kayiwa kanka mugunta, yan da haihuwar nan ta
zama se addu'a kana ji kana gani a son kuɗi se ka kai ɗan ka in da za'a halaka shi kwanan sa be ƙare ba"
Mama Usaina ta faɗa. Hajja ta karkace tace
"Kema dai kya faɗa, shi yasa kika ga nayi tsaye kan wannan yarinyar nace ta taho gida in da mun biye ta
tasu suman da ɗan nan yayi aka fasa kukan mutuwa da can a gurin su take ai da tuni an binne shi wlh.
Yana nan kullum yana zarya ta koma nace aa se tayi arba'in biyu tukun ta murmure ba zata koma da
ɗanyan yanka a cuce ni ba. Su dai wanda suka sallamawa duniya nasu yayan ai shikenan se yanda suka
gani".
Ina alwalar ina jiyo zantukan nasu se suka ma bani dariya, da zamu tafi Fadila take ce mun se sunzo, na
ɗauka yawon arba'in take nufi kwana biyu da yin haka ina kwance da hantsi aka buga gida in buɗe se
ganin ta nayi saɓe da babyn ta ga Abubakar da ƙatuwar akwatin kayan su. Da mamaki na basu hanya
suka shiga, se da na basu ruwa da lemo muka gaisa kafin take ce mun
"Kin ganmu se yau ko?, se ɗazu su Hajjan suka tafi jiya ruwa ya hana tafiyar se yau ina ga ma yanzu sun
sauka ai" Abubakar ya duba agogon hannun sa yace
"Ah ya kamata sun isa yanzu ina Kano ina Jos musamman kuma motar gida ai har hutawa ma sun yi
yanzu kam, bari naje Anty se Anjima" yayi mana sallama ya fita.
Ni dai ban fahimci kan zancen nasu ba, bana girki da rana tun da Bilal na gurin aiki amma zuwan Fadila
dole na tashi na ɗora mana. Da wuri Bilal ya dawo ranar, Fadila tayi ɗai ɗai a falo yanda kasan sun
shekara da zuwa duk inda ka duba kayan ɗan ta gashi da kuka masha Allah tun da suka zo kunne na be
huta ba tun ina mata kawaici ƙarshe na koma ɗaki nayi kwanciya ta ina jiran Yayan ta ya dawo naji
ba'asin zuwan su. Yana shigowa kuwa ya fara hargagi, nayi saurin shafa addu'a dan na idar da la'asar
kenan na fito na tarar dashi yana mata faɗa kamar ze mare ta, ashe kashi yaron yayi akan kujera ta
kwantar dashi babu ko zani balle aje batun diaper ko napkin ina doso falon ƙarnin da ban san ko na
menene ba ya fara hargitsamun zuciya.
Be amsa sannu da zuwan da na masa ba ya shige ɗaki se na bi bayan sa ina shiga kuwa ya rufe ni da faɗa
kamar ni na kwantar da yaron.
"Toh ni yanzu menene nawa a ciki? Ka gaya mun zata zo ne balle na san tanadin da zanyi musu?" Na
faɗa ina haɗe fuska, tsaki yayi, se a lokacin yake ce mun wai Hajja ce ta tafi Jos gidan ƙanwar ta zata yi
sati biyu shine tace Fadilan ta taho nan gidan.
"Se da nace mata kar ta zo ta nemi gurin da zata zauna ko ta koma gidan ta amma taƙi ji to wlh ba zata
zauna mun da wannan muguwar ƙazantar tata ba, ni mejego ko wadda ta zamar mun dole ma se naga
kamun ludayin ta kafin nasan zaman da zanyi da ita balle Fadila da duk wanda ya zauna tare da ita se ya
gane ƙazama ce ta bugawa a jarida. Ji yanda ta mayar da falon nan se kace na mahaukata toh wlh in kina
son ganin farin ciki na tun kafin na fito daga wanka ki sallame ta ta kama gaban ta" ya faɗa yana wani
kaɗa yatsa kafin ya shige banɗaki.
"Lallai ma" na faɗa a fili ina bin ƙofar daya bugo da kallo, wato in kore ta, ni ze shafawa kashin kaji
kenan? banda ma ya raina mun wayo me yasa shi da aka gayawa zata zo be ce aa ba se yanzu ni in
koreta in yaso a sakani a bakin duniya ace na kore ta daga gidan ɗan uwanta to wlh ba zanyi ba.
[1/20, 10:07 AM] Hauwa Galadima: *KURA A RUMBU*
*(Based on true life event, some parts are fictional to spice up the story)*
*Wattpad @MaryamahMrsAm*
*Ban yarda wani ko wata ya juya mun labari ta kowacce siga ba tare da izini na ba*
*Kuɗin karatu yana wakiltar mutum ɗaya ne, kiji tsoron Allah karki ɗauki hakkina ta hanyar fitar mun da
littafi*
*KURA A RUMBU littafin kuɗi ne, a biya naira 800, biya a asusun*
*1840175439*
*Access bank*
*Page 17*
Be ko saurari tayin abincin da na masa ba ya fice daga gidan bayan yayi wanka yana sake jaddada mun
Fadila ta bar gidan kafin ya dawo, bayan fitar sa na shiga gyara falon da tayi mun kaca kaca da shi dan
tun shigowar Bilal ɗin ta koma ɗaki na in da na sauketa. Na tabbatar taji banbamin da yakeyi tun da ba a
hankali yayi maganar da ze fita ba, na ɗauka daya fitan zata tuntuɓe ni da zancen amma shiru se ma
dawowa falo da tayi zata sake tarwatsa gurin na dakatar da ita ta hanyar ce mata ba nisa yayi ba yanzu
ze dawo. Ina kallon ta ta harare ni harda murguɗa baki ta koma ɗaki.
Ranar raba dare mukayi muna tashin hankali da Bilal tunda ya dawo gurin goma ya tarar Fadila bata tafi
ba ya tasa mun masifa tun ina bashi haƙuri da nuna masa rashin dacewar abinda yake son nayi har na kai
bango nace ba zan kore ta ba ai ƙanwar sa ce kuma gidan sa ne idan da gaske baya buƙatar zamanta ya
kore ta da kansa mana shikenan fa ina wuta ya sakani a ciki ya ringa zazzaga da tijara se naga ashe
abinda ya mun akan kifi ma somin taɓi ne. Dana gaji na kwanta na juya masa baya se dai na kasa bacci ga
ɗan Fadila da kamar ma sa gayya yake ta canyara uban kuka duk suka haɗu suka cazamun ƙwaƙwalwa.
Daƙyar na iya farkawa nayi sallah bayan dana samu bacci ya ɗauke ni, sosai kaina yake mun ciwo ga
zuciya ta da babu daɗi. Ina idar da sallah na sake komawa na kwanta ban farka ba se ƙarfe tara harda
wani abu. Se da nayi wanka sannan na fita daga ɗaki, Fadila na harɗe akan kujera da remote tana canza
tasha, yanda ta kalle ni se ka ɗauka kishiyar ta ce ta fito ta wani basar ta maida kai abinda takeyi nima
kallo ɗayan na mata na maida hankali na kan falon dake nan kamar yayi sati bega gyara ba ga kwanukan
abincin a ajiye har sun bushe alamar ba amfanin safiyar nan bane harda cup dana hango sauran shayi a
ciki.
Ji nayi zuciyata ta sake harzuƙa, ni ya kamata nayi jidali an kawo mun baƙuwa ba tare da an sanar da ni
ba kuma tazo tana nema ta mayar mun da gida wani dandalin yan datti ga wani sabon raini da ban santa
da shi ba tana nema ta fara gwada mun. Kitchen na wuce ba tare da na ce mata kanzil ba, ko me tayi
tunani kuma se ji nayi tace
Da lafiya na amsa mata na shige kitchen, nan ɗin ma kaca kaca komai yana zaune da ƙafarsa. Se da na
gyara gurin tas kafin na buɗe fridge in fito da abincin da Bilal yaƙi ci se in ɗumama mu haɗa da baƙin
shayi tunda banga alamar ya siyo abin karyawa ba, banga abincin ba se lokacin nayi realizing ai nama
wanke kwanon cikin kayan dattin dana tarar a kitchen ɗin. Tunanin wanda yaci na tafiyi, nasan ba Bilal
bane zuciyata ta raya mun Fadila ce.
Ina tsaka da jimamin irin wannan abu ta shigo kitchen ɗin tana haɗa fuska kamar zatayi kuka tace
"Kun san da masu jego a gidan saboda Allah se ku kwanta kuyi ta bacci? Ni wlh yunwa nakeji har jiri nake
gani asan yanda za'ayi dani".
"Wace abinci kuma kike nema bayan wanda kika ci?" Yanda tayi da ido kamae irin na mata ƙage se kuma
ta watsa ido tace
"Wai abincin cikin fridge? Yunwa ce ta hanani bacci tun dare naci wannan na duba ma naga ko da
dankali ko doya in soya mana naga babu se wani sauran bread na samu akan dining na haɗa shayi nasha
amma ji nakeyi ma kamar ƙara mun yunwar akayi". Tunda ta fara magana nake kallon ta har ta kai aya,
mamakin ƙarfin halinta nayi. Ɗan bread ɗin da take cewa fa kaɗan ne babu a guda in da dani da Bilal
muka ci har saura se yayi mana shine take cewa wai beje mata ko ina ba.
Rufe fridge ɗin nayi ba tare da nave mata komai ba na wuce store, banda shinkafa da ƙwarorin taliya da
macaroni babu abin da yayi saura a ciki, taliyar na ɗauka na haɗa da papper mix guda ɗaya daya mun
saura na dafa mana mukaci ina jinta a wasance tana cewa wai na bata abinci babu kifi babu nama nayi
kamar ban ji ba dan raina a ɓace yake bana so kuma na furta wani abu da daga baya ze zama abin
magana tunda naga su basa raina abin laifi. Bata tayani da ko cangwal ba na aikin gida se hayaniyarta
data ɗan ta data cika mun kunne. Ina gamawa na koma ɗaki na kulle ƙofa ta na bari akan tunda akwai
sauran taliyar taci da rana.
Tunda na kwanta bacci ya kwashe ni ban tashi farkawa ba se ƙarfe uku harda mintoci na rana. Sallah na
farayi kafin na leƙa naga halin da Fadila suke ciki, falon babu kowa se pillows dake hargitse kamar anyi
wasan dambe. Ɗaki na leƙa nan ma bata nan babyn ta ma baya nan balle nayi zaton ko banɗaki ta shiga.
Tunani na shigayi ina ta tafi? In da akwatin ta ke ajiye na duba nan ma babu hakan ya tabbatar mun da
fitar taje ta dawo tayi ba ƙila gida ta koma amma me yasa zata tafi bata gaya mun ba?
Ji nayi hankali na ya tashi, kar dai Bilal ya dawo ya kore ta, amma kuma da ya dawo gidan dole ze tayar
dani ko da yake tunda ba abin ƙwarai zeyi ba be zama lallai ya tashe ni ɗin ba tunda yasan zan hana.
Duk se naji babu daɗi, layin ta na shiga kira wayar tayi ta ringing ba'a amsa ba dana sake kira kuma se na
jita a kashe. Har na mayar da akalar kiran kaj Bilal se kuma na katse na bari idan ya dawo zanji dalilin da
yasa be haƙura ba ya koreta. Haka na ƙarasa wunin rai babu daɗi, biyar da rabi ya dawo sallama ma ciki
yayi be amsa sannu da zuwan da nake masa ba ya wuce ɗaki abin sa se na tashi na bishi. Ganin ya shiga
wanka se na koma na haɗa masa abinci, shinkafa da wake da mai da yaji dan bani da ko ƙwayar attaruhu
balle nayi miya ko jallof nasan kuma yanda yake fushin nan ba siyowa zeyi ba. Har ya zauna na manta
ban aje masa ruwa ba na koma na ɗakko da sauran zoɓo roba ɗaya daya rage Fadila bata shanye ba.
Yana ci ina satar kallon sa yanda kasan me cin guba, na tabba harda yunwa tasa shi ci ba tare da yayi
ƙorafi ba. Se da ya kammala ya dawo cikin falon kafin na matsa kusa dashi ina cewa
"Yanzu saboda Allah duk yanda nayi maka magana baka haƙura ba se da kace ta tafi? Haba Bilal, a zato
na ko can wata bare ce tazo gidan nan cin arziƙi ai beci ka koreta ba balle ƙanwar ka uwa ɗaya uba ɗaya
ashe ma duk faɗar da kake tana da matsayi a gurin ka duk surutu ne
gaskiya baka kyauta ba kuma ban ji daɗi ba gashi na kira wayar ta ma bata amsa ba nasan fushi tayi".
Kanzil bece mun ba, abu da me ciki abu kaɗan ke hasala ni u duk hidimomin su shara mopping yayi
shirin aiki ya fita. Se da ya tafi na tuna ban tambayeshi zan fita ba, a waya na kira shi nace masa zanje
gida na duba Amirah dan tayi zazzaɓi se yace na bari idan ya dawo se muje tare. Na sake gwada kiran
Fadila ta buɗe wayar amma haka ta ƙaraci ringing bata amsa ba se na kira Abubakar dan hankali na ya
kasa kwanciya ina so na tabbatar da lafiyarta tunda ko babu komai daga gida na ta tafi. Abubakar yace
mun ta koma can gidan su taje tana kuka ya tambaye ta meya faru taƙi gaya masa sanin da zeyi baze
wuce ita da Bilal bane shi yasa ma be biyo kadin dawowar tata ba kuma yau da safen ta tafi gidan Anty
Amina babbar yayar su. Ni dai tunda naji tana lafiya shikenan can su ƙarata da ɗan uwanta shi ya kore ta
ba ni ba.
Kwana uku tsakani Hajja ta dawo, ita da aka ce zatayi sati biyu. Tun ana gobe zata dawo ɗin Bilal ya gaya
mun dake naje gida na samo yan kuɗi se nayi amfani dasu nayo cafane nayi mata girki yan da naga Anty
Labiba tana yi idan surukar ta tayi tafiya ta dawo zata mata girke girke ta kai mata. Da wuri suka iso dan
asubanci suka yo kamar sanda zasu tafi, da la'asar bayan ya dawo aiki yayi wanka na kwashi kwanuka ya
goya ni a mashin muka tafi gidan, rabon ayi. Da ace nasan abin da yake jira na a gidan da ban yi giggiwar
zuwa mata sannu da zuwan ba. Da Yaya Uwani wadda Bilal yake bi muka fara cin karo a soro zata fita mu
kuma zamu shiga, da fara'a na shiga gaishe ta, irin kallon banzan data watsa mun haɗi da tsaki yasa jiki
na yayi sanyi laƙwas nabi bayan Bilal da dama be tsaya ba.
"Yanzu ke har kina da kunyar da zaki sake tako ƙafar ki cikin gidan uban Fadila?" Kalaman da Hajja tayi
mun maraba dasu kenan. Nayi zukuɗi ina ƙoƙarin tantance in da maganganun ta suka dosa amma na
kasa se kawai na zura mata ido ina jin irin fisaji da cin mutunchin data ke mun a maganganun nata nayi
nasarar gano akan Fadila takeyi. Bani kaɗai ba hatta iyaye na dake can gida basu san wainar da ake
toyawa ba se da suka amsa rabon cin mutunchi a gurin Hajjan,
"Daɗin abun tun kafin uban ki yasan zeyi arziƙi a duniya uban Fadila yayi da har zaki mata gorin gida
gidan ma na ɗan uwanta da idan ya faɗi ya mutu yanzu tana da gadon sa. Ko da yake ba laifin ki bane,
laifin sa ne daya barki kika bararraje har kike tunanin kin ci gida se wanda kika ga dama ze shiga ya
zauna" ta faɗa tana kumfar baki.
Sautin kukan da na keyi ƙasa ƙasa ya ƙaru, a duniya ka mun komai karka zagi iyaye na ko kaci mutunchin
su.
"Haba Hajja ki bari mana ya isa haka" naji muryar Bilal, se na ɗaga kai na kalle shi dan ban taɓa zaton
yana ɗakin a tsaye Hajjan take mun wannan tijarar kuma yayi shiru ba.
"Yanzu kana tsaye kana ji ana tuhumata da laifin daka aikata?" Na faɗa cikin kuka, ya kalle ni yace
"Allah shine shaida ta ban kori Fadila ba, idan kuma zata faɗi gaskiya ni ko kallon banza be haɗa ni da ita
ba balle nace ta bar gida. Ina ruwa na da zaman ta? Shi me gidan ai gashi nan shi yace baya buƙatar
zaman ta kuma Allah shaida sanda ya kore ta ma bana gurin kuma kana tsaye kana kallo ana tuhumata
ba zaka faɗi gaskiyar abinda ya faru ba" na ƙarasa ina kallon Bilal daya tsuke fuska yana muzurai.
"Ba shakka yau naga in da ake bariki, kai Bilal uwarka Halima na magana se ka rufe ni da duka saboda ma
mata ƙazafi". Maimakon ya kare ni se gani nayi ya juya ya fice daga ɗakin gaba ɗaya ita ko kamar an iza
wuta taci gaba da maganganu tana faɗar duk abin da yazo bakin ta. Daƙyar ina ganin dishi dishi na miƙe
jin tijarar bame ƙarewa bace, Allah ya taimake ni ina fita daga gidan na samu Napep kai tsaye na wuce
gidan mu. Ina rusa kuka na shiga gidan ba tare da na ko sallami me Napep ɗin ba ya biyo ni yana
tambayar kuɗin sa.
A ƙasa na zube ina cigaba da rusa kuka Mama dake kitchen ta fito kusan a guje tana tambayar waye?
Gani na yasa ta ƙaraso da sauri ta ɗago ni cikin tashin hankali tana cewa
"Meya samu Bilal ɗin?". Se da naji numfashi na na neman ɗaukewa kafin na haƙura na dena kukan
amma naƙi cewa komai tun Mama na tambayata harta tashi ta barni ta kira Abba a waya tace masa gani
nazo ina kuka naƙi cewa komai yace mata karta kira kowa gashi nan zuwa. Ina kwance ina jan rai, wani
irin azababben ciwon kai ya dirar mun lokaci ɗaya. Ina kwance riƙe da kai Abba ya dawo, tiryan tiryan na
kora musu yanda akayi tun daga zuwan Fadila har zuwa yau ɗin. Mama ta zabga tsaki tace
"Tun wuri ki nemi yafiya ta dan wlh kin ɗauki alhaki na gaba ɗaya kin tada mun da hankali na ɗauka ma
wani tashin hankalin ne ya afku" Abba ma miƙewa yayi yace
"Allah ya rufa asiri" daga haka ya fice daga ɗakin. Mama ta dira mitar ɗaga mata hankalin da kuka na yayi
kafin ita ma ta fita ta bani guri. Se naga su abun ma be dame su ba kenan, ba ma wanda ya sake bi ta kai
na se da akayi magriba Mama ta leƙo ni lokacin har baccin wahala ya fara fizgata kai na na ciwo sosai. Se
da naci abinci nasha magani nayi wanka kafin na kwanta. Bilal be kira ni ba har kuma bacci me nauyi ya
kawashe ni be zo ba se da safe Mama take cemun wai miji na yazo tayi ta tashi na ban farka ba shine
yace a barni kawai.
"Se ki maza ki gama abin da zakiyi Mu'azzam ya kai ki gida dan jiya har gurin sha ɗaya yana nan se kace
wanda aka ce za'a cinye ki" Mama ta faɗa. Nayi rau da ido nace
"Ni kuma a wane hurumi? Wannan ai tsakanin ku ne kun fi kusa shikenan kuma saboda kinyi ba daidai
ba maman mijin ki ta miki faɗa se na shiga na rama miki kike nufi ko me?" Mama ta faɗa. Se ko hawaye
suka ɓalle mun ta miƙe tana cewa
"Kin so dai ki ƙarawa kanki wata damuwar banda haka wanda ya siyi rariya ai dole dama yasan zata zub
da ruwa. Duk mutumin da Allah ya haɗa ka zama dashi se dai haƙuri da taka tsantsan kawai abinda ya
rigada ya faru kuma ai ya faru se dai ayi rigakafin wanda be zo ba" ta faɗa tana ficewa daga ɗakin.
Ba dan raina ya so ba se dan rasa goyon bayan Mama na tattara Mu'azzam ya kaini gida da yamma na
ringa share hawaye a hanya, an mun wulaƙanci na tafi gidan mu akan su shiga su ƙwatar mun yanci ba
daraja sun koro ni yanda gobe ma za'a ji daɗin sake ƙala mun abin da ban aikata ba aci mun mutunchi da
gangan. Yau na ga ranar Anty Labiba, ita kaɗai ce zata tsaya mun amma da nauyi abun daɗi be kaini
gidan ta ba yanzu se na kwashi matsala naje mata.
A gida muka tarar da Bilal, Mu'azzam be shiga ba ya gama sauke mun kayan da ban san dasu ba a nan
tsakar gida ya barsu yayi tafiyar sa. Ina ƙoƙarin saka key na buɗe ƙofar falo aka buɗe ta daga ciki Bilal ya
fito a wani hargitse kamar wanda ya kwana be runtsa ba yana gani na ya wani rungume ni da ƙarfi se
kace wanda ya shekara yana nemana se yau Allah ya bayyana masa ni, dana tuna yanda ya tsaya Hajjan
su na zagi na ya bece komai ba take ido na ya kawo ruwa na shiga ture shi amma yaƙi saki na seka ɗauka
ta da yayi cak ya wuce cikin ɗaki dani ina ƙoƙarin fizgewa be sake ni ba se da ya dangana ni da gado na
fashe da kuka sosai ina matsawa baya ya biyo ni yana cewa
"Me kike yi haka Halims? kin san irin tashin hankalin da kika jefani jiya kuwa? Me yasa zaki tafi baki kira
ni ba? Saboda Allah da kika je gidan me kika ce musu?"
Haɗe kai da guiwa nayi na shiga rera kuka, ya kaɗa ya raya nayi shiru na masa banza daya matsoni ze
sakani jikin sa kuma zan fasa wani kukan na janye se ya haƙura ya barni yana cewa
"Ni dai karki jiwa kanki ko abinda yake cikin ki ciwo na barki bazan sake taɓa ki ba amma ki dena wannan
kukan".
"Akan me zaka koreta kuma a ɗora mun laifi har azo ana zagin iyaye na da basu ji ba basu gani ba?" Na
faɗa cikin shashsheƙa. Kamar wani na Allah yayi ƙasa da kai kafin ya kwaso rantsuwa yace
"Ni na kore ta kenan kaima ka sake tabbatar da hakan?" Na faɗa ina fashewa da sabon kuka. Se ya taso
ya dawo in da nake ya jani jikin sa yace
"Ita tacewa Hajja kin barta da yunwa kuma da tayi miki magana ki bata abinci shine kika ce ba zaki bada
ba ta koma gidan mijin ta ko ta tafi gidan uban ta taci wai tazo ta takura miki ta hana ki sakewa a gidanki.
Tun kafin Hajja ta dawo ta kira ni ta gaya mun abinda Fadilan tace kin mata na kuma tabbatar mata
ƙarya be nasan ba zaki mata haka ba ita kanta se da na same ta na ja mata kunne shine ma nasa ta
tattara ta koma gidan ta kafin Hajjan ta dawo na ɗauka maganar ta mutu kin san Hajja ita kuma da ruƙon
magana in dai ba ta amayar ba bata jin daɗi amma nasan tunda ta rigada ta miki faɗa yanzu shikenan
maganar ta wuce musamman tunda ta tabbata hakan be faru ba ƙarya Fadila ta gaya mata". Haka ya
ringa lallashi na yana gaya mun maganganu har seda ya wanke baƙin sa da na gani na maida laifin
kacokam kan Fadila domin ita ta shirya komai na kuma yarda bashi da laifi abu ɗaya da naji ba daɗi da be
tsaya mun ya fitar da gaskiya ta a gaban Hajja ba, amma kuma dana tuna ita ɗin bata da daɗin sha'ani be
zama lallai ta fahimce shi a lokacin ba ta yuwu ma ta haɗa dashi yanda kuma take magana ba tare da
tauna kalami ba se ta faɗa masa wani abun mara daɗi da ze iya tasiri a rayuwar sa tun da mahaifiyar sa
ce.
Babu kunya kuma kwana biyu da yin haka da yamma ina zaune se ga Hajja da jikarta Mansura suka zo da
kwanukan abincin dana kai mata waccen ranar wai ta rakota ta bani haƙuri, ni abun ma se ya bani kunya
ya bani takaici. Ta ringa zagin Fadila tana cewa duk ita ta zugata se daga baya da Bilal ya zaunar da ita ya
mata bayani ta gane gaskiya tasan bata kyauta ba data hau kan magana kawai ta zauna ba tare da
bincike ba. Ni dai nayi ta Allah Allah ta tafi kafin ta sake samun wani abun da zata ce na mata laifi har
raina kuma na ƙudire tsakani na dasu gaisuwar mutunchi babu dogon zumunchi tunda na fahimci abun a
jinin su yake su rufe ido su ciwa mutum mutunchi idan abu ya haɗo ku daga baya kuma ba kunya su
waske.
*(Based on true life event, some parts are fictional to spice up the story)*
*LABARI/RUBUTAWA MARYAM FAROUK (UMMU-MAHEER)*
*Wattpad @MaryamahMrsAm*
*Ban yarda wani ko wata ya juya mun labari ta kowacce siga ba tare da izini na ba*
*Kuɗin karatu yana wakiltar mutum ɗaya ne, kiji tsoron Allah karki ɗauki hakkina ta hanyar fitar mun da
littafi*
*KURA A RUMBU littafin kuɗi ne, a biya naira 800, biya a asusun*
*1840175439*
*Access bank*
*Page 17*
Be ko saurari tayin abincin da na masa ba ya fice daga gidan bayan yayi wanka yana sake jaddada mun
Fadila ta bar gidan kafin ya dawo, bayan fitar sa na shiga gyara falon da tayi mun kaca kaca da shi dan
tun shigowar Bilal ɗin ta koma ɗaki na in da na sauketa. Na tabbatar taji banbamin da yakeyi tun da ba a
hankali yayi maganar da ze fita ba, na ɗauka daya fitan zata tuntuɓe ni da zancen amma shiru se ma
dawowa falo da tayi zata sake tarwatsa gurin na dakatar da ita ta hanyar ce mata ba nisa yayi ba yanzu
ze dawo. Ina kallon ta ta harare ni harda murguɗa baki ta koma ɗaki.
Ranar raba dare mukayi muna tashin hankali da Bilal tunda ya dawo gurin goma ya tarar Fadila bata tafi
ba ya tasa mun masifa tun ina bashi haƙuri da nuna masa rashin dacewar abinda yake son nayi har na kai
bango nace ba zan kore ta ba ai ƙanwar sa ce kuma gidan sa ne idan da gaske baya buƙatar zamanta ya
kore ta da kansa mana shikenan fa ina wuta ya sakani a ciki ya ringa zazzaga da tijara se naga ashe
abinda ya mun akan kifi ma somin taɓi ne. Dana gaji na kwanta na juya masa baya se dai na kasa bacci ga
ɗan Fadila da kamar ma sa gayya yake ta canyara uban kuka duk suka haɗu suka cazamun ƙwaƙwalwa.
Daƙyar na iya farkawa nayi sallah bayan dana samu bacci ya ɗauke ni, sosai kaina yake mun ciwo ga
zuciya ta da babu daɗi. Ina idar da sallah na sake komawa na kwanta ban farka ba se ƙarfe tara harda
wani abu. Se da nayi wanka sannan na fita daga ɗaki, Fadila na harɗe akan kujera da remote tana canza
tasha, yanda ta kalle ni se ka ɗauka kishiyar ta ce ta fito ta wani basar ta maida kai abinda takeyi nima
kallo ɗayan na mata na maida hankali na kan falon dake nan kamar yayi sati bega gyara ba ga kwanukan
abincin a ajiye har sun bushe alamar ba amfanin safiyar nan bane harda cup dana hango sauran shayi a
ciki.
Ji nayi zuciyata ta sake harzuƙa, ni ya kamata nayi jidali an kawo mun baƙuwa ba tare da an sanar da ni
ba kuma tazo tana nema ta mayar mun da gida wani dandalin yan datti ga wani sabon raini da ban santa
da shi ba tana nema ta fara gwada mun. Kitchen na wuce ba tare da na ce mata kanzil ba, ko me tayi
tunani kuma se ji nayi tace
Da lafiya na amsa mata na shige kitchen, nan ɗin ma kaca kaca komai yana zaune da ƙafarsa. Se da na
gyara gurin tas kafin na buɗe fridge in fito da abincin da Bilal yaƙi ci se in ɗumama mu haɗa da baƙin
shayi tunda banga alamar ya siyo abin karyawa ba, banga abincin ba se lokacin nayi realizing ai nama
wanke kwanon cikin kayan dattin dana tarar a kitchen ɗin. Tunanin wanda yaci na tafiyi, nasan ba Bilal
bane zuciyata ta raya mun Fadila ce.
Ina tsaka da jimamin irin wannan abu ta shigo kitchen ɗin tana haɗa fuska kamar zatayi kuka tace
"Kun san da masu jego a gidan saboda Allah se ku kwanta kuyi ta bacci? Ni wlh yunwa nakeji har jiri nake
gani asan yanda za'ayi dani".
"Wace abinci kuma kike nema bayan wanda kika ci?" Yanda tayi da ido kamae irin na mata ƙage se kuma
ta watsa ido tace
"Wai abincin cikin fridge? Yunwa ce ta hanani bacci tun dare naci wannan na duba ma naga ko da
dankali ko doya in soya mana naga babu se wani sauran bread na samu akan dining na haɗa shayi nasha
amma ji nakeyi ma kamar ƙara mun yunwar akayi". Tunda ta fara magana nake kallon ta har ta kai aya,
mamakin ƙarfin halinta nayi. Ɗan bread ɗin da take cewa fa kaɗan ne babu a guda in da dani da Bilal
muka ci har saura se yayi mana shine take cewa wai beje mata ko ina ba.
Rufe fridge ɗin nayi ba tare da nave mata komai ba na wuce store, banda shinkafa da ƙwarorin taliya da
macaroni babu abin da yayi saura a ciki, taliyar na ɗauka na haɗa da papper mix guda ɗaya daya mun
saura na dafa mana mukaci ina jinta a wasance tana cewa wai na bata abinci babu kifi babu nama nayi
kamar ban ji ba dan raina a ɓace yake bana so kuma na furta wani abu da daga baya ze zama abin
magana tunda naga su basa raina abin laifi. Bata tayani da ko cangwal ba na aikin gida se hayaniyarta
data ɗan ta data cika mun kunne. Ina gamawa na koma ɗaki na kulle ƙofa ta na bari akan tunda akwai
sauran taliyar taci da rana.
Tunda na kwanta bacci ya kwashe ni ban tashi farkawa ba se ƙarfe uku harda mintoci na rana. Sallah na
farayi kafin na leƙa naga halin da Fadila suke ciki, falon babu kowa se pillows dake hargitse kamar anyi
wasan dambe. Ɗaki na leƙa nan ma bata nan babyn ta ma baya nan balle nayi zaton ko banɗaki ta shiga.
Tunani na shigayi ina ta tafi? In da akwatin ta ke ajiye na duba nan ma babu hakan ya tabbatar mun da
fitar taje ta dawo tayi ba ƙila gida ta koma amma me yasa zata tafi bata gaya mun ba?
Ji nayi hankali na ya tashi, kar dai Bilal ya dawo ya kore ta, amma kuma da ya dawo gidan dole ze tayar
dani ko da yake tunda ba abin ƙwarai zeyi ba be zama lallai ya tashe ni ɗin ba tunda yasan zan hana.
Duk se naji babu daɗi, layin ta na shiga kira wayar tayi ta ringing ba'a amsa ba dana sake kira kuma se na
jita a kashe. Har na mayar da akalar kiran kaj Bilal se kuma na katse na bari idan ya dawo zanji dalilin da
yasa be haƙura ba ya koreta. Haka na ƙarasa wunin rai babu daɗi, biyar da rabi ya dawo sallama ma ciki
yayi be amsa sannu da zuwan da nake masa ba ya wuce ɗaki abin sa se na tashi na bishi. Ganin ya shiga
wanka se na koma na haɗa masa abinci, shinkafa da wake da mai da yaji dan bani da ko ƙwayar attaruhu
balle nayi miya ko jallof nasan kuma yanda yake fushin nan ba siyowa zeyi ba. Har ya zauna na manta
ban aje masa ruwa ba na koma na ɗakko da sauran zoɓo roba ɗaya daya rage Fadila bata shanye ba.
Yana ci ina satar kallon sa yanda kasan me cin guba, na tabba harda yunwa tasa shi ci ba tare da yayi
ƙorafi ba. Se da ya kammala ya dawo cikin falon kafin na matsa kusa dashi ina cewa
"Yanzu saboda Allah duk yanda nayi maka magana baka haƙura ba se da kace ta tafi? Haba Bilal, a zato
na ko can wata bare ce tazo gidan nan cin arziƙi ai beci ka koreta ba balle ƙanwar ka uwa ɗaya uba ɗaya
ashe ma duk faɗar da kake tana da matsayi a gurin ka duk surutu ne
gaskiya baka kyauta ba kuma ban ji daɗi ba gashi na kira wayar ta ma bata amsa ba nasan fushi tayi".
Kanzil bece mun ba, abu da me ciki abu kaɗan ke hasala ni u duk hidimomin su shara mopping yayi
shirin aiki ya fita. Se da ya tafi na tuna ban tambayeshi zan fita ba, a waya na kira shi nace masa zanje
gida na duba Amirah dan tayi zazzaɓi se yace na bari idan ya dawo se muje tare. Na sake gwada kiran
Fadila ta buɗe wayar amma haka ta ƙaraci ringing bata amsa ba se na kira Abubakar dan hankali na ya
kasa kwanciya ina so na tabbatar da lafiyarta tunda ko babu komai daga gida na ta tafi. Abubakar yace
mun ta koma can gidan su taje tana kuka ya tambaye ta meya faru taƙi gaya masa sanin da zeyi baze
wuce ita da Bilal bane shi yasa ma be biyo kadin dawowar tata ba kuma yau da safen ta tafi gidan Anty
Amina babbar yayar su. Ni dai tunda naji tana lafiya shikenan can su ƙarata da ɗan uwanta shi ya kore ta
ba ni ba.
Kwana uku tsakani Hajja ta dawo, ita da aka ce zatayi sati biyu. Tun ana gobe zata dawo ɗin Bilal ya gaya
mun dake naje gida na samo yan kuɗi se nayi amfani dasu nayo cafane nayi mata girki yan da naga Anty
Labiba tana yi idan surukar ta tayi tafiya ta dawo zata mata girke girke ta kai mata. Da wuri suka iso dan
asubanci suka yo kamar sanda zasu tafi, da la'asar bayan ya dawo aiki yayi wanka na kwashi kwanuka ya
goya ni a mashin muka tafi gidan, rabon ayi. Da ace nasan abin da yake jira na a gidan da ban yi giggiwar
zuwa mata sannu da zuwan ba. Da Yaya Uwani wadda Bilal yake bi muka fara cin karo a soro zata fita mu
kuma zamu shiga, da fara'a na shiga gaishe ta, irin kallon banzan data watsa mun haɗi da tsaki yasa jiki
na yayi sanyi laƙwas nabi bayan Bilal da dama be tsaya ba.
"Yanzu ke har kina da kunyar da zaki sake tako ƙafar ki cikin gidan uban Fadila?" Kalaman da Hajja tayi
mun maraba dasu kenan. Nayi zukuɗi ina ƙoƙarin tantance in da maganganun ta suka dosa amma na
kasa se kawai na zura mata ido ina jin irin fisaji da cin mutunchin data ke mun a maganganun nata nayi
nasarar gano akan Fadila takeyi. Bani kaɗai ba hatta iyaye na dake can gida basu san wainar da ake
toyawa ba se da suka amsa rabon cin mutunchi a gurin Hajjan,
"Daɗin abun tun kafin uban ki yasan zeyi arziƙi a duniya uban Fadila yayi da har zaki mata gorin gida
gidan ma na ɗan uwanta da idan ya faɗi ya mutu yanzu tana da gadon sa. Ko da yake ba laifin ki bane,
laifin sa ne daya barki kika bararraje har kike tunanin kin ci gida se wanda kika ga dama ze shiga ya
zauna" ta faɗa tana kumfar baki.
Sautin kukan da na keyi ƙasa ƙasa ya ƙaru, a duniya ka mun komai karka zagi iyaye na ko kaci mutunchin
su.
"Haba Hajja ki bari mana ya isa haka" naji muryar Bilal, se na ɗaga kai na kalle shi dan ban taɓa zaton
yana ɗakin a tsaye Hajjan take mun wannan tijarar kuma yayi shiru ba.
"Yanzu kana tsaye kana ji ana tuhumata da laifin daka aikata?" Na faɗa cikin kuka, ya kalle ni yace
"Allah shine shaida ta ban kori Fadila ba, idan kuma zata faɗi gaskiya ni ko kallon banza be haɗa ni da ita
ba balle nace ta bar gida. Ina ruwa na da zaman ta? Shi me gidan ai gashi nan shi yace baya buƙatar
zaman ta kuma Allah shaida sanda ya kore ta ma bana gurin kuma kana tsaye kana kallo ana tuhumata
ba zaka faɗi gaskiyar abinda ya faru ba" na ƙarasa ina kallon Bilal daya tsuke fuska yana muzurai.
"Ba shakka yau naga in da ake bariki, kai Bilal uwarka Halima na magana se ka rufe ni da duka saboda ma
mata ƙazafi". Maimakon ya kare ni se gani nayi ya juya ya fice daga ɗakin gaba ɗaya ita ko kamar an iza
wuta taci gaba da maganganu tana faɗar duk abin da yazo bakin ta. Daƙyar ina ganin dishi dishi na miƙe
jin tijarar bame ƙarewa bace, Allah ya taimake ni ina fita daga gidan na samu Napep kai tsaye na wuce
gidan mu. Ina rusa kuka na shiga gidan ba tare da na ko sallami me Napep ɗin ba ya biyo ni yana
tambayar kuɗin sa.
A ƙasa na zube ina cigaba da rusa kuka Mama dake kitchen ta fito kusan a guje tana tambayar waye?
Gani na yasa ta ƙaraso da sauri ta ɗago ni cikin tashin hankali tana cewa
"Meya samu Bilal ɗin?". Se da naji numfashi na na neman ɗaukewa kafin na haƙura na dena kukan
amma naƙi cewa komai tun Mama na tambayata harta tashi ta barni ta kira Abba a waya tace masa gani
nazo ina kuka naƙi cewa komai yace mata karta kira kowa gashi nan zuwa. Ina kwance ina jan rai, wani
irin azababben ciwon kai ya dirar mun lokaci ɗaya. Ina kwance riƙe da kai Abba ya dawo, tiryan tiryan na
kora musu yanda akayi tun daga zuwan Fadila har zuwa yau ɗin. Mama ta zabga tsaki tace
"Tun wuri ki nemi yafiya ta dan wlh kin ɗauki alhaki na gaba ɗaya kin tada mun da hankali na ɗauka ma
wani tashin hankalin ne ya afku" Abba ma miƙewa yayi yace
"Allah ya rufa asiri" daga haka ya fice daga ɗakin. Mama ta dira mitar ɗaga mata hankalin da kuka na yayi
kafin ita ma ta fita ta bani guri. Se naga su abun ma be dame su ba kenan, ba ma wanda ya sake bi ta kai
na se da akayi magriba Mama ta leƙo ni lokacin har baccin wahala ya fara fizgata kai na na ciwo sosai. Se
da naci abinci nasha magani nayi wanka kafin na kwanta. Bilal be kira ni ba har kuma bacci me nauyi ya
kawashe ni be zo ba se da safe Mama take cemun wai miji na yazo tayi ta tashi na ban farka ba shine
yace a barni kawai.
"Se ki maza ki gama abin da zakiyi Mu'azzam ya kai ki gida dan jiya har gurin sha ɗaya yana nan se kace
wanda aka ce za'a cinye ki" Mama ta faɗa. Nayi rau da ido nace
"Da yazo kin masa maganar abun da Hajjan su ta mun?"
"Ni kuma a wane hurumi? Wannan ai tsakanin ku ne kun fi kusa shikenan kuma saboda kinyi ba daidai
ba maman mijin ki ta miki faɗa se na shiga na rama miki kike nufi ko me?" Mama ta faɗa. Se ko hawaye
suka ɓalle mun ta miƙe tana cewa
"Kin so dai ki ƙarawa kanki wata damuwar banda haka wanda ya siyi rariya ai dole dama yasan zata zub
da ruwa. Duk mutumin da Allah ya haɗa ka zama dashi se dai haƙuri da taka tsantsan kawai abinda ya
rigada ya faru kuma ai ya faru se dai ayi rigakafin wanda be zo ba" ta faɗa tana ficewa daga ɗakin.
Ba dan raina ya so ba se dan rasa goyon bayan Mama na tattara Mu'azzam ya kaini gida da yamma na
ringa share hawaye a hanya, an mun wulaƙanci na tafi gidan mu akan su shiga su ƙwatar mun yanci ba
daraja sun koro ni yanda gobe ma za'a ji daɗin sake ƙala mun abin da ban aikata ba aci mun mutunchi da
gangan. Yau na ga ranar Anty Labiba, ita kaɗai ce zata tsaya mun amma da nauyi abun daɗi be kaini
gidan ta ba yanzu se na kwashi matsala naje mata.
A gida muka tarar da Bilal, Mu'azzam be shiga ba ya gama sauke mun kayan da ban san dasu ba a nan
tsakar gida ya barsu yayi tafiyar sa. Ina ƙoƙarin saka key na buɗe ƙofar falo aka buɗe ta daga ciki Bilal ya
fito a wani hargitse kamar wanda ya kwana be runtsa ba yana gani na ya wani rungume ni da ƙarfi se
kace wanda ya shekara yana nemana se yau Allah ya bayyana masa ni, dana tuna yanda ya tsaya Hajjan
su na zagi na ya bece komai ba take ido na ya kawo ruwa na shiga ture shi amma yaƙi saki na seka ɗauka
ta da yayi cak ya wuce cikin ɗaki dani ina ƙoƙarin fizgewa be sake ni ba se da ya dangana ni da gado na
fashe da kuka sosai ina matsawa baya ya biyo ni yana cewa
"Me kike yi haka Halims? kin san irin tashin hankalin da kika jefani jiya kuwa? Me yasa zaki tafi baki kira
ni ba? Saboda Allah da kika je gidan me kika ce musu?"
Haɗe kai da guiwa nayi na shiga rera kuka, ya kaɗa ya raya nayi shiru na masa banza daya matsoni ze
sakani jikin sa kuma zan fasa wani kukan na janye se ya haƙura ya barni yana cewa
"Ni dai karki jiwa kanki ko abinda yake cikin ki ciwo na barki bazan sake taɓa ki ba amma ki dena wannan
kukan".
"Akan me zaka koreta kuma a ɗora mun laifi har azo ana zagin iyaye na da basu ji ba basu gani ba?" Na
faɗa cikin shashsheƙa. Kamar wani na Allah yayi ƙasa da kai kafin ya kwaso rantsuwa yace
"Ita tacewa Hajja kin barta da yunwa kuma da tayi miki magana ki bata abinci shine kika ce ba zaki bada
ba ta koma gidan mijin ta ko ta tafi gidan uban ta taci wai tazo ta takura miki ta hana ki sakewa a gidanki.
Tun kafin Hajja ta dawo ta kira ni ta gaya mun abinda Fadilan tace kin mata na kuma tabbatar mata
ƙarya be nasan ba zaki mata haka ba ita kanta se da na same ta na ja mata kunne shine ma nasa ta
tattara ta koma gidan ta kafin Hajjan ta dawo na ɗauka maganar ta mutu kin san Hajja ita kuma da ruƙon
magana in dai ba ta amayar ba bata jin daɗi amma nasan tunda ta rigada ta miki faɗa yanzu shikenan
maganar ta wuce musamman tunda ta tabbata hakan be faru ba ƙarya Fadila ta gaya mata". Haka ya
ringa lallashi na yana gaya mun maganganu har seda ya wanke baƙin sa da na gani na maida laifin
kacokam kan Fadila domin ita ta shirya komai na kuma yarda bashi da laifi abu ɗaya da naji ba daɗi da be
tsaya mun ya fitar da gaskiya ta a gaban Hajja ba, amma kuma dana tuna ita ɗin bata da daɗin sha'ani be
zama lallai ta fahimce shi a lokacin ba ta yuwu ma ta haɗa dashi yanda kuma take magana ba tare da
tauna kalami ba se ta faɗa masa wani abun mara daɗi da ze iya tasiri a rayuwar sa tun da mahaifiyar sa
ce.
Babu kunya kuma kwana biyu da yin haka da yamma ina zaune se ga Hajja da jikarta Mansura suka zo da
kwanukan abincin dana kai mata waccen ranar wai ta rakota ta bani haƙuri, ni abun ma se ya bani kunya
ya bani takaici. Ta ringa zagin Fadila tana cewa duk ita ta zugata se daga baya da Bilal ya zaunar da ita ya
mata bayani ta gane gaskiya tasan bata kyauta ba data hau kan magana kawai ta zauna ba tare da
bincike ba. Ni dai nayi ta Allah Allah ta tafi kafin ta sake samun wani abun da zata ce na mata laifi har
raina kuma na ƙudire tsakani na dasu gaisuwar mutunchi babu dogon zumunchi tunda na fahimci abun a
jinin su yake su rufe ido su ciwa mutum mutunchi idan abu ya haɗo ku daga baya kuma ba kunya su
waske.
*(Based on true life event, some parts are fictional to spice up the story)*
*Wattpad @MaryamahMrsAm*
*TikTok @Maryamfarouk_Ummu-mahir Novels*
*Ban yarda wani ko wata ya juya mun labari ta kowacce siga ba tare da izini na ba*
*Kuɗin karatu yana wakiltar mutum ɗaya ne, kiji tsoron Allah karki ɗauki hakkina ta hanyar fitar mun da
littafi*
*KURA A RUMBU littafin kuɗi ne, a biya naira 800, biya a asusun*
*1840175439*
*Access bank*
*PAGE 18*
Haka rayuwa taci gaba da gangarawa; yau fari gobe baƙi. A yanzu da nake lissafa watannin aure na goma
sha biyar da Bilal shekara ɗaya da wata uku kenan, tabbas a zaman da mukayi nayi karatu da yawa
tattare da halayen sa waɗanda a baya ban san su ba. Babban abinda na fara naƙalta da Bilal shine
mutum ne me son abinsa. Tabbas Bilal nada son abin sa kuma ya kan iya rufe ido ya cima koma wanene
mutunci har idan ya shiga gonar sa, idan yayi wani abun se na shiga mamakin ta yanda har muka shafe
tsayin shekaru shida muna soyayya ya akayi ban taɓa fahimtar shi ɗin haka yake ba. Da fari abun ya
dame ni ko nace yana damu na, amma dana zauna nayi wani tunani na kuma yi amfani da maganar
Hausawa da suka ce idan mutum ya nuna yana son abun sa ka taya shi, se ku zauna lafiya. Hakan nayi
amfani dashi kuma nake zaune lafiya da Bilal.
Idan akwai abinda yake sosa mun rai wani lokacin be wuce yanda ni kullum na buƙaci wani abu a gurin
sa da yake ganin be zama dole ba ze rufe ido yaƙi mun amma ina kallo ko da bashi ne ze ci ya yiwa yan
gidan su. Tabbas ina jin babu daɗin hakan a raina; a ƙalla ko da ba a duk sanda na buƙata ba, na kan so
ace yana kamanta kyautata mun nima. Amma kuma wani sa'in idan nayi tunanin sai naga hakan ba
komai bane. Hajja mahaifiyarsa ce ita tilas ya hidimta mata suma kuma sauran yan uwan sa idan yayi
musu zumunchi yayi wa da wannan nake danne kaina musamman kuma da alhamdulillah duk abin da na
rasa a gurin Bilal na kan samu sama dashi a gurin iyaye na da basa gajiya da hidimta mun musamman
Abba kusan ko da yaushe naje gida ko mukayi waya ko wani cikin ƙanne na ze zo se ya bayar da saƙon
kuɗi ko abin amfani an kawo mun. Ita kanta Mama duk da yanda kullum Anty Labiba take cikin zugata
akai na wani sa'in taji wani sa'in ta toshe kunnenta; musamman tun da ciki na ya fara girma, wani tausayi
na take ji bini bini zata yo mun miya ta bayar a kawo mun se dai Bilal ya tafasa mana shinkafa ko taliya
muci.
Nayi zaton tun da ciki na ya fara girma Bilal ze yi tunanin ya kamata mu fara siyan kayan baby muna
ajiyewa, ban masa magana ba, saboda tun saɓanin da muka samu da babbar sallah akan naman layya
nayi alƙawarin ba zan saka masa baki a duk wani abu daya shafe shi ko kuma ya zama dolen sa ba.
Raguna guda biyu ya turke tun ana sallah saura kwana biyar wanda yace ɗaya Hafiz ne ya bashi ɗaya
kuma shi da Abubakar suka haɗa kuɗi suka siyawa Hajja. Ranar jajiberin sallah Babangida ɗan ƙanwar
Hajjan ne yazo ɗaukar Rago, guda ɗaya ya ɗauka ya tafi dashi ba'a rufa awa ɗaya ba se gashi ya sake
dawowa ina cikin ɗaki kukan ragon ne ya fito da ni dan sam banji motsin buɗe get ba ban ma san daya
fita be kulle mun ƙofar da kyau ba.
Ganin yana kici kicin kwance Rago yasa na dakatar dashi ta hanyar tambayar sa lafiya? Ina kuma za'a
kaishi?
"Hajja ce tace duka biyun za'a kai can gidan, na leƙo ina ta sallama na zata ma bacci kike baki amsa ba"
ya bani amsa. Mamaki ya kamani; me yasa za'a kai ragon kuma can gidan? Na tambayi kaina. Ban sake ce
musu komai ba ina tsaye ya gama kwance shi yaron da suka zo tare ya ja shi suka fita waje in da ya bar
mashin ɗin sa. Har na ɗauki waya zan kira Bilal a lokacin sr kuma na ce bari kawai se ya dawo, ina tsaka
da haɗa masa abin shan ruwa kuwa ya shigo. Daga yanda naga be damu da rashin ganin ragunan ba na
fahimci da sanin sa kenan aka kai can.
Se da aka sha ruwa bayan ya dawo daga sallar isha'i kafin na taso masa da zancen,
"Ni nace akai can dan nasan idan an bari a nan ke da kike fama da kanki ba iya aikin zakiyi ba ƙarshe ki
tara mutane su cinye" amsar daya bani kenan. Dama cike nake da haushin ƙin yi mun ɗinki da yayi
wannan sallar ma yace shi ba ɗinki ne a gaban sa ba ai ina da kaya na saka mana amma a gaba na ya
shigo da atamfofi uku harda lace ɗaya na Hajja da Fadila wadda ta sake dawowa gida zama yaƙi daɗi se
haushin ya zamar mun biyu ga wancan ga na ɗauke rago yanzu kawai na tashi na bashi guri ba tare da
nace komai ba.
Washe gari bayan an sakko daga sallar idi ya kira ni wai na shirya na tafi can gidan nasu muyi aikin nama;
se naji maganar ma kamar ta rainin wayau. Shi da yace ya kai can ne saboda ina fama da kaina ba zan iya
a gida na ba kuma yanzu in tafi taya su acan. Ce masa nayi kaina na mun ciwo se dai gobe, nayi kwanciya
ta haka na wuni ƙamshin suyar hanjin maƙwafta duk ya gama cika mun ciki na ringa ji kamar na yafa
mayafi na leƙa ɗaya daga gidajen a bani taɓi. Naci burin suyar naman sallah har spices na karɓo a gida da
naje amma ya wani ɗauka ya kai gidan su. Da magriba naji ba zan iya haɗiye kwaɗayi na ba kawai na kira
Mama nace ta bayar da hanji a kawo mun na ji daɗin da bata tsaya bin ba'asi ba tace toh ba a ɗauki
lokaci ba kuwa Imam ya kawo mun da zafin sa da alama sunyi daren aiki lokacin aka sauke.
A falo na zauna na baɗe hanjin da yajin daddawa ga zoɓo na me sanyi a gefe ina ci farin ciki na ratsa ni. A
haka ya shigo ya same ni; ya mun kallo ɗaya ya ɗauke kai. Ban damu ba na shiga yi masa sannu da zuwa
ya amsa a ciki ya wuce ɗaki ko me ya tuna kuma se gashi ya fito fuska a sake har ya zauna muka ci kayan
cikin tare yana mun mitar na rage cin yaji. A kitchen na tsunto farar leda daya ajiye da wani yan kayan
ciki kamar za'a bawa mage tun daga kalar suyar ma ji nayi zuciyata ta fara tashi na mayar in da na ganshi
na ajiye masa washe gari kuwa tun sassafe muka fita tare ya kaini can gidan su, yana fita nima na sulale
ban ko yiwa Hajjan sallama ba na tafi gidan mu shikenan salsalar laifin nawa. Har aka ci kwana uku da
sallah ban ga an aiko da namu rabon naman ba tsautsayi yasa nayi masa zancen shikenan ya balbale ni
da masifar da se da naji ina ban kula shi ba.
Wai har shi yake ce mun zalamammiya akan nama, dama tun da aka zo ɗaukan Ragon sun gaya masa
maganganun dana faɗa kawai shiru ya mun yanzun ma kuma yana sane ya hana a kawo dan yaga gudun
ruwa na amma na kasa haƙuri se da na tambaya ko mai se na nuna zalamata ba zan taɓa haƙuri na jira
naga abu ze tarar da ni ko kuwa se in fara maganganu ina kai magana gidan mu. Na ringa juya maganar a
raina wai nice zalamammiya. Kuna ya rasa akan me ma ze mun cin mutunchin se akan nama, naman da
bayan soyayye da dambu da kilishi har ɗanye aka kawo mun daga gidan mu na saka a freezer amma
shine yake faɗin nayi zalama akai.
A duk abinda yake mun babu wanda naji ciwon sa irin wannan duk yanda naso na danne zuciya ta kar na
maida masa da martani na ƙasa daga ƙarshe nace masa zalamamme ya san kansa domin tun kafin a
kawo lokacin ze ɗauki naman layya ya bani ni na bashi yafi sau ba adadi. Ina wuta kuma ya jefani a ciki?
Daga martani yace na masa gori, ya ringa jidali kwana da kwanaki be sauka ba se da yaga na kwanta riris
rai a hannun Allah muka je asibiti aka ce jini na ne ya hau kuma shikenan haka suka cinye naman ko
tsoka ɗaya ba'a bani ba ƙarshe ma saboda rashin kunya cikin nawa ya ringa ɗiba yana bawa abokanan sa
idan sun zo ni dai nawa ido kawai dan lamarin Bilal ya fara shallake mamaki tsoro ya fara bani.
A haka ciki na ya shiga wata na takwas har ya kusa tara amma ko pant be siya ko ya bani na siya ba. Ban
damu ba; saboda cikin abinda nake samu na siyi duk wani abu na buƙatar farko irin wanda nake so. Abin
da na sakawa raina shine ba zan taɓa tsayawa jiran Bilal a komai ba, idan ya ɗakko ya bani fine idan ma
be bani ba zanyi wa kaina na sakawa raina komai lokaci ne akwai ranar da dolen sa ze yin.
Tafiya ta taso wa Bilal zuwa Enugu zasu halarci wani taron bita. Tafiyar kwana huɗu ce, tunanin yanda
zanyi na shiga yi dan bazan iya zama ni kaɗai ba. Da farko nayi tunanin ko na tafi gida se kuma na canza
shawara kawai tun da Amirah suna hutu se na kira ta ta taya ni zama kawai. Da ze tafi yace mun
Abubakar ze zo ya zauna a gidan kafin ya dawo, dake an gyara fallen ɗakin dake tsakar gida nan ya fito
masa da katifar ɗakin sa tunda akwai banɗaki ze zauna a gurin.
Dubu goma ya bani yace idan na fita awo washe gari se na biya nayi yan tsince tsince kafin ya dawo
muga sauran abinda za'a siya.
Mama na kira na gaya mata Bilal yayi tafiya Amirah tazo ta taya ni zama da yamma kuwa se gata, ni shaf
na sha'afa ban gaya masa zan kirawo Amirahn bama se washe gari da muna waya yaji muryar ta yake
tambaya ta yaushe tazo na sanar masa tun jiya na kirata.
"Amma da kin gaya mun zata zo ai ba se Abubakar ya zo ba shi" ya faɗa se nace masa
"To yanzu ban da abinka meya haɗa zaman Amirah dana Abubakar? Na ɗauka ya zo ne saboda ko da
wani abu na emergency ze tashi akwai namiji a gida ita kuma kasan ai ina buƙatar me kama mun
ayyukan cikin gida shara da sauran su tun da kai kake yanzu kuma baka nan koma ba haka ba idan ciwo
ya tasar mun cikin dare Abubakar na can waje ta yaya za'ayi yi ya sani?"
"Toh ai da kawai se kiyi tafiyar ki gida idan na dawo se ki dawo amma meye amfanin a cika gida da
mutane" ya sake faɗa, se nayi shiru kawai dan nawa kaina alƙawarin dena biye masa amma har raina naji
zafin maganar zuwan Amirah yake nufin an cika masa gida da mutane tunda shi ya kawo Abubakar ai. Da
yamma muna zaune Abubakar ya shigo bayan mun gaisa yace mun ze wuce gida, ban tambayi ba'asi ba
tunda na san dalili mukayi sallama ya tafi. Har ya kwana huɗun sama muke gaisawa in ya kira sau ɗaya
shikenan shima ba wata doguwar hira zamuyi ba ze kashe. Haka ya dawo yana ta wani fizge fizge ni kam
ko a jiki na dan babu in da Amirah zata je ma se na haihu tunda hutun su da saura sosai.
Kwanan sa biyu da dawowa be dai ce mun komai akan zaman da takeyi ba amma yanayin sa na fahimci
ba'a son ransa ba, to mutumin daya kori ƙanwar sa ciki ɗaya ma me ze dame ni dan ya nuna baya
maraba da zaman tawa ƙanwar?
Kwana biyun a nan cikin ɗakuna na yake kwana rana ta uku da dawowar sa ya koma can part ɗin sa,
dana masa magana se cewa yayi wai babu privacy yana son ya sake babu dama saboda Amirah.
Murmushi kawai nayi na rabu dashi, da dare yayi na bishi can ɗakin yace da nayi zamana ai be kamata na
barta ita kaɗai ba; se kace wata jinjira; ko a fuska ban nuna masa na fahimci abinda yake nufi ba. Dan ya
kori yar uwarsa ni bazan bashi ƙofar da ze hana nawa yan uwan zuwa ba. Haka muka cigaba da zama
idan ya shigo ta gaishe shi se dai ya amsa a fizge ya wuce wani lokacin ma baze amsa ba Amirah da
saurin fushi tace ta dena gaishe shi tunda ma abun nasa wulaƙanci ne.
Ganin duk hakan be sa nayi fushi nace ta tafi ba har an cinye sati ɗaya se ya canza salo ta hanyar rage
cefane. Dama maneji nakeyi; a irin rayuwar dana tashi cikin ta soyayya ce kawai ta rufe mun ido bana
ganin gazawar Bilal a riƙon gida.
Duk da Mahaifina ba wai shahararren mai kuɗi bane irin yanda mutane suke ɗaukar sa; shi ɗin mutum
ne da idan ya samu naira ɗari ze kashewa iyalansa hamsin ya rabawa al'umar annabi hamsin. Baya tara
kuɗi; kuma a koda yaushe yana gaya mana jin daɗin da yake gwada mana a yanzu shi kaɗai ne abinda ze
bar mana koda bayan ransa mu ringa tunowa muna amsa addu'a. Musamman Mu'azzam da yake biyewa
abokai suna hura masa kai ɗan Alhaji yaƙi mayar da kai ga karatu Abban yana yawan tunasar dashi akan
ya tashi ya nemi na kansa. Ya kance
"Sanda mahaifina ya rasu gidan gadon mu kaɗai ya bar mana kuma munfi mu talatin akai wanda ko cewa
akayi a ɗaga shi a siyar a lokacin da wuya mu tsira da naira goma goma. Ban dan daɗin kuɗi ko kadarar
gado ba balle nayi kwaɗayin tara muku, abun da na fi yarda dashi ka gina yayanka ta yanda zasu rayu su
riƙe kansu ba tare da tunanin dogaro da wani ba shine babban gadon da zaka bar musu dan haka ku
tashi ku nemi na kanku jin daɗin rayuwa kam babu wanda ba zan baku ba har idan ina da hali amma
karku taɓa sawa a ranku zan tara muku dukiya".
Duk wata cima ta jin daɗi muna cin ta a gidan mu shi kansa Bilal ɗin shaida ne, abinci se dai sha'awa tasa
mu yishi babu nama ko kifi ba dan babu ba amma wai nice a gidan Bilal se in jera wata nama be shiga
cikin tukunya ta ba balle aje ga tsire ko balangu idan ba muna tsananin yar daɗi bane ze siyo kuma ya
cinye rabi in kwaɗayi ya dame ni se dai na bayar da kuɗi na ya siyo kuma ya fini ci. Dankali da doya kam
banda albakacin na azumi dana samu na manta rabon dana sarrafa su a cikin gidan tun da kuma suka
ƙare aka koma gidan jiya tun ma ina kwaɗayin har na haƙura. A ma ce su nama ba abu bane na kullum
hatta da kayan miya da kamar gaske ze siyo da ɗan yawa a ajiye daga baya yace wai ɓarnar su nakeyi
saboda na gansu a banza se dai kullum ya siyo ko ya isa ko karya isa oho wani sa'in se na gwammace nayi
mai da yaji dan kayan miyan ba zasu wadace ni yanda nake so ba musamman idan miya zanyi nan kuma
se ya fara bala'i yace ina kira masa tsiya a gida nayi mai da yaji. Abu dai iri iri ni kaɗai nasan me nake
shanyewa, ina buƙatar wanda zan tattauna dashi ya bani shawara kuma duk wanda nayi tunani se naga
dariya zasu mun su ce dama sun faɗa naƙi ji se kawai na bar damuwata a raina kullum addu'a ta da
fatana Allah ya canza mun shi kyawawan halayen sa su rinjayi na banzar dan dai yanzu sun yi kankan
kan.
Tun daren jiya nake ji na ba yanda na saba ba; yau ɗin mun tashi da walwala a gidan dan a ɗakin Bilal na
kwana kusan kwana goma kenan tun bayan dawowar sa ya ƙaurace mun duk saboda Amirah. Se da ya
fita aiki sannan koma na kwanta ina jin ciwon marar dake tsikarata idan ya tsinka sakan biyu uku kuma
se ya sake ni shikenan se wani lokaci. Tunani nayi ko didimar da muka sha ce ta janyo dan daman nasan
dole zanji jiki saboda yanda dani dashi ɗin duk muka manta da cikin gashi yanzu ni nake ji a jiki na.
Sanin se yamma ze dawo da Amirah ta tambaye ni me nake so naci nace ta mana taliya da manja; yar
murji ce da jiya ta taho mana da ita daga gida. Ina bacci naji kamar ana shafa fuskata, hankali na buɗe
ido naci karo da Bilal dake durƙushe kaina yana mun murmushi. Hanci na yaja yana cewa
"Gudowa nayi, duk kin tara mun gajiya so kawai nake na kwanta na huta" ya faɗa yana kashe mun ido
ɗaya. Kasa nayi da kaina ina murmushi kafin na sauke ƙafafu na ƙasa ina cije leɓe saboda wani sharp
ciwo daya ziyarce ni lokaci ɗaya kuma ya baje.
"Yunwa nake ji Halims me kuka dafa?" Ya faɗa yana shafa cikin sa. Na kalle shi, kamar in ce masa ai
yasan cefanen mu ya ƙare be siyo ba kuma be bada kuɗin siyowa ba amma bana so nayi ruining ɗan
farincikin da muka samu jiya zuwa yau se kawai nace
"Taliyar Hausa ce; bari nayi sallah lokaci na tafiya se na zuba maka" na ƙarasa ina nufar banɗaki. Yamutsa
fuska yayi kafin yace
"To bari nayi fitsari" na sake faɗa ina shigewa ciki. Daƙyar na miƙe bayan nayi fitsarin saboda yanda naji
ɗan ciki na ya takure mun a mara kamar yana danno ni. Alwala nayi na fito ina dafa bango, ganin baya
falo yasa na ƙwalawa Amirah kira ta fito daga ɗaya ɗakin da alama bacci ma takeyi se nace mata ta
haɗawa Bilal abinci zanyi sallah na koma ciki.
A zaune na tada sallar dan bazan iya tsayuwa ba, ina raka'a ta uku na jiyo hargagin Bilal; bana jin me
yake cewa se tashin muryar sa kawai kafin na jiyo ƙarar buga ƙofa bam. Ban ko tsaya addu'a ba ina
sallamewa na miƙe daƙyar ina dafe baya na da ya ɗauki ciwo na fita falon; da fasasshen tangaran na fara
cin karo se taliya da manja sunyi kaca kaca akan milk ɗin center carpet ɗina. Na buɗe baki zan kira
Amirah se gata ta fito daga ɗaki tana jan akwatin ta fuska shaɓe shaɓe da hawaye kafin nace wani abu ta
riga ni da cewa
"Wallahi tallahi darajarki kawai yaci, badai ya zagi ubana a cikin gidan sa yana ganin yaci banza ba? Allah
yasa yayi gigin zuwa gidanmu wallahi se na nuna masa nima na iya rashin kunya" ta faɗa cikin kuka.
"Ke Amirah baki da hankali har tinƙaho ma kike da kin iya rashin kunya kamar wata me faɗar abin arziƙi
wai ma tukunna dawa kike?" Na dakatar da ita. Ba tare da shakkar komai ba tace
"Dawannan butulun mijin naki da be dan halacci ba mana. Wai saboda na kawo masa taliya shine ya jefe
ni da farantin ba dan Allah ya saka na goce ba ƙila da yanzu shirin jana'izata ake ya yanka mun wuya har
yana zagin Abban mu yana ce masa matsiyaci mun zo zamu shafa masa tsiya a gida bayan shine babban
matsiya ci..." Kafin ta dire na kwashe ta da marin da se bayan na aikata kuma nadamar yin sa ta kamani;
dakewa nayi na shiga yi mata faɗa ina cewa
"Tarbiyyar da kika koyo a boarding ɗin kenan ta raina mutane saboda baki da mutunchi a gabana kike
cewa miji na matsiyaci?"
"Ubana fa ya zaga; kenan kin bi bayan mijin ki ko?" Ta faɗa tsabar yanda take jan kuka da magana a haɗe
kamar numfashin ta ze ɗauke.
"Zo ki fita daga gidan nan kafin na karya ki dan abu ta kazan ubanki" Bilal daya shigo yana naɗe belt a
hannun sa ya faɗa; Amirah ta zabura cike da rashin kunya tace
"Meye haka Bilal da Amirah zakayi faɗa saboda zubar da girma wannan wane irin abu ne?"
"Matsa mun Halima ko in haɗa dake da ita na koya muku tarbiyyar da ba'a muku a gida ba, ni wannan
tatsitaiyar yarinyar zata cewa matsiyaci kina tsaye kina kallon ta har kizo mun da wata maganar banza?
Da Allah malama matsa tun baki ja nayi abin da za'a ɗaure ni ba" ya faɗa yana ture ni gefe; dake ban zata
ba se na tafi luu Allah ya taimake ni na dafe kujera Amirah ma ta riƙe ni. Belt ɗin ya ɗaga da niyyar dukan
ta duk da azabar da nake ji saboda faɗuwar bazatan dana kusan yi ta tsinkar mun da zuciya haka na riƙe
belt ɗin ina kuka nace
"Wlh se dai ka dake ni; har idan ka dakar mun ƙanwa se kayi nadamar hakan Bilal ina mai tabbatar maka
da haka"
"Ni kike cewa zaki zaka nayi nadama Halima saboda zan hukunta mara tarbiyyar ƙanwar ki?" Ya faɗa
yana nuna kansa idanun sa suna sake rikiɗewa da ɓacin rai. A ƙasa ya jefar da belt ɗin ya nufi ƙofa yana
cewa
"Wallahi tallahi har idan na dawo na same ta a cikin gidana se na mata abinda idan an ga dama a kaini
kurkukun ƙasan ruwa" yanda yayi furucin ba ƙaramin tsorata nayi ba; jiki na ya ɗauki rawa kamar mazari
a ƙwaƙwalwa ta so nake na tantance da gaske Bilal ne ko wani daban? Ko kuma ya fara watsa ƙwayoyin
gusar da hankali ne bani da labari?
Ji nayi ciwon dake taso mun ma ya kama gaban sa, na yunƙura Amirah na riƙe dani tace
"Ni dama na daɗe ina zargin yana shaye shaye; daga yanda yake yi da idon sa baya ma iya buɗe su da
kyau za'a gane. Kowa se da yace karki aure shi kika ƙi, gashi nan ashe mahaukaci kika aura bamu sani ba"
ta ƙarasa tana fashewa da sabon kuka.
*(Based on true life event, some parts are fictional to spice up the story)*
*Wattpad @MaryamahMrsAm*
*Ban yarda wani ko wata ya juya mun labari ta kowacce siga ba tare da izini na ba*
*Kuɗin karatu yana wakiltar mutum ɗaya ne, kiji tsoron Allah karki ɗauki hakkina ta hanyar fitar mun da
littafi*
*KURA A RUMBU littafin kuɗi ne, a biya nairag 800, biya a asusun*
*1840175439*
*Access bank*
*Page 19*
Ba zan iya cewa ga ta yanda muka fita daga gidan ba ni dai kawai na san munje gidan mu; muna sauka
daga Adaidaita sahu Amirah ta sake ni na dafe gini saboda jirin dake kokawar kayar dani ita kuma ta tura
ƙofar get ta shiga tana rushewa da kuka tamkar wadda tazo isar da saƙon mutuwa. Daƙyar na cira ƙafata
na rufa mata baya ina yi ina dakatawa saboda ciwon marar dake taso mun, na dafe ƙofar shiga falon na
tsaya ina kallon mazauna ciki da suka rufu kan Amiran cikin tashin hankali suna tambayar ta ba'asin
kukanta; tabbas idan na canka dai dai kowannen su abu guda yake ayyanawa shine wani mugun abun ne
ya same ni.
Ƙarasawa nayi ciki ina cije leɓe, Abba ne ya fara gani na; "Alhamdulillah" ya furta a fili yana nufo ni hakan
ya ankarar da Mama da Anty Labiba suka waiwayo. A ƙasa na zauna duk suma suka zauna suna kallon
Amirah da har sannan take kuka ni ɗin ma ita nake kallo ina mamakin wannan dirama tata. Abba ne yayi
mata tsawa; cikin hasalar da sam ba ɗabi'ar sa bace ya nuna ta yana cewa
"Ga dai yar uwarki lafiyarta ƙalau, tun banyi loosing temper ba Sauda ki faɗa mun me akayi miki kike
wannan kukan" ya ambaceta da ainihin sunanta wanda kuma sunan Mahaifiyar su Mama ne.
"Ai wlh dab nake da kai mata duka; duk a zato na wani abu ne ya samu Haliman se gata da ƙafafun ta ta
shigo amma dan iskanci shine ta shigo tana irin wannan kukan me tsinka zuciya" Mama ta faɗa, ba
tareda Amirah ta dakata da kukanta ba gaba ɗaya tace
"Ai Allah ne kawai ya kiyaye da ba lallai ta dawo da ƙafarta ba se dai a shigo muku da gawarta; Bilal ne ya
rufe mu da duka, Allah ne kawai ya ƙwace mu a hannun sa da ƙila duk mu biyun ma ze kashe muku" ta
ƙarasa tana sake rushewa da wani kukan daya fi na farko. Duk su ukun ni suka zubawa ido in da ni kuma
na kafe nawa kallon kan Amirah mamakinta na neman dakatar mun da numfashi.
"Ai dan kar in magana ne ace na faɗi abinda ba shikenan ba amma dama ina ganin su nasan Bilal ne; ai
kuwa billahillazi ya dakarwa kansa masifa da bala'i yau" Anty Labiba ta faɗa tana miƙewa tsaye. Hannu
Abba ya ɗaga mata yana kallo yace
"Dakata Labiba, Halima gaya mun meya faru, gaskiya ne abinda ƙanwar ki ta faɗa?"
Ajiyar zuciya me nauyi na sauke haɗi da maida kallo na ƙasa; cikin muryata da firgicin abinda ya faru a
can gidan ya dasa mun na ce
"Ba gaskiya ta faɗa ba Abba, babu abinda Bilal ya mana kawai dai..."
"Wallahi ƙarya takeyi Abba dukan mu yayi kuma ya ringa zaginmu yana ce mana yayan matsiyata marasa
tarbiyya sannan yace mu bar masa gida kafin ya dawo idan ba haka ba se yayi mana abinda za'a ɗaure
shi" Amirah ta katse ni.
Jikin Anty Labiba kamar wadda ta taɓa wayar wuta har wata girgiza take tace
"Shi Bilal ɗin?" Se ta nufi ƙofa. A tsawace Abba ya kira sunan ta yana nuna mata kujera, na tabbatar
tsananin yanda take ganin mutunchin sa yasa ta dawo ta zauna, yanda take kaɗa ƙafa yasa na ja jikina na
matsa gefe domin kada mutanen ta su kawo ziyara ta fara ta kaina. Kallon Amirah Abba yayi da yanayi na
ɓacin rai ya nuna ta da yatsa yace
"Ita yayar taki kike ƙaryatawa ko? In sake jin bakin ki a nan gurin har idan ba ni na nemi kiyi magana ba".
Se ya sake juyowa kaina yace
"Ina jinki".
"Amirah ce, ban san meya haɗa su ba tayi masa rashin kunya har tana ce masa matsiyaci, shine yace ta
bar masa gida". Falon yayi shiru hatta da Amirah dake kuka ta dakata ina kuma jin dirin idanunsu a kaina
amma ban yarda na ɗaga kai na ba,
"Me ya haɗa ki da Mijin Yayarki har kika zage shi Amirah?" Abba ya tambayeta.
"Wallahi Abba babu abinda nayi masa, kawai ina bacci ta tashe ni tace na zuba masa abinci zatayi sallah;
shikenan daga na ajiye masa abincin yayi bal da farantin Allah ne ma ya rufamun asirin ban yanke ba dan
fashewa yayi ƙwalaben duk suka bazu a falon shikenan fa ya fara masifa yana zage zage wai mu yayan
matsiyata ne mun dafa masa taliya fara da manja bayan kuma be siyo kayan miyan ba balle a dafa masa
da miya. Ya ringa zaginka shine ni kuma na gaji nace ba dai ubana ba; shine y ɗakko belt lokacin Yaya
Halima ta fito daga ɗaki ya hau dukana yana zagi na data zo zata kare ni shine ya ture ta ta faɗi ya haɗa
dani da ita rufe mu da duka yana cewa wai ze koya mana tarbiyyar da ba'a bamu a gida ba" ta ƙarasa
tana fashewa da sabon kuka.
Mama dai kamar bata gurin Anty Labiba ko banda kaɗa ƙafa ba abinda takeyi.
"Kiji tsoron Allah Amirah; yaushe akayi haka?" Na faɗa ina kallonta kafin na juya kan Abba nace
"Wallahi ƙarya takeyi Abba be doke ta ba kuma ni banji sanda ya zageta ba kawai nasan yayi mata
hargagi yace ta taho gida kuma ita ta zage shi ta masa rashin kunya".
"Kinyi asara Halima, namiji ya zagi iyayenki har ya kira ki mara tarbiyya sannan kizo kina kare shi wallahi
kinji ɓutur, namiji dai kika ɗauka uba ko? Zako ki mutu marainiya. In dai Bilal ne gaki gashi nan ko yau be
dake ki ba muna nan ranar zata zo Halima zaki san ki fifita son miji akan mutunchin iyayenki" Anty Labiba
ta faɗa tana miƙewa, saboda fushi babbar rigar Abba ta shiga fizga a zaton mayafin ta ne dake ajiye kusa
da shi dan duk zaburar data ringa yi ɗazu zata fita babu gyale akanta. Gyalen Abban ya miƙa mata ta
fizge ta fita tana sake nanata
"Halima kinyi asara, Halima zaki gane baki da wayo a hannun namiji".
Se lokacin Mama ta sauke ajiyar zuciya ta tashi ta bita ba tare da tace komai ba, Abba ya kalle ni yace
"Ina ita kaɗai yace t taho gida ko harda ke?" Se na fashe da kuka nace
"Abba ransa ya ɓaci sosai, ina tsoron na zauna kuma ma ni bani da lafiya, marata ciwo take mun".
"Tashi mu tafi Asibiti" ya faɗa yana miƙewa tsaye, sunan Asibitin daya faɗa se naji kamar an mun
busharar ciwo lokaci ɗaya wani ciwon baya da mara da bansan yanda zan misaltasu ba suka kawo mun
ziyara. Hannu na shiga yarfewa ina cewa
"Bazan iya tashi ba, wayya Allah ina ga ma mutuwa zanyi ni dai". Kiran Mama ya shigayi da ƙarfi se gata,
ganin yanda nake dafe ciki ina nanata mutuwa zanyi yasa ta koma da baya se gasu tare da Anty Labiba.
Tare suka kamani suka sani a mota. Cikin ikon Allah da zuwan mu asibiti ban fi awa ɗaya ba na haifo ɗan
ƙaramin ɗana me tsananin kama da Bilal.
Anty Labiba ce taje ta siyo kayan da aka sakawa yaron da sauran abubuwan da zan buƙata kamar pad da
pant, kayan jikina dake dama riga d zani ne muna shiga na yaye zanin dan haka dana gyara jiki na nayi
wanka su na mayar duk se nake jin ƙyamar jikina. A hannun Anty Labiba na tarar da yaron bayan na fito
daga labor room ɗin, ta mun kallo ɗaya ta watsar dani da alama duk lahaula da salatin data ringayi tana
safa da marwa a bakin labor room duk na lokaci ne ba wai ta manta da fushi na dake ranta bane. Mama
kanta a fizge ta mun sannu tareda tambayar badai abinda nake ji nace mata eh, Abba ne kaɗai ya ringa
jera mun sannu yana mun addu'a kafin ya fita ya bamu guri.
Duk se naji jiki na yayi sanyi, na kwanta akan gado ina satar kallon su biyun Anty Labiba na riƙe da Baby
Mama kuma na ƙoƙarin haɗa mun shayi ta gama ta miƙo mun se ta ɗauki Hijabin ta ta saka tana kallon
Anty Labiba tace
"Bari naje gida Labiba naga idan Hasana tayi abinda nace mata; kin santa da shirme. Idan suka kawo
abincin ita se ta zauna ta kwana dasu ki tafi gida ko?" Bata jira amsar ta ba ta juyo kaina tace
"Se ki kira shi ki gaya masa za'a zo a ɗaukar miki kaya kar kuma yace an shigar masa gida ba izini".
Anty Labiba dai bata ce komai ba se ɗaukar Babyn hoto da take a wayar ta haka Mama ta fita ta barmu
kusan minti biyar a raina na tafi tunanin ko sun gayawa Bilal na haihu?
Anya kuwa? In da ya sani nasan baze kasa zuwa ba ko wani nasa, ina so na tambayi Anty Labiba aron
wayar ta na kirashin amma babu fuska se kawai na kama kaina na kwanta kawai, shi kansa Babyn ina
kwaɗayin na riƙe shi a hannu na na sake tantance kamannin sa dana hanga daga nesa amma nayi ƙarya
nace ta bani shi.
Kamar ta shiga zuciyata kuwa se gata ta miƙe ta iso kusa da gadon ta aje mun babyn tare da wayarta
kafin tayi ficewarta waje. Nayi murmushi a fili nace
"Antyna ta kaina kenan iyayen daru". Shagala nayi da kallon Babyn da kamar yasan guri na aka kawo shi
ya fara motsa baki yana wulla yan ƙafafun sa da hannayen sa. Na ɗauke shi na rungume shi, wani
farincikin mara misaltuwa ya tsarga rai da ruhi na. Na tuna sanda nake yiwa Hansa'u tsiyar bata da
kunya, a hotunan sunan yarta data haifa wata biyu kenan, ƙiri ƙiri Bilal ya hanani zuwa Abuja sunan
bayan har Maman mu se da taje. A kowanne hoto data tura mun tana rungume da yarinyar kamar za'a
ƙwace mata ita da nace bata da kunya tace mun bazan gane ba se ranar dana riƙe nawa ɗan zan fahimci
ba rashin kunya bane.
Motsin ƙofa yasa nayi saurin raba shi da jiki na na zata Anty Labiba ce kafin ta fara mun taratsi ashe
nurse ce, ita ta taimakamun tare da koya mun yanda zan shayar dashi. Dake tun kafin na haihu dama
ruwan nonon ya fara kawowa dan haka ba ɓata lokaci ya kama kamar dama a yunwace yake. Tana tsaye
har ya ƙoshi kafin ta karɓe shi ta sakashi a kafaɗa tana nuna mun yanda zan sakashi yayi gyatsa. Bacci ya
koma ta kwantar dashi tace na shanye shayin da aka haɗa mun zata yi mun allura ne. Se lokacin na tuna
ban ma kira Bilal ɗin ba, seda ta gama abun da zata mun ta fita kafin na danna lambobin sa a wayar Anty
Labiba takaici da dariya suka kamani lokaci ɗaya ganin sunan data masa saving, wai BILAL BATI. Lallai
Anty Labiba ta raina mun miji.
Kira uku nayi masa be amsa ba, dake ana shirin shiga sallar magriba ne se na bashi uzurin ƙila ko yana
alwala ko ma ya shiga masallaci ne. Hotunan da tayiwa Babyn na shiga dubawa ina murmushi ni kaɗai,
shigowar ta tare da su Mama Fauziyya yasa na aje wayar. Har ƙarfe goma wasu daga cikin yan uwan
Mama da suka zo harma dangin Abba basu tafi ba. Ashe har tayi sanarwar haihuwar a group ɗinmu na
family ta kuma tura hoton Babyn shi kuma Mu'azzam ya ɗauka ya tura ana ɓangaren Abba. Tunda nace
mata ban samu Bilal ɗin ba se kawai tayi waya gidan ta aka ɗakko mun dogayen riguna dan kiba kawai ta
fini da tsayi kaɗan kowa cewa yake ita na gado a rashin auki to yanzu cikin nan daya hura ni ma mun
kusa kai ɗaya. Haka na kwana da zullumin ko Bilal ya san na haihu? Idan yaji ya ya karɓi al'amarin dan
nasan abu ne me wahala idan be ji haushi ba ace sedai kawai ya tsinci zancen haihuwa ta a sama bayan
yana da haƙƙin daya kamata ace tun muna hanyar asibiti an kirashi an gaya masa. Haka nayi bacci cikin
zullumi.
BILAL
Se da ya fita daga gidan kuma ya ringa jin babu daɗi kamar abinda yayi ya zarce misali. Can gefe ya nemi
guri ya zauna yana tunanin ya koma ne ya bawa Halima haƙuri ko kuwa? Amma daya tuna Haliman da
irin son da take masa se ya samu nutsuwa yasan ba zata ɗauki abun sa zafin da ze iya zame musu
matsala ba amma kuma waccen ƙanwar tata mara kunya ita ce zata iya kai zancen gaba har ya zama
wani abu daban. Sau biyu yana miƙewa da niyyar komawa gidan idan ma ta kama ya basu haƙuri ne duk
su biyun zancen dai ya wuce karya koma kunnen yan gidansu amma shigiyar zuciyar sa me yi masa
huɗubar tsiya ta zuge shi akan ze siyawa kansa raini ne kawai ai itama Haliman ba zata fara bari zancen
yaje gidan ba.
Da haka ya bawa kansa ƙwarin guiwa, da yayi niyyar zama gurin yayi gadi ko da zata ce zata fita se kuma
ya fasa yayi tafiyar sa dan yasan babu in da zata je ita dai Amirah yasan dole zata bar gidan tunda Halima
na gudun ɓacin ransa. A masallacin unguwar yayi sallar la'asar yana zaune ya hango gilmawar su, har ya
miƙe da niyyar bin su kuma se ya fasa a ransa ya raya mafita ce ta samu. Yanzu duk inda aka je aka dawo
ze juya lefin ne ya koma kanta ta fita daga gidan sa ba tare da ya bata izini ba tunda ai ba ita yace ta tafi
ba. Komawa yayi ya ɗauki mashin ɗin sa cikin sa'a har ya fito bakin titi se lokacin suka samu abun hawa.
Se da ya rakasu har gida yaga sun shiga kafin ya wuce gidan su yana ayyana yanda ze canza maganar
idan ma ta tashi ance y zagi uban matar sa dukda yayi amanna Halima ba zata taɓa bari maganar ta fita
ba yasan ma baze rasa dalilin da ya saka tabi Amiran ba kenan dan kar taje ta faɗi abin da ba shikenan
ba.
Daya isa gidan suna gaisawa da Hajja abinda ta fara tambayar sa shine
"Wai yaushe matar ka zata tafi wanka ne ko kuwa kana nufin a gidan ka zata haihu su tatse maka tattalin
arziƙi?"
Zancen kenan kullum yaje kamar karatu tun cikin Halima be wuce wata shida ba take surutun se ta tafi
goyon ciki ai haka akeyi a al'ada, se kace ita nata yayan da cikin wata shidan suke tahowa kuma ma
banda Amina Babbar Yayar su shi be sake ganin wata tazo wani wankan gida ba se Fadila itama kuma
yasan dan Mijin yaƙi daɗin azanci ne dama neman tahowa gidan takeyi shi yasa suka fake da haihuwa
badan haka ba da Hajjan ce zata je ta zauna mata kamar yanda ta saba yiwa sauran shine zata takura se
Halima ta tafi tun da wurwuri.
Dukda dai shima yana da ra'ayin ta tafi wankan gida saboda ko babu komai za'a rage masa hidimomi da
yawa na yan barka har zuwa suna da abubuwan da zasu biyo baya; duk baya jin yan uwan Halima dan
tun auren su ze iya irga mutum nawa suka zo gidan kuma ko ta haihu ba zasuyi irin zuwan nan na takura
ba nasa dangin yake ji dan yana ganin yanda sukeyi a sauran gidajen yan uwansa idan anyi haihuwa wata
tun farar safiya zata taho se taci abincin dare sannan ta tafi gaskiya baze ɗauki wannan zaryar ba shiyasa
gara ta tafi can gidan su idan tayi arba'in suka gama yawon zaga dangi se ta dawo dukda ma ya gama
gane take taken Haliman bata so ta tafi gidan amma hakan ya zame mata dole tunda yana ra'ayi.
Yana ɗakin Hajja suna hira kiran Anty Labiba ya shiga wayar sa, abinda ya fara zuwar masa shine Amirah
taje ta ce ya zagi Abban su shine Anty Labiba ta biyo ba'asi hakan yasa ya maida wayar sa aljihu bayan ya
sakata a silent a ransa yana raya harka ta lalace musamman tunda wannan matar ta shigo ciki ko abun
beyi zafi ba se ta ƙara rura wuta. Se da aka kira sallah ya fita, bayan an idar Abdurrashid ya tsayar dashi
ɗaya daga cikin Yayan Baba Salahu ne kuma abokin Bilal ɗin dan suna buga ƙwallo tare. Da fara'a ya tare
shi bayan sunyi musabaha yace
Tunanin da Bilal ya tafi yana magana ne akan Halima nada ciki, se ya gimtse fuska kishi ya motsa wato
kalle masa mata ma yake yi yana sa mata ido tsabar kuma bashi da ta ido har ya iya tarar sa ya masa
barka wai matar sa nada ciki. Shi ko Abdurrashid bema gane sauyin fuskar Bilal ɗin ba yace
"Allah ya raya ya ɗayyaba, se munzo barka" daga haka ya saki hannun Bilal ɗin ya wuce abun sa. Sakato
Bilal yayi a tsaye yana ƙoƙarin haɗa maganganun Abdurrashid ɗin na ƙarshe, idan ya fahimta barkar
haihuwa ya masa ba ta samun ciki ba kenan kuma hakan yana nufin Halima ta haihu ne ko me?
Ƙarasa fita yayi daga harabar masallacin kafin ya sake samun guri ya tsaya ya riƙe ƙugu yana ƙoƙarin
haɗa lissafin, Nasir ne ya iske shi fuska a washe ya shiga zolayar sa da "Angon ƙarni".
"Be kamata ma na kulaka ka ba, ace se dai muji haihuwa a gari ba zaka iya kirana ka gaya mun ba ko da
yake yanzu kayi sababbin abokai yan GRA naga ai baka yayin irin mu yan ghetto".
"Ka aje maganar wasa Nasir dagaske ne wai Halima ta haihu?" Ya tambaye shi. Se Nasir ya kalle shi yace
"Bana son rainin wayau; matar ka ta haihu ka ringa tambaya ta wasa ne ko gaske? Mutuwa kayi ka dawo
da zaka ce baka san meya faru a duniyar ba ko wani salon wulaƙancin ne haka?"
"Dagaske nakeyi Nasir ban san Halima ta haihu ba. Tsayuwar da kaga nayi a nan yanzu Yayanta
Abdurrashid ya gama mun barka shine na tsaya ina jiran wanda ze zo ya faɗa mun gaskiya ko aka sin
zancen kuma se gaka, amma lallai mutanen nan sun raina ni. Ace matar tawa ta fara naƙuda har ta haihu
babu wanda ya kira ni ya gaya mun? Kenan da mutuwa tayi se dai kawai ace nazo na ga gawarta ko me?"
Ya faɗa cikin ɓacin rai. Nasir ya dafa shi yace
"Kar dai kayi saurin yanke hukunci; nima yanzu Fauziyya ta kira ni take gaya mun taga Zubaida ta saka,
ƙila yanzu ta haihu kuma kasan sharrin network ta yuwu ma sun kira ka be shigo ba. Tun da dai ta haihu
lafiya ai anyi me wahalar yanzu se ka kirata muji suna wane asibitin ne se muje".
"Zance ma kakeyi wlh, ai har idan an ɗauke ni da muhimmanci tun kafin a fita da ita daga gida ya kamata
a kira a nemi izini na kuma a gaya mun. Idan basu same ni a waya ba bani da dangi ne? Taku nawa ne
tsakanin mu dasu da ba zasu aiko a gayawa mahaifiya ta ko wani ɗan uwana yaje a tafi dashi asibitin ba?.
Ashe dai da ake faɗar irin wulaƙancin da masu kuɗi suke yi su mayar da mazajen yayan su ba komai ba
dagaske ne tunda gashi ya biyo ta kaina se dai ni ba shashasha bane da zan ɗauka wlh se na nuna musu
nasan mutunchin kaina" ya ƙarasa a fusace yana zaro wayar sa daga aljihunsa.
Lokaci ɗaya karsashin rashin mutunchin daya hau ya sake shi daya shiga jerin missed calls ɗin daya gani
akan wayar sa. Kafin kiran Anty Labiba da kusan minti talatin Abban su Halima ya kira shi har sau biyu,
alamar saƙon daya gani a saman wayar ya duba Abban ne dai ya aje masa saƙo yana sanar dashi Halima
tana cikin halin naƙuda ya rubuta masa sunan Asibitin da suke da har da kwatancen inda ɗakin haihuwar
yake. Kamar an watsawa kaza ruwa haka yayi laƙwas, Nasir yace
Kamar mara gaskiya ya mayar da wayar aljihunsa yana gyara zaman rigar sa yace
"Oho dai koma menene ba'a mutunta ni an bani ƙima ta ta mijin ta ba tun farko ma ai ni ya kamata ta
kira ta gayawa naƙuda ta kamata ba wai yan gidan su ba ai" ya faɗa tamkar bashi da masaniya akan ta
fita daga gidan. Nasir dake kallon sa kawai ya girgiza kai yace
"Kaji dashi, yanzu dai idan zamu je asibitin bismillah; idan kuma ba zaka je ɗin ba ni in kama gabana ina
da abinda zanyi a chemist".
"Babu in da zanje, idan ina da muhimmanci zasu zo har in da nake su buƙace ni" Bilal ya faɗa yana wani
buɗa hannu, hannu biyu Nasir ya ɗaga yana cewa
"Allah ya taimaka ya bada sa'a; idan ta dawo gida se ka sanar dani idan ma kuma can gidan su ta wuce
duk dai ka gaya mun, ko da yake karka damu zan ji a inda na samu labarin haihuwar kawai ba se ka kira
ni ba" daga haka ya juya yayi tafiyar sa Bilal ɗin na tsayar dashi be kula shi ba ya shige motar sa daya
ajiye gefeb masallacin ya tafi.
Gida Bilal ya juya, yana shiga ya tarar da Hajja na saka hijabi; da mamaki ya kalle ta yace
"Yanzu Fainusa tayo waya tace mana Halima ta haihu shine zamu je mu gano su" ta bashi amsa. Se ya
wani ɓata fuska yace
"Yanzu an kira ki ne an gaya miki haihuwar balle ki ɗauki ƙafa ki tafi? Ke da Fainusa waya fi zama a haƙƙu
da su kira? To ki koma ɗaki kiyi zamanki ko ni da nake uban ɗan basu kira sun gaya mun ba nima a wai
wai naji a gari dan haka babu in da zamu je, idan sunga muna da muhimmanci sun san inda zasu same
mu ai zasu zo" ya faɗa yana shigewa ɗakin Hajjan.
*(Based on true life event, some parts are fictional to spice up the story)*
*Wattpad @MaryamahMrsAm*
*Ban yarda wani ko wata ya juya mun labari ta kowacce siga ba tare da izini na ba*
*Kuɗin karatu yana wakiltar mutum ɗaya ne, kiji tsoron Allah karki ɗauki hakkina ta hanyar fitar mun da
littafi*
*KURA A RUMBU littafin kuɗi ne, a biya naira 800, biya a asusun*
*1840175439*
*Access bank*
*PAGE 20*
Washe gari har azahar banga Bilal kuma babu wani daga dangin sa se yan uwana da suke ta kaikawo a
gurin. A ƙa'ida da safe za'a sallame mu tunda na cike awanni shida na ƙa'ida amma da likita ya shigo
duba mu ya ɗauki yaron se yace akwai alamun jundice a tare dashi dan haka ba zasu sallame mu a
lokacin ba se mun ƙara 12 hours under observation idan abun is not severe da zamu iya tafiya gida tohm.
Nan da nan hankali na ya tashi saboda yanda nake jin labarin jundice ance yana kashe jarirai, shaiɗan da
saƙe saƙe tuni har na fara hasaso wai babyn ma mutuwa zeyi. Ina kwance nake wannan tunanin se kawai
na tsinci kaina da fashewa da kuka kamar har abun ya faru ne.
"Lafiya Yaya? Ko ciwon ciki ne?" Nan hankalin sauran mutanen ɗakin ya dawo kaina duk suka shiga jera
tambayar meya same ni? Ko wani gurin ke yi mun ciwo ni kuwa kamar suna tunzura ni na samu guri na
cigaba da Sheƙa kuka ba ji ba gani.
"Ku rabu da ita babu inda yake mata ciwo baze wuce akan wancan mijin nata da be san daraja da ƙimar
ta ba take wannan kukan. Ace ka haihu gari ɗaya ba wai daga wata nisan duniya ba miji ya kasa zuwa ya
duba halin da kake ciki ko abinda ka haifa ba? Ko da yake ita ta jawa kanta ba wani da dan haka namu
ido".
Maganganun ta suka buɗe musu fili kowa ta shiga tofa albarkacin bakinta dukdai be wuce zagin Bilal da
Ahalin sa ba.
"Ai wlh ko a wata jaha suke daga dai haihuwar ta tun jira da yamma zuwa yanzu azahar yaci ace ko
mutum biyu sun taso sun zo amma ce gari ɗaya ko shi uban cikin be zo ba balle wani nasa yayi kara
shima yazo? To Alla ya rufa asiri, duk irin abunda aka ringa hango mata kenan soyayya ta rufe mata ido
shima Yaya Aminu ya biyewa Yaya Salamatu, dan kai ka auri mace ka mata halacci se aka ce yarka ma
idan tayi irin auren zata dace? Tsabar lalacewa ma fa ase daidai da ginin gidan shi ya bashi maƙudan
kuɗaɗe ya ƙarasa duk a shawarar Yaya Salamatu. Wannan yaron yace mun a gurin sa aka siyi ƙofofi da
wundunan gidan yace saboda samun guri wanda ma sukayi magana da Yaya Aminun za'a bashi da yaje
se cewa yayi basu yake so ba ya nuna wasu daban kuma Yayan yace a bayar. Abun nan ya daɗe yana
cimun rai kawai nayi shiru ne dan kar ace a baki na magana ta fito".
Murmushi kawai Anty Labiba ta ringa yi tana gyaɗa kai irin abun ya mata daɗi, Anty Rakiya wadda yayan
maza suke da su Abba tace
"Kuma shine saboda su ɗin ba gadon arziƙi bane yayi mata lefe a leda; wato bata kai ko a cikin kuɗin da
uban nata ya bashi ya ragi wani abun ya siya mata akwati ba"
"Ke kuwa idan suka zubo a akwati ai abun tsiyar ƙara yawa zeyi, yo ina abun zubawa a akwatin ma banda
abinki Rakiya? An dai cuci yarinya kawai an kaita an baro" Gwaggo Hajiyayye ta faɗa. Se Anty Labiba tayi
caraf tace
Dana gaji da sauraron cin mutunchin da suke mun se kawai na tashi daga kan gadon na shige banɗaki.
Tunani nake dagaske Abba ne ya bawa Bilal kuɗin daya ƙarasa ginin sa ko dai surutun su ne kawai?
Da ace Anty Labiba ce ta faɗa zan iya cewa duk cikin son ta cusa mun tsanar Bilal ne amma kuma banga
hujjar da ze saka Anty Rakiya tayi ƙarya cikin wannan maganar ba, a karon farko naji haushin Bilal har
zuciyata. Idan har ta tabbata dagaske Abba ne ya bashi kuɗin nan amma har ya iya buɗe baki ya kira ni
da yar matsiyata ba sau ɗaya ba sau biyu ba lallai Bilal ban ma san a wane aji ya kamata na ajiye shi ba.
Kuka na se ya canza salo, dama ɗazu na jin daɗi ne yanzu ko dana samu dalili me ƙarfi se na shiga kukan
tausayin kaina. Bubbuga ƙofar banɗakin da akayi yasa na wanke fuskata na fito.
Abba, Baba Salahu se abokin Abba Baba Lawan ne suka zo, ban yarda mun haɗa ido ba na gaishe su Baba
Salahu ya shiga tambayar meya same ni ido na ya kumbura ba kunya Anty Labiba tace wai kumburin
haihuwa ne.
"Shine haka har ido kamar wadda tasha kuka?" Baba Lawan ya tambaya. Ni dai shiru nayi bance komai
ba, basu jima ba suka tafi. Haka yinin ranar ya doshi ƙarewa har la'asar banga Bilal ba ban kuma ga wani
daga ɓangaren sa yazo ba.
Zuwa lokacin har na rasa wane tunani zanyi akan ma'anar abinda Bilal ɗin yayi mun. Da kunne na naji
Abba yana faɗar ya kirashi be amasa ba kuma ya tura masa da saƙo tun sanda aka kawo ni asibiti;
sannan ni ma da kai na na kira shi da wayar Anty Labiba be amsa ba. Nama rasa wane tunani zanyi, shin
yana sane yaƙi amsa wayoyin kuma yaƙi zuwa ko kuwa akwai wani al'amari daban da bamu sani ba?
Haka muka sake kwana; ƙarfe goma na safiyar washe gari aka sallame mu. Gidan mu aka wuce dani, a
ɗakin Mama na kwanta dan na shiga tsohon ɗaki na in da yake na Amirah a yanzu ganin kayan ta a
barbaje yasa na fahimci ba a nan zamu zauna ba ƙila ko ɗakin baƙi za'a gyara mun.
Mama Fauziyya ce tayi mun wanka, nasha kuka amma kuma naji daɗin jiki na duk gajiyar dake tare dani
ta warware. Se da naci abinci kafin na kwanta, bacci nake so nayi se dai tunanin daya cunkushe mun
zuciya ya hanani.
Gaba ɗaya zuciyata babu daɗi, kwanaki biyu daya kamata su zama mafiya farin cikin a rayuwata sun juye
zuwa na akasin haka. Ace na haihu har kwana biyu uban ɗan yana raye amma be iya zuwa in da muke
ba, idan wani ne ya gaya mun haka zata iya kasancewa tabbas bazan yarda ba se gashi ni da kaina na
shaida hakan. Amma dana tafi lissafin baya tun daga goyon cikin da yanda sam ban shida irin ɗoki da
farin cikin da ƙawaye na suke bani labarin mazajen su na yi ba a lokacin da suka samu ƙaruwa se banyi
mamaki da abinda ya aikata mana a yanzun ba.
Na tuna sanda Hansa'u ta haihu, yar da a haifa ita ce ta goma sha biyu a jerin yayan mijinta amma
hakanan ya baro abin da yake yi a Dubai in da yake kasuwancin sa ya taho a ranar ya duba su sannan ya
juya ya tafi. Irin soyayyar da nayi tunanin a gurin yaro matashi sabon jini kaɗai ake samun ta se gashi
rayuwar Hansa'u da Mijin ta ta ƙaryata tunani na.
Sau tari har bana son buɗe status ɗin ta saboda abubuwan da nake cin karo dasu da suke sosa mun
zuciya har nake jin kamar da gayya ma take ɗorawa saboda na gani. Duk da shekarun mijinta baya
kunyar su fita tare su je guraren Shaƙatawa a ciki da wajen ƙasar nan suyi hotunan da kana kallo baka
buƙatar a faɗa maka su ɗin masoya ne dake cike da farin ciki. Tun da na auri Bilal sau ɗaya zan ce mun
taɓa zuwa wani guri shima ba wai haka nan ba dalili ne ya kaimu birthday budurwar wani abokin aikin sa
Patrick da akayi a wani garden. Duk sanda na roƙe shi da mu fita wani guri ko da gidan zoo ne mu sha
iska se yace ba yanzu ba.
"Yanzu ke ba zaki ji wani iri ba na ɗauke ki a mashin kawai muje kowa suna zuwa a manyan motoci masu
aji?" Abin da yake faɗa mun kenan duk sanda na masa maganar. Na kan yawan tunasar dashi akan
"Shi farin ciki babu ruwan sa da wadata. Shi yasa ma nake ce maka muje irin guraren da nasan munfi da
yawan waɗan da zamu tarar wadata ƙila mu zama abin kallo ma a gurin su da bayar da sha'awa. Sannan
duk ma inda muka ga damar zuwa ina ruwan mu da masu zuwa a motoci? Se ta yuwu muje mu kashe
dubu ɗaya wanda yazo a ƙatuwar motar se dai kawai yayi zagaye ya tafi ba tare da ya kashe ko sisi ba ni
ban san me yasa kake yawan damuwa da maganaganun mutane ba ko kallon da mutane zasu maka. A
baya da kake ɗauka ta a mashin ɗin muke zuwa me yasa baka taɓa tuna za'a raina ka ba se yanzu?"
Duk sanda mukayi haka daga ƙarshe abin rigima maganar take komawa yace na raina ƙoƙarin sa ina
hangen rayuwar da wasu sukeyi; idan nayi haƙuri nima wata rana zamu taka matsayin fa nake hange
hangen shi kenan se ya ɗauki fushi idan ba'a yi sa'a ba se anyi kwana biyu ina bin sa da rarrashi da ban
baki kafin ya sakko muci gaba da walwala a gidan.
Ƙarfe biyar bayan nayi wankan yamma babyn ma anyi masa ina zaune ina cin gasassun yan shilan da
Anty Labiba ta ajiye mun Mama ta shigo ɗakin.
"Kiyi sauri ki ƙarasa kada magriba tayi ku samu ku tafi" ta faɗa daga tsayen da take.
Kallon ta nayi da rashin fahimtar abinda maganar ta take nufi. Kamar ta fahimce ni fuska babu walwala
tace
"Abban ku yace ki koma can gidan ki". Se na ture kwanon gabana na fuskance ta da kyau nace
"Saboda haka yaga dama". Ta bani amsa, take hawaye ya ɓalle mun dan dama ba nisa sukayi ba, na
karanci akwai tausayi na akan fusakar ta amma ta dake tace
"Tun farko abinda na gudar miki kenan Halima amma kika kasa ganewa. Se kije kiyi ta haƙuri, ita dama
rayuwa haka take kowa da kalar nasa ƙalubalen" daga haka ta fita ta barni na haɗa kai da guiwa na shiga
kuka kamar wadda aka doka. Tuntuni dama dashi da iyayen sa kullum cikin yi mun shaguɓen na tafi gida
na haihu sukeyi yanzu kuma se ace na koma bayan ko da na haihun ma basu zo ba alamar basu damu da
ƙaruwar da muka samu ba kenan.
Kukan dana ringayi be hana Mama Fauziyya da Anty Labiba mayar dani gidan Bilal ba. A hanya suna ta
hira abun su ni ko na haɗa kai da window ina share hawaye. Gaskiya ba'a kyauta mun ba, an ma nuna
neman kai kawai akeyi dani shi yasa za'a tattarani kwana biyu da haihuwa ace za'a mayar dani gidan miji.
Da muƙulli na sukayi amfani suka buɗe gidan. Compound ɗin kamar ya shekara babu mutum a ciki ƙura
da ganyayyekin bishiya kasancewar sanyi ya fara kankama. Yanayin dana ga gidan yasa na fara shakkar
anya kuwa Bilal na gari? Domin Bilal ɗin dana sani in dai ba sharafa yakeyi ba babu yanda za'a yi ya bar
muhallin da yake zaune ciki a haka.
Yanayin falon ya tabbatar mun da zargina na Bilal baya nan, hatta da fasassun tangaran da taliyar daya
zubar tun shekaran jiyan suna nan ba'a kwashe ba. Ɗaki Mu'azzam ya shigar mana da kayayyakin baby
wanda duk a gidan mu aka siya tunda ko abun susar kunne banje dashi ba. Anty Labiba da Mama
Fauziyya suka gyara gidan tas, kafin a kira Magriba har tsakar gidan an nemo almajirai sun share sun
wanke. Har bayan sallar isha'i kafin sukayi mun sallama zasu tafi, na fashe da kuka ina cewa
"To zama kike so muyi Halima? Da can dawa kike zaune ba ke da mijinki bane?" Mama Fauziyya ta faɗa.
Na girgiza kai ina cigaba da kukan nace
"To ai yanzu baya nan Mama, kuma ko yana nan da da yanzu ai ba ɗaya ba ni ban ma san yanda zan kula
da yaron nan ba kuka yakeyi cikin dare Anty Labiba ce take goya shi kuma idan safiya tayi ya zan masa
wanka nima ya zanyi?" Na ƙarasa cikin kuka me tafe da shassheƙa. Shiru suka yi da alamu kukan nawa ya
taɓa su. Mama Fauziyya ta zauna kusa dani ta jani jikin ta cikin rarrashi tace
"Mijinki bashi da kirki Halima. Ta yaya za'ayi ace ki haihu har kwana biyu amma be zo ba wani nasa be zo
ba a gari ɗaya ba wai can nisan duniya ba? Kin fi kowa sanin sauƙin kai irin na mahaifin ki amma tunda
har yayi fushin da yace ki dawo gidan ki tabbatas abun ya ɓata masa rai. Da kansa ya kira Bilal ba wai
wani ya saka ya kira shi ba amma be amsa wayar sa ba har yanzun nan kuma be biyo sahun kiran ba,
dama ai ga akan yanda kuka rabu har kika tafi gida ko? Kiyi haƙuri ki jira shi ya dawo duk yanda kuka yi ki
kira waya domin mahaifin ki yace ba zaki koma ki zauna masa a gida ba har se da dalili, wato idan sakin
ki yayi".
Da sauri na kalle ta jin abunda ta faɗa daga ƙarshe, wai Bilal ya sake ni. Baki na har rawa yakeyi nace
"Yanzu bayan wannan kora da halin daya miki har kina tunanin cigaba da zama dashi ne Halima?" Mama
Fauziyya ta faɗa kusan da mamaki, se na shiga girgiza mata kai nace
"Bafa faɗa mukayi ba Mama, kuma ni jiki na ma yana bani ba lafiya Bilal yake ba ai dai kunga gidan nan
beyi kama da wanda mutum yake zaune a cikin sa ba tun da har can ɗakin sa kun duba duk babu alamar
yana kwana a gidan nan. Ni tsoro nakeyi koma wani mugun abu ne ya same shi" na ƙarashe cikin sabon
kuka.
Yanda Mama Fauziyya ta buɗe baki ze baka tabbacin ta rasa abin faɗa ne, a fusace Anty Labiba tace
"Dan ubanki ai se ki bazama ki binciko in da ya shiga. Ki tashi mu tafi idan kuma baki gaji da kwasar
takaicin bane se ki zauna ki taya ta kwana ni dai nayi nan" daga haka ta nufi ƙofa itama Mama Fauziyyar
ta miƙe ta bita ganin haka yasa na rufa musu baya ina fashewa da sabon kuka nace
"Ai kin san hanta maza tafi amma karki kuskura naga ƙafar ki kusa da motar mu ki jira idan muka tafi se
ki biyo bayan mu" cewar Mama Fauziyya. A bakin ƙofa na durƙusa bayan fitar su na ringa rusa kuka baji
ba gani, se da baby na ya fara kuka kafin na tashi daga gurin na ɗauke shi daga kan kujerar da yake
kwance na zura masa ido ina kallon sa hawayen dake saukar mun suna ɗisa akan fuskar sa. Rungume shi
nayi ina cigaba da kukan. Ban ma san me ya kamata nayi ba, an shiga an fita tsakanina da Abba na kawai
dan ba abinda za'a gaya mun na yarda wai shi yace a dawo dani gidan nan.
Jin yaƙi yin shiru yasa na miƙe na shiga ƙoƙarin goya shi, motsi naji kamar ana murzawa ƙofa muƙulli
kafin kuma aka shiga bugawa, sakko da yaron nayi da sauri na ƙanƙame shi kamar wadda aka zo ƙwace
shi, a hankali na nufi ƙofar, ta jikin yar ɓular leƙe na hangi waɗanda ke tsaye, Abubakar ne da Nasir sun
ruƙo wani da banga fuskar sa sosai ba saboda kansa yana jingine ne jikin kafaɗar Abubakar ɗin. Ganin
waɗanda na sani ne yasa naji hankali na ya kwanta dan haka na buɗe musu ƙofar. Gabana ya yanke ya
faɗi ganin wanda suka ruƙo ɗin, Bilal ne. A yanayin da yake yafi kama da wanda yasha daƙyar a hannun
yan fashi ko ɓarayin daji. Da sauri na matsa na basu guri suka shigo se lokacin na lura ashe har da Hajja
da Anty Amina Yayar sa.
Jikina har rawa yake ina kallon su, Hajja ta fashe da kuka tana cewa
"Dan Allah Hajja kiyi shiru, kin dai ji abinda likita yace yana buƙatar hutu sosai kar a dame shi da
hayaniya ko wasu tambayoyi shiyasa ma nace ku wuce gida kawai amma kuka biyo mu kin zo kuma zaki
cika masa kunne da hayaniya" Abubakar da suka kwantar da Bilal ɗin akan kujera ya faɗa, se kuma ya
kalli in da nake tsaye kamar me jiran a bani umarni na fice a guje yace
"Ba shakka, yanzu kina gidan nan kwana har biyu sama ko ƙasa ba'a san inda mijinki yake ba amma baki
biyo kadi ba Halima? Ko da yake baki da asara idan ma mutuwa yayi hankalin ki kwance tunda kin aje iri
se dai kiyi jiran lissafi kawai"
"Wai dan Allah wane irin abu kikeyi haka Hajja?" Anty Amina ta sake katseta cikin fushi, se ta miƙe ta
isko ni tare da karɓan yaron hannuna tana cewa
Zaman nayi ina zare ido dan gaba ɗaya kaina ya kulle da abinda yake faruwa. Daga kwancen da Bilal yake
ya miƙo mun hannu, na kalli fuskar sa da tayi luhu luhu kusan kamannin sa ma sun canza ban san sanda
na isa kusa dashi ba na durƙusa lokaci ɗaya na fashe da kuka.
Sha biyu ta gota sanda Hajja na Nasir suka bar gidan Abubakar da Anty Amina suka zauna zasu kwana
tare damu. Abubakar ɗin ne ya taimakawa Bilal yayi wanka bayan ya ɗan warware daga magagin da yake
tayi kamar wanda baya cikin hayyacin sa. Shayi kaɗai ya iya sha, a nan falo suka kwana ni kuma muka
kwanta a ɗaki da Anty Amina. Kwata kwata na gagara runtsawa, ga tunanin abinda ya samu Bilal dan har
sannan babu wanda yace mun komai ga babyn dake ta tsula kuka har ya zarce na kwanaki biyun da
mukayi a asibiti, haka muka kwana Anty Amina na jele dashi tsakanin ɗaki da falo idan ta gaji Abubakar
ya karɓa Bilal dai yasha bacci saboda magungunan daya sha dan se guraren takwas na safe ma kafin ya
farka yayi sallah.
**********
"Halima ta bani tausayi Labiba, be kamata ace a yanzu ne Yaya Aminu ze nuna fushin sa ba. A gani na da
haƙuri yayi a zauna a gida ko sati biyu ne tayi, idan har aka ja wannan lokacin be zo ba ina ganin
komawar ma bata da amfani kawai a kira shi ya bata takardar ta shikenan dama ƙila rabon wannan ɗan
ne kuma gashi an haifa".
"Anty Fauziyyah kenan, ni dai bazan tofa komai akan sabgar Halima ba amma lokaci ze yi alƙalanci" Anty
Labiba ta bata amsa. Da suka isa gidan ma seda Mama Fauziyyar ta sake yiwa Mama magana akan ta
taushi Abba Halima ta dawo gida.
"Duk ma wanda za'a tura ta zauna da ita ba kamar tana nan gabanki ba. Sanda ya kamata ku nuna mata
kuskurenta bakuyi ba ba se yanzu da hakan ze iya cutar da ita ko ya cutar da abinda ta haifa ba. Kuskure
ai an rigada anyi shi tun farko da aka biyewa son zuciya aka yi auren haƙuri kawai zakuyi ku tayata karɓar
ƙaddarar ta" cewar Mama Fauziyyar.
"Ban taɓa ganin ɓacin ran Abban su irin na wannan karon ba. Abinda yake ta nanata mun ya kira yaron
nan da kansa har sau biyu be amsa ba ya kuma aika masa da saƙo dukda haka be biyo baya ba, kenan da
ace mutuwa ma Haliman tayi haka ze wofantar da ita har ayi mata sutura a bunneta babu shi babu wani
nasa a gurin kome? Rantsuwa fa yayi akan ba zata zauna ba, duk ƙaunar dake tsakaninsa da Halima ya
yanke wannan hukuncin ai dole na ɗaga masa ƙafa idan ya huce nasan da kansa zeyi duk abinda ya
kamata. Ni yanzu damuwata ma wanda za'a tura matan. Na kira Gwaggo Habi tunda ita tace in dai tana
raye aka aurar da Halima ta haihu zata je mata zaman jego amma karkiji tijarar data mun wai na kira
Yaya Salamatun data ɗaure ƙugun ayi auren taje ta zauna mata.
Na yi tunanin ko Yabi ta gidan Alhaji Salahu to daga maganganun da suka ringayi jiya da suka dawo daga
asibitin ma kawai na fasa karma taje ta sake samo zancen da za'a yi yawo dashi a dangi, se dai ko Zainab
taje ta kama mata ayyukan gida idan yaso tayi masa magana can a dangin sa ya nemo musu me saka
ruwa da wankan jinjirin kafin ta iya".
"Oh Allah, yanzu Halima da gatan ta da komai ace ana kame kamen wanda ze mata zaman jego? Allah
dai ya wadaran kunnen ƙashi irin na yayan zamani. Shikenan; ki tura mata Zainab ɗin idan yaso ni na
ringa zuwa ina mata wankan mu gani daga nan dai zuwa kwana uku shi kuma Abban nasu kiyi ƙoƙari ki
lallaɓa shi ya barta ta dawo gida dan Allah. Ni badan bama se nacewa Abban su Sadam ya kira shi ya
taushe shi dan gaskiya Yaya Amina aka bar yarinyar nan a gidan can wlh zata lalace ne kawai ga jego ga
damuwar miji kar muje ya ɗora mata depression a kawai". Akan haka suka rabu dama Anty Labiba bata
ma zauna a ɗakin ba balle ayi tattaunawar da ita. Har cikin ranta tana tausayawa Halima, se dai rashin
sanin ciwon kan da Haliman take gwadawa yasa take danne duk wani tausayin ta take so a barta da
wayonta tunda tana ganin ze fishsheta.
WASHE GARI
Da wuri Nasir yazo yayiwa Bilal sauran allura guda ɗaya cikin ukun da aka ce za'a yi masa. Anty Amina ce
tamun wanka sama sama da ruwan heater shi kuma babyn ta dafa a gas ta masa a wani ɗan baho na
saitin kayan robobi na dan ba'a siya masa saitin baho ba. Cikin kayayyakin dana ɗan siya na ɗakko mata
riga ta saka masa mai ma se stella da nake shafawa na bata ta shafa masa dan haka nan na rasa ɓoye
duk kayan sa da muka taho dasu daga gidan mu. Tana shafa masa man take tambayata bamu siyi man
jarirai bane ko yaya da za'a shafa masa stella? Ni dai murmushi kawai nayi na ɗakko mata ledar da yan
kayan dana tsinta suke da dubu goman daya bani sanda zeyi tafiya nace mata
"Iya kuɗin daya bani kenan yace nayi siyayya waɗannan ma cikin kuɗin da ake bani a gida nake ragewa
ina siyan su".
Sak tayi, bata kuma sake cewa komai ba ta ƙarasa shirya yaron ta fita dashi nima na shiga shirya kaina.
Yini guda yan uwan sa nata zuwa jaje, a ya da na fahimci abun dai kamar dai ɓata Bilal yayi se jiya aka
ganshi. Wai duk wanda yazo se su ringa tambayar yaushe na haihu? Kamar dai labarin be iske su ba suke
nufi har da ita kanta Hajjan bayan tijarar data so ta mun daren jiyan data dawo yau ba kunya ta ɗauki
ɗan tana ta wata murna wai jiya duk hankalinta ba'a jikinta yake ba shiyasa bata fahimci komai ba.
*(Based on true life event, some parts are fictional to spice up the story)*
*Wattpad @MaryamahMrsAm*
*Ban yarda wani ko wata ya juya mun labari ta kowacce siga ba tare da izini na ba*
*Kuɗin karatu yana wakiltar mutum ɗaya ne, kiji tsoron Allah karki ɗauki hakkina ta hanyar fitar mun da
littafi*
*KURA A RUMBU littafin kuɗi ne, a biya naira 800, biya a asusun*
*1840175439*
*Access bank*
Ina ɗaki, hayaniyar yan dubiya duk ta cika mun kunne, tun da Anty Amina ta tambaye ni abinda za'a dafa
da rana na nuna mata shinkafa da mai wanda su kaɗai suka suka rage mana a gidan, ina ganin Hajja ta
shiga kitchen ɗin na fito na barsu. Ta biyo ni ɗaki tana tambaya ta sauran kayan girki nace mata iya
abinda muke dashi kenan, zata yi magana Anty Aminan ta jata waje shikenan nayi zamana a ɗakin ban
sake fita ba suma kuma babu wadda ta sake leƙa ni. Da yaron yana gurin su ma aka maido mun dashi
shikenan naja ƙofa ta na kulle duk da yunwar da nake ji dan da safe shayi kawai nasha su suka cinye
sauran abincin jiya dana dawo dashi yanzun ma dana rasa mafita shayin na sake haɗawa na sha da cake,
duk da ba wai na ƙoshi bane amma na rage hanya, ina gamawa na tattara komai na mayar cikin
wardrobe har ina mamakin kaina wai yau ni ce nake ɓoyon abinci?
Da yamma Mama Fauziyya da Anty Labiba da Anty Mimi se wasu ƙawayen Mama su biyu suka zo tare.
Tun da safe da Mama Fauziyyan ta kira ni akan zata zo tayi mana wanka na gaya mata yayar Bilal tana
nan se tace zasu shigo da yamma toh.
Zuwan su ne ya fito da ni na tsaya daga bakin ƙofa jin suna gaisawa da yan uwan Bilal. Duk su biyar ɗin
naji sun masa sannu, amma babu wacce ta tambayi ba'asin meya same shi suka tsallake suka shiga ɗaki
na. Se da muka gaisa na fita na ɗakko musu ruwa, ina shiga kitchen Fadila ta biyo baya na. Ban ko kalli in
da take ba na ɗebi ruwan a faranti na fita na barta a tsaye.
Ƙawayen Maman basu jima ba suka tafi bayan kowacce ta ajiye mu. Abin barka. Anty Labiba ce ta tafi
rakasu, bayan fitar su Anty Mimi tace
"Me kuma ya samu mijin naki Halima?" Mama Fauziyya dai na ta faman juya yaron kafin ita kuma tace
"Amma dai tun safe ba'a canzawa yaron nan kaya ba ko? Ga rigarsa nan har da stain ɗin manja a jiki".
"Nima ban san abin da ya same shi ba, bayan kun tafi jiya suka dawo dashi har yanzu kuma basu ce mun
komai ba" na faɗa bayan da Anty Labiba ta dawo ta sake maimaita mun tambayar Anty Mimi. Su ukun
suka haɗa baki gurin cewa
"Allah ya rufa asiri" kafin Anty Labiba ta wuce banɗaki ta haɗo ruwan zafi a bahon da aka ma yaron
wanka da safe ta fito tana cewa
"Se ki tashi kema kiyi wankan duk da wannan ruwan ɗauraye jiki kawai za kiyi ba wani wankan kirki ba.
Bari na kira Mu'azzam idan ze kawo Zainab ɗin su taho da babbar tukunyar nan da murhu, ki dai tsaya
kiyi wankan gaske wlh in ba haka na jikin ki zaki lalata".
Se da nayi jira ruwan heater ya ƙara tafasa kafin nan naci tuwon da Mama Fauziyya ta taho dashi. Ina jin
yanda suke kallo na amma na ɗauke kai na ci gaba da cin abincin dan yunwa nake ji sosai, kowa dai
yasan cikin jego babu yanda za ayi shayi ya riƙe ni tun safe dan da suka dafa shinkafar ko tayi basu mun
ba. Anty Mimi da bakin ta be fiya shiru ba ce ta kasa daurewa tace
"Na ci mana Anty" na bata amsa ina ɗauke kwanon gaba na, kafin kuma wani ya sake cewa komai na fice
dan kai kwanon kitchen. Motsin da naji a bayana yasa na juya da sauri naga Hajja ce. Fuska ba yabo ba
falla sa tace
"Naga sun zo miki da abinci ko? Se ki ɗebo a bawa mijin ki idan ma mu ba zaki bamu ba". Nayi shiru na
rasa abinda zan ce mata. Wato idon su na kana duk abinda ake wucewa dashi. Ganin ta juya ta fita yasa
na sauke ajiyar zaciya na bi bayan ta. Tunanin ta yanda zan ɗebo abincin na fito dashi ba tare da sun
mun surutu ba na shiga yi.
Cikin sa'a, ina komawa ɗakin na tarar da Anty Labiba na cin sauran tuwon dama malmala ɗaya ne tun da
uku ne na ci biyu. Se na wuce sum sum na shiga cire kaya na a raina naji daɗi ta wani gefen amma kuma
yanzu ban san ya zamu kaya da Hajja ba. Sanda na fito wanka Anty Mimi ta ce suruka ta na kira na, se da
na shirya kafin na fita. Duk jama'ar yan dubiyar sun watse se ita kaɗai a falon Bilal ɗin ma an mayar dashi
can falon sa yana tare da Abubakar.
"Wato saboda kin raina ni Halima nayi miki magana kiyi shigewar ki ɗaki ki bar ni ina zaman jiran ki ko?"
Ta faɗa fuska cike da fushi. Kafin na bata amsa Anty Labiba ta fito da kwanukan tuwon bata ko kalli in da
muke tsaye ba ta shige kitchen; se na yi ƙasa da kai nace
"Wlh mantawa nayi Hajja, se da na fito daga wanka suka ce kina kira na kafin na tuna kuma na tarar sun
cinye sauran abincin dama bashi da yawa".
"Dole kice kin manta mana tun da kin raina ni baki ɗauke ni a bakin komai ba; idan uwar da ta haife ki ce
ta faɗa miki magana zaki tafi sharafin gaban ki ne ba tare da kin aikata abin da ta umarce ki ba?" Ta faɗa
cikin tsananin fushi,
"Saboda tsabar baki da tausayi mutumin na kwance hajaran majaran bayan kece silar shigar sa halin da
yake ciki amma abincin da zaki bashi ya ci kike baƙin ciki a kai; mu da muka zo jinyar sa baki bar mu ba
kin haɗa mu da shinkafa da mai se kace wasu mabarata kika shige ɗaki kika bar mu wato kora da hali
kike mana ƙarara, to yanzu zamu tafi se ki ƙarata Bilal dai ba zaki canza masa uwa ko dangi ba ba kuna ki
isa ki hana wani nasa shigowa cikin gidan nan ba".
"Ikon Allah" na faɗa a zuciya ta dan ban hango dalilin wannan faɗan rashin dalilin nata ba; kuma ta ina
na zama silar ciwon Bilal? Kiran da Anty Labiba ta mun daga kitchen ya sa na sake cewa tayi haƙuri na
juya na tafi ina ji tana ci gaba da banbamin ta da faɗar maganganu.
"Me za'a girka miki kafin mu wuce?" Anty Labiban ta faɗa bayan dana shiga kitchen ɗin, se kawai na faɗa
jikin ta na fashe da kuka. Yanda tayi sak nasan jikin ta ne yayi sanyi kafin ta tattaro ƙarfin hali ta janye ni
tana cewa
"Dan Allah Anty badan hali na ba kiyi haƙuri" na faɗa cikin shassheƙa. Se ta ce
"Ni dai kiyi haƙuri dan Allah ki tausayawa rayuwa ta ki taya ni roƙon Abba ko sati biyu ne naje nayi a gida
idan na warke se na dawo" na sale faɗa, se tayi tsaki ta ce
"Ke baki da baki ne halan? Ni da Allah ki nuna mun in da kayan girki suke idan kuma bakya buƙata mu
tafi magriba ta kawo kai".
"Shinkafa kawai muke da ita se mai kuma kin ga bashi da lafiya balle ya bayar da abin da za'a yi cefane
ko kuma ya siyo" na bata amsa cikin kuka. Se ta kama baki tana kallo na tace
"Su yan uwan nasa da suka cika gidan duk cikin su babu wanda yasan hanyar kasuwa ko da zasu siyo
cefanen?"
Shiru na mata na ci gaba da kuka na. Duk yanda na ringa roƙon su akan su tafi da ni gida amma basu
saurare ni ba, ƙarshe ma fasa jiran zuwan Mu'azzam ɗin suka yi da zasu tafi Mama Fauziyya ta ce mai
aikin ta Baba Jummai zata dawo gobe zuwa jibi idan yaso se tazo ta ringa mana wanka Zainab kuma ta
taya ni raino da gyaran gida tun da yanzu Yayar Bilal tana nan base ita ɗin ta rin ga zuwa ta mana kamar
yanda ta yi niyya a farko ba.
Bayan sun fito Hajja ta tsayar dasu kamar gaske tana cewa
"Toh fa subhanallahi ashe abin da ya faru kenan" Mama Fauziyya ta faɗa cikin jimami, Hajja tace
"Wlh Hajiya. Abun dai ba daɗi, duk hankulan mu sun tashi ace mutum magidanci an neme shi a rasa har
kwana biyu abun akwai ruɗani".
"Ikon Allah, amma Bilal ɗin ya ɓata har kwana biyu amma ba'a sanarwa da matar sa ba?" Anty Mimi ta
faɗa, se Hajja tace
"To ai mu ma bamu san abin da ya faru ba se jiya da safe. Tun dai da ya baro can gidan waccen ranar
bamu sake ji daga gare shi ba na san kuma lafiyar Allah Bilalu baze kwashe kwana biyu bai je mana ba,
idan kuma tafiya ce ta kamashi dole ze sanar mun kuma ze kira a waya mu gaisa amma dai bamu ɗauki
abun da girma ba tun da ba wani labari muka samu mara daɗi ba.
Abokin ƙanin sa ne fa can ya gano shi a Asibiti, banda shaƙiyancin kuma irin na yan zamani maimakon kai
tsaye ya faɗa masa ga Bilal a asibiti kawai se yace masa wai ina yayan su? Ya kamata ya bincika shi yaji ko
yana lafiya. To tun da dama muna ta jimamin kwana biyu mun ji shi shiru shine fa yana faɗa mun hankali
na ya tashi muka taho nan gidan babu kowa se makwafcin sa yace mana ai yau kwana biyu kenan ba
kowa a gidan. A lokacin har Habubakar ɗin yace a kira Halima muji ko tana da masaniyar in da yake ni
kuma nasan in har ita wani abu ya same ta ba zamu kasa ji daga gare ku ba dan haka na ce masa aa kar a
tayar mata da hankali ga tsohon ciki mu tafi gurin yan sanda kawai a kamo shi abokin nasa daya fara
kawo zancen a tuntuɓi Bilal aji ko yana lafiya. Shine fa da aka kamo shi ya ce ya ganshi a Asibitin Murtala
se likita ne ya mana bayanin yanda aka kawo shi babu waya kuma baya magana shi yasa suka rasa ta
yanda zasu nemi yan uwan sa dama jiyan suke niyyar kai cigiya gidan radio".
"Toh Allah ya rufa asiri ya kiyaye faruwar na gaba bari muje mu har an fara kiran sallah" Anty Labiba data
gaji da sauraron ta ta faɗa tana yin gaba se Hajja tayi saurin tare su da cewa
"Nace mai zai hana ku tafi da Halima gida Hajiya? Tun da kunga shi mijin nata ba lafiya ga ɗanyan jiki
kada ɗawainiyar tayi mata yawa dan shi ɗin ma can gida na zamu wuce dashi yanzu".
"Babu damuwa ai Hajiya ku tafi da shi ɗin Allah ya bashi lafiya ita ɗin se tayi zaman ta za'a kawo mata
waɗan da zasu taya ta zama" Mama Fauziyya ta faɗa. Se Hajja tayi shiru kafin kuma ta tace
"Amma dai haihuwar fari a al'ada ai gida ake tafiya ayi wanka balle ita wannan da ga halin da ake ciki"
"Wace al'ada mu ai tuni muka yada zancen zuwa wanka gida, gara dai yarinya ta zauna a ɗakin ta. Dama
saka ruwa ne wahalar jegon ai kuma za'a kawo wacce zata ringa yi mata ina ganin ai babu wata
damuwa" Mama Fauziyyar ta sake bata amsa dan tuni Anty Labiba ta fice Anty Mimi kuma ta zama hoto
kallon Hajjan kawai takeyi.
"Ai shikenan tun da haka kuka zaɓa se ta zauna, amma kowa na ɗauke ɗan sa ya kula dashi ki zaku bar
taku bakwa ko tsoron ya lallaɓa da ɗanyan jego ya haike mata duk matsalar data sameta ai ku ne da
kuka na wani ba" Hajja ta faɗa cikin fushi fushi.
"Ba abinda ze same ta se alkhairi Hajiya idan ma kuma ya haike mata ai ba haramun bane matar sa ce,
Halima dai ba in da zata je a gidan ta zata yi jego" Mama Fauziyyar ta bata amsa itama cikin fushi daga
nan suka yi tafiyar su.
Komawa nayi na zauna kan gado na tallafe fuskata naci gaba da share hawaye ina jiyo Hajja na masifa da
faɗar maganganu bayan data tabbatar sun fice daga gidan. Ban san ya akayi ba kuma da Hajja ta tashi
tafiya basu tafi da Bilal ɗin ba kamar yanda tace. Na zata ita ma Anty Aminar ta tafi se bayan tafiyar su
Hajjan kuma naga ta dawo tace mun gida taje ta dawo, har da cefanen kayan miya tayo da nama da kaji
guda biyu a daren ta dafa mun ɗaya tace na zauna na ci, se da na ƙoshi kafin ta sakawa Bilal sauran yaci.
Da Bilal ya shiga ɗaki ze kwanta ta ce na tashi na je ko akwai abin da ze buƙata na taimaka masa tunda
har sannan jikin sa be gama yin karfi ba. Yana zaune akan carpet ya ɗora kansa jikin gado na shiga, cikin
sanyin da muryar sa tayi ya miƙa mun hannu yana cewa
"Zo Halima". Na isa kusa dashi na zauna ya kwantar da kaina a kafaɗar sa yana cewa
"Ki yafe mun Halima" ban san yafiyar me yake nema ba amma kawai naji hawaye sun ɓalle mun. Ya
rungumeni yana cewa
"Nasan haƙƙin ku ne ya kama ni amma na godewa Allah da ban mutu ba tareda na nemi yafiyar ku ba, je
ki karɓo mun ɗana na ganshi" ya faɗa yana saki na. Se da na share hawayen kafin na fita na karɓo shi, ya
haɗa ya rungume mu ni da yaron yana cewa
"Kiyi haƙuri da abin da nayi miki ke da Amirah waccen ranar wlh sharrin shaiɗan ne ban ma san meya
hau kaina har na aikata abin da nayi ba".
"Amma Bilal na haihu ka kasa zuwa, Abba na ya kira ka nima na kira ka kuma na san ko ba'a faɗa maka
ba ba zaka kasa jin labari a unguwa ba" na faɗa cikin shassheƙa. Ya sake rungume ni yace
"Na ga kiran Abba Halima; nayi zaton ƙarata kika kai akan abin da na yi wa Amirah shi ya sa na kasa
ɗagawa. San da naga saƙon sa na kin haihu a lokacin dare yayi sosai, na so na bari se da safe na zo amma
na kasa jurewa. Tunanin halin da kike ciki da kuma taraddadin kin haihu ko akasin haka yasa na kasa
jurewa. Ban san me ya faru ba, nayan na fito daga gida wasu suka tare ni daga nan ban sake gane kai na
ba kawai na tashi na ganni a asibiti kuma duk ƙoƙarin da na yi akan nayi magana na kasa. Se daga baya
na samu labarin wasu ne suka tsince ni suka kaini asibitin" yayi maganar ba tare da ya bari mun haɗa ido
ba.
Wani irin tausayin sa ne ya lulluɓe ni, ni dama na san Bilal baze wofantar dani haka kawai ba, ashe abin
da ya same shi kenan. Kuka sosai na fashe dashi da wani tunani ya ɗarsu a raina. Yanzu da ace kuma Bilal
ya rasa ransa ne fa ina zan sa kaina a duniyar nan naji sanyi?
Mun shafe kusan minti goma muna koke koken har se da yaron ya gaji da matsar da aka masa ya fara
kuka kafin ya sake ni na karɓe shi daga hannun sa na shiga jijjiga shi yaƙi shiru dole se da na shiga shayar
dashi kafin yayi shirun alamar har da yunwa ta dame shi. Se bayan da ya ƙoshi ya sake karɓar sa yana
kallo na yace
"Allah da gaske na keyi ke kyakkyawa ce Halima. Kina da kyau me sanyi irin wanda a duk kallo yake ƙara
ƙawata idanuwan me kallon ki; babbar ni'imar da ubangiji ya yi miki ita ce kyakkyawar zuciya, kin ga ko
kwatantan kyawun ki da nawa ma ai ɓata baki ne kawai. Ina addu'ar yanda yaron nan yayi kama ta zahiri
da ni, ya yi kama dake ta baɗini" Bilal ya faɗa yana kafe ni da ido. Murmushi na ringa yi kamar wawuya.
Ina kallon sa ya ɗago yaron bayan ya tashi zaune sosai ya shiga yi masa kiran sallah a kunnen sa. Se da ya
kammala kafin ya kalle ni ya ce
Nayi ƙasa da kaina ina murmushi, idan son rai na ne bani da zaɓin daya wuce sunan Abba na, amma na
san ƙila a ransa ze zo ya mayar da sunan mahaifin sa ne tun da ya rasu. Hakan ya sa na ce masa
"Duk sunan da yayi maka shi ne zaɓi na". Murmushi me kyau yayi mun kafin ya kammala masa huɗubar
kafin ya miƙo mun shi yana cewa
"Na daɗe da sanin burin ki na sakawa yaron ki na fari sunan Abba, ko kin manta kin sha faɗa mun kafin
mu yi aure?"
"Ni ne da godiya Halima kin yi mun abubuwa da dama a rayuwa da bazan iya biyan ki ba. Naji daɗi da
kika yi farin ciki, Allah ya raya mana shi ya sa ya gaji takwaran sa"
Da "Amin" na amsa ina sake rungume Abba na a jiki na. Badan dare yayi ba da yanzu zan kira Abba na
gaya masa ya samu takwara amma Allah ya kaimu safiya.
A ɗakin muka kwana rungume da juna cikin farin cikin da muka kwana biyu bamu samu kamar sa ba.
Hatta Abba na be yi koke koken da yake mana kwanaki ukun zuwan sa duniya ba da safe har Anty Amina
se da ta ringa masa tsiya wai ya ji ɗumin Dady yayi lif kamar babu jinjiri a gidan.
*******
"Wlh fa Anty, ni ma duk se jiki na yayi sanyi tun da muka shiga, ana kallon sa zaka gane yaji jiki wlh.
Kamar fa harda ɗinki na gani a gefen kan sa, gaskiya ya daku sosai da alama".
"Amma dai kun bani mamaki wlh, ku yanzu har kun kama ƙaryar waɗancan mutanen kenan?" Anty
Labiba ta faɗa se Mama Fauziyya ta ce
"Aa Labiba, wannan fa ba zancen ƙarya bane. Idan sun yi ƙarya akan ainihin abin da ya same shi wannan
daban amma a zahiri dai duk wanda ya kalle shi yasan wani abu na rashin daɗi ya faru dashi, gaskiyar me
ya faru kuma wannan se Allah. Kuma dama karki kuskura ki ce zaki sake zuga Yaya akan maganar Halima,
dan Allah ki bari yarinyar nan ta dawo gida dan ganin idon ki dai gashi abinci ma babu a gidan yini guda
jegon kwana uku amma ace sun kasa samar mata abin da zata ci da jikin ta yake buƙata ina ga an sake
kwana biyu? Gara ta taho tayi arba'in se ta koma".
Shiru Anty Labiba tayi bata ce komai ba, ita ta san halin Bilal ko da yanayin sa ya nuna da gaske bashi da
lafiya amma a yanda ta sanshi ba wani abun mamaki bane ace shirya wa yayi. Duk se da ta sauke su a
gida tunda a motar ta suka fita kafin ta wuce nata gidan, a hanya ta kira Mama taji ko Zainab ɗin ta tafi
Maman tace mata aa, Haliman tace mata Yayar Bilal da mahaifiyar sa suna gidan shi yasa ta dakata da
tura Zainab ɗin kar kuma suyi yawa. Idan sun tafi se taje in ma kuma su zasu zauna mata shikenan daga
nan sukayi sallama akan se washe gari zata je gidan su ƙarasa magana akan yanda za'ayi da kayan barka.
*(Based on true life event, some parts are fictional to spice up the story)*
*Wattpad @MaryamahMrsAm*
*Ban yarda wani ko wata ya juya mun labari ta kowacce siga ba tare da izini na ba*
*Kuɗin karatu yana wakiltar mutum ɗaya ne, kiji tsoron Allah karki ɗauki hakkina ta hanyar fitar mun da
littafi*
*KURA A RUMBU littafin kuɗi ne, a biya naira 800, biya a asusun*
*1840175439*
*Access bank*
*PAGE 22*
"Dagaske ne Anty, masu ƙwacen mashin ne suka bige shi; waɗan da suka kai shi asibitin ma na san ɗaya
daga cikin su tare muka fara Maitama Sule" Mu'azzam ya faɗa jin Anty Labiba ta dage akan ƙarya kawai
Bilal ya shirga ba wani abu daya same shi. Zuwan ta kenan ta tarar suna jimamin abun, Na kira Abba na
gaya masa an masa takwara sannan na ƙara da faɗa masa dalilin da ya saka Bilal be duba mu ba har na
bawa Bilal ɗin waya suka gaisa da Abban ya sake bashi haƙuri. Bayan mun gama wayar ne ya fito yake
gaya wa Mama yan da mu ka yi se ga Anty Labiban.
"Ƙarya ya ke yi, saboda maganar ma bata kama kunne na ba shi yasa tun jiyan ban faɗa miki ba, na
ɗauka ma su Yaya Fauziyya zasu gaya miki tun da naga se jiman ta abun suke yi. Haɗin baki ne kawai shi
da yan uwan sa saboda su goge laifin wofantar da Halima da suka yi" ta faɗa sanda Mama ta maimaita
mata abin da Abban ya gaya mata.
"Yanzu kai ka san haka ta faru da shi amma shi ne ka yi shiru baka faɗawa kowa ba?" Abba ya faɗa yana
kallon sa, se ya yi ƙasa da kai ya ce
"Ni ma ai se daga baya na sani Abba. Lokacin da muka mayar da ita gida bayan na dawo aboki na Najib
ya kira ni yake gaya mun masu ƙwacen mashin sun bige mai gidan da yaga mota ta a gurin kuma su suka
kai shi asibiti ma".
"Ikon Allah, toh Allah ya rufa asiri. Amma wasu irin mutane ne su da irin haka zata faru ba zasu sanar
mana ba tun da ai yanzu mun zama abu guda?" Abban ya sake faɗa. Anty Labiba da ta zabga wa
Mu'azzam harara ta ce
"In ma da gaske ne ba komai ya ja masa ba illah haƙƙin iyalin sa da baya saukewa kaga an wasu can a
banza sun ƙwata ta ƙarfi ai, Allah ya ƙara"
"Haba Labiba ya kuma da irin wannan maganar? Idan da abun ya zo da tsautsayi fa suka hallaka shi ko
suka masa wata illar da za'a gwammaci ma mutuwa ya yi fa? Wannan al'amari na masu ƙwacen waya da
mashin dai ya fara yawa se dai fatan Allah ya shirye su kawai" Mama ta faɗa cikin jimami.
"Bari na gani idan na fita se mu biya mu duba shi" Abba ya faɗa yana miƙewa, kafin ya zaro kuɗi a aljihun
sa ya miƙawa Anty Labiba yana cewa
"Gashi se ku ƙara kayan, kin san yanzu lissafi ya canza aboki ne kuma takwara. Ke ma ya kama ta ki ware
akwatin ki daban; idan kuma kin barwa su Fauziyya auren shikenan" ya ƙarasa cikin sigar raha. Ta karɓi
kuɗin ta na ɗan murmushi Mama kuma ta taka masa zuwa gurin mota.
"Dama ai son zuciya da kwaɗayin abin da Abban ze masa ne ya saka ya yi masa takwarar ba wai saboda
cancanta ya yi ba. Bilal kuma, ai se dai ya cuci wanda be san shi ba wlh amma ni nan kar na ke kallon su"
Cewar Anty Labiba bayan Mama ta dawo falon. Mu'azzam yayi dariya ya ce
"Wlh kin gano shi Anty. Tsabar son zuciya ne kawai. Ban da haka ina nasa uban ya mutu? Ba se ya yi
masa takwarar ba ko mun ce masa muna so ne?"
"Ai dai zan ga abin da Bilal ze yi ya muku gwanin ta kai da Labiba, ka tashi kaje gidan Hajiya Larai ka amso
mun saƙon da ka ce se yau zaka je, ke kuma muje ciki ki duba kayan se muga abin da ya kamata a ƙara.
Yau na cewa yan gidan su Abban su su zo su gani idan ya so go be kwana biyar se aje a kai musu ko?"
Cewar Mama. Labiba ta taɓe baki ta ce
"Ba dai zaki haƙura da wannan al'adar ɗaukar maganar ba? Meye wani abin zuwa a gani a kayan barka se
kace lefe? Kuma da zaki gayya to su suzo kai kayan kin dai san can gidan su Bilal bana zaton ko ƙyalle sun
tana da da zasu gabatar a matsayin kayan da suka yiwa yaron nan. So kike a maimaita ta lefe ko a sake
samun abun da za'a yi ta terere dashi a dangi, ai shikenan".
"Toh Labiba ya kike so na yi? Kin dai san haka suke al'adar su, yanzu idan ba'a kira su ba se ki ji ya zama
abin magana" Maman ta faɗa. Labiban bata sake ce mata komai ba ta wuce ɗakin da suka ajiye siyayyar
kayan barkar da suka yi ta shiga fito dasu. Cikin akwati set me uku da kit ɗin sa ta shiga shirya kayan.
Kaya masu kyau da tsadar gaske suka siya. Kusan duk wani abu da za'a buƙata na jego sun siya mata, har
da set ɗin feeding bottle da bath set komi basu manta ba duk da ana siya Anty Labiba na mitar mijin ta
ya kamata ya siya mata amma kuma itan ce me sake zaƙulo wasu abubuwan a siya har da gado ta basu
na minal ɗin ta a pre order ta siye shi kafin yazo har yarinyar ta fara tafiya se kawai ta ajiye shi yanzu
kuma ya zama rabon su Halima.
Mama dai na tsaye tana kallon ta har ta gama jera na yaron a babbar akwati da ta uku kafin ta shiga zuba
na Halima a ta biyun wanda duk an ɗinka su. Kala shida ne Atamfa uku lace biyu da shadda ɗaya se
mayafi harda takalmi da jaka set bibbiyu. Sauran tarkacen undies har da body sprays da body mist duk ta
zuba a kit ɗin, ta tayar da su tsaye kafin ta kalli Mama tace
"Tsakani da Allah ko mu muka mata cikin iya waɗannan kayan sun isa".
Mama tayi murmushi kawai tana kallon ta, Labiba akwai daru. Ƙarara take adawa da lamarin Bilal da
Halima amma yanda ta zage ta kashe kuɗi a sabgar auren Halima zuwa haihuwar ta ba zaka yarda bata
son auren ba.
Kuɗin da Abba ya bata ta ciro daga aljihun rigar jikin ta ta shiga ware su, ta miƙawa Mama wani kaso ta
ce
"Gashi nan ki rage asara wannan kuma zan haɗa akwai kuɗin ta tun na barkonon da muka taɓa siya zan
haɗa su na siya mata sarƙa ta samu ta fitar suna". Mama na dariya wai ta rage asara ta karɓi kuɗin tana
juya su tace
"To ko babu taro ai dai zatayi kwalliya na san kuma yan uwan sa ba zasu ƙi zuwa ba ƙila su zasu yi sunan;
Allah dai ya kaimu gobe muga zubin su, ko zasu mata ƙauri ma oho" cewar Anty Labiba. Sai Mama ta
bata amsa da cewa
"Ke ma da neman magana kike Labiba, cewa fa tayi har account ɗin sa sun yashe komai waɗanda suka
ƙwace masa waya. Idan ya samu sararin yin haƙiƙa ma ai yayi"
"Idan ma ƙarya ya ke Allah ya biya bakin sa ya sa a kwashe ɗin" Anty Labiba ta faɗa daga nan ta zura
Hijabin ra tayi wa Mama sallama akan zata je kasuwar rimi ta dawo.
*******************
Cike da walwala na ƙare yinin ranar ban da ma zuwan Hajja da ta so ta ɓata mana farin cikin mu amma
ban bari maganganun ta sunyi tasiri a raina ba. Dab da la'asar Abba tare da Baba Salahu da Baba Munzali
suka zo duba Bilal, tun aure na zuwan Abba na farko kenan gida na. Na ji kunya ta yanda ko ruwan robar
da zan basu babu a gidan balle a je ga lemo ko wani abu se pure water na juye musu a Jug duk su ukun
ma babu wanda ya sha basu jima ba kuma suma tafi.
Basu jima da tafiya ba Hajja ta zo tare wasu ƙawayen ta da suka zo dubiya da kuma barka. Ina ɗaki ina
shiryawa dan gama wanka na kenan Abba na kuma yana hannun Bilal yana masa wasa dan shi Anty
Amina ta fara yi wa wankan kafin tayi mun.
"Wato kinga gurin zama har da kafa murhu" Hajja ta faɗa bayan da na fito ba tare da ta ko amsa
gaisuwar da nake musu ba. Lanti, ƙawar ta ta ce
"Zancen da na ke yi a raina kenan na ce ita haihuwar farin ma ba zata tafi gida tayi wanka ba?"
"Ke ko jaraba irin ta yayan zamani mana. Nan na ke gaya miki jikar Saude ba yanda uwar ba tayi akan ta
tafi gida tayi wanka ba taƙi wai da wa zata bar mijin ta? Na ce Allah ya yafe mana mu da zamanin mu ake
arba'in biyu" ɗayar ƙawar ta ta da ban san ta ba ta faɗa. Shikenan ta samu fili ta fara zazzaga har tana
cewa tsabar mugun ta tasa naƙi tafiya.
"Duk ibtila'in daya faɗawa yaron nan amma saboda rashin tausayi ace ki zauna ki yi jego a gidan nan; ai
se ki zauna kici uwar da zaki ci" take ta maimaitawa. Ni se ta bani dariya ma na koma ɗaki na barsu ina
jiyo Bilal na mata magana akan ta yi shiru amma se ƙara volume ta ke Lanti tana taya ta. To wace uwa
kuwa zanci wadda ban saba ci ba? Tun ma da na dawo ɗin me Bilal ɗin ya yi mun da har zata ce ba'a jin
tausayin sa? Ni yanda yayi mirsisi be tambaye ni in da aka samo kayan da ake sakawa yaron ba ma shi ya
fi bani mamaki tun da dai dubu goma ce ta gifta tsakani na dashi akan sabgar haihuwa haka ko da wasa
be yi zancen asibiti ba balle ya tambayi waye ya biya kuɗin.
Basu jima sosai ba suka tafi, ina ɗakin Anty Amina ta leƙo ta ce mun zasu tafi itama zata bi su taje gida ta
dawo, a da ina ganin kamar tafi kowa zafi cikin yan gidan su Bilal amma a yanzu kam na tabbata duk ta
fisu kirki domin tayi mun abun da ko jini na ce iya kaci kenan. Daga bakin ƙofa nayi musu sallama na
koma ciki, se da na ji Bilal na kira na kafin na fita na koma falon.
"Ki bani aron wayar ki zan yi kira" ya faɗa se na koma ɗaki na ɗakko masa wayar na bashi sannan ya ce
na ɗakko masa wani littafi a can ɗakin sa. Numbobin abokanan sa waɗan da ya rubuta ya ringa sakawa
yana kira ya sanar musu da an masa haihuwa. Hafiz ya kira a ƙarshe bayan sun gama magana ya bani
muka gaisa yayi mun barka tare da ƙorafin me yasa ban kira Matar sa na gaya mata ba? Haƙuri kawai na
bashi kafin na mayar wa da Bilal wayar na tashi saboda Abba na daya fara ƙananan kuka.
"Kin ji me oga Hafiz yake cewa?" Bilal ya faɗa bayan daya gama bige bigen wayar, na girgiza masa kai ya
yi yar dariya ya ce
"Se kace masa me?" Na faɗa ina kallon sa tare da tuno maganganun da suka yi,
"Nace masa Dady aka saka, kin san surname ɗin ku ɗaya. Baki ji yanda ya ringa murna ba ina ga ma yau
zasu zo duk da yace suna Abuja ama jirgin 6 zasu biyo zuwa Kano dama".
Kallon sa kawai na ringa yi, yanzu shi Hafiz ɗin idan ba soko ba ne da ze yarda a wace dangantakar Bilal
ze yi masa takwara balle har ya saka sunan mahaifin sa ma?
"Kin san ya so ya sakawa yaron sa sunan Dadyn ne amma matar ta ce sunan mahaifin ta za'a saka shi
yasa yaji daɗi sosai yanzu dana ce masa sunan Dadyn na saka" Bilal ya sake faɗa yana ruƙo hannu na.
Duk yan da na so na ci gaba da murmushin da nake yi amma na kasa, ina ɗaki ɗazun na tsinci maganar
Hajja sanda take Lanti take tambayar sunan yaron ta ce mata Aminu, ina ji ta ce "lallai, baban ta aka wa
takwara kenan?" Ita kuma Hajjan ta ce mata
"Baban uban gidan sa dai". Dake nesa nake jiyo maganar se na ji kamar ta ce "Babban ubangidan sa" har
ina dariya na ce wato Abban ne kuma ya zama uban gidan Bilal ashe Baban ubangidan sa ta ce.
Wani abu naji ya tsaya mun a wuya, na buɗe baki amma na kasa ce masa komai se kawai na zame hannu
na daya riƙe na wuce ɗaki ina jin sa yana kira na amma ban tsaya ba. Kwanciya nayi akan gado ina
kokawa da abin da ya tsaya mun a wuya, amma ko har idan ta tabbata uban Hafiz Bilal ya yiwa takwara
tabbas ya gama raina mun hankali ya kuma mayar da ni shashasha da ban san abun da na ke yi ba. Ina jin
sa ya shigo ɗakin na rufe ido na, duk yanda ya ringa kira na da tambayar menene na yi masa banza har
ya yi fushi ya fi ce ya barni. Kuka na fashe da shi mara sauti.
Bayan magriba Nasir da matar sa suka zo, ina ɗaki har sannan duk shige da ficen da Bilal yake ta yi duk
be sake mun magana ba ni ma ban kula shi ba se da suka zo sannan ya shiga ya mun magana. A hannun
kujera na zauna muka gaisa da Nasir ɗin kafin na cewa Aisha mu je ciki taga babyn. Kusan ƙawata ce tare
muka yi islamiyya duk da dai ƙawancen namu bai wuce na gaisuwa ba idan ta kama ayi hirar duniya ko
yanzun da na auri Bilal aminin mijin ta zumunchin mu be sauya daga yan da yake a da ba dan ya fi
maraba da alaƙa ta da matar Hafiz akan Aishar Nasir da suka tashi tare.
Ina zaune na jingina kaina da gado na yi zurfi cikin tunani sam ban ji duk maganar da take ta mun ba har
se da ta taɓa ni sannan na farga.
"Tunanin me kike yi haka Halima?" Ta faɗa ta na kallo na. Na ƙirƙiri murmushi ina gyara zama na na ce
"Ai fa se a hankali zaki saba hala yana muku kukan dare?" Da kai na amsa mata alamar eh se ta ce
"Yaya Bilal ne ya ke kiran ki". Hijabin da na cire na mayar sannan na fita. Daga gefe na tsaya ba tare da
na kalle shi ba na ce "gani".
Nasir ya ce
"Hajiya Halima wai me ya faru ne tun da muka shigo na lura akwai yar damuwa a gidan".
"Babu komai Yaya Nasir" na bashi amsa ba tare da na ɗaga kai na ba, Bilal ya ce
"Wai yanzu kamar Halima bata san wasa ba? Daga fa munyi waya da Oga Hafiz na ce masa Dadyn sa na
yiwa takwara bayan mun gama na gaya mata shikenan fa ta fara kumburi har da shiga ɗaki tayi kuka".
Sauti a sama na ce
"Ai tun jiya ya kamata ka gaya mun sunan Baban abokin ka ka saka ba na mahaifi na ba kaga da be sha
wahalar takowa har gidan nan ya duba ka ba"
"Au dama ba dan Allah ya zo duba ni ba saboda na yi masa takwara ne?" Ya taso mun shi ma. Se Nasir ya
yi saurin katse shi ya na cewa
"Meye haka Bilal? Wace irin maganar shirme ka ke yi?" Ya juyo kaina ganin na miƙe ya ce
"Dawo ki zauna Halima". Kai dan kar ya ce na masa rashin mutunchi ya sa na koma na zauna na ja hijabi
na rufe fuska ta.
"Yanzu saboda Allah abun da be kai ya kawo ba kuke so ku bawa shaiɗan ƙofa ya hadda sa saɓani a
tsakanin ku. Yanzu kai menene na cewa sunan wani can baban abokin ka ka saka masa?"
"Ni fa ba haka na ce mata ba; waya muka yi da Hafiz ya ce amma shi zan yi wa takwara ni kuma na ce
masa aa sunan Dady aka saka saboda nasan sunan su ɗaya da Abban Halima. Shi kan sa ai yasan wasa ne
ba wai dagaske Dadyn nasa ma saka ba amma ai ze ji daɗi ita kuma dan na bata labari meye abin ɗaukar
zafi a ciki saboda Allah?" Bilal ya faɗa se na ce
"Saboda na san halin ka ne kuma ba abun mamaki ba ne dan ka saka sunan Baban Hafiz ɗin. Tun da na
ɗauki ciki safa baka taɓa siya ka kawo gidan nan ka ce na ajiye ba har zuwa yanzun dana haihu kallon ka
kawai na ke yi amma da matar Hafiz ɗin ta haihu ka kashe kuɗi ka cika leda da kaya ka kai musu kaga ko
ai sun fi ni muhimmanci dan haka ba wani abun mamaki bane idan ka saka sunan Baban sa tun da kuna
da wata alaƙa da bani da masaniya".
"Kar ki kuskura ki ce zaki zage ni ko ki mun rashin kunya Halima" ya faɗa cikin hasala yana miƙewa tsaye
duk da Nasir na riƙe shi amma be fasa cewa
"Na kai musu kayan da kuɗin ki na siya balle kiyi baƙin ciki? Ban siya miki ɗin ba kuma ba zan siya ba idan
ki na da ƙarfi se ki ƙwata mu ga ni"
"Wlh na fi ƙarfin na yi baƙin ciki akan abin duniya Bilal duk abin da kake zaton zaka yi ko ka yiwa wani
nafi ƙarfin sa, idan da na ina saka ido na akan abubuwan da kake yi da bamu kawo yanzu ba. Kuma ko ka
siya wa ɗan ka ko karka siya kai ta shafa dan idan da ina tsammatar kayi mun wani abu da ban ɗauki
cikin ba ma. Idan ka ga dama ka sauke haƙƙi kan ka ka taimaka ba wani ba" na ƙarasa ina shigewa ɗaki
har ina ture Aisha da hayaniyar mu ta fito da ita.
Ina jiyo yan da ya kw bambami kamar ze kama da wuta Nasir na tare shi da alama ɗakin ze biyo ni, a
yanda raina yake suya duk abin da Bilal ya ke ji da shi yau ni ma daidai na ke da shi wlh. Aisha ta biyo ni
ta na cewa
"Babu ruwan ki" na faɗa ina miƙewa. Wardrobe na buɗe na fara fito da kaya na ina ajiye wa a kan gado,
ta riƙe hannu na ta na ce wa
"Innalillahi wa inna ilaihi raji'un, wai gida ki ke tunanin tafiya Halima? To kije ki ce musu me ya haɗa ku?"
Kamar ta zare mun kuzari haka jiki na ya yi sanyi na gagara ci gaba da ciro kayan se na koma na zauna
akan gado zuciya ta na bugawa da ƙarfi, da gaskiyar Aisha, yanzu na je gida na ce musu me?
Ba wani sauraron maganganun da take yi na ke ba daga ƙarshe na tashi na shige banɗaki na barta. Ka fin
su tafi se da Nasir ya sake ƙoƙarin sasanta mu. Ban san me ya cewa Bilal ɗin ba na dai ga da na fito jikin
sa a sanyaye ba kamar ɗazu da yake fizga kamar ze rufe ni da duka ba. Ya ringa mana nasiha da ban baki
Bilal ma ya ce na yi haƙuri shi wlh ba abinda yake nufi na kenan shaiɗan ne kawai ya ke so so ya yi wasa
da zukatan mu. Sun tafiya na koma ɗaki na kulle ƙofa ta da muƙulli dan na ƙudurce a raina a wannan
gaɓar ba zan wa Bilal da sauƙi ba rantsuwar sa akan sunan Abba ya sa ba zata sa nayi saurin yarda da shi
ba.
Ina jin sa yana bugu da roƙon na buɗe na masa banza daga ƙarshe ya ce na miƙo masa Abba idan ma ni
ba zan fito ba. Ina jin yunwa amma haka nan na zauna har se da Anty Amina ta dawo cikin sa'a har sa
tsarabar farfesun jelar sa ta taho da shi, shi na ci da tea na kwanta raina babu daɗi. Har ga Allah ina so na
matsa daga kusa da Bilal na tafi gida amma ban san ya zasu karɓe ni ba musamman ace matsala ce tsaka
ni na da Bilal ta dawo da ni. Haka na raba dare na kasa bacci.
Washe gari guraren goma na safe Anty Amina ta ce na yi waya gidan mu na ce musu yau za'a kawo
kayan barka a turo waɗanda zasu karɓa. Anty Labiba na kira na gaya mata ta ce
"Se kace wani abin kirki zasu kawo har da yin gayya; to se mun zo. Dama muma yau zamu kawo miki na
nan gidan ai. Sun yanka abin ƙauri ne ko kuwa?" Ta ƙarasa da tambaya.
"Ni ma ban sani ba ƙila ko a can gidan su zasu yi" na bata amsa se ta yi tsaki kawai ta kashe wayar. Bayan
la'asar kuwa se ga yan gidan su Bilal ɗin yan uwan Hajja da matan yayyen sa da suke uba ɗaya dama
babu wacce ta zo barkar da su Farisa kusan su ashirin suka zo kawo kayan. Babbar akwati guda ɗaya se
leda baƙa me dan girma itama da kuma saitin bawo da net ɗin jarirai.
Bayan mun gaisa na koma ɗaki in da na bar su Hansa'u da suka zo mun katsahan ba zato. Ko jiya da
muka yi magana ta ce mun se bayan suna zata samu shigowa Kano kuma yau se gata. Naji daɗi sosai na
riƙe yar ta da tayi kuɓulɓul gwanin sha'awa irin goyon da na ke so na yi kana kallon ta kasan tana samun
kulawa me kyau.
"Anty Halima tsakani da Allah ya zaki mana haka?" Farisa da ta shigo ɗakin ta faɗa. Na mata kallo ɗaya
na ɗauke kai dan nasan ba ze wuce halin na ta na tsugudidi zata yi ba kuma ba zan so ta faɗi wani abu da
zata zubarwa da Bilal mutunchi a gaban ƙawaye na da dama duk ba son sa suke ba. Gefe na ta zauna
tana cewa
"Ni wlh duk se naji kunya, muna murna mun haɗo sha tara ta arziƙi mu taho tsaka ni da Allah a fito mana
da kaya kamar za'a buɗe shago wai na ɓangaren uwa ai da se ki ce kawai kin ya fe ba se mun kawo namu
ba ko kuma a saɓa rana". Kafin na bata amsa Khausar yar ƙanwar Abba ce ta ce mata
"Ke kuwa takwaran Abba guda ai bama ayi komai ba wannan somin taɓi ne, ki jira ranar suna sannan
zaki tabbatar da yaro ɗan gata ne kuma ɗan dangin ya kuma ci sunan babban mutum"
"Ai hakan ma mun gani dan wasu kayan har ya shakara biyu ma ba lallai su masa daidai ba" ta sake faɗa.
Ni dai tafi ki mutu ban ce ba, ba ta haƙura ba ta sake cewa
"Kuma a hakan ma fa mu karo karo muka yi kowa abin da tayi niyyar bayar wa ne Hajja ta ce a haɗa".
Wannan karon Hansa'u ce ta bata amsa ta ce
"Dama ai haka ake yi, da abin da uban ɗan ya bayar da na yan uwan sa ake haɗewa a yi abin da za'a yi ai
ba ku kaɗai kuke haka ba"
"Au, lallai" ta faɗa daga nan ta tashi ta fita tun da gulmarta ba tayi tasiri ba. Tana fita Baby Bashir ta ce
"Ai it's obvious munafunci take so ta haɗa, irin waɗannan fa ba'a basu fuska Halima yanda zata kwaso
gulmar wasu ta kawo miki kema haka zata ringa kwasar ta ki ta kai wani gurin se kin iya takun ki wlh"
shikenan hira ta koma kan munafukan dangi masu irin Halin Farisa.
Se bayan magriba gidan ya sarara da mutane, Anty Maimuna matar yayan su Bilal na biyu da zasu tafi ta
shigo ɗaki ta saka mun envelope a hannu na ta ce in ji mijin ta a siya wa takwaran sa turare. Dake da
Alhaji Balarabe na san shi ban ma taɓa sanin sunan Abba na ne da shi ba, na mata godiya sosai, ina
kallon Fadila da ta biyo ta tana ta leƙen hannu na dake rigar jiki na me aljihu ce se kawai na zura
envelope ɗin a ciki a raina ina raya ko nawa ne a ciki dan na ji da tudu ba laifi.
Raina ƙal ina cin gasasshen nama da aka baɗe da yajin daddawa ina kallon Anty Labiba da ke ta faman
ware kayan data hargitsa. Allah sarki Abba. Sa guda ya sa aka yanka da yammar da Baba Salamatu ta kira
shi ta ce masa ba'a yi mun abun ƙauri ba, a al'adar gidan mu kuma har yanzu suna yi kuma suna cin sa'a
mata da ake aurar wa suma in da suka zuwa ana musu dan haka sun mayar da shi kamar wani dole shi
ake rabawa mutanen da suka kai kayan barka da masu karɓa naman suna kuma ba'a taɓawa suya me
kyau ake masa a aje wa maijego tayi ta cin abun ta ta bawa wanda taga dama ƙaurin shi ake haɗawa da
yaji a rabawa dangi.
Dake yamma tayi sanda aka yi yankan se kawai ya ce a ɗiba wani kaso a kai can gidan su Bilal ɗin su soya
su rabawa mutanen su sauran kuma aka cire ɗanye na sadaka da wanda za'a gasa mun ragowar Mama
ta kira masu yi mata aikin sallah su ka hau aika ce shi.
Se da ta gama ware kayan tsaf ta nuna mun wanda ta zuba a bakko ta ce
"Waɗannan duk ba na amfanin yansu bane can gidan Mama za'a kai su a ajiye idan lokacin buƙatar su ya
yi se ku ɗakko ba za'a bar su a nan ya bi dare ya kwashe ba". Ɓata fuska na yi ita kuwa ko a jikin ta ta
tattare atamfofi guda biyu da lace ɗaya da suka sako mun ta ce
"Waɗannan ma dai ki ɗinke su kya ƙara na jego". Wato tsabar ta raina kayan ne shine ta ke cewa wai na
ƙara na jego da su, Allah ya yafewa Anty Labiba kawai. Har kusan goma sannan ta tafi tana jaddada mun
har idan ina so na yi taron suna toh fa na karɓi kuɗin duk abin da zan yi a hannun Bilal dan ko pure water
ba sake kawo mun za'a yi daga gida ba sun yi iya bakin yin su.
Da ke da Baba Jummai me aikin Mama Fauziyya aka taho Anty Amina se ta tafi gida. Ban ga Bilal ba se
washe gari da safe dan har Anty Labiba ta tafi bai shigo gidan ba ni kuma tafiyar ta ba jimawa nayi bacci
sai bayan na fito daga wankan safe na tarar da shi a falo da Abba na a hannun sa. Fuska ɗauke da
murmushi kamar bamu samu wani saɓani ba ya ringa kallo na ni kuma na ɗauke kai na shige ɗaki. Se da
Baba Jummai ta karɓi Abba zata yi masa wanka kafin ya biyo ni, ina ƙoƙarin zage zip ɗin riga ta ya
rungume ni ta baya ya ɗora kan sa a kafaɗa ta yana cewa
"Wai yaushe kika koyi fushi haka Halima. Ban za na masa ina ƙoƙarin janye hannayen sa da yake yawo da
su a jiki na.
"Na fa baki haƙuri me kuma kike so na yi ki dena share ni dan Allah?" Ya faɗa a marairaice mun.
"Ni ka rabu da ni" na faɗa ina cigaba da ture shi, be sake ni ba se ma jefa ni kan gado da ya yi ya bi baya
na. Yanda kasan ana kaɗa mazari haka jiki na ya ɗauki rawa saboda yanda ya birkice mun yana neman
canza layi, ko da ban samu ƙaruwa ba amma karen hauka bai cije ni ba da zan yarda ya kusance ni.
Saboda rikicewa na manta ai bani da tsarki, na riƙe hannayen sa ina girgiza kai lokaci ɗaya hawaye ya
ɓalle mun amma na kasa buɗe baki na masa magana. Muryar Baba Jummai ta cece ni, salati ta rafka dan
a buɗe ƙofar ta ke ta juya a sukwane tana sake jan dogayen salati sum sum Bilal ya ɗaga ni ya fice daga
ɗakin ni ko sai da na kwashi kusan minti goma kafin nayi ƙarfin hali tashi na shiga banɗaki na gyara jiki
na. Yinin ranar kasa haɗa ido na yi da Baba Jummai, me lalle da kitso Anty Labiba ta turo mun dama ta ce
mun na wanka kaina da nayi wankan safe na wanke dan haka tana zuwa ta fara saka mun han lalle bayan
ta gama ta hau mun kitso.
Tun da Bilal ya fita be sake dawowa ba, gashi babu waya a hannun sa balle na kira shi dan har lokacin ba
muyi zancen taron suna ba, bai ce mun komai ba nima kuma da ta ce na yi masa maganar ban masa ba.
Abin da ya sa ban wani damu sosai ba saboda akwai kuɗin da Yayan Bilal ya bayar aka kawo mun dana
duba rafar yan dubu dubu ne sababbi dubu ɗari cif sun ishe ni nayi duk wata hidima kuma tun da na ji
Anty Labiban bata sake yo waya ta tambayi yanda muka yi fa shi ba nasan a can gida ma ba zasu kasa yin
wani abu ba da zasu kawo.
*(Based on true life event, some parts are fictional to spice up the story)*
*Wattpad @MaryamahMrsAm*
*Ban yarda wani ko wata ya juya mun labari ta kowacce siga ba tare da izini na ba*
*Kuɗin karatu yana wakiltar mutum ɗaya ne, kiji tsoron Allah karki ɗauki hakkina ta hanyar fitar mun da
littafi*
*KURA A RUMBU littafin kuɗi ne, a biya naira 800, biya a asusun*
*1840175439*
*Access bank*
*PAGE 23*
Se bayan sallar isha'i Bilal ya shigo gidan lokacin ina wanka saboda kitso da lallen da bamu gama da wuri
ba se lokacin. Leda na ga ni da kuma ƙaramin kwalin biscuit a ajiye, sai bayan da na shafa mai na saka
kaya kafinna nufi falo muka gamu a bakin ƙofa yana shirin shigiwa dan haka na juya.
"Ga shi nan na suna ne se ki bawa waɗan da za su zo da safe" ya faɗa yana nuna mun kayan daya ajiye
ɗin.
"Har yanzu baka ce komai ba na ɗauka ma ai ka manta gobe ne sunan" na mayar masa da amsa ina
kallon sa, se ya ce
"To ni menene nawa a cikin abinda zaki yi na taron suna?" Ya faɗa, na kalle shi, da alama daga baya ya
fahimci maganar da ya faɗa ba ta kamata ba se na ji ya kuma cewa
"Amma ko da taron mu ne na mata ai haƙƙin ka ne da ka bayar da abin da za'a ci da wanda za'a yi sauran
hidima da shi" na faɗa ina kallon gefe.
"Halima, amma dai bakya buƙatar na sake maimaita miki abin da ya same ni ko? Ni a yanzu ba ni da
wasu kuɗi da zan baki kiyi hidimar suna da su yanzu ta lafiya ta na ke yi dan ko da kika ga ina fita ba wai
na gama warwarewa ba ne ba nan ƙafata kawai daurewa na ke yi ina takata jira na ke yi a yi salary na je
asibiti na sosai a duba ni" ya faɗa. Na yi shiru kawai ina kallon sa, na tuna ranar da aka kai lefe na a leda,
da ya zo yana lallaɓa ni har yana cewa na biyo shi bashi in sha Allahu zai biya ni da dozen ran da na haifar
masa Bilal junior ko little Halims. Hannu biyu na saka na fara share hawayen da suka ɓalle mun, ya ja
tsaki ya ce
"Daga magana se ki fara yi wa mutane kuka, gaskiya ta na faɗa miki, in ba sata kike sona yi na baki ba ya
kike so na yi? Ni ban hana ki kiyi ba idan kina da kuɗi, amma ni dai bani da abin da zan baki. Ban da ma
bakya tsoron Allah duk kuɗin da ake baki ki na ɓoye wa ni ban saka miki ido na ce ki bani ba shi ne har
zaki iya buɗe baki ki tambaye ni wani abu. To ba ni da su, idan ma saboda yan uwana na da zasu zo ya sa
ku dafa tsiyar ku ku cinye su ma za suyi na su a gida babu lallai ma kowa ya zo, Ni ta kuɗin ragon suna na
ke yi ba wani can shirmen abinci ba" ya sa ke jan tsaki kafin ya fice daga ɗakin yana ci gaba da mita.
Haɗe kai na yi da guiwa na shiga risgar kuka na ma rasa takamaiman tunanin me zan yi? Me ya canza
Bilal haka? Ko kuwa dama can haka ya ke ɓoye mun asalin halayyar sa ya yi se bayan da mu ka yi aure
tukun na?
"Kiyi haƙuri uwata, wannan kukan ba ze kawo miki mafita ba sai dai ki sake jefa kanki cikin wata
damuwar" Baba Jummai ta faɗa, ban san sanda ta shigo ɗakin ba amma yana yin yan da ta yi maganar a
sanyaye jikina ya ba ni duk yan da akayi ta ji yan da mu ka yi da Bilal tun da ba a hankali yayi maganar ba
kuma ƙofa a buɗe ta ke. Hannu na sa na shiga share hawayen amma suka ƙi tsayuwa, ta zauna gefe na
tare da da fa ni ta ce,
"A kwana biyun nan na fahimci abubuwa da yawa dangane da zaman ku uwa ta. Ina yawan jin zancen
mijin ki a bakin Hajiya tun ma kafin kuyi aure amma na ɗauka kawai dan basa son haɗin ku ne amma
yanzu na fahimci sun fi ki gaskiya.
Magana ta domin Allah, a ɗan zaman da nayi da ku na fahimci mutumin da dangin sa duk yan da aka yi
sun so ne su mayar da ke daddawar ɓurma, ke kuma So da ƙuruciya ya rufe miki ido kika kasa gane
hakan".
"Kallon rashin fahimta nayi mata dan ban taɓa ji ba balle na san ma'anar kalmar da ta faɗa daga ƙarshe;
ta ci gaba da cewa
"Ko a ƙauye ban taɓa ganin in da ake haka ba. Haihuwar fari dai ko mutum shi ya yankewa talauci cibiya
yana hoɓɓasa da taimakon dangin sa ya yi abu na bajinta balle wannan yaron da duk wanda ya kalle shi
ya san babu rashi a tattare da shi sai dai mugunta kawai ta hana ya yi miki abin da ya kamata. So ya ke
yan da ya aure ki ki zame masa hannun jari komai iyayen ki su ringa ɗakkowa suna baki toh ni dai ba
zuga ki na ke yi ba amma tun da sauran hasken rana duhu bai cimmiki ba ki ki farka ki kuma ƙwatarwa
kan ki yan ci domin har idan kuka miƙe a haka tabbas ke zaki sha wahala musamman da ya kasan ce ya
riga da ya gane son da kike masa ya fi na sa".
Mayar da kai na nayi ƙasa kawai ina sauraron ta, zuciya ta na so ta kama abin da take faɗa amma kuma
wani ɓangaren ya kore maganganun nata. Kullum haka suke cewa Bilal ba ya so na ni kuma ba zan taɓa
yarda da hakan ba. Abin da na jaddadawa zuciya ta shine Bilal ba shi da kuɗi sannan ya na da matsalar
rashin iya tantance kalmomin da ya kamata ya yi amfani da su a magana shi ya sa yake faɗar kowacce
irin magana ta zo bakin sa ba tare da ya taunata ba, wannan kuma ɗabi'ar mutane da yawa ce ba shi
kaɗai ne haka ba. Wannan tabbacin na bawa kai na ya kuma kore tasirin da maganganun Baba Jummai
suka so suyi a ƙwaƙwalwa ta.
"Bilal ya na so na, kuma na san ba shi da shi ne shi ya sa amma babu abin da ba ze yi mun ba Baba
Jummai" na bata amsa ina murmushin da be kai zuci ba, ta ƙura mun ido kafin ta ce
"Yanda ki ke kyautata masa zato Allah ya bawa maraɗa kunya a sanda zai samu wadatar yi mikin" daga
haka ta miƙe tana gyara goyon Al'amin kamar yanda Abba ya ce ba za'a saka masa wani sunan iyayi ba a
kira shi da hakan. Tana rufe mun ƙofar na sake fashe wa da kuka, ni ya ke cewa ba ni da tunani kuma ba
ni da tsoron Allah na ɓoye kuɗi ban ba shi ba.
Ƙarar waya ta ta sa na tashi na ɗakko ta, Anty Labiba ce. Sai da kirab ya katse wani ya sake shigowa
lokacin na dai dai ta kaina kafin na ɗaga.
"Bacci kika fara ne?" Ta tambaya nasan kuma murya ta da ta ji ne dalili, na samu gangara dan haka na ce
mata
"Eh wlh, na ga ji ne; na ɗan kishingiɗa ban ma san ashe bacci ya ɗauke ni ba"
"Sannu, toh ya kuka yi da Bilal ɗin?" Ta sake faɗa. Sabon kuka ne ya kusa ƙwace mun amma na danne shi
da ƙyar na ce mata
"Ni fa ban yi masa magana ba Anty saboda kin ga fa wayar sa da aka ƙwace sun yi amfani da ita sun
kwashe masa kuɗin account duka, kuma ba'a yi albashi ba ai se yaga rashin hankali na ma idan na yi
masa maganar wasu kuɗi yanzu, sannan gashi ba shi da lafiya ko fita ba ya yi a zo a tara masa hayaniya a
kai a babu daɗi".
"Kuma haka ne" ta faɗa amma se na rasa har ran ta tayi maganar ko kuma baƙar magana ta faɗa mun
tunda na san halin ta sarai, a sanyaye na sa ke cewa
"Kawai a bar taron ko Anty tun da dama yawancin duk waɗan da zasu zo sun je tun muna asibiti wa su
kuma sun zo nan gidan".
"Shikenan se ayi hakan, amma dai kin san yan Galadanci ko an ce babu taron suna ba zasu fasa zuwa ba
kuma jiya Mama duk ta sake aika musu da yaji wanda ya manta ma kin ga an tuna masa, amma dai
shikenan tun da mai gida ya ce ba za'a yi taro ba ai ba a zo masa gida ba bari na kira ta yanzu se a gaya
musu a can gidan ku za'a yi sunan dama ai ba wani abu bane taron sunan a haɗu ne kawai a ci abinci ba
lalali sai kina gurin ba".
"Aa fa Anty shi ba cewa yayi kar ayi ba" na yi saurin katseta kafin ta ƙulla wata maganar, ba ta ja zancen
da tsayi ba ta mun sallama bayan da ta ce itama ai ba cewa tayi shi ya hana ba ta fahimci maganata
kawai zasu yi taron su a gidan Mama shikenan. Ranar kasa bacci na yi har guraren ƙarfe uku sannan,
maganganun Bilal suka yi ta mun yawo a zuciya, se da na ji kaina yana neman tarwatsewa saboda ciwo
kafin na rarrashi kai na nayi bacci.
BILAL
A fusace ya fice daga ɗakin ya koma ɓangaren sa. A falo ya kwanta ya tada kansa da hannu biyu ya tafi
tunani,
Waccen ranar da ya gamu da tsautsayi bayan sun rabu da Nasir ya koma gidan Hajja ya tarar da ita ta na
shirin tafiya dubo Halima ya hanata, bayan sun koma ɗaki ta ke ce masa
"Amma yanzu idan ba mu je ba kar ace mun yi rashin kyautawa, musamman da Balarabiya ce matar
ƙanin uban ta ta shigo har nan ta gaya mun kaga ai ko da kai ba'a kira ka ba ni ai an gaya mun ka bari
kawai na je dai". Zama yayi ya kalallame ta da zance yana nuna mata ai matsayin su ya fi ace can wata
za'a aiko ta faɗa musu kawai ta ƙyale su idan ma za'a je ɗin se gobe da safe tukunna tun da yanzu dare
yayi. Har ƙarfe tara yana gidan Hajjan sai da ya ci abinci kafin yayi mata sallama ya tafi gida a bakin titi
suka sake haɗuwa da Nasir ya ringa masa masifa da ya ce masa bai je asibitin ba har sannan amma ko a
kwalar rigar sa ya ce shifa sai da safe sannan zai je. Sai da ya koma gida kuma gaba ɗaya ya kasa tsaye ya
kasa zaune. Har ya kwanta ya ringa jin kamar hakan da ya aikata ganganci ne musamman da bai san me
suka faɗa da suka je gidan ba kar wannan ƙin zuwan da zai yi ya sa a gasgata maganar su. Sha ɗaya tayi
amma haka ya zura jallabiya ya fita. Bai kuma yi nisa da fita daga layin su ba wasu da bai san ko su waye
ba suka tare shi, kafin ya yi ihu suka rufe masa baki su uku ne, mutum biyu suka masa dukan tsiya ɗayan
ya haye mashin suna gama jibgar sa suka zare wayar sa suma suka hau mashin ɗin su ka arce.
San da aka maida shi gida a lokacin da ya haɗa ido da Halima se ya godewa Allah da abin da ya faru da
shi domin da bai san da wane irin ido ze kalle ta ko ya kalli yan uwan ta ba dan haka nan ya yarda haƙƙin
barin ta da wahalar naƙuda ne ya jefashi halin da ya samu kan sa a yanzun amma kuma sanadin haka ya
shafe laifin sa a idon dangin ta babu wanda ze tayar da maganar ƙin zuwan sa asibiti. Amma kuma bai
zata za'a dawo da Halima gida ba, ya ɗauka daga haka zata wuce gida wanka amma kuma sai gashi an
maido da ita, wannan tabbas be yi masa daɗi ba saboda shi dai yana so ta tafi gida wanka ko babu komai
zai samu sauƙin wasu hidimomin amma ita ya rasa dalilin ta na son dole se ta zauna a gidan ba zata tafi
gidan su ba. Shi ya cewa Hajja ta yiwa su Anty Labiba magana akan su maida Halima gida shima can
gidan Hajjan zai tafi amma suka ƙi, zaman kwana biyar ɗin nan tabbas ba dan Anty Amina ba da bai san
yanda ze yi ba saboda shi dai bai yi wani tanadi ba.
Shi ya sa ya ci gaba da langwaɓewa yaƙi ƙarfafa jikin sa, ba ƙaramin daɗi ya ji ba ganin sun haɗo kayan
barka, ko da bai kama ƙafar wanda aka kawo daga gidan su Haliman ba amma dai sun fitar da shi kunya
dan da ace shi suka bari ya yi ko ya bayar da kuɗin ayi da tabbas ko rabin hakan babu lallai ya samu.
Yanzu ragon suna kaɗai ya rage masa, da yayi zaton tun da Abba ya yiwa takwara ƙila cikin halin dattako
irin nasa ya bashi rago kyauta a yankawa takwaran sa, amma saɓanin da suka samu da Halima akan
zancen sunan ya tabbatar masa da ko da ace Abban ya ambata ze bada tabbas ba zata bari ba domin ya
lura huɗubar Anty Labiba ta fara tasiri a ƙwaƙwalwarta tun da har zata iya ɓoye abu a ɗaki ta ringa ci ita
kaɗai yana kwance bashi da lafiya amma bata bashi ba; ya san kuma huɗubar Anty Labiba ce.
Already kayan abincin su dama saura ne ya san kuma kafin yan barka su janye zuwa ma sun ƙarasa cinye
komai sannan azo batun cefane da sauran kunji kunji, gaskiya shi ba shi da sukunin da zai iya kulawa da
maijego a yanayin da ake ciki, ya mata hannun ka mai sanda taƙi ta fahimta shi yasa kawai ya yanke
shawarar biyo mata ta wata sigar ya rutsata a ɗaki ko zata ji tsoro ta tafi amma duk da haka shi bai ga
alamar zata tafi ba tunda ma maganar taron suna ta ke yi.
Ko naman ƙaurin da aka kai gidan su da farko ya ji daɗin abun amma da ya je gidan Hajja se abub ya juye
masa zuwa ɓacin rai. Hajja ta ce masa wulaƙanci ne ya sa zasu aika musu da ɗanye nama saboda su ja a
zage su a gari bayan kowa ya san yanzu an dena wani ƙauri se su sarakan iyayi, idan dan Allah ne kuma ai
da gidan Bilal ɗin ya kamata a kai San a yanka idan so ake a siya masa mutunchi ba wai a wani sako musu
ƙafar baya ɗaya da rabin ƙirji a buhu a kai musu gida ba. Ta ringa masifa, hatta da kayan barka sai da tayi
ƙorafin saboda nan ma a nuna musu iyakar su ya sa zasu haɗo kaya kamar zasu buɗe kanti, ai ba
gwaninta suka yi ba, taƙamar mace ai ta gidan miji ce ba ta gidan uba ba idan so suke suyi bajin ta se su
buɗa masa Abba ya saka shi a harkokin sa shima ya samu kuɗi ta yanda ze ringa musu abu na bajin ta
yanda suke so. Maganganu dai ba kai ba ƙafa wanda shi kuma ya ji su kamar fami a ran sa dan daman
abinda ya daɗe yana ci masa tuwo a ƙwarya ne ya dai rasa da wa zai tattauna da zai fahimce shi shi yasa
yake yin shiru.
Yanzu tunanin ta in da ragon suna zai fito ya ke dan dagaske ba shi da wasu kuɗi a hannun sa kuma bai yi
yunkurin nema ba. Hafiz ya saka ran ze iya masa wannan rufin asirin tun da ya iya bashi na layya ma
balle wannan da ya jefi tsuntsu biyu da dutse ɗaya ya ce masa Dad ɗin sa ya yiwa takwara, to kuma
tafiyar gaggawa ta kama shi ranar da ya ce masa zasu dawo Kano se dare ya sake kira a wayar Haliman
ya ce masa ba ze samu shigowa Kano ba tafiya ta kama su zasu tafi Finland amma ze tura masa da saƙo
har yanzu kuma saƙon bai iso ba bai kuma san ta yanda zai same shi ya tuna masa ba. Kuɗaɗe da suke
haɗawa na abokanan su na unguwa ko karɓar su a hannu bai yi ba ya ce a bawa Kabir dama akwai
shaddojin da ya siya a gurin sa har an ɗinka bai ƙarasa biyan kuɗin ba da ya san Hafiz zai masa haka da
ragon ya siya da su idan ya so in akayi albashi sai ya cikawa Kabir ɗin. Da wannan fushin ya komada
niyyar karɓar wayar ta ya duba Hafiz ɗin ko ta Whatsapp ne amma ta tare shi da zancen shirme ta sake
ɓata masa rai.
Haka ya kwana yana juyi da tunanin ta in da rago zai fito, wani tunani ya yi, ya tashi da sauri ya shiga
laluba rigar da ya cire. Shaf ya manta da ya yo swapping na layukan sa. Rashin azanci ya sa ya manta bai
siyi ko ƙaramar waya me touch light ba, ta yuwu ma Hafiz ɗin ya tura masa kuɗi ta account bai sani ba.
Ɗan dama dama ya ji, duk da dai ko ya tura ɗin dole se ya je banki saboda ba asalin account ɗin sa
wanda aka ya she shi ya tura masa ba wanda ya ke saving a ciki ya bashi shi kuma dama bai yi activating
USSD transafer ba dole se ya je banki rufin asirin da Allah ya masa kenan da tuni nan ma sun yashe shi.
Da wannan murnar ya yi bacci, washe gari kuwa daga sallar asuba bai dawo gidan ba ya wuce gidan su in
da za'a raɗin suna daga can kuma bayan gari ya waye sosai ya wuce banki.
HALIMA
A makare na tashi saboda baccin da ban samu na yi da wuri ba. Kallo ɗaya za'a mun a karanci damuwar
da ke cunkushe cikin zuciya ta wadda fuskata ta gaza ɓoyewa. Ko da na yi wanka gado na sake komawa
na kwanta dan bani da kuzarin da zan iya yin wata kwalliya. Ina kallon Baba Jummai har ta gama shirya
Alameen ya yi kyau sosai ta ringa masa rawa kafin ta saka shi cikin gadon sa ta fita ta bar mu bayan da ta
sake jaddadamun akan na tashi na shirya kafin mutane su fara zuwa.
Ina saka kayan ina tunanin yanzu idan muka yi baƙin me zan basu? Sai lokacin na jinjinawa wautata, da
na sani kawai na cewa Anty Labiba ya bani kuɗin, har ga Allah ba zan so aga gazawar Bilal ba musamman
a irin wannan lokacin.
Tunani na yi ko na bawa Baba Jummai ta je tayi cefane idan ya so na kira maƙwafta na su Maman Yusuf
su yi abincin tun da ko jiya da rana sai da ta aiko ta tambaye ni akwai aikin da za'a yi na ce mata babu, ni
duk na manta ma ko ba'ayi abinci dan kowa ba ai na yi saboda maƙwafta na tun da dai ban gaya musu ba
zanyi taro ba kuma a cikim layin ko ba zasuyi taron suna ba su kan yi wani abu a aika gida gida.
"To ko snacks zan yi order?" Wata zuciyar ta raya mun, na zauna gefe gado haɗi da rafka tagumi. Ko ban
bawa Anty Labiba komai ba na san da na faɗa mata gaskiyar Bilal ya ce bashi da kuɗi ƙarƙari ta zage shi
amma za'a yi komai a kawo mun daga gida amma yanzu na ce mata ni ce bana son yin taron sunan ko
dai kawai na haɗa kaya na na tafi can gidan tun da su zasu yi taron a can? Amma kuma Bilal zai yarda?
Duk na ringa jerwa kaina tambayar da bani da mai amsa mun. Sanda na fito daga ɗaki tara har ta gota
amma kamar ba gidan suna ba babu wanda ya ƙwanƙwasawa mana ƙofa balle mutane su fara taruwa.
Har raina na ji babu daɗi na tabbatar kuma Mama ta faɗawa yan Galadanci kar su zo saboda bada haka
ba tun sassafe nasan tsofafin gidan mu zasu zo karɓar suna su kuma yan gidan su Bilal ba na ce ga abinda
ya hana su zuwa ba.
Da ƙyar na tura shayi da ƙwan da Baba Jummai ta soya mun, ina zaune zugui ni kaɗai dan Baba Jumman
ta shiga wanka, get na ji ana bugawa. Se da na dan zabura a raina na shiga addu'ar Allah ya sa kona
wanene ba daga ɓangare na bane. Mayafi na ɗakko a ɗaki kafin na fita na buɗe bayan da na tambayi
wanene. Maman Yusuf ce da surukar ta inna da kuma Maman Aliyu. Ina murmushin yaƙe na basu hanya
suka shigo, bayan sun zauna muka shiga gaisawa,
"Tun sassafe na cewa Sidi idan ya ga kun buɗe ƙofa ya gaya mun shiru shiru dai na ce bari mu shigo
yanzu" Maman Yusuf ta faɗa. Na yi murmushi kawai ba tare da na ce mata komai ba kafin na miƙe na
shige kitchen na samu jikin cabinet kawai na jingina ina tunanin me zan basu.
To dai ko bamu da dangi daga ni har Bilal ɗin ace yau ana suna a gidan mu ya ci a ce mun tattaro
maƙwafta sun rufa mana asiri balle daga ni har shi babu wanda za'a yiwa gorin yawan zuri'a amma ace
ko ƙuda babu da sunan ya zo taya mu murna. Muryar Baba Jummai da na ji ta sa na shiga share hawayen
da suka fara saukar mun da sauri, ta wuce ni, tukunyar da ke kan gas ta buɗe bayan ta ɗebo kwanuka ta
shiga zuba miya, na ringa kallon ta da mamaki ita dai bata ko kalle ni ba har ta gama zuba miyar ta jera a
try ta fita da su kafin ta dawo ta zuba tuwo shima ta haɗa da ruwa ta fitar musu da shi. Tabbas da na
farka na ji gidan na ƙamshin miya amma ban gasgata ba. Bayan tafiyar su Maman Yusuf dan basu ci
tuwon ba juye musu tayi suka tafi da shi ta ce na lissafa mata gidajen da za'a aika da tuwon. Baki na
kamar ze tsage dan farin ciki na ce
"Ba dai ke sakarya ba ce a garin ki rufawa miji asiri zaki tonawa kanki asiri banda haka a ina kika taɓa
ganin irin wannan rashin lissafin na ki? Yanzu ba dan nayi dabarar tashi da duku duku na yi tuwon nan ba
yanda mutanen nan suka shigo da me zasu fita su bada labari? Dama salin alin da an gama kai abincin
nan ki saka kayanki da na yaron nan a yar jaka mu tafi can gidan in ya so ma dawo da dare dan ni dai
tunda uwata ta haife ni ban taɓa ganin irin wannan kalan tsiya ba.
*(Based on true life event, some parts are fictional to spice up the story)*
*Wattpad @MaryamahMrsAm*
*Kuɗin karatu yana wakiltar mutum ɗaya ne, kiji tsoron Allah karki ɗauki hakkina ta hanyar fitar mun da
littafi*
*KURA A RUMBU littafin kuɗi ne, a biya naira 800, biya a asusun*
*1840175439*
*Access bank*
*PAGE 24*
A ƙaramar akwati na zuba mana duk abun da na san zamu buƙata a yinin, Baba Jummai ta goya Al'amin
tana tsaye tana jiran na yafa gyale na da na ajiye a gefe. Zama na yi a gefen gado ina rarraba ido kamar
wadda ta yiwa sarki ƙarya, ta kalle ni ta ce
"Ya kuma kika zauna? Tun da dai an kaiwa maƙwaftan nan abinci se ki tashi mu tafi kuma su ce zasu
shigo yinin suna".
"Naga abinda ya ishe ni ni Hasana, yanzu gidan ku ɗin da zaki tafi shine kike cewa baki gaya masa ba? Me
ze miki? Naga tun farar asuba ya fice ya bar miki gidan gashi har sha biyu ta taho ko ɗan tsako be leƙo
gidan nan daga dangin sa ba, kar kiyi ta kanki kin ji. Ni dai idan ma ba zaki tafi ba se in yi gaba abu na in
ya so ki saka ce gidan duk bugun da za'a yi karki buɗe tun da dai baki da abun bawa ma su shigo mikin"
Cewar Baba Jummai. Se na miƙe na yafa mayafin jiki a sanyaye, ta nufi ƙofa tana cewa
"Jira na taro mana ɗan sahu ba ma fita haka da akwati ana kallon mu ba" ta fita. Komawa na yi na zauna
na yi tagumi hannu biyu, ko a waya ba wanda ya kira ni se kace wata mara galihu. Tunanin in da Bilal ya
tafi na shiga yi, gashi ba waya a hannun sa balle na kira shi kuma gaskiya zan so na tafi can gidan nima
tun da zamana a nan dai a yau ba shi da wani amfani. Muryar Baba Jummai da na jiyo da wani da ban
gane ko waye ba ya sa na fita tsakar gida na tarar da ita tare da Abubakar da Saleh suna ƙoƙarin saƙale
Rago a jikin window ɗakin tsakar gida.
"Yanzu da ze yi yankan tun farar safiya ba'a yi ba se yanzu da rana ta take?" Na jiyo ta tana faɗa, su dai
ba su tanka mata ba suka gama ɗaure shi kafin suka shigo falon muka gaisa a tsatstsaye suka wuce. A
falon na zauna Baba Jummai kuma ta kwance Al'amin ta hau aikin gyara kayan ciki tana yi tana mita duk
ta cika mun kunne se kawai na koma cikin ɗaki na rufo ƙofa ta. Har bacci ya fara ɗiba na sama sama
hayaniya ta tashe ni, kamar na doka tsallen murna ganin su Amal da sauran cousins ɗina kusan su goma.
Zuwan su ya wartsakar da ni musamman da na gansu da tulin ruwa da lemo katan katan ga wasu kuloli
da suka ce saƙon Anty Labiba ne ta ce kar wanda ya taɓa se ta zo. Zuwa la'asar gida ya gama cika taf da
dangi na kusa da na nesa ana ta harkokin arziƙi har sannan kuma yan cikin gidan su Bilal babu wanda ya
zo.
Babu ce kawai Anty Labiba bata dafo ta kawo ba tun daga kan abinci zuwa snacks da abubuwan sha iri
iri. Nan gurin dining ɗina ta sa aka tura shi gefe ta zuba kayan suka ringa serving, daga yanda taƙi
matsawa ko nan da can daga kan abincin na fahimci ta shirya wani abu shi yasa har zuciya ta nayi farin
ciki da rashin zuwan dangin Bilal dan dai na san koma menene saboda su ne. Biyar da wani abu na shiga
canza kaya saboda me ɗaukar hoto da ya zo se ga yan gudan su Bilal zuga guda yan ɗakin su da kuma
yan uwan Hajja babu dai dangin Baban su ko ɗaya ko matan yayyen sa a ciki.
Dama tun da Khausar ƙanwar Mijin Fainusa ta zo take tambayar bata ƙaraso ba ne na ce mata eh bata
zauna ba kuma ta tafi dama jiki na ya bani sai ta kira Fainusan ilai kuwa se gasu manya da yara Anty
Amina ce kawai babu.
Falo na suka fara shiga suka gaisa da yan uwana da ke zaune kafin Fadila da Fainusa suka iske ni ɗaki,
Fadilan ta ce na basu key ɗin can falon Bilal tun da nan ɗin ya cika da mutane. Ban musa ba na ɗauka na
bata dan zan fi so su ware gefen.
A can na same su muka gaisa mai hoton ya fara shiga can muka yi hotunan kafin na dawo tsakar gida
muka cigaba. Na ɗauka za'a samu wanda zai yi tunanin basu abinci shi yasa na cigaba da sabgogina,
Ummi yar Anty Sauda yayar su ta biyu tazo tayi kira na wai inji Maman su. Na tarar da su kowacce fuska
a ɗaure kamar zasu rufe ni da duka. A gadarance ta ce mun
Duk da na fahimci in da maganar ta ta dosa dan banga ko ledar ruwa an ajiye musu ba amma na ce mata
"Iskanci ne wato ya saka aka barmu a gantale ko kuwa jira ake mu fito mu ɗibi abincin da kanmu?" Anty
Hauwa, ƙanwa ce gurin Hajja abokanan wasa suke ta faɗa. Se na miƙe ina cewa
"Kuyi haƙuri, ina ga sun shafa'a ne bari na je na musu magana, yanzu za'a kawo muku" na fita daga falon
ina ji suna bi na da ƙananun maganganu. Rasa ta yanda zan tunkari Anty Labiba na yi dan haka na ja
Amal gefe na ce ta ɗauki manyan kuloli a kitchen ta zuzzuba abinci idan Anty Labiba ta tambaye ta ta ce
ƙawaye na da zasu zo an jima za'a ajiyewa se ta kai mun ɗakin Bilal ta ajiye. Shiru shiru kusan minti goma
sai gata, da sauri na tare ta ina tambayar ina abincin ta ce mun Anty Labiban ta ce ba ze ƙare ba duk
wanda ze zo ma ze samu. Ban ji daɗi ba, na ringa jele tsakanin falon da ɗaki amma na kasa yi mata
magana. Bana so na yiwa wani babba maganar ta ce na kai ƙarar ta ko wani abu amma kuma a take
taken ta naga alamar ta shirya yi musu wulaƙanci ne kawai tun da ai taga zuwan su har gaisawa suka yi
kuma ita idan ta haihu naga ai tun ma kafin a fara rabawa mutane abinci take ware na dangin mijin ta.
Hansa'u na jawo akan ta yiwa Anty Labiban magana ta ce wlh babu ruwanta. Na kasa tsaye na kasa
zaune ga Ummi tsaye bakin ƙofa na san kuma ba ze wuce sake aiko ta akayi karɓar abincin ba kuma tana
ji Anty Labiban na yekuwar idan da me buƙatar ƙarin wani abu ya zo ya karɓa, ina kallo ta jinjina kai irin
zata je ta kai rahoto ta juya se kawai na yanke shawarar yin shahada na mata magana. Ina matsawa
gurin na jiyo Mama Sa'a matar kawun su Mama tana tambayar ta an kai wa dangin miji na abinci kuwa?
Anty Labiban ta ce
"Aa ba'a kai musu ba, na manta". Na sauke ajiyar zuciya a filiz na san ba ƙaramin mutunchin Mama Sa'ar
take gani ba da har ta bata amsa me daɗi haka, ina ji ta wuce tana ce mata
"To ki zuba a kai musu dan Allah ba daɗi kusan rabin awa da zuwan su kuma sun shigo sun tarar da
mutane na cin abinci"
"Za'a kai yanzu" ta sake bata amsa. Ta ke na ji sanyi a raina na waske na bar gurin ba tare da na ce mata
komai ba duk da a ƙasan raina na ji kamar na tsaya na ɗibarwa Bilal ban sani ba ko ze bawa su Nasir da
sauran abokanan sa na unguwa amma na san zata iya saka kaina a kular abincin shiyasa na haƙura ban
koma ba. Se da aka kira Magriba taro ya fara watsewa, na samu alkhairi ƙwarai da gaske Abba ma ya yi
goshi daga kan riguna kuɗi da kayan amfani su diaper da omon wanki da su sabulu mun same su babu
adadi zamu ja lokaci sosai kafin su ƙare mana.
Tun da naji za'a kaiwa su Fadila abinci ban sake bi ta kan su ba musamman da ƙawaye na da mu kayi poly
tare suka zo duk hankali na ya tafi ga maƙwafta masu shigowa da sauran yan uwa gaba ɗaya na sha'afa
da su sai da su Baby Bashir zasu tafi na fito raka su kafin ido na ya sauka kan ƙofar ɗakin Bilal ɗin da na
hango yara na tsere a ciki. Gaba ɗaya se na rasa nutsuwa, get na yi niyar taka musu amma na tsaya daga
in da nake na bar su da Hansa'u ta tafi raka su wajen ni kuma na wuce ɗakin Bilal. Babu kowa sai yara
dake wasa da wasu yan gidan su Abban mu yammata suna ɗaukar hoto. Ce musi na yi su fita na kullo
ƙofar dan key ɗin ma a jiki suka bar shi na jefa shi cikin aljihun rigata zuciya ta na bubbugawa dan na san
har dai zasu tafi ba tare da sun yi mun sallama ba tabbas da wuya idan ba Anty ta musu wani abun da ya
sosa musu rai ba ne. Haushin kai na ya kama ni, ko me ya sa ban tsaya na ga abincin da ta zuba musu ba
ko kuma na sake komawa gurin su na tabbatar an basu komai wadatacce, bana ma zaton ta basu
souvenirs ɗin da naga ta bawa ƙawaye na da suka tafi yanzu ƙila ko daga baya aka kawo su.
Haka dai jama'a suka ida watsewa ya rage na jiki waɗanda suka tsaya suka gyara mun gida tsaf ba zaka
ce anan aka sha didimar biki ba, abincin da yayi saura da yawa masu so sun ɗiba sun tafi da shi, ta
zuzzuba mun abinda ze ajiyu na saka a fridge miya kuma da nama na saka a frizeer haka sauran ruwa da
lemo kusan katan goma goma duk na lode su a store, basu bar gidan ba hatta kayayyakin da muka samu
na barka se da suka taya ni na ware su komai ya koma muhallin sa kafin kowa ya wuce gidan sa. Ina
tsaka da shafa mai bayan na watsa ruwa saboda jiki na da ya yi mun tsami sosai Bilal ya dawo.
Da Baba Jummai na jiyo suna gaisawa be shigo ɗaki na ba bayan na gama shiryawa kamar in share shi sai
kuma wata zuciyar ta ce na dai je. Dama na ware masa abinci na sake ɗumamawa na haɗa komai a try na
fito Baba Jummai ta bini da kallo ta na cewa
"Ba dai ɗakin sa zaki kai masa ba" na yi murmushi kaina a ƙasa dan na san baze wuce abin da ya faru jiya
ya sa tayi tambayar ba se kawai na wuce na ajiye su tsakiyar falo kan center table ina cewa
"Ya dai fi miki" ta faɗa tana wucewa ɗaki. Fita na yi na tafi ɗakin Bilal, a falo na same shi yana waya bakin
nan kamar ze tsage saboda farin ciki ina shiga ya yafito ni da hannu, ban matsa kusa da shi sosai ba na
tsaya daga gefe ya miƙo mun wayar na karɓa duk da ban san waye ba sai da na kara a kunne na kafin na
gane Hafiz ne.
Muka gaisa yana tambayar ina Dadyn sa tare da bani haƙuri akan rashin zuwan su wai uzuri ya taso musu
basa ƙasar, ya ce Shahida ta ce idan ta kira ni bata samu na faɗa masa na yi setting layi na private ne idan
ba ni da number kiran ba ze shigo ba se dai na ga missed call kuma tabbas na ga an kikkira ni da number
waje amma ban san ita ba ce shiyasa ban bi baya ba. Jin muna yin sallama Bilal ya raɗa mun a kunne wai
na yi masa godiya, ban san godiyar ta me ce ce ba amma haka na yi ya ce ba komai daga nan na mayar
masa da wayar sa na fita bayan na sanar masa ga abinci can yana jiran sa.
Na zata ba ze zo ya ci ba ganin kusan minti goma har na fara gyangyaɗi kafin ya shigo. Farat farat ba zaka
ce shi ya gama gasa mun maganganu jiya da daddare ba wai har yana tambaya ta ya taro an ce masa an
sha bidiri a gidan nan. Na yi murmushi kawai ina kallon sa yana cin abincin yana soko mun hira, a raina
na raya kenan su Fadila ba wani abu ya sa suka tafi ba tare da mun yi sallama ba ko kuma dai labarin bai
iso kunnen sa ba ne. Da ya gama ci naga alamar yana so ya ja hirar da tsayi na ce masa bacci nake ji, na
ringa kallon sa da mamaki jin ya ce na karanto masa account number na ya samu wasu kuɗi ni ma zai
tura mun wani abu.
Na gama karanta masa ya saka muka yi sallama yana shirin rungume ni na zille na shige ɗaki, na goge ido
na ya fi sau nawa a son na tabbatar da gaske kuɗin da na gani haka suke ko kuwa dai ban ga ni da kyau
bane ba. Dubu ɗari Bilal ya aika mun, dubu ɗari dai a tarihin rayuwa ta da shi tun da muke dunƙulalliyar
dubu goma bai taɓa ɗauka ya bani ba idan ba ta siyan kayan barka ba.
Duk baccin da nake ji sai na ji na wartsake, na rasa ma wacce kalar murna zanyi. Screenshot na yi na
turawa Anty Labiba, kafin su tafi ba kalar habaicin da bata mun ba ace haihuwar fari amma abincin da
za'a ci na suna se dai a dafo daga gidan ubana a kawo mun kuma a haka dan bani da kunya na cigaba da
yi musu kankanba ni me miji kuma yana so na ai ko auren haɗi ba za'a kwata abinda aka mun ba.
Ni dai abin da na ke raya wa a zuciya ta Bilal na so na, duk kuma abin da a ke ganin ba ya mun da ma ce
ba shi da ita ina kuma da yaƙinin wata rana zai mun ninkin abin da ma ba'a taɓa tsammata ba gashi
kuwa ya fara tabbatar da hasashe na. Bacci ma kusan rabi da rabi na yi, bini bini zan farka na ja waya na
duna dan in tabbatar kuɗin na nan ba su gudu ba.
GIDAN HAJJA
Tun safe suka ta shi da kacaniyar taron sunan da suka shirya zasu yi a can gidan. Ita ta ƙarfafawa Bilal
akan ba wani taron suna da Halima za tayi in dai ba can gidan su zata tafi suyi a can ba, daga baya kuma
ta rikiɗa ta ce ita zata yi taro a nan gidan ta, jikan ta na farko na ɗa namiji bai kamata ace ba a yi taron
suna ba. Da Anty Amina ta ce mata in dai ba Halima za'a bawa kuɗi ta yi taro ba se dai a haƙura haka ta
ringa faɗa ta na cewa ita ta kasa ganewa Amina, gaba ɗaya ta canza yi ta ke ma yanzu kamar Halima ce
yar uwar ta ba Bilal ba to ba za'a bata ɗin ba idan ta na so ta fitar da kuɗin ta tayi taron nan itama da
Fadila ta haihu ai babu ƙwandalar kowa su suka yi taron sunan su.
Da Bilal ɗin ya ce mata ba shi da kuɗi yanzu na Rago ya ke ƙoƙarin haɗawa ma ce masa ta yi ita ba
damuwar ta ba ne wannan idan ya so ma ya bari se ranar sati biyu sannan ya yi musu yankan. Haka nan
se da ya basu kuɗin kafin ya samu lafiya a hannun Hajjan. Da safe kuma bayan an gama raɗin suna bayan
da ya je banki ya tarar da Hafiz ya aika masa saƙon da ya girgiza masa lissafi. Ya san tabbas ze yi masa
abu na bajinta domin Hafiz akwai harkar girma amma be zata abun ze kai har haka ba. Babu bata lokaci
ya Abubakar ya ce ya zo ya karɓi kuɗi ya siyo Ragon shi kuma ya wuce wani uzuri.
A gurin da ya siya ya yanka aka feɗe masa kamar yan da Bilal ɗin ya ce ayi sannan ya wuce ya kai can
gidan ya na komawa gida marin sa ne kawai Hajja ba ta yi ba dan a yanda ta ce ta ɗauka yana da hankali
idan ya siyo zai yi tunanin ya fara kaiwa gidan ta ba wai ya wuce ya kaiwa Halima ba. Ta ringa sababi, se
kace wacce aka kai musu garke guda hatta da yayan ta sai da abin ya ba su haushi ga mutane duk suna
zaune suna jin ta take wannan abun. Suna tsaka da sabgogin su Fainusa ta je ta ke basu labarin yanzu
aka kira ta ana can ana bidiri a gidan Bilal, kuma wai duk se ransu ya ɓaci akan me ba'a gaya musu
Halima za ta yi taro ba, har Bilal ɗin Hajja ta kira ya ce shi bai san zata yi ba dan be bata ko sisi ba se dai
idan yan gidan su ne suka shirya abun su, haka suka zari jiki suka tafi har Hajjan da ta ce zata bisu suka
hana ta ta ringa jaddada musu akan duk abin da aka yi su taho mata da shi se gasu yanda suka je haka
suka dawo hannu na dukan cinye se ma asarar kuɗin mota da suka yi dan dai ko ruwa ba'a basu ba a
yanda suka ce. Suka ringa zagin Halima da yan uwan ta suna wassafawa Hajja irin liyafar da suka tarar
ana yi tun daga kwanukan almajiran da suke ƙofar gidan zaka san ana harkar girma a ciki amma tsabar
an raina su ba'a kuma daraja su ba haka nan aka bar su kamar wasu almajirai babu wanda ya bi ta kan su
suka gaji da zama suka taho.
Saboda yan da abin ya harzuƙa Hajja bata iya cewa komai ba, ta ringa kiran layin Bilal wayar na ringing
amma yaƙi ya amsa wannan ya sake ɓata mata rai, duk yan da aka yi da sanin sa shi ya sa ya zagaye ya sa
aka kai musu Rago ba tareda ya yi shawara da ita ba.
WASHE GARI
Tun da na yi wankan safe na ci abinci na sake komawa bacci ban farka ba se azahar lokacin har Baba
Jummai ta gama soya naman tas ta gyara gidan, ban yi mamakin ganin babu wanda ya zo taya ta suyar
naman ba. Se da na sake watsa ruwa sannan na fito, tambayar ta na yi ko Bilal ya shigo ina bacci ta ce be
fito ba ba ta ji motsin sa ba. Abinci na fara haɗa masa, sauran sinasir da waina na ɗumama na ɗibi nawa
na haɗa komai a try na faki idon Baba Jummai na tafi ɗakin. Sallah na tarar ya na yi, bayan ya idar ya
kalle ni da murmushi ya ce
"Sanda na shiga tana can tana soya nama, da kamar na yi mata magana na ga ta goya Al'amin ga hayaƙi
ga kuma zafin wuta kar su dame shi". Na zare ido ina dariya na ce
"Lallai, ka ce ka so ka siya mana magana ta ce ka mata rashin kunya. Ka san mitar Baba kuwa? Ɗazu fa
daga ta masa wanka ta ajiye shi taje zubar da ruwan naga towel ɗin ya buɗe ga farka a kunne na gyara
masa ta na zuwa ta fara mun taratsi wai me na ke dubawa a jikin sa kar na mata sharri na ce ta masa
wani abun" muka yi dariya tare kafin ya ce
"Amma tana da kirki sosai ga aiki, na lura sam bata son ƙazanta itama ko ina fes fes ɗakin ku yana ƙamshi
kamar ba na masu jego ba gaki kema ta na kula mun da ke sosai" ya faɗa ya na jana jikin sa. Ban musa ba
na je, yana shafa fuska ta ya ce
"Jegon nan ya karɓe ki My Halims, wani kyau kullum kike ƙarawa haƙuri na fa ya fara ƙarewa". Zabura na
yi na bar jikin sa da sauri ya fashe da dariya kafin ya ja try ɗin gaban sa ya buɗe ya na cewa
"Kamar kin san yunwa na ke ji sosai, ɗan ɗebo mun naman nan na taɓa. Idan kuma akwai sauran
peppered chicken ɗin jiya ki kawo mun". Zuwa na yi na ɗebo masa naman na haɗo da kazar da ya ce na ji
daɗi da na tarar Baba Jummai a garin lallaɓa Al'amin ta bi shi sun yi baccin tare se na ɗauki abinci na na
wuce da shi muka ci tare muna hira kamar lokacin ya dawwama.
"Akwai tafiya da zan yi, zamu je wani aiki Abuja daga office. Tun shekaran jiya waɗan da zamu tafi tare
suka yi gaba na bari ne dama se an yi suna nima jiki na ya sake warwarewa kafin na bi bayan su cikin
kuɗin aikin da aka bamu ne ma na tura miki wani abu daga ciki jiya" Bilal ya faɗa bayan da muka gama
cin abinci,
"Toh, yaushe kenan kuma zaka tafi?" Na tambaye shi. Ya ɗan ɓata fuska ya ce
"Gobe nake tunani dan suna ta mun waya akan na taho ni suke jira mu fara aikin".
"Amma fa har yanzu jikin ka da saura, na fa lura da kana sallah ƙafar ka daƙyar ka ke lanƙwasata a haka
kuma zaka tafi wani aiki ba zasu canza ka da wani ba?" Na faɗa cikin marairaicewa. Se ya miƙe ƙafar yana
cewa
"No na samu sauƙi fa, rashin yawan motsa jikin ne ma ya sa har yanzu nake ɗan jin ciwo amma babu
wata damuwa zan iya. Kuma ban da abin ki bayan har an bani kuɗi na kashe se na ce kuma ba zani ba
kenan zan mayar musu da kuɗin su".
"Bari na zo na je gidan Hajja, naga ta kira ni tun jiya ashe ban lura ba se ɗazu tukunna" ya faɗa ba tare da
ya bani amsar tambayar da na masa ba. Tattare kwanukan na shiga yi ina cewa
"Bari to na yiwa Baba magana ta raba naman se ka tafi musu da nasu kawai" na fice daga ɗakin. Ina shiga
kitchen na jiyo ana buga get, shi ya fita ya buɗe, gaba na ya faɗi jin muryar Hajja ta na cewa
"Bacci kuke ko me da za'a yi ta bugu ba zaku buɗe ba". Sauri na yi na kashe famfo na bar ɗauraye
kwanukan da na yi niyya da gudu gudu na wuce ɗaki na na shige banɗaki.
Kamar na fasa kuka sanda ya zo ya na ƙwanƙwasawa wai na fito ga su Hajja sun zo, se da na kwashi
kusan minti biyar kafin na fita falon kaina a ƙasa ba tare da na bari mun haɗa ido ba na samu gefe can na
zauna na shiga gaishe su. Bata amsa ba ta fara zazzage mun asalin abin da ya kawo ta wato bin ba'asin
wulaƙanta yayanta da yan uwanta da aka yi jiya.
"Har su zo miki taro a hana su abinci, ban da tsiya me akai aka yi abinci da har kuke rowar sa? Ko da yake
dama shi taka hayen arziƙi in be nuna halin sa ba ta ya za'a gane shi? Duk wata fuffukar da kuke yi kallon
ku kawai muke yi wlh har yaushe Aminun ya zama wata tsiya da har kuke ƙafafa, ai wanda bai san asalin
ungulu ba ne za'a ce masa daga masar take ya yarda. Ke ba dan mutuwa me tonin asiri ba har Aminu za'a
saka shi a jerin masu arziƙi ne balle ya haife ki kamar Bilal ya kalle ki ya aura ai ƙaryar ki" cewar Hajja.
Na rasa dalilin da ya saka a koda yaushe take ƙoƙarin cin mutunchin iyaye na. Idan ma laifi na mata me
yasa ba zata zageni ni kaɗai ba dole se ta haɗo da iyaye na da basu mata komai ba ta zage su ta yi musu
cin mutunchi? A karo na biyu Bilal na zaune akan idon sa da kunnuwan sa Hajja ta ke aibata ni da iyaye
na Lanti da suka zo tare tana taya ta amma be iya ce musu komai ba.
Baba Jummai ta fito daga ɗaki, na tabbata kuma hayaniyar su Hajjan ce ta tashe ta daga bacci tayi mici
mici da ido tana kallon ta ta ce
"Amma dai ko wacece ke baki da ɗa'a ba kuma ki da mutunchi. Ki shigo har ɗakin yarinya ki sakata a
gaba kina zagin iyayen ta da basu ji ba basu gani ba"
"Ni a uwar Bilal" Hajja ta bata amsa, hakan be saka Baba Jumman ta tausasa lafazi ba sai ma Kara
harzuƙa da ta yi ta ce
"Eh lallai ba shakka ashe rashin arziƙin na ku gado ne. Yanzu dai ban da bakya tsoron Allah har ke zaki
cewa wani bai gaji arziƙi ba alhalin ga tsiya nan har ta yi kuka a jikin ku tana neman a kawo mata ɗauki.
Ai wlh Halimatu ce da kaico domin ba tayi miji ba, banda ƙaddara ina ita ina ita ina haɗa hanya da
kwaɗayayyu irin ku? Da zaki ce sun zo suna an hana su abinci gayyar su aka yi ko kuma shi mara zuciyar
ɗan na ki ya bada ƙwayar shinkafa ya ce a dafa balle har ki tada jijiyar wuya saboda an hana su abinci? Se
ka ce dai ana yunwa zaki taho ƙafa da ƙafa kiyi rashin arziƙi saboda an hana abinci ba'a bayar ba ki ɗauki
matakin".
Nemar hawayen da na ke yi na yi na rasa, na zabura na miƙe tsaye tare da ɗora hannu biyu a kai ina juya
wuya kamar wacce aka tsare da bindiga tsabar yanda jini na ya daskare na ma kasa furta komai balle na
hana Baba Jummai cigaba da wannna ɓarin bakin da take kamar wacce aka kwancewa kai.
"Kana ji Bilal? A gaban ka Halima take zagi na?" Mamaki da tsoro suka dirar mun lokaci ɗaya, wai Halima
ta zage ta ni? Yaushe?
Bilal na kalla, fuskar sa ta yi jajir kamar an watsa masa barkono jijiyoyin goshin sa sun fito kamar an zana
su, cikin murya kamar wanda aka shaƙewa wuya ya ce
"Jummai dai ta zage ki Hajja ba Halima ba" se ta ƙarawa kukan ta ƙaimi tana cewa
"Wlh Halima ce ta zage ni, kalaman bakin ta ne saboda ba zata iya faɗa ba ne ta karanta mata idan ba
haka ba me ya haɗa ni da wannan matar? a ina ta sanni balle ta zage ni haka? Wlh duk Halima ce ta
shirya mata tun da dama ai ta san dole zan zo gidan" ta ƙarasa tana sake rushewa da wani irin kuka irin
wanda yake nuna zafin dake cikin zuciyar me yin sa.
"Ashe bayan tsiya har da sharri kuka iya" Baba Jummai ta sake faɗa se kawai na fashe da kukan da ya fi
na Hajjan tashin hankali, murya ta bata ko fita na ce
"Dan girman Allah kiyi shiru, ki tafi babu ruwanki wa ma ya kira wo ki haka kawai yanzu kin ga abinda
kika jawo mun"
"Haka kika kawo Amirah gidan nan ta zage ni yanzu kuma kin sake kawo wata ta zagi mahaifiya ta. Ni
Bilal ban yi lalacewar da zan ɗauki haka ba Halima, idan ni kin zage ni na shanye baki isa ki zagi mahaifiya
ta ba ko ki wulaƙanta dangi na na ɗaga miki ƙafa. Ki tafi gidan ku Halima ki tafi gidan ku.
*(Based on true life event, some parts are fictional to spice up the story)*
*Ban yarda wani ko wata ya juya mun labari ta kowacce siga ba tare da izini na ba*
*Kuɗin karatu yana wakiltar mutum ɗaya ne, kiji tsoron Allah karki ɗauki hakkina ta hanyar fitar mun da
littafi*
*KURA A RUMBU littafin kuɗi ne, a biya naira 800, biya a asusun*
*1840175439*
*Access bank*
*PAGE 25*
Ina zaune a falon har Baba Jummai ta gama haɗa kayan ta tana kukan da nake ji kamar na tashi na shaƙe
mata wuya idan ya so ta yi mai dalili. Ni da ta ke neman ta kashewa aure ai ni ce da kuka ba ita ba, akan
na ce ta tafi tun da ita ta janyo ni ma aka ce na tafin shi ne ta fasa kuka wai na mata rashin kunya tana
ƙoƙarin kare mun mutunchi na watsa mata ƙasa a ido. Ta shi na yi na goya Al'amin bayan da ta fito da
jakar ta daga ɗaki ina kallon ta na ce
"Kuma wlh karki gayawa kowa abin da ya faru, kawai ki ce musu kin gaji da zama a nan ne kika koma
gidan Mama".
"Allah ya shirya ki Halimatu Allah ya buɗe miki idanuwan ki tun kina da sauran lokaci kafin ki ƙarasa
makancewa, kuma baki isa ki saka na yi ƙarya ba, tun da baki da zuciya har namiji ya ce ki bar masa gida
ki share guri ki zaune zan je na faɗawa Hajiya Amina duk irin cin mutunchi da tijarar da ya ke miki ki ke
zaune da shi, kuma zaki san idan zamana yana da amfani ko ba shi da shi, zaki gane baki da wayo yarinya
ga ki ga Mijin nan ga kuma ɗanyan jego" Baba Jumman ta faɗa tana goge fuska.
Na zumɓuri baki ba tare da na sake ce mata komai na ta fice daga falon. Bin bayan ta na yi, se da ta fita
ta bugu kofar get ɗin da ƙarfi kafin na taɓe baki na koma cikin falon a fili ina cewa
"Haka kawai mata babu dangin iya babu na Baba zaki zo ki kashe mun aure, ko meye haɗin ta da Abban
da zata fi ni ɗaukar zafi saboda an zage shi? Ai dai ba Bilal ne ya zage shi ba. Hajja ce, faɗan iyaye ne za ta
wani tsoma baki ta janyowa mutum masifa" na yi tsaki na kwance Al'amin ma kwantar da shi na fita
falon. Sauran naman da su Hajja suka bari na ɗauke na kai kitchen, kashi uku Baba Jummai ta yi dama,
nawa, na dangi na da kuma na Bilal da nasa dangin bayan Hajja ta gama fisajin rashin mutunchi da kanta
ta shiga kitchen ta haɗe kashi biyu ta tafi da shi a roba ko murfi bata tsaya an bata ba.
Sai da na gama gyaran kitchen zuwa cikin falon kafin na koma ɗaki na kwanta kaina yana sara mun
saboda kukan da na yi. Motsin taɓa ƙofa da na ji ya sa na miƙe zaune da sauri ina raba ido ƙirji na na
bugawa kamar zuciya ta zata faso ta fito, ban san ya Bilal ze tarbi zaman da na yi ban tafi gidan mu
kamar yanda ya ambata ba.
A yanda ya fusata ɗazun ta yuwu zama na ya sake fusata shi. Ta shi na yi da sauri na buɗe wardrobe ɗita
na fara ciro kaya ina ajiyewa akan gado, ina jin an taɓa ƙofar ɗakina na saki kayan hannu na na haye kan
gado da sauri na matsa can ƙarshe gado haɗi da cusa kai na tsakanin cinyoyi na da sauri dai dai sanda ya
shigo ɗakin, saurare kawai nake ya rufe ni da duka ko makamancin haka musamman da na ji takun sa
yana kusanto in da na ke, tsoro na ya nunku har jiki na ya ɗauki rawa. Ga mamaki na se ji na yi ya kira
sunana kamar a rikice ya ce
"Kaya kike haɗawa Halims da gaske kenan zaki iya tafiya ki barni?"
Tsam na yi a gurin ba tare da na ɗago ba har sai da ya sake maimaita kiran suna na kafin na ɗago kai na
rabi ina jam ɗankwali na rufe rabin fuska ta, so na ke yi na tabbatar da gaske ne maganar da yake yi ba
wai yaudara ta ya ke so yayi na ɗago ya rufe ni da duka ba. Shammata ta ya yi ya rungume ni, lokaci ɗaya
kuma ya fashe da kukan da sai da zuciya ta ta tsallake bugu. Sake tsananta rungumar da ya yi mun ya yi
cikin kukan da ya ke yi ya ce
"Kai fa ka ce na tafi, kai ka ce na bar maka gidan ka fa" na faɗa ina fashewa da kuka ni ma, sai ya ƙara
ƙarfin rungumar da ya yi mun yana cewa
"Kiyi haƙuri ki ya fe mun Halima babu yanda zan yi ne amma har zuciya ta ba abinda nake nufi ba kenan
kuma na ji daɗi da baki tafi ba ki ka jira har na dawo da ace ban tarar da ke a gidan nan ba da ban san ya
zan yi ba" ya ƙarasa cikin kuka me tafe da shassheƙa.
Wani irin daɗi na ji ya mamaye ni, da na biyewa Baba Jummai shikenan da tuni ta saka ni a uku ni dama
na san da wasa Bilal ya ke yi se dai ya faɗi haka dan ya farantawa Hajja ba wai har ransa ba.
Kukan shagwaɓa haɗi da kissa na koma yi ina ture shi daga jiki na na ce
"Mahaifiya ta ce fa Halima ya kike so na yi? Kin dai san halin Hajja idan ranta ya ɓaci bata tauna magana
tsaf za ta iya yi mun baki idan na saka mata baki a cikin maganar ta shi ya da na yi shiru amma ni ma ban
ji daɗin abin da ta yi ba kwata kwata" ya faɗa yana sake riƙe ni a jikin sa, se na kwantar da kaina a ƙirjin
sa na ci gaba da kuka ba tare da na sake cewa komai ba shi kuma yana ta aikin rarrashi na da faɗa mun
kalamai masu daɗi irin waɗan da na ke da burin saurare daga bakin sa a koda yaushe.
Ɓoye fuska ta nayi a jikin sa ina ci gaba da gunjin kuka amma a zahiri zuciya ta fal farin ciki ji na ke yi
kamar na tashi na taka rawa. Mun fi minti talatin yana rarrashi na kafin na bar kukan da na ke. Kiran
sallar la'asar ya saka ya fita ya bar ni bayan da ya kwashe kayan da ma fito da su duka ya mayar, na ringa
tsalle ina juyi a ɗakin bayan ya fita. Ba saban ba. Wai yau ni Halima Bilal ya ke yiwa kuka ya na bani
haƙuri kamar a film ɗin India.
Ringing ɗin waya ta ne ya mayar da ni cikin hankali na, sai lokacin tunanin me Baba Jummai zata faɗa
idan ta je gida ya zo kaina, ƙila ma har ta je ta kitsa ƙaryar ta, Allah kaɗai ya san me da me ta faɗa kuma.
Ba Mama ke kira ba kamar yanda na yi tunani number ce babu suna dan haka na mayar na ajiye ba tare
da na amsa ba. Al'amin da ya farka na ɗauka na shiga shayar da shi bayan ya ƙoshi ganin baccin bai ishe
shi ba na goya shi na shiga kitchen dan na ga abinda zan sama mana mu ci da dare cikin raina kuma ina
ta zullumin yanda har sannan shiru babu wanda ya kira ni daga gida. To ko gidan Mama Fauziyya Baba
Jumman ta wuce kai tsaye? Amma kuma ko can ɗin ta je duk da Maman ba kamar Anty Labiba sarkin
masifa ba ce na san zata iya kira ta ji ta baki na akan abinda Baba Jumman zata faɗa mata, sai dai idan
kuma ba ta ce musu komai ba wanda na ke fatan hakan.
A can gida kuwa da kuka wurjanjan Baba Jummai t shiga bayan mai adaidaita sahu ya sauke ta. Amirah
na alwala a bakin famfo tayi maza maza ta ƙarasa kafin ta nufi Baba Jumman tana tambayar ta me ya
faru?
"Kada ki ga irin tijara da wulaƙancin da yar uwar ki ta mun saboda na tsaya mata a gaban sirikar ta da ta
tasa ta gaba ta na zagin iyayen ku shi ne ta kore ni wai zan kashe mata aure" Baba Jumman ta faɗa tana
sake rushewa da kuka. Bakin Amirah har kunne ta karɓi jakar Baba Jumman ta na cewa
"Mu je, kin kuwa ci sa'a Abba ya na nan" ta wuce falon Abba Baba Jummai ta bi ta. Tiryan tiryan tun daga
zuwan ta gidan da abubuwan da ta gani da wanda ta ji har zuwa yau ɗin da rashin kunyar da Haliman ta
yi mata duk babu wanda ta manta bata zayyanawa Abba da Mama da ke sauraron ta ba.
Amirah ta ce
"Alhamdulillah, sanda na faɗa ta ce ƙarya na ke yi yanzu ai ba ta gurin balle ta dake ƙarya ta wa. Ai wlh
dama ni na san tun da aka yi na farko ya ga an masa shiru..."
"Baki da hankali ko Amirah? Wa ya kira ki gurin nan ma da farko balle har ki buɗe baki waaa kina magana
se kace kin ga sa'an ki a nan? Wu ce kafin na kwaɗa miki mari a gurin" Mama ta katse ta cikin tsawa, baki
ta tura ta tashi tana waigen su. Ita da ta so ta sake ƙarawa abun gishiri ta yanda Abba ze fusata kawai ya
kashe wannan ƙaddararren auren na Halima kowa ma ya huta amma Mama ta kora ta waje.
Bayan fitar Amirah Abba ya dubi Baba Jummai da ke aikin goge hawaye ya ce
"Kiyi haƙuri Hajiya Halima ba ta kyauta ba kuma se na saɓa mata akan hakan ki je cikin gida nagode".
Kallon Mama ta yi Maman ta gyaɗa mata kai alamar ta yi abin da Abban ya ce dan haka ta miƙe ta fita.
Ta ɗauka a yanda ta zayyana musu abin da yake faruwa da Haliman za su birkice ne take su kira waya su
ce ta taho ko kuma ma takanas a tashi wani ya je ya taho da ita amma saɓanin haka sai ta ga kowannen
su kamar ma basu kama abubuwan da ta faɗa ba ko dai ma sun ɗauka ƙarya kawai ta shirga musu ne shi
yasa Abban ya ce ta tafi cikin gida.
Haushin kan ta ne ya kamata, ita da ta san da Haliman da iyayenna ta duk jirgi ɗaya ya kwaso su ba wani
damuwa suka yi dan an ci zarafin su ba ina zata haƙiƙan ce ta tare musu faɗa? Bata shiga cikin gidan ba
kamar yanda ya ce mata ta ɗauki Jakarta da Amirah ta aje mata a tsakar gida ta yi tafiyar ta, gara ta je ta
faɗawa uwar ɗakin ta ta yuwu ita ta fisu kan gado ta kuma fi su hangen matsalar da Haliman ta ke ciki
tunda taga su abun be wani shalle su ba.
"Gaskiya na gaji da lamarin auren nan na Halima, zan ɗauki komai amma ban da wulaƙanci da kuma
tozartawa. Idan wancan karon Amirah ce ta faɗa ta ƙaryata ta yanzu ai Baba Jummai ba zata mata ƙarya
ba to gaskiya ba za'a yi na uku da ni ba babu dole a ciki, su da suke da abun zagi ba'a zage su ba banga
dalilin da mu zasu ringa zagin mu ba" ta ƙarasa tana huci. Murmushi Abba da ke kallon ta ya yi ya ce
"Yanzu me kike so a yi Amina?"
"Gida zata taho tun da ba daina son ta muka yi ba da zamu bar musu ita suna gallaza mata, shi ya mata
yan uwan sa su mata uwar sa ta yi abun ya yi yawa ai ba zan ɗauka ba" ta bashi amsa a fusa ce tana
laluben lambar Halima a wayar ta. Gyara zama Abban ya yi ya ce
"Amma yanzu da kunnen ki kika ji ta ce shi Bilal ɗin ya ce ta taho gida, kin ha ta taho ɗin? Hakan ya nuna
miki tana son zama da Mijin ta a kowanne yana yi. Ni ba goyon bayan Halima nake yi ba ban kuma ƙarya
ta abin da Amirah ko Jummai suka faɗa ba amma ki sani ba zan taɓa yankewa Halima hukunci akan abin
da ya shafi rayuwar ta da shaidar wasu ba. Ita take zaman aure, da daɗi babu ta zaɓi haka ba kuma ta
taɓa zuwa ta ce ya mata wani abu ba dan haka na sakawa raina tana zaune lafiya da Mijin ta.
Son da take masa ya saka na amince na aura masa ita kuma duk ranar da ta nuna bata da ra'ayin ci gaba
da zama da shi zan wuce mata gaba na rabata da shi"
"Yanzu dai me kake nufi Abba?" Mama ta faɗa tana kallon sa, sai ya miƙe tsaye ya ce
"Ki cire idon ki da kuma kunnuwan ki akan abin da wani ko wata yake kawo miki akan Halima. Har idan
ba ita ta zo ta faɗa mun matsala ba, a guri na lafiya lau ta ke zaune dan haka babu wata magana da zan
saurara" yana gama faɗar haka ya shige ɗakin sa.
"To ke me ye naki a ciki Mama? Ai kamar yanda Abban ya faɗa ne, tun da dai ita bata ga aibun abin da
ake mata ba ko ta kawo ƙorafi ba kin ga ai lafiya lau ne a gurin ta, sai ki bar ta ki ci gaba da yi mata
addu'a kawai tun da haka ta zaɓawa kanta. Dan Allah yan da ya bar maganar ke ma ki shafe ta kamar
bata faru ba. Idan da ta ji zafin abin da aka mata kafin ma ace ta tafi zata yankewa kanta hukunci amma
an ce ta tafin ma taga guri ta zauna se mu cigaba da bin ta da addu'a Allah ya shiga lamarin ya kawo
rangwame" amsar da Anty Labiba ta bawa Maman kenan bayan da ta kira ta ta na mata ƙorafin yanda
Abba ya bagarar da maganar da Baba Jummai ta kawo akan Halima.
****************
Farar shinkafa na dafa tun da akwai sauran stew, sai da na gama jere abincin a dining kafin na tuna da
ban yi wankan yamma ba shima Al'amin ba'a masa ba. Ganin Bilal be dawo ba har na gama se na fita na
shiga kiciniyar hura wutar dan ma ita cen busasshe ne kuma garin akwai iska, ruwan ma kaɗan na saka
dan ya yi saurin tafasa na koma ciki na zuba abinci na ci dan yunwa nake ji sosai, sai biyar da rabi sannan
Bilal ya dawo lokacin har ruwa na ya tafa sa dan haka na kwantar masa da Al'amin na yi shirin wanka na
fita. A bokiti na ringa ɗiba ina juyewa a babban bahon da ke cikin banɗakin tsakar gidan, wani ruwan da
zan zuba a flask da na wankan Al'amin na ƙara sannan na shiga wankan a raina ina mitar Baba Jummai da
take cewa zan ga idan tana da amfani a guri na ko kuma ba ta da shi yanzu da ta tafin menene ban yi ba?
Girki ko kula da Al'amin ɗin ko kuma saka ruwan wankan? Wankan ma gashi zan yi da kaina dama ai na
mugunta ta ke yi mun ta yi jibga mun ganye idan nayi magana ta balbale ni dama masifa wai so na ke ta
ringa mun jiƙa jiƙa na lalace ace ita ta cuce ni.
Ina wannan mitar a raina na ciro ganyen da na bari a ruwa ya juƙu gashi da ma ya yi laushi da safe da
muka yi wankan na ji ta na cewa se an ɗebo sabo da yamma, ba tare da na ko girgije shi ba na yi
bismillah na lafta a gadon baya na. Lokaci ɗaya na fasa ihu saboda wani azababben zafi ya ziyar ci fatata
take baya na ya ɗauki raɗaɗi na jefar da ganyen a gefe na shiga tsalle ina shafo guraren da nake jin zafin
a jikin fata ta. Bilal dake zaune falo yana wa Al'amin wasa jin ihu na ya fito da gudu dai dai nan kuma aka
buga gidan. Banɗakin ya shigo yana tambayar lafiya ba bakin magana sai kawai na fashe da kuka ina
nuna masa bayana yanda ya rafka salati bayan da ya duba bayan ya sa na sake fashewa da wani kukan ya
ce
Zani na na ja na ɗaura kawai na fito ina cigaba da kuka shi kuma ya tafi ya buɗe ƙofa da ake ta bugawa.
Hajiya Inna ce Surukar Maman Yusuf, ina durƙusa gaban kujera ina kuka dan sosai baya na yake mun
raɗaɗi suka shigo falon tare, wai ashe idan an kwashe ruwan ya kamata na bari ya ɗan sarara kuma se an
girgije ganye kafin a fara bugawa tana ganin ganyen kuma ta ce ai dole na ƙone saboda ganye ya gama
dafewa. Daga ƙarshe da towel ta mun wankan ni dai har dare baya na be dai na mun raɗaɗi ba.
Ni na ce mata ba se an yiwa Al'amin wanka ba saboda yanayin garin akwai sanyi sanyi dama ba'a son
raina ake masa wanka biyun ba se mura ta zo ta kama shi a barni da wahala, da zamu kwanta na goge
masa jiki na saka masa kayan bacci kawai. Tsabar yanda yan ayyukan da na yi suka gajiyar da ni dan na
kwana biyu ban ba ina kwanciya bacci ya kwashe ni. Cikin dare azababben kukan da Al'amin ya ke ya
farkar da ni, na buɗe ido daƙyar ina kallon Bilal dake duƙe kai na ya na tashi na, daƙyar na yunƙura na
zauna ido na ko buɗuwa da kyau ba sa yi ya miƙo mun Al'amin ɗin ya na cewa
"Wane irin bacci kike yi haka Halima sai kace wacce ta mutu kusan minti ashirin yaro a kusa da ke yana
kuka amma baki farka ba".
Karɓar sa na yi na fara ƙoƙarin bashi nono amma yaƙi karɓa sai ƙara ware murya ya ke yana canyara kuka
kamar wanda ake wa wani abu, tun ina lallashin sa daga zaune har na miƙe na fara jele a cikin ɗaki sai
lokacin na ga ashe ƙarfe goma da rabi ma sannan ban fi awa ɗaya da kwanciya ba gaba ɗaya.
Tun Bilal na karɓar sa idan na gaji daga ƙarshe ya zare system ɗin sa daga jikin socket na ɗauka ɗaki zai
kaita ya dawo shiru shiru ban ji shi ba lokacin sha biyu har ta gota na saka dogon Hijab na saɓa Al'amin a
kafaɗa na bishi dan ba ze gudu ya barni ni kaɗai da rainon ɗan sa ba ga bacci da ke cin ido na kamar zan
tuntsira, ina murɗa ƙofar falon na fahimci ya rufe ta da muƙulli. Bugun duniya kamar babu mai rai a
ɗakin ga sauro na ta cizo na har na gaji na koma ciki ina kuka Al'amin na yi, ranar naga rayuwa ban samu
sararin runtsawa ba sai ƙarfe huɗu da mintoci dan har an fara kiraye kirayen sallah a wasu masallatan.
Daƙyar na buɗe ido na da na ke jin sa kamar an watsa mun barkono, ƙwaƙwalwa ta har wani yaji yaji
take mun tsabar bacci da gajiyar da ke tattare da ni. In da na kwantar da Al'amin na fara dubawa a zato
na ko yanzun ma kukan yake ta yi ban ji ba irin na daren jiya amma na ganshi yana baccin sa lakadan
kamar ba shi ya gama wujijjiga ni cikin dare ba. Ɗaya gefen na kalla in da Bilal ke tsaye fuska babu yabo
babu fallasa, shi ya tashe ni kenan.
"Amma kin san yau Monday ko?" Ya faɗa yana kallo na. Rufe ido na nayi kafin na sake buɗewa ina
ƙoƙarin tuna me za'a yi ranar Monday ɗin da yake tuna mun amma babu abin da ya zo mun a
ƙwaƙwalwa ta. Ya yi tsaki ya ce
Kallon sa na yi kamar ban fahimci abin da yake nufi ba, in tashi na samar masa abin da zai ci sai ka ce bai
san yanda na raba dare ina raino ba shi kuma ya kulle ƙofa ya sha baccin sa, ƙaramin tsaki na yi na juya
ba tare da na bashi amsa ba na mayar da haƙarƙari na dan ni kam bacci na ke ji. Ban kai ga rufe ido na ba
ya daka mun tsawar da na jita har tsakiyar kaina ta sake haɗe mun da gigitaccen kukan da Al'amin ya
fasa da alama kuma tsawar Bilal ɗin ce ta tsorata shi shima.
*(Based on true life event, some parts are fictional to spice up the story)*
*Wattpad @MaryamahMrsAm*
*Kuɗin karatu yana wakiltar mutum ɗaya ne, kiji tsoron Allah karki ɗauki hakkina ta hanyar fitar mun da
littafi*
*KURA A RUMBU littafin kuɗi ne, a biya naira 800, biya a asusun*
*1840175439*
*Access bank*
*PAGE 26*
Ko ba'a faɗa mun ba na san da wahala idan jini na bai hau ba, daƙyar na lallaɓa Al'amin ya yi shiru na
goya shi kafin na fita samawa Bilal abin da zai ci. Bamu da komai da zai ciyu da safe ban da taliya. Ita na
yi jollof da sauran miyar da ta rage na dafa masa baƙin shayi. Ya ringa kallon abincin kamar wanda na aje
wa mugun abu kafin cikin faɗa faɗa ya shiga tambayar babu nama a gidan ne da zan dafa masa tsurar
taliya ko me?
Haka na koma na ɗebo masa naman ina ajiyewa ya sake balbale ni da wata masifar wai ina kayan tea, na
kalle shi kawai, sai ka ce ua siyo ya ajiye. Ciwon da kai na ya ke mun ba ze bar ni na yi doguwar magana
ba Allah Allah kawai na ke yi ya fita na koma na kwanta amma naga alama shi jan magana ma yake so ya
yi. Wucewa na yi na koma ɗaki na ba tare da na bashi amsar kayan shayin da ya buƙata ba, ban san ya ya
ƙare ba dan bai biyo ni ba ina shiga na kwanta rubda ciki da Al'amin a baya na dan ba zan yi gangancin
sauke shi ya farka na shiga uku ba. Allah ya taimake ni har ƙarfe goma muna bacci kafin ya farka, ba wai
baccin ya ishe ni ba amma na rage, nauyin da kai na ya yi mun ma ya ragu.
Sauran taliyar na ɗumama na ci, babu wuta ni kuma gaskiya ba zan iya kunna ita ce ba, da ya ke garwar
wankan ta mu irin wacce ake haɗawa da gwangwani ce mara nauyi sai kawai na ɗora ta akan gas, na
sake goya Al'amin da yake ƙananun koke koke na shiga gyaran gidan ina gamawa ruwan ya tafasa. A
bokiti na ɗiba da zummar na fara yi masa kafin nan sauran ya sarara sai na yi kar na sake ƙona kaina irin
na jiya.
Duk abin da zan buƙata na ɗakko na ajiye zuciya ta cike da tsoro na zauna, a bokitin na surka ruwan na
shimfiɗa towel a cikin bahon wankan yanda na ke ganin turawa a TikTok su na yi ba irin wankan da Baba
Jummai ta ke yi masa ta cika baho da ruwa ta saka shi a ciki ba.
Cikin ikon Allah na masa wankan ba tare da na shaƙa masa sabulu ko ruwa a hanci ba abin da na ke
tsoro, kafin na gama shirya shi ya koma bacci. Na yi hamdala, na juye sauran ruwan na yi wankan soso
da sabulu kawai dan na aje wankan ganye gaskiya.
Na shirya daƙyar saboda wani irin ciwon baya da kwankwaso da suka tasar mun lokaci ɗaya kamar ba
wanka na yi da ruwan zafi ba, saida na sha paracetamol sannan na kwanta baccin ni ma.
Bamu farka ba sai bayan azahar tukunna na kuma samu sauƙin gajiya da baccin da yake damuna har
ciwo jikin duk na samu sauƙin su. Haka nan muka wuni ni da Al'amin mu kwanta can mu ta shi can muka
sha hotuna abun mu, da yamma ma a Gas na sake ɗora ruwa na yi wanka na fesa kwalliya tun da gida ya
zama namu daga ni sai miji na Baba Jummai ta tafi balle ta fara mun kwakwazo idan na yi kwalliya.
Cikin canjin hannu na na bawa almajiri ya yiwo mun cefane na yi masa sakwara da miyar agusi, a food
processor na niƙa doyar tayi luƙai bayan na gama na gama komai na turare gidan da ƙamshi sannan na
canzawa Al'amin kaya muka kame a falo abun mu muna jiran Dady. Sai da aka idar da sallar magriba ya
shigo gidan, fuska ba yabo ba fallasa ya yi sallama na miƙe tare da Al'amin a kafaɗa ta na nufe shi ina
masa sannu da zuwa. Takaddun hannun sa ya miƙa mun na karɓa shi kuma ya karɓi Al'amin ɗin na wuce
ɗaki jiki a sanyaye na ajiye masa su.
Duk kwalliyar da na yi amma ko kyakkyawan kallo ban samu daga gare shi ba. Haka na wuce kitchen na
ɗakko ruwa da lemo na fito, ban tarar da shi a falon ba na ajiye na leƙa ɗaki nan ma baya nan har can
ɗakin sa na leƙa duk ban tarar da su ba. Tunanin ina suka shige na tsaya ina yi?
Daga tsakar gida na jiyo muryar sa da wani, na leƙa na gan su su uku sun nufo falon hakan ya sa na koma
ciki da sauri na shiga ɗaki na lalubo mayafi. Mutum biyun duk ban san fuskar su ba yanayin su da
harshen su ma kamar ba hausawa ba ko ma in ce ba Musulmai ba. Ya gabatar mun da su a matsayin
abokanan aikin sa Patrick da Joshua sun zo ganin Al'amin.
Na haɗo ruwa da lemo na kawo musu, har zan tafi ɗaki kuma na fasa na koma kitchen ɗin na zubo nama
na sake kai musu. Ban kawo komai a raina ba da irin kallon da naga Bilal ya yi mun na karɓi Al'amin da ya
fara gungini nawuce ɗaki na bar su.
Shiru shiru ina jiran ya kira ni ya ce zasu tafi na ga har takwas ta yi babu alama sai ma tashar Ball da suka
kunna, sakwarar da na yi bata da yawa sosai leda uku ce kawai amma akwai sauran doyar da na dafa na
ga tayi yawa na saka a fridge, fito da ita na yi na mayar kan wuta ta sake tafasa kafin na niƙa ta na haɗa
kayan abincin na jera musu akan dining. Daga yanda Bilal ya watso mun ido sanda na musu tayin abincin
na san na kwafsa, ina kallo ya yi ƙwafa haɗi da ɗauke kai gefe. A raina na ce ikon Allah, ni a haka ma ina
gudun ya ce ban karrama su ba shi yasa na ƙara yawan abincin amma naga alamar kamar laifi na yi a
maimakon na yi gwaninta. Su da basu san dawar garin ba kamar dama jiran abincin suke suka tashi suka
zubo, ina tsaye suka gama duk suka kwashe manyan naman cikin miyar haka dai na zubawa Bilal sauran
na ɗakko ƙaramin try na ɗora masa akai na kai gaban sa na ajiye.
Indomie na koma na dafa na soya ƙwai kamar na san za'a yi haka da zan yi aiken na bada aka siyo mun
na wuce ɗaki na ci. Ko sallama bamu yi da baƙin ba na dai ji sanda suke sallama da Bilal ɗin bai kira ni ba
nima ban fita sai da ya kullo ƙofa ya dawo ya fara kwarara mun kira tun daga tsakar gida.
"Da izinin uban wa kika ɗauki abinci na kika basu?" Ya faɗa dai dai ina fitowa daga ɗaki. Shiru kawai na yi
ina kallon sa dan ban san me ya kamata na ce masa ba, hakan ya sake harzuƙa shi kamar zai rufe ni da
duka ya sake cewa
"Ina miki magana wato ga mahaukaci shi ne zaki mun shiru ko? Saboda baki da hankali baki san dai dai
ba, nan yan uwa na jini na suka zo gidan nan ku ka hana su abinci amma yanzu wasu kattin banza ba
dangin iya babu na Baba sun zo jikin ki na rawa kin ɗebo ruwa da lemo kin basu, bai ishe ki ba kin sake
kawo musu nama sannan abincin baki ko bari ma na ga kalar abin da kika girka ba kin kawo musu tsabar
kin mayar da ni banza shashasha sauran da suka rage zaki zuba ki kawo mun. Sai ki zo ki kwashe tsiyar ki
dan ni ba mahaukaci ba ne da zaki bani sauran arna na ci. Wace tsiyar kika ga sun kawo mana balle ki
ɗauki abinci na ki basu?"
Kallon sa kawai na ke yi yanda ya fitittike yana masifa sai kace wanda na aikatawa wani zunubi, daga na
karrama baƙin sa shikenan cibi ya zama ƙari? Maganar sa ta ƙarshe ta saka na fahimci ainihin dalilin
faɗan na sa, mamakin sa ya nunku a raina. Ban tsammaci a fili na furta
"Yanzu saboda basu kawo komai ba ne ya saka kake wannan masifar ashe" sai kuwa ya yo kaina yana
cewa
"Kika zage ni sai na naɗa miki duka a cikin gidan nan Halima daga ni sai ke babu mai ƙwatar ki a hannu
na". Da sauri na ja baya zuciya ta na bugawa da sauri. Da gaske na tsorata da yana yin sa, lokaci ɗaya
idanun sa suka rikiɗa suka yi jaa. Ya nuna kan sa yana cewa
"Saboda ba su kawo ɗin ba ne, ai ni ba ɗan iska ba ne da zasu zo su cinye mun abinci su tashi ko kuwa kin
ga gida na yayi miki kama da sansanin gajiyayyu da zan ringa ciyar da mutane kyauta?
Wannan ya zama karo na farko kuma na ƙarshe da wani ɗan iska ko yar iska zasu sake zuwa gidan nan ki
ɗauki wani abu ki basu ba tare da izini ni na ba, idan kuma kin cika ke bakya jin magana ki sake" ya faɗa
yana kaɗa yatsunsa biyu a fuskata.
Motsin da Al'amin ya yi ya sa na yi firgigit na kama jiki na guri ɗaya a tsorace kafin na fahimci shi ne na
nutsu ina sauke ajiyar zuciya. Na kasa yarda lafiyar Bilal ƙalau, abin da ya faru yanzu ya saka mun
kokwanto a zuciya ta, an ya kuwa Bilal baya shaye shaye? Gaskiya akwai abin da yake afawa a ɓoye da
yake gotar masa da saitin kan sa dan dai abubuwa da yawa da yake yi basa kama da na wanda yake fully
oriented.
Ban da ma sharrin ƙwaya, na ga daga abincin da yake masifar akai har zuwa naman da ruwan da lemon
babu wanda aka siya da sisin kobon sa. Cikin kuɗin da na samu na suna na yiwo cefane na, gishiri ne
kawai ban siyo ba amma hatta mai da maggi sai da na siya. Komai na mu ya ƙare Macaroni ce leda shida
da Taliya biyu sai shinkafa da nake zaton ba zata haura kwano ɗaya da wani abu ba shikenan abun da ya
yi mana saura. Niyya ta idan ya dawo ya ci abinci muka nutsu na yi masa zancen kayan abincin ga kuma a
yanda ya dawo gidan.
Ina so na je na bashi haƙuri na tambaye shi ko na dafa masa indomie ya ci kuma ina tsoron kar na je bai
gama hucewa ba na sake tada wani ballin daga ƙarshe dole na haƙura na bari sai da safe zuwa lokacin
duk ma abin da ya sha ya sake shi, sai da na wanke kwanukan da suka ɓata. Har na yi shirin bacci amma
zuciya ta ta gagara nutsuwa, ko da ace wani abun ya sha da gaske bai kamata na barshi shi kaɗai ba. Irin
fushin da na gani tattare da shi kar ya je ma ya yiwa kansa wani abun ina zaune ban sani ba. Wannan
tunanin da na yi ya saka na zabura na tashi na goya Al'amin na saka Hijab na tafi ɗakin sa.
Ta window na hango shi ɗai ɗai akan kujera da waya kare a kunnen sa, duk da ya bani baya ne amma
daga yanayin gefen fuskar sa na fahimci dariya ya ke yi. Wannan ya bani ƙwarin guiwar ƙarasawa na
murza hannun ƙofar sai na ji ta a rufe, ƙwanƙwasawa na yi a hankali tun da ya na kusa na san zai ji amma
bai amsa ba, na sake bugawa karo na biyu still yana zaune ko motsi bai yi ba hakan ya saka na ƙara ƙarfin
bugun ko wayar da ya ke yi ce ta ɗauke masa hankali sai kuwa ga shi ya taso, na ɗauka buɗe mun zai yi
ga mamaki na sai gani na yi ya kashe fitilun falon dan switch ɗin a kusa da ƙofar suke sannan ya koma ya
yi kwanciyar sa akan kujerar.
La shakka na san ya san da tsayuwa ta hakan da ya yi kuma yana nufin kar ma dame shi ne ko kuma baya
buƙata ta a gurin kenan. Na rasa me zan yi, haushi ya kamata na ji ko kuma dariya zan yi oho, haka nan
na ja ƙafafu na na koma ɗaki, ina sauke Al'amin Bismillahi ya ce dawa Allah ya haɗa mu. Ashe kukan da
ya yi jiya nafila ne. Yanda kasan wanda ake yankar naman jikin sa haka ya ringa zuga kuka, duk yanda zan
yi na lallashe shi na yi abu ya ci tura daga ƙarshe na kwantar da shi kawai nima na fashe da kukan yana yi
ina yi. Idan na tuna Bilal ya na cikin gidan yake tsala kukan da na tabbatar har maƙwafta suna jiyo shi
amma bai leƙo ya tambayi ba'asi ba sai na ji duniyar ta sake yi mun zafi.
Daƙyar ya yi shiru guraren ƙarfe ɗaya bacci ya ɗauke shi, ina durƙushe gaban gadon nima a haka baccin
ya ɗauke ni bana jin an yi ko minti goma cikakke ya sake farkawa da kukan da ya fi na farko.
Bani da wani zaɓi da ya wuce na ɗauki waya na kira Mama a lokacin tun da in sake komawa gurin Bilal
ma ɓata lokaci ne tun da ai shi ɗin ba kurma bane balle na ce bai ji duk kukan da yake yu ba ne. Kira uku
na yiwa Mama har wayar ta gama ringing bata amsa, ita kaɗai ce bata kashe wayar ta a gidan idan zata
kwanta sai ni saboda raba dare da muke yi muna waya da Bilal lokacin da nake gida amma har Abba
kashe ta sa yake yi su ɗin dai su zan nema su iya kawo mun agaji a kowanne irin yanayi a kuma kowanne
lokaci gashi ban same su ba haka nan na aje wayar na ɗauke shi, sai na ji jikin sa ya yi zafi alamar zazzaɓi
na san azababben kukan da yake yi ne ya haifar masa da shi.
Muna da paracetamol wanda aka rubuta masa a asibiti na ɗauka na bashi, haka na ringa jele da shi
kamar jiya sai da sanyin asuba ya fara busawa kafin bacci ya sake ɗaukar sa. Ina zaune dan baccin ma
yaƙi zuwar mun saboda gajiyar da na yi na jiyo motsin buɗe ƙofar Bilal, ban kawo zai shigo gurin mu ba,
to me zai yi mana? Kwatsam kuma na ji an buɗe ƙofar falon ban motsa daga in da na ke ba har ya shigo
ɗakin. Na ɗaga kai na dake mun ciwo kamar me na kalle shi, shi ɗin ma ni yake kallo fuska ba yabo babu
fallasa. Mayar da kai na na yi ƙasa cikin taushin da ban tsammaci ji daga muryar sa ba ya ce
Ɗaga kai na yi na zuba masa idanuwa na da suka ƙanƙance saboda kuka da rashin bacci. Da zan iya da na
kwarara masa ashar kafin na ce masa uban sa ne ya same shi ya ke kukan, amma harshe na ya yi mun
nauyi, ba zan iya zagin miji na ba, mijin ma kuma Bilal abin ƙaunata. Sake mayar da kai na nayi ba tare da
na ce masa komai ba. Ina jin sa ya matso in da na ke ya dafa ni yana cewa
"Mai ya samu idon ki haka Halima?" Baƙin ciki da takaici suka tsaya mun a wuya ban san lokacin da na
fashe da kuka ba.
"Dan girman Allah ka fita, idan ka tashe shi wlh Allah sai ya saka mun" na faɗa cikin kuka ina nuna masa
ƙofa.
"Ko ban yi maka Allah ya isa ba haƙƙin kukan da ɗan ka ya ringa yi kana jin sa kayi biris ba ze barka ba. Ka
fita Bilal ka fita bana son ganin ka" na sake faɗa cikin ɗaga sauti.
Kallo na ya sake yi na kusan minti ɗaya dai dai lokacin kuma aka fara tayar da Iƙama a masallaci, ina jin
sa ya sauke numfashi ya ce
"Na faɗa miki zan tafi wani aiki Abuja, Jirgin ƙarfe bakwai zan bi, idan zaki iya ki sama mun abin da zan ci
kafin na fita" yana gama faɗar haka ya fita daga ɗakin na rakashi da kallo idanuwa na na tsiyayar da
hawaye. Wai duk waɗanda suka auri Mazan da suke so haka suke kwasar baƙin ciki kullum ko kuwa ni ce
ban yi dace ba?
Ina kwance kan gado kwata kwata bacci ya ƙauracewa idanuwa na. Wani irin zafi da raɗaɗi nake ji tun
daga ƙasan zuciya ta har zuwa maƙogarona. Duk da bani da tabbacin idan ya dawo daga masallacin zai
sake shigowa ɗakin amma yana fita na rufe ƙofar da muƙulli. Bana buƙatar ganin sa a yanzu, ba dan na
tsane shi ba se dan kawai zuciya ta cike take da fushin halin ko in kulan da ya nuna mana. Ko rashin
zuwan sa asibiti lokacin da na haihu ban ji haushin sa kamar abin da ya yi mun jiya ba.
Sai da na tabbatar ya bar gidan tunda ya ce jirgin ƙarfe bakwai zai bi kafin na fito daga ɗaki. Akan center
table na tarar da farar takarda a ninke na ɗauka na buɗe.
"Kiyi haƙuri, ban san abin da ya hau kaina ba jiya, bana fahimtar komai ba kuma na iya tuna komai. Ki tafi
gida, sati ɗaya zan yi idan kuma na haura haka bazan wuce kwana goma ba" abinda ya rubuta a takardar
kenan. Sai na ji kamar ana yayyafa mun ruwan sanyi a zuciya ta.
Bana so na yarda da gayya Bilal ya wofantar da mu jiya, na fi gasgata baya cikin hayyacin sa ne gashi
kuma ya tabbatar mun yanzu, amma kuma yaushe Bilal ya fara shaye shaye? Ko kuma dama yana yi ni ce
ban sani ba? Wannan tunanin sai ya kawai da yar nutsuwar da na fara samu ta kasancewar ba wai cikin
hayyacin sa ya ke ba. Na zauna na buga tagumi akan kujera. Idan ta tabbata Bilal shaye shaye yake yi na
shiga uku, idan ma kuma hakan halayyar sa ce nan ma ban tsira ba. Gaba ɗaya na rasa tunanin da ya
kamata na yi. Ina zaune sai da na fara jiyo kukan Al'amin kafin na tashi na ɗakko shi.
Ƙarfe sha biyu na gama komai na zuge jakunkunan da na zuba mana kayan da zamu yi amfani da su. Har
na goya Al'amin sai kuma na koma na zauna na yi tagumi. Baba Jummai ta tafi tun shekaran jiya, babu
wanda ya kira ni ya ji ba'asin me ya faru? Ke nan bata faɗa musu abin da ya faru ba ne ko yaya kenan?
Da kamar wuya, kai ko da ace bata faɗi gaskiyar abinda ya saka ta barin gidan ba dole wani abun daban
ta faɗa ƙila kuma ya fi asalin laifin zafi shiyasa kowa yai shiru bai ce mun komai ba.
Har ƙarfe biyu ina zaune ina lissafin na tafi ko na zauna? Ban san me ta je ta faɗa ba, ƙila shi ne dalilin da
ya saka da na kira Mama cikin dare bata amsa ba kuma har zuwa yanzu bata biyo bayan kiran ba Allah
kaɗai ya san mai ta je ta faɗa ta haɗani da iyaye na. Idan na ce zan zauna, tashin hankalin kukan Al'amin
kaɗai ya isa ya zautani, ina buƙatar wanda zai tallafa mun, ƙila ma wani abun ne yake damun sa cikin
daren ni ban sani ba. Ni kai na ina buƙatar mai kulawa da ni dan ciwo nake ji ta ko ina gaba ɗaya bani da
nutsuwa a jiki na da zuciya ta gaba ɗaya.
Haka nan na shafawa ido na toka na tafi gida, kafin na sauka daga Adaidaitan da ya kaini ma na fi minti
biyar sai da ya gaji ya mun magana Allah ya so ni kamar an kori kowa babu mutane a layin na mu balle a
samu munafukan da zasu ce na zo gida daga nan a ƙulla mun munafunci. Ɗakin Mama na wuce kai tsaye
dan babu kowa a falo, bacci na tarar da ita tana yi, baccin rana ba ɗabi'ar ta ba ce sai dai idan bata da
lafiya ko kuma tsananin gajiya. Na kwance Al'amin da ke bacci shima na kwantar da shi a bayan ta
sannan na fita kitchen dan yunwa nake ji kamar me ga baccin da ban yi ba sai yanzu na ke jin sa.
"Yanzu Mama ta ce na yi sauri na gama abinda na ke yi zata aike ni gidanki, ashe kuna tafe". Murmushin
yaƙe na mata kawai dan bani da ƙarfin yin surutu yanzu, shayi na fara haɗawa na shanye daga tsayen da
nake Zainab dai sai kallo na take yi sai bayan na shanye kafin na ce mata taje bakin get ta ƙaraso mun da
akwati na ta wuce ni kuma na shiga buɗe kulolin da na gani na ɗebi abinci. A kan kujerar da na gama cin
abincin na kishingiɗa bacci ya kwashe ni ban farka ba sai ana kiran sallar magriba.
Kaso hamsin na abinda yake damuna ya saukar mun, na miƙe daƙyar saboda kwanciyar da nayi duk jikina
ya ɗaɗɗaure, ɗakin Mama na shiga in duba Al'amin na tarar da ita tana sallah sai na fito na wuce kitchen
in da na jiyo motsi na samu Zainab goye da shi ta ce
"Dama na cewa Mama magagin bacci kike yi, ya farka tun la'asar har ma na tashe ki kika bashi nono kika
ce na duba jakar ki na ɗakko paracetamol na bashi amma Mama ta hana" cewar Zainab.
"Hmmm" kawai na ce na juya na fita. Sai da na yi wanka na sake cin abinci lokacin Mama ta idar da
lazumin ta kafin muka gaisa. Irin kallon da ta ringa mun ya sa na ji duk na tsargu, na faɗa mata Bilal ya yi
tafiya shine na taho gida yanda ta amsa da Tohh kamar bata yarda ba ya sa na fara mata rantse rantsen
da gaske na ke yi ba wata matsalaba ce tafiya ya yi.
"Ni nace matsala ce ta kawo ki gida Halima? Haka kawai ma idan mutum ya bushi iska ya kan je gida ya
huta ai balle ke da dalili. An dai yi rashin sa'a mu ma tafiyar zamuyi jibi zamu tafi Umarah, in da kin yo
waya kafin ki zo da sai in ce kiyi zamanki kawai tun da kin kori yar zaman wankan ta ki ko kuma ki tafi can
gidan su Bilal ɗin ki zauna kafin ya dawo. Amma yanzu ma bata ɓaci ba, sai ki koma, idan kuma zaki iya
zama ke kaɗai shikenan dan har da su Imamu zamu tafi Zainab kuma gida zata tafi har mu dawo dama
kulle gidan zamuyi".
*(Based on true life event, some parts are fictional to spice up the story)*
*Wattpad @MaryamahMrsAm*
*Ban yarda wani ko wata ya juya mun labari ta kowacce siga ba tare da izini na ba*
*Kuɗin karatu yana wakiltar mutum ɗaya ne, kiji tsoron Allah karki ɗauki hakkina ta hanyar fitar mun da
littafi*
*KURA A RUMBU littafin kuɗi ne, a biya naira 800, biya a asusun*
*1840175439*
*Access bank*
*PAGE 27*
Na ɗauka da wasa Mama take yi sai washe gari da safe bayan mun yi wanka na koma rage baccin da ban
yi ba cikin dare saboda Kukan Al'amin ban jima da kwanciya ba Zainab ta tashe ni akan Mama tana kira
na. A falon Abba na same ta, muka sake gaisawa sai Abba ya ce
Ba tare da na kalle shi ba na amsa haɗi da gyaɗa masa kai dan haka kawai kuma kunyar Abban na ke ji
yanzu, ni dai jiki na bai bani aka Baba Jummai bata basu labarin abin da ya faru ba yanda kuma suka mun
shiru ya saka duk na sha jinin jiki na.
"Baki sanar mana da wuri ba kin ga da mun ɗaga tamu tafiyar zuwa lokacin da ze dawo, ke kuma a
yanayin da kike babu damar ace za'a tafi tare da ke" Abban ya sake faɗa. Da sauri na ɗago da zummar in
ce masa mai zai hana daga nan har bangon duniya zan je balle kuma Saudiyya da nake ta cin burin zuwan
ta har yau Allah bai kira ni ba. Duk cikin mu ni kaɗai ce ban taɓa zuwa ba, Mu'azzam har aikin Hajji ya yi
Imam da Amirah sun yi Umarah sau bibbiyu ni kuwa kamar wadda aka sawa hannu duk idan tafiya ta
taso ko dai na rasa visa ko wani dalili mai ƙarfi ya gifta da ina ji ina gani a tafi a barni yanzu ga wata
damar ta samu ina zan yi wasa da ita?
"Saboda kasuwar kurmi kika ji an ce za'a je ai dole ki ce a tafi da ke. Ke matsalata da ke rashin lissafi, idan
ma ƙalau ki ke ai dai kin san ba motar Zaria ba ce balle ki ce a tasha ake yankar ticket sai an nemi Visa
kuma passport ɗin ki ma tun yaushe ya yi expire, ko yana nan ma da wane tsarkin zakiyi ibadar?".
Hawaye na fara matsowa ina cewa
"Amma ai Abba kai ka ce in dai za'a sake yin tafiya da ni za'a je"
"Haka na ce, amma wannan tafiyar babu shiri ta zo kiyi haƙuri idan Allah ya kaimu azumi lokacin abokina
yayi ƙwari sai koma tare da Maman ku kuma in sha Allahu daga bana za'a fara kiran ki Hajiya Halima,
shikenan dai ko?" Abba ya faɗa yana dafa kaina. Baki na kamar ya tsage saboda murna, Mama dai ta
girgiza kai kawai ta yi murmushi tare da taya ni yin godiya. Har na miƙe zan tafi na fara baza labari Abban
ya dakatar da ni ya ce
"To yanzu zaki iya zama a nan gidan idan ya so a samo miki wata a Galadanci ku zauna tare ko kuma can
gidan Antyn ki zaki tafi?"
Yanda Mama ta kalle shi sai na ga kamar ba haka suka tsara ba da alama ya sauka daga layin maganar da
suka ƙulla kafin shigowa ta. Da sauri na ce
"Eh Abba, ko Baba Salamatu ma ko Innar su Salaha tun da babu abin da suke yi kuma ga Zainab sai mu yi
zaman mu".
"Daga haka ta koma gidan ta mana sai su je can su taya ta zaman menene amfanin zaman ta a nan bama
nan?" Mama ta faɗa, na marairaice fuska ina jira na ji Abban ya ce Aa sai ji na yi ya ce
"Hakan ma babu laifi ai, sai ki kira Yaya Salamatun kiji idan zata yarda taje can gidan nata, na san halin ta
dai zata ce gidan siriki ba zata zauna ba shi yasa na ce ta zo nan ɗin su zauna"
"Ni fa kulle gida na zanyi na gaya maka Zainab ma garin su zata tafi dama akwai bikin yayan ta da za'a yi
wani satin, Yaya Salamatu kuwa ba za'a ɗora mata hidimar Halima tana fama da kanta ba, iya kukan ɗan
ta kai kanka raba dare kayi jiya kana zarya balle ita da ba cikakkiyar lafiya ba. Gara ta koma can gidan ta
ta gaya masa ya samo mata wata cikin dangin sa su zauna kafin ya dawo tun da ai sati ɗaya ta ce zai yi ba
wai daɗewa zai yi a can ba" Mama ta sake faɗa sai Abba ya ce
"Gara da kika tuna mun, Halimatu maza ki shirya ki tashi Ibrahim ya kaiku asibiti, bari na kira Dr Lawal
kafin ku isa kukan da yaron nan ya ke yi bai yi kama da na lafiya ba".
"Mantawa dai kayi, ita sanda aka haife ta ba haka ta ringa kukan ba sai da muka kusan yada wanka kafin
ta daina shima na lokaci ne zai dai na" Mama ta faɗa. Bai saurareta ba ya zaro wayar sa yana cewa
"Duk kukan da ta ke yi jikin ta baya ɗaukar zafi irin yanda na sa ya yi kuma har ƙaƙƙafewa idanuwan sa
na ga suna yi kamar wanda zai suma". Sum sum na fice ina jin wani iri a zuciya ta. Daren jiya hatta da
Mu'azzam da ke bacci kamar gawa Al'amin na fara kuka ya farka haka suka ringa karɓa karɓa dan cewa
Mama ta yi na kwanta amma na kasa yin baccin. Na tuna yanda shi Bilal ko a jikin sa amma su duk
hankalin su ya tashi ba su samu nutsuwa ba sai da ya samu bacci dagaske dai ita soyayyar jini ba ta da
mahaɗi.
Haka muka tafi asibitin a raina ina tunanin yanzu Mama zata yarda na zauna a gidan ko kuwa dai korata
za ta yi?
Dr da muka gani ya gama jagwalgwala shi ya ce lafiyar sa ƙalau babu wani abu da yake damun sa ciki da
kunne da cibiya da kai da duk sauran guraren da zasu iya masa ciwo ya duba amma bai ga komai ba. Har
ƙafafun sa da hannaye da su baya ya duba wai ko da a garin ɗauka an gurɗe masa wani guri still dai komi
lafiya. Paracetamol ya rubuta mana kawai ya ce a ringa bashi sau biyu safe da dare ko gajiya ce ta ke
saka shi koke koken.
Muna hanyar komawa gida Suhaila matar Hafiz ta kira ni wai su na ta bugun ƙofa ko bacci na ke yi na
sanar mata ina gidan mu ai, address ta ce na tura mata, bayan na tura ta sake kira na akan na yi mata
sharing location kawai zai fi sauƙi basu gane kwatancen a rubuce ba. Da ke muna dab da gida ina shiga
na hau WhatsApp na tura mata sannan na shiga kitchen bayan na gayawa Mama zuwan na su. Frozen
snacks da Mama bata rabo da su na fitar da samosa na ce Zainab ta soya musu, sai dubulan da dambun
nama. Na zuba dambun shinkafar da ta gama na abincin rana da peppered chicken a warmers masu
kyau duk da bana zaton za su ci amma dai na aje mata komai yanda kawowa kawai za tayi idan sun zo.
Ba'a ɗauki lokaci mai tsayi ba kuwa suka ƙaraso, babyn ta ya girma masha Allah jikin nan luhu luhu
kamar an hura masa iska, tare suka shigo da Hafiz ɗin suka gaisa da Mama ya wuce akan zai je ya dawo
ita kuma ya barta. Kusan awan ta uku sai bayan la'asar kafin ya dawo suka tafi bayan sun sauke mana
tulin kayan tsaraba manyan ledoji guda uku cike da designers kayan jarirai da ko ba'a faɗa ba kana gani
kasan ba ƙananun kuɗi suka lashe ba ga kuma atamfofi super wax turmi biyu da wani arnen lace da ta ce
sirikarta ce ta bayar a kawo mun.
Haka Mama ta cika mata bokiti da dubulan da dambun naman da ta ce sun yi mata daɗi, dambun ma
tafiya ta yi da shi kamar yanda ta ce Hafiz na son Dambu ita kuma bata iya ba. Bayan tafiyar su Mama ta
tsare ni da tambayar ina na samo su? Na ce mata abokin Bilal ne ɗan gurin aikin su.
"Ikon Allah, abokin ma na gurin aiki ne amma ya yi masa wannan hidimar?" Ta faɗa. Na taɓe baki na ce
"Kuma basu wani daɗe tare ba, bayan auren mu aka kawo Hafiz ɗin ma kawai dai Allah ne ya haɗa jinin
su, shima sanda ta haihu baki ga kayan da ya siya musu da zamu je barka ba. Da babbar sallama fa Hafiz
ɗin har rago ya bashi da ke an ce Baban sa mai kuɗi ne sosai nasan Abba ma zai iya sanin sa dan shima
tsohon ɗan kwangila ne" na bata amsa. Ta yi jum kafin ta ce
"Ku dai kiyaye, duk dai a yanyin su babu kalar rashin gaskiya ko makamancin haka amma dai ku kama
kanku ku kuma guji abin hannun su ko dan saboda mutunchin ku"
"Shi dai, ni ina ruwa na da su? Ita ce ma take nacin sai mun yi mu'amala amma ni wlh idan ma ba ta kira
ni a waya ba mantawa nake yi da ita shine dai bini bini ya ke zuwa gidan su" na faɗa ina taɓe baki,
Mu'azzam da ya shigo ya ce
"Dama ai dole ya bi su tun da suna da kuɗi. Shi fa mijin nan na ki kwaɗayayye ne kawai, idan kika duba
circle ɗin abokanan sa kaf sun fi shi wadata, kowa a unguwar su ma ya sani an masa tambari baya abota
da talaka, idan kuwa kika ganshi da wanda ya fi rufin asiri to wlh aboki ne irin tun na ƙuruciya da ba
yanda ya iya da shi irin su Nura Tela, su ɗin ma da ta in da yake morar su shi ya sa yake tare da su".
"Kai kuma na hanaka magana akan yaron nan in dai ba alkhairin za zaka faɗa ba amma ka ƙi ji ko
Mu'azzam? Ai shikenan" Mama ta faɗa.
"Ni fa gaskiya na ke faɗi ba wani abu ba ko tun da na ke na taɓa yi masa sharri? Duk abin da zan faɗa
halin sa ne idan kuma ƙarya aka masa ai ga ta nan ta faɗo abokanan sa guda biyu da suke ƙasa da shi".
Ni dai shiru na yi kawai ina bin sa da kallo can ƙasan raina kuma ina ƙoƙarin lissafo abokanan Bilal ɗin da
ya ce wanda suke ƙasa da shi a wadata amma na gaza samo ko guda ɗaya a waɗanda na sani.
Abokanan sa da na yiwa farin sani mutum huɗu ne. Nasir chemist ɗin sa uku kuma na cikin unguwar mu
ma shi ne ƙarami a cikin su banda gidan gona da ya ke da shi yana siyar da kaji da ƙwai sai Abduljabbar
su maƙwaftan mu ne a da kafin suka koma Abuja da zama yanzu haka a CBN yake aiki, sai Nura Tela shi
ma kuma ni dai ba zan saka shi a layin marasa wadata ba domin a shaidar gani da ido ma a guri na ya fi
Bilal tun da matar sa ko makaho ya shafa jikin ta ya san tana cikin jin daɗi, gi da ne kawai za'a ce na Bilal
ya fi na sa kyau da tsari baya ga haka banga ta in da ya fishi ba sai kuma Aliko, shi kam ko a kantin Kwari
ma oga ne. Su ne kusan abokanan sa da duk wanda ya san shi ya san su, sauran ma kuma duk daga na
gurin aikin har na gari kowa da sabgogin sa, gaskiyar Mu'azzam Billa ba shi da abokanai talakawa. Amma
kuma wannan ba hujja ba ce da za'a ce masa kwaɗayayye ko mai son zuciya.
Sai da Anty Labiba ta zo ta ringa fitar da kayan tana faɗar kuɗin su jiki na ya sake sanyi da lamarin Hafiz,
a wata akwati ta zuba kayan dan rigunan duk manya ne ƙananan ciki ba su da yawa ta haɗe su da sauran
na barkar mu data ware ta ɓoye bayan ta gama ta ce
"Na san a ranki zagi na kike kina cewa na tattare muku kaya na ɓoye ko? Duk idan lokacin amfanin su ya
kai da kaina zan fito da su na kawo miki dan wlh ba za'a tattara kaya ki kaisu gidan na san ki sarai yanda
kika ringa kwasar suturun ki kina rabawa ƙannen sa suma haka zaki kwashe ki basu tun da ba sanin zafin
su kika yi ba. Ranar suna ina kallon Lace ɗin da figaggiyar ƙanwar nan ta sa ta saka ko kin zata ban gane
shi ba? Tun ranar ɗaurin auren ki bana jin kin sake sakawa shine kika bata, zanin da ta yi goyo da shi ma
na super da aka kai ki da ita a jikin ki ne".
Ƙasa na yi da kai dan bani da bakin kare kai na ina jin Mama ta na cewa
"Au da kika ce idan aka miki zani bayar da kayan zaki yi ashe da gaske kike yi? To yanzu ina sauran ko su
ma duk kin bayar da su?"
"Aa suna nan wlh duk ban ma taɓa sakawa ba, shima wancan ɗin ba fa bata na yi ba iya zanin ne shi ma
zuwa ta yi ta manto zanin goyo a gida shi ne na bata aro kuma ban san da shi ta tafi ba" na faɗa jin
Mama zata balbaleni da faɗa, ashe da na yi shiru ya fiye mun alkhairi ma nan kuwa ta shiga faɗan ta na
cewa
"Saboda ba da kuɗin ki kika siya ba ai dole ki ce baki san ta tafi da shi ba, meye amfanin rigar da
ɗankwalin toh yanzu? Da kin haɗa kin bata ko banza ta mora tun da sun fi ki sanin darajar sutura.
Shashsha, naga uban da zai sake siya miki kayan balle har ki wulaƙanta su" ta tattare waɗanda su Hafiz
suka kawo ta ce
"Wlh bari na gidan nan duk yan uba sun shiga sun fita sun gurɓata mun ke Mama gaba ɗaya kin koyi faɗa
bayan ba halin ki ba ne" bata kula ni ba ta wuce ɗaki ta bar mu da Anty Labiba. Sai bayan isha'i da Anty
Labiban zata ta fi ta ke cemun
"Gidan ta zaki je ki zauna kafin mu dawo tun da kin ce ba zaki koma gidan ki ba". Na yi rau da ido na ce
"To ba zaki zauna ba idan kuma kika cika mun ciki wlh yanzu zaki tattara ki koma gidan ki. Ina dama kin
zaɓe shi sama da nan ɗin? Da ya kore ki ya ce ki taho ba share guri kika yi kika zauna ba? Tun da haka
kika zaɓawa kan ki ai shikenan, shi dai mutunchi mutum shi yake siyawa kan sa tunda ke kin saryar da
naki ai shikenan" Mama ta faɗa cikin fushi tana gamawa kuma ta fice daga ɗakin ta barmu.
Anty Labiba da ke tsaye ta koma ta zauna kusa da ni haɗi da dafa kafaɗa ta, kamar ina jira na fashe da
kuka na faɗa jikin ta, ta ce
"Bazan ɓoye miki ba ran Mama a ɓace ya ke da ke Halima amma na lura rashin hankali sam bai bari kin
fahimci haka ba"
"Toh ai bata faɗa mun ba" na faɗa cikin kuka. Ta ɗago ni daga jikin ta ta ce
"Ke baki da tunani kenan, baki san abinda kika yi zai ɓata mata rai ba sai ta buɗe baki ta gaya miki?
Halima har sai yaushe zaki fara tunani daidai da shekarunki ne?
Yanzu bayan duk rashin mutunchin da Mijinki ya yi kin san kuma labari ya zo kunnuwan su, baki yi
tunanin ya kamata ko a waya ne ki kira ki bada haƙuri ba sannan sai yanzu ki iya ɗakko ƙafa ki zo gidan ki
ce zaki zauna. Na jinjinawa ƙarfin hali irin naki".
"Ke fa kika ce ko me zai yi mun na yi haƙuri na shanye, kuma na san idan na zo na faɗi wani abu akan
Bilal ke zaki fara cewa dama ai kin faɗa" na sake faɗa ina ƙoƙarin tsaida kuka na. Ta yi murmushin da
kana kallo zaka san na takaici ne kafin ta ce
"Yanzu ai kin gani da idon ki abin da na faɗa ɗin ko? Kuma saboda kar muyi magana shiyasa kika zaɓi ki
nuna masa iyayen ki ba su da mutunchi a idonki zai iya zagin su kuma ki iya cigaba da zama da shi ko?"
"Bilal bai zage ni ba Hajjan su ce, kuma wlh bayan sun tafi ya dawo ya bani haƙuri kuma ko cewa da yayi
na taho gida ya gaya mun saboda Hajja ne amma ba har ransa yayi maganar ba" na faɗa, sai ta sake ni ta
ce
"Ni wlh yanzu abubuwan da kike yi sun daina bani haushi tausayi kawai kike bani saboda baki san me
kike yi ba. Wannan haukan da kike yi ya wuce So Halima you are obsessed with him idan kuma baki yiwa
kanki faɗa kin fahimci zahiri ba zaki haukace a banza ranar da kika fahimci Son ma So wani kike yi. Yanzu
ke kin yarda da wasan da miji zai fututtuke ya ci miki mutunchi sannan ya dawo daga baya ya ce miki
wasa ya ke yi wasan ma kuma ya haɗa har da iyaye a ina ake haka?
Ke ki gwada yi masa irin wasan ki gani idan zaku kwashe lafiya, ba zagi ba, ki gwada ɗaga masa murya ko
kuma cikin wasan ki ce masa BANZA kawai ki gani a ranar idan bai sauya miki kamanni kafin ya kawo
mana ke ba.
A soyayya akwai sanin ciwon kai Halima, a soyayya akwai sanin martabar kai, a soyayya akwai mutunta
kai, akwai aji. So is not do or die affair Halima duk muna soyayya muna da waɗanda muke so amma
hakan ba shi ya saka muke banzatar da kanmu duk da sunan So ba zaman ki da ni bai amfana miki komai
ba domin babu abinda kika koya. Ba alfahari ba ni na yarda da kaina kuma na san na isa mace. Kin sani
da ace sakarya ce ni irin ki da ban kai labari a gidan Saleh ba. Na goga da dangin miji na goga da matan
bariki da na riƙe Allah na kuma yi amfani da baiwar da ubangiji ya mun a matsayi na na mace a gaban
idonki komai ya zama labari. In da na bari soyayyar sa ta rufe mun ido yanda kike yi a yanzu na bishi a
yanda na tarar da shi ƙila yanzu idan ban mutu da baƙin ciki ba da tuni na daɗe da zarewa sai ke akan
Bilal da bai wuci jariri a makarantar tantiran Maza ba.
Yau da ace Bilal is reciprocating, yana maida miki martanin abin da kike yi masa tare kuka zauce kuke
haukan ku babu mai ce miki dan me? Babu mai ganin baiken ki domin dama ai Hausawa suka ce ka gaida
mai gaishe ka amma a nan, ke kaɗai kike kiɗan ki kina rawar ki. Ya mayar da ke wawiya, sai idan buƙatar
sa ta tashi yana so ya cuceki ya miki wayo a lokacin ya ke gwada miki kina da amfani a gurin sa da zarar
kuma ya samu biyan buƙata shikenan da ke da babu duk ɗaya kuke a wajen sa.
Kalle ki, aure kusan shekara biyu amma kullum jiya i yau babu wani canji a tattare da ke wanda za'a ce
kin tsinci wani abu cikin auren soyayyar da kika na ce sai kinyi. Ki kalli ƙawayen ki da kike musu dariya
kina ganin sun auri waɗanda basu da ce da su ba, hatta da Hansa'u da kike cewa zata auri sa'an Babanta
idan akajera ku dake da kika auri yaro sabon jinin sai an ɗauke ta sau dubu ba'a ɗauki ki ba saboda ta fiki
walwala, ta fiki kyan gani da ka kalle ta baka buƙatar a faɗa maka tana cikin farin ciki a gidan auren ta ko
ita kaɗai ta ishe ki ishara da ki gane ƙuruciya ba ita bace soyayya a gidan aure, dacen abokin zama shi ne
kan gaba.
Yanzu ko sati biyu baki rufa ba haihuwar fari amma tun kina gadon Asibiti yake watangaririya da ke.
Mazan kirki ana roƙon su basa so ake ɗauke matan su a tafi da su gida wanka amma me tun yana miki
hannun ka mai sanda har ta kai ya fito ƙiri ƙiri ya kore ki wannan wane irin rashin daraja ne?
Yanda mata muke so mu auri miji mai aji haka kowanne namiji yake son samun macen da ta san kanta,
kisan kanki a sanda miji ya miki abin farin ciki haka ki san kanki a sanda ya ɓata miki rai amma ba ki zama
ballagaza ke son miji duk in da ya ja ki ya watsar nan zaki yi a lissafi na hankali ma kin san dole wata rana
ya ƙosa da halin ki. Wallahi idan baki shiga hankalin ba Halima akwai ranar da sai kin ɗora hannu aka kin
yi ihu a sanda Bilal ze gwada miki ke ɗin ba komai ba ce a gurin sa, a kan idon ki ze ɗakko mace mai aji da
ta san kanta ya riritata a sannan kowa zai zage shi ace ya wulaƙanta ki amma gaskiyar magana ke kika
fara wulaƙanta kanki ba wani ba".
Maganganun ta na ƙarshe suka tsaya mun a ƙahon zuci, Bilal ya auri wata mace bayan ni, ina addu'ar
idan akwai ƙaddarar auren wata mace a rayuwar sa bayan ni ubangiji ya ɗauki raina kafin na ga lokacin
domin ko ban mutu ba na tabbatar sai na kamu da ciwon da zai nakasta ni. Ta yaya ma za'a yi Bilal ya so
wata bayan ni? Wane irin mugun fata Anty Labiba take mun haka? Mai ya sa a koda yaushe ita bakin ta
baya taɓa faɗar alkhairi sai aka sin haka?
Ita ta mun baki akan Bilal, ita ta fara faɗin ko xa na aure shi bazan samu farin cikin da nake kwaɗayi ba
gashi da wasa wasa bakin ta ya na neman kamani.
Nayi juyi haɗi da ƙara toshe kunnuwana saboda yanda kukan Al'amin yake neman ya hanani yin tunani
mai kyau. Yau da wuri ya fara dan yanzu haka ƙarfe goma da minti biyar na dare. Tashi na yi jin kukan na
sa yana ƙaruwa, tun magriba na shiga ɗaki na kwanta da sunan kaina yana mun ciwo amma a zahiri
maganganun Anty Labiba na shiga ɗaki na ke ta tusawa a ƙwaƙwalwa ta. Ina buɗe ƙofa Mu'azzam na
turowa da Al'amin ɗin a hannun sa ya miƙo mun shi yana cewa
"Ungo ɗanki mun gaji" na karɓe shi na koma ciki. Ina tsaka da shayar da shi Mama ta shigo ɗakin da
tafasasshen ruwa a bokiti ta ajiye ta sake fita ta dawo da baho. Wanka ta masa da ruwa masu ɗan
banzan zafi ya ringa canyara kuka fatar jikin za ta yi jajir har ƙwalla na yi ita kuwa ko a jikin ta, kafin ta
gama shirya shi ya yi bacci. Ta kwantar da shi tana cewa
"Yanzu Fauziyya ta kira waya ta ji kukan sa shine Baba Jummai ta ce duk yanda aka yi wanka ne ba'a
masa ba ko kuma ruwan babu zafi yanda ya saba ji"
"Amma fa Mama likitoci sun ce a dena saka musu ruwa me zafi sosai wankan yammar ma su suka ce a
dena masa ai" na faɗa ba tare da na kalle ta ba. Ta harare ni ta ce
"Da ruwan zafin na kisa da baki girma kin kawo yanzu har kin haife shi ba, ni tun jiyan ma sha'afa na yi
kema haka kika ringa mana wannan kukan sai da Goggo Habi ta zo ta fara gasa ki haka sannan muka
samu lafiya to irin ƙashin ki ya gado, kuma na ga har yanzu idan kika gaji in ba kinyi wankan da ruwa mai
zafi ba bakya iya bacci".
Shiru na yi dan gaskiya ta faɗa, da na taho na ce na yada wanka amma tun jiyan da jikina ya fara gaya
mun babu wanda ya tuna mun na saka Zainab ta ɗora mun ruwa a gas ɗin waje na girkin sallah yana
tafasa na cewa Mama ruwa ya tafasa ta saka aka tsinko ganye a waje ta mun wankan sannan na ji daidai
a jiki na.
Cikin bacci na ji kamar waya ta tana ƙara, ido a rufe na laluba na janyo ta daga ƙasan pillow da nake kai.
'My world' da na gani ya saka na wartsake ba shiri na tashi zaune. Sai da ta katse ya sake kira, wani
ɓangare na zuciya ta na hanani da in amsa wayar amma gefen dake cike da bege da kewar sa ta ingizani
na danna.
"Fushi dai har yanzu My Halims" ya faɗa cikin wani sauti da ya sakani sakin ajiyar zuciya ba tare da na
shirya ba, ban amsa shi ba na yi shiru. Ya yi murmushi mai sauti da na ji har ƙasan zuciya ta kafin ya ce
"Allah ya huci zuciyar Hali dubu fitila mai haska duniyar Bilal".
"Nasan dariya kike yi, ni dama na sani ba zaki iya dogon fushi da ni ba".
"Yes, na shaida kina So na, masoyi kuma baya fushi da abin ƙaunar sa ai".
"Hmmm, da wannan kake fakewa kenan kana mun duk abinda kaga dama tunda ka san ina son ka" na
faɗa cikin karyewar sauti, so na ke ya ce mun ba haka ba ne, ya bani amsar da zata shafe maganganun
Anty Labiba amma maimakon haka sai ya canza maganar da cewa
"Tun jiya baki kira kin ji ya na sauka ba, ina Al'amin? Ya ji daɗin gadon Mama ya dena kukan banza ko?"
Kasa ce masa komai na yi shima bai damu ba ya sake cewa
"Ɗazu Oga Hafiz ya ke ce mun sun zo tare da Madam sun kawo muku tsarabar Finland, Al'amin ya sha
kaya na sa ni" ya faɗi ainihin dalilin kiran wayar, sai na saki murmushin takaici na cije leɓe na na ce
"Ai kuwa dai, sun zo, sun kawo masa kaya ya kuma gode dama abin da ka kira ka tambaya kenan?"
"Kamar ya ya abinda na kira na tambaya kenan haka na ce miki? Ai ke ya kamata ma ki kira ni tun sanda
suka zo ɗin ki gaya mun ba wai ki jira sai ni na kira ki ba. Kuma ni ba dalilin da ya saka na kira ki ba kenan
saboda ina so naji muryar ki ne tunda kin fara ɗaukar zugar mutane kin canza hali".
"Bacci na ke ji zamu yi magana da safe idan Allah ya kaimu" na faɗa saboda wani yanayi da naji yana taso
mun na san a kowanne lokaci zan iya fashewa da kuka. Yayi shiru kafin ya ce
"Shikenan, Allah ya tashe mu lafiya" ya katse wayar ba tareda ya tsaya ya tambaye ni me yake damuna
ko ya lallashe ni ba. Kife kaina nayi a pillow na fashe da kukan da takamimai ban san dalilin yin sa ba.
*(Based on true life event, some parts are fictional to spice up the story)*
*Wattpad @MaryamahMrsAm*
*Ban yarda wani ko wata ya juya mun labari ta kowacce siga ba tare da izini na ba*
*Kuɗin karatu yana wakiltar mutum ɗaya ne, kiji tsoron Allah karki ɗauki hakkina ta hanyar fitar mun da
littafi*
*KURA A RUMBU littafin kuɗi ne, a biya naira 800, biya a asusun*
*1840175439*
*Access bank*
*PAGE 28*
Washe gari da wuri na fara haɗa kayan mu dan komawa gidan Anty Labiba duk da jirgin dare su Mama
zasu bi amma da wuri nake so na tafi can ɗin dan ko rakiya ba zan tsaya yi musu ba. Gaba ɗaya raina
babu daɗi na tashi, na ɗauka Bilal zai sake kira na daga baya ko kuma da asuba amma shiru. Ina zuge
akwatin kaya na Zainab ta shigo ta ce mun na zo na yi baƙi, na ɗora mayafin doguwar rigar yadin jiki na
ina ƙoƙarin kawar da ɓacin ran dake kwance akan fuskata na fita falon.
Turus na yi a bakin ƙofa ganin Fadila da wata mata da na ga suna yanayin kama sai kuma wata tsohuwa
da ita ma ban gama tantance fuskarta ba. Sake tattaro fushin dana ɗauke a kan fuskata na yi na maido
da shi na ƙarasa da sallama ciki ciki. Da "ina kwana" na gaishe su baki ɗaya matar ta amsa fuskar ta
ɗauke da fara'a Fadila kuma ta gaishe ni baki a kumbure kamar an mata dole. Sai bayan na zauna na
gane tsohuwar Lanti ce wacce suka je gida na tare da Hajja har suka yi faɗa da Baba Jummai.
"Dama Anty Sa'adatu ce ta zo shine Hajja ta ce a rakota ta ga Aminu". Na watsa mata wani kallo jin
yanda ta ambaci Aminun garangatsau kana ji kasan da rashin mutunchi ta yi abun dama, matar ta harare
ta ta ce
"Sunan sa kenan ai Anty" ta bata amsa tana ƙoƙarin sakko yaron ta daga baya. Girgiza kai kawai na yi a
raina ina takaicin sakewa yarinyar tun farko, da nasan haka take bata da mutunchi da wlh bata isa na
mata abubuwan da na mata a baya ba. Mayafin da ke jikin ta ma nawa ne daga aro na ma manta da shi
sai yanzun tun da mukayi aure hatta da plates da cups sai da na ƙara mata a cikin nawa da muka je gidan
ta naga duk tarkace ne natan ba wasu na ƙwarai ba ni a ganina an zama ɗaya ina da su har sun mun
yawa na ɗibar mata amma tun daga zuwan da ta mana ta tafi ta ƙulla mun sharri ta fita a kaina ita ma
kuma ta dena ɓoye ɓoye ta fito mun a asalin halin ta yanzu.
"Ina maigidan nawa ne ko bacci ya ke yi?" Matar ta katse mun tunani, na ji kamar na ce mata Eh baccin
yake kuma ba za'a ɗakko shi ba amma hakan sai ta mun kwarjini dan haka na miƙe na wuce falon Abba
bayan na ce mata bari na karɓo shi.
Sai bayan da Mama ta fito kafin Fadila da Lanti suka gabatar mata da matar da suka zo tare a matsayin
ƙanwar Hajja ta Jos, dama ni ɗaki kom na cigaba da abinda nake yi. A ɗakin Fadila ta tarar dani, ban ko
ɗaga kai na kalle ta daga danna wayar da nake yi ba. Ta gama kalle kallenta kamar tayi ajiyar wani abu
kafin ta ceygg
"Hajja ta ce idan mun zo ki nuna mun kayan da Yaya Hafiz ya kawo muku".
Ban ko yi motsin da zai nuna mata alamar na ji me ta faɗa ba, a raina kuwa juya maganar na ringayi.
Hajja tace na nuna mata kayan da Hafiz ya kawo, to ya akayi ta sani? Sai dai idan Bilal ne ya gaya mata
shine zata turo ta tunda shi bai gani ba su suzo su gani ko?
Wane ɓangare na zuciya ta ya shiga ƙoƙarin kare Bilal ta hanyar gwada mun ba shi ya turo su ba amma
kuma tunani mafi rinjaye shi ɗin ne tunda ina da tabbacin Hafiz dai ba zai je ko ya kira su ya faɗa musu
ba.
"Zan je na faɗa mata kin ce na ƙarfi ne idan muna da gado a ciki mu taru mu ƙwata" ta sake faɗa kamar
wata yarinya ƙarama.
Sai lokacin na kalle ta, murmushin takaici ya ƙwace mun na girgiza kai na ce
"Ai ba yau zan fara sanin ke ɗin maƙaryaciya bace kuma masharranciya, kije ki faɗi hakan ni yanzu bani
da lokacin ki" na kwanta haɗi da juya mata baya. Ina ji ta ja ƙwafa kafin ta fita ta bugo mun ƙofa, da
Zainab ta sake zuwa akan nazo muyi sallama zasu tafi ce mata nayi ta ce ina banɗaki kawai. Sai da na
tabbatar sun bar gidan kafin na fito falo Mama ta bani dubu goma da turmin Atamfa Holland sai riguna
masu kyau guda uku in ji Hajiya Sa'adatu.
"Ai da kin ɗakko mata ta gani dai tun da har ta tambaya" Mama ta faɗa bayan da na gaya mata yanda
muka yi da Fadila, na taɓe baki kawai ba tare da na ce komai ba. Da gaske ban shirya sake ɗaukar
kowanne wulaƙanci daga gurin su ba, ko Anty Labiba ba ta ce na tashi na ƙwaci yancina ba nima a karan
kaina na ƙosa da abinda Hajja da yayanta suke yi mun, ko zan ɗaga wa wani ƙafa a cikin su yanzu ita
Hajjan ce darajar ta haifi Bilal, bayan haka babu wani da zan sake takurawa kaina akan sai ya so ni, miji
na ne kaɗai zan tabbatar da soyayyar sa gare ni ko ta halin ya ya.
Sai bayan la'asar na tafi gidan Anty Labiba saboda Abba da na yi ta jira ya dawo muyi sallama. A ɗakin ta
ta sauke ni, tun kuma daga zuwa na na san yanzu ne zan yi jegon gaske, gyaran da nake ta zullumin ta
ina zan fara da na zauna a can gida na nasan duk zata yi mun.
Har muka kwanta ina jiran tsammanin kiran Bilal ko dan zuwan su Fadila amma na ji shiru, sai da asubar
washe gari na ga missed calls ɗin sa kiran kuma gurin ƙarfe biyu da rabi aka yi shi. Ban bi sahu ba na
watsar da shi kuma ni da kaina na yi mamakin yanda na iya share shi duk da yanda zuciya ta take
azazzalata da kewar sa da kuma son jin muryar sa amma na kanne, ina so na tabbatar da gaske ni kaɗai
na ke haukana akan Bilal kamar yanda kowa yake cewa ko kuwa ba haka bane?
Ina cikin karyawa ya sake kira, ji na yi kamar an yi mun yayyafin ruwan sanyi, na saci kallon Anty Labiba
dake rirriga Al'amin naga sam hankalin ta baya kaina, dama shayi ya rage ban ƙarasa shanyewa ba dan
haka na miƙe da kofin har kuma na shige ɗaki aka yi sa'a bata ce mun komai ba. Ajiye wayar na yi ganin
ta katse kafin na kai ga amsawa na cigaba da kurɓar shayin da ya daina mun daɗi a baki, na saki ajiyar
zuciya jin wayar ta sake ɗaukar ƙara, duk da haka sai da ma ɗan ja aji kafin na amsa cikin shan ƙamshi.
"Lallai kin ji daɗin gida wato sai yanzu ma kika tashi" ya faɗa bayan da na amsa sallamar da ya farayi,
gaishe shi na shiga yi ya amsa kafin ya sake cewa
"Da na ce maka zuciya ta tayi zafi ne?" Na faɗa sai ya sake kwantar da murya ya ce
"Shekaran jiya, daga kalamanki na san bakya cikin yanayi me daɗi a lokacin shiyasa na barki har tsayin
jiya ki huta amma na kasa jurewa cikin dare bacci ya gaza ɗauka ta na kira ki amma baki amsa ba" ya
ƙarasa da wani munafukin sauti kamar me shirin fashewa da kuka. Take jiki na ya hau tsuma, So da
muradin kasancewa tare da shi irin wanda na ke ciki a koda yaushe suka motsa mun. Nima na narke
murya na ce
"Ashe ma ka fahimci bana cikin yanayi mai daɗi amma ka kasa tsayawa ka lallashe ni"
"To yaya ne? Saboda bani da muhimmanci ne ko?" Na ƙarasa ina fashewa da kukan kissa. Tamkar lokacin
yammatanci haka ya rikice ya shiga rarrashi na, ni kuma na samu yanda nake so na cigaba da kukan ina
faɗar maganganun da na tabbatar zasu ƙara hargitsa masa tunani. Mun fi minti talatin muna waya yana
rarrashi na ina ƙara botsarewa har kuma muka gama ban ji ya sako zancen zuwan su Fadila ba dan da
farko na zata ko ta kai gulmar ne shi ne ya biyo kadi ashe ba haka ba ne.
Wunin ranar da sauran ranakun da suka biyo bayan ta cikin farin ciki na yi su saboda yanda Bilal ya rikice
akan boren da na tayar masa, bini bini zai kira ni ya cigaba da bani haƙuri da maganganu masu daɗi haɗi
da tsayawa a zuciya.
Kwanan mu uku a gidan Anty Labiba wanda ya kama kwanan Bilal biyar a Abuja ya gaya mun zai dawo
jibi, kwanaki bakwai kenan kamar yanda dama ya sanar mun zai yi.
"Me zan samu idan na dawo My Halims? Kin san nayi kewar ki da yawa har ban san iyaka ba" ya faɗa
cikin marairaicewa, maganar da yayi ta sa na ji ina ma ina can gida na zai dawo dan gaskiya nima nayi
kewar sa da gaske musamman yanzu da nake ganin komai ya dai daitu idan ya dawo zamu cigaba da
gudanar da rayuwa ne irin yanda na ke mafarkin kasancewa da shi.
"Nima na yi kewar ka sosai, zan girka maka duka favourites, har da alawar madara da Iloka zan yi maka"
na ƙarasa cikin dariyar tsokana"
"Amma kin san ba abinda nake nufi kenan ba ko? Wane kalar abinci ne bana ci kin san a in da na sauka
kuwa a Abuja kin san kalar daɗin abincin su?" Cewar Bilal. A shagwaɓe na ce
"Kana nufin abincin su ya fiye maka nawa daɗi kuma baka kewar girki na kenan?"
"Ba haka nake nufin ba ai kin sani a guri na komai na ki daban ne kawai dai ina gaya miki akwai abin da
zan iya samu a ko ina akwai kuma wanda a gurin kaɗai zan samu na ci na ƙoshi kuma ya gamsar da ni".
Da maganar, da yanda ya yi maganar sai da na rufe ido saboda nauyi da kunyar da suka saukar mun, ina
jin sa yana cewa
"Kawai ki san yanda zakiyi da ni shiyasa ma na gaya miki tun yau idan ba dan haka ba sai dai kawai na ce
miki gani na dawo"
"Amma dai kasan jego nakeyi" na faɗa jin yana so ya mayar da maganar da gaske, ya ce
"And so? Ai kin fara sallah. Ni fa ba wani abu da zaki kawo mun uzuri da shi na karɓa, kawai ki shirya
tarbata Hajiya".
Haka na shiga zullumin yanda zata kaya tsakanina da Bilal domin dai ko karen hauka ya cijeni ba zan biye
masa muyi wani abu a cikin gidan Anty Labiba ba. Na ce kuma zan bishi na sani shine abu na ƙarshe da
zanyi tunanin aikatawa, tsine mun zatayi kawai na bi duniya. Na dai yi ƙarfin halin sanar mata da zancen
dawowar sa.
"Allah ya dawo da shi lafiya" ta faɗa na amsa da "Amin" daga nan muka yi shiru. Akwai shaƙuwa da
sakewa tsakanina da ita da zan iya tattauna maganar da mukayi da Bilal amma yanda abubuwa suke
tafiya yanzu a tsakanin mu nasan wani ruwan zan ɓallo duk da dai na lura dagaske kamar yanda ta faɗa
babu ruwanta da sabgata da Bilal ta zame hannun ta a ciki ba wasa take yi ba.
Ranar da zai dawo ɗin da kanta tace na duba kitchen naga idan akwai abin da zan buƙata da babu a siyo,
jirgin sha biyu ya ce zai biyo dan haka da wuri na fara girkin mai aikin ta ta taya ni kafin sha biyun mun
gama komai. Bilal na sauka ya kira ni ya gaya mun,
"Na biyo mu tafi ko zaki zo daga baya?" Ya faɗa. Na rasa me zance masa sai kawai na ɓige da cewar bana
jin sa na kashe wayar. Babu daɗewa ya sake kira na akan gashi a waje, da na gaya mata ta ce ya shigo
mana ko kuma gidan baƙon sa ne.
Nayi zaton yanda yake nanata yayi kewata idan muka haɗu zai yi kamar ya cinyeni amma sai naga akasin
haka, rungumar da ya mun ma ni ban wani ji ta ba, a gidan ya ci abinci yana ta mun hirar aikin da suka je.
Anty Labiba suka fita harda Al'amin ta ce zasu je karɓo ɗinki ba jimawa zasuyi ba na yi zaton zaiyi amfani
da wannan lokaci ya rage zafi kamar yanda yake ta kwakwazo a waya amma bai nuna alamar komai ba
ƙarshe ya ɓige da nuna mun hotunan da ya yi a gurare cikin sabuwar wayar sa Iphone da ya siya. Sai da
aka kira la'asar kafin ya ce mun zai tafi, ya ja ni jikin sa yana murmushin da ke wanke dukkan laifukan sa
a gare ni ya ce
Gefe na ɗauke kai ba tare da na ce masa komai ba, ya juyo da fuskata ya haɗe bakin mu guri ɗaya.
Yanda kasan na rufe kaina da duka saboda takaicin yanda na kasa riƙe kaina a gaban Bilal. Da ya kira ni
ma kasa amsa wayar na yi to na ce masa me bayan abin kunyar da na kusa tafkawa na je ina ta wani
rawar jiki shi da yake namiji ma bai nuna min zumuɗin sa ba sai ni.
Kwanaki ukun da suka biyo baya kullum zai zo da daddare bayan magriba muyi hira har zuwa ƙarfe tara
ko goma kafin ya tafi. Satin sa ɗaya da dawowa ya sake ce mun zai koma Abujan dama wai basu gama
aikin ba kawai kewata ta saka ya zo. Dama Anty Labiba ta fara ƙananan maganganu akan ɗan abincin da
yake ci idan ya zo abinda dama ko ya zo ko bai zo ba dole za'a dafa ba wai wani abu na daban na ke bashi
ba da ta ke mita akai.
A haka muka cigaba da gungurawa har muka yi arba'in, a ranar kuma na tattara na koma gidana dan tun
ana saura kwana uku aka je aka gyara mun Bilal ma ya dawo daga Abujar da na kasa gane abinda ya
samu a can da ya tattare kusan sati uku tun da ya zo ya tafi bai sake dawowa sai yanzun.
Satin farko na dawowar mu zan saka shi a jere ranakun jin daɗi da kuma farin ciki a rayuwar aure na. Irin
tarairaya da soyayyar da Bilal ya gwada mun ba ta nan kusa ba ce na kuma yarda da gasken da ya ce yayi
kewata haka ne, ban san dalilin sa na ɓoye hakan a wancan zuwan da yayi ba amma dai duk wani
haushin sa da nake ƙunshe da shi daga wancen lokacin sai da ya saka klin da hypo ya wanke fushin tas.
Kamar yanda aka ce yau da gobe bata bar komai ba tabbas haka ne domin kuwa yau na wayi gari babu
ko ƙwayar hatsin da zan sarrafa mu ci a safiyar Talata. Tun dawowar mu nake tsammanin Bilal tun da ya
san cewar komai na mu yayi ƙasa zaiyi ƙoƙarin ya siyo, kusan miya da soyayyen naman da na taho da su
daga gida ne ma suka ɗan ja mu sati ɗayan ba tare da na buƙaci cefane na dole dole ba. Ruwan shayi na
tafasa ma zuwa a flask nayi wanke wanke na gyara kitchen ɗin, indomie guda ɗaya da ta rage na tafasa
na ci dan yunwa nake ji dagaske ba zan iya jira har sai ya tashi daga bacci kafin ya ƙaro wata na dafa
mana ba dan dama na ɗauka guda biyu ce shiyasa ko da ya dawo jiya da dare bai shigo da komai ba ban
wani damu ba.
Ina cikin shirya Al'amin Bilal ya shigo ɗakin yana hamma haɗi da shafa cikin sa, yanda yake yi ko bai yi
magana ba na san yunwa nake ji, ya jefe ni da harar da ban tantance ta wasa ba ce ko ta gaske kafin ya
ce
"Ni na isa? Ba dariya nake yi ba ka san dai haka fuska ta take dama" na faɗa ina miƙa masa Al'amin da na
gama shiryawa. Ya karɓe shi ya zauna tare da shi a gefen gado ni kuma na wuce gaban wardrobe dan
ciro kayan da zan saka.
"Badai baki ɗora abin karyawa ba?" Ya faɗa yana bi na da kallo. Sai da na ware doguwar rigar atamfar da
na ciro kafin na kalle shi na ce
"Na dafa ruwan tea kai nake jira ka tashi ka siyo Madara da Milo tun da da sauran cake ɗin can sai a sha
da shi dan na san babu lallai a samu burodi tun da rana ta fara yi goma yanzu".
"Ban gane na siyo Madara da Milo ba, kina nufin babu kayan shayi a gidan ko me?" Ya faɗa kusan cikin
ɓacin rai, na dakata daga zuge zip ɗin rigar da nakeyi na ce
"Amma dai kai ne ƙarshen amfani da su jiya da dare tun kuma da zaka sha shayin sai da na gaya maka
sauran kenan na juye a container baka kula ni ba".
"Kada ki gaya mun maganar banza Malama, kina nufin saboda na sha shayi da dare dan haka na sha rabo
na ma safe ko me?" Ya faɗa yana miƙewa tsaye. Hannu biyu na ɗaga na ce
"Mai da wuƙar ni ba haka nake nufi ba amma dai kayan tea sun ƙare, ni da wannan sutun ma da
taimakawa kayi ka siyo dan yunwa nake ji sosai Indomin da na ci babu in da ta je mun".
Fita yayi ba tare da ya sake cewa komai ba, na cigaba da shiri na ina mitar yanzu kuma kayan shayi ne
zasu haɗa husuma da safiyar Allah, shi dai baya raina abin magana dama.
Madara biyu Milo biyu ya siyo na sachet sai burodi babba guda ɗaya, na ringa kallon kayan sai dai gudun
jan fitina ya sa ban ce komai ba na ɗora komai a try, sai da na ɗakko container sugar na ga shima ashe ya
ƙare burbuɗi ne a ciki na tattara na kai masa falo in da yake zaune yana jira. Har muka gama karyawa
babu wanda ya ce ƙala, yana gamawa ya wuce can part ɗin sa, ƙamshin turaren sa da na jiyo har cikin
falo na ya sa na gane wanka ya yi zai fita, ina nan ina sauraren ya shigo na ji yanda za'ayi da girkin rana
sai jin ƙarar rufe get na yi. Na tashi na fita da sauri amma ko ƙurarsa ban tarar ba sai ƙamshin sa da ya
baza tsakar gidan.
Komawa na yi na ɗauki waya ta na shiga kiran sa, kira uku bai amsa ba haka na haƙura na ƙyale shi. Shiru
shiru har sha biyu bai biyo kiran ba ga yunwa ta fara kawomun farmako dan Al'amin tsotso ne da shi ba
na wasa ba, sha ɗaya idan ya yi sai na samu wani abun na cike gurbi. A can gidan Anty Labiba da yake ba
na aikin komai sai dai na ci abinci na kwanta shi ya sa na cika na yi dam kamar ba jego nake yi ba yanzu
kuwa daga dawowar mu sati guda har na fara jin ƙashin wuya na ya bayyana.
Ganin tunanin da tsammanin dawowar Bilal ba zasu kaini ko ina ba ya sa na zura Hijabi na na fita neman
yaron da zan aika. Babu kowa a layin kasancewar rana ta take haka ta taka har bakin titi na yo cefane na
da kaina. Sai bayan la'asar ya dawo na ringa kallon sa kawai yanda ya shigo babu ko tsinke a hannun sa
sai fuska da ya haɗe kamar hadari amma da ya shiga kitchen ya fito sai naga ya ɗan saki fuskar ba kamar
sanda ya shigo ba. Sai a lokacin ya ke ce mun wai ya ga missed calls ɗina me ya faru?
Takaici yanda ka san na rufe shi da duka kuma kamar wadda aka kullewa baki na kasa amayar masa da
abinda ke cikin zuciya ta. Ban jinjinawa rashin ta idon sa na sai da ya tambaye ni ina abinci, haka na wuce
na haɗa na kawo masa ya zauna ya hau ci na ringa kallon sa kawai har sai da ya gaji ya ce mun
"Babu komai" na faɗa ina cigaba da kallon sa. Ya bata rai ya cigaba da cin abincin. Wayar sa da ya ajiye
akan dining lokacin da zai shiga kitchen ta ɗauki ƙara, ban motsa na har sai da ya ce na miƙo masa ita
kafin na tashi. Na ringa kallon sunan da ke yawo akan screen ɗin 'JALILA ABJ'.
A iya sani na Bilal ba shi da wata yar uwa ta kusa ko ta nesa mai irin wannan sunan, amma ko wanda
baya son sa in har zai bayar da shaida akan sa kowa ya sani Bilal bashi da kule kulen yammata kuma
nima zan shaidi hakan domin wayar sa ko password babu akai tun ina ɗauka na masa bincike ba tare da
ya sani ba har na saki zuciya ta na yarda ni kaɗai nake da dashi dan haka ko yanzun abinda na bawa
zuciya tabbaci akai shi ne Abokiyar aikin sa ce ba wata Mace daban ba.
*(Based on true life event, some parts are fictional to spice up the story)*
*Wattpad @MaryamahMrsAm*
*Kuɗin karatu yana wakiltar mutum ɗaya ne, kiji tsoron Allah karki ɗauki hakkina ta hanyar fitar mun da
littafi*
*KURA A RUMBU littafin kuɗi ne, a biya naira 800, biya a asusun*
*1840175439*
*Access bank*
*PAGE 29*
Kafin na kai masa wayar ta yanke dan haka da na bashi ajiye ta ya yi ya cigaba da cin abincin ba tare da
ya duba wanene ya kira ba. Duk yanda na so na mayar da hankali na kan Al'amin dake ƙananun rigima
sai na kasa ƙarshe kawai na goya shi na yi tsaye ina kallon Bilal da ke cin abinci wayar sa na ƙara alamar
shigowar wani kiran amma be amsa ba. Kamar me tsoron magana na ce masa
"Ana kiran ka a waya fa" ya ɗago ya kalle ni kafin ya ɗaga wayar ya karata a kunnen sa lokaci ɗaya yana
miƙewa tsaye.
"Ranki ya daɗe Hajjaju na" ya furta kalmar da naji ta dirar mun a ƙwaƙwalwa tamkar saukar aradu, ya
gota ni ya shige kitchen yana murmushi ko na ce dariya ƙasa ƙasa. Ina nan tsaye kamar mutum mutumi
ya fito fuskar nan kamar an masa bushara ya sake wuce ni ya koma kan kujera ua zauna ya cigaba da
amsa wayar sa.
Gashi dai ina gurin kuma kallon sa nake yi amma ba zan iya cewa ga abinda yake faɗa ba dukda ba wai a
hankali yake wayar ta yanda ba zan ji me yake cewa ɗin ba, Aa, gaba ɗaya kunnuwa nane suka toshe ko
kuma ƙwaƙwalwa ta ce ta dena fassara saƙon murya oho, kiran suna na da ya yi da ƙarfi ya maido da ni
hayyaci na. Na sauke ajiyar zuciya kafin a hankali na matsa kusa da shi ganin ya miƙo mun wayar sa.
Screen ɗin na fara kallo Jalila ɗin ce dai suke magana kuma har tsayin minti goma kenan minti na goma
da yin mutuwar tsaye.
"Ina wuni Maman Al'amin" ta faɗa bayan da na yi sallama cikin muryar da banyi zaton ta ji ni ba. Na
amsa da "lafiya lau". Da "Eh, A'a " na ringa amsa mata tambayoyin da ban ma san me take cewa ba har
ta gaji ta mun sallama ta kashe wayar ba tare da na maidawa Bilal ba.
"A can head quarter ta ke tare muka yi workshop ɗin da na je da ita, ta damu kullum muka yi waya sai ta
tambaye ni ke yau dai kun gaisa na huta" ya faɗa bayan da na miƙa masa wayar.
Na sauke numfashin da ban san dalilin yin sa ba haɗi da yin gajeran murmushin da iyakacin sa baki. Fita
yayi ya barni. Ban san tsahon lokacin da na ɗauka a zaune ba ban kuma san tunanin me nake yi ba har
aka kira sallar magriba kafin na iya tashi daga gurin da nake. Me ya sa ban tambaye shi matar aure ba ce
ko budurwa ko ba komai na samu cikakkiyar nutsuwa daga tunane tunanen da zuciya ta take ta raya
mun? Haka nan na yi sallah ina jiran ya dawo na ji cikakken bayani akan wacece JALILA? Daga muryar ta
zan iya fasaltata a shekaru talatin zuwa sama daga kuma maganar ta na tabbatar yar gayu ce, har na
fasaltata a idanuwa na irin matan Abuja jiki duk madarar nan. Wannan tunanin ya saka mun ƙunci da
rashin nutsuwa a zuciya ta amma kuma duk yanda ma zaƙu ya dawo na yi masa tambayar sai na kasa
lokacin da ya dawo.
Sai da aka yi isha'i ya sake shigowa falon lokacin ina cin sauran abincin da ya rage, ya zauna a kusa da ni
fuska a sake ya ɗauki Al'amin ya fara masa wasa ni dai kallo ɗaya na masa na mayar da kai na cigaba da
cin abincin da nake yi ina kokawa da zuciya ta dake azalzalata akan na tambaye shi wacece JALILA amma
na kasa.
"Akwai sauran abincin ne?" Ya tambaye ni, ba tare da na yi magana ba na girgiza masa kai kawai, ya sake
cewa
"Iya abin da na siyo kenan na dafa" na bashi amsa ba tare da na kalle shi ba, sai na ji ya ce
"Au, dama ba Gara aka kawi miki ba?". Na yi tsam kafin na waiwaya na kalle shi dan ban fahimci in da
maganar sa ta dosa ba, wace Gara kuma yake magana akai?
"Wace irin Gara kuma?" Na tambaye shi ganin ya tsare ni da ido, ya haɗe girar sama ya ce
"Nasan dai ana Garar aure ta al'ada, idan ita kake magana kuma an yi mun" na bashi amsa ina cigaba da
cin abincin gabana. Sai ji na yi ya d
Sake cewa
"Kawai ki ce saboda mugun hali ku a gidan ku bakwa yin Garar haihuwa ko kuma kece ba za'a yi wa ba
tun da ba'a sona?"
Mamaki, takaici da haushi duk suka kamani lokaci ɗaya. Bilal dai ba zai canza hali ba, sam bakin sa ba zai
taɓa koyon tauna kalami kafin ya furta su ba. Gyara zama na yi na kalle shi da kyau na ce
"Muguntar ce ta saka aka baka aure na, duk a cikin muguntar aka cika maka gida da kayan ɗaki aka kuma
haɗo ni da kayan abincin da har yau shekara biyu auren mu babu wata uku kake ci a cikin su ba. Sharaɗin
ciyarwa akan Namiji ya ke ba Mace ba, haƙƙin ka ne da ka kawo mun abin da zan ci a cikin gidan nan ba
wai ka zauna kana jiran a kawo daga gidan mu ba, baka ga duk ƙoƙarin da aka yi maka a baya ba ashe kai
nan jira ma kake yi bayan Garar aure a sake lodo ta haihuwa a sake kawowa kenan? Sannu Bilal" Na faɗa
ina tsare shi da ido.
"Gori zaki yi mun kenan?" Ya faɗa lokaci ɗaya fuskar sa na rinewa da ɓacin rai. Na ture kwanon gaba na
na miƙe na ce
"Gaskiya ce kawai na faɗa ba gori na maka ba, na zata ai yau sabon muna da kayan abinci ya sa ka manta
ka fita ba tare da ka bar mun abinda zan ci ba ashe kai duk a tunanin za'a kawo mun Gara daga gidan
mu".
Ya mun kallon bani da lokacin ki a yanzu kafin yayi tashin Magajin Dagacin Ƙauye da Al'amin a hannun
sa, na yi ta jira ya dawo ya rufe ni da masifar da ya saba amma shiru har na gama tunane tunane na
bacci ya kwashe ni bai shigo ba balle ya dawo da Al'amin ɗin sai cikin dare na farka na ganshi a kusa da
ni.
Bayan na yi fitsari na canza masa diaper muka sake komawa bacci. Gurin ƙarfe bakwai da rabi ina tsaka
da mopping dan tun asuba da na tashi sallah shima Al'amin ya farka ya kuma ƙi komawa dan haka na
goya shi kawai na shiga aika ce aika ce na naji ana buga get, Hijab na zura na fita, jin muryar Sunusi
maigadin maƙwaftan mu ya saka na buɗe kofar.
Ya gaishe ni na amsa ina mamakin tsadadden warmer na da na gani a hannun sa, a iya tunani na ban
tuna sanda na fitar da shi ba da har zai je hannun Sunusi. Miƙo mun ya yi da baƙar leda na karɓa ina
masa kallon rashin fahimta ya ce
"Yallaɓai ne ya bani tun jiya da dare ya ce a siyo Ƙosai da Kunu".
A kan dining na ajiye kayan na buɗe Ƙosan da basu fi ƙwaya goma sha biyar ba na rufe, Kunun ma ƙulli
biyu ne tsululu da shi da gani ma na masara ne ina jin ko ɗumin kirki babu sai wani ƙullin sugar abin dai
kamar na rusa kuka saboda takaici. A gurin na barsu na cigaba da abinda nake yi ina jiyo motsin buɗe
ƙofar sa lokacin ina mopping kan barander dan tun da ya dawo daga masallaci na jiyo shi yana share
compound ɗin ya kuma wanke na ɗauka ma harda barander ya wanke sai da na fita karɓo ƙosan na ga
gurin da datti shine na sake shareta na goge.
Fuska ba yabo ba fallasa ya tsaya yana kallo na, na gaishe shi daga in da nake tsaye ina ɗauraye mopper
ya amsa kafin ya shige cikin falon. Sai da na shanya mopper na kwashe kayan wankin da na manta ban
ɗauke ba jiya kafin na shiga falon nima.
"Ina abin karyawa?" Ya faɗa dai dai ina ƙoƙarin shigewa ɗaki na, na nuna masa kan dining ba tare da na
ce komai ba na shige ɗakin, ban fito ba sai da na yi wanka na yiwa Al'amin na tarar ya bar mun Ƙosan
guda bakwai sai ƙullin Kunu ɗaya, Hijabi kawai na saka na goya Al'amin bayan na juye Ƙosan a farar leda
na fita da su na bawa wani Almajiri sannan na wuce kanti na siyo abinda nake buƙata. Sai bayan na gama
karyawa sannan na lura da dubu ɗayar dake ajiye kan dining da yar takarda a samanta na ɗauka na buɗe
"Ga kuɗin cefane nan" abinda ya rubuta a jiki kenan. Na ringa juya dubu ɗayar ina kallon ta a raina ina
lissafa me zan siya da ita?
Cefanen yaushe ma yake nufi na rana kenan ko kuwa har da dare? Da yake na siyo Indomie da rana ita
na dafa da ƙwai na ci duk da ba wani ji na yi na ƙoshi ba ni tunda na dawo gidan ma nake ji na kamar
wacce ulcer ta kama komai na ci bana ƙoshi ga Al'amin da tsotso har na fara tunanin ko dai na haɗa
masa da madara ko zan samu sauƙi.
A hanya bayan na dawo daga cefanen girkin dare wanda sai da na yi cikon dubu uku kafin na samu siyo
abinda nake buƙata ina ƙoƙarin buɗe gida na jiyo Maman Yusuf na kiran sunana, sai da na zura ledar
hannu na ciki na janyo ƙofar kafin na juya ina murmushi a raina ina addu'ar Allah ya sa bata ga kayan
hannu na ba.
"Na aiko Khairat ta ce bakya nan sai Sunusi ya ce kin tafi cefane, maimakon ki bawa Sunusin ko kuma ki
aiko nan ko Hauwa ce na turo miki ta yo miki cefanen shine zaki ringa fita da kanki Amarya? Haka jiya ma
fa na ganki can bakin titi da tsakar rana har ina cewa mai kama da ke ce ashe dai ke ɗin ce dagaske ni na
zata ma Oga ya koma Abujan ne shiyasa kike yawon cefane da kanki ashe yana gari" ta faɗa tana kallo
na.
Na yi guntun murmushi na ce
"Aiken sauri ne kin san halin Sunusi kuma idan ka aike shi wani lokacin sai ka manta ma kafin ya dawo
Hauwa kuma ai na ji randa kika shigo kin ce ta je gida an musu rasuwa ban san ta dawo ba ai".
Na ɗauka zata wuce amma ta tsaya da alama shiga take so tayi ba'a son raina ba na buɗe ƙofar muka
shiga tare. Sai da na kai kayan kitchen kafin na dawo falo muka sake gaisawa ta ce
"Kiyi haƙuri kin sanni da shegen surutu da shiga abun da babu ruwana. Da safe Sunusi ya ce mun
maigidan nan ya aike shi siyan ƙosai da Kunu, naga an kwana da wuta Amarya ga blander ki babu abinda
bata niƙawa ɗan ƙosan da baifi kiyi na gwangwani biyu kuci har kuyi sadaka ba shine zaki bari a siyo
muku a inda baku san tsaftar sa ba? Kunun ma ai gara ki siyo geron kiyi gasara tunda yana so, In da kin
aiko ma ni ina da gasarar sai na baki ki dama".
"Ni ce nayi sha'awar kunu da ƙosan ma naga kuma kafin na yi zan ɓata lokaci" na faɗa ina murmushin
yaƙe, tayi jumm kamar dai ba iya maganar da ta kawo ta ba kenan kafin kuma ta miƙe tana cewa
"Shikenan dai bari na je dama baya zan zagaya gidan Maman Anisa kin san yaronta da ya tafi makarantar
Sojoji Aliyu shine ya faɗo daga sama suna training an dawo da shi gida jinya zan shiga duba shi".
"Ayya Allah ya bashi lafiya ya kiyaye gaba ayi masa sannu" na faɗa ina taka mata, a bakin ƙofa ta tsaya ta
ce
"Eh wlh girki zan yi da munje taren na faɗa ina kallon Bilal dake tahowa daga ɗakin sa mamakin sanda ya
dawo gidan ya kamani, ganin sa ya saka ta wuce ita ma ni kuma na koma ciki.
Tare muka shiga cikin falon ya dakatar da ni cikin ɗaga murya yace
"Daga yau na soke shigowar duk wata matar unguwar nan cikin gidan nan kema kuma na hana miki
hulɗa da su tunda a gurin su kike koyon duk wani rashin mutunchin da kikeyi".
Nayi kasaƙe ina kallon sa kawai, wai nake koyon rashin mutunchi, ya cigaba da cewa
"Ita ga munafuka ta fito kai tsaye ta ce kina fita cefane za'a ce Mijinki baya kulawa dake shine take ta
wani zagaye zagaye. Shi Mijin nasu da ya gina musu ƙaton gida ya basu motoci suke wani jin kansu waye
bai san ɗan damfara bane ba? In sake ganin ta a gidan nan wlh sai na mata rashin mutunchi aikin banza
kawai" fuuu ya fice.
"Ashe kasan mutane zasu ringa kallonka a matsayin wanda bai iya riƙe gidan nasa ba amma saboda
rashin son gaskiya zaka ɓige da faɗan rashin dalili. Da ya dawo can falon sa ya ce na kai masa abinci na
haɗa komai na kai masa bayan ya gama ya kira ni a waya ya ce na zo na kwashe kwanukan bayan na
kwashe ya ce idan na kai su kitchen na je yana son magana da ni.
Kayan abinci ya nuna mun da ban san sanda ya shigo da su gidan ba, ya ce
"Gashi nan na siyo kafin ki cigaba da yi mun Gorin tunda na aureki abincin da kika zo da shi daga gidan
ku kike ci". Ni dai na yi murmushi kawai yace na je na shirya na dawo yana jira na, na san me yake nufi.
Washe gari da safe sauran abincin dare na ɗumama muka karya da shi, mun tashi da walwala ba laifi
saboda yanda daren jiyan ya kasance mana. Har ya gama shirin fita banga ya fito da kayan abincin ya kai
su store ba dan haka na tuna masa, ina tsaye ya shiga kitchen ya fito da kwanuka na ringa kallon sa ina
mamakin mai zaiyi ya wuce ya koma can ɗakin ba daɗewa ya ƙwala mun kira na je, ya nuna mun
shinkafar daya auna cikin roba da ba zata wuce gwangwani uku ba sai mai da maggi, ya zaro ɗari biyar
daga aljihun sa ya miƙa mun. Na ringa kallon kayan da kuɗin gaba ɗaya na rasa kalmar da zan yi amfani
da ita gurin magana, shi kam ko a jikin sa ya ce
"Ki ɗauka zan rufe ƙofa sauri nake yi kada na makara". Haka na fito da kwanon shinkafa da mai da Maggi
na guda biyar akai kamar wacce ta je roƙo maƙwafta. Na daɗe a zaune baƙin ƙofar falo na mamakin abun
bai sake ni ba. Kenan awo Bilal zai ringa mun ko me? Ni bani da yancin da zan ɗibi abinci na dafa a cikin
gida na sai iya abinda yaga dama ya ɗebo ya bani shi zanyi amfani da shi kenan?
Mai yake damun Bilal? Wai dama haka yake ko kuwa dai wani abun ne ya canza shi da ban sani ba?
Yini guda na kasa kataɓus duk in na kalli shinkafar sai na ji duniyar ta mun duhu wani abu ya tsaya mun a
ƙahon zuci na ma kasa dafata balle na ci. Gashi na rasa wanda zan kira na samu sauƙin abinda nake ji a
raina, wai wa zan ma zan iya gayawa wannan abun takaicin? Haka nan daga ƙarshe na ganin la'asar ta
kawo kai na dafa masa da sauran cefanen da nake da shi amma ban iya ci ba cikin provision ɗin da na
ɗan yi nayi ta dama Golden morn da cornflakes yini guda ina sha. Da yamma daya dawo ya taho da
nama, kifi harda kayan miya. Haka ya zauna ya raba su ya ƙulla a ledoji ya zuba a frizeer tare da gaya
mun tsahon lokacin da yake da yaƙinin zasu kai kafin su ƙare.
Tun daga sannan muka ɗoru akan sabon tsari, yawanci da safe zai siyo Lipton da sugar da buredi, wata
rana in ya ga dama ya siyo madara da Milo ko ya siyo ƙwai. Su dankali, doya duk zai siyo ya ajiye sai dai
irin ikon da yake gwadamun akan abinci ya saka lokuta da yawa nake haƙura da ko menene ya kawo sai
dai na bar masa kayan sa ya ci.
Da rana kuma shi zai ɗiba mun iya abunda zan dafa cikina da nashi. Sau ɗaya na masa magana akan idan
kuma muka yi baƙi fa? Yaya zanyi tunda kulle ɗakin yake yi? Bai bani amsa ba nima kuma ban sake tayar
da zancen ba, sauƙin ta ban fiya yin baƙi daga ɓangare na ba, shima yan uwansan da suke zuwa a da
yanzu duk sun ɗauke ƙafa Abubakar ne kaɗai zan ce har yanzu alaƙar mu take nan bai canza layi ba sai
kuma Anty Amina ita kuma tsakanin mu gaisuwa a waya ne ko kuma idan mun haɗu a gidan Hajja.
A haka rayuwa ta buɗe sabon shafi, na yaye Al'amin na ɗauki cikin Sharifa. Tun ina ganin bazan iya
jurewa ba har na haƙura na saba abin ma ya dena damuna musamman da hakan ya kasance silar
dawowar nutsuwa da kuma walwala cikin zamantakewa ta da Bilal. Mun dena faɗa, soyayya da tattalin
da nake kwaɗayin ina samun su da na zauna nayi tunani sai naga dama ita rayuwa bata taɓa zamowa
mutum ɗari bisa ɗari yanda yake burin ta kasance masa.
Wasu matan sukan samu biyan buƙata na ababen more rayuwa amma kuma su rasa kula da farin ciki a
gurin mazajen su. Wasu kuma su rasa wadata amma su samu farin cikin. Ni da na faɗa a tsaka tsaki
domin dai ko da bana samun abinda na saba da shi ko nake so bai bar ni da yunwa ba. Sannan ina samun
soyayya da tattalin da na tabbatar ba kowacce mace ke samun irin haka a gidan auren ta ba, amma duk
da haka na sani Son da nake masa ne ya lulluɓe komai a ido na. Allah ya sani ina son Bilal son da ban san
iyakar sa ba ba kuma na fatan ruyuwa babu shi dan nasan bazan iya ba.
Cikin kuɗin da nake dasu a hannu na da na account nake cira nayi duk abinda nake da buƙata wanda bai
bani ba. Sau tari zuciya ta takan raya mun na siya abinda nake so na dafa na ci ni kaɗai idan baya nan
amma sam na kasa yarda da hakan, ko gida na je na samo abu bazan iya ɓoye masa ba. Tunda kuma ya
fahimci akwai kuɗi a hannu na ɗari biyar ɗin da ya fara bani a matsayin kuɗin cefane ma ya daina kwata
kwata. A cewar sa babu abinda baya siyowa bai kuma taɓa tunanin abinda yake siyowar ko yake ɗibar
mun baya isa ba. Zan dafa abinci da naman kaza ya ci har ya fini iko akai ba tare da ya tambaye ni a ina
na samu kuɗin da na siyi kazar ba.
Bai taɓa gani na da wata sutura ko abin kwalliya wanda ba shi ya siya mun ba kuma ya tambaye ni a ina
na samu, idan akwai abinda nake jin damuwa akai har ya jefa ni a tunani bai wuci yanda bai damu da
komai ba har idan ba hurumin sa na shiga ba. Amma kuma daga ranar da ya faɗa mun wata magana,
daga lokacin na fahimci kuskuren da mutane suke ta faɗin na yi akan auren Bilal, a ranar kuma na fara
shakkun sahihancin ƙaunar da nake tunanin yana yi mun ya saka mun kokwanto akan aihinin manufar sa
akan aure na.
Kuyi haƙuri, In sha Allahu daga yau har Friday zanyi post. Daga nan zamu tafi hutun azumi idan Allah ya
saka mun kasance cikin waɗanda zasu gani.
*(Based on true life event, some parts are fictional to spice up the story)*
*Wattpad @MaryamahMrsAm*
*Ban yarda wani ko wata ya juya mun labari ta kowacce siga ba tare da izini na ba*
*Kuɗin karatu yana wakiltar mutum ɗaya ne, kiji tsoron Allah karki ɗauki hakkina ta hanyar fitar mun da
littafi*
*KURA A RUMBU littafin kuɗi ne, a biya naira 800, biya a asusun*
*1840175439*
*Access bank*
Watan Al'amin goma sha takwas na yaye shi a kuma watan na samu wani cikin wanda ko kusa Bilal bai yi
maraba da samuwar sa ba.
"Wai dama bakiyi komai na tsarin Iyali ba? Ni na zata hankalin ki zai baki da kiyi ba sai an tuna miki ba,
kina kallon yanda abubuwa duke tafiya kuma kawai zaki kama ki wani sake yin ciki. To ni dai gaskiya ban
so haka ba" Abun da ya faɗa kenan lokacin da na shaida masa ina da cikin.
Gaba ɗaya sai na rasa yanda zan fassara maganganun sa. Fassara ta kai tsaye dai na san yana nufin baya
son cikin kenan sai dai nayi ƙoƙarin kyautata masa zato da bashi damar gyara maganar sa ta hanyar cewa
"Duk yanda kika ɗauka haka nake nufi ni dai na faɗa miki ban so kika sake samun wani ciki yanzu ba. Kina
sane tun ba yanzu ba na gaya miki a tsari na gaba ɗaya bana so yayana su haura guda uku, yanzu ƙasa da
shekara huɗu kina shirin yin yaya biyu" ya yi tsaki haɗi da tashi ya bar mun ɗakin.
Ko a mafarki ban taɓa zaton Bilal zai ƙyamaci abinda ya fito daga guri na ba. Na jinjinawa ƙarfin halin sa
da har ya iya runtse ido ya ke faɗar abinda ni da shi mun san ƙarya ne Bilal da yake cewa idan munyi
aure duk shekara zan ringa haihu muyi dariya na ce Akuya yake so na zama kenan amma wai yau shine
zai dubi tsabar ido na ya ce mun baya son cikin da yake jiki na.
A haka na rainin cikin Sharifa cikin ƙunci da baƙin ciki domin kwata kwata Bilal canzamun yayi. Sai mu
yini mu kwana bai ce mun komai. Da farko ya sakko lokacin da Mama ta ɗauki Al'amin ganin ina shan
wahalar laulayi, watan sa biyu a can gidan kafin aka dawo da shi. Dawowar ta sa ma da farko farko bai
wani nuna ɓacin rai ba sai bayan da siyayyar kayan ciye ciyen da aka haɗo shi da su ta ƙare ranar da na
fara masa magana zai fita nace ya taho masa da ƙwai da Ceralac dan har sannan ita kaɗai yake yiwa shan
ƙoshi sai kuma ƙwai haka ya rufe ido ya ringa zazzagamun masifa har yana faɗin idan da an san ba za'a
iya riƙe yaron ba akan me za'a ɗauke shi aje a lalata shi da ciye ciyen banza?
Ba zai siyo ba, ai dama tun farko ni na koya masa shan cereal ɗin har kunu Hajja ta haɗo ta kawo amma
naƙi bashi dan haka sai na cigaba shi baze iya ba. Ranar sai da na ji kamar na haɗa kaya na na bar masa
gidan amma bazan iya ba. Ina son sa ina kuma son zama da shi. Nayi uzurin cewa cikin da na samu ba
tare da shawarar sa bane ya ɓata masa rai na kuma ɗauki alƙawarin da zarar na haihu bazan fito daga
labor room ba sai na yi family planning har idan hakan zai faranta masa rai.
A haka na haihu, na samu ya mace wadda ya bani zaɓin akan duk sunan da nake so in saka mata na
kuma zaɓa mata SHARIFA. Sai ana gobe suna kafin ya bani dubu saba'in wai ko akwai abinda zan buƙata.
Nayi murmushi kawai na karɓa. Ba abinda nake nema wanda bani da shi. A lokacin na godewa gatan da
Anty Labiba ta mun na kwashe duk wani abu da muke da shi double lokacin haihuwar Al'amin ta ɓoye
mun. Riguna kawai na kwalliyar mata na siya dan duk wani unisex muna da su. Ban yi taro ba, duk da yan
uwan sa sun zo amma da suka ga babu kowa a gidan basu zauna ba suka tafi.
Haka na shiga rainon yara biyu sai kuma a lokacin kuma na fuskanci zaton da nake yi na zan iya ɗaukar
nauyin kaina da abinda zan haifa ba tareda na damu da abinda Bilal zai yi mun ba ba mai yuwuwa bane.
Abban da yake bani kuɗin tun da na haifi Sharifa ya janye mun tallafi. Sai na yi zuwa biyar gida ba tare da
ya bani ko sisi ba. Idan ma zai banin ya dena bani da yawa kamar da ƙarƙarin kyautar bata haura dubu
goma ko ashirin saɓanin da da duk watan duniya sai ya tura mun dubu hamsin wanda ko Mama bata san
da hakan ba kuma shi ya hana na faɗa mata. Sannan duk sanda naje gidan idan zan tafi zai bani na mota.
A sannu na fara gane ainihin abinda ake kira da yau da gobe bata bar komai ba, ga hidimar yara, ga
damuwar Bilal da gaba ɗaya zaman mu ya canza salo. Duk ta inda nake zaton matsala nayi ƙoƙarin
gyarawa amma tamkar ina sake rura wutar ne. Idan nayi abinci haka zai balbaleni da masifa ya ce na koyi
mugunta wai yanzu sai na ringa abinci kamar wanda za'a bawa bayi ba taste babu komai. Akwai ranar da
nayi tuwo da miyar kuka kamar yanda ya faɗa mun na yi kafin ya fita da ya dawo na kawo masa haka ya
saka ƙafa ya ture kwanon miyar ya ringa sababi har da yi mun Allah ya isa akan ɓarnar abincin da nake
masa kamar yanda ya ce. Abincin da ni da yaran sa muke ci amma shi ya ce ba daɗi baze iya ci ba, na
rasa gane kan Bilal na kasa fahimtar inda ya saka gaba.
Duk yanda nake tunanin na samo bakin zaren shirin baya wuce na kwana biyu zuwa uku zai sake
birkicewa. A sannu na fahimci hanya ɗaya ce take samar mun farin ciki tattare da Bilal shine samuwar
kuɗi a hannu na. Idan ina da kuɗin da zan girka masa abinci mai daɗi a ci zamu ɗauki tsayin lokaci ba tare
da kowa ya ji kanmu ba, daga sanda cefane ya canza na fara girka zallar abinda ya ajiye mana sai tashin
hankali ya ce ina lalata masa abinci. Ma fahimci abinda yake so, ko da ba zan ɗauki kuɗi na bashi ba yana
so na wahalata masa shine farashin soyayya ta a gare shi.
**********************
Daƙyar na iya buɗe ido na da suka mun nauyi dalilin kukan Al'amin da na jiyo. Na yunƙura daƙyar na
tashi ina dafe kaina da yake mun ciwo matuƙa. Waya ta na janyo na duba, biyu saura kwata lallai na
daɗe a kwance ashe. So nake na fita na ji dalilin kukan nasa tun kafin ya tashi Sharifah wadda a garin
lallaɓa ta ne bacci ya kwashe ni nima. Ajiyar zuciya na sauke saboda jiyo muryar Bilal a falon yana
tambayar me akayi masa, dukda cikin faɗa da hargagi yake maganar amma shirun da Al'amin ɗin ya yi ya
saka na samu nutsuwa har na miƙe daƙyar na shiga banɗaki.
Ina fitowa ya shigo ɗakin yana jan rai kamar numfashin sa zai ɗauke. Na janyo shi jiki na a hankali na ce
"Kasan idan ka bari kukan nan ya fita Dady ya ji muryarka zai dake ka ko? Wai me ma aka yi maka? Wa ya
ɗakko ka daga makaranta?" Bai bani amsa ba sai rungumeni da yayi, na ringa shafa bayan sa har saida ya
daina ajiyar numfashin bacci ya ɗauke shi daga tsayen da yake kafin na kwantar da shi na zare masa
takalman ƙafar sa sannan na miƙe daƙyar ina dafe kaina na fita falo.
Bilal na zaune kan 2 sitter kunnuwan sa saƙale da air pods yana danna wayar dake hannun sa fuskar sa
ɗauke da murmushi, lunch box da school bag ɗin Al'amin dake ajiye a ƙasa na ɗauke, motsi na ya saka ya
ɗago ido ya kalle ni nayi kamar ban ganshi ba na yi wucewa ta kitchen. Ina jin motsin alamar ya biyo ni
nayi maza na kullo kofar kitchen ɗin. Ina jin sa ya zabga tsaki ya ce
"Halima so kike ki ƙure haƙuri na ko? Tun jiya nake binki akan ki zauna muyi magana amma kinƙi wai me
yasa kike haka?"
Kwanukan da ban samu na wanke ba na shiga wankewa ba tare da na bi ta kansa ba. Jin har na gama bai
fita daga falon yasa na nemi kujera na zauna haɗi da jingina da cabinet dan gaba ɗaya bana jin daɗin jiki
na.
Sai da na jiyo kukan Sharifa kafin na fito daga kitchen ɗin na tarar da ita a hannun Bilal yana gani na ya
nufo ni yana cewa
"Jikin ta ya yi zafi sosai, kuma kiji numfashinta yanda yake yi". Karɓar ta nayi ta wuce ɗaki ba tare da na
amsa shi ba, na sake fitowa na wuce kitchen na ɗakko sauran kunun dana dama mata. Sauran madarar
da na ajiye akan dining na nema ban ganta, na ɗaga kai na kalli Bilal dake tsaye shima yana kallo na ya ce
"Am, bari na karɓo a shago nayi amfani da ita". Banza na masa na shiga shayar da ita shi kuma ya fita.
Daƙyar take shan nonon saboda hancinta da yake a toshe ta baki take numfashin.
Wata irin mura take yi me zafin gaske. Tunda ya kwashe su ya kai su gidan Hajja ranar Juma'a ko
cikakkiyar awa biyu basu yi da tafiya ba sai ganin su na yi jage jage cikin ruwan sama Salima yar Anty
Amina ta kawo su wai kuka take tayi shine Hajja ta ce a maido da ita. Tun ranar ta fara mura duk da na
basu loratidine da paracetamol, ta Al'amin kwana biyu ta warke ita kuwa kamar ana ƙara murar ga tari
da amai dukda na sake kai ta chemist an bata wani maganin amma a banza ganin abun na nema ya wuce
hankali ya saka dole na tattara kuɗin dake hannu na na kaita asibiti bayan an yi mata test suka tabbatar
mun infection ne, magungunan da aka rubuta mata antibiotics a pharmacy dubu ashirin da huɗu.
Bani da su ba kuma ni da ƙarfin halin da zan kira wani cikin yan uwana na roƙe shi kuɗi a yanzu.
Haka na koma gida na bashi takardar kai tsaye kuma ya ce mun bashi da kuɗi.
"Kina sane kika kaita wannan asibitin ai bayan kin san shegiyar tsada ce da su. Ni bani da wasu kuɗi da
zan baki ki siya mata magani yanzu sai dai ki jira zuwa jibi mu gani akwai abinda nake saka rai idan na
samu sai a siyo. Banda ma jaye jayen abu normal mura ce fa kin sani amma kinje sai an jawowa yarinya
wani ciwon daban" ya faɗa yana danna wayar sa da ta zama abokiyar hirar sa a yanzu ko da yaushe tana
hannun sa yana kallo yana murmushi.
Tunda ni na damu da lafiyar ta haka na siyar da zobe na guda ɗaya na siya mata magungunan da abincin
ta na yiwa Al'amin shopping ɗin abin tafiya makaranta dan cewa ya yi na ringa zuba masa duk abinda
muka karya dashi shi ba ze ɗaukar wa kansa ƙaryar da bazai iya ba.
Dama akan saka shi a makaranta ma sai da raina ya ɓaci cewa ya yi bashi da kuɗi yanzu sai dai a jira
zuwa second term.
"Kawai tsurfa ce irin taki, shekara uku ne zaki wani damu a saka shi a makaranta ni banyi lissafi da kuɗin
makaranta ba gaskiya a watannan watan da na gaba, sai dai ki jira second term se a kaishi idan kuma na
zaki iya jira ba ki saka shi tunda ke kike so" amsar da ya bani a lokacin har kuma aka cinye first term aka
shiga hutu bai tayar da maganar ba ƙarshe ni ɗin da na damu ni na nemi kuɗi na kaishi makaranta kuma
ya dawo zai yi mun haukan ƙarya akan me zan kaishi ko ce mun ya yi ba zai saka shi? Kuma shi ba wacce
na kai shi ya yi niyya ba sai a cire shi a mayar da shi wacce yake so.
Peak ya siyo leda biyu, na haɗa kunun na bata tana gama sha kuma ta koma bacci bayan na bata
magungunan ta na zuƙe mata majinar da hanata sukuni lokacin Al'amin ya tashi na masa wanka sannan
na zuba masa abinci. Ina zaune ina kallon sa yana cin abincin, a zahiri kallon sa nake yi amma a baɗini
nayi nisa cikin tunanin neman hanyar da zan ringa samun kuɗi tunda sune tikitin farin ciki na a cikin
gidan. Na sauke ajiyar zuciya jin Al'amin yana girgiza ni, ya gama cin abincin muka tafi kitchen na wanke
masa hannu sannan na bashi ruwa ya sha muna fitowa Ummi yarinyar Maman Yusuf da suke tafiya
Islamiyya tare ta shigo da suka fita.
Sai lokacin nima na ɗebi abinci kaɗan na ci. A mudubin banɗaki da na shiga alwala na tsaya na ƙarewa
kaina kallo, ni dama jiki ba auki ba damuwa duk ta sake tsotseni nayi baƙi kamar mara lafiya. Na ɗauro
alwala ina fitowa na ji Bilal yana kirana. Hijab na saka na fita ina ɓata rai ganin Abubakar da wani da ban
sani ba ya saka na ɗan saki fuska na zauna kan hannun kujera muka gaisa a gurguje suka tafi.
Tsareni yayi da ido shima yana wani murmushi dana tabbatar akwai wata manufa a ƙasan zuciyar sa, na
ɗauke kaina gefe saboda bana fatan nan kusa ya ci galaba akaina na sakko, ina fatan ya fahimci fushi na
kuma canza zuwa yanda nake fatan ya kasance.
"Na samu na siyo toh. Kina ta fushi wai kina zaton da gangan zan ƙi siya mata magani ne ahalin ina da
kuɗin siyan?" Ya faɗa yana wani karya harshe. Tsakin da ban zata ba ya ƙwace mun na miƙe tsaye ina
cewa
"Na tabbata ko maganin dubu ɗari ne Nasir ba zai ƙi yi maka lamuni ba, amma saboda baka damu da ta
rayu ko ta mutu ba faɗa kayi akan me zan kaita asibitin kuɗi a rubuta mata magani mai tsada. Ni da na
haifeta ina son abata kuma na nemi kuɗi tuntuni na siya mata magani dan haka ka mayar ka karɓo kuɗin
ka mungode" na wuce ɗaki saboda kukan da ya taho mun. Ina shiga na mayar da ƙofa na rufe na jingina
a jiki na fashe da kuka.
Bayan na idar da sallar la'asar ina lazumi na tuna da Oil ɗin da nake mata sirace da shi ya ƙare, goyata na
yi na ɗakko jakar da na zuba sauran kuɗin suka ce na ɗauke su in da na ajiye. Sai da na duba duk
jakunkunana da inda nake ajiyar kuɗi amma ban gansu ba, na koma na zauna gefen gado na zabga
tagumi hawaye suka fara tarar mun a kwarmin ido na. Waye ze ɗauka kuɗin gida daga ni sai yara.
Zuciya ta ta ringa raya mun Bilal ne kawai zai ɗauki kuɗin amma da wacce shaida zan kama shi? Tunda
muke bai taɓa ɗaukar mun kuɗi ba ba tare da sanina ba sai dai na ɗauka da hannu na na bashi amma
kuma idan ba shi ba waye ya ɗauki kuɗin??
Kuka na zauna na sha na godewa Allah. Yanzu idan na masa magana ko da ace shi ya ɗauka na san tashin
hankali zan janyowa kaina da sai na gwammace ban yi maganar ba idan kuma nayi shiru zan cutu dan su
kaɗai ne kuɗin da suka rage mun su nake so na lallaɓa a hannu na zuwa wani lokacin.
Kwanciya nayi na cigaba da saƙa da warwarar yanda zan ɓullowa al'amari na, Abban dai bani da kamar
sa shi kaɗai ya fahimce ni shi ne kuma ba zai gajiya da ni ba. Tashi nayi na ciro wayata daga caji, sau uku
ina danna layin Abba sai na katse dan ban san me zance masa ba.
A tsakanin shekara ɗaya sau biyu ya bani jari wanda da ace da gaske kasuwancin na yi da yanzu sun
haɓaka amma muka taru da ni da Bilal muka cinye su. Miliyan ɗaya ya bani da farko akan na je na kama
wani abun idan ya ga kamun ludayin sana'ar sai ya ƙara mun wani abu. A raina a lokacin Anty Labiba nayi
niyyar bawa kuɗin, tana siyar da kayan kitchen da kayan irin PAT PAT ɗin nan, na san ko a cikin unguwar
da nake zanyi cinikin su tunda kusan kowanne gida akwai yara ƙanana tsautsayi farin ciki ya saka na
bawa Bilal labari shi kuma ya kawo mun shawarar gwada Exportation.
Kamar yanda ya ce shima yanzu abinda yake so yayi kenan wani abokin sa yana harkar fitar da riɗi da
citta. Lissafin da ya mun dukda kuɗin basu da yawa acewar sa a zuwa ɗaya za'a iya samun ribar dubu ɗari
biyu zuwa sama kuma a ƙalla duk wata suna tura kaya sau biyu dan haka na bayar da kuɗin ya haɗa da
nasa sai mu ringa raba ribar haka na bashi ba tareda nayi shawara da kowa ba har yau kuma babu kuɗin
babu riba, da na masa magana bayan an shafe wata biyu bai ce mun komai ba sai cewa yayi wai motar
da ta ɗakko kayan daga ƙauyen da aka siyo su yan kidnapping sun ƙwace ta shikenan maganar ta wuce.
Haka na sake komawa a karo na biyu akan a ƙara mun jarin sai Abba ya bani zaɓi saboda ya ce kuɗin da
ya ware a lokacin wanda zai biya mun aikin Hajji ne. Idan na yarda ya bani rance a ciki tunda akwai
sauran lokaci da Sharaɗin zan maido da su kuma na karɓa tunda na san zance ne kawai yake yi in dai
Allah ya nufa tunda yayi niyya zai biya mun na je na san kuma ko da na mayar da kuɗin ba zai karɓa ba.
Wannan karon Anty Labiban na bawa aka kawo mun kayan yaran kuma Allah ya buɗa mun kasuwar kafin
kace me suka ƙare sai dai kafin na haɗa kuɗin na sake bata a kawo wasu na cinye rabi, da aka sake
kawowa dab da sallah ƙarshe ya saka na bawa yaran yayyen sa akan zai siya har yau kuma bai bani kuɗin
ba shikenan jarin ya karye ido da kunya kuma na sake komawa.
Sai da Abba ya kira sau biyu kafin nayi ƙarfin halin ɗagawa. Muak gaisa kafin ya ce
"Ina kan hanya ne sai da ma sauka yanzu naga kiran ki, kuma ɗazu na shigo unguwar taku wata gaisuwa
kamar na leƙo naga wannan maƙuyaciyar matar tawa da ake mun rowar ta sai kuma na wuce"
"Lah Abba da ka zo ai bata da lafiya ma shiyasa kwana biyu kuka ji mu shiru" na faɗa. Ya tambaye ni mai
ya sameta na gaya masa harda sunan magungunan da aka rubuta mata kafin ya mata addu'ar samun
sauƙi. Jin yana ƙoƙarin kashe wayar ya saka na ce
"Dama Abba likitan ya rubuta mana wani test ne yace idan ta sha maganin na kwana uku bata samu
sauƙi ba muyi kuma yau kwana ukun da sauƙi jikin amma ba yanda na zata ba shine nake tunanin ko zan
mayar da ita ayi"
"Ya kamata dai ayi test ɗin na ɗauka ma ai sai da sukayi kafin aka bata maganin, amma dai ba Dr Bashir
kuka gani ba dan na san shi baya rubuta magani kai tsaye in dai symptoms yana buƙatar ayi test sai ya
tabbatar da abunda yake damun mutum kafin nan" cewar Abba. Shiru nayi ya sake cewa
"Ki tabbata gobe kun koma anyi test ɗin Allah ya sa ba Pneumonia ba ce ba"
"Ai kuɗi ne bani da shi ma shiyasa da yau ɗin zan mayar da ita" nayi ƙarfin halin faɗa. Ya ɗan yi shiru
kafin ya ce
"Aa yana nan Abba, cewa yayi na bari cikin wanin satin ayi salary tukunna"
"Wace irin magana ce ita rashin lafiyar yarinyar za'a ce a jira har wani lokaci? Zan tura miki kuɗi yanzu ki
kama hanya ki mayar da ita Asibiti duk kuma yanda akayi ki sanar da ni" Abban ya faɗa kamar cikin fushi
dai dai lokacin Bilal ya shigo ɗakin nayi masa kallo ɗaya na cigaba da yiwa Abba godiya.
"Ya kamata kiyi ƙoƙari ki samu certificate ɗin NYSC a nema miki aiki idan ya so ki haɗa da business ɗin
gaba daya zai fi, duk da dai na ce ba zan sake magana akan hakan ba amma hakan ya kamata ayi".
"Shikenan Abba zan masa magana duk shawarar da ya yanke sai na faɗa maka" na faɗa murya ta na
karyewa, ya ce
"Ba zancen shawara bane Halima umarni nake baki, ya isa haka ya kamata ki san in da kika dosa a
rayuwa zuwa yanzu". Haka nan naji zuciya ta ta karye kuka ya taho mun amma na daure na ce
"Ko akwai wata matsala ne Halima?" Na toshe baki na da hannu dan kar sautin kukan da ya taho mun
lokaci ɗaya ya isa kunnuwan sa daƙyar na iya saita kaina na ce
"Babu komai Abba, nima dama zama hakan ya isheni dama ina so na fara aikin na haɗa da business ɗin
duka"
"Ya dai fi kam, Allah yayi miki albarka ki gaida maigidan naki" ya sake faɗa na amsa da " Amin" kafin na
kashe wayar na kife kaina akan pillow na fashe da kukan tausayin kaina.
*KURA A RUMBU*
*(Based on true life event, some parts are fictional to spice up the story)*
*Wattpad @MaryamahMrsAm*
*Ban yarda wani ko wata ya juya mun labari ta kowacce siga ba tare da izini na ba*
*Kuɗin karatu yana wakiltar mutum ɗaya ne, kiji tsoron Allah karki ɗauki hakkina ta hanyar fitar mun da
littafi*
*KURA A RUMBU littafin kuɗi ne, a biya naira 800, biya a asusun*
*1840175439*
*Access bank*
*PAGE 31*
Nayi mamakin yanda Bilal bai musa ba lokacin da nayi masa maganar service. Nayi sa'a a lokacin ana dab
da fara registration dama, ranar da aka buɗe kuwa banyi wasa ba na je na yi a matsayin mara aure
saboda ko da na gaya masan ya ce toh nayi zaton zai je ya fitar da certificate of marriage da domicile
letter waɗanda zan buƙata amma har ranar ta zo bai ce mun komai ba nima kuma banyi masa magana
ba dan ina gudun kada ya canza ra'ayi.
Posting ya fito aka kaini, ban wani damu ba tunda ba nesa bane nasan zan iya zuwa nayi registration a
ranar na dawo ba daga nan na nemi relocation dan ba zai yuwu nayi service ɗin a can ba. Sai ana gobe
shiga camp ɗin sannan na faɗa masa Jigawa fa aka turani kuma gobe zan je.
"To me kike so na ce yanzu? Ai ba yau kika san Jigawa aka kaiki ba ko da yake yanzu sai kin gama yanke
shawarar ki kike gaya mun kinga wata magana tawa bata da amfani sai ki je ai" amsar da ya bani kenan.
Washe gari kuwa na kama hanyar Jigawa da sassafe, saboda ban san sanda zan dawo ba Al'amin bai je
makaranta ba na kaishi gidan Mama. Cikin sa'a dake ranar farko ce kuwa kafin ƙarfe uku na gama komai
na karɓi exit, a Kano shida ta mun dan ma mota ta ɗan tsaya mana a hanya na wuce gida kawai ba tare
da na ɗakko Al'amin ba dan na gaji kuma goben Juma'a ce ya ƙara hutawa Monday sai ya koma
makarantar.
Ina tayar da sallar magriba wayata ta fara ƙara, yanda kira ya ringa shigowa daga wani ya katse ya ɗaga
mun hankali, daƙyar na kammala ina yin sallama na ɗauki wayar gaba na ya yanke ya faɗi ganin Bilal ne.
Ina shirin bin bayan kiran wani ya sake shigowa na ɗaga, cikin muryar dake nuna yana cikin tashin
hankali ya ce
"Hajja ce sukayi accident gamu nan a Emergency na Aminu Kano" ya faɗa lokaci ɗaya kuma ya kashe
wayar.
A fili na shiga nanata Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un, Hajja kuma Accident? A garin yaya? Ina suka je?
Bani da mai bani wannan amsar sai kawai na saka wayar a ajihun rigar dake jiki na na ɗauki Sharifa
muka fita. Sai da na je get na tuna ban ɗauki kuɗin da zan hau mota ba na sake komawa na ɗauka.
Daƙyar na samu abun hawa duk wanda na tare sai ya ce ba can ya yi ba, a hanya nayi ta sake gwada
kiran Bilal amma wayar taƙi shiga. Yanda na ji muryar sa na san da alama yanayin babu daɗi a raina na
ringa addu'ar koma menene Allah ya taƙaita wahala.
Hanani shiga securities sukayi duk yanda na roƙe su daga ƙarshe na koma gefe na cigaba da kiran Bilal
har sannan kuma wayar taƙi shiga. Ga gajiya ga yunwa dake damuna ga sauron bala'i a gurin haka nan na
tsaya a bakin ƙofa ina addu'ar Allah ya fito da shi ko wani da na sani ko zan samu su bar ni na shiga. Har
ƙarfe tara muna tsaye kafin mai gadin yaga dama ya bari muka shiga. Ido na shiga warewa ina laluben ta
inda zan hango su Hajjan amma ban dace ba. Wata Nurse na tambaya tace bata gane wa nake nufi ba,
haka na ringa bi gado gado a can ciki na same su.
Hajja na kwace kanta da hannunta ɗaya naɗe da bandeji sai ledar jini da aka saka mata amma idon ta
biyu. Ajiyar zuciya na sauke dan har ga Allah ban zaci haka zan ganta ba, irin yanda na ji muryar Bilal na
ɗauka zanzo na tarar da ita a halin rai da mutuwa ne. Muna haɗa ido ta ɗauke kai gefe, na kalli sauran
Anty Amina, Yaya Saude sai Fadila da Hadiza yar ƙanwar Hajja. Anty Amina ce kaɗai ta amsa sallamar da
na yi musu, na jingina da gadon dan har jiri nake ji saboda yunwa da gajiya kafin na shiga gaishe su da
tambayar mai jiki.
"Tun bayan magriba nake a waje maigadin ya hanamu shigowa ina ta kiran wayar sa kuma tun ina hanya
bata shiga" na faɗa. Ina rufe baki Fadila tayi tsaki ta ce
"Ƙaryar banza"
"Ke Fadila meye haka?" Anty Aminan ta tsawatar mata. Murmushi kawai na yi kaina a ƙasa, kusan minti
biyar duk munyi shiru sai ga Bilal da Hafiz sun ƙaraso gurin. A mutunce muka gaisa Bilal kuwa muna haɗa
ido ya mun kallon da na fassara da harara. Hafiz ya karɓi Sharifa dake bacci a hannu na yana tambayar
ina Dady na ce masa yana can gidan mu.
"Toh Allah ya ƙara kiyaye gaba Allah kuma ya sa ya zame mata kaffara" cewar Hafiz gaba ɗaya muka
amsa da "Amin".
Fita suka sakeyi da Bilal, na gyara tsayuwa ta dan ƙiris ya rage na faɗi babu kuma wanda ya mun tayin
gurin zama a cikin su bayan wani lokaci suka sake dawowa. Sallama yayi musu bayan ya aje musu kuɗin
da ban san ko nawa bane ba. Hajja ta ringa saka masa albarka haka su Yaya Saude kamar maroƙa sai
faman zabga masa godiya suke. Ina lura da Anty Amina dake ta faman cika tana batsewa bani da
tabbacin mai aka mata da alama kuma kamar bata ji daɗin rawar jikin da suke ta yi ba.
"Ba yanzu zaku wuce gida ba? Dare fa ya fara ga gurin da sauro kada a ɗibar ma Sharifa malaria". Naji
daɗi har raina da Bilal ɗin ya ce tafiya zamuyi Fadila da Hadiza ma suka ce tafiyar zasuyi muka fita gaba
ɗaya ya rage Anty Amina da Yaya Saude wadda zata kwana da Hajjan. A hanya Hadiza ta sauka Bilal ya
tare mata Adaidaita da zau ƙarasa da ita muka wuce tare da Fadila ban so kwanan da ta ce zata yi a
gidan mu ba. Har gida ya sauke mu, a hanya ya cewa Bilal
"Ya dai kamata fa ka samu mota ko ƙarama ce saboda irin haka" shi kuma yayi dariya ya ce
"Tukunna dai ai har yanzu ban isa riƙe mota ba, yanda rayuwa ta ƙara tsada mota ai sai irin ku dai manya
mu dai barmu mu cigaba da hawa Adaidaita sahun da muka fi ganewa". Hafiz ɗin ya yi dariya ya ce
"Gara ma kace baka da ra'ayin siyan mota zan fi yarda idan kuma haka ne ai ita Madam na san ba zata ƙi
ba sai ka siya mata ko dan saboda hidimar yara ko kema kin fi ganewa hawa Adaidaita sahun?" Ya jefo
mun tambayar, murmushi kawai nayi na ce
Hawa Adaidaita ai sai dole gara dai ya taimaka ya siya mana motar mu huta"
"To ka dai ji abinda Madam ta faɗa" Cewar Hafiz ɗin. Zancen motar suka cigaba dayi har muka isa. Ua
zaro kuɗi daga aljihun sa ya sakawa Sharifa a hannu sanda zamu sauka nayi masa godiya muka wuce.
"Yanzu ko kunya bakya ji da auren ki a gaban mijin ki kike washe baki kina magana da wani namijin
daban? To tun wuri idan ma zaki shiga hankalinki ki shiga dan Yaya Hafiz da iri na ya dace" ta faɗa tana
wani watsa hannu da juya ido.
Kallonta nayi cike da mamakin kalamanta na ce
"Da alama kinyi hauka ko Fadila? Ban gane na washe baki ina masa dariya ba? kin san me kike cewa?"
"Tsaki ta yi ta shige ciki kamar gidan ta. Na bita da kallo kafin na bi bayan ta zuciya ta na tafarfasa na ce
"A zaton ki kowa shashasha ce irin? Ko zamanin yammatanci na ban banzatar da kaina nayi alaƙar banza
da maza ba balle yanzu da nake da aure kuma wai da abokin miji na. Kije ke da Allah ƙazafin da kika
mun" na nufi ɗaki dai dai lokacin Bilal ya shigo, tana ganin sa ta shiga matsar hawayen ƙarya tana cewa
"Da Allah malama dakata duk naji abinda kowaccen ku ta faɗa, ki shiga hankalin ki ba kowanne iskanci
zan ɗauka ba yanzu" ya faɗa yana nuna ta da yatsa. Murmushi na saki raina fes da yanda karo na farko
ya tsaya mun na kalleta na ce
"Ba a koda yaushe ƙarya da munafunci suke cin nasara ba nan gaba kin san me zaki faɗa" na wuce ɗaki
Bilal ya biyo baya na.
"Saboda ba mahaifiyar ki bace a Asibitin shiyasa sai da kika ga dama sannan kika je ko? Ai da kinyi
zamanki kawai ma baki je ba dan banga amfanin da zuwan naki ya yi ba" ya faɗa take murmushi kan
fuskata ya gimtse. A hankali na ce
"Wace irin magana kakeyi haka Bilal? Wlh kana kashe waya na tafi, na fi awa guda a waje kafin security
ya barni na shiga kai kuma nayi ta kiran wayarka tun ina hanya amma bata shiga ba.."
"Dalla malama rufe mun baki maƙaryaciya kawai" ya dakatar da ni cikin tsawa. Wani sanyi na ji tun daga
kaina har ƙafafu na, na bishi da ido ganin ya nufi kan gado ina da na zube kuɗin da Hafiz ya bawa Sharifa
ya kwashe su ya fita daga ɗakin. A hankali na sulale a ƙasan in da nake tsaye saboda yanda ƙafafu na
sukayi matuƙar sanyi. Har ta fara kai mu ga zagi kenan? Kullum gaba abun yake yi a maimakon ya yi
baya.
Daƙyar na ƙarfafi jiki na na canzawa Sharifa diaper na fita na dama mata abinci Fadila na kwance kan
kujera tana waya na wuce kitchen na haɗo abinci na koma ɗaki, duk yanda nake jin yunwa haka ma
kwanta wani irin abu nake ji da ban san yanda zan misalta shi ba. Da asuba ina jiyo shi yana sharar tsakar
gida, sai da gari yayi haske kafin na fito ina takawa a hankali saboda yanda yunwa ta gama rarake mun
ciki. Sai da na fara haɗa baƙin shayi na sha yan hanji na suka warware kafin na shiga fere doyar da na
gani a kitchen ɗin. Ban san ya yake so ayi da ita ba dafawa za'ayi ko soyawa ko fate?
Na gama na kwashe ɓawon kafin na fita daga kitchen ɗin da niyyar zuwa na tambaye shi yanda za'ayi da
doyar sai gashi ya shigo muka ci karo a bakin ƙofa. Matsa masa nayi ya shiga, ya aje ledar ya matsa gaban
sink in da na ajiye robar da doyar take ciki ni dai ina tsaye ina kallon sa kafin murya kamar wanda aka
cusawa tsumma a baki ya ce
"Ki rabata biyu tayi yawa idan ya so kiyi mata fate da sauran da daddare. Murmushi na yi ma ce
"Ke baki san abinda ya kamata kiyi ba?" Ya hayayyaƙo mun, sai na wuce in da ya ajiye leda ina cewa
"Har yaushe na fara yanke hukunci akan abinda ka kawo cikin gidan nan? Ai sai yanda kace ayi. Soyawa
za'ayi da ƙwai ko sauce za'ayi mata?"
"Ki soya ki dama kunun gyaɗa ga gasara nan a ciki" ya faɗa. Kamar na ce masa gyaɗar bata da yawa ta
kuma ta Al'amin ce amma dai nayi shiru kawai na ɗauki tukunya na rage doyar kamar yanda ya ce yana
tsaye. Tare suka fita da Fadila bayan na gama haɗa abin karyawar. Na fashe da kuka ina kallon doya
ƙwara ukun da suka bar mun a matsayin rabona. Ganin ina kukan ya saka Sharifa ma ta saka kuka dole
na rarrashi kaina dan tayi shiru.
Kafin a sha biyu na kammala abincin rana na zuba na asibiti a zatona zai dawo ya ɗauka ko zai turo
amma har aka fara shiga masallaci bai dawo ba na kira wayar sa har sau biyu kuma bai amsa ba sai kawai
na shirya na tafi. Gidan Mama na fara biyawa na ajiye Sharifa, dama shinkafa da wake da mai da yaji na
dafa ganin sun gama abincin rana na canza fulasai na zuba miya a maimaikon Mai na haɗa komai. Mama
ce ta ce na jira Abba ya dawo daga masallaci sai muje tare da ita ta duba Hajjan, sai uku da wani abu
Abban ya dawo sannan muka tafi. Muna shiga asibitin zuciyata ta fara bugawa, na san da wahala idan
Bilal bai yi fushi ba ko da yake dole ma yayi fushi har ƙarfe uku da wani abu amma ba'a kawo musu
abincin rana.
Ina ga ganin Mama ya saka kai tsaye aka bar mu muka shiga sai dai kuma ban gansu a gadon jiyan ba.
Wata Nurse da jiyan naga ta zo ta duba jinin da aka saka mata na tambaya tace sun koma Retainer ship.
Ba yabo babu fallasa suka karɓe mu, ganin kwanukan abinci yasa hankali na ya kwanta tunda dai basu
zauna da yunwa ba. Mama bata jima ba ta musu sallama ta tafi bayan ta ajiye wa Hajja dubu ashirin
kuɗin dubiya. Har ga Allah banji daɗin yanda ko a fuska basu nuna jin daɗi ba balle su gode mata. Tare
muka fita na rakata mota muka ci karo da Anty Amina wadda da alama itama zuwan ta kenan suka gaisa
muka wuce.
"Amma dai ki dawo da wuri saboda waccen rigimammiyar da kika baro karta ishe mu da kukan ta na
rashin dalili" Mama ta faɗa bayan da ta shiga mota. Ina tsaye har suka tafi kafin na koma. A ɗakin na
tarar da Bilal na tabbatar kuma ya gammu tare da Mama tunda yanzu ya dawo amma bai tsaya ya gaishe
ta ba ya wuce ciki abunsa. Na samu gefe na zauna dan ɗakin yana da girma akwai kuma wadatar gurin
zama, bai ce mun ƙala ba nima ban ce masa ba suna ta hirar su har da Hajjan kace gidan biki ne na wai
Asibiti ba. Sai da aka kira La'asar ya fita, nima fita nayi na tafi in da naga an shimfiɗa kafet nayi sallah ta
acan. Ina gurin a zaune na hango Bilal yana tahowa da wasu mata biyu a bayan sa sai Namiji da kaya riƙi
riƙi.
Da farko ban zata tare suke da matan ba tunda mutane nata shige da fice a gurin sai da naga sun shiga
gurin da ɗakuna suke. Mayar da hankali nayi kan wayata da nake dubawa amma haka kawai zuciyata ta
ringa kaɗaita mun son sanin su waye baƙin. Ɗaya da facemask a fuskarta dan haka ban gane ta ba wacce
fuskarta take a buɗe kuma ban santa ba. Ƙoƙarin cire tunanin su nayi a raina amma na kasa, dole na
tashi na koma ɗakin ina tafe zuciyata na bugun da ban san dalilin sa ba.
Ina tura ƙofar ido na ya sauka cikin n mai facemask ɗin. Gaba na ya yanke ya faɗi nayi saurin yin a'uziyya
a zuciya ta. Ta zubo mun idanuwan ta masu girma haka nima na ringa kallonta dukda yanda kallon nata
yake sake assasa gudun zuciya ta. Farace tas farin gaske kuma ba na bleaching ba, tana da kyau wanda
ko mai hassadar mutum ba zai ƙarya ta hakan ba a shekaru kuma zata iya haura talatin dukda jikinta bai
nuna shekarun ba amma aka ce ido ba mudu ba amma ya san ƙima.
A hankali nayi sallama dukkan yan ɗakin suka zubo mun ido sai lokacin ita kuma ta ɗauke nata idon daga
kallo na. Na wuce gurin da na tashi na zauna ba tareda na kalli kowa a cikin su ba. Muryar Hajja na ji tana
cewa
"Halima baki ga baƙi a ɗakin bane?" Sai lokacin na ɗaga kai muka sake haɗa ido da ita ta sakar mun
murmushin da ya sake faɗar mun da gaba kafin cikin muryar ta da naji kamar na taɓa jin ta a wani guri ta
ce
"Halima ce?"
"Ita ce" Bilal dake tsaye kusa da ƙafafun Hajja ya faɗa yana kallo na. Na mayar da kaina ƙasa kafin na ce
Ban san sanda ta taso ba ƙamshin turaren da na ji dab da hanci na ya saka na ɗago kai ta kuma sakar
mun murmushi haɗi da miƙo mun hannun ta ta sigar musabaha tana cewa
"Sannu Maman Al'amin". Murmushi na ƙirƙira na miƙa mata hannun, hannuna na da laushi amma sai na
jishi tamkar na namiji a cikin nata. Ta dafa ni ta ce
Maimakon na bata amsa sai na kalli Bilal da ya zubo mana ido fuskar sa ɗauke da yanayin da na kasa
fassarawa.
"Ki dawo ki zauna mana JALILA ku da kuka sha hanya zaki tsaya surutu kuma" Hajja ta faɗa, sai na ɗaga
kai da sauri na kalleta bugun zuciya ta yana ƙaruwa. JALILA na ji ta ambata, JALILA abokiyar aikin Bilal ta
can Headquarter su ko kuwa wata daban?
Dama haka JALILAR take budurwa ce ba matar aure ba yanda nake tunani?
Haka kawai na ji zufa na tsatstsafomun dukda a ɗazu sanyin Ac har takura mun yayi shine ma dalilin da
ya saka na tafi waje nayi sallah. Ta sake sakar mun murmushi kafin ta koma in da ta taso tana kallon Bilal
ta ce
"Babu wanda zai ce ta haifi su Al'amin tafi kama da yayar su" ta sake faɗa tana yar dariyar da ta saka na ji
kamar numfashi na zai tsaya. A hankali na miƙe ba tare da na kalli kowa ba na nufi ƙofa na ci sa'a kuma
har na fita babu wanda ya dakatar da ni.
Na zauna kan bencin da ke ƙofar ɗakin haɗi da dafe ƙirji na da hannu biyu ina sauke numfashi. Ina nan
zaune suka fito gaba ɗayan su da suke cikin ɗakin banda Anty Amina ina jiyo muryar Hajja ma musu Allah
ya tsare hanya babu wanda ya lura da ni a cikin su suka wuce. Tashi na yi na bi bayan su, na tsaya daga
can gefe ina hango su jikin wata mota, gaba wacce suka zo taren ta shiga ita da Bilal suka shiga ba, ji na
ringayi kamar mafarki ne ba wai gaske abin yake faruwa ba. Na shiga laluba jiki na ina neman wayata
dan na kira shi na tabbatar da gaske shi ne suka shiga bayan mota da wata Mace ba ni ba ko kuma dai
idanuwa ne kawai suke hasashen gaibu?
Banji waya ta a tareda ni ba na tuna sanda na koma ɗakin a gefe na na ajiye ta ba cikin aljihu ba dan
haka na koma da sauri ina waigen motar da ta tashi har sun fice daga harabar gurin ajiye motocin. Yanda
kasan anyi ruwan sama an ɗauke haka sukayi shiru ina shiga ɗakin, ni ba ta su nakeyi dan ko sunyi
maganar ba bana zaton zan fahimci abinda suke cewa. Na ɗauki waya ta na fita ina jiyo yanda Fadila da
Hadiza suka sheƙe da dariya kamar wasu taɓaɓɓu harda tafawa. Ina kiran layin sa aka ce mun a kashe
yake ba tareda na koma nayi musu sallama ba kawai na fice daga Asibitin na wuce gida.
Nagode da masoya na haƙiƙa waɗanda ko sunyi fushi basu manta tunanin su, waɗanda suke yiwa
Marubuci kallon Mutum ba wai Bawa da suka siya da kuɗi ba.
*Wattpad @MaryamahMrsAm*
*Ban yarda wani ko wata ya juya mun labari ta kowacce siga ba tare da izini na ba*
*Kuɗin karatu yana wakiltar mutum ɗaya ne, kiji tsoron Allah karki ɗauki hakkina ta hanyar fitar mun da
littafi*
*KURA A RUMBU littafin kuɗi ne, a biya naira 800, biya a asusun*
*1840175439*
*Access bank*
*Maryam Farouk, se a tura shaidar biya a lambar Whatsapp ta sama*
*PAGE 32*
Sai da na fita kofar asibitin kafin na tsaya ina raba ido, ina zan nufa ne ma? Gida zan tafi ko kuwa gari zan
shiga cigiyar inda Bilal ya tafi? Na kai hannu na share laimar da naji akan fuskata wadda ban tantance
hawaye bane ko zufa kafin na shiga tare abin hawa, gidanmu na wuce, ban ko karɓi canji ba bayan na
sauka na shige gidan a bakin ƙofa na zauna kamar wata zararriya na fasa kukan da ya saka Mama ta fito
daga falo kamar zata hantsila da Sharifa a hannunta ta shiga tambayata mai ya faru?
"Mutuwa Hajjan tayi?" Ta faɗa tana kallona sai na girgiza kai ina turza ƙafa kamar ƙaramar yarinya na
sake gyara zama ina cigaba da kukan. Sai ta buga mun tsawa tace
"Bana son iskanci Halima haka nan zakizo ki faɗar mun da gaba na tambaye ki menene kuma kinƙi faɗa
to tashi ki fita tun ban rufeki da duka ba". Ganin ta ajiye Sharifa na san zata iya dukan nawa kamar yanda
ta faɗa hakan yasa na miƙe na shige falon da sauri ina cigaba da kukan. Bata sake bi ta kaina ba, sai da
nayi mai isata kafin na kama hanyar gida ba tareda nayiwa Mama sallama ko na ɗauki su Sharifa ba na
tafi.
Ina ƙoƙarin buɗe gida naji muryar Maman Yusuf tana kirana, na waiga ganin ta nufoni yasa na tura ƙofar
na shiga itama ta biyo bayana.
"Kin dawo kenan" ta faɗa tana kallona ba tareda mun haɗa ido ba dan bana son ta fara tuhumata mai ya
sameni na bata amsa da "eh na dawo".
"Ai har zan shigo ɗazun sai kuma naga kina da baƙi sai kawai na wuce dama can gidan Hajiya Zainab zan
ce miki ko zamu leƙa ta gamu da tsautsayi ta karye a hannu" ta sake faɗa, sai nayi jimm dalilin cewar da
tayi wai ɗazu taga nayi baƙi, su wa ta gani ko in ce suwaye suka zo gidan tunda no dai nasan kafin na fita
babu wanda yazo mun amma saboda bana son dogon surutu sai kawai nace mata
"Allah sarki Allah ya bata lafiya nima surukata ce bata da lafiya tana Aminu Kano a kwance". Jajantawa
tayi haɗi da yiwa Hajjan fatan samun sauƙi kafin tace zata yiwa su Amina magana in zasu samu dama ko
zuwa gobe su leƙa su dubata. A raina Allah Allah nake ta wuce shiyasa ma na tsaya ban bari mun shiga
falo ba, ganin bani da niyyar bata gurin zama ya saka tayi mun sallama akan in zasu samu zuwa dubiyar
gobe zata kirani nace mata toh.
Na ringa kallon tarkacen dana tarar cikin falona, daga kan kofunan da aka sha lemo da robobi har zuwa
disposable packs wanda ke ɗauke da sauran abinci ga kaza da aka yiwa cin wulaƙanci duk anyi mun kaca
kaca da gurin dana gyara tsaf na saka turare kafin na fita daga gidan. Ko ba'a faɗa mun ba nasan Bilal ne,
wani abu ya taso daga ƙasan zuciyata ya tokare mun maƙogaro. Kenan nan ya kawo su ya buɗe musu
ɗakina suka shiga ba tareda izinina ba? A hankali na ringa takawa saboda yanda nakejin tamkar zan faɗi
saboda ƙuncin daya mamayemun zuciya. Ɗaki na wuce na samu gefen gado ma zauna lokaci ɗaya
hawaye masu tsananin zafi suka ɓalle mun. Bansan adadin lokacin dana ɗauka zaune ba saida na jiyo ana
kiran sallar magriba lokacin kuma naji ana bugun ƙofa kamar za'a ɓalla ta.
Tun daga ƙofar falo na fara jiyo ihun kukan Sharifa, na ƙarasa da sauri na buɗe naci karo da Mu'azzam
fuskar nan kamar zeyi aman wuta yana ganin na buɗe ya direta a ƙasa ya juya ba tareda ya ce mun
komai ba haka na jasu muka shige cikin gidan Al'amin na gaya mun sun daɗe a tsaye suna ta buga ƙofa
ba'a buɗe ba.
"Mami me akayi miki kike kuka ko baki da lafiya?" Ya faɗa yana kallona dan guri na sake nema na zauna
ina shayar da Sharifan ina hawaye. Maganar sa ta saka na shiga goge fuskata can ƙasan zuciyata wani
ɓangare yana tunasar dani cewa
Sai ƙarfe sha ɗaya da mintuna Bilal ya dawo gidan ina zaune a falon da ban ɗaga ko tsinke daga abinda
na dawo na tarar ba naji motsin buɗe ƙofa, ban motsa ba saida naji an cire kwaɗon dake jikin get ana
ƙoƙarin zugeshi kafin na miƙe a tsorace saboda tun da aka ƙwace Mashin ɗin Bilal ba'a buɗe get ɗin
amma dana hangoshi ta window sai hankalina ya kwanta na koma na zauna, gunjin mota da naji ana
ƙoƙarin shigowa da ita gidan ya saka na sake miƙewa da sauri na tafi bakin ƙofa. Ina tsaye har ya gama
daidaita parking ya fita ya kulle get ua sake komawa cikin motar, motar da suka tafi daga Asibitin a ciki
ce ɗazu.
Sai da ya kwashi kusan minti biyar a ciki kafin ya fito waya kare a kunnensa ya wuce part ɗin sa ba tareda
ya nuna koda alamar yaga tsayuwata ba dukda nasan cewar ya ganni dan ƙofa a buɗe take. Kamar kazar
da ƙwai ya fashewa a ciki haka na koma na zauna ƙwaƙwalwata da zuciyata cunkushe har na rasa wane
tunani ya kamata nayi a lokacin, ina nan zaune ya sake fitowa ina jiyo takunsa kan barander nayi saurin
kwanciya kan kujera haɗi da lumshe idanuwana tamkar me bacci. Har raina naji tsakin daya ja bayan
daya shigo falon ya tsaya a kaina kafin ya shiga jijjiga ƙafata yana kiran sunana.
Na tashi na zauna ina kare idona tamkar daga baccin gaske na farka, da ido ya nuna mun tsakiyar falon
kafin ya ce
"Menene haka? Amma dai kin san na tsani kwana da datti a cikin gida ko?"
Na bi gurin da kallo nima kafin cikin zafin ran da ban taɓa sanin ina da shi ba na ce
"Mai ya hana ka faɗawa waɗanda suka ɓata gurin su gyara ko kuwa haka suka zo suka tarar dashi?"
Ga mamakina sai gani nayi ya saki murmushin dake narkar da zuciyata a duk sanda nayi katarin arba
dashi kafin ya zaune gefena harda ɗora ƙafafu akan cinyarsa cikin murya mai cike da annashuwa ya ce
Ji nayi tamkar ya daɓa mun wuƙa a ƙahon zuci, na janye ƙafafu na daga jikinsa haɗi da gyara zamana ina
kallonsa, sau biyu ina buɗe baki amma sautin muryata yaƙi bani haɗin kai gurin furta kalaman dake kan
harshe na sai kawai na fashe da kuka, abinda ya sake karyar mun da zuciya yanda ya miƙe tamkar baiga
hawayen da nakeyi ba ya wuce kitchen ya ɗakko tsintsiya da dustbin ya shiga tattare gurin, saida ya
share tas ya gyara gurin sannan ya dawo kusa dani ya zauna haɗi da jana jikinsa. Duk yanda na so na
ƙwaci kaina yaƙi bani dama.
Ban taɓa jin na tsani tarayya da Bilal ba irin na wannan daren, nayi kuka tamkar raina zai fita shi kuwa ko
a jikinsa daga ƙarshe da yaga zan ɓata masa lokaci ma ƙarfi ya sakamun yayi yanda yaga dama dani kafin
ya tsallake ya barni a nan falon ya koma part ɗinsa. Saida idanuwana suka daina kawo ruwa suka fara
mun raɗaɗi tamkar na yi kwalli da yaji kafin na haƙurewa kaina kukan na tashi na gyara jikina. Ranar
yanda naga rana haka naga dare, ina zaune inda na idar da sallar asuba ya shigo falon, kan kujera ya
zauna yana danna qayar dake hannun sa nayi masa kallo ɗaya na mayar da kaina ƙasa ba tareda nace
masa komai kusan minti biyar kafin ya ce
"Ga kaya can a kitchen ki haɗa abin kari na mutum uku ƙarfe takwas zan fita dashi ba sai kinyi wanda
za'a kai Asibiti ba" yayi maganar cikin sigar bayar da umarni. Sai na ɗaga kai na kalle shi, so nakeyi nace
ba zanyi ba amma kamar wadda aka ɗinkewa baki na kasa furta hakan, kusan minti goma bayan fitarsa
ya sake dawowa har lokacin kuma ina zaune a inda ya barni, a gabana ya tsugunna ya kama hannayena
yana murzawa cikin salon da yake yaudarar zuciyata da shi yace
"Kada ki fara abinda ba halinki ba Halima, tun jiya na lura shaiɗan yana yawo a cikin kanki idan kika biye
masa zai saka ki aikata abinda zakizo kina dana sani daga baya alhalin baki da wata hujja akan hakan".
Ina aiki ina tuna maganganunsa dana kasa basu fassara ɗaya harna kammala na zauna ina bawa Sharifa
dankalin dana soya Al'amin kuma yana ci da kansa. Muna zaune ya shigo cikin kwalliyar data saka
zuciyata bugawa, zama yayi yace na kawo masa nasa abin karin na tafi na ɗakko na ajiye masa yana ci
ina kallon sa rabin hankalinsa duk yana kan wayarsa dake kawo haske lokaci lokaci da tayi hasken kuma
zai ɗauka yayi yan danne danne kafin ya ajiye yaci gaba da cin abincin. Da zai fita ya ajiye mun dubu
biyar yace na bayar a siyo kaji tunda akwai kayan miya cikin kayan daya shigo dasu da dare nayi abinci na
mutum ukun zai turo a ɗauka. Muƙulli ɗakin sa ma nan ya bar mun shi ya fita tareda su Al'amin ya ɗano
su a mota kafin ya maido su ya wuce inda ban sani ba.
Ina tsaka da shiryawa bayan nayi wanka kiran Mama ya shigo wayata, bayan mun gaisa ta ce
"Babu komai ko wani abun kika gani Mama?" Na bata amsa, daga can ta sauke numfashi tace
"Babu komai kika zo kina rusa kuka jiya sannan har sanda Mu'azzam ya kawo yaran nan yace kukan kike
baki daina ba, shin Halima a duniyar nan idan baki faɗa mun damuwarki ba kinada wadda ta fini ne ban
sani ba?"
"Wani abu ne amma kawai kici gaba dayi mun addu'a Mama" na faɗa muryata tana karyewa daga can
tace
"Kullum cikin yi miki addu'a nake Halima, ban taɓa kai goshina ƙasa na tashi ba tareda na nema miki
taimakon ubangiji cikin lamuranki ba amma dukda haka kema sai kin miƙe tsaye kin ringa yiwa kanki
addu'a Halima na sanki sarai kina da sakaci gurin addu'a kullum kuma ina tunatar dake rayuwa ba zata
taɓa daidaitar maka ba muddin kace zakayita sakaka ba tareda ka saka Allah a gaba da komai naka ba".
Nasiha ta shiga yi mun nayi shiru ina sauraronta harta gama mukayi sallama, ina aje wayar kiran Bilal ya
shigo na amsa a taƙaice ya ce mun
"Ki bar girkin nan kawai yanzu zasu wuce" yana gama faɗar hakan kuma ya katse wayar. Nayi shiru ina
kallon screen ɗin tamkar zan hango waɗanda yake magana akansu ta ciki, la shakka nasan su JALILA ne
amma kuma maganganun sa na ɗazu sunyi tasiri a ƙwaƙwalwata da har naji nauyin da ƙirji na yayi mun
ya sauka, ko da bai fito ƙarara ya faɗa mun ita ɗin ba yanda nake zato bace a gurinsa amma abunda ya
faɗa na karna aikata abinda zanzo ina dana sani daga baya alhalin bani da hujja akai ya warwaremun duk
wani ƙulli da nake buƙatar amsa akai. Dukda haka walwalata bata dawo gaba ɗaya ba haka nayi wunin
ranar ko da wasa kuma banma kawo da na koma Asibiti gurin Hajja ba abinci ma tunda yace kar nayi na
safe da su banyi tunanin da rana nayi ba kuma shima daya dawo da yamma bai yi zancen ko an kai musu
abincin ba har ranar litinin tukunna da yamma yace idan akayi sallar magriba mu shirya za muje can
gidan ashe ma an sallamota yau da rana.
Nayi mamakin ganin motar ranar nan a ƙofar gida sanda muka fito zamu tafi gidan Hajjan a zatona ai ta
su Jalilan ce kuma sun tafi da abarsu musamman da ban sake ganinta yazo da ita gidan ba tun waccen
ranar. Da kansa ya buɗe mun gidan gaba na shiga na zauna ya zuba su Al'amin a baya, maigidan dake
jikin namu ya fito suka gaisa ina jinsa yana yi masa Allah ya sanya alkhairin motar ni dai ban ce masa
komai akai ba har saida muka hau titi sosai kafin ya kalle ni ya ce
Sai na juya na kalle shi cikin rashin fahimta, ya wani taɓe baki ya ce
"Mota na siya har mutanen waje suna mun Allah sanya alkhairi amma ke kinyi tamkar ma baki gani ba ko
a jikinki". Dariya ma maganar sa ta bani dan haka nayi murmushin da iyakar sa leɓe kafin na ce
"Au da kallon matsiyaci kike mun kenan?" Ya faɗa yana kallona, sai na girgiza kai nace
"Ko kusa, amma a yanda muke da kai banyi zaton kana da halin da zaka iya siyan ko keke ba a yanzu
balle aje ga batun mota. Allah ya sanya alkhairi ya tsare ka daga sharrin ƙarfe".
"Hmmm Halima kenan, shi mallakar abun duniya ai zuciya ne ba wai arziƙi ba, kuma su kuɗi ai basa
magana. Kin san akwai masu arziƙin da sai na kusa da su ne zai bayar da labarin alkhairin su akwai kuma
kuɗin da duniya ta san su amma kuɗin cizo ne gasu da baƙin ciki da hassadar wani ya raɓe su har yaci
arziƙin su. Mungode wa Allah daya haɗa mu da masu arziƙin bayarwa" ya sake faɗa, na kalle shi kawai
nayi murmushi nace
"Masha Allah, Allah ya ƙaro ire irensu ya kuma ƙara yalwata arziƙi mu kuma Allah ya ƙara mana wadatar
zuciya, dama ai hannun da yake bayarwa baya taɓa rasawa" sai ya ce
"Idan ma magana kike faɗa mun dama kika samu ki faɗa son ranki yarinya lokacin ki ne. Kuma ita rayuwa
ai kayi fatan Allah ya haɗa ka da mutanen da zakayi benefiting da su ba waɗanda zasu zame maka
liability ba. Ni shiyasa kika ga duk wani mutum da zanyi mu'amala dashi sai na duba ta ina zai iya
taimako na a rayuwa? Dan ba zan ɓata lokaci da wanda bashi da wani role da zaiyi playing cikin rayuwata
ba".
Bamu sake cewa komai ba har muka isa gidan Hajjan can cikin kaina dai ina ta nanata maganar da yace
shi duk wanda zai yi mu'amala dashi sai ya tabbatar da akwai rawar da zai taka a rayuwar sa. Maganar
Mu'azzam ta zama gaskiya kenan tunda gashi ya nanata hakan da bakinsa shima, kenan shi baya burin ya
taimaki wani sai dai shi a koda yaushe a taimake shi kenan.
Ko da mukaje babu ma wanda yabi ta kaina suna ta zancen mota kuma a hirar tasu na tsinci kamar dai
Hafiz ne ya bashi idan ma ba kyauta ba toh rabin kyauta ya masa dan da alama ba wasu kuɗi ya bayar
masu yawa ba aka bashi motar wadda in har siyanta zaiyi Bilal ɗin da na sani bai isa riƙe irinta ba. Bamu
jima sosai ba muka tafi abun Allah sai gashi har Rufaida ya kaimu kuma muka shiga tare yace na ɗauki
abinda muke so muka zauna a gurin muka yi ciye ciyen mu muka yi hotuna kafin muka wuce gida. Kafin
mu isa duk wani sauran ƙunci dake cikin zuciyata yabi sanyin yoghurt da ice cream ya zirare na ware na
koma asalin Halimata muna ta raha har muka isa gidan. Daren saɓanin dararen da suka gabaceshi munyi
shi cikin walwala da farinciki. A nan ɗakinsa na part ɗina muka kwanta bayan da muka gama shan
soyayyar mu bansan ƙarfe nawa ya bar ɗakin ba dan ni dai na farka ƙarfe huɗu da mintoci na tarar baya
nan da fari na ɗauka ma ko yana banɗaki na zauna ina jira ya fito na shiga jin shiru yayi yawa yasa na
tashi na ƙwanƙwasa kafinna buɗe naga babu kowa.
Saida nayi uzurina na fito kafinna fita falo na tarar dashi kwance kan kujera yana bacci waya kare a
kunnensa, mamaki ya kamani, wace waya ce haka cikin dare har kuma yayi bacci a haka? Matsawa nayi
kansa na kai hannu zan zare wayar na duba yayi firgigit ya farka haɗi da fizge wayar, nayi baya saboda
yanda ya taso kamar zai makeni ya shiga matse ido kafin yayi ƙaramin tsaki ya kalleni ya ce
"Na gaya miki ki dena mun irin haka kar wata rana na kai miki dukan da zan ji miki ciwo". Na tura baki,
yana yawan gaya mun baya son yanda nake masa idan yana bacci nace zan gyara masa pillow ko na karɓi
wani abu a hannun sa ina razana shi. Tashi yayi ya wuce ɗaki na bi bayan sa ina cewa
"Toh dawa kake waya a daren nan har bacci ya ɗauke ka baka sani ba?"
"Ni nace miki waya nakeyi ko kinji da kunnenki ina magana da wani?" Ya faɗa bayan daya kwanta akan
gado. Nayi tsaye ina kallon sa yayi ƙaramin tsaki bayan daya tura wayar ƙasan pillow daya kwanta akai
kafin ya rufe ido alamar bacci zai koma.
"Amma dai ka san babu kyau aje waya a ƙasan pillow ko" na faɗa yayi saurin katse ni da cewa
"Dan Allah Halims ki barni bacci nake ji". Fita nayi naje na duba Al'amin da Sharifa ina shiga tana farkawa
dan dama dai dai lokacin farkawata kenan na haɗa mata shayi na bata dan na dena bata Nono da dare
saboda ina so na yayeta kafin a fara Azumi, sai da ta koma bacci kafin na sake musu addu'a, jin an fara
kiraye kirayen sallah sai kawai na ɗauro alwala dan bacci ya bar idona. Ina tura ƙofar ɗakin Bilal dan
dama ban rufeta da kyau ba sanda na fita da sauri ya kife wayar sa, dukda na rigada na ganshi amma
bance komai ba na wuce na ɗauki Hijabi na na fita na ja masa ƙofar.
Sallah nayi raka'a biyu kafin na ɗauki alƙur'ani da tsakani da Allah na kwana biyu banyi karatu da shi ba.
Badan bana karatun alƙur'ani ba aa, na kan yi tilawar surorin dana haddace ko nayi amfani da wayata
musamman idan zan tisawa Al'amin karatu. Ni da kaina naji nutsuwa sosai a ruhi da gangar jikina
zullumin daya cika mun zuciya akan me Bilal yake a waya da yake ɓoye mun ina fara karatun ya barni. Sai
da aka kira sallah kafin ya fito ya wuce masallaci daya dawo ina lura da yanda ya kame fuska ta yuwu
yayi zaton zan masa maganar waya da kuma yaji banyi ba har na shirya Al'amin zan fita kaishi makaranta
yace na bari zai kaishi suka fita harda Sharifa kafin su dawo nayi maza nayi wanka nayi kwalliya.
Bayan mun karya ya ce mun ranar Alhamis zai tafi Abuja kuma zai iya yin sati ɗaya zuwa kwana goma
acan ɗin.
"Anty Sa'ada bata da lafiya ɗazu dana fita mukayi waya da Hajja take gayamun har an kwantar da ita a
Asibiti jiyan dan haka Fadila zata tafi can ta zauna da ita kafin ta samu sauƙi" ya faɗa. Cikin fuskar jimami
na ce
"Allah sarki Allah ya bata lafiya shiyasa bata zo duba Hajja ba ashe" ya amsa da Amin kafin ya ce
"Kinga idan Fadila ta tafi gidan zai zama babu kowa sai Abubakar kuma itama Hajjan jikinta ga yanda
yake kusan komai sai an taimaka mata takeyi saboda ciwon ƙafarta"
"Abinda zanyi magana kenan dama nace toh Hajja fa idan Fadila ta tafi tunda itama tana da buƙatar ta"
na faɗa, ya goge hannunsa da tissue kafin ya ce
"Na gaya mata zata dawo nan gidan ta zauna kafin Fadilan ta dawo".
*Wattpad @MaryamahMrsAm*
*Ban yarda wani ko wata ya juya mun labari ta kowacce siga ba tare da izini na ba*
*Kuɗin karatu yana wakiltar mutum ɗaya ne, kiji tsoron Allah karki ɗauki hakkina ta hanyar fitar mun da
littafi*
*KURA A RUMBU littafin kuɗi ne, a biya naira 800, biya a asusun*
*1840175439*
*Access bank*
*PAGE 33*
Banji komai dangane zaman da ya ce Hajja zatayi ba dukda nasan ba jituwa mukeyi da ita ba amma kuma
abinda yake so ne kuma wanda zai faranta masa ni kuma burina a koda yaushe kenan. Har ya fita ya
kirani a waya yace na shirya gashi nan dawowa zamu fita tare, da nace masa Al'amin fa kar lokacin tashin
su yayi bana nan sai ya ce ai ba jimawa zamuyi ba dan haka nayi maza na canza kayana na shirya Sharifa
ina jin horn ɗin mota na fita. Raina fes na kame a gaban mota ina jin wani farinciki na ratsani.
Na daɗe ina hakaito irin haka nida Bilal ɗina mu ringa zagaya gari a mota nasan duk inda muka gilma sai
an kallemu an kuma yaba dacewar mu dan sau tari na sha yin yunƙurin yiwa Abba magana akan ya
siyamun mota sai kuma na kasa toh gashi lokaci yayi ya mallaka da kuɗin sa ma. Murmushi nayi ina
kallon yanda yake murza sitiyari yayi irin zaman nan na yan birni sai ya ƙara kyau haɗi da kwarjini a
idona. Na ƙara rungume Sharifa da ta fara bacci kafin na karyar da murya na ce
"To yanzu yaushe zaka fara koyamun mota?" Yi yayi tamkar nai ji ni ba har saida na sake maimaitawa
kafin ya mun gajeran kallo haɗi da murmushi ya ce
"Ke da kika tashi gidanku cike da motoci har kyace baki iya tuƙi ba?"
"Idan da na iya ai tuntuni zaka sani" na bashi amsa ina kallonsa, sai ya ɗan taɓe baki ya ce
"Shiyasa ba'a haɗo miki da mota a gara ba kenan ko a siya miki daga baya". Yanda yayi maganar ya saka
nayi shiru ba tareda na sake cewa komai ba tun kafin hirar ta canza akala zuwa abinda zai haddasa mana
ɓacin rai. Ban sake crwa komai ba shima haka har muka isa Unguwar su Anty Labiba, sai da muka gota
gidanta kafin murnar da na farayi ta koma ciki dan na ɗauka bazata zaiyi mun yau dai muje gidanta da ni
da shi. Layin daya koma bayan su ya shiga na kalle shi na ce
"Na ɗauka gidan Anty Labiba zamuje" ba tareda ya kalleni ba yana ƙoƙarin tsayar da motar a ƙofar wani
madaidaicin gida na masu rufin asiri ya ce
"Ai saiki sauke". Ban fita daga motar ba bayan ya sauka sai da ya mun magana dan ban san ina muka zo
ba balle nayi garajen fita, ina tsaye ina ƙarewa layin kallo, duk gidajen gurin ƙanana ne na masu ƙaramin
ƙarfi ba kamar can kan layin su Anty Labiban ba. Kofar wani gida mai ɗan dama dama akan sauran ya
nuna na rufa masa baya, ya jera sallama sau biyu kafin daga ciki aka amsa tareda bayar da izinin shiga
sannan ya shiga na bishi a baya ina ƙarewa gidan kallo.
Ƙaramin gida ne dan gaba ɗaya ɗakuna uku ne a ciki falle falle sai banɗaki da kitchen duka a tsakar gidan
da rijiya amma tun daga waje zaka yabawa tsaftar mazauna cikinsa domin hatta da kwatar su tsaf take
an yasheta haka tsakar gidan daya sha fasassun tiles tsaf yake babu ko tsinke banda tabarmar da wata
mata mai matsakaicin jiki take zaune sanye da hijabi tana jan carbi da alama sallar walaha ta idar.
Cikin fara'a ta shiga yi mana maraba, na zauna gefen tabarmar Bilal kuma yaja kujerar tsugunno dake
gefenta ya zauna yana sunne kai tamkar wanda yake a gaban surukai.
"Sannunku da zuwa" ta sake nanatawa cikin fara'a na gaisheta ta amsa tana jan Sharifa amma taƙi zuwa
Bilal ma ya gaisheta haɗi da tambayarta ya ƙarin haƙuri hakan ya saka nima nabi bakinsa nayi gaisuwar
dukda bani da masaniyar mace ce ko namiji ma wanda ya rasun.
Tashi tayi ta kawo mana ruwan pure water da biscuit ta bawa Sharifa, bayan ta zauna ta ce
"Amma bata san da zuwanka dan bata yi zancen ba kuma yanzun nan basu ma jima da fita ba". Ji nayi
ƙirji na ya buga ras na ɗaga kai na kalli Bilal da cikin sa'a muka haɗa ido shima ni yake kallo kafin ya
ɗauke idonsa ya bata amsa da cewa
"Eh ban gaya mata zanzo ba gaskiya munyo ta nan haka ne nace bari mu ƙaraso Halima tayi muku
gaisuwa".
"Allah sarki aikuwa mungode Allah ya bada lada" ta faɗa ya amsa da amin ni dai ina sauraron su cikin
kaina kuma ina ƙoƙarin tantance wacece itan da suke magana akai?
Shiru ya gifta na kusan minti biyu shi kansa yana ƙasa sai ita matar dake jan Sharifa da har sannan taƙi
yarda da ita sai ya miƙe yana laluba aljihun sa yace
"Har zaku tafi?" Ta faɗa, na miƙe nima sai itama ta miƙe tsaye tana cewa
"Shikenan toh ku gaida gida Halima nagode Allah yayi albarka na amsa da "Amin" ina yin gaba. Ta gefen
ido naga ya duƙa ya ajiye mata kuɗin da ban san ko nawa bane na ƙarasa ficewa ina jiyota tana ta jera
masa addu'oi, na jingina da jikin mota ina sauraron fitowarsa gaba ɗaya kaina ya cika da tunanin nan ɗin
ina ne dan dai ban taɓa ganin matar ba balle nace danginsu ce kai ko a labari bai ma taɓa cemun suna da
yan uwa a nan unguwar ba dan da ace yar uwarsu ce tun sanda yake zuwa hira gurina gidan Anty Labiba
zan san da zamansu.
Sai da ya ƙara kusan minti biyar ina hangosu tsaye a soro suna magana kafin ya fito yana wani ɗauke kai
kamar baya so mu haɗa ido ya buɗe motar muka shiga, ban ce masa ƙala ba har saida naga yana ƙoƙarin
sake wuce gidan Anty Labiba kafin na ce
"Sauri nakeyi zan wuce gurin aiki" ya bani amsa sai nayi saurin cewa
"Shi kuma Al'amin ɗin wa kika barwa shi?" Ya sakw faɗa cikin tsare gida, zan sake magana ya ce
"Da Allah ki kyaleni in kin shirya zuwa ki saka rana kije amma yanzu babu inda zaki shiga". Haushi yasa
ban sake ce masa komai ba, ƙarin takaici na ɗauka gida zai mayar damu da ya hanani shiga gidan nata
amma sai gani nayi ya faka a junction ya zaro dubu ɗaya daga aljihun sa ya miƙa mun, ina kallonsa ya
cilla kan mota yayi gaba abinsa bayan mun sauka haka na tare Adaidaita muka wuce gida.
Yinin ranar da tunanin gidan da mukaje na yi shi, bai dawo da wuri na sai bayan sallar isha'i ya taho da
jakar kayan Hajja da wasu abubuwan buƙatarta. A ɗaki na ajiye mata kayan, saida ya zauna cin abinci na
kasa daure tunanin daya addabeni na ce masa
"Gidan Umma Zaliha ne ƙawar Hajja ce mijinta ya rasu sati biyu kenan". Kwata kwata ƙwaƙwalwata bata
kama maganar ba musamman a yanda ya wani tsare gida kamar mara gaskiya, nima haɗe fuska nayi
nace
"Wannan ɗin ce ƙawar Hajja matar da daga ganinta ba zata wuce sa'ar Anty Amina ba ma idan ma zata
girmeta da kaɗan ne"
"Ƙarya na miki kenan?" Ya faɗa yana aje cokalin da yake cin abinci, na kalli gefe na ce
"Ni bance ƙarya kayi mun ba amma kuma nasan ba gaskiya ka faɗa ba tunda kake zuwa unguwar gurina
ya akayi baka taɓa faɗa mun akwai ƙawar Hajja a gurin ba sai yau"
"Bana son hauka da shashanci Halima. Wato saboda kinga na sake miki kwana biyu shiyasa har kika
samu damar ki ajiyeni kina tuhumata kamar wani ɗan cikinki ko? Uwata ce ke ko me da kike zaton zan
miki ƙarya?" Yayi maganar cikin ɗaga murya. Sai na waiga na kalli cikin falon inda Al'amin da Sharifa suke
duk su biyun sun zubo mana ido da alama hargaginsa ne ya janyo hankalin su dan haka na sauke murya
na ce
"Da dai kayi haƙuri ka dena wannan ihun kaga yara suna kallonka". Ai ina wuta y jefani a ciki wai
mahaukaci ma na ɗauke shi kenan nace yana ihu, ya ringa surfa mun tijara kafin daga ƙarshe ya fice daga
gidan gaba ɗaya garin sauri kuma ya manta wayarsa dake kan dining bai kula da ita ba. A gurin na zauna
na rizgi kuka Al'amin da Sharifa suna tayani, ganin suna kukan ya saka na rarrashi kaina daƙyar nayi shiru
na goya Sharifa Al'amin kuma ya kwanta akan cinyata.
Muna zaune shiru a falo kamar marayu naji ƙarar wayarsa a gurin dining, kamar kar na kula amma zuciya
da shaiɗan suka ingizani ko babu komai zan samu amsoshin zarge zargen da suke mun yawo a
ƙwaƙwalwa sai na janye Al'amin na miƙe kafin na kai gurin kiran ya katse na ɗauki wayar na danna.
Password ɗin sa da na sani na saka suka ce wrong. Naja kujera na zauna na sake gwadawa ko ban shigar
daidai bane still bata buɗe ba, tagumi nayi ina ƙoƙarin tuna wata number mai muhimmanci da zai iya
sakawa a matsayin password ɗin sa daidai nan kiran ya sake shigowa gabana ya yanke ya faɗi da ganin
sunan dake yawo akan screen ɗin wayar "DUNIYA TA".
Cikin son in tabbatar da cewar Hajja ce ko ba ita ba domin kuwa a zatona ita kaɗai ce zata iya samun
matsayin wannan sunan a wayar Bilal tunda ni dai na san da HALIMS yayi saving number ta. A speaker na
saka wayar bayan dana amsa kiran, daga can naji muryar mace cikin sautin da ban tantance haka take
magana ba ko kuma shagwaɓa take masa tayi sallama take kaina ya sara, zuciyata ta shiga bugawa da
sauri haka gaba ɗaya ilahirin jikina ya ɗauki rawa zufa ta shiga keto mun tamkar wadda nake a gaban
murhu dukda kuwa falon a wadace yake da iskar fanka da Ac dan akwai wuta amma lokaci ɗaya naji na
fara ɗigar da zufa.
Dukda a zaune nake kan kujera amma sai na ringa jin kamar a tsaye nake har jiri yana neman kayar dani
dan haka na dafe table ɗin gabana da hannaye biyu muryar budurwar na cigaba da yi mun amsa kuwwa
tana tana nanata "Hello, Yah Bilal kana ji na kuwa?"
Allah ne ya taimake ni ta katse wayar daga can zuwa lokacin ba wani gane komai nakeyi sosai ba dan ji
nayi tamkar an ɗora mun gingimemen dutse a kaina ya danne mun ƙwaƙwalwa ya hanani tunani. Ƙarfin
halin sake ɗaukar wayar nayi, tunanin gwada shekarar daya gama secondary school nayi dan yana yawan
faɗar shekarar nada tarihi a rayuwar sa dukda ban san ko tarihin menene ba cikin sa'a kuwa ina sakawa
wayar ta buɗe kai tsaye na dirarwa Messages ɗin sa.
Number JALILAH da na fara cin karo da saƙon ta wanda bai jima da shigowa ba dan bai ma karanta ba na
buɗe. Zan iya cewa tunda nake a rayuwata ban taɓa shiga tashin hankali makamancin wanda na tsinci
kaina a lokacin ba, na ringa buɗe idanuwana da suka mun nauyi suna neman rufe kansu amma naƙi basu
damar hakan burina na karanta abubuwan da nake gani wanda duk kalma ɗaya nake jin ta tamkar ɗigon
dalma a zuciyata. Saƙon ƙarshe da tace ya duba Whatsapp ta ajiye masa saƙo na karanta dan haka na fita
daga message ɗin na koma Whatsapp.
Na miƙe tamkar wadda tasha tayi mankas ina tangaɗi goyon da nayi yana rinjayata, da bin bango na isa
ɗaki na maido ƙofar na kulle da muƙulli kafin na kwance Sharifa nayi zaman dirshen a ƙasa na buɗe
Whatsapp ɗin nasa. Unread messages biyar na gani wanda Jalilar ta aiko da alama kuma hotone, saboda
yanda zuciyata take bugawa ji na ringayi tamkar zata fito ta bakina wani irin tsoro da ban san dalilin sa
ba ya lulluɓe ni amma haka nan na buɗe chat ɗin nasu da nake jin wata murya a ƙwaƙwalwata tana
ƙoƙarin hanani buɗewa sai dai aikin gama ya rigada ya gama.
Da ƙarfin gaske na runtse ido na bayan dana saki wayar daga hannu na cikin furucin da babu sauti na
shiga nanata Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un sakamakon mugun ganin da nayi, nafi minti biyu ina ƙoƙarin
tattare hankali da ƙoƙarin na gane a zahiri ne abubuwan da suke faruwa ko kuwa hallucination nake yi?
Tamkar mai taɓa kunama haka na sake ɗakko wayar na buɗe idanuwa suka sake yin arba da mugun
hoton da na gani wanda ya sake tabbatar mun zahiri ne ba wai tunani nake ba, a hankali na sake kife
wayar a jikina na shiga sauke ajiyar zuciya tamkar wadda tayi gudun tsere, ratar minti ɗaya zuciya ta sake
ingizani na ɗaga wayar, nayi scrolling har zuwa farkon chat ɗin su kafin na fara tilawa ina karantawa
tareda sauraron muryoyin da sukayi musaya a tsakanin su duk da wata muryar tafi ƙarfin kunnuwa na su
saurara ba murya ba wani rubutun kansa ya girmi ƙwaƙwalwa ta da ta karanta shi.
Na ga tashin hankalin da ko bisa kuskure wani ya alaƙanta Bilal da wannan muguwar ɗabi'ar tabbas mai
rabani dashi sai Allahn daya halicce mu. Ashe dalilin daya saka ya koma kwana a ɓangaren sa kenan
shine kuma dalilin zaryar da yakeyi tsakanin Kano da Abuja ya kife ni da sunan aiki yake zuwa ashe alaƙar
da take tsakanin sa da JALILAr kenan?
Kasa cigaba da bin chats ɗin nayi saboda yanda abinda nake ji da gani ya ƙazanta, na kife wayar a cinyata
na fashe da kukan da ni kaɗai da na ci karo da wannan baƙin cikin sai kuma wadda ta taɓa tsintar kanta
wanda ta bawa dukkan yardarta a cikin irin wannan yanayin kaɗai zata iya hakaito abinda nake ji. Tabbas
Bilal yaci amanata ya kuma ci amanar yarda da SO.
Tambayar da na ringa yiwa kaina dame na rage shi da har ya zaɓi wannan hanyar? Ashe ban ishe shi ba?
Duk yanda nake ƙoƙarin ganin na kare masa haƙƙin sa ta yanda bazai ga haram a waje ta burge shi ba
ashe shi ba haka bane a gurin sa? Da nake masa kallon wanda mace bata dame shi ba har wasu lokutan
nake ganin kamar ina matsa masa da fitina ashe ni duk haukan banza na nakeyi ni ɗin ce ban isa ba ban
kai macen da zai ringa nuna zalamarsa akaina ba yana tareda ni ne kawai amma hankalinsa yana kan
wasu?
Na rintse ido na hotunan tsiraici JALILAH suka shiga gilma mun. Tabbas a inda mace kamarta take ni ɗin
ban isa komai ba sai dai kuma a yanzu na tabbatar da Bilal ƙasurgumin munafuki ne kuma maƙaryaciya
saboda yanda yasha faɗa mun shi cikar jikin Mace bata wani burgeshi yafi son komai daidai irin nawa ba
wanda zai rasa yanda zaiyi dasu ba amma gashi yanzu na kamashi yana tarayyar haram da mai irin jikin
da yake faɗar baya burge shi har yana faɗa mata kalaman da tunda nake dashi ni matarsa ta sunna ko
kusan bai taɓa furta mun ba.
Nayi kuka tamkar raina zai fita, sai da naji numfashi na ya fara yi mun sama sama kafin na fara ƙoƙarin
tsayar da kukan sai dai na kasa saboda yanda muryoyi da hotunan da suka samu mafaka a ƙwaƙwalwata
suke sake jefani cikin wani yanayi. Allah kaɗai yasan ire irenta nawa yake tarayya da su tunda nata kaɗai
na gani yanzu. Waya sani ko itama waccen da yayi saving da DUNIYAR SA itama irin mu'amalar da take
tsakaninsu kenan?
Ina nan zaune tamkar mara rai, kukan zahiri ya tsaya mun sai na zuci da na cigaba da yi, na yunƙura
daƙyar saboda buga ƙofa da kuma kukan da na jiyo Al'amin yanayi. Daƙyar na buɗe masa ƙofar dai dai
lokacin kuma Bilal ya shigo falon idanunmu suka faɗa cikin na juna nayi masa kallon da ko a mafarki ban
taɓa zaton zanyi masa irin sa ba, kallon tsana mai cike da dana sani da nadamar kasancewa a duniyar sa.
Gurin da na taso na koma na zauna haɗi da mayar da kaina baya na ɗora akan Gado, Al'amin ya kwanta
kusada Sharifa yaci gaba da baccin sa ina jiyo motsin Bilal a falo da alama wayar sa yake nema kafin na
jiyo yana kiran sunana cikin sautin da ban tantance ba dan sai naji kamar muryarsa a sanyaye take.
A yanzu muryarsa tana cikin sautikan da bana fatan sauraronsu a kusa dani, muryoyin da nayi matuƙar
ƙoƙarin koresu daga kaina suka shiga dawo mun, voice ɗin ƙarshe dana saurara wanda ba zan iya
maimaita kalmomin da suke ciki na suka shiga dawomun sai na saka hannu biyu na toshe kunnuwana ina
jujjuya kaina da nake jin tamkar zai tarwatse saboda azabar ciwon da yakeyi mun daidai lokacin kuma ya
shigo ɗakin ya tsaya daga bakin ƙofa yana kallona kafin ya ce
Ban amsa ba illah cusa kaina da nayi tsakanin cinyoyina dan bana son ganin sa, ina jinsa ya nufoni yana
sake nanata
"Mai ya faru? Wani gurin ne yake miki ciwo ko kanki ne?" Ya faɗa yana tsugunnawa a gabana. Daƙyar na
ɗaga kai na kalle shi na ce
"Ka tashi ka fita kai ka dame ni kaine bana son gani ko sauraron muryarka a kusa da ni".
"Kanki ƙalau kuwa Halims yau ni kike faɗin baki son gani na naki son jin muryata ko dai gamo kikayi da
Aljanu?" Ya faɗa yana ƙoƙarin kama fuskata. Cikin zafin nama na fizge take kuma na ɗaga hannu na
sauke masa mari a kuncinsa kafin na miƙe tsaye cikin kuka da hargagi nace
"La fitar mun daga ɗaki Bilal ka fita idan ba haka zan maka abinda har duniya ta naɗe na zaka manta da
ni ba".
Ya miƙe tsaye cikin tsananin mamakin abinda na aikata masa yana dafe da gurin da na mare shin yayi
taku biyu yaja baya yana kallona amma ya kasa cewa komai. Hargagina ya farkar da Sharifa ta ƙwala ihu
sai ya nufeta nayi saurin bangaje shi na ɗauke ta ina cewa
"Koda wasa kada ka kuskura ƙaramin hannunka ya taɓa mun ya, iya zunubin daka ɗiba ya ƙare a kanka
Allah ya isa tsakani na da kai Bilal kuma wlh har idan mugun halinka ya shafi yayana bazan taɓa ƙyale ka
ba" na ƙarasa ina kaiwa ƙasa dan gaba ɗaya jikina babu sauran kuzari. Har ya buɗe baki zai sake mun
magana idon sa ya sauke akan wayar sa dake ajiye a ƙasa dan haka ya tsugunna ya ɗakko, ina kallonsa ya
buɗe, a cikin chat ɗin nasu na barta kan wani video da ta turo masa ina kallo ya runtse idonsa haɗi da
dunƙule hannun sa kamar zai kai naushi kafin ya saci kallona.
"Kaji kunya Bilal wlh kaji kunya. Mumini a fuska ashe a zuciya tantirin ɗan is...."
"Ya ishe ki Halima kada ki kurkura ki furta abinda yake kan harshen ki idan ba haka ba sai kinyi nadama
wlh, kar kiga kin mareni na rabu dake na ɗauka bakya cikin hayyacin ki ne amma yanzu tunda na lura
kina sane kada kiyi gigin kawo mun wani hauka dan zanyi maganinki ne" ya dakatar dani cikin tsawa sai
dai duk maganar da yayi bai bari mun haɗa ido ba yayi ta ne yana kallon wani guri daban.
*Wattpad @MaryamahMrsAm*
*Ban yarda wani ko wata ya juya mun labari ta kowacce siga ba tare da izini na ba*
*Kuɗin karatu yana wakiltar mutum ɗaya ne, kiji tsoron Allah karki ɗauki hakkina ta hanyar fitar mun da
littafi*
*KURA A RUMBU littafin kuɗi ne, a biya naira 800, biya a asusun*
*1840175439*
*Access bank*
*PAGE 34*
Kwanaki biyu da suka biyo baya nayi su ne cikin taimakon ubangiji domin a kowacce daƙiƙa ji nakeyi
tamkar numfashi na zai iya yankewa. Babu abinda yake shiga cikina banda ruwa da paracetamol da nake
ta banka saboda azababben ciwon da kaina kama, ikon Allah kaɗai yake riƙe dani akan ƙafafuna hatta
yaran ma game game kawai nake musu duk abinda hannu ya kai nake haɗawa na basu su ci.
Nayi kuka har hawayena sun ƙafe ya zama sai na zuci nakeyi, a duk sanda na tuna abinda naji kuma na
gani dangane da Bilal sai inji na tsani kaina. Ban san ta inda na gaza ba, ba yabon kai ba na sani ko a cikin
mata samun irina mai kula da tsaftar jikinta ciki da waje sai an tona. A koda yaushe na kanyi ƙoƙarin na
kasance a yanda idonsa ba zai taɓa ganin wani abu da bazai so ba a tareda ni. Bana wasa da kyaran jikina
a duk sanda na samu kuɗi kafin nayi komai sai na ware wanda zan siyi duk abubuwan da nake buƙata na
amfanin kaina kuma saboda shi. Ina ɗaukar last kwabo na na siya abun daɗi naci saboda jikina ya samar
da ni'imar da zata gamsar dashi, ban taɓa damuwa da rashin yi biyamun buƙatu na yau da kullum da
yakeyi ba ni dai burina a kullum nayi abunda zan faranta masa amma ace ya rasa abinda zai saka mun da
shi sai wannan?
Wai tun yaushe ma yake aikata hakan ba tareda na sani ba? Tun kafin muyi aure dama haka yake ko
kuwa daga baya ne ya fara? Bani da mai bani amsa amma abinda nafi ƙarfafawa shine bayan aurenmu
ko ma in ce bayan na haihu tunda shine lokacin daya fara zaryar zuwa Abuja da sunan aiki ashe abinda
yake kai shi kenan. Na tuna lokacin da na tafi gida wankan Al'amin sanda yazo ganinmu bai ko nuna ɗoki
ko alamar yayi kewata ba har naji haushi a lokacin ashe dalili kenan. Tun bayan sannan dama ya koma
part ɗin sa gaba ɗaya da kwana kuma daga lokacin ya auri chat koda yaushe ya zauna wayarsa na hannu
yana danne danne ashe dalilin kenan.
Babban abinda ya sake bani mamaki dashi ta yanda tunda ya fita daga ɗakina wancen daren tsayin
kwana biyun bai sake tako ko da kan barander ta ba balle ya shigo yayi mun magana ko yayi mun wani
bayani da zai kare kansa balle har ya rarrasheni ko ya nuna nadama akan abinda ya aikata ɗin. Ko da
yake ni kaina bansan zaman me nakeyi a cikin gidan ba domin a yanda bake jin zuciyata bai kamata ace
na ƙara kwana a ƙarƙashin inuwa ɗaya da shi ba amma kuma na rasa ƙwarin guiwar yin hakan. Allah ya
sani ina Son Bilal irin Son da zuwa yanzu na yarda jarabawa ce a tattare dani a kusa ko a nesa kuma bana
fatan wani abu da zai rabani dashi amma a yanzu ban san me nakeji akan sa ba.
Da azahar ina kwance a tsakiyar falo ina juyi saboda azabar ciwon da cikina ya tasar mun da nasan yana
da alaƙa da horon yunwar da nake yiwa kaina. Al'amin dana aika ya kirawo mun Maman Yusuf suka
shigo tare, tana ganina ta ƙaraso da sauri tana salati haɗi da cewa
"Na shiga uku mai ya sameki Halima?" Da hannu na nuna mata cikina, ta ɗago ni zaune sai ta sake
ɗaukar salatin daya fi na farko tace
"Innalillahi wa Inna ilaihi raji'un kin ganki kuwa Halima? Kwananki nawa a kwance? Ina shi Baban nasu da
ya barki haka sai kin mutu sannan zai kira iyayenki ya basu gawa ko me?"
Jin ta tsaya kwakwazo ya saka na kamo hannunta daƙyar na ɗora akan cikina da muryata da bata fita
nace
"Ba zaki mutu ba in sha Allahu bari na kira Sadi mu tafi asibiti" ta fita kusan da gudu, ni dai ba zan ga
sanda ta dawo ba haka dishi dishi naji sanda aka kwasheni aka fita dani daga lokacin ban sake sanin
komai ba sai farkawa nayi na ganni a gadon asibiti Bilal na zaune a gefena. Mayar da ido na nayi na
runtse bayan dana fahimci a inda nake, ya miƙe tsaye haɗi da kamo hannuna yana cewa
"Kin tashi Halima?" Ban amsa ba sai janye hannun da nayi daga nasa na yunƙura na gyara kwanciya ta ta
hanyar bashi baya, ina jin sa ya sauke ajiyar zuciya kafin ya fita daga ɗakin ba'a daɗe ba suka dawo
tareda likita. Likitan ne ya kira sunana dan haka na gyara kwanciya ta ba tareda na amsa ba ya sake
maimaitawa yana cewa
"Ina jinka" na bashi amsa cikin muryar da bata fita sosai. Yace
"Masha Allah sannu kinji, ina ne yake miki ciwo yanzu?" Sai na girgiza masa kai alamar babu. Matsowa
yayi ya saka abun awon bugun zuciya a ƙirji na kafin ya cire ya ɗauki abun auna Bp ya saka mun a hannu
sai da ya gama sannan ya kalli Bilal yace
"Jinin ya sauka sosai yanda ya kamata bata cikin kowanne haɗari yanzu". Bansan sanda na saki tsaki ba
jin Bilal ɗin yana cewa
"Alhamdulillah har hankalina ya kwanta" duk su biyun suka kalleni ni ko dama basu nake kallo ba, likitan
ya sake cewa
"Bari naje idan ruwan ya ƙare sai kayiwa Nurse magana tazo ta cire mata ina ganin za'a sallame ku ma ba
sai ta kwana ba tunda jikin yayi sauƙi, ni zan shiga wata theater yanzu idan mun gama zan sake
zagayowa sai kayi mata bayani kuma" ya faɗa yana dafa kafaɗar Bilal ɗin. Bayan fitar Dr ya koma ya
zauna kan kujerar daya tashi cikin lafazin da a baya nake so yake kuma jefani cikin shauƙi da begen sa ya
ce
"Faɗuwar da kikayi ɗazu kafin muzo Asibiti kika fara bleeding, toh bayan mun iso da suka gwada suka ce
kina da ciki kusan wata uku" sai yayi shiru. Na gyara kwanciya ta na zuba masa ido ina so naji ƙarshen
maganar tasa, wai ina da ciki, a yaushe nake da cikin har kusan wata uku amma ban sani ba? Jin yayi
shiru ya sunkuyar da kai yasa nayi ƙarfin halin cewa
"Sai me ya faru daga nan toh?" Ya kamo hannun na fizge haɗi da jefa masa wani kallo sai ya matsa ya ce
"Dr yace a yanayin da kike barin cikin zai iya zame miki matsala shine na saka hannu aka ƙarasa fitar
dashi dan dama ya rigada ya lalace". Ban san sanda na yi dariyar da kana ji zaka san ta zallar takaici da
baƙin ciki bace na ce
"Ai dama na saba rainon cikin cikin ƙunci da rashin lafiya ko ka manta? Gara dai ka faɗa mun gaskiya
baka buƙatar cikin shiyasa kace a cire shi kuma hakan da kayi ba laifi bane domin ko ba'a cire yanzu ba
nima idan na sani ba zan barshi ba dan ba zan sake yarda na haɗa zuri'a da Maƙaryaciya, Maha'inci kuma
Mazinaci mara tsoron Allah irinka ba" na ƙarasa ina kallon cikin idon sa. Take idanunsa suka canza launi,
ya nuna kansa da yatsa ya ce
"Ban taɓa zaton haka kake ba Bilal, ka ci amanar So da yarda. Bilal mai nayi maka a rayuwa da ka zaɓi
saka halaccin da na maka ta wannan hanyar? Laifi ne da na So ka na ce sai kai? Laifi ne da na fifita
farincikin ka a kan na kowa? Dame na rage ka? Ta ina na gaza daka zaɓi zubar da ƙimarka da mutunchin
ka haɗi da barin ubangijin ka ta hanyar aikata abinda yayi hani da? Bilal Zina da aurenka?.... "
"Wlh kika sake cewa tak Halima sai nayi miki abinda baki taɓa zato ba" ya katseni cikin hargagin da saida
yayan hanjina suka juya. Ya nufoni idanunsa jajir har wani jirkicewa sukayi ya nunani ya ce
"Ki iya bakinki ki kuma san abinda kike furtawa idan ba haka ba" ya kaɗa yatsunsa biyu akan fuskata. Na
haɗe yawu daƙyar saboda har ga Allah na tsorata da yanayin sa, ban kuma sake cewa komai ba kawai na
maida kaina gefe hawaye suka shiga ziraro mun. Wannan shine a dake ka kuma a hanaka kuka, wannan
naɗe tabarmar kunyar da yakeyi cikin hauka kuma ya sake tabbatar mun da cewar duk abinda na gani
gaskiya ne. To ta yaya ma zai ƙaryata bayan da idona da kuma kunnuwana na ga shaida kuma a wayar sa
ba wai wani ne ya faɗa mun ba?
Sai bayan sallar Isha'i likitan ya bamu sallama, dana sakko daga gadon zuciyata ta raya mun in fita na tari
Adaidaita na tafi gidan mu sai lokacin na tuna banga yara na ba. Ina tsaye bakin ƙofar reception ya taho
bayan yayi settling bill ya tsaya ba tareda ya kalleni ba yace "muje mana"
"Suna gidan Alhaji Sani" (Gidan Maman Yusuf) shine dalilin daya saka na bishi na kwanta a bayan motar
ganin ya nufi wata hanyar daban ba wadda zata kaimu gida ba kamar nayi masa magana sai kuma nayi
shiru kawai. Can wani gurin siyar da kayan ciye ciye mukaje, ya fita ya barni ya ɗan jima saboda layi kafin
ya dawo yana shigowa motar naji ƙamshin gashi ko Kaza ko Nama ga wata ledar da nake zaton Fura ce
ko Yoghurt ya aje su a sit ɗin gaba ya tayar da motar. Ko kusan burgeni banji yayi ba, a lokacin Allah Allah
kawai nake mu isa gida naga yarana daga nan na zauna nayiwa kaina karatun abinda zai fishsheni.
Ɗaki na wuce kai tsaye na faɗa wanka dan shi nafi buƙata a lokacin, ina wankan ina kukan daya rigada ya
zame mun aboki a kwana biyun. Dana fito na jiyo surutai a falo dan haka na zura Hijab na fita na tarar da
Maman Yusuf ce da Anty Amina kishiyarta sai Al'amin da su Kursum da Alina suke guje guje. Sannu suka
shiga jera mun, na samu guri na zauna ina ɗan murmushi. Maman Yusuf ta ce
"Sannu Halima kinga ki har kin ɗan marmaro fuskarki ta ciki ba kamar ɗazu ba" ni dai nayi murmushi ba
tareda nace komai ba sai ta sake cewa
"Ina fita muka ci karo da Baban nasu ai nasan ba lallai kin san ma ya aka fita dake ba dan naga kamar
suma kikayi" sai tayi ƙasa da murya kafin ta ce
"Toh, ɗazun ne naga da nace ya kira iyayenki ya gaya musu kinga yanda ya hayayyaƙo mun kamar zai
rufeni da duka nace toh ko shima irin mazan nan ne da basa son faɗa idan wani abu ya faru a gidan su?"
"Yo rashin lafiya kuma menene abun ɓoyewa ai kamata yayi ma ace iyayen su za'a fara kira a gaya musu
idan abu yazo da ƙarar kwana ai dole a kirasu ace an mutu ai" Anty Amina ta faɗa suka jigaba da jajanta
mun kafin shigowar Bilal ta saka suka miƙe Maman Yusuf na cewa
"Ko dai mu tafi da Sharifa a ƙarasa yayen kawai?" Nayi yar dariya tace
"Ai bama ta da damuwa naga taci abincin ta sosai suka sha wasa tayi bacci ko sau ɗaya batayi kuka ba".
Har get na raka su ina musu godiya, a kitchen na hango shi yana ƙoƙarin ɗumama kaza a microwave na
wuce ɗaki na kimtsa kaina, bana jin yunwa ko dan ruwan da aka saka mun ne dan haka nayi sallolin da
suke kaina bayan na idar na haye gado na kwanta. Bilal ya sake shigowa ɗakin a karo na uku dan sau biyu
yana shiga sanda ina sallah, ya kwantar da Sharifa da tayi bacci akan gado kafin ya tsaya a kaina yana
kiran sunana.
Ban amsa ba haka nan ban motsa ba, ya miƙa hannu ya taɓa ƙafata na buɗe ido da sauri na kalle shi yayi
gajeran tsaki ya ce
"Da idonki biyu dan wulaƙanci kina ji na kenan kika yi shiru" ban tanka masa ba ya sake cewa
"Ki taso kici abinci ki sha maganinki". Sai lokacin na tashi zaune na kalle shi nace
"Ƙwarai magana nake so muyi". Ya zuba mun idanunsa da suka canza launi kafin ya ja stool ɗin gaban
mudubi ya zauna ya ce
"Ina sauraronki".
"Ka dubi Allah ka faɗa mun gaskiya Bilal dame na rageka a zamantakewarmu?" Na faɗa bayan shirun
kusan minti biyu da nayi ina ƙoƙarin kamo ta inda zan fara magana, yayi tsaki ya ce
"Wannan ita tafi komai muhimmanci a gurina domin ina so na san cikin zunubin ka ina da kaso ko babu"
nima na katse shi, sai ya kalleni kafin ya ɗauke kai gefe ba tareda yace komai ba. Kukan da ban so zuwan
sa a lokacin ba ya ƙwace mun dukda haka na ce
"Mai ya baka sha'awa a matan bariki Bilal? Mai ka taɓa nema nayi maka banyi ba daka gwammace ka
fita ka nema a waje?"
"Kina ji ko Halima kowanne mutum da kika gani a rayuwa yana da kuskuren sa kuma da za'a ce kowa a
tona nasa da ba lallai a samu sauran wanda za'a ringa yiwa kallon mutumin kirki ba a duniyar nan, idan
da kina da tunani bai kamata ki bari abinda kika gani ya dameki har ki nemi ki hallaka kanki a banza da
damuwa ba, kuma duk maganganun da kike faɗa kawai ina miki uzuri ne kuma ko da kike wannan
surutun baki da qata shaida akan abinda kike zargin na aikata. Abinda kika gani kawai normal abu ne
tsakanin Saurayi da budurwa amma gaba ɗaya kin wani mayar dashi kamar wacce kika kamani turmi da
taɓarya da ita, idan ba ban yafe miki ba sai Allah ya bi mun kadin ƙazafin da kike mun domin baki da
hujja" ya faɗa ba tareda ya kalleni ba.
Ni ko tunda ya fara magana hawayen da nakeyi suka tsaya, zuciyata ta shiga bugawa da ƙarfi mamakin
ƙarfin halinsa da kalaman da yake furtawa suka sumar dani a gurin da nake zaune. Ban san sanda na ce
"Ashe har kana da bakin da zaka iya kare kanka Bilal? Bilal da idona fa na gani na kuma saurari irin
fasiƙancin da kakeyi sannan har ka iya buɗe baki kace wai da ina da tunani bazan bari abun ya dameni ba
Normal ne, Zina ce ta zama Normal a gurinka? Innalillahi wa Inna ilaihi raji'un Bilal ina iliminka ina
saninka na addini da har ka bari duniya ta rufe maka ido kake kiran Zina da Normal abu?" Na ƙarasa ina
sakkowa ƙasa kan guiwoyina. Sai ya miƙe cikin fusata ya ce
"Halima idan kika sake dangantani da Zina wlh sai kin sha mamaki na"
"Ka faɗa mun abinda ya kamata na danganta dashi toh Bilal idan ban kiraka da Mazin...." Marin da ya kai
mun ya hanani karasa maganar dana fara, sai da na wuntsila gefe saboda yanda marin ya shige ni na fasa
kuka mai tafe da ƙara lokaci ɗaya Sharifa ma ta farka ta fasa mata kukan. Ko a jikin sa ya shiga cewa
"So kike sai kin ƙure haƙuri na, da zaki ringa ce mun Mazinaci da uwarki nayi Zinar?"
Tamkar dukan guduma haka naji maganar a kunnuwa, yau Bilal ne yake wannan zagin na rashin
mutunchi? Ban dawo daga shock ɗin farko ba yaci gaba da cewa
"Ki ɗauki duk matakin da kike ganin yayi miki Halima idan kinga dama ki tafi gidan Radio ki siyi fili ki
faɗawa duniya kinga ina Sex Chat da mace, amma kafin nan ki sani kanki zaki zubarwa da mutunchi bani
ba. Duk inda kika ɗauki laifina kika kai kafin a saurareki sai an miki dariya ko kin manta kin zaɓeni akan
kowa da komai naki? Duk kuma aje a dawo ba zaki taɓa iya rayuwa babu ni ba dan haka zaɓi ya rage naki
ko kiyi haƙuri da abinda kika gani mu cigaba da zamanmu cikin rufin asiri ko kuma ki tafi ki zubar mana
da mutunchi kuma ki dawo ɗin mu zauna, zaɓi ya rage naki" ya ƙarasa yana watsa hannaye alamar
matsalata ce ba tashi ba kafin yasa kai ya fice daga ɗakin.
Ban taɓa riskar dare mai tsayi irin na ranar ba, na ringaji inama ina da ikon janyo safiya ko kuma na fito
da masu abin hawa domin na samu wanda zai kaini gida? A cikin dare na haɗa mana kaya na fitar dasu
barander na ajiye dan na ƙudurce ko da jinin jaka Bilal ya tsafance ni da yardar Allah sai na karya asirin
yau na bar masa gidan sa koda kuwa hakan yana nufin tsayawar numfashi na a doron ƙasa. Ƙarfe shida
na goya Sharifa daƙyar dan tun cikin dare ciwon kai da zafin ƙirji ya sake dawo mun, na riƙe hannun
Al'amin dake tafiya daƙyar dan ko farkawa baiyi daga bacci ba ni na ɗaga shi na aje shi kan ƙafafunsa.
Muna fitowa falo naji ƙarar buɗe Get, wani dunƙule ya taso daga cikina ya tsaya mun a maƙogaro.
Haka na ringa jansa muka fito daga falon lokacin har ya fita da mota ya dawo yana zuge Get ɗin na kalli
kan Barander inda na aje kaya basa nan sai ji nayi ya ce
"Gasu can a mota muje na kaiku tunda kin san babu yanda za'a yi ku fita da sassafen nan da kaya duk
yan unguwa suna kallonki".
Nayi murmushin da yafi kuka ciwo, wato maganar yan unguwa yake gudu amma baya kunyar ubangijin
sa yake kiran Zina da Normal abu. Ina buƙatar na isa gidan da wuri na san kuma tafiyar tawa bata dame
shi ba zai ma fi farin ciki da hakan shiyasa na yarda na shiga motar muka tafi. Har muka isa gidan babu
wanda ya cw uffan a tsakaninmu har muka isa ƙofar gidanmu. Ina ƙoƙarin buɗe motar naji ya ce
"Ina sake jaddada miki dariyar da za'a miki sai tafi laifina da zasu gani yawa, infact sai kin tsani kanki
Halima muddin aibu na ya fita daga bakinki" sai na waiwaya na kalle shi na ce
"Barazana kake yi mun kenan?" Ya ɗage kafaɗa n ƙarasa ɓalle murfin motar na fita ban ko lura da Abba
dake tsaye bakin Get da maƙwafcinmu Alhaji Bala suna magana ba na shige ciki.
A tsakiyar falo na kwance goyon Sharifa dan ji nake kamar zan faɗi na mutu a gurin kai tsaye kuma na
shige tsohon ɗaki na sama sama ina jiyo kamar muryar Amirah tana kiran sunana amma ban tsaya ba.
*Wattpad @MaryamahMrsAm*
*Ban yarda wani ko wata ya juya mun labari ta kowacce siga ba tare da izini na ba*
*Kuɗin karatu yana wakiltar mutum ɗaya ne, kiji tsoron Allah karki ɗauki hakkina ta hanyar fitar mun da
littafi*
*KURA A RUMBU littafin kuɗi ne, a biya naira 800, biya a asusun*
*1840175439*
*Access bank*
*PAGE 35*
Amirah ta ɗaga Sharifa data saka kuka daidai lokacin da Mama ta fito daga kitchen lokacin kuma Al'amin
shima ya shigo Suraj na biye dashi da akwatin mu.
"Ku kuma daga ina haka da sassafe?" Mama ta tambaya, Suraj ya ajiye kayan yana cewa
"Yaya Haliman tana ciki itama". Tsaye Mama tayi kafin tace
"Gaskiya ba lafiya ba kinga fa jefar da Sharifa tayi ta wuce ina mata magana ko saurarona ma batayi ba"
Amirah ta amsa mata. Jumm tayi tana kallon Al'amin daya haye kan kujera ya kwanta alamar baccin sa
zai cigaba, sai ta juya kitchen ba tareda tace komai ba amma zuciyarta cike da saƙe saƙe.
Kan gado na faɗa bayan dana shiga ɗakin dafe da ƙirjina da nake ji tamkar an ɗaure ni da igiya, daƙyar
nake fuzgar numfashi, na ringa juyi a kan gado ni kaɗai tsayin lokaci kafin ubangiji ya kawo mun
rangwamen abinda nakeji ta hanyar rabani da numfashina na wani lokaci.
A waya Mama ta kira Abba, tambayar sa tayi ko Bilal yace masa wani abu ne tunda ance tare muka zo sai
ya ce mata
"Bai tsaya ba yana sauke musu kayan su ya juya ko gaisawa bamuyi ba"
"Ikon Allah, to mai ya faru?" Ta sake tambaya cikin jimami. Daga can yace
"Ni kam ina zan sani ne Amina? Ba gata nan a cikin gidan ki tambayeta mana", jin kamar ya fara fusata
ua saka tace
"Toh shikenan sai ka dawo" ba tareda ya bata amsa ba ya katse wayar dan ransa y sosu matuƙa da ko in
kulan da Bilal ya musu. Sosai yaji ba daɗi sanda Alhaji Bala da suke tsaye yace masa
"Wannan ba Mijin Halima bane naga yaja mota bai ko tsaya ya gaida mu ba? Koda yake yanda ta shige
itama kamar dai akwai matsala dan na lura bata ma ga tsayuwarmu ba, amma shi ai idan ɗan arziƙi ne
yaci ko matsala suka samu ya tsaya nan ya maka bayani ba yaja mota ya tafi ba".
Wannan maganar ta dame shi har ta saka ya fasa komawa cikin gidan da yayi niyya ya sallami Alhaji
Balan kawai ya wuce inda zashi ya a tafe kuma yana tunanin dalilin zuwan Halima da sassafen nan.
Sai gurin ƙarfe tara Mama tace Amirah ta shiga ta kirawo Halima ta karya lokacin har tayiwa su Al'amin
wanka sun ƙoshi sun shiga sabgogin su, ihun da Amirah ta fasa bayan shigar ta ɗakin ya saka Maman
tashi da sauri tamkar zata hantsila ta shiga ɗakin, gabanta ya yanke ya faɗi ganin Amirah tsugunne kan
Halima tana girgiza ta haditda kiran sunanta amma ko gezau bata motsa ba, cikin tashin hankali ta isa
gaban gadon ta ɗagota jikinta ta shiga jijjigata da ƙarfi amma bata koyi alamar zata farka ba.
"Ta mutu innalillahi mun shiga uku Yaya Halima ta mutu" Amirah ta faɗa hannu biyu akai cikin
matsanancin kuka Mama dake rungume da Halima ta ɗaga mata hannu tana cewa
"Bata mutu ba fita ki kira Mu'azzam, kiyi sauri dan Allah yazo mu kaita asibiti" ta ƙarasa tana ƙoƙarin
buɗe idanun Haliman. Da gudu Amirah ta nufi ƙofa sai kuma ta juyo cikin kuka tace
"Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un, Amirah ki fita kowa kika gani ki kira mu kaita Asibiti" Mama ta faɗa tana
fashewa da kuka itama. Tareda Samari biyu Amirah ta dawo wanda a waje ta taresu sun taho a mota su
suka ɗauki Haliman suka fito da ita daga Mama har Amiran babu wanda ya tsaya neman koda Takalmi
suka biyo su Zainab na kuka riƙe da Sharifa haka Al'amin dukda ba wai sanin mai yake faruwa yayi ba
kawai ganin sunayi ya saka shima ya kama. Suna ƙoƙarin sakata a motarsu Suraj ya iso ƙofar gidan dan
dama tare suka fita da Abba ya kaishi Airport zai tafi Lagos, motar sa Mama tace su sakata suka shiga ita
da Amirah ya ja motar da gudun gaske suka nufi asibiti.
Bayan tsayin lokacin dana ɗauka tsakanin mutuwa da rayuwa na farka, na buɗe idanuwana da naji
tamkar an manne mun su da super glue daƙyar na iya buɗe su na kalli in da nake saidai ban fahimci
komai ba hakan ya saka na sake mayar da idanuwan nawa na kulle ina jin sautuka sama sama kamar
daga can nesa. Mama dake zaune kan kujerar dake kusa dani ta miƙe da sauri saboda ƙafata dana motsa,
ta kira sunana, dukda ba wai na fahimci mai ta faɗa ba sautin da naji ya saka na sake buɗe idona na
sauke akan fuskarta. Ta kama hannuna hawaye na ziraro mata tace
"Kin farka Halima?" A hankali tamkar mai koyon magana na kira sunanta a rarrabe "Ma..ma" haɗi da
matsa hannunta data riƙe nawa dashi. Cikin kuka mai haɗe da dariya ta amsa da
"Na'am Halima kin farka? Alhamdulillah". Ji nayi maganganunta suna hau mun kai sai na sake mayar da
idona na rufe tayi azamar kamo fuskata tana cewa
"Ki tashi dan Allah kada ki sake komawa Halima dan Allah ki buɗe idonki ko hankalina zai kwanta" ta
ƙarasa cikin kuka. Na sake buɗe idona na kalleta, tabbas naga ƙauna mai tsanani haɗi da tausayi cikin
ƙwayar idanunta dake tsiyayar da hawaye, kalaman Bilal da ya ce "Da uwarki nayi zina" suka dirar mun
tamkar saukar mashi take wani abu ya taso ya sake tokare mun maƙogaro, ban iya yin abinda ta buƙata
ba na sake mayar da idanuna ruf na rufe su sai ta saki hannuna ta nufi ƙofa kusan da gudu ta fice daga
ɗakin ba jimawa suka dawo tareda likita da Nurses biyu. Sai da ya gama dubani kafin ya kalleta cikin
kalaman kwantar da hankali yace
"Kiyi haƙuri Hajiya na faɗa miki jikinta yana da buƙatar hutu sosai zata farka idan lokacin hakan yayi in
sha Allahu ki daina damuwa zata samu lafiya da yardar Allah"
"Likita ta farka fa, ta buɗe idonta har magana tayi mun kafin ta sake komawa dan Allah likita kayi wani
abun yarinya ta ta farka kaifa kace mun awanni kaɗan amma gashi kwana biyu kenan bata farka ba".
Kwana biyun data ambata ya saka na sake buɗe idona na kalle su, hannu biyu ta ɗaga tana cewa
"Alhamdulillah, ka gani ko idonta biyu". Ganin tana ƙoƙarin ɗago ni ya saka ya dakatar da ita, a hankali ya
kira sunana na kalle shi yace
"Kina jina Halima?" Nayi shiru badan bana jin sa ba sai dan bansan ta yanda zan amsa masa ba. Bakina
yayi mun nauyi tamkar an ɗaure mun harshe. Cikin taushi ya sake kiran sunana da maimaita tambaya ina
jinsa amma na kasa amsawa. Mama ta fashe da kuka tana cewa
"Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un Dr mai ya samu yarinyata dan Allah kayi mun bayani ni Musulma ce
koma menene zanyi haƙuri na karɓi ƙaddarar data samemu".
"Dan Allah Hajiya ki nutsu, idan ba zaki iya shiru ba kuma ki fita waje. An gaya miki babu abinda ya
sameta kawai tana buƙatar lokaci ne babu yanda za'ayi mutum ya tashi daga dogon suma irin haka kiyi
tsammanin nan take tunanin sa zai dawo tamkar yanda yake a da sannan wannan hayaniyar da kukan da
kikeyi shima kina ƙara mata wata damuwar ne cikin wadda take" ɗaya ɗaga cikin Nurses ɗin ta faɗa a
hasale, sai ta juya cikin kuka ta nufi ƙofa na bita da kallo ina so in tsayar da ita amma kuma banida ikon
yin hakan.
Wata yar fitila likitan ya kunna ya shiga haska idanuwana bayan ya gama ya zaro biro daga aljihun rigarsa
yace
"Idan kina jina ina so ki ringa bin biron nan da idonki duk inda nayi dashi kinji?" Na lumshe idona kafin na
buɗe nayi abinda ya ce. Ya mayar da biron aljihu yana cewa
"Yawwa Halima, yanzu ki motsa ƙafar ki na gani" nayi yanda yace sannan ya kama hannuna yace in
matsa hannun sa nan ma nayi sannan ya sakeni, cewa yayi na tashi na zauna. Nayi jimm dan kwata
kwata banajin alamar ƙashi ko tsoka a jikina ji nake tamkar a iska nace, sai da ya sake maimaitawa kafin
na yunƙura a hankali naja jikina Nurse tayi saurin saka mun pillow a bayana na jingina ina mayar da
numfashi tamkar wadda tayi tseren gudu. Hamdala yayi kafin ya karɓi folder dake hannun Nurse yayi
rubutu ya bata yace taje pharmacy ta karɓo abinda ya rubuta sannan idan ta fita ta turo masa Mama.
Tare suka shigo da Abba, Mu'azzam, Anty Labiba da Mijinta sai Mama Fauziyya. Gaba ɗayan su kallo
ɗaya zaka musu ka karanci hashin hankalin da suke ciki, Abba ya matso ya dafa kaina nayi karfin halin
tattaro kalmomi na haɗa na kira sunansa, "Abba" ya amsa yana shafa kaina
"Na'am Halimana kin tashi?" Sai na gyaɗa masa kai lokaci ɗaya kuka ya kwace mun Abba ya rungume ni
yana cewa
"Kuka kuma Halima menene? Kiyi shiru dan Allah kinga halin da kike ciki babu abinda zai faru ki dena
kuka kinji?"
"Ina ganin kuyi haƙuri ku koma waje ƙila ganinku ne ya dawo mata da wani abun kuma a yanayin da take
ciki yanzu bama son duk wani abu da zai sosa mata rai balle ya sake ƙara mata wata damuwar" likita ya
faɗa. Duka suka fita banda Abba dake rungume dani idanuwansa sunyi jajir tamkar shima zai yi kukan
yana ta bubbuga bayana da cewa nayi shiru, Nurse ɗin da Dr ya aika ta dawo da allurai da da drip ya
karɓa ya fara haɗawa, zai zare ruwan dake hannuna Abba ya dakatar dashi yace
"Dan Allah kada ka saka mata abinda zai sake mayar da ita wannan baccin"
"Amma Alhaji saboda lafiyarta ne" cewar Dr, sai Abba ya girgiza masa kai yace
"Na sani amma ka ɗanyi haƙuri ku bamu guri zanyi magana da ita". Tsayawa yayi kamar ba zai fita ba
kafin ya juya, Nurse ɗin da ta yiwa Mama magana ɗazun ta buɗe baki zata sake magana yayi saurin
dakatar da ita ta hanyar cewa su fita.
Sai sa suka rufo ƙofar kafin Abba ya ɗago kaina daga kafaɗar sa yace
"Tsoro nakeji Abba" na faɗa daƙyar kafin na kama hannunsa na ɗora saitin zuciyata da nakejin ciwo
tamkar an hura mun wuta nace
"Zuciyata zafi takeyi Abba mutuwa zanyi"
"Ba zaki mutu ba Halima har sai lokacin da ubangiji ya rubuta faruwar hakan, duk wani tsanani a rayuwa
yana tareda sauƙi kiyita nanata Hasbunallahu wani'imal wakeel a zuciyarki in sha Allahu zaki samu
salama kinji?"
Kai na ɗaga masa alamar naji take kuma na kama na shiga nanata Hasbunallahu a hankali a hankali na
fara jin abinda ya tokare mun maƙoshi yana zagwanyewa, zafin da zuciyata take mun ma ya fara raguwa
inayi Abba ma na biyawa a fili sannu sannu har bacci ya ɗauke ni. Ajiyar zuciya ya sauke ganin nayi bacci,
sai da ya ɗauke ƙwallar data zubo masa kafin ya gyara mun kwanciya akan gadon ya lulluɓa mun bargo
sannan ya koma kan kujerar dake gaban gadon ya zauna yana kallona.
Har ya sauka Lagos zuciyarsa babu daɗi gaba ɗaya hankalin sa na ga son sanin dalilin zuwan Halima gida
da sassafe haka da kuma yanayin daya ganta a ciki. Yana so ya kira Mama yaji ko ta faɗa mata wani abu
amma kuma baya son yaji abinda zai ɗaga masa hankali ya hanshi nutsuwar yin abinda zajeyi Lagos ɗin.
Da zai shiga meeting ya saka wayarsa a Flight mood dan haka sai bayan Magriba lokacin sun tashi gaba
ɗaya ya shiga hotel room ɗin sa kafin ya buɗe wayar yana so ya kira wani Abokinsa, Network na daidaita
kuma saƙon Mama ya faɗo tana gaya masa Halina na Asibiti sun sameta a sume a ɗaki har lokacin kuma
dukda bai san ƙarfe nawa ta tura saƙon ba bata farka ba kuma likita yaƙi ce musu komai yace dashi zai yi
magana.
Cikin tsananin tashin hankali ya shiga neman layin Maman amma bai samu ba dan haka ya mayar da
akalar kiran kan Mu'azzam wanda bugu ɗaya ya ɗauka kuma yanda ya jishi da bayanin da ya masa akan
yanayin Haliman ya saka yaji ba zai iya ƙara koda awa ɗaya a Lagos ɗin ba duk kuwa da bai kammala
uzurin da yaje yi ba, sai dai yayi rashin sa'ar rasa jirgi, haka ya kwana a zaune tamkar yanda suma a Kano
suka kwana cikin tashin hankali da zullumin halin da Halima take ciki da gari ya waye kuwa ko wanka bai
tsaya yiba ya hawo jirgi ya taho musamman yanda Mama ta kira tana rusa masa kuka akan yayiwa likita
magana ita dai ayi mata bayanin halin da yarta take ciki idan ma mutuwa tayi a gaya mata kawai saboda
tunda aka kawota take nan kwance kan gado bata motsa ba gara ta sani in mutuwa tayi ta ɗauki
dangana a basu gawarta su wuce gida su mata sutura.
Koda yazo ma babu wani gamsasshen bayani daya samu daga bakin likitan, abinda ya gaya masa kawai
zuciyar Haliman ta kumbura kuma jininta yayi hau sosai wanda yayi sanadiyyar samun partial stroke da
tayi sannan ta shiga doguwar suma. Shi dai Abba daya gama sauraronsa saida ya kwashi kusan minti
goma a zaune kafin ya iya buɗe baki yayi magana tsabar yanda ya shiga shock, suna raye a duniya wace
irin damuwa ce haka Halima take da ita da har take barazana ga rayuwarta amma basu sani ba?
Dr ne ya ringa kwantar masa da hankalin ganin yanda jikin sa yayi laƙwas ya kasa cewa komai sai ajiyar
numfashi kawai yakeyi. Haka nan ya shanye maganar a cikin sa duk yanda Mama ta ringa nacin ya faɗa
mata yanda sukayi da likitan amma yace mata babu komai, ta kaɗa ta raya tayi kukan duk a banza yaƙi
faɗa mata domin ya san damuwar da take ciki a yanzu kaɗan ce akan ya sanar mata da ainihin halin da
Haliman take ciki.
Buɗe ƙofar da akayi ya sake ya dawo daga dogon tunanin daya tafi, Alh Saleh mijin Anty Labiba ya tsaya
daga bakin ƙofar yana cewa
"Dan Allah Alhaji kazo kayi mata magana ko kai zata saurareka" sai ya miƙe yana cewa
"Wacece"
"Labiba mana, gata nan wai gidansu Mijin Halima zata tafi" ya bashi amsa jin haka ya saka Abba ya fita
da sauri dan dama tunda ya dawo ya tarar da rigimar Anty Labiba taje har can gidan Bilal bata same shi
ba ranar da aka kai Haliman asibiti taji ba'asin me yayi mata shine yanzun ma ta tada bala'i kamar zata
hau iskokai Mama da Mama Fauziyya na riƙeta tana fizgewa wai gidansu Bilal zata tafi idan ma bata
same shi ba sai ta saka an ɗaure Hajja ai dole ya fito duk ma inda ya shiga ya musu bayanin abinda
yayiwa Halima.
Tsawa Abba ya daka mata ganin yanda ake riƙeta tana fizgewa duk ta tara mutane sun tsaya suna
kallonsu, ta fashe da kuka tace
"Na rantse da girman Allah bai isa ya kasheta yaci banza ba har in wani abu ya samu Halima wlh sai na
ɗaukar mata fansa akansa". Cikin faɗa Abba yace
"Bana son shashanci Labiba da girman ki zaki ringa abu kamar wata ƙaramar yarinya shikenan Allah ba
zai jarabci bawa da lalura ba sai wani ya zama sila? Kada na sake ji, ku tashi ma ku wuce gida kawai
tunda hayaniya zaki tayarwa da mutane". Haka ya tattarasu duka da sauran yan dubiyar da suka zo
dukda babu wanda ake bari yana ganinta bayan su amma dangi kamar masu jira ana cewa bata da lafiya
suke ta tururuwar zuwa dubiya, gashi dai babu wanda ya san takamaiman abinda yake damunta haka
nan duk wanda yazo ya tafi zai haɗa nasa kalar labarin da ciwon da zai ɗora mata, amma dai maganar
data fi ƙarfi ta kuma fi shahara a gari ita ce Guba ta ci saboda Bilal zai ƙara aure kamar yanda wacce ta
fara kai labari Galadanci can gidan kakannita tace daga majiya mai ƙarfi ta samo bayanin gurin ɗaya daga
cikin ƙannen Bilal.
BILAL
Bayan daya sauke su kai tsaye gidan Hajja ya nufa, tuƙi kawai yake amma bashi da nutsuwa a tattare
dashi. Tsakanin sa Allah tun waccen ranar da Halima ta bankaɗo sirrinsa yake jinsa tamkar tsirara yake
yawo, kamar kowa ma yasan abinda yake aikatawa a ɓoye. Koda da yake nuna tamkar komai ba komai
bane kawai yana yi ne saboda ya ceci kansa amma shi kaɗai yasan kalar kunya da nadamar da yake ciki a
yanzu. Tsautsayi da ƙaddara ya saka koda ya lura ya bar wayarsa a gida bai koma ya ɗakko ba saboda
yasan Halima bata da ɗabi'ar bibiyar masa waya ko lokacin da baya saka password babu ruwanta da
wayar sa balle yanzu daya kulleta ya kuma san babu ta yanda za'ayi ta iya buɗewa koda ace ma tayi
niyyar hakan.
A tsakar gida ya tarar dasu Fadila tsaye da akwatinta tana ganin sa tace
"Kai kuwa ina ka jefa wayarka tun asuba nake kira baka amsa ba ko ka manta sammako zatayi? Shiyasa
fa tuntuni nace ka bata kuɗin motar ta a hannu saboda irin haka yanzu da ƙyar idan zata samu motar
farko sai tayi jira wata ta cika".
Cikin falo ya shige ba tareda ya amsa ta ba ya zauna kan kujera haɗi da dafe kansa da hannu biyu, Hajja
ta shiga tana cewa
"Ai tafiyar tata ba zata yuwu ba ma Hajja" ya faɗa yana gyara zama, sai ta zauna itama tana cewa
"Saboda me?"
"Mun ɗan samu matsala ne da Halima ta tafi gida, kinga kuma idan ta tafi ai ba zai yuwu ki zauna ke
kaɗai ba tunda har yanzu jikin ki da saura" ya bata amsa. Sai kuwa ta zabura tace
"Kaji yar abu ta kazan uba au saboda zanzo gidan shine tayi yaji?"
"Bafa dalilin zuwanki bane" yayi saurin katseta, Fadila tayi tsugul tace
"Wlh saboda haka ne dama ai na gaya miki wlh da wahala ta yarda ki zauna a gidan nan dan ji take
kamar na ubanta bata so kowa ya shiga sai ita da danginta".
"Ke, waya sako bakinki ko sa'anninki ne suke magana?" Ya faɗa yana ballawa Fadilan harara, Hajja ta
taso masa itama tana cewa
"Ko ba'a sako da ita ba ai gaskiya ta faɗa, to kuwa bata isa ta hanani zuwa gidan ka ba billahilazi tunda
haka ta zaɓa to kuwa ta tafi kenan sai ka tafa mata resit ka bita dashi kaga sai tayi zama mai lasisi kai
kuma ka samu sarari ka auro mutuniyar kirki da suka gaji arziƙi ka saka ina dama duk ita ta kanainaye
komai da anyi magana kace Halima to yanzu ta tafi Kuma in dai da yarda ne kar ta sake dawowa cikin
gidanka ya isa kuma haka a canza sheƙa".
Shiru yayi kansa a ƙasa, ya za'ayi Hajja tace ya saki Halima? Sannan kuma tayaya zai gaya mata shi fa ko
aure zaiyi ba Jalila zai aura ba ko dan bata san ainihin alaƙar dake tsakaninsa a Jalila bane?
"Ta dawo ina? Ai wlh kaji ma na rantse ta tafi kenan. Ba dai dama ni na dage sai ka aureta ba na ɗauka
dangin arziƙi ne ashe duk shigo shigo ba zurfi suka mana, tunda kuwa yanzu ta saka ƙafarta ta tafi to
kuwa ba zata dawo ba kama cireta maza daga ranka ka tattara hankalinka kan wannan yarinya Jalila ayi
maza ayi komai ita kuma can su ƙarata Allah sauki tsiya lafiya".
Da wata sabuwar damuwar ya fito daga gidan Hajja, can gefen hanya ya gangare ya kashe mota ya kife
kansa jikin sitiyari ya tafi tunanin haɗuwar sa da Jalila.
*Wattpad @MaryamahMrsAm*
*Kuɗin karatu yana wakiltar mutum ɗaya ne, kiji tsoron Allah karki ɗauki hakkina ta hanyar fitar mun da
littafi*
*KURA A RUMBU littafin kuɗi ne, a biya naira 800, biya a asusun*
*1840175439*
*Access bank*
*PAGE 36*
Ƙaddara da kwaɗayi haɗi da son zuciya irin nasa ya janyo masa faɗawa tarkon nadama. Dukda dai
tsohon halin sa ne, a baya lokacin samartaka ya kan kwatanta domin rage zafi kamar yanda hakan yake
ɗabi'ar dayawan Samari a wannan zamanin. Sun ɗauki hakan a matsayin wayo ko dabara a ganin su ai
basu aikata Zina a zahiri ba sai dai suna mantawa da hanin ubangiji da yace kada a kusanci Zina ba wai
kada a aikatata ba Aa kwata kwata kada a kusanci duk wani abu da yake da jiɓi da ita. Da yawan su sun
ɗauki hakan a matsayin ƙaramin zunubi domin wasu basu ma yarda cewa dasu da wanda ya keta haddin
macen da ba halalinsa basu da banbancin zunubi. Su kan manta ita kanta Zina ta kasu kashi da yawa, a
ciki akwai Zinar idanu da kuma ta baki da kunnuwa wadda suke aikatawa domin kuwa suna kallon
haram, su saurari haram su kuma furta haram da bakunan su wanda illolin hakan dai dai suke da wanda
yayi fasiƙanci da mace a zahiri.
Ko farkon haɗuwar sa da Halima ya so ya gabatar mata da irin wannan soyayyar sai dai bata bashi fuskar
hakan ba shima kuma bai takura mata ba daga baya ma kuma ya tuba ya bari har zuwa lokacin da sukayi
aure kafin lokaci ɗaya Jalila ta faɗo rayuwarsa ta wargaza komai ta sake jansa ruwa har ta kaishi da
aikata abubawan da suka zarce waɗanda yake aikatawa a baya.
Silar Hafiz ya haɗu da Jalila, ita ɗin tsohuwar budurwar Hafiz ce tare sukayi karatu a London dan har an
saka musu ranar aure ya rage saura watanni aka fasa sakamakon ganinta da mahaifinsa yayi tareda wani
abokinsa a France sunje wani taron kasuwanci ita kuma tayiwa Abokin nasa rakiya wanda ya kasance
Sugar Dadynta.
Hafiz bai taɓa sanin baɗinin Jalila ba, dukda ya san macece me rawar kai dan shi yake tsawatar mata
abubuwa da yawa saboda son da take masa kuma take ragewa kuma da yake shi ɗin bai zo mata da
fuskar da zasuyi irin rayuwar da takeyi a bayan idonsa ba sai ta ɓoye masa zahirinta, ko da wasa bai taɓa
sanin irin rashin jin da takeyi ba sai bayan da mahaifin ya kirashi ya gaya masa babu maganar aure a
tsakaninsa da ita ya nemo wata matar yar gidan mutunchi tunda wuri. Koda Dady ya sanar masa sa
abinda idon sa ya gani ma da farko har ransa bai yarda ba dukda ya san babu wani dalili da zai saka Dady
ya masa ƙarya ko ya hanshi aurenta. Sai sa ya ringa bibiyar takunta a hankali komai ya fito ya gane
zahirin wacece ita ya mata kaca kaca suka raba hanya a lokacin har kusan rataye kanta tayi saboda yanda
take masifar Son sa, tayi rantsuwa da yi masa alƙawarin zata daina duk wani abu da takeyi in har zai
aureta amma yace la la, in taga dama ta tuba saboda Allah amma ba dan shi ba domin ba zai taɓa
aurenta ba bayan yasan wacece ita.
Haka nan tayi naci, Tun tana bibiyarsa harta haƙura ta ƙyale shi tana ji tana gani ya fara soyayya da
Yasmin har suka yi aure daga ƙarshe ma ya bar Abuja ya dawo aiki a Kano. A hankali bayan wani lokaci
da naci da bin binin da take masa ya fara sauraronta suna gaisawa a matsayin abokai kamar yanda suka
faro tun asali kafin soyayya ta shiga tsakanin su, har ranta tana fatan a hankali ta shawo ya amince ko a
ta biyun ne ya aure ta bata damu ba dan tana tsananin son Hafiz sai dai shi clearly ya gaya mata kada ta
yaudari kanta domin ba zai taɓa aurenta ba. Ko da ya ke sauraronta a yanzu ma saboda yaga alamun ta
kintsune saboda ya rage mata raɗaɗin takunkumin da iyayenta suka saka mata tun bayanfallasar asirinta
da fasa aurensu yake yake sauraronta yana Kuma ƙara yi mata nasiha da nusar da ita gaskiya.
Jalila bata rasa komai ba domin mahaifinta hamshaƙin mai kuɗi ne haka mahaifiyar ta data kasance
Balarabiya itama mai kuɗin kanta ce. Babu abinda suka rageta dashi a rayuwa kusan ma gatan da ya
mata yawa yana da nasaba da silar lalacewarta. Tun tana secondary school take riƙe manyan kuɗaɗen da
suka shallake shekarunta tafiyarta Turai karatu kuma ya sake bata yanci a nan ta haɗu da ƙawayen da
suka buɗe mata ido da maza, da kuɗin ta take amfani ta mallaki duk saurayin da yayi mata idan ta gama
yayinsa ta sallame shi ta ɗakko wani kusan Abokin Dadyn Hafiz shi kaɗai ne saurayin da ta taɓa yi babba
kuma mai kuɗin kansa wanda shima wayewar sa da yanda ya iya soyayya irin wacce take so ta jata harta
biye masa suke fita ƙasashe tare har hakan ya zamo silar tonuwar asirinta.
Yanda suka haɗu da Bilal kuwa lokuta da dama musamman idan zata tafi Umarah yawanci ta Kano take
tashi dan haka a duk sanda ta shigo Kanon Hafiz take nema idan tana buƙatar wani abu, a irin haka wani
lokaci ta dawo daga Saudiyya lokacin Matar Hafiz ɗin ta haihu suna tare da Bilal ta kirashi akan yazo
Airport zai karɓi saƙo wa Baby a lokacin har yace ba zaije ba sai dai kuma ya canza shawara da yayi
tunani ko babu komai bai kamata ya wulaƙanta ta ba tunda ya san bashi ya ɗora mata sonsa ba daga
Allah ne duk kuma irin cin kashi da tijarar daya mata a baya bata saka ta fita a sabgarsa ba shiya kawai
yake jurewa yana biye mata lokutan.
Tare sukaje da Bilal ɗin suka amso saƙon wannan kuma shine haɗuwar su ta farko dukda gaisawa kawai
sukayi sama sama suka wuce. Ba'a fi wata ɗaya ba bayan nan ta sake zuwa Kano bikin wata ƙawar ta nan
ma ta kira Hafiz akan yayi mata booking hotel bayan ta sauka kuma ta sake kiransa akan ta fasa can
gidan bikin zata sauka dan Allah ya zo ya kaita yace ba zaije ba, data ringa masa magiya kawai yace mata
toh ya kashe wayar. Bilal da duk yaji yanda sukayi ya shiga bashi baki akan bai kamata ya ringa
wulaƙanta ta haka ba duk wanda ya ga yanda take kallonsa yasan tana son sa dan haka ko baya jinta a
ransa ya ringa nuna kulawa tunda dai abu ne na lokaci ba wai kullum ne take zuwa inda yake ba, daga
ƙarshe da Hafiz ɗin yace shi fa ba zaije ba shine yace shi ya bashi mota yaje ya kaita toh, haka kuwa akayi
ya bashi mota da number yaje ya ɗauke ta. Kwana ukun da tayi a Kanon shi ya ringa jigila da ita yawon
biki har suka gama ta tafi har sannan kuma babu wata shaƙuwa a tsakanin su kwatsam bayan nan suka
sake haɗuwa a Abuja lokacin da yaje wani workshop.
A reception ɗin hotel ɗin da aka sauke su ya ganta, sai da yayi mata dogon bayani ma kafin ta gane shi
sai kuma suka shiga hira har tayi masa godiyar hidimar da yayi da ita a Kano da zata wuce ta karɓi
number sa shikenan da dare kawai ta kirashi tace ko zasu fita yaga gari kar yayi ta zama a hotel tunda
yace mata bai san ko ina ba sai gidan su Hafiz da gidan Babban Yayansu shi kuma a lokacin ma suna Kano
sunje hutu. Ranar ta fita dashi suka sha yawo tayo masa shopping kayan sakawa har da waya Iphone dan
lokacin keypad ce a hannunsa bayan an ƙwace masa waya da babur. Sai da ta jera kwana uku tana fita
dashi kullum kuma haka zata yo masa siyayya kamar bata san ciwon kuɗi ba a kwana na ukun kuma ya
gama abinda ya kaishi amma tace masa ya zauna ya sake hutawa mana tunda dai ba wani abu zaiyi idan
ya dawo Kanon ba kuma yace matarsa ma tana gida taje wanka.
A lokacin ta fito fili ta faɗa masa ita fa tunda bata samu Hafiz ba zatayi madadi dashi domin duk abinda
take so a gurin Hafiz yana dashi har ma yafi Hafiz iya kalaman soyayya, da aure tazo masa dan da ace ya
amince tun a lokacin da ƙila kafin Halima ta dawo daga wanka zai auri Jalila amma sai yaƙi ya kawo mata
uzurin bai jima dayin aure ba yasan ba lallai mahaifiyar sa ta yarda ba da sauran uzuri dai amma ta bashi
wata shida zuwa shekara ɗaya zuwa lokacin ya sun shekara uku da aure ya san babu wanda zaiyi wani
surutu dan yace zai ƙara wata matar. Ta yarda da hakan, musamman da itama ya yarda da nata Sharaɗin
na yi mata duk abinda take so duk ya ce ba zai taɓa kusantarta ba har sai an ɗaura musu aure amma
kuma duk ɗaya domin shigarta ne kawai bayayi bayaga wannan babu kalar abinda baya mata, haka suka
dilmiya cikin ƙazamar rayuwar da suka zaɓawa kansu, ta sakar masa bakin aljihu tana jiƙa shi da kuɗaɗe
wanda koda wani lokacin yaji rashin dacewar abinda sukeyi ya fara janye mata tunda ta fahimci shi ɗin
masoyin kuɗi ne alert ɗaya zata masa ta girgizashi ba ma sai tace ya taho ba zai kama hanyar Abuja yaje
gurinta ko kuma ita tazo Kano dan har gida ta siya da sunan sa akan idan sunyi aure zata zauna a ciki dan
haka idan tazo can take sauka baki alaikum ba sai sunje hotel ba.
Haka suka cigaba da tafiya a sirrance dan daga shi har itan babu wanda yake so Hafiz yasan abinda yake
tsakaninsu musamman Bilal dan hatta yan uwansa da duk sanda tazo Kano sai tayi nacin ya kaita su gaisa
amma saidai yayi ta bata uzurin yau gobe a haka har ta gama kwanakinta ta wuce. Shammatar sa tayi ta
kai kanta gurin Hajja ta kuwa yi mata shatara ta arziƙi ta gabatar mata da kanta a matsayin budurwarsa
shikenan Hajjan ta gigice ta ringa faɗin ga arziƙin gaske ya tarar dasu har gida amma da yaje ya kwaso
musu yar masu kuɗin cizo dan abinda Jalilan ta kai mata a zuwa ɗaya ya fi duk hidimar da Halima ta mata
tun daga neman aurenta har zuwa yanzu.
Shikenan ta samu nayi kullum zancen ta yaushe zai tura ayi maganar aurensu ai yanzu ne zai yi mata
yarinyar jinin larabawa wanke hannu ka taɓa ga tarin arziƙi kuma hannunta a buɗe dan ba'a rufa wata ba
tareda tayowa Hajjan aike ba ta hannun sa wani sa'in kuma ta tasha zata turo musamman idan kayan
amfani ne haka kwana bibbiyu zata kirata a waya su gaisa kati kuwa da data duk zalamar Fadila sai dai ta
gaji ta ajewa Hajja wayar ta dan basa taɓa yankewa ita Jalilan ce ma ta saka aka buɗewa Hajja Whatsapp
a sabuwar wayar data siya mata wai ai batayi tsufan da za'a ce ba zata riƙe babbar waya ba.
Haka nan suke, yana jin daɗin mu'amalar sa da Jalila domin kuwa ta sake masa kuɗi yanda ya kamata ba
sai ya tambayeta ba yana zaune kawai zaiga alert kuma bata taɓa tura masa kuɗi kaɗan haka
kyaututtuka kusan tun da suka fara mu'amala zai ce bai sakw siyan sutura ko wani takalmi ko agogo ko
turare ba ita take siya masa kuma masu asalin tsada da kyau, bayan gidan da ta siya da sunan sa a yanzu
haka ya mallaki filaye biyu Manya da gona itama babba y siya babu daɗewa saboda yana so ya fara
noma.
Hatta wannan motar ita ta bashi kuɗi miliyan shida cis tace ya siyi mota, da farko cewa tayi ya zaɓi wacce
yake so zata siya masa sai kuma yayi tunanin rana tsaka a ganshi da mota zai zama abin surutu wannan
ya saka yace kawai ta bashi kuɗin ta kuma bashi sai ya raba biyu da niyyar ya siyi kamar ta 3m haka
amma da yayiwa Hafiz magana shine ya cika masa yace ya ɗauki wannan ɗin a gurin siyar da motocinsu.
A hakan ma ya sha surutu koma yace yana kan sha dan yanda yake dai da aikinsa kowa ya san an ɗan
lokacin nan bai kai ya tara kuɗin siyan mota haka ba amma duk wanda ya cewa ubangidan sa ne ya bashi
shikenan tunda da yawan abokanan sa sun san Hafiz ɗin sun kuma san yana da sararin da zai bashi fiye
da ita ma shiyasa yayi dabarar jona shi cikin zancen motar tun farko.
Matsalar daya fara fuskanta da Jalilan yanzu, a farkon tarayyarsu bata damu da Halima ba, ta gaya masa
ita ko mata uku yake dasu bata da matsala zata shiga a ta huɗu amma kuma da tafiya ta fara nisa sai
zance ya canza ta fara nuna masa ita fa ba zata iya haɗa shi da wata ba dan haka idan lokacin auren su
yazo sai dai fa ya zaɓa ko ita ko Halima wanda wannan abunda ta ɓullo dashi yana daga dalilin daya saka
neman nasu yin tsaho domin yace ba zai iya sakin Halima hakanan ba dan babu wani laifi da zai iya
danganta cewa tayi masa da zai saketa akan hakan amma ta bashi lokaci zai ɓullo da hanyoyin da ita da
kanta zata gaji ta nemi rabuwa dashi.
Sai dai fa a zuciyar sa kwata kwata ba son Jalila yakeyi ba kwaɗayin abun hannunta yakeyi. Dama a
wannan tsukin yake tunanin samo hanyar rabuwa da ita cikin sauƙi domin har ransa bashi da burin
aurenta, a lamarin aure yana buƙatar macen mai tarbiyya wacce zai faɗawa magana taji irin Halima ba
wacce zata zama ita ce mijin shi kuma matar ba balle kuma ita da ya rigada ya san halinta kuma sun
gama tambaɗewa ai babu zancen mutunchi ko zaman lafiya ma a tsakanin su idan su kayi aure.
Yana da burin ƙara aure nan kusa kuma ZULAIHA yake so ita ce zaɓin sa tun asali kuma ita zai aura kuma
ko a yanzun rabin abinda yake samu daga gurin Jalila ita yakeyi wahaltawa yake kuma yi mata tanadin
bayan auren su gashi yanzu garajen Halima na nema ya rusa masa lissafin daya shiryo.
Wayarsa dake ajiye gefe ta ɗauki ƙara abinda ya maido shi daga duniyar tunanin daya lula. Sunan
DUNIYATA dake yawo akan screen ya saka shi sauke ajiyar zuciya kafin ya ɗauki wayar ya amsa haɗi da
sakata a speaker. Daga can tayi sallama cikin muryarta me sanyi da sautin shagwaɓa, amsa sai taci gaba
da cewa
"Habibi lafiya kake kuwa yau kwana uku ina kiran wayarka sai dai tayi ta ƙara amma baka amsawa kuma
baka biyo baya ba?" Ta ƙarasa kamar zatayi kuka. Ya sauke ajiyar zuciya mai ƙarfi kafin ya ce
"Subhanallah, mai ya sameka?" Ta tambaya a ɗan rikice, sai ya sake yin ƙasa da murya kamar mara
lafiyar gaske yace
"Wayyo Allah ya baka lafiya Habibi ni dama na san sai dai ba lafiya ba shine kaɗai abinda zai saka ka kasa
amsa kirana, to yanzu ya jikin naka? Amma dai da sauƙi ko kasha magani?" Ya amsa mata da
"Eh da sauƙi kuma nasha kada ki tayarda hankalinki dama yanzu nake so idan nayi wanka na kiraki nasan
zaki damu kwana biyu baki jini ba".
"Wallahi ko na damu sosai tun waccen ranar da Umma tace mun kaje tareda Maman Al'amin na kira
kace kana driving zaka kirani shikenan fa da na sake kira da daddare ka amsa bakayi magana ba har naji
tsoro ko zuwan da kukayi da ita ya haifar da wata matsala ne yasa kake avoiding ɗina" tayi maganar
kamar zatayi kuka, sai ya saki murmushi yace
"Wace matsala zuwan Halima zai haifar? Kin san dai yanda nake sonki ko duniya zata taru babu wanda
ya isa ya shiga tsakanina dake ko?"
"Haka ne, toh yanzu yaushe zaka zo?" Ya ɗan yi jimm kafin yace
"Ina da uzuri yau da yamma zan tafi Abuja idan na samu jirgi amma kwana biyu zanyi zuwa asabar da
yamma ko lahadi da safe za dawo sai nazo". Shiru tayi bata ce komai ba, cikin kulawa yace
"Toh ai kana da uzuri kaga kuma ba zaka bari saboda ni ba" ta faɗa cikin rawar murya, sai yayi saurin
miƙewa zaune daga kishingiɗen da yayi dan alamun kukan da yaji a muryarta lokaci ɗaya ya tayar masa
da hankali yace
"Ki faɗa mun menene naji kamar zakiyi kuka ko kuɗi kike buƙata? Kayan abincin da aka kawo sun ƙare
ne?"
Maimakon ta bashi amsa sai kawai ta fashe da kuka daga nan kuma ta kashe wayar gaba ɗaya. Ji yayi
duniyar gaba ɗaya ta masa duhu hankalinsa ya tashi ba shiri ya tada mota ya cillata titi ya nufu gidan su
Zulaihan dan jin ba'asin kukan da takeyi. Daya isa bai ko jira an masa iso ba bayan da yayi sallama ya faɗa
gidan, suna zaune a ɗan ƙaramin falon su ita da ƙanwarta Jidda sai Ummansu jigum jigum ya samu guri
shima ya zauna.
"Magana daka sani ce dai Bilalu ba wata ba, babu jimawa Yayan mahaifinsu ya fita daga gidan nan sai
kaga irin cin mutunchi da tozarcin da yayi mata ya kuma yi rantsuwa akan ranar sadakar Arba'in ɗin
Malam kowaccen su ta kawo miji a ɗaura mata aure idan kuma ba haka shi zai zaɓa musu wanda yaga
dama ya ɗaura auren a ranar" Ummansu ta faɗa bayan da suka gaisa tayi maganar tana share hawaye da
Hijabin jikinta.
Yayi shiru a ransa yana ayyana "wata sabuwa kenan". Duk sai ya rasa mai zai ce musu, ranar Arba'in ɗin
Babansu nan da kwana Ashirin fa kenan ake nufi yanzu ta ina zai fara gyaro ɓarakarsu da Halima, Ya
yakice Jalila, sannan a auri Zulaihan duka a kwana Ashirin?
"Ai na san abu ne da kamar wuya amma shi kawun nasu ka sani mutum ne mai wuyar sha'ani babu
yanda banyi akan na fahimtar dashi ba amma daga ƙarshe sai cin mutunchi ne ya biyo baya kuma na
sanshi da magana ɗaya tunda yayi rantsuwa babu abinda zai saka ya karya ina ganin tunda abun ya
kasance da haka sai dai ayi haƙuri kawai a karɓi ƙaddara a yanda tazo, kai ka haƙura ita kuma ta karɓi
duk wanda Allah yasa ya zaɓa mata tunda ita Jiddah yaron da yake aurenta dama a shirye yake tana
kiran sa ta gaya masa yace babu komai gobe iyayen sa zasuje ayi magana to ai kaga ba kamar kai ba da
kake da uzuri kuyi haƙuri kawai".
Tashi Zulaihan tayi cikin kuka ta fice daga falon, Bilal ya bita da kallo yana haɗiye yawu daƙyar kafin ya
mayar da kallonsa kan Umman tasu. Ya ma za'ayi ace ya haƙura da Zulaiha? Yarinyar da ya raini soyayyar
ta a zuciyarsa tun bata kai munzalin data mallaki wani abu da zai kalla ya burgeshi har ya so ta saboda shi
ba?
A sanyaye yace
"Aa in sha Allahu Zulaiha rabona ce Umma, kawai dai nayi zaton zaiyi haƙuri tunda wata huɗu ya rage ta
kammala karatunta sannan sai a taso da maganar aure amma tunda hakan ta kasance babu abinda zai
gagara in Allah ya yarda zanje nima na samu nawa iyayen". Albarka ta ringa saka masa har ya tashi ya
fita, a soro ya tarar da Zulaihan tana kuka nan ya tsaya ya ringa rarrashinta da faɗa mata kalamai masu
daɗi bai bar gidan ba har saida fushinta ya yaye tayi dariya sannan suka fita tare ya siyo mata Ice cream
da Shawarma ya mayar da ita gida nan ma ya daɗe suna hira kafin ya mata sallama ya wuce yana jin kaso
tamanin na damuwar daya wayi gari da ita ya yaye.
Shekararsu kusan goma sha biyu tareda Zulaiha tun tana JSS1 lokacin da yayi TP a makarantar su a
lokacin Allah ya haɗa jininsa da yarinyar saboda ƙoƙarinta har kuma bayan daya gama gama saboda ita
yaci gaba da zuwa duk sanda ya samu lokaci kafin daga baya zumunchin su yayi nisa ya zama har gidansu
yake zuwa a hankali ya zama kamar wani babban yayansu kasancewar su uku iyayensu suka haifa duka
mata yayarta ɗaya sai ƙanwarta ɗaya. A sannu sannu shaƙuwar su ta fara rikiɗa zuwa soyayya duk kuwa
da cewa Zulaihan bata da wata suffa ko dalili da zai saka ya sota kasancewar kowa ya sani shi mutum ne
wanda tsarinsa na auren mace yar gayu ne kuma wayayyiya wadda ta fito daga babban gida ita kuma
Zulaiha cikin suffofi ukun babu wadda ta mallaka.
Babanta Talaka ne liƙis wanda bai aje cin yau ba balle na gobe haka nan bata da wani kyau na azo a gani
domin bata ko kai Halima ba balle ta kama ƙafar Jalila, tana dai da dirin jiki shima ba can ba, sanyinta da
baiwar murya mai cike da shagwaɓa da Allah ya bata shine kaɗai abinda za'a iya cewa zai ja hankalin
namiji gareta sai dai shi duk ba dan haka yake sonta ba gamon jininsu daga Allah ne.
Shi yayi ɗawainiyar karatunta tun daga junior secondary ya mayar da ita private daga ta gwamnati data
fara har zuwa yanzu kuma da take ajin ƙarshe a Jami'a shi yake cigaba da ɗaukar nauyinta harda
ƙanwarta Jidda, wata uku kenan daya siya musu wannan gidan da suke ciki watansu biyu da tareqa kuma
a ciki mahaifinsu ya rasu.
Rashin samun haɗin kan Hajja ne ya hana shi ya auri Zulaihan tun bayan data kammala secondary domin
Hajjan tace babu yanda za'ayi ya auro mata yar Allah baku mu samu, da wanne zaiji? Nauyinta dana yan
uwansa ko kuwa na matarsa da danginta tunda kaf ahalinsu a binciken da aka mata an gaya mata babu
mai samun cikakken ci uku a rana, ko hidimar da yakeyiwa su Zulaihan a lokacin a ɓoye yakeyi domin ya
san muddin ta sani toh fa ba zata bari ba shiyasa ko da ta hana shi aurenta a lokacin bai matsa ba domin
shi da kansa yana so ya aureta a sanda yake da damar bata kalar rayuwar da yake mafarkin sama mata
saboda yanda yake tausayinta a ransa.
Yana son Halima har ransa saboda ita ɗin tsarinsa ce sannan kuma tana masa son da ya yarda da wahala
ya samu qata mace da zata kwatanta masa irin sa sai dai kuma soyayyarta a zuciyar sa bata ko kama
ƙafar yanda yake jin Zulaiha a ransa ba. Kusan kwatankwacin irin son da take masa ne shi kuma yakeyiwa
Zulaiha har ga Allah kuma da ace ya samu irin damar da yake fata kafin ya aureta da Zulaihan zai aura ba
ita ba. Sai dai a yanzu da al'amura suka kasance ba yanda ya so faruwarsu ba Allah ya ƙaddara ita
Haliman ce matar sa ta farko ga kuma rabon da yake a tsakaninsu ya san ba zai samu matsala da ita ba
idan ya auri Zulaihan daga baya. Toh amma yanzu komai ya lalace ya tashi daga yanda yayi hasashen
faruwar sa kansa kuma ya kulle ya rasa ta ina zai fara gyarowa.
*Wattpad @MaryamahMrsAm*
*Ban yarda wani ko wata ya juya mun labari ta kowacce siga ba tare da izini na ba*
*Kuɗin karatu yana wakiltar mutum ɗaya ne, kiji tsoron Allah karki ɗauki hakkina ta hanyar fitar mun da
littafi*
*KURA A RUMBU littafin kuɗi ne, a biya naira 800, biya a asusun*
*1840175439*
*Access bank*
*PAGE 37*
HALIMA
Sati na biyu a Asibiti kafin aka sallameni zuwa lokacin kuma Alhamdulillah na samu sauƙi sosai ko in ce
nayi matuƙar ƙoƙarin gurin yakice damuwar dake raina ko dan in samu na bar gadon Asibitin domin a
zahiri basu da maganin matsalata kamar yanda kullum Dr yake nanata mun ni zan yiwa kaina maganin
matsalata in cire koma menene na saka a raina yake neman halakani. Zama yayi ya mun karatun Yaya da
ƙanwa kamar yanda ya ce,
"Ki dubi yanda hankalin iyayenki da yan uwanki duk ya tashi saboda ke, ki kalli yayanki da har yanzu basu
san ina suka dosa a rayuwarsu ba idan kika bari damuwar wani can ta kasheki su kika yiwa asara domin
tun kina raye dai kinga alamar cewa dake da babu a gurinda duk ɗaya tunda tun bayan da aka kawoki
banga wani da aka nuna mun a matsayin shine mijin ki kuma nasan kina da aure dan haka kiwa kanki
karatu Halima ki san mai ya kamace ki idan ma zaki mutu ki mutu akan abinda kike da daraja a gareshi".
Daga lokacin na fara ƙarfafar kaina domin dagaske na yarda idan na mutu iyayena da yayana suke kan
gaba gurin asara yanda kuma suke zagaye dani kullum cikin nuna kulawarsu idan na cigaba da ɗaura
musu damuwata na sani Allah zai iya kamani da haƙƙinsu. An sallameni da tarin gargaɗi akan abubuwan
da zan kiyaye, muka koma gida na sake buɗe sabon babin zaman ɗaki domin bana son kowacce hayaniya
yan dubiya da suke zirga zirga a gidan kuma takuramun sukeyi shiyasa na zaɓi da inyi zamana a ɗaki ko
na samu damar yin tunanin da likita yace in daina amma ba zan iya ba ya zama tamkar mahaɗin
rayuwata ne tunda ba zan iya buɗe baki in faɗawa kowa damuwata ba sai dai nayi ta tattaunata tsakanin
ƙwaƙwalwata da Zuciyata.
Ranar da nayi kwana uku da fitowa daga Asibiti har lokacin tsakanina da Mama tsantsar kulawa ce
tamkar zata mayar dani ciki ta sake haifoni haka take ji dani, duk sanda na kalleta tana mun hidima na
tuna furucin Bilal sai naji wani abu tamkar dutse ya danne mun ƙirji. Kamar kullum bayan ta taimakamun
nayi wanka na shirya ta fita ta dawo da try data ɗora mun breakfast, haka ta zauna tana tausata har
saida naci da yawa kafin ta ɗauke ta sake dawowa da ruwa ta fito da magunguna na ta bani na sha
sannan ta ɗakko mun wayata da jona mun a caji ta ajiye a kusada ni tana cewa
"Ga wayarki nan tayi caji sai ki kunna dan ƙila ana ta nemanki ba'a samu". Kaina yana ƙasa bance komai
ba naja wayar na turata ƙasan filo, damuwa zan ƙarawa kaina idan na kunnata dan haka gara tayi ta
zama a kashe kawai.
Ganin ta gyara zama tana kallona yasa naji zuciyata ta shiga bugawa da sauri dan na san da wahala idan
ba zancen Bilal zata mun ba. A tsayin sati biyun da nayi a kwance ko bisa kuskure banji wani ya ambaci
sunansa ba, na san kuma bai zo ba babu kuma wani nasa da yazo na san kuma dama babu yanda za'ayi
su cigaba da yi mun shiru dole akwai lokacin da zasu tambayeni dalilin zuwana gida da kuma dalilin ciwo
na amma bana zaton ina da amsar da zan bayar a nan kusa ko a gaba.
"Ta yaya zan faɗa musu alaƙar banza na kama Bilal yanayi da wata mace a waje? Da wanne ido zasu
cigaba da kallonsa? Ba shi ba ina zaton har yayana sai martabar su ta taɓu idan wannan maganar ta fita
shiyasa nayiwa kaina alƙawarin shanye baƙin ciki na ni kaɗai ba zan taɓa faɗawa kowa komai ba tunda
dama damuwata tace bai kamata kuma naci gaba da raba baƙin ciki na dasu ba.
"Halima magana nake so muyi" ta faɗa hakan kuma ya saka bugun zuciyata ƙara gudu, na kalleta kafin na
sakw sadda kaina ƙasa ina ji tayi murmushi mai sauti kafin ta kamo hannuna cikin nata tace
Jimm nayi amsoshi da yawa suna yawo a raina amma na rasa wacce ta dace da in bata, yanda take
kallona kuma nasan koma me zan faɗa da yake akasin gaskiya zata amma kuma dole inyi mata ƙarya
domin wannan gaskiyar ba mai faɗuwa bace. Cikin in ina nace
"Babu komai kika ce?, babu komai ya kawo ki gida ƙarfe bakwai na safe kuma tunda ya tafi bai sake
waiwayarki ba?" Ta faɗa tana tsareni da ido. Na ɗauke kaina gefe nace
"Tafiya zaiyi ai shiyasa ya kawo mu gida". Shiru tayi dan har saida na sace kallonta naga itama ni take
kallo da alama ta rasa abun faɗa ne shiyasa tayi shiru tana kallona, can taja numfashi tace
"Ba wasa nakeyi ba Halima ki faɗa mun wace damuwa gareki a aurenki da har take barazana ga
rayuwarki?"
"Na faɗa miki babu komai Mama idan da akwai ai kin san ba zan ɓoye miki ba zan gaya miki ko?" Shirun
ta sakeyi kafin ta miƙe a sanyaye tana cewa
"Shikenan" daga haka ta fice daga ɗakin na bita da kallo jiki a sanyaye ina jin kamar na tashi na bita na
faɗa mata amma kuma bazan iya ba. Cusa kaina nayi cikin pillow na fashe da kuka.
Tun daga ranar kuma Mama ta janye mun duk wata hidima da take mun da kanta ta saki sai Zainab ce
takeyi ko kuma inyiwa kaina hakan kuma ba ƙaramin ƙara mun damuwa yayi akan wacce nake ciki ba
duk gidan sai ya mun ba daɗi, Abba ya koma Lagos, Amirah ta koma makaranta Al'amin dama tun da aka
kwantar dani Anty Labiba ta tafi dashi gidanta har ta sakashi makarantar su Inaayah ya fara zuwa Sharifa
ma kuma Mama Fauziyya ta ɗauke ta da muka dawo saboda na huta karta ringa damuna da rigima dan
haka dagani sai Mama da Zainab sai kuma su Suraj a bakin Gate duk sai gidan ya mun faɗi babu daɗi
tarairayar da nake samu an janye mun tallafi kusan magana ma sai ta zama dole sannan take mun.
Ranar dana cika sati ɗaya da dawowa daga Asibiti wanda ya kama sati uku kenan da barowata gidan Bilal
ina zaune a falo na zubawa Tv ido, gajiya nayi da zaman ɗaki na fito ina zama kuma Mama ta tashi ta fita
can tsakar gida ta fara aikin da bansan na menene ba, ni dai na fahimci kawai zama tareda ni ɗin ne bata
so, har nayi kamar na bita sai kuma na fasa na zauna, dama tunda Anty Labiba tazo jiya naga tana wani
hararata na san sai ta sake zugata ilai kuwa gashinan.
Ina nan zaune a zahiri Tv nake kallo amma a baɗini nayi zurfi cikin tunani. Ni da kaina na san na zama
wata iri, nayi rama mara fasali duk da yanda Mama take matsamun kan cin abinci amma tamkar yana bin
rariya yana tsiyayewa ne dan babu abinda yake nunawa a jikina azabar tunani da ƙuncin daya cunkushe
mun zuciya su suka hana sassan jikina karɓar abincin su sarrafa shi yanda ya kamata.
Daga waje na ringa jiyo kamar muryar Hansa'u suna gaisawa da Mama, ba zan iya tuna rabon da nayi
magana da ita ba dan an ɗauki lokaci mai yawan gaske tun kafin na haifi Sharifa wani zuwa da tayi taje
gidana ta tarar da abincin da Bilal ya auna mun zan dafa tayi mun magana akan kada na kuskura na fara
rayuwar da a gaba zanzo ina kuka da kaina har tayi iƙirarin zata gayawa Mama halin da nake ciki a
sannan haka na rufe ido na gaya mata maganganu son raina kuma nace ta fita a duk wata sabgatar gidan
aurena ko da take ɗaga kafaɗa tana iyayi ai sai dai idan ba zata faɗi gaskiya ba amma itama tana da nata
matsalar ƙila ma halin da take ciki yafi nawa dan haka kowa yaji da kansa idan gulma zata ringa kawota
ni na yafe kada ta sake zuwa in da nake.
Haka muka rabu dutse a hannun riga ta kuma ɗaukar mun alƙawarin ba zan sake ganin ƙafarta a gida na
ba dama kuma duk cikin ƙawayen mu ita kaɗai ce take har sannan dan su Baby su Zainab mun daɗe da
yin uwaka ubanka tun bayan haihuwar Al'amin da suka sameni har gida zasu gaya mun maganar banza
akan wai labari ya baza gari komai daga gidanmu aka mun nan ma na musus tatas nace nagodewa Allah
inada gatan da za'a mun a gidan namu su dai da suke taƙama da miji randa bai musu ba sai in ga ina zasu
kama shikenan mukayi baran baran suka fita harkata.
Idona akan ƙofa harta shigo falon cikin kyakkyawar shigar Abaya data matuƙar karɓar ta. Ko dan na jima
ban ganta ba sai naga ta ƙara wani kyau da kwarjini ta sake zama bababar mace kana kallonta ba sai an
gaya maka nutsuwa da kwanciyar hankali sun bi jikinta ba. Da sauri ta ƙaraso in da nake tana kallona
kafin ta rungume ni lokaci ɗaya ta fashe da kuka wanda tamkar nima ina jira na fashe da kukan da na
daɗe ina so nayi amma damuwar Mama ta saka nake haɗiye shi. Rungume da juna muna kukan kamar
ƙananan yara muka shiga ɗaki na, kan gado muka zauna muka cigaba da kukan zuwa wani lokaci kafin ta
sassauta nata ta fara rarrashi na wanda daƙyar mukayi shiru a ƙarshe.
"Halima mai ya faru? Mai yayi zafi a duniyar nan kika mayar da kanki haka Halima kina kallon mudubi
kuwa?" Ta faɗa tana ɗauke sabbin hawayen da suka far zubo mata. Na kwantar da kaina a kafaɗar ta
nace
"Hansa'u ƙirji na zafi yake mun zuciyata ina jin tamkar zata fashe"
"Me kika aje a zuciyar? Ki amayar da koma menene Halima zaki samu sauƙi duk wani nauyi da kika ji zai
sauka" ta faɗa tana ɗagoni daga jikinta. Nayi shiru ina kallonta, tabbatas ina da buƙatar fitar da abinda
yake ci mun zuciya tun bai gama yi mun illar da ba zata gyaru ba, na buɗe baki da niyyar magana sautin
muryar Bilal ya shiga yawo a kunnena sanda yake cewa
"Kafin su zageni sai sun fara yi miki dariya sunce Allah ya ƙara Halima duk wanda kika faɗawa aibu na
laifinki zai gani ba ni ba" tuna hakan y aka na rufe bakina ba tareda na ce komai ba na zame daga riƙon
da ta mun na kwanta ina ajiyar numfashi. A hankali tace
"Bazan miki dole akan ki faɗa mun abinda yake damunki ba amma ki sani barin kashi a ciki baya taɓa
maganin yunwa Halima. Meye ribarki ki rayu cikin fushin iyaye Halima? Ace da ki faɗi damuwarki wacce
kulawa ce ma har ta saka aka damu da aji domin a nema miki mafita amma ke kin gwammace ki ƙara
jefa kanki cikin wani bala'in ta hanyar shiga fushin iyaye?
Ni dai ban sanki a haka ba ban kuma san mai ya canza ki ba shiyasa ko da nayi fushi dake nace zan fita a
sabgarki bana iyawa saboda nasan ke ɗin a yanzu ba Halimar dana sani a baya bace kuma kina da
buƙatar mu domin idonki ya buɗe ki gane gaskiya a yanda take ki fita daga iziyar zaton da kike ciki amma
kuma duk yanda muka so da mutaimakeki har idan baki so ba babu hali tunda ba zamu miki dole ba,
amma ina so ki sani rai ɗaya ne kuma a duniyar nan babu wani namiji daya cancanci sadaukarwar
rayuwa domin a yau kika mutu a gobe zai samu madadinki na sani kuma ko a yanzu kinga izina da ranki
baki mutu ba to kiyi hasashen makomar yayanki a bayan ba ranki sai ki yiwa kanki Hisabi kan abinda ya
kamata kiyi" ta ƙarasa tana miƙewa haɗi da ɗaukar jakarta.
Da sauri na ruƙota ina juya kai lokaci ɗaya hawaye ya ɓalle mun nace
"Anty Labiba fa?" Ta faɗa sai nayi saurin girgiza kai nace
"Gara kowa akanta". Murmushi tayi ta koma ta zauna ta dafa kafaɗata tace
"Ban sani ba ko har yanzu kina ɗaukata a irin matsayin da kike dashi a gurina". Nayi shiru ina kokawa da
muryar Bilal dake nanata mun kaina zan tozarta idan na tona asirinsa. Da hannu biyu na toshe kunne na
kafin na fizgo maganar da ƙarfi nace
"Matan banza yake bi Hansa'u" wannan maganar kuma tasa naji tamkar na buɗe wata ƙofa cikin zuciyata
dan haka tiryan tiryan na shiga koro mata bayani tun daga aurena da Bilal duk wani abu da na haɗiye
saida ya samu hanya ya fito da kansa na furtawa Hansa'u shi harda furucin da yayi akan Mama ban rage
ba saida na amayar mata. Haka muka rungume juna ni kuka ita kuka babu mai rarrashin wani, mun daɗe
a cikin yanayin kafin ta miƙe tana cewa
"Zanje na dawo Halima idan na zauna yanzu ina kallonki bazan samu ƙarfin guiwar ce miki komai ba
zanje gida amma komai dare zan dawo". Ban ɗago na kalleta ba na ɗaga mata kai alamar "Toh".
Bayan tafiyar ta ji na ringayi kamar an kwashe mun wani ɓangare na jikina, tsabar yanda nauyin da ƙirji
na yake mun ya ragu ina tsaka da kukan bacci ya kwashe ni dana farka kuma sai na ringa ji kamar bani
ba, babu wannan abun da nake ji yana mun yawo tsakanin ƙirji da maƙogaro, haka na ƙarasa yinin ranar,
har na fitar da rai da dawowar Hansa'u sai gata lokacin ƙarfe tara harta gota. Fuskarta duk ta tashi da
alama bayan tafiyarta kuka ta cigaba dayi, a ɗaki muka sake ƙulewa, ta faɗa mun maganganu da sukayi
tasiri sosai cikin ƙwaƙwalwata. Abu uku da na fi riƙewa cikin maganganunta tunatarwar da tayi mun akan
addu'a.
"Halima tun ba yau ba na sani kina da sakaci gurin addu'a. Ki sani Allah yana fushi da bawan da baya
roƙonsa. Ko da ace ubangiji ya hore maka komai a rayuwa ka kasance mai godiya a gareshi kuma ka
cigaba da yi masa naci da roƙon ya taya ka tattala abinda ya baka ba kuma shikenan idan buƙatarka ta
biya sai kuma sanda ka sake faɗawa cikin wata damuwar ne sannan zaka tuna da Allah ka sake roƙon sa
ba shiyasa sai ya barmu da iyawarmu muga idan zamu iya yiwa kanmu.
Abu na farko da zaki fara shine ki gyara tsakaninki da mahaliccinki, kinga addu'a Halima tasirinta yawa ne
dashi. Addu'a ta kan canza ƙaddara daga mummuna zuwa kyakkyawa, hatta da Bilal addu'a zata iya
canza miki shu. Ubangiji yana son bawa mai naci da ƙasƙantar da kai akan buƙatar sa. Wani kuka ko ajiye
abu a rai ba zai ƙareki da komai ba abinda yafi miki shine ki dage kiyita roƙon Allah karki gaji lokaci ya
wuce da zamu kwanta muyita bacci da cewar ai komai daga Allah ne haka ne amma kuma ba zaka taɓa
haɗa nasarar rayuwarka data wanda ya hana idonsa bacci ya roƙi ubangiji ba tamkar ka kwanta a ɗaki ne
kana tsammanin ayi ruwan sama abinci ya faɗo ka ɗauka kaci ba tareda ka fita kayi aikin da zai samar
maka da kuɗin da zaka siyi abincin ba.
Kada kuma ki ɗauka a sanda kika so a lokacin addu'ar ki zata karɓu ko kuma idan baki samu biyan
buƙatar ki ba a lokacin kice kin dena Aa, shi Allah ba haka yake ba. Ubangiji yafi mu sanin kawunanmu
yafi mu sanin abinda yafi zama alkhairi a rayuwarmu.
Wani lokacin mu kan nacewa abinda ba alkhairi bane a tattare damu shi kuma Allah sai ya barmu dashi
domin hakan ya zame mana izina idan kuma muka laƙanci kuskurenmu muka koma masa sai kiga ya
canza mana da abinda tun farko yake shine alkhairinmu amma muka guje masa.
Kina son Bilal kuma ni ba zance ki rabu dashi ba dukda ba zan miki ƙarya ba har raina zanyi fatan hakan
amma kuma bamu ke da rayuwarmu ba ba kuma mu isa mu kaucewa ƙaddara ba dan haka addu'ar dai
ita zakiyi ki kuma yi ƙoƙarin gyara tsakaninki da mahaifanki domin fushinsu ba ƙaramin masifa bane a
tattare dake shi kaɗai ya isa ya hana addu'ar ki yin tasiri ki nemi yardarsu sai kiga komai yazo miki cikin
sauƙi.
Abu ma ƙarshe da zan gaya miki shine koda Allah ya ƙaddara cigaban zaman ki da Bilal, dukda dai kin
rigada kin yi gini da tubalin toka amma lokaci bai ƙure ba da zaki iya rush ginin nan ki faro shi da sabon
foundation. Idan kin fahimci abinda bake nufi duk abinda zakiyi kiyi shi bisa gaskiya, aure ibadah ne ba
wai soyayya ba Halima sannan a cikin biyayyar auren kanta zaki iya kai kanki wuta a maimakon Aljanna
dan haka dole ku saka Allah ku kuma ɗora aurenku bisa doron shari'a domin samun dacewa".
Haka ta tafi ta barni cikin tunani, Tabbas na yarda da sakaci na gurin addu'a, ina ƙoƙarin kiyaye sallolina
na farilla idan na idar kuma zanyi yan gajerun addu'oina shikenan bana ɗorawa da nafila. Tun ina gida
Mama tayi iya ƙoƙarin ta gurin ɗora mu a hanya a duk sanda zata tashi cikin dare zata zo ta tashe ni wani
lokacin nayi sallar ido cike da bacci wani lokacin data fita zan maida kai na kwanta, haka azumin litinin da
Alhamis haka nan tun ina kirawa kaina ulcer ƙarya dan kar inyi har ta gaske ta kamani, a hakan ina
lallaɓawa da kuma na koma hannun Bilal sai komai ya sake taɓarɓarewa domin dai shima baya ga sallah
biyar ta farilla ban ce yana wata nafila ba haka azumi nasha in ce masa mu tashi da azumi ranar Alhamis
ko Juma'a yaƙi wani lokacin ma ni zan ɗauka ƙarshe sai ya saka na karya shi. Kai ko sallah nayi na zauna
ina doguwar addu'a muddin yana kusa sai ya san yanda ya tayar dani har cewa yakeyi wai idan mace
tana doguwar addu'a da wuya ba ƙarar mijinta take kaiwa gurin Allah ba, da sakaci irin nawa da rashin
ƙarfafawa dana samu daga gareshi duk ya sake taɓarɓara komai nawa ya zama sai a hankali.
Lissafina, rayuwata gaba ɗaya Bilal nez ko addu'ar zanyi shine, bani da wani buri a koda yaushe sai yanda
zanyi na burge Bilal na samu soyayyar ta yanda bani da wata addu'a sai tasa ban kuma taɓa banbacewa
ba domin zuciyata ta rigada ta amince shi ɗin shine alkhairi gashi kuma ubangiji ya mallaka mun shi sai
dai kuma mallakar tasa bata zamemin komai ba face fitina domin duk wani abu mata kyau da zai sameni
yana da nasaba da Bilal, a tarayyata dashi baki ɗaya zan iya cewa Al'amin da Sharifa su kaɗai ne abun
ƙwarai da zan ɗaga nace na samu a silar Bilal bayaga haka sai tarin nadama da dana sani.
Kwana nayi ina saƙa da warwarar mataki na gaba, barin Bilal ko kuwa cigaba da zama dashi? Kamar
yanda tace zaɓi na ne duk kuma abinda na ɗauka babu mai ce mun saboda me domin ni nasan daɗi na
kuma san wahalar dake tattare da zama dashi amma kuma dole na tsaya nayi tunani mai kyau ko saboda
goben yayana.
BILAL
*Wattpad @MaryamahMrsAm*
*Ban yarda wani ko wata ya juya mun labari ta kowacce siga ba tare da izini na ba*
*Kuɗin karatu yana wakiltar mutum ɗaya ne, kiji tsoron Allah karki ɗauki hakkina ta hanyar fitar mun da
littafi*
*KURA A RUMBU littafin kuɗi ne, a biya naira 800, biya a asusun*
*1840175439*
*Access bank*
*PAGE 38*
Madallah da mutane masu karamci. Nagode ƙwarai dagaske, ina lafiya wani aiki ne ya ɗauke ni tsayin
kwanaki amma Alhamdulillah mun kammala na kuma gode ƙwarai da haƙurinku ina fatan har mu
kammala babu wani uzuri da zai sake gifta mana 🙏🏽🙏🏽🙏🏽
*KURA A RUMBU littafin kuɗi ne 800, yake mai jira nayi posting ki fitar kiji tsoron Allah dakw da wacce
take jira ki turo ta karanta a bati ku guji haƙƙin komai ƙanƙantarsa. Duk wacce ta shirya sauke nauyi ta
tura mun kuɗi na a asususun 7061838488 Opay Maryam Farouk. Nagode*
BIlal
Tun barin sa gidansu Zulaiha komai ya sake jagule masa, tunanin sa ya tsaya kwata kwata ya kasa
tantance mai ya kamata yayi. Batun ace ya haƙura da Zulaiha ma bai taso ba domin kuwa hakan ba mai
yuwuwa bane ba amma bai taɓa zaton za'a masa titsiyen aurenta irin haka ba musamman a wannan
lokacin da yake cikin tsaka mai wuya tsakanin sa da Halima. Tabbas yana son Halima tana kuma da
matsayi na daban a zuciyarsa domin yasan halacci ya san kuma a zamanin yanzu samun mace da zata so
shi tsakani da Allah irinta ta kuma kyautata masa da jikinta da aljihunta abu ne mai matuƙar wahala.
Kawai shima bai san dalilin da ya saka ya kasa kwatanta mata kyautatawar da take masa ba, yanzun
kuma wannan abun daya gifta duk ya sake lalata komai tunda har kuma ta iya tafiya gida da kanta ya san
tabbas ta kai ƙarshe ne dan haka zai bata lokaci domin ya san fushin ta ba zai ɗore ba ƙila ko bai bi ta
bama idan ta sakko da kanta ita zata nemeshi kamar yanda suka saba fatansa kawai shine ta rufa masa
asiri kada ta furta wani abu da zai jawo zubewar mutunchin sa a idon yan gidansu musamman Abbanta.
Haka ya shirya ya tafi Abuja saboda Jalilah da take ta kiran sa har tana iƙirarin idan bai zo ba ita zata
taho. Satinsa biyu acan a tsayin kwanakin da yayi kuma har ita kanta saida ta fahimci baya cikin
nutsuwarsa.
Bai tsammaci zai damu da tafiyar Halima haka ba kuma ya kasa kiranta saboda zuciyar sa dake raya masa
idan ya kirata zai buɗe ƙofar da zata sake zuwar masa da wani rainin gara ya rabu da ita da kanta idan ta
huce yasan zata neme shi su daidaita sai dai kuma wani ɓangaren na zuciyarsa yana raya masa rashin
kyautuwar abinda yakeyi ɗin. Ya mata laifi kuma kamata yayi ya rarrasheta ya nuna mata ya karɓi
kuskurensa ba wai ya wofantar da ita haka nan ba.
A bakin Hajja yaji ashe ma bata da lafiya har ta kwanta a Asibiti ya kuma ji babu daɗi sosai dan a ranar
har sai da ya kira wayarta amma yaji ta a kashe kuma dai ko giyar hauka yasha ba zai fara kiran wani
daga cikin Ahalinta da sunan ya tambayi halin da take ciki ba dole ya haƙura ya bar damuwarsa a ransa
akan sai ya dawo tukunna yaje ya dubata yanzun yanda zai samu ya shawo kan Hajja data kunno masa
wuta akan zancen Jalila har ta samu Kawu Sani ta gaya masa ya sanarwa Yayyensu Bilal da suke Uba
ɗaya za'aje nema masa aure tuni har ta fara shelantawa dangi da maƙwafta da suke ta surutun an ce
baƙin cikin Bilal ne ya ɗorawa Halima ciwon zuciya ya kuma korata gida can iyayenta suyi jinyarta labari
na isketa ta ringa sababi tana tijara wai sun ɓatawa ɗanta suna saboda sun rufa mata basu faɗi abinda
tayi har ya koreta gidan ba shine su zata bibiye su da sharri?
Ba tsoron Allah ta ringa shirgawa mutane ƙarya akan wai aure zai ƙara shine ta nemi ta illata shi da nata
samu nasara ba shi ne ta ci shinkafar ɓera shine dalilin da ya saka ya mayar da ita gidansu karta mutu a
laƙa masa sharri.
Da ya nuna rashin jin daɗin maganar da suka ƙulla haka nan take kuwa ta rufe shi da faɗa tana cewa
"Ka fita daga ido na Bilal in kulle, ko ka shirya ko baka shirya ba ni na shirya aure zaka ƙara dan ma kaji
da jinka kuma zanje in samu Sani yau ɗin nan ba sai gobe ba su shirya su tambayo maka auren ayi kowa
ya huta. Banda ƙaddara dama ai Halima ba matarka bace iya zaman da akayi ya isa ka aika mata da
takardarta kawai in san kun rabu gaba ɗaya mu tattara hankalinmu akan wani abun kuma". Ko kafin ya
sake cewa wani abu ta katse wayar ta shiga mitar duk yanda akayi wani baƙin asirin aka yi masa ake so a
kautar da hankalinsa toh kuwa muddin tana raye Bilal ya gama zama da Halima domin aurenta bai musu
ranar da suka tsammata ba. Nan yayan ƙawayenta da suke auren yaran masu kuɗi tana kallon yanda ake
sauke musu kaɓakin arziƙi. Kayan azumi, turamen sallah masu tsada haka da babbar sallah a gwangwaje
su da tiƙa tiƙan raguna Hajji da Umarar nan duk an kaisu amma ita komai shiru saboda baƙin hali ita
kanta yar tasu ma mugunta suke mata suna jira sai dai miji ya mata toh ina dalili? Gara dai kowa ya kama
gabansa can ga irin wacce ta dace dashi ya samo wadda abun hannunta bai rufe mata ido ba kuma ba
yar gari ba balle a samu munafukainsu zugeta yanda aka zuge Halima tunda itan ma ai farko ba haka
take ba.
Da yammacin ranar ta kama hanyar gidan Kawu Sani ƙanin mahaifinsu Bilal ɗin, matarsa Suwaiba
mutuniyar Hajja ce dan tare suke yawon biye biyen Malamansu ko yanzun ita take mata yawace
yawacen saboda ciwon da taji a can kuma aka gaya mata ai Jalila ita ce matar arziƙin Bilal ba Halima ba
kamar yanda Malamin ya fara faɗa musu a farko ya kuma ce musu ba zai yuwu su zauna tare ba sai dai
ya saki Halima in dai yana so taurarinsa su haska dan ita take danne shi.
Sanda taje Malam Sani baya nan amma Suwaiba ta gaya mata ba nisa yayi ba dan haka suka ƙule a ɗaki
suka cigaba da tattaunawa, sai bayan Magriba ya dawo, dake Suwaiba ta rigada ta gama karanta masa
ƙarya da gaskiya akan abinda ya faru haka ya ringa faɗa har yana cewa sun haɗu da Alhaji Aminu a
masallaci ya masa kallon banza shi dama tun farko dan dai sun dage ne amma bai ga abinda suka hanga
a tattare da gidan Alhaji Aminun ba. Kan ta tafi ta jaddada masa ya san yanda zai sha kan yayyen Bilal ɗin
da suke uba ɗaya su tafi neman auren tare tunda gidan manyan mutane za'a je kuma yan boko ya
kamata shima su san ba banza bane yana da tsayayyu.
"In zai yuwu ma ni a ɗauro auren kawai ba sai an tsaya jeka ka dawo ba tunda naga yanzu ai haka akeyi
ko?" Ta faɗa tana zura takalmi daga nan sukayi sallama ta wuce tana sake jaddada masa kar a wuce satin
nan fa ba tareda an je neman auren ba.
Sati biyu yayi ya dawo da kuɗaɗe masu nauyi wanda Jalila ta bashi akan za'ayi gyaran gidan da zata
zauna. Sun gama magana akan nan da wata biyu za'ayi komai da komai na auren su saboda Dadynta
baya nan dan haka da zarar ya dawo za'ayi komai na auren su a wuce gurin. Ransa fes da samun kuɗin
domin kuwa zasu ishe shi yayi duk hidimar aurensa da Zulaiha dukda ba wani biki za'ayi ba ko da ba haka
ya so ba amma a yanda auren ya zo dole ya haƙura da duk wani buri da ya ciwa lokacin auren nasu.
Damuwar sa bata wuce ɗaya zuwa biyu ba, ta farko yanda zai shawo kan Hajja ta amince da al'amarinsa
da Zulaiha sai kuma Halima duk da ita ya san ba wata matsala bace sosai amma kuma har ransa yan jin
yanda zata karɓi auren da zaiyi itama. Ganin lokaci yana ƙurewa domin bai fi saura kwanaki biyar ya rage
cikar kwana arba'in da rasuwar mahaifin su Zulaihan ba kuma kamar yanda Kawun su ya sha alwashi
yace ranar zai aurar dasu dan haka ya yanke shawarar zuwa ya samu Baba Sani kawai kuma cikin ikon
Allah daya haɗo gabas da yamma ƙarya da gaskiya ya faɗa masa akan shi ba waccen yarinyar ta Abuja
yake so ba Hajja ce kawai take so ya aureta saboda yar masu kuɗi ce amma shi wannan ita yake so tun
ma kafin Halima Hajja ce taƙi, ya gama kawo masa bayanai wanda Kawun kuma gamsu dasu ya tabbatar
masa da ya kwantar da hankalinsa.
"Ni na rasa me yake damun Hajjaju, ita dai kuɗi kawai bata duban mutunchi. Yanzu idan da gidan
talakawan da suka san ƙima da mutunchi kayo aure ta ina haka nan yarinya zata kwashe kaya ta tafi
gidansu dan za'a mata kishiya kuma dake iyayenta ba dattijai bane a rasa wanda zai biyo sahu yaji dalili
aa suna jira mu mu bisu kenan muji me akayi mata da tayi fushi ta tafi ai wlh ka burgeni da ka rabu da ita
idan sun gaji da kansu zasu magantu ai tunda dai ba uban da zai so yarsa ta dawo gabansa da sunan
zawarci a wannan lokacin da muke ciki, rimi rimi lokacin auren nan kai kace mutanen kirki ne yanda
akayi harkar girma da arziƙi ashe abun bai kai zuci ba" cewar Baba Sani. Shi dai Bilal bai sake cewa komai
ba dukda he felt guilty yanda ya kawo sukar Halima domin wanke kansa kuma gashi Baba Sanin ya hau
yayi daram akai amma ya zaiyi?
Bai bar gidan ba sai da ya aje masa kuɗin aure da sadaki da zasu kai ya kuma yi masa ihisani mai tsoka ya
kuwa ringa saka masa albarka yana jaddada masa karya ji komai yaje yayi shirye shiryensa kawai Hajja
kuma ya barshi da ita ya san yanda zaiyi mata. Hankalin sa ya kwanta domin ya gama da wannan
ɓangaren, nan ya shiga gyaran gidan Jalilah domin dai ba zai haɗa Zulaiha da Halima gida ɗaya ba.
Hankali kwance ya shiga irgen kwanakin da suka rage gefe ɗaya kuma yana shirya yanda zai tunkari
Halima itama bayan ya gama da sabgar Zulaiha.
HALIMA
Ina kwance a ɗaki idanuwana rufe ina latsa digital counter dake hannuna laɓɓana suna motsawa a
hankali, tunda na zubar da komai na koma ga Allah na durfafi Istigfari, hailala, salatin annabi da wurudin
Hasbunallahu wani'imal wakeel na samu sauƙi sosai cikin al'amurana. Nauyin da nakeji a ƙirji na ya ragu
haka faɗuwar gaba da cushewar tunani haɗi da ɗimuwar da nake shiga duk sun barni.
Cikin abinda bai kai sati ba nutsuwa ta saukar mun sosai hatta da gangar jikina kuma ta nuna hakan
kuma ko jiya da muka koma Asibiti check up a gwajin da aka mun likita yace an samu cigaba sosai sai ɗan
abinda baza'a rasa ba kawai yayi saura. Dukda haka can ƙasan raina ina jin Bilal sai dai tasirin addu'ar da
nakeyi ya disashe duk wani abu da a baya nakeji a duk sanda na tuna shi, bana jin farin ciki haka bana jin
baƙin ciki, gaba ɗaya na zama neutral.
Dana fuskanci yawan shirun da nakeyi yake sakani tunani a dole na fara tilastawa kaina zama cikin
mutane dukda na rasa yanda zanyi da Mama akan fushin da ta ɗauka dani har magana nayi mata na roƙi
tayi haƙuri idan ma wani abu na mata daya ɓata mata rai take fushi dani amma tace babu komai a hakan
nake shisshige mata ina mata magana wani lokacin ta kulani muyi hira wani lokacin sai sai na haƙura na
tashi, Abba dai ba ruwansa daɗi sosai yakeji da canzawar da nayi dan haka idan yana gida muna tare dan
wani lokacin har sai na gaji ma da hira nace masa zanje na kwanta kafin zai rabu dani na kuma sha jin sa
yana yiwa Maman magana akan abinda yaga tana yi mun yanzu amma shima ɗin sai dai tace masa babu
komai.
Yau ɗin ma ni kaɗai ce a gidan Mama sun fita tareda Zainab da Sharifa dubo Inaayan Anty Labiba da bata
da lafiya. Har na shirya zan bisu kuma kawai na fasa dan na san gidan nata ba zai rasa yan dubiya dan
dangin Mijinta nasa raina abun taro ciwon kai wani yayi har idan sun samu labari haka zasu yo ƙungiya
suzo a wuni ana cecekuce.
Waya ta dake gefe ta ɗauki ƙara, sunan Suhaila da na gani yana yawo ya saka na janyota na amsa da
ƙaramar sallama. Daga can ɓangaren tace
"Ashe bacci kukeyi tun ɗazu ina ta buga ƙofa na ɗauka ma ko bakya nan". Na ɗan yi shiru kafin na
fahimci abinda take nufi can gidana taje dan haka nace mata
"Subhanallahi, dama Honey ya mun baki yace na kiraki kar nazo bakya nan gashi kuwa, idan ba nisa
kikayi ba sai in jira ki dan wuni nazo miki yau" ta sake faɗa a ƙoƙarin ta ƙyaleni ta tafi sai na ce
"Ai kuwa nayi nisa ina can gidanmu wlh" na ajiye wayar bayan da tace mun "toh shikenan".
Tunani na tafi bayan na ajiye wayar shin Mijinta bai faɗa mata bana gidan bane ko kuwa shima bai sani
ba? Amma dai da wahala yanda suke da Bilal ace bai sani ba dukda dai Aisha Matar Nasir ma ba'a fi
kwana uku ba ta kirani tana tambayar ina gida ne zata zo nace mata Aa, ƙila bai faɗawa abokanan sa ba
ko kuma ya faɗa musu matayen nasu ne basu faɗawa ba oho musu dai.
Jin an fara shirin shiga sallah da yake juma'a ce ya saka na miƙe na ɗauro alwala domin dai yanzu
Alhamdulillah na hau saiti ina matuƙar ƙoƙari gurin dai daita ibadah ta da kuma yinta akan kari, ina
raka'ar ƙarshe na jiyo sallamar Suraj daga falo, sai da na sallame kafin na fito har sannan kuma yana
tsaye ya ce mun wai nayi baƙuwa tana waje amma basu buɗe mata get ba dan basu santa ba gashi kuma
ni kaɗai ce a gidan sun ce ta kira ni a waya tana ta kira ban ɗaga ba. Wayar na ɗauko naga Suhaila ce ta
kira har sau huɗu nace ya buɗe mata ta shigo dukda nayi mamaki ban zaci zata ce zata biyo ni nan ba.
Sai da na kawo mata ruwa na koma na zubo mana abinci kafin na zauna muka sake gaisawa tana kallo na
tace
Nayi ɗan murmushi kawai ba tareda nace komai ba ita ɗin ma sakin maganar tayi ta kamo wata, bata bar
gidan ba sai bayan la'asar har sannan kuma su Mama basu tafi ba sai na ringajin kamar kar ta tafi dan
sosai kuma naji daɗin zuwanta dan Suhaila akwai hira, muna tsaye jikin motarta bayan dana rakata waje
ta kalleni tace
"Kinga zan manta Honey yace idan mun haɗu da Bilal in ce yana gaishe shi kuma Allah ya bashi haƙuri
idan laifi yayi masa haka da ya share shiz toh na bar miki sallahu tunda bamu haɗu ba" daga haka taja
motarta ina tsaye harta fice daga gidan kafin na koma ciki raina cike da tunanin sallahun data bar mun.
Yanda Bilal ya ɗaukaka Hafiz mai zai saka ace har yana cigiyarsa a gurina? Naga kusan kullum suna tare
idan ba a office ba Bilal ɗin ze je can gidansa ko gurin siyar da motocinsa, na taɓe baki a fili na ce
"Sun fi kusa" daga haka na shiga tattare gurin da muka zauna bayan na gama na shiga kitchen na fara
ƙoƙarin ɗora abincin dare ganin yamma tayi har sannan kuma basu dawo ba.
Ranar Juma'a ta kama sadakar Arba'in ɗin Mahaifinsu Zulaiha a ranar kuma kamar yanda kawunsu yayi
alƙawari bayan an sakko daga masallaci ɗaiɗaikun mutane suka shaid ɗaurin auren Bilal da Zulaiha sai
kuma Nuratu da Zahraddini angonga. A zauren gidansu aka ɗaura auren cikin mutanen da suka halarta
kuma mutum biyu ne daga ɓangaren Bilal, Kawu Sani sai Baba Mudan shima kawunsu ne abokanan wasa
suke da Kawu Sanin da kuna mahaifinsu Bilal. Shi kaɗai Kawu Sanin ya kira ya shaida masa komai suka
tafi tare, basu baro gidansu Zulaihan ba sai ƙarfe biyar da wani abu saboda Kawunta daya tsayar dasu da
waliyyan ɗaya angon ya nemi tayar musu da sabuwar rigima akan shi fa sai dai azo a ɗauke amare a yau
ɗin domin bai ga dalilin da zai saka a ɗaura aure kuma a bar yara su cigaba da zama a gida ba. Daga
Kawu Sanin har waɗancan waliyyan angon su kuma suka ce basu san zance ba domin aure yace azo a
ɗaura kuma sunzo yara kuma basu gama gyara in da zasu ajiye mata ba idan da yasan haka ne sai ya bari
ayi komai a nutse ba yanzu ya sake cewa zaiyi musu titsiye tofa sai a warware auren can ya aura musu
duk wanda yaga dama tunda abun nasa kuma ya zama da ɗiban albarka.
Kamar hatsaniya zata kaure har saida matan cikin gida dangin Mamansu da da wata yayar Babansu suka
fito ita ta tsawatarwa ƙanin nata ta basu haƙuri kafin suka watse kowa ya fito a fusace. Kawu Sani ya kalli
Baba Mudan ya ce
"Anya Mudansiru mutanen nan na kirki ne kuwa? kaga fa yanda mutumin nan yake zare mana ido kamar
wasu yayansa yana faɗa mana maganganu, ni wlh shaf na sha'afa na tambayi yaron nan ya ma yi bincike
da kyau akan asalin yarinyar ko kuwa dan ni kwatancen da ya mun sai da muka zo naga ashe ba
Sulaimanun da nake zato bane Babannasu". Baba Mudan yaja numfashi ya ce
"Gaskiya dai wannan ƙanin uban nasu ba za'a kwashe da daɗi dashi ba mutum ba lafazi ba magana mai
daɗi wai mu muka sani idan ma sama zamu kai su shi dai a kwashe masa yara daga gida ya dena ganinsu
ni wlh sai naga ma kamar ba cikakkun hausawa ba ƙirar jikinsu tafi kama data gwarawa". Haka suka
cigaba da tattaunawa har suka ɓullo layin su Anty Labiba, a ƙofar gidan suka ci karo da Mama suna shirin
shiga mota Anty Labiba na jikin get ta rako su. Maman ta gane shi tsaf saboda shi ya ringa zarya lokacin
auren Halima da Bilal, suna haɗa ido kamar mara gaskiya yayi saurin ɗauke kai gefe kamar bai ganeta ba
harda ƙara sauri suka wuce.
Anty Labiba da taga ta bisu da kallo ta tambayeta ko ta sanshi ne ta ce
"Surukin Halima ne ƙanin Babansu Bilal shi yayi masa walicci ma", Anty Labiba ta saki wani murmushi
haɗi da girgiza kai tace
"Allah sarki, ƙila bai ganeki bane" Maman ta bata amsa da cewa
"Da alama" sannan ta buɗe mota ta shiga, Anty Labiba ta zura kai ta window tace mata
"Ina fa yazo Labiba?" Mama ta bata amsa sai ta taɓe baki tace
"Toh Allah ya rufa asiri bari na koma kar su ce na barsu su kaɗai" daga haka ta koma cikin gida Mu'azzam
ya tayar da mota suka wuce.
Sanda suka dawo har na sauke jollop ɗin shinkafar da nayiz naji daɗi sosai yanda Mama ta nuna jin daɗin
girkin da nayi, a daren har hira mukayi na gaya mata zuwan Suhaila, ina so in mata zancen Hafiz da yake
cigiyar Bilal kuma naji tsoro kar na ɓata ɗan shirin da muka fara sai kawai nayi shiru.
A ɓangaren Bilal kuwa wunin Juma'ar cur kashe wayarsa yayi yana kuma gida sallar Juma'a kawai ya fita
ana idarwa kuma ya dawo ya sake kulle ƙofa, sanda Suhaila taje ma yana ji har ta gama bugu ta haƙura
ta tafi ya ɗauka matan unguwar ne masu zuwa gulma da sunan tambayar ko Halima ta dawo shiyasa ko
za'a fasa ƙofar saboda bugu yana ciki ba zai taɓa amsawa ba balle ya buɗe. Shi yanzu ko mazan layin ma
ba duka yake gaisawa dasu ba, sai kace akansa aka fara samun saɓani da mace har tayi yaji kowa da
dogon bakinsa sai ya tare shi yace zai masa faɗa wai bai kyauta ba ganin suna nema su raina masa wayau
ya saka ya dena tsayawa idan zai fita a mota glass ɗin sa a sama haka idan ya dawo in kuwa tafiyar ƙafa
ce ko zuwa masallaci nan ma zai haɗe fuska ta yanda ko ka masa magana zaiyi kamar bai ji ba ya share.
Yau ɗin ma sai da akayi magriba kafin yayi wanka ya shirya cikin wata sabuwar shadda yayi kyau sosai
kuwa ya hau mota ya fito. Jin sa yake kamar wani sabon mutum musamman daya kunna wayar sa saƙon
Kawu Sani ya shigo yana sanar masa an ɗaura aure idan ya kunna wayarsa kuma ya kira shi ko kuma yaje
gida ya same shi, itama Zulaihan ta yiwo masa text mai nuna zallar farin cikin ganin wannan rana a
rayuwarta da kuma ƙorafin rashin halartarsa gurin ɗaurin auren.
Gidan Kawu Sanin ya fara zuwa, a waje suka haɗu zai tafi sallar isha'i dan haka suka wuce masallacin tare
sai bayan da aka idar kafin suka keɓe Kawu Sani na kallon sa yace
"Munje an ɗauro aure amma fa wannan Kawun nata yaso ya mana hauka wai sai mu jira mu taho da ita
su ba za'a bar musu ya a gida ba bayan an ɗaura mata aure".
"Mai zamu ce masa kuwa? Muma buɗe masa ido mukayi tunda munga abinda yafi ganewa kenan dan
waliyyin ɗaya yaron ma cewa yayi sai a warware auren tunda abun nasa ya zama da iya shege a ciki idan
yaso in an shirya gaba ɗaya sai a dawo ayi". Bilal ya shafa kai yana murmushi Kawu Sani ya cigaba da
cewa
"Ni wlh duk sai jiki na yayi sanyi da al'amarin, anya kuwa ba gidan ƙananan mutane ka nemo auren nan
ba Bilal?"
"Shi ɗin shine me matsala Kawu dan baka san irin wahalar da suke sha a hannun sa bane wlh mutumin
bashi da kirki amma mahaifinsu ai kace k sanshi mutumin kirki ne haka mahaifiyar su ita kanta yarinyar
na gaya maka munfi shekara goma tare tun tana yar yarinya dan haka halayyarta babu wacce ban sani
ba babu wata matsala wlh" Bilal yayi saurin faɗa, Kawu Sani ya gyaɗa kai ya ce
"Toh Allah ya tabbatar da Alkhairi ya sa anyi a sa'a, gobe idan Allah ya kaimu zanjw in samu Hajjan in
mata bayani".
Sosai yayi masa godiya kafin ya cika shi da kuɗaɗe sukayi sallama ya wuce yana jin farin ciki na ratsa shi
ta ko ina.
Gidan su Zulaihan ya wuce dan bashi da wani buri kuma a yanzu illah ganin fuskarta kuma a matsayin
matarsa. A kan kwana sukayi clashing da Alhaji Saleh da Anty Labiba, fes ya gansu kamar yanda suma
suka ganshi sai da yaji kamar yayi reverse ko yayi layar zana ya ɓace ɓat kawai daga gurin. Tun da suka
dawo unguwar duk ranar da zaizo gurin Zulaihan tunda aka tashi hanyar da ake shigowa ta can baya sai
yayi doguwar Addu'ar Allah ya saɓa haɗuwar sa da duk wani wanda ya sanshi a unguwar kuma yana cin
sa'a addu'ar sa tana karɓuwa dan sau ɗaya ya taɓa haɗuwa da Alhaji Salen har suka gaisa a lokacin ya ce
masa gurin wani abokinsa ya zo can ƙasansu bai kuma damu ba dan ya san ba lallai ma ya ce mata ya
ganshi ita ɗin ma sau ɗaya ya taɓa hangen motar ta lokacin ma da mashin yake zuwa ya kuma gota gidan
sosai ya waigo ya hango ta fito ya san kuma bata ganshi ba amma a yau ɗin sai yake jin kamar duk
wanda ya kalle shi zai gane abinda yake faruwa.
Haka yaja mota jiki ba ƙwari ya wuce yana hangensu ta mirror, ita kuwa yi tayi tamkar ma bata ganshi ba
har sai da Alhaji Saleh yace mata
"Ina ganin sa jefi jefi a wannan motar, a nan ɗin ma mun taɓa gaisawa sau ɗaya yace gidansu wani
abokinsa yazo can ƙasa". Cikin rashin mayar da hankali tana danna waya ta ce
"Allah sarki".
Bilal kuwa ganin Zulaiha ya mantar dashi haɗuwar su dasu Anty Labiba. Sun daɗe a mota suna hira cikin
shauƙi dan basu farga da lokaci ba har sai da Ummansu ta turo Nuratu ta buga musu glass lokacin sha
ɗaya har da rabi da wasu mintuna kafin ta wuce ta barshi yana ƙoƙarin saita nutsuwarsa kafin ya tayar
da motar ya wuce gida. A hanya yana tafe shi kaɗai yana tunani, so yake ya kori waswasin da shaiɗan
yake ƙoƙarin cusa masa amma kuma tunanin yana nema yafi ƙarfin sa.
Bai tsammaci yanda Zulaihan ta sake dashi a tashin farko da irin haɗin kan da ta bashi ba. Sai ya tuna irin
wannan haɗuwar tasu ta farko da Halima, yanda ta ringa rawar jiki a lokacin har ƙarar bugun zuciyarta ya
ringa ji numfashinta yayi ɗumi baka buƙatar a faɗa maka a matuƙar tsorace take lokacin. Sun fi ƙarfin
wata shida kafin ta fara gane kan harkoki sosai dan ko kiss bata iya ba shi ya koya mata fara tarayyarsa
da Jalilah kuma ya sake fayyace masa tsakanin macen da ta saba da maza da yawa da kuma wacce namiji
ɗaya ta sani, akwai banbanci sosai domin duk ƙwarewar matar aure ba zata kamo ƙafar macen bariki ba.
Guri ya samu yayi parking abubuwan da suka gabata suka fara dawo masa daki daki. Ita ta fara kawo
hannu jikin sa, shi bai ma yi niyyar yi mata wani abu ba a yanzu ba bayan riƙe hannunta amma ta ringa
shige masa ƙila da bai kama kansa bama ya biye mata da a motar zasuyi mai gaba ɗayan. Ji yayi zufa ta
fara tsattsafo masa duk da sanyin AC da ta cika motar, can wani ɓangare na zuciyarsa ya ayyana masa ba
abinda yake zato bane Zulaiha ba zata taɓa zama irin waɗannan matan ba. Ya santa tun ƙuruciya ya
kuma yarda da tarbiyyarta hakan ba zai taɓa kasancewa halinta ba. Da wannan tunanin ya ringa tausar
kansa har ya samu nutsuwa duk da ba wai tunanin ya barshi gaba ɗaya bane ya kasa cire kokonton gaba
ɗaya amma ganin idan ya bari shaiɗan yayi galaba akansa ya saka masa wasi wasi na banza wanda ba
gaskiya ba dole ya kore komai ya tada mota yaci gaba da tafiya.
*Wattpad @MaryamahMrsAm*
*Ban yarda wani ko wata ya juya mun labari ta kowacce siga ba tare da izini na ba*
*Kuɗin karatu yana wakiltar mutum ɗaya ne, kiji tsoron Allah karki ɗauki hakkina ta hanyar fitar mun da
littafi*
*KURA A RUMBU littafin kuɗi ne, a biya naira 800, biya a asusun*
*1840175439*
*Access bank*
*PAGE 39*
Ko da ya koma gida daƙyar tunanin yanda Hajja zata karɓi zancen auren daya ɗaura ba tareda saninta ba
ya danne waswasin da zuciyarsa ta dasa masa akan Zulaiha. Wayarsa ma kashewa ya sakeyi bayan daya
shiga gida bai kuma kunnata ba sai washe gari gurin ƙarfe goma bayan daya shirya zuwa gidan Hajjan in
da daga can kuma yake so ya biya gurin Halima. A tsakar gida ya tarar da Hajja tareda Fadila suna duba
kayan da kallo ɗaya ya musu ya fahimci daga gurin Jalilah suka fito dan yanzu ta lalata Hajjan da suturu
masu tsada. Yana shiga kuwa ta ɗago baki washe tana amsa masa sallama ta ce
"Kinga ɗan halak, yanzu muka gama zancenka ashe ma kana tafe". Kan kujerar tsuguno ya zauna yana
gaisheta ta amsa cikin murna ta tura masa kayan tana cewa
"Ka ga abin arziƙin da yarinyar nan ta aiko da safen nan tayowa Fadila waya tace aje tasha a karɓo saƙo,
ni har na rasa ma abinda zance gaskiya uwayen yarinyar nan sunyi sa'ar haihuwa kai dai Allah ya cigaba
da haɓaka arziƙin kawai" ta ƙarasa tana ɗaga wani ɗanɗasheshen leshi da kana gani kasan an kashe kuɗi
gurin siyan sa. Fadila ce ta fizge shi daga hannunta tana cewa
"Ni zan ɗinka wannan Hajja" sai ko ta maka mata harara tace
"Tunda ubanki ya bani ai sai ki ɗinki ko kuwa an rubuto sunanki a jiki? Ai na gaya miki na gaji da shuka
dusa wlh, duk wata suturar arziƙi da ake kawowa ke kike ɗinkewa ki gama zaga garin ki dawo amma ko
kare baze biyoki da sunan yana sonki ba" ta juya kan Bilal tace
"Kaima na rasa baƙin ciki ne ko menene ya saka nayi nayi ka tallatawa yaron nan Hafizu ita ai ba ƙi zaiyi
ba amma ka ƙi, to wlh na fara gajiya da ganinki a gabana in sabon yaƙi samuwa sai ki nemo Sani ku
sulhunta ki koma tunda dama ai ke kika ce sai ya sakeki ba wai son ransa bane".
"Allah ya rufa asiri ai ba jaka bace ni da zan maimaita aji". Shi dai Bilal bai ce komai ba Hajja taci gaba da
ɗaga kayanta tana santi ta kimanta kuɗinsu, can ya nisa ya ce
"Bai zo ba, ya dai kira ɗazu yace yau zai zo akwai maganar da yake so muyi. Ni dai na faɗa masa idan ma
kuɗi zai roƙa babu dan dama nasan yanzu tunda akaga taurarinka sun fara haskawa Allah ya rufa mana
asiri kuma za'ayo mana rubdugu to babu wannan maganar kuwa" ta bashi amsa. Sai ya shafa kansa ya ce
"Nasan ma ba zancen kuɗi bane ai kin san Kawu Sani bashida wannan halin"
"Lallai kai zaka gayamun halin Sani ashe, to idan ba maula zata kawo shi ba menene? Naga dai zancen
tambayo aure ance sai nan da wata biyu to kuma me ze kawo shi?"
"Idan ya zo ɗin dai ai zakiji koma menene" ya bata amsa yana miƙewa, sai ta aje atamfar hannunta tana
kallon sa tace
"Aa, kawai mun haɗu masallaci ne jiya yace mun yau zai zo nan gidan". Kuri ta masa da ido tana kallonsa
kamar me son gano gaskiyar zancen sa kafin tace
"Da ganinka baka da gaskiya, to dan kaji da kunnenka idan ma zancen waccen yarinyar zaka turo shi ya
mun kar ma ya ɓata lokacinsa dan zama kam kun gama gara ma ka bata takardarta tun da mutunchi".
Komawa yayi ya zauna yana fuskantar ta ya ce
"Amma Hajja wai mai yasa kike so sai ma rabu da Halima ne? Ni fa ba tayi mun komai ba hasalima ni na
mata laifin da ya saka tayi fushi har ta tafi gidan sai kuma kawai in bita da tukuicin saki ai hakan ba adalci
bane ba". Kamar bata ji shi ba ta shiga tattare kayanta tana mayar wa cikin leda, ya sake kwantar da
murya yace
"To yanzu idan kika saka na saketa ya zanyi na zauna har wata biyu babu mata?"
Da sauri ta kalle shi kafin ta sauke kai tana sake tamke fuska tace
"Kai bana son iskanci da ɗiban albarka fa". Gyara zama yayi ganin kamar zai samu kanta ya ce
"Wlh ko yanzu da zan fito sai da maƙwafcina na jikin gidana ya tareni yana mun magana amma kinga ai
ba zance mahaifiya ta bace tace kar na dawo da ita".
"Saboda dama ni nace ka koreta ko ya akayi da zaka sakani a bakin duniya?" Ta katse shi, sai ya
marairaice ya ce
"Yanzu dai kiyi haƙuri Hajja ta dawo, ni da nake tunanin ma in ƙara wata kafin wata biyun ta cika sai in
kulle ƙofa da Jalilah yar gaban goshin ki". Kallon baka da hankali tayi masa kafin tace
"Saboda ka zama namamajo ko baka da wani lissafi a rayuwarka sai na aure? To ban yarda ba kuma bada
yawuna ba Halima dai ko da kaca aka ɗaura aurenku sai ka datse ka sallameta can Allah ya haɗa kowa da
rabon sa abinda akayi a baya ma ya isa Allah ya sa albarka".
"To yanzu idan na saketa zaki barni in auri wata kenan?" Ya faɗa cikin ɗar ɗar, ta balla masa harara kafin
ta miƙe ta shige ɗaki ta barshi a zaune. Jiki babu laka ya fita daga gidan suka ci karo da Abubakar dakw
shirin shigowa, kallo ɗaya Abubakar ɗin ya masa tamkar bai ganshi ba ya wuce ciki sai Bilal ɗin ne ya
dakatar dashi yana cewa
"Kai baka ganni bane? Yaushe kuka fito daga camp ɗin?" (Aikin custom ya samu sunje training). Cikin ko
in kula yace masa
"Na ganka mana, jiya na dawo" ya shige gida. Sai ya bishi da kallon mamaki domin ko da wasa magana
mai shige da raini bata taɓa haɗa shi da ƙanin nasa ba balle ya masa irin haka, to menene dalili?
A jikin motar sa ya tsaya duk ya rasa ina ya kamata ya dosa, ya kamata ya leƙa office ɗin su dan an tura
masa da query akan rashin zuwansa aiki dukda ya ɗauki leave amma hutun ya ƙare tuni kuma bai koma
ba haka nan bai tura saƙo abinda ya sa bai wani damu yanzu da aikin ba saboda harkokin da ya kama
yana ganin in ya cigaba sun isa su riƙe shi dama jira kawai yake shagon da Jalilah take shirin buɗewa a
nan Kano ya tabbata zai yi resigning saboda harkar fita waje da zai ringayi na shigo musu da kaya.
Wayar sa ce tayi ƙara ya zarota daga Aljihu, sai da gabansa ya faɗi ganin Hafiz ne yake kira a ƙalla kusan
sati uku kenan rabon da suyi waya balle su haɗu. Kamar kar ya amsa sai kuma dai ya ɗaga. Daga can
Hafiz ya ce
"Tuba nakeyi yallaɓai wlh tafiya ce ta sameni ba shiri mun tafi da Hajja can yakin Nijar gurin wani mai
magani jiya muka dawo dama yanzu ka ganni nake shirin fitowa zan kiraka naji gida zanzo ko office sai
kuma ga kiranka" ya shato ƙaryar da shi kansa sai da ya jinjinawa kansa. Cike da Jimami Hafiz ɗin ya ce
"Jikin ne har yanzu kuma? Amma me ya sa maimakon a mayar da ita Asibiti zaku tafi kuma gurin wani
mai maganin gargajiya?"
"Ai ka santa ko kwanciyar da tayi a Asibitin da yaya? Ai dan an fi ƙarfinta ne ita dai tafi ganewa masu
maganin gargajiya shiyasa ma na bita ɗin gudun kar a samu wata matsala kuma Alhamdulillah gashi jiki
yayi kyau ta warware harma ta aje sanda yanzu tana taka ƙafar lafiya lau" ya sake rattabo wata ƙaryar
har zufa ce ta tsattsafo masa yana yi kuma yana zare ido haɗi da duban gefensa ko da wani a kusa yana
sauraronsa.
Hafiz ya ce
"Toh masha Allah Allah ya ƙara lafiya ya tsare gaba in sha Allahu zan shigo sai na dubata, ashe shi yasa
Madam ta koma gida ni duk Suhaila ta tayar mun da hankali wai taje ta ganta a wani irin yanayi jiya kai
kuma gashi ina ta kiran layinka bana samu". Da sauri ya ce
"Babu komai naji kace ta ganta cikin wani hali ne ni kuma bata ce mun bata da lafiya ba amma bari yanzu
in je gidan in ganta kawai hankalina zai fi kwanciya" kafin Hafiz ya sake magana ya katse wayar. Mota ya
shiga ya kunna haɗi da kunna Ac dan zafi yakeji kamar wanda yayi gudu dukda garin akwai iska sosai
tana kaɗawa.
Yanzu da gaske Halima bata gayawa Suhaila komai ba ko kuwa dai kawai rufe masa yayi yake so ya bigi
cikinsa? Wayarsa tayi ƙara alamar shigowar saƙo ya duba Hafiz ɗin ne ya turo masa saƙo yana cewa
"Ka samu ka shigo office dan za'a iya samun matsala gaskiya" ganin saƙon ya saka ya tayar da mota ya
kama hanyar office ɗin a ransa kuma yana ayyana daga can gidan su Halima zai biya. Sau biyu Zulaiha ta
kirashi yana hanya amma bai amsa ba dan yana ganin sunanta maimakon yaji farin ciki irin yanda ya saba
sai kawai tunanin jiya ya faɗo masa daga ƙarshe ya kife wayar bayan ya sakata a silent ya cigaba da
kokawa da tunanin da ke neman ɓata masa yanayi.
HALIMA
Ina kwance rigingine akan gado ina amsa wayar Hansa'u, na gyara kwanciyata ina sauraronta tana cewa
"Kusan sati huɗu fa kenan ace babu waya babu zuwa balle aike kuma wani nasa bai biyo sahu ba iya
wannan ai ya isa ya shaida miki amsarsa akanki Halima". Ajiyar numfashi nayi kafin nace
"Da wahala idan yan uwansa sun san abinda ya faru tunda dama ba wai zuwar mun sukeyi yanzu ba balle
su san bana gidan, shi kuma nake ganin harda kunya ta hana ya zo"
"Ashe har yanzu akwai sauran uzurin da zaki masa Halima? Gaskiya da sauranki, duk abinda ya faru ace
kin cigaba da kare shi to gaskiya ban kuma ga wani abu da zai buɗe miki ido ki kalli gaskiya a yanda take
ba kuma ɓata yawun baki na kawai nakeyi da lokaci na ina miki magana shiga suke ta kunnen dama su
fice ta hagu" Hansa'u ta faɗa cikin ƙunar rai, nayi murmushi na ce
"Haba y zakice haka? Ai wlh duk wata shawara da kike bani na ɗauka kuma ina ganin amfaninsu, kawai
na faɗa miki nawa tunanin ne na wai lallai hakan bane ba".
"Dole kuwa ki canza tunani ko in ce ki bawa ƙwaƙwalwarki da zuciyarki dama su ringa tunanin daya dace
ba wai iya abinda kike so suyi tunani a kai ba. Wlh Halima muddin baki yiwa kanki faɗa ba zaki kashe
rayuwarki a banza ki ƙare a inda ba'a san mutunchinki ba. Yanzu ke ko dagaske kunyar yake ji idan yana
sonki kuma yana darajaki da son cigaba da zama dake zai ɗauki tsayin lokacin nan ba tareda yabi ta kanki
ba? Ki cigaba da mafarki kina yaudarar kanki, ko ki yarda ko karki yarda Halima Bilal baya sonki, idan ma
a baya ya soki to yanzu bakya gabansa. Ya daɗe yana miki kora da hali wanda idan kina da tunani ya
kamata ace tuntuni kin fahimci haka kin nemawa kanki mafita amma kin tsaya kina yaudarar kanki ke
gaki uwar yan uzuri toh sai ki cigaba Allah ya bada sa'a". Bata bani damar sake cewa komai ba ta datse
kiran.
Na tashi zaune ina sauke numfashi, ban san me yasa ba kowa ya kasa fahimtata. Waya ta ce tayi ƙara, na
ɗauka Hansa'u ce dukda na san ko zata huce ba nan kusa ba sai dai sunan da na gani yana yawo akan
screen ɗin ya saka gabana yankewa ya faɗi. Harta katse ina kallon screen ɗin wani kiran ya sake shigowa,
bana so, hannuna kansa ya so yaƙi bani haɗin kai amma bisa tirsasawar zuciyata na amsa kiran. Ban ce
komai ba na kara wayar a kunne na, daga can ɓangaren ina jin yanda ya sauke ajiyar zuciyar da na jita
har cikin magudanar jinin jikina kafin cikin murya mai taushi haɗi da rauni ya furta
"Halims ashe zaki iya dogon fushi haka dani?". Kamata yayi ace naji haushin furucin sa domin ƙarara
abinda yake nufi duk tsayin lokacin ni yake jira na kira shi Kenan shiyasa bai nemeni ba amma shirun na
cigaba da yi ina saurarensa ya sake cewa
"Nayi kewarki adadin da baki ba zai iya furtawa ba dan Allah Halims ko mai zai sakw faruwa tsakaninmu
a gaba ki hukuntani ta kowacce siga amma kada ki sake bari na, zan jure komai amma ba zan sakw iya
jure rashin ji da ganinki a duniya ta ba wlh na azabtu wahalar da na sha a tsakanin lokacin nan kawai sai
dai nayi fatan ta zame mun kankarar zunubi amma Halims kin sakani a wani yanayi da bana fatan na sake
shiga irin sa".
Jin da nayi kamar wacce aka ɗauraqa fuka fukai ina shirin fara shawagi a sararin samaniya na sakw hawa
gajimaren yaudarsa wanda sai nayi nisa ƙila ya sake girgijeni na faɗo na karye a in da ba zan ɗoru ba,
tattaro duk wata jarumta haɗi da ƙarfin hali na nayi na ja masa tsaki mai ƙarfi kafin na zare wayar daga
kunne na na kashe. Yanda kasan wacce ta sha tseren gudu haka na dafe ƙirji da hannu biyu ina sauke
numfashi, na bi wayar da kallon jin kira ya sake shigowa har ya katse ya sake kira kafin ya dakata sai
kuma ga saƙo sai a lokacin na ɗauke ta na buɗe na karanta.
"Na san kin huce, ina waje ki fito mu koma duniyarmu" abinda ya rubuta a ciki kenan. Kashe wayar nayi
gaba ɗaya na kwanta lokaci ɗaya hawaye suka ɓalle mun. Ashe kallon wacce ta haukace a soyayya kawai
Bilal yake mun yana ganin na manta ƙima da martabata a matsayina na mace shi yasa har yake tunanin
bayan irin abinda ya faru tsakaninmu baya buƙatar wanke kansa ko rarrashina kai tsaye zan manta komai
na sake komawa gareshi, lallai kuwa da na cika sakarya.
BILAL
Tsabar mamaki daskarewa yayi a tsaye lokacin da sautin tsakin Halima ya isa kunnuwansa. Ko a mafarki
bai taɓa kawo haka ba, Halimar da ya sani bata taɓa yi masa ko kallon banza ba balle ta jefe shi da irin
wannan tsaki da yake tafe da ma'anar tsana da kuma raini. Ya raya ya tafi kawai yabi unarnin Hajja ya
rabu da ita amma kuma ya kasa dan idan ya ce baya son Halima ko kuma yana da burin rabuwa da ita shi
kansa ya san ƙarya yakeyi, kai ko baya son ta a karon kanta zai so ta saboda zuri'ar dake tsakaninsa da ita
ballantana kuma yana son Matar sa, a duniyar nan kuma ya sani bashi da kamarta domin ita ta so shi ba
dan komai na sa ba ta juri duk wani wulaƙanci da tozarcinsa ba dan ta rasa yanda zatayi ba sannan ta
rufa masa asiri ta haɗiyi baƙin cikin sa ita kaɗai domin ta kare masa martabar sa.
Amma a yanda ya san tana son sa bai zaci za taji muryarsa tayi masa shiru ba, yayi amfani da salon da ya
san duk fushin da takeyi zai saka ta sakko amma a maimaikon haka sai tsaki ta biyo shi da shi.
"Ba ita kaɗai ba har mahaifiyar ta ka haɗa ka zaga" zuciyarsa ta raya masa. Ya runtse ido, wlh yayi
nadamar furucinsa idan da yana kuma da halin dawo da abinda ya wuce da ya goge waccen ranar ko
komai ba zai canzu ba kuwa da ya goge mummunan furucin da yayi shi da kansa ya san bai kyauta ba.
Sake kiranta yayi har sau biyu amma bata ɗaga ba, yana tsayen motar Abba ta iso ƙofar gidan maigadi ya
buɗe masa ya shiga ya san ya ganshi amma bai ko nuna alamar hakan wannan tasa ya koma cikin mota
ya zauna ya tura mata saƙo, jiran minti goma sha biyar yayi kafin ya sake kiran layin amma rashin sa'a ya
ji shi a kashe. Ba yanda ya iya yaja mota ya tafi a zuwan gobe zai dawo.
A karo na babu adadi Zulaiha ta sake kiransa, guri ya samu ya gangare ya kashe motar kafin ya kirata dan
tun da yamma da sukayi waya ya ce mata idan ya fito zaije amma ya manta dalilin hankalinsa da gaba
ɗaya ya tafi gurin Halima.
Kukan kissa ta fashe masa dashi bayan data amsa wayar nan da nan kuwa hankalinsa ya tashi ya shiga
rarrashinta, sai da yayi kamar zai yi yaya kafin tayi shiru ta shiga jero masa ƙorafin shikenan daga an
ɗaura musu aure yana ganin ta zama mallakinsa zai fara wulaƙanta ta dama ashe duk alƙawarin da ya
mata a baya ba gaskiya bane yanzu ne zai bayyana mata asalin halinsa. Ya ringa rantse rantse akan ba
haka bane tun safe yana office da gargaɗin da aka masa akan rashin zuwa aikin da bayayi.
"Amma na ɗauka kace can Headquartern ku na Abuja aka mayar da kai meye kuma haɗin ka da nan da
har zasu baka query?" Ta faɗa, sai yayi shiru dan ya manta abinda ya gaya mata kenan ya koma Abuja da
aiki data tambaye shi yawan zuwan da yakeyi. Sai ya ce
"Kin san wani aiki ne daban na samu a can ɗin kawai bana faɗa ne saboda ba na gomnati bane ba zanyi
saurin sakin wannan aikin ba sai naga wancan ɗin ya gama dai dai ta shiyasa kawai nake cewa
headquarter aka mayar dani". Hira suka cigaba bayan ya bata uzurin ba zai samu zuwa yau ɗin ba kamar
yanda ya mata alƙawari da farko.
"Amma wlh banji daɗi ba na gama saka ran zan kwanta a jikinka na ɗan yi bacci irin na jiya" ta faɗa kai
tsaye bayan da ta gama zagaye zagaye taga yana ta kaucew irin hirar da take so suyi. Shiru yayi kafin ya
ce
"Nima na so haka amma na faɗa miki uzuri na". Shikenan ta ɓallo hira, ta kuma sake goge masa hadda
domin yau ya gane ashe jiya ba komai ya gani ba. Duk yanda ya ringa danne maganar a ransa sai da ya
amayar ya ce mata
"Wai Zully ina kika koyi waɗannan abubuwan?" Kuma wai sai a lokacin ne taji kunya ta ce masa
"Gurin ƙanwar Umma Anty Sadiya tunda Baba ya tsayar da ranar ɗaurin aurenmu ba na gaya maka na
koma can gidan ba ita ce ta ringa koya mana".
Ji yayi maganar bata kama masa hankali ba amma kuma ta wani ɓangaren ya ɗan samu nutsuwa akan
abunda yake masa yawo a rai sai ya ce
"Tayi ƙoƙari amma a ɗan lokacin nan Zullyn da na sani ko ido bata iya haɗawa dani tayi wannan gogewar
lallai wannan Antyn tamu ba ƙaramar Malama bace"
"To kuma kunyar me zanji yanzu bayan na rigada na zama mallakinka ko so kake na tsaya wasa Maman
Al'amin ta ƙwace mun kai?" Ta bashi amsa, a ransa ya ayyana
"Halima baiwar Allah ita kam bata wannan rashin kunyar a sunnance take tata". A fili kuma sai ya ce
"Anya kuwa?"
"Idan kana musu yanzu kazo ka ɗauke ni mu tafi gida wlh yau sai na goge maka hadda dama ni a matse
nake".
Zuwa yanzu kam ko yaƙi Allah dole tsoron Zulaihan ya ɗarsu a ransa, budurqa fa wacce bata taɓa sanin
namiji ba take irin wannan sakin zancen, tattara nutsuwar sa yayi guri guda zuciyarsa na bugawa ya ce
"Kina da hankali kuwa Zulaiha? Duk ina kunyarki da na sanki da ita a da zaki iya ringa furta waɗannan
maganganun? Ko da an ɗaura mana aure har yanzu ba banbancin dake tsakanin da da yanzu fa kaɗan ne
domin bamu rigada mun zama ɗaya ba ya kamata ace har yanzu kina jin nauyina"
"Yanzu saboda ina ƙoƙarin faranta maka shine har kake nema ka faɗa mun magana? A fakaice ba so kake
kace mun yar iska ko mara tarbiyya kenan" ta faɗa cikin hasalar da bai taɓa saninta da ita ba, dake shima
zuciyar sa a kusa take sai ya ce
"Ki bawa kanki amsa ya kamata budurwar da bata taɓa sanin namiji ba ta ringa irin wannan abinda
kikeyi?"
"Zargina kake yi Bilal? Ƙazafin zina kake so kayi mun?" Ta faɗa cikin ɗaga murya kamar yana gabanta, sai
kawai ya zare wayar daga kunennsa ya katse kiran haɗi da kasheta gaba ɗaya dan ya lura idan ya biye
mata zasu iya yin ɓatacciya. Mamaki ya rufeshi yanda lokaci ɗaya halayen da bai santa da su ba suke
fitowa ɗaya bayan ɗaya. Zulaihar da ko haɗa ido batayi dashi ko zai yi me kuwa kanta na ƙasa duk
maganar da zasuyi har gara gara a waya ta kan ɗan sake dashi suyi hira har ta faɗa masa kalaman
soyayya amma ko tsareta yayi a zahiri yace ta maimaita sai dai tayi kamar zata saka masa kuka ya haƙura
ya ƙyaleta ladabi da biyya kuwa kamar zata kwanta masa idan ya faɗa mata magana ba zata tsallake ba
yanda take gudun ɓacin ransa kuwa wani lokacin har ji yakeyi kamar abun yayi yawa ya zama kamar
tsoronsa takeji amma yau ita ce ta kama sunan sa katsal abinda bata taɓa yi ba tana ɗaga masa murya
kamar zata rufeshi da duka?
"Gaskiya akwai matsala" ya furta a fili kafin ya tayar da mota ya nufi gidan Hajja.
*Wattpad @MaryamahMrsAm*
*Ban yarda wani ko wata ya juya mun labari ta kowacce siga ba tare da izini na ba*
*Kuɗin karatu yana wakiltar mutum ɗaya ne, kiji tsoron Allah karki ɗauki hakkina ta hanyar fitar mun da
littafi*
*KURA A RUMBU littafin kuɗi ne, a biya naira 800, biya a asusun*
*1840175439*
*Access bank*
*PAGE 40*
Tunda yaga babur ɗin Kawu Sani a ƙofar gidan gabansa ya shiga faɗuwa domin ya san abinda akw
ɓoyewa ya rigada ya bayyana. Sai dai kuma shima yana buƙatar hakan ko dan ya samu a wuce gurin
Zulaiha ta tare amma kuma ya san da wahala su kwasheta da daɗi da Hajja. Tun daga tsakar gida yake
jiyo maganganun Hajjan tamkar zata ari baki tsabar masifar da take zazzagawa, yana ɗaga labule suka
haɗa ido kallon data jefa masa sai da yaji yan cikin sa sun juya, ta ce
"Yawwa gara da kazo, dama Bilal idan har ni na haifeka ba canza mun kai akayi a Asibiti ba, bana buƙatar
jin kowacce magana daga bakinka a yanzu har sai bayan ka rubuta takardar saki yanzu an kaiwa waccen
kaskar da kuka munafurceni aka ɗaura maka aure da ita." Sai kuma ta fashe da kuka tana cewa
"Allah ya isa tsakanina da kai Sani dan nasan wannan abun shirinka ne Bilal ba zai taɓa mun haka ba,
dama shi ɗan uba duk in da yake ai ba zai taɓa sonka tsakani da Allah ba sai in yana da wata manufa, to
ka sani haƙƙin marigayi ba zai barka ba wlh tallahi domin ya ƙaunace ka tsakani da Allah in ba an faɗa ba
ma waye zai ce ba ciki ɗaya kuka fito dashi ba amma shine saboda zuciyarka cike take da mugun abu ka
rasa kuma akan wa zaka juye shi sai akan ɗan da yafi so tir da kai Sani" ta sake rushewa da kuka harda
fyace hanci.
Daƙyar ya ƙarasa cikin ya samu guri kusa da Kawu Sani da ya zabga tagumi yana kallon Hajja, murya a
dace kamar wanda ya tashi daga ciwo ya ce
"Kiyi haƙuri Hajja amma babul laifin Kawu Sani a cikin maganar nan domin ni na saka shi ya nema mun
aure ba wai gaban kansa yayi ba". Kamar an yi ruwan sama an ɗauke kuwa ta dakata da kukan da takeyi
ta kafe shi da ido alamun sauraron ƙarin bayani, ƙasa yayi da kai kafin ya cigaba da cewa
"Hajja kin fi kowa sanin irin son da nake yiwa Zulaiha amma a haka na haƙura da ita saboda kin nuna
bakya so a wancan lokacin, Hajja kin san yarinyar nan bakay buƙatar na sake gaya miki komai akanta
aurenta tamkar jahadi ne zanyi saboda na taimaketa kuma idan kika duba tsahon lokacin da muka ɗauka
tare tana jira na tun banyi aure ba har kuma nayi auren bata haƙura ba kuma yanzu nace na zan aureta
ba ai zai zama kamar na yaudareta ne kuma dama ai Hajja munyi yarjejeniya dake na faɗa miki duk idan
na samu dama a gaba zan aureta kuma baki ce ba haka ba".
Kukan da ya fi na farko Hajjan ta sake fashewa dashi shi kuma ya sake laƙwashe murya ya ce
"Hajja kin san bana miki musu duk abinda kika ce ko bana so ina yinsa, dan Allah zan roƙe ki ki mun
wannan alfarmar ki barni da Zulaiha, ina sonta nayi miki alƙawari ko me kike so zanyi amma kiyi haƙuri
dan Allah kada ki rabani da Zulaiha" ya ƙarasa yana zamowa gabanta ya dafa guiwarta hawayen da yake
kokawa dasu suka gangaro akan kuncinsa.
Cikin kuka Hajjan ta shiga cewa
"Ba maganar karna damu ba, wlh a kanta zan iya ɓata maka rai Bilal wlh" ta katseshi, sakw marairaicewa
yayi ya ruƙo hannunta ya ce
"Haba Hajja yanzu har kin fi son wata bare a kaina kenan?"
"Kai da ka nuna mun iyakata Bilal da raina ban mutu ba ka zagaya ka ɗaura aure har kana da bakin cewa
na fifita wani a kanka? Ai ko da bana so har idan dagaske kana martabani a matsayin uwarka ya kamata
ka gaya mun, amma shikenan, dama gashinan ƙanin ubanka ya fara cewa ni mai son zuciya ce na saka ka
auro waccen yarinyar ga yanda ake ciki yanzu ina so na sake turaka ka auro wata ba'a son ranka ba
shiyasa ka zagaya kayi aure baka gaya mun ba, shikenan kaje ba zan hanaka ba amma ba'a son raina ba"
ta miƙe tana kuka wiwiwi ta wuce ɗaki.
Gaba ɗaya ji yayi kansa ya kulle dan ko maganar da Kawu Sani ya shiga yi masa sauraronsa kawai yake
amma baya gane komai cikin abinda yake faɗa, ƙarshe kawai ya miƙe ya fice daga falon. Auren da take
so ta saka albarka a ciki ma ya ya ƙare balle wannan da tace bata so?
Kwanakin da suka biyo baya gaba ɗaya Hajja ta ɗauke masa wuta ko gidan yaje daga sallama bata sake
ce masa komai duk kuma magiyar da zaiyi da bata haƙuri ba zata tanka masa ba abin sai ya zame masa
goma da ashirin dan yanda ya tsammaci lamarin Halima zai zo masa da sauƙi sai kuma abun ya sha
banban. Washe garin daya sake komawa da yamma haka nan ya ƙara ci kiranta a waya amma bata amsa
ba daga ƙarshe ma ta kashe layin gaba ɗaya, ya tura mata text duka babu amsa haka ya haƙura ya tafi ga
ta ɓangaren Zulaihan itama ba wani sauƙi, fushi ta ɗauka dashi tun akan zancen waccen daren shi ya
ƙwafe yana jira ta kira ta bashi haƙuri irin yanda ya saba da Halima amma har aka kwana aka kusan wuni
shiru bai ji ta ba.
Haka nan sonta dake azalzalar zuciyarsa ya tilasta masa kiranta kuma ko kafin su shirya sai da ta masa
tatas ta amayar da duk abinda yake cikin ta kafin ta kammala da gargaɗi akan karya sake mata irin haka
wai kuma abin takaici ba yanda ya iya ya bita da ban haƙuri shikenan suka shirya har a daren yaje
gidansu kuma kamar yanda tace tunda ba'a masa gwaninta ta daina nuna masa kulawar hakan ce ta faru
dan ƙin yarda ma tayi su zauna a mota sai a soro sukayi zancen.
HALIMA
Ba ƙaramin ƙarfin hali nayi gurin danne zuciyata naƙi amsa Bilal ba, so nakeyi na tabbatar da matsayina a
gurin sa, ko da ya tafi zuwansa na farko na ringa ji kamar na kirawo shi na ce ya dawo amma da naga har
dare ya tsala safiya tayi bai sake kirana ko tura mun sa saƙo ba sai ba raina kaina na kuma fara tausayin
kaina akan igiyar zaton dana ƙulla na cewar Bilal ɗin dagaske yana ta tawa mutane kawai suke ganin ba
haka ba. Na ji sanyi har raina daya sake dawowa sai dai kuma ban biyewa zuciyar da ta ringa azalzata
akan na karɓi uzurin sa ba. Na tambayi kaina wane uzuri zan masa ne ma tunda shi dai bai furta ko
nunawa a aikace cewa ya yarda yayi mun laifi ya kuma nemi da nayi haƙuri ba maimakon haka a kalaman
da yake turo mun sunfi kama da wanda yake jaddada mun cewar ya san ba zan iya rayuwa babu shi ba
dan haka dole nayi haƙuri na koma masa kuma ko kusa bai ma nemi cewar na bashi dama mu zauna ko
zai wanke kansa ba aa kawai cewa yakeyi nazo mu koma gida tabbacin ko a jikinsa ma shi ya manta da
duk abinda ya faru.
Ba tareda kowa ya bani shawara ba na yankewa kaina shawarar ɗibar masa lokaci, zanyi ta jansa in ga iya
gudun ruwansa. Shin zai fahimci kuskuren sa ya biyo ta sigar daya kamata ko kuwa zai cigaba da yi mun
kallon ba zan iya rayuwa babu shi bane?
Na kwanaki huɗuya jera kullum yaje gidanmu daga zarar kuma yayi mun kira ɗaya ba zan bari yayi na
biyu ba zan kashe wayar. Na zuba ido naga gudun ruwansa tunda har aka kwana huɗun dai salo ɗaya
yake maimaitawa na kirana haɗi da tura mun text yana tunasar dani yanda yake a raina ba wai yanda ni
nake a nasa ran ba in dubi wannan nazo mu koma gida. Nasan Mama ta san yana zuwa amma ko da
wasa ɓata ce mun komai ba nima kuma ban ce mata ba a haka muka kwana huɗun a yini na biyar shiru
tun Magriba nake tsammacin naga kiransa amma har sha biyun dare ta gota shiru babu shi babu
labarinsa tils na cire rai sai kuma damuwa da ƙuncin da ban tsammata ba suka lulluɓe ni.
Washe gari haka na tashi sam babu walwala ba fara'a, komai ma baya mun daɗi dan ko abinci ɗan kaɗan
na tsakura na ture saboda yanda nakejin komai yana mun ɗaci a bakina. Bini bini zan ɗauki waya in duba
ko zan ga saƙon sa ko makamancin haka amma shiru har azahar tayi, bayan na idar da sallah ina zaune
kan sallaya ina lazumi wayata ta shiga ƙara, tun da gari ya waye ko message bai shigo mun ba ina jin
ƙarar wayar kuwa na zabura zuciyata tana raya mun Bilal ne dai dai lokacin kuma Mama ta shigo ɗakin.
Wayar na duba ganin baƙuwar number ya saka zumuɗi na raguwa dukda haka bam cire tsammanin shi
bane sai bayan dana kai wayar kunnena bayan na amsa naji murya daban ba tashi ba.
Zare wayar nayi na kashe ba tareda na amsa sallamar da wanda ya kira yayi ba, na saci kallon Mama jin
tana cewa
"Iska dai tana wahalar da mai kayan kara" kafin tayi ƙaramin tsaki ta nufi ƙofa tana cewa
"Ga Mudassir can a falo yana jiranki". Jiki ba ƙwari na biyo bayanta, bayan mun gaisa da Uncle Mudassir
ya tambayeni jiki na ya ce
"Na ɗauka kin karɓo posting letter ki Halima tuntuni ashe baki je ba". Ɗan ya mutsa fuska nayi na ce
"Uncle ba fa ni da lafiya, kuma ni ban ma san an fito daga camp ɗin ba". Daƙuwa yayi mun yana cewa
"Dan gidanku ni kike gayawa baki da lafiya tun yaushe kika samu sauƙi yau kwananki nawa da aka
sallamoki daga Asibiti? Naga alamar har yanzu baki san inda yake miki ciwo ba Halima, satinki nawa a
gidan nan? Ke ko ji bakiyi zaman ya isheki ba kina buƙatar samun abun da zai ɗebe miki kewa ko kuwa
dai saboda kanki aka fara mutuwar aure shikenan sai ki zauna ki lalata rayuwarki a banza ba zaki gyara
gobenki ba?"
"Ni fa Uncle aure na bai mutu ba". Ina kallo Mama ta jijjiga kai irin na zallar takaici shi kuma ya ce
"Oh har kina da bakin cewa aurenki bai mutu ba? Toh zaman uban me takeyi kusan wata biyu a gida?"
Ya ƙarasa yana kallon Mama. Hannu biyu ta watsa ta ce
"Gaka gata ƙila kai tunda tana ganin kanka da gashi ta gaya maka zaman me takeyi tunda mu da ta raina
ba yanda bamuyi ta girma da laluma ta faɗa mana mai ya faru ta taho gidan ba amma tace babu komai"
"Aa wannan kuma laifinku ne Anty, ai ƙarya ne wlh yarinya ta taho gida sama da wata ba wani
ƙwaƙƙwaran dalili ni duk ɗauka ta ya saketa ne kuma abinda yasa kika ga ban ko yi miki maganar ba
saboda naga babu amfani ne ko yanzun LGI ɗin ne ya kirani dan tuni an turo da relocation list har anyi
posting nasu dake nayi masa maganar ta da in da nake so a kaita ya kirani akan bafa ta je ba har yanzu
shiyasa ma kika ganni yanzu. Kuma shi Yaya Aminun ya zuba muku ido take ta zama bai ce komai ba?"
"Toh mai zai ce Mudan? Ita me auren an tambayeta tace babu komai shi kuma bai biyo baya ba haka
babu wani nasa da yazo toh ta ina zamu san meya faru?" Mama ta sake faɗa, ni dai kaina yana ƙasa ina
jinza ya kira sunana na sake sadda kai ƙasa sai da ya buga mun tsawa kafin na ɗago da sauri ya nuna ni
yana cewa
"Kar kiga kin girma ko kin haihu wlh dukan tsiya zan miki Halima kuma banga uban da zai ce dan me ya
saka ba, tun muna shaida juna dake ki faɗa mun mai ya saka kika taho gida yanzu ba sai anjima ba". Kuka
na fashe dashi bayan da naja baya daga kusa dashi dan na san dukan daya ambata zai mun tsaf zai aikata
dan zuciya ce dashi kamar kuturu duk cikin ƙannen su Mama yafi su zafi ba kuma ya wasa damu dama
shiyasa muke shakkar sa sosai. Tsawa ya sake bugamun bayan daya miƙe tsaye da alama neman madoki
yakeyi, dai dai nan Anty Labiba da Mama Fauziyya sukayi sallama da gudu kuwa na nufi Mama Fauziyya
na rungume ta ina sake fashewa da kuka ta ɓoye ni a bayanta tana tambayar mai ya faru nan kuwa ya
fara zazzaga faɗa akan me zan zo gida tsayin lokacin nan na sakina akayi ba kuma naƙi faɗar zuwan me
nayi wlh zai mun dukan tsiya idan ban buɗe baki nayi magana ba.
"Kai daɗi na da kai saurin hasala Mudassir banda haka duk maganar ai bata wuce ayita a zaune ba"
Mama Fauziyya ta faɗa, Mama ta ce
"Ai kuwa magana ta wuce ta sulhu dan tuntuni nake bin yarinyar nan akan ta faɗa mun mai ya faru tun
hankalina yana tashe da lamarin har na haƙura na fawwalawa Allah tunda naga alamar zan ɗorawa kaina
damuwa ne a banza alhalin wacce nakeyi akanta ita bata damu ba toh wlh nima yanzu na gaji, cikin biyu
dole ayi ɗaya. Ko dai idan sakinta yayi ta faɗa mu san zaman me takeyi ko kuma ta tattara ta koma
amma na gaji da zama da ita a haka kullum ina kallonta ina jin ɓacin rai".
"Hmmm mu dai anayi muna jin daɗi" Anty Labiba ta faɗa tana zama akan kujera irin ba abinda ya
shafeta ɗin nan, banda kuka ba abinda nakeyi, sai da Uncle Mudassir ya mun tatas kafin ya tafi akan
kada na kuskura ya sakw dawowa bai tarar da ɗayan biyu ba, ko dai in koma ko kuma ya samu tabbacin
zaman yanci nakeyi. Ba abinda ya sake ɗaga mun hankali irin yanda Mama take nanata ita ta gaji Mama
Fauziyyar da take kareni sai in tattara na bita amma ba zata cigaba da zama dani alhalin bata san ina ma
saka gaba ba. Duk sai suka sake jagula mun lissafi ga danuwar da na tashi da ita ga kuma wata sabuwa
data ɓullo na ringa jin inama ban biyewa huɗubar Hansa'u ba na saurari Bilal ƙila da na bashi dama zai
zayyana mun nadamar sa ya kuma nemi yafiyar tawa idan yaso sai in yanke hukuncin da nake ganin ya fi
mun yanzu gashi nan a garin jan aji ya tsinke gidan ma kuma zasu tasoni a gaba in rasa ina zan tsoma
raina.
Ɗaki na koma na cigaba da kuka sai da nayi mai isata kafin na haƙura na wanko fuskata na koma na
zaune bayan na ɗauki wayata zuciyata na ayyana mun na kirashi, tarin missed calls na gani da number da
aka kirani da ita ɗazu zai text guda ɗaya,
"Hafiz ne abokin Mijinki Bilal, idan kin samu lokaci ki kirani akwai abinda nake so mu tattauna" abinda
saƙon ya ƙunsa kenan. Na natata karanta saƙon yafi sau biyar a raina ina mamakin wace magana ce Hafiz
zai tattauna dani kuma mai muhimmanci kamar yanda ya ce?
Tunani na shigayi a zuwan Matarsa ko akwai wani abu dana faɗa mata da bai kamata taji ba amma ban
tuna ba, ajiye wayar nayi kawai ba tareda na kira shi ɗin ba kamar yanda ya buƙata dan ni banga dalilin
hakan ba. Bacci ne ya kwashe ni ina tsaka da tunanin neman mafita, sanda na farka gari har yayi duhu
alamar magriba ma ta wuce na ringa salati in mamakin wane irin bacci nayi haka tun azahar kuma ace
babu wanda ya tashe ni da akayi la'asar da ga magriba ma lallai dagaske da Mama tace ta gaji da zamana
ba wasa takeyi ba tunda gashi ko a jikinta bata ma ko yi tunanin mutuwa nayi ba ba wanda ya leƙo ni.
Hawaye suka ɓalle mun ina wanka ina kuka har na gama sannan nayo alwala ina jin cikina kamar zai
haɗe da bayana tsabar yanda yunwa ta gama rarakeni, daƙyar nayi sallolin da suka wuce ni kafin na fito
kai tsaye na faɗa kitchen neman abinda zanci.
Mama da Zainab na aikin ƙarasa abincin dare ko kallo na batayi ba sai Zainace ta ce
"Kin tashi Yaya Halima? Tun ɗazu nake leƙo ki naga kina jin daɗin baccin shiyasa ban tashe ki ba". Ban
amsa ta ba na ɗebi abinda na gani na fita, bayan mun gama ci tareda Sharifa ina shirin na koma ɗaki tun
kafin Mama ta fito falon Mu'azzam ya shigo, ba yabo ba fallasa ya ce mun
"Wane irin hauka ne haka ni zaka cewa ina da baƙo ko ka manta matar aure ce ni?"
"Wai matar aure" ya faɗa yana nuna ni kafin ya tuntsure da dariya harda buga ƙafa ya wuce yana cewa
"Idan zaki tashi kije Malama ki wuce kar ki ɓata masa lokaci".
Miƙewa nayi da zummar na bishi in ji ba'asin akan me da mutunchi na da kuma aure na har wani zai zo
gurina a shigo dashi har falo saiga Abban ya shigo, ba yabo ba fallasa shima ya kalleni ya ce
"Abba ya za'ayi da aure na ace wai wani yazo gurina in fita?" Na faɗa ina rau rau da ido kamar zan fasa
kuka, sama sama yace
"Bana son sakarci Halima ki wuce kuma tun kafin ranki ya ɓaci". Sum sum na wuce domin na fi kowa
sanin fushi ba ɗabi'ar Abba bace har kuma idan ransa ya ɓaci to fa baya yi da sauƙi.
Turus nayi a bakin ƙofa ganin baƙon, Hafiz ne abokin Bilal. Na ƙarasa ciki da ƙaramar sallama na samu
kujera can nesa na zauna kafin ma shiga gaishe shi ya amsa cikin kulawa yana tambayata yara na gaya
masa Al'amin yana can gidan Anty Labiba Sharifa kuma tana ciki.
"Kiyi haƙuri Halima kin ganni ba tareda kinyi mun izini ba, na yi ta jiran martaninki toh amma gaskiya ina
da ɗan uzuri ne wanda kuma ina son mu tattauna kafin na wuce dan ban san ko har zan dawo ba tareda
lokacin buƙatar hakan ya wuce ba" ya faɗa, ni dai kaina yana ƙasa ya cigaba da cewa
"Kiyi haƙuri Halima, na san zaki iya cewa menene nawa da shiga cikin maganarki da Bilal amma ki sani
ina da dalilin yin hakan, na san kin fi kowa sanin kusancin da yake tsakanina da Bilal. Allah ne ya haɗa
jinina da shi kuma Allah shine shaida ina jin sa a raina tamkar wanda alaƙar jini ta haɗa mu shiyasa ban
taɓa ƙyashin nayi masa wani abu ba, a zaman da nayi da Bilal na karanci wasu halayensa waɗanda na
ɗauka a matsayin tawaya da kowanne ɗan adam yake dashi dole idan ya zamo ya cika ta wani ɓangaren
ta wani gefen kuma za'a same shi da kuskure dan haka na karɓe shi a yanda yake ina kuma yi masa uzuri
a duk in da ya kuskure domin nima na sani dole akwai ta inda nake da giɓi sai dai ko kusa ban taɓa
tsammanin Bilal zai aikata irin abin nan ba.
Kiyi haƙuri Halima ni ne silar da har Bilal ya san Jalilah sai dai bani da wata masaniya ta ƙulluwar wata
alaƙa a tsakanin su domin daga shi har ita sun rufeni akan haka. Jalilah Ex ɗina ce kuma dalilin da ya
kawo ruɗani tsakaninki da Bilal shine silar rabuwar mu da ita har na fasa aurenta bayan har an yi mana
baiko. Yanda kike son Bilal haka Jalilah take so na, albarkacin wannan soyayyar ta saka kuma duk yanda
na so na yakice ta daga rayuwata taƙi fita na raga mata har muka cigaba da mu'amalar gaisawa.
Ban ɓoyewa Bilal komai akan Jalilah ba tun a sanda ya fara ganinta har yake tuhunata akan me yasa naƙi
aurenta bayan a nasa ganin tafi Suhaila komai na ya mace, na ɗauka abinda na gaya masa akanta zai
saka ya hankalta dukda ban taɓa kawo cewar wata mu'amala zata iya shiga tsakaninsu ba sai dai abin
takaici hakan ya faru kuma ya rufeni har ta kai a silar ta yana shirin rusa rayuwarsa ta hanyar rabuwa da
abubuwa masu muhimmanci ciki harda ke da kuma aikin sa.
Bazan cika ki da surutu ba amma Halima ina so ki san da cewa duk wani abu da kike tunani akan Bilal da
Jalilah na sani, na daɗe ina masa addu'ar gane gaskiya tun kafin ubangiji ya kawo irin wannan lokacin da
asirinsa zai fasu, kada kiyi tunanin shirun da kikayi yana nufin kin rufa masa asiri domin shi da kansa ya
ɗaurawa kansa ƙararrawar da zata yayata sirrinsa har ya isa ga kunnuwan kowa. Jalilah ba zata taɓa
yarda da cin amanar da yayi mata ba bayan ta gama ɓata lokacinta ta kuma kashe kuɗinta akansa da
tunanin zai aureta sannan ya zagaya yayi amfani da kuɗin ta ya auri wata hakan ba zai taɓa yuwuwa ace
ta ƙyale shi ba".
Kusan daga iya in da na dena fahimtar duk wasu maganganu daya cigaba da faɗa kenan, da farko na cika
da mamakin yanda yace ya san komai dake tsakanin Bilal da Jalilah sai kuma maganar da na tsinta ta
ƙarshe ta goge mun hadda ta kuma jefani a ɗimuwa ko in ce gushewar hankali na wucin gadi cewar da
yayi Bilal yayi amfani da kuɗin Jalila ya auro wata?
Har idan dagaske ta silar sa Bilal ya san Jalilah kenan sai bayan ya aureni hakan ta faru tunda ina gidan
Bilal suka haɗu da Hafiz hakan yana nufin bani ce wacce aka auro da kuɗin Jalilah ba kenan to me yake
nufi? Aure Bilal ya ƙara ko me?
*Wattpad @MaryamahMrsAm*
*Ban yarda wani ko wata ya juya mun labari ta kowacce siga ba tare da izini na ba*
*Kuɗin karatu yana wakiltar mutum ɗaya ne, kiji tsoron Allah karki ɗauki hakkina ta hanyar fitar mun da
littafi*
*KURA A RUMBU littafin kuɗi ne, a biya naira 800, biya a asusun*
*1840175439*
*Access bank*
A yayinda muke shirin kammala wannan littafi, idan kin san kina karantawa ba tareda kin siya ba kiyi
ƙoƙari ki sauke nauyi domin babu lallai in yafe haƙƙina. Account details suna sama 🙏🏽🙏🏽
A hankali na buɗe ido na jin saukar abu mai sanyi a goshi na, ganin na buɗe idon ya saka Mama janye
hannunta, ganin da tayi ina shirin sake komawa baccin ya saka ta ce
"Da dai kin tashi haka nan kuma ki ƙarfafa jikinki tunda dai zazzaɓin ya sauka". Na yunƙura na zauna ina
cije baki saboda kaina daya sara, dukda zazzaɓin da rafke ni ya sauka amma har yanzun bana jin ƙwarin
jikina. Banɗaki ta shiga bata jima ba ta fito tana cewa
"Ga ruwa can na tara miki kiyi wankan Zainab zata kawo miki abinci" daga haka ta juya ta fita na rakata
da ido ƙauna da kuma tausayinta suna sake ratsani. Allah sarki iyaye masu daɗi duk inda akaje aka dawo
su ɗin dai ko sun yi fushi a hakan zasuyi haƙuri su karɓe ka. Jiya ta gama nanata ta gaji da zaman da nake
gabanta amma hankalinta yafi na kowa tashi da yanayin da na shigo gidan bayan da na baro Hafiz.
Na runtse ido na saboda yanda tuna Hafiz ɗin ya dawo mun da zantukansa da sukayi matuƙar kiɗimani
haɗi da hargitsamun tunani, hawaye suka ɓalle mun, dukda har yanzun na kasa gasgata maganarsa wai
Bilal yayi aure amma tunanin hakan kaɗai da nakeyi ace da gaske ne ji nake zuciyata kamar zata ƙone
saboda zafin da takeyi mun, ba zan taɓa iya jurar ganin wannan baƙin cikin ba wata mace a rayuwar Bilal
sai kawai na haɗe kai da guiwa tareda fashewa da kuka mai sauti harda shassheƙa.
Ƙarar ruwa dake ta zuba ya saka na tashi daƙyar bayan da na haɗiye kukan nayo wanka haɗi da alwala na
fito, kan gado na sake komawa na zauna, gaba ɗaya komai ya sake jagulemun na sake komawa yanayin
da nasha wahala kafin na samu kaina daga cikin sa. Saƙe saƙe kala kala zuciya ta ringa kawo mun, daga
ƙarshe na yaƙi kaina ta hanyar tashi na ɗora dogon hijabi kan towel ɗin dake ɗaure jikina na shiga jera
nafila duk da cewar bayan la'asar ne magriba ma ta gabato lokacin.
Bayan sallar isha'i ina kwance a ƙasa, duk yanda naso na mayar da hankali na kan lazumin da nakeyi na
kasa gaba ɗaya tunani na ya tafi akan son sanin haƙiƙanin gaskiyar abinda Hafiz ya faɗa mun. Idan har da
gasken ne Bilal yayi aure toh wa ya aura? Ko Jalilan da suka gama sheƙe ayarsu a titi ya aura? ko kuma
wata daban?
Zuciya ta raya mun 'ko kuma duniyar sa ba? Ko wacce ya kaini gidansu gaisuwa. Duk a rana ɗaya na
sansu ranar da na bankaɗo sirrinsa da Jalilah ƙila ɗaya daga cikinsu ya aura. Sabbin hawaye suka ɓalle
mun, bai ko bani damar yi masa tambayoyi da yawa da suke cunkushe cikin zuciyata ba kafin na baro
gidan sa har a yanzun kuma daya dawo daga yanda ya ɓullo na fahimci baya buƙatar warware ƙullin baya
kawai so yakeyi mu ɗora sabon babi.
Da hannu biyu na rufe fuskata ina jan kuka, na rasa tunanin daya kamata nayi, mai yasa Bilal zai mun
haka? Duk haƙurin da nayi duk juriyar da nayi akan lamuransa lokaci ɗaya ya rasa irin sakayyar da zaiyi
mun sai wannan?
Jin ana ƙwanƙwasa ƙofa ya saka na shiga goge fuskata da sauri dan zaryar da Zainab take mun na san da
wahala idan ba CID Mama ta sakata ba, kuma daga yanayinta tun jiya da yanda Abba da kansa ya ce na
fita gurin Hafiz ɗin na tabbatar ma abinda na jima ina ɓoye musu ya rigada ya bayyana ma'ana ya faɗa
musu komai akan Bilal da Jalilah ga kuma wata sabuwa data ɓullo yanzu.
Ɗaga murya nayi na ce ta shigo bayan da na tashi zaune na jingina da Gado. Ganin Abba ya saka zuciyata
ta shiga bugawa da sauri da sauri, haka nan ban tuna sanda Abba ya shigo ɗakina ba tun ma zamanin
yammatanci balle yanzun na san dole abu ne me muhimmanci ya kawo shi. Kan bedside drawer ya zauna
ba yabo ba fallasa yana amsa gaisuwar da nake masa, muka yi shiru kafin can ya ce
"Kin san me yasa na biyo ki har ɗaki?" Na girgiza kai alamar aa, ya ce
"Saboda ki gane muhimmancin maganar da nake so mu tattauna dake". Bugun da zuciyata keyi ya saka
tsananta har wani ɗumi numfashina ya ɗauka gaba ɗaya a tsorace nake ban san wace magana zai mun
ba dukda bana raba ɗaya biyu akan Bilal ce amma me zai ce mun?
"Nasan baki manta ba ni nayi tsaye na goya miki baya kika auri yaron nan dukda yanda mahaifiyarki da
yan uwanta har ma da nawa yan uwan suke ganin rashin dacewarki dashi. Ki sani, abu biyu zuwa uku na
duba da har na amince da aurenku. Na farko, a iya binciken da nayi akansa ba'a same shi da wani mugun
hali wanda zai saka a ƙi bashi aure ba, dai dai gwargwado ya samu shaida ta mu'amala kuma ana
kyautata masa zato akan addininsa. Abu na biyu soyayyarki gare shi, yanda kike mu'amalantar sa ya tuna
mun yanda muka rayu da mahaifiyarki a lokacin da ban ma kai shi ba domin ni sanda na aureta banida
da ko tartibiyar sana'a amma a hakan ta ƙaunace ni har kuma Allah ya kawo mu matsayin da muke kai a
yanzu.
Na kyautata masa zato kuma son da nake miki da burin ganin na samar miki da farinciki a rayuwarki ya
saka na amince na bashi aurenki bisa kyakkyawan yaƙinin zai riƙe mun ke amana amma baki ɗauki dogon
lokaci a gidan aurenki ba na fara dana sanin biyewa zuciya, a ƙoƙarin son samuwar farin cikinki har hakan
ya rufe mun ido na kasa hasaso idan aka samu akasi wani hali rayuwarki zata shiga?
Duk da haka ban sare ba, na cigaba da yi muku addu'a na kuma ringa tallafa miki a ganina raguwar
ɗawainiyar zata taimaka gurin samun dai daito a zamantakewarku musamman tunda na fahimci halayya
da kuma ɗabi'ar mijin da kika zaɓi rayuwa dashi. Ko da baki taɓa zuwa kin faɗi laifin sa ba amma komai a
bayyane yake, kuma wannan hujjar na riƙe a duk sanda mahaifiyarki ta so yin bore ko kawo hargitsi cikin
zamanki da shi na kan nusassheta da cewar a gurinta ne take ganin gazawa ko matsi a zaman da kikeyi
amma ni a guri na lafiya kike zaune domin baki taɓa zuwa kin kawo ƙara ko kin faɗawa wani damuwarki
ba na kuma san ba dan baki da damuwar bane sai dan halin zurfin ciki da kuma soyayyar dake wahalar
dake kin kuma yarda zaki rayuwa dashi cikin kowanne irin yanayi sa'annan akwai nauyi da gudun kar ayi
miki dariya sanin kowa sai da ya ce miki kar kiyi kikace kinji kin gani.
Duk da dai da fari na ɗauka rashin wadata ne sanadin abubuwan da suke wakana a tsakaninku shiyasa
ban taɓa cewa komai ba nake kuma iya bakin ƙoƙari na gurin ganin na samar miki da abinda ya gagara
baki sannan kuma na hana mahaifiyar ki ko wani nata duk sanda sukayi yunƙurin ɗaukar wani mataki
akan zamantakewarku amma daga baya idona ya buɗe na kuma fahimci komai, tsantsar son kai da
mugunta ce kawai take damun sa ba wai babu bace.
Ina so san cewa ke kike son Bilal Halimatu kuma ko da ace yana sonki to ki sani bai kai ko kwatan
soyayyarki gare shi ba. Iya zamanki a gidan nan daga zuwanki zuwa rashin lafiyar da kikayi kawo yanzu ta
isa hujjar da zakiyiwa kanki Hisabi ba tareda wani ya ce miki komai ba, idan ba dan na samu tabbaci daga
wanda ba zai mun ƙarya ba da banzan taɓa yarda da cewar da igiyar aurensa akanki yayi miki irin
wannan tozarcin ba".
Sai lokacin na ɗaga kaina na kalle shi jin kalmar tozarci daya faɗa idanuwana basa ko gani da kyau
saboda hawayen da suke cikinsu, ya gyaɗa mun kai cikin tabbatarwa ya ce
"Babu wani namiji da yake ganin matarsa da ƙima da zaiyi kwatankwacin abinda Bilal ya aikata miki. Da
kansa ya ɗakko ki ya kawoki gidan nan saboda ya nuna miki cewar ke bakya gabansa, a sanadin sa kika
kusa rasa rayuwarki kuma har kikayi jinya kika gama shi ki wani nasa babu wanda ya tako yazo yaga ya
kike sai surutu da maganganun da suka ringa yawo da su suna faɗan abubuwa marasa daɗi akanki, duk
wannan bai isa ba tunda ya fahimci har yanzun kina yawo cikin duniyar mafarkinki shiyasa ya ɗaura aure
abunsa da wata.
Kin san duk me yasa na tsaya ina miki wannan dogon bayanin kafin na faɗa miki ainihin abinda ya kawo
ni?" Cikin kuka na ce
"Saboda na lura baki da tunanin kanki ba kuma kya gane komai sai abinda zuciyarki ta aminta dashi.
Tuntuni na tsammaci ganin sauyi tattare dake amma akasin haka na lura a maimakon sauƙi kullum
al'amuranki ƙara lalacewa sukeyi. A cikin zuciyarki nan na tabbatar duk lokacin nan kina jiran Bilal ya zo
ya lallasheki ya faɗa miki maganganu dai dai da waɗanda kike so kiji daga nan ku shirya ku koma shiyasa
kika zaɓi haɗiye baƙin cikinki ke kaɗai kika ƙi gayawa kowa dan kar hakan ya saka a baki shawarar ki
haƙura dashi ko?"
"Eh mana, Tunaninki kenan saboda har yanzu ƙwaƙwalwarki bata hasko miki illar rayuwar da kike ciki ba.
Halima babu iyayen da zasu so yar su tayi aure ta dawo sai dai idan abun yafi ƙarfin su domin burin
kowanne iyaye ne yayansu suyi aure a inda zasu rayu cikin aminci da walwala da kuma mutuntaka
wanda gaba ɗaya kika rasa. Ko wanda bai sanki ba kuka haɗu a hanya ya kalle ki in dai maganar nutsuwa
akeyi ta bayyana ƙarara baki da ita. Ko shekara talatin baki cika ba kin ɗorawa kanki hawan jini harda
kumburin zuciya akan namijin da kina raye ma ya wofantar dake ya auri wata balle kuma ki kashe kanki
saboda dashi bana zaton ko a addu'a zai ringa tunaki.
Ba shawara nazo baki ba, kamar yanda na tsaya tsayin daka na haɗa ki da shi haka yanzu nake so ki rama
mun nima ki faranta mun zuciya ta hanyar rabuwa dashi. Da na so na kira shi da kaina ya bani takardar
sakin sai dai kuma na tuna bani da sauran mutunchi a idon sa ko na kira shi ma ba zuwa zai yi ba tunda
mun sha haɗuwa a ƙofar gidana ma ya kalle ni na kalle shi ya wuce ba tareda ko ci kanka ya ce mun ba
balle kuma in ɗaga waya na kirashi ai sai abunda kuma na gani. Dan haka ko ki kirashi ko ma duk ta
yanda kika san saƙo zai fi saurin isa ki gaya masa kada ki kurkura satin nan ya ƙare kina cigaba da amsa
sunan matar sa a cikin gidan nan".
Tunda ya fara maganar kuka na ya tsaya tsak, yanda kasan zuciyata zatayi tsalle ta fito haka naji sanda ya
ce wai Bilal ya rubuto takardar saki ya kawo mun, ganin ya miƙe tsaye alamar ya gama magana daƙyar na
lalubo yawu na jiƙa maƙoshi na kafin na samu na fizgo maganar data tsaya mun a wuya na ce
Zumbur na miƙe kamar wacce aka tsikarawa Allura na shiga zagaye ɗakin ina nanata Innalillahi wa'inna
ilaihi raji'un, nayi zagaye ya kai hamsin kafin na zube gefen gado lokaci ɗaya na fashe da kukan rashin
mafita. Ya Abba zaiyi mun haka? Na ɗauki tsayin lokaci ina kukan kafin na fahimci hakan ba zai sama
mun mafita ba, falo na fito, Mama, Mu'azzam da Imam suna zaune gabansu ƙaton tray da gasasshen kifi
suna ci suna hira cikin nishaɗi irin su basu da wata matsala a rayuwarsu. A gaban Maman na zube na
kama guiwarta lokaci ɗaya na fashe da kuka har jikina yana jijjiga tsabar yanda nake janyo kukan tun
daga can ƙasan raina, ta sauke Sharifa daga kan cinyarta jiki na tsuma itama ta kamoni tana cewa
"Menene?" Ban iya ce mata komai ba in banda kukan dana ƙara ta hanyar ɗaga murya, Mu'azzam ya ce
"Wlh sai Allah ya saka mata wannan faɗuwar gaban da kike sakata, banda tsabar iskanci kawai idan kika
bushi iska sai ki hau kuka duk ki ɗagawa mutane hankali ke ko shekarunsu bakya dubawa? Ai gasu nan
kema kin haifa idan da daɗi abinda kikeyi zaki ji wata rana" yayi tsaki ya miƙe zai bar gurin dai dai nan
Abba ya shigo falon, ban yarda na kalle shi ba ina jin sa yana cewa Mu'azzam ɗin
"In sha Allahu yaranta ba zasu mata haka ba ita ma ɗin da takeyi mun yafe". Ya ƙarasa ya zauna kan
kujera ban saki Mama ba haka ban daina kukan ba sai da ya daka mun tsawar da tunda nake ban taɓa jin
ko wani can a waje yayiwa ba balle mu ɗin, cikin tsawa yace
"Saketa ki tashi daga nan sakaryar banza kawai wacce bata san ciwon kanta ba" ba shiri na saketa na
mataa gefe na haɗe kai da guiwa kamar marainiya na cigaba da kuka, Mama ta ce
"Saboda na ce ta karɓo takardar sakinta gurin wancan yaron ko?" Ya bata amsa, sai ta dafe ƙirji ta ce
"Kai wa ya aike ka?" Ya bita da kallon mamaki da kuma rashin fahimta sai ta ce
"So kake ta saka ka a bakin duniya tace kai ka kashe mata aure? Ai da kayi shawara dani da baka fara
wannan ɗanyan aikin ba". Tsaki yayi ya miƙe yana cewa
"Ni dai na faɗa mata, kuma dama gobe in Allah ya kaimu ta wuce ta karɓo posting letter ta idan ba haka
ba wlh Halima zakiga other side of me wanda baki sani ba tunda naga alamar sako sakon da ake miki ya
saka yanda kika mayar da kanki shashasha kowa ma kike so ki mayar dashi haka" ya wuce ɓangarensa.
Mama ma miƙewa tayi bayan da tace
"Allah ya rufa asiri toh" Imam ko yanda ka san baya falon kifin sa kawai yake ci yana bawa Sharifa, da
yaga kukana zai cika masa kunne ma remote ya ɗauka ya ƙara volume ɗin Tv, haka na ja jiki na sake
komawa ɗaki na cigaba da kuka kamar wacce aka ce za'a fillewa kai gobe. Sai da na gaji kafin nayi shiru
ina jan ajiya zuciya, ciwon da kaina yake mun kuwa ba zai mislatu ba har wani ɗin ɗin nake jin ƙara
kamar ta agogo a cikin kan nawa.
Dare ya tsala kowanne mai rai dake da nutsuwar zuciya yana kwance yana bacci amma banda ni ina dai
kwance akan gadon ina juyi daga wannan kusurwa zuwa waccen na gagara bacci haka nan ƙwaƙwalwata
ta kasa bani haɗin kan da zanyi tunani mai ma'ana da zai sama mun da mafita gashi, da ina da tsarki ne
ma sai inyi sallah ko zan samu nutsuwa. Ina tunanin firgici ne ya matso mun da period dan a lissafi sai
nan da kusan kwana huɗu zai zo amma ɗazu ina shiga banɗaki na ganshi.
Bansan me zanyi ba, umarnin Abba yayi mun tsauri, dukda cewar ni a karon kaina har yanzun ban yanke
shawara dangane da yuwuwar cigaba ko ƙarewar zamana da Bilal ba na bar hakan ne tukunna har sai ni
da shi mun zauna munyi magana ta gaskiya daga nan ne zan yanke hukunci akan abinda ya kamata nayi
amma shi Abba kai tsaye ya yanke nasa hukuncin yanzu yaya ake so nayi?
Idan kuma ya zama duk abinda Hafiz ɗin ya faɗa ƙarya ne ko ma duk abinda ya faru tsakaninsa da Jalilan
setup ne fa tunda ai da bakinsa ya ce basu san ya sani ba toh ta ina ya sani kenan bibiyarsu yakeyi idan
kuma haka ne dama akwai abinda yake so ya cimma shiyasa har yake binsu kenan?
"Amma kuma wace riba zai ci idan yayi hakan?" Ni da kaina na jefawa kaina tambayar da bani da
amsarta. A zahirance ma bani da wata hujja da zan jefa masa kowanne irin zargi domin Bilal bashi da
wani abu da har zai saka mutum irin Hafiz yayi framing nasa. Kuma ko da ace da gaske shirin ne idan
dama ba halin sa bane ko yana so ai babu yanda za'ayi ya biye mata tunda babu inda naga alamar ta
masa dole a cikin hirar su duk ba wannan bama ai da ba zai haɗa ta da danginsa ba har tazo duba
mahaifiyarsa da bata da lafiya.
"Ta yuwu ma ita ya aura tunda tana da kyau kuma tana da kuɗi dama kuma ai ya ce shi baya tarayya da
mutumin da ba zai ƙaru da shi ba" na faɗa a fili. Sababbin hawaye ne suka ɓalle mun na koma na kwanta
ina jin ƙuna a ƙirji na, na ringa tuna fuskarta haɗuwar mu a asibiti fara kyakkyawa mai diri duk hassadar
mutum bai isa ya kushe halittarta ba. Ji na ringayi tamkar numfashi na zai tsaya har saida na tashi zaune,
abunda na tabbatar shi ake kira da kishi ya turnuƙeni, lokaci ɗaya kuma hotunan waccen ranar suka
shafe na kyakkyawar fuskar Jalilah da nake gani, muryoyin da sukayi musaya suka shiga mun amsa
kuwwa a kunne, hannu biyu na saka na toshe kunnuwana na fashe da kuka mai sauti.
BILAL
Hankalinsa ya kwanta yanzu saboda ya samu nutsuwa akan kokonton dake neman hargitsa masa lissafi
akan Zulaiha. Dukda dama zuciyarsa bata yarda zai samu akasin abinda yake tsammani daga Zukaihan ba
sai dai canjin halayyarta na lokaci guda ne ya bashi tsoro, amma zuwan da yayi jiyan da hirar da sukayi ya
kwantar masa da hankali dan har haƙuri ta bashi sosai kamar zatayi kuka akan ɗaga masa muryar da tayi
a waya. Sun daɗe suna hira sosai irin yanda suka saba, da zai tafi ya shiga suka gaisa da Ummansu, har ya
miƙe ta dakatar dashi tana cewa
"Dama yan uwana ne sukayi magana akan suna so suje ganin gurin da zata zauna". Kansa na ƙasa dan
bala'in kunyarta yakeji har mamaki yake yanda bayajin nauyin Mamansu Halima irin yanda yakejin ma
Umman Zulaihan.
"Dama zuwa wani satin nake so idan an ƙarasa gyaran gurin nayi magana je a gani" ya bata amsa, ta
muskuta tana gyara hijabinta tace
"Toh madallah, kasan da yake sune jikokin ya mace na farko ni a gidanmu da za'a fara aurarwa duk
yayyena matan yayayensu maza ne shine fa kowa hankalinsa yana kan bikin nan, ga zancen kawo lefe
ma kasan abunka da masu ƙaramin ƙarfi sai anyi tanadi ya kamata idan za'a zo afaɗa da wuri saboda a
tanadi abun tarbar baƙi, su dai na Nuratu sun ce Asabar ta sama nan da sati biyu kenan da kawo lefen da
tariya duk rana ɗaya dan ya ɗauke ta ma sunje gurin tela an gwadata a ɗinke zasu kawo abunsu. To itan
ma ya kamata kaga mu sani in kuma kuɗin za'a bayar ma duk kaga sai a san shirin da ake ciki" ta ƙarasa
tana sosa kai kamar wata mara gaskiya.
"Ai Umma munyi magana da ita tace kince ba sai anyi lefe ba kawai ayi mata kayan ɗaki da kuɗin". Yanda
ta zaburo tace
"Inji ubanwa? Yaushe mukayi haka da ita?" Sai da abin ya bashi mamaki domin a iya saninsa da ita
kullum muryarta a ƙasa take fuskarta washe da fara'a. Itan ma da sauri ta gyara zama bayan da ta
fahimci abinda tayi ta shiga kame kame tana cewa
"Na rasa yaushe Zulai ta koyi magana biyu, ni bamu taɓa zancen lefe da ita ba, Mijin Nuratu dai da ya ce
ko yayi mata kayan ɗaki a madadin lefen to kuma yayyina suka ce Aa ai ba'a haka, za'a mata daidai ƙarfin
mu duk abinda bai masa ba daga baya ya sake mata toh ni dai iya zancen da nasan anyi kenan shine ta
canza magana ashe ta gaya maka haka ni yarinyar nan ganinta nake kwana biyu ma kamar wacce iskoki
suke taɓawa yanzu zata birkice ta fara masifa abunda ba halinta ba ko kuma duk zullumin auren ne ban
sani ba".
*KURA A RUMBU*
*Wattpad @MaryamahMrsAm*
*Ban yarda wani ko wata ya juya mun labari ta kowacce siga ba tare da izini na ba*
*Kuɗin karatu yana wakiltar mutum ɗaya ne, kiji tsoron Allah karki ɗauki hakkina ta hanyar fitar mun da
littafi*
*KURA A RUMBU littafin kuɗi ne, a biya naira 800, biya a asusun*
*1840175439*
*Access bank*
*PAGE 42*
A yayinda muke shirin kammala wannan littafi idan har kin san kina karantawa ba tareda kin siya ba kiyi
ƙoƙari ki sauke nauyi domin babu lallai in yafe haƙƙina 🙏🏽🙏🏽
"Yanzu dai Umma wanne ake so a ciki? Lefen ko kuma kuɗin za'a bayar ko ayi mata kayan yanda tace?"
"To ai ni ba na ce ba, kaga ita Nuratu dai kayan tace tana so to ita ya kamata ka tambaya itama kaji
wanne tafi so" ta bashi amsa sai ya girgiza kai ya ce
"Ai na gaya miki yanda mukayi da ita, dama kuma ni na ɗauka ma kunyi shawarane shiyasa ban tuntuɓe
ki ba dan har na bayar da aikinma, kawai ki faɗi wanda za'ayi a ciki tunda kince tariyar Nuratu nan da sati
biyu kamata yayi duka a haɗa ai ba wai ayi daban daban ba"
"Toh inaga a bayar da kuɗin ko dan naji Nuratu nata ƙorafi kayan duk masu duhu aka aka saka mata
inaga ya manta bai faɗawa musu haɗo kayan baƙa bace" ta faɗa tana yar dariya, wayarsa ya zaro yana
cewa
"Toh idan akwai account ɗin wanda za'a turawa kuɗin a kusa a kawo idan babu kuma sai ta tura mun in
fara saka mata wani abu kafin ƙarshen sati na cika dan na rigada na bayar da kuɗin kayan Wallahi yanzu
kuma ko nace musu na fasa ba zasu dawowa mun da kuɗin ba sai dai na nemi wani ya siya tunda
kamfani ne"
"Ai ka tura mata a Opay ɗin ta kawai tunda tareda Habiba ƙanwata zasuje kasuwar dama" cewar
Umman, sai yayi murmushi yace
"Ai kuɗin da yaww Umma idan aka saka mata a opay rufewa zasuyi account ɗin nata ba zai ɗauki kuɗi da
yawa ba"
"Ai kuwa yana ɗauka kwanaki can naji tace anyi buɗa mata shi har maliyoyi ma za'a iya sakawa a ciki
yanzu amma bari dai tazo muji kar ayi gwari" Umman ta sake faɗa kafin ta shiga ƙwalawa Zulaiha dake
laɓe tsakar gida duk tana sauraronsu kira. Sum sum ta shigo ta tsugunna daga bakin ƙofa, Umman ta ce
"Wai akawun ɗinki nace kamar naji kwanaki kince an buɗa miki shi zai iya ɗaukar kuɗi da yawa?" Da kai
ta amsa ganin Bilal ɗin yana kallonta, danne danne yayi a waya ya ɗago ya cewa Umman
"Na tura da miliyan biyu, idan na samu yanda nake so zuwa ƙarshen sati zan ƙara mata miliyan ɗaya idan
kuma bata samu ba zan saka ɗari biyar amma fa duka da kuɗin lefe dana sallamar amarya". Yanda kasan
Umman zata kwanta tsabar murna ne ko meye oho haka ta baza hijabi ta shiga masa godiya ƙarshe ta
fashe da kuka tana jera masa addu'a. Sai da ya sake ajiye mata cash na dubu ashirin daya ruƙo dama zai
mata ihisani kafin suka fita tareda Zulaiha zata rakashi.
Rungumeta yayi da suka isa soro ta janye tana wani ɓata fuska, bai haƙura ba ya sake kamota yana
dariya ta kuma janyewa tana cewa
"Ni dai bana so ni da kacewa yar iska daga gwada abinda aka ce idan ina maka zaka ƙara so na"
Ya ruƙo hannunta ya ce
"Banda sharri mana baby a yaushe nace miki haka? Kuma ai gaskiya aka faɗa idan kina mun hakan zan
ƙara sonki kawai na jiye miki tsoro ne kar na kasa riƙe kaina na haɗa Umma da gashin amarya" ya ƙarasa
yana kashe mata ido ɗaya, rufe fuska tayi da hijabinta cikin jin kunya tana dariya ya saketa yayi waje tabi
bayansa, sai da suka isa gurin mota ta sake haɗe fuska. Da mamaki yace
"Wai menene haka kuma? Minti kaɗan kina fara'a anjima ki haɗe rai ko dai dagaske ne da Umma tace
tana zargin iskoki suna taɓa ki?"
"Ni ba wasu iskoki kaine kayi mun laifi" sai ya tattara hankalinsa kanta ya ce
"Ba kaine kawai ka tashi ka haɗa kuɗin kayan lefe da na sallamar amarya ba? Yanzu wlh sai iya abinda
suka ga sama suka bani ni dai da kayi shawara dani Allah ba haka za'ayi ba".
Ajiyar zuciya ya sauke dan ji yayi hankalinsa ya tashi da tace wai ya mat laifi, shi fa baya son ɓacin ranta
Allah ma ya sani. Hannayenta ya kamo cikin kwantar da murya ya ce
"Shikenan kuma sai ki ɗaga mun hankali kice wai nayi miki laifi akan ɗan wannan maganar?"
"Oh yar magana ce ma a gurinka kenan?" Ta faɗa tana taɓe baki kamar me Shirin yin kuka. Zagaywa yayi
da ita ya buɗe mata sit ɗin mai zaman banza kafin ya dawo ya shiga driver sit ya tayar da motar suka fita
daga layin. Gadon ƙaya sukaje ya siyo mata shawarmar daya san tana so a hanya suka sasanta bayan da
suka daddale akan sai dai fa ya bayar da 3M ɗin nan idan ya so ta ɗauki 500k na hidimarta dan ta san
duk kashe kuɗin zasuyi ba za'a bata komai ba. Sauketa yayi ya juya yana tafe a ransa yana mamakin
dama Zulaiha ta san kuɗi haka?
A sanin sa da ita ko kyautar 20k ya mata a dunƙule sai tace sunyi yawa ya rage shiyasa idan ya tashi
kawai yake siya mata duk wani abu da yasan zata siya da kuɗi idan ya bata idan ta kama zai bata kuɗin
kuma baya wuce 5k tunda tun tana 200L ya samar mata mai Adaidaita da yake kaita makaranta ya kuma
ɗakko kuma yana saka mata Airtime da Data kusan duk sati dan haka ba wani abu zatayi da kuɗi ba
amma ita ce yau suke ja'inja har tana cewa 500k ɗin ma manaji zatayi dan ba isarta zatayi ba. Kamar ya
biya gidan Hajja sai kuma ya fasa dan ɗazu da safe da yaje ko arziƙin amsa sallamar sa ba tayi ba daga
ƙarshe ma ɗaki ta shige ta barshi fushi take bilhaƙƙi dashi amma ya san zata sakko nan ba da daɗewa ba
dan Hajjan bata iya dogon fushi dashi.
Halima ta faɗo masa a rai yayi ƙaramin tsaki a fili, idan so samu ne ta dawo kafin Zulaiha ta tare amma
kuma yaga tana nema ta kawo masa wasa itama sannan ga Hajja yanda take akan tsini yanzu bata huce
daga wannan fushin ba amma kuma gara tayi lokaci ɗaya ta gama a wuce gurin tunda dai gaskiya a
wannan karon sai dai tayi haƙuri amma ba zai iya sakin Halima ba ya san kuma har a gurin Allah baiyi laifi
ba tunda dai Haliman nan babu abinda tayi mata. Shi yanzu duk kewar yaransa ce ma take addabarsa
dan tun ranar daya kaisu gidan bai sake ganinsu ba, Al'amin ma a bakin malamin makarantarsu yaji wai
anzo an karɓar masa transfer sai ƙarya ya gilla masa ya ce eh ya koma can gidan kakanninsa ne da zama.
Daya isa gida falon Halima ya shiga, gurin tsaf tamkar tana ciki dan duk bayan kwana biyu sai ya share ya
goge ko ina ya kuma kunna turaren wuta dake winduna a rufe suke kuma babu zurga zurga sai turaren
ya sake kama gurin sosai. Ɗakinsa na nan ya shiga ya cire bedsheet ɗin kan Gadon ya canza wani dan yau
ɗin kawai yaji a nan yake son kwanciya, wanka ya shiga yana Allah Allah ya fito ya kirata yana wankan
yana shirya maganganun da zai faɗa mata a ransa, yana jiyo wayarsa na ƙara ya san ba zai wuce Zulaiha
ce take kira ba, sai da ya gama shiryawa kafin ya ɗauki wayar ya tarar da missed calls uku na Zulaiha
ɗaya sai na Jalilah guda biyu.
Murmushi yayi yabi bayan kiran Jalilan, dole ce kawai zata raba shi da ita ba dan yana so ba amma Jalilan
hannunsa ce ta kowanne ɓangare kuma da ce yana da tabbacin shi kaɗai take kulawa da zai iya danne
zuciyarsa ya aureta dukda ya san ba zai taɓa samun nutsuwa ba saboda kullum zuciyarsa zata ringa saƙa
masa ko da auren nasa zata iya bin wani a waje amma kuma wasu ɓangarorin da yake morarta ya saka
yake jin kamar zai iya haƙuri ya zauna da ita a hakan.
Muryar da take masa magana kaɗai a yan sakanni take hargitsa masa lissafi balle aje ga sauran lamura
daga Haliman balle Zulaiha da take nan bagidajiya (a ganinsa 🤣🤣🤣) babu wacce ta kamo ƙafarta a iya
kyau, iya kwalliya, gayu uwa uba kuma iya kula da namiji ta wannan fannin kam dole ma a karya mata
ɗan kwali. Yana can zancen zuci ta ɗaga wayar tana ta Hello Hello harta gaji ta kashe ta kira ya zare
wayar da sauri daga kunnensa saboda ƙara.
"Ina ka shige duk yau baka kirani ba" ta faɗa bayan daya amsa wayar. Kwanciya yayi akan gado ya kashe
murya shima ya ce
"Ba haka nake nufi ba honey tsokanarki naso nayi ban san kuma baki cikin yanayi me daɗi ba, yanzu dai
mai ya samu baby na?" Ya ƙarasa cikin sautin da ya san zai iya samun kanta. Tayi ƙaramin tsaki ta ce
"Ban san me yake damunka kwana biyu ba Bee kawai shiru nakeyi amma gaba ɗaya ka canza, kayi
cancelling tafiyarka a die minute sannan kana sane yau ya kamata na tafi amma baka ko kirani ba balle
kaji yaya nake ciki anya kuwa babu wani abu da kake ɓoye mun?"
Sai da yaji hanjin cikin sa ya kaɗa, duk ƙoƙarin da yakeyi na kada ya kuskure har ya bada ƙofar da zata
zargi wani shiri ashe ya bar baya ba zani, da sauri ya ce
"Kiyi haƙuri Honey pot kin san na gaya miki yanda nake ciki da gurin aiki na gaba ɗaya sun taso ni a gaba
gashi gida ma duk sai a hankali na gaya miki Halima ta tayar da rigima tunda taga chat ɗin mu yanzu
haka ma kusan 1 week fa tana gidansu kin san mutanen mu kuma family kowa ya ɗora mun laifi ana ta
cewa na fara wulaƙantata saboda zan kawo wata".
"Ta hutar da kanta ai sai ka aika mata da takardarta kawai dan dama ko bata tafi yanzu ba zata tafi idan
na zo dan ka san dai ba zan zauna da kishiya ba"
"Amma Babe munyi maganar nan kin ce kin haƙura ke da ba gidan ku ɗaya ba dan Allah menene
damuwar ki da ita kuma?" Ya faɗa kamar zai yi kuka, daga can tace
"Babu dole fa Bee, idan ita ka zaɓa sai kuyi zamanku ai ba cewa nayi ka saki matarka dole ka aureni ba.
Ni dan Allah duk ba wannan ba kazo ka ɗauke ni, kawai sai yau Salis ya sake tura mun da flight ticket ɗin
wai ashe ta Kano ya mun booking na zo kuma anyi shifting flight ɗin sai 8 na safe, duk raina a ɓace yake
wlh kazo ka ɗauke ni na samu nayi wanka ko zan ɗan samu nutsuwa".
Idan da ya san dalilin kiran kenan da ba abinda zai zaka yabi bayan kiranta kai da kashe wayarsa ma zaiyi
gaba ɗaya. A hankali ya ce
"Ayya sorry Babe shine baki kirani tun ɗazu ba kuma?"
"Ai gashi yanzu na kiraka dan Allah idan ba zaka zo ba na nemi taxi zaka cikani da surutunka da baya
ƙarewa" ta faɗa a hasale. Kamar ya ce ta nemi taxi ɗin sai dai ya ce
"Toh mai zai hana ki kama lodge mana anan kawai tunda da safe ne kar kuma kiyi nisa sosai"
"Tun yaushe ka fara shirya mun abinda ya kamata nayi da wanda ba zanyi ba Bilal?" Ta faɗa kamar wata
uwarsa, da sauri ya ce
Tashi yayi ransa duk ba daɗi, kamar ya kirata yace ta hau taxi kawai sai dai kuma baya so ya ɓata rawarsa
da tsalla gara dai su rabu lafiya idan buƙatarsa ta gama cika daga nan shima zai buɗe mata shafin nasa
rashin mutunchin. Haka nan badan ya so ba ya kama hanyar Airport ɗin sha ɗaya harta gota bai yi nisa
ba sai ga kiran Hafiz, sai da ya gangare gefen titi ya kashe motar kafin ya amsa cikin muryar bacci.
"Afuwan na tashe ka daga bacci" Hafiz ɗin ya faɗa, ya sake maƙale murya ya ce
"Ina zaune ne banma san baccin ya ɗauke ni ba". Daga can Hafiz ɗin ya ce
"Dama Jalilah ce ta shigo Kano, ka santa da hayyata ta kirani wai anyi shifting flight ɗin ta zuwa safiya in
samo mata mai Taxi da na sani dare yayi tana jin tsoro ita bata san Kano sosai ba shine na kiraka ko zaka
ma Abokinka me Uber ɗin nan magana idan bai tashi ba dan Allah yaje ya ɗauke ta ya sama mata hotel
nan kusa da Airport ɗin".
"Wai Ammar? Ai ya samu aiki Lagos yana can kusan wata shida kenan ya dena Uber, amma bari akwai
wani da ya ɗauke ni kwanaki nay saving number sa kuma ɗan nan kusa damu ne bari naji idan bai tashi
ba ka tura mun number ta" cewar Bilal ɗin, yana aje wayar kuwa Hafiz ɗin ya turo masa number ya wani
taɓe baki bayan daya kunna motar ya cigaba da tafiya. Rai ɓace ta zauna a motar bayan daya isa, haɗe
fuska yayi shima yana kallonta ya ce
"Na ce miki ina hanya shine kuma kika wani kira Hafiz ya nemo miki Taxi ko?"
"Gida na" ta bashi amsa tana danna kiran layin Hafiz. Fuzge wayar yayi da sauri ya katse kafin ya ce
"Zan gaya masa kazo ne mana" ta bashi amsa tana karɓar wayar, ya zare ido ya ce
"Kinyi hauka amma? Karfe sha biyun zaki ce masa nazo ɗaukar ki me kike so yayi tunani?"
"Oho" ta bashi amsa kafin ya sake magana yaji muryar Hafiz ɗin a speaker yana cewa
"Jalilah sa'arki ɗaya matata bata gari amma ko dan gaba kada ki sake mun irin haka ya zaki ringa kirana
tsakiyar dare?"
"Shikenan mu kwana lafiya ki kula da kanki" ya bata amsa bai jira tace wani abu ba ya katse kiran.
Bilal dake kallonta ya sauke ajiyar zuciya jin bata ambaci sunansa ba can cikin ransa kuma kishi ne ya
taso masa jin yanda take yiwa Hafiz ɗin magana a nutse cikin ladabi kamar me tsoron sa shi kuma yana
wani bata amsa a tsaye, ɗauke kai yayi ganin ta juyo ta kalle shi ta ɗan yi murmushi ta ce
"Akan Hafiz har Malamai na shiga amma shegen guy ɗin nan yanda kasan aljani na kasa samunsa"
"Bafa zan ɗauki wannan wulaƙancin ba ta yaya a gabana zaki ringa gaya mun kina son wani daban a
hakan kike so na aureki?" Ya taso mata, wani shegen kallo ta masa tace
"In aureka dai, ai nice mijin kaine matar ko kai a haka da kake kana zaton ka isa ka aureni?
Banda ma so banzan abu ne Bee ai ka san ni ba tsararka bace ko shi ubangidan naka nafi ƙarfinsa kawai
dai zuciya da baka da iko da ita tayi ta kwaso maka tarkace tana saka ka son su" ta ƙarasa tana soka
earpiece a kunneta. Ya kusa minti biyar yana kallonta yama rasa mai zaiyi ko mai zaice, tunda yake ba'a
taɓa masa zagi irin wanan ba, wato shine tarkace? Lallai Jalilah taga gadon baccin sa.
Haɗiye zuciya yayi ya tada motar, sai da suka fita daga Airport ɗin kafin a ƙufule ya sake tambayarta in
da zai kaita
"Nace maka gidana ko kunnuwanka sun toshe ne kuma baka ji da kyau?" Ta bashi amsa, wlh ba dan ba
sai ya gaggaya mata maganganu kuma ta fice masa a mota amma kuma yanzun dai bai isa ba amma
lokaci na zuwa, daya tuna abinda ya shuka dole ya sauke fushi ya gyara murya ya ce
"Aikin da akeyi a waje meya shafi ciki kuma ina kace an gama fentin cikin tun last week?" Ta tambaya
tana tsare shi da ido, titi ya mayar da idonsa kafin ya ce
"An gama amma ai kin san an kwashe kayan ni kuma da naji kince sababbi za'a zuba shiyasa ba'a mayar
ba dan wasu abubuwan ma na kyautar dasu"
"Su kuma kayana ka kaimun su ina?" Ta faɗa tana tsare shi da ido, kashe mata ido ɗaya yayi ya ce
"Na kaiwa Matata ta ringa sakawa kinga se na ringa ganinta kamar ke"
"Har ta mutu ba zatayi kyauna ba" ta faɗa tana juya ido, ya ruƙo hannunta yace
"Ni shaida ne yar balarabiyata, yanzu dai ina zamuje kinga idanuwanki sun nuna a gajiye kike ki samu ki
huta kar kiyi missing flight kuma goben"
"Muje gidanka toh tunda kace can babu gurin kwanciya" ta faɗa tana kallonsa.
"Gida na kuma?" Ya faɗa da sauri har yana sakin stirring, ta taɓe baki tace
"Zan so in kaiki mana amma kin manta na gaya miki matar gidan bata nan kuma kinga dai unguwarmu ba
kamar in da can gidan yake bane akwai yan sa ido yanzu a ganni na shiga gida da Mace ai na shiga uku a
garin nan bama unguwar ba"
"Ai kuwa ko dubu zaka shiga yau sai dai ka shiga dan wlh ba zan kwana a hotel ba a gida na yi niyyar
kwana tunda kuma ka kyautar mun da kayan gida ba tareda izini na ba sai ka kaini naka gidan ba wai
matarka bata nan ba ko tana nan wlh ba abinda ya mun zafi a nan zan kwana dan dama da baka zo ba sai
dai ka ganni a ƙofar gida kuma ko yanzu ka direni a nan ƙila sai na rigaka zuwa so baki alaikum ka wuce
mu tafi dan ni a gajiye nake wanka nake so nayi na kwanta nayi bacci" ta bashi amsa itama.
Duk yanda ya so ya fahimtar da ita ta masa banza ƙarshe mayafinta taja ta rufe fuskarta kamar me bacci,
ganin har ɗaya ta kusa suna gararanba akan titi bai kuma ga alamar zata canza ra'ayi ba ya saka kawai ya
kama hanyar gida a ransa yana addu'ar Allah ya sa kowa yayi bacci har masu gadin layin. Ya da sauri ya
kalli mirror jin ta ce
"Ga wata mota nan ma tun ɗazu take binka ƙila ma matar taka ce ko wani daya sanka" ta ƙarasa tana
dariya. Kallon motar yayi dakyau, sai tayi masa kama da motar Suhaila matar Hafiz amma kuma number
ta banbanta tata kamar ABJ wannan kuma ABC dukda dai bai tabbatar ba amma ya ƙarfafawa kansa
hakan ne dan ba zai iya hasaso cewa Matar Hafiz ɗin ce ko kuma ma shine da kansa ba iya tashin
hankalin da yake ciki yanzu ya ishe shi. Kamar me motar ya san me suke cewa kuwa yazo ya wuce su
dama a junction suke ya ɗauki wata hanyar daban Bilal ya sauke ajiyar zuciya kafin ya balla mata harara
ya cigaba da tuƙi.
Roƙonta ya ringayi akan ta rufe fuskarta sanda suka isa unguwar, duk wanda ya kalle shi dakyau sai ya
fahimci bashi da gaskiya haka ya lallaɓa ya shige Allah ya taimake shi mutum ɗaya ne zaune sauran masu
gadin duk sunyi bacci get ɗin kuma a buɗe yake dan haka bai ma taso ba tunda ya gane motar daga
zaune ya masa sannu da zuwa ya wuce dama kuma windows ɗin motar tint ne ta gaba ne za'a iya ganin
wanda yake ciki. Sai da ya shige da motar ya dawo ya kulle get kafin ya tsaya ya riƙe ƙugu yana sauke
numfashi. Ta fashe da dariya bayan da ta fito daga motar tana cewa
"Wai yanzu duk tsoron kar yan unguwa su ganka ne yasa ka birkice haka amma baka tsoron Allah kake
bajekolinka a hotel ko?"
"Dan Allah ki wuce ciki kum wlh tun kafin gari yayi haske zamu fita ba zaki zubar mun da mutunchi a
unguwa ba dama duk sun tsaneni tunda Halima ta bar gidan nan" ya faɗa yana wucewa gaba bayan daya
shiga ɗakin tsakar gida ya kunno Solar dan babu wuta tunda sha biyu ta wuce kuma ya san ba dawo da
ita zasuyi ba. Bayan tafiyar Halima da aka fara rashin wuta ya haɗa ta babba har Ac take ɗauka. Kan
kujera ta faɗa tana cewa
"Wash Allah, daɗi na da matar nan taka akwai tsafta ba wanda zaice falon me yara ne kamar na sabuwar
amarya komai na nan da sabuntarsa"
"Basu daɗe ba ai bayan haihuwar Sharifa ta canza su" ya bata amsa yana ɗaukar remote ɗin Ac ya kunna.
Ta miƙe tana ƙoƙarin cire doguwar rigar jikinta tace
"Dukda haka dai tana da tsafta gaskiya" sai ya wuce ɗaki yana cewa
"Ba laifi amma dai ni nake shara da mopping har wankin toilet duka" ta kuwa fashe da dariya tace
Indomie ya dafa mata bayan tayi wanka ya ɗumama Shawarmar daya siyo ɗazu a microwave dama guda
biyu ce ya dafa tea suka ci kafin ta kwanta a Asalin ɗakin Halima da tace gadon irin nata ne na gida dan
haka nan zata kwanta kafin ma ya gama wanke kwanukan da suka ɓata ya tattare falon har tayi bacci. A
falo ya kwanta bayan daya leƙa ta ya tarar tana bacci dan dama cike yake da taraddadin karta nemi suyi
wani abu dan gaskiya ba zai iya ba gaba ɗaya yanzu haka ma a mugun tsorace yake ji yakeyi kamar wani
zai iya shigowa ya tarar dasu yayi mamakin yanda yake ji ɗin dan ko kaɗan bayajin komai idan suka je
can gidan ta ko da yake yan unguwar kallon ma'aurata suke musu irin kamar a wani garin suke zama sai
hutu suke zuwa nan ɗin. Daƙyar bacci ya ɗauke shi yana yi yana farkawa gudun karsu makara gari yayi
haske bai fita da ita daga unguwar ba.
HALIMA
*KURA A RUMBU*
*Wattpad @MaryamahMrsAm*
*Ban yarda wani ko wata ya juya mun labari ta kowacce siga ba tare da izini na ba*
*Kuɗin karatu yana wakiltar mutum ɗaya ne, kiji tsoron Allah karki ɗauki hakkina ta hanyar fitar mun da
littafi*
*KURA A RUMBU littafin kuɗi ne, a biya naira 800, biya a asusun*
*7061838488*
*Opay*
HALIMA
Yanda naga rana haka naga dare, sai naji ashe ma jiya baccin daɗi nayi yaune nake ganin asalin baƙin
dare. Sai da aka idar da sallar asuba kafin na samu bacci ya fizgeni, sai dai ban wani yi nisa ba na farka
sakamakon kiran suna na da nake ta ji anayi.
Na tashi zaune daƙyar ina matse ido haɗi da dafe gefen kaina da nake ji kamar zai faɗo saboda ciwo.
Mama na tsaye ta ce
"Hala kin manta abinda Abbanku ya faɗa miki shiyasa kika shantake kina bacci har ƙarfe tara".
Gabana ya yanke ya faɗi, mai take nufi? Takardar ya turo ta karɓa ko me?
Muryata bata ko fita sosai saboda uban kukan da nasha jiya ga bacci da ciwon kan da suka mun rubdugu
na ce
"Kin yafe ba zakiyi bautar ƙasar ba kenan in je na gaya masa?" Ta katse ni. Na tabbatar har kunnuwanta
ƙarar ajiyar zuciyar da nayi ya isa jin ba abinda nake tunani bane, ta ja tsaki ta fice daga ɗakin tana cewa
"Ki tashi ki shirya tun ranki bai sakw ɓaci ba dan wlh a cike yake dake kin kuma san dai bai iya fushi ba".
Ina wanka ina hasaso ta inda zan samu mafita cikin wannan tsaka mai wuya da Abba yake ƙoƙarin jefa
ni. Yanzu shi ba bu ruwansa a ringa cewa aure na ya mutu kenan? Na tafi tunani dangi na uwa da uba
babu wata bazawara kamata, yawanci ma har manyan mutuwa ce ta rabasu da mazajensu ba sakin aure
na shikenan ni zan zama abar buga misali a dangi da unguwa, fatan da aka ringa mun zai tabbata na san
ƙila labari na babu inda ba zai kai ba har Facebook da Whatsapp groups.
Kan toilet na zauna na sha kuka na godewa Allah kafin na fito na sake zama kan gado na rafka tagumi.
Allah ya sani ina son Bilal, rabuwa dashi abu ne da ban taɓa hasasowa a nan kusa ba duk da abinda ya
faru yayi silar zabtarewar sama da kaso hamsin na yanda nake jin sa a zuciyata amma in ce na dena son
sa wannan ƙarya kawai nakeyi.
Hannu biyu na saka ina goge sababbin hawayen da suka ɓalle mun, da kaina kuma na shiga tugumar
kaina anya kuwa nayiwa kaina adalci idan na cigaba da son Bilal?
Babu wani abu da zan ɗorar a zamana dashi wanda zan dogara akansa har ya bani ƙwarin guiwar sake
bashi dama a karo na biyu bayan abinda ya faru. Ya gwada mun halayen ni da kaina na yarda zuciyar
dake cike da so ba zata aikata irin su ba abu mafi muni ya ci amanata a bayan ido na yana mu'amala da
macen banza sannan ya tozartani akan hakan har mahaifiyata yayiwa zagi mafi muni kuma dukda haka
nake jin zan iya yafe masa na cigaba da rayuwa dashi.
Ƙasa na durƙushe na sake fashewa da kuka ina nanata "Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un". Tabbas ina cikin
masifa ni kaina na sani ta yaya wanda ya aikata mun irin waɗannan zunuban zan cigaba da dakon
soyayyar sa a raina?
"Halima wai ba zaki ko duba ƙananun yayanki kiyi tunanin halin da zasu shiga idan babu ke ba kin dage
lallai sai kin ja wa kanki ciwon da zai kashe ki ko?" Ta faɗa tana kallo na, ban ɗago ba sai kukan da na
cigaba da yi, tayi ƙaramin tsaki ta ce
"Mu'azzam yana da uzuri kin zaka ya tsayar dashi ya ce ya kaiki idan ba zakije ba ki fita ki gayawa Abba
ya sallame shi ya tafi sabgar sa dan Allah"
"Mama kin dena so na, kwata kwata yanzu kin dena damuwa da abinda ya shafe ni kenan idan ma na
mutu yarana ne kaɗai suka rasa banda ke" na faɗa cikin kuka. Tayi ƙaramar dariya tana nufar ƙofa tace
"Mutum kuwa ya taɓa haifar ɗa a cikin sa yace ya dena sonsa Halima? Ke ɗin ce ai kin zama gomnati ba'a
miki kutse yanda aka dama da nace yaranki kuma kinga ai su ke kaɗai gare su ni kuwa Alhamdulillahi ku
huɗu Allah ya bani dama kuma daɗin haihuwar da yawa kenan idan wani bai faranta maka ba wani zai
saka ka farinciki. Ni dai idan ba zakije ba kije ki faɗa masa dan Allah ya sallamar mun yaro ya tafi dan shi
yana da abubuwan yi da zasu taimaki rayuwar sa".
Wato ni ce wadda bata da abinyi da zai taimaki rayuwata? Haka nan na haƙurtar da kaina na saka kaya
ban ko nemi mai ba balle aje ga batun turare ko in yi kwalliya, sai sa na gama shiryawa kuma sannan na
tuna ai Khaki ya kamata na saka kuma ban taho dasu ba suna can gidan Bilal.
Har raina naji daɗi dan dole ai yanzu a fasa fitar, falon na fito, ina buɗe ƙofa muka haɗa ido da Abba
dake tsaye da alama kuma ni yake jira. Kamar munafuka sum sum na zube a ƙasa murya ba amo na shiga
gaishe shi, bai amsa ba sai cewa da yayi cikin dakewa
"Tashi ku tafi".
"Idan sun dawo sai ta karya yanzu Mudassir ya kirani mutumin yana ta masa waya".
"Sai ku wuce ku tafi ai" Mama ta faɗa, na miƙe kamar kazar da aka tsamo daga ruwan zafi na nufi ƙofa
Abban ya dakatar dani yana cewa
"Suna can gidan ai" na bashi amsa ina kallon ƙasa. Da hannu ya mun alamar mu je, Mu'azzam yayi caraf
ya ce
"Bafa zasu barta ta shiga a haka ba yanzu doka na aiki ko colored hijan ba'a shiga dashi secretariat balle
taje musu da kayan gida, kalli shigar da ta yi ga fuskar ta duk a kumbure ɗauka za suyi ma mabaraciya
ce".
"Kuma dai? To sai ku bari sai gobe ai a cigita ko a cikin unguwa ai ba za'a rasa masu service ɗin ba su
bata aron uniform ɗin kan ta ɗinka wani" Mama t faɗa, sanyi na ji har raina sai dai kuma murnata ta
koma ciki jin Abba ya ce
"Tunda uniform ɗin makaranta ne da zaki ce ta aro? Su biya ta can gidan ta ɗakko ko babu muƙulli a
hannunki?" Ya ƙarasa yana kallona. Yau ɗin ganinsa nake wani daban kamar ba Abba na mai yawan
fara'a da wasa da dariya ba, da sauri na ɗaga masa kai alamar akwai kafin na juya cikin ɗaki na ɗakko
muƙullin dan yana ajiye dama a kan mudubi.
Har muka isa layin gidan ci kanki Mu'azzam bai ce mun ba nima kuma tawa ta ishe ni tunda na haɗa kai
da window ban ko motsa ba sai da naji ya tsaya na duba na ganmu a ƙofar gidan.
Karki ɓata mun lokaci Malama" ya faɗa yana wani ɓata rai kamar shine gaba dani, haka nan na ringa jin
wani iri a jikina. Na kalli layin daga farko har ƙarshe ina tuna ranar da na bar gidan. Sammani mai gadin
gidan Maman Yusuf ya taso da sauri gani na, dole na ƙago murmuyna ɗora akan fuskata sanda muke
gaisawa ya ce
"Abu nazo ɗauka dai amma dan Allah karka gayawa su Maman Yusuf na zo dan sauri nakeyi ba zan samu
damar shigar musu ba" na bashi amsa. Yana shafa kai ya ce
"Ai bata nan ma Hajiyar tana Umarah, Amarya kuma ai ta bar gidan kin san Alhaji ya ƙara aure shine ta
tayar da rigima har dai sai da ya saketa yau kwanata huɗu da tafiya ita Hajiya tana can Saudiyya ma duk
bata san meya faru ba".
"Allah ya rufa asiri" na faɗa ina zura key a jikin ƙofa har cikin raina kuma banji daɗin sakin Maman
Khadija da ya ce anyi ba, na tuna yanda suka ringa kirana a waya suna bani baki akan nayi haƙuri na
dawo aure duk zaman haƙuri akeyi dan duk a zaton su da sauran yan unguwa sakina Bilal yayi ashe itama
nata sakin na tafe.
Ganin motar sa ajiye ya saka nayi turus dan ban zaci zamu iya samunsa a gidan ba musamman tunda yau
ɗin akwai aiki kuma lokaci ya fara ja dan sha ɗaya har ta gota. Ji nayi kamar an ƙara bugun da zuciyata
take yi, na yi taku biyu da niyyar in basar amma naji ba zan iya ba. Komawa nayi waje, ba tareda na kullo
ƙofar gidan ba na buɗe mota na shiga.
"Yana gidan ba zan iya shiga ba" na bashi amsa ina dafe ƙirji na da hannu biyu saboda yanda bugun da
zuciyata yakeyi na ke jinsa kamar numfashi na zai ɗauke. Tsaki yayi ya kashe motar ya fita yana cewa
Sai da ya shiga gidan kafin nayi ƙarfin halin bin bayan sa. Banyi mamakin ganin ƙofar falon a buɗe ba
tunda ga motarsa a gida, babu kowa a ciki ko ina tsaf tsaf hakan kuma ba sabon abu bane a guri na
tunda na san wanene Bilal gurin tsafta. Ɗaki na na wuce Mu'azzam kuma ya tsaya, nayi turus ganin kan
gadon a hargitse alamar ba'a jima da tashi daga bacci ba ga kuma wani ƙamshi da nake jin kamar ma
sanshi a wani guri.
Bugun zuciya ta ne ya ƙaru sai dai ban bari tsoro da firgicin dake taso mun sunyi tasiri ba na wuce in da
na ajiye ledar kayan tun ranar da na je camp na ɗauka na buɗe su har sun fara warin ajiya dama ga warin
sabuntaka suna yi.
Kayan jikina na cire na saka KHAKIn, yanda ka san kyanwa haka nayi wata yar tsurut a cikinsu. Dama
sunyi mun yawa tun ranar dana dawo na duba naga over size ne, nayi niyyar na bayar a rage mun sai dai
kuma ban samu damar hakan ba abinda ya faru ya wakana. Cikin kayana na buɗe komai yana nan yanda
na barshi na ɗakko Abayar da na tanada saboda fita da Khaki na saka sannan na ɗakko farin PLAIN VEIL
cikin waɗanda na siya gurin *MARYAM ALL IN ONE EMPORIUM*. Hansa'u ce ta haɗa ni da ita lokacin da
muka taɓa yin hira nace mata ina so na fara gwada kasuwanci tace mai zai hana na gwada siyar da
mayafi musamman *PLAIN CHIFFON VEILS* da kasuwar su take ci a yanzu gurin yammata da matan
aure. Shine ta bani number ta na siyi half dozen na amfani na kafin na samu kuɗi na saro wanda zan fara
siyarwa.
Na yaba da kyawun yadikan da kuma quality domin idan ba an faɗa maka ba zaka iya ɗauka irin na Egypt
ne. Abinda ya fi burgeni sauƙin farashinta domin har tambaya nayi naji yana ƙasa da na kasuwa kuma ya
fi shi kyau ga colors irin wanda sai kayi zuwa nawa kasuwar ma baka samo su ba ƙarin daɗi tana delivery
zuwa ko ina a faɗin Nigeria abinda kuma ka siya shi za'a kawo maka.
(Yar uwa mai neman sana'ar da zaki gwada kin san dai yanda kasuwar mayafai take ci a yanzu
musamman PLAIN CHIFFON, ga in da zaki sara a ɗinkensu anyi packaging sai dai kawai ki tallata ki siyar
ba ruwanki da wuni a sabon gari ko kwari gurin sarin mayafi.
Masu siyan ɗai ɗai muna maraba da ku muna da kowanne size daga smalla, medium har big bayan haka
muna sa sauran kalolin luxury mayafai sai iya wanda kika zaɓa. Muna Kano muna aika kaya ko ina a faɗin
ƙasar nan da yardar Allah a tuntuɓe mu kai tsaye akan *09064960666*).
Na ninke kayan dana cire na saka su a leda, already dama na siyi farin cambass shi na ɗakko kan shoe rag
na saka dan waɗanda aka bani duk sunyi mun yawa. Wayata ta shiga ƙara na duba naga Mu'azzam ne na
san zaice na daɗe dan haka ban ɗauka ba na fita daga ɗakin.
Yana ganin na ya juya fita dan dama tsaye yake a bakin kofa, na waiga ina kallon falon kamar bana so na
fita daga cikin sa har hawaye ne ya tarar mun. A garin kalle kallen na hango can ƙasan kujera.
Ji nayi kamar an doka mun guduma a tsakiyar kaina, na saki ledar hannu na a ƙasa kafin na nufi gurin da
sauri dan tabbatar da zahiri nake gani ko kuma gizo ido na yake yi mun?
Ɗauka nayi na shiga ƙare mata kallo tsabar yanda zuciyata take bugu tamkar zata fito ta baki, ko a
lokacin da nake shayarwa duk yanda ƙirji na yake cika ban taɓa saka girman wannan size ɗin ba balle na
yi tunanin ko tawa ce na, kai ni ban ma taɓa ganin irin design ɗin ba dan ko da nake a rikice tar na gane
designer ce mai tsada ga kuma irin ƙamshin da na ringa ji a cikin ɗaki na nan a jikinata.
Sakinta nayi a ƙasa dai dai sanda na sakeyin wani mugun ganin, ɗan kunne, agogo harda zobe na mace
akan center table. Da baya na ringa tafiya ina jin kamar ana zare mun laka, kaina ya cushe ta yanda na
gagara tuna komai da ya kamata nayi a lokacin.
"Bilal ya ƙara aure" maganar Hafiz ta shiga dawo mun. Yaraf na zube kan kujera na dafe kaina da naji ya
mun wani yammm kamar an barbaɗa mun yaji.
Ban san tsayin lokacin da na ɗauka a zaune ba, nesa nake jiyo muryar Mu'azzam yana mun magana
amma ban fahimci komai ba sai bin sa da na ringayi da kallo, can kuma kamar an tsikareni na miƙe na
fice daga falon da sauri ya biyo ni yana kiran sunana amma ban tsaya na sai da na dangana da falon Bilal.
Taimakon da ubangiji yayi mun tsayuwar Mu'azzam ɗin bayana na tabbata ba dan haka ba yanda na tafi
idan da ace na samu nasarar kaiwa ƙasa tabbas a wannan karon babu lallai in warke domin da wahala
idan ban samu paralyze ba. Dukda yanda nake jin jikina tamkar an saka mun shocking haka na fizge daga
riƙon da Mu'azzam ya mun na juya baya domin na hana idanuwana cigaba da arangama da mummunan
ganin da nayi.
Bai sakeni ba sai rungumeni da yayi lokaci ɗaya na fashe da kukan da komai dakewar zuciyar mai sauraro
sai ya tausaya mun. Idanuwana a rufe suke amma hoton mugun abinda na gani yana nan tar tamkar a
lokacin nake kallo, Bilal kwance kan cinyar wata mace da ban san matsayinta gare shi ba tana shayar
dashi tamkar jariri.
A yanda nake a jikin Mu'azzam ya ringa tafiya da ni har ya sakani a mota, yanayin sa kaɗai ya bayyanar
da shima ya shiga shock da abunda muka gani. Sama da minti goma muna zaune a motar ni ina kuka ahi
kuma ya riƙe haɓarsa ya zurawa gaban motar ido.
BILAL
Bacci rabi da rabi yayi saboda alarm ɗin daya saita tun ƙarfe huɗu domin baya son wani dalili da zai
janyo har tsautsayi ya gifta gari yayi haske bai fitar da Jalilah daga unguwar ba. Tun kiran farko yayi
wanka ya zauna yana jira a kira sallah, ana fara kira kuwa ya shiga ɗakin ya fara tashinta amma tayi masa
banza sai ma gyara kwanciya da tayi, cikin ƙufula da halinta ya ce
"Dan Allah ki tashi, kin san dai yanzu zakiga gari yayi haske idan kuma ba so kikeyi ki makara ba". Bata
amsa ba ya gaji da tsayuwa yana mitar ta tashi jin har an tayar da sallah ya sa ya fita yana sakin ƙwafa,
shi yanzu ya ke tunanin kamar ma da biyu tace sai a nan zata kwana saboda taja masa wani bala'in a
unguwa. Hawa uku ya murzawa Get muƙulli kafin ya tafi, yana idar da sallah kuwa bai zauna ba ya fito da
sauri ya koma yana tafiya yana satar kallon mutane gaba ɗaya ya tsargi kansa gani yake kamar kowa ya
san mace ta kwana a gidansa a haka ya shige ya sakw kullo ƙofar ta ciki.
Duk yanda yayi da Jalilah akan ta tashi tayi sallah ta shirya su tafi taƙi ƙarshe ta balbaleshi da masifa akan
ya fita ya bata guri saboda tazo gidansa ne zai uzzura mata ya hanata bacci ai ta san da tafiyar babu
kuma sisinsa cikin kuɗin data biya balle yace idan ta rasa jirgi zata ja masa asara.
"Aikin banza kawai saboda na zo wannan akurkin gidan naka shine zaka ringa mun ihu akai in tashi to ba
zan tafi ba idan kana da ƙarfi ka ɗauke ni a wuya ka fita dani kuma wlh idan ka ishe ni sai in tashi na fita
ƙofar gida ka san ni sarai tijara zan maka nace ka kawoni kwanan gida ka hanani kuɗi na idan ya so sai
naga ƙaryar iskanci" ta faɗa tana balla masa harara.
Tsaf ya zuge bakinsa domin baya shakku zata aikata abinda ta faɗa ɗin haka ya wuce yana waigenta
tamkar zaiyi kuka ya koma falo ya zauna yana kallon agogo. Har ƙarfe bakwai ta gota bata fito ba ita da
tace jirginsu ƙarfe takwas, shahada yayi ya sake komawa ɗakin ya tsaya daga bakin ƙofa yana kallonta ta
tashi tana zaune tsakiyar gadon waya kare a kunnenta.
Murmushi ta sakar masa hakan ya bashi ƙwarin guiwar matsawa kusa da ita, da Mamanta take waya sai
bayan ta kammala ta buɗe masa hannu alamar ya zo, haka ya ƙarasa ya rungume ta ta ɗora kanta a
ƙirjinsa tana cewa
"Jalilah bakwai ta wuce fa kada ki makara" ya faɗa yana ƙoƙarin janyewa sai ta sake shige masa tana
cewa
"8pm ne fa flight ɗin ba morning ba". Yanda kasan ya kurma ihu saboda takaici, duk yanda ya so ya
cigaba da pretending sai da fuskarsa ta nuna ya zameta daga jikinsa yana cewa
Kallon banza ta watsa masa kafin ta miƙe tana banƙarewa ta sigar miƙa ya yi saurin ɗauke idonsa daga
kanta, toilet ta wuce abinta tana wata tafiyar iyashege. Ya zauna gefen gadon yana cika yana batsewa a
ransa yana ayyana yanda zai yi da ita su rabu ƙalau dan ya lura a shirye take data yanka masa nata rashin
mutunchin.
Tashi yayi ya matsa bakin ƙofar toilet ɗin jin tana kiransa, ƙaramin kit ɗin ta tace ta miƙe mata ya wuce
ya ɗakko shi yana buɗe ƙofar da niyyar ya bata ta ja shi ciki duk kuma yanda ya so da ya noƙe ko a jikinta
sai da ya mata abinda take so kafin ta barshi ya fito tayi wankanta. Haka take kamar mayya in dai ta so
abu to fa sai ta same shi ko ta daɗin rai ko aka sin haka.
Falo ya koma ya zauna bayan yayi wanka a ɗayan ɗakin ya dafe kansa da yaji kamar yana so ya masa
ciwo. Allah ya sani tun sanda Halima ta bankaɗo sirrin sa komai ya fita a ransa kuma yayi alƙawarin
dainawa amma kuma ya rasa yanda zai yi da Jalilah dukda ya fara janye mata kuma lokaci kaɗan yake jira
dama wannan tafiyar da zasuyi ce target ɗin sa na ƙarshe da zarar sun shigo da kayyakin an buɗe
company zai yi duk mai yuwuwa ayi rubutu ta yanda zai mallaki kaso mai tsoka cikin shares ɗin kamar
yanda tayi masa alƙawari idan ya so ko sun rabu ya san ya tsira da abinda zai cigaba da riƙe shi.
Kusan yanzu duk wasu kuɗaɗe da yake da su a hannu sun ƙare sai canji ga hidima kuma a gabansa dan
bayan ya gama da Zulaiha yana so ya yiwa Hajja gyaran gida dan har ya saka an fara duba masa gidan
haya da zata koma shekara ɗaya kafin a gama aikin gidan sannan idan ya samu yanda yake so duk a
shekarar nan yake so ya biya musu shi da ita aikin Hajji. Waɗannan burikan da sauransu ya saka ko ya ji
yana so ya kawo ƙarshen mu'amalarsu da Jalilah nan kusa sai ya sake ƙara mata lokaci.
Wayar sa ya zaro daga aljihu, tun daren jiyan ya kasheta saboda kada a samu tsautsayi Zulaiha ta kira shi
baya kusa a sake maimaita abinda ya faru tsakaninsa da Halima. Kunna wayar yayi, tana gama booting
kuwa messages ɗin Zulaihan biyu suka diro na farko ƙorafi tayi ta kira wayar sa a kashe sai kuma wanda
da alama yanzu da safen ta turo tana roƙon idan ya ga saƙon ya kirata ko hankalinta zai kwanta.
"Ban lura na sam a ƙoƙarin na rage volume ashe wayar na kashe gaba ɗaya" ya fada mata bayan da suka
gaisa. Motsin buɗe ƙofar da ya ji alamar Jalilah zata fito ya saka shi saurin yi mata sallama dan dama ya
ce mata har ya fita office ma yau yana da uzurin sassafe. Sake latse wayar yayi ya kasheta ya turata
ƙasan pillow ganin ta nufo shi tana murmushi.
Ya kasa ɗauke idonsa daga kallon adonta, Jalilah ta iya kwalliya duk kuma kamewar namiji in dai ta
giftashi sai ya ƙara mata kallo ɗaya, Allah ya mata wannan baiwar ba namiji ba ko mace da wahala ta
mata kallo ɗaya ta ɗauke kai dan bayan kyau na zahiri da take dashi tana da kwarjini da jan hankali.
Kan ƙafarta ta zaune tareda saƙale hannayenta a wuyansa babu ɓata lokaci ta haɗe bakinsu guri guda
shima kuma bai yi mata musu ba sai da ta sake shi dan kanta kafin ta narke fuska tana shafa cikinta ya
fahimci yaren yunwa take ji dan haka ya tashi suka shiga kitchen tana zaune tana masa hira har ya gama
haɗa musu abin kari suka dawo falon suka ci.
Bai san me ya saka duk motsin da tayi a falon sai Halima ta faɗo masa ba ko dan gurin ya daɗe babu
mace a ciki ne oho?
Zama sukayi ya kunna Tv ta kwanta haɗi da yin matashi da cinyarsa suna kallo abun su yanda kasan wasu
sababbin aure, Mamanta ta sake kiranta sai da suka gama magana tayi ɗan danne danne a waya kafin ta
kalle shi ta ce
"Tana can ɗaki na" ya bata amsa ba tareda ya kalleta ba, ajiye tata wayar tayi ta gyara kwanciya ta
fuskance shi ta ce
"Mom ce ta tura mun da kuɗi yanzu kaima na aika maka da 5m". Yanda kasan wanda ta ce ta xdxdqq ko
nawa ne.
Haɗuwar sa da Jalilah ta buɗe masa ido har ya fara raina abinda Hafiz yake masa wanda a baya yake
ganin kamar yanke talauchi yake bashi. Ganin fara cire ɗan kunnenta ya saka ya fahimci abinda take nufi,
ɗazun ya gama raya ba zai sake biye mata ba amma kuma abinda ta masa dole itama ya bata tukuici me
zafi.
Har ta fara cire undies ɗin ta sai kuma ya dakatar da ita ya ce su koma can part ɗin sa. Ashe ƙaddara da
rabon ayi ne suke tafe, suna tsaka da masha'arsu yayi nisa gurin yiwa Jalilan abinda ya san zai faranta
mata rai yana tsaka da tsotson ƙirjinta kawai yaji ta ce
"Wace ce wannan kuma?" Ya ɗaga kansa yayi mummunan gani Halima tsaye a kansu a wannan lokacin
ta kuma same shi cikin yanayin da ko shi yafi kowa iya lauya zance a duniya bai isa ya kare kansa ba.
Da saurin gaske ya tashi zaune tareda jan rigar sa ya jefawa Jalilan akan jikinta, ya sake kallon in da
Halima take tsaye saɓanin ɗazu da take kallonsu ta juya baya sai kuma a lokacin ya lura ba ita kaɗai bace
harda Mu'azzam.
"Halima ce" ya bata amsa yana kallon Halima da Mu'azzam suka bar falon, sai ta taɓe baki irin ko a
jikinta ta ce
"Kuma sai ta faɗowa mutane haka nan don tana taƙamar gidan ta ne ko me?"
"Dallah Malama ki rufewa mutane baki, ke wace irin mace ce? Baki ganin abinda kika sakamu a ciki har
kina da bakin cewa ta shigo ba izini ke bakiji kunyar abinda ta kamamu muna aikatawa ba ma kenan?" Ya
taso mata. Hannu ta ɗaga masa kafin tace
"Ko da wasa kada ka sake tunanin ɗaga mun murya domin ni ba tsarar ka bace, kunya kuma kai ka aikata
abin kunya ba ni ba dan kai ta sani" ta ja tsaki kafin ta miƙe ta jefa masa rigarsa daya rufa mata a yanda
take ɗin kuma ƙirjinta a buɗen ta fice daga falon.
Kasa motsawa yayi daga in da yake ya dafe kai da hannu biyu ya tafi laluben ya zaiyi? Yau da ace iya
Halima ce kaɗai ma zai iya cewa da dama dama domin ya san yanda ta iya riƙe wancan sirrin wannan ma
ba zata taɓa tonawa ba amma yanzu harda wannan ƙanin nata da ya fi kowa tsanar sa da tsanar
zamansa tareda Halimar.
Wai har tun yaushe ma suka shigo gidan har suka shigo falon bai sani ba? Shi da kunnen sa yake kamar
na maciji ko yaya motsi yake zai ji amma ya akayi har aka buɗe gidan aka shigo bai sani ba duk bai ji ba?
"Ta ina zakaji bayan tunaninka da nutuswarka sun yi nisa a cikin aikata saɓon ubangiji?" Zuciyarsa ta
tuna sar dashi.
Hannu biyu ya zura yana barbaza gashin kansa a fili cikin sauti kamar zai fasa kuka ya ce
"Na kwafsa, tun farko ma mai ya sa na biyewa Jalilah gashi ta kaini ta baro waya sani ma ko ita ta shirya
komai ta kira Haliman?" Shiru yayi saboda tunanin daya ɗarsu a ransa, haka kawai Halima ba zata zo
gidan ba ya sani dole wani ne ya gaya mata ko dai Jalilan da kanta ko kuma wani a yan unguwar ya
ganshi yayi mata waya ya gaya mata.
Ta shi yayi da sauri ya mayar da rigarsa ya fito dukda bashi da tabbacin sun tafi ko suna nan, cikin sa'a
yana buɗe ƙofar kuwa yaga mota a tsaye. Sai da ya tattaro duka ƙarfin halin da yayi masa saura ƙafin ya
shiga ƙwanƙwasa window gefen da take zaune.
HALIMA
*KURA A RUMBU*
*Wattpad @MaryamahMrsAm*
*Ban yarda wani ko wata ya juya mun labari ta kowacce siga ba tare da izini na ba*
*Kuɗin karatu yana wakiltar mutum ɗaya ne, kiji tsoron Allah karki ɗauki hakkina ta hanyar fitar mun da
littafi*
*KURA A RUMBU littafin kuɗi ne, a biya naira 800, biya a asusun*
*7061838488*
*Opay*
*PAGE 44*
Kafin na kai ga buɗewa Mu'azzam ya ɓalle murfin motar ya fita da sauri, gefe suka matsa, ina kallon su
amma ban san mai ya cewa Bilal ɗin ba na dai ga ya kama baki da hannu biyu cikin alamar ninkuwar
tashin hankalin da ya fito dashi akan fuskarsa kafin Mu'azzam ɗin ya nufo mota shi kuma ya biyo shi sai
dai bai ko sake kallon sa ba ya shiga motar ya tayar.
Na waiwaya ina kallon Bilal da ya bi motar da kallo cikin tashin hankali kafin na rufe ido na hoton ganin
da na musu tar tamkar a lokacin abun yake faruwa take na sake fashewa da kuka har muryata na
sarƙewa. Ci kanki Mu'azzam bai ce mun ba sai gudu da yake fellawa a titi kamar zamu bar gari hakan
kaɗai kuma ya isa ya sanar mun da ransa a ɓace yake.
Na ɗauka a yanayin da nake zaiyi tunanin mayar da ni gida ne amma akasin haka sai naga ya ɗauki
hanyar Jambulo, daƙyar na iya ce masa
"Ka mayar dani gida" ai kuwa kamar yana jira ya taso mun yana cewa
"Iya abinda kika gani yanzu ya isa idan har ba dusace a cikin kanki ba ki gane ya kamata ki nemawa
rayuwarki ma'ana ko dan saboda gobenki" ya ja tsaki mai ƙarfi kafin ya mayar da hankalinsa kan tuƙi.
Ban sake cewa komai ba na mayar da kaina tsakanin cinyoyina ina jin wani abu na mun yawo tsakanin
maƙoshi ga amai dake taso mun haka kaina yanda kasan ana kiɗan ƙwarya a ciki kai gaba ɗaya duniyar
ma juyamun takeyi. Da muka isa ban ko yi yunƙurin motsawa ba dan bana jin akwai sauran ƙarfin da zai
iya riƙe ni a tattare da jikina.
Uncle Mudassir ya kira a waya, ban san mai ya ce masa ba ya fita ya shiga gurin shi kaɗai ya ɗan jima
kafin suka fito tareda wani mutum babba. Ƙofar ɓangaren da nake ya buɗe na ɗaga kai daƙyar na kalle
su, mutumin ya ce
"Subhanallah, mai yasa zaku fito tana jin jiki haka? ai da ya kirani kawai ya gaya mun idan ya so daga
baya sai ta zo".
"Idan ma ɗaukar ki zaki ce nayi wlh ba zan ba" ya faɗa na girgiza kai lokaci ɗaya ina fashewa da sabon
kuka na ce
Buɗe baki yayi yana kallo na cike da mamaki, na kamo hannunsa ina cigaba da kukan na ce
"Dan Allah ka rufa mun asiri, kada ka duba ni ko shi ka duba Al'amin da Sharifa kada ka janyo...." Fizge
hannun sa yayi da ƙarfi ya buɗe motar ya fita, ban san ta inda na samu ƙarfin da na fita na bishi da sauri
ina kiran sunansa ba amma ko tsayawa bai yi ba. Dab da zan shiga falo na taka step na farko ina ɗaga
ƙafa zan taka na biyu juya ta ɗebe ni lokaci ɗaya wani duhu ya mamaye idanuwana ji da ganina suka
ɗauke a lokaci ɗaya daga nan ban sake sanin mai ya faru ba kawai na farka na ganni a gadon asibiti.
BILAL
Ya fi minti biyar a tsaye yana kallon hanya dukda tuni motar su ta ɓacewa ganinsa. Yanda kasan wanda
yake gaban tandar waina haka zufa take keto masa saboda sabon tashin hankalin da ya riska bayan
wanda yake ciki.
"Shawara ɗaya zan baka shine ka fita daga rayuwar yar uwata, idan kuma ba haka ba ka kuka da kanka
domin ina da hoto da kuma video abinda muka tarar da kai kana yi zan kuna watsa shi a duniya kowa ya
gani dan ba zai yuwu yar uwata ta cigaba da shaƙar baƙin ciki ita kaɗai ba" abinda Mu'azzam ɗin ya faɗa
masa kenan daya fito daga motar bai kuma tsaya ya bashi damar cewa wani abu ba ya juya ya tafi.
Shi yanzu ina zai tsoma rayuwar sa yaji sanyi? Idan ta tabba Mu'azzam ya ɗauke hoton su ai ya gama
yawo domin ya san yaron farin sani bashi da mutunchi kuma dama can ba ƙaunar sa yakeyi ba tsaf zai
aikata masa abinda ya ambata. Komawa yayi ciki yana jan ƙafa kamar wanda ya sauka daga iskokai, a
falon Halima ya zauna kan kujera ya dafe kai da hannu biyu cikin tsananin tashin hankali da rashin sanin
madafa.
Duk Jalilah ce ta janyo masa, shiyasa tun jiyan data kira shi kwata kwata bai yi farin ciki ba jikin sa kuma
ya ringa bashi kamar akwai wani sharri dake tareda ita ilai kuwa gashi nan ta jefa shi a masifa.
Ya shafe sama da awa biyu a zaune a gurin yana sharce zufa dan tunanin sa ma ya ƙi tsayuwa guri ɗaya
balle ya nemi mafita, Jalilah ko tana cikin ɗaki tana bacci abunta tamkar babu abinda ya faru. Ana ƙwala
kiran Azahar ya jiyo ana buga get. Zabura yayi ya miƙe, abinda ya fara zuwar masa yan gidansu Halima ne
suka zo kwashe kaya shikenan ta faru ta ƙare wai an yi wa mai dami ɗaya sata.
Kasa fita yayi ya buɗe sai da ya ji bugun na ƙaruwa nan kuma ya shiga tunanin idan Jalilah ta farka wani
sabon case ɗin ne dan haka ba shiri ya fita. Wayar sa ya ɗauka a bayan pillow daya ɓoyeta kafin ya fita ya
tsaya daga baya yana tambayar waye?
Muryar Fadila ya ji ta saka shi sauke ajiyar zuciya mai ƙarfi hankalin sa ya ɗan kwanta, amma kuma daya
tuna lokaci da kuma irin bugun da takeyi ya san ba haka kawai ta kawota ba, to ko yan gidansu ya
turawa? Amma kuwa da ya gama dashi. Har wasu maiƙon hawaye yaji a idon sa saboda tunanin da yayi,
amma kuma ai cewa yayi idan ya sake takurawa Halima yanzu kuma shi ko bin su bai yi ba ma ai.
Cigaba da buga ƙofar da tayi da ƙarfi ya saka ya zura muƙulli ya buɗe, tare hanya yayi ganin tana ƙoƙarin
shiga ya ce
"Dan Allah ka matsa na shiga ni na gaji ka san uwar ranar dana kwaso kuwa? Sannan minti na nawa a
tsaye ina bugu baka buɗe ba" ta bashi amsa tana ƙoƙarin raɓe shi ta shiga amma ya hanata. Babu wasa
ya ce
"Ke baki da hankali ko kwai mace a gidan ne da zaki ce zaki shiga ne?"
"Lallai ma Yaya Bilal sai kace ni ɗin ba muharramarka bace ko kuwa ma yau na fara zuwa gidan Haliman
bata nan?"
"To na canza tsari daga yanzu ba zaki sake shiga ba sai matar gidan ta dawo" ya bata amsa yana sake
babbake ƙofar. Shiru tayi kamar mai nazarinsa kafin ta ce
"Sai dai idan kuma wani abun kake ɓoyewa a ciki da baka so a gani"
"Ke ni kike gayawa haka dan ubanki sa'anki ne ni?" Ya taso mata. Tayi baya tana magana ƙasa ƙasa ta ce
"Zancen gaskiya dai ai ga alamun rashin gaskiya nan sun bayyana a tareda kai"
"Bar nan kafin na saɓa miki" ya faɗa yana nuna mata hanya, ta harareshi kafin ta ce
"Toh Hajja ce ta aiko ni in kira mata kai kuma tace kazo yanzu yanzu take son ganinka tun safe akw ta
neman ka a waya ka kashe har Yaya Hafiz ta kira ya ce baka je Office ba shiyasa ma tace na zo gidan ƙila
kana nan".
Cikin gidan ya koma bayan yace ta tafi zai zo kafin ya mayar da ƙofar ya rufe Wallet ɗin sa ya ɗauka da
key ɗin mota, sai da ya leƙa Jalilah dake bacci kamar a gadon Mamanta kafin ya fita daga gida bai ɗauki
motar ba ma gudun kar ƙarar ta ta tashi Jalilar.
A baki titi ya tarar da Fadila tana jiran abin hawa fuskar nan da ta sha mai tayi jajir saboda rana shi sai
lokacin ma ya lura, cikin sa'a yana zuwa suka samu Adaidaita. Bayan ya zauna ya kunna wayarsa tamkar
Zulaiha na jira kuwa ko gama kamawa batayi ba kiranta ya shigo.
Ya ɗaga, mita ta dasa masa akan katse wayar da sukeyi ɗazu da yayi kuma ya kashe gaba ɗaya daya sake
kira bata same shi ba ya bata haƙuri kafin ta faɗa masa ainihin dalilin kiran wai taji shiru cikon kuɗi.
"Ina ganin 2m da yawa sai da muka shiga kasuwa sai kaga yan kayan da muka siyo da ita. Ni wlh da na
san haka ne gara ka haɗa mun lefena da kanka na san sai ka fi sakin jiki ka zuba mun kaya masu kyau da
tsada" ta faɗa cikin shagwaɓa.
Mamakin maganarta ya kamashi amma dai bai nuna ba ya ce zai aika mata da saƙon kawai saboda Fadila
data baza kunnuwa dukda tayi kamar bata sauraronsa amma yasan hankalinta yana kansa. Suna sauka
daga Adaidaitan kiran Jalilah ya shigo wayarsa, sai da gaban sa ya faɗi dan bai zaci zata farka da wuri ba.
Waje ya tsaya ya amsa, cike da izza da kuma muryar bacci kamar wata uwarsa ta ce
"Ina ka tafi?"
"Na ɗan fita ne daga nan zan biya na siyo miki lunch" ya bata amsa, shiru tayi kamar na zata sake
magana ba kafin ta ce
"Karka zauna, Chinese rice nake so da grilled chicken kuma ka san ta inda nake so"
"Na sani ranki ya daɗe ai dama can zan je" ya faɗa cikin lallashi, tayi gajeran tsaki kafin ta kashe wayar.
Ajiyar zuciya ya sauke a ransa yana ayyana kalar rashin mutunchin da zai mata daga sanda ya kammala
shirinsa akanta.
Tun da ya ga takalma da yawa a ƙofar ɗakin Hajjan hankalinsa ya sake tashi amma haka ya daure ya
shiga da sallama, gaba ɗaya yayan ɗakin su su shidda shi na bakwai suna zaune sai kuma Hajja. Idanuwa
suka zuba masa kamar sunga bakuwar halitta hakan ya sake jefa shi cikin tashin hankali amma yayi
namijin ƙoƙari gurin ɓoye firgicinsa ya samu guri can nesa ya zauna kai a ƙasa saboda harar da Hajja take
aika masa.
Daƙyar ya buɗe baki ya fara gaisar da Hajjan ta dakatar da shi tana cewa
"Ni na isa? Riƙe gaisuwarka yau kwananka nawa rabon da ka tako gidan nan balle ka kira ni a su wa
Bilal?"
Ƙasa ya sakeyi da kai bugun da zuciyarsa take yi kuma ya ragu dan ya ɗan samu nutsuwa daga maganar
Hajjan ya fahimci wani abun daban ya saka ta kirashi ba wanda yake tunani ba. Anty Amina ce ta ce
"Amma dai koma menene tunda ya gaishe shi da kin amsa Hajja" ai kuwa ta taso mata tana cewa
"Ba zan amsa ba uwata Amina na ce bazan amsa ba idan ya so ki tsine mun in bi duniya saboda ban amsa
gaisuwar Bilal ba"
"Allah ya baki haƙuri" Aminar ta faɗa tana gyara zama, Hajja tayi ƙwafa ta ce
"Ba tareda ɓata lokaci ba zan gabatar da abinda ya saka na taraku, ba kuma wani abu bane illah ku zame
mana shaida tsakani na da Bilal". Da sauri ya ɗaga kai ya kalleta cikin rashin sanin mai yayi mata da har
zata kawo shaidu kuma?
Ta zaro takarda da biro daga saƙon kujerar da take zaune ta jefa masa tana cewa
"Gashi nan ka rubuta komai da zan faɗa maka". Gabansa ne ya yanke ya faɗi, tsakanin Halima da Zulaiha
gaskiya babu wacce zai iya saki a yanzu idan ma abinda Hajjan take buƙata kenan sai dai tayi haƙuri.
"Na ɗauki cikinka tsayin wata goma dan sai da ka haura wata tara a ciki na ka samu guri ka bararraje.
Duk yayan dana haifa babu wanda na sha wahalar laulayi da naƙudar haihuwarsa kamar kai. Faɗar
hidimar da nayi ta sunanka kuwa ɓata lokaci ne saboda akanka na fara haifar ɗa namiji. Tun da ka fara
taka ƙafarka ban huta saboda jaye jayen jidali, ka shiga ɗakin Saude kayi mata ɓarna haka zata yi ta surfa
bala'i tana mun gori banida kayan jere irin nata shiyasa nake turaka san ka lalata mata.
Sai da na daina gaisawa da kowa a unguwar nan saboda kai dan baka da aiki sai neman tsokanar yara a
unguwa ko a makaranta kai ko kallon banza yaro ya maka ka faɗa mun har gaban uwarsa nake takawa
naje na rama maka balle kuma mutum ya taɓa ka" ta fyace majina tana cewa
"Ai na san Amina da Ladi ba ku manta ba har a cell ɗin yan sanda sai da na taɓa kwana saboda Bilal, kaje
ka daki wani yaro ashe Babansa ɗansanda ne suka zo zasu tafi da kai na hana ƙarshe ni suka tafi dani.
Ban huta da jidalinka ba saida ka tafi Jami'a. Duk wani tanadi na da abinda nake dashi sai da ya ƙare
akanka bayan rasuwar mahaifinku saboda yanda ka ɗauki rayuwar jin daɗi da ƙyale ƙyale, daga sanda ka
gama makaranta ka samu aikinyi a maimakon ni da na sha wahalar ka ace ni zan mori samunka sai labari
ya sha banban" ta ƙarasa tana fashewa da kuka kamar wacce aka daka.
Kallonta ya ringayi cikin rashin fahimta kafin ya juya yana kallon sauran yan uwansa kowanne da kalar
yanayin da fuskarsa take ciki. A kan Hajja ya tsaida idonsa ganin yanda take kuka hankalinsa ya sake
tashi, shi sam bai fahimci in da waɗannan maganganun suka dosa ba kuma ta yaya ma Hajja zata ce wai
bata morar samun sa tsakani da Allah?
"Dan Allah Hajja kiyi haƙuri kiyi mun magana da yaren da fahimta duk mai ya kawo waɗannan
maganganun har kina kuka haka?" Ya faɗa yana matsawa gabanta. Ta fyace hanci da gefen ɗankwalinta
kafin ta ce
"Tun ina yar shekara goma sha huɗu aka saka mun lalle da ubanku kuma wannan ɗakin cikinsa aka kawo
ni yau shekarata arba'in da biyar kenan a cikin har ubanku ya mutu aka raba gado a nan ɗin dai nake
zaune kuma ginin shine tun na usuli babu abinda aka canza sai yan toshe toshe da manne manne da
akayi,
Ina zaune anan ɗin nan ace ɗan da na haifa na sha wahalar sa ya tafi can duniya ya samu wata uwar da
yan uwan daban yana bauta musu har ka siya musu gida kuma kai kake riƙe da su kan jiki kan ƙarfi, nan
da Fadila da Abubakar suka gama sakandire zasu tafi Jami'a cewa kayi sai sai ɗaya daga cikinsu ya haƙura
dan ba zaka iya ɗaukar nauyin su duka biyun ba amma can ba dangin iya ba na Baba a duniya ka ɗauki
nauyinsu har gaban abinda ya fi Jami'a ma to wlh cikin biyu dole ayi ɗaya, ko dai ka saketa ko kuma daga
yau ka nemi wata wacce zaka ringa kira da uwarka amma ba ni ba" ta sake rushewa da kuka.
Ƙasa ya sauke kai, shi kam yau tazo masa ba'a yadda ya tsammata ba wane irin bala'i ne haka wani na
bin wani?
"Ai wlh tallahi Hajja ba dan Bilal yana kama da mu ba ni zan ce canza miki shi akayi a Asibiti ba ɗanki
bane. Ai ko ɗan ruƙo ba zai yi abinda Bilal yayi ba caɓ" ta kyaɓe baki tana rufe baki Anty Ladi da Hadiza
ma suka ɗauka. Fadila ce ta ce
"Taɓ, to ai baki ji komai ba ma Hajja yanzu haka in kinji miliyoyin kuɗin ya basu wai kuɗin lefe sai kun
riƙe baki a haka ma kiransa take wai na zai isa ba ya ƙara musu" su ukun suka haɗa baki suna cewa
"Kinji ko, ai wlh ba haka suka barshi ba. Ba'a fita daga masifar Halima ba shine zai sake jajubo mana
wata"
"Ku dai ba zaku taɓa iya zama ku tashi ba tareda kun sako Halima a ciki ba? Yanzu kuma menene nata a
maganar da kukeyi?" Anty Amina da bata tsoma musu baki ba sai yanzun ta faɗa. Hajja ta ce
"Ai duk ita ce silar komai, tunda ya auri yarinyar nan kamar wanda aka sakawa hannu shikenan
al'amuransa suka taɓarɓare ni dai aurenta babu abinda ya tsinana mun idan ba ɓacin rai da baƙin ciki ba,
wannan auren da yayi ai da saninta amma da yake muguwa ce mai baƙar zuciya taja bakinta tayi gum
idan da ta faɗa mun tun farko ta ina zan bari haka ta faru?"
"Yanzun ma ai bata ɓaci ba Hajja yanda kikace dole ya saketa in dai yana so yaga haske a rayuwarsa.
Matar da tun babu aure yake musu wannan uwar hidimar idan ta tare kuma ai wlh janye shi zatayi ba
zaki sake ganinsa ba.
Ta bakin naki mugunta ta saka Halima yin shiru bata faɗa ba tunda ai ba zata ce bata san duk tsayin
lokacin nan mijinta na tareda wata ba shine saboda tsabar munafunci ta bar gidan ai in sha Allahu itama
ta tafi kenan itama wannan kuma ka sallameta ga mace har mace irin arziƙi na binka soko ka tsaya kana
bin wanda ba zasu tsinana maka komai ba" cewar Anty Habiba.
"Wlh tallahi ku kuka da kanku sanda haƙƙin Anty Halima zai tambayeku amma duk ba laifin kowa bane
laifinki ne Hajja saboda a gidan nan yanda kika dama haka ake sha.
Duk cikinmu babu mai iya miki musu, Allah ya hore miki yayanki mutum nawa ne suke addu'a da fatan
Allah ya ɗora su akan yayansu ta yanda zasu ringa jin maganarsu amma ke Allah ya miki wannan arziƙin a
maimakon kiyi amfani da hakan ki tarbiyyantar damu ta yanda ko bayan ranki za'ayi alfahari da abinda
kika haifa amma kin bari son zuciya da shaiɗan sunyi tasiri a zuciyarki suna kuma jagorantar
al'amuranki".
Tsit sukayi kamar ruwa ya cinye su suna sauraronsa, ya miƙe tsaye yana cigaba da cewa
"Wlh idan har baku canza wannan hanyar da kuke tafiya akai ba nan ba da daɗewa ba zaku fara dana
sani mara amfani, abinda Yaya Bilal yayi idan da da niyya mai kyau yayi shi ai ba aibu bane har a gurin
Allah kuma zai samu lada, amma yanzu kuwa aikin banza kayi domin ka tsallake farilla ka bar dolenka a
gida matar aurenka ka barta ɗauke da nauyin kanta dana yayanka ka tafi kana bautawa wasu. Kuma nan
ba da daɗewa ba zaka gane kallon kitse ka daɗe kana yiwa rogo" ya ƙarasa yana wata yar dariya mai cike
da ma'anoni daga nan ya fice daga falon.
Anty Ladi ce ta ce
"Ashe ba iya Bilal ne ɗan abu ta kazan uban ba, koda yake dama shiru shiru mutum ai kaji tsoron sa idan
suka tashi sai sunfi uban kowa iya iskanci toh wlh Hajja dole ma ki tashi a tsaye kina dai jin sa tun bai yi
aurenba ya iya tsayawa gabanki yana faɗa miki magana wannan ai kuma bamu san kalar matar da zai
kwaso ba ƙila haɗuwa zasu ringayi shi da ita suna zaginki"
"Allah ya kiyashe shi da zagin mahaifiyar sa balle har ya auro wacce zasu zageta tare" Anty Amina ta faɗa
sannan ta juya kan Hajja ta ce
"Kiyi haƙuri Hajja amma gaskiya Abubakar ya faɗa miki, idan muka gyaru kece haka idan muka lalace
duka ke za'a zaga. Yanzu wane kallo kike so duniya tayi miki ba'a gama da Halima ba yanzu ki ce sai ya
saki matar da ko tarewa ba tayi a ɗakinsa ba akan me?
Babu wanda ya ce abinda yayi yayi daidai ko ya kyauta amma kuma ya rigada ya faru tunda har ba wani
aibu bane a ciki ai babu hujjar kuma ace za'a raba aure ko makamancin haka.
Yanda kika ce kin haƙura kin karɓi ƙaddara kiyi haƙuri ki kuma bishi da addu'a shikenan amma ace da
kanki kike nema ki buɗe masa hanyar auri saki wace riba zaki ci akan hakan?
Ni wlh na ɗauka kiran da kika mana maganar Halima zakiyi, yanzu tsakani da Allah ace yarinyar nan
kusan watanta biyu a gida amma babu wanda ya bi sahu ko yaje bada haƙuri ai ko shirun da iyayenta
sukayi kaɗai ya isa ya saka ku sha jinin jikinku ayi abinda ya kamata domin dai sai dai mutum yaƙi Allah
kawai ya zagi Halima baya ga haka duk mun san irin haƙurin zaman da takeyi dashi a yanzu ko a gaba wlh
ba zai taɓa samun macen da zai taka kamarta su kwashe lafiya ba kuma har idan yayi kasadar rabuwa da
ita ban masa baki ba amma wlh ba zai maida kamarta ba ke kanki na zaki maida suruka kamar Halima
ba".
"Ni idan kina magana wlh mamaki kike bani Amina har yaushe kika sauka daga tafiyar da yanzu kike kira
ta rashin dai dai da har zaki ringa yiwa mutane wa'azi?" Habiba ta faɗa, Amina ta kalle ta tace
"Kema kika ce na sauka daga turbar ɓata na bi ta gaskiya toh Alhamdulillah tunda na gane kuma kuma
fatan da nake muku kenan ku gane kafin lokaci ya ƙure muku"
"Wato mu da Hajjan ne akan turbar ɓata?" Anty Ladi ta faɗa ba tareda shakka ba kuma tace
"Ƙwarai kuwa, kun ɗora ranku akan son zuciya da kwaɗayi ga gaskiya ƙiri ƙiri a gabanku ku rintse iso ku ƙi
kallonta. A shekarun Hajja yanzu dama akwai abubuwan da sai an fara mata uzuri, mu ya kamata idan ta
kuskure mu nusar da ita ba kuma mu cigaba da biye mata akan abinda mun tabbatar ba gaskiya bane
duniyar nan fa ba matabbata bace duk yanda ka so da sonta kuma akwai ranar da zaka barta dan haka
gara mu yiwa kanmu faɗa mu kuma yiwa goben mu ta ainihi tanadi. Ni dai idan har ba maganar yanda
za'ayi uwargidan sa ta dawo za'a yi ba kiyi haƙuri Hajja kada a sake kirana dan ba zan zo ba" daga haka ta
ɗauki jakarta ta fita tana jin Ladi da Habiba na faɗa mata maganganu amma bata tamka ba.
A hankali ba tareda ya haɗa ido da kowa ba ya bi bayan Anty Aminan yana ko Hadiza tana cewa
*Wattpad @MaryamahMrsAm*
*Ban yarda wani ko wata ya juya mun labari ta kowacce siga ba tare da izini na ba*
*Kuɗin karatu yana wakiltar mutum ɗaya ne, kiji tsoron Allah karki ɗauki hakkina ta hanyar fitar mun da
littafi*
*KURA A RUMBU littafin kuɗi ne, a biya naira 800, biya a asusun*
*7061838488*
*Opay*
*PAGE 45*
"Dan girman Allah Anty Amina kiyi mun wannan alfarmar, wlh nayi duk dabarata amma taƙi saurarona,
idan naje gidan bata fitowa haka idan na kira wayarta bata amsawa. Ɗazu da safe suka zo ba dan na
kulle gidan ta ciki ba ma da tuni sun kwashe kaya.
Ke shaida ce ina son Halima duk abinda kuma ya faru sharrin shaiɗan ne da kuma Hajja amma wlh ba a
son raina bane" ya faɗa bayan da ya tsayar da Anty Amina a ƙofar gida.
"Kaine shaiɗan ɗin ai ba wani ba zancen Hajja kuma ko da da gaske da saka hannunta ai kai ba
mahaukaci bane; da zaka ringa biye mata idan dama ba gangara kake nema ba ai ka san ta yanda zaka
lallaɓata ka zauna da matarka lafiya. Karma ka raina mun wayau na san kana sane yanzun ma Allah kaɗai
ya san abinda yake ƙasan ranka da kake so ka sake janyota ka cigaba da gasa mata aya a hannu, to ni dai
babu ruwana; yanda sanda ka koreta bakayi shawara da kowa ba yanzu ma sai ka san ta yanda zaka bi
idan itama bata gaji da uƙubar da kake mata ba sai ta dawo" ta faɗa tana ƙoƙarin buɗe motarta.
Riƙe murfin yayi tamkar zai fashe mata da kuka harda rage tsayi ya ce
"Na rantse da Allah bani na ce ta tafi ba haka kawai ta haɗa kayanta kuma babu yanda banyi da tayi
haƙuri mu zauna mu sasanta koma menene ba amma ta ce ita tafiya zatayi".
"Lallai Bilal, wato har yanzu bakayi laushi ba ka iya kallon tsabar ido na ka shirga mun ƙarya har kana
rantsuwa da Allah ko?
Ka san ko jikina kunnuwa ne ba zan taɓa yarda haka nan Halima ta sa ƙafa ta bar gidanka ba domin a
baya ka mata abubuwan daya kamata ta tafin amma ta shanye sai yanzu zaka ce haka nan ta tafi?
To bari kaji, babu ruwana; yanda baka godewa ni'imar da Allah yayi maka ta aurenta ba yanzu sai ka
godewa azabar sakacin da kayi har ka rasata" ta faɗa tana fizge murfin motarta. Ƙasa ya zube ya kama
ƙafarta yana cewa
"Dan girman Allah Anty karki ce haka; ke kaɗai nake saka ran zaki fahimce ni kuma ki mun uzuri na kuma
san itama ba zata ƙi sauraronki ba. Dagaske laifi nayi mata amma wannan tsakaninmu ne kuma na san
yanzu ta haƙura. Dan Allah ki tayani rarrashinta wlh na miki alƙawarin har idan ta dawo ba za'a sake jin
kanmu ba".
Ganin masu giftawa sun fara tsayawa suna kallon su ya saka ta daka maza tsawa ta ce
"Dallah tashi karka tara mun mutane" ya miƙe tareda riƙe hannunta, ta balla masa harara sai ya saketa
ya zare key ɗin motar dGa hannunta yana cewa
"Ka kaini ina? Kaga Bilal ka bani key ɗin motara na tafi; tunda kake shuka mata tsiya banje na tayata
ƙwatar yancinta ba sai yanzu da ta tasarwa kanta kake so naje saboda goyon bayan rashin gaskiya na ce
ta dawo taci gaba da zama da kai? To ba haka nake ba" ta faɗa cikin muryar dake nuna ba wasa take ba.
Hannu biyu ya dafe kansa kafin ya juya ya kalli ɗai ɗaikun yan unguwa dake satar kallon su ya ce
"Idan ka cancanci yafiya zan ga abinda zan iya". Saida ta zagaya ta zauna a kujerar mai zaman banza ya
rufe mata ƙofar kafin ya koma mazaunin direba ya tada motar suka bar layin, can gefen titi ya samu guri
yayi parking, sun fi minti biyar yana saƙa abinda zai gaya mata da zata yarda ita kuma tana danna
wayarta kafin yayi ƙarfin halin cewa
"Wayata ta ɗauka ta bincika shi ne ta ga chats ɗina da Zulaiha da kuma Jalilah. Ba tareda ta buƙaci wani
ƙarin bayani ba kawai ta hau zagina tana gayamun baƙaƙen maganganu; na faɗa mata ba abinda take
tunani bane duk su biyun auren su zanyi amma taƙi fahimta ta ringa zagina har da kama mun wuyan riga
wai na saketa ni kuma na zuciya na mareta shikenan ta haɗa kayanta ta tafi gida".
Yanda yayi maganar sai ka rantse da Allah gaskiya ya faɗa, Anty Amina da tayi shiru tana kallon sa ta ce
"Ka faɗa mun abinda hankali zai ɗauka in kuma ba haka ba ka daina ɓata mun lokaci ka rabu da ni na
tafi".
Wata rantsuwar ya sake kwasowa ya dire yana tabbatar mata da iya gaskiyar abinda ya faru kenan.
"Gaskiya ƙarya kakeyi, Halimar dana sani b zata zageka ba balle har ta kama ka da kokawa" ta sake faɗa,
ya marairaice fuska ya ce
"Amma Anty kin san dai ƙarya ba hali na bace kuma ke macece akan lamarin kishi kin san ba abinda ba
zaku iya yi ba. Ni kaina wlh idan wani ya ce mun Halima zata aikata hakan zan ƙaryata amma ya faru na
san kuma ba lallai duk wanda zan faɗawa ya yarda ba shiyasa kawai nayi shiru na bar maganar ina so mu
sasanta a tsakaninmu amma kuma hakan yana nema ya faskara. Wlh ina son matata kuma ni bana so
ace Zulaiha ta tare bata nan balle hakan ya buɗe hanyar da zata fara rainata shiyasa ma nayi shiru ko
Nasir ban faɗawa ba balle maganar ta fita har taje kunnen yan uwan Zulaihan".
"Na nawa kuma? Kaf dangi da yan unguwa wanene bai san bata gidanka ba?"
"Ai dai su can basu sani ba" ya bata amsa, kafin tayi magana ya ruƙo hannunta ya sake cewa
"Na san ina da laifuka a gurinta amma yanzu a shirye nake da na gyara komai ba iya alaƙata da Halima ba
da kowa ma duk wasu kuskure nawa ina so na gyarasu amma dawowarta rayuwata shi zai jagoranci
komai dan Allah Anty ki taimaka mun".
Yanda yayi sai da ta ji zuciyarta ta sosu amma ta dake bata nuna masa ba ta ce
"Ni dai na gaya maka ba zan shiga ba dan yarinyar nan na ganin mutunchi na haka kawai ban ma san
gaskiya ka faɗa ko ƙarya ba a xe ma gaskiya ne in shiga ta haƙura ta dawo ka cigaba daga inda ka tsaya ai
kaga nima ka mayar da ni mutuniyar banza a idonta"
"Yanzu baki yarda nayi nadama dagaske ba?" Ya faɗa kamar zai fasa kuka. Tayi gajeran tsaki ta ce
"Zan maka abu ɗaya, zan kira Yaya Aminu na faɗa masa, ko zata dawo gara ayi komai da shaidu ta yanda
ko ka cigaba da halinka ka san shi ba sa'an wasan ka bane".
"Yanzu ba zamu iya sirri tsakaninmu ba sai an sako wani a ciki?" Ya faɗa ta ce
"Shi Yaya Aminun ne wani? Lallai baka canza ba Bilal yaudara ta kawai kake so kayi"
"Haba kin san ba haka nake nufi ba kawai ina tunanin Hajja ne idan ta ji kin san dai ta hana saka su cikin
sabgogin mu" ya sake faɗa. Taso masa tayi da masifa ta ce
"Fitar mun daga mota mutumin banza kawai, dama na san ba zaka taɓa canzawa ba. To ai sai kaje Hajjan
ta dawo maka da Halimar kar ka sake sakoni a shirmenka wlh tunda ba zakayi hankali ba". Duk yanda ya
so ya shawo kanta ta ƙi sauraro, fata fata ta masa ya fita daga motar kamar zai fashe da kuka ya samu
gefen titi ya zauna ya dafe kai. Yafi minti ashirin a gurin yana jin wayarsa nata ringing amma bai ɗaga ba
sai da ya gaji ya zama kafin ya tashi ya tare Adaidaita ya wuce.
Hankalin sa ya ɗan kwanta da yaga duk missed calls ɗin Hajja ne da na Zulaiha Jalilah bata kira shi ba, sai
da ya siyo mata abincin kafin ya wuce gida ya tarar da ita a falo da kayanta cikin shiri tana waya sai da ta
gama fuska a sake ta kalle shi ta ce
"Ƙarfe uku kuma?" Ya faɗa yana zaro wayarsa da kira ya shigo, ta ɗauki takeaway ɗin ta buɗe tana cewa
"Haka ya ce, zaka ajiye ni ko na yi order bolt?"
Ɗaki ya shiga bayan da ya ce zai kaita airport ɗin duk ya sha jinin jikinsa a ransa ya ringa raya anya ba
wani sharrin ta sake ƙulla masa ba yanda ta ware tamkar babua abinda ya faru ɗazu.
Yanda ka san wanda ya ɗakko gawa haka ya ringa zare ido yana haɗa zufa sanda suka fita sai da ya hau
babban titi kafin hankalinsa ya ɗan kwanta. Bai zauna ba yana sauketa ya wuce dan suna hanya yaji tana
waya da Hafiz akan zasu haɗu a airport ɗin dan haka a parking lot suka rabu itama kuma bata matsa da
ya tsaya ɗin ba sukayi sallama ta shige.
Sai lokacin ya ji kamar an zare masa ƙaya a maƙoshi, guri ya samu ya tsaya yayi wa Zulaiha transfer na
sauran kuɗin da ya mata alƙawari dan ta masa kira ya fi ashirin daga sanda ya kunna wayarsa zuwa
yanzu wayar da sukayi ɗazu ma cikin fushi take har tana cewa idan ya san ba zai bata ba ya faɗa mata ta
cire rai ba wai ya ringa raina mata wayau ba.
Halin da yake ciki ya saka bai mayar da hankali akan maganar tata ba, jiya jiya fa ya bata 2m amma ko
24hrs ba'a yi ba ta addabe shi da waya akan cikon kuɗi.
Shi yanzu lamarin Halima ne ya tsaya masa a rai sam ya kasa samun ƙwarin guiwar kiranta balle ya taka
ya bita to mai zai ce mata? Duk wata ƙarya da zaiyi dan ya kare kansa na zai fita ba da ace ita kaɗai ce ma
da sauƙi ƙila ya iya manipulating nata amma yanzu wannan shegen ƙanin nata da dama can ba ƙaunar sa
yakeyi ba shi kaɗai ya isa ya lalata komai.
Gashi Anty Aminar da yayi tunanin zata iya taimaka masa itama ta botsare, tada motar yayi ya nufi gidan
Nasir. Yayi mamakin yanda ko da wasa bai masa zancen Halima ba dukda ya san Nasir ɗin yana sane da
basa tare amma bai san dalilin da ya saka ya masa shiru ba.
Sunyi saɓani dan yana zuwa matarsa tace yanzun nan shi kuma ya fita ya kira wayarsa bata shiga ba dole
ya tafi a ransa yana raya Nasir ɗin ne kaɗai yake jin zai iya gayawa gaskiyar abinda ya faru dan ya san zai
rufa masa asiri. Wata zuciyar ta ce ya gayawa Hafiz mana,
Halima na ganin girmansa ya san idan ya saka baki zata haƙura amma kuma ko giyar wake ya sha ba zai
taɓa faɗawa Hafiz gaskiyar abinda ya haɗa su ba; ko da ace ba da Jalilah bane domin a duk sanda zasu
zauna lokuta ɗai ɗai ne baya tunasar dashi akan duk rintsi kada ya yarda shaiɗan ya kwaɗaita masa biye
biyen mata har ya kan ji kamar Hafiz ɗin na da masaniya akan alaƙar sa da Jalilah.
Yanzu mai zai ce masa ya haɗa shi da Halima ya yarda? Dan dai ya san duk ƙaryar da zai masa zai gane
gaskiya ce kaɗai zata ƙwace shi a hannun Hafiz ɗin.
Haka ya ƙarar da yinin ranar daga nan yayi can kansa cike da tunanin ta ina zai fara tunkarar Halima?
Suna ƙare magana da Jalilah bayan sun sauka take yayi blocking nata a duk wata hanya da zata iya
samun sa ya kuma saka duka numbobinta a blacklist. Ya gama da shafinta ya haƙura da zancen shago da
kayan da zata zuba, tunda takardun gurin suna hannun sa hakan ma ya ishe shi zai siyar da gurin kamar
yanda ya siyar da gidanta idan ya so ya haɗa kuɗin ya kama wani business ɗin.
HALIMA
Farkawa nayi na tsinci kaina a gadon asibiti; cikin abinda bai gaza seconds uku ba kuma komai ya dawo
mun na abinda yayi silar zuwana asibitin. Na sake runtse ido na hotunan su suna gilmamun, ban lura da
mutane a ɗakin ba sai da na ji muryar Mama Fauziyya ta na cewa
"Wai yanzu haka za'a zubawa yarinyar nan ido ta salwantar da rayuwarta akan wani banza da bai san
darajarta ba?". Mama ta ja tsakin da naji har tsakiyar kaina ta ce
"To Anty ya za'a mata? Halima dai ba yarinya bace da za'a kama a doka; iya bakin ƙoƙari lallami da nasiha
har ma da faɗan an mata tunda abinda ta zaɓa kenan ai sai mu zuba mata ido kawai. Ni wlh na gaji, na
ma faɗawa Abbansu daga nan gidanta zata wuce taje can tunda dama ba wani ya ce ta taho ba haka
kawai ba zata kasheni da fargaba kafin lokaci na yayi ba".
"Ke kika so ai; tuntuni na ce ki tattara lamarinta ki aje a gefe kiyi rayuwarki amma kika ƙi sai kace ita
kaɗai kika haifa. Ni fa shiyasa tuntuni na kama bakina, ga labari yana ta ci na a zuci amma sanin idan na
faɗa ƙarshe tare zaku raba jinyar ya saka nayi shiru".
Haɗa baki Mama da Mama Fauziyya sukayi gurin cewa "labarin me?"
A jikina naji ta kalle ni dan ta tabbatar da har lokacin bacci nake kafin ta ce
"Auren da mijinta ya ƙara mana". Suka sake haɗe baki gurin cewa
Ji naji kamar ta soka mun mashi a zuciya, na sake runtse ido hawaye masu zafi suka ziraro ta gefen ido na
amma nayi ƙoƙarin saita kaina gudun yin motsin da zai ankarar dasu. Ina buƙatar jin ƙarshen zancen ko
babu komai zan samu amsar wacece na tarar a ɗakin Mijina tareda shi cikin yanayin da nake fatan in
manta saboda abinda tuna shi yake haifar mun a gangar jiki da zuciyata.
"Ranar da kuka zo duba Inaayah har kika ganshi ai gurin yarinyar zai je, a nan ƙasan layinmu suke kusa da
gidan Zinaru mai yi mun kitso basu ma daɗe da tarewa ba dan basu shekara ba shi ya siya musu gida a
gurin.
Tunda ya fara zuwa Zinaru ta faɗa mun tana ganin Mijin Halima a gidan ni farko ma na ɗauka ko yan
uwansu ne amma da naji Haliman ba tayi zancen ba sai kuma Zinaru ta faɗa mun ai yarinyar gidan yake
so, mun kuma sha haɗuwa yanda yakeyi bai ganni ba nima in ɗauke kai to kuma sai ji mukayi an ɗaura
aure".
"Ai dama duk wanda ya siyi rariya ya san zata zubda ruwa, to waya sani ko zancen auren ta ji yanzun?"
"Dagaske kenan dama saboda zaiyi aure tayo yaji ashe?" Mama Fauziyya ta faɗa, Mama ta girgiza kai
Anty Labiba kuma ta ce
"Ita ta sani, idan ma dan hakan ne dai ba abinda ya canza tunda gashi yayi auren sa in da kuma yana
sonta yana son zama da ita ko bai fasa aurenba ba zai mata wannan wulaƙancin ba. To ba ji take ba balle
ka ɓata lokacin ka ka mata magana ni shiyasa na sallamata bana iya kayan takaici ba".
Maganar suka cigaba da tattaunawa, na samu na gyara kwanciya cikin dabara na basu baya dan in samu
damar yin kuka dakyau, ita bata san abinda ke damuna ya zarce maganar auren Bilal ba wannan ai
tsohon zance ne tuntuni na samu labari. Sai da aka kira la'asar suka fita duk su ukun kafin na tashi zaune
sosai na fashe da kuka harda shassheƙa.
Ina tsaka da kukan wata Nurse ta shigo dubani, babbace dan ta haifeni ai kuwa ta rufeni da faɗa yanda
kasan zata dokeni tana cewa wai ni muguwa ce bani da imani na san a halin da iyayena suka kawoni
kuwa shine zan tashi na cigaba da kuka saboda na ƙara tayar musu da hankali?
A daren aka bani sallama Dr ya ce ba abinda zasu mun kawai na koma gida na cigaba da shan
magunguna na. Sai na ringaji na kamar marainiya wacce bata da sauran gata da muka koma gida a falo
aka barni kamar baƙuwa kowa ya kama sabgarsa saida na gaji da zama dan kaina na lallaɓa na shige ɗaki
na kwanta na shiga tunani.
Idan wacce Bilal ya aura yar unguwar su Anty Labiba ce kenan tana nufin gidan da ya kaini nayi musu
gaisuwa; in kuwa haka ne ba Jalilah da na tarar a ɗaki na ya aura ba, wancan mugun abunda na gani
suna aikatawa a waya ne ya cigaba har ta kai ya ɗakkota ya kawota gida shi tafiyata yanci ya samu mai
lasisi na kawo mata.
Na haɗa kai da guiwa ina hawayen tausayin kaina. Sam ba wannan ne Bilal ɗin da na faɗa soyayyar sa ba,
Bilal ɗina ba haka yake ba. Amma wai a yaushe ya canza Ina tareda shi ban taɓa fahimtar komai ba? Ya
akayi na bari soyayya ta rufe mun ido har na kasa fahimtar canzawarsa ina zaune da manemin mata
amma yardar da nayi dashi ko da wasa ban taɓa hasaso zai kasance haka ba.
Tabbas Bilal ya cuceni kuma ya yaudareni sannan ya ci amanar ƙauna. Wlh da ace Zulaihan ita ce na
kama shi yana chat da ita ba Jalilah ba zan iya yafe masa ko dan aurenta da yayi zai shafe komai amma
ƙazantar tayi yawa, Allah kaɗai ya san bayan ita mata nawa yake mu'amala da su ko ita Zulaihan ma ta
sani ko kuma itama ninketa yayi yanda ya mun? Allah kaɗai ya sani.
Haka na kwana cikin alhini, tausayin kaina da yayana musamman Sharifa ya cika mun zuciya. Da naga
kuka da tunani ba zasu kawo mun mafita ba sai na miƙe na ɗauro alwala na shiga jera nafiloli na mayar
da hankali akan addu'ar kar Allah ya kama ni ko yayana akan laifin Bilal.
Allah shaida ban rage shi da komai da har zai fita ya nema a waje ba idan ma ban ishe shi ba bai taɓa
faɗa mun ba na san Allah ba zai kamani da laifin haka ba.
Kafin wayewar gari na sake zugewa sai k ɗauka kwana nayi ina zawo tsabar yanda na zabge lokaci ɗaya.
Da Asuba bayan na idar da sallah ina zaune ina lazumi Mu'azzam ya shigo ɗakin, sai da gabana ya faɗi na
ringa kallonsa har ya zaune gefen gado shima yana kallo na ya ce
Ya taɓe baki ya ce
"Ban faɗa masa ba, na ce masa ne zaki faɗa masa da kanki saboda kin san ni ban iya ƙarya ba idan na
buɗe baki zan gaya masa gaskiya be kawai".
"Amma baka kyauta mun ba akan me zaka haɗa ni da shi? Ba sai kawai ka ce masa babu komai ba kawai
jini na ne yayi ƙasa?"
"Ke idan ya kiraki sai ki gaya masa" ya faɗa kafin ya sake cewa
"Ni ba wannan nw ya kawo ni yanzu ba, an jima ki shirya zamuje asibiti ayi miki test".
"HIV test da na sauran STDs". Yanda kasan kiɗan mandiri haka zuciyata tayi wani diri, na kafe shi da ido,
tsabar yanda abun ya dakeni na kasa cewa komai daƙyar na haɗa kalmomi na ce
"HIV kuma?"
"Eh, kin san sai ba'a raba yan bariki da ita dan haka tun da wuri gara a miki gwaji ki san makomarki" yana
gama faɗar haka ya fice daga ɗakin.
Ji na ringayi kamar na hau rollercoaster, daƙyar na lallaɓa na koma kan gado na rufa da bargo saboda
wani sanyi da naji yana shigata kamar zazzaɓi zai rufeni. Na ringa nanata Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un a
zuci har ta fito fili, tsoro mai tsanani ya lulluɓe ni.
Duk tunanin da ya taho mun sai in kore shi na idan ta kasance aka mun test ya zama positive ya zanyi?
Ban iya cin komai ba har ƙarfe goma ina kwance a ɗakin kafin Amirah da suka gama Exams jiya ta shigo
ta ce wai Mu'azzam yana jirana. Haka na fita yanda kasan zautacciya, fuska jeme jeme baki a bushe Kai
ba iya bakina ba komai na jikina ma ya bushe kamar wata tsohuwa haka na dawo a dare ɗaya.
Babu wanda ya tambayi ina zamuje muka kama hanya muka fita, can wani babban lab muka je, ikon
Allah ne kawai ya kaini har aka gama running test ɗin result ya fito ban mutu a gurin ba saboda tsoro. A
gurin ya buɗe ya gama dubawa kafin ya miƙo mun takardar ban karɓa ba na girgiza masa kai daƙyar na
ce
"Akwai ko babu?"
"Babu" ya bani amsa, sai na ji kamar an kwarara mun ruwan ƙanƙara tun daga tsakiyar kaina har tafin
ƙafata. Na ringa jera ajiyar zuciya tamkar jaririn da ya wuni ba tareda mahaifiyar sa ba, a hanya muna
tafe babu mai cewa kowa komai sai da muka kusa isa gida ba tareda ya kalleni ba ya ce
"Wannan ba shi yake nufin shima bashi da wani ciwo ba, ta yuwu baki da haƙƙin sa shiyasa Allah ya tsare
bai shafa miki ba dan haka ruwanki ki godewa Allah ruwanki ki butulce masa zaɓi ya rage naki yanzu.
Baƙuwar motar da na gani ya saka na fahimci anyi baƙi, bani da tabbacin gurin Abba aka zo tunda yana
gida ko gurin Mama koma su waye bana buƙatar haɗuwa da su dan haka na shiga ta ƙofar kitchen na
shige ɗaki ba tareda na bi ta falon ba. Wanka na farayi na ɗauro alwala na fito ina ji na kamar iska zata
kwashe ni saboda rashin nauyi. Ina zama Amirah ta shigo wai na zo nayi baƙi,
"Ban santa ba" ta bani amsa bayan da na tambaye ta su waye baƙin? Suhaila ce ta zo mun, na ɓata rai a
zuciyata ina cewa zuwan da mijinta yayi bai isa ba shine ya sake turota?
Ban fita ba bayan na shirya kwanciyata nayi sai da Zainab ta sake zuwa ta kirani kafin na yafa ƙaramin
mayafin abayar da na saka na fita, ba yabo ba fallasa na ƙarasa na zauna a ƙasa na shiga gaisheta, ta
amsa a sanyaye tana ƙare mun kallo, na sace kallon Mama dake danna wayarta kafin na mayar da kaina
ƙasa ina juya zoben hannuna.
"Ashe kuma abinda ya faru kenan Halima? Dan Allah kuyi haƙuri, wlh ban sani ba sai da aka daɗe
tukunna nauyi da kunya kuma suka hana in zo ko na kiraki saboda na san duk dalilin da zai saka ki baro
ɗakinki ba ƙarami bane duba da tarin ƙaunar da kikewa Bilal.
Na yiwa Mamanku duk bayanin da yayi mun, na san bai zama lallai abinda ya faɗa mun gaskiya bane
amma koma menene tone tone bashi da daɗi ayi haƙuri har idan da yuwuwar komawa kiyi haƙuri ki
koma, amma idan kinga cewa da cutuwa a lamarin zamanku wlh bana goyon bayan kici gaba da haƙuri
kiyi abinda kike ganin ya fi kwanta miki a zuciya" Anty Aminan ta faɗa.
Mama na sake kallo naga ta taɓe baki kafin ta miƙe ta bamu guri. Nayi shiru sai Anty Aminan ta sake
cewa
"Na san kina haƙuri da shi harma da mu da mahaifiyarmu baki ɗaya amma ki sani Halima babu wani
gidan aure da bashi da nasa kalar ƙalubalen kawai na wani ne ya fi wani da kuma yanda ma'auratan suka
iya riƙe sirrin su shine banbanci amma duk inda aka zaga hakan take shiyasa zakiji hausawa suna cewa da
sabon gini gara yaɓe".
"Bana zaton zan iya zake zaman aure da Bilal dukda ina son sa".
Kuji tsoron Allah masu fitar mun da littafi babu lallai na yafe haƙƙina wlh
*Wattpad @MaryamahMrsAm*
*Ban yarda wani ko wata ya juya mun labari ta kowacce siga ba tare da izini na ba*
*Kuɗin karatu yana wakiltar mutum ɗaya ne, kiji tsoron Allah karki ɗauki hakkina ta hanyar fitar mun da
littafi*
*KURA A RUMBU littafin kuɗi ne, a biya naira 800, biya a asusun*
*7061838488*
*Opay*
*PAGE 46*
"Kar kice haka mana Halima. Ke da na san ki jaruma shine zaki bari daga sama wata ta zo ta ƙwace miki
miji kuma ki sakar mata? Haba mana dan Allah karki bani kunya.
Na san abinda ya aikata miki dole kiji zafi ba ke ba hatta Hajja dake goyon bayansa a ko da yaushe a
wannan karon tana adawa da auren nan dan wlh ba dan mun tausheta ba rantsuwa tayi akan sai ya saki
yarinyar ba zata tare ba. Mu muka yi ta bata haƙuri saboda a ganina bai kamata ace a gyara ɓarna da
ɓarna ba, ubangiji ya rigada ya ƙaddara matar sa ce sai ayi haƙuri baki ɗaya a karɓi hakan ta yuwu silar
auren sai ki ga kina zaune ubangiji ya fitar miki da haƙƙin ki ya wanke ki a idon duk mai ganin laifinki"
Anty Amina ta faɗa cikin tausasawa.
Murmushin takaici nayi ina share hawayen da suka ɓalle mun, kowa ɗauka yake saboda Bilal zai ƙara
aure ne muka samu saɓani amma nayi mamakin yanda da ta tashi tahowa bikon bai faɗa mata gaskiya
ba ta yanda zata fi sanin hanyar da zata bi gurin shawo kaina idan ma hakan mai yuwuwa ne. Ina jin ta ta
cigaba da cewa
"Kiyi haƙuri Halima, kishiya da ciwo amma sau tari mace bata sanin matsayin ta a gurin namiji idan tana
ita kaɗai sai ranar da ya kawo mata abokiyar zama a lokacin shi kansa zai banbance tsakanin aya da
tsakuwa.
Balle Bilal Allah na tuba ni da ke mun san idan ba ke ɗin ba babu wata mace da zata iya jure halinsa suyi
dogon zango yanda kikayi,
ni da ace kinyi shawara dani tun farko zan ce miki ki danne zuciyarki ka bashi lokaci kawai ki kuma zuba
ido ki sha kallo zakiga zuwan da dawowar amma yanzun ma bata ɓaci ba hakan za'a yi kiyi haƙuri ki koma
ɗakin ki tun kafin amarya ta tare balle ta samu lagonki ta fahimci kina kishi da ita".
"Ko da ina son Bilal ina kuma tsananin kishin sa hakan ba zai saka na bijirewa umarnin ubangiji na so
kaina ba.
Ban ce banji zafin ƙarin auren sa ba amma wannan bai ko kama ƙafar abinda ya aikata mun da ya saka na
nisance shi ba. Kuma zuwan ki da maganganunki sun sake tabbatar mun da bai yi nadama ba, ba kuma
shi ya turo ki ba zuwan kanki ne kawai domin da ace yana buƙatar cigaba da zama dani ba zai rufe miki
ainihin abinda ya haɗa mu ba ya faɗa miki ƙarya" na ƙarasa cikin kukan da ya ƙwace mun.
Tayi shiru jiki a sanyaye tana kallona kafin tayi ƙarfin halin cewa
"Menene gaskiyar abinda ya shiga tsakanin ku Halima? Ni dama jiki na ya bani ba gaskiya ya faɗa mun
ba, na yarda da shi ne kawai saboda rantsuwar da ya mun ban kuma yi zaton lalacewar ta sa har ta kai ya
ringa rantsuwa akan ƙarya ba".
"Kiyi haƙuri amma ba zan iya furta miki komai ba domin bai zama lallai ki yarda da ni ba ƙarshe ma zaku
iya cewa sharri nayi wa ɗan uwanku". Miƙewar itama tayi ta ruƙo hannuna ta ce
"Ashe har yanzu kina kallo na kamar sauran Halima?" Na girgiza mata kai na ce
"Ko da ace kamar su kike kin mun alkhairin da ko me zaki mun zan ɗaga miki ƙafa. Maganar Bilal kuma
mu barta kawai kiyi haƙuri, idan zuwan kanki ne ba zan iya sake koma masa ba, Idan ma kuma shi ya aiko
ki ki faɗa masa; ko da ƙaddara ta kasance akwai sauran zama a tsakani na da shi ba zan koma ba har sai
shi da bakinsa ya faɗa muku abinda ya aikata mun" daga haka na wuce ɗaki na barta a tsaye da alama ta
rasa da kalmar da zata tsayar da ni.
Kan gado na faɗa na fashe da kuka bayan shigata ɗaki, Amirah dake shafa mai a gaban mirror ta waigo ta
kalle ni ta ce
"Wai Yaya Halima ba zaki dangana ki dena wannan koke koken banzan ba?"
"Ba zan iya ba Amirah, duk yanda na so na bari tunanin dake cunkushe a ƙwaƙwalwata ba zasu barni ba.
Ban taɓa zaton Bilal zai mun haka ba na kasa yarda mutumin da na so tamkar raina zai maida mun da irin
sakayyar nan" na faɗa cikin kuka har raina kuma na ji wani sanyi na samun wanda zan tattauna yanda
nake ji a zuciyata da shi.
Tunda Hansa'u ta fahimci ina shirin yafewa Bilal a faɗar ta shikenan ta fita a sabgata ta dena kirana kuma
ko da ni na kirata ba zata amsa ba kamar ma blocking ɗina tayi dan baya bayan nan idan na kira kullum
user busy ake ce mun. Mama da Abba kuwa sun zame mun kamar dodanni a yanzu, banda tsawa da
hantara ba abinda yake shiga tsakaninmu, Anty Labiba da ta kasance abokiyar shawarata tun asali na
ruguza alaƙar mu tunda na kafe akan auren Bilal, ita ɗin kuma bata da sauƙi ta kasa haƙuri ta rungume ni
tamkar yanda sauran sukayi kafin yanzu komai ya lalace.
"Kin aure shi cikin rashin sanin ainihin wanene shi, a yanzu da komai ya fito miki; idan kika sake biyewa
So ba kuskure bane bane abinda zakiyi ganganci ne, kin kuma san duk abinda aka aikata shi bisa
ganganci, idan aka samu akasi sakamakon sa ya kan zarce na kuskure.
Ya hanaki abinci kin ɗauke ido, ya zageki kin ɗauke ido, ya doke ki duka kin shanye saboda kina son sa
kina kuma son kiyi zaman aure sannan bakya so waɗanda suka ce kar ki aure shi suyi miki dariya shiyasa
kika haƙura kika zauna amma Yaya Halima har zuwa wane lokaci zuciyarki zata iya jurewa bayan kin san
mijinki yana da wata alaƙa a waje irin wacce take tsakaninku ma'aurata?"
Da firgici haɗi da mamaki na kalleta, ta gyaɗa mun kai cikin tabbatarwa kafin na buɗe baki ta ce
"Kar ma ki ɓata lokaci gurin tambayata a ina na sani, kowa kallonki kawai yakeyi suga iya tsayin lokacin
da zaki ɗauka kina rufa masa asiri.
Ba Jalilah sunanta ba? Har gidan da ta siya masa a Kano suke zuwa suna sheƙe ayar su a ciki an sani,
mota da kuɗaɗe duk da yake facaka da su zuwa yanzu kowa ya san karuwanci yakeyi tana biyansa.
Ke ce kike ta nuƙu nuƙu da abu a rai yana neman kashe ki a zatonki kin ɓoye sirrinsa bakya so
mutunchinsa ya zube bayan shi tuni ya daɗe da barbaɗar da mutunchi hotel hotel a gari, dan haka tun
wuri idan ma zaki saki ranki ki saki, idan kin ce zaki koma masa babu mai miki dole ki rabu da shi amma
kiwa kanki faɗa tun kafin duniya ta miki.
Kinga test ɗin da kuka je ɗazu? Toh Abba ne ya saka ya kaiki dan ina ji yana gayawa Mama idan kika dage
sai kin koma to fa duk abinda ya je ya dawo ki kuka da kanki, waya sani ko an gaya masa yarinyar da yake
neman bata da lafiya ne? Ke dai kawai ki godewa Allah bai shafa miki ciwo ba kuma kiyi ta kanki in kuma
kin na ce toh sai in ce miki Allah ya bada sa'a".
Yanda kasan wata uwar mata haka Amiran ta zauna tana tsara zance, duk maganganun nata ba wani
fahimtarta nayi ba hankali na ya tafi kan cewa da tayi kowa ya san abinda Bilal yake aikatawa. A hankali
na ce mata
"Babu ruwan Yaya Mu'azzam, ita magana ai kamar tusa take in dai an yita a sannu zata isa ko ina. In miki
mai gaba ɗaya, to hatta da cewa da Abba yayi kije ki ɗakko Uniform ɗin ki a gidan jiya yana sane yayi
haka ne saboda ki tarar da abinda idan kina da hankali ba zaki ko sake kallon in da Bilal ya gifta ba, amma
kika sake gwada masa ke ɗin fa kinyi nisa bakya jin kira.
To wlh tun wuri ki wa kanki faɗa dan Abba ya gama kaiwa bango da lamarinki, Sai kinji yanda ya yiwa
yayansa tas tas duk da ya ce shi bai san komai ba.
Ita kuma wannan Anty Aminar raina miki wayau kawai tazo tayi dan na tabbata su dai sun san komai"
Amiran ta sake faɗa daga haka ta tashi ta fara saka kayanta tana sake jaddada mun wai in wa kaina faɗa
na san inda yake mun ciwo sai kace wata uwata.
Jiki na yayi laƙwas da jin maganarta. Ashe ni duk bonono nake wai rufe ƙofa da ɓarawo, ina nan ina fama
da abu a ciki na ashe na bar baya ba zani kowa kallona kawai yakeyi. Yanzu ashe iyaye na sun ma san
abinda ni ban sani ashe su har sun san yana kai mata gida kenan.
Kuma mai ciwo na sake fashewa da shi, na rasa gane wace irin ƙaddara ce take yawo da ni haka, ina jin
zuciyata tamkar zata fashe saboda ƙunci da baƙin cikin halin da na tsinci Bilal a ciki amma kuma a wani
ɓangare babu ko ɗigo na soyayyar sa daya ragu, ji nakeyi ma tamkar ana sake rura mun wutar ƙaunar sa
a zuciyata. A fili na furta
"Ko sonka zai zama ajalina na haƙura da kai Bilal in sha Allahu na barka har abadah" na sake faɗawa kan
gado na cigaba da kukan da babu abinda yake rage mun saik ƙarin zafin zuciya da yake saka mun. Ina
tsaka da kukan Al'amin ya shigo, motsin buɗe ƙofar ya saka na ɗago muna haɗa ido wani sabon kukan
tausayinsu ya ɓalle mun. Ganin ina kuka ya saka ya taho da gudu ya faɗa jikina yana cewa
"Mami menene? Momy ta ce baki da lafiya dubaki muka zo yi ko naje na kirata ina ne yake miki ciwo?"
Rungume shi na yi na cigaba da kuka, abinda nake gudu ya rigada ya faru. Bilal ya cuce ni ya cuci yarana
ya ɓata musu suna ya kuma bar musu abin gori har duniya ta tashi. Sai da ya fara kukan shima kafin
daƙyar na lallashi kaina nayi shiru, ina lallashin sa Anty Labiba ta shigo.
"Ta Bilal bada kanki a sare ya jikin?" Ba tareda na kalleta ba na amsa da cewa
"Na tambayi Mama yaushe za'a je kwaso kaya ta ce ke za'a tambaya, yaushe zamuje? Dan na ji an ce
ranar asabar amarya zata tare ko kin bar musu kayan naki ne da su zata tare?"
"Au jiyan haka kika fito ziƙau baki musu aika aika kin kuma karɓo tikitin yancin ki ba?" Ta maida mun da
tambaya. Ƙasa na sauke kaina hawaye suka ɓalle mun Anty Labiba ta ce
"Toh Allah ya rufa asiri, daga yau zuwa gobe dai ki san me kike ciki gaskiya in za'a je kwaso kayan toh in
ma ba za'a je ba dai mu sani da wuri" daga haka ta miƙe ta fita tareda Al'amin.
BILAL
Kasa zaune yayi tunda sukayi waya da Anty Amina da safe ta ce masa ta yarda zataje gidansu Halima
amma tareda Yaya Aminu zasuje. Dukda ba haka ya so ba amma babu yanda ya iya, in dai Haliman zata
dawo shine muradin sa a yanzu.
Sai da ya dai dai ci lokacin ya kamata ace sun isa gidan su Halimar har sun gama abinda ya kai su kafin ya
kunna wayarsa dan tun farar safiya Zulaiha ta dira masa kira akan Kawunsu yana son ganinsa yau. Kasa
gane wasu maganganu da take masa akan wai idan ya je duk abinda Kawun ya ce masa ya ce Eh ya sani,
kawai ya katse wayar bayan ya ce mata bari zai kirata yanzu shikenan ya kasheta gaba ɗaya dan ya san
kira zatayi tayi ba zata ƙyale shi ba.
Shi kam tun da aka ɗaura musu aure yake ganin sababbin halayenta da a baya bai san da su ba abun na
ɗaure masa kai yana kuma bashi mamaki amma yanayin da yake ciki a yanzu ya sa baya bari abun ya
dame shi a rai kawai yake mata uzuri koma menene ya san idan suka zauna zai dai daita.
Wayar na kunnuwa message ɗin Anty Amina ya shigo ya buɗe ya karanta 'wayarka a kashe, idan ka
kunna ka sameni a gidan Hajja yanzun nan' abinda ta rubuta kenan.
Muƙullin mota ya ɗauka ya fita dukda bai so ta ce su haɗu a gidan Hajjan ba amma kuma ita ɗin dai
dama ita zata gayawa Hajja zancen dawowar Haliman dan shi ba zai iya ba. Basu gama da Zulaiha ba ma
balle ya sakw ɓallo wata rigimar.
Motar Yaya Aminu da ya gani ya saka ya ji tamkar ya juya amma ya makara dan suna tsaye a ƙofar gidan
shi da Baba Sani suna magana, ya gama ƙunƙunin sa kafin ya fito ya shige cikin gidan ba tareda ya ko
tsaya ya gaishe su ba. Yaya Aminu dake kallon sa ya yi ƙwafa ya ce
"Kana kallon yaron nan yanda ya wuce mu wato bamu ma ishe shi kallo ba kenan"
"Haƙuri za'a yi Aminu, yayan yau sai a barsu da halin su kawai amma ban taɓa zaton samun Bilal da irin
haka ba, ni har na rasa abin cewa ma wlh gaba ɗaya" cewar Baba Sani. Yaya Aminu bai tanka ba ya juya
suka shiga cikin gidan.
Daga yanda Bilal ya tarar da Anty Amina ya san cewa tafiya ba tayi yanda ake so ba. Gefe ya samu ya
zauna kan kujera ya shiga gaida Hajja da tayi masa banza tamkar bata ji shigowarsa ba, ya juya kan Anty
Aminan itama a ɗage ta amsa tana maka masa hararar da bai san dalili ba. Yaya Aminu da Baba Sani suka
shigo kowa ya samu guri ya zauna.
Tunda Yaya Aminub ya buɗe baki ya ringa ji ina ma ƙasa ta buɗe ya shige ciki ko kuma ya ɓace ɓat daga
gurin ko ya samu sauƙin tashin hankali, kunya da nadamar da suka masa rubdugu lokaci ɗaya. Zufa ta
ringa keto masa, tsabar yanda ya duƙar da kai take wuyansa ya fara ciwo amma bai ko yi yunƙurin
ɗagowa ya gyara zama ba balle yayi kuskuren haɗa ido da wani daga cikinsu.
A duk cikin maganganun babu abinda yafi ɗaga masa hankali irin cewar da Yaya Aminun yayi wai
mahaifin Halima ne duk ya faɗa masa waɗannan maganganun, ya akayi Abba ya san alaƙar aa da Jalilah?
Yanzu dama Halima bata rufa masa asiri ba kamar yanda yake zato duk ta faɗa musu komai?
Ya ringa share zufar dake keto masa, Yaya Aminu kuwa kamar zai aro baki tsabar masifa. Anty Amina sai
ƙafa take jijjigawa dan tun a mota bayan sun baro gidansu Halima Yaya Aminun ya balbaleta da masifa
akan me zata zubar masa da mutunchi ta sako shi cikin wannan maganar bayan ta san ta'asar da Bilal ɗin
yake aikatawa? Ta sha mamaki har ta kasa cewa komai domin idan ba dan ta san babu wani dalili da zai
saka Abban Halima yayi wa Bilal irin wannan ƙazafin ba da zata iya musawa. Ko da wasa wani ya ce mata
Bilal ɗin mutumin banza ne haka zata ƙaryata domin dai duk mugun halin Hajja da son zuciyarta tayi
ƙoƙari gurin basu tarbiyya ta san kuma da saninta Bilal ba zai aikata irin abun nan kuma tayi shiru ba.
Sai dai kuma Hajjan ta shayar da ita mamaki domin bata zaci irin amsar da ta ji daga bakinta bayan
Aminun ya gama zazzaga masifarsa ba. Kuka Hajjan ta fashe da shi tana cewa
"Wannan yarinya Halima ban san me take nema damu ba, yanzu a duniya ta rasa sharrin d zata bibiyi
Bilal da shi sai ta masa ƙazafin nema mata? Wlh Allah ya isa tsakaninmu da su kuma maganar nan ba
zamu barta ba sai munyi shari'a da su ba ta isa ta ɓatawa ɗana suna a banza ba sai naga uban da ya tsaya
mata".
"Wlh Hajja kiji tsoron Allah, ai duk abinda ya zama kece sila domin ya sani duk aje a dawo zaki san yanda
zakiyi ki kare shi. Tun ba yanzu ba duk iskancin sa yakeyi da yanda ya ringa azabar da yarinyar nan kina
kallo amma baki taɓa tsawatar masa ba sai ma ƙara zugashi da kike yi kin ɗauki karan tsana kin ɗora
mata saboda dama ba dan Allah kuka ƙulla auren ba kin so iyayenta su zame me muku bayi sai yanda
kukayi da su da dukiyar su da baki samu haka bane shine kika uzzuraqa yar su ba kalar uƙuba da jidalin
da baku mata ba amma ta jure take zaune da shi.
Saboda shegen ƙwadayi da son abin duniya ya rufe miku ido baki taɓa tunanin a ina ya samu kuɗi lokaci
ɗaya da yake buƙatu da suka zarce samunsa ba, ke dai kawai tunda yana kawo miki baki damu da ina
yake samowa ba. Wlh da ace Mahaifin mu zai dawo doron duniya sai yayi ala wadai da irin tarbiyyar da
kika ɗora yaran nan a bayan babu shi.
Abin takaici abin baƙin ciki ɗan ki ya zama karuwa, bama shi yake neman matan yana kashe musu kuɗi
ba saboda mutuwar zuciya shi yake biyawa mace buƙata tana bashi kuɗi wlh tallahi kayi asara Bilal ka
kuma zubar da ƙima da mutunchinka a idon duk wanda suke maka kallon mutumin kirki".
"Idan baka daina jifan ɗana da mugayen kalamai ba Aminu wlh idan na tashi kai ƙara harda kai zan haɗa,
dama ai ba ƙaunar mu kukeyi ba. Tunda ubanku ya mutu aka raba gado a cikinku waye ya sake
waiwayarmu sai yau da yake sharri ne shine zaka zo kana tada jijiyoyin wuya kana faɗar maganganu son
ranka toh wlh ka kiyaye ni" Hajja ta taso masa. Sai lokacin Baba Sani ya ce
"Wannan shine babbar matsalarki Hajara ƙin gaskiya kuma ban san lokacin da kika zama haka ba"
"Eh ai dama zaka faɗi haka tunda ka gama lasa a nan yanzu ka koma gindinsu zaka cigaba da maula a
haka dai zaka ƙare karen farauta kawai" ta zaburowa Baba Sanin.
"Tun da sauran mutunchi ka rubuta takarda ka aika musu da ita dan mahaifinta ya ce idan ka bari satin
nan ya wuce baka sakar masa yar sa ba ƙarar ka zaiyi, wlh kayi asara, kuma haƙƙin wannan yarinyar
kaɗai idan kayi wasa ba zai barka ka zauna lafiya ba domin karamchi ba kalar wanda ita da iyayenta basu
maka ba amma ka butulche musu ka zaɓi hanyar banza ta saɓawa ubangiji" daga haka ya sa kai ya fice
daga falon ba tareda ya saurari Hajja dake zaginsa ba.
Baba Sani ma tashi yayi ya bi bayansa ba tareda ya sake cewa komai ba. Suna fita Hajja ta miƙe ta rufe
ƙofa harda saka sakata kafin ta koma ta zauna tana kallon Bilal da yake nan zaune kamar mara rai ta ce
"Ba haƙuri zaka bani ba Bilal cewa nayi ka gaya mun gaskiya akan maganar da suka faɗa, da gaske ne
matan banza kake bi a waje ko sharri sukayi maka?"
*Wattpad @MaryamahMrsAm*
*Ban yarda wani ko wata ya juya mun labari ta kowacce siga ba tare da izini na ba*
*Kuɗin karatu yana wakiltar mutum ɗaya ne, kiji tsoron Allah karki ɗauki hakkina ta hanyar fitar mun da
littafi*
*KURA A RUMBU littafin kuɗi ne, a biya naira 800, biya a asusun*
*7061838488*
*Opay*
*PAGE 47*
"Ashe baka da mutunchi kai mutumin banza ne ban sani ba? Ban taɓa zaton haka kake ba, ashe abinda
kake aikatawa kenan a bayan idon mu kana can kana zubar mana da mutunchi kana tozarta kanka;
matan banza kake bi Bilal?"
"Ni wlh ba wasu mata da nake bi Hajja sharri kawai suka mun". Wani marin ta sake kai masa ya goce ta
ce
"Yanzu kake da bakin kare kanka kenan? Ni zaka kalla ka ce sharri ake maka saboda ka raina ni mai ya sa
a gabansa baka ce ƙaryar aka maka ba?
Karka ɗauke ni shashasha, ko da kaga a gabansu na kareka ina sane, na kuma san uban Halima ba zai
maka ƙarya ba idan ma ƙaryar yake babu yanda za'a yi Aminu ya yarda da maganar nan ba tareda ya
samu hujja ba dan ni na raba ku da su suna ƙaunar ku ba yanda za'ayi kuma a haɗa baki da shi ayi maka
irin wannan ƙazafin" sai ta rushe da kuka tana cewa
"Ba yanda banyi akan ka auri yarinyar nan ba amma duk in na tayar da maganar sai ka kawo wani uzurin
ka kauce alhalin ita burinta kenan kuyi aure yanzu da ace tun farko auren kukayi wane ɗan iska ne zai
samu abun faɗa akanmu?
Amma yanzu ka lalata mana zuri'a ka kuma janyo mana abin gori a gari wannan wane irin tozarci ne?
Tsabar lalacewa kuma har gidanka na aure kake kai macen banza ai dole Halima ta bar gidan baiwar
Allah muna nan muna ɗaukar haƙƙin ta ashe ita kaɗai ta san baƙin cikin da take ƙunsa bayan gallazawa
da azabtarwar da kake mata".
Yanda ta dage tana masa faɗa ba shi ba hatta Anty Amina ta sha mamaki domin ba zaka taɓa zaton
Hajjan da take ɗaure masa ƙugu yana duk iyashegen daya ga dama bace wannan yanzu ta shiga tashin
hankali har da kuka akan maganar da ta ji ba.
Shi dai Bilal kansa na sunkuye yana tsiyayar hawaye ya kasa sake cewa komai, Anty Amina ta kalli Hajja
ta ce
"Duk wannan maganganun da kikeyi ihu ne bayan hari Hajja domin ke kika bashi ƙofa tun farko kika
bashi goyon baya akan duk abinda yake aikatawa. Tun farkon ganina da yarinyar sai da na ce bata mun
ba,
Zubin ta da wayewarta tafi ƙarfin kula namiji irinsa ga uban hidimar da take masa sai dai idan tana da
wata manufa akan hakan. Amma me kika ce? Ɗan ki ya isa kowacce mace ta so shi ta kuma yi sha'awar
aurensa, babu tunanin komai ke da shi kuka mayar da ita saniyar tatsa tayi ta kashe muku kuɗi, kin san
ba shi da wani dalili na zuwa Abuja amma kullum yana hanyar can idan anyi ƙoƙarin nusar dake ki ce
muma hassada zamu masa.
Ko sau ɗaya baki taɓa tunanin ita ɗin a ina take samun kuɗin da take bashi sannan aikin me yake mata
da zata ringa masa irin wannan wadaƙar kamar a bishiya take tsinko kuɗin.
Na sha miki magana Hajja, babu inda son zuciya zai kaiki ƙarshe sai dai ya janyo miki ɓacin rai amma baki
ji ba tun akan Hafiz, yanda kika ringa biye masa kina zubar da girman ki kuna roƙon yaron nan har sai da
kuka ƙure shi ya janye jikinsa sannan ya sake kamo muku wani kifin kuka juya kanta. Ki godewa Allah ma
da ya zama ƙwadayin nasa iya bin mata ya kai shi ba maza ba da..."
"A'uzubillahi wace irin magana ce wannan mara daɗi Amina? In sha Allahu ba zanga wannan baƙin cikin
a zuri'ata ba" Hajja ta katseta. Anty Amina ta taɓe baki ta ce
"Ƙwadayi da son duniya su suke kai mutane ga halaka sai daga baya su zo suna dana sani mara amfani,
yanzu dai ƙwai ya fasu kowa ya ji warin, Halima kuma da a kullum baku da abin zagi da aibatawa sai ita
kinga irin abinda ta shanye ta rufawa ɗanki asiri.
Ita kuma wacce kike haƙilon ya auro mikin ku cigaba da shan romo anyi walƙiya yanzu kun san wacece
ita. Kuma na san harda haƙƙin Halima da ya fara bibiyarku, Fatana ɗaya ubangiji ya rufa maka asiri ya sa
ita wacce ka wulaƙanta uwargidanka akanta ka kashe duk kuɗin haram ɗin da ka samu akanta da
iyayenta karta zame maka kara da kiyashi dan wlh jiki na bai bani kayi dacen mace ba" ta ƙarasa tana
miƙewa tsaye da alama ta gama abinda ya kawota.
Daga Hajja har Bilal ɗin kallonta kawai suka ringayi har ta nufi ƙofa kafin ta tsaya ta waiga ta kalle shi ta
ce
"Karka ɓatawa kanka lokaci kace zaka koma ka bawa Halima haƙuri ko iyayenta domin ba zasu saurareka
ba. Ka kuma fi kowa sanin mahaifinta kaifi ɗaya ne, yanda ya toshe kunnensa a sanda kowa yake faɗin
baka dace da yarsa ba ya ɗauke ta ya baka haka a yanzu da ya buƙaci ka sakar masa ita bana zaton ko
duniya zata taru akansa akwai wanda zai saka ya haƙura ya barka da ita. Yanda ya ce ka kai masa
takardar sakinta salin alin kayi idan kuma ka shirya tonuqar asirinka wa duniya baki ɗaya ne toh kayi
gardama" daga haka ta buɗe ƙofar ta fita ta barsu.
"Amma me yasa kika ce haka Hajja bayan baki da wani buri illah na ganin na rabu da Halima a yanzu?"
"Ko a da ina so ku rabu yanzu na canza shawara. Ba zaka saketa ba, saboda idan suka samu abinda suke
so zasu tona maka asiri ne su watsa labarin a duniya, idan kuwa kuna tare dole su yi shiru domin sirrinka
sirrin yar su ne idan kuma suka fitar ba iya kai kaɗai zasu zubarwa da mutunchi ba" Hajjan ta faɗa. Ya
buɗe baki da niyyar magana dai dai lokacin Abubakar ya shigo daga tsayen da yake ya ce
"Tamkar ba ke kika gama kuka yanzu kina masa faɗa ba Hajja. Wai menene jin daɗin ki akan rayuwar
ƙunci da baƙin cikin da Halima takeyi a gidan sa? Me yarinyar nan ta tsare miki?"
"Ai duk ita ce sila, idan da ya samu abinda yake buri daya aureta a ina zai je ya haɗu da wannan
tsinanniyar yarinyar harta koya masa abinda ba halinsa ba? Dan haka yanda ta zama silar ɓacin sunan sa
haka zasu zauna tare su kwashi baƙin ciki ba ta isa ta rabu da shi ba wlh" Hajjan ta bashi amsa sai
Abubakar ya watsa hannu irin ko oho ɗin nan ya ce
"Ai kuwa sai ku shirya kwasar baƙin ciki ke da shi domin ko yaƙi Allah sai ya sakar musu yar su, kuma tun
yanzu ku fara tattara duk abinda kuka san kunci na waccen matar dan wlh ba zata barka ba, kada ka
ɗauka ka fita wayo, ka yaudareta kayi aure sannan ka salwantar mata da dukiya kaci banza na san
kallonka kawai take kuma zata yi lokacinka nan ba da daɗewa ba".
Sai da cikin Bilal ya juya ya zurawa Abubakar ido zuciyarsa na bugawa fat fat kamar zata huda ƙirjinsa ta
fito. Yanda Abubakar ɗin yake magana kamar yana da masaniya akan gidan Jalilah daya siyar da shagon
ta da yake shirin siyarwa a yanzu.
"Idan ta fasa yin lokacinsa bata ƙaunar iyayenta, roƙon ta yayi ko me? Dan Allah karta fasa ta kuskura ta
zo nan ta ce zata yi mana wani hauka taga yanda akeyi shegiya karuwa mai lalata yaran mutane" ta
cigaba da sababi.
Abubakar dai fita yayi ya basu guri Bilal ɗin ma jiki a mace kamar wanda ya sakko daga iskokai ya miƙe da
niyyar barin falon. Hajja ta ce
"Ka dai ji abinda na gaya maka ko kotun ƙoli zasu kaika kada ka kuskura ka saki Halima, sannan itama
waccen ta tare a satin nan dan karma tsautsayi ya saka magana ta fita su ce wani abu dan wlh basu isa
ka gama wahalta musu wani abu ya gifta su ce za'a warware auren nan ba ko zaka saketa sai mun fanshe
wahalar da ka musu sun maido maka da komai tukunna".
Shi dai ya fita mamakin Hajja na neman kashe shi. Sai kace wahainiya. Kwantar da sit yayi bayan da ya
shiga mota ya kwanta haɗi da rufe idonsa yana jin ina ma yana da damar maido da lokaci?
Ya daɗe yana hasashen irin wannan lokacin na tonuwar asirinsa sai dai bai taɓa zaton zai riske shi ba
saboda yanda yakeyin komai a tsare, a nasa wayon kuma ya zata zai iya yin komai har ya gama cikin sirri
ba tareda wani ya san mai ya aikata a rayuwarsa ba.
Halima ce ta fara kawo masa cikas, da ace bata duba wayarsa a waccen ranar ba da duk haka bata faru
ba amma ko da akayi hakan bai taɓa zaton cewa zata iya tona masa asiri ba.
"Idan kai ne ka ganta a irin yanayin data kamaka jiya zaka iya cigaba da rufa mata asiri?"
Kai tsaye ya bawa kansa amsa da ba zai iya ba, ya sani idan da ace ita ce a matsayinsa tun a ranar data
fara duba wayarsa daga lokacin dukkan wata alaƙa zata yanke a tsakaninsu baya jin kuma akwai wani
abu da zai saka yayi dakon irin wannan baƙin cikin a zuciyarsa da sunan rufa mata asiri ba tareda ya
amayar dashi tuntuni ba kuma ba wai dan baya son ta ba Aa, ya sani ba shi ba babu wani namiji da zai
iya wannan juriyar sai dai matan daman kuma daban Allah yayi zuciyarsu ya hore mata ƙarfin da zata iya
ɗaukar abubuwa da yawa ba kamar ta namiji ba.
Amma me yasa Halima ta zaɓi tozarta shi haka? Mai yasa bata fito kai tsaye ta faɗa masa rabuwa take so
suyi ba ya bata takardarta tunda ko da yana son cigaba da zama da ita mutunchinsa da martabarsa ta
fiye masa zama da itan amma ta zaɓi fallasa shi a gurin iyayenta?
Da sauri ya ɗauke ƙwallar da ta ziraro masa jin ana ƙwanƙwasa window motar, sai da ya dai daita kansa
dukda ya san a kallo ɗaya tilas a fuskanci yanayin da yake ciki kafin ya tashi zaune ya ɗago kujerar
sannan ya sauke window. Nasir ya gani tsaye, yayi masa murmushi ya ce
"Ko in ce yau na taki sa'a na ganka ba? Ka san zuwana nawa gidanka da shago bana tarar da kai? Ko ba'a
faɗa maka?"
Zagayawa Nasir ɗin yayi ganin haka Bilal ya cire lock ɗin motar ya buɗe ya shiga ya zauna yana cewa
"Sau ɗaya dai Madam ta ce mun ka zo shago ma ina ga sau biyu Salman ya gaya mun kazo kuma duk
idan aka sanar dani sai na kiraka a waya amma bata shiga, na ce mutumin ko amarya ce ta canza maka
layi ne aka dena samunka"
Murmushin Bilal ya sakeyi kawai ba tareda ya ce komai ba sai Nasir ɗin ne ya sake cewa
"Bata tare ba weekend ɗin nan dai zata tare in sha Allah"
"Allah ya nuna mana, Maman Al'amin ba zatayi taro ba kenan dan banji Aisha tayi maganar ba" cewar
Nasir. Bilal ya sake yin shiru sai dai kuma zuciyarsa ta raya masa shiru fa ba zai yi masa magani ba yana
buƙatar wanda zai bashi shawarar yanda zai ji da al'amarin nan a kaf abokansa kuwa idan akwai wanda
zai iya buɗewa cikinsa ba tareda wata fargaba ba toh Nasir ɗin ne.
"Wani shirme na tafka Nasir gashi yanzu komai ya kwaɓe mun na rasa yanda zanyi". Tiryan tiryan kamar
an matsi bakinsa ya shiga zayyanowa Nasir tun daga haɗuwarsa da Jalilah, irin mu'amalar da suka ƙulla
har zuwa kama shi da Halima tayi da kuma zancen Zulaiha da zaman Haliman a gidansu zuwa abinda ya
faru yau ɗin.
Motar tayi shiru tamkar babu wata halitta mai rai a ciki sai ƙarar Ac dake aiki da kuma gunjin inji, Nasir,
mamaki ne ya kashe shi a zaune gaba ɗaya kalaman bakinsa suka tafi hutun wucin gadi duk wacce ya
kamo da niyyar haɗa jimla sai ta zille dole yayi shiru kawai yana kallon Bilal ɗin yana sake bitar
maganganun daya faɗa masa a ƙwaƙwalwarsa.
Sun kwashi minti kusan goma a haka kafin Nasir ɗin ya iya cewa
"Gaskiya kayi kuskure Abokina; mai ya shiga kanka wane irin tunani kakeyi da har ka jefa kanka a irin
wannan halin?"
"Da ƙwadayi da son zuciya ba? Wlh ko da na san halinka akan son abun duniya ban taɓa zaton zuciyarka
zata iya kwaɗaita maka saɓon Allah a matsayin harkar samun kuɗi ba, Zina da aure? Abun yayi muni
gaskiya"
"Ni fa ban aikata zina ba, duk na faɗa maka iya abinda nayi amma Allah ya sani ni ban taɓa shiga jikinta
ba" Bilal ɗin ya faɗa cikin jin zafin maganar Nasir ɗin amma kuma ba yanda ya iya babu damar ya ce zai
rama tunda laifinsa ne kuma neman mafita yakeyi yanzu.
"Dama akwai wani banbanci ne tsakanin abinda ka aikata? Ko da yake duk ba wannan ba yanzu ya rigada
ya faru sai dai Allah ya kiyaye na gaba ni a cikin maganar nan gaba ɗaya ma ban fahimci mai kake so nayi
maka ba" Nasir ya sake faɗa. Bilal ya taso cikin fushi ya ce
"Kamar ya baka fahimci abinda nake so ka mun ba? In gama buɗe maka cikina kaji komai sannan kce
baka san ya zaka taimaka mun ba? Toh shawara nake so ka bani ta yanda zan shawo kan Halima tayi
haƙuri dan ni dai ba zan iya sakinta ba"
"To akan me zan saketa? Tana so na nasan kuma ko yanzu tilasta mata akayi ba wai son ranta bane dan
na san a ra'ayinta ba zata taɓa son rabuwa da ni ba" Bilal ya faɗa yana kumbura baki.
"In dai saboda Son da take maka ne ina tayata roƙo ka dubi girman Allah ka sawwaƙe mata Bilal"
"Wace irin magana ce haka ni na ce maka bana sonta?" Bilal ɗin ya sake faɗa Nasir ya tare shi da cewa
"Ƙwarai kuwa baka son yarinyar nan; kai baka ma taɓa sonta ba. Tunda dai Allah ya sa ka samu wacce
zuciyarka take so to ka rabu da ita haka taje, ka zauna da wacce kake so itama ƙila a gaba Allah ya bata
wanda zai so ta kada ɗaukar haƙƙin yayi yawa. Ta yaya za'a yi ga rashin so sannan ka nemi dawo da ita
rayuwarka dawwama tana kallonka baƙin cikin abinda ta ganka da idanuwanta kana aikatawa su kasheta
tun kafin wa'adinta ya cika?
In dai shawara kake so na baka toh babu abinda zan ce maka bayan wannan ka rabu da Halima kuma
shine mafitarka domin wlh idan ka sake yaudarar yarinyar nan ka maido da ita gidanka idan haƙƙinta ya
tashi bibiyarka sai ka rasa inda zaka tsoma ranka kaji sanyi.
Akan me zaka ringa amfani da rauninta ka cutar da ita? Ni dai akanka na taɓa ganin inda soyayya ta zama
laifi yarinyar nan ta nuna maka ƙauna ita da iyayenta sun maka halacci amma Bilal ka zaɓi saka musu ta
hanyar azabtar da ita da tozartata wlh bana raba ɗaya biyu ko wannan masifar daka jefa kanka ba komai
bane sila illah haƙƙin Halima kuma saboda bata da rabon cigaba da shan wahala shiyasa ubangiji ya
janyeta ya kawo maka wacce zaku wanke allonku tare"
"Nan gaba zaka fahimci abinda nake nufi, ni dai yanzu idan iya wannan ce maganar dama toh ka mayar
dani in da ka ɗakko ni"
"Gaskiya ni ba zan iya sakinta ba, alfarma ɗaya nake so kayi mun yanzu. Ka kirata a waya ka ce kana so
ku haɗu idan ta zo shikenan ka gama mun komai na san da zarar mun haɗu zan warware duk wata
huɗuba da suka mata suke so su raba mu" Bilal ɗin ya marairaice yana faɗa. Nasir ya rasa me zai ce
masa, ya ringa masa magiya daga ƙarshe ya ciro wayarsa daga aljihu ya miƙa masa yana cewa
"Gashi nan ka kirata da kanka dan wlh ba zaka sakani a ciki nima ta dena ganin mutunchi na ba".
HALIMA
Ina kwance a ɗaki na tun bayan da na dawo daga kiran da Abba ya mun in da ya zayyana mun yanda
sukayi da Yayan Bilal.
"Na faɗa masa ya aiko miki da takardar saki idan ba haka ba satin nan ya cinye basu kawo ba zan maka
shi a kotu ne kawai" Abban ya faɗa. Baba Salahu wanda ban san tare sukayi zaman ba ya ce
"Na ce kabar maganar kotun nan Aminu, yanda arziƙi ya haɗa idan akayi haƙuri sai a rabu ta haka. Kuma
ni sai nake ganin bai kamata ka matsanta ba domin bai zama lallai ita a ranta tana son rabuwar tasu ba"
Kallon Abban nayi in ga yanayinsa da yanda ya karɓi maganar Baba Salahun, ya kuwa lafta mun hararar
da ta sa ma mayar da kaina ƙasa ba shiri dan ban zaci ni yake kallo ba. Baba Salahu ya sake cewa
"Ka dena hararta, ita ce mai zama da shi idan taga a hakan zata cigaba da haƙuri ai mu bisu da addu'a
Allah ya shirye shi na san kuma tunda har haka ta faru in dai ba shaiɗan bane a tare da shi ai kunya kaɗai
ta isa ta saka ya sauka daga layin banzan da ya hau tunda dama can ba halinsa bane"
"Yanzu Yaya idan ɗaya daga cikin yayanka ta zo da irin wannan matsalar irin hukuncin da zaka yanke
mata kenan?" Abban ya faɗa cikin ɓacin rai yana kallon Yayan nasa, Baba Salahu ya ɗan yi jim kafin ya ce
"Karka canza mun magana Aminu. Ni bance abinda yayi dai dai bane abinda ya saka har kaji nayi wannan
maganar kawai saboda na san halin Sadiya, ban manta irin dambaruwar da aka sha da ita ba babu yanda
kowa bai yi akan ta haƙura da auren yaron nan ba amma ta kafe ina jiye maka tsoron ka takura a raba su
daga baya kuma su koma au ɗinke ta hanyar da ba za'a so ba tunda dai tana son mijinta"
"Kayi haƙuri ka ajiye duk wani tunaninka ko shawara a yanzu, Halima yatace, da yardata ta aure shi a
yanzu kuma da na hangi cutarwa a zamansu zan datse alaƙar dan haka kowa ya riƙe shawarar sa bana
buƙatar su na rigada na yanke hukunci kuma ko mutuwa zatayi wlh sai sun rabu" Abban ya faɗa yana
kallona. Hawayena suka ƙara gudu har sannan dai kaina yana ƙasa ban sake ɗagowa ba ya cigaba da
cewa
"Kin ɗauka shirun da kikayi zai tabbata gaskiya ba zatayi halinta ba kenan? Tun zuwan da yaron nan
abokinsa yayi da maganganun daya faɗa mun na saka mutane suka mun bincike na kuma ringa bibiyar
duk wani motsinsa a sannu kuma na gane gaskiyar komai har abinda bai faɗa mun ba na gano da kaina
dan shi da ya zo ce mun yayi kawai ko da ace kin nuna buƙatar komawa gidan Bilal mu hanaki saboda
Bilal ɗin ba wanda muka sani a baya bane cigaban zamanki da shi kuma zai iya jefa ki cikin halin da zamu
zo muna da na sani.
Ba sai na faɗa miki abinda na binciko ba dan kin rigani sanin wasu amma tunda naga har yanzu
hankalinki bai tsaya guri ɗaya ba a hakan kike tunanin sake koma masa to babu wannan maganar,
yanzun ma na kiraki ne dan kar idan yayi taurin kai na maka shi a kotu ki ce an tozarta uban yayanki, dan
haka tun da girma da arziƙi ki faɗa masa ya sallameki".
Na ringa kallon Baba Salahu in ji ko zai sake magana amma bai ce komai ba da alama yaji gargaɗin Abban
da ya ce baya buƙatar shawarar kowa. Haka na tashi ina share hawaye jiki ba ƙwari na koma ɗaki na
kwanta na cigaba da sabuwar sana'ata.
Ƙarar wayata ta saka na waiwaya na kalli in da take, sunan Yaya Nasir da na gani ya saka na ɗakko ta
amma kafin na amsa ta katse. Ajiyewa nayi ina tunanin ko me ya saka ya kirani sai Allah. Ƙila haƙuri zai
bani ya ce in koma gidan Bilal ko kuma shima irin Hafiz ɗin ne cin dunduniyar Bilal zaiyi ya ce kar in
koma?
Tambayar kaina na shigayi wai ma shi Hafiz meye ribarsa duk a cikin maganar nan? Yanzu ladan me ya
samu daya zubarwa da Bilal mutunchi a gaban iyayena? Wani haushinsa ya kamani, wato shiyasa aka ce
makashinka yana tareda kai yanzu idan ba halin ɗan adam na rashin tsoron Allah da munafunci ba ta
yaya za'ayi abokinka ko ma in ce amininka ne zai kawo sukarka gidan surukai shi da ya kamata ace ko
wani aibunka ya ji sai inda ƙarfinsa ya ƙare?
Kiran daya sake shigowa ya tsayar mun da tunani na ɗaga da sallama muryata a dashe saboda kukan da
na sha. Daga can ɓangaren Bilal ya sauke numfashi tamkar jaririn daya yini yana kuka, na zare wayar
daga kunnena ina kallon screen ɗin dan in tabbatar da waye ya kira amma naga number Nasir ɗin ce dai.
"Dan Allah karki kashe Halims" ya faɗa kamar ya san abinda nake shirin yi kenan. Na dakata da waya a
kunne ba tareda na ce komai ba daga can ɓangaren ya marairaice ya ce
"Duk abinda aka faɗa miki ba gaskiya bane wlh so kawai sukayi su raba mu"
"Abban nawa ne yake ƙarya kenan?" Na faɗa cikin dasasshiyar murya, da sauri ya ce
"Aa wlh ba shi nake nufi ba su waɗanda suka faɗawa Abban nake magana ai kin sani dama duk ba
ƙaunar ganinmu tare sukeyi ba dan Allah karki bari suyi galaba akanmu kinji my Halims na sani kina so na
zaki mun uzuri duk abinda ya faru sharrin shaiɗan ne amma ina neman alfarma ki bani dama mu zauna
in warware miki komai na san zaki fahimce ni daga nan sai kiyi mana alƙalanci".
*Wattpad @MaryamahMrsAm*
*Ban yarda wani ko wata ya juya mun labari ta kowacce siga ba tare da izini na ba*
*Kuɗin karatu yana wakiltar mutum ɗaya ne, kiji tsoron Allah karki ɗauki hakkina ta hanyar fitar mun da
littafi*
*KURA A RUMBU littafin kuɗi ne, a biya naira 800, biya a asusun*
*7061838488*
*Opay*
*PAGE 48*
Abinda ya fi tsaya mun a rai yanda duk sanda zamuyi magana sai ya ce ya san ina son sa, kenan shi baya
so na kuma yana ɗaukata wawuya saboda ina sonsa dole na jure duk wani abu da zan fuskanta daga
gare shi ko me?
"Dan Allah karki ce Aa Halims ki taimaka mu haɗu kada ki bari mahassada suyi galaba akanmu" ya sake
faɗa cikin marairaice kamar zai fashe mun da kuka. Cikin dakiyar da na aro na azawa kaina na ce
"Haba Halims me yasa ki...." Ban tsaya sauraron mai zai ce ba na katse wayar na jefar da ita gefe na dafe
ƙirji na da yake duka uku uku.
Siririn kuka na saki, ina jin yanda zuciyata take yamutsawa dalilin famin ciwon son da ya cika ta. Na jima
ina kukan sai da aka fara kiraye kirayen la'asar kafin na tashi nayi sallah bayan na idar nayi wanka, ko mai
ban shafa ba na zura doguwar rigar abaya na ɗaure kaina da ɗankwalinta na fita falo. Tunani nakeyi
yanda Mama zata barni na bi Anty Labiban.
Mama kaɗai na tarar a falo tana shan fura Sharifa na kwance tayi matashi da cinyarta tana bacci na
zauna kan kujera ina kalle kalle kafin na ce
"Eh, Amirah sun fita da Zainab wai zasu karɓo awara a gidan Sahura ta bayar ayi musu" Maman ta bani
amsa a sake yanda banyi zato ba ganin yanzu mun koma kamar wasu abokanan faɗa a gidan kullum cikin
ɗaure mun fuska take.
"Tun ɗazu ta wuce dama wai hanya ce ta biyo da ita ba zama sukayi ba"
"Lah shine basu mun sallama ba na so fa in bita" na faɗa a sanyaye, na saci kallonta jin tayi shiru itama ni
take kallo kamar me karantar gaskiyar dake bayan maganar da nayi sai kuma ta ce
"Kina gurin Abbanku ai sanda suka tafi, sai ki bari gobe in Allah ya kaimu ki je ai"
"Yau ɗin dai na so in je sai na kwana gobe na dawo" na sake faɗa, ga mamaki na sai na ji ta ce
"To sai ki shirya ai ki tafi yanzu tunda Magaji yana nan sai ya sauke ki". Ajiyar zuciya mai ɗan nauyi na
sauke kafin na miƙe na wuce ɗaki. Kaya kala ɗaya na zuba a jaka sai ɗan abinda zan buƙata na undies na
zura Hijabi na fito har sannan Mama na zaune ta bini da kallo bayan da na mata sallama. A compound
muka haɗu da Abba da alama fita zaiyi, naji kamar na juya amma ya rigada ya ganni dole na ƙarasa na
amsa masa tambayar da yake mun akan ina zanje.
Shi ya sauke a gidan Anty Labiban, kamar mai tunanin zan tafi wani gurin bai matsa ba sai da na shige
gidan nayi murmushi kawai ina cewa "ko Abba ya zata guduwa zanyi ne ya kasa ya tsare".
Ban ɓoyewa Anty Labiba dalilin zuwana gidan ba, tayi shiru tana kallona kafin ta ce
"Ban rigada na yanke shawara ba Anty amma In sha Allahu yau zan sanar da ke matsayata". Tayi jimm
kamar tana so ta ce wani abu amma kuma ta fasa sai ta ce
"Zaki tanadar masa wani abu ne?" Ta tambayeni, sai da nayi ɗan murmushi kafin na ce
Ta fashe da dariya ta ce
"Ai ko shi na san sai yayi shakkar cin wani abu a gidan nan yau" na bata amsa ta wuce kitchen tana cewa
"Toh ai shikenan, bari in ɗorawa mijina abinci yana hanya". Tashi nayi na bita na kama mata aikin, hirar
duniya muka taɓa tun ina amsawa kaɗan kaɗan har na ware abinda na manta rabon da inyi doguwar
magana irin haka harda dariya inaga tun ranar dana dawo daga Camp ɗin NYSC.
BILAL
Tamkar zai fasa kuka ya faɗawa Nasir inda Halima ta ce su haɗu,
"Wa? Ni? Idan ka ganni a lahira toh kaini akayi. Ai kayi mai wuyar tunda har ta amince ku haɗu ai akwai
haske a lamarin kawai kaci gaba da addu'a shine ya rage yanzu".
Bilal ya goge zufar da ta keto masa dukda sanyin Ac daya cika motar kafin ya ce
"Toh dan Allah zaka rakani gurin Kawun su Zulaiha, ta ce yana son ganina yau saboda ita ma na kashe
wayata tun safe idan ba haka ba addabata zatayi da kira".
"Ita amaryar ce tun yanzu ta fara isarka? Ikon Allah. Haɗe rai Bilal yayi ya zaro wayarsa daga aljihu ya
kunnata tun bata gama saituwa ba kuwa sai ga kira ya faɗo ko suna bai fito ba alamar contacts ɗin ma
basu gama booting ba amma ya gane number Zulaiha ce. Ya nunawa Nasir yana cewa
"Bala'i, sai kace bokanya? Ta hango ka kunna wayar a madubinta. Alamar yayi shiru Bilal ya masa kafin
ya amsa wayar, yanda kasan ɗan da ta haifa tanaji ya amsa ta ce
"Wannan wane irin kut****uba ne zaka kashe waya ayi ta kiranka ba'a samu?"
Sai da ya zare wayar daga kunnensa ya duba screen ɗin ga sunanta nan ya fito yanzu DUNIYATA kafin ya
sake mayar da ita kunne mamaki na neman kashe shi da jin abinda ta faɗa, ita kuwa ko a jikinta ta
balbale shi da masifa akan me y kashe waya gashi nan ya janyo Kawunta ya kira yana ta musu tijara su da
Ummansu akan rashin zuwan da bai yi ba.
"Ya ce kazo ka same shi a nan gidan bayan sallar magriba idan kaga dama karka zo na rantse da girman
Allah sai ka gane baka da wayo sai na nuna maka kai ƙaramin yen yen ne" ta ƙarƙare maganar kafin ta ja
dogon tsaki ta kashe wayar.
Bilal dai kasa cire tasa wayar yayi daga kunne yayi sakato kamar wani wawa tsabar mamaki. Nasir daya
gama jin komai, duk yanda ya so ya hana kansa yin dariyar data taso masa dole ya saketa jin tana nema
ta shaƙe masa maƙogaro, Bilal ya kalle shi da idon sa da suka kaɗa sukayi jajir sai kawai ya ɓalle murfin
motar ya fita waje ya ringa sheƙa dariya kamar wani taɓaɓɓe.
Bilal ya sauke ajiyar zuciya bayan daya ajiye wayar maganganun Zulaihan na masa amsa kuwwa a kunne,
a fili ya ce
"Aljanu ko?" Nasir daya buɗe kofar motar ya faɗa yana sake sheƙewa da dariyar data fi ta farko. Sai da
yayi da gaske kafin ya iya riƙe kansa ganin Bilal ɗin ya cika yayi fam kamar zai fashe. Suna tafi Nasir na
cewa
"Amarya, Amarya bata laifi ko ta kashe ɗan masu gida" shi dai Bilal tafi ka mutu bai ce masa ba har ya
sauke shi a ƙofar gidansa.
"Dan Allah ka shirya da wuri" Bilal ya faɗa bayan Nasir ɗin ya sauka, Nasir ya danne dariyarsa kafin ya ce
"Baka da matsala mutumina sai ka zo" ya wuce ciki yana sake tuntsurewa da dariya.
Bilal kuwa gida ya wuce, sai da ya shiga gidan ya tuna ashe ko breakfast bai yi ba yau ɗin. Sai lokacin ya
haɗa tea ya sha da ya ringa jin sa kamar maɗaci, yanzu Allah kaɗai ya san mutum nawa suka san halin da
yake ciki. Ƙila har yan unguwar ma sun sani yanzu da ya shigo sai ya ga kamar masu gadin layin daya
wuce sunyi gulmar sa gaba ɗaya ya tsargu ji yake kamar duk in da ya wuce kawai kallonsa akeyi amma
labari ya gama baza ko ina ga halin sa.
Zuciyarsa ta raya masa komai zai wuce da zarar Halima ta dawo kuma Zulaiha ta tare, musamman tunda
dama maganar daga ɓangaren Haliman ta fita idan aka ga ta dawo gidansa hakan zai aka kokonto a
zukatan mutane domin da wahala ace bayan wannan abun ya faru kuma ta sake komawa gidansa amma
idan akayi haka kuma gashi yayi aure za'a iya cewa ma saboda ƙarin auren ya saka tayi masa yarfe yanda
mata suka saba yiwa mazajensu idan zasuyi aure.
Wannan tunanin da yayi ya sanyaya masa zuciya har ya ɗan samu nutsuwa ya shiga kiran Agent ɗin daya
bawa tallar shagunan Jalilah. Duk ma abinda zai faru a ƙalla ya tsira da abinda zai riƙe kansa surutun
mutane mai wucewa ne da sunyi sun gaji zasuyi shiru. Agent ɗin ya sanar masa an samu mai siyan gurin
kuma da daraja sosai dan haka gobe yaje a ƙarƙare magana dan dagaske suke kuma da kuɗin su a hannu.
Wannan labarin ya sake faranta masa rai, yana kashe wayar ya kira Engineer dake aikin gyaran sabon
gidan da ya siya wanda Zulaiha zata zauna a ciki. Sabon gini ne bene na zamani wanda har plaster anyi
matsuwa ta saka mai shi siyarwa kuma ya same shi kwasha kwasha, ɗan gyara kaɗan akayi na abinda
baiyi masa ba, jiya da ya je an gama komai ƙwayayen wuya ake ƙarasa sakawa dan har yaran da zasu
share gidan su wanke ya tarar an samo yana kiran Engineer kuwa ya gaya masa ai an gama komai yanzu
ya bar gidan muƙullin yana hannun maigadin gidan da yake jikin nasan dama shi ake barwa ya ma tura
masa video ta WhatsApp tun ɗazu.
Godiya ya masa, a ransa ya ayyana da gidan zaiyi bikon Halima. In dai ta yarda kawai ita ta koma can
idan ya so a canzawa Zulaihan penti ta shiga nan ita tunda babu abinda gidan yayi a matsayinta kuma ko
wanda bai kaishi ta samu ba ai sai dai ta godewa Allah ita kuwa Halima dama gidan bene shi ya dace da
ita tunda daga cikinsa ta fito.
Ƙarfe shida ya fesa wanka ya tafi gidan Nasir daga can zasu wuce gidansu Zulaiha dukda idan ya tuna
abinda ta faɗa masa ɗazun sai ya ji kamar kar ya je sai kuma zuciyarsa ta tuna masa ba laifinta bane
iskokin da Ummansu ta faɗa ne suke taɓa ta sa wannan ya taushi zuciyarsa ya isa gidan Nasir ɗin.
"Kaga na Halima angon Zulaiha ga kuma Jalilah a gefe" Nasir ya tsokane shi bayan ya fito, ya haɗe rai
tam ya ce
"Bana so"
"Na bari Allah ya baka haƙuri". Suna tafe suna yar hira har suka isa unguwar, sai da suka tsaya sukayi
sallar magriba a masallacin layin su Anty Jalilah kafin suka fara wucewa gidansu Zulaiha dan yana sallah
ta turo masa text wai ga Kawun fa ya iso.
A tsakar gida suka zaune, Zulaihan da Ummansu sai Nuratu sun sha hijabai kamar masu takaba kowacce
ta raɓe a gefe tana zare ido sai Kawun nasu dake zaune kan farar kujerar roba yana girgiza ƙafa. Tare
suka isa da Mijin Nuratu wanda shima suka zo tareda wani abokinsa, suka gaisa gaba ɗaya kafin akayi
musu iso suka zauna kan tabarmar da aka tanadar musu.
Cewa Kawun yayi Nasir da abokin Faruk Mijin Nuratu su ɗan basu guri.
"Ai komai yana son sirri, dukda ku aminanku ne amma ai akwai abinda ba zaku so suji akan matanku ba
ko?" Kawun ya faɗa, Ummansu Zulaiha tayi saurin cewa
"Ni dai ban sako bakinki ba idan kuma ba zaki iya yin shiru ba kema ki tashi ki bamu guri" Kawun ya taso
mata. Hannunta Zulaiha ta kama cikin alamar tayi shiru, Kawun ya ja tsaki ya ce
"Na san dai dukkaninku ba yara bane tunda kuma kuka yarda har kuka ɗaura aure da yaran nan toh kunji
kun gani kuna son su a yanda suke ne musamman kai" ya nuna Bilal. Kallonsa Bilal ɗin yayi yana jira yaji
ƙarin bayani Kawu ya cigaba da cewa
"Tone tone dai babu kyau tunda abinda ya faru ya rigada ya wuce amma dukda haka dole in ja musu
kunne shiyasa na taraku gaba ɗaya, babu kawo ƙara dan iya shari'ar da nayi a baya masa Allah ya bani
lada na gaji. Duk wacce ta muku ba dai dai ba kuci ubanta dai dai gwargwado amma banda dawowa gida
iya gatan da zaku musu kenan dan wlh duk wacce ta kuskura aurenta ya mutu ta sani ba sake auruwa
zatayi ba dan suma ɗin ba ƙaramin jahadi sukayi ba da suka.... "
"Haba Shafi'u wannan wane irin abu ne?" Ummansu ta sake katse shi. Zulaiha ta ruƙo ta ganin tana
shirin miƙewa Nuratu dai na gefe kanta a ƙasa Kawun ya ce
"Mariya, ko dai rufa rufa kuka yiwa yaran nan shiyasa kike ta katseni kar in faɗi gaskiya?"
"Rufa rufar me? Ai duk cikinsu babu wanda bai san tsanar da ka mana ba da irin sharrin da kake
bibiyarmu da shi kullum. Kai nake so na rufawa asiri karka zubar da mutunchin ka a gabansu amma ka
saki baki bayan duk wanda yake sauraronka yasan tsantsar hassada da baƙin cikin Allah yayiwa yara gata
ya basu mazaje irin wanda yayanka basu samu ba shiyasa kake so ka ɓata su toh ta Allah ba taka ba"
Umman ta faɗa cikin masifa.
"Sai dai ki naɗe tabarmar haukarki da kunya amma ni ɗan gaskiya da gaskiya ne kin sani kuma dole in
tabbatar ba'ayi kitso da kwarkwata ba".
Bilal dai kallonsu kawai yake, shi dai Umman da ya sani sama da shekara goma idan aka saka mata hannu
ba zata ciza ba amma yau ita ce take tada jijiyar wuya haka tana masifa ana riƙeta kamar zata daki
Kawun?
Faruk ne ya ce
"Dan Allah kuyi haƙuri, ni dai a ɓangarena babu wata matsala dan babu abinda Nuratu ta ɓoye mun
kuma iyayena basu nema mun aurenta ba sai da sukayi bincike kuma da yardarsu da komai na aureta
dan haka ni dai a gurina babu wata matsala In sha Allahu".
Bilal ya kalle shi, kansa ya fara kullewa. Wai toh meye ake cewa an sani da shi bai sani ba?
"Nima haka".
"Toh madallah Allah ya taya ku ruƙo sai aje ayita haƙuri. Ranar Asabar in Allah ya kaimu aka ce tariya ko?
Dama babu wani taro da za'ayi, mutum biyu sun isa daga kowanne ɓangare suzo su ɗauki amaren"
Kawun ya sake faɗa.
Umma ta zauna tana sauke numfashi kamar wacce tayi gudun tsira, daga nan Kawu ya miƙe ya musu
sallama Faruk ma ya fita bayan ya ce Nuratu ta biyo shi aka bar Bilal da Umma sai Zulaiha data sunkuyar
da kai kamar wacce take gaban Alƙali. Yafi minti goma ya gagara ce musu komai suma haka sai da Nasir
ya kira shi a waya kafin ya miƙe yana musu sallama ko motsi Zulaihan batayi ba Umman ma kamar a
tsorace ta masa Allah ya tsare ya fita, a soro ya tarar da su Nuratu tana rungume jikin Faruk tana kuka ya
giftasu yaa jin sa yana cewa
"Ki dena kuka, kowa da kalar ƙaddararsa a rayuwa kuma na gaya miki ko me kika aikata a baya ina sonki
a haka tunda dai kin tuba kin dena kuma har kika iya faɗa mun na tabbatar dagaske ne kin bari karki ji
komai In sha Allahu daga ni har dangina ba zaki samu matsala da kowa ba".
Ya ringa juya maganar a ransa, to ko dai abun iya ita Nuratun ya shafa shiyasa Zulaiha bata gaya masa
ba? To menene ma? Ya ringa tambayar kansa a garin tunani har ya wuce gidan Anty Jalilan ma sai da
Nasir ya ankarar dashi.
A falon baƙi suka zauna, ya ringa kallon Al'amin da yayi kamar bai sanshi ba dan da suka shiga yana
kallon su ya juya ya wuce sai da Nasir ya kira shi ne ya tsaya amma yaƙi zuwa gurin Bilal ɗin Nasir ɗin ma
daya riƙe masa hannu bai sake da shi ba Alhaji Sale na shigowa kuma ya fizge ya tafi gurin sa.
Faran faran suka gaisa da Alhaji Salen da bai daɗe da shiga gidan ba daga tafiya, masallaci zai fita sallar
isha'i dan haka suka tafi gaba ɗaya. Can falon ya ce a kai musu abinci bayan sun dawo suka ci tare Nasir
dai ya ware ya kashi abincin sa Bilal kuwa dukda yana jin yunwa kaɗan ya ci dan haka kawai yake ji
kamar wata manaƙisar aka shirya masa idan ba haka ba shida yake da laifi a gurinsu shine harda bashi
abinci?
Sai da aka kwashe kwanukan kafin Alhaji Salen ya wuce ciki ya turo musu Halima. Ta shiga da ƙaramar
sallama kai a ƙasa kamar farin shigar maita haka Bilal ya zuba mata ido yana kallonta, rabon da ya sakata
a ido tun ranar daya kaita gida. Ramar da tayi ta taɓa shi dan sukda hijab ne har ƙasa a jikinta ramarta ta
fito ƙarara.
A hankali ta ringa tafiya harta isa kujerar da tafi kusa da ƙofa ta zauna, murya ba amo ta gaida Nasir da
tausayinta ya rufe shi lokaci ɗaya. Halima mace yar gayu amma kalli yanda ta lalace lokaci ɗaya ta zama
kalar tausayi. Miƙewa yayi ya fita dan ya basu guri, yana rufo ƙofa Bilal ya tashi da sauri ya nufeta, da
sauri itama ta miƙe tayi baya ganin rungumarta yake shirinyi.
Ta galla masa hararar da ta saka gabansa faɗuwa domin ko a mafarki bai taɓa ganin ta da irin kallon nan
ba.
HALIMA
Ganinsa nayi tamkar baƙin kumurci lokacin daya nufoni, hoton fuskarsa akan cinyar Jalilah ya gifta mun
da sauri na miƙe na ja baya ganin yana rungumata.
"Meye haka Halims? Kin san adadin kewarki da nayi kuwa? Dan Allah ki tsaya inji ɗumin ki ko zan samu
nutsuwar zuciya nayi kewarki har bansan adadi ba wlh" ya faɗa yana sake nufo ni.
Tsawa na buga masa da dukkan ƙarfin daya rage mun, ya tsaya can a inda yake cikin mamakina, ban
damu ba na nuna shi ina cewa
"Ka koma in da ka taso idan ba haka ba zan tafi ba kuma zaka sake samun damar magana dani ba har
abadah"
"Haba my Halims sai kace wacce zata mutu?" Ya faɗa yana ja baya bai dai koma kan kujerar daya tashi
ba, nayi tsaki na ce
"Ba wasa nakeyi ba, minti goma kake dashi idan kuma ya cika baka nutsu munyi maganar data kawoka
ba kada ka tsammaci zaka sake samun irin wannan damar a gaba". Ganin da gaske nake ya saka ya koma
kan kujerar ya zauna yana kallo na, nima zama nayi kaina a ƙasa dan ba ƙaramin ƙarfin hali nake ba ji
nake kamar an jona mun mayen ƙarfe yana jana in je gare shi amma na dake.
"Wlh Halima duk abinda ya faru ba laifi na bane sharrin shaiɗan ne" ya faɗa yana zamowa daga kujerar
kamar zai durƙusa a ƙasa. Ban kalle shi ba ya cigaba da cewa
"Kuma wlh duk abinda kike zato ba haka bane tsakanina da Jalilah. Kawai ƙananan romance ne irin
abubuwan da na so mu ringayi lokacin da nake neman aurenki kika ƙi amma wlh ban taɓa kusantarta ba
kuma idan baki yarda ba zan kira miki ita ta faɗa miki da bakinta".
Shiru yayi dan shi bai tuna abinda take magana akai ba, ya san dai ƙi tayi, duk yanda ya kaɗata ya raya ko
hannunta ya kama bisa kuskure a lokacin ne kaɗai yake ganin ɓacin ranta har ta iya rufe ido ta masa
rashin mutunchi daga baya ya rabu da ita tunda bata so kuma yana samu a wasu gurin a bati ma wasu so
suke ya taɓa su.
"Kiyi haƙuri" ya faɗa. Na ɗaga kai na sama saboda hawayen da yake shirin zubo mun sai da suka ɗan
tsahirta kafin na kalle shi na ce
"Kin haƙura ko my Halims? Ni dama na san soyayyar da kike mun ba zata bari ki yarda a rabamu ba"
"Sonka, soyayyarka kullum maganarka kenan, duk idan zakayi magana sai kace son da nake maka ya saka
ko soyayyar da nake maka ba zata bari nayi kaza ba Bilal mai ka ɗauke ni?" Na faɗa ina cije leɓe na. Ya
ɗan yi shiru kafin ya ce
"Bilal ka taɓa so na?" Na jefa masa tambayar da take cin raina, ya zaburo zai matso in da nake na ɗaga
masa hannu sai ya koma baya yace
"Mai ya sa duk sanda ka tashi magana baka taɓa cewa nayi abu saboda son da kake yi mun ba sai dai
kace saboda son da nake maka" na sake jefa masa wata tambayar.
Kamar an doki bakinsa maganar ta fito
Da hannu biyu ya dafe baki bayan daya fuskanci abinda ya faɗa. Na saki murmushin daya taho tareda
hawayen da nake ta riƙewa na sake ɗaga masa hannu ganin ya sakw nufoni yana cewa
"Wlh ba abinda zan faɗa ba kenan, cewa zanyi son da nake miki yafi wanda kike mun yawa".
"Amsar da nake buƙata kenan kuma na sameta. Nagode da alfarmar da kayi mun ka zauna dani tsahon
lokacin nan albarkacin son da nake maka, nagode da duk abinda ka mun a tsayin zamanmu.
Na san yanda zuciya takeji a lokacin da abinda bata so yake mata naci, kayi ƙoƙari daka iya kasancewa
tareda ni tsayin lokacin nan, daga yau ka yantu, ba zaka sake kwanciya ka tashi da tunanin ganin wacce
zuciyarka bata muradi ba.." kukan daya sarƙe ni ya hanani cigaba da magana. Biro da takardar da na
taho dasu na zaro daga aljihun rigar jiki na na ɗora akan center table ina cewa
"Gashi nan, ka datse alaƙar da take tsakanina da kai ka samarwa zuciyoyinmu yanci".
"Ba zan iya sakin ki ba Halima wlh ina sonki" ya faɗa bayan daya rarrafo ya kama ƙafafu na. Haɗe kai da
cinya nayi na shiga rusa kuka tamkar wacce za'a rataye, jin yana ɗagoni, lokaci ɗaya cikin wani fushi da
ban san sanadinsa ba na ɗago na wanke shi da marin da ni kaina sai da naji a jikina saboda raɗaɗin da
tafin hannuna har zuwa ƙasusuwan hannun suka ɗauka saboda ƙarfin marin.
Yayi baya ya zauna wanwar yana kallona cikin mamaki, takardar na nuna masa na ce
"Ka ɗauki takardar nan ka rubuta abinda na buƙata. Sanyin halin Halima ka sani, kada ka bari in nuna
maka ɗaya ɓangaren domin ba lallai idanuwanka su iya jurar kallo ba".
"Ke karki ga ina lallaɓa ki ki nemi raina mun hankali, ba dai a hannuna igiyar auren take ba? To ba zan
saki ba idan kina da ƙarfi ki danne ni ki ƙwata ko ki turo wani ya ƙwatar miki. Ƙaryar banza ƙaryar wofi
kawai ni da ke mun sani Halima wlh ba zaki iya rayuwa babu ni ba gara ma ki rufawa kanki asiri mu koma
tun lokaci bai ƙure miki ba" ya faɗa cikin fushi bayan daya miƙe tsaye.
"Ba dan kar inyi saɓo ba dana tsinewa ƙaddarar data haɗa ni da kai, wlh Bilal ko ban ce komai akanka ba
da sannu sai kaga sakayyar butulcin da kayi mun, kaje Allah ya isa tsakanina da kai za kuma ka gani tunda
kaƙi sakina ta lallami wahala zata sa ka saki ko baka ƙaunar Allah" na faɗa ina fashewa da kuka na juya
zan bar falon dai dai lokacin da Nasir ya shigo da alama hayaniyarmu ta janyo hankalinsa.
"Tsaya Halima, kai Bilal menene haka? Mu da muka zo sulhu kuma zaka ɓige da rashin hankali?" Nasir
ɗin ya faɗa. Na coge a tsaye dan ya tare hanyar ina jin Bilal na cewa
"Dallah rabu da ita aikin banza laifi na ne da na zo shiyasa har ta samu damar yi mun wata fuffuka. Na
faɗa kuma ba zanyi sakin ba a saka kaina gabas a yanka. Ya ne iyayen naki basuyi su hanaki aure na ba
amma kika nace, kina gidana sau nawa suna cewa ki kashe auren kika ƙi, sau nawa kika zaɓe farin ciki na
akan nasu sai yanzu ne zaki zo kina wasu maganganu? To ba'a son naki kuma ba za'a sakeki ba kiyi
abinda zakiyi. Idan kinga dama ki dawo in ma kin so kiyi ta zama a gidan naku har duniya ta tashi ni ba
matsalata bace"
ya nufi ƙofa fuuuu ya bangaje Nasir sai ganin sa mukayi kamar an chillo shi ya dawo baya ya faɗi tim a
ƙasa.
*Wattpad @MaryamahMrsAm*
*Kuɗin karatu yana wakiltar mutum ɗaya ne, kiji tsoron Allah karki ɗauki hakkina ta hanyar fitar mun da
littafi*
*KURA A RUMBU littafin kuɗi ne, a biya naira 800, biya a asusun*
*7061838488*
*Opay*
*PAGE 49*
Kafin mu gana gane me ya faru Mu'azzam ya shigo ɗakin babu kuma ɓata lokaci ya zare belt ɗin jikinsa
ya shiga dukan Bilal yanda ka san Allah ya aiko shi. Gefe na ja da sauri cikin tashin hankali na ɗora hannu
biyu a ka na fasa ihu ina kiran sunan Mu'azzam ɗin, abin takaici Nasir da yake namiji daya kamata ko
murɗe Mu'azzam ɗin yayi ya ƙwace bulalar idan ma yana tsoron kaiwa Bilal ɗin agaji ya haɗa da shi wai
sai ya tsaya daga gefe yana ce masa ya bari.
Bilal kuwa kamar mace haka ya shiga birgima a ƙasa dan ya kasa kare dukan, Anty Labiba ta shigo da
alama ihu na da na Bilal be ya janyo hankalin ta tana ganin abinda yake faruwa ta shiga salati tana cewa
"Babana memene haka? Ya zaka rufe shi da duka? Bari dan Allah ko ma menene ai bai kai ayi duka ba sai
ayi haƙuri a sasanta da baki" ta ƙarasa ta riƙe Mu'azzam ɗin. Dakatawa yayi daga dukan Bilal ɗin ya nuna
shi yana numfashi ya ce
"Ba ka ce ta ƙwata ta ƙarfi ba? Ko ta turo wanda zai ƙwatar mata? Toh wlh ko ka rubuta sakin nan yanzu
ko kuma mun ɗaura da kai daga yau duk in da na ganka sai na haɗa maka jikinka har randa zaka gaji ka
saketa".
"Daɗi na da kai wauta in ba haka ba meye naka na shiga tsakanin ma'aurata? Ita tace ka ƙwatar mata ko
yaya? Idan Halima ce wlh zaka sha mamaki yanda zata watsa maka ƙasa a ido gara ka barta dashi. Da
Allah wuce muje kayi haƙuri Bilal ka san Mu'azzam da zuciya" Anty Labiba ta faɗa tana jan Mu'azzam ɗin
suka fita daga falon.
Bin su nayi da kallo, daga yanda take magana kawai a jiki na naji duk yanda akayi wannan abun shiri ne
wlh da saninta. Na maida hankali kan Bilal dake kwance maganshiyyan yana jan numfashi Nasir na
gefensa yana masa sannu shi ɗin ma sai na ga kamar ƙunshe dariya yakeyi yana masa sannun.
"Miƙo mun takardar can" Bilal ya faɗa daƙyar Nasir ya tashi da sauri ya ɗakko takardar ya bashi. Yana
yarfe hannu saboda zafi dan ta ko ina Mu'azzam ya ringa zuga masa belt ɗin duk jikinsa ya ɗauka yayi
gajeran rubutu ya jefo mun jotter yana cewa
"Na sake ki Halima, kije na sani soyayyata ba zata taɓa bari ki zauna lafiya ba kuma ko ba daɗe ko ba jima
sai kin kawo mun kanki da ƙafarki" dai dai lokacin Mu'azzam ya dawo falon Anty Labiba na biye dashi
tana kiransa akan ya tsaya amma yaƙi sai da ya shigo ai kuwa Bilal ya zabura ya miƙe sai kuma ya saki
ƙara ya dafe bayansa Nasir ya riƙe shi ya nuna Mu'azzam yana cewa
"Shammatata kayi, kuma wlh baka daki banza ba zamu haɗu a kotu sai naga uban daya tsaya maka".
Jotter data faɗi kan ƙafafu na Mu'azzam ɗin ya tsugunna ya ɗauka kafin ya kalle shi ya ce
"Allah ya taimake ka sai kaje ka cigaba da karuwancin da hujja kuma wlh ko da wasa ka kuskura naga
ƙafarka a hanyar gidanmu da sunan kazo biko sai ka gane baka da wayo"
Haka Nasir ya ja Bilal sa bakinsa bai mutu ba suka fice Mu'azzam ma ya fita ya rage ni da Anty Labiba
dake ta faman mun magana amma ko kusa bana jin ta balle na gane abinda take cewa.
Kalmar "Na sake ki Halima" da Bilal ya ambata ce kaɗai take mun amsa kuwwa a kunnuwana. Da ƙarfi ta
jijjigani abinda ya maido ni hayyaci na na kalleta ina zare ido ta ce
"Bacci? Aa mutuwa kikayi kika dawo" ta mun ba'a. Kallon falon na shiga yi komai yana nan a yanda yake,
hular Bilal da na hango a gefe ta saka na fahimci dagaske abinda ya faru a zahiri bane ba mafarki nakeyi
ba. Hannu biyu na ɗora a kai sai dai kamar an sace mun murya ihun da nayi niyyar yi yaƙi fitowa sai
hawayene suka shiga wanke mun fuska tamkar an buɗe famfo.
"Wai kuka kike saboda ya sake ki? Toh Allah ya duba miki, ki wuce ciki ki samu guri mai kyau kiyi kukan
nan za'a gyara Baban Amir zai yi baƙi yanzu" ta wuce ta barni a gurin.
A kan gadonta na zube na shiga kuka kamar wacce aka gama jana'izar iyayenta, na kasa yarda wai Bilal
ya sake ni dukda ga takardar sakin da rubutunsa ɓaro ɓaro akai Mu'azzam ya ajiye mun bayan da yayi
snapping a wayarsa sannan ya wuce gida.
Anty Labiba ta shigo ɗakin tana kallo na fuskarta fes yanda kasan babu wani abu daya faru ta kama baki
tana cewa
"Aure na ne fa ya mutu Anty ba zanyi kuka ba?" Na faɗa cikin kukan ina tashi zaune. Ta gyara fuska da
gani dariya ce ta taso mata kafin ta matsa gaban mudubi tana cewa
"Gaskiya dai abin kuka ne ya sameki gara kiyi". Sai na haɗe kai da guiwa ina cigaba da kukan na ce
"Ban taɓa zaton akwai tsananin da zai saka Bilal ya iya sakina ba"
"Ai yanzu gashi kin gani da idon ki ba wai tunani ba, kuka kuma ba zai miki maganin komai ba kamata
yayi ki tashi kiyi alwala kiyi sallah ki roƙi ubangiji Allah ya sa hakan ya zame miki alkhairi a rayuwarki ba
koke koke ba" ta sake faɗa sai na miƙe na faɗa jikinta ina cewa
"Wlh ina son sa ba zan iya rayuwa babu Bilal ba Anty ki taimaka mun"
"Ai kuwa sai dai ki mutu dan ubanki dan wlh ko zakiyi hauka ba zaki koma gidansa ba" ta faɗa tana tureni
daga jikinta. A ƙasa na zauna na cigaba da sheƙa kuka sai da naji na fara jin jiri daga zaunen da nake
alamar Bp na yayi high kafin na lallashi kaina na koma sauke ajiyar zuciya. Takardar na janyo na saka
karanta abinda ya rubuta a ciki.
"Ni Bilal na saki matata Halima saki biyu bisa tirsasawar iyayenta".
Sabbin hawaye suka ɓalle mun sai na cukuikuye takardar na jefa ƙasan gadon Anty Labiba dai dai lokacin
ta turo ƙofa ta shigo
"Bata ko kalle ni ba ta wuce ta zauna gaban mudubi ta fara cire sarƙa da ɗankunnen da tayi kwalliya da
su. Murya a dashe na tambayeta ta paracetamol saboda ciwon da kaina ya ɗauka ta buɗe drawer ta
janyo ta wullo mun na ɗauka na miƙe daƙyar ina dafe bango na fita kitchen. A can na tsinci wayata da na
bari sanda nake shiryawa su Bilal abinci na ɗauka bayan da na sha maganin na zauna na buɗe ganin
alamar message akan screen ɗin
"Wlh Halima sai kinyi dana sanin cewa na sakeki, kuma ki haɗa kayan yarana gobe za'a zo a ɗauke su ba
kuma zaki sake ganinsu ba har abada" abinda saƙon ya ƙunsa kenan.
Ɗakin Anty Labiba na koma muka ci karo a hanya tana shirin fitowa jiki na yana rawa na bata wayar ta
duba message ɗin kafin tayi tsaki ta ce
"Da uban waye ya ce masa za'a riƙe masa yaya? Ai dama ko bai faɗa ba mayar masa da su za'a yi dan
ba'ayi zaman mutunchin da har za'a masa wannan karar ba" ta faɗa ai kuwa na fashe da kuka ina cewa
"Wlh babu wanda zai rabani da yarana, kun san ba zaku riƙe su ba akan me zaku kashe mun aure? Toh
wlh ba zan yarda ba in dai ba za'a riƙe ni da su ba sai dai a barni in koma"
"Ki dai nemi wanda ya kashe miki aure tun dare bai miki ba kome kuma ai kina da dama wata uku cir kan
kiyi iddah idan kin so ma yanzu maza ki bishi ku sasanta daga can ku wuce gobe in Allah ya kaimu sai a
tattaro miki kayanki da yaran naki a biyo ki da su, ai duniya ce Halima gaki gata babu wanda zai sake ce
miki kiyi ko ki bari" Anty Labiban ta faɗa cikin sautin daya nuna ranta ya fara ɓaci da al'amarin nawa.
Zama nayi niyyaryi a bakin ƙofar zan fara tijara ina cewa
Uncle Saleh ya daka mun tsawa kafin ya balbaleni da masifa yana cewa
"Ke wace irin yarinya ce mai shegen taurin kai ne haka Halima? Da kika san kina son zama da mijinki da
halinsa tun farko waya ce ko taho gidan? Ki kama kanki, idan ba haka ba wlh zan saɓa miki tunda naga
alamar raini da iskanci ne abun naki da kunne na naji kina cewa ya sake ki ba zaki koma ba sannan yanzu
zaki zo da haukan ƙarya kina cewa sun kashe miki aure to in sake ji zakiga yanda zanyi da ke kuma babu
in da zaki je a nan gidan zaki zauna har ki gama iddah wawuya kawai kin girma har kin haihu amma
bakiyi hankali ba" ya ƙarasa yana zare mun manyan idanuwansa irin na Nufawa.
Tsaf na haɗiye kukana dan sosai tsawar da yanda yayi maganar cikin fushi da gargaɗi suka shigeni. Uncle
Saleh bashi da daɗi ba kuma shi da sakewa dan ko doguwar hira ba'ayi da shi idan ko kaji dariyarsa to da
matar sa ne ita kanta kuma duk buyaginta tana shakkar sa.
Haka na raba dare ina kuka amma ba mai sauti ba dan ina jiyo magangan sama sama daga falo da alama
mugayen miji da matar basuyi bacci ba kafin ya lafta mun mari da hannunsa mai kama da na maƙeri.
Gurin ƙarfe uku Anty Labiba ta sake shigowa ɗakin lokacin ina zaune a ƙasa na rafka tagumi hannu
bibbiyu abin duniya duk ya taru ya mun yawa, shikenan fa na zama bazawara.
"Da wannan zaman ke ba bacci ba da tashi kikayi kika ɗauro alwala kikayi sallah sai kiji sanyi a ranki" ta
faɗa tana kallona. Na haɗiye yawu daƙyar kafin na gyaɗa mata kai alamar "toh".
"Ba kuka na ce ki mun ba ki buɗe baki muyi magana ta fahimta kawai nake so"
"Ina jin zafin abinda ya mun har raina Anty amma ina son sa, ji nakeyi kamar ba zan taɓa iya rayuwa da
wani namiji bayan Bilal ba" na faɗa bayan da nayi ƙoƙari tsayar da kukan da na fara.
Ta dafa kaina ta ce
"Kuma ina duba makomar yarana idan mun rabu kinga gashi yanzu har ya fara cewa zai ƙwace su"
"Ki faɗa mun duk abinda yake ranki, ko da ban taɓa makauniyar soyayya irin taki ba amma nima ina son
mijina ina kuma da yaya, ko bisa kuskure nayi tunanin wata rana zan iya rabuwa da shi ina jin zafi har
raina dan haka zan miki uzuri har idan kina da ƙwaƙƙwarar hujja kuma na gamsu na miki alƙawarin zan
wuce miki gaba in fahimtar da Mama da Abba har suma su fahimce ki".
"Ni babban abinda ya fi damuna dama kowa sanda zan aure shi sai da ya ce suna nan zan dawo, ba iya
ku na cikin gida ba dangi da mutanen unguwa duka kowa idonsa da kunnuwansa na nan kawai jira ake
aji aurena ya mutu a fara yi mun dariya da Allah ya ƙara" nayi ƙarfin halin sanar mata da damuwar da
take cin raina.
Wani uban ranƙwashi ta sakar mun a tsakiyar kai kafin ta lailayo ashar ta maka mun kamar ma ta manta
da tsakiyar dare ne ta balbaleni da faɗa tana cewa
"Dan ubanki sai munyi dariyar Allah ya ƙara kuma tun daga sanda ya fara auna miki abinci muke miki ita.
Wato saboda gudun kar ayi miki dariya ya saka zaki zauna ki lalata rayuwarki ki kashe kanki ƙarshe ya
ɗakko ciwo ya shafa miki ya ƙara jefaki a masifar da ta fi wacce kike ciki ko? To ki kiyaye ni, kuma wlh
maganar nan ta mutu daga nan.
Na rantse da Allah kika koma gida kika ce zaki cigaba da tayarwa da su Mama hankali sai irin dukan da
Mu'azzam yayiwa jakin zan saka ke ma ya miki tunda gashi nan bugu ɗaya da yaji wahala ba ja in ja ya
baki takardarki to kema idan aka miki irinsa salin alin iskokan da suke taya miki kina iskanci da layla da
majnun ɗin kan nako duk zasu kama gabansu".
Ni dai sosa in da ta ranƙwashe ni kawai nake hawaye ya cika mun ido amma ba damar na bari su zubo
dan da alama nata mutanen suna kusa karta mun rotse. Ashe dagaske ita ta saka Mu'azzam ya daki Bilal,
"Tashi ki ɗauro alwala kiyi sallah, tunda kika auri shaiɗani ibadarki ma sai a hankali dama ta ina kike
zaton zakiga dai dai a lamuranki?"
Haka na tashi na yo alwalar kuma da na fara sallar musamman dana tattara hankalina sai na ji nutsuwa
ta fara saukarmun hatta ciwon kai da jirin da nake ji kafin na idar da sallolin duk sun ragu, kamar gaske
lokacin da Hansa'u ta zo har addu'oi ta bani da wurudai ina yi kuma sosai na samu nutsuwa a lokacin ban
san yanda akayi na watsar na sake komawa yar gidan jiya ba.
BILAL
Asibiti Nasir ya ce zai kai shi bayan sun bar gidan amma yaƙi ya ce ya kai shi gida.
"Amma dai da munje, ba fa ƙaramin duka ya maka ba wlh kar kaje ya bugeka a in da zai iya maka illah"
Nasir da har ransa daɗi ya ji na dukan abokin nasa da akayi ya faɗa. Cikin sauƙi Allah ya ƙwatar mata
haƙƙinta dukda yaga alamar Haliman kamar kurarin banza kawai takeyi kamar dai har yanzu tana son
abokin nasa.
"Ni dai ka kaini gida, kuma wlh idan na ji maganar nan a bakin wani Nasir ba zata mana da daɗi ba" Bilal
ya faɗa da ƙyar dan yana jin jiki. Nasir ya guntse dariyar sa ya cigaba da tuƙi yana satar kallonsa.
"Wlh sai na nuna masa shi ƙaramin mahaukaci ne, sai ya san ya dakeni" Bilal ɗin ya sake faɗa shi dai
Nasir bai ce komai ba har suka isa gidan ya shigar masa da mota ya rakashi ciki ya tambaye shi ko akwai
abinda yake buƙata ya ce babu daga nan ya masa sallama ya wuce gida akan zai dawo da safe ya duba
shi.
Kwana yayi yana saƙa da warwara akan matakin daya kamata ya ɗauka akan Halima domin duk ita ta
shirya komai, yayi ƙwafa ya ɗauki wayarsa ya kunna. Message ɗin Zulaiha ya shigo dama kuma saboda
itan ya kashe wayar suna fitowa daga gidansu dan karta dame shi da kira yana gurin Haliman bai ko
karanta ba ya lalubo number Halima ya aika mata da saƙo akan karma ta ɗauka ta ci galaba akansa kuma
zai karɓi yaransa, maganar yaran ya san ita kaɗai ta isa ta sake zargo masa wuyanta dan ya san
ƙulafucinta akan yaran ba zata taɓa yarda a raba su ba.
Yana gama turawa ya latse wayar zai sake kashewa sai ga kiran Zulaiha ya shigo, ya amsa, cikin asalin
muryar da ya santa da ita mai laushi cike da kunya da kuma nutsuwa ta masa sallama.
Ya saki ajiyar zuciya, abinda yake akanta ya motsa masa sai ya gyara kwanciya yana cije baki saboda
yanda duk jikinsa yayi tsami a hakan ma dan ya gargasa da ruwan zafi sannan ya shafa Aboniki kuma ya
sha pain relief.
Ta gaishe shi abinda rabon da ta masa tun randa aka ɗaura musu aure.
"Ashe ɗazu kazo Yaya Bilal" ta faɗa. Ya buɗe ido da mamaki kafin ya ce
"Yanzu Umma take gaya mun da duk abinda Kawu ya muku, dan Allah kayi haƙuri, na rasa mai muka
tsarewa Kawu a duniya da kwata kwata baya ƙaunar mu kullum bashi da wani buri illah na ya tozarta mu
mu da mahaifiyarmu" ta sakw faɗa cikin shirin yin kuka. Da sauri ya tare ta da cewa
"Me aka ce yayi mana? Ni ai babu wani na rashin jin daɗi daya faru amanarku kawai ya bamu ya ce baya
son kawo ƙara duk abinda ya faru muyi hukunci da kanmu in dai ba abun yayi girma bane"
"Kawai ba zaka faɗi gaskiya bane amma Umma ta gaya mun ya ci muku mutunchi sosai" ta faɗa tana
sakin kuka. Duk sai ya diririce ya ringa mata rantsuwa akan shi wlh ba abinda Kawu ya musu idan ma yayi
toh hankalinsa baya gurin bai fahimta ba.
"Shikenan toh tunda ka ce haka, ya Anty Halima? Ya su Al'amin kwana biyu ko motsinsu bana ji" Zulaihan
ta sake faɗa bayan ya gama lallaɓa ta tayi shiru. Ya sauke numfashi ya ce
"Yau suna can gidansu sun je yini zanje na ɗakko su kuma kaina ya fara ciwo shine kawai na ce su kwana
acan" ya lafta mata ƙarya. Tayi wani miskilin murmushi ta ce
"Allah sarki, Anty Halima dai akwai haƙuri gaskiya ko sau ɗaya banji kace tayi rigima irin yanda mata
sukeyi idan za'a musu kishiya ba, ko dai bata sani bane?"
"Waya gaya miki? Tayi abunta mana kawai dai ba da yawa yanda mata sukeyi ba; kin san na faɗa matata
ta dabance ita" ya bata amsa. Ya ji sauyi a muryarta ta ce
"Hmm" kawai.
"Amma ɗazu kika ce bakya nan muka zo bayan kuma na ganki har magana munyi?" Ya canza akalar
maganar, sai ta ce
"Wlh kwana biyu na rasa mai yake damuna. Tun bayan da aka ɗaura mana aure ni dai sai in ringa ganin
abubuwa suna faruwa kamar mafarki nakeyi. Umma ta ce kamar wai iskokai ne suke taɓa ni wani lokacin
sai na canza nayi ta abubuwa kuma daga baya idan na dawo hayyacina ba zan tuna mai ya faru ba" ta
faɗa. Bilal yayi shiru yana juya maganganun a ransa kafin ya ce
"Amma dama kina da matsalar jinnu ne tsayin lokacin nan ban taɓa sani ba?"
"Wlh nima ban sani ba amma Umma ta ce wai ƙila na gado ne itama haka suka mata sanda aka mata
aure amma tana tarewa shikenan suka barta dan ko magani ba'a nema mata ba Kakarsu tace idan aa
mata magani za'a gayyato mata wasu ne dan su waɗannan ɗin da kansu zasu tafi ko ba'a musu komai ba
toh shine yanzu da Anty Habiba har ta ce muje Ɗanfodiyo Umman ta ce a dakata dai zuwa in tare idan
basu rabu da ni ba sai muje"
"Da aljanun zaki tare kenan?" Ya faɗa kamar a tsorace. Tayi dariya ta ce
"Duk ɗaya ai, kin san yanda kike birkicewa kwana biyun nan kuwa? Harfa zagina kikeyi"
"Subhanallah zagi?" Ta faɗa cikin rawar murya, jin zata saka masa kuka yayi saurin cewa
"Wasa nakeyi amma dagaske dai in zai yuwu gara a fara neman maganin tun yanzu dan gaskiya bana jin
daɗin yanda kike canzawa har na fara tunanin ko dama dai haka halinki yake ɓoye mun kikayi?"
"Yanzu tsahon shekarun da muka ɗauka Yaya Bilal har akwai wani hali nawa da zai ɓoyu ace baka sanshi
ba?" Ta faɗa cikin kuka. Yayi tsaki ya ce
"Kin san ba abinda na tsana kamar kukanki kuma ni ba cewa nayi kin ɓoye mun wani abu ba cewa nayi
na fara zato amma yanzu da kika faɗa mun sanadi kinga ai na fahimta ko?"
"Toh yanzu wai yaushe za'a je ganin gida in ji su Anty Habiba?" Ta tambaya bayan da ya gama lallaɓata
tayi shiru, ya ce
"Har jibi? Yau fa litinin, saura kwana biyar fa tariyar ya kamata ace zuwa yanzu ma an yi jere kaga fa
gobe za'a fara jeren Nuratu ita tub wancan satin aka ga gida" ta faɗa cikin shagwaɓa. Ya ɗan yi shiru, nan
gidan ya so ya bata amma yanzu Halima ta wa kanta ya fasa kaita sabon gidan nan ɗin zata dawo bayan
ya gama koya mata hankali. Numfashi ya sauke ya ce
"Goben toh sai suzo, ke ma ki shirya idan naji dama dama gobe ko da daddare zanzo na ɗauke ki muje ki
gaida Hajja" daga haka sukayi sallama bayan tace Allah ya nuna musu goben.
Washe gari da wuri dukda yanda yake jin jikinsa ba daɗi haka ya lallaɓa yaje gidan Hajja dan ya gaya
mata zancen zuwan yan jeren Zulaiha.
"Ai ba gida ɗaya zan haɗa su ba, akwai gidan da Hafiz ya bani aro kafin muga yanda hali zai yi" ya mata
ƙarya. Ta taɓe baki ta ce
"Ai shikenan"
"Yanzu me zan bayar na abinci da sauran abubuwan da za'a yi? In Allah ya kaimu ranar Asabar zata tare".
Banza ta masa har kuma ya gama surutunsa bata sake ce masa komai ba dama kuma tunda ya shiga ya
lura a fushi take ya zata kuma maganar jiyan ta wuce ai tunda kafin ya tafi harta koma tsohon saitinta bai
sani ba yanzun kuma fushin me takeyi.
Gida ya koma, kamar ya kira Anty Amina sai kuma ya fasa daya tuna ita ba Hajja bace abinda ya aikata ba
zai taɓa gogewa a idonta nan kusa balle ta sake sauraron sa ba. Ƙarshe Anty Habiba ya kira, bai yi
mamaki ba da yaji bata masa zancen abinda ya faru ba da alama Hajjan bata gaya musu ba kuma ya
godewa Allah domin ko da suke ciki ɗaya ya san muddin maganar ta wuce Anty Amina toh kamar duk
jama'ar gari sun ji ne.
Da dare ya lallaɓa yaje ya ɗakko Zulaiha, yan uwan nata basu je ganin gidan ba ranar sai da ya je ya
ɗauketa a hanyar dawowar su daga gidan Hajja wacce tunda suka gaisa ta shige ɗaki bata sake fitowa ba
sallama ma Zulaihan ce ta leƙa ta ce mata zasu tafi tace a gaida gida haka Fadila sai da Bilal ya mata
tsawa kafin ta gaisheta Abubakar kuwa ko kallon arziƙi bai musu ba daga ita har Bilal ɗin suna shiga ma
ya fice daga gidan ya barsu.
Jin tayi shiru tunda suka fito ya saka ya ce mata
Ta muskuta ta ce
"Sai sa aka je ɗebo kaya gurin kafinta wai tsabar mutumin nan bashida mutunchi ya ce wai wasu kaya
kuma za'a ɗauka? Tariyar ma dai ina ga da wuya idan zata yuwu a wannan satin sai dai a sake saka
lokaci"
"Wai fa kuɗin da aka bashi miliyan uku na kayan gadonmu da kujera mu biyu duka ya haɗa yayi aikin
Nuratu da su, ni dama tunda na ga kayan na cew Anty Habiba sun fi ƙarfin na kuɗin da aka ce ayi tace ba
haka ba, sai da aka je ɗakko nawa wai ai shi da duka kuɗin yayi amfani yayi wancan kayan bai fahimci na
mutum biyu ake nufi ba" cikin kuka ta cigaba da cewa
Ni tun farko dama abinda nayi gudu kenan na ce kawai na haƙura da lefe kayi mun kayan ɗaki kamar na
san wannan matsalar zata faru".
Shiru yayi yana juya maganar a ransa. Ta yaya za'a yi a bawa mutum aiki na mutum biyu ya ce ya ɗauka
na mutum ɗaya aka ce? Ba su suka zaɓi abinda suke so akayi lissafi suka biya kuɗi ba?
"Ke komai sai ki fara kuka, yanzu toh ya akayi? Wace matsaya aka samu akan kayan?"
"Wace matsaya kuwa? Dama ai an kwashe na Nuratun tun wancan satin toh aka ce za'a mayar masa ya
bayar da guda biyun wai ba zai karɓa ba tunda zaɓar design ɗin akayi yayi su ba wai a ajiye suke dama
aka ɗauka ba. Har ma an kai gidan nata yanzu sai Umma ta ce nayi haƙuri abinda aka samu na
gudummawa idan Nuratun ta tare sai a haɗa ayi mun wasu"
"Wannan ai ba magana bace, kenan ke ba zaki tare ba ko kuma zaki tare babu kaya ne?" Ya faɗa a ɗan
fusace. Ta sake fashewa da kuka ta ce
"Toh ya kake so nayi? Ka san dai ba zance aa ba dan ko nawa ne zan iya ɗauka na bayar saboda asirin yar
uwata ya rufu. Kana kallo wanda zata auran ɗan manyan mutanene masu kuɗi idan aka kaita babu kaya
ai abin gori zai zamar mata".
Kallonta ya ringayi jin abinda ta ce, wato shi da yake ɗan talakawa shi yasa zata tare masa babu kayan
ɗaki ko kuma a ɗaga tariyar har sai randa suka samu kuɗi kenan ko me take nufi? Kamar ta shiga
zuciyarsa tayi saurin cewa
"Karka fassara maganata da wata ma'ana naji kayi shiru, na san kai ni kake so ka kuma sha faɗar ko da
tabarma aka kawoni gidanka baka da matsala dukda hakan ma ba zata faru ba. Shi kuwa Faruk har
tausayin Nurati nakeji dan wlh ni dai banji a jikina tayi dacen miji ba"
" Ya zaki ce haka? Ni dai ganin da na masa banga wani aibu a tareda shi ba yana da nutsuwa sannan yana
son ta" cewar Bilal, ta ce
"Hmmmm" irin ba zaka gane ɗin nan ba kafin suka sake yin shiru har suka isa gida.
"Abinda ya sa har nake faɗa maka saboda kai an rigada an zama ɗaya dukkanmu masu taruwa mu
rufawa juna asiri ne dan ba yau aka fara ba" cewar Umman, yayi shiru kafin ya ce
"Babu damuwa Umma ba za'a ɗaga tariyar ba, dama akwai kayan da na ce miki na bayar da kuɗi a yi
sanda ta ce kayan ɗaki take so ba lefe ba, zan masa magana idan ba'a siyar ba tunda dama basu maido
mun da kuɗi na ba sai a karɓa idan ma an siyar sai a samo wasu tunda suna da kayan a zube a gurin".
Umman ta ringa zuba masa godiya harda hawaye haka Zulaihan data rakashi duk sai tausayin su ya rufe
shi, ya san basu da shi, shi ba dan Umman ta ce a basu kuɗin lefen ba dama niyya yayi ya mata kayan
ɗaki kuma ba zai barta haka ba zai mata ko akwati biyu ce ta kayan sakawa. Ya ɗan jima dan mota suka
shiga murnar kayan ɗaki tuni ta manta da cewar da tayi ba zata sake yin wani abu dan ta faranta masa
rai ba sai ta tare, shima kuma da yake kwana biyu bai samu ba ba Halima babu Jalilah ya biye mata
dukda ba wani nisa sukayi ba ta shige gida shima ya wuce.
Tun daga bakin get mamakin mai ya faru a gidan ya kamashi saboda ganin kwalaye da ledoji harda
kofuna da robobin take away dana Rufaida duk an watsar dasu a ƙofar gidan. Ya sauka ya buɗe get nan
ya tarar da tsakar gidan ma kaca kaca da wasu tarkacen a ajiye, komawa yayi ya kashe motar dan ba zai
iya shiga da ita a yanda gurin yake ba ba shiga yana mamakin meya faru? Ko ɓarayi ne suka shiga? Amma
kuma da wahala ace ɓarayi su shiga gidan bayan layin a kulle yake da get kuma masu gadin basa
matsawa ko ina.
Ta window kitchen ya hango saman drawers ɗin ta dake cike da kwalayen flask da sauran kayan amfanin
da bata buɗe ba babu komai a gurin, gabansa ya faɗi, da sauri ya tura ƙofar falon ya buɗe ido yana kallon
gurin da ke nan fili fetal kuma an share tas babu ko tabarma a ciki. Sai lokacin ya lura ai dama bai hango
labule ba tun daga waje.
*Wattpad @MaryamahMrsAm*
*Ban yarda wani ko wata ya juya mun labari ta kowacce siga ba tare da izini na ba*
*Kuɗin karatu yana wakiltar mutum ɗaya ne, kiji tsoron Allah karki ɗauki hakkina ta hanyar fitar mun da
littafi*
*KURA A RUMBU littafin kuɗi ne, a biya naira 800, biya a asusun*
*7061838488*
*Opay*
*PAGE 50*
Turus yayi yana bin falon da kallo zuciyarsa tana ƙara gudu, shiga yayi ciki da kyau har sannan yana
ƙoƙarin gane abinda yake faruwa. Ƙofar ɗakin Halima ya tura, nan ya tarar da gurin shima tamkar falon
babu ko tsinke anyi shara da alama ma har mopping akayi. Sakin ƙofar yayi ya matsa ya buɗe ta ɗayan
ɗakin da yake mazaunin nasa; a nan ne ya tarar da kaya zube a ƙasa wanda kallo ɗaya ya musu ya
fahimci nasa ne.
Ɓacin rai haɗi da baƙin ciki suka kamashi lokaci ɗaya, fita yayi daga nan ya wuce part ɗin sa da sauri
domin zuwa yanzu ya fahimci su Halima ne sukayi gidan tsirara. Ta window nan ɗin ma ya hango filin
gurin sai tsirarun kayan da suke mallakinsa na falon kamar DSTV decoder sai wani teburi da sai bayan
tafiyarta ya kawo shi gidan ya ɗora computer akai dan yana shirye shiryen fara Forex trading da zarar ya
haɗa kan kuɗaɗen shagunan Jalilah daya siyar.
Bai shiga ɗakin ba dan ya tabbatar yanda yaga falon an masa tik haka zai tarar da cikin ma saboda dai
komai da yake gidan ya sani mallakinta idan aka cire kayan sakawarsa sai yan tsirarun abubuwan da ba
za'a rasa ba. Tunga ya ja yana saƙa da warwara a ransa, bai taɓa zaton zasu kwashe kaya ba domin ya
san basu rabu da Halima ba, Halimar daya sani ba zata iya rabuwa dashi haka salin alin ba tilas ta dawo
masa ko kwashe kayan ma ya sani ba zai wuce wannan yar abu ta kazan ƙanwar Babar tata bace Labiba
dan dai ko Mama yana da yaƙinin ba zata ce azo a kwashe kaya daga yin saki jiya ba.
Guri ya samu cikin tarkacen da suka watso tsakar gidan ya zauna saboda kansa da ya ji ya sara masa, shi
da ya gama lissafi akan kawai Zulaiha zata tare a nan gidan shiyasa ko da suka kawo zancen babu kayan
ɗaki bai musa ba idan ya so daga baya a hankali sai ya shiryawa Halima can gidan idan ta tashi komowa
ta tare a can ɗin shine suka masa akuya suka rusa masa lissafi.
Ko me ya tuna kuma ya miƙe da sauri kamar wanda aka zabura ya fita. A ƙofar gidansa ya tsaya yana
ƙwalawa Iliyas, ɗaya daga cikin masu gadin bakin layin kira yanda kasan duniya ce zata tashi. Ilyas ɗin ya
taso da sauri jin kiran kamar ba na lafiya ba, ya ɗan rusuna ya ce
"Lafiya Alhaji?"
"Wace lafiya? Kuna ina ɓarayi suka hauro mun gida suka kwashe kaya suka fita da su?" Bilal ɗin ya faɗa
cikin kiɗimar ƙarya, Ilyas ya kalle shi ba yabo ba fallasa ya ce
"Ɓarayi kuma?"
"Eh, ko da yake ba ma zai yuwu ace ɓarayi bane sai dai idan da ku aka haɗa baki, wato kunga matar
gidan bata nan shine kuka daidaici na fita kuka shiga kuka kwashe mun kayan gida ko? Toh wlh kotu ce
zata rabani da ku, sai kun gwammace kiɗa da karatu zaku san kun jangwalowa kanku tsiya" Bilal ɗin ya
faɗa yana zaro waya a aljihu.
"Ji mana Alaji, karka kuskura ka sake ce mana ɓarayi idan ba haka ba zaka sha mamaki wlh. Dan muna
aiki a nan ba yana nufin bamu da ƙima ko daraja ba da kowa zai taka mu yanda yake so, da kuma zaka zo
kanawa mutane haukar ƙarya, waye bai san ka saki matar gidan ba?
Ta zo ta kwashe kayanta, kawai ka ce yanzu ka rasa in d zaka ringa kawo matan banza ne shine zaka fiti
kana wani ƙaramin hauka"
"Kai, dan abu ta kazanka ni kake faɗawa haka?" Bilal ya zaburo kamar zai kama shi da kokawa. Alhaji
Bashir, mijin Maman Yusuf da mai gidan da yake jikin nasa Alhaji Sharif suka ƙaraso gurin da sauri dukda
tun daga nesa duk sun ji abinda Bilal ɗin da kuma masu gadin suke tattaunawa. Su suka shiga tsakani
ganin Basiru ya tattare hannun riga yana jira Bilal dake hargagi kamar zai kai masa duka Ilyas yana
riƙeshi.
"Haba Alhaji Bashir, wane irin abu ne haka da girmanka zaka tsaya kana irin wannan abun da yara?"
Alhaji Sharif da ya shiga tsakani ya faɗa. Bilal yayi tsaki yana kallon masu gadin ya ce
"Sata suka mun a gida na tambayi ba'asi kuma shine zasu mun rashin kunya".
"Me aka satar maka?" Alhaji Bashir ya tambaya kafin Bilal ya bashi amsa Ilyas yayi saurin cewa
"Ranka ya daɗe tabarmar kunya kawai yake naɗewa da hauka, dama kusan wata biyu kenan ai matar
gidan bata nan to shine yau suka zo suka kwashe kaya da alama aure ya ƙare shikenan fa zai sauke
fushinsa akanmu sai kace mu muka saka ya saketa".
"Yanzu menene amfanin haka saboda Allah? Sanda aka kwashe kayan nan babu kowa ma a layin sai su,
ni kaina ba dan yar uwarta data shiga gidana neman abu ba ba zan san meya faru ba amma yanzu ka fito
kana hayagaga a layi har masu wucewa ka sanar musu da kun rabu da matarka" Alhaji Bashir ya faɗa
kafin ya juya kan masu gadin ya ce su wuce bakin aikinsu kowa ya fashe suka barshi shi kaɗai yana
muzurai da zare ido. Sai da ya gaji da tsayuwa kafin ya koma ciki ya tsaya cike da tunanin mai ya kamata
ya yi yanzu? Ko bargo baya tunanin akwai da zai shimfiɗa ya kwanta akai kafin wayewar gari, haka ya
ɗauki tsintsiya a daren sai da ya share compound ɗin tas ya watsa sharar waje yanayi yana tsinewa yan
uwan Halima da suka masa wannan abun.
Ɗakin sa ya shiga ya tsinci kaya kala biyu ya saka a leda dan yana ayyana abinda zaiyiwa Halima akan
wannan tozarcin da ta saka aka masa, hatta takardunsa da suke cikin jakunkunanta sai da suka zazzage
masa balle kayan sa na cikin akwati tunda dama ai ba shi ya siya mata ba suke nufi. Kulle gidan yayi
bayan ya saukw wutar gaba ɗaya dan ba ƙaramin baƙin ciki ke kama zuciyarsa idan yaga kangon da aka
bar masa ba.
Hotel ya tafi ya kama ya kwana yana Allah Allah washe gari tayi yaje ya saukewa Halima kwandon rashin
mutunchi, banda dai su sun gaji tsiya sai kace wasu kayan Gwal ne aka saka mata da dan an saketa
zasuce zasu kwashe kaya ya tabbatar masu arziƙin gaske ba haka sukeyi ba kuma tsabar rashin mutunchi
har ajiye ajiyen sa na cikin fridge da freezer suka tattara suka tafi kamar ubansu ya siya masa.
Haka ya kwana saƙe saƙe, washe gari da wuri ya fita gurin kafinta dan ya samo kayan da za'a jerawa
Zulaihan. Ya rigada ya karɓi kuɗin sa na kayan daya fara aka farayi tuni ƙarya kawai yayi mata, ya je ya
samu ready made kaya kuwa na wata amarya da akayi sai kuma aka fasa auren, dake yana tsaye suka
gama magana da kafintan daya karya wa kayan farashi saboda tsabar mugunta tamkar ba'a gurinsa
sukayi ba wai ai tunda an rigada an ɗauka kaya sun zama second sai kuma da Bilal ɗin ya nuna yana son
su ya nemi raina masa wayo zai siyar masa a sababbi daƙyar dai ciniki ya faɗa ya ɗaukar mata su set ɗin
gado da kujera masu kyau harda dining ya ƙara wani set ɗin gadon ɗaya da zai saka a can ɗakinsa, har
kujera ya so ya siya sai dai kuma abinda yake account ɗin sa ba zai ishe shi ba dan akawai sauran
abubuwan da yake so yayi bayan nan.
A gurin ya bar musu akan gobe Alhamis za'a je a ɗauka dan yana so a ɗan sake fentin gidan yau dukda ba
abinda gurin yayi amma dai amarya ce zata shiga ya kamata a gyara mata. Daga nan ya wuce gidan Hajja
ya faɗa mata Halima tazo ta kwashe kaya,
"Matsitana banza da wofi, ka rabu da ita taje tayi ta yawo da aurenka a kanta ba kaya ba koma me ta
kwashe a banza dan wlh ba zaka saketa ba" Hajjan ta sake jaddada masa. Shi dai bai ce komai ba dukda
yayi niyyar ya gaya mata ya saki Haliman amma yanda ta haƙiƙance tana jaddada ba za'a saketa ba
shiyasa yayi shiru dan ba laifi yau ɗin ya samu ta sake masa fuska dan a gidan ya tarar da Anty Habiba ya
san kuma ba zai wuce zancen tariyar Zulaiha sukeyi ba tunda ya tura mata kuɗin da tace zasuyi yinin biki
da shi tun jiya.
"Yanzu ina kuka tsaya da ita waccen shaiɗaniyar kuma?" Hajja ta dakatar dashi ganin yana shirin tashi,
bai fahimci wa take nufi ba gane hakan ya saka ta ce
"Jalilah mana, ka san dai kamar da ƙasa aurenka da ita dan bata isa ta iskanta mun kai ta zubar mana da
mutunchi sannan kuma ta ce ba zata aureka ba" cewar Hajjan. Abun sai ya ma bashi dariya, sai kace
shine macen irin saurayi ya yaudareshi Hajjan take cewa dole sai an aure shi kuma. Anty Habiba ce ta ce
"Yanzu Hajja ba zaki bar maganar nan na har sai ta fita inda ba zamu so ba ko? Abinda ya faru ya faru sai
mu lulluɓe magana ta wuce amma so kike sai kin ɗaga ta, tsakani da Allah yanzu ko ce miki yayi zai
aureta sai ki yarda? Mai za'ayi da mace irinta? Bayan shi kika san maza nawa take ta'ammali dasu da har
zaki ce kina so ki haɗa zuri'a da ita bayan abinda ya faru? Toh Allah ya rufa mana asiri gaskiya ba zaki
bankaɗa mana ba kuma babu wannan maganar kai Bilal babu kai babu ita ka kama matanka ka riƙe Allah
ya yafe maka abinda ya faru a baya kawai".
Haka ya lallaɓa ya fice, anan unguwar ya samu wanda zasu masa aikin fenti suka tafi tare suka duba ya
basu kuɗin da suka buƙata na abinda zasu siya daga nan ya wuce gidan Hafiz wanda ya kira shi akan idan
babu damuwa yana so ya ganshi.
Shi kam yanzu idan ba Hafiz ɗin ne ya kirashi ba mantawa ma yakeyi da wnazuwarsa a duniyar nan baki
ɗaya. To dama dalilin bibiyar Hafiz ɗin ai saboda abun hannunsa ne da bajintar da yakeyi masa yanzu
kuwa da ya fara kama ƙasa shima gani yake Hafiz ɗin ba komai bane dan sai ya ga kamar Jalilah ma tafi
Hafiz ɗin kuɗi saboda irin kyautar da takeyi masa a dunƙule tashi ɗaya sai Hafiz ya rabata gida goma ko
fiye da haka.
Fuska a sake kamar babu wani abu tsakani Hafiz ɗin ya tarbeshi, Suhaila ce dai ya karanci canjin fuska a
gurinta hakan kuma ya saka ya zargi ko dai Halima ce ta kai masa ƙarar sa shine yar taya ɓera ɓuruntu
take tayata fushi da shi.
"Baka kyauta ba, ko me Halima tayi maka bai kamata ace zaka turata gida saboda ka samu wata ba"
Hafiz ɗin ya faɗa masa dalilin kiran, ya wani yi kinini da fuska ya ce
"Gaskiya ni ban fiya son ana tsoma mun baki cikin sabgar gida na da iyalina ba shiyasa ko iyayena bana
kaiwa ƙara balle wasu mutane can bare".
Hafiz dai jijjiga kai yake yana kallon sa yan kuma sauraron abinda yake cewa, wato shine baren? Ko da
yake tuni lamarin Bilal ɗin ai ya gama bashi mamaki ko mai zaiyi yanzu sai dai ya kalle shi da ido kawai.
"Ni bani da lokacin da wani zai ajiyeni yanzu ya ringa gaya mun abinda ya kamata nayi da wanda ba zanyi
ba, ita bata san dama haƙuri kawai nake ina zama da ita ba dan da ita namiji banbancinsu kaɗan ne a
guri na. Saboda kuna na ce zan auro wacce nake so shine zata tada fitina, tace na saketa tun ba'aje ko
ina ba shine zata fara bibiyar neman sulhu? Toh wlh ko zan mayar da ita sai ta ji a jikinta ta yanda ko
wani ya sakw zugata ta mun abinda tayi a baya ba zata kuskura ta ji ba".
Mamakin jin wai ya saketa ya hana Hafiz sake ce masa komai sai kallonsa kawai da ya ringayi, daƙyar ya
ce
"Ai bata gaya mun ba, toh Allah ya sa hakan shi ya fi alkhairi a tsakaninku amma gaskiya kamar kayi
ganganci"
"Ba wani ganganci ni nake zaune da ita ni na san halinta ku kawai daga nesa kuke mata kallon ta ƙwarai
amma yarinyar nan bata da mutunchi, kawai dan ni ba mai tona sirrikan mutane bane amma dai
shikenan" ya sake faɗa kafin yaja farantin kayan ciye ciyen da sai da Hafiz yayi magana kafin Suhaila ta
saka mai aiki ta kai masa.
Shi dai Hafiz kallon sa kawai yakeyi bakin sa na so ya furzar da maganganun da suka cika shi taf amma ya
danne domin komai yana da lokaci. A hankali ya ce masa
"Yarinyar da na shafe sama da shekara goma da ita kake tambaya na san halinta? Kamar yanda na san
kaina kuwa" ya bashi amsa, Hafiz ya sakeyin shiru sannan ya ce
"Allah ya sanya alkhairi toh, ni na ɗauka ma yar gida za'ayi da uwarɗakin naka dukda kana ɓoye mun,
ashe kai da Target ɗin ka a gefe".
Dukda Hafiz bai ambaci sunanta ba amma ya gane wa yake nufi cewar da yayi kuma wai dukda suna
ɓoye masa ta saka lokaci ɗaya tashin hankali ya rufto masa har sai da ya ƙware da lemon da yake sha ya
shiga tuttula tari shi dai Hafiz sannu yake masa a ransa yana dariyar wautar Bilal ɗin. Shi fa duk a zatonsa
ya fi kowa wayo ne ko me yake nufi oho?
"Wacece uwar ɗaki na?" Yana kallon Hafiz ɗin ƙasa ƙasa shi kuma ya gyara zama ya ce
"Jalilah mana. Ai ta gaya mun soyayya kukeyi a yanda ta ce nan da yan satittika ma za'a fara maganar
aurenku, amma na san bata da labarin auren da kayi ko? Dan na santa da baƙin kishi gaskiya da taji da
yanzu ta tayar da hankalinta musamman da na fahimci tayi nisa a soyayyarka kuma da gaske take. Amma
wai yaushe duk hakan ta faru bani da labari?"
Bilal dai yanda kasan wanda za'a rataye haka ya tsure, fuskarsa kaɗai zaka kalla ka hangi tsantsar tashin
hankalin da kalaman Hafiz suka jefa shi a ciki.
Tunani yakeyi, me da me Hafiz ɗin ya sani? Iya kacin zancen soyayyar su? Ko kuwa harda ɓoyayyiyar
alaƙar da take tsakaninsu? Kai ko ma dai Halima ta faɗa masa komai kawai wasa yake masa da hankali
ne?"
Ya akayi ne duk ka wani firgice daga zancen Jalilah kar dai kaima tsoronta kakeyi?" Hafi ya faɗa cikin
wasa kafin ya cigaba da cewa
"Allah ne ya kamata dan na tabbatar yaudararka kawai takeyi amma Jalilah ta fi ƙarfin matasa irinmu
yanzu ai ta yuwu sai dai kawai kaji tayi aure dan akwai ƙishin ƙishin ɗin da naji kan wani Senator da yake
sonta kamar har an kai gaisuwa ma"
Sai ya ji kamar an tsundumashi a ruwan ƙanƙara har ajiyar zuciya mai nauyi ya sauke Hafiz kuwa canza
akalar hirar tasu yayi zuwa zancen office wanda shi ya bar gurin yanzu ya koma jagorancin ɗaya daga
kamfanonin mahaifinsa dama shi ya nace akan aikin gomnati amma Babansa baya so yanzu kuma da
kansa ya saki, farin ciki ya mamaye Bilal, bai wani damu da ce masa da yayi gaskiya idan bai yi wasa ba
za'a iya sallamarsa daga aiki saboda sunce sun gaji da abinda yakeyi gashi dama anyi sabon DG a ministry
akwai shirye shiryen kora da ɗibar sababbin ma'aikata kuma yanda Ogansu na nan yake ƙorafi akansa
yana tsoron kada abun ya rutsa da shi.
Ko a jikinsa domin ko an koreshi ya san zai samu in da zai lafe a kamfanin Hafiz ɗin. A gidan ya kusan
wuni suka sha hirar yaushe gamo har ya tallatawa Hafiz shagunan gurin Jalilah wanda ya ce na wani
yayan abokinsa ne saboda waɗancan mutanen da aka ce suna so yaga alamar wasa a lamarin su yana
kwatantawa Hafiz ɗin in da suke kuwa ya nuna sha'awa har ya ce bari rana tayi sanyi sai suje su duba
dan dama yana neman shaguna zai siya.
HALIMA
Sosai naji daɗin sallar da nayi, har gabannin asuba kafin bacci ya fara fizgata amma na daure sai da nayi
sallahr asuba sannan na kwanta. Gurin ƙarfe takwas Anty Labiba ta tashe ni, na kalleta ganinta cikin shiri
da key ɗin mota a hannu.
"Zan fita, ga abin kari nan a dining, ki tashi da wuri dan Allah kiyi lunch kin san za'a kaiwa yara makaranta
idan akwai abinda kike buƙata a taho miki dashi daga gidan Mama kuma ki kirani anjima dan kar in
manta" ta faɗa tana kallona. Na yamutsa fuska, abinda ya faru jiya ya shiga dawo mun sai nayi narai da
ido na ce
"Yana falon sa kije ki gaya masa" ta bani amsa tana nufar ƙofa, sai na miƙe ina cewa
"Ni dai wlh gidanmu zan tafi in dai na son a takurawa rayuwar mutun ba ta yaya za'a ce ya zauna a nan
gidan?"
Bata ko kalleni ba tayi ficewarta dan haka na haɗiye kukan da na so in fasa mata na koma na kwanta
tunda ta ce Uncle Saleh yana nan amma da zarar ya fita zan kama gabana dan ba zan zauna a gidansu ba
wlh.
Bacci na so ta koma amma na gagara yi sai kawai na tashi nayi wanka na shirya kafin na fita na karya.
Bayan na gama na ɗauki wayarta a shiga latsawa dan babu wani aiki da zan mata a gidan sun gama
komai, fitowar Uncle Saleh ta saka na shiga taitayina na sauka ƙasa na shiga gaishe shi sai ya dakata ya
samu guri ya zauna, nasiha ya shiga mun amma da yake muryar tasa kullum a kaurare take fuska kuma
babu fara'a sai na ringa jin maganganun nasa kamar faɗa. Ya gama ya fita kaina na ƙasa sai da na ji ya
rufe ƙofa kafin na kona kan kujera na zauna ina sauke numfashi.
Ni kaina ba kamar yanda na kwanta jiya ba yau ɗin da na tashi na jini sakayau kamar an sauke mun wani
nauyi a jikina, tabbatas sallolin da nayi sun taimaka mun matuƙa gurin samun nutsuwa amma dukda
haka isanyna tuna wai Bilal ya sakeni sai hawaye sun tarar mun a ido ban dai basu damar zubowa bane
na daure.
Kan wayata na koma na lalubo number Hansa'u dan ina tura mata text dan ta nan kaɗai nake samunta
yanzu shima sai taga sama ne take maido mun da amsa, ido na ya sauka kan sabon saƙo daga Bilal
wanda naga time tun biyar bata gama cika ba aka turo, maganganu dai marasa kan gado ya aika mun
yana sake jaddada mun sai nayi nadamar rabuwa da shi. Sai naji abun ya bani dariya ma, a fili na ce
"Allah ba dan halina ba ka yaye mun jarabtar son bawan Allah ka bani ikon nuna masa ni ba banza bace
yanda yake kallona". Hawaye suka shiga silmiyo mun, Bilal kallon ballagaza yake mun akansa dukda ba
laifinsa bane ni na nuna masa hakan nake a soyayyarsa amma yanzu idan Allah ya yarda zanwa kaina
faɗa, ko da ace akwai rabon sauran zama a tsakanin mu zai nemawa kaina mutunchi.
"Ashe baki haƙura ba kenan?" Zuciyata ta tuhumeni ban bata amsa ba na kawar da zancen ta hanyar
rubutawa Hansa'u saƙo "Bilal ya sake ni, dan Allah idan kina gari ki zo idan ma bakya nan muyi waya dan
ina tsaka mai wuya ina buƙata shawara" abinda na aika mata kenan ko minti biyu cikakku kuwa ba'ayi ba
sai ga shi ta kira, sai da ta gama ihun murna da hamdala kamar kafin muka shiga magana ta nutsuwa
kuma ta fahimta. Yinin ranar sur maganganunta na ringa tisawa wanda zallar gaskiya ce a cikinsu na
kuma samu ƙwarin guiwa domin yana daga dalilin da ya saka nake son Hansa'u, za muyi faɗa ta zageni
amma kuma ba ta gajiyawa zata faɗa mun gaskiya ta sigar data san zan fahimta saɓanin Anty Labiba da
take ganin faɗa da masifarta ne zasu saka na gane abinda take haska mun.
Sai dare Anty Labiban ta dawo da akwatunan kayana harda uniform ɗin NYSC na nan take labarta mun
sunje sun kwashe kaya.
Har shara da mopping mukayi, duk albarka da arziƙin da kika je da shi gidan mun kwashe abin mu. Ni wlh
badan Yaya Fauziyya ta hana ba so nayi a nemo yan gwangwan muyi musi gwanjon ƙofofi da windunan
gidan tunda da kuɗin Abba aka siya amma tace wai ba haka ba. Haka kitchen cabinets ɗin nan nayi
takaici Allah bana jin ma zan haƙura sai na koma an ɓalle su"
A hankali na fara sakawa kaina dangana na shiga Iddah, dama kuma washe garin da akayi sakin da
yamma sai ga period wanda na tabbatar damuwa ce ta matso mun da shi domin akwai sauran lokacin
zuwansa. Anty Labiba ta ringa cewa
"Ai gara kiyi ki gama tun kafin ɗan akuyar ya ce zai waiwayoki dukda ko da uwarsa yake tafe bai isa ya ce
zai maidake kafin ki gama iddah ba wlh Mu'azzam zan saka ya sake tare shi a hanya ya masa dukan tashi
kasha gishiri ya ƙarasa miki ɗayan kawai a huta" ni dai jin ta kawai nake ina murmushi, wani nishaɗi naga
tanayi, ba ita ba, har Mama da mukayi waya jin muryarta nayi a washe ba kamar lokutan baya ba tana ta
ce mun
"Babu komai ki kwantar da hankalinki komai kika ga ya faru a rayuwa da sanin Allah addu'ar da muke yi
muku kuma a kullum in sha Allahu ba zata faɗi a banza ba kada ki wani saka danuwa a ranki".
Allah sarki ni, ana baƙin ciki da mutuwar aure amma nawa kowa aka faɗawa sai dai yayi hamdala haɗi da
yi mun barka, ɗaya daga cikin fargabata na kar ayi mun dariya ta kau domin dai da alama tausayi na ma
ake ji a maimakon kuma a zageni yanda nayi tunani sai barka ake mun kamar wacce ta fito daga hannun
kidnappers.
Hankali na ya sake kwanciya ganin har sati ya ƙare Bilal bai sake turo mun da wani saƙo ba sannan babu
wanda ya zo ko yayi waya daga ɓangarensa akan yara, dama fargabata ta biyu kenan ace za'a rabani da
su sai dai na samu nutsuwa dan Abba da kansa da na ce masa Anty Labiba ta ce za'a mayar masa da su
Al'amin ya ce Aa in kwantar da hankalina wasa take babu wanda ya isa ya rabani da yarana.
BILAL
Allah Allah ya ringayi Asabar tayi Zulaiha ta tare ko zai huta da masifar mita da bani banin da suka tasashi
gaba, shi gaba ɗaya ma ya kasa ganewa al'amarin, naira miliyan uku ya bata kuɗin lefe da hidimar biki
amma daga kan kayan gadon da suka ɗora masa zuwa sauran abubuwan da ta sake bijiro masa da su sai
da ya sake kashe wata miliyan ukun harda ɗori akai.
*Wattpad @MaryamahMrsAm*
*Ban yarda wani ko wata ya juya mun labari ta kowacce siga ba tare da izini na ba*
*Kuɗin karatu yana wakiltar mutum ɗaya ne, kiji tsoron Allah karki ɗauki hakkina ta hanyar fitar mun da
littafi*
*KURA A RUMBU littafin kuɗi ne, a biya naira 800, biya a asusun*
*7061838488*
*Opay*
*Maryam Farouk, se a tura shaidar biya a lambar Whatsapp ta sama*
*PAGE 51*
Ranar Alhamis suka je jere ko ya ce ganin gida tunda dai shi yayi jere, yan buhun hunan da suka je da
abinda suka kira kayan kitchen tsabar takaici kallo ɗaya ya musu ko gaisuwa mai kyau basuyi ba ya fita ya
barsu da yayyensa banda Anty Amina da sukaje tarar masu jere. Bai san munafukin daya gayawa Hajja
shi ya siya mata kayan ɗaki ba ai kuwa ya sha tijara wannan kuma ya sake ruguza ɗan shirin da suka
farayi ta kuma ja masa kunne akan ba fa zata saɓu ba, ita da wahalar haihuwa da raino can wasu a gefe
da cin moriyar arziƙin sa dan haka daga wannan idan ya kuskura ta sake jin magana makamanciyar
wannan tabbas za'a ji su a rana.
Kayan kitchen dai tarkace suka jera yanda ka san a ƙauye, shi rabon da yaga Risho wlh ya manta amma
sai gashi wai shi aka kawowa Zulaihan. Tunani ya ringayi a ransa a ina ma za'a samu kalanzil dan bashida
tabbacin har yanzu ana siyarwa. Yanzu banda tsiya ina laifi ko camping gas ne ko 1kg su siya mata kai shi
wlh gara ma a haɗota da murhun kurfoti ya fi wannan Risho ɗin da suka kawo masa gida.
Ta ce masa suna da labule dan ita ta faɗa masa kalar labulen ma da zai zaɓi kujeru ta kuma ce akwai
carpet, fridge, Tv harma da gas ɗin amma bai ga ko ɗaya ba haka yan jere suka zo ziƙau daga su sai
tagayyararrun kayan kitchen ɗin su.
A haka kuma bayan sun koma ta kira shi murya ba walwala tana masa ƙorafi wai an ce mata gidansa na
Goron dutse zata zauna.
"Kai da ka ce mun a Rijiyar zaki gida na ya ke ya akayi kuma yanzu akace in da Maman Al'amin take zan
zauna?" Ta faɗa, a sama yake dan gaskiya lamarin jeren nasu ya ɓata masa rai yanda baiyi tsammani ba.
Duk miliyoyin daya kashe mata ace wannan abun za'a kawo masa tsabar rainin wayau?
Abinda ya ringa sake hasalashi yanda zuciyarsa ke ta hasko masa zamanin Halima, sai da akayi sati ana
mata jere idan ya shiga gidan a lokacin har baya son ya fita ga yanda Abokanansa suka ringa kambama
abun yana masa daɗi gidansa kamar gidan wani sarki amma yanzu ko gado da kujerar daya siya da kansa
a can gurin ya gansu masu kyau amma da aka kawo aka zuba sai ya gansu kamar bola, kujerun sukayi
wani yan tsurut a falon ba kwarjini irin na kujerun Halima haka ɗakin ji yayi ransa ya baci daya kalli kayan
sai ma ya gansu kamar tsofaffi toh ya saba ganin Made in Turkey a ɗakin, katako da gilasai suna dalle
masa ido da hasken su.
Kitchen ɗin kansa da yake shiga yayi ta ɓuruntu ga utensils kala kala yanzu sai tsalli tsallin multi colored
kwanuka da rabinsu na roba ne.
"Lallai, a gida ɗaya zaka haɗa mu? Gaskiya ba zai yuwu ba tun wuri ma ka sake shawara dan ba haka
mukayi da kai ba tun farko".
Kamar ya ce mata
"Ke kika sani" amma gudun ɓacin ranta da yakeyi dukda haushinta da ya cikashi haka ya kanne ya ce
Acan ɓangaren Zulaiha da tana sane da cewa Haliman bata gidan kawai so takeyi taji gargar ɗin maganar
ta ce
"Ni ban tambaye su ba wannan, kuma sun ce wai gado ɗaya aka saka kuma ɗaki biyu ne kuma ba'a saka
labulaye ba" ta sake soko wata maganar. A hasale ya ce
"Kina ji Zulaiha, nayi iya yina abinda yake haƙƙina da ba nawa ba duk na haɗa na miki. Daga yanda suka
ga gidan duk abinda babu ko bai muku ba wlh sai dai kuyi da kanku amma tsinke ba zan sake siya in saka
ba".
Muryar Ummansu ya ji daga gefe tana salati kafin ta rufeta da faɗan da bama gane mai take cew yake ba
dan haka ya katse wayar sannan ya kasheta gaba ɗaya. Duk Halima ce ta janyo masa, idan da bata
kwashe kaya ba ai da bata tona masa asirin gida ba, gurin da yake jin sa kamar Villah, baya shakkar kawo
ko wanne irin baƙo, su Hafiz da Jalilah da suka juƙu da naira suke kuma shiga gidaje na alfarma sai da
suka yaba kyau da tsarin jeren Halima amma yanzu gida ya koma kamar wani sansanin yan hijira a
idonsa. Yayi tsaki a fili ya furta
"Wlh sai kin gane kurenki, sai kin san kin ɓata mun rai".
Rana bata ƙarya aka ce sai dai uwar ɗiya taji kunya in ji hausawa, haka ne kuwa domin Asabar ɗin da ake
ta kira ta zo a ranar kuma yan uwansa suka ɗan yi yini a gidan Hajja itama amarya a can gidansu ranar
sukayi yinin wanda dukda rantsuwar da yayi akan ba zai sake kashe mata ko sisi ba sai da ya karya ya kai
musu buhun shinkafa dan kusan azahar sukaje zai nunawa Abokinsa Alhaji Sani da zasu je ɗakko amarya
gidan ya tarar da mata har ƙofar gida suna ta zuba hamma ga yara nata koke koken yunwa wata nata
bala'i an san ba'a da abinda za'a girka akan me aka kai musu goron gayyata su ba'a barsu sun dafa a
gidajensu sun ci ba an kawo su nan ana musu izaya da yunwa.
Kunya da takaici suka sake turnuƙeshi amma haka ya koma bayan ya sauke Alhaji Sani da ya kasa shiru ya
ce
"Kai kuwa Bilal wane rufa ido aka maka kaje irin gidan nan neman aure? Ka san fa akwai banbanci
tsakanin Talauci da kuma Tsiya, to kai dai da alama gidan matsiyata kayo aure wlh da matarka ta rufin
asiri yar manyan mutane haka kawai ka jajibowa kanka abinda zai dameka".
Shiru ya masa zuciyarsa na kumbura da fushi har suka rabu tsabar rainin wayau daya sauke shi sai ce
masa yayi ya tuna ma yana da uzuri ba zai samu zuwa ɗakko amaryar ba amma zai kwatantawa Lamin
gidan su sai su je. Haka ya wuce ya je ya siyi shinkafa da kayan cefane ya koma ya kai babu kunya kuma
suka karɓe kamar dama ana jiransa ba ko arziƙin godiya kuwa sai ma wata tsomararriyar mata da yaji
ama cewa Habi ce take ce masa wai ai da ya haɗo da ko ƙashi ne abincin ya fi zaƙi.
Daga nesa ya hango amaren sun fito daga wani gida, Nuratu kallo ɗaya ya mata kuma ko kaffara ba zaiyi
ba ya san Faruk ne ya ɗinka mata leshin jikinta daga zubinsa har ɗinki ya san ba siyayyar waccen matar
da Zulaihan ta ringa cewa wai ta san gayu da ita suka so siyayyar lefenta bane abin baƙin ciki tasa
amaryar ko da daga nesa yake hango su atamfar data saka da aka yiwa wani ɗan iskan ɗinki da ko a
mafarki ba zai yarda Zulaiha zata saka irinsa ta fita ba kallo ɗaya ya mata ya fahimci roba ce ko ma leda.
Cikin fushi ya taka mota ya bar gurin yana gani kuma ta ringa kiransa amma yaƙi amsawa ƙarshe ya
kashe wayar ya wuce hotel ɗin daya kama tun da aka kashe kayan Halima.
Bayan sallar isha'i aka kai Amarya, gidan Hajja suka fara zuwa da ita abun dai ba girma balle arziƙi ko ɗan
abincin da akeyi na yan kawo amarya hanawa tayi a basu balle kuɗin siyan baki haka suka wuce suna
zagin Hajjan aka garzaya da ita gidan Bilal.
Yan kawo Amarya dai sukayi ta santin gida domin a gurinsu Zulai fa tayi goshi. Dama kuma ai gida da
kyansa kuma ko kayan da aka saka a ciki sunyi kyau kawai dan an saba ganin wanda suka fi su ne shiyasa
yake ganin gurin bai yi masa yanda yake so ba.
Da suka ga Bilal ɗin da gaske yake ba zai ƙara komai a gidan ba kamar yanda ya ce dole safiyar Asabar ɗin
suka yanko labulayen da su Fadila suka ce tsofaffi ne aka kafa, ya dai fi babu dukda basu wadaci gurin ba
a winduna biyu kawai suka saka da yake kuma an saba ganin gurin cike da labulaye sai yayi haske fayau
yan uwansa suka ringa taɓe baki suna kallon gurin babu wannan haɗaɗɗun kujerun da carpet na alfarma
da frames da aka ƙawata bango dasu balle Cinema TV irin ta Halima haka suka bar gurin ga dai Tv stand
da yake haɗe da kujerun da Center table amma ko center carpet babu alamar sun kawo tunda ko da ba'a
shimfiɗawa saboda kar a tattake yayi datti amma dai ana ajiyewa a gefe yanda kowa zai san dashi.
Dama kulle kitchen sukayi sai kace wani abin arziƙi suka zuba ta window wanda suka sawa ransu sai sun
ga komai suka ringa leƙawa. Haka aka watse yan uwan Bilal suka tafi da gulma ana ta yi masa Allah ya
ƙara. Kowa cewa yake da matarsa ta rufin asiri kuga jarabar daya kwaso wannan amarya kana kallon
idonta kasan kunya bata isheta ba amma maganin Hajja kenan har da shi kansa ɗin dama kuma ai haƙƙin
Halima baiwar Allah ba zai barsu ba.
Wanda ma basu san Haliman bata nan ba lokacin suka sani anan kuma labarin sakin ya fita amma su
Fadila suka ringa ƙaryatawa suka ce tana dai gidansu tayi yaji amma bai saketa ba Huwaila wacce take
auren Kawun Halima a Galadanci kuma ta ce aure fa babu shi dan taji labari a cikin gida an ce saki biyu
ma ya mata ga kuma babbar shaida har ya saka wata a gidan idan yaji kawai tayi ai ba zata kwashe kaya
ba balle a saka wata matar a ɗakinta.
Sai gurin sha ɗaya kafin ya shiga gidan dan a yanda ya wuni cikin ɓacin rai ji ya ringayi ma kamar karya
koma amma daga ƙarshe dai ya tattara ya tafi babu rakiyar aboki ko ɗaya ya shiga gidan bayan ya tsaya
ya siya mata tsire da yoghurt sai lemuka dan sanda ya je gurin mai naman kaza ta ƙare shi kuma ya gaji
bai ji zai iya tafiya wani guri nemo mata kaza ba.
Tsakar gidan kaca kaca kamar anyi yaƙi, ga ƙofar falon a buɗe sai uban hayaniyar ƙawayenta da yake
jiyowa mamaki ya kamashi har sai da ya duba agogon hannunsa sha ɗaya har da rabi ta gota, basu da
hankali ne? Ko a gidan suke nufin zasu kwana da har suka kai wannan lokacin?
A waje ya bar motar ya shiga ya ɗauki tsintsiya ya fara share gurin dan ba zai iya kwanciya bacci gidansa
da wannan bolar ba kuma ya ajiye motarsa a ciki, ya gama ya jona mesa a famfo ya hau wanke gurin a
ransa yana ayyana yau zaiga ƙarshe haukan ƙawayen Zulaihan da ita kanta. Yana wanke gurin suka fara
fitowa harda ita duk sukayi turus suna kallonsa, wata mai shegen kauɗi ta ce
"Dama na ce muku naji an buɗe get kuka ce babu wanda ya shigo ai". Bai ko kalle su ba ya cigaba da
abinda yakeyi sai da ya ji muryar Zulaihan cikin fushi tana cewa
"Yanzu tsabar wulaƙanci ka shigo gidan kana jin ƙawaye na kuma ka san ku suke jira amma ba zaka iya
shigowa ku gaisa ka sallame su ba shine zaka hau wani aiki sai kace boyi boyi?"
Kallo ɗaya ya mata ya wuce ya kashe famfo dan ya gama abinda yakeyi. Gurin ya masa yanda yake so
dukda hancinsa yana jiyo masa wari wanda ya tabbatar daga banɗaki dake tsakar gidan ne amma yanzu
ya gaji sai da asuba zai bi ta kansa. Fita yayi zai shigo da mota ya hango masu gadi sun tsayar da wasu
motoci biyu sun hana su shiga layin suna ganinsa Iliya ya nufe shi Basiru kuwa ɗauke kai yayi sama dan
ko yanzu da zai shigo a wanda ya ce masa komai a cikin su tun ma waccen ranar idan ma basu ga dama
ba wani lokacin sai yayi ta horn kafin zasu buɗe masa ya fita ko ya shiga layin.
"Wai yammatan da suka kawo amarya zasu ɗauka" Ilyas ɗin ya faɗawa Bilal, sai ya koma ciki ba tareda ya
ce masa komai ba suna tsaye curko curko murya kamar wanda aka cusawa tsumma a baki ya ce
"Ana jiranku a waje" ya juya abunsa.
"Lallai ma Bilal, wato wulaƙanci ka tasarma yi mun a daren nan kana nufin ba zaka basu kuɗin siyan baki
ba ko me?" Zulaiha ta buɗe murya bata ko duba dare ba balle kasancewarta amarya, ƙawarta Suwaiba
da suke kira Suby ce ta jata suka koma cikin falo ta ce
"Ke fa banza ce Zulaiha, so kike ki ruguzawa kanki shiri kenan a wannan daren? To wlh kibi a hankali
karki tunzura shi ki ɓallowa kanki ruwa bayan kin san dama a ruwan kike"
"Kin san bana ciki da abu ta kazan uba, na gaji da pretending wlh gara in warware masa tun wuri ya shiga
hankalinsa ya kuma kama kansa"
"Ai sai ki bada himma, ni ba wannan ba kin dai saka abun nan ko?" Suby ta sake faɗa ta kuma yin tsaki ta
ce
"Toh asha amarci lafiya karki manta kuma ki rage mana kaza dan da wuri zamu zo" suka tafa kafin suka
fito lokacin sauran har sun fita Bilal ya shigo da mota yana ƙoƙarin rufe gida da muƙulli. Harda rusunawa
Suby tayi ta gaishe shi amma bai ko kalleta ba ya buɗe ƙofa ta fita ya mayar ya rufe. Kai tsaye ɗakin sa ya
wuce bayan ya shiga falon da ba ya ko son ganinsa a yanzu ya zube mata ledojin daya shigo dasu.
Zulaiha kuwa dama ɗaki ta wuce abunta ta fara shiri a ranta tana ayyana yanda zata ci kan uwarsa a
faɗarta tunda ya rigada ya zo hannu zai san bashida wayo. Ta gama shiri ta fito falon ta zauna tana
ƙarewa gurin kallo tana tsaki, da ta san ba zai saki jiki ya mata irin jeren data zata ba wlh da bata biyewa
Umma ba kuɗi zata cire tawa kanta abu na birgewa tunda tana da shi. Tsaki ta kuma ja mai ƙarfi, sai
lokacin ta lura ashe ko Tv ba'a saka mata ba. Wayarta ta buɗe ta lalubo wata number babu fargaba balle
tsoron komai ta danna kira kamar mai wayar kuwa yana jira ya ɗaga daga can ya ce
"My baby, irin wannan kiran ba zata haka kamar kin san kewarki ce ta hanani bacci wlh"
"Ƙaryar banza, to karka manta dai matar aurece ni yanzu kuma ba shashanci na kira muyi ba" ta faɗa a
wani dake, daga can ya sheƙe da dariya ya ce
"Su matar aure manya, to ina angon naki kike waya ƙarfe sha biyun dare?"
"Tv nake so" ta faɗa masa dalilin kiran ya tambayeta inchi nawa ta faɗa masa bata bari ya ja hirar kamar
yanda ya so ba ta katse bayan ta gaya masa da safe Suby zataje ta karɓa ta taho mata d ita idan zasu zo.
"Ina son fridge da cooker gas ma amma su ba gobe ba sai an kwana biyu" ta sake faɗa yayi ƙasa da
murya cikin barikanci ya ce
"Wannan sai kin kawo mun ziyara tukunna sai ki zaɓi waɗanda kike so ki tafi da su".
Motsin taɓa ƙofa ya sa tayi saurin katse wayar ta kasheta gaba ɗaya ma ta gyara zama yanda tayi kuma
ba zaka taɓa hasaso alamun rashin gaskiya ko wani abu a tattare da ita ba.
Bilal ya samu guri ya zauna kamar mara lafiya yana kallonta, ya rasa abinda ya sa ya kasa jurewa ya zo,
sonta yake kamar rai can ƙasan zuciyarta yana raya masa ya shareta amma ya kasa har ya kwanta haka
ya taso ya taho wai yaga taci abin da ya ajiye mata ko bata ci ba?
Murya ba amo ya ce
"Ka bani ne?" Ta mayar masa da tambaya tana wani tsare shi da ido, a ransa ya shiga karanta a'uziyya
yana ayyana mutanen nata ne suka motsa kenan. Ya matsa ya shiga ware ledojin, ta kayan tea sai
lemukan da har sun fara hucewa tsiren ma yayi sanyi ya buɗe mata yana cewa
Sai da tayi dagaske kafin ta danne ashar ɗin data taho bakinta, tsire za'a kawo mata a siyan baki?
Ganin ya nufo bakinta da tsiren ya saka ta haɗiye abubuwan da suke kokawa suna ƙoƙarin fitowa ta ƙarfi
ta buɗe baki ya saka mata, ganin ta karɓa ya saka ya tashi ya shiga kitchen dan ya ɗakko kofi amma bai
ga irin wanda yake nema ba haka ya ɗakko wani dakw haɗe da jug na roba ya fito yana ƙaramin tsaki. Ya
ringa kallonta da mamaki ganin taci rabin tsiren dukda yana sa yawa na dubu goma ne kuma yankan
naman nasu nada girma.
Haka dai suka raka ya ɗan ci abinda ta rage saboda yunwar da yaji ta taso masa lokaci ɗaya, dukda haka
sai daya ɗebi ruwan zafi a banɗaki dan babu butar tafasa ruwa ya haɗa tea wanda itama ta ce zata sha
ya haɗa mata kafin ya tattare kayan ya adana komai a inda ya kamata dan miƙe ƙafa tayi tana shan Ac
tana sauke numfashi. Sukayi sallah raka'a biyu da yana ji tana ƙunƙunin wai ita bacci takeji. Ɗaki ta wuce
bayan sun idar da sallar, ya leƙa da niyyar ya mata sai da safe saboda bacci yakeji ga kansa da yake masa
azabar ciwo amma ƙamshin wani turare da bai san ko na menene bane ya sake buga masa kai, ba zai ce
ga sanda ya isa gareta ba daga nan kuma labari ya canza.
Dukda yanda turaren da yawan shakaryda yake masa yawan yanda ya ringa fitar dashi daga hayyacinsa
amma hakan bai sa ya kasa tantance akwai matsala a tafiyar da aka fara ba dan haye shi tayi yanda
kasan ita ce mijin shine matar musamman da jikinsa ya mutu sai yanda tayi da shi kawai. Bai san me ta
shafa masa ba lokaci ɗaya ya ji jikinsa ya kawo ƙarfi har ya juya ta koma ƙasansa babu ɓata lokaci kuma
ya nemi hanyar sa da ya ji ta kamar filin kasuwa ƙarfe ukun dare ma'ana babu wani cinkoso ko wani
matsatsi ko tangarɗar da zata hanshi wucewa.
Lokaci ɗaya duk wani abu dake yawo akansa ya yaye hatta da mayen dolen da ta sakashi lokaci ɗaya ya
wartsake sai dai duk yanda ya so ya saketa saboda yanda takaici da baƙin ciki suka kashe duk wani
zumuɗin da yake ciki amma kuma abinda bai san ko menene bane ya riƙe shi kamar mayen ƙarfe haka
kuma ba dan daɗi ko yana so ba ya ringa abinda har kuka sai da yayi na baƙin ciki gashi yana so ya daina
amma kamar wanda inji yake sarrafawa ya kasa raba jikinsa da nata wanda a nata shirmen ta ɗauka na
daɗi ne nan kuwa ta ware baki ta manta da ya kamata ta nuna cewar farin shiga ce ita ta shiga taya shi
kukan wanda nata na gaske ne na jin daɗi.
Sai da dan kanta ta gaji lokacin Bilal ya gama shiga uku ya ma dena kukan hawaye ya koma na zuci kafin
ya samu kansa dukda bai san ta yaya ta rabashi da abinda ya gagara hana kansa dainawa ba. Ya zube kan
gado yana mayar da numfashi kamar wanda yayi gudun famfalaƙi haka itama Zulaihan numfashi take
mayarwa murna mara misaltuwa ta cika mata zuciya domin kuwa Bilal ɗin ya mata har ya wuce yanda
tayi zato, ta yi mu'amala da mazan da ba zasu irgu ba amma zata cw bata taɓa samun wanda ya mata
kamar sa ba ko dan shi ɗin tana son sa ne saɓanin waɗancan da take basu kanta saboda kuɗi kawai?
Hannu ta kai da niyyar shafa ƙirjinsa ya doke hannun nata da ƙarfi kafin ya tashi daƙyar yana tafiya a
duƙe ya fice daga ɗakin, ta bishi da kallo sai kuma ta saki murmushi mai kama da dariya tana godewa
Suby da taimakon da tayi mata. Ta tashi tana jin jikinta ko ina yana amsawa ta kunna filila, kamar
mahaukaciya ta sheƙe da dariya tana kallon bedsheet ɗin da tana sane ta canza asalin wanda aka
shimfiɗa daya kasance mai duhu ta saka fari gashi kuwa yayi kaca kaca da fake hymen (jinin budurcin
ƙarya) da Subyn ta siyo mata.
Banɗaki ta shiga ta ɗan ɗauraye jikinta a maimakon tayi wanka gaba ɗaya ta dawo ta kwanta akan gadon
a yanda yake a ranta tana raya ai ba jinin gaske bane bata ko ƙara minti biyar ba kuma bacci mai nauyi ya
kasheta.
Bilal kuwa ɗaya ɗakin ya shiga yana tafiya a sunkuye dan ji yake kamar wanda akawa operation, marar sa
ta ƙulle, duk wannan bala'in daya gamu dashi kusan awa biyu yana abu ɗaya amma bai fitarta komai ba,
ga gajiya, da baƙin cikin abinda ya tarar ga kuma wani kata'in ya sako shi a gaba.
Haka yayi wanka ya ringa zarya tsakanin falo da ɗakin kamar mai naƙuda kafin ya samu komai ya lafa
masa ya nemi kan kujera ya kwanta yana mayar da numfashi haɗi da tunanin abinda ya faru. Duk abinda
zai haɗa dan kareta hakan ya gaza karɓuwa a zuciyarsa. Ko dai mahaukaci ne shi kuma ko bai taɓa aure
ba ya san ba haka mace budurwa take ba kai ko wacce ba budurwar ba matarsa mai haihuwa biyu ma
bata ko kai rabin buɗewar haka ba.
Bai san ya akayi ba kuka ya ƙwace masa, Zulaiha ta cuce shi kuma ta ha'ince shi. Yarinyar da yakeyiwa
kallon salaha bata san komai ba bagidajiya ita ce ta juye ta zame masa wani abu na daban da bai ma san
me ya kamata ya kirata da shi ba. Maganganun Kawun su ya faɗo masa sanda yake cewa sun san komai
dai ko? Ya tuna Faruk ya ce ya sani, kenan ya san su ɗin ba yayan arziƙi bane amma a hakan yaji ya gani
ya auri Nuratun ko dai shima irin sa ne an ninke shi a baibai sai yau zai gane ainihin abinda Kawun yake
magana a kai.
"Yanzun kai da ka sani ɗin mai zakayi akai?" Sai kuma ya gagara bawa kansa amsa kawai ya sake fashewa
da kuka dan shi kaɗai ne hanyar da zai rage raɗaɗi da nauyin da zuciyarsa take masa a yanzu.
[5/16, 10:52 PM] Zee Bagus: Read My Book "HALYSAAH" on
ArewaBooks::https://www.arewabooks.com/book?id=681294ff01c6bd900451c8e6
✨✨ HALYSAAH✨✨
By _Khaleesat Haiydar_
✍🏻
19....
Ranan friday wajen karfe sha daya na safe Khaleesat ta gama Laundry da take a kitchen ta fito, a reading
nook din parlon ta tarar da Housemate dinta yana duba textbooks dinsa, cikin few seconds ya dau
wanda zai dauka ya dawo cikin parlon yana kallonta yace "Har kin gama kenan" Kai kawai ta gyada masa
ta fara tidying din parlon, rana na farko kenan da ta fara ganinsa yayi shiga irin ta Hausa cikin fararen
kaya, Taji yace "Hope you are studying well Halysaah" kai kawai ta gyada masa, yace "Alright, till later"
Ta ɗan kallesa tace "Are you Nigerian?" Ya buda ido yace "Why do u ask?" Tace "Kawai nayi zatan ko
daga Chad kake, or Niger" Dariya yayi yace "Hope it's fine now tunda kin rama?" Hanyar dakinta ta nufa
ba tare da ta basa amsa ba, ya dau makullin motarsa ya nufi kofar parlon, sai bayan da ya fita sannan ta
dawo cikin parlon ta tafi gun window ta ɗan bude drapery din jiki tana leka garage, ganin har ya tafi ta ci
gaba da aikin da take yi a parlor. Wajen karfe biyar na yamma Khaleesat na kitchen tana girki at the
same time suna waya da Abdul, tun 40 mins ago ya kirata suke magana har sannan, duk kwanan nan dai
lafiya suke waya da shi, ya kuma ɗan rage mata wasu abubuwan da yake mata, he is being a little caring
these days, a rana sai su yi waya sau biyu wani lkcn har sau uku har hakan na bata mamaki kamar dai ba
shi ba, yanzun ma shi ne yayi encouraging dinta ta tashi ta fara girkin da take yi don bata yi niyyar girki
ba, for weeks now kullum Housemate dinta ke masu takeaway na dinner wani lkcn har lunch, this made
her soo lazy to go to the kitchen, breakfast dama tea and cookies take ci yawanci ko kuma ta ci da bread
idan Housemate dinta ya siyo, wani lkcn ta ci french fries da kwai ko ketchup, kwankwasa kofar parlor
taji ana yi, ta ɗan zaro ido sanin bazai wuce Housemate dinta ba, kilan ya mance makullinsa ko kuma
yayi misplacing dinsa as usual, ta kalli wayarta dake ajiye a kan kitchen cabinet har sannan Abdul was on
the line kuma a handsfree ta sa wayar, tana ɗan kame kame tace masa "Can u excuse me pls, i will call u
back in the next 2 minutes pls" Abdul yace "Why? Me zaki yi? Is the call hindering you from doing
anything?" Da sauri tace "Noo" don bata son tayi laifi, sai kuma a hankali tace "Just want to round up the
cooking ne, na kusa gamawa ai" Yace "But my call isn't preventing you from doing so, wayan ba a ajiye
yake ba? Continue with ur work kawai" Knocking ta sake ji, ta ma san Housemate dinta ne cause haka
yake knocking dinsa, ta kalli wayarta tace "Ohk then" Abdul ya ci gaba da maganar da yake mata, a
hankali ta dau wayar ta fita daga kitchen din almost tiptoeing kamar tana tsoron yaji sound din tafiyarta,
ta nufi kofar parlon ta bude at the same time tana kokarin yi ma Housemate dinta alamar da yayi shiru
ta hanyar dora finger dinta daya a lips dinta, lkci daya taji komai nata ya tsaya cak, a hankali ta zame
finger dinta daga lebbenta tana kallonsa bata ko kiftawa zuciyarta na bugawa, ta cire wayar dake
kunnenta looking speechless and Surprise at the same time, Calmly yace "Ko in koma ne?" Ta zaro ido
cikin in ina tace "No, no, not at all, i... i was just being surprise, sannu da zuwa" Da sauri ta koma gefe
zuciyarta na bugawa da karfi, Ya katse wayar dake kare kunnensa sannan ya shiga parlon, ta bi sa da
kallo still shocked, gani take kamar she is daydreaming, ta kikkifta idanuwanta ta bude to be sure but still
she is still seeing him, har sai da ya karasa cikin parlon ya zauna sannan ta bi bayansa, a hankali ta duka
kusa da shi tana yaƙen karfin hali tace "Wai dama all this while kana garin nan ne? I am so confuse" Yace
"Gashi kin gan ni, in baki yarda ba sai ki taɓa ki ji don ki tabbatar" Still feigning smile tace "I am seriously
surprise, this is the least thing i expected today wallahi..." Sai kuma ta tashi da sauri tace "Let me get u
water" Kitchen ta tafi zuciyarta na bugawa, sai da ta jingina jikin cabinet ta dafe kirjinta a hankali tace
"Innalillahi wa inna ilaihi raji'un, na shiga uku" Tasan at anytime Housemate dinta zai iya shigowa gidan
don yamma yayi sosai, cikin hanzari ta bude fridge ta dauko masa ruwan gora da drink with glass cup
sannan ta fita da sauri, tana kirkiran murmushi ta durkusa gabansa ta ajiye masa tace "Tun yaushe kake
garin nan amma?" Ya dau ruwan goran yana kallo yace "You are buying expensive water now? Sannu er
gayu" Tayi dariyar karfin hali tace "Not at all, miyar ma ya kusa yi sai in zuba maka abincin, ko dama shi
sa kace sai nayi girki?" Kawai murmushi yayi bai bata amsa ba, ta mike ta koma kitchen, gaba daya she is
confuse on what to do, ta fara dube duben wayarta ta tuna ta ajiyesa kan kujera a parlor, fitowa ta sake
yi ta tarar Abdul yayi picking din kiran da ake masa ta waya, cikin dubara ta dau wayarta ta nufi dakinta
da sauri tana kallonsa ta gefen ido taga attention dinsa na kan wayar da ya fara, bandakinta ta shige ta
kulle tace "Na shiga uku" Da ta tuna bata ma da lambar Housemate din nata ta sake jin mugun tashin
hankali, yanzu ya zata yi? Da sauri ta fara dialing number Salem, ai ko yana fara ring ya daga, murya can
kasa ta gaishesa without waiting for his full reply tace "Plsss how can i get in contact with my
Housemate? ina son zan masa magana ne urgently" Salem yace "Ohk, muna ma tare, gashi nan" Bata
san sanda ta sauke wani irin ajiyar zuciyar relieve ba, taji muryar Housemate dinta yace "Hello Halysaah,
is everything alright?" Ta girgiza masa kai da sauri kamar yana ganinta tace "Plss i am sorry amma kar
kace zaka dawo yau, my fiance is around, he just came without notice" Yace "Tohhhh, haka kuma aka yi
ashe?" Ta wani turo baki kamar yana ganinta, yayi murmushi yace "Alright Halysaah, keep ur cool, duk
sanda ya tafi sai ki sanar min" A hankali tace "Thank you" Yace "Not a problem" Shi ya fara katse wayar,
ta kalli screen din sannan ta sauke ajiyar zuciya ta fito da sauri bayan ta bar wayar a dakinta, har sannan
ta tarar Abdul bai gama wayar da yake ba, da alama business call ne, Khaleesat na tafiya a hankali ta tafi
kitchen don saka masa abincin da ta girka, har sannan she is shock, babban damuwarta yanzu
kasantuwarsu su biyu kadai a gidan, a da bata jin tsoron kasancewa da shi guri daya and that was almost
4 years back, but not anymore, he is complete changed all of a sudden in just a year, da tunanin nan ta
fito daga kitchen, ta karasa har gabansa ta ajiye masa abincin, yana kallonta yace "How about ur
Housemate, bata nan ne?" Ta ɗan yi murmushin karfin hali tace "Yeah bata nan" Ta mike ta koma edge
din kujera ta zauna kamar bakuwa a gidan, a hankali tace "Ya su Momy da Aunty Hafsah?" Yace "Lafiya
lau" Bata sake cewa komai ba, Ya kalli abincin da ta ajiye masa yace "I am full, ki rufe sai dai anjima" A
hankali tace "Ok tafiya zaka yi da shi?" Yana dubanta yace "In tafi da shi ina?" Ta kirkiri murmushi tace
"A'a ai tambaya kawai nayi" Yace "Na riga nayi lodging out of the hotel, i was in Maryland since
morning" Khaleesat was speechless, bata gane yayi lodging out of the hotel ba, to ina zai kwana ko kuma
wani hotel din zai kama? kai bata ma yarda ba don in yayi lodge out to ina trolley din kayansa yake, Tana
murmushi da kyar tace "To ina akwatin ka?" Yace "Tana cikin mota" Ta hadiye abu da kyar tace "Motar
wa?" A takaice yace "Ban sani ba" sunkuyar da kai tayi bata sake cewa komai ba, yace "Ko kina da plans
ne yau? Naga kinyi mamakin zuwana da gaske" Ta zaro ido tace "Not at all wallahi, ai kai ma kasan daga
schl babu inda nake zuwa, kawai dai nayi mamakin muna ta waya tun daxu ashe kana garin nan" Ya mike
yace "To ki dena mamaki tunda ba ke kika siya min ticket din ba" Ta sunkuyar da kanta tayi shiru, dakinta
ya nufa yace "Let me take a shower" Khaleesat ta gyada masa kai kawai ta bi sa da kallo, a very tall and
masculine guy he is, just like her Housemate, and they are all handsome in their own different ways
kamar su suka yi kan su, sai dai ita tafi ganin kyan Housemate dinta ko me yasa, a zahiri duk macen da ta
samu Abdul in dai mayyar kudi ce kuma tana son namiji me tsantsan kyau ga kuma qualities na cikakken
namiji pertaining to body structure not behavior... to duk walakancin da Abdul zai dinga mata zata jure
tayi ta shanyewa don mijin nuna ma sa'a ne shi din, that is if behavior isn't included, amma Khaleesat dai
dai da rana daya qualities din nan biyu na Abdul bai taɓa dada ta da kasa ba, a haka stepsisters dinta ko
ga maciji basa yi da ita all because of Abdul, kiri kiri suke nuna mata jealousy dinsu daga su har iyayensu
a fili, ba su kadai ba hatta wasu daga sa'aninta a anguwa sun dena kulata saboda shi, basu san baƙin cikin
da take kunsa day by day ba, she wish zai koma ma daya daga stepsisters din nata da ita kam ta huta,
kwantar da kanta tayi jikin kujera tana jin hankalinta na kara tashi, yana nufin kenan bazai tafi anytime
soon ba? kilan ma yace nan zai kwana fa? Sosai hankalinta yayi mugun tashi da tunanin hakan, after a
while ta mike a sanyaye ta dau abincin da ta zubo masa ta tafi da shi kitchen ta rufe, ana haka har lkcn
sallan magarib yayi bai fito daga dakinta ba, Khaleesat dake ta zaune a parlor kamar bakuwa a gidan ta
kalli kofar dakin nata a sanyaye, sai kuma ta tashi walking slowly ta nufi dakin, a hankali tayi sallama sai
da ya amsa sannan ta bude, ta samesa zaune saman darduma alamar sallah ya idar yana danna wayarsa,
gaba daya dakin ya cika da kamshin turarensa, murmushin karfin hali ta kirkiro ta dau hijab dinta tace
"Sallah zan yi" Sai kuma ta juya zata fita yace "Ina zaki yi sallan?" Ta sake juyowa cikin sanyin murya tace
"Parlor" Mikewa yayi ya bar kan darduman yace "Pray here, dama kin saba sallah a parlon ne?" Ya koma
gefen gado ya zauna still pressing his phone, da kyar ta karasa kan darduman ta fara sallan, bayan ta idar
ta dinga addu'ar Allah ya taɓa zuciyarsa ya tashi ya tafi ya bar mata gidan ita dai, muryarsa taji yace
"Make me a cup of hot chocolate" Ta gyada masa kai tace "To" Mikewa tayi ta nufi kofa ta fita zuwa
kitchen, abinda yace tayi ta masa sannan ta koma dakin rike da mug din, bedside drawer ta ajiye masa
tace "In kawo maka abincin?" Yace "Aa bazan ci abinci ba, me yasa kike yawo da Hijab kamar matar
liman" Tana murmushin karfin hali da kyar tace "Aa ina jiran lkcn isha ne" Yace "Cire Hijab din nan" Ba
musu ta cire a hankali ta linke ta ajiye, yace "Ke kin ci abincin ne?" Duk da bata ci ba ta gyada masa kai
don gaba daya ta nemi appetite dinta ta rasa, gun reading material dinta ta tafi ta zauna ta kunna laptop
dinta tayi kamar karatu take, ya gama danne dannensa a waya ya dau chocolate dinsa ya fara sha, gaba
daya Khaleesat bata fahimtar me take dubawa a laptop din gabanta, sun kusa awa daya a yanda suke, ita
dai har sannan tana gaban laptop taki tashi, ta gefen ido ta kallesa ganin ya mike daga inda yake zaune,
taga sallan isha zai yi, sai da ya idar sannan ita ma ta tashi ta tafi tayi sallan, nan ma babu kalan addu'ar
dabata yi ba kan Allah ya taɓa zuciyarsa ya koma hotel dinsa, after a while ta mike ta dauke darduman ta
linke ta ajiye, ya mike ya kamo hannunta yana kallonta yace "Why are you uncomfortable kamar kina
tare da stranger a gidan nan ne Khaleesat?" Tayi dariyar yake tace "Stranger kuma Ya Abdul? Ai kai ba
stranger bane, kai yayana ne, kuma da ai ka sha kwana gidan nan farkon da na zo kasar, kana kwanciya a
parlor ni kuma in kwanta a daki" Yace "Kinsan da haka kike dari dari?" Ta sunkuyar da kanta ganin kallon
da yake mata, zuciyarta ya dinga bugawa, har ji take kafafuwanta suna neman kasa daukarta, ya matso
da ita dab da shi har tana iya jiyo breathing dinsa, calmly yace "Kinsan menene yasa nake kwanciya a
parlor a sannan?" Ta girgiza masa kai without looking at him don she is soo uncomfortable with him
drawing her closer to himself, yayi kasa da murya yace "Saboda u were still a baby sannan" Ta daga
idanuwanta da kyar ta kallesa amma ta kasa cewa komai, yace "Yanzu kuwa ke ba baby bace, how old
are you?" Ta kasa basa amsa, ya ɗan mata tsawa yace "Tambayarki nake?" Ta hadiye wani abu da kyar
tace "I am 20" yace "To a sannan ina keeping distance between us because i was still grooming you" Ta
kauda kai seeing how closer he was coming to her, juyo da kanta yayi yace "Meye haka?" Muryarta na
rawa tace "This is against the teaching of islam Ya Abdul, ni ba muharramarka bace" Yace "Oh really?
Dama wani ne zai aure ki ba ni ba ashe?" Ta kasa ce masa komai lkci daya hawaye ya cika idonta, duk
tsiyar da yake mata da yaga hawaye idonta yake calming down, ya jawota jikinsa yayi kasa da murya
yace "Kin zata ke irin matan da zan yi using inyi dumping ne Khaleesat? You are diff from them, ke matar
da zan aura ce" Ta kasa basa amsa hawaye na zuba idonta, ita kanta tasan Abdul so na aure yake mata, a
shekarun da suka yi tare iyaka yakama mata hannu babu dadi babu kari, amma daga 2 years back labarin
ya sauya har bata son ya zo inda take don sai ya mata wasu abubuwa dake damunta, in ya tafi ta sha
kukanta kuma ta kan yi kwana da kwanaki bata dawo dai dai ba, amma bai taɓa attempting saninta ba,
muryarsa ne ya dawo da ita daga tunanin da ta tafi, as if whispering yace "I have tried Khaleesat, i
abstained from doing anything that will distabilize you all this years because i want you to have the best
education ta yanda zan iya nuna ki a ko ina as my wife, amma kullum ina jin urge dinki a raina I've tried
so many times to ignore the urge, but menene ya rage yanzu? You have just a year and few months to
round up, aurenmu kuma ko yau aka ce a daura babu abinda zai hana daurasa, i came all the way from
Nigeria because all this days my feeling for you is distabilizing me and making me go nut Khaleesat, so
now trust me, relax and keep calm pls baby gal" Khaleesat ta dade bata shiga tashin hankalin da ta shiga
a sannan ba, don sarai ta fahimci inda maganarsa ya dosa, kuma lkci daya yake magana yana cire mata
hijab din jikinta, common ya taɓa ta idan taki ta karfi yake yi mata balle wnn, gashi gaba daya yanayinsa
ya canza alamar ya fara fita hankalinsa ma, ta kamo hannunsa jikinta na rawa tace "But kwanakin da
suka rage ai basu da yawa ko Ya Abdul, why not be patient pls..." Ya kalleta da idanuwansa da suka kada
strictly yace "I can't wait any longer" Muryarsa kadai sai da ya tsoratata hakan yasa tayi gum da bakinta,
tana jin zuciyarta kamar zai fito daga kirjinta tsabar tashin hankali, kafin ya rabata da kayanta tayi kasa
da murya still holding his right hand tace "Ohk pls ka bari inyi wanka tukun, kai ma ai ka yi" Ya dinga
kallonta da idonsa da suka yi ja, ta sunkuyar da kanta trying to control herself kar ta fashe da kuka tace "I
won't take long" Saketa yayi ya koma gefen gado ya zauna, tana tafiya da kyar ta nufi bandaki tana
kallon wayarta dake gaban dressing mirror, ta ɗan kallesa, taga bin ta yayi da kallo, ta dake da kyar tace
"Zan dau shower gel dina" Gaban mirror dinta ta nufa, dai dai sanda ya fara cire rigar jikinsa da sauri ta
dau wayarta da wani Container din lotion da tayi pretending shower gel ne sannan ta shige bandaki ta
kulle kofa, tap ta bude jikinta na rawa hawaye na sauka idonta ta fara dialing number Salem, yana fara
ring ya daga, da kyar tace "Plss i want to speak to my Housemate plss" Salem yace "Oops wllhi bama tare
yanxu" Ko rufe baki bai yi ba tace "Don girman Allah ka turo min lambarsa yanzu" Yace "Ohk let me send
you" Yana katse wayar ta dinga kallon screen dinta tana jiran shigowar lambar Housemate dinta, her
body was just shaking, ga wani bugawa da zuciyarta yake, cikin few seconds sai gashi ya turo mata
lambar, da sauri tayi dialing ya fara ringing amma har ya katse bai daga ba, ta sake kira nan ma bai daga
ba, sau uku tana kiransa bai daga ba, ta saki kuka ta durkusa kasan bandakin tace "Na shiga uku" Sake
dialing number Salem tayi, yana picking tace "Pls bai daga ba ko zaka..." Salem bai jira jin sauran
bayaninta ba yace "Bari in tura maki number Ajay, nasan dama ba lallai Jay ya daga ba don ba ko wani
kira yake dauka ba, sai kice ma Ajay ya basa suna tare yanzu" Tana gyada kai da sauri tace "Ohk to
Nagode" yana katse wayar sai gashi ya turo mata number Ajay, tayi dialing number da sauri hannunta na
rawa, ai kuwa yana fara ringing da few seconds aka daga, da kyar tace "Plsss ina son zan yi magana da
Housemate dina ne" Shiru taji yayi as if processing the voice, sai kuma a takaice yace "Waye wannan?"
Ta fara shesshekar kuka muryarta na rawa tace "Don Allah kayi hakuri ka rufa min asiri ka basa ina son
zan masa magana" Yace "Me ya faru?" Cikin kuka tace "I need his help plss" katse wayar taji yayi,
hankalinta in yayi dubu ya tashi a moment din nan, ta shiga uku ta lalace, yanzu ya zata yi, ko dai ta kira
Safiyyah, number Safiyyah ta duba da sauri tayi dialing amma har ya katse bata daga ba, ji tayi kamar za
a bude kofar bandakin tayi saurin tsoma wayar hannunta cikin ruwan da ta fara tarawa a bath tub a
gigice, ashe kunnenta ne ma yaji kamar an taɓa kofa amma ba kowa gun kofar, ta ciro wayarta taga
screen din yayi baƙi, ta dinga yarfe ruwan da ya shiga tana kokarin kunnawa amma yaki kunnuwa, hade
kanta tayi da bath tub hawaye masu zafi na sauka idonta....
*For continuation of the book Halysaah, pay 500 into 3276052019 Fcmb Hauwa Bello Jiddah*
_And ur evidence of payment via 07087865788_
✍🏻
*My special thanks to those that have already patronized since the beginning of this book, Thank you so
much and i appreciate you*🥺
*KURA A RUMBU*
*Wattpad @MaryamahMrsAm*
*Ban yarda wani ko wata ya juya mun labari ta kowacce siga ba tare da izini na ba*
*Kuɗin karatu yana wakiltar mutum ɗaya ne, kiji tsoron Allah karki ɗauki hakkina ta hanyar fitar mun da
littafi*
*KURA A RUMBU littafin kuɗi ne, a biya naira 800, biya a asusun*
*7061838488*
*Opay*
*PAGE 52*
Kwana yayi yana tunanin yanda akayi Zulaiha ta yaudareshi, tsayin shekarun da suke tare ace bai taɓa
tunani ko hasashen tana da wani hali na daban bayan wanda ya santa da shi ba. Yaran da talauci da
matsin rayuwar da suka tashi a ciki ya saka basuda kataɓus ko a cikin unguwa ɗaiɗaikun mutane ne suke
mu'amala da su balle makaranta.
Shigar sa cikin rayuwarsu ne ya kawo musu ɗauki har suka samu yanci dukda hakan kuma suna gabatar
da rayuwarsu ne cikin takatsantsan dan ya sha tambayarta mai yasa bai taɓa ganinta da wata da sunan
ƙawarta ba sai ta ce Ummansu ta hana wai bata so suyi ƙawaye kada zuciyarsu ta ringa ƙawata musu
abubuwan da basu da halin mallaka dan haka bata da wata ƙawa daga unguwa har makaranta kuwa sai
dai yayan yan uwa da ya kan gansu jefi jefi.
A saninsa kuma babu in da suke zuwa daga makarantar boko sai Islamiyya kuma suk inda zasu je ɗin
cikin shigar Hijabi harda safa da Niƙab babu wata suffa ta a tattare dasu da zata taɓa bayar da hanyar da
za'a zargesu da wani abu mara kyau. Ashe dai su ɗin Abin tsoro ne wai KURA A RUMBU.
Kalaman Kawun su zuwan da yayi suka ringa masa yawo a kai kamar tilawa ya ringa haɗasu da labarukan
da take bashi akan sharrin da Kawun nasu yake musu dalilin karatun jami'ar da shi ya ɗauki nauyinta
amma Kawun sai ya ce yawon lalatarta kawai takeyi ba wani karatu ba da yanda ta ce mutanen unguwa
suna surutu akan alaƙarsu ana cewa iskanci sukeyi shiyasa yake wahalta mata ashe duk raina masa
wayau kawai ta ringayi tsayin lokaci Allah kaɗai ya san irin rayuwar da take yi a bayan idonsa.
Haka ya raba dare har asuba yana tunani, sai da aka kira sallah kafin ya tashi daƙyar saboda ciwon kai ga
cikinsa daya ɗaure kamar an saka masa dutse. Haka ya lallaɓa yayi alwala, dukda haushinta da yake ji
haka nan zuciyarsa ta tilasta masa zuwa tashinta. Munsharinta yayi masa maraba, sabon baƙin ciki ya
turnuƙeshi. Fitilun ɗakin ya kunna gaba ɗaya haske ya gauraye ko ina a zatonsa irin Halima ce da duk
baccin da takeyi aka kunna fitila sai ta farka amma ina Zulaihan kamar matacciya munshari kawai take ja.
Ya matsa yana ƙarewa gadon da ya ɓaci da jini sai kace wanda aka yanka kaza a kai, mamaki ya kamshi,
daga ina aka samu jinin b dai daga jikinta ba? Domin shi dai ya san free get ya wuce sai dai idan kuma
shine ya zubar da jinin ba zaiyi mamaki ba. Sai lokacin ya tuna da zaiyi wanka ma yaga jinin a jikinsa
amma da yake lokacin ba'a nutse yake ba bai mayar da hankali ba. A saitin kanta ya tsaya yana matse
fuska, ji yake kamar ya sharara mata mari a baƙar fuskarta da yaga tayi masa muni irin wanda bai taɓa
ganinta da shi ba.
Ya ringa kokawa da zuciyarsa dake ingizashi akan wai ya sharara mata mari ta tashi tayi masa bayanin
abinda yake ci masa zuciya amma ya kasa ƙarshe ya shiga kiran sunanta ya ringa maimaitawa amma ko
gezau baiga alamar zata amsa ba sai ya shiga dukan katakon gadon nan ma ya fi minti biyar kafin tayi juyi
cikin muryar bacci take cewa
"Ki tashi, kalli fa cikin ƙazantar da kike kwance" ya bata amsa yana sake kallon gadon, tayi tsaki kawai
tana sake gyara kwanciya, ya kai mata duka mai zafi ta zabura ta miƙe zaune kamar zata mayar da
martanin dukan amma ta tsaya tana hararasa da manyan idanuwanta da yaji shakkar kallonsu ta
kamashi. Ganin ta tashi zaune ya saka ya juya yana ce mata
"Ki tashi kiyi sallah" ya fice daga ɗakin haushin kansa yana kama shi.
Tsaki tayi ta koma baccinta ba tareda tayi abinda ya ce ɗin ba. Bilal kuwa a kan dardumar daya yi sallah
bacci ya kwashe shi dama ga gajiya bai farka ba sai ƙarfe tara da mintuna sakamakon bugun ƙofar da ya
ringa jiyowa kamar za'a karyata.
Ya tashi zaune daƙyar yana dafe kansa da a maimakon baccin da yayi ya saka ciwon ya ragu ƙaruwa ma
yayi, dai dai lokacin Zulaiha kuma ta fito daga ɗakin ɗaure da towel wanda da kaɗan ya wuce
mazaunanta jikinta da kumfa alamar wanka takeyi bugun ya fito da ita, suna haɗa ido ta watsa masa
wani shegen kallo kamar wacce taga kashi tayi ƙofa tana sakin ƙaramin tsaki. Ya kira sunanta da
dasasshiyar murya ta tsaya ba tareda ta waiga ta kalle shi ba, a hankali ya miƙe yana dafa kansa sai da ya
isa kusa da ita kafin ya ce
"Aa daga turu aka kwantoni ƙarewar hauka, da kana ji ashe tsabar wulaƙanci baka tashi ka buɗe musu
ba". Tsayawa yayi yana kallonta da mamaki ita kuwa ko a jikinta ta juya ɗaki tana kaɗa masa mazaune.
Ya haɗiye abinda ya tsaya masa a maƙogaro kafin ya fita jin masu bugun basu da niyyar dainawa.
Ƙawayenta na jiya ne su huɗu Suby kaɗai ya gane a cikinsu, ya matsa suka shigo fuska a haɗe babu ko
wacce ta gaida shi suka wuce ciki da kayan da suka taho dasu kwalin Tv sai ƙananan kwalaye da bai san
menene a ciki ba haka ya rakasu da ido har suka shige falon yana jiyo yanda suka fasa ihu da alama su da
Zulaihan ne abin mamaki sai kawai ya mayar da ƙofar ya rufe ya wuce ɗakinsa yana sauke ajiyar zuciya
kamar wani maraya.
Kwanciya yayi ya sake faɗawa tunani, babban abinda yake damunsa, har ransa haushin Zulaiha yakeji
kamar ya kamata ua rufeta da duka har sai yaji yanda akayi tayi masa wannan cin amanar amma kuma a
hakan bai ji ko ɗigo ɗaya na daga son da yake mata ya ragu a zuciyarsa ba. Tun daren jiya yake ayyana
gari na wayewa zai ce ta tattara ta wuce gidansu ba zai iya zama da ita ba amma kuma zuciyarsa ta kasa
bashi haɗin kai akan hakan.
Ya ɗauki wayarsa daya bari a ɗakin tun daren jiyan ya kunna amma kuma ya rasa wa zai kira ya raba
baƙin ciki da shi ko zai samu sauƙin abinda yakeji a ransa. Dariya za'a masa ma, ba yan uwa ba ba abokai
ba ya tabbatar muddin wani ya san halin da ya tsinci kansa sai ya shiga uku a gari.
Haka ya ringa juyi yana jiyo ihu da hargowar Zulaiha da ƙawayenta suna da sabgogi kamar ma tsakar
gidan suka fito, ƙamshin ƙwai daya ringa jiyowa ya tayar masa da yunwar daya kwana da ita. Tun yana
jira yaga ta kawo masa ko tazo ta kirashi ya karya har agogo ya buga sha ɗaya ba Zulaiha babu breakfast.
A waya ya kirata murya kamar wacce akawa dole ta amsa da
"Ina breakfast ɗina?" Tayi shiru kafin kuma ta kashe wayar ya tashi daƙyar ya shiga banɗaki yayi brush ya
fito yana jiranta.
Zulaiha kuwa da Asuba bayan daya tasheta baccinta ta koma bata kuma farka ba sai ƙarfe tara shima
saboda kiranta da Suby tayi ta sanar mata gasu nan a hanya sai lokacin ta tashi tana jinta sakayau
saboda kwanciya da tayi akan katifa mai kyau ba irin siɗaɗɗiyar tasu ta gida ba. Rai fes take jinta burinta
ya cika ta mallaki sahibul karɓinta Bilal ita da shi kuma mutu ka raba.
Tana son Bilal kusan akansa ta fara sanin menene so dukda kafin shi tayi soyayyar ƙuruciya da wani yaro
Nura a tsohuwar unguwar su. Yaron babansa nada kuɗi da wannan kuma ya ringa hillatarta da yake ita
ɗin Allah yayita da ƙwadayi da son cin daɗi sai dai kuma sun tashi a gidan da ci uku ma wahala yake
musu a lokuta da yawa. Da wannan yaron mai suna Nura yayi amfani ya ringa siya mata kayan ƙwalama
da sunan yana sonta, lokacin data shiga JS1 ya ce zata ringa zuwa gidansu ta haɗu da ƙannensa a ringa yi
musu extra lesson tunda ya fahimci tana da ƙoƙari da kuma son karatu.
Ummansu wacce ita ce sila ko ace musabbabin lalacewarta ta goyawa abun baya dukda mahaifinsu ya
nuna ƙin amincewa amma tayi masa tatas kamar yanda ta saba duk sanda magana ta tashi akan yaran
sai ta ce yanda ya barta dasu baya tsinana musu komai karya kuskura yace zai ringa tsoma musu baki a
sabgoginsu. Shikenan ta fara zuwa extra lesson wanda ba karatun sukeyi ba ɗakinsa yake kaita tun bata
son abinda yakeyi mata har ta saba ya zama ko bai kirata ba ko ba ranar lesson ɗin ba zatayi ƙaryar zuwa
wani guri ta tafi gurin Nura, tun a lokacin kuma mutane da yawa sun sha kaiwa Ummansu maganar
saboda ba a iya gidansu ba har shagunan abokansa suke zuwa amma duk wanda ya faɗa mata zagi da cin
mutunchi ne zai raba su tace an yiwa yarta ƙazafi.
A haka suka kwashe kusan shekaru biyu da Nura kafin ya tafi ƙasar waje karatu tun daga nan kuma har
kawo yau bata sake ko jin labarinsa ba dan dama ba yan Kano bane daga baya suka bar can unguwar tun
ma kafin su Zulaihan su bari. Rabuwarsu da Nura ta saka ta rasa abubuwa da yawa waɗanda yakeyi
mata, babu tsoron Allah Ummansu ta ce ai ba zasu zauna haka ba, tunda dai ko da batada fuskar da zata
burge maza dukda ƙananan shekarunta da yake tana da garin jiki ai ba zata gagara nemo musu abinda
zasu ringa kaiwa bakin salati ba.
Daga nan ta fara zuwa gurin masu shaguna, wasu su biye mata su bata kuɗi ko abin amfani masu tsoron
Allah su kai ƙara gurin mahaifinsu wanda yake tamkar hoto dan ko ya faɗa ba ji zatayi ba tunda uwarta
ta tsaya mata. A haka Bilal ya shiga rayuwarsu zuwansa kuma ya kawo sauƙi cikin al'amuran domin kan
jiki kan karɓi yake tallafa musu kuma shi yayi fafutuka ya samawa Babansu motar haya da yake direba ne
yake hawa abinda yake samowa da wanda Bilal ɗin yake basu ya taimaka ƙwarai har Zulaihan ta hau saiti
ta mayar da hankali kan karatu.
Sai dai kuma daga sanda ta shiga shekarun budurci na sosai a lokacin mahaifin su ya samu hatsari ya
gamu da jinyar da bai warke ba har ya koma ga mahaliccinsa sai ya zamana Bilal ne kaɗai madogararsu
dan haka ta sake komawa ruwa har tayi nasarar jan ƙanwarta Nuratu da huɗubar Ummansu wacce
kullum take mata tilawar ba zai yuwu ta zauna yar uwarta ta nemo a ci da ita ba tunda itama tana da
abin bayarwa idan ta zauna duk idan aurenta ya tashi kada tayi kuka da kowa ta kuka da kanta.
Tafiyar kuma ta canza salo sanda ta shiga Jami'a ta haɗu da gogaggun da suka fita ido a harkar, haka ta
ringa zuba sharafinta cikin takatsantsan kuma Allah ya ara mata lokaci musamman da suka koma
unguwar da babu wanda ya sansu suka fara sabuwar rayuwa.
Kullum ƙawayenta suna mata mitar basuga amfanin kuɗin da take samu ba domin dai kullum ka ganta
tana nan kalar tausayi cikin tsumma ba sutura mai kyau mayukan gyaran fata da turaruka ma saboda
ƙorafin mazan da take ta'ammali dasu ya saka ta fara siya saboda ta gyara jikinta duk a salon kada a
fahimci halin da take ciki ya saka take takatsantsan da gudun mallakar duk wani abu da zai janyo
hankalin mutane kanta, suna dai cin daɗi a cikinsu amma abubuwan more rayuwa dole ta haƙura da su
saboda gujewa zargi sai dai tayi ta tara kuɗin idan sunyi yawa ta siyi wani abu kamar zobe ko fili ta ajiye.
A silar Nuratun asirinsu ya tonu har yan uwan mahaifinsu suka san halin da suke ciki dukda suna ji a jita
jita wanda kuma da yawa Bilal da kowa ya san yana wahalta musu har gida ya siya musu shi mutane
sukewa kallon abokin shashancin nata domin dai a rayuwar da muke ciki yanzu haka kawai wani bare ya
ringa maka hidima kwatankwacin wacce yake musu tabbas abar dubawa ce dukda na Allah basa ƙarewa
a duniya.
Ciki Nuratun tayi wanda baƙin cikin haka shine silar ajalin mahaifinsu. Ita bata kai wayewa da buɗewar
idon Zulaihan ba kusan ma tursasawata sukayi ta shiga rayuwar da ba tata ba, bata ma san da tayi cikin
ba har saida ya bayyana kansa fallasa kansa tukunna aka sha gurmi da dangin Babansu duk kuma yanda
Umman da Zulaiha suka kaɗa suka raya tace ba zata zubar ba iya zunubin data kwasa harta same shi ya
isheta ba zasu ɗora mata wani ba da Allah kuma ya nufa ba mai taka ƙasa bane tayi ɓari dukda da saka
hannun su Zulaihan daga nan kuma ta tuba ita kanta Zulaihan daga lokacin ta rage abubuwa da yawa
musamman kuma da Bilal ya fara taso da maganar aurensu ta shiga tsoron kar maganar ta koma masa a
samu matsala dukda dai na Nuratu ne ya fito fili ita aka san bata ji amma ta san hakan zai iya shafarta
shiyasa ta tattara hankalinta guri ɗaya ta saki harkar dama kuma tayi alƙawarin daga sanda aka saka
musu rana zata bari to hakance ta kasance ta dena zuwa gurin kowa sai dai yan dabaru na waya data
cigaba domin cigaba da samun kuɗin riƙe kai zuwa sanda zatayi auren.
Sai da ta cire Bedsheet ɗin da ɗaure shi a leda domin ba zata iya wankewa ba dama kuma amfaninsa
kenan bata shimfiɗa wani ba ta shiga wanka a gurguje sai dai tana saɓa sabulu ta jiyo bugun ƙofa ta kasa
kunne taji ko Bilal data leƙa falo ta ganshi a kwance zai tashi ya buɗe amma shiru shine ta zuciya ta fito
da kumfa a jikinta zataje ta buɗe musu.
Wankan ta koma bayan sun gama iyashegensu suna tsokanarta wai amarya suka ringa dariyar da su suka
san dalilinta sanin yana gidan kuma ya saka suka kama bakunansu dake cike da maganganu da son jin ya
aka ƙare, abubuwan da suka kashe kuɗi tayi dan ta lulluɓe rayuwarta ta baya sun ci ko kuwa an samu
akasi?
Wanka ta koma ta barsu suna haɗa TV da suka biya suka karɓo mata, Asmy ta ce bata karya ba gashi dan
wulaƙanci bata ajiye musu sauran kaza ba kamar yanda ta ce sun cinye dan haka ta duba kitchen babu
komai sai kayan shayi da burodi, ganin akwai ƙwai da mai babu albasa dai haka ta fitar da camping gas
tsakar gidan suka ɗora ruwan tea bayan ya tafasa aka soua ƙwai dan ma Suby ta taho mata kayan spices
garda garlic powder da yayarta ta bata gudummawa shi suka saka a ƙwan da suka fashe kusan rabin
creat suka baje a falo suka karya tareda amarya bayan ta yi sallah ta fito.
Suna tsaka da jin labarin yanda akayi ya kirata, tayi tsaki bayan ta kashe wayar ta ce
"Banda rashin Imani ya raba dare yana sukuwa akaina yanzu gari ya waye ya ce wai in bashi abin kari
maimakon shi ya dafa mun".
Sadiya ta ce
"Maganar gaskiya ba shiya kamata ki haɗawa abinci harda farfesu ma saboda ya mayar da jinin jikinsa
dan abinda kika zuƙe ya fi ƙarfin ruwa ma" gaba ɗaya suka sheƙe da dariyar shaƙiyanci suna tafawa. A
wani shegen tea flask iya ta da ta zuba masa ruwan zafin data taro a banɗaki ta haɗa da guntun bread
ɗin da suka rage da sauran Milo dan sun shanye ledar Peak 500g daya siyo, a hannu ta riƙe kayan Suby
na cewa ta ɗora a try mana tayi wucewarta.
BILAL
Kallon sama zuwa ƙasa yayi mata kafin ya tsayar da idonsa kan hannunta yana duban abinda ta ruƙo
harta dungurar dasu a gabansa tana cika tana batsewa ko me ta tuna kuma sai ta saki fuska kaɗan ta
zauna a gefensa ta shiga gaishe shi tana ƙoƙarin shiga jikinsa cike da kissa. Janyeta yayi ya miƙe zaune
daƙyar dan kwanciyar da yayi zazzaɓi ya rufe shi, ya dafw kansa dake bugawa yana kallon kayan dake
gabansa kafin ya ce
"Menene wannan?"
"Breakfast mana" ta faɗa tana sake matsawa kusa da shi dan ganinsa da tayi babu riga ya saka ta fara jin
muradin kasancewa dashi dan abubuwan data sha jiya basu gama sakinta ba dukda taga alama shi nasa
ya sake shi.
"Ni zanci wannan sauran biredin sai kace wani almajiri kuma ina madarar?" Ya faɗa, ta yamutsa fuska ta
ce
"Ai dai kana kallo baƙi nayi ka godewa Allah ma daka samu sauran madara kuma sun shanye"ta ƙarasa
tana harararsa. Da mamaki ya ce
Kasa ce mata komai yayi ya tsaya kawai yana kallonta kafin ya sauke ajiyar zuciya ya koma ya kwanta
saboda yanda zazzaɓin yake nuƙurƙusar jikinsa ya ce
Haka ya ringa tura ƙwan daya ga kamar da gayya aka ƙone shi ga ga uban ƙarni daƙyar ya iya haɗa Milon
a kofin robar data haɗo masa da shi. Safiyarsu ta farko da Halima ta shiga dawo masa, dukda yanda ta ke
a wani yanayi na shiga sabuwar rayuwa haka ta ringa kai da kawowa bata nutsu ba saida ta cika masa
dining da lafiyayyun breakfast bayan dankali da ƙwai nama kansu kusan kala uku ga sauran kazar amarci
ga wanda aka taho mata da su daga gida komai cikin kwanuka na alfarma suna ci suna annashuwa amma
yau shine aka bawa sauran biredi a gidansa da shayi a flask ɗin roba da kofin roba kuma babu yanda ya
iya ya ci.
Baccin wahala ya sake komawa bayan ya sha paracetamol Zulaiha kuwa dama tunda ta dangwarar masa
da ƙwan ta koma gurin ƙawayenta suka cigaba da sabgarsu.
HALIMA
Dole ta saka nake ƙarfafa jikina domin na yiwa kaina alƙawarin ƙaryata Bilal da yake cewa dole ya san
zan neme shi. Ina son sa ba zan ƙaryata hakan ba amma kuma ni da kaina dana nutsu na fahimci cewar
rabuwata da shi shine alkhairi a tare da ni.
Daga kalaman daya kalli idona ya faɗa mun na tabbatar dagaske yakeyi baya so na, albarkacin soyayyar
da nakeyi masa ta saka ya aureni idan ma kuma yana so na ɗin tunda ya fahimci so na ya fi nasa yawa ya
sakawa ransa zan zauna dashi komai wahala zan jure shine dalilin daya saka ya ringa azabtar dani a fili da
baɗini har kuma da yake gargadar rasani bai yi nadamar hakan ba sai ma ƙara tabbatar mun da yakeyi ya
sani ba zan iya rayuwa da waninsa ba.
Tsayin wata biyu da nayi tun barowata daga gidansa bai biyo ni ba ko a waya bai kirani ba sai yanzu haka
wani nasa bai zo ba duk sai bayan da iyayena suka ɗauki matakin da suke ganin shi zai kawo mun
maslaha a rayuwata.
Abu uku ne dama fargabata idan na rabu da shi, Soyayyata, makomar yarana sai kuma yanda mutane
zasu karɓe ni.
Soyayyar da nake masa batayi mun rana ba, bata amfana mun komai a zamantakewata da shi ba face
wahala, baƙin ciki, ƙasƙanci da zubewar mutunchi. Na bashi zuciyata, rayuwata da komai nawa. Na zaɓi
kasancewawa dashi sama da farin cikin dangina amma abin da ya mayar min da shi? Cin amana, ƙarya da
yaudara.
A yanzu na fahimci wata soyayyar ba rahama ba ce kamar dai soyayyata da Bilal azaba ce.
Da ace Bilal ya mutuntani ko da baya so na ya kare martabata ya kuma riƙeni amana ƙila ba zan taɓa
fahimtar komai ba Soyayyata zata cigaba da riƙe aurenmu har zuwa lokacin da ubangiji ya ɗiba mana
amma sai ya kasance mai butulci, a sanda ya gama cin moriyar ganga kamar yanda Anty Labiba da
Hansa'u sukayi nasarar haska mun gaskiyar abinda na rintse ido a baya naƙi yarda dashi. Ya mayar da ni
daddawar ɓurma, ya ɗana tarko dani. Ta yuwu ya samu iya abinda yake farauta shiyasa amfanina ya ƙare
a gurinsa ko kuma na gaza samar masa da abinda yake muradi shiyasa ya watsar dani.
Bana son tuna ƙazantar da kunnuwana suka jiye mun da wanda idanuwana suka gane mun yana
aikatawa shi da Jalilah, a yanzu dana tabbatar da ba ita ya aura ba, buri na na ƙarshe shine sanin da me
wacce ya aura ɗin ta fini? Ta ina na gaza? Me take da shi wanda ya ɗauki hankalinsa da ni bai samu a
tattare da ni ba? Ta yaya tayi nasarar cafkar soyayyarsa? Domin na tabbatar tunda ba Jalilah bace toh
wannan da yayiwa lakaɓi da DUNIYARSA ya aura ita ce kuma ya kaini gidansu a unguwarsu Anty Labiba.
Da hannu biyu na share hawayen da tunanin da na tafi mai zurfi yayi mun sanadin zubarsu, zan daina
kuka na sani amma ba yanzu ba domin ciwon da yake danƙare a zuciyata bai ko kama hanyar warkewa
ba balle na dena kukan zugi da raɗaɗin da yake mun.
Wayata dake aje saman kaina ta shiga ƙara, agogo na fara dubawa karfe tara da rabi lokacin, duk da
naga mai kiran Maman Yusuf ce maƙwafciyata amma sai na mayar da wayar na ajiye dan bani da
sukunin da zan iya amsata a lokacin na san kuma ba zai wuce zancen kwashe kaya zatayi mun ba tunda
Anty Labiba ta ce ta shiga gidan neman guduma dukda bata tarar da ita ba sai yara amma na san sun
bata labari.
Ganin tana ta kira ya saka na ɗaga ba'a son raina ba, murya can ƙasa na mata sallama ta amsa cikin
yanayin dayayi kama da wacce take cikin damuwa tace
Nayi murmushi na ce
"Wlh ko da aka ce mun an kwashe kaya ban kawo dagaske ba zaki dawo ba tunda nawa akayi irin hakan
kuma aka koma? Ga Amina (Ƙishiyarta da aka saka) itama cikin satin nan zata dawo kuma har kayan ta
kwashe. Sai da naji hayaniyar mata da guɗa kafin da Ummi ta dawo take ce mun wai amarya aka kawo
gidanki, wlh na ɗauka ko haya ya bayar sai da Abbansu ya ce wai ai dama yayi aure tuntuni tariyarce sai
yanzu. Kiyi haƙuri amma Baban Al'amin ɗan abu ta kazan uba ne" ta kora masa ashar.
Murmushin na sakeyi kamar tana gabana ban kuma iya sake ce mata komai ba har ta gaji da surutu ta
mun sallama akan zata samu lokaci tazo dukda tayi nauyi abinda ya saka ban ganta ba kenan ma tuntuni
amma sun so suzo biko. Bayan da mukayi sallama kamar in kashe wayar sai kuma na fasa na kunna Data
na shiga Whatsapp.
Cewar da tayi an saka amarya a gidan sai ya nemi ya hargitsa mun lissafi. Wato dama jira yakeyi a
kwashe kaya kenan ya saka amaryarsa? Lallai ta tabbata bana gaban Bilal yaudarar kaina kawai nakeyi
amma ya daɗe da kulle shafina.
Kenan da ya ce ba zai sakeni bama so yayi ya cigaba da azabtar dani ta hanyar barina da igiyoyin aurensa
ba wai saboda yana buƙatar mu sasanta bane. Status ɗin Fadila na lalubo dan idan har dagaske amaryar
Bilal ta tare na san ko kowa bai saka abinda ya shafi bikin ba ita zata saka ilai kuwa ina kunnowa naha
write up
'Allah ya sanya alkhairi bro' ga kuma sauran status nan da suka biyo baya hannu na rawa na shiga buɗe
su ina fatan in ga fuskar amarya cikin sa'a hoto na biyu kuwa na ci karo da ita, a falon Hajja aka ɗauketa
tana durƙushe tsakiyar waɗanda suka kawota amma fuskarta ta fito tar da yake da Iphone aka ɗauki
hoton.
Hutun wucin gadi na tafi ina kallon amaryar Bilal. Baƙa ce kuma mummuna domin ko da nima ba farar
bace amma akanta balarabiya ce ni ba kuma sai an gaya mun ba na san ta girmeni kuma tana da jiki
dukda dai da gani ƙibar tata ta sama da ƙasa ce ba duka jiki ba.
Ji nayi wani kaso na abinda nakeji ya yaye, ko da aka ce yabon kai jahilci amma dole in yabi kaina wlh na
mata zarra a ajiyeni a ajiyeta sai na fita yin kasuwa.
"A hakan kuma ta ƙwace miki miji" zuciya ta raya mun nayi fatali da tunanin a fili na ce
"Ba ƙwace ta mun ba, ya raina ni'imar da Allah yayi masa shiyasa aka haɗa shi da daidai halinsa yanzu".
Cigaba da kallon hotunan nayi sauran a can gidan a ɗakunana a da amma akayi su, sai na ringa jin kamar
ma na san fuskarta a wani guri, a hoto na ƙarshe naga Suwaiba, cousin sister Hansa'u ce ina ganinta
kuma na tabbatar da tabbas na san fuskar amaryar Bilal ɗin tareda Suwaibar na taɓa ganinsu kenan
amma me cece alaƙarsu? Itama yar uwarsu ce ko kuwa ƙawar Suwaibar ce kenan?
Ba yar uwarsu bace gaskiya domin da ƙila Hansa'u zata san ita ce ya aura ta yuwu dai ƙawarta ce. Haka
kawai na shiga zullumin son sanin alaƙar Suwaiba da Amaryar Bilal, har na kashe wayarna sake kunnawa
nayi screenshot ɗin hoton da Suwaibar ta fito na turawa Hansa'u.
*KURA A RUMBU*
*Wattpad @MaryamahMrsAm*
*Kuɗin karatu yana wakiltar mutum ɗaya ne, kiji tsoron Allah karki ɗauki hakkina ta hanyar fitar mun da
littafi*
*KURA A RUMBU littafin kuɗi ne, a biya naira 800, biya a asusun*
*7061838488*
*Opay*
*PAGE 53*
"Lallai su Bilal anyi Amarya, toh Allah ya zaunar lafiya" amsar da Hansa'u ta bani kenan duk kuma yanda
na so da naji ƙarin bayani bata sake cewa komai ba, Da na isheta da tambaya ma balbaleni tayi da faɗa
tana cewa
"Wai menene haɗin ki da matarsa ne Halima? Mutum ya rabu dake tuni ma shi ya manta ya taɓa rayuwa
da wata Halima har yana shirin fara rayuwa da wata amma ke ashe kina nan kina dakon wahala sai anyi
magana ki fara rantsuwar kin cireshi a ranki gashi kina bibiyarsa".
Tilas na bar maganar amma kuma na gaza hana zuciyata tunani da hasashen Bilal da amaryarsa a
wannan dare. Zuciyata ta ringa zafi, ina kwance lamo akan gado har sha biyu bacci ya gagara ɗaukata,
daren mu na farko na ringa tunawa, a hankali na saki kukan da nake ta ƙoƙarin dannewa na cusa kaina a
cikin pillow na shiga yin sa a hankali. Na daɗe ina kukan sai da naji sauƙin abinda ya tsaya mun a rai kafin
na tashi na ɗauro alwala na shiga yin Nafila har sai da bacci ya fara fizgata kafin na kwanta.
Washe gari da safe ina haɗawa su Amir abincin da zasu tafi Tahfiz da shi Anty Labiba ta shigo kitchen ɗin,
ganin tana kallona da wani murmushi na sha jinin jikina ilai kuwa sai ji nayi ta ce
"Ke ashe amaryar Bilal ta tare jiya". Nayi kamar ban jita ba, bata damu ba ta cigaba da cewa
"Sadiyar Shehu ce ta koma tana bawa su Nasiba labari wai sai suka ga gidan kamar kango ba kamar
sanda aka kai ki ba, a hakan ma wai an ce shi ya mata kayan ɗaki".
Ni dai ta tafasa sauke ban ce mata ba na cigaba da abinda nakeyi amma cewar da tayi wai Bilal ne yayiwa
Amaryarsa kayan ɗaki ya tsaya mun a rai. Bilal da yayi mun lefe a leda kuma a tsayin zamana dashi cokali
bai taɓa siyowa ko ya ɗauki kuɗi ya bani na siya ba shine yanzu yayiwa mace kayan ɗaki ɗungurungum?
Ko da yake ba abin mamaki bane tunda an ce shi ya siya musu gidan da suke zaune ma. Tambayar kaina
na shiga yi wane irin So yake yiwa yarinyar haka?
"Irin soyayyar da kike masa" na bawa kaina amsa. A fili can ƙasa na ce
"Ya Allah na roƙeka, yanda ka jarabceni akan mutumin nan shima ka ɗanɗana masa kwatankwacin
wahalar da na ci akan soyayyar sa"
"Iska na wahalar da mai kayan kara" Anty Labiba ta faɗa tana ficewa daga kitchen ɗin na rakata da
harara dan haushinta ne ya kamani. Ko menene manufarta na gaya mun ma oho? Haka nayi yinin ranar
sukuku gaba ɗaya tunani na yana can yanda take kasancewa da Bilal da sabuwar amaryarsa. Dagaske fa
ya gama da babina tunda gashi har ya samu madadina, ko da yake dama ko a sanda nake tareda shi ina
gurin ne kawai amma ni da babu duk ɗaya. Da naga ina nema na sake mayar da kaina ruwa bayan duk
alƙawarin dana ɗaukar wa kaina dole na yaƙi tunanin na kwaso Khaki na na shiga wankewa bayan ya
bushe na hau guga sannan na fitar da duk abinda zan buƙata dan washe gari litinan zan je nayi reporting
a PPA na.
BILAL
Sai bayan Azahar ya farka dalilin surutai da ya ringa ji a tsakiyar kansa. Ya tashi zaune yana matse fuska,
zazzaɓin daya kwanta dashi ya sauka amma kuma jikinsa sam babu ƙarfi ga hayaniyar data cika gidan
daya rasa ta mecece, tashi yayi a hankali ya fita falo, yayi turus a tsaye ganin mata sun bararraje kamar a
ɗakunansu suna cin abinci suna hayaniya sai kace masu cin kasuwa.
Wacce take saitin ƙofa ce ta ankara da tsayuwarsa tayiwa sauran alama duk suka juya suna kallon sa,
kallon sa kafin waɗanda daɗin hira ya saka suka cire kallabinsu suka shiga ɗauka suna yafawa. Shi dai
tsaye yayi yama rasa abinda zaiyi, yanzu ace duk girman falonta da ɗakuna biyu ga tsakar gida bai ishe su
suyi didimarsu ba sai sun dangana da ɗakinsa? Tukunna ma mai suka zo yi?
"Baby ka tashi ashe" Zulaiha data shigo falon da ƙaramar kula a hannunta ta faɗa tana masa murmushi.
Kallo ɗaya ya mata ya juya ciki haɗi da rufo ƙofa sai ta ajiye kular hannunta ta bi bayansa ɗaya daga cikin
ƙawayenta ta ce
"Amma Zully baki da M, dama yana ciki shine kika kawo mu nan gashi mun saki baki muna ta zuba har
Billy tana cewa zata shiga tayi kashi ashe Allah ya rufa mata asiri"
"Hirar me kukayi?"
"Ke labarin duniya ne kawai ba wani abu ba" wata mai kama da yan sholisho ta faɗa. Sai ta sauke
numfashi ba tareda ta sake cewa komai ba ta shiga ɗakin.
Ƙarar ruwan da taji yasa ta zauna tana jira ya fito, ya mata kallo ɗaya ya wuce gaban mirror bayan daya
fito daga ɗakin baƙin ciki goma da ashirin, shigen atamar jiya ce a jikinta, ashe ba leda bace kawai munin
da atamfar tayi a idonsa ne ya sa ya ganta kamar ledar. Tashi tayi ta matsa kusa dashi ta rungume shi ta
baya tana cewa
Ya tureta, bata haƙura ba ta ƙanƙameshi tana shinshinar jikinsa kamar wata mayya tana cewa
"Baby haba mana, kasan dai babu gurbin fushi a fuskar sabon ango"
Janyeta ta sakeyi bayan daya juya ya fuskanceta, so yake ya tuhumeta akan daren jiya. Ya zura mata ido,
tabbas shi shaida ne Zulaihar dake gabansa a yanzu ba Zulaihar daya sani a baya bace akwai sauye-sauye
da yawa a tattare da ita amma bai taɓa zaton bayan sababbin ɗabi'u da halaye da ya fuskanta a tareda
ita ba harda na mutunchi da tarbiyyar da ya santa da su tun usuli. Gefe ya ɗauke kansa kafin ya buɗe
baki ya fara magana sai dai a maimakon kalaman da suke kan harshensa sai yaji wani sautin daban, ya
ɓige da cewa
"Wane irin raini da wulaƙanci ne ya sa zaki kawo mun wasu banzaye ɗaki Zulaiha?"
Ta haɗe fuska ta ce
"Ba banzaye bane ƙawaye na ne, kuma walima suka zo mun can falo na ya cika kuma su ɗin ko cikin
ƙawayena na daban ne shiyasa na kawo su nan" ta bashi amsa tana kallon idonsa babu shakka balle
tsoro.
Duk sai ya zama confused, ba abinda yake so ya tambayeta ba kenan bai kuna san sanda ya canza
shawarar yin hakan ba amma kuma amsar data bashi a yanzun ta sake kashe shi da mamakinta har ya
rasa abinda zai sake ce mata. Daƙyar ya iya cewa
"Su fita, ba su kaɗai ba ki sallami duk wata mace da kika tara mun a cikin gida kar na fito na tarar da ko
mutum ɗaya idan ba haka ba" ya mata kallon data fahimci tsaf yana nufin zai yi rashin mutunchi ne.
Guri ta samu gefen gado ta zauna tayi ƙasa da kai kamar dagaske ta shiga cewa
"Tun daka shigo jiya kake ɓacin rai tamkar wanda zai shiga kabari, bama jiya ba, tun bayan da aka ɗaura
mana aure ka canza. Gaba ɗaya ka zama wani abu daban da yanda na sanka, duk tarin alƙawarurrukan
da ka yi mun na farinciki da kulawa idan na zama taka babu ɗaya daga ciki da naga yiwuwar faruwarsa
sai wulaƙanci da ƙasƙanci da kake nuna mun.
A daren farkonmu Bilal haka ka tsallakeni kayi tafiyarka falo ka kwanta baka damu da wane hali nake ciki
ba tunda ka rigada ka samu biyan buƙatar ka shikenan duk kuma nayi haƙuri na jure duk hakan bai yi
maka ba yanzu so kake yi ka tozarta ni a gaban ƙawaye na ka ƙarasa nuna musu cewar bani da mutunchi
ko daraja a gurinka ko?
Ni ba zan koresu ba amma kai ban hanaka ka fita ka koresu ba sai dai kafin nan ka fara sallamata dan ba
zan iya wannan rayuwar ba" ta ƙarasa tana fashewa da kukan da ya jishi har tsakiyar ransa. Bai san sanda
ya durƙusa gabanta ba dukda ya kasa ce mata komai ita kuwa kamar wacce ya saka bulala yana duka
haka ta ringa kuka irin me shassheƙar nan tana nanata sai ya saketa tunda dama ya aureta ne dan ya
wulaƙantata ba sonta yakeyi ba.
"Mai yasa kika ɓoye mun kin rasa budurcinki a waje?" Ya tattaro duka ƙarfin guiwarsa ya amayar da
abinda yake cikinsa. Lokaci ɗaya kukanta ya tsaya ta ɗaga kai da sauri ta kalle shi da firgicin da ta kasa
ɓoyewa kafin kuma ta sauke kai kamar munafuka ta sake fashewa da kukan daya fi na farko tausayi da
narka zuciya. Cikin kukan muryarta na rarrabewa ta ce
"Ban sani ba"
"Kamar ya baki sani ba?" Ya faɗa cikin fushi sai dai kuma sautin muryarsa a ƙasa. Ta kife kai jikin gado
tana cigaba da kukan da wanda bai san dawar garin ba dole ya tausaya mata kafin ta ce
"Ina shekaru bakwai a duniya wata rana Ummanmu ta aike ni da daddare siyo maganin sauro ruwa ya
sakko na fake a wata rumfa, ban san wanene ba ban kuma san mai ya faru da ni ba amma Umma ta ce
sai da akayi nemana na kwana uku kafin aka sameni a Asibiti kuma ma'aikatan Asibitin sun ce wata mata
ce ta kaini tace musu tsintata tayi suka ce ba zasu karɓe ni ba sai ta zo da yan sanda shine ta ajiyeni tace
zataje ta dawo daga nan basu sake ganinta ba kuma basu san daga wace unguwa ta kawoni ba balle a
bayar da cigiya. A dalilin haka har lalurar yoyon fitsari na gamu da ita daƙyar da taimakon Allah na samu
lafiya" ta sake rushewa da kuka.
Bilal da jikinsa yayi laƙwas yayi shiru yana kallonta tausayinta mai tsanani ya shiga ratsashi. Har ransa yaji
ya yarda da abinda ta ce ya faru da ita, ya ɗagota jikinsa yana cewa
"Umma ce tace ba sai na faɗa maka ba, wai abun ya daɗe kuma ina yarinya lokacin"
"Shikenan, amma ya kamata muje asibiti gaskiya a dubaki dan.." sai kuma yayi shiru, ta ce
"Saboda me?"
"Bana tunanin an dubaki da kyau a wancan lokacin ta yuwu kina buƙatar ɗinki" ya ƙarasa a hankali.
Kusan minti goma ya ɓige da rarrashinta dukda har ransa yaji ya gamsu da maganarta amma kuma
ƙuncin da yake ji a zuciyarsa bai ragu ba dannewa kawai yakeyi yana rarrashinta. Ganin tana nema ta
canza musu akala daga rarrashi ya saka ya tureta yana ɓata fuska. Bata ja ba itama ta kama kanta ta bar
masa ɗakin babu kowa a falon dan suna shigewa ɗakin suka tattara suka koma can falonta.
"Kinga abinda na faɗa miki ko? Sai da nace kiyi ɗinki kika ce ba haka ba, anyi ɗinkin ma ya Allah ya cika
wanda ma basu taɓa aure na suke ganewa balle shi toh yanzu mai kika ce masa?" Suwaiba ta faɗa taba
zare ido bayan da suka shige banɗaki Zulaihan ta faɗa mata yanda sukayi da Bilal.
Sai da ta yarfe gumin da ya tsattsafo mata kafin ta labarta mata ƙaryar data shirya masa, Suby ta buɗe
ido da mamaki ta ce
"Kuma ya yarda?"
"Hmmm ya yarda mana, wlh ni kaina nayi mamaki yanda ba jeka ka dawo lokaci ɗaya ya sakko bakiga
yanda tausayina ya rufe shi ba" cewar Zulaiha. Suby ta zauna kan WC tana cewa
"Ke wlh ya yarda, in sa bai yarda ba na sani ba zaiyi shiru ba sai ya sake cewa wani abun ko kai tsaye ya
ce ƙarya nakeyi. Yanzu dai ya ce zamuje Asibiti ayi mun ɗinki shine ma naji tsoro kar na je ko setup zai yi
mun su tona mun asiri" Zulaiha ta faɗa muryarta da fuskarta suna nuna damuwa. Suwaiba ta ce
"Sai ta yuwu, amma ai ba zaki bari haka ta faru ba idanma niyyarsa kenan. Yanda kikayi wasa da
hankalinsa a farko haka zaki ƙarasa wasan, ke zaki faɗi Asibitin da zakuje ko ma kawai ki kira Nurse Binta
tazo gida ta miki baki alaikum idan ya nuna ba haka ba kice masa idan kukaje Asibiti ai zai zama kamar
tonon asirinku in ma kuma Asibitin dai za'aje ba za'ayi a gidan ba to kuje in da take aiki asirinki a rufe
babu wanda zai ji bare ya gani".
"Shiyasa nake sonki ƙawata haka za'ayi" Zully ta faɗa tana bata hannu suka tafa Suby ta ce
"Toh sai ki kama kanki ki kuma dakata karki sake shafa masa maƙale mata in ba haka ba wlh ya harbo
jirginki da wuri"
Su Suby ne Zahra kaɗai sukayi saura sai da suka tayata suka gyara gidan tsaf kafin suma suka mata
sallama suka wuce lokacin Bilal ya fito zai tafi sallar la'asar suka gaisa har sannan dai fuska ba yabo ba
fallasa ya ce mata zai je gidan Hajja daga can wannan ya sa su Suby suka fasa tafiya suka zauna ƙulla
yanda za'ayi kar bomb ya tashi.
"Amma fa ko wannw Malami ya miki aiki wlh ya iya Zully bai ci miki kuɗi a banza ba" Zahra ta faɗa.
Zulaiha tayi murmushi ta ce
"Haba Hajiya, a wannan karon dai ƙarya kike wlh rufe masa baki kikayi" Zahran ta sake faɗa Zulaiha ta
rantse tana cewa
"Har Umma haka take cewa wai da asiri na samu Bilal kuma wlh tallahi ke ni ko a sallah bana addu'a a
akansa kawai ikon Allah ne".
BILAL
Yana dab da gidan Hajja wayarsa da sai a lokacin ya kunnata tun daren jiya ta shiga ringing, ya cirota ya
duba ganin Hafiz ke kira ya saka ya gangare gefen hanya ya ɗaga dan dama so yakeyi idan ya fito daga
gidan Hajjan ya wuce gurinsa su ƙarasa zancen shaguna da suka fara.
"Dama maganar takardun gurin can ne, na bawa Barrister ya duba ya ce ba original bane, idan original
ɗin suna kusa ka kai masa please sai ka turawa da Turad account ɗin da za'a saka kuɗin idan kuma a
wanda yake da shi ne sai ka kirashi a waya ka gaya masa kawai".
Mamaki ne ya rufe shi jin abinda Hafiz ɗin ya faɗa, takardu ba Original bane kuma kamar yaya? Cikin
duburburcewa ya ce
"Ka dai san in dai aiki ne Barrister Umar ya san aikinsa, so tunda ya ce papers ɗin nan ba original bane na
yarda, amma idan kana da ja akan hakan kaje ka same shi idan ya so sai kuje tare gurin waɗanda ka siya
idan ma kuskurensu ne duk za'a gane" Hafiz ya sake faɗa daga nan kuma ya masa sallama.
Ajiye wayar Bilal yayi y dafe stirring zufar tashin hankali na keto masa. Ya ma za'ayi ace takardun shago
ba original bane bayan da shi akayi komai akayi sealing deal, shi ya biya kuɗin kuma a hannunsa ya karɓe
su ko Jalilar gani kawai tayi amma daga na gidan har waɗannan ɗin a hannunsa suke bata taɓa riƙe su
ba.
Wayar ya ɗauka ya shiga kiran Kamalu wanda ya musu hanyar shagunan cikin rashin sa'a aka ce wayarsa
a kashe. Fasa zuwa gidan Hajjan da yayi niyya yayi ya juya ya tafi gurin Barrister Umar, yayi shiru yana
kallon takardun daya baje masa, nasa da wasu yana nuna masa banbancin original takardu da kuma nasa
da ya ce forging ɗin su akayi.
"Shiyasa ake cewa idan zakuyi cinikayya ku ringa saka expert da suka san kan abun amma saboda ɗan
kuɗin da zaku biya sai ku gwammace kuyi daga ku sai dillalai bayan dillalan nan wasu marasa tsoron
Allahn property ɗaya sai su siyarwa sama da mutum biyar sai dai wanda yafi ƙarfi ƙarshe yayi nasara
akai. Yanzu dai gaskiya waɗannan takardun naka da su da takardar tsire basu da banbanci tun wuri kuma
kayi abinda ya kamata kafin su sake siyarwa da wani su bashi takaddun gaske" Barrister Umar ya faɗa.
Da wannan sabuwar damuwar Bilal ya koma gida dan gaba ɗaya ya rasa mai ya kamata yayi gashi wayar
Kamalu a kashe ya kuma je har inda yake zama an ce baya nan wai yayi tafiya kuma basu san lokacin da
zai dawo ba.
Gida ya wuce ya birkice takardunsa ya fito da na gidan daya siya bayan ya siyar da asalin gidan Jalilah.
Zama yayi ya duba takaddun tsaf yana tuna abubuwan da Barrister ya nuna masa da suke nuna
banbancin original da fake takaddun, ya sauke ajiyar zuciya mai ƙarfi bayan daya tabbatar na hannun
nasa original ne. Tunani ya shiga yi to na gidan daya siyar fa? Suma fake ɗin aka basu ko kuwa na gaske
ne? Sai kuma ya taɓe baki a fili ya ce
"Oho koma wannene can su ta shafa tunda ni dai na rabu dasu" wannan ya ɗan samar masa da nutsuwa
har ya shiga gurin Zulaiha da yana shigowa ta taho tana masa oyoyo amma ko kallonta bai yi ba ya wuce
ɗakinsa bata yi zuciya ba kuma ta bishi ta ajiye masa ruwa da lemo mai sanyi dama ya tarar da kwanukan
abinci amma ba ta su yake ba sai da nutsuwar sa ta dawo kafin ma ya tuna da yana jin yunwa.
Washe gari kuwa kamar yanda ya ce da safe ya ce ta shirya suje Asibiti dan daren jiya duk yanda ta so ta
kama kanta yanda Suby ta ce kasawa tayi amma da yake batayi amfani da turaren kan tace ba shiyasa
har ya samu damar tureta wai ya gaji bacci yake so yayi. Abun ya mata ciwo ƙwarai amma ta danne tara
shi zatayi zata rama komai sala sala da zarar komai ya sake hawar mata saiti. Tayi dana sanin ƙin jin ta
Suby da tun farko tace tayi ɗinkin ciki da wajen a ganinta iya gyara da kayan matsin da tayi amfani dasu
sun isa amma gashi an samu akasi.
Marairaicewa tayi ta tsarashi akan idan sukaje Asibiti ai tonon silili zai yi mata. Ta ce zata kira Binta
wacce ta ce masa Yayar Suby ce tazo gida kawai ta mata amma ya ce Aa, daga ƙarshe dai sukaje Asibitin
da Bintan take aiki dama kuma tun jiya sun sanar mata dan haka dama a shirye take ko ta kirata taje
gidan ku suje Asibitin su sameta tayi mata ɗinkin tace mata
"Wannan uban buɗewa ke kuwa Zully kamar wacce ta haifi yaya goma? Gaskiya kinyi ganganci ki kuma
godewa Allah dan mutumin nan yana sonki in da wani tun jiyan sai dai ki ƙarasa daren a gidanku wlh".
*KURA A RUMBU*
*Wattpad @MaryamahMrsAm*
*Kuɗin karatu yana wakiltar mutum ɗaya ne, kiji tsoron Allah karki ɗauki hakkina ta hanyar fitar mun da
littafi*
*KURA A RUMBU littafin kuɗi ne, a biya naira 800, biya a asusun*
*7061838488*
*Opay*
*PAGE 54*
Jinyar stitches ɗin Zulaiha ta saka Bilal baya fita ko ina idan ba masallaci ba, duk ayyukan gidan shi
yakeyi, sannan ya kula da ita a ɗan taƙin lokacin kuma ya ɗan fara samun nutsuwa daga tsoron sababbin
halayen da ya ringa gani a gurinta tun bayan da aka ɗaura musu aure. Ranar data kwana uku ƙanwar
Ummansu Anty Habi taje gidan ta kai mata gamje gamjen magunguna da ta ce na Aljanun da suke
shafarta ne. Shi ya ringa jigilar dafa mata na wanka safe yamma kuma ya hura mata coal tayi turare,
maganin na sati ɗaya ne ranar data cika satin tana yi kuwa Aljanun suka tashi.
Lokacin ya fita siyo kayan miya ya dawo ya tarar da ita su Suby sun daddanneta tana wasu abubuwa suka
ce masa wai a haka suka tarar da ita suma. Dukda dai yayi mamakin ta inda suka shiga gidan tunda ya
rufe daya fita ita kuma sun ce sun sameta ta hau iskoki to waya buɗe musu ƙofar?
Haka ya fita can masallaci ya samo wanda zaiyi mata ruƙiyya, suka ringa kafa masa Sharuɗan kar a ringa
ɓata mata rai, kar ayi mata faɗa da sauransu in ba haka ba zasu dawo daga haka dai suka fice sai kuma
suka riƙe mata ƙafa, sati biyu taci tana jinya kafin ta ware gaba ɗaya suka durfafi sabuwar rayuwar
amarci tunda ɗinki ma ya warke, duk yanda take ƙoƙarin dannewa kar tayi abinda zai sake jefa zargin
wani abu a zuciyar Bilal ɗin ta kasa.
Ranar da suka sake gamuwa dukda shi ya fara nuna buƙatar abun amma tun kafin ayi nisa taga ya canza,
karsashin daya fara da shi ya sakeshi sai ƙananan tsaki da ya ringa saki, bata damu ba ta cigaba da
shafashi a ƙoƙarin mayar dashi kan network amma sai kawai ya tureta lokacin da wayar sa tayi ƙara.
Abun ya mata ciwo matuƙa, tana sauraron wayar da yakeyi data gane da Hajja ne kuma masifa take
masa dan sai bata haƙuri yakeyi kafin ya kashe bayan ya ce mata gashi nan zai zo gidan yanzu da yake da
yamma ne.
Tayi ƙwafa ta bishi da harara sanda ya shiga banɗaki, sai kuma ta tashi da sauri ta ɗakko Humrar
kiranyenta ta shafa sannan ta ɗebi maƙale mata a hannunta ta koma ta zauna tana murmushin
mugunta, Tunda ba zaiyi dan Allah ba toh kuwa zai yi dan dole.
Bilal kuwa daya shiga banɗakin sakin ruwa yayi akansa dukda garin da sanyi sanyi amma bai damu ba,
duk da ya san gaskiyar abinda ya sameta amma kuma zuciyarsa ta kasa karɓar abun har yanzu. Yana son
Zulaiha tamkar rai, amma da zarar ya tuna cewar bai sameta a Mace ba sai yaji duniya ta masa zafi, duk
sanda buƙatuwar ta ta motsa masa kuma da zarar ya tuna abun sai ya ji komai ya mutu kamar dai
yanzun a matse yake ya kuma yi ƙoƙari ya kawar da tunanin amma suna farawa abun ya zo masa take
yaji komai ya mutu duk yanda ya so daya daure ko dan ganin kamar itama tana so ɗin amma ya kasa.
Wani tunanin ne ya sake gifta masa wai me yasa ita bata tsoronsa?
Kashe shower yayi ya zauna akan toilet yayi shiru kamar mai jira wani ya bashi amsar. Ya tafi tunanin
farkon aurensu da Halima daƙyar sai ya matsa take iya kallonsa babu riga amma ita wannan haka take
ƙure shi da ido kamar mayya har lashe baki takeyi idan da ya biye mata ma da tuni tun kafin ɗinkin nata
ya warke ma zata bashi kanta kwata kwata babu kunya ko jin nauyinsa a tareda ita ko da kuwa tayi
ƙoƙarin nuna hakan bai san mai yasa yake ganin kamar na ƙarya ne ba.
Ji yayi kansa na nema ya fara ciwo dole ya kore tunanin ya miƙe ya shiga wanka, sanda ya fito tana
kwance akan Gadon amma ya san ba bacci takeyi ba tunda bai ji munshari ba, ya wuce gaban mirror zai
ɗauki wayarsa ya bar mata ɗakin hancinsa ya fara shaƙo masa wani ƙamshi, kansa ya sara, kamar wanda
aka ja da igiya haka ya tafi kamar kuma waccen ranar yau ɗin ma haka ya ringa aiki tun yana na jin daɗi
har ya koma na wahala sai gashi yana kuka wiwi duk kuma yanda ya so ya bari abu ya gagara sai da ita da
kanta ta gaji kafin ta yakiceshi daƙyar ta gudu banɗaki ta kulle ƙofa.
Bilal kuwa kwanciya yayi riƙe da ciki yana juyi cikin azaba, ya gaji amma kuma so yake yayi abun, daƙyar
ya lallaɓa ya fice daga ɗakin ya koma nasa ya shiga wanka, sai da yayi kusan saɓi uku har cikin hancinsa
ya wanke kafin ya daina jin ƙamshin turaren a hankali kuma nutsuwa ta fara saukar masa ya fita ya
kwanta akan gado yana sauke ajiyar zuciya a jere. Gaskiya ba haka kawai ba akwai wani abu dan shi dai a
rayuwarsa bai taɓa gamuwa da irin wannan bala'in ba. Sai gurin ƙarfe tara ya iya tashi yayi sallar magriba
da Isha'i, yana zaune ya jiyo tana ƙwanƙwasa masa ƙofa haɗi da kiran sunansa kamar na zai tashi ba sai
kuma ya miƙe yana rangaji yaje ya buɗe mata.
Sum sum ta wuce ta ajiye try ɗin data shiryo masa kayan abinci akai, ba tareda ta kalle shi ba ta miƙa
masa wayarsa tana cewa
"Tun ɗazu ake kira" ya karɓa yana kallonta sai kuma ya ji tausayinta yana ratsashi babu dalili. Abincin
data zuba masa ya jata jikinsa suka shiga ci, jollop ɗin shinkafa taji nama ga kuma peppered chicken
daban a gefe da salad sai lemon exotic babban kwali mai sanyi sosai. Sai da ya kai geji kafin ya shiga
tantance abincin. Ɗanɗanon da ƙamshi harda yanda aka shirya abincin ma bai yi kama da girkinta ba.
Zulaiha bata iya girki ba bai kuma yi mamakin hakan ba domin ya fi kowa sanin daga gidan daya ɗakkota,
yayi gyaran murya ya ce
"Ai nasan bamu da ingredients ɗin da zakiyi irin wannan girkin, ya kamata ma a samo fridge gaskiya
saboda ajiyar nama da kayan miya na gaji da siyan guntu guntun nan" daga haka ya ɗauki wayarsa ya
shiga duba missed calls ita kuma ta kwashe kwanuka ta fita da su ranta ƙal.
Kiran Kamalu ya fara bi dukda yaga missed calls ɗin Hajja kusan guda goma, basu wani ja gaisuwa mai
tsayi ba Kamalu ya ce masa
"Eh wlh kuma nayi ta kiran layinka kullum a kashe, dama maganar shagunan nan ce na bawa lawyer na
takardun ya duba amma ya ce fake ne" Bilal ya bashi amsa.
"Haka ya ce, nima nayi mamaki amma kuma dana haɗa su da wasu takardu na ga banbancin da ya ce
akwai tsakaninsu da original ɗin".
"Gaskiya toh bansan a inda aka samu matsala ba dan kai shaida ne takardun nan hannu da hannu yanda
aka bani su take na miƙa maka ban ko tafi dasu wani guri ba balle ace ni na canza su" Kamalu ya faɗa.
"Ai ba ina zarginka bane Alhaji Kamalu nima abun ya bani mamaki ne kaga kenan daga can gurinsu da
suka siyar mana sune macutan, sun karɓi kuɗin mu ƙila zasu sake siyarwa da wasu kuma"
"Gaskiya a sanin da nayiwa Alhaji Balarabe ba zai taɓa yin haka ba, na fi shekara goma sha biyar muna
harkar ƙasa da shi ba'a taɓa samun saɓani ba, amma abinda zai faru gobe idan Allah ya kaimu kazo office
ka sameni sai muje gurinsa duk ma abinda ya faru sai a warware" Kamalu ya sake faɗa daga haka sukayi
sallama.
Dukd dare ya farayi haka ya tafi gidan Hajja tareda Zulaiha, sai da ya tsaya a hanya yayi mata siyayyar
toshiyar baki kafin suka isa gidan. Fadila na falo tana kallo ita da Abubakar shi kuma yana cin abinci suka
shiga, ta gaishe shi ba tareda ta ko kalli Zulaihan ba Abubakar dai tamkar bai ji shigarsu ba sai da Bilal ɗin
yayi masa magana kafin ya ɗaga kai tareda yi masa sannu a taƙaice ya cigaba da cin abincin sa.
Ɗaki ya wuce da Fadila ta ce masa Hajjan ta kwanta, ya zauna daga gefen ƙafarta yana gaisheta dan ba
bacci takeyi ba kafin ta miƙe zaune fuska ba yabo ba fallasa ta ce
"Kotu suka ce zasu kai ni Hajja ni kuma naji tsoro kar su fitar da waccen maganar shiyasa kawai na
saketa".
"Ai shikenan, yanzu yaushe zaka karɓo yaran toh?" Hajja ta sake faɗa. Da sauri ya kalleta ya ce
"Au, ni kake zaton zan riƙe maka yaran ma kenan? Ita waccen ɗin daka auro menene amfanin ta? Da
zuwa kawai tayi ta samu guri taci arziƙi kenan ko me?"
"Ka saurareni da kyau dole ka karɓo yaran nan saboda ta hakane zaka ƙuntata mata da ita da iyayen nata
kuma zamu samu damar jansu a ƙasa yanda muke so a dalilin yaran sannan itama wannan yar
matsiyatan daka ɗakko ba zaman banza zatayi ba dole tayi maka wahalar yaya".
"Yayi tafiya ne kusan wata uku baya ƙasar" ya shata mata ƙarya, ta taɓe baki ta ce
"Yanzu saboda mugunta da hassada ƙiri ƙiri kaƙi kayi masa maganar Fadila ko? Tunda kai kayi mana
baƙin ciki Allah ya kawo mana mai taimakonmu har gida amma ka kwaɓar da damar shine itama kake
mata baƙin ciki karta samu in da zata huta har muma mu mora"
"Amma Hajja na gaya miki maganar nan ba mai yuwuwa ba ce ba, mutumin nan da matarsa yana sonta
bai taɓa kallon Fadila a matsayin wacce zai iya so ba kina gani saboda rashin hankalinta ta ringa shige
masa har sai da ya fahimci abinda take nufi in da yana ra'ayi ai da zai amsa amma daga haka mai ta
janyo? Janye jikinsa yayi ya daina zuwa gidan nan kuma shine kike so ni na tallata masa ita gaskiya ba zan
iya ba" ya bata amsa ba tareda ya kalleta ba.
Tayi ƙwafa ta ce
"Ai shikenan nan"
"Kiyi haƙuri idan na ɓata miki rai Hajja" ya sake faɗa cikin sigar rarrashi,
"Yanzu ita yaushe zata dawo ayi maganar auren?" Ta sake soko masa wata maganar, ya fahimci wa take
nufi amma ya waske da tambayar wacece
"Ita shaiɗaniyar yarinyar nan mana" ta bashi amsa a fusace. Ya marairaice fuska ya ce
"Yanzu Hajja ko ni na dage zan aureta dan Allah sai ki barni nayi?"
"Akan mai zan hanaka? Dama ai abinda ya kamata kenan ko kuwa kana nufin taci banza ta lalataka
sannan taƙi aurenka? Toh wlh ba zai yuwu ba" ta bashi amsa. Ya buɗe baki zai sake magana wayarsa ta
shiga ƙara dan haka ya dakata ya zarota gabansa ya yanke ya faɗi ganin international number ko ba'a
faɗa ba kuma ya san Jalilah ce.
Ji yayi zufa ta fara keto masa ya danna wayar a silent ya mayar da ita Aljihu ya miƙe yana kallon Hajja ya
ce
A falo Zulaiha kaɗai ya tarar tana ganinsa kuwa ta miƙe yayi gaba ta bi bayansa. Sai da suka zauna a mota
kafin ta ce masa tana so taci Shawarma ta faɗa masa kuma ta inda take so. Ya kalleta da mamaki jin inda
ta faɗo ɗin, kallon daya mata ya saka ta gane ta kwafsa dan haka tayi saurin cewa
"Saurayin Zahra ne yake siyo mata ya kai mata School, na taɓa ci sau biyu tayi mun daɗi sosai shiyasa na
riƙe sunan gurin". Bai amsa mata ba suka tafi, tana ta sako masa hira dan ta kawar masa da tunani amma
da Eh ko Uhm yake amsa mata kawai. ATM ɗin sa ya bata ya ce taje tayi order dukda yanda gurin yake
cike da Maza amma yana buƙatar space ɗin ne saboda number ɗazu da ake ta sake kiransa da ita. Tana
fita kuwa kiran ya sake shigowa, saida ya kashe motar kafin ya ɗaga murya can ƙasa kamar mai bacci yayi
sallama.
Muryar Jalilah ta sauka raɗau a kunnensa
"Yau dai Allah yayi na sameka a waya" ta faɗa, ya sake narke murya ya ce
"Nayi kewarki Babe, mai nayi miki? Kin toshe duk wata hanya da zan iya samunki phone call, Whatsapp,
IG duk kinyi blocking ɗina what have i done to deserve such punishment Jalilah?"
"Saɓo kikeyi kema kin san hakan ba zai taɓa zama gaskiya ba ya za'ayi nayi blocking ɗin ki?"
"Ai shikenan dai, kwana biyu? Nayi missing ɗin ka sosai" ta rage murya ta faɗa. Ya gyara zama yana cewa
"Ya kamata ace jiya zan dawo sai kuma na wuce gurin Mom bata jin daɗi" ta bashi amsa
"Subhanallah, mai ya sameta? Amma da sauƙi ko?" Ya faɗa a cikin rikicewar ƙarya ta amsa masa
"Da sauƙi, kaya fa har sun kamo hanya kuma ba zasu daɗe ba dan ƙila ma su rigani isowa dan haka ka
saka a gyara gurin da kace zamu mayar dashi store kafin na dawo a fara loading kamfani, sai kaga
kayayyakin da muka samu abubuwa da yawa ma basu tura mana ba sai da nazo na gansu na so tare
muka zo kaima na san da ka sake ganin wasu abubuwan da zamu iya ƙarawa da su".
"Menene pin ɗin?" Ya danne speaker wayar kafin ya gaya mata ta koma Jalilah ta ce
"Eh ta dawo" ya sake bata amsa. Zancen kaya ta cigaba dayi masa yana sauraronta yana kuma kallon
hanya dan kar Zulaiha ta taho bai lura ba kusan minti goma kafin ya cewa Jalilan zai kirata idan sun isa
gida ya ajiye wayar ganin Zulaihan tareda wani ya ruƙo mata ledar abinda ta siya. Kallonsu ya ringayi, da
farko ɗauka yayi ko yaron shagon ne sai da suka matso yaga Normal kaya ne a jikinsa ba rigar ma'aikata
ba kuma magana yakeyi mata dukda fuskarta bata nuna sauraronsa takeyi ba amma yanda suka jero
kamar ma jikinsa na gugar nata ya harzuƙa shi bai san sanda ya buɗe motar ya fita ba dai dai lokacin da
suka ƙarasa ta nuna Bilal ɗin tana cewa
"Ga Mijina nan tunda na faɗa maka baka yarda ba shi sai yayi maka bayani" ta fizge ledar ta shige mota
ta barsu a tsaye. Haƙuri mutumin ya shiga bashi kafin ya juya da sauri ya bar gurin shi kuma ya koma
motar cikin fushi ya ce mata
"Ni a yaushe na kula shi? Kuma idan da mun fita tare da kai ai babu wanda ya isa yayi mun magana
amma kayi zamanka a mota ka turani tsakiyar maza saboda baka kishina" ta ƙarasa idonta na kawo
hawaye. Tsaki yayi ya tayar da motar har suka isa gida bai ce mata komai ba.
Part ɗin sa ya wuce yana fita itama ta sakawa falon muƙulli ta fitar da Shawarmarta da Smoothie ta shiga
ci bayan ta kunna kallo, wayarta tayi kara, tayi murmushi ganin mai kiran ta ɗaga. Mutumin da suka
haɗu ɗazu ne, ba tayi niyyar kulashi ba dan daya mata magana kai tsaye tace masa ita matar aure ce
amma bai yarda ba da zata biya kuɗin siyayyar da tayi ya ce ta barshi taƙi shine ya zuba mata cash ɗin da
sai da tazo gida yanzu taga dubu ɗari biyu ce a ledar. Ta san ba zai wuce a gurin Teejay ɗaya daga cikin
yaran gurin ya samu number, Ahlan da ta gani a true caller kuma ya saka ta gane shi ne dan sunan da
yake kan complement card ɗin daya haɗa mata da shi kenan.
Ba tsoro ko fargabar komai ta shiga yin wayarta kamar yanda ya ce aurenta ba matsalar sa bace in dai ta
yarda su ƙulla alaƙa. Har sha biyu da wani abu kafin sukayi sallama ta wuce ta kwanta ba tareda ta bi ta
kan Bilal ba wanda yake can shima yana sheƙe ayarsa da Jalilah dan daga waya ta fara hillatarsa da
abinda yayi rantsuwar ba zai sake ba ya tuba sai gashi bai san sanda yayi unblocking nata a Whatsapp ba
da kansa kuma ya kirata Video call sukayi abinda bayan sun gama kuma yayi bacci dan sai lokacin yaji ya
samu nutsuwa. Duk daɗewar da yayi da Zulaiha wuya kawai ya ci amma yanzu a ɗan lokaci ya samu
nutsuwar da ya daɗe bai sameta ba.
Tunani ya ringayi ko dai ta Hajjan ya yarda ya auri Jalilah ne? Aurensa da ita riba biyu ne, ga kuɗi ga
kuma jin daɗi domin ita ɗin ta san ta kan duniya amma kuma kishi ba zai taɓa bari ya zauna lafiya da ita
ba dan zuciyarsa ba zata samu nutsuwa ba zai yi ta zargi da hasashen tana kula wasu a bayan idonsa
wannan ya saka ko yaji zuciyarsa na son kwaɗaita masa auren Jalilah da abinda zai samu a silar hakan zai
kore tunanin domin dai bariki ta haɗa su a nan kuma zasu rabu.
Washe gari kamar yanda sukayi da Kamalu yaje ya same shi sun tafi gurin Alhaji Balarabe mamallakin
plazar da Jalilah ta siyi shagunan. Alhajin ya karɓi takaddun take kuma ya kira Lawyer da wanda aka ci
sa'a yana ta gurin dan haka ba'a wani ɗauki lokaci ba ya je ya same su.
"Gaskiya waɗannan takardun ba namu bane" Lawyer ya faɗa bayan daya gama dubasu. Alhaji ya tashi ya
ɗakko wata folder ya ringa fitar da original takardu na sauran shagunan da ba'a siyar ba yana miƙewa
Bilal da Kamalu suna dubawa, ya kwashe su ya mayar sannan ya ɗakko photocopy ya ware su ya cire
masa na ainihin shagonsu ya bashi yana cewa
"Kaga photocopy ɗin original ɗin da muka baka nan" ba wani dogon bincike Bilal da kansa ya gane
banbanci ƙarara na takardun hannunsa da photocopy waɗanda akace sune wanda aka bashi. Duk kansa
sai ya ƙulle, ya kuma tuna tabbas irin waɗancan aka bashi domin bai manta stamp ɗin su da yake a kai ba
wanda sai yanzu ya lura babu shi a na hannun nasa.
Alhaji Balarabe ya ce ya tafi da photocopy ɗin sannan a shirye suke domin su taimaka masa t duk inda
zasu iya idan buƙatar hakan ta taso.
"Kayi tunani ko takardun sun shiga hannun wani bayan kai kar ka ce cire kowa walau ya uwa ko Amini
muddin sun je hannunsa toh abin zargi ne domin babu yanda za'ayi a tashi rana ɗaya ace takaddu sun
canza daga yanda suke zuwa wani abu na daban dole wani ne ya canza su" cewar Lawyer Alhaji
Balarabe.
Haka ya bar gurin cikin damuwa duk kuma yanda zaiyi ya gano abinda ya faru ya kasa, to wa ma zai zarga
bayan daga shi sai Jalilah da waɗanda suka siya a hannunsu ne kaɗai suka san da maganar ita kuma a
hoto kawai ya tura mata su bata gansu a zahiri ba. Haka yayi ta kame kame daga ƙarshe ya watsar ya
kama sabgoginsa tunda lissafin sa na farko ya wargatse ya sake dawo da Jalilar rayuwarsa sai dai ya jira
kuma ya sake shiri.
HALIMA
Na fara Bautar ƙasa na gadan-gadan, wani Private Research Center aka kai ni, mai gurin Abokin Uncle
Mudassir ne na sha mamakin lokacin da naje gurin dan ban taɓa sanin wanzuwarsa a Kano ba. Guri ne
mai ɗauke da Laboratories babu adadi ga kayayyakin aiki yyanda kasan a irin fina finan Turawan nan na
Scientist haka da yawan ma'aikatan gurin duk fararen fata ne kaɗan ne baƙaƙe iri na.
Fara aiki na ya sa na yarda dagaske da aka ce zaman banza ne yake kashe zuciya har mutum yayi ta
tunane-tunanen banza da wofi mai abunyi sau tari ya kan manta da duk wata matsala idan ba wacce ta
shafi aiki ko sana'arsa ba. Toh nima hakan ce ta kasance dani domin ban rufa sati ba na fara ɗaukar saiti,
na tattara duk wata damuwa na watsar na kama aiki na domin gani nayi tamkar ban taɓa zama a aji ba
komai sai ya zamar mun baƙo a lab ɗin da aka kaini, da yake kuma har raina a shirye nake da na mayar
da hankali na koyi abin sosai sai na ware duk wani test da akayi idan na koma gida zan zauna nayi
Reserch a waya har sai na samu cikakkiyar fahimta akan abun, na ƙulla abota da ChatGPT, duk abinda ya
shige mun dubu shi zan tambaya ya warware mun musamman da na gano yana jin hausa shikenan na
samu abinyi ko Whatsapp sai in wuni na kwana ban leƙa ba ina can ina kwasar romon ilimi har na fara
hasaso kaina na koma makaranta nan da wani ɗan lokaci nima na zama babbar Scientist tamkar
mamallakin gurinmu dukda a hoto kawai na taɓa ganinsa sai dai ya burgeni, matashi don bai kai
shekarun Uncle Mudassir ɗin ba ma idan kuma ba hoton ne ya mayar dashi yaro ba amma har mamakin
irin abubuwan da yayi nayi wanda suke rubuce cikin tarihinsa da akayi bango guda a cikin reception ɗin
gurin.
A cikin satin daya mutu na kammala iddar Bilal, mun rabu kenan ko in ce na cire duk wani sauran fata da
nake dashi akan al'amura zasu iya canzawa ko da ace akwai sauran zama a tsakaninmu toh fa sabon lale
ne, sabon nema, sabon ɗaurin aure wanda na tabbatar abu ne mai matuƙar wahala ace waliyyai na su
sake karɓar maganar auren Bilal, sai dai ƙaddara mai girma irin wacce ta haɗa mu a baya wadda a yanzu
ni da kaina bana fatan ta sake giftawa.
Aurensa y
[5/24, 12:01 PM] Hauwa Galadima: *KURA A RUMBU*
*Wattpad @MaryamahMrsAm*
*Ban yarda wani ko wata ya juya mun labari ta kowacce siga ba tare da izini na ba*
*Kuɗin karatu yana wakiltar mutum ɗaya ne, kiji tsoron Allah karki ɗauki hakkina ta hanyar fitar mun da
littafi*
*KURA A RUMBU littafin kuɗi ne, a biya naira 800, biya a asusun*
*7061838488*
*Opay*
*PAGE 55*
Tarin missed calls ɗin da ya gani daga Alhaji Lawan mutumin daya siya gidan Jalilah a hannunsa ya
tabbatar masa da ba lafiya ba, a maimakon ya kira Alhaji Lawan ɗin kai tsaye sai ya fara kiran Nasir
domin shi yayi hanyar cinikin.
"Yanzu nake shirin kiranka dama; kana ina?" Nasir ya faɗa bayan daya amsa wayar Bilal ya ce
"Mai ya faru naga mutumin nan daya siya gida a hannuna yana ta kirana a waya ban lura ba sai yanzu?"
"Shiyasa na ce kana ina? Akwai matsala gaskiya" Nasir ya bashi amsa. Bilal ya girgiza kai kamar yana
gaban Nasir ɗin kafin ya ce
"Ina Abuja, ka faɗa mun abinda ya faru dalilin daya saka na fara kiranka kenan kafin na bi bayan nasa
kiran"
"Wasu mutane ne suka je gidan, a faɗar su sun siyi gidan ne dan har takardu suka nuna masa kuma daya
ɗakko musu nasa aka haɗa sai ya gane na gurin sa fake ne su suke da original ɗin" Nasir ya faɗa.
Wata hajijiya da bugawar ƙirji suka ziyarci Bilal lokaci ɗaya, a hankali ya sulale ya zauna akan gado zufa ta
shiga keto masa kamar wanda yayi gudu. Yana jiyo Nasir ta cikin wayar yana cewa
"Idan kuskure ne tun wuri ka nemo hanyar da zaka gyara dan wlh Alhaji Lawan bashida daɗi musamman
akan maganar kuɗi; yanda ya kirani kuma yanzu na san a shirye yake da yin koma menene dan haka
asirinka a rufe ko dai ka mayar masa da kuɗinsa ko kuma su waɗanda ka siyarwa yanzun su haƙura ka
basu kuɗinsu tun kafin magana tayi nisa".
Kusan minti biyar yana zaune ya rasa tunanin da zai kama, Su waye suka siyi gidan? Kuma wanene ma ya
siyar musu? Yanzu da Nasir yake cewa ya mayarwa da Alhaji Lawan kuɗinsa ina ya gansu? shi da dubu
ɗari ma yanzu sai dai a ɗaure shi dan bashida ita. Watansa biyu rabon daya samu albashi, da yaje yayi
ƙorafi sai lokacin ma ya san wai ashe an sake bashi query toh bai ma sani ba balle yaje yayi depending
kansa daga amsar da account ɗin kuma ya bashi wai yaje yayi ta addu'a ya san abu ne mai wahala idan
bai rasa aikinsa ba.
Abun mamaki kuma, a cikin shirinsa harda barin aikin da zarar abubuwan da yake shiryawa sun tabbata
amma kuma sai yaji hankalinsa ya tashi sosai yanzun ko da yake dole, duk abubuwan da yake lissafawar
sun ruguje, da kuɗin shagunan Jalilah ya so yayi jari zai fara harkar Import and Export ya gama saita
komai amma kuɗi sun ƙi samuwa kamar asiri an rasa mai siyan shagunan duk wanda aka samu sai an
fara magana kamar gaske sai wasa ya shigo ciki gashi duk kuɗaɗen da suke account ɗin sa ya kashe su
akan auren Zulaiha ɗan canjin daya rage masa ya san ko cikakken cefanen wata ɗaya ba zai musu ba ga
wata ya taho gangara itama Hajja zai yi mata nata cefanen ya kuma bata kuɗin da yake bata duk wata.
Wayar daya kashe bayan sun gama magana da Nasir ɗin ya ɗauka da niyyar kunnawa ya kira Jalilah
domin dai daga shi sai ita ne a cikin maganar gidan dukda bashida tabbacin samunta a wayar; yau kusan
sati biyu kenan rabon da suyi magana tunda ta kirashi ranar tace masa kayan da ta turo sun sauka suna
Lagos zata tura masa number wanda zai kira sannan zata tura masa kuɗin da za'ayi clearance shikenan
yaji shiru, ya gama shirya da zarar ta tura kuɗin ya dafe su zai sake danna mata block suyi rabuwar
ƙarshe sai gashi kwana da kwanaki shiru kuma idan ya kira wayarta a kashe haka ko a Whatsapp baya
ganinta.
Ya ɗan shiga damuwa da tunanin ko wani abu ne ya sameta dan har Hafiz ya tambaya ya ce masa tana
lafiya sunyi magana, hakan ya bashi mamaki har yayi niyyar ya tambayeshi yaushe sai kuma ya fasa
gudun kada Hafiz ɗin y zargi wani abu.
Kunna wayar yayi zuciyarsa ta raya masa daya kira layinta na Nigeria cikin sa'a kuwa yana kira ta shiga
murna kamar ya taka rawa sai dai har wayar ta ƙaraci ringing ta katse ba'a amsa ba. Sake kira yayi nan
ma shiru bata ɗauka ba, sai kawai ya miƙe ya shiga saka kaya dan dama daga wanka ya fito, a ƙalla tunda
ya samu wayar a kunne ai magana ta ƙare komai zai zo da sauƙi.
Yana taje sumar kansa Zulaiha ta shigo ɗakin cikin kwalliyar da idan zata fita kaɗai yake ganinta da ita.
Daga bakin ƙofar ta tsaya tana jifansa da kallon daya fi kama dana raini ta ce
"Zan fita"
"Bada yawuna ba" ya bata amsa yana zura wayarsa a aljihu, tamkar ɗan data haifa haka ta taso masa
tana cewa
"Ai kuwa wlh baka isa ba fita kamar naje na dawo, haka kawai; sai kace wata dabba zaka turkeni a gida
ba kulawa ba walwala ka kuma hana ƙawaye na zuwa balle na gansu naji daɗi sannan kace ba zan fita
waje in shaƙata ba ai wlh kasan ƙarya kakeyi kuwa".
Kallonta ya ringayi dukda tuntuni ya dena mamakinta ya kuma fahimci dagaske wannan itace asalin
Zulaiha; Ƙazamar mace, mara kunya kuma mara tarbiyya. Sanin da yayi mata a kamila, nutsattsiya kuma
mai kunya duk yaudara ce kamar yanda ta yi nasarar lulluɓe halayyar tata da sunan Aljanu wanda duk sai
a hankali da zama ya fara nisawa ya fahimci haka take babu wasu Aljanu ko wata iska da take shafarta
kuma ba iya ita ba.
Ya gyaɗa kai tareda raɓeta ya wuce yana jin ta saki tsaki haɗi da cewa
"Ƙaryar banza" kafin ta bi bayansa, kafin ma fita da mota ya kulle gidan ita har ta kusa titi, ya na ƙoƙarin
tsayawa ya ɗauke ta tare Napep ta shige abinta tamkar ma bata ganshi ba. Ya sauke numfashi mai nauyi
yana shafa kansa. Yayi zaton samuwar Zulaihan zai zame masa cikar burika da kuma samun nutsuwa sai
dai daga ranar data fara amsa sunan matarsa shi dai kullum komai ƙara lalace masa yakeyi.
Zulaiha ta raina shi, raini irin wanda bai taɓa zaton wani mahaluki zai yi masa a duniya ba. Da fari zama
ya fara yin daɗi a tsakaninsu, yana ƙoƙari gurin ture abinda yake hanashi sukuni akanta ya tarairayeta
irin yanda ya daɗe yana mata tanadi itama kuma tana ƙoƙari matuƙa gurin kyautata masa sai dai abinda
ya fara haɗasu kwashe-kwashen ƙawayenta.
Ya mata magana ya fi sau shurin masaki akan mutanen da take tarawa suyi masa kaca kaca da gida kuma
su tsallake su tafi su barshi a haka itama da take zaune a gidan ba zata gyara ba haka zata zauna cikin
ƙazantarta tayi ta danna waya ko tayi kallo idan yayi magana ta ce dare yayi an hanata shara da daddare
tunda shi kuma ba zai iya bacci da datti a in da yake ba dole komai dare haka zai gyara gidan hakan kuma
ba zai hana washe gari su sake dawowa su maimaita abinda sukayi jiyan ba.
Ga Almubazzaranci, buhun shinkafa daya ajiye bai ko rufa musu wata biyu ba tace ya ƙare duk kuwa da
ba wai shi kaɗai bane akwai su taliya, macaroni harda couscous, kada kayan shayi suji labari dama, idan
ya siyo madara ta leda ko gwangwani yau in sha Allahu kwana uku yayi yawa sai dai ya tarar da burbuɗi a
ciki balle ƙwai da idan ta tashi shida take soyawa idan bai tashi ba haka zata cinye ita kaɗai su Nama,
kaza kuwa tunda ya siyo na farko bayan an kawo mata Freezer da ta ce Mijin wata Antyn ta ne ya siya
musu ita da Nuratu ya yiwo cefane da yawa aka zuba, shi dai bai irga sau nawa ma ya ci abincin nata ba
balle ya ci Naman ba'a rufa sati biyu ba zai fita ta ce masa ya aiko da naman da za'ayi girki, ya rufeta da
faɗa bata saurara ba itama ta haye masa tana cewa
"Karka kuskura ka zageni akan nama wlh, banda tsiya da ƙaranta mai akayi akai nama da har zaka ringa
tada jijiyoyin wuya akansa? Dama ba saboda na ci ka siyo ba ko kuwa ado zanyi dashi a Freezer? Toh wlh
karka sake, ba kuma ka isa ka mun shamaki da wani abu a gidan mijina ba zan ci abinda nake so kuma
dole ka kawo dan haƙƙina ne dole ka bani abina" ta faɗa tana wani zare masa ido kamar uwarsa.
Ya ringa kallonta cike da al'ajabi ba tareda ya shirya ba kuma ƙwaƙwalwarsa ta tafi masa tariyar lokutan
baya zamanin Halima. Ya tuna lokacin da yake mata tijara akan abinda ya siya da kuɗinsa ko wanda aka
kawo mata daga gidansu, dai-dai da rana ɗaya bata taɓa ɗaga kai ta kalle shi ba balle ta mayar masa da
raddi idan ya gama kuma ta bashi haƙuri.
"Kin fi kowa sanin ba'a bishiya nake tsinko kuɗi ba dan haka tun wuri ki shiga hankalinki ki kuma koyi
tattali" daga haka ya wuce shi da kansa mamakin kansa ya kamashi. A wata biyun ta masa abubuwan
daya kamata ace ya rufeta a ɗaki ya mata dukan tashi kisha gishiri amma ko magana mai zafi zuciyarsa
bata taɓa yarda ya furta mata ba ko yayi niyya kawai sai yaji ba zai iya ɓata mata rai ba sai dai ya shanye
komai a cikinsa shi kaɗai.
Gajiya yayi da tafiya ya samu gefen titi yayi parking, sai da ya matsar da kujera baya ya kwanta haɗi da
tallafe kansa ya lula tunani. A lissafe yake komai ya rasa kuma ta inda ya kuskure abubuwa suke neman
su lalace masa haka.
Wayarsa ya ciro daga Aljihu yaga sake ganin Missed call ɗin Alhaji Lawan, ya ja tsaki a fili to wai mai yake
so yayi masa ne?
Yana ƙoƙarin sake kiran Jalilah kiran Alhaji Lawan ɗin ya sakw shigowa, ya kuma zabga tsaki kafin ya tashi
zaune dakyau ya ɗaga wayar. A gajarce suka gaisa Alhajin ya ce
"Da sassafe mutane suka buga mun gida, na fita na same su suke sanar mun da sun siyi gidan ne kuma su
ba'a faɗa musu ma da akwai yan haya a ciki ba dan mutumin tafe yake da yara da zasuyi masa shara su
wanke gidan wai amarya za'a saka nan da sati ɗaya dan ya ce zuwan da yayi na ƙarshe lokacin ana aikin
gyaran gidan kuɗi ne bai cika ba sai yanzu aka bashi muƙullin gidan".
Bilal ji yayi kamar ba hausa mutumin yakeyi masa ba, lokaci ɗaya kuma tunaninsa ya tafi akan tabbas sai
dai idan asalin wanda aka siyi gidan a gurinsu ne suka sake siyarwa da wani kuma Jalilah ce zata warware
wannan matsalar tunda ita ya san waɗanda ta siyi gida a hannunsu shi takardu da muƙulli kawai ta bashi
idan bai manta ba tace gidan na saurayin wata ƙawarta ne.
"Ka kwantar da hankalinka Alhaji in sha Allahu yanzu zan kira asalin wanda na siyi gurin a hannunsa duk
yanda ake ciki zaka ji ni" ya bashi amsa cikin kwantar da murya. Alhaji Lawan ya ce
"Gara dai, dukda ni kam na haƙura dan idan baka manta ba sai da nayita nanata maka bana son rigima,
idan ka san gurinka akwai rigimar gado ko ta gwamnati akansa ka faɗa mun dan na shiga irin haka banji
daɗi ba ƙarshe sai asara na ɗauka dan filin gomnati ne mutumin yayi ginina ciki na siya amma kace babu
komai, to ni dai na haƙura ka dawo mun da kuɗi na kawai ka riƙe gidanka, dama tun safe na kira lawyer
na na shaida masa komai zaizo ya sameka yanzu haka ka gammu har munci ƙarfin kwashe kaya daga
gidan dan haka ina sauraron kuɗi na" daga haka ya katse wayar ba tareda ya bari Bilal ɗin ya sake cewa
komai ba.
Tsaki Bilal yayi bayan daya sauke wayar daga kunnensa yana cewa
"Ai da sauƙi ka tunda ka saba ɗaukar asara wannan karon ma haka zakayi haƙuri wlh".
Jalilah ya sake kira, wayar na dab da katsewa aka ɗaga ya sauke ajiyar zuciya sai dai kafin yayi magana
muryar Namiji daya ji ta saka murnarsa ta koma ciki
"Tana cikin uzuri, idan saƙo mai muhimmanci ne ka faɗa sai a sanar mata" mutumin da muryarsa ta nuna
ba asalin bahaushe bane ya faɗa. Tunani ya tafi akan wane uzuri takeyi? Ba zai wuce tana tareda wani
namijin suna lalata ba dai ya san, yayi tsaki wani abu mai kama da kishi ya taso masa murya a cuskule ya
ce
Gidan Hajja ya wuce, ya tarar da ita da Fadila da tulin kaya dangin atamfa, leshi da materials suna ta
dubawa bakin nan kamar zai tsage saboda murna ko sallamarsa duk su biyun ba su ji ba saida ya shiga
cikin falon kafin suka lura da shi.
"Yawwa kamar kasan dama yanzu nake so na kiraka ka zo" Hajjan ta faɗa bayan data amsa sallamarsa.
Yana kallon kayan ya ce
"Waɗannan fa?"
"Lefen ƙanwarka ne" ta bashi amsa tana tura masa wani ɗaurin kuɗi da a ƙalla zasu iyayin miliyan ɗaya
ko sama da haka. Cikin muryar data bayyanar da farincikin da take ciki tace
"Miliyan biyar ya bata kuɗin lefe da sadaki, kaga siyayyar da tayi akwai wasu a ɗaki da kuma sauran da
ba'a kawo ba ga dai abinda yayi saura nan sai ka haɗa ka siya mata kayan ɗaki irin na Halima da aka fitar
dan ka san ba ƙaramin gida zata shiga ba. Hassadar da kayi mata ka ƙi ka mata hanyar abokinka gashi ta
zame mata taki Allah ya kawo mata wanda ya dokeshi a arziƙi".
Shi dai kallon Hajjan kawai yakeyi harta kai aya kafin ya ce
"Yaushe Fadila ta samu miji har aka karɓi sadaki bamu sani ba? Kuma su Baba Sani ne suka karɓa ko su
Yaya Aminu?"
"Uwar su Baba Sani da Aminu ce ta karɓa, ni ce zan zake soko Sani a cikin sabgata? Ai har abada wlh.
Kuma Fadilar budurwa ce da sai wani ya karɓar mata sadaki ko me? Kai ma ɗin abinda ya sa na faɗa
maka yanzu saboda kai zakayi kayan ɗaki ne idan ba haka ba cikin yan gayya zaka fito sai ya rage kwana
biyu ɗaurin aure kafin a sanar muku" Hajja ta bashi amsa. Ya sauke ajiyar zuciya ya ce
"Allah ya sanya alkhairi, zan kuma bayar da gudummawa abinda ya samu amma batun nayi mata kayan
ɗaki bai taso ba tunda dai ba'a faɗa mun da wuri ba balle nayi tanadi dan bani da wasu kuɗi a halin
yanzu".
Hannu Hajja ta shiga tafawa tana salallami yanda kasan wacce taga bala'i tsirara kafin ta lailayo ashar ta
watsa masa tana cewa
"Lallai Bilal, ni zaka kalli tsabar ido na kace mun baka da kuɗin da zaka yiwa yar uwarka kayan ɗaki amma
ai kana da kuɗin yiwa yar iskar fitsararriyar matsiyaciyar matarka ko?"
Runtse idonsa yayi dan sosai yaji zafin kalaman data jefi Zulaiha da su, yana ji ta ringa sababi tamkar zata
aro baki tana zagin Zulaiha da iyayenta dashi kansa.
"Karka ɗauka shirun da nayi maka kafi ƙarfi na ne ko kuma bani da yanda zanyi da kai, wlh Bilal; kaƙi yin
abinda nace a lokacin zan nuna maka asalin kalata daka manta. Tunda ka auro yar iskar yarinyar nan ka
ɗaga waya ka kirani ma ya zama sai sa'a balle ka tako ƙafarka ka zo cikin gidan nan sai dai idan taka ce ta
kawoka, to ba duniya na haifawa kai ba, babu kuma wasu yan iska da basu tayani shan wahala da
rainonka ba da zasu fini jin daɗinka a yanzu dan haka kayi duk yanda ka so nima ba zan fasa yin abinda
na so ba" tana gama faɗar haka ta shige ɗaki ta barsu.
Yana tafe yana lissafa sabon jidalin daya same shi, yanzu tsakani da Allah a ina Hajja take so ya nemo
kuɗin da zai yiwa Fadila kayan ɗaki a sati uku kuma ma wai irin na Halima ita ya san nawa ake siyar da
irin kayan ne?
Gurin Nasir ya wuce suka sake tattauna batun gidan yana sake nanata masa
"Wlh Alhaji Lawan bashida daɗi, rufin asirinka ɗaya kuɗin sa ya fito tunda ya ce ya haƙura da gidan idan
ba haka ba ina jiye maka tijarar mutumin nan wlh"
"Ai sai dai yayi koma menene ciniki ne kuma ya biya an bashi gida da takardu ya rage tsakaninsa da su
can suje wanda yafi ƙarfi ya mallaki guri" Bilal ya faɗa, Nasir dai bai sake ce masa komai ba ya kamo wata
hirar wacce batayi tsayi ba Bilal ɗin ya masa sallama ya wuce dan gaba ɗaya babu abinda yake jin daɗi
yanzu komai ya masa zafi mafita kawai yake nema.
Yawo ya ringayi a gari har yamma kafin ya koma gida har sannan kuma Zulaiha bata dawo ba dukda ba
sabon abu bane dama idan ta fita kawai sai an ganta. Kitchen ya shiga ya duba ko zai samu abinda zai ci
dukda ya san da wahala, ya gama buɗe-buɗen kwanukan daya gani amma babu komai a ciki ya wuce ya
buɗe freezer yana tsaki, bai taɓa shiga kitchen ɗin bai samu abinda zai ci ba a sanda Halima tana nan.
Bayan leftovers da take ajiyewa ga kayan ƙwalama kala-kala har sanda aka janye mata tallafi daga gida in
dai ta samu kuɗi ko yaya ne sai tayi wani abun na taɓawa ta ajiye kuma duk shi yake cinyewa har idan ta
rigashi ta cinye abinda yayi saura ma ya samu bakin yin masifa.
Da mamaki ya kalli cikin freezer dake danƙare da kayayyaki, kaji, jan nama, kifi kala-kala gasu nan. Ya
rufe yaja baya ya tsaya yana tunanin daga ina aka samo su? Domin dai tun cefanen farko daya mata irin
haka ta cinye bai sake siyowa da yawa irin haka ba, da Halima ce sai ya ce daga gidansu aka kawo mata
amma Zulaiha fa, ya sani kaf danginta na uwa da uba babu mai iya yi mata haka.
Fita yayi daga kitchen ɗin har zai fice daga falon gaba ɗaya kuma ya fasa ya wuce ɗakinta. Yanda kasan
ɗakin Namiji ko ina an zubar da kaya wankakku da masu datti, ya ringa yamutsa hanci yana tattare mata
kayan sai yaji ɗakin ma har wani tashi yakeyi. Tsaf ya gyara kayan daya kwashe ya ɗaure mata su a zani
dan ko laundry basket bata da shi, ya cire bedsheet ɗin da ya fi wata ɗaya akan gadon sai da ya sha
lalube kafin ya samo wani ya shimfiɗa.
Wardrobe ɗin tata kanta kamar ta yara komai da mazauninsa daban, ya ringa hasaso wardrobe ɗin da
take a gurin da ƙatuwar gaske data sha ado da mudubi kowanne compartment da abinda take sakawa a
ciki, ɓangarorin atamfa daban hala lace da sauran kayanta ga ƙamshi Halima ko bata fesa turare ba a
hakanta ma ƙamshi takeyi.
Gefen gadon ya samu ya zauna yana shafa goshinsa da hannu ɗaya, sanda suke tare ya raina tsaftarta, a
hakan gani yakeyi bata iya ba ko shara tayi in dai yana nan sai ya sake maimaitawa ko idan tanayi ya
ringa kushewa kenan ya ce nan bai sharu ba bata goge can ba can batayi kaza ba sai kace ba mace ba
aikin gida ma ace shi Namiji ya fita iyawa duk idan yayi mata hakan sai dai tayi murmushi kawai bata
taɓa nuna ɓacin rai ko tayi fushi ba sai dai ma ta nuna jin daɗi dan tana yawan faɗa tsaftarsa tana cikin
abubuwan da take so a tattare dashi.
Tashi yayi idonsa ya sauka kan drawer dake saman mudubi wacce sai an lura da kyau sannan za'a gane
ana iya buɗeta, ya buɗe ido cike da mamaki yana kallon abubuwan da suke ciki, rafar yan dubu-dubu
daya gani ya ɗauka guda ɗaya ya shiga juyawa a hannunsa kafin ya mayar ya ajiye ya ɗauki wata yar
kwalba data ja hankalinsa.
Instruction ɗin jiki ya karanta take kuma ya samu amsar abinda ya daɗe yana ci masa tuwo a ƙwarya
cikin tarayyarsu da Zulaihan. A aljihu ya jefa kwalaben guda biyu ya rufe mata drawer ya koma kitchen
ya dafa indomie sannan ya koma ɗakinsa.
Wai duk a yaushe Zulaiha ta samu irin wayewar nan bai sani ba? Shi dai a shekarun da suka shafe ko da
wasa bai taɓa ganin wata alama da zata ɗarsa zargi ko wani abu zuciyarsa ba. Yana cin abincin
maganganun Kawunsu suka shiga dawo masa. Toh ko dama abinda yake magana akai kenan? Ko kuwa
akwai wani abun bayan wannan ma?"
Ƙarar wayarsa ta katse masa tunani da sauri ya aje cokalin ya ɗauki ruwa ya sha ganin mai kiran, Jalilah
ce ya ɗaga.
"Ina gida mana mai ya faru?" Ya bata amsa, ji yayi kamar an ƙwanƙwasa Get kafin a shagwaɓe yaji ta ce
Ai sai yaji kamar an tsinka masa mari a bazata, yayi firgigit ya miƙe tsaye kamar wanda ya farka daga
suma ya ce
"Nace ina ƙofar gida kazo ka buɗe, dan Allah I'm stressed enough for today Bilal daga Airport kai tsaye
na wuto na gaji kazo ka buɗe mun tun ban faɗi a inda nake ba" Jalilar ta bashi amsa cikin muryar dake
nuna gajiyar tata dagaske. Laluben key ɗin motarsa ya shigayi bai ko tsaya saka riga ba dan single ce da
three quarter wando a jikinsa ya zura takalmi ya fita bayan ya jefa wayar aljihu ba tareda ya ko katse
kiran ba.
Buɗe ƙofar yayi ya leƙa sukayi ido huɗu da Jalilah dake tsaye da ƙaramar akwati a gabanta tana danna
waya fuska a haɗe, da sauri ya mayar da ƙofar zuciyarsa ta shiga luguden daka. Bai tsammaci dagaske
take ba ya ɗauka dai ta shigo Kanon shiyasa zai tafi ya tarota a inda take ya nemi in da zaiyi mata
masauki ashe ita harta ƙaraso ma.
Bai amsa mata ba ya wuce ya kunna mota, sai kuma ya fito daya tuna dole dai sai ya buɗe Get ɗin tunda
dai motar ba zata fita ta saman katanga ba. Yanda ka san maraya haka ya narke fuska ya nufeta yana
cewa
"Bari na ɗakko mota sai muje na kaiki masauki dan Allah". Akwatinta taja ta wuce shi ta shige gidan tana
cewa
"A nan naga damar sauka" ya bita da sauri ya riƙe akwatin ta sakar masa ta shige ciki kamar gidanta tana
kallon compound ɗin daya sha sabon fenti. Murmushin da Bilal bai san dalilinsa ba ta saki tana cewa
"Gyara aka yiwa gidan ashe? Gashi kuwa ya ƙara kyau" ta wuce falo shi dai kamar wanda aka dasa ya
tsaya a guri ɗaya ya kasa bin bayanta.
Turus tayi tana kallon cikin falon kafin ta waiwaya ta kalli Bilal daya sauke kai ƙasa tamkar an ƙure
munafuki, har ta buɗe baki zatayi magana sai kuma ta fasa ta ƙarasa shigewa tana kallon gurin. Kusan
minti biyu kafin Bilal ya samu ƙarfin guiwar bin bayanta ya shiga falon ta kalleshi fuska babu yabo ba
fallasa ta ce
"Ashe dai kayan gurin ne suka ƙara masa kwarjini yanzu kuwa ana shigowa an san gidan gwauro ne" ta
ƙarasa da wani murmushi kafin ta miƙe ta nufi ɗaki tana cewa
"Allah sarki Halima sai kuma na ɗan ji tausayinta kaɗan yar yarinya ka mayar da ita bazawara".
"Amm an daɗe ba'ayi amfani da gurin ba muje can ɗakina" ta masa kallon daya saka yaji kamar ya fasa
kuka dan gani yayi kamar ta gane komai kafin kuma ta saki murmushin daya kasa gane dalilin sa ta juya
ya bita a baya suka fice daga falon. Sai da tayi wanka Bilal na tsaye a ɗakin kamar dogari ya kasa zaune
ya kasa tsaye har wani zazzaɓi yaji yana neman saukar masa saboda tashin hankali.
A ƙasa ta saki towel ɗin bayan ta fito ta buɗe akwatinta ta shiga shafa mai shi dai tunda ya kalleta sau
ɗaya bai sake ba ya mayar da idonsa ƙofa yana amsa mata maganar da takeyi masa da Eh ko Aa kawai
harta gama shiryawa lokacin aka kira sallar magriba ta kalleshi ta ce
"Toh bari nayi sallah" ya bata amsa da sauri kamar yana jira. A ɗakin yayi sallah ya jirata itama tayi kafin
suka fita ta shiga mota bayan ya kunna yace mata yana zuwa ya koma ciki da sauri. Akwatinta ya ɓoye
cikin wardrobe da sauran kayan data bari akan gado.
Sai da suka hau titi kafin ta faɗa masa in da zasuje, Calido suka zauna jiran mutumin da zata gani ɗin shi
dai Bilal ya samu guri ya zauna fuskarsa har ta rame saboda tashin hankalin bazata daya sameshi ita tayi
musu order abinci tana danna wayarta tana kallon Bilal jefi jefi tana sakin murmushin da ita kaɗai ta san
ma'anar sa. Sai da suka fara cin abincin kafin mutumin suka iso su biyu, hannu suka bawa Bilal suka gaisa
kafin suka zauna tace suyi order suka ce Aa a ƙoshe suke sun gode.
"Wannan Ahlan kenan, kuma shine wanda na siyarwa da gidan nan na Rijiyar Zaki, amma kuma ɗazu da
safe yaje gidan wai ya tarar da mutane a ciki kuma mutumin ya tabbatar masa da siyan gidan yayi ba wai
aro aka bashi ko haya yakeyi ba" Jalilah ta faɗa tana nuna mutumin da tun zuwansu Bilal yake jin kamar
ya sanshi a wani gurin. Bilal dake zuƙar lemo yayi saurin furzar dana bakinsa saboda yanda ya tasarma bi
masa ta hanyar wucewar iska, ya shiga tari kamar ba gobe gaba ɗaya suka rufu kansa suna yi masa
sannu. Kusan minti uku ƙafin ya lafa masa idanuwansa sunyi jazir sau ajiyar numfashi yakeyi yana zare
ido.
"Wannan shine Bilal kuma shine caretaker gidan, kamar yanda na gaya maka ka kwantar da hankalinka
babu wata matsala zai yi bincike duk abinda yake da akwai zaka ji mu yanzu sai kuyi exchanging contact
ko?" Ta ƙarasa tana kallon Bilal daya zama hoto a gurin daƙyar ya iya miƙawa Ahlan ɗin wayarsa ya saka
masa number yayi dialing kafin sukayi musu sallama suka wuce.
"Yanzu ya akayi har wani ya shiga gida ya zauna har yana iƙirarin siyan gidan yayi kai kana nan baka sani
ba?" Jalilah ta faɗa bayan wucewar su Ahlan. Bilal dai shiru yayi dan zuwa yanzun ya gane kawai so
takeyi ya tona kansa da kansa amma ta rigada ta san komai dukda bai san zurfin abinda ta sani ɗin ba,
ƙaramin tsaki yaji tayi kafin ta miƙe tana kallonsa ta ce
"Oh, to muje na fara ɗauka sai mu dawo". Suna dab da fita daga gurin idonsa ya hango masa wata kamar
Zulaiha tareda mutum biyun da suka rabu da su yanzun nan, tsayawa yayi yana kallon su da yarinyar ta
juyo kuma sai yaga ba Zulaihar bace dan kayan jikinta ma ba wanda Zulaiha ta fita dasu bane kawai
shaiɗan ne ya haska masa take kuma ya tuna a inda ya san fuskar mutumin wanda ya biyo Zulaiha ne
ranar da sukaje siyan Shawarma.
Sai da suka shiga layin gidan kuma yaji daya sani fara kaita Hotel ɗin yayi kafin ya dawo ya ɗaukar mata
kayan yanzu idan Zulaiha ta dawo gida fa?
A mota ya barta ya shiga, ganin ƙofar falo a buɗe ya tabbatar masa ta dawo dan haka take sau dubu zai
rufe mata ƙofar sai ta buɗe halayyar yan ghetto dai ga fanka ga Ac amma wai iska take sha. Kamar
ɓarawo haka ya ringa sanɗa har ya shiga ya ɗakko akwatin, yana kaiwa Get yaji muryar Zulaihan a
bayansa tana tambayar yaushe ya shigo, bai kulata ba ya fita itama ta taɓe baki ta koma ciki abunta.
Sau sha biyu saura ya baro gurin Jalilah kuma har suka rabu bata sake tayar masa da maganar gida ba ta
dai ce ya zo da safe da wuri, ya wuce zuciyarsa fal tambayoyin daya kasa yi mata. Bashida tabbacin ta
san shi ya siyar da gidan ko ba haka ba sannan kuma in dai ita ta siyar da gidanta da kanta kenan tana
sane ta bashi fake takardu idan haka ne kuma na Shago ma ita ta canza su, toh zarginsa takeyi dama ko
me?
Yaji daɗi da Zulaiha bata je ɗakinsa ba dan bai ko kwanta ba kwana yayi yana safa da marwa idan ya gaji
ya zauna tunani kamar ƙwaƙwalwarsa zatayi bindiga yanzu yaya zaiyi? A ina zai nemo Miliyan Hamsin da
biyar ɗin da zai biya Alhaji Lawan kuɗin sa? A ina zai samu kuɗin da zaiyiwa Fadila kayan ɗaki ya gujewa
fushin Hajja? Ya zaiyi da batun aikinsa wanda a yanzu ne ya fahimci kasassaɓar da yayiwa kansa da yayi
wasa da shi? Sannan duk bayan wannan ya zasu kwashe da Jalilah?
*Wattpad @MaryamahMrsAm*
*Ban yarda wani ko wata ya juya mun labari ta kowacce siga ba tare da izini na ba*
*Kuɗin karatu yana wakiltar mutum ɗaya ne, kiji tsoron Allah karki ɗauki hakkina ta hanyar fitar mun da
littafi*
*KURA A RUMBU littafin kuɗi ne, a biya naira 800, biya a asusun*
*7061838488*
*Opay*
*PAGE 56*
Kwana uku Jalilah tayi a Kano ta wuce Abuja bayan ta bar alhakin sauke kayan da suka fara isowa a
hannun Bilal. A tsakanin kwanakin har rama yayi; duk wanda ya sanshi kallo ɗaya zakayi masa ka fahimci
yana cikin damuwa matuƙa, duk in da yake tunani zai buga lissafi ya fita abu ya gagara, idan ya haɗo nan
sai can ya rushe ga Alhaji Lawan ya taso shi a gaba da zancen kuɗinsa dan tuni ya kwashe kayansa ya bar
gidan kamar yanda ya ce har Ahlan mamallakin gida na asali ya saka an sake gyara ko ina sai jiran shigar
amarya kawai.
Yana kwance idanuwansa a rufe kamar mai bacci amma a zahiri idonsa biyu, Zulaiha ta shiga ɗakin tun
kafin kuma ta isa gareshi ya shaƙi kamshin turaren da yake jansa gareta tamkar mayen ƙarfe duk sanda
ya shaƙe shi, bai motsa ba dukda yanda lokaci ɗaya hankalinsa ya fata tashi kuma jikinsa ya amsa har ta
iskoshi ta zauna gefen ƙafafunsa cikin salo ta shiga shafa sangalalen ƙafarsa tana kiran sunansa a hankali,
duk yanda ya so ya daure amma ina sai da taci galaba akansa.
Haka ya ringa aiki da iya ƙarfinsa tsayin lokaci har saida ya gaji kafin ya saketa ya kwanta a gefe yana
mayar da numfashi. Cikin hayyacinsa dai bai taɓa irin wannan daɗewar ba sai fa sanda take saka masa
wannan abun daya ɗauke ya kuma yi mamakin yanda bata tambayeshi ba ko da yake ai da kunya.
Tsaki mai ƙarfin da Zulaihan ta saki ya saka ya juya ya kalleta da mamakin dalilin tsakin, ta tunzura ƙaton
bakinta gaba kafin tace
"Wai wane irin wulaƙanci ne haka Bilal? Yau kwana nawa baka ko shiga ɗakina ba balle ka sauke mun
haƙƙina? Sannan yanzu ni na kawo kaina babu wani dogon wasa ba komai ka faɗa mun kalli ko minti 5
bakayi ba ka wani jibge kamar wani kayan wanki toh wlh ni ban gamsu ba, dama na san kai lusari ne
shiyasa nafi gane inyi da kaina amma kaƙi; toh wlh ka tashi dan ni ban ma fara jin komai ba" ta ƙarasa
tana ƙoƙarin hayewa jikinsa.
Bilal dake kallonta cike da al'ajabi yayi saurin janyewa kafin ya kalli agogo dan ya tabbatar da minti biyar
ɗin da tace, karfe takwas da minti goma t shigo ɗakin yanzu agogo yana buga takwas da rabi har da
mintoci a sama a ƙalla suk ɗauki sama da minti 15 tare amma shine take cewa minti 5 tsabar ta raina
ƙoƙarinsa?
Ganin da gaske takeyi tana neman danneshi da ƙarfi ya saka ya buga mata tsawa kafin ya tashi zaune
yana kallonta ya ce
"Ni babu abinda na sha kuma lafiya ta ƙalau lafiyar ce ma ta kawo haka kai zan cewa mai yake damunka?
Malam ka nemi maganin sanyi da basir kawai dan ni ba irin tsohuwar matarka bace" ta faɗa tana wani
juya ido. Sai ya kasa ce mata komai kawai ya zuba mata ido yana kallonta, shi dai tunda yake da Halima
bata taɓa raina ƙoƙarinsa ba kullum cikin kwarzantashi takeyi tana nuna masa shi ɗin sadauki ne nagaske
amma yau shi Zulaiha ta kalla ido da ido ta kirashi da lusari?
Ya sha tsallake Halima a lokacin da shi da kansa ya san tana buƙatar kasancewa tareda shi amma bata
taɓa ƙorafi ba, sau da yawa zata iske shi amma ya ce mata bacci yakeji kuma haka zata barshi bai ko taɓa
damuwa da wane hali zata shiga ba amma yau ga wata bayan ya biya mata buƙatar ta raina har tana
ƙoƙarin danneshi da ƙarfi
"Ni dai ban yafe ba wlh" ya tsinci kalaman Zulaiha kafin ta sake sakin tsaki ta fice daga ɗakin ta barshi a
tsaye cikin maɗaukakin mamaki. Wanka ya shiga tun yana ciki kuma yaje jiyo ƙarar wayarsa dan haka
yayi sauri ya fito a zatonsa Hafiz ne dan ya kirashi yana so ya masa zancen salaryn sa ko akwai yanda zai
taimakeshi sai dai bayan daya fito ya duba wayar ya tarar Alhaji Lawan ne ya kirashi. Tsaki yayi ya ajiye
wayar ya shiga shiryawa dukda dare ya farayi amma dole ya fita.
Sai da ya hau titi kafin ya sake duba wayar, saƙon daya gani ya buɗe, ƙirjinsa ya huga dum kansa ya sara,
gefen hanya ya samu yayi parking ya shiga ƙoƙarin neman layin Nasir amma cikin rashin sa'a akace a
kashe yake. Gidan Nasir ɗin ya nufa kai tsaye, Nasir yayi shiru yana saurarensa har yayi shiru kafin ya ce
masa
"Ya kirani tunda yamma ya faɗa mun idan ya kiraka baka ɗauka dan haka ya yanke shawarar kai maganar
gurin shari'a, tun farko Bilal sai da nace maka ka haɗa kuɗin mutumin nan ko da ace basu cika ba ka rage
masa wani abu a zauna ayi rubutu ka faɗi nawa zaka ringa bashi kuma zuwa tsahon wane lokaci amma
kaƙi, yanzu ga abinda nake guje maka nan yana shirin faruwa".
Tsaki Bilal yayi ya ce
"Au saboda me ma kake tambaya?" Nasir ya faɗa cike da mamaki, tsaki Bilal ya sakeyi kafin ya ce
"Look Nasir, ni fa ba wasu kuɗi da zan biyashi. Gida ya siya kuma d shaidu da komai ya biya kuɗi an bashi
takardu akan me yanzu zai zo da wani rainin wayau? Nima fa gidan nan siyan sa nayi kuma na siyar
masa, ai kamata yayi ya nemi wanda ya zo ya ce shima ya siyi gida idan ma shari'a ce dashi ya kamata
yayi"
"Toh idan aka je gaban shari'ar na tabbatar in dai ba mahaukacin Alƙali aka samu irin ka ba abu na farko
da za'a farayi shine kowa ya zo da wanda ya siyi gida a gurinsa nan kuma wa zai kawo?" Nasir ya faɗa
yana buɗe murfin motar, Bilal ya watsa hannu alamar Oho, Nasir ya girgiza kai cike da takaici ya ce
Daga gidan Nasir Bilal gidan Hajja ya wuce, fuska ba yabo ba fallasa ta karɓe shi abinda bai zata ba dan
tun waccen ranar bai sake zuwa gidan ba a waya ma sau biyu ya kirata kuma duk bata amsa ba shiyasa
daya ga fuskarta a sake yanzun abin ya bashi mamaki ya kuma sha jinin jikinsa dan ya san da wahala idan
ba tarko zata masa ba.
"Ka ji ɗan albarkan yaron nan yace ba sai ta tafi da komai ba ya rigada ya zuba abunsa" Hajjan ta faɗa
masa, yayi ɗan murmushi ba tareda ya ce komai ba sai Hajjan ce ta sake cewa
"Amma Hajja wai a gurin wa akaje neman auren da har aka tsayar da lokaci?" Ya faɗa yana kallonta ta
zabga masa harara tace
"Amma ni Hajja mun daɗe da yarinyar, na santa na san iyayenta na kuma san duk halayyarta sa'annan ni
namiji ne shari'a ta yarjemun da na wakilci kaina a neman aure. Gaskiya ya kamata ace anyi bincike asan
wanene wanda zata aura ɗin asan asalinsa da kuma menene sana'arsa, zamanin nan da mugaye sukayi
yawa mutum yazo yana wasan kuɗi irin haka ai ya kamata a saka masa alamar tambaya" ya faɗa kansa a
ƙasa.
"Ni fa wlh Hajja bani da wasu kuɗi yanzu, kafin lokacin idan na samu zan bata amma ban ɗauki alƙawarin
siya mata Gwal ba" ya bata amsa, ta watsa masa wani kallo kafin ta kai ga magana ya rigata kamar zai
fasa kuka ya ce
"Wlh Hajja ina cikin matsala. Duk yan kuɗaɗen da suke hannuna sun ƙare a harkar bikin nan waɗanda na
saka ran zan samu kuma abin bai yiwu ba yanzu haka account ɗina wlh ko dubu ɗari bani da ita".
"Wannan kuma kai ta shafa ba ni ba, wato ni da wuyar naƙuda da shan wahalar raino harka girma sai da
ka zama abin moro sannan zaka koma bawan can wata ƙatuwa da iyayenta ko? To wlh baka isa ba ko
sata zakayi kaita shafa ni dai na gaya maka ka siya mata sarƙa da ɗankunne" Hajjan ta bashi amsa cikin
ko in kula. Har kusan sha biyu yana gidan, sai da Abubakar ya shigo har ya kulle ƙofa ma ya tarar da Bilal
ɗin a falo shi kaɗai dan tuni Hajjan ta shige ɗaki ta kwanta Fadila kuma dama tana gidan Anty Habiba wai
ta fara gyaran jiki.
Kamar Abubakar ɗin ba zai kula shi ba dan har ya juya ko mai kuma ya tuna sai ya koma ya shiga falon
yana kallon Bilal ya ce
Agogon dake ɗaure a hannunsa ya duba ya buɗe ido ganin lokaci kafin ya ce masa
"Ya kamata ka tashi toh dan naji iska tana kaɗawa kamar hadari ne yake tasowa" Abubakar ya sake faɗa,
sukayi shiru kafin ya ce
"Kana aikawa da yaran can abubuwan buƙata kuwa?"
"Su Al'amin, kana aika musu da kuɗin abinci da na sauran buƙata? Sannan kuɗin makarantarsa da sauran
abubuwan duk kana kulawa da su?"
"Ai ita ta matsa na saketa kaga kenan ta shirya kula da su" ya bashi amsa ba tareda ya kalle shi ba.
Abubakar yayi murmushi ya ce
"Ai sabon abu bane, ko a sanda take gidan naka ma ai ita take ɗauke da nauyin kanta da na sun kaga ba
zai zame mata sabo ba dan taci gaba. Wlh Yaya Bilal kayi babbar asara, samun mace tamkar Anty Halima
a zamanin nan sai sa'a kuma tunda ka rabu da ita ba zaka mai da irinta ba ko mace dubu zaka aura wlh
ba dai ka samu irin Halima ba
Ta soka saboda Allah, ta wahalta maka da jikinta da aljihunta amma ka biyewa duniya ka yi mata sakayya
da sharri, wlh ko bata buɗe baki ta nemi sakayya a gurin Allah ba haƙƙinta ba zai taɓa bari ka zauna lafiya
ba ga kuma haƙƙin yayan daka barta dasu, baka san cinsu ba baka san shan su ba sutura, rashin lafiya,
karatunsu babu wanda ka damu dashi.
Bana zaton tun ranar da suka bar gidanka ka sake sanya su a idanuwanka, idan baka dubi Allah ka sauke
haƙƙinsu daya ɗora maka na dole ba ai ya kamata ko dan duniya da gobenka ka jiƙansu ta yanda kaima
gaba lokacin da ƙarfinka ya ƙare zasu tausaya maka".
Har ya isa gida yana tilawar maganganun Abubakar kamar karatu, har ya wuce falon Zulaihan sai kuma
ya koma a ransa yana jin babu daɗi dukda bai san dalilin hakan ba. Ƙofar a buɗe take dan haka ya tura ya
shiga da sallama, Tv na kunne amma an yi muting volume falon kaca kaca daga gani baƙi tayi kuma bata
ji zata iya gyara gurin bayan tafiyarsu ba ta tsallake ta barshi a haka.
Kayan dake zube ya tsaya yana kallo, kwalayen pizza, ga raps ɗin shawarma, ragowar kaza sai kwalaye da
gwangwanayen lemo d sauran kayan ciye-ciye dai iri iri. Kayan daya gani a freezer waccen ranar suka
faɗo masa dan haka ya wuce ɗakinta,
"Haba mana Babe" ya tsinkayi muryarta tana faɗa haɗi da ƙaramar dariya, burki ya ci a bakin ƙofa dan a
buɗe ɗakin yake ya shiga kallon kan gadon ta cikin ɗan hasken da yake shigowa daga falo dan ta kashe
fitulun ɗakin.
"Yes Babe cigaba I'm enjoying" ta sake faɗa tana sakin nishin daya saka gabansa faɗuwa, yanayin da tayi
maganar da nishin da tayi sai ya zo masa tamkar ire-iren lokutan da suke phone sex da Jalilah. Nishin
data sakeyi ya saka shi kiran sunanta da ƙarfi lokaci ɗaya kuma ya kunna fitulun ɗakin gaba ɗaya haske
ya gauraye ko ina.
Zulaiha dake cikin bargo suna waya da Ahlan, guy ɗin data haɗu dashi ranar da sukaje siyan Shawarma
da Bilal, har ga Allah tunda aka ɗaura mata aure tayi alƙawarin barin duk wasu abubuwa da takeyi kuma
ta daina ɗin amma ita kanta bata san dalilin daya saka ta kasa tsallake tarkon Ahlan ba, ko da ya fara
kiranta ta yaƙi zuciyarta akan ba zata zake amsawa ba dan har blocking layin tayi sai dai yana canza wani
layin ya kirata ya kanainayeta da daɗin baki akan shi ba wata mu'amala mara kyau yake so su ƙulla ba
kawai ta burgeshi ne yana so su zama yaya da ƙanwa shikenan ta biye masa suka fara waya.
A hankali kuma tunda dama biyu ce ta haɗu kafin ta ankara ya mayar da ita ruwa, dukda waya kawai
sukeyi amma tun bata biye masa harta fara suke zantukan da basu kamata ba, ganin kuma ko hoto bai
taɓa nema ta tura masa ba iya zancen wayar ne ya saka ta saki jiki ga kuɗi yana tura mata kamar bai san
zafinsu ba dama kuma ta farayin broke ta kuma lura da take-taken Bilal shi ɗin ma dai irin sauran mazan
da ake bayar da labari ne.
A waje kamar zasu tsinke kansu su bawa mace saboda ƙauna da zarar sun sameta kuma sai a fara zaman
haƙuri, tunda sukayi aure watanni kusan huɗu kenan naira biyar bata shiga tsakaninsa da ita ba. Zai yi
cefane duk abin buƙata zai siyo ya ajiye mata yana ƙorafi yana mita amma dai ba zai bata kuɗi a hannu
ba, toh hakan ma bai dameta ba tana son sa a hakan kuma zata zauna dashi sauran buƙatunta kuma zata
nemi kuɗi tayiwa kanta ita wannan ba zai zama matsala tsakaninsu ba tunda dai baya saka mata ido
akan harkokinta ko abubuwan da yake ganinta da su.
A bazata taji saukar muryarsa; lokaci ɗaya kuma ta daskare a gurin da take tayi luf a kwance kamar
matacciya dan hatta zuciyarta bata bugawa da kyau. Yaushe ya shigo gidan har ya shiga ɗakin bata ji
ƙarar buɗe get ko dirin motarsa ba? Ta san dai dama a buɗe ta bar ƙofar falon dalili kuma saboda tana
jiransa dan tayi duk yanda zatayi jarabar dake cinta taƙi ta kwanta, yana fita kuma ta koma ɗakinsa ta
bincike tsaf amma bata gano abinda ya ɗauke mata ba dan tun ranar data dawo taga an gyara ɗakin tana
dubawa bata ga abun ba ta san shi ya ɗauke su kuma tun ranar ta cewa Suby ta sake siyo mata wani
amma wai ya ƙare a gurin matar sai an sake kawowa tayi baƙin ciki matuƙa dan ta lura ba zata taɓa
samun haɗin kansa yanda take buƙata ba idan bada abun ba sai dai kawai ya jagwalgwalata ya barta da
wahala.
Yanzun ma rasa yanda zatayi ya saka ta kira Ahlan ɗin da kanta, a falo suka fara wayar tsoron kada ya
shigo ya saka ta dawo ɗaki sai gashi tayi gudun gara ta tarar da zago. Sunanta daya sake kira da takunsa
da taji alamar yana matsawa kusada gadon ga Ahlan da shima yake ta Hello Hello jin tayi shiru, lokaci
ɗaya ƙwaƙwalwarta ta kawo mata mafita cikin abinda bai wuce seconds biyar ba ta aiwatar, ta latse
wayar ta kasheta gaba ɗaya kafin ta turata tsakanin kan gadon da katifa tayi juyi kamar a cikin barci ta
cigaba da sakin maganganun da suka fi wanda ya fara ji girma.
Tsayawa yayi yana cigaba da kallonta a hankali kuma harzuƙa da fushin da ya taso masa lokaci ɗaya suka
fara sauka kafin ya ya matsa ya shiga buga ƙafarta yana kiran sunanta amma kamar wacce yake zugawa
sai ma wani motsi data farayi kamar wacce take tareda Namiji. Duka mai zafi ya ɗana mata a cinya, taji
dukan har ƙwaƙwalwarta ba shiri ta wartsake ta tashi zaune zumbur tana sosa gurin idanuwanta suka
kawo ƙwalla, Bilal dake tsaye a kanta ya ce
"Kai zan tambaya akan me kawai ina bacci na zaka zo ɗana mun duka irin haka?" Ta faɗa yaye rigarta
gurin daya doke ta ɗin, gefe ya ɗauke kansa dan har pant ɗinta sai da ya fito saboda janye rigar da tayi
ya ce
"Bakiyi addu'a ba da zaki kwanta baccin sai wasu sambatu kikeyi marasa kan gado ga ƙofofi kin bari a
buɗe kuma ko ina shara" ya nufi ƙofa. Ajiyar zuciya ta sauke a fili kafin ta bi shi da harara haɗi da yin
ƙaramin tsaki ta koma ta kwanta tana shafa in da ya doketa. Yanzu da ace ya gane mai takeyi yau ina
zata saka kanta? Gaskiya dole fa ta ringa takatsantsan kar taje kwaɓarta tayi ruwa tun ba'a je ko ina ba.
Tashi tayi tabi bayansa jin yana harhaɗa ledoji da kwalayen da suke falon, a nan ɗakinta ya kwana; tun
kuma yanayin na son rai har dai yaga ita bata da geji ya tashi ya koma falo bayan yayi wanka ya barta
tana tsaki bai kuma san yanda ta ƙare ba bacci ya kwashe shi.
Washe gari da wuri ya fita saboda tunanin daya kwana dashi a ransa, store ɗin da suka ajiye kaya yaje
bai kuma ɓata lokaci ba dan a gurin ya tarar da wanda zai karɓi kayan ya buɗe suka ɗiba babu bata lokaci
kuma suka tura masa da kuɗinsa cis yanda sukayi ciniki. Jin kuɗaɗe masu nauyi a account ɗin sa ya saka
nutsuwa ta saukar masa duk wasu tunani da zullumi da yake fama dasu a kwanakin suka kama gabansu
ya shiga sharholiyarsa, 1M ya bawa Fadila gudummawa wanda daƙyar Hajja ta karɓa tana zaginsa tana
faɗar maganganu amma ya toshe kunnensa sauƙin daya samu gyaran daya tayar ayi mata kafin bikin
Fadila nan da kwana goma da angon da kowa bai sani ba daga ita sai Hajja da Anty Habiba sai Anty Ladidi
su suke shirin biki dan ko Abubakar da yake kwana a gidan ya ce bai san komai ba balle sauran.
HALIMA
Da wuri na tashi daga aiki ranar Alhamis, ƙarfe tara nake zuwa mu tashi ƙarfe biyu amma yau ɗin saboda
monthly clearance da zanje ya saka na tashi karfe 12. Ina tsaka da wanke hannuna bayan na fito daga
banɗaki, Juwairiyya wacce muke service a gurin tare ta shigo ta kalleni ganin na cire lab coat ɗina ta ce
"Guduwa kuma sai kace wata ke?" Na bata amsa cikin raha tayi murmushi tace
"Ai da alama yau zaki zama ni ɗin sai dai kinyi wrong timing dan yanzu Dr Sa'id ya shiga lab ɗin mu ya ce
kowa ya zama cikin shiri CEO yana hanya".
"Kuma ya rasa ranar da zai zo sai yau da nake da uzuri? Tun fa last week aka ce zai zo?" Tana gyara
fuskarta da powder ta ce
"Ai kuwa dai sai yau kuma wlh har waɗanda basu da duty yau gashi can Dr Sa'id yace a kirasu a waya duk
kuma wanda bai zo ba ya ce babu ruwansa dan haka kiyi haƙuri kawai ki jira na san ba jimawa zaiyi ba".
Kamar zanyi kuka haka na koma office na zauna, tun last week aka ce zai zo Dr Sa'id kuma ya jaddada har
ranakun da bamu da duty mu kasance cikin shiri za'a iya cewa mu fito saboda yace yana so ya gana da
duka staffs ne idan ya zo. Ina duba agogo ina zabga tsaki, mutumin da aka ce an ɗakko daga Airport tun
12 gashi har ɗaya ta gota basu iso ba ko dai dama basu taso daga can Abujar bane lokacin da aka tafi
ɗakko shin sai Allah. Da wannan mitar na tashi nayo alwalawa ganin zaman ba zai fissheni ba nayi sallah,
ina addu'a Dr Sulaiman ya shigo office ɗin yana ganina ya ce na fito da sauri dan haka na shafa na miƙe
shaf na manta ban mayar da Lab coat ɗin ba na fita da Abayar dana saka nayi sallah.
A reception na tarar da duka staffs harda cleaners anyi layi na tafi inda naga sa'annina da alama
tsayuwar matsayi aka bi, yanda kasan waɗanda zasu tari wani Gwamna ko Shugaban ƙasa haka muka
nutsu muna kallon ƙofa kusan minti uku kafin suka shigo, Dr Sa'id ne a gaba sai wasu mutum biyu da ban
sansu ba da alama tare suka zo da CEO ɗin sai kuma shi Dr SALMAN ABDULLAHI AGI da wasu mutum
biyun a bayan sa, ɗaya daga gani PA ɗin sa ne sai kuma ɗayan da yayi kama da security.
Fuska ba yabo ba fallasa ya ringa kallonmu suna tayi masa sannu da zuwa banda ni dana zuba masa ido
ina ƙare masa kallo kamar mai neman wani abu a jikinsa. Duk yawan shekarunsa ba zasu kai 40 ba
yanzun ne na sake tabbatar da haka dana ganshi a zahiri. Dogo ne sosai dan har ranƙwafawa yayi, a kallo
ɗaya kuma dukda suit ce a jikinsa zaka fahimci yana da kirar ƙarfi irinta masu ɗaga ƙarfe.
Bashi da wani shahararren kyau kuma baƙi ne mai ƙananan ido amma akwai wani abu a tattare da
idanuwansa da bai zai barka kayi masa kallo ɗaya ba tareda ka ƙara ba, gayu da iya ɗaukar wanka ya saka
ya ƙaƙalo kyawun a dole amma ba dan asalinsa mai kyau ɗin bane irin su Bilal da aka haife su da kyan su,
amma maganar gaskiya a ture duk wani ƙaƙale-ƙaƙale, Dr Salman ya haɗu; ga kuma tarin ilimi abin ba'a
cewa komai.
Yanda nake kallonsa shima haka ya tsayar da idonsa a kaina sanda ya kallo ɓangarenmu, naga sanda
laɓɓansa suka motsa alamar magana yayi amma kunnuwana basu jiye mun sautin mai ya faɗa ba ganin
kuma mun haɗa ido ya saka nayi saurin sadda kaina ƙasa ina jin haushin irin kallon ƙurillar daya kamani
ina yi masa. Juwairiyya ta zungureni na kalleta da son jin ƙarin bayani, da ido ta nuna mun CEO ɗin da
har sannan ashe ni yake kallo na zare masa ido cikin rashin fahimtar dalilin kallon da yake yi mun.
"Tambaya yayi wai baƙuwa akayi?" Juwairiyya ta raɗa mun a kunne, still ban fahimci kan zancen ba sai
da Dr Sulaiman ya ce
"Sallah tayi garin sauri kuma ta manta ta fito a haka". Sai lokacin na lura ashe ni kaɗai ce a gurin babu lab
coat a jikina cikin yan Lab, nayi ƙasa da kai ina kallon takalman ƙafarsa kafin na ɗaga kai a hankali jin
yana cewa kowa ya gabatar da kansa. Sai kace za'a gudu ba zai bari aje a zauna ba tukunna. Da ɗai-ɗaki
kowa ya ringa gabatar da kansa da kuma position ɗin sa har aka zo kan coppers mune kuma ƙarshe,
Juwairiyya dake kusa da ni tayi tana gamawa na buɗe baki zan fara magana wayarsa tayi ƙara sai ya ɗaga
mun hannu alamar na dakata ya karɓi wayar daga hannun PA ya amsa kafin ya fara tafiya suka shige
Elevator shida muƙarrabansa suka barmu a tsaye musammani, ni ce fa kaɗai na rage banyi introducing
kaina ba maimakon ya bari nayi sai su wuce gaba ɗaya yanzu ko mai yake nufi sai Allah, zamu tsaya ne
yaje ya dawo ko kuwa shikenan taron ya watse? Wai dama iya dalilin daya saka aka tsayar damu kenan
ko da saura?
Dr Sa'id ne ya dawo ya ce zamu iya tafiya wai amma gobe kowa ƙarfe takwas tayi masa a gurin za'ayi
meeting. Haka muka fita ina mita ga rana ta take babu lallai kuma na tarar da masu clearance ɗin suma
tunda ƙarfe biyu ta rigada tayi amma haka nan na biya tunda idan na ce na bari gobe Friday kuma ban
san sai ƙarfe nawa zai sake mu ba. Da haushin rashin samun clearance ɗin na wuce gida dan munyi waya
da Anty Labiba tace mun suna gidan Mama.
Ban san ɗaya matar da muka hau Adaidaita tare cikin unguwa za'a shigar da ita ba tunda tace Sabon titi
kawai na ɗauka a bakin hanya zata sauka ni kuma ya wuce dani sai da muka je naga yana ƙoƙarin shiga
layin Gidan Ƙanƙara layin su Bilal kafin nayi masa magana.
"Ba ciki sosai bane Hajiya kuma kan hanya ne inda zata sauka sai mu fita ta baya Hajiya" mai Adaidaitan
ya bani amsa. Ƙoƙarin mayar da kaina kan wayata da nake dannawa nayi amma na kasa sai na zurata
cikin jaka na shiga kallon hanya ina tuna zuwana gurin na ƙarshe ranar da muka zo duba Hajja bayan
mun dawo daga gidansu Duniyarsa.
A kan layinsu Bilal ya tsaya, na leƙa ina hango ƙofar gidansu daya sha sabon fenti ga mata suna ta shige
da fice kamar ana wata hidima a gidan,
"Ko mai akeyi sai Allah" na faɗa a fili kafin na ɗauke kai na koma kallon mai Adaidaitan dake irgawa
matar data sauka canji.
"Gadon ƙaya" muryarsa ta sauka a kunnena tamkar dirar aradu kafin ƙamshin turarensa da tunda na
sanshi bai taɓa canzashi ba ya mamaye iskar da take yawo yawo a gurin, na ɗago; har ya zauna a gefena.
Dukda na razana da ganinsa amma ban bayyanar da hakan a kan fuskata ba sai na mayar da hankali na
kan mai Adaidaitan na ce
"Malam drop fa na ɗauke ka, itama saboda naga hanya ɗaya zamuyi kuma abin hawan yana wahala
shiyasa na bari ka ɗauketa"
"Kiyi haƙuri Hajiya, Malam yi haƙuri ka sauka ba can zamuyi ba" mai Adaidaitan ya faɗa, sai lokacin Bilal
ya kalleni idan kuma nayi rantsuwa na san ba zanyi kaffara ba tsabar wulaƙanci ne ƙarya yakeyi ya ce bai
san ni bace a ciki sai a lokacin.
"Halima" ya faɗa muryarsa da idanuwansa suna bayyanar da mamaki, na ɗauke kai a raina ina cewa
"Ƙaryar banza wlh ka san ni ce" kafin kuma na saita fuskata na kalle shi da irin yanayinsa na ce
"Kun san juna ma ashe? Toh mu ɗauke shi ko zai sauka?" Mai Adaidaita dake kallonmu ta cikin mudubi
ya faɗa, shiru nayi dan har ga Allah ƙarfin hali kawai nakeyi sai Bilal ɗin ne ya ce masa
"Bari sai na sauka a titi tunda ciki zaku shiga" ya tayar da mashin ya juya sai lokacin na ƙaƙalo murmushi
ganin yana kallona na ce
"Ya su Hajja?"
"Amma baki faɗa mun zaki ringa fita wani guri ba, ko kin manta har yanzu ina da iko akanki tunda kina
cikin iddatah?" Ya faɗa yana kallona cikin sauti mai kama da raɗa dan nima ba dan shi nake kallo ba bai
zama lallai na ji abinda ya faɗa ɗin ba. Na saki murmushin irin na tura takaici wanda ni kaina ban san na
iya ba kafin nima na sauke murya yanda yayi na ce
"Da alama amarci ya sa ka faa manta lissafi, ko dai in saka ayi maka babbar calendar da zaka ringa duba
watanni da ranaku saboda gudun manta abubuwa masu muhimmanci irin haka?"
"I'm serious Halima, 28th of this month ya kamata ki fara cycle ɗin ki na uku" ya sake faɗa, ganin mum
kawo kan titi mai Adaidaitan na neman cigaba da tafiya ya saka nace masa
"Ya sauka a nan" sai ya dakata, na kalli Bilal da shima ni yake kallo kafin na ce
"An zo titi Malam", kallona yakeyi kamar wanda yaga wata halitta ta daban dan haka na kaɗa yatsuna
akan fuskarsa ina sake maimaita masa cewar an zo titi,
"Ki fara shiri, na mayar dake ɗakin ki" ya faɗa yana sauka daga Adaidaitan, bansan lokacin dana fashe da
dariyar da har mai siyar da ƙanƙara a inda kuka tsaya da mutanen dake gurin saida suka kallemu ba, da
hannu na nuna kaina ina cewa
"Za'a ga wanda yake hauka tsakanin ni da ke" ya wuce ya tsayar da wani Adaidaitan ba tareda ya tsaya
karɓar canjinsa ba, abun nasa yayi bala'in bani dariya; lallai bansan Bilal mahaukaci bane sai yanzu. Wato
shi yana can yana mun lissafin Iddah kenan? To da bai haɗu dani ba yanzu wa zai aikowa da saƙon ya
mayar dani ɗin?
Ni kaɗai na ringa dariya mai Adaidaita dai sai satar kallona yakeyi da alama magana ce fal bakinsa amma
ya kasa furtawa har ya saukeni ƙofar gida nayi wucewara tunda Bilal ya biya mun, lallai yau kam za'ayi
ruwan sama harda ƙanƙara Bilal ya biya mun kuɗin mota.
[5/28, 11:06 PM] Hauwa Galadima: ❤️*ƊANLARABAWA INVESTMENT! Kyau Da Ƙima A Hannunku!* ❤️
https://chat.whatsapp.com/Loht5sGuLJO3LXYE9OkqNs
*Za ku more da kallon kayayyaki na ƙawa bisa ingantaccen farashi da rahusa mai kama da kyauta. Sayen
nagari, mayar da kuɗi gida.*
*KURA A RUMBU*
*Wattpad @MaryamahMrsAm*
*Ban yarda wani ko wata ya juya mun labari ta kowacce siga ba tare da izini na ba*
*Kuɗin karatu yana wakiltar mutum ɗaya ne, kiji tsoron Allah karki ɗauki hakkina ta hanyar fitar mun da
littafi*
*KURA A RUMBU littafin kuɗi ne, a biya naira 800, biya a asusun*
*7061838488*
*Opay*
BILAL
Yana kwance a gida Hajja ta kirashi wai ya kawo musu kayan miyan da za'ayi tuwon ɗaurin auren Fadila
da za'a ɗaura a gobe Juma'a. Da yake a tsini suke yayi mata laifi shiyasa bai musa ba ya tashi ya tafi
kasuwar Yankaba ya yiwo musu cefanen ya tafi ya kai. Zagayewa yayi yaje ya samu Kawu Ɗayyabu,
Yayan Hajja ne da suke uba ɗaya da yake mutum ne mara ɗaukar raini shiyasa duk rashin mutunchin
Hajjan take shakkarsa ko da wasa kuma bata bari wani abu ya gilma a tsakaninsu shi Bilal ɗin yaje ya
samu ya gaya masa zancen auren Fadilan da yanda ita da Hajja suke shirya komai basu saka kowa a ciki
ba.
"Wane irin rashin hankali ne haka? Ita Hajara wai sai yaushe zata girma ta fara abu irin na mutane masu
hankali? Dama mace ta taɓa aurar da kanta ne ko kuwa uwa ce take bayar da auren yarta? Daga ku har
uwar taku sai a rasa wayafi wani tunani, kaima nan zancen ya iskeni ance ka saki uwargidanka dama
kuma duk ina jin labarin irin ɗiban albarkar da kai da uwarka da yan uwanka kuka ringayi mata, toh
hausawa dai suka ce duk wanda bai yi sharar kasuwa ba zaiyi ta masallaci dan haka tun wuri in dai da
gyara ina baka shawarar ka dawo da matarka dan ba zaka gane illar da kayiwa kanka ba sai a gaba. Ita
kuma Hajara zan kirata" akan haka suka rabu.
Washe gari kuwa ya kira Hajjan yace taje gida ta sameshi yana son magana da ita ba musu kuma ta
shirya ta tafi yayi mata tatas sannan yace su dakatar da duk wani shiri da sukeyi Fadila ta gayawa yaron
yaje ya gaida iyayenta maza tukunna idan sukayi bincike sukaga bashida wani aibu sannan su bashi
lokacin da zai turo ayi magana.
Ta koma gida ta saukewa Bilal tijarar da batayi a gaban Kawu Ɗayyabun ba tunda shi ya kai masa gulmar
amma kuma dole tayi abinda yace ta kira Baba Sani yaƙi ɗauka sai a wayar matarsa ta sameshi shima
daƙyar ya karɓa sukayi magana tana gaya masa dalilin kiran kuma yace babu shi a cikin wannan magana
"Kin manta kashedin da kika mun akan yayanki Hajara? Ai ko ni na kawo rashin zuciya duniya ba zan sake
tsoma baki cikin abinda ya shafeku ba, bani kaɗai bane ɗan uwan ubansu ai muna da yawa ki nemi wani"
ya bata amsa daga haka kuma ya katse wayar. Daga ƙarshe dai sai babban yayansu Bilal ɗin Alhaji Salisu
ta taka har gida ta samu dan Kawunnansu duk wanda ta kira sai yace yana Aa dan kowa nada labarin
ɗibar albarkar da tayiwa Baba Sani da Aminu akan zancen Bilal.
Fadilan ce ta raka shi gurin Yayan nasu akayi sa'a ashe ma sun san juna akwai hulɗa ta cinikayya
tsakaninsu, kamar yanda ya cewa Hajja a tsayin lokacin daya san Alhaji Ahlan saurayin Fadilan ya san
mutumin kirki ne kuma yayi tambaya akansa an tabbatar masa da mutumin kirki be kuma yana da asali
mai kyau dan Babansa nada sarauta acan Zarian ma. Ya taɓa aure sau biyu, ta farkon rasuwa tayi suna
da yara biyu Mace da Namiji ta biyun kuma rabuwa sukayi, shikenan aka cigaba da shirin biki, maza
sunzo sun sake kawo kuɗin aure da Sadaki bayan wanda ya rigada ya bata.
Bayan ya gama sauke musu kayan miyan a tsaitsaye suka gaisa ya wuce saboda zaije ya ɗakko Jalilah ne
a airport.
Motarsa ce taƙi tashi, ganin zata ɓata masa lokaci ya barta ya kira wani abokinsa dake siyar da motoci a
Gadon ƙaya yace zaizo ya karɓi mota yanzu, da wannan saurin ya faɗa Adaidaitan daya gani a bakin layin
ashe rabon su haɗu da Halima ne.
Harga Allah har ya zauna bai san ita bace a ciki dan hankalinsa na kan wayarsa sai da tayi magana kafin
yaji muryarta ya kuma yi mamaki matuƙa amma bai nuna hakan ba har ransa kuma sai yaji rashin daɗi da
bai san dalilin sa musamman ganin da yayi mata ta canza tayi wani kyau fatarta har wani ƙyalli takeyi
baka buƙatar a faɗa maka ta samu hutu da kwanciyar hankali. Shi da yake nan yana tunanin tana can
cikin halin ƙaƙanikayi soyayyarsa ta hanata sakata ko wacce daƙiƙa cikin dakon kiranta yakeyi domin ya
tabbatar ba zata taɓa iya rayuwa mai ma'ana ba tareda dashi ba.
Daɗewar da akayi yanzun ma bata waiwayeshi ba ya sani cikin biyu, ko dai an ƙwace wayarta ne tunda
kowa nata ba son su tare yakeyi ba ya san zasu iya ƙwacewa dan kar ta kirashi kuma a hanata fita idan
kuma ba haka ba toh bata da lafiya, yana kuma lissafe da kwanaki jira yakeyi sai ya rage saura kwanaki ta
fara period ɗin ta na ƙarshe sannan zaije ya mayar da ita sai dai su mutu da baƙin ciki a lissafi kuma yau
saura kwana goma sha biyu ya aiwatar da shirinsa tunda saura kwana sha biyar a calendar ta da take
cikin wayarsa sai kuma kwatsam gata a yanayin da bai tsammaci ganinta ba ita ashe tuni tayi move on
har ta buɗe sabon babi a rayuwarta.
"Ba zai yuwu ba, ba zan taɓa barinki ba Halima. Kece silar lalacewar komai dan haka duk yanda rayuwa
ta juya tare zamu fuskanceta".
Daga Airport ɗin kai tsaye store suka wuce, a hanya Jalilah take ce masa
"Amma ban taɓa zaton Sudais zai iya cin amanata ba"
"Ai kallonki kawai nakeyi, ban fahimci ko rashin yarda bane ko menene ya saka ni baki bani keys ɗin
gurin ba kika bawa wani, gashi yanzu abinda ya faru" ya faɗa ba tareda ya kalleta ba. Jalilah dake danna
waya ta ɗaga kai ta kalleshi haɗi da yin ƙaramin murmushi amma bata ce komai ba. Da suka isa shi ya
riƙe mata jakarta, ajiyar zuciya mai nauyi ya sauke sanda ya zura mata keys ɗin daya zare ranar da zata
koma Abuja yabi bayanta kamar yana wani murmushi irin na samun nasara.
Bai zaci komai zai zo masa da sauƙi ba, ana gobe zata tafi wancan zuwan da tayi suka zo ta nuna masa
store ɗin da kuma kayan da aka sauke ta kuma nuna masa Sudais da tace ɗan ƙawar Momynta ne store
ɗin na Babansa ne ya basu aro. Ko a fuska bai nuna mata jin haushi ba sanda ta maidawa da Sudais ɗin
muƙulli da zasu tafi a hanya tana ta yabon yaron da irin amanarsa ransa ya ƙara ɓaci ya ringa ji kamar
jurwaye take masa mai kamar wanka wato shine mara amana kenan?
A mota ya tsinci muƙullin bayan ya dawo daga kaita Airport, har yayi niyyar kiranta kuma ya fasa da
daddare kuwa sai gashi ta kirashi akan yaje ɗakin data zauna ya duba mata ta manta spare keys na store
da Sudais ya bata, har yayi niyyar ya ce mata suna gurinsa kuma kawai ya fasa yace mata toh kawai, da
safe kuwa bai ko je Hotel ɗin ba ya kirata yace yaje an duba basu ga komai ba daga nan kuma zuciyarsa
ta fara raya masa akan ya ɗibi wasu daga cikin kayan ya siyar tunda yana tsaka da buƙatar kuɗi kuma
babu yanda za'ayi asirinsa ya tonu tunda dai ba'a sakashi a cikin sabgar ba.
Sai da ya saita hanya ta yanda ba wata ƙura da zata iya biyo baya kafin ya fitar da kayan ya karɓi
kuɗaɗen sa yake ta kashe gararin gabansa dasu, ko da yake a yanzu yanda yake ji baya tsoron Jalilan ta
sani dan a shirye yake domin daga yanda Alhaji Lawan yake threatening nasa ya san dole allura zata tono
garma duk kuma abinda zai faru ba dai za'a kashe shi ba kuma ba zai kullu ba dan shari'a yanzu kuɗi ce
kuma ya shirya shiyasa ko da ya tura masa da message jiya akan kowanne lokaci za'a iya kawo masa
sammaci mayar masa amsa yayi da cewa
Bayan sun gama da can suka kama hanya yana murmushin da shi kaɗai ya san ma'anar sa ya tambayeta
ina zai kaita yanzu?
"Muje can gida na huta tukunna idan yamma tayi sai ka kaini gidan Hajja na gaisheta kwanaki da yawa ko
a waya idan na kira bana samunta" ta faɗa tana lafewa a cikin kujera. Gabansa ya faɗi, wai mai take nufi
da mayar da gidansa gurin saukarta yanzu? Amma dai bai ce mata komai ba ya kama hanya abinda ya sa
bai damu sosai ba ya san zuwa yanzu Zulaiha ta tafi gidan Hajja tunda sunyi magana tun sanda zai fito ta
faɗa masa zataje.
Clashing sukayi da wata mota suna shiga layin ita kuma tana fita sai da suka wuce ƙwaƙwalwarsa ta
tariyo kamar fuskar Zulaiha ya gani a gaban motar, ita kanta motar sai yaga kamar ya santa a wani guri
amma ya manta a ina ne. Saida yayi parking Jalilah ta fita ta wuce part ɗin sa kafin ya kira Zulaiha.
"Kina ina?" Ya tambayeta bayan data amsa daga can tace masa
"Gidan Umma kuma? Baki tafi gidan bikin ba kenan?" Ya sake tambayarta bayan daya sauke ajiyar zuciya
ta samun nutsuwa. Sanar masa tayi wai Umman ce bata jin daɗi tana shiri zata fita Nuratu ta kirata shine
ta fara zuwa can gidan kuma ta kira wayarsa ta gaya masa amma bata sameshi daga nan sukayi sallama
bayan yace ta zauna a gidan Umman kawai ta kula da ita zaije ya ɗakko ta bayan isha'i.
Ganin Jalilah ta fito ya saka yayi saurin kashe wayar yana kallonta, ta yamutsa fuska ta ce
"Na fasa ka kaini Hotel kawai". Bai damu ba suka sake fita, yana tareda ita har gurin goma kafin ya mata
sallama ya biya gidansu Zulaiha ya ɗauketa suka wuce gida.
Washe gari bayan an sakko daga sallar Juma'a aka ɗaura auren Fadila da angonta Alhaji Ahlan. Kusan
suman zaune Bilal yayi lokacin da sukayi arba da angon Fadilan, mutumin daya siyi gidan Jalilah, wanda
ya biyo Zulaiha ranar da sukaje siyan shawarama kenan gidan ne za'a saka Fadila a ciki. Ji yayi kansa ya
na nema ya kama ciwo ya sulale ya fita daga masallacin yana shiga mota wayarsa ta fara ƙara ganin
Zulaiha ce ya ɗauka a taƙaice ta sanar masa wai yayi baƙi, ya tambayeta su waye tace wai bata sansu ba
Mace da Namiji ne.
"Toh ke mai kika zauna yi dama baki taho gidan bikin ba?" Ya tambayeta, daga can tace
Bai gane motar daya gani a ajiye ba dan haka shima yayi parking a waje ya kuma tsaya yaƙi shiga gidan
wani abu mai kama da tsoro ko fargaba ya ɗarsu a ransa, to wai wane baƙo ne haka da shi ba zai kirashi
a waya ba sai dai Zulaiha? Kuma da yace ta basu waya yaji su waye suka ƙi karɓa wai surprise zasu yi
masa. Ƙarfin hali yayi ya buɗe gidan ya shiga yana ayyana koma dai menene ya san ba abin cutarwa bane
tunda bai ji wata fargaba ko tsoro tattare da Zulaihan ba.
Takalmin mace da namiji, bai gane na namijin ba amma na macen tsinin takalman kawai ya gani ya
fahimci na wanene, gabansa ya yanke ya faɗi lokaci ɗaya kuma kansa ya sara, cikin takatsantsan kamar
wani ɓarawo ya juya da niyyar komawa muryar Zulaiha da yaji a bayansa ta saka yaci burki ya shiga
mayar da numfashi kamar wanda yayi gudu.
"Allah ya so ka da kunyi saɓani" ta faɗa, sai da yayi matuƙar ƙoƙarin gurin saita yanayinsa kafin ya juya ya
kalleta yana ɗan murmushi ya ce
"Ina baƙin?"
"Suna ciki shirin tafiya ma sukeyi, gaka nan gaka nan tun ɗazu sai kace wanda ya taho daga Kaduna ai da
sun tafi ka huta kuma ga wani saƙon can an kawo maka sammaci daga kotu" ta sake faɗa hankali kwance
ta wuce shi ta shige ɗakin Solar. Nepa aka ɗauke shine ta fito zata canza ta ganshi dan basu ji motsin
buɗe get ɗin ba ma.
Dafe kansa daya sake sarawa yayi yana nanata sammaci a zuciyarsa, Sai da ya ga zata fito kafin ya lallaɓa
ya nufi falon yana ƙaƙalo murmushi a ransa yana haɗa kalaman da zaiyi amfani dasu gurin yi musu
magana, Hafiz da Jalilah suka ɗaga kai a tare suka kalle shi haɗi da amsa masa sallama. Ya saki
murmushin yaƙe ya nufi Hafiz ya bashi hannu suka gaisa yana cewa
"Lallai kuwa an bani babban surprise, kuma da na san kaine da zance mata karta buɗe maka ƙofa"
Murmushin daya saka zuciyar Bilal fara gudun wuce ƙa'ida tayi kafin ta ce
"Ni da aka ɓoyewa amaryar ai ni naci albarkacinka". Ya haɗiye miyau kafin ya samu guri ya zauna yana
kallonta ya ce
"Zuwana kenan" ta bashi amsa tana gyara zama idonta akansa. Gyara zama yayi yana murmushin da
gara kawai a bashi fili ya fashe da kuka, magan yake so yayi amma wai duk tarin kalaman kare kai daya
ke da haddarsu a ka duk wacce ya kamo sai ta zille ya rasa kalaman da zai haɗa yayi magana sai kawai
yayi shiru ya sadda kai ƙasa kamar wanda Alƙali ya tsura. Can ya miƙe ganin ba'a ajiye musu ko ledar
pure water ba ya shiga kiran Zulaiha, tana ƙofar ɗakin Solar tana replying message ɗin da Ahlan ya turo
mata.
Sunyi akan zasu haɗu yau tunda zataje gidan Hajja tana tsaka da shiri baƙin Bilal ɗin sukazo haushin rusa
mata plan ya sa ko ruwa bata basu ba suna zaune sama da awa guda kenan suna jiransa. A bakin ƙofa
suka haɗu zata shiga shi kuma zai fito yayi ƙasa da murya yana ce mata
"Babu wani abun taɓawa ne a gidan da ba ki basu ba naga ko ruwa ma baki ajiye musu ba?"
"Babu, ruwa kuma pure water muke dashi kuma naga su ɗin ba kalarsa bane shiyasa ban basu ba" ta
bashi amsa, ya maka mata harara ya ce
"Ina dambun naman dana gani jiya? Kuma yau kwana nawa dana siyo ruwa katan biyu? Nufinki kin
shanye ko me? Kuma ai akwai lemo a fridge kawai kice so kike ki wulaƙanta ni shiyasa kika wulaƙanta
baƙi na" yayi tsaki ya koma ciki tabi bayansa. Kitchen suka shiga ya ɗauki try ya kwashi ruwan da tace
babu dukda babu sanyi ya ɗora akai, da mamaki ya kalleta bayan daya buɗe fridge ɗin; lemuka kala kala
a ciki harda Champagne. Gefe ta ɗauke kai, yayi ƙwafa ya kwashi lemukan ya haɗa da cake ɗin daya gani
ya fita ya ajiye musu.
Hafiz da Jalilah suka bishi da kallo, dariya ce ta kama Hafiz ya danneta amma dukda haka saida wata ta
fito sai ya fake da tari Bilal ya shiga yi masa sannu kafin ya koma ya kofuna ya ajiye musu ya bi Zulaiha
data shige ɗaki da harara duk akan idon Hafiz, sai ya girgiza kai kawai ya ɗauki kofi ya tsiyaya lemo ya
miƙawa Jalilah bata karɓa ba ta masa alamar aa da hannu tana cigaba da danna waya, ya karɓi kaɗan
kafin ya kalli Bilal ya ce
"Suna can gurin Mamansu" ya bashi amsa yana satar kallon Jalilah. Hafiz ya sake cewa
"Allah sarki, kwanaki na ganta kuwa a Alpen ina ta ɗaga mata hannu amma bata lura da ni ba, ta canza
sosai ta ƙara kyau da farko ma nayi tantamar ita ɗin ce kuwa sai da naga ƙaninta sannan na yarda ita ɗin
ce dagaske, gaskiya zawarci ya karɓeta idan ba'a faɗa bama zaka ɗauka budurwa ce wlh".
"Hmmm" kawai Bilal ya iya faɗa take kuma haushin Hafiz ɗin ya kamashi amma dai bai nuna ba yaci gaba
da satar kallon Jalilah dake ta danna waya alamar wani abun take rubutawa. Kiran sallar la'asar da aka
farayi yasa ta miƙe kamar wacce aka tsikara tana kallon Hafiz tace
"Muje ko?"
"Wai mai ya faru ne gaba ɗaya kin canza ba kamar yanda muka fito ba?" Hafiz ya tambayeta. Ta kalli Bilal
kafin ta mayar da kallonta kan Hafiz tayi murmushi tace
"Na gaya maka maganar kayan da aka satar mana a store shine duk ya canza mun mood" ta faɗa tana
langwaɓar da gefe kai. Mota ya rakasu basu ja sallamar da nisa ba suka wuce shi kuma ya jingina da ƙofa
yana mayar da numfashi. Ta faru ta ƙare anyi wa mai dami ɗaya sata, shi dama ya daɗe yana hasashen
shigo shigo ba zurfi kawai Hafiz yake yi masa da yakeyi kamar bashida masaniyar komai akan alaƙarsu,
idan ma kuna dagaske ne bai sani ba toh yau kam ya san Jalilah ta gama farke masa laya shiyasa suka
haɗo kai suka zo su ƙureshi amma ba zaiyi saurin kaiwa ƙasa ba dole ya nemi mafita domin shirun da
Jalilah tayi ya sani tabbas ba alkhairi bane.
Ciki ya koma yana zura kai sukayi karo da Zulaiha dake shirin fitowa, tayi baya ta dafe kai kafin tayi tsaki
ta raɓeshi har tana tureshi ta fice ya bi bayanta da kallo. Ɗakinsa ya shiga ya ringa safa da marwa tunani
kamar kansa zaiyi bindiga ya tarwatse, yanzu ina zai kama? Jalilah tasan yayi aure da alama kuma tana
da masaniya akan shi ya ɗauki kayan idan ma kuma bata sani ba toh tabbatas tana dabda sani bai kuma
san irin matakin da zata ɗauka akan hakan ba, ga Alhaji Lawan ya makashi a kotu shi yanzu ina zai tsoma
ransa yaji daɗi a faɗin ƙasar nan?
Tsabar ruɗin da yake ciki bai tuna baiyi sallar la'asar ba sai da yaji ana kiran sallar magriba tukunna yayi
alwala ya haɗa su yayi. Yana nan zaune gida shi kaɗai har ƙarfe goma Hajja harta gaji da kiransa tun
magriba wai suzo suyiwa Fadila faɗa kafin a tafi rakata ko faɗan mai zaiyi mata oho?
Ganin har ƙarfe goman Zulaiha bata dawo ba ya sa ya kirata tace masa suna gidan Amarya ba'a tafi kaita
da wuri bane amma yanzu zasu taho. Haka nan zuciyarsa ta raya masa wani abu take kuma yayi na'am
da hakan nan da nan ya shiga haɗa abinda zai buƙata a yar jaka, yana haɗa kayan yaji tsayuwar mota a
ƙofar gidan, yanda kasan mara gaskiya ya fita da sauri ya leƙa.
A ƙofar gidan motar ta tsaya, ganin an buɗe ƙofa kuma ya saka mai motar yayi gaba, tsaki ya koma ciki
amma bai rufe ƙofa ba yana kallon motar dake kunne har sannan. Kusan minti uku yana tsaye kafin ya
koma ciki ya ɗauko jakar ya saka a mota ya buɗe Get ya fice.
A daren ya kama hanyar Minjibir, sai da ya nemi abinci yaci dan yunwa yake ji sosai kafin ya karɓi key ɗin
ɗaki ya shiga. Wayarsa ya fara kashewa ya saka a cikin drawer bayan ya turawa da Zulaiha saƙo akan
tafiyar gaggawa ta sameshi ta tafi gida idan ya dawo zaizo ya ɗauketa sannan yayi wanka ya kwanta
bacci.
JALILAH
Tun daga sanda ta tabbatar da yayi blocking ɗin ta ta gasgata abinda zuciyarta ta daɗe tana raya mata
akan Bilal yana so yayi amfani da ita ne kawai ya cimma burinsa sannan ya watsar da ita kamar yanda ya
yiwa matarsa Halima. Harga Allah da aure take son Bilal dukda banbancin matsayi da yake tsakaninsu
amma da yake shi So babu ruwansa da wannan tunda ta ganshi taji yayi mata, tayi masa uzuri a lokacin
daya nuna mata cewar ba zai iya aurenta ba wannan dalilin ya saka ta buɗe masa bakin aljihunta a
ganinta rashin wadatace ta saka yace ba zai aureta ɗin a lokacin ba amma a maimakon aure sai ya bijiro
mata da abinda take ƙoƙarin bari harta yanke hukuncin auren nasa.
Tabbas Bilal shi ya fara nemar su ƙulla alaƙa ba kuma tayi musu ba ta biye masa, irin yanda kuma yake
tafi da ita da jin daɗin da yake bata ya saka bata ƙyashi yi masa komai dashi da mahaifiyarsa da tun
haɗuwar farko ta fahimci ƙwadayyace kuma a gurinta Bilal ɗin yayi gadon ƙwadayi.
Sau tari zuciyarta ta kan raya mata tarayyarsu bata gaskiya bace yana binta ne domin cikar buri tamkar
yanda ya yiwa matarsa Halima har wasu lokutan ta kan yi yunƙurin datse alaƙar amma sai ta kasa, daga
ƙarshe ta yaƙi kanta ta kuma tilastawa kanta yarda dashi da amincewa da duk zancen daya zo mata dashi
wanda sau da yawa ta kan tuhumin kanta akan hakan, abinda ta yarda dashi Bilal ɗin yana da wata
baiwa ta iya yaudara da asirce zuciyar mace shiyasa ko da ace tayi niyyar yaƙar zuciyarta ta rabu dashi sai
ta kasa.
A karo na biyu ta sake bijiro masa da maganar aure wanda wani babban dalili ya janyo hakan ta kuma
bashi sharaɗin idan har zai aureta toh fa sai dai ya rabu da matarsa wanda bai musa hakan ba kuma ya
amince har suka fara shirye-shirye.
Ta siyi gida wanda tayi niyyar mallaka masa ya sakata a ciki idan sunyi aure, shagunan da Mamanta ta
siya mata su kansu shi taso ta mallakawa domin tana so ya tsaya da ƙafarsa idan sunyi aure bata so ya
zamana ita zata cigaba da ɗaukar ɗawainiyarsa.
A hannun Hafiz ta siyi gidan kuma a lokacin ta faɗa masa alaƙar da take tsakaninta da Bilal harda
matsayin da suke kai a lokacin, batayi mamaki yanda Hafiz ɗin yace mata ya sani ba domin alaƙarta da
Bilal a bayyane take. A lokacin ya ce mata
"Ki kula dai domin KURA A RUMBU, ABAR TSORO CE" bata damu ba dan bata ma san ma'anar karin
maganar ba, sanda ya bata takardun gidan data shaida masa Bilal ta siyawa, a lokacin ne ya ce mata
"Yanzu bakya tsoron duk bayan kin gama kyautata masa ya guje ki tamkar yanda yayiwa matarsa? Jalilah
Bilal ba mutumin kirki bane na shaida hakan, ta silata kika sanshi, daga sanda kika buɗe masa ido da kuɗi
na zama mara amfani a gurinsa kamar yanda ya wulaƙanta matarsa, ina baki tabbacin kema haka zai
watsar da ke da zarar ya samu wadda ta fiki dan haka kiyiwa kanki tunani. Bance mutum baya canzawa
ba, ta yuwu dagaske yake sonki kuma ba zai butulce miki ba amma kada ki zura jiki domin duk alkhairin
da kikayi masa ba zai kai wanda matarsa tayi masa ba kuma daga ƙarshe ya saka ƙafa ya tankwaɓe"
Ganin da Halima tayi musu a gidansa ya sakw tabbatar mata da tabbas Bilal ɗin ba mutum bane domin
bata tsammaci bayan hakan kunya da nauyin matarsa zai bari ya cigaba da wata alaƙa da ita ba sai gashi
a daren ranar ma sai da yaje gurinta, ta ringa hasaso ace ita ce Haliman a lokacin tabbas babu abinda zai
hana ta kulle ƙofa ta kunna musu wuta sai dai duk abinda zai faru ya faru amma a maimakon haka sai
kawai ta juya ta fita tana kuka wannan al'amarin ya saka ta canza niyyarta ta aurensa domin kuwa ta
tabbatarwa da kanta Bilal ɗin ba miji bane kamar kuma yanda Hafiz ya sha faɗa zai iya aikata komai akan
kuɗi.
Da wannan ta wuce Dubai a lokacin kuma har ranta ta yanke rabuwa dashi ta gaske. Ita sam bata ma
ankare da yayi blocking ɗinta ba dan bata nemeshi ba sai da aka kwana biyu kawai Hafiz ya kirata yana
gaya mata wai Bilal ya siyar da gida. A lokacin ta sake tsinkewa da lamarinsa, dukda kafin ta taho dama
ta fara zargin wani abu akan zancen renovation data bashi kuɗi ayi amma da yake ta mata hanya-hanya
tunaninta sai ya tafi akan ya kashe kuɗin ne kawai ba'ayi aikin ba ashe shi mai ɗungurungun yayi ya siyar
da gidan.
Ta jinjinawa basirar Hafiz daya shaida mata takardun hannun Bilal fake ne, yayi zargin haka kuma ya sani
idan ya gaya mata ba zata yarda ba shiyasa yayi shiru ya barta taga abinda yake haska mata da kanta.
A lokacin dukda Hafiz ya ce karta nuna masa komai amma ta kasa, ta ringa nemansa ta duk wata kafa
amma ta gagara samunsa, ya rufe layinta kuma idan ta kira da wata number suma basa shiga alamar nan
ma ya toshe kira ba zai shiga wayarsa da lambar da bai yi saving ba.
A haka labarin sakin Halima da auren da yayi tun tana Nigeria ya sake riskarta. Da kuɗinta ya auro wata
ya siyi gida da kuɗin gidanta zai sakata a ciki, bata gama warkewa daga wannan shock ɗin ba Hafiz ya
sake kiranta wai Bilal ya kai masa tallan shagunanta, ta shiga tambayar kanta a ina ya samu takardun
shagunan? Domin dai bata bashi ba. Ta birkice ƙaramar akwatinta wacce takaddun suke ciki nan suka ce
ta ɗauke su in da ta ajiye hakan kuma ya ankarar da ita tabbas ɗauka yayi, yanzu da ba Hafiz ɗin ya kaiwa
ba shikenan ya dirata da ka bata ci ba bata sha ba.
Ta daɗe tana lissafa ta inda ya kamata ta rama, yana ɗaukar kansa mai wayau ya kamata ta koya masa
hankali ta muna masa wayon banza gareshi lissafinsa kuma ba daidai yake tafiya ba. Akan haka ta shirya
dawowa, ta hillaceshi da abinda ta san ba zai kaucewa ba wato kuɗi sai gashi kuwa yayi unblocking ɗinta
da kansa.
Abu na farko data farayi shine siyar da gidan daya rigada ya ci kuɗinsa ga tsohon abokin harkarta Ahlan.
Abinda ya rabasu shi ɗin ya fiya tsalle-tsalle sannan kuma yana shan giya, ita kuma duk namijin da zata
kula ta fi so ya zama ita take da iko dashi shiyasa tafi harka da waɗanda tafi kuɗi a yanda zata ringa
juyasu yanda take so. Ahlan matashi ne da yake cikin late thirties ɗin sa, yana da kuɗi sosai yana kuma
kashewa mata su tamkar a bishiya yake tsinkosu. Tantiri ne na gaske, ko bunsuru albarka a neman mata.
A hanyar dawowa suka haɗu a jirgi hira tayi hira yake bata labarin wata yarinya mai shegen taurin kai
daya haɗu da ita yayi yayi taƙi bashi haɗin kai shi kuma ya rantse tunda yawunsa ya tsinke sai ya
ɗanɗana dan haka yanzu ya yanke shawara zai aureta daya samu biyan buƙatarsa ya saita mata hanya.
Tana jin haka tace masa ai kuwa tana da gida na siyarwa, da farko ya ce mata Aa, auren da ba zai wuce
na kwana ɗaya ba da an ɗaura zai fanshe kuɗinsa ya saita mata hanya sai kuma bayan kwana biyu da yin
haka ya kira wai yana son gidan ba wani ja in ja ya tura mata kuɗinta ya karɓi Original takardu a hannun
Hafiz.
Wani abin al'ajabi kuma bayan sun bar gidan Bilal ɗin tana duba status taci karo dana ɗaurin auren
Ahlan, kawai ta fashe da dariya ba shiri ganin wacece Amaryar, Fadila fa ƙanwar Bilal lallai sata ta saci
sata.
[5/28, 11:06 PM] Hauwa Galadima: ❤️*ƊANLARABAWA INVESTMENT! Kyau Da Ƙima A Hannunku!* ❤️
*Muna tura kayanmu ko'ina a fadin Nijeriya da ƙasashen ƙetare. Cikin mutuntaka da cika alƙawari in sha
Allah*
https://chat.whatsapp.com/Loht5sGuLJO3LXYE9OkqNs
*Za ku more da kallon kayayyaki na ƙawa bisa ingantaccen farashi da rahusa mai kama da kyauta. Sayen
nagari, mayar da kuɗi gida.*
*KURA A RUMBU*
*Wattpad @MaryamahMrsAm*
*TikTok @Maryamfarouk_Ummu-mahir Novels*
*Ban yarda wani ko wata ya juya mun labari ta kowacce siga ba tare da izini na ba*
*Kuɗin karatu yana wakiltar mutum ɗaya ne, kiji tsoron Allah karki ɗauki hakkina ta hanyar fitar mun da
littafi*
*KURA A RUMBU littafin kuɗi ne, a biya naira 800, biya a asusun*
*7061838488*
*Opay*
*PAGE 57*
BILAL
Yana kwance a gida Hajja ta kirashi wai ya kawo musu kayan miyan da za'ayi tuwon ɗaurin auren Fadila
da za'a ɗaura a gobe Juma'a. Da yake a tsini suke yayi mata laifi shiyasa bai musa ba ya tashi ya tafi
kasuwar Yankaba ya yiwo musu cefanen ya tafi ya kai. Zagayewa yayi yaje ya samu Kawu Ɗayyabu,
Yayan Hajja ne da suke uba ɗaya da yake mutum ne mara ɗaukar raini shiyasa duk rashin mutunchin
Hajjan take shakkarsa ko da wasa kuma bata bari wani abu ya gilma a tsakaninsu shi Bilal ɗin yaje ya
samu ya gaya masa zancen auren Fadilan da yanda ita da Hajja suke shirya komai basu saka kowa a ciki
ba.
"Wane irin rashin hankali ne haka? Ita Hajara wai sai yaushe zata girma ta fara abu irin na mutane masu
hankali? Dama mace ta taɓa aurar da kanta ne ko kuwa uwa ce take bayar da auren yarta? Daga ku har
uwar taku sai a rasa wayafi wani tunani, kaima nan zancen ya iskeni ance ka saki uwargidanka dama
kuma duk ina jin labarin irin ɗiban albarkar da kai da uwarka da yan uwanka kuka ringayi mata, toh
hausawa dai suka ce duk wanda bai yi sharar kasuwa ba zaiyi ta masallaci dan haka tun wuri in dai da
gyara ina baka shawarar ka dawo da matarka dan ba zaka gane illar da kayiwa kanka ba sai a gaba. Ita
kuma Hajara zan kirata" akan haka suka rabu.
Washe gari kuwa ya kira Hajjan yace taje gida ta sameshi yana son magana da ita ba musu kuma ta
shirya ta tafi yayi mata tatas sannan yace su dakatar da duk wani shiri da sukeyi Fadila ta gayawa yaron
yaje ya gaida iyayenta maza tukunna idan sukayi bincike sukaga bashida wani aibu sannan su bashi
lokacin da zai turo ayi magana.
Ta koma gida ta saukewa Bilal tijarar da batayi a gaban Kawu Ɗayyabun ba tunda shi ya kai masa gulmar
amma kuma dole tayi abinda yace ta kira Baba Sani yaƙi ɗauka sai a wayar matarsa ta sameshi shima
daƙyar ya karɓa sukayi magana tana gaya masa dalilin kiran kuma yace babu shi a cikin wannan magana
"Kin manta kashedin da kika mun akan yayanki Hajara? Ai ko ni na kawo rashin zuciya duniya ba zan sake
tsoma baki cikin abinda ya shafeku ba, bani kaɗai bane ɗan uwan ubansu ai muna da yawa ki nemi wani"
ya bata amsa daga haka kuma ya katse wayar. Daga ƙarshe dai sai babban yayansu Bilal ɗin Alhaji Salisu
ta taka har gida ta samu dan Kawunnansu duk wanda ta kira sai yace yana Aa dan kowa nada labarin
ɗibar albarkar da tayiwa Baba Sani da Aminu akan zancen Bilal.
Fadilan ce ta raka shi gurin Yayan nasu akayi sa'a ashe ma sun san juna akwai hulɗa ta cinikayya
tsakaninsu, kamar yanda ya cewa Hajja a tsayin lokacin daya san Alhaji Ahlan saurayin Fadilan ya san
mutumin kirki ne kuma yayi tambaya akansa an tabbatar masa da mutumin kirki be kuma yana da asali
mai kyau dan Babansa nada sarauta acan Zarian ma. Ya taɓa aure sau biyu, ta farkon rasuwa tayi suna
da yara biyu Mace da Namiji ta biyun kuma rabuwa sukayi, shikenan aka cigaba da shirin biki, maza
sunzo sun sake kawo kuɗin aure da Sadaki bayan wanda ya rigada ya bata.
Bayan ya gama sauke musu kayan miyan a tsaitsaye suka gaisa ya wuce saboda zaije ya ɗakko Jalilah ne
a airport.
Motarsa ce taƙi tashi, ganin zata ɓata masa lokaci ya barta ya kira wani abokinsa dake siyar da motoci a
Gadon ƙaya yace zaizo ya karɓi mota yanzu, da wannan saurin ya faɗa Adaidaitan daya gani a bakin layin
ashe rabon su haɗu da Halima ne.
Harga Allah har ya zauna bai san ita bace a ciki dan hankalinsa na kan wayarsa sai da tayi magana kafin
yaji muryarta ya kuma yi mamaki matuƙa amma bai nuna hakan ba har ransa kuma sai yaji rashin daɗi da
bai san dalilin sa musamman ganin da yayi mata ta canza tayi wani kyau fatarta har wani ƙyalli takeyi
baka buƙatar a faɗa maka ta samu hutu da kwanciyar hankali. Shi da yake nan yana tunanin tana can
cikin halin ƙaƙanikayi soyayyarsa ta hanata sakata ko wacce daƙiƙa cikin dakon kiranta yakeyi domin ya
tabbatar ba zata taɓa iya rayuwa mai ma'ana ba tareda dashi ba.
Daɗewar da akayi yanzun ma bata waiwayeshi ba ya sani cikin biyu, ko dai an ƙwace wayarta ne tunda
kowa nata ba son su tare yakeyi ba ya san zasu iya ƙwacewa dan kar ta kirashi kuma a hanata fita idan
kuma ba haka ba toh bata da lafiya, yana kuma lissafe da kwanaki jira yakeyi sai ya rage saura kwanaki ta
fara period ɗin ta na ƙarshe sannan zaije ya mayar da ita sai dai su mutu da baƙin ciki a lissafi kuma yau
saura kwana goma sha biyu ya aiwatar da shirinsa tunda saura kwana sha biyar a calendar ta da take
cikin wayarsa sai kuma kwatsam gata a yanayin da bai tsammaci ganinta ba ita ashe tuni tayi move on
har ta buɗe sabon babi a rayuwarta.
"Ba zai yuwu ba, ba zan taɓa barinki ba Halima. Kece silar lalacewar komai dan haka duk yanda rayuwa
ta juya tare zamu fuskanceta".
Daga Airport ɗin kai tsaye store suka wuce, a hanya Jalilah take ce masa
"Amma ban taɓa zaton Sudais zai iya cin amanata ba"
"Ai kallonki kawai nakeyi, ban fahimci ko rashin yarda bane ko menene ya saka ni baki bani keys ɗin
gurin ba kika bawa wani, gashi yanzu abinda ya faru" ya faɗa ba tareda ya kalleta ba. Jalilah dake danna
waya ta ɗaga kai ta kalleshi haɗi da yin ƙaramin murmushi amma bata ce komai ba. Da suka isa shi ya
riƙe mata jakarta, ajiyar zuciya mai nauyi ya sauke sanda ya zura mata keys ɗin daya zare ranar da zata
koma Abuja yabi bayanta kamar yana wani murmushi irin na samun nasara.
Bai zaci komai zai zo masa da sauƙi ba, ana gobe zata tafi wancan zuwan da tayi suka zo ta nuna masa
store ɗin da kuma kayan da aka sauke ta kuma nuna masa Sudais da tace ɗan ƙawar Momynta ne store
ɗin na Babansa ne ya basu aro. Ko a fuska bai nuna mata jin haushi ba sanda ta maidawa da Sudais ɗin
muƙulli da zasu tafi a hanya tana ta yabon yaron da irin amanarsa ransa ya ƙara ɓaci ya ringa ji kamar
jurwaye take masa mai kamar wanka wato shine mara amana kenan?
A mota ya tsinci muƙullin bayan ya dawo daga kaita Airport, har yayi niyyar kiranta kuma ya fasa da
daddare kuwa sai gashi ta kirashi akan yaje ɗakin data zauna ya duba mata ta manta spare keys na store
da Sudais ya bata, har yayi niyyar ya ce mata suna gurinsa kuma kawai ya fasa yace mata toh kawai, da
safe kuwa bai ko je Hotel ɗin ba ya kirata yace yaje an duba basu ga komai ba daga nan kuma zuciyarsa
ta fara raya masa akan ya ɗibi wasu daga cikin kayan ya siyar tunda yana tsaka da buƙatar kuɗi kuma
babu yanda za'ayi asirinsa ya tonu tunda dai ba'a sakashi a cikin sabgar ba.
Sai da ya saita hanya ta yanda ba wata ƙura da zata iya biyo baya kafin ya fitar da kayan ya karɓi
kuɗaɗen sa yake ta kashe gararin gabansa dasu, ko da yake a yanzu yanda yake ji baya tsoron Jalilan ta
sani dan a shirye yake domin daga yanda Alhaji Lawan yake threatening nasa ya san dole allura zata tono
garma duk kuma abinda zai faru ba dai za'a kashe shi ba kuma ba zai kullu ba dan shari'a yanzu kuɗi ce
kuma ya shirya shiyasa ko da ya tura masa da message jiya akan kowanne lokaci za'a iya kawo masa
sammaci mayar masa amsa yayi da cewa
Bayan sun gama da can suka kama hanya yana murmushin da shi kaɗai ya san ma'anar sa ya tambayeta
ina zai kaita yanzu?
"Muje can gida na huta tukunna idan yamma tayi sai ka kaini gidan Hajja na gaisheta kwanaki da yawa ko
a waya idan na kira bana samunta" ta faɗa tana lafewa a cikin kujera. Gabansa ya faɗi, wai mai take nufi
da mayar da gidansa gurin saukarta yanzu? Amma dai bai ce mata komai ba ya kama hanya abinda ya sa
bai damu sosai ba ya san zuwa yanzu Zulaiha ta tafi gidan Hajja tunda sunyi magana tun sanda zai fito ta
faɗa masa zataje.
Clashing sukayi da wata mota suna shiga layin ita kuma tana fita sai da suka wuce ƙwaƙwalwarsa ta
tariyo kamar fuskar Zulaiha ya gani a gaban motar, ita kanta motar sai yaga kamar ya santa a wani guri
amma ya manta a ina ne. Saida yayi parking Jalilah ta fita ta wuce part ɗin sa kafin ya kira Zulaiha.
"Kina ina?" Ya tambayeta bayan data amsa daga can tace masa
"Gidan Umma kuma? Baki tafi gidan bikin ba kenan?" Ya sake tambayarta bayan daya sauke ajiyar zuciya
ta samun nutsuwa. Sanar masa tayi wai Umman ce bata jin daɗi tana shiri zata fita Nuratu ta kirata shine
ta fara zuwa can gidan kuma ta kira wayarsa ta gaya masa amma bata sameshi daga nan sukayi sallama
bayan yace ta zauna a gidan Umman kawai ta kula da ita zaije ya ɗakko ta bayan isha'i.
Ganin Jalilah ta fito ya saka yayi saurin kashe wayar yana kallonta, ta yamutsa fuska ta ce
"Na fasa ka kaini Hotel kawai". Bai damu ba suka sake fita, yana tareda ita har gurin goma kafin ya mata
sallama ya biya gidansu Zulaiha ya ɗauketa suka wuce gida.
Washe gari bayan an sakko daga sallar Juma'a aka ɗaura auren Fadila da angonta Alhaji Ahlan. Kusan
suman zaune Bilal yayi lokacin da sukayi arba da angon Fadilan, mutumin daya siyi gidan Jalilah, wanda
ya biyo Zulaiha ranar da sukaje siyan shawarama kenan gidan ne za'a saka Fadila a ciki. Ji yayi kansa ya
na nema ya kama ciwo ya sulale ya fita daga masallacin yana shiga mota wayarsa ta fara ƙara ganin
Zulaiha ce ya ɗauka a taƙaice ta sanar masa wai yayi baƙi, ya tambayeta su waye tace wai bata sansu ba
Mace da Namiji ne.
"Toh ke mai kika zauna yi dama baki taho gidan bikin ba?" Ya tambayeta, daga can tace
Tsaki yayi ya kashe wayar kafin ya kunna motar yana tafe yana tunani wane mace da Namiji ne zasuje
gurinsa? Hafiz ya kawo da matarsa dan shi kaɗai ne dai yake tunani dukda baya zaton ganin Hafiz a
gidansa saboda tun ranar daya sanar masa daya saki Halima ɗan shirin da suka dawo yi ya sake ja baya
balle matarsa daya fahimci ta ma fishi ɗaukar ɗumi akan lamarin.
Bai gane motar daya gani a ajiye ba dan haka shima yayi parking a waje ya kuma tsaya yaƙi shiga gidan
wani abu mai kama da tsoro ko fargaba ya ɗarsu a ransa, to wai wane baƙo ne haka da shi ba zai kirashi
a waya ba sai dai Zulaiha? Kuma da yace ta basu waya yaji su waye suka ƙi karɓa wai surprise zasu yi
masa. Ƙarfin hali yayi ya buɗe gidan ya shiga yana ayyana koma dai menene ya san ba abin cutarwa bane
tunda bai ji wata fargaba ko tsoro tattare da Zulaihan ba.
Takalmin mace da namiji, bai gane na namijin ba amma na macen tsinin takalman kawai ya gani ya
fahimci na wanene, gabansa ya yanke ya faɗi lokaci ɗaya kuma kansa ya sara, cikin takatsantsan kamar
wani ɓarawo ya juya da niyyar komawa muryar Zulaiha da yaji a bayansa ta saka yaci burki ya shiga
mayar da numfashi kamar wanda yayi gudu.
"Allah ya so ka da kunyi saɓani" ta faɗa, sai da yayi matuƙar ƙoƙarin gurin saita yanayinsa kafin ya juya ya
kalleta yana ɗan murmushi ya ce
"Ina baƙin?"
"Suna ciki shirin tafiya ma sukeyi, gaka nan gaka nan tun ɗazu sai kace wanda ya taho daga Kaduna ai da
sun tafi ka huta kuma ga wani saƙon can an kawo maka sammaci daga kotu" ta sake faɗa hankali kwance
ta wuce shi ta shige ɗakin Solar. Nepa aka ɗauke shine ta fito zata canza ta ganshi dan basu ji motsin
buɗe get ɗin ba ma.
Dafe kansa daya sake sarawa yayi yana nanata sammaci a zuciyarsa, Sai da ya ga zata fito kafin ya lallaɓa
ya nufi falon yana ƙaƙalo murmushi a ransa yana haɗa kalaman da zaiyi amfani dasu gurin yi musu
magana, Hafiz da Jalilah suka ɗaga kai a tare suka kalle shi haɗi da amsa masa sallama. Ya saki
murmushin yaƙe ya nufi Hafiz ya bashi hannu suka gaisa yana cewa
"Lallai kuwa an bani babban surprise, kuma da na san kaine da zance mata karta buɗe maka ƙofa"
"Idan ni ba'a barni na shigo ba ai ba za'a hana uwarɗakinka shigowa ba ko ba haka ba Hajjaju?" Yayi
maganar yana kallon inda Jalilah ke zaune ta harɗe ƙafafu tana latsa waya sai ka rantse bata san da
wanzuwarsu a gurin ba.
Murmushin daya saka zuciyar Bilal fara gudun wuce ƙa'ida tayi kafin ta ce
"Ni da aka ɓoyewa amaryar ai ni naci albarkacinka". Ya haɗiye miyau kafin ya samu guri ya zauna yana
kallonta ya ce
"Zuwana kenan" ta bashi amsa tana gyara zama idonta akansa. Gyara zama yayi yana murmushin da
gara kawai a bashi fili ya fashe da kuka, magan yake so yayi amma wai duk tarin kalaman kare kai daya
ke da haddarsu a ka duk wacce ya kamo sai ta zille ya rasa kalaman da zai haɗa yayi magana sai kawai
yayi shiru ya sadda kai ƙasa kamar wanda Alƙali ya tsura. Can ya miƙe ganin ba'a ajiye musu ko ledar
pure water ba ya shiga kiran Zulaiha, tana ƙofar ɗakin Solar tana replying message ɗin da Ahlan ya turo
mata.
Sunyi akan zasu haɗu yau tunda zataje gidan Hajja tana tsaka da shiri baƙin Bilal ɗin sukazo haushin rusa
mata plan ya sa ko ruwa bata basu ba suna zaune sama da awa guda kenan suna jiransa. A bakin ƙofa
suka haɗu zata shiga shi kuma zai fito yayi ƙasa da murya yana ce mata
"Babu wani abun taɓawa ne a gidan da ba ki basu ba naga ko ruwa ma baki ajiye musu ba?"
"Babu, ruwa kuma pure water muke dashi kuma naga su ɗin ba kalarsa bane shiyasa ban basu ba" ta
bashi amsa, ya maka mata harara ya ce
"Ina dambun naman dana gani jiya? Kuma yau kwana nawa dana siyo ruwa katan biyu? Nufinki kin
shanye ko me? Kuma ai akwai lemo a fridge kawai kice so kike ki wulaƙanta ni shiyasa kika wulaƙanta
baƙi na" yayi tsaki ya koma ciki tabi bayansa. Kitchen suka shiga ya ɗauki try ya kwashi ruwan da tace
babu dukda babu sanyi ya ɗora akai, da mamaki ya kalleta bayan daya buɗe fridge ɗin; lemuka kala kala
a ciki harda Champagne. Gefe ta ɗauke kai, yayi ƙwafa ya kwashi lemukan ya haɗa da cake ɗin daya gani
ya fita ya ajiye musu.
Hafiz da Jalilah suka bishi da kallo, dariya ce ta kama Hafiz ya danneta amma dukda haka saida wata ta
fito sai ya fake da tari Bilal ya shiga yi masa sannu kafin ya koma ya kofuna ya ajiye musu ya bi Zulaiha
data shige ɗaki da harara duk akan idon Hafiz, sai ya girgiza kai kawai ya ɗauki kofi ya tsiyaya lemo ya
miƙawa Jalilah bata karɓa ba ta masa alamar aa da hannu tana cigaba da danna waya, ya karɓi kaɗan
kafin ya kalli Bilal ya ce
"Suna can gurin Mamansu" ya bashi amsa yana satar kallon Jalilah. Hafiz ya sake cewa
"Allah sarki, kwanaki na ganta kuwa a Alpen ina ta ɗaga mata hannu amma bata lura da ni ba, ta canza
sosai ta ƙara kyau da farko ma nayi tantamar ita ɗin ce kuwa sai da naga ƙaninta sannan na yarda ita ɗin
ce dagaske, gaskiya zawarci ya karɓeta idan ba'a faɗa bama zaka ɗauka budurwa ce wlh".
"Hmmm" kawai Bilal ya iya faɗa take kuma haushin Hafiz ɗin ya kamashi amma dai bai nuna ba yaci gaba
da satar kallon Jalilah dake ta danna waya alamar wani abun take rubutawa. Kiran sallar la'asar da aka
farayi yasa ta miƙe kamar wacce aka tsikara tana kallon Hafiz tace
"Muje ko?"
"Wai mai ya faru ne gaba ɗaya kin canza ba kamar yanda muka fito ba?" Hafiz ya tambayeta. Ta kalli Bilal
kafin ta mayar da kallonta kan Hafiz tayi murmushi tace
"Na gaya maka maganar kayan da aka satar mana a store shine duk ya canza mun mood" ta faɗa tana
langwaɓar da gefe kai. Mota ya rakasu basu ja sallamar da nisa ba suka wuce shi kuma ya jingina da ƙofa
yana mayar da numfashi. Ta faru ta ƙare anyi wa mai dami ɗaya sata, shi dama ya daɗe yana hasashen
shigo shigo ba zurfi kawai Hafiz yake yi masa da yakeyi kamar bashida masaniyar komai akan alaƙarsu,
idan ma kuna dagaske ne bai sani ba toh yau kam ya san Jalilah ta gama farke masa laya shiyasa suka
haɗo kai suka zo su ƙureshi amma ba zaiyi saurin kaiwa ƙasa ba dole ya nemi mafita domin shirun da
Jalilah tayi ya sani tabbas ba alkhairi bane.
Ciki ya koma yana zura kai sukayi karo da Zulaiha dake shirin fitowa, tayi baya ta dafe kai kafin tayi tsaki
ta raɓeshi har tana tureshi ta fice ya bi bayanta da kallo. Ɗakinsa ya shiga ya ringa safa da marwa tunani
kamar kansa zaiyi bindiga ya tarwatse, yanzu ina zai kama? Jalilah tasan yayi aure da alama kuma tana
da masaniya akan shi ya ɗauki kayan idan ma kuma bata sani ba toh tabbatas tana dabda sani bai kuma
san irin matakin da zata ɗauka akan hakan ba, ga Alhaji Lawan ya makashi a kotu shi yanzu ina zai tsoma
ransa yaji daɗi a faɗin ƙasar nan?
Tsabar ruɗin da yake ciki bai tuna baiyi sallar la'asar ba sai da yaji ana kiran sallar magriba tukunna yayi
alwala ya haɗa su yayi. Yana nan zaune gida shi kaɗai har ƙarfe goma Hajja harta gaji da kiransa tun
magriba wai suzo suyiwa Fadila faɗa kafin a tafi rakata ko faɗan mai zaiyi mata oho?
Ganin har ƙarfe goman Zulaiha bata dawo ba ya sa ya kirata tace masa suna gidan Amarya ba'a tafi kaita
da wuri bane amma yanzu zasu taho. Haka nan zuciyarsa ta raya masa wani abu take kuma yayi na'am
da hakan nan da nan ya shiga haɗa abinda zai buƙata a yar jaka, yana haɗa kayan yaji tsayuwar mota a
ƙofar gidan, yanda kasan mara gaskiya ya fita da sauri ya leƙa.
A ƙofar gidan motar ta tsaya, ganin an buɗe ƙofa kuma ya saka mai motar yayi gaba, tsaki ya koma ciki
amma bai rufe ƙofa ba yana kallon motar dake kunne har sannan. Kusan minti uku yana tsaye kafin ya
koma ciki ya ɗauko jakar ya saka a mota ya buɗe Get ya fice.
A daren ya kama hanyar Minjibir, sai da ya nemi abinci yaci dan yunwa yake ji sosai kafin ya karɓi key ɗin
ɗaki ya shiga. Wayarsa ya fara kashewa ya saka a cikin drawer bayan ya turawa da Zulaiha saƙo akan
tafiyar gaggawa ta sameshi ta tafi gida idan ya dawo zaizo ya ɗauketa sannan yayi wanka ya kwanta
bacci.
JALILAH
Tun daga sanda ta tabbatar da yayi blocking ɗin ta ta gasgata abinda zuciyarta ta daɗe tana raya mata
akan Bilal yana so yayi amfani da ita ne kawai ya cimma burinsa sannan ya watsar da ita kamar yanda ya
yiwa matarsa Halima. Harga Allah da aure take son Bilal dukda banbancin matsayi da yake tsakaninsu
amma da yake shi So babu ruwansa da wannan tunda ta ganshi taji yayi mata, tayi masa uzuri a lokacin
daya nuna mata cewar ba zai iya aurenta ba wannan dalilin ya saka ta buɗe masa bakin aljihunta a
ganinta rashin wadatace ta saka yace ba zai aureta ɗin a lokacin ba amma a maimakon aure sai ya bijiro
mata da abinda take ƙoƙarin bari harta yanke hukuncin auren nasa.
Tabbas Bilal shi ya fara nemar su ƙulla alaƙa ba kuma tayi musu ba ta biye masa, irin yanda kuma yake
tafi da ita da jin daɗin da yake bata ya saka bata ƙyashi yi masa komai dashi da mahaifiyarsa da tun
haɗuwar farko ta fahimci ƙwadayyace kuma a gurinta Bilal ɗin yayi gadon ƙwadayi.
Sau tari zuciyarta ta kan raya mata tarayyarsu bata gaskiya bace yana binta ne domin cikar buri tamkar
yanda ya yiwa matarsa Halima har wasu lokutan ta kan yi yunƙurin datse alaƙar amma sai ta kasa, daga
ƙarshe ta yaƙi kanta ta kuma tilastawa kanta yarda dashi da amincewa da duk zancen daya zo mata dashi
wanda sau da yawa ta kan tuhumin kanta akan hakan, abinda ta yarda dashi Bilal ɗin yana da wata
baiwa ta iya yaudara da asirce zuciyar mace shiyasa ko da ace tayi niyyar yaƙar zuciyarta ta rabu dashi sai
ta kasa.
A karo na biyu ta sake bijiro masa da maganar aure wanda wani babban dalili ya janyo hakan ta kuma
bashi sharaɗin idan har zai aureta toh fa sai dai ya rabu da matarsa wanda bai musa hakan ba kuma ya
amince har suka fara shirye-shirye.
Ta siyi gida wanda tayi niyyar mallaka masa ya sakata a ciki idan sunyi aure, shagunan da Mamanta ta
siya mata su kansu shi taso ta mallakawa domin tana so ya tsaya da ƙafarsa idan sunyi aure bata so ya
zamana ita zata cigaba da ɗaukar ɗawainiyarsa.
A hannun Hafiz ta siyi gidan kuma a lokacin ta faɗa masa alaƙar da take tsakaninta da Bilal harda
matsayin da suke kai a lokacin, batayi mamaki yanda Hafiz ɗin yace mata ya sani ba domin alaƙarta da
Bilal a bayyane take. A lokacin ya ce mata
"Ki kula dai domin KURA A RUMBU, ABAR TSORO CE" bata damu ba dan bata ma san ma'anar karin
maganar ba, sanda ya bata takardun gidan data shaida masa Bilal ta siyawa, a lokacin ne ya ce mata
"Yanzu bakya tsoron duk bayan kin gama kyautata masa ya guje ki tamkar yanda yayiwa matarsa? Jalilah
Bilal ba mutumin kirki bane na shaida hakan, ta silata kika sanshi, daga sanda kika buɗe masa ido da kuɗi
na zama mara amfani a gurinsa kamar yanda ya wulaƙanta matarsa, ina baki tabbacin kema haka zai
watsar da ke da zarar ya samu wadda ta fiki dan haka kiyiwa kanki tunani. Bance mutum baya canzawa
ba, ta yuwu dagaske yake sonki kuma ba zai butulce miki ba amma kada ki zura jiki domin duk alkhairin
da kikayi masa ba zai kai wanda matarsa tayi masa ba kuma daga ƙarshe ya saka ƙafa ya tankwaɓe"
Ganin da Halima tayi musu a gidansa ya sakw tabbatar mata da tabbas Bilal ɗin ba mutum bane domin
bata tsammaci bayan hakan kunya da nauyin matarsa zai bari ya cigaba da wata alaƙa da ita ba sai gashi
a daren ranar ma sai da yaje gurinta, ta ringa hasaso ace ita ce Haliman a lokacin tabbas babu abinda zai
hana ta kulle ƙofa ta kunna musu wuta sai dai duk abinda zai faru ya faru amma a maimakon haka sai
kawai ta juya ta fita tana kuka wannan al'amarin ya saka ta canza niyyarta ta aurensa domin kuwa ta
tabbatarwa da kanta Bilal ɗin ba miji bane kamar kuma yanda Hafiz ya sha faɗa zai iya aikata komai akan
kuɗi.
Da wannan ta wuce Dubai a lokacin kuma har ranta ta yanke rabuwa dashi ta gaske. Ita sam bata ma
ankare da yayi blocking ɗinta ba dan bata nemeshi ba sai da aka kwana biyu kawai Hafiz ya kirata yana
gaya mata wai Bilal ya siyar da gida. A lokacin ta sake tsinkewa da lamarinsa, dukda kafin ta taho dama
ta fara zargin wani abu akan zancen renovation data bashi kuɗi ayi amma da yake ta mata hanya-hanya
tunaninta sai ya tafi akan ya kashe kuɗin ne kawai ba'ayi aikin ba ashe shi mai ɗungurungun yayi ya siyar
da gidan.
Ta jinjinawa basirar Hafiz daya shaida mata takardun hannun Bilal fake ne, yayi zargin haka kuma ya sani
idan ya gaya mata ba zata yarda ba shiyasa yayi shiru ya barta taga abinda yake haska mata da kanta.
A lokacin dukda Hafiz ya ce karta nuna masa komai amma ta kasa, ta ringa nemansa ta duk wata kafa
amma ta gagara samunsa, ya rufe layinta kuma idan ta kira da wata number suma basa shiga alamar nan
ma ya toshe kira ba zai shiga wayarsa da lambar da bai yi saving ba.
A haka labarin sakin Halima da auren da yayi tun tana Nigeria ya sake riskarta. Da kuɗinta ya auro wata
ya siyi gida da kuɗin gidanta zai sakata a ciki, bata gama warkewa daga wannan shock ɗin ba Hafiz ya
sake kiranta wai Bilal ya kai masa tallan shagunanta, ta shiga tambayar kanta a ina ya samu takardun
shagunan? Domin dai bata bashi ba. Ta birkice ƙaramar akwatinta wacce takaddun suke ciki nan suka ce
ta ɗauke su in da ta ajiye hakan kuma ya ankarar da ita tabbas ɗauka yayi, yanzu da ba Hafiz ɗin ya kaiwa
ba shikenan ya dirata da ka bata ci ba bata sha ba.
Ta daɗe tana lissafa ta inda ya kamata ta rama, yana ɗaukar kansa mai wayau ya kamata ta koya masa
hankali ta muna masa wayon banza gareshi lissafinsa kuma ba daidai yake tafiya ba. Akan haka ta shirya
dawowa, ta hillaceshi da abinda ta san ba zai kaucewa ba wato kuɗi sai gashi kuwa yayi unblocking ɗinta
da kansa.
Abu na farko data farayi shine siyar da gidan daya rigada ya ci kuɗinsa ga tsohon abokin harkarta Ahlan.
Abinda ya rabasu shi ɗin ya fiya tsalle-tsalle sannan kuma yana shan giya, ita kuma duk namijin da zata
kula ta fi so ya zama ita take da iko dashi shiyasa tafi harka da waɗanda tafi kuɗi a yanda zata ringa
juyasu yanda take so. Ahlan matashi ne da yake cikin late thirties ɗin sa, yana da kuɗi sosai yana kuma
kashewa mata su tamkar a bishiya yake tsinkosu. Tantiri ne na gaske, ko bunsuru albarka a neman mata.
A hanyar dawowa suka haɗu a jirgi hira tayi hira yake bata labarin wata yarinya mai shegen taurin kai
daya haɗu da ita yayi yayi taƙi bashi haɗin kai shi kuma ya rantse tunda yawunsa ya tsinke sai ya
ɗanɗana dan haka yanzu ya yanke shawara zai aureta daya samu biyan buƙatarsa ya saita mata hanya.
Tana jin haka tace masa ai kuwa tana da gida na siyarwa, da farko ya ce mata Aa, auren da ba zai wuce
na kwana ɗaya ba da an ɗaura zai fanshe kuɗinsa ya saita mata hanya sai kuma bayan kwana biyu da yin
haka ya kira wai yana son gidan ba wani ja in ja ya tura mata kuɗinta ya karɓi Original takardu a hannun
Hafiz.
Wani abin al'ajabi kuma bayan sun bar gidan Bilal ɗin tana duba status taci karo dana ɗaurin auren
Ahlan, kawai ta fashe da dariya ba shiri ganin wacece Amaryar, Fadila fa ƙanwar Bilal lallai sata ta saci
sata.
*Wattpad @MaryamahMrsAm*
*Ban yarda wani ko wata ya juya mun labari ta kowacce siga ba tare da izini na ba*
*Kuɗin karatu yana wakiltar mutum ɗaya ne, kiji tsoron Allah karki ɗauki hakkina ta hanyar fitar mun da
littafi*
*KURA A RUMBU littafin kuɗi ne, a biya naira 800, biya a asusun*
*7061838488*
*Opay*
*PAGE 58*
HALIMA
Cike da haushin Dr Salman na koma gida ranar Juma'ar, haka nan ya san banda mu zasuyi meeting ɗin
amma ba'a gaya mana ba saida muka rigada muka je tukunna sannan babu damar tafiya haka mukayi
zaman banza har sha biyu kafin muka tashi. Dama-dama da na ji na samu nayi clearance ɗina kafin na
wuce gida.
Bayan sallahr magriba Anty Labiba tace mu shirya muje gidan Uncle Mudassir yaronsa na biyu Khalil ya
faɗi ɗazu da safe ya samu karaya, muna shirin fita Mama ta kirata tana tambayarta yaushe zamuje duba
Khalil ɗin tace mata yanzu sai tace toh mu biya mata mu tafi tare kawai.
Mun tarar da yan uwan Anty Ummi matarsa sunzo su da yawa dubiyar sun cika falon dan haka tace mu
shiga can falon Uncle Mudassir yana nan dama, tun daga bakin ƙofa na fara jin ƙamshin turarensa, ina
son turare shiyasa duk inda naji wanda yayi mun daɗe nake riƙe ƙamshin duk kuma idan na ji irinsa a
wani guri sai na tuna da asalin inda na fara saninsa.
Suna zaune kan two sitter dining dake gefe a cikin falon da farantan abinci a gabansu, Uncle Mudassir
har ya ci fin rabin nasa amma shi bai ko taɓa ba yana danna waya sallamarmu ta saka ya ɗago kai caraf
muka haɗa ido. Sake ƙanƙance ƙananun idanuwansa yayi yana kallona nayi ƙasa da kaina na wuce ina
gyara riƙon Sharifa a jikina har kuma na zauna ina jin alamun har sannan kallona yakeyi. Ba tareda na
bari mun sake haɗa ido ba na yi musu gaisuwar haɗaka shida Uncle Mudassir ɗin daya taso ya dawo
cikin falon yana mana sannu da zuwa.
Na saci kallonsa ganin shima ya taso, ya zauna a gefena kan 1 sitter kafin ya ɗan zame ya shiga gaida
Mama cikin girmamawa, bayan sun gama gaisawa ya juya kan Anty Labiba Uncle Mudassir yayi saurin
dakatar dashi yana cewa
"Karkaga ta kusa cika two sitter ka ɗauka wata babbace ƙanwarka ce itace autarmu" duk sukayi dariya
banda ni da nake kallonsa ya wani shafa kai yana murmushi kafin suka shiga gaisawa. Har gurin goma
muna gidan sunata hira, ni dai zaman Dr Salman ne ya takurani na kasa sakewa ƙarshe ma jin baƙin cikin
gidan sun ragu yasa na koma can tareda Inayah da Sharifa da suka fara bacci.
Anty Ummi ce ta leƙo tace na fito mu tafi, na tada Inayah kafin na ɗauki Sharifa muka fita, nayi tsaye ina
kallon Dr Salman a raina ina mamakin zaman me yakeyi da har sannan bai tafi gida ba? Tare muka fita
muna gaba yana binmu a baya har muka hau babban titi kafin kowa ya kama hanyarsa. Bayan mun sauke
Mama Anty Labiba ta fara mun taratsi wai dama mutumin nan Oga na ne shine na masa wata gaisuwar
jeka ka mutu?
"A hakan kike so su baki aiki idan kin gama service ɗin alhalin bakya mutunta Oga? Wlh daga yanda naga
yana kallonki na san yaji haushi tun wuri ma ki san ta yanda zaki fara bashi haƙuri". Ni dai ban ce mata
komai ba har muka isa gida, Amir da baiyi bacci bane ya ke gaya mana Uncle Faisal ya zo ga saƙo can ma
daya bayar a ajiye mun.
Sai da nayi wanka nayi shirin bacci dan munci abinci a gidan Uncle Mudassir kafin na buɗe saƙon da
Faisal ɗin ya kawo mun, customized pouch ne na wayata, sai water bottle mai kyau shima da sunana a
jiki da kuma jotter mai kama da diary. Na cire asalin pouch ɗin wayar na saka sabon ina murmushi. Shi da
ya ce yanda yake jin Khadija a zuciyarsa (Matarsa) ba zai iya yi mata kishiya ba amma kuma na rasa
dalilin zuwan da yakeyi da ƙananan kyaututtukan da yake yi mun, duk sanda zai zo gidan sai ya taho mun
da wani abu amma kuma ya ce shi ba zawarci na yakeyi ba.
Gyara kwanciya nayi bayan na kashe filila na rufe ido na amma bacci ya gagara ɗaukata, tunanin
haɗuwarmu da Bilal jiya ya shiga dawo mun. Tashi nayi zaune na jingina bayana da allon gadon haɗi da
rungume ƙafafuwana na zubawa wardrobe ɗin dake kallona ido ta cikin duhun daya mamaye ɗakin.
Babu wata alama data nuna kewa ko damuwa a tattare da Bilal, dukda na sani shi ɗin gwani ne gurin iya
ɓoye labarin zuciyarsa ta yanda yake matuƙar wahala ka iya karantar yanayinsa ta cikin ƙwayar ido ko a
kan fuskarsa amma nayi tsammanin na tsinci wani abu musamman da nake yawan jin ana faɗar Maza
sukan shiga wani hali idan suka rabu da matansu musamman idan ya kasance su suka zalinci matan
amma ya akayi ni a kaina abin ya zama akasin haka?
Babu wata damuwa a tattare da Bilal, idan ma ba idanuwa na bane sai naga kamar har haske ya ƙara da
kyau alamar bashi da wata matsala a rayuwarsa. Idanuwana suka kawo ruwa nayi saurin share su kafin
su fara ɗiga sannan na koma na kwanta ina jan numfashi ta baki a ƙoƙarin kwantar da zuciyata. To wai
ma mai zai dame shi ne bayan yana tareda Duniyarsa? Abar ƙaunar sa ya kuma rabu da kaskar da liƙe
masa ai dole.
Cusa kaina nayi cikin pillow na saki kukan dana kasa haɗiyewa. Na yarda shi dai Bilal bai taɓa so na ba
kawai ni nayi ta cusa kaina na kuma kasa gane hakan tuntuni. Nasha ji da karanta labaran mazaje sa suke
cin amanar matayensu da wasu a waje amma ban taɓa cin karo da irin Bilal ba, yanzu nake ganin kamar
ma da gayya ya bada ƙofar da zan fahimci abinda yake aikatawa har ma kuma ya barmun shaidar da ko
na ci gaba da zama dashi to fa ba zan sake samun kwanciyar hankali ko nutsuwa a tareda shi ba.
Idan na tuna musayar kalamansu da Jalilah da kuma ganin da nayi musu a cikin gidana sai in kasa gane
dalilin daya saka har yanzu nake jinsa a zuciyata. Ya kamata ace tun da daɗewa ya fita a raina irin azabar
daya ganawa zuciyata har ma da gangar jikina amma dukda haka amma a koda yaushe cikin yi masa
uzuri nake. Rabuwa da hawayen nayi sukayi ta shatata tsayin lokaci kafin na tashi na ɗauro alwala na
shiga jera raka'oi har saida naji nauyi da ƙuncin daya tasarma mamaye zuciyata ya sauka. Na daɗe a
zaune ina tasbihi da yiwa annabi salati har saida idanuwana suka fara rufewa kafin na shafa addu'a na
haye gado ban ko ƙara ko minti biyu ba bacci mai cike da nutsuwa yayi awon gaba dani.
Alhamdulillah, tunda ubangiji ya lamunce mun na durfafi kai masa kokena koda ace guguwar ƙaunar
dana rasa yanda zanyi da ita akan Bilal ta taso mun dana kalli gabas zanji komai ya wuce tunanina ya
saitu na dawo kan hanya.
Washe gari ta kama asabar kusan wuni nayi ina aikin yiwa Al'amin da Inaayah snacks da zasu kai
makaranta a gobe Lahadi zasuyi picnic shine kowanne ɗalibi zai kai wani abu daga gidan Anty Labiba tace
nayi musu cake da samosa. Sai yamma lis na gama nayi wanka, bayan sallar magriba ina azkar na kunna
Data dan yinin ranar gaba ɗaya ban hau online ba, ina kallon saƙonnin da suke ta shigowa, number da na
gani ta saka na ɗauki wayar da sauri ina dubawa.
Na goge duka numbobinsa amma haddarsu bata goge a ƙwaƙwalwata ba dan haka ina gani na gane
shine dukda wannan layin ba sosai yake amfani dashi ba a lokutan da yake yawan tafiya Abuja ne yake
kirana dashi dukda banyi saving ba amma na haddace number.
Kife wayar nayi ba tareda na karanta abinda saƙon ya ƙunsa ba, na san ba zai wuce shirmen daya fara yi
mun waccen ranar da muka haɗu ba ne zai cigaba ni kuma banida lokacinsa a yanzu.
Sai da nayi sallar isha'i kafin na tashi daga gurin na zuba abinci na fara ci kenan Anty Labiba tace mun wai
Abba yana ta kirana bana ɗauka in kirashi yanzu hakan ya sa na tashi na ɗakko wayar.
Abban na fara kira bayan mun gama maganar da zamuyi har zan ajiye wayar zuciya ta ƙwadaita mun son
ganin saƙon daya turo dan haka na shiga Whatsapp ɗin na buɗe.
"Na san ko duk duniya zasu juya mun baya ke kaɗai ce ba zaki gujeni ba My Halims, ina cikin wani
mawuyacin hali ina kuma buƙatar taimakonki. Idan kin amince zaki taimakamun ki dawo mun da amsa
cikin gaggawa ki kuma shirya zan tura miki da address ɗin in da zaki sameni, na tanadar miki da
amsoshin da kika daɗe kina bukatar jin su daga gareni, duk abinda ya faru shiri ne na tabbatar kuma zaki
fahimci haka idan kika saurari bayani na. Bilal ɗinki." abinda ya rubuta a saƙon kenan.
"Ni da kika ganni ina tarayya ne da mutanen dana san zasu mun amfani a rayuwa, da zarar amfanin
mutum ya ƙare kuma zan ajiye shi dan ni bana son liability" maganganunsa na wani lokaci suka shiga
dawo mun. A fili na furta
"Tabbas na shaida hakan, ya watsar dani a lokacin da yake ganin amfanina ya ƙare a gurinsa ashe kuma
da saura". Blocking ɗin number na sakeyi dan dama nayi ban san dalilin daya saka na buɗe daga baya ba.
Da naga tunanin yana neman ya hanani sukuni sai na ɗakko system ɗina na tura research proposal ɗin
da Dr Sulaiman ya tura mun akan idan ina sha'awa na shiga ayi dani. Wannan ya ɗauke mun hankali har
zuwa sanda na gaji na kwanta bacci.
BILAL
A tunaninsa ɓatan dabon da yayi shine mafita, Minjibir shine in da yake ganin zai iya zama na wani lokaci
kafin abinda yake jira ya samu ya koma gida. Abinda kuma ya saka ya zaɓi can ɗin kasancewar gurin
wajen gari ya sani da wahala ace ya haɗu da wata fuskar sani saɓanin idan hotel ya kama a cikin gari.
Yayi tunanin ko dai ya kira Zulaiha ne yace ta taho? Amma kuma daya tuna Zulaihan ba wacce ya sani a
baya bace sai ya fasa, baya zaton zata rufa masa asiri koda ya faɗa mata gaskiyar halin da yake ciki, ba ita
ba ko yan uwansa ya san ba zasuyi shiru ba a yanzu a duniyar nan kaf Halima ce kaɗai wacce yake da
tabbacin ko mutum ya kashe zata rufa masa asiri.
Ya kunna wayarsa amma ya barta a flight mode, tunani ya ringayi anya kuwa bayan duk abinda ya faru
Halima zata sake dubansa? Zuciyarsa ta bashi ƙwarin guiwa akan fushin Halima akansa ba mai dogon
zango bane, dukda shi da kansa ya tabbatar da yaga canji amma ko a shekaran jiyan ya hangi ɓurɓushin
soyayyarsa da bata ida mutuwa ba a ƙwayar idonta.
Ya san mai take so, soyayyar sa da kuma tattali da kulawa da zarar kuma ta same su zata manta komai.
Da wannan ƙwarin guiwar ya ɗora wani tsohon Data sim da ya siya bai zaci ma yana aiki har lokacin ba
yayi recharging nasa kafin ya cire layukansa biyu da aka sanshi dasu ya zuba a zip ɗin jakarsa sannan yayi
sub ya buɗe sabon Whatsapp da layin ya tura mata saƙo.
Tun yana tsammanin samun amsa har ya fitar da rai dukda cewar ta buɗe saƙon, ganin har tara ta gota
bata ce komai ba ya yanke shawarar kiranta voice call amma cikin rashin sa'a bata online cikin jin haushi
ya kashe wayar gaba ɗaya kafin ya kwanta yana juyi akan gado cikin rashin sanin madafa.
Kwanciya yayi yana lissafin mafita, ya sani ƙarshe Jalilah ta nemi ya biyata kuɗin kayan daya ɗiba dan
bayan su duk wani abu daya mallaka masa daga haɗuwarsu zuwa yanzu kyauta ce ba kuma roƙarta yayi
ba dan haka bata isa ta nemi wani abu daga ciki ba. Kuɗin kayanta kuma da kuɗin Alhaji Lawan basu
wuce chicken change ba idan abinda yake jira ya sauka
Life time saving ɗinsa ya tattara, duk kuɗaɗen daya ringa samu a hannun Hafiz da Jalilah harda kadarorin
daya siya duk ya siyar ya haɗa kuɗin ya zuba a hakar fitar da kayayyaki ƙasashen waje.
Tun kafin ya auri Halima akwai abokinsa Yahya ne da sukayi University tare shi Yahya yana harkar Import
and Export na kayan noma irinsu Citta, Barkono, Riɗi da su Zoɓo.
Akwai tarin alkhairi a cikin harkar musamman idan ka shigeta da jari mai ƙarfi supply ɗaya idan kayi sai
ka samu riba kusan ninkin jarin daka zuba. Tun bayan da suka gama Jami'a a lokacin yana ta fafutukar
samun aiki shi kuma Yahya ya fara harkar a sannan ma kayi nayi yakeyi ya nemo kayan wa masu siya a
sallame shi har ya samu jarin daya fara siya shima Allah ya saka masa albarka a abun ganin kuma ya fara
fasowa gari ya saka Bilal shiga shima.
Yan kuɗin daya fara dasu ba wani na azo a gani bane amma dukda haka ba laifi idan an siyar ana samun
riba dan da kuɗin ya fara ginin gidansa kafin harkar birni da ɗawainiyar Zulaiha suka sa ya dakata kafin
daga ƙarshe ƙwadayinsa da son zuciya suka rabashi da Yahyan. Cewa yayi sai Yahyan ya bashi jari mai
ƙarfi tunda yanzu Allah ya buɗa masa ya faso gari shi kuma ya ce sai dai ya bashi aro idan ya yarda zai
ranta masa ko nawa ne amma kuma ba zai ringa karɓar riba ba har sai ya gama biyansa. Nan fa ya yi
masa rashin mutunchi har yana ce masa maƙetaci, bayan duk abinda ya masa sanda suna Jami'a shine
yanzu ba zai iya bashi wasu yan kuɗi ba sai dai bashi.
Ya akayi kuma ya koma yana bashi haƙuri sannan kuma ya yarda zai karɓi bashin shi kuma a lokacin
Yahya ya canza shawara ya ce ya fasa ba zai bashi ba, a bashi bai shiga tsakaninsu bama ya rufe ido ya
masa cin mutunchi ina kuma ga ya tambayeshi kuɗi dan haka ya fasa. Sukayi kaca kaca suka rabu.
Ya riƙe abun a ransa wata rana sai ya bawa Yahya mamaki shiyasa ya ringa tara kuɗaɗe har saida suka
kai yanda yake ganin zai shiga harkar da ƙarfinsa. Bai koma ta hannun Yahyan ba sai ya nemi wani
abokinsa daya san tare suke komai Yusuf, shi ya bar fitar da kaya ya koma noman shinkafa kamar yanda
ya gayawa Bilal ɗin.
Shi yayi hanyar wani kamfanin a Turkiyya da suke siyan Citta da Zoɓo. Kusan wata shida kenan da aka
tura kayan, yau ne gobe ne zasu isa shiru yana ta jira domin ba ƙananan kuɗi ya narka ba haka ribar da
yake tsammanin samu ba yar kaɗan bace sai da Yusuf ɗin ya bashi shawara daya rage kuɗin yayi yawa
ba'a zura jiki a kasuwanci musamman shi da zai fara yanzu amma yaƙi,
Yayi tunanin kayan zasu iya isa a ƙasa da wata biyu kamar yanda aka ce masa da zarar kuma an sauke
zasu bashi kuɗinsa cas haɗama ta saka bai dubi za'a iya samun akasi wata matsala ta faru ba ya tattar
kuɗaɗe kawai ya narka sai gashi an tafi rabin shekara shiru kaya na kan ruwa sai a cikin satin daya mutu
aka ce kaya sun isa amma ba'a sauke su ba.
Yanzu zaman da zaiyi a nan na jiran a sauke kaya ne su tura masa kuɗinsa ya biya Alhaji Lawan ya samu
yanci ya warwasa ya taka duk wanda yaga dama. Neman shiri da Halima kuma da yakeyi saboda ko da
ace an samu akasi an ja lokaci har asirinsa ya tonu an gano maɓoyarsa a ƙalla ya samu wanda zai tsaya
masa dan ya tabbatar duk fuffukar da Abba yakeyi sai dai idan Haliman bata birkice masa ba sai yayi
mata abinda take so.
Hajja na zaune tsakar gida ita da Anty Amina da Anty Habiba, kiransu tayi kamar yanda tace tun ranar
Juma'a rabon da taji daga pBilal da Fadila. Bilal bai ko shiga gidan ba gurin ɗaurin aure an ce mata ya
hau mota ya wuce ita kuma Fadila washe gari da tayi aike a kdagai mata wasu saƙo data sa aka karɓo
mata aka tarar gidan a rufe, ta kirata kuma suna fara magana tace tana zuwa zata kirata toh fa har yau
kwana bakwai kenan idan an kira layin nata ma a kashe kuma cikin ikon Allah su duka babu mai number
angon balle a kira aji ko lafiya.
"Nima nayi ta kira bana samunta, zuwansu Hajar biyu kuma gidan a rufe amma kuma da alama akwai
mutane a ciki dan sunce rariyar gidan da ruwa, abinda ya sa hankali na bai tashi ba ai lafiya itace take
ɓuya. Kuma dama tace ya gaya mata idan ta tare sai sunyi sati biyu kafin su fara buɗe gida dan baya so
mutane su damesu su hanshi cin amarci".
"To dai ko bunsuru ne shi dai ai ba zai kwana ya wuni yana abu ɗaya ba dole za'a tsaya a huta a ci abinci
a lokacin hutun kuma a kunna waya ai a gaisa da yan uwa kowa ya san halin da ake ciki, kuma shi baya
sallah ne? Ko kuwa sallar ma a cikin gida yake yinta da ba zai buɗe ƙofa ba?"
"Ni yanzu ya za'a yi na sani Hajja?" Habiba ta faɗa. Anty Amina sai dai ta kalli bakin duk wanda yayi
magana bata ce musu kanzil ba, Hajja ta sake cewa
"To shi kuma Bilal ɗin fa? Ko da yake dama shima tunda ya auro wannan tsinanniyar yarinyar sai ya shafe
satin ma bai zo ba bai kuma kirani ba nima ɗorawa kai ne ya saka na damu da shirun nasa na manta ya
saba dama. Ita Fadilar dai nafi damuwa gaskiya dan haka ƙalau na san ba zata ki kiran waya ba ni dai
jikina yana bani akwai wani abu, dan haka yanzu abinda nake so dake da Amina ku tashi kuje gidan ku
gano da kanku, zancen yayan nan naki masu azabar ƙarya ba abin kamawa bane. Ku tambaya har
maƙwafta kuji ai in dai da mutane gidan ba za'a rasa jin motsi ba".
Haka suka kama hanya a motar Anty Aminan, Anty Habiba ce ta kwatanta mata dan ita bata je kai
Amarya ba dare nayi ta kaɗa yayanta masu aure suka wuce gidajensu ta kwashi sauran suka tafi gida.
Cikin sa'a suna isa suka tarar da get a buɗe za'a fito da mota, Anty Habiba tace
"Ahaf, ai na faɗa suna nan ga angon nan, tsiyarsu suke shukawa kawai shiyasa suka kulle gida amma
Hajja duk tabi ta damu kanta". Gefe sukayi parking sai da ya fito da motar ya sauka zai kulle get kafin
suka fita, tsayawa yayi yana kallonsu sama da ƙasa, Anty Habiba ta washe baki ta shiga gaishe shi, yanda
ya amsa yana ƙare musu kallo ya saka Anty Amina cewa
Ba yabo ba fallasa ya ce
Daga Anty Habiba dake murmushi kamar sokuwa har Anty Aminan buɗe ido sukayi suna kallonsa da
mamaki, cikin dakewa Amina tace
"Ban fahimci ya akayi ba? baka ji abinda nace maka bane mu yayintane ko kuwa ba zamu zo gidan
ƙanwarmu ba sai da dalili?"
"Bismillah" tayi tsaki ta wuce Habiba tabi bayanta tana waigen Ahlan daya zaro waya daga aljihunsa yana
dannawa. Anya kuwa shi ɗin ne saurayin Fadila da kamar zai kwanta mata tsabar biyayya idan yaje zance
Fadilan na gidan? Kofa a kujera baya zama idan zasu gaisa ƙasa yake sauka amma shine yau yake cewa
bai ganeta ba lallai akwai ƙatuwar matsala toh.
Ƙwanƙwasa ƙofar falon Anty Amina ta shiga yi a fusace a ranta kuma tana ayyana dama ta san za'ayi
haka, amma kuma Tsuntsun daya ja ruwa shi ruwa zai doka. Yanda ta buɗe ƙofar zaka san a tsorace take,
su biyun suka zuba mata ido cike da son tabbatar da Fadilan ce ko kuwa wata mai kama da itace aka
samu.
Cikin yanayin tsoro da kuma murna a haɗe ta ƙaƙalo murmushi ta shiga kiran sunansu tana cewa
"Kune? Ku shigo mana" ta juya ciki suka bi bayanta. Ga dai gida har gida, falonta tamkar na wani babban
attajiri ko ɗan siyasa amma a kallo ɗaya zaka fahimci matar gidan tayi hannun riga da kwanciyar hankali.
Zama sukayi suna kallon Fadilan dake ta murmushin yaƙe tana musu sannu da zuwa kafin ta zauna a
shiga gaishe su cikin ladabin da basu san yaushe ta koyeshi ba.
Sukayi jugum jugum bayan gaisuwar, Anty Amina na ƙare mata kallo tana karantar canzawar da tayi a
cikin sati ɗaya, rama har a fuska Fadila dake da cikakken jiki dukda bata da kiɓa amma jikinta irin me luf-
luf ɗin nan ne haka fuskarta cike take da kumatu musamman dab da bikin kayan matan data ringa sha
suka sake cikata amma a sati duk ta zaizaye sai kace wacce tayi amai da gudawa, ga dai haske tayi irin na
mai zama guri ɗaya musamman kuma ga Ac amma fa duk tsokar data zo da ita a jikinta t zaizaye.
Ta sauke ajiyar zuciya jin Anty Habiba data gama ƙarewa falon kallo na tambayar ruwan sha, sai ta miƙe
da sauri tana cewa
"Kuyi haƙuri, murnar ganinku ta saka ma manta" ta wuce kitchen ba jimawa ta dawo da ruwan faro
ƙwara biyu akan try sai kofuna suma biyu ta ajiye musu.
"Yanzu idan baƙin kunya ne suka ce ki basu ruwa haka kuwa zaki dakko tsurar ruwan ki basu Fadila sai
kace wacce taba jin hausa?" Anty Habiba ta faɗa, kafin ta bata amsa Anty Amina tayi saurin katseta da
cewa
"Dama Hajja ce tace kwana biyu ta jiki shiru ko a waya shine tace muzo mu duba mata ke, tunda kuma
kina lafiya shikenan mu zamu wuce" ta miƙe, yanda kasan a ƙaya Fadilan take itama ta miƙe tana cewa
"Ai wayar ce ta faɗa ruwa amma zan kirata nagode ku gaida gida". Habiba zata sake magana dan abin ya
ɗaure mata kai Anty Amina ta katseta, ganin kuma Ahlan ɗin ya fito daga kitchen dukda basu san sanda
ya shigo ba ya saka tayi shiru suka tashi suka fita tana musu Allah ya kiyaye daga inda take tsaye bata ko
ƙara taku ɗaya ba.
Duk su biyun sunji ƙarar marin daya kifa mata da ihun data fasa kafin ƙofar ta ƙarasa rufuwa, da yake
window duk a rufe suke kuma basu ji cigaban abinda yake faruwa ba, Anty Habiba taci burki tana cewa
"Sai ki koma ki rama mata tunda dama dake aka haɗu aka tura motar" Aminan ta bata amsa tana nufar
get, Habiba tabi bayanta tana cewa
"Na shiga uku, wlh mutumin nan shigo-shigo ba zurfi yayi mana daga ganin Fadila tana cikin tashin
hankali wlh kuma a haka zamu tafi mu barta?"
"Ni dai kin san bakuyi shawara dani ba sanda zata aureshi, hasalima sai ranar ɗaurin aure naji sunansa na
kuma fara ganinsa dan haka yanzu kada wanda ya tsomoni a cikin shawarar yanda za'ayi dan ban zan
hawa ba ba za'a nemi gangara dani ba" ta faɗa tana buɗe motarta. Har suka isa gida kuwa da kunne take
sauraron Habiba dake ta amma bata tanka mata ba, sai da suka je ƙofar gidan Hajja kafin tace mata
"Kinga idan kika gayawa Hajja na ɗaya zaki tayar mata da hankali ƙarshe hawan jininta ya tashi sa'annan
ita kanta Fadilan ki ƙara jefata a wani taskun dan dai ganin idonki kinga alamar baya buƙatar kowa yaje
masa gida itama kuma ta yarda da hakan domin da tsarin bai mata ba ai tana da ƙafafu ba kuma kulleta
yakeyi ba zata nemi hanyar gida da kanta, ke ko kulleta yakeyi har idan taga zaman bai mata ba zata
nemi mafita dan haka ki kama bakinki kawai.
Hajja ta washe baki jin sun samu Fadilan kuma sun ce lafiyarta ƙalau kafin tace
"Ja'ira wato ita miji daɗi, toh ya na ganku hannu na dukan cinya? Bata bayar da komai a kawo mun bane
ko kuwa a mota kuka manta?"
"Tace zasu zo a cikin satin nan ai" Anty Amina tayi saurin bata amsa ganin Habiba ta buɗe baki, sai ta
taɓe baki tace
"Ai shikenan Allah ya kawo su lafiya". Ta ɗaga pillow ta zaro takardu ta miƙawa Amina tana cewa
"Kuna fita waccen yarinyar matar Bilal tazo, to dai itama tace tun ranar Juma'a tana gidan kai amarya ya
kirata yace daga can ta wuce gidansu wai tafiyar gaggawa ta kamashi idan ya dawo zaije ya ɗakko ta, toh
mayyar bata tafi ba ta zauna. Ni nafi zaton Abuja ya tafi gurin waccen ɗaya shaiɗaniyar Bilal dai ba zai
daina sakani magana ba".
Su kuma takaddun na menene?" Anty Amina ta tambaya tana juya takardun hannunta, Hajja ta watsa
hannu tace
"Na iya karatu ne ni balle ki tambayeni? Shiyasa ai na ajiye su ina jiran Abubakar ya shigo tunda kun
rigashi sai ki buɗe ki gani ƙila sakinza tayi".
Anty Amina da Habiba suka kashe da dariyar maganarta, wai ƙila sakinsa tayi, Hajja kenan ko a ina mace
take sakin namiji sai Allah.
Dariyar Anty Amina ta katse ta ɗora da salati tana duba takardar Hajja da Habiba suka zuba mata ido da
son jin ƙarin bayani dai dai lokacin kuma Abubakar yayi sallama tareda Abdullahi babban ɗan Anty
Aminar duk suka shiga sahun masu tambayar mai ya faru?
"Sai anyi haka dame? Wai mai aka rubuta dan ubanka ka wani ninketa ba kai mana bayani ba?" Hajja ta
zaburo masa, ya zauna yana cewa
"Sammaci ne daga kotu, gidan da wannan budurwar tasa ta siya ya siyarwa da wani mutum ba tareda ta
sani ba, yanzu kuma ita ta siyarwa wani dan haka wanda ya siyarwa ya makashi a kotu bisa zargin
damfara. Ɗayar takardar kuma ita budurwarce ta yi ƙararsa itama akan zargin sata, da kuma yaudara da
zamba cikin aminci".
"Amma Allah ya tsinewa wannan yarinyar Jalilah, dama ashe ta shigo rayuwarmu ne dan ta jefa mu a
masifa ta lalata mun ɗa shine yanzu zata masa sharri ta haɗashi da hukuma saboda bai aureta na ko
me?"
"Wlh na sharri ta masa ba duk abinda ake zarginsa ya aikata da bakinsa duk ya faɗa mun, yanzu dai ku
nemo shi kawai dan wannan sammacin ma na biyu ne kuma da gargaɗi kotu zata iya ɗaukar kowanne
mataki idan bai bayyana gabanta nan da kwana biyu ba" Abubakar ya sake faɗa yana duba takardar.
Hajja ta fashe da kuka tana salallami duk sai jikin Anty Amina yayi sanyi tace
"Yana zaman-zamansa yana lallaɓa rayuwarsa da yar matarsa haka kawai ya rakitowa kansa masifa, ina
amfanin tarayya da wannan shaiɗaniyar yarinyar gashi yanzu tana nema ta tozarta mu ta jefa shi a
masifa? Ni wlh tun ganina da ita dama hankali na bai kwanta ba, kawai dan shi ɗin yace ba komai ne
amma dama matan Habuja tun duniya na kwance ma makiraine, mutanen da suke kashe mazajensu dan
suci dukiya balle kuma yanzu da duniya ta tashi tsaye makirci ai sai wanda aka gani ni dai Allah ya isa
tsakanina da ita wlh" Hajja ta sake faɗa cikin kuka.
"Daga baya kenan, yanzu dai ki gwada duka layukansa da kike dasu ki faɗa masa ya dawo ayi komai a
mutunche idan kuma ya zaɓi asirinsa ya tonu kowa ya san halin da ake ciki shikenan" Abubakar ya faɗa
yana ficewa.
Anty Amina ce ta shiga kiran wayar Bilal amma layukansa biyu da take da duk aka ce a kashe suke, ta
kalli Hajja dake sharɓar kuka kamar yar yarinya tace
"Hajja baki da wani layin nasa ni na kira wanda nake dasu duka a kashe"
"Guda biyu ne MTN da Airtel nima su ɗin ne" ta bata amsa tana fyace majina. Anty Habiba ce tace
"Tace dai bata sani ba amma ban sani ba ko ƙarya takeyi" Hajja ta bata amsa dai-dai nan Abubakar ya
dawo falon ya zauna yana cewa
"Halima?"
"Eh, akwai wani layi da ya ɗan yi amfani dashi can da daɗewa, na duba shi naga banyi saving ba amma
ƙila a samu a gurinta ita" ya sake faɗa.
"Ga matarsa wacce Halima za'a samu number sa a gurinta?" Anty Habiba ta faɗa, ya kalleta ya ce
"Sai ta yuwu dan zata rufa masa asiri ko mutum ya kashe" Hajja ta faɗa a sanyaye, ya miƙe yana cewa
"Kuma da Kinsan da haka kika goya masa baya ya rabu da ita, matar da duniya ma ta shaida abokiyar
rufin asirice. Ai dai wlh ya tafka asara, gashi nan ya ƙare da yan balaja'u a gida da waje".
"Ni dai ba zan kirata ba wlh" Anty Amina tayi saurin faɗa ganin Hajja na kallonta, sai ta ɗauki wayarta
tana cewa
HALIMA
"Toh na ƙoshi" yayi saurin tashi daga kan kujerar sa ya nufo ni yana cewa
"Ai kuwa baki isa ba, harfa kakarin amai kikeyi saboda yunwa kuma ko spoons biyar bakiyi ba kice kin
ƙoshi? Ashe zan yi miki ɗura kuwa" ya ƙarasa yana naɗe sleeve ɗin farar rigar jikinsa. Ji nayi kamar in
tashi na taka rawa amma na kanne na ɓata fuska nace
Ƙarar da wayata dake aje kan table tayi ya saka duk muka kalli gurin, sunan Hajja na gani yana yawo, na
ɗago wayar ina buɗe ido dan na tabbatar da ita ɗin ce ko kuma idanuwane suke gizo? Ganin kiran na
neman katsewa ba tareda na amsa ba Dr Salman dake tsaye kaina ya zare wayar daga hannuna ya amsa
tareda sakata a speaker.
"Ina jin ki Hajja ina wuni?*" Na faɗa bayan dana amsa mata sallamar, ta amsa da
Sai naji wani banbarakwai, ashe sun san da yayansu a hannuna? Shiru nayi ban amsa mata ba ta cigaba
da cewa
"Dama lambar Bilal nake so ki tura mun, banda Mtn ɗin sa da Airtel idan kina da wata daban su duk ba'a
samunsa a su"
"Ai ni banida kowacce number sa ma yanzu Hajja" na bata amsa a dake, tayi shiru kafin tace
"Abubakar yace ba zaki rasa ba, ki taimaka wata matsala ce ta taso kuma ana ta nemansa a waya ba'a
samunsa idan kuma kin san inda yake kawai ki faɗa mana aje a same shi"
Na saci kallon Dr Salman daya koma kujerarsa ya kafeni da ƙananun idanuwansa kamar farin shigar
maita kafin nayi ƙasa da kai nace
"Sai dai ki kira Yaya Nasir ba zai rasa sanin inda yake ba ko ya baku number" sai tayi jumm kafin tace
"Shikenan, kya gaida Mamarku sai anjima" daga haka ta katse wayar.
"Tashi mu tafi toh" Dr Salman ya faɗa yana miƙewa tsaye. Na kalleshi, fuskarsa ta canza, yar fara'ar da
yakeyi tunda na shiga office ɗin duk ta gudu ya dawo boss ɗin sa ga ƙananun idanuwan sun sake
ƙanƙancewa. Ganin banida niyyar tashi ya saka ya wuce yana cewa
Kada wadda ta tambayeni mai yake faruwa ko yaushe aka fara? Nima ban sani ba kuma daga nan zamu
tashi 😂😂😂😂
*Wattpad @MaryamahMrsAm*
*Ban yarda wani ko wata ya juya mun labari ta kowacce siga ba tare da izini na ba*
*Kuɗin karatu yana wakiltar mutum ɗaya ne, kiji tsoron Allah karki ɗauki hakkina ta hanyar fitar mun da
littafi*
*KURA A RUMBU littafin kuɗi ne, a biya naira 800, biya a asusun*
*7061838488*
*Opay*
*Maryam Farouk, se a tura shaidar biya a lambar Whatsapp ta sama*
*Zanyi amfani da damar nan in roƙe ku, Dan girman Allah kada wacce ta haɗa mun Document. Ban taɓa
yin Allah ya isa ba ko wata mummunar addu'a akan fitar mun da rubutu ba tareda izinina ba amma Allah
ya sani ba zan yafewa duk wacce ta haɗa mun Document ba. Dukkanmu musulmi ne mun kuma san
girman haƙƙi dan haka mu kiyaye.*
Sai dana tabbatar ya fice daga building ɗin gaba ɗaya kafin na fita daga office ɗin ina kalle-kalle kamar
mara gaskiya, ganin babu kowa ya saka na shige Elevator da sauri, a reception na haɗu da Juwairiyya ta
kalleni fuska ba yabo ba fallasa kafin tace
"Dr Sulaiman yana neman ki?" Na amsa da "Toh" ba tareda na tsaya ba na fita.
A can kan hanya ya tarar dani, fuska ba annuri ya sauke glass yana kallona kafin ya ce
"Get in".
"Amma cewa nayi ki sameni a mota ko?" Ya faɗa bayan dana zauna, na kalli gefe na ce
"Ni fa gaskiya bana son abunda kakeyi, yanzu wane kallo kake so a ringa yi mun kawai a wani ringa
ganinmu tare?"
"Ko?" Ya faɗa yana ɗage gira ɗaya, na tura baki cike da shagwaɓar dana daɗe da daina yinta tun lokacin
da Bilal yace haushi nake bashi idan ina abu kamar wata sakaltacciyar yarinyar idan ma kuma nayi ko a
jikinsa, sai yanzu da naga alamar idan nayi zan samu kulawa na ɓata fuska na ce
"Ni dai dan Allah ya zama sirri bana so kowa ya sani"
"Hakan yana nufin kin amsa tayi na kenan?" Ya faɗa yana mun wani kallo da najishi har cikin jini da
ɓargona. Nayi ƙasa da kai ina sakin murmushi ba tareda nace komai ba,
"Leemahh.." ya kira na ɗaga kai kamar mai ciwon wuya na saci kallonsa, yanda ya kwanta cikin kujera
yana mun wani lalataccen kallo ya saka nayi saurin sauke kaina ƙasa ya sake maimaita kiran sunan da
sautin daya fi na farko taushi kafin ya ce
Na sanya tafukan hannayena biyu na rufe fuska ina sakin murmushi kamar wata wawuya, ina jin nasa
sautin murmushin kafin ya tayar da mota muka bar gurin. Har muka isa gida babu wanda ya sake cewa
komai a tsakaninmu, lokaci-lokaci muna haɗa ido tareda sakarwa juna murmushi. A hankali na ce
"Gobe bani da aiki" ina ƙoƙarin buɗe motar amma najita a kulle, ganin kuma bai yi yunƙurin buɗewa ba
ya saka na koma na zauna ina kallonsa.
"Wanene Bilal?" Ya faɗa ba tareda ya kalleni ba, nayi shiru ina kallonsa, ganin ya juyo ya sa nayi saurin
sauke kai ƙasa ina jin idanuwansa na yawo a kaina. Kusan minti uku bai sake cewa komai ba alamar
amsata yake jira kafin a hankali nace
"Ina da kishi sosai Leemah, bana tunanin akwai wani abu da yayi saura a tsakaninku; idan ma kuma
akwai ina so ki gaggauta datse shi ko kuma ni ki datse ni"
Da sauri na kalleshi jin abinda ya faɗa, ya mun kallon dake tabbatar da gaskiyar maganarsa kafin ya
cigaba da cewa
"Har idan mahaifiyarsa zata kiraki tana tambayarsa kenan kuna tare"
"Wlh bama tare, ni rabona dashi tun ranar daya sakeni ko yanzun ban san dalilin daya saka ta kirani ba"
nayi saurin faɗa har muryata tana rawa.
"Na yarda". Na saki ajiyar zuciya ina dafe goshina take kuma haushin kaina ya rufeni, to rikicewar da nayi
mata mecece? Sai kace wacce Alƙali ya rutsa. Wata jakar takarda ya ɗakko a kujerar baya ya ɗora mun a
cinya yana cewa
"Gobe zan koma Abuja, ya kamata idan na tafi a ƙalla na ɗauki tsayin wata biyu ko sama kafin na
waiwayo Kano amma babu hali tunda na ajiye mutum"
Nayi murmushi jin wai ya ajiye mutum kafin a hankali nayi masa godiyar abinda ban san ko menene ba,
da kansa ya fita ya buɗe mun ƙofa na fita ina jina kamar wata sarauniya, sai da na shiga gida kafin ya ja
motar ya wuce nima na shige ciki.
Anty Labiba na zaune a kan kujera tana waya dan haka na wuce ciki kawai bayan na mata sannu da gida,
kayan jikina na shiga ragewa na tafi tunanin da Dr Salman ya hanani yi.
Mai ya faru ake neman Bilal har Hajja zata kirani? Na zauna gefen gado, saƙon daya turamun ranar nan
ya faɗo mun a rai sai naji hankalina yana so ya tashi. Wayata na ɗauka na shiga Whatsapp na lalubo chat
ɗin, bai sake mun magana ba tun waccen ranar. Na shiga sake biya saƙon, matsalar mecece? Na shiga
tambayar kaina amma bani da amsa dan haka na ajiye wayar na shiga wanka ina jin yanayi na gaba ɗaya
ya canza daga farincikin dana shigo dashi zuwa damuwa.
Haka na ƙarasa yinin ranar sukuku sai bayan Magriba da Faisal ya zo ne ma na zauna muka ɗan yi hira
amma ina kwanciya na sake shiga tunanin, kasa bacci nayi daga ƙarshe na bi abinda zuciyata take ta
saƙamun. Sai da na murza key a ƙofa kafin na shige banɗaki na lalubo number na kira. Ringing biyu aka
ɗaga, daga can ya kira sunana ya ce
"Maganar ba zata yuwu a waya ba My Haleems muna buƙatar mu zauna idan kin amince zaki zo zan turo
a ɗauki gobe".
"Babu wani abu da yayi saura tsakanina da kai Bilal, Hajja ta kirani tana neman number ka daga
yanayinta kuma na fahimci akwai wani abu da yake faruwa shiyasa kawai na kiraka".
"Ni dama na san ba zaki daina so na ba Haleems, kada ki biyewa su Anty Labiba kin sani dama tun usuli
bata taɓa son tarayyata dake ba. Ina sonki, kuma nayi nadamar duk wasu abubuwa sa suka faru a baya
and nayi miki alƙawarin soyayya da farinciki mara yankewa har idan kika dawo gareni kiyi haƙuri kinji My
Haleems".
Zare wayar nayi daga kunnena, har zan kashe sai kuma na fasa naja numfashi na ce
"Ba zan iya zuwa in da kake ba, amma ka faɗa mun abinda yake faruwa idan ina da halin taimaka maka
zanyi"
"Wata yar matsala ce ta faru, wasu kuɗi Jalilah ta bani nake juyawa kuma tsautsayi ya faɗa musu suka
narke shine ta makani a kotu akan na biyata kuɗin sannan akwai gidanta da yake hannuna shima da aka
siyar ban sani ba ashe gidan takaddun bogi yake dasu yanzu kuma ta zagaya ta sake siyarwa da wani
daban ta haɗani rigima da wanda ya siya a hannuna" ya faɗa tamkar zai fashe da kuka.
Tunda ya ambaci sunan Jalilah wani abu mai ɗaci ya taso ya tsaya mun a maƙogaro, ba abinda nake gani
sai hotonsu ganin da nayi masa na ƙarshe yana kwance akan cinyarta, daƙyar na buɗe baki na ce
"Wlh na rabu da ita Halima shiyasa nace miki ina so mu haɗu akwai maganganu da yawa da nake so na
faɗa miki wanda ba zasu yiwu a waya ba" yayi saurin tarata, na ja hanci saboda hawayen da suke neman
ƙwace mun na ce
"Ya kamata tuntuni ka san cewa alaƙarka da ita ba zata taɓa kasancewa mai riba ba, ka biye mata ka
kaucewa haryar Allah da tarbiyyar addininka, da aurenka Bilal ka zaɓi bibiyar macen banza a waje mai ya
sa? Dame na rageka?" Na ƙarasa ina sakin kukan dana kasa riƙewa.
"Kiyi haƙuri Halima, tabbas na zalinceki kuma nayi nadamar duk abubuwan da suka faru a baya, dagaske
nakeyi ki yafe mun nayi miki alƙawari abinda ya faru a baya ba zai maimaita kansa ba"
"Yanzu kana ina?" Na faɗa bayan dana tsagaita kukan, ya ɗan yi jumm kafin ya ce
"Hajja tana nemanka kuma hankalinta a tashe yake ya kamata ka kirata ta san kana lafiya" na faɗa ina jin
yana ƙoƙarin sake yin magana amma na katse wayar take kuma nayi blocking layin. Kwanciya nayi lamo
cikin yanayin da ni kaina bazan iya fasaltawa ba ina sauraron bugun da zuciyata takeyi. Na rasa yanda
zanyi in daina jin sa a zuciyata, ina jin haushinsa da zafin abinda ya aikata mun amma kuma zuciyata ta
kasa daina sonsa.
Vibration wayar ta shigayi na ɗagota na duba, nayi zaton shi ya canza layi ya sake kira amma sai naga Dr
Salman ne. Sai da na duba agogo sha biyu saura kwata kafin na tashi zaune dakyau na amsa murya can
ƙasa kamar wadda ta farka daga bacci nayi sallama.
"Eh" mukayi shiru, kusan minti ɗaya kafin yaja iska yace
"Baki kirani kinji ya na isa gida ba anya dagaske na samu karɓuwa kuwa Leemah?"
"Mantawa kikayi?" Ya faɗa cike da mamaki, nayi saurin rufe baki na kamar yana gabana nace
"Aa ba haka zan faɗa ba cewa zanyi inata aiki ne ban san dare yayi haka ba so nakeyi idan na gama sai na
kiraka"
"Amma kika ce bacci kikeyi? Ko dai Bilal ne ya ɗauke miki hankali?" Ya jefo mun wata tambayar, nayi
narai-narai da fuska kamar ina gabansa kafin nace
"Shikenan na yarda, toh ya kike ya dare?" Ya faɗa daga haka muka shiga hira wacce zancen tafiyarsa
gobe ne. Dama shi hirarsa kenan aiki da sabgoginsa na rayuwar yau da kullum ni kuma sai dai nayita
binsa da Eh ko Aa dan a gurina wannan ba hira bace, a matsayinsa na mai neman gurin zama a ganina ya
kamata hirar sa ta kasance ta ƙoƙarin kafa kansa a gurina amma shi sam ba haka yake ba. Sha biyu na
bugawa yayi mun sallama, kashe wayar nayi gaba ɗaya dan tun muna magana nake ta jin shigowar kiran
Bilal.
Tunanin fara maganarmu da Dr Salman na tafi, washe garin ranar da muka haɗu dashi a gidan Uncle
Mudassir mun fita tareda su Al'amin da yamma siyo Popsicles muka haɗu dashi a gurin. Har ga Allah ban
so kulashi ba dukda mun haɗa ido musamman da na ganshi tareda wata mace da wani abokinsa ina
tsaye gurin biyan kuɗi ya tarar dani sai jin muryarsa nayi a bayana yana cewa
"Barka da yamma Malama Leemah". Da farko dukda naga tsayuwarsa ban ɗauka dani yake ba
musamman sunan daya kira wai Leemah dan haka ban amsa ba, sai da ya sake matsoni sosai yana
kallona ya maimaita maganar kafin kuma kunya ta kamani na shiga gaishe shi kai a ƙasa. Shi ya biya
kuɗin abinda muka siya ya rakamu har mota kawai ya miƙa mun wayarsa wai na saka masa number na.
Haka na koma gida cike da mamakinsa bai kirani ba sai washe gari Monday lokacin mun fita break, tsarin
number dama gani kawai jikina ya bani shine, ilai kuwa bayan na amsa yace naje na sameshi a office,
tareda Uncle Mudassir na tarar dasu babu kuma jeka ka dawo a gaban Uncle Mudassir ɗin ya ce wai nayi
masa tun ranar daya fara ganina a lokacin ma bai san nice Niece ɗin Mudassir ba kawai yaji yana so na
dagaske kuma idan na amince aurena yake so yayi.
Uncle Mudassir yace masa babu ruwansa shima yace bai sakashi a ciki ba abinda ya saka ya faɗa a
gabansa kawai saboda ya san dagaske yakeyi koda yaji labarin wani zai masa shige ya faɗa cewar yana
ciki, ni dai na tafi na barsu kawai, shikenan ya fara kirana a waya, ban kuma ɓoye masa ba na faɗa masa
na taɓa aure har ina da yara biyu, nayi mamakin jin wai bai sani ba dan na faɗa masa ne saboda ya ji
daga bakina dukda ina da yaƙinin ya sani Uncle Mudassir ba zai ƙi ya gaya masa ba amma yace mun bai
sani ba.
"Bakiyi kama da wacce ta taɓa aure ba har kuma ace kin haifi yara biyu amma ke nake so, aure ko
haihuwa ba zasu canza hakan ba" abinda ya faɗa mun kenan. Soyayyar sa a bayyane take kuma da zafi
yake yinta.
Dukda cewar baya faɗarta da baki amma a bayyane take a duk ayyukansa ba kuma ya shakka ko jin
nauyin wani ya sani kamar yanda nake jin tsoron fallasuwar alaƙarmu a office ɗin, ya mutane zasu kalli
abun ace daga zuwansa kawai soyayya ta ƙullu tsakaninmu? Ba yan office ba hatta da mutanen gidanmu
bana bana so maganar ta fita su ji ban kuma san dalilin haka ba.
Ban sani ba ko kulawar da yake bani ce ta saka zuciyata ƙoƙarin kware masa, yanda yake mun idan yana
tareda ni yana sakani ina jina tamkar sarauniya, abu ɗaya ne cikas ɗin, baya mun kalaman soyayya irin
waɗanda kunnuwana suke da muradin sauraro, amma dukda hakan zan gwada.
HAJJA.
"Toh ki kira Nasir ɗin aji, ni bari na wuce duk yanda zake ciki sai muyi waya" Amina ta sake faɗa tana
miƙewa daga haka tayi musu sallama Anty Habiba ma ta miƙe suka bar Hajjan ita kaɗai.
"Kana kallo duk sunyi tafiyarsu kamar ma halin da ɗanuwanku yake ciki bai damesu ba" ta faɗawa
Abubakar. Yana danna waya ya ce mata
"Toh Hajja me kike so suyi? Shi fa ya jefa kansa a koma menene idan sun zauna mai hakan zai canza?"
"Amma ai sa ɗebe mun kewa su kwantar mun da hankali ko?" Ta sake faɗa, ya miƙa mata waya ganin
Nasir ya amsa kiran ya fice ba tareda ya sake cewa komai ba. Nasir ɗin ma kamar Halima ce mata yayi ya
kwana biyu rabonsa da Bilal yana ta kiran layukansa kuma baya samu sai da yaje can gidan matarsa tace
ai yayi tafiya. Ya ce mata
"Na san dai kin san mai yake faruwa Hajja, ki faɗa masa duk ma inda ya tafi ya dawo dan wannan ba
mafita bace gara yazo kawai ayi abunda za'ayi asiri ya rufu".
"Wai har dubu nawa ne kuɗin da zai saka ya gudu?" Hajja ta tambayi Abubakar bayan data gama wayar,
ya watsa hannu kafin ya ce
"Ai shikenan" Hajjan ta faɗa kamar abar tausayi, har ya miƙe sai kuma ya koma ya zauna ganin tayi
tagumi lokaci ɗaya fuskarta harta wani rame damuwa ta cikata.
WASHE GARI
HALIMA
Ƙarar waya ta ce ta tayar dani daga baccin da ban jima da komawa ba dan tun asuba bayan na idar da
sallah Dr Salman ya kirani bai kuma barni ba har sai da aka fara sanarwar jirginsu zai tashi zuwa Abuja
wayar sama da awa biyu kunnuwana har ciwo naji suna neman kamawa daga ƙarshe a speaker na sakata
na kwanta ina amsa shi da Eh da Aa. Ban jima da komawa baccin ba aka sake kira, na tashi zaune daƙyar,
har wani yaji-yaji kaina yake mun, na ɗaga nayi sallama cikin muryar bacci, sai daya amsa sannan na
fahimci wanene mai kiran dan banga sunan da kyau ba.
"Na tashe ki daga bacci Anty Halima na ɗauka ai kina gurin aiki ma" ya faɗa, nace
"Yau banida aiki shiyasa" daga haka muka gaisa ya ɗan yi jimm kafin ya ce
"Na san ko ba zai kira kowa ba zai kiraki ta yuwu ma ya faɗa miki in da yake, dan Allah ki bani number da
ake samunsa Anty Halima idan kuma ba haka ba nazo ki kirashi sai ki haɗa mu a wayarki"
"Ni bamuyi magana dashi ba amma akwai wata number sa da nake tunanin zaka iya samunsa a ita bari
na tura maka". Sallama mukayi na aika masa da number kafin na kashe wayata na koma bacci.
Abubakar kuwa tana tura masa number ya dannawa Bilal kira, sau uku ya kira bai amsa ba sai ya tura
masa message cewar Hajja tana kwance a Asibiti kuma tace a kirawo mata shi dan jikin yayi tsanani ya zo
idan ba yana so ya mutu da nadamar ƙin zuwan ba.
Yana turawa ya kashe wayarsa ya tafi uzurinsa, ya sani Bilal ɗin yana girmama lamarin Hajja da wahala
kuma ya share alhalin an ce tana kwance a gadon Asibiti.
Tunaninsa kuwa ya zama gaskiya dan lokacin daya kirashi yana zaune yana karyawa ne kuma cikin shiri
yake dan yana so yaje gurin Yusuf da yake ta kira tun daren jiya baya ɗauka bayan sunyi magana ya gaya
masa an sauke kaya ya sauraresu a kowanne lokaci zai iya jin alert tunda sun karɓi details ɗin sa da
komai dama, yana ganin kiran Abubakar ya san tabbas Halima ce ta bashi number.
Niyyar kashe wayar yayi gaba ɗaya ganin yana ta kira sai ga saƙonsa ya shigo take kuwa hankalinsa ya
tashi ba shiri ya kama hanyar Kano. Yana tafe a hanya yana sake gwada kiran Yusuf ɗin shiru har sannan
tana ringing amma ba'a ɗauka, yana guraren Yankaba ya same shi, haƙuri ya bashi wai wayar ce yara
suka saka masa a silent bai lura ba sai yanzu daya ɗakkota yaga tarin missed calls yace ya sameshi a
office yanzu dan haka ya karya akalar motar daga hanyar asibitin da suke zuwa in da yayi tunanin an kai
Hajja zuwa gurin Yusuf ɗin.
Ji ya ringayi kamar ana jijjigashi tsakanin sama da ƙasa, dukda sanyin Ac daya cika office ɗin amma zufa
ta shiga keto masa ya ringa kallon Yusuf ɗin yana sake kallon Tablet ɗin daya kunna masa video.
"Kayi haƙuri Alhaji Bilal, shiyasa na ringa maka magana akan ka rage yawan kuɗin nan amma kaƙi ji,
yanzu ka shiga harkar nan mu mun daɗe da yin wayo a cikinta. Yanda ake samun riba kamar hauka haka
idan Allah ya juyo abun asara ta afku nan ma sai kaji kamar zaka haukace amma kuma idan ka tuna a
baya Allah ya baka dan ya jarabceka yanzu dole kayi haƙuri. Toh yanzu ma haƙurin zakayi mu kumayi
addu'ar Allah ya kawo ninkinsu a gaba, amma gaskiya nafi zargin canza kayan nan sukayi dan irin packing
ɗin da akayi da wahala ace wai ruwa ne ya tarar dasu har yayi wannan ɓarnar sai dai idan dama can
lalatattun ne" Alhaji Yusuf ya faɗa yana dafa kafaɗarsa.
Cike da ƙarfin hali kawai Bilal yake ɗaga masa kai, gaba ɗaya basu fi buhu goma sha zuwa ashirin bane
aka buɗe su lafiya lau sauran komai ya lalace ba ga Zoɓon ba ba cittar ba sun yi funfuna cittar kuwa da
yawan buhunhunan har ta siƙe kamar yanda sukace ta zama kamar ƙurar katako.
"Kaga lissafin iya abinda aka samu nan, sai ka sake turawa da Abu Amar details ɗin sai ku ƙarasa magana,
yanzu bari naje ana jirana idan kuma yanzu zaka wuce sai mu tafi tare ka saukeni dan ba da mota na fito
ba" Alhaji Yusuf ɗin ya sake faɗa, yanda yake magana ba zaka ɗauka da wanda ya tafka asarar Miliyoyin
kuɗaɗe yakeyi ba kamar ma ba komai. Da laluben bango Bilal ya fita daga office ɗin, Yusuf ɗin ne yaja
motar dan ce masa yayi baya gani sosai ya taimaka ya kaishi gida kawai.
"Haba Alhajin Allah kada ka bada maza mana, ni idan na faɗa maka irin ibtila'in daya ringa saukar mun bi
da bi sai kayi mamaki amma dana mayar da komai gurin Allah ba gashi ya wuce ba? Ita rayuwa dama
akwai samu akwai rashi ai, kuma sau tari jarabta tana zama matakin nasara idan kayi haƙuri sai kaga
Allah ya maido maka da dubunsu" Alhaji Yusuf ɗin ya faɗa Bilal sai jin sa kawai yakeyi ba dan yana gane
komai ba.
Har ƙofar gida ya kaishi kafin ya masa sallama ya wuce yana sake jaddada masa kada fa ya sakawa kansa
damuwar da zata haifar masa da wata rashin lafiyar yayi biyu babu, dukiya dai ta tafi ba dawowa zatayi
ba, a waya ya shiga kiran Zulaiha dan baya jin zai iya fita daga motar da kansa. Ƙirjinsa ya masa nauyi
haka kansa sara masa yakeyi sosai tamkar wanda ale kiɗan gangi a cikinsa.
Ya kira Zulaihan yafi sau biyar bata amsa ba daga ƙarshe haka ya lallaɓa baya ko ganin gabansa ya fita
daƙyar bai ko kashe motar ba balle ya kulleta ya fita yana bin bango har ya tsaya jikin get ɗin kafin ya
shiga bugawa da duka ƙarfin daya rage masa.
ZULAIHA
Tana kwance tana baccin huce gajiyar da Ahlan ya tara mata a haɗuwar da sukayi jiya. Tunda suka fara
mu'amala babu wani abu daya taɓa shiga tsakaninsu, zai ɗauketa su fita yawo gari ko suje Hotel amma
ba abinda yake mata sai dai suyi hira duk shaye-shayen da yake ƙoƙarin koya mata sai jiyan tukunna ta
kasa riƙe kanta dan tunda Bilal ɗin ya tafi ita kaɗai ta san a halin da take ko da ba wani samun yanda take
so takeyi sosai a gurin nasa ba amma yafi babu, yanzun da baya nan ga hirarraki da wasannin banzan da
sukeyi da Ahlan ɗin kullum idan ta koma gida har kuka takeyi kafin ta samu tayi bacci, jiyan ji tayi kamar
ya zuba mata wani abu a lemon da suka sha dan sai bayan komai ya lafa kuma ta shiga jin haushin kanta
haɗi da nadamar abinda ya faru ƙarshe bata ko jira shi ba ta hawo Adaidaita sahu ta koma gida.
Tun bayan tafiyar Bilal ta samu free get, gari na wayewa zata yi wanka ta fice sai dare zata dawo,
hankalinta kwance take al'amuranta. Ɗaki Ahlan ɗin ya kama musu ko bai kirata ba zata tafi tayi
kwanciyarta ta wuni a can irin yanda ta saba a lokacin da take gida sau da yawa zata fita da sunan
makaranta amma hotel zata wuce can zata wuni sai magriba ta koma gida abunta.
Duk yawon makarantar data ringayi asar kuɗi kawai ta ringa yiwa Bilal amma ba karatun takeyi ba, canjin
department ɗin ta na uku kenan yanzu ita daya kamata ace tayi graduation kamar yanda Bilal ɗin yake
zato amma maganar gaskiya 200L take shima da taimakon wani saurayinta da yake HOD a wani
department shi ya shiga ya fita idan ba dan haka da tuni an koreta tareda su Suwaiba. Toh yanzun ma dai
bata da banbanci da korarriyar dan tuni semester tayi nisa har ana shirin fara exams amma bata san ta
yanda zata fara sanarwa da Bilal ɗin zata koma makatanta ba.
Ƙarar bugun da yakeyi tamkar zai ɓalle ƙofar ya farkar da ita, a gigice ta rarumi zani ta ɗaura ta fita tana
murza ido, sai data tareshi ganin yana shirin faɗowa. Jiki na rawa ta kamashi suka shiga ciki ya zube akan
carpet yana sauke numfashi kamar mai cutar Asthma. Yanayin da yake ciki ya saka ta wartsake babu shiri
ta rarumo wayarta ta shiga kiran layin Hajja.
Hajja na zaune tareda Anty Ladidi tana bata labarin halin da ake ciki, Ladidin tayi tagumi tana cewa
"Tun jiya Yaya Habiba ta kirani ai ta gaya mun harda yanda suka tarar da Fadila itama. Ashe ɗan abu ta
kazan uba mijin nata mayaudari ne, ya zo ya yiwa mutane lamɓo an bashi yarinya yaje yana gana mata
azaba kamar wanda dama yayi auren ɗaukar fansa? Ai nace mai yasa suka barota a gidan basu tasota a
gaba sun taho ba? Ko sai ya kasheta tukunna sai ya bugo waya yace azo a ɗauki gawarta ko me?"
"Auta mana ko muna da wata Fadilar ne bayan ita?" Ladidin ta bata amsa, kafin ta sake magana wayarta
dake kan cinyarta tana jiran kiran Bilal tunda Abubakar ya gaya mata ya tura masa saƙo ta shiga ringing,
ɗagawa tayi kawai ganin number daga can muryar Zulaiha ta cika mata kunne cikin tashin hankali take
sanar mata ga Bilal ya zo ita dai bata gane kansa ba gashi nan numfashinsa yana sarƙewa.
Miƙewa Hajjan tayi da sauri kafin kuma ta koma kamar wacce aka ja tayi zaman yan bori, cikin tsananin
azabar data ziyarci bayanta zuwa ƙugunta ta saki wayar hannunta tana wayyo Allah dai-dai nan
Abubakar ya shigo, ganin yanayin Hajjan bai ko tsaya jin ba'asi ba ya kinkimeta daƙyar, tare suke da
Abokinsa Isma'l ya shigo ya gayawa Hajja abokin zai shiga su gaisa kenan dan haka ya sakata a motar
Isma'l ɗin suka wuce Asibiti da sauri.
A hanya yake tambayar Anty Ladidi mai ya faru tace masa bata sani ba an dai kirata a waya ne ta miƙe
tsaye kuma ta koma ta zauna gashi sun baro wayar a gida balle subi ba'asin kiran ko na menene?
Aminu Kano suka kaita sun ci sa'a babu ɓata lokaci aka karɓeta emergency, a ransa ya ringa jin babu
daɗi, ƙaryar da yayi saboda Bilal ya zo gashi Allah ya tabbatar da abun. Layin Bilal ɗin ya shiga kira cikin
sa'a Zulaiha dake ta sake gwada layin Hajja taji ƙarar waya a jikinsa ta zaroshi ganin Brother ya saka ta
ɗaga da sauri kafin ma yayi magana ta shiga karanto masa halin da ake ciki.
Salati ya shiga yi jin wata sabuwa kuma take kuma ya fahimci dalilin faɗuwar Hajjan, ya balbaleta da
masifa yana cewa
"Ke mahaukaciyar ina ce da zaki kirata? Mai yasa baki nemi wani daga cikinmu ba?"
"Da Allah Malam dakata mun, ina da number ku ne ko ya aka soma? Toh ban kira ɗin ba idan kaga dama
ka tsaya masifa kada Allah ya sa kazo ka taimaka masa" ta bashi amsa haɗi da yin tsaki kafin ta kashe
wayar.
Tashi tayi ta wuce ɗaki ta sako doguwar riga kafin ta fita waje ta nemo wanda zasu kama matashi kawai
ta kaishi Asibitin, ta manta da mota shiyasa ma har ta tsaya neman taimako zai zo yana nema ya faɗa
mata magana.
Mamaki ya kamata ganin babu mota a ƙofar gidan, amma kuma data tuna a yanayin daya shigo sai
mamakin ya gushe tunda dai ba zai iya tuƙi a hakan ba ta yuwu wani ne ya kawo shi. Ganin motar Alhaji
Zakariyya mai gidan dake jikinsu tana tahowa ta shiga ɗaga masa hannu, bayan ya tsaya ta faɗa masa
abinda yake faruwa, shi ya kira masu gadin kan layin suka shiga suka ɗakko Bilal ɗin suka sakashi a mota
kamar matacce kafin ta shiga suka wuce Asibiti.
Wani private Asibiti ya kaisu dukda ta gaya amsa Aminu Kano suke zuwa amma yace gara aje mafi kusa,
idan yanayinsa ya dai-daita ya fita daga hatsari sai a mayar dashi ko ma inane. Suna tare da Alhaji
Zakariyyan yana ta kwantar mata da hankali Bilal kuma yana ciki tareda likitoci har sanda Abubakar da
ɗaya daga cikin masu gadin ya gayawa Asibitin da Alhaji Zakariyyan yace zasuje ya isa. Ya ballawa Zulaiha
harara kafin ko ya ɗauke ido itama ta maka masa tata, yayi ƙwafa ya wuce suka gaisa da Alhajin yana
amsa godiya sai lokacin ya wuce bayan ya musu fatan Allah ya bashi lafiya.
Ba jimawa Likita ya fito, Zulaiha ta tashi d sauri haka Abubakar ya kallesu yana cewa
"Eh ni matarsa ce" ta bashi amsa da sauri Abubakar ya sake hararta kafin ya ce
"Ya jikin ɗan uwana likita? Mai ya same shi dan Allah?"
Office yace su bishi, a taƙaice yayi musu bayanin jinin Bilal ɗin ne yayi mugun hawa sakamakon wata
damuwa ko tashin hankali daya fuskata a bazata.
"Mun bashi duk wani taimako da yake buƙata a yanzu ya kuma samu bacci zamu jira zuwa ya farka kafin
kuma mu san mataki na gaba" Likitan ya faɗa. Godiya suka masa suka fita Abubakar ya wuce gurin biyan
kuɗi ya bada abinda aka buƙata. Yana gurin Anty Amina ta sake kiransa dan suna hanyar kai Hajja Asibiti
ya kirasu duka ya faɗa musu harda Fadila da ya samu number ta cikin sa'a, suna gama waya da Zulaihan
kuma ya sake kira ya sanar musu halin da Bilal ɗin yake ciki, akayi sa'a kuma Anty Amina tana ta gurin
Asibitin Malam ɗin dan haka tana zuwa tace ya tafi gurin Bilal ita da Ladidi zasu tsaya da Hajja kafin su
Habiba su ƙaraso.
Kira tayi tana sake tambayarsa jikin Bilal ɗin yace musu da sauƙi da kuma abinda aka ce yana damunsa.
"Itama Hajjan sunce jininta ne ya hau" ta faɗa masa, yayi ajiyar numfashi ya ce
"Nayi tunanin haka dama, amma dai babu wani abu bayan wannan ko?" Ya tambayeta. Tace
"Haka muke fata amma dai basu ce komai ba yanzu sun ce sai ta farka an gani"
"Shikenan, bari na tambaya nan ɗin naji idan zai yuwu mu ɗauke shi kawai a dawo dashi nan ɗin dan nan
Asibitin bai yi mun ba gaskiya" Daga haka sukayi sallama.
Gurin likitan ya koma ya faɗa masa buƙatar sa sai likitan yace suyi haƙuri dai zuwa ya farka idan ma zasu
kaishi wani gurin.
"Ka raina kulawarmu kenan Alhaji" Likitan ya faɗa yana murmushi, Abubakar ya ce
"Ba haka bane, mahaifiyarmu ce itama babu lafiya tana can AKTH ɗin, idan aka haɗe su guri guda
hankalinmu zai fi nutsuwa guri ɗaya shine dalili"
"Haka ne gaskiya, Allah ya bata lafiya babu damuwa kuma da zarar naga yanayin jikin nasa yayi yanda
za'a iya motsashi zuwa wani guri sai ayi hakan" cewar Likitan.
Zulaiha ya bari ya koma can gurinsu Hajja, itama ya tarar tana bacci. Su Anty Habiba harda wasu daga
cikin yan uwan Hajjan suna gurin Fadila ce kaɗai babu suka wuce gida tareda Anty Amina ta ɗebowa
Hajjan abubuwan da zata buƙata daga can suka biya gurin Bilal suka tarar da yan uwan Zulaihan
Ummanta da ƙanwar Umman Anty Habi sai Nuratu da Mijinta. Har sannan bai farka ba. A nan ya bar
Anty Amina ya wuce ya kai kayan Hajjan, haka sukayi ta jigila tsakanin Asibitoci biyu har dare kafin yan
dubiya suka wuce gidajensu sai masu jinya aka bari.
Abinda ya saka ya ɗan da sakewa Zulaiha fuska jin tace zata kwana da Bilal ɗin daya ce ta wuce gida shi
zai zauna tace Aa har kaya ma taje ta ɗakko shima ta haɗo masa abinda zai iya buƙata idan ya farka. Sai
lokacin ya tambayeta motar Bilal ɗin fa? Tace masa ita dai data fita nemo wanda zasu taimaka mata bata
ganta a wajen ba.
Washe gari da Asuba Bilal ya farka gaba ɗaya dan ya farka da yammacin jiyan amma suka sake mayar
dashi bacci saboda jinin bai sauka yanda suke buƙata ba. Jikin yayi kyau sosai dan da kansa ya tashi ya
shiga banɗaki dukda dai yaba dafe kansa da yace yana sara masa har sannan. Tarar dashi ido biyu da
Abubakar yayi ya saka yace a basu transfer kawai su koma can gaba ɗaya likita kuma bai ɓata lokaci ba
ya basu aka ɗauke shi a Ambulance shi dai Bilal kallonsu kawai yakeyi dan tunda ya farka bai yi wata
doguwar magana ba har aka kai shi ɗakin da Hajja take a Retainership.
Bayan da Anty Amina taje aka ɗauketa itama daga General Emergency da aka fara kaita aka mayar da ita
can tunda suna da file kuma account ɗin su is loaded, ɗaki ɗaya aka kwanar dasu, ganin Hajja da har
sannan bata ko motsa ba ya saka ya magantu ya shiga tambayarsu mai ya sameta?
Sai yammacin ranar Hajja ta farka wannan ya saka hankalinsu ya sake kwanciya sai dai bata ko yi awa
ɗaya ba jiki ya sake rikicewa kuma aka rasa abinda ya sameta sai daga baya wata nurse ta lura da
kumburin da guiwarta tayi baby ɓata lokaci aka wuce da ita X-ray, ashe faɗuwar da tayi ne karayar da
tayi a guiwar wancan lokacin ƙashin ya sake gocewa dan dama lallaɓa ƙafar kawai takeyi tun lokacin ba
wai ta koma dai-dai bane. Sabon ɗori aka sakeyi mata sannan aka raba musu ɗaki da Bilal saboda yan
dubiya da likitan yace surutansu zasu dameta, shi kansa Bilal ɗin sun ƙi su barshi ya samu isasshen hutun
da yake da buƙata balle ita da aiki ya dawo sabo.
Sai da suka kwana uku a Asibiti kafin Fadila da Mijinta sukaje. Allah ne kawai ya ɗorata a kansa, duk irin
kuka da kururuwar data ringayi bayan Abubakar ya kirata a waya ko kallonta Ahlan ɗin bai yi ba daga
ƙarshe data ishe shi ya kamata ya mata shegen duka wanda dama ya riga ya zame mata tamkar abinci,
idan bata ci da safe na zata ci da rana ko da dare sai dai idan Allah bai saka tayi kuskuren da yaga ba zai
iya ɗauke ido ba.
Tunda yan rakiyarta suka gama ficewa daga gidan ta tashi ta gyara kwalliya tayi amfani da duk wasu
abubuwa da aka bata saboda lokacin ta fita falon saman ta zauna tana jiran Ango da sai da dare ya fara
nisa kafin ya shigo gidan ya kuma fara da kwance mata jakar tsabar rashin mutunchi da tijarar daya
tanadar mata.
Bai ko iya jira gari ya waye ba, a daren tana naɗe kan kujera tana dakon zuwan Habibinta su murji
soyayya cikin aminci. Burinta ya cika tayi irin auren da take fata, ta samu matashin mai kuɗi kuma
kyakkyawa ga gida na nunawa sa'a da kayan alatu cike duk masu yi mata dariya da cewar alhakin Umar
tsohon mijinta ne yake bibiyarta gashi nan tunda suka rabu ta kasa samun miji shi kuwa tuni yayi aure
har matarsa tayi haihuwa biyu basu san tanadin da Allah ya mata ba yanzu sai su banbance tsakanin ita
da shi waye yafi wani samun cigaba?
Tana tsaka da wannan tunanin ta ji ana kwarara mata kira kamar yaƙi daga ƙasa, da fari bata ɗauka
muryarsa bace sai da ya fara hawowa saman sukaci karo a bakin ƙofa zata fito yana shirin shiga ya kuwa
kwaso ashar ya watsa mata yana tambayar shi ɗin sa'an uwarta ne da tana ji yana kiranta amma tayi
masa banza?
"Lafiyarka kuwa Ahlan? Mai kasha haka?" Take kuwa ya naɗe hannun riga ya gwada mata aikin marasa
lafiya na gaske. Ya mata dukan tsiya sannan ya tankaɗa ƙeyarta ciki ya kwanta da ita cikin mafi ƙasƙancin
yanayi sai kace wata dabba kafin ya tsallaketa yayi ficewarsa bata sake sanya shi a ido ba sai washe gari
da yamma zuwa lokacin tayi kuka har idanuwanta suna neman su daina gani ba kuma ta jira wani ya biya
mata karatun ba ta fahimci in da kwaɗaiyi da son zuciyarta data mahaifiyarta ya jefo ta.
Da yammacin ranar kuma ya ƙarasa warware mata komai, kamar yanda ya sanar mata shi tun farko bai
yi niyyar aurenta ba, rashin amince masa da batayi a waje bane ya saka ya canza shawara dan tunda
yawunsa ya tsinke to fa ba zai haɗiye ba sai ya ɗanɗana shiyasa ya yanke shawarar aurenta da niyyar ya
saketa bayan burinsa ya cika amma kuma bayan faruwar komai yaji tayi masa yanda yake so dan haka ya
fasa ba zai saketa ba sai dai ta sani babu soyayya a zamansu, zata zauna ne kawai a matsayin abun biyan
buƙatarsa domin ita ɗin bata kai ya kirata da matarsa ba.
"Sharaɗin zaman lafiyarki a gidan nan na farko ban yarda wani daga cikin makwaɗaitan danginki ko
uwarki suzo gidan nan ba, balle aje kan ƙawaye ko wasu tarkace hakanan kema ba zaki fita ko ina ba" ya
faɗa mata. Ya lissafa mata sauran Sharuɗan sa, ta ringa kuka tana roƙonsa daya taimaka mata ya
sawwaƙe mata amma yace bai san zance ba ko tana so ko bata so sai fa ta zauna dashi kuma ya ƙwace
wayarta. A ɗan lokacin nan taga bala'i ganin idonta, babu rashin ci babu na sha ga muhalli mai kyau Ac
har ta isheta kuma bata isa ta kashe ba idan ya so mugunta haka zai ƙure sanyin duka Ac gidan idan
kuma yan iskansa suna kusa yace ta cire kayanta tayi ta yawo tsirara yana kallonta bata isa kuma tayi ko
jimm kafin ta aikata abinda ya umarceta ba zai rufeta da duka duk ya canza mata kamannin fuska saboda
mari da hauri da ƙafa.
Yau ɗin ma tayi mamakin yanda tana zaune kawai ya shiga yace ta shirya suje duba Hajja. A hanya toshe
kunnuwanta kawai tayi saboda cin mutunchi da zagin da ya ringa mata da iyayenta kuma bata isa ta yi ko
tari ba balle ta mayar da martani.
Kallonta suka ringayi kamar sunga wata baƙuwar halitta, ga dai Lace har Lace a jikinta da mayafi na garari
amma sai tayi daban a cikin kayan kai idan ba wanda ya mata mugun sani ba ma ba lallai a kallo ɗaya ka
gane Fadilan bace. Hajja dai sai ido, duk inda Fadilan ta motsa sai ta bita da kallo kawai ko sannun da
take mata ta kasa amsawa. A ɗar ɗar Fadilan ta ringa gaishe su tana satar kallon Ahlan ɗin daya kame a
gefe yana kallonsu a ɗage kamar yaga kashi, sai da ya mula kafin kuma ya musu gaisuwar jam'u kuma ta
raini wai
"Sannunku" sai kace ba yayyen matarsa ba harma da iyayenta dan akwai ƙannen Hajja biyu da matan
Baba Sani a gurin.
Daƙyar ta iya tambayar Yaya Bilal suka ce mata yana ɗakin dake kallon wannan, ta saci kallon Hajja
wadda da alama mamaki ne ya kulle mata baki kafin cikin murya tsantsar ladabi ta ce masa suje can
ɗakin su duba Bilal. Rafar yan dubu-dubu guda biyar ya zaro ya ajiye akan drawer dake gefen gadon kafin
ya juya cike da taƙama ya fice daga ɗakin duk suka rakashi da ido itama ta bishi simi simi kamar
marainiyar kyanwa.
"Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un mun shiga uku dama haka mijin Fadilan yake?" Anty Habiba ta faɗa tana
tafe hannu, nan ta buɗewa masu jira fili suka fara sakin maganganun da suka cika musu baki, Anty Amina
ta miƙe tana cewa
"Amma dai kun san nan ba gurin mayar da zance bane ko? Dan Allah ku fita, dama ai sun ce anyi yawa a
ragu haka ko ta samu ta koma bacci ta huta".
Su Fadila kuwa ɗakin da Bilal yake suka shiga, ita ta fara shiga ya tsaya yana amsa waya. A nan ta tarar da
Abubakar, sai da tayi dagaske gurin danne kukan daya so ƙwace mata dalilin ganin wanda take ganin shi
kaɗai zai iya cetota daga bala'in da take ciki amma bata isa ta faɗi wani abu a yanzu da suke tareda
Ahlan ɗin ba. Gaban gadon da Bilal ke kwance ta isa tana amsa sannu bayan ta gaida Abubakar daya
zuba mata ido cike da mamaki yana kallonta, ta gaisa Zulaiha dake zaune gefensa dai-dai nan Ahlan ɗin
ya shigo ɗakin da sallama kamar bashi ba.
Fuska a sake ya miƙawa Abubakar hannu suka gaisa kafin ya matsa gaban gadon yana yiwa Bilal dake
kallonsa kamar ya samu Tv sannu.
Gyara tsayuwa yayi kafin ya shammaci Zulaiha da ganinsa ya saka tayi suman zaune ya mintsineta a
gefen ciki. Ba ƙaramin ƙoƙari tayi gurin hana kanta yin ihu ba, sai ta mike da sauri ta fice daga ɗakin ya
zauna a inda ta tashi yana sake yiwa Bilal sannu ya gyaɗa masa kai alamar amsawa.
"Baya magana ne?" Fadila ta tambayi Abubakar, ya ce mata
"Wai mai ya same su Yaya?" Ta sake tambaya idanuwanta suna kawo ruwa, Abubakar ya ce
"Hawan jini ne dai duk su biyun, silar sa kuma bamu sani ba har yanzu tunda itama Hajjan kinga bata
magana gara shi yana yi kawai yaƙi faɗar abinda ya same shi ne"
"Toh fa hawan jini duka su biyu toh Allah ya basu lafiya ya mayar musu kaffara kuma" Ahlan ya faɗa yana
miƙewa. Ganin ya nufi ƙofa Fadila ta bishi ya dakatar da ita yana cewa
Can nesa ya hango Zulaiha ya nufeta, a firgice ta waiga ta kalleshi ta shiga zare ido tana dubawa ko wani
yana kallonsu kafin murya na rawa tace masa
"Yanzu dama ƙanwar Mijina kake aure amma shine...shine" sai ta kasa ƙarasawa saboda tashin hankalin
daya mata rubdugu har muryarta ta bayyanar da hakan.
"Wlh idan ka kashe mun aure Allah ba zai barka ba" ta faɗa hawaye na ɓalle mata. Yayi dariya kafin ya ce
"Sai dai idan ke kika so ki kashewa kanki aure, tun ranar dana fara ganinki na san alaƙarki da wacce nake
shirin aure a lokacin. Kin mun, da ace kuma baki da aure na gaya miki da zan aureki, tunda kuma mun
samu sararin da zamu mori junanmu menene aibu a ciki? Ni dai maganar nan ba zata taɓa fita daga
bakina ba idan har wani ya jita to sai dai daga gurinki. Kuma mijin naki da kike magana akai kina zaton ko
kamamu yayi zai ɗauki wani mataki akan hakan ne? Kafin kiyi shi ya fara ko baki da labarin abinda ya
rabashi da matarsa ne?
Ni yanzu ki san yanda zaki zille muje mu dawo dan wlh tun waccen ranar kin barni da kewarki ko yi nawa
zanyi da ita bana jin na ƙoshi sam bata da juriya kamarki" ya ƙarasa yana ɗage mata gira cike da iskanci.
"Ni dai kayi haƙuri ka rabu dani babu wata sauran alaƙa tsakanina da kai" ta faɗa kafin ta raɓe shi ta bar
gurin. Murmushi mai kama da dariya yayi yana binta da wani kallo ya ce
"Baki isa ba yarinya, Ahlan bai taɓa neman wani abu ya rasa ba tunda kuma aka fara sai an cigaba har sai
idan ni na daina yayinki tukunna".
*KURA A RUMBU*
*Wattpad @MaryamahMrsAm*
*GODIYA TA MUSAMMAN*
*Dukkan godiya ta tabbata ga Allah (SWT) daya hore mun lafiya da tsayin kwana har na kammala rubuta
wannan littafi. Salati da aminci su tabbatar ga fiyayyen halitta, katimul anbiya'i, Nabiyyina Muhammad
(SAW). Ya Ubangiji ka sake cika zukatanmu da imani tareda soyayyar mafi soyuwar halittarka Annabi
Muhammad (SAW).*
*Ina roƙo Ubangiji ya haɗa mu a ladan abinda na rubuta na alkhairi ina kuma roƙonsa da ya shafe
zunubin kura-kuren da na aikata a cikin rubutuna. Allah Alhamdulillah nagode da ni'imar da kayi mun*
*Godiya musamman gareku makaranta da kuka bada lokacinku cikin wannan doguwar tafiya ta littfain
KURA A RUMBU. Idan nace zan lissafo sunaye toh tabbas littafi mai shafi dubu yayi mun kaɗan. Littafin
nan bai zama cikakke ba sai da gudunmawar ku, da kalmomin ƙarfafawa, shawara da goyon bayan da
kuka bayar, Nagode ƙwarai da karamci haɗi da soyayya ina fatan ubangiji ya fini yabawa. Ina roƙon Allah
Ya saka da alheri ga kowane ɗaya daga cikin ku. Allah Ya sanya wannan rubutu ya kasance hanyar tunani,
gyara, da faɗakarwa ga duk wanda ya karanta shi.*
*Idan littafin KURA A RUMBU ya taɓa zuciyarku ko ya ƙara muku hangen nesa game da rayuwa da
soyayya, to lallai burina ya cika, ina fatan zakuyi amfani da saƙon da yake ciki ku watsar da duk wani abu
daya ci karo da tunani ko rayuwa ta zahiri*
*LUBNA SUFYAN yau Allah ya nufa kwana uku ta cika 🤣🤣🤣🤣 na gode ƙwarai da karamchi da ƙarfafa guiwa.
Allah ya raya miki Yusra*
*MARYAM FAROUK*
*(UMMU-MAHEER)*
*LAST PAGE*
Ranar da Bilal ya kwana bakwai a Asibiti aka sallame shi sai Hajja wacce tun zuwan Fadila jikinta ya sake
rikicewa sauƙin data fara samu komai yaja baya bata da aiki sai kuka da Allah ya isa ga Ahlan da tace ya
yaudaresu ya auri autarta yaje yana azabtar mata da ita.
Ganin jikin Bilal yayi sauƙi sai abinda ba za'a rasa ba ya saka aka sallameshi bayan likita ya ja masa kunne
sosai akan kulawa da lafiyarsa. Sosai Zulaiha ke tsaye a kansa tana kulawa dashi, yanda Bilal yayi wani
sanyi ƙalau lokaci ɗaya dole ya baka tausayi gashi tambayar duniya yaƙi faɗawa kowa abinda yake
damunsa sai dai ya samu guri ya zauna shiru wani wani lokacin har idanuwansa su tara ƙwalla da gani
akwai wani abu da yake cin ransa amma ya kasa furtawa.
Ranar wata talata daya kama kwana huɗu da sallamo shi daga Asibiti, suna zaune tareda Abubakar da
Nasir sai Alhaji Sani Abokinsa da kuma Anty Amina suna jajanta batun motarsa da zuwa lokacin ta
tabbata sacewa akayi. Ya ce musu a waje ya barta waccen ranar kuma da muƙullin a jiki sanda ya koma
gidan. Kwana biyu kenan daya fara buɗe baki yana magana sosai har yayi hira da masu zuwa dubashi.
Ranar da aka sallamo shi Abubakar yake tambayarsa batun motar tunda Zulaiha tace sanda ta fito itama
bataga mota a gurin ba kawai ya saddaƙar itama Azal ta faɗa mata an sace.
Abubakar ɗin ne yaje har gurin masu gadin layin ya tambayesu tunda ba yanda za'ayi ace an sace mota
suna gurin suce basu lura ba suka ce masa tabbas suna zaune aka fita da motar amma basu lura bashi
bane a ciki tunda sunga shigarsa kuma dama ko horn bayi musu yakeyi ba yanzu balle sallama shiyasa
suma da ya taho kawai zasu buɗe masa get ya wuce ne ba ruwansu dashi.
"Ai kaga illar rashin zaman lafiya da mutane, banda sakarci ta yaya za'ayi ka ringa faɗa da masu gadi?
Yanzu da lafiya lau kuke zaune ai ko banza ka taho ka saba musu magana idan suka ji shiru zasu iya
zargin wani abu ƙila da haka bata faru ba. Yanzu ai sai a kai report police station idan da rabo ƙila a dace
a gano wanda ya ɗauka" Alhaji Sani ya faɗa.
Nasir ya buɗe baki zaiyi magana kenan Zulaiha ta shiga falon da sallama.
"Jami'an tsaro ne" ta bashi amsa dai-dai lokacin da baƙin su biyar suka yiwa kansu iso zuwa falon.
Ciki suka shiga, wanda yake Shugabansu ya zaro ID card daga aljihun rigarsa fuska babu wasa ya ce
Gaba ɗaya suka kalli Bilal ɗin daya sunkuyar da kai ƙasa cikin yanayin na tashin hankali dan lokaci ɗaya
zufa ta fara keto masa tamkar wanda ya zauna akan kunama. Abubakar ne yayi ƙarfin halin cewa
Kana da ‘yancin yin shiru, domin duk abin da ka faɗa yanzu zamu iya amfani da shi a matsayin hujja a
gaban kotu.
Kana da ‘yancin ɗaukar lauya domin kare kanka, dan haka yanzu zamu tafi da kai office domin ci gaba da
bincike. Officer, saka masa ankwa" ya ƙarasa maganar yana kallon Ɗansandan dake riƙe da ankwa yana
jiran umarni. Gurin Bilal ɗin da yayi mutuwar zaune ya ƙarasa ya kamoshi babu ɓata lokaci ya buga masa
Ankwa.
Salati Anty Amina da Zulaiha suka shiga yi kafin suka fashe da kuka a tare, Nasir da Alhaji Sani suka miƙe
tsaye kowanne cikin tashin hankali. Cike da damuwa Abubakar ya ce
"Amma ranka ya daɗe baya cikin yanayin d zai iya fuskantar shari'a a yanzu bashida lafiya bai daɗe da
fitowa daga Asibiti ba".
"Zaka koya mana aiki ne Malam? Ko a gadon Asibiti yake dole doka zatayi aiki akansa batun rashin lafiya
ko wani abu kuma wannan bincike ne zai tabbatar duk kuma abinda ya kamata za'ayi."
"Ranka ya daɗe amma da anyi haƙuri ba sai an saka masa Ankwar ba sai a tafi a haka" Alhaji Sani ya faɗa
ba tareda ASP ya kalleshi ba yayiwa yaransa alama da su wuce haka suka tasa Bilal da ko uffan bai iya
cewa ba kuma bai kalli kowa ba suka fice daga gidan Alhaji Sani da Nasir suka bisu.i
"Kubar kukan haka Anty, bari mu bisu dan Allah ki kira Yaya Alhaji ko Yaya Aminu sai su samemu a
station babu abinda zai faru insha Allah amma dan Allah kada ki bari Hajja taji maganar nan" Abubakar
ya faɗa.
"Kaima ka san su Yaya ba zasu yarda su shiga maganar nan ba tuntuni irin wannan ranar nake guje masa
amma yaƙi ji itama Hajja ta ringa goya masa baya yanzu wa gari ya waya?"
"Yanzu ba lokacin mayar da magana bane Anty bari naje" ya bata amsa yana ficewa da sauri jin tashin
jiniya alamar sun wuce ko ya akayi basuji zuwansu bama oho?
"Ki kwantar da hankalinki insha Allahu komai zaizo da sauƙi bari naje muga yanda za'ayi" cewar Anty
Amina Zulaiha dake kuka ta ɗaga mata kai. Anty Amina na fita itama Zulaihan ta canza kaya ta bar gidan
cikin tashin hankali, dukda rana ce amma mutane sun cika bakin layin anata mayar da magana kowa da
kalar nasa narration ɗin dukda babu wanda ya san mai ya faru.
Bayan fitar Anty Amina a hanya ta kira mijinta ta gaya masa abinda yake faruwa ya tambayeta station
ɗin da suka tafi tace bata sani ba amma ya kira Abubakar daga nan ta wuce gidan Baba Sani dan tace ba
zata iya kiran Alhaji Aminu ko Yaya Alhaji ba kamar yanda Abubakar yace ta san ma da wahala Alhaji
Aminu ya saurareta har gara Yaya Alhajin dukda shima ranar daya je duba Hajja tana kwancen haka ta
ringa zaginsa tace wai dashi aka haɗa baki aka cuci Fadila ya san ba mutumin kirki bane amma ya bari ya
aureta.
Duk irin ƙoƙarin da su Nasir da Mijin Anty Amina sukayi akan a basu belin Bilal abu bai yuwu ba kamar
yanda suka ce gobe za'a turashi kotu dan haka su nemi lauyan da zai tsaya masa kawai.
Cike da damuwa Zulaiha ta kalle Alhaji Mudan, tsohon saurayinta ne kuma babban mutum ne mai faɗa
aji. Gurinsa ta tafi ta roƙe shi akan ya shiga maganar ya fito da Bilal; kai tsaye ya kira CP kuwa yace ya
bashi lokaci zai bincika ya kira shi sai bayan Magriba Alhaji Mudan ɗin ya kirata yake gaya mata sai dai
tayi haƙuri for babu dama amma sunce gobe za'a kai shi kotu zai ga duk abinda zai yuwu a kotun kada ta
tayar da hankalinta.
"Abinda kuka kasa ganewa kenan ku tsallakemu ku auri yaran da yawanci banda ɓacin rai da damuwa
babu abinda kuke tsinta a auren nasu. Duk yanda akw ciki you keep me update, dukda zanyi tafiya goben
amma idan kin kira layina baki samu ba ki kira Bashir duk abinda ake buƙata zai yi" Alhaji Mudan ɗin ya
faɗa mata tayi masa godiya kafin ta kashe wayar tana sharw hawaye.
"Aikin banza aikin wofi, haka kawai kika nace sai shi ba yanda banyi dake ba tunda mun rigada mun
gama cin moriyar ganga mu yar da fata mu huta kika ce ke ba haka ba yanzu tun ba'aje ko ina ba gashi
nan, na ma rasa wane munafukin ne ya kawo zancen unguwar nan ɗazu kina fita Usainar Hadi ta shigo
wai daga gidan Larai take taji ana zancen an kama mijinki wai ashe ɗan damfara ne. Tunda zance yaje
gidan Larai kuma ai duk Kano ta ɗauka dama cike take da baƙin cikin Allah ya rufa mun asiri kun tashi
lokaci guda."
"Amma Umma duk duniya dai kin san ba zan taɓa samun mijin da zai so ni saboda Allah ba kamar Bilal.
Kina kallo duk abinda ya faru amma ya karɓeni a hakan muna zaune sau ɗaya bai taɓa nuna rashin
amincewa ko zargina ba kina zaton da ace ba shi na aura ba da yanzu ban dawo gidan nan ba?"
"Yawon kika cigaba dayi ko me?" Umman ta tambayeta tana dafe ƙirji, tana goge fuska da hijabi ba
tareda ta bata amsa ba ta shige ɗaki. Da shirin wanka ta fito, ta shige banɗaki ana idar da sallar Isha'i ta
cewa Umman zataje ta kaiwa Bilal abinci.
"Au ke abinci ma kike shirin tafiya kai masa? Toh bari kiji, bafa zata saɓuba wlh. Tunda akai auren nan
ɗan abinda yake kawowa da yanzu ya daina. Rabon daya ajiye mana buhun shinkafa a gidan nan tun
watan aurenku, haka kuɗi yanzu ko ya ya zo dubu biyar ce ko goma Allah na tuba mai zasu mun?
Ni ba haka na zata ba dan haka an yi akan gaɓa mun samu mafaka sakin ki kawai zai yi can ya ƙarata ki
nemi mijin gaske ki aura."
"Idan kika ga na rabu da Bilal Umma to kice shi ya sakeni ko ya ce baya buƙatar cigaba da zama dani. Ina
son Mijina, abinda ya sameshi kuma ba zai sa in daina son sa ba dan ya karɓe ni da abinda ya fi nasa
muni bai gujeni ba dan haka sai inda ƙarfi na ya ƙare amma ba zan taɓa bari ya tozarta ba" tana gama
faɗar haka ta fice daga gidan.
Take away mai kyau tayi masa sannan na siya masa tabarma irin mai soso a ciki da pillow harda net kafin
ta wuce station ɗin. Ta tarar da Abubakar da Nasir a can da kuma Lawyer da aka ɗaukar masa mai suna
Barr Sajid, yini ɗaya kacal amma sai ka ɗauka har an kaishi gidan yari ne duk ya fita a hayyacinsa
musamman da Cell ɗin da aka sakashi sai a hankali, da dabaru irin nata da kuma kuɗaɗen hannunta ta
saka aka canza masa cell mai ɗan dama-dama. Har after ten suna gurinsa ta ringa kwantar masa da
hankali kafin suka tafi tareda su Abubakar zasu sauketa a gida.
Washe gari ƙarfe sha ɗaya aka fara shari'ar Bilal, babu jeka ka dawo ya amsa laifinsa dukda Lawyer a jiya
ya faɗa masa idan an je kotu ya musa zargin da ake yi masa, a lokacin da za'a bayar kafin a sake zama
zaiyi duk mai yuwuwa ya wanke shi amma daya kwanta cikin dare ya aksa bacci sai tunani daga ƙarshe
ya yankewa kansa shawarar karɓar ƙaddara a yanda tazo masa kawai.
Sati biyu Alƙali ya bayar, kotu ta watse duk kuma yanda lauyansa ya shiga ya fita nan ma Beli bai samu ba
aka kai shi kurkuku kafin zagayowar ranar da za'a sake zama.
Yana kallon Jalilah dake tareda Ahlan tana masa murmushi irin na bakaga komai ba ma tukunna a lokacin
da aka fito dashi za'a sakashi a motar gidan Kurkukun. Haka ya sauke kansa ƙasa ya kasa kallon yan
uwansa da duk suka halarci zaman kotun Hajja Anty Habiba ne kaɗai basu zo ba ita tana can tareda
Hajjan. Takanas wata maƙwafciyarsu taje da daddare daƙyar ma aka barta ta shiga ashe labarin kama
Bilal taje kai mata. Yanda maganar ta baza gari lokaci ɗaya abun mamaki, lungu da saƙo dangi kowa
labari ya isar masa yanda kasan an yi yekuwa.
Haka aka wuce dashi Prison tun kuma daga isarsu ya fahimci ashe jiya a Aljanna ya kwana, yana ganin bai
taɓa riskar dare mai muni irin na jiya ba yana isa Kurkukun ya fahimci Alƙiyamarsa ta tsaya, lokacin fara
girbar abinda ya shuka tun a duniya ya zo. Haka ya canza kaya ya rungumi sabuwar rayuwar da Son
zuciya da kwaɗayi suka jefashi a ciki.
Dare ya tsala, yana kwance kan dandaryar ƙasa, tun yana kore sauro da wasu ƙwaruka da suke binsa da
bai ko tantance waɗanne iri bane ƙarshe ya haƙura ya zubawa taurarin da sukayiwa sama ado idanuwa
tamkar mai ƙirgasu amma a zahiri yayi nisa cikin tunanin rayuwa ne.
Ya amince duk abinda ya faru shi ya jawa kansa, kwaɗaiyi da son zuciyarsa ya kawo shi wannan
matsayin. Ya ringa tariyo rayuwarsa tun daga sanda ya fara sanin kansa, shi ɗin ya taso da burika da
dama. Tabbas Hajja tayi ƙoƙari akansu, ko da sun rasa mahaifinsu tun suna da ƙananan shekaru amma
bata barsu sunyi kukan maraici ba. Iya ƙarfinta ta sama musu abinda wasu masu uban a raye ma basu
samu kamarsa ba, musamman shi daya kasance na daban ko a cikin sauran tana sonsa kuma bata ɓoye
hakan ko a cikin yanda take tafiyar da lamuransu.
Ko da bai samu kuɗi yanda yake fata ba amma ubangiji ya rufa masa asiri domin yana samun abinda zaiyi
buƙatun yau da kullum ba tareda ya nemi taimakon wani ba. Sai dai ido da hange-hange da kuma burika
suka saka ya raina ni'imar da Allah yayi masa, hakan ya saka ya zama kullum yana cikin neman hanyar da
zai samu kuɗi amma fa daga kwance ba tareda ya sha wahala ba domin kamar yanda yake cewa su Nasir
a sanda suke yawo cikin ruwa da rana suna fafutuka ya kan ce shi ba kalar wahala bane ruwan jin daɗi
aka masa dan haka yana zaune arziƙi zai tarar dashi ba sai ya fita ya nema kamar yanda sukeyi ba.
Cikin sa'oinsa da suka gama karatu tare shi ya fara samun aikinyi, sannan ubangiji ya hore masa macen
da ya sani samun kamarta a wannan zamanin sai dace. Bata dubi abinda yake dashi ba, bata taɓa
damuwa da mai zai bata ba, ta san yana dashi amma ta ɗauke kai ta wadatu da abinda take dashi sannan
bata taɓa yin ƙyashin bashi abinta ba. Ta shanye baƙin ciki, ta ɓoye damuwa, ta jure tozarci da wulaƙanci
amma daga ƙarshe ya biyewa shaiɗan ya barta.
Tabbas, yanzu da bulalar nutsuwa ta sameshi ya fahimci kura-kuren daya tafka a zamantakewatarsa da
Halima ya kuma yarda da cewar da mutane da yawa sukeyi haƙƙinta sai ya bibiyeshi.
Duk abinda ya samu ta silarta ya rasashi, waɗanda sukayi saura ma ya sani yana dab da rasa su uwa uba
ya rasa mutunchi da ƙimarsa.
Ya ringa tafka kuskure a koda yaushe yana raya cewa nan da lokaci kaɗan zai daina, zai gyara kura-
kurensa sai dai a duk sanda ya yi yunƙurin dainawar sai zuciya ta sake angizashi ta sake kwaɗaita masa
wani abun ya sake ƙudurce idan ya same shi zai tuba a haka yayi ta zurmawa har aka kawo wannan
lokacin daya faɗa cikin rijiya mai gaba dubu. Bai fahimci talala ubangiji ya ringa masa ba sai yanzu daya
kama shi dumu-dumu.
A haka ma kuma ya godewa Allah domin ya masa gata da bai barshi ya mutu a kan ɓarna ba, yana addu'a
da fatan abinda ya faru ya zame masa ishara da sauran masu hali irin nasa.
A haka ya shafe sati biyu a kurkuku cikin yanayin da shi kaɗai zai iya fasaltawa. Sai ya kwana ya yini bai
saka komai a cikinsa ba dan hatta da ruwan gurin baya iya sha. Shopping sosai Zulaiha tayi masa harda
miya da soyayyen nama ta kai masa amma yana shiga ciki wasu suka ƙwace bai kuma iya yin ko tari ba
domin fuskokinsu kaɗai daya kalla ya san babu abinda suke jin tsoro, zasu iya yi masa komai tunda dama
ba barin gidan zasuyi ba da yawansu ɗaurin rai da rai aka yi musu. Haka ya shafe kwanakin cikin wahala
da ciwo, ga zazzaɓi ga damuwa da tashin hankali kafin cikar lokacin idan ka ganshi sai ka ɗauka shekara
goma yayi ba wai sati biyu ba.
Yayi baƙiƙƙirin, tunda yaje sau uku yayi wanka shima ba soso ba sabulu haka kayan jikinsa sai da wani da
suke cell ɗaya ya taimaka ya wanke masa. Abu ne ya haɗu da mai son jiki wanda bai saba da wahala ba
shiyasa abin ya masa yawa, yan uwansa babu wanda bai zubar da hawaye ba lokacin da aka kawoshi za'a
shiga dashi kotun.
Hajja data dage sai an je da ita haka ta kware baki ta fashe da kuka tana cewa
"Sai kace wanda yayi kisan kai kalli yanda suka mayar mun dashi?"
"Koma menene shi ya janyowa kan sa ai Hajja, kuma babu wanda ya masa komai, Abubakar ya ce baya
cin abinci baya wanka ai dole ki ga ya zama haka. Kawai kici gaba da addu'a Allah yasa shari'ar ta zo a
yanda muke fata kawai" Anty Ladidi ta faɗa mata.
Sai da akayi Shari'a biyu kafin aka zo tasu, bayan maganganu daga kowanne ɓangare, Lawyer Alhaji
Lawan ya tabbatarwa da kotu an mayarwa da Client ɗinsa kuɗaɗen daya bayar na siyan gida ciff ba
tareda ko naira biyar tayi ciwon kai ba. Shima lawyer Jalilah ya faɗi an mayar musu da wani kaso na daga
jumullar kuɗin kayan da aka ɗiba, kuma client ɗinsa ta amince da roƙon da yan uwan wanda ake ƙara
sukayi na cewa za'a ringa biyanta kuɗin a hankali har a warware. Abinda yayi saura tsakaninsa da kotu
ne domin jin matsayin laifukan daya aikata a matakin dokar ƙasa.
Alƙali Yakubu Bechi daya gama sauraron jawabi daga bakin lawyoyi yayi rubuce rubuce kafin ya fara
karanto hukunci kamar haka.
"Bayan sauraron kowanne ɓangare, an gabatar da hujjoji masu ƙarfi da suka tabbatar da cewa Bilal Saleh
ya fasa store da Jalilah Muhammad ta ajiye kaya in da ya ɗebi kayan da kuɗinsu ya kai kimanin naira
miliyan talatin (₦30,000,000)."
A firgice Bilal ya ɗaga kai ya kalli inda Jalilah take zaune, ta kuwa sakar masa murmushi harda kashe
masa ido ɗaya. A ina ya ɗebi kayan miliyan talatin? Amma ya zaiyi? Bai isa ya musa ba ko na miliyan
dubu tace ya ɗiba haka nan zai amsa tunda shi ya jawa kansa.
"An samu shaidar hoto mai motsi daga CCTV camera da kuma shaidu na gani da ido wanda suka ga
lokacin da aka fita da kayan.
Haka kuma, an tabbatar da cewa ka damfari Alhaji Lawan Isiyaku in da ka siyar masa da gidan da Jalilah
Muhammad ta baka kake kula mata dashi bayan ka gabatar da bogi, ka karɓi naira miliyan hamsin da
biyar (₦55,000,000)".
Ka amsa laifinka tun farko ba tare da wasa da hankalin kotu ba. Sannan kotu ta samu tabbaci da shaidar
mayarwa da Alhaji Lawan kuɗinsa da kuma wani ɓangare na kuɗin kayan Jalilah Muhammad bayan kotu
ta fara sauraren shari’ar.
Sannan, a zamanka a kurkuku ka nuna cikakkiyar nadama da bayyanannen yunkurin gyara ta hanyar
ayyukanka waɗanda ma'aikata suke lura da shi.
Wannan kotu ba ta tsaya kan hukunci ba kawai, tana kuma la'akari da gyara da dama haɗi da niyyar
shiriyar wanda ya aikata laifi. Saboda haka, kotu ta yanke hukunci kamar haka:
1-A kan laifin fasa store da sata, kotu ta yanke maka hukuncin shekara biyar (5) a gidan gyaran hali,
amma za a dakatar da aiwatar da hukuncin zuwa nan gaba idan aka sake samunka da aikata wani laifin
(suspended sentence) a tsawon shekara biyu.
2-A kan laifin damfara, kotu ta yanke maka hukuncin shekara bakwai (7), sai dai saboda ka mayar da
kuɗin da kuma nadamar da ka nuna, kotu ta sauya hukuncin zuwa shekara uku (3) ko kuma tarar naira
miliyan goma a matsayin diyya ga wanda aka damfara, sannan da aikin taimakon al'umma (community
service) na tsayin shekara ɗaya a ƙarƙashin kulawar hukumar gyaran hali. Sannan ba zaka tsaya takarar
siyasa ko samun wani promotion na aiki ba a tsakanin shekaru biyar masu zuwa.
3-Zaka biya gomnati tarar naira miliyan 5 diyya ga gwamnati a matsayin horo da kuma darasi akan
laifukan daka aikata. Karya ɗaya daga cikin Sharuɗa ko saɓawa doka yana nufin kotu zata dawo da
cikakken hukunci haɗi da ƙari a kai.Ina fatan hakan ya zame maka darasi a rayuwarka da sauran masu
aikata laifuka irin naka." Daga haka ya buga guduma wacce take nuna tabbatuwar kammala hukunci.
Bilal dake jingine da katakon box ɗin da yake ciki ya ɗago idanuwansa cike da hawaye, tsananin nauyi da
kunyar da yakeji ta saka ya kasa ɗaga ido ya kalli ɓangaren da masu sauraron Shari'a suke. Yana jin
nauyin idanuwa akansa amma bashi da ƙarfin guiwar da zai iya haɗa ido da kowa a yanzu. A hankali ya
zame a gurin, ya fashe da kukan da bai shirya yin sa ba.
Bai san inda aka shiga aka fita har aka nema masa yanci, sau ɗaya lawyer da aka ɗaukar masa yaje
gurinsa a prison shima basu wani yi magana mai tsayi ba ƙorafi yayi masa akan amsa laifinsa da yayi a
kotu bayan ya tsara masa duk abinda zai faɗa idan anje.
Abubakar da Nasir ne a duk sanda sukaje suke bashi tabbacin ya kwantar da hankalinsa Insha Allahu
komai zai dai-daita. Koma dai mai akayi ya godewa Allah ya kuma godewa ɗanuwansa da Amininsa Nasir
da basu dubi halinsa sun wofantar dashi ba.
Kamar an ce ya sake ɗaga kansa karaf suka haɗa ido da Halima dake zaune a row ɗin dake kusa da ƙofa.
Ji yayi gabansa ya faɗi, tayi masa wani irin kwarjini, kallon da takeyi masa daya fassara na baƙin ciki da
jin kunyar abinda ya aikata. Kasa daina kallonta yayi kamar yanda itama take kallonsa kafin ta miƙe a
hankali ta fice daga ɗakin kotun wani wanda bai san ko wanene ba da sai lokacin ya lura dashi ya bi
bayanta riƙe da jakarta data bari akan table.
Sam bai ji maganar da ɗansandan dake kusa dashi yakeyi masa ba sai da Barr Sajid ya ƙaraso gurin yana
murmushi da yi masa barka. Ya sauke ajiyar zuciya mai nauyi yana amsawa dukda hankalinsa gaba ɗaya
yana kan Halima da tunaninsa ya tafi akan sanin wanene wancan daya bi bayanta?
A wajen kotun bayan murna da jaje daga yan uwa, Hajja dake riƙe da hannunsa kamar wani zai ƙwaceshi
ta kalli Barr Sajid da yace zasu tafi da Bilal ɗin a ƙarasa cike takardu. Kamar zata fashe da wani kukan
tace
"An sallame shi Hajiya, amma dole sai munje anyi cike-ciken takardu tukunna. Ganin harda Abubakar
suka tafi ya saka hankalinta ya ɗan kwanta suka wuce gida tareda su Anty Amina da sauran yan uwa da
suka halarci zaman kotun.
Dab da magriba su Bilal suka isa gidan Hajja a motar Nasir shi da Nasir ɗin sai Abubakar. Yanda yake jin
jikinsa tamkar wanda aka haƙo daga rami ya so ace kai tsaye gida suka fara kai shi yayi wanka tukunna
ko Asibiti ma dan shi kaɗai ya san abinda yake ji amma dai yayi shiru har suka isa gidan Hajjan. Nasir ya
musu sallama da addu'ar Allah ya ƙara kiyayewa. Abubakar na kallon Bilal ya ce
"Yaya Nasir yayi maka ƙoƙari, duk tarin abokananka shi kaɗai ya tsaya da jikinsa da aljihunsa har Allah ya
ƙwatoka. Ka gode masa kuma kada kayi wasa da abotarku dan shi ɗin mai sonka tsakani da Allah ne"
"Haba Abubakar ai babu zancen godiya tsakaninmu duk abinda nayi saboda Allah ne ba dan a gode mun
ko wani abu ba. Ni dai fatana ya kiyaye Allah kuma ya sake tsare mu baki ɗaya" Nasir ya faɗa daga haka
yaja motarsa ya wuce su kuma suka shige ciki ganin unguwa da yara sun fara taruwa suna kallonsu.
Falon Hajjan cike da yayanta da yan uwanta da suke jiran dawowarsu, gida ya sakw cika da murna da
kuma jaje. A ƙofar ɗakin da Abubakar yake ya hangi Zulaiha tsaye yana masa murmushi, bai ganta ɗazu a
kotu ba, ko kuma bai lura bane oho haka dai suka shige falon Hajja bayan ya ɗaga mata hannu. Abubakar
ne yace yaje ya huta suma matan kowa ta wuce gidanta haka kuma abun ya isa.
"Ka samo mana Adaidaita na gaji wlh kamar zan faɗi nakeji"
"Ga ruwa can ai naga ta kai maka ka samu kayi wanka bari naje na samo maka abu mai ɗan ruwa ko
yoghurt ne, ga magungunan da Yaya Nasir ya taho maka dasu yace idan kasha zaka samu sauƙin ciwon
jikin kafin safiya sai muje Asibiti" Abubakar ya bashi amsa yana nuna masa Zulaiha dake tsaye ƙofar
banɗakin tsakar gida, ya kalleta ya kalli Abubakar ɗin, bai dai yi magana ba ya wuce ɗakin da ta shiga
zuciyarsa cike da tambayoyi.
Ɗakin na nan yanda yake Katifa ce Gado huta a ciki sai ƙaramin carpet a tsakiyar ɗakin daga gefe kuma
ga alwatuna da yake zaton kayansa ne dana Zulaihan a ciki. Towel ɗin data fitar ta bashi ya cire kaya ya
ɗaura ya yafa wani ƙarami kafin ya fita yana sunkuyar da kai ya shiga wankan. Bokiti uku ta ajiye masa
sai da ya gamsu dan kansa da wankan da yayi kafin ya fito yana jinsa kamar wanda aka sake haihuwa. Bai
san inda zai tsoma ransa ba da ta tabbata zai yi zaman kurkuku na shekarun da yaji ana ambatowa. Ko a
ina aka samu kuɗaɗen da aka ce an biya masa bashin ma sai Allah domin dai bashi da su bai kuma bawa
wani ajiya ba.
Kaɗan ya ci abincin da Zulaiha ta shirya masa bayan yayi sallar magriba da aka kira yana wanka. Yana
jingine da bango yayi shiru Abubakar ya ƙwanƙwasa ƙofa ya bashi izinin shiga dan Zulaiha bata ɗakin.
Ledar Rufaida yoghurt ya ajiye masa da magunguna yana masa sannu.
"Na san dai da takura amma ba yanda za'ayi da nayi tunanin ko nemi haya toh ga wani sabon lissafin
kuma ya sake tasowa. A haka ma Allah ya rufa asiri kaga gidajen da aka siyar duka sunyi daraja sosai
shiyasa har aka samu aka rage kuɗaɗen" Abubakar ya faɗa. Bilal dake kallonsa ya ce
"Shine maganar da nake yi maka, an siyar da gidanka na Goran dutse da kuma wancan na Rijiyar Zaki sai
filaye guda biyu, takardun uku na gani amma biyu ne suka siyu ɗayan dillalan sunce hanya ce kaima kayi
ganganci daka siya".
"Miliyan goma aka bata" ya bashi amsa, ya ɗago kamar a firgice ya zaro ido ya ce
"Goma? Saura Ashirin fa kenan, a ina zan nemo miliyan ashirin banda yanzu waccen tarar? Na shiga uku
da wahala dai idan ban yi zaman kurkuku ba dan ban san in da zan samo kuɗin nan ba" ya faɗa gwanin
tausayi kamar zai fashe da kuka.
"Alhaji Hafiz ya biya duka tarar, yanzu ina hanya Barr Sajid ya kirani yake cewa ya kirashi yace ya tura da
account number da za'a saka kuɗin, ya tura masa na san kuma ya saka dukda bai sake kirana ba".
"Shi dai Hafiz abokinka. Badan shi ba ai da wahala wannan yarinyar ta haƙura. Na fahimci ba wai kuɗin
ne a gabanta ba burinta ta wulaƙanta ka dan shi kansa Alhaji Lawan ɗin ita ta ringa zugashi sai da Hafiz
ɗin ya shiga maganar kafin suka haƙura."
"Eh taje nima bamuyi sallama ba gaskiya ta wuce" Abubakar daya miƙe ya bashi amsa. Sai ya sake karyar
da murya ya ce
"Wanda zata aura ne" ya bashi amsa cikin halin ko in kula. Yanda ka san dirar mashi haka yaji maganar,
ya gwale ido yana kallon Abubakar ya ce
"Haka tace mun" Abubakar ya sake bashi amsa. Sai ya koma laƙwas ba tareda ya sake cewa komai ba
Abubakar kuma ya fice daga ɗakin.
Kwana yayi a zaune, dukda ya tsammaci rasa sauran abubuwan daya mallaka domin dai babu mai biya
masa bashin daya ci wa kansa amma kuma bai zaci abin zai dame shi haka ba. Shikenan yanzu ko gidan
da zai zauna bashi da shi ya dawo ɗakin ƙaninsa da zama dan asalin nasa ɗakin samartaka a soro yake shi
aka shigowa Hajja dashi aka ƙara mata a falo bayan da aka raba asalin ɗakin ya koma ciki da rumfa
sannan aka mata banɗaki da sauran a cikin ɗaki. Shi gashi yanzu ɗakin ma falle ɗaya suka samu banɗaki
sai sun fita tsakar gida, hatta da kayan gadon sa da na Zulaihan duka dasu akayi gwanjon gidan kayan
kitchen ɗinta da sauran abubuwanta kawai ta fita dasu.
Abu ɗaya da ya saka ya ɗan ji dama-dama yanda bai ga damuwa sosai akan canjin muhallin a tattare da
Zulaiha ba. Ba yabo ba fallasa take sabgoginta, daya gama cin abinci ta tattare kwanuka ta fita dasu ta
dawo ta tambaye shi ko akwai abinda yake buƙata yace babu shikenan tayi kwanciyarta.
A haka ya kwashe kwana uku yana jinyar malaria daya kwaso a prison, ba inda yake fita yana ɗaki ko
falon Hajja sai ta fito tana ta ƙwala masa kira musamman idan yan jaje da yace munafunci suke zuwa
suka zo kafin zai shiga yafi ganewa ya zauna a ɗaki kawai yayi shiru yana Istigfari da tunanin duniya.
Ranar daya kwana huɗu da yamma yana kwance a ɗaki ranar an samu sauƙin yan jaje dan tun safe babu
wanda yayi sallama, yana kwancen yana jiyo Hajja nata sababi wanda kuma ya san ba zai wuce da
Zulaiha take ba. Tun washe garin daya dawo ya fahimci za'a samu gagarunar matsala tsakanin Hajja da
Zulaihan a zamansu.
Hajja tamkar shi take, gurinta ya gado shegiyar tsafta da rashin son ganin shirgi a guri. Idan ka shiga
gidanta kamar ba na tsohuwa ba shiyasa sanda Fadila take zawarci Hajjan take gwammace ta tafi gidan
Anty Habiba saboda tace ɓata mata gida takeyi, da ciwon ƙafar da komai haka zatayi shara ta wuni tana
kaye-kaye ko leda iska ta kwaso mata idan bata ɗauke ba bata jin daɗi toh yanzu ga Zulaiha kuma da
shegiyar ƙazanta.
Bata mata aikin komai, dai-dai da kwanukan abinci idan aka kai masa dan ita bata wani ci sai kayan
kwaɗayi yanayinta ma sai yake ganin kamar tana da shigar ciki dukda bai tabbatar ba amma haka zata
haɗo na rana da dare ta fito dasu ƙofar ɗaki da safe sai dai Safiyya yar Anty Ladidi ta ɗauke ta wanke.
Tun bayan da aka sallamo Hajjan daga Asibiti ta dawo gidan da zama saboda yanzu ko tafiya sai da
sanduna biyu take yinta Safiyyan ce take mata komai haka su ma hatta sharar cikin ɗakin ita take shiga ta
musu.
Yau ɗin Safiyyar ta tafi rubuya Jamb tun safe kafin ta fita kuma sai da ta yiwa Hajjan komai har abin
karyawa, tun sha ɗaya yana ji tana kiran Zulaiha ta fito ta ɗora abincin rana tunda Safiyya bata dawo ba
amma tayi kunnen uwar shegu tana danna waya shima ya maimaita mata amma bata ko kalle shi ba yayi
shiru ya zura mata ido ana kiran Azahar ta ɗaura zani ta fita ta juye ruwan zafin da Hajjan ta ɗora a
kurfoti ta shige wanka shine yanzu ta fito ta gani take sababi.
Tashi yayi ya saka riga saboda jiyo tashin muryar Zulaihan da yayi kamar tana amsawa Hajja maganar da
takeyi, yana fita kuwa ya jita tana cewa
"Ai na faɗa miki ni ba yar aiki bace zaman aure nakeyi idan ma zan girkawa wani abinci toh mijina ne
tunda kuma kince ke zaki ringa bashi abinci sai kiyi tayi ku dafa ko karku dafa matsalarku ce ko kinga ina
cin abincinku ne?"
"Ni kike faɗawa haka" Hajja ta faɗa tana kallonta, Zulaiha ta ɗauke kai gefe ganin Bilal ɗin ya fito ba
tareda tace komai ba shirun da sukayi kuma ya saka suka ji sallamar da ake ta dokawa tun farkon fara
muhawarar tasu. Duka su ukun suka kalli ƙofa, Halima dake tsaye riƙe da hannun Sharifa Al'amin da
Inaayah na tsaye kusa da ita hannayensu riƙe da ledoji ta sake maimaita sallama.
Ba Bilal da Hajja ba hatta Zulaiha sai da taji wani iri da zuwan Haliman da sauri ta shige ɗaki ta bar Bilal
da Hajja da suka ƙame a tsaye aka rasa wanda zai amsa musu.
HALIMA
Ganin duk suna kallonmu sun kasa magana ya saka na shiga ina faɗaɗa fuskata, tabarmar da na gani
shimfiɗe kan barandar ɗakin Hajja muka zauna tareda yaran sai lokacin sukayi firgigit kamar waɗanda
aka watsawa ruwan sanyi Hajja cikin murmushin da kana gani kasan na yaƙe ne haɗi da kunya mai
tsanani ta shiga yi mana sannu da zuwa tana cewa mu tashi mu shiga ciki.
"Ku tashi ku shiga ciki kunji kai da ɗakin matarka ace ku zauna a tabarma".
A raina nace "ikon Allah" kafin na miƙe nabi bayanta. Kallon falon na ringayi, tunda naje gidan Bilal nake
masa nacin ya kamata ya gyarawa Hajja ɗakinta ƙarshe cewa yayi nima idan nayi mata ai ba laifi bane shi
in rabu dashi a lokacin har na niyyata zanyi ɗin da surutu na faɗawa Mama tace kar taji karta gani na
fishi sanin ya kamata ne ko kuwa da zance zan gyarawa Babarsa ɗaki gashi yanzu Allah ya nufa an mata
shi ɗin ne ko Abubakar ne sai Allah.
Al'amin ta cewa ya buɗe fridge ya ɗebo mana ruwa da lemo nace mata a barshi daga gida muke ma
mungode"
"Kai tashi ka ɗebo, rashin ƙafa ya saka har aka fara ganin damata ana maida mun magana" Hajjan ta faɗa
sai na kama bakina nayi shiru kawai ina duba wayata da tayi ƙara dai-dai nan Bilal ya shigo falon da
ƙaramar sallama kamar Almajirin dake jin yunwa.
A kujerar dake bakin ƙofa ya zauna, sai da na kalli Inaayah da Al'amin da suke kallonsa kamar sunga wani
baƙo kafin suka gaishe shi, ya miƙawa Sharifa hannu ta sake lafewa a jikina dan tunda Hajja tace taje da
a zaune take a kujerar ta tashi ta haye jikina.
"Au kaima ubanta kenan, toh bari na shafawa kaina lafiya" Hajja ta faɗa, na kalleshi kafin na gaishe shi
haɗi dayi masa jaje ya amsa yana mun kallon ƙurilla kamar wanda ke neman wani abu a jikina. Falon yayi
shiru, ƙarar da wayata tayi ya saka na miƙe ina cewa
"Dama kawo su nayi su dubaku bari muje ana jiranmu a waje"
"Sai kace wanda ake korarku Halima gashi ko ruwan ma baki sha ba balle ki barsu suma su sha sai kace
wanda suka zo baƙon guri ko baki gaya musu nan ɗin tushensu bane? Mu jininsu ne basu da sama
damu?" Hajja ta faɗa. Kamar inyi shiru sai kuma nayi murmushi na kalleta nace
"Ina fa zasu manta tushensu Hajja? Ai idan ita Sharifa bata sanku ba shi Al'amin daya bar gidan da
wayonsa ai ba zai mantaku ba. Ita ɗin ma da ace tana ganinku ba zata muku ƙiwa ba in da zataga
Abubakar yanzu zaki san da gaske ta san jininta" ina rufe baki Abubakar ɗin yayi sallama tun kafin kuma
na san su biyu ne ƙamshin turaren Dr Salman ya isarmun da saƙon.
Da gudu kuwa Al'amin ɗin ya nufi Kawunsa itama Sharifan ta zame tana kiran "Uncle" ya ɗaga su duka su
biyun yana juyi dasu suna dariya. Sai na rasa jikin wanda ya fi wani yin sanyi tsakanin Bilal da Hajja
musamman da Dr Salman ya ƙaraso ya zauna gefena. Suna gama gaisawa na miƙe ina nuna mata ledojin
da muka shiga dasu shi kuma ya ajiye musu rafar 1k guda biyu na fita yana biye dani a baya dan
Abubakar ya fita da yaran.
Amarya na tsakar gida ta shimfiɗa sallaya a inda rana bata tarar ba tana shan rake, na ce mata "Sannu"
ta amsa mun da "Ina wuni" muga gaisa daga tsayen na mata jajen abinda ya samu Mijinta kafin nayi
waje.
A soro Bilal ya tsayar dani, kamar wani mai jin tsoron kada a jishi kai a ƙasa ya ce
"Na san abubuwa da yawa sun faru a baya da ban samu damar wanke kaina ba Halima. Dawo da
maganar bashida amfani amma ina so ki sani na gane kuskure na kuma yarda cewar na zalunceki a
zamantakewatarmu. Dagaske nake miki wannan maganar tun daga ƙasan zuciyata ina mai neman
gafararki Halima kiyi haƙuri ki yafe mun duk wani abu dana miki daga ranar da kika fara sanina har zuwa
yanzu da muke tsaye. Ko ba'a faɗa mun ba na san abubuwa da suke faruwa harda haƙƙinki Halima. Na
sakaki kuka sau babu adadi a sanda kike taredani tun bayan rabuwata dake nayi kuka sau babu adadi
nim. A hankali abubuwa da yawa suna ta faruwa da suke ankarar dani girman laifukan dana ringa aikata
miki wanda nake kallo a matsayin ba komai ba a wancan lokacin dan Allah kiyi haƙuri ki yafe mun" ya
ƙarasa kamar zai durƙusa mun.
Murmushi nayi na ce
"Na daɗe da yafe maka Bilal, sau da yawa mu kanyi baƙin ciki idan wani al'amari ya samemu wanda
kuma daga baya hakan sai kaga ya zame mana alkhairi amma bama fahimtar hakan da sauri har sai
munyi haƙuri tukunna. Tsakanina da kai idan akwai mai laifi nice dana cusa maka kaina ta ƙarfi dukda ka
yi iya ƙoƙarin ka gurin nuna mun baka muradin hakan. Kayi haƙuri ka zauna dani tsayin lokaci. A yanzu na
fahimci ba'a yiwa so dole, sannan Soyayyar da kake so ake sonka ita ce soyayya"
"Da baka barni ba da ban haɗu dashi ba hakan yana nufin da nayi asarar ingantacciya kuma
nagartacciyar soyayya wacce babu algus a cikinta. Saurayine bai taɓa aure ba amma ya zaɓeni mai yaya
biyu akan tarin yammatan da suke karakaina akansa, wannan kaɗai nasarace na kuma godewa Allah"
daga haka na sa kai na fice na barshi tsaye yana bi na da kallo.
A hanya Dr ya kalleni ya ce
"Amma kika ce kinfi jin daɗi da Abbansu baya zuwa dubasu". Ba tareda na kalleshi ba nace
"Ba gaskiya bane, idan kinfi son haka mai yasa kika nuna jin zafin rashin kulawar tasa kuma ɗazu a
gabansa?"
"Ni kuma nayi me?" Na faɗa ina buɗe masa ido, shima buɗe idon yayi kafin ya ce
"Wai sai yaushe zaki daina sonsa kwata-kwata? Dame ya fini Halima? Ina zaune a mota ina kallonki kina
ta washe masa baki har kina nunoni Allah kaɗai ya san mai kike gaya masa a kaina ƙila cewa kike ni maye
ne na nace miki ko?"
"Ni dama na san kana kallonmu" na faɗa da sigar zolaya. Ya haɗe fuska kamar gaske yana cewa
"Wlh na raina ajinki ma dana ganshi sam ashe ma baki ga taste. Kalleshi ba sai kace wani sahorami fuska
kamar mace. Dama ta yaya wancan zai san darajar mace kamarki? Da kike ta wahalar dani kike garani
kamar wani ball na ɗauka zanga wani namijin gaske wanda ya fini banda girman idanuwa da tsinin hanci
baya ga haka na kereshi a komai har ma abinda baki rigada kin sani ba duk na san zan fishi wlh dan daga
ganinsa ba wani ƙoƙari zai yi na azo a gani ba".
Baya na fara kallo naga hankalin yaran gaba ɗaya yana kan Tab ɗin da suke kallo ko da ma ƙasa ƙasa yayi
maganar na toshe kunnuwana biyu da hannu ina cewa
"Kai dai kaji tsoron Allah kuma ni a yaushe nace maka har yanzu ina sonsa?"
"Idan bakya sonsa akan me tunda aka ce an kamashi hankalinki yaƙi kwanciya? Kin ganshi a kotu amma
dukda haka baki haƙura ba kika wani fake da yara saboda kizo ki ganshi yanzu dai hankalinki ya kwanta
ko?" Yayi maganar yana kallona. Shagwaɓe fuska nayi ina kallonsa nace
"Amma dai ka san asirin da kayi mun ya ci dan bana iya cikakkiyar awa ɗaya ba tareda nayi tunanin ka
ba" ya saki murmushinsa mai kyau kafin yace
"Ni dai kika asirce ina nan kuma ina addu'a Allah ya ɗorani a kanki kada ki mayar dani bita zai-zai dan
tunda har Hajiya tace ta lura ina sonki dagaske na tabbata gaskiya duk inda kika kai sunana ba'a ci miki
kuɗi a banza ba".
"Haka fa yan office suke cewa wai daga zuwa na asirceka duk ga mata nan da suka kwashe shekaru a
gurin babu wacce kake yiwa kallo biyu sai ni gani ɗaya zaka fara so na?"
"Sai ki ce musu dama ke nake jira shiyasa bana iya yiwa kowacce mace kallo biyu sai a kanki na fara". Ji
nayi kaina ya fasu, yanda yayi maganar haɗi da mun wani kallo yana lumshe ido da yake tabbatar da
gaskiyar abinda ya faɗa ya saka naji kamar in fasa ihun murna. Gidan Mama muka koma ina tsaye muna
sallama Abba ya fito dan haka na shige gida na barsu suna gaisawa dariya ta kamani ganin Salman kamar
zai kwanta a ƙasa ana gaida suruki.
"Kin je hankalinki ya kwanta dai ko?" Anty Labiba ta faɗa ina shiga, Mama Fauziyya ta tare mun tana
cewa
"Menene laifi a ciki Labiba? Zuri'a fa ta rigada ta shiga tsakani babu yanda za'ayi a raba. Tunda kunce ba
zamuje ba ba'a mata kara ba ai sai taje da kanta"
"Tunda wani yace yaja ya damfari mutane ina ruwanmu da zuwar masa jaje? Dama ai ita take da jiɓi
dashi idan ma zuwan ne ita ya kama kuma taje" Mama ta goyawa Anty Labiba baya. Zama nayi tunda
Mama Fauziyya na nan na san ba zata bari su mun rubdugu ba.
"Ina Dr ko ba tare kuka je ba?" Anty Labiba ta sake soko wata maganar, na ɓata fuska Mama tace
"A haka dai shima kamar Namijin gaske amma ya zauna yarinya ƙarama tana juyashi. Tsabar sakarci wai
har zaman kotu ya rakata ashe, dama zan gayawa Mudassir idan ba dagaske yakeyi ba ya kama gabansa
in kuma auren zaiyi ya fito ayi a wuce gurin tun bata mayar dashi shashasha irinta ba. Ni na rasa wannan
azababbiyar soyayya da kike yiwa Bilal sai kace wacce ya wanke ya bawa ta sha" Mama ta sake faɗa cikin
fushi.
Miƙewa nayi na wuce ɗakin Amirah ina jin Mama Fauziyya tana cewa
"Sai a hankali, irin su Halima suna da yawa fa kawai dan ita muka fara gani shiyasa abun ya zo mana a
sabo. Idan suka so abu kafin su barshi gaba ɗaya sai sun samu madadinsa. Wuyarta ɗaya ta samu wanda
zai ringa mata irin soyayyar da take ƙulafuci a gurinsa shikenan zai zama tarihi kuma idan ba'a yi wasa ba
idan ta tsane shi sai a ringa roƙonta data sassauta ƙiyayyar. Kawai dai yanda kika ce idan auren zai yi ya
fito ayi a wuce gurin".
Haka sukayi ta juya maganar ni dai na shige ɗaki na kwanta bacci na fara fizgata wayata dana ajiye a
saman pillow da nake kwance ta shiga ƙara ba shiri na tashi zaune ina tura baki kamar wani ya ajiye mun.
Salman ne, sai da ta kusa katsewa kafin na amsa da sallama ya amsa ya ce
"Abba ya ce in turo ko kina so ko bakya so ya bani ke, zaɓi biyu ki zuba ruwa a ƙasa kisha idan kina
farinciki ko ki bari idan aka kaiki ɗakina ki haɗe zuciya amma karki mutu dan nima binki zanyi".
A gurguje
BILAL
Ganin da yayiwa Halima sai ya sake dawo masa da komai saboda, mutumin daya ganta tareda shi kuma
ya tabbatar masa da cewar tayi masa nisa. "Dama da irin sa ta dace ba kai ba" zuciyarsa ta ringa ƙara
masa zafi. Duk juyin da zaiyi sai ya tunata, idan kuma ya tuna ya da yaransa suka nuna basu sanshi ba sai
yaji dagaske dai ya tasarma rasa komai a rayuwarsa. Ya rasa duk abinda ya mallaka, ya rasa Halimarsa
sannan yana shirin rasa yaransa amma ba zai bari hakan ta kasance ba.
Haka ya cigaba da jinya tsayin wata guda baya zuwa ko ina hatta masallaci sai da Hajja tayi dagaske kafin
ya fara fita tace zamansa a gida ba zai canza komai ba sai dai tunani da damuwa su ƙarasa kassarasu
kawai. Ita yanzu kacokam damuwarta tana kan Fadila da kowa yake cewa wai ta haƙura ta ɗauke kai
tunda dai Fadilar taji ta gani zata zauna a cikin uƙubar da take ita na menene zata ringa ɗora danuwarta
ranta kullum jininta yayi ta hawa sama?
Bayan dawowar Bilal Fadilan da mijinta sunzo gidan har yayi alƙawarin warwarewa Bilal ɗin sauran
bashin da yake tsakaninsa da Jalilah. Haka Hajja ta manta da haushinsa takeji ta ringa masa godiya harda
hawaye, Bilal dai ko a fuska bai nuna jin daɗi ba balle ma yayi masa godiya. Bakinsu ɗaya, kuɗin da yake
maganar zai bata kuma dama ƙarya ce bai ci ba dan kayan daya ɗiba miliyan bakwai da motsi ya siyar
dasu ya san kuma dukda karyar dasu yayi sunyi wutar duniya ace miliyan goma ba talatin ɗin data
ƙaƙaba masa ba. Amma ya ya iya? Dama an ce tsuntsun daya ja ruwa ai shi ruwa zai doka.
Shikenan maganar Jalilah ta mutu dan kwana biyu a tsakani ta kirashi da kanta kamar ba zai ɗauka bama
amma ya amsa, ta faɗa masa Ahlan ya biya masa sauran kuɗin da take binsa dan haka ya faɗawa
lauyansa yaje kotu ya ƙarasa warware abinda yayi saura.
"Dukda mugun halinka Allah ya taimakeka ya haɗaka da mutanen kirki a rayuwarka. Ban zata Hafiz zai
sake waiwayarka ba sai gashi ya biya maka tara. Toh ka saurareni da kyau, kada ka ɗauka shikenan iya
wannan taskun dana sakaka kaci banza. Daga yau ba lallai ka sake jin ko da labarina ba amma kafin na
fita daga rayuwarka ina mai tabbatar maka sai na bar maka tabon da har ka koma ga Allah ba zai taɓa
gogewa daga zuciyarka ba Bilal" daga haka ta katse wayar shima yayi tsaki ya danna mata block.
Tunda sun rigada sun warware babu wani abu data isa tayi masa idan ma batayi wasa ba a yanzu zai ita
ɗaura ɗamarar yin wasan Kura da ita tunda ba ita kaɗai ta iya haɗa sharri ba ai.
Haka rayuwa ta cigaba da gurgurawa tsakanin Hajja da Zulaiha ana zaman doya da manja, ba Hajja kaɗai
ba hatta da shi kansa zama suke kamar wasu roommates na Hostel ya rasa dalili yanzu idan zasu kwana
su wuni idan ba shi yayi mata magana ba ba zata ce masa uffan ba ko maganar yayi mata ma sai taga
dama zata mayar masa da mai daɗi. Idan zaman gidan ya isheta ta gaji da sababin Hajja tayi wanka ta
fice tace ta tafi gida.
Satinsu shida a gidan tace masa tace masa ita ta gaji, ko dai ya sama musu wani gidan su koma bata
damu ba ko gidan haya ne mai ɗaki ɗaya yafi mata zaman nan ko kuma ta tafi gidansu, bata ce ya saketa
ba amma zata tafi zuwa duk sanda ya samu sarari da zai samar mata inda zata zauna sai ta dawo.
Shi kansa a takuren yake toh amma bashida halin da zaice zai nemi gidan haya a yanzu. Yan kuɗaɗen da
sukayi saura da Abubakar ya bashi a ciki yacd yayo musu siyayyar kayan abinci da zasu ɗan ja lokaci
sauran kuma ya rike ya juya masa tunda bayan aiki Abubakar ɗin yana taɓa kasuwanci kuma ba laifi abun
ya karɓe shi banda sabgar Bilal ɗin daya laƙume masa fin rabin jarinsa dole ya ture maganar aurensa
data taso a gefe yanzu yake ƙoƙarin sake farfaɗo da jarin.
Tunani yayi ko ya karɓi wani abu a hannun Abubakar ɗin ya kama gidan sai kuma ya fasa dan har ga Allah
ƙoƙari yakeyi ya gyara kura-kurensa na baya. Yanzun ya zama ba sawa babu hanawa, ba ruwansa da
kowa daga gida sai masallaci tunda ta tabbata an koreshi daga aiki dama kuma shi ba wata sana'a ya iya
ba balle yace zai yi shiyasa ma yace Abubakar ya juya masa kuɗin, idan
sai idan kaɗaici ya dameshi ya tafi Chemist Nasir na nan unguwar idan yana nan kenan dan yanzu kuzan
branch huɗu gareshi a unguwanni daban daban, diploma da Bilal yake masa iskanci akanta wai ba abinda
zata tsinana masa ya tafi suyi degree gashi da ita ya fara kuma ita ce tushen duk abinda ya samu a yanzu.
Ganin yanda Hajja da Zulaiha suka zama kamar wasu sa'anni kullum cikin kacenace wanda yake ganin
kamar da gayya Zulaihan take yin abinda ta san Hajjan zatayi magana dole ya nemi sharar Nasir akan
zancen neman gida ya ce masa hakan babu laifi dama ya sani da wahala zaman ya yuwu baya ga haka
akwai takura dan haka ya barta ta tafi gida idan ya so sai ayi ƙoƙarin a nema masa ko ƙarami ne da zasu
zauna kafin kuma aga tanadin da Allah yayi a gaba.
Ranar Juma'a yana kwance a falon Hajja bayan an sakko daga sallar Juma'a, da zazzaɓi ya tashi ranar dan
daƙyar ya iya fita masallacin yana dawowa kuma shine ya kwanta. Yana kwancen wayarsa ta shiga ƙara,
yayi mamakin ganin mai kiran, Hafiz ne. Ji yayi yana jin kunyar magana dashi dan haka ya kasa ɗagawa
har saida ta katse wani kiran ya sake shigowa kafin yayi ta maza ya amsa.
Muryar Hafiz a sake suka gaisa yace masa yana waje. Fita yayi ya tarar dasu su uku suka shiga ciki sai da
sukayi jiran Hajja dake sallah a cikin ɗaki ta idar kafin ta lallaɓa ta fito suka gaisa. Damuwar Fadila data
saka a ranta ta saka lafiya take mata wasa hawan jininta ya tsananta har ta dawo shan magani kullum.
"Idonka kenan Hafizu" Hajja ta faɗa bayan data zauna ba kunya, yayi murmushi suka gaisheta ta
tambayeshi iyali sai lokacin Bilal yaji ashe Suhaila ta sake haihu mace.
"Ɗaurin aure muka zo can ƙasa, shine nace bari na ratso mu gaisa dan na jima ban yuwo ta nan haka ba"
Hafiz ɗin ya faɗa. Hajja tace
"Allah sarki ai kuwa ka kyauta. Munji abin arziƙi da akayi ubangiji ya sa a ɗauka a gaba, tun lokacin nake
cewa zamuzo har gida muyi godiya toh ka ganmu daga ni har shi ɗin mun zama lafi-lafiya, yau lafiya gobe
ciwo"
"Allah ya rufa asiri ya ƙara lafiya" cewar Hafiz kafin ya juya kan Bilal da yayi shiru yana sauraronsu ya ce
"Wani abokinmu ne yayi aure, ba shiri ma fa tambaya aka zo ɗazu da safe kawai iyayen yarinyar suka ce
a ɗaura aure. Shine yace dan Allah su bari a sakko Juma'a kafin nan ya sanarwa mutanensa na kusa aka
taso mu babu shiri sai da mukaje gaisuwa bayan an ɗauro auren abin mamaki naga ashe Halima ce
amaryar".
Yanda Bilal yayi sai ka ɗauka bindiga ko wuƙa aka nuna masa amma ya kasa cewa komai sai idanuwa da
yake zarewa, Hajja ce ta tambayi wace Halimar ya bata amsa da
"Halima dai Maman Al'amin tsohuwar matarsa. Wlh nasha mamaki na kuma yi masa musu murna shi da
ita dan kowanne ya dace da abokin zama na ƙwarai. Halima mutuniyar kirkice shima kuma Salman babu
laifi na san shi junior na ne a secondary school kafin muka zama abokai a Jami'a sama da shekara ashirin
da ɗori muna tare har familyn mu an zama kamar yan uwa".
Haka Hafiz ya tafi ya bar Bilal cikin yanayin da bai taɓa zaton zai shiga akan Halima ba. Ƙasa ya zame y
zauna ya saki hawayen da suka cika masa ido, Hajja kanta ɗaki ta koma duk jikinta yayi sanyi. Zuwan da
Halima tayi yanda taga ta zama wata babbar mace ko makaho ya shafata ya san tana cikin nutsuwa da
kwanciyar hankali saɓanin Bilal da tunda ya rabu da ita iftila suke dirar masa daga wannan sai wannan.
Tun ranar take lissafa ta inda Bilal ɗin zai fara gyaro ɓarnar daya tafka. Dukda Abubakar yace mata
wanda suka zo tare wai Mijin da zata aura ne amma bata sare ba. Iya zuwan da tayi ya isa shaidar har
yanzun akwai ɓurɓushin soyayyarsa a zuciyarta ba kuma za'a sha wahalar dawo da komai ba. Tana ganin
idan har Allah ya yarda Haliman ta dawo Bilal ɗin zai samu madafa domin dai Mahaifin Halimar baze
barshi haka ba sai kuma ga wannan magana wai ta ɗaura aure.
Bilal kuwa ɗaki ya koma ya kwanta yana jinyar jiki da zuciya. Bayan sallar isha'i yana zaune in da yayi
sallah ya jiyo Hajja na ƙwala masa kira, yanda take kiran kamar ba lafiya ba ya fita da sauri a tsakar gidan
ya tarar da ita da rarrafe ta fito daga ɗakin tana haki tace yayi maza ya nemo mata Adaidaita sahu da zai
kaita gidan Fadila.
Taƙi ta masa bayanin komai dole ya fita ya taro mashin ɗin kafin yazo ya kamata suka kama hanya ko
gidan bai rufe ba saboda yanda duk ta firgita shi. A hanya take ce masa "Kirana tayi tana kuka azo a
taimaka mata zai kasheta saboda ya kawo karuwa gidan tace yaji tsoron Allah shine ya hau dukanta ya
turota ta faɗo daga bene har yana cewa ni uwarta nice mazinaciya ba, tana can cikin jiini kuma wai ciki
ne da ita" Hajjan ta faɗa tana rushewa da kuka.
Ranar da Halima ta buɗe wayarsa ya tuna har ya mareta ya kuma danganta mahaifiyarta da zina ce ta
dawo masa, ya runtse ido ba tareda ya ce komai ba. Da suka isa suna tura ƙofar gidan ta buɗe suka shiga
yana riƙe da Hajja dan bata ko taho da sandunanta ba saboda kiɗima. A falon ƙasa ta zauna suka ringa
kiran sunan Fadila shiru tace ya hau sama ya dubo mata yarta. Haka nan ya ringa jin gabansa yana
faɗuwa duk taku ɗaya da yayi akan benen, ƙofar falon saman ma a buɗe take an turo bata ƙarasa rufewa
ba dan haka yana hango mutum biyu Mace da Namiji dake zaune Namijin yayi matashi da cinyar Macen.
Tura ƙofar yayi, dai-dai da gama buɗewa gaba ɗaya kuma idanuwansa sukayi kyakkyawan gani, irin ganin
da Halima tayi masa a cikin gidanta shi yayiwa matarsa Zulaiha da Mijin ƙanwarsa.
Kwanansa uku a Asibiti kafin aka sallameshi tunda ya yanke jiki ya faɗi bayan kyakkyawan ganin da yayi.
Zulaihan ce tayi jinyar sa dan bayan da aka kaishi Asibiti ita Hajja tace a kira tunda ta gudu yanzu da
wahala tazo sai ta dawo tayi jinyar Mijinta. Da ace Hajja ta ganta a gidan Fadilan iya kumburin da
idanuwanta sukayi ya isa ya sa ta fahimci mai ya faru dan Ahlan da Fadilan ce mata sukayi yana shiga
falon ya yanke jiki ya faɗi tunda kuma ta san dama bashi da lafiya suka tafi bata musa ba.
Daga Asibiti bayan an sallame su ya cewa Zulaiha ta wuce gida, shi da ita ne a ɗakin ta fashe da kuka haɗi
da durƙushewa a gurin tana cewa
"Wlh tilastani yayi. Cewa yayi idan ban amince ba zasu mayar da kai gidan yari dan girman Allah kayi
haƙuri karka sakeni ina sonka kum wlh iya abinda ka gani ne kawai babu abunda ya shiga tsakaninmu
banda wasannin daka gani".
Yanda take magana ya tuna masa da kansa sai dai a maimakon nadamar daya gani tattare da ita shi a
lokacin cikin izza da nuna isa yake nasa bayanin. Dama tun ranar daya fahimci shine wanda ya gani
tareda Jalilah jikinsa ya bashi hatta da auren Fadila shirinta ne, ashe ba Fadila kaɗai ba harda matarsa
cikin tarkon nata wannan ne abinda take zata masa da har ya mutu ba zai taɓa mantawa ba kenan gashi
kuwa tayi nasara domin har ta mutu ba zai taɓa goge wannan mugun ganin daga idanuwansa ba kamar
yanda ya barwa Halima tunani mafi muni irin wannan akansa. Wai ta yaya ma har Halima ta iya sake
kallonsa da idanun rahma? Lallai ta cika jaruma. Haƙƙin ta ne, yaga sakayya tun a duniya yana fatan
kuma ya zama iyaka hukuncinsa ba zai tafi lahira da haƙƙin Halima ba.
"Ki faɗa mun gaskiya kada ki ɓoye mun komai hakan ne zai saka na yarda dake ko akasin haka, bayan shi
sai kuma wa kike kulawa" ya faɗa da ƙyar dan wani abu yaji ya tsaya masa a wuya shi bai fita ba kuma
bai koma ciki ba.
"Wlh tun bayan da mukayi aure babu abinda ya haɗani da wani Namiji shi kaɗai ne kawai kum dole ya
mun" ta faɗa cikin tsananin kuka, ya girgiza kai ya ce
"Halinki ne ba dole yayi miki ba Zulaiha. Na daɗe ina zargin haka amma a koda yaushe zuciyata tana cikin
yi miki uzuri kwatankwacin uzurin da Halima ta ringa yi mun akan laifukana. Ki tafi gida ba zan sakeki ba
domin idan na rabu dake akan laifin da nima na aikata bansan wace kalar jarabar ubangiji zai ƙara ɗora
mun ba. Ki tafi kawai har zuwa lokacin da zan nemeki amma ina so wannan maganar ta zama sirri a
tsakaninmu bana fatan wani ya jita.
MURFI
A ba zata saƙon ɗaurin aurena da Salman ya iskeni domin ko da ya samar mun a safiyar Juma'ar iyayensa
zasu zo tambayar masa aurena kamar yanda Abba ya buƙata a wasa na ɗauki al'amarin, a lokacin da
Mu'azzam ya shigo yayi kirana kawai na amsawa Baba Salahu cewa na amince a ɗaura mun aurene
badan na yarda da gaske hakan ce zata faru ba sai dai amincewar da nayi ta zamo hukuncin da bana
nadamar yinsa, kuma idan ana sake aure sau dubu toh tabbatas Salman zan zaɓa.
Ya zame mun Mijin, Aboki, Yayan da duk wani matsayi da wani ɗan adam yake iya takawa a rayuwa.
Rayuwar auren dana ringa mafarki wacce ta zamemun Fantasy a gidan Bilal comes to reality bayan dana
auri Salman. Ya gatatani, ya riritani, yan uwansa sun ƙaunace ni tamkar jininsu, har bayan shekaru goma
da aurenmu daya ƙaro mun abokiyar zama domin ni ba kishiya aka yi mun ba na cigaba da kasancewa
lamba ɗaya a duniyar Salman.
Na gasgata zancen Mama Fauziyya da tace akwai sanda za'a wayi gari na manta da Bilal tabbas hakan ta
kasance domin sai da takai a wasu lokutan na kan manta da cewar ba Salman ne uban yarana biyu na
farko ba saboda kyakkyawar alaƙar daya gina tsakaninsu bai taɓa banbantasu da yaya ukun dana haifa
masa bayan su ba. Na godewa Allah na kuma godewa dalilin da yayi silar barina rayuwar da bani da gurbi
a cikinta.
ALHAMDULILLAH