DANGIN NONO WRITERS ASSOCIATION
{Da Inganci Mukayi Fintinkau}
Bismillahi wabihi nasta'in
Godiya ta tabbata ga Ubangijinmu daya halicci alk'alami, yasanar da bawa
abinda bai saniba.
Salati da aminci da d'aukaka su k'ara tabbata ga farin jakada,babba d'an
Abdullah Muhammadu-Sadiqul-amin,da alayenshi da sahabban shi da wad'anda ke kan
tafarkinshi har zuwa ranar rarrabe tsak'anin k'arya da gaskiya (Alk'iyama).
Godiya ta musamman ga Umar Dalha.Dakai muka kai ga gaci.
Kima:-
Kimarku muke gani Katsinawan Dukko d'ak'in kara,mun gaisheku gaisuwar kima,
musamman Maskawan k'aramar hukumar Funtua da ahalin Muhammadu Me-ruwa dana Tankon
Marka anan BCG,dana garin Gadagau.
Dan tunawa da:-
Gwanarmu a duniyar marubuta littafan Hausa.
Marubuciyar 👇
{Dare ga mai rabo...}
Halima Abdullahi (Amma).
My One & Only Aminu A.Baba.
Lovely Sister Badi'atu Ibrahim.
Son Aliyu Yahya Namadi.
Little peerless Ali Yahya Namadi (Malam Garga)
Ubangijinmu ya kyautata makwancinku😭
Sadaukarwa:-
Ga d'aukacin Hausawa da Fulani...musamman Ya'yan Ibrahim ako ina kuke a fad'in
duniya...😊
...GWAJIN DAFI 💔
Almost true story
Daga alk'alamin🖊
Ya'yan Ibrahim
Saudat A.Baba (Asdilat KD)
Da
Bara'atu Ibrahim (Ra'ibs)
Shafi na d'aya.
A kwance yake cikin damuwa, hawayen da suka cika idanunshi suka
fara zubowa ta gefe da gefen fuskar shi suna gangarawa jikin matashin daya d'ora
kai,a haka bacci ya d'aukeshi.Da sallama tashiga dak'in,kwanan abincin tabud'e,
yananan yadda tazubashi, ALLAH ma yasa ya bud'e ya ga abinda yake ciki,da sanyin
jiki tad'ago tana kallanshi,bacci 6arawo kamar yadda ake fad'a,to da alama saceshi
yayi,tagirgiza kai cikin tsantsar k'aunarshi da tausayin halin da yake ciki,komai
yana nan rad'am kamar yan awannin da suka shud'ene abin yafaru.Tausayin shi yadad'a
mamayar zuciyar ta,dak'yar tamik'e daga tsugunan zuwa D'akin-girki tad'ora musu
abincin rana.Bata koma dak'in ba sai da aka fara kiraye-kirayen sallar azahar daga
mabambantan masallantan unguwa.
"Julaib... Julaib... Julaib...
Cikin natsuwa take kiranshi.Dak'yar yabud'e idanunshi da sukayi jawur saboda damuwa
ga kuma bacci me nauyi daya kamasu.Tad'anyi murmushi"yi hak'uri na katse maka bacci
lokacin sallah ne yayi.Yabita da kallo kamar bai fahimci abinda tafad'a ba.Tabud'e
baki zata sake magana sai kuma tayi shiru tawuce dan sauke nata faralin.
Yana dawowa daga masllaci takawo mishi abinci "Ta kalleshi,barka da
dawowa" a zuba maka yanzu ne?"shiruma amsace. Yad'auke kai daga kallan da take
mishi.Da sigar rarrashi tazauna agefenshi"Julaib... kayi hak'uri,zama da yunwa ba
shine mafita ba,ba shine zai magance damuwar zuciyarka ba,zama da yunwa k'ara
dagula maka lissafi kawai zaiyi, Dan ALLAH Julaib kadaure kaci kome k'ank'antar shi
zai samar maka da natsuwa, natsuwarce kuma zata ba ka dama na tsayawa kai da fata
wajan yawaita addu'a agaresu.Tazuba mishi faten waken dayaji kayan had'i
k'amshinshi yagauraye d'akin."Dan ALLAH kadaure kaci, tamik'a mishi farantin amma
yak'i kar6a, tabishi da kallo tana murmushi "To abaki zan ba ka? Tad'ibo a cokali
indai hakan kake so ni a wajena abune me sauk'in gaske,takai cokalin tsakanin
la66anshi na sama dana k'asa"Haaa bud'e bakin ka kaci kayan k'arin lafiya da gina
jiki.
Dakata haka malama!
Yajuyo da 6acin rai me yawa a tashi fuskar yana mata wani irin kallo data kasa
fassarawa"ni na ce miki inajin yunwane?Ko nasafe ban ciba amma kin sake dafo wani
saboda almubazzaranci?Tabud'e baki zatayi magana yayi saurin katseta"Keee! kwashe
kayanki ki fita bana san hayaniya.!Yahaye gado kanshi na mishi wani irin
matsanancin ciwo kamar ana buga mishi guduma.
Tabishi da kallo cikin mad'aukakin mamaki,tsawon zamansu da duk
halin-ko-inkulan dayake mata tana mishi uzuri,akwai damuwa me yawa atare dashi,to
amma yau itace rana ta farko daya 6ata mata rai,cikin raunin murya dake shirin
fashewa da kuka tace"Julaib... hawaye masu d'umi suka zubo mata sharrr...
Julaib...dama na san baka so na,to yau na dad'a tabbatar da hakan,na zama maka
matsala ko?Adole kake zaune dani ko? Tasauke numfashi toh, ai ALLAH yanaji yana
kuma gani na yi iya iyawata dan kawar da damuwar zuciyarka amma hak'ata bata tadda
ruwaba,na sani za fi da rad'ad'in da kakeji bazai ta6a barin zuciyarkaba matuk'ar
kana numfashi a doran k'asa, to amma ya kamata ka sassautama ranka,"Shekaru uku ba
kwanaki uku bane"A shekara kwanaki d'ari uku da sittin muke dashi,to kwanakinnan
sun ninka kansu har sau uku,kaga kwanaki dubu d'aya da tamin,kwanakin da sukayi a
mace kenan"kukan mutuwa baya dawo da matacce"kasama ma zuciyar ka salama kayi
rayuwa kamar yadda kowani d'an Adam me numfashi a doron k'asa yake yinta.
Julaib...to wai me yasa baka jin tausayina na mace me raunine?
Tasake binshi da kallo sai kuma ta gyad'a kai,saboda kawai baka so na?To shikenan
amma ina so kasani ni har kwanan gobe ina k'aunarka duk da bana samun irin kulawar
data dace,ni na yadda da abu daya,aure bautar Ubangijjne dan haka zan cigaba da
dauriya dan nima kamar yadda Abbana yafad'a min"ina kwad'ayin babban rabo a gidan
gaskiya(Darul-karamah)ni zan sauke nauyin dake kaina,amma tunda ba ka san ganina,ba
ka san abincina,ba ka san hayaniya da duk wata kulawa tawa to ko Insha-ALLAH zan
kiyaye, zan killace kaina a d'akina,amma fa k'ofata a bud'e take ina maraba dakai,a
duk lokackin dakake da buk'atar tallafina kasanar dani kai tsaye,ni kuma zan baka
tallafi irin wacce tadace da buk'atarka, karambani ne dai bazan kuma ba tunda kai
ba a maka gwaninta...
Tajuya da gudu zuwa d'akinta, gado tafad'a tana wani irin kuka,
kukan data kasayi agabanshi hawayen sharrr...sharrr...suke zubowa, tad'aga hannayen
ta sama"Ya ALLAH kataimaki mijinah...kayaye kunci da damuwar zuciyarshi, kamaye
hakan da natsuwa...Ya ALLAH Ju..Jul.. Julaib..d'in...sauran kalaman suka mak'ale
saboda kukan yaci k'arfinta,takifa fuskarta a jikin matashin hawayen nacigaba da
zubowa.
Kalamanta sun sanyaya mishi jiki, yarintse idanunshi da k'arfi
yana jin kanshi kamar zai rabe gida biyu,"Wayyo ALLAH nah?!yafad'a a wahalce yasa
tafukan hanneyen shi yak'ank'ame kan,jijiyoyin wajan sun fito rad'am kamar shatin
bulala suna kuma harbawa da k'arfin gaske. "Wai...Wayyoh ALLAH...!Sai yafara fad'in
"Babu tsimi babu dabara sai ta Ubangijjnmu.wucewar wasu dak'ik'u ciwon kan yad'an
sarara mishi...sai kuma zuciyarshi tafara tunatar dashi.
"Iyayanta sun maka halacci, sun maka karamci,sun taimakeka a
lokacin da kake buk'atar taimakon,lokacin da ba ka da kowa ba ka da komai, lokacin
da ba ka san a wace duniyar kakeba.
Ruqayya matarka tana sanka tana k'aunarka,ka ga haka,ka kuma san da
haka tun ganin farko daka mata bayan ka bud'e idanunka tsawan kwanaki,makonni da
watanni a wata duniya daba zaka bada labarin wani abu guda d'aya na cikin
taba,idanunka da ita suka fara yin tozali,haba Julaibib wannan ba halin girma
bane,dan halal ai baya manta alheri,sai dai me halin kaji"Ci ka goge baki"abinda
yake damunka bai shafe taba,ba ita takar zomo ba bai kamata ta d'auki rataya ba...
Kai musulmi ne kayi imani da k'addara kuma yana daga cikin cikar
musulunci, wannan al'amarik'addararrene tun daga lauhul-mahfus.. Zuciyar shi
tacigaba da tunatar dashi. Yasauke numfashi da ajiyar zuciya, k'irjinshi ya mishi
nauyi yana kuma mishi suya,yahad'iye wani zazzafan abu kamar garwashin wutan da aka
bad'e shi da dakakken barkono d'an munci.
Yamik'e zaune dak'yar sannan yaziraro k'afafunshi k'asa zaije ya
rarrashi Ruqayya dan yana jiyo sautin kukanta, amma jirin dake shirin kaishi k'asa
yasa yakoma yazauna ranshi ba dad'i...Yanzu ace mahaifin Ruqayya yashigo,ya zaiji
idan yajiyo kukanta?Tabbasss ko bai nuna ba amma bazaiji dad'iba,gaskiya iyayanta
sun maka karamci fa.Yajijjiga kai cikin gamsuwa,sai yamaida tafukan hannayenshi
yarufe fuskarshi cikin tunanin rayuwarshi.
➿➿➿➿➿➿➿➿➿➿➿➿➿➿➿
Zonkwa ne shalkwatar (Headquater) k'aramar hukumar Zangon-Kataf d'in
kudancin Jahar Kaduna.Babban garine matattarar jama'ar sauran jahohin Nigeria da
sauran yankunan nahiyarmu ta Africa,mutanan Zonkwa wayayyun mutane ne saboda masu
ilmine,babban abun sha'awar,yadda ake zaune lafiya duk da tarin bambance bambance
ta fuskar addini da al'adu,ga kuma k'asar noma me albarka.Manyan yaran wannan yanki
guda biyu ne Kaje(Kajawa)amma bayan yak'in Zangon-Kataf sai suka zamanantar da
sunan suka koma kiran kansu da Bajju.
Baranzan da matarshi Zamburan sune asalin tushen Kaje,su d'in
mafarautane da suka taso daga yankin Bauchi da Jos,ance saboda sunk'i kar6an
jihadin D'anfodio.ance kafin su k'araso nan, matarshi Zamburan da wasu daga cikin
tawagarshi sun mutu,amma ita Zamburan ta mutune a garin Forest sai sukazo suka kafa
sansaninsu a saman dutse suna kiran wajan da Kufai(Kufayi) kamar yadda akasan
maguzawa nayi a can bayan gari, amma yanzu gine gine ne masu ban sha'awa awajan na
sarkinsu (Agwam Bajju) hausawa masu yawan fatauci suna zuwa harkar cinikayya irin
ta da,ta bani gishiri in baka manda a tsakaninsu,ga zaman lafiya, zaman lafiyar da
tasa idan sun shigo cikin gari talla sai da kayayyaki kamarsu citta,daddawa,zuma
dasauran dangogin su,indai kuna shiri kukace kuna son yarsu ko d'ansu to ko Insha-
ALLAH zasu baku sun kuma zama naku har abadan duniya,lokaci zuwa lokaci idan sun
shigo cikin gari za suzo suganku, kuma zaku kaisu wajansu lokaci zuwa lokaci.ALLAH
Alhakimu sunk'i musulunci,amma sun bama musulmai kyautar mutum sukutum da guda,sun
kuma san musulunci da sallar za suyi,sai su taso su girma suna musulmai,d'aya daga
cikin k'ananan yaran da suka taso a cikin musulunci yar asalin k'auyan Narom
ce...Itace Khadijatul-kubra inda wasu bayin ALLAH mutanan Daura su suka nuna
soyayyarsu gareta mahaifanta kuma suka yadda suka bar musu ita,Bintan Daura tazama
uwa a wajanta,mijinta Garban K'aura yazama uba a wajanta, tagirma suka mata aure
itama ta hayayyafa d'aya daga cikin ya'yan data haifa itace kakarsu Sudaida tawajan
uwa,kuma shi Abubakar (Garban K'aura) aikin d'an sanda yakawo shi garin Zonkwa
shekaru masu yawa,suka zauna a gidan Amasaye itace kakar,kakarsu Sudaida ta wajan
uwa.
Asalin wad'anda aka tarar a k'waryar cikin garin Zonkwa Fulanine masu
kiwon shanu,da mutane suka fara yawaita sai suka tashi suka dad'a nausawa cikin
daji kamar dai yadda al'adarsu take, dan shanunsu su samu wadatacciyar ciyawa da
ruwan sha,ba tare da sun takurama wani ba,shima kuma bai takura musu dasu da shanun
suba,Ance adai-dai wajan da aka tarar da Fulani makiyayannan anan wajan aka gina
musu k'aton masallacinsu na Juma'a kuma masallaci na farko a garin,kusa dashi aka
gina gida da Limamin da masarautar Zazzau ta turo musu dan yadinga musu
limanci,yana kuma karantar dasu addini.
Ibrahim Nabarandi asalin Bakatsine ne masu yawan fatauci,bayan tashin
Fulanin nan shine yak'afa cikin garin Zonkwa,gidanshi babban gida ne kun dai san
zamanin da daba siyan fili a ke yiba kai zaka shaci yadda yamaka kayi gininka,
shine yazama Sarkin hausawa,duk wani bak'o a gidanshi yake sauka kafin a bashi
muhallin zama.Manyan zauruka(soraye) irin nada sun kai goma anan duk wani bak'o
indai namiji ne zaiyi zamanshi,mata kuma akwai d'akuna a cikin gida da aka gina
musamman saboda irinsu,suna mishi kirari shi Ibrahim Nabarandi da:
(Naladi bawan bak'o,yan gari kuma bayinka)
Su kuma Kataf(Katafawa)suma bayan yak'in Zangon-Kataf d'in sai suka
zamanantar da sunan suka koma kiran kansu da Atyap,Su kuma ana tunanin asalin
maguzawan Kano ne suka fito suka kafa sansaninsu a wajan,Masu yawan fatauci
musamman Kanawa kowa ai yasan mutanan Kano ba cima zaunan al'umma bane,harkar
kasuwanci a jininsu yake tun tale-tale,idan suka zo a nan suke ya da Zango bi
ma'ana suke hutawa daga doguwar tafiyar da sukayi,bayan sun huta sai su shiga
k'auyuka da sauran garuruwa dan harkar fataucinsu, to dalilin hakan garin yasamu
wannan suna na Zangon-Kataf...Shi kuma asalin ma'anar"Zango Ciwon kurkunune"da yake
fito ma mutum a k'afa,ko ad'an yatsa sai yakasa tafiya saboda tafiyar k'asa da
akeyi a da bana wasa bane,wani zarene yake fitowa a wajan sai yayi kamar zai tsinke
yatsa ko k'afar,to a inda mutum yazauna zaman jinyan da zaiyi har sai ya warke zai
iya tafiya,to sauran abokan tafiya ba jiran mutum za suyiba,to idan aka had'u da
wasu,ko kuma suka koma gida sai afara tambaya"ina wane? Sai abokan tafiyarshi suce
ai ya ya da zango.
Akan kasuwa akayi wannan yak'in na Zangon-Kataf,su Katafawa sunce
sai dai a tashi daga inda ake cin kasuwar a koma inda su suke so, tak'amarsu ai
sune tushen wajan,kowa yazo a bayan sune,dan haka yadda suke so dole haka kowa
zaibi,Su kuma Hausawa da Fulanin wajan sukaja tunga ALLAH yakashesu kasuwa baza ta
tashi daganan ba...Kaya-kaya-kaya kowa yaja ya kafe nashi ra'ayin za abi...
Atakaice kenan.
Sarkin Zazzau na wancan lokacin adalin sarkine,daya samu labarin
bayyanar wad'annan mutannan sai ya turo wakilanshi dan su musuluntar dasu, sai dai
kash... Wakilan sarki sunci amanar sarki basuyi abinda yakamata ba,sai suka bi
yarima suka sha kid'a,suka sasu a k'angin bauta,su kama mata da ya'yansu wacce duk
tamusu sumata fyad'e,su kwashe musu katti majiya k'arfi su tafi dasu masarautar
Zazzau a matsayin bayi dan haka akwaisu da yawa a masarautar Zazzau,d'aya daga
cikin ire-irensu shine Yakowa wanda har gwamnan kaduna yayi kafin ya mutu,shi yasa
suke wata wak'a wai (Ba zamu ramaba ALLAH ne zai rama mana🤔)
Suka tafi suka bar baya da k'ura dan da yawan matan da suka ma fyad'e
sun samu ciki kuma basu zubar ba sun haihu sun mayar da ya'yan irinsu kaico! kuma
da yawansu an turasu Biafara Inda Ojuku shima ya jazama k'abilarshi ta Igbo
haramcin yin shugabancin k'asar Nigeria har abadan duniya"garin neman gira an rasa
idanu"Bayan yak'i suma sun kwaso ganimar yak'i,duk macen data musu suma sun taho da
ita yankinsu dan suma anjaza musu salalan tsiya tunda basu da kowa duk sun mutu a
wajan yak'i.
Suna cikin k'unci da damuwar abinda aka musu kuma ba daman ramawa
kasancewar su bayi sai ga bayyanar wakilan kiristanci(Missionaries)Su basuyi abinda
wakilan Sarkin Zazzau suka yiba,suka taimakesu da duk irin taimak'on dasu kaga ya
dace su basu, suka dinga musu wa'azi akan addinin kiristanci (Christianity) shine
addinin gaskiya,su kuma sukayi na'am da hakan suka rik'e addinin da hannu biyu,nan
da nan suka waye ga kuma bayyanar ilmin boko an gina musu makarantu,asibotoci da
duk abinda ake buk'ata,shine sai suka bar zaman kan dutse suka kafa k'auyuka da
garuruwa suka warwatsu tunda dama sunada mugun yawa, kamar irinsu:-
Fadiya.
Fadan Kaje
Madauci.
Madakiya.
Katsit.
Kamurun Kaje.
Ladduga.
Zonkwa.
Da sauran su kuma ance wasu daga cikin sunayen Ya'yan uban Bajju d'inne Baranzan
aka sama k'auyuka da garuruwan.
Suma Katafawa suka kafa nasu k'auyuka da garuruwan kamar irinsu:-
Asha a wuce.
Bakin gogi.
Dama kasuwa.
Mashan.
Unguwan wakili.
Gora Bafai.
Samarun Kataf.
Zangon Kataf.
Da sauransu da sauransu.Amma duk da haka Kajawa da Katafawa(Bajju da Atyap) masu
yawan gaske sun zama musulmai iyaye da kakanni,suna kuma musuluncin da gasken-
gaske,d'aya daga cikinsu Maryam Gid'ad'o Idris, inda tazo garinsu Samarun-Kataf
tagina asibiti, masallacin juma'a da makarantar addini me suna
(HAYATUDDEEN ISLAMIYYA SAMARUN-KATAF)
Musulman wannan yanki Hausawa da Fulani sun amfana kwarai da gaske da wannan
makaranta wanda ta sanadiyyarta suka fara halartar gasar Musabak'ar Alqur'ani me
girma ta Jahar Kaduna,dan manyan malamai masu addini tad'auko daga Bauchi da
Adamawa,sai wasu daga garin Samarun-Kataf,da Zangon-Kataf da Zonkwa, sune suke
koyarwa.
Shekaru masu yawa sun shud'e, an cigaba da mu'amala cikin kwanciyar
hankali kowa yana neman kud'inshi lafiya lau.Wannan kenan atakaicen takaitawane.
Doctor Julaibib Abdullahi D'ansarai asalinshi d'an D'ansarai
ne,k'auyene dake k'aramar hukumar Malumfashi a Jahar Katsina,suma a wayansu suke
saboda ilminsu,shi k'wararran likitan mata da k'ananan yarane,yayi aiki a jahohi
biyar daga nan gwannati ta turoshi wannan gari a matsayin babban likitansu,garin
yama Doctor Julaibib dad'in zama shida Iyalanshi,yayanshi guda uku suka cigaba da
karatunsu,suma sauran yan'uwa na D'ansarai duk wanda yazo dan ziyara sai garin
yamishi dad'in zama dan haka sai yanemi canji aiki yadawo nan da iyalanshi suyi
zamansu,da haka danginsu na D'an sarai suka dawo Zonkwa gaba d'ayansu aka cigaba da
hayayyafa.
bayan ya gama aikin aikin gwannati (retired) Sai bai koma D'ansarai
ba,yan'uwa da zai koma ko dansu to suna zaune anan,yagina k'atan gidanshi yacigaba
da rayuwarshi a haka har Ya'yanshi suka girma sukayi aure,da matar d'anshi Bishir
ta haihu sai Bishir yama Babashi kara yasa sunan mahaifin Doctor Julaibib wato
Abdullahi.Ai ko Dr.Julaibib yaji dad'in wannan kara dan haka yad'auki san duniya
yad'orama Abdullahi,kome nashi na Datti ne kamar yadda yake kiranshi,Abdullahi ya
taso cikin gatan daya zarce na duk sa'anninshi.
zai shiga aji d'aya a secondary ALLAH yama Doctor Julaibib rasuwa
mutuwar data dakesu sosai,sannu ahankali kuma zafi da rad'ad'inta yanata
raguwa,kafin matarshi tagama idda itama tace ga garinku nan.
Mahaifansu suka cigaba da kula dasu.koda yagama Secondary sai
yafad'ama mahaifinshi yafi sha'awar kasuwanci fiye da cigaba da karatun
boko,mahaifinshi yayi na'am da hakan duk shi d'an boko ne ma'aikacin gwamnati, yace
kowa da abinda yake sha'awa a rayuwarshi, idan aka hana mutum abinda ya keso to an
shiga hakkinshi, sai dai idan abinda ya keso d'in shari'a bata yadda dashi
bane.Yakawo kud'i masu tsoka yabashi tare da mishi addu'ar ALLAH ya sanyama
kasuwancin na shi albarka.Haka rayuwa tacigaba da tafiya kamar yadda tasaba har
suma mahaifan nasu suka kwanta dama.
Alhaji Abdullahi dattijon arzik'ine, matarshi ta aure guda d'aya da
albarkan ya'ya uku, Karima,Asma'u da kuma autansu Julaibib da suke kira
D'ansarai,musamman mahaifinshi.Alhaji Abdullahi yanaji da Julaibib sosai dan bai
manta gata da soyayyar da Dr. Julaibib ya mishi ba.
Julaibib ya taso cikin tarbiyyar musulunci,ALLAH sai yatarfama
garinsu nono yarone me jin magana,duk yadda iyayan nashi suka d'orashi a haka
yataso.Yana gama secondary yasamu gurbin karatu a Kaduna State College Of
Education(KSCOE)Gidan-Waya,shida abokinshi kuma d'an uwanshi Musaddiq.Duk wata
d'awainiya ta karatun Alhaji Abdullahi ne yayita ba tare da mahaifin Musaddiq kuma
Kawu a wajan Julaibib d'in ya bada ko sisin kwabo ba.
Alhaji Ibrahim shine aminin Alhaji Abdullahi tun zamanin k'uruciya
abin kuma bai rusheba har girma,Alhaji Abdullahi shi yaga kanwar abokinshi yace
yanaso itama ta amince aka d'aura musu aure.
➿➿➿➿➿➿➿➿➿➿➿➿➿➿➿
Ibrahim Me-Lambu shine tushensu Alhaji Ibrahim,dan haka Ya'ya da
jikoki da Ya'yan jikokin gidan suna amfani da Me-Lambu a k'arshen sunayen su na
makaranta,wasu ma da wane ko wance Me-Lambu suke amfani.Ibrahim Me-Lambu ya samu
sunan Me-Lambu ne saboda sana'arshi ta saida kayan lambun kamarsu:-
tumatur,tattasai, albasa, alaiyaho,yalo,latas, karas,lafsir da sauransu da
sauransu.
Asalinsu yan k'aramar hukumar Tsanyawa ne ta Jahar Kano.Cirani
yakawosu garin Zonkwa Iyaye da kakanni,dad'in garin da kuma k'addarar ALLAH inda ya
rubuta maka zama to ba makawa anan d'in zaka zauna kome dad'i ko rashin dad'in
waje,da suna zuwa ganin gida daga baya suka daina sai kalilan daga cikinsu dan suna
da yawan gaske a Zonkwa,wasuma basu da sauran dangi na jini a Tsanyawa,Unguwa
gudace dasu k'atuwa ta musamman da ake kira"Lungun Kanawa.Sukayi zamansu a nan suka
hayayyafa.
Alhaji Ibrahim matanshi na aure guda biyune,Mama itace uwargida kuma
mahaifiyarsu Musaddiq,Khausar,da sauran kanninsu maza da mata.Sai Umma mahaifiyarsu
Aminu,Adnan,Sudaida da tarin kaninsu maza da mata.Kan ya'yansu a had'e yake saboda
matan sunada fahimtar juna,mijinsu kuma yana musu adalci dai-dai iyawarshi.
➿➿➿➿➿➿➿➿➿➿➿➿➿➿➿
Julaibib yana zaune atsak'ar gidansu yana nazarin wani littafi duk
da wancan makon suka samu hutu.Musaddiq yashigo da sallama,yad'an daki kafad'ar
Julaibib "Haba malam an samu hutu kaima ya kamata ka hutafa"Julaibib yayi kamar ba
dashi yake maganaba.Musaddiq ya jijjiga kai"gaskiya na gaisheka"yawuce dak'in Inna,
tana zaune a inda ta idar da sallar walha,sai yasaki labulan"to barinje na dawo
anjima".Daga ciki ta amsa"shigo ai na idar.Yazauna suna gaisawa,sai yafara mata
hirar Safiyya budurwarshi da sak'on data bashi yakawo mata.
Aminu shima yashigo da sallama yana fad'in shi wai D'ansarai baya
gajiya da karatune Inna?Yakama ha6arshi da hannun dama"Tabbb ina ruwan Alhuda-
huda,koda yake bazai gajiba tunda yafi sha'awar zaman gida, gaskiyar magana wannan
da macece da sai ince ALLAH ya kashe ya ba mijinta kakarshi ta yanke saka
wallahi.Inna takalleshi"kamar yaya?Yawaiwaya inda Julaibib yake zaune"o Inna aishi
ya huta da fitinar mata tayawan tambayar unguwa, zani gidan wance,anyi haihuwa zan
shiga barka, zanje dubiya dan gidan wance an mishi shayi, muna da biki agabas,gobe
suna a arewa,jibi tarewar yar gidan wance a yamma, zani, zani, zanin mata ai bata
k'arewa.Inna tayi dariya.
Julaibib yakalleshi ba laifinka bane, ka ci bashi zan kuma
rama.Aminu yagyad'a kai"Nima zan so haka,ina nan ina jira,yashige D'akin-girki
yad'auko kunun tsamiyarshi yafito"Inna yau naci aikine kamar ba gobe,tun daga
sallar asubahi sai yanzu zan koma gida.Inna takalkeshi da tausayi "Wayyo sannu,a
lallai ka aikatu neman kud'i makahon aiki, ALLAH dai yak'aro masu albarka.Amin Inna
nagode barinje in kwanta.To ALLAH huta gajiya.
Kasham...da yaransu na Bajju yana nufin abu me kyau.kuma a zahirin
gaskiya wannan suna ya dace da ita dan me kyance, matsakaiciyace a tsawo,me k'irar
kalangu,gata da yalwataccen gashi me tsawo da santsi,shi yasa ba kasafai take kitso
ba, manyan idanunta masu maik'o(Oil eyes)da d'an k'aramin bakin ta su suka k'ara
mata kyau na musamman,wankan tarwad'a ce a yanayin kalar fatar jiki,itama dalibace
anan Kaduna State College Of Education(KSCOE) Gidan Waya.Aranar farko a kuma kallan
farko data ma Julaibib so da k'aunarshi suka mamaye zuciyar ta ba tare data shirya
hakan ba, duk tarin samarin dake mata nacin suyi soyayya sai taji ba wanda yamata
nan duniya daya wuce Julaibib,ta so k'warai a ranar suyi magana amma hak'anta bata
tadda ruwaba, saboda kwarjinin daya mata lokacin data tunkareshi,ashe gaba da
gabanta aljani daya taka wuta.To amma me san d'an tsuntsu shi yake binshi da
jifa"naci da shishshiginta yasa suka fara gaisawa duk da idan ba ita ta gaishe
shiba ko zasu had'u sau dubu a rana bazai nuna yama ta6a ganin taba.
Duk inda tasan zata ganshi to in dai ba tana da lecture ba to tana
wajan,yau da gobe sai ya fahimci tana neman wuce makad'i da rawa sai yadad'a
kamewa,amma da Musaddiq sun saba dan suna d'an ta6a hira dan shima yana da
miskilanci idan baiga dama ba,amma gangaran d'in miskilai sai "Julaibib Abdullahi
D'ansarai ".
Musaddiq yana zaune a capteria yana cin abinci tazo tasa meshi tana
fad'a mishi "Wallahi Musaddiq na ka sa danne zuciyata,na ka sa yin yak'i da
ita,gaskiyar magana ina san Julaibib zan aureshi".
Cikin tsoro da mamaki yace kina san Julaibib?Yagirgiza kai"to gaskiya
ki cigaba dayin yak'in wajan ganin kin cireshi a zuciyarki,baza ki samu abinda kike
so...ta tareshi da sauri"me yasa za kace haka? Saboda baki dace dashi ba"wai d'an
dambe ya d'auki adda"ni nasan Julaibib farin sani wallahi,kinga kuma addininmu ba
d'aya bane. Idanunta suka ciko da k'walla,"wai yau ita ake fad'ama namiji ba zai so
taba a yadda take d'in nan me kyau...
Tayi jimmm..na wucewar wasu dak'ik'u "Musaddiq kafad'a mishi "ni
Kasham tanuna kanta ina sanshi,ina neman goyon bayan shi ya yadda muyi aure,na
mishi alk'awari zanyi abinda yakeyi (Sallah)zanbi addininshi (Musulunci) Abincin da
bai gama ciba kenan yamik'e dan zata dame shine kawai.Tabishi da kallo dan ALLAH
kafad'a mishi.Ya amsa da To.
Rannan tana zaune a d'akin karatu, nazari da bincike(Library) ta ka sa
yin abinda yakaita tunanin Julaibib ne kawai yacika kanta,kamar ance ta d'ago kai
sai kawai gashi yashigo dak'in,yaja kujera yazauna.
Ganinshi yak'arasa kashe mata jiki, tanajin wani sabon yanayi daya
tsirga ilahirin jiki da zuciyarta,gefe guda kuma tana jin takaicin k'in kar6an
tayin soyayyar data keta mishi naci duk da kasancewarta k'wararriya data isa da
kanta in dai a fagen hilatar d'a namiji yafad'o tarkon tane,ba wanda ta ta6a
d'anama tarko bai fad'aba sai Julaibib,ta rasa me zatayi dan shawo kanshi,dan
abinda takeji game dashi ba irin abinda takeji game da sauran maza bane,wani irin
abune me sark'ak'iya,me zagaye ilahirin gangar jiki da zuciya,ita kanta bata san ya
zata fassara shiba wallahi.Tasake kallanshi rubutu yakeyi cikin natsuwa,takad'a
kai.
"Julaibib...you're an enigma".
Ahankali ta furta hakan,sannan tabi d'akin da kallo mutane dayawa sun gama abinda
yakaisu sun fita,saita samu k'warin gwiwa koda zai wulak'anta ta bazai mata ciwo
dayawa ba tunda mutane kad'anne. Tamatsa gaban kujerar dayake zaune,tasunkuyo tana
kallan fuskarshi"Sannu da aiki Julaibib...tafurta hakan da wani salo irin na ta na
yanga.Bai d'ago ya kalletaba kamar yadda take fa ta,bai kuma amsaba "shiruma
amsace"rubutun shi kawai yakeyi.
Tatsareshi da manyan idanunta masu maik'o,ya mata kyau cikin fararan
kayan,yau kanshi ba hula,kwantaccen bak'in gashin kanshi yanata sheki da k'amshin
irin mayukan gyaran gashi da yake amfani dasu,jikinta ya gama mutuwa murus,ga
k'amshin arabian perfumes d'inshi yadad'a jefata a wani irin yanayi,ta lumshe
idanunta wani murmushi ya su6uce mata "ALLAH dai yakai damo ga harawa ko baiciba
yayi burgima"taja dogon numfashi tana zuk'e k'amshin,ahankali kuma tafara fesar da
iskar tabaki ta hanci sannan tabud'e idanunta tacigaba da mishi kallan k'auna me
cike da shauk'i har yagama rubutun,yatattara takaddun daya shigo dasu a gefe,
yakwashi wad'anda yad'ibo a d'akin yamayar dasu mazauninsu.
Magana take mishi amma yayi kamar ALLAH baiyi ruwan tsiran taba,ganin
haka yasa tayi saurin k'arasawa bakin k'ofar da zai fita ta tare hanya sai yaja
yatsaya.
Please...Julaibib...
Magana nake so muyi please...tahad'a tafukan hannayenta alamar magiya."please
Julaibib, wallahi with all my heart ina sanka,kana burgeni, me zai hana ka aureni?
Yagirgiza kai"Bazan iyaba.Idanun ta suka ciko da k'walla"wai kai
wannan amsar ta "Bazan iyaba"bazata bar bakinka bane D'ansarai? Wai me zan yine da
zaka so ni Julaibib?Yakalli agogon dake d'aure a hannunshi nadama tana 6ata mishi
lokaci fa.
Ki matsa zan wuce.Tasake kallanshi "Julaibib zanyi sallah
fa...yad'ago yana mata rikitaccen kallanshi "Ki bani hanya nace ko? Yafurta hakan
da 6acin rai a fuskarshi.
Yamata wani irin kwarjini data kasa aiwatar da k'udurin zuciyarta.Sai
tagyad'a kai ta kuma matsawa a kofar"shi kenan zo ka wuce.Ya ra6a ta gefenta kamar
wanda akace idan ya ta6ata ya gama amfani a doron duniya.
Tabi bayanshi da kallo har ya6ace ma ganinta...sai tayi d'an yak'e
mak'alallun k'wallan cikin idanunta suka samu damar d'igowa a kyakkyawar fuskarta,
sai kuma wani sanyi-sanyi data faraji, tsigar jikinta yana tashi alamar zazza7i
yana so yakawo mata ziyara.
Harshenka zakinka idan kasa keshi yacin yeka"...
11 Rabi'a Thani 1441
8 December 2019
We Ibrahim's Daughters👇
Asdilat KD...2 geda with Ra'ibs.
DANGIN NONO WRITERS ASSOCIATION
{Da Inganci Mukayi Fintinkau}
Bismillahi wabihi nasta'in.
...GWAJIN DAFI💔
Almost true story
Daga alk'alamin🖊
Ya'yan Ibrahim
Saudat A.Baba (Asdilat KD)
Da
Bara'atu Ibrahim (Ra'ibs)
Shafi na biyu.
Musaddiq yashigo da sallama, yad'auki ya zauna yasha,sannanya kalli
Julaibib "sak'o aka bani wajanka...sai kuma yaja yayi shiru. Yad'an d'ago ya
kalleshi"Uhun ina jinka sak'on me? Yaciro d'an k'aramin kati launin ruwan k'asa
yanata kyal-kyali yamik'a mishi "karanta kagani.Kasham ce take gayyatar su party
dan murnar zagayowar ranar da aka haifeta(Birthday) ranar talata a Bigard Hotel.
Yad'ago yana mishi wani rikitaccen kallo "nasha fad'a maka yarinyar
nan ta daina aiko ka wajena kana zuwa kana fad'amin ko?Ya jijjiga kai"to ba laifi
ka cigaba amma abinda zan maka zaka sha mamakinshi wa...bai bari ya k'arasa ba
shima yatareshi"ba laifinka bane nawane ainan d'in tace za tazo tasame ka da kanta,
ni kuma sanin da nayi baka san hakan yasa nace mata ka tafi Matsirga amma takawo in
ajiye maka da...shima Julaibib ya tare da sauri..."na tafi Matsirga,na tafi
Matsirga fa kace?To saboda me zaka min k'arya?Ganin ranshi ya 6aci yace"kayi
hak'uri D'ansarai.Baice komai ba yakoma yakwanta,duk sukayi shiru,zuwa can Musaddiq
yasake kallanshi."Kasham da gaske tana sanka Julaibib, ko zamu d'an lek'a matane ko
na rabin awa dan itama taji dad'i yaba kyauta tukwuici.Yagalla mishi harara"idan
zakaje to ni ina ruwana?Musaddiq yayi murmushi"D'ansarai autan Inna me duniya.Inje
kuma?To ni asuwa?Kare da gudun laiya?Da dai zakaje dana maka kara na rakaka.
Yamik'e ni ga ka tafiya ta wajan Safiyya,yamik'a mishi hannu sukayi
musafaha"Ka gaisheta.Musaddiq yad'an zaro idanu dan mamaki "Wuuu yau wace rana
Julaibib yaji zanje wajan masoyiyata yace agaisheta? Julaibib yamik'e zaune da
sauri,yana k'ok'arin kai mishi naushi yagoce yana dariya, ah ka ga mugu da
6allallan kafad'a kake so inji hirar"uu tambayata kakeyi?To tsaya yanzu zaka gani
ya yunk'ura zai mik'e Musaddiq yafito daga d'akin da gudu yana fad'in "mu had'u a
gidan Hajiya bayan sallar la'asar".
Agajiye yashigo gidan,dawowar shi kenan daga Kaduna.Yaya Karima ta
tareshi "oyoyo barka da dawowa.Yauwa Yaya Karima.Yacire takalman shi masu
rufi,sannan ya zauna a tabarmar tsakar gidan suna gaisawa.Inna tafito daga D'akin-
girki"lale D'ansarai autan Innar shi"sukayi dariya to gashi,ruwa tabashi a k'aramin
kwanan sha.
Yakar6a"nagode Inna.Da bismillah yafara shan ruwan,ruwan randan Inna
me dad'in gaske ga wani irin sanyi,kowa kuma ya san ruwan randa sanyin shi baya
cutarwa,ga k'amshin saiwoyin da take sawa a ciki da suke k'arama ruwan armashi
wajan sha.Kad'an yarage sannan ya ajiye kwanan cikin hamdala ga ALLAH.Yakalle
ta"Inna ruwan randarki gard'i da d'and'anonshi har yafi ruwan roba Swan.Sukayi
dariya.
Abdullahi babban d'an Yaya Karima yayi sallama ya shigo yana rik'e da
hannun k'anwarshi Kamila da take kuka."Mama ga tanan tak'iyin shiru tunda ta dawo
daga makaranta,wai me yasa baki bari an taso suba kikayi tahowarki.?Ya k'arasa
wajan Kawunshi cikin murna "Kawu sannu da zuwa,sannan ya gaisheshi.Yarik'o
hannunshi "Yauwa Abdul yakaratu?Ya d'ibo Inibi to ga tsarabar ka.Abdul yasa hannu
biyu yakar6a"nagode Kawu ALLAH amfana.
Karima takalleshi kwana biyu ka daina zumunci sai Musaddiq kad'ai
yake sadar da ita."Baban Abdul dai yagaji shine yace in biyo sawu ko mun maka
laifine"?Yayi murmushi yana shafa kai"Yaya Karima ba kumun laifi ba,bana samun
lokacine amma Insha-ALLAH wannan Juma'ar zan shigo kin san tsarin karatunmu ba
d'aya bane.Ta gyad'a kai"hakane Ubangiji yanuna mana Juma'ar.Ya amsa da amin.
Wata magana zamuyi.Sai ya tattara hankalin shi ga sauraran abinda
zata fad'a."Julaibib me zai hana kafito da yarinyar da kake so a had'a bikinka dana
Musaddiq?Ina sha'awa k'warai ace yadda kuke kome tare to lokacin aure ma ku
angwance tare.Yagirgiza kai"ni bani da budurwa ma, ki tayani addu'a ALLAH yakawo
tagari.To amin. Amma duk yan matan Gidan-Waya ba wacce ka k'yasa?Yad'anyi tsaki'ni
fa ba tsayawa kallansu nake yiba,abinda yarabani daku,yakaini can d'in shi nakeyi
(karatu)
Musaddiq yashigo yatarar da zancen, yace tab shi autan Inna sai a
hankali kuma gashi da farin jini a wajan yan matan amma kowacce sai yace bata da
kamun kai,bayan shi kanshi ya sani a shari'ance ba haramun bane dan mace ta yaba da
kai tafurta maka kalmar k'auna.Musaddiq yaja dogon tsaki yana hararar Julaibib
saboda tuno abinda yata 6ama yar course d'insu.....
Atikah Aliyu Kagoro.
Jikar Sarkin Kagoro ce tana da hankali da natsuwa kuma k'wak'walwannar dai Ubangiji
ya hore mata shi na fahimtar karatu,Malamai ma ji da ita sukeyi bari d'alibai yan
karankad'a miya.Tunda taga Julaibib tace nan duniya ba wanda yamata da aure
kamarshi.sai dai kashhh...yawatsa mata k'asa a idanu.Atikah Aliyu Kagoro tayi kukan
rashin shi.
Rannan tazo wajan Julaibib d'in amma bata same shiba sai Musaddiq
shine take fad'a mishi zata bar makarantar saboda ba zata iya cigaba da ganin
Julaibib ba bayan yace baya ra'ayinta,ita tanaso yasota da zuciyarshi ne ba yaso ta
dan an tursasa shi an mishi dole ba,amma badan haka ba tana kai maganar nan wajan
Me Martaba to anyi angama maye ya auri ramammiya, Julaibib zai zama mijinta dan bai
isa Sarki yabashi auren jikarshi yace baya so ba"ai wata fuskar ta fi gaban mari
har abadan duniya"tad'ibo wasu damin sababbin kud'i tabashi,ya girgiza kai ki
barshi kawai.Sai tad'an harereshi "kai karfa ka 6atamin rai dan ka san kai ba
Julaibib bane,dogarai zansa su baka na jaki".Sukayi dariya.Yagyad'a kai"wannan
gaskiya ne ranki yadad'e.
Ta sake mik'a mishi"To d'an ALLAH ka kar6a.Yasa hannu biyu ya kar6a
yamata godiya, sannan ya d'an kalleta"yanzu Atikah kin bar karatunki kenan?
Tagirgiza kai"zan koma wajan Mahaifina a Saudi-arabia,dama tun daga yaye zamana ya
d'ore anan,bayan na gama Secondary d'ina yaso k'warai in koma can in cigaba da
karatu amma nace nafi san nan,ba dan ya so ba yahak'ura,saboda ni tagaban goshin Me
Martaba ce,abinda nake so to dole kowa ma yahak'ura yasoshi indai yana neman zaman
lafiya dashi.
Da jami'ar Abuja zan tafi amma nace ni nan nake so,ni kaina kuma ban
san dalilin dayasa na za6i nan d'in ba,ashe k'addarar had'uwa ta da wannan miskilin
d'an uwan na kane zai zama silar koma wata wajan mahaifina wanda dama ba abinda
yake so sama da ya ganni kusa dashi,saboda mahaifiyata lokacin da data haifi
k'anina ko ganinshi batayi ba ta rasu,da yammacin ranar shima abinda ta haifa yace
ga garinku nan,mutuwarta ta dakeshi sosai saboda suna san juna suna zaman lafiya.
Yadad'e baiyi wani aure ba,auran da yasa ke ma Me Martaba ne yagaji da ganinshi
haka ya aura mishi matar. Saboda ni duk lokacin daya samu sarari yake zuwa Nigeria
kasarmu ta gado.
Musaddiq ya kuma jan dogon tsaki fiye dana d'azu ALLAH
yashiryeka.Julaibib yayi murmushi"amin shiriyar da ba ta ALLAH ba shirme da
shiririta ce kuwa ,amin nagode".
Shi da Inna suna zaune a tsakar gida,yana 6arar gyad'a Inna kuma tana
gyaran tsakin masara, jefi -jefi suke magana, saboda shirin da suke sauraro a gidan
rediyo.
Assalamu alaikum.
"Inna tana nan...?
Daga zauren gidan suka jiyota.Cikin murmushi suka amsa sallamar.Inna
tarage sautin rediyon "maraba da yar gidan Inna,to shigo mana kya tsaya a zaure
kamar wata bak'uwa?Tashigo tana yar dariya"Inna na yi laifi na zaci kinyi fushi ne
shi yasa naji tsoron shigowa kai tsaye"Dan ALLAH Inna kiyi hak'uri.Tazauna tana
kallanshi"barka da warhaka Yaya Julaibib,Ina kwana.Yad'an shafa kai,tare da dauke
kai daga kallan da take mishi.
Sudaida...Lafiya lau, ya karatu'?
Alhamdulillahi gashinan muna tayi ba kama hannun yaro.
Tajuya wajan Inna tana gaisheta. ALLAH Inna jiya dakika aiko mantawa
nayi da aka tashi daga makarantar allo ban shigo ba.Inna ta girgiza kai"ba kome
nima nayi tunanin haka.Tasa hannu ta d'ibo gyad'ar tana tayashi 6arewa,yau za musha
fate kenan?Inna tace wai da dambu zanyi. Tad'an k'aryar da kanta gefen dama"kai
Inna gwamma dai faten,kin san Hajiya(Kakarsu)tafi san shi,zaifi armashi ma idan
Yaya Julaibib yaje yasiyo mana tantak'washi.Yad'ago kai yana kallanta"ni zanje
insiyo miki tantak'washi?Tace to ai da Hajiya da Inna za musha.Baice komai ba
yamik'e yashiga dak'inshi, bai dad'e ba yafito yanasa hula,yama Inna sallama
yafita... Sudaida tad'an d'aga murya karfa ka manta kaji?Yak'arasa ficewa.Shiruma
amsace.
Sai bayan sallar azahar suka shigo shida Musaddiq.Tace yauwa na ma
huta dama yanzu nake shirin biyoku shago.Musaddiq yakalleta "ta samu kenan,idan
kaji gangami da labari.Yabud'e kwanan data ajiye agabansu,tana murmushi"Yaya
Musaddiq chips d'in gwaza namuku tunda baku cika san shan fateba"Yad'auki d'aya
yakai baki,kai wannan yarinya da iyayi kike wai zuwa kashin rana da fitila.To Yaya
Musaddiq chips lallai sai da dankalin turawa?Gobe ma da dankalin hausa zanyi.
Julaibib yamik'e"kici lafiya...kai zo mutafi gidan Hajiya baza a rasa abincin
arzik'i acan ba.Haushi yakamata"to wannan na tsiya ne?A ah sai dai shima chips d'in
bazan ciba.
Inna tasa baki"kai baza a maka gwaninta ba kenan?Ya waiwaya ya kalli
Sudaida da wani irin kallo data kasa fassarawa"ni nasa ki? Tagalla mishi harara dan
ba k'aramin haushi yaba taba,shiruma amsace ta shige D'akin-girki dan k'arasa
abinda takeyi.Taja tsaki"shi wannan D'ansarai autan Innan ALLAH yasawwak'e mishi".
Yana wankin kayanshi tashigo gidan, Asma'u ce ita yake
bi.Takalleshi"manya ba a ganinku sai an cike foam,foam d'inma sai wanda ake buga
mishi stamp.Yayi murmushi"Yaya Asma'u ban kai nan ba,wa ne kare da hantar kura?
Barin dai k'arasa inzo mugaisa.Tawuce d'akin Inna suka gaisa,sai ta mik'e"barin
lek'a d'akin autan na ki ko zan samu abun sawa a bakin salati.Tashige ciki tana
mishi bincike. Yagama shanya kayan sannan yabita,baiji dad'in abinda ta mishi
ba,gaba d'aya ta hargitsa mishi d'akin,har kayan sawanshi na cikin akwati sai da ta
bincike.Yazauna yana kallanta cikin zancen zuci "Yaya Asma'u yar sa'ido ce ta gaban
kwatance, da shiga sharo ba shanu,kamar wata yar C I D,kaza dai garin tone-tone
wata rana zata tono wuk'ar yanka ta.
Takalleshi"kai d'akin na ka ba wani abu da mutum zai kai bakinshi zuwa
uwar hanji sai tarin littafai kala-kala?Yana tattara littafan data hargitsa yace"to
dama me zaki samu a d'akin talaka kuma d'an makaranta?Aike zaki taimakamin koda da
yar dubu goma in k'ara na Hand-out da 'yan wasu abubuwan,kinga kinyi halin
girma,ladanki yana wajan ALLAH.Lallai yaran nan ka ci abinci sauranka ruwan sanyin
randan Inna.Yanzu duk cikinmu akwai wanda ke cin kud'in Baba kai harma da Innan
kamar ka? "Ni?yanuna kanshi da d'an yatsanshi"sharri dai ba kyau Yaya Asma'u.Tad'an
harareshi tana dariya" za ka fad'i haka mana.Yagyad'akai"ALLAH Yaya Asma'u tunda ke
hajiya ce kamata yayi ace kin d'auko ma Inna yar aiki,kina biyanta duk k'arshen
wata,ni jarin nawa baiyi k'wari bane dani zanyi hakan.
Tamishi wani kallo"ALLAH sarki, Inna ce za a d'auko ma yar aiki?To
ina abun yake wai maye ya cinye jariri?Tabbb...kai akwai ka da san kashe kud'i na
ba gaira ba dalili,amma fa harda dan baka san yadda ake wahala wajan nemo su
bane.Na sani mana tunda nima ina sana'a.Ta tareshi da sauri "A ah ban yadda ba
sana'ar taka har wata sana'ace da zaka fad'i wahalhalun cikinta?Kuna komawa Gidan-
Waya Baba zai cigaba da kula muku da kome, kaga ai yafiku shan wahala daga kai har
Musaddiq d'in,ko zirga-zirgan da yake yi tsakanin nan da Kaduna ai bakwayi.Hun
Julaibib arzik'i gashin hancine rabuwa dashi ba dad'i,kabari sai ka gama karatun,ka
fara sana'a ka'in da na'in sai muyi zancen. Yace to Ubangiji yanuna mana lokacin.
Dama so yake yaji me za tace, amma ai ya riga yasan halinta na
rowa,indai maganar kud'ine kuma itace zata bayar tofa sai anyi tata6urza,sa6anin
idan itace zata kar6a yanzu mutum zai sha dogon lissafi da sharhi.Tamike" kai ni
barinje wajan Inna baza a rasa abun kaiwa bakin salati ba.Yagirgizai kai"yanzu haka
da abinda yakawota gidan,kuma abun tirrrr d'in tana da rufin asirinta dai-dai
gwargwado dan tafi Yaya Karima ne sa ba kusa ba, amma Yaya Karima ta fita wadatar
zuci.
Da safe kafin Inna tafito ya gama had'a karin kumallo,yashare tsakar
gidan,ya wanke bayi,tafito tana shi mishi albarka kamar yadda tasaba "Ubangiji
yamaka albarka, yarufa maka asiri duniya da lahira.
Yayi murmus"Amin Innar mu ALLAH yabar manake, yad'an kalleta"nifa yar
aiki zan d'auko miki Insha-ALLAH kafin mukoma makaranta, ayyukan suna miki yawa,ni
kuma a yanzu ina san ganinki cikin jin dad'i da hutu.Tayi yar dariya"to banda
abinka Julaibib ina aikin yake da har za a d'auko maiyi?Dagani sai Alhaji,idan kana
garine muke mu uku fa.Tagirgiza kai "ni kam nagode,da duk ya'ya haka suke jin
tausayi da soyayyar mahaifansu to da al'umma ta kasance cikin tsabta da kwanciyar
hankali mara yankewa,nagode maka gaya amma kabar zancen yar aiki,kai baka san 'yan
aikace-aikacen ma motsa jiki bane?Na sani Inna"to kibari asamo miki koda wacce zata
dinga miki hidimar tsakar gida,ke kuma kicigaba da yin abinci.
Ga kayan motsa jikina nan ba sai ki dinga amfani dasuba.Inna takama
ha6a🤔tana dariya"Wuuu rabani da wuyu"kashin k'ota"kayan motsa jiki na zamani ai sai
ku,ni ina zan iya da wad'annan k'arafa da na'urori? ALLAH dai yamaka albarka
autana.Yayi murmushi yana shafa kwantaccen bak'i gashin kanshi me shek'i da kyallin
irin mayukan gyaran gashin da yake amfani dasu. Suna gama karyawa yamata sallama
yatafi shagonsu dan neman na halali,dansu an d'orasu a kan dogara da kai a hakan
kuma suka taso,ba dogara da kud'in mahaifa ba...
Yana sanye da farar shadda,kanshi da farar hula zita,sai bak'in takalmi
sau ciki,kafad'arshi ta dama rataye da dudduma,dawo warshi kenan daga sallar
juma'a.A tsaye yake a k'ofar gidan yana tunanin kawun nashi jarumin mutum ne me
kamanta adalci a komai nashi,ga shi yanaji da mahaifiyarshi da gasken-gaske,yana
mata wata irin k'auna ta ban mamaki,kafin asamu me halinshi sai an tona,dan
yafifitata sama da mata da ya'ayanshi,yar gatan tsohuwa kenan data kerema duk
tsofaffin k'arninta, kai ita Hajiya ALLAH yamata gyad'ar dogo sama ya'ya,k'asa
ya'ya tsakiya ma ya'ya,gaba d'aya ya'yanta takwas babu k'ashin yarwa.
Kai Julaibib ka tsaya awaje kamar wani bak'o me jiran abashi izinin
shiga?Hajiyace, yakalleta da murmushi"to ai dama ke nake jira "bismillah
muje...Suna tafiya suna hira har suka shiga cikin gidan.Musaddiq yafito daga
d'akinshi, kaga ban tsaya jiran kaba, wallahi a sahun makararru natsaya,idan su
Baba suka fito suka hangoni a haraban masallaci kasan zan sha fadane.Kamar ba dashi
yake magana ba yashige d'akin yad'ebi wasu takaddu zai fita,Musaddiq yakalleshi
bari akawo mana abinci mana dama kai nake jira. "Bazanciba" Ah bazaka ciba kamar
yaya? "Azumi nakeyi" yabashi amsa atakaice. Azumi yau juma'a? Yagyad'a kai "Eh
azumin tsakiyan wata sha uku,sha hud'u,sha biyar,to yau sha uku ga wata.Yagyad'a
kai"ALLAH yabada lada"yafara kiran Sudaida,Sudaida,shiru Khausar nan ma shiru sai
yamik'e to ina jin basanan barin d'auko da kaina,suka fito tare shi yawuce wajan
Hajiya, Musaddiq kuma yatafi D'akin-girki d'auko abincinshi.
Sha d'aya da rabi a sanda hantsi yadubi ludayi na safiyar asabar aka
taso su daga makarantar allo, tana sanye da bak'ar abaya da farin hijab,da wasu
littafan addini a jakar data rataya a kafad'a,allanta kuma ta rik'e a hannu.Suna
zaune a dogon dakalin tazo tawuce kamar bata ganshi ba. Yamik'e da sauri
yabita"haba ranki yadad'e Sudaida Sarauniyar Sinan,me yayi zafi haka idanu suke cin
wuta?Takalleshi da 6acin rai"wai dan ALLAH kai baka da wajan zamane sai a cikin yan
maro (Wiwi)? Zama da mad'aukin kanwa fa yana kawo farin kai. Yagirgiza kai cikin
damuwa "Sudaida ba yadda zanyi da sune,ina zaune zaman jiranki suma sukazo suka
zauna,wajene na kowa to ya zan musu?Khausar tazo tawucesu da takaicin Sudaida,ta
rasa abinda yaja hankalinta wajan soyayyar Sinan.
Bakice kome ba.Sinan yakatse shirun. Tad'an harareshi"ALLAH yaso ka na
na huce.Yayi dariya tare da shafa k'irjinshi bangaren da zuciya take.Yauwa ko
kefa,kinga yanzu hankalin masoyi ya kwanta.Sukayi hirarsu sannan yataka mata kad'an
sukayi sallama,yaso yarakata har k'ofar gida amma tace nan ya isa, dan tasan su
Yaya Musaddiq suna wajan da autan Inna,kuma ba tasan wannan rikitaccen kallannashi
me ban haushi dan ba magana zai yiba..Taja tsaki"ALLAH yasauwak'e mishi wannan
halin...
Nagari ake so ba d'an gariba.
13 Rabi'a Thani 1441
10 December 2019
We Ibrahim's Daughters👇
Asdilat KD... 2geda with Ra'ibs.
DANGIN NONO WRITERS ASSOCIATION
{Da Inganci Mukayi Fintinkau}
Bismillahi wabihi nasta'in.
...GWAJIN DAFI💔
Almost true story
Daga alk'alamin 🖊
Ya'yan Ibrahim
Saudat A.Baba (Asdilat KD)
Da
Bara'atu Ibrahim (Ra'ibs)
Shafi na uku.
Kasham tabaro k'auyansu Madauci da yammacin ranar talata,bayan taji
sauk'i daga jinyar da tayi na tsawon awanni ashirin da hud'u.Tashiga cikin
makaranta da d'okin ganin Julaibib ta kuma hango shi a inda suke zama.Tak'arasa da
saurinta "Barkanku da yammaci"Maimun abokin karatunshi ya amsa"Yauwa barka
dai.Tatsare Julaibib da manyan idanunta masu maik'o cikin kallan k'auna me cike da
shauk'i "kai bazaka amsaba kenan?Iskar data d'ibo tama bata isheshi kalloba.Tayi
jimmm...na wucewar wasu dak'ik'u tana kissima wani abu a zuciyar ta,sai tad'an
motsa kafad'a any way...sai anjima. Tajuya tayi tafiyarta tana murmushi.
Julaibib my enigma man...Salonka yana k'ayatar dani wallahi"...
Maimun yakalleshi"Kai nifa bangane ma wannan bita da kulli"dukan kabarin
kishiyan ba"Meye had'inka da itane duk inda taganka sai tazo wajan?... Julaibib
yafad'a mishi kome.Maimun Yagyad'a kai "to ka yadda mana tunda har ta amince za
tayi sallah ba kuma wanine ya tilasta mataba,ai inaga ba wata matsala,kuma kayi
jihadi ne,gata kuma Masha-ALLAH kyakkyawace.Yamik'e yana mishi wannan rikitaccen
kallan nashi"bazan iyaba.Maimun zai sake magana yad'aga mishi hannu"dakata haka
malam, taso mu tafi.Maimun yagirgiza kai "ba d'akin da zan tafi yanzu gwamma in
d'anyi shawagina.Yajuya yayi tafiyarshi to shikenan.
Yana shiga d'aki ya ajiye Hand-out, yasa hannu yana 6alle botiren
gaban rigarshi tare da lumshe idanunshi a kasalance,yacireta rigar yajefa a saman
kujera,ya gaji lik'is ga rashin bacci,dan baiyi wani baccin kirki a daren jiya ba
saboda karatu da binciken wasu littafai da yake yi na tafsirin Alqur'ani me
girma,idanunshi har wani yaji-yaji sukeyi,a a hankali yafurta"yau da wuri zan
kwanta...
"Zanzo tayaka kwana...
Bazato yaji an mishi wata irin runguma ta baya,zuciyarshi tabuga
dammm...dan wallahi yaji tsoro...
"Zanzo tayaka kwana tunda Musaddiq baya nan.Tafad'a cikin rad'a
Kasham...zuciyarshi taraya mishi, tabbasss ita d'ince danga k'amshin
turaranta nan... Yayi k'ok'arin raba ta da jikinshi amma ya kasa,dan ruk'on kura
taga nama ta mishi...
Kanshi yayi wani irin sarawa.
Tafara mishi wani salo da hannayen ta a cikin gargasarshi dake
kwance lufff bak'ink'irin da sheki...kar...kar...kar...Jikinshi yad'auki
rawa"baah...ba... bahh..banasooo!...dak'yar yafuzgo furucin.Tayi lallausan murmushi
tad'ago kanta tana kallan kwantaccen bak'in gashin kanshi...
Meye baka so din...???
Yayi shiru.Tagyad'a kai"tayaka kwannanne baka so ko wannan din?tacigaba da mishi
wani salo da hannayenta a dai-dai saitin zuciya... Jikinshi ya mutu murusss...
My enigma say something hun"
Tasake fad'a cikin rad'a da wani irin salo na ta nayanga.Yadaddage ya
hankad'eta...tafad'i tabaya akan katifarsu.Hanyar fita yayi sai dai abin mamaki
"talaka da mata hud'u har da k'wark'wara me gari gwauro"ta kulle k'ofar dan dama
baiji shigowarta ba.
Daga kwancen take kallanshi, yasunkwui da kai,gaba d'aya ya jike
sharkaf da zufa kamar wanda yad'auki awanni yana matso jiki.Wata jijiya tafito
asaman goshin shi rad'am kamar shatin bulala ranshi in yayi dubu ya 6aci...Amma
jikinshi ba k'arfi kona sisin kwabo kamar wanda aka zarema laka.
Sai kuma jikinta yayi sanyi, tasan itace tasashi a damuwa tamik'e
tsaye"Kayi hak'uri Julaibib "tahad'a tafukan hannayenta"Dan ALLAH kayi hak'uri ba
naso ace ta dalilina kashiga damuwa,danni me k'aunar kace,farincikin ka shi nake so
ba damuwa ba.k'walla yacika idanunta... muryarta tafara rawa
Bazaka hak'ura bane D'ansarai?
Yadda tayi furucin a hankali da wani irin salo,yasa yad'ago zai kalleta,itama shi
take kallo caraf idanunsu yahad'u,yakauda kai dasauri yanajin wani irin abu yana
zagaye ilahirin jiki da zuciyarshi,shi yasa baya san kallan wannan manyan idanun na
ta masu maik'o.Kawai sai ta fashe da kuka,tsoro da mamaki suka baibayeshi to me aka
mata wai???
"Kasham...
Yafurta sunan dak'yar.Tad'ago da sauri tana kallanshi.Sai kuma yayi shiru kamar me
koyan had'a kalmomi da yadda ake furtasu.Idanunshi sun kad'a jawur.
Julaibib kayi hak'uri dan ALLAH".
"Bakomai...Tayi murmushi yau wace rana ya mata wata magana ta daban ba
amsar daya saba fad'aba na "Bazan iyaba"saita kalleshi "to za ka aureni?Yayi shiru
kanshi ak'asa.Tad'an motsa kafad'a. Tana zuwa kusa da k'ofar ya matsa da sauri
kamar zai hantsila.Tayi yar dariya"Matsoraci kawai "ni ba abinda zan maka yanzu
amma duk ranar daka shigo nan tanuna tsakiyar tafin hannunta na maka kattt...kisan
mummuk'e,sai tayi d'as d'as d'as da yan yatsunta wani murmushi ya su6uce mata.
Tamishi wani kallan k'auna me cike da shauk'i...Tabud'e k'ofar tayi
tafiyarta.Yasauke gwauran numfashi "wallahi da basu da lecture gobe da sassafe da
yau yayi tafiyar shi gida kamar yadda Musaddiq yatafi.Yamaida k'ofar yarufe da
sak'ata yasa mukulli sannan ya kwanta cikin wani irin yanayi.
Tana zuwa d'aki tafasa ihu tafad'a gado.Lidiya da suke yan'uwa kuma
d'akinsu d'aya sai dai kowa da abinda yake karanta kamar dai Julaibib da Musaddiq
tabita da kallo sai juyi take cikin wani irin yanayi,tabar yanka ganyen Ogu da take
yi na abincin darensu,tazauna agefen gadan.
"Inzayadami Kasham?(Meyafaru Kasham)
Kasham tacigaba da juye-juyenta cikin wani irin yanayi,zuwa can kuma
tamik'e zaune, tajingina kanta ajikin gadan cikin sanyin murya tace " Julaibib ne"
"Jesus Christ! Holy ghost fire!!!
Lidiya tafad'a tare da dafe kirji da duka hannayenta,tabita da kallan
takaici taja dogon tsaki, wallahi kinji kunya,wai dan ALLAH me kika ganine
ajikinshi daya tafi da hankalinki haka? Dogone k'akk'arfa,kar kuma kimanta Baranzan
wanda kukayi alkawarin aure dashi,shima haka yake,ke ya mafi Julaibib tunda shi
Sojane training d'in da yakeyi shi ko rabin-rabinshi ba ya yi, sunansu kuma
d'aya"Maza"ko akwai wani abu bayan haka?Tayi lallausan murmushi"taja dogon numfashi
a hankali take fitar da iskar tabaki ta hanci.Sannan tace"Hummm...Lidiya kenan ai
maza kama suka tara amma halinsu ya bambanta. Tagalla mata harara"kin gama asara,ni
dai banga abin so a wajen me shegen girman kai ba,shi ba kowan kowa ba dillalin
kashi.Sannu wannan dazai amsa miki da yauwa sai yaga dama amma ke kina neman
haukacewa saboda shi...kai tirrr...wallahi tayi d'as da yan yantsunta takoma kan
girkinta tana mita Rubbish girl...
Kasham tazame takwanta"duk abinda zaki fad'a indai akan san D'ansarai
ne bazai ta6a tasiri a zuciyata ba har abadan duniya, ina san shi koda shi aka
tarama munanan halayen jama'ar duniya,ni na san ko waye Julaibib,ba shi da wani
girman kai"so hana ganin laifi...
Suna zaune a shago jadawalin bikin Musaddiq d'in suke dad'a dubawa,dan
saura kwanaki goma sha biyu.Tayi sallama daga waje tana sanye da riga da zani da
dankwali na atamfa ruwan goro da ratsin k'ananan filawoyi ruwan madara da
Bak'i,tayafa bak'in mayafi takalmanta bak'ak'e abinci takawo musu.
Wa alaikumussalam shigo.Tana shiga idanunsu yahad'u,yad'an saki
fuska"yau Baba yayi tafiya sai zuwa yammaci zai dawo, ni kuma ban san irin garar da
yake had'a muku ba idan kun kawo abinci"rake zan sha"sai Maths text book da Graph-
book da za a sai mana ni da Yaya Khausar.
Banza yar k'auye,tafi kibamu waje, ba dama a tambayeta me take so sai
tace"rake"to ba za a sai rakenba.Julaibib yad'aga mishi hannu "a ah malam shan koko
fa kwanciyar rai,to me yamaka zafi?Yamaida kallanshi wajanta"koda yakema idan
fitsari abin banzane kaza ma tayi mana.Ta sunkwui da kai"kowa yayi zagi a kasuwa ya
san da wanda yakeyi,shine ko nama a wasu lokutan baya iyaci duk san shi da nama
kamar kura sai gani sai hange idan ciwon hak'orinshi ya motsa.
Me kace? Musaddiq yatambaye shi fuska a yamutse.Abinda kaji na
fad'a"ke Sudaida jeki ki...sai kuma yamik'e ina zuwa.Dakanshi yasiyo musu Maths da
graph d'in yakuma kar6o musu gasassun kaji guda biyar,d'aya ki kaima Inna,biyu nasu
Mama,ku kuma dukkanku kuyi hak'uri ku raba biyun.Tasa hannu biyu takar6i
ledojin"mungode Yaya Julaibib".Yakauda kai daga kallan da take mishi.Jeki kinji
karki daka ta wannan da hidimar aure tasa kanshi yake shirin yin gobara... mutum
bai kar zomo ba sai kiga yana shirin ba shi rataya.Tawaiwaya inda Musaddiq d'in
yake,shima su yake kallo.Sai ta toshe bakinta da sauri kar dariyar da take 6oyewa
ta su6uce mata tashiga uku,idan yakoma gida da daddare zai iya bata na
jaki...tajuya dasauri tabar shagon.Julaibib yabita da kallo fuskarshi da murmushi.
Yauma Musaddiq ya rigashi komawa gida tun ranar laraba yatafi,Maimun ma
an aiko mahaifiyarshi bata da lafiya shima yatafi.Yana fitowa daga masallaci yanufi
d'akinsu dan yanajin yunwa shi kuma yafi gane yadafa abinda zaici fiye da yaje
capteria,yana da miya dan haka yadora farar shinkafa yazauna yana yayyanka kabeji,
tumatir albasa da gurji.Tana jingine da bishiyar barankaci tana hangoshi dan
abaranda ya zauna saboda cikin akwai zafi kuma ba wuta,tana mishi kallan k'auna me
cike da shauk'i,shi ko baima san tanayi ba kunu a mak'ota.Tasauke numfashi tana
kiran sunan shi a saman la66anta wani murmushi yasu6uce mata ranar da duk ALLAH
yabani sa a akanka?....Hummm tagyad'a kai"d'aurin gwarmai za kasha amma na
k'auna... tajuya tafiyarta.
Hajiya tashigo da sallama.Ya amsa cikin murmushi"Sannu da zuwa
Hajiyarmu, yashimfid'a mata tabarma.Tace a ah mutanan Gidan-Waya saukar yaushe?Ai
tun safe ina garin nan,wajejen k'arfe sha d'aya naje gida ba kyanan.Tagyada
kai"Tabbas anyi haka,naje asibiti gaishe da Liman na masallacin juma'a ne.Yace
"ALLAHU-AKBAR"ashe har yanzu ba a sallameshi ba?Ubangiji yabashi lafiya,zaman
jinyar kuma yasa kaffarace. Ta amsa da amin,amin.Anjima ya kamata kuje kugaishe shi
Yagyada kai "Insha-ALLAH.
Kai kadaine agidan?A ah Inna tana wankane"Tamishi kallan nazari"ni
wannan zuwan sam baka min kyan ganiba,duk kayi wani firgai-firgai sai kace angon da
hidima tasha kanshi kud'ad'en aljihu sun k'are,ko dai bakaji dad'i kwana biyu bane?
Cikin yar dariya yace "to da Musaddiq kike wannan gugar zanan.Kai tafi can Musaddiq
d'in wa?Shi da za a mishi auran gata,dakai nake yi.Yagirgiza kai"Hajiya ni dai
lafiya ta k'alau.Cikin kad'a kai tace"amma dai sanin hali ai yafi sanin kama,idan
ta kumbura tafashe tayi wari zamuji.
Bismillahi tamik'e"ni bazan zauna zaman jiran uwarka ba wannan halin
nata tun na k'uruciya ashe bata barshi ba,taja tsaki haka takeyi idan tashiga bayi
kamar tasamu gadon bacci da daddare,wani lokacin sai na bita da bulala take
fitowa,shiga bayi ai lalurace da kake sauri ka kawar da ita kafito.Julaibib yad'an
yamutsa fuska"Kai Hajiya"takalleshi saboda uwarkace sai ink'i fad'an halinta?
Yagirgiza kai. Tace"to wooo ashe dai kowa yana san wawa haihuwarshi ce ba a so,dama
wajanta nazo kwana biyu bangan taba"To kijirata mana.Wa?Ai tunda na mik'e sai dai
kuma tabiyoni nawa gidan,tunda na ganka ai shi kenan ko baka gode bane? Aiko nagode
miki ba kad'anba Hajiyarmu.Barin taka miki. Suna tafiya a hankali suna hirarsu,har
gida yarakata sannan yawuce gidan Yaya Karima.Yaya Karima tadabance wallahi saboda
halin dattakonta.
Rana bata k'arya saidai uwar d'iya taji kunya,ranar juma'a aka d'aura
auran Musaddiq da Safiyyah,abokan karatunsu sunzo d'aurin auran nan Motoci har
hud'u cike tam da jama'a.Maimun yace gaskiya garin Zonkwa yamin ba zata yadda nake
tunanin garin ashe yawuce haka.Aminu yagyad'a kai"k'warai kuwa muna yin addininmu
da komai namu kamar yadda hausawa,musulmai sukeyi a k'asar Hausa tunda akwai
malamai masana addini a fannoni mabambanta,ga makarantu sai wanda kaza6a.
Maimun yakalli Julaibib cikin tsokana "Yah D'ansarai inane k'auyan
mutuniyar takane?Na ta6a tambayarta tace min Mabushi ko Madakiya?Ko mene?Ni na
manta.Shiruma amsace. Yagyad'a kai "To da alama yan miskilancin sun motsa
kenan.Aminu yamik'e"Maimun zo muje muyi shawagi kaji,zama waje d'aya tsautsayi.Suka
bar Julaibib a d'akin,sunyi yawo sosai har Fadar Sarkin hausawan garin saida yakai
Maimun yakwashi gaisuwa,Sarki me kirki da karamci yayita sa musu albarka yamusu
addu'ar sumu ALLAH yabasu mata nagari,sai bayan la'asar suka koma gida dan shirin
tafiya wa'azin maza da za ayi agidan Bak'i,bayan sallar magriba aka rufe taro da
addu'a abokansu suka dauki hanyar Gidan-Waya, Aminu dai yarik'e Maimun wai dole sai
ya kwana.A kwana d'aya da sukayi sunyi sabo naban mamaki kasancewar duk su biyun
baki abin magana ne, sukayi sallama da alk'awarin kaima juna ziyara a duk lokacin
da suka samu sarari.
Yafito daga cikin dalleliyar motarshi kirar Toyota bak'a wuluk sai
walainiya takeyi a cikin hasken rana.Yana sanye da kakin soja,tafiya yakeyi cikin
isa da gadara dajin cewa eh ya ne kayi hattara,ka kuma kiyaye ni ko kasha na
jaki.Kwan kwan kwan...ahankali yake rank'washin k'ofar kwan kwan kwan...Just come
in... yajiyo muryarta daga ciki.Yasa hannu a marik'in k'ofar yamurd'a yashiga.
Yabita da kallo tana kwance ruf da ciki da kayan bacci,dasauri yak'arasa
gadon ya d'agota...suka kalli juna na wucewar wasu dak'iku, sai ta kauda kai a
maimakon tabashi sumba kamar yadda tasaba.Yajuyo da fuskarta yana k'ok'arin
sumbantar ta amma ta fuzge da sauri. Takoma ta kwanta "Beauty...tashi muje asibiti
me ke damunki ne haka? Nace maka bani da lafiya ne? Hey don't fool me,idan ba ciwo
ba me zai ramar dake haka?Idanun ta suka ciko da kwallah sai kawai tafad'a
kirjinshi tafashe da wani irin kuka.
Lidiya tashigo da murnan ta sai kuma tayi saroro tana kallansu,Ya juya
yana kallanta. Lidiya me yasamu Beauty haka?Tad'an motsa kafad'a"Ga kai ga k'afa ka
tambayi me aka yanka? Ai ita zata fad'i meke damunta.Baranzan yayita rarrashinta
dak'yar yasamu tayi shiru.Ya gewaye hannayenshi ajikinta,yana mata magana a hankali
"na fa shirya mana party na Birthday d'inki da akayi bana nan.Lidiya tabashi hannu
suka tafa. "Good Baranzan a ina za a yi?Yakalli Kasham yana murmushi"Kasham Hotel
Kafanchan"Lidiya tayi d'an tsalke tana ihu "Hallelujah".
Tad'an daki kafad'arshi ta hagu,suka kyalkyale da dariya.Tad'auki
jakarta"to yah ne? Bani kud'i zanje inyi nail fixes da gyaran gashi.Ya zarosu da
yawa baiko tsaya k'irgawa ba ya bata.Tak'arba tare da sara mishi"Yes Sir ta buga
kafarta da dama a k'asa"Thank you Sir.Tafita da sauri.Yasaki Kasham ya kunna taba
sigari, yamata kyakkyawan zuk'a sannan yafara fesar da hayak'in tabaki ta hanci
cikin shakara yana mata wani kallo.
I miss you deadly Beauty...
Yamik'a mata karan taban,tagirgiza kai "No I'm not in the mood"yakalleta
nifa gaskiya yunwa nakeji saboda d'okin ganinki ko karyawa ban tsaya na yiba dan
nasan zaki dafamin abinci me rai da motsi amma gashi baki da lafiya "Tashi muje in
nemi abinda zanci".
Tacanja kayan baccin jikinta da wando legging ruwan zinare da wata
shirt checker,tana sa ma6allan gaban rigar shi kuma ya d'auko katon ribbon ruwan
zinare ya tattara gashinta daya hargitse yad'aure, yana kallan d'an k'aramin
bakinta daya d'an bushe dan bata shafa mishi mai ba"ni fa da yunwan kome na zo,
kema kuma kin sani,amma na ga kamar hak'ata bazata tadda ruwa yadda nake so ba ko?
Tayi kamar bataji abinda yake fad'aba.Tarik'o hannunshi"dan ALLAH mutafi dan idan
nakoma na kwanta wallahi ba inda zani".
Yana sanye da fararan kaya, bak'ar hula da bak'in takalmi sau ciki
yayi sharrr dashi,ya rataya bak'ar jaka a kafad'arshi.Daga bayanshi yaji k'arar
mota, sai ya kauce gefe.Tasauke gilashin bangaran da take zaune.
"Barka da safiya D'ansarai...
Yayi kamar ba dashi take yiba, yacigaba da tafiyarshi har yasha kwanar
lecture hall d'insu ya6ace ma ganinta.Baranzan yaja motar yana tambayarta"waye
wannnan ana mishi magana yayi banza da mutane?Tamaida kanta jikin kujerar motar"Ina
ga baiji bane dan naga da headphone a kunnuwanshi.Jikinta yayi sanyi bata so
yaganta da Baranzan ba wallahi,duk maganar da yake mata tamishi shiru kamar me
bacci.
Wannnan party baiyi wani armashi kamar yadda suka saba yin chasu da
rawar mak'osa ayi shaye-shaye yadda a kaga dama,dan gaba d'aya bata da walwala
banda ma ya takura mata da ba inda zataje, kwananshi uku awajanta sannan yayi
shirin komawa Jaji Barrack bakin aiki amma yayita rok'onta idan ta samu sarari
tabiyoshi,ta amsa da to,amma tayi alk'awari ba wanda zata sake bi har ta kwana
dashi indai ba Julaibib ba.
Ranar talata Musaddiq baije ko ina ba yana zaune a D'akin-shak'atawa
yaji ana k'wank'wasa k'ofar,yace shigo dan yasan kila Asma'u ce amma sai ta fad'a
mishi dalilin ta na k'inyi sallama,amma me?Kasham yagani a tsaye. Kasham? Yafad'a
da mamaki kece?Dama kinsan gidana ne?Takasheshi da lallausan murmushinta "Kabar
mamaki,dan matambayi ai baya 6ata.
Naji kayi aure shine nazo tayaka murna, I'm I not wellcome? Bata
jira amsar shiba tama kanta mazauni a d'aya daga cikin kujerun d'akin,tad'anbi
D'akin-shak'atawar da kallo, sannan takalleshi "To ina amaryar taka?Yamike bari
akirata yashige d'aya d'akin sannan ya kullo k'ofa"Safiyya takalleshi lafiya?
Yarungume hannayen shi a k'irji lafiya lau,tashi kije ku gaisa wata yar makarantar
muce tazo mana ALLAH yasanya alheri.Tamishi kallan tuhuma"Oh wanda tamaka a
makaranta bai gamsar da itaba har sai ta biyoka gida?Yayi murmushi"Haba amaryata
yaushe akai daren da gari zai waye? Kasham...she mean nothing,ai kece komai na,
yafara Istirja'i, shaid'anne yake so yasak'a miki mummuna,kinji amaryata?Tayi
murmushi suka fito tare.
Wani Ovation take dubawa tad'ago tana murmushi"Amarya barka da
fitowa,tanuna Musaddiq kinga mijin kin nan kirkinshi ragaggene a wajena tunda har
zaiyi aure amma bai fad'a minba,ni kuma ai naga abin farin cikine to meye na
6oyewa,?To koma dai yayane ba a gayyace niba amma danaji labari gashi na zo"
Musaddiq ina tayaku murnar aure,kuyi hak'uri Ku zauna lafiya for better for
worst.Suka mata godiya, tace haba ba komai fa,wata kilama mutumin nakane yace karka
fad'amin. Kamar bai gane wanda take nufiba yace"Wa kenan? Tad'an kalleshi "Wa kake
dashi a Gidan-Waya daya wuce D'ansarai?Yayi murmushi"au shi kike nufi?To ba
ruwanshi,Julaibib bai ta6amin maganar kiba.
ALLAH da gaske!???
Ta tambayeshi cikin mamaki zata cigaba yatari numfashinta"Indai
maganar D'ansarai zakiyi tona rok'eki kiyi shiru kawai tunda bashi da wani
amfani.Yafad'a miki gaskiya... Takatseshi da sauri "Karkasa jinina ya hau,danni
nayi alk'awari ko ana ha maza ha mata sai na auri Julaibib dan ina sanshi,takalli
Safiyya" Madam ku taimakeni dan na san za ku iya wallahi,sallah ne dai da banayi
yasa kuke k'ok'arin nisantani daku ko?To nace zan iya, ai ko bai kamata a k'wacemin
gatarin danace zan iya had'iyaba...
Safiyya ta jijjiga kai kenan a yadda take magiyar nan ta dad'e
tana yak'in neman soyayyarshi ALLAH ne kawai yatsare shi daga
fad'awatarkonta,tasake kallanta masha-ALLAH tanada kyau najan hankali,d'an k'aramin
bakin ta da manyan idanunta masu maik'o su suka k'ara mata kyau na musamman ga ta
da yalwan gashin kai,gashi kuma da alama ma'abociyar kwaliyar jan hankalice,dabara
tazo mata dan haka ta kalli Musaddiq cikin tashin hankali"Dama baka fad'a mataba?To
bari kiji Kasham kike kowa?Ki bud'e kunnnuwanki ki saurareni dakyau"Julaibib yana
da matar aure karatu ake jira tagama musha biki kuma kanwata ce,dan haka kitashi
kibar min gida.Tamik'e rai a 6ace ta wuce cikin.
Takalli Musaddiq shi kuma yayi saurin kau da kai"Shin da gaske ne
abinda tafad'a? Yagyad'a kai "Aishi yasa tun farko nafad'a miki Julaibib bazai
aureki ba danna sanshi farin sani.Tamik'e tana sa6a jakarta akafad'a" Shikenan amma
ba hakan yana nufin na hak'ura da shi bane,ku ai musulmai mata hud'u kuke iya
aura,dan haka ban damu ako tanawa zanzo ba,ni dai burina in mallaki Julaibib a
kowani irin hali da yanayi,zanje inyi tunanin abinda zai fishsheni.
Tana fita Safiyya tadawo.Yayi murmushi yana mik'o mata hannayenshi
"Amma gaskiyar magana kin burgeni"bata mika nata hannayenba,tagalla mishi
harara"Shi me gayyarma ba shiga shirginta yakeyiba sai kai,ba kamar kid'iba sai
kayan ganguna? Yafuzgota da k'arfi" Haba Safiyyahhh... Kina ganin wani abu zai
shiga tsakanin mune?Kasham bata gabana. Tashagwabe murya"ai ba anan takeba an danne
bodari aka,ni dai kawai ko?Tad'ago tana kallanshi.Yagyad'a kai" Uhun ke me? Ni dai
kawai maganin kar ayi to tun wuri kar a fara..Yayi yar dariya yana d'an jan karan
hancinta"To ranki yadad'e zan kiyaye"Yakamata kuwa hakan.Sai yad'an bata marin
soyayya suka k'yalk'yale da dariya.
Kwanakin Julaibib uku a Kaduna sannan yadawo ranar laraba da
yammaci,wata yar Seminar sukayi da k'ungiyar"Ansaruddeen"yana rataye da bak'ar
jakar matafiya,godiya yakeyi ga ALLAH daya kaishi lafiya yadawo dashi lafiya sannan
yashige gidan da sallama.Inna ta amsa sallamar da murnan ganinshi "Maraba da autana
"Yazauna agefen tabarmar cikin murmushi,Iyaye dad'in ganine dasu,musamman idan kayi
dace da masu ilmi da sanin yakamata. Fatanshi har kullum ALLAH yabashi ikon jiyar
dasu dad'in rayuwa kamar yadda suka jiyar dashi,musamman ilmin addini dana boko da
tarbiyar Al'Isamiyya da suka bashi.
Yacire takalmanshi masu rufi da safa sannan yagaisheta"Inna ya
zafi"?Tagyada kai "Zafi kam akwaishi,sai dai yakusa k'arewa tunda damuna nagab da
sauka.Yadi6o ruwan randa yanasha yaji dad'i har ranshi saboda k'amshin saiwoyin
datake zubawa aciki dan k'arama ruwan armashi wajan sha yana zancen zuci"Inna duk
lokacin da bana gida ruwan randan nan naki nake fara kewa,ya ajiye kofin.To
Ubangiji yabamu damuna me albarka.Inna ta amsa da Amin.Yaciro mata tsarabarta
sannan yamik'e yasa takalmanshi"barinje gidan Hajiyar mu"To ka gaisheta.
Daga gidan Hajiya yawuce gidan Kawunshi,yaran gidan suna zaune a
D'akin-shak'atawa suna kallo,k'ananan suka taso aguje suna murnan ganinshi"oyoyo
Yaya Julaibib,oyoyo Yaya Julaibib duk suka mak'alk'aleshi dan D'ansarai indai wajan
kyautane to ba daganan ba,sam abin hannunshi baya rufe mishi idanuba, suna ganin ya
bud'e jaka suka fara tsalle kowa yana fad'in "Yaya Julaibib bani, a ah ni zaka
ba,nima ai na iya rabo Yaya Julaibib....yace a ah bari aba babba Sagir maza kaima
Khausar taraba muku, yanunata da yatsa"banda ke a ciki,rabo irin na adalci kawai za
kiyi a tsakaninsu.Tayi yar dariya"To shikenan Sagir kawo ledan."waisu Mama basa nan
ne? Eh sunje gidan suna. Yajuya shikenan na dawo anjima.
A zaure sukayi kaci6is,taja baya da sauri"Sannu da zuwa"ya amsa da
yauwa.Daga ina kike? "Gidansu Nasmat.Ka siyo min tsaraba?Yad'an kalleta "Haba dai,
babba dake acin tsaraba?Tayi yar dariya "Yanzu dan ALLAH Yaya D'ansarai wani
girmane dani?Ina abin yake wai maye yacinye jariri?Ai duk girmana ban kai Hajiya
ba,daga gidansu Nasmat naje gidanta na kuma tarar da ita tana cin tuffa kuma tace
tsabarar dama kai matane.
To dake da Hajiya dayane?
Daga baya suka jiyo muryarshi.Tad'an karyar da kai gefen dama"Kai Yaya Aminu yanzu
ni banfi Hajiya ba?
Ke dalla tafi kabamu waje, irinki goma baza su kama k'afar
Hajiyarmu ba bare su fita,to ke asuwa?Karankad'a miya dake. Julaibib yace"ah to kin
daiji ko?Ya tambayi Aminu"akwai ragowar kunun tsamiya a d'akinka? Kaima ka san ba a
rasa nono a riga sai dai idan rigar bata Fulani bace.Yace yauwa to kije ki d'auka
kiyi farau-farau dashi.Tajuya zata shige gida"ai ni kunu koda d'uminshi ba d'ad'ani
da k'asa yayi ba bare ragowa, zanzo har gida in kar6a,sai kaba Innarmu ta ajiyemin
koda na zo baka nan...
...Kome na rayuwa naci dana sha an halicceshine dan d'an
Adam,shakeru aru-aru tun kafuwar doron duniya,za kuma kaci har kagaji,basa k'arewa
sai dai kagama rayuwarka katafi kabarsu...
...Rabo na me rabo ko kura tagani haramiyarta.
15Rabi'a Thani 1441
12 December 2019
We Ibrahim's Daughters👇
Asdilat KD...2geda with Ra'ibs.
DANGIN NONO WRITERS ASSOCIATION
{Da Inganci Mukayi Fintinkau}
Bismillahi wabihi nasta'in
...GWAJIN DAFI 💔
Daga alk'alamin 🖊
Ya'yan Ibrahim
Saudat A.Baba (Asdilat KD)
Da
Bara'atu Ibrahim (Ra'ibs)
Shafi na hud'u.
Monday ranar aiki ko nasara na tsoronki.Ranar litini aka koma
makarantun boko a zangon karatu na farko.Sudaida da Khausar sunfi kowa farin ciki
saboda shigarsu aji d'aya a k'aramar Secondary,kuma a wannan lokacin aka turo yan
TP(Teaching Practice) Julaibib na d'aya daga cikin wadanda aka turo makarantar
su,to kamar yadda su Sudaida ke murna haka Kasham ma tayi murna dan makarantarsu
d'aya.
Dasafe yashiga gidan cikin shigarshi ta fararan kaya.Yagaishe da su
Mama, sannan yakalli Sudaida da take karyawa"idan kika bari nafito daga d'akin Kawu
baki gamaba to ni tafiyata zanyi.Tamik'e tsaye tana addu'ar gama cin abinci nama
gama barin kira Yaya Khausar sai mujiraka a mota.Gaisawa kawai sukayi da Kawun
nashi yafito suka tafi.
Kasham tana zaune a farar kujerar roba a inuwar dalbejiya kullum
tana ganin irin zirga-zirgan da Sudaida takeyi idan an tashi tara(break) tsak'anin
wajan saida kayyakin da wajan da Julaibib yake yawan zama,da alama ita yake aika
tasiyo mishi abinda yake buk'ata. Tasauke gwauran numfashi wato dai yana
magana,kalli yadda Sudaida take dariya, duk yadda akayi shi yayi furucin daya sata
darawa.
Bayan an koma aji yamik'e yashiga d'akin malamai(Staff Room)sai
ganinta yayi zaune a tebur d'inshi magana zamuyi tafad'a cikin murmushi.Ranshi a
6ace yama rasa abinda zai fad'a sai kawai yajuya dama alli(chalk)zai d'auka to
gwamma yatafi Principal Office yad'auki wani acan.Tabiyoshi da sauri"ji mana
Julaibib,ka tsaya kaji abinda zan fad'a maka,idan kuma kaki to ina biye da kai duk
inda kasa kafafunka.Bai saurareta ba yayi tafiyar shi,sauri yake yi har yana
tuntu6e, abin yabata dariya"To wai shi Julaibib tsoronta yakeji da bayaso ya tsaya
kusa da ita ko me?Ta tuno ranar data mamayeshi ta rungumeshi a Gidan-Waya yadda
ilahirin jikinshi yakama rawa.Toh ni dai bana gane ma wannan tsoron naka wallahi.
Lidiya tak'araso wajan tana mata kallan takaici nama na jan kare"ai
ke dai kin gama a sara Kasham,namiji yana gudunki amma ke kina ta shige mishi sai
kace shine mahad'in numfashinki?Taja dogon tsaki"to kidai yi a hankali kafin
dalibai su farga,dan kin san ba dad'i zaki jiba idan suka tasaki a gaba da
wak'ok'in shak'iyanci.Tagyad'a kai"zan so hakan indai zasu danganta ni da Julaibib
a cikin baitocinsu.Ke Lidiya bazaki gane kome ba dan baki fad'a tarkon so ba. Ai ko
na fad'a tarkon so bazanyi hauka da wawanci da rashin aji a wajan da nasan ba a
maraba dani ba.tawuce tabata waje."Iska dai na wahalar da me kayan kara.
A sanda hantsi ya dubi ludayi na ranar a sabar,yana zaune a shagonsu
yana lissafin mutanan da suke bi bashi kuma su kai shiru mak'atau balaguro a
lahira"kamar sun sha nonon uwarsu,d'ago kan da zaiyi caraf idanunsu yahad'u.Yafara
ambatan ALLAH a zuci.
Tana tsaye a barandar shagon cikin shigar shadda me maik'o ruwan
makuba riga da zani bata d'aura d'ankwalin shaddar ba sai ta yafa k'aramin mayafi
ruwan madara a saman gyararren gashinta data d'aureshi da k'atan ribbon ruwan
makuba jaka da takalmanta ruwan madara,fuskarta,ta d'auki kwalliya,ta rungume
hannayenta a k'irji tana k'are mishi kallo,yana sanye cikin yadi ruwan madara
kanshi ba hula saisayan dayayima gashin kanshi da k'asumbarshi sun mishi kyau,ya
fito sharrr dashi k'amshin arabian perfume d'inshi ya mamaye har inda take tsaye.
Yamaida kallanshi cikin littafin amma ya kasa cigaba da abinda
yakeyi. A hankali tafara taku d'ai-d'ai har tashiga shagon.Hucin numfashinta kawai
yaji a gefen fuskarshi"Dan Sarai barka da hutun k'arshe mako".
Ke malama na fad'a miki kifita harkata ko ana soyayyah dole ne!?
Tamishi fari da idanun ta sannan tafara magana da wani salo irin nata na yanga
"Kana ganin ba a soyayyah dole?Tagyad'a kai "To ko ba ayi za a fara hakan akan
mu,kaga zamu shiga kund'in tarihin duniya"Julaibib da Kasham"what a perfect match..
Wai kai sai dubu nawa kake so in fad'a maka ina sanka, zanyi sallah koda zan 6ata
da kowa nawane sannan za ka yadda dani? Haba Julaibib lokaci fa yayi da zan tunkari
iyayena da maganar ka,kabani goyon baya,kaga mun kusa gama karatunmu sai kawai muyi
aure hankalin mu zai kwanta"kanwa ta kar tsami k'wannafi ya kwanta.Tayi taku biyu
tad'auki ragowar ruwa da yasha,tafara kur6a tana kallan shi danjin abinda zai
fad'a,amma har ta shanye baiyi wani motsi ba.
"Jesus christ"!
tafad'a cikin kad'a kai,miskilancin ka yawane dashi wallahi,wanda bai sanka ba
zaiyi zatan kai kurma ne awasu lokutan fa.
Bai kalletaba yace nima sau dubu nawa kike so in fad'a miki bazan
iya auren kiba kafin ki yadda dani?!
No No No tad'aga mishi hannu ni ba irin wannan banziyar amsar zaka
bani ba.
Musaddiq yashigo da fara'arshi ganinta yasa shi d'aure fuska.Suka
gaisa a tak'aice tana tambayarshi ya d'aliban makarantar da yake TP?Ya amsa da
lafiya lau a tak'aice.Yamik'ama Julaibib hannu sukayi musafaha. suka cigaba da
maganganun su zuwa can Musaddiq ya kalleymta"Wai lafiya kuwa? Tamishi wani
kallo"Kaima ai kasan tatsuniyar gizo bata wuce k'ok'i "Musaddiq ban sanka da irin
wannan halin ba.Yadauke kai daga kallan datake mishi "Eh ai kinsan kamawa takeyi a
d'aure me d'aurewa,Zama da mad'aukin kanwa kuma shi ke kawo farin kai.
Musadd...yatareta da sauri "A ah kiyi hak'uri kawai matata tace bata
yadda magana tadinga shiga tsakanin muba. Matarka?Ta tamabaye da mamaki Eh haka
nace matata.Tad'an ta6e baki"to kenan tsoronta kakaji? A ah Ba tsoronta nake ji
ba,sai dai bana san 6acin ranta kona sisin k'wabo.Ahaf,tawatsa hannaye "ba cinya ba
k'afar baya.tama Julaibib lallausan murmushin ta"ni zan wuce sai mun had'u ranar
litini a makaranta"tajuya tayi tafiyarta.
Ranar litini itace da darasin farko a ajinsu Sudaida tana shiga ta
tarar dasu a tsaitsaye suna caccar baki.Tabisu da kallo "Lafiya kuka cika ajin da
hayagaga bud'ar kan karya?Linda tafara mata bayani "ranar juma'a Sudaida tana cikin
yan weekend-sanitation na wancan makon, amma takama hanya tayi tafiyarta ba tare da
tayi kome ba,shine yanzu muke fad'a mata wannan juma'ar dole ta tsaya suyi ita da
Dinatu,shine tafara masifa wai ba wanda ya isa yasata tayi sai idan taga damar
tsayawa tayine kawai zata tsaya,wancan makon ne take da aiki batayi ba kuma ai
yariga ya wuce. Kasham tace"baki kyautaba maimakon ki bada hak'uri kome yawuce
shine sai ki rufesu da masifa?Sudaida ta turo baki gaba"to ai bani kad'ai bace
Dinatu ma tafito indai gaskiyane abun.Tatsareta da manyan idanunta masu maik'o"Idan
kuma karya ne fa?Sudaida tad'an motsa kafad'a"shikenan sai tayi zamanta dama idan
aka tsaneka ko ruwa ka fad'a sai ace ka ta da k'ura"tafara k'unk'uni.
Kasham tajijjiga kai"ban ta6a dukan kowa ba tunda nazo makarantar
nan,amma yau za kisha na jaki,jeki Staff-Room ki jirani.Yan ajin suka zaro idanu,
wasu suka d'ora hannayensu aka"Yau Sudaida zata kad'e har ganyanta a wajan
malamai.Har ta kusa fita daga ajin sai kuma takirata"Hey come back"Sudaida tadawo
tana kumburi"Kneel down here"takai gwiwoyinta k'asa tana k'unk'uni.Kasham tanunata
da yatsa ke"If you dare say something again...I will deal with you.
Takira Dinatu tana tambayarta me yasa baki tsaya an gyara ko in dake
ba? Cikin rawar murya"Tace bani da lafiya ina kwance a hostel ranarma ban shigo
ajiba". Hakane? Ta tambayi sauran d'aliban suka amsa da eh.sai tadan dafa
kafad'rta"Amma yanzu kinji sauk'i?Eh malama naji sauk'i.To jeki zauna ko.Tajuya
gaban allo tafara rubutu,tagama rubutawa tajuyo tana fuskantar d'aliban tana musu
bayanin sabon darasin da suka shiga.
Sudaida tasake kallan siririn farin agogon fatar dake daure
ahannunta na dama,lokacin tama ya kusa k'arewa amma dan wulak'anci ta barta a
durk'ushe, gwiwoyinta har sunyi tsami dan rashin tausayi da imani,tabi k'eyarta har
zuwan gashin kanta da harara, wannan uban gashin k'aryane ba na ta bane wig ne,ga
wani d'inkin rashin mutunci da tayi da atamfar jikinta,koya tayi tasa oho?Taja
dogon tsakin dayasa duk yan ajin suka kalleta da mad'aukak'nn mamaki.
Kasham tasake jijjiga kai"ni keki jama tsaki ko?Wallahi yau sai
nayi maganin bakin rashin kunya.Tashi kafad'a min abinda yasa kikaki tsayawa ranar
juma'a.Taturo baki gaba"to ai Yaya D'ansarai ne yace shi bazai zauna jirana yarasa
sallar juma'a ba,ni kuma shine na bishi. Wani lallausan murmushi yasu6uce mata har
kyawawan fararan hak'oranta suka bayyana,jin ta ambaci D'ansarai wato dama
k'anwarshice wannan? Kawai sai ta rik'o hannunta suka fita.
Ajin yakaure da hayaniya,wasu suna mata ALLAH yak'ara gwamma ayi
maganin bakin tsiwan, wasu masu raunin zuciya har idanunsu sun cika da kwalla na
tausayin halin da zata tsinci kanta aciki indai tashiga dak'in malamai,musamman
kuma da Kasham tayi wannan murmushin sai suke ganin lallai na tanadin wuyane da
ALLAH ne kad'ai zai ceci Sudaida.
Sun d'anyi nisa da ajin sannan suka tsaya.Kasham tadafa kafad'arta
"Kidaina irin wannan halin bashi dakyau,masoya da mak'iya ba a guzurinsu halinka
zai baka su a duk inda kaje"Next time karki sake binshi sai kinyi aikinki kingane
ko? Tagyad'a kai.Nima kiyi hak'uri da abinda namiki.Tayi mirmishi "bakome jeki aji
ga malamin lissafinku can zai shiga"Always be a good student.
Takoma aji tana wata tafiya irin ta eh yane naci dubu sai
ceto.D'aliban suka zaro idanuna suna binta da kallan sama da k'asa alamar"a ah abin
mamaki wai Baturiya da suna manga.Dan ba hawaye ba wata alama ta an bata na
jaki,amma ba damar tambayarta ya akayi aka haihu a ragaya?Danga Malamin lissafi nan
yahad'e girar sama da k'asa,dan shima k'wallan shegene shi yasa ko d'an k'us k'us
k'us d'in nan na d'alibai basuyiba sai an tashi tara za a baje kome a fai-
fai.Sudaida tamusu fari tana wani lallausan murmushi sannan tazauna awajan
zamanta,Suna had'a idanu dashi itama tashiga taitaiyinta.
Suna ciye-ciyensu dasu A'isha a sanda aka buga tara,sauran yan
ajin sun zagayesu ana tambayarta an daketa kuwa?ya akayi tabarta tadawo aji da
sauri?Sun dauka har a buga tara basu gama horata ba,bulala nawa aka mata?Tawani
hura hanci cikin kuri kamar gaske "tama isa ta dakeni ne?Ai wallahi ko kura ta san
gidan me babban sanda.Suka kyalkyale da dariya suna ihu;shegiya yar gidan Ibrahim-
Mai Lambu, tad'aga musu hannu"a ah kar wasa yayi wasa a tsikari uwar miji fa.Ni yar
sunna ce dan haka kar wacce takuma shegan tani ehemmm.
Kasham dasuke zaune a benci ita da wasu malaman suna hirarsu ta
k'walamamata kira tayafito ta da hannu.Sudaida tadanja tsaki"nifa wannan malamar
tana neman shigarmin hanci da k'udundune. Suka sake kyalkyale da dariya"kila yanzu
ne zata hukunta ki a bainan-nasi.Dammm...zuciyarta tabuga tsoro ya baibaye ta, kuma
kila hakane,ba mamaki tajuyo maganganun sune tunda dama ba a hankali sakayi
taba.Bata kulasuba tamik'e tana Istirja'i.
Ga ni tafad'a cikin ladabi "dole gyad'a tai mai idan tak'i tasha
matsa"Kasham tabita da kallo,haka kawai taji tana santa,tunda k'anwar masoyin
tane.Lidiya tace"meye haka kuma?Kin kira yarinya kin tasata a gaba da kallo kamar
wata magiji.Tasauke gwauran numfashi, tasa hannu a jaka ta zaro kud'in dabata
k'irgaba tamik'a mata"ungo kije kisai abinda kike so. Sudaida tabita da kallan
tsoro da mamaki kamar yadda sauran malaman sukayi "to da wace hujjar nasara zaiyi
hawan k'aho?
"Kar6a mana Sudaida.
Tajuya ba tare data kar6a ba"bar abinki nima ina da nawa.Lidiya tadaka mata
tsawa"ke k'aramar mara kunya dawo.Sai kawai tasa gudu.Tayi kwafa zamu had'u dake
gobe aji.Kasham tahad'a tafukan hannayenta"Dan ALLAH Lidiya karki daketa dan bata
miki kome ba.How dare you Kasham kice bata min kome ba ni sa'ar wasan tace dazan
kirata tak'i zuwa?Saboda ita kanwar wancan me shegen girman kan tsiyan?To niba
ruwana abu kazan uban ta zanci.Haushi yakama Kasham sai kawai tace"ai ko abu kazan
uban ta yafi k'arfinki har abadan duniya.Cikin tafasar zuciya Lidiya tanuna kanta
da yatsanta"Kasham ni kikema wannan rashin mutuncin saboda wasu tsinannun hausawa?
Ban miki wani rashin mutunci ba, magana kikayi ni kuma na baki amsa.Banda shiga
sharo ba shanu ina ruwanki da ita?Ko ke kika kirata? Kome tamin ni naja,idan naga
dama in mata hukunci,idan naga dama in k'yaleta bai shafeki ba"wannan sa kai a uku
ne takaban siriki.
Suka farar cacar baki malamai suka shiga tsakani daga nan taran
yawatse dan an koma aji. Takoma Staff-Room dan bata da darasi a kowani aji har a
tashi sai kuma gobe.Tabishi da kallo cikin harara dan kwana biyu taje yajin aiki
akanshi, duk yadda takejin san shi ba ta kulashi sai dai tayita kallanshi.Tamaida
kanta jikin kujera ta lumshe idanunta tana wata kisima a zuci "Julaibib
kyakkyawane"Melanin beauty"tayi nazarin shi dakyau baya san hayani,wani abun ba
wulak'anci yake mataba haka halinshi yake bashi da yawan magana,tana so ta aureshi
tahaifi yarinya me irin kwantaccen gashinshi, tana san Julaibib ta rasa ya zatayi
da rayuwarta"Ciwon so" data san inda zata nemo maganin shi tasha ta warke daga san
D'an Sarai ne?
"Oh my God!, ta dunk'ule hannu ta naushi iska"
Dasauri tamik'e zuwa wajanshi D'ansarai takira sunanshi.Yad'ago
yakalleta yacigaba da abinda yake yi,sai ta rasa me zatace...Dan ALLAH bani aran
correction pen. Yaciroshi a aljihun gaban rigarshi daya soke yamik'a mata.Tashafi
hannunshi sannan ta kar6a "nagode idan nagama zan kawo maka.Yagirgiza kai "Kirik'e
kawai.To nagode,tasa ajaka dama neman magana ne itama tanada nata fa.
Duk ranar alhamis suke House Assembly, wani ikon ALLAH sai akasa
Kasham da Julaibib a house d'aya,Sudaida ma anan take. Kasham a matsayinta na
sabuwar malama ita tafara musu bayanin kanta da yar nasiha,sai malamai biyu duk yan
TP sai Julaibib cik'on na hud'unsu.Cikin natsuwa yake musu bayani sannan yad'ora da
nasiha a kan su dage da karatu ba kawai sai lokacin jarabawa ko za ai wata kaci-
kaci da muhawaraba, kullum Ku zama masu nazari da bincike da tambayar duk abinda
baku ganeba, da wanda baku saniba da hakane ake samun ilmi me yawa,ita k'wak'walwa
d'an Adam ne yake cikata da aiki,idan kuma baiyi hakan ba to ita zata cika mishi da
abubuwa na shirme wanda bazai amfaneshi akaran kanshiba,bare har al'umma ta
amfana,ina fata zaku dad'a sa k'wazo duk da nasan kunayi amma Ku k'ara, ina kuma
fata zaku zama masu amana kamar yadda sunan gidan na ku yake "Amana House.
D'alibai suka d'auki tafi.A'isha da take bayan Sudaida tace"Amma
gaskiya ina san Yayanki Sudaida,yanayinshi me sanyine,sukayi murmushi.Mr Julius
shugaban house d'in shima yatafa mishi,yau bani da abin fad'a.Yanuna Julaibib da
yatsa"This great teacher of ours has said all".Yad'an bubbuga kafad'arshi sukayi
murmushi,sannan yakalli d'aliban yad'an motsa kafad'arshi"shikenan you can go back
to your classes" duk suka watse.
Maimun yakawo musu ziyarar bazata ranar juma'a da yamma,sun kuma ji
dad'in haka sunata ba juna labarin makarantun da aka turasu har Maimun yasako mishi
maganar Kasham...Yayi kamar badashi yakeyi ba.Zuwacan kuma yagirgiza kai"ni fa ba
zanyi abinda zai zama min matsala ba,aure ba abin wasa bane, ba kuma yin auran ne
yadameni ba,a ah samun matar data dace dani me mutunci da mutunta kai.Kasan ALLAH
Julaibib Kasham tana sanka,wannan soyayyar da take maka zaisa tamaka biyayya tabi
umarninka.Yagirgiza kai"Kyaleta kawai Maimun. Maimun bai kuma maganarba suka cigaba
da hirar data shafesu har Musaddiq yafito suka tafi k'wadago neman halali.
Baranzan yajuya yana kallanta"Ke wai meye damuwarki ne?Wani haushin
shi takeji gwamma tabar mishi d'akin dan batayi maraba da zuwan shiba,idan tazauna
za ayi d'anyan aikine dan shima bashi da mutunci idan yana 6acin rai.A fusace
tajuya zata fita,caraf taji yarik'o dantsen hannunta kamar zai k'aryata.
Tarinse idanu dan azaba. Yasunkuya akan fuskarta"sai kin fad'a min
da uban wa kika fara soyayya da har kike guduna? Sake min hannu.Yasake rik'eta
tamau.Sai fa kin fad'amin da uban wa kika fara soyayyah? Haushinshi yadad'a ninkuwa
a zuciyarta Kawai sai tace da"Ubanka...bata gama rufe baki ba taji saukan mari hagu
da dama,idanunshi suka kad'a jawur"za kimin rashin mutuncine?Uba na sa'ankine?
Yafad'a da karfi cikin tashin hankali da alama allurar soja ta motsa.Uba na ko?
Tagyad'a kai duk da a zabar rik'on data keji.Kikace eh? Yashak'eta,manyan idanunta
suka fir-firto numfashinta yazo wuya,yasake kifa mata mari hagu da dama,sai da taga
wasu k'ananan taurari sun tarwatse, gefen bakinta ya fashe,ji da ganinta suka
d'auke na wucin gadi..
Wannene abin so?... A tari fitsari a wanke zawo?
18 Rabi'a Thani 1441
15 December 2019
We Ibrahim's Daughters👇
Asdilat KD...2geda with Ra'ibs
DANGIN NONO WRITERS ASSOCIATION
{Da Inganci Mukayi Fintinkau}
Bismillahi wabihi nasta'in
...GWAJIN DAFI💔
Almost true story
Daga alk'alamin 🖊
Ya'yan Ibrahim
Saudat A.Baba (Asdilat KD)
Da
Bara'atu Ibrahim (Ra'ibs)
Shafi na biyar.
Dak'yar aka 6an6areta a hannunshi bayan tasha wahalar
duniya.Yarafff... tafad'a gado tana wani irin tarin wahala tana fuzgo numfashin ta
dayake k'ok'arin kufcewa.Shima ya fuzge daga rik'eshin da akayi ana ta bashi
hak'uri,yayi kanta,aka sake rik'eshi
Lidiya tashigo da gudunta dan bata san abinda ke faruwa ba yanzu aka
kai mata rahoto"haba Baranzan kazama namiji mana, jarumin namiji me kwanan daji
irinka me zai sa katsaya fad'a da mace?Kasham fa kwana biyu bata da lafiya ya
kamata kamata uzuri.Anki a mata uzurin wa tafad'a ma bata da lafiya? Yabita da
kallo tana kwance sambal,gashin kanta a hargitse kuma ta rame ba haka yasan Beauty
d'inshi yar gayu ba.To kitashi muje asibiti. Shiruma amsace.Yad'ibo wasu damin
kud'i yaba Lidiya wai tarakata asibiti ta tabbata an dubata ankuma bata magani me
kyau.Tagyad'a kai tare da sara mishi "Yes sir tabuga k'afar damanta a k'asa.
Tarakashi da adawo lafiya sannan ta rufo k'ofar ta zauna a bakin
gadon,tasa hannu tashare mata jinin da yake gefen bakin ta,tabud'e idanunta suka
kalli juna.Lidiya tad'an d'age gira"wallahi kashin kare baya taki" Baranzan shine
yadace dake ba wancan tsinannan bahaushen ba,danni bazan fasa fad'a miki gaskiya
ba,kome naku d'aya da Baranzan"Hun wai saboda wani bare da bai san ALLAH yayi ruwan
tsiran kiba kike ga ba dani,indai bani namiki magana ba ke bazaki minba. Tamaida
idanunta tarufesu"ita abinda yadami zuciyarta shi d'in ne yadameta"daga ita har
Baranzan basu d'ad'ata da k'asaba"kowa da kiwon daya kar6e shi mak'ocin me akuya ya
sai kura".
A'isha tabiyo Sudaida dad'an gudunta da aka buga tara"Ke malama
jirani"Tatsaya tana kalllanta har ta k'araso"Kefa kika ce ba inda zaki".Aisha
tagyad'a kai"Eh nafa sane naga gaba d'aya ajin an watse an barni kamar mayya,me
zaki siyane?Ta tambayi Sudaida"Ba abinda zan siya dan bana jin cin kome na
makarantar nan yau.Wajan Nasmat zani.Tarik'o hannunta"Dalla shareta zo muje wajan
Yayanku tad'an turo baki me zanje in mishi?Ke shifa Yaya D'ansarai ba yaso a
dameshi.Ke dai zo muje mana ni wallahi ina sanshi.Sudaida tamata wani kallo sannan
ta ta6e baki"Lallai kinji jiki, Yaya Julaibib d'in kike so?.Eh wallahi"Yanayin shi
me sanyi ne,baya san hayaniya.
Wa alaikumussalam.Ya amsa sallamar su. A'isha tamata nuni wai su
zauna,ita kuma tana nok'e kafad'a.Yad'an d'ago yakalle su,sai yacigaba da nazarin
d'aya daga cikin tarin littafan dake gefan shi,hannunshi rik'e da jan biro da alama
hannu yake sawa akan aikin daya basu.Yasake d'agowa yakallesu ganin sun zauna
sunata kallanshi"yaya wani Abu ne?Aisha tayi tsagal "Yaya Julaibib dama... da...
sauran kalaman suka mak'ale saboda wani rikitaccen kallo da yake mata,sai ta mik'e
"bakome Sudaida taso mutafi.Har sun jiya Sudaida taji kiranshi.Ta tsaya sannan
tajuyo tana kallanshi ya yafitota da hannu.Tak'arasa wajan"Yaya Julaibib gani
"Yad'anyi murmushi"hala kud'in taran na ku ba yawane yau?A ah wallahi muna da
kud'inmu. Yamik'a mata wasu kud'in"duk da haka sai Ku k'ara,tasa hannu biyu
takar6a"Mungode ALLAH yak'ara bud'i.Yad'an bita da kallo yana murmushi.
A'isha taja tsaki kawai anzo wajanka amma saika wulakanta mutane.
Sudaida tad'aga mata hannu"a ah wallahi Yaya D'an Sarai bashi da wulakanci, kuma
baki ga abinda yakeyi bane?Ai dama nafad'a miki shi fa baya so adameshi...Nasmat
tak'araso wajan tatarar da Aisha tana k'unk'uni "Ke da wa kuma?Da Yayanku d'an
wulak'ancin can mana tanu mata Julaibib d'in da d'an yatsa.Nasmat ta kyalkyale da
dariya miskili kafi mahaukaci ban haushi"to amma shi da baya shiga shirgin mutane
to me yahad'o ki dashi? Tawatsa hannu"shareshi kawai suka cigaba da tafiyarsu suna
hira.
A sanda hantsi yadubi ludayi na safiyar lahadi suna hirarsu da Inna
Khalifa d'an mak'otansu yashigo da gudunshi"Yaya Julaibib ana sallama dakai"To kace
ina zuwa. Suka cigaba da hirarsu,ganin bashi da niyyar tashi Inna tace"Tashi katafi
mana.Yamik'e To Inna yad'auki rigarshi daya cire yana sawa,a zaure yak'arasa
sawa,yana fitowa caraf idanunsu yahad'u,yamata wani irin kallo data kasa
fassarawa.Tayi yar dariya"Malam D'ansarai kenan wato ganina yasa ka canjawa kamar
kaga me tagayyara rayuwarka har abadan duniya ko?To ni dai nazo gaisheka ne,wancan
makon ko sau d'aya ban samu nazo makarantaba dan bani da lafiya kuma a dalilin
sanka nashiga halin dana shiga amma ko katambaya"Lafiya kuwa Kasham bata zuwa
makaranta?To koma dai yayane Thank God naji sauk'i,ina kuma so kamin jagora zan
shiga gaishe da Mama."Bata nan"Yabata amsa a takaice. Takama ha6a🤔D'ansarai wallahi
bakayi kama da masu zabga k'arya a kalaman suba,nafa tambayi yaran yacemin
tananan,inaso muyi kome cikin mutunci da girmama junane shi yasa ban shigo kai
tsaye ba,amma kai naga kamar ba hakama kake so ba,idan natsaya rarrashinka kuma
raina ne kawai zai 6aci a banza,tunda har yanzu baka d'aukeni wata tsiya ba,ko
albarkacin k'aunar da nake maka ban ta6a ciba.
Koma inda kika fito,tunda ba gayyatoki nayi ba.Tagirgiza kai idan
kamin haka tsakani da Allah baka min adalci ba,tanuna mishi Bible d'in hannunta
daga majami'a (Church) nake,ana tashi nashigo cikin gari ko gida ban koma na ajiye
Bible d'in ba,duk dan d'okin ganinka.Yau d'aya dai kamin adalci a matsayina na yar
Adam bama masoyiyar kaba.
Inna tafara jiyo hayaniya."Na rantse da girman ALLAH idan kika tako
inda nake sai na 6allaki.Inna tajuyo furucinshi cikin fad'a.Kai dawaye Julaibib?
Inna ta tambayeshi bayan tashigo zauren.Cikin tafasar zuciya yajuya yakalli Inna
idanunshi jawur"ni da wancan mara kamun kance.Zuciyar ta tabuga Dammm...Kasham wato
kwana biyu da bataji d'uriyar taba ta zaci ta hak'urane kamar yadda taita zuwar
mata kwanakin baya. Inna dai hakuri take bata tunda maigayyar yace baya so, zuwan
ta nak'arshe da Inna tafad'i haka yar dariya kawai tayi tamata sallama tatafi .To
yau kuma kwatsam ba zato sai gashi tadawo.
Kasham daga waje tace"Mama kice yabarni in shigo dan ba wajanshi shi
kad'ai nazo ba har dake,idan kuma ba haka ba zan mishi abinda har abadan duniya
bazai manta dani ba.Wata jijiya tafito rad'am agoshin shi kamar shatin bulala"ni
kuma sai dai baki k'araso wajan nan ba amma wallahi sai na 6allaki"ke! yafad'a a
tsawace idan kin fasamin abinda bazan mantaba har abadan duniya ke ba...Inna
tatareshi"Kai Julaibib dakata! Inna wallahi...tad'aga mishi hannu na dai ce ya
isako?Yasunkwui da kai.."haba Julaibib idan rai ya6aci bai kamata hankali ya gushe
ba,wai kamanta da sharrin mace har yafi na shaid'an kaifi?.Bai sake magana yasa kai
yafita.
Kasham tashigo zauran suna gaisawa,Inna tabita da kallan tausayi"Iska
na wahalar da me kayan kara.Takai gwiwoyinta k'asa tahad'a tafukan hannayenta
alamar magiya idanunta sun ciko da k'wallah "Mama ki taimakeni mana".
Inna tajijjiga kai"Zanso k'warai Julaibib ya aureki ko dan
matsananciyar k'aunar dakike mishi,kuma ya tsamoki daga duhu zuwa haske amma
hak'ata bata tadda ruwaba,to kema me zai sa bazaki hak'uraba? Sharrr...hawayen masu
d'umi suka zubo a kyakkyawar fuskarta "saboda ina san shi Mama,Julaibib d'an kine
na san zaiji maganarki,idan kikace dole ya aureni ai bazai k'i miki biyayya ba.Inna
tadafa kafad'arta "Kasham kenan, kasancewar Julaibib d'a na ne ba yana nufin in
tilas tashi yin abinda baya so bane,Julaibib yana da hakki akaina, kamar yadda nake
da hakki akanshi,shi aure ba abin wasa bane,zaman aure kuma ana yin shine bana
wucin gadi ba,a ah zaman din din din ne da ba a san rabuwa sai dai idan k'addarar
hakan ta kasance ba yadda za ayi,kinga shi yasa ma ake so mutum yaza6i abokin
rayuwar daya kwanta mishi arai, kowa yanajin k'auna da soyayyar d'an uwanshi da
gasken-gaske,tayadda idan an samu sa6ani za ayi fad'a, idan an huce za ana juna
uzuri,za a yafema juna, amma idan d'aya a dole yake zaune da d'aya to abu kad'an
d'in da bai ta ka kara ya karya ba sai rigima ta 6alle wanda daga nan auran zai
lalace an rabu, to ina amfanin 6ata goma biyar bata gyaruba?
Suna cikin haka saiga Alhaji Abdullahi yashigo shima da nasiha yabita
me ratsa jiki.Tagyad'a kai"Eh tabbas duk abinda suka fad'a gaskiyace wacce daga
k'inta sai 6ata. To amma fa ita har kwannan gobe tana san D'an Sarai bata kuma cire
rai da auran shiba.
Bayan sun gama cin abincin dare.Alhaji Abdullahi yakalli Julaibib
"D'ansarai na san ba abinda ke tsakaninka da wancan yarinyar amma duk da haka sai
ka k'ara yin taka tsantsan,dan shaidan baya raina k'ofa,kai kace bazaka aure
taba,ita kuma bata hak'ura ta daina bibiyarka ba.Kanemo mata kayi aure dan shine
kwanciyar hankalinka damu kanmu,bana so kad'auki wani dogon lokaci ba tare da iyali
ba.Yashafa kwantaccen bak'in gashin kanshi "Sannan ya amsa cikin ladabi.Amma cikin
zuciyar shi inda kizo ke sak'ar wacece yake jin santa? Dammm...Zuciyar shi
tabuga,yayi maza yakawar da tunaninta a,Yasauke gwauran numfashi " Yau ake yin ta
wai anyi da mutum ya ji"...
Hajiya takalli Sudaida da 6acin rai"Kai wannan yarinya da kafirin
taurin kai take kamar mutanan farko,za ki d'auka kisha ko sai na sa6a miki? Ta turo
baki gaba"ni fa wallahi na ji sauk'i"ke tafi can kinji sauk'i amma kwana biyu kina
kwance?Ni na ta6a jin inda akayi haka? Baka da lafiya bazaka sha magani ba,baza a
maka alluraba?To ko duk tsiyarki gobe sai kin tafi makaranta dan naga abun na ki
"Tsiya ne d'inkin ludayi.
Ya shigo da sallama.Tabishi da kallo "Yaya Julaibib ina atilan dana
ce kasiyo min"?Yayi kamar ba dashi take magana ba, yazauna a kujera suna gaisawa da
Hajiya.Tad'anyi tsaki"ALLAH yasauwak'e maka wannan halin... takauda kai daga kallan
da take mishi tafara k'unk'uni saiga Sinan shima ya shigo"Tace yauwa Sinan kamar
kasan ina mararin ganinka.Yagaishe da Hajiya tare da tambayar ya akaji da me jiki?
A Alhamdulillahi ai taji sauk'i tunda har tana k'in shan magani, shekaran jiya da
bata san inda kanta yake ba ai ina bata take kar6a tashanye ba musu ba
gaddama.Sudaida ta turo baki gaba ni fa kaina ba inda yatafi yabarni muna tare har
a k'abari.
Sinan yamatsa kusa da gadan da take kwance ta lullu6e jikinta da
bargon Hajiya fuskarta kawai ta bari a bud'e.Yamata wani kallo"Sannu sarauniyar
Sinan" tagyad'a kai cikin murmushi.Yafara mata magana k'asa-k'asa. Takyalkyale da
dariya tad'an zaro idanunta"Kaiiii Sinan wallahi ba ruwana.Sai yamik'e tsaye daga
sunkuyan da yayi a kusa da ita"Me zan kawo miki anjima"?Tad'an harari Julaibib
caraf idanunsu yahad'u tadauke kai,sannan tad'an marairaice "atile"dame kuma?Sai
kuma yaba kanshi amsa"da masoyin sarauniyar Sinan rake.Tayi murmushi" Wallahi
nagode maka ba kad'an ba Sinan.Tad'aga hannu tana mishi adabo"adawo lafiya.
Filin wajan da malamai suke ajiye mashina da motoci taje,tad'are
mashin d'in Shunkut dan yayi saiti da inda Julaibib yazauna a barandar d'akin
malamai,tana kare mishi kallo...Tayi murmushi cikin sauke numfashi "Julaibib da ka
san matsanan cin son danake maka wata kila daka ceci zuciya ta da take shirin yin
gobara.
Holy ghost fire!
Lidiya tafad'a dan Kasham batama san tazo wajan ba.Akan wancan tsinannan bahaushen
kina neman zama mahaukaciya"For Christ sake wai me yashiga k'wak'walwarkine? Lidiya
kome zaki fad'a min indai akan son wancan bahaushen ne tamata nuni da inda yake
zaune, to ina maraba dashi,kin sani tun ganin Julaibib a kuma kallanshi farko so da
k'aunarshi suka mamaye zuciya ta,shi kanshi ya fad'a min uncountable times bazai
aure niba and I don't know why har yanzu nake jin kaunar shi deep down my heart".
Tadafa kafad'arta ki tayani addu'a duk ranar da ALLAH yabani sa'a
yashiga nan ta nuna tsakiyar tafin hannunta,yad'and'ani zak'i da gardin zuma ta,to
wallahi na mishi katttt...kisan mummuk'e.Lidiya ta kyalkyale da dariya"gaskiya iska
tana wahalar da me kayan kara,malama dame kama ake yin k'ota.Wancan me shegen
girman kanne kike tunanin za ki yaudare shi?To yaushe ma yatsayi kulaki bare har
hilarki tayi aiki akanshi? Wallahi kinga dai bana san shi amma na jinjina mishi 👍
zan kuma iya bada shaidarshi harkar mata baya yinta, dan da yanayi wallahi ko sau
d'aya ne tun zuwanshi Gidan-Waya da mun sani,kema ai kin san mune idon gari a
makarantar nan,wannan harkar sai sojanki Namamajo,ke dai kawai ALLAH yaganar
dake,amma banda 6atan basira mutum yace baya sona to nima banga abinda zai sa ya
kuma d'ad'ani da k'asaba tunda shi d'in ai ba mahad'in numfashi na bane,ko yaranmu
d'aya dashi zan hak'ura in kyaleshi,bare wani hausawa me girman kan tsiya,shiba
kowan kowaba dillalin kashi,kin sani ni nak'i jinin hausawa, ke ba hausawa kad'ai
ba duk wani me sallah bana sanshi da inda k'arfin iko na rantse miki da ALLAH ba
wasu tsinannun masu sallah dazasu zauna mana a gari.Taja tsaki fuskar nan tarine da
6acin rai ruwan kafircine zallah babu gauraye da haske da tausayi da Imani ko na
sisin kwabo, jikar kajawace (Bajju) gaba da baya"bana san ma su sallah.Kuma ba
yadda za kiyi dasu "sun zama kuturwar uwa dole a zauna dake.Kasham tabata
amsa,sannan tasauko akan mashin d'in tawuce bayan aju-juwa da aka k'awata wajan da
shuke-shuken filawowi masu ban sha'awa,tadinga bi tana tsinkosu kaloli mabambanta
masu k'amshi tacika hannunta sannan tasa zaran ulu,ruwan hoda tadaure tawuce d'akin
malamai zaman jiranshi.Dak'ik'a biyar da buga k'ararrawar canjin darasi sai ga shi
yashigo,saida tabari ya zauna a kujerarshi yana hutawa ba ajin dazai kuma shiga sai
gobe.Yakwantar da kanshi a jikin kujerar, idanunshi a rufe wani bacci me dad'i
yafara shirin saceshi sai kawai yaji an shafa mishi wani abu a daidai hancinshi me
wani irin k'amshin dad'i, yabud'e idanunshi da yanayin bacci har sun d'anyi ja.
Tamishi lallausan murmushinta "perceive the natural fragrance of this
bounch of flowers.Tafurta hakan da wani salo irin na ta nayanga sannan tacire daga
hancinshi ta d'ora mishi a saman tebur.Yakauda kai daga kallan da take mishi kamar
kura taga nama.Wallahi yama rasa abinda zai ce mata.
Tayi k'asa da murya ganin wasu malaman sun fara sa musu na mujiya"ai
nasan ban kyauta maka ba ko?Kai dai ba a maka gwaninta,d'an motsa kafada tayi
"karka damu dani,kar kayi la'akari dacewa nice nakawo maka,tagirgiza kai kayi
la'akari kawai da tarin amfanin da k'amshin furen filawa yake dashi ga d'an
Adam.How I wish Jualiabib ka bani dama na nuna maka irin kaunar danake maka,
tagirgiza kai cikin damuwa "How I wish ka tallafi zuciyata ka magance min damuwar
cikinta...sai dai kash!Ban samu hakan ba,saboda baka san illar kaso a
k'ikaba,tabbas daka san haka da baza kabari zuciyata tayi gobara ba.Tahad'a tafukan
hannayenta alamar magiya "Don't let the love that I have for you to go in vain
please...!
Yad'ago yakalle ta,sai yaji wani abu ya tsirga ilahirin jiki da
zuciyar shi,har ya bud'e baki zayi magana sai kuma yagirgiza kai"a ah Julaibib
daure kawai, maganin kar ayi to tun farko kar a fara"kawai sai yamik'e yabar
d'akin.
Shunkut ya sunkuyo a fuskarta yana murmushi"Ke ki hak'ura dashi mana
ai ba a soyayyah dole, yanuna kanshi da yatsarshi"ni d'in nan namiji ne duk abinda
yake dashi namazan taka nima ina dashi,kiyadda kawai muyi soyayyah.A fusace ta
tureshi"you fool! dawa za kayi soyayyah Shunkut?Tayi d'as da yan yatsunta over my
dead body.Tagalla mishi harara sannan taja mummunan tsaki"ruwa ai ba sa'an kwando
bane"sai yajuya yana tafiya "Amma kuwa za kiyi 6atan 6akatantan...
A gajiye lik'is yashigo,gidan shiru dan Inna tana gidan Hajiya,yazauna
yana hutawa, ya6alle botiren gaban farar rigarshi,yamaida kanshi jikin kujera tare
da lumshe idanunshi sassanyar iskar bayan la'asar tana ratsashi. Mafarkan da kwana
biyu nan yakeyi sun tsaya mishi a rai"Kasham yake gani cikin kyakkyawan kirar
kalangunta,sanye da kayan fulani,gashinta yasha gyara ta tufkeshi a baya,amma kuma
idan tayi magana muryar Sudaida yakeji"ya rasa kan wannan mafarki.
Hayaniyar shigowarsu Kamila yasashi bud'e idanunshi,aiko suka shigo
sunata zuba surutunsu, sunata mishi tambaye- tambaye.Shigowar Musaddiq yasa suka
koma tsakar gida suna wasannin su,yadaki kafad'ar shi"kai malam tashi da ALLAH
magana nazo muyi. Uhun ina jinka.Musaddiq yabishi da kallo"Julaibib ka nemi A'isha
kawarsu Sudaida mana tunda dama ta nuna tana sanka kaine baka bada goyon baya,tana
da hankali kuma ko su Baba idan sukaji ita kake so za suji da...yatari numfashinshi
a hasale "bata min a matsayin matar aure ba,dan haka akai kasuwa".Yakalle shi da
mad'aukakin mamaki"To me yayi zafi da har idanu za suci wuta haka? Tagyada kai "To
yayi,indai har A'isha bata maka a matsayin matar aure ba to ashe gulmace da
kai,kana kuma kallan mata za kuma ka iya za6a,amma da zarar magana ta tashi sai
kace ba sa gabanka,to kuma harsu Baba sai sunji zancen nan.
Yanunashi da yatsa"Idan kai zaka min zaman auran ai sai in
aureta.Yamaida idanun shi ya rufe, shi wai ma wacece wata A'isha?Wasu lokutan dai
Sudaida tana fad'a mishi"A'isha tace tana gaisuwa"ko kuma A'isha tace kaza da kaza
game kai,sai dai bazai iya tuno me take fad'a d'inba, dan ba itace a gaban
shiba,shi dai bai san tana sanshi ba,dan ko Sudaida bata ta6a fad'a mishi wai
A'isha tana san shiba, kila Musaddiq d'inne kawai yake san had'awa.
Sallar a zahar Julaibib yayi yagama azkar d'inshi sannan yafito daga
masallacin makarantar,yau ba ayi wani karatun kirkiba saboda Inter-House ya kusa,ga
dalibai nan sunyi rukuni rukuni na irin abinda suke so, suke dad'a yin gwaji
(practice)yajingina da bishiyar giginya tare da rungume hannayanshi a kirji yana
kallan Sudaida yadda take d'aga mulmulallan bak'in k'arfen discus da yadda take
jefashi cikin k'warewa da nishad'i a bokan wasanta suna mata tafi wasu suna mata
ihu dan tanayi yadda yakamata.Yayi murmushi yatuna lokacin da yake makaranta yayi
wasannin kala kala,wasan kwallo ne bai ta6,a burgeshi ba wannan sai Musaddiq,saboda
kwazanshi a fannin wasannin shine yarik'e shugaban wasanni na lokacinsu (Game
Prefect) yakalli Khausar sune yan Javelin, Nasmat kuma ana bangaran Long jump.
Yabar jikin bishiyar yana tafiyarshi cikin natsuwa har yaje Staff-Quater zai kar6i
wasu littafai a wajan Mr Julius.
K'arfe uku tanayi yasake komawa filin wasannin da Nasmat yafara cin
karo yace"Ke idan ba zaku tafi gida bane ni kunga tafiyata.Dan ALLAH kajiramu barin
kirasu tayi cikin filin da dan gudunta.
A mota suka sameshi ya musu wannann rikitaccen kallan nashi Sudaida
tabud'e baki za tayi magana yanu nata da yatsa"kul naji bakinki.Tad'an harareshi ta
zauna tana turo baki gaba.Yaja tsaki"kunje kun shagala da wasanni ko sallar azahar
ma baku yiba ga la'asar ta kusa,kufa kuna da ka'ida da bambanci tsakanin ku da
wad'anda dama basu san kome ba sai duniyar, wallahi idan lokacin sallah yayi banga
mutum a masallaci ba gobe...yayi kwafa, Nasmat tace"shi fa wannan Game Master
muguntar shi har tafi ta Discipline Master.Ke tafi can shi ai ba makaho bane yana
ganin k'atan masallaci ai a makarantar,na kuma tabbata da kun fad'a mishi sallah za
kuyi bazai hana kuba,ai kowa ya san duk inda musulmi yake ba a rabashi da
sallah,sai dai in sallarce bata dame shiba...Yaya D'ansarai... yatari numfashin
ta"ke ba nace kar inji bakin kiba?Tasunkwui da kai"wannan mutumin wallahi yanada
matsala,tafad'a a zuci,tad'anja tsaki. Nasmat takalleta"ke Sudaida tun d'azu kiketa
k'unk'uni abin harda jan tsaki ke da wa? Shiru ma amsace.
A k'ofar gidansu yatsaida motar bai k'arasa dasu gidansu kamar yadda
yasaba ba,yakashe motar yafito yashige gida.Sudaida itama tabud'e bangarenta tafito
tana masifa"aikin banza sammakon gaida makiyi,aiko ba a motarka zamu dawo gida.
Aminu yana hangota yafara dariya"ke fa Sudaida naga alama raguwa za a
yi.Ta turo baki gaba "Yaya Aminu me nayi to? Kinga fuskarki kuwa?Gaskiya yunwar
makaranta ba ta dad'i har na tuna lokacin da mukayi makaranta a Bauchi.Yad'an
kalleta kinsan yau me su Mama sukayi a gidan? Tagirgiza kai "Tuwon shinkafa miyar
shuwaka"Sai kawai tad'ora hannayenta aka"Wayyo ALLAH! ni gaskiya yau ana ta 6ata
min rai.Suwaye suketa 6ata miki rai?Takaryar da kai gefen dama ta marairaice "Yaya
D'ansarai da su Mama,wallahi gidan Hajiya zan tafi ina canja kaya,dan bazan mutu da
yunwaba.Yamik'a mata wasu nannad'ad'd'un carbon paper,Top-bond,babban pensir HB
dawasu k'ananan tarkacen zane-zanenshi(Artistry Euipment) to tafi min dasu
gida,yanzu haka Bakin Gogi zan tafi wani aikin signboard zanyi.Tasa hannu biyu
takar6a "Yaya Aminu ALLAH yatsare.Amin Sudaida suka daga hannayensu suna ma juna
adabo,sukayi murmushi sannan kowa yajuya yacigaba da tafiyarshi.
...Dare da rana suna aiki tuk'uru a kanmu,to muma kamata yayi mu zage
dantse muyi aiki tuk'uru a cikinsu.Ubangijinmu kabamu rabo me amfani fid-dunya wal
aakhirah.
21 Rabi'a Thani 1441
18 December 2019
We Ibrahim' Daughters 👇
Asdilat KD...2geda with Ra'ibs.
DANGIN NONO WRITERS ASSOCIATION
{Da Inganci Mukayi Fintinkau}
Bismillahi wabihi nasta'in
...GWAJIN DAFI💔
Almost true story
Daga alk'alamin🖊
Ya'yan Ibrahim
Saudat A.Baba (Asdilat KD)
Da
Bara'atu Ibrahim (Ra'ibs)
Shafi na shida.
Da yammacin juma'a jikokin Hajiya sun cika gidan,tun daga zaure za ka
fara jiyo hayaniyarsu sun tasata a gaba da shak'iyanci. Sudaida da Nasmat suma suka
shigo,suna k'are mata kallo tasha had'ad'd'an leshin auduga ja da k'ananan fararan
duwatsu,wuya,hannayenta, da d'an kunnanta na zinare sai d'aukar idanu sukeyi. Suka
kalli juna suka k'yalk'yale da dariya"Hajiya manya wannan irin cakarewar k'uda a
gefen gyambo?inji Nasmat. Sudaida tagyad'a kai "Gaskiya kin had'u saura had'uwarki
da ALLAH, wannnan k'ure adaka haka?To dawalakin goro a miya,bazawarin tane zai iso
da yammacin nan. Gaba d'ayansu suka kuma k'yalk'yalewa da dariya, abinda yahanasu
jin abinda Hajiyar take fad'a.
Aminu yashigo sai suka sa ihu da tafi "Yehhh... gashinan, gashinan
shine bazawarin data k'urema adaka.Yakama ha6a🤔 wai wai wai, ai kowa ya san Hajiya
ba dani take yiba,dan ta san ni bazan juri al'alarta na bani bani kamar mak'ogwaro
kullum a bashi ba,bani da wannan hak'urin,kusa idanu anjima kad'an za ku ganshi.
Khausar tace Alkasim ne.Aminu yace gajan hak'urine dake koma wanene za ku ganshi.
Yamatsa wajan Hajiyar suna maganarsu.
Sudaida tafara shak'o k'amshin turarenshi da iska takad'o mata kafin
tayi magana yashigo yana musu wannnan rikitaccen kallan na shi"ku wallahi kun cika
hayagaga bud'ar kan karya,sai kusama mutum ciwon kai.Sudaida da dama takejin
haushinshi tace"sai dai dama can mutum da ciwon kanshi yashigo,kace kawai a baka
magani za kasha. Suka k'yalk'yale da dariya.
Nasmat tace"su autan Inna manya, kace kawai kazo tad'i wajan Hajiya
kuma katarar mun tare inda za ka zauna.Sudaida tad'anja tsaki tana mishi kallan
sama da k'asa yana cikin fararan kaya yayi shar dashi"Kuma wai haka zai zo hannu
rabbana"Yatsareta da idanun shi"ke yarinyar nan wai meye damuwarki da ni ne?
Yanunata da yatsa"za fa kisha na jaki,idan baki daina shiga harka ta ba.Ta turo
baki gaba"Indai aka k'i jininka ko ruwa kafad'a sai a ce ka tada k'ura,ni kad'ai
nayi magana?Ni kamayar marainiyar wayon ka ko?Tahaye gadan Hajiya tana k'unk'uni.
Hajiya tace"kai Julaibib yi tafiyar ka anjima sai kadawo muyi hirar mu cikin dad'in
rai,lokacin duk sun kama gabansu.Yayi murmushi yana kallan Sudaida data juya musu
baya.
Sudaida...
yakirata.Sai tamishi kunnan uwar shegu.Ke Sudaida ba kiranki nake yiba? Hajiya tasa
baki"yau na ji yarinya ba dake yake yiba?Shiruma amsace. Hajiya tashiga tafa
hannaye da sallallami.Yad'aga mata hannu"kyaleta Hajiya na jaki kawai zata sha.Eh
gwamma haka tunda abin nata tsiyane d'inkin ludayi.Yace"ke Asma'u d'auko min
bulalan can.Tana jin haka tafara"Ihu sai tajawo k'atan bargon Hajiya ta duk'unk'une
aciki.Yayi murmushi "k'aramar mara kunya kawai,fito a cikin bargon kika yadda zan
miki walmukalifatu "wallahi bazan fito ba.Yama Hajiya sallama sai bayan sallar
Isha'i zai dawo.
Suna hirarsu da Inna tasako mishi maganar A'isha.Yasunkwui da kai
tad'anyi murmushi dan ta san halinshi indai yayi haka to zaiyi wuya yayi
magana.Kaga kwantar da hankalin ka niba dole zan maka ba,munyi magana ta fahimta da
Musaddiq nima banga aibun taba shawara kawai nake ba ka, kanemi auran ta Insha-
ALLAH ba kome sai alheri amma fa karka takura kanka idan ba ka so,dan aure ba abin
wasa bane zamane da ake fatar yinshi har k'arshen numfashi.Yad'an shafa kwantaccen
bak'in gashin kanshi sannan yad'ago cikin natsuwa ya kalleta "nagode Inna ALLAH
yak'ara girma na kar6i shawararki da hannu biyu.Tayi murmushin jin dad'i "Ubangiji
yamaka albarka ya taimaki rayuwarka. Amin Innarmu.
Wannan makon ya so zuwa wajan A'isha to amma bai samu sarari ba
saboda sun gama TP(Teaching Practice)sun koma makaranta. Sai bayan makonni biyu
sannan yasamu yashirya ranar juma'a cikin shigarshi ta fararan kaya kanshi da farar
hula zita.Yana shiga lungun gidan yahango ya'yan gidan maza suna wasan Hockey.
Nasir abokin Abdul yana hangoshi yak'arasa wajanshi yana dariya yace
"Kawu" kamar yadda yaji Abdul yana fad'a "yau kaine a k'ofar gidanmu? Ko kazo
gaishe da Mamanmu ne?Yagyad'a kai"eh nazo gaisheta ne amma ba shiga zanyi ba ka
gaisheta zamuzo da Musaddiq na musamman mu gaisheta.Yayi tsallan murna"to zan fad'a
mata.Aisha tana ciki? Julaibib ya tambayeshi.Eh tana ciki inkira maka itane?
yagyad'a kai. Nasir yashige gida da gudunshi yana k'wala kiran sunanta.
Tayi mamaki tare da k'aryata Nasir.Nasir yafara rantse-rantse da
gaske ne yana k'ofar gida.Tarik'o hannunshi "To muje ai ba a k'arya kusa da
gida,amma na rantse da ALLAH idan ba shi bane?tayi kwafa wallahi ka san sauran"Eh
na yadda.Kanshi a k'asa kamar yana k'irga tsakuwan da suke yashe a wajan.Sai tasaki
hannun Nasir da yake mata dariya ai dama na fad'a miki,yajuya wajan wasansu.
Yaya Julaibib...
Tafurta sunan kamar tana cikin shakkar shi d'inne ko wani me kama dashine?Yad'ago
yad'an kalleta"na'am A'isha... Wani murmushi ya su6uce mata "ALLAH da gaske kaine a
k'ofar gidanmu? Lallai yau farar rana ce me kyakkyawar suna "Juma'a.A mutunce ta
gaishe shi,sai tayi shiru dan bata san abinda yakawo shiba.Shima shirun yayi na
wucewar wasu dak'ik'u.Yad'an sake kallanta "na zo gaishe kine,inafatar banyi laifi
ba?Tagirgiza kai"wani irin laifi? Gaskiya nagode da wannan ziyara ALLAH yabar
zumunci. Ina Yaya Musaddiq? Ya tafi Kaduna.Hirar tasu jefi-jefi,bai wani dad'e ba
yamata sallama yatafi.
Tabi bayanshi da kallo har yasha kwanar lungunsu ya bace ma ganinta
tana tsaye a wajan cikin mamakin ganinshi a k'ofar gidan su,kuma wai wajen ta yazo
dan sada zumunci, tasake juya kwalban turaren arabian perfume d'in daya
bata,tabud'e tashaki k'amshin me wani irin dad'i,bata zata za suyi magana irin na
yau ba,dan sunsha had'uwa ta gaisheshi amma sama-sama yake amsawa.Ashe dai Sudaida
gaskiya take fad'a mata,Yaya Julaibib fa yana da matuk'ar kirki,shi kawai baya san
a dameshine,kuma baya san magana da yawa. Tajuya zuwa cikin gida ba tare data kawo
kome a zuciyarta game da zuwan shiba.
Bayan Musaddiq yadawo suka tattauna. Musaddiq yakad'a kai"gaskiya da
ka sani kafad'a mata dalilin zuwanka"ai da zafi-zafi a kan daki k'arfe.Yagyad'a kai
na fahimceka nagode yamik'a mishi hannu sukayi musafaha.
Ranar juma'a data zagayo yaso kwarai yaje wajan A'isha d'an yafad'a
mata kome,to amma hakan shi bai tadda ruwa ba" dan sun fara jarabawa me zafin
gaske,ba wanda yakoma gida dan itace jarabawarsu tak'arshe a College Of Education
Gidan-Waya,sai kuma a zauna zaman girbe abinda aka shuka.ALLAH yaba me rabo sa a.
Lidiya tabita da kallo ita da d'akin, dan ta had'a k'aramin hazo ne
da hayak'in taban da take ta zuk'a, takalli Ash-tray d'in da take karkad'e tokar
guntayen taban data zuk'e,sai tazaro idanu da mad'aukakin mamaki,"Eh ta san Kasham
tana shan taba amma sai ran ta yayi mugun 6aci,kuma bai wuce tasha kara uku ba,amma
yau bata san ko kara nawa bane,tamatsa jikin taga tad'aga labulan tare da bud'e
gilasan,hayak'in da gauraye d'akin yafara raguwa.
Kasham...
Lidiya takirata,tad'ago tana kallan ta manyan idanunta masu maik'o sun kad'a jawaur
fuskarta har ta kumbura saboda kukan data sha bana wasa bane.
"Inzayadami Kasham?(Kaham me yafaru)
Shar...shar...wasu hawaye masu d'umi suka fara sintiri a kyakkyawar
fuskarta"Kasham...dasauri ta d'aga ma Lidiya hannu "Don't dusturb me!
Lidiya tagyad'a kai,tarungume hannayenta a k'irji tana
kallanta,Tabud'e dirowa tana dube-dubenta "oh no dammed it"ta dunk'ule hannu ta
naushi iska,da alama bata ga abinda take nema ba,takoma ta zauna tasake kunna taba,
tabi taban da kallo da tunanin yadda karan zai kare a zuk'a d'aya,takai baki tamata
wata irin zuk'a data kusa tafiya da numfashin ta,nan take kuma tari ya sark'afeta.
Tari tadinga yi kamar na shika, abin har yaba Lidiya tsoro ta kamo ta
suka fito waje dan tasha iska. K'irjinta yana mata wani irin suya,mak'ogwaranta ya
bushe k'amas kamar miyau bai ta6a bi ta wajan ba. Tad'ago a galabaice takalli
Lidiya" ruuwa.Lidiya tagyad'a kai"o barin siyo miki,tana k'ok'arin jinginar da ita
ajikin bango dan ta fara wata irin shakuwa abinda yadad'a rikitar da Lidiya kenan.
Hey...please come and help meee...!!!
Yadda akayi furucin cikin yanayin tashin hankali da tsoro yasashi
waiwayawa inda yajiyo sautin. Tasake yafito shi da hannu... Tabbasss ko su wanene
wad'ancan taimako suke nema sai yatafi wajen.Bai gane Kasham da Lidiya bane sai da
yakusa k'arasawa inda suke yaji Lidiya nafad'in ban san me yashiga kwakwalwarki da
zaki karar da karan taba a zuk'a d"aya ba, gashi nan za kije ki kashe kanki
abanza...wani irin abu yaji da yabi ilahirin jiki da zuciyarshi"Kasham kwance
wanwar a k'asa,farin wandan legging d'inta yayi dabbare-dabbare da k'asa...
Dan ALLAH ka taimake mu karta mutu,har lokacin tana dafe da k'irji
tana wani irin numfashi,gefe da gefen fuskarta busassun hawayen wahala ne,idanunta
suna rufewa da bud'ewa bak'i ciki yana 6acewa.
K'amshin arabian perfume d'in data shak'a yasa tad'ago dak'yar
takalleshi...sai tamik'a mishi hannunta na dama.Tausayinta yakamashi dan tana cikin
wani irin mawuyacin hali,wallahi mutum ba a bakin kome yake ba"Ubangiji👏kamana
kyakkyawan k'arshe.D'azu- d'azun nan yahango su,da yan course d'insu sunci kwalliya
mazansu da matansu suna ta hotuna suna hayaniyarsu ta dandazon d'alibai.
Sai da ya durk'usa sannan ya tabbatar lallai tabar tasha dan gaba
d'aya warin ta takeyi"me zan baki ne?Dak'yar tayi furucin"ru.rr... ruwa...yabud'e
ragowan ruwan swan d'in daya ke hannunshi.Ya waiwaya inda Lidiya take durk'ushe dan
ta taimaka mata ta tashi, amma bai ganta ba.Sai kawai yad'agata ta jingina da
bango, yamik'a mata ruwan.Saida tashanye shi duka sannan ta sauke gwauran
numfash."Sannu...Yace mata da yana yinshi na natsuwa"Kwallah suka cika
idanunta,inama inama ace sunyi aure ne yake bata wannan kulawar?Bata ta6a zatan
D'ansarai zai taimaketa idan ya ganta a mawuyacin yanayi ba,saboda halin-ko-inkulan
da yake nuna mata.
"Kasham...yakira sunan ta.Tad'ago tana mishi kallan k'auna me cike da
shauk'i,wallahi kasancewar su a tare,sai ta jita garas...kamar ba ita bace a
mawuyacin hali d'azu ba.
Haba Kasham kina mace me kima, amma ace kema kina k'arama sama hazo?
(shan taba) abin nan ya bani mamaki fa,ga ki da ilmi kina kuma ganin abinda su masu
yin tabar suke rubutawa ajikin kwalin"Mashaya taba suna iya mutuwa da
k'uruciyarsu"haba Kasham meye amfanin shan taba sigari ne?Kina sane da
"nicotine"gubar dake cikin taba ba karamin jazama hunhu matsala yakeyi ba.Dan
ALLAH... yahad'a tafukan hannayen shi 🙏alamar magiya kamar yadda take mishi "Ki
daina shan taba sigari dan babu kome a cikinshi sai illah.
Wata irin k'auna da soyayyarshi ta dad'a mamaye zuciyarta"Oh
God...ALLAH kamallaka min wannan bawa na ka.Tajijjiga kai "shikenan D'an Sarai
nagode,na kuma maka alkawari ko muna tare ko bama tare, na sha taba na k'arshe a
rayuwata,daga yau d'in nan na barta har abadan duniya.Yad'an saki fuska"yauwa
Kasham.Ungwai bu gangan(Kasham nagode sosai) dakika kar6i nasiha ta.Tad'an zaro
idanun ta"kaii dama kana jin yarenmu?Saita kyalkyale da dariya dai dai da dawowar
Lidiya da roban ruwa swan.Sai kuma tayi saroro cikin mad'aukakin mamaki "wannan me
shegen girman kan dama d'azu takira?Lallai hankali ke gani ba idanu gululuba.Shima
mik'ewa yayi bai sake magana ba yajuya yayi tafiyarshi.
Tadinga binshi da idanunta har sai da yayi nisa ya6ace ma ganinta
sannan tamik'e tsaye itama tana yar dariya,wallahi wani irin nishadi ta tsinci
kanta a ciki, takad'a kai" ALLAH dai yakai damo ga harawa ko bai ciba yayi
burgima.Dama duk tunanin rabuwa dashi ne yajaza mata 6acin ran daya sa ta dinga
k'arama sama hazo na rashin hayyaci.
Lidiya taja dogon tsaki "mahaukaciya kawai, ya gama zaginki ke kuma
kamar wata wawuya kina jin dad'i.Wani murmushin yasake su6uce mata"karki d'auki
alhaki dan D'ansarai bai ta6a zagina ba,bare kuma yau da yamin nasiha,na kuma
kar6eta da hannu biyu. Lidiya ta jefeta da ruwan swan d'in rubbish girl.Dasauri
tacafe ruwan tana dariya"kanki akeji Lidiya...
Haka nafi so an cema makaho je ka ka gani.
23 Rabi'a Thani 1441
20 December 2019
We Ibrahim's Daughters👇
Asdilat KD...2geda with Ra'ibs.
DANGIN NONO WRITERS ASSOCIATION
{Da Inganci Mukayi Fintinkau}
Bismillahi wabihi nasta'in
...GWAJIN DAFI💔
Almost true story
Daga alk'alamin🖊
Ya'yan Ibrahim
Saudat A.Baba (Asdilat KD)
Da
Bara'atu Ibrahim (Ra'ibs)
Shafi na bakwai.
Kasan mafarkin danayi daren jiya kuwa? Musaddiq yagirgiza kai.Wai
Julaibib ne da Kasham suke kiwon shanu a wani k'aton fili iya ganinka me cike da
koren ciyayi.Musaddiq yakyalkyale da dariya"D'ansarai fulani ka koma har matarka
take taya ka kiwo saboda tsabar k'auna?Musaddiq da Maimun d'in da yayi mafarkin
suka kalleshi yana zuba d'anyan na'a na'a, d'anyan citta da ya'yan algarib a ruwan
shayin da yake dafa musu,zuman da suke shan shayi ya k'are,sai yazuba sikari d'an
kad'an dan dukkansu basa san zak'i,yamaida murfin tukunyar yarufe,yayi kamar baiji
abinda suke fad'a ba.
"Julaibib.
Maimun yakirashi.Yajuyo da saurinshi yana amsawa"na'am.Bakaji abinda nafad'a bane?
Shiruma amsace.Yad'auki wasu kud'i a saman tebur yamik'a ma Musaddiq "Malam tashi
ka kar6o mana biredi.
Cikin natsuwa yake tafiya dawowar shi kenan daga gidansu A'isha amma
cikin rashin sa a yatarar wai sunyi tafiya,ya dai barma Nasir sallahu idan ta dawo
yazo yafad'a mishi.Sudaida tana hangoshi tafara murmushi dan ta kwana biyu bata
ganshiba,jiya da akace ya zo, taje ta gaisheshi bata jeba.
"Yaya D'ansarai sannu da zuwa...
Iskar data d'ibo tama bai kalla ba bare yasan ALLAH yayi ruwan tsiranta.Ita da
Sinan d'in daya ke shirin yimishi sallama suka bishi da kallo har yashige cikin
gidan.Sinan yakad'a kai"Julaibib sai a hankali.Suka gama hirar su sukayi sallama.
A D'akin-girki ta tarar da Mama.Mama tace yauwa d'auki abincin nan ki
kaima D'ansarai.Haushinshi takeji ta turo baki gaba"Mama shi yace miki yana jin
yunwa?Mama tabita da kallan mamaki,sannan tamata dak'uwa gidan ku"Sai yace yana jin
yunwa za a bashi abinci a gidan nan?ke wace irin yarinyace?Jiyama danace kiji ki
gaisheshi ashe ko bakije ba,saida zai tafi yake tambayar ki sai Sagir ne yace kina
d'akinku kin kulle k'ofa.Sa an kine D'ansarai? Tad'auki abincin tabar Mama na mata
addu'ar shiriya.Dak'yar tayi sallama dan tasan idan ma bata yiba,sai ya korata ta
yishi.Ko kallanta bai yiba har ta ajiye abincin tajuya.
Umma tashigo D'akin- shak'atawar dan lokacin da yashigo tana
sallar.Yagaisheta cikin girmamawa.Tayi murmushi"D'an Sarai yaro ne me hankali,
yasan ya kamata sosai"Karatu ya k'are sai jiran sakamako ko?To Ubangiji yabada
abinda ake nema.Yad'an shafa kwantaccen bak'in gashin kanshi."amin ya rabbi Umma".
Tamik'e to bakaci abincin ba?Yakalli kwanon abincin"ai ni ban san ni takawo ma
ba,dan a jiyewa tayi tafita.Kai kawai tagyad'a tafita.
Tana cin na ta abincin Umma tasa meta batace kome ba hannunta kawai ta
damk'o,rik'on data matane yasa tasan cewa lallai bana wasa bane"Umma me nayi?Bakiyi
kome ba ko?Sai tafara tirjewa dan wallahi idan ta yadda Umma takaita d'akinta to na
jaki zata sha ba kad'an ba dan Umma ba sauk'i,shi yasama ba ta wani wasa dasu
akwaita da zafi,sam ba ta d'aukar rashin kunya shi yasa kowa yake shakkarta a
gidan,yana yinsu ba d'aya bane da Mama,da wasu lokutan suke maida ita kamar wata
kakarsu,sai tazo ta tsawatar musu suke daina wani abun.
Umma dan girman ALLAH kiyi hak'uri na tuba nabi ALLAH na biki,kiyi
ha...saukan marin yasa sauran kalaman suka mak'ale. Idanunta suka ciko da k'wallan
wuya, dan marin ya ratsata yadda yakamata.Tasa ihu Mama dan girman ALLANMU zo ki
ceceni,wayyo ALLAH! Ke...!Umma tace tana kallanta cikin zaro idanu "rufemin baki ke
mara kunya ko?Ai ina jinku da Mama a D'akin-girki..Umma dan darajar Annabi
Muhammadu kiyi hak'uri.... Mama wai kina inane?!
Mama tak'araso wajan da saurinta"a ah to me tamiki kuma?Ni tama laifi
dama jira nake Musaddiq yashigo in fad'a mishi.Sudaida kuka takeyi da gaskiyar ta
ita dai aba Umma hak'uri dan idan ba itace da bakin ta,tace ta hak'ura ba to lallai
sai tayi dukan nan ko kuma ta had'a ka da Adnan shima kwallan shege a wajan iya ba
da na jaki.Mama takan cemishi "Sarki zalimu dan dai ba ya'yanka bane,baka san zafin
suba shi yasa kake musu wannan dukan na rashin tausayi.Sai yayi dariya "ai ko su
d'in ne haka zan musu indai sukace baza su bi abinda zan fad'a musu ba
wallahi.Dak'yar takwace Sudaida a hannun Umma.Sudaida tace" nagode"to amma Mama
kibata hak'uri.Tagyad'a kai"ai zata hak'ura ne.Umma tace"na rantse da girman ALLAH
zan hak'ura ne kawai idan taje takaima D'ansarai ruwan sha,tamatsa da abincin
gabanshi, takuma gaisheshi tabashi hak'urin dangwarar da abincin da akace takai
mishi.Idan ba haka ba tayi d'as d'as d'as da yan yatsunta ta shige d'aki.
Duk yadda taso dakewa idan zata shiga d'akin abin yaci tura.Cikin kuka
tayi sallama.Yad'ago yana kallanta ta ajiye ruwan ta d'auko abincin,wani haushinshi
yacika mata zuciya saboda shi aka so a bata na jaki,da Mama ba tanan a yadda ran
Umma ya6aci ba k'aramar wahala zata shaba,shi ba a ganin abinda yakema mutane na
halin-ko-inkula sai ita?Dak'yar tace"Ina wuni...wani sabon kuka ya kufce mata wai
har hak'uri sai tabashi? Yaya...kayi hak'uri... tausayinta yaka mashi koma menene
yasan Umma ce ta sata wannan ban hak'urin.Nayi hak'uri Sudaida ai dama baki min
kome ba,to zuba min abincin kad'an, tadauki faranti tazuba ta mik'a mishi.Yayi
bismillah yafara ci.
Kafanchan ne garin dasu A'isha suka tafi. Babban gidane a Magiya
Street me sassa guda bakwai sai dai a kulle suke da kwad'o saboda mutanan ciki
ma'aikatane a garuruwa mabambanta,idan ana sha'ani ko sun samu hutun aikine za kaga
gidan ya cika da jama'a. Sashin Kaka dana kusa da itane kawai koda yaushe a bud'e
jama'a na kai kawo.
Gidan yayi shiru saboda sauran yaran gidan sun tafi makaranta sai
kukan tsuntsaye da suke ta shawaginsu."Hantsi ya dubi ludayi rana ta haska ko'ina.
Hashim bacci yake so yayi amma wani nishad'd'd'an al'amari ya hanashi sak'at bare
yabarshi yarintsa.
"Aishahhh...
Yafurta sunan a zuci sannan yabud'e idanunshi cikin agogon dake manne
a bangon d'akin "goma da rabi na safiya.
Sai yamik'e, sashin Kaka yanufa Alhamdulillahi"yafad'a daya fara jiyo
dariyar ta, hira sukeyi da Kaka.Yayi sallama sannan yad'aga labulan dak'in,caraf
idanunsu yahad'u tace"Hum manya gatan wasa,akwana a hantse... Kaka ta 6alli goronta
tajefa a baki sannan ta d'an harareshi"to kar dai kanka yayi girma dan tace haka.
Yak'arasa shiga yazauna a d'aya kujerar suna fuskantar juna da A'isha.Shi dai
A'isha tana burgeshi baya gajiya da kallanta da duk wani abu data keyi.Yamaida
kallanshi ga Kaka saboda me kikace kar kaina yayi girma?Tace naga dai wannan
kirarin kyawawa akema. Aisha tasa baki "yanzu Hashim yana da makusa neKaka?Aiko
makaho yashafa wannan k'ayatacciyar fuskar zaice me kyauce. Yad'an motsa kafad'a"Ah
to gane min hanya...wai yaushane tafiyar taki?Tawatsa hannaye"ganinan dai, amma ba
wani dad'ewa zanyi ba, tare dasu Mama zamu tafi,kasan har yanzu bamuyi hutu ba,
amma da zamana zanyi wallahi garin bai ishe niba.
Yagyara zama"Shikenan sai a miki babban gida kawai yadda zai dad'a
burgeki,kidinga jin dad'in zama.Cikin rashin fahimta tayi yar dariya "Kaji Hashim
fa babban gida sai kace wacce zata dawo da zamanta gaba d'aya? Yagyada kai"To
menene A'isha dan kin dawo gaba d'aya? Ai kamar ba matsala bace garin da kike so
ne,ga kuma mutanan da kike so.
Yakalli Kaka da take ta cin goronta "Ke dai kamar mayya haka kike da
goro.Eh koma dai mecece ni ba daina ci zanyi ba ko kai kake siyomin?Ya yamutsa
fuska"To da wacce hujjar nasara zaiyi hawan k'aho? Tamishi dak'uwa idan baka siyo
ba ai ubanka zai siyo.Shi da Aisha suka d'aure fuska wai su an ta6a musu Iyaye.
Hashim yace"a ah Kaka wasa kar yayi wasa a tsikari uwar miji fa.A'isha tagyad'a
kai"gaskiya ne dan uba baifi uba ba "Kaka tafara tafa hannaye cikin sallallami.Sai
suka kyalkyale da dariya.Ba shakka wuyanku ya isa yanka. Tad'auko carbi zata
shaud'ama A'isha ALLAH yabata sa a tayi tsalle gefe"Tabbb yanzu dan ALLAH sai ki
shaud'amin wannan k'irgin carbin na ki me siffar rodi?To dawo ki gani
mana.Tagirgiza kai"a ah wallahi ai sai in kwanta jinya, suka gama mata shak'iyanci
san ransu sannan suka fara hirar arzik'i.
Hashim yadad'a gyara zama sannan yakalli Kaka cikin natsuwa"Kaka
gaskiyar magana nifa A'isha nake so ba wani 6oye-6oye dama karatune yahanani sak'at
to yanzu kam sai dai godiyar Ubangiji an gama har kuma an samu abun yi basai
maganar iyaliba? Kaka tad'aga hannayenta sama tanama ALLAH godiya"Ashe tuntuni
dakake fad'in Aisha ce matarka na d'auka na k'uruciyane nan gaba idan aka maka
zance za kayi tawaye?To masha-ALLAH,ALLAH yasanya alheri,naji dad'in wannan
al'amari,dakan d'aka shik'an d'aka tankad'en bakin gado.
Hashim yayi yar dariya"Aiko dai ba wani tawaye da zanyi yakalli Aisha
ta sunkwui da kai amma labarin zuciya a tambayi fuska murmushi takeyi.Kaka tamik'e
zata shaud'a mata carbin"Munafuka ana zance auranta ta nemi waje ta zauna saboda
rashin kunya irin na ya'yan yau.Tashige d'akin baccin Kaka da gudu dan wallahi
bata manta dukan carbin Kaka ba akwai mugun zafi.
Hashim yayi murmushi Kakarmu ta kanmu ALLAH dai yabamu i taku.tsufa me
amfani acikin hayyaci da tunani.To Amin Hashimu,amma ba abinda yake kawo tsufa me
kyau me amfani sai aikin k'warai lokacin k'uruciya"tsohon banza daga yaran banza
yafara"kurik'e karatun"Alqur'ani da sauran kyawawan dabi'u da halaye, kuyi gaskiya
da adalci a kome,idan kuka d'ore a haka Insha-ALLAH babu ta6ewa a rayuwarku.
IImi shine jigon rayuwa,shine abinda yake gyara d'an Adam,yagayara
tunaninshi dan haka ku kara zage dantse da kwazo wajan nemanshi,Ilmi ko wani irine
to yanada amfaninshi. ALLAH yama rayuwarku albarka. Amin Kaka.
Hashim da A'sha sai rawar kai sukeyi kamar k'adangaran gobara,daga
ranar yakoma cin abincin darenshi a d'akin Kaka abinda da ba yayi sai can nisan
dare sannan yake tafiya na shi d'akin wani lokacinma Kaka ce take korarshi yatafi
yabasu waje za su kwanta. Kafin su A'isha subar garin Kafanchan sai da aka tsaida
magana tana gama makarantar secondary za ayi bikinsu ba wata matsala da aka samu
kasancewar su Ya'ya mazane kuma duk Kakace ta haifi Iyayan nasu. Shi kuma nan da
nan yafara aikin ginin gidanshi a Zaria Street.
Kasham tana shafa ma faratanta jan farce (nail polish)ruwan
k'asa,Baranzan yashigo cikin kakin soja. Suka kalli juna na wucewar wasu
dak'ik'u."Beauty ina kikaje tun d'azu nake ta jiranki?Kamar ba da ita yake magana
ba,zuwan can kuma bayan ta shak'i iska ta baki ta hanci sannan tace kasuwa naje
siyo wannnan tanuna mishi nail polish d'in.Yazauna"anjima zani Jos amma kwanaki uku
zanyi,to na baki time kafin indawo ki shirya kayanki zamu wuce barrack.
Barrack kuma?Ta tambayeshi cikin mamaki"Eh barrack kin gama
makaranta to zaman me za kiyi?Mutafi kafin lokacin auran mu yayi nafa gaji da zama
ni kad'ai kingane ko?Bai jira amsawarta yajuya yayi tafiyarshi.Tabi bayanshi da
harara lallai za ayita dan wallahi tayi rantsuwa ba wanda zata sake bi har takwana
dashi indai ba D'ansarai ba,bata ga kuma wanda ya isa sata canja wannan ra'ayi na
taba har abadan duniya.Ita ya ma sosa mata inda yake mata k'aik'ayine,cikin gari za
taje wajan Julaibib ta kwana biyu bata ganshi azahiran ceba amma kullum dashi take
kwana dashi take tashi a cikin zuciyarta.
Tacanja kayan jikinta da dogon buje na velvet bak'i sai rigar shirt
checker me d'amewa ta yafa siririn bak'in mayafi a gyararren gashinta data mishi
ponytail style,jaka da takalmanta masu tudu bak'ak'e,tasa wasu manyan d'ankunne
masu kama da awarwaro suma bakak'e sai siririyar sark'ar rosery a wuyanta.
Kai tsaye tashiga shagon.Abdul yana zaune yana aikin gida da aka
had'osu dashi daga makaranta a darasin tattali (Economics) tak'arema shagon kallo
ya dad'a cika ba kamar kwanakin baya ba, za taso taga irin canjawar da D'ansarai
yayi.Tadawo da kallanta ga Abdul "Kai d'an samari ina Julaibib d'in? Fuska a had'e
ya amsa "Baya nan.Haushi take bashi ita ba wani abu za ta siyaba amma sai tazo tana
damun mutane yad'anyi k'unk'uninshi.
Taja kujera tazauna tana mishi kallan nazari,wani murmushi ya su6uce
mata "wai shima k'arami dashi ya iya had'e girar sama data k'asa,tana so ta mishi
wasu tambayoyi game da Julaibib amma ta san ko tayi a banza talaka ya girmi sarki
bazai bata amsaba"Kai k'aninshine? Uhh yace batare daya bud'e bakiba. "Ina Sudaida?
Ya yamutsa fuska shifa baya san adameshi, dak'yar kamar me ciwon baki yace "Ta tafi
makarantar allo.Bata sake tambayar shi kome ba ta dai gane wannan halin nasu na
rashin san magana a jinin sune.Itama sai ta bud'e Ovation d'in hannunta tana
dubawa amma rabin tunaninta na ga Julaibib da inda yatafi.
Da d'an hanzarin shi yashigo shagon tare da sallama dan ya san lokacin
makarantar allo yayi ba ya so Abdul ya makara.Caraf idanunsu yahad'u"La'ila
ha'illah anta subhanaka inni kuntu minazzalimin"tabbas da bata ganshi ba komawa
zaiyi.Tamik'e tsaye tana mishi kallan k'auna me ciki da shauk'i " Yayi shar dashi
cikin fararan kaya kanshi da bakar hula dara takalmanshi sau ciki farare,k'amshin
arabi'an perfume d'inshi ya mamaye shagon,D'ansarai d'an gayu ne,me tsabta na gaban
kwatance dan ba wanda zai juri sa fararan kaya sai ma'abocin tsabta.Idanunsu yakuma
had'uwa...sai sukaji wani irin yanayi a ilahirin gangar jiki da zuciyarsu,da sauri
yakauda kai yana Isti'aza.
"My enigma ma You're wellcome.. Julaibib bazan gaji ba ga shi na sake
biyo ka,wallahi ba saboda kowa nashigo cikin gari da safen nan ba sai dan kai.Abdul
yad'auki allanshi "Kawu na tafi.To Abdul ALLAH yabada sa a. Yara6a ta gefensu
yawuce yana amsawa da"amin ya rabbi.
"Julai...yatari numfashinta"Kiyi hak'uri bazan ta6a miki k'arya wai dan
kiji dad'i ba,bazan iya auran kiba, kiyi hak'uri dan girman...k''iris ya rage ta
rungumeshi yayi taku biyu baya da sauri sai ta biyoshi har yafita a shagon yajuya
da sauri yacigaba da tafiya.Tabishi da kallo har yasha kwana ya6ace ma ganinta.
Damme what an enigma man.Tafurta tana furzar da hucin takaicin,ta rik'e
k'ugu tana kallan shagon"Ya tafi yabar mata shagon duk da kayan mak'udan kud'in da
suke dank'are a ciki amma ko a jikin shi, wai an yak'ushi bishiya"shi D'an Sarai ta
rasa me yasa yakeyi kamar yana jin tsoronta a wasu lokutan? Ba saurayin data ta6a
yi da baiyi kwad'ayinta ya nuna maitarshi a fili ba sai shi, To me yasa!!!???
Yanzu duk abinda yamata za ta iya d'auka ko? Sai kuma ta girgiza
kai"Aiko ba kayan Julaibib bane baza ta iya d'aukaba tunda ba na ta bane,idan tayi
haka ai tazama 6arauniya"which is forbiden".Taja kujera tazauna dan bazata tafi
tabar mishi shago a bud'e ba tunda ita tasashi tafiya,da batayi yunk'urin rungume
shiba ta san zai tsaya.
Aminu ne yashawo kwanar yana rik'e da bokitin fenti da roller daga wajan
neman halali yafito. Tamik'e da sauri tana fad'in"yauwa dan ALLAH Aminu ka
taimakeni kajirama D'ansarai shago yaje gidane ni kuma sauri nake yi ban san abinda
ya tsaya yiba.Ya ajiye kayan aikinshi aciki yajawo buta ba matsala.Sukayi
sallama.Yayi alwala ya gabatar da sallar walha da aiki yanashi yi a dai-dai lokacin
daya sabayi da zarar rana ta 6ullo.Shima gajiya yayi da jiran dawowarshi yaduba
mukulli ya kulle shagon, a gajiye yake yaci aikine kamar ba gobe,yanzu zai je gida
ya huta,gaskiya neman halali da wuya kowa kagani a inuwa to ba shakka ya sha rana.
Tunda yakoma gida yarasa sukuni wani abu a can k'ark'ashi zuciyarshi
yana damunshi,shi dai yasan Kasham tana san shi da gaske, to amma ya rasa gane
fargabar da take mamaye zuciyarshi game da ita.Ga wasu irin rikitattun mafarkai da
yakeyi,ya rasa gane ma'anarsu,sai dai shi har kullum yana mik'a al'amuranshi a
wajan ALLAH,yana yawaita sadaka.
Da daddare suna zaune a tsakar gida ita kanta Inna ta lura dashi,
abincin ma k'adan yaci dan yasan Inna tana saurin gane yanayin shi da bazai ci ba
dan cikinshi a cunkushe yake."Autana yau dai ko baka jin dad'ine?Yabud'e idanun shi
daya rufesu kamar me bacci sun d'an canja kala"Inna kai nane naji yana d'an
saramin.Tamishi kallan tausayi me cike da soyayya irin ta d'a da mahaifi"wayyo!
Sannu...ai na ganka yau ba wata walwala,ya kamata kasha magani,ALLAH yasauwak'e.
Yagyad'a kai "Amin Inna, ai nasha magani".
Alhaji Abdullahi ne yashigo da sallama Julaibib yakar6i kayan hannunshi
"Sannu da zuwa Baba" Yauwa D'ansarai mun wuni lafiya? Yau ka rigani dawowa. Yazauna
yana hutawa.Inna tad'auko mishi abinci tana mishi nata sannu da zuwan.Ya amsa da
kulawa.Yafito da kaya d'inkakku kala biyar dukkansu farare yana nuna ma Inna.To har
anyi d'inkin ne? Amma sunyi kyau madalla Ubangiji yasa rai aka yiwa.Ya amsa da amin
yana kallan Julaibib"Ina alfahari dakai D'an Sarai tunda kana san ganin tsohonka ya
fi na kowa,amma ni gaskiya nan gaba kar a sake d'in kamin kaya duka kala d'aya yo
wannan idan hira nake zuwa ai sai budurwar tawa tace min d'an anace,wanke
kamayar,itafa bazata gane cewa kullum wani sabo nake sawaba.Julaibib Yad'an shafa
kwantaccen bakin gashin kanshi "kai Baba wani irin zuwa hira kuma,yanzu sai kama
Inna kishiya?A ah kaji D'ansarai da wata magana fa, ba a aurowa aka auro ta?Inna
tana yunk'urawa za ta tashi yafara dariya"Dakata mana ina za ki?Ko sauraran shi
bata yiba"kanka akeji...yad'an daga murya"zo mana Maimunatu...tashige d'aki.Alhaji
Abdullahi yakad'a kai "Uh uh uh mata duk haka suke da kishi ba babba ba yarinya,ka
ganta nan tunda k'uruciya indai zanyi maganar k'arin aure to zata tashi tabarmin
wajen.Julaibib ya sunkwui da kai dan maganar ta mishi nauyi.
Yasake kallan Julaibaib sannan yanuna shi da yatsa "Ita mace dad'in
mu'amala ne da ita amma sai ka fahimci halinta,ka kuma sauke duk wani nauyi na ta
daya ke kanka,to sai kaga ALLAH yahore maka ita kaji dad'in zama da ita,ai ka sani
dai-dai da tsinken da zatayi sakacen naman da ka siyo mata idan tagama ci kai zaka
kawoshi ko?Yagyada kai "Eh Baba na sani".
Yace to mace yar gatace gaba da bayanta, kar kayi la'akari da kome yayin
da zaka mata kome face cewa aure bautar Ubangijine, shid'in ne yace haka za a mata
bad'an kome na taba.Kuma babban jigon zaman aure shine HAK'URI za kayi hak'uri da
ita a wajan gazawar ta irinta yar Adam,kaima za tayi hak'uri dakai a wajan gazawar
ka irin na d'an Adam,dan babu wani mutum a doron duniya da yake cikakken da bashi
da nak'asu sai Annabinmu Muhammad sallallahu alaihi wa ahlihi wasallam.Dan haka sai
ana kauda kai ana yafiya,dan wasu lokutan idan suka kwafsa maka sai kaji kamar ka
karairayasu,kashafe su a doron duniya,to amma hakan bazai yiwuba dan namiji ne yake
cika mace,macece take cika namiji,taimakeke niyace atsakanin juna.
Kadinga tuna cewa tunaninka da nata ba d'aya bane,ko a gidan fiyayyan
halitta za6abban za6abbuma sun nuna irin halin nasu,kuma hakan shine cikar macen
taka,haka ALLAH yaga damar halittarsu. Yagyad'a kai cikin ladabi" To Baba nagode.
Maza dangin gurjiya sai an fasa ake sanin me k'waya.
25 Rabi'a Thani 1441
22 December 2019
We Ibrahim's Daughters👇
Asdilat KD...2geda with Ra'ibs
DANGIN NONO WRITERS ASSOCIATION
{Da Inganci Mukayi Fintinkau}
Bismillahi wabihi nasta'in
...GWAJIN DAFI💔
Almost true story
Daga alk'alamin🖊
Ya'yan Ibrahim
Saudat A.Baba (Asdilat KD)
Da
Bara'atu Ibrahim (Ra'ibs)
Shafi na takwas.
Baranzan yashigo gidan da d'okin ganinta, yanata k'wala mata kira
amma shiru bata amsaba. Yashiga d'akin da niyyar tashinta dan ya san bacci ne kawai
zai hanata amsa kiranshi da kuma fitowa ta mishi Oyoyo cikin d'okin ganinshi
itama.Yaja yatsaya da mad'aukakin mamaki yana kallanta,tana zaune kwalliya take
fuskarta,yanuna ta da yatsa"au dama kina jina amma kika ki amsawa?Wai lafiya kuwa?
Yabita da kallan nazari cike da shakka.
"Beauty wai lafiya kuwa?
Tafurzar da hucin takaici sannan tace"da wannan kiran irin na yan
farauta zan amsa maka?Tacigaba da zizara ma girarta jagira"ni gaskiya bana san
rashin natsuwa.Yayi saroro kawai yana kallanta tagama kwalliyarta tajawo kayanta
tana sawa bujen jeans ruwan bula da d'amammiyar riga mara hannu ruwan madara, yau
tayi k'ananan kitson kalaba ta tubkeshi da ribbon ruwan madara sai d'an kunnan
beads ruwan bula data sa,wallahi tayi kyau k'irar kalangunta ya fito rad'am,ta
sunkuya tana sa takalmi ruwan madara sau ciki me tudu,tagama sawa tamik'e tsaye
tana saba jakarta a kafad'a kalar takalmanta ruwan madara,tana shirin fita yakirata
"Beauty...Taja ta tsaya sannan tajuyo fuska a yamutse take mishi wani kallan uku
ahu"wani abune?Kamar yaya wani abune?Tad'aga misho hannu"kaga malam ya za muyi
canjan tambaya ba amsa?Ni fa wallahi sauri nake yi idan ba ka da abin cewa...Yayi
murmshi dan wannan kwalliyar ta tsumashi.
"Kurum Ishshi Bazinzira(Akwai kud'i sosai, na rantse miki da ALLAH)
Yanuna mata aljihunshi yaushe kike so muje Kasham Hotel muci ubansu?
Da kud'i da maciji maganinsu kisa"sai yamik'a mata abinda ya nannad'e a warraping
sheet.kallanshi tayi kamar bata gane abinda yake nufi.Yagyada kai "yes take it's
yours...ta d'auke kai daga kallan da yake mata,ta san Champagne ne,to ita da ne zai
bata Champagne taji ya burgeta ya mata gwaninta, cikin jin fushi tace" baa na
so.Kamar ya bakya so? Mutumin na ki nefa?Tagalla mishi harara"so bloody what?To
hell with it.Ba na sha,bazan k'ara sha ba,dan haka karka k'ara kawo min.Beauty...
tad'auki agogonta na fata tana d'aurawa kana da lokacin 6atawa amma ba da Kasham
ba,tayi tafiyarta.Yayi murmushi yakai d'aki ya ajiye mata, ya san za ta sha yanzu
dai ranta a 6ace ne, ko me yasame ta haka oho yad'an motsa kafad'a shima yajuya.
A waje suka had'u da Lidiya yake fad'a mata abubuwan da Beauty take
mishi sunyi yawa fa,she bai gane me yashiga k'wak'walwar taba.Takad'a kai cikin
takaici "Ranar wanka ba a 6oye cibi...dan haka ta k'yank'yasa mishi abinda ke
faruwa. Yajijjiga kai "lallai biri yayi kama da mutum"To yanzu kina nufin cikin
gari ta tafi wajan shi?Ko shakka babu,abin takaicin kuma nama na jan kare sai
shishshigi da k'wala kai a faranti amma ba kwarjini.
Oh damme.Yadunk'ule hannu ya naushi iska ran maza ya 6aci, allurar soja
ta motsa.Ya kalli Lidiya za muyi magana anjima? Tagyad'a kai "shikenan.
Yashiga mota ya zauna yana sauraran wakar"Who let the dogs out..ya
kunna taba yana zuk'a, amma zuciyarshi k'ara tafarfasa take yi idan ya tuna duk
abinda Beauty take mishi wai saboda wani filthy stupid bahaushe d'an cikin gari
ne.Yadinga tuna beautiful life d'in da sukayi,suna matukar son juna,kuma Beauty
kome na ta daban ne,musamman shi da take son shi tana bashi kome da yake so cikin
dad'in rai,bayan alakoro har gyara take k'ara mishi.Wata soyayyarta ta dad'a
tsumashi sai kawai yaja motar dama cikin gari za shi yabiya kud'in k'ofafin da yace
a mishi na dank'areren gidan da yake gina ma Beauty ita da kids d'in da za ta haifa
mishi.
Yana tsaye a Mak'era suna magana da me aikin k'ofofin kawai ya hango
ta goye a bayan wani me mashin sunata dariya. Ranshi in yayi dubi ya 6aci zuciyar
shi ta raya mishi wannan ne tsinannan bahaushen da take bi cikin gari,sun gama
abinda za suyi yanzu kuma zai maida ita gida.Lallai yau za a yi ta sai yashige mota
yabi bayansu sai dai kash... Kafin yak'arasa har me mashin d'in ya sauketa ya k'ara
gaba dan Samaru zai wuce shi yasa Baranzan bai ganshi ba.
A tsakar gida yasame ta, ta d'ora k'afa d'aya akan d'aya tana cin
k'osan rogo tana wata yatsina kamar dole a ka mata sai ta ci.
Beauty daga ina kike?Yayi tambayar cikin d'aga murya da tashin
hankali.Itafa Baranzan ko k'aunar ganinshi ba tayi dan haka tajuyo cikin jin
haushin tambayar da wanda yayi ta"daga Inda ka aikeni mana. yanuna ta da yatsa"ke!
kar ki min rashin kunya fa, manufuka kawai,ba daga wajan tsinannan bahaushen nan
kike ba?Tayi lallausan murmushin tura haushi "Thank God tunda ma ka sani,wani abu
ne? Tamishi tambayar cikin wani malalacin kallo sannan tacigaba da cin k'osan rogon
ta hankali kwance tana wakar "Hail Mary mother of Jesus.
Bazato taji saukan mari hagu da dama yafara zaginta ta uwa ta uba ya
kaima k'osan kutifo ya tarwatse a tsakar gidan, hannayenta dafe da kuncinta
idanunta sun kad'a jawur suna fitar da hawayen azaba. Hakan bai mishi ba kawai yasa
hannu ya zaro belt d'in daya d'aure k'ugunshi yadinga labtarta har sai da ya
tsistsinke ya jefar yana huci"ke dan abu kazan uban ki har kin isa kiyi soyayya da
wani bayan munyi alk'awarin aure dake?Ina raye da raina da lafiya ta?Bazinzira (na
rantse da ALLAH)idan kika kuma zuwa wajanshi abinda zan miki sai yafi wannan
stupid,rubbish girl.Yagaji dan kanshi yayi shiru yajuya zai bar gidan.Dak'yar
tamik'e dan ma zuciyarta ta bushene amma yadda tasha na jakin nan ai ko d'aga yatsa
baza ta iyaba,tasha gabanshi"har ka gama kenan?Tagyada kai tare da had'e tafukan
hannayenta.
"Ungwai bu gan gang (Nagode sosai)
Amma ka sani daga yau,yanzu d'in nan na gama soyayya da kai "I
jilt"har abadan duniya.Wani kuka ya kufce mata amma bakinta bai mutuba, cikin kukan
tanuna mishi d'akin ta shiga ka kwashe kayan sawanka da duk wani abu daka san na
kane kabar mana gida.
Jikinshi yayi sanyi"wai an jefi kaza da gishiri"bai ta6a tunanin haka
ba"haba Beauty yayi d'an murmushi "It sound phony,to ma me yayi zafi ne da har
idanu za suci wuta haka? Me yayi zafi? Ta tambayeshi cikin tashin Hankali. To meye
ma bai tafasa har ya k'one ba bare wani zafi? Bana son ka Baranzan, kuma ko ban
auri D'an Sarai ba kai dai na gama soyayyah dakai,tad'aga murya cikin kuka haka ake
soyayyah?Haka ake nuna soyayyah? Kai baka iya kome ba sai duka? Julaibib ya nuna
baya so na kai har yagaji yafad'a min inyi hak'uri shi dai bazai aure ni ba, yana
nuna ina damunshi,duk abinda nake mishi baya so d'in amma dai-dai da rana d'aya bai
ta6a d'aga hannun shi yace zai mareni ba sai kai,tanuna shi da yatsa sai kai me
ik'irarin kana so na, kana so muyi aure in haifa maka Ya'ya,a haka ne zamu zauna
zaman auran for better for worst till death due part us?
Dukan da kamin ko Mamana da take da zafi bata ta6a min irin shiba
tunda takawo ni doron duniya, tacire rigar ta,ta jefar tana nuna mishi wani k'aton
tabo a kafad'arta"wannan ma tabon dukan kane wanda yariga ya zauna kenan har abadan
duniya,kalli yadda ka farfasa min jiki?Tasake fashewa da kuka me cin rai,na rantse
da ALLAH ta dankwali k'asa a d'an yatsanta ta la sa,na barka har abada kamar yadda
na bar nonon uwata.Kai Baka da hankali baka san yadda zaka sace zuciyar mace ba,
abinda ka iya shine ka kama mace ka yita duka kamar ka kama 6arawon da yayi fashi
da makami da kakin soja a jikinshi da bindiga a hannunshi,wallahi ba ka iya kome
ba,kaje ka koyo,sai kuma takoma sambatu Julaibib ya iya tafiya ta natsuwa,baya san
hayaniya shi shigar shi kullum ta fararan kayane,ai kaima kasan ba me jure sa
fararan kaya sai me tsabta na gaban kwatance"he is a gentle melanin beauty that I
have never meet before.
Yarik'o ta kiyi hak'uri Beauty raina ne ya6aci zuciyata tana ta
tafarfasa abinda yakaini ga zagi da dukanki kenan, na ka sa danne temper na amma ai
kinsan ina sanki, zai rugumeta tayi wani ihu ta k'wace da k'arfin bala'i"tamishi
kallan uku ahu"ALLAH sarki ai ban san haka zuciyar ta ka tayi ba,da dai naga tiriri
yana fitowa ta kirjin kane to da na yadda, taja dogon tsaki "kai koma menene da
menene wallahi ba wajan kuka na bane mutuwar uwar kishiya,ai kome yazo k'arshe.The
game is over. sunan wata wak'a.
Yajuya yayi tafiyarshi ai yasan tashi da Beauty bata 6aci sau nawa
suna fad'a kuma su dawo su d'inke kamar wani abu bai faruba.Ran tane kawai ya6aci
amma da zarar ta huce za su daidaita..
Bai koma gidan ba sai kwanciyar bacci sunje Kasham Hotel Kafanchan
sunyi holewarsu da yan mata,yayi tatil da uwar laifi(giya) tamik'e da sauri dan
saura kad'an yafad'o a jikinta,Itama ta kasa bacci ne dan gaba d'aya jikinta ya
mata tsami dan ma an mata allura tasha magunguna,dak'yar ta canja kayan baccin ta
da wando jeans da bakar rigar sanyi me hula tazuba k'ananan abubuwan da zata
buk'ata a jaka tabar d'akin tana surutai"ai kin banza talaka ya girmi sarki idan ma
kayi aman ka kai zakata gyara d'akin gobe da safe.
Yana tashi yaja doguwar hamma baki a bud'e yana mik'a tare da
addu'ar"Our father who is in heaven,I love you thy name...bai k'arasa ba ganin ba
Kasham kwance a gefe kamar yadda suka saba,yafito tsakar gida suka gaisawa da
Babanta sannan ya tambaye shi " Ina Beauty ne? Baban yace wai ba ta d'akin? Eh bata
cikin.To bata kwana a gida ba ko kuma yanzu tafita.Kai yaushe kashigo?Baranzan yasa
ke yin hamma"ba a gidan ta kwana ba ke nan, dan a d'akin nakwana yanzu natashi daga
bacci,Baba barinje gida in dawo.To Baranzan a dawo lafiya(Oh🤔 mu Ya'yan Ibrahim
ALLAH d'aya gari bamban.Abin da mamaki wai talaka da mata hud'u harda k'wark'wara
amma me gari gwauro)
Sai yamma lik'is rana ta tafi tana shirin fad'uwa sannan Kasham ta
koma gida,tafara masifa ganin bai d'auki ko tsinken sakacen shiba, a fusace tafara
watso duk wani abu na shi tsakar gida ai na fad'a maka"I jilt.. Is over,Is totally
over...na rantse da ALLAH zan mishi rashin mutuncin da har ya mutu bazai manta dani
ba. Babanta yafito daga d'aki yana kallanta da kayan da take watsowa tsakar gida da
mad'aukakin mammaki "Kasham me ya ta6a k'wak'walwarki haka?Ya za ki dinga watso
mishi kaya tsakar gida?Cikin hayagaga...tad'aga mishi hannu"hey! ba ruwanka ai tun
jiya nace ya kwashe kome na shi.Yarik'o hannayenta "Baranzan da za ki aura kayan
shine fa kike watsowa? Tak'wace"Baba ka kyaleni a cikin hayyacina nake ban sha giya
ba bare kace tafad'a min ba gaskiya ba,soyayyarce kawai bazanyi ba,na fasa auren
nashi,kuma na yi alk'awari ko na rasa mijin aure to da in auri Baranzan gwamma in
mutu ba aure.Baza ki auri Baranzan ba to saboda me?Wa zaki aura? Saboda bana son
shi,kuma D'ansarai zan aura.Yakalleta da sauri yana maimaita sunan D'ansarai?
Dansarai? Waye kuma haka?
D'ansarai shine wanda nake so kuma a cikin gari yake,shi zan aura
zan kuma yi abinda yake yi,shi musulmi ne,nima wallahi sai na musulunta na yi
sallah. Yatafa hannaye cikin kad'a kai"Jesus Christ.Yabita da kallan nazari sai
huci takeyi kamar ta ci babu.Yanunata da yatsa"to ban yadda ba.Tagyad'a kai"ni ai
na fad'a maka ne dan ka sani,ba wai dan ka yadda ba,tunda dai ai ni zanyi zaman
auren ba wani ne zai min b...saukan marin da aka mata yasa sauran kalaman suka
mak'ale...
Kasham ai ban san baki da hankali ba sai yau, a duk zuri'ar mu ba me
salla sai ke ce za kice za kiyi? Tayi d'as d'as d'as da yan yatsunta"to baki
isaba,ina tagirgiza kai wannan ba za ta sa6uba bindiga a cikin ruwa, dama abinda ki
ka dinga yi kenan a makaranta bin mazan hausawa?Tama Maman na ta wani kallo me kama
da harara"ni ina ruwa na da rashin sallar zuri'arku?Kuma aike ma kin san mazan
hausawa ba k'ashin yarwa,sau dubu nawa ina kawo miki kayayyaki kinaci,kin kuma sani
sarai su d'inne suke bani,baki ta6a k'in kar6a ko ki min fad'a akan in rabu dasu
ba, sai yanzu dan nace ina san zama irinsu?Ashe kowa yana san wawa haihuwar shice
ba a so? Tsamaninki banza kika dinga ci? Takai mata wani mari amma tagoce dasauri
yabi iska, tamata dak'uwa kinci uwaki,dan abu kazan ubanki ba za kiyi sallah
ba,abinda ba mayi dake sa'in'sa amma gashi daga fara cewa kina san wani tsinannen
bahaushe har kina min rashin kunya kina fad'amin maganar dakika ga dama...Tabuga
cinye na rantse da ALLAH baki isaba sai dai idan bana numfashi za kiyi
sallah.Kasham tagyad'a kai"To maji ma gani ai...an binne tsohuwa da rai.
Lidiya tashigo suka had'u suna ta zagin ta amma ko a jikinta wai
anyak'ushi bishiya.Tad'an motsa kafad'a tare da ta6e baki "Kanku ake ji...ta d'auki
jakarta"bazan iya wannan bud'ar kan karyan ba, kuci kanku kusha bak'in ruwa.
"Kasham ani yake?(Kasham ina za ki?)
Tajuyo muryar Maman a tsawace.Tayi taku biyu sannan taja ta tsaya"Ani yake?Tasake
tambayar ta,ko a jikinta tace.
"Ana kari Julaibib(wajan Julaibib zani)
Dawo ki zauna karki kuskura ki bar gidannan.Tad'anja tsaki sannan
tak'arasa ficewa da saurin ta"idan na dawo kar ki barni inshigo"kuma ko ku mutu ko
ku rayu wallahi sai na yi sallah kuma ALLAH zai taimakeni in auri D'an
Sarai...ALLAH dai yakai damo ga harawa...
Tajuya kan mijinta cikin tafasar zuciya ni dai ka sani gaba d'aya
zuri'armu babu wanda yake sallah,sai dai in wancan ne yake yaudare min yarinya,yake
so tabi layin shi,to kaji na rantse da girman ALLAH bazan yadda ba, zanje har cikin
gidanshi inci mutuncin shi, ba ki yamana ga shi nan yana shirin kama Kasham, dama
ya dad'e yana fad'in idan munki sallah to Insha-ALLAH Ya'yanmu sai sunyi.Yagirgiza
kai cikin damuwa yasan matarshi bata da mutunci, to shima dai dan uwan na shi
Yayanshi uwa d'aya uba d'aya Shedrak,wanda a yanzu yake amsa sunan Alhaji Hafiz ba
barin ta kwana yake yiba shima mafad'aci ne wallahi.
Kiyi hak'uri Dinatu mu zauna musan abinyi,nima ba na goyon bayan
abinda tazo dashi,kuma da kike fad'in Shedrak ne yake yaudare ta to yaushe rabonshi
da zuwa garin Zonkwa bare har yashigo k'auyan Madauci?Tayi shiru.Yawatsa hannaye
kingani ko?Ai shekarun da yawa ko Kasham baki haiifa ba a lokacin. Muje wajan
Pastor ayi addu'a ko Baptismal idan yaka ma sai a sake mata.Tamik'e cikin gyad'a
kai"eh to ka kawo shawara to tasu mutafi ai bamuga ta zama ba da zafi-zafi akan
daki k'arfe.
Kasham bata kwana a gidan ba,sai washe gari da hantsi.Lokacin kuma
Mamanta ta dad'e da tafiya kasuwa,dama ita take fita ta nemo musu abinda za suci
dama sauran buk'atunn rayuwa,yar kasuwa ce sosai da take cin kasuwancin ta gari da
k'auyuka na nesa dana kusa,shi kuma mijin kullum yana gida yana aikacen-aikacen yau
da kullum da akeyi a gida har girki ma a wasu lokutan idan ba kowa shi yake
yi.Yad'ago yana kallanta "Kasham zo mana ganin tana shirin shigewa d'akin ta,tayi
kamar ba ta ganshi ba kuma har had'a idanu sukayi lokacin da za ta shigo.
Tazauna a d'aya farar kujerar robar,ko sannu bai samu arzk'in tace
mishi ba bare in kwana (Oh mu Ya'yan Ibrahim🤔inda ranka ka sha kallo...sunan wani
shiri a Freedom Radio)A ina ki ka kwana Kasham?Tazuba mishi manyan idanunta masu
maik'o"wannan wace irin tambaya ce haka Baba? Yagirgiza kai "ai na ga ke a gida
kikafi kwana shi yasa na tambayeki kuma Baranzan yazo nemanki na san ba a wajan shi
kika kwana ba.Baba ba ruwanka da inda na kwana. Tad'ora k'afa d'aya akan d'aya tana
karkad'a kafar dama,tana wata yatsina da hura hanci alamar bala'i takeji da gasken-
gaske.Ta sauke gwauran numfashi Ka na ji ko Baba? Eh ina jinki.ALLAH sai na auri
Julaibib,ka san yadda nake jin k'aunar shi a zuciya ta kuwa?Takad'a kai"no matter
how zan kwatan ta maka ba za ka gane me nake jiba...sai tafashe da kuka duniyar ta
cukurkud'e mata wallahi,rana zafi inuwa k'una,to a ina ake so tasamu sassauci ne?
Julaibib,Iyayanta,Baranzan, Lidiya, da yan uwan ta kowa yana jin haushinta? To ita
tace ma zuciyar ta ta k'aunaci D'ansarai ne???
Tausayi irin na d'a da mahaifi ya mamaye zucyarshi,saboda shi yana da
san Ya'ya sai dai abinda tazo dashi me girma ne, amma ga dukkan alamu tana san
wannan D'an...menene ma sunan na shi oho ya manta, tunda har ta yadda tabar
Baranzan da suka shafe shekaru hud'u suna soyayyar su hankali kwance ba abinda ya
ta6a shiga tsakanin su na tashin hankali amma akan shi wannan bahaushen sun fara
fad'a,dama duk cikin Ya'yansu ai daga Kasham sai Rahab ne basa canja samari kamar
yadda ake canjin kayan sawa,kuma su biyun ne suka maida hankali ka'in da na'in akan
karatu, sauran maza da matan suna can suna cin karansu ba babbaka. Matanma sai su
shafe watan ni takwas basu lek'o gida ba, suna can wasu garuruwa da jahohi suna
zaman kansu suna kuma sheke ayarsu yadda yaka ma ta,galibi ma zuwan su gida sai da
dalili me k'arfi kamar lokacin Christmast,New-Year, da Esther,su kanzo a Valentine
amma ba kowane Valentine ba.
Kiyi hak'uri Kasham dak'yar ya rarrashe ta tayi shiru,manyan idanunta
masu maik'o sun kad'a jawur "Kiyi hak'uri Kasham ni kin san matsala ta ba babba
bace,zan iya barin ki kiyi sallah tunda kina sanshi, za kuma cigaba da kasancewa
'ya ta,bazan tauye miki yanciba" you have human right"kuma shekarunki sun kai na
duk wani d'an Adam me hankali,babbar matsalar "inda gizo ke sak'ar Dinatu baza ta
ta6a amince miki ba,idan kinki ji to na san za ta yafe ki a cikin Ya'yanta, za ta
barma hausawa ke forever kinga kuma baki mata a dalci ba, ta so ki ta kula dake ta
miki kome na rayuwa...kema ba za kiji dad'i ba.Yakalleta yad'an motsa kafad'a ya
cigaba da gyaran waken da yake yi na girkin rana.Itama tamik'e tana
k'unk'uni.Yad'anyi murmushi k'uruci dangin hauka,Kasham baki san rayuwa ba.You know
nothing but wannan soyayyar data rufe miki idanu." So makaho...
Lidiya tabita da kallo "to wai ke da kike ta wannan hank'oran,kike
k'ok'arin 6atawa da kowa akan wannan tsinannan kun dai-dai tane ya yadda zai aureki
zai zama miki uwa da uba dasauran danginki da za ki rasa? Dan abu kazan ubanki ina
ruwanki?Babbar manufuka kawai,bitch ai na san ke ki ka k'yank'yasa ma Baranzan!
Lidiya ta k'yalk'yale da dariya dan abun bai ba ta haushi ba,ta kuma
k'yalk'yakewa da dariya tana tafa hannaye Jesus Christ of Nazareth gaskiya kin fara
cin kai (Hauka)
Kasham ta fad'a gado ta rufe idanunta zuciyar ta tana wata irin
bugawa,da bata d'auki alk'warin dai na shan taba ba to da yau ALLAH ne kad'ai
yasan ko kwali nawa za ta sha,ba ma kara ba,ta dunk'ule hannu ta dinga naushin
matashi idanunta na tsiyayar da hawaye masu d'umi " So babbar cuta...
Lidiya ta dafa kafad'arta sai tamik'e da sauri kamar wacce kuna ta
harba"get the hell out this house...ta fad'a a haukace.Lidiya tamik'e sai dai in
bar miki d'aki amma ba gida ba,dan kema ba na ki bane. Wawuya kawai da har yanzu ta
kasa gane san maso wani take yi... Sai kinyi 6atan 6akatatan za ki gane ashe shayi
ma ruwa ne madara da bournvita ne ya canja mishi kala.
Mamanta tana dawowa daga kasuwa ko hutawa batayi suka tasata a gaba
sai gidan Pastor.Dama yasan da zuwansu dan haka suka zauna zaman jiran fitowarshi
Yashigo D'akin-shak'atawar cikin bak'in suit, rigar ciki shirt, takalmanshi da
mashak'in wuya (neck-tie)ruwan k'asa,wuyarshi da sark'a rosery.
Yana rik'e da King James Bible.Da fara'arshi yake musu sannu da zuwa
shi ma yazauna suka gaisa sannan ya nuna Kasham da kanta ke hayaki ta d'ora kafa
d'aya akan d'aya"ke kina so ki bamu matsala me yahad'a ki da bahaushe ne?Tagalla
mishi harara tana mishi wani kallan uku ahu "ah kaji k'arfin hali 6arawo da
sallama,yanzu kurace za ta cema kare maye? Shi har yana da bakin da zai ma wani
fad'a yaushe-yaushe aka gama rigima d'an shi na cikinshi yama wata yarinya yar
Kurmin-Bi ciki,yanzu haka yarinyar tana cikin gidanshi sunyi auran leda (auren da
ba Pastor ne ya d'aura shi a majami'a ba Church)wai sai ta haihu za a yi auran
gaskiya dasa albarkan Iyaye.Yasake kallanta ba magana nake miki ba?To me ko zai
had'ani dashi banda soyayyay.Ina son Julaibib zan kuma aureshi ko kamin addu'a
bazai kama niba,ai wallahi gwamma ni ba ciki a kamin ba.Maman za ta mareta yahana
kowa yayi zagi a kasuwa yasan da wanda yake yi, ki barni da ita kawai Dinatu.
Pastor wannan abun yana cimin tuwo a k'warya,Ya'yanmu da zarar sun
girma sun yi soyayyya da hausawa sai kaji suma suna san zama masu sallah, sai su
gudu su aure su ko muna so ko bama so,to a kan me za su dinga yaudare mana Ya'ya
suna mana d'auki dai-dai suna converting d'insu zuwa musulunci?Sannan su Ya'yan
hausawa mata basa ta6a yadda suyi soyayya dana mu Ya'ya mazan,abun yana k'ok'rin
shige makad'i da rawa fa,na rantse maka da girnan ALLAH Ya'yanmu mata da suke
sallah a cikin gari sunyi yawan da ko mun fara k'irgasu lissafin zai k'wace mana,to
gaskiyar magana sai kun k'arae zage dantse da k'wazo wajan preaching ta yadda za Ku
dak'ile wannan al'amari suma suji suna k'yamar mazan hausawa kai ba su kad'ai ba da
duk wani me sallah kawai(😊Up up up Diniyal-Islam👏).
Yagyad'a kai"Ki kwantar da hankalin ki Dinatu wannan matsalar ita
muke tattaunawa a taranmu na Christian Association Of Nigeria(CAN) har yanzu muna
kan aikine,ai kowa yaci tuwo damu miya yasha, wannan makon ma a kawai babban taro a
Jos har daga kasar waje za muyi bak'i.Wani murmushin mugunta ya su6uce
mishi"wallahi za muma duk wasu masu sallah na Southern Kaduna(Kudancin
Kaduna)wankin babban bargo a k'aramin k'oko'.Suka gyad'a kai cikin gamsuwa "yauwa
Pastor ALLAH yataimake ku. Amin,amin.
Pastor ya dad'e yana jero addu'o'in shi su kuma Iyayan sun durk'usa
gwiwa bibbiyu sun rufe idanusu tare da had'e tafukan hannayansu idan yayi addui'ar
sai yace In Jesus name we pray sukuma suna amsawa da Amen,amen,amen,ameeennn....
Ita dai kallansu kawai takeyi har zuciyarta ta lula tunanin Enigma
man d'inta D'ansarai.Tayi murmushi "Julaibib idan ka aureni za kaji dad'in rayuwar
ka,zan saka farin ciki na karanci"Catering & Hotels Management.Na san Food and
Nutrition zan dinga shirya maka abinci me rai da motsi, ingantaccen abinci me gina
jiki da k'ara kuzari,za kaci har sai ka ture..bata san Pastor ya gama 6aragadar
shiba har sai da Babanta ya ta6ata"Kasham tashigo mu tafi gida an gama ganin
idanunta a rufe sun zaci ko itama amsawa ta dingayi.
"Gobe ma ku dawo".
Tajuya tama Pastor d'in wani malalacin kallo sannan tajuya,wallahi ba
inda zan dawo idan za a ma mutum addu'a lallai dole-dole sai yana wajan? ALLAN ai
yana jin kome...
Abinda yafi kome mahimmanci a rayuwar d'an Adam ya fi kome sauk'i,sai
Ubangijinmu bai horema kowa mallakan shiba dan kar a k'unta ta ma bayinshi, sannan
bai horeshi kaasatan (ake6e) ga bayinshi na gari ba, a ah yabarshi kowa
yasamu,Ubangijinmu me rahama da tausayin bayine...
Iskar da muke shaka ta ALLAH ce ba wani me iko da ita.
Ruwa da kusan shine rayuwa duk rintsi duk wuya akwai shi.
Rana kullum sai ta fito itama ta ALLAH ce babu wani me iko da
ita.dasauransu...
ALLAH mungode maka da kayi mu musulmai masu bin tafarkin Manzanka,ba
dan mun fi wasu girma da daukaka ba a ah ganin da markace kawai.
Ya Ubangijinmu!Kaine me jujjuya zukatan bayinka...ka tabbatar da
zukatanmu a kan addinin da ko a wajanka ka kirashi da musulunci.
27 Rabi'a Thani 1441
24 December 2019
We Ibrahim's Daughters👇
Asdilat KD...2geda with Ra'ibs.
DANGIN NONO WRITERS ASSOCIATION
{Da Inganci Mukayi Fintinkau}
Bismillahi wabihi nasta'in
...GWAJIN DAFI💔
Almost true story
Daga alk'alamin🖊
Ya'yan Ibrahim
Saudat A.Baba (Asdilat KD)
Da
Bara'atu Ibrahim (Ra'ibs)
Shafi na tara.
A gida Nasir yasamu Julaibib yana fad'a mishi jiya da daddare su Aisha
suka dawo.Yauwa Nasir nagode maka ba kad'an ba, yad'ibo dabino me yawa yabashi.Yasa
hannu biyu yakar6a cikin murna.Nima nagode Kawu.
Bayan sallar la'asar suna tsaye a k'ofar gidan tafito sanye da farin
hijab tana murmushi.Tagaishe su a ladabce.Musaddiq yace to ya gajiyar hanya? Sai
kawai kiyi tafiya ba sallama?Tad'anyi murmushi Yaya Musaddiq a min afuwa bazan sake
ba.Yagyad'a kai to shikenan. Yayi gyaran murya karmu 6ata lokacin mu tunda lokaci
jarin d'an Adam ne,Aisha magana ta gaskiya za muyi.Yad'an kalleta tana tsugune
natsuwarta na ga sauraran abinda zai fad'a. Julaibib yana sanki, za ki iya
auranshi? Shiru ya ratsa wajan, ta had'a kai da gwiwa dak'ik'u nata tafiya bata ce
kome ba.Aisha yi magana mana. Yakalli Julaibib to wata kila ni take jin kunya barin
ba ku waje"dama shirun budurwa yaddan ta... bawazara kuma sai ta tanka.
Tad'ago da sauri kwallah sun cika idanunta"a ah ka tsaya kawai hawaye
masu d'umi suka zubo mata sharrr...Lafiya kike kuka kuma? Tagirgiza kai inafa
lafiya Yaya Musaddiq na shiga rud'ani,zuciya ta tana min zafi, tunani na yana
shirin rikicewa.Saboda me? Musaddiq ya tambaya cikin mamakin kalaman ta.Saboda
soyayyar mutane biyu"wa zan za6a?Takad'a kai cikin takaici"Kaiyah...Yaya Julaibib
bakamin adalci ba,kaci amanar k'auna.Yakalli Julaibib sannan yakalleta"banga ne ba
kamar yaya Aisha?Ta share hawayan da suke gudu a fuskar ta sannan tamik'e tsaye"Na
so Julaibib amma dole tasa na hak'ura saboda banga fuska ba,kwatsam kuma sai ga ku
da tayin soyayya a lokacin da yariga yak'ure. Musaddiq yad'an kalleta kin daina san
na shine? Ko d'aya har yanzu ina san shi to amma ya zanyi?Akwai alk'awarin wani a
kaina.
Yaya julaibib ka ci amanar k'auna, kwarai na so ka,kai ka k'i bani
goyon baya. Aisha ki taimake mu.Takalli Musaddiq da mammaki kamar yaya?Eh ni a
ganina lokaci bai k'ureba tunda ba auran aka d'aura ba, gashi kin tabbatar da bakin
ki kina san shi,amince mana kawai kome zaizo gidan sauk'i,su Baba zasu shiga cikin
lamarin.Julaibib yana sanki,za kuyi zama cikin amana...ta tareshi da sauri"haba
Yaya Musaddiq wannan san kai da yawa yake, me yasa kake aran bakinshi wajan cin
albasa? Kai ni nama game ba wani so na da yake yi.A ah Aisha karki fad'i haka dan
Julaibib ya zo wajanki ba sau d'aya ba ba sau biyu ba to a tunaninki zuwan me yake
yi? Sada zumunci,ziyarace ta sada zumunci,kullum haka yake fad'a kuma haka na
da'uki zuwan na shi.To Aisha....
Julaibib ya katse shi"kar muyaudari kanmu Musaddiq,neman aure akan
neman aure haramun ne a musulunci,ni na yadda da hukuncin Ubangiji duk abinda ba ka
samu ba to dama can rubutacce ne tun daga lauhul-mahfus ba na ka bane.Yad'an
kalleta Aisha ina miki fatan alheri da dacewa a gidan aurenki.Yarik'o hannnun
Musaddiq yamata sallama sukayi tafiyarsu.Tabisu da kallo har suka 6ace ma
ganinta.wata sabuwar soyayyar shi ta dad'a mamayar zucyarta.Hashim ma yafad'o mata,
shima tana kaunarshi da wata irin soyayya ta daban. Tagyad'a kai"lalalai wannan
muk'addari ne"rabon kwad'o baya hawa sama... Tad'an cije le6enta na k'asa sannnan
ta juya zuwa gida..
Da daddare bayan sun gama cin abincin dare ya fad'a ma Iyayanshi kome
game da Aisha.Sukace ba kome sai a nemi wata.Ya amsa cikin ladabi Insha-ALLAH.
Danbarwa me yawan gaske akayi tsakanin Kasham da Baranzan kafin ya
yadda ya tattara kome na shi yabar gidansu tare da alk'awarin tunda tak'ishi saboda
wani tsinanne to ko ba jima ko ba dad'e shine nan yanuna kanshi da yatsanshi shine
zai zama ajalin Julaibib. Yanunata da yatsa"ni nake fad'a miki wannan maganar ki
rubuta ki ajiye.Idan ka kashe shi ba tare da ya maka kome ba shari'a ai ba kyaleka
za tayiba,kaima zakabi bayanshi ne.
Tabi k'ofar da ake ta kwankwan sawa da wani malalacin tsaki tadad'a
d'ora kanta ajikin matashin "Yes come in"suka shigo sama da k'asa take musu wani
kallan uku ahu.Sisters ne su biyu "menene?Cikin d'oki me rik'e da madaidaicin kofin
silver tabud'e murfin sannan ta mik'a mata"Shekaran jiya Reverend Father yadawo
daga Jerussalam(Darussalam)to jiya Pastor yaje mishi ban gajiya shine yabashi Holy
Water(Ruwan Zamzam)me yawa anba kowa ya sha,ke kuma bakije majami'a ba shine aka
d'iban miki ta ajiye kofin a gaban ta.Tamik'e zaune da sauri daga kwanciyar da
tayi,tasa k'afa ta ture kofin.Kafin suyi wani yunk'uri ruwan yabi carpert d'in
d'akin.Suka bita da kallo cikin mad'aukakin mamaki"Kasham Holy Water ne fa?Tawatsa
hannaye cikin halin-ko-in kula"dan Holy Water ne sai me?Suka 6ata fuska gaskiya
baki kyauta ba.Tagyad'a kai "to sai a yanke min hukunci.Suka juya har sun kai k'ofa
d'aya ta juyo"mun manta Pastor yace mu fad'a miki anjima ki shirya za ku tafi a
miki baptismal.
Taja dogon tsaki"Allah suturi bukwui inji kishirya k'onanniya" Ku
fad'a mishi bana so dan haka ba inda zani wallahi.Takalleta na wasu dak'ik'u Kasham
da kinyi hak'uri an miki kinga ran...Cikin hayagaga da tafasar zuciya tamik'e
tsaye"na ce bana so,to a kyaleni ko ana dole a rayuwane? Daku dashi kuje kuyi
baptismal d'in ko ba daku suke fornication d'in ba?"Get lost dan abu kazan
ubanku,get the hell out of my room tanuna musu k'ofa yan iska kawai kuje kuji dana
ku zunubin"dan nace ina san D'an Sarai shi kenan sai yazama zunubin da har sai anyi
baptismal (wankan tsarki)?Ko wani abune yazama zunubi? Za su sake magana tayi wani
ihu ta buga tebur d'in tsakar d'akin sai da littafin kai suka zubo k'asa"now get
out dan abu kazan uban ko wace shegiya!.Suka fita ka me da ha6a🤔lallai Kasham ta ci
kai(hauka)dole ko a mata wankan tsarki ko za ta samu lafiya.
Tafad'o gado cikin takaici da damuwa da kuma matakin d'auka.Ba zato
wani tunani yazo mata.Tamik'e da sauri har tana bugewa da katakon gefen gadan,tayi
tsalle tana wani ihun jin dad'i"Halelujah...Diary d'inta ta d'auka tayi waje da
gudu hurrayyy.
Babanta tasamu yana zaune a inuwar barankaci yana sauraran rediyo a
cikin shirin tambayoyin addinin kirista.Tazauna a gefen shi cikin walwala,yabita da
kallo ba Pastor yana kiranki bane?Tayi yar dariya "Ba kirana yake yiba ya dai cene
a fad'amin gobe da yamma inshirya za a min baptismal d'in.Yagyad'a kai Ohooo.
Yacigaba da sauraran rediyonshi ita kuma tana bud'e diary d'inta tana
karantawa.Wacewar wasu dak'ik'u tad'ago tana kallanshi"ni ko Baba in tambayeka
mana. Uhun tambaye ni ina jinki.Tad'anyi rubutu a diary sannan ta kalleshi "wai
brother d'inka daka ta6a bamu labarin shi har ka nuna mana hotonshi tun da dad'ewa
yana nan kuwa?Yad'aure fuska"me yadameki da Shedrak? Ina ruwanki da jin labarinshi
kuma?Yayi d'ad d'as d'as da yan yatsunshi ki karkad'e kunnuwanki ki jini da kyau
"Shedrak is no more in our family,mun dad'e da yafeshi mun barma musulmai shi,kamar
yadda shima yazabi zama musulmai da addininsu. Ta ta6e baki
"Basakut Baba(Kayi hak'uri Baba)
Dan na ga kamar ranka ya 6aci,ni abinda yasa na tambayeka a cikin wani
littafi d'azu dana ke karantawa naci karo da sunanshi shine na tuno da wannan d'an
uwan na ka,ai kaima ka san tunda muke dakai ban ta6a maka zancen shiba.Yakashe
rediyon dan sun gama shirin.To woo na d'auka kina san jin labarin shine.Tad'an
motsa kafad'a ko d'aya Baba dan labarinshi ba zai amfane ni da kome ba.Tamik'e Baba
barinje unguwa amma ba dad'ewa zan yiba.Yad'aga mata hannnu yana mata adabo.
"Sai aburak" ( Sai kin dawo).
Sakamokon jarabawar su na fitowa Water Fall Hotel matsirg suka d'auke
ta aiki amma k'ememe tace ba ta so duk da albashinta me tsokane.Mamanta takalleta
cikin takaici to saboda me ba kya so?Saboda Baranzan yana da hannun jari a hotel
d'in ni kuma na gama amfanuwa da duk wani abu indai a kwai Baranzan a ciki wallahi
bazan yiba.Suka had'u suka dinga zagin ta amma tayi kunnan uwar shegu dasu ko a
jikinta an yak'ushi bishiya.
A sanda rana tatafi tana shirin fad'uwa Kasham tashigo gidan da kaya
nik'i nik'i ta zauna tana hutawa.Rahab da Mamanta suka bita da kallo daga ina kike
ne?Tabud'e manyan idanunta masu maik'o da suka d'an canja kala kamar me jin
bacci"daga kasuwa nake tamik'a musu tsire da lemun kwali Don Simon tashige d'aki.
Rahab tabiyota wai kashe-kashen kud'in nan da kikeyi ko dai kin yi
sabon saurayine? Tamata wani malalacin kallo kamar za tayi magana sai kuma tayi
shiru tad'auko diary d'inta tana rubutu.Tagama abinda takeyi takwanta da tunanin
wanda zai zo yasiye aladunta gaba d'aya dan kud'i sosai take buk'ata,dama ita da
Rahab kiwon aladu sukeyi da shi suke rufama kansu asiri shi yasama basa harkar tara
samari barkatai,mazan ma ba sa, ba su na jaki kamar yadda suke ma yan matan bariki
dan sun san ba da kud'insu suka dogara ba,a dating zata watse. Yauma aladu biyar
takama tasiyar dan ba ta da kud'i.
Dasafe tasamu Babanta a d'aki yana kallo tazauna tana tayashi suna
hira. Baba ka san abinda yake bani mamaki?Yagirgiza kai"to wai shi Shedrak da aka
yafeshi a cikin dangi yana jin dad'i?Yatsaida idanunshi a kanta tsawon lokaci,
nazarin ta yake yi"Kin dameni da maganar Shedrak a yan kwanakin nan me ki ke so
kiyi ne? Me ki ke shirya wane? Banza bata kai uwar akuya kasuwa,Meye a zuciyar kine
Kasham?Cikin dariya tace kai Baba ALLAH ba abinda nake shiryawa,ni abinda yake bani
mamaki ace mutum ba shi da yan uwa blood relatives saboda zai yi sallah kuma shi ya
yadda da haka? Ni fa shi yasa nafara canja tunani a kan Julaibib saboda zo mu zauna
zo mu sa6ane,to idan munyi fad'a wajan wa zani inji dad'i ku kun yafeni? Yagyad'a
kai "Ehem yanzu kika zo inda muke so kizo, yanzu kin gane abinda muke k'ok'arin
nuna miki kenan amma ki ka k'i sauraran mu gashi daga fara addu'a kin fara dawowa
hayyacinki.
Yayi yar dariya"God bless you my daughter. Wani murmushi ya su6uce
mata amin Baba.Tagyara zama"gaskiya Baba ni yanzu na amince gobe muje a min
baptismal.Yayi kyau Kasham,Yakad'a kai cikin damuwa "Hum Shedrak? Kar kiyi tunani
irin na shi fa.Tagyad'a kai"haka fa.Ko yanzu yana ina ne oho mishi.Yace wa? Shedrak
ai nasan inda yake da Dinatu ma tana zuwa gidanshi a shekarun baya...bai k'arasa ba
tad'an ta6e baki tare da mik'ewa cikin halin-ko-in kula da maganar,Baba barinje
inyi wanka dan yau zanje a min nail fixes.Tana shiga d'aki tayi tsalle tafad'o gado
Hak'anta za ta tadda ruwa Halelujahhhhh...
Ranar lahadi duk suna ta shirin tafiya majami'a(Church)ita kuma tana
zaune tana shafama faratanta da taje aka sa mata na roba jan farce.Mamanta ta
kalleta ke baza ki shirya ba sai kin makara? Ta yamutsa fuska"ni fa yau ba inda
zani"baki da lafiya ne?Rahab data fito daga d'aki take tambayarta.Lafiya ta k'alau
zuwan ne kawai bazan yiba.Shikenan sai ki mana abincin rana.Tagyad'a kai To
Mama.Tad'aga hannu tana musu adabo sai kun dawo.
Tamaida k'ofar gidan ta kulle sannan tashige d'akin Baban wajan daya
ke ajiye muhimman takaddunshi tanufa,d'aya bayan d'aya take dubawa cikin
tsanaki,wasu takardun ma tun na makarantar Primary suna nan saboda ya iya
ajiya,anan taci karo da wani tsohon hoto Baban ne da Maman suna ganiyar k'uruciya,
tamayar da hoton tana dariya,kakaf binciken ta bata ga abinda take nema ba.Rai
a6ace taja dogon tsaki"Ohhh no damme,ta dunk'ule hannu ta naushi iska.Tayi jifa da
wani tsohon wallet k'ananan katunan ciki suka tarwatse a tsakar d'akin.Tadafe kanta
dake barazanar ciwo.
Wucewar wasu dak'ik'u tana zaune cikin tafasar zuciya,ta tsuke bakinta
kamar za ta rufeshi amma bata rufe ba tana zuk'ar iska, ta zuk'eshi da yawa sannan
tafara fesar da iskar ta baki ta hanci ta sauke gwauran numfashi tamik'e ranta in
yayi dubu ya baci ta tura hannunta acikin gashin kanta,tasake dunkule hannu ta
naushi iska"Damme...a kasalance tamayar da takaddun, sannan ta tsuguna tana kwashe
tarwatsastsun k'ananan katunan a cikin ma'ajiyarsu,idanunta suka kai wajan guda
d'aya daya kusa shigewa k'ark'ashin kujera,tad'auko shi tana dubawa.
Complementary card ne me d'auke da sunan Alhaji Hafiz Donatus,sunan
unguwar da yakeyi,sai lambar waya na gida dana wajan aiki.Tayi tsalle cikin dariyar
murna,ta k'ank'ame katin a kirji"Hallelujah...wallahi wani karfi da karsashi ne ya
mamaye ilahirin gangar jiki da zuciyarta.Batayi niyyar yin abincin ba amma farin
cikin data tsinci kanta a ciki yasa ta zauna ta shirya musu abinci da abun sha me
rai da motsi(Yummy).
A sanda hantsi ya dubi ludayi na safiyar talata tagama shirya kayanta
a yar madaidaiciyar jaka trolley,tana zuge zip d'in Mamanta tashigo tana mata
kallan nazari
"Ani yake ?(Ina za ki)
Kamar da gaske tajuyo cikin damuwa suna kallan juna,tad'an sosa kunnen
ta na dama"Ramai zani wajan Tina tun jiya da rana nasamu labarin an mata
Operation,tun ajiyan naso tafiya to bani da kud'ine.Wayyo! takad'a kai cikin damuwa
ALLAH yabata lafiya, kigaishe ta,tasa hannu a mata sun gane(Lalita)taciro kud'i to
kenan ko na mashin baki dashi? A ah ai na samu Mama ina da wanda zai kaini.To gashi
kya kara wannan zai miki amfani, dan na san zaki tarar da ita da wata buk'atar,kin
san majinyaci.Takar6a tana d'an murmushi "Nagode Mama. Maman tarakata har sai da ta
hau mashin tana dad'a jadda dama me mashin d'in Ramai za ka kaita kayi tafiya da
ita a hankali,dan jiya na hau mashin d'in wani wawan yaro saura kad'an yazubar
damu.To Mama zan tafi a hankali kar in zubar miki da wannan kyakkyawar yarinyar ni
da zaki bani ita wallahi ina so.Shi da Maman sukayi dariya ita kuma ta d'aure
fuska"Kai malam ina da abinyi dallah ja mutafi. Mama sai na dawo.Yauwa Kasham ALLAH
yakaiku lafiya.
Suna zuwa kwanar da zata sadasu da cikin gari tace shiga nan yad'an
juyo ya kalleta ba Ramai a kace zan kai kiba? Eh can ne amma na fasa mushiga cikin
gari idan nagama abinda nake yi ka kaini tasha.Yaja mashin"to amma kin san kud'inki
ya k'aru da yawa tunda har sai na jiraki kin gama abinda za kiyi a cikin garin ko?
Tagyad'a kai "Indai kud'i ne to ka kwantar da hankalinka kamar ka mari uwar
soja,wallahi abinda ka yanke da bakin ka shi zan ba ka.Yayi yar dariya "godiya nake
yi me kyau, wallahi irinku nake so.
Tanata mishi kwatance har suka zo gidansu Julaibib amma k'atan kwad'an
da suka gani a k'ofar gidan yabata tabbacin mutan gidan ba sa nan tace su wuce
shigon shi sai dai kash...nan d'in ma a kulle. Tasauko tana waige-waigenta ta
hangota.
"Hey Sudaida Ibrahim Me-Lambu...
Sudaida tajuyo,idanusu yahad'u tak'araso wajan tana murmushi"Malama Kasham ke ce?
Ina kwana. Takamo hannunta"Lafiya lau Sudaida,ya karatu? Alhamdulillah. Sukayi d'an
shiru na wuce war wasu dak'ik'u.Kasham tasake kallanta"yanzu ajin ki nawa?Aji uku
zamu shiga idan aka koma hutun nan.Tagyad'a kai"yayi kyau,kidage sosai kinji ko?
Ina Ya'yanku na ga shagon a kulle? Sudaida tabi kofar shagon da kallo"Yaya
D'ansarai ai baya gari,watanni biyar kenan har yanzu bai zo gida ba,Shida Yaya
Musaddiq zuwan shi uku.Suna ina? Tad'an kalleta "Suna Zari'a k'aro karatu.Tad'anyi
murmushi "Julaibib ya tafi Jami'a zai d'ora degree a Islamic Studies kenan,tun a
Gidan-Waya taso canja course,da ace shima Special Education yake yi irin karatun
Musaddiq wallahi da sai ta koma irin karatun,da yanzu itama ta nemi addmision ta
bishi can.
"Hummm my enigma man wish you all the best"...
Takalli Sudaida to me zan bakine? Tazuge zip d'in jakarta taciro yar
k'aramar "Damask rose-flower"ta rabo me kyan gaske tashak'i k'amshin sannan ta
mik'a mata"gashi ba yawa.takar6a da godiya.Kasham ta sake ciro wani rufaffen
envelop tamik'a mata"wannan ki ba Yayanki D'ansarai duk lokacin da ya dawo dan
ALLAH ki adana shi dakyau,kar kuma kimanta, tahad'a tafukan hannayenta please...
Sudaida tayi yar dariya ganin yadda tawani marairaice mata tagyad'a kai"Malama
Kasham Insha-ALLAH I will do as you say"tadafa kafad'arta"Yauwa Sudaida thank you
very much,I really appreciate sukayi dariya.
Tabud'e wallet d'in hannunta kud'ine sababbi yan naira d'ari tad'ibo
su dayawa bata tsaya k'irgawaba tamik'a mata, amma Sudaida bata kar6a ba. Tamata
kallan nazari"Me yasa?Ba kome kawai ki barshi.Ba zato Sudaida taji ta rungumeta
"Kar kimin haka Sudaida,ni kaina ban san dalilin da yasa nake k'aunar duk wanda
yake da alak'a da Julaibib ba,ban san dalilin ba, hakanan nake jinku a
jinina,tanannad'e kud'in tasa mata a tafin hannu, ai ni naba ki ba rok'ona kika
yiba,sai ta sake ta a hankali.
Kiyi karatu Sudaida,dan shine hasken rayuwa,shine abinda baya k'arewa
kullum kina tare da abinki ba a fashin shi duk rintsi duk wuya yana cikin
kwakwalwarki,Ina miki fatan alheri,ki gaishemin da D'an Sarai,Julaibib my enigma
man dakyau da kyau.Me mashin d'in yatayar tahau,Sannan suka d'aga hannu suna ma
juna adabo🙋Sudaida tad'an d'aga murya dan har sun kusa shan kwana"Malama Kasham
kema ina miki fatan alheri nagode.Kasham tamata murmushi"Toh nagode suka sha kwana.
Suka 6ace ma Sudaida.
Cikin sa a suna zuwa tasha motar saura mutane biyu ta cika tabiya
kud'in mutum biyun sannan ta sallami me mashin da kud'in da baiyi zatoba dan ta
ninka mishi abinda yace tabayar,yatafi yana mata godiya.Tana shiga tazauna ta
d'aura belt direba yaja motar sai...
KADUNA garin gwamnahhh...cibiyar ilmi,wayewa da iya d'aukar wankan dake
bin jiki.Oh yessss...mune the KD's mune nan,kowa kagani da wanka rainan mune,a
wajan mu ya koya...😎
Me neman ruwa yatafi randa.
Me neman jini yatafi kwata.
Me neman labarin wuta ya tambayi tsire.
Masu mura suke da majina.
Masu ruwa suke da kifi.
Masu abin fad'a ba sa fad'a.
3 Jumaada Awwal 1441
29 December 2019
We Ibrahim's Daughters👇
Asdilat KD...2geda with Ra'ibs.
DANGIN NONO WRITERS ASSOCIATION
{Da Inganci Mukayi Fintinkau}
Bismillahi wabihi nasta'in
...GWAJIN DAFI💔
Almost true story
Daga alk'alamin🖊
Ya'yan Ibrahim
Saudat A. Baba (Asdilat KD)
Da
Bara'atu Ibrahim (Ra'ibs)
Shafi na goma.
Motarsu na tsayawa a kawo tad'auki shatar taxi,dak'ik'u kad'an suka
iso unguwar saboda ba cunkoson abubuwan hawa, tabi wajan da kallo bayan tasallami
me taxi,tasake kallon wajan da tunanin ina za tabi dan hanyoyin sun karkasu.
Yan makarantar Islamiyyar rana sun fara tafiya,wasu yara guda biyu
maza za su wuce ta tsayar dasu "Sannunku yan makaranta. Suka amsa da yauwa
sannu.Dan ALLAH tambaya nake yi gidan
"Alhaji Hafiz Donatus"
Tamik'ama babban katin hannunta, yad'an kalleta da mamaki bayan ya duba
katin, sanin Alhaji Hafiz da yayi mutumin kirki me rik'o da addini,dan babban d'an
Alhaji Hafiz abokin Kawun sune, to ita kuma wannnan me zak'o-zak'on faratan rumfar
shaid'an fa?Kuma ko mayafi babu haka take tafiya kamar wata namiji,a gidan Alhaji
Hafiz ma basa mu'amala da kome sai hijab,to kuma meye darin gamanka da ita?
Tamabayarka tayi idan ka sani fad'a mata,idan baka sani ba fad'a mata.Zuciyarshi
tafad'a mishi haka.sai yagyad'a kai.
Yamik'a mata katin,gidan wanda nasani nake kuma kyautata zatan shine
to kinga wancan titin yanuna mata titin da d'an yatsan shi tagyad'a kai tana kallan
titin, to kimik'e shi,kwana tafarko zaki shiga,gida na hudu nan ne gidan ai zama
kigani idan kika duba katin. Tahad'a tafukan hannayanta"nagode.A ah ba kome yarik'o
hannun k'aninshi suka tafi.
Tacigaba da tafiya har tazo gidan me k'atuwar k'ofa ruwan zinare,tayi
tsai...na wucewar wasu dak'ik'u,ta kai hannu zata fara rank'washin k'ofar kenan sai
gata a bud'e wata farar mota kirar marsandi tana fitowa, yabita da kallo ta cikin
madubi,itama shi take kallo, yashiga tunanin a ina yasan wannnan fuskar ne?
"Mahaifiyarshi"abinda yafad'omishi kenan daya ga manyan idanunta masu maik'o da
yanayin k'irar jikinta,sai yayi ribas tabbas wannan yar'shice,yar d'an uwanshi
Kantiok ga kamanni nan,yafito daga motar suna kallan juna,itama tagyad'a kai cikin
gamsuwa tabbas wannan dan uwan Baban tane sai dai shi bak'i ne,Babanta kuma
fari,yana sanye da dogayan fararan kaya,bak'ar hular dara akanshi da bak'in
takalmi,yanata k'amshin turare me sanyin dad'i wajan shak'a.
Tayi yar dariyar murna"Uncle.Yayi murmushi"na'am.Rahab ce ko Kasham ko
Judith? Uncle Kasham ce.Masha-ALLAH sannu da zuwa, yakulle motar yazare makullin"to
bismillah yanuna mata hanya mushiga ciki,yakar6i trolley d'in har suka shiga wani
babban D'akin-shak'atawa me cike da ni'ima,wani sassanyar iska da k'amshin turaran
d'aki ya mamaye ko'ina,kome agyara tsab a muhallinshi,tazauna a kujera tare da
lumshe idanun ta tana zuk'e k'amshin tana zancen zuci "Lallai Uncle yana jin dad'in
shi,tasauke numfashi sannan ta bud'e idanunta, suka kalli juna sai ta d'anji kunya
ta kauda kanta gefe.
Yayi murmushi kinsha hanya ai na san kin gaji,yad'auko abinci da
ruwa da lemun kwali na biyar a raye (five alive) yamik'a mata kofi,tazuba ruwa
tafara sha sannan taci abincin ya kuma mata dad'i taci to k'oshi dan bata wani
tsaya bak'unta ba,kad'an tasha lemun ta godema Jesus Christ,Yesu almasihu me ce to.
Saida da tagama suka fara hirar yaushe gamo?Shi dama bai san taba dan
tun kafin a haife ta rabonshi da kauyansu Madauci.Ikon ALLAH banyi zaton wani a
cikin ku zai zo inda nake ba,wai Kantiok ne da kanshi yafad'a miki inda nake?
Tagirgiza kai"a ah ba shi bane,ni nayi ta bincike har naga complementary card
d'inka, ni ba ma wanda yasan wajan ka na zo dan na fad'a ma Mama wajan k'awata Tina
za ni.
Yayi yar dariya"Dinatu kenan,wato me hali baya fasa halinshi,amma ba
abinda yafaru ko?Eh Uncle ba abinda yafaru kowa lafiya.suka cigaba da hirar yan uwa
ya tambayeta wannan,ya tambayeta wancan, wata amsar ta bashi dariya, wata kuma
tabashi tausayi, wata tambayar kuma tace bata gane ko suwa yake nufi ba,dan tun kan
a haife ta fa,har suka gangaro kan yan uwanta.
Alhamdu Ya'yanshi nawa yanzu? Tad'an ta6e baki ita kanta tana dad'ewa
bata ganshi ba"ai duk cikinsu Bitrus ne kawai yayi auran majami'a,amma Alhamdu ai
gaba d'aya ya koma D one(D'orawa one)yana tsiran naman kare,baka ga yadda ya lalace
ba saboda shaye-shayen miyagun k'wayoyi,amma watannin baya budurwar shi ta haihu ta
kawo mana yarinyar data haifa mun gani.Yakad'a kai cikin damuwa,wannan irin rayuwa
dame tayi kama?
Yakalleta ke kuma na ki Y'ayan guda nawane?Bazaice kaso nawa bisa d'ari
ba dan ba shi da k'ididdiga amma dai ya san samun cikakkun 'yan mata(Virgin)a
cikinsu,ba masu yawa bane saboda wata irin rayuwar san zuciya,taci barkatai da suka
za6a suke yinta cikin kwanciyar hankali.Tagirgiza kai"Uncle ban ta6a haihuwa
ba,kuma duk abinda muka yi da Baranzan"I repent"Ya yadda da ita,yajijjiga kai"toh
ya karatu kin gama secondary ko anan zaki k'arasa?Ta ajiye kofin lemun a saman
tebur sannan ta bud'e jakar hannunta taciro wani babban envelop ruwan k'asa ta
mik'a mishi.
Yad'ago cikin mamaki da murmushin jin dad'in ganin sakamokon
jarabawar ta na College of Education.Kinyi k'ok'ari kuma na yadda lallai baki tsaya
shashanci ba"wai rok'o a gidan bebe"suka cigaba da tattauna al'amura mabambanta har
Kasham tafad'a mishi gaba d'aya abinda yakawota.
Yakalleta lallai kin yadda za ki musulunta Kasham?"Eh Uncle na yadda
zan musulunta.Yagyad'a kai"To ki sani musulunci yana da sharud'd'a guda biyar duk
wanda kika ganshi a cikin musulunci to tabbaci hak'ik'a sai da ya yadda da
wad'annan sharud'd'an, Sharad'in farko kuma mafi girma a cikin su shine kalmar
shahada.
Shaidawa babu abin bautawa da gaskiya, bisa cancanta sai ALLAH,kuma
Annabi Muhammad bawan shine kuma manzan shine.
Ma'anar kalmar { }الإلهtana kore duk wani abin bauta ne koma bayan
ALLAH{}إالاللهwannan kuma tana tabbatar da bauta ne ga ALLAH shi kad'ai ba tare da
abokin tarayya ba.
Sharud'd'an kalmar shahada kuma sune:
1.Ilimi wanda yake kawar da jahilci.
2.Yak'ini wanda yake kawar da kokwanto.
3.Ikhlasi wanda yake kawar da shirka.
4.Gaskiya wacce take kawar da k'arya.
5.Soyayya wacce take kawar da k'iyayya.
6.Janyuwa wajan yin aiki wacce ke kawar da k'in yin aiki.
7.Yadda wacce ke kawar da juyarwa.
8.Kafircewa da kin yadda da duk wani abin bauta koma bayan ALLAH.
Tare da sanin cikakken bayani danga ne da"Shahdatu anna Muhammadan
rasulullah.
Ma'anar kuwa:Gasgata Manzon ALLAH a duk abinda yaba da labari,da yin
biyayya ga abinda yayi umarni dashi,da nisantar abin da yaja kunne ko yayi hani
dashi,da kuma bautawa ALLAH dai-dai da koyarwarshi.
Bayan wannan sai sauran sharud'd'an musulunci sune Sallah,Azumin watan
Ramadan, Zakka ga wanda yake da dukiyar data kai nisabin yin Zakkar,Aikin Hajji ga
wanda yasamu iko. Kingane ko?Naga ne Uncle, kuma na yadda da duk abinda kafad'a to
yanzun nan za ki kar6i musulunci.
Ashhadu anla'ila ha'illallahu wahdahu laashari kalah...Wa ashhadu anna
muhammadan abduhu wara suluhu.Yana fad'a tana fad'a har suka zo k'arshe. Yayi
murmushi Alhamdulillahi yanzu kin zama musulma, ALLAH yamiki albarka. Acikin
sunayan musulunci da kike ji wanne kike so a dinga kiranki dashi?Tad'anyi
jimmm...na wucewar wasu dak'ik'u sannan tace"Uncle Sumayya nake so...Yayi murmushi
ALLAHU-AKBAR kin za6i suna me daraja a tarihin addinin musulunci,Sumayya mace ta
farko data kar6i addinin musulunci.
Tunda kin zama musulma to akwai wankan shiga musulunci dan haka nake
so ki natsu kiga yadda zan kwatanta miki.Yadinga mata bayani dalla-dalla sannan
yace ta mishi bayanin yagani inda tayi kuskure ya gyara mata.
"Dafarko tsarki zan fara sau uku,sai in wanke hannayena zuwa mad'aurin
agogo sau uku,kurkure baki,shak'a ruwa a hanci da fyacewa sau uku,wanke fuska daga
matsirar gashin kai zuwa k'arshen ha6a,daga gefen kunnan dama zuwa gefen kunnan
hagu sau uku,wanke hannun dama zuwa gwiwar hannu sai uku,wanke hannun hagu zuwa
gwiwar hannu sau uku,shafan kai daga matsirar gashin kai zuwa keya,a kuma dawo
dashi da duka tafukan hannaye sau d'aya, sai shafan kunnuwa ciki da waje sau
d'aya,wanke k'afar dama saman k'afa da tafin k'afar ko ina ya jike da ruwa zuwa
k'wauri ko idan sawu sai an tabbatar ta wanku,ta hagu ma haka za a mata, wannan
itace cikakkiyar alwala.
Sannan sai in zuba ruwa a kaina da duka tafukan hannayena in cuccud'a
in tabbatar gashin kaina ya jik'e da ruwa,zanyi hakan har sau uku,sai in wanke
barin jikina na dama har zuwa tafin k'afar dama,sai in wanke 6arin hagu har zuwa
tafin k'afa,sai ingame jikina da ruwan in tabbatar ko ina ya jik'e da ruwa,lungu da
sak'on jikina.
Idan kuma na so bayan nayi tsarki sai kawai ingame jikina tun daga
kai har zuwa tafin k'afafuna da ruwa in cuccud'a ko ina nanma wanka yayi.Tad'an
kalleshi amma Uncle wannan wanka zaifi dad'i a shower(shaya)ko?Yayi murmushi wannan
sharhin kine amma ko ba shaya mutum idan yaso zaiyi abinshi.Kin burgeni yadda kika
kowa kome dalla-dalla kamar yadda na fad'a miki,da alama zaki fahimci kome a d'an
k'ank'anin lokaci.
Wannan wankan shi za kiyi duk lokacin da jinin al'adarki tad'auke,shi
za kiyi idan janaba tasa meki, shi za kiyi idan jinin biki yadauke,bambancin dake
tsakaninsu kawai wajan niyya ne.
Cikin d'an shakku takalleshi "to Uncle kana ganin Julaibib zai aure
ni?Sumayya sanin gaibu sai ALLAH, tunda yafad'a miki ko zakiyi sallah shifa bazai
iya auran kiba,amma babban abinda za ki fara yanzu shine addu'a"Allah ai maji
rok'on bawane,ba kuma abinda ya gagara a wajan ubangiji".
Yanzu kinga za kiyi wankan tsarki amma dole fa sai kin cire wannan
faratan roban(nail fixes)dan a addinin musulunci sa shi haramun ne,tad'auki abin
yanke farce tafara k'ok'arin ciresu,data gama yakaita wani d'aki, kishiga kiyi
wanka,d'akin yar uwan kice,kome yana zaune a muhallinshi Dammm...Zuciyar ta tabuga
saboda irin wannan k'amshin a d'akinsu Julaibib ta ta6a jinshi wallahi ranar data
mamayeshi tashiga.Ta tsuke baki kamar zata rufeshi tana zuk'e sassanyar k'amshin
tabaki ta hanci tare da lumshe idanunta,tana wata kissima a zuci,wani murmushi ya
su6uce mata wucewar dak'ik'u masu yawa, tasauke gwauran numfashi sannan tarage
kayan jikinta tashiga wanka.
Yakoma D'akin-shakatawa yazauna, tunanin ya cika k'wak'walwarshi har
baiji fitowar taba.Uncle na gama tafad'a lokacin da take k'ok'arin zama,ya kalli
agogon dake d:aure a hannunshi lokacin sallar la'asar ya gabato.Yamik'e "zani
masallaci,daga nan zan wuce in d'auko mutan gidan,ko kin jini shiru karki damu dan
wata kila zamu had'u da cunkuson abubuwan hawa.Ta amsa da"to Uncle a dawo
lafiya.Tad'auki wani littafi data gani a saman kujera"Islamic Perspectives On
Reproduction, Health ChildBirth Spacing In Nigeria.Tafara karantawa.
Miqdad ne yafara dawowa a sanda rana ta tafi za ta fad'i magriba na
shirin kunno kai,ya san ba kowa a gidan shi yasama yatafi da mukulli amma yana ta6a
kofar yajita a bud'e,yasa kai cikin murmushi tare da sallama bak'uwar fuskar yagani
a kwance tana karanta littafin da ya ajiye a saman kujera jiya da daddare, tamik'e
zaune daga kwanciyar da tayi,tajuya inda taji sallamar Dammmm...Zuciyarshi ta buga
da suka had'a idanu,Hafsa yake gani a fuskar ta,hatta manyan idanunta masu maik'o
irin na Hafsa ne.
Tad'anyi murmushi"Sannu da zuwa. Yagyad'a kai"yauwa.Tanuna mishi
kujera"kazauna mana, mutan gidan ba sa nann ne Uncle ya tafi d'auko su.Yasake
kallanta jin tace Uncle wannan yar uwarsu ce ta Zonkwa yayi yar dariya sannnan ya
zauna"kema sannunki da zuwa,daga Madauci ko?Tagyad'a kai.
Fara kiraye-kirayen sallar magriba daga mabambantan masallatai na
nesa dana kusa yasa shi mik'ewa barinje masallaci? Bai jira amsar taba yajuya
yafita.
Bayan sallar Isha'i suka shigo gaba d'ayansu dama Alhaji Hafiz ya
fad'a musu kome tun a hanya.Hafsa ta rungumeta tana dariya "Yaya Sumayya ina tayaki
murna da shiga addinin gaskiya.itama tasa hannayenta ta rungumeta tana murmushin
jin dad'i suka saki juna suna kallan kallo.
Alhaji Hafiz ya kalleta"Sumayya wad'annan sune iyalina.Yanuna ta wannan
Maman Hasan kenan kasancewar haihuwarta uku duk yan biyu take haifa kuma maza amma
ba sa dad'ewa suke komawa ga Ubangijinmu,akan wannan yanuna Miqdad haihuwar tafara
tsayawa daga shi sai Hafsa, Zuhair da Khadija.Takalli Miqdad"Ashe babban Bros
d'inmu ne shine baka fad'a min ba?
Tamatsa wajan Maman Hasan tana gaishe ta"gaskiya Mama nima ina san yan
biyu,kimin addu'a ALLAH yaba ni.Sukayi dariya dan bata wani nuna bak'unta ba kamar
ta ta6a zama dasu.Maman Hasan ta jijjaga kai "ALLAH buwayi gagara koyo,duk wanda
yakalli Sumayya ya kalli Hafsa yasan Yaya da kanwa ne,lallai jini abune me k'arfin
gaske ko Khadija batayi kama da Hafsa ba kamar yadda Hafsa tayi kama da Sumayya.
Hafsa ta d'auko abinci amma ba wanda yaci dan a k'oshe suke sai
Miqdad kawai yaci,yana gama ci Maman Hasan takalleshi d'auki abincin nan ka kaima
almajirai tun kafin ya lalace.Yad'an 6ata fuska dan baiso fitaba"Maman Hasan yanzu
a ina za a ga almijiri?Dare fa yayi.Tad'an harareshi"kai malami ba kasan gidan
almajiran kasan layin nan bane? Yad'an shafa kai"na sani. To can za ka kai musu
suma suci da d'uminshi.
Zuhair ya mik'e"Yaya Miqdad barin d'auka muje in rakaka.Yauwa Zuhair
nagode.Suka fita Zuhair yana bashi labarin abinda yafaru d'azu a gidan Malam
Muhammad Aminu (Kakansu).
Sunyi hira sosai suna dad'a wayar mata da kai,ita kuma duk abinda
bata gane ba kai tsaye zata tambaya karfe goma Alhaji Hafiz yakallesu to ya kamata
kowa yaje yakwanta haka, Sumayya sai ALLAH ya kaimu gobe zamu fara karatu.Hafsa
tamik'e"Baba Insha-ALLAH yanzu kafin muyi bacci zamu fara.Yagyad'a kai cikin
gamsuwa"yauwa Hafsa ALLAH yamiki albarka.Su kayima juna saida safe.
Hafsa matashiyar budurwa me ji da ilimin addini dana zamani,ajinta biyar
Secondary a fanni kimiyya (Science)Suka shige d'akin baccinsu suna jin k'aunar
junansu a zuciya.Taje tayi alwala tafito sannan takalleta "Yaya Sumayya kema kije
kiyi alwala ganin tana shirin kwanciya.Alwala kuma Hafsa?Ba d'azu nayi alwala nayi
sallar...tayi shiru sallar me ma?Ta tambayi Hafsa.Sallar Isha'i.Hafsa tabata amsa
tana murmushi.Tagyad'a kai Yauwa shi.Hafsa ta zauna a gefen gadon "wannan alwalar
idan za a kwanta bacci a keyin ta dan ita kariyace daga shaid'anu,shifa zama da
alwala yana ba mutum kariya sosai a rayuwa amma ba kowa yake iya jure yiba,shi yasa
Baba da Yaya Miqdad suke burgeni saboda sun rike wannan,wallahi basa zama ba
alwala,nima dai wasu lukutan nakan kwatanta.
Mako d'aya,biyu,uku shiru makatau balaguro a lahira,ba Kasham ba
labarinta.Rahab taja dogon tsaki saboda gajiya dajin mitan da Maman take yi a kan
rashin dawowar Kasham. Tadago takalleta"To wai menene abin damuwa dan har yanzu
bata dawo ba? Kasham fa ba k'aramar yarinya bace.Yakike irin wannan maganar Rahab?
Kasham ba 'ya ta bace, ya bazan damu ba.Yar kice amma kin san lafiya ita kesa aji
mutum shiru, tad'anyi murmushi amma Mama kema sometimes bakya ganewa...ta tari
numfashin ta kamar ya bana ganewa? Rahab tamik'e zaune daga kwanciyar da tayi ta
d'an ta6e baki"ni wallahi na san ba yadda za ayi Kasham tayi wad'annan makonnin a
Ramai,ni nafi kyautata zatan tana cikin gari wajan saurayin nan data nace tana
so.Tadaki kirjinta da karfi"Jesus christ...ta jijjaga kai lallai biri yayi kama da
mutum ni banyi wannan tunanin ba,yanzu barin shirya intafi Ramai d'in ga kai ga
k'afa ai ba tambayar me aka yanka.
Matina tana zaune a shagon kitson attachment d'inta ta hagonta Tamik'e
dasauri ta tarota "oyoyo Mama sannu da zuwa"tabata wajen zama sannan ta kar6o mata
ruwa da lemon mirinda da manyan cincin guda biyar a faranti. Tazauna suka
gaisa.Mama kwana biyu ni da Kasham ba wanda yakawo ma wani ziyara,ni dama wannan
Sunday d'in zanzo. Tafara girgiza kai tana tafa hannaye"Jesus Christ"Kina nufin
Kasham bata wajanki makonni uku da suka wuce?Tace an miki Operation za tazo
gaisheki? Matina ta kama ha6a"kaji muguwa zata jazamin masifa to ni Mama lafiya ta
kalau ba abinda akamin.Takad'a kai"wato gaskiya ne abinda Rahab tafad'a Kasham tana
cikin gari wajan wannan tsinannan bahaushen?Anya Mama Kasham tana wajan Julabib?Kin
san yace bazai aureta ba...Ke tafi can idan takai mishi kanta yana ganin ta fad'i
gasassa zai yi wani yunk'urin korarta ne?Matina tagirgiza kai"Kin san ALLAH Kasham
bata wajan D'an Sarai dan bata ta6a 6oye min kome game dashi ba, kinga ko a
makaranta bai tsaya kulata ba dan bata gabanshi,lokacin nema yake zaune zaman yanci
da aikata abinda yake so dan ba idanun wani babba na shi,bare kuma yanzu dayake
cikin iyaye da yan uwa?
Tina nifa ban yadda ba idan kin san gidansu kawai ta shi mutafi ki
rakani,tasan gidan har shagonshi sun ta6a zuwa da Kasham, to amma ta san halin Mama
bata da kirki,yanzu zataje ta tada hayaniya bayan ta san wallahi Kasham bata
wajanshi,to sai dai itama ta fara tunani ina Kasham za ta tafi tayi wannan
dad'ewar?Bata saba haka ba dole kuwa Mama ta damu, amma dayake Judith da halin tane
haka ai bata ma maganar ta sai ranar da aka ganta kawai.
Shiru na nucewar wasu dak'ik'u zuwa can Tina ta numfasa"Mama na fi
tunanin Kasham tana Kaduna?Cikin rashin fahimta tace Kaduna kuma?To wajan wa?Ko
tayi sabon saurayine a can?Kasham bata da wani saurayi acan,sai dai kwanaki tafad'a
min matuk'ar za ku takura mata,ku hanata auran Julaibub to lallai zata koma wajan
Uncle d'inta dayake sallah.Tadafe kirjinta dan taji kamar ruguzowar wani abu a
zuciyarta,ranta in yayi dubu ya 6aci.Takalli Tina "nagode,gobe dole zan tafi Kaduna
na rantse da ALLAH ban haifi yarinyar da zatayi sallah ina numfashi a doron k'asa
da raina da lafiya ta ba, Kasham taci k'arya ta kwana da yunwa ta tashi a rame.To
maji magani an binne tsohuwa da rai.
Cikin rashin sa a ta isa Kaduna,sai dai almajirai ta tarar agidan bayan
sun gaisa da malamin take tambayarshi Alhaji Hafiz yad'an kama baki "Wai wai wai ai
Alhaji Hafiz yafi shekara goma sha biyar da barin gidan nan,danshi yabani yace
halak malak acigaba da koyarwa, kuma yanzu hakama basa k'asarnan shida Iyalinshi
sun tafi aikin hajji.To ko kasan unguwar daya koma? Ban rik'e sunan ba,saboda shi
lokaci zuwa lokaci yana zuwa mu gaisa,amma Lado ya sani.
Kai Lado...Lado dayake biyama wasu almajirai karatu yad'ago yakalli
Malam,Malam ya yafito shi da hannu zo mana.Yak'araso cikin ladabi.Ya sunan unguwar
da Alhaji Hafiz yakoma? Ya amsa da ladabi unguwan Kanawa,amma Malam kafin tafiyarsu
aikin hajjinnan mun had'u da Miqdad yace sun tashi sun koma Unguwan Rimi G.R.A inzo
muje inga gidan,ni kuma ranar baka nan ni zanma yara darasu shi yasa ban bishi ba,
amma na san idan sun dawo zaizo har nan ya daukeni muje.Malam yace"to kinji ko?
Tayad'a kai tamusu godiya.
Tadawo gida agajiye lik'is ga mugun 6acin rai,tadinga zagin Shedrak
zagin tsamen nama tun mijinta yana tayata har abin ya isheshi yayi shiru dan abun
na ta ya wuce makad'i da rawa,zagin shi takeyi kamar cin kwan makauniya, yadda take
mishi tofin alatsine sai yaji ba dad'i "Lallai na ka na kane ko ya cinyeka bazai
tauna k'ashin ba"ai koda suka yafeshi suka barma musulmai shi amma dai ai still
blood brother d'in shine.
Dakarfi yabuga sandar hannunshi a k'asa"Wannan zagin da kike ma
Shedrak ya isa haka for what?Tanunashi da yatsa Shedrak d'inne baka so a zaga?To an
zageshi matsiyaci kawai,ai dama yadad'e yana mana wannan mugun baki "Dinatu ya ishe
kifa" yafad'a a tsawace dan banga abinda yamiki ba,shine yazo yatasa k'eyar Kasham
sai sun tafi koko itace ta saci jiki tafi har inda yake?
Ta tafa hannaye cikin bala'i"Holy Mary mother of christ yanzu saboda
Shedrak kake min wannan hayagagar...Ashe kai munafiki ne, tunda har kake fad'a dani
akan masu sallah?To kasani tayi d'as d'as d'as dayan yatsunta"as from today an
daina dafa abinci a gidan nan kowa yazage yanemi kud'i yaciyar da kanshi,idan
Kasham tadawo shikenan everything will be normal.
Jikinshi yayi sanyi,fushin daya taso dashi yane mishi yarasa,sai
yakoma rarrashi madadin shi da za a rarrasa"hun kud'i k'are magana.Yaro da kud'i
abokin tafiyar manya.Hajiya naira Zainabu-Abu me maganin surukan zamani... Inji
Sadi Sidi Sharifai.ALLAH ka azurtamu da arzik'i na halali.ALLAH muna niman tsarinka
daga masifar talauci👏.Idan tahana shi abinci ai ya kad'e har ganyanshi, baya aikin
kome,tunda aka sallameshi daga leburancin daya keyi na titin jirgin k'asa,to dama
aikin ba wani na azo a gani bane,sai dai motsi yafi la6ewa indai ba niman ka a keyi
ba...
Dabara ba ta d'aure kaya dole sai da igiya.
6 Jumaada Awwal 1441
1 January 2020
We Ibrahim's Daughters👇
Asdilat KD...2geda with Ra'ibs.
DANGIN NONO WRITERS ASSOCIATION
{Da Inganci Mukayi Fintinkau}
Bismillahi wabihi nasta'in
...GWAJIN DAFI💔
Almost true story
Daga alk'alamin🖊
Ya'yan Ibrahim
Saudat A.Baba (Asdilat KD)
Da
Bara'atu Ibrahim (Ra'ibs)
Shafi na goma sha d'aya.
Hajiya Sumayya Kantiok Donatus...
Ta canja tayi kyau na ban mamaki, kome na musulunci ya fara ratsa ta,sai
dai ko a d'awafi baiwar ALLAN nan bata manta da Julaibib ba.Kullum addu'arta ALLAH
yamallaka mata shi yazama mijinta,dan ita har kwanan gobe bata ga wani namiji kamar
Julaibib ba.
Makonsu biyu da dawowa tafara zuwa makaranta Sanawiyya kansancewar ta
me k'wak'wa da san karatun kullum iliminta k'aruwa yake yi,dan addu'o'in cikin
Hisnul-Muslim wallahi kad'an ne bata haddace ba,a kwaita da tambaya sai kuma akayi
sa a mutan gidan suna da ilimi dai-dai gwargwado suna mata bayanin kome dalla-dalla
ba jibge.
Maman Hasan tabita da kallan tausayi"Iska na wahalar da me kayan
kara"ta tsuniyar gizo ba ta wuce k'ok'i"Julaibib,D'an Sarai ko Enigma Man,wad'annan
sunayan dai duk wayewar garin ALLAH sai ta kira d'aya daga cikin su,sun san labarin
Julaibib a baki duk da basu ta6a ganin shiba.
Rannan dai Miqdad ya galla mata harara"Ke malama kar ki damume da
maganar wani D'ansarai mutumin da ko hoton shi baki dashi.Wani lallausan murmushi
yasu6uce mata"na rantse maka da ALLAH inada hotunanshi,ni ban san yadda akayi da
nazo nan ban gansuba ina tunanin Lidiya ce ta bincike min jaka ta kwashe su amma da
hannuna na sakasu.Bros karka damu duk ranar danaje Zonkwa bazan dawoba sai da
hotunan shi"za kaga kyakkyawan bak'in mutumi na,me tsabta,ma'abocin sa fararan
kaya.
Sumayya...a d'an firgice tad'ago sannan ta amsa"Na'am.Lafiya kika
zabga wannan tagumin?Takad'a kai kwallah sun cika idanunta tamaida kanta jikin
kujeran dan ba ta so su zubo "Maman Hasan Julaibib ne na kasa yin yak'i da
zuciyata wajan cireshi a cikinta, kullum sai na yi mafarkin shi sai dai ban kwanta
bacci ba me yasa?Saboda abinda kika sa a zuciyarki kenan tunanin shi,duk abinda ka
kwallafa rai da shi to a mafi yawan lokaci sai kayi mafarkin shi"sa rai a ci shi ke
kawo jin yunwa"
Takamo hannayenta,Sumayya ki fahimci wani abu"D'an Adam da kike
ganinshi to shi yake saima kanshi mutunci da daraja,shi zai kame kanshi sannan
mutane su d'aukeshi da mutunci su girmama shi"Haja ita takema kanta kud'i.kin damu
dashi da yawa,sannan abin takaicin bai san kina yi ba harara a duhu..kilama ya
manta ya ta6a ganinki,shi yana can hankalin shi a kwance yana gudanar da al'amuran
rayuwar shi,ke kina nan kin takure kanki cikin tunanin shi"wannan fa kamar aikin
banza ne sammakon gaida mak'iyi.
...Julaibib yana da matar aure makaranta ake jira tagama musha
biki,kuma k'anwata ce...kalaman matar Musaddiq kenan ranar dataje musu murnar
aure...
Tasauke numfashi"to amma ai banyi laifi ba ko a addinance.Maman Hasan
tajijjiga kai"kwarai kuwa bakiyi laifi ba,hakan ya halatta sai dai a yadda muka
saba a al'adance namijine yake furta hakan ga 'ya mace,saboda kawaici irin na
Hausa-Fulani,sai dai ban san sauran al'ummatai ba,ba kasafai matan suke yin haka
ba.Kiyita addu'a ALLAH alhakimune ba yadda ba ya shirya al'amura. Jikinta yayi
sanyi ba wata gaskiya bayan wannan"a hankali tayi furucin nagode Maman Hasan da
wannan tunatarwa.
Miqdad yafito daga d'akinshi yana karya hula.Sumayya tabishi da kallo
yanayi da d'abi'unshi suna mata shige dana D'ansarai shima ma'abocin sa fararan
kayane.Yayi murmushi ganin kallan da take mishi"Sumayya ya akayi ne? Tayi yar
dariya"wallahi Bros kayi kyau ba k'arya wannan shigar sunnan ta k'ayar dani fa. To
nagode,yau ba Islamiyya ne?Akwai sai zuwa anjima.
Hafsa tafito daga D'akin-girki tana kallanshi "Yaya Miqdad baza ka
tsaya kaci abincin bane?Yad'an sosa kunne"fita zanyi.Tad'an marairaice"ALLAH sarki
Yaya Miqdad inata sauri ne fa,wallahi na kusa gamawa. Yakalli agogon dake d'aure a
hannun shi na dama"Ina bazan tsaya ci ba gaskiya.Ta turo baki gaba gaskiya ni dai
banji dad'iba.Sai kawai tajuya tana k'unk'uni. Yarik'o hannunta"baba tawaje
nah,kiyi hak'uri kiran gaggawa aka min a wajan aiki,yadafa kafad'arta yad'an d'age
gira cikin murmushi"Yaya Miqdad ne fa?Tad'an harareshi tana dad'a turo baki ni
dai...yatari numfashin ta"kinga kwantar da hankalin ki"bayan sallar azahar zan aiko
a kar6a sai inci acan shikenan ko?Tad'anyi tsallan murna"yauwa Yayanmu to adawo
lafiya"tabashi hannu sukayi musafaha suna dariya.ALLAH yasa tawaje nah...suka d'aga
hannu suna ma juna adabo.
Julaibib tunda yatafi sau d'aya yazo sai yanzu da suka samu hutun
Semester, haka yadinga zaga gidajan yan'uwa yana gaishesu.Suna zaune shi da
Musaddiq suna tattauna al'amuran daya shafesu Safiyya tayi sallama tashigo D'akin-
shak'atawar sanye da dogon hijab suka gaisa cikin mutunta juna ta tashi tafita,bata
sake shigowaba sai da tagama abincin rana tahad'a duk ahinda za su buk'ata a babban
tire takai musu.Musaddiq yakar6eta da saurin shi"yauwa Safiyya,ALLAH dai yak'ara
miki albarka da lafiya.Shida ita suka kalli juna suna murmushi,ta tsuguna da niyyar
zuba musu yace"a ah wallahi amaryata ai kinyi me wuyar jeki kawai tuzuru zaiyi
kome.
Julaibib yayi kamar bai gane shagu6en ba,yad'auki kofi yazuba lemun
kashu da abarba,yayi hismillah yafara kur6a.Musaddiq yace kai ni bangane bane anyi
yamma da kare ni baza ka zuba min bane?Ya ajiye kofin yana nuna kanshi da yatsa"ni
kace zanyi kome ko tuzuru? Ni sunana Julaibib ban san wani tuzuru kake nufi ba, ka
san dama ni ban saba da sai anyi service d'ina ba, yazuba abincin a faranti yafara
ci.Musaddiq yagalla mishi harara"wa za ka raina ma hankali? malam kayi aure kaji
dad'in rayuwar ka,dawani tuzuru ne bayan kai?Yayi kamar ba dashi yake magana
ba.Musaddiq yad'auki cokali to ajiye abincin muci mana. Yajanye farantin da sauri"a
ah yau bazan ci abinci dakai ba,tashi katafi wajan matarka taba ka abincin abaki ma
wannan ba damuwata bace.Au haka za kace?Yad'an d'age gira yana mishi wannan
rikitaccen kallan nashi"Eh haka nace da magana ne?A ah ba ni da tacewa...wai ankama
6arawo da kayan sa ta.
A sanda hantsi ya dubi ludayi na safiyar alhamis Sudaida da d'an
d'okinta na san ganinshi ta tafi gidan Inna,amma irin amsa gaisuwar daya mata yasa
jikinta yayi sanyi"wai an jefi kaza da gishiri,baiko d'ago kai ya kalleta daga
tarin littafan daya barbaza a saman tebur ba,a dak'ile yake amsa gaisuwar da take
mishi da lafiya...Tazuba mishi idanu na wucewar wasu dak'ik'u sannan ta d'ora
envelop d'in hannunta a saman tebur d'in gabanshi.Yakalli envelop d'in a gajarce
yacigaba da rubutun shi ba tare kuma daya d'ago kanshi ba yake tambayar ta"na meye?
Haushinshi yakamata,ta galla mishi harara tajuya"nima ban sani ba.garammm tabugo
k'ofar da k'arfi.Sai lokacin yad'ago yakalli k'ofar,yad'an motsa kafad'a yacigaba
da abinda yakeyi har aka fara kiraye-kirayen sallar azahar bai gama ba, turesu
kawai yayi gefe yayi alwala yatafi masallaci.
Bai samu damar bud'e envelop d'in ba sai daya zo kwanciyar bacci"D'an
k'aramin frame ne me hoton ayatul Qursiyu,a kasanshi wani tsibiri ne me ban sha'awa
ruwa yana gudu...sai d'an takadda anyi rubutu sad'ara hud'u.
...Julaibib...na san kome zan ba ka a banza zaga ganshi,amma wannan na
tabbatar ma kaina koda ba ka so na,na san za ka alkinta shi ko???
I dore you my Enigma...
Kasham Kantiok Donatus.
Yakaranta yasake karantawa,yakai hancinshi yana shinshina frame d'in
daya ke k'amshin irin turaran ta.Yayi lallausan murmushi dan yaji dad'i har ranshi
yajijjiga kai"Tabbas kin bani abinda zan alkin ta Kasham...na kuma gode. Sai ya
d'orashi agefen gado yakwanta yana azkar d'in bacci, yanata kallan frame d'in yana
tuna had'uwarsu da Kasham tun ranar farko da kallan farko da sukama juna a haka har
bacci yayi awan gaba dashi.
Azaure sukayi kaci6is taja baya da sauri jakar hannunta ta su6uce zata
fad'i a k'asa,cikin zafi nama yacafe,yamik'a mata, takar6a tana gaishe shi.
Idanunshi akanta"wa yabaki envelop d'in nan?Tamishi wani irin kallo fuska a d'an
yamutse"Malama Kasham.Tun yaushe?Baku dad'e da tafiya Zaria ba.Yad'anyi murmushi
cikin gyad'a kai"To nagode,Kawu yana ciki?Eh yana ciki.Yajuya zuwa cikin gidan
tabishi da kallan mamaki D'ansarai kamar kuli-kuli yake da ba a gane gabanshi
wallahi,Jiya fa shine yamata halin-ko-inkula amma yanzu har da wani murmushi taja
dogon tsaki "Kai ALLAH yasauwake maka.
Sumayya ta zage dantse tana kwankwad'ar madarar ilimi,gaba d'aya ta
canja ta zama wata ta musamman"Unique charisma"fatar jikinta ma ta canja saboda
canjin cima,a gidan Alhaji Hafiz za a ci abincin safe me kyau me gina jiki,da
ranama haka a mafi yawan lokuta ba sa kasafai suke yin girki da daddare ba,sai dai
asha su gwanda,Inibi,tuffa,dabino a kora da madara idan kuma abincin za ayi to mara
nauyi za a dafa.
Tana zaune a D'akin-shakatawa sanye cikin bak'ar doguwar riga kirar
Saudiya,tayi rolling da mayafin tana nazarin"Dealing with Depression Islamically na
Dr.Bilal Philips.Ta gaji lik'is a gangar jiki,amma zuciyar ta, tana k'ara
k'arfafarta tad'aure ta k'arasa.Karo na uku kenan tana kallan d'an siririn bak'in
agogon dake d'aure a hannunta ta k'osalokacin dawowar Hafsa yayi daga makaranta ta
tambayeta wani abu.Tatsiyaya ruwa a k'aramin kofi daga babban tambulan takai
bakinta da bismillah kad'an kad'an take kur6a tana jujjuya kofin kamar tana nazarin
ruwan har ta shanye,ta ajiye kofin tana fad'in Alhamdulillah...
Ahankali ta d'ora kanta ajikin kujerar tare da lumshe idanunta tana
addu'a "Yahaiyu Yaqaiyumu birahmatika astagis,aslihli fi sha'ani kulluh,wala
takilni ila nafsika d'arfata ainin" wato "Ya Rayayye dauwamamme,da rahamarka nake
niman taimako ka gyara min al'amurana gaba d'aya,ALLAH karka barni da kaina koda da
k'iftawar idanu ne".
Miqdad daya shigo yatarar tana wannan addu'ar ya amsa da amin Sumayya.
Tabud'e manyan idanunta masu maik'o da suka d'an canja kala saboda baccin da yake
shirin kamasu.
Abrugo? (Ka dawo)
Yagyad'a kai dan shima yanajin yaran,Alhaji Hafiz ya koya musu kuma duk
sun iya ko Maman Hasan tanaji.
Umburak (Na dawo)
Wannan addu'ar muhimmiyace daya kamata ace kowani musulmi yana yinta
kullum ta ALLAH.Yad'auki littafi d'aya daga cikin tarin littafan data barbaza a
saman tebur yana dubawa, yaciro biron daya soke a aljihun gaban rigarshi yana gyara
mata wata kalma data rubuta ba dai-dai ba,yanuna mata kinga yadda ake rubutata,
wancan wata ma'ana ta daban tabayar ba wacce aka tambaya ba.Tagyad'a kai "na
gane,nagode Babban Yaya.
Yamik'e zai shige d'akinshi, danshi ba ma'abocin zaman D'akin-
shak'atawar bane. Tad'an kalleshi"afwan Yaya Miqdad ga wata tambaya,yakoma
yazauna"Uhun ina jinki"Tace yau Malam nasiha yamana da muke rik'e sunanil rawatib
kar muyi sakaci dasu,to ni kuma gaskiya ban san meye su d'in ba,to kuma dana
tambaye shi shima bai fad'a min wai ya bani jinga (Assignment)in tambayo gobe yana
jiran amsa. Yayi murmushi gaskiya Sumayya kina burgeni nan gaba da alama babbar
malama za ki zama. Tajijjiga kai"Insha-ALLAH nima sai na ba al'umar manzon ALLAH
gudummawa daga d'an abinda Ubangijinmu yanufeni da sani na ilimi,ka san fatana Yaya
Miqdad?Yagirgiza kai.Fatana ALLAH yabani miji me ilimi wanda zai dad'a d'orani akan
tafarkin dai-dai, wanda zai sa in zama productive akaran kaina,how I wish Julaibib
ya aure ni...
Yanunata da yatsa"ke dai da Julaibib d'in nan?Enigma man ko?Tayi yar
dariya ai kuwa, yana da wuyar fahimta sai dai ni na fahimce shi, baya so adame
shi,baya san hayaniya,baya shiga abinda ba da shi akeyi ba,amma ni har yanzu ina
san shi"so gamon jini"yakad'a kai"ga shi kuma so ba samu ba,sai dai fatanmu har
kullum ALLAH yaji6anci al'amuran mu.Amin big Bros.Sukayi murmushi.
Mukoma kan tambayarki abinda ake nufi da sunanil rawatib sune
sallolin da akeyi na nafila kafin sallar farilla ko bayan sallar farilla kamar :-
Sallah raka'a hudu kafin sallar azahar da kuma rak'a biyu bayanta.
Sallah raka'a biyu bayan la'asar.
Sallah raka'a biyu bayan magriba.
Sallah raka'a biyu kafin sallar asubahi.
Babu wani musulmi dazaiyi wad'annan sallolin (Nafila) raka'a goma sha biyu(12) a
kowace rana yana me d'a a da ganin girman ALLAH da k'ank'antar da kai a gareshi ba
tare da ALLAH ya gina mishi gida a Darul-karamah (Aljannah) ba.
Sumayya ba ki da burin samun gida a aljannah?Tayi dariya so
kai.Yagyad'a kai "To ki d'auki sahawarar da annabin mu,annabin rahama daya bamu,
kidinga yin wad'annan sallolin.Tad'an kalleshi"Bros bayan sallolin farilla dasu
shafa'i da wutri,raka'atal fajri da sallar walha ne zan dinga yin wad'annan sunanil
rawatib d'in.Eh Sumayya. Tagyad'a kai"na gane Bros I'm very glad, Godwilling daga
yau zan fara ina kuma neman taimakon ALLAH da d'orewar shi har k'arshen numfashi na
kataya ni addu'a. Ya amsa da To Sumayya Ubangiji yayi jagora.
Suna kwance da Khadija tana duba Hadisin Annawawis Collection a cikin
littafin Islamic Studies na B.A'isha Lemu(ALLAH Yajik'an ta.ALLAH yakyautata
makwanci👏)baturiyar Ingila (England) data musulunta ta auri babban alkali d'an
jahar Niger (Minna) Sheikh Ahmad Lemu tayi karatun addini me yasa take bada
gudummawa da tarin iliminta ga al'umar manzan ALLAH shekaru masu yawa.
Dawowar Alhaji Hafiz daga masallaci sallar la'asar yasa takalli Khadija
data ke kwance a gefenta,ta gaji da wasanta tayi bacci,sai ta gyara mata kwanciya
sannan ta tafi D'akin shak'atawa.
"Yauwa Sumayya.ya amsa barka da dawowan data mishi.Takalleshi cikin
natsuwa "Uncle na ji wa'azi sosai daga bakunan malamai mabambanta game da girman
zumunci da irin matsayinshi a addinin musulunci da hukuncin me yanke shi dame sadar
dashi, Uncle ni da kai a jinsi yaran Bajju ne,amma a addini mu musulmai ne, kuma
addininmu na musulunci bai hana mu sadar da zumunci ga yan'uwanmu wad'anda ba
musulmai ba, to amma kai me yasa ba ka sadar da zumuncin ka da sauran yan'uwanka na
jinsi Bajju?
Yakad'a kai"Sumayya ban k'i sadar da zumunci dasu ba har sai da naga
suna niman kasheni... bari kiji abinda yafaru tun kafin a haifeki.
"Wata rana hanya tabiyo dani ta Zonkwa sai kawai na k'arasa K'auyan mu
Madauci dan mu gaisa tunda na kwana biyu ban jeba, wallahi kamar jira ta sukeyi sai
ganin Kantiok, Dinatu da wasu daga cikin yan'uwanmu matasa a bayansu d'auke da
kokara da adduna, nafito daga cikin motar ina kallansu da mamaki "Kantiok ina za
kuje da tsakar rana haka?...ban gama rufe baki ba naji an sakar min adda a tsakar
ka,aiko nan take jini ya 6alle,wani ne daga cikin yan'uwan mune da wannan aikin,
danaga da gaske k'ara saramin yake shirin yi aida gudu nakoma motata amma kafin
inyi wani yunk'urin tayar da ita sun fara dukar motar,gilasanta sun farfashe,banyi
aune ba naga sun fincikoni wasu suna ba da umarnin a samin taya in babbake kawai
kowa ya huta,wallahi na ci na jaki da gasken-gaske.
Dak'yar Kantiok ya ceceni bayan ya samu nashi rabon,suka haushi da
zagi ai ba haka suka shirya ba dan me zai 6ata musu shiri?Yana hawaye yake basu
hak'uri,dak'yar suka hak'ura suna cigaba da zagina idan ban daina zuwa inda suke ba
sai sun kasheni tunda sun riga sun yafeni,sun barma musulmai to inje in k'arata can
dai gasu gada zomo ya ji kid'an farauta.
Kantiok shi yakaini asibiti kwanana uku nad'anji sauk'i nace mishi ni zan
tafi yadinga bani hak'uri wai ba laifinshi bane,ba yadda zaiyi ne "Naka na kane ko
ya cinyeka bazai tauna k'ashin ba,nace mishi ba kome,nabashi complementary card
d'ina,dama na zo in fad'a musu na yi sabon gida,wanda muka tashi a ciki na ba wani
malami halak-malak acigaba da koyar da karatun alqur'ani da sauran littafan addini
ina fatar ya zamar min sadakatul-jariya bayan numfashina ya k'are a doran duniya.
Yakar6a yana tayani murna da kuma bani tabbacin duk lokacin daya samu
dama zai kawo min ziyara bazai bari Dinatu tasan sabon gidan na ba,namishi ihsani
kamar yadda nasaba mishi mukayi bankwana.Sai dai har yau d'in nan bai zoba,amma
lokaci zuwa lokaci muna magana dashi tawaya daga baya kuma na daina jinshi ko na
kira lambar ta shi ba ta shiga,amma yanzu Insha-ALLAH za muje gaba d'ayanmu.
"Uncle to ya akayi ka musulunta? Yayi yar dariya"shekarun dayawa
Sumayya,ina secondary aka kawo mana yan bautar k'asa (corpers) anan na had'u da
Corper Muhammad Aminu,shi yake koya mana lissafi (Mathematics) kin san ko wani
malami yana san d'alibin daya ke gane darasin shi,to haka abin yakasance tsakani na
da shi,har mukayi sabo na ban mamaki har aikena yakeyi wasu lokutan in siyo mishi
kayayyakin buk'ata na yau da kullum idan baya jin zuwa cikin gari,sai washe gari in
taho mishi dasu.
Har Staff-Quarter ina binshi idan yana da abun bani naci ko nasha yaba
ni,idan babu muyi hira,wasu lokutan kuma yak'ara min haske akan lissafi.Yakan dafa
kafad'ata yayi murmushi "Shedrak kwakwalwarka tana ja sosai akan lissafi,kaje ka
karanci Accounting nan gaba kazama Accountant General Of The Federation. "Malam
bani dame tsaya min inyi karatu iyayena sun mutu.Yayi murmushi dan Iyayenka sun
mutu ba shine zai dakatar dakai daga san abinda kake san zama a rayuwa ba,kai
namiji ne gwagwarmaya da rayuwar za kayi"babu maraya sai rago"zan taimake ka kayi
karatu idan ka gama secondary ka kawo min takaddun ka zan samo maka addimision a
jami'ar Ahmadu Bello(ABU)ga tallafin karatu da za a dinga ba ka,kuma ai sana'a zaka
fara yi sai kaga kome yana tafiya.
Corper Muhammad Aminu me sauk'in kaine da bai d'auki rayuwar duniya
kayan gabas me k'amshin turaren d'an goma ba, a hankali dabi'un shi suka fara
burgeni banyi aune ba sai kawai najini rannan ina karanta"Innas safa wal marwata
min sha'a'irillah.Ni ban san kome ye ba amma nasan a irin karatun dayake yawan sawa
ne,dama su bismillahi na iya saboda indai zaici abinci ko abinsha sai yafad'a dan
wasu lokutan ma yana zubawa a faranti d'aya yace muci,tun ina jin nauyi da kunya
har nasaba.
Gab da zasu tafi sun gama hidimar k'asa nasame shi a d'aki yana
karatun Qur'an sai da yakai aya,sannan nazauna ina gaisheshi dan ranar bai shigo
makaranta ba"Malam yau baka shigo ba.Yagyad'a kai "Bana jin dad'i,ban dad'e da
dawowa daga asibiti ba"Yadai? Yatambaye ni. Nad'anyi murmushi"ni dai malam ina
sha'awar addininka sai dai baza a barni a gida ba.Yamik'e zaune daga kwanciyar da
yayi yana fad'in Shedrak kai namiji ne,ka kuma fara mallakar hankalin kanka dan
haka kanada damar yin musulunci tunda shi kake so.Da wannan nasamu k'warin gwiwa.
Ranar da zasu yatafi nasha kuka shi ya rarrasheni"haba Accountant
General Of The Federation wannan ba girman ka bane,share hawayenka maza basa kukan
hawaye,wannan ai d'abi'ar yarane.Da haka mukayi bankwana. Direbansu yaja motar ni
da sauran dalibai dawasu daga cikin Malamanmu muka d'aga hannu muna musu adabo🙋har
motar tayi nisa ta 6acema ganinmu."We may or may not see each other again.
Gaba d'aya sai makarantar ta gundireni kamar akan k'aya nake,a
dadddafe nak'arasa.Muna gamawa nafara zuwa kasuwa, dako nake yi dan bani da kud'in
da zan yi sana'a, nasha wahala amma na tara kud'i masu yawan danake ganin intayi
ruwa rijiya idan bata yiba Masai,sannan natara yan uwanmu nafad'a musu k'udiri na
nasan zama musulmi.Sai sukayi tsalle suka dire ALLAH yakashe su ban isaba, bazan
yiba meye yata6i kwakwalwata haka?Nima naja tunga nakafe sai nayi sallah.Da suka
rasa yadda za za suyi dani sai suka dinga zagina suna fad'in sun yafeni acikin
zuri'a da jinsinsu na Bajju,har abadan duniya basu ba ni,ban bi takan suba na
d'auki jakata sai cikin gari.
Agidan Liman tsoho anan na zama cikakken musulmi na za6i sunan Hafiz
nacigaba da harkokina da musulmai,ina kuma zuwa kasuwa ina yin dako dan incigaba da
rufa ma kaina asiri duk da kome ana bani amma ban yadda na zama cima zaune ba.
Rannan kamar wasa ina gwada lambar Corper Muhammad daya bani sai
kawai naji ta shiga dan ban ta6a samun shiba sai ranar.Yad'aga da sallama nima ina
murmushin jin dad'i dan nasan ma'anar sallamar dakuma muhimman cinta a
musulunci"Malam ina wuni. Yad'anyi Jimmm...nawuce war wasu dak'ik'u cikin tunanin a
ina yasan wannan muryar? Zuwa can naji ya amsa tare da fad'in "I'm I talking with
the Accountant General of the Federation?Na kyalkyale da dariya ina gyada kai dan
sunan fa yana sa ina jin kaina a duniyar wata"Yes Malam you're...mukayi
dariya.Bayan mun gaisa nake fad'a mishi na gwada layin shi sau shurin masak'i ba ta
shiga.Yace matsalar network d'in k'auyen kune,kuma ai laifin kane kadaure kawai
Accountant kasamar muku na'urar sadarwa me k'arfin zango...nayi dariya kawai dan na
san zolayata yake yi.
Nafad'a mishi kome.Yaji dad'i sosai yadinga ambaton ALLAH cikin
shauk'in murna,tundaga ranar sai muke yawan yin waya danma wasu lokutan ni ina
samun tangard'an sadarwa sai dai shi yakirani,muna haka ALLAH yama Liman tsoho
rasuwa.Iyalinshi basu kore niba amma sai naji gidan ba dad'i, rannan muna waya sai
na fad'a mishi damuwa ta yace ba kome inzo Kaduna insa meshi,aiko washegari
dasassafe nayi sallama da mutan gidan Liman tsoho nad'auki hanyar KD.
Malam Muhammad yana aiki da ma'aikatar Ilimi ta jahar Kaduna(Ministry
of Education)Ina zuwa yad'orani akan kasuwanci dan ya tambayeni zan tafi jami'a
karatun ne? Nace mishi a ah nafi san kasuwanci d'an tunda nafara dako a Zonkwa naji
dad'in kudi,yasani a makarantar addini,da daddare ma ba barni na zauna ba,ina
makarantar Islamiyya ta maza,ina karatu ina sana'a, k'ank'anin lokaci kuma ALLAH
yasama kasuwan cin nawa albarka,wallahi duk abinda nata6a sai yazama bud'i daga
Indallahi.
Shekaru na biyu a Kaduna muka had'u da wata Atika muna soyayya har an
kai kud'in aure da sadaki amma Iyayanta suka dawo da shi wai su baza su ba tubabbe
auran yar su da a ka haifeta musulma iyaye da kakannin kakanniba,Ina ai wannan
ganganci ne zagin uba ranar sallah.
Ran Malam Muhammad in yayi dubu ya 6aci yadinga fad'a wannan ma ai
jahilcine to ko musuluncima ai da tubabbun yafara yacigaba da bunk'asa har zagaye
ko ina lungu da sak'o nafad'in duniya gaba d'ayanta.
A ranar bayan munyi sallar la'asar a masallacin unguwarmu yatsaida
mutane dan su shaida.Yad'aura min aure da yarshi mace guda d'aya da ALLAH yabashi
daga cikin Ya'ya maza guda bakwai Ummulkhair me kimanin shekara goma sha uku dan
lokacin ajinta hud'u a secondary.Yakalli Sumayya yana murmushi kin san abinda yace
min? Tagirgiza kai.Bayan an kaita gidana yadafa kafad'ata "Hafiz ga Ummulkhairi nan
kaji tsoron ALLAH karik'e ta da amana,Idan tayi ba dai-dai ba ka nuna mata
kuskurenta nan take,ka kuma muna mata yadda za tayi dai-dai,shi icce tun yana
d'anye ake tank'warashi...Kome daza ka d'orata akai to a yau d'innan za ka fara
k'ok'arin gina matashi a cikin zuciyarta,ko ba ta so to kai kajajirce karka karaya
Insha-ALLAH sai kayi nasara.Ubangiji ya albarkaci auranku...abinda yafad'a min
kenan yajuya yayi tafiyarshi. Sumayya tajijjiga kai"Malam Muhammad Aminu yacika
jarumin maza Ubangijinmu kasa ka mishi da mafificin sakamakon ka.Amin,Amin Sumayya.
Shigowar Maman Hasan yasa yanuna ta da yatsa"kin gan ta nan Sumayya har
yanzu muna zaman lafiya.Tazauna a kujera tana kallansu"Eh gani nan,to me namaka
kake ta nunani da yatsa?Tayi furucin da wani salo irin na shagwa6a.Sumayya tayi
murmushi ganin wani irin kallon k'auna me cike da shauk'i datake mishi.Tsam tamik'e
za ta shige d'aki "Sumayya dawo kiyi zamanki mana...dasauri tak'arasa shigewa ta
rufo k'ofar tana girgiza kai "wanan kallan da abinda zai biyo bayan shi ba dani ba
gaskiya"ga d'a da fatalwa.
Bayan shekara d'aya Sumayya ta gama karatunta,har tasamu gurbin karatu
a jami'ar Kaduna (KASU) tad'ora degree a Islamic Studies ta kuma k'ara zage dantse
tana kwankwad'ar madarar ilimin addinin musulunci, dama can a goge take ga Ilminta
na Catering &Hotel Managements,gashi kuma yanzu wani fannin na daban take
karanta,yanzu larabci kamar dama can dashi ta taso sai dai me zurfi daya wane ba ta
ganewa har sai ta duba k'amus d'in larabci...
Sai dai weak point d'inta Julaibib musamman da sukaje taran Muslim
Student Society Of Nigeria(MSSN)a jahar Katsina ta ganshi ganin idanun ta yayi
kyau,yadad'a zama d'an gayu,shigarshi kamar ko yaushe ta fararan kaya.Shine
shugaban kungiyarsu ta ABU,har tagaban shi tawuce suna tsaye shi da Maimun amma ba
ta ga Musaddiq ba,wallahi daurewa kawai tayi ba ta musu magana ba amma ta dad'e a
tsaye a gefensu tana k'are mishi kallo tana wata kissima a zuciya,har had'a idanu
sunyi amma bai gane taba saboda tasa nik'abi ta kuma rufe k'wayar idanunta da
gilas.Tunda taganshi d'aliban da suke k'ark'ashin kulawarta suka ka sa gane kan
Amirarsu Sumayya...Da akace tazo zasu yi magana da yan Jami'ar Ahmadu Bello
kasancewar su yan Jaha d'aya ne,kwanciya tayi wai bata jin dad'i,dan wallahi idan
taga Julaibib har kuma sukayi magana to tsohon mikin k'auna ne zai 6alle gwamma
daga nesa-nesa kallan kura...
Yafito yana sa links d'in hannun riga Maman Hasan tanuna mishi
Sumayya.Sai yazauna yana kallanta"Tatsuniyar gizo bata wuce k'ok'i,abu d'aya yahana
shi zuwa yasamu Julaibib suyi magana akan Sumayya shine yace baya son ta,to ko
dabara kad'ai bazata d'aure kaya ba dole sai da igiya.Yakira ta da kakkausar murya
tunanin me kikeyi?Tun d'azu kin tasa kofi a gaba kin kasa san shayin.Yatsareta da
idanu cikin d'aurewar fuska,ganin haka yasa ta sunkwui da kanta tayi shiru.
Kina sane da maganar danace za muyi?Eh Uncle.Yanunata da yatsa"Ina
sane da abinda ke faruwa, banyi niyyar magana ba,to sai dai naga abin yana
k'ok'arin shige makad'i da rawa,mutane uku suna zuwa da niyyar auranki amma kina
korarsu,wannan kuma ba dai-dai bane tunda ba haka zaki dauwama ba dole za kiyi
aure,dan haka akwai abokin kasuwanci na dayace yana sanki to nayi na'am da shi dan
mutumin kirki ne,kuma ban 6oye mishi kome game da keba, shima ya amince yana sanki
a haka.To jiya yasame ni dan niman izini yana so zai zo ku gaisa.
Sumayya karki 6oye min kome idan ya zo baku dai-dai ba,dan ba auran
dole zan miki ba kin gane ko? Me zatace?Tagyad'a kai"Uncle zan zama me biyayya zan
kar6i duk hukuncin daka zartai,dan haka ko wanene shi na yadda zan aureshi dan na
san baza kamin za6en tumun dare ba.Yayi murmushi kin amince kenan?Tajijjjiga kai"eh
Uncle na amince.To ALLAH yamiki albarka,yasa ki gama da duniya lafiya,ki kuma yi
hak'uri da kome akan Julaibib, Sumayya wani hanin ga ALLAH baiwa ne.To Uncle
nagode. Yamik'e shikenan ki daure kisha shayin.Takai kofin tsakanin la66anta kamar
tana sha,suna fita shi da Maman Hasan da take mishi rakiya tadire kofin a k'asa
tawuce d'akin baccin su takwanta tare da lumshe idanunta, kwallan da suka cika
idanun suka samu damar zubowa sharrr...ranta ba dad'i sai ta fara karanta"ALLAHU-
ALLAHU Rabbi laa'ushrika bihi shai'an.Tana ta maimaitawa har bacci yayi a won gaba
da ita,sai da lokacin makarantar yakusa Maman Hasan tashiga ta tasheta.
...Aiki ke koran bak'o d'an gida ya dad'e da sabawa.
...Nagaji sai rago😊
10 Jumaada Awwal 1441
5 January 2020
We Ibrahim's Daughters 👇
Asdilat KD...2geda with Ra'ibs.
DANGIN NONO WRITERS ASSOCIATION
{Da Inganci Mukayi Fintinkau}
Bismillahi wabihi nasta'in
...GWAJIN DAFI💔
Almost true story
Daga alk'alamin🖊
Ya'yan Ibrahim
Saudat A.Baba (Asdilat KD)
Da
Bara'atu Ibrahim (Ra'ibs)
Shafi nagoma sha biyu.
Tana yankema Khadija faratan ta Hafsa tashigo da sallama,tazauna a
hannun kujerar tana kallansu cikin murmushi sun sha wanka da kwalliya kayan su iri
d'aya,doguwar riga k'irar Bahrain ruwan makuba, k'amshin turen ta ya mamaye d'akin.
Tad'an kalli Hafsa"bakin ki da magana. Tayi yar dariya"Yaya Sumayya
ba wata magana,amma fa kina da bak'o a waje.Tayi luuu da idanun ta kamar zata
rufesu,sai kuma tabud'e su gaba d'aya a fuskar Hafsa "bak'o?Ta tambayi Hafsa
itama."Eh bak'o ne a wajan ki amma wasu lokutan nakan ganshi tare da Baba.Tad'aga
idanu takalli agogon da ke manne a jikin bangon d'akin k'arfe uku saura minti goma
na yammacin. Tagyad'a kai "fad'a mishi ina zuwa.Ta amsa da to.Sumayya tabita da
kallo da tunanin irin mutumin da idanun ta za su gane mata wani daban,ba D'ansarai
ba.Tayi wani d'an huci cikin kad'a kai,sai da tagama yanke mata faratan duka sannan
ta d'auki farin dogon hijab d'inta a saman kujera tasa.
Miqdad yana zaune a D'akin-shak'atawar yana cin abincin rana yad'an
kalleta ganin ta nemi waje ta zauna"Sumayya ba jiranki ake yiba?Tamishi nuni da
Maman Hasan data basu baya tana kallan taga,waya takeyi.Ya watsa hannu"kije kawai
ai ta san da zuwan shi ita ta aiki Tawaje nah(Hafsa)tafad'a miki,kema ai kin san
gama wayar Maman Hasan ba yanzu ba,idan suka fara hira da tsoho me ran k'arfe Malam
Muhammad Aminu sai kin sike ko kuma kud'in wayar ya kare an katse sadarwar
tasu.Tarik'o hannun Khadija Miqdad ya girgiza kai "saketa kiyi tafiyar ki,ke
Khadija zo nan ya yafito ta da hannu.Bata so ba sai dai ba yadda za tayi ne,yanuna
mata kujera zauna anan kijira ta,ba dad'ewa za tayi ba kinji ko? Tagyad'a kai
idanun ta sun cika da kwallah,yayi kamar bai gani ba yacigaba da cin abincin shi.
Yana zaune a dakalin dake harabar gida yana duba wani d'an k'aramin
littafi Dammm...taji ruguzowar wani abu me k'arfin gaske a k'ahon zuciyar ta, ta
dafe kirji cikin Istirja'i dak'yar tak'arasa wajan da sallama.Yamayar da littafin
aljihun gaban rigar shi yana amsa sallar. Yana d'ago kai zai kalleta caraf idanun
su ya had'u,shi dama ya san ta,dan d'ai-d'ai kun ranane baya ganin ta lokacin da
take zuwa Sanawiyya, itace dai yau tafara ganinshi.
Takauda kai ba wani babba bane dan ita tayi zatan sa'an Uncle za ta
gani tunda yace abokin kasuwanci shine,dogo ne kuma shima yana da nashi kyau da
fasalin, yana sanye da shadda me maik'o ruwan siminti, hularshi k'ube ruwan siminti
da ratsin bak'i, sai bak'in takalmi sawu waje.Yakatse shirun"ranki yadad'e barka da
fitowa.Sai lokacin ta gaishe shi,yamik'e tsaye yana nuna mata wajan Bismillah ga
waje ki zauna "tagirgiza kai "bak'on ka annabin ka"kai yafi cancanta daka zauna.
Nagode amma ki barni a tsayen,ni namiji ne zan jure tsayuwar koda awanni biyu
ne.Bata ce kome ba tazauna "Yad'anyi gyaran murya "Malama Sumayya kin san abinda
yake tafe dani ko?Fuska a d'an yamutse ta amsa"Uhhh" ba tare data bud'e bakin
taba.Yabita da kallan nazari dama Alhaji Hafiz ya sanar dashi kome shi yasa take
amsa mishi a d'ad'd'age kenan,sai yayi murmushi cikin kad'a kai.Sai fa ya yi
hak'uri dan ya san jin kan mata sarai bare kuma ga matsalar k'auna.Wayyo!Sumayya
kema sai kinyi hak'uri,ni da shi ba d'aya bane koda kuwa uwar mu d'aya uban mu
d'aya ne.
"Sumayya kin san wani abu kuwa? Yadda yayi furucin kamar irin sun dad'e
d'in nan ya zo da saurin shi yana so yabata labrin wani abu da d'umi-d'umin shi.Sai
tayi saurin d'ago kai tad'an kalleshi amma bata ce kome ba.Idan mukayi aure,ALLAH
yabamu haihuwa d'anmu na farko indai namiji ne to ni d'in nan yanuna kanshi da dan
yatsa, na miki alk'awari ki rubuta ki ajiye,da bakinki me albarka zaki mishi
hud'uba da sunan Julaibib... dan ki tabbatar ni masoyinkine na gaskiya me san
abinda kike so.Cikin mamaki da dariyar data kasa dannewa na jin dad'i ta kalleshi
kai tsaye ta d'an bud'e idanunta"to ya akayi kasan sunan shi? Yanunata da yatsa"an
ta6o inda yake miki k'aik'ayi ko?
Shi Salim wani irin mutum ne da duk abinda yake so yana yin k'ok'ari
wajan sanin wasu muhimman abubuwa game dashi,ta yadda bazai sha wahala wajan
mu'amala dashi ba.Ya gane soyayyar da take mishi wata jarabtace daga Ubangiji,tunda
ya fad'a mata bazai aure taba,kuma ta yi hak'uri ta fauwalama ALLAH duk da yana
ranta,to yanzu ga shi,shi ya zo zai maye gurbin shi da gyara harda alakoro Insha-
ALLAH sai tayi alfahari dashi a matsayin mijin sunnah.
Kayi alk'awarin sama d'anka sunan shi?Yajijjiga kai"Eh wallahil-azim na
yi alk'awari. Tamishi wani lallausan murmushi sannan ta kauda kai daga kallan juna
da sukayi nawasu dak'ik'u.Daga nan hira ta6alle...
Zuhair ne yakatse musu hirar ta hanyar kawo ma Salim ruwan alwala a
buta dan mukhtarin la'asar yayi.Tanata kallanshi yana alwalar cikin nutsuwa kuma
cikakkiya har yagama yamaida hular shi kanshi sannan yamik'a mata butar,sukayi
sallama dan an fara kiraye-kirayen sallah daga mabambantan masallatai,Miqdad ma
yafito shi da Zuhair sun tafi masallaci dan sauke farali.Tabi bayanshi da kallo har
yafita daga harabar gidan "Yanada saurin shiga rai.
Fuska a sake tashiga gida. Maman Hasan tace"Yaya dai Sumayya?Sai ta
zauna a kujera tana yar dariya wallahi haka kawai take jin nishad'i,rabon data
tsinci kanta a irin wannan yanayin tun ranar da D'an Sarai yamata nasiha data daina
k'arama sama hazo(shan taba) Maman Hasan ta tayata da murmushi"a Alhamdulilla
labarin zuciya a tambayi fuska.
Da safe tana shan shayin na'ana'a, kalla,kanumfari,da ya'yan algarib sai
tiriri yake yi da k'amshi me dad'in dake k'ara mishi armashin da ko bakayi niyyar
sha ba idan aka baka sai ka sha.Hafsa tashigo da waya d'akin baccin su dan yau bata
fita D'akin-shak'atawa ba,anan ta zauna tana karyawa tana nazarce-nazarcenta.
Tamik'a mata wayar"ga shi ana magana"takar6a takai kunnan ta da
sallama,ya amsa sallamar yana tambayar ta ya gida ya karatu?A takaice ta
amsa"Lafiya...Alhamdulillah. Sukayi shiru na wucewar wasu dak'ik'u"wake magana?
Takatse shirun.
"Salim ne.
Salim... Salim...
Tafad'a ta maimaita cikin tunanin ga no wa ye haka?Sai yatari numfashin
ta,a d'an marairaice"Innalillahi...Ina zan sa kaina...? Mummuna ya ga mata.Kar dai
ace baki gane Salim d'in ba?Haba Sumayya to Salim d'in kine fa. Ta d'an bud'e
idanu"Oh...Ya Rahman afwan Salim ka san bani da lambar ka.Yayi yar dariya"na sani
nima jiya ne na kar6i ta ki lambar a wajan Alhaji,yana nufin Alhaji Hafiz.Kin san
ranar dana zo k'aunar ki ta mamaye k'wak'walwa ta har natafi ban baki ba,nima ban
kar6i ta kiba.Suka gaisa a mutunce"Sumayya da yammacin yau nake san zuwa wajen ki
shin kina da lokacina?
Tad'anyi murmushi"haba Salim girman ka ya wuce haka,ai ko ba lokacin
ka to dole a k'irk'iroshi bare ma a kwai,amma I'm really sorry to say...ka san
yanayin karatu,yau k'arfe goma na safiyar nan zan tafi makaranta kuma gaskiya sai
biyar da rabi za mu gama lectures sai dai gobe.Yagyada kai"ba damuwa da yau da
goben duk d'aya ne.Kad'an suka ta6a hira sukayi sallama.
Sumayya da Salim k'ank'anin lokaci suka aminta da juna.Sumayya har
ranta take jin ta samu abokin rayuwa,saboda Salim mutum ne me sauk'in kai,bai cika
d'aukar al'amura da zafi ba.Dariya takeyi saboda kalaman shi,yabita da kallo cikin
zancan zuci,wallahi kome na ta akwai tsabta,hak'oranta farare tas kamar ba dasu
take tauna duk abinda yake shiga cikin cikin taba.
"Sumayya dawani man goge baki kike amfani ne?Takatse dariyar"man goge
baki kuma?Yajijjiga kai eh dan na ga hak'oranki sun bambanta dana mutane da yawa
cikinsu kuwa har da ni d'in nan yanuna kanshi,kamar bakya 6a tasu da abinci sai
d'aukar idanu suke yi.
Kana so kasan sirrin?Sosai kuwa.To ka zama me yawan aswaki ba sai
lokacin alwala kad'ai ba, kuma musamman kasa mu aswakin al'araq,wannan shine sirrin
ga shi kuma sunnane.Kuma ka san ko masana a harkar bincike na yanzu da suke ganin
sune tushen ilimin kome,to sunyi bincike kuma sun ga no sun kuma tabbatar yin
aswaki goge hak'ora da chewing-stick magogi,ba brush ba yana k'ara k'arfin dasashi.
ALLAU-AKBAR tsarki ya tabbata ga ALLAH. Manzan ALLAH sai da yace ba dan kar ya
takura ma al'umma ba da ya farlanta mana yin aswaki. Salim ya jijjiga kai gaskiya
kin tunatar dani abinda na manta,nagode miki Sumayya lallai tunatarwa tana amfanar
da mumini.
Sumayya ki bani dama in tura Iyayena,ai mun d'an fahimci juna,yanzu
mun san wasu daga cikin halayan junan mu ko? Duk da dai ba a sanin maci tuwo dole
sai miya ta k'are. Takalleshi cikin natsuwa"Salim a da zuciya ta, tana rayamin inyi
musulunci saboda Julaibib ne, kuma koda na kar6i musulunci na kar6a ne saboda
shi,amma cikin k'udirar Ubangiji sai zuciya ta,tacanja daga wancan tunanani da
niyar.A yanzu na yadda saboda zatin ALLAH nake musulunci,da taimakon su Uncle ta
fuskar nasiha da zuwa Islamiyya da sauraran wa'azi daga bakunan manyan malamai
mabambanta duk su suka cusa min yin abu saboda ALLAH,na san na rasa D'an Sarai amma
zuciya ta bata aminta da barin musulunci ba,dan na gamsu addinin musulunci shine
addinin gaskiya,ina zaune kwatsam sai Uncle yazo min da maganar ka,a lokacin na
amsa mishi ne saboda kawai tsakani na da Uncle ba musu har abadan duniya,wallahi
kome rashin jin dad'in abu in dai yabani umarni inyi ko in bari zan yi,dan na san
soyayya ce a tsakanin mu,har fa zuciyata ta fara min sak'a da mugun zare amma ban
biye mata ba,nayi ta addu'a ina neman rok'on Ubangijin mu yakawo min agaji kar in
biye ma sharrin ta.
Amma a ranar da idanuna suka fara yin tozali da kai,kalamanka da
kome naka sai suka burgeni, zuciya ta tayi wasai...A ranar na kar6e ka kamaye
gurbin Julaibib,tad'an sake kallanshi cikin natsuwa Salim har yanzu ina jin wani
abu game da D'ansarai amma ba soyayya ba,saboda sanadiyar shi nabar kowa da kome,
harkar da nake yi nabin maza da tara abinda duniya daga garesu yabar zuciya
ta,fatana kawai in mallake shi,to sai nagane a yadda yake me natsuwa da kamewa
hak'ata bazata tadda ruwa ba, sai na bijiro mishi da maganar aure, na sadak'ar
zanyi sallah ba dan kome ba sai dan kawai na k'wallafa rai shi d'in kawai nake san
mallaka,manyan idanunta masu maik'o suka cika da kwalla.Ubangijin mu alhakimu
ne,sai gashi ya canja min da wani daban kuma zuciya ta ta aminta da shi,dan haka
Salim kai nake so soyayyar da ba ka da abokin tarayya.Julaibib dai yana da lada a
wajan ALlAH saboda halayan shi masu kyau da tsabta wanda addinin musuluncine yazo
dasu da kuma karatun addinin da yayi shine ya siffantu da siffofin,nima sai yanzu
nagane wasu halayanshi da, a da nake mugun mamakin me yasa shi baya kaza?Me yasa
yake kaza? Tad'aga hannayen ta sama ALLAH kahad'ashi da macen albarka,kamilalliya
me addini.ALLAH kasamu daga cikin wad'anda ta sanadiyyar mu wasu za su samu haske
irin na addinin ka.Ubangiji ka kara mana lafiya ka kara inganta mana Imanin
mu.Yanata kallanta cikin so da k'auna,sai yadad'a aminta da ita dan Alhaji Hafiz ya
mishi bayanin kome dalla-dalla ba jibge.
Sumayya...
Bata amsa ba tad'ago a hankali suka kalli juna"Sumayya yau rana ce ta
musamman a wajan mu ko?Tasunkwui da kai daga kallan da yake mata tana murmushi.
Sai da a ka tsaida ranar auran Salim da Sumayya,Miqdad da budurwar shi
Zainab sannan Alhaji Hafiz yatashi Miqdad d'in musamman dan zuwa k'auyan su Madauci
wajan d'an uwanshi,bai ta6a zuwa garin ba amma da tambaya sai gashi a k'ofar
gidan.Yanata sallama yaji shiru ba a amsaba,zuwa can sai yatuna to su ina ruwansu
da wata sallama?Sai yakai hannu yafara rank'washin k'ofar.Yana gyangyad'i kamar a
sama yaji ana buga k'ofar yamik'e dasauri yana fad'in"kai wanene haka daba zai
shigo ba,bayan k'ofar ba kulle ta akayi ba amma yatsaya awaje?Sukayi kallan kallo
na wucewar wasu dak'ik'u sannan ya matsa mishi yashigo,suka zauna a fararan kujerun
robar tsakar gidan har yanzu kallan juna sukeyi "daga ina haka d'an Samari?Kantiok
ya tambaye shi.Miqdad yayi murmushi daga Kaduna nake.Ai yana jin haka sai yamik'e
ya rungumeshi yana dariyar murna"haba no wonder naji a jikina kamar na san ka to
sai dai a ina?
Kai yaran Shedrak ne ko?Ina Kasham? Ya baku zo tare ba?Su ma suna
nan zuwa.Yasaki Miqdad yafita dasauri,lemun kwali Don Simon,ruwa da kofi yakawo
mishi gashi nan kasha barin kar6o maka abinci... ya tareshi da saurin"a ah kabar
shi kawai.Yaja yatsaya yana kallanshi"Kazo gidana amma baza ka ci abincin mu ba
saboda me?Yad'an shafa fuskar shi"Kayi hak'uri Kawu ina azumi ne amma da ba abinda
zai hana ni ci.Yadawo yazauna to kai saboda ALLAH za kayi tafiya ba sai kabar
azumin ba?Ya amsa mishi cikin girmamawa"Kawu azumin yana da muhimmancine.
Suna ta hira kamar sun saba. Miqdad yabashi sak'on da aka aiko shi
wasik'a ce Alhaji Hafiz d'in yake sanar dashi"Kasham tana wajan shi tana kuma
sallah,yanzu kuma ta samu mijin aure,dan haka zai aurar da ita,amma bayan bikinza
suzo Insha-ALLAH,sai takardan kud'i (cheque)an rubuta mak'udan kaud'ad'e an sa
hannu sai zuwa gidan kud'in(Bank)a Kar6a "Hallelujah..yafad'a saboda mamakin adadin
kud'in daya gani a rubuce,gaskiya shi har yagama aiki bai ta6a kar6an rabin-rabin
wannan ba,yana ta dariyar murna,shi kuma Miqdad tasbihi yakeyi a zuciyar shi"ALLAH
buwayi gagara misali hatta wushiryar shi irin ta mahaifin shine,sunyi kama sosai
sai dai wannan fari ne, mahaifanshi kuma baki ne.
Kiran wayar ta tashigo yad'aga da sallama"Yaya Miqdad ya hanya ka
sauka lafiya ko? Yagyad'a kai"na sauka lafiya Sumayya gani ga Kawu na ganshi ganin
idanuna.Tayi yar dariya."to masha-ALLAH ba shi wayar.Yamik'a mishi.Yana jin
muryarta yayi dariyar jin dad'i "Kasham sai kuma yajuya harshe zuwa yarensu na
Bajju,sun dad'e suna hira sannan yafara gyad'a kai da alama wata magana me
mahimmanci take fad'a mishi yake gyad'a kan cikin gamsuwa"amin Kasham nagode ALLAH
yamiki albarka.Miqdad yakad'a kai"wato kowa dai ya san akwai ALLAH yadda da shine
dai ba kowa yayi ba.
Yana shirin tafiya yace ni har zan tafi banga Maman Sumayya baWai Kasham
ce ta koma Sumayya?Eh kawu"Yayi murmushi kawai, Maman Kasham ta tafi kasuwa gashi
kuma sai yamma za ta dawo,to ka kwana mana.Yayi yar dariya"Kawu ina da ayyukan da
zanyi da yawa amma zan zo na musammma idan nasamu sarari zan kwana in ga sauran yan
uwan mu.To shikenan ALLAH yakaimu"yarakoshi har inda ya ajiye motar shi yana bashin
tabbacin zaizo ayi d'aurin auran su dashi.To Kawu aiko za muji dad'i ba kad'an
ba,yad'auko rafar kud'i yan naira ashirin guda d'aya yabashi,sai yagirgiza kai,haba
My Son ni ban ba ka kome ba ai kuma bazan kar6e na kaba, kabarshi kawai nagode,ga
cheque na kud'i me yawa da zan kar6a.Miqdad yakalleshi cikin natsuwa"Kawu ai wancan
d'an uwan kane yabaka,wannan kuma d'an kane yabaka,tashi kyautar daban,tawa ma
daban,sai dai ban sani ba d'an uwa ya fi d'ane a wajanka?Yasake mik'a mishi sai
yakar6a yanata mishi godiya,sukayi sallama cikin farin ciki.Yad'aga hannu yana
mishi adabo tare da addu'ar ALLAH yatsare ya kiyaye mishi hanya,har motar tasha
kwana ta6ace ma ganin shi, sannan ya juya,yak'are ma gidan kallo lallai gyara yazo
tunda kud'i sun samu.
Lokacin daya k'arasa cikin gari har an idar da sallar azahar dan haka yayi
alwala yayi sallarshi raka'a biyu ta k'asaru yayi azkar d'inshi sannan yakoma mota
yana bin shagunan bakin titin da kallo yana kuma tunano kalaman Sumayya "Idan kaje
Rahama Store to ka tambayi shagon Julaibib za a kai ka,yana tambaya kuwa aka nuna
shi shagon sai dai kash...Musaddiq ne a shagon, daya tambayi Julaibhib yace yana
gida sai bayan sallar la'asar zai fito.Yamik'a mishi wata yar madaidaiciyar jaka
ruwan k'asa"Idan ya fito abashi "Miqdad yasake mik'a mishi hannu sukayi musafaha
yajuya ya fita daga shagon.
Shima ya so ganin wannan D'ansarai d'in da Sumayya take bala'in so,yayi
murmushi ganin yadda tayi da yace bazai kar6i sak'on wani Julaibib ba dan shi ba
d'an aiken ta bane, wallahi idanunta har sun cika da kwallah ta sunkwui da kai
k'asa bata kuma magana ba,sai tabashi tausayi.Sumayya yakira sunan ta,tana d'ago
kai sharrr...hawayan masu d'umi suka zubo a kyakkyawar fuskar ta,tasa hannu ta
share su sannan ta amsa a raunane"na'am...Yad'an harareta ke fa raguwa ce daga wasa
sai hawaye? Tagirgiza kai"ni ma ban so hakan ba, ban kuma san ya akayi suka zubo
ba,ni da Julaibib ai ba wata alak'a kuma sai ta yan uwan takan musulunci,sak'on
dazan ba ka wallahi tun a Makka nasiyo mishi,da kuma na san zan had'u dashi a taron
MSSN d'in nan na Katsina dana tafi dashi na bashi...ni a yanzu ina san D'ansarai ne
saboda shi mutumin kirki ne me addini,amma karka manta ina da jan gwarzo na,dubu
jiran mutum d'aya tad'an d'age gira tana wani lallausan murmushi sannan tafurta
sunan Salim.Yayi yar dariya "Sumayya kenan so gamon jini.yashige mota yazauna ya
d'aura belt sannnan yatayar cikin ambatan sunan ALLAH yad'auki hanyar Kaduna garin
gwamna.
Musaddiq yana lissafin wasu kud'ad'e bayan sallar la'asar Julaibib
yashigo da sallama yazauna yana kallanshi har yagama yayi rubuce-rubucen shi a
littafin da suke rubuta kome na kud'ad'en kasuwan cinsu yamayar cikin dirowa sannan
ya ajiye mishi jakar a gaban shi "dazu aka kawo maka.Inji wa?Musaddiq ya dauki
mukullin motar julaibib d'in zai fita sannan yabashi amsa "Wallahi ban san shiba
bak'o ne"ni nafi. Yagyad'a kai " To Allah yatsare.
Yabud'e jakar dabinon ajwa yagani, ruwan zamzam da farin miski sai
envelop da sunan shi yake jiki 6aro-6aro da manyan bak'ak'e
"JULAIBIB ABDULLAHI D'ANSARAI...
Yabud'e da tunanin wa ya aiko mishi da wannan sak'on?
Assalamu alaikum warahmatulla. Julaibib ina gaisheka gaisuwa irin ta
addinin musulunci.Ya su Mama?Ya karatu?ALLAH yamaka jagora.Julaibib kasance wata
yau raye a cikin musulunci ba wayau da dabara ta bace,a ah ganin damar
Ubangijinmune"Alhamdulillahi bi ni'imatil Islam.Wallahi a duk inda naje babu rauni
da tsoro zan bayyana identity d'ina saboda addini na yafi kowane addini tunda ALLAH
mahaliccin muma yafad'i hakan a Alqur'ani cewa"Addinin musulunci shine addini ko
awajan shi "Subhanallahi addinin mu kome anyi programming d'inshi an ba mu.
"Julaibib na san kai mutumin kirkine me k'ok'arin bin dokokin ALLAH
gwargwadan iko, dafatar baza ka canja daga yadda na sanka ba. Dan ALLAH kar kabari
shaid'an ya rud'eka, rayuwar jami'a ta canja ka.
Daga k'arshe nake mana barka da shigowa sabuwar shekarar musulunci.Me
maka fatan alheri a rayuwa.Musha ruwa lafiya...
Sumayya Kantiok Donatus(Kasham)
Dammm...zuciyar shi tabuga da k'arfin gaske.Sumayya...Sumayya yafad'a ya
maimaita cikin san tantance wai wace Sumayyar?Yad'auki wasik'ar yakaranta yasake
karantawa,kenan ita ce Amira Sumayya da ta musu lecture akan"Media Influence?
(Tasirin kafofin sadarwa)Kasham dai daya sani wacce sukayi College of Education ita
ce ta musulun ta?ALLAH buwayi gagara misali,ko shekaran jiya sun samu sak'o ta
k'ark'ashin k'ungiyar da take jagoran ta akan Islamic Vacation Conference(IVC)yayi
zuru cikin tunano wasu kalamanta da suka ta6a had'uwa da ita a wata seminar da
akayi a"National Teachers Institute Kaduna akan"Post Primary Institution
Programmed"(PPIP)alokacin ta d'aga hannu aka bata damar yin magana"Tace a gajeran
tunani na a kirashi da Propaganda zai fi armashi fiye da Program... bata gama rufe
baki ba d'akin yad'auki kabbara kowa yayi na'am da hakan,wallahi shi yasha jin
wannan sunan Sumayya Kantiok Donatus to sai dai ko sau d'aya bai ta6a tunanin wai
Kasham ce ba...Yatuna ranar farko da daddare a wajan seminar abincin alfarma me rai
da motsi aka aiko mishi dashi wai inji Amira Sumayya to ganin sauran ma an basu sai
bai kawo kome ba"ashe albarkacin kaza k'adangare kan sha ruwan kasko
"Amira... Sumayya Kantiok Donatus...
Yafurta sunan a zuci...sai yaji wani irin yanayi ya ziyarci ilahirin
gangar jiki da zuciyar shi game ita na farin ciki.Ashe shine bai gane taba saboda
nikabin data sa,har da gilashin data rufe idanunta"Ina mana barka da shigowa
sabuwar shekarar musulunci.Musha ruwa lafiya"abinda ta rubuta a k'arshen wasik'arta
kenan.Yajijjiga kai "Tabbas yau goma ga watan"Muharram"yau kuma ga duk musulmin
daya samu iko yana azumin "Ashura"Itama tana azumin kenan kamar yadda shima yake
yi?Yakad'a kai cikin farin ciki.
"Sumayya ina miki fatan alheri a rayuwa,ALLAH yadauwamar dake a
musulunci har k'arshen numfashin ki,ALLAH yaba ki mijin da zai rik'eki da
amana,mijin da zai ha6aka miki ki cigaba a rayuwa...
Yad'auki jakar ya rataya a kafad'a yana kulle shagon sai ko ya hango
wani d'an k'auyan su Kasham daya ke aikin share-share a Fajumali-Hotel yakira
shi...yak'ara so da fara'ar shi"idan kaji gangami da labari,wallahi kamar ka san
yunwa nake ji.Yakalleshi da natsuwa ai ba abinci na ce zan ba kaba,kuma ai yanzu
lokacin cin abincin rana ya wuce k'arfe hud'u da rabi na yammaci fa?Yabuga k'atuwar
hamma baki a bud'e kai da kake a k'oshe kenan wallahi rabo na da abinci tun daren
jiya sai yan kame-kame dana yi da safe,ka taimaka min da abinda zan sai abinci dan
ALLAH.
Yagirgiza kai"K'wandala ta bazan ba kaba tunda na san mashayar D'one
za ta tafi...zai fara mishi rantse-rantse yakatse shi da sauri"kaga in dai yunwar
da gaske kake ji to jeka katako kace ma Umma tabaka tuwo na yadda zai isheka in
jini...Yad'aga hannayen shi sama"Praise the Lord,Thank you God"yajuya da sauri yaje
ya kar6o yazauna zai faraci Julaibib yasake kallanshi cikin natsuwa"Kasham tana ina
ne yanzu? Kasham...Kasham... yakalli Julaibib wace Kasham d'in?Kasham kanwar su
Alhamdu.Yata6e baki "Kasham ai ta dad'e da barin gida wai ta zama me sallah irin
ku,ance wai tana Kaduna amma ni"I don't give a damme ko ma a ina take da me take yi
fa.Hakane to idan ka gama ka mayar mata da kwanan.Yajuya yayi tafiyar shi...
Sautu a kasuwar wauta jahilci.
14 Jumaada Awwal 1441
9 January 2020
We Ibrahim's Daughters👇
Asdilat KD...2geda with Ra'ibs.
DANGIN NONO WRITERS ASSICIATION
{Da Inganci Mukayi Fintinkau}
Bismillahi wabihi nasta'in
...GWAJIN DAFI💔
Almost true story
Daga alk'alamin🖊
Ya'yan Ibrahim
Saudat A.Baba (Asdilat KD)
Da
Bara'atu Ibrahim (Ra'ibs)
Shafi na goma sha uku.
Rana ba ta k'arya sai dai uwar d'iya taji kunya,ranar juma'ar d'aya ga
watan Rabi'a Thani aka d'aura auran Salim da Sumayya,Miqdad da Zainab a ranar kuma
ko wacce ta tare a gidan mijinta,sai dai mahaifin Kasham bai samu zuwa ba saboda
zazzabin da yake yi.
Sumayya sune zaune lafiya suna da fahimtar juna,suna ma juna uziri shi
yasa suke da kwanciyar hankali,suna kuma fatan hakan yad'ore har k'arshen numfashin
su.
Yana karya hular k'uben dazai sa tashigo da sallama,ta kar6i hular
tak'arasa karyawa tasa mishi. Yad'anyi gyaran murya"Ya dai Sumayya yau fa na ganki
wata iri.Me ka gani? Shiru yayi yana mata kallan nazari "banga kome a fuskar kiba
amma yana yinki ya nuna akwai wani abu,yadafa kafad'arta "kar kiji kome Sumayya ni
mijin kine,ba ki da wanda za ki fad'ama damuwar ki sama dani.
Yamata wani kallo"Sumayya mecece matsalar?Fad'a min in har akwai wannan
amincin dake cikin zaman na mu. Tamayar da turaran data gama fesa mishi sannan
tajuyo cikin d'an murmushi"Miji na nawa ni kad'ai ko?Yagirgiza kai"ai na fad'a miki
Sumayya a yanzu bani da buk'atar sake aure,kuma in dai zaman na mu yad'ore a haka
to ai ko kin isheni rayuwar duniya, yakalleta amma fa ba alk'awari na miki daga ke
ba wata har abadan duniya ba.Tajijjiga kai"d'aya daga cikin abubuwan da suke
k'aramin k'aunar ka a zuciya ta kenan fad'ar gaskiya kome d'acin ta. Sukayi
murmushi.
Tasake kallanshi cikin natsuwa"tun daren jiya nayi mafarkin Mama kuma
har yanzu mafarkin ya tsaya min a rai sosai,dan haka nake neman alfarma kabarni in
je in ganta,ka san Uncle ya hanani zuwa wai sai nayi aure idan miji na ya barni
shikenan ban san dalilin shi na hakan ba.A yanzu na san kima da girman da uwa take
dashi,lallai ta cancanci a mata kome dan a samu albarkar ta, rayuwa tayi kyau duk
da rashin sallar da ba tayi, ina san ganinta kewar ta ta dameni,zan kuma yi
k'ok'ari wajan ganin na shawo kanta mun dai-dai ta,wata kila tsawon shekarun da
mukayi bamu sa juna a cikin idanu ba yasa idan taganni ta yafe min,ni dai ina ta
addu'a ALLAH yasa sanyi a zuciyar ta,na san ba abinda yafi k'arfin Ubangijin
mu.Yajijjiga kai"gaskiya ne Sumayya iyaye suna da girma da daraja a wajan Ya'yansu,
a addinin mu na musulunci suna da mafificiyar daraja sama da kowa.To yaushe kike so
mutafi? Bani da za6i,sa mana lokaci.Yad'auki agogon shi yana d'aurawa "Shikenan za
muyi magana da Alhaji idan naje kasuwa.To nagode.Yayi murmushi kawai
Tafiyar Dinatu Kaduna waja taransu na zumuntar mata a babban majami'ar
su dake Sabon Tasha"Evangelical Church Winning All" (ECWA)na tsawon makonni biyu
yabashi damar gyare-gyaran dayace zai yi, gidan yafito rasss har da sabon fenti
ko'ina yanata kyalli.Ranar data dawo ta cika da mad'aukakin mamaki tana ka me da
ha6a take tambayar shi"ni dai tun kafin in tafi Kaduna da ma na lura da wasu canje-
canje saboda yawan kashe kud'in da kake yi,kai ko a ina ka samu mak'udan kud'ad'en
da kayi wannan gyaran?Anya kuwa Baban Alhamdu ba ka daga cikin masu zuwa cikin gari
suna fasa shagunan hausawa?Dama kwanakin nan abinda ake ta musu kenan.
Yagalla mata harara"ai kema kin sani ko lokacin dana ke ganiyar
k'uruciya banyi sata ba,bare yanzu da girmana da kome ALLAH yasauwake.To me kake
siyarwa da bazan yi tunanin haka ba?Ba kome. Tazuba mishi idanu "gaskiyar magana
bazan yadda dakai ba in dai ba fad'a min in da kasa mo kud'in nan kayi ba.
Yamik'e"ai nima ba so nake yi ki yadda dani d'in ba. Tabishi da kallo har yafita.
Da daddare har ya fara bacci ta tashe shi,fuska a yamutse yake kallan
ta dan yanzu shima ya daina d'aukar raini tunda hatimin nasaran nan yana
dashi"lafiya kin katsemin bacci kuma baki ce kome ba?"Baban Alhamdu please...
kafad'a min in da kake samun kud'i,dan hankali na ya k'i kwanciya.Yasake d'aure
fuska"Brother na Shedrak shi ya aiko min da cheque na mak'udan kud'ad'e,kuma ina so
ki sani Kasham tabbas tana wajan shi,kuma tana sallah, bayan haka ma tayi auri
wancan watan, na so zuwa ma to sai dai zazza6in dana yi yahana ni tafiya kuma suna
nan zuwa, ina fata yanzu hankalin ki zai kwanta.
Tadaki k'irji cikin ambaton Yesu alhamisu me ce to(Jesus Christ)tamik'e
cikin tafasar zuciya"Kasham tana sallah bayan haka ma ta yi aure ni mahaifiyar ta
ba tare da sani na ba?Tayi d'as da yan yatsunta ban ta6a sanin kai munafiki bane
sai yau,wato ka tura Kasham taje tayi sallah dan adinga kawo maka kud'i ko?Haba no
wonder baka wani nuna damuwar ka lokacin da muka neme ta muka rasa.Wallahi
tirrr...da halin ka,kai munafikin addini ne tunda kana supporting masu sallah
tacika gidan da hayagaga...
Da abin ya ishe shi shima ya daka mata tsawa kin dameni fa,ki rufe ma
mutane baki ke baki san dare bane?Tagirgiza kai, ai idan kaga na yi shiru to
kafad'a min in da Shedrak yake a Kaduna gobe in buga sammako in d'auko yarinya ta
dan bazan barma wasu tsinannun hausawa ba.Yayi shiru kamar ba dashi take magana
ba,zuwan ca kuma ya d'ago ya kalleta"To tunda baza kiyi shiru ba, bari kiji kafin
ki tafi Kaduna ni zan rigaki yin sammmakon tafiya,kuma na rantse miki da ALLAH
tafiya ta bata dawowa bace,nima na bar gidan nan kenan har abadan duniya muje muci
gaba da yin sallah sai in ga wanda zaki dinga wanke ma hannu a ka.Taja dogon tsaki
"karka bari sai da safe yanzu ma kahad'a kayan ka dan ka tafi sai me?Mutuwa za a
fasa ko hijabi? Tajuya garammm tabugo k'ofar,sai dai fa maimakon bacci yayi awon
gaba da ita kamar yadda suka sa ba duk dare sai tane mishi tarasa sai kalaman mijin
ta suka dinga dawo mata.
Kusan mako d'aya kenan bataje kasuwa ba wai dan kar yatafi Kaduna
bata sani ba,yayi dariya Dinatu kenan idan nayi niyyar tafiya Kaduna zaman ki
acikin gidan nan bazai hanani tafiya ba...Dan ALLAH ba wannan nake san jiba,kace
kawai ka fasa tafiya,kayi hak'uri da abinda na maka raina ne ya 6aci kayi hak'uri.
Yakalleta ai dama kece za ki sani tafiya ba tare dana shirya hakan ba, amma idan
muna zaune lafiya ai bazan yi tunanin tafiya wani waje ba tare dake ba"we're
together for better for wost till death due part us.
Yana waya tashigo D'akin-shak'atawar ta zauna a hannun kujerar daya ke
zaune tana kallan shi, ganin wayar ta k'i k'arewa yasa tamik'e zuwa taga,tad'aga
labulan tagar tana kallan mutane na kai kawo a cikin yamma cin.Bataji zuwan shi ba
sai maganar shi taji cikin rad'a, tajuyo da sauri tana yar dariya"Kai Salim da
girman ka da kome kake irin wannan furucin? Yagalla mata harara "Kaji yar rainin
hankali ke kuma...sai ta sunkwui da kai tana murmushi.Toh shi kenan adai bar kaza
cikin gashinta kawai.Ta girgiza kai"Uh uh gwamma kawai a yankata a dafata acinye ta
kowa ma ya huta.Yamata wani kallo cikin d'an d'age gira,itama tarama irin kallan da
manyan idanunta masu maik'o sai ko ya kyalkyale da dariya"Hun Sumayya me
duniya...Za ko a yi yadda kika ce da kazar, tad'an motsa kafad'a, sukayi murmushi.
Yakalleta cikin natsuwa"to ya jikin na ki? Abinda yadawo dani daga kasuwa
kenan dan na kira wayarki ta ki shiga matsalar sadarwa"naji sauk'i sai dai bani da
k'arfi kuma bakina ba d'and'ano.Yagayad'a kai"to Alhamdulillahi, k'arfin jikin sai
a hankali za ki da wo dai-dai,ya6are vitamin c guda d'aya yasa mata a baki.
Yakamo hannunta suka zauna a kujera "kuma na zo miki da wani
albishir.Albishir?ta tambaye shi"eh albishir.Tayi murmushi fad'i albishir d'inka
yanzun nan in wanke ka tasss...da ruwan tukwuici.Yakalleta da natsuwa yana
murmushi"d'azu munyi magana da Alhaji akan tafiyar mu Zonkwa ya ce idan mun shirya
shima a shirye yake musa rana, to nafad'a mishi jibi idan ALLAH yabamu a ran rai da
lafiyar za mutafi,dan haka sai ki fara shiri yau,gobe da sassafe zan tafi kasuwa
duk abinda kike so asiyo sai ki fara rubuta shi tun yanzu kin gane ko?Wani dad'i
yamamayi zuciyar ta sai ta dad'a jinta garau ba sauran ciwo,ta k'ank'ame shi cikin
murna"nagode mijina lallai ka cancanci tukwuici sai ta fara mishi wani irin salo na
ta,da sauri ya k'waci kanshi yana dariya har hular shi tana fad'uwa"Ke wannan ne
tukwuici?Ni na zaci wasu mak'udan kud'ad'e za ki sa min a asusun ajiya ta ta gidan
kud'i?Tagirgiza kai"A ah wannan ai somin ta6i ne"tayi furucin da wani salo irin na
shagwa6a. Yagayada kai"ah nima na aga alama to amma jama'a na jira na akasuwa amin
afuwa sai na dawo anjima.Tam adawo lafiya suka d'aga hannu suna ma juna adabo🙋
Cikin nishadi suke tafiyar Alhaji Hafiz da Sumayya suna fad'a musu
sunayan garuruwa da k'auyaukan da suke ta wucewa,sannu a hankali har suka shiga
garin Zonkwa.Alhaji Hafiz yajuya yana kallan Maman Hasan"yanzu zamu shiga
shalkwatar k'aramar hukumar Zongon-Kataf sai ku bud'e idanu ku fara kallo "tafiya
mabud'in ilmi "Hafsa tace Zongon-Kataf d'in na gaba kenan?Eh Hafsa yana gaba ina
gama idan zamu koma tacan zamu biya kuga garin sai mu bi ta Pambegua mu kuma gida.
Jikin Sumayya yayi sanyi tunda matuk'in motar Miqdad yakusa shiga
k'auyansu Madauci dan ta san halin Mamanta bata da mutunci "ALLAH kamin maganin
abinda bazan iyaba...bani da kowa sai kai...
Sumayya...
A sama taji kiran Alhaji Hafiz"na'am Uncle me kace? Nace na ga an samu
cigaba me yawan gaske,kinga wancan asibitin?Takalli asibitin"Eh Uncle.Da nanne
wajan da muke buga k'wallon k'afa.Sukayi dariya, Zuhair yace dama Baba kayi wasan
k'wallon k'afa?Eh Zuhair amma da ne.Yad'anyi tsallan murna"nima daga yau zan dage
in koyi buga k'walan k'afa.Yakalleshi da kulawa "a ah Zuhair bana maka sha'awar
k'wallan k'afa,na fiso kayi karatu sosai kazama"Cheif Judge"ko ka fasa zama alkali
me adalcin ne? Yakyalkyale da dariya yana bud'e idanun shi"Wallahi ban bafasa
ba.Yauwa Zuhair d'ina ALLAH yamaka albarka.
A inuwar barankacin k'ofar gidan Miqdad ya tsaida motar,yabi gidan da
kallo an gyara shi gwanin sha'awa,ba kamar zuwan da yayi watan nin baya ba,itama
Sumayya abin ya mata dad'i tana rik'e da hannun matar Yaya Miqdad Zainab suka shiga
gidan da sallama" Baban na ta kamar ko yaushe yana zaune shi kad'ai a tsakar gidan
yayi tagumi da duka hannayen shi"labarin zuciya a tambayi fuska,ranshi a 6ace
yake,yasa hannu ya share hawayan da ya zubo mishi sharrr...yana d'ago kai idanun su
ya had'u yamik'e da sauri da sauri cikin mad'aukakin mamaki"
Kasham...yanunata Kasham ke ce?
A sanyaye ta amsa"na'am Baba...
"Kasham kece nake gani haka? Halelujah suka rungume juna cikin
murna"naji dad'in ganin ki Kasham...
Hankalin ta yad'an kwanta ganin shima ya saki ranshi"Baba ai bamu
kad'ai bane...bata gama rufe bakin taba sauran suka shigo.yasake ta ya rungume
Miqdad yana shafa kanshi"My son sannnu ku da zuwa.
Miqdad yanuna mishi Alhaji Hafiz"Here is your elder brother sai suka
hau kallan kallo na wucewar wasu dak'ik'u aannan suka rungume juna suna ta
kyalkyala dariya kamar wasu kananan yara
Awunba wan Shedrak(Shedrak Dan'uwa na)
Alhaji Hafiz ya janye jikin shi yana gabatar mishi da sauran,duk aga
gaggaisa sai a k'arshe yasake nuna Salim wannan shine surukinmu mijjn Sumayya.
Salim yak'arasa wajan shi cikin girmamawa dan ya gaishe shi,sai kawai ya rungumeshi
cikin jin dad'i "Kaine karik'e mana yarinya da amana irin haka? Gaskiya naji dad'i
nagode,ALLAH yama auran ku albarka,ALLAH yaba ku zuri'a masu amfani.Salim ya
sunkwui da kai yana murmushi a ranshi yake amsawa da amin.
Daga wani d'aki suka fara jin wani irin tari matsanan ci, bayan tarin
yad'an lafa cikin galabaitacciyar murya aka fara magana"Baba dan ALLAH kazo kabani
ruwa" duk suka bishi da kallo
"Judith...
Abinda zuciyar Sumayya ke fad'a mata kenan. Tasake kallan Baban ranshi a
6ace yakesai kawai tashige d'akin Dammm... zuciyar ta tayi wata rin bugawa da
k'arfin gaske tayi mutuwar tsaye,numfashin ta yatafi wucin gadi na wasu yan
dak'ik'u Judith ce a kwance marabanta da k'warangwal ya mushashshiyar fatar data
rufe kasusuwan jikinta sai kuma numfashin da take yi.
Da rawar murya ta furta Kasham...sai lokacin Sumayya tadawo hayyacin
ta, tafara Istirja'i sai ta fashe da kuka ko ba a fad'a mata ba ta sani cutar
k'anjamau ce, tunda dama ba abinda take yi sai yawan ta zubar... Judith ta tare
ta"Kasham kar ki zubar da hawayen ki a banza ni ai tawa ta riga ta k'are, taimake
ni kawai da ruwa yau ban san laifin dana ma Baba ba,gaba d'aya yaki shigowa d'akin
nan.Takalleta wa yake jinyar ki?
A hankali tace Baba.Tazuba mata idanu"Kin tafi yawan ta zubar d'inki kin
manta da kowa a lokacin dakike cin duniyar ki da tsinki, ko gida bakya zuwa sai
lokacin da kika bushi iska kizo zuwan asha ruwan tsuntsaye ki k'ara gaba,sai yanzu
da kika ga mutuwa zaki dawo ki d'orama Baba abinda baiji ba bai gani ba?Tasake
fashewa da kuka al'amurar rayuwar su ta taci barkatai da suke yi hankali kwance ya
dawo mata, itama ba wayo da dabararta ne ya ku6ubtar da ita ba,ALLAH ne kawai
yamata wannna gata da suturar da yanzu itama tana nan tana wannan kwamacalar.
Kukan Sumayya daya tsanan ta ne yasa suka shiga d'akin dan gane ma
idanun su abinda yake faruwa.Adai-dai lokacin kuma zawo ya 6alle ma Judit tana
kwance kamar gawa sai k'arni da wari daya cika d'akin.
Baban yabiyo su"dan ALLAH ku fito kubar wanna yar iskar yarinyar kar
ku kwashi cuta,dan Sumaya tana jin k'arnin zuciyar ta ta tashi,tafara kelaya
amai.Yakaisu D'akin- shak'atawar gidan kome atsare yake mayan kujeru da carpet
ruwan k'asa sai kayan kallo a gefe da nu'urar sanyaya abubuwa(fridge) shima agefe
duk sun zauna jungun-jungun saboda ganin Judith, kowa da kalar tunanin shi akan
wani irin ciwo ne haka sannan me yasa ba a kaita asibiti ba? Me yasa Baban yake
cemata yar iska a irin wannna hali na rai kwakwai mutu kwakwai? amma banda Sumayya
da Alhaji Hafiz da suka riga suka san dawan garin.
Baban me fara'a ne shi yadinga jan su da hira har dai suka saki
jiki.Suna cin abincin da Hafsa ta girka musu yau an hutashshe da Kawunta.Dinatu
tahigo gidan cikin kwala kiran sunan Kasham...Kasham... Kasham..
Sumayya ta cire hannunta a abincin tana Istirja'i kafin tashigo Sumayya
ta mik'e, a k'ofar d'akin sukayi kaci6is,takalle ta sama da k'asa sai tayi
murmushi"Hail Mary...tarungume ta.Sumayya ta rintse idanun ta tana jiran saukar
dundu a gadan bayan ta amma bataji hakan ba, har suka saki juna tana dad'a k'are
mata kallo, wani kyau da annuri na musamman tayi"Sannu Kasham tad'an dafa
kafad'arta"na ji dad'in ganin ki suka shiga d'akin takalli Alhaji Hafiz"Sannu
Shedrak shima ya canja mata gaba d'aya to yaushe raban data sa shi a idanun ta
shekara da shekaru yayi kyau mijin ta kuma ya tsufa sai yaza kamar shine gaba da
Shedrak.Suka shiga gaggaisawa.Ranar dai suna cikin farin ciki musamma Dinatu ganin
duk wanda yazo musu sannu da zuwa sai ya yaba irin kyan da Kasham tayi kamar wacce
take zaune a wata k'asa,kowa na so yaga na shi cikin wadata.
"Lallai zaman Kaduna ya miki dad'i.Inji Lidiya.Sumayya tayi lallausan
murmushi"kawai kishirya kayan ki mutafi.Tagalla mata harara"ai ko da kikayi wannan
kyan banga abinda zai rud'eni in bar addinina ba.Itama ta galla mata harara"a ina
kike da addinin?Kina da maraba da pagan ne? Kasham kar fa ki zageni.Sumayya tasake
yin murmushi"come on Lidiya ni dake ai mun san gaskiya ko dan kawai d'aci gare ta?
Ba fa yau na sanki ba,na sanki farin sani kamar yadda kika sanni farin sani,ranar
Lahadi kina zuwa majami'a? Sai ta mik'e cikin borin kunya"bana zuwa kuna bazan je
ba sai kiyi abinda za kiyi dani.Tafice fuuuu tana surutai rubbish girl...tabita da
kallo haba yarinya ba abinda zanyi dake,za kuma ki dawo ne da k'afafunki.
Sumayya tasa mu Maman a d'aki, ta tazauna akusa da ita sannan tafara
rok'on ta "Mama dan ALLAH kiyi hak'uri kiya femin laifin dana yi, na san da ciwon
haka azuciyar ki.Cikin fushi ta kauda kai"bazan yafe ba ki tashi ki bani waje.Haba
Mama kiyi hak'uri kisa min albarka,ai har kwanan gobe ina sanki ina alfahari dake a
matsayin mahaifiya,dan kinyi d'awainiya me yawa akaina tun ina cikin cikinki har
kika haifeni, wallahi bani da abinda zan biya ki dashi.Tasake tuno girman hakkin
Y'aya akan mahaifansu musamman uwa da addinin musulunci yazo dashi kaico! Wanda ba
ya cikin musulunci wallahi yana cikin duhu me girma, inama-inama tana da wani iko!?
Da ayau d'in nan kowa na ta sai ya zama musulmi.
Takoma hannun ta Maman ta fizge da sauri"ke sakar min hannu mara jin
magana kawai"kiyi hak'uri Mama na miki alk'awari bazan sake 6ata miki rai har kiji
ciwon hakan ba Insha-ALLAH matuk'ar bai sa6a ma addinin musulunci ba.Tamata kallan
uku ahu"Shari'a law" bata amsa ba tafara kuka haba Mama yanzu bazaki yafe min ba?
Duk duniya bani da kamarki fa(In the whole wide world)
Takalleta cikin fushi"kin san da haka amma nace kar kiyi sallah sai
kika gudu wajan Shedrak har kina min k'arya wai an ma Tina Operation?Tagirgiza
kai"gaskiya ban yadda ba kin nuna min Shedrak ya fini.Ba haka bane Mama. Tasake
galla mata harara"to yaya ne? Tamarairai ce"Mama tafiya ta Kaduna wajan Uncle da
duk abubuwan da suka biyo baya"It's a destiny (K'addara ce) suka kalli juna Sumayya
tajijjiga kai "Ki yadda dani Mama wannan k'addara tace daban isa in kauce mata ba
no matter how,kuma ai gwamma tawa tafiyar sau dubu tunda gashi na dawo a cikin
hayyaci, koshin lafiya da kwanciyar hankali kuma kowa ya yaba,yayi sam barka to ai
ko Alhamdulillah.
To amma Mama Judith fa...? ran Maman yak'ara 6aci Sumayya
tacigaba"Judith ta tafi amma bata dawo a cikin hayyaci, k'oshin lafiya da kwanciyar
hankali ba, kuma kowa tirrr... da ALLAh wadarai yakeyi daganin ta, ba kuma wanda
yakuma damuwa da ita sai ku.Ba aure tayi ba fornication shine sana'ar ta" which is
forbiden"ba addinin daya yadda da hakan Islam ko Christianity sai dai san zuciya
kawai,san zuciya kuwa 6acin ta yau ga Judit a ciki kuma Mama...ta tare ta dasauri
ya isa haka Kasham jikinta yayi sanyi duk irin alwashin data d'auka ranar duk da
sukayi ido hud'u da Kasham sai ta nemi shi tarasa,gaskiya Kasham tafad'a sai ta
rungumeta"naya fe miki kome ALLAH ya albarkaci auran ki, wancan d'in shine
Julaibib?Tagirgiza kai tana murmushi"ba shi bane.. taba ta labarin duk abinda
yafaru da ita bayan barin ta gida.
Tazuba mata idanu"to ni me zance miki Kasham? Sallah ne dai kin riga
kin fara kuma ko na ce miki ki daina na san bazaki daina ba, kuma ma ban miki
adalci ba,tunda duk a cikin Ya'yana dana haifa daga ke sai Rahab da Bitrus kune
kawai masu jin magana, kune kuka maida hankali a karatu gashi nan kuma kune rayuwar
ku tayi kyau,yanzu Bitrus shine personal manager a Bajju Community Bank(BCB) Rahab
ta gama karatunta har ta fara aikin ta a asibiti, anjima kad'an za ta dawo gida
tunda aikin rana wannan makon takeyi,ke kuma gashi kinyi aure hankalin ki akwance
kuma kina cigaba da karatu.Rahab d'inma ta kusa yin aure.Sumayya tana ta godema
Ubangiji daya sauk'ak'a kome fiye da zatan ta, tasaki jiki sunata hirar yaushe gamo
suna kyalkyala dariya "Da da mahaifa sai ALLAH.
A babban D'akin-shak'atawar gidan suka yi jam'in sallar su saboda
k'auyan gaba d'aya ba masallaci tunda babu me sallah.Suna jam'in sallar Isha'i
Rahab ta shigo da d'okin ganin Kasham dan tun a hanya tasamu labarin zuwan su,
d'agowar su daga ruku'u Rahab ta tafi zata rungume ta Maman ta dakatar da ita"Ke
Rahab karki ta6a ta baki ga sallah suke yiba?.Taja da baya da sauri"Oh Basakut"ta
tuna idan suna sallah ko magana basa yi.Tajingina da bango tana kallansu"yadda suke
tsayuwa,suyi ruku'u su d'ago, su tafi sujjada,su d'ago,su sake komawa sujjada suyi
zaman tahiya har zuwa sallama kowa yafara karanta azkar d'in bayan kowace sallar
farilla.
Cikin murmushi tajuya wajan Rahab. Rahab takama ha6a cikin mad'aukakin
mamaki tayi tsalle ta rungumeta tana ihun murna Jesust Christ Halelujah"Kasham kece
kika zama wata big madam?What a suprise, ta daki kafad'arta"tell me the
secret.Sumayya tashafa wajan"gaskiya fa akwai zafi"suka kyalkyale da dariya.Rahab
ai kema kin canja kinyi kud'i fa"mint note"suna shiga asusun ajiyar ki duk k'arshen
wata suka saki juna. Rahab tasake binta da kallo daga sama har k'asa gaskiya
canjawar da nayi ba irin wacce kika yi bace"wonderful"tashafa kyakkyawar fuskar ta
data ke ta hasken musulunci da Imani"wannan irin kumatu da kika fara ajiyewa ga
fari, ni dai ko shafa man sa fari kika fara ne?(bleaching)Ba Sumayya ba hatta
sauran sai da sukayi dariya dajin yadda Rahab taketa kod'a ta.Tazauna suka gaisa
d'aya bayan d'aya take tamabayar Sumayya sunayan su.Salim yabisu da kallo ga dukkan
alamu suna san junan su suna da kirki dama Sumayya tafad'a mishi Maman suce kawai
sai a hankali to itama bata nuna kome ba banda farin ciki da ganinsu.
Sumayya,Hafsa,Zainab da Rahab su suka gyarama Judith jiki da d'akin
dayake ta k'arni kudaje sai budiri sukeyi,tana kwance cikin hawaye"wallahi da ace
zan warke babu abinda zai hanani binku Kaduna in zama musulma.Hafsa ta amsa da
sauri "ai ba dole sai a Kaduna ba, ko yanzu za ki iya k'ar6an musulunci.Wani dad'i
yakama Sumayya.Ki yadda ki amince kina da rabo ne. Judith ko baki warke ba ALLAH
zai kar6eki a haka Tagirgiza kai "uh uh ku kyaleni kawai dan bazan iya sallah ba
tunda k'arfina ya riga ya k'are.Sumayya takalleta cikin natsuwa"ai addinin
musulunci sauk'i gare shi Judit, ba dole sai a tsaye ko kina da k'arfi a gangar
jiki za kiyi sallah ba matukar akwai lalura ko a yadda kike akwancen nan akwai
yadda za kiyi sallah.
Rahab tagalla musu harara sannnan taja dogon tsaki"addinin
ta'addancin kike sha'awa Judith?Tamik'e a zuciye zata bar d'akin Sumayya tarik'o
hannunta.Rai a 6ace tace "malama sakarmin hannu kishiga hankalin ki fa.Tagyad'a kai
sannan tasake kallan ta ckin natsuwa"to kiyi hak'uri kizauna magana za muyi Takoma
ta zauna fuska a yamutse.Shiru ya ratsa d'akin na wucewar wasu dak'ik'u. Tad'ago
kai a zuciye"bana san wawanci fa, ke nake sauraro kin kuma yi shiru.To ai naga
ranki a6ace yake shi yasa nayi shiru har sai kin d'an huce karr in k'ara miki
zafi.Tamik'a mata lemon biyar a raye(five alive)d'an jik'a mak'oshin ki mana.Kasham
I'm I your toy to play with?Tayi yar dariya "absolutely no kiyi hak'uri, amma ina
so ki sani addinin musulunci ba addinin ta'addanci bane,addinin sauk'i da salama nw
ga mabiyanshi.Tawatsa hannaye "ahab...ba cinya ba k'afar baya"ko d'azuma abinda
wani musulmin ku Adam yagama fad'a min kenan awajan aiki.Nidai banga dalilin da zai
sa inyi sallah ba,ina da yanci bazan koma inda bani da wani yanciba.
Zainab ta tareta da sauri"ai ko addinin musulunci shine yabaki cikakken
yanc me lasisi ma, musamman a matsayinki na 'ya mace,kina da yanci kamar yadda
namiji yake da yanci,sai dai mu addinin mu, duk da yancin daya k'wato mana ya nuna
mana namiji shine a sama da mace,idan banda addinin musulunci wa yake girmama 'ya
mace ne?
Rumawa da suke kiran mace"Devil" shaid'aniya? Wai mace shaid'aniyace ana
neman tsari da ita kamar yadda ake neman tsari da shaid'an.
Persia su kuma sun d'auki mace wulak'antacciya k'asa da duk wata halitta
wulak'antacciya.
Yahudawa su kuma sun d'auki mace kamar baiwa,da zatai tama namiji hidima,
ita kuma ba ta da wani hakki akan namiji
Zamanin jahiliyyar larabawa kuma idan aka haifi macen sai ma adinga zuwa
maka jaje kai kuma kana 6uya,amata rik'on wulakanci,ko kuma tanaji tana gani da
ranta da lafiyar ta a tona k'asa abinneta.
Wanne daga cikin wad'annan suka ba mace yan cinta?
To a duniyar musulunci da gidan musulunci ne kawai mace take yar ga ta,yar
lele, sarauniya kome yi mata ake yi,kome kud'in ta k'wandala na ta na k'ashin kan
ta sai ta ga dama za ta kashe.Duk masu yeekuwar yan cin mata indai ba wannan da
addinin yabasu bane to wallahi k'arya ce,haushi suke ji, suna so ne ku fito ku sha
wahala.
Rahab ta ta6e baki"ni kalaman naki duk a matsayin tazo muji ta tawuce ta
bayan kunne na d'aukesu. Sumayya tagirgiza kai"ai ko sun wuce tazo muji ta tawuce
ta bayan kunne wallahi.A baya dana ke kamar ke ina fad'in haka, amma a yanzu dana
san hak'ik'anin musulunci ai na san k'arya ce. Rahab kije kiyi bincike ki ga ne
menene addinin musulunci na gaskiya da abinda ya k'unsa,ba abinda kike ganin gama-
garin musulmai suke aikatawa ba, ba abinda kike karantawa a mujallu da jaridu ba,ba
abinda d'ai-d'ai kun mutane suke fasara musuluncin ba,kije kiyi karatu da bincke a
cikin littafan musulunci,ki saurari preaching da luctures d'in malamai,ba abinda
wasu gur6atattun musulmai da rashin ilmi ko san zuciya yake musu jagoranci ba.
Musulunci bai yadda da ta'addanci ba ko misqala zarratin,kuma duk wanda
yake fakewa da musulunci to gaskiyar magana san zuciyar shi yabi... Rahab ta tari
numfashin ta"za ki fad'i haka mana tunda kema kin zama musulma..."Eh zan fad'i haka
dan na zama musulma na kuma san d'an abinda ALLAH yanufe ni da sani na daga
ilmominshi.
Rahab barin baki misali Christianity bai yadda da shan giya da karuwanci
ba,hakane? Rahab tagyada kai.Takalleta cikin natsuwa"to yanzu abinda Alhamdu da
Judith suke yi sai ace addinin Christianity ne yace suyi?Sai taki magana. Sumayya
ta d'an motsa kafad'a kin gani ko? To kamar haka addinin musulunci yake.Ki yadda
kawai Rahab ki kar6i musulunci wallahi sai kinfi jin dad'in rayuwar ki.Ta ta6e baki
tana hararar ta.
Sumayya tagyad'a kai tana murmushi "ALLAH kuwa gaskiya nake fad'a miki
tabi hotunan d'akin da kallo kin gani,ko Jesus da Mary irin shigar musulunci suke
yi a duk irin hotunan da zaki gani an za na su.Tajawo wata mujallar "Jehovah
Witness"tana bud'e shafukan ciki Zainab da Hafsa kuzo kutaya ni gani a duk shafukan
ciki kunga me"mini skirt da strap top kai ba d'ankwali? Suka kar6i mujallar suna
dad'a gani,bayan sun gama dubawa Zainab tagirgiza kai"har shafin k'arshe ba
bu,kowacce cikin mayalwacin kaya da lullu6i.Sumayya tace"to mazan fa"?Hafsa tace
"suma suna cikin dogayan kaya ga gemu da k'asumba wasu ma har da rawani.Suka zuba
ma Rahab idanu.Kingani ko?Wannnan shi yake nuna miki addinin gaskiya mukeyi"ai ko
Annabi Isah Alaihissalam Jesus d'in musulmi ne.
Judith cikin hawaye tace"wallahi na yadda daku.Zainab takalleta cikin
natsuwa" to ki kar6i musulunci mana.Tagirgiza kai"I seek repent from God and I know
he will forgive me.Hafsa takad'a kai cikin damuwa.Sumayya tadafa kafad'arta karki
6ata ranki"dan shiriya ba ta wajan kowa face mahaliccin mu,shi yake shiryar da
wanda yaso a lokacin daya so.Tajijjiga kai "wannan gaskiya ne Yaya Sumayya.Haka
suka kwanta zuciyoyin su ba dad'i kowacce da irin tunanin ta musamman ganin yadda
Judit tazama "k'ashi da rai.Ubangiji kamana kyakkyawar k'arshe.
A sanda hantsi yadubi ludayi tana zaune a inda tayi sallar walha kiran
Salim yashigo tad'aga tana dariya"Humm mijina na wa nakai na.Yataya darawa "Sumayya
ta tawa ni kad'ai fito waje muyi hira.Yazuba mata idanu har ta zauna a gefen
shi,tabi wajan da kallo "wai kana nufin anan zamu zauna?Mushiga gida mana.A ah
gwamma muyi zaman mu anan,mu shak'i natural air, ta tacciya me kamshi kinga turawa
sun mana wayo sai su tafi "Bar beach"suje su shak'i iska tatacciya dan jikin d'an
Adam yana buk'atar hakan,wajan da ba hayaniya kayi refreshing d'in gangar jiki,
zuciyar ka da k'wak'walwarka.
Nayi kewarki fa.Tabud'e idanun ta data rufesu tamishi wani kallan k'auna
me cike da shauk'i"nima haka"sai sukayi dariya.
Salim...
Takira shi a hankali. Yakalleta... Tagyad'a kai"samun masoyi na gaskiya
shine buk'atar kowani d'an Adam,masoyi me amana, masoyi me girmama abinda masoyin
shi yake so matuk'ar ba sa6on ALLAH bane,masoyi me k'ok'ari da jikinshi,da kalaman
shi, da aljihun shi, da lokacin shi wajan ganin masoyin shi ya samu abinda yake san
samu"Godiya ta tabbata ga Ubangijin mu a kowani hali da yanayi. Wallahi ba ka da
abokin tarayya a irin k'auna da soyayyar danake maka.Yayi Murmushin jin dad'i"Ina
alfahari dake nagode Ubangijin mu daya mallaka min ke a matsayin mata"Sumayya ALLAH
yamiki albarka ya lull6emin ke da rahamar shi.Kwanan su hud'u suka musu sallama
suka koma Kaduna garin gwamna.
Yau da gobe karyar ALLAH kome gudun ka sai ta ka mo ka.
Tsufa labari...mutuwa k'arar kwana.
18 Jumaada Awwal 1441
13 January 2020
We Ibrahim's Daughters👇
Asdilat KD...2geda with Ra'ibs
DANGIN NONO WRITERS ASSOCIATION
{Da Inganci Mukayi Fintinkau}
Bismillahi wabihi nasta'in
...GWAJIN DAFI💔
Almost true story
Daga alk'alamin🖊
Ya'yan Ibrahim
Saudat A.Baba (Asdilat KD)
Da
Bara'atu Ibrahim (Ra'ibs)
Shafi na goma sha hud'u
Zaman su lafiya cikin girmama juna. A yanzu fatansu bai wuce ganin
Sumayya ta sauka lafiya ba.Tana kwance a doguwar kujera da yammacin tana ta
nazarce-nazarcenta,tsohon cikin bai hana ta yin wasu abubuwan ba,taji muryar
Mamanta.Wayyo!zama dak'yar ta shi da dabara kafin ma tayi yunk'urin ta shi ita ta
shigo.
"Oyoyo Mama sannu da zuwa...
Da har na cire rai da zuwan ki. Taje ta d'auko ruwa da kanta
tasha"Haba Kasham ya za ayi in k'i zuwa, bayan ni nace miki zan zo,kin san yanayin
taran na mune yanzu haka ma sun tafi, ni a motar haya zan koma gida.Tabita da
kallan tausayi"Sannu Kasham ALLAH yasauke ki lafiya, kwanaki ina ta mafarki wai kin
haifi 'yan biyu. Tad'anyi murmushi kawai suka cigaba da hira.
Wannan karan bazan bar Kaduna ba har sai kin kaini gidan
Shedrak.Tagyad'a kai"to Mama"takira Salim a waya dan baya gari.
"An ya Sumayya zan barki kifita kuwa? Ba likita ta ce banda yawan
zirga-zirga ba?"Na sani kuma ban manta ba,dama Yaya Miqdad zan kira a waya yazo
yad'auke mu.To idan baya kusa ko yana wani uzirin na shi baza ki takura mishi
ba?"karka damu ai ta mu dashi bata 6aci,zan nemi alfarma na kuma san za a min.To
shikenan ALLAH yatsare,kiyi zaman ki acan,nima Insha-ALLAH zuwa bayan Isha'i zan
shigo sai inzo in d'auke ki.To nagode"ALLAH yak'ara tsare hanya yadawo mana da kai
lafiya.Amin Sumayya nima nagode.
Makonni biyu da tafiyar Maman ta haifi kyakkyawar 'yar ta sunyi murna
sosai dan ba a samu tangard'an kome ba,ranar suna yarinya taci sunan mahaifiyar
Salim d'in da tadad'e da rasuwa Ruqayya suna kiranta da Ummi.Gidan Alhaji Hafiz
takoma Maman Hasan tana kula dasu yadda yakama ta,jegon ya kar6esu dan sunyi shar
dasu saboda cimar abincin me amfani me gina jiki da k'ara kuzari ai shine jego
"Abincin ka lafiyar ka...
Cikin wani dare tana tsaka da bacci kiran Mama yashigo tad'aga cikin
fargaban abinda kunnuwan ta za suji dan ta san tabbass ba lafiya ba.Kasham Judith
ta mutu tafad'a tana kuka "lallai soyayyar d'a da mahaifa sai ALLAH"kalli irin
wahalar data basu amma Maman take wannan kukan?Itama mutuwar tadake ta,duk da sun
san k'arshen alewa k'asa.To amma ai ba yadda za suyi dan mutuwa dole ce ko mutum ya
yadda ko bai yadda ba idan ajali yazo to fa silke baya tarewa, Kukan mutuwa kuma ba
ya dawo da matacce.
Babu addu'a tsakanin musulmi da kafiri dan haka sai tashiga rarrashinta
da kalamai masu dad'i har tasa mu tayi shiru"nagode, ALLAH yamiki albarka bawanda
yakwantar min da hankali sai ke"To za kuzo funeral service d'in ne?A ah Mama ba
wanda zai zo kuyi abinku,amma Insha-ALLAH idan mukayi arba'in za muzo ai.Shikenan
sai da safe takatse wayar.Tun daga nan har garin ALLAH j'arasa wayewa Sumayya bata
kuma rintsawa ba,sai juye-juye take tayi da tunani barkatai daya cika
k'wak'walwarta.
Suna hirar su da Hafsa a D'akin-shak'atawa sukaji sallama tare da
k'wank'wasa k'ofa.Hafsa tabud'e k'ofar tana amsa sallamar. Yana tsaye tad'anyi
murmushi"au kaine tabashi hanya bismillah shigo "cikin ladabi yadurk'usa har k'asa
yana gaishe da Sumayya.Tagirgiza kai" tana nuna mishi kujera"ta shi ka zauna meye
na durk'usan? Bai zauna a kujeran ba sai yayi zaman shi a carpet d'in yana d'an
murmushi"ai nan d'in ma yayi.Mamana bata nan ne?Hafsa tayi yar dariya "Aikuwa dai
Maman Hasan yau tayi nisan kiwo tana can wajan tsoho me ran k'arfe Malam Muhammad
Aminu.
Alhassan d'aya daga cikin yaran da suke zama ma Salim a kasuwa ne, yaro
ne me hankali da sanin ya kamata,tunda yaji sunan Maman Hassan shikenan yake ce
mata Mamanshi, shi kuma Usainar shi ta rasu tun suna k'anana. Itama Maman Hassan
tana yi dashi sosai indai yazo tana gida to sai ta san abinda tabashi kome
k'ank'antar shi, tun yana jin nauyi baya kar6a har ya saba dan takance"Kai Alhassan
anya wannan Mamana da kake kirana ba a fatar baki kawai ya tsaya ba? Uwa ta ta6a ba
d'anta abu yaki kar6a? Tun daga nan yaba ta hak'uri idan tabashi sai yasa hannu
biyu yakar6a yayi godiya.
Ya ajiye ledar hannun shi a gaban Sumayya"Alhaji ne yace in kawo.Wai ya
kira layinki ya k'i shiga,sai bayan la'asar zai shigo.Bakome Alhassan,nima ina ta
kiran shi bata shiga akwai matsalar sadarwa yau"kace ina gaisuwa sai ya zo
d'in"Yamik'"Zai ji"yad'an kalli Hafsa "idan Mamana ta dawo nima amik'a min sak'on
gaisuwa zan dawo ranar Juma'a musamman dan in gaishe ta.Tagyad'a kai" tam za
taji"sukayi sallama.
Tana gama wanka suka tafi Zonkwa ita da Hafsa sun sauka lafiya kowa yayi
murnan ganin su.Kwanan su biyar da tafiya da yammacin ranar sai kawai ganin Salim
suka yi.Takalleshi cikin kulawa da mamaki"ba ranar Alhamis mukayi da kai za kazo
ba?Yamayar da kanshi jikin kujerar"ranar alhamis ne amma na ka sa daurewa ne,amma
yanzu ai hankali na ya d'an kwanta danazo na ganku"gobe kenan za ka koma? Yabud'e
idanun shi daya fara rufewa yakalle ta da sauri"wai kina nufin tafiya zanyi in
barku? Tagyad'a kai"haka nake nufi ga waya muna magana da juna.Yad'an harareta"kina
wasa ne ko?Wani irin wasa kuma?Ai naga kwana goma kaba mu to yau munyi biyar ba
saura biyar ba?
"Sumayya...
Yakirata...suka zubama juna idanu na wucewar wasu dak'ik'u yasauke
numfashi yasa hannu yana yata6a kirjinshi dai-dai saitin zuciya "kina so na kuwa?
Takalleshi baki a bud'e saboda mamakin furucin shi"haba Baban Ummi me yasa za kamin
irin wannan tambayar?Yad'ora hannayan shi a saman tebur "saboda kince gobe zan tafi
ma'ana ni kad'ai? Sumayya akwai ayyuka masu yawa agabana amma naturesu gefe duk da
mahimman cinsu naza6i zuwa wajanki,sai dai kash...hak'ata baza ta tadda ruwa ba,
dan na ga kina so ki watsamin k'asa a cikin idanu.
Tad'an 6ata fuska ni dai gaskiya... Yatari numfashin ta"haba Sumayya ta
tawa ni kad'ai yad'an d'age gira"bazan iya hakurin jure rashin ki bane,magana awaya
kad'ai ni dai bata gamshe ni ba shi yasama kika ganni ganin idanunki yamata wani
kallo"mhm me kika ce ne?
Tasunkwui da kai"haba Sumayya yi magana mana,Salim mijiki ke kad'ai ne
fa.Tad'an harareshi bayan kace ba alk'awari kad'auka ba,dan dai dole sai ka k'ara
auren nan.Yagyad'a kai"gaskiya banyi wannan alk'awarin ba,kar baki yaci idanu su zo
suna jin kunya.Tace"Uhhh madallah to yanzu kake so mutafi?A ah ai yamma ta yi kuma
kinga Mama bata dawo daga kasuwa ba dole ai sai mun mata sallama, gobe da sassafe
sai muwuce.
Sumayya takoma makaranta dan hutun da aka basu ya k'are,karatu sosai
sukeyi ba kama hannun yaro saboda wannan shekarar za su gama.Sumayya ba ta da wata
gagarumar matsala a bangaran karatu duk abinda bata gane ba, to tana dawowa gida
Salim zai warware mata shi,bata ta6a sanin me tarin ilmi bane sai bayan auransu
data shiga wani d'an d'aki dayake yin nazari da bincike wallahi tasha mamakin irin
tarin littafan addinin data gani.bai ta6a nuna mata ya san wani abu ba sai da zama
yahad'asu. Salim jarumine me damuwa da damuwar iyalinshi.
Suna hirarsu a D'akin-shak'atawa cikin nishad'i yajuyo kukan Ummi daga
d'akin baccinsu ta tashi daga bacci kenan, yaje yad'auko ta,yabata ruwan zamzam
d'in da suke bata tasha ya mik'a mata ita" ga ta ki bata abincin ta yunwa take
ji.Tamarairaice Sumayya a wajan shayarwa ba ta da jarumta"kai ma ka san daga ta
shinta a bacci baza tasha ba.Yagalla mata harara"ba yunwa take ji ba amma take ta
k'ok'arin kai hannuna bakinta? Kar6eta mana.Tamika hannu ta kar6eta Tad'an 6ata
fuska"ai ban san kana harara ba sai na ga idanun a k'asa.Yayi yar dariya"Hunn
Sumayya ta ke dai bata abincin ta kawai ba na san neman magana.
Sun gama karatu lafiya kuma sakomako yayi kyau Malam Muhammad Aminu shi
yasamo mata gurbin karatu a Jami'ar Madina dan babban d'anshi a can yake da zama
shi da iyalinshi Salim shi yanemi wannan alfarmar kuma aka mishi amma ba da san
zuciya ba, a ah adadin makin da suke nema to na Sumayya ya kai...anata mata shirin
tafiya inda zataje ta yi Masters a kan dai Islamic Studies.Kamar wasa tafara rashin
lafiya yau ciwo gobe sauk'i,suka tafi asibiti aka mata gwaje-gwaje har aka gano
abinda yake damunta ciwon siga(diabetes) amma sun d'ora ta akan magani da wasu
sharud'd'ai da dole sai ta kiyayesu in dai tana san zaman lafiya,kuma sun bata
kwanakin da zata sake komawa asibiti dan su tabbatar magungunan suna aikin da ake
so ? Idan basa yi sai a canja wasu.
Abokan karatunta kullum suna tafe, basa gajiya da zuwa gaisheta saboda
halinta na karamci "masoya da mak'iya ba a guzurin su duk inda kaje halin ka zai ba
kasu"abun hannu ta bai ta6a rufe mata idanu ba.Ranan Salim yakalleta "yaushe na
baki kud'in da har za kice sun k'are Sumayya?Tad'an marairaice"Baban Ummi ni dai
dan ALLAH kataimake ni kawai,akwai wacce mukama alk'awarin ba ta tallafi a
k'ungiyarmu ni wallahi na manta,anjima za tazo k'ar6a ai da bazan kashe wadan can
ba aciki zan bata" haba nijina duk abinda kaba wani shine na ka,wanda kaci kashi
yake zama,wanda kake ajiyewa ba lallai kai d'in ne za kayi amfani dashi ba, wata
kila sai dai magada su gada.Alheri dank'one da baya fad'uwa k'asa banza.
Yak'irgo adadin data fad'a yabata"ina sanki Sumayya ta tawa ni
kad'ai"Tasa hannu biyu takar6a nima haka mungode madallah Ubangiji yak'aro bud'i.
Yad'an d'age gira yana mata wani kallo. Tagyad'a kai"Eh mana you're a good
samaritan"Yad'an bata marin soyayya suka kyalkyale da dariya.
Abu kamar wasa k'aramar magana ta zama babba,ciwo ya tasa Sumayya a
gaba, kullum magani akeyi ciwo yana dad'a k'aruwa, watan ta d'aya cur tana kwance a
gadan asibiti sannan tad'an dawo hayyacin ta,ita tamatsa aka sallame ta tare da
k'arin wasu sharud'd'ai da zata kuma kiyayewa dan ta zauna lafiya.
Yazuba mata idanu bacci take yi, tayi bak'i ta fita hayyacin ta,shima
wallahi jinshi yake kamar mara lafiya.Yadad'a rungume Ummi da take bacci bayan ta
gama rigimar a bata abincin ta kuma an yaye ta,ya had'a mata shayi amma tak'i
sha,dak'yar dai ya rarrashe ta takoma bacci sai ajiyar zuciya take yi.Ya sauke
gwauran numfashi "ALLAH yabaki lafiya Sumayya,ALLAH yasa kaffara ce".
A hankali tabud'e idanun ta takai hannu tana d'an shafa kan Ummi sannan
ta kalleshi "sannu Baban Ummi wai har yanzu baka fita ba?Yakad'a kai"Kayyah...
Sumayya duk inda naje tunanin halin da na barki bazai barni inyi wani sukuni ba.
Amma ai yau naga jikin na ki da sauk'i ko?To me za ta ce? Ita kad'ai tasan azabar
ciwon da take ji,ba tasan yawan k'orafi tunda yana matuk'ar k'ok'ari da
jikinshi,aljihunshi,kalamanshi da kuma lokacin shi, duk tsadar magana bai ta6a nuna
gazawarshi wajan siyo mata shi ba, haka irin kalar abincin da akace shi zata dinga
ci dayawa yasiyo mata ya ajiye. Tad'an yi yak'e dayafi kuka ciwo"Alhamdulillahi ala
kulli halin".
Ummi tasa hannu a baki tana tsotsa cikin dabara yazare hannu sannan ya
kwantar da ita yana tambayar Sumayya abinda za taci da rana duk da a yanzu cin
abincin na ta,ba wani na azo a gani bane,wasu lokutan ma sai yanuna 6acin rai
sannan take d'an tsakura.
Salim...tabishi da kallo yazauna a gefen gadan yana kallanta shima ya
d'anji mamakin kiran sunan shi da tayi yanzu kai tsaye.Yarik'o hannayan ta yana
kallan yadda tafin ciki ya d'ashe kamar mara jini amma ko d'azu da safe Doctor
Zainab ta tabbatar mishi tana da jini dai-dai yadda ake so baiyi kad'an ba"Uhun me
kike so kifad'a min ne?Sharrr...sharrr...wasu hawaye masu d'umi suke zubo
mata"muryar ta tafara rawa"ni dai nagode ma Ubangijin mu daya min gata da samun ka
a matsayin miji. Ina san ka Baban Ummi...tamishi wani irin kallo da yasa zuciyar
shi bugawa da k'arfin gaske.Yakauda kai "Sumayya me za kici?Yasake tambayar ta.Kar
ka damu zan sha shayi.Yasa hannu yana share mata hawayen"ki daina kuka ALLAH zai ba
ki lafiya mukoma cin had'ad'd'an abincin ki me rai da motsi.Tabishi da kallo cikin
kissima wani irin yanayi a zuciyarta.Hawayen suka sake zubo mata sharrr...idan
tafad'a mishi yadda take ji a cikin jikinta tayar me da hankali za tayi zai rasa
sukuni dan haka taja bakinta tayi shiru.
Ranar da taje gidan Alhaji Hafiz suka wuni suna hira sai bayan isha'i
yazo ya d'auke su.Sun kwanta lafiya lau cikin farin ciki sun dad'e suna hirar su
kafin bacci yayi awan gaba dasu, amma cikin dare nishinta metsananin k'arfine
yafarkar dashi daga bacci, yakunna wutar d'akin tana kwance cikin mawuyacin hali.
Sumayya...!ko kallanshi ba tayiba, dan ba ta cikin hayyacin ta ne, idanunta sai
rufewa da bud'ewa suke yi kamar wacce tasha kayan maye ta bugu sosai,bakin ta a
bud'e ya bushe k'amas,ta rasa inda za ta tsoma ranta taji dad'i sai tafara wata
irin shak'uwa,a gigice ya d'auko ruwa yana bata amma bata iya had'iya ba haka yake
biyo gefen bakinta yana zubewa tana wata irin jijjiga... Sumayya...! Yafara girgiza
ta Sumayya kalleni...!Ina hankalin ta baya jikinta tana gargara..."Laahaula wala
quuwata illa billah "kome na ta ya saki a hankali tafara jan numfashi me tsawo sai
ta sauke shi a hankali,sai takuma janshi sai yayi kamar ya tafi bazai dawo ba zuwa
can sai ta sauke shi a hankali, haka tadingayi,yakwantar da ita yafara neman
makullin motarshi amma tsabar rud'ewa wallahi sai yarasa a inda ya ajiyeshi,a fizge
tafara kalmar shahada abinda yadad'a gigitashi kenan...zuwa can kuma kamar anyi
ruwa an d'auke sai yaji d'ifff...
Sumayya...!yakira sunanta da k'arfi yata6a kirjinta difff...Numfashi
baya shiga da fita...Sumayya! Yad'aga hannun ta na dama yarafff...yafad'i a kan
katifa.Abubuwa da yawa suka yamutsa k'wak'walwar shi bangaran tunani sai yaji
ruguzowar wani abu a k'ahon zuciyar shi da k'arfin gaske Dammm...!!!
Ta mutu...!Sumayya ta mutu...?!!!
Sai yafara k'arya ta zuciyar shi dan idanun sun fara mishi gizo sun
nuna mishi ga tanan tana numfashin ta"Sumayya au dama baki mutu ba? Yasake kallanta
idanun ta a k'ak'k'afe ruwan ciki yak'ame k'amas suna kallan sama tayi tsawo da
wani irin kyau na ban mamaki shi bai ta6a ganin wannan kyan ba ko lokacin da take
ganiyar lafiyar ta take kwalliya da gayu...bai san awani yanayi yake ba har sai da
aka kirashi a waya.
Miqdad ne yake tambayar shi lafiya kuwa ban ganka a masallaci sallar
asubahi ba,ko jikin Sumayyan ne?Asanyaye yace"Sumayya ta mutu.Cikin k'araji Miqdad
ya sake tambayar shi"ta mutu? Yaushe?Wasu irin hawaye masu d'umi suka zubo mishi
sharrr...sai kawai ya katse wayar yakifa kanshi a kusa da fuskar ta, ya rasa abinda
yake mishi dad'i sai yafara Istirja'i...Miqdad shi yaje gida yad'auko su Alhaji
Hafiz suka d'unguma gaba d'ayansu zuwa gidan hankali a tashe.Amma Salim yayi
dauriya dan shi yamata wanka yashirya ta tsab aka mata sallah aka d'auketa a makara
sai makwancinta na gaskiya kabari d'aki a cikin kasa"Uh uhun duniya rumfar
kara...Wata rana zai fad'i.ALLAH yajikanki Sumayya yasa k'arshen wahalar kenan!
Lokaci d'aya Salim yayi wata rin rama kamar wanda ya shekara yana
jinya.A ranar Iyayanta suka zo.Maman tana kuka ta rungume Ummi tana sambatu "Holy
Jesus why? Why? Me yasa Kasham za ta mutu yanzu? Me yasa za ka bari a kashe min
yarinya...To wallahi bazan ta6a yafewa ba...me Kasham ta tare muku ne?
Alhaji Hafiz ya k'araso wajan da sauri "haba Dinatu ya kike irin
wannna kalaman ne? Mutane fa za suyi zatan kasheta akayi.To dama ba kasheta akayi
ba? Kaima ai ka sani ko har ka manta tunda ba 'yar ka bace? Yakad'a kai cikin
damuwa"ko na sani a yanzu dai na manta,mudai a addininmu na musulunci duk wanda
yamutu to tabbaci hak'ik'a kwananshine kawai yak'are, amma ba mayune suka kashe
shiba "ai sara da sassak'a basa hana gamji toho...a ah Shedrak wallahi Kasham dai
kashe min ita akayi, ba ta zo sun ganta cikin rufin asiri ba?Takuma yin kururuwa
cikin tafasar zuciya"Wai...Wayyoh...ALLAH!!! Kasham ta mutu...Judith ta mutu...oh
Jesus Christ of Nazareth!
Shedrak!
Tazuba mishi jajayan idanun ta da suka rine da 6acin rai tadad'a
rungume Ummi"bazan yafe ba. Yagyad'a kai"to naji amma dan ALLAH kiyi hak'uri da
kukan nan muje ga abincin ku can kije ki k'arya.Bana ci, tasa gefen zaninta tana
share hawaye da majina an kashe min Kasham an bar min grandchild cikin maraici...
for God sake Shedrak Ummi guda nawa take da zata iya d'aukar wannan tashin
hankalin?
Yakalli Ummin"tabbass Ummi ba ta san kome ba,bata ma san me ake kira da
mutuwa ba bare har yatashi hankalin ta,guda nawa take?Ko shekara uku batayi ba to
amma ya za suyi da hukuncin ALLAH?Yadda duk yaso haka yake zartar da hukuncin
shi"idan yaso yafitar da rayayye daga jikin matacce,idan yaso yafitar da matacce
daga cikin rayayye"Qaadiran alaa manyasha'u.Dak'yar yasamu ta yi shiru da wannan
sambatun da take tayi cikin kuka da d'aga murya.
Makon su d'aya sukayi shirin komawa k'auyansu Madauci,Maman ta so
k'warai abata Ummi ta tafi da ita amma Salim da Alhaji Hafiz suka bata hak'uri akan
hakan bazai yiwuba kasancewar addini ba d'aya ba.Salim ma yasake ba ta hak'uri tare
da alk'awarin kawo musu Ummi lokaci zuwa lokaci suna ganin juna.
"Mutuwa ba ta zama masifa ga mumini,mutuwa hutuce ga wanda yadace da
kyakkyawar makoma...ALLAH ba yana nufin 6atama bawa bane dan ya d'auki wani bangare
najin dad'in shi Iyaye, mata, miji,Ya'ya da yan'uwa.. Alhaji Hafiz yadafa
kafad'arshi "Salim...na san kai namiji jarumi ne,to na rok'eka da girman ALLAH kayi
hak'uri kaga yadda kazama kuwa a yan kwana kin nan? Sumayya ta riga ta tafi
rayuwarta ta doron duniya ta riga ta k'are,ba abinda take buk'ata awajan mu yanzu
sama da addu'a...Addu'a itace abincin mumini...to mu yawaita aika mata dashi.Kaima
ka natsuwa kacigaba da zuwa kasuwa ALLAH yabaka macen albarka.Yahad'iye wani abu me
d'aci dak'yar yayi furucin" nagode Alhaji ALLAH yak'ara girma...
Ummi tana gidan Alhaji Hafiz dan shi yanemi wannan alfarmar,amma Salim
ya dai basu ita dan kawai sun cika mishi idanu ne,saboda yadda yake sintiri ba dare
ba rana.Suna hira a D'akin-shak'atawa zuwan shi gidan a aranar karo na uku
kenan.Alhaji Hafiz yakalleshi cikin natsuwa "Salim kayi aure mana.Yad'an yi
murmushi kawai. Kayi shiru bakace kome ba?Alhaji ba auran ne bana so ba, tunani
nakeyi anya zan samu mace kamar Sumayya?Wani irin zama mukayi me cike da amana, me
cike da girmama juna,zan samu macen daza ta rik'e min Ummi da amana? Yagyad'a
kai"me zai hana Salim?Kai da can abaya ka san za kuyi irin wannan zaman da Sumayya?
To karka cire tsammani daga al'amarin Ubangiji mana.jikinshi yayi sanyi wannan
gaskiya"nagode Alhaji ALLAH yak'ara girma.
Ummi ta shigo da gudunta dan taji muryarshi"Abba na baka tafi ba?Uh
ban tafi ba.Tayi dariya"to muje ka kaini Galaxy...in kira Yaya Zuhair mutafi tare?
Yakalleta da kulawa "Ummi baza muje Galaxy ba, lokacin makaranta ya kusa,baza mu
sake zuwaba sai an bada hutu kinji ko?Ta6ata fuska sai kawai tajuya tayi tafiyar
ta, kwallah sun cika idanun ta.Suka bita da kallo har tafice.
Me yasa kayi haka Salim?Dama taku da Ummi zata 6aci?Lallai yau na ganku
a rana.Yad'an yi murmushi"ai ba duk abinda take so nake biye mata ba,wani lokacin
ko akwai abin ina hanata saboda ta taso cikin sanin ba ko me da mutum yake so a
rayuwa yake samu ba, ko da kuwa yana ganin abin baifi karfin shiba, kauna da
soyayyar dana ke ma Ummi ba makauniya bace...
Lokaci k'ank'ani Salim suka dai-daita da 'yar limamin unguwarsu aka
daura musu aure,shima sai ya samu sauk'in zirga-zirga tsakanin gidanshi dana Alhaji
Hafiz saboda Ummi.Mariya tana kula mishi da Ummi gwargwadan ikon ta, shima ya yaba
da hakan sai suka samu kwanciyar hankali dan kowa yana yaba k'ok'arin
dan'uwanshi,sai tak'ara bada himma tana mata rik'on tsakani da ALLAH kamar yadda
zata rik'e Ya'yan cikinta"yaba kyauta tukwuici.
Yana sanye da wandon chinos ruwan zinare sai riga me dogon hannu da
ratsin ruwan zinari da bak'i,kwantaccen bak'in gashin kanshi yanata k'yallin hair
fruits,k'amshin Arabian perfume d'inshi ya cika d'akin. Alk'asim da suke abokan
wasa tawajan uba yashigo yana kallanshi "Lallai mutumin nan kana jin dad'in ka,
kaga yadda kazama wani d'an matashin bak'in bature kuwa? Yabashi hannu suka yi
musafaha.To ya karatun? Alhamdulillahi ai ya zo k'arshe tunda na gama rubuta
Project d'ina.Ah lallai sai shirin tafiya bautar k'asa to Ubangiji yasa aje a sa
a.Amin nagode. Yad'auki remote yana canja tasha baya san labaran CNN d'in nan,yan
kanzagin Amurka (America)kanwa uwar gami ce,da yad'a propagandar k'arya akan
addinin musulunci da musulmai.Yacire wayar shi da yasa a caji ta cika,suka fita
zuwa gidan Hajiya sai dai gidan na ta da kwado sai sukayi zamansu a dakalin k'ofar
gidan suna hira.
Aminu yak'araso yana kallan Julaibib cikin raha yace"hey dude what's up?
Yagalla mishi harara "Amincin ALAH zaka rok'amana ba wannan ba..yatare shi cikin
dariya"kar ka wani harareni kai kayi shiga irin ta su ai dole in maka irin
al'adarsu,shima yazauna sannan yamik'a musu hannu sukayi musafaha.
Suna ta hira amma ya dai na jin abinda suka fad'a tunda ya
hangota"indai yana gari to ranakun k'arshen mako irin haka yana ganinta.A natse
take tafiya irin ta 'ya macen data san abinda take yi wato gefen hanya, yanata
kallanta har tasha kwana.Wani murmushi yasu6uce mishi"Yarinyar can ya yaba da
hankali da natsuwar ta.Aminu yayi yar dariya"Dan Sarai kenan biri yayi kama da
mutum fa...na rantse maka ALLAH da zafi-zafi ake dukan k'arfe idan katsaya kallan
ruwa...irin na Aisha to ko ba abinda zai hana kwad'o yamaka k'afa. Yajijjiga kai
"tabbass zancen ka dutse...
Washe gari lahadi yakafa ya tsare sha d'aya da rabi yabar Musaddiq a
shago yaje dakalin wajan yazauna yana fatan ganinta,dai-dai lokacin aka ta shi daga
Islamiyar su,wucewar wasu yan dak'ik'u sai ko gata ta zo zata wuce,yabita da kallo
tana sanye da dogon hijab me hannu ruwan sararin samaniya kafad'arta rataye da
bak'ar jaka.
"Assalamu alaikum...
Karo na biyu kenan yamata sallamar.Dafarko tayi tsammanin ba da ita yake yiba shi
yasa tayi shiru, sai da yasake maimaitawa,a hankali tad'an juyo ta kalleshi sannan
ta amsa.Da sauri yamik'e daga dakalin ganin ta juya taciga da tafiyarta... "am...
Dan ALLAH...Jimana.Tatsaya ba tare data juyo ba tana jiran abinda zai fad'a.Yayi
k'asa da murya "kinga yanzu sauran d'aliban za su firfito kuma kamar zamu takura
musu idan muka tsaya anan, ko zamu d'an matsa daga can bakin Library? Batace kome
ba suka k'arasa wajan yad'an jingina da k'arfen allan bayani(signboard)d'in yana
kallanta ta sunkwui da kai.
Ya Ilahi...sai yarasa abinda zai fad'a ta mishi arwa.Wucewar wasu
dakk'ik'u tad'ago kai ta kalleshi cikin natsuwa dan shirun yayi yawa "Malam lafiya?
Yad'an sosa kunne"Kiyi hak'uri da na san gidan da kike bazan tsaida ke a hanya
ba,can d'in zan biyo ki dan kambamawar data dace dake kenan"Dan ALLAH ina ne gidan
ku?Tagirgiza kai"ni ba yar garin nan bace karatu nake yi a Nursing School a cikin
makaranta nake zama.
Ayyah...to ya muka ji da shan geron Sunday?(garin kwaki/rogo)yadda yayi
furucin cikin jimami yasa tad'anyi murmushi"har da kai? Yagyad'a kai"eh ai duk
kanwar ja ce,nima d'alibi ne gobe war haka ai na tsufa a makaranta.Atakaice yamata
bayanin kanshi itama haka da garin data fito.
Adai-dai lokacin suka shawo kwana dawowar su daga makarantar allo
kenan.Juyowar dazaiyi dan sunyi sallama da Bilkisu caraf idanun su yahad'u dana
Sudaida"wani irin yanayi mara dad'i yatsirga ilahirin gangar jiki da zuciyar ta,
tagalla mishi harara sannna takauda kai,cikin fushi tayi gaba su Khausar suka tsaya
gaisawa suna d'an tsokanar shi"a k'ofar gidansu Nasmat tatsaya dan allanta yana
hannun Nasmat d'inne kuma rubutu za tayi da wallahi bata tsaya ba"Khausar takalleta
"to ke wai saurin meye haka kike yi?Sauri kuma ba wajan zuwa ba tunda gashi dole ta
tsaya jiranmu.Tamusu wani malalacin kallo"shiru ma amsace.Nasmat tacigaba"anya
waccan ba budurwar D'ansarai bace?Cikin tafasar zuciya ta fizge allanta"kya tambayi
kaza hanyar rafi...?Fuuu tayi gaba tana k'unk'uni.Suka bita da kallan mamaki cikin
tunanin abinda ya caza mata k'wak'walwa haka.Nasmat tad'an motsa kafad'a "wallahi
can da yawarki yarinya.
Tun daga ranar D'ansarai bai kuma yadda sun had'u da Bilkisu a kwanakin
k'arshen mako ba. Ranar wata Juma'a yayi shigarshi ta fararan kaya yad'auki
motarshi sai Matsirga anan yayi sallar Juma'a.Yana fitowa daga masallaci yadinga
bin kwatancen Bilkisu kasancewar shi ba bak'o bane a garin sai ko gashi a k'ofar
gidan.Wani dogon dattijo kyakkyawan farin Bafulani yahango, shi da wani da bai
k'arasa shi a tsufa ba suna magana, sun dad'e suna maganganunsu sannan sukayi
sallama.
Julaibib yatare shi cikin sallama...
Malam Lamid'o ya amsa sallamar yana mik'a ma Julaibib hannu dan suyi
musafaha amma ya nok'e a haka ya gaishe shi cikin girmamawa.Malam Lamid'o sai ya
yaba da natsuwarshi yayi murmushi"samari daga ina? Cikin ladabi ya amsa"Baba ni
bak'on kune. Yagyad'a kai yana kara nazarinshi"af to,to madallah sannu da zuwa to
bismillah shigo ciki,yabud'e mishi d'akin zauran suka shiga yanuna mishi wajan
zama"zauna ina zuwa"yajuya zuwa cikin gidan sai gashi ya dawo da damammiyar fura da
nono tasha zuma da ruwan sha "bismillah samari"to Baba nagode"yajuya yasake fita
dan yabashi waje. wucewar dak'ik'u talatin yasake shigowa lokacin Julaibib yad'an
sha fura dan baya wani jin yunwa.
"Samari daga ina kake?
Julaibib Abdullahi D'ansarai...
Shine cikakken sunana daga Zonkwa nake.
Yabashi labarin kome game da had'uwarsu da Bilkisu...Ita kanta ba ta
san zanzo nan ba.Ni nazo wajan kane Baba indai bakama Bilkisu miji ba to idan ka
amince zan turo maka manyana.Yamishi kallan nazari" yanzu misali idan na amince ita
kuma Bilkisu bata amince dakai amatsayin miji ba fa?Yad'anyi jimmm...sannan yad'ago
cikin natsuwa yakalleshi "bazanji dad'i ba amma bazan ji haushi ba ,dan na san kome
na rayuwar bawa yana rubuce ne,yana kuma tafiya daki-dakine kamar yadda numfashi
yake shiga da fita ajikin d'an Adam,zan mana addu'a ni da ita Ubangiji yahad'amu da
abokan zama na arzik'i.
Malam Lamid'o yabishi da kallo cikin zancen zuci"wannan d'an matashin
tun yanzu yana da halin dattako to inaga ya dad'a girma,ilmi yadad'a cika
k'wak'walwarshi? Julaibib idan har Bilkisu ta amince da kai to nima na amince dakai
dan ni bazan ma Bilkisu auran dole ba sai wanda ta yadda tana so dan haka,kaje na
yadda ka nemi soyayyar ta. Irinka nake ma Bilkisu sha'awa kasancewar ta me d'an
ilmi duk da bai taka kara ya karya ba,to amma na san idan tazama matarka za ka
ciyar da ita gaba,ta inda taka sa zaka taimaka mata har itama ta tsaya da kafafunta
wata rana.
Nayi karatun addini dana zamani dai-dai gwargwado,shi yasa na hana Jauro
auran ta saboda ba abinda ya iya ba abinda yasani sai kiwon shanu,ni na san illar
zama da jahili dan bazai amfanar da ita da kome ba,d'an abinda tasani d'in ma idan
ba tsananin raboba a haka zai k'are.Katuro min manyanka za muyi magana gemu da
gemu.Ubangiji yasa Bilkisu rabonka ce.Yasunkwui da kai yana murmushi labarin zuciya
a tambayi fuska.
Tana goge kayan sawanta abokiyar karatunta tazo mata da sak'on daya bata
mamaki"Julaibib kikace yana nema na?Eh ai kibar wani mamaki dan ga kai ga k'afa ai
ba tambayar me aka yanka, jeki wajan da ake ajiye abubuwan hawa za ki ganshi ganin
idanunki.
Dogon hijab me hannu ruwan k'asa tasa, yana hangota yafito daga cikin
motar.
"Bilkisu me gadon zinare...
Tagaishe shi cikin natsuwa.Ya amsa yana murmushi"Yau dai gani ALLAH ya
nufeni da zuwa a wannan yammacin,da zan bari sai gobe to amma dana tuna yaufa
Juma'atu babbar rana ce sai kawai nace barin dai k'araso in k'ar6i goron juma'a ta
kawai.Tad'anyi murmushi "goron juma'a kake so? Ai ko ka tara ka samu sai ta mik'a
mishi lemon Schweppes d'in hannun ta.Yasa hannu biyu yakar6a "wannan kyautar goron
juma'ar ta faranta min rai naji dad'i na kuma gode dashi zanci tuwon dawar Inna
miyar kuka.
"Bello yace a gaisheki"
Takalleshi tabbass ya je Matsirga tunda basuyi maganar yan'uwan taba,
Bello kuma shine autansu. Yaushe kaje?Duk suna nan lafiya? A lafiyarsu kalau,suma
suna gaishe ki dakyau. Yad'auko bak'ar leda yaba ta "Malam ne yace in kawo
miki.Tarungume ledar cikin farin ciki "nagode.Yad'an kalleta sannan yasanar da ita
abinda yake tafe dashi.Tasunkwui da kai"bazance kome ba sai abinda Malam
yace"fad'uwa ta zo dai-dai da zama kenan"Malam ai ya amince dani Bilkisu.A kunyace
tace to ai shikenan.Sukayi sallama dan rana ta tafi za ta fad'i magriba na shirin
kunno kai.
Ana bikin duniya ake na k'iyama.
Akwai lauje cikin nad'i...
20 Jumaada Awwal 1441
15 January 2020
We Ibrahim's Daughters👇
Asdilat KD...2geda with Ra'ibs.
DANGIN NONO WRITERS ASSOCIATION
{Da Inganci Mukayi Fintinkau}
Bismillahi wabihi nasta'in
...GWAJIN DAFI💔
Almost true story
Daga alk'alamin🖊
Ya'yan Ibrahim
Saudat A.Baba (Asdilat KD)
Da
Bara'atu Ibrahim (Ra'ibs)
Masu k'orafin dan me Sumayya bata auri D'ansarai ba,da masu zaginmu
wai labari ya d'auko dad'i sai kuma kawai a kashe Sumayya to duk mun ya fe muku
bak'ak'en maganganunku, ALLAH ya yafe mana gaba d'aya.Sai dai ku sani shi
Ubangijinmu baya ta6a barin wani dan wani, madamar wa'adin barin duniyar ka ya cika
to fa ba tsimi ba dabara dole sai ka barta.Kuma ya kamata kufahimci wani abu,shi fa
labarin nan idan kuna duba duk shafukan da suka gaba ta,ai muna rubuta"ALMOST TRUE
STORY"ba k'irk'irar shi muka yiba,kaso casa'in na cikin shi ya farune,to sai ku
gane ba dukkan abinda kake so ne kake samun shi a rayuwa ba,kuma dole ka kar6i
rayuwar a yadda tazo maka,canja wani bangare na labarin to yana nufin canja labarin
gaba d'ayan shine.
...GWAJIN DAFi💔Labarine me jigo kusan biyar d'unkule cikin d'aya,dan
auna fahimtar makaranta.
Your comments is beyond our expectation...
Ibrahim's Daughters really appreciate.
1.Zainab Tijjani Ahmad (Ummu Bilqis)
2.Abdullahi Lawal Abdullahi (D'an Sarai).
3.Me Sunan Manya Khadija Kafanchan.
Ya'yan Ibrahim suna godiya,dan kulawa yabawace.
1.Ummu Ammar.
2.Salima Uba D'an Zainab.
3.Maimunatu Ibrahim.
4.Bilkisu Muhammad (Darling)
5.Zaynerb bello 36
6.عيناء ابرهيم عبد المؤمن
7.Ummul Ameen.
8.Shamsiyya Sani 661
9.Ummee Umar Musa.
10.Samira Garba.
11.A'isha Rabi'u.
12.Zainab A.Sulaiman.
13.Hafsa A.Sulaiman.
14.Khadija Bashir(Ummu Hanan)
15.Ummu aimanal habashiyya(Maman Kinanata)
16.My Sau'ash( Asdilat💋 for real)
17.Nasiba Namadi 'Yar Zonkwa😀
18.Khadija A.Muh'd (Ummu A'isha)
19.+234 813 109 04..I don't really no your name,but you care.
20.A'isha Nura Sani (Dr.Maidiyam)
😀 Asdilat
21.Saudat Ibrahim Yahya.Takwarata wannan sunayen na kifa sune rayuwatani
KD...ina yinki fiye da shurin masaki.
Shafi nagoma sha biyar.
Soyayyarsu ta bazu a dangi,wasu sun yaba sunyi sam barka,yayin dawasu
suka koma gefe suna k'unk'uni an rasa gane manufarsu. Suna hirarsu da Hajiya yake
fad'a mata"Megado tace a gaishe ki,wannan k'arshen makon baza tazo Islamiyya ba
suna jarabawa.Dan haka sai kisa ta a addu'a.Tagyad'a kai"Ubangiji yasa a fara a sa
a, yasa asamu kuma abinda ake nema.Amin Hajiya.
Sudaida tana share tsakar gidan tad'an ta6e baki"ni ana fad'in ban iya
girki ba sai na iyayi,to su kuma Fulani kona iyayin ma ai basu iyaba,to su da
abinda suka iyane banda tatsan nono da tallanshi gidaje da kasuwanni ne?Kai ALLAH
yasauwake.Taja dogon tsakin dayasa Julaibib da Hajiya juyawa suna kallanta"lafiyar
ki k'alau kuwa Sudaida?
Ta'ajiye tsintsiyar bayan ta kwashe sharan ta zubar.Takauda kai daga
kallan da suke mata"kalau d'ina Hajiya gida zan tafi... fuuu tawuce cikin fushi ko
sallama bata musu ba.Hajiya tabita da kallo cikin nazari...sai kuma tayi yar
dariya"dawalakin goro amiya.
Julaibib yasauke numfashi "Hajiya kwana biyu yarinyar nan sai ta
dinga cimin mad'aci,wallahi jiya data shigo wajan Inna tana kallona amma tad'auke
kai ba ko gaisuwa kamar bata ganniba.Hajiya tace"yan wasan ne bata jin yi
dakai,kaima ba sai ka share ta kaji da hayagagar...su Nasmat ba?Yayi d'an murmushi
"Hajiyar mu ALLAH yaja nisan kwana me amfani. Amin Julaibibi amin.
Malam Lamid'o dattijon arzikine yayi karatun addini dana zamani me
zurfi a yanzu hakama likitan dabbobine(Veterinary Surgeon) abinda yatarfama garinsu
nono kenan Ya'yanshi suke yin karatun boko me zurfi.Bilkisu itace 'yarshi ta
biyar,ya barta ta cigaba da karatune kasancewar ta me san karatun,kuma tun data
gama Secondary ba wani tsayayye sai Jauro shi kuma yace bazai ba Jauro auran
taba,data ce ga abinda takeso ta karanta aikin jinya da unguwar zoma,yaji dad'i ya
k'arfafeta dan karatun da za tayi zai amfani mata yan uwanta.Shi da matarshi sunyi
tufka me kyau da k'wari wajan tarbiyyar Ya'yansu, sai Ubangiji yadubi niyyarsu sai
suka ta so cikin tsoron ALLAH da ganin girmanshi ga kunya da sanin mutuncin mutane.
Nurse Bilkisu Muhammad Lamid'o...
Farace Kyakkyawar matashiyar budurwa,kyau irin na tsurar fulani da bashi
da gauraye da kowace kabila dan gaba da bayanta, uwa da uba typical Fulani ne, kome
na ta irin na mahaifin tane sai dai bambanci na ita macece shi kuma namiji
ne,yanayin maganarta da muryar ta shine kawai irin na mahaifiyar ta.
Bilkisu Megadon zinare...idan tayi murmushi ko dariya kai ko magana
tayi sai kaga kamar da san a sanine...takeyi dan kawai tanuna yar
lotsar(dimple)dake gefe da gefen fuskar ta da kuma yar siririyar wushiryar ta,
abinda yak'ara mata kyau na musamman bak'in gashin kanta me yawa da tsantsi irin na
asalin tsurar fulani,sai tattausan jajayan la66anta kamar ta turasu da jan
jambaki... Bilkisu me kyauce ga sauk'in hali dan bata rud'u da kyawun halittar da
Ubangiji yamata ko ilminta ba,kome na ta a natse take yinshi cikin mutunci da sanin
kimar kai(a very meek damsel)Tun tana k'aramar Secondary ta sauke Alqur'ani me
girma,har yanzu kuma tana karatun littafan addini.
Sauri take yi tana kuma addu'a ALLAH yasa tasamu abin hawa dan gaba
d'aya d'alibai sun gama watsewa a hanyar,Khausar ma ai ta tsufa a gida taimakon ta
d'aya da Khausar ta tafi mata da jaka, da harda jakar da littafan ciki da ita kanta
ruwan saman da yake shirin sauka zai k'are akansu.
Takad'a kai cikin damuwa"gaskiya wanda duk baiji bari ba zaiji
hoho,dama su Nasmat sun fad'a mata kar tasha maganin mura da tsakar ranan nan bacci
zai sata,tamusu kunnan uwar shegu tawuce dispensary na makaranta takar6i maganin
tasha aiko tun a masallaci suna sallar azahar bacci yafara kawo ma idanun ta
ziyara,duk k'ok'arinta na korar baccin abin ya ci tura,ganin haka yasa tama Metron
magana dan tasu da Sudaida ta zo d'aya sai ta bud'e mata Hostel"Clerkin's House"har
kwanar Kakus d'inta, yar ajin suce amma sunan su d'aya da Hajiya dan haka suke
kiranta da Kakus ta haye gadonta ta kwanta aiko bacci yayi awan gaba da ita har aka
tashi bata sani ba,bata farka ba sai biyar saura na yammacin amma taji ta garau
zazza6in da yake shirin rufe ta ya sauka,sallar la'asar tayi ta d'auki takalmanta
tana sawa,lokacin Kakus ta takawo mata jik'ak'k'en k'anzon alkama da madara(corn
flakes).
Na ga kina sa takalmi badai tafiya za kiyi ba? Tagyad'a kai tana
murmushi"yanzu kuwa"tazauna agefen ta"to amma ai kya tsaya kici abinci na san baza
ki iya cin garau-garau d'in dining ba shi yasa na had'a miki wannan me d'an ruwa-
ruwa tunda kina fama da mura,tamik'a mata kofin.
Kakus...tasake dubu agogon dake d'aure a hannunta na dama.Uhun Jikalle
me kike so kifad'a baza ki sha ba ko me?Tad'an marairaice"ALLAH Kakus...Sai kuma
tayi shiru, tasa hannu biyu takar6a,cokali hud'u tasha ta'ajiye
"nagode"taharareta"wannan dai dan kar ince baki sha bane kawai.Tadaki kafad'arta'ke
yar rainin hankali, to ko akan me zan cika cikina da wanna bayan na san abinci na
me rai da motsi yana jirana a gida.Ta tafa hannu cikin salati"Oh ni zamani! yanzu
Jikalle ni kike dukar ma kafad'a saboda wuyanki ya isa yanka.Yadda tayi furucin
kamar irin Kakar nan ta gaske yasa Sudaida ta kyalkyale da dariya,sai kuma tad'an
marairaice itama"come on Kakus don't be upset"kema kin san bana miki haka,to yau
d'aya dai ya kamata ki kar6i uzurina, Yaya Khausar ta dad'e da tafiya gida,kuma
kinga hadari yana ta had'uwa sai cida akeyi bana so ruwa yatareni.Tadafa
kafad'arta"na fahimce ki. Suka mik'e...muje in rakaki.Har gate d'in k'arshe nafita
daga makarantar tarakata,dan ALLAH ni dai karki manta gobe ki taho min da
soyayyiyar gyad'a,tad'an harareta"to anawa?A neman albarka tad'an zaro mata idanu
ko bakya san albarkan manya?Sukayi dariya"so kai"sukayi sallama, sannan suka d'aga
hannu suna ma juna adabo.
Iska me k'arfi tafara ta sowa garin yahad'e yayi bak'i sai cida akeyi
ba k'ak'k'autawa, abubuwan hawa suka dinga k'ara guda dan tsira daga dukan ruwan
watan bakwai,tak'ara sauri akwai gidan yar ajinsu Zamburan agaba sai ta samu
tafake,amma ina hak'anta bata tadda ruwa ba,kad'an-kad'an yayyafi yafara sauka
tanad'e hannayanta a cikin hijab,sanyi yafara ratsata tarintse idanu"wayyo ALLAH
na! Shikenan sabuwar mura zata dawo!
Dagudu motar tazo tawuce ta,wacce yahango tacikin madubi yasa yayi
ribas har yak'araso inda take,Caraf idanun su yahad'u yana bud'e motar,wani sanyin
dad'i ya mamayeta. Yabud'e mata"to shigo mutafi mana kina ganin ruwan yana
k'aruwa...tad'an harareshi sannan tashiga kamar wacce zata zauna a garwashin wuta.
Yaja motar"me kika zauna yi a makaranta? Kamar ba da ita yake magana
b.Ba tambayar nake yi ba? Dak'yar kamar me ciwon baki dan haushin shi takeji
tace"baccine yad'aukeni a dormitry"bai sake magana ba yacigaba da tuk'inshi cikin
natsuwa,sai dai ruwan daya cigaba da zuba kamar da bak'in k'warya yasa shi
gangarawa gefen titi yatsaya har sai yad'an tsagaita.
Yaya D'ansarai...
Yad'an kalleta"na'am.Taturo baki gaba"nifa gaskiya in dai ba so kakeyi in k'arasa
mutuwa ba to kashe wannan mukayyib d'in(Air Condition) ...kafin tagama rufe baki
tafara atishawa,sai da tayi biyar ajere"Yar hamukallah "yace mata bayan ta godema
ALLAH."Yahdi kumullahu wayuslih baalakum"tasa hannu tana jan hancin ta daya fara
toshewa,k'wallah yacika idanun ta dan wallahi sanyi takeji bana wasa ba gashi kayan
jikinta ajik'e suke.Sai da yamaida ita heater sannan tafara dawowa hayyacinta motar
ta d'auki d'umi,ruwan yad'an tsaigaita motocin dasuka tsaya kowa yaja yacigaba da
tafiya.
Suna shiga gida Mama tace"Masha-ALLAH dama yanzu nake dad'a yima Adnan
magana yad'auki mashin yabita makaranta yad'aukota"Yayi d'an murmushi"a hanya muka
had'u dawowa ta daga Kaduna kenan.Adnan yafito daga d'akinshi yana mita"Mama banda
kece da kanki kin cika min idanu kin shak'emin wuya da wallahi ba inda zani ruwa
bai gama d'aukewa ba. Tagyad'a kai"to kayi zaman ka mana.Yak'arasa kulle k'ofar
tashi"a haba dai Mama ai wata fuskar tafi gaban mari har abadan duniya.Yana shiga
D'akin-shak'atawar yagansu...yauwa yayi yar dariya"kai madallah da autan
Inna.Yamik'a mishi hannu sukayi musafaha,yajefama Sudaida mukullin"kai min d'aki".
Khausar tashigo da lemu ta'ajiye agaban shi bismillah fa.Yagirgiza
kai"bazan shaba,kirasa abinda za ki kawomin sai lemu me sanyi bayan yanzu aka gama
tsuuga ruwan sama har da k'ank'ara?Yamik'e dai-dai da shigowar Mama."Mama na wuce.A
ah ka tsaya yanzu nasa Sudaida takawo maka kayan bud'a baki.Yad'an shafa kai"Nagode
Mama amma kiyi hak'uri sauri nake yi dan gidan Hajiya zani kafin in wuce gida" To
ai ba kome musha ruwa lafiya.Amin Mama.
Hey autan Inna...
Zai shiga mota yaji kiranta yajuya yana kallanta ta canja kayan
jikinta da riga da wando kirar Pakistan ruwan k'asa da yarfin k'anana filawoyi
ruwan hoda me haske,tad'ora farar rigar sanyi tasak'a da farar hula me harafin
M.Gashi inji Mama.Bai kar6i ledar ba yace me wannan harafin M d'in yake nufi?Takai
hannu tashafa harafin"Masoyi na Sinan ko da wani masoyi ne bayan shi?Yamata wannan
rikitaccen kallan nashi takauda kai "gashi ni sauri nake yi. Yashige mota ya
zauna"ki kaimin gida yayi tafiyar shi.Tabi danjojin motar da kallo har ta 6ace ma
ganin ta.Takalli ledar taja dogon tsaki"kawai dan kabani wahala,shi dai wannan
halin na shi ALLAH yasauwak'e mishi...tashige gida tana k'unk'uni.
A safiyar asabar suna hirarsu da Inna yana shan shayin na'a-na'a da
ya'yan algarib tashigo da sallama, tagaishe da Inna sannan tazauna a kusa da ita
tana fad'a mata sak'on Hajiya.
Yamaida hankalin shi ga sauraran wak'ar wani balarabe yana wake
Habibti d'in shi da irin soyayyar daya ke mata wai"ya kamu da yunwar son ta,kuma
ita kad'ai take da irin nau'in abincin da za ta bashi idan yaci sai yadawo hayyacin
shi,dan yanzu shi ya zama kamar gawane da rai"yad'auki remote yad'an rage k'ara
yana cigaba da sauraran tsadaddun kalmomin da yaketa bayyana irin k'aunar shi
gareta me sanya zuciya bugawa a cikin shauk'in so,har baitin k'arshe sannan ya
canja tasha.
Kiran daya shigo wayar shi yasa yamik'e yafita,Sudaida tabishi da
kallo sai kuma tamik'e itama dan makarantar allo za ta wuce.
Yana tsaye a k'ofar gida yana wayar cikin sakin fuska,yayi k'asa da
murya yana gyad'a kai"na sani Megado amma na manta ne,ALLAH yamiki albarka da
wannan tunatarwan.Yayi jimmm...yana sauraro"to shikenan karki damu kinji
ko?...yauwa to nagode sai na shigo.
Tawuce kamar bata ganshi ba.
"Am Sudaida...
Takalleshi fuska a had'e.Yayi yar dariyar data bata mamaki dan ba kasafai yake
hakan ba.Yauma kin shigo gidan nan kin kuma ganni ganin idanun ki amma baki
gaisheni ba,wai in tambayeki mana? Kallanshi tayi batace kome ba "Sudaida... wannan
cin mad'acin da kike min bana jin dad'in shi kona miki wani laifi ne?Tad'an turo
baki gaba sannan ta kauda kai"ni ba kome.Anya zan yadda dake kuwa?Takalli siririn
agogon dake d'aure a hannunta sai kawai tajuya "gwamma da kai auran ka da gata kar
inje insha dukan makara.Ki tsaya muyi sallama dan baza ki dawo makaranta ki same
niba.Jikinta yayi sanyi amma bata tsaya ba tacigaba da tafiya"To ALLAH yakiyaye
hanya ai zamuyi waya.Ki tsaya ki kar6i"tasa gudu nifa bana so.Yabita da kallo yana
wata kissima a zuci.
Jikokin Hajiya sun cika mata gida sunata sha'anin gabansu.Sudaida
takallesu"kun san ALLAH cikin makaranta zan koma(hostel)na gaji da trekking sai
randa aka ga dama za a zo a d'aukemu.Nasmat takama ha6a"to makarantar allon kiyi
yaya da ita? Idan an ba da hutu na dawo gida sai in d'ora daga in da natsaya.Hajiya
tasa musu baki"yanzu ke saboda makarantar boko za ki bar makarantar Mahammadiyya?
Bayan shine a hakku akanki?Taturo baki"ai ba cewa nayi na daina ba,kuma ai nafad'a
ma Baba ya kuma amince.Hajiya tamata dakuwa"to ni ban amince ba zai kuma zo
yasameni bokon banza bokon wofi, bokoko a wuta. Nasmat ta kyalkyake da dariya"Ke
Hajiya bokon kike ma wannan zagin kamar bakiyi ba?eh na zaga,dan kayi karatun boko
indai ba karatun Muhammadiyy ai shirme kayi...ko ba ga sunan ba marasa addinin
k'wararrune a fagage mabambanta na cigaban rayuwa amma sai kika mutum wai yasa
abinda zai bautama sai saniya ko rana ko kwad'o...wannan ba 6atan basira bace da
rashin sanin tauhidi?Ai ba abinda zai baku rayuwa me inganci sama da Alqur'ani da
hadisan Manzon ALLAH dan ya tattara kome shak'undum kenan.
Washe gari kuwa data je gaishe da Baba yake fad'a mata komawarta
cikin makaranta an soke shi, Hajiya tazo da magana abar dubawa,yamik'a mata babban
envelop foam ne guda biyar a ciki,ki kaima Nasmat na ta gida ko wacce tacike ranar
Juma'a zaku fara zuwa makaranta,tasa hannu biyu takar6a"to Baba ta tashi tafita.
"HAYATUDDEEN ISLAMIYYA SAMARUN-KATAF"
yanzu har Samaru zamu dinga zuwa?Wallahi duk Hajiya ce da wannan aikin saboda kawai
nace zan koma cikin makaranta shine har ranakun k'arshen makon ma bazata barmu
mud'an sarara ba?Taja tsaki tana k'unk'uni,tad'auki biro tana ciccike inda ake so
aciken.
Maganar Julaibib da Bilkisu ta kan-kama sun kai kome da a ke kaiwa an
kuma tsayar da lokacin biki watanni uku masu zuwa dai-dai da gama karatun ta.
Julaibib ya tafi bautar k'asa,jahar Bauchi aka turashi angama basu horan sati biyu
a sansaninsu(camp)yakoma inda zaiyi service d'inshi a k'aramar hukumar Azare.
Sai da yayi wata d'aya sannan ya dira a Zonkwa dawani yammacin laraba
rana ta tafi zata fad'i magriba na shirin kunno kai,yatsaya yayi sallar magriba
sannan yatafi gida.Inna tayi murnar ganinshi dan bazata ya mata bai fad'a mata ko
awaya ba.Baije ko ina ba sunata hirarasu ta yaushe gamo yana cin abinci ita kuma
tanata kalan hotunan dasuka d'auka lokacin da a ke basu horo(training)tad'aga wani
hoto tana murmushi ashe kunsha wahala?Yagyada kai"Eh Inna akwai wahala dan sojojine
suka bamu horon cikin dare zasu kafa su tsare kowa sai yafito su fara bamu horo
tayi yar dariya"lallai kun zama k'ananan sojoji.Amma ni ban wani sha wahala ba.
Tagyada kai"ai baza kashaba tunda ka saba motsa jiki da manyan k'arafa yanzu har
mata sai sunyi wannan?Eh har su sai sunyi masu tsohon ciki ne kawai naga an d'aga
musu k'afa.Taja tsaki wannan tsarinne kawai bai min ba.Yad'anyi murmushi"To ya
zamuyi Inna tsarin ne yazo da haka amma Insha-ALLAH bama cire rai da wata rana za a
samu manya a harkar masu addini da zasu zamantar da abin dai-dai da shari'ar
musulunci a raba mata musulmai da irin wannan shigar a bainan-nasi.Inna tad'aga
hannu "Allahumma amin Julaibib.
K'arfe shida na safiya sukayi kaci6is akwanar gidansu,dawowar shi
kenan daga masallaci sallar asubahi,k'afafunta sanye cikin takalmi sneaker fari
igiyoyin d'aurewa ruwan bula,wando ruwan bulu,farar riga sai hijab iya gwiwa ruwan
bula sun sha guga tana goye da bakar jaka da Maths-set a hannunta.Tad'an bud'e
idanu cikin mamakin ganin shi"Kai Yaya D'ansarai saukar yaushe? Yabita da kallo duk
da garin bai gama wayewa ko ina yayi haske ba amma dai tayi kyau"Jiya gab da
magriba.Excursion za kuje? Tasake kallan farin agogon dake d'aure a hannunta na
dama"ba wani excursion Mr Goje malamin turanci(English)ne yabamu jinga
(Assignment) kuma to be submitted before seven O'clock"to shine kike wannan saurin
kamar za ki tashi sama?Tagyad'a kai"eh mana wallahi ji nake kamar inyi
tsuntsuwa,wai dan ma ba acikin makaranta muke ba shine yad'aga mana k'afa,su yan
cikin hostel ai k'arfe shida yabasu,duk wacce tawuce shida koda da dak'ik'a d'aya
ne bazai k'ar6a ba,shikenan kuma fa a matsayn C.A test d'in mune,kuma nayita rok'on
Yaya Adnan yakaini yace ba abinda zai fitar dashi awannan sanyin,ai dai ALLAH
yajik'an Yaya Aminu ba dan yamutu ba dayana gida na san zai kai ni.Tayi gaba da
sauri.
A bayan ta taji horn yabud'e mata kofa"ke Sudaida zo ki shiga
mutafi.Yad'an kalleta bayan sun hau titi"lallai baku raina Mr Goje ba.Yaya Julaibib
wargi waje yake samu,shi wannnan Malamin mugune na gasken-gaske gashi kuma yanzu
shine Labour Master,ya yanka ma mutum k'atan fili iya ganinka yace sai ka nome shi
wallahi k'aramin abu ne a wajan shi.
Hankalin Sudaida bai kwanta ba har sai da taganta a Staff-Room agaban
tebur d'inshi ta'ajiye littafin ta kuma sa hannu,tafito tana sauke numfaahi"wai
ALLAH na! nayadda k'wallan mangwaro na huta da kud'a.Takoma wajan Julaibib yanata
kallanta ta gilashin motar yana kissima wani abu a zuci,tad'auki jakarta. Yad'ora
hannun damar shi a saman sitiyarin motar"kin ko karya?A ah.Yakalli agogon motar ai
da sauran lokaci kafin kuyi assebmbly ko muje Staff-Quater gidan abokina Aminu
Idris ki karya a can?Tagoya jakar"barshi kawai Yaya Julaibib,ai Yaya Khausar zata
kawomin.Sukayi sallama,yad'an lek'o da kai "kuyi hak'uri yau akwai inda zani dana
dawo na d'auke ku"tad'aga hannu tana mishi adabo ba matsala nagode,tabi motar da
kallo har yafita daga gate d'in farko sannan tajuya zuwa ajinsu tana murmushi.
Kwanci ta tashi asarar me rai,biki saura wata d'aya,awannan lokacin
Julaibib baya samun zama saboda zirga-zirga tsakanin Azare da Zonkwa,Yadad'a gyara
bangaranshi dan anan zasu zauna tunda bai gama ginin shiba.Dasafe yaje gaishe da
Kawunshi sunata hira musamman abinda yashafi kasuwancinsu,sai da zai tafi yamik'a
mishi wasu mukallai na gidan kane,na baka d'aya daga cikin gidaje na na Unguwar-
Rama daura da masallacin Yarbawa hakak malak. Julaibib yad'ago kai bayan ya duba
takardar shaidar mallakar gidan sunan shinei ajiki"Kawu nagode ALLAH yasa da
mafificin sakamakon shi, ALLAH yak'ara girma.Amin.wannan ai ba kome bane.
Yad'auki Musaddiq sukaje suka ga gida,sabone dal sai k'ura dayayi
tunda bakowa yasa yara suka wanke lungu da sak'o na gidan.Kafin yakoma Azare sun sa
kome da ake buk'ata suka kulle sau ranar daza a kawo amarya.
Yajingina da bishiyar mangwaran k'ofar gidan yana kur6an madarar
shanun tatsar lokacin,hirarsu sukeyi cikin nishad'i irin ta masoyan juna.Bilkisu
har naji kin fara k'amshin amarci fa.Tad'anyi murmushi.Yayi tsai da idanun shi yana
kallanta"Megado baki ce kome ba? Takauda kai"Kazo ka tafi bana so kayi dare a hanya
daga nan zuwa Azare tafiyace me tsayin gaske"Megadon bana san tafiya yau
"Takalleshi cikin kulawa"saboda me?Yanunata da yatsa.
Tad'anyi luuu da idanunta kamar zata rufesu sai kuma ta sunkwui da
kai"Julaibib ai kai nawane,ni d'in nan ta kace Insha-ALLAH,amma bazan so ace nice
silar ta6ar6arewar al'amuranka masu mahimmanci ba,bautama k'asa a matsayin ka na
d'an bautar k'asar dole ne,kome kuma za kayi to kayishi yadda ake buk'ata,kazama me
amana; tafiyarka ai ba itace rabuwar muba,koda munyi nesa da juna to amma ai
zukatanmu suna tare,kuma ga waya muna gaisawa,muna chatting, har video call duk
munayi,tad'ago cikin natsuwa da kulawa tad'an kalleshi"duk basu wadatar ba
D'ansarai?
Yanad'e hannayan shi a k'irji yana murmushi "sun wadatar Megado,ke
macen alheri ce da bata taya 6era 6ari.Yamik'a mata kofin madarar yashiga mota
yazauna yana d'aura belt "ALLAH yamiki albarka Bilkisu "tarufe mishi murfin"Amin
D'ansarai nagode,sukayi sallama. Tabi bayan motar da kallo a hankali yake tuk'in
har ya6acema ganinta.Tajuya zuwa cikin gida tana mishi addu'ar sauka lafiya.
Inna tabita da kallo"har ya tafi?Sai lokacin tasan Inna tana tsakar
gida,ta zauna a gefan tabarmar tana d'an murmushi,kumatun ta suka lotsa ciki"a
kunyace tace ya tafi Inna"sai kuma tamik'e da sauri ta shige d'aki.
Tana shan rake tana 'yan wak'ok'inta cikin nishad'i,Khausar kuma tana
karanta wani littafi"The secret of occultics powers"su Nasmat suka shigo suna
hayaniyarsu,A'isha tace ya naganku haka?Khausar takalle su "to da ya kike so ki
ganmu? Tazauna a gefan gadon"banga kun shirya ba,za muje ganin d'akin amaryane.
Khausar ta ajiye littafin"har kin tunamin ance da mahaukaci baya duka.Tabud'e
wadrobe tad'auko hijab sannan takalli Sudaida"to mayyar rake badai za kice jiranki
za muyi har sai kin gama shaba?
Tamusu kallan uku ahu"kuyi tafiyarku dan ni bana zuwa gayyar sod'i.Suka
bita da kallo cikin mad'aukakin mamaki"gayyar sod'i fa kikace? Zuwa gidan Yaya
Julaibib d'in?Tayi kamar bataji suba...zuwa can bayan ta shaki iska ta baki ta
hanci tafesar tana wani tsuke baki"Eh shi d'in fa wani abu ne?Ni dai wallahi banga
abinda zanje gani wanda ban san shiba,ban ta6a ganin shi ba, taja dogon tsaki"gado
ne fa da sauran tarkace, tad'ora hannun damar ta a katakon gadan su, wannan ai
gadone ko?To gashi na gani akaima nake bacci,sauran tarkacenma muna dasu a D'akin-
shak'atawa da D'akin-girki,kuma bama amaryace za tazo da suba,ta kuma jan dogon
tsaki cikin tafasar zuciya"kai ALLAH yasauwak'e ma Fulani,wai ace kome mijine
zaiyi,ga uban sadaki da suka yanke mai,dubu hamsin sai kace siyar da ita za suyi"ai
dai k'arancin sadaki yawan albarkar aure wallahi.
Khausar ta tareta da sauri"ke dakata haka malama ai a addinance dama
mijine yakeyin kome na d'aki yakuma biya sadaki,dan hakkin akanshi yake ba akan
iyayan taba,mu hausawa mune muka fifita al'ada sama da addini a wannan
bangaran,kema ai kin sani sarai ban san abinda yasaki wannan furucin ba.
A'isha ma takalleta"lallai ma yarinyar nan yanzu idan ma siyar da itan
za suyi sai su siyar da ita a kud'i me mugun rangwame haka? Dan ALLAH nawa ne 50K?
Kai Sudaida me yake damun kine naga alama bakya san
Nurse Bilkisu Muhammad Lamid'o...
Ni kuma wallahi tana burgeni saboda sauk'in halinta,wallahi sam bata
d'auki duniya kayan gabas me k'amshin turaran d'an goma ba, haka fa ranan nan da
muka had'u da ita a hanyar Islamiyyar su itafa tafara gaishemu amma kikayi banza da
ita,bakyau irin wannan halin ko Yaya D'ansarai da baya san kula mutane amma idan
kika mishi magana zai kulaki ko sama-sama ne.
Nasmat tana ta nazarin kalaman Sudaida tayi yar dariya tana tafi
tasake kallan Sudaida"kina kishi ne?Takusa k'warewa da raken da take sha Dammm...
zuciyar ta tabuga tamata wani kallo"kishi kamar yaya,me zai sani yin haka?
So...Nasmat ta bata amsa.Duk sai suka zubama Sudaida idanu"biri fa yaso yayi kama
da mutum. Numfashinta yad'auke na wucin gadi... tamik'e cikin fushi tana kallan
Nasmat "so fa kika ce?Tagyada kai"eh kwarai kuwa so.Sai tafara hayagaga..."eh so ne
sai me?Suka kyalkyale da dariya ganin yadda take masifa"eh ina san nashi amma ba
irin soyayyar da kike tunani bane, soyayyace irin ta yan uwan taka, karki manta ina
da masoyi na da makaranta yake jira in gama sai in koma k'ark'ashin shi ta inuwar
aure.
Nasmat ta daki kafad'arta tana dariya "ahaf ba mage ba miyauuu...Takalli
su A'isha"kuzo mutafi kunji tunda baza tajeba.Tabisu da kallo har suka gama fita a
d'akin.Tad'auki hijab tasa gwamma kawai tabisu,sai wani irin abu mara dad'i ya
tsirga ilahirin jiki da zuciyar ta,kawai sai ta koma ta kwanta,tad'ora tafin hannun
damar ta a saman goshin ta dayake barazanar yin ciwo, ta yamutsa fuska tana hura
iskar bakinta tana jin wani d'aci kamar tasha mad'aci.
Mama uwargidan Alhaji Ibrahim macen albarka,macen k'warai dattijuwa
me yakana da karamci, uwargidan cinta na dalci da amana takeyi,abinda yahaifar da
kwanciyar hankali kenan,yasa zuri'ar gidan suka dunk'ule suka zama tsintsiya
mad'aurinki d'aya.Duka Ya'yan gidan ta d'aukesu abu d'aya kamar ita ta haifesu.A
d'aki tasamu Sudaida a kwance idanun ta a rufe,amma ba bacci takeyi ba.Ta zauna a
gefan gadan,Sudaida tabud'e idanun ta da suka d'an canja kala.Mama takalleta da
kulawa"wai mantawa kikayi da Sinan a waje?Tadad'a kwantar da kanta a saman matashi
"Mama kaina ne yake min ciwo"sanin hali yafi sanin kama"sai tayi murmushi kawai"To
ai ya kamata kije kifad'a mishi kar yayi jiran gawon shanu ko?A ciki ta amsa kamar
ranta bai mata dad'i ba"to Mama na ji.
Tana fitowa yatareta"Sudaida Sarauniyar Sinan"taturo baki gaba tana
d'an harararshi"kai baka san kaina ne ya dameni da ciwo kuma Mama ta matsamin dole
nafito"yayi murmushi wani lokaci haka take abu kamar wata 'yar k'aramar yarinya wai
an matsamata dole tafito.Sai ya marairaice"Oh ALLAH! Wayyo! Sannu Sarauniyar Sinan
taso muje ki kar6o magani? Tagirgiza kai'ai ma navfara jin sauk'i.Yasauke
numfashi"kai nagode ma ALLAH,dama ni ne maganin ko?Sukayi dariya.
Tana d'ago kai za tayi magana caraf idanun su yahad'u dana Julaibib,yana
sanye da shadda ruwan k'asa yayi shar...shar dashi,magana yakeyi a waya yaja
yatsaya nesa dasu.Tad'an ta6e baki"wayar tak'ici tak'i cinyewa,ba mamaki shi da
wannna Bafulatanar ce.Yagama wayar sannan yamata wannan rikitaccen kallan da
tadad'e bataga ya mataba,dama baya kulasu in dai yatarar suna hira ko magana
tamishi sai yayi kamar ba dashi take yi ba"kunnan uwar shegu"tabishi da kallo har
yashige cikin gidan.Takalli Sinan ni zan wuce"Shikenan anjima zan bada masoyin
Sarauniyar Sinan akawo miki (rake) tayi d'an murmushi "nagode.
Ranar Juma'a suna gidan Yaya Karima sunje mata ziyara sai gashi yashigo
da sallama.Yazauna suna gaisawa da Yaya Karima tana tsokanar shi"Kai autan Inna har
wani haske naga ka fara ko kaima kana gyaran angwancinne dasu halawa da dilka?Yakai
hannu yana sosa k'asumbarshi yana yar dariya"Kai Yaya Karima duk sukayi
dariya;banda Sudaida da ta tayi kamar bataji me aka fad'a ba,tacigaba da cin
sinasir d'inta,Nasmat tace"wai ina masar Bauchin dana ce ka kawomin tsaraba?Haba ke
kuwa Nasmat ai k'aton aiki za ki bani ace tun daga Bauchi har Zonkwa in rik'o masa?
Gaskiya bazan iyaba,indai za kici kantu(rid'i)to kije wajan Inna ki kar6a.
Ni masa nake so tunda baka kawo min ba ai shikenan nagode ALLAH kuma
yabamu lafiya, amma da Bilkisu ce tace tana san masar ai baza ka d'auki hakan a
matsayin k'aton aiki ba ko? To dake da Bilkisu Megadon Zinare...d'aya ne? Sudaida
tamik'e"uh wannan Bilkisun dai ko gadon Mahogany ba ta dashi"tajuya za ta bar
d'akin. Yarik'o gefen hijab d'inta..kafin yayi magana tajuyo cikin fushi"Yaya
D'ansarai sake min hijab ka san dai bana wasa da maza.Su Nasmat suka kyalkyale da
dariya kaji wata magana kuma? Yakalketa cikin natsuwa"idan kuma ban sake ba fa?
Tayaye hijab d'in gaba d'aya daga jikinta tajefa mishi a fuska "kaje ka kai
mata"fuuu...tafita mayafin Yaya Karima tajawo a igiya tayafa.Duk suka bita da
kallo.Yaya Karima takama ha6a"to ana wata ga wata aure ya mutu ga gara.Takalli
Julaibib ya sunkwui da kai"ranshi a 6ace yake,amma ta san bazai yi magana ba tunda
yayi haka,wannan halin shine tun yana yaro indai ya sunkwui da kai.
Yamik'e da hijab d'in a hannun shi "Yaya Karima ni zan wuce idan Baban
Abdul yadawo kya mik'a min sak'on gaisuwa.To auta mungode kwarai kagaishe dasu Inna
sai na shigo.
Har yakoma Azare Sudaida bata yadda sun kuma had'uwa ba ko gidan Inna
bata sake zuwa ba dan kar ma su had'u sai bayan data tabbatar ya tafi sannan
taje.Yakirata sau d'aya a waya tak'i daga wa shima bai sake kira ba.
Tana zaune a dakalin k'ofar gida da tunanin inasu Mama suka suka tafi
haka harda kulle gidan gaba d'aya bayan sun san za su dawo daga makaranta?Sagir
yazo da gudunshi zai kwashi kayan wasa a inda ya6oye can wani sak'o, tarik'o
hannu"su Mama ina suka tafi?Matsirga su da Yaya Musaddiq da akwatuna,tasake shi
yatafi. Lefe sukaje kaiwa kenan? Tad'an ta6e baki.
Gidan Yaya Musaddiq tawuce. Safiyya tace"wata sabon gani.Tazauna a
kujera tana yar dariya"ALLAH Yaya Safiyya ba lokacine kullum muna hanyar
makaranta.Tagyad'a kai"na yadda,to shiga D'akin-girki kizubo abinci danna san kin
kwaso yunwa,tak'arasa kwanciya a kujerar "ai azumi ma nake yi,ke me yahanaki zuwa
garin Fulani kai lefen?Uhun ke dai bari har na shirya sai ga baki na yi ba zato ba
tsammani basu dad'e da tafiya ba.Takuma ta6e baki tamaida idanun ta tarufe kamar
tana bacci amma ranta in yayi dubu ya 6aci,taja tsaki tanata juye-juye,data gaji
sai tamik'e tafito da littafin lissafinta tana nazarin Quadratic Equation.
Julaibib da Bilkisu suna tsaye a wajan da ake ajiye motoci na cikin
makarantarsu, tana tambayar shi "ya me jiki? Yagirgiza kai"ni fa ki daina tambaya
ta ya me jiki, idan kina san sanin ya take ai zuwa za kiyi ki gaishe ta ko? Haba
Megado wallahi kin bani kunya ace Yaya Asma'u takwanta a asibiti kwanaki goma kenan
amma ki kasa zuwa gaisheta,aiko ba soyayya a tsakanin mu to akwai hakkin musulmi
akan musulmi koda ba dangin Iya ba na Baba,gaishe da mutum idan ba shi da lafiya
yana daya daga cikin hakkoki biyar akan musulmi da musulmi.
Tasunkwui da kai"kayi hak'uri D'an Sarai Insha-ALLAH zan je.Yagyad'a
kai"to muje in rakaki. Nagode zan je ni kad'ai suka d'an ta6a hira kad'an suka yi
sallama. Abakin a sibitin ta tsaya ta sai kayan marmari sannan tashiga.
Sudaida ce tabud'e k'ofar,suka kalli juna Bilkisu ba girman kai sai ta
gaisheta,tatsuke baki cikin yamutsa fuska ta amsa mata dak'yar sannan tabata
hanya.Tashiga da sallama ta durk'usa ckin natsuwa me had'e da kunya tagaishe da
Hajiya tana tambayar ya me jiki?Dan ALLAH amin uzuri da banzo da wuri ba yanayin
karatun mune sai a hankali,Tamatsa jikin gadan tana gaishe da Yaya Asma'u da
tambayarta karfin jiki.Tayi murmushi"jiki Alhamdulillahi tunda gobe ma za a sallame
ni.
Hajiya ta kalli Sudaida"kawo mata ruwa mana.Tajuya tama Bilkisun wani
kallo"Hajiya ita tace miki tana jin k'ishi?Mutanan d'akin suka bita da kallo in ka
d'auke Bilkisu da Hajiya.Bilkisu ta sunkwui da kanta,Hajiya kuma tana nazarin
Sudaida a karo na barkatai kenan tana nuna halin-ko-inkula da duk wani abu daya
shafi Julaibibi tun lokacin da maganarsu da Bilkisu ta kan-kama, takad'a kai"lallai
da magana karuwa ta ziyarci tuzuru.
Yanzu sai ta ce tana jin k'ishi za a bata ruwa Sudaida?Bak'on ka
annabin ka.Tamik'e tana k'unk'uni tad'auko ruwan ta dangwarar a gabanta.Hajiya
tadafa kafad'ar Bilkisu da sigar rarrashi dan abinda Sudaida tayi bai kyautu ba
sam"kiyi hakuri Bilkisu"Tad'anyi murmushi me had'e da kunya"ba kome Hajiya,dan kar
suce taji haushin furucin Sudaida ne da baza ta shaba tunda ba ta jin k'ishi,kad'an
ta tsiyaya a kofi tana kur6.
Sudaida ta galla musu harara, tabud'e jakar ta tad'auko earphone
tamak'ala a wayarta sannan ta toshe kunnuwan ta dashi, tashiga bin wak'ar, zaman
d'akin ya gundireta sai tafita tabasu waje ganin hadari yana had'uwa yasa tawuce
gida
Feshin ruwan yafarkar da Khausar daga baccin data fara,ga littafan
data barbaza a saman tebur har sun fara jik'ewa,tarufe taga tasuke labulan sannan
takalli Sudaida "saboda ALLAH kina ganin ruwa zai jik'a min littafai amma kika ki
rufe taga?Tayi kamar ba da ita take magana ba,sai ta fizge wayar"bakya jine ina
miki magana?Tabita da kallo"ke wai kwana biyun nan lafiya kuwa?Eh ita takawo
haka,tamik'a mata hannu bani waya ta.Tabata wayar tana gyad'a kai"lallai kam nima
naga alama lafiyar ce takawo haka,tayi d'as da yan yatsunta"to amma fa karki manta
duk kanwar ja ce,baki fini tsummaba bazan zauna kina 6ar6ad'eni da k'wark'wataba,
wallahi ban kar zomo;tanunata da yatsa ke baki isa ki kisa ni d'aukar rataya
ba.Sudaida tabita da wani malalacin kallo"ALLAH sarki.
Suna tsaye kusa da rafin Matsirga D'ansarai yad'aga kai yana kallan
Qudirar Ubangiji duk da ba ranar yafara gani ba,Tsawon tudun yayi gidan sama hawa
uku tanan ruwan yake fitowa yana gangarawa wani rami a can k'asa me tsananin zurfi
kuma a saman turawa sukayi titin jirgi k'asa kuma har yanzu tanan d'in yake
wucewa,sa dai gaskiya duk wanda yafad'a ramin nan to ya gama numfashi a doron
duniya wallahi.
Bello yarik'o hannun Bilkisu "Adda zo mu tafi gida kinga hadari
yafara had'uwa kar ruwa ya 6alle.Julaibib ya kalleshi"to mutafi suna tafiya suna
d'an ta6a hira har suka zo k'ofar gidan.Julaibib yabud'e mota yad'auko wasu wara-
warai (Awarwaro)masu kyan gaske a d'an gidan su"wannan kyautar soyayyace ta
musamman ga wacce tayi nasarar mallake zuciyar Julaibib... Bilkisu Megadon
Zinare...Bilkisu Zinariya kike kinfi azurfa.Yamik'a mata tasa hannu biyu ta kar6a
"nagode k'warai Julaibib D'ansarai".
Ke kad'ai nake so Megado...
Tasunkwui da kai tana d'an murmushi cikin jin kunya kumatunta suka
lotsa.Yad'an d'age gira"au baza kice kome bane?Tad'an d'ago takalli Bello ya ko
zuba musu idanu kuriii yana kallansu. Yayi murmushi"Oh na fahimta,a dinga sara ana
duba bakin gatari ko?Tagyad'a kai.Sukayi sallama a gaggauce dan an fara yayyafi.
A sanda hantsi yadubi ludayi amma har lokacin garin da sanyi saboda ruwan
saman da aka dinga tsuugawa kamar da bakin k'warya tun dare har wayewar gari sai
wajan k'arfe bakwai da rabi ruwan yad'auke,Iska tana ta k'adawa. Tibishi yakalleshi
amma jiya ka burgeni.Yakai mishi duka"wani burgewa ka sa inata tari kamar zan
shid'e,sukayi dariya suka tafa"ai da haka za ka zama k'wararre.Tibishi yad'an ta6a
shi"kai ga mutuniyar ta ka can,yajuyo da sauri "haba dai? Bai gan taba dan ta riga
ta sha kwana" amma dai bata ganni bako? Yagalla mishi harara "kaji d'an iska to
idan ma ta ganka sai me? Yamik'e"a ah wallahi da matsala,katafi kawai anjima anjima
zan nemeka a waya.
Tabishi yarik'o rigarshi ta baya "dakata malam ai ba haka mukayi dakai
ba,sai ka bani kud'i indai kana so katafi,baiyi magana ba yaciro d'ari biyar
yabashi yajuya da sauri dan kar tayi nisa.Tabishi yabishi da kallo yana kyalkyala
dariya"Sinan shegen duniya,kura da fatar akuya yad'an yi tsaiii...nawucewar wasu
dak'ik'u yana kissima wani abu a zuci sai kuma yad'an motsa kafad'a"any way akwai
dai ranar k'in dillanci ranar da hajar me gari zai 6ata.
Gudu-gudu sauri-sauri har ya cimmata yasha gabanta"haba Sudaida
Sarauniyar Sinan ai ya dace ki tsaya ki saurareni ko?Tagirgiza kai"bai dace ba"
Sinan katafi kabani waje karka 6ata min lokaci a banza a wofi.Yakwantar da murya
yadinga mata kalaman rarrashi da bambaki har sai da yaga tana murmush"amma ai kai
kafad'a min da bakin ka ka daina kulasu Tibishi amma ayyukanka suna k'aryata
furrucin ka,jiya da yamma gab da za a fara ruwa tare naganku ka goyo shi a mashin
kunyi hanyar D'One takalleshi cikin natsuwa wajan shan giyar koko ka kaishi da
kanka Sinan?Yanzu kuma na sake ganinku tare kuna hirarku kuna ta dariya har da tafa
hannaye; Sinan wai mantawa kake yi da d'abi'a tana na so? Zama da mad'aukin kanwa
yana kawo farin kai fa. Haba Sinan me...
Yatari numfashinta"Kiyi hak'uri Sudaida amma wallahi Tibishi shi ke
bibiyata,ni kuma abinda yasa nakasa korarshi muyi baran-baran ina mishi kwad'ayin
musulunci,wata kila ta dalilin Sinan masoyinki sai kiga ya samu dacewa zuwa addinin
gaskiya kina wannan ai babban jihadi nevko?Tajijjiga kai"mutum d'aya yashiryu ta
dalilin ka yafi abaka jajayan rak'uma guda dubu "Yad'an shafa k'irjinshi bangaren
zuciya"Oh ALLAH nagode maka"sukayi dariya yad'an taka mata sannan sukayi sallama
tawuce gidan Hajiya.
Shi kuma yakoma wajan Tibishi yana fada mishi"abinda nake so dakai
mudaina had'iwa a cikkn gari,ni idan inada buk'atar ganinka zan biyo ka har
D'One.Yamishi wani malalacin kallo cikin fesar da hayak'in maro (wiwi) tabaki ta
hanci "saboda wata Sudaida?To in tamabaye ka mana "haka zaka aure ta bata san kome
a tare da kai ba sai halin waliyai?Ranar da duk tagano kana kanaga zata zauna dakai
cikin aminci da amana? Yatareshi cikin hayaniya"kar kamin sanadin 6acin rai da
sanyin safiyar nan dan zan gwada maka rashin mutum ci dan abu kazan uban ka,kafin
Sudaida tasan kome ai na daina.Tibishi yagyad'a kai "wannan shine tazo muji ta
tawuce ta bayan kunne.Yanuna shi da yatsa"indai muna tare da Sudaida to karka
kuskura ka doshi wajan.Angama ranka yadad'e yajuya yayi tafiyar shi yana ma Sinan
dariyar rainin wayo.
Kafin tayi wani yunk'urin tashi dan ta jiyo muryar shi,har sun shigo
D'akin-shak'awar. Musaddiq yakalle ta"d'auko kayan da Baba yabaki kiba Julaibib
tamik'e "to. Musaddiq yamik'a mishi hannu sukayi musafaha"to ALLAH yatsare hanya
shi Musaddiq a Kaduna yake bautar k'asa yanzu zai koma.Yazauna zaman jiran ta sama
da dak'ik'u talatin bata kawo mishi ba ya kira wayar ta ta k'i d'agawa,sai yamik'e
zuwa tsakar gidan ana yasame ta sunata hirar su dasu A'isha.
Ke ina kayan ne? Tayi kamar bata ji ba. Khausar tabita da kallo
tabbass wani abu ya samu k'wak'walwar Sudaida a yan kwanakin nan, d'azu ma haka
sukayi da Yaya Aminu yace ta dama mishi custard;ta tafi d'aki tayi kwanciyar ta
shima dagaji da jira yabiyo ta yana tambaya sai tace"Oh Yaya Aminu yi hak'uri na
d'an mantane, barin je in dama maka.Yakalli agogo yagirgiza kai"idan natsaya
gaskiya zan makara.Yad'aga mata hannu sai na dawo ko? Wallahi da sarki zalimu Yaya
Adnan tama haka aida ta kwashi kashin ta a hannu.
Ke Sudaida!
Tamishi wani kallo bata amsa ba "d'auko min kayan mana sauri nake
yi"Oh ga su can a kusa da d'akin Yaya Adnan.Yagyad'a kai "Khausar kawo min mota
yajuya yana amsa kiran waya...tabi bayan shi da kallo tana wata kissima a zuci
tad'anja tsaki tashige d'akinsu,tad'aga labulan taga yana jingine da motar shi har
lokacin wayar yake yi,tad'an cije lebanta na k'asa sannan tasaki labulan takwanta a
gado...
Ruwa da dorina da kada shigar shi sai dai Kwarawan asali.
24 Jumaada Awwal 1441
19 January 2020
We Ibrahim's Daughters👇
Asdilat KD...2geda with Ra'ibs.
DANGIN NONO WRITERS ASSOCIATION
{Da Inganci Mukayi Fintinkau}
Bismillahi wabihi nasta'in.
...GWAJIN DAFI💔
Almost true story
Daga alk'alamin🖊
Ya'yan Ibrahim
Saudat A.Baba (Asdilat KD)
Da
Bara'atu Ibrahim (Ra'ibs)
Shafi nagoma sha shida.
Yafito daga mota yana kallan ta, tana sanye da shadda me maik'o ruwan
makuba tayi kyau sosai a cikin yammacin"Bilkisu Megadon zinare...zinariya kike
kinfi azurfa,na rasa yadda zanyi in fasalta miki irin kyan da kike k'arayi amaryar
D'ansarai.Tasunkwui da kai ganin wani irin kallo dayake mata,abinda yake so
tattausan jajayan labbanta kamar ta turasu da jan jambaki "wai yau saura kwana nawa
yarage muzama abu d'aya?Tagirgiza kai"nima ban sani ba,dan bana lissafi.Sai yakama
kai"Innalillahi Megado bakya lissafi?Lallai baki damu dani kamar yadda nadamu dake
ba.Tayi murmushi me sauti, kumatunta suka lotsa"ai ba anan take ba Julaibib, abari
agani mana an ba bature 'yar bak'ar fata. Yagyad'a kai"kema kince wani abu,ALLAH
yabamu rai da lafiya yanuna mana lokacin.
Sudaida takalleshi"Sinan jiya inata d'aga maka hannu.Fargaba taka ma
shi, da d'an rawar murya yace"jiya da yaushe?Tayi shiru cikin nazarin shi kamar ya
shiga rud'u"jiya da yamma, lafiya kuwa?Yasa hannu yashare zufan daya tsatstsafo
mishi a goshi"jiya ya yi kato6ara amma da rana abin yafaru.Yad'anyi murmushi"a ah
ba kome, kiyi hak'uri ban ganki bane. Nima ai na san da ka ganni baza ka shareni
ba.
Tibishi aka sauke akan mashin yak'araso wajan cikin tam6ele da
sambatun da kamru uwar laifi take haifarwa,yamik'ama Sinan hannu"sai ka bani kud'in
da zan sallami me mashin ko?Dasauri yaciro yabashi; yajuya cikin irin tafiyar
bugaggun mashaya"ka rufa ma kanka asiri da wallahi yau allura sai ta tono
garma,banza kawai,wawa.Suka bishi da kallo Sudaida toshe da hanci saboda wari da
hamamin daya cika wajan,ta tsirtar da miyau"kai ALLAH ya sauwak'e...ya amsa da
amin.Ya bud'e baki zai mata magana sai ga Tibishi yasake dunfaro su"kai d'an iska
kura da fatar akuya.Sinan yamik'e da sauri"Sudaida shiga gida kawai anjima zan
dawo,tajuya da sauri dan cikinta ya fara hautsinewa saboda warin Tibishi. Yaja shi
suka bar k'ofar gidan.
Danbarwa sosai sukayi da Tibishi bayan mayen uwar laifin ta
sakeshi"Yahankad'e shi yafad'i tabaya,Sinan yafara nuna shi da yatsa"kar ka sake
biyoni wajan Sudaida.Yamishi wani kallo"ALLAH ko?Na Sudaida ba da kanka asare idan
kaje gida kace ya fad'i,haka kirarin na ku na hausawa yake ko?Eh hakane saura na
Katafawa,yayi dariyar tura haushi"ai sama-sama kake jin yaran Kataf dan haka kona
maka ba zaka fahimta ba,yamik'e yana kakka6e bayan wandan shi"ajuri zuwa
rafi...wannan ma karin maganar ku ta hausawa ce ko?Sinan yakai mishi naushi cikin
tafasar zuciya,shima da zafin nama yakauce yana fad'in"yau dai baka san gani na,to
gwamma cikin girma da arziki in san inda dare yamin,yad'aga hannu yana mishi adabo
sai mun had'u a D'One.
Aminu yana aikin sticker na wani biki da aka bashi kwangila,Sudaida
tashiga da sallama, yace yauwa dama ina neman d'an tayan aiki na leka d'akin ku
banga kowa ba,tazauna tana tayashi suna hira har suka gama,sannan ta tambaye shi
abinda take so ta tambayar shi "Yaya Aminu Sinan baya shaye-shaye kuwa? Yamata
kallan nazari"me yasa kikayi wannan tambayar Sudaida?Saboda duk abokan dayake
mu'amala dasu yan maro ne (wiwi)Tibishi kuma bayan maro har uwar laifi yana
korawa,idan hali bai zo d'aya ba anya za'ayi abota?Ni kwanaki ya min bayani amma
danayi d'an nazari sai nake ganin kamar akwai lauje cikin nad'i.
Gaskiya a iya sani na dashi baya shan kome,to amma kinzo da magana abar
dubawa,kibar kome a hannuna,zan bincika koma menene zamu gano Insha-ALLAH,yad'an
d'age mata gira"kinga ne ko?Tayi yar dariya na gane, ALLAH yabarka da
Siddika.Tazama sarauniyar Aminu kamar yadda kika zama sarauniyar Sinan ko?Sukayi
dariya.Tana jin k'aunar Aminu fiye da duk sauran Yayyin su saboda sauk'in kan
shi,yana jan su ajiki kamar ba babba ba,wasu lukutan har wajan budurwar shi Siddika
tana raka shi hira,ko kuma yaba ta abu takai mata,shi Yaya Adnan shine me irin
halin Umma baya san raini ko kad'an,da shine babban gidan nan ai da sun gama
kad'ewa har ganyan su dan har yafi Yaya Musaddiq za fi.
'Yan lek'en asiri yasa amma basu gano mishi kome game da abotar
Tibishi da Sinan ba.Yakalleta da kulawa,sun dai tabbar suna tare kuma sauran suna
shaye-shayensu amma ko karan taba su dai da idanun su basu ga Sinan dashi ba,dan
haka shawarar da zan ba ki tunda kin yadda dashi a matsayin mijin da za ki aura to
karki tsananta binciken shi, babu wanda za'a tsananta ma bincike face sai an kama
shi da laifi,su Baba sun amince dashi,kuma basuyi hakan ba sai da sukayi bincike,na
kuma tabbatar da yana da babbar illar da zata shafi zaman takewar auran ku to baza
su yadda dashi amatsayin surikiba,kiyita addu'a kina kuma nusarshe shi illar zama
da irin wad'annan mutanan.To Yaya Aminu nagode. ALLAH yaba ka Siddika.Yayi
murmushi.
Tana gidan Hajiya taji sallamar Julaibib.Yanad'e hannayen shi
ak'irji yana kallan ta"kina kwance anan gashi can anata karatu a makaranta.Tad'an
harare shi"uh na gajine yau da gobe ai sai ALLAH,dan dai rana d'aya mutum ya huta
sai afara binshi da k'orafi? Yatsuguna yana duba wasu tsofaffin littafai adirowan
Hajiya"hutun jaki da kaya aka ba.Tad'auki man zafi asaman kujerar"kai baka san
k'afafuna ciwo suke yiba "me zai hana su ciwo tunda jiya kinsha rawar samba" daga
baya suka jiyo muryar shi, Musaddiq ne.
Yagalla mata harara,sai ta sunkwui da kai"tashi ki wuce makaranta,
tamarairaice"dan ALLAH Yaya Musaddiq...yatari numfashin ta shhh...yad'ora yatsan
shi abaki,in dai ba so kike yi ki kwashi kashin ki a hannu ba to tashi kawai
"tafara matso kwalla aranta tana addu'ar ALLAH yakawo Hajiya ita kad'aice zata ta
ka mishi burki,itama d'in idan ta ga dama.Julaibib yasa musu baki"amata hak'uri
mana tunda tana da lalura"wa zan ma hak'urin?Wannan yarinyar? Yanuna ta da yatsa"ai
da lalurar arzikice da har pain-relief zan k'arama ta dashi,ai ka san jiya anyi
Inter-School a Saint-Francis College to nan suka tafi tun safe har biyar da rabi ba
makarantar da suka je ta allo data Islamiyya,ashe yauma basuje ba da safe suka
kwanta bacci wai sun gaji,to d'azu ina gidan Umma takorasu kasan sun maida Mama
kamar sa'ar wasan su koda tayi magana basu jiba,to su sauran sunji maganar Umma sun
tafi ta yamma sai ita shafaffiya da mai tazo nan tayi kwanciyarta?Tafara kuka"ni
dai ALLAH yanaji yana kuma gani banyi rawar samba ba.Yakalleta cikin fushi" karya
zan miki ko?Me zai za k'afufunki suyi ciwo bayan wasan discuss kike yi indai ba
rawan kika yiba?
Hajiya tashigo"yayane Sudaida kike kuka kuma?Musaddiq yayi kwafa"kyale
ni da ita kawai Hajiya samun waje ne kuturu da gad'a a rama.Julaibib yadafa
kafad'arshi"ka kyaleta mana wata kila bayan ciwon k'afafun akwai hujjar datasa
tak'i zuwa,ka san hali da dabi'ar mata Iyayanmu, yan'uwanmu,k'anninmu sai hak'uri,
sai ana kawar dakai awasu lokutan idan ba haka ba,sai su maida kai wani iri,yazame
hannun Julaibib daga kafad'ar shi, yajuya yayi tafiyar shi;tasauke numfashi sai a
lokacin tashak'i iskar yanci"kai Yaya Musaadiq barkono ne,yanzu haka yakema Safiyya
wannan halin?Hajiya tace"barin kira miki shi yaba ki amsa dan wak'a abakin me ita
ta fi dad'i.Takama ha6a"wuuu...Tabbb Hajiya rufa min asiri kar k'ilu taja bauuu...
Ya tashi sahur azumin nafila na ranar alhamis yana juya zuman dayasa a
shayin na'a na'a da 'ya'yan algarib yayi tsai...cikin tunano mafarkin dayayi da
daddare...
"Kasham yake gani da kayan fulani tayi kyau k'irar kalangunta ya fito
rad'am,amma idan tayi magana muryar Sudaida yake ji.
Shekarun baya yayi wannan mafarkin to yanzu ma mafarkin ya dawo shi ya
rasa gane kan wannan mafarkin.Yayi bismillah yafara kur6a amma ko kwata bai sha ba
kome ya gundire shi,shayin yamishi wani irin d'and'ano mara dad'i,ya ajiye kofin a
saman tebur.Yad'auki farar hular zita yasa yad'auki Alqur'ani me girma yana
karantawa har aka kira assalatu daga mabambantan masallatai na unguwar,yayi
raka'atal fajri sannan yafito suka tafi masallaci shi da Baba.
Tana fitowa daga asibiti motar shi tana tsayawa,yabita da kallo tayi kyau
a cikin fararan kayan riga da wando da d'an madaidaicin farin hijab,suka kalli juna
sai yamik'a mata hannu ta san me yake so dan haka tamik'a mishi ragowan Schweppes
d'in da yake hannun ta"ya ajiye a mota dashi zan yi bud'a baki "Megado kinga kyan
da kike k'arawa kuwa tun bamu fara cin Shahrul-Asal (Honey Moon) ba?Ya d'aga kai
sama alamar tunani"Bilkisu k'wak'walwata 6angaren nazari da tunani ta gaza gano
yadda zan fasalta irin kyan da kike tayi,wai meye sirrin ne?Yazubama tattausan
jajayan la66anta idanu;tayi dariyar da tun had'uwar su bata ta6a irinta agabanshi
ba, kumatunta suka lotsa ciki sosai yar siririyar wushiryar ta,ta dad'a k'awata
fuskar ta,Ya ilahi... shi da kanshi ya kauda kai yana jin wani irin yanayi a
ilahirin gangar jiki da sararin zuciyar shi game da ita.
Wai kai kwana biyun nan me yake damun kane sai kadinga wasu maganganu
kamar lokacin kafara gani na?Yamata wani kallo"yunwar so ke damun zuciya ta.
Matsirga zan tafi,takawar da wannan maganar.Yakalleta cikin makaki"wani irin
Matsirga kuma da safen nan?Haba kibari kid'an samu bacci koda awa uku ne,kinga
aikin dare kika yi na san baki yi bacci ba,idan kika d'an huta bayan azahar ba sai
ki tafi ba?"ni dai dan ALLAH yanzu nake san tafiya kar inyi hutun jaki da kaya
aka,agida sai in huta gaba d'aya.A ah Megado ban yadda ba,ba ranar lahadi da yamma
kika dawo daga Matsirgan ba?Tagyad'a kai"Inna nake san gani, tayi yar
dariya"wallahi gobe da safe zan dawo Insha-ALLAH.Ba ga waya ba kikara ta
mana.Tad'an marairaice"ni dai nafi so inganta ganin idanu na.Yad'an
harareta"shikenan tunda kin na ce sai kin tafi to muje in kaiki,idan muka kwana sai
mubugo sammako da sassafe dan nima Zari'a zani a goben.
Tad'an bud'e idanu dan mamaki"ka kwana a ina?Bai bata amsa ba yashiga
mota yazauna sannan yakalle ta"shigo mutafi mun... kiran wayar Baba takatse shi
yad'aga da sallama "kazo yanzu na yi baki suna jiran ka a shago.Ya amsa cikin
ladabi"to Baba gani nan zuwa.Yad'anyi jimmm...D'ansarai lafiya kuwa?Kiyi hak'uri
Megado na so kwarai mutafi tare to sai dai hak'ata bata tadda ruwa ba,akwai bak'in
da suke jirana a shago.A ah ba kome" tashiga ta zauna yaja motar.
Tasha yakaita yasata a motar haya, gidan gaba yabiya kud'in mutum biyun
dan ta zauna ba takura,suna ta hirarsu yana fad'a mata wasu kalamai masu
nauyi,tad'an harareshi sannan ta sunkwui da kai "ka san ALLAH idan baka daina fad'a
min wad'annan kalaman ba zan daina sauraranka,kuma ko waya ka kira bazan d'aga ba,
yayi yar dariya"ni kuma ban san inda kike bako? kaji yar rainin hankali kamar wata
k'aramar yarinya, ba aikin asibiti kikeyi ba? Wancan makon ba d'akin yan hatsari
kuma maza aka kaiku ku musu dressing ba?Wani dare ne jemage bai gani ba?
Tasa hannun damar ta tashafa dogon karan hancin ta,tayi kamar bata gane
me yake nufi ba.Akwai dararan da jemage bai gani ba fa.To wani dare ne kuwa?Shima
yatambaye ta. Tamishi wani kallo daya sa zuciyar shi bugawa Dammm...bai kuma san
dalili ba.Daren da aka haife shi da daran mutuwar shi ko ya gani? Yagirgiza
kai.Kiran Adnan yashigo wayar shi, yad'aga da sallama.Adnan ya amsa sannan ya
tambaye shi"kana ina ne D'ansaarai?Ina tashar mota.Tashar mota kuma?Me kakeyi a
tasha? Bilkisu zan sa a motar Matsirga.Tam dama Hajiya zan kai unguwa Yaya Aminu
yafita da motar gida. Shikenan zo ka kar6i mukullin.Suka cigaba da hirar su har
Adnan d'in yak'araso suka gaisa da Bilkisu a mutunce yakar6i mukullin motar yatafi.
Shafff...ya manta da kiran Baba sai da kiran shi yasake shigowa sannan
ya tuna"Baba ayi hak'uri gani nan zuwa"yamayar da wayar aljihu "Bilkisu barin je in
dawo.Takalleshi cikin natsuwa "bak'i fa kukayi kafin kugama abinda za kuyi ka dawo
ai na tsufa a gida,sai dai munyi waya. Yagyad'a kai"shike nan nagode ALLAH yamiki
albarka.Amin.
"Sai munyi waya...suka fad'a atare.
Sannan suka kalli juna sukayi murmushi yad'aga hannu yana mata adabo
yajuya da d'an sauri dan kar Baba yasake kiran shi,tabi bayan shi da kallo har ya
tsallaka titi ya6ace ma ganinta,tamaida kanta jikin kujera tana sake kiran lambar
Inna dan ta kira sau shurin masak'i amma bata shigaba,saboda matsalar na'urar
sadarwa. Motar su ta cika suna shirin tashi ta tura ma Julaibib sak'on murya(voice
note).
"Julaibib yanzu motar mu ta tashi... Ina sauka kai zan fara kira,ta
mishi sautin sumba muahhh... 💋"
Abinda yaketa rok'on ta ayan kwanakin nan tamishi kenan,amma k'ememe
tace wai ita bata iya ba,rannan data bashi haushi yace"kar ALLAH yasa ki iya d'in
za ki zo hannu duk sai kin biyani bashi dalla-dalla.
Yadawo daga sallar azahar zai shiga d'aki kiran Bilkisu yashigo,yayi
murmushi "haba Nurse Megado ko dak'ik'u talatin bakuyi da tashi bare kice har kin
sauka, yad'aga da sallama "hayaniya da kururuwane ya cika kunnuwan shi "Bilkisu
lafiya kuwa?Wata murya ta amsa"ba Bilkisu bace kazo Wadom yanzu-yanzu sunyi hatsari
ne"Innalillahi Wa'inna'ilahi raji'un" Istirja'in shi Inna taji fito daga D'akin-
girki da sauri. Yajingina kanshi da bango jikin shi a sanyaye "lafiya kuwa
D'ansarai? Sai ga Musaddiq ya shigo duk suka zuba mishi idanu su. Musaddiq yace"me
yafarune?Inna tawatsa hannu"abinda nake tambayar shi kenan kashigo.Yadafa
kafad'arshi"yi magana mana Julaibaib..."Megado ce sukayi hatsari.Inna da Musaddiq
suka yi Istirja'i suma, yaja hannunshi"to tsayuwar me muke yi?Inna sai mun
dawo.Tabisu har zaure bakin ta d'auke da addu'ar Ubangiji yatsare musu hanya.
Gudu sosai Musaddiq yayi.Wajan ya cika dank'am da mutane da jerin
motoci,wani hukuncin Ubangiji kuma daga Bikkisu sai wani dake gidan baya sune
sukaji mummunan ciwuka, sauran dai k'uk'k'urjewa kawai sukayi, shi dama d'an Wadom
d'in ne yan'uwan shi sun zo sun d'auke shi zuwa asibiti.
Ruguzowar wani abu yaji a k'ahon zuciyar shi lokacin daya ga Bilkisu a
kwance sambal cikin jini fuj'atan, zuciyar shi tafara wata irin bugawa da k'arfin
gaske kanshi yasara, yahad'iye wani abu me zafi,yasa hannayenshi biyu ya cicci6eta
zai sa a mota sai kawai wajan ya kaure da salati, masu ihu na yi,masu fad'in Jesus
Christ,Holy Mary nayi,masu d'ora hannaye aka suna sambatu da yarukan su na yi, bai
fahimci kome ba sai da yaga Musaddiq ya d'auki farin hijab d'inta da yarine da jini
ya koma ja,yad'aure mata kai,ashe kan tsagewa yayi ana hango ciki, yashimfid'eta a
bayan mota.
Jama'ar wajan na musu fatan su sauka lafiya, ita kuma ALLAH yata shi
kafad'a yasa kaffarace.Shi kanshi Musaddiq ta maza yayi yake tuk'in saboda ya shiga
rud'u da damuwa,a haka har suka koma Zonkwa.
"Saint Louis Hospital 6angaren hatsari da taimakon agaji na
gaggawa(Accident and Emergency) aka wuce da ita,Julaibib ya kasa zaune ya kasa
tsaye sai kai-kawo yake yi a barandar wajan.Musaddiq yarik'o hannun shi suka
zauna"kayi hak'uri Julaibib na kira Malam Lamid'o a waya yanzu haka suna hanya.
Suna zaune jingum-jingum har su Baba da Malam Lamid'o da Yayyin
Bilkisu Maude da Tukur sukazo, zaman awanni biyu sannan zugan likitocin da
ma'aikatan jinya suka fito daga d'akin.Gaba d'aya suma suka mik'e kowanne hankali a
tashe,Babban likitan yace ku biyoni office.
Cikin natsuwa yad'ago yana kallansu bayan ya gama yan rubuce-rubucen
shi a wani fallan takadda me sunan asibitin"kuyi hak'uri Insha-ALLAH kome zai zo da
sauk'i,yanzu dai mun bata taimakon gaggawa wanda za mu iya amma gaskiya abin ya fi
k'arfin mu dan ya shafi k'wak'walwarta sai dai kuwuce da ita Shika, Ahmadu Bello
Teaching Hospital Ubangiji yaba ta lafiya,yanad'e takaddan yamik'a ma Malam
Lamid'o"Idan kunje ku ne mi...
"Doctor Garga Ibrahim Manogi...
Maude yagyad'a kai"Alhamdulilahi Doctor Manogi k'wararren ne akan abinda yashafi
k'wak'walwa (Neurology) kuma k'anwar Innar su yake aure, dan haka fad'uwa ce tazo
dai-dai da zama.Suka koma d'akin da Bilkisi take kwance, jikinsu yayi mugun
sanyi,wallahi mutum ba a bakin kome yake ba, Ubangiji kamana kyakkyawan k'arshe👏
Tukur yace muna 6ata lokaci ai gwamma muyi harama.
Malam Lamid'o da Tukur agaban motar sai Julaibib da Bilkisu a
baya,su Baba dasu Musaddiq suka lek'o to Ubangiji yakaiku lafiya. Maude yace gobe
sammako za muyi da Inna, Malam Lamid'o yagyad'a ka.Tukur yaja motar, suka bisu da
kallo har suka fita daga asibitin suka hau kwalta.
Julaibib yazuba mata idanu zuciyar shi na bugawa da k'arfin gaske
d'ik d'ik d'ikkk...wuyan ta ya karye an sa mata stiffness collar,kanta yana cinyar
shi har lokacin jini bai daina zuba ba,bandejin da aka nannad'e kanta dashi saura
kad'an yajik'e,hannunta nadama akwai karaya guda biyu,idonta na dama ya zurma ciki
sosai alamar ya fashe ruwan ciki ya gama tsiyayewa,idonta na hagu kuma ya kumbura
suntum har wani kyalli yakeyi,gaba d'aya kamanninta ya canja saboda kumburin da
fuskarta tayi. Idanun shi sun kad'a jawur kanshi yana wani irin sara mishi,yakad'a
kai cikin maimaita Istirja'i yana tallafe da kanta... motar tsittt kowa da yadda
abin yadake shi,wucewar wasu dak'ik'u hannun hagunta da yarik'e yaji ya saki tayi
wata ajiyar zuciya Dammm...zuciyar shi tabuga!Yasake zuba mata idanu yana ta6a
wuyan ta,harbawan da yake yi ya tsaya cakkk...Tukur yana kalkanshi ta madubi a
hankali yagangara gefen titi yatsaya.Malam Lamid'o tun shigar shi motar kanshi
ak'asa yad'ago"Tukur lafiya?duk suka juya baya,Tukur yabud'e motar yakoma baya yana
tatta6a ta,da rawar murya yace"Malam kamar fa bata numfashi.Sukayi shiru nawasu yan
dak'ik'u.Malam Lamid'o ya tabbatar Bilkisu ta mutu!
"Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un!...KULLU NAFSIN ZAA'IK'ATIL MAUT!kowace rai sai
ta d'and'ani mutuwa😭Ubangiji mun tuba,dama kowane d'an Adam me kuskure ne,sai dai
mafi kyawun masu kuskure sune masu tuba.Ubangijin mu kamana gam da katar da
kyakkyawan k'arshe,mu mutu cikin da'a da dokokin ka😭...
"Julaibib yace Malam Bilkisu fa bata mutu ba,dogon suma tayi.Tukur
ma yagyad'a kai"nima haka nake tunani yakoma gidan gaba yazauna yana k'ok'arin
tayar da motar"Malam inaga jinin da take ta zubarwa ne yahaifar da haka.Juya da
motar nan mukoma gida a mata wanka akaita d'akin ta na gaskiya Ubangiji yasa
k'arshen wahalar kenan Bilkisu,kwallah suka cika idanun shi,yasa gefen babbar rigar
shi yagoge. Julaibib da Tukur sukace "a ah Malam Bikkisu bata mutu ba,Insha-ALLAH
kuma za ta warke. Malam Lamid'o yadafa kafad'ar Julaibib"kar muyi haka daku mana,
ni tunda naga Bilkisu dama na san indai ba wani hukunci na Ubangiji ba to baza ta
rayu ba,idan ma ta rayu to za ta samu tasgaro me yawa arayuwar ta,kuyi hak'uri
Bikkisu ta riga ta tafi ni naga mutuwa ba d'aya ba ba biyu ba.
A asibiti ma likita yabasu tabbacin ta rasu,dukkansu hawayene yake
zubo musu sharrr... sharrr... Wayyo ALLAH!Duniya gidan ci rani,duniya gidan azo a
wuce! kowa sai ya koma gidan shi na asali (Lahira)
Gidansu Julaibib suka wuce da gawar Bilkisu dan Malam Lamid'o ya ce
ba sai sun tafi Matsirga ba,duk inda musulmi yamutu ai za a iya yi mishi wanka a
mishi sallah akwaishi makwancin shi.
Inna da Musaddiq da Hajiya suna zaune cikin jimami sai ga Julaibib
yashigo cikin tashin hankali "Lafiya kuwa Hajiya ta tare shi,me yadawo da kai? Ya
zauna a kujera idanun shi sun kad'a jawur,wata jijiya ta fito rad'am a gefen goshin
shi kamar shatin bulala, yabisu da kallo sai kuma yamik'e, jikinsu ya basu dan haka
cikin zafin nama Musaddiq yarik'o shi"Hajiya tace kayi hak'uri... mutuwa ba ta jira
ALLAH baya barin wani dan wani, ALLAH shi yayi Bilkisu, dama aran ta aka ba mu,to
lokacin tafiyarta ta yi dan haka bamu isa mu hana ba,suka cigaba da rarrashin shi
da kalamai masu taushi,Musaddiq yafita wajan su Malam Lamid'o dan har an shiga da
ita D'akin-shak'atawar Inna.
Maude ne yazo da Inna,tana ganin ta a kwance sambal fararan kayan
aikinta sun rine da jini sun koma kalar ja,tayi fari fattt...ta d'ashe alamar babu
sauran jini ajikinta.Inna ta zuba mata idanu cikin hawaye"Bilkisu ke ce kika zama
haka? takad'a kai cikin sarewa da al'amarin rayuwa, kamanninta sun canja ta zama
wata irin halitta,a fuskarta ba irin halittar d'an Adam ba amma wai hukuncin
Ubangiji sauran gangar jikin ta lafiya lau ko k'warzone ba bu na ciwo,in banda
hannun damar ta "Bilkisu kece mace d'aya acikin 'ya'yana na so ganin auran ki sai
dai kash... Kana na ka ALLAH na na shi kuma na ALLAH shine dai-dai,ALLAH yamiki
rahama yasa k'arshen wahalar kenan,Bilkisu kin dace Insha-ALLAH dan kin mutu a
d'aya daga cikin ranakun da babu tambayar kabari akan mamaci,kin mutu ranar
alhamis, tasa hannu tashare hawaya ta fuskanci su Innan Julaibib "mu mata abinda
aka fiso ama mamaci da gaggawa,su uku suka mata wanka suka samata likkafani suka
sata a makara Innan tad'auko fallan zani aka lullu6eta,Maude da Julaibib suka fita
da ita aka mata sallah sai makabarta! Sun dad'e suna ne ma mata gafara musamman
mahaifinta da masoyin ta Julaibib da Yayyinta su Maude da sauran yan'uwa da abokan
arziki.
"YA ALLAH!KA GAFARTA MATA!YA ALLAH KABA TA TABBATA!
Suka juya zuwa cikin gari jikinsu a sanyaye,zuciyoyin su cike da
alhini da d'acin mutuwa.
Malama Lamid'o da iyalinshi suka fito za su tafi.Julaibib yana
tsugune a gabansu ya sunkwui da kai,kukan shar6e yake yi hawayen suna ambaliya a
fuskar shi, ganin haka yasa Tukur yarik'o hannun Inna da take matsar kwallah zuwa
mota"Inna zauna.Cikin dauriya Malam Lamid'o shima yatsuguna yadafa kafad'arshi"kayi
hak'uri Julaibib hak'ik'a wannan mutuwar babu wanda ta dake su kamarmu iyayanta da
kai,to duk mu d'auki hak'uri kowa zaman jiranta yake yi,tabbasss da ina da wata
'yar bayan Bilkisu to dana ba ka, amma zan cigaba da maka addu'a"ALLAH yaba ka
wacce tafi Bilkisu,yayita rarrashin shi sannan sukayi sallama dasu Baba.Tukur yaja
mota suka tafi. Julaibib yabi bayan motar da kallo har tasha kwana ta6ace ma ganin
shi sharrr...sharrr...wasu zafafan hawaye suka zubo mishi. Yakad'a kai cikin
maimaita Istirja'i.
Bayan sallar magriba Inna ta kawo mishi kunun tsamiya da
kosai.Julaibib daga dawowa daga masallaci sai kuma ka kwanta? Tashi kayi bud'a baki
mana.Yamik'e zaune dak'yar dan kanshi na wani sarawa "Inna bana jin yunwa cikina ya
cunkushe kamar na ci abinci"Tajijjiga kai"na sani D'ansarai to amma dai ai ka san
an umarce mu da gaggauta bud'a baki,azumi fa kayi daure kaci dabino kaji... yakar6i
guda d'aya haka dai yaci amma wallahi baiji d'and'anon shi ba dakyar ya had'iye.
Malam Abdullahi yashigo shima yazauna yadafa kafad'ar shi"Malam
D'ansarai ai wannan lokacin yana d'aya daga cikin lokutan amsa addu'a,to ba sai
kayi amfani da wannan damar wajan rok'ama Magado gafara dama kai kanka ba?Duk da
yana cikin damuwa amma sai da yad'anyi yake ganin yadda suke ta rarrashin shi Inna
wai ita sai ta bashi kunnun ma abaki wallahi kuma yau a d'akin baccin ta za su
kwana tare "Karki damu Inna zan sha amma sai zuwa anjima kin san ba sosai nake cin
abinci daga shan ruwa ba.Eh haka ne ,tamik'e ta barshi da Baba.
Washe gari su Julaibib da iyayan su motoci guda uku sukayi dan zuwa
Matsirga ta'aziyya sun tafi da manyan kololin shake tam da abinci ,kullum sai sunje
har sai da akayi addu'ar uku.
Yana rik'e da agogon da aka cire a hannun Bilkisu lokacin da za'a
mata wanka sai jujjuya shi yakeyi,tunaninta da irin hirarra kinsu ya cika
k'wak'walwar shi"Bilkisu a very meek damsel ta tafi ta barshi,burin su na zama
ma'aurata bai cika ba.
"Sai na kira...
kalmar da suka fad'a ma juna ta k'arshe shi da ita kenan,sai sak'on muryar data
turo mishi,yasake kunna sak'on muryar yana sauraro a karo na barkatai sau shurin
masaki,ya kad'a kai"uh uhun mutuwa rigar kowa...
Sudaida tashigo tana kallanshi cikin zancen zuci"shi ko wani irin so
yakema wannan Bilkisun?Kullum taganshi sai taga ya dad'a ramewa,tausayinshi
yamamayeta dan ba ta jin dadin ganin shi a haka,itama tayi nadamar abinda tadinga
ma Bilkisu wanda ita Bilkisun ko a fuska bata ta6a nuna ta ji haushi ba"Yaya
Julaibib dan Allah kayi hak'uri,kaga yadda kake ta ramewa? Yad'an kalleta"to
nagode.Ta ajiye rediyon tafita. Inna tafio daga D'akin-girki tana kallanta tana sa
takalmi"ba dai tafiya za kiyi ba?Tafiya zan yi Inna dan zanyi rubutun allo yau
akwai darasu,amma idan nagama zan dawo in sha fate na.To shikenan, ALLAH yamuku
albarka"Amin Innarmu.
Malam Lamid'o yana zaune a d'akin zaure yajiyo sallamar
Julaibib.Yafito da sauri kaine haka?To maraba yashiga suka gaisa.Malam Lamid'o yace
ikon ALLAH dama Tukur nake jira yadawo anjima za muzo wajan na ku.Ya amsa cikin
girmamawa"Malam shi yasa ma nazo dan Baba yafad'a min yadda kukayi ta waya"Indai za
kuzo ne dan kawo wani abu game da kayan auran Megado to kubari.
Malam Lamid'o yagirgiza kai"sam-sam baza ayi haka ba.Ya amsa cikin
ladabi"wallahi Malam kome da aka kawo saboda Bilkisu na bar muku har abadan duniya
arabama yan'uwa da abokan arziki bazan kar6a ba.Malam Lamid'o yayi shiru cikin
jinjina wannan al'amari,sai kawai yad'auki wayar shi yakira Alhaji Abdullahi
yafad'a mishi abinda Julaibib yace"Baba yayi murmushi "haba Malam dan D'ansarai ya
ce haka har sai ka kira?Tunda yace ya bari to ya bari d'in ne,kutaya mu addu'a
kawai Allah yabashi macen alheri.Ya ajiye wayar cikin sanyin jiki.Karka damu Malam
Julaibib yafad'a."Julaibib ALLAH yamaka albarka,ALLAH yasa kagama da duniya lafiya,
ALLAH yaba ka wacce tafi Bilkisu.
Yamishi jagora zuwa cikin gidan. Innan Bilkisu tana ganin shi tafara
kuka,ya sunkwui da kai cikin wani irin yanayi,ga tausayin ganin yadda Innar Bilkisu
ta zabge,tayi bak'i, idanun ta sun k'ank'ance saboda yawan kuka"Inna kiyi hak'uri
Bikkisu ba kuka take buk'ata a wajan muba,addu'a tafi buk'ata.Inna takad'a kai
cikin hawaye "kaiya d'an nan ba kukan rabuwa da Bilkisu nake yi har yanzu ba,ina
kuka ne saboda wata rana za a manta da Bilkisu wajan yi mata addu'a kaasatan(a
ke6e) saboda bata bar baya ba,dama Ya'ya sune duk rintsi baza su gaji dama mahaifa
addu'a ba,har sai ranar da suma suka koma ga Ubangiji.Yajijjiga kai haka ne,to amma
Inna ya zamuyi da hukuncin Ubanguji?ALLAH bai k'addari za tayi aure ba, bare har ta
haifi Ya'ya,Inna duk hukuncin Ubangiji akan bawan shi adalcine,duk da bata haihu ba
to ai akwai sadakatul-jariya,sadaka me gudana kamar mutum yana raye adoron duniya
ni zan je cikin k'auye inda duke wuyar ruwa zan gina mata rijiya...Malam Lamid'o
yatari numfashin shi"a ah basai ka sake kashe kud'in kaba kabari kawai tunda kabar
mana kome to zan gina mata da kud'in sadakinta...Inna tafashe da kuka ALLAH yabaka
wacce tafi Bilkisu d'an nan, hakika kai masoyin Bilkisu na gaskene dan ka nuna mana
haka duk da bata cikin doron duniya.
Idanun shi suka kad'a jawur"ni gobe zan koma wajan bautar k'asa dama
sallama nazo muyi sai an kwana biyu,suna sallama Bello yashigo da gudu yana haki
yana dariya"Yaya D'ansarai ina dabinon ajwa na da inibi na?Suka zuba mishi idanu ba
abinda yadame shi sai tsallan shi yakeyi"k'uruci dangin hauka.Yamik'a mishi ledar
daya shigo da ita a hannunshi.Yakar6a cikin tsallan murna"Yaya D'ansarai nagode ya
k'ank'ame ledar akirjin shi"to yaushe zaka dawo? Yakalleshi da kulawa"zan dad'e ban
dawo ba. Bello yad'an zaro idanu"kaiii kaima irin tafiyar da Adda tayi za kayi?Inna
fa tafad'a min wai ita baza ta sake dawo wa ba sai dai muje mu same ta,ni fa shi
yasa baza ni ba,kai ai za ka dawo ko?Insha-ALLAH Bello... Idanun Julaibib suka sake
kad'awa jawur ya tuno da Bilkisu da take cewa gobe fa zan dawo Insh-ALLAH... Cikin
wani irin yanayi suka yi sallama yaja motar shi yatafi,ya dad'e a Water-fall d'in
Matsirga yana kallan ruwan yadda yake gudu cikin Qudirar Ubangiji ba dare ba rana
shekara aru-aru.
Sagir yafito da gudu yana kiran shi" Yaya Julaibib wai katsaya.Inji wa?
Yana hakin gudun da yayi yace"inji Yaya Sudaida.To ya shiga mota ya zauna yad'aura
belt,k'afarshi d'aya tana waje.Tak'arsso wajan yana waya,wucewar wasu dak'ik'u
sannan yagama wayar ya ajiye a gafenshi sannan yad'an kalleta kince in tsaya me
zaki bani? Tabud'e gidan baya ta ajiye mishi wata madaidaiciyar leda ruwan
hoda"Donut na maka, tarufe murfin tadawo wajanshi,wallahi tausayi yake ba ta duk
yayi sanyi dama shi bame san hayani bane"sai yaushe zaka dawo?Ba rana sai dai kun
ganni.Idanun ta suka cika da kwallah"dan ALLAH Yaya D'ansarai ka dinga cin abinci
kaga yadda kazama kuwa?Ina cin abinci mana Sudaida ai d'an Adam bazai rayu ba
abinci ba.Tad'an marariraice"to amma dai d'an tsakura ka keyi, kadinga ci
dayawa,yamaida k'afarshi cikin motar tarufe murfin.Nagode Sudaida.kadinga cin
abinci kaji?Tasake fad'a.To ya fad'a a tak'aice. Tasunkuyo"Allah ya kaika
lafiya.amin Sudaida yaja motar tabi bayan motar da kallo har yayi nisa ya6ace ma
ganinta,wani abu na mata kai-kawo a zuci,tasauke numfashi tabaki ta hanci sannan
tajiya zuwa cikin gida ran ta ba dad'i.
A sanda hantsi yadubi ludayi na safiyar alhamis suna cikin hutun
makarantar boko na ranar yara(Children's day)kuma yau ba makarantar allo ba
Islamiyya kowa yana abinda yake so ne, dan duk sun gama ayyukan gida.Tana kwance
ranta ba dad'i tunda Julaibib yatafi sau uku kawai sukayi waya yauma takira shi
sama-sama suka gaisa yakatse,tasake kira yad'aga da sallama"Yaya Julaibib na maka
laifine? A ah baki min kome ba.To me yasa kike min wani iri? Yad'anyi
murmushi"Sudaida kenan ni ban miki wani iri ba fa zan shiga aji ya katse
wayar...Tayi lamooo a gadan,tunani barkatai ya cika k'wak'walwarta ta rasa na za6a
tayi.
Nasmat suka shigo suna hayaniyarsu kamar yadda suka sa ba,suka
kalleta suka kwashe da dariya"Sudaida uwar tafakkuri (tunani)me kuma yafaru?Khausar
ta ta6e baki tabud'e wadrobe ta d'auki kayan da zata goge a D'akin-shak'atawa
tafita...Bata basu amsar tambayar su ba,takalli Zainab"ya maganar bikin saukar mu?
Ta zauna a gefan gadan"ai Malam yayi tafiya sai ranar asabar zai dawo.A'isha
tamik'e "barinje muk'arasa kallan mu dan yau bazan dad'e ba,angona Hashim anjima
yana hanya.Nasmat tad'an daki kafad'arta"to gaggawa hannu hagu a romo mutumin da ko
tasowa bai yiba.suka mik'e ita da Zainab.Nasmat tabi da Sudaida da kallo "dan ALLAH
me yake damun kine?Tamaida kanta saman matashi"na fad'a miki ba abinda yake damuna
to ki rabu dani mana.Sudaida na damu dake shi yasa nadamu da halin dakike ciki.
Tamaida idanun ta tarufe...Nasmat ki kyaleni bana san hayaniya fa.Tamik'e ALLAH
yabaki hak'uri, amma ina zargin wani abu koda yake...sai tad'an motsa kafad'a
shikenan can da yawarki yarinya.
Sai da aka cinye zangon karatu d'aya sannan Julaibib yazo gida.Yau
alhamis ranar da ake bikin saukar Alqur'ani me girma nasu Sudaida,kome an shirya
shi cikin mutunci, bangaran maza daban na mata daban Liman yabud'e taran da addu'a
yama daliban addu'a Allah yasa suyi amfani da abinda aka koya musu a kowani irin
hali da yanayi suka shiga na rayuwa...aka biyama d'aliban allunan su sannan aka
cigaba da wa'azi da fad'akarwa akan neman ilmi dan shine yake sanya rayuwa tayi
kyau tayi albarka.
Bayan angama kome sannan aka shiga yin hotuna da rabama d'alibai
kyaututtuka aka rufe taro da addu'a,Sudaida tasunkwui da kai abinda yaba
mak'alallun k'wallan cikin idanun ta damar zubowa k'asa sharrr... wannan taran me
tarin albarka mutane da yawa sun halacceshi amma banda Sinan,to me ya hanashi zuwa
tunda ya sani?Tayi kwafa wallahi za mu had'u ne.
Tana d'ago kai,caraf idanun su yahad'u, wani sanyi dad'i taji a
ilahirin gangar jiki da sararin zuciyar ta. Alk'asim yak'araso wajan "gaskiya yan
matan nan kun had'u,zai mik'a ma Sudaida rufaffen envelop A'isha takai hannu za ta
kar6e,yajanye hannunshi da sauri"a ah ya haka? Tagyad'a kai"eh haka nake nufi,kai
kaga hakan zata sa6u bindiga acikin ruwa? Wasa tare ci bamban?Khausar tace ko muma
abamu ko itama tarasa. Yayi yar dariya "mata problem kunga fa ba wani abu bane a
ciki,rubutune kawai akayi da biro bulu.Eh koma dai menene to abamu na mu. Nasmat ta
katseshi"to wai ma yahaka?Ana zatan wuta a mak'era sai ga ta kuma a masak'a?Wallahi
wanda nayi hasashen zai bata kyautar kaasatan bai yiba sai kai?Yamaida envelop d'in
aljihu "shikenan karku samu damuwa za kuji a salansa, Sudaida sun hana in baki
hannu da hannu zan aiko miki dashi gida,yajuya yayi tafiyarshi bai saurari
hayagagar da suke mishi ba.Suka jera suna tafiya zuwa gidan Hajiya"Aisha tace wai
me yahana Sinan zuwa wajan saukar mu,naga har Hashim daba d'an gari ba ya zo?
Tawatsa hannu"nima ban sani ba amma ina ga kamar ba k'alau ba.
Dayammacin ranar sai ga shi da kaya nik'i-nik'i lemukan gwangawani
dana kwali, yana zaune a dakalin k'ofar gidan tafito cikin fushi Sagir na biye da
ita da kayan,takar6a ta ajiye mishi "Sinan ba wad'annan nafi buk'ata ba,zuwanka
wajan ya fi duk abinda za ka bani. Tajuya...Yasha gabanta da sauri yahad'a tafukan
hannayen shi da sigar rarrashi"Sarauniyar Sinan kiyi hak'uri "Tagirgiza kai"ban
hak'ura ba sai ka fad'a min abinda yahana ka zuwa.Yad'anyi jimmm... na wucewar wasu
dak'ik'u"za ki yadda dani?Tayi shiru sai yacigaba"to ni dai na san na miki laifin
da ban ta6a miki irin shi ba,Sudaida baccine yayi awan gaba dani,to ya zanyi?To
wayar ka amfanin me takeyi na kira ka sau shurin masak'i baka d'aga ba,sai kace me
baccin mutuwa? Yakad'a kai cikin damuwa"lallai na cancanci abani horo,itama fa
wayar a yanayin shiru nasa ta,kiyi hak'uri Sudaida "ALLAH yana san masu
hak'uri,masu had'iye fushi, suna da dama su rama abinda aka musu amma sai suke
hak'ura su yafe,su maida kome ba kome ba saboda ganin girman ALLAH...yacika da
dad'ad'an kalamai har sai da yashawo kanta. ALLAH da gaske ke nake so Sudaida
alk'awari ba karyawa ni da ke sai mun zama abin kwatance mutu ka raba takalmin
kaza. Da haka yaba Sagir kayan yamayar dasu cikin gida..
Kwana biyu da fara azumin watan ramadan yashirya shi da Musaddiq sai
Matsirga. Inna tana zaune a d'aki taga ana shigo da kayayyaki tasa hijab tafito
tsakar gida tana tambayarsu daga ina wad'annnan kayan? Sai ga Bello yashigo da
murnar shi yana fad'a mata su Yaya Julaibib ne.Jikinta yayi sanyi tabi kayayyakin
da kallo cikin zancen zuci"wato k'auna ta gaskiya tana d'orewa koda ba wanda ake
k'aunar a doron duniya. Bello yarik'o hannunta "Inna na shigo dasu. Tayi
murmushi"lale maraba,sannunku da zuwa bismillah tajuya zuwa cikin d'aki suka
bita,cikin girmamawa suka gaisheta"Iyayan na ku k'alau ko? A lafiya k'alau Inna
suna gaishe ku.To madalla ALLAH yamuku albarka,ku bakwa gajiya da hadima?Musaddiq
yace"haba Inna ai bakome... yiwa kaine.To Ubangiji yasa ka muku da mafificin
sakamakon shi;ALLAH yasa hakan amizaninku na kyawawan aiyuka. Amin,amin Inna.
Inna su Malam basa nan ne?Eh d'azu shi da Maude suka tafi Zango wajan
k'annin mahaifanshi,Tukur kuma jiya yakoma makaranta. Suka d'an ta6a hira sannan
suka mata sallama taciko musu jarkoki da kindirmo da manshanu, Bello yasa kuka shi
dole sai sun tafi dashi Inna tayi-tayi ya zauna amma ya kafe ya nata ihu shi dai
zai bi su,duk yamak'alk'ale Julaibib ya 6ata mishi farar shaddar da yasa da majina
da ruwan hawaye,yarik'o hannun shi.
Inna bari muje waje muyi magana tabisu da kallo,a mota suka dinga
rarrashin shi "kaga idan muka tafi dakai Malam bai sani ba idan ya dawo zaima Inna
fad'a muma zai mana fad'a, yamak'ale kafad'a"uh uh ai idan tace kaine bazai yi
fad'an ba,kuma kana da waya kafad'a mishi na san zai yadda,ni dai kawai ALLAH
mutafi"to naji na kuma maka alk'awari idan aka samu hutu Insha-ALLAH zan zo in tafi
dakai Zonkwa.Yad'ibo dabinon ajwa da yawa a aljihunshi idan ka yadda sai in bar
maka wannan dabinon,yakalleshi sannan yakalli dabinon" to duka zaka barmin?Yayi
murmushi"eh mana sa hannunka ka kwashe ma, yana ta d'auka da d'ai-d'ai da d'ai-d'ai
yana sawa a aljihunshi har ya kwashe duka sannan yayi dariya aina kwashe, to sai ka
zo d'in barinje in nuna ma Inna,yauwa Bello mutumin kirki barin rakaka,har ciki ya
kaishi ya kuma fad'a mata yadda sukayi tayi murmushi kawai sannan suka sake yin
sallama sunama juna asha ruwa lafiya.
Rana ta tafi zata fad'i magriba na shirin kunno kai,an kusa shan ruwa
takashe rediyon da take sauraran tafsirin Alqur'ani me girma a gidan rediyon jahar
Kaduna(FRCN)farin gida kafin Sardauna.Tayi doguwar hamma tasa tafin hannun dama
tarufe bakin ta, tana Isti'aza yau ba laifi tana jin azumin nan ajika dan ma yau
Khausar ce da aiki da wallahi bata san yadda za tayi ba kanta har barazanar ciwo
yake yi,daga can D'akin-girki tajiyo kiran Umma tamik'e da sauri tafita.
Umma gani.Umma tamata wani kallo "ba tun d'azu nace ki d'auki dabgen
Hajiya ki kai mata ba?Baki ji bane ko zuwan ne baza kiyi ba? Tad'an sosa kai Umma
fa boss ce,bata d'aukar raini ko na sisin kwabo"Yi hak'uri Umma barin d'auko
hijab,tasa hijab ta d'auki kwanan samiran sannan tad'an kalketa cikin shakka"Umma
dan ALLAH daga nan zan biya gidan Inna.Tayi shiru kamar bata jiba sai da tagama
zuba wani dabgen a wani samiran ta rufe sannan takalleta"adawo lafiya suma ki tafi
musu da wannan.Wani murmushi yasu6uce mata dan ba k'aramin aikin Umma bane
tahana"nagode Umma tarik'o hannun Hanifa'yar Musaddiq ta fari suka tafi.
Tana shiga sai ga Nasmat itama takawo ma Inna hadaddan kunun aya kafin
a kira sallar magriba sunyi alwala,ana kiran sallah sukaci dabino da lemun 6awo da
ruwa me rangwamen sanyi sannan suka tada kabbarar sallah.
Julaibib da Baba suka shigo da sallama sukama juna barka da shan ruwa
sannan ya ajiye ledan hannunshi a gaban Inna.Nasmat tajawo ledan gabanta tafara
shan abarban da yake ciki da kankana yankakku tana fadin"kyan rawa da
makar6i.Sudaida ma tasa hannu ta d'auki kankana tana cema Hanifa sa hannu ki
d'auka...Baba yayi murmushi ganin irin kallan da yake musu,yayi k'wafa yajuya zuwa
d'akin shi Inna tana mishi dariya itama.Sudaida ta ka sa cigaba da sha, ranta ba
dad'i har yanzu bai dawo yadda tasan shiba, ba wani kyan gani da yayi,yabar
k'asumba ba wani gyara,kana mishi magana zai bika da wannan rikitaccen kallan,ya
ya6a maka bak'ar maganar da ko barinje (mahauci) iya karta kenan.
A sanda hantsi yadubi ludayi na safiyar laraba yana nazarin wani littafin
tafsirin Alqur'ani me girma Hajiya tashigo da sallama,yamik'e da sauri yataro
ta"maraba da zuwa Hajiyar mu,ta ture shi"kai tafi can matsa kabani waje,ta zauna a
kujera tana murza k'afafunta,ya d'auko man zafi zai shafa mata tajanye k'afafunta
da sauri"bana so.Yayi murmushi"haba Hajjaju makkatu wal madinatu gwiwata a
k'asa,kaina bisa wuyana.Oho ashe kaima ka san kayi laifi,saboda ALLAH Julaibibi
tunda kazo garin nan sau d'aya rakkin rak kazo gidana,ba fad'a to me yakawo wannan
gabar? Kiyi hak'uri Hajiya bana jin dad'i ne.Tajijjiga kai tana mishi kallan
nazari"kai Julaibibi tunanin Bilkisun ce yake susuta ka haka?Yagirgiza kai "haba
dai Hajiya ba wannan bane.
Yamik'e da sauri ya d'auko madara da maltina da kofi.Hajiya tabishi
da kallo cikin mad'aukakin mamaki"ciwon har yakai ba ka iya yin azumi ne Julaibibi?
Yadafe kai "Innalillahi.Ina yi, wai dama ke zan kawo ma na man tane.Tamik'e wa?Ni
kaga tafiya ta.Yarufo gidan"barin taka miki suna tafiya suna hira"anjima da daddare
zan zo miki hira sai ki tanadar min garwashi zan zo da d'anyan masara in gasa
mana"To ALLAH ya kaimu har gidan Kawun shi yakaita.
A D'akin-shak'atawa Sudaida ce kawai tana kwance a doguwar kujera tana
waya,tamik'e zaune saboda shigowar su,kusan dak'ik'u goma sannan tagama
wayar,tad'ago tana kallan Julaibib bayan ta d'ora ha6arta a kafad'ar
Hajiya"Hajiyarmu you're welcome.Kin san abinda bature me jan kunne yake nufi da
haka?Tajijjaga kai"tun kafin in haifi uban ki ya haifeki kuwa.Tad'an turo baki,
Julaibib yayi murmushi yana shafa k'wantaccen bak'in gashin kanshi"Yo kya 6ata
fuska ba tambaya kikayi nabaki amsa ba?
Mu turancin mu ma gangariya masu abu da abun su kura da kallabin
kitse, turanwan ne fa suka koya mana baki da baki,To me yasa bakya yi?Tad'an
kalleta kaji wata magana to yaran turanci yarena ne?Ni yarene hausa idan takama ayi
turan cin inayi mana"do you get me? Sudaida takyalkyale da dariya saboda yadda
Hajiya tayi furucin tagyad'a kai"yes grandam.Su Mama suka shigo suna gaishe da
surukar ta su cikin girma da mutuntawa.
Da daddare yana gidan Hajiya suna hirarsu takalleshi"tunda katafi Azare
kayi zaman ka shiru ba amo ba labari ko wata bafulatanarce takuma rik'e mana kai?Ya
jujjjuya masarar sannan yad'ago yakalleta"ko d'aya Hajiya.To in dai haka ne ya
kamata ka nemi wata,ga yan mata nan burjik a cikin dangi sai ka za6a ka darje,kana
gani ganin idanun ka Musaddiq Ya'yan shi biyu ga cikin na uku nan.Cikin wasa
yace"Hajiya banga wacce nake so ba ko za ki tayani nema?Tagyada kai"anyi an gama
maye ya auri makauniya.Bai wani dad'e ba yamata sai da safe, saboda akwai tashi
cikin dare domin yin munajaati ga ALLAH buwayi gagara koyo ga kuma tashi yin sahur.
K'arfe-k'arfene sai dai a cikin k'arafan akwai zinare da azurfa.
Idan baka san gari ba...saurari daka.
Abdullahi Lawal Abdullahi (D'ansarai)
Saudat Ibrahim Yahya (Takwara ta)
Mungode da tunatarwan ku bisa wani kuskure da mukayi a shafi na goma sha biyar..
Falmata Maiduguri mungode da kulawa.
28 Jumaada Awwal 1441
23 January 2020
We Ibrahim's Daughters 👇
Asdilat KD...2geda with Ra'ibs.
DANGIN NONO WRITERS ASAOCIATION
{Da Inganci Mukayi Fintinkau}
Bismillahi wabihi nasta'in
...GWAJIN DAFI💔
Almost true story
Daga alk'alamin🖊
Ya'yan Ibrahim
Saudat A.Baba (Asdilat KD)
Da
Bara'atu Ibrahim (Ra'iba)
Shafi nagoma sha bakwai.
Bayan sallar asham Julaibib yawuce gidan Hajiya anan yatarar dawasu
daga cikin jikokinta maza anata hira da ciye-ciye.Yajawo kaskon data cika da
garwashi gaban shi, Musadduq yaja tsaki"Lillahi warasulihi yauma karasa abinda za
ka kawo mana sai bushashshen masara?Kai ALLAH yasauwake.Ya amsa da amin "dan ka
kawo mata bushasshen nama wai shi kilishi ba shi zai hanata cin gashashshiyar
masara ba.Musaddiq yagirgiza kai"kai Malam ai yanzu ba lokacin cin kilishi
bane,watan ramadan muke gasassun yan shila nakawo mata me ruwa-ruwa da yajin
tafarnuwa ya ji kayan lambu.Yaturama Julaibib k'unshin duba kagani.Yayi kamar ba
dashi yake magana ba yafara gasa masararshi yana tambayar Hajiya ta saurari tafsir
na karfe uku da yammacin yau?
Kwanci tashi har anyi azumi takwas, agida tasame shi yana shirin komawa
Azare "tazauna tana kallan shi"Yaya D'an Sarai tafiya ba sallama?Yacigaba da shirya
kayan shi a jaka ba tare daya d'ago ya kalle taba"ai naje gidan akace kin tafi
Hayin-Dogo"haka ne to yaushe za ka dawo? Yarufe jakar yad'auki agogo yana d'aurawa
a hannun damar shi"sai ALLAH ya kaimu sallah idan muna raye,ta taya shi kwashe kaya
zuwa mota yayi sallama da Inna suka fito,tajingina da motar tana kallan shi cikin
kissima wani abu a zuci yana zuba ruwa a lagireto har yagama yashiga mota yazauna
yana d'aura belt.
Yad'anyi murmushi"duk kinyi wata iri ko za ki bini ne?Ta turo baki
gaba"da inada wannan damar ai da ba haka ba wallahi.Baiyi magana ba,yabata wasu
kud'i"bayawa.Tasa hannu biyu takar6a"nagode Yaya D'ansarai ALLAH yak'ara bud'i,suka
d'aga hannu suna ma juna adabo.
Sun dawo makaranta suka tarar da Asma'u kanwar Sudaida ta ci kuka ta
gode ALLAH idanun ta sun kumbura sun kad'a jawur"lafiya Asma'u? A tare suka tambaye
ta,sai tasake jin wani sabon kukan ya kufce mata tafi minti goma sannan tafara rage
sauti tana ta jera ajiyar zuciya"ke wai kukan me kike yi ana tambayar ki kin ma
mutane shiru wacece sa'ar ki anan? Khausar ta tambaye ta.Taja majina tana hura
iskar bakin ta"labarin zuciya a tamabayi fuska ranta in yayi dubu ya 6aci,cikin
hawaye tafara magana"wai arasa wanda za a bani a matsayin mijin aure sai Yaya
D'ansarai...wasu hawaye masu d'umi suka sake zubowa sharrr...sharrr...Sudaida
tamik'e zaune da sauri kamar za ta hantsila,duk suka bita da kallo ganin yadda tayi
sai kuma ta koma ta kwanta batayi magana ba dan ta ma rasa abinda za ta fad'a
wallahi.
Asma'u tacigaba bayan kowa ya san Alk'asim nake so amma ance a ah wai
shi yaro ne ko Secondary bai gama ba,takad'a kai cikin takaici"saboda ALLAH wai
Yaya D'ansarai. Khausar takalleta cikin natsuwa"bakya san shine? Dasauri tace"eh
mana me zanyi dashi bak'ink'irin dashi kamar bak'in gashin kanshi...bata gama rufe
baki ba taji saukar mari hagu da dama"Yaya D'ansarai kike za gi?To dame kwad'o yafi
gaya?Ba gwamma shi bak'i kyakkyawa bane.Asma'u tamik'e cikin hawaye"amma wannan
rashin 'yanci da yawa yake,ga mari ga tsinka jaka?Takalle ta "wallahi Yaya Sudaida
bana san shi,tafita a d'akin da gudu cikin shashshekan kuka.
Tadunk'ule hannu ta naushi iska"da kin tsaya k'aramar mara kunya da
kinga yadda zan yi dake.Khausar takalle ta"ai baki isa ki kuma dukan taba akan me?
Dan tace ba ta san shi shine ya zama laifi?Yaya Julaibib d'in?Kwarai kuwa shi
wanene da kowa sai ya so shi so?Wa kika ta6a gani ko jin labari kowa na doron
duniya ya so shi? Ko wanda yayi mu an samu wanda basa san shi ta hanyar k'in yadda
da duk abinda yace ayi,da wanda yace abari,bare wani Julaibib ordinary human
being,ai dama na dad'e ina zargin wani abu bani da tabbasss shiyasa naja bakina
nayi shiru; to amma yau na samu yak'ini san Julaibib d'in nan ki keyi,to dake dashi
d'in duk sai kuje kuji da manufurcin ku,ai shima ina lura da takunshi akanki.Yaya
Khausar daza kice haka shi kuma Sinan d'in ina zan kai shi?Tawatsa hannu"ke kika
sani...
Cikin bugun zuciya tafara harhad'a littafan data barbaza a kan gado da
niyyar yin nazarin su,ta tsuke baki tana yamutsa fuska Khausar tayi yar dariya tana
rage kayan jikinta za ta shiga wanka Asma'u ta D'ansarai bak'ak'e biyu kila za su
iya samar da wankan tarwad'a ko fari ko sarauniyar Sinan?Bata kula taba tamak'alama
wayar ta earphone tana k'ok'arin toshe kunnuwan ta dashi. Khausar ta fizge"ke
malama kirufa mana asiri karki zama kanwar kurma,so nawa ni da ke munajin bayanan
da likitoci k'wararru a bangaran kunne,mak'ogwara da hanci(E N T) sukeyi,yawan
amfani da earphone yana kawo matsala a bangaran ji"tagyad'a kai "naji bani
wayata.Tamik'a mata, kita shi kisan abinda za ki d'ora tunda su Mama basa nan ko
miyar shuwaka za ki mana mun kwana biyu bamu ciba wallahi,ta san Sudaida bata so
dan tayi tsokana tafad'a. Yaya Khausar"ai bazan hana kiyi idan kina so ba"kuturu da
kud'in shi alkaki ba sai na k'asan kwano ba?Gaskiya ne to d'anje kifara wanke min
shuwakar kafin in fito wanka.
Kwana biyu da maganar ranan Asma'u ce da aiki tasame ta a D'akin-girki
tana kad'a miya sai ta kar6i maburgin barin taya ki,Asma'u tad'anyi murmushi "Yaya
Sudaida saboda ALLAH ko kuma cin tuwon kishiya...?Duka biyun.Sukayi dariya, Asma'u
tana zuba mata garin kuka tana cigaba da burgawa har suka gama, tad'an jefa kanwa
kad'an wucewar wasu yan dak'ik'u tasauke to d'orama Yaya Aminu ruwan da zata dama
mishi custard aranta tana mita"gaskiya Siddika ta shiga uku da shan kunu,ga fa
kunun tsamiya can Inna ta aiko mai dashi amma duk da haka wai dole-dole sai ta dama
mishi custard,ruwan yana tafasa ta dama tajuye mishi a flask.
Tamatsa gefe tana cema Asma'u ai dai na taya ki,dan haka zo ki dora ruwan
tuwon ki. Takalli Asma'u da natsuwa bayan tad'ora ruwan "waye yace za a ba ki
Julaibib a matsayin mijin aure?Tayi d'an tsaki"na manta.Kin manta?Eh,to ban sa a ka
ba inji 6arawon tagiya,sai kuma tayi kwafa"ba Hajiya ce da wannan neman maganar
ba,haka kawai ga wanda zuciyata take marari... Tad'auki flask batace kome ba tajuya
tafita. Asma'u tabita da kallo"yauma kinji haushi dan na ce ba shi nake so ba ko?
Tad'an motsa kafad'a,sai dai kiyita jin haushin me zanyi dashi?Tad'auko garin dawa
za tayi talge dan har ruwan ya tafasa.
Littafan tane a saman tebur ta barbaza, nazarin su take so tayi d'aya
bayan d'aya saboda ranar Litini za su fara jarabawa,tad'auki littafin lissafi tana
dad'ayin nazari akan darasin da aka musu wancan makon Simultenous Equation sai dai
ko dak'ik'u goma bata had'a ba taji ta gaji,ta kasa fahimtar kome duk da kuwa a
wajan lissafi babbar k'waruwace,ita dai azumi yana ba ta wahala da mutum zai iya
biya a mishi aikin ibada to ita dai azumi za ta dinga biya,kome a wahale takeyi,ta
ture littafin gefe idan ba haka ba yanzun nan kanta zai fara ciwo kuma yau itace da
aikin abin bud'a baki,a hankali taza me takwanta a doguwar kujera gwamma tad'an
rintsa kafin lokacin aiki yayi,tad'anyi tsaki tun yanzu jikinta ya mutu murusss...
ALLAH dai yasa Umma karta ba ta aiki me wahala.
Kamar a mafarki tashak'o k'amshin arabi'an perfume tare da
sallama.Dasauri tabud'e idanunta da suka canja kala dan bacci ya fara awon gaba da
ita,yana jingine da k'ofar shigowa yayi sharrr...sharrr dashi cikin farin yadi me
k'ananan huji-huji kana hango farar singilet d'inshi, bak'in gashin kanshi ya sha
gyara yanata kyallin hair fruits,ba laifi yafara maida jikinshi sai taji dad'i a
ranta.
Tamik'e zaune cikin mamaki"Yaya D'ansarai?Yabar duba wayar hannun shi
yad'ago yana kallanta "na'am,ina ta sallama baki amsa ba szumin tun yanzu ya fara
duka kenan.Tayi murmushi"tad'anyi tsaki kai dai bari kawai, wai ba ka ce sai sallah
za kazo ba?Yak'arasa shiga D'akin-shak'atawar"eh,yau da safe nazo anjima kad'an zan
koma na manta wasu muhimman takaddune abinda yadawo dani kenan,yad'aga kiran daya
shigo wayar shi, baiyi magana ba bayan sallamar da yayi,sauraro yakeyi... zuwa wasu
yan dak'ik'u ya amsa da"nagode Maimun musha ruwa lafiya.Yasa wayar a aljihu,yana
d'ago kai caraf idanunsu yahad'u yakauda kai...daga can tsakar gidan suka fara jiyo
Asma'u cikin nishad'in ta,tana rera wasu baiti daga cikin baitocin wakar Sadi Sidi
Sharifai da Maryam A.Baba(Sangandale)suka rera...tana tafe tana tafa hannaye.
🎶🎵Taho malam,taho gani nan da soyayya nafito daga gida🎵🎶
🎶🎵Ina shaidama a yau ne nasamu sak'onka, ina zaune a gida sai naji shi begen
ka🎵🎶
🎶🎵Shine nafito in duba ko zan ganka🎵🎶
🎶🎵Amsar sak'onka na yarda in zam matar kazamo megidahhh...🎵🎶
Tana shigowa suka bita da kallo.Kunya da haushin shi suka rufe ta,tayi
jimmm...fuska a yamutse tagaishe shi,bata jira amsawar shi ba ta d'auki abinda
yashigo da ita"tin-opener"a saman tebur tajuya.Asma'u yakira ta.Sai tayi kunnan
uwar shegu tak'ara sauri.A k'ofa sukayi kaci6is da Mama,takalleta da kulawa"saboda
ALLAH Asma'u a wannnan gwalagwalan kwanakin nagoman k'arshe kika tsaya rera
wak'a...?Tayarfe hannu "dan ALLAH Mama kiyi hak'uri kar Umma tajiyo ki, yanzu
tashigo gidan daqowarta daga unguwa. Astagfirullah...Mama tayi murmushi"ALLAH
yadad'a shirya ku.
Sudaida tabishi da kallo bata ga wani yanayi a fuskar shi ba,yakalli
agogon dake d'aure a hannunshi na dama,lokaci ya ja gashi har Matsirga yake so yaje
kafin yawuce. Yad'an kalle ta"ke na wuce.Ta taka mishi har k'ofar gida inda ya
ajiye mota"Yaya Julaibib ALLAH yatsare hanya, musha ruwa lafiya.Amin Sudaida
nagode.Tajuya zuwa cikin gida tana zancen zuci"Yaya Julaibib bai san da maganar
Hajiya akan an ba shi Asma'u ba. Asma'un kawai Hajiya tafad'a ma.
Yau take sallah...kowa kagani yayi sharrr dashi dashiga ta burgewa ya
kure adaka.Bayan an sakko daga sallar Idi Hajiya da wasu daga cikin jikokin ta suka
mata rakiya zuwa gida.Me musu fid'an ragon sallah har yazo na Hajiya yake fara
gyarawa kafin yawuce sauran gidajan, suna d'an hira da Sudaida tana kallan yadda
yake yi cikin sauri da k'warewa.
Julaibib yashigo da sallama,yana sanye da babbar riga,'yar ciki da
wando na farin voil,takalminshi sau ciki da hular dara bak'a, k'amshin arabi'an
perfume d'inshi ya cika tsakar gidan kamar lokacin yake fesawa, gyaran fuskar
dayayi sai yak'ara mishi kyau"har ka cire kwalliyar sallar?Ba dole ba autan
Inna,zanyi aikin fid'a da farar shadda ne?Zai shiga d'akin Hajiya yace "ka daiyi
sauri kagama dan ga na Inna can yana jiranka.Tabi bayan shi zuwa d'akin.
"Happy Eid-eel Fitr sarauniyar Sinan.
D'an gajeran sak'on Sinan daya shigo wayar ta kenan,tayi
murmushi.Tazauna tana kiran A'isha dan Kafanchan ta tafi wajan Kaka acan tayi
sallah. Tad'aga da sallama,Sudaida ta amsa sannan tad'ora"zakara ya ja kaza kinyi
sallah lafiya?Ta amsa"a ah mantawa kikayi takalmi ne yaja k'afa.Sudaida taja tsaki
"ai wallahi sa a ma kika ci dana kira ki,keda za kiyi zaman ki shi Hashim d'in yazo
nan yayi sallar wai sai kawai kika wani bishi...A'isha ta tari numfashi" ke dakata
haka malama karki d'oramin jakar tsaba kisa kaji sudinga bina,wannan sallar nafara
zuwa Kafanchan?Ni ba wajen shi naje ba wajan Kaka naje.Tasake jan tsaki"ba cinya ba
k'afar baya. Itama ta amsa"a ah ALLAH yasa k'afar kafad'a ce, ke kika sani,ba
Khausar wayar.Yaya Khausar gida tawuce ni ina gidan Hajiya.Tam barin kirata sukayi
sallama. Asama taji Hajiya tana fadin"to na samo maka matar aure.Matar aure wace
iri kamar yaya? Yatambayeta cikin rashin fahimta.Takalleshi"au ka manta yadda
mukayi dakai cikin azumi?Ba ka ce in samo maka bane?Yakama kai"Innalillahi,Hajiya
ni fa wasa nake miki.Tawatsa hannaye "kai kajiyo, amma dai aikin gama ya gama duk
dai ban fad'a ma kowa ba sai yarinyar,to amma tunda kaima na fad'a maka to zan
fad'a ma Iyayan na ku kowa yaji yakuma sani.Wacece ita?Tagirgiza kai"uh uh ba
yanzuba ina so ne tad'an kara girma da hankali lokacin an kawar da Yayyinta.
Shi da Sudaida suka kai juna.Yakauda kai cikin rashin sanin abun
fad'a,yasauke numfashi,d'an madaidaicin kofin hannun shi ya ajiye a saman
tebur."akara maka ne?Yakalli Hajiya kamar be ji abinda tafad'a ba na'am, a ah
Alhamdulillah wannan d'inma ban shanye dukaba, yad'auki murfin yarufe kofin.Yad'an
karkace kad'an yaciro rafar yan naira ashirin guda d'aya ya'ajiye agabanta"Hajiya
ga nawa goron sallar ba yawa. Tayi murmushi"Julaibibi me yawan kenan ALLAH yayi
albarka nagode madallah.Sai ga Nasmat ta shigo da babban foodflask cike tam da
tuwon sallah"godiyar me wannan tsohuwar take yi?
Idanun ta yasauka akan kud'in takama ha6a wai wai wai sai ta
zauna"Hajiya lillahi warasulihi keda mutuwa tafara k'wank'wansa miki k'ofa me za
kiyi da sababbin kud'i?Tamik'a mata hannu kawo su kawai,to ke me ma za ki siya ne?
Hajiya ta d'auki kud'in ta"zancen ki dutse,zan kuma rasa ba ki, ki zauna jiran
gawon shanu kinji ko?Takalli Julaibib"Autan Inna yau take sallah fa.Yamata wannan
rikitaccen kallan na shi yayi-yayi tadaina kiranshi da wannan sunan amma tak'i "yan
mata kyau da sallah idan tawuce sun zama jakai.
Tagalla mishi harara"wallahi ALLAH yasauwak'e ai kaima ka san ba ma
cikin irin wad'annan kucankan 'yan matan. Adai fad'ama wanda bai sani ba"ai kaima
ka sani kana kuma gani ganin idanunka.Yad'an kalleta"uh ke dai abar tuna ba ya
kawai wai gyartai ya ci sarauta,yajefa mata rafar 'yan naira biyar guda d'aya"ga
shinan gaba d'aya 'yan matan dake zuri'ar Hajiya za ku raba,kowacce ki tabbata kin
ba ta dan ba wacce zan kuma ba sisin kwabo na, yanuna Sudaida sai ki fara da
ita.Tasa kud'in a jaka tabbb... Wannan shine tazo muji ta tawuce ta bayan kunni
wannan nawane ni kad'ai kai dasu wallahi...bai saurare taba yama Hajiya sallama
yatashi yatafi.
Yaya Julaibib tabishi zaure.Yajuyo "na'am.Dan ALLAH rake za ka siyo
min idan za ka dawo anjima.Yakalleta cikin natsuwa"Sudaida a ina zan samu rake yau
sallah fa ai basa fitowa. Tad'an marairaice "ALLAH bayan sallar la'asar za a samu
wanda yafito.Yad'an motsa kafad'a"idan an samu to.Nasmat da Sudaida su suka gyara
naman suka soya ma Hajiya,dan dama sun iya kome an horasu da aiki.
Yadda yake juyi a kan gadon cikin sulusin dare dan ba ya jin
bacci,haka yake juya kalaman Hajiya"to na samo maka matar aure...amma dai aikin
gama ya gama...yagyara rufa yana dad'a d'ora kanshi a saman matashin
"hummm...wacece matar?Wacece ita? Yakad'a kai cikin sauke numfashi"ALLAH yajik'anki
Megado... Wani tunani yad'arsu a zuciyar shi game da Sudaida,sai kuma yagirgiza
kai"abun dakamar wuya...toh yanzu da Hajiya take wannan maganar "idan yarinyar bata
mishi ba fa?Yana jinjina irin zaman da za ayi na har k'arshen numfashi ne fa,
yagyad'a kai"abu mafi sauk'i suyi magana da Hajiya tafad'a mishi ko wacece,idan
bata mishi ba toh a canja mishi da wata tun kafin Iyaye suji maganar.
Daga masallaci sallar asubahi yaje yasa mu Hajiya da maganar amma fau-
fau tak'i yadda suyi ta"wai ai yarinyar da d'an sauran ta,za ta fad'a mishi a
lokacin daya da ce,kuma ba ta dawani makusa dole ma ya so ta tunda itama
macece.Dole ya hak'ura yatattara yakoma inda yafi wayau...Ko hutunan da suka d'auka
dasu Hajiya bai tsaya ya kar6a ba,dan Hajiya tace bata san wani hoto a waya,dole
suka kira Misbahu me hoto ya d'auke su na kati,bai ma yi sallama da yan'uwa kamar
yadda yasa ba ba.
Tana wanke kayan makaranta Asma'u takawo mata waya"ga shi ya damemu
da kira.Waye?Bata yi magana ba ta ajiye wayar a gefen ta,tajuya tayi tafiyarta. Aka
sake kira tad'aga tana d'an turo baki kamar yana ganin ta"ni dai ALLAH na yi
fushi.Shi yasa nake ta kira kika k'i d'agawa?A ah wayar tana d'aki na sa ta a
caji,ni kuma ina tsakar gida ina wanki,ALLAH da gaske Yaya D'ansarai naji haushi
dana je gida neman ka Inna tace wai asubanci kayi.To kiyi hak'uri. Nayi. Yauwa
nagode ALLAH yamiki albarka. Amin. Sudaida...yakira ta. "Na'am.Baki fad'amin
hotunan da mukayi a masallacin Idi sunyi kyau ko basu yi ba?Tayi yar dariya"sunyi
kyau musamman wanda muka yi da Hajiya.To d'an turo min ta whatsapp"tabbb...ai kawai
kayi hak'uri idan kadawo ka gani ganin idanun ka.Yayi murmushi "wato kin rama ko?To
shikenan ki ajiye min,nima a makon nan zan shigo,kin ko ajiye min dambun naman ko
duka kika ba wannan yaron?Ta gane wanda yake nufi amma sai tace"Yaya Julaibib wani
yaro zan ba dambun nama har da na ka? Saurayin ki...yafad'a a dak'ile.Kai dan ALLAH
Sinan d'in ne yaro?To dame kwad'o yafi gaya?Zak'i. Yabata amsa a tak'aice kafin
tace wani abu ya katse wayar.
Julaibib Abdullahi D'ansarai...Yana gama degree d'in shi na farko ya
d'ora degree na biyu(masters) a dai Islamic Studies baya wani samun zama kullum
cikin zirga-zirga tsakanin Zonkwa da Zari'a har ya kammala kome sai karatu da za a
fara ba kama hannun yaro yazo gida yayi mako d'aya sannan ya tattara yakoma dan
cigaba daka inda aka tsaya,shi dai Musaddiq bai cigaba ba sai harkar kasuwancin su
ya keyi,yana kuma yin kome tsakani da ALLAH,kome a rubuce yake sai Julaibib ya zo
ya nuna mishi.
Sudaida tana zaune a tsakar gidan su Swachet wata yar ajin su ce ta je
kar6o takaddun WAEC na shekara uku da suka wuce wanda Yayan ita Swachet d'in ya
rubuta,tana so tad'anyi nazarin su,tana zaune zaman jiran Swachet takwaso matasu a
d'aki.Tayi tsai...na wucewar wasu dak'ik'u da tunanin waye to da wannan aikin?Karo
na uku kenan ana lek'owa ana komawa,to mutanan da suke shiga gida kai tsaye ko
macece ko namijine indai ba mara gaskiya ba wazai yi haka?
Tamik'e cikin sand'a dan san ganin ko waye.Caraf idanun su
yahad'u,tabud'e idanu cikin mad'aukakin mamaki da tsoro, tanuna shi da yatsa"Sinan
kaine kake lek'e?Me kazo yi anan unguwar? Ya sosa kai yana mata d'an murmushi" wai
dama kece?me kika zo yi anan?Tayi jimmm... tana mishi kallan nazari kamar ba shi da
gaskiya sai waige-waige yake yi"kar mu maimaita tambaya ba amsa mana. Yasake sosa
kai yana murmushi "Sudaida sarauniya ta... wallahi na fito shan iskane kawai, sai
kuma naga wata kamar ke shine nake lek'awa,yakalli agogon dake d:aure a hannunshi
"kai jama'a lokaci fa ba wuya,kin san yau akwai wa'azin maza a gidan bak'i, muje
mana,yad'ago yana kallanta har yanzu itama shi take kallo "lafiya kuwa Sudaida?
Tagirgiza kai"ni mamaki kake bani wai duk girman cikin gari karasa inda za kaje
kasha iska har sai ka shigo nan daba bahaushe ko musulmi me sallah ko d'aya? Ni fa
wallahi Sinan ba na ga ne ma wasu al'amuran na kafa gaskiya.Anya Sinan...?Yatare da
sauri cikin dad'in baki da rantsuwar ba abinda yakawo shi,har sukayi sallama yajuya
da sauri yabar unguwar. Takama ha6a "Sinan fa kamar ba shi da gaskiya tajijjiga kai
akwai lauje cikin nad'i.
"Hey Ibrahim...
Swachet ta dafa ta,me kika fito yi a waje? Sudaida tajuyo cikin sauke
numfashi,sannan tasa hannu tazame hannun Swachet daga kafad'arta"na sha fad'a miki
mu addinin mu na musulunci yaba Iyaye girma na alk'adari akan Ya'yan su, mu kome
sunan mahaifin kane ba ka kiran sunan shi kai tsaye ba dan ya haife kaba sai dai
dan yaci darajar sunan mahaifin ka ko mahaifiyar ka,ni sunana Sudaida to banga
dalilin da zai sa ke kuma kidinga kirana da sunan mahaifi na ba,wannan al'adar
turawar ba da Sudaida ba gad'a da fatalwa.
Swachet tawatsa hannaye cikin halin-ko-inkula"ni banga wani abu ba
fa.Takar6i takaddun tana gyad'a kai "tunda baki gane me nace miki ba ko?Tad'an ta6e
baki tana yar dariya"Sudaida kin cika shagwaba tun muna JSS Class idan an miki abu
sometimes sai kin turo d'an k'aramin bakin nan naki kamar gidan tsutsa gashi har
yanzu as a matual baki bari ba haka zaki haifi Ya'ya idan sun baki haushi kidinga
musu? Takai mata duka. Sukayi dariya.Muje in taka miki amma ba da yawa ba, dan
akwai wanda nake jira.Sudaida takalleta da sauri"waye shi?Ko kema kin fara zuwa
kwanan gidan ne.Tayi d'as da yan yatsunta"God forbid bad things ni da zan zama
sister,ni bani da saurayi ma, sak'o kawai zai kawo min in kaima budurwar ta shi.
Tibishi yatare shi"wai har ka dawo sai kace akan k'aya kake?Yafad'a
kujera tare da lumshe idanun shi na wucewar wasu yan dak'ik'u sannan ya bud'e su"ai
ban ma k'arasaba na had'u da Sudaida.Yacire kofin bommi(ruwan kwakwa) dayake shirin
kaiwa bakin shi,yana mishi kallan uku ahu"to me kake nufi?Ya ajiye kofin a saman
tebur yahad'a hannayan shi waje d'aya yad'ora ha6arshi akai"wai tsoron yarinyar nan
kakeji?Har yanzu baice kome ba,ya daiyi tagumi yana zancen zuci"zan bar abinda
nafara kawai tun kafin wankin hula yakaini ga dare,kwata-kwata bani da kwanciyar
hankali.Tibishi yaja dogon tsaki sannnan yamik'e yabar d'akin yana zagin Sudaida,
Sinan,hausawa dama duk wani wanda yake sallah harda Katafawa yan'uwanshi a jinsi da
d'aukacin masu sallah na doron duniya gaba d'aya.
Yatsaya a k'ofar D'akin-girkin yana kallanta tana kwasan tuwon dare,tayi
kyau cikin riga da zani da d'ankwali na atamfa ruwan hoda da ratsin k'ananan
filawoyi ruwan makuba,d'an k'aramin bakinta yanata kyalkyallin man le6e ruwan
hoda"miyar me kikayi?Ta yamutsa fuska tana turo baki"labarin zuciya a tambayi fuska
"miyar shuwaka.Yayi yar dariya"da kan ki? To Yaya Julaibib ya zanyi?Sarkin yawa ai
ya fi sarkin k'arfi shi sukace suna so,na ce bazan yiba,Umma ta ce wai dole shi
zanyi duk da itama fa ba wani so take yiba,ai wallahi gidan Hajiya zani bazan rasa
abin sawa abakin salati ba.To yi sauri ki gama sai mutafi tare nima can zani
barinje mu gaisa dasu Mama.
A gidan Hajiya tana cin sinasir da miyar taushe,Julaibib da Hajiya
suna hirar data shafe su,saiga Sinan yashigo da sallama.Hajiya ta amsa sallamar"wa
alaikumussalam lale maraba da Sinan,bismillah.Yashiga yazauna cikin girmama yana
gaisheta.D'ansarai yad'aure fuska ko kallan shi bai yiba yacigaba da duba wayar
shi.Sinan yakalli sarauniyar ta shi kamar itama batayi maraba da zuwan shiba,yad'an
sosa k'eya bayan ya ajiye ma Hajiya ledar d'aya shigo da ita,Maltina da madara ta
ruwane a ciki "Hajiya ba yawa ni zan wuce."Hajiya tamishi godiya da sa albarka.Har
yasa takalman shi Sudaida ba ta da niyyar ta shi.Hajiya takama ha6a tana kallanta
ta"Oh ni 'yasu, Sudaida kar6i nan tamata dak'uwa.Tamik'e tana k'unk'uni.
Shima Julaibib yamik'e"Hajiya magriba ta gabato.Tabishi da kallo "gaskiya
ne gwamma ai harama dan a samu jam'i.Yazo yawuce su a k'ofar gidan kamar bai
gansuba.Sinan yasauke numfashi "D'ansarai ALLAH yayi miskili,magana ta fatar baki
bayan sallama rabon da muyi ta har na manta shekarar.Tad'an harareshi"ai dai ba ga
ba yake yi dakai ba tunda zai maka sallama, rashin maganar ma ai kamawa takeyi a
d'aure me d'aurewa.Yayi murmushi kawai"ba ta so ayi maganar Julaibib yanzu sai taji
haushi,kad'an sukayi hira sukayi sallama dan anfara kiraye-kirayen sallah daga
mabambantan masallatai.
Tibishi yatari numfashin ta ta hanyar kyalkyalewa da dariya"mahak'urci
mawadaci ne Zigwai, yabud'e hannunshi na dama, ya fa riga ya shigo tsakiyar tafin
hannunki kin riga kin mishi kattt...kisan mummuk'e, bashi da wani kata6us sai yadda
mukaja da akalar shi musamma ma ke; yad'auki kofi yazuba mata bommi"sha kijik'a
mak'oshinki "tanasha suna dad'a tattauna yadda za su 6ulloma al'amarin,yanzu abinda
za ayi ki kirashi a waya yazo yad'auke ki,idan kuma bazai samu zuwa ba to da yamma
yazo Fajumali-Hotel.
Tagalla mishi harara"kaima fa wasu lokutan shawarar ka ba ta d'auka
bace.Kamar yaya ba ta d'auka bace?Tamik'e tana sa6a jakarta a kafad'a"to tayaya zan
kama d'aki a Hotel d'in dake cikin gari tsakiyar hausawa?Sannan shi kuma kana ganin
zai yadda ko hanyar yabiyo bare har aganmu tare?Yabata hannu suka tafa "shegiya yan
mata wannan k'wak'walwar ta ki ba laifi tana ja,amma kafin ki wuce ya kamata kid'an
bani na kashewa.Ta6alle jaka tawatsa mishi dubu biyu"kai kudin ka ba sa k'arewa a
kome sai a burkutu(giyar k'ok'o) yanzu na san D'One zaka tafi.Suka fito yakulle
d'akin yana bata amsa"kamar kin sani dan Alhamdu ma yana bina bashi.
Cikin fushi yashiga d'akin tana zaune a kujera tana chatting,sai ta
ajiye wayar tana mishi wani murmushi tare da gewaye hannayen ta ajikin shi tana
mishi wani irin salon jan hankali"hey dude just chill up" abinda take mishi ya ka
sa daurewa,dan haka yabiye ma yarima aka sha kid'a,wucewar wasu dak'ik'u sai ga shi
yana kwasar dariya,yad'an shafa cikin shi"wallahi yunwa nake ji rabo na da abinci
tun na safe.Tajawo abincin gaban shi "kaci ka k'oshi dakai na nadafa maka,dan ka
fara zama na musamman a cikin zuciya ta,tasake kashe murya da wani irin salon na
yan duniya"Sinan ALLAH ban had'a soyayyarka dana kowani namiji ba,saboda samun irin
ka a cikin maza sai anyi da gaske,ina sanka Sinan.Yayi murmushin jin dad'i "ALLAH
dagaske Zigwai?
A yangance ta amsa"ga kai ga k'afa ai ba tambayar me aka yanka. Yakai
loma bakin shi yana gyad'a kai"gaskiya na gani ganin idanu na, yagama cin abincin
yamatsar da sauran gefe, wayar shi da aka kira ta katse musu hanzari, yad'aga cikin
ladabi"a ah bana kusa amma dai yanzu zan zo,yakatse wayar yana kallanta "Babana ne
yake son gani na yanzu.Tamotsa kafad'a"ba matsala,amma ai za ka dawo ko?
Yamik'e"wannan dole ne bani mukulli idan nadawo ba sai nazo inata k'wank'wasawa ba
koda kinyi bacci.tad'an taka mishi zuwa bakin k'ofa"kasiyo min balangu. Yagyad'a
"kin samu balangu kin gama.
Tibishi yak'araso yana dariya"akwai ranar kin dillanci...a ranar za ka
gane da gero ake koko.Zigwai ta 6ata fuska"gaskiya ka daina zagin saurayi
na.Yashige d'akin yana zagin ta"kaji yar duniya,saurayin ki ko dadironki? Tawatsa
hannaye "what ever,idan ba haka ba zan fad'a mishi.Yaja tsaki"idan kin fad'a mishi
sai me?A saran wa? Kafin me riga yarufa,me bargo yayi gumi. Yak'arasa cinye abincin
da Sinan yarage,yana ta janta da hira tace"a ah zo kawai kayi tafiyar ka dan yace
zai dawo.Yamik'e"to sai da safe,yakamota yana k'ok'arin ba ta sumba,ta ture
shi"katafi mana indai ba kwa6armuce kake so tayi ruwa ba.
Yak'ara matsawa kusa da ita"haba 'yan mata,dan dai d'an alakoran daza
ki bani ai bazai sa ba bazai rage ba,tamu dake ba ta 6aci, yazuba mata idanu"anya
banyi ihu da kirari na da6ama kaina wuk'a ba? Tagirgiza kai"bakayi haka ba
Tibishi"marakiyi ai ba abokin tafiya bane" tamishi rad'a a kunni,ya bud'e idanu
yana kallanta "ta jijjiga kai"na rantse da ALLAH da gaske nake yi,suka kyalkyale da
dariya suka tafa"shegiyar duniya to mukwana lafiya,amma kirage min kayan dad'in
daya kawo miki, tagalla mishi harara"ba zan ajiye ba d'an rainin hankali,kura da
shan duka gardi da k'wace kud'i?
Tibishi yana hango Zigwai ta sauka a kan mashin yatareta"me za kiyi
a cikin gari?Tamishi wani kallo"ji wata banziyar tambaya kai me kazo yi?Ni cikin
gari wajan zuwana ne.To nima haka zani wajan Sinan ne kwanaki hud'u kenan baya amsa
wayata na tura mishi sak'onni sun fi guda goma nan ma ba amsa dan haka zani ingani
ganin idanu na ko lafiya?Yad'aure fuska"ke Zigwai ina fata kina sane ke ba wata
tsiya bace a wajan Sinan? Tayi shiru, yakalleta"to rashin jinshi a waya kuma ya
samo asaline da irin zirga-zirgan bikin shi daya gaba to,kin san suna gama WAEC za
ayi auran to saura kwanaki sugama zana jarabawar. Dammm...zuciyarcta buga.
"Sinan zai auri Sudaida???!!!
Tayi d'as da yan yatsun ta"incredible! Haka mukayi da kai Tibishi?To ko
ba haka mukayi ba to ke kina ganin kai tsaye za kice Sinan yabar auran tane bai
d'auki ke wacce taci kai ba? (hauka)Tarik'e k'ugu tana kallanta d'ai-d'ai kun
mutanan da suke kai-kawo a cikin hantsin saboda sanyin da akeyi, suna tsaye sai ga
su Sudaida sun zo sun wuce a mota,tabi motar da kallo har ta harba saman
kwalta.Sudaida ma tagansu"wai a wannan mugun sanyin amma tayi irin wannan shigar me
kama da tsirara,takada kai"ALLAH yasauwake.Tibishi yasauke numfashi"muzauna musan
na kwatanci fa,kar k'aramar magana tazama babba, tagirgiza kai"ni fa yau sai na ga
Sinan.Yad'aga murya dan tafara bashi haushi"wai ba na ce miki Sinan ba ya gari ba?
To indai haka ne gwamma in koma gida dan ba saboda kai nafito a wannan sanyin
Jauran ba.Yad'aga mata hannu "sauka lafiya.
Sudaida tabishi da kallan tuhuma saboda karo na bakwai kenan ana kiran
shi a waya yak'i yad'auko ta daga aljihu ma,bare yaga me kiran.Yad'an motsa kafad'a
"share kawai.A share kamar yaya?Bai yi magana ba yaciro wayar a aljihu yana nu na
mata kingani sunan Zigwai yafito 6aro-6aro a fuskar wayar sai yamayar aljihu yana
mata bayani"wajan aikin mu d'aya dashi,to wasu takaddu yabani in cike,na kuma san
tambaya ta zaiyi idan na cike su in kai office,ni kuma gaskiyar magana zuwa wajan
ki yafi kai takaddun mahimmanci...ba zato sai ga Tibishi "jaba Sinan irin wannan
abun da kakeyi ba kyau,ya kama ta aba duk me hakki hakkin shi.
Cikin fushi Sinan yatare shi da hayagaga har abun yaba Sudaida tsoro
da mamaki saboda irin zagin daya mishi"dan abu kazan uban ubanka baza a bayar ba
ayi wacce za ayi dan dan iska kawai...idanun Sinan sun kad'a jawur saboda 6acin rai
yanuna Tibishi da yatsa "ka6ace min da gani kafin in 6alle ka.Au haka kace?
Yajijjiga kai"eh haka nace dan abu kazan ubunka.Yajuya yana kwafa"na rantse da
ALLAH Sinan za ka gane da gero ake koko,za ayi walkiya kuma kowa zai gani ganin
idanun shi;kura ce lullu6e da fatar akuya.Sudaida takalleshi"me kalaman Tibishi
suke nufi ne?Yawatsa hannaye "Oho mishi ba mamaki yaje ya shata ne bata fad'a mishi
gaskiya ba,zanbi shawararki kawai gwamma muyi hannu riga dan nagaji da rashin
mutuncin shi.Tayi tsai tana kallanshi "rashin mutunci,to me yahad'aku da yake maka
rashin mutunci?Bai bata amsa ba yasauke numfashi, yabata tsaraban Kaduna sukayi
sallama.
Tunda yakwanta yakasa bacci sai juyi yakeyi,zuwa can yamik'e yad'auki
mukullin mashin yafita, gidan au Zigwai yatafi,tana tsaka da bacci yata sheta,
tamik'e zaune akan gadan tana mitstsike idanu kamar gaske"na gaji da jiranka,tafara
mishi abinda tasa ba, yarik'o hannayen ta,yakalle ta cikin natsuwa"Zigwai kiyi
hak'uri da duk al'amuran da suka faru a tsakanin mu,kin sani aure zanyi,dan haka ba
zan dinga barin matata ina zuwa wajan kiba,yaciro rafar d'ari biyar guda d'aya
yad'ora mata a cinya "ga shinan ba yawa,amma a hakan idan kikayi maleji zai isheki
kija jari, basai kin cigaba da sai da mutuncin ki a wajan sauran maza ba.Tafizge
hannayen ta"me make nufi? Kana nufin mun rabu kenan? Incredible!rabuwa da kai ba
abu me sauk'i bane,sai ta fashe da kuka,kuka me ta6a zuciyar duk wanda yaji bare
kuma shi da ake kukan saboda ana son shi,ba a son rabuwa dashi.Idan yacigaba da
zama za tasamu lagonshi dan haka yamik'e,dasauri tasha gaban shi"idan kamin haka
kaci amanar kauna,wai duk irin sadaukarwar dana ba ka a soyayya?Yakalleta cikin
tausayi da tafasar zuciya"ya bud'e baki zaiyi magana sai kuma yayi shiru,tagyad'a
kai cikin hawaye"fad'i duk abinda za ka fad'a dan wanka da gari ba maganin yunwa
yake yi ba"to kiyi hak'uri kawai ai ni da ke ba alk'awarin zama na har bada mukayi
ba, bare kice na ci amana.Yajuya zai tafi.
Tafara mishi wani salo daya sa shi tsayawa"Sinan na yadda za mu rabu
amma ina fata baza ka sani a kwandon sharaba,idan mun had'u zamu dinga
gaisawa.Yagyad'a kai"dan wannan karki damu.Takashe shi da murmushi "saura abu d'aya
tsakani na da kai,kuma alk'awari kayi ranar birthday d'ina za kazo"you're the
special quest of honour" idan ka halacci wajan to ka gama biya ta,kuma ka fita ko
ba sabulu.Karki damu. Tasake shi yatafi.
Tabishi yafito daga bayan labulen daya zagaye d'akin,nan yashige
lokacin dayaji tsayuwar mashin yalek'a ta taga yaga Sinan ne, sukayi dariya suka
tafa,yakai hannu zai d'auki kud'in a saman tebur tariga shi.Yakalleta "banga ne
ba.Tagyad'a kai"ai nima zan fiso kaita zama cikin rashin ganewan,wallahi idan na ba
ka dayawa dubu biyar.Yakarkace kai yana kallanta da mamaki"dubu biyar zan samu?
Tazuba mishi idanu"to ina laifi dubu biyar a wannan marran,karanka ne yakama?
Yakad'a kai"lallai kin cika yar duniya hayak'in taba.Takwanta tana dad'a jan
bargo"maraina kad'an dai 6arawone,malam idan za ka kwanta kazo ka kwanta,idan ba ka
jin bacci to ta shi kasan nakwatanci karka hanani bacci gobe sammako zan buga zuwa
Zuturung. Yagalla mata harara"zuwa wajan wani dadiron na ki?Takyalkyale da
dariya"ina da wani dadiro ne daya wuce kai?Hummm...bari dai mugama da wancan shegen
bahaushen sai muzo mufara shirin aure.
Suna cin dafaffiyar masara tashigo da sallama tazauna tana gaishe da
Hajiya tare da fad'in "Hajiya gani ance kina kirana"Hajiya tabita da kallanta
nazari, tarame tayi wata iri ba ta cikin wal-wala gidan na tama yau kwanki biyar
kenan bata zo ba,shine ta aika akira ta"kwana biyu ban gan kiba ko lafiya?Lafiya
lau"ta amsa a tak'aice.Hajiya ta gyad'a kai"to d'auki masaran kici mana,ni fa
gaskiyar magana yarinyar nan ba ta da lafiya,Julaibibi wai ko kuna ganin yadda take
k'arewa kamar kud'in guzuri? Dammm...zuciyar shi tabuga daya d'ago Yakalle ta,
yacigaba da kallan ta ba tare daya ce kome ba.Hajiya tagyad'a kai"ah to kaima ka
gani ko?
To tunanin auran ne yamaida ke haka kome? Shima Sinan d'in kwana biyu
shiru ko dai kunyi fad'a ne? Zuciyar ta tayi rauni,ba abinda take son yi sai
kuka,bata 6ata lokaci ba tafara sharar kwallah a hankali sautin kukan kefitowa
hawaye sharrr...sharrr...masu d'umi suka fara sintiri a fuskarta,tacigaba da kukan
ta har da sheshshek'a;ba wanda yahana ta sai da taci tak'oshi sannan dan kanta tayi
shiru,tahaye gadon Hajiya ta kwanta.Julaibib yayi shiru ran shi ba dad'i"mecece
matsalar Sudaida ne?Kira yashigo wayar ta tad'aga da dishashshiyar murya"ina gidan
Hajiya ne,tad'anyi sauraro...kayi hak'uri Sinan bana jin dad'i ne kabari sai gobe
ko kuma kaba Yaya Khausar za ta ajiyemin...Cikin shashshek'ar kuka tace"to Sinan
nagode...
Hajiya tata fa hannaye cikin sallallami "Oh ni jikar mutum hud'u,amma
wannan yarinya ALLAH yashirye ki,ba yanzu nagama tambayar ki ko ba ki da lafiya ne
kikace ke kalan ki ba?To ai shi kenan kowa rai yama dad'i barin me shine. Tamik'e
tana sa hijab.Sai ina? Julaibib ya tambayeta.Tad'auki mukulli tana kallanta Sudaida
"idan kin gama kwanciyar jin dad'in za ki tafi gida ban dawo ba to dama karki
kuskura kibar min k'ofa a bud'e,tamaida kallanta ga Julaibib"gidan Sahura za
ni.Hajiyarmu adawo lafiya,nima dana gama cin masarar hannuna zan tafi.
D'akin yayi shiru wucewar wasu dak'ik'u har yagama cin masarar ya
ajiye totuwar yamik'e yana kallanta"tabbasss duk wanda yayi ihu to taimako yake
nema"Sudaida ALLAH yadafa miki akan damuwar ki.A raunane ta amsa"amin Yaya Julaibib
nagode.Yaja numfashi yafitar da iskar tabaki ta hanci"ni gobe zan koma makaranta,
inaga sai ranar d'aurin aure Insha-ALLAH da sassafe zan taso,na san zan samu d'aura
aure,su Nasmat duk sun fad'amin abinda suke so in sai musu,ke ma me kike so in sai
miki?Tamik'e zauna da sauri cikin rawar muryar data rasa dalili"sai ranar d'aurin
aure?Kana nufin bazan sake ganin kaba sai ranar da ALLAH yayi?Kwallah yacika idanun
ta.Cikin rashin fahimta yakalleta"kamar yaya sai ranar da ALLAH yayi? Yaya Julaibib
ranar d'aura aure to a ina zan ganka? Kuma ranar za a kaimu gidan aure,washe gari
za ka koma makaranta to yaushe zan ganka? Kana nufin sai ranar danazo gida idan
kana gari sai mu had'u?Ko zaka dinga zuwa gida na?Yagirgiza kai"me kike so Sudaida?
Yayi tambayar da wata irin murya data sa Sudaida d'ago kai da sauri tana kallan shi
cikin dukan zuciya.
Yadafa k'irjinshi dai-dai saitin da zuciya take"zuciyata ayan kwanakin
nan tana min wata irin bugawa da ban san abinda zan kwatanta miki ba Sudaida, na
kuma rasa gane dalilin haka,ni fa tun bayan rasuwar marigayiya(Bilkisu)har yanzu
ban samu kwanciyar hankali ba,bana yin ishashshen baccin da masana a harkar
binciken lafiyar d'an Adam suke bada shawarar a kalla duk dare kayi baccin a wanni
takwas.
Yasake kallan ta cikin natsuwa "Sudaida kome da kika ga ina yi dauriya
ce kawai; amma ciwon yana nan a zuciya ta kamar yan awannin da suka shud'ene,yad'an
yi yake"koda yake baza ki fahimci radad'in rabuwa da masoyi ba!!!toh ina miki fatan
alheri a gidan auran ki dafatan zama na har abada,mutu ka raba takalmin kaza,ina
miki fatan samun babban rabo a alk'iyama Darul-karamah dake da zuri'arki...Yaya
D'ansarai...yakauda da kai,yakuma riga ta magana"tunda baki fad'i abinda kike so
ba,toh zan ba Asma'u gudummawa ta, zata kawo miki har gida.Bai jira amsawar taba
yajuya da sauri yatafi.Tabi bayan shi da kallo dan ya mata susa a inda yake mata
k'aik'ayi.
"Rad'ad'in rabuwa da masoyi!...
Tafad'a tasake maimaitawa,rad'ad'in rabuwa da masoyi!!! Sai tasa kuka wasu zafafan
hawaye suka zubo mata sharrr...sharrr...wallahi Yaya D'ansarai nima ina jin
rad'ad'in... wai...! wayyoh...! ALLAH na!!!!
Nasmat data shigo tayi tsai...tana kallan ta cikin nazari,tarik'e
ha6a"ikon ALLAH nazaune ya fad'i,a zaure sukayi kaci6is da Julaibib yana cikin
damuwa tana mishi godiyar gudummawar daya ba yar a ba ta,sai yamata wannan
rikitaccen kallan na shi yayi kamar baiji abinda take fad'a ba yayi tafiyar
shi,tana tunanin me yasa meshi tashigo, toh ga Sudaida itama a wani irin yanayi.
Tazauna a gefen gadon sannan tadafa kafad'ar ta"jimamin rabuwa da Yaya D'ansarai ne
yasa kike wannan kukan ko me? Tarungumo ta"ni fa na shiga rud'ani, Nasmat ban san
abinda yake damun zuciyata ba wallahi,amma ko a yanayin bugawarta ta canja,tsoro
nake ji... tasaki Nasmat tana tsaida kukan"Nasmat bana san auran nan...Dama kawai a
kyale ni.
Takad'a kai"lallai ma Sudaida na ki wasa ne;kema kin san baza ta
sa6uba... Idanun ta suka cika da kwallah"to ni wai ya zanyi ne? Ya za kiyi dame?
Har ta bud'e baki za tayi magana sai kuma tayi shiru.Nasmat tayi yar dariya"Sudaida
sarauniyar Sinan,kin san me? Kuka bai ta6a zama mafita a cikin matsala ba"ALLAH
mahaliccin me kowa da kome za ki kaima kukan ki,zai taimake ki ta inda ba kya
zato,nima na yadda ciki ba dan aci tuwo kawai akayi shiba,tabbasss a kwai abubuwan
daya kamata yazama sirrin kane,sirri ne kawai tsakanin ka da zuciya.Tamik'e tana
rik'o hannayan Sudaida"kin san a kwai makarantar Islamiyya lokaci kuma ya
kusa,gwamma muje mu shirya dan ina tsoron ALLAH ina kuma tsoron dukan makaran Malam
Jama'are da wannan shar6e6iyar dorinar,tamik'e suka kulle ma Hajiya k'ofa...
Ana dara ga dare ya yi...
Da sauran kuka anci gumba an hana maye.
2 Jumaada Thani 1441
27 January 2020
We Ibrahim's Daughters 👇
Asdilat KD...2geda with Ra'ibs.
DANGIN NONO WRITERS ASSOCIATION
{Da Inganci Mukayi Fintinkau}
Bismillahi wabihi nasta'in
...GWAJIN DAFI💔
Almost true story
Daga alk'alamin🖊
Ya'yan Ibrahim
Saudat A.Baba (Asdilat KD)
Da
Bara'atu Ibrahim (Ra'ibs)
Shafi nagoma sha takwas.
Julaibib yana gidan Yaya Karima yana mata sallama Baban Abdul
yashigo,yamik'a mishi hannu sukayi musafaha"Malam D'ansarai ya karatu? Yayar ka ta
fad'amin wai gobe za ka koma nace haba-haba dai ba shekaran jiya kazo garin ba?
Yad'an sosa k'asumbar shi"ai yanayin karatun ne sai a hankali.Baban Abdul yagyad'a
kai "maganar iyali kuma shiru mak'atau bulaguro a k'iyama tun bayan rasuwar
marigayiya,ga shinan kana kallo k'annin ka mata shida za a aurar.Yayi
murmushi"ALLAH yaba su zaman lafiya,amma gaskiya ni yanzu ba aure agaba na.Baban
Abdul yanu na shi da yatsa"kai Malam D'an Sarai kar kayi butulci fa...yatare shi da
sauri"ba haka bane Baban Abdul,shi aure d'an lokaci ne idan lokaci yayi mutum ko
bai shirya ba dole sai yayi.Haka ne kuma"To Ubangiji yaba ka macen albarka,amma
idan a kasa himma abun zaifi tafiya yadda yakama ta,a kawo k'arshen zaman tuzuran
cin nan.Yayi yar dariya kawai sukayi sallama.
Ango ka sha k'amshi.Yayi murmushi. To ya shirye-shirye ance aski idan
yazo gaban goshi ya fi zafi ko?...Tacika shi da surutu yatare ta"Zigwai nagode da
gaisuwa yakatse wayar. Tasake kira yad'aga,cikin dariya tace"haba na Sudaida ba da
kan ka asare idan kaje gida kace ya fad'i,ai ban gama ba.Baki gama me ba?Kamar
Yaya,me ye tsakani na dake? Babu,sai dai abu d'aya yarage a tsakanin mu,idan kuma
kacika alk'awari to ba kare bin damo maganar birthday party na.Na sani ban kuma
manta ba,zan cika miki wannan alk'awarin.Yauwa very good.Ita tariga shi katse
kiran.
Umma tashiga d'akin tasame ta a kwance"ke Sudaida me yasa kin cika
kafiya ne kamar mutanan farko?A raunane takalle ta"Umma kaina ciwo yake yi
matsananci kamar zai rabe gida biyu.Umma tad'aga murya"ki shirya kutafi makaranta
kin nok'e ba kya jin dad'i, kici abinci kin kafe ba kya jin yunwa,kisha magani kin
bud'e taga kin watsasu waje,to me kike so a miki?Tayi shiru idanun ta sun ciko da
kwalla.To ki tashi maza-maza kifita yana jiran ki a waje.Tamarairaice Umma...Umma
ta tari numfashin ta,tanu na ta dayatsa"ke kul...tashi nace.Jiki a sanyaye tamik'e
tana goge hawayen da suka zubo mata da gefen farin hijab d'inta.
Ba kowa a k'ofar gidan,sai kawai tayi zaman ta a d'an k'aramin
dakalin dake tsakanin filawoyin wajen"Sinan gajiya yayi kenan yatafi?A hankali
tsigar jikin ta yafara ta shi,sanyin yana ratsa ta, a takure tahad'a kai da
gwiwa,tafara karkarwa hak'oranta suna dukan juna,tamik'e dak'yar zata koma
gida.Yana tsaye ya nad'e hannayen shi a k'irji,yabi ta da kallo tana sanye da
doguwar riga na atamfa me duhu da farin silifas, d'azu a gidan Hajiya riga da zani
da dankwali na shadda ruwan toka ne a jikin ta,fuskar ta tayi fayau babu
kwalliya,idanun ta sun kod'e dagani ba tambaya taci kuka ne fiye dana d'azu ta gode
ALLAH.
Luuu tatafi kamar za ta fad'i saboda jirin daya fara d'iban ta,a
hankali takoma ta zauna,tasa duka tafukan hannayenta tarufe fuskarta tana k'ank'ame
jiki dan bata daina jin sanyin ba."Sannu Sudaida jiri ko? Tagyad'a kai. Sudaida
yakira ta.Tacire tafukan hannayenta a fuska sannan takalle shi,yamik'a mata Farm-
pride yoghort d'in hannun shi"ki daure kisha.Tawani marairaice"Yaya Julaibib bazan
iya sha ba,amai zanyi.Yazauna a gefen ta sannan yayi k'asa da murya cikin
rarrashi"haba Sudaida kiyi hak'uri kisha zai miki magani,rashin cin abincin ki ya
dame ni,Sagir ya fad'amin kinfi mako d'aya a haka,kullum sai Umma ta tasa ki a gaba
kike cin d'an kad'an,yabud'e mata "d'an daure kisha kinji ko?
Yaya Julaibib amai zanyi zuciyata tana ta tashi fa.Yagirgiza kai"uh uh
kar6i kisha baza kiyi amai ba rashin cin abincin ne yasa miki ta shin zuciyar.Tasa
hannu biyu takar6a,kad'an ta kur6a tamik'a mishi, yagirgiza kai"d'an kara...da haka
har sai da tasha rabi,yakar6a yarufe yamik'a mata anjima kidaure kishanye zai miki
amfani,kinga yadda kika zama kuwa Sudaida?Takaryar da kai gefen dama"kai baza ka
shaba? Uh kisha kawai. Tamik'a mishi hannu"d'an ban dabino... baya rasa dabino a
aljihu yasa hannu ya d'ibosu"guda uku suka rage.Tasa hannu biyu takar6a tana ci.
A mashayar"Beer Parlour"suka had'u da Zigwai.Yaja kujera ya zauna yana
kallan ta tana shafama faratanta jan farce ja,tad'ago takalle shi"daga ina kake tun
d'azu ka shanya ni?Daga cikin gari mana,na je samo kud'in kashewa ne tunda ke
muguwa ce fiance d'inki ba shi da kud'i amma baza ki iya taimaka mishi ba.Tagalla
mishi harara"in taimaka maka fa kace?Kai bakaji kunya ba kura da shan duka gardi da
kar6e kud'i? Yamotsa kafad'a"a very stingy woman,ba wata kunya dana ji,kin san da
ina dashi bazan tambaye kiba,tare ma zamu kashe su.
Tagama shafe faratan ta sannan tasa nailpolish d'in a jaka,tabi wajan da
kallo ya cika dank'am da mutane maza da mata ga hasken disco light kore,ruwan bula
da ja,wasu na shaye-shaye,wasu suna bin wakar da aka kunna a k'atuwar
rediyon,tamaida kallan ta ga Tibishi "birthday party na bazai yiwu a ranar lahadi
ba,na maida shi ranar juma'a.To saboda me?Tad'ora duka hannayen ta a saman tebur
d'in"dole ranar juma'a zan yi shi saboda ranar juma'ace d'aurin auran Sinan ka gane
manufa ta?Yajijjiga kai"na ga ne,kinyi tunani me kyau,amma fa a tsorace nake kar
kwa6armu tayi ruwa.Yaba ta k'warin gwiwa "hey just chill up"kwa6armu baza tayi ruwa
ba,duk abinda zai faru indai munci gari ba damuwa,ai ranar biyan buk'ata rai ba a
bakin kome yake ba inji k'uda.
Da yammacin ranar laraba,rana tayi sanyi Hajiya takira layin Julaibib
yad'aga da sallama yana yar dariya"Oh Hajiyar mu na yi kewar kifa"taja tsaki"kai
tafi can kaba ni waje,ka yi kewa ta amma tunda kasa k'afa kabar garin nan kaka sa
kirana?Ayya Hajiya ta ke kad'ai,kin san d'an makaranta yana fama da geron
Sunday(garin kwaki\rogo)ba ta siyan katin waya nake yi ba.Yadda yayi maganar cikin
jimami da tausayin kai yasa Hajiya tayi dariya"Julaibibi kana dani amma katsaya
fatarar katin waya?To bari yanzu za kaji alert..Yauwa Hajiya ta nagode miki ba
kad'an ba Ubangiji yak'ara girma.Amin Julaibibi. Hajiya ina cikin damuwa,na ka sa
samun natsuwa.Ashsha me yake damun ka Julaibibi?Tun ranar dakika fad'amin kin samo
min matar aure,Dan ALLAH Hajiya ba wai butulci zan yi da za6in ki ba,dan na san
baza kimin za6en tumun dare ba,to amma alfarma d'aya nake nema kifad'amin wacece
ita?Taja tsaki"na d'auka wata lalura ce ke damun ka?To yar gidan Kawun kace.Wane
Kawun nawa?A ah to kuma nan d'aya ni dai nafad'a maka sai ta k'ara girma,yo data
isa aure tare za a had'a dana su Sudaida ta k'arasa karatun a gidan ka.Yar karama
ce kenan,ajin ta nawa?A ji d'aya take a ka'aramar Secondary idan kuma kana so ayi
bikin ta girma a d'akinta to,kayi rainon ta yadda kake so.Yayi shiru kamar baiji
abinda tafad'a.Hajiya tayi dariya"Julaibibi na to sai anjima ta katse wayar.Yahura
iskar bakin shi bayan ya maida wayar shi aljihu,yayi tsai...cikin tunani Kawun nan
na shi ai suna da yawa,kuma kowanne yana da tarin ya'ya mata,yayi iya tunanin shi
amma bai canko ko wacece ba, yarik'e kugu yana bin d'akin na shi da kallo...
Sinan yana tsaye da mahaifin shi yana ba shi sak'on wasu kayayyaki da
zai siyo mishi a Kaduna,Zigwai tak'araso wajan,tana sanye da matsatstsun riga da
buje na material ruwan d'orawa an mishi d'inkin rashin mutunci da rashin sanin
kimar kai,tantirancinta ya bayyana, tana rataye da bakar jaka,takalmanta masu rufi
da tsinin diddige bak'ak'e"Sannu Alhaji tad'an rusuna tana gaishe da mahaifin
shi,wani abu yadaki zuciyar Sinan, yad'auke kai daga kallan k'urullan da take
mishi.Alhaji yakalle shi sai ya sunkwui da kai.Zigwai tayi wata yar dariya irin ta
yan duniya"Malam Sinan angon Sudaida.Yad'ago yana murmushin yak'e,sai ta mik'a
mishi envelop "sak'o nakawo maka.Yak'ar6a yana mata kallan tuhuma.
Tajuya tayi tafiyarta tana murmushi"za ka gane da gero ake koko, Sinan ai
sai dai muyi biyu babu. Suka kalli juna shi da mahaifinshi "yadafa
kafad'arshi,Sinan ba girma a ganka kana mu'amala da irin wad'annan k'adangarun
barikin, ka san shaid'an baya raina k'ofa.Yagyad'a kai "Baba baka yadda dani bane?
Sinan ba rashin yadda ce tasa na fad'a maka haka ba,illah gyara kayan ka...ai kai
ba k'aramin yaro bane,sai dai tunatarwa tana amfanar da mumini,ai mun ba ka
tarbiyya gwargwadon iyawarmu,idan kaje kayi wani abu sa6anin wanda muka d'oraka a
kai,to ai ALLAH yana ji yana kuma gani wannan tsakanin ka dashi ne,bazai kama mu da
sakaci ba,ni dai idan za kayi sara to kadinga duba bakin gatarin ka, kasan da irin
mutanan da za ka dinga mu'amala, ina jiye maka kaidin irin wad'annan da suke ji
kamar su juwo mutum ta k'arfin tsiya ya dilmiya. Jikin shi yayi sanyi,yayi nadamar
abinda yafara "nagode Baba.Alhaji Kamal yashige motar shi yatafi. Yazauna a wajan
cikin damuwa"to wai ma me yakai shi k'ulla mu'amala da Zigwai?
Sun gama jarabawa anyi speech and prize giving day anyi angama
lafiya,kowa ya koma gida zaman jiran sakamakon girbe abinda aka shuka.Maganar biki
ya dad'a kankama anata shirye-shirye,amare ana shan gyara Umma ce a wannan harkar
dan kunsan ita bata d'aukar raini kona sisin kwabo ko ba dan ALLAH ba kowa sai ya
bi.
Jajibarin auren su Sinan kai ya d'auki zafi baya samun zama,yana sa
takalmi Tibishi yashigo yana kallan shi"maganar birthday party na Zigwai zan tuna
maka fa.Yakalle shi rai a 6ace"Tibishi karabu dani,dan ba wannan ne a gabana
ba.Yajijjiga kai"nima na sani to amma karka manta alk'awari kad'auka.Yagama sa
takalmi yamik'e "Tibishi ta shi katafi akwai inda za ni,suka fito Sinan yakulle
d'aki kowa yayi hanyar shi.
Bai dawo ba sai kwanciyar bacci a na ta dad'a gyara gidan amarya,sai
da ya tabbatar kome ya kammala sannan hankalin shi ya kwanta, sai lokacin yasamu
damar kiran Sudaida.Tana ganin kiran shi tad'an harari wayar tana k'unk'uni, sai da
yakira sau uku sannan tad'aga"Sudaida sarauniyata...tatari numfashin shi"ni ba wata
sarauniyar ka tunda tun safe baka nemi ni ba,na kira ka na jita a kashe,ni fa kana
6ata min rai. Wayyo ni Sinan to kiyi hak'uri ina can ina hidimta ma muhalllin
kine,amma ko ina naje to tabbaci hak'ik'a kina cikin zuciya ta, ina son ki
Sudaida... Tace hum...yacigaba'irin soyayyar da baza ta fad'uba,yayi yar dariya
ALLAH dai yakai damo ga harawa ko baici ba yayi burgima,gobe war haka kin zama
sarauniyar Sinan ta hak'ik'a,farin cikina zai fara daga gobe ne...yayita maganganun
shi batace kome,basu wani dad'e yamata sallama dan zai kwanta ya gaji lik'is.
Farar rana me kyakkyawar suna, wato juma'a.Yan'uwa da abokan arziki
cike da gidajan biki an karkasa ayyukan shi yasa nan da nan akayi aka gama.K'arfe
sha biyu da rabi Julaibib yasamu isowa garin.Yashiga D'akin-shak'atawar Inna ana
gaisawa.Yaya Karima takalle shi"ai na d'auka baza kazo ba.Yad'an shafa kwantaccen
bak'in gashin kanshi"Yaya Karima yanayin karatun ne sai a hankali.
To ALLAH yataimaka.Amin.Yawuce d'akin shi dan shirin masallaci.Yana sanye
da babbar riga,'yar ciki da wando na farar shadda getzner,hular shi k'ube da aikin
babbar rigar shi ruwan toka da ratsin fari da bak'i, takalmishi sau ciki fari,agogo
da zoben shi na farin azurfa sai d'aukar idanu sukeyi saboda hasken su, k'amshin
arabian perfume d'inshi me dad'in shaka,ya cika wajan.Duk suka bishi da kallo.Yaya
Karima tace "gaskiya autan Inna kayi sharrr...dakai kamar wani ango,Yayi murmushi
kawai"kice ma Inna na tafi masallaci.
Yau gaba d'aya hud'ubar akan aure da ma'aurata akayi,bayan an idar da
sallah anyi addu'o'i an shafa,auran Hashim da Aisha aka fara daurawa,sai Muhammad
da Zainab,Abdullahi da Maryam,Abdulkarim da Nasmat,Huzaifa da Khausar...sai na
Sinan da Sudaida da ake shirin d'aurawa,to amma wani wawan burki da aka taka sai da
yatshi hankali jama'a,wasu suka fito daga masallacin dan ganin abinda yake faruwa.
Sinan ne yafito daga cikin motar yana sambatu da tam6elen
mashayar...Su...Sud... Sudai...damata...ta..taceba...wanda...zai...raba ni da
ita... alk'...wari...ba karyawa mutu ka raba takal...min kaza. Ciki da wajan
masallaci kowa yayi d'ifff...ya cika da mad'aukakin mamaki na ganin Sinan a wannan
yanayin, a hankali k'ananan surutai yafara ta shi.
Alhaji Kamal sai da numfashin shi yad'auke na wucin gadi yayi mutuwar
zaune,dan abun ya kad'a shi"Innalillahi Wa'inna Ilaihi raji'un yake maimaitawa,
Liman yakalle shi"dama ka san d'an ka yana shan giya? Yakad'a kai cikin damuwa
"Liman bazan maka k'arya ba wallahil-azim ban sani ba,ban san kome game da Sinan ba
sai halaye masu kyau.
Sinan d'in aka fitar daga masallacin dan yafara kakarin amai.Liman
yakalli mahaifin Sudaida meye abin yi? Kafin yayi magana Alhaji Kamal ya amsa"ba za
a d'aura ma Sudaida d'an giya ba,irin wannnan hukuncin zan zartar ko 'ya tace
wallahi,dan haka ina rok'on alfarma a d'aura auran nan da k'anin Sinan,yanuna
Hamidan dake zaune a gefen shi cikin 6acin ran abinda Sinan yayi.Liman yabi sauran
jama'ar da kallo,yasauke numfashi"k'warai zan so haka,to amma wani hanzari ba gudu
ba idan aka had'asu aure Sinan bazai barsu suyi zaman lafiya ba, zumuncin dake
tsakanin su na shak'ik'an juna zai samu tasgaro, indai ba tsananin sa a a kaci
Sinan d'in me hange nesa da maida al'amura ga ALLAH bane.Alhaji Kamalu kayi
hak'uri,ni na san da wanda zan had'a auran nan yanzu da izinin ALLAH gida bai
k'oshi ba ai baza a ba dawaba. Yaciro dubu ashirin d'in da kaba bashi zakkarsu
dazai taho masallaci "yanzun nan zan d'aura auran Julaibib da Sudaida akan sadaki
naira dubu ashirin lak'anan(lakadan) Masallaci yad'auki kabbara.
Alhaji Kamalu mutumin kirki me karamci shi yakar6ama Julaibib auran
Sudaida, dubban nin jama'a sun shaida wannan aure. Hamidan yasauke numfashi,sai
yanzu yashak'i iskar yanci dayaji ba dashi aka d'aura ba, yama Julaibib da Sudaida
fatan alheri da sauran angwaye da amaren,yamik'e yayi tafiyar shi yana rok'ama
Sinan shiriya...ALLAH kenan buwayi gagara misali,namiji baya auran macen da ba ta
shiba,hakama mace bata auran mijin da bana ta ba...al'amarin aure,al'amarine daga
Indallahi,shi yake had'awa sai dai wani yazama silar faruwar shi.
Baban Abdul dake gefen shi yayi murmushi"ango ka sha k'amshi,aure
d'an lokaci ne,idan lokaci yayi ko ba a shirya ba haka dole za ayi...ka tuno hirar
mu ta kwanaki?Wannan gaskiya ne shirye-shiryen a yi daga baya,yamik'a mishi hannu
sukayi musafaha suna murmushi, wallahi shima haka yake ganin abun kamar almara,har
suka fito yan'uwa da abokan arziki sun baibaye shi suna taya shi murna da fatan
alheri"Dare ga mai rabo...hantsi.Sunan wani littafi na gwanarmu (Halima Abdullahi
Amma)Ubangiji ya kyautata makwanci👏
D'ansarai...yaji an kira shi.Yad'ago kai bakin shi d'auke da
addu'ar"Alhamdulillahil-lazi bi ni'ima tihi ta tummussalihat"jin an daki
kafad'arshi.Aminu ne yazare mishi idanu"toh daga yau sai yau na zama surukin ka,dan
haka ba sauran raini,idan ba haka ba in k'wace k'anwata ka gane ko?Kome girma-girma
kamar tusar jaki. Julaibib yamishi wani kallo "ai aikin gama ya gama,wuk'a da nama
yanzu a hannu na suke da dai kafin a d'aura ne to danaji kurarin ka,nagaba yayi
gaba Alhaji...Su Musaddiq suka yi dariya.
Yara kowa yafara noman kare(gudu) dan yaje kai rahoto kuma kowa so
yakeyi ace shine na farko, tun daga zaure Abdul yake k'walama Inna kira iya k'arfin
shi har yashiga tsakar gidan,duk suna tsaye cirko-cirko cikin tararrabin abinda
Abdul din zai shigo dashi na tashin hankali"lafiya kuwa Abdul?Sai numfarfashin
gudun dayasha yake yi,yana haki da dariya yace"Inna Kawu D'ansarai aka d'aura ma
aure. Asma'u dake tsaye kusa dashi batayi k'asa a gwuiwaba ta d'auke shi da wani
bahagon mari,ji da ganin shi sai da ya d'auke na wucin gadi"wato wasan da takeyi da
kai har yakai haka? Ka dinga mata kiran yan farauta tun daga waje duk ka tashi
hankalin mu sannan kashigo mana da maganar banza"wa D'ansarai ya aura?K'anwar
ubanka? Yadafe wajen dan ya maru idanun shi suka kawo ruwa,ya kasa magana sai kawai
yajuya zai fita. Inna tarik'o rigar shi "Zo mana Abdul d'ina mai gida ran gida,me
gida takobi...tayi furucin da sigar rarrashi,tasa hannu tashare mishi hawayen da
suke zubo sharrr..."fad'amin gaskiya Abdul,me yafaru a masallaci... bata gama rufe
baki ba sai ga Adnan yashigo da sallama,suka bishi da kallo, yaja kujera
yazauna.Cikin jimami yafad'a musu kome. Masu murna na yi masu komawa gefe suna
k'unk'uni na yi.Asma'u tajuya zata ba Abdul hak'uri taga ya fita.
Asma'u tana jin abinda Sagir ya gama fad'a takai goshinta k'asa cikin
sujudush-shukuri "yanzu ne za suyi rawar gaban hantsi ita da Alk'asim,tad'auki
jakar da Sudaida tace tashiga d'akin Yaya Aminu tad'auko takai mata gidan
Hajiya.Tana dire jakar a k'asa tayi tsalle cikin ihun murna ta rungume
Sudaida"albishirinku?Duk amaren da suka sha wanka da kwalliya suka bita da kallo.Ta
lumshe idanun ta cikin jan numfashi "wai me yafi dad'ine an tambayi na d'aure?
Saki...tayi lallausan murmushi sannan tabud'e idanun ta"toh an d'aure lafiya an
kuma gama lafiya, sai dai an samu akasi Yaya Sudaida dai da autan Inna aka
d'aura...
"Da Julaibib???
Suka had'a baki wajan tambayar ta cikin mad'aukakin mamaki.Nasmat ta san halin
Asma'u ba mamaki tace da wasa take yi.A'isha ta d'aure fuska"ke Asma'u wacece sa ar
wasanki a cikin mu?Tafara rantse-rantse gaskiya take fad'a...Daga tsakar gida suka
fara jiyo tafa hannaye cikin sallallami.Nasmat talek'a Yaya Aminu ta hango suna
masu Hajiya bayanin abinda yafara, a hankali tasaki labulan tana jijjiga kai"ga kai
ga kafa ai ba tambayar me aka yanka.Maryam takada kai cikin damuwa "amma dai Sinan
bai kyauta ba,ya 6ata rawar shi da tsalle.Zainab ta ta6e baki"wannan kuma ai can
gasu gada kura ta ji kid'an farauta... kowacce ta tofa albarkacin bakinta.
Sheshshekan kukan Sudaida sukaji, gaba d'aya suka juya suna
kallanta.Aisha tace kiyi hak'uri Sudaida ALLAH yaso ki da rahama yato na asirin
shi,da an d'aura auran ne bayan kin zama matar shi fa? Ai ko za a raba auren ku a
yadda yake son ki ai ba k'aramar tata6urza za ayi ba.
Takalli A'usha"wai da D'ansarai fa wannan me miskilancin tsiyan?
Khausar tagalla mata harara sannan taja dogon tsaki"rainin hankalin ki yana da yawa
wallahi.Su Aisha suka kyalkyale da dariya"duk miskilancin shi ai taku dashi ta zo
d'aya,har hira fa kunayi.Takoma ta kwanta a ranta tana mita"maganar da sai ya ga
dama yake yi.Aisha tasake kallanta"a shekarun baya dana fara k'orafi a kan halin
shi kece fa me k'alubalantar kalamaina,bayani sosai kike min har nima daga baya
nagane,tadafa kafad'arta haba ta D'ansarai ki daina asarar hawayen ki dan Julaibib
mijin nuna ma sa a ne wallahi...tayi shiru kamar bataji me suke ta fad'a
ba...tacigaba da zancen zuci"tabbass tana son Yaya Julaibib,to amma yanzu da
fad'uwar tazo dai-dai da zama, kayan suka tsinke a gaban kaba sai ranta bai so ba.
Tarintse idanu hawayen suka sake zubowa a kyakkyawar fuskar ta me d'auke da hasken
amarci.Sinan baka kyauta ba, ka ci amanar k'auna, wato ranar da aka kira wayar shi
a bai-bai yarufe ta,saboda sunan Zigwai suna sa ma maza suna sa ma mata,ashe
kalaman Tibishi duk gugar zana ne,tadafe kanta daya fara barazanar ciwo,ai ko ba ta
san Sinan to dad'ewar su tasa sun yi sabo na ban mamaki.
Biki sai yadad'a komawa gidan Inn,bayan sallar Isha'i kowace amarya
aka sadata da d'akin miji gidan aure, aure yak'in mata inji hausawa...Su angwayan
da tawagar abokan su,su suka yanke shawarar a fara raka Julaibib gidan shi.Aminu
dake cikin tawagar abokai yarik'o hannun shi"dare fa na dad'a yi zo muje kama
Innarmu sai da safe,dan ka san bazan lamunta kadinga share waje kana barin k'anwata
a gida ba,yanuna shi da yatsa"sai fa ka kula da kyau idan ba haka ba har gidan zani
in tasa k'eyarta zuwa gida.Julaibib yakai mishi naushi a kafad'a amma bai same
shiba dan ya goce da sauri"kar ka 6alla min kafad'a kasa gobe in shiga uku,aikin
billboards ne dani guda wajan takwas.To ni ai bata shafeni ba.Yagyad'a kai"gaskiya
ne ba ka da asara ko na miyan bacci.
Inna tayi murmushin jin dad'i yau ALLAH ya nuna mata auran autan
ta.Ta musu nasiha gaba d'ayan su sosai akan su zauna lafiya da matayan su.Alhaji
Abdullahi shima ya d'ora"Ku kyautata musu Manzon ALLAH yace mafifici a cikin
ku,mafifici a kyautatama Iyalin shi,ni na fiku kyautatama Iyalina,kuji tausayin
su,kuyi hak'uri da dabi'unsu dan da k'ashin hak'ark'arin hagu aka halicce
su.Yakalli Julaibib"Malam D'ansarai ai ka san ina yawan fad'a maka shi zaman aure
gaba d'ayan shi hak'uri ne ko? Toh yau ka shiga daga ciki,yanzu za ka fara aiwatar
da wannan nasihar a aikace,aure hak'uri ne,d'awainiyace me tarin yawa, shi yasa ake
buk'atar juriya da jajircewa. Yarufe nasihar ta shi da wannan addu'ar ga wanda yayi
sabon aure...
"Barakallahu lakum,wabaraka alaikum, wajama'a bayyana kuma fi khair.
Duk suka had'a baki wajan amsawa da amin,amin,amin.
Inna da Baba suka bisu da kallo bayan sunma juna sai da safe suna
fita d'aya bayan d'aya daga D'akin shak'atawar,kowanne yayi sharrr... dashi cikin
farar shadda.
Garin yayi tarwai da hasken farin wata, sassayar iska tana kad'awa a cikin
daren,ga k'amshin furen filawar sarauniyar dare(Queen of the night) d'in k'ofar
gidan yamamaye ilahirin ciki da wajen gidan. D'akin- shak'atawar a gyare yake, sai
dai yau gyaran na musamman ne,k'amshin amarci ya cika ko ina.Suka zazzauna,aka d'an
ta6a hira kamar yadda akan yi idan an rako ango sannan suka mik'e.Aminu yad'an daga
murya "toh amarya mukwana lafiya, mun sai bakin ki akan kud'i masu tarin yawa,mun
kuma damk'asu a hannun angon ki, dan haka yana shigowa mik'a hannu yaba ki yan
kud'ad'enki,idan kuma kinci girma kin bar mishi to kinyi mafi kyawun karamci, duk
ke d'in ce dai za ki amfana...Huzaifa yature shi"saboda ALLAH meye haka?Yad'aga
mishi hannu"muje na ka gidan kaji abinda zan fad'a ma ta ka amaryar, suka fita suna
mishi mita.
Julaibib yarakasu k'ofar gida yadawo bayan ya kulle ko ina.Yarike k'ugu a
tsakiyar D'akin shak'atawar cikin karatun wasikar jaki na wucewar wasu
dak'ik'u,yasauke numfashi sannan yasa hannu yad'auki ledar da Musaddiq yaba shi
yanufi d'akin da sallama.Yashak'i wani k'amshin turarenta dana turaren
d'akin,k'amshin ne me sanyin dad'i,ya lumshe idanu yana dad'a shak'ar k'amshin
cikin jan numfashi...
Oh Ya Salam...dausayin ni'imahhh...
A hankali yabud'e idanun shi yana bin d'akin da kallo,kome an tsara
shi,ya zauna a muhallin shi,abun ya burge,ya k'ayatar duk da anyi shi a k'urarren
lokaci,yau d"in nan fa.
Shauk'in k'aunar daya mamaye ilahirin gangar jiki da sararin zuciyar
shi tun bayan d'aurin auren sai yadad'a ninkuwa sau shurin masak'i,yaja stool
yazauna yana k'are mata kallo tun daga k'afafunta da suka sha jan lalle da yarfin
baki,har zuwa polish lace d'in data sa,zani da riga ruwan k'waiduwar kwai(beig)da
mayafi ruwan kwai me shara-shara,k'ananan sabon kitson ta yar-yar-yar yadad'a fito
da kyan fuskar ta,hannayen ta suma sunsha jan lalle da yarfin baki,d'an kunne,
sark'a,zobe da siraran warawaranta na zinare sai d'aukar idanu sukeyi,ga kuma
hasken amarci, yana kallan fuskar ta kome ya tarwatse mishi,murna ta koma
ciki,saboda damuwa da tashin hankali dasu ke tattare da ita ruwan hawaye ne suka ta
sinsitiri a kyakkyawar fuskar me d'auke da hasken amarci, yahad'e hannayen shi
yad'ora ha6arshi akai"kar dai tsugune bata k'are ba...an sai da kare an sai biri?
ALLAH dai yasa ba shi kad'ai yake kid'a da rawar shi ba!
'Sudaida..Yakira sunan ta cikin natsuwa.
Tayi shiru...sai yayi k'asa da murya "Sudaida ban san damuwar kiba,amma
ina so ki sani daga yau,yanzu d'innan duk wata damuwa dakike ji da ita,to nima
zanji kwatan-kwacinta,kiyi hak'uri ki bani goyon baya dan in samu k'warin gwuiwar
faran ta miki,akowani irin hali da yanayi.Toh me zata cene?Wallahi wani iri take
ganin shi, kamar wani bak'o,nauyin shi take ji,ga kuma kewa da rabuwa da gida dasu
Nasmat da akayi shekara da shekaru ana gwagwarmayar rayuwa da makaranta, musamman
Khausar da kullum suke kwana daki d'aya, gadon bacci ne kowacce da na ta,amma har
wardrobe d'in su d'aya,suyi fad'a su shirya,toh wai yau kowa a wani muhalli na
daban zai kwana,ga Aisha da ta musu nisa tana Kafanchan idan suna san ganin juna
fuska da fuska to sai sunyi tafiyayyiya a mota, kewan kowa da kome yalull6eta sai
kawai tasa kuka(Hummm Sudaida aure yak'in mata inji hausawa...toh yanzu kin shigo
filin shukuwa... Sai ki had'iyi k'wayar hak'uri ki kora da ruwan jarumtaka da
jajircewa dan aikin aikine wallahi"an ba kuturu tallan jakai)
Tun shigowar shi d'akin sai yanzu tacire tagumin datayi tad'an saci
kallan shi,Bai cire kome nadaga shigar shi ba sai takalmi,k'afafun shi cikin safa.
Sudaida...
Yasake kiran ta"tashi muyi sallah...Tasunkwui da kai tafara shashshekan kuka.
Tagirgiza kai"uh uh Sudaida yau fa ba ranar kuka bace,rana ce da za ki k'ara godema
Ubangiji dan kin shigo gidan aure, auran nan kuma hanyace da zata sadaki da Darul-
karamah..
Yad'auko Kofi yazuba madara yamik'a mata"kar6i kisha.Itafa ya dame
ta,kad'aici take buk'ata wallahi,dan haka tace bata sha. Sudaida..Ta tari numfashin
shi"Yaya Julaibib nifa gaskiya bazan iya zaman auren nan ba...tacigaba da kuka.
Yayi tsaiii...na wucewar wasu dak'ik'u yana kallanta"idan rai ya 6aci
toh hankali yanemo shi,abinda yatuna kenan yamata uzuri dan shima yaji rad'ad'in
rabuwa da Bilkisu fuj'atan. Yagyad'a kai"To naji, amma d'an daure muyi salla ko?
Dak'yar tamik'e ita fa wani irin hali da yanayi ta tsinci kanta a ciki kamar
almara. Bayan sun idar da sallar yayi wannan addu'ar ga wanda yayi sabon aure..
"Allahumma inni as'aluka khairaha wakhaira ma jabaltaha alaihi,wa'a'uzu
bika min sharriha wa sharri ma jabaltaha alaihi"
Duk sukayi shiru na wucewar wasu dak'ik'u, a hankali yad'ago yana
kallanta,sai yaciro wayar shi yasaita ta yana d'aukarta hotuna,tana d'ago kai caraf
idanun shi yahad'u,tasunkwui da kai da sauri tana dad'a rufe fuskar ta da mayafin,
bazato taji ya cire mayafin yarik'o ta yana d'aukarsu tare"Yaya D'an... sauran
kalaman suka mak'ale saboda wannan rikitaccen kallannan na shi daya mata,ta turo
baki gaba idanun ta sun cika da kwallah. Sai da yagaji dan kanshi yabari.
Hucin numfashin shi taji a gefen damanta,yayi k'asa da murya"ALLAH
yabaki hak'urin zama dani...Yagewaye hannayen shi a jikinta"Kin gaji da yawa ya
kamata kiyi wanka da ruwa me d'umi sai ki kwanta kiyi ishashshen bacci ko?Dak'yar
tayi furucin"ni ba sai nayi wanka ba. Yagirgiza kai"uh uh sai kinyi wanka za ki
kwanta... yasake ta"kije kiyi wanka,yajuya yafita.
Har tayi wanka takwanta sannan ya shigo tana kwance irin kwanciyar
mage.Har kin kwanta"uhhh tace.Yaja stool yazauna yana kallanta"gobe fa sammako
zanyi in koma makaranta kilama baki tashi daga bacci ba.Sai taji ranta ba
dad'i.Tayi shiru kawai...ko za ki bini mutafi tare?Tad'an dago suka kalli
juna"yad'age gira yana mata wani kallo"in shirya miki kayanki yanzu?Tawani
marairaice tana zancen zuci"sai kawai aji tabi shi makaranta?Yayi yar dariya yana
mik'ewa"kiyi baccin ki kinji,ni akwai nazarin da zanyi"Lailatun sa'ida...fi amanil-
lah.Ya tafi D'akin- shak'atawa yana had'a wasu littafai da zai tafi dasu.
Sinan bai farka daga nannauyan baccin daya d'auke shi bayan ya gama
aman giyar daya shaba sai cikin sulusin dare.Yafarka da wasu miyagun mafarkai daba
su da tushe bare makama, yabi d'akin da kallo zuwa kayan jikinshi,yashiga rarraba
idanu"me yakawo shi d'akin Hamidan kuma?K'wak'walwar shi tafara aika sak'onni zuwa
bangaren tunanin shi"me yafaru dashi? Yaufa ranar d'aurin auren shine,rana ce ta
musamman a gare su shi da sarauniyar ta shi,a kuma daren su nafarko cikin angwanci,
yakad'a kai ai sam-sam baza ta sa6uba bindiga cikin ruwa, ruwa baya tsami
banza,tar-tar yafara tuno abinda yafaru kafin gushewar hankalin shi.Dammm...Yaji
rikitowar wani abu a k'ahon zuciyar shi,kafin kiftawar idanu yajik'e sharkaf da
zufa kamar wanda yayi wanka da kayan jikin shi, da sauri ya sakko a gadon kamar zai
hantsila yawuce D'akin-shak'atawa anan yaga Hamidan yana bacci a doguwar
kujera,kuma d'akin wayammm ba kowa,ba kamar jiya da yan'uwa da abokan arziki suka
cika ko ina ba.A rikice ya sunkuya dai-dai fuskar Hamidan yana kiran sunan shi,yasa
hannu ya yarfe zufan dayake ta tsatstsafo mishi a goshi a karo na barkatai,yahadiye
wani abu mezafi.
Hamidan yayi juyi sannan yabud'e idanu, dan a sama yaji kiran"tashi
Hamidan ka zauna.Hamida yatashi yazauna yana kallan shi cikin 6acin rai,wallahi da
shine babba sai ya zabga mishi barin makauniya dama da hagu,yakad'a kai"labarin
zuciya a tambayi fuska sai kawai yajuya mishi keya.Cikin tashin hankali Sinan
yace"dan ALLAH an d'aura aure na da Sudaida?
Yajuyo yamishi wani kallo"tabbasss an d'aura auren Sudaida amma da
dan'uwanta D'ansarai dan Baba ma bai goyi bayan a d'aura mata aure da d'an giya
ba,yanzu haka tana d'akin mijin ta...yatare shi cikin k'araji da tafasar zuciya"ya
ishe ka! Yafad'a kujera yana Istirja'i k'urunk'usss...ta faru ta k'are an yima me
dami d'aya sata. Idanun shi sun kad'a jawur Tibishi da Zigwai sun kai shi sun baro.
Yau bak'ar rana ce a gare shi me bak'in muni...yafara tuno abinda
yafaru wayewar garin juma'a, a sanda hantsi yadubi ludayi yadawo daga ciro kud'i a
ATM dazaiyi hidimar abun sha na walimar dare da za ayi bayan an kai amarya,yasa
mukulli zai bud'e d'akin shi kenan sai ganin Zigwai yayi ta shigo gidan na su
tak'aramar k'ofa, me gadi yana d'akin shi yana sallar walha,lallai idan ya barta
Baba zai iya fitowa kowani lokaci,ga kuma bak'in yan biki,da sauri yazare mukullin
daga jikin kofar yamayar aljihu,yaja hannunta da sauri suka bar gidan,suna fita
yasaki hannun ta ya wanka mata mari san ya angijeta tayi baya tafad'i,yafara yarfa
mata ruwan bala'i"dan abu kazan uban ki meye darin gamata da ke dahar za ki biyo ni
gida? Ba mun gama ba,ba kare bin damo?Tawani marairaice"dan ALLAH angon Sudaida
kayi hak'uri,ban san ranka zai 6aci irin haka ba, amma nima ai daga yau ba k'ari
wankan wuta,na kira lambar ka sau shurin masak'i kaj'i d'agawa, kaga ai dole tasa,
dan wajen Party yayi cikar farin d'ango amma ba special quest of honour,tacigaba da
marairaita har tasamu fushin daya taso mishi yafara lafawa"dan ALLAH kazo muje ana
gama yanka cake sai kadawo. Yagalla mata harara"baza niba ko dole ne?
Dasauri takai gwuiwoyinta k'asa tana mishi wani irin murmushi na yan
duniya da jan hankali" haba Sinan dan darajar k'auna da soyayyar daka kema
sarauniyar ta ka,yau d'aya dai karka watsa min k'asa a cikin idanu bayan na gama
sakankan cewa,ai ka gani ko a jikin katin gayyata an buga kaine bak'o na musamman
me girma.kuma na fad'a maka tuntuni ka kuma amince da haka,haba Sinan ai alkawari
bai ce haka ba,da tun farko ka fad'amin baza kaje ba ai da na canja ka da
wani,tamik'e cikin hawaye tana kallan shi"shine nan nagode...nagode tajuya tayi
tafiyarta.
Yabita da kallo,sai yaji ran shi ba dad'i yasake kallan agogon dake
d'aure a hannun shi,har yanzu k'arfe goman safiya bata k'arasa ba, bari kawai yaje
tunda alk'awari yamata,zuwa goma da rabi sai yamata sallama yazo yak'arasa abinda
zai yi kafin lokacin masallaci yayi. Da wannan tunanin yabita,yasha gabanta da mota
yabud'e mota gidan gaba tashigo ta zauna"kiyi hakuri Zigwai.Tagirgiza kai"na hakura
angon Sudaida,ALLAH zan so ganin ka anjima dan na aan wankan da za kayi zai
bambanta da duk wani wanka da kata6a yi,yayi murmushi kawai.
Wajan party ya had'u da had'ad'd'un yan duniya hayak'in taba,dashi aka
yanka cake,sai dai agurguje yake yin kome yana kuma yawan duba agogon dake d'aure a
hannun shi dan kar lokaci ya shammace shi. Tabishi da kallo"wai wannan duba agogon
na meye?Duba agogon me kuma?Sai ta share zancen"me zan kawo maka ne kad'an jik'a
mak'oshi?Yaharareta.Tayi yar dariya "ka d'auka ba abinda zaka iya shane?Dan dai
kak'i yadda ne amma bommi ba giya bane, ko a zuba maka d'an kad'an?Yagirgiza kai"a
ah kusha abun ku,ni dai na san giya ne bommi,tunda idan mutum yasha yana gusar
mishi da hankali.Tata6e baki "idan kai baka sha ba ai hausawa dayawa yan uwanka sun
sha.Toh Ubangiji ya shirye su.
Taje tad'auko katan d'in lemun bakwai a raye(seven alive)ta6arke ledan
a gaban shi tazaro d'aya, tabud'e murfin sannan ta d'auko kofi ta tsiyaya kusan
rabin kofin sannan takalle shi"ko a cika maka kofin? Yamik'a hannu yakar6a "wannan
d'in ma ya isa nagode, yana kai kofin tsakanin la66an shi tayi murmushin mugunta,ta
dunk'ule hannu ta naushi iska"k'aramin arne ka had'u da gawurtacciyar arniya.Sinan
sai dai muyi biyu babu,baza ka auri Sudaida ba nima ban aure kaba kowa yaji idan da
dad'i.Tayi wata irin dariya irin ta yan duniya ganin ya shanye lemun duka "ALLAH
yakai damo ga harawa...
Wucewar wasu yan dak'ik'u sai yafara gani garara-garara yanayin shi
yana canjawa,d'aukacin jama'ar wajan yafara ganin su suna kasuwa kashi-kashi yana
ganin Zigwai da Tibishi suna magana a gaban shi cikin dariya da tafa hannu amma
bazaice ga abinda suke fad'a daga haka bai san abinda yakuma faruwa ba.Ashe maganin
bacci da gusar da tunani,kuma wanda yawuce ka'ida(over dose) suka zuba acikin
wannan lemun guda d'aya,sun kuma yi ma kwalin alamar dasu kad'ai za su gane.
A gida kuma Alhaji Kamal da Hamidan sun tun sha biyun rana suke neman
Sinan amma ko sama ko k'asa basu ganshiba, hakama lambar wayar shi sun kira sau
shurin masak'i na'ura me k'wak'kwalwa tana fad'a musu a kashe take,haka suka gaji
sukayi shirin masallaci suka tafi.
Sinan sai da yayi bacin awanni biyu sannan suka tasheshi,har lokacin
bai gama dawowa dai-dai ba,sai suka dura mishi giya nan fa yadad'a rikicewa.Wani
abokin Tibishi yakalli Sinan"wannan ba yau za a d'aura mishi aure ba amma yazo nan
yashare waje ko auran dole za a mishi? Dammm...zuciyar shi tabuga duk da yana cikin
maye.Yata shi yana tangad'i da tam6ele yashiga mota.Yana tafe jama'a na kaucewa da
ababan hawansu, yana kuma shan zagi da tsinuwa daga bakin wasu,saboda k'iris yarage
yahad'a hatsari mummuna,a haka har ya isa masallacin juma'a wajan d'aurin
auren...wasu zafafan hawaye suka zubo mishi"Zigwai tasa ya zubar da mutuncin shi
dana gidan su abainan-nasi, kalaman Sudaida suka dawo mishi duk da k'anka'ntar
shekarun ta amma tayi hagen nesan da san zuciya yahana shi hangowa...
Zama da madaukin kanwa...wai kai ba ka da wajan zamane sai acikin yan
maro(wiwi)?...yatuno da maganar mahaifin shi na wancan makon"Sinan ba girma aganka
kana mu'amala da wad'annan k'adangarun barikin... mun baka tarbiya gwargwadon
iyawarmu... tunatarwa ce kawai...Yamik'e cikin tafasar zuciya "lallai yau za ayi ta
tak'are me raba shi da Tibishi da Zigwai sai ALLAH Hamidan yakalle shi ganin yana
bud'e kofa"Ina za ka a wannan daren Yaya? Ko kallan shi baiyiba yasa kai yafita.
Tana kwance hankali kwance iskar fanka tana kad'ata.Yadamk'o gashin
dokin daya cika kanta tozon rak'umi guda.Zafi yaratsa ta tabud'e idanu cikin
gigita,suka kalli juna,sai ta dad'a rikicewa.Yanemi abun duka bai samu ba dan haka
yad'auki belt d'in daya gani a gefen gadon, yafara dukan ta ba ji ba gani sai da
belt d'in yatsitstsinke amma duk da haka bai hak'ura ba,yafara tattaka sai da yaga
ta daina motsi sannan yatsallaketa cikin jini yafita, amma har lokacin bai huce
abinda suka mishi ba,wasu jijiyoyi sun fito a gefen kanshi kamar shatin bulala,ran
maza ya 6aci iya 6aci.
Adaren yakoma neman Tibishi sai dai duk inda yasan zai ganshi yaje
amma cikin rashin sa a bai ganshiba...tabbasss da aun had'u sai wani ya rasa ranshi
ko kuma suyi mutuwar kasko.Yakama hanyar gida zuciyar shi a cunkushe, kaci6is
sukayi da mahaifin shi da Hamidan za su tafi masallaci sallar asubahi. Sinan
yasunkwui da kai ya ga 6acin ran da bai ta6a gani a fuskar mahaifin na suba"yanzu
duk abin kunyar dakayi jiya hakan baisa ka kwana a gidaba? Yanuna shi dayatsa" anya
Sinan,anya rayuwar gaba za tayi kyauvda albarka idan ba a tsaya an inganta rayuwar
da ake ciki a yanzu ba? Anya Sinan kana tuna tsohon banza daga yaron banza yafara?
Sinan yayi shiru a ranshi yana nadamar sanin Tibishi da Zigwai a rayuwarshi..Alhaji
Kamal yakad'a kai"shikenan sai kaje ka shirya kafito masallaci, yakalleshi "kama
rama sallolin jiya daka kwanta wannan baccin asaran?Tsoro yakama shi" shi Sinan
yashiga ukun shi wallahi sai yanzu yatuna.Asanyaye yagirgiza kai"yanzu zan rama.
Yakalli Hamidan"kaji,Ubangiji yashirye shi. Hamidan ya amsa da sauri amin Baba.
Suka tafi masallaci kowanne ranshi ba dad'i.
Yana durk'ushe agaban mahaifiyar shi yana bata hak'urin abinda yafaru
amma fau-fau tak'i sauraran shi, tanuna mishi k'ofa"ta shi kabani waje ganin ka
yana k'ona min rai,Sinan ka bani kunya...tirrr da wannan halin na ka, albasa batayi
halin ruwa ba wallahi. Yayi k'asa da murya "Mama bana shan giya,makirci kawai a ka
kulla min...ta tare shi a zafafe" kai karka maidani sakarya,wa zai kulla maka
makirci?Makirci da munafurci har yawuce wanda kadad'e kana aikatawa,ko kawai dan
dubunka ta cika? Alhaji Kamal yashigo"haba Mamansu idan rai ya 6aci to bai kamata
hankali yagusheba,d'an yau ne ka haifeshi baka haifi halin shiba.Takalleshi a
rikice "yanzu kana goyon bayan shine,har kana ba shi lasisi?Tad'ora hannayenta
aka"oh ni yar mutum biyu" na rantse da ALLAH Alhaji idan yaron nan bai tashi
yafitaba to zan d'aga mishi nono...Tabud'e baki da niyar sake magana sai kalaman
suka mak'ale saboda 6acin rai.Tasa hannu tashare hawayen daya zubo mata.
Sinan yasake shiga wani tashin hankalin gobarar gemu fiye dana
d'azu"lallai ka shiga uku, rayuwarka tana cikin garari tunda har za kasa mahaifiyar
ka zubar hawaye saboda mummunan laifin ka. Yanzu wa zai yadda dashi akan baya shan
giya? Abu d'aya yasan yana sha a 6oye shine taba sigari,itama ba koda yaushe
ba,wazai yadda dashi?Yadafa goshi"ko Alqur'ani d'ungurungum zai had'iye bashi da
mafita. Nadama,haushi da bak'in ciki suka baibayeshi, kome yaji yafice mishi a rai.
Alhaji Kamal yadafa shi"tashi katafi d'akin ka.Gwiwa a sage
yamik'e.Alhaji Kamal yakalli matar shi "abinda Sinan yayi tabbasss bai kyauta
ba,kuma bana goyon bayan shi,to amma wani hanzari ba gudu ba, idan fa yatuba bai
kuma aikata hakan ba har abadan duniya,to ALLAH me gafara ne,zai kar6i tuban shi ya
yafe mishi tunda bamu yama laifi ba face mahaliccinmu gaba d'aya, dan haka karki
tsananta,ke uwa ce addu'arki har kullum ita ake buk'ata, kullum addu'armu da
fatanmu ace Ya'yanmu sunyi zarra fiye da duk wasu Ya'ya wajan natsuwa,sanin ya
kamata, mutunci da tsantseni,to inga yanzu kin mishi baki? Bazai amfani kan
shiba,bazai amfane muba,bazai amfanar da sauran al'umar manzon ALLAH ba,kin 6ata
goma biyar bata samuba,baya ba zani kenan...
Yana rik'e da marik'in k'ofar d'akin shi kafin yamurd'a tabud'e jiri yayi
awon gaba gaba dashi yifff...yasha k'asa.K:arar fad'uwar tashi megadi yaji.Yayi
cikin gidan da sauri yana kiran Alhaji da Hamidan,sun yayyafa mishi ruwa amma shiru
kamar an shuka dusa,dan haka suka wuce dashi asibiti.
Tsakanin d'a da uwa sai ALLAH, hankalin mahaifiyar tashi a tashe,takira
Hamidan tana tambaya"ya jikin na shi?Yakalli roban k'arin ruwan da aka sa mishi a
hankali yake d'iga a cikin siririyar robar yana shiga jijiyarshi zuwa cikin
jikinshi"Mama ya samu bacci saboda allurar baccin da aka mishi,likita yace jininshi
yayi mugun hawa.To Alhaji fa?Tasake tambayar shi cikin damuwa. Sun fita shi da
likita.To Ubangiji yasa kaffarace nima anjima zan shigo. Yagyad'a kai"To Mama sai
kin shigo a iso lafiya.Yauwa Hamidan ALLAH yamaka albarka.Amin Mama.
Tibishi yad'ora hannayen shi aka yana zare idanu"Holy ghost
fire!...Inzayadami?(Me yafaru)Tafashe da kuka tana kad'a kai"ina katafi kabarni
acikin wannan mawuyacin halin? Na neme ka a waya banji kaba.Yakoma yazauna"sha
kuruminki Zigwai wayata nasiyar nayi kud'in mota zuwa Kafanchan kasuwar aladu, na
kuma je da k'afar dama and'aukeni lodi mutanan k'asar China sunzo siya, lodin
tirela hud'u mukayi,ba k'aramin kud'i nasamu ba,dan haka murabu da Sinan dan naga
hak'armu baza ta tadda ruwaba.Me kake nufi? Yazuba mata idanu jikinta duk a
farfashe yake"gaskiyar magana tunda Sinan yamiki irin wannan dukan kawo wuk'an to
babu wata rana dazaki kuma mishi koda kun rage daga ke sai shi a doron duniya bazai
kuma sauraran kiba.Tunda na samu abin yi kishare shi kawai,d'an iska yadaije amma
ai munci gari,nima kwana biyu zan kiyayi zuwa cikin gari da duk inda nasan zai
ganni,dan na san zai nemeni ruwa a jallo.
Takalleshi amma tunda bai auri Sudaida ba na san zai koma ruwa tsundum.
Yamata wani kallon sauna"ke Sinan fa ba sin ki yakw yiba shishshigi da nacinki yasa
kika samu kanshi,kuma koda kika samu kan shi ai ba wani d'ad'ashi da k'asa
kikayiba,ak'arshe ma bazuwa yayi yaba ki hak'uri akan kuyi hannun rigaba?
Yamik'e"nidai buri na ya cika,dama yarinyar ce bana so ta aure shi saboda girman
kanta,kin san sannu wannan ta fatar baki bata ta6a cemin ba,duk da tasan nid'in
abokin saurayin tane aibtasha ganin mu atare,idan nabari ya aureta to za ta rabamu
tunda na san zaiji maganar ta dan yana son ta.
Zigwai takwanta"ai dai munyi biyu babu. Tibishi yakalle ta kisa ranki
a inuwa,barinje kasuwa in miki siyayya,yana fita ta kyalkyale da dariya"haba
Tibishi ai linzami ya fi k'arfin bakin kaza,kai ka had'ani da Sinan dan yazama
saniyar tatsarmu,to mun tatseshi yadda yakamata, yanzu idanu na a bud'e suke ina
ganin kowa garauuu ba ka da kud'in dazan aure ka,bari dai mucinye wanda kasamo,za
ka nemeni ko sama ko k'asa karasa,garin zan bari dan yamin zafi saboda rashin
Sinan, zan tafi wata jahar in bud'e sabuwar rayuwa da sababbin alhazan birni masu
aljihu da kud'i ba irin kaba tsami ragowar burkutu giyar k'ok'o da hayakin maro da
taba dayaci yacinye ka,sai na sai gida da mota,sannnan zan yi aure...toh maji
magani an binne tsohuwa da ranta...
Haka ya yi an sai da gonar rago an sai mishi fura.
Farar dabara shiga rijiya da fura.
10 Jumaada Thani 1441
4 February 2020
We Ibrahim's Daughters👇
Asdilat KD...2geda with Ra'ibs.
DANGIN NONO WRITERS ASSOCIATION
{Da Inganci Mukayi Fintinkau}
Bismillahi wabihi nasta'in
...GWAJIN DAFI💔
Almost true story
Daga alk'alamin🖊
Ya'yan Ibrahim
Saudat A.Baba (Asdilat KD)
Da
Bara'atu Ibrahim (Ra'ibs)
Shafi na goma sha tara.
Kwanaki biyu Sinan yayi a gadon asibiti yasamu sauk'i sai dai likita
bai sallame shiba sai zuwa gobe.Yakar6i wayar Hamidan dan ta shi ko ta fad'i ko
kuma su Tibishi sun sace ta,yadaddanna lambobin ta sannan ya d'ora lambar a
kira.Tad'aga da sallama,wani abu yatsirga ilahirin jikinshi,ta kuma yin sallama jin
ba ayi magana ba sai ta katse.Yacire wayar a kunnenshi yana jujjuya ta,idanun shi
sun kad'a jawur,tabbasss kukan zuci yakeyi.Yaya Sinan ba a d'aga bane ko matsalar
na'urar sadarwa?Yajuya yakalli Hamidan d'in,sai ya gyad'a kai"zan cigaba da gwadawa
wata k'ila tashiga.Sai da ya danna kira sannan yace"Hamidan dan ALLAH kaje gida
Mama tadama min kunun tamba.Yamik'e yana murmushi"a lallai yau jikin
Alhamdulillahi,a had'o da abinci ko?Yagyad'a kai"amma me d'an ruwa-ruwa.
Yana fita yakai wayar kunnenshi,tad'aga da sallama.Yasauke numfash
sannan ya amsa sallamar,yakira sunan ta Sudaida...Zuciyoyinsu suka buga,sukayi
shiru na wucewar wasu dak'ik'u.Da rawar murya take fad'in"Sinan ya jikin?Ance kana
kwance a gadon asibiti,Sinan me yasa kabiye ma son zuciya bayan ka san son zuciya
6acin ta...dama da gaske kura ce lull6e dafatar akuya?Sinan kai masoyina ne,
wallahi ban ji dad'in abinda yafaru ba ko kad'an...ALLAH yashirye ka dana... yatari
numfashin ta"na rantse miki da girman ALLAH bana shan giya"ba ka shan giya to ya
akayi kasha? Ba fa a wasan kwaikwayo kafito ba.Yakad'a kai, matsalar kenan ba wanda
zai gasgata shi"Sudaida na san na rasa ki,to amma duk da haka bazan barki cikin
duhu ba,ranar wanka ba a 6oye cibi... yafara ba ta labarin had'uwarsu da Zigwai
wanda shi kanshi yasha mamakin sauk'in halin ta,saboda irin wulak'ancin dayake
mata,amma tashanye kullum bata fushi kwantar da kai take mishi na gasken-gaske da
haka har taja ra'ayin shi yafad'a tark'onta.
Cikin kuka tace"ai na fad'a maka dabi'a tana na so,maganin kar ayi to
tun farko kar a fara,dan shaid'an baya raina k'ofa.Sinan ina maka fatan alheri a
rayuwa,dan ALLAH kacanja abokai da mutanan kirki.Nagode Sudaida,kema ina miki fatan
alheri da samun natsuwa a gidan auren ki.Sudaida sarauniyar Julaibib.Yagoge lambar
ta daga cikin wayar sannan ya ajiye,yana jin ranshi ba dad'i sunyi sabo na ban
mamaki da Sudaida tun tana yar k'aramar yarinya...Lallai sabo turken wawa.
Julaibib daya jingina da k'ofar D'akin-shak'atawar yak'arasa shiga
yazauna,ganin shi baisa ta daina kukan ba.Yakalleta cikin kulawa"kukan na menene
Sudaida?Ai k'addara ta riga fata"rayuwar mu ba a hannu take ba,ALLAH ne yake
tafiyar mana da ita,ta duk yadda ya so,shiyasa so ba samu bane,haka kuma samu ba so
bane a wasu lokutan;yasa hannayen shi yagewayeta yana mata wani salo a hankali,yana
kuma fad'a mata wasu kalamai sai ga shi tasa hannu ta share hawayen ta kuma yi
shiru,tana k'ar6an sak'onnin dayake bata a ilahirin gangar jiki da sararin
zuciya,wucewar wasu dak'ik'u sannan yad'ago fuskar ta suka kalli juna tayi saurin
kauda kai"idan kunne na sun jiyo min dai-dai a cikin kalamanki naji kince shaid'an
baya raina k'ofa ko? Ba baka sai kunne...jikin ta ya mutu murusss kai kawai
tagyad'a.Yamik'a mata hannun damar shi "bani wayar ki.Tasa mishi a tafin
hannun,yasa ta aljihu...
Sudaida...Yakira tatad'ago tad'an kalleshi. Kin san me yasa nakar6i
wayarki?Uh uh.Yasauke numfashi"to na kar6i wayar ki saboda ba na so wata mu'amala
tacigaba da kasancewa a tsakanin ku,yanzu ke matar aure ce,shi kuma wani k'ato ne
daba muharraminki ba,ba dangin Iya bare na Baba;shi kuma shaid'an baya raina
k'ofa.Yabata wata sabuwa galleliyar waya da layi sabo a ciki.Tasa hannu biyu ta
kar6a"Yaya Julaibib nagode da da tunatarwanka.
Bayan sallar isha'i yashigo"Ina amaryar? Ta shaida muryar ko da acikin
magagin bacci take, tafito sanye da hijab d'in data idar da sallah "sannun ku da
zuwa...Yayi murmushi"yauwa amarya sha gud'a.Ya ba ta kunya ba kad'an ba,ta kuma ji
abun banbarak'wai namiji da suna kande, wai Yaya Musaddiq da tsokanar ta,dama shi
da Yaya Adnan sam ba shak'uwa a tsakanin su, wannan sauk'in halin sai Yaya Aminu.
Cikin girmamawa ta gaishe shi tare da tambayar ya Yaya Safiyya?Yagyara
zama"ai itace ma ta ai ko ni,wai tana gaishe ki,kin san yanayin na ta,tafiyar
wahala take mata amma dai za ta k'ok'arta tazo.
Taje takawo musu abinci Musaddiq yamik'e"a ah wallahi kuci kayan
ku.Julaibib yazuba mishi idanu saboda me? Yad'an daki kafad'ar shi"ni kuma nawa da
yake jirana a gida inyi Yaya dashi?Yamik'a mishi hannu sukayi musafaha.Suna tsaye a
bakin k'ofa sukayi k'us-k'us d'insu sukayi dariya suka tafa.Tabisu da kallo"maza ma
sun iya tsegumi?Tayi yar dariya wai itace ba su so taji kenan"Yaya Musaddiq mukwana
lafiya.To Sudaida ALLAH yatashe mu lafiya.
Tana kwance cikin damuwa saboda fad'an da Julaibib yarufe ta dashi kamar
zai ba ta na jaki,sannan ya hanata tofa albarkacin bakin ta, na ganin da yama
k'anwar Sinan a gidan; kila zaton shi Sinan ne ya aiko ta tunda zai kira lambarta
yajita a kashe,ita kuma Maman suce tabata turaran wuta da su humra kala-kala takawo
mata,dama ta siya ta ajiye idan tazo gidan saita ba ta toh kuma ga yadda al'mura
suka kasance.
Yanuna ta da yatsa idanun shi sun kad'a jawur"idan na kuma ganin wata ko
wani a cikin gidan nan daya danganci Sinan na rantse miki da ALLAH abinda zan miki
har ki mutu baza ki manta shi ba...Idanun ta suka ciko da kwallah Yaya D'ans...ke!
nace ki rufe min baki ko?Yayi d'as d'as d'as da yan yatsun shi"baki sanni bane,yaja
dogon tsaki yawuce d'akin shi.
Tasauke numfashi da ajiyar zuciya,tasa hannu tana share hawaye,tabi k'ofar
da ake k'wank'wasawa da wani malalacin kallo,ta maida kanta jikin matashi tana
dad'a gyara kwanciya.Aka cigaba da k'wank'wasa k'ofar,dole tamik'e cikin fushi tana
jan tsaki a ranta tana mita"na ci dambun kuturu.Tasa hannu tabud'e k'ofar caraf
idanun su yahad'u,ta gallama Sudaida harara. Sudaida tayi kamar ba ta gani ba,tayi
d'an tsallen murna fuskar ta cike da d'okin ganin ta tafad'a jikinta"oyoyo
Hajiyarmu sannu da zuwa...suka shige D'akin-shak'atawar,Hajiya ta ture ta"ke gafara
can karki 6alla ni,tazauna a k'asa tana dafe k'afafu da alama ciwon k'afar yana son
motsawa.
Da sauri Sudaida tad'auko man zafi ta d'urk'usa a gabanta tana murza mata
a k'afafun tana maimaita"sannu da zuwa Hajiyar mu gaskiyar magana naji dad'in
ganinki ba kad'an ba. Hajiya tasake galla mata harara"amma shine kika barni a waje
ina ta k'wank'wasa k'ofa?Tayi yar dariya"kai Hajiya gidan amarya fa kikazo ni
k'wank'wasa k'ofar kine ma yatashe ni daga bacci.Hajiya takalli agogon bangon dake
d'akin sha d'aya saura minti goma na safiya"Toh ALLAH ko yasauwak'e da wannan
baccin asaran. Tagirgiza kai"ba amin ba,ai lokacin abu ayi shi, amarci ai ba k'arya
bane,ba kuma abinda ba ya sawa.Hajiya tazuba mata idanu cikin kallan nazari"amarcin
ne yadad'a k'arar dake kamar bushashshen takand'a?Ke ko cikar d'akin bakiyi
ba.Takai hannu tashafa wuyanta"sharri dai ba kyau Hajiya ni ba bushewar danayi
wallahi,toh so kike kiga na zama ta shi da nishi?Tamata dak'uwa"kar6i nan aiko
Iyayan ki na fi k'arfin in musu sharri bare ke karankad'a miya.Tad'an turo baki
gaba"ai baza ki musu sharri ba tunda Ya'yan kine kina son su,nice dai ba kyau
so.Hajiya takad'a kai kawai.
Ina Julaibibi ne rabona dashi tun shekaran jiya da daddare.Haushin shi
yamamayi zuciyarta,to amma Hajiya babbace ko yaya tanuna wani yanayi za ta iya gano
ta bare kuma yadda ta tsare ta da idanu.Tamik'e tana rufe man zafin"ke Hajiya ai
yanzu ba da bane dazai dinga zuwa gidan ki yana share waje,ni kuma dawa zai barni?
Hajiya ta tafa hannaye tana sallallami"ba shakka rasa kunya 6aren tanka...lallai
wuyan ki ya isa yanka.
Sudaida tawuce tana dariya,ta kwana biyu bata shiga d'akin ba,k'amshin
arabi'an perfume da k'amshin turaren d'aki ya gauraye sai yaba da wani irin nau'in
k'amshi me sanyin dad'i wajen shak'a,carpet d'in d'akin kore da ratsin ruwan madara
dawasu kyalli-kyalli masu d'aukar idanu,hakama labulayen d'akin ruwan madara da
ratsin filawar rose yan shara-shara,sassayar iskar da take shigowa d'akin ta
tagogin da suke a bud'e suna kad'a labulayen suna rangaji saboda rashin nauyin
su,ya canja gadon daga inda tasani zuwa d'aya bangaren, wardrobe ma yacanja daga
zuwa bangaren yamma,shoe-rack(ma'ajiyar takalma) cike tam da takalma mafi yawansu
farare ne,kuma masu rufi(sau ciki)
Yad'ago yana mata wannan rikitaccen kallan nashi da yake ba ta
haushi,yamaida kanshi ga tarin littafan daya barbaza a saman tebur,yana kuma yin
rubutu a na'ura me k'wak'walwa da alama wasu abubuwan yake shigarwa"lafiya za kizo
ki tsaya min akai bayan kingani ganin idanun ki aiki nakeyi.Wulak'ancin D'an Sarai
har yakai haka?Ta tambayi kanta,zuciyar ta tayi rauni idanun ta suka kawo ruwa amma
bata bari hawayen sun zubo ba,ta kad'a kai"ba kome dama saboda ka ma ake cin
k'asa,tasaki marik'in k'ofar"Hajiya ce take magana.Suna had'a idanu yagalla mata
harara "dama ai duk wanda kika ga ya ci kaza to shine da ita.Tayi kamar bataji
abinda yafad'a ba.
Yasauke numfashi zuciyar shi ba dad'i ganin damuwar data shiga,ko
kukan d'azu datasha kuka har tak'oshi yaji ba dad'i,to amma dole yayima tufkar
hanci,kar garin kallon ruwa k'wad'o yamishi k'afa,ita da Sinan ai sun so juna, yau
da gobe kuma bata bar kome ba,shaid'an baya raina k'ofa, dama ba abinda yake so
sama da 6ata tsakanin ma'aurata,toh dole sai ya toshe duk wata kafa da yasan alak'a
zata had'ata da Sinan dan yatserar dasu da auransu daga fad'awa halaka.Wani
lallausan murmushi yasu6uce mishi "humm Sudaida za tafahimce shi,shi masoyin tane
da babu kamar shi a doron duniya,shi da ita mutu karaba takalmin kaza,har lokacin
da gangar jiki zai daina numfashi, rai yatafiii...
Yazauna suka gaisa da Hajiya.Tanuna shi da yatsa"kai Julaibibi kazama
jarumi dan a haka nasan ka, karka biye ma wannan malalaciyar matar taka tamaida kai
rago, ace kazauna kana sharar bacci har hantsi yadubi ludayi?Yashafa kwantaccen
bak'in gashin kanshi yana d'an murmushi"Hajiya wane ni da wannan aikin;ai sai manya
gatan wasa,amarya sha gud'a suka kalli juna shi da Sudaida tad'an harareshi tana
turo ba ki gaba.
Wasu muhimman bayanai nake ta shigarwa ashafin mu na yanar
gizo.Tagyad'a kai "Toh Ubangiji yayi jagora.Sunata hira da Hajiya cikin jin dad'i a
wanta d'aya a gidan sannan takalle su"to ai na gaishe ku,barin tashi inje gidan
Musaddiq jiya Safiyya bataji dad'i ba,wannan girman ciki ko yan hud'une a ciki iya
ka kenan, ALLAH dai yaraba lafiya,suka amsa da amin. Julaibib yafita k'ofar gida
inda ake sallama dashi.
Hajiya takalleta cikin natsuwa"wato kink'i tsayawa ki kwantar da
hankalinki ki rungumi kaddarar Ubangiji ko?Tasunkwui da kai.Hajiya tacigaba shi
aure dakike ganin shi ai ALLAH ne yake had'a shi ba mutum d'an Adam ba;ko shi Sinan
ai ya dangana dan yazo har gida ya fed'emin biri har bindi, ban kuma kullace shi
ba,na san shi mutumin kirkine,sharrin shaid'an dana zuciya ne suka rud'e shi,tanuna
ta da yatsa"tun wuri ki saki ranki ki rungumi auren ki dan shine gatan ki na d'iya
mace,ga sauran yan'uwanki can kowacce tayi sharrr gwanin ban sha'awa da kyan
gani,ke kuma kinanan jiya i yau,ke da Julaibibi ai kun zama k'arfe da mayen
k'arfe.Tayi shiru kawai a ranta tana mita"ai Yaya D'ansarai yakamata ajama kunne
tunda shine baya son ta,auren dole aka mishi a tunanin ta"rashin sani karen gwauro
yakori bazawara.Sukayi sallama tad'an ta ka mata zuwa harabar gidan.Tare suka koma
ciki da Julaibib..Ke Sudaida zo nan...tayi kunnen uwar shegu tashige wanka.Yakad'a
kai yana yar dariya"Sudaida k'uruci dangin hauka...
A sanda hantsi yadubi ludayi na safiyar talata,tana had'a lemun abarba
da kashu ta toshe kunnuwanta da earphone,tana sanye da riga da zani na atamfa ruwan
makuba da ratsin filawoyi manya da k'anana masu ruwan hoda da baki tayi wani irin
d'auri na burgewa gashin kanta ta tubke shi da k'aton ribbon ruwan makuba,ta juya
za ta d'auki siga caraf idanun su yahad'u, yana tsaye a k'ofa yanad'e hannayen shi
a kirji,tad'auke kai cikin basarwa kamar bata ganshi ba,dan har yanzu a wuya take
dashi, ba Yaya Julaibib d'in da tasani a da to yanzu ba shi bane,gaba d'aya ya
canja Hali,d'azu-d'azu yagama yarfa mata ruwan bala'i wai yaran Kawun su yazo,ita
kuma ta manta bata sa hijab ba tazauna suna shan hira da dariya.
Tagama aikinta tazo za ta wuce yatare hanyar yana kallanta cikin natsuwa
kamar wani abu bai faruba,ko da yake shi tsakani da ALLAH yamata nasiha irin haka
bai dace ba dan kayan sun kamata kome na ta ya bayyana,itace dai ta maida cibi
yazama k'ari.Na yi sallama baki amsaba,na tambayeki abinci na nan ma kinyi shiru
lafiya kuwa?Taturo baki gaba"shiruma amsace. Sudaida ba magana nake miki ba? Nan ma
tayi shiru.Me yasa kike jamin zarene kin san halina fa. Tamishi wani kallo me kama
da harara,cikin fushi tace"to sai me?Me tsoron ta mutu ai shi yake maho.Yayi
jimmm...Yana cigaba da kallanta cikin nazari,wucewar wasu dak'ik'u sai
yajuya...tabi bayan shi da harara"ALLAH raka ta ki gona...Yaja yatsaya zai juyo sai
kuma yafasa yayi tafiyar shi kamar baiji abinda fafad'a ba.
Tana azkar d'in yammaci bayan ta idar da sallar la'asar tana tunanin a
ina Yaya D'ansarai yatsaya bai dawo gida yaci abincin rana kamar yadda yasaba
ba,duk da ba wani d'asawa suke yi ba,...shiru-shiru har bayan sallar isha'i haushin
shi yakamata ita kuma ta k'i kiran shi a waya taji me yatsaya yi taje tayi
kwanciyarta tana zencen zuci"wato ko da, da take son shi take kukan rabuwa dashi,to
shi dai ba ta ita yake yiba tunda gashi suna zaman aure yana mata yadda yaga dama,
tadad'a gyara rufa tana k'wafa aikin banza kawai tura agwagwa cikin ruwa,jikinta
yayi sanyi "lallai san maso wani k'oshin wahala, har bacci yayi awon gaba da ita
bataji shigowar shiba.
Da safe tana tsaye a jikin taga ta zubama motar Julaibib idanu,tun
jiya bai fita da ita ba,sanda yadawo gidan tariga tayi bacci kuma bai tashe taba,
anyama ya dawo gidan? dan yadda ta ajiye mishi abincin dare haka taba almajiri
dasafe, bai ta6a ba,har d'akin shi taleka yanzu kuma ba ya nan,to ina yatafine?Wata
kila tun daga sallar asubahi yawuce gidan Inna ko gidan Hajiya,ta lumshe idanun ta
tana mamakin canjin halin Yaya D'an Sarai.
A hankali ake k'wank'wasa k'ofar. Tasauke numfashi,ranta ya mata dad'i
Julaibib ne dan haka yake buga k'ofa na natsuwa.Tabud'e cikin d'okin san ganin shi
ta ma manta da rashin jituwar su.Suka kalli juna yamata murmushi, murna ta koma
ciki,zuciyarta tayi rauni,kwallah yacika idanun ta,ta rasa hujjar hakan wallahi,
yarage fara'ar fuskar shi,yagyad'a kai labarin zuciya a tambayi fuska"ba kya maraba
dani ko?Sai kawai yajuya, dasauri taruk'o gefen rigarshi tabaya"wallahi ba haka
bane,yajuyo fuskar shi ba walwala"toh yayane?Taja da baya tabashi hanya dan
yashiga,yakad'a kai"bazan shiga ba.
Tamarairaice"Yaya Aminu dan girman ALLAH kayi hak'uri kashigo,wallahi na
yi kewarka ne,tunda aka kawo ni Lillahi warasulihi sai yau d'in nan kazo duk yadda
muke da kai..tayi furucin da yanayin shagwa6a.Yashiga D'akin-shak'awar yazauna a
kujera"to banda abinki Sudaida yaushe zan ta zirga-zirga a gidanki? Tashige
D'akin-girki dasauri takawo mishi kunun tamba yasha madara "Yaya Aminu ga
mutumin.Yabud'e kofin yagani"to nagode Sudaida,kad'an yasha saboda ya riga ya
k'oshi,a gida ma yana da wanda bai shaba na wajan Innan D'ansarai.
Sun d'an ta6a hira sannan yace mata kishiga d'akin mijinki ki d'auko
min mukullin motarshi zan kai ta gyara, ba yadda banyi dashi akan yad'auki tawa
yayi tafiyar ba amma yak'i,sai tasha naraka shi yashiga motar haya,kuma a ranar
yanada jarabawa...har tabashi mukullin yatafi hankalinta yayi mugun tashi"yanzu
D'ansarai zaiyi tafiya yabar garin amma ko sallama bazai mata ba? Itako wace irin
kiyayya yake mata haka? Ai ko kafin suyi aure yana mata sallama bare yanzu da take
cikin gidan shi a k'ark'ashin igiyar aure.Tayi k'wafa"ai ba lallai ba tilas,yaje
yadawo tana sauraren shi da duk ma wacce zai zo.
Kwanakinshi biyu da tafiya,shi bai kira ba, itama bata kira ba,a
kwana na uku ne dai takasa daurewa dan abin tsoro yafara bata...sai taga bata kyau
taba itace a k'asa dan haka tasauke ...rawanin tsiyar tanemeshi.
"Lafiya?
Tamabayar daya mata kenan daya d'aga wayar,bai kuma jira amsar taba
yakasheTacire wayar daga kunnenta cike da mad'aukakin mamaki" wai me wannan mutumin
yake nufi ne? haushi da damuwa suka kamata.. tajafa wayar a kujera ko tunanin taci
screen bata yiba, tawuce D'akin-girki tasauke dafadukan taliyan data dafa, tazuba a
faranti takoma D'akin-shak'ata dan taci, sai dai tanata kallan taliyar har yayi
sanyi baza ta iya ciba,ai ko almajiri yana kwala barar"allazi wahidin"tabud'e k'ofa
tajuye mishi duka a robar shi.Yakar6a da rawar hannu data murya.
"Iya ALLAH yabi yaki,ya yaye miki matsalar rayuwa.Tabishi da kallo
tana fad'in"amin d'an Malam.Sauri yakeyi kamar zai ta shi sama dan kada sauran
almajirai su farga da abinci a kwanon shi su rufar mishi, gashi kuma wasu gardawa
ne guda biyu suka sashi ya barato musu abinci,idan bai kai musu ba ba k'aramin na
jaki zai shaba,kuma ba shi da mataimaki sai ALLAH.
Abu kamar wasa k'aramar magana ta zama babba,yau makon Jukaibib d'aya
kuma koda wasa bai kira taba...Abun yak'ara jefata a kokwanto da fargaba"to lafiya
kuwa?Gashi ba wanda za ta tambaya,haba ai da kunya sai a mata tirrr...wasu kuma su
mata dariya su d'auketa sakarya ita da mijin ta amma bata san a halin da yake ba?
Taja tsaki"to shi d'in ya kira tane?Ko ko dai idan akak'i jininka ko ruwa kafad'a
sai ace ka tada k'ura?Wucewar wasu dak'ik'u tana zaune tunani barkatai ya cika
k'wak'walwarta ta rasa na za6a tayi shi da gasken-gaske,ta tsuke baki kamar za ta
rufe shi tana fitar da iska,gaskiyar magana kawai ta kasa samun natsuwar zuciya dan
haka tak'arya 6illenta tad'auki waya takira shi.
Bugu d'aya yad'aga kamar dama jiran ta yakeyi.Yayi sallama muryar shi
a dake.Ta amsa sallamar tana gaishe shi.Asik'e ya amsa"lafiya...Gwiwoyinta suka
sage,sharrr... sharrr...hawaye yafara sintiri a fuskarta shashshek'ar kukan na ta
na fitowa a hankali. Yatare ta muryar shi ba sassauci"ke! Dakata, dakata haka
malama! ni na ta6a fad'a miki ina sha'awar jin sautin kukan ki,bare yanzu da kike
jinyi ki kirani?Yaya Jul...Kittt...Yakatse wayar. Haushi da mamaki suka rufe
ta,ranta in yayi dubu ya6aci "Lallai ma D'ansarai...To ko da aka ba ka ni, idan ban
maka ba sai ka sallame ni...tacigaba da kuka.
Julaibib yacire wayar a kunnen shi yana murmushi"kulawa yabawa ce,ya
kamata yakoma gida haka dama kullum idan sunyi waya da Hajiya sai ta mishi ciwon
bakin yaje ya share waje kamar mara Iyali.Baba ma jiya sai da yace"Malam D'ansarai
ka k'ok'arta duk lokacin daka samu dama kazo gida wajan Iyalin ka kaji ko?Ya amsa
da ladabi"eh Baba Insha-ALLAH. Yakulle k'ofar d'akin shi dan tafiya masallaci,
masallatai mabambanta sunata kiraye-kirayen sallar azahar.
Da yammacin ranar talata rana ta tafi tana shirin fad'uwa,magriba na
kunno kai tana zaune a tana nazarin littafan Islamiyyarta,motsin shigowar Julaibib
taji yana shiga da kayayyaji D'akin-girki,sai da yagama yashiga D'akin-shak'tawar
da wata babbar leda,a gajiye ya zauna yana kallanta yasa hannayen shi yana 6alle
botirin gaban rigar shi,bata wani nuna d'okin ganin shi ba,fuskar ta ba yabo ba
fallasa tace mishi"sannu da zuwa.Yagyad'a kai"yauwa yana cigaba da nazarin ta.
Sudaida...Yakira ta.
Bata d'ago ta kalle shi ba ta amsa "na'am.Duk sukayi shiru,ta sunkwui
da kai amma ta kasa cigaba da nazarin kallan littafin kawai takeyi amma baza tace
ga abinda aka rubuta ba. Ana fara kiran sallar magriba yafita.
Tana kwance bayan ta idar da sallar Isha'i,zuwa wannan lokacin zuciyar ta
ta gama tafarfasa ruwan ciki ya k'one k'urmus har ya kama da wuta,zuciyarta tayi
gobara saboda takaicin D'ansarai autan Inna;tayi kwafa taja dogon tsaki tun wajejen
k'arfe goma sha d'aya da rabi na safiya Hanifa tazo tafad'a mata"Baba D'ansarai ya
dawo,har ya bata Inibi da dabino me yawa, tashigo ma da Inibi tana ci,wani sanyin
dad'i taji a ilahirin gangar jiki da sararin zuciyarta,duk da bawani d'asawa suke
yiba,ta tambayeta to yana ina? Hanifa tace yana gidan su"Kawu Adnan shi da
Babana(Musaddiq)
Nan da nan ta dad'a gyara ko ina tayi wanka tayi kwalliya tafeshe jiki
da turare,ta turara d'akunanan gidan da turarukan d'aki ko ina yad'auki k'amshi da
kyalli;to amma saboda tsiya d'inkin ludayi wai sai gab da magriba yaga damar
shigowa gidan,kuma ko dak'ik'a goma cikakku bai yiba yasake ficewa,bai kuma sake
shigowa ba sai yanzu awa biyu da idar da sallar Isha'i. Tamaida idanun ta tarufe
kamar me bacci.
Yatsuguna yana tashin ta,dak'yar ta tashi tazauna tana turo baki
gaba,yakoma kujera yazauna"zan samu abinci?Takauda kai"banyi girki ba,dan wanda
tadafa mishi da rana,bayan la'asar tajuye ma almajiri.To ko shayi ne had'a min
yunwa nake ji.Batayi magana ba dan dai ba yadda za tayine da baza ta had'a
ba,tad'an ja tsaki"aikin banza harara a duhu,shi baya gajiya da shan shayi, shayin
ma daba a sa madara sai kace jikan buzaye,tahad'a takawo mishi lokacin ya shiga
wanka,yafito cikin fararen kaya na shan iska, botiran gaban rigar a bud'e suke
gargasar shi akwance lufff...bak'ink'irin da shek'i.
Yad'auki shayin da bismillah yad'an kur6a sai yakalleta"me yasa kika
samin siga bayan ga zuma?Tad'an harare shi"ni siga nake sawa a shayi,ai ba mutuwa
za kayi ba.Yayi murmushi yana kad'a kai"k'uruci dangin hauka ga abinda aka tambaya
ga amsar da take bayarwa "Sudaida mutan Matsirga suna gaishe ki,suna nan zuwa.Shiru
ma amsa ce.Yabita da kallo"ke wai lafiyar ki kuwa? Ko dawowar tawace baki so?Ni fa
shi yasa bana san zuwa,tunda raina ne yake 6aci.Tamishi wani kallo me kama da
harara"na rantse da girman ALLAH ni...sauran kalaman suka mak'ale saboda haushin
daya mamaye ta,takaicin ta ace yazo garin tun farar safiya,bai shigo yaganta
ba,amma ya tafi Matsirga ba dangin Iya bare na Baba,dangin-dangirere wata tsohuwar
budurwar shi data dad'e a kushewa,itace 'yar gwal har yanzu itace a sararin
zuciyarta shi.Cikin fushi ta kwashi littafai da daddumar data yi sallah fuuu...
Tawuce d'akin baccin ta.
Ya ajiye kofin shayin a saman tebur yayi shiru da yanayin damuwa"me
yasa Sudaida take mishi haka?Ai itace k'arfin dawowar shi a yau,amma ta watsa mishi
k'asa a cikin idanu;duk yadda ya d'okantu da ita a yau d'in amma da ta shi
mazantakar tamotsa sai ya danne zuciyar shi bai bi ta d'aki kamar yadda zuciyar
take raya mishi ba,ya kwaso wasu littafi yana nazarin su.
Tacire wayar ta a caji tahaye gado sannan ta kunna data,sak'onni suka
dinga shigowa bata ta6a wayar ba har sai da suka gama shigowa sannan ta fara duba
Status d'in su Khausar,haushi yadad'a kamata,ganin kowacce tana cikin shauk'in
k'auna ita da masoyin ta...A status d'in A'isha ne taga Hashim ya zage yana daka
shakwara a turmi tana ce mishi baiyi laushi ba sai ya k'ara dakawa,shi kuma yana
fad'in nagaji fa gaskiya..ga wanda suke cin sakwaran da miyar Ogu suna dariya.
Ga na Khausar nan ita da Huzaifa sunyi wani irin kyau na ban mamaki
gaba d'ayan su sun canja,ta d'ora ha6arta a kafad'arshi suna dariya, d'ayan kuma
wasu irin kalamai ne na tsananin k'auna ta rubuta shi ga hoton zuciya an gewaye ta
da adon filawar Damask rose-flower.
Na maryam kuma hummm sallah ba a magana,ta yi mugun mamakin abinda ta
d'ora a irin yanayin zaman da tayi da kuma kayan jikin ta,a k'asa ta rubuta"My
Snuggle...I miss you deadly... tabbb...ai bata gama kallo ba tabari tana zagin ta
"abinda yasa meki ALLAH yasa kar yasamu sauran dangi.Tayita kira layin ta a kashe,
duk da ta san taza6i wad'anda za su ga Status d'in na tane,amma ita sai hakan bai
gamshe taba gaskiya.
"Nasmat tamata magana"
Hummm...Amaryar autan Inna kuna shan sharafin ku fa..
Sudaida ta6ata fuska"a ah abinda yafi sharafi muke sha.
Nasmat takyalkyale da dariya...nima naga alama shi yasa sai jefi-jefi a
ke ganin ki online...har yanzu kanwa bata kar tsamin bane k'wannafin yakwanta?
Sudaida taja dogon tsaki"ke dai kika sani da neman magana ni sai da
safe...kawai ta kashe data ta kwanta;bata duba sak'o ko guda d'aya ba,tunani
barkatai ya cika k'wak'walwarta "hummm yunwar ya tashi"taja dogon tsaki wallahi ai
ba lallai ba tilas.
Washe gari ma da sassafe yabar gidan wai suna da taro a Zango Urban
kamar tace yasiyo mata d'anbagalaje amma ta shareshi,ta d'auki wayar ta takira Yaya
Aminu tana tambayar shi"kaima kana Zangon ne?Eh Sudaida.Dan ALLAH Yaya Aminu
d'anbagalaje nake so amma me taushi.Kai kai kai Sudaida ai gwamma me k'arfin kinga
za ki motsa muk'amuk'inki da dasashi ko kuwa? Tad'an marairaice"Yaya Aminu ni dai
me taushi.To zan siyo miki Insha-ALLAH. Yauwa Yaya Aminu wallahi, shi yasa nake son
ka ALLAH yabarka da Sidddiqa tazama sarauniyar ka.Amin Sudaida. Sukayi dariya.
Abubuwa suke ta maimaituwa na rashin fahimtar juna a tsakanin
su,musamman Sudaida da take d'aukar fushi a abinda bai kamata ayi fushin ba,abun ya
k'i ci ya k'i cinyewa kamar cin k'wan makauniya.Yauma tunda yatafi masallaci sallar
asubahi bai dawo gidan ba.A hankali taji ana k'wank'wansa k'ofar gidan ta san
shine, dan taji tsayuwar motar shi.Tatashi tabud'e takoma tayi kwanciyar ta.Yatsaya
a tsakiyar d'akin hannayen shi nad'e a k'irji.
"Sudaida bak'in Matsirga sun zo.
Dammm...zuciyar ta tabuga da k'arfin gaske.Tafara zancen
zuci"Kutumelesi wato zuwa yayi dakan shi yad'auko su?Su suna da mutunci da kima a
idanun shi,ya kuma damu dasu amma ita ko oho ko?
Tajijjiga kai wani...kumallon mata yata so mata har wuya,amma ba tayi
ko kawa da zuciyar ta bata amayo shiba.Tad'ago takalleshi"Oh sun zo?Tagyad'a
kai"toh sannun su da zuwa. Yabita da kallan nazari ganin tana dad'a gyara kwanciya
har da jan bargo ta lullu6a"ke wai menene haka?Kitashi kije ku gaisa mana.
Tayamutsa fuska sannan tajuya mishi k'eya "gaskiya ni har yanzu bacci ne a cikin
idanu na kum...Yatari numfashin ta "Innar su Bilkisu ce fa?
Furucin shi yamata sukar wuk'a a k'ahon zuciya wallahi ta kasa
daurewa,idanun ta suka kawo ruwa"shikenan kuma dan kayi bak'i bazan yi bacci
ba,bayan idanu na har wani zafi da yaji-yaji suke min saboda rashin baccin?Ni fa na
rantse da girman ALLAH bazan iya wannan zaman ba,tunda baka d'auke ni wata tsiya
ba,toh ba dani ba wannan takuran,ko dan kaga gidan kane? Tagalla mishi harara"an
hak'ura ana shan kukar k'azama kuma dole sai tayi tsada?Wallahi sai a hak'ura tunda
ba mutuwa za ayi ba ehemmm.
Suka zubama juna idanu cikin kallan-kallo nawucewar wasu dak'ik'u kowa
zuciyar shi ba dad'i. Sudaida tana jiran martani ne tayi abinda idan ta tafasa za
ta k'one,sai shi kuma yamata shiru,dan yadda ta6ata mishi rai idan yatsaya toh
aika-aika za ayi,sai kawai yagyad'a kai"ki cigaba da abinda kike yi,amma fa kowa
yaci ladan kuturu sai ya mishi aski,wanda ya girmama iyayen wani to bana kowa ya
girmama ba sai na shi.Yakai hannu yak'ara mata gudun fankar "shikenan kiyi baccin
ki.Yajuya yafita fuskar shi ba walwala,labarin zuciya a tambayi fuska.
Tad'aga murya"eh yanzu kuwa zanyi baccin.Sai kuma tamik'e jikin ta
yayi sanyi gaskiyar magana bai kamata tayi haka ba"ai bak'on ka annabinka, wanda
yadamu dakai shine zai zo inda kake to bai kamata kanuna mishi halin-ko-inkula
ba"bak'in karen masoyinka ai yafi farin ragon mak'iyinka.
Yayi jimmm...nawucewar wasu dak'ik'u a bak'in k'ofa,Sudaida ta k'i fitowa
ta musu sannu da zuwa to me zai fad'ama Inna?Sai yajuya zuwa D'akin-girki yad'ibo
musu kofuna da lemun biyar a raye da ruwa har zuwa lokacin bai samo amsar dazai ba
Inna ba,yahura iskar bakin shi"lallai Sudaida zata gane da gero ake koko yacigaba
da tafiya,zai fad'a mata Sudaida bata nan.
Yamurd'a k'ofar D'akin-shak'atawar da sallama yashiga,sai dai abun
mamaki Baturiya da suna manga Sudaida yagani durk'ushe a gaban Inna tana gaisheta
cikin girmamawa"kun zo lafiya? Yasu Malam da sauran mutan gidan?A Alhamdulillahi
lafiya lau,duk suna gaishe ki,sannu mungode.Daganin yadda Inna take amsawa itama
taji dad'in shimfid'ar fuskar da Sudaida tamata wacce tafi ta tabarma.Tamik'ama
Bello hannu sukayi musafaha "d'an kanina kaga dana iya yaren fulatanci toh da yau
duk hirarmu da fillanci za muyi shi. Bello yad'an bud'e idanu"kai dama baki iya ba?
To kisa Yaya D'ansarai ya dinga koya miki mana,kinga lokacin da Adda batayi wannan
tafiya me nisan nan ba to idan yazo da fillanci suke magana suyi ta dariya,ranan
nan ma yace mata wai...Kai Bello Inna ta tari numfashin shi'ba na hana ka fad'an
abinda ba a tambaye kaba? Sai yayi shiru.
Da sauri Sudaida tamik'e ta kar6i kayan ta zuzzuba musu lemon a kofuna
sanna tashiga D'akin-girki ta d'auko musu abincin data dafa tajuye a food-flask
tana mita a ranta"kai ALLAH yasuwake da halin D'ansarai yanzu da suna da yawa dole
sai tayi wani sabon girkin. Inna tasha lemon amma tak'i cin abincin.Sudaida ta
karyar da kai gefen dama"haba Innarmu idan baki ciba ai baza muji dad'i ba,ni 'ya
ce awajen ki,uwa kuma ai bazata k'i cin abincin 'yar taba ko da tak'oshi za tasa
albarka,Inna idan bakiciba sai inga kamar da wata a k'asa a yadda muka d'aukeki ni
da Yaya D'ansarai ke ba haka kika d'auke muba...suna had'a idanu tad'an harare shi
sannan ta kauda kai. Inna tace"ba haka babe Sudaida, karki kuma furta irin
wad'annan kalaman,ni na d'aukeku kamar Ya'yan dana haifa,ALLAH yamuku
albarka,yabaku zuri'a d'ayyiba. Dole ta d'auki cokali tayi bismillah sannan tad'an
ci kad'an, Bello kuma yace shi baya shi dan bayajin yunwa yanata cin meatpie da su
Inibin da Julaibib ya bashi.Da za su tafi Sudaida tabata turmin atamfa,taba da
Shadda yadi goma da turare wai aba Malam tana kuma gaishe shi,tak'aro ma Bello
meatpie dayawa dan jiya tayi kuma ba wanda yazo gidan shiyasa bai k'areba.Yakalleta
yana ta murmushi "kince za ki Matsirga?Tagyad'a kai"eh Bello zamu zo Insha-
ALLAH.Yamik'a mata hannu sukayi musafaha "Adda Sudaida sai kinzo zan tatso miki
madarar saniyata da Malam yabani karsana guda biyu nawa ni kad'ai ina kaisu kiwo
har rafin Matsirga nake kaisu susha ruwa sai mudawo gida,sukayi dariya.Sannan ta
rakasu haraban gidan suka shiga mota.Sudaida tasunkuyo tana maimata" ALLAH yatsare
Innarmu,ALLAH yakaiku gida lafiya.Amin Sudaida, Inna tadinga shi mata albarka,tasa
gefen hijab d'inta tana share ruwan hawaye,yau mutuwar Bilkisu ta dawo mata
sabuwa.Suka d'aga hannu suna ma juna adabo.Julaibib yaja motar cikin karsashi,yana
murmushi jin dad'i abinda tama Innar Bilkisu ya kankare duk wani bak'in laifi data
mishi dayake jin haushi...wata irin k'auna da kewar ta suka mamaye ilahirin gangar
jiki da zuciyar shi.
Yadawo yatar da jarkokin kindirmo dana manshanu da sauran tsarabar da
Inna takawo a inda yatafi yabar su.Yatsaya a gabanta hannayen shi suna cikin
aljihun doguwar farar rigar shi,yakalleta cikin natsuwa"Sudaida ya baki adana suba?
Saboda bani da buk'atar sune. Tagama wanke-wanken da take yi tamik'e tana yarfar da
ruwan hannayen ta,tawani tsuke baki kamar me shirin yin fito.Yagyad'a kai"toh bani
abinci sauri nake yi zan tafi Samaru.Cikin fushi tace"na rantse da girman ALLAH tun
kafin wankin hula yakaika ga dare kasan inda za kaje kaci abincin ka,danni ba baiwa
bace. Yazuba mata idanu"ji wasu soki burutsu da yarinyar nan take fad'a,yakalleta
cikin natsuwa"nine bawan ki kenan, tunda duk rintse zan fita in nemo in kawo miki
ki ci ko? Taturo baki gaba"ko bani dolen-dole kafita ka nemo,to ni guda nawa nake
cin abincin?
Kinga ba wannan ba d'auko min abinci na fad'a miki sauri nake yi"na
daina girki a gidan nan, tunda ko a tsarin shari'a ai cewa akayi miji yaciyar da
matar shi bawai mace tayi girki ba.Yagyad'a kai"to amma dai yin girki a wajen mace
dole ne,tunda kyautatawace idan miji yafita ya nemo muku,ke kuma sai ki dafa muku,
a kuma al'adar duk mutanen dana sani galibi matane suke yin girki haka aka taso
anayi Iyaye da kakanni tun tale-tale.Ba sai da so da k'auna za ayi hakan ba?Tafara
k'unk'uni.Shima sai yanzu ya harbo jirginta...kumallon mata ke d'awainiya da ita,to
amma me san d'an tsuntsu shi yake binshi da jifa.
Yarik'o ta tana k'ok'arin fizgewa sai yamata rik'on kura ta samu
nama,sai ta koma tayi lamooo "Sudaida a duniyar ALLAH me namiki da bakya so na?
Yad'ago fuskar ta suka kalli juna"haba Zaujatiii...Dan girman ALLAH fad'amin abinda
zan miki dan in samu k'auna da soyayyarki.. yagewaye hannayeshi a jikinta yana mata
wani salo...yayi k'asa da murya yana mata wasu irin kalamai na rarrashi da bambaki
me k'aryar da damuwar data mamaye sararin zuciya.
Sak'onnin na shi yana shiga ilahirin gangar jiki da zuciyarta duk da
bata so hakan ba amma zuciyar ta tak'i bujirema hakan,k'aunar shi da haushin shi
yamamaye ta,sai kawai ta fashe da kuka ta k'wace tashige d'akin bacci tafad'a gado
takifa fuskar ta a jikin matashi tana jin wani irin abu dabata san ko menene ba.
A tsakiyar d'akin yaja yatsaya yana kallanta"to meye abun kuka?Kai
sha'anin mata a wasu lukutan sai su wallahi,banda dabi'arsu ta rauni da kuma dai
shagwa6a wai tarwad'a da kukan k'ishin ruwa.Agefen gadon yazauna,yarik'o
hannunta"kinga kukan ya isa haka share hawayen ki dan yana ta6a min zuciya,zai
hadda sa min rud'ani fa...ta tureshi"Kalaman ka baza suyi tasiri a zuciya
ta.Yagyad'a kai"toh na nawa kuma?
Yaya D'ansarai ba ka so na dan tunda aka kawo ni gidan nan nayi adabo
da farin ciki,kazo garin nan tun farar safiya amma sai gab da magriba za ka shigo
gidan, sannan sai kadinga nuna min wasu can sun fini mutunci tunda za kaje wajen su
kasahare waje kuyi hira,ni kuma ko oho,idan nakira ka a waya sai kadinga min
fad'a... kaza da kaza haka tadinga fad'in duk abinda yazo bakinta"ni gaskiyar
magana na gaji da matsalolin ka,idan cuta tak'i ci tak'i cinyewa ai rai take nema.
Yayi yar dariya"wato laifi tudune...ba nine sama da ke ba?Ko ba aure
tsakaninmu ai bai kamata zan fita kice min"ALLAH raka taki gona ba.Kin San wannan
kalmar ta min ciwo ta kuma bani mamaki wai daga bakin ki tafito?Dan na miki fad'a
akan abinda yake dai-dai?Dama gyara kayanka yana zama sauke muraba Sudaida?
Tasunkwui da kai,itama ta gane tayi kuskure"Yaya D'ansarai...ta kira shi,sai kuma
taja tayi shiru. Yakalle ta"na'am ya aka yine?Da rawar murya tayi furucin kayi
hak'uri na gane kuskure na...Idanun ta yaciko da kwallah.
Tad'ora ha6arta a kafad'arshi ta dama" kayi hak'uri...Na yi Sudaida
ni ai ina son ki a kowani hali da yanayi kece dai kika ce sai kina sona za kimin
girki ko?Tayi shiru cikin alamar kunya.Yakalleta yanzu dan girman ALLAH babu
soyayyata dank'are a taki zuciyar?Tad'an ta6e baki a zuwan furucin shi bai gamshe
taba ko a kwalar rigarta.Tajanye ha6arta tana mishi wani kallo cikin turo baki
gaba,da yanayin shagwa6a ta tambaye shi"me kake cewa?Shima yarama irin kallan data
mishi"a ah bance kome ba.Takyalkyake da dariya. Yawatsa hannaye "magulmaciya kawai
ana so ana kaiwa kasuwa;uhhh yakama ha6a"wato an hak'ura ana shan kukar
k'azama...kafin yak'arasa tarufe mishi baki da tafin hannunta na dama"ai dai na ce
kayi hak'uri...
Yasauke numfashi"ni dake muna san auren nan ba na dole aka mana
ba,fad'uwa ce tazo dai-dai da zama,sai dai fa Sudaida bani da lafiya.Tad'ago tana
kallan shi.Yalangwa6e kai "bakiga yadda na rame bane Zaujatiii... tamishi kallan
tsafff sai taga hakan har a kan fuskar shi, tabud'e idanu cikin tsoro"toh me yake
damun ka!
Kayi rashin lafiya ne ban sani ba lokacin kana makaranta?Yagyad'ai"eh
ai kullum a cikin ciwon nake...Cikin fargaba tasake binshi da kallo"ciwon me?Toh me
yasa baza kaje asibiti ba Yaya Julaibib?Ai ciwon son kine bana ganin likita ba,nayi
fama da kewarki sau shurin masak'i Zaujatiii.. So ba k'arya bane,wani mikine a
zuciya ta"Sudaida ki furta min kina so na,kina k'auna ta, za ki zauna dani,muyi
hak'uri da juna tunda zo mu zauna zo mu sa6ane.
Tajijjiga kai"ni na yadda na amince,ina son ka,ina k'aunar ka akowani
irin hali da yanayi mun zama k'arfe da mayen k'arfe Zaujiii... Yagewayeta da
hannayenshi"hankali na ya kwanta, bani da sauran shakku,ba abinda za kimin yasake
bani tsoro.Tayi murmushi"uh uh fa Yaya D'ansarai karkamin kurifa?Yagirgiza kai"ai
nagane logonki yarinya,ba kuri bane,duk abinda za kiyi a banza wai talaka ya girmi
sarki.Tagyad'a kai"ALLAH dan dai na tuba ne...sukayi dariya zuciyoyin su
fesss...Hummm...Fushin masoya hutuhhh....
Nurse A'isha Muhammad Jibril{Asdilat for real💋} Ubangiji ya kiyaye min ke da
kiyayewar shi,yatsare hanya,yakaiki Nursing School Mak'arfi lafiya. Ubangiji kama
karatun na su albarka.Kasa su amfani kansu su amfanar da d'aukacin al'ummar Manzon
ALLAH,da ita da duk wata Nurse dake fad'in KD garin gwamma da sauraran Jahohin mu
na arewa,dana sauran yan'uwa musulmai na duniya kaafatan👏
Bar ganin ka ta ra...kiyayi me nema.
A sara a kasuwanci jari.
15 Jumaada Thani 1441
9 February 2020
We Ibrahim's Daughters👇
Asdilat KD...2geda with Ra'ibs.
DANGIN NONO WRITERS ASSOCIATION
{Da Inganci Mukayi Fintikau}
Bismillahi wabihi nasta'in
...GWAJIN DAFI💔
Almost true story
Daga alk'alamin🖊
Ya'yan Ibrahim
Saudat A.Baba (Asdilat KD)
Da
Bara'atu Ibrahim (Ra'ibs)
Shafi na ashirin.
Yaciro sakamakon jarabawarta a cikin jaka ya bata tana gani,ta samu
sakomako me kyau credits shida har da lissafi da turanci"toh tunda kince kina so
na,za kicigaba da karatun ki kwanan na.ALLAH da gaske Yaya Julaibib? Yagyad'a kai
Insha-ALLAH.Tak'ank'ame shi tana bashi sumba da godiya...gaskiya na k'ara son ka
ninkin ba ninkin,malala gashin tinkiya.Suka kalli juna suna dariya.
Safiyya ta haifi sankacecen yaron ta me girman ban mamaki.A gidan suka
had'u dukan su suna ta hirar yaushe gamo ta baki da baki duk da kusan koda yaushe
suna had'uwa a Whatsapp. Khausar tasake kallan yaron sannan tayi yar dariya"gaskiya
Yaya Safiyya duk girman cikin nan ki ban zaci d'a d'aya za ki haifo mana ba.
Tagalla mata harara"toh madallah ke idan kin ta shi sai ki haifo yan hud'u.Tagyad'a
kai"za ko kisha mamaki. Zainab takama ha6a"ke Khausar yau she akayi daren da gari
zai waye ne?Yi hak'uri Maman Hanifa.Safiyya tayi murmushin mugunta"ai akan tafe kan
isa Khausar,ALLAH dai yabamu rai da lafiya za kiji jin jikinki,ki kuma gani ganin
idanun ki...
Sai bayan sallar azahar Sudaida tawuce gidan Inna,anan ta tarar da
Nasmat taje gaishe da Inna da bata ji dad'i ba kwanaki biyu da suka wuce.Tazauna
tana tayata ninke kayan wankin Inna suna ta hirar su suna shan dariya, basuji
shigowar shi ba sai ganin shi sukayi tsaye a bakin k'ofar yanad'e hannayen shi a
k'irji"hirar me kuke yi haka ina ta sallama ba wacce tajini bare ta amsa.Nasmat
tace"au yi hak'uri autan Inna bamu ji bane.Yagyad'a kai yana kallan Sudaida"d'an zo
mana.
Tamatsa wajen shi suna k'us k'us k'us d'in su,Sudaida tana kyalkyala
dariyar kalaman daya fad'a mata.Nasmat taja tsaki"ke tunda maganar taku ba tak'are
bace,to nifa tafiya zan yi kina 6ata min lokaci sai kace ba gida d'aya kuka kwana
ba.Yajuya jeki Zaujatiii wannan yar sa'idanu ce.Tad'an d'aga murya"Yaya D'ansarai
karfa kamanta. Idan na manta ki tuna min tawaya kafin in dawo.To adawo lafiya.
Nasmat tabita da kallo"wato ke da D'ansarai abun nema ne yasamu matar
falke ta haifi jaki. Kamar yaya?Tayi mumushi"ke dashi d'in duk kuna matuk'ar
k'aunar junan ku,sai yanzu k'wak'walwata take hasko min wasu yanayi da nake gani a
tattare daku na tsananin kishin juna a kowani hali da yanayi,kishi kuma baya
k'ayatarwa matuk'ar ba soyayya,toh ALLAH ya dauwamar da k'auna har Darul-
karamah(Aljannah) Sudaida tayi lallausan murmushi"ai ba ja kare ya mutu a juji.Ina
son Yaya Julaibib amma halin miskilancin shi wasu lokutan yana bani haushi.Nasmat
ta kyalkyale da dariya"miskili ka fi mahaukaci ban haushi.Abdul yashigo da rake
ferarre,atile,yalon Bello da d'anbagalaje yakaima Inna a D'akin-girki wai inji
Kawu,tana dubawa tamik'a mishi ledar "wannan dai Sudaida zaka kaima,maza tana
D'akin-shak'atawa.
Nasmat ta tafi,amma ita har dare tana gidan.Bayan sallar Isha'i Alhaji
Abdullahi yashigo. Tamik'e da sauri takar6i kayan hannunshi tana mishi sannu da
zuwa,yasa6a babbar rigarshi fuskar shi cike da fara'a"a ah Sudaidan Malam D'ansarai
ce?Ta sunkwui da kai.To sannu da zuwa,yashiga D'akin-shak'atawa ita kuma takai
kayan D'akin-girki sannan taje ta gaisheshi cikin ladabi."Lafiya lau,kunanan lafiya
ko?Tad'anyi murmushi tana murza zoben hannunta,itafa har yanzu nauyin Baba take ji
tunda akayi auren nan. Yacigaba,
"ALLAH yamuku albarka,ayita hak'uri rayuwar duniyar ma gaba d'ayan ta
hak'uri ce,idan akayi hak'uri da yawa aka jajirce, agaba sai kiga anyi nasara a
koma menene.Yasa hannu a aljihun rigarshi yar ciki yad'ibo kud'i yan d'ari biyar
dabai san ko nawa bane yabata.Tasake sunkwui da kai "Baba kabarshi nagode.Yakad'a
kai"Sudaida kinga...tad'an d'ago takalleshi"ai ba wanda yake k'in alheri sai
shaid'an, ke ai ya tace,a kowani lokaci naga dama zan iya miki kyauta ko da baki zo
ba,to zan iya aika miki dashi har gidanki.Tasa hannu biyu takar6a"nagode Baba ALLAH
yak'ara girma.Amin Sudaida. Yamik'e yatafi d'akinshi.
Har tafara bacci a gadon Inna yashigo gidan.Baba yarufe shi da
fad'a"kai Malam D'ansarai ban sanka da yawo kamar wanda yaci k'afar kare ba ko da
daba ka da Iyali bare yanzu, ina katafi ina ta kiran layinka bata shiga?Ya amsa da
ladabi"amin afuwa Baba,wallahi Gidan-Waya natafi game da karatun Sudaida,sai kuma
nayi rashin sa a sai mako me zuwa,ni kuma ba na nan, kuma na tsaya ganin Provost
d'in makarantar ne. Wayata kuma mutuwa tayi saboda rashin caji. Yagyad'a kai"to
ALLAH yataimaka,amma maganar karatunta ai ba damuwa ko da baka nan,zan sa Aminu
yayi kome.Yakalle shi kwanaki nawa za kayi kadawo?Baba nima ban sani ba sai dai
kawai anganni.
Yanunashi da yaysa"to kadinga kiyayewa da da da yanzu bambancinsu na da
yawa,bazan ji dad'i ba idan kana tafiya kana share waje kayi zaman ka iyalinka kuma
ko oho ba,a zaman takewar iyali ba abinci da abun sha kad'ai ake buk'ataba a ah har
da kai gundarinka,kuma kullum kadinga tunawa kai shugabane za kuma a tambaye ka
game da hakkin shugabancin da aka baka kana ji ko?Cikin girmamawa ya amsa"eh Baba
nagode ALLAH yak'ara girma.
Inna takalkeshi"kai Julaibib dare na dad'ayi kashiga kaci abinci.To
Inna,yashigo yazauna yana cin abincin,yana kallan labaran k'asa amma rabin
tunaninshi na wajen Sudaida da take bacci,daya gama ci yakai kwanon D'akin-girki
sannan yazo yatashe ta suka wuce na su gidan.
Dasafe Aminu yaje gidan suka tattauna akan karatun Sudaida.Yakar6i
k'ananan hotunan ta, Sudaida tashigo da sallama ta ajiye jug d'in hannunta a gaban
Aminu"dama ina ta sauri dan karka tafi.Yad'ora duka hannayenshi a saman tebur
d'in"ban tafi ba amma ba sha zanyi ba.Tacire murfin"kagani Yaya Aminu kunun tsamiya
ne mutumin ka.Yayi murmushi"toh idan nasha na ki inyi yaya da Innarmu da yake
jirana? Julaibib yace wannan za kasha tunda kullum na Inna kake sha,da rana sai
kasha wancan.Yamik'e kai Malam damun manya ai yafi na yara gard'i kusha
abunku,yabashi hannu sukayi musafaha "ALLAH yakiyaye hanya,sai munyi waya.Julaibib
ya amsa da amin,nagode.
Sudaida Ibrahim Me-Lambu ta fara karatun lissafi da kimiyyar na'ura me
k'wak'walwa (Mathematics/Computer Science)sai dai tana shan zirga-zirga,lallai ilmi
ba a samun shi da sauk'i, sai anyi gwagwarmaya kamar zuma yake ga zak'i ga
d'ankaran harbi.Yau tana gidan Hajiya tana shan rake suna hirar Julaibib da suka
gama magana dashi ta waya,shima yana can yana fafatawa da karatun.
Gajiyace da samun waje wai kuturu da gad'a,bayan ta gama shan raken
bacci yafara kawoma idanun ta ziyara.Hajiya tatashe ta,tamik'e zaune tana
mitstsik'e idanu"Hajiya lafiya?Tagyad'a kai"lafiya k'alau,kishiga d'aki ki kwanta a
gado mana.Takalli agogon dayake d'aure a hannunta nadama tad'an yi tsaki"lokaci ya
ja sosai,sai tamik'e tanasa hijab,tad'auki jakarta tara taya "Hajiya gwamma in tafi
gida yamma tayi sosai. Hajiya tace shikenan sauka lafiya,sukayi sallama tatafi.
Bayan sallar Isha'i tana zaune tana nazarin littafan data barbaza
akan daddumar datayi sallah, hankalinta yayi nisa akan karatun kamar a sama taji an
maida k'ofar D'akin-shak'atawa an rufe,ba tare dataji motsin shigowa ba,tamik'e
dasauri kamar za ta hantsila littafin hannunta yafad'i k'asa,tarintse idanun ta
tana Istirja'i zuciyarta tana bugawa da k'arfi saboda tsoro, d'akin yayi tsit ba
motsin kome sai karar agogon bango tik tik tik...Tasake kasa kunne,nan ma shiru
bataji kome ba,sai tabud'e idanun ta wato kawai tsorata tayi?Takad'a kai"wallahi
mutum rahama ne,yanzu ma dan dare yayi ne amma da gidan Inna za ta tafi,ALLAH
yakaimu gobe na daina kwana ni kad'ai.Caraf idanun su yahad'u,yana tsaye nad'e da
hannayenshi a k'irji, kafad'ar shi tadama rataye da jakar matafiya ruwan toka,yayi
sharrr...dashi cikin farin yadi da farar hula zita.Tanunashi da yatsa"Yaya
D'ansarai kaine da gaske ko kuma gizo ne?Yak'arasa kujera yazauna "matsoraciya
kawai,to da gaske ni d'inne.
Tasauke numfashi"wai ALLAH to sannu da zuwa,sai kuma tad'an turo baki
gaba"amma gaskiya ka tsora tani,kuma d'azu munyi waya amma baka fad'amin yau zaka
dawo ba?Nasamu sarari ne shi yasa nace yau kome dare sai nazo na ga
Zaujatiii...Takawo mishi ruwa da lemu,yad'auki ruwan yanasha yana mata kallan
nazari ta dad'a ramewa.Ya ajiye kofin yarik'ota"Zaujatiii...me yake damun kine?
Tad'ago kai takalleshi kamar bata ji ba"na'am me kace?Sai kuma tagirgiza kai"ni ba
abinda yake damuna,tamik'e barin maka abinci me sauk'i ko yar dafadukar taliyace...
yabita da kallo bawai jikin na ta yake k'arema kallo ba,a ah tunanin irin ramar
datayi kawai yakeyi,kuma acewarta wai ba kome?
Yatashi yabita"ni fa bazanci wata taliya da daddaren nan ba gaskiya.To me
zaka ci? Yakar6i albasar da take 6arewa ya mayar ma'ajiyarta"dafamin shayi
kawai.Tayamutsa fuska "shayi dai shayi dai?Taturo baki gaba"nima gaskiya baza ka
sha wani bak'in ruwa da daddaren nan ba,kai baka gajiya da shayi kamar wani d'an
Niger?Yayi yar dariya"bari sujiki ba ruwa na,ke dan baki san sirrin da yake cikin
wannan shayin nasu bane da neman shi zaki dingayi ruwa a jallo.
Takyalkyale da dariya"ALLAH yasauwake in nemi shayin da ba madara.Hum
yarinya baki san amfanin wad'annan ganyayyakin bane. Takalleshi"toh meye amfanin
su?Yagirgiza kai"zan fad'a miki amma ba yanzu ba.Sai yaushe?Sai lokacin dana koya
miki sha,idan nafad'a miki amfanin nasu zaki yadda dani d'ari bisa d'ari dan kinji
a jikinki,amma yanzu idan nafad'a miki,ba lallai ne kiyadda ba"gani ya kori
ji.Tashagwa6e ni dai tunda baza kaci taliya ba to kaima baka shan shayin sai dai
muje kaci donut da yoghort.Yarik'o hannunta"na yadda muje.
Dasafe tafito tsab cikin shigar kamala da mutunta kai"Tazauna a hannun
kujerar da yake"Yaya D'ansarai taso ka kaini na kusa makara.Batare daya d'ago
yakalle taba yanuna mata abinci"zauna ki karya kafin in gama abinda nake yi asibiti
zamuje a miki General-check up. Tabishi da kallo cikin mad'aukakin mamaki"asibiti
kuma? Tagirgiza kai ni dai gaskiya lafiya ta k'alau ba abinda yake damuna.Yad'ago
yakalleta a gajerce yacigaba da danna na'ura me k'wak'walwa"kizauna kici abinci
nace ko?
Ni fa banajin yunwa kuma ai...sai yad'aga mata hannu ya isa.Duk sukayi
shiru nawucewar wasu dak'ik'u,tasake kallanshi"Yaya D'ansarai zan makara fa.Yayi
kamar baiji abinda take fad'a ba.Haushi yakamata tamik'e tsaye"ni na tafi.Nan ma
shiru yayi.Tajuya tayi tafiyarta tana surutai"da baka sa min rai ba da tuntuni
banyi tafiya taba?Dama ai na saba tafiya ni kad'ai, ALLAH yasauwak'e maka wannan
halin.
Da yamma tadawo daga makaranta a gajiye,ba abinda take buk'atar yi sai
bacci danko jiya ba wani baccin kirki tayi ba Julaibib ya hanata sakattt...Tana
shawo kwanar gidan su tahango wata mota me d'aukar hankali fara karrr...sai d'aukar
idanu takeyi a cikin hasken rana,wata kyakkyawar macece me garin jiki wankan
tarwad'a tabud'e motar tafito tanama Sudaida sallama. Sudaida ta amsa sannan suka
gaisa a takaice... tacigaba da tafiyarta,matar tace"Dan ALLAH jimana "tajuyo tad'an
kalleta sai ta matsa kusa da ita,matar tagyara farin medicated glass d'in data rufe
idanun ta. Takalleta sama da k'asa wani murmushi yasu6uce mata,tanunata da yatsa
"Sudaida ko?Sudaida tad'ago suka kalli juna,sai ta gyad'a kai kawai dan bata san a
ina matar tasanta har tasan sunan taba.
Toh kiyi hak'uri na tsayar dake ba tare da kin san koni wacece ba,ina
fata mijinki D'ansarai yafad'a miki zuwa na?Tak'ara kallan matar"wallahi ba k'arya
hutu ya gama ratsata,ido ba muduba amma ai yasan kima,kayan jikinta na alfarma,a
inda Sudaida taji dama-dama wai kibiya a cikin idanu shine shigar sanin darajar kai
tayi harda hijab d'inta tsawonshi yawuce gwiwa da kad'an,tarasa amsar da zata bata
tunda Julaibib bai mata maganar wata za tazoba gaskiya,sai tayi murmushi tana
gyad'a kai"sannu da zuwa,toh bismillah "suka jera suna tafiya har tabud'e D'akin-
shak'awa tanuna mata wajen zama taje takawo mata abin motsa baki suka sake gaisawa
sannan tamik'e"bari a mishi magana.
Suka kalli juna yana mata wannan rikitaccen kallan nashi da bata so
dan haushi yake bata,yafito daga wanka yana shafa mai.Yaya Julaibib wani irin mutum
ne me tsatstsauran ra'ayi da baza ka ta6a gane inda yadosa kai tsaye ba a wasu
lokutan."kayi bak'uwa. Fuskarshi ba walwala "wacece ita da baki san sunan taba?
Tajuya"oho nima a ina nasan ta,kafito ka ganta mana ganin idanun ka.Sai da yagama
shiryawa sannan yafito, yana ganinta yasaki fuskar shi yana mata barka da zuwa,
yazauna suna gaisawa da tambayar me jiki."jiki Alhamdulillahi.Ni da Baban Humaima
ne yana mota. Yafita yashigo dashi..
"Doctor Garga Ibrahim Manogi "babban likitane da ake ji dashi a Teaching
Hospital na Zaria,k'wararre ne akan abinda yashafi k'wak'walwa(Neurology) likitan
da akace sune ma idan sunje Shika lokacin da Bilkisu tayi hatsari, shine yake auren
kanwar Innar Bilkisu.
Sudaida takawo musu abinci.Doctor Manogi yanaci yad'ago yana
kallansu"gaskiyar magana abincin nan yayi d'an karen d'and'anon daya burgeni,kai
Ustazu haka yake kiran Julaibib dole za kayi tumbi kwanan nan,yakalli Sudaida"kin
gane ko idan ya6ata miki rai karki hana shi kome da yake so sai wannan Palatable
girkin na ki tunda shi baya san cin abincin waje kinga ai kin horashi duk da ya iya
dafawa amma dai kafin yadafa ai ya d'and'ana ko?Sukayi dariya.Doctor Manogi haka
ALLAH yayi shi da sauk'in hali da raha sai yanayin shi yamata shige dana Yaya
Aminu.Yakalli matar shi"Bongel Ustazu da matar shi basu burge kiba?Tayi
murmushi"sun burgeni musamman ita, kaga bata sanni ba amma har tabarni nashigo mata
gida duk da taji na ambaci sunan mijin ta,ka san wasu matan da kishin rashin
hankali. Yad'an harareta"toh waya fad'a miki bata kishin shi? Kawai ta hak'urane
dan ta san itace kad'ai a zuciyar shi, kin san jiya muna tare dashi bayan sallar
magriba sai kawai yace min wai gida za shi,nayi-nayi dashi yabari yau mu bugo
sammako amma yanok'e"wai ai yau d'in da sassafe zai dawo,amma kinga d'an rainin
hankali gashi nan a zaune har bayan la'asar.Julaibib yasa hannu yana shafa
kwantaccen bak'in gashin kanshi yana murmushi.
Bongel tad'an kalli Julaibib"ina son ganin Adnan Ibrahim Me-Lambu inji
abinda yahana shi dawowa makaranta yayi B.ed d'in shi. Ai Adnan ya san dad'in kud'i
ya zama d'an kasuwa kwanaki na mishi magana yace wai shi bazai iyaba wanda yayi
abaya ALLAH amfana.Tace kash...na mishi sha'awar karatun saboda yaron yanada
k'ok'ari yana d'aya daga cikin d'alibaina yan gaban goshi. Da muna magana ta waya
daga baya na daina samun shi. Eh wayar tashice tafad'i yanzu wani sabon layine
dashi.Ai ko zaka bani zamu muyi magana...
Sai yanzu Sudaida ta fahimci wacece ita.Bongel Lecturer ce,yaren turanci
(English) take koyarwa a FCE Zaria,lokacin da Adnan yake karatu tasha jin sunan
Malama Bongel a bakinshi da irin kirkinta,da taimakonta ga d'alibai,bata san
d'alibai wad'anda basu da himma,tafi matsa ma irinsu da yawan tambayoyi dan zaburar
dasu, masu san karatun suna zage dantse ko dan kar susha kunya a gaban d'umbun
jama'a yan uwanshi d'alibai,yan abi yarima asha kid'a,yan kyalekyale suna adawa da
irin halaiyarta musamman na zuwa musu aji a bazata ta na musu jarabawar gwaji,irin
su Adnan a lokacin sune yan gaba gaba,baya yadda yarasa laccanta sai da dalili me
k'arfi.Malama Bongel ALLAH yabata k'warewa da juriyar koyarwa,ga kuma ilmin tsurar
shi Ubangiji me kyauta da k'ari ya ba ta,babban kuma abinda yak'ara mata farin jini
shine bata kada d'alibai a jarabawarta (carry over)
Sunyi sabo da Adnan,saboda wani ciwo da yayi taje gaishe shi anan
take tambayar shi d'an wani gari ne?Yafad'a mata Zonkwa,tayi murmushi kace kai d'an
gidane,shikenan dazarar anyi hutu zata ba shi sak'o yakaima Innar Bilkisu a garin
Matsirga,kanwartace uwa d'aya uba d'aya.A wasu lokutan ma takan ai ko shi takanas
da kud'in mota yakai mata sak'o yakoma Zari'a a ranar. Malama Bongel tana da
sauk'in kai,ba ta d'agawa da ilmin da take dashi,sai dai tana fama da ciwon
idanu,tasha wahala dan akwai lokacin data ajiye aikin koyarwa saboda kome sai da
lafiya akeyi, cutar glaucoma tayi mugun kamata,sai da suka tashi tsaye sannan
tasamu lafiya,suka kuma ba ta medicated glass da take amfani dashi.
Sudaida tasake kallanta cikin zancen zuci"kowani d'an Adam tara yake bai
cika goma ba,kowa da irin tashi matsalar.Wato wannan zuwan kuma Innarsu Bilkisu ce
ba ta da lafiya kenan,dan dasafe taji Julaibib yana tambayar mai jiki tawaya
lokacin datake shiryawa,sai dai bata tambayeshi waye ba lafiya ba,shima bai fad'a
mata ba,dan idan bai ga damaba ko ta tambaye shi,shiru zai mata kamar baiji ba.
Shi kuma Julaibib sun had'u da Doctor Manogi ne a wani taran MSSN da
akayi a jahar Taraba,sun fito sallah dan Julaibib shi yamusu limanci,suna yar hira
yake tambayar shi shi d'an wani gari ne?Yafad'a mishi Zonkwa amma a Zari'a yake
zama a halin yanzu dan shi d'alibine a jami'ar Ahmadu Bello.Doctor Manogi yanuna
shi da yatsa"kar dai kai ne D'ansarai sarauyin wata Bilkisu data rasu?Yajijjiga
kai"eh ni ne.Yace ALLAHU-AKBAR yamishi ta'aziyya sannan shima yamishi bayanin ko
shi waye...daga nan hira ta 6alle har suka dawo Zari'a suka cigaba da mutunci da
zumunci.
Sunyi hira sosai sannan suka shirin tafiya, Bongel tadafa kafad'ar
Sudaida"naji kin fara karatu me tsada na masu k'wak'walwa,toh ina tayaki murna.Ki
zage dantse kiyi ilmi kema kiba al'umma gudummawa da d'an abinda ALLAH
yabaki,musulmin kwarai shine wanda zai amfanar da yan uwan shi da alherin
shi.Sudaida kinyi sa ar kama zuciyar D'ansarai dan ba shi da wata magana sai
taki,dan ALLAH kiyi hak'uri da shi, shima dole yayi hak'uri dake,zo mu zauna zo
musa6ane,ALLAH yabaku zuri'a masu albarka. Sudaida tasunkwui da kai bata amsa ba
tana d'an murmushi,ta bata wasu biscuit da alewa"gashi aba su Humaima"Bongel
takar6a tana godiya"su Humaima sun gode.Doctor Manogi yamik'e yana kallan
Julaibib"zaka d'auko jakar taka mutafine? Yayi yar dariya yana sosa k'asumbar
shi"sai ranar jumma'a Insha-ALLAH. Yagyad'a kai'ALLAH ya kaimu,toh madam mu zamu
wuce.Yaciro rafar kud'i yan ashirin guda d'aya ya ajiye mata a saman tebur,tamishi
godiya.Sukayi sallama Julaibib yatafi rakasu.
Bayan sallar Isha'i yashigo ta mishi sannu da zuwa.Ya amsa da yauwa
fuskar shi ba walwala takalleshi na wasu dak'ik'u"Yaya Julaibib za muyi bak'i amma
shine baka fad'a min ba?Yayi kamar ba dashi take magana ba.Haushi yakamata. Yaciro
wayar shi a aljihu sai ta fizge. Yad'ago yana mata wannan kallan da yake bata
haushi,bai yi magana ba sai hannunshi daya mik'a mata alamar tabashi wayar,itama
tayi kamar bataga abinda yayi ba"me yafaru ne ina maka magana kayi shiru?Oh baki ma
san abinda yafaru ba ko?Tagyad'a kai"ALLAH ban sani ba.Yayi shiru kamar bazai yi
magana ba zuwa can kuma yace"Da safe bana ce miki asibiti zamu tafi ba amma ki kayi
tafiyarki makaranta saboda kin raina ni ko?
Tawani marairai"dan ALLAH kayi hak'uri, to amma Yaya Julaibib ni fa lafiya
ta k'alau.To ramar me kike yine?Tashafa wuyanta"oh ni Sudaida kowa haka yake fad'a
ni kuma ban gani ba.Yad'an harare ta"ni ai nagani bakya san abinci ne ai da safen
ma bakici abincin ba kika tafi, yanuna mata ledar da yashigo da ita,tamik'e
tad'auko faranti a D'akin-girki tajuye mishi balangun me koren
tattasai,albasa,kabeji da cucumber ga yajin tafarnuwa,ta tura mishi gaban shi"ai na
kine zauna ki cinye shi.Yaba kyauta tukwuici"sai ta mishi godiya dafatar k'arin
bud'i amma har ga ALLAH ita ba ta wani jin balangu, yanka biyu taci,ta d'auki
rakenta tafara sha.Shi kuma yana dad'a fad'a mata lallai ta dinga cin abinci kar
cutar gyanbon ciki(ulcer)takama ta. Yaya D'ansarai ba fa rashin cin abinci yake
kawo cutar gyambon ciki ba.Yabar rubutun da zai yi yakalleta"to me yake kawo shi?
Ta6alli rake ta taune ta zuke ruwan tazubar da 6awon sannnan tace"rashin cin abinci
akan ka'ida shi yake haifar da cutar gyambon ciki.Kamar yaya bangane ba.
Yanzu misali ka saba cin abincin safe k"arfe takwas kullum haka kake
yi sai kuma kazo ka daina ci a dai-dai lokacin...toh shi ruwan matsarmama da yake
d'iga ya narkar da abincin shima ya saba saukowa ya d'iga karfe takwas to kullum
haka zai dinga d'iga ko kaci abinci ko bakaci abinci ba,idan akai rashin sa a
bakaci a dai-dai lokacin ba to sai yad'iga a cikin cikinka shikenan wajen ya zama
ciwo...ciwon da mutum zai zo yashiga wani mawuyacin hali na ni ya su.. Yakalle ta
cikin natsuwa"ahab ba cinyaba k'afar baya...
Ni dai na fada'a miki ki dinga cin abinci"toh Yaya D'ansarai
nahhh...tayi furucin da wani salo na yanga da shagwa6a.Suka kalli juna sukayi
murmushi,bata gama shan raken ba ta ajiye dan yau tayi d'amarar hana karatun daren
nan,shi dai kullum cikin bincike da nazari,a makaranta karatu a gida karatu?Rai ai
dangin goro ne yana buk'atar ban iska...batayi magana ba kawai zama tayi a gefenshi
ta gewayeshi,a hankali tafara mishi wani salo...salon daya tilas tashi ajiye
littafin nazarin yafara bin yarima dan su sha kid'a.
Hantsi yadubi ludayi na alhamis bataje makaranta dan basu da
lacca,tana kwance a doguwar kujera Hajiya tashigo da sallama, tamik'e zaune"lale
marhabun Hajiyar mu,sannu da zuwa.Tasa hannu tad'auki ledar da Hajiya tad'ora a
saman tebur"me nasamu haka? Tabud'e talek'a sai tasa hannu tad'auki guda d'aya
awarar madarar shanu ce,tagutsira sannan takalli Hajiya "nagode ALLAH amfana.
Tanaci suna hira,Hajiya kuma tana ta kallanta cikin nazari dan yar
shimice ruwan madara ajikinta,ta yi kyau sosai amma ta rame"ni wai ramar nan dakike
dad'ayi to ko dai ciki ne dake?Sudaida takama ha6a"wuuu..ciki?Tad'an ta6e baki"uhun
rufani ki saya.Hajiya takad'a kai"eh lallai ba shakka k'uruci dangin hauka,cikin ne
kike neman tsari dashi?Ke ba a haihuwar aka haifoki? Ya'ya da kike ganin su ai
rahamane jin dad'in rayuwa ne,su Khausar ba gashi har sun fara zuwa asibiti awon
cikin ba.Tamaida bayanta jikin kujerar tana cin awararta"hu'un to ni dai Hajiya
bani da wani ciki.Ai ban musaba"ALLAH na tuba shi ciki ai d'an dumane a hankali
yake yad'o.
Julaibib yashigo da sallama yazauna a d'aya kujerar suna fuskantar
juna da Hajiya"Hajiyarmu kin shigo?Ta amsa da eh Julaibibi.Yakalli Sudaida"lallai
yarinyar nan,wasa tare ci bamban ko?Zanga me siyo miki rake anjima.Tad'auki ledar
ta zauna a k'asa kusa da k'afafunshi"duba kagani,kaifa kake fad'in awarar madara
bata dameka ba.Yad'auki guda d'aya"ai ba cewa nayi kwata-kwata bana ci ba.Tamishi
wani kallo a marairaice"to afwan Zaujiii...yayi murmushi koma dai toshiyar baki
kika bani yau dai baza ki sha rake ba,kema muk'amuk'inki su huta.Haba
Zaujiii...kaima kasan"I can't do without sugarcane" tayi furucin da salon
shagwa6a.Yamata wani kallo "au bama ni ba?Tasake wani narkewa"na rantse da girman
ALLAH har da kai Yaya D'ansarai nahhh...Hajiya tagalla musu harara"oh Ya'yan
zamani.Sudaida takalleta"da mukayi me kuma? Hajiya wai kin manta gidan amare kika
zone?Hala kin manta hud'ubar dakika dinga manane a gidanki?
Takalleshi"Yaya D'ansarai kome tace mu muku indai bai sha6ama shari'a
ba,ko menene shi bata togance ko abu d'aya ba.Hajiya tayunk'ura tamik'e"toh barin
barku kuci karen ku ba babbaka.Shima yamik'e"Hajiya kiyi zaman ki,ni dama wayata
dana sa a caji nashigo d'auka. Yacireta dan ta cika.Tagyara zaman hijab d'in ta"ai
ba ganin ka yasani tafiya ba dama nayi niyya ne. Yasa wayar a aljihu"ALLAH huta
gajiya Hajiyarmu sai nazo.Inji Sudaida.Tagyad'a kai"sai na ganki. Suka fita da
Julaibib.
Bai dawo gidan ba sai da yamma tana D'akin-girki yamik'a mata raken"karki
isheni da mita anjima.Tasa hannu biyu takar6a"shukran jazilan Ustazu. Yakalleta da
sauri"au har dake? Yagyad'a kai tana yar dariya"har dani.Toh bar d'aura girkin nan
kizo muje unguwa.Yaya Julaibib da wannan yammacin?Yad'aure fuska"ko da sulusin dare
ne bazaki bane?Ta tsame hannunta daga cikin kayan miyar da take gyarawa"ALLAH
yabaka hak'uri"ya amsa da amin.Kiyi sauri ki shirya ina jiranki a waje.Tabi
bayanshi da kallo "zuciyar ta na raya mata wasu al'amura game dashi, takad'a
kai"ALLAH yakyauta maka wannan halin wallahi.
Yana kallanta tafito amma sai da wasu dak'ik'u suka wuce sannan
yabud'e mata motar tashiga tazauna tana d'aura belt.Ganin sun bar cikin gari yasa
ta tambayeshi inda za su,amma yayi kamar bai ji taba.Itama sai taja bakin ta ta
d'inke,tamaida bayanta jikin kujerar tare da lumshe idanun ta,tana sauraran wa'azin
daya kunna na Ahmad Ibrahim(Bamba)sai da yatsai da motar sannan tabud'e idanun ta
tana kallan wajen,nan kuma ina ne?Ta tambayi kanta"fito muje mana..taji maganar shi
a sama,tafito suka jera zuwa gidan.
Inna tayi murna da ganin su kwarai, irin kambamawar data musu yasa jikin
Sudaida yayi sanyi, wato su wasu irin mutane ne masu karamci da girmama d'an
Adam,suna da shiga ran da ciresu a sararin zuciya bazai zama abu me sauk'i ba wai
cire wando taka,shi yasa Julaibib yakasa mantawa dasu duk da babu wacce tazama
sanadin had'uwar ta su a doron duniya.Inna tad'an kalli Julaibib"ai munyi waya da
Bongel take fad'amin gobe zaka koma lallai abaka madara katafi musu da ita wai
wanda suka tafi da ita sun tsaya a Gama-gira wajen wata k'awarta shine tabata
duka,dama Maude nake sauraron shigowar shi in bashi yakawo maka ikon ALLAH kuma sai
ga Ku.Ya amsa da ladabi"eh Inna nima ta kirani ta fad'a min,sammako zanyi a goben
shi yasa nace barin zo in k'ar6a daga nan kuma Sudaida ta gaishe ki.Ai kuwa naji
dad'i ALLAH yamuku albarka.Suka sake sabuwar gaisuwa da Sudaida tamata sannu da
jiki.Jiki ai Alhamdulillahi naji sauk'i sosai.
Da zasu tafi Sudaida tace gashi ni dai nazo banga Bello ba.Inna
tad'anyi murmushi"ai da ya san da zuwanki da bazai raka Malam Zango ba.To agaishe
shi. Zai ji.Julaibib yamata alheri me yawa,ada tana damuwa da irin hidimar da yake
musu har tazo ta daina,tun ranar daya kalleta cikin natsuwa da girmamawa"Inna ki
d'auke ni matsayin d'a,idan kika d'auke ni a haka toh na san duk abinda zan baki
zaki kar6ane da dad'in rai kina kuma shimin albarka tare da min addu'ar dacewa a
doron duniya da lahira.
Megado ita tahad'a mu,koda ba ta, bazamu rabu ba dan kuma baku k'ini
ba.Inna tajijjiga kai tasa gefen hijab d'in ta tana share kwallah"gaskiya ne d'an
nan,toh ALLAH yamaka albarka,ALLAH yabaka zuri'a d'ayyiba,ALLAH yasaka maka da
mafificin sakamakon shi, yasa hakan a mizanin kyawawan ayyukanka.Yanzuma irin
addu'o'in data dinga musu kenan shi da Sudaida.Suna ta amsawa da amin,amin.
Gidansu Sudaida suka wuce...Sauran k'anninta suka dinga murnar
ganinta,itama taji dad'i sosai dan basa wani zuwa gidan ta,to yaushe ma suke da
lokacin yawo?Daga andawo makarantar boko za a tafi ta allo,ko ta Islamiyya da
daddarene kawai suke da lokacin kansu,idan ma ranar ba a had'o mutum da aikin gida
ba (home work)Tasaki hannnunsu,taje ta rungume Mama kawai sai tasa
kuka,Umma,Julaibib dasu Asma'u suka bita da kallan mamaki yanzun nan fa tagama
kyalkyala dariyar shirmen gwarancin da Nana take mata...
Mama tace ashsha"to me yayi zafi haka da idanu za suci wuta?Tana
k'ok'arin d'ago ta Sudaida tadad'a k'ank'ameta.Umma ta fusata"ke menene haka yau
naji shashanci rok'o a gidan bebe.Mama tad'aga mata hannu"na ki idanu 6arin mai a
yashi.Umma takyalesu suna magana da Julaibib.
Mama tayi k'asa da murya"to d'agani tunda bazaki daina kukan ba.Tayi
shiru tana share hawayen sannan tad'an marairaice "Dan ALLAH har yanzu baki zo na
ganki ba,ai dama na san ke kad'aice za ki zo,ko Umma ce tazuga ki?Mama tayi
murmushi"au dalilin kukan kenan?Eh mana Mama.To karki damu inanan zuwa ni ba wacce
ta isa ta hanani zuwa inda kike.Yauwa Mama ALLAH yabar mana ke,suna ta hira sai da
Baba yafito yace su tafi gida haka dare yayi gashi sammako Julaibib zai yi.Sudaida
tabi Umma d'aki tafito daga bayi alwala tayi tanasa hijab Sudaida tashigo.Suka
kalli juna sai Umma tad'anyi murmushi"za ku tafi ne?Ta amsa cikin ladabi"eh
Umma.Kun san Umma Boss ce bata d'aukar raini.Tabata wasu humrah masu k'amshin fita
hayyaci"gashi nan dama ke kad'aice ba a kai miki ba.Tasa hannu biyu takar6a tana
godiya. Umma to yaushe za kizo? Ke! Umma tafad'a cikin d'an bud'e idanu.Sudaida
tasunkwui da kai.Sai kuma ta sassauta murya"Sudaida me zanzo in miki ne?Duk abinda
kike so kima Mama waya ko ni,ko ki turo mana ta sak'o a rubuce ba shikenan ba?A
sanyaye tagyad'a kai sannan sukayi sallama.
Tafiyar Julaibib da yammacin ranar tadawo makaranta tana so tayi girki
tatafi gidan Inna sai ga Asma'u tashigo.Tataro ta cikin murna 'oyoyo Yaya Asma'u
sannu da zuwa.Ta amsa da yauwa tashige D'akin-shak'atawa,ganin haka yasa Sudaida
tayi sauri tagama markad'a kayan miya taje suka gaisa,kamar kullum yau ma haka ta
amsa gaisuwar cikin halin-ko-inkula tun bayan auren ta da Julaibib Asma'u take mata
wani gani-gani data kasa gane manufarta.Tabi d'akin da kallo sannan ta sauke idanun
ta akan Sudaida, tana sanye da riga da zani da dankwali na kamfala, ta ta6e
baki"ina D'ansarai?Baya nan yatafi.Yatafi fa kikace?Tajijjiga kai"eh ya tafi.Toh
yayi kyau... bani sak'ona sauri nake yi.Sudaida tagirgiza kai "bai bani kome in
ajiye miki ba.Bata sake magana ba wayar ta taciro ta kirashi.Yana d'agawa ko
sallamar daya mata bata amsaba tafara hayagaga...
kai D'ansarai haka mukayi dakai? Tayi shiru tana sauraranshi...wucewar
wasu dak'ik'u sai kawai taja dogon tsaki"kai malami wallahi daga bayane sadaka da
karuwa...eh to naji sai ta mik'a ma Sudaida wayar "Zaujatiii... kud'in dana baki
kin kai gidan kud'in ne?(bank)A ah sai gobe Litini...Yauwa toh kiba Yaya Asma'u
dubu goma a ciki,ki bar sauran idan nadawo nabaki duka sai ki kai kinji ko?To Yaya
Julaibib, ALLAH yadawo dakai lafiya.Tamik'a mata wayar sannan take ta d'auko takawo
mata,a wulak'ance takar6a kamar wacce aka bata najasa.
Sudaida takawo mata meatpie da lemu dan bata gama abinci ba.Tagirgiza
kai"bani dankalin turawa da kwai zanje in soya a gida, tamik'e bani leda,inda suke
ajiyewa ta nufa, Sudaida tabiyo ta da ledar tana fad'a mata amma fa kwan ya
k'are.Sai tabi d'akin da kallo gwangwanayen madarar Nido tagari guda biyu dana
Ovaltine guda d'aya sai siga me y'aya na kwali(cube sugar)sai tasa hannu ta d'auki
gwangwanin madara d'aya da siga kwali biyu a ranta tana mita"ni nasan D'ansarai
baya shan shayi da madara,yanzu nan ita za taita shansu? To aiko bazata shanyesu
ita kad'aiba dan nima wannan ai yafi min dankalin.Sudaida tabita da kallo itama
tana jiinjina k'arfin hali fin me kora shafawa irin na Yaya Asma'u.Toh sata za a
kira wannan abun kome?Tunda bata tambayi wanda yasiyo ba.
Abinda Yaya Karima bata dashi kenan ganin gari da san na Bello-badin,ko
wajen Inna taje haka take mata d'auki d'ai-d'ai d'in duk wani abu daya bata
sha'awa,abin mamaki kuma Baturiya da suna manga,kamar ba Inna da Baba ne Iyayen
taba dan su sun san mutumci da karamci wallahi.Idan an mata magana ta ta6e baki
tana fad'in to menene a ciki? Sata a gida ai rance ne...bare ita ai bama sata tayi
ba tunda a gaban idanu take d'aukar abu.To amma dai ai ba ace an ba taba kai ALLAH
yasauwake. Takar6i ledar tasa a cikin sannan tajuya"sai anjima.To Yaya Asma'u ki
gaida gida.
Kwana biyar bayan nan da yammacin la'asar tadawo daga makaranta kawai
tawuce gidan Inna. Asma'u tana zaune tana cin dafaffiyar masara takalli Sudaida
sama da k'asa bata amsa gaisuwar da take mataba,sai tambayar ta tayi"hala daga awo
kike? Fuska a d'an yamutse dan tafara gajiya da irin abubuwan da Asma'un take mata
tace"awon me? Asma'u tamata wani kallo me kama da harara "awon me mata suke zuwa yi
a asibiti? Tamotsa kafad'a tare da watsa hannu"oho nima ban sani ba tunda ba ta6a
zuwa nayi ba.Tawuce randar Inna tad'ibo ruwan sanyi,tashiga D'akin-girki tazuba
abinci, tayi bismillah ta faraci.
Inna ta idar da sallar la'asar tajuyo tana shima Sudaida albarka"kin
kyauta dakika bata wannan amsar.Ke Asma'u tanuna ta da yatsa"me yasa kike san zama
babbar kwabo ne?Asma'u tamik'e"to yanzu Inna me nayi?Ni fa dama kullum a gidan nan
a ban iyaba aka d'auke ni.Eh ai halinki yake ja miki.ALLAH yabaki hak'uri Inna ni
tafiya ma zanyi,me zaki bani?Inna ta d'aure fuska"ba abinda zan ba ki sai dai in
omon wanke-wanken da kika kawo min za ki koma dashi.Kai Inna haba-haba dai,tashige
d'akin bacci tana fad'in"ni ai na ga abinda nake so,sink'in sabulu da man shafawa
guda d'aya ta d'auko. Inna takalle ta"Asma'u na ba ki ne?Tayi yar dariya tana
turawa a jaka"Inna kayan ALLAH ai na annabine,ba sid'i ba sad'ad'a ma kinyi kyauta
ga wasu bare kuma ni?Tajuya na tafi Inna,idan Baba ya dawo a gaishe shi.Suka bita
da kallo kowacce da abinda zuciyar ta ke rayawa.
Kwanci tashi a sarar me rai...Shekara d'aya da auren su
A'isha,Khausar da Nasmat ne suka fara haihuwa,A'isha da Nasmat rana d'aya,ranar
suna Sudaida tarasa inda za tayi ga makaranta,ana tashi Kafanchan tawuce gidan
A'isha aka sha suna,ba ita taje gidan Nasmat ba sai da akaci aka kusa cinyewa dan
ma na ka na kane...a yadda tagaji lik'is d'in nan,gida za ta tabi lafiyar gado.
Tak'arema jaririyar kallo tad'ago cikin murmushi "ALLAH na rasa da
wanda tayi kama,ranar da aka haife ta sak babanta yau kuma ta canja batayi kama da
ku ba, tamaida ita k'irji ta rungume ta lumshe idanun ta"ina son yarinyar nan ki
bani ita mana.Nasmat tayi murmushi"ai dama ta kice na kuma bar miki.Tabud'e idanun
ta suka kalli juna sukayi dariya.Nasmat ta kalle ta"d'azu dangin mijin ki bakiji
irin habaicin da suke yi ba wai wasu sai dai suci su juye shi a masai,wani abin
mamaki kuma Yaya Asma'u itace shugaba,sai da Hajiya ta musu wankin babban bargo
sannan sukayi shiru.Sudaida ta d'auki kunun aya tana sha"kar ki wani ce abin
mamaki,yau kika san Yaya Asma'u da halinta?A ah ai ni abinda yabani mamakin shin ke
d'in ba matsayin kanwar ta kike ba? Tad'anyi murmushi"da ne nake kanwarta lokacin
ina gidan mu,toh yanzu kuma ai k'aninta nake aure ina zaune a gidan shi,ita kuma
dangin miji ce,wasu dangin mijin kuma ba mutunci suka sani ba.
Asma'un ce tashigo ma da Nasmat farantai takalli Sudaida sama da
k'asa cikin ta6e baki "hamshak'iya,maduga ke sai yanzu kika ga damar zuwa? Komu da
muke tare da Iyali ai hidimar su bata hana mu zuwa anyi kome damu ba,bare kuma ke
da kike zaune ke d'aya ba wata hidima a kanki.Sudaida tayi lallausan murmushi"toh
Yaya Asma'u dan ALLAH ina ruwan maza da wankan jego?Abinda tafad'a mata kenan
tajuya suka cigaba da hirarsu dasu Nasmat.
Ta koma gida tayi wanka tana so tatafi gidan Inna,kiran Julaibib
yashigo tad'aga da sallama"Zaujiii...afwan yanzu nake shirin kiranka "kasha ruwa
lafiya?Yau banyi azumi ba Zaujatiii... bana jin dad'i.Wayyo! Sannu ai naji muryar
ka wata iri,sannu kasha magani sai ka kwanta,dan ALLAH yau dai karka tsaya yin wani
nazarin karatu,lafiya ai tafi kome.Toh nagode,kin tafi gidan Inna ne?A ah sai nayi
sallar Isha'i.Kiyi zamanki ina hanya.ALLAH yatsare, yakawo ka lafiya.Amin,nagode
Zaujatiii...Sai kuma tad'an turo baki kamar yana ganin ta"ni dai ALLAH na tsani
dawowar cikin daren nan.Yayi murmushi"sai nazo kawai.
Jakar Magori take ji a k'aramar rediyo taji kwankwasa k'ofa,talek'a ta
taga sai tagan shi a tsaye. Tabud'e ta k'ar6i jakar shi"sannu da zuwa Yaya Julaibib
ina motar?Bazan iya tuk'i ba shi yasa nashiga tahaya.Har ta ajiye jakar bai shigo
ba tasake fita sai taga a hankali yake tafiya,yashigo D'akin-shak'atawa yazauna
tare da maida kanshi saman kujerar ya rufe idanun shi.Tazauna a hannun
kujerar"sannu...ALLAH yasauwake.Bai amsa ba yamik'e wani jiri yakwashe shi
luuu...sai ya durk'usa a gaban ta,yadafa gwiwoyin ta dan saura k'iris yasha k'asa.
Sannu Yaya Julaibib. Yagyad'a kai ya yamik'e da sauri yafita,tabi bayan shi"Yaya
D'ansarai ina za ka?
Abakin famfo yatsuguna yana amai,itama ta tsuguna tana ta jera mishi sannu,
yagama aman yabud'e famfo yana taro ruwan da tafukan hannayen shi yana wanke kanshi
zuwa fuskar shi.Yad'an kalleta yamik'e dakyar jikinshi a mace kamar yayi awanni
yana aikin dabai huta ba,yasake kallanta...yayi magana amma bataji me yafad'a
ba,tamatsa kusa dashi "me kake fad'a Yaya D'ansarai?Idanun shi sun k'ank'ance, luuu
kawai taga ya tafi zai sha k'asa,a tsorace tarik'o shi wani abu mara dad'i ratsirga
ilahirin gangar jiki da zuciyar ta,nauyin shi ya rinjaye na ta, gaba d'aya sukayi
jikin bango,dakyar yasa hannunshi nadama yadafe bangon, kome yana hautsine
mishi,kanshi na mishi matsanancin ciwo kamar zai rabe gida biyu,cikin dukan zuciya
tafara kiran sunan shi"Yaya D'ansarai... Yaya D'ansarai... zuciyarta tayi rauni
sharrr... sharrr...hawaye suka fara sintiri a fuskarta,jikinta yafara rawa"Yaya
Julaibib ta fara jijjigashi sai tana Istirja'i dan wallahi a tsorace take,tana sake
shi ko shakka babu zai zube mata a wajen,gashi baza ta iya rik'eshi gaba d'aya ba,
k'arfin namiji da mace bambancin a bayyane yake.
Dak'yar tazame suka zauna a k'asa ta jingina bayanta da bango...tazuba
mishi idanu a cikin hasken farin watan tana zancen zuci"gashi bata fito da waya ba
bare takira wani daga cikin Yayyinta su zo su taimaka mata,takai hannu tana d'an
ta6ashi"Yaya D'ansarai kata shi,Yaya D'ansarai dan ALLAH kabud'e idanun ka ka ji?
Bazan iya bane dana kaika d'aki,a hankali yabud'e idanu yad'an kalleta sai kuma
yamayar rufe...Tanata kallanshi tana ayyane-ayyane a zuci tana kukan shar6e,
wucewar wasu dak'ik'u masu yawa sannan taji hucin numfashin shi me zafin gaske
"Sudaida ki daina kuka naji sauk'i.Tahad'iye kukan tana kallan shi ta san fad'a
kawai yayi dan hankalin ta yakwanta amma ko wannan hucin numfashin me zafi ai bana
lafiya bane"Yaya Julaibib to za ka iya tafiya mutafi d'aki?Yagyad'a kai tamik'e
tarik'o hannayenshi duka biyun sannan shima yamik'e suka tafi yakwanta, dan yak'i
cin abincin data kawo mishi,shayin ma bai shaba...
Yi dai-dai dan dai-dai,dai-dai ne ba dan wasu sunyi dai-dai ba.
Facebook:باب.سودة ا
Facebook:Bilkisu Ibrahim Bilkisu Ibrahim
Email:Saudatibrahim333@gmail.com
23 Jumaada Thani 1441
17 February 2020
We Ibrahim's Daughters👇
Asdilat KD...2geda with Ra'ibs.
DANGIN NONO WRITERS ASSOCIATION
{Da Inganci Mukayi Fintinkau}
Bismillahi wabihi nasta'in
...GWAJI DAFI💔
Almost true story
Daga alk'alamin🖊
Ya'yan Ibrahim
Saudat A.Baba ( Aadilat KD)
Da
Bara'atu Ibrahim (Ra'ibs)
Shafi na ashirin da d'aya.
Dasafe yayi wanka yana sanye da yadi ruwan madara mara nauyi,yayi
lamooo a cikin kujera.Tashigo da sallama tabi kayan abincin da kallo yana nan yadda
ta ajiye"Yaya Julaibib har yanzu baka karya ba? Yagyara zama"na d'an sha kunun
gyad'an, ina jin bakina ba d'and'ano ne.Tad'ago tana mishi kallan tuhuma bayan ta
bud'e kofin"na ce bakaji sauk'iba ka ce ba haka ba,yanzu wannan kunnun an sha shi
kenan?Kur6a d'aya kayi ko? Yad'anyi murmushi"afwan Zaujatiii...zan sha anjima.A
hankali yamik'e"barin je gidan Inna ko za kimin rakiya?Uh uh adawo lafiya.ALLAH
yasa.Ta amsa da amin tabi bayanshi da kallo wata irin k'auna da tausayin shi suka
tsirga ilahirin gangar jiki da zuciyarta,bata ta6a ganinshi a irin wannan yanayin
na daren jiya ba.Tasauke gwauran numfashi"Ubangiji yasa kaffarace Yaya D'ansarai
nah... Takoma D'akin-girki tak'arasa ayyukanta sannan taje tayi wanka ta shirya
cikin shigar mutunci da sanin kimar kai kamar ko yaushe tatafi makaranta.
Bayan sallar Isha'i yashigo yana kallanta, itama ta idar da sallah
tana azkar,tagama ta mishi sannu da zuwa zata cire hijab yarik'o ta"bar hijab d'in
ki muje kimin rakiya gidan Hajiya d'azu ban samu na shiga ba, muna ta hidimar
jama'a a shago.Tad'an turo baki gaba"a hakan da ba ka da lafiya me makon kadawo
gida kayi kwanciyar ka,kaima kahuta ma ranka?Ai naji sauk'i. Tazuba mishi idanu
nawasu yan dak'ik'u sannan tace"tun safe har zuwa yanzu me kaci?Na sha shayi a
gidan Inna. Tad'an harareshi"shayi dai shayi dai ai sai kaje kayi ta sha, toh yanzu
ga abincin dare na jiranka muje kaci sai mutafi gidan Hajiyan.Yagirgiza kai"bari mu
dawo sai in ci yanzu banajin yunwa.
Hajiya tana shan dabgen bindin sa suka shigo da sallama.Sudaida tasa
hannu wai wai wai gaskiya matar nan kina sha'aninki wallahi,tagalla mata
harara"kema wa yahanaki na ki sha'anin? Sakarya kanki kawai kika sani,toh maza
d'auki faranti ki zubama mijin naki mana.Yad'aga hannu"a ah barshi kawai Sudaida
bazan iya ciba.Suka zuba mishi idanu"har yanzu jikin ne Julaibibi? Hajiya ta
tambaye shi.A ah naji sauk'i Alhamdulillahi.
Ganin ya sake anata hira yasa suka saki ransu.Hajiya ta ajiye tsinken
data gama sakacen naman daya mak'ale mata a hak'ori"to ko wannan zirga-zirga da
kukeyi ai dole yakarar daku daga kai har matar taka,duk da yanzu na ga tafara
sabawa, tana maida jikinta a hankali.Yad'anyi murmushi yana kallan Sudaida"ai
Insha-ALLAH zirga-zirgan zai ragu dan an d'aukeni koyarwa a Gidan-Waya, farkon wata
me kamawa zan fara zuwa.Hajiya tafad'ad'a murmushinta zuwa dariya"kai Masha-
ALLAH...Wow Congratulations.
Suka kyalkyale da dariya"Hajjaju makkatan ashe dai baki manta karatun
ba?Inji Sudaida.Tamata dakuwa"ungo nan,mu turancin muma gangariya turawa yan
misionaries su suka koya mana baki da baki.Toh Hajiya kingama aji bakwai d'in
danaji ance anayi a zamanin da amma bakiyi aikin gwamnati ba?Oh oh k'arya ciwo aji
hud'u nayi Baba ALLAH yajik'anshi da rahama yamin aure.Sudaida takalleta cikin
natsuwa"toh kema nan kunyi soyayya ke da mijin naki?Hajiya tafara tafa hannaye
cikin salati da sallallami.
Sudaida tad'an yamutsa fuska "daga tambaya sai ki fara salati.Hajiya tajawo carbi
zata shaud'a mata tamik'e dasauri tafita da kwanan da tagama cin dabgen tawanko
hannunta sannan tadawo tana kallan Julaibib daya tsaida gwiwoyinshi yasa duka
hannayen shi ya rungumesu,tazauna kusa dashi tad'an marairaice" Yaya D'ansarai anya
kaji dad'in zaman nan?Yakalleta me kika gani?Kamar kana jin sanyi...Tabbasss sanyin
ne yafara ratsashi amma bai nuna ba,sai yamik'ar da k'afafun na shi yasa hannu yana
shafa kwantaccen bakin gashin kanshi "ba kome fa.Tagyad'a kai.Hajiya kuma tagalla
mata harara "to iyayin yace me?Julaibib yakalli Hajiya "Sudaida fa amaryace kin
kuma san amarya bata laifi,idan kina matsa mata to abu me sauk'i ne tayi yajin zuwa
gidan nan.
Takad'a kai tana yar dariya ALLAH sarki wacece amaryar? A in da ba amarya
dai a kira ta da hakan,to dan ta daina zuwa gidan nan sai me? Sudaida takalle
shi"lallai naji da kunnene dan haka Yaya Julaibib tashi mu kama gabanmu wannan
farin watan sai yamana illah gwamma dake Hajiya auren ki da gata.Hajiya tagyad'a
kai"ba shakka ai wuyanki ya isa yanka.Suka mata sallama tarako su har zaure "ALLAH
yamuku albarka nagode,nagode Ubangiji yabamu alheri, yatashe mu lafiya.Amin Hajiya.
Suka jera suna tafiyarsu a hankali suna hira har suka zo gida.Takawo
mishi abinci yabud'e yana gani tuwon alkama miyar ku6ewa d'anya,yad'an kalleta a
marairaice"Zaujatiii...dare yayi fa...itama ta kalleshi"uhun me yafaru?Yamayar da
murfin miyar ya rufe"bai kamata in ci abinci me nauyi da yawa ba tunda kwanciya zan
yi.Tayi shiru kamar bataji abinda yafad'a ba.Zaujatiii...ba ki jine?Na ji...amma da
kasan baza kaci ba tun farko ai da mun tafima da almajirai suma suci da
d'uminshi,takalleshi cikin kulawa"toh yanzu me za kaci?Yasake wani marairaicewa
yanata kallanta yak'i magana,ta kyalkyale da dariya dan abin dariya yabata"Yaya
D'ansarai wai meye haka kake ta wani kallo na kamar wata bak'uwarka? Me za kacine?
Za ki bani abinda nake so?Tana yar dariya tagayd'a kai"ALLAH zan ba ka.To ni dai
shayi zaki had'a min kuma dan ALLAH kar kimin mugunta kisa min siga,dan haka take
mishi wani lokacin idan ba taso yasha shayin shi kuma ya nace sai yasha.
Angama autan Inna"ke zo nan dawa kikeyi ne? Tashige D'akin-girki da wanda
ya tsargu nake yi.Taje tahad'o kofi biyu tamik'a mishi d'aya ta rik'e d'aya yabita
da kallan k'arin bayani,tagyad'a kai "tayaka shan abinda kake so zanyi ko ban
kyauta bane?Yayi murmushi"kin kyauta mana,tad'ibo donut tabashi amma baici ba haka
yasha na shi,itace dai taci guda d'aya suka gama takai kayan D'akin-girki sukaje
suka wanke baki sannan sukayi shirin bacci.
Cikin sulusin daren yaketa juyi dan ya kasa bacci,yatashi
yazauna,yakoma yakwanta yayi hakan kusan sau biyar,har bacci yafara d'aukeshi
yasake tashi zaune yakama kanshi da duka tafukan hannayenshi abin ba sauk'i wai
ciwon arna,wani zazzafan zazza6i yarufeshi sai kuma sanyi yafara
ratsashi"Sudaida...a hankali yafara kiranta ita kuma baccinta yayi nisa,yakai hannu
yana d'an bubbuga k'afarta Sudaida...kamar a mafarki taji kiran tayi juyi sai
tasake jin kiran tabud'e idanun ta taganshi jingine da gadon yana cigaba da
kiranta,dasauri tamik'e zaune kamar zata hantsila zuciyarta na bugawa da k'arfin
gaske tayi Istirja'i"Yaya Julaibib wai meke faruwane?
Wani irin ciwone haka sai cikin dare? Yadamke hannunta gangam Sudaida
sanyi nake ji rufeni.Tagyad'a kai" tabbasss garin akwai sanyi ga sanyin farin wata
daya haske doron duniya kaafatan, dole mara lafiya yaji sanyi,to amma jikinshi yayi
mugun zafi kuma yana jin sanyi to bai kamata kuma a rufe shi da abu me nauyi ba dan
ba a so zafin yakoma jikinshi.Yana karkarwa yace"Sudaida rufeni sanyi nake
ji,dakyar yayi furucin,tamik'e ta d'auko zanin a tamfa ta rufeshi. Yagirgiza
kai"ban daina jin sanyin ba d'auko bargon mana,ta lalla6ashi yakwanta"yanzu zan
d'auko kaji?Tarik'o hannunshi"kayi hak'uri Yaya D'ansarai tajik'a k'aramin tawul a
ruwa tana fara goge mishi jiki yarik'e tawul d'in tamauuu"kyaleni bana so,kwanta
kiyi baccin ki.Takwanta tanata kallanshi har wani baccin wahala yad'aukeshi dan
daga ganin yanayin fitar numfashin ka san baya jin dad'i.
Yashigo da sallama yazauna a kujera yana kallanta har ta idar da
sallar,ta sunkuyo tana mishi sannu da jiki tana ta6a jikinshi har yanzu da zafi, a
ranta tana yaba k'ok'arinshi dakyar yayi alwala saboda ciwon kan bai sake
shiba,amma a haka yagangand'a yatafi masallaci dan samun jam'in sallar
asubahi"ALLAH gari na dad'a wayewa asibiti zamu tafi,ni ciwo cikin dare tsoro yake
bani.Yayi yar dariya"tsoro kikeji kar in mace miki? Sudaida ai ko da rana idan
lokaci yayi tafiya zan yi. Tamishi wani kallo dayaji tasirin shi har a zuciya"ni
bana san irin wannnan kalaman fa gaskiya,cuta ai ba mutuwa bace, wata kilama ni zan
rigaka macewa,ba dai wanda yasan gawar fari"ALLAH dai yasa mucika da kyau da
imani.Amin Zaujatiii...yazame yakwanta yanata kallanta tana shige da ficenta har
wani bacci yasake awon gaba dashi.
Sai da tagama shiryawa sannan ta tasheshi yaje yayi wanka su tafi
asibiti.Yamaida kanshi saman kujera yana kallanta cikin shigar doguwar rigar atamfa
da dogon hijab me hannu"ba makaranta za ki tafi bane?Can ne amma sai mun gama da
asibiti zan wuce.Yamik'a hannu yakar6i jakarta yasa mata kud'i a ciki yamik'a
mata,tasa hannu biyu takar6a tana godiya "ALLAH yak'aro bud'i Yaya Julaibib.Yayi
murmushi kawai sannan yamik'e muje in taka miki.Takalleshi kayi wanka dai mutafi
ko? A ah naji sauk'i fa ni anjima kad'an ma Kafanchan zan tafi.Takalleshi wani iri
kamar za tayi magana sai kuma tayi shiru.
Yau da wuri tadawo sai kawai tawuce gidan Inna suka sha hirar su
Inna tamusu faten tsaki sai bayan la'asar tamata sallama takoma gida,tana ganin
kiran Julaibib tad'aga a kame sallama kawai tamishi tayi shiru"Zautajiii...kin dawo
daga makaranta ko kina can in biya in d'auko ki.A takaice ta amsa"nadawo.Lafiya
kuwa?Tasake amsawa da"Uh batare data bud'e baki ba.Baki da lafiya ne najiki wata
iri"k'alau nake.Yasauke numfashi"toh shikenan ganinan zuwa.Ta amsa da uhun.
Taje tayi wanka tana zaune a gaban madubi tana kwalliya ya shigo da
sallama ta amsa sallamar tare da mishi sannu da zuwa tacigaba da abinda takeyi bata
wani damu da ganin shiba,yanad'e hannayen shi a k'irji yana k'are mata kallo,yau ta
mishi kyau fiye da kullum,yak'arasa wajen ta da karsashi "Zaujatiii...kinyi kyau
fa.Ganin ya d'okantu da ita yasa tad'an tsuke baki kamar me shirin yin fito,kamar
bataji abinda yafad'a ba tacigaba da shafama la66anta jambaki ruwan hoda.
Sai yad'ora mata ledar raken a jikinta"ga mutumin ki.Tad'anyi tsaki.
Yabita da kallon nazari"tun a waya nakiji wata iri yanzu kuma tsakin me kikeyi
Sudaida?ALLAH dai yasa banine na 6ata miki rai ba.Tad'an harareshi tana
k'unk'uni.Ke karki sani a uku fa kin san ina k'aunarki.Ganin ta mik'e zata bar
d'akin yasa yarik'ota da sauri sannan yakalleta cikin natsuwa"fad'a min laifina zan
baki hak'uri,durk'usama wada ba gajiyawa bane.
Haushin shi yakamata"na rantse maka da girman ALLAH idan bakazo munje
asibiti ba to ko ciwon ka yatashi cikin dare ni karka tasheni ina tsaka dajin
dad'in bacci na eheee,yasan za a rina...wannan fushin,haba-haba dai ke kuwa ya zaki
fad'i haka? Yanzu lalurata ba taki bace?Takwace hannayenta tana turo baki gaba"eh
batawa bace,ta kace kai kad'ai dan haka kaje kaji da ita kai kad'ai tunda na baka
shawara baka jiba...Yayi yar dariya"kinga to kisha kuruminki Sudaidan D'ansarai
yajata suka zauna a kujera sannan yaciro ledar magani da d'an k'aramin katin shi na
ganin likita"duba kigani"daga asibiti nake abinda yasa ban dawo da wuri ba
kenan,likita yamin test,wai typhoid ke damuna ga magungunan daya bani da
allurai"anjima bayan sallar Isha'i za ki rakani allurar,kin san bana son allura
idan nak'i tsayawa sai ki d'an bud'e idanun ki nan da nan sai kiga na tsaya amin ba
tare da ankai ruwa ranaba ko kuwa?Tayi dariya"lallai kuwa wannan shine ta6ara
megida da kukan yunwa.
Tad'auki rakenta tafara sha da bismillah"da fa yau har yajin shan
raken nan zanyi da bakaje asibitin ba.Ke d'in kuwa?Ke mayyar rake ce kuma ban ta6a
k'in siyo miki ba,amma ni idan nace ki had'a min shayi sai kawai ki kama fushi wai
bazan sha bak'in ruwa ba to haka a ke rayuwa?Kowa ba da abinda yafi so ai ko kuwa?
Tajijjiga kai"ka fini gaskiya, toh kayi hak'uri na dai fushi da shan bak'in ruwa...
tawani shagwa6e"nima ai gashinan a hankali na fara koyan sha,shekaran jiya ba tare
muka shaba? Yagyad'a kai"Yau me kike dafa mana be?Tad'an kalleshi"ni fa da bazanyi
wani girki ba,idan zamuje allura muje gidan Inna kaci tuwo ni zan sha Yoghort dan
bana jin yunwa.Yamik'e"to shikenan,yatafi d'auro alwala dan anfara kiraye-kirayen
sallar magriba daga mabambantan masallatan unguwa.
A hankali cigaban rayuwa take zuwa daki-daki har zuwa sanda bawa zai
had'u da aljalinshi,alokacin numfashi da duk wani abinda ALLAH yarubuta zai samu ko
zaiyi a doron duniya ya gamayin shi.Julaibib Abdullahi D'ansarai a yanzu yasake
samun cigaba daga matakin lecturer zuwa senior lecturer.
Yana zaune a D'akin-shak'atawa yana yan rubuce-rubucen shi a na'ura me
kwakwalwa,yayi k'iba yak'ara kyau da wayewa,bak'ar fatarshi tanata shek'i dan ta
jik'e da hutu da kwanciyar hankali,shigarshi kamar kullum ta fararen kaya,hularshi
dara daratsin fari da ruwan k'asa, agefe kuma Ya'yanshine Ya'yan abokinshi
amininshi,kuma d'an'uwan shi Musaddiq suna zaune tankwashe da k'afafunsu cikin
ladabi suna cin abincin rana. Asma'u tayi sallama tashigo. Julaibib yad'ago yana
amsa sallamar yana mata sannu da zuwa,tazauna suka gaisa sannan tabi d'akin da
kallo"ina madugar baza ta fito mu gaisa bane? Yagirgiza kai"Sudaida baza tak'i
fitowa ku gaisa ba matuk'ar tana cikin gidan nan ko da kuwa bata jin dad'ine.Tata6e
baki"haka fa, toh madallah.
Suka cigaba da hirarsu ta zumunci,a hankali har tasako mishi zancen
k'arin aure"Lillahi warasulihi ka dinga zama kenan da mace juya? D'ansarai ai kowa
yana son ganin d'a na kanshi. Yad'anyi murmushi"haihuwa ai d'an lokacine Yaya
Asma'u.Tawatsa hannu" kai tafi can,tunda an maida kai hannun zani dole za ka fad'i
haka mana,ka barta tana ta karatu to yaushe kuwa zata yadda da haihuwa, haihuwa
yaja mata koma baya a wajen karatunta,na sha fad'a maka yarinyar nan tsarin Iyali
takeyi,idan ba haka ba me zaisa har yanzu bata haihuba? Su sauran da akayi bikinsu
rana d'aya ba ga shinan daga me haihuwa biyu sai me uku ba?
Jiya kuma nake jin wani k'arin abin haushin,abin duka ba sanda wai
Gidan-Waya sun fara degree program dan haka ka barta tacigaba,haba dan ALLAH
D'ansarai ina hankalinka da tunaninka suke ne?Ganin yayi shiru yasa tacigaba da
zugashi da k'ara tabbatar mishi lallai tabbasss Sudaida ita take hana kwanshi zuwa
duniya.
Zuciyarshi tafara mishi tubka da warwara game da kalaman Asma'u.Tasake
kallanshi "D'ansarai wai kai har yanzu baka ga biri yaso yayi kama da mutum bane?
Yazuba mata idanu yana zancen zuci"anya Sudaida za ta mishi haka?Yana lura da
ita,ita kanta fa tana san Ya'ya dan duk lokacin da za suje siyayya a kasuwa taga
unisex riga indai ya mata kyau to sai ta siya,ran nan yashiga d'akin baccin su
yatarar da ita tana jera kayan a babban a kwati trolley;yazauna yana kallanta
"Zaujatiii...wai wa kike sai ma wad'annan kayan ne?Tad'anyi murmushi
idanun ta sun ciko da kwallah alamar zuciyarta tayi rauni "takauda kai sha'awa suke
bani Yaya D'ansarai musamman wad'annan biri da wandon(over roll) duk lokacin da
ALLAH ya bamu d'a toh na shine ko na tane...kawai sai ta fashe da kuka"d'azu A'isha
takirani wai ta kuma haihuwa d'a na uku kenan ta haifa... Maryam ta kusa haihuwan
na ukun...kowacce tana da Ya'ya mu kad'ai ne bamu dasu...yafara rarrashi"kiyi
hak'uri Zaujatiii... ALLAH yana sane damu bai manta damu ba,kome d'an lokaci
ne,wata rana sai labari yayi ta rarrashinta har yasamu tayi shiru sannan yakalleta
cikin natsuwa "Zaujatiii... ki daina wahalar da kanki a kan tara kayan yara na
sha'awa duk wannan me sauk'i ne in dai ALLAH ya azurtamu da samun d'an, dan kyale-
kyalen kullum sabunta su akeyi"budurwar bana tafi ta bara...
Bayan haka kuma kullum gidan nasu cike yake da Ya'yan yan'uwa in dai
tana gida,kai ko bata gidan in dai shi yana nan kuma ba makaranta za suje ba toh
zama sukeyi su jirata,saboda san su da takeyi da kuma irin garar da take had'a
musu,duk abinda yaro yake so in dai tana dashi to anyi angama maye ya auri
makauniya"in dai abin ta6akalashe ne. Toh Lillahi warasulihi me irin wannan halin
ce,za a ce baza ta bar nata Ya'yan suzo duniya ba saboda karatu?Anya kuwa?Yariga
yasan Yaya Asma'u kowa ma za ta iya kushewa tazaga in dai taku batazo d'aya
ba.Yakad'a kai cikin sauke numfashi"ALLAH yakyauta. Tabishi da kallan mamaki"ALLAH
yakyauta fa kace? Eh Yaya Asma'u to me zance daya wuce haka?
Tadad'a gyara zama"kai ko kake da abin cewa,cene da ita aure za
kayi...kayi auren ka amarya tazo taita haifa maka Ya'ya,toh idan taga Ya'yan kake
so taga amaryar taka tafara cika maka gidan da sanyin idanu to ai zata daina abinda
takeyi na tsarin iyali ko kuwa?Toh zanyi tunani.Tamik'e"ya dai kamata,ni me zan
samune a gidan? Tana fad'in haka ta nufi d'akin da suke ajiye kayayyaki tagama
dube-dubenta tafito"kome ma ya k'are.Yauwa gwamma da kika gani ganin idanunki,dana
fad'a miki ba kome ba yadda za kiyiba,kin san ni d'an albashine ga shi kuma wata
yakai tsakiya,abubuwan sai dai godiyar Ubangijinmu a kowani hali da yanayi.
Taja dogon tsaki tana mishi kallon uku ahu"amma a hakan kake
k'ok'arin biya mata wasu mak'udan kud'ad'e dan tacigaba da karatu, tamik'a mishi
hannu"ni bani abinda kayi niyyar bani kawai in tafi.Zan ai ko miki dashi har
gida,Yaya Asma'u kidinga tausaya min mana.Tanunashi da yatsa"kai d'in?Na rantse da
girman ALLAH ba ka da matausaya.Yakalleta da mad'aukakin mamaki yana nuna kanshi"ni
d'in ne bani da matausaya Yaya Asma'u?Ko shakka babu dan ni banga matausayan ba,ba
d'a ba jika to ko hidimar me kakeyi da har za a tausaya maka saboda yawan buk'atu?
Daga kai sai matarka kuke cin karanku ba babbaka,takalleshi"za ka bani ne ko sai
madugar ta dawo in zo in kar6a? Baice kome ba yasa hannu a aljihun gabar rigarshi
yaciro kud'ad'en ciki yana nuna mata"kingani yan canjine wallahi bani da kud'i.Tasa
hannu takar6a"eh kawo da hanau gwamma mannau ni na wuce.Yabita da kallo har tafita
a D'akin-shak'atawar, yagirgiza kai "Yaya Asma'u matsala,ALLAH yashirye ta da masu
hali irin na ta.
Sun dawo sallar la'asar da yammacin,shi da Musaddiq suka tsaya a k'ofar
gidan suna tattauna al'amuran daya shafi kasuwancinsu ta dawo daga makaranta,ta
tsaya suka gaisa da Musaddiq sannan tawuce ciki da mamakin kallan k'urillan da
Julaibib yake binta dashi wanda ba halinshi bane yawan kallan da har sai kaga munin
mutum.Tana kwance a tsakar d'akin yashigo,tamik'e zaune suna kallan-kallo na
wucewar wasu dak'ik'u "Yaya D'ansarai lafiya kuwa? Me yafaru ne? Yasunkwui da
kai,sai gwiwoyinta suka sage dan ta san wannan halin na shi tuntuni in dai
yasunkwui da kai to bazaiyi magana ba ko da menene,tajingina bayanta da kujera tare
da lumshe idanun ta,tunani barkatai ya cika k'wak'walwarta"ita dai tasan lafiyar
ALLAH suka rabu har tana tsokanarshi
"Zaujiii...kafin in dawo kamana faten tsaki mana.Yagalla mata harara"na
rantse da ALLAH tun kafin wankin bargo yakaiki ga dare ki tsaya kiyi abinki, danni
ba bawa bane.Takyalkyle da dariya wato ya rama abinda ta ta6a fad'a mishi shekarun
baya,farkon auren su kenan.Tawani marairaice"haba mijin Sudaida tamu dakai fa ba ta
6aci,kar fa faten tsaki yasa a ganmu a rana,tarik'o hannayenshi"dan darajar k'auna
da soyayyata da take dank'are anan tad'an daki k'irjinshi dai-dai saitin da zuciya
take, kamana faten tsaki,sukayi dariya,yagyad'a kai"eh zanyi amma ba fate ba tunda
nima a wancan lokacin ba a hanani ba sai dai an jamin zarene.
Yamik'e,tabishi da kallo"Yaya D'ansarai... takira sunanshi.Yakalleta
kawai"dan ALLAH kayi hak'uri idan na maka wani abu ne.Yayi kamar baiji abinda
tafad'a ba,zuwa can kuma yasake kallanta sai yad'anyi murmushi yad'auki mukullin
mota a saman tebur yafita.Ta lumshe idanun ta tanata ayyane-ayyabe a zuci.
A sanda hantsi yadubi ludayi rana ta haske ko'ina na safiyar
talata,tana zaune a in da ta idar da sallar walha Hauwa'u tashigo tana fad'in"ina
wannnan mijin naki me bak'in idanu da ba ya san zuwa gaisheni? Abokan wasa suke da
Julaibib Ya'ya maza amma tasu da Sudaida ta zo d'aya,suna mutunta juna.Sudaida
takama ha6a"yanzu mijin nawane me bak'in idanu Hauwa'u? Tajijjiga kai 'tabbasss,to
ni duk zuri'ar D'ansarai da wanda yafishi bak'i ne?Sudaida tad'an harareta"lallai
daga yau na san in da zan ajiyeki tunda kike cima rabin raina fuska a gaban
idanuna,to amma kuma kyau tsagwaron shi da wanda yakama k'afar Yaya D'ansarai nahhh
a duk zuri'ar Doctor Julaibb D'ansarai? Bata bata masa ba taje tad'auko lemun
peach.
Sudaida tawatsa hannaye"ahab ni dama na san irin abin nan ne na na
makaho da yace ido da wari.Hauwa'u tayi murmushi"mu ai gaba d'aya a zuri'ar Doctor
Julaibib Abdullahi D'ansarai kyawawane.Sudaida tagyad'a kai"muma ai hakan take a
zuri'ar Ibrahim Me-Lambu.Sukayi dariya sannan suka gaisa suna hirarsu ta yaushe
gamo dan sun d'an kwana biyu basu ga juna ba saboda yanayin karatun Sudaida da baya
barinta zama a gida musamma tada fara karatun degree.
Hauwa'u tafara ba Sudaida shawara"ku k'ara komawa asibiti mana ko wannan
karan ALLAH zai sa a dace.Takalleta cikin natsuwa"Hauwa'u a asibiti ake ba da
haihuwa?Tagirgiza kai"ba a asibiti bane,amma idan kunje d'in ai zasu k'ara
dubaku,idan har yanzu ba me matsala a cikin ku za su iya canja muku magunguna da
k'arin yan shawarwari ko kuwa? Tagirgiza kai"uh uh ni dai bazan koma ba,sauran
magungunan ma na daina sha shekaran jiya na zubar dasu nagaji da shan k'waya kullum
kwanan duniya bayan an tabbatar mana lafiyar mu k'alau, na fauwalama ALLAH duk
yadda yayi dai-dai ne.
Duk san mu da haihuwa idan ALLAH bai k'addaro mana ita a rayuwarmu ta
doron duniya ba, toh fa bawani magani da dabaru da likita zai bamu da za suyi
amfani,tad'an yi murmushi"ki cigaba da tayamu da addu'a itace babbar makamin
mu.Hauwa'u tarik'o hannayen Sudaida cikin k'auna da tausayi "wannan halin na ki na
maida al'amura wajen ALLAH me kowa da kome yasa nake dad'a k'aunarki,addu'a ina
tayaku da ita kuma zan k'ara,Ubangiji yamana jagora ya iya mana kar yabarmu da
iyawarmu dai-dai da k'iftawar idanu.Amin Hauwa'u.
Asma'u tashigo da sallama tana musu wani malalacin kallo ganin
hannayen su a had'e"to fa wani sabon salo ne wannna zuwa karuwanci da uwa? Hauwa'u
ta amsa"eh mana to ya san ranki Ma'u?Kafin tayi magana Habiba Yayar Hauwa'u
tashigo,tafad'a kujera tana wata yatsina wai ta gaji daga shagon d'inki take.Asma'u
takar6i ledar ta zazzage kayan"toh bari muga style,material ne da da leshi kuma
d'inkunan sunyi kyau sosai,wai ankon sunan da za ayine idan ta haihu.Hauwa'u ta
d'auki material d'in tana dad'a gani dan shine ya burgeta "gaskiya da ina da kud'i
da sai na yi shi.
Asma'u tace"tunda baki da kud'in wannan ai akwai atamfa ta yaku bayi,dama
ai dai-dai ruwa dai-dai k'urji.Habiba ta cafe"ah to shi mutum ba zai tashi ya nemi
na kai ba,kome an dogara da miji har abinda ba wajibinshi ba a gida yakamata
Iyayenshi su mishi amma basuyi hakan ba,kai ni wannan rashin tausayi dame zan
kwatantashine?Kome dai miji?Taja dogon tsaki,toh gwamma dai mutum yasani shi mijin
nan ba dan mace d'aya aka halicceshiba,ko bajima ko ba dad'e dole wasu mata ukun da
izinin ALLAH sai sun shigo an dama dasu suma.
Sudaida tayi tsaiii...cikin nazarin kalaman Habiba,babu kome a cikin su
daya wuce shagu6e. Hauwa'u da bata gano dawar garin ba tace kai"sharri dai ba kyau
wallahi,kuma kun sani ai ina sana'a sai dai banyi k'arfi bane,yaro kuma ai da
rarrafe yafara,ni kuma dan san a sani yaji da kwarin miji da banten suriki da d'an
masu gida bazan kwashe jarin nawa dan yin ankon suna na rana d'aya in dawo in
tsuguna ba,kuma da kuke maganar kome miji toh dan girman ALLAH wace macece a doron
duniya da baza taso ace kome mijin na tane yake mata harma da wanda iyayen nata
suka kasa mata ba?Kudinga adalci a kalamanku fa...Asma'u da Habiba suka kalli juna
suka kyalkyale da dariya Asma'u tace"ballagaza bankaura, sakarai ba ta da
wayau...inji Sa'adatu(Barmani Choge)
Sun so wacce sukai hakan dan ita ta tanka amma sai batace kome ba
tashige d'akin baccinsu tad'auko material da leshi launinsu d'aya dana Habiba sai
dai zanen jiki ya bambanta,tana fitowa ta d'orama Hauwa'u a cinya"gashinan ki
d'auki d'aya,wannan karan dai na ceceki,dan haka daga yau ki tashi haik'an da niman
kud'i dan ki huce takaicin zamani,duk da dai na ga zafin nema ba shi yake kawo samu
ba,haka kuma dare d'aya ALLAH kanyi bature, indai kina da wadatar zuci to abun kowa
bazai tsone miki idanu ba.Hauwa'u Tajijjiga kai "tabbasss zancen ki dutse.
Tabi kayan da kallo"kai ko wanne fa ya d'auku,sai dai kawai in rintse
idanu in d'auki d'ayan. Sudaida ta koma ta zauna"toh barinyi maganin ruwan idanunki
kawai,kirik'e su duka na bar miki.Hauwa'u tad'an zaro idanu cikin mamaki"duka na
wa?Kin barmin? Sai tafad'ad'a murmushinta zuwa dariya"kai masha-ALLAH jazakillah
khaira-khaira jaza'ih...ALLAH yabarki da Alhaji D'ansarai me bak'in idanu har gaban
abada.Takallesu ku tayani godiya mana.
Zuciyar Asma'u ta gama tafarfasa har ta k'one,ankon fa takema D'ansarai
magiya yamata yace shi bashi da kud'i shine yanzu matarshi har take kyauta da kala
biyu,itafa d'aya ma tace mishi tana so..Lallai wanna akwai shegiyar yarinya wato
kome na shi ya tattara mata kenan?Taja tsaki"itama Inna tana da matsala(🤔kunji
fa)wai idan an fad'a mata sai tace wannan dai sa'idanune a abinda bai shafe kaba,
ita ba matar shi bace?Ai ko ba aure a tsakaninsu yan'uwan junane,kuma duk
Ya'yantane,tanuna Asma'u da yatsa"wallahi kina tare da wahala idan baki bar wannan
banzan halin na kiba,ke wayasan damfarar da kike ma mijin ki da wannna shegen wayan
na ki?Tasake jan tsaki Inna bazaki gane irin bautar da yakema wannan yarinyar ba
wallahi dan ba kyau zuwa gidan nan kina gani ganin idanunki ne.
Habiba ce taja dogon tsaki"kina ta wani zuba godiya kamar wacce a kamata
gafara,ba fa sai kin gode ba tunda kowa ya san ai k'oshin wake na ruwa ne,da kud'in
d'an uwanki D'ansarai aka siyesu, kuma ko ke zai iya sai miki wanda suka fisu ma...
Hauwa'u ta tari numfashinta"a ah wallahi k'arya da ciwo gyambo da wari.
Sudaida tayi dariyar tura haushi"ah toh gwamma dai da kika tuna
mata,takalli Habiba tana murmushi"wad'annan da kike ganinsu tanuna kayan data ba
Hauwa'u ni na siyesu da kud'i na,ai idan zan siya da kud'in Yaya D'ansarai toh
bazan sai wad'annan masu rangwamen farashin irin ta gama-gari yakubayi ba,tunda
kud'in ni nake zamansu.
kufa yan uwane ba dole ne ya mukuba,sai dai yayi dan kara yasamu ladan
zumunci, idan kuma yak'iyin haka ba wanda zaice dan me?kuma ko a wajen ALLAH bashi
da laifi ko na sisin kwabo tunda ku ba a hakk'unshi bane,ni ce nan tanuna k'irjinta
da kwibinta ni ce k'ashin hak'ark'arinshi,kinga ni ce nazama dolenshi, wallahi idan
ana san zaman lafiya dani toh fa sai na fad'i irin wanda nake so,idan an kawo naga
kalar bai min ba dole yakoma yaza6o wani, ko kuma in ce yad'ibo su da yawa in za6i
wanda suka kwanta min a rai...Habiba ta tari numfashinta"tabbb ai ko baki isa
ba,tamata wani kallan uku ahu kai... ALLAH ko ya isa da wannan iko sai kace ke kika
kawo shi duniya.
Sudaida ta kalleta cikin kukawa"Habiba kenan kisa ranki a inuwa dan ko
ba iko dama ALLAH ai ya isa da kome,shine dama me kowa da kome na doron duniyar
nan. Asma'u tamik'e"ke fa yarinyar nan wato salan mulkin ki kenan ki hana mutum
rawar gaban hantsi ko? Batayi niyyar maida martani ba to amma Yaya Asma'u ta dad'e
tana shiga mata hanci da k'udundune ya kamata ta fyaceta,kuma kunyar mara kunya ai
asarace,idan babba ya yadda girman shi to ai ba laifi bane dan an taka.
Sai tagyad'a kai"ai kuwa dai Yaya Asma'u na zama kuturwar uwa zama
dani dole,kuma duk wanda zai zauna dani d'in to d'aurin gwarmai nake mishi.Habiba
da take ji kamar ta shak'e Sudaida dan haushi tace"to ai barewa baza tayi gudu yar
ta tayi rarrafeba.Sudaida ta kyalkyale da dariya"ai dama kyan rawa da makar6i,kyan
d'an yagaji ubanshi. Asma'u tafara tafiya "to Sudaida na yi gida amma dai kiyi a
hankali dan ni bazan mulku ba, idan kuma kika matsa da yawa to abu ne me sauk'in
gaske cire wando taka inyi waje dake.tak'arasa fita ba dan bata da sauran abin
fad'a ba,a ah sai dan kar k'ilu taja bauuu...ga Hauwa'u nan itama munafuka ce idan
anzo maida magana Sudaida za ta goya ma baya sai a d'ora mata sata da maitar,amma
lallai sai tasa Dannarai ya k'ara aure, itama Sudaida ta so data tsaya ta ba ta
amsa dan haka duk sunji ciwon kalaman juna.
Tacire hannun Hauwa'u da tayi tagumi dashi tana kallan su kawai,ta kashe
ta da lallausan murmushi tunda ance iya ruwa fidda kai."kiyi hak'uri ba kud'i a
hannuna amma idan bafade na autan Inna yadawo ranar jumma'a to zan turo miki shi
wallahi har gida yazo yabaki kud'in d'inki dana takalmi da hijab,dan kin san ni a
gidan nan k'arfine dani na gaban shari'a kum...Hauwa'u tasa tafin hannun ta rufe
mata baki"dan girman ALLAH ya isa haka Sudaida.
D'akin-shak'atawar ya d'auki shiru na wucewar wasu yan
dak'ik'u.Habiba tayunk'ura tamik'e cikin fushi bata musu magana ba tayi hanyar
fita.Sudaida tad'an d'aga murya"toh uwar biyu sauka lafiya sai kin kiramu,ALLAH
yaraba lafiya.A ciki ta amsa da"uhun.Tana fita Hauwa'u ta kyalkyale da dariya"matar
D'an Sarai yau kin burgeni.Takad'a kai"ni har ga ALLAH banyi niyyar kula suba to
amma naga abun na su yana neman wuce gona da iri ne,shiru-shiru kuma ai ba tsoro
bane gudun magana ne"dodo d'aya akema tsafi,ba su suke aure na ba Yaya D'ansarai ne
dan'uwan ku,duk fad'in mutanan doron duniya idan za suce yarabu dani idan yana so
na,yana san zama dani to ba wanda ya isa ya rabamu,tunda ba wanda yake mishi auran
nan,shi d'in da kanshi yake abinshi,haka kuma idan yace ba yayi ba wanda zai
tilasta mishi zama dani.Hauwa'u tajijjiga kai "tabbsss zancen ki dutse"ALLAH
yashirye su da sauran dangin miji masu mugun hali na mugunta "abun wani banza na su
dukiya.
Tana kallan shirin Akhbar-Al'an tana cin awarar madarar shanu Khadija
yar Khausar tashigo da gudunta cikin d'oki tafad'a jikinta"Inna Mamace tace in zo
in tambayeki wai anjima za tayi tuwon shinkafa miyar shuwaka,shine tace wai a
k'aton kwano guda nawa za a zuba miki? Sudaida tayi murmushi ta san wayau aka mata,
kafin tayi magana kiran Khausar yashigo"Nana Khadija ta k'araso kuwa?Eh gatanan ta
kuma fad'a min sak'on,ina za ki?Asibiti zan kai Misbahu ta kuma na ce dole sai
munje da ita.Wayyo! har yanzu jikin ne?Shine Sudaida daren jiya kusan kwana mukayi
bamuyi bacci ba saboda kukan shi. Toh ALLAH yasauwake zan shigo anjima idan kun
dawo. Sukayi sallama.
Inna me zan fad'a mata?Takalleta da kulawa"bari sai anjima idan nayi
wanka sai muje can muci ko?Toh Inna amma kamar kinyi wanka ga shi kina ta k'amshin
irin turaren Baba D'an Sarai,ina son k'amshin. ALLAH Khadija?Khadija tayi d'an
tsallan murna kamar yadda yara keyi"ALLAH Inna,to maza shiga d'aki ki d'auko kema
in fesa miki,da gudunta ta d'auko Sudaida tafesa mata.Nagode Inna.Tad'an kama
ha6arta"yauwa Khadija ga yoghort can kije ki d'auka,tad'an mak'ale kafad'a"Inna ni
dai nafi son Caprisonne.Tamik'e shikenan muje in baki.
Sudaida tazuba mata idanu cikin tasbihi ga Ubangiji,k'udurar ALLAH
dayawa take,wai yaushe-yaushe akayi auren su amma gashi har an haifi yar da za a
aikota daga wani gida zuwa wani gida da k'afafunta da bakinta"oh ALLAH kaine
ALLAH.Sharrr...sharrr...hawaye masu d'umi suka zubo mata"anya za taga gudan jininta
a doron duniya kuwa?Ta rungumeshi a k'irjinta yaji d'uminta na uwa itama taji
d'uminshi na d'a?Ta tuno da bak'ar magana habaici da dangin Julaibib suke
mata,wanda in dai da mutum shi yake da ikon ba kanshi haihuwa to kuwa da tayi
zuciya ta haifo musu yan hud'u a haihuwar farko,to ina ALLAH ne,ba kuma a mishi
dole...tasake tuno kalaman Inna,Mama,kai rannan har Umma sai da tadinga kwantar
mata da hankali akan dai tayi hak'uri tayi hak'uri,kullum haka suke fad'a mata
musamman idan sun ganta cikin damuwa ko da ba wannnan ne abinda yake damunta ba
"kiyi hak'uri Sudaida hak'uri kan tadda rabo,wata rana sai labari..
Khadija tamatsa wajenta"kukan me kikeyi Inna?Waya dake ki?Tarungumeta
kawai tacigaba da kuka Khadija na tayata,sai da sukaci suka k'oshi dan kansu sannan
sukayi shiru a hankali kuma bacci yayi awon gaba dasu.
Kiran wayar Julaibib yatashe ta daga bacci"wash ALLAH
Zaujiii...yatare ta da sauri"me yafaru ne Sudaida?Tayo k'asa da murya"ba kai bane
ina cikin baccina me dad'i ka tashe niba.Yayi murmushi"to fa tawa tasameni kenan
malami da tallan jigida,kiyi hak'uri ki koma baccin anjima mayi magana.Uh uh ai
kuma ko na koma baccin ba lallaine yazo ba sai dai in ta juyi"goben zaka dawo?Na so
haka to amma bazai yiwuba dan gobe muna da serminar a jahar Katsina idan na dawo
kuma akwai jarabawar da zan ma d'alibai,nima na so zuwa dan zan ba Inna wasu
kud'i,amma barin miki transfer idan kika ciro sai ki kai mata,yanzu zan kira ta in
mata bayani.Ranta bai mata dad'i ba amma ta daure ta amsa da to tare da addu'ar
ALLAH yakiyaye hanya,sukayi hirarsu ta kewar juna sukayi sallama.
A sanda hantsi yadubi ludayi na safiyar laraba tabawa ranar sa
a,Nasmat tazo gidan,suka rungume juna"oyoyo Nasmat...Sudaida ta d'auki Ahmad tana
mishi wasa shi kuma ya bud'e wawulan bakinshi yana kyalkyala dariya.Nasmat taje
tad'auko lemun sprite tabud'e tana mita "Sudaida kin zama abinda kika zama
wallahi,abinda yasa meki ALLAH yasa kar yasamu sauran dangi.Tamata kallan k'arin
bayani...Nasmat tagyad'a kai"in dai na zo gidan nan ni zan ba kaina ruwa ko abinci?
Haka ake ma bak'o?Taja tsaki"na d'auka wani laifin nayi to kar kisha ruwan mana
cikin wa zai shiga?
Takama ha6a"kar dai zama da mad'aukin kanwa Yaya Asma'u ya sa kema kin
zama abinda kika zama? Haushi yasa Sudaida tak'i magana tanama Ahmad wasa yana
cigaba da dariya.Itama tamik'e zuwa wajan taga tana amsa waya,tagama wayar tad'an
kalli dai-dai kun mutanen da suke kai-kawo a safiyar sannan tacema Sudaida"na biyo
miki ne muje duba yar gidan Yaya Asma'u da jiki.Hu'un tafad'a ba tare tadata bud'e
bakintaba.Menene kuma hu'un?Nasmat ta tambayeta.Tamik'e zaune daga kwanciyar da
tayi tad'ora Ahmad a cinya"ke ni fa bazani in da raina zai dinga 6aci a banza
ba,dan na riga na k'una bana tsoron wuta.A ah Sudaida kiyi hak'uri kawai idan an
miki kan kara karkice za kiyi na itace.Tayi wani huci cikin kad'ai"ai na rantse da
girman ALLAH ni yanzu har na gungume zan iyayi yadda zai shekara yanaci,kawai sai
tarufe idanu tana zazzaga fad'a,Nasmat bata kar zomo ba amma an bata rataya.
Tazuba mata idanu har tayi tagaji dan kanta tayi shiru,sai kuma tayi
kwafa"banda ina duba darajar yan'uwantaka da dangantaka kinaga zan bar Yaya Asma'u
tacigaba da cin dunduniyata tana min hawan k'awara yadda taga dama?Nasmat tagirgiza
kai sannan ta amsa cikin natsuwa"a ah baza kiyiba, to amma karki manta hak'uri kan
tadda rabo...idan ka gaida wada da tsawonka zaka mik'e...Sudaida ALLAH yana son
masu hak'uri masu had'iye fushi,da dama su rama abinda aka musu amma sai suyi
hak'uri ba saboda kowa da kome ba sai saboda zatin ALLAH... tacigaba da rarrashinta
har fushin daya mamaye zuciyarta yalafa,ta kuma yi nasarar janta suka tafi
dubiyan...
Da kunu da miya har abadan duniya ba za su had'uba sai dai a cikin
ciki.
27 Jumaada Thani 1441
21 February 2020
We Ibrahim's Daughters👇
Asdilat KD...2geda with Ra'ibs.
DANGIN NONO WRITERS ASSOCIATION
{Da Inganci Mukayi Fintinkau}
Bismillahi wabihi nasta'in
...GWAJIN DAFI💔
Almost true story
Daga alk'alamin🖊
Ya'yan Ibrahim
Saudat A.Baba (Asdilat KD)
Da
Bara'atu Ibrahim (Ra'ibs)
Shafi na ashirin da biyu.
A wulak'ance da halin-ko-inkula kamar yadda tasaba haka yauma ta amsa
gaisuwar Sudaida, amma tanata jan Nasmat da hira suna shirin tafiya sai ga Hauwa'u
itama ta zo dubiya,suka tsaya ana gaisawa, Hauwa'u tamatsa kusa da Sudaida "yar'uwa
yayane jikin ne ko garin ne,ko wannnan bak'in mijin na kine dayaje yashare waje a
Gidan-Waya?Takai mata duka a kafad'a,tagoce da sauri yabi iska.Kin sama mijina
rabin raina idanu fa,meye darin gamarki dashine wai?Asma'u da wata k'awarta yar
duniya me irin halinta sukayi dariya suka tafa"haka fa kullum ana nuna ana k'aunar
miji amma an k'i nuna mishi k'aunar a zahirance,ta hanyar barin Ya'yanshi suzo su
shak'i iskar duniya,takad'a kai cikin ta6e baki"kullum ana ba mutum amma har yanzu
ya kasa yin zuciya yak'ar6a ko da sau d'aya ne,sai dai ayi ta asara,a wanke abun
yabi rariya.
Hauwa'u takalleta"ke wai Asma'u kullum ba ki da abinyi sai gori?Sannan
ma dake ake magana me ko ko ita tace miki ba tajin dad'i?!Nasmat ma ranta ba dad'i
tace"haba Yaya Asma'u wannan ba girmanki bane wallahi,kin san duk me gori matuk'ar
bai tuba ba to yana haramtama kanshi rabon alheri ne a lahira, sannan wannnan gorin
ma d'an Adam d'in doron duniya ba shi da iko akanshi,wannan ba huruminki bane Yaya
As...kafin tak'arasa sai ga Hajiya tashigo d'akin tana d'agama Nasmat hannu "dakata
Nasmat in dai gori ne ta tara ta samu, Hajiya tanuna kanta"ni d'in nan yau har
goruba zan mata, zanyi maganin iya shegen nan k'auri da kare.
Tayi d'as d'as d'as da yan yatsunta"ki bud'e kunnuwanki da kyau ki
saurareni,na rantse miki da girman ALLAH in har Sudaida bata haihuba to ba itace ba
ta haihuwaba,k'aninkine Julaibibi,matan kakanku ai su biyune uwargidan shice
mahaifiyar ubanki,su uku tahaifa,amma amaryar shi sai da ta haifa mishi Ya'ya goma
shabiyu, ubanki gashinan shima Ya'ya uku yahaifa,d'aya kanin na shi yahaifi Ya'ya
biyu, d'ayan kuma ai har yakoma ga ALLAH bai haihuba,matar shi data gama takaba
tayi wani auren bagata can da Ya'ya bakwai ba?
Karima Yayarki Ya'yanta biyu,ke kuma yarki d'aya jallin-jal kamar rai,sai 6ari da
kika ta6a yi sau d'aya duk shekarun da kukayi a gidan miji,mata nawane ta dangin
kakar ta ku ga sunan a gidajen miji ba haihuwa sai dai suci su k'oshi suje masai su
juye kayansu?Ai suna da yawa saboda ku ba irin haihuwa bane,toh Sudaida fa?Su goma
sha takwas ne a gidansu,kuma duk cikin Ya'yana ba uwarki ce kawai me Ya'ya uku ba?
Tanuna ta da yatsa"to dan haka ahir d'inki hawainiyarki takiyayi ramar Sudaida,
kuma ko yanzu da k'anin na ki zai rabu da ita,toh idan ma na rantse ba kaffara a
kaina bazata rufe shekara a wani gidan auren dazata yiba za ta haifo gudan jininta
takuma sa zani tagoye abunta,ai ga sa'o'in auren na ta nan kina ganinsu ganin
idanunki kowaccensu ta fara kafa na ta Iyalin...
Tambayar me jikin da batayiba kenan ta ajiye ledar ayaba da lemun
tajuya cikin fushi"jahilar addini kawai wacce bata yadda kome muk'addari ne tun
daga lauhul-mahfus ba,na rasa a ina kika d'auko wannan bak'in halin na ki,banda ma
ke shimmeruwa uku ce(sha-sha-sha)Sudaida ba yar'uwarki bace da zaki iya tare mata
fad'a a inda kikaga za a wukak'anta taba?Toh karki daina abinda kikeyi ai hassada
ga me rabo ta kice...Nasmat da Hauwa'u sukayi lallausan murmushi suna shima Hajiya
albarka"ALLAH yak'ara girma me amfani Hajjaju makkatan...kaza dai garin tuno-tone
take tono wuk'ar yanka kanta...baki shi ke yanka wuya.Sai da Hajiya tabar gidan
sannan Asma'u tafara nad'e tabarmar kunyarta da hauka.
Da wannnan 6acin ran Sudaida tawuce ATM taciro kud'in da za ta kaima
Inna,sukayi kaci6is da Aminu shima ya zo ciren kud'i yabud'e mata murfin
motar"shigo ki jirani tunda yau na ga ba layi.Dak'ik'u basu wuce goma ba
yadawo.Yaya Aminu gida za ka koma? Yana tayar da mortar yake amsawa "Jos zani,amma
ke zan mayar gida wani abune?Tasa hannu ta share hawayen da suka zubo mata
sharrr... "mutafi kawai sai ka saukeni a Gidan-Waya.
Sun d'auki hanya sosai sannan yajuyo cikin kulawa yakalleta"wai yau waya
ta6a kanwata rabin raina ne?Tad'anyi murmushi"share kawai Yaya Aminu ni da Yaya
Asma'u ce.Yakama ha6a wuuu... Asma'u ciwon idanu sai hak'uri,ai ko jiya danaje
dubiya nima sai da muka hau sama muka fad'o,wai nayi kud'i bana son zuwa
gaisheta,kinji sai kace wata Yayata.
Sudaida takawar da zancen ta hanyar tambayar Siddiqa nan da nan ko yayi
lallausan murmushi suka shiga hirar arziki har suka iso Gidan-Waya,har k'ofar gidan
da Julaibib yake yakaita anan rukunin gidajen malamai,yasake kallanta cikin
kulawa"Sudaida kiyi hak'uri na san kinayi amma ki k'ara wata rana sai labari,ai duk
abinda yayi farko to tabbasss yana da k'arshe,wallah-azim da ana siyan haihuwa da
kud'i toh dana sai miki kome tsadarshi,toh ina abin na ALLAH ne "ance da kare me
sunan maza.Tajijjiga kai"na sani Yaya Aminu na kuma gode, duk cikin Yayyina kaine
taurarona"Ina sonka sosai.Sukayi murmishi"nima nagode kanwata rabin raina data
za6eni sama da kowa a matsayin tauraronta,toh me kike so in siyo miki a matsayin
tsaraban mutan Jasawa?Tagirgiza kai"bani da za6i kasiyo min ko menene nagode.
Yayi yar dariya"tunda kin bani wuk'a da nama Insha-ALLAH za6in nawa zai
burgeki,idan nadawo zan shigo in baki tsaraban,sai in kar6i kud'in da kikace zan
kaima Inna,kiyi hak'uri ko?Nagode Yaya Aminu tabud'e motar tafito,tarufe
mishi"adawo lafiya ALLAH yatsare,suka d'aga hannu suna ma juna adabo.Tabi danjojin
motar da kallo har ya6ace ma ganinta.Tarik'e k'ugu tana fesar da iska ta baki ta
hanci sannan tasa hannu a jaka ta d'auko mukullin gidan tabud'e tashiga.
Wani k'amshin turaren d'aki da sassanyar iskar da take shigowa ta
tagogin da suke bud'e yamamaye ilahirin gangar jiki da zuciyarta,sai taji ta samu
natsuwa ta lumshe idanunta tana jan numfashi"Yaya D'ansarai wallahi me tsabtane,ji
yadda yazauna yagyara gidan kamar mace. Tashige d'akin bacci,tazauna a gefen gadon
tad'auki wani d'an k'aramin hotonta da ya ajiye a dirowar gefen gadon,ta d'auki
hotonne a wani excursion da sukaje a Wadom akan harkar gona tun tana aji biyu a
k'aramar secondary,tak'arema hoton kallo tana tuno irin kyan da Julaibib d'in yace
wai tayi...Wanda ita dan haushin irin munin da tayi ta turo baki gaba zata yaga sai
gashi ya shigo gidan shine yakar6a,tamaida hoton ta ajiye tana murmushi ita tama
manta ta ta6ayin hoton.
Taje tayi wanka tabud'e wardrobe tad'auko riga da zani na shadda
ruwan makuba dan dama akwai kayanta a gidan,wasu lokutan idan tazo makaranta ba ta
komawa Zonkwa sai tayi zamanta koda ba Julaibib a garin tunda baya samun zama yau
yana Zari'a gobe yana Katsina, jibi yana Kaduna,haka dai haka dai ake ta
gwagwarmaya da zirga-zirga a cikin rayuwar.
Tana azkar d'in yammaci bayan ta idar da sallar la'asar Aminu
yashigo ya ajiye mata injin d'in matse ruwan rake tagama azkar d'in sannan
takalleshi cikin murna da shakka tanuna injin d'in tana kallanshi"Yaya Aminu da
gaske?Yajijjaga kai "Sudaida ko da nake da raha ai na san irin rahan da nake yi da
kowa,bazanji dad'i ni akaran kaina amin irin wannan kyautar bayan na sa hannu na
k'ar6a,sai kuma a kar6e wai wasa akeyi,dan haka bazan ma wani ba, bare ke kanwata
da nake ji da ita a cikin k'annina,yad'an kalleta a kwai rake a gidan nan? Tamik'e
ai ba a rasa nono a riga sai dai idan rigar ba ta tsurar fulanin asali bane,a
na'urar sanyaya abubuwa(fridge)tad'ibo ferarrun rake guda biyar takawo mishi,yauwa
d'auko wuka kigani.
Yakar6i wuk'ar yak'ara yankasu k'anana sannan yasa a ciki,yan
dak'ik'u kad'an yad'auki Kofi yajuye mata tataccen tsurar ruwan rake, yamik'a mata
tasa hannu biyu takar6a takai tsakanin la66anta da bismilla takur6a,sai kawai
tacigaba da sha har sai da tashanye duka.Suka kalli juna,yad'an dage gira"toh ya?
Takyalkyale da dariya tana jijjiga kai "Alqur'an yayi ba k'arya,nagode Yaya Aminu
ALLAH yasaka maka da mafificin sakamakon shi.Amin Sudaida"ke ma muk'amuk'inki sa
huta da tauna,to kai baka shaba?Yagirgiza kai"sanda za a nuna min sahihancin injin
d'in an matsa min na sha. Yamik'e yana gyara zaman hular shi"to barin kama
hanya,taje ta d'auko mishi kud'in da zai kaima Inna sukayi sallama.
Tana wanke d'anyen na'ana'a yashigo D'akin-girkin a
d'okance"Zaujatiii...saboda ALLAH dama kinzo garin amma baki fad'a min ba?Yazuba
mata idanu"to yanzu dana wuce Zonkwa ne fa? Tad'an motsa kafad'a"duk d'aya 6arin
manshanu a miya.Yarik'ota cikin kewa sai kuma yasake ta barinje in sallami d'aliban
da suke jira a waje yawuce D'akin-shak'atawa yad'ibo wasu takaddu yafita.
Sai da yayi sallar Isha'i sannan yashigo yazauna a kusa da ita yana
ganin rubutun da takeyi a na'ura me kwakwalwa"barka da shigowa Yaya
D'ansarai.Yagyad'a kai"barkanmu kema kinzo lafiya?Tayi shiru kamar bataji
shiba,wucewar wasu dak'ik'u kuma tad'an kalleshi"yayi murmushi kina k'ok'ari fa
ALLAH yak'ara basira.A tak'aice ta amsa da "amin.Sai kuma tarufe Laptop d'in
tamayar ma'ajiyarta.
Ta dawo tazauna a d'aya kujerar suna fuskantar juna,zama nesa dashi
da tayi yabashi tabbacin akwai maganar da zata fad'a mishi me mahimmaci dan haka
take yi,dan haka shima yadad'a gyara zama dan yaji yau kuma dame tazo?
"Yaya D'ansarai kana k'aunata kuwa? Baiyi tunanin abinda za ta fad'a
kenan ba,amma sai ya 6oye mamakinshi ya amsa mata kai tsaye"eh Sudaida ina
k'aunarki.To na rok'eka da girman ALLAH karabani da damuwa,kome yanada iyaka to
tsakani da ALLAH abinda zuciyata za ta iya d'auka kenan,idan ba haka ba to ba
abinda zai hanata kumbura ta fashe k'arshen rayuwata a doron duniya ya zo
kenan,tanuna kanta da yatsa,ni na san ba autar mata bace dan haka zan tayaka addu'a
ALLAH yabaka wacce tafini, wacce zata haifa maka sanyin idanu tunda ni na kasa,
nima ALLAH yabani dai-dai ni.
Yakalleta cikin natsuwa"me aka miki da kike zancen rabuwa?Da mamaki
takalleshi"au yanzu baka gani ba?Saboda bakai ake ma ba?Tayi wani huci cikin kad'a
kai"toh madalla,amma Yaya Julaibib gaskiya ni dai bazan iya wannan zaman ba,duk
lokacin daka shirya nima a shirye nake zan ba ka sarari.Tamik'e.Jinan Sudaida koma
ki zauna. Bata zauna ba sai kawai ta durk'usa a gabanshi tafara kuka
"Yaya D'ansarai kaji tausayina mana bazan iya jure wani wulak'anci da
bak'ak'en maganganu ba dan kawai ban haihuba,bana so zumunci ya6aci ne amma na
rantse maka da girman ALLAH da da kaina zan d'auki mataki.Tasake fashewa da
matsanancin kuka,kukan abu biyu take yi,gana rashin haihuwar akaran kanshi,gana
wulak'anci da tozarcin da ake mata akan dai rashin haihuwar me makon ma abarta taji
da abinda yake damunta.Haka ta dinga fad'ar duk maganar data fito daga bakinta ba
tare data tauna ba.
Yad'ago ta fuskarta sharkaf da hawaye da majina yazuba mata idanu na
wucewar wasu dak'ik'u saboda ya rasa abinda zai fad'a mata,sunyi waya da Hajiya
kuma tafed'e mishi bire har bindi "tabbasss an dad'e ana mata wannan cin k'ashin,
amma shi da ita bata ta6a fad'a mishi ba,ko ya ganta cikin damuwa idan ya tambaya
za ta girgiza kai"tace ba kome ko tace wani abu kazane ba gorin rashin
haihuwaba,yayi tsaiii...har yasamo bakin zaren,sai yayi murmushi"kinga Sudaida
share hawayenki tabbasss ni D'ansarai ina k'aunarki dan haka zan rabaki da bak'in
ciki da damuwa.Takalleshi kallan k'arin bayani"Yajijjiga kai"kiyi hak'uri kibani
lokaci zanyi tunanin yadda al'amuran za su kasance ba tare da an 6ata zumunci kamar
yadda kika hango haka ko?
"Zaujatiii...ina so kimin alk'awari zaki bani lokacin ba tare da kin
sake tambaya taba har sai na zo miki da zancen,lokacin na samu mafita...za tayi
magana yatari numfashinta"dan ALLAH kar kice kome,ai kin san ba zanyi abinda zai
cutar dake ba. Tayi shiru kawai tana share hawaye tamik'e zuwa d'akin bacci
takwanta tare da d'ora kanta a saman matashi.
Kad'an yaci abincin daren sannan yaje yayi wanka yasa kaya marasa nauyi
na shan iska,yazauna a doguwar kujera ya barbaza wasu takaddu yana aikin cikesu
d'aya bayan d'aya sai dai ya kasa jure rashin Sudaida,kewarta ta dame shi dan haka
yamik'e zuwa d'akin.Suka kalli juna tana kwance da wani littafin lissafi tana
nazarin shi,tamaida kanta cikin littafin amma ta gagara cigaba da nazarin,yazauna a
gefen gadan sannan yasa hannu yakar6i littafin.
Tawani 6ata fuska"Yaya D'ansarai gobe fa muna da jarabawa shi yasa nake
nazarin nan.Yamata wannan kallan da yake ba ta haushi yagyad'a kai"uh na sani...ni
ma gobe zan tafi Katsina yaya kenan? Tad'an turo baki gaba tana dad'a gyara bargon
data rufa"toh kowa sai yakwanta yayi ishashshen baccin da ake so mutum yayi duk
dare,gobe kowa sai ya tashi a watstsake katafi Katsina,ni kuma in shiga makaranta
ba shikenan ba?
Takauda kai daga kallan dayake mata, tafara jero azkar d'in kwanciya.Ai
ko ba shikenan ba,ki sallameni.Tagyad'a kai"toh jeka na sallame ka, ALLAH ya
lullu6eka da rahamarshi da albarkarshi, asubah tagari.Yayi murmushi sannan yasa
hannu yana mata wani salo...salon data kasa daurewa tamik'e zauna tana dariya"Yaya
D'ansar...sauran kalaman suka mak'ale sakamakon wani sak'o d'aya bata me girman ban
mamaki me sa a fita a hayyaci.
Da safe yagama shirin shi tsab natafiya cikin shigar farar shadda
yana zaune a D'akin-shak'atawa, yayi shiru cikin nazarin kalaman Sudaida dan ko da
asubahi sai da tadad'a tabbatar mishi tana nan akan bakanta,ta kuma bashi sarari
tana zaman jiran shi.Yadda yake juya zuman da yasa a shayi haka yake juya
kalaman;tafito daga d'akin baccin su cikin shigar mutunci da mutunta kai kamar ko
yaushe za ta shiga makaranta.Tazauna a hannun kujerar "Yaya D'ansarai wai har yanzu
shayin ne baka shaba?Tun kafin in shiga wanka fa nakawo maka.Yasunkwui da kai.Sai
kawai tamik'e tad'an kalleshi nawucewar wasu dak'ik'u
"Yaya D'ansarai ALLAH yakiyaye hanya...
Tad'an sunkuya tabashi sumba sannan tayi furucin da wani salon shagwa6a"sai munyi
waya ko?...tajuya tayi tafiyarta dan tasan ba magana zaiyi ba in dai yayi wannan
sunkuyar da kan"sanin hali ai yafi sanin kama.
Yabita da kallo yana lallausan murmushi yayi d'as da yan yatsunshi"hak'ata
zata tadda ruwa Insha-ALLAH ai ni dake mutu karaba yarinya.Yakalli agogon dake
d'aure a hannunshi na dama,lokaci yaja a gurguje yagama karyawa,yad'auki jakar shi
ta matafiya ya rataya a kafad'a da mukullin mota yakulle gidan yana addu'ar fita
daga gida"bismillah tawakkaltu alallahi walahaula walaquuwata illah billah.Yashiga
mota ya zauna yana d'aura belt yana kuma amsa wayar wani abokinshi na koyarwa da za
suyi tafiyar tare.Tun daga ranar Julaibib yacanja taku tunda abin iya ruwa ne...
A sanda hantsi yadubi ludayi na safiyar litini (Monday)ranar aiki ko
nasara na tsoron ki tana kwance cikin bargo tana baccinta na tofan gira dan yau sai
yammaci zata shiga makaranta kiran wayar Inna yashigo tad'aga da fara'a"Innarmu
Sudaida takirata tana yar dariya"na'am yar gidan Inna,suka gaisa Inna tace"na ji
autana shiru ni da Alhaji har mun gaji min kira layinshi sau shurin masak'i,da tana
shiga baya d'agawa amma daga baya kuma ta daina shiga kwata-kwata.
Dasauri cikin d'an bud'e idanu dan mamaki tace"shi Yaya D'ansarai d'in Inna?
Eh shi d'in,ko baya jin dad'i ne kuke 6oyewa?Fargaba takamata dan kwana biyun nan
itama fa bata gane mishi wallahi"a ah Inna lafiyar shi k'alau,yanzu ma yana cikin
makaranta bari ya shigo inji abinda yafaru.Toh ALLAH yadawo dashi lafiya,ALLAH ya
jishshemu alheri sukayi sallama Sudaida tana amsa addu'ar Inna da amin,amin Inna.
Tafito D'akin-shak'atawa kawai taganshi kwance a doguwar kujera.Yaya
Julaibib takira sunan shi. A hankali yabud'e idanun shi yana kallanta"har ka dawo
ne amma baka nemi ni ba? Ni banji shigowar kaba.Yauwa sai tajuya ta d'auko
wayarta"munyi waya da Inna d'azu barin kirata,yafizge wayar ta bishi da kallo
yakasheta gaba d'aya sannan yatura a aljihun gefen rigarshi ta dama"rabu da ita
Sudaida.Tazauna a k'asa gefen k'afafunshi tana bud'e idanu da mad'aukakin mamakin
furucinshi"Innarce za a rabu da ita? Bai bata amsa ba yamaida idanun shi yarufe.
Tasake bin shi da kallo cikin tsoro da shakka"to ko dai Yayi Julaibib ya
fara k'arama sama hazo ne?data isheshi da tambaya sai kawai yamik'e yashige d'akin
baccin su har yanasa mukulli,bai fito ba sai da za shi masallaci sallar
azahar.Tamik'e ta tare k'ofar.Yad'an yamutsa fuska "ke bani hanya yanzu za tada
sallah.Tagyad'a kai"ba in da za ka har sai ka fad'amin abinda yake damunka da har
za kace a rabu da Inna..
"Adai-daita sahu a had'a kafad'a...
Suka fara jiyowa daga masallaci yad'an kalleta cikin natsuwa"barin dawo daga sallah
sai muyi maganar ko?
Daga masallaci makaranta yawuce bai koma gidan ba,tagaji da jiranshi,itama
tatashi tabishi,yana jin an kwankwasa k'ofar ya amsa daga ciki"na'am bismillah
shigo,bai zaci itace ba.Takulle k'ofar tazare mukullin"Yaya D'ansarai ni fa ka sani
a rud'ani wallahi, wai me yake damunka ne Inna za tayi magana dakai kace wai a rabu
da ita sannan ka k'wace waya ta ka kashe,ta kama ka kashe me yafarune?Ni ma kwana
biyun nan kwata-kwata bana gane maka.Yamaida kanshi jikin kujerar"to Inna me za
tamin?Inna bata da maganin damuwata fa.
Da rawar murya tafara nuna shi da yatsa"Kai Yaya D'ansarai
Innarce..ba..ta da maganin... damuwarka?To duk fad'in duniyar nan ma kana da kamar
tane?Takalleshi cikin takaici"to wa yake da maganin damuwarka?!
Yajanye kanshi daga jikin kujerar yad'ora duka hannayenshi a saman
tebur d'in sannan yakalleta cikin natsuwa"Zaujatiii...ke ce maganin damuwata,ina
k'aunar ki, ina jin takaicin ace wai ni Julaibib yanuna kanshi da yatsanshi wai ni
zan rabu dake dan kawai ba kya haihuwa, ni ina son ki a kowani irin hali da yanayi
na rayuwa,Sudaida ko baki haifa min Ya'ya ba ba na nadamar aurenki.
Ni yanzu abinda yake damuna yahanani rawar gaban hantsi shine na kasa
samo mana mafita ta yadda zamu rabu salin-alin ba tare da Inna ko Kawu ran wani
daga cikin su ya sosuba, kema kuma na san kin k'osa amma kina min biyayyane kawai
saboda na rok'i alfarma kar kice kome...Dammm... Zuciyarya tabuga...tanajin wani
irin yanayi mara dad'i yana bin ilahirin gangar jiki da zuciyarta,gaskiya idan
tarabu da Yaya Julaibib...kai anya? Sai tabar wannan ayyane-ayyanen na zuci.
Yawani marairaice"ALLAH yamiki albarka Zaujatiii...yarik'ota da wani
salo"ko ke zan d'aurama wannan aikin na lalubo mana mafita danni dai har yanzu na
ka sa, amma ko bama tare Zaujatiii...ki rik'e wannan a zuciyarki "ke ce mace ta
farko dana fara k'auna,k'auna irin wannan ta aure zan kuma cigaba da k'aunarki ko
da bama taren.Jikinta yadad'a yin sanyi da jin kalmar nan ta rabuwa...ganin hakan
da tayi sai yacigaba da zugata ta hanyar kambama halayenta na kwarai,da kuma
mamakin da yakeyi wai ita da kanta take ikirarin saki bayan ta san hadisin Manzon
ALLAH da yace duk macen data nemi mijinta yasake ta batare da wata hujja ta
shari'aba toh k'amshin aljannah ma bazata shak'aba,kuma shi k'amshin aljannah ana
fara shak'arshine tun daga tafiyar shekara d'ari biyar,haba Zaujatiii...da ilminki
da wayonki da kome na ki,tayaya wasu dangin miji can za su rabamu,bayan basu suka
had'amu ba,ni fa nake auren nan ba wani ne yakemin ba,ai nine zan miki gorin
haihuwa kece kin d'anji haushi ko?Karki kuma d'aga hankalinki a kan duk maganar
masu magana,sau nawa muna zuwa ganin likita akan rashin haihuwa ana kuma bamu
tabbacin dukkanmu lafiyar mu k'alau lokacine kawai baiyi ba,ba da bakinki kikace ke
kin daina shan wata k'waya dan neman haihuwa kin barma ALLAH ba?Me Yaya Asma'u za
tayi ta6ata miki rai?Yau kika san halinta?Ai tun kafin mu zama ma'aurata kin sani
dan ko gidanku taje sai tanuna wannan halin na ta,kin gani ganin idanunki ke
ganauce kuma jiyau..
Rashin haihuwa ba k'ask'anci bane wallahi,Idan kika duba gidan Manzon
ALLAH a duk matanshi ba wacce ya keso sama da Nana A'isha kuma har ta koma ga ALLAH
bata haihu ba,bayan ita a kwai wash matayen na shi da basu haihu ba,to me garage
darajarsu?Annabawan ALLAH nawane da basu haihuba?
Ganin damar ALLAH me idan yaga dama yabaka Ya'ya maza zallah,ko yabaka
mata zallah,ko yahad'a maka maza da mata,haka kuma ganin damarshice yabarka
bakarare(Mara haihuwa) kinga da...
Bai k'arasa furucin shiba ta k'ank'ameshi tana kuka,yayi lallausan
murmushi dan hak'anshi ta tadda ruwa,yacigaba da rarrashinta"Zaujatiii...ni
D'ansarai ni ne me auren nan kuma na ce mutu ka raba,ko kin haifa min Ya'ya ko baki
haifa min Ya'ya ba,kuma na miki alk'awari zan yima tufkar hanci,ba me kuma samun ke
a damuwa a dangina,su suje su rungumi mazajensu cikin annashuwa ni kuma su dagulama
Zaujatiii...nah lissafi?Toh karki damu kinji ko?Tad'ago takalleshi"Ya'ya D'ansarai
nagode maka da wannan tunatarwar ta ka"idan rai ya 6aci to bai kamata hankali ya
gushe ba...kai mijin alheri ne;tasauke gwauran numfashi
"Rayuwata idan babu kai a cikinta za a samu tasgaro me tarin yawa,tadad'a
k'ank'ameshi tana shak'ar k'amshin deodorant da arabi'an perfume d'inshi,yad'ago
fuskarta suka kalli juna yad'an dage kira yana mata wani kallan k'auna yana
murmushi "mun zama k'arfe da mayen k'arfe ko? Tajijjaga kai"eh wallahi autan
Inna,D'ansaran Baba,Zaujiii... Ustazun Sudaida yar Ibrahim,jikar Ibrahim Me-
Lambu.Suka sumbanci juna yace kuma"mayyar rake abin ma yasamu shiga wai d'an wake a
hotel har da injin d'in matse ruwan ko da ta zama tsohuwa ba hak'ora ko?
Tad'an daki k'irjinshi,shi kuma yabata marin soyayya suna
dariya.Tad'auki wayarta a saman tebur d'in ta kunna"toh kira Inna gaskiya dan ta
damu da rashin jinka tunda har takirani.Yagirgiza kai "gwamma mutafi Zonkwa ayi
kome idanu na ganin idanu"zan fad'a mata kece kika hanani.Tad'auki jakarshi taraya
a kafad'a suka fito daga office d'in, suka jera suna tafiya zuwa inda ake ajiye
motoci da mashinan malamai tana fad'a mishi"Inna baza ta ta6a yadda ni na hanaka
kiran taba,tunda ni kullum sai mun gaisa ko ta kirani ko in kirata.
Watannin Sudaida bakwai kenan da tafiyarta Gidan-Waya,duk wannan
watannin zuwanta Zonkwa sau hud'u,yanzuma tanata mishi magiya yabarta taje tunda
sun samu hutu amma ya hana,wai tayi zamanta a in da mijinta yake ai shine zai fi
mata kwanciyar hankali,tagyad'a kai"ni ma na sani ai bawani dad'e wa zanyi ba mak'o
d'aya dan ALLAH, amma ya hana,haka dole ta hak'ura,dangin Julaibib kuma sun barta
tana rawar gaban hantsi bata san me yafaru ba,amma tabbasss...ta dad'a yadda da
kalaman shi kamar yadda yace ba me sa mishi mata a cikin damuwa.
Da safe tana kwance tak'i tashi tahad'a mishi shayin shi ko ruwan
wanka,shi yamusu kome,yagama shiryawa sannan ya zauna a gefen gado"Sudaida yakira
sunanta.Tad'ago tana kallanshi yana sanye da babbar riga yar ciki da wando na farin
yadi yana karya hular zita"har yanzu baza ki tashi daga kwanciyar k'asan nan ba?
Tasauke idanunta k'asa"ni dai nafi jin dad'in nan.Yagyad'a kai"sauri nake yi
damunje asibiti.Tamik'e zaune dakyar"ba sai munje asibiti ba,naji sauk'i Yaya
D'ansaarai.Yagirgiza kai"za dai kiji sauk'i,tun yaushe nakai miki ruwan wanka amma
har yanzu baki tashi kinje kin yiba?Yamik'a mata hannayen shi"ta so muje in cud'a
ki.Tayi yar dariya"bayan ka shirya?Ai zaka 6ata adon ka,yi tafiyarka yanzu zan
yi.Yad'an motsa kafad'a"uh to menene a ciki,ba sai in canja wasu kayan ba? Tamik'e
tana mishi rakiya,kad'an ta taka mishi ta dawo tayi kwanciyar ta dan dama bata so
tayi wankan,idan tafad'a mishi to sai ya tilasta ta yin wankan ko ta so ko tak'i.
Har yadawo tana kwance yayi tsaiii...yana kallanta yana bin d'akin da
kallo,ba abinda tayi yakad'a kai cikin damuwa"wannan ba halin Zaujatiii...bane
tabbasss bata da lafiya.Dakyar yatashe ta sai wani narkewa takeyi, amma tanayin
wanka sai tajita garau...yana kallon tashar larabawa suna nuna yanayin al'adunsu
yana cin gasashshiyar kaza me kayan lambu tashigo yabita da kallo tana sanye da
material bak'i me yarfin filawoyi ruwan k'asa, d'an kunne,sarka da warawarenta na
zinare sai d'aukar idanu sukeyi saboda kyallinsu,fuskarta shar da kwalliya, bakinta
yana kyallin jambaki ja.
Tazauna suna kallan juna "Zaujatiii...kinyi kyau dame kike son tukwuici?
Tad'ora ha6arta a kafad'arshi tayi furucin da wani salon shagwa6a "agada(plantain)
yajuyo yakalleta"kin cinye wannan agadan dana siyo miki ne?Ta amsa kai
tsaye"wallahi tun jiya.Yabud'e baki dan mamaki saboda ada shi yake matsa mata
tasoya musu dan ba wani dad'ata da k'asa yayi ba,amma a yan kwanakin nan cin agada
takeyi kamar ta samu abincin gado,d'an kullum, ranshi yadad'e me martaba tuwo miyar
kuka abincin hausawa.Kai shifa bai yadda ba sai da yaje yaduba in da suke ajiyewa
yaga ba kome sannan yadawo yana cemata lallai kinyi k'ok'ari,yad'auki waya yana
kiran wani mak'ocin shi da yau yatafi Jos kuma anjima zai dawo dan ALLAH yasiyo
mishi agada.
Yasake kallanta bayan yagama wayar amma fa na d'auka bakya jin dad'i danaga
tun safe kina ta bacci har shabiyun rana.Ai na fad'a maka lafiyata k'alau kawai ni
dai nafiso in kwanta in yi baccine.Ya mata nuni da kazar.Tagirgaza kai dan ko
sha'awar ci batayi,tad'auko lemun peach tana sha suna hira jefi-jefi suna kallansu
har suka gama shirin,sannan yamik'e zai koma makaranta "adawo lafiya.Takashe kallan
tad'auki wayarta ta kunna data zuwa duniyar yanar gizo...
Da daddare kafin yadawo daga sallar Isha'i Sudaida tayi baccinta a inda ta
idar da nata sallar. Yatasheta"Zaujatiii...ga agadan an kawo.Dakyar tad'an bud'e
idanunta da yanayin bacci takalleshi sai ta mayar ta rufe,tayi wani juyi tana dad'a
shemewa a dadduma"barshi sai da safe ni bacci nake ji,tacigaba da baccinta sai kuma
tamik'e zuwa d'akin bacci.
Yabita da kallo har tashige.Shi kad'ai yayi zaman D'akin-shak'atawa yaci
abinci kad'an, yaje yahad'a shayin shi da baya gajiya dasha.Yagama yan rubuce-
rubucen shi har zuwa sanda bacci yafara kawoma idanun shi ziyara,yashiga d'akin ta
kashe wuta,yakunna fitilar wayar shi yana hasketa" tana kwance a k'asa kuma yau
tsabar jin bacci ko kayan bacci bata tsaya sawaba,yad'anyi murmushi yana cigaba da
kallanta numfashi na shiga da fita cikin kwanciyar hankali,sai tamishi wani irin
kyau na musamman, ya dad'a gyara mata rufa dan yasan ko ya maida ita gadon to sai
ta sauko wai ita k'asa yafi mata dad'i,yakashe fitilar yakwanta yana musu azkar
d'in bacci.
Abinda yaketa maimaituwa kenan,kullum bata da kuzuri,bata san yin kome sai
kwanciya,yau dai abin ya isheshi,dan haka yana dawowa daga Kaduna jakarshi kawai
ajiye,yatasata agaba sai tashirya sun tafi asibiti dan daren jiya kusan kwana
sukayi tana mishi wash...wash...mararta tana mata ciwo amma abin mamaki baturiya da
suna manga gari na wayewa sai tamik'e wai ta warke,yanzu kuma yadawo ya ganta
lamooo bata da wani kuzari sai bacci-dai bacci dai bata gajiya...Yabita d'akin
tanata nuk'u-nuk'unta"Zaujatiii...hijab d'in ne baki gane ba kome?Tabud'e wardrobe
tad'auko.
A k'ofar gida sukayi kaci6is da motar Musaddiq tsayuwar shi kenan suka
fito shi da Hajiya. Sudaida tarungume ta tana murna"oyoyo Hajiyarmu sannu da
zuwa,suka koma ciki.Julaibib yayi murmushi"yau farar ranace agaremu me kyakkyawar
suna.Hajiya ta ajiye kofin lemun"to ance ka gaida me gaisheka,kunzo nan kun share
waje kun manta da kowa kuna sha'anin gabanku.Julaibib yasa hannu yana shafa
kwantaccen bak'in gashin kanshi "munata fama dai da ayyuka da d'alibai Hajiya.
Ganin Hajiya yasa Sudaida ta nemi kasalar data rufeta tarasa,tashige
D'akin-girki tana k'ok'arin shirya musu abincin data cema Julaibib ita yau baza
tayi wani girki ba,yad'an motsa kafad'a" duk d'aya 6arin manshanu a miya, dan shima
ba kullum yake cin abinci me nauyi da daddare ba.Musaddiq dai bai tsaya cin wani
abinci ba Sudaida tafito suka gaisa yamusu sallama suka fita da Julaibib.Har suka
gama cin abinci bai dawo ba, takwanta suna hirarsu me dad'i da Hajiya,bacci yafara
d'aukanta sama-sama, sannan taji sallamarshi yashigo musu da gashashshiyar
kaza,bata tsaya ciba tamusu sai da safe taje tayi kwanciyar ta tana jinsu sunata
hirarsu, ita kuma baccinta rabi-da rabi tayishi saboda ciwon maran d'aya matsa mata
daren jiya to yauma daren yayi shine yace bari ya motsa.
Yadawo daga masallaci sallar asubahi yaganta tsugune a bakin famfo
tana ta yunk'urin amai amma yak'i zuwa,Hajiya tana mata sannu,tarik'ota suka koma
D'akin-shak'atawa takwanta a doguwar kujera jikinta a mace yake murusss"sannu ALLAH
yasauwak'e"Hajiya ta zauna tana mata fifita ganin yadda tajik'e sharkaf da zufa
kamar wacce tafita motsa jiki da sanyin safiya.
Yazuba mata idanu zuciyarshi ba dad'i saboda yadda take dad'a rintse
idanunta tana mirgina kai gefen hagu zuwa dama tana yarfe hannuwa,tana ta6a mararta
da take mata wata irin d'aurewa tamauuu...ita kad'ai tasan azabar da take ji,
wucewar wasu dak'ik'u cikin ta ya dad'a yamutsewa ciwon yana k'aruwa,mararta kamar
zata 6alle,Hajiya itama ta shiga cikin damuwa"Sudaida wai meke damunkine?wai!
Wash...wayyohALLAHnan...uhhh...washhh.. tasake yarfe hannun hagu na dama na saman
mararta,da kyar tayi furucin"Wayyoh! Hajiya marata ce take ciwo. Julaibib yajuya
dan tsayuwar ba amfani, motarshi kuma ba ishashshen mai"Hajiya barin samu mai yanzu
mutafi asibiti.Tagyad'a kai"to hanzarta dan naga abun yana dad'a k'amari.
Wayyo ALLAH! tafad'a a galabaice tayi nishin wahala...uhhh...Hajiya
marata!"sannu Sudaida yanzun nan Julaibibi zai zo mutafi asibiti.Ta cije le6enta na
kasa ta yunk'ura zata mik'e zaune amma ta kasa;Hajiya ta taimaka mata,tad'ora kanta
a kafad'ar Hajiya idanunta na rufewa da bud'ewa cikin azabar ciwo,cikinta na cigaba
da hautsinewa ciwo na k'aruwa,da marar tayi wata irin murd'ewa sai ta k'ank'ame
Hajiya tana Istirja'i da salati, tasake k'ank'ame Hajiya iya k'arfinta tayi wani
nishi sai kawai taji wani ruwa me d'umi ya 6alle mata da kyar taduba sai taga
jinine,cikin yan dak'ik'u zanin jikinta ya jik'e sharkaf,zata tashi jiri
luuu...yayi awon gaba da ita ta zube a jikin Hajiya cikin d'aukewar numfashi.
Hajiya ta rikice tashiga jijjigata amma ko motsi ga jini na cigaba da
zuba, saboda rikicewa sai tarasa me ma za ta matane?Tana cikin wannan halin
Julaibib ya turo k'ofar yashigo.Cikin tsinkewar zuciya yake kallansu saboda ganin
Sudaida da yayi kwance cikin jini male-male,k'wak'walwarshi bangaren tunani da
adana bayanai yafara tariyo mishi shud'add'en abinda yafaru a shekarun baya lokacin
da Bilkisu take kwance sam6al cikin jini fuj'atan.Dammm...yaji ruguzowar wani abu a
k'ahon zuciyar shi"Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un...baiyi wata-wata ba yasa
hannayenshi ya cicci6eta cikin tashin hankali yayi mota da ita,Hajiya tabiyo shi.
Sun 6ata lokaci suna dubata sannan wata ma'aikaciyar jinya
takirasu"kaine mijinta? Yajijjaga kai kawai.Tad'an kalli Hajiya sannan tamaida
kallanta gareshi"yarinyar nan gaskiya tana mugun jin jiki kuma matsalar ta fi
k'arfin mu,tunda sai an mata aiki kuma likita baya nan,to sai ku gaggauta kaita
wani asibitin,irin wannnan zubar jinin idan yazo da k'arar kwana sai a rasa
mutum."ALLAH yabata lafiya yasa kaffarace.
Tajuya tayi tafiyarta.Hajiya ta kalli Sudaida bata san wanda yake kanta
ba.Julaibibi mu san abinyi mana.Idanun shi sun kad'a jawur,yayi wani huci cikin
tashin hankali sannan yaba motar wuta,a guje yafito daga harabar asibitin suka
fad'a kwalta zuwa wani asibitin.
Dasauri suka d'auketa zuwa d'akin agaji da taimakon gaggawa suma sun
6ata lokaci sannan likita tafito suka bi bayan ta zuwa office suna tambayarta me
yafaru?Yajikin na ta?Ku kwantar da hankalinku.Tadanyi rubuce-rubucenta a katin data
shigo dashi tagama taturashi a aljihun Labcoat d'in ta, sannan tad'ago cikin
natsuwa ta kalli Julaibib"ka gane ko,matsalar matarka sai an mata aikin gaggawa,
idan ba haka ba za ta iya rasa ranta,saboda ciki tasamu amma ya zauna a bayan
mahaifa.
Shi da Hajiya suka kalli juna sannan suka kalleta cikin murna da
mad'aukakin mamaki.Yayi yar dariya"ciki likita?Tajijjiga kai"eh ciki.Suka shiga
tasbihi ga buwayi gagara koya dan furucin likita ya zo musu a bazata."Julaibib yayi
sujudush-shukri.Likitar ta cigaba to amma an samu matsala dan cikin har ya fashe,
abinda yasa take wannan serious bleeding d'in kenan (rupture ectopic pregnancy)kuma
wannan aikin dole sai Gynea Doctor(likitar dake mu'amala da abinda yashafi
lalurorin mata)kana...Julaibib yatari numfashinta"to ke fa?
Ni nan da dak'ik'u talatin zan shiga wani aikinne(operation) amma karku
damu dan nayi waya da Doctor Kagarko itama kwararriyace yanzu haka tana kan
hanya.Tabud'e dirowa tad'auki wani fallen littafi tayi rubuta sannan ta fad'a mishi
adadin kud'in da zai biya,tamik'a mishi wannnan fallen littafin kaje kabiya kud'in
sannnan kaje a d'auki sample d'in jininka idan yazo d'aya danata basai an siyaba.
Yamik'e yaje yabiya kud'in,kuma yasa hannu sannnan yawuce aka d'auki jinin shi ana
dubawa akaga yazo d'aya sai aka wuce dashi laboratory dan tantance sahihancinshi
kafin ak'ara mata.
Doctor Khadija Aminu Kagarko tak'araso, matar me hankali da natsuwa
ga tarin ilmi da ya ratsata,ta gaishe da Hajiya cikin girmamawa"ki mana addu'a
Ubangiji yasa a dace.Hajiya tagyad'a kai"ALLAH ya amsa yar nan.Hajiya da Julaibib
sunata kai-kawo bakunansu d'auke da addu'o'i tunda aka shiga da ita d'akin
theatre,har akayi aikin aka gama aka fito da ita agadon marasa lafiya ana turata a
hankali dan zuwa d'akin hutu,idanunta a rufe bata san in da takeba,ta d'ashe saboda
rashin ishashshen jini,yasauke gwauran numfashi"Alhamdulillahi an tsallake tsirad'i
d'aya na yin aikin cikin nasara,saura na farfad'owarta,ALLAH yasa tafarfad'o cikin
hayyaci da lafiya.
A sanda rana tatafi zata fad'i magriba na shirin kunno kai Sudaida
tad'an motsa da alama maganin da suka ba ta na anaesthetic ya fara
sakinta...wucewar wasu dak'ik'u kuma tayi motsi da fatar idanunta sai kuma tad'an
bud'e idanun tana bin Julaibib da Hajiya da suke rige-rigen yi mata sannu,a hankali
bakinta yamotsa tana salati, sai kuma ta yunk'ura zata tashi,yarik'eta da sauri
"Zaujatiii... kiyi hak'uri kinga aiki aka miki kar a samu matsala,takoma takwanta
ta damk'i hannunshi tamau tafara kuka mara sauti saboda jikinta ba k'wari"ni dai ku
yafemin mutuwa zanyi furucin a hankali yake fita muryar kamar bana taba, sai kuma
tafara sambatu
"Dan ban haihuba sai a dinga min cin kashi? Ni zan ba kaina haihuwa?
Shima autan Inna ai ina jin haushin shi dan bai kawo min agada ba,har madidi nace
yasiyo min amma yak'i...Hajiya cikina ciwo yakeyi marata... wai...wayyoh
Zaujiii...ni fa ba na san wannnan kallan na ka dan haushi yake bani...kai fa
ran...da sauri yasa tafin hannun damarshi yatoshe mata baki dan kartayi kato6arar
da zai sa shi jin kunyar Hajiya tunda ba a hayyacinta take ba kome ya d'arsu a
zuciyarta fad'arshi za tayi.Ganin tak'i sakin hannun Julaibib dan yakira likita
yasa Hajiya ta tafi kiranta"to fa tashin hankali gobarar gemu...
Magani a shaka badan yunwa ba.
Kome tsawon giginya daga k'wallo tafara.
2 Rajab 1441
25 February 2020
We Ibrahim's Daughters👇
Asdilat KD...2geda with Ra'ibs.
DANGIN NONO WRITERS ASSOCIATION
{Da Inganci Mukayi Fintinkau}
Bismillahi wabihi nasta'in.
...GWAJIN DAFI💔
Almost true story
Daga alk'alamin🖊
Ya'yan Ibrahim
Saudat A.Baba (Asdilat KD)
Da
Bara'atu Ibrahim (Ra'ibs)
Shafi na ashirin da uku.
Kwanakin su uku Doctor Khadija Aminu kagarko tabasu sallama dan
Alhamdulillahi ta samu sauk'i, wata ma'aikaciyar jinya tana tsokanar Julaibib
saboda yadda yadamu da Sudaida,lokacin ba da magani (medication)nayi idan basu zo
ba da kanshi za shi yakira su"ALLAH dai yasa d'an daza'a haifa yamaka kara yayi
kama da kai dan ba k'aramar hidima kayi ba.Yayi murmushi kawai yana shafa
kwantaccen bak'in gashin kanshi.Mutan Zonkwa ma d'ai-d'ai kune wad'anda basu zo
dubiya ba a cikin yan'uwa da abokan arzik'i.
Doctor Kagarko takalli Sudaida cikin kulawa"ki kula da kyau kinga
aikine a jikinki,banda aiki bare d'aukar abu me nauyi okey?Sudaida
tagyad'a.Tarakasu har wajen mota, Sudaida tashiga tazauna sannan ta rufe musu
motar, tad'an sunkuyo ta taga"Hajiya ALLAH yakiyaye hanya. Madam adinga kula da
dressing d'in wajen yadda yakamata, kidawo akan lokaci kar fa kiyi sakaci.Tad'aga
hannu tana musu adabo,suma godiya sosai suke mata.Doctor Khadija Aminu Kagarko ta
san ya kamata.
Julaibib da Hajiya su suka cigaba da kula da ita da ayyukan gida.Watannin
Hajiya hud'u tafara musu zancen tafiya.Sudaida tawani marairaice"Lillahi warasulihi
Hajiya yanzu sai ki tafi kibarni?Tagalla mata harara"to da ni zan tayaki zaman
auren?Taware yatsunta hud'u watannina haka a gidan nan,ai ko na yi iya abinda zan
iya.Julaibib yagama abinci yazubo musu a faranti"sannu da aiki Zaujiii...Yayi
murmushi kawai,yashige bayi yahad'a mata ruwan wanka
"Sudaida ga ruwan can kije kiyi wanka.Hajiya takama fad'a"kai Julaibibi bana
ce kadaina kai mata ruwan wanka ba?Ruwan kawai da za ta bud'e famfo ta tara sai an
mata kai haba,tanuna shi da yatsa "kazama jarumi dan a haka nasanka.Sudaida tamik'e
kaji matar nan da wata magana to ko wankan ma idan takama ba shi zai min ba?Tamata
dakuwa"ungo nan,zancen banza kawai dan an miki aiki shikenan kuma ke bazaki dinga
motsa jikin kiba? Sudaida tawuce batayi magana.
Ita kuma Hajiya tana dad'a jaddada mishi gobe Insha-ALLAH zan koma in
da nafi wayau Zonkwa.Yagyad'a kai sannan cikin girmamawa yace"ALLAH ya nuna mana
goben da ran mu da lafiya...mungode kwarai Hajiya ALLAH yak'ara nisan kwana me
amfani.To amin kaga ai kai ka san yakamata,ita wancan matar taka ai bata gode min,
niko ba in da zan fara azumin watan ramadana sai a d'akina. Kiyi hak'uri Hajiya
bari tafito ai dole kuwa tagode miki.
Suka cigaba da hirar su har Sudaida tafito,yad'ago yana kallan surarta a
cikin hasken farin watan daya haskesu"kinyi kyau Zaujatiii...Hajiya tagalla musu
harara musamman Julaibib daya kasa daina kallanta,takad'a kai"ba shakka ai kinji
sauk'i tunda kika iya zama kiyi wannan kwalliyar abin ma bai tsaya anan ba kikabi
jiki kika shafeshi da wannnan shu'umin humran me k'amshin fita a hayyaci,to ni kuwa
zaman me zan kumayi?
Sudaida tayi lallausan murmushi"haba Hajiyarmu ban fa sanki da halin
sa'idawa ba,yanzu har wani kwalliya nayi?Ko unguwa ai zan iya fita a haka.Eh to in
dai kai kikaci(hauka)ai bazan musa ba.Suka kalli juna ita da Julaibib tamishi wani
kallo ta kashe mishi ido...Yakai hannu yana shafa kwantaccen bak'in gashin kanshi a
hankali ya motsa la66anshi,Sudaida ta matsa kusa dashi"ni dai Yaya D'ansarai ban
gane me kake fad'a da la66a ba gaskiya.Hajiya tamik'e"abin nayi ne to ALLAH ya
tashemu lafiya.Sudaida tace kai Hajiyarmu yau da wuri haka zaki kwanta?Eh dan gobe
sammako zanyi Julaibibi sai da safe.To Hajiya ALLAH ya tashemu lafiya.
Washe gari tun daga sallar asubahi bai shigo gidan ba sai da hantsi
yadubi ludayi da kaya nk'i-nik'i,duk suka bishi da kallo har yagama shigo dasu
sannnan yazauna suka gaisa.Hajiya tace"ai na zaci guduwa kayi saboda kar in tafi
dama nace anjima kad'an tafiya ta zan yi ko kadawo ko baka dawo ba tunda duk
wayoyinka a guda kabarsu. Mantawa dasu nayi sai da nayi nisa da tafiya sannan na
tuna.Jos natafi na miki siyayyan tsaraba dana azumi.Hajiya tabi manyan ledojin da
kallo tana jinjina k'ok'arinshi tare dasa mishi albarka"Ubangiji yayi albarka,
yabaku masu muku madallah nagode nagode Julaibibi. Yayi murmushi"ai ba kome Hajiya,
yad'an kalleta cikin natsuwa "na so kwarai da dakaina zan kaiki to amma hakan bazai
yiwuba saboda yanayin aiki,yanzu ma Kafanchan zan tafi amma na ma wani direba
magana k'arfe d'aya na rana zai zo kutafi,yasake bata wasu kud'ade sannnan yamik'e
dan shirin tafiya Kafanchan.
Sabo turken wawa...kowa yayi fushi da bak'o ya ji kunya,da Hajiya
tatafi sai taji gidan ya mata girma gashi shima Julaibib ba ya nan tagaji da
nazarin da takeyi a cikin na'ura me k'wak'walwa ta rufe, tasa bayan tafin hannunta
na hagu tana Isti'aza tare da rufe bakinta saboda hamman da tayi.Julaibib yashigo
da sallama, yazauna a kujera a gajiye lik'is yacire riga yabar farar singlet. Sannu
da zuwa Yaya D'ansarai.Ya aikin? Yafurzar da iska tabaki ta hanci"aiki ba dad'i
kuma ba dama a bari.Wayyo! neman halali da wuya,kowa ga ganshi a inuwa tabbasss ya
sha rana sannu Zaujiii...nah,tad'an shafa kwantacciyar gargasarshi"ubangiji yak'aro
lafiya ta gangar jiki da natsuwar zuciya,tad'ora ha6arta a kafad'arshi,tagewaye
hannayenta tana mishi tausa. Yasauke numfashi yana jin gajiyar data lullu6eshi tana
tafiya a hankali a hankali"Shukran jazilan Zaujatiii...Yad'an bud'e idanun shi daya
rufe yakalleta "kin cinye agadan?A ah ai yanzu kad'an nake ci dan yafara fita
kaina.Yayi murmushi.
Kafin tagama abinci takawo mishi bawan ALLAH har yafara bacci sai da
ta tashe shi tana mishi dariya"yau baza ayi nazarin karatu anjima ba kenan?Yayi
mik'a yana salati"gaskiya yau ba nazarin karatun dazanyi,kin san tun a office nake
gyangyad'i saboda baccin da kika hanani daren jiya.Takama ha6a tana yar dariya"Kai
Yaya D'ansarai nice na hanaka baccin?Yagyad'a kai.Tayi yar dariya"au to shikenan ta
kwana gidan sauk'i daga yau bazan kuma hanaka bacci ba shikenan ko?Yamata wannan
kallan da bata so yayi bismillah yafara cin abincin data zuba mishi.Takauda kai
tana k'unk'uni dan wallahi haushi kallan yake bata.
Ramadan wata me albarka,wata me alfarma.Tana kwance ta kifa fuskarta
a cikin matashin,ya san ba bacci take yiba tsabar jin jikine kawai,tunda ko da da
take ita kad'ai azumi wahala yake bata bare yanzu ga ciki,bataji shigowar shiba sai
da yazauna a gefen gadon yadafa bayanta "Zaujatiii... Tamik'e zaune dakyar tana
kallan shi bata da kuzari kona sisin kwabo.
yakalli cikinta yayi girma yanayinta ya canja gaba d'aya,tausayinta da
k'aunarta suka mamaye ilahirin gangar jiki da zuciyarshi "Zaujatiii... Ki hak'ura
da azumin nan mana,kinga wahala kike sha,barin had'o miki shayi kawai.Tawani
marairaice "haba Yaya D'ansarai kalli agogo kagani k'arfe uku saura kwata na rana
sai in karya azumi? Uh to menene ai kina da lalurane.A ah kayi hak'uri ai azumin ma
ya kusa k'arewa tunda nayi ashirin to ai ko tara ko goman dasuka rage bazasu gagara
ba Insha-ALLAH za k'arasa dani,nima ina kwad'ayin dacewa da daren"lailatul
qadri".Yagyad'a kai"Toh ALLAH yasa mudace da wannan dare daya bambanta da darare
dubu a daraja,ALLAH yabaki nak'uda kafiifan(me sauki) Tayi murmushi"amin Yaya
Julaibib.
Yarik'o hannunta tamik'e suka fito waje suna d'an tattaki har zuwa
bayan gidan in da sukayi yan shuke-shuken su kamar su alaiyahu,ganyan ogu,
timatir,attarugu,zogale,d'ad'd'oya(scent leave)da sauran su, dakyar ta zauna a d'an
k'aramin dakalin wajen tasa hannu tana tsinkar lemar kwad'i/naman k'asa(mushroom)ya
tsuguna yana tayata tare da tambayar ta"yau kuma me za kiyi dashi?
Tun safe natashi da sha'awar shan romon shi(mushroom sauce) yad'an kalleta"ni
fa yau a tsarin abincin mu ba shinkafa.Toh Yaya Julaibib,ni ma ba da wani abu zan
had'a ba haka kawai zanyi romonshi in sha. Suka gama tsinka sannan suka wuce
D'akin-girki yakar6a yawanke ya yayyanka mata, yad'uko kaskon suya yazuba magyad'a
kad'an yad'ora a wuta sannan yakalleta"to na miki me wuyan zo kibashi tsoro.
Tad'an kalleshi a marairaice nagode,to amma Yaya D'ansarai...sai kuma tayi
shiru"uhun menene kuma?
Tanuna mishi abinda take so yayi.Yad'auki wuk'a da albasar yana mita"ni fa a
duk aikin gida ba abinda yake bani haushi irin yankan albasa,tagyad'a amma kuma
kafi kowa san albasa me yawa a girki,jiyama ai miyar albasar kasani nayi dayake ba
kai kake yankawa bako? Eh mana...sukayi dariya yana fara yankawa idanun shi suka
fara ruwa, yarintse su"Zaujiii...Karfa kayanke"eh ai kin san zan iya yankewa amma
kika sani,da sauri yayi yagama yana fad'in"kai gaskiyar bahaushe da yace albasa
batai halin ruwa ba, yawanke hannayen shi da omo,yanad'e hannu riga toh aikin dai
aikine an ba kuturu tallan jakai"yad'auko abin markad'e(blender)ina karas d'in dana
gyara d'azu?Ai na had'a maka lemun,yana cikin fridge.Yawarware hannun rigar"yauwa
Zaujatiii...Kin kyauta nagode ALLAH yamiki albarka.
Yanzu barinje in yi alwala lokacin tafsir ya kusa,kuma yau d'in nan
Insha-ALLAH nake tunanin zamu rufe sai ALLAH ya kaimu ramadan me zuwa ga masu
tsawon rai.Toh Yaya Julaibib adawo lafiya, kuma dan ALLAH ana idar da sallar
magriba ka dawo gida da wuri kasha ruwa,tazuba mishi dabinon ajwa a aljihu daya
manta bai d'iba ba kaji Yaya D'ansarai?Yad'an dafa kafad'arta"Insha-ALLAH nagode
Sudaida.Tabi bayan shi da kallo cikin yaba k'ok'arinshi da wata irin k'aunarshi da
take dad'a narkewa a sararin cikin zuciyarta.
Safiyar sallah garin yayi lullumi a sanda hantsi yadubi ludayi ta yi
k'ok'ari tagyara gidan da taimakon shi,ko ina yana k'amshin turaren d'aki,
sassanyar iska tana kad'a fararen lubayen da ratsin ruwan hoda saboda rashin nauyin
su.Tana sanye da voil-lace ruwan sararin samaniya(sky blue)doguwar riga dan d'aura
zani wahala yake mata yanzu,d'an kunne,sark'a da warawaran hannayenta da zobe na
zinare,suna ta d'aukar idanu saboda kyallinsu,ga jan lallanta me yarfin bak'i da
tayi k'afafu da hannaye sun k'ara haskata,bata d'aura dankwalin kayan ba sai tayafa
k'aramin mayafi ruwan sararin samaniya me shara-shara,gashin kanta yasha gyara
daren jiya a wajen gyaran gashi da Julaibib yarakata.
Takoma D'akin-shak'atawa tazauna tana kallan shirye-shiryen wasannin
sallah a tashoshi mabambanta aranta kuma tana mita"Yaya D'ansarai ya hanata tafiya
gida taje tayi sallah a cikin Iyaye, yan'uwa da abokan arziki,sannan tun d'azu aka
sakko daga masallacin Idi ya aiko a kar6a musu tuwon sallah shi da abokanshi kusan
awa d'aya kenan,taja tsaki ai ko danko sukeci yaci ace zuwa yamzu sun gama ya
shigo,a hankali tazame takwanta a doguwar kujera tacigaba da kallan amma ranta sam
ba dad'i.
Taji ana sallama tare da k'wank'wasa k'ofa, taja malalacin tsaki a yadda
taji dad'in kwanciyar nan data sani tabar k'ofar a bud'e koma waye tad'aga murya
tace a shigo,tamik'e dakyar taje tabud'e, bakinta yak'i rufuwa saboda mamaki sai
bin yaran takeyi da idanu,suma sunata tsallen murna sunzo gidan Inna Sudaida,za
suci dad'i,yarik'o hannun wasu daga cikin yaran"kai kuzo kawai in maidaku wajen
Iyayenku dama daga masallacin Idi natarkato miki su,ban tsaya tambayar kowa
ba,yad'aure fuska ganin sunk'i motsawa"mitafi nace ko? Wasu suka mak'ale kafad'a,
wasu har idanun su yaciko da kwallah.
Tarik'o hannushi"haba Yaya Aminu talek'o ta koma kenan,yagyad'a kai" eh
mana tunda baza ki bamu hanya mushiga ba basai mu koma in da mukafi wayau ba?Oh dan
ALLAH kayi hak'uri murna da mamakin ganinku ne yamantar dani abinda zan yi tun
farko,tamatsa yaran sunata rige-rigen shiga,suka zazzauna suna tsallan murna wasu
suna fad'in su sun dawo nan gidan Inna baza su wani koma Zonkwa ba.
Yaya Aminu naji dad'i wallahi,tazauna suna gaisawa tare yima juna barka da
sallah ALLAH yamaimaita mana na bad'in bad'in bad'ad'a...tana tambayarshi mutan
gida.Kowa lafiya k'alau Sudaida, mutuniyarki Nasmat ta bani sak'o yana mota,yakalli
yaran sun baje suna cin abinci, hakanan zuciyata taraya min dama kaje wajen
Sudaida, nace musu nan zanzo shine suka dinga rok'ona ALLAH annabi wai suma za
suzo.Tayi yar dariya"ai kuwa nagode daka zo min dasu ALLAH yabar zumunci,dama
kad'aici ya dameni.Yakalleta cikin tausayi dan cikinta ya girma"sai hak'uri
kanwata,kafin mu shigo na ga Julaibib d'in mutane sun mishi yawa,na san haka kawai
bazai kyaleki ke d'aya ba.
To Yaya Aminu kaci abincin mana. Yad'auki wayarshi yana duba sak'on karta
kwana da aka turo mishi"ke ni dama kunu kika kawo min. Takalleshi wani iri "kai dan
ALLAH wani irin kunu yau take sallah fa.Yamaida wayar aljihu"uhun ba a shan kunu
ranar sallah ne kome? Yayi bismilah loma biyar yayi a tuwon sannan yad'auki cinyar
kaza yad'an gutsira yamayar ya ajiye dan baya wani jin yunwa,ai kin san halina ni
nama ba d'ad'ani da k'asa yayi ba, wannan sai su autan Inna kura kyaci da
gashi,tad'an yamutsa fuska"to ai bashi kad'ai bane har da Yaya Musaddiq, yakama
ha6a wuuu...au haka ne?Babbar magana ance da mak'asau bawa,barin kama bakina.Tayi
yar dariya.
Julaibib yashigo aka cigaba da hirar dashi, ranar wunin farin ciki
sukayi,sai bayan sallar la'asar Aminu ya kwashi yaran dayazo dasu cikin
mota,Sudaida takawo musu cin-cin,nama da goron sallarsu,kowa ta bashi a
hannunshi,sunata murna da rige-rigen fad'in" Inna Sudaida nagode,ALLAH amfana.
Takalli Aminu"na rasa me zan baka rabin raina. Julaibib yadafa kafad'arta"juye
mishi ragowar kunun safen nan yatafi yayi farau-farau dashi.Tagalla mishi
harara,yad'an d'age gira yana mata wannan rikitaccen kallan na shi"eyehhh...ni kike
harara?Kinga Sudaida Aminu yakirata,tabishi da kallo daina hararshi haka,yad'auko
sak'on Nasmat data rufeshi da wrapping sheet me zanen zuciya da rafar kud'i yan
naira ashirin guda d'aya"nawa goron sallar.Julaibib yasa hannu biyu yakar6a"toh
Yaya Aminu mungode ALLAH yak'ara bud'i,ALLAH yabarka da Siddiqa tazama tauraruwarka
har gaban abada.Yadda yayi furucin yasa sukayi dariya.
Sudaida tarufe musu motar itama tana godiya,Julaibib yasunkuyo"toh
kagaishe mana da Hajiyarmu kace mata munanan zuwa mata yawon sallah ta ajiyemin
dambun nama,tasa amin kilishi me tsomen aya,yanzu ma zan kirata in fad'a mata.
Yad'aura belt yana dariya"toh kura duk kai kad'ai? Yaran sunata tsalle daga cikin
motar suna d'aga hannu sunama su Julaibib adabo,a hankali yaja motar suka bi
danjojin motar da kallo har tayi nisa tasha kwana ta6acema ganinsu.
K'arfe hud'u na yammacin asabar motar Julaibib ta tsaya a k'ofar gidan
Hajiya.A D'akin-shak'atawa suka sameta tana waya,tagama tasauke wayar a kunnanta
tana murmushi"lale marhabun,yau ina da manyan baki. Takalli Sudaida cikin tausayi
dan ta kasa zama a kujera, zama tayi ak'asa tana matsa k'afafunta da suka fara
kumbura alamar ciki ya tsufa wash...tafad'a tana yamutsa fuska"sannu Sudaida ALLAH
yaraba lafiya.
Kai Julaibibi Sudaida tadawo kenan sai ta haihu ko?A ah jibi zamu koma ni
bazan tafi in bartaba. Hajiya tagyad'a kai"madallah,to idan haihuwar tazo sai kuyi
yaya?Hala ka ta6a kar6an haihuwa ne? Yashafa kwantaccen bak'in gashin kanshi"wannan
karan dai zanyi,Hajiya bar wannan maganar kinji,ai haihuwar ma da saura,yad'an
kalleta kuma ni gaskiyar magana"I can't do without Zaujatiii... besides me.
Bashakka Julaibibi zama da mad'aukin kanwa...ni dai na sanka me kawaici
amma wannan matar taka me suffar takand'a ta fara koya maka rashin ta'ido ko?To
kaji dakyau baza tabikaba,to me zata maka da wannan tsohon cikin?Sudaida tayi
murmushi tana zancen zuci"lallaima Hajiya ni ce na koya ma Julaibib d'in rashin
ta'ido?Yaya D'ansarai wallahi gwani na gwanaye ne bar ganinshi haka Ustazu-Ustazu
baya san magana hummm... takyalkyale da dariya tuno abinda yagama fad'a mata daren
jiya data keta wani sha mishi k'amshi dan ta karance tsabbb...da abinda yake so.
Tad'an turo baki gaba"Hajiya ai gwamma in zauna a suffar takand'a da
dai in zama tashi da nishi...bakiji kirarin muba?Bena bakya tsufa sai dai kiyi
girgiza ki sake sabon gashi,kuma waya jazamin wannnan k'aramin jikin idan ba ke ba?
Takalli Julaibib"Yaya D'ansarai...Kasha kuruminka k'afata k'afarka ai tare ta
gammu.
Yauwa Zaujatiii...tabashi hannu suka tafa, tad'an yafito shi zo kaji,yamatsa
kusa da ita tasaita bakinta a kunnanshi tana rad'a mishi wata magana, suka kalli
juna,yad'age gira yana nunata da yatsa cikin yar dariya"da gaske Zaujatiii...? Ta
amsa kai tsaye"na rantse maka da girman ALLAH.Hajiya takama ha6a ba shakka"wato ana
nuna miki ma'aiki kina rintse idanu,da wannan tsohon cikin kike wannan iya shegen
k'auri da kare? Tawatsa hannu"to ai shikenan jiki magayi baki kuma mafad'i.Yamik'e
barinje shago wajen su Baba"ke sai na dawo zamu tafi gidan Kawu ko? Toh adawo
lafiya.
Yana fita Sudaida tamatsa kusa da Hajiya takalleta cikin
natsuwa"Hajiya na rantse miki da girman ALLAH nima na fiso in zauna a nan sai bayan
na haihu,toh kin san halin Yaya D'ansarai da banyi haka ba ni zai rufe da
fad'a,kilama yace nina kira a waya na fad'a miki,saboda ni ma ina ta damunshi ya
dawo dani gida,shi kuma yana cemin a ah acan zan haihu,dana fara nak'uda wai
asibiti za mutafi, mutumin da a wasu lokutanma har na fara bacci bai shigoba.
Kin san halin miskilancinshi idan suka motsa, maganar duniyar nan za ki
mishi,sai dai yamiki kunnan uwar shegu,yasunkwui da kai bazai yi magana ba ko da me
za kiyi,yamaida mutum kamar wanda yaci kai(hauka)to Hajiya me zuwa fada ga banza
bare kuma Sarki na kira?Hajiya tajijjiga kai"eh lallai kinyi hikima da siyasar
rayuwa a nan, dama idan kasan mutum to sai kaci maganin zama dashi, barni dashi zai
zo zamu sake tattaunawa.
Suna cin abincin dare kiranshi yashigo tad'aga da sallama,ya amsa
muryarshi a dake"har yanzu kina gidan Hajiya ne?Eh Zaujiii... dama yanzu zan kiraka
dan na jika shiru...yatari numfashinta"kin jini shiru,ke makauniya ce dabaza ki iya
tafiyaba dole sai da d'an jagora ko?Tad'anyi murmushi wannan fad'an dawalakin goro
a miya,ba mamaki taran dangi aka mishi akan dole yabarta anan,sai ta fad'a a
tausashe duk shi d'in yace ta zauna idan yadawo za suje gidansu"Esbeer Yaya
D'ansarai nahhh...ganinan zuwa.Hajiya takalleta"karki nuna mishi kin fahimci abinda
yasa shi a damuwa,tarataya jakarta"toh Hajiyarmu mukwana lafiya. ALLAH yasa
Sudaida.
Da sallama tashiga D'akin-shak'atawar, yakalleta a d'age yakauda
kai.Bismillah,wash...ALLAH! tafad'a sanda ta zauna a k'asa dirshan tana maida
numfashi kamar wacce gudun famfalak'i"Yaya D'ansarai na dawo. Yayi kamar ba dashi
take magana ba,ganin haka tasama ma kanta lafiya ta hanyar kunna data tana turama
A'isha sak'o,wucewar dak'ik'u kusan arba'in sannan yamik'e zaune daga kwanciyar da
yayi yakira sunan ta.
Takashe data tana amsawa da na'am.Kishirya gobe da sassafe zamu koma. Gobe
kuma?To saboda me?Hummm...ki bari kawai wai har da Baba a fad'a min ya kamata a
barki,ni kuma bazan iya ba, Sudaida ko baza kimin kome ba to ni dai ina san zamanki
kusa dani,yabud'e idanun shi daya fara rufewa gaba d'aya a kanta"Zaujatiii... ina
k'aunarki ba tare da wani dalili ba,zan cigaba da k'aunarki a kowani hali da yanayi
na rayuwa kingane ko?Tajijjiha kai"na'am na gane Zaujiii...ALLAH yabarmu tare,mutu
karaba takalmin kaza.
Ta sauke numfashi to amma Yaya Dansarai... wani hanzari ba gudu ba,Baba
da duk wanda yace kabarni anan umarni suka ba ka ko shawara?Yad'ago
yakalleta"shawarace ba umarni ba.Tawani marairaice"to in ko hakane bai kamata
kawatsa musu k'asa a cikin idanu ba "Yaya D'ansarai tsakani da ALLAH ba wanda zai
so ya haifi d'a a cikinshi bayan fad'i tashin da yayi a rayuwar d'an nan har yazama
abinda yazama a doron duniya,sannan wani abun yata so,su bashi shawara a matsayinsu
na masoyin shi da suka fi kowa k'aunar shi bayan ALLAH da manzon ALLAH amma yawatsa
musu k'asa a cikin idanu ta hanyar kin kar6an shawarar da suka ba shi ace ransu
bazai sosu ba?Duk fad'in duniya duk wani me da'awar yana k'aunar mu toh daga bayane
sadaka da karuwa,dan da Iyayen na mu basu maidamu mutane a sanda bamu da kome baza
mu iya amfana ma kanmu kome ba to da bamu girman da duk wani me son mu ya so muba.
Tasake tausasa murya"Zaujiii...gyara kayan ka baya ta6a zama sauke mu
raba,nima yanzu d'an mune a cikin cikina,to ai baza muji dad'i mu bashi shawara
bayan mun maida shi mutum yak'i kar6a,bayan kuma shawarar bawai ta sa6ama shari'a
bane"Yaya D'ansarai kayi hak'uri kabarni anan d'in,na tabbatar dan haihuwar
farice,amma da baza su d'aga idanu su kalli rayuwarmu da abinda yake gaban muba, in
dai bamu muka fad'a musu dan neman shawara ko kuma addu'a ba.Zaujiii...Aljannarka a
k'ark'ashin Iyayanka take sai ka bisu ka kyautata musu zaka sameta fa.Tayi murmushi
kasha kuruminka mijin Sudaida ni zan dinga zuwa maka hutun k'arshen mako(weekend)a
6oye,wallahi ba wanda zai sani sai Yaya Aminu dan na san ba zai k'i kawo ni ba.
Kalaman Sudaida gaskiyace wacce daga k'inta sai 6ata,zuciyarshi tayi
wasai,d'aya daga cikin jin dad'in doron duniya samun mace tagari "Zaujatiii...Ke
macen alheri ce,ALLAH yamiki albarka. Kiyi zamanki ba sai kin dinga zirga-zirga
tsakanin Zonkwa da Gidan-Waya ba ni duk lokacin dana samu sarari zan zo ko a
k'arshen mako ko a ranakun mako(weekdays)ALLAH yamiki albarka yabaki nak'uda
kafiifan.
Yana had'a kaya a jakar da zaiyi tafiya da ita yana dad'a jaddada
mata"Zaujatiii...kullum fa kisha ruwan zamzam d'in nan,kici dabino,ki yawaita
addu'a ba dare ba rana,gobe Insha-ALLAH zan ai ko miki da hulba ki fara tafasashi
kina shiga,da kinji alamun nak'uda ki d'ibeshi ki had'a da zuma ki cakud'a kidaure
kishanyeshi kinji ko?Jikinta yayi sanyi sai take ji kamar kar yatafi,ko kuma su
tafi tare tana lumshe idanunta mak'alallun kwallan da suka cika su,suka samu damar
zubowa sharrr...yayi kamar bai gani ba,yagama shirya kome a jakar ya rufe yatafi
yayi wanka yashirya cikin shigarshi ta dogaye fararan kaya kanshi da hular dara
bak'a.
Yagama d'aure bak'in agogo a hannun damarshi,sannan yagewayeta yana
magana cikin tausayi da k'auna"haba Zautajiii...kuka kuma! yafara share mata
hawayen ai ke macen albarkace Sudaida,ban ta6a nadamar zama dake ba ko na sisin
kwabo...haba Sudaidan D'ansarai...Ki k'arfafamin gwiwa kamar yadda ki kayi jiya
mana,wannan hawayen na ki sai su sa autan Inna a uku fa...yacikata da kalaman
k'auna da kambamawa... Itama ta gewaye shi tare da d'ora ha6arta a kafad'arshi
"Zaujiii... na yi shiru...ALLAH yamaka albarka. Yayi murmushi"amin.ALLAH
yatsare min kai, yakiyaye ka da kiyayewarshi,tasa hannu tad'an shafa
k'asumbarshi...wucewar wasu dak'ik'u sunata kallan juna, a hankali suka saki juna
yad'auki jakar shi sannan yad'aga hannu yana mata adabo...Yajuya yatafi sai ta
d'aga labulan taga tana cigaba da kallan shi yashiga mota yad'aura belt yayi azkar
yasa mukulli yatashi motar...har yabar haraban gidan tana cigaba da kallan danjojin
motar yayi nisa ya6ace ma ganinta sai taji wasu zafafan hawaye suna zubo mata
sharrr...shar...tasaki labulan takoma ta kwanta cikin kewar masoyiii...
Shekaru goma sha uku kenan cifff...da auren Julaibib Abdullahi D'ansarai da
Sudaida Ibrahim Me-Lambu. A wad'annan shekarun ALLAH ya zurta su da Ya'ya sanyin
idanu da Bilkisu...kyakkyawar yarinya data d'auko kyan Iyayenta,bak'in gashi me
yawa da tsantsi irin na mahaifinta, sannan ALLAH yabata farar fatar da bana
Iyayenta bane ganin damar Ubangiji ne kawai.Bilkisu yarinyace data yi farin jini a
zuri'arsu kaafatan,gata da natsuwa bata da yawan magana kamar mahaifinta,idan kaji
dariyarta toh dashi suke magana, ga ta da k'wak'walwa duk abinda aka koya mata sau
d'aya toh ya zauna kenan ba ta buk'atar maimaici,tana da kaifin basira.
Bilkisu Julaibib D'andarai...
Shekarunta biyar a yanzu haka tana primary one a makarantar boko,bangaren Islamiya
kuma tana da haddar Izifi goma sha biyar daga Yasin zuwa nasi duk in da kaja mata
Insha-ALLAH zata cigaba.
Sai Maimunatu Julaibib D'ansarai... kanwarta takwarar Inna suna
kiranta Walida me shekaru uku.Sai kuma wani cikin da take dashi.
Julaibib ya d'auki son duniya ya d'orama Y'ayan nan musamman Bilkisu
son ta yake kamar me, saboda dalilai masu yawa,na farko ya sameta a sanda baiyi
zato da tsammani ba,na biyu tayi kama da Innarshi,na uku sunan marigayi daya so
auren ta kamar me amma ALLAH bai k'addari za suyi aure ba,na hud'u Sudaidan da yake
so yake k'auna ita ta haifa mishi,na biyar yarinyar akwai ta da k'wak'walwa da
sauransu da sauran...
A gajiye lik'is yashigo gidan da sallama,suka gewaye juna tana mishi tausa
a hankali yalumshe idanunshi wata natsuwa ta mamaye ilahirin gangar jiki da zuciyar
shi "Zaujatiii...ta iya biyar dashi da lak'antar abinda yafi kwantar mishi da
hankali,yad'an shafa kanta"nagode Zaujatiii...Takawo mishi ruwa yasha,sannan yaje
yayi wanka yasa kaya k'ananan wandon chinos ruwan k'asa da shirt mara nauyi fara,
yazauna yana hutawa,Sudaida tabishi da kallo.
"Zaujiii...kayi kyau,sai ka zama wani d'an matashin saurayi.
Yayi yar dariya"wani saurayi kina ganin Zaujiii...gemu da k'asumbarshi duk
furfura...Ni dai a ah ai bawani tsufa kayi ba gaskiya,kai dai girman kawai kake
so.Sudaida ai ko girma ya zo gasu Baba ga ku ga sauran bataliyar daza ki
haifamin...Yaran suka shigo da gudu dawowar su daga makaranta kenan,suka haye
jikinshi suna mishi surutu.Tace"Oya to muje ku canja kaya...sai suka dad'a
mak'alewa a jikin Julaibib "ku tashi mana.Julaibib yad'aga mata hannu"kyalesu sai
sunyi wanka zasu canja kaya. Tagyad'a kai tatafi tacigaba da ayyukanta.
Tana aikin abincin dare Bilkisu tashigo D'akin-girkin tasha kwalliya
da wata yar rigar turawa mara nauyi ruwan hoda da dogon wando da d'an k'aramin
hijab ruwan hoda,tanata k'amshin arabi'an perfume d'in Julaibib fuskarta shar da
kwalliya,tayi murmushi kawai dan ta san aikin shine,haka yake zama yamata wannan
kwalliyar musamman idan tamata laifi tace baza tayiba,shi kuma zai rarrasheta
yamata.
Tafara ta6e-ta6e irin na yara"Mama in dai tuwo za kiyi ni bazan ci ba
na fad'ama Baba yace to ki mana doya da kwai da nama,kuma ki had'a mana lemun citta
da karas,ni natsani tuwo tana wani yamutsa fuska.Sudaida tajuya takalleta"ALLAH
Hajiya Bilkisu?Bilkisu tagyad'a kai tana sake fuska 6ata ALLAH kuwan Mama.Tayi yar
dariya"Hummm wato ke dai kullum aci me dad'i ko?Kalleki kamar za ki fashe duk kin
fi kowa na gidan nan ki6a,toh yau tuwon dawa miyar kuka nake yi,kuma ba lemu tuwo
za a ci asha ruwa.Tad'an buga k'afa cikin shagwa6a "ni dai ALLAH bazanci wannan
bak'in tuwon ba,gidan Inna zan ce Baba yakaini ai ita zata bani nama,Baba yace ni
ce amaryar shi tana nufin Alhaji Abdullahi,shi kuma zai bani madara da yoghort da
biscuit short cake.Tagyad'a kai"toh a sauka lafiya ni dai yau d'an gado nake yi.
Tagama kome tagyara D'akin-girkin sannan tafito tasame su yana koya
musu aikin gida da aka had'osu dashi daga makaranta amma Bilkisu tanata ta6ara shi
kuma yana wani lalla6ata,suka bata haushi kamar ta dake su.Bata dai kula suba itama
ta zauna tana nazarin wani project...Basu gama aikin ba amma da Bilkisu tamatsa a
tafi sai kawai yabiye mata taje tad'auko mukullin mota yakalleta"Megado nan da
gidan Inna sai munje a mota? Tawani shagwa6e"eh Baba.Yakar6i mukullin to shikenan.
Zaujatiii...Za kije ne?Idanun ta na kan Laptop d'inta ta bashi amsa"uh
uh adawo lafiya. Yakalleta na wucewar wasu yan dak'ik'u" Sudaida yakiraya.bata
amsaba tad'ago suka kalli juna said yawani kashe mata ido d'aya,takauda da kai
kamar bata gane me yake nufi da hakan ba.Yayi d'as da yan yatsunshi"kin ci bashi
wallahi.Tagyad'a kai"eh ba kome bashi ai hanji ne yana cikin kowa,kafad'i ko nawane
zan biya.Yajuya ba fashi kuwa ina dawowa za ki bani.
Tana jin barar"Allazi wahidin...tabud'e k'ofa takar6i robar almajirin
tajuye mishi tuwon tunda d'uminshi dan ta san ko sun dawo shima ba wani ci zaiyi
ba,wanda za taci kawai tabari,yakar6a cikin rawar jiki data murya"Iya ALLAH yabiya
buk'ata duniya da lahira.
Har bayan sallar Isha'i shiru basu dawo ba, taja tsaki ranta ba dad'i
abinda yake ma yaran nan yana neman wuce makad'i da rawa fa,haka Bilkisu take mata
wannan iya shegen k'auri da kare in dai tayi tuwo kai bama tuwo ba ko menene in dai
bata ga dama ba to baza taci ba,sai tace ita wani abu na daban take so,tana ganin
ya dawo zata fara shagwa6a ita yunwa take ji Mama bata ba ta abinda take so ba...
Shi kuma sarki me Bilkisu sai yafara fad'a shifa baya so ta dinga bar
mishi Megado da yunwa tunda ba ta son wannan ba sai a bata wanda take so ba? Ai
Bilkisu yarinyace sai da rarrashi wata rana za ta daina,wani lokacin su shiga
D'akin-girki yadafa mata abinda take so baya wuce soyayyen kwai,ko taliyar
yara(indomie)ko yoghort da donut, wasu lokutan kuma yaje yasiyo musu gasassun kaji
ko nama,itama mayyar naman ce haka za su zauna suci su k'oshi,shi yasa kumatu a
wajenta har da na sai dawa,to ganin haka itama Walida ta ara tayafa in dai tuwo ne
to baza su ciba sai dai in baya gari ta musu jan idanu shine zasu d'an tsakura su
bar mata..
Ita har ga ALLAH tana ganin wannan abun idan aka d'ore a haka to za a
samu matsala fa,ace kome yaro yake so sai an bashi?Haka yake so su taso su basu san
babu a rayuwa ba?Wasu lokutan ko fad'a take musu sai yawani 6ata rai alamar baya
son hakan duk da bai ta6a furta wa ba to amma ai labarin zuciya a fuska ma ana
ganin alama,shi yasa ita kuma in dai Bilkisu ce za tace ayi kaza to baza tayi shi
ba,kamar yanzu da tace atafi gidan Inna, tana son zuwa amma tace baza taba,shi dai
Bilkisu bata laifi a wajen shi kome tayi,idan tafara mata fad'a sai yayi
murmushi"haba Zaujatiii...Bilkisuna guda nawa take ne? Ai za ta bari wata rana.Toh
yaushe ne wata ranar bayan kullum k'ara wayau take yi,dad'a sabawa da hakan take
yi?Itace dai tun yana d'anye ake tank'warashi idan ya girma bazai tank'waru ba sai
dai ya karye.
Dare ya farayi tayi tsayuwar motarshi, yashigo da Walida tayi bacci ya
kwantar da ita ya koma yakulle gidan sannan yad'auko Bilkisu,ai yana kwantar da ita
tafara mutstsuke idanu sai ta mik'e zaune"Baba ina sauran nama na?Naman ki yana nan
kuje kuyi bacci dare yayi sai gobe za kici abinki ko? Tamak'ale kafad'a ni dai a
d'akin baccinka yau zan kwana...
Yayi kamar baiji abinda tafad'a ba.Sudaida tayi murmushi a ranta tana
fad'in"yayi kyau... Tarik'o hannunshi"Baba a d'akin baccinka zan kwana dan
ALLAH.Yagyad'a kai"yashafa kanta na ji Megadona,to maza aje a wanke baki, tatafi
dagudu ta d'auko brush da maclean takawo mishi, yamatsa mata taje tayi tanata
tsallan murna "yau tare da Baba zata kwana, yarik'e hannunta suka tafi. Sudaida
taje takwantar da Walida ta tofeta da azkar d'in kwanciya tagama abinda za tayi
tanufi d'akin.
Suna kwance tamak'alk'aleshi tak'i yin bacci tana bashi labarin yan
makarantarsu da Inna dasu Kawu Aminu,tabisu da kallo Bilkisu wai lallai sai ya mata
tatsuniyar d'an fulani me kiwon shanu dayaje birni.Yayi hamma yasa tafin hannun
dama yarufe baki yana Isti'aza"ni dai gaskiya ban iya wannan tatsuniyar ba
Megadona,dan ban san abinda yayi a birni ba. Takyalkyale da dariya tana d'an bud'e
idanu dan mamaki" Baba ba kace Innace Mamanka ba? Yakalleta da kulawa"eh Bilkisu
itace Mamana.Yad'an yamutsa fuska"amma bata baka labari ba?To gobe zan rakaka
wajenta sai tabaka labari ai muma ita take take bamu labari,har fa da tatsuniyar
gizo da k'ok'i. Sudaida tace"Bilkisu surutun ya isa tashi kije ki kwanta...Julaibib
yatari numfashinta"kyale ta bata jin bacci ko Megadona?Tagyad'a kai a shagwa6e"ai
haka takeyi idan ba kanan wai muje mukwanta.Haushinsu yakamata kawai sai tajuya"dan
ALLAH ku kwana kuna hira.
Sak'onshi yashigo wayarta"Zaujatiii... Kar kiyi bacci fa...ina
lalla6atane.Takashe wayar tayi kwanciyarta"kai ka sani.Sai da baccin Bilkisu yayi
ni sa sannan yabita...yakunna fitilar wayarshi yana haske mata fuska,tasa hannu
takare fuskarta sannan ta bud'e idanu"Zaujatiii baki ga sak'ona bane? Na gani.
Tafad'a a taik'aice...Sudaida ta kin fahimce ni amma kika share ni kina ji Bilkisu
ta tasani agaba.Tadad'a gyara rufa"uh ai duk a cikin lokacin tane, yaushe ko za a
bar ranta ya6aci sarauniya me D'ansarai.Yad'an daki bayanta yana matsa mata hannu a
hankali"yau haka kike jin fad'ar sunan nawa D'ansarai gatsau ba ko sakayawa?Tayi
shiru kamar ba da ita yake magana ba.
Yagewayeta"to gani na zo a bani bashi na... duk da ranta a 6ace yake amma
bata hanashi abinda yake so ba...shima ya fahimci haka shi yasa yake jinta wata ta
musamman a sararin zuciyarshi, Sudaida ba dama ne wallahi,ta gama lak'antar shi,a
cikin ruwan sanyi take hukunta shi sai yazo yana bata hak'uri da bakin shi dan a
zauna lafiya...Yawani narke kamar k'aramin yaro"Zaujatiii... Ina k'aunarki fa I
can't do without you.Batace kome ba tacigaba da bashi wasu sak'onni sai shima ya
biyema yarima su sha kid'a...
A safiyar asabar yara sun sami hutun makaranta Sudaida tamatsa sai sun
tafi Zonkwa dan watanninsu biyu basu je,tagama shirinta tsafff sannan tashiga
d'akin...baki bud'e take kallansu da mad'aukakin mamaki baccinsu sukeyi hankali
kwance ya lull6esu da bargo,tun d'azu fa tahad'a ruwan wanka za ta musu yace tabari
zai musu taje tahad'a musu abinda za suci suna gamawa sai tafiya amma shine bayan
fitarta suka koma su kayi kwanciyarsu,wato sune masu idanun jin bacci ko? Tayaye
bargon tana tashinsu ya bud'e idanu,ta6ata fuska "haba dan ALLAH Yaya D'ansarai kai
bakiyi wankan ba,su baka musu ba?
Yaziro k'afafunshi k'asa"kin san akwai sanyi ban san sanda baccin
yasake awon gaba dani ba barinje in yi...tunda yashiga wanka ta san ko ya fito
bazai musu ba, dan haka tatashi Walida taje tamata sai da tagama shiryata sannan ta
tashi Bilkisu tamata tad'auko shadda getzner ruwan makuba yasha aiki da zare ruwan
zinare da wasu k'ananan duwatsu masu d'aukar idanu saboda kyallinsu riga da buje da
d'an kwali,tana ganin kayan tawani shagwa6e fuska wai ita baza ta sa kaya irin na
Walida ba wanda Baba yasiyo mata dayaje Umrah doguwar rigar larabawa shi za tasa.
Sudaida ta dafa kafad'arta da sigar rarrashi"kisa wannan kinga anko fa
za kiyi ke da k'anwarki, yanzu zan miki wannan kwalliyar sai kuyi Selfie da waya
ta.Walida tayi tsallan murna"Yehhh...ni ma na iya tsayuwa da shan baki a
selfie,Bilkisu ta ta6e baki ita yar gata haihuwar samu sai kawai tafashe da kuka
tana bubbuga k'afa ita fa dole rigar larabawan nan za a d'auko mata.Sudaida ta
tsare ta da idanu"idan ban d'auko ba fa?Kawai sai ta kwanta a k'asa tana burgima
tana k'ara fashewa da kuka dan ta san Julaibib zai shigo...Haushi yakama Sudaida
tagyad'a kai "lallai mugun gata asara,rashin shi kwata-kwata illah...
Tanunata da yatsa"ke Bilkisu ki rufe min baki.Bilkisu tacigaba da ihu
da burgima tana kiran Julaibib"Baba kazo ka d'auko min doguwar rigar larabawan daka
siyo min,Mama wai bazan sa ba. Sudaida ta kifa mata mari ba za a d'auko ba...
taduba yar k'aramar dorinar ta take musu barazana da ita tarasa kawai sai ta jawo
wayar caja tanad'e ta a hannu"baza kiyi shirun ba ko?Ga mamakinta kawai sai
tagyad'a mata kai alamar eh.Ai batayi wata-wata ba shaud'a mata iya k'arfinta caraf
a kan idanunshi.
Bilkisu tagigice dan taji dukan yadda yakamata tak'ara fashewa da kuka
kamar zata shid'e, ya d'auketa ya zubama wajen data shaud'a mata idanu,cajar ta
fito rad'am da kwanciyar jini a wajen toh jikin hutu ko ina lukwui-lukwui da tsoka
ga kuma farar fata,yakalleta fuskar shi ba wal-wala"Sudaida baki da hankali kasheta
kike so kiyi? Dan tace ga kayan da take so sai yazama laifin da har sai kin mata
wannan dukan?An siyo kayan dan ayi meye dasu?Ya rufeta da fad'a kamar zai
daketa,Sudaida tayi shiru tana zancen zuci"wai ita ce za ta kashe mishi 'ya saboda
ta daketa sau d'aya.
Tashi ki d'auko mata rigar.Takalleshi cikin idanu"na rantse da girman
ALLAH ba zan d'auko ba!Yashare ma Bilkisu hawaye"to fad'a min in da take in
d'auko...Cikin fushi tace"wannan rigar haramiyar ta har abadan duniya wallahi.Shima
cikin fushi yajuya rungume da Bilkisu"kar ki d'auko ki dafa kici...
Sharrr...sharrr wasu hawaye masu d'umi suka zubo mata akan Bilkisu suke wannan
ja-in-jar da Yaya D'ansarai?Ranta in yayi dubu ya 6aci wai shi wani irin so yake ma
wannna yarinyar da har zai ga laifin ta amma yakasa tsawatar mata?Wannan makauniyar
soyayyace wacce daga k'arshe baza ta haifar da d'a me idanu ba wai Zaujiii...Shine
yake mata wannan hayagagar...za ta kashe mishi 'ya... tadafa rigar taci tunda baza
ta bata ba...taci kukan ta ta k'oshi tayi shiru tunani barkatai ya cika
k'wak'walwarta...yawa-yawan Ya'yan da suke samun matsala a rayuwar su to hakan yana
samo asaline daga irin mugun gatan da ake nuna musu tun zamanin k'uruciya.
Sai da hantsi yadubi ludayi sannan Walida tashigo d'akin cikin wata
shiga ta daban riga da wando da k'aramin hijab yan kanti...ran Sudaida ya kuma 6aci
wato fitan da yayi sababbin kaya yayafi ya siyo musu kenan? Walida
takalleta"kingani Baba ya siyo mana wasu kayan?Tagyad'a kai"na gani Walida. Mama
kuma na ce mishi ALLAH amfana... tad'an shafa kanta"yauwa Innarmu ALLAH yamiki
albarka haka ake so duk wanda yabaki abu kisa hannu biyu ki kar6a kuma kiyi
godiya...tayi yar dariya"wanda yagode sai ALLAH yak'ara mishi haka kika fad'a min
ko? Eh Innarmu ashe baki manta ba.To nagode da kike rik'e duk abinda nake fad'a
miki. Tad'anyi jimmm...sannan ta kalli Sudaida"Mama ita Yaya Bilkisu fa da Baba
yakawo sai tace wai basu da wani kyau sai da yahad'a mata lemun tuffa da karas
sannan ta yadda tasa...wai ita dai na Umrah nan take so,shine yace sai ya koma wata
Umrah,damu zai tafi muje can muza6a irin wanda muke so da kanmu...
Walida... Suka jiyo muryar shi daga D'akin-shak'atawa yana kiranta,sai ta
d'an bud'e idanu "Mama...Baba ne yace wai kizo mutafi na manta... tafita da gudu
tana amsa kiran na shi.Takoma tayi kwanciyarta"da bata hak'ura ba baza suyi tafiyar
ba kenan kome?Tayi k'wafa"wallahi abu d'aya zai sa tabisu dan tafad'a ma su Baba
abinda yake yi, da ba in da za taje,gwamma ayi ma tufkar hanci,ai gabama da gabanta
aljani ya taka wuta,ita baza ta iya cigaba da ganin kayan takaicin nan ba nama na
jan kare.
Ko kallanta bai yiba,to itama a cikin fushi take dan haka ba wanda
yakula wani har suka isa Zonkwa. Inna taji dad'in ganinsu sai ina za a saka ina za
a aje takeyi da jikokinta haka suka yi wunin farin ciki.Bayan sallar magriba Sagir
k'aninta daya yazama matashin saurayi takira yaraka ta wajen gyaran gashi har
Julaibib yadawo basu dawo ba shima yazauna ana ta hira,Bilkisu Megadon Zinare an
samu abinda ake so dafadukar cus-cus me nama da kayan lambu take ci,ga Baba ya kawo
mata yoghurt tana taci tana sha cikin jin dad'i da kwanciyar hankali.
Sai wajen takwas da rabi suka shigo Sagir yasake gaishe dasu Baba
sannan yamusu sai da safe,ita kuma taje tayi sallar Isha'i ta zubo abinci
tanaci;yad'an saci kallanta tayi kyau sosai amma ko nahiyar da yake bata kallaba
har tagama ci takai farantin D'akin-girki sannan ta dawo ta zauna tad'an kalli
yaran"kutafi D'akin-shak'atawa ku kalli wannan shirin na Balarabe da bai iya gaza
gurasa ba...Suka mik'e da Sauri"ehhh kuwan Mama...
Tad'an sunkwui da kai cikin ladabi"Baba ina son magana da ku.Yagyad'a
kai"to Sudaida... Julaibib yayi wani huci"me wannan yarinyar take nufi? K'arar shi
za ta kawo wajen su Baba?Ina jinki Sudaida me yafaru?Muryar ta tafara rawa alamar
zuciyarta ta karye"ni dai Dan ALLAH Bilkisu zata dawo gidan nan da zama zan had'o
kayanta... Inna tace"ashsha to me yayi zafi idanu za suci wuta har haka Sudaida?
Inna kusan kullum sai mun samu sa6ani da Yaya D'ansarai a kan ta,wai d'azu da safe
har yana fad'a min zan kashe mishi 'ya saboda na daketa,kuma agaban idanunta ya
rufeni da fad'a kamar zai dakeni,Lillahi warasulihi Inna ace kamar Bilkisu sai
abinda take so za a dinga yi a cikin gidan nan?Sannan ita ba ta laifi, ba ta
kuskure kome tayi dai-dai be a wajen shi, wannnan abinda yake yi ya dace da tsarin
ingantacciyar tarbiyya!?
Ni dai ta zauna a wajenku kawai.Inna ta numfasa to me yakawo dukan?
Sudaida duka ai baya ba da tarbiyya sai dai yakangarar,ni ma ba na son duka.Wani
haushi yamamaye ta wallahi mantawa tayi kuka takawo gidan mutuwa"ai kamar yadda
Bilkisu take hantar Yaya D'ansarai to haka abun yake a wajen Inna son ta take kamar
me,shi yasa ba gidan da take son zuwa kamar nan dan Inna tana biye mata ne,yanzu ma
abincin daren ta daban tadafa mata.
Tasa hannu ta share hawaye"shikenan Insha-ALLAH daga yau ba ruwana da
duk abinda Bilkisu za tayi ai ALLAH yagani bani da wani k'arfi ne dan haka zan
kyamaci kome a zuciyata.Auna had'a idanu ya gallamata harara"ai dukan yayi yawa ne
har ciwo kika ji mata to me zaisa bazanyi fad'a ba.
Baba yayi tsaiii...yana nazarin kalamansu d'aya bayan d'aya,yakad'a
kai"Maimunatu wannan hukuncin na ki na adalci ne kuwa?Tsakani da ALLAH Sudaida ta
fiku gaskiya;kar k'aunar yarinyar nan tarufe idanunku fa,idan an ciza to yakamata a
hura...yanuna Julaibib"Malam D'ansarai da ilminka da girmanka amma kana irin wannan
abun?Kiwo aka ba ka game da sha'anin Iyalinka fa,shi itace tun yana d'anye ake
tank'warashi...kana nunama Bilkisu tsananin gata amma ba kwa6a to an yi ba ayiba
kenan...an 6ata goma biyar bata samu ba,dan me za tayi laifi ba za a hukunta taba?
Mahaifiyar tace fa idan ba a nuna mata abinda takeyi kuskure ne tun yanzu ba,to a
gaba ma cigaba dayi za tayi,kuma duk fad'an da zaka ma Sudaida to na rok'eka da
girman ALLAH kadaina yi a gaban Ya'yanku,hakan yana gur6ata tarbiyyarsu,dan ALLAH
Malam D'ansarai idan rai ya 6aci to bai kamata hankali yagusheba kaji ko?
Yanuna ta"ke kuma Sudaida ba ke za ki yanke hukunci na rad'in kan ki ba
kome ya miki,tunda shine ubansu shine a hakku a kansu dan shine shugabanku ke da
yaran gaba d'aya.Ubangiji ya muku albarka,sannan duk yadda ranki ya6aci kiyi
hak'uri dasu kinga banji dad'in furucinki akan Bilkisu ba,ke uwace bakinki
amsashshene akan ta,dan haka ki janye wad'annan kalaman na ba babu ruwanki da duk
abinda za tayi,ai kece kuwa me ruwa da tsaki yaushe za ki biye ta wani D'ansarai
Ya'yanki kadararki su shiga garari,duk abinda ya kumayi ki bugo waya ni dake ki
fad'a min zai sha mamakin yadda zanyi wallahi ALLAH kinji na rantse ko?
Kalaman Baba sun tausashi zuciyarta"to Baba nagode ALLAH ya k'ara
girma.Inna ma tajijjiga kai toh na gano kuskure na kiyi hak'uri Sudaida ALLAH
yamuku albarka,ku tashi kitafi gida dare yana dad'a yi,ta lek'a D'akin-shak'atawa
duk sun yi bacci Inna tace suyi tafiyarsu kawai.
Suna zuwa gida taje tayi wanka tayi kwanciyarta shi kuma yatafi
D'akin-girki zai dafa shayin na shi na fama taja tsaki sai kaje kayita
sha...takwanta cikin tunanin tsohuwar soyayyar su..ita dai ta san da son Julaibib
ta girma kuma ba tajin da wani abu dazai rage k'aunarshi a sararin zuciyarta,to
amma wannan yawan sa6anin da saka fara samu ita tata k'arfin k'aunar ta zuciyarshi
ce ta koma kan Bilkisu da kuma kud'in da yakeji yayi?Ko kuma giyar Ilmi da dukiyace
tafara bugar dashi...!?
Tad'auki wayarta takira"Umma kiyi hak'uri na kiraki da daddaren nan
wata magana nake so muyi.Ba kome me yafaru ne?Hawaye suka zubo mata"Umma ni da Yaya
D'ansarai ne...sai kawai tafara kuka,Umma bata hanata kukan taba sai da taci ta
k'oshi tabari dan kan ta...Umma tasauke numfashi "Sudaida kiyi hak'uri ni bazan
shiga tsakanin ki da D'ansarai ba ai kunfi kusa,kuma ai ba a ta6a zaman tare ace
wani bazai sa6a ma wani ba...fuskantar matsalolin aure irin wannan ai dole ne dan
haka ki k'ara hak'uri kuma ki yawaita addu'a kome yayi farko yana da k'arshe...kuma
in dai akan Bilkisu ne to fa dole sai kin kawar da kai...ba kome za ki nuna ya dame
ki ba...ki dai kiyi k'ok'ari ki jata ajiki kinga ai tafi shak'uwa dashi ko? Eh
Umma...to ko ni nan a yanzu nagano wasu kura-kurai danayi game da tarbiyyarku to
amma har kwanan gobe ina godema ALLAH ina godema Mama wacce ba dan ita ba da kuma
kun samu tasgaro dan haka ki natsu ki san abinda kike yi game da sha'anin
tarbiyyarsu...
haba Sudaidan D'ansarai kika juya shi yayi wasu abubuwan da bai so ba sai
kuma wannan za ki fara raki? Ki bi dashi ta siyasar rayuwa ko bai daina wasu
abubuwan ba to amma ai za ki samu sauk'in wasu,Umma tad'anyi murmushi"taurin kan
Bilkisu da kafiya kema fa haka da kike k'arama kinyishi,shi yasa bana miki da
wasa...ita kuma sai abun yahad'u mata da gata...
Julaibib yashigo lokacin suna sallama da Umma.Yakar6e wayar"k'arata
kika sake kaiwa,me kika fad'a mata?Abinda kunnuwanka sukaji.Yayi murmushi"ALLAH ko?
Tajijiga kai"bawai...yashiga rarrashi"kiyi hak'uri Sudaidan D'ansarai ni ma na gane
kuskure na,bai kamata ace Bilkisu ce zata shiga tsakanin muba,ai tare tazo ta
ganmu,lallai ke macen albarka ce dakika jajirce dan ganin na dawo kan hanya nagode
Zaujatiii...ALLAH yamiki albarka ya saukeki lafiya.Sai taji zuciyarta ta yi
wasai"ta marairaice Zaujiii..to idan banyi hak'uri ba me zanyi bayan mun zama
k'arfe da mayen k'arfe,mutu karaba takalmin kaza...?Hummm fushin masoya hutuhhh...
Rawa da k'afa d'aya sai gwani.
Da ba 'yan koyo da gwanaye sun k'are...
5 Rajab 1441
28 February 2020
We Ibrahim's Daughters👇
Asdilat KD...2geda with Ra'ibs.
DANGIN NONO WRITERS ASSOCIATION
{Da Inganci Mukayi Fintinkau}
Bismillahi wabihi nasta'in
...GWAJIN DAFI💔
Almost true story
Daga alk'alamin🖊
Ya'yan Ibrahim
Saudat A.Baba (Asdilat KD)
Da
Bara'atu Ibrahim (Ra'ibs)
Shafi na ashirin da hud'u.
Gobe zan tafi Sudan fa...takalleshi wani iri" haba dan ALLAH shine
baka fad'amin ba sai da daddaren nan?Yagyad'a kai"ai dan ma mun shiryane da sai na
tafi zan turo miki sak'o ni nawuce sai ALLAH yamin dawowa. Tad'an harareshi"gaskiya
banji dad'i ba,ba fa abinda na shirya maka.Uh bakome kibani abinda yasauwak'a,kin
san ni bana raina kad'an"da hanau ai gwamma mannau. Tare suka shirya kayan
tafiyar.Washe gari jirginsu yad'aga.
A wad'annan shekaru goma sha ukun Julaibib Abdullahi D'an Sarai ya
taka matakai da yawa a bangaren ilmi har ya zama shehin malami ferfesa
gangaran(Professor)Yasai k'aton fili yana gina had'ad'd'iyar makaranta ta zamani
bangare biyu bangaren addini da bangaren boko,aiki tuk'uru ake yi k'asa tanata cin
kud'i,makarantace tun daga matakin prenursery,nursery,primary da secondary,abubuwa
k'alilan suka rage mishi a bud'e makarantar,yana kuma da buri nan gaba yad'ora
makarantar zuwa Jami'a me zaman kanta, yana kuma fatan makarantar tacigaba har
bayan rayuwarsu,Ya'yansu su cigaba har jikoki...ta shahara har zuwa sauran k'ananan
hukumomi da jahar Kaduna da d'aukacin sauran jahohin dake tarayyar Nigeria.
Abubuwan rashin jin dad'in da suka faru kuma shine tun bayan yak'in
Zongon-Kataf da yak'in da akayi a k'waryar cikin Kaduna na k'addamar da shari'ar
musulunci wani hargitsi da kisan rayuka bai kuma faruwa a k'aramar hukumar Zangon-
Kataf ba,to amma a 'yan kwanakin nan manyan kabilun yankin Bajju da Atyap da sauran
kabilu da basa sallah sun fara neman hana musulmai rawar gaban hantsi,takalan fad'a
ba irin wanda ba sayi to amma bai damu hausawa ba,saboda duk fad'in doron duniya
kowa ya shaida duk in da kaga musulmi kuma bahaushen mutum to ba wani abu yakai
shiba face neman ilmi ta yadda zai bautama Ubangiji ba tare da jahilciba,sai kuma
neman kud'i,kuma musulmi na da sauk'in halin da basa son tarzoma,wannan dalilin
yasa suka d'an sararama hausawa amma ba hak'ura sukayi gaba d'aya ba,aka cigaba da
zama cikin aminci da amana kamar yadda zuciyar bahaushe take a ko ina.
Tana kwance a d'akin baccinsu lullu6e da bargo tana chat da Nasmat,video
call d'inshi yashigo ta d'aga da sallama,ya amsa da wani salo irin nashi yana
murmushi"eyehhh... kaga Hajiya baki da wata matsala.Tayi yar dariya"godiyar
Ubangiji a kowani hali da yanayi Zaujiii...Yagyad'a kai"ina yaran?Suna gidan Inna
wai a can zasu kwana,yad'auki kofin gabanshi ya kur6i abinda yake ciki yamayar ya
ajiye. Me kake shane?Shayi tad'an yamutsa fuska"asha lafiya.
Zaujatiii...Yakirata.Na'am.Nayi kewarki, bakya barina inyi ayyukan
dake gabana,gangar jikina ne kawai a Sudan amma tunanina da zuciyata suna gida
wajenki,gashi kwanakin basa sauri,anya ba visa za kiyi ki taho ba?Tawani
marairaice"ni ma nayi kewarka,Yaya D'ansarai...Esbeer kaji?Kamai da hankali akan
aikin da kaje yi,ai kamar yaune zaka dawo gida katarar da zuri'a da Iyalinka cikin
k'oshin lafiya Insha-ALLAH,ka yi kwanaki goma sha shidda,saura kwana hud'u kacal
ai...
Zaujatiii...na rantse miki da ALLAH daga shi ba wani kece duniyata,ina
k'aunarki fa.Tagyad'a kai cikin gamsuwa da kalamanshi bawai shaci fad'i bane"ni ma
haka Zaujiii...Ina k'aunarka a kowani hali da yanayi, baka da abokin tarayya a irin
k'auna da soyayyar da nake maka"in poor and in rich,in sickness and in
health...till death due part us''Yaja numfashi yafesar da iskar ta baki ta hanci"oh
ya rahman...wani shauk'i da d'okin ganinta yamamaye shi...sun dad'e suna musayar
kalaman k'auna sannan suka fara magana akan kud'in daya turo aka sai wasu kayan
aiki na ginin makaranta.
Hantsi yadubi ludayi tashirya cikin doguwar riga kamfala,tatafi gidan
Inna suna tattauna wasu al'amura daya shafesu,Abu me aikin da Julaibib ya d'auko ma
Innar tashi tashigo da sallama ta ajiye farantin hannunta a gaban Sudaida tana
tsokanarta "uwar biyu tashi kici kwad'on zogale na miki naga kwanaki biyu in dai
kinzo abinda kike tambaya kenan, yau kuma naji baki tambaya"tamik'e zaune dakyar
tana murmushi"nako gode miki Abu ba kad'an ba,sannu da aiki,tad'iba da bismillah
takai bakinta, tafara taunawa cikin gyad'a kai "gaskiyar magana wannan k'uli-k'uli
akwai d'ankaren dad'i da d'and'ano, tasa hannu a jaka taciro dubu biyu tabata"yaba
kyauta tukwuici Abu.Abu takar6a tana godiya "madallah ALLAH yak'ara bud'i,yasaukeki
lafiya... tad'anyi murmushi kawai,sai Innace ta amsa da" amin. Abu tajuya takoma
D'akin-girki tana yaba halin kirkin zuri'ar Hajiya.
Bilkisu tashigo cikin shagwa6a ta rungume Sudaida tabaya"Mama kince za
ki kira min Baba mu gaisa.Tad'an harareta"kin fa dameni idan nace na fasa sai ayi
yaya dani?Asma'u da shigowarta kenan ta amsa dama me hali baya fasawa"wallahi abu
me sauk'ine muyi k'uli-k'ulin kubura dake.Bata kula Asma'u ba tafara kiranshi,cikin
d'oki Bilkisu ta manna wayar a kunne"Baba afqadtuka(nayi kewarka) Yayi dariya ALLAH
Megadona?ALLAH kuwan Baba jiya ma nayi mafarki wai ka dafa mana naman talo-talo
naci nak'oshi...tanata mishi shirme yana dariya... toh ni dai gaskiya idan bazaka
dawo ba zan sa Kawu Aminu yakawoni in da kake ai yasan wajen ko Baba?Eh yasani.Ina
Walida?Tatafi da Kawu Aminu siyo kindirmo a riga ni dai nace baza niba,shine wai
yace idan suka dawo suma bazasu sammin ba,Baba kace Mama yau ta soya min dankalin
turawa da kwai. Yagyad'a kai"to Bilkisu na har da lemun kwakwa ko?
Tajijjiga kai tana tsallan murna"zan rage maka har kadawo,yaushe zaka dawo
d'in?Insha-ALLAH gadan bil-lail.Tawani fasa ihun murna Sudaida takwace wayar ta
buge mata baki"ban hanaki wannan ihun murnan ba?Kawai ki cika mana dodon kunne.Inna
tafara fad'a"nifa Sudaida ban san sanda kika 6aci da saurin hannu ba,tad'anja
tsaki"haba ina amfanin irin wannan?Tayafito Bilkisu da hannu"zo nan muga
bakin...yauwa kingani ko har ya fara kumbura.Sudaida tace"kiyi hak'uri Inna,Inna
bata kulataba sai da tagama lalla6a Bilkisu ta daina kuka sannan ta kalli
Sudaida"ya wuce amma a dinga kulawa... tayi murmushi"to Inna a ranta tana fad'in
"wuuu na manta ashe hantar Inna nata6a a gaban idanunta.
Dawowar shi da kwana biyu ya tasata a gaba wai dole sai ta raka shi
wata seminar,sun gama abinda za suyi suka wuce kasuwa yasai kayan wuta na mak'udan
kud'ad'e da za a sasu a makaranta.Sudaida tayi tsaiii...cikin tafakkurin abinda za
ta sai ma Yaya Aminu wanda zai burgeshi har yayi amfani dashi,saboda abubuwa da
yawa basu d'ad'ashi da k'asa ba.Zaujatiii...tunanin me kike yi haka?Takalleshi"Yaya
Aminu na rasa me zan sai mishi bani shawara"yayi murmushi"turare da kayayyakin da
yake ayyukanshi dasu(artistry equipment) sune kawai zai yaba ko?Yauwa Yaya Julaibib
wannan shawara taka ta samu kar6uwa nagode.
Bayan sallar Isha'i taje gida tasame shi a D'akin-shak'atawa yana shan
fura da nono,ya maida ludayin cikin kofin yana amsa sallamarta"Sudaida kece haka da
daddaren nan,ina autan Innan?Ta zauna a k'asa tana maida numfashi kamar wacce tayi
gudun famfalak'i saboda nauyin da cikin ta yayi"su Bilkisu yatafi d'aukowa a gidan
Inna,ni kuma nagaji da jiranshi shine nayi tahowata.Da sauri ya d'auko ruwa ya zuba
a kofi ya mik'a mata,har ta kai tsakanin la66anta da bismillah yasa hannu yakar6i
kofin"yi hak'uri ina zuwa,bulkodi(glucose D) yad'auko yazuba mata babban cokalin
cin abinci d'aya a cikin ruwan yajujjuya sannan yabata,ta shanye duka,suka kalli
juna suna murmushi"yaya a k'aro?A ah Yaya Aminu nagode kwarai taurarona.
Yazauna"da kinyi zamanki, kina kirana a waya ai kin san bazank'i zuwa
ba.Yaya Aminu ba kome ai nima ina motsa jiki ne.Ya kalli k'afafunta da suka
kumbura,har ranshi yaji tausayin ta"mata suna shan wahala da ciki fa,duk mace me
ciki ai kana ganin yanayin ta ka san abin ba a cewa kome"lallai biyayya ga mahaifa
dolen-dole ne ga duk mai son gamawa a doron duniya lafiya".Sannu kanwata to baza
kije asibiti su baki magani ba? Tayi yar dariya ganin yadda yadamu dama haka yake
nuna mata tausayi duk sanda suka had'u,tasa hannu tana murza k'afafun"wannan ba
kome bane,ba shi da wani magani wasu suna yi yayin da cikin su ya tsufa wasu kuma
ba sayi,duk cikina bai wani girma amma gashi na fara wancan makon ma naje an dubani
kome nawa lafiya lau.
Yakad'a kai"toh Ubangiji yaraba lafiya.Amin Yaya Aminu nagode"ga
wannan.Yakar6i ledan, yad'ago yana murmushin jin dad'i bayan yaga abubuwan da suke
ciki "yanunata da yatsa duka na Aminu ne shi kad'ai?Tajijjga kai.Toh nagode ba
kad'an ba"ALLAH yamiki albarka Sudaidan D'an Sarai. Sukayi dariya.Sun d'an ta6a
hira har zuwa takwas da rabi sannan yace ta tashi yarakata gida dare ya farayi,suka
jera suna tafiya a hankali suna magana har suka zo k'ofar gidan"shige gida kinji
dare na dad'ayi ga hasken farin wata kar yasa miki mura.Sai da safe ko?Tagyad'a
kai"ALLAH ya tashemu lafiya tabi bayanshi da kallo har yasha kwana ya6ace ma
ganinta.
Ranar wata laraba a watan Rabi'u Awwal kabilun garin suka tashi da
neman rigima ba wanda yataka ko ya zubar musu suka fito suka dinga zage-zage da
k'one-k'onan tayoyi nan da nan gari yafara rikicewa kowa yatashi a wajen sana'arshi
sai gida hankali a tashe, basu suka daina wannan abun ba sai wajen k'arfe d'aya na
dare.
Sudaida ta sauke gwauron numfashi "Zaujiii...garin nan yafara bani
tsoro,sallolin yau gaba d'aya kowa a gidanshi yayi bayan ga masallatai nan, amma
saboda tsoron wasu marasa sallah an rasa wanda zai fita?To wai me aka musu? Yayi
murmushi "kome zai wuce Insha-ALLAH gobe za a tattauna da Agwam Bajju (Sarkin
Bajju) kin san shi mutumne me san zaman lafiya na san kuma zai ja musu kunne Kwanta
muyi bacci kinji"gobe asubanci zanyi zuwa Gidan-Waya, har Sudaida tayi bacci amma
shi idanun shi biyu yana tunanin al'umara mabambanta, lokuta da dama shima yanaji
kamar yatattara yabar garin,to amma idan ya bar garin ai anyi gudu ba a tsira
bane"gudun da ba a tsira ba kuwa kwanciya ta fishi".
Gaba d'aya zuri'arsu a garin suke Iyaye da kakanni,ai duk in da za shi dole
dai sai ya dinga zuwa duba Iyaye da yan'uwa dan ya san mahaifanshi ba yadda za
suyi su bishi ba,yasauke numfashi "zaman su a garin Zonkwa cikin wad'annan kabilu
muk'addari ne tun daga Lauhul-mahfuz, k'addara ta riga fata,sai dai ya kamata suyi
ho66asa dan suna so su fara musu cin kashi, shekaru kusan goma da suka wuce haka
suka zauna cikin fargaba saboda fad'an d'aya 6arke sakamak'on k'addamar da shari'ar
musulunci da akayi a Kaduna, a cewar su wai an kashe musu mutane da yawa a Kaduna
dan haka suma za su d'auka fansa a kan musulman da suke zaune anan,tsawon lokaci
haka suka zauna cikin tashin hankali,har dai kuma Ubangiji ya kawo k'arshen abun ba
tare da sunyi kome ba...da wannan tunane-tunanen bacci yayi a won gaba dashi.
Sai dai cikin baccin na shi yayi mafarkin daya dinga na shud'ad'd'en
shekaru"Kasham dai yau ma yasake gani cikin shigar Fulani kirar kalangunta ya fito
rad'am kamar dai wancan lokacin amma idan tayi magana sai yaji muryar Sudaida...ya
farka yanata nazarin wannan mafarki"toh me yak'un sane?...baccin da bai kuma komawa
ba kenan har aka fara kiraye-kirayen sallar asubahin farko...
Hausa/Fulani Community Development Association(HAFCODA)Taza6i manya daga
cikin su, suka tafi fadar sarkin Bajju,ya kuma kar6esu cikin mutuntawa, sun gabatar
da abinda yakawo su,nasan zaman lafiya,da hak'uri da juna,shima Agwam Bajju a
zahirance dai ya nuna 6acin ranshi"dan sanin asirin ciki sai hanji,ya kuma tabbatar
musu su kwantar da hankalinsu lallai zai tsawatar musu ta hanyar yin gargad'i a
dukkan majami'u(churches)ga wad'annan samari yan zauna gari banza masu son tada
hargitsi,idan kuma basuji ba to lallai zai buga musu sandar shi(a al'adarsu idan
har agwam Bajju yace zai buga sandarshi to duk abinda mutum zaiyi to ba zaiyi
nasara ba)
Wad'anda ba son zaman lafiyar suke yiba suka had'a taron su.Shugaban nasu
yabisu da kallo d'aya bayan d'aya"kunji abinda yake faruwa, dama hausawa masu san
zaman lafiya ne tunda duk abinda muke musu basu ta6a mai da martani ba...toh ni dai
kawai bana son ganinsu a garin mune,kome sune suke dashi sama damu sannan hakan bai
wadatar dasu ba kullum aure mana Ya'ya suke k'arayi,wani abin takaicin ko da wasa
baza kaga wata yarsu kace kana sonta zaka aureta ta yadda da kaiba,sai tace bata
yadda ba tunda baka yadda da addinin taba,kunaji suna fad'a kakar za6e me zuwa zasu
za6i mutum biyu daga cikinsu su tsaya takarar Chairman to kuna gani za su yadda su
sake dangalama wani na mu k'uri'arsune?Yaja dogon tsaki"infact I'm sick and tired
of seeing all those masu sallah bounch of idiot,we've to do something,something
seriously againts them.
Wani daga cikinsu me rangwamen kafircin yace"da munyi hak'uri kawai
ai mun riga mun zama d'aya,ga Ya'yanmu a cikinsu idan munyi yak'i mun kashe mazaje
to yaya zamuyi da tarin mata da Ya'yansu?Nifa Ya'yana guda uku ne masu sallah.Cikin
fushi shugaban nasu ya daka mishi tsawa"enough of this stupidity,so bloody what da
Ya'yanka uku ne a cikinsu? Ko akwai 'yata a cikinsu na rantse muku zan iya kasheta,
ba sune shegu masu kwad'ayin abin hannun hausawa ba? To da irin suma zan fara
kisa,so dubu nawa suna wulak'antasu? Yanuna mishi k'ofa yana mazurai"now get out!
Kai baka cikinmu.
Yasake bin sauran da kallo,suma shi suke kallo suna jijjiga kai alamar
gamsuwa da matakin daya d'auka,fuskokin nan babu rahama da tausayi kona sisin
kwabo,idanuwa jawur saboda shan burkutu da hayakin maro."nayi dai-dai?Suka had'a
baki wajen amsawa"kayi dai-dai.Yakyalkyale da wata irin gur6atacciyar dariya da
bata da dadin ji saboda giya da hayaki sun gama lalata hunhunshi"that's very good
of you... Suka rufe k'ofa suna cigaba da k'usk'us d'insu na yadda zasu canja salon
takunsu akan hausawa, d'akin ya kaure da dariyarsu dan sun gamsu d'ari bisa d'ari
da matakin da suka d'auka...
Hankulan jama'a ya kwanta an cigaba da harkoki kamar yadda aka
saba,sai dai kuma watanni kad'an a hankali abubuwa suka fara rinca6ewa za a koma
yar gidan jiya,aka sake komawa cikin zaman d'ar-d'ar,basu da wani kwanciyar
hankali, harbin bindigogi daga daji haka yake shigowa cikin gari ba dare ba rana
alamar suna koyan harbi amma abun duka ba sanda da yake kuma dama bahaushen me ban
haushinne na tanko me kan bashi,hakan bai d'ad'asu da k'asa ba,su dai neman
halalinsu kawai. Mtswww ALLAH yakyauta.
Gidan shiru saboda yaran yanzu a gidan Inna suke kwana a duk ranakun
k'arshen mako,Julaibib ya d'auko musu abinci,tamik'e zaune dakyar suka faraci da
bismillah yana kuma mata bayanin aikin kafa ma'adanar littafai(bookshelves)da aka
fara a d'akin nazari da bincike na makarantar (library)Tayi lallausan
murmushi"Ubangiji yacigaba da rufa mana asiri duniya da lahira,gaskiya naji dad'i
wallahi.Amin Zaujatiii...
Cikin firgici ta farka daga bacci a sulusin daren,wasu irin munanan
mafarkai takeyi duk dare,har fargaba duk lokacin da rana tatafi zata fad'i magriba
ta kunno kai,saboda da zarar ta kwanta baccin dare zata fara wannan mafarkan masu
tashin hankali da sanya damuwa a zuciya.Julaibib yana zaune yana cike wasu bayanai
a na'ura me kwakwalwa yaji motsinta,yajuya yana kallanta,tana zaune a tsakiyar
gadon ta kama kanta da duka hannayenta cikin maimaita Istirja'i,rigar shimin dake
jikinta ta jik'e sharkaf da zufa"Sudaida lafiya?Zafi kikeji haka?
Yamik'e barin kunna miki mukayyib. Takalleshi a rikice"Yaya D'ansarai
ba zafi nake jiba,jikinta yakama rawa"kasan abinda nake gani kuwa?Wai...yatari
numfashinta ta hanyar sa tafin hannun damarshi ya rufe mata baki sannan yakalleta
cikin kulawa"ba wai bana so inji abinda zaki fad'a bane a ah ina miki kwad'ayin
samun lada saboda bin umarnin Manzon ALLAH dan yayi hani da bayyana mummunan
mafarki,duk abinda kike gani to ki nemi tsarin ALLAH akan abinda kike ganin,kiyi
tofi a gefen hagunki sau uku"A'uzu billahi minashshaid'anir rajim "sai ki juya daga
gefen da kika kwanta zuwa d'aya gefen.Wannan shine abinda yadace.Ta rungumeshi tana
sauke numfashi"nagode da wannan tunatarwan.
Ranar wata Litini aka bud'e makarantar Julaibib a zangon karatu na farko
me suna...
"Alfurqan Science Academy.
Musulman Zonkwa sunyi murna da farin ciki da samuwar wannan makaranta,Ya'ya dayawa
an ciresu daga wasu makarantu an dawo dasu nan.Julaibib ya so kwarai ya zauna da
Iyalinshi dan bata jin dad'i,sai dai hakanshi bata tadda ruwa ba dan da yammacin
ranar ya mata sallama yakama hanyar Gidan-Waya washe gari da sassafe zasu tafi Jos
asibitin k'ashi na Bima abokin karatunsune yayi hatsari a hanyar shi takomawa garin
na su na Jos yakakkarye.
Sai k'arshen mako yazo,gidan Hajiya yafara zuwa kamar yadda yasaba,su
Hajiya an dad'a tsufa sai dai Alhamdulillah tsufa me amfani tayi dan bata rikice
ba,tana gane kome da kowa,sun dad'e suna hairarsu kamar yadda suka saba.Bilkisu
kuma tagaji da jiranshi kamar yadda Sudaida tace mata ta zauna ta jirashi ba sai ta
bishi ba ai zo.Tanata k'unk'uni tana turo baki gaba,Sudaida tana shiga D'akin-girki
Bilkisu tasa dogon hijab d'inta har yana jan k'asa,wai haka sabuwar malamarsu ta
Alfurqan take sawa,shine tace lallai itama haka zata dinga sawa Julaibib kuwa
yad'inka musu ita da Walida kala-kala,tayi sand'a tafice da sauri.
Hajiya tana ganinta tace kai wannan yarinya da gaggawa kike hannun hagu a
romo"sarauniya me D'ansarai ai ban ce zan rik'e miki uba ba.Julaibib yayi yar
dariya ya tuno da Sudaida itace me fad'a mata haka musamman idan tana jin haushin
su.Bata kula Hajiya ba tarungumeshi tawani shagwa6e"Baba tun d'azu kazo kayi
zamanka anan.Yashafa kanta "Esbeeer Megadona yanzu zamu tafi.
Takalleshi cikin farin ciki"Baba yau Mama ta barni ni na had'a maka lemun
karas,kashu da citta"kaji d'and'anon kuwa?Yagirgiza kai.Wallahi sooo
luciousss...yadda tayi furucin yabasu dariya. Shima yace"thank you sooo very much
my dear Bilkisu. Yarik'o hannunta suka mik'e"Hajiya barinje in sha lemun nan tunda
sanyin shi. Bilkisu tad'an zaro idanu tana kallan Hajiya"ALLAH na mantane amma
yanzu zan kawo miki naki dama Mama bata san nafito ba.Hajiya tace"tafi can sai
yanzu kika tuna dani to bana sha.Tabi Julaibib da sauri da yasa takalmanshi yafara
tafiya"ALLAH kuwan sai kin sha idan ba haka ba nima bazan kuma shan dabgenkiba.
Da daddare Julaibib yatafi kai Bilkisu da Walida hutun k'arshen mako
gidan Inna,Sudaida tana shan rake taji tauuu...tauuu...tauuu...!k'arar harbin
bindiga har tana hango kyallinshi ta tagar da take bud'e,raken hannunta ya su6uce,
tarintse idanunta cikin matsanancin tsoro duk da abin ya zame musu jiki to amma na
yanzu ya firgitata wallahi, tana Istirja'i yashigo da sallama yazauna yana
kallanta"lafiya kuwa?Tad'ago tana kallan shi cikin mad'aukakin mamaki"kai bakaji
harbin bindigar da akayi yanzu a jere har sau uku ba?
Yaya D'ansarai anya garin nan za a samu kwanciyar hankali a cikin shi?
Yamaida kai da bayanshi jikin kujerar yana murmushi"matsoraciya kawai...Ta tsare
shi da idanu. Yad'an kalleta" ke ba kome fa na...Ta girgiza kai"ba kome fa kace?
Haka shekaran jiya danaje gida muna magana da Baba shima yace wai ba kome,to ni
abinda bangane ba,a ba kome d'in me yakawo wannan harbe-harben ba dare ba rana?Anya
ba koyan harbin suke yi ba? Baza kusa yan lek'en asiri su binciko muku me ake ciki
ba Yaya Julaibib? Yaciro wata takadda daga aljihun gaban rigarshi da biro yafara
lissafe-lissafenshi a ciki"to me kika ga anyi?Koma me sukeyi bata shafe muba...tayi
shiru tana kallan shi aranta tanata maimaita Kalmar"kome sukeyi bata shafe muba...
Yagama ya bud'e Laptop d'inshi yayi yan rubuce-rubuce a ciki ya rufe sannan ya
kalleta"gobe Insha-ALLAH zani Kaduna mun tura kud'in kayayyaki amma har yanzu shiru
tun wancan makon muke waya da manager na wajen amma sai wani hanya-hanya yake mana
toh zani inga koma meye ganin idanuna.
Takalleshi wani iri ranta ba dad'i"nifa tafiye-tafiyen nan naka ya
fara shigar min hanci da k'udundune wallahi,yana hanani rawar gaban hantsi, jiya fa
yakamata kazo garin nan baka zo ba,na kauda kai banyi magana ba,yau kazo sai kuma
gobe kace Kaduna za ka tafi washe gari da sassafe ka koma Gidan-Waya?A k'arshen
makon ma baka hutaba?Ni gaskiya ban yadda ba shi Yaya Musaddiq d'in yatafi
mana.Yayi yar dariya"Zaujatiii...uwar gidata anan duniya har a aljannah;ai ko
Musaddiq yaci ya huta ko da yaushe shi yake tafiya,rabona da inje Kaduna saro kaya
na kusa shekara fa,ko wannan karon bashi yace inje ba nine naga dacewar hakan shima
yad'an huta...Kyan rawa da makar6i,amma kisha kurumunki Sudaidan D'ansarai ai na
kusa ajiye koyarwar da nakeyi in dawo kan wannan makarantar gaba d'aya, kinga tafi-
tafiye ya k'are sai mu manne kamar k'arfe da mayen k'arfe kullum muna tare mutu ka
raba takalmin kaza ko?Yad'age gira yana mata wani kallon k'auna.Tayi shiru ta
kyaleshi,dan wannan tafiyar da zaiyi ta 6ata mata rai sosai wallahi.
Shi kuma yacigaba da maganar shi duk da bata kulashiba,ai ya san
tanaji tunda ba kurma bace,ranar litini d'inma bazan bar garin nan ba har sai munje
an sake miki scanning ni wannan girman cikin yana bani mamaki a watanni biyar
kacal.Hummm kawai tace tazame ta takwanta dakyar.
Da safe suna karyawa yazuba mata idanu yana zancen zuci ganin ta tsame
hannunta a abincin wai ta k'oshi kuma ba wani cin kirki tayiba "wannan cikin gaba
d'aya ya canja mishi Sudaida,ga yawan laulayi,ga rashin samun ishashshen bacci
saboda munanan mafarkai,ga wasu k'ananan k'uraje da suka fito mata a duka la66anta
ba irin magungunan da bata shaba dan su warke amma abin yaci tura,tayi sanyi
sosai.A hankali tajingina bayan ta da jikin kujera tana yamutsa fuska"wash
ALLAH!... Zaujiii...bakaji bayana ba kamar zai 6alle.Yafara mata tausa "sannu
Sudaida. Tad'an kalleshi kawai.
Aminu yashigo da sallama shima yakalleta cikin tausayi"Sudaida ko
asibiti zamu tafi ne? Tad'an yi luuu...da idanunta kamar zata rufe sai kuma
takalleshi"Yaya Aminu sai gobe za muje.To ALLAH yaraba lafiya,yamik'a ma Julaibib
hannu sukayi musafaha sannan yazauna suka gaisa da Sudaida. Suna hirarsu da
Julaibib amma suna sakota,wani abun tayi magana wani kuma ta musu shiru. Aminu
yamik'a mishi katin za6enshi(voters card)ni dai wannan karan bazan yi za6e ba,tunda
ko ka za6a wanda kakeso to a k'arshen wanda su suke so shine sai lashe za6en da
kuri'a mafi rinjaye,magud'i kiri da muzu haka ake yinshi.Bai wani dad'e ba yamusu
sallama yatafi.Shima Julaibib yayi shirin tafiya Kaduna.
Yazauna a hannun kujerar da take kwance suna kallan juna na wucewar
wasu dak'ik'u, tarik'e hannunshi"ban so tafiyar nan ba har ga ALLAH, ina ji ajikina
kamar ba zamu sake had'uwa ba, idanunta suka kawo ruwa.Haba Zaujatiii...me yasa
kike wannan furucin? Insha-ALLAH kafin magriba ai na dawo,sharrr...hawayen suka
zubo mata,yafara goge mata"kiyi hak'uri Sudaida kome ya kusa zuwa k'arshe,kullum
muna tare har sai kin gaji da ganina,yazame hannushi daga cikin nata,yamik'e yana
gyara kwalar farar rigarshi"zo muje kawai kiyi zamanki a gidan Inna ko gidan Kawu
idan na dawo sai in tsaya in d'auke ki.Uh uh ba kome idan naji bazan iya zaman ba
to sai in tafi,tawani marairaice"
Tafiyar za kayi Yaya D'ansarai? Eh Sudaida ina 6ata lokaci gwamma inyi maza
in tafi tunda ba kwana zanyi ba.Yasunkuya yabata sumba,tashafa k'asumbarshi sukama
juna adabo.Har yakai k'ofa takirashi"Yaya D'ansarai...yatsaya cak sannu yajuyo
"na'am Zaujatiii...suka sake zubama juna idanu na wucewar wasu dak'ik'u,tasauke
gwauran numfashi a sanyaye tagyad'a kai "shikenan adawo lafiya.
A gidan Inna ma Bilkisu kuka tasa mishi ita bazai tafiba,ta had'a kai da
bango tana sheshshek'a,dakyar shi da Inna suka dinga lalla6ata sannan tayi shiru
ita da Walida suka rakoshi k'ofar gida tana k'ananan hawaye,yashiga mota ya zauna
yana d'aura belt tarufo mishi motar"Baba ALLAH yatsare a dawo lafiya...Walida ta
koma Gidan-Waya da gudu ita bata wani damu sosai ba.Tad'aga hannu tana mishi
adabo,yaja motar yatafi,zai sha kwana ya leko tana tsaye, tad'aga murya"Baba Qad
uhibbbuka... shima yamata adabo sannan yasha kwana yana murmushi furucinta"My dear
Bilkisu kenan nima ina k'aunarki.
Tafiya yake yi amma yanaji kamar yajuya wajen Iyalinshi,ranshi ba dad'i
har yashiga Kaduna garin gwamna,kiran Sudaida yashigo yad'aga da
karsash"Zaujatiii...gani a garin gwamna.Nayi tunanin dama yanzu ka shiga.To ya
jikin? Ya tambayeta cikin kulawa.Da sauk'i yanzu bana jin wani ciwo sai dai na yau
da gobe kawai irin na mace me juna biyu,yanzu ma na idar da sallah walha,na kuma
maka addu'a ALLAH yatsare min kai a duk in da za ka shiga,nima na rok'i ALLAH
yarabani da cikin nan lafiya,yabani nak'uda sassauk'a,sannan nace barin kira
D'ansarai mijin Sudaida inji muryarshi da kalamanshi su k'aramin nishad'i.
Oh ya rahmanu rahim...nagode ma Ubangiji da yabani ke a matsayin
mata,ke macen albarkace,kece uwargidata har a aljanah,yasake yin k'asa da murya
yana fad'a mata wasu kalamai wanda sirrin sune,tako kyalkyale da dariya"kai
Ustazu...? Shima dariyar yake yi"na rantse miki da girman ALLAH Zaujatiii...Ko baka
rantse ba na yadda da kai,ba abinda yake fitowa daga bakin ka game da soyayyarmu
sai gaskiya"ALLAH yamaka albarka Abu Bilqisss...sai ka dawo d'in.Ya amsa da to
sannan sukayi sallama ya zubama tashi wayar daya cire a kunne idanu,yayi lallausan
murmushi yana shafa kwantaccen bak'in gashin kanshi"Ummu Bilqisss...ya fesar da
iska ta baki ta hanci,sannan yasa wayar a aljihu.
Duk yadda yaso ya koma gida a ranar hakanshi bata tadda ruwa ba, sai
dai sun gama kome da Manager,ashe daga can Lagos aka samu matsala amma kome ya dai-
daita.Washe gari kuma wayewar gari litini yana shirin barin garin gwamma gari
yarikice anata k'one-k'onen tayoyi da kisan rayuka na babu dalili,cikin damuwa
Sudaida takirashi"ka riga ka taso ne?A ah.Sukayi shiru na wucewar wasu dak'ik'u"to
ALLAH ya sauwak'e wai meye musabbabin wannan fad'an?Sudaida ai kin san idan guguwar
siyasa tafara kad'awa sai dai Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un"
Tagyad'a kai"hakane,muma nan d'in sai a hankali,wallahi mutane dayawa
suna ta kwashe muhimman abubuwansu suna tafiya wai sai angama za6e kome ya dai-
daita sannan zasu dawo,Abu me aikin Inna ma yanzu tazo tamin sallama zata tafi
k'auyansu, hankalin jama'a da dama yak'i kwanciya tunda sukaji Kaduna ba
lafiya,yanzu mu kuma sai yadda hali tayi kenan?Ta tambayeshi.Eh Sudaida amma nan in
da nake ba a kome sai dai ansa matakan tsarone ba shiga ba fita, amma Manager yayi
waya da babban d'an shi sojane yanzu zai zo yafitar dani tunda dama rigimar a cikin
garine.Ta amsa a sanyaye"to ALLAH yasa.
Tana zaune cikin tsananin tsoro da damuwa na rashin mafita Aminu
yashigo"ke Sudaida ki d'auki abinda zaki iya d'auka me mahimmanci yanzu zamu bar
garin barinje in dawo...ta tari numfashinshi "har dasu Baba?Yakoma ya zauna tun
safe nake magiya da rok'onsu su shirya mubar garin"gudun hijira wajibi ne idan kaga
ba dama ka tsere...inji Garba Super,sunk'i toh ni dai gaskiyar magana tafiya zanyi
dan wuya ko da magani ba dad'i, sunce basu hana duk me tafiya tafiya ba su dai
sunanan,barinje ATM ki zama cikin shiri kafin in dawo. A sanyaye ta gyad'a kai
sannan tasake kiran Julaibib sai dai tak'i shiga tabi D'akin-shak'atawar da
kallo"to me zata d'auka?
To suma da suka ankare mutanan garin suna tafiya sai suka tare hanyoyi
ba shiga ba fita dan suna da wani k'uduri a zukatansu amma a zahirance fad'i suke
ba kome ba kome,dole Aminu ya hak'ura.Bayan sallar la'asar wata motar roka shak'e
da abinci da mutane hanya tabiyo dasu ta garin suma da gani ba tambaya yan gudun
hijirane ko da wani gari suka fito? ALLAH masani.
Direban a rikice yake sunata tsayar dashi amma yak'i tsaya"wanda
maciji ya sare shi idan yaga tsumma sai gudu...Kawai yayi k'undunbala zai bi
takansu sai suka tarwatse daga tsakiyar titin ya wuce cikin tashin hankali suka
rufa mishi baya, saboda rikicewa sai sitiyarin yakwace mishi,take ta daki sabon
masallacin mak'era da ake kan aikin ginawa, kowa yayi ta kanshi dan sun kusa cin
musu,suka fantsama cikin gari gidajen mutane a kid'ime,su kuma ganin wannan ya
dad'a tayar ma da mutane hankali musamman mata.Sudaida tashiga D'akin-girki ta
sauke abincin data d'aura dan bata da kwanciyar hankalin da zata iya k'arasawa dama
tun karin safe bata kuma sa kome a bakin taba.
Takira Julaibib amma yana ganin kiran yak'i d'agawa a k'arshema yasa
wayar a yanayin shiru (silent)saboda d'azu ta sake kiranshi akan kar yadawo, yabari
ko zuwa gobe ne dan suma garin ya fara rikicewa, sai yace mata bazai iya ba yau
d'in zai dawo yana ma hanya ta kwantar da hankalinta ba kome fa,kuma ta dafata
mishi shayi,tayi abinci me kyau yana azumi kome dare bazai yi bud'a baki da kome ba
bayan dabino sai abincinta ko da bai shigo kafin magriba ba,bai jira amsawar taba
yakatse kiran ya kira Musaddiq yana tambayar shi"wai meke faruwane Sudaida ta
dameni kar in dawo?
Yayi tsaki"kai rabu da ita,da da wata babbar matsala ai dana fad'a
maka,sun d'anyi zage-zagen sune d'azu ko dak'ik'u talatin ba suyiba suka koma
k'auyukan su,in dai wannan hatsaniyar ne yau suka fara?Ka san halin mata basa raina
abin tsoro,watama cinnaka za kaga tanama ihu da kururuwa a zo a kashe mata kar ya
cijeta.Uh uh Musaddiq sharri dai ba kyau...to suwaye suke ta guduwa?Julaibib yasake
tambayarshi.Masu guduwa dama yan ciranine amma ni dai a ganin idanuna banga wani
zaunanna gari daya tafi ko mutum d'ayaba.To ALLAH yakyauta.Musaddiq ya amsa"Amin
D'ansarai ka iso lafiya.Da wannan dalilin yasa yak'i sake d'aga wayarta.
Sai da yashigo cikin gari sannan ya d'auki wayarshi zai tsokani
Sudaida,sai dai missed call d'ari da yagani yasa zuciyarshi bugawa da k'arfin gaske
kira daga kowa na zuri'arsu lambar Inna yafara kira amma tak'i shiga,fargaba ta
kamashi lallai ba lafiya...
A bakin hanya kuma sunyi kaca-kaca da kayan dake cikin rokan sannan
suka banka mata wuta.Me neman kuka ne aka jefe shi da kashin a waki,wai saboda
yak'i tsayawa suka fara k'ona shagunan bakin hanya...ALLAH Sarki shagon Ashiru
Chindo suka fara k'onawa...Mtswww bahaushe me ban haushi na tanko me kan
bashi...wai sai a wannan lokacin suka san eh lallai wad'annan mutanan da gaske
sukeyi,suka fara neman mafita a sanda lokaci yariga yak'ure musu, dan ba a fafe
gora ranar tafiya...kumamar tsanyar da wuri take tila...Dana sani mara
amfani...suka cigaba da k'ona tayoyi suna watsa borkonon tsohuwa(tear gas)wallahi
abu kamar wasa k'aramar magana ta zama babba,garin yayi bak'ink'irin ga har6e-
har6en bindigogi ta ko ina.
Yana cikin wannan hali kiran Sudaida yashigo yad'aga da sauri,cikin
rawar jiki data murya tafara magana"Yaya D'an Sarai na rok'eka da girman ALLAH
karka k'araso garin nan...me yafaru ne?Yak'i a keyi ka koma dan wallahi sun fara
kashe mazaje suna k'ona gidajeee...tak'arasa maganar cikin sarewa saboda harbin
bindiga shima yaji hakan jin kunnuwan shi.Kina ji? Ta amsa da eh
ina...in...inaji...yana d'ago kai yaga gungunsu sun mishi k'awanya...zufa tasake
karyo mishi Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un yafad'a,a wayar kuma yana jiyo
hayaniya da surutai barkatai... wasu suna ihu wasu suna kabbara,anan kuma suna
jiran fitowar shi"gaba kura baya siyaki.
Sudaida tafi gidan Inna Insha-ALLAH zan zo in sameku a can yayi
jarumtar fad'a mata haka. Tarintse idanunta saboda a zaba wai...wash...uhhh...
bazan iya tafiya ba wallahi!wai...ALLAH na!Tafara nishin azaba Zaujiii...nak'uda
nake yi haihuwa zan yi...wai...Wayyo!Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un dan ALLAH
ka yafe min Yaya Julaibib mutuwa zan yi!A ah Sudaida ba nak'uda bane cikin naki fa
watanni biyar ne...wallahi shine bakaji marataba!Tayarfe hannu. Yasake d'ago kai
yakalleshi basu k'araso in da yake ba dan sun san ba ta in da zai gudu,yaga abinda
bai gani ba d'azu bindigogi AK47,pistol, shar6a-shar6an wuk'ak'e gayama jini na
wuce,adduna,tayoyi da jarka wanda ya tabbatar fetur ne a ciki,ga nishin da Sudaida
takeyi cikin tsananin ciwon daya had'u da tashin hankali,sai yaji wasu zafafan
hawaye sharrr... sun zubo mishi"yanaji yana gani amma ba shi da damar da zaije ya
taimaketa...
Sudaida kiyi hak'uri kiyi addu'a ALLAH yana tare dake,bata amsaba
nishin azaba kawai take yi tana kiran sunayen ALLAH wai...ALLAH ka taima... bata
k'arasa wasu suka shigo gidan.Wayyo! Yaya D'ansarai ga sunan...wani yad'auki wayar
dama a k'asa take ta bud'e maganar"me D'ansarai ya isa ya hanamu yi?Zuciyar
Julaibib tafara lugude...malam karka ta6a min mata yafad'a cikin
k'araji.Yakyalkyale da dariya "matsoracin banza matsoracin wofi kaje ka 6uya kana
magana ta waya,to idan ka isa kazo gidan na ka muyi gaba da gaba mana,I swear a
gabanka zan zamu mata yankan rago kai ma mu maka,wawa kawai"filthy bastard...
"Wallahi ALLAH ya fiku...yasake kyalkyalewa da wata irin dariya"eh
ALLAH ya fimu mu kuma munfiku kaga dai mune zamuci gari,kabimu a hankali dan zakara
a rataye baya caara.Bazan biku ba wallahi.Yajijjiga kai"that's very good,mun shigo
gidan ka dan muyi bincike ance kuma kunada bindigogi to amma tunda kace bazaka
bimuba za muyi maganin taurin kanka, kuma duk inda ka6uya a fad'in garin nan sai an
binciko ka an kawo min kai gabana na maka yankan rago kamar yadda muka fara yima
sauran tsinannun yan'uwanka.
Yakalli Sudaida da take durk'ushe tana matagugu dafe da ciki,yayi
murmushin mugunta"sai nayi abinda naga dama da wannan banziyar matar taka, ya
kyalkyale da dariya.Kalamanshi suka soke Julaibib da Sudaida suk'ar wuk'a a k'ahon
zuciya. Ambaton ALLAH takeyi a galabaice dan zuwa wannan lokacin k'arfinta ya riga
ya k'are,d'an cikinta ya dunk'ule waje d'aya,wucewar wasu dak'ik'u kawai sai jini
ya 6alle mata,tana kwance ko motsin kirki ba tayi,idanunta sun fara canja kala
kad'an kad'an bak'in ciki yake 6acewa.
Yayi jimmm...yana kallanta,yayi d'as d'as d'as da yan yatsunshi sannan
yagyad'a kai bayan ya kalli sauran da suma shi d'in suke kallo"tunda kin min
buk'ulun abinda nayi niyya to kema baki da sauran amfani a doron duniya,yad'aga
bindiga yana gyara kunamar jiki(trigger)zan fasa k'ok'on kan matarka
D'ansarai...Julaibib yafara karaji karka kasheta dan girman ALLAH kabari in zo ni
ka kasheni a madadinta... yakyalkyale da dariya wannan daga bayane sadaka da
karuwa...shege d'an iska ai kowa ya tuba dan wuya ba lada"may her gentle soul rest
in hell...suka had'a baki wajen amsawa da"amennn...Dai dai da har6e kanta da yayi
tauuu...tauuu...sai biyu jini yayi kaca-kaca a jikin bango rai yayi halinshi,suka
zuba fetur sannan suka sake harba bindiga wuuuhhh...wuta ta tashi suka fita da gudu
wayar ta katse.
Julaibib yashiga cikin tashin hankali,ya tabbatar sun kashe Sudaida.Yayi
Istirja'i yana kiran sunanta,ihun kiran sunan yasa wad'anda suka mishi k'awanya
suka bud'e motar suna mazurai suka jawoshi "da uban wa kake magana tun d'azu a
waya? Ko kana fad'ama sauran yan'uwanku masu sallah su kawo muku taimakone?To su zo
d'in ba abinda zasu iya mana dan munfi k'arfinku har abadan duniya, yabisu da kallo
duk fentin da sukama fuskokin su bai hanashi gane suba, wasu mak'otan shine,wasu ma
akwai kud'ad'en da suke binsu bashi,bazato yaji an buga mishi bakin bindiga"you're
very stupid ka tsaremu da idanu ba tambayarka muke yiba?Yarintse idanunshi dan yaji
bugun har k'wak'walwarshi,bai gama dawowa dai-dai ba suka rufeshi da duka, naushi
da mangari baji ba gani.
Wasu tarin matasan hausawa suka hango sun samu mafaka,abinda yasa suka bar
dukan Julaibib kenan suka rufarma wad'ancan.Julaibib yamik'a hannu yajawo wayarshi
data fad'i yasa a aljihu,dakyar yashiga motar yatashe ta yana gani dishi-dishi
saboda jinin da yake zuba dan sun farfasa mishi jiki bana wasa ba,yana zuwa k'ofar
gidansu yaci burki wani abu mara dad'i yatsirga ilahirin gangar jiki da
zuciyarshi"ina Innarshi? Baba?Walida da Bilkisun shi!?Zuciyarshi tana bugawa da
k'arfin gaske saboda ganin gidan ya gama k'onewa har ya rufta,ya tabbatar koma
menene a gidan ya k'one bashi da sauran amfani a doron duniya.
Yafito daga motar yana jiri yana bin bango har yak'arasa gidanshi,yana
cikin tafiyar ya yanke jiki yafad'i,awanni nawa yayi a kwance a wajen bai sani
ba,ya farkane yaji mutane nabi takanshi cikin neman ceton rai, yarik'o k'afar
wani"dan ALLAH taimakeni in tashi,yafizge k'afarshi"wannan rana ce ta kowa yayi ta
kanshi,kalleni da kyau harsasai guda takwas ne a cinyoyina amma ina tafiya sai kai
kana kwance babu alamar rauni me tsanani a tare da kai?Yayi gaba dan ALLAH kayita
kwanciya har su zo su same ka a wajen...ai bai san da gaske zai iya tashiba sai da
yaji hucin wutar da suka banka ya ta6i jikinshi.
Dakyar da sid'in goshi yak'arasa gidanshi nanma ya gama ci da
wuta,wani wajen kuma da sauran hayak'i,yana shiga D'akin-shak'atawar yaji kamar an
sa adda an sare mishi k'afafu saboda tashin hankalin abinda idanun shi suka gani.
Wayyooo...!!! Sudaida ce ta k'one k'urmus,maik'on jikinta male-male a wajen kamar
anyi 6arin mangyad'a,tabbasss da a waje yaga k'onannan gawar nan to ba zai gane
Zaujatiii...ce ba! Kuka yak'wace mishi jikinshi da zuciyarshi suka d'auki
rawa"yanzu irin kisan gillan da akama sauran zuri'arsu kenan!?da sauran yan'uwanshi
al'ummar Manzon ALLAH? Yahad'iye wani abu me zafin gaske kamar garwashin wutan da
aka barbad'eshi da dakakken barkono d'an munci wayyo! Innalillahi wa'inna ilaihi
raji'un!!!Lahaula wala quuwata illah billahil aliyul azim!!! Idanunshi suka kad'a
jawur sai yaji kome yafice mishi a rai... zafafan hawaye suna zubo mishi sharrr...!
sharrr...!
kira yashigo wayar daya manta da al'amarinta yacirota a aljihu
Musaddiq...yad'aga da sauri yana fad'in Musaddiq sun kashe Sudaida sun k'onata ina
sauran Iyayan mune? Suna ina?Kaima kana inane?Musaddiq ya amsa cikin tashin hankali
"saurara kaji abinda zan fad'a maka dan tun d'azu nake gwada kiranka bata shiga sai
yanzu.Sun kashe su Baba a masallaci, gidajanmu, Iyayanmu, matanmu da Ya'yanmu sun
banka musu wuta kafin sufito su gudu!Musaddiq yafara kuka sai dai mu bisu da addu'a
kafin wa'adinmu yacika,D'ansarai sunci k'arfinmu, sunyi galaba...!D'ansarai bamu da
abinda zamu kare kanmu dan nima haka nafito daga gida hannu rabbana...dakyar
furucin nashi yake fita... Musaddiq me yasame kane?Saurareni kawai Julaibib meye ma
bai sameniba!?Menene ban gani ba?Yak'ara fashewa da kuka"a gaban idanuna akama
Adnan da Sagir yankan rago...!!!
Kaiii ALLAH yatsinema arna...Julaibib k'afafuna a karye suke ga sara
ba adadi a jikina,ga harsashin da suka harbeni yana cikin cikina...dakyar yake
furucin Julaibib yadad'a manna wayar a kunnanshi dan maganar tashi k'asa take dad'a
yi,kaima sunata neman ka ruwa a jallo dan haka ni shawarar da zan baka idan kasamu
ma6uya to wallahi ka6uya,tunda ba abinda zaka kare kanka dashi...yafara tari da
nishi duk tarin da yayi jinine yake fita ta baki ta hanci,yafara numfarfashi sama-
sama, numfashin yana san d'aukewa,yafara magana a fizge D'ansarai mu yafema
juna...abinda duk yake tsakaninmu na kud'ad'e da sauran al'amuran rayuwa duk mu
yafema junaaa...!rayuwata...ta...k'are ina ji ajikina bazan kuma rayuwa a doron
duniya ba!Cikina kamar ana huramin wutahhh...!!! Wai...washhh,Yayi nishi me
k'arfi...jini yana zubowa tabaki ta hanci.. Ju...l...lai...bib...kumaaa...ina!yayi
iya yinshi furucin yak'i fitowa yana nishi cikin tsananin ciwo...
Kaskon wuta me wuyar tallafa.
Na gaban wuta shi yake jin d'umunshi.
9 Rajab 1441
3 March 2020
We Ibrahim's Daughters👇
Asdilat KD...2geda with Ra'ibs.
DANGIN NONO WRITERS ASSOCIATION
{Da Inganci Mukayi Fintinkau}
Bismillahi wabihi nasta'in
...GWAJIN DAFI💔
Almost true story
Daga alk'alamin🖊
Ya'yan Ibrahim
Saudat A.Baba (Asdilat KD)
Da
Bara'atu Ibrahim ( Ra'ibs)
Shafi na ashirin da biyar.
Cikin tsananin tashin hankali yake fad'in Musaddiq...Musaddiq kana
inane!?Shiru ba amsa yacire wayar ya duba har yanzu a had'e suke,wucewar wasu
dak'ik'u Julaibib yana cigaba da kiran sunan shi Musaddiq!Dakyar ya amsa.Kana
inane? Musaddiq yamirgina kai cikin ciwo"bazaiyi amfanin kome ba,na san mutuwa zan
yi tawa ta riga ta k'are,D'ansarai...kab... ka6uya... k...kak... kaw... wai.Zuciyar
Julaibib tasake tsinkewa yafara kuka"na rok'eka da girman ALLAH kafad'a min inda
kake zan zo in taimake ka...kai kad'ai karage min d'an uwa na jini a doron duniya!
yacigaba da magiya har Musaddiq yabud'e baki dakyar yace"ina wajen masallaci.Wani
masallacin? Wanne Musaddiq?
Yayi tambayar a gaggauce jin wayar shi tayi k'ara alamar caji saura
kad'an yak'are... Musaddiq ya kasa magana sai nishin azaba yakeyi... Wanne daga
cikin masallacin Muss...kafin yak'arasa fad'in sunan difff wayar takashe
kanta.Yafurzar da wani huci yana kallan k'onannun k'asusuwan Sudaida sai yaji kukan
cakkk...Ya tsaya,yamik'e tsaye yana mata addu'ar dacewa da rahamar
Ubangiji"Zaujatiii...ya fad'i sunan yana jijjiga kai"sai ALLAH yahad'a mu a
lahira... uwargidata ta duniya da lahirahh!...
Koma wani masallaci ne Insha-ALLAH sai ya gano Musaddiq ya bashi
taimakon gaggawa iyakar iyawarshi,zuciyarshi tabushe,wallahil-azim shima sai yayi
kisa sai dai idan bai had'u da arne ba;koda zasu kashe shi,yana fita kuwa yaga
k'aramar bindiga an kashe wani arne ta fad'i a hannunshi, yad'auka ya lalube
aljihunshi yakwashe sauran harsashin yaloda a ciki sannan yafara tafiya cikin
sand'a yana bin bango,daga nesa yahango gungunsu sun dumfaro inda yake,a hankali
yazame yakwanta a cikin gawarwaki kamar shima mataccen ne.
Suka zo suka wuce suna surutai da yaren Bajju,a d'an abinda yake
tsitssinta daga yaren ya fahimci harsashin sune yak'are zasu koma gida su k'ara
sabon lodi,dan haka yad'aga bindiga yasaita su daga kwancen ALLAH ya taimakeshi ya
harbe guda uku nan take suka zube a k'asa matattu,sauran suka fara gudun ceton rai
suna zage-zage a cikin gawarwakin nan akwai wanda bai mutu ba, amma dan abu kazan
uban mutum yabari muje muk'ara shiryawa wallahi zai gane da gero ake
koko...Julaibib yasake harba bindiga yasamu wani a kai shima ya fad'i yana ihu da
kururuwa,sai da yak'ara mishi harsashi biyu sannan ya tashi yabar wajen kafin su
dawo,zuciyarshi tana tafarfasa da kalaman wanda ya harbe Sudaida"zan fasa k'ok'on
kan matarka...bata sauran amfani a doron duniya"may her gentle soul rest in hell...
Julaibib a gaban idanuna sukama Adnan da Sagir yankan rago...ank'ona su Inna a
gidajansu... sun kashe su Baba a masallaci...kalaman da suka dinga mishi amsa kuuwa
a k'wak'walwarshi kenan.Sai yaji wani k'arfi yasake zuwa mishi.
Yana cikin tafiya yaci karo da gawar Abdul d'in Yaya Karima an
daddatsashi abun ba kyan gani,bai tsaya ba dan tsayuwar bata da amfani tunda ya
riga ya mutu,su da arnan kuma kowa k'ok'arin kashe kowa yakeyi haka yakeya cin karo
da gawarwaki kisan wulak'anci!Julaibib yayi yawon bin masallatai amma baiga
Musaddiq ba,a wajen masallacin Malam Murtala yaga wasu mutane guda biyu an sa musu
taya sun k'one k'urmusss...ba ta yadda za ayi ka gane ko suwaye wallahi,yaciga da
tafiya zuciyarshi na tafarfasa daga baya yaji an harbe shi a kafad'a ashe wasu daga
cikin su sun hangoshi... yajuya yana harbinsu shima har sai da harsashi
yak'are,yatura bindigar a aljihu yakwanta yana a k'asa cikin mawuyacin hali jini
yana zuba.
A wannan rana ta litini kwana akayi ana gumurzu tsakanin musulmai da
arna,duk da musulmai masu kayan aiki k'alilan ne amma sunyi k'ok'ari da k'arfin
zuciya suma sun kashe arna ba wanda yayi galaba akan wani,kare jini biri jini
akayi"ragasss mutuwar kasko.Toh wayewar gari ranar talata kenan kowa ya galabaita
ba sauran k'arfi ba kayan aiki,ba abinda mutum zai sa a bakin salati,irinsu
Julaibib masu azumi ranar litini babu kome a cikinsu sai abinda sukayi sahur a
daren lahadi, ga raunuka a jikin mutane da yake buk'atar taimakon gaggawa amma
kayan agajin(first aidbox) tun dare yak'are.Su kuma wad'ancan anata dafa musu
abinci da kayan sha na k'arin k'arfi suna zuwa suna cika cikinsu, bayan haka kuma
wad'anda akayi gumurzun dare dasu, sai suka dinga komawa gida, wasu matasan na
daban suna shiga cikin gari da sababbin kayan aiki.
(Tabbasss ni 'yar Ibrahim Asdilat KD...ganauce, ALLAH yasa inga Annabinmu Muhammad
Sallallahu alaihi wa'ahlihi wasallam...yadda naga wannan al'amari ganin idanuna)
Kuma a wannan safiyar ta talata jirgin k'asa yashigo garin musulmai suka fara
hamdala ga Ubangiji cewa an kawo musu d'auki...Tabbasss d'auki a kawo ta hanyar
k'arama barno dawaki dan k'ungiyarsu (CAN) ce takawo musu k'arin makamai,to a
wannan lokacin ne sukama musulmai ainihin kisan k'are dangi, suka tarwatse kome da
kowa na garin...musulmai sai kabbara da addu'o'i sukeyi a duwatsu suna harbinsu...
amma ko gezau basuyi ba...sarkin yawa ai yafi sarkin k'arfi...Zakara a rataye baya
caara;wasu na shiga gidaje sai sunma gida k'ark'af da kayan ciki sannan su banka
mishi wuta,haka shaguna da koma inane, shagunan bakin hanya kuma sun kwakkwashe
kome amma basu k'ona suba saboda wai anan zasu fara sana'o'insu.
A wannan mawuyacin halin sukayi a rangama da Julaibib yayi matuk'ar
galabaita yana numfarfashi,wata Juli ce tanuna shi"yauwa ga shegen da muke ta nema
tun jiya,yabisu da kallo idanunshi sun kad'a jawur,dan tsabar rainin wayo da samun
waje "kuturu da gad'a a rama.Wai har da mata suna rik'e da wuk'ak'e gayama jini na
wuce,wanda za su iya harbi da k'ananan bindigogi sun rik'e,wasu da kokara da
gorori, Kauuu...bazato yaji an buga mishi kokara akai"dan abu kazan ubanka you've
no respect muna tsaye kaima kana tsaye?
Kaci sa a ba bindiga a hannuna dana fasa k'ok'on kanka,Juli tamik'a mishi
na hannunta"ga wannan"yature hannunta"rabu dashi ba yanzu zamu kasheshi ba sai yaci
naman ubanshi me dogon gemunnan gashashshe; Now just kneel down,rise up your hands
and close your eyes"haka yakai gwiwoyinshi k'asa yayi yadda yace.Wani da yayi tatil
da uwar laifi yafara tambayarshi da yanayinsu irin ta mashaya"kai ne D'ansarai
Lecturer a Gidan-Waya da nace kasamo ma yata gurbin karatu kace bata da credits
d'in da za a d'auketa ko?
Yayi kamar baiji abinda yafad'a ba.Sai yabuga mishi gora a
kafad'a"childish monger I'm I not talking to you?Zuciyarshi tak'ara bushewa wallahi
shak'a d'aya zai wannan ragowar ruwan burkutun numfashinshi yad'auke har abadan
duniya a doron k'asa,sai kawai yamik'e tsaye yana kallanshi cikin idanu"Yes
Indeed,I'm D'an Sarai Lecturer in Kaduna State College of Education Gidan-Waya.Wani
yazo gabanshi"how dare you baka da kome amma zaka nuna mana zafin kai?Ka san harda
wancan tsinanniyar makarantar taka daka bud'e yasa mukayi yak'innan?Dan na san
halinka sai kasa wasu daga cikinmu sun zama irinku masu sallah,dama yara nawa kasa
suka zama irinku?
To suma duk mun kashe shegu saura kai...bai gama rufe baki ba Julaibib
yayi kukan kura ya cafki mak'ogwaranshi,idanunshi suka firfito yafara kakari dakyar
suka 6am6areshi,yafad'i gefe yana tari da maida numfashi,sai kuma ya mik'e ya
dunfaro shi, yana nunashi da yatsa"yau ka gama kad'ewa har ganyanka
wallahi.Julaibib da zuciyarshi tariga ta bushe baiyi wata-wata ba yakai mishi wani
irin naushi da k'arfin bala'i a muk'amuk'i ahhh...yayi ihu ya tsuguna kame da wajen
dan yaji naushin yadda yakamata,yana zubar da jinin bakinshi sai ga hak'ori biyu a
k'asa yasake fasa ihun takaici kaciremin hak'ora?
Julaibib yajijjiga kai zai sake kai mishi wani naushin yaji an bank'areshi
ta baya...yayi iya k'ok'arinshi yakwace amma ya kasa dan rik'on kura taga nama suka
mishi tamauuu...Idanunshi suka k'ara kad'awa jawur gangar jiki da zuciyarshi mazari
sukeyi,wata jijiya ta fito rad'am a gefen goshinshi kamar shatin bulala saboda
rik'on da suka mishi me bala'in azaba.
Wanda aka fasama bakin ya goge jinin sannan yamik'e tsaye suna kallan
kallo da Julaibib zuciyoyinsu na tafarfasa,har ya kar6i bindigar ya saita kirjinshi
dai-dai satin zuciya sai kuma yayi wurgi da ita kaiii...yafad'a cikin k'araji"idan
na kasheka one time naji haushin kaina wallahi...yakallesu kuci buhun abu kazan
ubanshi yadda zaku iya,yatattaro miyan bakinshi me had'e da jini da kakin majinan
da yayi yatofama Julaibib a fuska"filthy bastard.Yatasa matan agaba sukayi
tafiyarsu. Aka fara ba Julaibib na jaki ba ji ba gani suna jaddada mishi"ai ko ba
makami da hannuma zamu iya kasheka har lahira.
Wayyooo...ALLAH!!!!Julaibib ya daku iya dakuwa sun mishi walmukalifatu da
jiki!har ya daina numfashi,suka dinga janshi har zuwa inda wasu tarin gawarwaki
suke suka jefashi,anjima zamu gasaku gashin kan saniya ba irin gashin tsire ba,suma
suka juya sunata haki da numfarfashi...
Wani sanyine yafara ratsa har 6argonshi kamar wanda a ka ajiyeshi a
sararin dusar k'ank'ara ba kaya ajikinshi,ko ina nashi na karkarwa har ya'yan
hanji,abinda ya dawo dashi cikin hayyacinshi kenan, dakyar da sid'in goshi ya bud'e
idonshi guda d'aya,dan d'ayan ya kumbura suntum fatar idon tayi bak'ink'irin alamar
duka da kwanciyar gurbataccen jini,wajen wani irin wari,k'arnin jini da hamami
ciwukan dake cikin gawarwakin yakeyi, k'udaje kuma sukace ga sunan yau take sallah
a wajen su.Abubuwan da suka faru kafin ya suma suka dawo mishi tiryan-tiryan,wasu
zafafan hawaye suka fara zuba daga idonshi me lafiya sharrr... sharrr...
Yafara Istigfari wucewar wasu dak'ik'u kuma ya mirgina kai cikin
ciwo"ALLAH kaine mahaliccina! ALLAH ka fini sanin halin k'uncin da nake ciki,
kataimakeni.Yayi iyakar iyawarshi ya d'aga hannunshi ya kori mayatattun k'udajen da
suka baibaye fuskarshi ga kuma hayaniyarsu amma abun yaci tura, k'afarshi d'aya a
karye take hannayen shima haka,zuciyarshi tayi tsananin rauni yana buk'atar
taimako, mak'ogwaranshi ya bushe k'amasss kamar ruwa bai ta6a wucewa ta wajen
ba,miyau ma dakyar yake tsatstsafowa a bakinshi, yahad'iye wani abu me zafin gaske
kamar garwashin wutan da aka barbad'eshi da dakakken barkono d'an munci,kanshi
yasara,yafara mishi wani matsanancin ciwo kamar zai rabe gida biyu.A wannan
tsananin ya hango gungunsu da jarka,suna zuwa suka bud'e fetur ne a ciki suka fara
juyema gawarwakin har dashi sai da suka matsa daga wajen sannan suka harba bindinga
tauuu... nan take wuta ta kama wuuuhhh...suma suka juya sukayi tafiyarsu suna wata
irin dariya ta rashin hankali da imani.
Wayyo wai ALLAH!Wato idan kaji k'i gudu to Alqur'an sa gudune bai zo
ba...shi dai Julaibib bai san ya akayi ba sai gashi ya mik'e...yana barin wajen
wuta tabi takan sauran.Yana dafe da bango yana d'ingisa k'afa d'aya me lafiyar
dakyar...wani irin jiri ya wulwulashi ya buga da k'asa yadunk'ule yana
matagugu,numfashinshi fita ya keyi wani baya shiga, zuciyarshi na mishi suya tana
bugawa da k'arfin gaske kamar zata fasa k'irjinshi ta fito!Wucewar wasu yan
dak'ik'u sai gashi ya zube a k'asa wanwarrr cikin d'aukewar numfashi difff!
Bayan da k'urar ta lafa manya-manyan matasan arnan da akayi yak'in
dasu irinsu Nuhun gidan Diryan,Julius,Shekari da sauransu da sauran su,sune suka
dinga tasa k'eyar mata da k'ananan yara zuwa Police Station d'in garin suna musu
zagin tsame nama da mugun alkaba'i,su kuma suna biye dasu wasu na kukan zuci,wasu
na nasarari,wasu ba uh ba uh uh,haka suke tsallake gawarwaki abun ba kyan gani,kaga
gawa ta kumbura ta fashe kayan ciki a waje,awani wajen kuma sun saki aladunsu suna
danasha da gawarwakin...Kai ALLAH ka k'ara tsinema arna!dan wata shari'ar billahil-
azim sai a lahira!.
Zuwan sojoji da jiniyarsu (siren)da wasu masu kud'in suka hayo kuji fa?
Daga wasu garuruwan dan su fitar da yan'uwansu tunda har lokacin basu bud'e hanya
ba,haka ake ta zama a Police Station cikin mawuyacin hali,amma wasu daga cikin
arnan suna ta kawoma yan uwansu masu sallah abinci da sauran kayan buk'ata.Yayin da
wasu bak'in ciki kamar ya kashe su da suka ga maza da yawa na daga musulmai sun
fito da ransu da lafiyarsu,sunata mamaki da takaici, to su wad'annan a ina suka
6oya ne a cikin garin da har basu gan suba? Sun manta cewa"zakaran da ALLAH ya nufa
da caara toh fa ko ana muzuru ana shaho wallahi sai ya yi.
(Alhaji Umar Millionaire Doka,Wallahil-azim baza mu manta k'ok'arin da kayi na
fara turo da sojoji Zonkwa ba har abadan duniya,Ubangiji yasaka maka da mafificin
sakamakon shi,yasanya hakan a mizanin kyawawan ayyukanka)
Wannan jiniyar tasa duk wani wanda ALLAH yasa yana da sauran numfashi
a doron duniya na daga maza musulmai daya 6uya yafito,nan da nan suka fara d'aukar
wad'anda suke kwance cikin mawuyacin hali zuwa asibitocin garin dan a basu
taimak'on gaggawa, masu gudun hijira suka fara d'aukar hanya,wasu daga su sai kayan
jikinsu dan an k'one kome nasu,wasu kuma ba a k'one ba,masu sauran yan uwa a wasu
garuruwan suka shiga kiransu su taimako da mota azo a d'auke su an bud'e
hanya...kai rayuwa bata da tabbasss! idan ka san farkon ka,toh baka san
k'arshenka,Ubangiji kamana gamdakatar da kyakkyawan k'arshe👏abinda aka tara shekara
da shekaru rana d'aya da wuni d'aya an tarwatsashi har abadan duniya sai dai a fara
sabon nema daga farko!.
Julaibib yana cikin wad'anda aka kwasa magashiyan zuwa asibitin"Zonkwa
Medical Center" Suna kwance a k'asa a d'akin da ake zama kafin aga likita
(reception)sai dai tunda aka kawo su ba wanda yakallesu tsakanin likita da
ma'aikatan jinya bare susa rai da wani taimakon gaggawa.Wata ma'aikaciyar jinya
tashigo tana yarfa musu ruwan bala'i kamar su suka kawo kansu "gwamma ku bud'e
kunnuwanku dakyau ku jini ba wanda zamu duba sai ya bamu kud'i,idan ba haka ba to
sai dai ku dauwama a haka har ku k'arasa mutuwa,taja dogon tsaki" ku d'in nan kuna
da taurin kan tsiya to amma hakan kuma ai yana dakyau tunda kunji a jikinku,sau
nawa muna muku hannunka me sanda?bama k'aunarku, bama k'aunar zamanku a garinmu
kona sisin kwabo amma naci dambun kuturu kun kafe kai da fata,sai kuma tayi
lallausan murmushi"ai gashi mun muku kattt...Kisan mummuk'e.
Tajuya tana cigaba da fad'an kalmomin wulak'anci da tozarci.Julaibib
daya sake farfad'owa ya mirgina kai cikin tsananin ciwo da tausayin kai"banda
rashin imani a ina mutum yake da wani kud'i a yadda yake d'innan da har zai basu
sannan su dubashi!?Tsananin yayi tsanani a gareshi shi kad'ai yasan abinda yakeji a
gangar jiki da zuciyarshi sai kuma wanda yashiga mawuyacin hali irin wanda
yashiga,suna buk'atar taimako toh sai dai kuma baiga ta inda taimakon zai
zoba...sai kuma yayi saurin fad'in.
"ALLAH na tuba,k'udirarka tafi gaban tunanin duk me tunani! Ya
Ubangajin sammai da k'assai!Ya Ubangijina na mik'a duk al'amurana gareka! Muryarshi
tafara rawa alamar karyewar zuciya💔Ya Ubangijina bani da k'arfi bani da dabara sai
abinda kazartai a kaina! Ubangiji ka iya mana! Yamaida idonshi me lafiyar ya rufe
dan d'ayan kumburan daya dad'ayi yasa kanshi ya mishi wani irin nauyi kamar an
d'ora mishi buhun duwatsu,a hankali yacigaba da maimaita addu'ar"Allahumma lasahla
illah maaja'altahu sahlan wa'anta taj'alul hazna izaa shi'ita sahlan...
Wallahi abu kamar wasa k'aramar magana ta zama babba kwana biyu
sunanan a haka kamar yadda wannan ma'aikaciyar jinyar tafad'a mutanan d'akin sai
mutuwa suke yi...wari da k'udaje kam ba a magana.Doctor Bode Davis mamallakin
asibitin da wasu matasa suka shigo d'akin yana nuna musu"kun gansu sune nake so a
fita dasu daga waje muna so a gyara wajen...wani a cikin majinyatan yafara
zaginsu"kai Bode ALLAH yak'ara tsine maka albarka,kuma in ALLAH ya yadda kaima sai
sun maka abinda suka mana,ka sanni farin sani har family card nake dashi a asibitin
nan amma yanzu kace bazaka dubani ka ciremin harsashin dake cinyoyi naba har sai na
baka kud'i!
ALLAH yatsinema gamayyar da zaka nemi taimako a wajen wanda kuke
gamayyar yak'i taimaka maka a sanda kake tsananin buk'atar haka, tirrr da irinka,
wallahi nayi nadamar duk wata mu'amala data ta6a shiga tsakaninmu!Wani yakai mishi
kutifo"how dare childish rat...Zai sake kai mishi kutifo Bode yace kyaleshi yaji da
abinda yadameshi,in dai kanada kud'i to zamu cire maka,ko da ATM card d'inkane in
dai yana aljihunka sai mu d'auka kafad'a mana pin-number mu ciro kud'in muzo mu
cire maka.
Yana daga kwancen ya d'ud'd'ura musu zagi sannan yace"gwamma in mutu da
in baku ATM d'ina gidan kud'i su rik'e kud'in na bar musu har abadan duniya. Kai
bakinka ba zaiyi mutu ba duk da kana kwance sai yadda a kayi da kai? Eh bazai mutu
ba ALLAH ya fiku, mutuwata da rayuwata ba ta hannun ko wani kafiri,a hannun ALLAH
take tunda gashi nan har yanzu da raina, ai ba a san ranku muke numfashi ba,kuma na
rantse da girman ALLAH sai na d'auki fansa,sai na rama abinda kukama Babana da
k'anina!
ALLAH dai yabani lafiya zan tafi Maiduguri,na rantse da girman ALLAH duk
wanda ya kwanta toh da safe sai dai ku d'auki gawarshi ku rubuta ku ajiye alk'awari
ne wannan,idan ko mutum bai mutuba to ya daina baccin dare sai dai in zai dauwama a
kwanan zaune dingirgir.Kai! suka daka mishi tsawa"kamana shiru komu k'arasaka.Idan
kun fasa k'arasani kuba jikokin Baranzan da Zamburan bane,dan kun kashe ni ai a
kwai sauran matasa irina da zasu maye gurbina insha-ALLAH. Basu sake magana ba suka
tafi.Suna fita yafara kuka yana numfarfashi,yana cigaba da zagin su...Wucewar wasu
dak'ik'u sai ga wasu matasa guda biyu sun zo sun d'auke shi.
Julaibib yabi bayansu da kallo yana zancen zuci"kowace irin azaba zasu
sake gana mishi oho!zuciyarshi tak'ara rauni hawaye yafara zubo mishi,ba zato yaji
ansa hannu ana share mishi hawayen"kayi hauk'uri ni zan taimakeku,dan banji dad'in
abinda aka muku ba sai dai"I have no power da zan hana.Yakalleta da idanshi me
lafiyar"ma'aikaciyar jinyace tana sanye da riga da buje farare kanta da k'arin
gashi tozon rak'umi guda,yakauda kai... tabbasss shima da yana da k'arfin da zai
iya magana to da shima ya d'ud'd'ura mata zagi bayan ya mata dukan mutuwa wallahi.
Tabisu da kallo cikin tausayi"casualties ne rututu all of them
ramshackle.Tayi tsaiii...cikin tunani ta yaya zata taimakesu?Sai kuma ta jijjiga
kai tana murmushi yes,tayi d'as da yan yatsunta "fad'uwace tazo dai-dai da zama,sai
tajuya da sauri tafita.
Julaibib yasake mirgina kai bangaren dama cikin matsanancin ciwo,ga
yunwa ta ci ta cinye k'irjinshi ya mishi nauyi,yana tunanin ma ya gamu da gyanbon
ciki,numfashinshi yafara fita sama-sama kamar zai d'auke,a cikin zuciyarshi yake
fad'in "Qadarullaahi wama sha'a fa'al...a hankali yafara jin wani abu na sukarshi
kamar allura a ilahiran jikinshi me zafin gaske wucewar wasu yan dak'ik'u sai
numfashin shi ya d'auke yayi doguwar suma.
Bobby!...takira sunan shi a rikice ganin wata shar6e6iyar wuk'a gayama
jini na wuce daya fito yana karkad'ata sai walainiya take yi a hasken rana, yana
wak'ar shi cikin nishad'i da karsashi:
Into my heart...come into my heart love Jesus...
Come in...to stay...come into my heart love Jesus...
Tajijjiga kai tana amsa mishi da"amennn.Yayi yar dariya"amennnn,fa kikace are you
kidding me? Tagirgiza kai"Absolutely no...duk da zuciyarta lugude take yi karfa ya
da6a mata wuk'ar a ciki"eh haka nace amennn,mu musulmai ai mun yadda da Annabi Isah
Alaihissalam a matsayin d'an aike daga ALLAH,kune dai baku yadda da Annabinmu
Muhammad Sallallahu alaihi wa'ahlihi wasallam ba.Tajuya harshe zuwa yaren Bajju.
"Ashyyeaggo(Ina kwana
Yace oh basakut(yi hak'uri) ashe bamu gaisaba
"Ashyllafiya(kin tashi lafiya) yafad'i hakan a gaggauce ya nufi k'ofar
gidan zai fita.
Bobby ani yake?(ina zaka)ya tsaya cak sannan yajuyo suna kallan kallo na wucewar
wasu dak'ik'u,idanunshi sun kad'a jawur da 6acin rai,takauda kai,yasauke numfashi
amma baice kome ba,ita kuma tacigaba da maimaita"ALLAHU-ALLAHU rabbi laa'ushrika
bihi shai'a.
Kira yashigo wayarshi yad'aga"kuyi gaba zan biyoku yanzun nan.
Jikinta yak'ara yin sanyi dan ta tabbatar cikin gari zasu sake komawa
dan an kawo mishi rahoto d'azu;hausawan daba a k'ona gidajen suba suna ta zuwa suna
kwashe kayayyakinsu. Kwallah suka cika idanunta,ta had'a tafukan hannayenta alamar
magiya
"Bobby I beg you In the name of Almighty ALLAH karka sake komawa cikin
gari.Yaja dogon tsaki yana harararta"ba abinda zai hanani komawa.Yasa hannu zai
cire sak'atan k'ofar gidan tasha gabanshi,muryarta tana rawa"haba Bobby wannan wani
irin rashin tausayi ne?Me mutanan nan suka muku ne?Haba Bobby kuma fa kuna da
yan'uwa a garuruwan da musulmai sune majority while ku kuma minority,yanzu idan
sukace suma sai sun rama abinda ku kama yan uwansu na nan yaya za kaji a cikin
zuciyarka?
Tacigaba da fad'a mishi kalaman da suka sa jikinshi yayi sanyi,haba
Bobby nima bazan so ace an kashe ka batare da kayi laifin kome ba,addinina daban da
addininka amma duk da haka you're my cousin,kuma ina son ka,wannan soyayyarce ma
tasa nake zuwa in da kuke,hawaye suka zubo mata sharrr...sharrr...Bobby ka mantane
"Kyan a ayyia ni anaatsi kpa shya?(Duk abinda ka shuka to a k'arshe shi zaka gir6e)
" Da anyi wyi yet kasham(me munine ko kyau)
Tafara kuka kasani sarai Bobby biblically ba ace kuma wani addini haka, toh abinda
kukeyi kana ganin
Kaza baa chat?(ALLAH yana so)
A hankali ya girgiza kai.Tace to na rok'eka dan girman ALLAH kayi hak'uri kazauna a
gida.Ya amsa kai tsaye sai dai idan tare zamu zauna muyita chatting for all day
long.Eh na yadda.Yasake kallanta bayan haka za kimin pepper chicken,za kimin pepper
soup,da irin wannan hamburger da kuka zi mana dashi da fruit salad yanunata da
yatsa"concur?Tajijjiga kai"hundred percent"muje katayani ai wannan abu me sauk'ine
k'wace goruba a hannun kuturu.
Alhaji Salim yasaki labulan ganin sun tafi D'akin-girki,yasauke
gwauran numfashi cikin dukan zuciya,al'amarin ya ritsa da sune bayan ya kawo Ummi
kamar yadda yasaba idan sunyi hutu a makatanta,ko kuma ranakun k'arshen makon da ya
samu damar yin hakan,amma baya tafiya yabarta,tare suke yin kwanaki biyu ko uku
sannan su koma,jikinshi yayi sanyi sosai, anya zai kuma zuwa Zonkwa bare har
yashigo k'auyen Madauci?
Yagirgiza kai"shi dai yazo wannan yanki na k'arshe har abadan
duniya,amma idan Ummi tayi aure ta ga za ta cigaba da zumunci da dangin
mahaifiyarta toh shi dai bazai hana taba,tunda matar Mazon ALLAH Sallallahu alaihi
wa'ahlihi wasallam Safiyya tana zumunci da yan'uwanta na jinsi Yahudawa,wannan bai
zama haramun ba.
Yana wannan zancen zucin Rahab tashigo"Baban Ummi.Yad'ago yakalleta ba
tare daya amsa ba.Tayi k'asa da murya"Mama ta fitane? Yayad'a kai.Sai ta zauna
sannan ta fad'a mishi abinda yake faruwa a asibitin da take aiki"na san zaka
taimakesu, mu an hana mu musu kome da tun ranar da aka kawo su dana fara basu
taimakon gaggawa.
Jikinshi ya dad'a yin sanyi"nagode Rahab da kika fad'a min wannan
maganar Insha-ALLAH zan taimakesu.To kazo muje ka gansu dan kasan ya azayi kafin
goben.Yagirgiza kai"bazan fita in bar Ummi da Bobby kad'ai a cikin gidan nan
ba.Tayi yar dariya"kana tsoro kar ya soke ya 6arke maka 'ya da wuk'a ne?Tad'an
motsa kafad'a"na san ba abinda zai mata amma dan hankalin ka yakwanta barin kira
Kuno da Yachat su tayasu zama kafin mu dawo ko? Yagyad'a kai"yauwa yanzu naji dama-
dama wai kibiya a cikin idanu.Takama ha6a kuma dai? To anyi ba ayi ba kenan.
Bayan sun idar da sallar magriba Ummi take tambayarshi"Abbana d'azu
naga kun fita da Aunt Rahab ina kuka jene?Yakalleta da kulawa "ceton ran wasu bayin
ALLAH yan'uwan mu musulmai naje,gobe dasu zamu wuce Kaduna.Bobby yad'aga labulan
d'akin "ke Ummi baza kizo muyi hirar bankwana bane ko me?
Tad'anyi murmushi"zuwa kai amma kabari muyi sallar Isha'i.Yasaki
labulan yak'arasa shiga cikin d'akin yamik'a mata wata babbar waya samfurin
Samsung"to ga wannan idan kun gama you shoud let me know zani Fadiyan Guga
ne.Takar6i wayar ranta ba dad'i, a daren litini yashigo da manyan wayoyi sunfi
hamsin,da su na'ura me kwakwalwa wai duk tsintar yayi a cikin gari da tarin
kud'ad'e a cikin buhu"lallai wata shari'ar sai dai a lahira wallahi!.
Washe gari da sassafe sukayi sallama da kowa suka d'auki hanyar garin
gwamma,ko a hanya basu samu wata matsala da jami'an tsaro ba dan kowa ya san abinda
yafaru a Zonkwa, idan musulmai ne su jajanta tarebda addu'ar"ALLAH yasa
kaffarace,idan kuma arna ne suji dad'in ganin mutanan da suke kwance cikin
mawuyacin hali,da da dama da sun k'arasa su da bindiga,wanima gallama Alhajin Salim
harara yayi"to wad'annan dai ai kuna 6atama kanku lokaci me wajen kaisu
asibiti"repetitive strain injury ne dasu fa ko baku gani bane?Mun gani sai yaya?
Alhaji Salim ya tambayeshi.Yamotsa kafad'a yana ta6e baki"they are in coma I don't
think they will survive. Alhaji Salim yaja motar ba yare da yace kome ba.
Motarsu tana tsayawa a harabar gidan sauran yaran suka fito da gudu"
oyoyo Abbanmu... oyoyo Yaya Umminmu,suka ringume juna cikin farin ciki.Hajiya
Bara'atu farar mace,jaruma me k'ok'arin adalci da gaskiya a duk al'amuranta
tak'arasa saukowa daga matattakalar benen,fuskarya d'auke da murmushi, Ummi tasaki
k'annanta ta rungumeta "Mamanmu nayi kewarki,kullum sai na yi mafarkinki. Tarik'e
hannunta suka zauna"nima haka,toh ya fargaba?Ummi takad'a kai"Mamanmu al'amarin ba
kyan gani sai ma kinga wad'anda muka kai asibiti mutum a raye amma ya fara ru6ewa
tsutsotsi suna fitowa a jikinshi!takama goshinta da hannun dama kwallah sun ciko
idanunta "kai! Mamanmu arna basu da imani kona sisin kwabo kuma...sallamar Alhaji
Salim daya tsaya gaisawa da mak'otanshi da katseta daga abinda zata fad'a.
"Sannu da zuwa Alhaji.Ya zauna"yauwa sannu da gida ya akaji da yara?
Tayi murmushi kawai wanna ta tambayi ya masu jikin?Toh godiyar Ubangiji a kowani
hali da yanayi,yakad'a kai amma abin kam ba gyan gani.
Hajiya Bara'atu tama mijin na ta wani kallo dasu biyun suka san
ma'anarshi duk da yana cikin damuwa sai da yayi dariya,sauran k'annin Ummi suka
shiga tayashi darawa duk da basu san abinda yasashi dariya ba,Ummi ce kawai taga
abinda yafaru tace musu "to kiyi shiru Ku fa a wasu lokutan baku da wayau,dan kawai
kunga ana dariya sai kuma ku fara?Yaran suka kalleshi"kaima Abbanmu ALLAH sai kayi
shiru.Toh nayi shiru ya daina dariyar,sai suma sukayi shiru.
Ummi tamik'e"Mamanmu barinje in watsa ruwa,kuma kuzo muje daga nan
kowa yabani labarin abin dad'in da Mamanmu tabashi da bama nan.Suka mik'e
Yehhh...wallahi munji dad'i,munje kasuwar baje koli,munje gidan dabbobin daji har
munyi selfie da 6auna da giwa da d'awisu kuma hotunan suna wayar Mamanmu tace dama
zata nuna muku.Suka bisu da kallo cikin so da k'auna irin ta Iyaye da babu kamarta
a wajen kowa sai su d'in har suke shige d'akin Ummi,sai tasama k'ofar mukulli dan
kar wani yafito"toh duk ku zauna sai na fito daga wanka zan baku tsarabar dana siyo
muku ta d'auko wayarta ta kunna musu wak'ar"Adam wa Hauwa na Ihab Taufiq nan da nan
suka fara bin wak'ar.
Mutane goma Alhaji Salim yad'ibo daga Zonkwa tare da d'aukar nauyin
kome nasu na magani har zuwa sanda zasu samu sauk'i,sai dai a cikin watanni biyu da
zuwan su"44 Nigerian Army Hospital"mutum d'ayane"Julaibib Abdullahi D'ansarai shine
ya zama ZAKARAN GWAJIN DAFI.
Sai dai shima a watanni biyun nan sau d'aya rakkin-rak ya farfad'o daga dogon suman
da yayi yana kuka da sambatun kiran Bilkisuna,Innarmu, Musaddiq, Zaujatiii...
Walida,Sudaida,da sauran sunayen yan'uwa amma wad'annan su yafi kira ko a cikin
baccin shi.
Sai kuma yau da yasake farfad'owa sai dai Alhamdulillahi wannan karan
cikin hankali yadawo hayyacinshi,a hankali ya bud'e idanunshi yana bin d'akin da
kallo,ya gane a gadon asibiti yake kwance, duk in da yasamu karaya an gyara,na
hannayen shima sun warke sai dai k'afarce har yanzu da saura, ya maida idanunshi
kan Ummi da take zaune nesa dashi tana magana a waya.
Wacece wannan?Ya tambayi kanshi yana kuma k'ok'arin tunano a in da yata6a
ganinta sai dai bangaren tunani da adana bayanai na kwakwalwarshi sun bashi
tabbacin bai san taba,bai kuma ta6a ganin taba sai yau d'in,abu d'aya da zai iya
tunawa shine wata ma'aikaciyar jinya tace zata taimakesu bayan nan kuma k'irjinshi
yafara mishi suya sai jin wani abu kamar allura yana tsikarin jikinshi daga nan
kuma ya numfashin shi ya d'auke.Idanunshi suka sake kad'awa jawur,yanzu ne yake jin
asalin ciwo a jikinshi ko ina yayi tsami.
Kwanakinshi hud'u kenan da dawowa daga hayyacinshi,amma ba wanda
yasani saboda yana jin alamar za a shigo zai maida idanunshi ya rufe, yauma jin za
a shigo da yamaida idanunshi ya rufe a haka har baccin gaske ya d'auke shi.Sai
farkawa yayi yafara jin sheshshek'an kuka ana magana a hankali"kiyi hak'uri Ummi ki
bar kukan nan dan banga amfaninshi ba,kar yajawo miki matsala".
Mamanmu ni tausayi yake bani,duk wanda muka zo dasu sun mutu sai shi
kad'ai yarage, sannan yanzu duk azabar da yasha an sake karya k'afar wai bata zauna
a saiti ba?Takalleta cikin natsuwa"ba kina wajen akayi hoton k'afar ba? Kuma ai
kinji bayajin da likitan yayi dan haka ba kome Ummi, ai gwamma ayi abinda ya dace a
lokacin da yadace tunda ko an bar k'afar haka to daga baya dolen-dole dai sai an
dawo an gyara"ayi agama ai yafi gobe adawo.
Da wannan yawan kukan da kike yi ai gwamma ki dinga mishi addu'a"ALLAH
yatashi kafad'a, yasa kaffarace wannnan wahalhalun rayuwar da yake ciki ko?Tagyad'a
kai"to amin Mamanmu. Hajiya Bara'atu tayi murmushi"barinje wajen A'isha mu gama
maganar kayan danace takawo min sai in zo mu wuce gida yamma na yi.Julaibib yasake
tambayar kanshi"su wad'annan su wanene?Sune dai suka kawo shi asibiti suna cigaba
da kula dashi ko shakka babu,kullum addu'arshi a garesu"ALLAH yasaka musu da
mafificin sakamakonshi ya sanya hakan a mizanin kyawawan ayyukanshi.
"This is my hijab...I will never remove.
Wak'ar Ahmad Bukhatir data sa a matsayin ringtone d'inta tafara
tashi,abinda yasa Julaibib yazabura tare da bud'e idanunshi yana kallanta.Itama
abin ya bata mamaki,tabbasss da k'afarshi ba a sagale take ba,ba abinda zai hanashi
mik'ewa.
Tad'aga wayar da sallama,jikin Julaibib ya dad'a yin sanyi saboda
ringtone d'in Sudaida kenan tun saninshi da ita da waya bata ta6a canja waba, haka
kuma idan tana cikin nishad'i wak'ar da zaiji tanayi kenan,wanda a wasu lokutan
shima ba zato sai yaji yana wak'ar,har rannan yakalleta "Zaujatiii...bakya gajiya
da wannan wak'ar,ta masa"eh Yaya D'ansarai ai kalmomin cikin wak'ar ne babu na
yarwa,ni duk wak'ok'in Ahmad Bukhatir ina sansu tunda ba harigido, gaskiya da
gaskiyace kawai.
Yamaida idanunshi ga kallanta. Tagyad'a kai"na'am Insha-ALLAH,tayi
jimmm...tana sauraron abinda ake fad'a daga d'ayan bangaren,wani d'an lallausan
murmushi ya su6uce mata gefe da gefenta fuskarta suka lotsa ciki
sosai(dimple)sannan tace"fi amanillah...Ilal-liqaa.Tacire wayar a kunnanta tana
kallan d'an siririn farin agogon dake d'aure a hannun damarta,tayi rubutu a wayar
sannan tasata a jaka.
Tamatsa kusa da gadan da yake kwance tana farin ciki da
farkawarshi,cikin muryarta ta natsuwa tace mishi"sannu...ya jikin?Sai kawai
idanunta suka kawo ruwa saboda tuno ranar data fara d'ora k'wayar idanunta a
kanshi"yana kwance magashiyan wasu sassan jikinshi inda akwai sara da suka naman
wajen yayi kore yana fitar da wani ruwa me wari,tsutsotsi yammm...sunata fitowa ta
wajen, sai dai yanzu Alhamdulillahi yanata samun sauk'i,ta sauke idanunta akan
k'aton d'inkin da aka mishi a kai da kafad'unshi duk sun d'auko warkewa.
Tasake kallan fuskarshi sai taji irin abinda taji a ranar farko
ruguzowar wani abu kamar gini a k'ahon zuciyarta,ta kauda kai da sauri,shigowar
wasu ma'aikatan jinya guda biyu sanye da kakin soja ya bata tabbacin lokacin bada
magani yayi.Tad'an sara musu dan suna aikin su yadda yakamata"aikinku yana
kyau"bravo.Sukayi murmushi"Thank you. Tagyad'a kai"you're well come,tajuya tafita a
d'akin tare da rufo musu k'ofar a hankali.
Makonni uku bayan nan Julaibib yayi kyan gani fiye da zato saboda yana
samun kulawa ta musamman da kuma cimar abinci me inganci da gina jiki,k'afar da aka
dad'a gyarawa itama yana d'anyi tattaki da ita amma da taimokon sandunan da yake
dogara jikinshi(crotch)a gajiye yashigo d'akin ya had'a zufa kashirban saboda d'an
tafiyar da yayi,ya yar da sandunar yana goge zufan fuskarshi,tunani barkatai sun
cika k'wak'walwarshi na abubuwan da suka faru, yanajin d'acin mutuwar kamar yanzu
yafaru.
Aka turo k'ofar tare da yin sallama. Yad'ago idanunshi da suka kad'a
jawur ya amsa sallamar,bai kuma cewa kome ba har Alhaji Salim ya zauna yanata
kallan Julaibib d'in cikin tausayi yana ayyane-ayyane a zuci,yasauke
numfashi"Qadarullahi wamasha'a fa'al.
Julaibib sai hak'uri dan ALLAH mahaliccinmu ya fika sanin halin da
kake ciki,idan ka dogara gareshi zai samar maka da mafita a ragowar rayuwar da
zakayi ga kuma tarin lada na maida al'amura gareshi.Nagode Alhaji, kuma bani da
bakin da zan gode muku sai dai Ubangiji yasaka muku da irin sakamakon shi,dama kuma
ina son sanin kud'ad'en da ka kashe min a asibiti nan.Alhaji Salim yagirgiza kai"ni
duk abinda na maka na yi shine dan girman zatin ALLAH a matsayinka na d'an uwana
musulmi me buk'atar taimako,ba wai na yi shine idan ka warke ka biyani ba,ni a
wajen ALLAH nake neman ladana.
Yagyad'a na sani Alhaji ban kuma man taba,kuma har abadan duniya bazan
ta6a mantawa da wannan karamcin na kaba,to amma ina da kud'ad'e da yawa a asusun
ajiyata ta gidan kud'i... idanunshi suka sake kad'awa jawur bani da kowa... idan
ban baka kud'in ba to me ma zanyi dasune?Wa zan ba?Iyaye da Iyali da sauran yan'uwa
ko? Toh duk sun rigamu gidan gaskiya, yakad'a kai cikin alhini da tsananin tausayin
kai.
Zuri'ata tatafi abadan,babu me dawowa har a nad'e doron duniya!!!
Yad'aga hannayenshi"Ya Ubangijina!ka jikansu, ka gafarta musu!kasasu a cikin
shahidan bayinka wad'anda zasu tashi ranar alkiyama jinin jikinsu da aka zubar yana
k'amshin turaren almiski.Alhaji Salim yana tayashi da amsawa da"amin amin ya rabbi.
Wucewar wasu dak'ik'u d'akin yayi shiru,Alhaji Salim yakatse shirun ta
hanyar kallan Julaibib cikin natsuwa sannan yace"ai ko kai kake da abinda za kayi
da kud'i.Julaibib yakalleshi kallan k'arin bayani.Alhaji Salim yajijjiga kai"abinda
nake nufi ka samu damar da zakayi sadaka me gudana ga Iyaye da Iyalanka da
wad'annan kud'ad'e ladan hakan yacigaba da binsu kamar suna rayene suna aikata
aikin alherin da kansu ko kuwa?Julaibib yajijjiga kai yana wani lallausan murmushin
da yamanta rabon da yayi hakan, labarin zuciya a fuska ma ana ganin alama,sai
yamik'a mishi hannu sukayi musafaba "nagode,nagode kwarai da gaske da wannan
tunatarwa taka Alhaji"Jazakallahu khaira-khaira jazaa'ih.
Haka rayuwar Professor Julaibib Abdullahi D'ansarai tacigaba da tafiya
Alhaji Salim yana kan hanyar zuwa dubashi kullum ta ALLAH, wasu lokutan kuma har da
Iyalanshi,basu ta6a k'osawa ba har zuwa lokacin da likita yaga dacewar ya sallame
shi dan ya warke sai d'an abinda ba a rasaba,wanda yau da gobe kuma da bata bar
kome ba zata k'arasa warkar dashi.
Alhaji Salim yad'aukeshi suka tafi gidanshi, babban gida kwarai da aka
k'awatashi da filawoyin hibiscus da Queen of the night.Wannan gidanane ina fata
zaka iya zama a cikinshi,kasan abin talaka sai a hankali,suka fito daga motar
sannan yaba Julaibib mukullin d'aki guda d'aya daga cikin d'akuna shida da suke
harabar gidan,yasa hannu biyu yakar6a yana ta godiya har Alhaji Salim yad'an dafa
kafad'arshi"ba kome wannan ai...yiwa kai ne,ka shiga ka huta, yamik'a mishi hannu
sukayi musafaha.Alhaji Salim ya wuce cikin gida.
Julaibib yasa mukulli yabud'e d'akin... wani sanyi da k'amshin turaren
d'aki suka daki k'ofofin hancinshi,yad'an lumshe idanunshi,rabon da yaji k'amshi me
saukar da natsuwa a ilahirin gangar jiki da sararin zuciya tun Sudaidanshi tana
raye, yabud'e idanu yana bin d'akin da kallo kome a kwai baya buk'atar k'arin kome
sai tufafin sawa,yakwanta a gadon rigingine yayi matashin kai da hannayenshi tunani
barkatai ya cika k'wak'walwarshi a haka har bacci yayi nasarar yin awon gaba dashi.
God'iyar liman ba gudu ba ka ye.
Alamar shiga masallaci cire takalmi.
14 Rajab 1441
8 March 2020
We Ibrahim's Daughters👇
Asdilat KD...2geda with Ra'ibs.
DANGIN NONO WRITERS ASSOCIATION
{Da Inganci Mukayi Fintinkau}
Bismillahi wabihi nasta'in
...GWAJIN DAFI💔
Almost true story
Daga alk'alamin🖊
Ya'yan Ibrahim
Saudat A.Baba (Asdilat KD)
Da
Bara'atu Ibrahim (Ra'ibs)
Shafi na ashirin da shida.
A mando sansanin Alhazai(hajji camp)wasu yan gudun hijirar Zonkwa
suka yada zango musamman wad'anda basu da takamaiman in da zasu zauna,tabbasss suna
samun tallafi to amma kun san k'asar tamu kome kashin dankaline...sune sukayi sama
da fad'i da mak'udan kud'ad'en sai d'an abinda ba a rasaba talakwa suka samu,zasu
cinye hakkin jama'a su kuma je lahira su biya a in da ba a biyan bashi da tsurar
kud'i sai aikin alherin da aka aikata a doron duniya, da tallafin gidauniyar
"D'angote Foundation" ta naira dubu d'ari-d'ari da aka ba mutane
dashi suke jalauta rayuwar,Julaibib bai samu ko sisin kwabo ba,kuma hakan bai dame
shiba,dan kud'i ba matsalar shi bane,sai dai ma yaba wasu,lokaci zuwa lokaci ya
kanje Mando a gaisa da abokan arziki harma yayi ihsani ga wad'anda tasu wahalar
tafi ta wasu.
Julaibib ya d'auko wayarshi yana jujjuya ta makonni biyu kenan da
siyan wayar tare da yin swap d'in layinshi sai dai har yanzu ya kasa kunnata, sai
yayi kamar zai kunna sai kuma ya mayar ya ajiye, yau ma har ya mayar sai ya dad'a
d'auko ta yayi jimmm... Sannan ya kunna,tana gama sai tuwa kira ya dinga shigowa ba
k'ak'k'autawa"Yad'aga da sallama... kirane daga malamai abokan koyarwa da
d'alibai;ya amsa waya sunfi hamsin kai a k'arshe gajiya yayi yasata a jirgi sannan
yasamu damar fara karanta sakwanni na ta'aziyya kala-kala,daga nan ya bud'e wata
wak'a da aka turo mishi wai Karmataka Studio Kano suka yi wak'ar ta'aziyya shi irin
wak'ok'in nan basu dad'ashi da k'asa ba,yafara sauraro sai yaji har da yan'uwanshi
yagama jinta har k'arshe,sannan ya kunna d'aya wak'ar sai yaji tsohuwar wakar da
Rabi'u Usman Baba kano yayi tun lokacin yak'in Zangon-Kataf bai gama
sauraroba,yakashe ya kunna yak'in Zonkwa
"Zonkwa Genocide"anan yake ganin abinda bai gani ba ganin idanun
shi...sun maida makarantar daya kashe miliyoyin kud'i wajen ginata filin ALLAH,haka
babban masallacin juma'ar garin da aketa kashe mata miliyoyin kud'i wajen zamanar
dashi,sai dai basu rusashi gaba d'aya ba,sun rataye k'aton kan allade a gaban
masallacin,tarin kwalaben giya kam ba a magana da alama mashaya suka mayar da
wajen.
Yajijjiga kai "Manzon ALLAH sallallahu alaihi wa'ahlihi wasallam yayi
gaskiya da yace babu amana tsakanin kafirai da musulmai kona sisin kwabo,duk yadda
kuke dasu kuwa,taci na ciki wallahi. Sai ya tuno da wata magana da wani ALLAH
Magani yata6a fad'a lokacin da yaga anata gudun hijira da ake fad'a a Kaduna"Wai
musulmai suna ta tafiya to dawa za suyi yak'i?Ai sai sun dawo sun saki jiki tukuna
zasu k'addamar musu... Ilai kuwa gashinan sun gani ganin idanun su.
Yacire wayar a jirgi yafara gwada wasu lambobi amma ba wacce ta
shiga,zai sake kira,wani kiran yashigo,ya zubama lambobin idanu anya ban san me
wannan layin ba?Har ya katse ya sake shigowa yana gab da katsewa ya d'aga da
sallama aka amsa tare da tambayar"dan ALLAH D'ansarai ne me wannan layin?Ya amsa
kai tsaye"eh shine.Tace cikin farin ciki ALLAHU AKBAR D'ansarai Bongel ce.Nan suka
gaisa tanata mishi ta'aziyya muryarta tayi rauni"mun gwada lambar ka sau shurin
masak'i bata ta6a shiga ba,Baban Humaima yaje Zonkwa amma bai samu kowa na kaba,har
Mando ni dashi munje amma ba labarin kome"wayyo duniya!lallai wata shari'ar sai dai
a lahira.
Julaibib yace dan ALLAH ki turo min lambar Doctor dana Innan
Matsirga,yasake famo mata wani miki,cikin kuka tace"baka san abinda yafaru a
Matsirga ba D'ansarai?Duk sukayi shiru sai yaji ta katse wayar.Yatallafi kanshi da
duka hannayen shi yanajin wani irin yanayi mara dad'i yana tsirga ilahirin gangar
jiki da zuciyarshi kamar wanda zai yi zazza6i.To me yafaru a Matsirga?Tambayar daya
kasa samo amsarta kenan a k'wak'walwarshi, yad'auki wayar da niyyar sake kiranta
sai kuma yaga gwamma yaje ya samu Doctor Manogi ya maida wayar aljihu yasa farar
hula zita yafita.
A harabar gidan suka yi kaci6is da Alhaji Salim da Ummi.Ummi tad'ago
ta kalli Julaibib wallahi sosai take jin tausayinshi,takad'ai kai cikin
jimami"ALLAH sarki kowa da irin tashi k'addarar rubutacciya tun daga Lauhul-mahfus.
Alhaji zani Zari'a ne.Yau d'in nan? Yagyad'a kai"Insha-ALLAH yanzun
nan.To ALLAH yatsare,bai damu da sanin abimda zaije yi a Zaria ba. Yakalli Ummi
shiga D'akin-shak'atawa ki d'auko min mukullin mota yana nan a hannun doguwar
kujera, taje tad'auko Alhaji Salim yakar6a sannan ya mik'a ma Julaibib,sai ya
girgiza kai Alhaji kabarshi kawai zan tafi tasha.Yasaka mishi mukullin a aljihun
gaban farar rigarshi"motar haya ai lalurace Julaibib,kai kanka za ka fi jin dad'in
tafiya a wannan.
Suka yi tafiyarsu suka bar Julaibib, yayi tsayuwar a kawu yafurzar da
wani huci, can cikin zuciyarshi yana jinjina halin karamci irin na Alhaji
Salim,kullum abincin nan sau uku a rana,idan ma anyi wani abu bayan abinci na
ta6akalashe to shima haka za a ciko mishi kwano,shi ko da me zai saka musu bayan
addu'ar da yake musu kullum,wani irin tagomashi zai musu?Lallai yaba kyauta
tukwuici ko??? Yajijjiga kai"toh shima zai musu abinda baza su manta dashi ba har
abadan duniya.
Da wannan tunanin yashiga mota yad'aura belt sannan yatasheta
bakinshi na ambaton ALLAH,yana tafiya yana tunanin al'amuran rayuwa me hawa da
sauka,me cike da sark'ak'iya,me d'acin da ya zarta na mad'aci a wasu lokutan,me
zak'in daya zarta na zuma a wasu lokutan"Dawaamulhal minal mahal (no condition is
permanent) ba wani yanayi da yake din din din abadan a doron duniya sai buwayi
gagara goyo Ubangijinmu me kowa da kome.
Ya isa Teaching Hospital ya ajiye motar a inda ake ajiye motoci
sannnan ya nufi office d'in Doctor Manogi amma yatarar a rufe,wani Likita yafad'a
mishi yana Emergency yazauna ya jirashi idan ba sauri yake yiba...Yaciro wayarshi
yashiga yanar gizo a kafar sadarwa ta Facebook,sai dai yasha mamaki kwarai da gaske
da yaga tarin arnan Zonkwa da suka turo mishi da rok'on gayyata dan su zama
abokai,wasu yan gaggawa hannun hagu a romo har sun tura mishi da sak'o ta messenger
sai dai bai karanta ko guda d'aya ba ya gogesu yana tsaki"suna da wayau amma in da
hankali yake to su basuje wajen ba,basu mayi tunaninshi ba.Masu lambarshi suma
sunata mishi magana ta Whatsapp amma bai bi takan suba.
Doctor Garga Ibrahim Manogi yacire farin gilas d'in da yarufe idanunshi
yana nuna Julaibib "wa nake gani haka?Sai lokacin Julaibib yad'ago kai yaga Doctor
Manogi da yayi wasu yan dak'ik'u kawai yana kallanshi,yamik'e tsaye suka rungume
juna "ALLAH me iko Ustazu dama kana raye? Suka saki juna yabud'e musu office suka
shiga,nan fa hira ta 6arke na abubuwan da suka faru har Doctor Manogi yabashi
labarin abinda yafaru a Matsirga nan d'in ma kisan wulak'anci sukama musulmai
wad'anda kwanansu yake gaba sun sha dakyar,sun tasa shanunsu gaba d'aya sun tafi
dasu k'auyan kansu,su dai abinda yake hannnun musulmai yana tsone musu idanu,yana
hanasu rawar gaban hantsi,sai dai na gaba ya dad'e dayin gaba,kuturwar uwa tilas
zama dake,su cinye dukiyar su dawo gidan jiya cin busar doya da magwaro a matsayin
abinci,irinsu Innan Bilkisu da sauran yan'uwansu Bongel sun musu yankan rago;a
cikinsu Bello ne kawai yasha dakyar,mun dad'e muna fama da k'wak'walwarshi kafin ta
dai-daita saboda irin halin firgicin daya shiga.
Amma yanzu Alhamdulillahi ya warke garas,na samo mishi gurbin karatu
a Jami'ar Madina yana can,amma ko jiya da mukayi waya wallahi sai da ya tambayeni
har yanzu ba a ga wani daya dangance kaba ko mutum d'aya?Julaibib yad'anyi murmushi
"Bello kenan,yakar6i lambar wayar shi,sai ya koma gida zai kirashi.Doctor Manogi
yakalleshi"ka san ALLAH kawai zagewa za muyi kamar yadda musulman Kafanchan
sukayi,duk wanda yasan yana cikin irin wad'annan mutanen to shima yazama cikin
shirin ko ta kwana da makaman kare kai"tunda ba kwanciya akafi kare ba,sai dai a
fishi da abun rufa.
Haka suka ma musulman Kamatan haka, haka,hakaaaa sai da suka tashi
garuruwa goma sha uku,amma dan rashin mutumci da da rashin hankali wasu tsinannu
suke iya bud'e baki suce wai musulmai yan ta'addane,kuma gwamnati tanaji tana gani
ba a d'auki wani mataki a kan suba,toh gobe ma idan sukaji sha'awar hakan ai basu
da fargabar kome dan sun san idan sun kashe musulmai suna jin kamar sun kashe
kiyashi ne,kuma da yake bahaushen mutum shima wani k'aton sakarai ne har yasake
yadda ya koma garin Zonkwa wai da sunan cin kasuwa...na rasa ina hankali da tunanin
wasu daga cikin mu yake.
Sai da sukayi sallar azahar sannan suka tafi gidan Doctor Manogi,shi da
Bongel suka dad'a yima juna ta'aziyya,yaba su Humaima kud'i,ran Doctor Manogi da
Bongel bai musu dad'i ba saboda kud'in da yawa.Julaibib yad'anyi murmushi"kusa
ranku a inuwa yanzu D'ansarai bashi da zuri'a,toh idan ban ba sauran yan'uwa abokan
arzik'i na musulmai ba wa zan ba?ALLAH dai yasa tamu k'arshen tayi kyau, jikinsu
yayi sanyi,suka amsa da amin.Sukayi sallama yaja motar yatafi,suka bi danjojin
motar da kallo har tayi nisa ta6ace ma ganinsu.
Yana zaune a harabar gidan yana alwala Misbahu k'anin Ummi yakawo
mishi k'aramin Identification card(ID Card) d'in shine na"Zonkwa Internally
Displaced Person daya manta dashi jiya a motar.Nagode ko?Misbahu yayi murmushi
sannan yajuya yana fad'in barin d'auko hulata mutafi masallacin.
Shehin malami(Professor)a Jami'ar Usman D'anfodio Sokoto(UDUS)Maimun
AbdulQadir ya kawo ma Julaibib ziyara,sun sha hira har sun gaji,tun safe suke tare
har bayan sallar la'asar,lokacin ne yake haramar tafiya.Cheque ya rubutama Julaibib
na miliyan biyar.Julaibib yagirgiza kai"Professor kar muyi haka dakai mana wannan
kud'in to ai ka kwashe kud'in asusun ajiyar takene.
Yagalla mishi harara"idan ma zagina kakeyi a kaikace toh nagode,kuma
ka kirani da Maimun kawai.Bazan iya ba Professor;matsayi ai ALLAH yake bayarwa kuma
ya baka dan haka dole in baka,bazan k'i kiranka farfesaba.Maimun yace "uhum... wa
yaga farfesa ciki fal geron sunday.Sukayi dariya dan sun tuno lokacin.Julaibib yace
ai dane,yanzu cikin farfesa cike yake da dajjaja da labanun.Ya ajiye mishi cheque
d'in"ba fa zan kar6a ba,na ma gode kwarai da kayi takakkiya kazo in da nake,dan me
san kane zai damu da kai har kuma yazo takanas inda kake dan yaganka kuyi zumunci
duk da tazarar dake tsakanin mu.
Maimun yakalleshi cikin natsuwa "D'ansarai kar muyi haka dakai
mana,wallahi da ina da lambar asusun ajiyarka da sai dai kaji alert. Julaibib kai
ai abokin aminci da amana ne,har abadan duniya bazan ta6a mantawa da karamcinku kai
da marigayi Musaddiq ba,duk in da zan ba da tarihin rayuwata to tabbasss sai kun
fito a ciki.A lokacin da muke karatu a Gidan-Waya na baka wannan labarin yanzu ma
zan sake ba ka"tun ina ciki mahaifina yakwanta dama,a haka mahaifiyata ta haifeni
tacigaba da kula dani da sauran Yayyina su hud'u duk dani mu biyar,bata samu wani
tallafi daga dangin mahaifinmu ko na ta dangin ba,kasancewar suma babu ta musu
katutu,duk da haka munfi wasu daga cikinsu duk da mahaifinmu shima ba shi dashi,to
amma ALLAH yatarfama garinmu nono gidan da muke ciki na shine ba haya muke
yiba,wasu da yawa daga cikinsu kuma haya sukeyi,wasu kuma suna zaune a gidan da aka
musu alfarma su zauna har zuwa lokacin da ALLAH ya yassare musu sukayi na su.
Mahaifiyar mu tunda jajayen sawunta take sana'o'i mabambanta ta ajiye
maganar aure a gefe ta kuma toshe kunnuwanta ga duk abinda zaije ya dawo na zamanta
a haka ga k'uruciya ga rashin aure ba irin sharrin da ba a mataba,ita dai kawai
burinta ta inganta rayuwarmu,a haka da taimakon ALLAH dana yan'uwa d'an abinda ba a
rasaba ta gangand'a ta aurar da Yayyina matan,muka cigaba da gara rayuwar a yadda
tazo ba a yadda muka so tazo mana ba,rannan dai ganin wahalar tayi yawa nace mata
ni kawai zan fara bin mota in zama kwandasta idan na iya in samu mota in zama
direba.Idanunta suka kawo ruwa tana kallona cikin jarumtacciyar zuciyarta me
k'arama mutum juriya da hangen wata rana sai labari.
Maimun ni da mahaifinka ba irin rayuwar da muke so kayi ba
kenan,kullum burinmu ace Ya'yanmu sunyi zarra wajen ilmin addini,dan haka kayi
d'amara kabani goyon baya dan girman ALLAH karka watsa min k'asa a cikin
idanuna,tanuna kanta da yatsanta"madamar ina numfashi a doron duniya to Insha-ALLAH
sai ka zama abin kwatance sai anyi alfahari an mori tarin ilminka...
Idanun Maimun suka kad'a yanajin kamar a lokacin ta zaunar dashi tana
fad'ama mishi kalaman.Julaibib mun sha wahalar rayuwa,har k'anzon abincin gidajan
mak'ota take kankaro mana muzo muci.Kullum kalamanta na k'arfafa gwiwane "Maimun
kayi hak'uri wata rana sai labari ba wani yanayi da yake din din din a doron
duniya,a haka dakyar da sid'in goshi muka gangand'a na gama secondary,sai da nayi
k'wadagon shekara uku sannan na had'a kud'in registration nafara karatu a Gidan-
Waya.
wasu lokutan inji kamar in gudu dan bak'ar wuya amma idan natuno da
kalaman mahaifiyata sai inji k'warin gwiwa dan na san tanacan tanata k'ok'arin tara
min wasu kud'ad'e kafin buk'atarsu ta taso,har zuwa lokacin da kuka shigo
makarantar,tamu tazo d'aya kuka fahimci halin da nake ciki kuka taimakeni tun kafin
in furta hakan,kuka yadda na dawo d'akinku gaba d'aya da zama inci abincinku,in sa
kayan sawanku...da sauransu da sauransu,kun d'auke min abubuwa masu yawa game da
karatuna, kuma kuna bani girma a matsayina na d'an Adam bakuyi duba da cewa k'asa
nake da kuba.
Mun gama karatu lafiya har na samu koyarwa,D'ansarai kazo ka d'aukeni
muka tafi Jami'ar Ahmadu Bello wai ka samo min gurbin karatu...Yakalli Julaibib ban
ta6a ganin mutum me irin zuciyar kaba,kai ka biyamin kud'in registration.Da
taimakon ALLAH dana mahaifiyata da kai nakai matsayin da nake,toh ta yaya zan manta
wannan d'imbun alheran Malam D'ansarai?
Ya share hawayen da yazubo mishi sai dai shi ALLAH baya barin wani dan
wani...ina matakin Senior lecturer mahaifiyata itama takwanta dama an gama cin
mad'aci za a fara cin zak'in....ALLAH ya jik'anki mahaifiyata da sauran Iyayenmu
kaafatan.
Yakalli Julaibib"to dan na baka d'an wannan kud'in da bai wuce kacika
matorka da mai ba (full tank)kawanice bazaka kar6a ba?Julaibib yayi yar
dariya"D'ansarai ko tayar keke bai dashi bare mota. Babu damuwa motar ma tananan
tafe Insha-ALLAH,ka kuma fara shiri dan Umrah na bana da kai zamu tafi muyi azumin
ramadana a can.Julaibib yayi godiya sosai sannan yarakoshi wajen mota,anan ma sun
6ata wasu dak'ik'u kafin sukayi musafaha yashiga motar ya zauna direban yaja
motar,shi da Maimun suka d'aga hannu suna ma juna adabo.
Miliyoyin kud'ad'e Julaibib ya samu daga abokan arziki da gwammati,dan
haka yasai fili babba yasake gina makarantar da tafi ta garin Zonkwa kome da kome
gefen makarantar ya gina d'an madaidaicin gida.Ya ajiye aikin koyarwa na duk
makarantun da yake zuwa, yadawo makarantarshi daya gina,suna cigaba da koyarwa da
wasu malaman daya d'auka.
Alhaji Salim yakalleshi cikin natsuwa bayan sun dawo daga masallaci
sallar Isha'i"Julaibib na so kwarai da da matarka ta aure ka tare a gidan ka.
Yad'an bud'e idanu dan mamaki"Alhaji aure kuma?Sai yagirgiza kai"zanyi zamana a
haka har zuwa lokacin da nima zan daina numfashi a doron duniya.Alhaji Salim
yakad'a kai dan shima ya d'an d'and'ana irin abinda Julaibib yake d'and'ana amma ba
kamar na Julaibib ba.
Lallai zasu tattauna cikin tsanaki,ai yana da ilmi zai kuma fahimci
zama da auren zai fi mishi fiye da yak'arasa rayuwar a haka,tsananin martaba aure
irin na bahaushe yasa kome tsufan mutum sai kaga yayi auren koda kuwa irin na
butane kamar yadda suke fad'a.
Wata d'aya bayan nan Julaibib yana zaune a D'akin-shakatawar gidan shi
yana kallan kwanukan abincin da Misbahu ya ajiye,duk da yabar gidan amma kullum ta
ALLAH basa gajiya sau ukun nan sai an kawo mishi abinci, yanzu idan yace a daina
kawo mishi bai san yadda zasu fassara al'amarin ba, abu d'aya zaisa a daina kawo
mishi wannan abincin shine suga macen aure a gidan,shi kuma bayajin wani aure a
ranshi,jiya ma abinda Maimun yagama fad'a mishi kenan wai da yana da 'ya mace da
tuni ya aura mishi ita"Julaibib yayi murmushi"haba farfesa gwamma da ALLAH ma yasa
baka da ita 'yar tawa zan aura?Ya jijjiga kai"ai hakan shine dai-dai taci karanta
ba babbaka.
Ranar Juma'a bayan an sakko daga masallaci Julaibib ya tsaya suna
gaisawa da Alhaji Salim,yakalleshi maganar Iyali har yanzu dai shiru bakace kome
ba,yad'an shafa kwantaccen bak'in gashin kanshi"zan duba...ko kuma ma dai Alhaji
kasamo min yar mutunci a unguwar nan tunda ka dad'e a unguwar ka san yar babban
gida.
Alhaji Salim yayi murmushi"fad'uwa tazo dai-dai da zama,yakalli
Julaibib "ka bani wuk'a da nama nagode,amma wani hanzari ba guduba idan kuma kaga
yarinyar kaji bata kwanta maka ba fa?Ya amsa kai tsaye"zata kwanta min ko yaya take
dan na san baza kamin za6en tumin dare ba, zan aureta zan kuma girmamata.
Alhaji Salim yasake kallanshi"yanzu me zakayi a gida?Yad'an motsa
kafad'a"bakome.To zo muje gidana akwai maganar da zan fad'a maka suka shiga mota
suka tafi.
Sai da suka gama cin abincin rana sannan Alhaji Salim yakalleshi cikin
natsuwa"Julaibib zan baka auren 'ya ta Ummi kana son ta?Julaibib yaji wani irin
yanayi na girma da nauyin Alhaji Salim,ai wata fuskar ta fi gaban mari har abadan
duniya wallahi,Ummi a yadda ya karanceta ai bata da wani aibu tana da natsuwa da
hankali,gata da ilmi,kai ko da ace ballagazace a dai irin karamcin da Alhaji Salim
yamishi to wallahi ba abinda zai hanashi auren ta "Insha-ALLAH kuma sai ya d'orata
a kan hanyar dai-dai bare kuma a kauwamen ta take.Ya amsa cikin girmamawa"to Alhaji
nagode ALLAH yasaka da alheri.
Yagyad'a kai"Julaibib ya kamata kasan wacece Ummi da kuma
mahaifiyarta.Yayi shiru yana sauraro...Alhaji Salim yabashi labarin aurenshi da
Sumayya,'yar data haifa mishi da kuma rasuwarta...Ni tun ranar daka farfad'o na
tambayi sunan ka kace min Julaibib na gane ko wanene kai,da irin k'aunar da
marigayiya take maka,dan haka Ummi yar wajen Sumayya(Kasham) ce,ita zan baka idan
kaga kana sonta.Julaibib yabud'e idanu dan mamaki...zuciya da k'wak'walwarshi
bangaren adana bayanai ta koma baya da gudu tana tariyo mishi kome daki-daki tun
had'uwarsu ta farko da Kasham a Gidan-Waya ranar da sukaje yin registration... har
zuwa ranar data aiko mishi da wasik'a,ruwan zamzam,farin miski da dabinon ajwa da
abinda tarubuta mishi"Musha ruwa lafiya...ranar azumin ashura tara ga watan farko
na musulunci Muharram...Da abinda ta rubuta a k'arshen wasik'arta
Sumayya Kantiok Donatus(Kasham)
Yayi shiru yana tasbihi a cikin zuciyarshi"ALLAH Alhakimu gwanin iya
hakima, ALLAH buwayi gagara misali...Qudirarka da yawa take"ni Julaibib Abdullahi
D'ansarai ni zan auri 'yar da Sumayya ta haifa?Lallai ba wanda yasan abinda gobe
zata haifar sai ALLAH,dan shi wallahi har ya manta da wata Kasham da Sumayya a
rayuwarshi...A hankali mafarkan da ya dinga yi na shekara da shekaru suka dawo
mishi wannan mafarki me ban mamaki da yarasa gane ma'anarshi
"Kasham da yake gani cikin shigar kayan fulani idan tayi magana sai
kuma yaji muryar Sudaida.
Wannan yana nuna Sudaida matar shice,haka kuma zai auri wata kenan me
alak'a da Kasham d'in?Gashi kuwa ya tabbata 'yar data haifa a cikinta...kayan
fulanin kuma yana nufin kenan Bafulatana ce?Yajijjiga kai"ko shakka babu tunda
Alhaji Salim Iyayenshi Fulanine amma girman birni dan ko Iyayensu basuyi kiwon
shanu ba bare kuma su... La'ilaha'illallah.
Sai yasake tuno ranar da Maimun yake fad'a ma Musaddiq mafarkin da
yayi"Wai shi da Kasham ne suke kiwon shanu a wani k'aton fili iya ganinka me cike
da koren ciyayi"Musaddiq yakyalkyale da dariya"D'ansarai fulani ka koma har matarka
take tayaka kiwo saboda tsabar k'auna?A lokacin bai kula suba.Yayi ma Alhaji Salim
godiya sosai,amma har yabar gidan bai daina mamakin wannan al'amarin ba.
Bayan tafiyarshi Ummi tashigo d'akin da sallama,ta zauna tana
kallanshi"Abbana kace za muyi wata magana idan ka dawo daga masallaci, yana
murmushi yace ban manta ba Ummi,ya san yana da yak'ini zata amince,sai yafara mata
nasiha akan biyayya ga Ya'ya a wajen Iyayensu wajibine matuk'ar abinda suka zo
dashi bai sa6ama shari'ar musulunciba,a hankali kuma yafara kambama halayenta na
k'warai, ganin tana ta murmushin jin dad'i,sai ya maida abun zuga"ai na san baza ki
bani kunya ba;baza ki watsa min k'asa a cikin idanu ba,ni a duniyar nan ban ta6a
ganin yarinya me tsananin biyayya ga mahaifanta ba irinki,nima kinga shi yasa nake
miki wata irin k'auna mumaiyiza(ta musamman)
Tagyad'a kai"tabbasss ta yadda Abbanta yana mata k'auna ta musamman
d'in dan kome nata na musamman ne wallahi a wajen shi. Cikin d'oki tace"me kake so
in maka ne Abbana? Yakalleta cikin kulawa"aure zan miki Ummi,kuma ni da kaina na
za6ar miki mijin.Da sauri ta sunkwui da kai dan batayi tsammanin abinda zai fad'a
kenan,tanajin wata irin kunya na lull6eta.
Yacigaba da magana "shekaru da yawa da suka wuce ina da labarin shi,
mutumin kirkine... kuma nima a yanzu nayi nazarin shi tsafff...naga hakan ganin
idanuna,hasashena yana bani zai rik'eki da aminci da amana,burina kullum a kanki
Ummi shine kiyi aure,kiyi bautar cikin aure tunda ibadane, ranar alk'iyama ki samu
sakamako mafi kyau da daraja,kisamu shiga darul-karamah (aljannah) aljannarma ina
miki kwad'ayin samun mad'aukakiya (firdausss)
Yayi shiru yana kallanta"Ummi kiyi magana mana ai ba auren dole zan
miki ba,idan kina da za6inki na kuma bincika naga shima mutumin kirkine,toh shi zan
aura miki,zan kuma ba wancan hak'uri na san zai fahimceni,tayi k'asa da murya cikin
jin nauyinshi"Abbana ina fata in biku in muku biyayya a duk abinda kuka umarceni ko
da bana so,zan tilastama kaina so,dan na san baza ku cuceniba,dan nima inaso agaba
a bini,na san kuma sai na biku na samu albarkanku,nima zanga da kyau a rayuwata ta
gaba.
Yayi lallausan murmushi yana yaba hangen nesan ta"toh kin yadda da
za6in Abban naki koda mutumin me gemu da k'asumba cike da furfura kamar na Abbanki?
Tasake sunkwui da kai"shi wallahi haka Abba yake magana wasu lokutan sai yaba ka
kunya.
Haka rannan yace ma Mamansu wai tana ta wani shashshare shi,to shi
gaskiya ya gaji da wannan shariyar,aure zai k'ara kuma sa'ar Ummi zai auro.Ita kuma
ta galla mishi harara"dan ALLAH ka auro wacce bata kai Ummi bama.Sai yafara dariya
yakalleta"ke Ummi ki zama shaida ai kinji abinda tace ko?Batayi magana ba,sai
guduwa d'aki tayi ta barsu,yanzu ma tashi tayi yana kiranta amma bata dawo
ba.Alhaji Salim yana da shak'uwa sosai tsakanin shi da Ya'yanshi,dan haka zaiyi
wuya yafad'a musu abinda yake so na ayi ko abari kaga basubi umarnin na shiba.
Haiya Bara'atu tak'arasa shigowa"to ai Alhaji wannan al'amari yayi dan
shirun budurwa yaddan ta,bazawara kuma sai ta tanka.Tamishi wannan kallan nata dasu
biyu suka san ma'anar ta"ko kuwa?Yana dariya ya amsa"ai zancenki ba ja kare ya mutu
a juji.
Ranar wata alhamis ba makarantar Islamiyya kuma dama ta gama secondary
ana zaman jiran sakamako kafin a d'ora zuwa Jami'a,suna D'akin-girki Alhaji Salim
yabisu yana musu sannu da aiki.Suka amsa mishi cikin sakin fuska.Yakalli Ummi "bar
kwa6in nan ana sallama dake a waje.Tad'anyi jimmm...Hajiya Bara'atu ta kalleta
cikin kulawa"jeki mana Ummi.
Tajuya jikinta a sanyaye tana sanye da riga da zani na atamfar
classic,tasa bak'in silifas da hijab tafita,sai dai bata ga kowa ba sai
Julaibib,tasha jinin jikinta,ta gaishe shi duk da d'azu tagan shi a hanya da take
dawowa daga gidan Alhaji Hafiz kuma ta gaisheshi.Yak'araso in da take tsaye"ai ni
nake sallama.
Sai tasunkwui da kai k'asa batace kome ba tana wasa da gefen hijab
d'inta"to yaya na miki?nan ma shiru tayi sai yacigaba kinga karfa kiga dan na kwana
biyu gemu da k'asumba sun cika fuskata toh na iya soyayya sai na zama
tauraronki.Sai kuma yayi shiru yana kallanta ganin har lokacin batace kome ba.Sai
yakad'a kai cikim jimamai"Oh D'ansarai marayan ALLAH ba uwa da uba ba sauran dangi
da alama baka samu kar6uwa ba dan haka sai ka d'au na Annabawa kawai.Yadda yayi
furucin cikin tsananin tausayin kai yasa tad'an d'ago tana murmushi,amma ba shi
take kallo kai tsaye ba"Yaya Julaib...ba haka bane ai tunda Abbana ya gamsu da kai
bani da ja...shima kallan fuskarta yayi..ALLAH buwayi sai lokacin yake ganin
kamanninta da Sumayya har jerarrun hak'oranta farare, da manyan idanunta masu
maik'o,wad'annnan sune abinda ta d'auko na ta kai tsaye da kowa zai iya
ganewa.Kad'an sukayi hira yamata sallama dan ya lura a takure take.
Watanni uku bayan nan aka d'aura aurensu Alhaji Hafiz yatsaya a
matsayin waliyinshi, aka kai amarya gidan mijinta ana musu fatan zaman lafiya. Ummi
tashiga bautar gidan aure da duka k'arfi da kuma iyawarta,zaman nasu ba yabo ba
fallasa, suna mutunta juna,tana bashi girma a matsayinshi na babba kuma mijinta
sama yake da ita,shima yana jin tausayinta amatsayinta na k'arama kuma mace me
rauni...
Yasauke gwauron numfashi a sanda k'wak'walwarshi bangaren tunani da
adana bayanai tagama tariyo mishi kakaf rayuwarshi daki-daki.
Yauma abinda yasa yamata haka jiya yatafi Gidan-Waya yakwaso kayansu
anan yaci karo da kayayyakin Iyalinshi...abinda ya famo mishi wani miki kenan haka
ya kwana ranshi ba dad'i... Ummi bata kar zomo ba sai ya bata rataya...yayi huce
haushin kaza a kan dami.Yajijjiga kai"gaskiya Ummi bata cancanci haka ba,ai idan
d'an kaciya baici kazaba toh tsakani da ALLAH bai kamata kuma yayi baraba...Har
lokacin yana jiyo sautin kukanta dan haka ya mik'e dakyar duk da har lokacin kan
nashi bai daina ciwo ba.
Ruqayya...tanaji amma tak'i amsawa "haba Ruqayya...sai ya zauna ya
gewayeta"Ruqayya Esbeer...ni me laifi ne,laifina kuma babbane...amma na gane
kuskurena gani a gabanki na zo ki yafemin...d'ago kanki ki gani na san ke macen
albarka ce,baki furta kalamanki ba har sai da kika rasa hanyar bi wajen shawo kan
matsalar gidanki,ni d'innan nina tunzira zuciyarki,amma Insha-ALLAH zan kiyaye
furucina...ni dai ki taimakeni ki yafemin...ta tari numfashin shi tamik'e zaune
tana kallanshi da idanunta da suka kad'a jawur"na yafe maka.
sukayi shiru na wucewar wasu dak'ik'u sannan ta cigaba da
magana"Julaib...ina tabbatar maka kana d'aya daga cikin bayin da ALLAH yake so
Insha-ALLAH idan katuno da jarabawar Annabi Ayuba Alaihissalam"ya kamu da ciwo
tsawon lokaci, Ya'yanshi suka dinga mutuwa,duk jama'a suka k'aurace mishi to amma
da yayi hak'uri ya mik'a al'amura a wajen Ubangijin mufa?ALLAH mahaliccin mu yace
mishi "madallah da wannann bawa nawa me yawan hak'uri da juriya.
Julaib...karage tunanin nan,ka sani wanda duk ya mutu toh ya mutu kenan
abadan,babu sauran soyayya da k'auna da zaka nuna mishi face ka yawaita aika mishi
da abincin shi(addu'a)idan kana da hali ka mishi sadaka me gudana,toh Julaib...ka
musu anata aika musu da ladan kullum ta ALLAH, kaima kullum kana musu addu'a,nima
ina musu, Abbana...Mamanmu, kai da d'aukacin al'ummar Manzon ALLAH ga wad'anda suka
ga kisan gillan da aka musu,da wad'anda sukaji labari da sauran yan'uwanmu musulmai
na garin Jos da Maiduguri da sauran arewacin k'asarnan.
Duk masu ta'addancin nan tun daga duniya zasu fara ganin sakamakonsu,da
izinin ALLAH fashewar kwai a saman kwalta za suyi,mutuwar kare a saura.Tad'an
kalleshi"dan ALLAH kayi hak'uri ka saki ranki muyi rayuwar aure kamar yadda sauran
ma'aurata suke yi cikin nishad'i da karsashi.Yasauke numfashi"Ruqayya ke macen
alherice...ALLAH yamiki albarka.Tagyad'a kai"amin,shukran jazilan...Qad
uhibbuka...yatari numfashinta kafin ta k'arasa furucinta"hubban jammahhh...sukayi
murmushi"to yanzu muje ki bani abincin yunwa nake ji cikina ba kome sai yan hanji.
Bayan ya gama cin abincin yasha magani yad'an huta,sannan tafara
mishi bayani a kan gidauniyar"D'ansarai da Me-Lambu Foundation"da suka kafa
musamman dan taimakon marayu da zawarawa yan gudun hijirar Zonkwa da ta samar da
kud'i me tarin yawa,d'azu bayan tafiyarka masallaci Maman Hasan ta kirani tafad'a
min.Baba Alhaji ma (Alhaji Hafiz) ya sake bamu gudummawa kamar yadda yasaba,sai dai
wannan karan kayan masarufi muka samu kasancewar watan ramadana yanata matsowa.
Abbana ma zakkarshi ta bana daya fitar d'ungurungum yabamu
kud'in,shi tun jiya bayan tafiyarka Gidan-Waya yakira yafad'a min idan ka samu
lokaci kaje ka kar6o dan ya kira lambarka bata shiga.Jikinshi yai sanyi "Ruqayya
Ubangijine kawai zai saka muku,ina kuma rok'onshi yasaka muku da mafificin
sakamakon shi. Yaciro wasu kud'ad'e masu yawa yana mata bayani "wad'annan farfesa
Maimun AbdulQadir ne ya aiko dasu.Tagyad'a kai"mungode kwarai ALLAH yasaka
mishi.Amin.Bayan la'asar sai inji in kar6o na wajen Alhaji zuwa jibi sai mutafi
Mando mu raba musu,tunda kowa kika gani a wajen yana cikin halin ha'ula'i ne.
"Julaib...wai har yanzu gwamnatin jahar nan ba wani tallafi da zata
bayar ne? A yanzu dai kam babu amma bamu san a gwamnatin gaba ba tunda wannan ai
kinga saura shekara d'aya tak'are tenure,ke dai Ummi Ubangiji yacigaba da rufa mana
asiri duniya da lahira wanda yasamu kud'i ko yaya sai yafara sana'a kome
k'ank'antarta yacigaba da addu'a ALLAH yasa mishi albarka sai kiga kome ya wuce,ai
da rarrafe yaro yake tashi.
Rannan naji a labarai agwam Bajju yana dad'a ba musulman Zonkwa
hak'uri akan abinda yafaru wai ba a san ranshi hakan yafaru ba.Julaibib yakad'a
kai"rabu dashi ai bakinsu d'aya,in banda haka a ina suka samu wad'annan mugayen
makaman? Kud'in baikon da suke bayarwa duk ranar lahadi a majami'unsu bai isa
yasiye suba...Gari ne dai an bar musu,ai k'asar ALLAH fad'i gareta,masu murnar
sunyi kud'i da kud'in hausawa to yanzu baki gansuba"garin banza dama a farau-farau
d'in bamza yake k'arewa.
Ringtone d'in Ummi"This is my hijab...I will never remove.yafara
tashi.Rahab ce dan haka ba tare da tayi sallama ba tad'aga.Rahab ta fashe da
kuka"Ummi Bobby ne...Me yasa meshi ne haka Aunt? Tayi tambayar da kulawa.Cikin
kukan take mata bayani"wai sun tafi Fadan Karshi d'auko akwatin gawa (coffin)na
wani abokin su daya mutu, to a hanyarsu ta dawowa motar takama da wuta sun k'one
k'urmusss. Ummi tayi jimmm...to me zata cene? Idan batace kome ba tabbasss Aunt
Rahab baza taji dad'i ba,Bobby shine babban d'anta,kuma tana son ta,dan ko bata
kira taba to ita tana yawan kiranta kusan rabin yaren Bajju ita ta koya mata a
cewarta dole ne tayi haka tunda da Kasham tana raye zata koya mata, toh tunda ta
mutu ita meye amfanin ta idan bata koya mata ba? Sauran kuma ta koyeshi a gidan
Alhaji Hafiz da take zuwa.
Ta tausasa murya"Aunt basakut (kiyi hak'uri)Kuka bazai dawo da Bobby
ba"I know it's hurt, but you've to bear it,since you already know that sooner or
later each and every one we will go back to our creator...tacigaba da rarrashinta
har tayi shiru amma bata yadda ta mishi addu'a ba dan musulunci ya haramta hakan ga
duk wanda ya mutu bai yadda da manzancin Manzon ALLAH Sallallahu alaihi wa'ahlihi
wasallam ba.Rahab taji dad'in kalaman Ummi sosai "Thank you very much my dear Ummi
for this condolence.Sukayi sallama.
Sunyi shirin tafiya Umrah a can zasuyi azumin ramadana,d'aya ga wata
kuwa jirginsu ya d'aga zuwa k'asa me tsark'i,garin Manzon ALLAH me safa me
marwa,garin dabino da ruwan zamzam... ruwan zamzam me tarin albarka da duk buk'atar
da kashashi zata biya Insha-ALLAH.
Dabinon ajwa sukaci da tataccen ruwan inibi da tuffa,bayan angama
kiran sallar magriba, shi da Ummi suka kalli juna suna murmushi yad'aga hannayenshi
sama dan wannan lokacin amsa addu'a ne kafin a tada sallah"Ya ALLAH bayinka da aka
kashe bada hakkin suba a ko ina suke a doron duniya al'ummar Manzon ALLAH!
Ubangijinmu albarka wannan rana,albarkan wannan d'aki na ka me alfarma ka yafe
musu!Ya Ubangijinmu mahaliccin kowa da kome jinin nan nasu daya zuba a doron
k'asa,kasa yazama sanadi na samun d'aukaka da darajarsu!Ya Ubangijinmu kasa hakan
yazama sandin shigarsu darul-karamah (Aljannah) Jannatul firdausss al'a'ala.
"Ya Ubangiji!Miyagun da suke ma al'ummar manzonka kisan gillan nan
idan wad'anda za su shiryune to ALLAH na rok'ek'a kashiryar dasu, idan kuma
6atattune abadan Ila yaumil k'iyamah... ALLAH! Kai ka haliccemu gaba d'aya, kuma
gareka zamu koma gaba d'aya mun bar kome a hannunka kamana maganinsu.Ya Ubangiji!
Muda mukayi saura a raye da imani to ka k'ara inganta mana imanin,idan kuma ka
tashi kar6an rayukanmu muna maka magiya da sunayenka mafiya kyau,daraja da d'aukaka
to ka kar6i rayukan namu muna masu imani,ranar rarrabe tsakanin k'arya da gaskiya,
ranar da kud'i da Ya'ya basu da tasiri sai dai wanda yazo da ayyuka nagari...!ALLAH
kahad'a fuskokinmu a darul-karamahhh...
Ya ALLAH!me saukar da littafi,me gaggawan sakamako!Ka karya k'ungiyoyin
abokan gaba.Ya ALLAH!Ka karyasu,ka girgiza su...!!!
Ummi dake gefenshi itama ta d'aga hannayenta sama tana amsawa da"amin
Julaib... aminnn ya rabbi... aminnn... k'arshe.
Kome yayi farko tabbasss yana da k'arshe.Mu Ya'yan Ibrahim Godiya muke
ma ALLAH marashin k'arshe daya nufemu yau da kammala rubuta labarin Julaibib
Abdullahi D'ansarai ZAKARAN GWAJIN DAFI.
19 Rajab 1441
13 March 2020
We Ibrahim's Daughters👇
Asdilat KD...2geda with Ra'ibs
Saudat Ibrahim Yahaya😂kisa ranki a inuwa kamar kin mari uwar Soja...Mu Ya'yan
Ibrahim zamu rakaki gidan D'ansarai har D'akin-shak'atawa ki zauna kisha bak'in
shayi...sai ki tambayeshi baki da baki dan wanga batu🙊gaskiya ba damu ba gaad'a da
fatalwa🏃
Muhad'u a sabon littafinmu👇
Dasabon gini...
A Facebook:
Ibrahim's Daughters Novels.
Insha-ALLAH.
Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un!!!
Baba Aminu Inuwa Ibrahim(Wambai)
Jiya Alhamis ALLAH yamishi rasuwa...yan uwa kutayamu rok'a mishi gafarar
Ubangiji,jinyar da akayi yasa k'arshen wahalar kenan😭
ALLAH YAJIK'ANSHI!
ALLAH YABASHI TABBATA!👏
YAU JUMA'A AKA KAISHI GIDANSHI NA GASKIYA... D'AKI A CIKIN K'ASA! SHIKENAN FA
RAYUWAR😭
Alhamdulillahi alakullu halin Wa'a'uzu billahi min amali ahalin nar.
Subhanakallahumma wabihamdika ashhadu anla'ila ha'illa'anta astaqfiruka wa'atubu
ilaika.