0% found this document useful (0 votes)
87 views33 pages

Ahlilkitab 1

The document is a fictional narrative centered around a girl named Nura who faces pressure from her family to abandon her faith and convert to another religion. It depicts her struggles, including physical and emotional abuse, as she seeks to maintain her beliefs and ultimately finds support within a community that accepts her. The story culminates in her conversion to Islam and the formation of new familial bonds through marriage, highlighting themes of faith, resilience, and community support.
Copyright
© © All Rights Reserved
We take content rights seriously. If you suspect this is your content, claim it here.
Available Formats
Download as TXT, PDF, TXT or read online on Scribd
0% found this document useful (0 votes)
87 views33 pages

Ahlilkitab 1

The document is a fictional narrative centered around a girl named Nura who faces pressure from her family to abandon her faith and convert to another religion. It depicts her struggles, including physical and emotional abuse, as she seeks to maintain her beliefs and ultimately finds support within a community that accepts her. The story culminates in her conversion to Islam and the formation of new familial bonds through marriage, highlighting themes of faith, resilience, and community support.
Copyright
© © All Rights Reserved
We take content rights seriously. If you suspect this is your content, claim it here.
Available Formats
Download as TXT, PDF, TXT or read online on Scribd
You are on page 1/ 33

[10/31, 16:57] Shaxeee Marubuciyan Ahalikita: *AHALILKITAB*

📓📓📓📓📓📓📓

*ZAMANI WRITERS ASSOCIATION*

*dasunan Allah mairahama maijin kai, dukkan yabo ya tabbata ga Allah subahanahu
wata ala wanda yabani ikon fara wannan littafin*

*wannan labarin kirkirarsa nayi duk wanda ya juyamin shi Allah ya tsaida mu ranar
kiyama yayi mana hisabi dashi anmin nafarko to duk wanda yasake ban yafeba.*

*FOLLOWING US ON THIS DETAILS*


---------
*LIKE OUR FACEBOOK PAGE*
👇🏻
*fb.me/ZAMANIWRITERSASSOCIATION*
---------
*CHECK OUR BLOG'S*
👇🏻
*zamaniwriters.blogspot.com*
-------
*DROP YOUR COMMENTS AND REPORTS ARE HIGHLY WELCOME ON THIS EMAIL ADDRESS:*
👇🏻
*Zamaniwritersassociation@email.com*

*NA: SHAXEEE*

*PAGE 1&2*

" tunda kika ce saikin bar addinin mu kindawo musulma, ko saikin sha bakar huya
agunmu, kibar ganin nina haifeki saina azabtar dake 'yan uwanki bawanda yake da
hali irin naki bansan halin wanda kikawo ba, kazama kawai." Wata dattijuwar matace
mai wannan fadan.

Wata yarinya na gani akwance daga gani ta gala baita duk jikinta shatin dukane
idonta ya yi jajir.

Dun gureta da kafa wannan dattijuwar tayi tafuce daga d'akin, ta kulle shi daga
waje.

Dakin karamine gashi duk shara ce aciki da shirgi acikinsa anan wannan mata shiyar
take kwance.

Cikin wani katon falo datti juwar nan ta shiga, falon yasha kayan alatu kamar baza
a mutuba.

Wani dattijo ne azaune suna kallo dashi da wani saurayi sai budurwa daya.

Zama tayi akan kujera cikin 'bacin rai.

" momy narasa wace irin yarinya ce, ace wai zata shiga wancan addinin wadanda basa
sonmu, ko 'kada'an, shiyasa nima na tsanesu. Saurayin ne yake wannan maganar.

Wadda aka kira da momy ce ta furzar da wata iskar ban haushi.

Cikin bacin rai tace." Kaidai bari chali narasa yadda zanyi da ita, har yanzu taki
dawowa hanya, duk huyar data sha, amma bari gobe tayi nasan kalar azabar da zan
mata wadda dole saita hakura."

Cikin 'kunar rai dattijon yace. " momy guloriya sonake ki wahalar da ita sosai ni
kaina na tsaneta, gwara ta mutu akan tashiga, wancan addinin mutanan nasu manyan
kunnuwa."

Budurwar ce tace." Daddy kaidai bari nima na fiso goben tayi muga abinda momy zata
yimata."

Murmushi momy tayi tace. " guloriya kizuba ido kinsha kallo, nizata nunawa iskanci,
kan mutafi choci saina wahalar da ita."

Duk cikin turanci suke wannan maganar.

Misalin karfe 11 na dare duk suka watse suka tafi suka kwanta.

Ita kuwa yarinyar nan. Tana zaune inbanda kuka ba abinda takeyi.

Cikin kuka take magana. " dole in musulinta kozaku kashene, bazan cigaba da bautawa
abinda bashida amfani, tunda naga rashin amfanin sa da ido." Ahaka tayi barci
gahunwa ga sauro wanda ayanxu tasaba da cizonsa.

************

Safiya nayi 'yan gidan kowa yatashi, anata hidima domin yauce lahadi za.

Suna kallo momy tace." Chali duban kaga rana tafuto sosai."

Tashi chali yayi yabude taga ya leka." E momy tabude kamar ta dafa mutun saboda
zafinta, wannan duk wanda yafuta ba mota ai saiya fara 'kamshin suya, saboda
gasashi zatayi."

Dariya sukayi gaba d'ayansu.

Tashi momy tayi tace. " kubiyoni kuga ni yadda zanwa waccan yarinyar."

Gaba daya suka bita abaya, suna zuwa dakin data ke suka bude suka shiga, tana zaune
tayi ta gumi, domin har jiri takeji saboda hunwa.

Damko gashinta momy tayi tana janta a'kasa.

Saida suka futo tsakiyar filin gidan, tukun momy ta saketa.

Magana momy ta fara. " setepni zaki hakura da misilinta, ko kuwa in azabtar dake
har ki mutu, dan azabar yau bazaki iya jure taba."

" har abada momy bazan bar musintaba, mai amfanin gunkin damuke bautawa, kina ganin
abinda yafaru rannan agabanshi, aka kashe wani bai temakeshiba, taya zan bautawa
wanda za a biyoni gabanshi akasheni bazai iya temakona ba, kuma jibi rannan huta ta
kama a choci sai shiga akayi aka dakkoshi har ya fara 'konewa, mai amfanin sa tunda
bazai iya temakon kansaba ma, bare yate makemu.'"

daddy ne ya fara magana cikin bacin rai takushe musu allansu. " to dakika ga bai
temakeshiba har aka kasheshi, ai bayason yawan magana ne shiyasa baice komaiba,
kuma dahuta takama ai alokacin barci yake shiyasa baisan huta takamaba, tunda kinki
hakura, duk abinda Za ayi miki bazance komaiba."

Momy ce ta kamota. " Chali ku temakan incire mata kaya dan ubanta."
Tuni suka kama kokawa da ita, suka cire mata kaya, kamata sukayi suka kulle mata
hannu da 'kafa suka sakata cikin rana.

Mustu mutsu takeyi, saboda zafin ranar tanaso tafuta daga ciki amma ta kasa.

Saida ta gala baita tafi minti 40 tukun suka futo da ina.

" guloriya jeki dakkon yaji a kichin." Inji momy kenan.

Gidan tashiga ta dakko takawo wa momy. " momy gashi."

Amsa tayi ta bude shi.

Murmushin mugunta tayi. " chali da daddy ku kamata ku gwalemin idonta inzuba mata
."

Rirriketa sukayi suka gwale mata ido takuwa zazzaga mata.

Inbanda ihu ba abinda takeyi saboda azaba.

Tarasa inda zata saka ranta taji dadi.

Saboda azaba tayi azabama, kwanciua tayi tana burgima.

Maiyar mata da kayan jikinta sukayi.

Ruwan dimi da gishiri momy ya himata wanka dashi.

Wayyo Kawai take cewa saboda dama jiya anzaneta jikinta duk ya farfashe ga kuma
ruwan dimin da aka zuba mata da gishi.

Zuwa yanzu ma ta dena motsi ta sadaukar mutuwa zatayi saboda azaba.

Anan suka barta suka koma cikin gida sukayi wanka sukasha kwalliya.

Suka futo suka shiga mota sukayi tafiyarsu choci bauta.

Da kyar ta bude idonta basosai take ganiba.

Da rarrafe ta shiga cikin gidan, ruwa ta dauka tasha ta isheta ganin dari. Uku tayi
akan tebur.

Dauka tayi tafuto tana bin bango.

La'bewa atayi harsai da taga mai gadin gidan yashiga bandaki.

Aikwa tayi sauri ta futo daga gidan.

Cikin sa a taga wani adaidai ta.

Tsayar dashi tayi tashiga.

Saida sukabar unguwar tukun mai adaidaita yace. " hajiya ina zan kaiku baki
fadaminba."

Cikin muryarta wadda bata futa tace. " babban masallaci zaka kaini inda kasan
manyan mala mai suke zama." Dayake ta iya hausa sosai.
Tuni mai adaidaita yadauki hanya, gudu kawai yakeyi.

*muje zuwa taku har kullun.*


*shaxeee.*
[10/31, 16:57] Shaxeee Marubuciyan Ahalikita: *AHLILKITAB*
📓📓📓📓📓📓📓

*ZAMANI WRITERS ASSOCIATION*

*FOLLOWING US ON THIS DETAILS*


----------
*fb.me/ZAMANIWRITERSASSOCIATION*
---------
*CHECK OUR BLOG'S*
👇🏻
*zamaniwriters.blogspot.com*
--------
*DROP YOUR COMMENTS AND REPORT ARE HIGHLY WELCOME ON THIS EMAIL ADDRESS:*
👇🏻
*Zamaniwritersassociation@email.com*

*🦋NA:SHAXEEE*

*PAGE 3&4*

wani babban masallaci ya kaita.

" hajiya gashi munzo daga ganima daurin aure akayi aciki dannaga da ragowar mutane
aciki." Mai adaidai tane yake wannan maganar.

Kud'insa ta bashi ta sauka, masallacin tashiga ciki, mutannan ciki basufi mitin
goma ba.

Kare musu kallo tayi, sannan tace. " wanene babban malami anan."

Gaba daya d'agowa sukayi suna kallonta, wani mutunne wanda baifi shekara 48 ba
yasha babbar riga da rawani yatashi tsaye yace.

" nine yarinya karaso guna."

'karasawa kusa dashi tayi ta tsugunna, sannan tafara magana.

" sunana setepni ni kiristance, inason in misilinta, da 'yan uwana suka sani shine
suka kulleni suna ganamin azaba, yau nasamu na gudu agidan, kuma na iya wasu daga
cikin littafanku dayake tun ina yarinya nakeso in shiga addininku domin nagane
shine na gaskiya, kuma har sallah na iya yadda kukeyi amma iyayena basunsan na
iyaba, kutemakan kuban addininku." Cikin kuka ta 'karashe maganar tata.

Kowa nagun saida yayi kwalla, saboda ko ba fadaba kowa ya ganta yasan ta azabtu,
amma ahaka tajure ita saita misilinta, Allah maiyadda yaso da bayinsa.

Kabbara sukayi gaba dayansu." *ALLAHU AKBAR*"

zama sukayi gaba dayansu, malaminne yabata kalmar shahada, abin yabasu mamaki,
ganin tana biyawa dai dai bakamar wasuba da sai ansha huya tukun.

Kabbara suka kumayi.


Malaminne yace. " wane suna kikeso asamiki dan yanzu kinzama 'yar uwarmu misilma."

Cikin murmushin farin ciki tace. " inason sunan nana aisha, dan naji tarihinta
sosai shiyasa nakeson sunan."

Cikin farin ciki malamin yace. " kinzabi suna mai kyau yarinya, yanzu zan tafi dake
gidana kiyi wankan shiga musilinci, kuma zandinga koya miki karatu kuma insaki
amakaranta."

Wani dattijo ne yatashi yace. " ala gafarta malan ina son wata alfarma inza
ayimin."

Kallonsa malan yayi yace. " alhaji yakub kafada muji Allah yasa alherine."

Wanda aka kira da alhj yakub yace." Sonake abawa d'ana nura aurenta, saboda nima
inaso in temaka mata, kuma na d'auki alkawarin bata karatu na addini, kuma inzame
mata uwa da uba, harda dangi."

Kowa yayi farin ciki saboda sunsan, cewa alhj yakub mitimin kirkine, gashi da son
temako.

Malamin ne yace. " nayi farin ciki dosai da jin wannan zan can naka, kuma nayarda
da kai, amma dole sai ta amince tukun."

Kallonta yayi yace. " 'yata kinji abinda wannan mutumin yace, shin kin amice ta
abunda yace."

Murmushi tayi tace. " na amince malan kuma ina farin cikin zama acikinku."

Nan danan aka daura aure akan sadaki dubu hamsin malan shiya zama waliyin nura alhj
yakub kuma wakilin aisha.

Ana gamawa aka bata sada kinta ahannunta.

Mota suka shiga alhj yakub yajasu suka fara ta fiya.

Abinda yake d'aure masa kai shine ganin mugun kamanninta yake da khadija kan warsa.

Katse masa tunani tayi datace. " abba naji dadin temakon dakayimin, kuma nima
sainaji kamar kaine kahaifeni, kuma inaso wata rana zan gaya maka wani babban
sirrina dana gano wanda yasani amincewa da dole saina misilinta."

" karki damu 'yata duk sanda kika shirya gayamin, kawai kizo kifadan, kuma nafi son
adinga cemiki nana."

" to abba nima haka nafi so acemin Ko ahade duka acemin nana aisha."

Unguwar ja,in suka shiga, awani babba gida yayi hon, aka bude masa yashiga.

Yana yin fakin ya futo itama tafuto, wani pat yayi da ita, suna shiga falon yagaji
da haduwa, zama sukayi akan kujera.

Waya ya dauka yakira wata nomber.

" hello maman nafisa kuzo pat dina keda su nafisa har da usman."

Yana gama fada takashe wayar.

Wata nomber yakira. " hello hjy karima kizo pat dina keda yaran duka." Bai tsaya
jin maizata ceba yakashe.

Tunani yake irin tashin hankalin dazai faru, dan yasan sai anyi amma ya dauki
alwashin ko za à mutu saiya temaka mata...

*muje zuwa*
[10/31, 16:57] Shaxeee Marubuciyan Ahalikita: 📓📓📓📓📓📓📓
*AHLILKITAB*

*ZAMANI WRITERS ASSOCIATION*

*FOLLOWING US ON THIS DETAILS*


------------
*fb.me/ZAMANIWRITERSASSOCIATION*
----------
*CHECK OUR BLOG'S*
👇🏻
*Zamaniwriter.blogspot.com*
--------
*DROP YOUR COMMENTS AND REPORT ARE HIGHLY WELCOME ON THIS EMAIL ADDRESS:*
👇🏻
*Zamaniwritersassociation@email.com*

*🦋NA:SHAXEEE*

*PAGE 5&6*

Sallama ce ta katse masa tunaninsa.

Wata matace tashigo ita da yara biyu mace da namiji.

Dago kai abba yayi. " maman nafisa kun karaso zauna."

Zama tayi tana tunanin mai ya faru yake musu kiran gaggawa, kuma dazu suka rabu
dashi yatafi daurin aure, kuma taga wata budurwar "ya agefe amma bari tayi shiru
taga ikon Allah.

Bude kofar akayi wata dattijuwa ce tashogo ko sallama babu, tana ganin maman
nafisa, ta hade rai sai harare harare take.

Zama tayi akusa da abba, sannan wani matashi yashigo tare da budurwa, kallo daya
zaka yimata kasan bata da kunya.

Abbane yafara gyaran murya sannan yace. " abinda yasa nakiraku shine." Gaya musu
yadda komai yafaru, yana rufe bakinsa ammi ta tashi afusace. " maikake nufi alhj
karasa wadda zaka aura dana nura sai *AHLILKITAB* bazai yuha wallahi gwara ma tun
farko kayiwa tufkar hanci, yanzu nura yasaketa kanemi wani, nura maza yimata saki
uku wallahi bazan taba lamuntaba."

Azafafe abba yatashi. " duk ranar da nura yasaki nana to wallahi wallahi kema saina
sakeki adadin sakin daya yimata, kuma hukuncine nariga da na yankeshi banga wanda
ya isa yacanza shi, maman nafisa kitafi da ita pat dinki zan nemo malamin dazai
koya mata karatu, nanda wata biyu sai ta tare agidan ta." Juyawa yayi yakalli nura.
" kaji abinda nace ko kuma kagayawa matarka karta kuskura tace zata hulakantan 'ya,
kutashi kubani gu."
Maman nafisa ce tafara tashi, nafisa kuma ta kama hannun nana suka fuce daga pat
din.

Nura kuwa jiyayi duk duniya bawanda ya tsana sama da nana, shi cewa yayi yanasonta
za a aura masa ita baga yahya ba maiyasa sai shi, aikwa wallahi saita yi nadamar
shiga rayuwarsa,pat din ammin sa yakoma.

Ammi kuwa dakyar takai kanta pat dinta,ita alhj zai ciwa mutunci harda cewa zai iya
sakinta agaban kishiyarta, yarinyar nan tajawa kanta.

Wata iska ammi tafesar ta bakin ciki.

Nurane yafara magana. " yanzu abba yarasa abunda zaimin sai ya hadani aure da
*AHLILKITAB*kuma harya dinga jamin kunne, wallahi ni bazan iyaba."

Wata matashiyace tace. "Ammi wai me yake faruwane, mai abba yace naganku dukanku
damuwa."

" kedai bari karima alhj yau yahula kantamu fiye da yadda kike tunani."

Gayamara duk abinda yafaru tayi.

Asukwane karima ta tashi." Dama abba bason aurena da nura yake ba, kuma yarasa
damai zai sakamin saida kishiya kuma ma tubabbiya." Cikin kuka ta karsa maganar.

Tasowa ammi tayi tazauna kusa da ita. " kwantar da hankalinki ai ba dadewa
zatayiba, azaba zamu gana mata harta gudu da kanta, kema kuma karki saurara mata,
shima nuran ubanta zaici, kinga tana ganin bazata iyaba zata and koma inda ta
futo."

Wani murnushi karima tayi. " wai ke hajarat bakice komai ba.I'd to&q
[10/31, 16:57] Shaxeee Marubuciyan Ahalikita: 📓📓📓📓📓📓📓📓

*AHLILKITAB*

📓📓📓📓📓📓📓📓

*ZAMANI WRITERS ASSOCIATION*

*masoyana ina alfari daku aduk inda kuke ina ganin sakonninku akan novel dinnan
bantaba zaton masoyansa sukai hakaba Allah yasa ka da alheri*

*FOLLOWING US ON THIS DETAILS*


----------
*fb.me/ZAMANIWRITERSASSOCIATION*
---------
*CHECK OUR BLOG'S*
👇🏻
*zamaniwriters.blogspot.com*
--------
*DROP YOUR COMMENTS AND REPORT ARE HIGHLY WELCOME ON THIS EMAIL ADDRESS:*
👇🏻
*Zamaniwritersassociation@email.com*
*🦋NA:SHAXEEE.*

*PAGE 7&8*

" to mai zance ai hada irin muguntar dazan mata nake, ai zan hulakanta rayuwarta
wallahi." Cikin rashin kunya hajarat take wannan maganar.

Murmushin mugunta nura yayi. " karima tashi kitafi gida akwai inda zanbiya tukun
indawo gida."

" to nuree, saika tawo ammi bara in tafi." Sallama tayi musu ta tafi gida.

*********

" yasunanki 'yata." Momy ce mai wannan maganar.

A sanyaye nana tace. " nana aisha."

" suna mai dadi tashi kuje dakin nafisa kuci abinci kiyi wankan shiga addininmu,
nafisa zata koya miki za ta baki kaya kisa."

Kama hannunta nafisa tayi suka shige dakin ta.

Tunani momy take Allah yayi darabon zata shiryu, amma taso yahya alhji ya aurawa
ita dataji dadi kuma tariketa hannu bibiyu, amma tasan halin ammi huya zatasha.

*************

Tunani kawai abba yake.


" mai yasa naji duk duniya inason hadata da nura, bayan nasan halin ummansa,
maiyasa yarinyarnan ta tsayamin arai haka, jinake kamar da wani abu a tsaka nina da
ita, kai Allah ya sa hakan shiyafi alheri." Tashi yayi yashige daki.

*********

Haka nana take rayuwa cikin kwanciyar hankali, ga malaminta yana koya mata sosai
tana ganewa, momy ma tana koya mata nafisa ma haka, har yahya ma shima yana kokari
yaga tashiga farin ciki.

Yau watan nana biyar da musulinta ya goge a addini sosai ga kwakwalwa, tagoge sosai
amma tanashan bakaken maganganu agun ammi amma tamaida komai bakomaibane.

abbama yana nasa kokarin yana bata kulawa sosai.

Momy ta koya mata duk wani dabarun zama da miji da kishiya har makaranta tasata
dantakoyi komai.

*****************

Ammice taketa safa da marwa a dakinta, zama tayi tadau waya takira nura.

Yana mota domin komawa gida yaji karar waya.


" hello ammi ya gida yasu hajarat, yau bansami damar shigowaba wallahi aikine yamin
yawa."

Gyara zama ammi tayi tace. " bakomai aidama tunda naganka shiru nasan bakasami dama
ba, abunda yasa nakiraka shine, inaso yau kazo gun alhj kace kanaso waccan
*AHLILKITAB* din tadawo gidanka zaka dinga kula da makarantar ta ahaka mukuma
zamusan yadda zamuyi tabar garinma gaba daya kowa yahuta."
" to ammi ahakanma yayi bayan sallar magariba zanzo, sai anjima." Kashe wayar yayi
yana tunanin ammi takawo shawara mai kyau, shikanshi yanaso yarabu da ita.

Yana zuwa wani madai daicin gida, hon yayi mai gadi yabude masa ya shiga.

Yana shiga falon, bakowa, karewa falon kallo yake, rabonsa da shara yau kwana shida
kenan, ga kwanuka nan a baje, wasuma sunyi tsutsa wasu kuma sunyi wari, tsaki yayi
yahuce dakinta.

Tana kwance akan gado daga ita sai daurin 'kirji, tunjiya take fama dashi, dakinta
gaba daya a har gitse gashi anzubo dayan kwaba ga takalma akan gado dawani faranti
alamun indomei,taci.

" yanzu dan Allah karima, baki gyara gidannan ba, jibi kema yadda kike kaca kaca
dake, to waima meyake wari a dakin dan Allah." Yana magana yana toshe hanci.

Soshe soshe takeyi alamun dauda ta dankare ajikinta. " wallahi dazune nayi kashi a
masan, shine naji karar wayata, saina matanta bankoraba nafuto na amsa wayar bara
inje inkora."

In ran nura yayi dubu to yabaci, cikin fada yace. " lallai watarana ma akwano
zakiyi kashi, to maza kitashi kigyara gidan, kuma kan infuto inga ko ina a gyare."
Yana gama fada yafuce.

Karewa dakin kallo tayi. " niyanzu taya zan iya gyara gidannan ni kadai." Tashi
tayi tahade kayan gaba daya ta tura a kwaba, ta dakko tsintsiya tashare baima
futaba, ta futo falon kwanukan ta hade takai kicin tashareshi bazancan goge kayan
kallo barema mopin, tana gamawa ta tafi kicin tadora masa jalof din taliya.

Yana shiga dakinsa shima duk datti, amma dadan sauki tunda wataran yana dan kadewa,
bandaki yashige domin yayi wanka, yana futowa yasaka jallabiya, yafuto falo.

Kallon falon yayi balefi anrage datti, zama yayi akan kujera.

Ita kuma tana kicin tana chat tukunyar ma abude take kicindin ba kyan gani, jin
alamun yafuto falo tayi saurin tashi ta dakko plat duk kura ajikinsa, ta daga
tukunyar tajuye ta dakko cokali tasaka, ta futo.

Ajiye masa tayi tahuce daki, cokali yadauka yakalli abincin shiba jaba kuma ba
yaloba.

Daurewa yayi yayi kai bakinsa, wani dandano yaji amma haka yadaure saboda hunwar
datake damunsa.

Yana juyawa domin kara cokali daya yayi karo da wani 'katon kyankyaso yadahu lugu.

Aguje yatafi bandaki yafara amai..

*muje zuwa.*
[10/31, 16:57] Shaxeee Marubuciyan Ahalikita: 📓📓📓📓📓📓📓📓

*AHLILKITAB*

📓📓📓📓📓📓📓📓

*ZAMANI WRITERS ASSOCIATION*

*inamika gaisuwa gareku ina alfahari daku wallahi*


*king boy*
*queen*
*kamala*
*zuwaira madara*
*yar mutan arkilla*
*Allah yakara zakin hannu*

*FOLLOWING US ON THIS DETAILS*


---------
*fb.me/ZAMANIWRITERSASSOCIATION*
------------
*CHECK OUR BLOG'S*
*zamaniwriters.blogspot.com*
---------
*DROP YOUR COMMENTS AND REPORT ARE HIGHLY WELCOME ON THIS EMAIL ADDRESS:*
*Zamaniwritersassociation@email.com*

*🦋NA:SHAXEE.*

*PAGE 11&12*

yana gamawa yakora da ruwa, yafuto daga bandakin ya kwanta a kan gado.

Saida yahuta tukun yatashi yasauya kaya, yadauki mukullin mota da wayarsa yafuto.

Kotakan karima baibiba saboda yadda yakejin haushinta inya ganta zai iya marinta.

Mota yashiga yatafi gidan abinci.

Saida yaci ya koshi tukun, yaji daidai amma indai yatuna da wannan kyan kyaso sai
zuciyar sa ta tashi.

'kazantar karima harta huce yadda yakeji ana fadar kazamai sunayi.

Kiran salla yaji, yatashi yase wani abincin yasaka a mota saboda dare, alwala yayi
yatafi masallaci yayi sallar magariba.

Yana kidarwa yayi lazimi yahuce mota yatafi gidansu dan haduwa da abba.

****************

Zuwa yanzu nana ta gama makarantar koyan zama damiji, gata da tsafta da biyayya
momy tanajin dadin zama da ita.

Dan yanzu momy batayin komai saidai su suyi mata iyakarta kawai taci ta kwanta
harta ruwan wanka kaimata suke, dama bata dauki *"yar aikin gidaba* acewarta
mainene aikinta.

************************

Yana zuwa gidan yayi yaga abban afarfajiya azaune.

'karasawa kusa dashi yayi ya tsugunna.

" barka da dare abba."

Cikin farinciki abba yace. "Barka nura ya iyalin naka."

"Sunan kalau dama abba gurinka nazo."

Gyara zama abba yayi. " inajinka maiya faru."

" dama cewa nayi maizai hana nana tadawo gidana inyaso sai malamin yacigaba dazuwa
can yana koya nata."

" nayi matukar farinciki daka nuna kulawarka akan nana kuma naji dadi saidai, ina
maka tuni kayi adallici inkaci amana to Allah bazai barkaba, yau saita bika kuma
zanga yawa malamin nata yaje can yadinga yimata, kuma dama ba boko takeba tunda
tagama jami, à shiga ciki ganinan zuwa."

Tashi yayi yashiga pat din ammi tagaya mata yadda sukayi da abba.

Murna sosai tayi.

Pat din momy abba yaje yagaya mata bukatar nura, badan ranta yasoba ta yadda
dantasan wannan shirin ammi ne, banasa, tashi tayi taje tagawa nana suka fara hada
mata kayanta, kuka kawai suke nafisa kamar ta shide saboda kukan rabuwa, momy ma
saida tayi kuka.

Momy tabata littattafai na addini duk da itama tanada su, ta kuma yimata nasiyya.

Futo mata da kayan sukayi abbane da yahya suka zuba mata a motar nura.

Nura yana futowa yayi musu sallama ammi sai washe baki take kamar da gaske tanason
nana.

Dan janyo nura ammi tayi tarada masa akunne " gobe kubude kofa da asuba zanzo
kaji." Gyada mata kai kawai yayi bawanda yakula dasu sai momy.

Mota nura yashiga yajasu suka tafi.

Bawanda yacewa da kowa kala harsuka je saka mai gadi yayi ya kwashe mata kayan
yashiga dasu ciki.

Wani daki akabata wanda in anyi baki suke kwana aciki.

Dakin duk kura da yana, gaba daya gidanma ganinsa tayi uwa ba mutanene suke kwana
acikiba.

*muje zuwa*
[10/31, 16:57] Shaxeee Marubuciyan Ahalikita: 📓📓📓📓📓📓📓📓

*AHLILKITAB*
📓📓📓📓📓📓📓📓

*ZAMANI WRITERS ASSOCIATION*

*godiya gareku masoyana soyayyarku a bargona take*

*FOLLOWING US ON THIS DETAILS*


----------
*fb.me/ZAMANIWRITERSASSOCIATION*
------------
*CHECK OUR BLOG'S*
*zamaniwriters.blogspot.com*
-------
*DROP YOUR COMMENRTS AND REPORTS ARE HIGHLY WELCOM ON THIS EMAIL ADDRESS:*

*Zamaniwritersassociation.Email.com*

*🦋SHAXEE..*

*PAGE 13&14*

zagewa tayi ta gyara dakin tawanke bandakin dayake akwai bandaki akowane dakin
gidan.

Tana gamawa tajera kayanta nabandaki takai, durowar mudubi ta bude ta saka bokitin
cicin dinta da cake da miyarta mai yawa tasha kaji momy ce duk tazubo mata dayake
bata rabo da su.

Tana gamawa ta ci cake ta kwanta.

*****************

" momy nafisa gobe su nura zasu tare asabon gidansu, dama sonake sanda nana zata
tare sai su koma gobe karfe 8:00 nasafe zamuje mudaukesu." Abbane mai wannan
maganar.

Murna sosai momy tayi, waya abba yadauka yakira ammi yagaya mata.

***********

Asuba tanayi nura yatashi karima taki tashi, haka ya hakura ya futo dan tafiya
masallaci karya makara.

Yana zuwa falo yaga dakin nana da huta kuma yaji sautin karatun kur ani abin
yabashi mamaki, amma haka ya yafuce kawai.

Yana dawowa yakwanta afalo.

Misalin karfe takwas yaji sallamar su abba tashi yayi.

" sannu dazuwa abba."


Duk kunya tagama kamashi gidan ba kyan gani ga shi wari kawai yake.

Ita kanta ammi taji kunya gidan danta ahaka kuma ga kishiyarta.
Zama sukayi gaba daya suka gaggaisa.

Abbane yafara magana. " dama gidan dana gina makane nakeso yanxu kutare dan haka
maza kaje kagayawa matanka suhado kayansu."

Cikin girmamawa nura yace. " To abba."

Ammi da hajarat sukayi tsulum suka shige dakin karima.

Momy da nafisa suka shiga dakin nana,daidai lokacin tafuto daga wanka.

Tayi murna sosai da ganinsu,tayata hada kaya sukayi suka futo jiran su ammi.

Sukuwa su ammi dakyar suka iya hada mata kaya saboda gaba daya ba niki saima warin
ruma suke.

Nurama yadibi abinda yake bukata suka futo suka shishshiga mota,motar abbace agaba
suna binsa.

Wani tafkekyan gida suka shiga sakin baki sukayi gaba dayansu, pat biyune gidan
tsakanin kowane pat da nisa kan kaje dayan.

Dukansu suka futo suka tsatstsaya.

Abbane yafara magana. " to nura ga gidannan pat din can na karshe shine na nana,
nafarko kuma na karima kumuje mufara ganin nafarkon."

Suna shiga na farkon katon falone sai kicin aciki shima babba da dakuna guda uku
nafarko nata saina nura da kuma dakin baki ko yara.

Pat din yayi kyau komai anzuba mata ba lefi. Sai wani daga kai karima take tana
yiwa nana gwalo, wai ita tafita matsayi anmata kayan daki.

Suna gama zazzagayawa suna yiwa abba godiya da fatan gamawa lafiya.

Futowa sukayi Domin shiga pat din nana.

Duka fasalin dayane amma saida su karima suka raina kansu, saboda kayan nana bama
na kasar nan bane gaba daya pat din adon fink ne da ash komai ma abin kallone a pat
din, kujeruntama girmansu yayi biyun na karima.

Ammi saura kadan ta fashe saboda haushi.

Momy kuwa kamar tazuba ruwa akasa tasha dan dadi.

Hatta tsin tsiya ma tana ura aka saka mata itama nura yanada daki a pat din.

Fucewa su ammi sukayi saboda shiga dakin gadon nana harta kwabarta cike take da
kaya komai akwai abba yace kayan lefantane da ba ayimataba, kayan ko lokacin bikin
karima ba ayimata rabinsuba.

Nana godiya kawai takewa abba harda kukanta.

Momy su suka taya nana jera kayanta ta kwashe wasu tazuba a akwati saboda yawansu.

Su ammi suna zuwa pat din karima, karima tazube tana kuka. " ammi kinga cinmutuncin
da abba yayimin ko jibi dukiyar daya kashe mata nima kisa nura yayimin irinsu
kosufi nata."
Cikin bacin rai ammi tace. " ai dole asake miki su bazai yuhuba tarainaki wallahi
zataci ubanta."

" ammi maganar gaskiya kinsan banida karfin yimata irin wancan kayan barema su
fisu, tayi hakuri kawai innasamu saina sake mata wasu." Cikin facin rai mura yake
wannan maganar domin yaji haushin maganar da karima tagawa abbansa.

Tashi yayi yafuce, ita kanta ammi tasan nura bazai iyaba domin alhji yayi barnar
kudi sosai.

Lallashin karima kawai ammi tayi, hajara kuwa huci kawai tayi yadda kukasan da
kudinta akasiyewa nana kaya.

Abba yana zuwa tafiya yabawa nana mukullin mota. '' motar tana farfajiyar gidannan
karki fara hawanta yanzu, kinji yata."

Godiya sosai nana tayi masa.

Tafiyarsa abba yayi da momy da nafisa sukabar su ammi dansunce basu gama gyara pat
din karimaba.

Sunajin tafiyarsu suka shiga kicin suka dora ruwa a gas.

Saida yadawu tukun suka dauko shi suka tafi pat din nana, suna shiga ita kuma
lokacin tafuto falo.

Basu tsaya wata wataba suka watsa mata ruwan a kafafunta.

Wani ihu nana tayi ta durkushe agun.

Cikin masifa ammi take magana. " shegiya mayya kin mallakemin miji kinsa ya aura
miki dana kuma yana kashe miki dukiya, to wallahi baki isaba, sainayi maganinki
asararriya tubabbiya kawai."

Dauke ta da mari ammi tayi karima ma ta mareta har sau uku hajarama haka sukafuce
daga pat din.

Suka bar nana bata motsi.

*muje zuwa*
[10/31, 16:57] Shaxeee Marubuciyan Ahalikita: 📓📓📓📓📓📓📓📓

*AHLILKITAB*

📓📓📓📓📓📓📓📓

*ZAMANI WRITERS ASSOCIATOIN*

*FOLLOWING US ON THIS DETAILS*


--------------
*fb.me/ZAMANIWRITERSASSOCIATION*
--------
*CHECK OUR BLONG'S*
*zamaniwriters.blogspot.com*
------------
*DROP YOUR COMMENRTS AND REPORT ARE HIGHLU WELCOM ON THIS EMAIL ADDRESS:*
*zamaniwritersassociation@email.com*

*🦋NA:SHAXEEE.*

*PAGE 15&16*

Sallama amme tayiwa karima ta tafi, ammi taji haushin karima saboda ita nacace mai
son abata abin duniya.

Mita ammi tafara. " nifa abinda yake hadani da karimannan rowar tsiya, tafiya son
abinta ko dan wani abu taban bata banba."

Kwabe fuska hajarat tayi. " ni kodan kayan kwalliya ma taban bata banba, rannan fa
akan wani kayanta danace ta ban aro amma tacimin mutun ci, duk fa wannan abin da
muke saboda ita fa muke."

" nifa bayan mungama ciwa yarinyar nan mutunci tsorofa nafara ji, kar fa tagawa
abbanku mushiga uku."

" nifa duk jikina yayi sanyi wallahi."

Haka suka tari adaidaita suka tafi gida kowa da dan tsoronsa.

*************************

Nana kuwa saida washe gari tayi sannan ta farfado, Allah yate maketa kunar bata
kamata sosai ba, ko tashi bata yiba.

Amma kafar tayi jajir abinka da farar fata.

Da kyar take iya taka kafar.

Danma malaminta dayazo ta gaya masa konewa tayi yana kawo mata tufi.

Ita ma kuma tanayi.

Bata wasa da ibada salla akan lokaci ga yawanjin kur ani ga addu,oi.

Matsalarta daya dayake abba baizuba musu abinci a suto ba yace nura yazuba.

To abinci sai wannan kayan da momy ta bata suma sunkare.

Ga kudi a acont dinta amma badamar fita ba izinin miji.

Inama taga mijin bare ta tambayeshi.

Zuwa yanxu tafara gala baita dan ko tafiya bata iyayi.

Ga gefan cikinta da yake yimata ciwo.

Kuma kullun tana waya da momy da abba amma bata taba gaya musuba.

Ganin zata kashe kanta yasa ta tashi dan ta dakko waya takira nafisa dan ta turata,
ta ciro mata kudi.
Tana tashi jiri yade beta tafadi asume.

*************************

" wallahi cutar rabi tana damuna sosai, har yanzu bata magana yadda kikasan wata
tababbiya, gashi kullun cigiya muke amma har yanzu shiru." Abbane yake wannan
maganar.

Cikin jimami momy tace. " nikaina ina damuwa amma wallahi muta nannan Allah bazai
barsuba."

" duk randa aka kamasu wallahi saina hukuntasu fiye da tunanin mai tunani."

*************************

Yau tsawon kwana uku da suman nana haryau bata farfadoba.

Karima kuwa kazanta taci gaba dan gaba daya pat dinta ba zakaso kashigaba.

Nura yana zaune yaji kamar antsi kareshi.

Tunawa yayi ai bai kaiwa waccan yarinyar kayan abinciba to mai take ci.

Tashi yayi tatafi pat din.

Ganinta yayi a kwance bata nunfashi.

Tsayawa tunani yayi shin wannan ce koba ita bace danshi sau biyu yataba ganinta
arayuwar sa.

Daukarta yayi yafuto sakata amota yayi mai gadi yabude masa kofa yafuta.

Asibitin kusa dasu ya kaita,

Ansarta sukayi da gaggawa suka shiga da ina.

Nura kuwa yakasa zama yanzu maizai cewa da abba.

Saida akayi wajan awa daya da shigarta sannan likita yafuto fuska ba wal wala.

*kuyi hakuri da wannan azimin yau yadan juyani*


[10/31, 16:57] Shaxeee Marubuciyan Ahalikita: 📓📓📓📓📓📓📓📓

*AHLILKITAB*

📓📓📓📓📓📓📓📓

*ZAMANI WRITERS ASSOCIATOIN*

*ina mika gaisuwata Clasic feedo Allah yabar mana ke*

*masoyan AHLILKITAB ina gaisheku sosai Allah yabar kauna*

*dear sister nasmat ina alfahari dake kuma ina jinjina miki sosai Allah yabar min
ke*
*zamaniwriters kuma ban manta dakuba Allah yakara daukakaki yasa mufi haka*

*FOLLOWING US ON THIS DETAILS*


----------
*fb.me/ZAMANIWRITERSASSOCIATOIN*
----------
*CHECK OUR BLONG'S*
*zamaniwriters.blogspot.com*
-----------
*DROP YOUR COMMENRTS AND REPORT ARE HIGHLY WELCOM ON THIS EMAIL ADDRESS:*
zamaniwritersassociation*

*🦋NA:SHAXEE*

*PAGE 17&18*

dasauri Nura yaje gunsa." Likita yajikin nata."

Cikin facin rai likita yace. " mai yasa zaku barta ba wada taccan abinci gashi har
olsa ta mata mugun kamu, amma tanzu munshawo kan matsalar ammata allurar barci
nanda minti 30 zata farka dan haka kayi saurin samo mata abinci mai kyau." Yana
gama gaya masa ya yi shigewarsa.

Wata ajiyar zuciya nura ya saki.

Futa yayi daga asibitin ya sami gidan abinci yasai mata yahada mata da kayan
marmari yasai mata kaza wadda aka yimata gashin ruwa ruwa tasha albasa 😋😋 yasai
mata yagot mai sanyi, ya koma asibitin.

Sanda yaje harta farka matsawa kusa da ita yayi. " sannu ya jikin."

Daga masa kai kawai tayi dan bazata iya magana ba.

" tashi kici abinci kinji likita yace kici sosai."

Ba musu ta tashi da kyar, fulo yasa mata abayan ta ta jingina.

Abincin ya dakko mata, amsa tayi tafara ci kamar wadda ta shekara bata ciba, tanaci
tana share hawaye.

Yana kallonta ji yayi kamar shima yafashe da kuka duk shine sana di yanzu data mutu
maizaicewa Allah da kuma Abba, wai maiyasa shi aikata hakan.

Saida ta cinye tukun lemo ya mika mata ta ansa ta shanye, wata ajiyar zuciya
tasaki.

Nura jiyayi wani tausayinta ya kamashi, hunwa ba dadi.

Ahankali nura yafara magana. " dare yayi zaki iya zama ke kadai intafi gida ko in
kira miki momy."

Ahankali tace. " A a zan iya kwana kaje saida safe."

" dama haka muryarta take da sanyi." Azuciya yake wannan maganar.
Sallama yayi mata yatafi.

Yana futa Nana tatashi zaune, ta dau kazarta ta ci tasha yagot dan maganin da aka
bata hunwa yake sawa.

Kayan marmarinma taci saida taji uwa tayi amai tukun ta jingina. " wallahi nadena
shan wahala innabiye ta hakuri mutuwa zanyi abanza a hofi daga yau karima ammi nura
hajara kujira ni saina baku mamaki zaku gane koni wacece wallahi." Duk afili take
magana.

Murmushin mugunta tayi tana kada kai.

Kwanciya tayi.

**********************

Nura kuwa yana tuki yana tunani gwara yasauke hakkin da Allah yadora masa.

Yana zuwa gida, yatarar kamar karamar bola.

Kota kan karima baibiba yashige daki.

Shi Allah yayishi mai son tsafta amma gashi Allah yahadashi da kasamar mata.

Abincin daya tawo dashi yaci ya kwanta.

**********************

Safiya tanayi nura yatashi yayi wanka yashirya yafuto falo.

Karima yagani tana zaune akan kujera duk yahun barci afuskarta, sai murza ido take.

" To ni zanfuta dan akwai inda zan biya kan intafi kasuwa."

" To nuri katawomin da abin dadi."

Kota kanta baibiba yashiga kicin ya dakko fulas din shayi duk yayi kura dakansa
yawanke shi tas tafuto yatafi.

Karima kuwa mamaki take mai Nura zaiyi da fulas din shayi, tayu siya zaiyi yasha.

Yana futowa yaje gun maishayi aka cika masa fulas din da ruwan shayi aka soya masa
kwai yasai biredi yatafi, shago yashiga yasai madara da sugar yatafi asibitin.

Yana shiga dakin ita kuma Nana tana zaune tana game awayar ta, sallama yayi yagigo.

Cikin yanga Nana tace. " yaya ina kwana."

Wani dadi yaji dan rabon da karima ta gaisheshi har ya manta.

" lafiya kalau yajikin naki."

" da sauki dan sunce da yamma zasu sallameni."

Wayartace tayi kara, dubawa tayi taga sunan abba.

Dagawa tayi. " ina kwana Abba yasu momy, lafiya kalau abba ai yanzu ina kicin ina
dora shayi, baitashiba tukun zaiji Abba."
Nura yaji dadi yadda bata fadawa Abba cewa tana asibiti.

" abba yace ingaisheka dan nace kana barci, kasan mai kuwa wallahi yaya kwata kwata
shigar nan bata yima kyauba, kaga yadda ka koma kuwa." Kwashewa tayi da dariya.

Karewa kansa kallo yake saiyaji gaba daya ya muzanta, gani yake kowama ashe
kallonsa yake yana dariya.

Fucewa kawai yayi yashige mota.

Ita kuwa Nana yana futa takwashe da dariya kadanma kafara gani wallahi.

Har yayi hanyar kasuwa yajuya motarsa ya yi hanyar gida, gani yayi inyaje kasuwa
dariya suma zasu yimasa, gashi shadda yasaka blue sai hula baka da bakin takalmi
amma kuma ace baiyiba.

Yana shiga gidan yahuce dakinsa tsayawa yayi ya na kallon kwabar tasa, yanzu wanne
zai saka.

Kananun kaya ya sanja sannan yafuta, kotakan karima baibiba saboda ko motsinta
baijiba.

***********************

Nana saida tayi wanka amma bakayan sakawa, haka tamayar danata.

Zama tayi abakin gado ta dakko wayar ta ta kamo nomber ammi tana murmushi. " kece
ta biyu yanzu zan fara dake."

Wallahi na gaji kuyi hakuri da wannan


[10/31, 16:57] Shaxeee Marubuciyan Ahalikita: 📓📓📓📓📓📓📓📓

*AHLILKITAB*

📓📓📓📓📓📓📓📓

*ZAMANI WRITERS ASSOCIATION*

*FOLLOWING US ON THIS DENTAILS*


---------
*fb.me/ZAMANIWRITERSASSOCIATION*
---------
*CHECK OUR BLONG'S*
*zamaniwriters.blogspot.com*
--------
*DROP YOUR COMMENT AND REPORTS ARE HIGHLY WELCOM ON THIS EMAIL ADDRESS:*
*zamaniwritersassociation@email.com*

*ina tayaki murnar gama littafinki rukky byba Allah yakara daukaka Allah yasa a
amfana da abinda kika fadakar ameen*

*🦋NA:SHAXEE.*
*PAGE 21&22*

Tana shiga, taga falon uwa na mahaukata gawani wari dayake tashi.

Kuma bakowa, a falon alamun ma basu tashiba.

Dayake tasan kan pat din tunda iri dayane dana ta.

Dakin karima ta shiga ahankali, ganin karima tayi, ba kaya ajikinta domin daurin
kirji tayi kuma garin barci ya yi gefe, abinsa bama tasaniba ita.

Murmushi Nana tayi, tabude ledar kararan nan ta barbada akan gadon gaba daya, saita
kulle ragowar tayi sadaf sadaf tafuce, cikin ikon Allah bawanda yaganta, pat dinta
tahuce tana sheka dariyar mugunta.

Ita kwa karima tanata juyi akan gado hankali kwance, duk jikinta ya kwashe
kararannan, cikin barci taji uwa cinnaka yana mintsininta.

Wani uhu ta kurma tana soshe soshe. " wayyo nura kaikayi kunama tanata harbina
nashiga uku."

Jin ihu ne yasa nura futowa asukwane, yayi dakin karima, ganinta yayi tanata soshe
soshe tana ihu. " ke lafiyar ki kalau kuwa, kiketa yimana ihu da sanyin safiyar
nan, ta ina zakiga kunama agidannan uwa ajeji."

Cikin kuka karima take magana. " wallahi nura jikina duk kaikayi yakemin natashin
hankali, kate makan kasosamin dan Allah."

Ganin abin yayi yana nema yahuce gona da iri. " tashi muje kiyi wanka tayu dauda ce
ta taru tayi miki yawa."

Aguje tayi bandaki ta fara wanka, wayyo Allah jitayi abun har yafi nada.

Bashiri ta futo daga bandakin tana ihu.

Abun yafara bawa nura tsoro, yama rasa mai zaiyi mata.

Fanka yakure mata yafara tayata susa, kuka kawai take, danji tayi uwa tayi hauka.

Saida tafi awa biyu ana fama, sannan tafara jin daidai, kaya tasaka ta futo falo,
duk jikinta yayi jajir uwa wadda akawa duka.

Nura yana ganin tadan dawo daidai, yasa ya futo yayi hanyar pat din Nana.

Itakwa Nana dariya kawai take dan tana jiyo ihun karima.

Sallamar Nura tajuyo. " yaya sannu dazuwa ina kwana."

Murmushi yayi mata. " lafiya kalau ya jikin naki."

" Jiki da sauki yaya muje ga abin kari."

Binta yayi zuwa tebur din cin abinci dan yasan in baiciba to inya futa saiya siya,
kuma bazai yi dadin wannan ba.

Shayine sai kwamshi yake, yasha kayan kwamshi, sai tayi musu yam boll wanda yasha
nama da attaru😋 Nura loma kawai yake kaiwa, saida yajishi dam tukun yayi hamdala.
" ammafa nagode da wannan abinci mai dadi haka inaga saina ma biyaki."

Murmushi tayi dan taji dadin yabon abincinta dayayi. " a a yaya basai ka biya indai
abincine to kullun kadinga zuwa kanaci. "

" habadai ban takura kiba kuwa."

" bawani takura yaya, bara inje in hadama ruwan wanka naga bakayiba, kuma kakusa
makara."

Bata jira abinda zaiceba ta tashi tashige dakinsa na pat dinta.

Dama kullun saita gyara shi, ruwan tahada masa tare da abin kwamshin wanka tafuto.

Lokacin yayi zurfi atunaninsa. " yaya kaje ka yi wankan nahada maka." Tashi yayi
yashige daking.

Ganin dakin yayi abin sha awa sai kwamshi yake, ko mai tsaf tsaf adakin.

Bandaki yahuce shima abin sha awa, kayansa yacire yafara wanka cikin nidashadi.

Yana gamawa yafuto, gani yayi anfuto masa da jallabiya sabuwa, sai kwamshin turare
take.

" kai yarin yarnan tana so ta shagwaba ni, amma dukda haka ta iya kula da mutun,
dama haka maza masu aure sukejin dadi, amma ni saiyanzu nakeji." Duk afili Nura
yake wannan maganar.

Mai yashafa ya saka kayan yafuto falo ita kuma tana zaune tana kallon hotuna awaya.

" yahya harka gama."

" E wallahi nagama kedai Allah yayi miki albarka, bara inje inshirya intafi kasuwa,
maikike so natawo miki dashi."

Murmushi tayi. " katawon da kankana da abarba."

" to shikenan saina dawo."

" Allah yabada sa a Allah yakiyaye."

Wani dadai yaji ba a taba yimasa addu,a in zai futa. " ameen kidafan abinci na
gargajiya."

" to yayana zanmaka kuwa." Rakashi tayi har bakin kofa yatafi, jinsa yake uwa
asabuwar duniya.

Yana shiga pat din su, yaga karima taci damara ta rike kugu, tana girgiza jiki.

Cikin masifa tace. " sannu dazuwa namamajo, watakan nizaka munafunta ko, kace
katsaneta kuma baka sonta, amma maiyakaika pat dinta da safe har kafi awa uku acan,
sannan kadawomin kayi wanka kacanza kaya ko,watakon inga sheda ko, yanzu nagane ma
kaikayin jikin dazu danayi ashe asirine tamin dan ta haukatani ko, kaikuna aka maka
na bita zaizai, amma wallahi yau sainayi maganinta.."

*koya zata kaya muje zuwa*


[10/31, 16:57] Shaxeee Marubuciyan Ahalikita: 📓📓📓📓📓📓📓📓
*AHLILKITAB*

📓📓📓📓📓📓📓📓

*ZAMANI WRITERS ASSOCIATOIN*

*yar fulani kawo monografia ina mika gaisuwa a gareki allah yabar kauna*

*FOLLOWING US ON THIS DETAILS*


---------
*fb.me/ZAMANIWRITERSASSOCIATOIN*
-----------
*CHECK OUR BLONG'S*
*zamaniwriters.blogspot.com*
----------
*DROP YOUR COMMENRTS AND REPORTS ARE HIGHLY WELCOM ON THIS EMAIL ADDRESS:*
*zamaniwritersassociation@email.com*

*🦋NA:SHAXEEE.*

*PAGE 19&20*

harzata kirata saikuma tafasa message, ta tura mata, tare dayi mata taransifar kudi
na dubu ishirin.

*" Ammi ina kwana ya gida ya hajara, Nana ce gakudinnan bayawa kasai kati kihuta
lafiya."*

Tana gama turawa ta hada shayi tana sha abinta.

****************

Ammi tana zaune ita da hajara taji sako yashigo tare da alat, dauka tayi ta duba,
ganin abinda sakon yakunsa ne yasa tayi murmushi.

" hajara kin kinsan waya turo sako yanzu"

" a a Ammi saikin gayan."

" waccan *AHLILKITAB* dince taturon da dubu ishirin, shegiya ci zanyi wallahi wajan
zama take nema kuma bata da shi wallahi."

" ai Ammi duk da haka tafi waccan marowaciyar wallahi, muna tayata yaki ita kuma
tana make hannu."

" ai hajarat rabu da ita, zatayi hankali nan gaba nasani, tashi kije kizubo mana
abin kari yunwa nakeji."

Tashi hajara tayi ta tafi kicin.

**********************
Yamma tayi Nura yatashi daga kasuwa ya tawo asibiti.

Sanda yazo har ansallameta tarabar da ragowar kayan abincinta shikadai take jira.

Yana zuwa suka futo suka hau mota.

Suna cikin tafiya Nana indai taga abu sai antsaya ansiyamata.

Suna zuwa gida ta futo daga motar.

" yaya tayani kwashe kayan kasan bazan iyaba, ni kadai."

Samun kansa yayi da kinyimata musu tayata kwashewa yayi sukayi hanyar pat din ta.

Budewa yayi dayake mukullin yana hannunsa, shigar mata da kayan yayi.

" kirubuta abinda kike so nakayan abinci zanje kasuwa yanxu in siyo."

" to yaya ban aron biro da takadda."

Cirowa yayi daga aljihunsa ya bata, amsa tayi tadinga rubutu shikanshi abin har
yafara bashi tsoro, dan shi wani abinma mai san shiba.

Tana gamawa tabashi yafuce, karewa dakin kallo tayi, kura kawai yayi.

Zagewa tayi tagyara ko ina, takunna turaren huta, tashiga bandaki tayi wanka ta
futo, riga da siket tasa yan kanti daidai ita, bata daura dan kwaliba ta yi bakin
kai yasaha ribuna da abin adon kitso, batayi wata kwalliya sosaiba, ita kanta tasan
tayi kyau.

Hijjabi ta dauka har kasa tasaka ta futo farfajiyar gidan, wajan mai gadi taje.

" ina huni baba ya aiki."

Cikin mutunci mai gadi yace. " lafiya kalau 'yata."


" baba dan allah kasan inda zan sami karara, mai shegen kyaikyayi kuwa."

" 'yata inada shi dayake bandade da dawowa daga garinmuba, amma kikula yana kusan
saka mutun hauka saboda kyaikyayinsa, bara indauko miki."

Dakinsa yashiga ya dakko mata aleda.

" gashi 'yata kikula sosai."

" na gode baba, dama inaso in tamba yeka watake baka abinci."

" 'yata ai kullun maigida ne yakeban kudi insiya safe da rana da dare."

" daga yau kadena amsar kudin kace nace kullun kadinga zuwa kana amsa a guna kaida
wancan yaron maibawa shuka ruwa da shara."

" kai ammafa mungode 'yata allah yayi miki albarka."

" ameen baba nagode sai a jima."

Pat dinta ta koma tana farin ciki.

Zuwa tayi taboyeshi a kicin, tadawo falo tacire hijjabin.


Bata dade da zama ba saiga Nura yana shigo da kayan Abinci yana kaiwa stoto, na
firinji kuma yana sakawa yanayi yana satar kallonta, dan ji yayi inama ace
karimace, saida yagama tukun yazo futa.

" yaya dan allah yimin hoto wayata ba caji, innayi caji saika turon gobe."

Kawai wayar yadakko daga aljihu yafara yimata.

Salo take canzawa kala kala, saida tayi wajan kala goma tukun tace ya isa.

Fucewa yayi daga dakin saboda yaga yarinyar yar cali calice.

Yana zuwa pat dinsu, karima ita kuma tana zaune akan kujera tana, kallo.

" sannu dazuwa nure."

" yauwa." Kawai yace yashige daki.

Wanka yafara yi tukun ya dakko ragowar cake dinsa yaci yasha lemo, jinsa yayi uwa
baiciba saboda hunwar da take tare dashi.

Kwanciya yayi akan gado yadakko watarsa yana kallon hotunanta, murmushi kawai
yakeyi. " ashe haka yarinyar nan take da kyau amma nake nema inyiwa kaina sage
getuwa, to wai menenema laifunta kamata yayi mujata ajikinmu dan wasu ma w suji
dadin shigowa addininmu, amma daga yau zan dawo cikakken mumini mai son temako da
kyautatawa mutane." Duk azuciya yake wannan maganar.

Jiyayi hunwar ta isheshi, shiyasa ya tashi dan yafuta ya siyo abinci.

Dubawa yayi ashe yamanto mukullinsa a pat din Nana.

Futowa yayi yanufi pat dinta, jitayi wani kwamshi ya na tashi, sai hadiyar yahu
yake.

Yana shiga yaga ta futo daga kicin da kuloli a hannunta.

Atebur din cin abinci ta ajiye. " yaya kai ne kashigo."

Saita nutuwarsa yayi dan ya shagala da kallonta. " E wallahi mukullin mota na manta
anan."

" E nagani bayan kafuta, tunda kashigo saikazo muci abinci "

" a a akoshe nake kedai kici kawa."

Cikin shagwaba da alamun kuka tace. " aidama nasan bazaka ciba, tunda katsaneni
kaga maizaisa kaci abincina." Tanayi tana share kwallar karya.

" to mai nene nafadar haka indai abincine zuban naci shikenan ko."

Gyada masa kai tayi zuwa tayi ya yi yazauna, tazuba masa, shinkaface soyayya tasha
hanta da koda, gefe kuma kosulo ne yasha kwai da mafara.

Wani yahu ya hadiye, ci yafarayi wani sadine yafara ratsashi, aikwa yadinga kai
loma yana shan lemo, saida yacinye, takara masa shima ya share shi tas, yakora da
lemo saida yajishi nak tikun yafarga da abinda yayi.

Wata kunyace ta kamashi, jiyayi uwa kasa ta tsage ya shige ciki, shida yace ya
koshi amma yashar wannan uban abincin.

Ita kuwa tausayi yabata, yadda taga yana cin abincin uwa ya shekara bai ciba. " zan
ajiye komai na abinda kukaimin, zan temakeka kodan alkairin da abba yayimin, zan
jawoka jikina inbaka kulawa sosai." Duk azuciya take wannan maganar.

" to ni na tafi saida safe."

" Allah yakaimu yaya."

Abincinta taci tayi shirin barci ta kwanta.

Nura kuwa yana zuwa dakinsa yahuce danyanzu, baicika biye ta karimaba, kwanciya
yayi yana dariya abinda yayi yau. " kai amma Allah yayiwa yarinyar Albarka, yau
tasami ladana." Afili yake fadar haka.

*******************

Gari yana wayewa Nana tayi komai har abun kari tayi, tabawa masu gadi nasu.

Tayi wanka dakko wannan karara tayi tana murmushi. " yau zan fara rama abinda
akayimin."

Futowa tayi tanufi pat din su Nura.

*muje xuwa*
[11/1, 00:07] Shaxeee Marubuciyan Ahalikita: 📓📓📓📓📓📓📓📓

*AHLILKITAB*

📓📓📓📓📓📓📓📓

*ZAMANI WRITERS ASSOCIATION*

*sadaukawa ga yahya yakub yahya.*

*FOLLOWING US ON THIS DENTAILS*


---------
*fb.me/ZAMANIWRITERSASSOCIATION*
---------
*CHECK OUR BLONG'S*
*zamaniwriters.blogspot.com.*
----------
*DROP YOUR COMMENRTS AND REPORT ARE HIGHLY WELCOM ON THIS EMAIL ADDRESS.*
*zamaniwritersassociation@email.com

*🦋NA:SHAXEEE.*

*PAGE 23&24*
" yanzunan wallahi batasan koni waceceba shiyasa zata tsokaloni."Ko kallonta Nura
baiyiba yayi shigewarsa.

Karima dad'a kular da ita yayi, aikwa futowa tayi ta nufi pat din Nana.

Tana zuwa tashege ko sallama batayiba, ganin Nana tayi tana kwashe kayan abinci.

" to karuwa maibin mazajen mutane, wato dan kinsan ba kulaki yakeba shine kika
yimasa asiri irin naku na kafurai, to wallahi ahir dinki nafi karfinki, kuma komai
zakiyi, wallahi Nura bazai taba zama nakiba."

Wani kallo Nana tayi mata, cikin ko ajikina tafara magana. " ke wacece dazaki
shigomin daki kina haushi, kincikamin kunne da haya niya, zaki iya futa kibarbin
daki, ko iyi maganinki."

" kan uban can, nice karyar wallahi kintabo tsuliyar dodo." Kan Nana karima tayi
ta cakumeta da kokawa.

Aikwa Nana ta tur musheta tana jibgar ta, da azaba tayi azaba karima tafara ihu
tana neman ceto.

Nura yazo futa yaji ihun karima a pat Nana, nufar pat din yayi, kafin yakarasa
Karima ta daku sosai.

Yana shiga yayi kokarin raba fadan dakay ya rabasu Nana sai haki take, Karima kuwa
kuka kawai take fuska duk tayi dameji.

Cikin fushi Nura yace. " yanzu mai amfanin haka karima, yanzu wa gari yawaya jibi
yadda aka sanja miki kamanni, kindawo uwa wadda tayi hatsari, huce muje."

Ran karima yabaci tadauka zai rama mata amma saiya 'buge da yimata fada, agaban
Nana.

Shigewa tayi shikuma yabi bayanta, saida yakaita pat dinta sannan yace. " saiki
sami ruwan zafi ki dimama jikinki, kisha panodol ki kwanta."
Cikin masifa Karima tace." Au hakama zakace ko, kana kallo tamin duka amma kakasa
cewa komai, to wallahi bata daki banza ba."

" matsalar kice wannan inkin koma kuma ta karya miki kafa kowa yahuta." Yana gama
fada yayi fucewar sa.

Ita kanta Karima tasan bazata iya komawaba, dan karfin dataji Nana dashi yabata
tsoro.

Tashi tayi ta dauki mayafi da kudi da waya tafuce daga gidan.

Kai tsaye gidansu Nura tahuce wajan ammi, samun ammi tayi tana zaune ita da karima
suna kallo.

Fashewa tayi da kuka tagawa ammi karya da gaskiya, ran ammi yabaci. " tashi muje
wallahi saina ci mutuncinta fiye da tunanin mai tunani." Tashi tayi tashiga daki
tadau mayafi ta futo.

Fucewa sukayi gaba dayansu suka tafi gidan.

Suna shiga gidan sukayi pat din Nana, Amma Karima taki binsu.
Suna bude kofar falon sukaji karatun kur,ani yana tashi ga 'kamshi.

Nanda nan zuciyar su tayi sanyi, saboda jin karatun kur,ani maiyaye bakin ciki da
bacin rai.

Karasa shiga sukayi suka zauna, Nanace tafuto daga kicin saboda tana shirye shiryen
dora girki.

Tana ganin su ammi ta karaso da sauri ta tsugunna. " ina kwana ammi ya gida yasu
Abba."

A gajarce Ammi tace. " lafiya." Hajara kuwa ko 'kala bata ceba mamaki take dama
haka Nana take.

Tashi Nana tayi tashiga kicin tadinga kawo musu abubuwa kala kala dambun nama cake
da su frut, su ammi anga gara, suka hauci tama manta maiya kawosu.

Suna gamawa Ammi tace. " bara mutafi gida rana tanayi."

" to Ammi ina zuwa." Daki tashiga ta debowa hajara kayan kwalliya Ammi kuwa les mai
tsada da turare ta dakko mata tafuto falon.

Tsugunawa tayi tamika musu. " Ammi gashi bayawa."

Washe baki sukayi. " haba 'yar nan harda wahala haka, to angode." Amshewa sukayi
suka futo, saida tarakosu har bakin kofar pat dinta sannan ta koma.

Hajarace ta bude ledarta taleka taga kaya hadaddu, dariya tayi tace. " Ammi wallahi
yarinyar nan tanada mutunci jibi yadda tayi mana jibi kaya.'"

" kedai bari hajarat ai haka akeson mutun mai bayar wa." Tafiyar su sukayi dan
sunma manta da wata karima.

Karima kuwa dataji shiru yasa tafuto ta leka, taga maiyake faruwa dan bataji ihuba.

Tana futowa taga sunhuce suna dariya ga ledoji ahannunsu. " tab d'ijan kardai suma
ta asircesu, wallahi bazai yuhuba gun umma zani ta rakani gun bokanta nima in yi
maganin su gaba daya."

Daki ta koma ta canza kaya tafuto ta tafi.

************************

" daddyn chali bazai fa yuhuba dole mu dad'a dagewa, wajan neman yarinyar nan karfa
asirin mu yatonu mushiga uku." Momy ce mai wannan maganar, babar Nana kanta gudu
daga hannunsu.

Cikin tashin hankali daddy yace. " nima abinda nake gudu kenan, kuma kinsan garkuwa
ce ahannun mu ko, in ba ita kudirinmu bazai cikaba, dole mudage mu nemota, in
burinmu na shekara 19. Ya cika saimu koreta, komu kasheta."

" hakan yafi dacewa daddyn chali, amma yanzu mudage sosai har mu ganota."

*koya abin yake wannan wane burine harda aka dau shekaru da dama ba a cika shiba
kuma harzai janyo mutuwar nana, kozasu ganta kuwa🤔 bara mujira muji*
[11/2, 15:18] Shaxeee Marubuciyan Ahalikita: 📓📓📓📓📓📓📓📓
*AHLILKITAB*

📓📓📓📓📓📓📓📓

*ZAMANI WRITERS ASSOCIATOIN*

🍒🍒🍒🍒🍒🍒🍒
*ZUBAR HAWAYE*

*duk wanda yazubar da hawaye to bai karabta littafinnan ba, yafadakar kuma ya wa a
zantar allah yasa mu amfana da abinda yake ciki, ina tayaki murnar gamawa tawan
sister zeety allah yasa afi haka*

*FOLLOWING US ON THIS DETAILS*


-------------
*fb.me/ZAMANIWRITERSASSOCIATOIN*
-------------
*CHECK OUR BLONG'S*
*zamaniwriters.blogspot.com*
---------
*DROP YOUR COMMENRTS AND REPORTS ARE HIGHLY WELCOM ON THIS EMAIL ADDRESS.*
*zamaniwritersassociatoin@email.com*

*🦋NA:SHAXEE.*

*PAGE 25&26*

Karima tana futa gidansu tahuce, tana shiga ta tarar da umman tata zata futa. "
yauwa umma, nazo kirakani gun bokanki, wallahi wannan kafurar zata rabani da nura,
burina yaki cika, shiyasa nayi azama na tawo."

Cikin masifa umman Karima take magana. " tab dijan wallahi bazai yihuba tasan huyar
damuka sha kan nura ya aure ki kuwa, kuma bamu cika burinmu ba ace ta wargaza mana
to wai ma maiya faru gayan."

" kedai umma muje ahanya zan gaya miki kiji."

Fucewa sukayi suka shiga motar umman tata suka nufi hanyar kyauye.

********************

Abba ne ya futo da akwati shida momy, nafisa kuwa ta yo musu rakiya.

Abbane yafara magana. " nafisa ki hada kayan ki ki tafi gidan yayan ku nura,
kizauna a pat din Nana, tunda bakowa agidan yakub kuma shi namijine zai iya zama a
gidan shi kadai."

Cikin shagwaba nafisa tace. " momy ku gaida anty, kuce yajikin nata, dan allah
karku huce sati biyun kunji zanyi kewar ku."

Momy ce ta shafa bayan ta. " karki damu bazamu dadeba, kikula da kanki da yar
uwarki nana."
Mota suka shiga yakub yajasu suka tafi.

Suna futa Nafisa ta shiga ta dakko akwatinta da mayafi tafuce, sai gidan su Nura.

Nana kuwa wainar shinkafa tayi a yi kyau da ita, saitayi miyar taushe tasha tanta
kwashi da ita sai kwamshi take.😋

A kuloli hadaddu ta zuba tabawa mai bawa shuka ruwa da wanki, tace yakaiwa Nura
kasuwa, tabashi kudin mota, dayake yasan kasuwar ya ammsa yatafi.

Su Baba maigadi kuwa ansha gara dan adan kwana biyun nan har tumbi yayi. Lol

Nana tana gamawa tashiga daki tayi wanka tayi salla tayi Addu,a tadawo falo ta
kunna tv takwanta akan kujera tana jiran nafisa, dan momy ta gaya mata awaya.

Bata dade da zamaba kuwa taji sallamar nafisa, tashi tayi da gudu ta rungumeta.

" dama jiranki nake wallahi yanzu nasamu maitayani hira wallahi."cikin farin ciki
Nana take wannan maganar.

Zama sukayi akujera sunata hira abinsu, saida karfe 3:00 tayi Nana tace. " nafisa
tashi muje kitayani aiki indorawa yaya girki."

Sakin baki Nafisa tayi. Dariya Nana tayi tace. " kedai muje kicin zan baki labari."

Tashi sukayi suka huce kicin, Nana tana bawa Nafisa labarin suna dariya.

Nura kuwa sanda, deeni, yakawo masa yana waya da abba, yana gaya masa karima ta
tawo gidansa, saida yagama tukun yakashe, yace. " Deeni amma dai lafiya naganka
akasu war mu kuma nasan ban bar maka sakon dazaka kawominba ko."

Zama Deeni yayi yace. " E wallahi anty karama ce tace inkawo maka abinci gashi."

Wani dadide ne yarufe nura, dan duk duniya yanaso akawo masa abinci daga gidansa
suci shida yaransa da abokanansa.

Amsa yayi yabawa Deeni kudin mota ya tafi, abokanansa yakira da yara da yaransa
suka fara dina, kowa sai santi yake, harda masu bawa amarya tukwiyci akai mata,
Nura kuwa sai washe baki yake.

***********************

Su Karima ne A zaune agaban boka.

Boka ne yake magana. " naji bukatar ku, kuma nayi bunkice naga bazamu taba iya
cutar da wannan yarinyarba, domin tanada karfin ibada ga jin karatun kur ani, bata
wasa da addu a, komai zatayi saita yi addu a."

Hankalin su yatashi su umma sosai, ummace ta daure tace. " to boka a bari inbata da
tsarki sai ayi aikin ko."

Wani surkulle boka yayi yace." Bazai yihuba domin tana yin alwala kuma tadinga
addu,oi tana jin kur awani sosai, in kuma kuka matsa zaku iya nakasa domin aljanu
insukaje zata konasu, sukuma surama akanku."

Sunajin haka, bashiri suka tashi suka tafi, sunje waje yafi biyar amma maganar
dayace dai, sai wani suka samu yace zai iya ya amshi kudinsu, domin malamin karyane
basu saniba.

Haka suka dawo gida suna murna domin cewa sukayi ayimata na warin jaba.

Suna dawowa Karima ta dawo gidan ta da farin cikinta.

********************

su Abba nagani wani katon falo azaune shida, momy da wata mata uwa mai ta'bin
hankali, sai wata kuma matar agefe.

Abbane yake magana cikin damuwa. " Sadiya har yanzu binciken ba nasara kuwa."

Wannan matar tagefe da aka kira da sadiya tace. " yaya bawani nasara, domin har
yanzu yaya Muhammad, yaki fadar ko su waye ko kamanninsu yaki fadi, yace yarsa
datake hannunsu indai yagada zasu illatata, shikuma da ya fada su illata masa
'yarsa daya dayafi so gwara ya dawwama a gidan yarin, ni al amarinma yafara sikemin
wallahi."

Cikin jimami momy tace. " ita kumafa mai likitoci sukace akan ciwonta."

" maganar dai dayace, sunce duk randa ta hadu da abinda take son gani, ko abinda
yafaru da ita yakuma faruwa to zata tuna komai kuma zata dawo daidai."

Abbane yakuma cewa. " mudai bazamu hakuraba tunda munada gaskiya, zamu cigaba da
'boye khadija, har tadawo daidai, tafada mana yadda abin yakasance da kuma inda
abubuwan suke mudakko, mu nunawa kotu ta saki Muhammad, duk randa na hadu da
mutanan nan zasuga rashin imani wallahi."

Cigaba da tattauna war su sukayi.

*********************

Nura yana dawowa ya nufi pat din karima yayi wanka yashirya yatafi pat din Nana.

Yana zuwa sukayi masa sannu da zuwa sukaci abinci suka, zauna hira.

Nura tunani kawai yake, yanzu bayaso Nafisa ta fahimci baya kula da Nana, zata iya
gayawa momy ita kuma momy ta gayawa abba, yasan in abba yaji kashinsa yabushe,
dabarace ta fado masa, tashi yayi yana hamma.

" Nafisa kije ki kwanta, ni nashige daki, Nana saikin tawo." Shigewa yayi dakinsa
na pat din.

Wata ajiyar zuciya Nana ta sauke, dan ta nunawa Nafisa komai yadai daita tsakanunta
da nura.

Tashi sukayi suka shige daki, Nafisa tasa Nana wanka ta dau kayan barci fitunannu,
tasha turarurruka, kala kala, nafisa ta dakko wani tsimi a jakar ta tabawa nana. "
momy ce tace inkawo miki dan tasan wadan can sun kare ko."

amsa Nana tayi tasha ta dau hijjabi amma Nafisa ta hanata.

Haka ta futa ta tafi dakin nasa.

Nafisa kuwa duk ta ganosu, kuma fatan ta kan tabar gidan komai yadawo daidai.
Bana tana shiga Nura yadago kai yana kallonta, yama manta duniyar dayake, ita kuwa
duk ta ji kunya ta kamata tarasa yazatayi, Nura bai san sanda yatashi ya rungumeta,
dama amatse yake dan rabonsa da mace harya manta kazanta tahanashi zuwa gun Karima
gashi koyadaure yaje baya jin daidai dan bata gyara.

Shafata kawai yake dan yama rikice gaba daya.

Ita kuma tanason guduwa amma tana tuna abinda malaminta yace, indai mijinki
yakiraki shinfudar kikaki zuwa to mala iku saisun kwana suna tsine miki.

Ahaka har ya kaita kan gado, yarabata da kayan jikinta gaba daya..

*suba ta gari*

*muje zuwa*
[11/3, 02:19] Shaxeee Marubuciyan Ahalikita: 📓📓📓📓📓📓📓📓

*AHLILKITAB*

📓📓📓📓📓📓📓📓

*ZAMANI WRITERS ASSOCIATION*

*FOLLOWING US ON THIS DENTAILS*


--------------
*fb./ZAMANIWRITERSASSOCIATON*
------------
*CHECK OUR BLONG'S*
*zamaniwriters.blogspot.com*
----------
*DROP YOUR COMMENT AND REPORTS ARE HIGHLY WELCOM ON THIS EMAIL ADDRESS:*
*zamaniwritersassociation@email.com*

*🦋NA:SHAZEEE.*

*PAGE 27&28*

gari yana wayewa nayi saurin komawa dakin dan in dakko muku rahoto, inashiga dakin
naga.

Nurane ya dauki Nana uwa yar byba, yayi bandaki da ita, ruwan zafi ya hada mata ya
sakata aciki, duk abinnan da ake, Nana idon ta arife yake takasa bodewa.

Cikin zolaya Nura yace. " ko inmiki wankan bazaki iya ba naga alama." Ruwan yafara
zuba Mata tayi sauri rike masa hannu. " dan Allah yahya kabari wallahi zan iyayi da
kaina."

" kin tabbata zaki iya." 'Daga masa kai tayi.

Mur mushi yaya futo daga bandakin, jinsa yake cikin farin ciki uwa sabon aure, dan
ko randa aka kawo karima ma da bacin rai yakwana.
Da kansa ya gyara dakin, ya yi sallah yana kidar wa ya tsaya mazimi.

Nana kuwa tana bandaki tana gasa jikinta sosai tana mamaki dama haka yaya yake,
yabata mama ki sosai ashe yanada saukin kai. " aikwa zan dage da gyara kaina in
mallake mijina ba boka ba malam, zancire duk wata kunya inkula da mijina, da ma
kunyace take cutar matan hausawa."Duk azuciya take wannan maganar.

Tana gamawa ta daura tahul tafuto.

Nura yana ganin ta futo, yatashi yaje gurunta bai tsaya saurarartaba ya dauketa uwa
yar byba.

Kan gado ya ajiyeta, yadakko man kan mudubi yafara shafa mata. " kinsan yanzu sai
an lalla'baki uwa jinjiniya saboda kar kiyi kuka." Dariya tayi dan tasan tsokanar
ta yake, kukan data dinga yimasa jiya ne, shine yake tsokanar ta, yana gama shafa
mata ya dakko mata, jallabiyar sa sabuwa, dan bata da kaya adakin, dubawa yayi babu
hijjabi adakin. " bara inje in dakko miki hijhabi." Fucewa yayi yatafi dakinta.

Yana futa nana ta sakko 'kasa tayi sijjada, tagodewa Allah daya amshi addu,arta.

Nafisa kuwa har ta tashi salla, tana cikin sallar Nura yazo, yana murda kofar
yajita abude, shiga yayi yabude kwaba yadakko mata doguwar riga da hijhabi.

Futowa yayi yakawo mata tacire ta jikinta tasaka tata tasa hijjabi, yajamusu jam i.

Suna kidarwa sukayi karatun kur,ani sukayi addu,oi suka koma suka kwanta abinsu.

*********************

Safiya tanayi Karima ta tashi ta nufi dakin Nura dan akwai abinda takeso ta
tambayeshi.

Turus ta tsaya dan ganin babu shi acikin dakin kuma ba alamar aciki yakwan.

Tashin hankali, tuni gumi yafara tsatstsafo mata ta ko ina. " kaddai Nura a dakin
waccan matar yakwan, indai kuwa wani abu yashiga tsakaninsu nashiga uku nida
ummata, burinmu zai lalace." Cikin tashin hankali take wannan maganar.

Dakinta ta koma asukwane ta dau waya takira ummanta tagaya mata.

Itama hankalin yayi mugun tashi Domin akwai sharadin dawani boka yakafa musu kan
Karima ta auri Nura.

*********************

Ammi ce azaune abakin gado rike da kanta, dan juya mata yake gaba daya.

Zuwa can kuma saiya dena, jitayi gaba daya uwa ba itaba, abubu duka dinga dawo mata
ahankali.

Cikin mamaki Ammi tace. " to maiyasani aikata haka bayan nasan gaskiyar abu, garin
ya nake adawa da kishiya ta bayan muna zaman lafiya, mai yasa nabar Nura ya auri
karima." Duk tarasa wadannan amsoshin nata tashi tayi tashi bandaki tayi wanka tayo
alwala ta dawo dakinta tayi salla.

*********************

Nura yariga Nana tashi, ahankali yafuce zuwa falo, ganin Nafisa yayi tana gyara
dakin, gaishe shi tayi ya amsa. " inkin gama muje muyi abin kari, dan bata jin
dadi."

Mamaki ne yakama Nafisa rabon da da taga wannan hali agun Nura tun rigimar auren
sa da Karima, da suna zaune abinsu lafiya amma komai daga baya ya war gaje.

Batace komai ba tabishi sukaje kicin suna aiki suna hira abin sha awa, Nana kuwa
data tashi, ta ga bayanan saita futo taje dakinta, taga ba Nafisa futowa falonta
tayi, anan tajiyo hirarsu akicin, shiga tayi taga sunata aiki suna hira, abin
yaburgeta sosai. " dama wayo kukamin kuka ki tashina kuke aikinku ko."

Cikin farin ciki Nura yace. " to bagashi yanzu kin tashiba, mukuma munkusa
gamawa."

Dariya tayi, tace. " aikwa sai ankarasa dani."

Tayasu tayi suka gama suka kawo falo, sukaci suna dariya, abinsu, suna gamawa Nana
ta temaka wa Nura ya yi wanka ya shirya yafuto, ta rakashi yashiga mota yatafi.

Dawo wa Nana tayi ta tarar da Nafisa tana kallo, zama tayi tace. " Nafisa nafus
kanci wani abu atattare da yaya kuma kema naga wani abu a fuskarki yau, inaso
kigayan komai domin in gane kan al amuran."

Nufasawa Nafisa tayi, tace. " yanzu zan gaya miki komai kuwa tundaga farko, amma
abin akwai al ajabi da ban haushi harma daban mamaku, farkon abin shine.....

*kuyi hakuri da wannan☹*

*muje zuwa*

You might also like