Ali Gadanga Complete-1
Ali Gadanga Complete-1
*
🏹🏹🏹🏹🏹🏹
*_Short Story_*
Page1⃣
Yammace Sakaliya shida da mintina ana gab da kiran sallar magriba Tawagar "yan
gangi suka dawo daga sana,ar tasu ta gangin
Yau Tun asuba suka futa don har farauta sukaje kuma sun dawo cike da sa,a A fitar
tasu
sunkai kimanin su ashirin suna tafe suna tada kura ana -kide Kide da -ife ife da
yin kirari ga shugaban nasu uban tafiyar cikinsu dayasha kayan sak'i masu ado na
yan gangi da farauta daka ganshi awannan yanayi saika furgita don yanayin dayake
ciki bana wasa bane ga kayan wukake masu kaifi soke ajikinsa sunkai biyar suna
walainiya na sheki ga mashi asoke a wandansa hannayansa rike suke da sanduna
fuskarsa tasha farin kwalli gashi majiyin karfi faffada me baiwar kwanji kowa
agarin tsoronsa yake Allah yabashi kwarjini da karfi gashi kyakykyawa black
american nan dogone ashi qaunar raini *ALI GADANGA* Kenan dan cikin kauyan Marina
Saida sukaxo dai,dai mahad'a kuma maraba sannan suka tsaya suka fara yin sallama ga
juna ana kawo gaisuwa gun oga ana tafiya shiko amsawa kawai yke da hannu baya
magana fuskarsa babu fara.a tamkar afutar da sukai basuyi sa.aba
Mutane biyune kawai suka rage agun suka take masa baya xuwa cikin layin gidansu
manyan yaransa kenan Wawurau da hangamau (kunjifa wasu sunaye da ake gaya musu na
banza kuma dan haushi su amsa alhalin kowannensu sunansu me kyaune da dadi daga
ibrahim sai yusuf)
Inna kulu kakar Ali tana tsakar gida tana kada miya tajiyo ana faman busa kaho
Duk da gabanta yafadi amma ta godewa Allah da taji dawowar Gadanga dinta lfy domin
tana fargabar tafiyarsa daji ko yin gangi ko futa farauta sbd qaunar da take masa
ji take kamar baxai dawo da raiba duk da tasan jikan nata gwarxone wajen kwarewa da
gwanantaka a iya fadan takuba da masu da sanduna namun daji ma basa galaba akansa
balle namiji kamarsa
Inna kulu bata qaunar wannan dabi,a tasa dan ba yadda zatayi dashine gashi tana
sonsa sosai tana gudun bacin ransa akullum dai addu.ar shiriya take masa don
burinta kawai taga yaxubda komi yai aure duk da "Yammatan garin na tsoronsa yarinya
daya ke like masa take nacin sonsa Zainabu yana basarwa ama shima yana sonta takun
girma dai yake mata itace sonta yafuto fili kowa yaganeta asati sau biyu ko daya
yake xuwa zance gidansu Zainabun ita ke xuwa zance asauran ranakun gidansu Alin.
Saida suka kawoshi har kofar gida kana sukai Ms gaisuwar bangirma suka juya suka
nufi nasu gidan
Yana shiga ko amsa sallamarsa bataiba tahu masa kirarin data saba masa
Ya katseta yana murmushi "cau !cau dai inna Allah dai yabiya yakaremin ke!
Inna kulu tace " zafi kuma babana duk xafin nan da akeyi...
Yace " nasan da hakan jikina ke tsami yau anyi gwagwarmaya arangama mukai da wasu
qungiyoyi nagaji da yawa.
Yawuce yashige dakinsa tabishi da kallo tana girgixa kanta " oh! Ya Allah ka
kawomin karshen abin nan.
Duk wasu layu da guraye dake jikinsa ya cire dagashi sai gajeran wando yafada
bandaki don yin wanka
€€€€€€€€€€€€€€
Yarane suka cika layin fal sunata murnar ganin motar Alh Tahir wakili dake kofar
gidan mahaifiyarsa Iya zulai makwabciyar Inna kuluce
Iya xulai tsohuwace me kirkin gaske suna dasawa da inna kulu katangarsu daya saidai
iya zulai gidanta na bulo da bulo ne kaf kauyen gidanta ne na bulon siminta har
abin kwatance yaxama don danta yatsaya mata Alh wakili a birni yake da xama me
kudin gaskene duk lahadi yake xuwa ganin gyatumarsa yana bata kulawa sosai shi daya
ke gareta sai autarta dake Aure acan birnin itama amma mijinta bame kudi bane tana
da manyan yaya itama saidai shi Alh wakili diyarsa daya jal tilo dayake ji da ita
Khalisat sunan yarsa bata dade da dawowa daga turai ba ta kammala karatu bata xuwa
kauyen sosai saboda yanda take da kyamar talaka da kuma tsantsami gata yar
wulakanci da jijji dakai.
Ali gadanga yana daga ckn dakinsa kwance yaji hayaniyar tayi yawa awaje da sauri
yafito dan jin meke faruwa
baiyi mamakin ganin yaran ba don yasan suna samun abin arxiki gun Alh wakili kudi
yake raba musu harda dattijan layin da samari
Dayake suna tsoron Ali gadanga tuni suka fara darewa ganin yabiyu da mugun kallo
ransa abace
Tuni suka dare suka tafi sum sum ammafa buya sukai suna hango kofar gidan suka
lallabe anesa suna jiran fitowar Alhn.
Yarara biyu gadanga yasa suka jido masa ruwa yafito da soso da omo hau wanke motar
Alh wakili kamar yadda yasaba
Ckn mintina motar tahau kyalli duk kurar data dauka na kauyen ta gushe
Ali gadanga yasaba wanke motar Alh aduk randa yaxo inhar yaxo yatarddashi badan
komiba sai dan kaunar da yakema Alhajin dakuma yanda Motar ke burgeshi kana bayason
kazanta
Alh yasha yi masa alkairi saiyaki karba hakan yasa jininsu yahadu sosai suna
mutunta juna ko xuwa kauyen yayi saiya shiga yagaida ina kulu yana mata alkairi
itama
Alh yanada kirki da son talakawa hakan yasa kaf kauyen suke sonsa ake girmama iya
zulai
Koda Alhaji yafito yagani yaji dadi sosai yayi murmushi ya ayyana abin alkairin
daxai yiwa gadanga ayau
Bayan yagama rarraba kudi ga yara da manya saiya shiga gidan inna kulu da
sallamarsa
Ta amsa daga daki tana lekowa data ga shine tahau fara.a tana masa maraba ta
shinfia masa tabarma yaxauna suka gaisa
Yaji shigowar Alhajin baiyi niyyar xuwa ba saida yaji kira kana yafito ya gaidashi
har kasa
Alh ya amsa yana masa kallon kauna arai yace a inna " inna naxo da alfarma me girma
da nauyi Allah yasa kiyimin ita.
Ta gyara xama tana fadin " fadi komeye Alhaji xanm ita inhar batafi karfina Ba
AlhaJi yace da ita " dama inbaxaki damuba inaso ki amince nadauki Aliyu na tafi
dashi birni yaxauna agidana nabashi wani aikin kodon ci gabansa
Da sauri gadanga yadago kansa ya kalli Alhaji yakalli innarsa yaga itama shidin
take kallo yaji wani abu aransa naganin idonta yakawo kwalla shima xuciyarsa ce ta
karye yasan me inna keji tabbas shima yaji bakua zai iya rabuwa da innar saba wacce
tun yana yaro yarasa iyaye itace uwarsa da ubansa....
_Muje zuwa_
*Short Story*
page 2⃣
_Alherin ALLAH YAKAI INDA KIKE AMINIYATA FRESH UMMIEY XEEY DA KUMA AYSHA B
NASIR .A.K.A._INAYINKU💘💋
&
*Ummi Aisha*( wani haske)
*Ali* Gadanga ya sunkuyar dakansa kas ya zurfafa akogin tunani baima san yaxai ce
da Alhajiba don yana matuqar jin nauyinsa baxai iya budar baki ya musanta masaba
yana kaunar Alhji sosai aransa zaiso kuma yajishi akusa da Alhajin Amma shi bason
zaman birni yakeba don yanada masaniya akn yan burni sunada rainin hankali bare ma
shida baison raini gashi baida ilimin daxai iya yin zamantakewa a burni
Inna kulu ce ta katseshi da cewa " Gadanga bakace komiba kayi shiru kanajin bukatar
Alhaji akanka kayi magana mana.
Ahankali ya dago da kansa yasaka idonsa acikin idon Alhjin yace dashi " baxan
bujire maganarka ba Alhaji saidai inaso kabani lokaci me tsaho zanyi shawara
Alh yace " haba haidar saikace wani yaro karami ko mace wace irin shawara kuma
kamar wani babban abu na roka agunka
Inna kulu tace " kayi hkr Alh tunda har yace abashi lokacin to abashin domin nasan
halin kayana akwai abunda yake hange bawai ki xaiyiba kasan babban mutum.. takarasa
maganar da raha tana kallon gadangan duk don yasaki ransa
Amma gogan dayake ba gwanin yin fara.a bane ko hakora bai budeba idonsa ma agefe
yake
Alh yace " to ba matsala bari naje ina sauri inkoma don gobe zan tafi dubai zanyi
wata biyu dan hka ina dawowa xaku ganni nadawo kan wannn bukatar.
Yadafa Ali gadanga yace dashi " kada kashiga damuwa haidar nasan sabo da dadi
rabuwa da ciwo kadaure kai namijine dole kuma inba rabuwa nesa akwai mutuwa kaida
innarka amma inaso kasani bawai dan natakuraka xan tafi dakai burniba akwai abinda
nake hange akanka wata dama ce gareka kai namijine dole sai kanada dashi darajarka
zata kara cia a idon al,umar karkarar nn.
Inna tace " hakane Alh kabar magnar ahannuna zaimaxo burni insha Allah, Allah yasa
zuwan nasa yazame masa Alheri.
Yadubi Ali gadanga yace "to mutumina nixan koma ka kula banason xaman banxa ina
son kaxama gwani ackn gwanaye domin kai na daban ne Aliyu haidar.
Ali gadanga ya gyada kansa tabbas yayi na.am da batun Alh kua yaji dadin kalmansa
zaikuma yi kokari wajen ganin yacika wa Alh burinsa xai bashi hadin kai donya
faranta masa.
Alh yana futa inna ta rafka tagumi tashiga tunanin rabuwar da xatayi da Ali.
Yace " haba innata daga wannan yar maganar zaki shiga damuwa saikin kamu da ciwon
zuciyata inkuma narasaki ainazama marayan gasken kima saka aranki ba inda xani
kawai xanta jirgashine harya kyaleni haba yama za.ai natafi burni nabarki ke kadai
anan kauyen alhalin bakida kowa.
" ina da Allah gadanga bakomi kada kaki bukatar Alh bawai kuka nake naxaka tafi
kabar niba kawai kukan zakai nesa dani baka daina halayar kaba nakeyi
" kanada halayyar bakar xuciya *ALI GADANGA* gashi xakaje inda bakasan kowaba
babu wanda yasan yanda kake dan Allah kadan rage wasu halayyar tunda bakasan
halinsuba.
Ya kura mata ido xaiyi kuka abinda yamanta rabon dayayi yace " innata kinason
kirabu dani ashe ?
Ta matse kwalla tana kakaro murmushi tace " ba haka bane kaga bana son dama wannan
futar farautar da gangin naku amma kaga mafita taxo min hankalina zai kwanta inkayi
gefe kacanxa sana.a mekyau tunda natabbatar inkaje burni zaka sami abinyi me nauyi
Yace da fushi " inna kin tsani wannan harkar tawa alhalin tashi nayi naganta agun
kakana mijinki shiya koyar dani farauta yakuma sakani akan hanyar yin gangi tun ina
yaro to meye dan naxama dan gado wannan fa abin alfaharine kima daina cewa komi
akai dan walh ko naje burni baxan bar komi ba zankuma ringa xuwa duk wata guda ina
taba harka.
Nan tahau masa kirarin data saba yi masa yanajin dadi tana kambamashi
€€€€€€€€€€€€
Baifi minti biyar da tsyuwarsa akofar gidansu zainabun ba yaron daya aika yakira
masa ita yafuta yana sanar masa cewar tana zuwa kafin yarufe bakinsa saigata tafito
kamar tare suka futo
Dama akwadaice take dashi kwana hudu bata sashi a idoba tajejje bata samunsa
Saida yayi fin minti biyar kana yadago yakalleta da niyar mata magana saiyaga ashe
shi kawai take kallo kamar ta lasheshi
Ta murmusa kawai don ranta yai mata dadi jin muryarsa akwance da sanyi tasan yau da
arxiki yaxo mata
Yau gani yayi ta kara masa kyau fiye da kullum dukda kwalliyar ta bata mata fuska
tasha xanen kwalli ga jan baki fal baka yasha diso
Yayi jim can yace " kinbarni atsaye kamar wani soja yau babu abun zaman ne.?
Ta shafa fuska akunyace tace "kayi hakuri walh ina saurin inxo inganka na sha.afa
amma bari naje na dauko.
Harta juya xata shia gida yakamo tsintsiyar hannunta ya juyo da ita yamatso gab da
ita suna jin numfashin juna yakura mata idanu yace " barshi ba dadewa xanyiba
magana ce me muhimmanci ta kawoni.
Jitayi kamar tarungumeshi amma baxata iyaba inama shi ya kawo harin
Zabura tayi taja baya dayake tana da saurin kuka take tafara kwalla yakamota
yahadata da jikinsa yana cewa '" bafa yanxuba kada ki tada hankalinki andai fara
maganar ne magana daya nakeso ingaya miki kirike amana banda mata saike
Kukanta ya tsaya cak ganin ya sharce mata hawaye yana suda aharshensa takura masa
ido cikonso lallai Aliyu na qaunarta itama dole tazama jarumarsa
Yace " kixo gobe gidan inna zamuyi babbar magana me muhimmanci agabanta.
Yasaketa yai mata sallama yatafi yana son zainabu sbd tanada hakuri kuma tana
sonsa tana bin maganarsa ga iyayanta yan mutumci duk da marainiyace mahaifinta
yarasu amma danginta da mamanta n sonsa
Saida yakule da mintina kana ta shiga gidansu tanajin mugun sonsa na kara shigarta
murmushi kawai take tana tuna lokacin dayake shan hawayenta tabbas tanason *Ali
gadanga...*
*Short Story*
page 3⃣
*Nabilancy Luv*💘
{Auntyn S&S}
Aranar Da Ali gadanga yaje gidansu Zainabu kwana tayi tana juyi tana faman fara.a
xuciyarta cike da farin ciki nakasancewarta da abin sonta ayau bayama inta tuna
yanda yajanyota jikinsa numfashinsu ya gauraya ji tayi baya wannn rana ta yau inama
ta dawwama ajikinsa da tafi kowa murna
Da Safiyar Allah ta,ala kuwa ko karyawa bata tsaya yiba ta caba uban ado taci
damara ta tafi gidan inna kulu dan inba da wuri tajeba to baxata samu Aliyu
agidanba yau ranar xuwa farauta ce
sallamar zainabu ce tafito da inna daga daki tana amsawa
Inna ta amsa mata amutunce ta shimfida mata tabarma tace mata " zauna kishiyata
kafin na kawo miki dumame.
" don me xan bari, aiko sai kinci don cin tuwon kishiya ramako ne ,ko so kk gadanga
yadawo yatarar nabar matarsa da yunwa
Gaban zainabu yafadi kada dai duk sammakonta harya tafi aikin farautar,
Jin tayi shiru kanta akasa tana murmushi inna tace " lafiya dai ko ? Naganki jiki
ba kuxari dafatan ba wata matsalar bace?
Zainabu ta mur
usa tace
"Dama...Dama aliyu ne yace inxo yau gidanki zamuyi magana dashi dake me muhimmanci.
Inna tayi dariya tace " hhhmmm toshine kk wani rabe rabe ni nasan maganar amma bari
nabari inyaxo ayita
inna tace " yafita sana,ar tasa tun kiran assalatu sallah kawai yayi yafice shida
ayarinsa.
Zainabu ta mike tace " to bari naje zan dawo da yamma kawai.
Xainabu sarkin yan murmushi da shiru shiru tahau dariya tana fadin "kiyi hkr inna
narigada na karya shiyasa
€€€€€€€€€€€€€€€
Gab da magriba zainabu ta dawo gidan inna tayi babbar sa.a kuwa gadanga bai dade da
shigowa gidanba
Zainabu tasha kadan ta dire tana baxa idanun taga ta ina Aliyu zai fito
Da sauri ta dauke kanta daga kallonsa ganin yafito daga bandaki dagashi sai gajeran
wando zallarsa
Gashin kirjinsa yai luf bakikkirin ga faffadan kirji ga kwanji daya tara
Inna nakusa da zainabu wacce jikinta yadau tsima naganin aliyunta awani yanayi na
tada sha.awa
Tsigar jikinta saida yatashi taji kaunarsa takaru aranta tanason namiji me fadin
kirji da gasu
Ta bude baki xatayi maga inna tacafe da cewa " kaga kada kaji haushinta ko kaga
laifinta narashin xuwa da wuri sarkin yan fushi, taxo tun safe lokacinma futarku
knn
Yajinjina kai yace " Zainabu nah nakira kine gaban inna tazama shaida akanki na
tunin son da nake miki nakuma yi mk alqawarin Aure insha Allahu nanda dan lokaci
domin zan koma burni da zama badan naso ba da xarar kuma nakoma xanyi kokarin samun
aikinyi yi domin ganin nasamu abinda xan dogara dakaina nakuma iya rike iyalina
dakyau dan haka kirike amana ga inna itace sheda inada kishi kada wataran adawo
nakamaki da cin amanata dan walh inhar nga wani tare dake to tabbas saidai wani
bashiba zan kasheshi nakashe banza ke kuma in hukuntaki.
Inna ta kama baki tana kallon shi tama rasa bakin magana
Yabita abaya yana karewa surarta kallo ta iya tafiya gata da diri gata doguwa
Har kofar gidansu yakaita kana yaja tunga yace da ita " kalle ni Abu nah.
Yasa hannu yadago habarta jikinsa yai sanyi ganin hawayenta na xuba
Yagoge mata hawaye da tafin hannunsa ya murmusa yace '" Abu nah bansa ranar tafiya
ba tukunna. Akwai wani abune?
Wata kunyace ta lullubeta sam bazata iyaba dan akwai mutane masu wucewa inshi
bayajin kunya da tsoron mutane ayanxuma da take jikinsa don baxata iya xamewa bane
data gudu.
Ganin tana nuku,nuku yasa ya turarta da fushi yace mata " to nagode jeki gida tunda
ban isaba.
Shiko yajuya yatafi yana murmushi yace aransa " Zainabun *Ali gadanga* badai kunya
ba.
*Auntyn Sayyada da shahida*💘
*ALI GADANGA...*
🏹🏹🏹🏹🏹🏹
*Short Story*
*NabilancyLuv*💘 {_AuntynS&S_}
page4⃣
Sati guda dayin hakan shiru shiru Zainabu batasa Gadanga a idon taba
Jikinta yagama bata tabbas fushi yke da ita akan yace tayi masa abu takasa yi
To ai kasawa tayi sbd tanajin nauyinsa kuma tana gudun bakin mutune kada aganta
taji kunya
Saitaji inama tayi masa kawai ta huta dan rashin Aliyunta ba karamin gashin quma
bane agunta
Ta jejje unguwar gidansu kawarta atika amma bata sami ganin Aliyun ba
Tasan yana sonta kawai miskilancinsa yafi gaban komi yana kuma basarwa ne dan yasan
shi din me kyau ne kuma wanda yakai asoshin
Ali gadanga bai taba furta yana son wata diya mace a kauyen ba
Dayake kuma zainabun mekyauce dakuma biyayya saita rinjayeshi dasuka hadu aranar
farko ya karbi tayinta
Tabbas ayanda take son Aliyu zata iya jure komi dantaga tasameshi
Aranar kwana na goma da tayi narabonta da ganin Aliyu ta wanke kafafunta tayi
karfin halin nufar gidan innarsa kawai tunda tasan da soyayyarsu gara taje tagaya
mata kota saka baki ahuce fushin da akeyi da ita.
Ahanyarta ta xuwa gidansu Gadangar ne taga wani D'an nacin saurayi dayake like mata
tana nuna masa kiyayya ba dan unguwar bane amma yakan shigota jefi jefi shida
abokansa unguwanninsu suna makwabtaka ne sunansa Amadi.
Ganinsa yasa ta hadr ranta takara sauri donta wuceshi amma ina saida yacimmata
yasha gabanta ta kauce yafi sau uku tamkar tasaka hannu aka tayi kuka ganin yanda
ake kallonsu
Ita bakomi take jin takaicinsa ba mummunane shi gashi baki gajere
Batada niyyar magana ma sai kai data juyar gefe ranta abace
Yai murmushi yana shafa dan munafukin gemun daya tsayar kamar na bunsuru
"Yam matana ba magana ne ,haba zainabu me tagwayen suna kinsan ina sonki kamar in
mutu amma kike basarwa yaya kk so nayi ,koso kike sonki yakarni,
Yaci gaba " gaskiya yau bani barinki saikin gaya min da bakinki matsayina
Ta nunashi da yatsa "bani guri na wuce ko kaga rashin mutumci.
Yasheke da dariya yace " hakan nakeso ai, kome zakiyi ban matsawa walh harsaikin
gayamin kina sona ko kuma kiyi dariya inyi ko zamu kwana nn tsaye baxan matsa
mikiba inko bakiyimin daya cikin suba to walh zan rungumeki agaban jama.a.
Gabanta yafadi yau tashiga uku gashi layinsu gadanga ne ya knn zatayi ta tsira?
Batada amsa bakuma tada xabi saina tayi dabara kawai taxabi daya don ya barta kawai
Take ckn kissa da dabara tahau yak'e tana cewa ina sonka mana Ahmadi yama xa.ai
nak'i ka kayiwa Allah nidai kabani hanya sauri nake aikena akai.
Jin ta faranta masa rai yasa yabata hanya ta wuce dasauri yana dariya shima "
to,to naji nagode masoyiya jeki aikenki zanzo zance gida.
Tabdijan! Allah sarki zainabu Abu me tagwayen suna kokunsan tausayi tabani naganin
yanda nahango Ali gadanga acan karshen layinsu yana hango komi daga nesa xuwansa
kenan gurin idonsa ya nuna masa zainabunsa nayiwa wani fara.a suna tadi ckn nishadi
wato hira tayi dadi knn. Shedan yaita masa kida da xuga akunne
Wato tun kafin ma yabar kauyen ta canxashi lallai mata sai abarsu ashe yaudararsa
take tabbas yau xaiyi maganinta kafin yaje ga dan,iskan nata
Afusace yashi ckn gida inna tana tsakar gida tana tankade sai ganin dawowar gadanga
tayi ckn yanayin bacin rai
To fa! Wa kuma ya tabo Ali maxan fama Ali gadanga kuar yaki
Tayi tsaye tana jiran intaganshi ya futo da makami to tabbas wani yatabo matashi
awaje fada ne xai tashi knn aiko dai baxata bariba zata kwace inya futo
Sallamar da Zainabu tayine yadawo da hankalinta gunta ta amsa mata tana mata lale
marhabin
Suna ckn gaisawa saijin tayi gadanga yaguto da wayar wuta yahau dukan zainabun
Takaita dakinta tana rarrashinta " kiyi shiru kada makwabta suji su shigo tsegumi.
Ita dai zainabu ba bakin magana kuka kawai take tana faman murza jiki
Inna tadawo tsakar gida ta taddashi yana faman huci yana buga kafa akasa
Dayaga xatayi masa kuka tuni yadawo hankalinsa don bayason tashin hankalin inna
yann mugun sonta bayason ranta yabaci balle ganin hawayenta yana sashi awani hali.
Yayi tagumi da hannu bibbiyu yace " inna kinfi kowa sanin halina banason raini.!
bana son yaudara!!banason karya ko!!?
"To Abunah ta aikata min su dole ne ta karbi humunci dai dai da abinda tayi.
Naganta yanxu tana zance da ita da Amadi dan gidan mahauta suna zance suna nishadi
Alhalin dama tayimin laifi shine taxo layinmu tana xance danta sake kunnani kenan
to walh bata isaba zankumayi maganin sa shima.
Kafin inna tayi magana saiga zainabu tafito daga dakin tana xubda hawaye jikinta
asanyaye ta taho ahankali tawuce inna taje gabansa ta durkusa ckn muryar kuka tace
dashi " kayi hakuri kagafarceni walh banda niyyar yaudararka ko kusa bana son Amadi
shiyake bibiyata yana takuramin sosai natsani ma ganinsa yanxuma shiya taren hanya
wai baxan wuceba harsai nace ina sonsa ko insaki rai inyi driya kana yaban gu
Walh bada son rai nayi dariyaba dan bayadda xanyine baxan sakeba
"To kaji fa yanda akai sarkin "yan fushi da xuciya kadaina yanke hukunci da wuri
kada kaje wataran ka kashe aurenka koka kashe "yar mutane.
Ta dubi zainabu " kiyi hkr kinji Abu baxai sake ba kada ki fada agida. Yana sonki
tsananin kishinki yaja hakan.kin fahimta?
Zainabu tagyada kanta kawai tareda mikewa tayi waje tana share kwalla
Ita dai fatanta Allah yasa ya yarda da ita yafahimci ba son Amadine arantaba
Sam ba kukan dukan dayai mata takeba ganin ransa yabacine ita bataji xafin dukanba,
daxai kwana yana dukanta ma ba komi agunta ganin datayi masa ayanxun yakwantar mata
da hankali agobe zata dawo don sake bashi hakuri don itace da laifi.
Inna tayita masa fada don bataji dadin wanan yanke hukuncin ba
Tace" naji to amma kaje anjima kabata hakuri yarinyar nan taa sonka gadanga.
Sai daga baya yaji a dadi aransa daya sani yahauyi yana tausan zaibunsa tabbas
xaije ban hakuri
Ammafa Ahmadi xai gane kuransa saiya huce akansa dama akwai jik'akk'iyar gaba tun
da to gashi yakuma tsokano tsuliyar dodo.....
*ALI GADANGA...*
🏹🏹🏹🏹🏹🏹
*Short Story*
*Nabilancy Luv*💘
{ _Auntyn S&S_}
*Dis page dedicated to my Sisters*
*Batul mamman* 💖 (Al,adun wasu)
&
*Ummi Aisha* ( Wani haske)
page 5⃣
Magribar fari Ali gadanga yahau shirin zuwa zance gun zainabu domin yatanadi
kalamai dad'ad'a naban hakuri.
Wata shadda yasaka tsanwa dinkinta har kasa sawa na biyu knn yau tun dayasaka ranar
daurin auren babban yaronsa wawurau
Inna tafito da turare d'an d'uri ahannunta akamar kwalba tana fadin " ga tawa
gudunmawar ajewa Abu da qamshi.
Ta kama baki tace " ni na isa indaina son mijin fari, kawai dai ba yanda zanyine
tunda biko za.aje.
*****
kamar kullum yadda tasaba biyo dan aike yauma hakan tayi
Yayi mamakin hakan don yayi tsammanin ko fushi take dashi sai anja aji kana afito
Amma bakamar kullum ba yanayinta don yau asanyaye tafito tana taku ahankali kamar
kazar da kwai yafashewa aciki
"Nasan ban kyauta miki ba kiyi hakuri nayi miki hukunci akan rashin sani ki yafeni
sonkine yaja hakan.
Ji tayi kamar taje ta rumgumrshi amma tana jin kunya kuma tana gudun wani yaxo
wucewa ta lungun nasu ya ganta ta tafka abin kunya don har tsufanta ta kade
Amma jira kawai take taji yace ta sumbaceshi tabbas yau bazataki ba don zataso
hakan tayi kewarsa sosai
Saiji tayi yace mata "zan tafi Abu ki kula da kanki ki kuma kama kanki ina sonki.
Da xarar yafadi abinda ya kawoshi zai tafi koda ita bata gama ba to meyesa hakan?
Ta share hawaye akuncinta tanason Aliyu sai fatan Allah ya mallaka matashi
amatsayin miji.
€€€€€€€€€
Ranar wata lahadi Ali gadanga yatashi da ciwon kai baifuta farauta ba don ranar
basa fashin futa amma ba yanda ya iya don kan ya matsa masa yaransa ne suka futa
Alhaji ckn damuwa yatambayi inna meke damun Aliyun haka yaganshi kwance yadafe kai
Iya zulai tace " toko juko zansa namadi yayo masa.
Inna kulu tace "kayya ai ko ankawo basha yakeba sam gadanga bai yadda da jike
jikeba sai yace wai suna lalata hanji da hanta dasu k'oda.
Alh yace "da gaskiyarsa tunda dai yasha maganin zai sakeshi da yardar Allah bari
nakama masa kan.
Nan Alhajin yakama kan Ali gadanga yana tofa masa Addu,o,i
Bacci ne yadauke gadanga baisan tafiyar su Alhajinba yadaiji kafin yarufe idon sama
sama Alhajin nafadawa inna yaxo su tafi birni da shi Amma tunda baida lfy zai dawo
rana ita yau su wuce.
Sai Asuba yafarka kuma cikon ikon Allah yajishi sakayau kan yasaki Allah yaye masa
Saida yagabatar da salloli har wanda ake binsa kana yafito ya gaida inna
Tace "Lahadi Alhaji zai dawo kutafi yabar sallahu kancewa kazauna cikin shiri yabar
kudi yace insai kayan abinci don inka tafi wata biyu zakayi kafin kadawo
Taga yanayinsa yacanxa jikinsa yai sanyi tabbas itama natan yai sanyin jin har yau
saura kwana shida gadanga yatafi birni yabarta lallai xatayi kewarsa tun dare ta
kwana da tararrabin abin dan dai ba yanda zatayine addu.a kawai take Allah yasa
hakan shine mafi alkairinsa zata karfafa masa guiwa ne kawai dan karya sare dan ko
inhar ta nuna damuwa to zai iya fasa tafiyar....
_Muje xuwa_
*ALI GADANGA..,*
🏹🏹🏹🏹🏹🏹
*Story Short*
*Nabilancy Luv*💘
{Auntyn S&S}
Page 6⃣
A ckn "yan kwanakin daya ragewa gadanga yatafi birni duk yakoma wani iri baya
tabuka komi ko futa farauta yadaina kullum yana gida
Akullum kuma sai yaje gurin zainabunsa wata shaguwace ta shigesu soyayya ta karu
Yarage mata miskilancinnan nasa da jinkai Da ixza kamar dan sarki yakan kuma dade
atare da ita suna hirarsu
Hankalin zainabu akwance dan baigaya mata tafiyar tasu ba kawai dai taga canji na
wasu abubuwan
Sai ana gobe xai tafi ranar asabar yazo mata da maganar hankalinta yai matukar
tashi takasa dannewa tahau kuka
Sai alokacin yaji tafiyar tafita aransa badan inna ba da takeso da tabbas zai
fasata sbd ganin yanda Abun sa ta rikice masa
"Haba Abu nah kiyi shiru dan Allah kinsan yanda nakejin kukan nan naki kuwa to walh
har raina
Badan naso xantafiba sbd inna ta matsa ne kuma bansan ko Alkairi ne ke kiranaba
inkuma bakison na tafi to sai inhakura infasa kawai...
Ta dago kai da sauri ta kalleshi
Ya gyada kansa da sauri yakuma daga mata gira "kwarai kuwa inhar xaki shiga wani
hali sbd rashina gara naxauna amma ki sani baxan taba yin Aureba har sai in nasami
aikinyi
Tayi dariyar kuwa tana fadin " da gaske fa nake Aliyu zan hakura amma dai baxaka
dade ba ko?
Yayi dariya yace " eh! mana inkuma naji gidan baiyiminba to sati biyu kawai zanyi
indawo abina
Shiko kallonta kawai yake yanajin dadi aransa yau yaga takara masa kyau ainun
Inbadan tana bata fuska da fente fenten janbaki da gaxal ba daxatayi simple make up
da kyanta ya rikita maxa
Aranar ya dade agun masoyiyarsa suna shan hira ana raha kamar karsu rabu
******
Da safiyar lahadi kuwa yagama shirinsa tsaf yana tunanin Abunsa yaji sallamarta
Atsakar gida inna ta tarbeta tabata gurin xama taxauna suka gaisa
Yasha wani bluen yadi taxarce ya kure gayu amma bakyauye sak!
Ya amsa yana cewa " yasu inasu gwaggo suna nan qalau?
Tace "lfy qalau sunce ma suna maka fatan Alkairi Allah yakiyaye.
Yace "Amin.
Inna tace "gadanga kada kamance da nasihata karike da kyau fa shi birni daban yake
ba irin karkaraba saika kiyaye asaka hkr arai arage xafin xuciya akuma kula dan
Allah.
Shiko ido ya lumshe yana karanto addu.a aransa ya bude idonsa yaxubasu akan fuskar
zainabu yaga yanda fuskarta ta canza
Alhaji yaji dadin ganin Aliyu ashirye suka gaisa iya xulai na tsokanarsa saura
inkaje burnin dadi yasa kaki dawo mana koka yo mana kishiya
Alhaji yacika su inna da mutan unguwa da abin Alheri yatada mota suka tafi Ali
gadanga na gaba ya nutsu yana kallon hanya.
Koda suka isa ckn kwaryar kano kalle kalle kawai yaringayi na yanda benaye da
manyan gidaje masu get da fulawowi suka yawaita sai abin yabashi sha,awa
Megadinsa ya wangale get Alhaji yashigar da motarsa gun da ake farking kusada wasu
manyan motoci masu kyau
Gadanga yasha mamaki ganin wata bufurwar matashiya tafito aguje da kananan kaya
ajikinta ta rungume Alhaji tana fadin
"Oyoyo my dady ina granny? Yaka barota?
Alhaji yahau fara.a yana fadin " munbara lafiya tace agaidaki tunda kinki xuwa inda
take.
Ta xobara baki ckn shagwaba tana fadin " niko me zai kaine wannan kaxamin kauyen
haba Allah ya kiyaye dady ita dai inta damu taxo taganni.
Wani haushinta gadanga yaji najin furucinta lallai wannan yarinyar yar rainin wayo
ce kauyen nasu ne kaxami lallai taci darajar mahaifinta daya koya mata hankali.
Alhaji yasha mur yace " khalisat bakiga bako ba? Ki gidashi anan xai xauna.
Wani mugun kallo tabi gadanga dashi saida tadau mintina kana tace masa "hay! Ya
kke !
yahade rai baice mata ko kanzil ba yaharde hannaye akirji yana kallonta
Alh yace " mamudah ga bako nan dan,uwana ne daga yau yazama dan gidan nan ka share
dakin kusa dakyau nan xai xauna ga kayansa can abut ka dauko ka kai masa dakin.
Suka shige ciki ya rufa musu baya yana kallon yanda yarinyar ke karayraya kamar ta
karye ajikin daddyn nata
"Da alama dai yarinyar nan batada tarbiya kuma zan gyara mata zama. Gadanga yace
aransa....
*Short Story*
*Nabilancy Luv*💘
(Auntyn S&S)
Page 7⃣
Zaman gidan Alhaji yayiwa gadanga dadi naganin yanda Alhajin ke bashi kulawa gakuma
hajiya Laila na girmamashi da mutumtawa
Tun aranar daya iso gidan Alh yasadashi da Haj. Yaji matar ta burgeshi bayama da
Alh yabata amanarsa takumace ta karb'a xakuma ta rike bisa amana tamkar d'an
cikinta
yakuma fara gani da idonsa domin akullum saita fito taga lafiyarsa har daki
Musamman tagyawa me aikinta dije kan cewa ta tabbatar ta bambanta abincinsa dana
"yan aikin gida dana me gadi danshi d'an masu gidane takuma gargad'eta akan taringa
kula da lokacin cin abincinsa kada taringa bashi ak'urarren lokaci
Ali gadanga baiyi gidadanci da kuma bak'untaba don sosai yasake agidan yakuma
q'ulla abota da mamuda da wasu kecr masa mudi
A koyaushe suna tare da mudi afarfajiyar gidan kan benci suna hirar duniya mudi na
bashi labarukan almara daban dariya da abinda ke wakana abirni
Shikuma gadanga nabashi labarikan kauye da abubuwan dasukeyi agun farauta da gangi
Jininsu yahadu sosai wani sa,inma tare suke cin abincin rana kona dare
Abu daya ke tsaye masa arai ganin yanda khalisat ke wulakanta ma.aikatan gidan
daxarar tsautsayi yasa sunyi kuskure kadan to yanxu catayo kansu da fada harma
tayita bori akan sai ancire mutum abakin aikinsa ankawo wani
Masu musu girki kuwa tacanxasu yakai sau biyar daga dawowarta daga turai
Dije tana kiyaye kaidojinta akan kari take yi mata komai jiki na bari bata yarda
tayi kuskure tana mata biyayya fin yanda takewa matar gidan
Hajiya laila mace me hakuri magana bata dameta ba sai ayi abu akan idonta amma
dakyar xata tanka bayama abinda zai jayo mata bacin rai
Sau dayawa in khalisat tayi ba dai dai ba to bafa ta iya ta tsawatar mataba inhar
dadynta na gurin
Yanzu yahauta da fad'a yana cewa antakura mata shikam abar masa yar lele ta sake
gidan ubantane bana wani ba
Duk da abin na q'ona mata rai bata nuna masa saidai taja bakinta tayi shiru
khalisat yarinyace me girman kan tsiya ga rashin ganin girmn nagaba da ita koda
mutum yahaifeta ne
Gata da fadin ran tsiya gata da kishi me tsanani ko kaya tasako taxo wucewa taga me
irin kayan to dava ranar ta barshi
Shima dan nigeria ne amma mazaunin kaduna ne iyayensa masu kudine babansa ne
mataimakin gwamna
Safraz yana son khalisat amma sonta yafi nashi domin shi yanada yammatansa a boye
suna shanawa bata saniba
Ita kuwa batada kowa bata yarda ta hada sonsa dana kowaba.
Yanda suke gudanar da soyayyarsu aturai dasuka dawo kasarsu ma basu chanxaba agaban
kowa zasu rumgume juna suyi kiss basuji kunyaba
Duk sati biyu ko daya yake xuwa kano yasauka a hotel yayi kwana biyu atare da ita
Tanada kawa me suna khairat wacce suka hadu a shopping yar manyace itama don da
body guard take yawo babanta k'usane a k'asar nan.
Khairat "yar karya ce ta bugawa ajarida bata mu.amula da " yayan talakawa bakuma
ta soyayya da dan talaka ga ixxa da ji da kai hhhhmmm dan ma da abin dan
abin.....😊
******
Zaune suke akan benci suna hirarsu hankali kwance gadanga na baiwa mudi labarin
zainabunsa da yanda take sonsa take masa biyayya
Labarin abinda yawakana na dukan dayai mata na rashin sani yake bashi
Sun tsunduma ahirar tasu
Taxo kansu ta tsaya tana kada mukullayen mota riga da wando ne na pakistan ajikinta
kanta yasha attach har baya tayaneshi da siririn gyale
" kai! Wane irin wawaye ne ku ana muku sallama kuna shashanci
Ta nuna mudi da jikinsa ke tsuma ya sadda kansa kasa ckn biyayya yace " kiyi hakuri
ranki ya dade bamujiba ne.
Ta nunashi da bacin rai " kai rufa min baki kafin nasallameka daga aiki maza tashi
ka kaini unguwa tunda ilu dreba baya nan.
"Ali gadanga...!
Tace "inma DAMANGA NE ' ni baruwana da wani gadangar ka doka xan kafa dole abi kuma
"Uhhuumm kanaji ko, daga yau adaina zaman majalisar nan ka kama wani aiki agidannan
baxa.a ci dakai abanxa ba inba hakaba kuma insa amaidaka kauye
Ransa yai quna ya mike tsaye ya nunata da yatsa "ke ki iya bakinki maxa bisa kanki
karamar alhaki kawai wacce baifi na matseki ahammata ba mara kunya.
Tayo kansa da hargagi tana fadin " ni kake gayawa haka? Walh yau saina nuna maka
kurenka zakasan kataboni zaka bambance matsayina agidan nan walh saika koma kauye
dan akuya kawai.
Babu wanda yataba gaya masa wannan kalmar me xafi sai ita kuma dole saita gane
kuranta saiya nuna maya akuyanci saitayi dana sanin fada masa haka...
_Muje zuwa_
*Short Story*
*Nabilancy Luv*💘
{ _Auntyn S&S_}
Page 8⃣
Ali Gadanga yananan Zaune ransa na masa suya yakasa yatsare yana jiran dawowarsu
khalisat dan ya dau mataki akanta
Yau me rabashi da ita sai Allah xaiyi mata hukuncin dazaisa tayi shakkun kowane da
namiji yanda koda wasa baxata sake kallon kwayar idon wani namijin tasake kiransa
da dan akuyaba koda karamin yarone
"Gadanga dan Allah kaxubda wadannan halayen naka ka canxa da masu kyau wadanda
xa.a yabeka ko bayan ranka
Ka kadance me hakuri ako,ina aduk abinda akai maka koda kaine da gaskiya karinga
koyi da halin ma.aikin Allah kkoda mutum ya takaleka karinga danne xuciyarka kada
ka zama kumurci sarkin fada kaxama salihi gadanga na...!"
Yaja wata doguwar ajiyar xuciya tabbas yakamata yafara jin maganar innarsa ko don
yaxama me faranta mata dayin alfahari da hakan
To amma baxai iya barin khalisat taci abinci akan saba ko xai hakuri akan komi to
banda wannan baxai dauki rainin taba.
Da sauri mudi ya rufe masa baki yana waigen bayunsu gudunsa kada wani yaji.
"Bari fadan haka kada ajika, yar masu gida ce ko me zatayi bme mata kallon hakan.
Mudi yace " ai da futarmu tayi ta fada ita kadai inajinta kamar taci babu nidai ko
kallonta banyiba kada ta hucr akaina, can ta gaji takira daddynta tagaya masa yanda
kukayi tana kuka,to bansandai me yace matab da alama rarrashinta yayi.
Filin jirgi tasa nakaita ta muka dauko saurayinta dayaje wata seminer can
Mudi ya gyada kansa yace "kwarai kuwa ai duk lokacin dayaxo ina kaita inbarota acan
in dare yayi saiya dawo da ita amotar wani abokinsa
Gadanga yace "tab lalli yanzu yarinyar nan tana haka amma Alh yasani baya mata
fada?
Mudi yace "kai ka kuwa san son da Alhajin keyi mata to ko fad'a bai tab'a yi mata
ba balle kallon banxa wanda duk yai mata ma ransa ke b'aci
Kaima inaso inbaka shawara akan kada ka k'ara d'aga mata murya sbd shed'aniyace ba
abinda baxata iyayiba don ganin an bak'anta maka rai
gadanga yace "hhhmmm kasan Allah mudi saina nuna mata nafi karfinta saita gane
kurenta agidan nan zan nuna mata ni dan akuyan ne yanda ta kirani kuma in xauna lfy
Dan anmaidani ko ajikina dama har yanxun kewar garinmu bata sake niba.
Gyada kai kawai mudi yayi bai kara cewa komi ba dan bai hango tsoro a idon gadanga
ba zai iya yin komi akan wannan lamari
*****
Anyi haka da kwana biyu gadanga yana zaune shi kadai akan benci yanajin labarai a
Aminci Radio
Mudi ne yabashi don ta ringa tayashi hira shikam yabar xaman xaibi doka
Alh ne yafito xai futa yanata sauri dayaga Aliyu saiya tsaya
Ckn fara.a Alh ya amsa yana cewa "badai wata matsala ko?
"To!to! Aishikenan dama inaso ingaya maka ma xaka fara xuwa Aiki a kamfanina na
kera Alminium akwai matsayin da neso kasamu aciki office nasaka agyara maka don
haka kafin agama shirye shiryen abubuwan inaso karinga kai khalisat duk inda zataje
kafin drebanta ilu yadawo daga garinsu
Duk da abin bai masa dadiba nakai kalisat unguwa da xai ringa amma bayanda xaiyi
baxai iya ma Alh musuba
Yana ckn tunani yasamo mafita dan yaci burin wulak'anta ta amma ko ta wannan hanyar
saiya rama abinda tayi masa.
Itanma acan b'angarenta murna takeyi gadanga yaxama drebanta na "yan wasu kwanaki
wanda ta hakan zata yi masa wulak'ancin da bata taba yiwa wani d'a namijiba saiya
gwammace dama baizo birniba
K'awarta khairat tabata wannan shawarar kan cewa ta mayarsa dreba kawai don tasamu
hanyar wulakanta ta tunda shi tsagerine baya ganin martabarta na "yar manya
Tunda gadanga ya muxantata taji ta tsaneshi ta damu matuqa harta gayawa khairat kai
hatta SAFRAZ saida tagaya masa
Yana xaune kan benci yana jan carbi yayi sallar magriba
"Kai ji mana.
"Ni ba kai bane bakuma xaniba har sai kin kirani da sunan dana gaya miki kin kuma
yimin sallama kana zan kaiki.
Ta ciji yatsa taso tayi masa rashin mutumci saikuma ta tuno abinda take da shirin
masa insun futa saita kanne data tuno yanda khairat ta tsara mata nan tayi masa
sallamar ckn wata murya
Tace masa " Ali kake kowa katashi ni ka kaini unguwa dinner gareni kada ka batan
lokaci
Yai mata kallon banxa yace " kinsan da cewa ba inda nasani agarin nan ai dan haka
saikije kisamo me kaiki badalar ki amma baniba da nk bako
Ta danne abinda ke ranta tace "ai nasan kai bakone so nake dama yazamo nice silar
budewar idonka abirni zan ringa nuna maka hanyoyi tunda ai ko akauye dole ayiwa
kidahumi uzuri
Tana gama fadar hK tayi gaba tana karayraya tana cewa "inkuma baxa.a kainiba inbuga
ingayawa dady yanxun nan.
Jin ta sako babanta aciki ya mike yabi bayanta yana ayyana abubuwa da dama da xai
yiwa yarinyar nan arayuwa na gyara mata xama.
Dayake Ali gadanga gwani ne a iya tukin mota dan yana tab'a tuki na manyan motoci
da "yar b'urb'ur da akori kura sai tukin motar bai bashi wahala ba amma ahankali
yake tukin tamkar d'an koyo
Ta d'au k'afa d'aya tasaka masa akafad'arsa taci gaba da yin wayarta hankalinta
kwance....
*Auntyn Sayyada da Shahida*💘
*ALI GADANGA..*
🏹🏹🏹🏹🏹🏹
*Short Story*
page 9⃣
Da taji baiyi maganaba saita sauke kafar tata tana waya da karfi dan yaji
"Gani nan zuwa kawata muna gab da isowa gun, duk kun taru knn?
"A,a ina bani nake tukin ba wani ba kauyen dreba na samu bai wani kware atukinba
dayake bai saba shiga irin tsala tsalan motocin nan ba ahankali yake tukin ,
" kawai dai hakuri nake dan bakiji motar ba kawata sai tsami take
"To bansaniba dai ko kwari ne suka mutu acikin motar ko kuma andade ba'ayi wanka
bane..,. "K'uuu! Yataka birki da sauri zancenta ya daki kirjinsa yakasa jurar
abinda take masa
Afusace tace masa "kai meye hakan ance maka munxo gurin ne
"Walh kayi kad'an ka wulkantani wacce kala gareka banda wacce ban saniba ta
kauyanci kai baka isa ka d'aga min murya inkyalekaba...
Yana tsayawa yahango "yammata sunyi su biyar suka nufosu da yanga da yauk'i da
alamar suma "yan jiji dakaine
"Yayi yayi babbar yarinya!saikinyi ko garin ba kowa !!dole abiki azauna lfy!!!
Shikam kallonsu yake yana Allah wadarai aransa naganin irin banxar shigar dasukai
ta rashin tarbiya kowacce tasaka kaya na ashsha babu tsari
Khalisat ta kalleshi awulakance tace masa "kadawo karfe goman dare kadaukeni kada
kasake kawuce hakan
Baiko kula taba yaja burki yatayar musu da kura yabar gurin
Allah nema yataimakeshi da har ya iya gane hanya yadawo gida batareda yasha
wahalaba koya b'ata ahanyar
Tabbas zai nunawa khalisat shidin dan kauyenne domin yaci alwashin saiya mata
wulakanci nan ba da dadewa dan bazai bari tad'au lokaci me tsayi tana masa hakan
ba agaban mutane sam baxai iya juraba
Ita kuwa ranta ne ya sosu naganin yanda yai mata babu wani biyayya na shi din
makaskancin tane agaban kawayenta tabbas zata gyara masa zama
******
Hankinsa kwance yai baccinsa ya mance da wani komawa dauko khalisat ahotel bata isa
tasashi yakoma ba Alh ne kadai zai masa gadara da dole
Ita kuwa tana can da aka tashi ranta abace har goma da kwata bai dawo daukan taba
gashi ankusa watsewa
Lallai wannan dan kan sane da alama zatasha wuya dashi kafin ta lankwasashi ya zama
bawanta
Taji inama mudi tasaka da tuni yaxo daukanta dan dai tana da qudiri akansa na
daukan fansane
Allah yataimaka mata saurayin kawarta lubna yaxo daukan lubnan nan tayi dabara tace
su ajiyeta agida antaho daukanta mota ta lalace ahanya
Ko da tashigo gida ta hango kofar dakinsa arufe ta tabbatar yana ciki da alama ma
bacci yake wato da biyu yai mata hakan
Tayi nufin tabarshi xuwa safe ta hada masa sharri gun dady amma sai wata xuciyar ta
ayyana mata mugun abu akansa gara tashiga dakin kawai tafara xaxxaga masa rashin
mutunci ko ta huce
Yana kwance harya fara bacci yaji anbude masa kofar daki anshigo babu ko sallama
To amma yana darajta mahaifinta gara yau yakoya mata hankali tunda yasamu babbar
dama takawo kansa dakinsa gara yakoyarta darasi ta hanyar babbar illar dazai mata
arayuwa
*Muje zuwa*
*Nabilancy Luv*💘
{_Auntyn S&S_}
&
*Ummi Aisha*
(Dan Asali)
page 🔟
Yau dai khalisat taga ikon Allah tarasa yanda zatayi ta kwaci kanta domin karfin ta
baikai rabin na Aliyu ba
Gadanga yafice Ahayyacinsa k'ok'arinsa kawai yaga ya cimma burinsa na yaga mata
mutumcinta
Da ALLAH Yabashi sa,a yaxira guga arijiya aituni yafara d'ebo ruwa,
Ita kuwa mutuniyar taku saitayi likimo ta wani narke ta daina motsin da take na son
kwatar kan nata
Kokunsan wani dadine yaringa ratsa mata kwanya domin zullon da Gadanga keyi akanta
yana _shakking_ *Safraz* bai iyashiba
Taji daban takumaji dadi na daban wanda bata taba jin anjiyar da itaba irin na yau
Tabbas ba haka yaso ba yazaci xai sameta acikakkiyar budurwa sai gashi yajita wayam
Baida burin ya faranta mata ko kadan ai take yai zimbur ya sauka akanta
Yana salati axuciyarsa yana dana sanin yanda ma yabiyewa sharrin zuciyarsa yasab'i
Allah
Ita kuwa kasa tashi tayi tanata wani lumshe ido irin na tsoffin "yan iska
yane kanta da d'an figil d'in gyalenta ta suri "yar jakarta tafice ad'akin
Bata tsaya ba data fito da sauri-sauri tashige cikin gidan dan kar wani yaganta
amasu aiki
Baitaba yin zinaba sai yau tabbas shaidan ya rinjayeshi bakuma zai karaba da yardar
Allah
Abinda yafi daure masa kai shine ya akai baisami khalisat cikakkiyar maceba, ashe
dama futar da take knn budurcinta take talla?
Take tsoro yaxiyarceshi na tuno cutar an me karya garkuwar dan adam wato kanjamau
Yatashi cikin dare yayi sallolin nafilfili yana rokon gafara da tsari gun ubangiji
Babu cutar dayafi jin tsoronta irin kanjamau
Wata xuciyar tace masa "habadai saidai inkai xaka gujeta amma Abun ka bazata taba
gudun kaba kome gareka.
Aiko dai bafata yakewa kansaba shikam baxai iya cutar da zainabu ba inma hakan
takasance saidaima yaiwa kauyensu nisa
To wazai Aureni?
Yatambayi kansa
Afili yafirta "Allah ya sauwake niko me zanyi da ita tagama zibda mutuncinta awaje.
******
Inama yakara sha.awarta yasake mata hakan aiko dai baxata hanaba bakuma xatayi
ihuba
Ta k'ank'ame filo tana murmushi yanayin daxu da suka kasance yaringa dawo mata
ranta fari qal ba ita ta iya bacciba sai biyun dare dan ma bacci barawone
Alokacin da baccin yadauketa shikuma gadanga alokacin yana kan sallaya gaban
ubangijinsa ya daga hannu yanata kwararo addu,o,i na tuba ga Allah
Da gari yawaye ma kasa fitowa yayi don ji yake kamar angano abinda yayi da khalisat
jiya
Har rana bai fitoba haji ta leko ta masa sannu don dije takawo masa abincinsa dakin
taji mudi na masa sannu shine taje tagaya hajiyar
Da daddare bayan sallar ishsha,i Mudi ya leko dakinsa yace masa "mutumina kaje inji
me gida,
Saida gaban gadanga yafadi najin Alh nakiransa tsoronsa kada dai ko khalisat ta
gaya masa ne.
Take nadaa tak'ara shigarsa yanxu to me zaicewa Alhajin to ai ma Allah yasoshi babu
wanda yaga shigarta da futarta kawai zai karyata ne shine mafita agareshi
Don kuwa yasan inhar Alh yakamashi da laifin hakan korarshi xaiyi gashi yafara son
xaman birni gashi ma Alh yasaka masa rai zaibashi aiki me kyau da albashi me tsoka
wanda tahakan ne zaibashi damar mallakar zainabunsa....
*Short Story*
*Nabilancy Luv*💘
{Auntyn S&S}
_masoyan *Ali gadanga* yace yana godiya yana jin sakwanninku nayanda kuke tayashi
takaicin yanda yafada tarkon shaid'an yanaso kuyi masa fatan alkairi yana yinku
kamar yadda kuke yinsa_
Page 1⃣1⃣
Jikinsa asanyaye yayi sallama ckn falon yashiga anitse ya zauna nesa kadan da dadyn
khalisat wanda yake kallon Aliyun cike da kauna ya amsa masa sallamar fuskarsa
dauke da fara.a
Alh yacafe da cewa "in kan naka bai daina ciwon ba kafada mutafi asibiti Aliyu
kada ka cuci kanka inaso kadaukeni tamkar mahaifinka.
Ganin baiga khalisat afonba baikuma ga alamar bacin rai afuskar iyayenta ba yasa
hankalinsa yakwanta zarginsa ya gushe
"Aliyu Aikin office din danake so yaxama mallakinka ya kammala sai fara xuwa aiki
da xakayi ranar monday abu daya ne kawai nake tunani akai ko zaka iya?
"Office dinka ya ta allaka ne akan b'angaren shige da ficen duk wani kaya na
amfani na da kuma karbar duk kwangilar da zata shigo
Kaga knn mamallakin office din yana kyau ace yana da sani akan harshen turanci ko
kuma iya lissafi to bansaniba ko ka iya daya daga ciki? Don inhar lissafi bai
wadace kaba zan iya saka maka sakatare acikin oficce din da zai ringa lurar maka
lissafe lissafen kai kuma karinga rubutawa kana ajiyewa da baiwa mutane reciept to
wanne ka iya ciki?
Gaban Aliyu yafadi bai iya math ba amma dayake yayi primary yana iya karatun
turanci harma yarubuta amma kowacce kalma yake ganewa ba shiko lissafi da sauki
daga plus sai minos ya iya baiyi nisa ba gaskiya
Ckn nutsuwa yace da Alh "bangaren rubutu banda matsala amma lissafi banyi nisaba
baxan iya lissafi akan makudan kudade ba.
Murmushi Alh yayi yace "to ai ba matsala akwai wanda zansaka maka a office kuringa
yi tare har wataran ka iya da kanka amma shima turancin inaso ka ingantashi sbd
zaka ringa cudanya da yan kasuwa wadanda basajin hausa dan haka asatin daka fara
zan sai aka foam a makarantar koyar da harshen turanci ta *M.M. HARUNA*
dan haka saika dage kaxamo zakaran gwajin dafi aga kabar zaman gia knn duk weekEnd
inba aiki k makaranta ko,
Gadanga ya daga kai cikin matuqar farin ciki yace "nagode Alh Allah yasaka da
Alkairi
hajiya tace "kai Amma naji ddi sosai zanbaka gudunmawata ta kudin da zaka sayi
kayan sawa masu kyau tunda kazama babban mutum dole karinga shiga ckn kaya masu
tsada da kyau dan kar arainaka
Murmushi Alh yayi yace "kwarai ma kuwa inkin bashi zan kara mishi akai dan haka
zuwa gobe sai insa mudi yakaika Grand squar ko Shop rite kayi sayayyrka can
Gadanga yaringa musu godiya sannan yakoma dakinsa ransa fari qal
Tabbas yana hango ci gaba arayuwarsa baxai taba mantawa da Alh ba tunda har ya
inganta masa rayuwa
*******
Dubu hamsin Alh yabashi haj kuma talatin haka yahadasu guri guda yaita kallonsu
yana mamaki wai wannan kudi duk nasa ne,kuma na siyan sutura kawai,!
Lallai ana barna abirni tabbas inbakada kudi baxa kayi harkaba
Lallai duk lokacin daxai koma kauye saiya kashewa zainabunsa da innarsa kudi a
albashinsa na wata biyu dubu dari knn hamsin zai ringa dauka
Alh yamasa gatan da bakowane xai masaba wanda mudi yace masa sai mutum yanada
hanya ne ma koda kwalinka zaka dauki salary sama da talatin ko k'asa shiko me zaice
da Alh tabbas shima yakamata anan gaba yasaka masa da abinda yai masa.
Koda sukaje siyayyar ma dayawa mudi me yaringa masa xabin shaddoji masu tsada da
kyau kalar fatarsa duk da gadanga ba fari bane wankan tarwada ne
Agoguna biyu da takalma biyar da huluna na dubu talatin suka siya na karamin kudade
ne
Saida sukajene ma telan yace Alh yayo waya kan cewa yagwadashi yayi masa yayi total
zai bashi kudin
Gadanga yaji dadin hakan nan yabaiwa mudi dubu goma kyauta
Mudi yayi godiya sosai dan dama yanada bukatu agefe
Asatin daya fara zuwa aiki ma mudin ne yakaishi har ckn kamfanin
Yakuma ce masa "ai mutumina kagama morewa inama nine kai fatana kawai kada
kayardani inka shigo gari ka kuma ringa addu,a domin wani zaiji haushin ya dade da
Alhaji shi ba.a daukakeshiba sai wani daga sama kasan dai mutane
Gadanga yayi murmushi yace "kwarai hakane kam abokina mutum mugun icene zankuma yi
addu.a zankiyaye.
Inama suna gurin suga yanda Yaxama wani yaxama me matsayi a office
Bakaramin kyau yayi acikin office din ba ga shaddar jikinsa ta haskashi hular tayi
masa kyau sai sheki yake kyansa yakara fitowa kai bakace gadangan kauyen marina
bane yakoma Aliyu haidar dan birni
Ma.aikatan kamffanin sun shisshigo sungaggaisa kowanne yaji sunansu yayinda shima
yasanar masu da nasa sunan
Tukur shine sakatarensa wanda zai ringa kular masa da duk wani lissafi daza.ayi
Tukur matashine me hankali yana baiwa Aliyu girma sosai dan Alin ya girme masa
Haka zai fito yana tashin kamshi yasha sabbin kaya yashiga mota mudi yaishi tamkar
wani gwaska
Asatin kuma yafara xuwa m.m haruna inda yafara daga ajin farko
Nanma abin yakanxo masa da sauki tunda yataba zaman aji kuma yanada saurin fahimta
ga kwakwalwa
Alokacin kuma ilu dreban gidan yadawo shi yadawo yana kaishi dan dama mudi shikoki
yake ban ruwa da kuma sauran yam aiyukan gidan
matsalar daya fara fuskanta agun ilu ne dan shi mutum ne me nuna bakin cikinsa
afili
Ran gadanga yafara baci da hakan amma bai masa magana sai in yakaishi makura
tukunna
Ranar wata likitin yagama shirinsa ckn purple shadda da hula purple tayi masa
shegen kyau ga fatarsa na sheki cocoa butter ya karbeshi
Itama khalisat ta fito ckn shiri zataje unguwa takira ilu tace masa maxa yawanke
mota zataje asibiti
Ilu yace "Ranki ya dade zankai Aliyu office saidai ko zaki shigo inna ajiyeshi sai
inwuce dashi kada yai latti... ta daka masa tsawa
"Kai!ilu kasan me kake fada kuwa. Harni yar masu gida zaka hada ni ckn mota da dan
kauye kuma ma dan isa ace sai anfara kaishi to babu wanda ya isa maxa shige ka
kaini hospitan yatafi akafa tunda bai saba shiga mota ba dama sai anan.
Karaf akunnen Gadanga yafito yana gyara hula ta bayanta yatsaya yanajinta yakuma
d'auri d'amarar ya mayar mata da martani ayau.....
*Short Story*
*Nabilancy Luv*💘
{Auntyn S&S}
Page 1⃣2⃣
"Ke karamar mara kunya juyo kiga wanda yafi rashin kunya "yar masu gida.
Da sauri ta juyo gabanta ya fadi ganin Ali atsaye yasha kyau ga wani annuri atare
dashi sai buga kamshi yake
Ya murmusa yana gyara agogon hannunsa yace da ita "kinsan Allah koki kama gabanki
kibari akaini gun aiki kokuma yanxun inkoya mk hankali akaro na biyu.
Cikin mamaki tace dashi "baka isa ba walh babu inda xnje inka fasa baka cika dan
halakba, kai harka isa kayimin gadara nida gidan ubana walh inbakai wasaba sainasa
anmaidaka kazamin kauyenku....kau!kau!! Ya wanketa da mari
Saida ilu ya tsorata ganin karfin hali da tsaurin ido irin na gadanga lallai
yatsokano tsuliyar dodo dan ko mahaifinta bai taba gani yai mata fada ba balle
yakai hannunsa jikinta
Ko ajikinsa ma saima maganganu yaci gaba da yaba mata " idan kina yin rashin
mutumci toki san wanda zaki ringa yiwa dan wannan gadangan na gabanki ba irin
solobiyoyin maxajen da kk juyawa bane ki iya bakinki dan zan mk komi kuma inzauna
lfy.
Ya dakawa ilu tsawa "maxa shige ka kaini office ta tuka kanta ko tafasa futar.
Ilu daya shiga taitayinsa yaji wani shakkar Gadangar tashigeshi tuni ya wuce da
sauri jiki na tsima
Yatada mota Aliyu yashiga, megadi yawangale get suka fuce
Khalisat tafashe da kuka tahau dire diren kafa ta koma ckn gida da shagwaba ta fda
jikin momynta tana kuka
Hjy laila tace "meya faru diyar dady? Keda waye haka ?
Khalisat tace "wancan dan kauyen ne ya mareni agaban mutane walh yau saiya bar
gidan nan.
Momy ta dafe kirji tace '"mari kuma? Me kk yi masa dahar zaiyi wannan gangancin,
Khalisat tace " kawai dan nace ilu yakaini hospital din shine yace baza,a kainiba
shi za.akai dan nace bai isaba shine ya mareni har sau biyu
Momy tace "to ai laifinkine khalisat kawai dai kice rashin kunya kkyi masa
Futarsa fa tafi taki muhimmanci tunda shi aiki zashi kuma aikinma na mahaifinki ne
ke kuwa ke kkso wahalar da kanki futa tunda inhar kinxauna agida likitanmu zataxo
har gida ta dubaki kuma kin iya tuki ko ba ,a kaikiba zaki iya kai kanki ga motoci
nan sai wacce kkso zaki hau
Momy ta kama baki tace "a,a bawani bayansa danabi gaskiya ce na fada khalisat
kinsan halina bani qaunar inga ana wulakanta mutum dan anganshi makaskanci to balle
shi Aliyu ba kamar sauran yakeba ba dan Aikin gidan nan bane tamkar dan,uwa yake
gun mahaifinki kuma kokin gayawa dadynki bazai masa hukunciba tunda yadaukakeshi
gara ma ki hakura saiki kiyaye agaba.
Khalisat ckn shagwaba tace '" walh baxan hkr ba saina nuna masa kurensa kuma sai
dady yadaukar min mataki akai.
Ana haka saiga dadyn ya ya sauko daga sama da jallabiya ajikinsa kukanta ne
yatasheshi abarci
Ya xauna akan two siter ya janyota jikinsa yana rarrashi duk da ransa ya sosu najin
Aliyu ya mareta to amma yasan da laifin khalisat din bai kuma isa ya nuna ba yanxu
ta tubure masa shikuma baisan damuwarta gara ya lallabata kawai yafi
Takashe da shagwabarta "nidai dady kawai ka koreshi agidan yakoma can kauyensa yafi
banason ganinsa.
Hajy laila tahau girgixa kai tana takaicin halin "yarta duk da tana ganin da laifin
Alhajin ack na yanda yake shagwabata
Dady yace "kibani lokaci baxan koreshi akan ya marekiba sai inyasake mk laifin
dayafi hakan xan dau kwakkwaran mataki akansa kinga ban dade da bude kamfani naba
gashi kuma yahabaka komi yana tafiya dai dai sbd shi kinga zantanadi wanda zansaka
amatsayinsa daya sake kwatanta mk hakan zan cireshi inmaye wani agurbinsa
Nan taji sanyi aranta ta hkr ammafa saitayi yanda tayi taga Aliyun yabar gidan
zataita tsokanarsa da fada inya taya kuma yajawa kansa
haj laila tace "ki koma dakinki kawai inyiwa doctor waya tazo har gida taganki.
Hjyn tace "ato kuma ke kkjiyo ba.a fushi da lafiya dama ke kikace kinajin ciwon
ciki da mara kuma tunda kince kin hkr ai sauki ya samu knn
Khalisat ta mike kawai tabar falon takoma daki ranta abace takira Safraz awaya bugu
nabiyu yadaua yace "dear ya hospital din me sukace ?
"Sbd me dear kada kiki xuwafa gara kije a ko akira doctor taxo gida taduba ki ta
tabbatar mk da abinda yk damunki
"nifa matsala ta babba ce dear banaso agano agida shiyasa banaso liktan taxo gida
don ina zargin ko cikine dani last mounth banyi period ba yau 2week shiru atsorace
nk fa
Yayi tsaki yace "kidaina wannan maganar dear zargin kine dai hakan amma daga ciwon
ciki da mara sai ace cikine dan cikin baida wahalar shiga sau d'ayanefa kawai nayi
ba condam
Cikin d'aga murya tace dashi "wai bakaji nace maka banga period dinaba sati
biyu..."to saime dan baki ganinba, ke nifa inma cikin ne inason kayana don baban
saida suka shekara goma da aure shida mom kana suka haifi yayana haka yayana ma
saida yafi hakan kana ya haihu dayai auran kinga ni bansan matsayina bama innayi
zanfi shekarunsu ne ko bama zan haihun ba innayi auren...
"Saime dan munyi hakan babu wanda zai hanamu aure,dad yanada kudi haka kema naki
iyayan sunada arxiki linga d'an ko "yar baxata wulakanta ba.
Tace "kai bari kajifa,niko aure nayi banida burin naga na haihu da wuri to balle
ina waje so kake inji kunyar iyayena.
Yace "to bbyna bafa hakanma bane zargin kine dai kawai kima kwantar da hankalinki
HOO!khalisat knn !!
Muje
Xuwa
*Short Story*
*Nabilancy Luv*💘
{Auntyn S&S}
Page 1⃣3⃣
*Aranar Gadanga wuni yayi zur a office zuciyarsa na masa quna na abinda khalisat
take masa
Baxai bari taci gaba da rainashiba, da d'aga masa murya bayason rainin hankali
kwata kwata
Yasan inhar Alh yaji cewar ya mari gudaliyar yarsa to aikam baxaiji dadi ba tunda
yasan yadda ake ji da ita
Saikuma yaji yana nadamar marin dayai mata domin ji yayi baikyautawa Alhajinba
gashi yana karya alqawarin dayaiwa innarsa na yawan zafin xuciya da daukar mataki
da gaggawa
Wata xuciyar tace dashi '"to ai khalisat dince saida gashin quma inba hakaba saita
kashe mutum kwanansa bai kareba
Koda yataso daga aiki karfe biyar ilu yaxo daukarsa yaxaci xaice dashi ko Alhajin
na nemansa ne saikuma yaji bai masa mgnrba
Haka daya koma gidanma yana zaune a benci shiru shikadai yanata tunanin abunsa
tabbas yakama yaje yagansu karshen wata yagaji da kewarsu
Mudi yaxo yaxauna kusa dashi suka shiga hirar duniya yai tsammanin ma ko Alh ne
yaturo mudin kiransa don mudin ya dade baixo sunzaua hirarba saidai su gaisa
atsatsysaye saboda gudun kada khalisat taganshi yake tadau mataki kamar yadda ta
fada musu abaya ta kafa dokar ta hana zaman hira agun
Shiko gadanga kusar yaki ai harya mance da anyi hakanma tunda yasan bata isa yaji
tsoronta ba shi baiga namijin ma daxai bashi tsoroba ballan tana mace
Aiko dai suna xaunen nn gab da magriba sai kwatsam gata ta futo Allah yabaiwa mudi
sa,a ya ankare tuni yamike sadaf sadaf kafin ta karaso gun ya fece
Gadanga bai fahimci mudin guduwa yayib dan baiga nufowar khalisat dinba
Saida yaja numfashinsa Sama yadire dakar jin saukar sanyin ruwan kamar na
kankara afuskarsa
Kafin ya magantu harta rigashi tana rike da k'ugu cike da tsiwa tace "Kai maloho
bakauye ban hana xaman hirar nan ba wato kaine me taurin kai ko to walh duk abinda
nayi mk kaika siya don baxan bari aringa gulmar mutanen gidan ina ganiba
Taja baya tana nunashi "walh kasake yau jikinka yataba nawa saina maka sharri gun
dadyna wanda bazaka taba fidda kankaba don xance masa naji kuna gulmarsa kuma xan
fada masa kayimin fyade inkuma ba hakaba nayarda mudafa qur,ani
Lokaci daya jinin gadanga yatsaya da gudana yatsaya cak! Yabita da kallo lallai
mace makirace
Yanunata da hannu yace "meye ajikinki da za.a yiwa fyaden abinda aka gama baiwa
"yan waje mara mutumci kisani cewa ackn mata ke fanko ce mata kk rako duniya ko
sadaka kuma aka bani irinki masu mutumci da sanin darajar mutum ma bazan karb'aba
balle ke da bakida mutumci da kima aguna.
Duk da taji qunar furucinta aranta amma saita dake tace "oho dai ko me zakace dani
baxan fasa yi maka sharrinba inhar kataba fatar jikina ayau.
Gadanga yakoma kan bencin yaxauna zuciyarsa na tausarsa yana kuma tuno kalaman
innarsa
Yakoma dakinsa yasake kaya dama farar jallabiyace ajikin nasa duk zob'on ya b'ata
ta
*******
Tunda khalisat tayiwa Gadanga boren xatayi masa sharri gun dadynta tasami lagonsa
akusan kullum saita sami abinda zatai masa na ganin ta k'untata masa duk tsokanar
da xatayi masa naganin yaji yaji haushinta bata fasaba yi take amma abinda ke bata
mamaki bai tab'a d'aga kai yakalle taba ballantana taga fuskarsa ta canza duk
habaicin da zatayi masa baya jin haushi
Batasan cewa tarata yake ba shiru kawai yayi mata ya qudiri aniyar saiyayi mata
abinda bazata manta dashiba wanda saitayi dana sanin yi masa hakan
Dubu hamsin yabiya gadanga kamar yadda yatsara zai ringa bashi duk wata
Aifa gadanga na ganin uban kud'aden nn yafara shirin tafiya kauye harda tsaida
ranar tafiya
Saidai kash dayajewa Alh da zancen tafiya nan Alh yakansile masa don yace ma.aikaci
irinsa baya barin guri yabari da gaggawa har sai inyakama gurin ahannu yabari
yakara sabo agun
Baiji dadin hakanba dan yasa rai sosai da ganin zainabu da innarsa akwanakin nan
Wani watan daya zagayo baisa rai da tfy ba kada Alh yahaashi ma yaji ba dadi ammafa
xuciyarsa tagama cika da kewar masoyiyarsa da innarsa yasan suma suna can suna xuba
idanunsu
Saida yai wata uku da fara aikin kana Alhajin da kansa yatsaida masa ranar tafiya
yakuma bashi dubu hamsin na daban yace yayiwa inna siyayya banda salaryn daya bashi
Dubu dari biyu gadanga yahada cas ahannunsa yaringa jujjuyasu yana farin ciki
Ashe zai mallaki tarin kudade masu yawa lallai kaji shawarar manya ma aduniya yayi
arayuwa daya biyewa zuciyarsa bai dauki maganar inna yazoba da baisamesuba
Ai saiya hau tunanin wai gashi nan yana tuka mota mekyau zainabunsa na ciki a
tsohon ciki sun dawo daga asibiti sunshiga tanfatsetsen gidansu
Mudine yashigo dakin nasa yaxauna akusa dashi yana tsokanarsa "lallai mutumina
wannan kudi haka nawaye kake rike dasu.?
Gadanga ya murmusa tare da turasu ckn jaka yace "wannan duk salary nane da kuma
wanda Alh yabani nayiwa inna siyayya.
Mudi yakama baki "ah, lallai yakamata gobe lahadi muje kayo musu tsarabar tasu
ko. ?
Gadanga yace "insha Allah kuwa dan har waya nakeso nasiya nakuma saiwa Zainabu na.
Mudi yayi dariya yace "ho! Ali gadanga na zainabu kanaji da zainabun nan fiye da
kowa aduniya ai dole yaxamo nixan kaika kauyen nan dan inga zainabun Aliyu.
Dariya gadanga yayi yace "ai zainabu tayi ga kyau ga nutsuwa ga biyayya ga asali
ga...
"Ka godewa Allah inhar ta hada duk abubuwan nan inka sameta aika gama komi basai ka
kara mata kishiyaba
Gadanaga yace "to aini ko bata mallaki wadannan abubuwan ba banida burin inga
naxauna da mata biyu.
Aranar lahadi kuwa mudi yakaishi store ya lodo wa inna da zainabu tsaraba tayi ta
dubu dari harda tsaleliyar waya kirar TECHNO yasaiwa zainabu da layinta MTN da glo
aCiki me two sim ce keypard
Haj laila ma tabada sako kaiwa inna bakin kifi bushashshe dasu taliya da makaroni
katan katan da wake da klin manya
Tun ahanya yake ganin yaransa amma baiwa kowa maganaba don suma basu zasi gadangan
bane ackn mota don na waje baya ganin naciki saidai naciki yaga nawajen.
Suna dira akofar gidan inna yara suka baibaye motar sun zaci ko Alhajine yazo
Aiko ganin aliyu yasa suka bazama suna fada a ckn unguwa ga gadanga yadawo
Da labarin dawowar gadanga yaxowa zainabu murna taringayi kamar tayi tsintsuwa taje
taganshi taringaji taso zuwa babarta tahana tace mata "kibari yahuta tukunna mana
kokuma kiyi hkrn dare yayi mana ainasan dole zaixo gidan.
Itako inna murna harda tsalle taga gadanganta tahau masa kirarin data saba masa
Suna zaune dukansu kan tabarma mudi nashan kunun tsamiyar da inna ta dama musu inna
nabasu labarirrikan kauyen.
Mudi yacewa gadanga "nifa zantafi sai juma.a xan dawo ko?
Har gidan iya kulu yashiga sukasha hira tana tsokanarsa "gadanga kaganka kuwa walh
kacanxa kamar ba kaiba ka kara haske da kyau .
Da yamma kofar gidansu yacika dam da yaransa sunyi 20 kaf dinsu sunzo ganin uban
gidansu
*Short Story*
*Nabilancy Luv*💘
{Auntyn S&S}
Baifi mintina goma da tsayuwa ba akofar gidan yaron daya aika kiranta ya fito
yasanar masa cewar gatanan zuwa
Fuskarta dauke da murmushi tanata xuba masa fara.a ahakikatan yaga tsagwaron murna
da farin ciki a fuskarta
Lallai zainabunsa na sonsa gashi ta nuna azahiri itanma tayi kewarsa knn
Tace "amma dai ba saukar knn ba? (Saikace bataji lokacin dawowar saba oh!zainabu
kknn ☺
Yace "tun daxun na dawo saida nasamu nutsiwa sannan na nufo masoyiyata da tarin
tsarabarta
Ya mika mata ledoji manya guda biyu da tambarin Shop rite jiki
Ta karba da nishinta dakyar ta iya rikesu tana fadin " kai !kai !! Aliyuna wadannan
kaya duk ni kad'ai ?
Yace "kedai jeki kaisu gida maza ki fito ki karbi abinda xaifi faranta miki rai ma.
Koda ta kai kayan ta fito tasha matukar mamaki dan Aliyunta ya shammaceta na ganin
babbar kyauta dayayi mata na waya kirar techno da layin mtn aciki
Taringa tsalle tana k'ank'ame da kwalin wayar akirjinta tamkar za.a kwace mata ita
Gadanga yaita mata dariya yace "amma dai kya nutsu in nunnuna mk ita ko,
Ya kunna wayar yaita nunnuna mata yadda xatayi control din komi ba wahala atsanake
Dake tanada fahimta kafin yatafi tarike wasu abubuwan ciki harda yanda zata daga
waya dakuma kiran waya da danna handsfree dakuma kunna radio
Ya daga kansa "sosai kuwa harma kinga inna bugo saiki ringa kaiwa inna muyi mgn
ko??
Aiko dai gwaggwon tayita shi masa albarka na ganin abin arxiki da tayi
Dayake shima gadangan yahada waya ahannunsa toching ce ma mekyau kirar geonee
Ya iyata sosai tamkar educated in yana yin amfani da ita duk da dai M.M. Harunan da
yake zuwa tana haska masa kwakwalwa da kaifafa masa basira don yafara jin turanci
da iya rubutu aharshen hausa da english din
Ckn kwanaki da Ali gadanga yayi da zuwa kauyen nasu wata muguwar shakuwa takara
shiga tsakaninsu shida Abun sa
Koda yaushe suna tare ko abokansa da yaransa baya zama dasu sosai
Duk da sun danje yawon farautar da yin gangin amma saiyaji abin ya fara sire masa
duk yajishi afagen daga tamkar wani dan koyo
Hatta inna dama bason futarsa farauta takeba sakashi takeyi agaba suyita hirar
burni yacikata da hirar hajiya laila da Alh.
*********
Ana Gobe zai tafi ne yataho shida yaransa guda biyu zasu je farauta da yamma
Wani yaro dan tsegumi a ckn tsukun kauyen yatari gadanga da sauri ya tsurkunta masa
cewar wai ga Amadi can gun zainabu wanda suke takara tare suna xance da Abun...
Ran gadanga yai matuqar baci jin ckn yaran nasama wani yace dama yataba ganin
Amadin yaje zance gun zainabun kuma tafito gunsa
Ran gadanga yagama baci inzuciya taciyoshi har huci yake yi ajere masu matumar dumi
don nishi kawai yakeyi yana fudda hucin ta baka tamkar yakunna karan sigari haka
farin hayaki ke futowa abakinsa gadanga knn infa ransa yabaci abin tsoro yake
komawa
Azuciye suka rankaya kofar gidansu zainabu yayinda suka taradda Amadi atsaye
yaharde hannayensa yajingina da
Bango
Aifa suna xuwa inda yake babu wani bayani suka haushi da duka da sandunan hannunsa
Ita "yar tahalikar ma batasan yana kofar gidanba tazaci yariga da yatafi tun
mintina goma dasuka wuce daya aiko taxo ita kuma taki futa ashe kaddara ce
tatsaidashi
Murna tayi da hakanma tasan ayanxune zata sami salama na takura matan dayake na
xuwa kofar gidansu
Tasha gaya masa bata sonsa gadanga ne mijin da zata aura saiyace mata bata isaba
soyayya dolene ayita
To yau dai karshen tika tiki tik! Ankawo mata karshen abin
Ita godiya ma tayiwa Allah da gadanga baixo gun yatararta agunba da tabbas da ita
zai had'a
Sosai Amadi ya doku gunsu gadanga har saida aka yayyafa masa ruwa ashe suma yayi
daya farfado aka sami wasu zaratan samari suka sakashi abaro suka turashi aka
kaishi can dan kauyensu dake da makwabtaka danasu gadanga
Shima dayake yanada yara da "yan tawaga sun tsorata sosai ganin yanda akaiwa
ubangidansu tamkar matacce haka suka kwasheshi said'an karamin asibitin garin
Saida yakwana biyu yasami kansa yafara gane mutane abincima abaki ake bashi me ruwa
ruwa dan bakinsa akumbure yk andai canxa masa halitta
Kafatanin yaran sa dasuke futa harkar dabanci da fashi sun kufula sunkuma dauri
damarar xuwa daukarwa ubangidansu fansa agun duk wanda yayi ms hakan koda za.ayi
yakin daxai kifar da kauyen.
Shiko gadanga hankalinsa kwance yama mance da zancen yayi duka balle yazauna yatari
abin don shirin komawa burni yahauyi ma
Ana gobe zai tafi ya dade da zainabu a kofar gidansu suna tadin soyayya
Yana dad'a jaddada mata irin son da yk mata kuma yana kara jan kunnenta akan tarike
ms amana
Yaita kwantar mata da hankali tunda ga waya kamar suna tarene kullum ai zasuyi waya
Mudi ya jinjina kyan Abu tabbas yaga kyawu tsagoransa wanda ya hasko da ace abirni
take rayuwa da anyi kallo tunda ta ninka khalisat biyar a kyawu☺
Ya cika inna da kudi wanda zai isheta amfani kafin yadawo wata uku
Tayita shi masa albarka dan taga canji tattare dashi takuma fara jiyo kamshin
alkairin dazai samu anan gaba addu.a dai bazata daina yi masaba nasamun ci gabansa.
Zainabu ma yashaka mata kudi wanda taita juyasu ahannu dubu goma ne amma tagansu
kamar dubu dari lallai gadanganta yaxama me kudi😄 akauye waxai baka dubu biyar ma
tab to goman ma sadakin wata ne
Aiko dai tun ahanya suketa waya da zainabu har suka shiga kano shiya ringa kiranta
suna shan hira
Gadanga kenan Allah sarki da kasan me zai faru akauyenku da baka taho ba😭
Wayyo......
_Muje zuwa_
*fans ina godiya da nuna kulawarku akan gadanga kuyi hakuri najinsa shiru munyi
biki ne amma yanzu mungama zaku ringa ganin post kullum*
*Short Story*
_ina kuke dimbin masoyan_ *ALI GADANGA*_ina matukar yinku ina kuma jin dadin yanda
kuke nuna doki akan ganin ganin posting dinsa dajin dadin yanda labarin ke tafiya_
_masu yawan tambayar Novels dina to ga sunansu saisu nema a grps nasan zasu samu_
*"yar makafi*
*"yar mace*
*Tauraruwa me wutsiya*
*Tagwaye*
*zaman marina*
*Ranar wanka*
*Gajimare*
*idan kunne yaji*
*Ali gadanga*...
_Jinjina gareku masu loving din novel din Ali gadanga musamman_*Snaanerh*Ummu
Aleesha grp*
*maman gausiya MUSHA KARATU NA YBK* grp
*Nancy MMN USSEEY GRP*
*Nabilancy Luv*💘
(Auntyn S&S)
page 1⃣5⃣
Tabbas gaskiyar '"yan magana da suke cewa RANA DUBU TA BARAWO...rana d'aya jal kuma
ta me kaya
Domin kuwa yau khalisat idonta ya raina fata don dawowarta knn daga asibitin kudi
wanda bata yarda taje asibitin da suke da file ba dan kada agano abinda take xargi
iyayenta suji
Hankalinta ya matuqar tashi najin wai tana da shigar ciki na wata d'aya
Abinda ma yafi daga mata hankali shine na yanda ta kikkira wayar SAFRAZ amma tajita
akashe
"kawata nashiga uku kinji wai ashe cikine dani...wani uban tsaki khairat taja tace
" to saime dan kina da ciki shine xaki damu harda wani yin kuka haba kawata saikace
wata yarinya karama me kk tsoro?
Khalisat taja ajiyar xcy tace "ke! Dady na da momy mana walh zasuyi fada nasani duk
da sunaji dani amma kinsan zasu iya juyamin baya suji sun tsaneni kuma zasuce
nabasu kunya
Khairat tace "aikin banxa ke yanxu saiki bari suji ma? To bari kiji maxa kishirya
kifito da sassafe muje mu xubdashi tunda baiyi kwari ba nifa wancen satin na zubda
na uku gaya mk ne banyiba kuma duk Auwal ne yayi min amma yace zai aureni akwaima
wanda yaki xubuwa akasar nan saida nafita waje kana aka samu yazubu amma naci
wahala momy nace ma ta rakani
Kima cire tsoro aranki walh ai indai iyaye nasonka to baxasuso suganka ackn damuwa
su kara maka damuwar ba kin gayawa SAFRAZ din?
Khalisat tace "nakikkira wayarsa akashe amma na tab'a yi masa hasashen hakan saiya
nuna min rashin damuwarsa
Khairat tace "tura masa sako kisanar masa yayinda duk yakunna wayar zai gani.
Ta tura masa bayanin da likita yasanar mata n tanada shigar ciki na wata guda
Shiru shiru bataji kiransaba bakuma taga sakon saba sai dare bayan magriba ta gwada
kiransa saitaji ta shiga amma har 2 missed call bai daga ba
To me SAFRAZ yake nufi ta tabbata yaga sakonta Allah yasa dai lfy
Yinin ranar ko sallolin azahar da la,asar bata samu damar yiba saboda damuwar da
take ciki ko magribar ma batasan anyiba duk da akwai masallaci ajikin gidan nasu
wanda awani lokacin ma tana jiyo muryar gadanga yana kwada kiran sallah amma dayake
tasan yayi tafiya bata tsaya sauraraba ayau
Shiko gadanga alokacin daya dawo ma gajiya ce ajikinsa bai shiga masallaci yai
kiran sallaba saida aka shiga yayo alwala yatafi agaggauce don bada farali na
sallar magribar
Tana zaune ta xuba uban tagumi taji kara alamar shigowar sako wayarta
Tayi sauri ta daua ta bude ashe kuwa SAFRAZ dinne yaturo mata reply
_Khalisat ina mai baki hkr najin ban d'aga kiran kiba ina cikin wani hali walh
dadyna yamatsamin saina bar k'asar nan agobe gobe kuma ya d'aura min Aure da "yar
k'aninsa ajiya da ita ma zamu tafi egipt kiyafeni ina sonki..._
tashin hankali wanda ba.a sa masa rana yau khalisat tashigeshi domin kuwa hannu
tasaka aka tarafka uban ihu
Aifa jin shigowar wani sakon yasa tayi shiru da sauri ta rarimi wayar ta bude again
SAFRAZ dinne
_ciki kuma inkinga zaki zubar to ki zubar din kawai inkuma kinga zaki barshi to kya
sanar dani dan insan jinina na duniya dan ina sonshi ki huta lfy sai wataran_
wani uban ashar ta kurma tareda cilli da wayar gefe ta dafe kanta tana kuka da
idonta wanda ta mance rabon taxubda hawaye tabbas tashiga rudani ya zatayi da son
da take masa?
Tadauki wayar asukwane donta kira khairat tasanar mata amma sai wayar taki kunnuwa
Aguje ta futo daga dakin nata nufinta ta tafi gidansu khairat din donsu samu mafita
ayau
Adaidai lokacin da tafito daga sashin nata afirgice shikuma gadanga yadawo daga
masallaci
Takusa bangajeshi sauran kiris su gogi juna ya matsa da sauri yabata hanya
Saidai yalura atashin hankali take don kuka ma kawai take tana fadin tashiga uku
Yaja yatsaya yaga tashiga mota ta tasheta ta matsa hon da karfinta ta fizgi motar
tafice agidan
Sauran k'iris tabuge baba me gadi aget wajen bude mata get d'in banda yai tsalle
gefe guda
gadanga yalura da ita da alama akwai babbar matsala jikinsa yabashi ba qalau ba
kawai saiyaji gara yabita yaga ko lfy
Yabi bayanta
Sunyi nisa akan titin saiya hango wasu motoci guda biyu masu glass da tintek sun
shige gabansa aguje suna masa fitila
Abin ya daure masa kai tosukuma wadannan suwaye haka dasuka fishi sauri da alama
suma suna ckn tashin hankalin
Ganin sun dauke hanya kuma sunbi hanyar da khalisat din tabi yasa shima yarufa musu
baya amma sun dan rage gudun
Abin mamaki babu yawaitar abin hawa da mutane a arear din da suka biyo sun sauka
atiti
Can yahango sun saka motar khalisat atsakiya sun rikitata da horn
Motar gabanta ta tsaya itama dole taja tatsaya ta waiga taga motar bayanta itama ta
tsaya anma jikinta yabata wani abun dan motar bayanta iri dayace data gabanta
Sai gani tayi maxa biyu sunfito amotar gabanta da bakaken kaya harda bindigu
ahannunsu
Hantar cknta ta kada take tsoro yashigeta tahau kiran sunan Allah aranta
Suka nuno mata bakin bindiga suna fadin ta bude maxa ta fito
Gadanga yayi saurin tada motarsa yabisu dasauri ganin abinda ke faruwa daga nesan
daya tsaya kada dai "yan fashine ko masu garkuwa
Aikafin ya isa harsun tashi motarsu sunyi gaba aguje bai cin musuba tunda sun
gwanance a iya tuki
k'iri-k'iri yanaji yana gani suka take masa suka b'ace baya hangosu yatsaya da
motar tasa ya buga kansa ajikin sitiyarin motar tashin hankali yanxu yazaiyi ?su
waye wadannan da suka dauke khalisat? Yaxaice da Alhaji knn?
Duk baida amsoshin tambayar mafita guda kawai yakoma gida baibi takan motar da
khalisat tafito ack ba tunda hannu daya baya daukar jinga taura biyu bata taunuwa
dole saidai indawowa xaiyi daga baya yadauketa gashi baida nambar ilu awayarsa
yakira mudi kuma bai dagaba ballantana yace masa yabiyo bayansa a abin hawa
Yana xuwa gida ya faka motar a farking space yashiga ckn gidan afurgice Anyi sa.a
dadyn yadawo suna falon shida momy
Sun furgita suma ganin gadangan yashigo afurgice ckn damuwa yazayyane musu abinda
yafaru
Kuka momy tahauyi tana fadin "nashiga uku sun d'auke min "ya d'aya tilo Allah
katallafa mana ka karemin "yata ya ubangiji
Dady kuwa innalillahi kawai yake cewa yakira kwamisanan yan sanda yasanar masa yace
maza abaxa jami,an tsaro ahanyoyi yabada kwatancen kalar motocin da nambar motocin
kamar yadda gadanga yasanar masa
Gadanga ckn sanyin rai yace "momy ba kuka zakiyiba alwala zakije kiyo kisallah ki
gayawa ubangiji
Dady yace "maxa Aliyu muje masallaci inmunyi sallar ishsha,i inbada sadaka akwana
ana tayani addu,a
Suka rankaya masallaci atare kaf mutan gidan aranar kowa yaji abinda yafaru har yan
unguwa anshiga tashin hankali
Yanda gadanga yaga rana haka yaga dare don bai runtsaba gizo abin yaringa masa take
yaringajin tausayin iyayen khalisat din hatta ita kanta khalisat din tausayin tane
yamanne masa aransa ko wane hali take ciki?
Tun dayayi sallar asuba baifito dg masallacin ba yanata lazimi yana addu,o,i
gabansa yanata faduwa yanaji ajikinsa akwai wani abun tabbas da zai faru dashi
yaita hailala yana salatin annabi
Wajen karfe goman safe yakoma ckn gida jikinsa asanyaye ganin polisawa sunzo gun
Alh sun kawo masa bayani kan cewa bawani bayani naganin yan ta,addan
Amma sunxo da bayani kan cewa kwamishina yabada umarni akan cewa sutaho da
gadanga don ya masa tambayoyi domin suna xarginsa ko da sa hannunsa aciki
Alh bai amince ba yace musu ya yadda da Aliyu baxaici amanarsa ba yace musu sukoma
suce da kwamishina yature wannan maganar gadanga dan,uwan sane kada akara dora
zargi akansa
Koda suka tafi Alh ne yadafa kafadar gadanga dayake xubda hawaye yace "kada kadamu
Aliyu babu wanda zaiyadda da zarginsu na yadda dakai Allah zaibayyana su da karfin
addu.a zata dawo itama.
Koda yakoma dakinsa ma kasa nutsuwa yayi wato shiyasa yaji gabansa keta bugawa
abinda zaisameshi knn naqalen sharrin yan sanda lallai Alh na qaunarsa tunda har ya
yarda dashi yakamata yayi wani abu akai yataimaka masa don "yarsa ta dawo to wace
hanyar?
Wayarsa ta katse masa zuxxurfan tunanin daya shiga kafin yadauka harta katse
Yana duba wayar yaga ashe Zainabun sace har 15 missed call
Kai tsaye yana kira daya yaji ta d'aga tana kuka tana fad'in " wayyo Allah gadanga
munshiga uku kaxo sun kashe mana inna....
Ya mike tsaye da sauri afusace yace da karfi "wacce innar suka kashe?
"Suwaye suka kashe min inna? Mesukai mata ?me tayi musu?
Zainabu ckn kuka tace "yaran Amadi ne wai sukazo d'aukar fansa wayyo gadanga inna
ta mutu tabarmu......
_muje zuwa_
*Short Story*
*Nabilancy Luv*💘
(Auntyn S&S)
Page 1⃣6⃣
Adaidai lokacin daya fad'ine mudi yashigo d'akin da sauri don yakawo masa labarin
wad'anda sukai kidnapping din khalisat sunyo waya suna bukatar mak'udan kud'ad'e.
Sai farkawa yayi yaganshi ajikin mudi fuskarsa ajike da ruwa da alamar ruwa aka
shafa masa
Yaja ajiyar doguwar zuciya wanda saida yaji kirjinsa ya motsa yaji wani nauyi
idonsa yayi
Dakyar ya iya bude idanuwa yatashi zaune saida yadau mintina yadawo hayyacinsa ashe
momy laila da Alh suma suna dakin kusa dashi
Dasauri Alhajin yajanyoshi jikinsa yana fadin "sannu Aliyu ka farfado,sannu meya
faru dakai?
Hjy laila ma tahau antayo masa tambayoyi '"Aliyu me akai maka harka fadi ka
kasuma?
Wasu hawaye ne masu quna suka xubo masa lallai inhar da gaskene abunda zainabu
tafada to za.ayi tashin hankali kuwa dan baxai bar wanda yakashe masa inna da raiba
kakar dabaida kamarta wacce ta maye masa gurbin iyaye baisan maraiciba baisan
wahalaba itace kominshi tun yarinta tayi aikatau sbd taga yaci yasha yasa sutura
itace surfau wankau da saide saide na kayan miya danye da bushashshe da kuma saida
itace saida yagirma tarage yin wahala
Hankalinsa ya dugun xuma ransa yabaci idanunsa sukai jajir kwanjinsa suka tashi
suka murde kumatunsa yahau rawa lebensa yahau motsi duk ckn bacin raine
Dady yadafashi yana rarrashinsa don yafara fahimtar wani abun atattare dashi yasan
akwai matsala
Gadanga yaja wata sassanyar ajiyar xuciya yana hawaye yace "dady sun cuce ni sunmin
illa sunkuma yimin gibi arayuwata...yafashe da kuka me tsima rai
"Sun kashe min inna yanzu aka bugo aka gayamin walh baxan barsuba.
Zumbur dady ya mike tsaye yadafe kai yana fadun "innalillahi wa inna ilaihir
rajiun.
Momy ma rikicewa tayi harda hawayenta hannunta aka tana fadin "lahaula wala quwwata
illaillah...
Mudi ma hannu yasaka aka yana fadin "wayyo Allah inna ta mutu? suwaye suka kasheta?
Aliyu yahau kuka yana basu labarin da zainabu tabashi wai daukan fansa sukazo yi
masa shine suka kashe inna.
Dady yace "Amma kosu waye saimun dau mataki akansu maxa shirya muje kauyen.
Ba wani shiri da Gadanga xaiyi sai mikewa yayi kawai yai waje suka mara masa baya
Allah sarki dady yamance damuwar ma dayake ciki na rashin d'iyarsa wanda ahalin
yanzuma waya sukayo kancewar inbai basu naira miliyan ukuba to zasu kashe masa
"ya.
Dukansu suka tafi har mudi da ilu a mota daya banda momy
Don ita zuciyarta akarye take bazata iya xuwa taga gawar innarba gashi dama ba lfy
ce ta isheraba tunda aka rasa khalisat take fama da rashin lfy
********
Koda suka isa kauyen ba.a kai taba shi ake jira amma anhadata
Sosai yan kauyen suka shiga tashin hankali ancika kofar gidan inna makil kowa yai
jigun jigun gefe guda yaran gadanga ne sunata kuka
Tafi kowa shiga tashin hankali kuka kawai tana kiran sunan Allah
Mudi na rike da hannun gadanga wanda ke xubda hawaye dukda cike yake da jarumta
amma yakasa tsaida hawayen
Ya dade tsaye akan gawar inna yana kuka ana hanashi don bata bukatar kukansa sai
addu.arsa
Zainabu na can kurya tana jiyo sautin kukan Gadanga itanma kukan take sosai
gwaggonta na kusa da ita
Gadanga yai matuqar jarumta da akaje makabarta don kukan sa daukewa yayi shiya rike
kafafunta aka shigarta kabari
Saida aka dawo gida suna xaxxaune akan tarbarmi suna karbar gaisuwane yaji hawayen
yadawo masa natuno inna dayanda take masa kirari inya dawo daga farauta ko gangi...
Cau!cau!!inna Allah dai yabiya.abinda yake ce mata knn intana masa wadannan
dad'ad'an kirarin baisan suna masa dad'iba sai yau
Shikenan yarasa me faranta masa knn yanzu wazai ringa masa kirarin nan masu dadi!?
Yaso ya kebe da yaransa donjin mafita ammaba dama gun acike yake dam da al,umma
harda na makwabtaka da kauyen sunji labari sun zoxxo
Ashe Alh yayiwa yan sanda waya aranar sadakar uku saigasu motoci biyu sukai
shammata a kauyensu Amadi aka dank'o yaran amadin har amadin da baida ishashshiyar
lfy tunda shiya turasu su kashe Ali gadanga sukuma suka kashe masa inna
Mutane na kallonsu ana musu tofin alatsine akai birni dasu don mikasu ahannun
hukuma aimusu hukunci daidai da abinda sukai
Dady yasan inba hakan yayiba to tabbas za.ayi barna yasan gadanga zai iya komi
shikuma bayason azo ayi danasanin barna gara yasa hukuma aciki
Ranar sadakar uku Alh yatara yaran gadanga yai musu nasiha akan sudaina yin gangi
su zauna agidajensu sukama sana.a yafi musu mutunci yakumace subar mgnr kada su
tayar don zasu girbi abinda suka shuka
Yana shirin yi musu sallama yakoma birni aka bugo masa waya da bakuwar namba
Wadanda suka dauke masa khalisat ne ba nambar da suka kirashi kwanaki bace da suka
bukaci kudi sun rufe ta wannan etisalat ce
Da kakkausar murya suke masa worning da tuni kan cewa inhar bai turo kudin nan da
sati gudaba to kada yakara tunanin yanada "ya aduniya zasu sheketa
Tace "dady dan Allah katuro musu kudin kosa sakeni walh zasu kasheni yauma sun
kashe wasu awahalce nake dady....tsit suka katseta
Yadaina jin yar tasa sai muryar namiji yaji yana fadin "yaushe zaka kawo mana
kudin?
Dady yace a gobe ko yau inkun fadi inda zan kawo muku.
Gadanga ne ya warce wayar ahannun Alhajin don yaji komi ransa abace yahau fadin
"waiku su waye ne marasa mutunci.!!!
Aka sheke da muguwar dariya akace masa "yan garkuwa ne wadanda basu san raini ka
iya bakinka don inkai mana shishshigi zamu kasheta kudaina jinmu
Jikin gadanga yahau tsima "metayi muku kada ku kasheta ko nawane za.a baku.
"Zamu fada muku gurin dakuma sharadai masu tsanani don inhar kuaka karyasu to baku
ba "yarku.
Diffff!yaji sun kashe wayar "yan rainin wayone na karshe sunkuma iya yawo da
hankali.
Gadanga yaita fadin "hello!hello
Dayaji shiru yaduba yaga ashe sun kashe saiya mikawa Alh wayar asanyaye yana hawaye
Alh yakarbi wayar yadafa shi yana fadin "kada ka damu Aliyu haka Allah yakaddaro
mana jarabtace abinda yafi kawai mubisu ahankali har Allah yakawo rabda zasu bamu
itan zankuma tanadi kudin nasu don jiran kiransu
"To amma Alh kasanar da hukuma aduk lokacin da suka baka kada ayi abu aboye
atabbatar ankamasu
Yatafi ko mahaifiyarsa bai gayawa halin da yake cikiba kada hankalinta yatashi
tunda tana ckn alhinin inna
Gadanga abunne yahadar masa amma harga Allah yaso yabi Alh ayi komi yananan domin
ashirye yake dayai gaba da gaba da "yan garkuwan nan.
Tunanin khalisat yarungayi yana tausayinta don yasan tafuta hayyacinta kuma kamar
horo sukai mata hakan zaisa tarage wasu halayyar tata marasa kyau
Ya qudurta aransa ana sadakar bakwai zai koma birni cikin shirin kota kwana don
dole zaije ceton khalisat shiya kamata yakai musu kudin don ya isar da qudurinsa
akansu......
_Muje zuwa_
*Nabilancy Luv*💘
(Auntyn S&S)
&
*Ummi Aisha*(Dan Asali)
Page 1⃣7⃣
ANA gobe sadakar bakwan inna mallam baffale wani dan,uwan innar da suke "yan maxa
zir daga nijar yazo suka keb'e shida kawun Zainabu agidan iya zulai suka tattauna
akan daurin Auren da suke da shirinyi da safe in anyi addu.ar bakwai su daura Auran
gadanga da zainabun wanda ko gadangan baisan bikin da akeyiba
Suka gama shirya komai iya kulu ce tabada kudi dubu ashirin da d'anta yabata kafin
yatafi amatsayin sadakin gadanga baffale yaita gode mata tace "ai ba komai gadanga
nima ai nawane balle yanzu rikonsa na hannun d'ana
Kawun zainabu yace su sanarwa gadangan da zarar andaura yadauketa kawai yatafi da
ita birni
Washe gari kuwa ana yin addu,ar bakwai aka hau daurin aure tun mutane basu watseba
dama adaren baffale yaje yasiyo goro da alawa
Gadanga yasha mamaki najin andaura masa aure batare daya saniba
Yarasa bakin magana yai shiru kansa yadaure yama rasa mezaice yashiga wani yanayi
shin farin ciki xaiyi ko bakin ciki?
Yanaji yana gani aka daura masa Aure akan sadaki naira dubu 20 lakadan ba ajalanba.
Akaita tayashi murna ana masa Allah yasanya Alkairi yanata washe baki yana amsawa
Yaringa jinsa wani iri waiyau yazama ango,angonma ga wacce yake so,
Saida aka watse yahau farin ciki wai zainabu taxama matarsa to yanzu yakenan zaiyi
baida kudaden da xaiyi mata hidimar aure gashi gidan innar babu wani kyakykyawan
gyara balle ya ajiyeta ack
Yana zaune shikadai ackn gidan yana tunanin inna yana ckn kadaicinta yasan rashin
tane yasa akai shawarar yi masa aure don su faranta masa.
Iya tazauna akusa dashi haka shima baffalen zaman yayi yana ce masa "gadanga kukan
me kake kaxauna kana hawaye kamar karamin yaro.
Baimasan hawayen naxuba ba saida baffale yafada yai saurin saka hannu yafara gogewa
yana kirkiro murmushin dole
Iya kulu ta gyara xama tace "Allah dai yasa ba karanbanin da mukai maka na aure ba
shawara bane yabak'anta maka rai har kake xubda hawaye ba?
Gadanga yace "a,a haba dai iya kada kiyi wannan tunanin sam banji haushinkuba komai
kukai akaina daidai ne baxaku taba yin abinda xai cutar niba kumafa iyaye ne aguna
ko bana son xainabu baxanji haushin kuba balle ina sonta godiya ma yakamata nayi
muku dan nasan manufar ku danku faranta minne.
Baffale yace "wannan haka yake gadanga nasanka da hankali da bin nagaba dakai kaga
wannan tsohuwar ka gode mata itace ta kawo wannan shawarar mekyau takuma bada
sadakin da aka baiwa zainabu na auranka munkuma yi hakanne sbd mu maye maka zuciya
da farin ciki don munsan zcyrka na cike da bakin cikin rashin kakarka
Iya kulu ta cafe da cewa "gadanga inaso kadaukeni tamkar yadda inna take agunka
banaso kabar kauyennnan kwata kwata inaso inka tafi karinga waigomu nasan inba
zainabun aka bakaba inhar kayi aure a birni baixama lallai muringa ganinka akan
kariba yanxu kuwa nasan koka tafi da zainabu to dole wataran xaka ringa xuwar mana.
Gadanga yai murmushi yace "to ai iya baxan tafi da xainabu yanxun ba saidai nan
gaba inna sama mata matsuguni tukunna.
Iya kulu tace "akan me , a,a katafi da matarka kawai don nasan baxaka rasa dakuna
agidan Alh ba
Akwai qudiri aran gadanga shiyasa yakeso yaxille tafiya da xainabu don so yake ya
gina kansa yakuma sami gidan kansa ba karereba gashi inya koma yanxun yanaso ya
shirya futa artabu da "yan garkuwa
Duk yadda su iya kulu suka so yatafi da zainabu birni gadanga yaki yai musu dabaru
kancewa saiwani xuwan in yayi zaije yayi mata shiryeye
Sannan ne suka hkr suka barshi ammafa suntausaya masa don harya fad'a
Adaren yaxiyarci amaryarsa xainabu wacce tunda taji andaura musu aure take ckn
farin ciki d'okinta kawai angonta yaxo taganshi
Aiko dai dayaxo din tamkar ta rumgumeshi taringaji gashi dai kunyarsa takeji gashi
kuma babu fuska gun gadangan ba yabo ba fallasa tunda inna tarasu ma basu kebe ba
tasan yana ckn alhini shiyasa tayi masa uxuri takuma tausaya masa ganin yarame
Basuyi wani hirar arxikiba kamar yadda suka saba inyazo ita tafara masa mgnr tafiya
ma
"Yaushe xaka koma birni.?
Saita kasa amma tayi addu.a ckn ranta Allahv yasa yace mata hakan
"Ki kama kanki banaso kiringa futa koina infutar taxama dole ki kirani awaya
kigayamin tunda yanxu kinxama matar aure dole ki kiyaye inna tafi baxan dade ba xan
dawo intafi dake
Yakawo dubu biyar yabata (Alh yabashi kudi kafin yatafi yakuma sami kudin sadaka.)
Tayi godiya kamar tafashe da kuka suka rabu ckn shaukin juna
Yaso yatafi da itan amma ba dama saiyayi shiri gashi yanajin wani abu atare da ita
Itanma tashiga wani shauki dabata taba jinsaba mijinta xaiyi nisa da ita.
******
Ilu ne yaxo daukansa tun sassafe
Yayi sallama da kowa yatafi sungaisa da ilu dayake ganin girman gadangan yanzu
Ilu akwai surutu yaita zayyanewa gadanga halin da ake ciki na labarin khalisat
Ilu yace "kudin suna hanun sipeta musa jami,in nan dan tsamirmiri me kama da
k'olawa sunce kada afadawa jami,an tsaro inko aka taho da hukuma to za.a rasa
khalisa
Gadanga yace "inkasan gidan sipeta musan ka kaini can, nixan karbi kudin nakai musu
amma kada kagaya kowa nadawo akwai abinda nakeso nacimma karike wannan alqawarin.
Ilu yahau gyada kansa "to...to.,angama ranka ya dade.(ilu nashakkar gadanga don
yaga bayason wargi yakuma ga yadda akai maganin uwar gidansu khalisat agabansu
yakuma xauna lfy.)
Koda suka shigo kano kai tsaye gidan inspector musa yakaishi kai tsaye
Koda suka kebe gadanga yabayyana masa qudirinsa nason yabashi kudin yanada shirinsa
akansu zaikuma karbo khalisat ckn kwaciyar hankali
Yanayin gadangan ne yagamsar da insp. Amma yatambayeshi cewar "amma bakaga zaka iya
fuskantar matsala koka taki wani abunne?
Gadanga yace "nayo shirina tsaf daga kauyen mu nasha maganin bindiga da wuka babu
abinda suka isa suimin ashirye nake dana kara da "yan boko haram ma kada kaji komi
inspector saina danko maka duk wanda yashigo hannu na aranar acknsu.
Insp. Yakarewa gadanga kallo yana gyada kai don yaga k'irar karfi atattare dashi ga
kamannin "yan maxa ma atare dashi to amma duk da hakan saiya bashi tsaron sirri
baxai bari yaje shikad'ai ba sbd gudun tab'aci......
_Muje zuwa_………
*Short Story*
*Nabilancy Luv*💘
( Auntyn S&S)
Page
1⃣9⃣
Kowa saida yakadu dajin wannan batu na mutumin hatta likita saida ya mamakantu
lallai duniya abin tsoro ce wanda kaba amanna shike neman halakarka
Gadanga ma yaji mamaki tunda yasan Safraz din abokin sheke ayarta ne lallai zai
gane kuransa dan ba.a barshiba
Hajiya laila ta hau gyada kai tana masa allah ya isa ackn ranta
Alh kuwa kasa magana yayi don takaici nacin amanar nan me ban al,ajab
Mutumin yahau kwana kwana yanaso yabada bayanan bogi dan asake amma abin yaci tura
domin duk unguwar daya ambata take insp.musa zai hau tambayar sa gidan waza.ace
domin shi din haifaffen kd ne aikine yakawoshi kano yasan koina akaduna
Ganin zai raina musu hankali yasa suka fara dukanshi ba tausayi duk da yana gadon
asibiti
Dady yace "kubarshi hakan, kuma tunda yafada kada abarshi atafi ashi kawai yaxama
jagora yafi.
Hakan kuwa akayi dama don sunga yana kwance agadon Asibitine shiyasa basui niyyar
xuwa dashiba amma dasuka gano nufinsa na sanfewa dole dai aka tusa shi gaba aka
nufi kd unguwar T/wada dashi
Koda suka isa kaduna amotarsu ta aiki tareda jami.ai hudu da insp.musa ack suspect
din yana baya atsakiyarsu yana daure da ankwa yai tsuru tsuru dashi
Da yammaci suka isa gdn mahaifin safraz ya dawo gidansa shida baki suna farfajiya
ckn wata yar rumfa suna tattaunawa sai ganin motar yan sanda sukayi ta shigo har
ckn gidan
Horn sukaita matsawa me gadi dole yabude suka shiga basubi takansaba dayake dan
filanin rigane atsorace yabude musu
Sukai faking kuda da rumfar dasu Alh Zakari suke suka fito sudukansu banda suspect
din da jami,i daya dake tsaronsa
Alh zakari mahaifin safraz yayi mamakin ganin jami,ai har ckn gidansa take jikinsa
yabashi da alamar Safraz ne yaja masa magana yau kwana biyar baisakashi a idoba
yabar gidan yana hkr da halin safraz gashi shi kadai Allah yabashi yakuma
jarrabeshi da mugun hali yana basu wahala ainun suna matukar nuna masa so kuma
Azaton Alhn ma ko duka yaiwa mutumin ckn motar dayagani kusada dan sanda fuska a
kumbure
Ya kadu matuqa dajin abinda yakawo su insp. Domin bai zaci abin yakai nan ba
Dan sa safraz yazama dan garkuwa? To yaushe yazama hakan? Meya nema yarasa duk
arxikinsa bai nema gunsa ba zai nema ahanyar haram tabbas mugayen abokaine suka
sashi ahanyar hakan.
Alh zakari yagoge kwallar takaicin data xubo masa yadubi insp musa yace "ayau nayi
tir da haihuwar safraz banxaci zai iyayin wannan muguwar ta.adarba duk da ina
tsammanin mugayen abokai ne zasu sakashi yin hakan tunda nakaishi kasar waje yai
karatu shikenan kyawawan halayensa suka canxa ayanzu hakan zaman da kukaga munyi da
wadannan abokan nawa zancensa muke aure xamu kulla atsakaninsa da yar abokina duk
dan yagyara halinsa yau kwana biyar bansashi a idoba bansan kuma inda xance muku
xa.a sameshiba
Insp. Musa yace "to mudai kam xuwan da mukai baxamu tafi ba sai dashi kokuma kamaye
gurbinsa har saiyashiga hannunmu kana musake ka.
Take abokan Alh sukahau fada akan baxa.ayi hakan ba sunata cacar baki suna fadin
akan me zaku yarfatashi kunsan matsayinsa kuwa walh ba,za ayi haka muna kalloba……
Alh zakari yadaga musu hannu yace "kada kufadi hakan komi da kuka gani yafaru
akaina kaddarata tace kuma aidama dan kuka shike jawa uwarsa jifa kumuje kawai.
Yamike xaibisu knn yaji ankurma ihu ana kuka
Hjy jamila knn matarsa mahaifiyar safrax cewa take "walh Alh baxaka tafi kabarni da
tunani b saidai in ahada dani atafi
Abokansa suka hanata tana kokarin shiga motar tana kuka hkr suke bata amma ina
saida ta sami mazauni dama da hijab dinta ajiki taji komi akunnenta dama taga
shigowar motar yan sandan
Alh zakari yace "kubarta muje taren kunga dole labari zaije masa cewar iyayansa
duka suna hannu hakan zaibashi damar mika kai inhar yana sonmu kamar yadda muka
soshi .
Abokan Alh zakari sunji ba dadi aransu sosai su ukune manyan aminansa na arxiki
aiko dai sai suka baxa jami.an tsaro da "yan gari neman safraz
To ashe mutuminku safraz yana wata mabuya aboye yanada labarin iyayen Khalisat
sunji komi ahalin yanxu tunda sunkama yaronsa yasan dole inyaji wuya zaifadi
gaskiya dole tasa ya buya ko gidan iyayansa baya xuwa
yana shirye shiryen barin kasar knn yakunna television yaga ana nemansa ruwa
ajallo daya mika kansa zuwa state C.I.D kano don ankama iyayansa adalilin anxo
kamashi ba.a sameshiba
Ya girgixa ainun harda xu da hawaye take yakunna wayarsa daya dade da kasheta
Take yaringa ganin sakonnin bayanin kama iyayansa nashigo daga abokansa "yan arear
Bashiri tafiya abroad ta fasu yanufi kano don yamika kansa sbd yana son iyayansa
ainun bakuma zaiso sukunyata ba
Jami,an tsaron basuyi mamakin ganin saba don dama sunsan hakan xai iya faruwa
ansha yin hakan kuma
Koda aka damkeshi aka turashi sell sai aka fito da iyayansa
Hjy jamila kuka tayi tayi tana cewa "kacuci kanka safrax ga abinda rashin jin mgnr
iyaye yaja maka
Shiko uban cewa yayi "kaje munyafe ka kada kasaka ran zan fito dakai dakudina sbd
kacutar dani bantaba shiga sell ba sai adalilinka
Haka yanaji yana gani suka tafi
*****
Koda khalisat ta samu sauki tafarko hjyrta tafara gani akusa da ita
Hjy takama hannunta tana fadin "sannu khalisat Allah yasaka kinji wannan abu
dasukai miki baxamu yafeba sun miki ciki gashi har Allah yasa yabare Sannu mungode
Allah ma da kk kubuto dg garesu amma da kokarin Aliyu komi yazo mana ckn sauki har
muka gane wanda yai xamo silar da aka saceki.
Arikicd ta tashi xaune tace da momyn "waye momy ?plz waye yasa akaimin hakan?
Hjy laila tace "wanda aka kama daya dg cikin yan garkuwar yace saurayinki Safrax ne
……
Ta dafe kirji idonta awaje tace "innalillahi wainna ilaihir rajiun. Safraz kuma
momy,?shida yace min zaibar kasar zaikoma karsa waje auren dole za.ai masa da "yar
kanin babansa amma Allah ya isana safraz aibansan macuci bane sai yau Amma nayi
nadama yacu eni yaimin ciki gashi har.... 🤭 sub'utar baki tayi tayi saurin yin
shiru tana kuka
Momy ta kura mata ido tace "wato dama ashe ma kina makale da cikinsa baki gaya min
ba amatsayina na uwarki amma kinbani mamaki khalisat to ai gashinan yakaiki yabaro
don ma mun samu yaxube da bamusan yazamui da abin kunyarba don kin san dole
asirinmu yatonu dabai xube ba tunda in yana hannu yazamui da cikinsa
Kukan da khalisat keta sharbawa na nadama yasa taja baki momyn tayi shiru don
bataso tasata adamuwa
Nadama sosai tayi ayau taringaji inama batasan safrax ba gashi yaso yazama ajalinta
yaci amanarta
Ta lumshe idonta tana tuno artabun da gadanga yayi da yan garkuwar nan tabbas
yagama burgeta ashe haka yake da karfi shine yazo cetonta tabbas baxata mance a
alkairin saba taji wani qaunarsa aranta duk tsanar datayi masa taji tagushe fuskar
gadanga taringa mata gixo lallai naka sai naka yau gashi gadanga yai mata rana
inama zai maye mata gurbin safrax...
Khairat na dagawa tahau tambayar momyn ko gaisawa basuiba "momy ya labarin khalisat
dafatan sun basa ita.?
Momy tace "inkina gia kitaho yanzu Nabnur hospital muna can ansamu nasarar karbo ta
kizo yanzu maza.
Ckn gaggawa khairat tahau shiri bata tsaya jiran dreba yakawata bama ta tuko kanta
sai gata a ckn asibitin ta faka a farking space takira momy donta fada mata lambar
dakin da suke momyn tace mata ta taho lambu tasameta tana can
Can bayan dakunan dake ckn asibitin aka ajiye kujeru ckn wani dan lambu nashakatawa
Data iso lambun tahango momy tanufota da sauri tagaidata har kasa
Khairat
Momy tazayyane mata komi tana kuka tana cewa "bansan khalisat lalata take yi inta
futaba saiyau data furta min cewa ckn daya zube na safrax ne dole zan damu najin
haka khairat amatsayina na uwarta zanso inga tayi aure to gashi ta lalata rayuwarta
ta bata lokacinta abanza gun dan iska mayaudari yanzu waye xai aureta alhalin tana
wulakanta samari acan baya gashi kuma tagama xubda mutumcinta?.
Khairat ta dafe kanta "oh my god! Momy kiyi hkr komi zaizo ckn sauki wannan tamkar
wata kaddarar tace haka Allah yarubuta dole sai hkn yafaru kada kisa abin aranki
yadameki plz momy addu,a zakiyi mata akan Allah yafuto mata da mjn aure kawai amma
yanzu na tabbata itama tana ckn damuwa olx mom.
Hjy laila tace "ba damuwa nagode khairat zantayata da addu.ar kema kuma inaso
kiringa bata shawar me kyau dan Allah kuzama nutsatstsu kuyi aure kafin mutuwarku
ta riskeku agidan iyaye aure shine mutuncin "ya mace da kuma ci gabanta arayuwa.
Cewar khairat.
*Short Story*
*Nabilancy Luv*💘
*Dedicated to Batul mamman & Ummi Aisha*
Page 1⃣8⃣
Ali gadanga baiyi rintsaba yana kan dadduma yanata yin nafilfili yana addu.a akan
Allah yadorashi akan wadannan muggan mutanen da xai tunkara
Dayake sunyi dasu ckn dare karfe biyu su hadu awata mahada da babu gine gine a
arear
Ta wayar inspector suke communicating sbd yaboye matsayinsa na ma,aikaci yace musu
shi kanin mahaifin yarinyar ne ,don sun kafa dokar kada asake asanarwa jami,an
tsaro inhar suna son "yar su to dole abi dokarsu.
Baida nufin yaje da kowa amma gadanga ya karya masa qudiri yace lallai shi xaije
musu da kudin yakarbo khalisat sbd wata manufarsa kuma yace kada yagayawa Alh dan
baxai barshiba
Insp. Musa yagargadeshi akan ya kiyaye inyaje garesu yabi dokarsu da kaidojin da
zasu kafa masa kfin su hadu
Tare suka tafi mahadar ya ajiyeshi tare da bashi jakar kudaden shikuma yabuya a
wata mabuya
Gadanga yafi minti goma atsaye ckn duhun daren kan wani dutse yadauko wayar
insp.dake aljihunsa yaduba yaga biyu da kwata na dare
Sosai sunyi targeting din komi shida inspecta kan cewa zai taimaka masa da kawo
hari garesu na harbi inyaji wata hatsaniyar.
Yadauka tareda karawa akunne "dafatan kazo gurin da mukace mk kuma dafatan kai
kadai kaxo?
Subiyune jal maxane daya yaiwa khalisat kyakykyawan rikon da baxata kufceba ko
motsi takasayi ahannunsa k'akk'arfane na gaske amma baikai gadanga kwanjiba
Wanda ke rike da khalisat ya dubi dan,uwan nasa yace "maxa jeka yabaka kudin inyaso
mubashi ita.
Gadanga ya gyara tsaiwa tareda ajiye kudin akasa mutumin naxuwa yaduka xai dauki
kudin knn yaji muguwar shaqa awuyansa saida gadanga yakaishi kasa yabuga masa
hannunsa aka take mutumin yafadi sumamme
Wanda ke rike da khalisat ya harxuka ya shake wuyan Khalisat tahau kakari yakai
mata naushi ack
"Gara nakasheta tunda baka son yar,uwarka gashi ka fanshi ran dan,uwana anata zan
kasheta kuma natafi da kudin kaima kuma baxan barkaba.
Gadanga yace "kai karamin dan,iska matsoracin maxa kabarta kaxo gareni inba tsoro
ba...kufula yayi yai wurgi da khalisat gefe yayo kan gadanga
Ji kake k'ummmm!!!
Tafada kan wani dutse me tsini take goshinta yabugu yafashe yahau xubda jini haka
cikinta ma yabugu nan take abinda ke cikinta yafito yabare cikin jini yahau
kwaranyowa
Tafita hayyacinta amma ihun data saki kafin takai kasa yakai kunnen insp.musa take
yafito dg abuya yanufo gunsu gadanga
Yana xuwa yaga suna artabu sai caskalen dan bidda suke gadanga nakai masa naushi
shima mutumin yana kawowa gadanga shikuma gadanga na kaucewa
Insp.yasaki harbi sama take mutumin yagigice yatsorata ainun ya ari ta kare yanausa
ckn daji
Yahau cewa insp. "Wayyo inspecta ta mutu kaga bata motsi yaxamuyi ..
Insp. Yatabata yaduba sosai yace "da ranta bata mutuba sata amota muwuce da ita
asibitin dasuke da file acan.
Gadanga yace" to amma kayi kokarin daukar motar mutanen nan gatacan kasaka wancan
atafi dashi asibitin da alama suma yayi kaga inya farfado sai ayi bincike akansu.
Insp. Yadauko jakar kudaden yasaka amotar mutanen yakuma janyo mutumin nn dake sume
akasa yasashi ckn motar tasu 😅 yaji dukan maza
Amotar dasukaxo ta insp. Yasaka khalisat yaja yanufi NabNur special hospital dayake
yajejje sau uku duba hjy laila data taba kwanciya
Saida sukaje asibitin aka basu gado sannan inspecta yakarbi wayarsa gun gadanga ya
kira Alh yasanar masa duk yadda akayi amma insp yace yakwantar da hankalinsa kada
yataho ackn tsohon daren nan ciwon na khalisat dinma kadanne likitoci na kanta
Dakyar Alh ya iya barin akai sallar asuba sannan yahau shirin tafiya asibitin koda
yagayawa hjy laila itanma cewa tayi bataga taxamaba tabiyoshi
Ilu ne yakaisu ahanya yake gaya musu aitun jiyan shiya dauko gadanga akauye
yakaishi gidan insp.
Lallai gadanga yai ms komi baxai manta da alkairin saba yau yakara yarda gadanga na
masa son gaskiya dole yakara masa riko mekyau kuma xai kara masa matsayi ackn
gidansa da gun aikin sa.
Koda sukaje asibitin Alh yatausayawa yarsa ganin yanda duk ta koma ta rame fuskarta
tayi fiyaut ga goshinta da bandage anyi kokarin yin komi akanta jinin datake
xubdawa yatsaya
Duk sun taru akanta gadanga,insp musa,ilu,Alh da hajiya likita yashigo donyi musu
jawabi
Likita yadubi Alh yace "Alh ai anyi babbar sa.a ma da bata sami wata babbar matsala
acknta ba don ta bugu dayawa sakamakon hakan ma cikin dake jikinta yaxube...
"Ciki!Ciki!!???
Likita yace "to ai da alamar cikin bai dade da shigaba na kwanannan ne koma dai
meye mugodewa Allah kar mutsaya bude bude tunda har ya fita ta sauki ma
Hjy laila tasauke ajiyar zuciya tana goge hawaye wato ashe mugayen har ciki sukaiwa
"yarta? Lallai dole tayi musu Allah ya isa.
Likita yace "eh munsamu yafarfado amma anyi masa allurar bacci domin da sambatu
yafarko.
"To munaso yadawo dai dai sbd suspect ne zamu kawo yan sanda gunsa akwai binciken
da zamuyi akansa sosai, cewar Alh
Gadanga waje yafice yana tunanin wananna Al,amari na xancen ckn daya futa ajikin
khalisat zuciyarsa tashiga wasi wasi Allah yasa dai bacikin sa bane, take wata
zuciyar ta kwabeshi daina wannan tunanin ma kamanta cewa tasaba bin maxa bakaine
farau ba,kuma ai baka xuba mata aciki ba kafuta kaga kenan banaka bane dama.
Yazauna akan baranda yadafe kansa tabbas khalisat ta cuci kanta domin yasan ba yan
garkuwane sukai mata cikinba dama ashe knn da abinta ajikinta.,!
*****
Sai dare dan garkuwa yafarko ckn hayyacinsa yana bude idonsa yaga jami,an tsaro
akansa sunkai 6 kowanne da kakinsa da bindigu ahannu
Yatashi zaune dakyar don jikinsa yai tsami na bugun dayasha gun gadanga gashi
goshinsa akumbure yake yataba yaji bandage
A bayan kanta aka sashi yai tsuru tsuru ana masa tambayoyi masu tsauri
Abinda yafara fada shine si dan kadunane kuma uban gidansu ne yasaka su su sato
khalisat
Alh yana gurin yai xaton ko ackn wad'anda yake huld'ar kasuwanci ne sukai masa
hakan to ashe ba haka bane jin wannan mutumin yace " Saurayin yarinyar ne sunanshi
SAFRAZ……!!!
_MUJE ZUWA_
*Short Story*
*Dis page Dedicated to my sisters Batul mamman &Ummi Aisha*
*Nabilancy Luv*💘
(Auntyn S&S)
page 2⃣0⃣
Takarasa gareta da sassarfa ta janyota jikinta tana fadin "kawata sannu kinji
kinganki kuwa walh dun kin rame.
Khalisat tahau kuka tana fadin "khairat Safraz ya cuceni Allah ya isana shiya
sakani awannan halin ashe dama ba sona yk tsakani da Allah ba ashe dama maganar
daya gayamin karyace yace xaibar garin sbd za.ai masa auren dole? Walh yacuceni
yasa ansaceni don ya sami kudi.yasa ansaceni don acutar dani walh kinganni tunda
naje baci ba sha sbd tunani Allah ya isana badan Aliyu gadanga ba datuni sun cutar
dani da mahaifina
Khairat tajanyota xuwa kan gadon suka zauna tace "bani labarin me gadangan yayi
musu har yau kk yabonsa mutumin da kk tsana.
Khairat ta goge hawaye tareda lumshe ido tana cewa "tabbas Ali gadanga kusar yaki
ne yaci sunansa sbd yai artabu da mutanen nan wanda saida ya sumar da daya daga
ciki duk don ya cetoni da kudin mahaifina walh tun alokacin ina hannunsu naji Allah
yadasa min sonsa araina har kawo yau kuma sonsa karuwa yayi jin cewa ma ashe wanda
nake yima zallar so shine yasa akaimin hakan
Walh kawata ayau ina cike da tarin nadamar abubuwan dana ringa yiwa Aliyu duk don
fadin rai da son zuciya nabiyewa rudin shedan., tafashe da kuka me cinrai
Khairat tahau rarrashinta "kiyi shiru kawata nasan tunda har kk furta to tabbas da
gasken gaske zuciyarki take akan Aliyu kada kidamu ai abune me sauki shima zai soki
nikaina gayen yaimin tun wani lokaci danaxo gidan yadawo daga aiki naga baiwar da
Allah yai masa ta kyau da kira
Tabbas naso nakai hari gunsa domin nayi nazarin inhar yaji kiwo babban mutum ne na
nunawa sa.a alokacin shiru kawai nayi ban gaya mk ba sbd nasan zakiyi challenge
akai kiga kamar na fado to amma tunda zuciyarki tayi karfi akai xan taimaka mk naga
kin mallakeshi kawata kinga yanxuma mun tattauna da momy tagaya min tashiga damuwa
nahalin da kuka kasance da safraz gashi yakaiki yabaro yanzu momy so take inkin
wartsake kiyi aure tunaninta kawai to wazai aureki kina wulakanta mutane
Khairat ta tsahirta jin khalisat din batai maganaba yasa taci gaba "kinga yanzu
dole ki canxa halayenki kixama macen kwarai donki burge Aliyu yaxama kina masa
biyayya da bashi girma ke inaso ma kizama me yi masa komi tun daga sharar daki da
girki da duk wani abunda zaiji dadi aransa har yaji kin burgeshi
Khalisat tace "kai!kawata baxan iya zama yar aikin saba akarkashin mahaifina fa
yake saikuma ni inxamo akarkashinsa kai haba never!
Tsaki khairat taja "ashe baxaki iya janyo hankalinsa akankiba kina mace lallai to
xaki rako mata duniya kinsan kuwa kyautatawa najanyo soyayya? Kuma krmeda kk so
kiga gaba kinzamo matarsa inbakiyi yagani ba kina zaton zai yarda da xaki iya yi
masa wahala amatsayinki na wacce bata saba ba.?
Khalisat tanisa tace "toh! Xan gwada kawata Allah yasa na dace.
Sukai tsit suna kallon gadanga wanda yasha wata shadda milk da hula milk yayi kyau
ainun
Yagyada kansa "eh ankamo iyayansa dafarko da ba.a sameshiba Sai yau kuma yakawo
kansa dayaji shine aka sakeshu shi aka kamashi.
Takai kallonta kan gadanga dayake ta latse latsen wayarsa ta lumshe idonta ta
girgixa kanta alamar baxata ci ba knn.
"To " kawai tace tasan tanajin yunwar ranta ne kawai ba dadi.
******
saida ta warke tsaf kana aka sallamota suka koma gida
Iyayan khairat sunxo dubiyar khalisat gidan kullum sai anyi baki nayin jaje
Yanaso yadaukota to amma yafiso yasami gidan kansa bayaso yakawota gidan sbd
khalisat yana tunanin xata bashi matsala
Koda hakan takasance da khalisat baiji wani tausan ta ba har yanzun tsanar dayai
mata nanan daram aransa duk abubuwan datayi masa yakasa mantawa dasu
Amma wannan karan yaninkawa gadanga salary yace zairinga bashi dubu dari duk wata
na abinda yai masa na ceto yarsa yaji dadin hakan sosai bai zaci jarumtar Alin
takai hakan ba
Alh yace "baya ganan ma mota nasiya maka tana can a parking space honda ce naga ka
iya tuki shiyasa nabaka ita kyauta duk da ba sabuwa bace amma ina mk fatan kasai
sabuwa wataran da kanka Aliyu
Hjy laila tace "kai Amma naji dadi alhaji ina tayashi godiya Allah yabar xuminci
Alh yace "Amin, saidai inaso Aliyu kayimin wani taimako badan wai danka taimaka min
din adole ranka baiso ba nabaka motar a,a inaso kayimin taimakon nan tsakani da
Allah ne Aliyu
Gadanga yadago kai yakalli Alh yace "fadi ko mene zanyi shi zuciya guda babu
tantama Alh nadaukeka tamkar mahaifina xantaimaka da komeye Alh.
Da sauri gadanga yakalli Alh yasadda kai kasa gabansa yahau dukan uku uku
Alh yaga firgice sosai a idon gadanga amma saiya matse yaci gaba "nasan xakayi
mamaki domin abinda khalisat tayi bakowane zai iya aurenta yarufa mana asiri ba
saikai na hanga nahango kaine zaka iya zama da ita ckn rufin Asiri munyi shawarar
nan ne da momynta fatana ka amince domin inhar ka amsamin to walh ko tanaso ko
bataso bata isa tabujere minba inko har tanuna rashin amincewarta to saidai ta nemi
wani uban bani ba.
Gadanga kansa akasa yarasa tacewa "rana xafi inuwa quna. Tabdijan, ya auri khalisat
yafaranta musu rai shikuma nasa ya quntata mezaiyi da fanko? Ga gredinsa can akauye
kodan Alh baisan yai aureba shiyasa zai kawo masa zancen yarsa? Toko gara ya sanar
masa ko zai janye kudirinsa.
A hankali yace"Alh nayi aure aranar sadakar bakwan inna aka daura min Aure da
yarinyar da muke soyayya zainabu iya kulu ita ta bada sadakima ayanzu hakama shirye
shiryen danake naje nataho da ita nan garin
Alh yace "to wannan ba matsala bace inhar ka amince da khalisat din sai inbaka gida
kyauta a GRA me part 2 kazauna dasu kada ka damu dole tazauna da matarka ai.
Hjy laila ma hakan bae daga mata hankaliba najin gadangan yai aure itama fatanta ya
amince musu.
Gadanga yadulmiya tunani "to inya amincewa ai baikyautawa ubangidan saba bai masa
adalciba yanemi abu yaki masa harya bashi gida da mota da karin salary duk don ya
auri yarsa, hhhhmmm yasan kuma yana khalisat ta tsaneshi baxataji dadin hakan ba
inhar taganta yau amatsayin matarsa dole zata koka ta ciji yatsa kuma shi dama
akullum burinsa yaga ya rama abubuwan data ringa masa to ai dama ce tazo masa ckn
sauki, to meya rage masa kawai ya amince shi yafi……
*Short Story*
*Nabilancy Luv*💘
(Auntyn S&S)
Gadanga ya dago da kansa yakalli Alh yace "na,amince Alhaji Allah yasa hakan yaxamo
Alkairi agareni.
Yau gadanga yafarantawa Alh rai akaro na biyu tun xuwansa gidansa dole shima
yaxamto me faranta masa ya murmusa tareda fadin "Nagode Aliyu abinda kaimin Allah
yai mk na kyautatawa kuma inaso kasani badan na cuceka nai hakanba don inkara
dankon zumuncine duk da kataimaka min ma domin nasan aurenka da khalisat zai zamar
min ci gaba nida ita domin natabbata duk halayenta daba na kwaraiba dole zata
xubdasu sbd tana shakkarka kuma nasan kaine kadai zaka rufa mana asiri aduk yadda
kasameta kuma nasan ko bayan raina xaka riketa dakyau baxata wulakantaba nagode
Aliyu kaidin jan gwarxone me amana da kyawun hali Allah yayi maka albarka yakuma
jikan iyaye da kakanni.
"Amin..cewar gadanga
dady yace "yaushe kake ganin xa,a tsaida ranar da xa.a dauka auren ? Don baniso
adau dogon lokaci
Gadanga yace '"duk lokacin daka tsaida yayi saidai inaso inje kauyenmu sbd intaho
da zainabu.
"To ba matsala tunda gobe friday inyaso ranar Sunday sai adaura Auren naku in an
idar da sallah ko baka nan bakada matsalar sadaki zanbada a aljihuna ……
Momy takatseshi da sauri "A,a dady nizan bada sbd gadanga d'ane nima aguna
Hooo!😅gadanga dan gata shikam yaji dadinsa kowane sadakinsa kyauta ake bashi
saidai yakwashi garabasa knn
Dady yace "barni nabiya momy zanbada naira dubu hamsin inyaso sai ke kiyi musu wata
hidimar
Tace " to aishikenan in "yata zainabun tazo ita nayi mata kayan daki.
Gadanga yahau murmushi farin cikine aransa jin za.a gatanta zainabunsa lallai
mutanen nan suna sonsa
******
Ranar Juma,a da sassafe suka dauki hanyar kauyen marina shida drebansa abokinsa
kuma wato mudi
Suna tafe suna hira mudu nayi masa jinjina na yanda yayi artabu da yan garkuwa
Nan gadanga yagaya masa yanda sukai da iyayan khalisat yagaya masa cewar xa.a daura
auransu ranar lahadi
Mudi yakama baki yana dariya yace "kai mutumina ammafa ka more dayawa dama nine
haka dan gata
"Inafa gata anan zadai atakuramin nida amaryata xainabu walh banda ina ganin girman
dady da babu yanda xa,ayi inkarbi fankon yarsa haba ai nacutu xayawa inhar nayi
rayuwar aure da ita ……
Mudi yace "to amma dai komeye gareta ai xa.asha kudi ko? Yafada yana dry
Tsaki gadanga yaja yace "hhhmmm kai idon cin nera ne baxaka duba yadda akeso
kasamawa "ya"yanka uwa tagariba saidai nera kake hange wanda kuma inkace zaka nuna
kwadayinka to kana tareda takaici kuma dole kajuri wulakanci
Mudi ya sosa keya yace "kuma fa hakane da wannan dan wannan, nasanka mutimina da
tsaro da rashin jan mutum ajiki kada kaga an baka kyautarta kace xaka gallaxa mata
kayi adalci tsakaninsu kaa kanuna kafi son uwar gida xainabu.…
gadanga yace "hhhhmmm fada ma bata bakine mudi ai dole khalisat ta dauri damarar
yin hkr atare dani sbd kaima kasan akwai banbanci tsakaninsu balle xuciyata zainabu
take so itako "yar sadaka baxan taba son taba ko kallon arxiki bazata isheniba
intaga zata xauna ta zauna inko baxata iya hkrn xamaba to xata iya kara gaba nikam
dai bana rigada na amsaba to banda laifi agun Alh inhar ta bijire ita zasuga laifi
baniba
"Hhhmmm kaima kuwa xakai laifin inhar kaiwa diyarsa rikon sakainar kashi tunda
kasan baxaiji dadin yaga kana gallaxa mata ba yardace yasa yabaka itafa.…
"Kaga murife wannan maganar tun kafin mushiga kauyenmu don banaso kowa yaji ma
"Eh banaso taji sbd banaso ta tashi hankalinta kasan kishi gun mata fa. Dama ita
ba kiba ba taje tarame.
Gadanga yace "itama tanasona dayawa kaga kuwa kaso me sonka ba laifi bane.
Da mudi xai tafi iya kulu ta hada tsarabar kauye tabashi yakaiwa surukarta hajiya
laila
Har bakin mota gadanga yabiyoshi yana jaddada masa kan cewa yadawo ranar litinin
yadaukesu shida amaryarsa
Mudi yace "gaskiya kai d'an gatan ma,aikacine bakaje yau juma,aba gashi monday ma
baxakajeba lallai kanacin salary a b'agas kyanta nadawo lahadi nadaukeku inyaso
kaga monday baxakai fashiba ko?
Gadanga yakai masa bugu na wasa yace "kaifa matsala ce dakai meye ack dan nayi
fashi alhali mune da gurin kuma akwai me kular min da komi inbana nan.
"Ba matsala nafara kwashe komi akaina nakusa daina xuwama tunda in turancinne
ayanzu xan juya haka lissafin ma baxai xillemin ba.
Mudi yace "to aishikenan sai lahadin knn agaida amarya zainabu.
Mudinma dariyar yake yatafi yana jin son gadanga aransa bayason rabuwa da gadanga
shiyasa yafison yaga cewar shizai kaishi koina jininsu yahadu sun shaku tun xuwansa
gidan shiya tarbeshi yazama abokin hirarsa dukansu kusan tsaran juna suke yana jin
dadin tarayyarsu da gadanga don gadangan baida girman kai duk da yanxun yaxama
babban yaro yana kama nera bai nesa dashiba yana kuma yi masa ihsani.
Sunsha hira da iya kulu kuma bai boye mata komiba jinta yake tamkar innarsa haka
yazayyane mata duk yadda akai na sace khalisat da kuma alqawarin daurin aurensu da
Alh ya kulla.
Iya kulu bataso hakanba domin tasan halin jikarta batada kunya ga girman kai da
kyamar talaka gashi an shagawabata bata ganin girman nagaba da ita anya xaman nasu
zaiyuwu kuwa dantasan halin gadanga baya jurar banxan hali
Basu shaku da khalisat ba irin yanda suka shaku da gadanga tunda khalisat bata zuwa
inda take saidai in ita taje gidan su hadu kuma bata shiga jikinta amatsayinta na
kakarta tafi shigewa angin momy dayake masu kudine hakan na konawa inna rai sbd
batada wasu jikokin aduniya sai ita tunda kuma taga yarinyar ba yar arxiki bace ta
yardata tasa ta agefe bata tunota kwata kwata batada kawazuci balle abin yadameta
Iya kulu takalli gadanga tace "to nidai abinda xance maka anan shine kaxama m
adalci atsakaninsu baxan hana ba tunda bansan me Allah xaiyi agababa fatana ka kula
mana da zainabu kada tacutu abirni batada kowa saikai yarinyar bame hayaniya bace
gata da hkr kaga tunda aka daura muku aure takanzo tagaidani ta tayani aiki ta tafi
inajin dadin hakan tana bani girma sosai dan Allah gadanga kariketa amana kaji.
Ya gyada kansa yana cewa "insha Allahu iya xanriketa bisa amana kitayamu da Addu,a
kawai
Yace "eh da ita zantafi sbd Alh yace akwai gidan da zai bani me sashe biyu sai
insasu ack
"To madalla Allah yabada xaman lfy yasa abokan arxikin kane.
***
Dare nayi yaje ga amarya zainabu bataji xuwansa kauyenba saijin zuwansa akofar gida
tasha mamaki
Tafita tayi masa iso har ckn gidan yagaida iyayanta dayake babanta yarasu sai mijin
mahaifiyarta mutumin kirki suka gaisa da gadanga ckn mutunci
Yace "ke dawo nan jikina kibani abaki yanxu fa bakamar da mukeba ni mijinkine komi
kikai zaki sami ladana,
Dayaga dagaske take baxata iya motsawa bama saiya mike asannu yariko hannayenta
yazuwa kan doguwar yar kujerar dakin yazauna sannan yazaunarta kan cinyarsa
Duk taji kamar ta nitse kunya kamar me !! wai Allah yau itace a cinyar namiji!!
Ya janye lullubin fuskar datayi yace "bude idonki ki ciyar da mijinki Abun na kada
ki kwari kanki ko kiyi sake wasu matan abirni su fiki iya kula da miji su kwace mk
ni ……
Da sauri tazaro manyan idanunta tace "kamar yaya su kwacen mini kana nufin kanada
wacce tafini acan ?
Yace "a,a babu amma inbakiyi abinda xai farantamin rai ba to zan iya samun wacce
zata faranta min acan.
Zainabu akwai kishi tuni ta saki jiki anmata wayo tadauki cokali tahau diban
shinkafar ahankali tana bashi abaki shiko yana ci ckn yauki da yanga waishi nan dan
gata 😅
Amma bata yarda sun hada idoba karfin hali kawai take don son ta faranta masa rai
kada yaji son wata aburni ba itaba
Yakura mata ido yace " Abunah ina bukatarki akusa dani kifada agida ranar litinin
zankoma tare zamu tafi mutum biyu kawai zamu bukaci yan rakiya sai iya kulu kinji .
Yasan taji dadin hakan kawai dai tanuna azahirine baxata iyaba Abun gadanga kenan.
Ranar asabar washe garin dayazo baije gun abun ba yana tare da abokansa da yaransa
yana musu nasiha akan sudaina futa yawon gangi da farauta yai musu alqawarin xai
ringa daukarsu daya bayan daya yanakai su birni yana samo musua aiki
Sunji dadin hakan sosai kuma sun masa alqawarin daina farauta da fadace fadace
Suka bashi labarin Amadi dan takararsa cewar har lokacin suna bursin aburni anyanke
musu wasu shekaru a tara shida yaransa dayasa su suka aikata ta,asar
Shi gadanga ma ya mance dasu shidai kawai akullum yanaiwa innarsa addu,a dan tashi
ma da xa,a fito dasu ko ajikinsa suda ubangijinsu kuma
Ranar lahadi ana gove zai tafi birnin yadade tareda zainabunsa adakin yayanta yana
jiyaeta soyayya tafara sakin jikinta yashafa jikinta ckn salon sa na burgewa ta
matsu iya matsuwa yasha bakinta yajiyarta dadin duniya wanda har jitaringayi dama
su dauwama ahaka
Koda yatafi tadade bata iya rintsawaba tanata tuno yanda takaya atasakaninsu ta
kankame filo tana murmushi lallai jikin masoyi akwai dadin tabawa haka harshe yake
da zaki? Tab dole tazage wajen nunawa mijinta soyayya kada wata takwace matashi
aburni don ta tsani kishiya arayuwarta ……
*Short Story*
*Nabilancy Luv*
(Auntyn S&S)
*BUHARI YUSUF*
*PEN WRITERS NVLS*
&
*DR. ZAIN* *ONLINE HAUSA NVLS*
&
*YA,U TATTA Me waka*
page
2⃣2⃣
Aranar litinin Akayi taron biki agidansu Zainabu danginta suka cika gida anata
bidiri ana kidan kwarya kowa na farin ciki
Amarya tasha kyau dayake iyayenta sunyi mata dinkuna tunda ango baiyi kayan lefe ba
a Al,adar kauyen duk macen da ba,ai mata lefe ba to kowa sai yaji anyita tsegumin
knn ana cewa miji baya son matar shiyasa
To amma wannan Aure na dabanne domin kowa yasan yanda gadanga da zainabu suke son
juna tunda anga yanda ya illata Amadi akanta kuma babu wanda ya isa yai tsegumin
zancen gadanga bai mata lefe ba sbd tsoronsa da akeyi ta koina kuma yaransa ne
agarin su kadaima sun ishi kowa
Dubu hamsin dama yabaiwa iya kulu takai gidansu zainabu itada wata makwabciyarta
amatsayin kudin komi da bai mataba
Gidansu xainabu sunji dadin kudin dan da ace lefen zaiyima ba wani kashe kudin
xaiyi dayawa ba a fanteku biyu ake zuba kayan kuma basufi kala takwas ko bakwai ba
takalma biyu da dan madina da cover shoe da plate shoe komi na kyali ma biyu akeyi.
To amma wannan kudi sai aka dankasu ahannun wata yayar gwaggonta da za.ayi rakiyar
amarya da ita akan insunje ayi mata siyayyar kayan daki da ita (lol 🤔 wani abun sai
yan kauye wato hamsin ce xatai musu kayan daki tabdija zakuwa ku tsaya a iya
katifuwa 😅 )
Kudin farko dama da aka bayar amatsayin sadaki wanda iya kulu tabada agudummawarta
cancakas aka siya mata kiwo dashi don ba.a taba kudin sadaki akauyen cewa akeyi
Aure baya karko in har ba kiwo aka siyaba
Inko kayi dace kiwon da aka siya taringa hayayyafa tofa wai haka amaryar ma zatai
ta hayayyafan itama
Inko sukaga kiwon nan bata "yaya dayawa ko bata yin haihuwar kwata kwata to nanfa
xakuga sun canfa suce shikenan wannan amarya fa baxata biyo wannan kiwon nataba
kunjifa fans 😁
Gadanga aranar yasha kyau shima domin sabuwar shadda yasha ruwan hoda da tsaleliyar
hula kalar kayansa harda tsadadden agogo da takalmi me kyau tabbas daka ga gadanga
kaga dan birni zammm
Wani kyalli yaringayi yana shining kowa yakalleshi saiyace yayi kyau
Tun safe mudi ya iso kauyen dashi aka ringa bidiri domin abokan gadanga da yaransa
sun hada masa hidima ta biki anata shagulgula harda su gangi afilin kauyen aka cika
dam ana kallo abu gwanin sha,awa
Sai karfe kusan shida aka tafi kai amarya amotar mudi wanda gadanga na gefensa sai
"yan,uwan gwaggon zainabu su biyu abaya da amaryar da iya kulu
Zainabu tayi shiru atsakiyar iyayenta kanta lullube da mayafi sai kamshi takeyi
zuciyarta cike fal da farin cikin yau zata shiga burni wanda ada sai labarinsa da
takeji tayi godiya ga Allah daya nufeta da Auren gadanga gashi har xatayi xaman
Aure dashi agarin da takeso burni
"Yan rakiya sai kalle kalle suke abinsu sunshigo birni suna ganin dogayen gine
gine iya kuluce ba sabon abu ba agunta don takanxo in wani abu yafaru agidan dan
nata akanje adaukota amma takanyi shekaru kfn taxo din
Kai tsaye masallaci gadanga ya wuce Mudine yashigar dasu ckn gidan
Ankawo musu kayan cima barkatai agabansu duk da saida suka bada faralli na sallar
magariba kana suka fara aikawa
Danbun shinkafa yaji kabeji da hanta suka faraci sai kuskus agefe da shinkafa da
miya da naman kaji aciki
Cikin ladabi hjy laila ta warewa iya plate ta zuba mata ta mika mata
Hjy laila tana son "yar tsohuwar sbd itanma tana nuna mata soyayya insunje kauyen
Momy tashiga dakin khalisat tasameta kwance tayi rigin gine tamkar me bacci idonta
arufe nanko ba bacci takeba tunani kawai takeyi nayanda xatayi xaman Aure da
gadanga Alhalin shi ba sonta yakeba gashi ma yabar garin sbd tsananin k'in dayake
mata
hawaye yaxubo mata me quna tana son gadanga Amma batasan yazatai tasa masa sonta
aransa ba dolene ta nemo mafita kota halin k'ak'a tana son taga gadanga yasota
shima
Tasa hannu ahankali tahau goge hawayen adaidai lokacin ne momynta tashigo taga
tana goge hawayen tayi sauri ta zauna akan gadon tajanyota jikinta tana fadin
"To inba komai din meyasaki zubda hawaye haka ? Ko sbd Andaura
Miki Aure da Aliyu?
Momyn taci gaba "kinga inma xaki daina kuka gara ki daina domin wannan Aure da Aka
daura tamkar jahadine agun gadanga sbd yataimakeki ba karami ba kinga inba shi
dinba duk wanda kk Aura to awulakance xai dinga kallonki sbd kingama xubda
mutuncinki awaje shiyasa akullum akeso mutum yakasance me kama kansa da rikon
mutumcinsa bawai shan kamshi da wulakanta nakasa dakai ne kama kaiba a,a kada ka
ballagaxar da kanka kabada matancinka ga wanda ba mijinkaba kinga koshi wanda kk so
din dayai mana hakan da ace shi zaki aura dinma to abanxa zaki kasance agunsa
bakuma xai dokantu da auran nakiba balle har kuyi xaman dadi tunda akullum inkin
futa azargi zai ringa kallonki sbd irin watsewar da kukai awaje to kinga kuwa samun
gadanga agunki alkairine kisa aranki ayanxu asirinki yarufu fatana kiyi masa
biyayya maza tashi kije ki gaida bak'i afalo harda iya kakarki akaxo.
Khalisat ta yatsina fuska tace "meya kawosu kuma gidan Alhalin ba taron biki zamuyi
ba.?
Hjy laila tayi murmushi tace " koma dai meye yakawosu ba ruwanki kije kigaidasu ckn
mutunci shi yafi mk.
Ta mike asanyaye tafuta xuwa falon ita duk azatonta ko bikinta sukazo
Momy tana sane taki gaya mata cewar matar Aliyu gadanga suka rako sbd dady yace
kada agaya mata yana da mata akauye shi gadangan dakansa yagaya mata yafi tsoronsu
kada tayiwa "yan rakiyar wulakanci sun san halinta sarai
Garama ta d'an zauna kadan na mintina kusa da iya kulu suka gaisa ta tashi tabar
musu gurin kwata kwata hankalinta baikai gun zainabu ba wacce kanta ke k'asa itama
Daki guda aka warewa baki alallausar katifa iya kulu ta kwana harda jibgegen
bargonta wanda dady dakansa yakawo mata
Bacci sukai harda saleb'a jin dumi adakin dan AC aka kunna musu me d'umama d'aki
Sai sallar Azahar suka fara shirin komawa kauye dayake gadanga yace iya kada
tafadawa zainabu labarin khalisat har suka tafin kuwa iya bata mata zancen ba don
tagano nufin gadanga na boyewar aiko dai zainabu harda kukanta dataga zasu tafin
Saida suka rarrasheta da yi mata " yan nasihohi na zama da miji lafiya
Dataga momy tajata ajiki tana hilatarta da hira saita dan saki jiki
Momy tahada musu sha tara ta arxiki da zasu tafi harda kawo shadda tabasu tace
akaiwa mahaifin zainabu ace inji dady haka suma tabisu da atamfofi masu kyau da
tsada sukaita murna da godiya
Suka kawo dubu hamsin din da xa.a saiwa xainabu kayan daki suka bata
Momy tace saidai ta ajiyewa zainabun kawai Amma sunrigada sunyi mata kayan daki
komi da komi har kayan kicin
Sosai sunji dadin hakan sunyi farin ciki sukaita godiya lallai gadanga yadace da
uwar daki
Mudine yamaidasu kauyen aiko koina labari ya isar akan abin arxikin da akaiwa
zainabu agidan Alh
*****
Su zainabu anzama "yan burni momy najanta ajiki takuma saki jiki da momyn haka dije
me aiki takanxo falo gun Zainabun su zauna suyi hira kosu zauna xaman kallo in
momyn ta kunna
Ackn satin da taxo gidan sau biyu suka hadu da gadanga yashigo gaida su momy
tagaidashi itama
Dady yamasa bayanin cewa nanda sati za.a kammala kwaskwarimar da akeyiwa gidan da
zasu zauna in anyi jere kuma saisu tare arana daya don kayan daga dubai za.a taho
masa dasu yabaiwa abokinsa kudin zaisiyo masa acan.
Gadanga yai farin ckn hakan godiya kawai yaringa zubawa Dady ya gama masa komi
arayuwa
Ranar wata lahadi Zainabun tana zaune afalo tana kallon TV dadin kowa akeyi shirin
tashar Arewa 24 ta dulmiya ckn kallonta tana fahimta sosai takumaji dadin shirin
saijitayi andaka mata tsawa "Ke!! Wacece ke?
Da sauri tajuya takalli me daga mata muryar khalisat ce ta fito da matsatstsun kaya
ajikinta kanta yasha gashin doki
Zainabu batayi maganaba amma ta tsorata ainun kodon ita bame son hayaniya bace
saitajita atakure tayi shiru kanta akasa
"Baxakiyi maganaba knn daga ina kikaxo dahar zaki sami damar bararrajewa afalo kina
kallo ko aiki aka kawo ki shine zaki shantake afalo baxakiji kiyi aikinkiba.?
girgixa kai zainabu tayi tace ahankali "A.a ba aiki nazoba daga kauye aka kawoni.
"To aikin kenan kikazo yi tunda daga kauye kkzo don bamuda hadi da "yan kauye maxa
tashi ki kama aiki...
"Ni matar...… ni matar gadan... momy ce tashigo falon dasuri tajiyo hayaniyar
kafin zainabun tagama furta abinda takeson furtawa har momyn takatseta
Adakile khalisat tadubi momy tace "nida wannan yar kauyen nake momy tazo ta hakince
a falo kamar na ubanta.
Momy ta bata rai "ki iya bakinki khalisat kinsan ita din wacece kuwa? To itace
wacce aka daurawa gadanga Aure da ita kuma ganin da kkyiwa su iya sunxo ita suka
kawo ayanxuma zaman da take agidan nan na yan lokacine domin da zarar ankammala
gyara muku gida tare zaku tare da ita dan haka ki iya bakinki ki kuma bata girma
tunda uwar gida take agunki kishiyar kice dolene ku hade kanku don hk tun wurima
gara kijata ajiki inkinason zaman lfy.
Momy nagama fadin hk ta wuce ciki abinta
Tabar khalisat atsaye sororo tana kallon zainabu wanda itama zainabun kallon
khalisat take da mamaki me momy ke nufi da cewar khalisat kishiyar tace ?nufinta
knn fa khalisat din matar gadanga ce kai bata yardaba to yaushe akai hakan?
itanma khalisat din tambayar kanta take dama gadanga nada Aure ashe bata saniba?
Tab aiko baxata zauna da kishiyaba kishiyar ma yar kauye lallai dasake dole gadanga
yaxaba ko dai yasaki zainabu ko kuma yamayar da zainabu kauye, ita ya zauna da ita
abirni …….
*Short Story*
*Nabilancy Luv*💘
(Auntyn S&S)
*Hoooo😅 gaskiya Zainabu tanada masoya ashe*? *Hhhmmm tabbas na yarda don mata
dayawa sun tayata kishi akan khalisat kai harda maza suma sun nuna tsagwaron
kishinsu akan khalisat harda masu ce mata shigege "yar sadaka batada power da zata
baiwa gadanga zab'i haba fans kud'an tausaya mata mana* 😂😢 _itama fa star ce kuma
wataqila ta dalilin gadanga ta dawo mumina saliha ko kuwa?_
page
2⃣3⃣
Jiki asanyaye khalisat tabar falon zuciyarta cike da qunci wai yanzu waccen
bakauyiyar ce kishiyarta, inama tanada damar rabata da gadanga da saita rabasu ayau
Can wata xuciyar tata tace mata kinada dama sosai ¡¡!!
Rufff da ciki tayi akan gado tana kuka amma jin abinda xuciyarta tace yasa ta tashi
da sauri don tana bukatar mafita da gaggawa
Ki kaita gun teacher kawai me zafin hannu ayi mata abinda zaisa taji tatsani
gadanga harta nemi saki agunsa kokuma taji kano tayi mata xafi ta koma inda ta fito
kawai.
Ta hau gyada kanta tana dan murmushi jin mafitar da xcyrta tasamo mata
Da sauri tadauko wayarta dake kan stool din gado tayi dailing nambar khairat aiko
bugu daya tadauka take tahau bata labari
Ta xayyanewa kawarta komi tundaga kan Daurin aurensu da gadanga yanda aka daura
babu ango agun yatafi kauye dakuma yanda yadawo mata da mace wai matar sace
Ita kanta khairat ta girgixa dayaks itanma akwai danyen kishi sai tahau zugata
"Tabdijan aiko dai baxamu bartaba dan walh kalarki ta wuce kixauna da kishiya
hhhmmm kishiyarma bakauyiya haba kawata sha kuruminki akwai gun wanda zan kaiki sha
yanzu magani yanzu
Khairat tace "to kitanadi kudi masu tsoka dan farraqu zamui musu kifito gobe da
safe muje dan garin da nisa kuma kan tsauni zamu hau
"Kin manta andauramin Aure aiwalh nasan momy baxata bariba balle ni yanzu momy
tsanani takemin ko magana me dadi bata shiga tsakaninmu haushina sukeji tun wannan
abin daya faru najin cikin dake jikina na safrax ne sukejin haushina kokinsan
hakanne yasa suka shiryi yimin auren dole anufinsu inji haushi shine suka hadani da
gadanga basu san gata sukaimin ba da ragen wata hanyar ta wahalar neman soyayya
Dariya khairat tayi tace "gaskiyane ki godewa Allah da kk samu Aliyu abagas dan
haka saiki dage wajen sanin hanyar mallakarsa.
Khalisat tace "to yanzu ya xa.ai ko kudi zan turo mk ta account saikijemin kawai?
"a,a malama kawai kiyi karya kifito muje innaje miki yau gobe wazaije miki? Keda
zakiyi tayi abu basau daya za.a tsayaba kedai kawai kisan yadda zakiyi kifito ko
kice mata zamuje yin gyaran jiki ko hotuna a *BALANCY*
Koda dare yayi khalisat tasamu iyayanta afalo suna kallo dady yagama cin abinci
suka amsa sallamarta
Tashigo asanyaye tazauna anesa dasu kanta akasa tace "dady sannu da hutawa.
Kanta akasa tace "momy inaso gobe da safe inje khairat tarakani gurin wata me
gyaran jiki ……
momy takatseta da cewa "basai kinjeba nasa akawo wata shuwa arab zatayi muku jibi
zataxo.
Gaban khalisat saida yafadi bataso taga anmata togajiya na futa take tayi saurin
lauya zancen "To dama banda ma zuwa gyaran jiki zamuje da ita gurin me daukar
hotuna zamuyi da kawayenmu.
Momyn tace " to naji amma kinsandai kinada Aure akan ki bamu keda alhakin barinki
futaba mijin kine ko?
Momy taci gaba " dan haka saikije kitambayi mijinki Aliyu bamuba
Tace "to, asanyaye ta mike tayi hanyar waje ahankali take daga kafarta tamkar kaxar
da kwai yafashewa a ciki.
Yayi zaton yanda yaga motion nata yacanxa ko rashin kudine ahannunta saiyasa hannu
ackn jakarsa yadanko kudi bandir yamika mata ta karba tana godiya
Tana futa daga falon momy taringa fada akan yanda yake mata nashagwabawar dayake
mata "kai kenan bazakai mata fada ba dady bakaga yanda nake mata bane bafa tsanace
tasa nake mata hakanba duk don tasan tai mana kuskurene to amma kai baruwanka ko
canji bata gani daga garekaba harma da bata kudi tunma bata bukataba haba dady
gaskiya yakamata ka gyara domin tun farko kaika b'ata "yarka ……
Dady ya daga mata hannu "ya isa haka momy yanxu meye laifina anan dan nayiwa yata
ihsani to inban bataba wazai bata ?
Momy tace "ni ba xancen kudinne ma yafi damuna ba yanda kake nan nan da ita
yakamata karage b'ata ta sbd gdn Aure zataje kuma duk randa babu mu ita xata
wahala...
Momy tace "Amin . Tareda jan bakinta tayi shiru ganin ransa yafara baci
Koda khalisat ta futa kai tsaye babu fargaba tanufi dakin gadanga da sallama ta
shiga
Aiko dai dole tasa taja tunga ganin gadangan akwance rashe rashe yabaje akatifa
yana waya da xainabu cikin kwantar da murya yake ban hakuri agareta "kiyi shiru
Abunah, ina sonki ina qaunarki babu wacce zata fiki aguna kiyi hkr kibar kukan
hakan bada son raina na Aure taba …
Karaf duka akunnen khalisat take ta ranfo da wacce yake waya _it means_ knn bada
son ransa ya Auretaba harma hkr yake baiwa yar kauye lallai sunkamashi ahannu
tabbas zata dauki mataki
Bata nuna bacin rantaba ko kusa dan nunawa ma tayi tamkar bataji komiba
Har zata futa daga dakin taji yakira sunanta "ke khalisat zonan ! Da izza da
gadara fa🤗
Yace "meya shigo dake dakina adaren nan ko yauma taciyoki ne irin wancan karan da
kk rinjayeni na aikata ashsha wanda nake nadamar yin hakan. Meya kawoki dakina ! Da
daga murya yasake tambayarta
Atsorace tace dashi "hhuumm …dama...dama momy ce tace naxo natambayeka zanje unguwa
Tamkar yadara saikuma ya maze ganin yanda yafurgitata da muryarsa wato rashin kunya
takare
Yace "koma ina zakije kije mana babu ruwana yawone dai nasan bazaki fasaba sai dai
Allah yakiyaye ni.
Taja quttt! Natakaici wato zarginta yakeyi knn kuma bama ya kishinta yake nufi
lallai ita keson gadanga shi baisonta
*********
Da safiyar Allah tana karyawa ta shirya tafuce abinta amma saida taji tashin motar
Dady yafuta sannan taji futar gadanga ma kana itama tafuta a motarta
Allah sarki zainabu ita kanta tausayin kanta takeyi najin tanada kishiya taji inama
bata Auri gadanga ba don taki jinin taji wannan kalma ta kishiya!
Duk da yai ban baki yai rarrashi yabada hkr yatsarata over amma kishin khakisat
nanan makale akasan ranta
Tunaninta zata zama wulakantacciya anan gaba tunda ita tamkar marainiya take batada
gata saina Allah to ina ita ina xaman kishi da "yar masu kudi? Banda tana yiwa
gadanga so bana wasa ba to da ta hakura tabarwa khalisat shi don ita batason tashin
hankali arayuwarta takumasan khalisat masifaffiyace baxa taso zaman lfy ba.
Taci kukanta ta gode Allah har garin Allah yawaye ammafa batayi bacciba don akan
sallaya ta kwanama saida ta tashi ckn dare tagayawa ubangijinta damuwarta tanemi
yakawo mata dauki cikin lamuranta yakuma shige mata gaba dan shine gatanta
Dayake tasan takan sanin addu,o.i tana xuwa islamiyya sosai akauye gashi sanin
ilimin islama yai mata rana don tafara jin saukin kishin aranta
Hisnul muslim ne agefanta tayi addu,oin safe tana kwance bacci yafara daukarta
hannunta dauke da dan littafin dake da sunayen Allah dari ba daya. Asma,ul lahil
husna...
Adaidai lokacin data fara wannan baccin me dadi tashiga mafarki me dadi itada
gadangan ta suna sheke daddad'ar soyayyar
Sukuma su khairat da khalisat adai dai lokacin sukuma suna gaban bokansu sun gama
zayyane masa bukatunsu da kukansu
Boka yace "so kike Ayi mata kurciya tabar garin ta nausa dawa ko kuma asa musu
tsanar juna ?
Boka yace "to kowanne ai xaiyiwu amma akwai sharadai dole dakuma abinda zai biyo
bayan kowanne inhar aka samu tasirin addu,a akai har abinda mukai yakarye.
Suka gyara zama donjin meye sharadan
Boka yaci gaba da fadin "kinga inhar muka nausa ta dawa to da zarar sungano anyi
wani abu akai inhar suka karya da addu,a to ki tabbatar watarana zata dawo kekuma
zakije inda taje koda birnin sin ne to dolefa zakije kuma akafa...duuummm! Faduwar
gaba gun khalisat ba mgn
Boka yaci gaba "nabiyu kuma inhar mukai abinda yaji yatsaneta to zai saketa ne
yazauna dake to ammafa shima hakan indai suka karya da Addu,a tofa ki kuka da kanki
dan zai miki tsanar da har gara tata ne sbd da jikin jab'a da mushen kare akeyin
abin kuma kokun rabu dashi bake bayin wani auran don babu wanda zaixo gunki kina
warin jab'a yaya kin Amince ………
*Short Story*
*Nabilancy Luv*💘
Page
2⃣4⃣
Jikin khalisat ne yahau tsima dajin wadannan mugayen sharuddan da baxata iya
amincewa dasu ba
Ta mike tsaye zatayi hanyar waje tana cewa '"ban amincewa ko dayaba nikam na hkr
taso maza khairat mukoma gida na hakura.
Shiko boka cewa yayi "jeki mana inma kin tafi zaki dawo wataran kida huma farin
shiga kawai.
Koda suka futa khairat tayita mata fada akan wai bata kishin kanta shiyasa tayi
hakan "ke kam walh kinrako mata duniya bantaba ganin mace irinkiba meye naki
nafitowa batareda antsaida matsayaba haba khalisat ina wayo da hankalin naki suka
tafi gaskiya kinbadani
Khairat taja tunda tace "kinsan Allah ko mun bar nan wani wajen zankaiki don ayi
mk aykin nan inba hakaba kece abin tausayi kuma dawo kinyi dana sani akan fasawar
da kikayi
Koda shima suka xayyano masa batu sai yahau gyada kansa7 tareda daukar wani
bantaren mudubi yace takira zainabu sau uku inhar zainabu ta amsa to xataji ta
tashi datsanarsa Aranta
Kamar yadda yasata hakan tayi sau uku takira sunan xainabu tana kallon mudubin nan
saiga hoton zainabu dinguringum tabayyana akwance Akan sallaya hannunta rikeda
hisnul muslimi fuskarta tana annurin haske
Bokan yaiwata kaxamar dariya yace "wannan da kk gani babu wani mahaluki daxai iya
mata mugun abu yakamata domin addu,a da kariyar ubangijinta ne ke lullube da ita
abu daya yakamata kiyi kawai ki mallake miji bawai kiyi mata mugun abuba
Khalisat tace "Inaso duk irin son da yake mata yadawo kaina yaji ni kadai yafi son
gani ba itaba ta dawo bora nadawo mowa.
Boka yace "wannan baxai gagaraba saidai hanyoyin mallakar sunada yawa wadanda
sukafi karfi guda biyu xuwa ukune nafarko akwai wanda zansadu dake inyi amfani da
sparm dinki sai nabiyu kuma Zan yanka gefen gabanki insaka miki wata sihirtacciyar
laya adinke mk ita aciki saikuma wanda zanmiki rubutu akan nonuwanki da jinin
hailarki sai awanke kisa masa alemo to tabbas duk wadannan ba kamarsu a aikin
gaggawa kuma baxai karyeba zakuma kiyi faharin hakan dan haka xabi yarage naki
Khalisat tahau girgixa kai tana fadin "ciki babu wanda xan iya gaskiya in akwai me
sauki agayamin amma walh baxanyi wadannan ba.
Bokan yahade rai yace "Ashe ba mallakar kikazo yiba, maxa kutashi kuficemin anan
tunda da wasa kukaxo.
Sumsum kuwa ta mike tafice khairat tabi bayanta tana mata tsaki danta kularta
dayawa
Suna futa suka jingina ajikin mota sukai shiru kowacce tana nata tunanin
Khalisat tace "nayanke shawarar hakura kawai domin naga wannan hanya bame billewa
bace aguna haba khairat yama za,ai nabaiwa wannan kazamin tsohon jikinah tabdijan!
walh baxan taba bari yayankamin fatar gabana ba shiba likitaba Bakomaiba kuma
natabbata inharma na rubutun jinin hailar nayi abanxa zanyi don bana jin gadanga
xaisha abu ahannuna ayanxu batare dana tare agidansaba shima nasan sainayi da
gasken gasken
Khairat taja tsaki tace "kinsan Allah kinbani mamaki kina abu tamkar ba maceba
kinganni walh danice da tuni anwuce gurin
Khalisat tace "to tunda bake bace sai awuce gurin mukoma gida na hkr kawai abinda
Allah yayi Annabi sai ceto
Tabude mota tashige sit din dreba khairat ma ta shiga ranta abace
Khalisat ke tukin zuciyarta cike da mamakin wadannan bokayen ashe kenan duk wacce
kaga aikinta yaci take to ta saba hanya knn? Lallai masu bin bokaye da malamai
sunyi nisa kuma suna tafka tsiya ita kam bada itaba.gara ta jajirce wajen ganin
tasamo soyayyarta gun gadanga da kissarta yafi
Ta ajiye khairat agidansu ta wuce babu sallamar arxiki atsakaninsu dantaga khairat
din haushinta takeji
******
Momy jajirtacciyar uwa domin tasa anxo har gida ana yiwa amare gyaran jiki
Haka magungunan mata bata bambanta suba kowacce kai daya tabasu tsumi dana tsarki
da sha da madara
Sanin khalisat abude take tasa ita nata harda na matsi tabata don inta tuna "yar
tata tasheke ayarta awaje ranta quna take taringaji inama zainabu yarinya
nitsatstsiyace "yarta
Da aka tsaida ranar tariya ma ana gobe zasu tare tasa wata kawarta takawo musu
farfesun nama kwalli bakwai bakwai kowacce da ruwan rubutu aka dafashi da magunguna
aciki shi wannan abadan yana jikinka inkaci sai namiji yarasa kansa zaijishi ackn
kogi,fadama,rijiya😂 kunemi mai wannan hadin ta hannun Nabilancy
Kayan furnitures sunyi matukar yin kyau yan dubai dubu dari biyar biyar haka
yakashe w kowaccensu
Kicin din amare cike taf da tsadaddun kaya wannan daga hjy laila ne momy
Aranar da za.a kai amare kuwa kaya iri daya momy takai musu
wani tsadadden less ne wanda yafi karbar zainabu dan yadace da kalar fatarta sbd
milk ne da kwalliyar pink ita zee choculet kala ce khalisat kuwa fara ce kar
Itanma khalisat bab ayaba saidai ina! Da gami baxata kamo ziza zee zee bah
Kutara a next page fans kuji wace zata fara shan wannan dadin na gadanga ????
*Short Story*
*Nabilancy Luv*💘
(Auntyn S&S)
page
2⃣5⃣
Tankwasheshen gidan Gadanga yafi kowane gida alayin kyau da fasali shankwamemen get
ne agidan wanda aka kawo me gadi daga kauyensu mudi yafara aikinsa tun kafin akawo
amaren
Ba wasu gayya momy tayi akai amaryar ba motoci biyune jal daga ta amarya khalisat
saita amarya zainabu
Kawayen momy su biyune sukazo mata kara sai "yan uwanta guda uku don danginta kaf
suna Zamfara da sakwkwato a ranar daurin Aure wasu sunzo sun kwana daya suka wuce
sud'in masu kudine na gasken gaske.
Hjy Aisha da Hjy ma,inna sune yayyen momy sune ackn motar da khalisat take sai
khairat aciki babbar kawa
Amotar Da zainabu take ciki kuwa mummyn khairat ce aciki sai kawayen mummyn Sai
dije me aiki databiyo ayari amatsayin kawa itama
Kowacce aka mikata part dinta wanda yaxamo babu wani bambanci atsakani koda na
kujeru da kayan kallone haka labulaye iri dayane
Yanda sukayiwa khalisat Nasiha haka akayiwa zainabu ma dama tun agida momy da dady
sun hadesu anyi musu nasihohi akan su hade kansu su kyautatawa mijinsu
Yanda aka watse aka bar zainabu ita d'aya tsuru sai abin yabata tsoro bataji motsin
komiba saina karar AC data jiyo acan falo Shuuuuu
Banda Allah yasa tafara sabo da jin karar na,urar data kudunduna don tsoro to
tanajin karar agidan momy
Gadanga sai karfe taran dare yasho bangaren nata mudine yakawoshi yanata masa tsiya
ahanya
Dayake saida suka tsaya a yahuxa suya yasai kaji guda biyar kulli daya aka saka uku
dayan kullin kuma aka saka biyu shine na khalisat
Bata falon saiya nufi bedroom yaganota kwance tsakiyar gado tafara bacci
Tabishi da kallon takaici don tayi tsammanin adakinta xaifara kwana lallai wannan
ai dixgine salon yarinya ta rainata xai nuna mara rashin matsayinta knn
Takaici yasa batabi takan namanba ma balle sallar ishsha,in dake kanta nan ta
bingire tahau baccinta dan ita kam akwai saurin bacci
Ita kuwa zainabu idonta ko gexau ba alamun bacci ina zata iya bacci bataga gadanga
yashigo ba
Saida tashi sallamarsa yashiga kana taja ajiyar zcy wanda saida yajita
Yazauna kusa da ita da murmushinsa yajata jikinsa yace "my zee kingaji da jiran
angwanki ko yi hkr naji kina ajiyar zcy bakiyi fushiba ko?
Saida taji zai wuce gona da iri kana ta rike hannunsa dake ckn rigarta wanda yake
gogar breziyyarya
Tace "a,a kai nake jira kazo sai inyi don bansan inda zanshiga insamo bandakibane
Yajanyo hannunta yasauko da ita dg kan gadon yanufi toilet da ita yanunnuna mata
komi yabarota tana alwala
Saida yaciyarta naman kazar nan ta koshi ya diddika mata yoghurt dakyar ta iya cin
rabin kazarma
Itakam yau gabanta keta faduwa don tasan anxo gurin fatanta dai Allah yasa Aliyunta
yai mata da sauki a yau ……
*Short Story*
*Nabilancy Luv*💘
(Auntyn S&S)
Page
2⃣6⃣
Yau yasha Amarci wanda yamantarshi abubuwa da dama ciki harda mancewa da wata matar
dayake da ita wai khalisat
Tabbas Aure akwai dadi kusan kwana yayi yana gurxar Amaryarsa yana jiyar da kansa
dadi yayinda ita takeshan wuya amatsayinta na cikakkiyar mace
Tasha kuka da ihu haka yasha cixo da yakushi duk don azabar datakeji amma gadanga
bai bartaba sai gefin asubahi
Ajigace baccin yadauketa tanata ajiyar xiciya tab🤔 ai dole Zee taga banu sau hudu
fa yayi yana hutawa
Koda aka kira assalatu shiya fara tashi yashige toilet yayi wankan tsarki tareda
dauro alwala yazo yayi nafilfilinsa
Amma takasa tashi daya fahimta saiya dauketa calak yakaita har ckn kwami yace
tayo wanka tayi alwala yana jiranta afalo
Dayake yahada mata ruwan dumin saita fara, ganin yafuta domin baxata iya
agabansaba don kunya
Ya amsa yana me shi mata albarka " zainabu Allah yayi mk albarka Allah yabaki
aljanna yakuma baki yara masu kyakykyawar tarbiyya irin taki da ace haka kowacce
mace budurwa take rike budurcinta bata yadashi a kwararo tabbas da mata sunburge
agun maxajensu kuma da sun xama abin koyi naji dadi sosai dana sami abar sona
acikakkiyar mace fatana dai Allah yabamu yaya masu albarka
Ahankali tace "Amin, itakanta tayi farin ckn hakan taringa murmushi kasa kasa
Sai wajen karfe sha daya na safe kana yashiga bangaren khalisat ba dan ransa yasoba
don dai yashiga yafutarda hakkine kawai don ko babu komi inyashiga yaga yata kwana
zai fita agun ubangiji
Daya shiga yaita mata sallama yaji shiru yakutsa kansa dakinta yaganta abararraje
akan gado sai shararr bacci takeyi
Haushine fal aranta nayanda yatafi jiya da dare yabarta babu wani tarayraya ko wani
making love amatsayinta na yar,uwarsa
Yace "ke baxuwa nayi kiyimin shan qamshiba naxone inga ko kina bukatar wani abun da
bakidashi akicin insiya miki sbd infita hakki.
Ta yatsina fuska tace "ni ai babu abinda nakeso ayanzu bayaga mijina kuma tunda
yaimin nisa shikenan . Karasa maganar da xumbura bakinta
Yace "tabbas nayi mk nisa inma zaki cireni arai gara ki cire.
Ranta abace
Yace da gadara "eh haka nace din ko har kin manta irin karan tsanar da kk doramin
ada can
Yaci gaba "ai banxaci akwai ranar da har zaki budi baki kinuna muradinki muraran
akainaba
Aidama duk mutimin da akace yasaba harka to tabbas inya dade baiyiba to akwai
matsala dole maita ta fito muraran toki sani gara ma tun wuri yawunki yakoma don
kwalelenki ni din mallakin xainabu ne
Inkinga zakiyi xaman gadi tokiyi baxan matsa mk ba zankuma fita hakkinki ta gun
abinci da tufafi amma kisani bakiyimin ba sbd kin gama xubda mutumci da darajar da
Allah yayi mk awaje gun maxan banxa dan haka ki kama bakinki tam ! Yaja tsaki
yafice
Harda hawayenta to me Aliyu kenufi wato knn saidai yakalleta baxai lasa mata xumaba
knn tab aiko walh bai isaba dan ko da halin danbe saiya bata hakkinsa ko ayi uwar
watsi bari kwananta yaxo
Khairat tace " to me xance mk khalisat ai kuma banda tacewa akanki tunda baxaki
nemi taimakon malamaiba nikam saidai inbaki hkr ko insa ido...kiyi hkr kawata
shawararki nakeso ko yaya take natuba
Khalisat tace " wama yasani bai min bayaniba sbd banda matsayi
Khairat tahau fada "walh kada kibari namiji yarainaki kawata tun wuri ki kwato
"yancinki kafin kixama bora tunda baxakiyi asiriba
Khalisat tace ckn kwantar da murya "to yaxanyi _plz give me gud advise_
khairat tace "to nikam dai solution daya yakamata kifara kafin musan mezamuyi dg
baya kiringa kissa kala kala tarinjayarsa sannan kizama mekwantar da murya agunsa
da biyayya kiringa shige masa da nuna masa dirinki me kyau tahanyar bayyanawa inya
shigo kuma kice lallai lallai kinaso yadawo dakinki agobe kokuma ki gayawa su dady
sbd inkika barshi zai iya sati kuma tunda tare aka kawoku kinga matsayinku daya ba
uwargida acknku duk amarene kada kibari ace itace gaba dakema ato. 😏
Nan sukai sallama taxabga uban tagumi tana tunanin Anya wannan hanyar zata b'ille
mata kuwa……??
*Auntyn Sayyada da Shahida ce*👌🏼
*ALI GADANGA...*
🏹🏹🏹🏹🏹🏹🏹
*Short Story*
*Nabilancy Luv*💘
(Auntyn S&S)
Page
2⃣7⃣
Kwance suke Ackn bargo suna manne da juna zainabu ta shige jikinsa sosai tana
magana da shagwaba "Dan Allah Aliyunah kada karabu dani ina sonka karikeni amana
kaga ni marayniyace inka rabu dani mutuwa xanyi dan baxan juri zama aduniya babu
kai atare dani ba kada kajuyan baya nan gaba don..…… yatoshe mata baki da hannunsa
Dayan hannun kuma yahau shafa mata baya dama ba kaya ajikinsu
"Kiyi shiru Abunah kidaina zancen rabuwa atsakaninmu ina mk son da babu wacce zan
iya yiwashi arayuwa nima ba iya rayuwa zanyi babu ke ba kinjiyar dani dadin da
bantaba jiba kuma baxan taba jiba inba ina taredakeba kuma nima fa marayan ne
hargara ke to aname zan iya rabuwa dame bani gata ta marairaita ni haba zee ai babu
wannan maganar
Yaji wani magana disu yana shigarsa yaji sha,a warsa data tafi na mintuna biyar
baya tana shirin dawowa gashi zainab din tana masa wani abu akunne me kamar busar
algaita
Ya birkitota samansa tayi rufto akan kirjinsa saida tace "wash!! Cikin kissa
Duk da takusa tafiya itanma amma saita hau kukan karya tana fadin "darling kabari
sai anjima mana ina bukatar hutu haryanxufa bandaina jin zafin ba
Yasan tabbas tana juriya sbd ayanxun ma sau biyu yayi sha,aninsa kuma dagasken
tanajin zafi to ai sai ahankali komi zai dawo normal
YYi dif ya kyaleta yana maida ajiyar zuciya amma ya ruk'umk'umeta ajikinsa kamar
wanda za.a kwace masa ita
Yace mata "Zee ina jinki araina gashi gobe inaso inkwana bangaren khalisat...!!
Wani giiirrrr! Zainabu taji akirjinta banda ya ambaci sunan khalisat din ita tama
mance da cewar ma tanada wata aba kishiya
Tayi diff tadaina masa wasan da take yi masa na shafa kansa da take
"Kingane ne bawai da wani abu nafada ba kodon ina so inje inji wani abu agunta a,a
kawai dai nufina anan shine kinga itama budurwace dole innayi mk sati to itanma
satin zan mata dole kuma bazan iya kwana bakwai banji dumin kiba kinga gara muyi
dabara inyi mk biyu inje itanma inmata biyun inkuma kinaso inyi maki satin ne
itanma inje inyi satin agunta to?
Tace ckn sanyin murya "a,a ka koma goben yafi gara muringa kwana bibbiyun amma
wacece uwar gida ackn mu?
Yace "kece mana zainab ai itama tasani kowama yasani tsiranku da tazara kinfi wata
da zama matata kana aka bani ita amatsayin mata duk da kunshigo gidannan tare kuma
ubantane yabani gidannan yamaidani cikakken mutum hakan baxai saka inmaisheta uwar
gidaba dole kece amatsayin babba zee sai abinda kk ce zamuyi dagani har ita
Ahhh!😅su gadanga ne haka? Ahhh lallai anji dadin wani guri dole akwantar da kai
yamance zainabun daya lakada akan wani yamance zafin ransa toko dai ya canxane???
zainab datayi lakwas tace "to aikamata yayi kataramu agu daya kafada kowa yaji kuma
kayi mana nasihohi akan zaman tare kakuma kakuma kafa mana dokokinka amatsayinka na
mijinmu kokuwa ?
Yahau gyada kansa "tabbas hakane, kinmin tini kuma ayau za,ai hakan tashi muyi
wanka sai inkirata taxo bangarenki ayi maganar.
******
Haka kuwa akai Domin daya shirya kai tsaye yashiga part din khalisat yasameta
akwance akan doguwar kujera daganinta kuka tayi dan idonta yayi jajir alamar ansha
kuka
Yace "oh sannu may be tunani yasa mk ciwon kan kinsan tunani dasa abu arai ba yanda
bayayi kinsha magani?
Hhhmmm gadanga kenan da gayya yafada dan yasan halin mata ko karya takeyima
Yace "to taso muje dakin zainabu zanyi magana daku duka?
Taji sarai rantane yabaci dajin hakan dan wannan ai wulakancine da xaice mata wani
wai taje dakin zainabu aname dan akaskantar da ita.
Tace masa "naji mana gani nayi baka tausayina bayan nace banda lfy kuma sai asani
tafiya wani waje in andamu ayi maganar dani ace ita tashigo part dina mana.
Yace "baxance taxo dinba ke nace kije nata kuma dole nace bajin ra,ayi ba.
Yajuya yace "maxa kibiyo bayana kitaho inba hakaba baxaki kara ganin kafata
adakinkiba.
Dataga dagaske yake maganarsa ai tuni ta tashi tabishi xugui xugui da kananan kaya
ajikinta mini skert da body hug me karamin hannu ta dameta kamar yadda siket din
yamatseta kanta tasa hula ta yayi
Yaso yace takoma tasako hijab to amma gudun kada ta bata masa lokaci kuma gidan su
kadaine yasa yakyaleta kawai
Zainabu tana zaune akan two siter kallo takeyi hankali akwance taji shigowarsu
Kwalliya ta tsala da wani swiss less takashe dauri mekama da ture kaga tsiya hhhhh
dije ta iya koyar da dauri dakun gani dakunsha dariya to amma fa kayan yafito da
ita dan tayi azababben kyau wanda ko randa aka kawota datasa galila bata kai yau
kyauba
Khalisat kanta saida ta furgita da ganin kyan da zainabun tayi taita kallonta sai
ayau tagano ashe haka zainab keda zallar kyau
Taringaji inama ita keda kyan zainabu da baxata zauna tayi rayuwar nigeria ba sai
turai
Tayita kokwanto shinma gashin xainab dinne ta xuboshi har gadon baya ko itanma irin
natane na kari ??
Bata samo amsar ba gadanga yakatseta da cewa
"Ke khalisat kinsan da cewa zainabu itace matata tafarko kuma bawai na karbi
aurenki bane don bana sonta na karbi auren kine dan wasu manufofi ciki harda rufin
asirinki...takatseshi
"Dakata dan Allah wannan fa kamar cinfuska kakeso kaimin knn dama kiran kenan?
Ya girgixa kai yace "banyi wannan maganar da nufin ci mk fuskaba na tarakune danna
nunawa kowacce matsayinta aguna da kuma matsayinta ackn gidannan da kuma fadakar
daku yanda zaku xauna dani lfy domin kunganni banason tashin hankali saidai inyazo
adole nake karbarsa
Inaso ki sani ke zainabu kece amatsayin uwar gida kowa yasani babu me canxa hakan
dan haka inaso kixama me kama girmanki kada kizamo kinxama me tada rigima
atsakaninku duk da bansanki da tarxomaba haka kuma akiyaye bacin raina banida dadi
duk wacce tayi badaidaiba zan mata hukunci me tsanani sannan ku hade kanku ku hade
kanku inhar kunason zama dani.
"Kema nadawo kanki inaso amatsayinki na karama kece karama yazamo kinbata girma
kuma banason yaxama kinxamo me tada min fitina don baxanyi tolerating nonsens daga
garekiba nasanki nasan halinki nan gidan Aurene bawai gidan haya ko gidan zaman kai
ko gaban iyaye da za.ayi iya shege ba dolene ayi biyayya in anason zaman lfy dan
haka kisani uwar gida zainabu ta yanke shawarar indawo dakinki agobe kawai tanaso
inringa muku kwana bibbiyu kawai dan haka saiki gode mata data zamo uwar gida
agunki me adalci ……
Su khalisat anshaka ankasa hkr ta karkace baki tareda jan tsaki tace "Allah ya
kiyaye inyi godiya gun wannan kucakar yarin...
Ya mike afusace zaikai mari tuni zee tayi saurin rikoshi tana fad"haba habibi
saurin fushi ba naka bane bakyau dukan macen Aure kayi hkr shi yaro hakuri ake
dashi akoyaushe. Kambu 😅 zee ta jangwalo rigima
Khalisat ta nunata "ke bakauyiya ki iya bakinki niba yarinya bace mara aji irinki
yarinya tana can kauye adakin kasa me rufin kara
Zainabu taso ta mayar mata dacewa "ita me ajice tunda ba sadaka aka badataba to
amma ba dama dan gadanga ya hankada khalisat din waje yana mata fada kamar yadoketa
Zainabu harda kwallarta najin xafin maganar khalisat tabbas dole tazama me baki
bazata bari taringa taba mata iyayeba don iyaye sunfi komi taci darajar gadanga
amma ajuri xuwa rafi ……
*Short Story*
*Nabilancy Luv*💘
(Auntyn S&S)
Page
2⃣8⃣
Aliyu Gadanga yadawo kusada Zainabu yana rarrashinta ganin tana hawaye
Saida yaga ta hkr ta daina xubda hawayen kana hankalinsa yakwanta yajata xuwa
dakinsa don yakara mata rarrashin na musamman
Itako khalisat zarya taringayi afalo tana cizar yatsa domin wannan abu yatsaya mata
arai wai yau ita gadanga zai mara sbd wata? Yau ita akaiwa cin fuska
Saida ta zubda hawayen bakin ciki kana taji ranta yai sanyi wannan Auran kuwa zata
iyashi? Ta tambayi zcyrta
Zaki iya mana amma inkin kwantar da murya!!!,inkin ringa tausasa kalaminki!,inkin
zamo mebin mijinki,!!!inkin zamo meyiwa mijinki ladabi da biyayya!!!uwa uba inkin
xamo me rokon Allah akan yarinjayo mk zuciyarsa kanki!!!!...
Ta zauna tayi tagumi wadannan zantukan nayawo aranta wato dai wadannan sune
mafitar?
Tace Afili " Aliyu ina sonka zanzamo meyin biyayya agunka dabin maganarka Amma ta
yaya za.ai kasoni kamar yadda nake sonka?? Meyasa baka sona ne Aliyu?why??
Lallai yakamata tayi hakan shima yana ckn kissar da kawarta tace taringayi wani
namijin yanada zcyr tausayi da raguwar zuciya akan mace to shin Aliyun nada tausan
kuwa???
Batada wannan amsar ita dai kawai taci damarar samo soyayyarta kawai shine
Saikuma ta hade ranta data tuna cewar wai waccan yar kauyen ce tabada umarnin
yadawo mata, tana nufin knn ita ishashshiya ce agun miji watoma baida ra,ayin kansa
sai nata lallai saitayi da gaske kan yarinyar can inba hakaba xata mallake gidan
itako baxata juri iskancin kishiyaba duk da bata mata kallon kishiya sai kallon yar
Aiki yar kauye.
Da dare masoyan suna manne da juna tayi lakwas ajikinsa tana masa shagwabarta
"Yanzu Mijina gobe baxanji dumin jikin kaba nawata xakaji bani ba...
Ya toshe mata baki yana cewa "hakanace mk zanji dumin wata ? Kinga alamar ina
muradin jikinta ne ? Itanma tasan ban damu da komi nataba ki kwantar da hankalinki
ke kadai nakewa kallon mace kuma ke kadai ce zanwa so baxan hada sonki dana wata ba
fatana ma kece uwar "yayana
Hhhmmm mata da kishi ake haba zee yakamatafa kiji tausan yar uwarki mace kada
kishin mijinki yarufe mk ido,domin ma khalisat tafiki bukatar abar, tunda tarigaki
d'and'anar bananar gadangan!!Au kada zainabu taji nahada fada😷😅😅
*******Aranar da Angonta zai dawo dakinta tayita rawar jikin yin komi
Akayi masa girki kala uku duk bawani dahuwa yayi yanda akeso ba tunda ba.a iya ba
ba girki take agidaba ansaba cin na "yan aiki a littafi ta karanta tayi ko kamshi
bai fito ackba garama kuskus yai kamshi tunda yaji kifi da curry da albasa
Ta xauna akan kujera sharaf ta ringa nishi hhhmmm mata anyi aiki angaji
Saida tahuta na mintina 20 sannan na mike da sauri ganin magrib ta kusa tasan
lokacin dawowar gadanga yayi don bataji shigowar mota gidanba
Kwalliyace kawai agabanta to agida anraina iyaye ba.a bin maganar uwa balle ayi
koyi da ita momy tayi iya bakin kokarinta na ganin khalisat t taso da ibada amma
ina Allah bai bata ikon daukaba don intayi fada saidai tayo mata gunguni tana kuka
tana dire dire wai ita antakura mata daddy yayo kan momy da fada adole komi ta xuba
mata ido baiwar Allah tanajin ciwon abun haka ta hkr to garanar taxo anyi aure ba.a
kware akomi ba
Tatsalo kwalliya da english waers "yar b'igil din riga iya cibiya yellow da jan
wando pencil yazauna akan diri ga kirji yaciko yasha breaziyya me k'ok'o gashin
kanta sai kyalli yake yaji gyara
Ta dawo falo ta hakince ta kunna kallo MBC 2 ne wani american suka sako amma ita
hankalinta ba.a gun yakeba don bata fahimta kwata kwata tadai xuba idanune amma
hankalinta nacan gun Aliyu tana ayyano irin soyayyar da zasuyi ayau
Aliyu bai shigo gidan da wuriba dan sai bayan magriba yaje gidan dady ne akan
muhimmiyar maganar da dadyn akawowa gadangan
Dady so yake Gadanga yakwaso abokansa da yaransa kaf yadawo dasu kano zai basu Aiki
kowanne dan cigabansu yake so
Akwai vacancy sosai saidai yafi so yakawo nasa kafin yaxuba yan gari don yanajin
yan kauyensu tamkar yan,uwansa suma suna sonsa sbd yanda yake yi musu tabbs da ace
zai futo dan takararsu zai samu quri,unsu
Dady yace masa "to Aliyu meye na godiyar dan kaina nayi kuma dan Allah duk da komi
xasu samu ta dalilinkane kaima inaso inga ina faranta makane sbd rikon amanarka da
kaunar dake tsakanin mu gashi kuma kana yiwa "yata rikon amana
Tabbas dady mutum ne kuma ubane agunsa yakamata yanda yake masa shima yasaka masa
da khairan
Yaji aransa baikamata yaringa yiwa khalisat abinda yake mataba zuciyarsa ta karye
akan abubuwan da yake mata duk da ita tajanyo to amma ai akullum baiga tayi nadamar
halayen taba
Koda kuma xai mata sassauci baxai iya hada sonta dana Zee din saba
Part din zainabu yafara shiga duk da yau kwanan na khalisat ne to amma ai dolene
yashiga yaga abar sonsa suyi sallama
Ita bata zaci bama zaixo mata ayau din datajishi shiru
Yayi murmushi yace "anya kuwa dear kodai rashin lfyr tafiyata wani dakinne
yakamaki?.
"Kiyii hkr zainab kada kitashi hankalinki kullum fa muna tare babu kuma abinda zamu
fasa can fa kwana kawai xanyi babu abinda zanyi acan.... "a,a ni ban hanaka bata
hakkin taba kada Allah yakama mu baruwana
Yace "ok, kinga yau na dade ko? To walh ddy ne yazomin da wani zance me dadi kinsan
me yace ?
Yaci gaba "dady yace inje kauye inhado kan abokaina da Duk yarana zai basu aiki a
sabon kamfanin daya bude nashinkafa...
Da sauri ta mike daga kwancen da take da murnarta tace "kai naji dadi amma, yaushe
zaka tafi kauyen?
Ckn marairaita tace "to amma dai dani zaka tafi ko?
Ya kyalkyale da dariya yace "inafa so kk gwaggwonki tayi mana fada itada iyata suce
daga aure munzo tare kibari sai kindau ciki sai muje tare nan da wata uku ko
Itako kunya taji tayi saurin rufe fuskarta tana fadin "nidai a,a gaskiya ba yanxu
zanyi cikinba.
Yariko hannunta tareda dago fuskar yace mata "to sai yaushe?
Saida yasadata da farin ciki sannan yabarta yatafi part din khalisat ……
*Short Story*
*Nabilancy Luv*💘
(Auntyn S&S)
part 2⃣9⃣
Khalisat na nan afalo ranta na quna tasan Aliyu nacan tareda zainabu wato yama
mance da ita knn tunda taji shigowarsa kusan awa guda knn
Da saurinta ta taso tazo tayi masa sannu da zuwa tareda kawo hannu zata karbi breaf
case dinsa (jakar Aiki)
Yaso yahanata to amma kuma yaga hakan baidace ba itama fa matarsace kuma duk abunda
zai mata na cusgunawa iyayenta baxasuji dadiba insunji
Saida sukaje ckn daki ta ajiye tana fadin "sannu da xuwa mijina.
Tafada tana kallonsa tana murmushi
Ganin zai sille kaya yasa tafita tashiga kicin ta dauko abinci takai masa falo akan
center table ta ajiye
Tashiga da sallama dakin ta tararsa yasa ka jallabiya tace masa "ga abinci can
nakai maka falo
Yakalleta da hade rai har zaice mata ya qoshi kuma saiya fasa ganin ta marairaice
fuska kuma sai yanxu yaga kayan jikinta yakare mata kallo tayi kyau Amma yaji inama
xcyrta ma me kyance
Taji wani dadi ganin yana kallonta ckn kissa tajuya tana rangwada duwai dinta na
motsawa gwanin sha,awa don khalisat akwai hips
Ga fatarta akwance tana sheki yabita da kallo banda sha,awarsa anesa take da tabbas
zata iya tashi ayanzun
Saida yadauro alwala yasallaci ishsha,i kana yafito yayi sallarsa adakin sannan
yafita zw falon
Yana zama akan 3 seater yadau remote yacanxa tasha zuwa Arewa don kallon maimaicin
shirin dadin kowa
Tana kusa dashi akan 2 seater saitayi sauri ta sauko kaza tahau zuba masa kuskus
din a plate
Harda juice ta hada yayi sanyi kuwa dan shirme harda indomie fa ga kuma joloup na
shinkafa
Ta miko masa plate din kuskus din da ladabi yakarba yafara ci da bismillah
Lomarsa uku dakyar ya iyaci magi baijiba bai dahuba babu wani gud testing sai
kamshin kawai
Ya tsiyayi ruwa yakora don lemo ba best drink dinza bane dama dai xobo ne
Tana kula dashi bata kawo aranta ko rashin dadin girkin nata bane yasa ya ajiye
saita hau bude masa sauran kwanukan "azuba maka wannan ??? Ta tambaya tana
kallonsa
Yagirgixa kansa yace "na koshifa na biya gidan momy taxuba min abinci naci.
Tace masa "Allah sarki momy amma dai tace tana gaidani ko?
Babu fara.a afuskarsa yace "eh tace tana gaisheku tabani kaya aleda ma tace nakawo
muku yana but din mota.
Hhhmmm wato harda zainabu tabada knn aitasan momy bata kishinta batasan me yasa
takeson yarinyar can ba me kama da bulala.
Yasan tambayar su mudin datayi najan baki ne don yace wani abun aibai mantaba yanda
take ciwa su mudin mutumci alokacin tana hida sukuma shakkarta sukeyi to yanzun
meye nawani tambayarsu
Daya gaji da xaman ma tashi yayi yabar mata falon yakoma daki yakwanta bafa baccin
yakejiba
Karaf akunnenta taso takoma amma saita dake tadage tarinjayi xuciyarta domin akwai
qudirinta ayau
Ta durkusa gaban gadon tafuskanceshi ckn rage murya kamar xatayi kuka tace "Aliyu
dan Allah kayi hkr da duk abinda ya taba wakana mara dadi atsakaninmu natuba nayi
nadama baxan sake ba
Tahau kukan karya "walh baxan sakeba na tuba nagane ba abune me kyauba wulakanta
dan,adam haba mijina inasonka inaso yaxamo naxami aljanna tasanadinka
Taci gaba "walh xanmaka biyayya Aliyu duk abinda kace inyi zanyi kuma zanyi biyayya
ga zainabu amatsayinta na uwar gida bazamuyi hatsaniya ba insha Allahu.
Tuni yadauka hakanne data fada yatashi zaune yakalleta da nutsuwa yace "kintabbatar
abinda kk fada har zuciyarki ne?
Yaja ajiyar zuciya yace "naji nayarda shikenan komi yawuce Allah yasa dagaske ne
kuma sainagani akasa.
Tayi murmushi tace "zaka gani ma insha Allah.
Ganin hakan yasa taje ga sif dinta taciro kayan baccinta hadaddu taxira tareda fesa
turaren bacci me sanyi da tada sha,awa taje bayansa ta kwanta ta matsu dashi
yanajinta baiyi mata maganaba
Har ransa yafara sakkowa kuma inya tuna ta baiwa wani kanta harda yin ciki saiyaji
kuma wani abu yatokare masa arai yaji sam baxai shiga ba don yanada kishi gadanga
kowa yasani
Har bacci yakwasheshi batayi baccinba don taso ace ayau tarinjayeshi amma taga
Aliyun baida sha,awa akusa dole ta hkr gadai suga akusa da ita amma ba damar
dandanawa har sakala hannunta tayi ajikinsa amma ina baisan tanayibama yayi
baccinsa
Da asuba yatashi yaje yai sallah yadawo yatararta tana baccinta hankali kwance
Yagirgixa kai da takaici da alamar bata saba sallar asuba akan lokaci ba tab yatuna
xainabunsa jiya ita ta tasheshima aranar farkone ma yatasheta don yai mata uxurima
sbd agajiye take amma yatabbatar zainabu tanada ibada
Tahau yamutsa fuska wai nan bacci bai ishetaba ganinsa atsaye akanta yasa tayi
saurin tashi xaune
Yace mata "maxa tashi kije kiyi sallar asuba kada lokacinta ya gudu.
Yazauna gefen gadon yace mata "ban ganeba?kina nufin bakiyi sabo da yin salla akan
lokaciba,?to baxamu taba shiryawa dakeba domin ita sallah itace kan gaba a addini
kuma itace xata ceceka akabari sannan Allah fa muke gaidawa kuma alamun munafiki
zaibayyane ne muraran inya kasance meqin sallah bakuma xan iya xama dake inkina
kinyin sallah akan lokaciba.
Tajishi sarai takuma yarda da batunsa da sauri ta mike ta shige toilet dan dauro
alwala
Baccinsa yakoma baitsaya ganin tayadda take sallar ba dakwa tasha gyara
Yarigata tashi da safe harya shirya yafuta bata tashiba saida ta tashi taga wayam
Saida yashiga dakin zainabu yaganta tagaidashi yayi mata kiss akumatu yace "akwai
wani abunne? Tace "a,a babu.
Amma yadade a part din zainabu sunsha hirarsu ta masoya yabata sakon momy wata
laffaya ce ackn ledar da turare da doguwar riga yayan tane ya dawo daga saudiyya ya
aiko mata da kayayyakin
Yayan momy me kudine sosai yanaji da momyn ita ke binsa a katsina yake
Yanda kayan ckn ledar zainabu yake haka ma na khalisat din yake
Zainabu tayi murna sosai dukda ba iya nada laffaya xatayiba ama doguwar rigar tayi
mata kyau
Khalisat tana can adakinta tashaqa sosai domin taji dawowar gadanga tun yamma amma
bai shigo mataba sai bayan magriba
Bata isa ta nuna jin haushin taba tunda so take tasamo kansa
Yau kam taso Aliyu yajiyarta dadin amma yai mata biris duk yadda takwanto abayansa
tana masa tausa hakan baisa yatabata ba ammafa yaji maganad'isu nashigarsa wato
sha,awa dai tafara motsuwa 😅 muje zuwa khalisat mahakurci mawadaci
*******
Wata guda dayin tariyarsu Alokacin gadanga yaje kauye yahado kan mutanen da zasuyi
aiki a kamfanin dady sunyi mutane 40
Sosai mutan kauyen sukaji dadin hakan babu wanda yanuna baxai xo burniba murna ma
sukai su to wannan ai cigabane yaxo musu to albashifa dubu talatin talatin zasu
samu wanda akauyen duk buga bugar da suke awata basa samun 20 aikin gini da diban
yashi a jaki yafi karfi ma akauyen sai masu hakan rijiyafa da masai wasu kuma dama
yan zaman banza ne sunfi yawa
Ba tsofaffi ciki duk samarine da magidanta masu aure masu jini ajika
Gidaje dady yakama musu na haya kafin yagina musu dan Estate da zasu zauna kowanne
gida mutane hudune aciki dubu hamsin shekara zai biya
Sunkuma fara aiki ka,in da na,in basusha wata wahalaba don akwai wasu ma,aikatan
baya gasu
Gadanga ma yana kula da kamfaninsa na Rooffing Saman gida dasu kayan gini na zamani
dai wanda ake shigo dasu daga waje
Alokacin suna wata biyu da tarewarsu agidan zainabu tafara laulayi bata cin komi
kullum tayi amai yakai uku arana ko kamahin turaren gadanga batasonji
Momy ta aiko mata da dije takula da ita dasuka dawo gida don kwananta uku a
asibitin aka sallamesu
Har lokacin Aliyu baibada kai bore yahau ga khalisat ba kullum kuma cikin nuna
kissarta take donta rinjayeshi
Yafara cin abincinta domin tafara gyarawa tun zuwan khairat tayi mata taci taji
yanayin girki baikai acishiba aiko taringa mata fada "ke yanzu haka kk yiwa miji
girki baya dahuwa kk saukewa bakuma yajin maggi lallai xaki kashe kanki to tun
wurima gara ki gyara don kinganni nan walh duk hutun da nake ciki agidanmu inayin
girki ina shiga kicin in taya mommyn mu sbd dadyna bai yarda dame aikiba
Nanfa taringa nunnuna mata akwanakin da zainabu takwanta a asibitima kullum take
xuwa tana koya mata wasu abubuwan har girki sukai aka kai asibitin
Aranar momy taji dady har ranta don tayi zaton khalisat din zaman daditake da
zainabun batasan duk khairat ce tamatsa sujeba duk don su burge Aliyune kuma yaji
dadi shima
Abinda khalisat ta dage dayi shine addu,a akan Allah yarinjayo mata mijinta kanta
dan yabata hakkinta
Addu,arta kuma ta karbu alokacin da zainabun tana asibitin don kasa jura yayi saida
yashiga rijiyar khalisat din
To sai lokacin hankalin khalisat yakwanta ganin Aliyu yajiyarta dadi yakuma fara
sassauta mata lallai addu.a takobin mumini ce ta yarda
itako zainabu takanta takeyi don koda aka sallamota bata ta gadanga ko yana dakinta
bata bashi hakkinsa ji tayi abin yafuta aranta ma
Sbd son dayake mata yasa yai mata uxuri kuma yana samu agun khalisat saidai baikai
yadda yakesoba kamar gun zee dinsa
Saida cikinta yashiga wata biyar sannan ta dawo dai dai komi yai normal tadawo yi
masa girki inyana dakinta tafara bashi kanta amma ada bata iya komi to koyaushe
bacci kasala batacin komi inma taci amai ne kwadon xogale kawai takeci fa sai tuwon
dawa da dijen ke mata sai ruwan lipton datakesha amma data dawo komi yai nrml sai
dije takoma gidan momy shima yahuta da kawo dafaffen zogale
Ma,aikatan dady hankalinsu kwance suke aikinsu suna daukar salarynsu duk wata
mutun goma wasu ke xuwa kauye ganin gida insunyi sati saisu dawo wasu suje da haka
har sukai sabo da burni yaxamo ma sai sunga dama suke tafiya saidai suyi aike kawai
dady yana musu adalci sosai haka akeso kuma, Allah yabamu shuganni adalai
Ranar wata lahadi watan zainabu uku da kwanciya a asibiti knn tana kwance agado da
cikinta qurbibi kamar ankifa kwarya ajikinta
Safiyace wajen 11am tunanin gadan takeyi yana dakin khalisat haushine fal ranta
yasaba fito da safe tara ko takwas inba ranar aiki bane to amma yau gashi har shine
fin shadaya lfy?
Tananan shiru tana kallon agogon wayarta taga har sha daya ta sake gotawa da kwata
amma bataji yashigoba tasake shaqa
Duk laifin na Gadanga ne yakoyarta gane agogo sannan yai mata sabon dawowa da wuri
dakinta to gashi yau yayi laifi ……
Muje zuwa😅
_Fans laifin dadifa zai kare domin saura one page Ali gadanga yakare muku domin
akwai wani shaharerren novel da zaizo muku me suna_ *"Yar fillo* _dan haka inaso
kununamin farin cikinku akan yanda kukafi jin dadin wani guri ackn Ali gadanga
kokuma kubayyana rashin jin dadin ku awani gurin haka kuma in akwai gyara ko
shawara ina maraba hakan shixai karamin kwarin guiwa sainajiku nabilancy luv_
*ALI GADANGA...*
🏹🏹🏹🏹🏹🏹🏹
*Short Story*
⬇
*THE* 🔚
*KARSHE*
*Nabilancy Luv*💘
(Auntyn S&S)
page
3⃣0⃣
Gadanga bashi yashigo dakin zainabu ba sai sha biyu na safe yatararta tana cika
tana batsewa
Yasan meyasa sai yahade ransa don bayaso takawo wani korafi
Cikin shagwaba tace masa "to bakaine kaje kai xamanka dakin matarka ba kamance dani
sai yanxu
Yayi dry yace "to kema bakiji me bakinki yace ba, dakin matata fa kk furta kinga
knn ai banyi laifiba ko?
Tayi sakato tana kallonsa mamaki take toko dai Aliyu yafara son khalisat bata
saniba?
Yakatseta dacewa "zamu futa da khalisat zankaita asibiti taga likita batajin dadi
daga nan zan wuce da ita gidan momy sai dare zamu dawo.
Tabishi da kallo harya fice gadanga ya fara canxa mata kodai anhadosune lallai dole
ta tashi da addu.A ta neman tsari dan kar ashiga tsakaninta da mijinta asa yarabu
da ita donko tasan mutuwa zatayi kawai zaifi mata dadai araba da Aliyunta wanda
yaxama rayuwarta ahalin yanzu baxata iya xaman kauye ba tayi sabo da jin dadin
rayuwa zaman birni yafi na kauye nesa ba kusaba balle kana xaune dame sonka aika
gama samun jinddin rayuwa
Aliyu gadanga yanzu ya goge yakara kyau yazama dan burni zam fatarsa tacanxa yayi
haske yYi fresh har saje yatara agefen fuska ga turanci yaxauna abakinsa lallai m.m
haruna ta taimaka masa duk da yashiga wata daban datafita karatu
-*******
Khalisat kwana tayi ba lfy jikinta zafi rum ga ciwon ciki da take fama dashi
zazzafan zazzabi ne ajikinta
Azatonsu ma ko cikine da ita Amma likitan daya kawo musu sakamako sai jikinsu yayi
sanyi don ba cikin bane Maleriyace dakuma typhod daya shigeta kawai
Abinda yafi daga mata hankalima sakamakon da likita yafada agame da mahaifarta yace
baxata haihuba don kwayayan haihuwarta sun gaxa sau daya rak zata dau ciki kuma ta
dauka yaxube abaya.
Taci kuka tagodewa Allah Aliyu gadanga yaita rarrashinta donta bashi tausayi
Taringa kuka tana cewa tayi nadama gashi Allah yajarabceta Alokacin datake bukatar
haihuwa yahanata.
Aliyu yace mata "kidaina fadin haka ba hanaki yayi ba jarabtace kiyi kokarin cin
jarabawarsa kawai kisa hkr aranki kiyita Addu,a akan yayafe mk yadubeki da idon
rahama zai iya baki agaba kada kiyarda da fadar likita don komi na iya faruwa amma
inkinyi tawakkali.
Saida yaga ta dan kwantar da hankalinta sannan suka wuce gida domin tace tafasa
xuwa gun momyn ba dama zuwanta daya tunda tayi Aure daya kaisu da zainabun suka
gaida su dady da daddare
Khalisat tasaka abin aranta duk da tadau shawararsa tana addu,o,in ammafa kullum
tunaninta shikenan yanxu ba ita ba ganin kwanta aduniya
Aiko dai jikinta yai tsamari ba shan maganin da likita yarubuta mata takeba
Maleriya kuma tayi mata ragargaxa ko daga hannunta bata iya yi ga damuwa data tarar
mata kullum jikinta azafafe take kwana rumm
Kullum zaunabu na hanyar dakinta tana kula da ita tunda taganta taringa tausaya
mata dama gata da tausayi da raguwar zuciya koda taga khalisat din duk ta rame har
kuka tayi mata
Ita kanta khalisat taxaci mutuwa xatayi taringa neman afuwar zainabu tana cewa ta
yafe mata abinda taringa mata don Allah kada tariketa
Itako zainabu takance ni ban rikekiba inma kinmin wani abun bansaniba to nayafe mk
Allah yabaki lfy
Har wata guda khalisat bataji saukiba zainabu na hidimarta ga cikinta yafito sosai
wata bakwai duk ta kumbura dayake sunyi test Ance musu twins ne duk mata saiya zamo
dije me aikin momi ta dawo gidan da zama a part din khalisat saboda khalisat tafi
bukatar taimako dan dai duk biyun take yiwa hidima ne
Da momy da dadynta sukaga abin yakici yaki cinyewa Aliyu na bakin kokarinsa sungani
sai suka fitar da ita kasar waje
Gadanga baiso binsuba dan bai isa yamusa bane tunda dady yabukaci hakan amma yaso
yai zamansa a nigeria tunda yanada patient zainabu itanma tana bukatar taimako
Da taimakon Allah da taimakon likitocin malesia jikin khalisat yafara samuwa domin
da gasken gaske suka tsaya akanta ana mata magunguna da kuma wankin mahaifa ana
bata magungunan larurarta
Koda aka sallameta suka dawo kasarsu ma ba.a tsaya dayin magungunan ba domin momy
taringa kawo mata magungunan hausa da rubutu akan mahaifarta data sami matsala
sannan tasa asauke mata alqur,ani
Alokacin cikin zainabu wata takwas duk ta kumbura batayin komi dijece ke mata
hidima haka khalisat ma takan shiga gunta ta tayata hira
Aliyu yaji dadin hakan don hakan shima sai yadaina musu bambanci saidai dole
zainabu nada wani matsayi na daban ackn ransa amma baya nunawa khalisat ta gani don
kada asami matsala
**********
Aranar da Nakuda takama zainabu Aliyu bayanan yana gun Aiki khalisat itace tayi
mata kokarin kaita Asibiti amotarta
Ckn awa biyu "yanbiyu suka iso duniya ba atare suka zoba saida suka bada ratar
minti talatin talatin atsakaninsu kowacce nakudarta daban
Khalisat tayita kallon yaran tanajin wani abu aranta qaunar yaran takeji da
sha,awar inama natane amma inta tuna cewar jinin gadanga ne sai taji ddi domin
itanma yanxu tadaina fidda ranta tunda Allah me yanda yasone ga bawansa xai iya
bata alokacin dayaso yabata
Zainabu qalau take shiyasa aka sallameta taringajin son yaran nata
Khalisat ta bugawa momy tagaya mata aiko ba bata lokaci saigata da kayan jarirai
data siya dama sunkai arbain abut
Khalisat tashammaci gadanga domin saida tagayawa momy ba kana takirashi tayi masa
albishir da samun "yan biyu
Yaji dadin wannan albishir din yace "yaushe akai hakan shine ba.a kirani
asibitinba?
Tace "wannan shiri nane banaso atayarwa da mijinmu hankali shiyasa,walh bakaga
yaranba masu kyau sunyo kyan uwarsu
Gadanga yaji dadi sosai yace "nagode khalisat zan baki goron Albishir da zakiji
dadi kema.
Koda yadawo gidan yatarar da momy sai yaringajin kunyar yadaumi yaran agabanta
Wani dadine yaringa shigarsa yana kallonsu yanzu wadannan kyawawan yaran duk
nashine?lallai yagodewa Allah mai kowa mai komai mai kyauta da karawa shikam ko
haka Allah yabarshi yaji dadi mata Ai rahamane gasu kyawawa kamarsu da uwarsu
futuk.daya tuno inna saida yayi kwalla yagogeta ba wanda yagani sai zainabu tasan
kukan dadine amma dasuka kebe adaki saida ta tambayeshi tace "Abban twins meyasaka
ka hawayene dazun?
Yace "ummun twin natuno inna ne inama tananan taga yaran gadanga da zainabu,inna
tafi kowa son taga munyi aure nidake akaf kauyen nan yabaxan kokaba ayau ga kwanmu
aduniya ita bata duniyar
Gadanga yasa hannu yagoge hawayen nata yana cewa "zainabu kin gamamin komi kin
haifamin yara masu kyau kamarki saidai ina neman Alfarma gunki.
Yajanyota jikinsa yana shafa fuskarta "so nake insaka sunan khalisat akan hussaina
hassana kuma inna ko yaya kk gani?
Ta murmusa tace "hakan yayi mana nima tun A asibiti dasukazo duniya na ayyana hakan
kaga damuwata zata ragu kuma tayimin taimakon da dan,uwana na jini xaimin takuma
nuna murnarta daxuwansu fatana itama Allah Yabata itama.
Sai ana gobe suna ma gadanga yafada mata hussaina fa sunanta zataci
Dan hakanma saida ta kama wani gun akai partyn suna *Nabnur event Center*
Dama gadanga yayi musu dinkuna iri daya ma kala biyu suka samu daga gunsa
Momy ma tayi musu dinkin tsadadden less don itanma ranta yayi fari dataji ansa
sunan khalisat a kan baby hussaina
Iya zulai taxo daga kauye a bangaren zainabu tadira itace me wankan jego
Khalisat ma takawo kayan jarirai amma dole saida ta banbanta na takwararta yafi
yawa
Zainabu tayita mata dariya tana cewa "Auntyn Hussaina bandafa banbanci kinsan
Abbansu baxaiji dadiba inkin nunawa innarsa banbanci
Khalisat tace "to nadaina momyn twins daga wannan ne kawai banaso aga laifina.
Khalisat tayita nan nan da iya zulai tana kama kafa da ita
Iya tace "toni me tayimin aibatayimin komi ba kowa yai nagari dan kansa.
Khalisat harda kukanta wai yanxu tagane tayi hankali itace kakar daya kamata taja
ajiki
Iya zulai dai ta hkr tasake mata har kwana tayi a part dinta kafin ta tafi
Da zainabu tayi arba,inma tare dukansu har khalisat sukaje kai iya kauye
Khalisat takwana daya gidan iya daya gidansu zainabu kuma bata nuna kyamaba komi
aka kawo mata ci take hankali kwance
To kansu dai hade yake dan haka hankalin gadanga akwance yake shima
Shekarar twins biyu zainabu tasake samun ciki anan hussaina takoma gun takwararta
khalisat da zama zainabunce tabata kyauta ammafa kullum suna part din zainabun
kwana kerabasu zasu tafi sashinsu
Duk siyayyar da zatayiwa baby khalisat haka zatayiwa inna karama bata musu banbamci
Zainabu ta haihu lfy tasami namiji wannan karanma gadanga yayi kara dan sunan dady
yasaka Tahir akece masa jinior
shima wannan Taron suna yakawatu ainun dady yayi rawar gani yayi hidima keko
takwara ba doleba
Shekarar junior guda akasaka twins amakaranta don suna magana radau shekararsu uku
khalisat ke kaisu ta daukosu amotarta sch din ba nisa sosai
Gadanga yanata samun budi ba laifi yabude account yanata ajiya kudadensa aciki daga
karshem uwar gida zee tabashi shawara yabude gun car wash da bude gidan buredi da
gidan pure wata *Al,kaleezai Car wash* da *Twins Bired* da *Tahir pure water*
ya ringa samun nasibi takoina a business din
Dady ya aikowa zainabu motar yar panadol extra tayita murba hargida yakaisu tayi
godiya khalisat ce me kaita koyo ckn watanni kuma tafara iyawa
Gadanga kuwa visa yayi mus xuwa kasa mai tsarki kudin kujera uku dama watan tafiyar
Alhazaine sukaje hajji suka sauke farali tareda taya Khalisat addu,ar Allah yabata
haihuwa itama
Sunyoyyo tsarawa wa mutanen arxiki shi gadanga dady dasu mudi da "yan kauyensu
yayowa tsarabar
Ita kuma zainabu momy da iya zulai da yan gidansu tayowa sai yaranta da kanta
Zainabu tanuna mata jin dadinta afili tanajin tausayin khalisat shiyasa har kullum
take tayata addu.a aduk sallolinta to ai dolene tunda ciwon "ya mace na "ya macene
Zaman lafiya ya wanxu ackn gidan gadanga matansa tankar ya da kanwa khalisat
nabaiwa zainabu girma amatsayinta na uwar gida ita kuma zainabun tana baiwa
khalisat girmane amatsayinta na wacce tabata shekaru biyar
Allah maji rokon bawansa wata guda da dawowar khalisat dg umara Tafara laulayin
ciki atare suka fara itada uwar gida zainabu itama cikinne da ita
Alokacin da sukayi nauyi basa futa saidai in awo zaikaisu dan EDD dinsu wata daya
yakama tsiran satine likitan yasa musu a result
Asatin khalisat ta haihu aka fara hidimar bikin kawarta khairat wacce zata Auri
wani malamin makaranta Mal.Anwar dan ta sauko tace Auren talaka shine samun
kwanciyar hankali kuma sunfi iya tsadaddiyar soyayya ❤😅
kyakyawar baby khalisat ta haifo me kama da ubanta tace lallai asaka mata sunan
zainab tanaso
Zainabu taji dadi kuma har lokacin hussaina tana can gunta bata karbetaba don
kyauta tabata don tana mata raino twins sun girma anfara zama "yammatafa
Satin khalisat biyu da haihuwa zainabu ta haifo santaleliyar baby itana mace steel
me kama da ubanta
iya Zulai dama tananan tunda tazo da khalisat ta haihu aiko dai yan kauye sai aike
akai musu na sanarwar haihuwa
Bayan suna gadanga yana manne da zainab akan gado suna tadi tace masa "Abban twins
kaifa angon karnine yakamata kayi turaka sbd irin haka munhada mk gwarama babu inda
zaka fake
Yaja dogon hancinta yace "ba matsala ko banyi turakaba zanci gaba da kwana bibbiyun
ahakan har kuyi arba,in
"hhhhmm nikuma inajin dadin za.a cikamin gida da albarkar iyali,plz uwar gidana
kada kiyi tsarin iyali inaso wata shekara kihaifamin me sunan gwaggo...
Taturo baki "ni kam inaso n nahuta haka haba honey 4 fa aiyakamata kuma nabarwa
khalisat ta dora akan inda natsaya.
Yace " inaso kiyi goma ita kuma tayi biyar.... "laaalaaa tab …… yakatseta da sauri
ta hanyar saka bakinsa anata yakamo harshenta yafara sha....
tofa gadanga nabarku lfy na fece Allah yakara dankon kauna kaida iyali 🤚🏻🤚🏻🙌🏻 byeee
*"YAR FILLO*
_Dijen kauye_