Noor Iman (Complete) by Gureenjo.
Noor Iman (Complete) by Gureenjo.
*01*
Tafiya kawai nakeyi sam ban san inda nake jefa kafana ba bare na kula da hanya,
hawaye kawai ke kwaranya daga cikin kurmin idona zuwa kan kumatu na.
Tsananin damuwan da nake ciki be sa na kula da kan hanya na jefa kaina ba seda naji
wani wawan bugu yayinda students na arean suka saki salati wasu na ihu, runtse
kyawawan idanuna kanana nayi cikin jin zafin bugun tun daga kafana har tsakiyar
kwakwalwana amma ko kad'an zafin be kai na zuciyata ba.
A hankali na waiga na kurawa bakar meserati wadda gabad'ayanshi baki ne har glasses
d'in ido don ganin ko ze fito ya bani hakuri amma ko motsi kofan motar be yi ba
bare ayi alamun bud'ewa.
Mikewa nayi na d'ingisa kafana da nasan yayi mugun buguwa na koma gefe na zauna,
wasu na min sannu wasu kuma cewa suke Allah ya kara dama yarinyan kullum tana
tafiya kaman mahaukaciya sam bata da hankali a kanta me makon a kaita psychiatric
amma an kawo ta nan makaranta ko me zata d'auka oho.
Kuma runtse ido na   nayi ba su kad'ai ba duk inda zan gilma sau d'aya sau biyu zasu
ce psycho ce ni ba   wai dan wai yanayin shigar jikina ba, a'a tsantsar rashin
natsuwa da damuwan   dake d'auke a yanayina da fuskana ke sa su zaton haka duk da
sanyi na a abubuwa   dayawa.
Karan wucewar motar da speed shi ya dawo dani daga duniyar tunani na, kafana na
riqe da zarazaran yatsotsin hannuna na dinga matsawa har naji dama dama amma na
tabbatar akwai matsala jin irin azabar dake shigana.
Agogon dake d'aure a tsintsiyar hannuna na kalla 7:50 ajiyar zuciya na sauke kan na
mike na ci gaba da tafiya a hankali Ina d'ingisa kafan na nufi auditorium sbd achan
nake da lectures karfe takwas gashi yanzu 7:50.
Ban isa auditorium ba se takwas da kusan mintuna takwas hall d'in tsit kaman anyi
ruwa an d'auke a hankali na tura kofan na shiga bakina d'auke da sallaman da
iyakarshi pink lips d'ina a hankali na ci gaba da takawa da nufin karasawa ciki In
samu wurin zama.
Seda nayi tsakiyar hall d'in kan naji an ce "who the heck did yhu think yhu are!!!
Will you get out of my class jor" sam muryanshi bata da hayaniya dukda tsawa yayi
ba don microphone da yake amfani da ita ba ko rabin ajin baza su ji tsawar nashi ba
bare lectures d'inshi.
Juyawa nayi na mishi kallo d'aya yayinda shi kuwa idonshi ke kan damin lecture note
d'in hannunshi.
'Fa tabarakallahu ahsanul khalki' na furta akan lips dina ban kara gangancin
kallonshi ba na juya na fita a sanyaye still cikin d'ingishi kujeru irin na zaman
d'alibai dake gaban hall d'in na samu na zauna Ina sauke ajiyar zuciya.
A rayuwana ban ta'ba ganin namiji me irin kyaunshi a fili ba sede a tv, tv d'inma
se tashoshin larabawa ko indiyawa kwata kwata ban san yadda zan fasalta kyaun shi
ba sede na san yana da bala'e'en kyau ga fari me d'aukan hankali.
Share tunaninshi nayi sbd damuwana ya fi karfin tunanin kyaun wani halitta, ya
zanyi da rayuwana, wai laifin me na aikata da ake hukunta ni da abunda ban san
hawanshi ba bare saukanshi? Why always me? A shekaruna na 23 a duniya nayi aure sau
hud'u duk ba wadda na mishi kyakyawar wattanni biyar.
Yes inada kyau daidai misali amma kyauna ba me d'aukan hankali bane sbd fata me
duhun haske ce dani wato 'chocolate' color ba kallo d'aya zakamin ka fahimci kyaun
da surar da Allah ya bani ba shiyasa tun ina shekaru sha takwas a duniya samari
suka min rutututu kowa so yake ya mallakeni.
Ashe ni kam maza sune kaddarana ganin kullum za'ayi sallama ace ana kiran Noor Iman
yasa baba na yanke shawaran In fidda miji ya min aure.
Dukda bana so sbd Ina matukar son karatu kan aure amma ba yadda na iya kasancewata
me tsananin biyayya yasa na fidda wani saurayina da ya nace min tun Ina jss class
ba 'bata lokaci a randa na cika sha takwas cib a ranar aka d'aura min aure da bello
sede abun takaici a ranar da aka kaini gidanshi a ranar Bello ya dankara min saki
har uku ba tare da na san laifi na ba.
Cikin tsananin tashin hankali na dawo gida da safiyar ranan amma se babana da 'yan
uwanshi suka rufu akaina da duka ba tare da sunji ta bakina ba, ba don mama ba
'yaddiko na, wato kishiyar mahaifiyata' da inaga ban yi rai ba a ranan.
Bakaken maganganun da na sha ko seda nayi dana sanin zuwa na duniya dayawa suna
cewa rashin kai budurcina gidan mijina yasa ya min wannan wulakncin yayinda maganan
yayi tasiri akayi ta yad'ata unguwa da 'yan uwa.
Amma abun takaici ko kallo ban ishi umma na ba, bare sannu ko kuma ta ajiye ni taji
damuwa ta hakan yafi komai yimin ciwo a rayuwa ban san daad'in uwa ba, ban san
abinda ake cewa uwa ba a kaina kam sede Ina ganin yadda take kula da kannena kaman
zata maida su ciki.
Abun na min ciwo fiye da tunanin me tunani, mutuwar aurena na farko yayi sanadiyar
tashinmu a rijiyar lemu, muka koma gadon kaya da zama sbd ban isa fita ba haka 'yan
gidanmu, Babana na matukar sona kan faruwan mutuwar aurena na farko, wani irin so
yake min da ban san iyakarshi ba.
Sbd tausayin da nake bashi, komai sede kishiyar uwata ta min, tun Ina karama umma
ke banzantar da ni wai ita alkunyar 'yar fari a yadda baba ya fad'amin kenan amma
har yau ban yarda ba sbd abun yayi yawa.
Ban san kula ba se a wurin mama, ban san yadda ake shagwa'ba a gaban uwa ba se a
gabanta, ban da wadda zan kaiwa kuka na se mama, da farin cikina da bakin cikina
duk tare muke rabawa se ince ta fini shiga damuwa akan mace macen aurena.
Hayaniyar d'alibai masu fitowa daga auditorium hall ya tabbatar min da an gama
lectures d'in, d'ago idon da zanyi se ya fad'a cikin nashi ko second idonshi be yi
a kaina ba ya manna bakin space akan sparkling brown eyes d'inshi tare da nufar
motanshi cikin takun isa da kasaita, se a lokacin na gane ashe wadda ya kad'e ni a
hanyar shigowata shine lecturer d'inmu na yau.
Kallonshi nake yadda farinshi ke d'aukan ido ga baki wuluk d'in gashin kanshi dake
kwance lublub har kasan keyanshi se sheki yakeyi, irin gashinne cike da giranshi
haka sune gargasan dake kwance a hannunshi zuwa saman kirjinshi da ya fito kad'an
sbd V neck black shirt da ya saka.
Ina mamakin wannan bawan Allahn anya d'an nijeria ne? Bakaken kananan kayan dake
sanye a jikinshi ya kara fitar da farin fatarshi, kananan maganganun da d'alibai
suka fara akanshi ne yasa ni kauda kaina daga kallonshi na mayar kasa Ina me
kokarin sake zundumawa duniyar tunani na naji an zauna gefe na.
A hankali na waiga se   naga wata kyakyawar matashiyar yarinyar da tunda na fara zuwa
makarantan take yawan   ce min sannu bayan ita ban ta'ba magana da wani d'an ajinmu
ba, alhalin Ina cikin   sati na hud'u kenan da na fara zuwa makarantan ta BUK inda
nake karantar B.sc Ed   Biology.
"Sunana Zarah Ahmad Malabo and yhu?" Da kyar na iya yi mata yake don murmushi
wahala yake min nace "Saudah Hafeez ana kirana Noor Iman".
*•Assalamu alaikum 'yan uwa ga fah Gureenjoh da sabuwar littafi hope zaku so shi
kaman sauran books d'ina, promise yhu will never regret reading my book, in shaa
Allah, comments for more pages•*
🖤Gureenjo🖤
🥀NOOR IMAN🥀
*02*
“Wow nice name, kiyi hakuri fah da abinda Dr. Abdurraheem ya miki haka yake da
wulakanci ga dizgi wai shi In har ya shiga aji to ba me shiga a bayanshi, amma ke
baki jima da fara zuwa ba ko? Gashi an ci rabin semester na san baki yi catching up
wasu abubuwan ba, zan dinga koya miki karki damu daga yau mun zama friends”.
Lord!! Wannan bade surutu ba mutum kaman aku, na raya a raina a fili kuwa murmushi
na mata Ina son inyi karatu sossai inga na zama wata a duniyan nan yanzu ban son
aure ban son wani magananshi karatu kawai hakan yasa nake son yin kokarin yaki da
zuciyata In kuma kau da tasiri da maganan mutane ke min inyi karatu tukuru.
Jinjina kai nayi don son kawar da magananshi na ce “Toh yaushe zaki fara koyamin
karatun?” Tace “duk sadda muke da interval tsakanin lectures se mu dingayi ko In
mun gama da wuri kuma bamu da wani se mu d’an yi kan mu tafi” wannan karon
murmushin da na mata tun daga cikin zuciyata ya fito, wara brown eyes d’inta
kad’an tayi kan itama ta saki murmushi tace “wow I like your dimple and your
wushirya” na kuma yin murmushi nace “nice meeting yhu zarah”.
Tace “same here” hira ta ci gaba damin ni kam se nodding da d’an murmushi tunda na
shiga 18 zan iya rantsewa ban ta’ba mintuna biyu ba tare da damuwa ko tunani ba
amma gashi yau samun mutum a kusa dani kuma me faran faran ya sani sakewa da ita
sossai har na manta da damuwana na wani lokaci.
Eleven nayi muka shiga another lectures na chemistry sossai na maida hankali kuma
ba laifi na fahimta don ni d’in ba laifi me d’an kwakwalwa ce.
Karfe d’aya muka fito muna fitowa zarah ta kalleni tace “har anzo d’aukana muje mu
sauke ki a gida ko Ina Gandun albasa kike kikace?” Kai na gyad’a mata Ina d’an
murmushi nace “nop ke kam yi wucewarki, se in mun had’u gobe” na san irin gulman
mutane yanzu a fara rad’e rad’en na fara bin maza ana saukeni a manyan cars dama
yanzu ma ban tsira ba.
Ba yadda zarah batayi ba amma naki haka ta tafi ni kuma na ci gaba da takawa a
hankali sbd kafana da ya d’an suntuma zuwa lokacin, ban wani ‘bata lokaci ba na
tare napep na shige tare da fad’a mishi inda zani.
Bayan mun iso na sallameshi na fara takawa cikin taka tsantsan kaina a kasa kaman
kullum daga gefe majilisan ‘yan unguwa ne na samari gaba kad’an kan gidanmu na
tsoffi.
Kullum In har zan bi ta wurin na wuce se na zub da kwalla dayake mutuwar aurena har
biyu a unguwan na Gandun albasa ne, ‘ka ganta nan ashawon, ta fito yawon karuwanci
da sunan makaranta’ runtse ido nayi Ina jin zafin sunan amma daga yanzu nayi
alqawarin bazan kara yi musu kuka ba.
Ina jin wani daga ciki yace ‘wai itace me aure auren?’ Wani yace ‘kwarai kuwa
aurenta na farko sako ta akayi a daren farko sbd bata kai budurcinta ba’ da
sassarfa na karasa wucewa dukda zafin da kafana ke yi, haka zuciyata kaman an saka
a tukuban tsire.
Ina isa wurin manyan mutanen na duka har kasa na gaidasu suka amsa ba yabo ba
fallasa amma nayi musu farin sani na san ina bada baya za’a dasa maganata dukda ba
koyaushe sukeyi yadda zanji ba amma sun hana ‘ya’yansu kap huld’a dani wai zan
‘bata su.
Ina shiga gida hawayen da nake rikewa ya fara gangara umma ta na tsaye jikin igiya
tana shanya baba zaune a kan taburma kasan bishiyar umbrella (almond) yana shan
iska don ya dena fita majalisa sbd habaice habaice da bakar maganganun da ake ya’ba
mishi gashi ya ci alwashin baze ta’ba chanza wani unguwan ba sbd ni, rijiyar lemo
da Gadon kaya sun isa.
Har kasa na duka gefen taburman baba nace “sannu baba Ina yini?” Kau da kaina nayi
daga kallon banzan da yake watsa min Ina jin yadda ya ja dogon tsaki, gwiwa a sage
na mike na karasa kofan mama nayi sallama daga ciki ta amsa ni tana cewa “lale lale
‘yar albarka barka da dawowa” murmushin yake nayi na karasa parlorn na zauna.
Ikhram da ikhlas dake zaune saman kujera suka ce “sannu da dawowa yaya iman” nace
“yauwa” mama ce ta fito tana kallona tace “naga kaman duk kin gaji tashi kije kiyi
wanka ki zo ga abinci nan kizo kici” wani yaken nayi Ina mikewa nace “Toh mama na
gode” taku d’aya biyu nayi naji ta saki salati tsayawa nayi na san sbd kafana ne
itace kad’ai!!
Itace kad’ai a duniyata da zata ganni da damuwa ta magance min, ita ce kad’ai me
sona nan duniya haka nima Ina sonta har raina sbd son da take min ban damu da
kasancewarta kishiyar uwata ba “na shiga uku Iman me ya samu kafankin?” Na juyo Ina
murmushi nace “mama bugewa nayi” tace “ashsha zo muga” wurinta na koma tana gani ta
waro ido “maza juya mu fice gidan malam iro ya gyara miki daga gani gurd’ewa ce ko
tsagewar kashi”.
Baki na turo Ina shirin mata musu har ta shige d’aki tana fitowa ta sani a gaba
muka fice zuwa tsakar gida ta kalli baba tace “malam yarinyarnan Noor Iman ta samu
matsala a kafanta bari muje gidan malam iro ya duba mata” bata jira cewar shi ba
muka wuce don ta tabbatar ba amsa ze bata ba inde akan maganan da ya shafeni ne
kaman yadda nima na san da hakan.
Muna isa ya tabbatar da gocewar kashi ne a rike ni ya gyara da kuka da komai aka
gyara mama se mita take wai na cika ragwanci, biyanshi tayi muka fito muka dawo
gida ina share hawaye, wanka nayi na shirya cikin riga marar nauyi duk a d’akin
mama komai na yake don ban ci darajar a bani d’aki na ni kad’ai kaman sauran ‘yan
matan gidan da yanzu suke gidan mazajensu ba.
Ido na a lumshe nake taryo rayuwarmu na baya, Malam Musa Muhammad d’an asalin
kauyen wudil ne na nan jahar kano yana da mata d’aya da yara takwas ya jima yana
sana’an driver kuma har Allah ya kar’bi rayuwanshi sana’anshi kenan, da Sana’an ya
sayi gida anan hayin rigasa suka dawo nan da zama anan cikin kano gabad’aya
yaranshi sukayi karatu kasancewarshi me son boko, dukda shi be yi ba, baba shine na
hud’u a cikin ‘ya’yanshi yana da kanne hud’u.
Yayyunshi uku duk maza ne bappa Yushe’u, se bappa Mu’azu se bappa sama’ila kan
baba, duk mazan sunyi karatu daidai gwargwado iyawar mahaifinsu kan rasuwarshi inda
babana yayi diploma d’inshi a fannin mass com, ya auri ummana (Aisha) ne a chan
garin malumfashi na nan katsina inda ta kasance ‘ya d’aya tilo a wurin iyayenta
batayi wani karatun kirki ba iyayenta suka cireta suka aurar da ita.
A lokacin ya fara aiki a matsayin karamin ma’aikaci a gidan rediyon freedom, suna
son junansu don zaman amana da soyayya sukeyi wadda jigonshi ya kasance hakuri, har
ummana ta shekara hud’u bata ta’ba koda ‘Batan wata ba, hakan yasa su goggonina da
inna mahaifiyar baba suka matsa ya karo aure yaki sam amma se suka fi karfinshi
inda ya auri kanwar matar bappa yushe’u.
🖤Gureenjo🖤
🥀NOOR IMAN🥀
*03*
Hadiza wato mama kenan, zuwan mama da kwanaki kad'an ciki ya bayyana a jikin ummana
sossai baba ya d'auki son duniya ya d'aura akan cikin, su inna kam da suka ji
labari se kunyan yadda suka dinga mata ya baibayesu suka dawo suna son cikin suma
kaman su janyo ran haihuwanshi.
Kwarai umma ta wahala a wurin haihuwa na har Allah ya sa ta sauka lafiya inda ta
sameni ba karamin farin ciki su inna da baba sukayi da hakan ba, har mama kaman
zata had'iyeni zan iya cewa son da take min yafi na ummana a ganina fa kenan, aka
saka min sunan inna "saudah" yayinda mama ta saka min inkiya "Noor Iman" shekaruna
biyu a duniya ummana ta kara haihuwa nan ma mace "hafsa" sunan mahaifiyarta ce bata
yarda kuma a boye mata suna ba.
Bayan hafsy da shekaru biyu ta haifi Nafeesah daga ita da shekaru biyu ta samu
Al'amin se Ihlam yayinda ikhlas ta kasance auta, har rana yi ta yau mama bata samu
haihuwa ba kuma sam bata nuna damuwanta akan hakan tunda ta d'aukemu a matsayin
'ya'yanta itama karshe ma kyauntana sukutum baba ya bata ganin yadda take kulawa da
ni kamar ita ta tsuguna ta haifeni.
Mun girma da son boko kaman yadda baba ya tusa mana ra'ayin kanmu a had'e yake da
sauran 'yan uwana mata yayinda suke tausayamin ganin yadda umma ke nuna halin ko In
kula da rayuwana zan iya cewa ban ta'ba mintuna biyu cikakke muna magana da ita ba
kwata kwata bata san komai nawa ba.
A haka har na girma nayi wayo maimakon In ji na tsaneta amma sonta da son ta kulani
suka shigeni, se in dinga shishige mata tana hantarana watarana har dukana takeyi
In na matsa mata da magana In ka shigo gidanmu kaga yadda takemin zaka rantse 'yar
kishiya nake a gareta, ban san daad'in uwa ba sam ban san d'uminta ba, ko d'akinta
na shiga se ta korani waje.
Ina girma suffan jikina na kara   bayyana da kyaun da Allah ya bani wadda In ka ganni
da ummana kaman photocopy banda   kiba haka kuma banda rama jikina a murje yake da
kalar fatata me d'aukar hankali   sbd a chocolate dinma me tsada ne don haka yawan
mutane suke fad'a Ina da dimple   guda d'aya a 'bangaren kumatuna na dama.
Ina jss 2 maza suka fara layi a kofar gidanmu don Allah yayini da farin jinin
samari hakan yasa baba ya sha alwashin aurar dani da na gama secondary dukda yadda
yake so nayi karatu don nice ta gaban goshinshi yana son cika min burina na zama
babbar lecturer a duniya amma yana shakka yadda ake zuwa mishi da magana na har
tsoro yake bashi.
Kaman yadda na fad'a a baya tun jss 2 bello ya fara takuramin da nuna yadda yake
sona ya kuma tabbatar min baze iya rayuwa ba ni ba, tun Ina shareshi har na fara
sauraranshi, Ina cikin zana jarabawata ta kare secondary baba ya kirani ya tabbatar
min ba zan ci gaba da karatu ba ze aurar dani In miji na ya yarda inci gaba so in
turo da wadda nakeso.
Abun takaicin kuma yawancin nasihanshi na karkatuwa ne ga girman laifin zina wato
shima ya yarda da rashin kai budurcina ya sa bello sakina hakan na sani kuka sossai
da kunar rai, bayan mutuwar aurena da bello da watanni bakwai na had'u da Ahmad
matashin saurayi me ji da kud'i a asibiti muka had'u bamu wani jima muna soyayya ba
ya nemi turowa na fad'awa baba ya dinga ci min albarka.
Ba 'bata lokaci aka yi buki aka d'aura min aure da Ahmad, bayan d'aurin aure
angwaye sun kasance suna turowa amarensu sakon jin daad'insu amma ni sakon bakin
ciki da takaici Ahmad ya turo min, bayan an watse ya kirani a waya ya ci min
mutunci akan ni bazawara ce bamu fad'a mishi ba muka cuce shi ashe ni 'yar iska ce,
wai ashe yawon iskancin da nakeyi yasa mijinan chan ya sakeni.
Nayi kuka har na gaji da wannan sharrin haka aka kaini tunda aka kaini kullum
wulakanci har dukana yana yi sede be ta'ba kusantata ba bare ya san gaskiyata na
wahala sossai a gidan Ahmad na wata shidda kan ya sakeni na dawo gida, a lokacin
hawan jini ya kama baba, kaman aurena na farko har gida su goggo kamila suka zo
gabad'ayansu suka lakad'amin na jaki.
******
Ta'bani da mama keyi yasa ni dawowa daga duniyar tunanin da na fad'a "Iman tashi
kinyi bacci bakiyi sallahn isha ba gashi har karfe goma, tashi maza kiyi sallah"
salati nayi ina mikewa daga kwancen da nake na fad'a bayi, alwala nayi na fito na
samu mama ta gama shiryawa zata tafi d'akin baba da yake itace dashi, sallama
mukayi ta fita ni kuma nayi sallahna kan na koma gado na kwanta.
Ruri wayana ya fara yana neman agaji a kasalance na sa hannu na d'aga, Haka kawai
wani lokacin se in manta Ina da waya sbd ba me kirana en uwana se na kirasu sbd duk
haushina sukeji har gwara hafsy amma sauran kannena da sukayi aure ba me kirana
haka goggonina ko na kirasu ba d'agawa sukeyi ba, na rasa kaddarannan kam ni na
d'aurawa kaina ko ko Allah ne ya d'auramin.
Sake shigowar call wayana ya dawo dani daga tunanin da na fad'a da sauri na d'aga
"salamu Alaikum" na furta cikin sanyin murya, murmushi na saki jin muryan zarah
tana cewa "Amma baki da mutunci Noor Iman yanzu bakiyi saving number na ba? Don
daga jin yadda kikayi sallaman nan baki san who's in the line ba" cikin murmushi
nace "sorry zarah, wallahi shap na mance banyi saving ba amma karki damu yanzunnan
zanyi".
"Ni de Allah nayi fushi tun fah d'azu nayi saving numbernki da my besty amma ke
bakiyi ba" cikin mamakin halin sangarci irin na zarah nace "amma ke zarah 'yar
autace ko?" Tace "yes Anty Rumah, ya Abdul, ya hafeez, Anty kalthum duk auta suke
ce min har ummu da Abbu" na lura zarah yarinyace don na tabbatar zan bata akallah
shakaru hud'u zuwa biyar amma zan d'auketa kawa don tana da daad'in zama kuma ma ni
ta fini kiba da tsawo don duguwace sossai ba kaman ni da nake tsaka tsaki ba.
🥀NOOR IMAN🥀
*04*
A Karo na biyu na kuma dunfaro class d'inshi 6mins past eight, dayake ban samu
bacci cikin dare sossai ba sbd period pain da nayi fama da shi ban samu salama ba
seda jinin yazo gabannin asuba kan nayi bacci.
Bani na farka ba se karfe bakwai, kan nayi wanka na shirya na taho takwas da
mintuna shidda, zuciyata na dukan tara tara sede banjin zan iya komawa da baya sbd
bana son samun matsala da course d'inshi sam gashi yanzu attendance na biyu ke
shirin wuceni.
Nannauyar ajiyar zuciya na sauke kan na tura kofan a hankali na sa kai, muryanshi
dake tashi a hankali cikin sanyin da yake naturally ne ya doki dodon kunnena wadda
har seda naji faduwar gaba da na rasa dalili, ba tare da na kalli inda yake ba na
nufi karasawa cikin ajin sede ko taku biyu ban yi ba na ji shi yana cewa.
"Hey yhu!!!! Get out of my class" 'Dago eyeballs dina nayi da niyyar bashi hakuri
amma me? Bakina kwata kwata yaki bani had'in kai wurin motsashi har muryan ya fito,
sbd hardewa da idanunmu yayi cikin na juna.
Wani irin disgusting look yake jifana dashi da ya sa ba shiri na juya na fice
jikina na tsananta rawa, Ina jin tsakinshi cikin microphone kan ya ci gaba da
bayanin cikin natsatsiyar muryarshi me tafiyar da hankalin me saurare.
Wuri na samu na buga tagumi cike da jimamin sake makara a class d'in bawan Allahn
nan Dr. Abdulraheem kaman yadda zarah ta ambaci sunanshi, ina nan zaune har ya gama
lecturing ya fito kaman jiya yau ma bakaken kananan kaya ne a jikinshi ko don ya
san suna mishi kyau ne yasa yake sakawa? Oho, idona na kanshi har ya bud'e wata
Mercedes benz ya shige itama baka yaja da gudu kaman de jiya ya fice.
Ajiyar zuciya na sauke tare da kauda kaina daga hanyar da motar ta bi jin hannu a
kafad'ana, kallon me hannun nayi murmushi na saki ganin zarah, fuskantan nan a
turbune kaman zatayi kuka cikin dariya nace "lafiya autan ummu?" Kara turo baki
tayi tace "yhu know what yhu did is not fair right? Me yasa kika zo late plz,
wallahi dr. Abdul cewa yayi In baka da 75 percent attendance d'inshi you will not
sit for his exams"
Matsa mata nayi ta zauna Ina me sauke ajiyar zuciya nace "In shaa Allahu bazan kara
ba, yau ma da dalilin hakan" girgiza kai tayi tare da cewa "and in kin san kinyi
late karki dinga shiga wallahi it hurts to see him humiliating yhu In public ba
mutunci ne dashi ba" girgiza kai kawai nayi shiru ya d'an ratsa kan nace "tashi
muje mosque mu d'an yi karatu tunda se 2 muke da wani lectures din".
Mikewa tayi muka fara tafiya muna 'yar hira har muka isa masallaci daga chan baya
muka zauna muka baje handouts na chemistry ta fara koyamin duk abinda ban gane ba,
ba mu muka motsa daga nan ba se karfe d'aya muka yi sallah muka fito zuwa cafeteria
abinci muka ci wadda zarah ce ta biya kud'in duk da yadda nayi kokarin hanata.
Multipurpose muka nufa mukayi education 2-4 wadda sossai na fahimta kuma lectures
din ya min daad'i har nake jin nan gaba karatun ze iya d'aukemin duk wata damuwana,
"muje muyi sallah kan azo d'aukanki ko?" Na fad'a Ina kallon zarah dake chatting a
wayanta kirar iphone 11pro ba tare da ta kalleni ba tace "yes sure, kin san kanon
nan in yamma tayi holdup d'in bala'i ne da ita kan ka isa gida past five".
Murmushi kawai nayi ina mamakin surutun zarah Abu d'aya zaka tambayeta amma ta baka
amsa sama da ashirin, a natse muke takawa musamman zarah 'yar gayu da tafiyarta ma
kad'ai abun kallo ne, ga shiganta ba wai me nuna tsiraici ba a'a kawai de da ka
kalleta zaka san daga gidan arziki ta fito hutu ne ko ta Ina a jikinta.
Kallon jikina nayi ba laifi sanye nake da material doguwar riga da bakin hijab da
bakin takalmi se bakin agogo da d'an side bag d'ina, daidai gwargwadon talaka me
madaidaicin karfi, na san mutane zasuyi ta zagina da zund'en na makalewa 'yar masu
kud'i wasu dayawa suna son kawance da zarah amma na kula ko ta kansu bata bi.
Bayan munyi sallah mun fito muka nufi hanyar barin school din tun kan mu shiga ta
kira driver d'inta akan yazo ya d'auketa hakan yasa bamuyi wani nisa ba muka hangi
motar wadda ni ban ma gane ba dayake ba da shi aka zo d'aukanta jiya ba, yau ma
tayi tayi dani In shiga su saukeni naki har fushi tayi ta tafi.
Hmm zarah kenan da kin san irin maganan da shiga motar gidanku ze jamin da baki
fara min tayi ba, na raya a raina Ina tarar machine da yazo wucewa ciniki mukayi
dashi kan na d'ane yaja muka tafi.
*****
"Yauwa ranki shi dade...." "Noor Iman" wara ido yayi   kan yace "masha Allah suna me
daad'i, kar na 'bata miki lokaci gashi na tsaidake a   titi na san ba mutuncinki bane
amma ba yadda na iya ne" ajiyar zuciya ya sauke yana   tuna irin maganganun da aka
gayamishi akanta tunda ya fara zuwar ma abokinshi da   zancen yana son yarinyar.
"Sunana Hamza Noor Ina sonki, so na tsakani da Allah kuma aurenki nake son inyi"
hawaye ne ya ciko idona tun bayan barina gidan Ahmad ba wani namijin da ya ta'ba
tarana da sunan so se hamza sbd wani irin bakin fenti da jama'a suka shafamin ba
tare da sun san kaddara bane kuma yana kan kowa, "aurena biyu, ni bazawara ce" ga
mamakina murmushi naga yayi yace "ko menene kike ni Ina sonki kuma zan aureki ba
wadda ze iya hanani se Allah se kuma idan baki sona sarauniya".
Murmushi nayi kan na ce "ni ban ce ba, Allah ya za'ba mana abinda yafi alkhairi"
cikin jin daad'i Hamza yayimin godiya yayinda ya rakoni har gida don dama na shigo
layinmu, soyayya me tsafta ce ta shiga tsakaninmu da hamza dukda irin maganganun da
ake gayamishi a kaina ya toshe kunnuwanshi iyayenshi kuma masu fahimta sam basu
nuna kina ba se adu'ar Allah ya tabbatar da alkhairi.
Har na gaji da jin wannan kalaman nashi, na san kaddara ni ko shi ba wanda ya isa
hana Allah abinda yaso In har rubuttacce ne a cikin shafin kaddarana, wasa wasa
lokaci ya matso inda walima kawai nayi shima don tirsasawar hamza, rana bata karya
a ranar 17 ga watan d'aya 2019 aka d'aura aurena da hamza da karfe goma na safe, a
kuma lokacin Allah ya kar'bi ran Hamza bayan an gama shafa fatiha.
Mutuwar da yamin ciwo fiye da komai a duniya nayi kuka har kaman raina ze fita sede
ba yadda na iya ba iya dawo dashi zanyi ba, har abada bana jin zan manta wannan
rana zan kuma manta wannan rashi na mijina me kaunata tsakani da Allah, se namijin
kwarai ne irin Hamza ze iya jurar irin maganganun dake yawo a kaina ya toshe kunne
yace duk duniya se ni.
Nan kam ba yadda baba da 'yan uwanshi suka iya tunda mutuwane amma fah maganganun
mutane na watakila Ina da miji cikin jinsin aljannu ya fara tasiri akansu sbd abun
akwai d'aure kai, nide nawa adu'a na tabbatar ba wani aljannin da ya aureni kawai
de haka Allah ya tsara mini, bayan wata da mutuwan Hamza su goggo hindatu suka fara
kawo min magani da wasu jike jike wai na kariya duk suka nan ba sha nakeyi ba sede
In ajiye mama ma sam bata goyi bayan In sha ba suna tafiya zata tayani zubarwa.
Ummana!!! Hmmm umma bata ta'ba nuna ko digon damuwanta akan lamarina ba hakan yasa
na lalace na kara fad'awa, Ina rayuwane cikin duhun kai dukda na san mama na sona
amma akwai abubuwan da se uwa ce kad'ai zata iya ma d'anta zan iya cewa ko azkar
wannan banayi iyakacina lokacin da nake zuwa islamiyya In naje nayi karatun qur'ani
achan ban sake bud'ewa se kuma In na sake zuwa yanzu da na bar islamiyyar ma se ayi
sati biyu ban bud'e alqur'ani da sunan karantawa ba.
********
"Malama!!! Baiwar Allah!! Baiwar Allah!" Firgigit nayi na dawo daga duniyar tunanin
da na fad'a ashe ma mun iso tuntuni yayi magana har ya gaji hankalina be kanshi se
hawaye wasu samari ne suka tayashi dawo dani cikin tunani na, sauka nayi nace "kayi
hakuri baba" don babba ne me acha'ban murmushi yayi yace "ba komai d'iyata ki dinga
kokarin boye damuwarki duk wani tsanani yana tare da sauki komai maganinshi Allah,
ki dinga kaiwa Allah kukanki kinji?".
Gyad'a kai nayi Ina mika mishi kud'in shi "In shaa Allahu na gode" da sauri ya
girgiza kai "barshi 'yar nan je ki Allah ya kawo miki mafita" nace "Ameen Ameen na
gode Allah ya saka maka da alkhairi" jan machine d'inshi yayi ni kuma na tsallaka
kan na juya kuma ban hangeshi ba ko da gilmawanshi, ban damu ba na nausa cikin
layinmu.
🖤Gureenjo🖤
🥀NOOR IMAN🥀
Tsaye yake hannu a kwankwaso yana karewa room d'in kallo cikin takaici da bakin
ciki, tied vest ce baka sanye a jikinshi da black three quarter me zips dayawa a
jiki, wadda hakan ya bayyana murd'ewar jikinshi da de gani ma'abocin gym ne damar
bayyana.
Jikinshi gargasa ne bakake sidik a kwance gwanin sha'awa, hannunshi dake waist
d'inshi d'aya ya d'aga ya shafa kwancaccen gashin kanshi da ya ji gyara tare da jan
tsaki a lokaci d'aya, ya zaiyi ne wai wani irin mata Allah ya bashi? Me ta nema ta
rasa da bazata iya natsuwa ta nemi lahirar ta ba se aukin yawace yawace da sunan
business.
Tsaleliyar wayarshi ya zara ya danna kira, cikin yanga da wani irin iyayi da zaka
iya rantsewa ko mace bazata iya irin yanganshi ba, yace "Ki zo Lil, am in my home"
be jira amsanta ba ya sauke wayan tare da kwad'ata kan gadon kaman itace ta 'bata
mishi rai, zarya ya ci gaba da yi cikin tafiyanshi da izza da jin kai, Allah ya
gani be san ya ze yi da Hamna ba duk yadda ya d'auki lamarinta a da ya wuce nan.
Duk wani nasiha da wa'azi da yake 'bata nyaun bakinshi yake mata a banza shiga ta
nan yake yi ya fita ta chan, ummu ma da yake iya gayamata matsalarshi ya fad'a mata
amma wai yarantace zata dena, Ina yaranta a jikin me shekaru 25 ko Lil d'inshi dake
18 and half wallahi tafi hamna iya duk wani aiki na 'ya mace a gidan aurenta.
Hakurinshi ya kai makura akan hamna wallahi mafita kawai yake nema ko ta wacce
hanya, bud'e kofan part d'inshi da akayine ya dawo dashi cikin tunaninshi, kurawa
kofan brown oily eyes d'inshi yayi kaman me nazartar wani abu, se kuwa gata ta
shigo to my biggest surprise Zarah ce tana kallonshi tace "Ya Abdul gani" tsaki
yaja kan ya harareta yace "Ai ban da ido, gyaramin part d'in nan".
Tura baki gaba tayi zata fara diddira kafafu ya watsa mata harara da idanunshin nan
nasa masu firgita 'yan mata da gigitasu da fidda su cikin natsuwarsu kai har wasu
mazan ma, da sauri ta zare gyalen jikinta ta nufi corridor d'in site d'in don dubo
kayan da zatayi anfani dasu a zuciyarta se mita takeyi.
Mutum da matanshi amma itace baiwa komai yake so lil kaza Lil kaza bata isa yin
musu ba yaci ubanta In na muguntan na kusa dukda shi ba mutum bane me saurin kai
hannu amma yana da zafi fiye da tunanin me tunani, ga riko amma In ka sanshi kuma
yana da sanyi da tausayi fiye da zato haka kuma yana son 'yan uwanshi son da baya
had'ashi da kowa, musamman ummu.
Ya tsani karya da munafunci haka baya da shishigi akan harkar da ba'a sanyashi ciki
ba kai ko da kuwa na cikin gidansu ne. Dr. Abdulraheem Ahmad malabo kenan AKA Dr.
Malabo sunan da friends d'inshi da students ke kiranshi.
A natse tayi komai har ta gama a gajiye sossai sbd ko gida bata karasa ba daga
makaranta ya kirata yace tazo haka tasa driver pasa shiga layinsu yayi kwana ya
shige layin gidan yayan nata dake duk cikin unguwa d'aya wato Nasarawa GRA, kwance
ta ganshi akan duguwar kujera kafafunshi na lilo sabida tsawonshi da ya zarta
kujerar idanunshi a lumshe hannunshi kwance kan flat tummy d'inshi.
Ita har ga Allah tausayi yake bata ace mutum da aurenka da komai amma kai baka san
daad'in mata ba? Ajiyar zuciya ta sauke tace "hamma mi timmini, d'ume bo a
yid'i?"(Hamma na gama me kuma kake so?) bud'e idanunshi yayi ya kura mata na
mintuna kan yace cikin slang fulatancin shi "wala, dillo tan mi andi a somi, yah
sewtu"(nothing, tafi kawai na san kin gaji, je ki huta).
Kai ta gyad'a kan ta fice ta shige mota driver yaja ya fice da ita zuwa gida, a
gajiye ta shiga ciki a parlorn kasa taga hamma Hafeez da ummu zaune suna hira,
zubewa tayi a jikin ummu tana cewa "wayyo ummu am na gaji" kyakyawar bafulatanan
mace da tajiku da kud'i, don jikinta kawai ka kalla zaka tabbatar da haka photocopy
d'in Abdulraheem don ba abunda ya bar mata kyakyawace ta ajin karshe dukda she's at
her early 50's.
Tace "Eyyah autana sannu, je kiyi wanka ko za kiji karfi se ki zo In miki tausa"
murmushi me kyau ta saki tana mikewa tace "Ohk ummu bari nayi sauri, Hamma Hafeez
barka da gida" bata jira amsanshi ba ta haura sama.
********
"Hammad wallahi na gaji da magana akan rashin auren nan naka, haba mutum ka girma
baka san ka girma ba? Shekaru Talatin da biyar bakayi aure ba kam wai se yaushe
zakayi? Am fed up na baka nan da three months ko ka kawo mata ko kuma na za'ba maka
duk wacce raina ke so, haba!!!!"
Wadda aka kira da hammad ne naga ya d'ago a marairaice yace "am sorry dad ba nufi
na In 'bata muku rai ba don Allah kuyi hakuri" tsaki dad din ya ja cikin yanayin
fushi yace "just get lost na gama magana na" kallon mom hammad yayi da nufin ta sa
baki se ta ta'be bakin nufin ba ruwana, tare da ci gaba da taunan chewing gum
d'inta.
Ba yadda ya iya hakan yasa ya mike ya fita cikin damuwan 'bacin ran da ya sa
iyayenshi, shi fa ba wai auren ne baya so ba, ba kuma sha'awar ne baya ji ba, kawai
de shi har yanzu be ga wacce ta mishi bane sam a duniyarshi kuma yana ci gaba da
adu'ar Allah ya had'ashi da irin matar da ya dad'e yana mafarkin aure.
Kaninshi na uku ma yanzu d'a d'aya gareshi amma gashi shi har yanzu zaune a
matsayin tuzuru, motanshi ya fad'a tare da figanta ya fice a guje direct Zoo road
yayi gidan Amininshi Uwais wadda yaranshi uku yanzu kuma sa'annin juna ne, da
sallama ya shiga parlorn yaran dake wasa tsakiyar parlorn suka taso da gudu suka
rungumeshi suna "oyoyo Uncle, oyoyo" karamin ya d'aga sama ya shilla tare da
ca'bewa yana fad'ad'a fara'arshi.
Yace "Ina Abba da mama?" Babbar tace "suna kitchen suna mana dinner" kama baki
hammad yayi kan yace "manya!! Oya Abida kira min Abba kice ya sameni a mota" fita
yayi niyyar yi bayan ya ajiye Aiman akan kujera yaro kam ba se ya wangale baki ya
hau kuka ba, murmushi hammad ya kuma sakewa dukda ba'a rabashi da murmushi sam a
rayuwanshi amma In yana tare da yara se ya d'inga jin kaman Aljannah aka mishi
bushara dashi sbd tsabar soyayyarshi da yara.
Duk inda ya ga yaro tofah da kuka da komai yaron ze rabu dashi tsabar yadda ya iya
tafiyar da su, Uwais ne ya fito sanye da apron abun gwanin ban dariya duk filawa a
fuskanshi da jikin apron, hakan yasa yaran da hammad kwashewa da dariya had'e rai
yayi yana zare apron yace "ban cike da halin iskanci hammad ka kiyayeni na gayama,
Abida oya kama kannenki kuyi d'aki har Aiman".
Kama hannun Aiman tayi ze yi rigima Uwais ya zaro mishi idanu a take yabi yarshin
da tafiyanshi da yayi kwari sossai, zama uwais yayi yana cewa "man ya kaman kana
cikin damuwa?" Hammad yace "sossai ma Dad ya bani wata uku In fiddo mata ko ayimin
auren dole" dariya Uwais ya kwashe dashi ganin yadda hammad ya karasa maganan, zeyi
magana kenan matarshi Hajara ta shigo da lullu'binta hannunta rike da tray wadda
aka d'aura drinks da snacks akai ta ajiye gaban hammad tana gaidashi at same time.
A ladabce suka gaisa kan ta wuce zuwa d'akin yaranta don ganin me sukeyi, "wallahi
dad yayi min daidai, banza tuzuru kawai Ai hakan shine maganinka Haka kawai mutum
ya ki aure ya kuma zauna yana aikin shan lemun tsami da lipton wallahi In kayi wasa
dad zan kira ince ya matso da watanni ukun da ya baka zuwa sati biyu".
Cewar uwais "aaaaa Kwana d'aya ne ka manta ya za'ayi In zo maka da damuwa na amma
se ka zauna kana wani surutun da ba shine ba, Wallahi ni Uwais har yanzu banga
macen da ta min ba, kaima ka san macen da nake burin aure" tsaki Uwais yaja kan
yace "ba wani abinda na sani mace de sunan ta mace yanzu Inba iskanci ba ace duk
matan kano baka ga wacce tayi maka ba? Haba Aboki ni yanxu ba abinda zance sede
kaima ka san waye dad tunda ya furta se ya aikata gwara ka bazama neman mata ehe".
Tsaki hammad yaja yana mikewa yace "ba anfanin zuwa wurinka wallahi kaga se anjima"
be jira cewar Uwais ba ya fice abin shi shrugging kafad'a Uwais yayi kan ya mike ya
nufi neman matarshi.
*****
"Wallahi na gaji da ganinki? Don kawai ba yadda na iya ne da maganan inna wallahi
da se de ki nemi gidan wani uban, haba ga mace har mace amma se d'an banzan bakin
hali to wallahi na gaji, hotonki zan d'auka In kai massallaci duk wadda yaga kin
mishi ko wanene, makaho, kuturu, gurgu, almajiri kai ko menene aura miki shi zanyi
in rabu da banzan iri, aikin banza kawai, mtsewwwww".
Baba kenan ke zuba wannan sababin daga gaisuwa, uban da ya haifeni ya kasa yarda da
qaddarata Toh wa ze yi? Kallon ummata nayi dake tankad'en garin tuwo daga gefe ko
kallon inda muke batayiba hankalinta kwance harda 'yar wakarta da fillanci, hawayen
idona na goge ina me tuna mutuwar aurena na karshe, wadda a lokacin ne kad'ai umma
ta iya bud'e baki tace "Allah ya kyauta" bayan na dawo gida.
Isma'il da uwarshi da kannenshi suka had'u suka min dukan mutuwa don baba ne ya
kawoshi kuma yace kar na fad'a mishi komai akan rayuwata ya riga ya mishi bayani
soyayya sama sama mukayi don irin mutanen nan ne masu zafin zuciya da bakin hali,
yana son kowa ya dinga jin tsoronshi cikin har matar aurenshi matarshi d'aya da
yara hud'u, had'uwarmu da auren be fi sati biyu ba, ba yadda na iya sbd bana sonshi
amma baba ya nace haka akayi aure.
Har nayi sati biyu a gidanshi a lokacin ne ya fara jin jita jitan mutane a kaina
ashe ba tun ranan ya fara ji ba, wani abokinshi ya ta'ba fad'a mishi amma se ya
karyata abokin ya kuma tabbatar mishi duk randa ya kusanceni to wallahi mutuwa ze
yi don haka aka ce (kuji sharrin bil adama) hakan yasa ko d'akinta baya shiga tun
be yarda ba har ya samu shedu dayawa a kaina wadda duk na karya ne don ba wadda ya
san waceceni se ni kaina.
'Yan uwanshi ya gayawa ni da ubana mun munafurceshi haka suka min dukan mutuwa suka
kuma koreni ba tare da sun ban ko sisi na kud'in mota ba daga katsina zuwa kano, a
rayuwata ban ta'ba roko ba se a lokacin na zama marokiyar karfi da yaji, da kyar na
samu d'ari hud'u na taka zuwa KSTA na sami kano line suma da kyar da wulakanci suka
d'aukeni sbd kud'in be cika ba.
Haka da muka iso kano da kafa na dinga takawa har gidanmu na ci azaba kafana kaman
ze 'balle da kuka da komai na ba su baba labarin abinda ya faru a lokacin ne umma
tace "Allah ya kyauta" tayi tafiyarta inda mama ta dage akan ba me ta'ba ni haka
yayyun baba suka ce a barni ba laifina bane laifinshine wannan karon ga wahalan da
na sha.
*satin nan gabad'aya baza kujini ba daga gobe in shaa Allahu sbd Ina da wasu jiga
jigan exams guda biyu kuyi hakuri mu had'u Friday*
                    🖤Gureenjo🖤
🥀NOOR IMAN🥀
*06*
Bappa Mu’azu da kanshi ya kirani a waya yace in same shi a gidanshi dayake babban
d’an kasuwane kuma ba laifi ya tara kud’i don duk cikin su baba ya fi kowa kud’i,
bayan naje mun gaisa da matanshi sama sama don duk basu yarda nayi hulda da su bare
yaransu da suke ‘yan uwana wai zan ‘bata su, har parlornshi ya kirani mu biyu
kad’ai.
Nasiha sossai yayi min wadda na yarda na kuma tabbatar shine kad’ai me tausayina
cikin ‘yan uwan baban, daga karshe ya ce “me kike so a duniyan nan mamana?” Wani
irin farin ciki marar misaltuwa ne ya rufeni na manta da duk wani ‘bacin rai da
damuwana inda ba ‘bata lokaci nace “makaranta bappa” kai ya gyad’a cikin tabbatarwa
yace.
“Na miki alkawari zakiyi karatu yadda kike so in sha Allahu kiyi ta adu’a sannan ki
maida hankali banda abinda ba shine ba, zan san yadda zanyi convincing inna, don ta
Amadu ba matsala bane” godiya sossai na mishi inda ya ban kudad’e ya kuma fad’amin
yaranshi ‘yan mata biyu zasuyi jamb so ze biya mana tare tunda Ina da neco da waec
d’ina.
Cikin jin daad’i na dawo gida duk wadda ya   kalleni a lokacin ze tabbatar da cewa
Ina cikin farin ciki marar misaltuwa, mama   kad’ai na ba labarin ta ji daad’i sossai
kuma she was glad zan cika burina, maganan   da naken nan a lokacin anyi auren duk
‘yan uwana biyu mata, a lokacin da maganan   yazo kunnen baba kin yarda yayi sossai
suka kai ruwa rana da yayan nashi har seda   inna ta sa baki kan ya amince nayi jamb.
Inda naci sossai ba ‘bata lokaci ya nema min Admission a nan BUK na kuwa samu
course d’in da nake so wato Bsc.Ed biology, bappa mu’azu shi ya bani kud’in yin
komai har sabbin kayan sawa irin de na fita reni, haka duk sati yake turomin dubu
biyar don baba ya rantse biyar nashi baze shiga cikin karatuna ba......
*********
“Duk inda kike ki tabbatar kin dawo gida before fad’uwar ranar gobe” kitt ya kashe
wayanshi tare da jefarwa kan kujera, ya gaji wallahi da hali irin na hamna amma ya
ze yi tana da goyon bayan su ummu, komai tayi shine me laifi.
Ta ‘bangarenta kuwa tsaki tayi tana kallon best friend d’inta Jawahir tace “wallahi
mutumin nan ya takurawa rayuwata, haba!! Mutum ya tashi a turai yayi rayuwa a turai
amma se ya d’inga yin wani abu irin na dakikan kauyawan Nigerians, if not because
Ina son Abdul wallahi da na rabu dashi.”
Jawahir tayi murmushi tana sipping cocktail d’inta tace “hmm Ai duk laifinki ne
hamna ace mutum yayi ta baki shawara bakya d’auka!! Da nine da Allah se Abdul ya
rena kansa, mutum se d’an banzan gadara da fi’ili?” Dariya hamna tayi kaman ba
mijinta aka zaga ba tana danna wayanta tace “hmm ban san me yasa jinin ku be zo
d’aya da boo ba, bari kiga Inyi booking flight na san na kai mutumin karshe tunda
har yayi magana In ban koma ba ma matsala ne”.
Hararanta jawahir tayi “ke kam haka zaki kare wallahi, aikin banza In nice bazan
koman ba inga abinda ze faru” waro ido hamna tayi tana girgiza kai “uhm uhm jawahir
duk iskanci na wallahi Ina tsoron Malabo baki san halinshi bane shiyasa, kuma baza
ki gane ba” mikewa jawahir tayi tayi gaba tana cewa “Allah ya hanani sani mtseww”.
Booking flight hamna tayi kan ta bi bayan kawarta tana murmushi itama ko ba komai
tayi missing d’in jikinshi sossai sati kusan uku rabonta da nigeria.
*****
“Wato baka ji fad’an dad d’inka ba ko?” Shagwa’be   fuska hammad yayi kan yace “plzzz
mom na san zaki iya ki rokar min shi don Allah ya   kara min time” ta’be baki tayi
kan tace “na fa riga na gama magana dad d’inku ya   gama hakurin da ze yi da kai, ko
na je korata ze yi” ajiyar zuciya ya sauke kan ya   ci gaba da cin abinci jiki
asanyaye, dole ya nemi mata cikin watannin nan.
Don Allah ya gani ba ze iya bari dad ya za’bar mishi wata kuchaka ba, da irin
tunanin nan ya gama cin abinci ya mike ya fita, mota kawai yaja ya fara zaga gari
yana neman mata, abin ma dariya yake bashi wallahi, duk wacce ya gani se ya kare
mata kallo amma ba wacce keda quality d’in da yake so 100% ya zagaya har ya gaji ya
dawo gida ran nan a chunkushe, part d’inshi kawai ya shige yayi kwance kan gado
yana tunanin mafita.
*******
“Iman zo   In aikeki gidan inna” cewar mama dake zaune a parlor tana kirgen kud’in da
aka kawo   mata yanzu na bashi, fitowa nayi ina tura baki nace “dan Allah de mama,
nide ban   son zuwa gidan Allah sbd kin san halinta Sarai a gareni” hararata mama
tayi kan   tace “Toh bari na yafa mayafi na je da kaina” daga jin yadda tayi maganan
zaka san   gatse ne, hakan yasa na koma d’aki na sanyo khimar kan doguwar rigana na
material   hannuna rike da takalami na fito na kar’bi sakon.
Tare da kud’in napep na fice, umma dake zaune kofanta tana gyaran farce na kalla
nace “umma naje gidan inna” dukda na san ba amsani zatayi ba amma hakan ya zama
kaman al’ada bana iya fita ban mata sallama ba ko da kuwa baza ta amsa ba, da kafa
na taka zuwa bakin hanya, bana kallon kowa balle takaici ya kamani na zund’e ko ko
kana nan magan ganun mutane.
Me makon na tari napep kaman yadda na kar’bi kud’in kawai se na tsinci kaina da
hawa machine muka nufi court road, daidai wuraren BUK holdup ya rike mutane ga me
machine d’in nawa se kutsa kai cikin ababen hawa yake duk ban lura ba sbd tunani na
ya tafi gabad’aya wurin irin wulakancin da inna zata min a gidanta.
Kiiiii naji taka birkin d’an acha’ban a hankali nace “kayi a hankali malam Dan
Allah” ba tare da yace komai ba ya taka birki ya tsaya, kaman ance In waiga se ko
idona ya fad’a cikin nashi da sauri na kawar da kaina ina jin gabana na fad’uwa,
hakan be hanani tuno wulakancin da ya min ba, ban san yadda akayi na tura baki gaba
Ina kunkuni da ni kaina ban san me nake cewa ba.
Ta ‘bangarenshi kuma kallo biyu ya mata ya kau da kai, Sarai ya ganeta itace ta
shigo mishi class sau biyu bayan ya shiga, yadda ta tura baki tana kunkuni ya bashi
dariya sbd ya san haushinshi take ji, hakan ya sashi sakin murmushi, “hasbunallahu
wani’imal wakeel” ya furta akan la’bbanshi ganin yadda me acha’ban da take kai ya
figi machine d’in kaman zasu kife sbd bada hannun da akayi.
Sake had’a idanu sukayi Ai ko ya sakar mata harara kan ya kau da kanshi shi har ga
Allah haushin masu acha’ban nan yake ji da masu hawa Haka kawai suyi ta risking
life d’inka a banza yanzu dan Allah duba amma ita ko a jikinta yayi tsaki yafi
abinda yafi kan ya karasa cikin BUK ran nan a ‘bace, wadda ya rasa dalili.
Da fargaba ta karasa gaban su inna ta duka har kasa tace “sannu inna barka da rana”
tun kan inna ta amsa goggo saratu ta kar’be zancen da cewa “au yau su jawaran ne a
gidan innanmu?” Magananta ya dawo da hankalin su goggo hindatu kaina carab goggo
kamila tace “jawara ko ashawo, saratu kin san duk abinda yarinyar nan ke aikatawa a
bayero kuwa? Hmmm yawo ma batayi se da yaran masu dashi”.
Goggo hindatu tace “Kai kamila wa ya fad’amiki?” Goggo kamila tace “kin san Ai abin
duniya bata ‘buya akwai wata makwabciyata da ‘yar ta ke chan ita na sa ta dinga
kularmin da wannan Shegiyar wai don zumuncin dake tsakani, in kinji abinda yarinyar
take gayamin zaki sha mamaki aji ma bata shiga se malami ya shiga tayi ta karairaya
don ya gani ya kyasa a sashi a layi”.
Hawaye ne ya cika min ido tab ga zuciyata dake min zafi kaman ze bar kirjina, in
naji irin waennan maganganun a bakin bare ba kasafai ya cika damuna ba kaman yadda
nake jin zafin In naji a bakin ‘yan uwana na jini, bud’an bakin inna se cewa tayi
“mtseww d’an Allah ku dena damun kanku a kan yarinyar nan, Allah ya gani kunyi iya
kokarinku, Allah na gode maka da ka amshi ran maigida be yi tsawon ran ganin wannan
abun takaicin a zuriyarshi ba, ni na jima da sallamawa duniya ke saude bakya cikin
jikokina wallahi don bazan iya ba.
“Eeeeh Lallai yarinyar nan yanzu na yarda da abinda ake cewa d’ari bisa d’ari,
zagina kikayi? Nice ban san musulunci ba da har zaki gayamin kaddara, tashi ki bar
min gida shegiya gayyar tsiya kika sake tako kafanki gidana se na ci mutuncinki,
kuma zan kira ubban naki inji In shi ya d’aure miki gindin yin iskanci” ajiye mata
sakon da mama ta bani nayi tare da ficewa Ina hawaye sossai.
Tafiya kawai na dinga yi ba tare da na san inda nake jefa kafana ba har na fita
daga layin na ci gaba da takawa ba tare da na nemi abin hawa ba, tafiya yake yana
duba abu a sit d’in baya, abu ya manta a office d’inshi har hakan yasashi shiga
makarantan ranar lahadi, yanzu ma gidan Sauban ya nufa don bashi wasu takardu shine
yake dubawa be hankara ba sitiyarin ya kubce mishi saura kad’an ya bugeta yayi
saurin taka birki yana kallonta.
Amma ita bata san anyi ba hankalinta kwata kwata baya jikinta mamaki sossai ya
kamashi ita kuwa lafiyanta? Randa ya fara ganinta kuka take yi tana tafiya akan
hanya wadda har yayi sanadiyar da yasa ya bugeta, haushin da ta bashi ne ya hanashi
fita ya bata hakuri sbd Shi a ganinshi me ze kawo mutum me hankali kan titi gatsal
tana tafiya tana hawaye kaman wacce aka sako daga psychiatric.
Toh ga yau ma dukda be kai ga bugeta ba, amma me ya sata kuka bayan yanzu ya ganta
lafiyanta kalau? Ajiyar zuciya ya sauke yana cewa kanshi “Ina ruwana?” A hankali ya
ci gaba da tafiya yana kallonta ganin ta nufi babban titi yasa yayi saurin parking
ya fita da sauri yaje ya sha gabanta wadda hakan ya sata tsayuwa “hey!! are yhu
alright?” kallonshi tayi se kuma ta kalli inda take da sauri ta goge fuskanta tare
da kakalo murmushi ta gyad’a kai, ta’be baki yayi kan ya juya ya tari napep.
Empty one, ba tare da ya kalleta ba yace “get in” shiga tayi ya zare dubu sabuwa
gal ya mikawa me napep d’in kar’ba yayi, ba tare da ya kara magana ba ya koma
motarshi ya ja yayi gaba.
🖤Gureenjo🖤
🥀NOOR IMAN🥀
*this page is dedicated to all my friends (I mean readers of my book) duk wani me
son littafin nan wannan page d'in nashi ne, kuyi yadda kuke so, Ina jin daad'in
comments d'inku sossai, Allah ya bar zumunci ❤️❤️ big hearts from here*
*07*
Seda me napep d'in ya fara tafiya kan yace "hajiya ina muka nufa?" Cikin sanyin
murya nace "gandun albasa" Haka kawai na iya furtawa kan na fad'a tunanin me yasa
Dr. Abdulraheem taimakana? Ya gane ni ne? Ko kuwa dai taimakone irin ta addini da
ya had'amu? Allah masanin gaibu, haka na ci gaba da sake sake ba tare da na ci gaba
da kukan ba, gobe monday we are having his class as early as 8 so dole nayi bacci
da wuri don na ci alwashin In shaa Allahu bazan sake missing class d'inshi ba.
Ya rab!! Yau ma mutumin nan bakake kaya ya saka, wai ko Lafiyanshi da bakaken kaya
kaman wani shaid'an? Bari In kira zarah kwana biyu bamuyi lectures ba so bamu had'u
ba, yau ma haka gashi bamuyi waya ba, wayana kirar Tecno M3 na fiddo na danna mata
kira ringing biyu ta d'aga "hey besty ya kike?" Nace "Lafiya kalau besty ya gd?"
Tace "kalau wallahi, kina raina besty tun d'azu nake shirin kiranki se kika rigani"
Ina murmushi nace "ba wani nan kawai don kin ga na riga kira ne".
"Allah ba haka bane ki tambayi ummu kiji se maganan ki nake tun d'azu" ta karasa da
shagwa'ba kan nayi magana naji muryan babbar mace cikin kamala tace "Assalamu
Alaiki" diriricewa nayi wato seda zarah ta bai wa ummu wayar seda nayi gyaran murya
nace "wa'alakumussalam ummu Ina yini?" Tace "Lafiya kalau ya mutan gidan?" Na amsa
da "Lafiya kalau ummu" Tace "Toh ma shaa Allah, auta bata fitinarki da surutun ta
na tsiyan nan ta hanaki karatu ko?".
Murmushi nayi kan nace "ko d'aya ummu Ai zarah na da daad'in zama" tana murmushi
tace "Toh masha Allah, Allah yayi muku albarka a gaida mutanen gida" na amsa mata
da zasuji mun gode, kan ta mikawa zarah wayan muka ci gaba da hira ta dinga
jaddadamin In zo da wuri gobe In zo da wuri da haka mukayi sallama.
Ina isa gida nacewa umma "umma   na dawo" ba tare da jiran amsanta ba na wuce d'akin
mama a parlor na taddata itama   haka na ce mata ba tare da na jira amsanta ba na
fad'a d'aki tare da zubewa kan   gado, yau umma ce da girki kuma bata yarda in
taimaka mata da komai da kanta   take kayanta hakan yasa na kwaso takarduna na fito
tsakar gida na fara karatu ina   cikin yin karatun su ikhram suka dawo daga islamiya.
Da gudu suka nufo kan taburman suka zauna ko wacce na ban labarin abunda ya faru
yau, Ina ta murmushi nace "Kai ikhlas surutunku se ku, kuje ku tu'be uniform nan,
baku da assignment na school ne?" Ikhram tace "muna dashi Anty Noor bari inje In
kawo ki gani?" Ta mike kenan umma ta fito daga d'aki zare ido tayi kan ta daka musu
tsawa "Kai baku da hankali??? Wa yace kuyi mata magana ban hanaku ba?" A tsorace
yaran sukayi wurinta ta kuwa kama kunnensu ta murd'e suka saki kuka.
Idona na kanta amma hawaye ne ke zuba "Anya uwata ce" ba tare da ta kalli inda nake
ba ta jasu sukayi ciki, karatun da banyi ba kenan na tattare takardun nayi ciki,
har yamma ina d'aki ko parlor ban leko ba Ina ji suna ta hayaniya yayinda mama da
umma ke hiransu suna dariya Ina ji baba ya dawo ban fita ba, a d'aki nayi magrib da
isha kan na fita d'aukan abincina.
A kan taburma na tararda ahalin gidan zaune suna hiransu gwanin sha'awa baba na ta
wasa da dariya dasu ikhram wadda hakan ya sani tunawa da yarantata da mahaifina me
sona da kauna na, har na d'auko abincin na fito bayan mama ba wadda ya kalli inda
nake dukda na musu sannu maman ce kawai ta amsa.
A parlorn na yada zango ina tunanin wani irin iyaye nake dashi da basu yarda da
kaddara ba? Kode imaninsu be cika bane ba? Da sauri nace "Astagfirullah, Allah ka
ganar dasu" da ba don mama ba na tabbatar da na jima da collapsing, a haka na
tuttura abincin ba wai don Ina jin daad'inshi ba sbd kawai kar nayiwa kaina illah
da yunwa, Ina gamawa na mike na fita da kwanon na dawo nayi sallahn isha na bi
lafiyan gado.
*******
"Oyoyo booo shine kaki zuwa tarana a airport ko?" Ta fad'a a shagwa'be bayan ta
zube jikinshi, ba tare da ya mayar da runguman da ta mishi ba yace "da ni na kai ki
airport d'in" baki ta turo gaba cikin shagwa'ba tace "Kai Hamma Abdul bakayi
missing d'ina ba? I really missed yhu wallahi" ta'be baki kawai yayi, raurau tayi
da ido ba 'bata lokaci ta fara hawaye don ta san lagonshi kenan kuka musamman na
'ya mace.
"I know I've wronged yhu da na tafi ba tare da izininka ba plz forgive me bazan
kara ba wannan karon ma shagona ne yayi kasa and I need to choose any single thing
in there myself amma kuma kaki that's why na gayawa ummu, I'm sorry plz" be kalleta
ba ya ci gaba da kallon TV d'in da yake jin kukanta ya fara damunshi ne yasa shi sa
hannu ya rungume ta sossai tare da kissing forehead d'inta yace "I missed yhu"
murmushin cin nasara tayi.
Abinka da mata da miji tuni sun shirya har yare ya chanza tuni sukayi d'aki don
Allah ya gani dauriyace kawai irin nashi, hallitanshi daban ne a cikin maza yana da
karfin sha'awa ba kad'an ba shiyasa yaci burin matarshi bazata dinga yin nesa dashi
ba sbd kaucewa halaka se ga irin wacce Allah ya had'ashi da ita.
Bayan sun gama samun natsuwa ta tattara ta fice d'akinta yana kallonta be iya ce
mata komai ba, to me ze ce? Sau nawa yana gayamata ya fi son jin matarshi a
jikinshi ko da ba abinda ze shiga tsakani amma taki yarda sam da su d'inga kwana
d'aki d'aya shi ya rasa dalili, sede tazo suyi abinda zasuyi ta tafi girgiza kai
kawai yayi tare da mikewa ya shige toilet.
Tana shiga d'akinta ta bud'e bedside drawer ta d'auko wasu pills ta had'iya kan ta
fad'a toilet.
Kiran sallahn farko akan kunnenshi wadda yasa shi yin mika tare da sakin salati
kaman baze sauka ba chan de ya zuro kafanshi kasa kan lallausan carpet d'inshi ya
ajiye fararen kyawawan kafafunshi, nan ma yafi minti biyu zaune kan ya mike
gabad'aya ya fad'a bayi, alwala yayi ya fito tare da nufan inda yake ibada wadda
aka ware a cikin d'akin aka kawata shi sossai gwanin ban sha'awa d'akin kad'ai se
yayi girman wani gidan talakan.
Don gefe parlor ne me d'auke da set d'in kujeru cip da Tv plasma a makale jikin
bango, kan inda gadon yake kenan komai a d'akin Ash and black ne ba ta yadda zan
iya kwatanta muku had'uwar d'akin nan, ku kiyasta da kanku, nafilfili ya yi tayi
kan ya bud'e shelf na littatafan addini dake gabas dashi ya d'auko alqur'ani ya
fara karantawa cikin natsuwa da kamala seda yaji kiran sallah kan ya mike ya d'auki
chasbi ya fice don tafiya masallaci.
Ba shi ya shigo gidan ba seda gari ya d'an fara haske, direct toilet ya fad'a wow
toilet d'inma ya had'u iya had'uwa banda kofan shigowa akwai wani transparent door
a tsakiya wadda yaci gabad'aya fad'in toilet d'in filin dake tsakanin first door da
second door d'in mirror ne me tsananin kyau black gefenshi daga jikin bango shelf
ne me d'auke da towels manya da kanana masu kyau.
Har bathrobe akwai a ciki gefe wasu sets d'in perfumes ne masu tsananin kamshi dake
Allah ya halliceshi da son kamshi a rayuwan shi se karamin wardrobe me d'auke da
jallabiyoyi kala kala masu kyau da tsada, In ka shiga next transparent door d'in
gefe shower ce itama a zagaye take gwanin sha'awa se jacuzzi babba me kyau shima
don da gani ba karamin kud'i yaci ba, gefenshi hand shower ne a makale.
Chan kuma daga gefe Hand basin ne shima na yayi, komai na toilet d'in black ne da
ratsin fari, wanka yayi cikin natsuwa bayan ya cika sabulan wanka masu kamshi da
jacuzzi d'in a cikin bayin ya tsane jikinshi kan ya fito ya zauna gaban madubi ya
fara shafe shafe da kalkale kalkale kaman wata mace Allah ya gani yana tattalin
fatanshi sossai da kuma gashin kanshi yana basu lokacinsu ne sossai.
Bayan ya gama yayi wanka da turare kan ya nufi real closet dinshi, yana budewa nace
'wow' ciki kayayyaki ne kala kala komai neat gasu a goge a jere reras ba irin kayan
mazan da babu ko waenne da bangaren da aka jera su, kuma rabi da kwata bakake ne
jefi jefi ne zaka tsinci wata kalar ko fari ko ash shi kuma haka Allah yayishi be
son komai colored thing in ba baki ba, fari ko Ash.
Kananan kaya ya zaro riga da wando na companin Armani ya saka rigan se ya mishi
kaman body-hug sbd ya d'an matseshi guntun hannu gareshi wadda hakan ya baiwa
damtsenshi dake cike a kuma murd'e damar bayyana, a izzance ya wuce wurin
takalmanshi ya za'bo normal Aldo sliffers ya saka wow zo kuga yadda ya had'e,
briefcase d'inshi kawai ya d'auka ya fito asalin main parlor na saman a kan kujera
ya ajiye ya wuce kitchen ya san har yanzu hamna bata tashi ba bare tayi tunanin
had'a mishi breakfast ace mutum In ba yawo ba to fah yana bacci?.
Coffee ya had'a ya fito parlor yana sha yana kallon agogo sharp sharp ya gama sha
ko damuwa da zafin be yi, ya d'auki briefcase d'inshi yayi waje cikin bakaken
motocinshi ya za'bo wata Ford ya shige tare da warming d'inta kan ya ja ya fice
daga katuwar tsakar gidan nashi, takwas daidai ya taka kafanshi cikin hall d'in
tare da jan kofa a bayanshi.
Cikin tafiyanshi na isa da kasaita ya haura tare da d'aura briefcase d'inshi kan
desk d'insu na lecturers, class rep ya kira da hannun ya taso ya zo, bayani ya
mishi na abubuwan da ze d'auko a office d'inshi, su projector da microphone kiran
wani class rep d'in yayi suka fice don d'aukowa, ta cikin dark space d'inshi yake
karewa d'aliban kallo, matan se wani karairaya da iyayi suke.
Ko wacce ta kure adakar kwalliya, kaman masu zuwa wurin party, kaman ance ya kalli
wurin ya kuwa hangeta zaune kusa da zarah kanta a kasa tana wasa da yatsun
hannunta, fuskanta kad'ai ya kalla ya san tana cikin damuwa gashi minti minti tana
share hawaye da alamu kuka take, kan zarah ya maida idonshi se surutu take zuba
mata kasa kasa ba tare da ta lura da halin da kawar nata ke ciki ba.
Me matsalan yarinyar nan wai? Me ke damunta haka!! Allah masani ace yarinya karama
haka me kananan shekaru kullum tana cikin rud'u da damuwa!! Wayanshi ya fiddo
faskekiya da ita ya shiga massage ya rubuta "yhu are very stupid" ya turawa zarah,
da sauri ta d'ago ya kuwa banka mata harara don ya cire glass d'in, kus tayi kuwa
don class d'in tsit ba ko motsin kirki, sbd wargi ma wuri yake samu, Ina suka ga
fuska a nan.
Yana shirin yin magana ne ya ga shigowan class rep, hakan yasashi fasa fad'in
abinda yayi niyya, da kanshi ya sauka ya had'a komai kan ya fara lectures cikin
kwarewa ga iya jefa tambayoyi kawai se yayi pointing d'inka yayi tambaya, in macece
tayi ta karairaya tana amsawa, wacce ta iya fine wacce bata iya ba ya ganar da ita
abinda yake nufi, kaman daga sama taga yayi pointing d'inta, zarah ta dafa kirji
alamun "me" se ya girgiza d'an yatsan ya nuna Noor, a tsorace a kuma rud'e ta mike
ta tsaya.
🖤Gureenjo🖤
🥀NOOR IMAN🥀
*08*
A d'an tsorace ta mike tana kallonshi ita har ga Allah tana class d'inne kawai amma
bata san me ake ba, tunaninta na ga irin wulakancin da ta sha a wurin baba yau da
safe, har marinta yayi sbd abunda ya faru a gidan inna jiya, hakan yasa kwata kwata
duniyar ya fice mata a kai, har tunanin irin matakin da zata d'aukarwa rayuwanta
take.
"Yes!! What did I said it's Fungi in hausa?" Ya kuma jefo mata tambayar a karo na
biyu, nan ma Shiru tayi hakan ya sa ya tabbatar da cewa gangar jikinta ne kad'ai a
class d'in hankali da ruhinta sam basa jikinta.
Tsallaketa yayi ba tare da ya kuma kallonta ba yayi pointing wani ya bashi amsa, be
kara bi ta kanta ba ya ci gaba da abinda ke gabanshi wadda hakan yasa ta zamewa ta
zauna kanta a kasa, hannun zarah taji a nata hakan ya sata maida hankali kanta,
girgiza mata kai tayi a hankali tace "sorry, karkiyi kuka" murmushi ta sakar mata
ita wannan be kai ya sata kuka ba sam.
Aiko cigaba da tunanuka nayi har ya fita ban ma sani ba, hayaniyar da class d'in ya
d'auka ne yasa ni dawowa cikin hankalina Ina kallon zarah dake ta kallona ban san
dalili ba nace "wai har ya fita?" Hannuna ta kama muka mike muka fita ba tare da ta
furta komai ba, har seda muka samu wurin da ba mutane sossai tukuna ta dakata, "wai
me ke damunki ne haka besty? Wallahi ko makaho ya shafa fuskan nan naki ya san kina
cikin damuwa kar ki kuskura kicemin ba komai, jibeki? Duk a birkice!!".
Hawaye ne ya cika   min ido a zuciyata nace "baza ki gane bane" amma a fili se na
kwakwulo murmushi   nace "ba fa komai besty, kinga muje ki koyamin abinda akayi a
class yau, kan 11   muyi Botany" zatayi magana na ja hannunta Ina sakin murmushi, ba
yadda ta iya haka   ta bi ni, muka koma hall d'in da mukayi lectures yanzu, ba mutane
dayawa hakan yasa   muka samu wuri muka zauna ta hau min bayani In taga kaman zan
tafi tunani se ta   san yadda tayi ta hana.
It is   really fun zama da zarah tana da wani baiwa da Allah ya bata wadda baza ka
ta'ba   zama da ita bata saka farin ciki da nishad'i ba, ba ta da girman kai irin na
yaran   masu kud'in zamanin nan sam, 11 na yi mukayi second lectures d'inmu zuwa 1
tukun   muka fito.
Seda nayi sallah kan na fito don gidan hafsy dake low cost zani, tuni zarah ta
wuce, cikin natsuwa ta nake tafiya ina yaki da zuciyata wajen hanashi fad'awa
tunanin da ze sani yin wani shirmen akan titi don na saba, a kasa na dinga tafiya
har bakin gate kan na samu adaidaita na hau tare da fad'a mishi inda ze kaini.
Bamu fita layin BUK road ba wani ya tare me napep d'in dama ba shata na d'auka ba
sbd bani da kud'in yin hakan mussaman irin napep na kano, wani fitinennen kamshi ne
ya min sallama, wadda har seda ta sani lumshe ido na bud'e a hankali, dukda raina
na bani in kalli me wannan kamshin amma ego na ya hana seda naji husky voice
d'inshi na cewa "sallamu alaikum" ni da me napep d'in muka amsa, a lokaci d'aya.
Idona na sauka cikin nashi nayi saurin kawarwa na mayar kan titi, "low cost nayi"
me napep d'in yace "fad'uwa ta zo daidai da zama muma chan mukayi" be kara magana
ba se faskekiyar wayarshi da ya fidda ya fara dannawa, cikin seconds naji yana amsa
call "yes plz kazo BUK road gefen wani mini super market zaka ga mota ta a wurin,
na shiga na siya abu se kuma ta ki tashi, the key is with the securities just
collect it there".
Ban ji me aka ce mishi a d'ayan 'bangaren ba se de naji yana godiya tare da kashe
wayan, Shiru shiru ko motsin kirki banayi har muka kusa isa, shi kuwa ta
'bangarenshi kallo d'aya ya mata ya tabbatar ya samu irin macen da yake so, don
tayi mishi d'ari bisa d'ari ga natsuwa da ya lura tana da shi.
Don sam ta kasa sakewa ji tayi ya cika mata ido sossai, ganin har ga Allah ba ze
iya barin wannan daman ta wuce shi bane yasashi cewa "sunana Muhammad bashir ana ce
min hammad and yhu?" Bata tabbatar da ita yakeyi ba seda ta kalleshi taga ba waya
yakeyi ba, se ma murmushin da yake ta sake mata har fararen hakwaranshi na bayyana.
Itama murmushin tayi kan tace "Noor Iman" yace "wow nice name amma ba asalin suna
bane ko?" Kai ta gyad'a kan tace "asalin Saudah" wani murmushi me sauti ya saki
yace "sunan manya, sunan mom d'ina fa gareki" murmushi kawai tayi, a take ya ci
gaba da janta da hira duk ta kasa sakewa har suka isa daidai inda zata sauka, ta
cewa me napep d'in "zan sauka a nan" da "Toh hajiya" ya amsa tana shirin sauka taji
Muhammad yayi saurin cewa "Noor Iman".
Waigowa tayi se taga waya yake miko mata at the same time yana murmushi yace "samun
number d'inki plz ma dinga gaisawa" d'an Shiru tayi tana kallon wayan seda ya kuma
cewa "dan Allah" kan ta kar'ba ta saka mishi, "thanks" yace bayan ya kira yaji
ringing d'inshi a jikinta, umarnin tafiya ya ba me napep d'in don yaji tana shirin
bud'e jaka don d'auko kud'i.
Girgiza kai tayi bayan wucewarsu kan ta nufi karamin kofan gidan hafsyn da sallama
ta shiga a tsakar gida ta ga maman mijinta zaune tana cin goro, dukawa tayi ta
gaisheta, amsawa tayi tana me kare mata kallo har Noor ta dunfari parlorn hasfy
taji matar nan tace "tsaya wannan ba yayar hafsatu sarauniyar zaurawa ba? Me aure
aure da ta kasa zama sbd bin maza ya bi jikinta?".
Wani irin bugu zuciyata tayi a lokaci d'aya naji Ina shirin dena gani da kyar na
iya juyawa na kalleta nace "itace de, sede kar masu fad'in hakan su manta kaddara
ce tana kan kowa kuma bata fi karfin kowa ba, an haihu de" salati matar ta saka, ko
karasa sauraron salatin nata banyi ba na fad'a parlorn hafsa kujerar da ya fi kusa
dani kawai na samu na zauna a kai Ina dafe kirji.
Abubuwa sun min yawa har ga Allah sede In na tuna Allah baya d'aurawa bawa abinda
yafi karfinshi se ince "Astagfirullah wa atubu ilaih" amma Ina tunanin zuwa yanzu
akwai abinda ka iya samun zuciyata don kiris ya saura ta tarwatse gabad'ayanta,
"Yaya Noor ce, sannu da zuwa" muryan hafsy ya katse min bakin cikin da nake ciki
murmushi na kwakulo ganin yadda take fara'a nace.
"Nice Hafsy fatan bakiyi fushi dani ba, wallahi tunda kikayi 'barin nan nake ta sa
ranan zuwa dubiya Allah be yi ba se yau, Allah de ya kiyaye na gaba ya baki me
anfani" tana murmushi tace "ba komai wallahi yaya noor, na gode Ai yanzu da lokacin
ma duk d'aya ne tunda de kinzo. Bari na kawo miki ruwa" ta mike ta fice chan ta
shigo ranta ba daad'i hannunta d'auke da katon faranti me d'auke da plate d'in
jollof da ruwan pure water guda biyu.
Da mamaki nace "Lafiya kuwa hafsy?" Murmushi tayi wadda daga gani na san na yake ne
tace "ba komai, ya su mama da umma? Ya school?" Kan na bata amsa se ga uwar mijinta
nan da mijin shi kanshi, "au wato da nace kizo kice mata ta fice min daga gidan d'a
shine kikayi biris da maganata ga shashasha nan ko? Asararriya irin wannan
ballagazan yar taki".
Cewar uwar mijinta, da sauri hafsy tace "a'a hajiya wai dama nace ko ruwa ne tasha
kan ta wuce, daga makaranta take kuma dubiya da jajen 'ba...." da tsawa mijin ya
katseta "Hafsah da uwata kike ja In ja? Lallai ashe hajiya gaskiyanki ne wannan yar
tata munafuka annamimiya itace ke shirin fara hure mata kunne amma ba haka take
ba".
Kuka hafsa ta fara da sauri na mike na d'au jakata Ina danne hawayena nace "kuyi
hakuri In shaa Allahu bazan sake zuwa ba bare har na hure mata kunne, hafsy dan
Allah kiyi hakuri" a sama sama nake jin muryan habu yana cewa "gwara kam, kuma
wallahi hafsat kika bari wanchan tsohuwar guzumar ta kara shigomin gida ba tare da
izinina ba a bakin auren ki, zan kira baban don ki tabbatar uwata tafi ta kowa ta
bada tarbiyya me kyau ga duka 'ya'yanta ba'ayi watsatsiyar da zata shigo ta zageta
ba".
Kafewa yayi, a yanayin da nake cikin nan bani da wani karfin yin musu da shi hakan
yasa na bud'e gefen me zaman banza na zauna yaja yana tambayata "wace unguwa?" Nace
cikin sanyin murya "gandun albasa" tafiya mukeyi Shiru shiru kan yayi breaking
silence d'in da cewa "Damuwa da tunani be dace da kyakyawar fuskar nan ba sam".
                        🖤Gureenjo🖤
🥀NOOR IMAN🥀
*09*
"Noor magana nayi baki ce komai ba, ko zan iya sanin damuwanki? In da hali In
magance miki?" Nan ma Shiru tayi, kaman bazata ce komai ba se kuma tace "damuwana
yafi karfin tunaninka, ba me iya magance min ita se wadda ya busan numfashi" Shiru
ya ratsa na mintuna kan yace "hkne but komai Ai yana da sila, I understand sbd baki
sanni bane yasa bazaki iya fad'amin damuwanki yanzu ba.
But with time zan san me ya dameki nima zaki san me damuwana, sbd alaka ta har
abada nake son kullawa dake, kallo d'aya na miki na tabbatar na samu irin macen da
nake so kab duniya, Ina sonki" wani irin bugu da zuciyarta yayi seda tayi tunanin
ze iya ji, inaaa bata shirya ba, bata shirya wani tozarcin ba, ba ta yadda za'ayi
tayi aure yanzu wallahi.
Cikin rawar murya tace "a'a kayi hakuri dan Allah ka nemi wata" hankalinshi kwance
yace "ni ke nake so ba wata ba, bazan rabu dake ba se kin ban kwakwaran dalilin yin
hakan" Kai tsaye tace "ni bazawara ce" d'an Jim yayi kan yace "hakan ba dalili
bane" dukda he was not expecting that, "aurena har hud'u ba d'aya ba" waro ido yayi
yana kallonta har be san sadda yayi losing control ba tare da bumping wata bakar
mota dake gabanshi.
Birki ya taka tare da sakin ajiyar zuciya, ba 'bata lokaci ya bud'e motar ya fita
don yayiwa na gabanshi 'barna kad'an, tana nan zaune taga de yana knocking glass
d'in motar ta gabansu, kuma taga an bud'e bata ji me suka tattauna ba, ta de san
maganan da sukayi bata wuce na minti biyu ba, taga wanchan d'in yaja motarshi yayi
gaba, bud'e kofan da hammad yayi ne yasata kallonshi har seda ya zauna kan ta
d'auke kanta.
"Dan Allah ban son wasa Noor kinga abinda kika ja sbd kawai kina so in rabu dake se
kicemin aurenki hud'u da kananan shekarunki?" Shiru tayi don baze fahimta ba, amma
tana fatan yana ajiyeta a unguwansu a tare shi a bashi labari, nuna mishi hanya ta
d'ingayi har kofan gidansu, "na gode" shine kawai abinda ta furta kan ta sa Kai ta
fice, Ai ko de kaman yadda tayi tunani be fita a unguwan ba aka tareshi aka bashi
labarinta na karya da gaskiya wadda yasa shi fita cikin natsuwarshi, gashi Allah ya
sa mishi sonta farat d'aya a ranshi.
Ze 'boyewa mom don ya san In har ta sani bazata ta'ba yarda ya aureta ba, gashi shi
kuwa baze iya rabuwa da ita ba, gida ya nufa da nufin yayi tunani ta yadda ze shawo
kan mom kan tayi bincike, don haka take In har d'anta ze yi aure da kanta take
bincikar halin surukarta da yanayin gidansu, sede kash yana parking mom na fitowa.
"A'a hammad ya na ganka haka? Me ke damunka?" Shiru yayi na mintuna kan yace "mom
ba ko..." katseshi tayi "kul karka kuskura yaushe muka fara wasan haka da kai, zaka
fad'amin ko se ranka ya 'baci?" Dayake Allah ya halliceta da son nata gata da zafi
bata yarda komai ya samu d'anta bata d'au mataki ba, ba yadda ya iya hakan yasa
yace "na samu matar aure".
In disbelief take kallonshi kan ta sake murmushi tana cewa "Toh shine abun tada
hankali? Kode tsoron gayamata kake In shige gaba don na sanka da tsoron mata"
murmushi yayi yana gyad'a kai, tace "toh ya sunanta? Kuma wani unguwa take?" Ko
yayi karya se ta gane don ba halinshi bane "sunanku d'aya amma ana kiranta 'Noor
iman' unguwansu kuma gandun albasa.
Tana murmushi tace "masha Allah, ka san tsari na, kar naji maganan nan a bakin
mahaifinka ni da kaina zan gayamishi" sawa ranshi kawai yayi ya rasa Noor don In
har mom taji abinda yaji Toh kuwa baze ta'ba aurenta ba ko mutuwa yake yana
farkowa, amma kuma ance Ai ba abinda yafi karfin Allah, da wannan tunanin ya wuce
part d'inshi.
*********
Tassss Tass taji saukan mari akan kuncinta hagu da dama a razane take kallonta,
Umma!!! Bata ta'ba shiga harkata ba se yau, bata ta'ba d'aga hannu da sunan dukana
ba se yau, "ana cewa baki da hankali da natsuwa ban ta'ba yarda ba se yau, Toh bari
kiji bazata ta'ba sa'buwa ba yadda kike kashe aurenki sbd iskanci irin naki ki
kashewa 'ya'yana ba, wallahi ki kiyayeni ba abinda bazan iya miki ba In har kika
kuskura auren 'ya'yana yayi rawa ta dalilinki, su ba gur'batattu bane sun san me
sukeyi" kan baba dake zaune gefe ta maida kanta.
"Ka jawa 'yar ka kunne Hafeez Wallahi tallahi ta kara taka kafanta zuwa gidan
'ya'yana zan yi mugun bata mamaki" bata jira cewarshi ba ta juya ta fad'a d'akinta,
da kallo baba ya bi ta kan ya maida idonshi kaina, ina tsaye ne kawai amma wallahi
zan iya rantsewa jini be tafiya a jijiyar jikina, i am more than shock da kalaman
umma, nafi mintuna biyar kan naji zuciyata ta fara bugawa da karfi tana wani irin
zafi, wasu zafafan hawaye suka fara rolling a idonanuna da kyar na taka zuwa d'akin
mama, baba de be ce min komai ba se kallona da yakeyi har na kule.
Mama bata nan hakan ya bani daman fad'awa kan gadonta na fashe da wani irin kuka me
ban tausayi, me tayi ne a duniyanta da take fuskantan irin wannan bakin rayuwan?
Wani laifi ta aikata haka me girma da yake hunting d'inta like this? Innalillahi
wainna ilaihi rajiun uwa de da ta haifeta a cikinta, ta raine ta na wata tara tasha
wahalan nakuda amma shine take mata haka?.
Me babancin dake tsakanina da 'yan uwana da har za'a fifita su sama dani? A kuma
raba tsakaninmu, me nayiwa umma ne?? Da irin wannan tunanukan take kuka tambayoyi
ne fal a raina akan rayuwata sede banda wacce zan iya tambaya, sede tayi kuka me
isanta kan ta mike ta fad'a toilet tayi wanka, seda ta fito daga wanka kan taga
mama murmushi ta kakalo tace "sannu da dawowa mama".
"Yauwa Iman lafiya kuwa na ganki wata iri" ba tare da ta kalli maman ba tace
"Lafiya bacci na d'anyi" girgiza kai kawai mama tayi don ta san ba haka bane, kallo
ta dinga binta dashi har ta shirya cikin normal English gown tare da zura hijab,
seda ta tada sallah kan maman ta d'auke kanta daga kallonta, tana nan zaune har ta
idar da sallah, ta juyo tace "me za'a d'aura mama?" Mama tace "babanku ya kawo
aleyaho se kiyi miyan da tuwon shinkafa" da Toh ta amsa tana mikewa da hula a hannu
ta fice.
***********
"Ai rayuwar gidan Abdul ba karamin gyara bane a cikinshi, da wannan matar tashi da
da ita da babu duk d'aya" cewar Anty Rumah kanta na kan bama d'anta Arfat nono,
Kallon Abdul d'in dake kwance kan doguwar kujera Kalthum tayi tana son yin magana
tana tsoron kar ya zageta amma ganin idanunshi a lumshe kaman ba magananshi ake yi
ba yasa ta cewa.
"Wallahi kau Anty Rumah baki ga da na shiga gidanta da safe ba, ko wurin zama na
kirki babu tsabar tarkace da datti, wai da na mata magana shine take neman yi min
rashin kunya kaman ba shekara na bata ba" Hamma Hafeez yana dariya yace "Toh
sarauniyar son girma, amma Ina suna da namiji cleaner?".
Zarah da ta fito daga kitchen hannunta d'auke da tray da cups na smoothie akai
flavor kala kala dayake kowa da irin flavorn da yake so, tana ajiyewa tace "hmm ina
ko ze iya zama da masifan Anty hamna" Anty Rumah tace "Da gwara macece ma amma Ina
shegen kishinta na tsiya ze iya bari ta nemi me aiki mace", Hamma Hafeez kai tsaye
yace "Da nine Abba wallahi aure zan karamishi" Anty Rumah na dariya tace "Se kace
baka san halin gayen ba? Ai ko Abban ne se yaga dama ya amshi matan, balle kuma kai
da kace da kai ne, Ai magana ta 'baci".
Zarah tace "Da kuwa na za'ba mishi nitsatsiyar matar da babu irinta" kaman daga
sama sukaji muryan ummu tana cewa "Lallai yaran nan kun cika, Yanzu fisabilillahi
akan 'yar uwarku kuke irin wannan mugun fatan? Kar fah ku manta da ni da uwarta
uwarmu d'aya ubanmu d'aya, to bari kuji in fad'a muku hamna ita kad'ai zata zauna a
gidan Abdulraheem In har na isa dashi, kuma kuyi ku tattara ku fice min a gida
tunda kune masu hure mishi kunne.
Shima In ba shashasha ba taya za'ayi ya zauna kuna zagin matarshi yana ji be kare
ta ba, to Abdulraheem kajini da kyau In har Ina numfashi matarka d'aya hamnah" daga
bakin kofa sukaji Abba yace "A'a Rashida Ina miki rantsuwa da Allah a yau Babana ya
kawo wata macen yace yana so in aura mishi, Toh fah se inda karfina ya kare, Allah
ne fah ya bashi daman zama da mace fin d'aya In har baya jin daad'in na farkon,
karki zata ban san duk halin da yake ciki da matar tashi ba Ina sane, sannan 'yan
uwanshi nada gaskiya dole su zauna su nema ma d'an uwansu mafita In har da gaske
suna sonshi, ban ga dalilin d'aukan zafi akan abinda ba shine ba" kallo kawai ummu
ke bin Abba dashi kan ta juya ta haura a zuciye a ganinta 'ya'yanta Da mijinta sun
tsani 'yar 'yar uwarta tunda har zasu iya cewa a yi mata kishiya su kuma suna zaune
gidajensu su kad'ai, Toh kuwa zata ga uban da ya isa yi ma Abdulraheem aure tunda
d'anta ne, tana da hakki a kanshi kaman yadda shi Abban ke dashi a kanshi, sannan
se ta jaa wa su rahma shati akan shiga harkar da ba nasu ba, duk zasu gamu da ita.
🖤Gureenjo🖤
🥀NOOR IMAN🥀
*010*
Duk kasa suka sauka suna gaida Abban banda Abdulraheem, dayake duk se yanzu suke
ganinshi sa'banin Hafeez da tare suka je sallahn asuba kuma sun gaisa achan amma
yanzu ma seda ya kara gaidashi, amsawa yayi da fara'a yana tambayansu rahma
iyalansu duk da lafiya suka amsa, "auta ina nawa smoothie d'in ko yayunki kawai
kika sani?" Ya ja zarah da wasa idonshi na kan Abdulraheem da ya mike zaune daga
ganinshi ka san ranshi a matukar 'bace yake sede sam hakan be nuna a yanayin
fuskanshi da idanunshi ba sbd Allah yayishi mutum me danne 'bacin ranshi irin
Abban.
"A'a Abbana Ai In kana nan Ina na san wasu Anty rahma? Yanzu kaima zan je In maka
irin zobon da kake so" duk dariya sukayi Abba yace "yauwa 'yar albarka bari In je
parlor na In jiraki" da gudu ta mike tayi kitchen suna mata dariya, wucewa Abba
yayi parlornshi yayinda Abdulraheem ya tashi a kasalance ya bi bayanshi.
A kasa ya zauna kanshi kasa yace "ranka shi dad'e barka da rana" Abba yayi murmushi
kan yace "yauwa babana ya ayyukan?" 'Bata fuska yayi kan yace "so stressful wallahi
ni Abba na gaji da lecturing d'in nan, haba Abba ga aikin gomnati ina dashi, sannan
ga business inayi Amma ka sawa mutanen nan hope akan zanyi aiki dasu".
"Rayuwa d'an hakuri ne Babana musamman harkar mata ka kara hakuri amma In kaga zaka
cutu ka kara aure, ban de goyi da bayan ka saki matarka ko ka wulakantata ba kaga
de 'yar uwarkace" kanshi a kasa yace "In shaa Allahu Abba, bari naje Ina da
meeting" Abba ya ce "Toh Allah ya bada sa'a ya taimaka, Allah yayi muku albarka" da
"Ameen" ya amsa yana mai jin daad'in adu'ar ya fice.
A parlorn Ummu ya tsaya tare da bankawa su Anty Rahma harara kaman baze yi magana
ba kuma se yace "Munafukai kun had'ani da uwata ai kun huta" dariya suka kwashe
dashi Hafeez yace "mu de ba ruwanmu ai kun fi kusa wa ze san shiryawarku?" Kalthum
tace "yanzu haka se a shirya dashi mu ba'a shirya damu ba" Anty rahma tace "kya
fad'a 'yar uwa" kara hararinsu yayi kan ya haura saman Ummun da sallama ya tura
d'akinta ciki ciki ta amsa.
Seda yayi murmushi ya girgiza kai kan ya karasa ya zauna a gefenta tare da d'aura
kanshi kan kafad'arta yace "Allah huci zuciyar uwa ta gari, ki dena damun kanki plz
akan zancensu Kalthum, ba me ta'ba miki 'yar gwal d'inki bare kuma ayi maganar yi
mata Kishiya ita kad'aice ba Kari in shaa Allah" a take ta saki fuska tace "yauwa
Son ko kaifa se yanzu na ji magana su kuma kilbabbun chan zasu gamu dani Ina daidai
da zamaninsu".
Murmushi ya saki tare da d'an ta'be baki yana mikewa yace "muna neman albarkanku
ummu zan wuce" tana murmushi ta shafa kanshi tace "Allah yayi muku albarka
gabad'ayanku, ya tsareku daga sharrin masharranci ya bada sa'an aiki" yace "Ameen
thumma Ameen" kan ya fice tana bashi sakon gaisuwa wurin d'iyarta.
***********
"Assalamu Alaiki yake ma'abociyar kyau da kwarjini" d'an ta'be baki tayi kan tace
"wa'alaikassalam, Ina yini" yace "Lafiya kalau dear ya gd? Ya su ummanmu?" Tace
"Lafiya" yace "ya kaman baki gane me magana ba? Lallai na san matsayina wato ko
numberna ba'ayi saving ba?" Siririyar dariya ta saki tace "yanzu fisabilillahi ni
yaushe nace ban gane me magana ba?" "Toh Ai yadda kike amsawan ne kaman baki gane
me magana ba, Toh In kin gane bawan Allahn, me sunanshi?".
"Ya hammad" ta fad'a tana wasa da harshenta, lumshe ido yayi yana jin daad'in sunan
nashi daga bakinta, a hankali yace "ni de ba yayanki bane" tace "Toh me kake so in
kiraka dashi?" Yace "honey, dear, sweetheart, baby and rest" bata san sadda ta fara
dariya ba Lallai ma hammad d'in nan, shima yana murmushi yace "au dariya na baki
ko?" Tace "sossai ma" yace "Toh na kuwa ji daad'i tunda nayi silan dariyarki Allah
na gode ma" wani murmushin ta kuma yi kan tace "mama na kirana bari inje" yace "Ohk
baby take care, I love yhu".
Dip tayi bayan kashe wayan, ba maman dake kiranta kawai ta fad'i hakan ne don
yanayin da taji ta fara shiga akan hammad tabbas yana da kirki kuma yana da saurin
sabo, idan har Allah yayi ta aureshi toh fah tayi sa'ar miji, sede tsoronta d'aya
kar shima irin sauran ne dukda be yi yanayi da su ba, kirkinshi kaman hamza 'Allah
sarki Allah yaji kanka ya gafarta maka' ta jima tana irin tunanukan nan kan ta mike
ta fita parlor.
*********
Tuntu'be yaci da bottle d'in cock har yana shirin fad'uwa da sauri ya daidaita kan
ya maida idanunshi kan bottle d'in a hankali ya fara juya idon yana karewa parlorn
kallo a take yaji ranshi yayi bala'in 'baci, parlorn kwata kwata ba kyan gani duk
da kayan alatun dake zube a cikinshi, tun cups da plates da tayi using d'inshi daga
jiya da safe zuwa yanzu da yamman nan suna zube a parlorn, trow pillows duk ba
wadda ke wurin zaman shi kai har wasu kujerun.
Center table d'in ma yana manne da jikin gini ga d'ankwalinta da riganta ga empty
bottles na drinks, parlorn de kaca kaca abin takaici, ashe gwara parlorn kasa da
nan tunda shi ba komai na kaya sede kura, shi d'inma sbd bata zama cikinshi ne, rai
'bace ya nufi room d'inta da kafa ya banke kofar ya shiga tana kwance kan gado daga
ita se wani half gown gashin nan baja baja ba d'ankwali a kai.
Tana da gashi kam masha Allah, da sauri ta mike zaune ganinshi kanta ko sallama
babu kuma ta san ba halinshi bane 'shittt' se yanzu ta tuna da gargad'inshi na
safe, fuskewa tayi tace "boo ka dawo?" Harara ya zabga mata kan yace "a'a Ina chan,
hamna me na ce miki kan na fita?" Juya ido tayi kan tace "ni me ka cemin?" Ranshi
kara 'baci yayi ganin tana shirin raina mishi hankali alhali yasan ta tuna.
"Ina me miki rantsuwa da Allah na shiga nayi wanka na fito na samu baki yi abinda
na saki ba ranka In yayi dubu zai 'bace, hamna karki yarda na fara nuna miki the
other side of me!! Ki kiyaye ni na gayamiki, na tsani kazanta da mai yinta" fita
yayi ta kuwa ta'be baki ta koma tayi kwanciyarta.
Har yayi wanka ya shirya ya fito cikin shigar shan iska three quarter da sleeveless
shirt parlorn nan na yadda yake ba abinda ya chanza, ranshi a matukar 'bace ya
shiga d'akinta yadda ya barta haka ya dawo ya sameta da waya a hannu tana danne
danne, fisge wayan yayi ya buga da kasa cikin 'bacin rai yace "hamna wuce kije ki
share parlorn nan kiyi moping" itama cikin fushi tace "me haka Abdul? Sbd wani
banzan sharan parlor shine zaka fasa min waya? Ka kuwa san nawa na cire na saya?
Wallahi baze ta'ba sa'buwa ba kuma sharan bazan yi b....."
Tasss taji saukan mari a kuncinta hannu tasa ta dafe kuncinta tana mishi kallon
mamaki Don duk abinda zata mishi be ta'ba kai hannu jikinta ba se yau, kuka ta
fashe dashi ya daka mata tsawa "ki wuce kije ki share parlorn nan kiyi moping kuma
ki girka min abinda zanci kan In kakkaryaki a wurin nan" sautin kukanta ta kara jin
wai harda girki wani tsawar da ya kuma daka mata "get up jare!!" Yasa ta saurin
sauka kan ta kara jin wani marin ta fita tana kuka.
Da kuka da komai akayi Shara da moping d'in shi ma ba wani fita yayi ba sbd bata
iya sossai ba, girki kuwa daga indomie se ruwan tea ta iya dafawa hakan yasa ta
mishi indomien da Kwai se ta dafa mishi coffee ta had'a a tray ta kai d'akinshi,
yana kishingide a three seater d'in d'akin yana kallon wrestling a kan center table
ta ajiye har lokacin tana Hawaye kallo d'aya ya mata ya kau da kai shi ba halinshi
bane dukan mutum musamman macen amma hamna In ba da Haka ba bazata ta'ba shiga
taitayinta dashi ba.
Yayi alkawarin baze sake dukanta ba daga yau sede barazana da hakan tunda ya ga ta
tsorata dashi, dukda ta bashi tausayi amma be ce mata komai ba har ta fice,
wayanshi ya d'auka ya mata transfer d'in 350.000 Ya san kud'in wayanta kenan, kan
yasa fork ya fara cin indomien, tana shiga d'aki wanka tayi kan tazo wurin
fasasshen wayanta ta d'auki SIM card d'inta a wani karamin wayanta ta sanya.
Se kuwa taga kud'in bata san sadda murmushi ya subuce mata ba, a take ta shirya
cikin riga da wando ta yafa gyale d'an karami ta d'auki keyn motarta ta fice don
sayo sabon waya.
Washegari
Tafe suke suna hira da zarah duk akan test d'in da dr malabo yace ze yi next week
"dr malabon nan daga gani questions d'inshi zasuyi tsauri ba kad'an ba" murmushi
noor tayi, ita har yanzu bata san wai zarah sister d'inshi bace sbd ta ma manta da
surname d'in zarahn balle ta d'ago daga nan, tace "kayya zarah tuntuni kike mita
akan test d'innan, ba wani tsaurin da zeyi In har kinyi karatu tunda de dole abinda
ya yi mana shi ze tambayemu".
Zarah tace "na lura kare mutumin nan kikeyi bayan sarai kin san halinshi na
wulakanci" girgiza kai noor tayi tana tuna taimakon da yayi mata tace "kayya zarah
ba wani karewa daad'in abun kan yayi wulakancin se ya fad'i abinda bayaso so be da
laifi don yayi hakan, kayi abiding rules se ka zauna lafiya".
Zarah da mamaki take sauraran noor Tab da ita ce ya Abdul yayi ma abinda yayiwa
noor da zagi kam se ya sha cikin kwanduna amma ji yadda take kareshi🤔 wakar da
wayanta ya d'auka ne yasa ta kallon wayan "Ya Abdul" shine sunan da ya bayyana da
hearts a gabanshi, da sauri ta d'aga tace "hamma" yace "sallaman fah? Ko shine
hamman?" Baki ta tura tace "Toh salamu alaikum, jam banduna(ina kwana) Hamma?" Yace
"wa'alaikissalam jam gaaji(lafiya auta) sameni a office" ya kashe wayan.
Kallon wayan tayi ta kalli noor tace "brother na yace In sameshi office d'inshi
muje plz ki rakani" noor tace "dama ku fulani ne?" Zarah tace "Eh duk iyayenmu
'yan adamawa ne zama ne kawai ya kawo mu kano" noor tace "Tab zan so kuwa koyan
fulatanci don daad'i yake min, gashi yaren ummana" zarah tace "amma bata muku ne
yasa baki iya ba ko?" Shiru noor tayi tana tuna halin ummanta.
Bata iya cewa zarah komai ba har suka karasa varender d'in da office d'in yake,
bata kalli kofan ba balle ta ga sunan da aka rubuta a jiki kawai sa kai tayi a
bayan zarah suka shige da sallama muryan da taji ya amsa sallaman sun ne yasata
saurin d'ago kai gabanta na fad'uwa, karab idonsu ya fad'a cikin na juna da sauri
ta kawar da kanta gefe, dama yayan zarah ne shine zarah bata ta'ba fad'a mata ba se
ma zaginshi da takeyi a gabanta? Allah ya taimaketa da ta kasance me zagin mutane
da taji kunya gaban zarah, muryan zarah da taji tana sake gaidashi ne yasa ita ma
tace "Good morning sir" kaman baze ce komai ba kuma se yace "morning" yana kallon
zarah yace "Da nace kizo na ce kimin gayya?".
🖤Gureenjo🖤
🥀NOOR IMAN🥀
         *this page is dedicated to yhu Hafsat Sulaiman Mrs Ibrahim Allah ya barku
tare, a jima ayi lasting🥰*
*011*
"Khaih Hamma gayya toi mi wad'i? Useni ta viwu ko d'ume fahin to a andi Allah,
sobaje am on"(gayyan me nayi? Plz karka ce komai kuma, kawata ce), baki ya ta'be
tukun ya mika mata wasu manyan files guda biyu yace "ga wannan kaiwa sauban pls
kiyi sauri, ta jiraki anan sbd na san In ku biyu ne bazaki yi sauri ba" "Toh Hamma,
noor zauna bari inje In zo sorry".
Zama iman tayi kanta na kasa taji fitan Zarah, wani irin uneasiness take ji na
zaman su su kad'ai a office d'in zuciyarta kuwa se race yake yi shi kad'ai har
hannunta na had'a zufa tsaban nervousness, daurewa tayi ta fara karewa office d'in
kallo ko hakan ze rage mata abinda take ji, office d'in babba ne sossai akwai manya
manyan shelves me d'auke da littatafai Arabic da boko a kowace kusurwa na office
d'in.
Se babban desk da desktop d'inshi ke kai desk dinma kad'ai abin kallo ne sbd
had'uwarshi ta bayan desk d'in kujerarshi yake kaman yadda kuka sani, kujerar ma me
irin juyawan nan ne, a gefen desktop d'in files files ne dayawa amma a tsare suke
so clean and neat, kasan desk d'in akwai extension wear wani babba gefenshi babban
printer ne da blue gate.
Kasan office d'in shimfide da tattausan red carpet ba abinda ke tashi a office d'in
se kamshin air freshener da sanyin Ac gefe chan leather cushion ne three seater,
sossai office d'in ya mata kyau gashi a tsare daga ka gani zaka san ba na kananan
lecturori bane, wani kofa ta kalla tana tunanin ko wannan kuma kofan me? Allah
masani amma tafi kyautata zaton toilet ne, satan kallonshi tayi don ganin me yakeyi
Ai ko se suka kuma had'a ido a tare suka kawar da kai.
Gyaran murya yayi kan yace "sarauniyar kuka" kallonshi tayi da mamaki se taga shima
ita yake kallo, juya idonta tayi da ya kasance d'abi'anta kan tace "ni dr.?" Yace
"Yes yhu were always crying what's your problem?" Shiru tayi tana tunanin
matsalolinta raurau tayi da ido tana kallonshi, waro nashi brown oily eyes d'in
yayi yace "sorry plz don't cry, I just ask ne ko zan iya taimakawa but tunda kuka
zakiyi you don't have to answer".
Zatayi magana wayanta ya hau kara bud'e jakanta tayi ta fiddo wayan ganin hammad ne
yasata murmushi kan ta d'aga "Assalamu alaikum" yace "wa'alaikissalam Cutie barka
da rana, ni Kin min adalci kenan yau kwata kwata fah baki neme ni ba" murmushi ta
saki tana girgiza kai rigiman hammad se shi "sorry lectures nayi da safe yanzu
fitowa na shiyasa ban kiraka ba but kana raina, ya ciwon kan?" Dayake jiya ya ce
mata headache na damunshi, yace "naji sauki, ni bazan yi hakuri ba se an ce min
sorry darling ko sorry sweetheart" murmushi me kyau ta saki wadda yake fitar da
dimple d'inta guda da kuma wushiryarta.
Ita kanta ta san tana kyau in tayi irin murmushin sede ba kasafai takeyi ba, kallo
kawai yake binta dashi wadda ya rasa dalilin kallon, wayan kyau yake mata in tayi
magana da muryarta se yaji wani natsuwa na saukar mishi tsabar rashin hayaniyarshi
da sanyinshi, lasan lips tayi tace "nop zan fad'a amma ba yanzu ba" yace "se
yaushe?" Tace "In naje gida" yace "Ohk baby ki kular min da kanki, plz kar ki bari
ko wani namiji yaji wannan muryar taki da da hali ma da na hanaki magana da kowa"
murmushi kawai tayi tace "ohk bye".
Ta kashe wayan tana murmushi a lokaci d'aya tana taune lip d'inta na kasa, sharp ta
manta office na waye take seda ta d'aga kai suka kuma had'a ido kau da kanshi yayi
yana mamakin kanshi, Allah ya gani shi ba mutum bane me shiga harkar mutane bare
kuma me kachokan kafin ya d'aga ido ya kalli mutum hmmm amma ya rasa ya akayi yau
ya sa 'yar mutane a gaba yana mata kallon kurilla, karan wayanshi ne yasa shi
kallon wayan.
"Alexandra" sunan da ya fito akai kenan, d'agawa yayi da hello, kan yayi Shiru yana
saurari cikin mintuna kad'an ya mike ya fara zuba masifa cikin wata had'ad'iyar
British ascent da ya sata kallonshi da kyau wow sossai turancin ya mata daad'i
tabdijam Ai idan tayi turanci gaban wannan se a mata dariya don gani za'a yi bata
iya ba, masifa kawai yake da bama ta gane me yake cewa, kafe fararen Zara zaran
tender fingers d'inshi tayi da ido mai d'auke da wani had'ad'an azurfa, sossai
yatsun hannunshi suka mata kyau.
Imagining take da hannun mace ne da idan yasha jan lalle irin kyaun da ze yi,
tsabar tsabtarshi faratunshi a yanke suke a gyare tsab farare sol, kau da kai tayi
da sauri kar ya kamata tana mishi kallon kurilla gashi yana masifa kar ya sauke
kanta, ajiyar zuciya ta sauke ganin shigowar zarah, zama zarah ma tayi tana kallon
yayanta, ta juya ta kalli noor ta kuma kallon time, se ta mike tazo kusa da noor
tace "besty tashi mu tafi se mufi hour anan hamma be gama wayan nan ba, gashi
20mins kawai ya saura mu shiga lectures".
Mikewa noor tayi ta kuma satan kallonshi gaskiya bata gaji dajin muryarshi na zuba
British English d'in nan ba amma ba yadda ta iya haka ta sa kai ta fita zarah tabi
bayanta bayan ta d'agawa Abdul d'in hannu.
Cikin sauri suka karasa hall d'in ba tare da sun samu lokacin magana da juna ba
lecturer da ze musu lectures lokacin ya shigo, Bayan sun fito daga lectures d'inne
noor ta dubi zarah tace "amma ke yarinyar nan baki kyauta min ba, yanzu da kullum
zagin wanki nakeyi da ya zaki ji?" Zarah na dariya tace "Toh me zanji? Ni ba abinda
zanji baiwar Allah" girgiza kai kawai noor iman tayi suka ci gaba da takawa har
suka isa inda motar gidasu zarah take, nan fah zarah ta kafe akan se noor iman ta
shiga sun sauketa gida ba yadda batayi ba amma zarah taki rabuwa da ita haka ta
shiga suka tafi.
Da kwatance suka isa har kofar gidansu zarah tace "muje In gaida umma da kullum ake
min maganarta amma anki had'ani da ita" a tare suka shiga gidan da sallama gabanta
na fad'uwa tana tsoron kar umma ta wulakanta zarah me kirki da mutunci, zaune gaban
murhu suka ga umman tana tankad'en garin masara da sauri zarah ta karasa kusa da
ita ta duka tace "ummanmu sannu da aiki mun sameku lafiya?".
'Dago kai umma tayi ta kalli noor iman da ke tsaye tana ta adu'ar Allah yasa ta
amsa mata, ta kuma kallon zarah se tayi murmushi tace "Lafiya kalau ya chan gidan
naku?" Zarah tace "Lafiya Alhamdulillah" Tace "Toh masha Allah" kan ta maida kai
taci gaba da abinda take cikin sanyin murya noor iman tace "sannu da gida umma"
amma se bata amsa ba, da sauri ta maida dubanta kan zarah dake mata kallon mamaki
tace.
"Zarah tashi mu karasa ki gaida mama" mikewa zarah tayi suspicious tabi bayan noor
iman zuwa parlorn mama, nan suka sameta tana kallo da fara'a sossai suka gaisa da
zarah da kanta ta kawo mata ruwa, zarah kuwa ta d'an sake sukayi fira ma kuwa kan
ta tashi tana cewa "na bar driver a waje bari naje. Se anjima mama" mama ta amsa da
"yawwa zara'u ki gaida su hajiyar taki" fita sukayi da noor a tsakar gidan de ta
tsaya tayiwa umma sallama da "yauwa" kawai ta amsa ta juyawa aikinta jiki a sa'bule
zarah ta tafi noor na d'aga mata hannu.
Tabbas tana zargin wani abu tsakanin noor da ummanta, amma bata san yadda zata sa
abun ba, watakila kuma noor d'in ta mata laifi ne yasa take hakan, a haka ta ajiye
maganar gefe ta ci gaba da chat a wayanta.
"Yauwa dare yayi kuma I'm very sure kina kwance kan gado ke ke kad'anki se ki cika
alkawari" cewar Hammad, waro ido tayi tace "wani alkawari ni 'yasu?" Yace "Tab aiko
baki isa ba se kin tuna" a shagwa'be tace "ni ba abinda zan tuna na sani tunda ba
alkawarin da nayi" alamun yayi fushi yayi kan yace "ya miki kyau na gode da
wulakanci" kittt ya kashe wayan.
Ajiyar zuciya ta sauke kan ta shiga message ta fara tunanin me zata tura mishi, da
kyar de ta rubuta "kar ran miji na gari ya 'baci sbd wannan mata tashi a tausaya a
yafe mata, ba don halinta ba" ta tura mishi kan ta kuma rubuta "sweet dreams
Zaujii" ta tura tare da kashe wayanta tana murmushi, (hmmm Allah sarki baiwar
Allah).
Cikin jin daad'i hammad ke kallon screen d'in wayanshi wani irin soyayyarta yake ji
na kara ratsa shi, waro ido yayi ganin sunan mom na yawo 'baro 'baro a d'arare ya
d'auka, ji yayi tace "Sameni d'akina" mikewa yayi jiki a sa'bule ya fice zuwa part
d'inta.
Kan gado ya ganta zaune hakan yasa ya zauna daga kasa a gefenta kanshi kasa, cikin
kaushin murya tace "Muhammad ka san abinda kake shirin jefa kanka kuwa? Ka san
yarinyar da kake son aure kuwa? Toh bari In fad'amaka aurenta d'ai d'ai d'ai d'ai
har 4 kaine zaka shiga layin na 5, dan Allah salun alun ka rabu da yarinyar nan tun
kan maganar ya kai kunnen mahaifinka".
Zuciyarshi na bugawa yace "mom na sani, a haka nake sonta, mom aure rai ne dashi
kuma tun kan Allah ya halicceta ya kiyasce mata auren da zatayi a duniya mom ita
kanta na san ba yin kanta bane kaddararta kenan, a haka nake sonta kuma In shaa
Allahu saina au......" tasss yaji saukan mari a razane ya d'aga yana kallon mom
d'in tashi what!!! Did she just slapped him? Abinda be ta'ba shiga tsakaninsu da
ita ba kenan a zafafe tace.
"Baka isa ba wallahi Muhammad, wallahi Wallahi wallahi kaji rantsuwar musulmi ko to
In har Ina raye baza ka ta'ba auren yarinyar nan ba, ko da na mutu ka aureta ban
yafemaka ba Allah ya isa", a matukar razane yake kallon ta, har abin ya kai Haka?
Me yayi zafi bud'e baki yayi da niyyar bata hakuri ta daga mishi tsawa "tashi ka
fice min daga d'aki!!!" A hankali ya mike ya fice yana jin jiri na kwasarshi.
🖤Gureenjo🖤
🥀NOOR IMAN🥀
                          *012*
A razane ta d'aga tana kallon mahaifin nata a lokaci d'aya jikinta ya d'auki rawa,
me baba ke nufi ne da rayuwarta? Wai se Baba Yaga tarwatsewar zuciyarta kan hankali
shi ze kwanta ne? Me yasa ita ta fito duniya a haka ne? Hasbunallahu wani'imal
wakeel ta dinga nanatawa a zuciyarta har ta d'an ji sauki, tsawarshi taji a kanta
"ke wai ba da ke nake magana bane kin min zuru kina kallona da ido kaman na mayu,
Toh kiji da kyau na baki sati biyu ki fitar da mijin aure In ba haka ba wallahi
masallaci zan kai hotonki duk wadda yace kin mishi ko wanene kuwa aura mishi zanyi
kinji nace wallahi".
Kukan ma yau ta kasa tsabar kad'uwa da maganan baban, me ta tare mishi ne ita a
duniyar nan? Ita Ina zata samu miji cikin sati biyu, da jiri da komai ta karasa
d'akin mama ta zube akan gado se lokacin kuka ya zo mata sossai ta fashe dashi
kaman ba gobe kirjinta na mata wani irin zafi, da ma zata mutu da ta huta.
Shirin fita lectures tayi amma bazata iya fita a haka ba, don ta san ko taje ba
abinda zata fahimta, tuna maganan me acha'ban da ya ta'ba kawota gida tayi, tabbas
tana mantawa da kai kukanta wurin me duka, iyakarta sallaloli biyar nan da suka
zama wajibi a kanta ko alqur'ani se ta manta yaushe ta bud'e shi bare kuma ayi
maganar nafilfili da kai kuka wurin Allah.
Mikewa tayi ta fad'a toilet tayi alwala dama da hijabinta kanta, Alqurani ta Zara
tare da zama kan dadduma ta bud'e ta fara karantawa cikin natsuwa, tafi awa zaune
tana karatun dukda taji shigowar mama kuma ta san ita take jira suyi magana, amma
ta kasa tsayar da kanta har maman ta fice, kiran da ya fara shigowa wayarta ba
kakkautawa ne yasata tsayar da karatun ta duba wayan.
"Hammad" shine sunan da ya bayyana a saman fuskar, murmushi tayi don sossai karatun
ya sauke mata duk wani nauyi na zuciyarta, ya gusar mata da damuwarta, ya bata wani
kwarin guiwar da da bata dashi, ya goge duk wani hawaye dake fuskanta haka ya hana
wasu zubowa tabbas alqur'ani rahama ne ga masu karantashi, kwanciyar hankali ne ga
duk wani tashin hankalin bawa.
Ta yarda kuma ta tabbatar yau, da wani irin kwarin guiwa ta d'aga wayan kan yayi
magana ma tace "ya hammad Ina kwana? Ya gd? Dan Allah da gaske kana so na tsakani
da Allah?" Shiru yayi na mintuna kan yace "lafiya kalau iman, kwarai na soki
tsakani da Allah kuma har yanzu Ina sonki sede...." kan ya karasa ta katse shi "Toh
baba yace in gabatar mishi da wadda nake so nan da sati biyu, happy?" Cikin rawar
murya yace "kenan ni kike so?" Dariya tayi kan tayi maza ta kashe wayan cikin
yanayin jin kunya.
*******
"Innalillahi wainna ilaihi rajiun!" Ya dinga nanatawa tun da ta kashe wayan, kwata
kwata daren jiya kasa bacci yayi yana tunanin ta yadda ze iya rabuwa da noor iman
ba tare da tayi tunanin yaudararta yayi ba, be kuma son fad'a mata mahaifiyarshice
ta sashi rabuwa da ita don kar ta tsani mahaifiyar tashi, da kyar ya samu ya
harhad'a 'yan kalaman da yake son gayamata, amma ta fad'a mishi abunda baze iya
tunkararta maganan rabuwarsu ba.
Mikewa yayi ya fad'a wanka sharp sharp ya shirya tare da d'aukan key d'in motanshi
ya fice, kana ganinshi zaka san yana cikin damuwa ko be furta maka ba, direct gidan
Uwais yayiwa tsinke ba tare da ya shiga ciki ba ya kirashi a waya "dan Allah in
kana gida ka fito akwai maganan da nake so muyi" daga d'ayan 'bangaren Uwais yace
mishi yana office ya sameshi chan.
Asibitin da Uwais ke aiki ya nufa minti minti yana dukan sitiyarin motar tare da
taune lips, har Allah ya kaishi office d'in lafiya, zama yayi ya zubawa Uwais ido
yana kallo har Uwais d'in ya sallami patient da yake dubawa yace "Lafiya kuwa
abokina?"
Sighing yayi kan ya fara bawa Uwais labarin duk abinda ke faruwa.
Sossai Uwais yayi jimami kan ya bashi shawara "Hammad why not ka zauna da yarinyar
kaji gabad'aya labarinta da dalilan mutuwan aurenta a ganina In har ba wani abu na
tashin hankali bane ya rabo ta da gidajen aurenta se mu ma mom bayani mu kuma roke
ta yadda zata gamsu da maganan auren naku." Gyad'a kai hammad yayi cike da gamsuwa
yace "haka ma yayi zan kirata inji sadda zamu had'u se in tambayeta".
*******
Karkad'a kafa kawai yakeyi yana jiran fitowarta daga toilet, kallo d'aya zaka mishi
ka san ranshi a matukar 'bace yake, lectures yayi shirin zuwa kasancewar ya bar
karamar wayanshi a d'akinta jiya ya sa shi shigowa ya d'auka a shirye yake tsab
cikin shirin fitanshi ya shiga d'akin.
To his biggest surprise ya ganta zaune a bakin gado tana ganinshi ta mike ta tsaya
tare da fara wasa da fingers d'inta tace "dan Allah Hamma Abdul ka barni inje yola
In ga umma bata da lafiya sossai, kayi hakuri nayi garaje nayi booking flight tun
kan In sanar da kai tafiyartawa" kallonta yayi na mintuna kan ya ta'be baki a
lokaci d'aya ya d'aga kafad'unshi.
Me ke damunta haka? Maganin ya d'auka cikin kad'uwa yake kallon maganin what!!!!
Maganin hana d'aukan ciki!! Hannunshi rawa ya dingayi tsabar irin shock d'in da ya
shiga, Hamna! Hamna!! Hamna!!! Ya fad'a kasan numfashinshi tare da nausan gini har
seda zafi ya ratsa har 'bargonshi.
Safa da marwa ya fara a tsakiyar d'akin yana tunanin me yarinyar take nema dashi a
duniyar Allahn nan, me be yiwa Hamna ba da ta za'bi kin bari su haihu, yadda yake
son haihuwan nan!! Me ze mata yaji saukin abinda.... jin kanshi na sarawa ne yasa
shi neman wuri ya zauna tare da d'aura kafa d'aya kan d'aya yana karkad'awa.
Mintuna kad'an ta fito daga wankan da mamaki take kallon shi kan tace "booo baka
tafi ba har yanzu? Ko akwai abinda k..." makalewa maganan yayi, sbd idonta da ya
sauka kan maganin dake hannunshi, kallon fuskanshi tayi kan ta fara taku baya baya,
kaman kiftawar ido ta ganshi gabanta yayi grabbing dantsen hannunta da karfi.
"Me wannan??" Ya furta trying so hard to control his self in ina ta fara "ba....
a... fa.... abinda" "shut up you bastard!!" Ya daka mata tsawa, wani irin tsoro ne
ya d'arsu a ranta ganin yanayin shi ta san yanzu ta sake ta harzuka shi ba abinda
ze hana shi Lakad'amata na jaki, itafa bata ga wani laifin da tayi ba aaa jiki
jikinta haka kuma ciki cikinta ne don bata ga damar d'aukan yaro ba se me, gaskiya
ita bata shirya tsufa yanzu ba Haka kawai.
Magana   ze yi amma sam maganan yaki fita don   haka Allah ya halicceshi In har ranshi
ya kai   matukar 'baci ko magana baya iya wa,   tureta yayi har seda ta fad'i kan ya sa
kai ya   fice, ya gama yanke shawara kuma duk   duniya In ba mahaliccinshi ba ba wadda
ya isa   hanashi abinda yayi niyya, ze shayar   dasu ruwan mamaki daga ita har iyayen
nasu.
********
"Tabbas kinyi matukar kokari iman, na san abun ba me sauki bane haka na tabbatar
dauriya ce kawai irin naki, da da yadda zanyi iman da babanku da nayi don hanashi
abinda yayi niyya amma wannan karon karki tona kiga yadda muka kai ruwa rana dashi
amma yaki lankwasuwa, na kira inna sbd na san In yayi irin wannan kafewar itace
kawai me iya lankwasa shi amma ita ma ta watsamin kasa a ido tace ta bada goyon
baya d'ari bisa d'ari nan da sati biyu wallahi In baki kawo wadda kike so ba da
kanta zata bugo hotunanki dayawa ta tayashi rabarwa a massalatai.
Iman ki taimakeni ki fitar da wadda kike so kar a bada sadakarki, don hakan yafi
komai bakanta rai, babban abinda ya kona min rai wai Ina waya da inna akan zancen
nan ummanku ta kar'ba tace mata 'inna na san manyan yayyunshi zasuyi kokarin
hanashi sbd suna son ita munafukar ga shawara duk yadda zasuyi kada ki yarda In sun
matsa ki musu barazanar tsinuwa'" kuka mama ta fashe dashi tana share hawaye tace.
"Na rasa wace irin uwa ce ummanku, na rasa me ke damunta wallahi...." ta karasa da
shesheka, d'ago idon da zatayi kawai taga noor kwance a kasa sumammiya ihu ta sanya
tare da yin kanta da gudu tana kwala kiran sunanta, baba da shigowarshi kenan da
sauri ya karasa ciki ya kuwa rud'e ganin ta kaman mattaciya da azama suka d'auketa
zuwa karamar starlet d'in baban, mama ta shiga ya ja suka fice umma na zaune abinta
tana gyaran farce ko a gyalenta.
General hospital ya nufa da ita, suna parking yana parking kifa kai yayi kan
sitiyari yana tunanin hukuncin da ya gama yankewa nan d'in ma ya zo ne don neman
shawaran dr sauban Amininshi, jin hayaniya a gefenshi yasashi juyawa yana kallon
mirror waro ido yayi ganinta kwance akan gadon da ake tura marasa lafiya fuskanta
ya fito tar se kan idonta da suka kumbura tsabar kukan da ta sha.
Doguwar rigar material ne jikinta gashinta baje akan gadon sbd ko hijab mama bata
tsaya sakamata ba tsabar rud'ewa, da sauri ya fito daga motar yayi cikin asibitin a
baya ya dinga binsu har aka shige da ita emergency ze juya kenan se suka ci Karo da
dr sauban cikin sauri yace "Malabo jirani office na plz I've an emergency".
Be jira cewarshi ba ya wuce, shima jiki a sanyaye ya karasa office d'in sauban d'in
amma se ya kasa zama safa da marwa ya dinga yi yana tunano moments d'in da ya ganta
ba sau d'aya ba ba sau biyu ba, duk kuma cikin tashin hankali da kuka, me ke damun
yarinyar nan ne? Ze so jin labarinta amma ko da ze iya taimaka mata amma ta yaya?
Yana yawo yana duba agogo.
Kusan one hour yayi a tsaye yana yawo kan sauban ya shigo yana goge gumi, cikin
takaici ya buga desk din gabanshi yana furta "what the fuckk!!!!" Ya kuma bugawa
yace "shiiiiiitt" Abdulraheem yace "wani irin iskanci ne wannan sauban? Komai ya
faru bazakayi salati ba se ka dinga ambatan kalmomin da arna ne ya kamata su dinga
amabata?" Cikin rawar murya yake maganan, girgiza kai sauban yayi tare da lumshe
ido yace "I didn't make it" "whatttt!!".
🖤Gureenjoh🖤
🥀NOOR IMAN🥀
*013*
Banko kofan da akayi ne yasa su duk maida hankali kai wata nurse ce ta shigo se
faman haki take tace "Doctor!! Doctor!!! She's still breathing" da azama dr sauban
ya fice har yana had'awa da gudu, wani irin wawan ajiyar zuciya ya sauke yana zama
kan kujera a gabad'aya rayuwanshi ze iya cewa be ta'ba jin tsoro irin na yau ba, he
was really scared, to amma sbd me? Amsan da be sani ba kenan.
Ya jima zaune a wurin har be san iya adadin lokutan da ya d'auka yana jiran sauban
ba, finally se gashi ya turo kofa ya shigo a gajiye, zama yayi a normal cushion
dake office d'in tare da furta "wash Allah" Abdul yace "sannu fah" sauban yace
"yauwa, wallahi naji tausayin yarinyar nan, baka ganta ba 'yar karama da ita amma
wai tana fama da matsanancin hawan jini ya hau fiye da tunanin me tunani, don In ta
kara collapsing haka da kyar In bata samu matsala ba, ga ciwon zuciyar da ke
barazanar kama ta".
Cikin damuwa Abdul yace "seriously?? Allah sarki Allah ubangiji ya bata lafiya"
sauban yace "Ameen, se Allah ya San damuwanta" mikewa Abdulraheem yayi yana gyara
riganshi yace "na tafi sauban" mikewa zaune sauban yayi yace "wani irin zaka tafi?
I thought ka shigo muyi magana me muhimmanci ne as yhu said but you're leaving ba
tare da munyi maganan ba".
Yana kallon wani wuri daban yace "as I can see ka gaji yanzu zan dawo ko after asr
prayer ne se muyi maganan" sauban yace "ohkey then, Se ka juyo" ficewa Abdul yayi
daga ka ganshi zaka san akwai abunda ke damunshi duk daga yadda yake ta kokarin
'boyewa, har ya nufi fita se kuma se ya fasa ya nufi emergency daga jikin kofa ya
tsaya se kuma ya juya ya fice da sauri.
Toh ma ya shiga as wa? A fili yace "kawai taimako irin ta addinin musulunci, bayan
haka ba wani abu" Shiru yayi yana tunanin irin tsoron da yaji d'azu, "ko shi kuma
sbd me?" Ya fad'a yana shafa suman kanshi da sauri yace "sbd na santa, Yes hakane
sbd na santa yasa banji daad'in ganinta ba lafiya ba" sake sake kawai ya dingayi
har ya isa gidanshi.
Nan ma kasa samun natsuwa yayi duk abinda ya san ze yi don gusar da tunaninta yayi
amma abin ya ci tura, buga remote d'in hannunshi yayi da kasa yana furta "what the
f***k is happening to me?" Wayanshi ya d'auka ya danna kiran sauban ringing biyu ya
d'aga ba tare da ya jira cewar sauban ba yace "Ayi transferring d'inta to amenity
right away and pls ka bata special care I pity her".
Kit ya kashe wayanshi tare da yima sauban mobile transfer d'in kud'i masu yawa ya
kuma tura mishi sakon "used it in be isa ba yhu should let me know", da mamaki
sauban ya ke kallon wayan nashi this is unlike Malabo, really? Ta'be baki yayi tuna
irin tausayin shi, amma Ai be fad'a mishi iyayenta marasa karfi bane.
Ficewa yayi don aiwatar da abin da abokinshi ya sashi, Ai ko yana zuwa ya samu baba
na mitan shi fa baze iya ba d'an kud'in shi da yake kaffa kaffa dasu zata kama tazo
ta cinye mishi bayan ba abinda ta kareshi da shi har abada ma be yi tunani ba, da
mamaki sauban ke kallon wadda ake referring as mahaifin yarinyar chan, ita kuwa
wani irin uba Allah ya bata?.
Gabansu ya karasa yace "salamu alaikum" baba ya juyo yana amsawa da
"wa'alaikassalam aaa Doctor ne" sauban yace "Eh Alhaji, am dama na zo In muku
albishir da cewa wani bawan Allah ya d'auke nauyin gabad'aya charges na asibitinku
har zuwa a sallameku" washe baki baba yayi cikin jin daad'i yace "masha Allahu mun
gode, mun gode, Allah ya biyashi da gidan Aljannah" da "Ameen" sauban ya amsa kan
ya kira wata nurse ya bata umarnin kaisu amenity room 13, ba 'bata lokaci aka
ciresu daga d'akin yawa zuwa amenity.
**
"Ikon Allah, ko lafiya ya Abdul be zo yayi lectures ba yau bayan ya tara mutane?"
Bari de in kira inji kiranshi tayi cikin ringing na karshe ya d'aga "Assalamu
alaikum ya Abdul ina kwana?" Yace "Lafiya kalau auta, ya akayi?" Tace "naga baka zo
kayi lectures bane yau so I decided to check on yhu, hope all is fine?" Yace "yes
sure, wani abu ne ya rikeni" Tace "Ohk bye" yace "bye" kan ya kashe wayan.
Ajiyar zuciya ta sauke "Toh Alhamdulillah saura Noor" ta furta a fili tana danna
kiran number d'inta, seda ta kira sau kusan hud'u kan aka d'aga muryar yarinya
karama taji tana cewa "Salamu alaikum. Adda Noor d'in bata da lafiya an kaita
asibiti" "subhanallah me ya sameta?" Ikhram tace "nima ban sani ba" kashe wayan
zarah tayi tare da cewa driver ya kaita gidansu noor, har kofan gidan yayi parking
ta sauka ta shiga.
Still ikhram ta gani da wayan noor hannunta dukawa tayi gabanta tace "ya sunanki
'yan mata?" Tace mata "ikhram" murmushi zarah tayi tace "suna me daad'i, ba kowa ne
a gidan?" Ikhram tace "umma na ciki" shiga cikin parlorn tayi hannunta rike da na
ikhram zaune kawai suka tarar da umma seda tayi sallama sau biyu kan ta amsa tace
"sannu da zuwa bismillah karaso mana".
Shiga tayi ta duka har kasa Tace "Ina kwana umma" umma tace "Lafiya kalau, ya mutan
gida?" Zarah tace "suna lafiya, dama naga noor bata shiga school bane shine na kira
number d'inta kuma ikhram ta d'aga take ce min bata da lafiya har abin ya kai
asibiti shine nace bari Inzo inji wani asibiti ne." Shiru umma tayi na mintuna kan
tace "kya iya karbar wayarta ki kira mamanta kiji, ni kam ban sani ba kuma banda
ra'ayin sani".
Da mamaki Zarah ta kalleta amma ganin she's serious yasa ta cewa "Toh umma" kar'ban
wayan tayi Allah ya sa ba password ta duba numbern mama ta kira ba jimawa ta d'aga
"Assalamu Alaikum, mama zarah ce kawar Noor na kira ne inji asibitin da kuke da
kuma room number".
Fad'a mata mama tayi bayan ta   amsa sallaman, mikewa tayi tacewa umma "na tafi umma
se anjima" ikhram tayi saurin   cewa "zan bi ta wurin Adda noor umma" tsawa umma ta
daka mata "ke! Ke!! Ki kiyaye   ni na gayamiki ba inda zakije, wuce ki bani wuri
anan" da sauri ikhram ta fice   tana kuka, da matukar mamaki zarah ta fice.
Da sake sake dayawa a ranta suka isa asibitin direct d'akin da mama ta fad'a mata
ta nufa, da sallama ta tura kofan noor dake kwance ido biyu ce ta amsa a hankali,
da sauri zarah ta karasa tace "besty!! Sannu me ke damunki haka? Ya jikin?" Noor
tace a hankali "hmm da sauki zarah" Zarah zatayi magana kenan wayan noor dake
hannunta ya fara kara dubawa tayi se taga "ya hammad" kallon noor tayi da kai noor
tayi mata alamar ta d'aga.
Sallama hammad yayi ta amsa kan ta fara mishi bayanin noor ba lafiya tana asibiti
cikin tashin hankali da jimami ya ke tambayanta me ke damunta tace bata sani ba
tambayanta yayi asibitin da kuma room number ta fad'a mishi, ya tabbatar mata
gashinan zuwa, sallama sukayi a lokacin mama ta fito daga toilet suka kara gaisawa
kan tace "yauwa tunda kinzo kiyi hakuri ki d'an zauna da ita, bari inje gida in
d'auko wasu abubuwan In dawo".
Zarah tace "Toh mama ga driver na a waje ze kaiki se ya dawo dake" godiya mama tayi
kan ta fice zarah ta kira drivern ta sanar dashi aikin da ze yi, bayan ta kashe ne
ta kalli noor tace "besty wai me ya sameki haka? Kwanciya asibiti farat d'aya?"
Girgiza kai noor tayi cikin sanyin murya tace "Doctor be fad'a ba tukuna, Dr.
malabo yayi lectures yau ko?" Dariya zarah tayi kan tace "Kai besty kina kwance
gadon asibiti amma tunanin lectures d'in ya Abdul kike?".
Noor tace "ba dole ba zarah kin san na rasa attendance d'inshi sau biyu am afraid
of failing his course" zarah tace "bazaki fad'i ba In shaa Allahu be ma yi
attending class yau ba" ajiyar zuciya noor ta sauke tana dafa kanta dake sarawa
sossai da sossai, dr sauban ne ya shigo da mamaki yake kallonta "what har kin tashi
kina surutu? Lallai jininki me karfi ne, I have to inject yhu another injection
yadda zakiyi bacci da kyau, with this your condition ba'a so kina yawaita surutu".
Murmushi kawai noor tayi zarah tace "ya sauban" yace "laaa autan ummu, dama kin san
patient d'ina?" Zarah tace "she's my best friend" yana had'a injection yace "wow,
so ya kk ya su ummu?" Tace "ummu tayi fushi tace kwana biyu ka ki zuwa gaisheta
haka ka ki kawo su Amir" yace "oh ni kar ummu tayi fushi dani yau d'innan zanje In
bada hakuri" ya karasa yana tsikarawa noor allure a hannu, zarah tace "Da ya fi
kam" hira suka ci gaba da yi kan kace kobo noor ta yi bacci.
Yana shirin fita hammad na shigowa musabaha sukayi kan sauban ya fice hammad kuma
ya karaso ciki, mikewa zarah tayi ta bashi kujera ya zauna ita kuma ta zauna bakin
gadon noor suka kuma gaisawa ya tambayeta ya jikin inda tace "Da sauki
Alhamdulillah" Shiru sukayi na mintuna kan ya mike yace "ga wannan na san mara
lafiya da son kayan fruits, in ta tashi ki ce mata hammad yazo in shaa Allahu zan
shigo da dare duba jikin nata".
"Toh In shaa Allahu, mun gode se anjima" shima yace "se anjima".
***
Se after five ya shigo asibitin yayi wanka ya sauya kaya fuskanshi na nan yadda
cike da damuwa da suka kasu mishi gida biyu, direct office d'in sauban yayi, ya
kuwa ci sa'ar samunshi zaune yana aiki zama shima yayi bayan sunyi musabaha, shiru
ne ya ratsa na mintuna kan Abdul ya fara fad'a mishi damuwanshi da irin hukuncin da
ya yanke, sossai sauban ya bashi goyon baya akan hukuncin yayi daidai suka kuma
tattaunawa.
Sauban ya fad'a mishi abunda yaji baba na cewa inda ya kara da "daga gani mutumin
akwai son zuciya da ba don kaiba da Allah ne kad'ai ya san irin hukuncin da ze
yanke akan yarinyar don ma ba private ya kaita ba" mikewa kawai Abdul yayi ba tare
da ya amsa shi ba ya juya ya fice, da kallo sauban ya bishi kan ya girgiza kai.
🖤Gureenjo🖤
🥀NOOR IMAN🥀
*014*
Yana fita yayi amenity room d'in da sauban ya gayamishi take ya ja tunga ya tsaya,
contemplating ya d'ingayi ya shiga ne ko kar ya shiga, bud'e kofan da akayi ne yasa
shi saurin juyawa da nufin barin wurin se yaji muryan zarah tana kiran sunanshi,
tsayawa yayi har ta karaso kusa dashi tace "yaya me kakeyi anan haka?" Kallon kin
raina min wayau ya mata kan ya juya se kuma ya juyo "waye ba lafiya?" Tace cikin
damuwa "wallahi besty ta ce tun da safe nake nan, baka ganta ba duk ta fige yini
d'aya".
Tura baki tayi ta kara da "gashi yaya sauban ya ki barinta ta huta daga ta farka ze
kuma yi mata wani alluran baccin wai tana bukatan hutu" girgiza kai yayi In I don't
care tune yace "kina gayamin ni me nawa did I ask yhu?" Kuma turo baki tayi girgiza
kai yayi ya juya ya fara tafiya bin bayanshi tayi ta rike hannunshi "pls Hamma ka
shiga mana ka duba jikin nata baka ga ba da safe tana farkawa Kai ta fara tambaya
ta zaci kayi class yau".
Tsaki yaja kan yace "zan sa'ba miki, wuce ma in kaiki gida" sakin shi tayi da wuri
zatayi magana ya harare ta, "my handbag" ta furta kan ta koma d'akin ta sallami
mama da se ci mata albarka take sbd abincin da ta sa aka sayo musu daga restaurant
abincin da taga an kakkawo duk be mata kama da wadda mara lafiya ze yi sha'awar ci
ba.
A yinin yau kawai da ta zauna da noor taga abubuwa kala kala da sukayi matukar bata
mamaki suka kuma d'aga mata hankali daga wurin 'yan uwan noor d'in, duk wacce zata
shigo se tayi bakar magana ko kuma gugar zana a fakaice dukda wacce akeyi da Itan
ma bata san sunayi ba, abinda ya bata tsoro shine wacce taji ance itace kakar noor
mahaifiyar babanta tace.
Wai ko de ciki ne da ita taga tayi wani iri lokaci guda, ba de abinda jama'a suke
fad'amata akan Saude ne yake shirin tabbata ba, sam zarah bata ji daad'in maganan
ba amma ba yadda ta iya tunda taga ba wadda ya tanka innar se ma masu kara mata
petur, Ai ko tsohuwa kam ta kafe bazata tafi ba se taji gaskiyar alamari, zarahn ce
taje ta kira wata nurse daga waje ta fad'a mata abinda zata gayamusu.
A tare suka dawo nurse d'in na kallon inna tace "mama dan Allah kuyi hakuri ku ragu
ba'a son ana hayaniya akan mara Lafiya haka" ba yadda innar ta iya ne yasa ta fice
tana sababi 'yan koronta suka bi bayanta su goggo saratu.
"Zarah!!" Firgigit tayi tana kallonshi yace "are yhu alright?" Tace "yes sure,
akwai abinda ya d'auremin kai yaya da noor zan so jin labarinta" Shiru yayi na
mintuna kan yace "wace noor kuma?" Tace "friend d'ina dake asibitinsu yaya sauban,
yaya kullum tana cikin damuwa da naje gidansu nayi noticing abubuwa dayawa, and
today abun yafi yawa".
"Yanzu ke a kankantar Kin nan har zaki sani if something is fishy? Toh fad'a min
abubuwan da kikayi noticing muji" ya fad'a cikin son jin d'an wani abu da ya shafi
damuwarta, ba 'bata lokaci zarah ta bashi labarin yadda minti minti noor zatayi
maganan ummanta amma da taje gidan se taga ba haka ba, ta bashi labarin abinda ya
faru again yau a gidansu noor d'in tsakaninta da umma, Inda ta d'aura da labarin
yadda su inna da goggoninta suka d'inga misbehaving a asibitin yau.
She ended up with irin abincin da aka kawo mata, zarah yake kallo amma mind d'inshi
na chan wani wuri daman, what could it be? Tabbas 'yan uwanta baza su d'inga
mocking d'inta ba se in da akwai abinda tayi but har mahaifiyarta? Is this really
serious?? Ta'ba shi zarah tayi yayi saurin gyaran murya yace "Hakane gaskiya akwai
ayan tambaya anan, ni ba abinda zan iya mata sede In ce ki taya ta da adu'a ko
menene matsalanta Allah ubangiji ya kawo mata mafita" Tace "In shaa Allahu zan taya
ta".
Har zata fita yace "wait!! Nace In ba matsala se ki dinga sa maids d'innan abinci
kina tafiya mata dashi" had'a yatsu biyu tayi suka bada sauti, tace "yess bro, yhu
d best" girgiza kai yayi kan ya fita suka shiga gidan a tare, ummu dake zaune
parlor tace "oh Ashe tare kuke" Abdul yace "Eh ummu naje wurin sauban se muka had'u
a asibitin shine na dawo da ita dama nan na yo".
Ummu tace "madallah, auta ya kawar taki da jiki" Tace "da sauki sossai ummu, bari
inje In watsa ruwa" har kasa ya duka ya gaida ummun kan ya mike ya zauna kan kujera
cikin kasa da murya yace "ummu na gaji da halin hamna, kuyi hakuri duk hukuncin da
zakuji na yanke for the first time a zaman mu da ita pls ki bani goyon baya" had'e
rai ummu tayi tace "Kai magananka kenan kullum hamna kaza hamna kaza, haba me yasa
ita bata kawo korafi kullum se kai?".
Runtse ido yayi hafeez ne ya iya cewa "haba ummu meyasa for the first time baza ki
saurareshi ba? Kullum ita bata laifi a idonki duk irin rashin mutuncin da zata
mishi? Tunda har kika ga hamma Abdul ya....." "dakata min!!! Ba da kai nake magana
ba kuma ba akan matarka ake magana ba, dama dukkanku burinku kenan kuga tayi laifi
ku aibatata kaman ba 'yar uwarku ba, me tayi nace?".
Abba ne da zarah suka sauko a tare tana bashi labarin kawarta da bata da lafiya, be
yi magana ba seda suka zauna tukun Abdulraheem yace "maganin hana d'aukan ciki take
sha" Abba da hafeez har zarah sukace 'what!!' Hafeez yace "yanzu duk son haihuwan
da kakeyi da duk shekarun da kuka d'auka tare tana sane kuma take shan magani?
Unbelievable!!yarinyar nan is unbelievable" shiru kawai Abba yayi zarah ma kasa
cewa komai tayi se ma tausayin yayanta da ya rufe ta.
In har ka san Abdul to zaka san yana son yara waenda ze haifa a cikinshi ya nuna
kuma yayi tutiyar nashi ne, amma bata kyauta ba kuma In har ummu ta hana yaya Abdul
d'aukan mataki ta cuceshi, kai yanzu Abba ne ma ya kamata yayi magana, duk ummu
suka zubawa ido suna jiran ta kareta yadda ta saba, cikin sanyin murya tace "anya??
Anya kuwa Abdul gaskiya kake fad'a" wani malolon abu yaji ya taso ya tsaya mishi a
zuciya.
Yau ummu ke karyatashi sbd hamna aka ta'ba? Ita ta haifeshi ze iya bugan kirji yace
duk duniya ba wata mace da ta sanshi irin ita, ta sanshi shi mutum ne straight
forward kuma baya ta'ba yin karya ko kasheshi za'ayi amma kuma take karyatashi? Toh
yayiwa hamna karya ya samu me? Mikewa yayi kar yayi magana ya aikata ba daidai ba,
Ummun na kiranshi be tsaya ba ya fice Abba ya tashi yabi bayanshi.
Zarah ma haurawa sama tayi, haka hafeez ma ficewa yayi, Tashi ummu tayi ta nufi
d'akinta yau ta tabbatar ta ta'ba family d'inta itama ta san bata kyauta ba amma
kuma ya zatayi? Bata son 'yar uwarta guda d'aya tal a duniya taga bata rike mata
'ya tsakani da Allah ba, kiran hajiya umma tayi mahaifiyar hamna.
"Hello Adda ya kk? Ya gd?" Ummu tace "Lafiya kalau Ummakalthum hamna ta isa
lafiya?" Hajiya umma tace "Lafiya kalau gata tana ta baccin gajiya" se kace a mota
tayi tafiyan, umma tace "masha Allah, umma akwai abinda ya taso kuma gaskiya anan
hamna bata kyauta ba, sbd me zata dinga shan maganin hana haihuwa da yarantarta In
ta 'bata mahaifanta fah?".
Umma tace "Adda don hamna ta sha maganin hana haihuwa wani abu ne? Kiyi mata adalci
mana dan Allah, tana fah running business Ina zata iya had'a business da renon
yaro? And Ai bata ce bazata haihu kwata kwata ba" Shiru ummu tayi na seconds ita
kanta ta san bata yiwa d'anta adalci ba amma se ta kasa yiwa 'yar uwarta musu tace
"shi kenan zan san yadda zanyi da shi da mahaifinshi" umma tace "Toh gwara se
anjima". Sallama sukayi.
"Babana" tsayawa yayi jin muryan Abba, murmushi ya d'aura a saman fuskanshi kan ya
juyo "na'am Abba" Abba ya karaso tare da dafa kafad'anshi yace "kayi hakuri kaji?
Sannan ka sani duk wani shawaran da ka yanke In har ba saki bane ko duka ina
bayanka, ka hukuntata daidai laifinta na san halinka bazakayi abu ba tare da tunani
ba, Allah yayi maka albarka".
Murmushi me kyau ya saki yace "Ameen Abbana na gode" kiran sallahn magrib da ake
dokawa a massallacin kofan gidansu ne ya sasu nufan wurin flowers sukayi alwala
daidai sun gama Hafeez ya fito suka rankaya massallaci duka, da aka idar zama yayi
ya d'auki qur'ani ya fara karatu cikin natsuwa ba shi ya motsa ba har se da aka
kira isha, yayi adu'o'inshi kan ya mike aka gabatar da isha dashi.
Zaune take kan gado hannunta da drip an jinginata da pillow tana shan pepper soup
da zarah ta aika aka sayo, a hankali take komai cikin natsuwa, ido ya kura mata
rigan de safen ne jikinta sede yanzu kanta da hula fuskanta yayi fayau da shi
idonta kuwa har yanzu da alamun kuka, ajiyar zuciya me karfi ya sauke, ya jima
sossai a wurin yana tsaye yana kallonta kan ya juya ya fice.
Tunani yake yadda za'ayi ta shiga harkanshi, wani malalacin murmushi ya saki da ya
tuna da maganan zarah "tana farkawa Kai ta fara tambaya ta zaci kayi class yau"
murmushin na fuskanshi ya kira class rep d'insu ringing d'aya ya d'aga ya fara
gaidashi cikin ladabi, "Inform all your colleagues I'm having my CA test 2morrow by
8am" dip ya kashe wayan ya jefa sit d'in gefenshi ya ci gaba da tuki cikin
nishad'i.
****
Se After 8 Hammad ya dawo asibitin ya ci sa'an samunta ido biyu tana zaune kawai
akan gadon, tana ganinshi ta saki murmushi shima murmushin ya sakar mata yaja
kujera ya zauna "sannu princess ya jikin?" Tace cikin murya irin ta marasa lafiya
"na warke ni kam" yace "Allah ko? Ko zamu gwada 'yar tsere ne yadda zan fahimci kin
warke da kyau?" Waro ido tayi tana dariya Tace "rufamin asiri In ba so kake Amin
karin jini ba ruwa ba" murmushi yayi yana kallonta ledan hannunshi ya ajiye yana
cewa "ba kowa ne?".
Tace "a'a mama tana waje taje d'auraye plate da naci abinci yanzu"   yace "Ohk" hira
ya ci gaba da mata yana sa ta dariya har mama ta shigo sossai tayi   farin cikin
ganinshi kamilalle natsatse dashi, gaisawa sukayi a mutunce kan ya   mike yace "seda
safe mama Allah ya sawaka" Tace "Ameen Ameen mun gode" hannu kawai   ya d'agawa noor
iman itama ta d'aga mishi, ya juya ya tafi.
Dauriya ce kawai irin nashi amma shi kad'ai ya san damuwan da yake ciki Allah ya
gani baze iya fad'awa noor iman abinda mamanshi ta fad'a tana gadon asibiti ba amma
lokaci tafiya yake In ya tuna tace nan da sati biyu baba yace, gwara ya fad'a mata
tun wuri ta gabatar da wani saurayin nata kan lokaci ya kure, amma ta yaya tana
gadon asibiti?.
                        🖤Gureenjo🖤
🥀NOOR IMAN🥀
*015*
"Yanzu ke dama iman kina da saurayi irin wannan shine kike d'aga hankalinki akan
maganan mahaifinki?" Cewar mama tana kallon noor iman, cikin jin kunya noor tace
"Ai na fad'a mishi abinda baba yace mama" cikin jin daad'i tace "masha Allah, na
san in sunje babanku baze sa bukin da nisa ba kiyi ki warke mu je In fara gyara ki
'yata" murmushi kawai noor tayi tana girgiza kai.
Wayanta ta janyo ta kunna data bata cikin wasu groups dayawa haka bata da contacts
dayawa ta tabbatar a whatsapp d'inma In ba hammad na nan bane ba me d'ebe mata kewa
d'an gwara zarah, ganin sako a cikin group d'insu na school ne yasa ta shiga ciki
don ganin me aka turo, wani irin fad'uwa gabanta yayi "Doctor malabo ze yi test
gobe?" Ta furta a fili cike da damuwa.
Toh ya zatayi bari doctor yazo ita kam zata ce a sallameta ta warke In tayi missing
test d'innan da matsala, karan shigowan wani sakon ya sata maida hankali kan wayan
zarah ce "me mara lafiya ke yi whatsapp a irin wannan time d'in?" 'Bata fuska tayi
tare da yin typing "zarah kinga abinda na gani a group? Yayanki fah test ze yi gobe
ban san ya zanyi ba".
Zarah tace "haba dae?😳" noor ji tayi idonta ya cika da hawaye se take ganin kaman
da gayya yayi hakan zarah tace "kar ki d'aga hankalinki plz besty, yanzu rubuta
mishi sako zakiyi na baki da lafiya kan In shiga school d'in se in biyo In kar'ba
se In ba class rep ya bashi watakila In kin warke ya miki make up" noor de cikin
sanyin jiki tace "Ohk na gode da shawaranki zarah bari yanzu In rubuta".
Kallon mama tayi tace "dan Allah mama Ina son yin rubutu a paper ya za'ayi?" Mama
tace "toooh babanki yacemin ze zo kan ya wuce gida bari In ce mishi ya sayo miki
foolscap d'in da biro" godiya noor tayi mama ta kirashi da kyar ya yarda ze sayo,
bayan ya kawo ta natsu ta rubuta letter d'in cikin kyakyawan handwriting d'inta
bayan ta gama ta nad'e ta Adana.
Wata nurse ce ta shigo ta yi mata wasu allurai nan take bacci ya kwashe ta.
*****
"Wato ni zaka nunawa iyakata ko Muhammad? Akan yarinyar da bata da tarbiya da kamun
kai kake neman yi min jayayya? Toh yayi kyau, Ina so ka bud'e kunnenka da kyau ka
jini har abada kana ji? Har abada ni mahaifiyarka ban amince ka auri yarinyar nan
ba ko bayan raina ka aureta ban yafe maka ba, itama yarinyar In asiri ta maka zan
je har gidansu in nuna mata kaina ta ganni da kyau wallahi na fi karfin asirinta
bade zuri'ata ba".
Hammad ya ce "mom kiyi hakuri plz wallahi zan rabu da ita ba se kinje gidansu ba,
abinda yasa har yanzun ma ban rabu da ita ba bata da lafiya ne tana asibiti ba zan
iya gayamata cikin situation d'in da take ba, In shaa..." katse shi tayi "na hutace
ka zan gayamata da kaina" cikin sanyin murya yace "dan Allah m..." "tashi ka fice
ka bani wuri" mikewa yayi jiki a sanyaye ya fice.
Dole ba yadda ya iya yau In ya shiga wurinta ya fad'a mata tayi hakuri ta nemi wani
shi kam an mishi iyaka da ita.
*********
Cikin nishad'i yayi test d'inshi ya gama, test d'in da ya basu wahala magana d'aya
kayi out, sannan ya kama masu satan amsa dayawa waenda ya yi cancelling test d'in
nasu, bayan ya fita ne class rep ya bishi har office ya bashi letter d'in iman akan
she is sick bata samu zuwa rubuta test d'in ba, kar'ba kawai yayi ya wuce abinshi.
Kurawa handwriting d'inta ido yayi yana kallo na mintuna kan ya fara karanta
lettern, tayi sakon ne cikin hankali ba hayaniya sam wadda hakan ya sashi jin ba
daad'in test d'in da yayi da gayya amma shi a ganinshi hakan ne kad'ai hanyar da ze
samu don yi mata tambayoyi akan rayuwanta, bud'e briefcase d'inshi yayi ya Adana
lettern kan ya hau duba tests d'in da yayin yana cikin dubawa kuma se aka kirashi
zasuyi meeting, mikewa yayi ya wuce d'akin taron.
Ya san maganan bata wuce zuwa seminar ba wa ze je, wa baze je ba, shi yana da
abinyi wannan karon hakuri zasuyi da sake saken nan ya karasa, Ai ko de maganan
seminar ne za'ayi a Lagos kuma shi aka wakilta, tsaki yaja ya so cewa baza shi ba
se kuma ya tuna Abba, mtseww ya kuma jan wani yana duba date, kenan gobe ne ze wuce
kuma ze yi kwana uku.
**********
Abinda ya faru jiya shine ya faru yau, amma sede yau idanunta biyu akasin jiya da
bacci takeyi bata ji komai ba, yau kayan takaici har ummanta da farko ta d'auka ta
zo ne don duba jikinta har daad'i ya rufeta amma kuma se jikinta yayi sanyi ganin
irin kallon da take jefanta dashi haka su goggo saratu, da inna, maganganu maras
daad'in ji suka dinga jifanta dashi na 'batanci wadda ko makiyinka ne baza ka so
kaji ana mishi irin wannan cin mutuncin ba.
Dr. Sauban ne ya shigo dukda shigowar tashi be sa sun dena maganganun su ba, da
mamaki yake kallonsu ze yi magana inna tayi charab tace "yauwa Allah ya kawoka
likita, gwajin ciki nake so kayi mata yau In ciki ne dake na yawon karuwancinki se
Hafeezu ya cire ki daga cikin 'ya'yanshi ya kora daji kinji na fad'a miki, baza mu
iya ci gaba da zama da d'an shege ba bayan duk hakurin zama dake da mukayi kina
kashe aure kina dawowa kina ja mana magana".
Dr sauban yace "hajjiya kuyi hakuri ku tafi plz a condition d'in yarinyar nan ba'a
son abinda ze dinga sakata damuwa dubi yadda take kuka dan Allah, ko kuna so
zuciyarta ya samu matsala ne?" Bud'an bakin umma se cewa tayi "ya buga ma mu huta,
haba yarinya kaman shed'an" wani irin zafine yake ratsa kirjinta, haka lokaci d'aya
kanta kaman ana sarawa ranta In yayi dubu to fah ya 'baci kallon umma tayi tace.
"Wai dan Allah umma me na tare miki ne a duniyan nan? Me yasa duk cikin 'ya'yanki
ba wadda kika za'bi wulakantawa se ni? Ko kin manta ba uwa bane kad'ai ke da hakki
akan 'ya'ya har 'ya'yan ma suna da hakki akan uwa? Yau In na mutu baki nemi
yafiyata ba me zaki je ki cewa Allah akan banzantar da ni da kikayi tun daga
haihuwana ba tare da na san takamammen laifina ba? Da kuwa ana kiran mutuwa da ana
neman shi a samu da ni da kaina zan neme shi ya d'aukeni, na gaji da duniyarnan da
tunda aka haifeni ban ta'ba d'and'anan gard'inta ba, na gaji..."
Kuka ne yaci karfinta ta fashe dashi dr sauban cikin tausayawa yake kallonta, ya
kuma kalli su inna a hankali yace "hajiya zaku iya tafiya a duk gwaje gwajen da
muka mata ba ciki se hawan jini da ciwon zuciyar da yake barazanar kamata" umma da
ya lura jikinta yayi sanyi ya kalla tabbas itace asalin mahaifiyar noor iman ko
daga kammaninsu da ya 'baci to amma me yasa take cikin masu kuntata mata?.
Fita sukayi yabi bayansu zuwa get ya bawa securities d'in umarni ko sun dawo kada a
barsu su shiga, kan ya koma d'akin har yanzu kuka takeyi cikin sanyin murya yace
"saudat Ina mama?" Cikin muryan kuka tace "zuwansu yasa taje gida yin wanka da
d'auko wasu abubuwan" girgiza kai kawai yayi tare da had'a wasu allurai ya mata,
yace "gyara ki kwanta da kyau kiyi hakuri komai na duniya me wucewa ne kuma ki
yarda da maganar hausawa da sukace bayan wuya se daad'i In shaa Allahu akwai
lokacin da zaki ji daad'i".
Murmushin yake ta mishi tana me share hawayen fuskanta, ba wai don ta aminta da
magananshi ba, yana nan tsaye har bacci yayi awon gaba da ita, fita yayi yana juya
maganganun mutanen nan, Haka kawai ya za'bi ya kira Malabo ya bashi labari seda
wayan ya kusa tsinkewa kan ya d'aga, Bayan sun gaisa se Allah yasa malabon ya fara
tambayar shi.
"Ya patient d'inka na jiyan nan?" Sauban yace "to de jikin da sauki kan zuwan wasu
marasa imani, mu da muke fata jini ya sauka amma se kara hawa yayi" Da sauri malabo
ya mike tsaye yana nufan kofa yace "ganinan zuwa se mu tattauna maganan" sauban
yace "Malabo!!" Da sauri malabo yace "dama Ina ta arean asibitin In baka so na
shigo kuma shikenan" baya son sauban ya zargi wani abu dukda ya san se ya zarga
d'in tunda shi ba mutum bane me shiga shirgin jama'a amma na yarinyar nan ya d'aga
mishi hankali.
Kashe wayan yayi ya fice direct asibitin yayiwa tsinke bayan ya zauna ne sauban ya
fara bashi labarin abinda ya faru gabad'aya ya kai mintuna 30 yana juya maganganun
sauban ya kasa cewa Komai Allah ya sa aka zo aka kira sauban emergency wadda hakan
ya bashi damar mikewa ya fara safa da marwa.
Aure Aure! Ciki! Umma!! Sune abubuwan da sukayi matukar d'aure mishi kai, he just
can't even imagine his life ba kulawar uwa, amma ita Haka tayi dauriyar rayuwa ba
mahaifiya? Kuma kayan takaici harda mahaifiyarta ake mata zargin ciki ne da ita,
naushin iska yayi a fili yace "how on earth did she manage to live her life like
this?" Nanma Be ji gabad'aya labarinta ba.
Ficewa yayi zuwa jikin windown d'akin yauma a bud'e yake ya lura yarinyar bata son
zafi don jiya yaga bayan fanka ga windown dake d'age tana fifita, kallon fuskanta
yakeyi cike da tunanuka kala kala, daga ganin fuskanta ya san baccin ma ba na
daad'in rai bane tayi wani iri da ita ta rame se karan hanci da d'an haske da tayi.
Ya jima tsaye anan kan ya juya ya fice gabad'aya daga asibitin duk wani puzzles da
ze had'a da kanshi a kan rayuwarta se ya wargaje ya rasa ta Ina ze kama, how could
this be possible ace mutum ya d'auki d'a a cikinshi na about 10months yayi nakuda
ya haifa kuma ya tsani yaron from that instant?, how on earth za'ace yarinya kaman
wannan tana aure aure? And zargin ta fa sukeyi da karuwanci? Innalillahi wainna
ilaihi rajiun, be san me ke damunshi ba, be san taya akayi ya fad'a tarkon tausayin
yarinyar nan ba, wani irin tausayinta yake ji da be ta'ba ji akan wani bawa ba se
ita.
Mace da aka sani da raunin zuciya amma ta iya d'aukan waennan abubuwan ba karamin
kokari tayi ba, ze taimaka mata in shaa Allahu even it will cost all what he have
in this world ze taimaka mata for sure, amma se yaji labarinta daga bakinta ta
hakan ne ze sa ya fara shirya abinda ze yi ya taimaka mata. "I most help her, It's
a promise" ya furta yana ajiyar zuciya.
🖤Gureenjo🖤
🥀NOOR IMAN🥀
*016*
Dawowan mama ta samu tana bacci so bata d'auka wani abin ya faru ba, se kawai tayi
zaman ta kan kujera, har magrib noor iman ta kai tana bacci don har zarah ta kawo
musu abinci ta duba jikin nata duk tana bacci, se da aka idar da sallar magrib
tukun ta farka a hankali ta mike zaune mama tazo taimakonta Tace "kar ki damu zan
iya mama, na gode" ta fad'a har yanzu with bitterness in her tongue, bayi ta shiga
tayi abinda zatayi kan tayi alwala ta fito a zaune ta rama sallar la'asar da magrib
da ya d'an wuce bata wani jima da idarwa ba aka kira isha ta gabatar kan ta ci gaba
da zama.
Mama ce Tace "zarah ta zo kina bacci ta kawo abinci yarinyar 'yar albarka ce tana
sonki sossai shiyasa take d'awainiya damu haka, In zubo miki?" 'Dan murmushin yake
tayi kan ta gyad'a kai tabbas zarah na sonta zata iya cewa bata ta'ba yin kawa dake
sonta irin zarah ba, tsakaninta da Allah take sonta, pepper soup da irish pottage
da yaji veggies da mama ta ajiye mata ne ya dawo da ita daga tunanin da ta fad'a, a
hankali ta sa spoon ta fara ci kaman me taunan magani.
Tana mamakin me ya hana hammad zuwa yau? Ta duba wayanta kuma ko missed call
d'inshi bata gani ba, da wannan tunanin ta gama cin abincin duk da daad'inshi don
daga kamshin zaka san yayi daad'i amma bata wani ci sossai ba sbd bakinta d'aci
yake mata.
Ta mike kenan don komawa gado tana d'an hira da mama sukaji an bud'e kofa da
sallama duk juyawa sukayi suna kallon kofan hammad ne ya shigo, murmushi ta saki
ganinshi taji d'an sauki a zuciyarta dukawa yayi ya gaida mama cike da ladabi kan
ya d'ago yana mata ya jiki, ta amsa da "da sauki Alhamdulillah" mikewa mama Tayi ta
fice.
A tare sukayi parking da hammad kuma a tare suka nufi bangaren amenity ganin ya
nufi kofan d'akinta ne ya sashi fara tunanin waye kuma wannan, windown de ya kuma
zagayawa ya tsaya yana kallonsu.
Kasa kallonta yayi jiki a sanyaye ya fice ko waiwaye babu, wuri guda ta kafawa ido
ko motsi ta kasa yi tsabar kad'uwar da take ciki har bata san mama ta shigo ba seda
ta ta'ba ta.
Firgigit tayi tana kallonta "Lafiya kuwa iman?" Cikin rawar murya tace "Lafiya
klau" Da sauri ta kwanta ta juyawa mama baya, gyara blanket mama tayi akan sallaya
tayi kwanciyarta don Allah yayi ta da baccin wuri.
Murmushin takaici ya saki in disbelief yana juya idanu kaman mace, in ya fahimta
daidai saurayinta ne yayi breaking up da ita while she's in sick bed with high Bp
and heart attack, a fili ya ce "ya subhanallah" ya karasa da shafa kanshi yana
lasan lips d'inshi da yaji sun bushe, baze iya kwatanta how broken she is in there
ba, yana nan tsaye yana ta aikin kallon bayanta Pakistan ne a jikinta riga da wando
pink se gyalenshi da ta d'aura akanta.
Kallon bayanta ya ci gaba da yi anan a tsaye kaman an dasa shi ya san for sure se
tayi kukan wannan rabuwan, Allah sarki gashi she don't have any shoulder to cry on,
Ai ko kaman yadda ya tsammata yana nan tsaye ta mike zaune a hankali ta sid'ad'a ta
zura silifas d'inta ta nufi kofa.
Da sauri shima ya zagaya don kar ta 'bace mai se kuma suka kusa cin karo don itama
bayan ta nufa bata kula bama shine ta wuce abinta a hankali zuwa wurin wani itace
dake d'an chan gaba, wurin duhu ne zalla sbd ya d'an bar jikin amenity d'in.
Hannu tasa a bakinta kan ta zame a hankali ta zauna tare da fashewa da kukan dake
cinta a rai, a bayanta ya tsaya yana kallonta with so much pity, wani abu yake ji
da be san menene ba ke taso mishi daga kasan zuciyarshi zuwa kan harshenshi zafin
kukanta yake ji kaman ana zuba mishi ruwan zafi a zuciya, ajiyar zuciya ya d'inga
saukewa kaman shine ke aikin kukan, ta kai mintuna goma tana kukan bata ko hutu
hannunta kuma still yana toshe da bakinta.
Ganin baze iya jurewa ba yasa ya karasa ya zauna kusa da ita wadda hakan ya sata
saurin yin Shiru tana share Hawaye handkerchief ya mika mata fari sol kaman baza ta
amsa ba se kuma ta kar'ba ta kai fuskanta, wani kamshine me daad'in ji ya bugi
hancinta wadda bata ta'ba jin wani me irin turaren ba, "Karki manta Allah yana nan
kuma ya na kallonki, gareshi kad'ai zaki kai kukanki hawaye da damuwa ba sune
mafita ba, Allah ya yaye miki damuwanki" ya fad'a cikin husky masculine voice
d'inshi, yana karasa fad'in haka ya mike ya fice ba tare da ya kar'bi hankyn ba,
bayanshi tabi da kallo bata samu daman ganin fuskanshi ba sbd duhun da wurin yake
dashi bayanshi kawai tabi da kallo.
Ta de san bakaken kananan kaya ne jikinshi a saman riganshi akwai jacket me hula
shima baki kuma ya sanya hulan, hakan yasa tayi ta kallonshi har ya fice ta de san
ingarman namiji ne don ko daga tafiyarshi za'a iya gane hakan, hankynshi dake
hannunta ta maida ido kai, ta jima tana kallon hankyn yayinda hankalinta ke kan
magananshi se kuma take ji kaman ta ta'ba jin muryan, mikewa tayi ta koma d'aki
tare da fad'awa toilet tayi alwala tazo ta tada sallah.
A hankali take komai sbd jikinta da ba karfi ita karan kanta ta san karfin hali
kawai takeyi amma iska me karfi ze iya kadata.
Be tafi ba seda yaga shiganta d'aki kan ya sauke ajiyar zuciya   ya ja motanshi ya
fice, be san me damuwa da shiga tunani ba se akan yarinyar nan   Kwata kwata
kwakwalwanshi yaki barinshi ya huta da tunaninta, ringing d'in   wayanshi ne yasa shi
maida hankali kan wayan "Hajiya umma" ya gani yana yawo ajiyar   zuciya ya kuma
saukewa shi ya manta ma da wata hamna Allah ya gani.
Rage speed yayi kan ya d'aga "Assalamu Alaikum umma mun yini lafiya?" Cikin fad'a
tace "lafiya, ba wai na kiraka don mu gaisa bane na amsa gaisuwanka, na kiraka In
fad'amaka halin da kanwarka take ciki tun jiya taki cin abinci taki ko da shan ruwa
ne sbd kai ta kira layinka In be yi sau 100 ba ze yi hamsin amma ka ki d'agawa akan
wani dalili?".
Ta'be baki yayi a kan lips d'inshi yace "oops ashe?" be san taji ba ashe kuwa taji
se cewa tayi "Abdulraheem ni kake cewa oops ashe? Wato ga sa'an ka ko? Ina a
matsayina na surkarka kuma kanwar mahaifiyarka ina fad'amaka matsalar da matarka
take ciki sbd kai shine kake ce min Ashe? Yayi kyau" tana jira ya bata hakuri se
cewa "whatsoever" kit ya kashe wayanshi.
*****
Waii ina wuta hajjiya umma ta saka malabo inda take shiga bata nan take fita ba,
masifa take kaman ta ari baki, tanayi tana kallon hamna dake zaune bakin gado tana
kuka, cikin kuka Tace "kayya de umma ki bar masifan nan ki zo ki nema min mafita,
tun fah kan na auri Hamma Abdul kika ce In na aureshi se yadda nayi dashi ke fah
kika ciremin son Hafeez kika sa na Abdul sbd Abdul yafi shi kud'i amma gashi kullum
ni akan korafi da damuwan hali irin nashi ke baki d'auki wani mataki ba, har fah
dukana fah yakeyi".
Waro ido uwar tayi tace "duka? Duka fah kikace auta shine baki ta'ba fad'amin ba?
Lallai Adda Rasheeda d'anki ya ja muku gabad'aya matsala babba ba karama ba, gobe
da asubar fari zamu tafi mambila chan taraba akwai wani kwararren boka da Hajja
Zubai ta min magananshi aikinshi ci yake kaman yankan huka, bari kiga In kirata ma
drivernta ne ze kaimu tunda shi ya san wurin" hamna tace "yauwa se a kara kama
ummun nan ma naga kaman jikinta na yin sanyi idan waennan fakarun yarantan sun mata
magana, a kara kama mana ita se yadda mukace kuma bazata ta'ba ganin laifinmu ba"
hajjiya umma tace "haka za'ayi 'yata, watakila ma mu samu wannan ya kama mana shi
banzan mijin naki da kyau tunda duk waenda muka kashe makudan kud'i muka mishi a
banza yake tafiya" hamna tace "Ameen dae, yayi ta fushinshi yanzu lokacinshi ne
bari ya dawo tafin nan" ta yi maganan tana nuna tsakiyar hannunta wani irin dariya
uwar tayi tace "Ai har dukanki se kin rama" dariya suka sake tare da shewa suka
tafa se kace wasu kawaye.
*****
"Aisha je ki ki kiramin yayanku babba" mom ta fad'a tana kallon autanta da yanzu
take da aure da yaro kwaya d'aya, Aisha ta mike ta fice, Amina dake gefe tace "wai
ni mom me yake damunshi ne haka tunda muka zo naga ko da su Arif be sake kaman
yadda ya saba ba daga gaisuwa kawai ya shige yayi tafiyanshi" murmushin takaici mom
tayi tace "sbd na hana shi soyayya da bazawara karuwa" Khalid da shine d'anta na
uku yace "subhanallah mom ba fa a shedar karuwanci ba'a tabbatar ba plz ki tuba kar
Allah yayi muku hisabi ranar gobe sbd furucinki".
Mom tace "kayya Khalid wani hisabi bayan kowa ya sheda aurenta fah hud'u duk ba
wadda tayi mishi kwakwaran wata hud'u ta fito ta ci gaba da yawon bin mazanta yanzu
ma haka wacce na sa ta min bincike akanta tace tana kwance a asibiti cikin shege ne
da ita" Amina tace "a haka kuma yake sonta kuma yake son aurenta?" Mom tace "kwarai
kuwa muhammad da be ta'ba min musu ba se gashi yana min sbd yarinyar nan nafi
kyautata zaton asiri tayi mishi shegiya 'yar gidan mayu kawai".
Ahmad da shi ke bin Muhammad yace "plz mom ki dena, ko me tayi be kamata ki dinga
zaginta haka ba ita chan ta sani tunda kin hana hammad d'in aurenta" Shiru mom tayi
tana kwafa ita kad'ai daidai lokacin Aisha da hammad suka dawo a tare zama yayi
akan kujera yana karewa kannenshi kallo ganin irin kallon da suke mishi ganin baza
su dena ba yasa shi cewa "wai lafiya? Haaa'aa kun sa mutum a gaba kuna ta kallo
kaman na ci muku bashi ban biya ba?" Da zafi zafi yayi maganan, Mom na kallon Ahmad
tace "ba kun ga abinda nake fad'a ba?" Aisha tace "this is unlike yhu ya hammad,
baka da fad'a yaushe ka fa..." cikin harzuka yace "just shut up!!" Duk Shiru
sukayi.
Khalid kam tausayinshi yaji don ya san wannan yarinyar itace wacce ya fara mata son
so a duniya bayan mahaifiyarsu tunda har ya zama haka don an raba su, ganin irin
hararan da yake watsawa Aisha da Amina ne yasa mom Tace "tashi ka fice ka bani wuri
kar ka kora min yara daga zuwa ganin uwarsu" dariya duk sukayi da a da ne shima
dariya ze yi ya fara mayar da zolaya amma se ya harzuka ya fice fuuu kaman
kwa'babben fulawa da aka saka mishi yist😅
Mikewa Khalid yayi yabi bayanshi, kan gadonshi ya sameshi rub da ciki zama yayi
gefen gadon yace "I'm so sorry bro, karka manta da Allah ya ce karka sawa ranka
abinda kake so dole se ka samu sbd ze iya zama ba alkhairi bane a wurinka, ka
fawallawa Allah ze kawo maka wacce tafita" Hammad yace "baza ka gane bane Khalid,
yarinyar chan is innocent, she really is, Khalid am a jerk da na iya furta mata
kalmar rabuwa tana gadon asibiti tana fama da hawan jini da heart attack, kha..."
rawa da muryanshi ya fara ne yasashi yin Shiru, matsawa Khalid yayi tare da hugging
d'inshi, a hankali hammad ya furta "I really love her" hawaye na gangaro mishi.
*Assalamu Alaikum jama'u ya kuke ya gd😊 hope duk kuna cikin koshin lafiya Allah ya
sa haka ameen, kuyi hakuri na rashin jina kwana biyu na d'anyi zazza'bi ne amma
yanzu Alhamdulillah naji sauki, na gode fah da damuwa da kulawar da kuka nuna a
kaina ko ince akan Noor iman....... Ahhhh am jealous 😡, shaa Noor Iman is saying
hi from here🖐 thank yhu.
                      🖤Gureenjo🖤
🥀NOOR IMAN🥀
*017*
Aiko kaman yadda suka tsara asubar fari suka tashi suka shirya suka fice tafiyar
kusan 8 hours ya kaisu har mambila suka parker motar suka dinga hawa tsaunuka kaman
yadda duk wadda ya san mambila ya san garin Allah yayisu da baiwar tsaunuka, sun
wahala sossai kan suka karasa wani kungurmin dutse me duhun tsiya. Fili ne kawai
babba daidai wani d'an rami suka ji an daka musu tsawa, "Kai ku dakata daga nan"
tsayawa sukayi aka ce "barkanku da zuwa hanyar 'bata tabbas kun zama 'batattu 'yan
uwan shaid'an daga kun taku kafafunki cikin nan kun zama 'yan wuta masu taya
shaid'an hira a cikin jahannama, ku rufe idanunku".
Rufe ido sukayi mintuna biyu sukaji ance "ku bud'e" budewa sukayi se suka ga wani
bukka gabansu, ku shigo sukaji an fad'a da karfi shiga sukayi wani warjejen mutum
suka gani kato dashi mummuna (Astagfirullah) ko kyaun gani bashi dashi, bajewa
sukayi a gabanshi suna mishi kirari, kan suyi magana ma ya fad'a musu abinda ya
kawosu, da mamaki suke kallonshi yace "ku dena mamaki, Aljannu sun riga da sun
fad'amin komai, saide ku sani Mijinki ze yi aure, ba da jimawa ba kuma baze ta'ba
kamuwa ba sbd yana da wani baiwa daga Allahnshi".
Cikin tashin hakali hamna tace "boka ba yadda za'ayi ka hanashi? Ko ka kassara
matar? Who dears to cross my way?" Wani irin dariya bokan yayi kan yace "ba ta
yadda za'ayi a hana auren sede zamu bi ta 'bangaren mahaifiyarshi zamu sa mata
tsanan yarinyar daga baya kuma In muka samu wani d'an 'buli daga yarinyar se mu yi
aiki akanta, karku damu zaki mallake duk dukiyar Abdulraheem".
Hamna zatayi magana hajiya umma tace "Toh boka mun gode, mun gode ka taimakemu Ai
da yanzu bamu ma san ze yi wani aure ba, munafukar uwarshi ma ta 'boye mana" dariya
ya dinga 'ba'bakawa kan yace "maza ku sallami aljnnu ku 'bacemin da gani lokacinku
ya kare" kud'i hajiya umma ta cire bandir na 1k biyu ta ajiye mishi, suka mike da
baya baya suka fice.
Hamna de se kumbure kumbure take itafa bokan nan be mata ba tunda ya kasa hana
Abdulraheem kara aure, seda ta kasa hakuri ta furtawa hajiya umma, hajiya umma tace
"ke Ai ba da boka kad'ai zamu dogara ba, kinga yanzu In ya mana aiki akan Adda
rasheeda, idan har shi Abdulraheem d'in ya bayyana auren nashi se ki d'aga hankali
ki hanashi zaman lafiya, in hakan be sa ya daddara ba ana kai ita shegiyar Amaryan
washegari zan bayyana kuma a gidanki zan sauka se mu san yadda zamuyi maganinta har
ta gudu da kafanta, ko kuma In boka ya samu hanya akanta ya 'batar mana da ita a
duniya".
Cikin Jin daad'i hamna tace "wow yhu the best mom, gaskiya shawarankin nan yayi,
haka za'ayi duk wata 'yar iskar da zata shigo gidan Abdulraheem se ta d'and'ana
kud'arta a wurina, shima na rasa me yasa ko wanni boka ke cewa baze iya mishi aiki
ba sbd yana da wani baiwa daga Allah" kwafa kawai hajiya umma tayi itafa har ga
Allah ta tsani Abdulraheem nan kawai ba yadda zatayi dashi ne, da wannan hiran suka
karasa wurin mota a gajiye, ba 'bata lokaci suka kama hanya ba su suka shiga yola
ba se after 10 seda driver ya ajiyesu Wuro hausa kan ya juya ya nufi gidan aikinshi
bayan sun mishi alkhairi.
********
Jin kanta takeyi wani iri zuciyarta fayau ba tunanin komai, don da gaske tayi iya
yadda zatayi daga jiya zuwa yau ta shafe maganan hammad a rayuwarta, ta ci gaba da
adu'a Allah ya za'ba mata abinda yafi alkhairi In har tallarta ko tace sadakarta da
mahaifinta ze yi da ita shine alkhairi Allah ya bashi dama, itama zuwa yanzu ta
gaji da rayuwar gidansu ta gaji ba kad'an ba.
Wayanta da take sauraren qira'ar sheik Abdulrahman sudais ne ya d'auki kara, dubawa
tayi se taga hafsy, d'agawa tayi suka gaisa cikin muryan tausayi hafsy tace "kiyi
hakuri Adda iman baki ganni ba, wallahi umma ce ta cewa Usman kar ya kuskura ya
barni na zo gaidaki, ban ji daad'i ba wallahi" d'an Shiru noor tayi kan tace "ba
matsala hafsy karki damu na warke ma ai Ina kyautata zaton ko gobe da safe za'a
sallameni, kiyi ma mijinki biyayya plz" cikin rashin jin daad'i hafsy tace "Toh
Adda na gode, ki kuma kara hakuri da umma plz komai me wucewa ne" murmushi kawai
iman tayi a zuciyarta tace tunda har na shekara 23 ban ta'ba tunanin ze wuce ba,
sallama sukayi.
Qira'arta ta ci gaba da ji tana duba contacts d'inta bata bar wani kofa da damuwar
abinda umma ta gayawa mijin Hafsy ze dameta ba, daidai kan numbern Nafeesah dake
aure a bauchi ta tsaya kan tayi dialing ringing biyu ta d'aga "Assalamu alaikum
Adda iman yau an tunda damu kenan?" Murmushi iman tayi kan tace "wa'alaikissalam
warahmatullah, dama chan bamu manta da ku ba, ya Abulkhairi?" Tace "yana lafiya ina
ummana da mama?" Tace "umma na gida mama kuma na asibiti tare da ni" Nafeesah tace
"oh haka fah inna ta kirani take gayamin abinda ya faru, yanzu ya za'ayi da cikin?
Kema Adda iman be kamata ki dinga abinda kikeyi ba kin san de haramcin zina, da
irin azabobin da Allah ya tanadarwa masu yi, Adda why not wannan karon ki tuba ki
samu miji na gari kiyi aure ki natsu a d'ak...."
"Dakata Nafeesah ba wa'azi na kira ki min ba, last time I check na rigaki sannin
abubuwan da kike fad'an nan, na kiraki ne mu gaisa mu sada zumunci ki shafamin kan
Abulkhairi, se anjima" bata jira cewar Nafeesah ba ta kashe wayanta, tana me runtse
ido Allah ne kad'ai ya san yawan mutanen da inna ta fad'awa tana da ciki, ji take
kaman ta tashi tayi ta tafiya kawai se inda Allah ya kaita, tayi nesa da family
d'inta sossai yadda har abada baza su kara ganinta ba.
Bud'e kofan da akayi ne yasata maida hankali kai zarah ce ta shigo, murmushi suka
sakarwa juna kan ta zauna bakin gadon tace "bestynah ya jiki?" Noor tace "jiki da
sauki sossai besty, da kin daina d'awainiyar nan haka wadda kika yi ma mun gode"
hararinta zarah tayi kan tace "rufemin baki, Ina mama" noor na murmushi tace "Mama
na waje ta shimfid'a taburma tana shan iska inaga bata lura da wucewarki ba" zarah
tace "Ai ko nima ban kula ba kin san ance hankali shine gani" noor iman tace
"hakane, ya anyi lectures yau?".
Zarah tace "Eh amma na miki attendance Allah ya sa be kira suna ba" gyad'a kai noor
tayi, zarah tace "yauwa Besty se inga kaman kina cikin damuwa ga waswasi da
zuciyata takeyi plz ki bani labarinki waye asalin mamanki? Kinga ai yanzu mun zama
d'aya ba abinda zamu 'boyewa juna" ajiyar zuciya Noor ta sauke tare da mikewa ta
zauna da kyau tace "besty kina so ki sani kuka kenan, amma de bari na baki but plz
don't judge me".
Natsuwa Zarah tayi   nan fah noor iman ta fara bata labarin rayuwanta tun daga farko
har karshe da kuka   ta karasa yayinda zarah ta jima tanayi, bata ta'ba zaton nan
duniya akwai wadda   ze yi rayuwa kaman wadda Noor iman tayi ba, ashe ita har yanzu
bata san me rayuwa   ba tunda da gatanta da komai kowa na gidansu na sonta yana ji da
ita.
Hugging noor tayi tana bubbuga mata bayanta yayin da itama hawayenta yaki tsayawa,
abin ka da farar fata tuni fuskan zarah ya kumbura yayi jajir, seda suka tsagaita
kukan tukun zarah tace "In nace zan yi magana akan rayuwanki ba abinda zan iya cewa
besty sede ince kiyi hakuri wadda na san shi duk me tausayinki yake furtawa a
gareki but trust me ze wuce ne, zaki ji daad'i soon in shaa Allah, sannan hammad be
kyauta ba sam kuma wallahi se ya san yayi abinda yayi marar mutunci kawai, mu ci
gaba da adu'a In na fita zan yi sadaka gobe Thursday in shaa Allahu zanyi azumi
samun In miki adu'a da kyau tunda ke baza ki iya ba sbd medication da kike taking,
Allah ze kawo mafita kan karshen wani satin".
Noor na girgiza kai tace "na san ba abinda yafi karfin Allah but Zarah am scared
ban san wani irin miji Allah ze za'ba min ba, ban damu da talaka bane ko me kud'i,
ban damu ko yana da wani nakasu ba babban damuwana zarah shine ze iya rikeni? Zarah
naga wadda suka nuna suna sona ma basu iya rikeni ba se wadda za'a bashi sadakata,
be san darajata da komai nawa ba?" Zarah tace "karki manta ba abinda yafi karfin
Allah, da yardarshi mijin da zaki aura yanzu shine mijinki na har aljannah" cikin
sanyin murya tace "Allah yasa, na gode zarah na gode da kika maida damuwata naki,
and plz karki ce zaki nemi hammad ki kyaleshi da dalilin hakan na sani" tsaki zarah
taja, tana kau da maganan da cewa.
"Batun Umma da baba kuma besty kina ganin anya Haka kawai ne?" Se yanzu ma noor ta
tuna da ashe tun shekaranjiya da baba ya zo da dare be sake zuwa ba har yau, ya
samu an d'auke mishi nauyinta Ai shi a daad'inshi, girgiza kai tayi kan tace "ba
wani besty son ransu kawai suke aikatawa bazan d'auki hakkin wani da wannan tunanin
ba beside waye ze musu asiri don su tsaneni ni d'aya tal duk cikin 'ya'yansu?".
Zarah tayi Shiru na mintuna kan tace "hakane kuma amm....." ringing d'in wayanta ne
ya sata fasa fad'an abinda zata fad'a, kokarin fidda wayan tayi daga cikin jaka kan
ta d'aga ma ya tsinke, ganin Hamma Abdul ne yasata sake kira "Assalamu alaikum
Hamma barka da rana" yace "wa'alaikissalam warahmatullah kina Ina gaaji? Kin san 4
zan tafi shine kika tafi yawonki ko?" shagwa'be fuska tayi tace "Ayya Hamma am
kaima ka san bazan iya tafiya yawo inyi nisa ba bayan na san zakayi tafiya, ganinan
zuwa yanzu" yace "Ohk ki sameni gidana na riga na sallami su ummu" Tace "In shaa
Allahu" kan suka tsinke wayan.
Mikewa tayi tana kallon noor tace "kinga besty bari In tafi Hamma Abdul ze yi
tafiya gashi mun saba tun Ina karama In har ze yi tafiya ni kad'ai ke raka shi har
airport" murmushi noor iman tayi tace "Ohk se gobe In kin zo, na gode" tayi maganan
tana d'agawa zarahn hannu, har zarah ta fita ta dawo da sauri ta d'auki wayan noor
ta bud'e ta d'auki numbern hammad ta fice tana cewa "bye take care besty" murmushi
kawai noor tayi.
*****
Tana isa ya fito dama an riga da an sa mishi karamar jakanshi a mota so car d'in da
zai kaisu airport kawai suka shige, duk a baya suka zauna, kallo d'aya ya mata yace
"me ya faru kika yi kuka auta?" 'Dan Shiru tayi ita ba abin tayi karya ba tsab se
ya gane, and bata son mishi maganan noor sbd se ta kara mishi bayani sossai kan ya
ganeta dukda yana da gane mutane ta san wani sa'in har da iyayi.
Da waswasi tace "ka tuna friend d'ina na abitin su ya sauban? Har nake ce maka
kaman tana cikin da...." yace "yes Saudah right?" Da mamaki ta kalleshi, yace "uhm
me ya faru? Rasuwa tayi?" Shagwa'be fuska tayi tace "wani irin fata ne wannan Hamma
dan Allah?" Yace "Toh na sani? Me ze saki kuka kanta In ba rasuwa tayi ba?" Nan ta
fara bashi labarin noor iman, ba wai don tona asiri ba ko rashin sirri kawai sbd
duk rayuwanta shine kawai abokinta kawarta kan ta san Noor, wani irin shakuwa ne
tsakaninsu me wuyar fassaruwa, tas ta bashi labarin noor daga farko zuwa yanzu
yadda noor ta bata.
Yanzun d'inma da hawaye ta karasa, tana gamawa ana sanarwan 'this is the last and
final call for passengers traveling on Air max flight AI 104 to lagos' ba tare da
ya bari ta kalli fuskanshi ba yace "bye habeebty take care, we will talk about her
when am back" ya fice da sauri, yana zama a sit d'inshi hawayen da ya cika idonshi
na gangarowa da sauri yasa hannu ya share, tare da kwanciya ya lumshe ido shi
kad'ai ya san abinda ke yawo ranshi har jirginshi ya d'aga.
🖤Gureenjo🖤
🥀NOOR IMAN🥀
*duk naga comments d'inku na gode and na hakura, Allah ya bar kauna, and this page
is dedicated to yhu guys, duk me yin Noor iman Ina yinshi irin over d'innnan,
thnks*
*018*
Allah sarki baiwar Allah ashe haka tayi rayuwa shiyasa kullum tana cikin damuwa,
tunanin wani irin uba da uwa Allah ya bata kawai yakeyi, har ya sauka a Lagos
tunanin mafita yakeyi, seda ya shiga taxi tukun ya sake wani kayattaccen murmushi a
fili yace "I will see how heartless yhu are, I will definitely see how much yhu
dislike your daughter" yayi maganan yana danna kiran Abba.
Bayan sun gaisa ya tabbatar mishi yana da wani magana me matukar muhimmanci randa
ya dawo zasuyi, direct room d'in da aka mishi booking ya wuce bayan ajiye shi da me
taxi yayi a harabar hotel d'in, wanka yayi ya shirya tare da zubewa kan gado ya
janyo wayanshi ya kira sauban, "hey dude ya kk?" Sauban yace "am good how is your
trip?" Malabo yace "Alhamdulillah, plz ina neman alfarma ko yarinyar nan ta warke
karka sallameta se nan da four days, Ohk?" Sauban yace "ko menene dalili?" Malabo
yace "we will talk about it when am back kaima ka san I will definitely tell yhu,
so plz just do as I said" sauban yace "Ohk" sallama sukayi.
******
"How dare yhu treat such a humble soul like that? Did yhu know how broken and hurt
she is? Ka kuwa san wahalan da ta sha a rayuwa shine zaka saka mata da rabuwa while
yhu know she is in need of yhu?" Hammad yace "I'm sorry ma'am who are yhu referring
to? Wait who are yhu?" Cikin masifa zarah tace "what!! Mannin hauka kai, baka san
wacce kayi broken heart d'inta ba? Dole kace haka Ai tunda ka ji daad'in soyayya da
wata har ta baka abinda ita iman bata baka ba".
Ajiyar zuciya ya sauke yana dafe kai yace "na shiga uku, am sorry plz" wani irin
dariya tayi kan tace "ba uku kad'ai ba har tara ka shiga, yhu don't have to, yes
sbd sorry ba abinda yake ragewa se ma karawa, yhu definitely don't know how mess
yhu are in se munyi ido hud'u da kai" in disbelief ya saki murmushi me sauti a
zuciyarshi yace 'toooh ko dawa kuma Allah ya had'ani?' Cikin masifa tace "are yhu
just laughing at me? Wato ganan mahaukaciya ko?" Shiru yayi ta dinga masifa kaman
wata uwar mata, kuma ta fi bragging akan In suka had'u ba, cikin murmushi yace.
"Why not mu had'un yadda zaki samu yin masifanki da kyau, In ma dukan ne se in
kwantar da kai amin, tunda sorry be wadatar ba by the way na san nayi laifi but yhu
have to calm down and hear me out Ohk? Please" ya karasa da muryan roko, ajiyar
zuciya ta sauke kan tace "Ohk Ina zamu had'u?" Yace "cilantro restaurant" Tace "Ohk
tomorrow by 4pm" har ze kashe tace "wait! Wait!! Wait!! Ba fa wai na yarda ne don
in yi sparing life d'inka ba trust me in silly reason gareka a wurin zaka san ka
ta'bo untouchable lady".
Kit ta kashe wayan, wayan yabi da kallo murmushi na su'buce mishi, se kuma ya
girgiza kai ya ci gaba da abinda yakeyi a office d'inshi.
******
"Dr. Na warke ba za'a sallameni haka ba?" Yace "no da saura se naga kinyi garas
kaman normal mutane kan zan sallameki" shagwa'be fuska tayi tace "but am normal
yanzu ma fah" yace "nooo har yanzu da damuwa a ranki and bp d'inki be koma daidai
ba" a sanyaye kuma tace "Ai baze ta'ba komawa normal ba, damuwa a jini na yake"
kallonta yayi na mintuna kan yace "zan sallameki but se nan da three days" zatayi
magana yace "shhhh no but's" murmushi tayi ganin yadda yayi kaman wani da yaro
karami yake dealing shima murmushi yayi kan ya juya ya fice.
Mama ce ta shigo bayan fitanshi fuskanta da alamun damuwa zama tayi tana kallon
noor tace "iman inace kin fad'awa Muhammad d'innan ya turo ne?" Noor tace "na fad'a
mishi mama" mama tace "to kin fad'amishi ya akayi har yanzu Shiru ko zaki sake tuna
mishi?" Shiru noor tayi na mintuna kan tace "wani abun ne ya faru? Inna, baba ko
umma? Me sukace?" Mama tace "inna ta kawo calandar hotonki baki gani ba abin
takaici".
Wani paper haka dogo mama ta fiddo daga cikin jakanta a nannad'e ta mikawa noor,
kar'ba tayi hannunta na wani irin rawa zuciyarta a tsinke ta bud'e, hotonta ta fara
cin karo dashi daga sama an rubuta 'sadaka! Sadaka!! Sadaka!!!' Daga kasa aka
rubuta "Ni malam Hafeez Musa Muhammad Ina me farin cikin sanar daku nayi sadaka da
'yata Saudatu hafeez fisabilillahi, aurenta hud'u duk wadda yaga ze iya yazo ya
aureta ba tare da ko sisi ba, har sadaki na d'auke mishi"
Cikin kuka noor tace "Mama wa yayi abun nan amma ba baba ba ne ko?" Mama tace "Da
safen nan inna ta kawo mishi tace gudumawarta" wayanta ta janyo ta fara kiran layin
baban rabon da ta kirashi da wayanta ta manta, seda ya kusa tsinkewa ya d'aga
"Lafiya??" Shine sallaman da ya mata cikin matsanancin kuka tace "baba kaji kaina,
ka tausayamin ko da sau d'aya ne a rayuwana dan Allah kar ka raba abinnan, naji na
yarda zan zauna da duk wadda kaga ya dace dani amma ka dubi Allah ka kona papers
d'in Innan nan, ba don halina ba" Shiru yayi na mintuna kan yace "taya kike tunanin
zan banzantar da fad'in uwata sbd ke?" Cikin kukan tace "ka tausayamin rashin
soyayyarku gareni kad'ai ya isheni baba, ba se ka kara sawa mijin da zan aura da
kuma 'yan uwanshi rashin ganin darajata ba Dan Allah baba".
Ba tare da ya amsa mata ba ya kashe wayanshi, kuka taci gaba da yi kaman ranta ze
fita, Mama tayi ta bata baki amma sam ta kasa Shiru ranta ya 'baci da abinda innan
nan tayi kuma baba yaki amsa mata yanzu wannan abun ze rabarwa mutane kaman zamanin
da? Yanzu da gaske ana abu haka a fili ba a labari ko hikaya ba? Wayanta ta kuma
d'agawa ta kira Zarah.
Tana d'agawa tace "Zarah Dan Allah ki zo, Ina bukatar shawararki, yanzu plz" bata
jira cewar zarah ba ta kashe wayanta ta ci gaba da kukanta, har zarah ta shigo kuka
take cikin damuwa zarah ta zauna tana tambayar Mama lafiya? Mama da lokacin tayi
Shiru tana ta aikin kallon iman d'in tace "toh zarah gashinan dai lafiyan yayi
karanci bari In barku ku tattauna" ta mike ta d'auki taburma ta fita.
Kafad'anta zarah ta dafa ganinta cikin situation d'innan kawai yasa idonta cika tab
da hawaye tace "besty menene ya faru kuma?" Cikin kuka noor iman tace "Zarah inaga
duniya zan shiga" waro ido zarah tayi tace "what??? Noo baza ki shiga duniya ba
besty kina tunanin don iyayenki sun miki laifi don kawai basu baki soyayya ba shi
ze sa Allah ya kasa kamaki da hakkinsu In kin shiga duniya? Tukuna ma me ya faru?".
Calendar d'in ta mika mata kar'ba tayi ta bud'e bata san sadda ta zauna ba, dafe
kai tayi kan ta d'ago ta kalli Iman da itama kallon nata takeyi tace "Wa yayi
wannan abin?" Iman ta kauda kanta cikin takaici tace "inna, and ta sa baba dole wai
se ya rabarwa mutane massalatai massalatai I even call him begging him not to do
that, but se hanging min wayan yayi a kunne, Zarah menene shawaranki?".
Zarah tace "ki kwantar da hankalinki In shaa Allahu zan samo mana mafita baze raba
ba da yardar Allah" hawaye ne kawai yaci gaba da gangara a idonta tana girgiza kai
tace "zarah baki san baba bane, tunda har inna ce ta saka shi Toh fah baze
lankwas...." Zarah ne ta katseta "In shaa Allahu zamu samu mafita, I will seek
advice from a trust person of mine kuma zakiga munyi nasara, plz ki kwantar da
hankalinki ki dena kukan nan kin san de bpnki har yanzu be sauka ba, Bari kiga In
kira ya sauban yazo ya kara miki allura samun ki huta kukan nan ya isa haka plz".
Kiran dr sauban tayi a waya ya tabbatar mata baya nan amma ze turo nurse tayi mata
allura, kashewa tayi ba'ayi minti goma ba se ga nurse tazo ta mata allura nan kuwa
bacci ya tafi da ita, mikewa zarah tayi ta fita cike da damuwa hannunta rike da
calandern, a mota ta zauna tana dafe kai, ta jima a haka kan ta d'aga wayanta ta yi
snapping calendern, tare da shiga WhatsApp ta turawa Malabo, kiranshi tayi yana
d'agawa ta fashe da kuka.
A rud'e yace "zarah lafiya? Me ya sameki me ya faru kike kuka?" Ganin ya shiga
damuwa yasa tace "ka duba whatsapp se muyi magana" kashewa yayi a take ya kunna
data ya hau kan sunanta da yayi saving da 'fav. Sis❤️' hoto ya gani hakan yasa yayi
downloading, mikewa tsaye yayi yana kara karanta rubutun dake jikin calendern, da
sauri ya fita ya shiga calls ya kira Zarah.
Tana d'agawa yace "Allah ya sa basu rabar ba" zarah tace "I don't think Hamma, plz
me kake gani zamuyi mu taimaka mata bakaga irin halin da ta shiga ba sbd wannan
tozarcin da ake shirin mata" d'an Shiru yayi na seconds can yace "I know what to do
karki damu, and plz stay with her ki kwantar mata da hankali" sbd saninshi da
tausayi da tayi yasa bata kawo komai a ranta ba tace "Toh Hamma" yace "bye" tare da
kashe wayan.
********
Safa da marwa ya fara tare da dunkule d'aya hannunshi yana bugawa a tafin d'ayan,
ba plan d'inshi ba kenan duk wannan seminar ne ya hanashi aiwatar da plan d'inshi
yadda ya tsara, yanzu me ze yi don baba ya fasa raba abun nan? Kanshi ya d'an
bubbuga yana cewa "think! Think plz" had'a yatsunshi biyu yayi ya murd'e suka bada
sautin 'dasss' kan yace "yess that's what am going to do" wayanshi ya d'auka ya
kira Abba.
Bayan ya d'aga cikin ladabi suka gaisa kan yayi gyaran murya cikin natsuwa ya baiwa
Abba labarin noor iman kab ba abinda ya 'boye sbd be son Abba yaje aiwatar mishi da
idean d'inshi a samu wani wadda ze gayamishi karya da gaskiya yace ya fasa don ya
san Abba mutum ne in yace yes ba wadda ya isa maidashi no haka in yace no to ba
wadda ya isa maidashi Yes.
Kaman yadda ya zata sossai Abba ya tausayawa noor balle kuma da yaji karamar
yarinyace da irin wannan kaddaran, cikin sanyin murya yace "Toh babana kai yanzu me
kake gani shine zamuyi mu taimaketa sbd taimakon irin wannan jahadi ne, dukda ni ba
mutum bane me yarda da tsubacce tsubacce ba wai nace babu ba amma yanzu samun na
gaskiyan wuya ne dashi, se In ga kaman yarinyar ba'a barta haka ba, ko da ba mutum
ba ze iya yiwuwa tana da aljannu, taya akayi baiwar Allahn nan ta rayu da irin
wannan kalubale da in wani me karamin zuciya ne da ya dad'e da mutuwa, Ko kuwa ta
shiga duniya ta aikata abinda ake jefanta dashi da kyau yadda za'a samu hujja".
Hmm kawai malabo yayi yana girgiza kai shi kad'ai ya san irin tausayin da yake ji
akan yarinyar cikin karfin gwiwa yace "Abba aurenta nake so inyi" ya zata Abba baze
yarda ba se kuma yaji yace "masha Allah that's wonderful idea" Abdul yace "and Abba
bana so mu nunawa iyayenta dukiyarmu yanzu I mean if possible muje musu a talakawa
marasa karfi, ni karan kaina in je musu a matsayin mashayi, I want to see how
extent ya kai da kin yarinyar nan" Abba yace "Allah na gode ma, Allah yayi muku
albarka" malabo yace "Ameen, Abba plz kaje wajenshi yau samun kar ya raba hotunan
tozarcin nan and plz it should be secret ko ummu kar ta samu labarin auren nan sbd
ka santa In abu yazo da maganan ta'bo hamna" a haka suka ajiye kan sukayi sallama.
******
"Assalamu alaiki hajiyar fad'a ban sani ba amma zuciyana na bani daidai na chanka,
duk toshewar nan sbd a mazge ni ne?" Ya fad'a da zolaya, kara had'e rai tayi dukda
dariya da magananshin ya bata, se kawai tace "wa'alaikassalam" zama yayi ya koma
serious kan yace "Zarah right? In ba na manta ba" zarah tace "hkne uhm Ina jin
reason d'inka" yace "zarah baza ki gane yadda nake son iman ba amma ba yadda na iya
Allah be za'beta a matsayin matata ba, zarah ya kike so d'an da uwarshi tayi
rantsuwa sau uku tace muddin ya auri yarinyar da yake mutuwar so bata yafe ba
duniya da lahira ko da kuwa bayan ranta ne?" Ya karashe idonshi na kad'awa.
Cire glass d'in idonta tayi tana kallonshi se kuma ya bata tausayi she can feel it
sincerity d'inshi yake gayamata, ya d'aura da "kiyi hakuri sannan ki tayani ba iman
hakuri ban san hawan jini da heart attack ke damunta ba seda na furta mata kalmar
rabuwa, tabbas na so bari se ta warke In gayamata amma mom tace zata je har
asibitin ta sameta tsoron kar taje ta tozartata yasani gayamata, na so jin ko
labari iman ne ko da ba da aure bane in ga in zan iya taimaka mata amma yanzu bazan
iya fuskantanta ba".
Hawayen da ya zubo mishi ne yayi saurin d'aukewa, a sanyaye zarah ta fara bashi
labarin Iman se ga hammad ya rufe fuska da handkerchief har ta gama be iya bud'ewa
ba ya jima a haka yana jin yadda zarah take fitar da nata kukan kan ya goge
fuskanshi ya fiddo wani ya mika mata, kar'ba tayi tana goge fuskanta ganin hankalin
wasu ya fara yowa kansu, ya jima sossia kan ya iya magana "kina ganin hammanki ze
iya taimaka mata?" Tace "kwarai kuwa Ina da tabbacin hakan, ko da ba ze iya ba
bazan so ka sake shiga magananta ba don ta riga ta kokarta cire ka a zuciya Allah
ya sa ba wai ta fad'a dayawa bane, sannan ko bata cireka ba bazan so kaki jin
maganar mahaifiyarka sbd mace ba, na fahimceka yanzu, na gode".
Mikewa tayi tace "zan tafi se anjima" da kallo ya bita har ta shiga mota yau ita ke
ja bata taho da driver ba dama chan ta iya rigima ne irin nata ta matsawa Abba ya
sama mata driver wai driving na gajiyar da ita, Muhammad ya jima sossai zaune anan
kan ya mike ya fice zuciyarshi cike fal da tausayin iman Adu'a yayi alkawarin sata
har ta samu kwanciyar hankali a rayuwanta ze cigaba da adu'a Allah ya bawa Abdul
daman taimakonta, sannan ya barta da mutane irin su zarah da mama, ya karkato
hankalin iyayenta kanta ba se sadda ta musu nisa ba.
******
Bayan isha baba na zaune kan taburma a tsakiyar gida yana jin rediyonshi yaji yaro
yayi sallama ya shigo yace "wai ana sallama da malam hafeez inji wani a waje" yace
"to to waye kuma yake sallama dani?" Yaron yace "wani ne ban sanshi ba" mikewa baba
yayi ya zura silifas yabi bayan yaron, Abba ne tsaye daga shi se riga da wando na
wani yadi wadda a cikin kayanshi gabad'aya ze iya cewa shine me karamin kud'i dukda
ya kai 20k amma In ba ka san kan yadudduka ba baza ka ta'ba ganewa ba sannan be
d'aura babban rigan ba hannunshi ba agogo takalmin kafanshi kuwa lufas ne na wankan
shi.
Musabaha sukayi da baba kan yace "Lafiya kuwa malam kake nemana?" Abba yace "Lafiya
klau se alkhairi, wato malam d'ana ne yaga 'yar wajenka Saudah yace min alambaran
duniya ba wacce yake so se ita, kuma baya son auren ya d'au lokaci sannan gaskiya
bazan 'boye maka ba yana d'an ta'ba shaye shaye" ya karasa yana furta
"Astagfirullah" a zuciyarshi baba yace "to masha Allahu fad'uwa yazo daidai da zama
dama chan miji nake nema mata ido rufe Ai Don yana shaye shaye ba wani abu bane ze
dena ne, ni de a matsayina na mahaifinta na bashi ita duniya da lahira in da hali
ma yazo juma'an nan a d'aura musu aure".
*dukda nayi niyyar yin pages biyu ban samu dama ba amma ga wannan long chapter d'in
ya ninka kowanne tsawo a kafta, and plz don't forget to comment*
🖤Gureenjo🖤
🥀NOOR IMAN🥀
*019*
Da tsananin mamaki Abba ke kallon baba, wani irin uba ne wannan? Wani irin ubane ze
so 'yarshi ta auri mashayi bayan ya san outcomes na zaman aurenta? Ya yarda ze bada
'yarshi ba bincike ba komai? Yanzu kai be ma san me ze iya cewa akan baba ba, Da
kyar ya iya had'a "Toh Toh zamu duba In zamu iya had'a komai kan juma'an" baba yace
"a'a ba se kun had'a komai ba ma na hutace ku har sadaki ni zan biya mishi" Abba
yayi saurin cewa "A'a wannan kam ze biya amma sauran abubuwan se a hankali ze mata
ka san yanayin rayuwan", godiya baba ya d'inga yi kaman wadda aka ce an baiwa
kujerar Makkah alhalin jin daad'in ya rabu da kaya yake yi kuma yayi alkawarin
wannan karon ta kashe auren wallahi se ta bar mishi gida.
Cike da tausayin iman Abba ya tafi, se yaji wani sonta a matsayin 'ya ya shige shi
kai koda ace rabuwa sukayi da Abdul, ba fata yake yi ba baze ta'ba barinta ta dawo
gidan nan ba ze ci gaba da riketa har Allah yasa ta samu wani mijin kuma.
******
Tun 8pm suka fara presentation d'in amma sam hankalinshi kwata kwata baya kan
abinda akeyi tunani kawai yake ko me Abba yake tattaunawa da baba? Ko ya yarda ya
bada auren? "Dr. Abdulraheem Ahmad Malabo do yhu have anything to say?" Da sauri ya
mike yana cewa "yes sure" kan ya tattari abinda ze yi presenting ya fita ya farayi
cikin had'add'iyar turancinshi.
******
Tunda ta farka daga alluran take kwance kawai ita kad'ai ta san abinda take sakawa
a zuciyarta, Allah ya gani tayi iya hakurin da zata iya yi, ta gaji hakanan, so ta
yanke shawaran ana sallamanta daga asibitin nan bazata jira wani auren tozarcin da
baba ze mata ba, zata tafi chan inda ba wanda ya santa tayi irin rayuwar da zata ji
daad'i, ta'ba kafanta da akayi ne yasata maida hankali kan wadda ya ta'ban.
Murmushi tayi kan ta d'auke idanunta tana mikewa zaune tace "zarah kin dawo?" Zarah
tace "yes sarkin tunani na dawo, meyasa kike son takura kanki da tunani ne? Ko kin
manta duk abinda ya faru da bawa Allah ya riga ya rubuta tun kan a hallice shi? Ki
d'auki matsalanki a matsayin ba komai ba zakiga ya wuce". Iman tace "kayyah zarah
kowa haka yake cemin ze wuce ze wuce amma banga alamu ba".
Zarah tace "chuppp ze wuce in shaa Allahu" zama tayi ta d'iba mata abincin da ta
kawo a plate tare da gyara zama da kyau tace "haa open your mouth" dariya iman ta
saka tana cewa "ke me haka se kace wata baby? Come on bani zan iya ci da kaina"
zarah tace bata san zancen ba ai bata da lafiya se ta bata cokali take ta kokarin
sawa a bakinta yayin da ita kuma take ta kawar da kai tana sa hannu cikin dariya
suke tayi seda zarah taga iman tayi dariya sossai kan ta mikamata chokalin tana
murmushi.
Kar'ba tayi ta fara ci zarah na ta bata labarin ban dariya, yawanci duk   akan 'yan
gidansu da yadda take musu rigima da fad'an ummu In an ta'bo Anty hamna   da fad'an
Abdul da hamna, da yadda suke kawo kara kullum musamman hamna se dariya   iman keyi
musamman yadda zarahn ke yi da fuska duk irin labarin da zatayi se tayi   expiration
d'in so childish.
A haka iman ta cinye abincin plate d'in tas ba tare da ta lura ba, dafa kafad'an
zarah tayi tace "thank yhu zarah, kin ragemin damuwana sossai, In Ina tare dake har
mantawa nake da wani damuwa" zarah tana murmushi tace "you are welcome dear, bari
inzo In tafi yau nayi dare a waje" Iman tace "Eyyah de karki tafi plz ki kwana dani
yau" zarah tace "Da ummu zata yarda da nafi kowa farin ciki amma bata yarda in
kwana a ko Ina".
Har zarah ta mike iman ta tsinci kanta da cewa "Hamna matar Dr. Malabo ce?" Zarah
ta juyo tana 'bata fuska tace "yes matar yaya Abdul ce, and cousin sister d'inmu
baki ga ba yadda take rayuwar aure kaman wata jahila shide yaya Abdul be yi sa'ar
mata ba gashi ummu kwata kwata bata son laifinta kwanaki fah har pills yaya ya
kamata tana sha amma da yayi magana ummu ta goyi bayanta, duk da ta san irin son
haihuwan yaya, auren fa is getting to five years amma taki yarda har yanzu ta
haihu, yucks I hate her".
Iman da ta bud'e baki tana kallon zarah, tayi wani murmushi tace "Kai zarah
tamabaya fa d'aya na miki, ke dama zubaida aka sa miki ba fatima ba" dariya zarah
tayi kan tace "ni na tafi se da safe" iman tace "jira in rakaki mota samun In taka
kafafuna na gaji da zaman wuri d'ayan nan" fita sukayi tare zarah na ci gaba da
mata surutu, iman tace "ai ni ba gane hiran kin nan nake yi ba sbd sunayen da kike
kiran ban sansu ba" zarah tace "duk zaki sansu ne bari gobe zan baki labarinmu
gabad'aya yadda In Ina hira zaki fahimceni".
Har mota iman ta rakata kan ta juyo tayo d'akinta zuciyarta wasai gaskiya zama da
zarah akwai daad'i, ba kad'an ba, tana zama a mota ta fiddo wayanta ta kira
hammanta seda ya kusa tsinkewa kan ya d'aga a daidai lokacin ta tada mota tana
reverse "Assalamu alaikum hamma barka da dare" Yace "wa'alaikissalam yauwa barkanki
dae, me kike yi har yanzu a waje zarah?" Tace "wallahi na d'an tsaya da iman ne
kad'aicin kar ya mata yawa" yace "hakan yayi kyau" Tace "Hamma plz ka samo mana
shawara?" Yace "yes na samu" Tace cikin farin ciki "Alhamdulillah menene gobe in je
mata da albishir na san zatayi farin ciki sossai" seda ya d'an murmusa kan yace
"Abba ya nema min aurenta" waro ido tayi in disbelief tace "dan Allah dae yaya da
gaske kake?" Yace "dama mun saba wasa irin haka dake?".
Wani irin ihu ta sake da seda ya matsar da wayan daga kan kunnenshi se kuma tayi
d'an Shiru yace "menene kuma?" Hawaye ne ya gangaro mata tace "ashe iman da gaske
takeyi yaya? Ashe baza ta ta'ba samun farin ciki me d'aurewa ba? Ashe bazatayi
auren soyayya kaman yadda take buri ba?" Cikin kasa da murya yace "wa ya gaya
miki?" Tace "gashinan yaya zaka aureta ne out of sympathy, na so mata farin ciki a
rayuwa" yace "kina tunanin bazan iya bata farin ciki ba" zarah tace "yaya ba haka
bane amma a sanin da na maka baza ka ta'ba d'aukanta da muhimmanci ba tunda ba
sonta kake ba, and na tabbatar se ta fuskan ci kalubale sossai wurin Anty hamna da
ummu".
Shiru ya mata tace "ya akayi Abba ya yarda ya nema maka aurenta?" Ya d'an yi Shiru
ta gane ya fara gajiya da surutun ne, ta san sbd ita ce ma ya sa ya jima da su Anty
Rahma ne da ya jima da kashe wayanshi "I told him everything single thing about
her, and believe me yanzu inaga Abba yafi sonta akaina da ke ma" murmushi zarah ta
sake har tana had'awa da dariya tace "bade ka fara kishinta ba?" Tsaki yayi, tana
dariya tace "Ohk yaushe zaka dawo Hamma?" Yace "tomorrow evening" Tace "and yaushe
ne baban yasaka auren?" Yace "hey I'm pissed off da surutun kin nan, Friday za'a
d'aura after juma'at prayer, and mind you karki fad'awa kowa maganan auren nan kin
san what ummu is up to In aka zo maganan hamna, har ita karki fad'amata".
Tace "Ohk tohm, yhu know am good at keeping secrets" yace "look who's talking" tana
parking a harabar gidansu tace "yauwa Hamma ka sayomin chocolates dayawa plz" tsaki
yaja kan ya kashe wayan, murmushi kawai tayi ta karasa cikin gida, Alhamdulillah
tayiwa Iman murnan samun miji irin hammanta a zamanin nan samun irinshi se an tona,
haka shima ta mishi murnan samun mace irin iman amma tsoronta d'aya irin zaman da
zasuyi kan su fahimci juna don shi mutum ne me murd'ad'en hali.
Gashi ba sonta yake yi ba bare tace abin ze d'an daidaitu amma ba matsala zata yi
iya kokarinta wurin ganin ta fahimtar da Iman waye Abdul tunda duk duniya zata iya
cewa tafi saninshi akan kowa bayan ummu, tunanin ummu kad'ai ya sa gabanta fad'uwa
what if ummu ta tsani Iman? Yadda ummu ke son hamnan nan ta san definitely bazata
bada goyon baya akan auren nan ba, Allah sarki iman bazan so ki shiga wani tashin
hankalin uwar miji ba kuma amma ya zamuyi?.
Ummu da ta fito daga kitchen tuntuni tana ma zarahn magana bata ma jita ba seda ta
ta'ba ta kan tayi firgigit tace "ummu" ummu tace "tunanin me kikeyi haka da
kankantar shekarun Kin nan?" Shagwa'be fuska tayi kan tace "haba ummu kema kya
tambaya bayan kin san besty na na asibiti?" Girgiza kai kawai ummu tayi ba don ta
yarda ba tace "Toh tashi ki hau kiyi wanka ki huta yau tun safe kike asibiti har
warin asibiti kikeyi" zata fara rigima ummu Tace "chupp bance ki min shagwa'ba ba
ni bazanyi magana da me warin asibiti ba" baki zarah ta turo gaba tana mikewa tace
"ni bana warin asibiti Allah" nufan ummun tayi da iya gaskiyarta take son ta
shunshunata taji ko tanayi, ummu se ta matsa baya tana dariya, hannunta na toshe da
hancinta.
Hafeez da shigowarshi kenan yayi saurin sa hannu a hanci yace "uhm uhm uhm ummu me
kika samu me wari a parlorn nan haka" Da hannu ta nuna mishi zarah tace "gata nan"
a zuciya zarah ta haura sama tana bubbuga kafa su kuma suka sa dariya.
********
Washegari da safe sauban ya sallami iman dayake sunyi waya da Malabo a jiyan yace
ze iya sallamanta In har ta warke ya sauya plan, sauban be tambayeshi komai ba sbd
ya san tunda yace ze fad'a mishi ze fad'a d'inne, Ai ko iman sossai taji daad'in
sallaman da ya mata, ya juya ze fita kenan tace "Dr." yace "yes" Tace "plz ko zaka
iya had'ani da wadda ya biyamin gabad'aya kud'in jinya na In mishi godiya?" Yace
"a'a shi wadda ya Biyan yace ba se na bayyanashi ba don Allah yayi ba don ki gode
mishi ba, in short ko sunanshi be yarda in furta miki ba" juya kai gefe tayi kan
tace "shikenan kayi mishi godiya, Allah ya biya shi da gidan Aljannah" yace "Ameen"
kan ya juya ya fice, ba 'bata lokaci suka had'a 'yan kayyayyakinsu kan su gama ma
zarah ta zo so da motanta suka nufi gida.
Da sallama ta shiga gidan dayake itace a gaba, baba dake zaune akan taburma yana
karyawa be ko amsa sallaman ba yace "jibi zan d'aura miki aure, ban bukatar jin
komai daga bakinki, for ur information ba taron da za'ayi a gidana, sbd kud'ad'en
da na kashe a aurenki na baya sun ishe ni kayan d'akinki de tun na aurenki na farko
shi za'a kaimiki don d'a me tarbiya da biyayyya ne ake yiwa kayan d'aki me ma'ana
da kyau, and Ina so ki sani wallahi na rantse da girman Allah kika kashe aurenki
kika dawo gidan nan ko gidan wani d'an uwa nawa Allah ya isa ban yafe ba kai ko
Ziyara ban yarda ki kawo ba se sadda na nemeki kinji na gayamiki".
Be jira cewarta ba ya shige d'akin umma, kukan ma yau kam kin zuwa mata yayi don
haka se taci gaba da tafiyanta a hankali zarah ce ta dafa kafad'anta tare da
bubbugawa alamun de rarrashi, Mama ma ta dafa d'ayar se kawai ta tsinci kanta da
murmushi ko ba komai mutane biyun nan sun isheta soyayyarsu gareta ma ni'ima ce
Alhamdulillah.
Bayan tayi wanka ta shirya suka karya da zarah da mama shima de abincin zarah ce ta
kawo amma umma bata kawo musu wani abinci wai don sun yi dawowar sassafe ba, kuma a
lokacin ta gama breakfast, don har ikhram da ikhlas sun tafi school, Bayan sun gama
Mama ta mike ta fice zarah ta gyara zama akan gadon Mama tace "are yhu ready?" Iman
tace "ready for what?" Zarah tace "au kin manta nace zan baki labarinmu yau?" Iman
tace "oh oh na tuna am all ears" gyaran murya zarah tayi kan ta fara......
🖤Gureenjo🖤
🥀NOOR IMAN🥀
*020*
Mai Martaba sarkin Adamawa na goma sha hud'u Alhj. Muhammad barkind'o Aliyu
Mustapha (lamid'o) shine wadda ya Haifi Abbanmu 'yan asalin kauyen Malabo ne dake
kasan fufore local government, Adamawa state. tun farkon sarautar Adamawa a hannun
familynsu yake har kawo yanzu, matanshi guda biyu hajiya nenne da Hajiya mama,
nenne itace uwargida kuma itace mahaifiyar Abbanmu 'ya'ya goma Allah ya bata bakwai
maza biyu mata, Uncle Aliyu, Uncle mustapha, Abbanmu, Uncle hamza, Uncle Mukhtar,
Uncle Sadisu se uncle sabi'u, matan kuma Anty Saliha da Anty Murja sune kuma
kanana.
Yayinda hajiya Mama ke da hud'u duk mata Aunty Maimuna, Aunty zulfa'u, Anty fatima
se Anty maryama, akwai kishi me tsanani tsakanin hajiya nenne da hajiya mama dukda
akalar kishin gabad'aya akan hajiya Mama ne da asalin sunanta ya kasance hauwa,
hajiya nenne wadda asalin sunanta saudah macece me tsananin hakuri da kawaici,
sarauta a jininta yake kasancewarta 'yar sarkin gombe yanzu haka yayanta ke mulkan
gombe, shi yasa ta kasance me miskilanci kan ta d'aga kai ta kalli mutum ma aiki ne
a gareta sa'banin hajiya mama da badaga gidan sarauta aka aurota ba.
Dukda yadda lamid'o ya so 'ya'yanshi su zamanto masu had'in kai amma inaa hakan be
faru ba sbd hajiya Mama ta hurewa yaranta kunne basu son 'ya'yan hajiya nenne ko na
miskala zarratin, gaba me tsanani sukeyi dasu, a ta 'baganren nenne yaranta basu
damu da hakan ko kad'an ba kasancewarsu maza kuma ba yara kanana ba har gwara ma
matan.
Lamid'o yana da kani guda d'aya Abdulraheem wadda ya kasance galadiman Adamawa, a
hannun nenne ya karasa girmanshi kasancewar iyayensu da suka rasu tun kan yayi
wayau, yana matukar son nenne da yaranta sbd itama tana mishi so ne na tsakani da
Allah, be yi aure ba seda aka haifi Abbanmu da shekara biyu ya auri 'yar wazeerin
Adamawa Salma aurensu da shekaru biyu ta haifi Ummun mu wacce asalin sunanta
Rashida.
Ganin bayan ummu kaman basu da rabon samun wani d'an yasa suka d'auki son duniya
suka d'aurawa ummu kowa rashida har cikin sashin nenne yaranta sossai suke son ummu
musamman Abba, ba wadda ya isa ta'bata a kafatanin masarautar be rama mata ba har
yayyunshi kuwa, sede In iyaye, hakan yasa Baba galadima da nenne petel wato 'nenne
karama' yi mishi alkawarin bashi ummu In ta isa aure.
seda ummu ta shekara bakwai kan aka haifi Hajiya umma (hafsat) wato mahaifiyar
hamna, so Kin san de son da za'a nuna mata baze kai na ummu ba, ba wai itama ba'a
sonta ba a'a, gashi Allah ya yita da tsananin rashin kunya da iyayi da gadara se
kace lamid'on ne karan kanshi ya haifeta, tunda ta mallaki hankalinta taga Abba
suna soyayya da ummu hankalinta yayi mummunan tashi sbd ita a duniya ba wadda ta
gani tana so se shi sede kash bata ma gama JSS class ba akayi aurensu da ummu.
Yaran me martaba mazan duk ba wadda yake aiki a yola se Uncle Aliyu wadda shine
yarima me jiran gado duk sun watse wasu har a kasashen waje ma suke aiki a cikinsu
akwai barristers, doctors, engineers se Abba da ya kasance business tycoon, matan
kuma d'aya na aure Sokoto gidan sarautar chan d'aya na aure Abuja se yaran hajiya
mama da uku sunyi aure d'aya na gabanta duk cikin yola sukayi aure.
Auren ummu na shekaru hud'u ta samu haihuwar Anty Rahma bayanta da two years aka
haifi Hamma Abdulraheem wadda ya ci sunan baba galadima da   kanshi ya hana a 'boye
mishi suna, se Hamma Muhammad wadda muke kira hafeez, se a   lokacin Hajiya mama tayi
aure da kyar ta auri wani mai rufin asiri ba don ta so ba,   se don Baba galadima ne
ya za'ba mata mijin da kanshi ba don ta so ba de don gidan   sarautanmu ba'a jayayya
da za'bin iyaye yasa ta hakura ta aureshi.
Amma be da sakat a gidanshi se abinda tace sannan za'ayi bata shekara ba ta haifi
kubra wacce suke kira hamna, bayan haihuwa Anty hamna da one year ummu ta haifi
Anty kathum, haihuwar Anty Kalthum da three years aka haifeni, tunda hamna ta tashi
koyaushe tana hanyar kano da sunan hutu ko mahaifinta baya son zuwanta se hajiya
umma ta sata gaba ta kawota ba yadda ya iya, Allah ya d'aura mata son ya Hafeez
sede shi duniya In akwai wacce ya tsana to ya biyo bayanta sbd shegen iyayinta da
nuna isa kaman 'yar wani ga rashin kunya, abinda yasa basa shiri kwata kwata da
Hamma Abdul kenan sbd baya son masu irin halin nan nata.
Dukda ma yana gama secondary ya bar kasan se in yazo ne itama ta zo suke had'uwa a
haka ma kullum fad'a don in har yana wuri tayi abu se ya hantareta cewa yake bani
na iyanta yawa ne dashi, bamu san ya akayi daga baya ta koma son Hamma Abdul ba,
shima ya tashi da son business amma se karatunshi ya banbanta da abinda yake so,
zallar Bsc. biology ya karanta degree d'inshi se ya koma Entomology yayi Masters da
phd d'inshi wato study of insects anan ya ci gaba da musu aiki a matsayin lecturer
dukda ba so yake ba.
Ganin zamanshi a London d'in ya fi yawa ne yasa Abba had'a hannu dashi suka bud'e
kafanin fata wato de suna sarrafa fatun dabbobi, gabad'aya natsuwarshi ya tattara
ya ba companyn yana jin daad'in aiki da turawan sossai sbd basu da wani hali irin
na 'yan nijeria, In ji shi da fad'a. Bayan ha'baka companyn da yayi ne ya ajiye
aiki da university d'inshi ya koma harkar companynshi.
Nan Hajiya umma ta bawa ummu shawarar had'a su aure da hamna don wai zaman mutum a
kasar waje ba mata matsala ne a lokacin kuma tana AUN wadda Abba ne ke biya mata
tana karantar Economics, ummu ne ta tilasta Ya Abdul auren hamna da kyar ya yarda
sbd shi mutum ne me murd'ad'en hali seda Tayi barazanar tsine mishi kan ya yarda
akayi auren amma yaki yarda ta bishi London a nan unguwanmu ya sayi gida ya ajiyeta
ba yadda basuyi ba yaki, sede ya dinga zuwa.
Da hakan tayi anfani da Abba tasa aka tilasta mishi dawowa Nigeria wai ita baza ta
iya ya dinga zuwa yana komawa ba tunda yaki ta bishi, Abba ya bashi za'bin ko ta
bishi ko ya dawo Nigeria da zama se ya za'bi dawowa nigeria inda BUK da kansu suka
nemi yayi aiki da su daga jin labarin ze dawo nigeria suma ki yayi wai bazeyi
lecturing ba musamman a nigeria seda Abba ya sa baki kan ya kar'bi offer d'in, nan
Abba ya bashi Director na steel companinshi dake nan kano wadda ya Hafeez ke
jagoranta kasancewarshi business ya karanta.
Anty Rahma tayi aure da jimawa da yaranta uku suna nan cikin kano da zama a hotoro
se Anty kalthum da bata jima da yin aure ba tana zaune ne a zoo road da d'anta
d'aya, Anty hamna na running business manyan shagunan kayayyakin mata da yara take
dashi a nan BUK road, "To Kinji yadda muke" gyad'a kai iman tayi tace "masha Allah,
Zanso wataran in je Adamawan nan don wallahi Ina son fulani" zarah na dariya tace
"zakije ne har ki gaji da zuwa" ta karasa maganan tana mikewa "uhm bari Inzo In
tafi kafin ummu ta fara kirana don tace ta gaji da yinin da nakeyi waje, yauwa bari
In kirata tace in nazo In kirata ta gaisheki da jiki".
Iman tace "plz karki kirata" zarah tace "au bakya son magana da ummun tamu?" Iman
tace "ba haka bane wallahi wani iri nake ji In zanyi waya da babban mutum bazaki
ga..." sa mata waya zarah tayi a kunne wadda sallaman ummu ya sata yin shiru ba
shiri, tana hararan zarah tace "ummu barka da rana" ummu tace "yauwa Iman ya jiki?"
Tace "da sauki Alhamdulillah, an sallamemu ma" ummu tace "masha Allah, Allah ya
kara sauki yasa kaffara ne" iman tace "Ameen Ameen mun gode" sukayi sallama ta ba
zarah wayan zarah ta sanar da ummu tana nan dawowa yanzu.
Tana kashewa tace "saura Abba" waro ido iman tayi tare da mikewa tayi kan zarah
tana kokarin kwace wayan Ai zarah da gudu ta mike tayi waje yayinda iman ta rufa
mata baya seda suka zagaya parlorn maman sau biyu kan iman ta zube a kan kujera
tana haki hannunta dafe da kai, da sauri zarah ta yo kanta tana cewa "ba kinga ba,
mutum beda gashin wacce yace ze yi kitson wacce da de kina lafiya ne se muyi tayi
har gobe ma ni be dameni b.." bata karasa ba iman ta damke hannunta ta fisge wayan
tare da mikewa da gudu ta fad'a d'akin mama tare da rufe kofa tana sauke numfashi
harda "wayyo wayyo" take had'awa.
Tana kan sauke numfashi tace "zarah wallahi na kamaki zaki gayawa 'yan garinku Haka
kawai kisa mutum gudun da be shirya ba, da fuskanki kaman na dr. Malabo a wurin
masu farin larabawa kawai, wayyo Allahna" tana jin zarah na dariya tana cewa In ba
tsoro ba ki bud'e mana ta shareta tare da kallon wayan, duba fuskan wayar zarahn da
zatayi se taga "Blood💞💞" dubawa ta karayi da kyau se taga ba kira ake ba call ne ke
reading duration d'in ma ya kai 5mins waro ido tayi tana sa hannu a baki tace.
"Ke zarah waye blood kinga mun kira garin shiriritarmu na san se magana yake be ji
komai ba se shirme" zarah tace "credit na kashe kashe da kyar ya Hafeez ya sa min
cati jiya wai Ina shirmen banza dashi" iman tace "ke dallah tambayarki fa nayi waye
blood bazan kashe ba se kin fad'amin, ma bazan kashe ba punishment d'in gudun da
kika sani kenan" zarah tace "Toh wallahi Ya Abdul ne kuma...." kan ta karasa taji
salatin iman ta san zuwa yanzu ta kashe Ai ko de tun bata karasa cewa Abdul ba tayi
hanzarin kashewa tana salati.
"Zarah kin kasheni, Allah ya sa be ji nace da fuskanku iri d'aya ba, da kuma farin
ku kaman na larabawa ba" dariya zarah ta kwace dashi tana cewa "gen gen gen
shikenan yaji, mutum da carry over kuma sun kulla abota gashi 3credit unit, ba
ruwana" cikin muryan kuka iman tace "shikenan na shiga uku" dariya zarah ta ci gaba
da yi tana tsokanarta se da taji da gaske kukan take kan ta lalla'beta ta bud'e
mata kofan ta fara aikin rarrashi don sossai hankalin iman ya tashi.
*******
Murmushi ya dinga sakewa yana girgiza kai wato yaran nan daad'i ne ya musu yawa
harda gujel gujel, wani lalatacciyar dariya ya saki tuna wai da fuskan zarah kaman
nashi a wurin, Da kuma farinsu kaman na larabawa a fili yace "zaki maimaita ne
yarinya" tare da mikewa ya koma d'akin hotel d'inshi dama waje ya fita shan iska se
kuma yaga kiran zarah d'in duk haukan da suka dingayi a kan kunnenshi ko ba komai
yaji daad'in samun lafiyanta, shirin tafiya kano ya fara don jirgin yamma ze bi ya
koma gida.
*******
Da kyar zarah ta lalla'bata tayi shiru, tare da mata sallama akan zata koma gida da
yamma zata je d'auko malabo a airport, se de su had'u gobe In ta dawo daga
lectures, iman tace "gobe akwai Lectures ne?" Zarah tace "Eh akwai na ya Abdul"
iman ta waro ido kan Tace "zanje In shaa Allahu Ina ni da missing class d'inshi"
zarah tace "baki fah warke ba baza ki kara haku..." katseta Iman tayi da cewa "ke
karma ki 'bata nyaun bakinki se naji, samun ma in mishi maganan test d'in da yayi
Allah na, Allah ya sa kar ya ki yimin" suna tafiya zuwa waje suke maganan.
Parlorn umma suka shiga tayiwa mama da umma sallama mama se godiya takeyi kan Iman
ta rakota jikin mota suna d'agawa juna hannu ta wuce.
                       🖤Gureenjo🖤
🥀NOOR IMAN🥀
*021*
Se da ta kwanta bacci tukun tunanin auren da baba yace za'a d'aura mata a jibi ya
dawo mata, ta fara tunanin ko da wani irin miji kuma Allah ze had'ata? Me mutunci
ne ko akasin haka, shi yace yana sonta ko baba ne ya roke shi ya aureta? Har ga
Allah tana tsoro sossai irin sossai d'in nan wadda take so yake sonta ma ya aka
kare bare kuma wadda bata sani ba be santa ba? Hawaye ne ya gangaro mata da sauri
ta goge ta furta a fili "na gaji da kukan nan haka" ta mike ta fad'a toilet tayo
alwala tare da fitowa ta tada sallah.
Ta jima tana nafilfili In tayi sujjada se tafi minti ashirin tana yiwa Allah kirari
tana kai mishi kukanta seda taji ta samu natsuwa kan ta mike ta hau gado ba 'bata
lokaci kuwa bacci ya saceta, ta manta when last tayi bacci cikin kwanciyar hankali
taji baccin ya mata daad'i irin yau da kyar ta tashi sallan asuba ta lalla'ba tayi
kan ta mike mama ce da girki hakan yasata nufan kitchen kai tsaye aiko ta samu har
ta hura icce har kasa ta duka "Ina kwana mama?" Mama tace "Lafiya klau iman ya kika
fito yanzu kije ki kwanta ki huta na san har yanzu jikinki be yi karfi ba".
Murmushi tayi kan tace "Mama na ji sauki fah, school ma zan shiga ina da aji karfe
takwas" Mama tace "a'a wani makaranta kuma iman? Yaushe aka sallamoki daga
asibitin? Baza ki kara hutawa ba" Shagwa'be fuska tayi tace "Mama na warke fah In
ban je ba akwai matsala wallahi gashi yayi test ina asibiti" Mama ta girgiza kai
kan tace "ke kika sani, kije ki zauna In fara sa miki ruwan wanka In yaso kika juye
se in d'aura sanwar" juyawa tayi ta d'auki tsintsiya ta fara share kasar gidan.
Tsab tayi shara mai kyau ta gama kan ma ta gama Mama ta juye mata ruwan a bucket ta
d'auka ta shige toilet bata wani 'bata lokaci ba ta fito ta shirya duk de kayanta
yawanci materials ne atampha In za'a mata se na dubu ko dubu da biyar wato robber
kenan shiyasa gwara ta d'inga material d'inta, cikin wani fari da jan material ta
shirya dayake ta d'an yi rama se rigan ya nemi yi mata yawa.
A haka de ta sanya ta sa red robber himar d'inta ta fito da farin   flat shoe d'inta
da kuma karamin hand made side bag d'inta, sama sama ta sha kunun   da mama tayi bata
ma tsaya jiran d'umame ba ta fice, In tace zata hau keke napep ba   abinda ze hanata
makara hakan yasata hau machine takwas saura minti uku ya sauketa   a kusan hall d'in
da zasuyi lectures d'in.
Waro ido tayi ganin shi a kafa da alamu ya d'an tsaya office kuma a chan ya bar
motan, da hanzari yake tafiya irin de tafiyar maza masu ji da jini a jika Ai bata
san sadda ta fara gudu ba har yayi stepping kafanshi cikin class ya juya da nufin
rufe kofa kenan ya hangota tana gudu se ya dakata tana isowa ya kauce ta shige kan
ya ja kofanshi a bayanta ajiyar zuciya ta sauke tana hakki, se kuma ta d'aga kai
don kallonshi se carab suka had'a ido, ko second idonshi be kai cikin nata ba ya
kawar da kanshi tare da haurawa stage.
Da mamaki ta karasa ta zauna me ke damunshi haka? Ko de ita ne take ganin kaman
'bacin rai shimfid'e a fuskanshi? Kallonshi ta ci gaba da yi as usual black pants
ne jikinshi da Armani shirt baki se wasu shegun timberland suma bakake sanye a
kafanshi gashin nan ya sha gyara har ya gaji se yau taga abinda d'alibai da wasu
lecturers d'in ke kiranshi yayi daidai da yanayin shi da komanshi. a kan lips
d'inta ta furta.
"Youngest biologists" bata hangi zarah ba duk jujjuyawan da tayi kuwa se kawai ta
bud'e littafinta ta fara jotting abinda yakeyi, tabbas ranshi a 'bace yake ranan
Kuma cike yake da damuwa sbd jiya bayan isowanshi hamna ta iso, dukda yayi mamakin
ganinta amma se be nuna ba, sema shareta yayi yaci gaba da harkokinshi dayake da ya
dawo be shiga gida ba yasa bayan isha yayi wankanshi tare da shiryawa ya fito
parlorn sama.
Nan ya ganta tana kallo ba tare da ya kula ta ba ya nufi sauka, wani irin turirin
bakin ciki ne ya taso mata yanzu fah wurin buduruwarshi zashi ko? Ga wani fitinanne
kamshi irin nashi da ya bule parlorn tun kan ya fito haka zashi wurinta? Bata san
sadda ta sha gabanshi ba, se kawai ganin mutum yayi kerere rike da kwankwaso cikin
rashin kunya tace "Ina zaka?".
With so much surprise yace "wow!! Yaushe muka fara wasan haka dake ban sani ba?"
Tace cikin rigima irin nata "Ai haka zaka ce tunda zaka je wajen buduruwarka ba ko
kuma ince karuwarka maci amana kawai Ai na ji labari, baka san an dena kiwon dabba
yanzu se mutum ba?" Girgiza kai yayi dukda zafin karuwarka da ta fad'a na sashi jin
kaman ya d'auke ta mari haka ya danne ya ra'ba ta gefenta ze wuce se yaji ta rike
mai riga tana fad'in.
"Wallahi ba inda zaka je ba wurin wata shegiyar da zaka, 'yar iska 'yar gidan mayu
wallahi ta kuskura ta shigo gidan nan sede gawanta wallahi se na da'ba mata wuka In
kuma da'bawa kaina komai ze faru sede ya faru, munafuka 'yar gidan munafuk...."
Tass ya d'auketa da mari ya kuma kara mata, bata san sadda ta sakeshi ba cikin
kaushin murya yace "nan gidan shine gidan zamanta na har abada do your worst,
wawiya marar hankali kawai".
Ya wuce ya fice abinshi ihu ta kwala kaman wata mahaukaciya tare da nufan d'aki
daga ita se wani banzan crazy jeans da crop top a hakan ta d'auki hula ta sa a
kanta tare da zaran keyn mota ta fice da gudu kaman wata mahaukaciya se yanzu ta
tabbatar auren ze yi da kokonto da maganan boka takeyi.
Direct gidan Abba tayi da kuka da komai ta shiga se kuwa ta ganshi zaune parlorn
kasan da umma da kuma Hafeez, me makon tayi shiru se ta kara karfin ihunta taje
gabanshi ta tsaya "baka isa ba wallahi, baka isa ba azzalumi macuci kawai baka isa
ba Abdulraheem...." ta karashe da matsanancin kuka a zuciye ya mike ya nufi gaban
stand d'in ummu ya fisgo wayoyin wutan dake wurin yayi kanta.
Ihun da ta tsala yasa Abba shigowa da sauri dama yana kusan shigowa cikin parlorn
da sauri ya rike hannun Abdul da ke shirin sauke mata bulalar "subhanallah,
hasbunallahu wani'imal wakeel, Abdulraheem??? Matarka ta sunna?" Tsabar baccin rai
jikinshi har rawa yake yace "Abba na gaji wallahi na gaji da halin kubra wata rana
zan iya karyata In bata kiyayeni ba" Ummu tace cikin mamaki "Lallai Abdulraheem ka
cika, a gabana ka kalli cikin idanuna kace zaka karya 'yar uwarka kuma matar
aurenka? Ke hamna me ya had'aku?" Hamna dake jikin ummu take aikin kuka tace "ummu
aure naji ana ta magana a gari ze yi, Da na tambayeshi shine..... shine ya wankamin
maruka har biyu and he said I should do my worst......" ta karasa da kuka sossai.
Cikin tsananin shock ummu tace "Aure Abdulraheem? Da gaske take?" Shiru Malabo yayi
cikin tsawa tace "Aure? Da izinin uban wa?" Abba yace "enough rashida, Aure ze yi
kuma jibi In Allah ya kaimu ba da izinin kowa ba se na mahaifinshi and In na isa
dake yhu should just sit back and watch, and yhu also" ya karasa maganar da maida
akalarshi kan Hamna.
Abba karan kanshi ze iya cewa be ta'ba ji ta kira sunanshi haka ba se yau danne
mamakinshi yayi yace "Na rantse da ubangiji Abdulraheem se ya auri Saudah duk
duniya ba wadda ya isa hanani se mahaliccina, ko da kuwa shi Abdulraheem ne ko kuma
me martaba, wallahi duk kuwa Abdulraheem be zama mijinta ba ki tabbatar kuma
yaranki su shaida ni ni Ahmad Muhammad Malabo se na zama mijinta, mark my words".
Juyowa yayi kan Abdulraheem yace "and yhu wallahi duk sadda naji ko a labari ka
kara d'aga hannu ka daki matarka se na mugun sa'ba maka senayi mugun 'bata maka
rai, wawayen maza marasa daraja sune masu dukan matansu" se kuma ya sassauta murya
yace "Allah mad'aukakin sarki seda ya gindaya sharudda uku kan ya kai ya duka
dukan ma ba irin wannan ba na san ka sani so plz ka kiyaye" ya juya kan hamna yace
"Kubra" Tace "na'am" yace "Kin san baki fi karfin In Zane ki ba ko? Toh duk sadda
mijinki ya kawo min karan ki se na mugun 'bata miki rai shi ba sa'anki bane ba kuma
ba wadda zaki yiwa rashin kunya bane ba, kar kiji nace kar ya kara dukanki kice
zaki bud'e mishi babin rashin kunya kar ki kuskura a fara jin kanki dani".
Be kara kallon ummu ba ya wuce part d'inshi, Malabo ma juyawa yayi ya fice daga
gidan cikin damuwa, wai me ke shirin faruwa tsakanin iyayenshi? Baze ta'ba zama
silar samun matsalan gidansu ba In har be zama me gyarawa ba, ya fara kokonton
auren Saudah sede In ya tuna halin da take ciki da wadda zata shiga gaba se yaji
baze iya ba, dafashi da yaji anyi ne yasa shi juyawa se yaga hafeez.
Fuskanshi na bayyana damuwar da yake ciki shima cikin tashin hankali yace "Hamma me
ke faruwa?" Ajiyar zuciya Abdul ya sauke kan yace "kira zarah kace ta samemu part
d'inka" juyawa yayi ya wuce part d'inshin shi kuma ya kira zarah a waya seda ta
fito ta iso inda yake kan suka nufi part d'inshi tare, a kishingid'e suka sameshi
kan kujera zama duk sukayi.
Da kyar yace "zarah bashi labarinta" ba 'bata lokaci ta bashi labarin iman kab,
seda yayi hawaye tsabar tausayawa, kallon Abdulraheem yayi yace "Hamma wallahi
jihadi zaka yi In ka auri yarinyar nan, In kuwa kana ganin sbd hamna da ummu ne ka
bari ni zan aureta ko don kwad'ayin ladar ubangiji, zan iya aurenta In ajiyeta a
gidana ita kad'ai har Abada ba tare da na kuntata mata ba, zan zama mata uwa da uba
da ta rasa a baya In har ba son...." "enough" Abdulraheem ya furta cikin sanyinshi
kan ya mike ba tare da ya kara cewa Uffan ba ya fice.
Motanshi ya shige ya fice daga gidan a guje ya jima yana yawo a gari kan ya koma
gida wanka yayi ya shirya cikin kayan baccinshi ya fad'a gado amma bacci yaki zuwa
juyi ya dingayi tunanuka fal dayawa cikin ranshi ya tabbatar zuwa yanzu ummu bazata
ce baze auri iman ba sbd rantsuwar da Abba yayi, ya tabbatar tafi kowa sanin Abba
akan kalmominshi sede ya san shi bata barshi haka ba, kuma bazata ta'ba barinshi
haka ba.
Knocking da akayi kofan office d'inshi ne ya sashi dawowa cikin tunanin shi da
muryarshi dake a sanyaye yace "yes come in" tura kofar tayi ta shigo tare da
sallama kanta kasa nannauyar Ajiyar zuciya ya sauke tare da kafeta da shanyayyun
idanunshi, a take jikinta ya d'auki rawa cikin rawar murya tace "Ina kwana malam?"
Wani kasalalliyar murmushi ya saki da shi kad'ai ya san ma'anarshi yace "Eyyah sede
ba malam a office d'innan" sam ta kasa d'ago kai tace "am uhmm Ina nufin Dr. Ina
kwana?" Yace "Lafiya me ke tafe dake?" Tace "malam amm Dr. na zo ne akan test d'in
da kayi bani da lafiya ne yasa banyi attending ba i even wrote a letter a gave it
to class rep ban san ko ya baka ba".
Tunda ta fara magana idonshi ke lumshe wani irin murya Allah ya ba baiwar nan? Ya
subhanallah, ganin yayi Shiru yasa ta zata ko baze saurareta bane hakan yasata fara
hawaye shikenan course d'inshi ya dawo mata ya gama, duk laifin zarah ne da ta
yarda sun shigo tare da watakila ya yarda ko don sbd ita amma gashinan bata ma san
sheshekarta ya fito ba, da sauri ya bud'e ido tare da kafeta dasu in disbelief ooh
Allah na shiga uku daga magana se kuka? Ya Ayyana a ranshi a fili kuma yace "hey"
ta d'ago ta kalleshi.
Da sauri ya kawar da kai zuciyarshi na bugawa what the hell did just happened, wani
irin abu yaji da be ta'ba ji ba daga kallon crying eyes d'inta, be kara kallonta ba
yace "ki je I will decide when to give a makeup test, but mark you bance zanyin ba
I will decide what will please me" tana share fuska tace "thank yhu sir" ko ba
komai tana saka ran ze yi d'in.
Fita tayi a office d'in ta nufi inda ta bar zarah anan d'in ta tadda ta tana danna
waya duka ta d'aka mata a baya wadda ya sata mikewa tana sosa bayan "me nayi miki"
hararanta tayi tace "Da be yarda ze yi maka up test ba da nayi ta dukanki har gobe
da safe, Haka kawai kika ki rakani seda nayi ta mishi kuka kan ya amince ze yi"
dariya zarah ta fashe dashi har tana dukawa cikin dariya tace "kuka? Akan test?
Hahaha" zuciya iman tayi ta juya ta fara tafiya da sauri zarah ta bita tana "besty!
Besty!! Besty!!!".
*sorry for yesterday but here is a long chappy you should plz manage with it,
lectures ne ya sha min kai dayawa*
🖤Gureenjo🖤
🥀NOOR IMAN🥀
*022*
Tsaye Abba yake yana magana da mijin Anty rahma tambayar izininshi yayi ko ze iya
aikan rahama wani kasa yau? Cikin ladabi mijin ya tabbatar mishi da ko Ina yake so
taje ze turota, godiya Abba ya mishi yana kashe waya yayi kira Airport nan da nan
yasa aka mata arranging tafiya dubai.
Mijinta na kashe waya ya dubeta yace "Rahma Abba yace ki shirya ze aikeki wata
kasa" waro ido tayi tana cewa "wata kasa kuma? Tooh bari In tashi In shirya" yace
"ki shirya su kabeer ma ki kaisu gidan Abban se ki bar su chan" amsawa tayi kan ta
mike ta shige d'aki cike da mamaki Ina Abba kuma ze aiketa? Trolley karama ta
d'auka ta shirya kayanta 'yan daidai a ciki, har ta d'auko wadda zata saka kayan su
halima kuma se ta tuna akwai kayayyakinsu gidan Abban ma.
Gyalenta ta d'auka tare da janyo trolleyn parlor ta barshi nan ta shige d'akin
yaranta kabeer ta gani zaune gaban tv yana playing game halima kuma kwance kan gado
yayinda nanny ke sawa fuad kaya wadda shine bata jima da yayewa ba, tafa hannu tayi
tace "oya a tashi zamu je gidan granny" da ihu suka tashi suna tsalle dama a shirye
suke se ficewa sukayi bayan sunyiwa babansu sallama.
Mikewa rahma tayi ita wallahi tayi murna sossai finally d'an uwanta ze samu kulawa
ya san yayi aure, part d'in Abba tayi tana mamakin me yasa take kiran ubanku ubanku
haka ba abin fad'an ummu bane, watakila Abba ya goyama Abdul baya shiyasa take jin
haushinsu duka, Da wannan tunanin ta karasa parlorn a kasa ta zauna tana gaida Abba
amsawa yayi "jam koid'um ni, na tashe ki kina zaune ko? Amm nayi miki booking
flight zaki je dubai ki had'owa Babana kayan aure and Ina so kiyishi a gobe
gabad'aya ki dawo jibi plz" kanta kasa tace "Toh Abba yaushene zamu wuce d'in?"
Yace "karfe hud'u na yamma".
Tace "Toh Abba" har ta mike yace "ga wannan check d'in In be yi ba se ki min
magana" Tace "Toh Abba" tare da ficewa direct d'akin zarah ta nufa, a corridor ta
gamu da hamna tsaye tana waya da alamu kuma da uwarta take magana ko kallonta
batayi ba haka itama bata kalleta ba bare kuma ta nemi gaisuwa suka gogi juna suka
wuce, girgiza kai tayi tana furta "Alhamdulillah Allah ya nuna mana gobe da rai da
lafiya, Ayyirrirriiii" ta sake gud'a.
Wani irin malolon bakin ciki ne ya tasowa hamna se ta fashe da kuka tana cewa "umma
ba kinji ba gobe ne fah auren ni dan Allah ki zo, gashi 'yan uwanshi se wulakantani
suke" murmushi rahma tayi kan ta fad'a d'akin zarah zaune ta sameta bakin gado tana
chatting da gudu ta taso ta rungumeta "oyoyo Anty rahma yanzu na kori three
musketeers d'inki suka zo suka addabeni, na sauka miki oyoyo ummu ta koroni"
murmushi rahma tayi tace "ke bar surutun nan ki shafamin yanzu In kira kalthum In
shafa mata" zarah ta zauna yayinda Anty rahma ta zauna gefenta.
"Dan Allah Anty rahma karku tsani iman sbd labarinta na tabbatar ba laifinta bane
tana da saukin kai sossai ga sanyin hali, sam bata da hayaniya bare wani hali na
ki, amma kaddararta be zo mata da daad'i ba" Anty rahma tace "ke ni ba surutu na
tambayeki ba" nan Zarah ta bawa Anty rahma labarin iman daga farko har karshe se ga
Anty rahma da kuka wadda hakan yasa zarah ma hawaye sun jima zaune shiru tukun Anty
rahma tace "Allah sarki baiwar Allah, Allah ya kara mata hakuri da juriyar kaddara
irin nata" zarah tace "Ameen" Anty rahma tace "Ai ko zan had'a mata lefen da zai
bawa su ummanta da Babanta da kuma wannan innan mamaki, se na za'ba na darje zan
d'auka mata Abba sede yayi hakuri aljihunshi ba karamin kuka ze yi ba" dariya zarah
tayi kan tace "wai ke zaki had'a lefe?" Tace "kwarai ma kuwa yanzu haka da shirina
na zo karfe hud'u zan d'aga dubai" ihu zarah ta yi cikin murna tace "ni wallahi
Buki ma na so a mata a turawa su Goggo saratun nan haushi, da wannan hamnan" dariya
Anty rahma tayi kan tace "ke kin san abinda za'ayi?" Girgiza kai zarah tayi.
Rahma tace "mu kira nenne mu fad'amata Abdulraheem ze kara aure amma shi da Abba
sunki a mata event sbd hamna, ta sa azo yola ayi" zarah tace "good idea, kan nan mu
bata labarin iman d'in se inga kaman ba haka aka barta ba ko da adu'o'i zata
taimaka mata na san nenne sarai" Anty rahma ce ta fiddo wayanta ta danna mata kira
ringing biyu ta d'auka "Assalamu Alaikum Rahama hande 'be numti be am kenan"(yau an
tuna da ni kenan) dariya Anty rahma tayi kan tace "wa'alaikissalam pul debbo dama
chan kina ranmu ba'a mantawa dake, noi shomri noi saare"('yar tsohuwa, ya gajiya ya
gida?)
Duk shiru sukayi kowa da abinda yake sakawa, chan nenne tace "tooh Allah ya mana
mai kyau, Zan yi magana da mai martaba da shi Ahmad d'in, ba ta yadda za'ayi ayi
bukin nan haka, a d'aura auren ku tattaro duka ku taho zamu shiryamata buki na ji
da fad'a, sannan zan yiwa baba na fufore magana banyi tunanin Haka kawai aka bar
yarinyar nan ba, da izinin me duka kuma wannan shine Aurenta na dindindin karku
damu kunji?" Zarah harda tsalle daad'i tayi tana fata iman ta shirya da ummanta
koman daren dad'ewa kuma ta san yadda baba na fufore ya shahara da malamta da kuma
iya bada ayoyin karya sihiri se inda karfinshi ya kare.
Godiya sossai suka dinga mata kaman sune iman d'in kan sukayi   sallama, Anty rahma
ta kira Anty kalthum ta fesa mata aiko itama taji daad'i sede   bata ji daad'in yadda
ummu ta d'auki maganan har take jin haushin family d'inta ba,   ta kuwa ce yau zata
nemi izini gobe a gidan zata yini a tare ma za'a wuce yola da   ita don ba za'a barta
a baya ba.
Da wuraren d'aya Abdul ya shigo gidan, yaran rahma da ita kanta da zarah ke zaune a
parlorn yaran suna wasa yayin da iyayen ke ta aikin hirar yadda auren ze kasance
Anty rahma na ganinshi ta saki gud'a hannu a kan hanci, murmushi yayi yana girgiza
kai yaran sukayi kanshi da gudu d'aya bayan d'aya ya dinga d'agasu yana saukewa
fu'ad da ya d'aga karshe ne ya rike shi da kyau yana zama gefen Anty rahma.
"Ango Ango ka sha kamshi na Iman bada kanka a sare kaje gida kace ya fad'i,
hoo...." hararinta yayi tare da saurin cewa "dan Allah ki rufamin asiri kar ki kara
min laifi wurin ummu" zarah tace "hamma wai iman Tace zakayi makeup test?"
Hararanta itama yayi kan yace "wai yarinyar nan don kin raina ni shine kika kama
kika kira wachan tsohuwar matar sarkin nan kika fad'amata zanyi aure ko?" Waro ido
tayi tare da d'aga hannu sama tana girgiza kai, se kuma tayi saurin nuna Anty rahma
tana cewa "ba ruwana wallahi Hamma itace" Anty rahma tace "laaaa zarah ni zakiyiwa
sharri? Yaushe mukayi haka dake?".
Zarah zata Musa Anty rahma ta kai mata duka da gudu ta mike tana dariya, murmushi
kawai yayi Anty rahma tace "yauwa Abdul ina kud'in lefe? Yanzu haka shirin tafiya
airport nake zanje dubai had'o maka lefe da izinin Abba kuma ya bani kud'i amma
gaskiya lefen kece raini nake so in had'o sbd 'yan bakin ciki su gani haushi ya
kashesu".
Girgiza kai kawai yayi yana mikewa "Abdul da kai fah nake magana" ko kallonta be
kara yi ba ya haura saman ummu a zaune ya ganta da hamna, hamnan ta d'aura kanta
kan kafan ummun se aikin kuka take, shi fa mamakin kishin hamna yake ita da bata
sauke mishi wani hakki na aure yadda ya kamata don ze kara aure ne ze d'aga mata
hankali? Sannan ga ummu da daga ganinta zaka san tana cikin tsananin damuwa sbd
kawai za'a yiwa hamna kishiya, Abun na bashi mamaki se kace Abba ne ze yi auren?
Sallama ya kuma yi, kan ummun ta d'ago ta kalleshi.
"Me ya kawoka wurina ni da bani da amfani a gareka ban kuma isa In fad'a ka ji ba?"
Zama yayi a kasan kafanta kanshi kasa yace "ummu dan Allah ki dena damun kanki akan
maganan auren nan haka, kin san wannan halin da kike ciki ze iya tada miki hawan
jininki? Ummu ke ma fa kin san karin auren nan be haramta a gareni ba tunda ba wani
abun sa'bawa Allah bane ba, na san kin san yadda rabo yake In ya rantse beside me
hamna take mini a duniya da zan kalla inji daad'i In san nayi aure? Babu kullum ni
kenan banda kwanciyan hankali da natsuwa kaman na kowani mijin aure, ban isa ince
tayi tayi ba, haka ba isa cewa kar tayi ta kiyi ba, bata ta'ba shiga kitchen don yi
min girki ba kullum In ba Ina gidan nan ba Ina restaurant, zan iya sati biyu ban sa
hamna a idona ba tayi tafiyarta wani kasa ba tare da izini na ba, don zanyiwa irin
wannan matar Kishiya shine abin damuwa? Na rantse da Allah yanzu hamna bata raina
ince ma bata ta'ba shiga ba ko da iman bata shigo rayuwata ba Ina da niyyar karin
aure se kuma Allah ya kawota a lokacin da ya dace, duk abinda hamna take so ummu
kina sani dole ko bana so se na mata wannan karon plz and plz ki barni inyi abinda
raina ke so for once a rayuwana, na barki lafiya".
Ya mike ya fice abinshi jikin ummu ba karamin sanyi yayi ba amma wani abu daya
tokare mata kirji ya ki bari tayi la'akari da lamarin Abdul har ta juya magananshi,
hamna da ranta ke 'bace ta d'aga waya ta danna kiran wata kawarta da ta sata tayi
bincike akan iman kuma tayi ta kirata ta fad'a mata d'azun, bayan ta d'aga tace "ke
zuby ga ummu nan Ina so ki mata irin bayanin da kika min, ta san fah irin 'bara
gur'bin da za'a kawo mata cikin zuri'arta".
Nan fah zuby ta yi gyaran murya tare da fara bada labarin iman na karya da gaskiya
wani abin ma ko huka aka d'aurawa iman baza ta iya aikatawa ba, Ai ko ummu ta
d'auka d'an magangnun Abdul da suka fara tasiri tuni sun watse wani irin haushin
Abba da duk yaranta take ji akan wannan irin bakar munafukar da suke shirin kawo
mata cikin zuri'ah tsanan yarinyar take ji tun kan ta ganta.
A zuciye ta mike tayi part d'in Abba dawowanshi daga sallar azahar kenan suna zaune
da Abdul suna tattauna kiran da nenne tayiwa Abban akan zuwa yola ayi buki kuma ya
yarda d'ari bisa d'ari tsarawa sukayi ayi d'aurin auren kawai karfe takwas se su
wuce yolan da wuri, se ganin mutum sukayi bata zauna ba tace "wai ka san irin
yarinyar da ka yarjewa Abdulraheem aurenta? Bazawara ce fah aurenta biyar shine na
shidda kuma.....".
Hannu ya d'aga mata "ba abinda ban sani kanta ba kuma a haka nake so ya aureta,
sannan ku shirya daga ke har kubra da kika hanata komawa gidan mijinta zamu wuce
yola gobe bayan d'aurin aure a chan za'ayi buki" ummu tace "yanzu ka san ita d'in
karuwace? Ka san ta zubar da ciki sunfi biyar? Ka san irin asirin da ta dingayiwa
tsoffin mazajenta tana juyasu son ranta ta rabasu da iyaye..." cikin tsawa Abba
yace "enough Rashida bana son kara jin irin waennan kalmomin akan Iman dukda ban
ta'ba ganinta ba am very sure yarinyace me kamun kai da ilimi ga tsoron Allah tunda
har ta iya tsallake wannan bakar kaddara, so na fad'amaki abinda zakiyi In baza
kiyi ba fine".
Ya maido da kanshi kan Abdul da yake ta kallon ummunshi gaskiya an chanza mishi uwa
ba haka take ba sam, yace "kana ganin events ukun ya wadatar?" Abdul yace "Eh Abba
samun mu dawo da wuri kaga tana school kar a tsayar mata da karatu" kuka ummu ta
saka musu cikin tashin hankali Abdul ya mike yana furta "ya subhanallah, ummu dan
Allah kiyi hakuri kiyi Shiru hawayenki ba alkhairi bane a gareni karkiyi min haka"
ya karasa a karye tace "toh ka za'ba ko umarnin mahaifinka ko nawa? Na rantse da
Allah kana auren yarinyar nan Abdulraheem bazan kara koda kallon inda kake ba har
duniya ta nad'e kuma sena tsine maka albarka, so yanzu se ka za'ba ko ni ko ita?".
*Anjima da dare zaku samu wani In shaa Allahu, Amma fah se na ji ra'ayoyinku*
🖤Gureenjo🖤
🥀NOOR IMAN🥀
*023*
"Ummu" ya furta muryanshi na rawa ta daka mishi tsawa "just choose I said!!"
Wayanta ne ya d'auki kara hakan ya sa ta maida hankali kai Abbu ta gani da sauri ta
d'aga ta d'aura a kan kunnenta se jin muryanshi tayi cikin fushi da fad'a yana cewa
"Abinda kike yiwa mijinki da 'ya'yanki kenan dama Rashida?" Cikin kasa da murya
tace "Abbu ba fa haka bane ba yarinyar da za..." tsawa ya daka mata "shut up!!! Toh
bari kiji da kyau ina me miki rantsuwa da Allah duk kika tilastawa Me suna ya
za'beki a kan matar da yakeso na cire ki daga cikin 'ya'yana sede ki nemi wani
uban, kuma rashin kunyar da kika d'auka kika yafa wadda ba halinki bane ki ci gaba
karki fasa ki bari mijinki ya sake kawo min kararki zanzo har kanon In sa'bamiki a
gaban 'ya'yanki In yi dawowa ta don kin haifi samarin 'ya'ya ba shi ze baki lasisin
'bata tarbiyarki da mai da kanki wata kabila ta daban ba".
Me yasa ba wadda ze fahimceta ne? Me yasa take ji kaman In Abdulraheem ya kara aure
mutuwa kawai zatayi? bata san sadda ta fashe da kuka ba, se jin muryan Nenne petel
tayi tana cewa "Haba rashida ke da kike da tunani da hangen nesa me ze sa kiyi
tunanin hana d'anki kara aure bayan ba haramun bane a addini? Ko aka gayamiki don
yana auren 'yar uwarshi se baze auro wata ba? Ke fa ba yarinya bace meyasa rashida
ba'a ji kanki da mijinki tun kina yarinya ba seda kika girma kika mallaki fiye da
hankalin kai? Kar ki 'bata wayonki na gayamiki wannan ba yi bane, and ki sani kaman
yadda mahaifinki ya fad'a matukar kika yi sanadiyar da yasa yaron nan fasa aurenshi
to ki nemi wasu iyayen ba mu ba". Se ta kashe wayan.
Kuka sossai ummu ke yi wadda yasa Abdul jin hawaye ya cika mishi ido. Yanzu shine
sanadiyar hawayen mahaifiyarshi? Takawa ya farayi a hankali ze je gareta se Abba ya
mishi hannu da ya fita, fita yayi Abba ya tashi yaje kusa da ita ya zauna tare da
sa hannunshi ya kamo nata se kawai ta kwanta jikinshi ta kara fashewa da wani
kukan, bayanta ya dinga shafawa a hankali da alamun rarrashi, Mamakinta sossai Abba
ke yi, me ya samu rashida haka? Ba haka take ba, ta d'auki abinda ba shine ba ta
d'aurawa zuciyarta, tabbas da ze iya da ya hana Abdul aure sbd kwanciyar hankalinta
amma kuma Saudah d'in fah?.
Da kyar ya samu tayi shiru jin ba kukan yasa shi zame jikinshi yace "ki shirya
akwai tafiyarmu yola goben, bayan d'aurin aure amma mu nan flight zamu bi da
amaryar se 'yan uwanta su bi mota" Kai ta gyad'a mishi kan ta mike ta fice.
A inda ya barsu nan ya fito ya samesu zarah na kallonshi ta san ba Lafiya ba don
idonshi ya kad'a sossai fuskanshi yayi ja abinka da farin namiji, goshinshi ya fito
da wani jijiya babba, Anty rahma ta mike tana cewa "Lafiya kuwa Abdul?" Zarah tace
"me ya faru Hamma?" Ko kallonsu be yi ba ya fice daga parlorn, da sauri zarah ta
bishi har ya d'aura hannu akan handle na mota ta d'aura hannun ta akan nashi
kallonta yayi da alamun gargad'i.
Ta dukar da kanta tace "yhu can't drive in this situation, plz let me drive" sake
mata handle d'in yayi ya bud'e baya ya shiga, shiga itama tayi ta danna button d'in
key tare da jan motar gate man ya bud'e mata ta fice, har suka isa gidanshi kanshi
na jikin kujera yana son mahaifiyarshi fiye da zato ko kad'an baya son abinda ze
bakanta mata rai amma gashi yau shi ne yasa iyayenta yi mata fad'a harda barazanar
tsinuwa da girmanta.
"Idan ummu ne kayi hakuri Hamma ka kara mata lokaci tabbas Ina matukar zargi da
kokonto kaman ba haka kawai ummu ke abinda takeyin nan ba, duk don da takeyiwa
hamna ta san daidai ta san akasinshi, kar pressure d'inta ya sa ka fara dana sanin
aikata aikin ladan da kayi niyya, haka karka manta komai rubutacce ne ko kana so ko
baka so, ko ummu na so ko bata so kai ko duk duniya suka taru suka ce basa so In
har Allah ya riga ya rubuta ba yadda aka iya, so dan Allah karka tsani kawata" ta
bud'e motan ta fita d'ankwalin kanta ta warware tayi gyale har ta fara tafiya ya
fito yace "Auta" ta juyo ya nuna mata motan alamun ta d'auka tare da kakaro
murmushi ya sakarmata be kara kallon inda take ba ya shige gidan.
Dawowa motar tayi ta shiga tare da ja ta fice, Bata ma shiga gida ba Anty rahma ta
fito da akwatinta ta shiga motar tare da cewa "kaini Airport kawai zarah" jan motar
kuma ta sake suka fice Shiru duk sukayi chan de Anty rahma ta fara bawa zarah
labarin abinda ya faru kaman yadda Abba ya sanar mata, zarah tace "da be kirasu ba
ai yanzu ya karawa ummu tsanar iman" Anty rahma tace "ke wai meyasa damuwanki iman
ne kawai bakya tunanin akwai abinda ya faru da ummu? Haka take?" Shiru zarah tayi
yanzu Anty rahma ranta 'bace yake In tace zata ci gaba da magana ba karamin aikinta
bane ta maketa, har suka isa Airport ba wadda ya sake magana, seda taga tashinta
kan ta juyo kan motan ta nufi hanyar gida se kuma ga kiran Nenne.
'Dagawa tayi da sallama "wa'alaikissalam Fatima zan turo miki isassun kud'i yanzu
Ina so ki samu best designer da take da ajiyayyun gowns da za'a iya sayawa Saudah
se kije ki d'auketa ku za'bo size d'inta. And plz look for a presentable gown, ba
na shirme ba kinga abin ya zo urgent ba wani d'inki za'a jira ayi ba" zarah tace
"Toh nenne amma fah ita iman bata san waye mijin ba bakya tunanin hakan ze sa ta
cikin damuwa In ta sani tun yau?" Nenne tace "ko me zatayi ai ba za'a fasa auren ba
so do as I say."Zara tace "yes ma'am" nenne ta kashe wayan, searching contacts
d'inta tayi ta lalu'bo numbern Maymz kawar Anty kalthum ce so suna da contact d'in
juna.
Bayan ta d'aga sun gaisa tace "Ermm Anty Muna da Amarya ne kuma a gobe zamu wuce
yola so muna son wasu sets d'in wedding gowns daga gareki Allah ya sa za'a samu?"
Tace "Eh I think za'a samu zuwa de gobe karfe bakwai kaman guda nawa and colors da
size?" Zarah tace "kaman biyar I think yanzu haka ina hanyar gidansu amaryan ne
zamu zo wurinki yanzu se a d'auki measurement d'inta" Tace "Ohk se kunzo and ki
tambayi events d'in sbd mu san yanayin gown d'in da za'a bata" zarah tace "Ohk se
mun zo" suka datse wayan, nenne ta kuma kira "hello nenne nace events d'in me da me
dame za'ayi?" Nenne tace "na sa a fara de shirin walima gobe da yamma In kun zo se
dare ayi dinner washegari da safe se ayi sukuwa bayan nan se su tare a part d'inshi
na nan in yaso daga baya ya tsara yadda zasu koma".
Sallama sukayi ta kira Anty kalthum "Anty if possible plz mu had'u malabis zamu
za'bawa iman dresses d'inta na events" Anty kalthum tace "Ohk toh ganinan zuwa"
suna kashe wayan zarah na parking kofar gidansu iman, da sallama ta shiga ta samu
mama ma bata nan se umma suka gaisa bata tambayeta iman ba kawai ta shige d'akin
Mama nan ta sameta kwance akan gado ta takure kan gado wai gobe ake aurenta amma ba
kowa gidan nasu kaman gidan mutuwa.
Tun d'azu Mama ta fice ta gayamusu angon ya turo a fad'awa baba cewar gobe da asuba
kan a d'aura aure a had'a 'yan uwan amarya da zasu d'auki people choice biyu nauyin
kud'in mota da abinda zasu ci duk yana kanshi kar su samu damuwa duk wadda zashi
kawai ya shirya, dukda baba yayi mamaki da aka ce people choice biyu kuma Adamawa
bayan uban yace basu da kud'i talakawa ne amma se ya share duk abinda za'ayi ayi
ruwansu ya ayyana a ranshi damuwanshi kawai a d'aura auren.
"Iman lafiya kike?" Iman tace "wallahi zarah kaina ke bala'in ciwo na rasa inda zan
sa kaina zarah zanyi aure ban san miji ba ban san 'yan uwanshi ba, 'yan uwana ba
wanda ya damu se ma matsuwa da sukayi da ayi aure a tafi dani su huta, zarah Angon
fah cewa baba yayi baya bukatar ko tsinke a kai mishi me makon baba ya Musa ko yaji
ba daad'i se daad'i ya dinga ji yana ambatun kud'inshi ya huta, zarah abinda za'aci
In an zo bukin ma kin saya yayi wai be gayyaci kowa ba amma da angon ya turo
buhuhunan abinci se gashi da kanshi yake gayyatan 'yan uwanshi" tana maganan ne
tana kuka duk In ka ganta zaka san a firgice take.
Rungumeta zarah tayi tana dinga shafa bayanta "is Ohk besty, is okay komai me
wucewa ne kuma Ina miki albishir da kiyi farin ciki mijinki irin mijin da kan a
sameshi se an taki sa'a ne, zan iya cewa duk cikin 'yan uwanki ba wacce ta auri
irin mijin da zaki aura, ki dena damun kanki Ina tare dake haka kuma na san mijin
da zaki aura baze ta'ba bari ki zubda hawaye ba" Da sauri iman ta d'ago "kin san
shi zarah?" Zarah ta gyad'a kai "waye ne shi? Plz gayamin?" Zarah tace "Abdulraheem
Ahmad malabo" wani irin hantsulowa Iman tayi idonta kaman zasu fad'o tace "Fatima
dan Allah ki gayamin In da gaske kike?".
Zarah tayi murmushi tace "wallahi da gaske nake yayana zaki aura, so damuwa ya kare
yanzu kin san mijinki ba wani me mummunan hali bane and plz ki barshi a ranki karki
gayawa kowa kar ki nuna kin san mijin don ban yarda da 'yan uwanki ba sorry to say
kema kin sanni abinda na san shine gaskiya ta nake gayamiki" iman de har yanzu
shock d'in be sake ta ba, zarah ce ta lalu'bo mata hijab ta sanya saman doguwar
rigar material d'in jikinta ta janyo hannunta ta cewa umma "umma mun fita" umma de
bata amsa ba se idon da ta bi su dashi.
A mota ta sanyata itade ta shiga, tana shiga kuwa seda ta san motan na waye don
kamshinshi ba boyayye bane sam, ita Allah ya gani bata san me zatayi ba, bakin ciki
ko farin ciki? Gatanan de kaman mutum mutumi zuciyarta sam ba tunanin komai har
suka isa malabis bud'e baki kawai tayi tana kallon wurin da irin designers gowns da
suke wurin kaman ba mutum ke d'inkawa ba.
Sun samu Anty kalthum ma ta rigasu isa iman na ganinta ta gane 'yar uwarsu zarah ce
sede bata san ko rahama bace ko kalthum seda taji zarah tace "Ina yini Anty
kalthum" kanta na kasa itama ta gaidata murmushi Anty kalthum tayi kan tace "masha
Allah Amaryarmu ta had'u" zarah tace "Ai kuwa fari kawai Anty hamna Zata nuna mata"
wayan zarah ne ya fara kara ta d'auko ta kalli fuskan ta kalli su Anty kalthum tace
"Ango fah ke kira" kan ta d'aga "salamu alaikum hamma" yace "kina Ina ne?"
Ta mishi bayanin inda take da abinda sukeyi se taji yace "nima abinda yasa na
kiraki kenan, ba wa maymz d'in wayan" mika mata tayi suka gaisa kan yace "ermm plz
ki had'a mata da wrappers d'in da zata sa a gida ba wedding gowns d'in Kawai ba,
and bana son anything zani yeah, ehmm something like skirt and gowns and bana son
atamphopi masu saukin kud'i".
Cikin ladabi ta amsa mishi ya kara da "just send me the bill through this number"
ta kuma amsawa kan ta dinga godiya suka tsinke wayan da yake a handsfree yake su
Zarah sun ji komai kallon juna sukayi da Anty kalthum suka sake shewa zahra tace
"amm bana son anything zani yeah, something like skirt and gown" tayi maganan da
yanayin accent d'inshi suka kwashe da dariya yayinda Iman taji kaman ta nitse cikin
kasa.
🖤Gureenjo🖤
🥀NOOR IMAN🥀
*this is dedicated ta ANNUR HAUSA NOVELS a gaskiya Ina   matukar jin daad'in comments
d'inku irin sossai d'in nan ga wannan page d'in kyauta   ne kuyi yadda kuke so dashi
naku ne, Allah ya bar zumunci and 🚎🚎🚎🚎🚎 ga motocin fah   da zasuyi yola an kawo inji
Abdulraheem duk wadda ya shirya yazo da jakar kayanshi   kar ayi babu shi😅😅*
🛩🛩wannan kuma yace na 'yan MU KARU DA JUNA Ne yana son ganin khadija Queen a gaban
jirgi da kawata ta jikin window🤣🤣
*024*
Nan fah suka za'bi matching colors duk abinda suka san zasu bukata basu manta ba
sukayi list ta had'a kud'in gabad'aya ta turawa Abdul ba'ayi minti biyar ba alert
ya shigo mata, ta kirashi tayi ta godiya ta tabbatar kuma bazata bashi kunya ba In
shaa Allahu duk kayan da zata had'awa iman se ya so su, Anty kalthum ne tace "Toh
zarah kud'in da nenne ta turo d'in nan bakya tunanin mu saya mata jewelries da
shoes and pose da su? Tunda kinga dae Anty rahma se jibi zata dawo bare ace a jira
na lefe".
Zarah tace "hakane Anty akwai wani jewelry store nan kusa da nan shagon muje wurin
suna da d'an kunne masu kyau da tsada dukda ba gold bane amma basa fading" mikewa
sukayi iman de bata iya ko d'aga kai, har kasa maymz ta rakasu suka wuce, Da kafa
suka taka suka fad'a shagon zarah da Anty kalthum de se hirar bukin sukeyi suna jin
haushin ya akayi yazo a kurarren lokaci Ai da ba Haka
Ba, zarah tace "donma fatan Besty fresh ne be da wani ta'bo ko kuraje da Ai an samu
matsala Amarya ba gyaran jiki" Anty kalthum tace "Ai kuwa, kuma na tabbatar se
nenne ta sa an mata na kwanaki biyun nan da zatayi a part d'inta kuma na san zatayi
kyau".
Juyawa tayi ta kalli iman tace "kinga bestyn Auta kuma matar yaya ki dena jin
kunyana plz ki sake muyi hira" murmushi kawai iman tayi zarah tace "hmm Ai kan ta
sake dake se kina da fitina da irin surutu nawa" Anty kalthum tace "kenan nima
surutun zan d'inga mata har ta sake don bana son wannan kunyan, kuma In gayamiki
gaskiya? Toh ya Abdul be son wannan kunyan yafi son rayuwan turawa In gayamiki"
wani irin kunya ne ya kara rufe iman.
Da wannan hirar suka shige jewelries stores d'in suka za'bi d'an kunnaye da sarkoki
masu abin hannu harda masu sarkar kafa golden da silver masu tsada da kyau, itade
iman kud'in abubuwan kawai takeji tana mamaki musamman kayayyakin wai itace da sa
atampha na fiye da dubu arba'in hamsin? Lallai duniya kenan baba da be ta'ba
sayamata atamphar dubu biyar ba sbd wai asarar kud'inshi zeyi, to yau gashi mijin
da ze aureta ya kashe mata kusan million a lokaci d'aya kuma kayan da basu fi kala
goma sha biyar ba.
Tana nan tana ta aikin tunanin rayuwarta yadda ya zama kaman wani kwallo har suka
karasa wurin takalma nan ma su zahra suka za'bi matching colors da gowns d'inta
kuma hills itade kallonsu kawai takeyi ba wai don zata iya sakawa ba, Anty kalthum
tace "wai zarah lalle da wanke kai da kuma kitso fah? Se yaushe za'ayi?" Zarah tace
"kin san nenne ce ta shirya komai watakila In mun isa I think flight d'in 10 ma
zamu bi" Anty kalthum tace "nice kad'ai kenan banyi booking ba na san ku Abba ya
muku, bari kiga inyi ta wayana tunda baban fadeel ya yarda inje".
"Wai Ina yake ne ma? Shi da ba'a yaye ba bade har kin fara barinshi gida ba" Tace
"ke to bazan iya ba isana yawo dashi yake yi wallahi" ta waya ta musu transfer d'in
kud'insu suka fito suka dawo harabar malabis sukayi sallama, Anty kalthum ta shiga
motanta zarah da iman suka shige na Malabo suka wuce.
Da mamaki iman ke bin gidansu ganin yadda ya cika pim da 'yan buki ko kuma tace
'yan gulma daga yamma zuwa yanzu ne gidan nan ya cika haka? Har fa da 'yan wudil
duk sun zozzo, Ana ganinta aka fara shewar ga Amarya ga Amarya, ko murmushi ta
kasayi haka ta bisu ta dinga gaishesu d'aya bayan d'aya wasu na amsawa tsakani da
Allah wasu kuma suna yi suna ya'ba mata bakar magana.
Zarah de sama sama ta gaida su tana kallon 'yan matan dangin yadda suke hararan
Iman kaman ta ci musu wani abu, itama hararsu tayi sunje wucewa kusa dasu taji wata
Tace "watakila ma wani me ruwa d'an cin rani baba hafeezu ya had'ata da shi" d'ayar
tace "ke me ruwa Ai kin kai da nisa kila de me kwasan kashi" suka kwashe da dariya
d'ayar tace "ke salma baki da kyau ko kinyi wanka wallahi" d'ayar Tace "Ai gaskiya
ta fad'a In ba hakan ba wa ze kwasa irin ta" har Zarah ta taka zuwa gabansu da
niyyan gaya musu magana Iman tayi saurin rike hannunta ta ja ta gaba, haushi seda
ya kawo zarah wuya a gidan nan sbd maganganun 'batanci da akeyi kan Iman.
Daga karshe ma sallama ta mata tace zata dawo gobe da sassafe ana idar da sallar
asuba, da haka sukayi sallama Iman na mata godiya tayi saurin cewa "No thank yhu In
friendship so bana so in sake ji, bye bye take care" har ta kai kofa ta juyo tace
"besty" iman ta d'ago, tace "wallahi kina da hakuri inaga kan a gama bukin nan se
na gurje bakin wata" ta juya ta fice murmushi iman tayi tana girgiza kai.
Seda ta kai hakarkarinta gado kan ta fara tunanin Abdulraheem, wallahi mamakin da
tayi baze iya fad'uwa ba wani irin ikon Allah ne wannan? Anya bata kai kanta da
nisa ba? Ina ita Ina Abdulraheem ga mata kyawawa masu class a duniya? Gaskiya tana
bukatar karin bayani ta ya akayi abu ya kasance a haka? Kanta gabad'aya ya d'aure
ba irin tunanin da batayi ba, ta tuna ko kallonta me kyau bayayi tana ga ko
kammanninta be sani ba, watakila baba ne yaje ya dinga rokonshi ya aureta, kai baze
yiwu ba, watakila kuma Zarah ce ta rokeshi don ta tausaya mata.
Da sauri ta mike zaune har ta d'auko wayanta don kiran zarah taji don In har
hakane baza ta iya aurenshi ba da alfarmar kanwarshi kaman ta shiga hakkinshi ne ta
d'aurawa zarah damuwar da ba nata ba, In ta tuna daidai kuma a labarin da Zarah ta
bata Ummu na matukar son hamna bata son abinda ze 'bata mata rai kenan ummu is
against auren su, kenan Abdulraheem ze aureta ba da yardar mahaifiyarshi ba? Baza
ta samu soyayyar uwar miji ba, bazata samu soyayyar miji ba abin ya mata yawa ita
kenan haka rayuwanta ze kare? Duk auren da zatayi ba jin daad'i, kuka ta fashe
dashi tana kifa wayanta kan katifar da take, cikin sanyi take kukan yadda ba wadda
ze iya jinta, sossai tayi kuka kaman ranta ze fita kan ta mike ta fad'a toilet tayo
alwala tazo ta fara nafilfili tana rokon Allah alkhairin auren, In ba alkhairi bane
Allah ya wargaza maganan tun kan a d'aura.
*******
Tun bayan sallahn Asuba ba wadda ya koma bacci gidan se wanka ake yi wasu kam ma
tun kan asuban yayi sun yi wanka, dayake abin aure kan kace kobo an had'u an had'a
breakfast na kunun gyad'a da kosai wadda duk cikin aljihun Abba, tun kan su gama
motocin sun zo, baba da kanshi yake za'ban waenda zasu tafi yake kuma shirya
arrangement d'in zaman, Inna de ta riga kowa shiga se su goggo saratu da sauran
'yan uwa, lokaci kad'an suka cike people choice biyun nan pim ba 'bata lokaci suka
tashi.
Se a lokacin zarah ta iso sanye da normal riga ready made da gyalenshi kanta,
hannunta rike da karamin jaka wadda komai na amarya da Zata saka yau yana ciki don
seda ta biya gidan maymz ta kar'bo, Mutane kad'an ta samu a gidan daga umma se wasu
'yan uwan da basu tafi ba, da suma yau zasu watse, d'akin Mama ta shige nan ta samu
Iman zaune bakin gado tana kallon wuri d'aya alamun tunani takeyi.
Har yanzu jikinta be dawo ba wallahi sam kana ganinta ka san damuwa dayawa na
tattare da ita, dafa kafad'anta zarah tayi tace "wai tunanin me kike ne besty bayan
kin san mijin da zaki aura se me kuma?" Iman tace "me yasa bazanyi tunani ba zarah
duk aurarrakina daga wahala se wadda ya sakeni a daren farko na se kuma wadda ya
mutu a wurin d'aurin aure, zarah bakya tsoron wani abu ya sameshi daga taimako?"
Hawaye ne ya fara zuba a idonta, Cikin kuka tace "zarah dr Abdulraheem yana da
kirki rasa shi na tabbatar ba karamin razanarwa ne ba ga family d'inku, bana so
wallahi na fasa auren In har shi zan aura, I can't bazan iya ba, za.....rah bana
son komai ya sa...me..shi ta sanadina" ta karashe cikin kuka.
Zarah tace "wa ya gayamiki shi Abdulraheem kaman sauran mazajen da kika aura ne? In
shaa Allahu yayi musu fintinkau ba abinda ze sameshi se Alkhairi" girgiza kai tayi
cikin rashin yarda da maganan zarah ba wai tana ja da ikon Allah ba a'a sam ko
d'aya kawai tana tsoron abinda ze je ya zo ne, waya zarah ta d'auka ta danna mishi
kira yana cikin shiryawa yaga call d'in zarah.
'Dagawa yayi tare da sallama, amsawa tayi kan ta d'aura da "Hamma ga Iman tun d'azu
take ta kuka wai a ce maka ta fasa bazata iya auranka ba sbd tana tsoron kar ka
mutu kaman yadda hamza yazo da niyyan taimakonta ya mutu" d'an Shiru yayi kan ya
zauna yana furta "bata wayan" mika mata tayi se ta ki kar'ba, zama tayi a gefenta
tare da sa mata wayan a kunnenta, sheshekar kukanta ne ya sashi gane tana kan
layin.
Lumshe ido yayi ya kuma bud'e a lokaci d'aya cikin husky voice d'inshi yace
"Saudah!!" Kuka ta fashe dashi sossai kukan da ya bayyana damuwa da tashin hankalin
da take ciki, ga fargaba da ya kara mata daga jin muryanshi "God" ya furta a kasan
makokoronshi, se kuma ya bud'e murya yace "Ki dena kukan nan haka ki tashi ki
shirya, kuma ki kwantar da hankali nothing will happen to me there are many
differences tsananina da sauran waenda suka aureki so plz relax, Ohk?" Kai ta
gyad'a tana share hawayenta, cikin sanyi murya tace "promise me yhu will not die,
please..." yace "you have my words, I repeat nothing will happen to me, and yhu
should also promise me you will never shed tears again" tace "bazan yi ba" se ya
d'an yi Shiru kan kuma ya tsinke wayan.
Mukawa zarah wayan tayi kan ta mike ta fad'a wanka cikin kankanin lokaci tayi ta
fito zarah ta shiryata tsab Allah ya sa ta iya make up sossai da d'auri ta
chanchara mata make up bayan ta d'auko kit d'inta daga mota, ta kafa mata d'auri me
d'aukan hankali se ga Iman ta chanza kammanni.
*****
A harabar gidansu ya Parker motar tare da bud'ewa ya fito Hafeez da Abba ya gani
tsaye alamun suma shirin tafiya auren suke, Abba na ganinshi yace "dama na sani ai,
Hafeez ka ga?" Hafeez yayi murmushi dama seda Abba yace yauma bakaken kayan ze saka
kaman shed'an Ai ko su d'inne jikinshi getzner baka me kyalli, bakar hula da bakar
cover shoe gaban babban rigan ya sha zubi da zare baki me d'aukar hankali.
Hannunshi Abba ya kama zuwa parlornshi wani farin kashmiya me layi layi tsirara
baki da ya sha guga akan kujeranshi riga 'yar ciki da babbar riga ya d'auka ya mika
mishi, kallon kayan Yayi kaman ze Musa se kuma ya sa hannu ya kar'ba zubin da baki
da farin zare akayi har ya fi na asalin kayan da ya saka kyau, da mamaki Abba ke
kallonshi yadda ya kar'ba ba musu a aurenshi da hamna ba yadda ba'a yi da shi ba
yasa wasu color d'in kayan yaki fir haka aka kyaleshi, se gashi yau ya kar'ba.
'Dakin Abba ya shiga ya chanza se ya bar bakar agogon fatan dake hannunshi wadda na
company d'inshi ne, haka takalmi cover d'inshi ya bari shima na company d'inshi ne
da akayi da zallar bakar fata, se hulan zanna da ke kanshi shima fari ne yaji guga
ya zauna d'as ya fito a asalin angonshi yayi kyau har ya gaji farinshi se sheki
yake, turarukan Abba ya feffeshe kan ya fito hannunshi Abba ya kama sukayi waje.
Mota d'aya suka shiga su uku motar Abdul d'in bakar benz d'inshi latest one d'in,
ba 'bata lokaci suka isa Al-Furqan mosque dayake anan za'a d'aura auren sun kuwa
samu an cika pim mutane ko ta Ina dayake Abba ba karamin gayyata yayi ba tun daga
randa yaje wurin baba, baba yace ya bashi ya buga kati a washegarin ya aikawa duk
wani wadda suke huld'a a kanon nan manyan mutane har sarki se gashi ya zo, har
governor ya gayyata but be samu zuwa ba se ya tura deputy d'inshi.
Baba da su Bappanun iman are very very speechless sun rasa ya abun yake gashi baba
ya ce musu yayi bincike yaron de bashi da karfi sossai amma se gasu ga sarki ga
kuma mataimakin gomna baba har hawaye yayi, be ta'ba mafarkin ze yi Musabaha da
sarki ba se gashi ta dalilin Iman yayi, ba 'bata lokaci aka d'aura auren Dr.
Abdulraheem Ahmad Malabo da Amaryarshi Saudatu hafeez Muhammad akan sadaki naira
dubu d'ari biyar.
Kusan suma baba yayi, duk cikin zuri'arsu babu wacce ta kar'bi sadaki kwatan wannan
se Iman, kallo kawai yake bin mutane dashi kaman mutum mutumi, be zaci haka ba sam,
hafeez ne ya fiddo wayanshi ya turawa zarah sakon an d'aura.
*****
Wani irin gud'a ta sake wadda yayi sanadiyar zuban hawayen iman shikenan rayuwanta
kuma se abinda Allah yayi, Mikar da ita zarah tayi suka fito daga d'akin Mama tana
kallon wata 'yar uwar babansu da tazo daga wudil, ta bud'e baki galala tana kallon
Iman dukda kwalliyanta ya ragu sbd rashin lalle amma tayi kyau har ta gaji komai na
jikinta fari ne In ka cire head, pose, jewelries da shoe da suka kasance silver.
Yaddiko cikin rawar murya tace "Aishatu! Aishatu!! Kuzo kigani" fitowa sukayi
gabad'aya se sukayi turus suna kallon Iman, d'ayar tace "oh duniya yanzu Iman Don
kinyi kawa me kud'i se ki roketa ta yi miki d'inkin da zaki sa a aurenki? Wani irin
ta'bewa ne wannan?" Zarah tayi charab tace "Ina wadda kuka mata? Kunyi ne kunga
bata sa ba? Toh ma bari kuji ba ni na mata ba mijinta da yake 'wa' na uwarmu d'aya
ubanmu d'aya shi ya sayamata da kud'in guminshi" duk waro ido sukayi suna kallon
kud'in da aka kashe a jikinta.
Hotuna Zarah ta fara mata se ga baba ya shigo babbar riga a hannu yana zare idanu
ya kalli Iman yace "ke wa kika kawomin ya aureki?" Da mamaki tace "baba ba kai ka
za'bamin shi ba nima ban sanshi ba" innalillahi wainna ilaihi rajiun ya furta
"karde d'an yankan kaine ya yanke min kan 'yan uwa gabad'aya, harda innata" umma
tace "me ya faru ne?" Yace "dubu d'ari biyar fah ya biya sadaki" duk salati suka
sake.
Zasuyi magana suka ji sallama Anty kalthum ce ta shigo ta kalli zarah ta kalli
mutanen da sukayi cirko cirko se ta d'an duk'a tace "am Abba yace kuyi hakuri en
uwanmu duk suna nesa ba wadda ya samu zuwa d'aurin aure sbd abun yazo a kurarren
lokaci, ni sunana kalthum kanwar ango nazo d'aukan amarya ne sbd jirgin goma zamu
bi zuwa yola" "jirgi fah, jirgi kika ce d'iyarnan?" Wata cikin tsoffin ta fad'a
zarah tace "kwarai kuwa" tare da janyo hannun Iman zuwa gaban umma da baba ta saka
musu hannayenta ciki nasu kan tace.
*in kun jini gobe toh, In baki jini ba kuyi hakuri ga long page*
🖤Gureenjo🖤
🥀NOOR IMAN🥀
*025*
“Umma, baba kun san ko Iman na da laifi a mutuwar aurarrakinta kun fita laifi da
zunubi? Umma aure fah aka ce ba wai zaman kwana biyu ba, baba ko min ‘batawar Noor
gareku be kamata ku ki ta haka ba, umma, baba idan har kuna son wannan auren na
Noor ya zama na karshe kuma ya zamana gidanta na har Abada ku taimaka ku dubi
girman Allah kusa mata albarka ko da sau d’aya ne, rashin sa albarkanku kaman shine
yake zama jagoran ‘bata mata sauran aurarrakinta.
Umma ko da Iman ba ‘yar ki bace ‘yar kishiyarki ce zaki iya bud’e baki kice Allah
ya sanya alheri bare kuma noor dake ‘yar cikinki” kasa ta duka Noor ma tayi yadda
tayi hawaye na aikin kwaranya daga cikin idanunta, baba da jikinshi yayi sanyi ya
kurawa Zarah ido yana kallo, umma kam baza ka gane yanayin da take ciki ba, cikin
damuwa zarah tace “Don darajar manzon Allah umma da baba ko da wannan shi ze zama
magananku na karshe da Noor ku sanya mata albarka kuyi mata fatan Alkhairi a zaman
gidan Aurenta” baba ne ya fara bud’e baki yace “Allah ya sanya alkhairi ya bada
zaman lafiya” se ya juya ya fice, umma zarah ta kurawa pleasing eyes d’inta tana
kallo, kaman bazatayi magana ba har ta juya zata shige d’aki se sukaji tace “Allah
yayi albarka” tayi shigewarta ba tare da ta juyo ba, rungume zarah iman tayi tana
kuka sossai.
Da wani irin baki zatayiwa Zarah godiya? Yau zarah tayi sanadiyar samun albarkar
ummanta a gabad’aya rayuwanta abinda ta jima sossai tana murd’in samu, ‘yan sauran
en uwan da suka saura ne d’aya daga ciki ta duka ta d’agota sukayi waje sauran suka
rufa mata baya, zarah ma ta mike Anty kalthum ta rike mata hannu tare da bubbuga
kafad’anta da d’ayan hannun cikin kasa da murya tace “proud of you lil” murmushi
kawai zarah tayi suka fito.
A motar Abba da Anty kalthum ta taho a ciki aka sakata a baya dayake driver ne ya
kawo ta yana zaune a mazauninshi, zagayawa Anty kalthum tayi ta shiga, zarah taje
ta shiga nata motar suka ja suka fice, direct GRA sukayi a harabar gidan driver
yayi parking Anty kalthum ta taimaka mata ta fito kanta kasa suka shige ciki, a
parlorn ummu suka dakata.
Zarah ta kalli kalthum, kalthum ta kalleta basu san ya zasuyi ba, sam be dace ta
shigo gidan bata je ta gaida ummu ba sede kawai su had’u a jirgi gashi suna tsoron
su kaita ummu tayi mata wulakanci, kalthum ce ta yanke shurun da “Iman muje ki
gaida Ummu ko” Kai ta gyad’a kan ta d’aga kafa ta fara tafiya gabanta na tsananta
fad’uwa, da sallama suka haura parlorn saman, zaune suka hangi ummu ta ci ado na
fitar hankali ba wai kwalliya a fuska ba a’a wata arniyar milk da pink less ta saka
ta kafa d’auri da d’ankwalin daga abinda yayi wuyanta, kunnenta da hannunta duk
gwala gwalai ne In ka ganta zaka d’auka wata matar shugaban kasa ce, farin babban
gyalenta na ajiye gefenta da farin handbag se farin flat shoe d’inta.
Trolley d’inta na zaune gefe, idanunta sanye da medicated glass hannunta waya ne
tana dannawa, a kasa Iman ta zube ba tare da ta d’ago kai ba tace “Ina kwana ummu?”
Shiru ummu tayi kaman bata ji ba, ta sake nanatawa nan ma Shiru, Zarah tace “ummu
ana gaisheki” wani banzan harara ta sakarwa zarah kan ta ja tsuki ta mike ta shige
d’akinta.
Ajiyar zuciya kalthum ta sauke kan tace “zauna da kyau Iman kiyi hakuri kuma da
abinda ummu ta miki sam ba haka halinta yake ba” zarah ma ajiyar zuciya ta sauke
kan ta mike “Anty kalthum zanje nayi wanka na fiddo akwatina kan su Abba su shigo,
Besty Bari inje In zo ko muje tare kiga room d’ina?” Kai Iman ta girgiza murmushi
Zarah tayi kan ta fara tafiya tana cewa “zaki shiga ne ma wata rana”.
Shiru Anty kalthum tayi tana tunanin sabon halin da ummu ta fara wadda basu ta’ba
gani tanayi ba ko su Mama da yaranta batayiwa wannan hali su da suka nuna basa
sonsu karara, Iman ma tunanin Abinda ummun ta mata take Allah sarki mata me mutumci
zata ‘bata mata rayuwa da tsanarta Ai da ba haka take ba, sau nawa suna gaisawa ta
wayar zarah amma yanzu gashi ta shiga tsakanin d’a da uwa.
Wani irin fisgan gyalen saman kanta da akayi wadda ba shiri ya sata yin baya tana
d’ago kai, wata farar kyakyawar buduruwa da zatayi tsara da Anty kalthum ta gani
sanye cikin wata arniyar bakar lace riga da skirt sun kama ta tsam kaman zasu yage
fuskan nan ya sha wata irin makeup da zan iya cewa In ba don iman amaryace kuma
bata saba makeup ba akayi mata yanzu, da se ince Tafi ta had’uwa.
A take Iman tayi guessing wacece cikin kasan makoshi tace ‘Hamna’ don sossai
kamansu ya fito da Abdul kuma farinta irin nashi, se iman ta ganta mummuna a
gabanta gata baka, yana da irin wannan matar me ze yi da ita? Zuciyarta ya tsinke
ita kam Ai maid zata zama a gidan waennan, lumshe ido tayi tana ji Anty kalthum
tace “me haka hamna?” Hararanta hamna tayi tace “madam ba ke nayiwa ba so ba
ruwanki”.
Kallon fuskan Iman tayi kan ta kwashe da dariya tana kallon Anty kalthum tace
“yanzu dama akan wannan Useless human being ko ince Animal kuke Min wulakanci”
hahahaha ta kuma kwashewa da dariya ta juya ta kuma juyawa tace “ke bakar munafuka,
magajiyar karuwai Ina so ki kalleni sama da kasa ki kalleni da kyau nayi tsarar
zaman kishiyoyi da ke?” Shiru Iman tayi, hamna tace “ke ‘yar kauye bana magana amin
banza se in kifa miki mari wallahi kuma In kwana lafiya, wallahi na fi karfin yinki
kai ko uwarki.........” Shigowar Abdul ne yasa tayi shiru da bakinta.
Kasa Iman tayi ta kanta tare da janyo mayafinta tayi saurin yafawa Anty kalthum da
ta mike tsaye ta kalleshi don san tabbatar da yaji abinda hamna take cewa ko be ji
ba, aiko expression na fuskanshi ya tabbatar mata yaji, ko kallon inda hamna take
be yi ba ya duka gaban iman tare da d’age gyalenta se suka had’a ido murmushi ya
sakar mata ganin ba d’igon hawaye fuskanta.
Itama bata san sadda tayi murmushin ba, kafad’unta ya kama ta mike tsaye, ya
gangaro da hannunshi ya sanya cikin nata lumshe idanu sukayi a tare jin wani irin
electric shock ya ratsa su a lokaci d’aya taushin hannayen junansu ya nemi rikitar
da su, ciki kasa da murya yace “Kalthum kira ummu mu wuce” daga nan ya ja hannunta
suka nufi kasa, ko kallon inda hamna take be yi ba bare ya san anyi wata hallita
wurin.
Wani irin murmushi kalthum ta saki tare da sake gud’a tana nufan d’akin ummu tana
wakar “er yarinya..... kin ji haushine....” tanayi tana kid’an da bakinta, wasu
irin hawaye ne suka zubowa hamna kutmelesi ita Abdul ze wa wulakanci a gaban
kucakar amaryarshi? Lallai daga ita har shi basu nemi zaman lafiya ba kuma wallahi
bashi suka ci se tayi maganinsu, zarah ce ta fito cikin shirinta sanye da green
lace tayi matukar kyau janye da trolley d’inta tana kallon Hamna tace “Anty Ina
besty?”.
Cikin fad’a hamna tace “ban sani ba ko Ajiyar ta kika bani?” Ta’be baki zahra tayi
kan tace “ahh ba ni na kar zomon ba” Anty kalthum da ta fito daga room d’in ummu
tace “ko ratayar ma ba’a baki ba auta am, mu tafi su ya Abdul suna jiranmu a tsakar
gida” ta janye trolleyn ummu ta fice zarah ta bi bayanta suka bar hamna da haushi,
tana nan tsaye ummu ta fito lullu’be da gyalenta kallon hamna tayi tace “lafiya
kuwa?” Shiru tayi ma ummun kaman wata sa’anta kan ta juya ta shige d’akin da ummu
ta sauketa ta d’auko trolley d’inta da bakin gyalenta tsiriri dashi iya wuya ta
yafa tare da d’aukan black handbag d’inta ta fito.
Mota uku sukayi Abba, ummu da Hafeez a d’aya, Abdul, Iman da hamna a d’aya sun
sashi tsakiya, se kalthum da zarah a d’aya duk drivers ke jansu suka nufi hanyar
Airport a hanya su zarah suka rabu dasu sukayi wurin maymz don d’auko sauran
kayayyakin Iman, a harabar Airport d’in suka sauka drivers d’inne suka janye
trolleys d’insu zuwa ciki.
A mota suka ci gaba da zama Hafeez da hamna ne suka fice zuwa arrivals hamna ta
zauna shi kuma ya shige inda Abba ya aikeshi, Shiru suke zaune a motan kanta kasa
yayinda shi kuma yake danna wayanshi be matsa daga gareta ba sam cinyoyinsu na
gogan juna kamshinshi duk ya cikata ga fargaba da take ciki jikinta se rawa yake
zuciyarta na aikin bugu.
Suna nan zaune har su zarah suka karaso suka shige ciki, tana nan de zaune da ta
gaji da sunkuyar da kan se ta d’ago tare da juyawa tana kallon window tana kallo su
Abba suka sauka suka shige ciki, satan kallonshi tayi yana nan yana aikin danna
wayanshi, ajiyar zuciya ta sauke tare da maida kanta kasa ta janyo gyalenta yadda
yake, se da yaji ana sanarwar jirginsu kan ya matsa ya bud’e ya fita ya cire babbar
rigar kam daga shi se na ciki da wando se hula dake kafe kanshi.
Zagayawa yayi ya bud’e mata ta zuro kafanta ta sauko tafiya ya fara a hankali ta
fara bin bayanshi dakatawa yayi tare da juyowa ya dawo dab da ita har tana jin
numfashinshi ya sanya hannu ya janye gyalenta zuwa baya, d’ago ido tayi se suka
had’a ido d’auke kai yayi tare da sanya hannunshi cikin nata suka fara tafiya
majestically har ciki, da suka je hawa stairs na jirgi ne ta dakata tare da matse
hannunshi cikin nata hakan ne ya sanyashi tuna ashe bata ta’ba hawa jirgi ba.
Sake hannunta yayi batayi aune ba se jin hannunshi tayi a kwankwasonta ya zagayeta
tare da d’aura kanta kan kafad’anshi suka ci gaba da tafiya duk yadda take so haka
yakeyi sbd takalmin kafanta In tace zatayi garaje fad’uwa zatayi tunda bata saba
ba, duk ido kansu ya dawo ko a jikinshi seda suka had’a ido da ummu ne ya d’an
sunkuyar da kai ganin irin hararan da take jefanshi dashi, hamna ma kaman zata
fashe kuma se aka ci sa’a sit d’insu Manne da na juna, Sbd basu samu VIP ba don
sunyi late booking seda ta zauna tukun ya tsallaka ya zauna daga jikin window da
hannunshi ya sanya mata belt zarah da kalthum se kus kus sukeyi suna dariya, da
akayi sanarwar kashe waya ma shi ya bud’e jakanta ya d’auko nata tare da jujjuyawa
se kuma ya danna ya kashe tare da jefata aljihunshi itade tsabar kunya ko iya d’ago
kai ta kasa.
Dirin tashin jirgin da taji ne yasa tayi saurin kama hannunshi dake hannun sit gam
murmushi ya saki kan ya maida nata cikin nashi lumshe ido tayi har jirgin ya
daidaita a sama kan ta bud’e nan ya saketa ya sanya ear pods tare da jingina da
jikin kujeran ya lumshe ido, har suka sauka be d’ago ba, manyan motoci da dogarai
da masu busa da ganga irin ta sarauta ne suka cika Airport d’in daga ji zaka san ba
kananan mutane bane suka sauko garin ba ‘bata lokaci sukayi checking aka tattari
kayansu zuwa mota, wannan karon da zarah ya kyaleta yayi gaba don baze iya tafiyar
hawainiyar nan ba, se tsokannata Zarah take har suka shiga mota se Unguwan lamid’o.
🖤Gureenjo🖤
🥀NOOR IMAN🥀
*026*
Nenne ce da kanta tazo ta tarbeta hannunta ta kama har part d'inta kanta a kasa so
bata samu damar karewa masarautar kallo ba amma de ta tabbatar Allah yayisu da
yawan kuyangu ko bayi don duk inda suka bi gaisuwa ce kawai ke tashi amma ba wadda
ke amsawa wadda hakan ya sata jin ba daad'i bata san haka gidan sarauta yake ba.
Ke'bantaccen d'aki babba sossai nenne ta kai ta zarah de na binsu a baya Ummu da
Abba kam tuni sunyi site d'insu yayinda hamna tayi wurin nenne petel don a chan
sukayi zasu had'u da ummanta, Hafeez da Abdul kowa site d'inshi ya tafi, "Feel at
Home Ohk?" Nenne ta furtawa Iman, gyad'a kai iman tayi tana murmushi, ko ba'a fad'a
mata ba ta gane wannan itace nenne mahaifiyar Abba, tsohuwa me mutunci da sanin ya
kamata.
Fita tayi wasu mata suka shigo d'auke da manyan trolleys har guda uku, zarah dake
mata masifar ta bud'e kanta haka ta sha iska ta dakata tare da juyawa ta kallesu, a
tare suka ce "barkanku da isowa, Hajiya Nenne ce ta turo mu don fara yiwa Amarya
abinda ya kamata" murmushi zarah tayi kan ta gyad'a kai tana janye gyalen fuskan
Iman "Toh madam se ki mike za'a fara miki gyara" kallon matan tayi kan tayi
murmushi suma suka mayar mata.
Akwati d'ayar ta bud'e ta d'auko wani silk farin riga da iyakarshi be wuce gwiwar
ta ba ta bata "ranki shi dad'e bismillah" kar'ba tayi ta kalli rigan ta kuma kallon
rigan ita zata saka wannan a gaban mutanen nan? 'Bata fuska tayi zatayi musu zarah
tace "wallahi if I hear pim Nenne zan kira" Sarai ta san halin zarah hakan yasa ta
mike ta shiga toilet ta sako da kyar ta fito ya kuwa amshi jikinta se tattakurewa
take gashi hannunshi irin na vest.
Zama tayi bakin gadon tana kallonsu dariya zarah ta kwashe dashi bata san sadda ta
banka mata harara ba, d'ayar ce ta katsesu da cewa "ranki shi dad'e In ba matsala
zan iya bud'e kanki?" Kai ta gyad'a matar ta matso ta bud'e kanta ba laifi gashinta
na da tsawo sossai zuwa de wuyanta kuma ba datti amma dukda haka matar tace "ranki
shi dad'e kan yana bukatar wanki zamu iya karasawa toilet?" Wani irin abu iman ke
ji In manya mutane irinsu suna mata magana haka cike da girmamawa kuma se suyi
maganan kaman neman izini suke.
Mikewa tayi ta bita suka shiga bayin tas ta wanke mata kai cikin natsuwa ba
hayaniya zata iya rantsewa bata ji ko alamun zafi ba haka ruwa ko kad'an be hau
kanta ba, suna fitowa taga d'ayar ta had'a wani karamin kujera gefen sockets
bismillah tayi mata kan ta karasa ta zauna, wacce ta wanke mata kai d'ince ta fiddo
hand dryer ta had'a ta fara busar mata da kai yayinda d'ayar ta d'auko lallen da
bata san sadda aka kwa'ba ba ja da baki ta fara mata jan.
Yayinda d'ayar ta fiddo wasu abubuwa kaman kurkur da su madarar turaruka ta fara
had'awa, mikewa zarah tayi tana yafa gyalenta tace "Bestie bari inje sashin baba
yarima yanzu zan dawo" Kai iman ta gyad'a itafa yanzu bakin magana ma bata dashi,
abinda ya kamata ace a gidansu kuma 'yan uwanta ne sun mata se gashi en uwan miji
sun had'a gabad'aya sunayi, tsoronta ma kar hakan ya zama abin gori a gareta gashi
gidan sarauta yadda take jin labarinsu kad'ai abin tsora ne bare kuma ta zama topic
of discussion.
Cikin awannin da basu wuce uku ba an gama mata had'ad'en lalle ja da baki har an
kankare, gashinta an zuba mata nyinyirin two step kaman ka lashe tsabar had'uwar
kitson da kankantarshi, jikinta An mulkeshi da dilka, 'yan mata ne hud'u a d'akin
bayan zarah, Nabeeha, Ameerah, teemah da zee yaran baba yariman ne kuma kusan
sa'anni ne da zarah, musu suke akan wacce ta fi kyau tsakanin Hamna da Iman duk
d'akin ya kaure da hayaniya Zee ce tace "wallahi Iman tafi kyau ku tsaya kuji
hujjojina" Shiru sukayi suna sauraranta ta d'aura da.
"Kunga Iman na da wushirya Adda hamna bata dashi" kallonsu tayi tace "kuce d'aya
mana" suka had'a baki suka ce "d'aya" ta kara da "Iman na da dimple Adda hamna bata
dashi" sukace "biyu" ta d'aura "Iman na da manyan boobs dukda ba har chan ba amma
tafi Adda hamna" sunkuyar da kai Iman tayi cike da kunya su ko ko a jikinsu se cewa
"uku" da sukayi, "yauwa Dukda Adda hamna tafi Iman bombom, iman ta fi ta hips me
d'aukan hankali" shewa sukayi kan suka ce "hud'u" "kai hasken fata ne fah kawai
Adda hamna zata nunawa Iman da baka ce se a hankali, ga yangan tsiya kaman wacce ta
fi kowa, abu na karshe da ya zama hujja na shine ku lura da kyau Idanun Iman sexy
eyes ne irin na Hamma Abdul banbancin kawai nata black nashi kuma brown yayinda
idon Adda hamna suka kasance kanana kaman na 'yan China".
Dariya suka sa har Iman Lallai a gaishe da zee, hiransu suka ci gaba dayi iyakaci
iman tayi dariya In sunyi abun dariya sede sam bata sa musu baki ba, ta sani ko min
lalacewar d'an uwanka fa baza ka so a zageshi a gabanka ba tana da wannan wayon
hakan yasa duk Aibata hamna da suke bata saka musu baki ba, tsab matarnan ta dirje
ta har halawa tayi mata sega Iman an fito Amarya sak se wani yalki take, se lokacin
en matan suka mike akan zasuje suyi wanka su shirya zuwa walima don sune manyan
kawayen Amarya.
Ficewa sukayi aka barta da zarah kad'ai se lokacin tayi magana "su kuma ya kuke
dasu bestie?" Zarah tace "yaran baba yarima ne matanshi hud'u hakan yasa duk su
hud'u aka haifesu shekara d'aya sede banbancin kwanaki, Inda baba yarima ya burgeni
ya tsaya a gidanshi sossai irin sossai d'in nan, shiyasa Kika gansu kaman 'yan
hud'u ko kawaye, Ai kin gane sunayensu ko?" Iman tace "Eh na gane, bari inyi wanka
ruwan yana hucewa" wacce ta mata dilka ce ta had'a mata ruwan wanka me had'e da
turaruka kala kala, seda ta lumshe ido da ta shiga ruwan ita karan kanta ta san ta
chanza ba se wani ya fad'a mata ba, ji take kaman lallenta kar ya ta'ba gogewa har
Abada tsabar yadda ya tsaru.
********
"Umma cewa fah kike inyi hakuri In baki lokaci ni wallahi na gaji da jin wannan
kalaman, ko kallo fah ban isheshi ba" kuka ta fashe dashi tana cewa "a gaban
mahaifiyarshi fah yayi rantsuwar ban ta'ba shiga zuciyarshi ba kuma bazan shiga ba"
umma tace "Haba Hamna me yasa kike abu se kace ba 'yar da na haifa a cikina ba?
Nace ki bar komai a hannuna da Sannu duk zasuyi jawabi kuma ki dena musu kuka se su
mai dake sakarya.
Kaman yadda na fad'amiki tare zamu koma, mu bud'ewa 'yar iska wuta se ta gaji ta
gudu da kafanta, kafin mu tafi kuma zamu je mambila mu samu boka ya rufemana bakin
duk wadda ze ga aibun zamana gidanki, ke har shi yayi iya yinshi ya taimaka ko me
zamu iya kashewa ya kasa kusantar yarinyar nan yaji tana mugun wari yaji ya
tsaneta" dariya Hamna ta sake tana cewa "that's my mom idea d'inki yayi Allah ya sa
ya tafi daidai" Umma tace "aaa damu za'ayi? An isa a ta'bamin 'ya a zauna lafiya
ne".
Hamna zatayi magana kenan Nenne Petel ta shigo wadda hakan ya sata yin Shiru, zama
tayi bakin gadon d'akin tace "kubra" hamna ta amsa da "na'am" Tace "Ina ta so inja
hankalinki, auren nan da Me suna yayi ba shine yake nuna baya sonki ba, kaman yadda
Allah ya bawa duk wani namiji umarni ze iya auren mace daga d'aya zuwa hud'u In har
ze yi adalci a zaman nasu, haka sunna ne sbd fiyayyen halitta matanshi sunfi goma
haka sahabbanshi da wuya ki samu me mata d'aya kinga kenan ke wacece da Baza'a miki
Kishiya ki zauna da ita ba? Ki guji tada fitina a gidanki dan Allah, ki kiyaye duk
abinda ze zama tashin hankali a tsakaninku, banda yawan kai kara sbd yana janye
kimar mace a idanun mijinta haka kuma banda kishi irin na jahilci, kai ya waye
yanzu ba'a kishi irin na hauka se na hankali akan miji zaki nuna kishinki ba'a kan
Kishiya ba, sannan ki za......" mikewa Hamna tayi tana waro ido "laaaaa Nenne petel
yi hakuri plz ina zuwa minti d'aya ashe ya Abdul yace In kaimishi fruit salad na
manta" ta fice da sauri.
Murmushi umma ta saki ta san karya ce kawai hamna ta shirga don ta gaji da jin
wa'azin Nenne petel d'in, kuma bata ga laifinta ba haka kawai adakeka a hanaka
kuka, shigowar ummu ne ya katsewa umma tunaninta bata san sadda ta ja tsaki ba
ganin yadda Nenne petel ke farin ciki da ganinta "lafiya?" Ummu ta tambaya umma
tace "kalau" mikewa Nenne petel tayi tana cewa "Rashida biyoni yanzu babanku ya
gama magananki yace In kin shigo inyi maza In kaiki wurinshi" murmushi ummu tayi
tana cewa "Allah sarki babana nayi kewanshi muje Nenne petel" fita sukayi da harara
umma tabi bayansu tana ta'be baki.
********
Karfe uku daidai ya musu a kofar masarautar lamid'on Adamawa ganin inda suke shirin
shiga yasa inna cewa "Kai dreba Lafiya kuwa? Ina kake shirin kaimu?" Yace "gidan su
Angon ba hajjiya, ko be gayamiki shi jikan sarkin Adamawa bane?" Goggo saratu Tace
"Kai haba dallah jikan sarki a ina? Alfarmar alqur'ani ka kaimu inda muka gama
wassafawa zamu gani ba nan ba ta Ina zata ga jikan sarki har ta aureshi?" Goggo
kamila tace "aiko kya tayani tambaya".
Wata daga chan baya tace "tooh ko de da gaske yake tunda Ai shi aka ce ya d'aukomu
kuma ya san inda ze kaimu ku bari ya shiga inma 'Batan kai yayi shi ze daku a wurin
dogarai Ina ruwanmu" murmushi ya saki yana girgiza kai tunda suka kamo hanya yake
jin yadda suke aibata wannan Amarya tun be san sunanta ba har ya rike tun yana
ganin kaman gaskiya suke fad'a har ya dawo kokonton karya ne ko gaskiya don abinda
suke fad'a be yi kama da gaskiya ba, yana Jin yadda kowa ke wassafa yadda ze yi In
yaje ya kasa cin miyar kukar da dangin ango zasuyi, dukda an tsaya gombe sunci
abinci ba ko sisinsu Abba ne ya ciyar dasu bayan yayi magana da me shagalinku
restaurant duk abinda suke so a basu shi ze biya kud'in don wawanci irin nasu ba
wadda ya tambayi nawa ne kud'in ko wa ya biya suka ci suka gyatse suka hau mota
suka ci gaba da tafiya, yana ga ko sun zata kyauta ake rabarwa oho! Toh ga karshen
hassada.
Bud'e get d'in da akayine ya sasu maida hankali bakin kofan dogaran dake wurin sun
kai ashirin da wasu polices suka fito suka dudduba motan suka tabbatar wadda Abba
ya fad'a ne kan suka musu hannu suka shige, baki wangale suke kallon katoton
masarautar had'ad'e kaman a wata kasa suke, kuyangi da Bayi ke ta aikin kai kawo,
saukowa sukayi suna rarraba idanu kaman waenda sukayiwa sarki karya.
Wasu mata biyu da shigar alfarma suka gani sun nufosu bayansu kuyangi ne akallah
zasu yi goma, har gabansu suka karaso suna murmushi suka ce "barkanku da zuwa
masarautar Modibbo Adama, ni sunana Dada nice uwargidar wazirin masarautar nan"
d'ayar tace "zaku iya kirana nenne petel uwargidan Galidiman masarautar nan kuma
kaka ta 'bangaren uwa a wurin Surukinku" gaishesu suka kuma yi suka amsa, kan d'aya
daga cikin kuyangin tace "barkanku da zuwa ku biyomu don ganin masaukinku, nice
shugabar kuyangin nan gabad'aya sunana sahura mu ke da alhakin kulawa daku cinku,
shanku da makwancinku daga yanzu har randa zakuyi sallama da masarautarmu me
albarka".
Inna de ido fah ya raina fata hausawa suka ce d'an hakin da ka raina...... bin
bayansu sukayi kowa gwiwa a sage yhu guys know that feeling right? Irin feeling
d'innan da zaka gama sa ranka ga abinda zaka kalla se kaga akasin haka🤣 masaukinsu
aka kaisu part guda aka ware musu me cike da komai na jin daad'in rayuwa Ac da Tv
kad'ai inna ta sani a duk cikin kayan alatun part d'in se ta zama 'yar kauye
musamman da ta shiga bayin.
"Zakuyi wanka ku shirya yanzu akwai taron da za'ayiwa Amarya har ta gama shiri ma"
goggo hindatu tace "ta gama shiri fah kikace? Mu da muka barta kano?" Murmushi
sahura tayi kan tace "Ai su jirgin sama sukabi sun iso tun safe" salati suka saka
se kace wasu en kauye inna tace "wannan Ai bakin hali ne da wariya mu se aka turomu
a mota muka yini muna tafiya ita kuma aka d'aurata a jirgi, Toh bakar munafuka
dad'in abin ma nima na ta'ba hawa jirgin nan tunda naje kasar da bata ta'ba zuwa
ba, kum..."
Goggo hindatu ce ta katseta tana kallon sahura tace "zaki iya tafiya, yanzu zamu
Shirya" fita tayi tana mamakin en uwan Amaryar nan kaman ba danginsu ba? Abinku da
masarauta me kunnuwa tuni zance ya fara yawo Ai Amaryar yarima Abdulraheem mujiya
ce cikin en uwanta.
Cikin lokaci kankani sukayi wanka suka shirya suka ci abinci kan suka fito da
niyyar tafiya taron da za'ayin a mota aka d'aukesu inna ta kasa Shiru Tace "har Ina
ne za'ayi taron malam? Yanzu fah muka baro kan hanya kafafu na har sun kumbura kuma
a kara d'aukarmu zuwa wani wurin?" Yace "Ba nisa nan cikin masarautar ne amma
bazaku iya zuwa a kasa ba shiyasa aka turo mu d'aukeku" Shiru duk sukayi har suka
isa katon hall d'in dake bayan masarautar wadda daga waje ma zaka ga irin kayatuwar
da yayi.
Yaji decoration har ya gaji zallan mata ne wurin manya masu ji da kud'i da mulki
duk kuma family ne, abinda ya sa aka yi saurin cika kuma aka zozzo sbd Nenne ce da
kanta ta aikawa kowa katin gayyata wadda be zo ba kuwa ba abinda ze hanata kiranshi
ta ci mishi mutunci, Mama da yaranta gabad'aya zaune a 'bangare d'aya, 'bari d'aya
aka warewa 'yan uwan Amarya chan aka musu iso suka zazzauna.
Basu jima da zama ba na hango wasu gayya sun kutso kai waro ido nayi a fili nace
"ikon Allah su kuma waennan wa ya musu iso zuwa nan?" Gayyan en ANNUR HAUSA NOVELS
ne gaba sanye da ankonsu na jallabiyoyi masu kyau da tsari duk milk amma design
daban daban kowacce ta yafa gyalenta gwanin sha'awa, Ummu Ameer, Ummu haneef, Ummu
Aslam da Adama Aliyu ne gaba se wani cin magani suke irin ba rainin nan, Anty
kalthum ce ta karasa dasu wurin zamansu suka zazzauna suna jiran walima, har na
d'aga kafa Don zuwa garesu na kara gani wasu gayyan na MU KARU DA JUNA Maman
khalil, kawata Aisha da Khadijah Queen da Maijidda ne gaba sanye suke suma da
ankonsu na jin wa'azi wato jallabiya suma wurinsu aka basu suka kame ba raini sun
had'u.
Basu jima da zama ba kuyangi suka fara shigowa suna watsa flowers a hanyan suna
kuma fesa turare baya baya sukeyi inda Iman ta bayyana sanye da Ash fitted gown
irin na amare yaji design kana ganinshi zaka san ba karamin kud'i yaci ba fuskantan
nan ya sha makeup d'in zarah taci d'auri da ash head, Ash pose da Ash hill shoe ta
sanya saman kayan kuma alqyabba ce Baki da Ash wayyo had'uwa, tayi kyau har ta gaji
su Inna kam kasa ganeta sukayi har Goggo saratu ke cewa "wannan kam watakila itace
sarauniyar masarautar".
Inna tace "ze iya yiwuwa bakiga irin kyaun da tayi ba? Ga fadanci kam kaman za'a
mata sujada" goggo hindatuce tace "inna Noor iman ce fah" waro ido sukayi Ai kuwa
ita d'ince tsaki inna taja tana kallon su zarah da suka biyu bayan ta suma sunyi
kyau dukda ba anko bane jikinsu amma sunyi matukar kyau, kan wani tattausan carpet
irin na masarauta aka zaunar da ita kan su teema suka zagayeta, wata malama ce ta
shigo ta zauna akan kujera kwara d'aya dake saman stage d'in ta fara zanzaro
wa'azi. Daga chan karshe na hango en Wattpad ma fah sun natsu suna jin wa'azi suna
gyad'a kai😅.
🖤Gureenjo🖤
🥀NOOR IMAN🥀
*027*
Walima akeyi me class wadda ya ratsa duk wani me sauran imani kan a tashi kuyangi
suka fara shigowa da abinci kala kala suna rabawa da souvenirs da ban san sadda
akayi ba, a cikin paper bag me d’auke da hotunansu su biyu rike da hannun juna ita
kanta bata san sadda akayi ba, cikin jakan kuma dardumar sallah ce babba me tsadar
da azkar wadda ya had’a na safe dana yamma se na bacci da bayan sallah a jikin ba
hotonsu sede sunayensu, se memo me d’auke da hotonsu kala kala masu kyau.
Dukwadda ya taka kafanshi wurin seda ya san eh fah wannan walimar ta had’u, ‘yan
Annur hausa novels harda fad’a wurin karbar souvenirs bayan nenne ta fad’a musu
kowa ze samu😜, ana tashi zarah ta kama hannun Iman suka fice bata bari sunyi
magana da en uwanta ba sbd kar su ‘bata mata rai ranar farin cikinta, mota suka
shiga aka wuce dasu, cikin sanyin murya iman tace “Zarah Ina son ki kaini wurin
nenne”.
Kallon drivern zarah tayi tace “Part d’in Fulani” yace “An gama ranki shi dad’e”
murmushi Iman tayi tace kasa kasa “er air se kace gaske na lura kema jinin sarautar
nan na yawo kanki kaman d’an hayakin yayanki” ta karasa kasa kasa kaman batayi
niyyar fad’a ba, dariya zarah tayi tana cewa itama kasa kasa “Eyyeh Lallai ma
matarnan yayan nawa ne kanshi ke hayaki?” Dariya Iman tayi zatayi magana zarah ta
d’aura da “ba dole ba kin san aka ce In kazo inda aka san waye kai ka kama ajinka
da girman ka sbd bama son raini ya shigo ciki, sannan abinda kika fad’a kaman a
kunnen yayana kuwa don wannan sako ne”.
Girgiza kai Iman tayi tana waro ido zatayi magana kenan motar ta tsaya, se kuma
wasu dogarai suka bud’e musu, fita sukayi zuwa kofan part d’in nennen, Shiru kaman
ba me rai a ciki dukda en bukin da suka cika gidan amma ba kowa part d’inta sbd ita
bata son hayaniya da yawan mutane a wuri, iso suka nema kuyangarta ta shiga ta nemo
izini aka ce su shiga.
Babban parlor ne da ya amsa sunansa kafatanin rayuwar iman zata iya cewa bata ta’ba
shiga parlor irin wannan ba, dukda a part d’in ta sauka amma ‘bangare daban daga
chan baya me karamin parlor da bedroom d’in da suke da zarah, bata karaso nan ba
balle ta san ya yake kuma ta chan be cika yawan dogarai da kuyangi kaman nan ba,
room d’in dake facing d’insu zarah ta mata jagora zuwa ciki, kamilalliyar tsohuwar
na kishingid’e akan tuntu d’akin karan kanshi duniya ne komai na ciki na asalin
gidan sarauta ne.
Wasu kuyangi ke mata tausa, murmushi ta sakarwa Iman wadda ya bayyanar da hakorin
makkanta me kyau da yalki, hannu ta ma kuyangin suka fice, da sassarfa Iman ta
karaso gabanta ta duka se kuma ta fashe da kuka, ita da zarah duk ido suka zubata
kan Nenne ta mike ta iso gabanta batayi zato ba taji tsohuwar tayi hugging d’inta
wani sihirtaccen kamshi me sanyi da zata ce bata ta’ba jin turare me kwantar da
hankali ba irin wannan ke tashi a jikinta.
“Gimbiyarmu meke faruwa ne? Ko wani ne ya ‘bata miki?” Kai Iman ta girgiza tace
“Kin min abinda duk duniya ba wadda ya isa ya min, kin farantamin kin kankaro
darajata a idon en uwana da masarautar nan, ni kuwa nenne me zanyi in biyaki wannan
alkhairan naki gareni?” Murmushi nenne tayi kan ta saketa tayi baya kad’an zuwa kan
tattausan carpet irin na sarauta ta kishingid’a kan tace “Ba abinda zakimin da ya
wuce adu’a tun dana ji labarinki daga bakin Zarah naji wani irin tausayi da
soyayyarki ya shigeni, rashin kulawar uwa ba karamin illa bane ga ‘ya musamman
mace, Ina so ki d’aukeni a matsayin uwa wacce zaki dinga fad’awa damuwarki a ko
yaushe kinji?”.
Kai Iman ta gyad’a kan Tace “In shaa Allahu Nenne zan ci gaba da yi miki adu’a har
karshen rayuwana Allah ya biyaki ya saka miki da gidan Aljannah” da Amin ta amsa,
kan ta harari zarah, baki zarah ta zum’buro tare da cewa “aaa ya da harara ni kuma
me nayi?” Tace “wayace ki kawota nan, bayan kin san kuna da shirin dinner a
gabanku? Oya tashi kuje tayi sallah ku fara shiri sannan ki tabbatar taci abinci”.
Kai zarah ta gyad’a tare da cewa “Nenne Ina tsohon mijinkin nan me ran karfe?”
Murmushi nenne tayi kan tace “yarinya kau da idanunki akan shi kin san yafi
karfinki, ana fakewa da ce mishi tsoho bayan sonshi ake kaman za’a mutu” Turo baki
gaba zarah tayi tana ‘bata fuska iman bata san sadda murmushi ya su’buce mata ba,
nenne ma murmushi tayi dama abinda take son gani kenan.
Hakan yasata cewa “ko kefa ‘yata ki dinga murmushi, baki ga yadda take miki kyau
ba” ‘boye fuskanta tayi tana kara sakin wani murmushin a zuciye zarah ta mike zata
fita nenne tace “Eh dai ko me zakiyi kiyi, baza ki gane min miji ba ehe” mikewa
Iman tayi tana ci gaba da murmushi tace “mun barki lafiya ranki shi dad’e” Kai ta
gyad’a, itakuma tabi bayan zarah.
Tana fitowa ta fara dariya me sauti wallahi zarah ta bata dariya itace da tambaya
sanan ita ce ke fushi, musamman yadda take ta ‘bata fuska yafi komai bata dariya
bata kula ba, alkyabbar jikinta ya tad’iyeta abinka da ba sabon ba, shikenan yau
kam fad’uwa zatayi ta karya kafa ko hannu Don wannan tiles d’in ta tabbatar ta kai
kasa ba abinda ze hanata karyewa.
Wani wawan ajiyar zuciya ta sauke jinta a hannun mutum, dayake da tazo fad’uwa
hulan alkyabbar tayi gaba zuwa kan fuskanta so bata ga wadda ya taimaketa ba amma
kuma kamshin tabbas ta sanshi, a hankali ta d’ago kanta jin har yanzu be saketa ba
hannunshi d’aya zagaye da kwankwasonta d’ayar kuma a kafad’anta, tana d’agowa suka
had’a ido.
Bazata iya jurar kalllon cikin kwayar idonshi ba hakan yasa tayi saurin kawar da
kanta tana daidaita tsayuwarta, saketa yayi ba tare da yayi mata magana ba ya
zagayeta ya shige d’akin nenne abinshi, bata san ta rike numfashi ba seda ya wuce
taji tana shirin mutuwa ba shiri ta saki numfashi me karfi, d’ago kai tayi se suka
had’a ido da zarah da sauri ta sunne kai yayinda zarah ta kwashe da dariya.
Gaba tayi ta barta nan tana kunkuni, har suka zagaya inda ta sauka zarah bata bar
dariya ba tana cewa “osheeee yau naga wani irin love” suna shiga Iman ta fad’a
toilet ta barta nan da surutunta, wanka tayi da ruwan d’umi sossai Don duk a gajiye
take jin kanta, kan tayo alwala ta fito, tana tunani da mama aka zo amma bata ganta
ba ko me dalili? Gashi tunda ya d’auki wayanta a jirgi be dawo mata dashi ba, se
yanzu ta tuna duk had’uwansu bata ta’ba gaidashi ba fah kar ya d’auka bata da
kunya.
Zarah ce tace “tunanin me kike ne matar yaya?” Harara ta sakar mata “zarah ki fita
idona in rufe, wannan kuma wani irin suna ne?” Dariya Zarah ta saki tana cewa
“karya nayi? Ko ke ba matar yayanan bane? Kingama daga yau sunan da zan dinga
kiranki dashi kenan, matar yaya” kanta Iman ta nufa da gudu ta yi toilet tana cewa
“tuba nake matar yaya” murmushi iman tayi tana girgiza kai.
Cikin kayan da nenne ta aikomata d’azu ta zabo wani cotton duguwar riga me guntun
hannu ta saka tare da zaro hijab ta tada sallah, magrib tayi ta ci gaba da zama
tana azkar dayake ta haddace, Haka kawai taji tana sonyi dama ba kullum takeyi ba
se ta bushi iska, tana nan zaune zarah ta fito itama tayi wanka sede da towel ta
zauna bayan ta shafa mai, ta bud’e makeup kit d’inta ta fara goge brushes d’inta
dayake tana fashin sallah.
Ganin ta gama azakar se kawai ta fara karatun qur’ani da ka, tun daga Nasi ta fara
tana cikin izu na biyu aka kira isha, ta mike ta gabatar tana sallamewa ana sallama
kofa wasu kuyangi ne suka shigo bayan zarah ta basu umarnin shigowa da manyan trays
a hannunsu na abinci seda suka ajiye kan suka duka suka kwashi gaisuwa zarah ta
amsa tana wani ‘bata fuska.
Suka mike suka fice bayan ta basu umarni, kallon iman tayi dake kallonta tace
“Lafiya matar yaya? Why are yhu eying me?” Murmushi kawai Iman tayi kan ta mike ta
ninke sallayar da hijabin ta isa gaban trays d’in ta bud’e kular farko couscous ne
a ciki me rai da lafiya da yaji veggies ta d’iba kad’an tare da bud’e kula na biyu
pepper chicken ne part d’aya ta d’auka ta d’aura gefen couscous d’in ta nufi gado
ta zauna.
Allah sarki en uwa se ta fara tunanin ko en uwanta sunci abinci? Tsintar kanta tayi
da adu’ar Allah ya sa irin abinda aka kawo mata aka kai musu suma suci daad’i, tana
gamawa suka fara kwalliya da zarah se lokacin take tambayarta “Ina Su teema ne?”
Zarah tace “suna chan suna makeup, yanzu anko zamuyi Don akwai wani yadi haka me
yanayi da less da Mommy ta d’inka mana dukkanmu so ban saka nawa ba suna basu saka
ba sbd munyi se sallah ne zamuyi anfani dashi tunda kinga azumi ya gabato, toh kuma
se ga bukinki zamu saka shi as anko, ga colors d’in blue and pink ne ke!! Hasko
had’uwarmu kawai”.
Iman tace tana ta’be baki “dukde abunku baza ki kaini ba” zarah Tace “eyeeeh Lallai
ma wannan Amaryar marar kunyace ashe?” Dariya iman tayi zarah na tayata, a haka
suka gama kwalliyar suna gamawa Su teema na shigowa sun kuwa fito kaman ka sace
kowacce makeup d’inta abin yabawa ne, cikin Jin haushi zarah tace “wato nice kashin
baya an barni da towel Ina yawo kowa ya shirya, Toh Amarya de bazata fita ba In har
ban gama ba”.
Nabeeha tace “kin isa yarinya?” Zee tace “har ta wuce ma kin manta itace angon? Ko
mata na fita bada izinin mijinta bane?” Teema tace “Ina fah In ba so take tagamu da
fushin Allah ba?” Ameerah ta d’an duka kaman yadda kuyangi ke yi tace “Allah ya ja
zamanin yarima jikan sarki, gaba sayaki baya sayaki, me tafi....” hannu zarah ta
d’aga mata kaman yadda sukewa kuyangi, kan tace cikin yatsina “fad’i damuwarki”
kara dukawa Ameerah tayi tace “Ranka shi dad’e muna neman izinin tafiya da matarka
ne zuwa wajen dinner tare da umarnin Fulani” d’an Shiru Zarah tayi kan tace cikin
yatsina “ku jira daga waje zan duba” dariya suka kwashe dashi har Iman abin ya bata
dariya sossai, wato ma sun san irin mulkin da suke shimfid’awa bayi.
Teemah tace “er Air kin ko yi kama da hamma Abdul sossai da kina shakiyancin nan”
zarah tace “Sweetheart” tana kallon Ameerah, Ameerah Tace “Eh za’a cuceni kenan,
fad’i Ina jinki” zarah tace “plz love ki taimaka ki mata head bari nayi makeup kar
a barni baya, plzzzz” hararanta tayi kan tace “ba don halinki ba” zarah tace
“thanks” mikewa Iman tayi ta zura doguwar rigar ta milk da Flowers kanana kanana
golden, rigan yayi wani irin amsan jikinta ne ba d’inkin kawai abin kallo ne.
Head d’inta golden Ameerah ta d’aura mata ya kuwa fita d’as ya zauna, a jikin saman
d’an kwalin ta Makala mata gyalenta milk an zagaje bakin da flowers golden irin na
rigar me d’an girma, sarka da d’an kunneta Teema ta sakamata suma golden yayinda
Zee ta saka mata takalminta shima golden, hill ne abinda Iman bata so Don zuwa
yanzu kafanta har kumbura ya fara abinda ba sabon ba haka de ta sanya.
Zarah na gama shiryawa wata babbar mace ta shigo, duk Sannu suka mata suna ce mata
mommy, Iman ma gaisheta tayi ta amsa da fara’a kan ta bud’e handbag d’in hannunta
ta fiddo turaruka masu asalin kamshi ta feshe Iman dasu har seda taji sun fara hawa
mata kai, kallonsu zarah tayi tace “kuyi gaba, yanzu zamu taho da Amaryar In kun
isa kada ku shiga ku jira isowarta” suka amsa da Toh kan suka fice.
Motoci ne kala kala a harabar gidan ba na kananan mutane duk ciki, tuni jama’a
dayawa sun fice wurin dinnern, har su Inna sun tafi ba yadda ba’ayi da itaba ta
zauna su tafi ta ki tace se ta je, mama dake ta kallonsu goggo saratu ta kalla tace
“wai lafiya kuwa Anty? Se naga kaman tunda muka zo bakya jin daad’i ga idanunki duk
sun suuntuma” goggo hindatu tace “Ai ko de, jiya na lura ko Waliman nan bata samu
zuwa ba” Mama ta kirkiro murmushi kan Tace “wallahi zazza’bi ne da gajiyar hanya
suka had’umin amma yanzu na ji sauki sede bazan je dinner d’in nan ba” goggo kamila
tace “Allah ya kara sauki” suka amsa da amin, kan suka fice suka barta anan part
d’in suna fita ta fashe da kukan da na rasa dalili, ikon Allah.
Mommy da wata da taji mommyn ta kira da Anty Dada suka fito da Iman d’in zuwa jikin
wata arniyar Bakar mota suka bud’e mata ta shiga, tare da rufowa, suma duk suka
shishige motocin dake wurin a jere motocin amaryar suka nufi fita dayake ba cikin
masarautar suka shirya event d’in ba, a razane ta d’ago jin kamshinshi ya
subhanallah yana motar shima zaune a gefenta ya jingina da jikin kujera.
Sanye da milk shadda da yaji ado da milk zare, irin d’inkin zamani aka mishi da ake
kira half jumpha me wani style me d’aukar hankali rigan me dogon hannune hakan yasa
be d’aura agogo ba se links d’in da ya saka golden color, hulan kanshi milk ce da
d’an adon golden se takalmin kafanshi half cover milk yayi kyau har ya gaji,
kamshinshi da nata suka had’u suka bada wani kamshi me kashe jiki da wuyar
fassarawa.
Duk cikin seconds da basu fi talatin ba ta gama kare mishi kallo, ko d’agowa be yi
ba, kaman be san da zaman mutum gefenshi ba, fuskanshin nan ba’a had’e ba ba kuma a
sake ba yana nan dae yadda ta saba ganinshi, ajiyar zuciya ta sauke kan ta maida
kanta kasa tana wasa da zoben hannunta, cikin sanyin muryarta Tace “Ina yini?”
Kallonta yayi se kuma ya d’auke kanshi be zaci zata gaisheshi ba, hakan yasa seda
yaja lokaci kan yace “fatan kina lafiya” Tace “Alhamdulillah”.
Shiru sukayi basu kara magana ba har aka isa wurin dinner d’in, basu fito ba seda
aka bud’e musu kofa fita yayi, itama ta fito seda ta zagayo inda yake kan suka jera
su Ameera ma sun jera biyu biyu, yayinda abokanshi sun riga da sun shige ciki, wasu
kuyangi ne suke zuba flowers a gabansu masu kamshi suna takawa suna wucewa, yayinda
masu busa da kid’i irin na masarauta suka fara aikinsu, nan fah jin kai ya tashi
wani irin tafiya su zarah sukeyi irin na asalin sarauta se na Abdul ya dame nasu ya
shanye.
Kun gane Ai irin kana jin algaitar nan tana ratsa jikinka, wayyo seda suka burge
kowa har Iman dukda ba irin tafiyar ta iya ba sede itama a hankali take tafiya
daidai shi, tattausan hannunshi ya saka ya kama nata a tare suka kalli juna se ya
sakar mata murmushin gefen baki yana d’auke idonshi, seda suka zauna tukun masu
busa suka fice dj ya saki kid’a.
Taro fa yayi taro su Inna de an zama se kallo baki ya mutu murus sun tabbatar na
gaba yayi gaba na baya se labari, Ahhh daga bayansu Iman Hamna ta shigo itama da
gayyar kawayenta da suka ci anko, ita kuma tana sanye da red swiss lace taci
kwalliya seka rantse itace amaryar kawayenta ankon blue suma sukayi sede ba mix
bane irin na su zarah, haushi har wuya zarah taji sede bata ce komai ba, Iman kam
ko a jikinta sema kyaun da suka mata yayinda uban gayyan ko kallon inda suke be yi
ba bare ya tanka.
Mc ya fara gabatar da taro, bayan en gaishe gaishe da jawabai aka kira babbar kawar
Amarya ta bada labarin Amarya fita zarah tayi ta kar’bi mic ta bada biographyn
Amarya sede bata fad’a duka ba iya makaruntun da tayi se halayenta ta fad’i cikin
harshen turanci, aka kira babban abokin ango ma Sauban ne ya fito ya bayar, nan fah
aka fara shagali, buki fah yayi buki ba abinda kake gani se ruwan liki.
Kannen ango aka kira don taka rawa se kawayen amaryar gabad’aya suka fito, suka
cashe gashi basu da kunyar rawa, bayan sun zauna aka sake kiran kawayen amarya su
fito da abokan ango fitowa sukayi aka basu gasar da zasuyi wato na rawa aga waenda
suka fi iyawa kowa kuma shi ze za’bi wakar da za’a sanya mishi, nan fah aka fara ba
laifi abun yayi kyau sossai dayake abokan Abdul shakiyai ne haka kawayen amaryar ma
rawa sukayi kaman ba gobe, kan aka sallamesu bayan kawayen Amarya sunci gasar.
En uwan Amarya aka kira wasu daga ciki suka fito suka d’an tattaka har da su Inna a
filin rawa, bayan sun tafi se Mc ya kira en Annur Hausa Novels wayyo zo kuga rawa,
kowacce rawa tayi na kece raini abin se wadda ya gani😎, bayan sun tafi en wattpad
ma suka fito sukayi nasu daga su fah se na hango en Mukaru da Juna sun fito waai
ashe haka mutanen nan suka iya rawa ban sani ba🤥 Ni sun barni a baya ko hannu ban
iya juyawa da kyau ba bare rawa☹️.
En uwan Abdul fah sun zuba liki ba kad’an ba haka abokanshi, Iman de na zaune tana
kallon kowa waenda suka bata dariya tayi ta murmushi musamman waennan kungiya masu
sonta tsakani da Allah, rawar da har Abdul ma seda yayi murmushi suka sha, bayan
kowa ya gwangwaje aka kira Ango da Amarya su d’an taka se su yanka cake, Abdul ya
fara mikewa tare da mikowa Iman hannu, kallonshi tayi ya lumshe mata ido alamun ta
saka, sanya hannu tayi ya taimaka mata ta mike suka fito, shifa ba wai bai iya rawa
ba sarai ya iya sossai Don duk cikin abokanshi ya fi su iya rawa amma anan be yi ba
se d’an jujjuyawa da yake da ita bayan ya mannota da jikinshi, waiii had’uwa,
kawayenta suka fara fitowa suna mata liki kan abokan ango se en uwa amma banda en
uwanta kayan takaici, bayan sun gama suka karasa inda cake d’insu me hawa kusan
shidda yake,da milk shima akayi Icing d’inshi, bayan an kirga Harrufan sunanta suka
yanka, ita ta fara yanka d’an kad’an ta kai bakinshi da umarnin Mc budewa yayi yana
dafa hannunta ta saka mishi, shima ya yanko ya kai bakinta kad’an ta bud’e ya
sakamata hakan yasa gefen lips d’inta ‘baci, hannu ta sa da niyyar sharewa se yayi
saurin rike hannun ya kura mata ido kur yana kallo itama shi take kallo da
tilastawarshi don ya rike mata ido cikin nashi ya hanata kata’bus, babbar yatsarshi
ya d’aura akan lips d’inta a hankali ya tafi dashi yadda janbakinta baze goge ba ya
cire mata icing d’in shagala sukayi da kallon juna, dj kuwa ya sake musu sautin
wakar soyayya ta turanci me ta’ba zuciya, be san sadda ya fara matsowa gareta ba
har ya had’e fuskansu yana shirin d’aura bakinshi kan nata Hamna ta saki karar da
ya sashi saurin janyewa ya wani basar kaman ba shi ba🤣.
*Wayyo sorry baku jini jiya ba lectures ne ya hanani yi wallahi na dawo na gaji,
amma ga wanna 3288 words hope zakuyi hakuri dani*
🖤Gureenjo🖤
🥀NOOR IMAN🥀
*this page is dedicated to yhu Aisha Gazara Mrs. Bello, Allah ya kara dankon love
yasa bad'i war haka mu gwangwaje, Allah ya barku tare har Aljannah, much love dear*
*028*
Kowa ido ya zuba mata yana kallo har shi uban gayyan kawai se ta mike ta fice da
sauri, tsaki yaja kan ya kama hannun matarshi suka koma mazauninsu, nan aka fara
niyyar cin Abinci serve ur self ne, kowa mikewa yakeyi ya d'ibi abinda ya san ze
iya ci ga abincika kam kala kala, kai na dafe hango Rukayyah farouk, bushira,
herpcert sabee'u, Maman two girls da cool ramcy tsaye kowacce rike da plates d'inta
tana jiran layi ya zo kanta, ban hankara ba fa naji an bankad'e ni har takadda da
birona yayi kasa, a zuciye na d'ago se naga Adama Aliyu, maman khalil, khadija
Queen da Kawata Aisha ne tuni sunyi gaba bama su san sun bangaje ni ba, dariya na
fara ganin suna kokarin yi ma maijidda da Zuwaira Musa satan layi.
Girgiza kai kawai nayi na juya kenan na hango maman habeebty, rabiya basiru, Aysha
Adam, hussaina A sidi da khadeeja hussaini sun shige chan lungu suna dambe akan
cinyar kaza🤣🤣🤣, juyawa nayi na fara neman Namesy na zahra iliyasu, faizadikko, ummu
Ameer, ummu haneef da ummu Aslam Don su zo su raba su amma duk ☹️ ba wadda ya
kulani se ma nunawa da sukayi basu sanni ba don kowacce ta ciko plate da kaji😋.
Ban hankara ba na juya naga abinci ya kare kap neman wadda ze tsammin nashi na
fara, Hanifatulkhair(didi) na fara nufa ta juya kaman bata sanni ba tayi gaba
abinta🥺 Mmn habeebty, mommy Anwar, Mrs Abmin, hajara Aminullah, hadixa da shafa'atu
duk kowa ya hanani ya juyan keya😭.
High table na nufa da sauri kawai naga Smeenarl, meenerl, hasfatsafyan da sameera
Ahmad sun kwashe na gaban Ango kam sun fece ganin yana ta yanga ko kallon inda
abincin yake be yi ba, se bowl d'in fruit salad da ya d'auko tare da sa spoon ya
d'ibo kaman ze sha kuma se ya juya ya kai bakinta, d'ago ido tayi ta kalleshi da
ido ya nuna mata spoon d'in alamun ta sha, a hankali ta bud'e bakinta ya saka mata,
su zarah ne suka takalo camera man suna nuna mishi high table, mastowa yayi ya fara
haskasu ko a jikinshi se ci gaba da bata da yayi itace ma kunya duk ya hanata sakat
dukda ma hankalin kowa be kansu se su inna suna yagan kaza suna kallon kwakwap.
A hankali tace "na koshi hamma" kasa kasa ya kalleta yace "are yhu sure?" Tace "Eh"
kafanta ta ke ta lankwasawa tun kan ya fara bata fruits salad d'in ya lura, cikin
kasa da murya yace "are yhu okey? Your legs me ya samesu?" Cikin daburcewa kaman
wata marar gaskiya Tace "ba komai" Kau da kai yayi ba don ya yarda ba, ana gama
asalin dinner aka fara shirin tashi yanzu ma tare zasu tafi, duk tayi ta duba su
zarah bata gansu ba bata ma san sadda suka fice ba.
Ganin ya mike yana ta sallaman manyan bakin da suka zo yasa itama ta mike ta tsaya
gefenshi iyakaci tayi murmushi shi ke aikin godiya da sallama, kan kace kobo hall
kam ya watse kaman ba yanzu aka gama fad'an kaza ba😜 Su Mmn Nurr da kawata jamila
idris (ummu Afreen) har guzuri seda sukayi, se tsiraran abokanshi da baza'a rasa
ba, tsayuwan da tayi se ya kara karawa kafan gajiya, har wani jiri take ji yana
kwasarta, juyowa yayi ya kalleta ya kuma kallon kafan kan ya kamata ya zaunar da
ita.
Da tsananin mamaki take kallonshi don ganin ya durkusa kan gwiwanshi, zarazaran
yatsunshi ya sanya a hankali a kan fatar kafanta wadda sanyin hannun ya sa ta d'an
razana tsikar jikinta suka tashi, takalmin ya cire mata ya fara mammatsa mata kafan
zuwa kan yatsunta lumshe ido tayi yayinda sauran abokanshi suka saki ihu, ko kula
su be yi ba seda ya gama ya koma d'ayar kafan ya d'an mamatsa mata kan ya kawar da
takalmin.
Ya mike bata hankara ba se jin kanta tayi a sama ya d'auketa chak kaman wata 'yar
tsana, hoto sauban ya matso ya d'aukesu sauran de se dariya sukeyi kunya ya sata
shigar da kanta kirginshi ta sa hannayenta biyu ta zagaye wuyanshi, har mota ya
kaita driver yayi saurin bud'e musu ya sanyata, ya juyo ya d'agawa abokanshi dake
bin bayanshi yatsarshi na tsakiya tare da sakar musu wani munafukin murmushi yana
d'age gira, zaginshi suka fara da sauri ya zagaya ya shiga yayiwa driver hannu suka
fice, dariya me sauti ya d'anyi sanin ya kular da su kuma kaman bashi ne ya d'auka
en Iskan se sun rama.
Itakam kunya yasa ko d'ago kanta ta kasa se mamakin dariyarshi take dama gayen na
dariya? Tsintar magananshi tayi yana cewa "karki sake sa irin takalminchan, ko
daad'in ciwon da yake ji miki kike ji?" Kai ta girgiza, Shiru yayi kaman baze kara
magana ba se kuma yace "wai ke kurma ce?" Da sauri tace "A'a, naji in shaa Allahu
bazan kara sakawa ba" yace "better" suna parking ya sauka har ta bud'e kofa da
niyyar sa kafanta kasa yayi saurin dakatar da ita da cewa.
"kina da hankali kuwa? zaki taka bare foot d'inki kasa bayan kin san ba kyau ga
mace?" Shiru tayi ya d'anyi tsaki kan ya duka ya d'auketa kuyangi da dogaran da
suke arean se kuskus suke ko kallonsu be yi ba ya shiga da ita har parlorn tukun ya
sauketa, a hankali tace "na gode" juyowa yayi ya kalleta se ta dukar da kai, ta
sake cewa "Ina so inyi magana da mama tunda tazo ban ganta ba" da mamaki yake
kallonta Don zatayi waya da mama se ta nemi izininshi?.
Ganin be fa fahimta ba yasa tace "wayana" yace "oopss sorry zan aiko miki later,
shikenan?" Kai ta gyad'a mishi, ya juya ya fice yana cewa "seda safe" ajiyar zuciya
ta sauke kan ta nufi cikin d'aki nan ma bataga zarah ba tooh Ina kuma tayi? Cire
kayan jikinta tayi tare da sanya rigar da ta saka d'azu ba tare da ta saka
d'ankwali ba ta zauna bakin gado tana tunanin en uwanta gaskiya ya kamata taje ta
gansu ace suna gida d'aya amma basu had'uwa!!.
Bud'e kofan bedroom d'in taji anyi dayake ta ba kofan baya so ta d'auka zarah ce
Don ta san kuyangin basa shiga basu nemi izini ba, surutu kawai ta fara tana cewa
"Allah harinyar nan baki had'u ba sam ko kinyi wanka, wa ya gayamiki kawaye na
tafiya gabad'aya su bar amarya?" Bata juya ba bata kuma jira amsan zarah ba ta
d'aura da "ke dama haka yayankin nan yake? Shi be jin kunyan mutane? Da yayi
kissing d'ina yau a wurin nan da inaga kasa ne kawai zata bud'e In shige bazan kara
kallon kowa ba har Abada!!! Waii".
Jin ba'a amsata ba yasa ta juyowa da sauri tana cewa "wai kin san d'a...." makalewa
maganan yayi sbd idonta da ya fad'a cikin nashi yana tsaye jingine da kofa ya
hard'e hannunshi da kirji tare da zuba mata idonshin nan, rasa abinyi tayi
natsuwarta duk ya bar jikinta a lokaci d'aya jikinta ya d'auki rawa, da sauri tayi
kasa da kanta, murmushi ya saki ganin yadda ta rud'e ya kula tana da saurin rud'ewa
musamman In yana wuri, takawa ya farayi a hankali zuwa gabanta yana kare mata
kallo.
Ba laifi yarinyar tana da kyaun jiki ba kad'an ba be ta'ba mata kallo irin haka ba
sbd ta kasa d'ago kanta bare shi ya kauda idonshi gashinta ya mishi kyau sossai
dukda na Hamna yafi nata yawa sede kuma nata yafi mishi kyau da tsari sbd baki ne
sid'ik yayinda na hamna ya kasance ja, nata Virgin ne yayinda hamna ke saka
relaxer, gaskiya baze yarda ta 'bata mishi gashin nan ba.
Don ya ga yadda zatayi yace "yarinyar nan kin raina ni fa, first of all kince
farina irin na zarah da me ma..." ya sa hannu a ha'banshi alamun yana tunani se ya
ce "na ma manta yanzu kuma kince banda kunya, nine marar kunya?" Waro fararen
idanunta tayi a kanshi cikin In ina tace "wallahi ba haka nake..." bakinshi ya ciza
yana kau da ido kanta yayinda ita kuma maganan ya makale ta rasa ma me zata ce
mishi.
Gabanta ya matso sossai ya kama hannunta ya d'aura mata waya, tare da dukowa kanta
yace "kin kyauta tunda zagina abu ne da yake miki daad'i ki ci gaba" ya juya ze
tafi tayi saurin riko hannunshi ba tare da ta sani ba da karfi ya janyo hannunta
yana juyowa ta fad'o jikinshi hannu ya sa ya zagaye kwankwasonta hawayen da suka
cika mata ido ne suka gangaro ta bud'e baki ta ce "dan Allah Kayi hakuri ba zaa.."
bakinshi ya rufe da nata hakan ya sata waro ido shima ita yake kallo da sauri kuma
ta lumshe nata, yayi kissing d'inta son ranshi kan ya saketa yana cewa "first
punishment na zagin farko, night" ba tare da ya jira amsanta ba ya juya ya fice
yana murmushi.
Ta kai mintuna biyar tsaye wurin kaman an dasata hannunta na d'aure bisa saman lips
d'inta ji take kaman har yanzu bakinshi na kan nata, shigowar zarah ne ya dawo da
ita hayyacinta ta sauke hannunta tana kakalo murmushi tace "Ina kika biya ne? Kika
tafi kika barni" zarah tace "wallahi Ummu ce tayi kirana" tayi maganan kaman ba
zarah ba da alamu wani abin na damunta, cikin sanyin murya Iman tace "Lafiya kuwa
me ya faru?" Murmushi zarah ta kakalo tace "kalau" wayan da malabo ya d'aura mata a
hannu ta d'ago Don kallo se taga wata wayar ba nata ba, kaman ma irin na zarah,
sede wannan pink ne yayinda na zarah ya kasance red, matsowa zarah tayi tace "wayan
waye?" Iman tace "yanzu hamma Abdul ya bani" murmushi zarah tayi tace "congrats"
iman tace "thanks" kunna wayar tayi wadda ya kasance iphone X max, dayake tana
kar'ban na zarah ta d'an iya kallon time tayi taga ashe dare yayi sossai bari ta
bari se safe tayi kiran en gidansun.
Don taga sim d'inta ne a kai, zarah de bata kara magana ba ta tu'be kayan jikinta
ta shige toilet da kallo Iman ta bita tabbas akwai abinda ke damunta sede ta kasa
fad'amata ne, Adu'a tayi Allah sa de lafiya ummun take kan ta kwanta tana janyo
blanket ta rufe jikinta tare da lumshe ido tunaninshi gabad'aya ya cika mata
kwakwalwa, wannan wani irin mutum ne shi? Ta rasa gane kanshi, ta rasa dalilinshi
na aurenta sede ta tabbatar duk duniya bata da kamarshi yayi abinda duk mazajenta
basu mata ba, ya taimaketa be mutu kaman yadda hamza ya mutu ba, kuma be mata
wulakanci kaman sadda sauran mazajenta a daren aurenta suke mata ba.
Tana ji zarah ta fito ta shirya cikin kayan bacci tazo ta hau gado ta kwanta ba
tare da ta ko d'auki wayanta ba Zarah da komai gajiyanta se ta danna waya kan take
bacci adu'a tayi mata na Allah ya yayemata damuwarta In bazata iya fad'awa kowa ba,
tana nan tana tunaninshi itama bacci ya tafi da ita ba tare da ta sani ba wani irin
gajiya take ji dama har 'bargonta.
*******
"Wallahi umma bazan iya jira a gama auren nan ba, In ban yi da gaske ba kan a watse
taron nan ze kusanceta In shiga uku, umma bazan iya ganin wata macen kwance kan
kirjin Abdul ba In ba ni ba, tayi kad'an ta dasa min bakin ciki." Ta karasa da
kukanta, umma tace "hamna me yasa kike son tada zaune tsaye bayan na ce miki zamuje
Ai zam....." cikin tsawa tace "umma kissing d'inta fah yayi niyyar yi a bainar
jama'a badon na dakatar dasuba da ba abinda ze hanasu yi, umma kince nayi kwalliya
irin na amare naje nayi amma ko kallo ban isheshi ba, ki duba fah ko event d'aya be
zo ba a bukinmu bayan d'aurin aure wai ayyuka sun mishi yawa amma se gashi a
wannan".
Umma tace "dan Allah ki kwantar da hankalinki Hamna, naji goben da asuba zamu bar
masarautar nan duk abinda nenne zata fad'a sede ta fad'a" share hawayen fuskanta
tayi tana cewa "haba ko ke fa umma" ta tu'be ta kwanta bayan uwarta, In ba
shashanci ba ace wai tana kishin mijinta ne shine tunda tazo garin bata ta'ba zuwa
makwancinshi ba, bata san cinshi ba bare shanshi ko had'uwa sede ta ganshi ya
gitta, Allah ka tsaremu da irin wannan zaman.
*****
Abinda ya faru kuwa da zarah tun kan a gama dinner d'in Anty kalthum ta kirata ta
fad'a mata akwai matsala ummu fah ta kuma rikice musu akan auren nan musamman da
ake event nan se kace wata me aljannu, ta hanata zuwa dinner d'in haka hafeez ma
tace In yaje bata yafe mishi ba, Abdul yaje ma ta hana a barshi ya shiga ganinta
kuma tayi rantsuwa in ya kara bari suka had'a hanya da shi har ya nuna mata
fuskanshi da auren Iman a kanshi se ranshi yayi mugun 'baci.
Itama tana ta nemanta layinta ne yaki shiga, fita zarah tayi ta shiga mota driver
ya ja yana tambayarta Ina tayi, cikin sanyin murya tace mishi gida, gidan ya kaita
har part d'in Ummu, ya bud'e mata ta fice, zata shiga kenan Abba ya rike hannunta,
kallon shi tayi tace "Abba Ina yini" yace "lafiya klau ina daughter na?" Tace "basu
dawo daga dinner ba" yace "Ohk, ina so karki shiga wurin ummunku yau se kun gama
buki karki bar Iman ita kad'ai ba wadda ta sani nan d'in se ke, in da hali ki sa
numbern ummunkun black list zuwa gobe".
Hawaye ne ya gangaro mata tace "Abba me ya samu ummu ne? Ba haka take ba sam ina
zargin akwai wani abu, dukda tana son hamna amma son da take yiwa hamma Abdul yafi
yawa ta ya zatace kar ya kara zuwa inda take In be saki iman ba, Anya Abba ba
chanza mna ita akayi ba?" Abban karan kanshi ya fita zargin hakan kuma duk shima
hankalinshi ba kwance yake ba mamakin rashida sam yaki barinshi, ita macece ba irin
kowacce mace ba tana da hangen nesa da sanin ya kamata duk abinda yake so ko bata
so to fah se ta so amma yanzu ga Abinda take musu ze iya cewa tunda suka shigo ko
magana bata kara mishi ba har yanzu. Cewa yayi "Ki kwantar da hankalinki In aka
watse buki zamu zauna kinji?" Kai ta gyad'a yace "oya je tafi ki kwanta dare yayi"
juyawa tayi tana mishi se da safe, tayi part d'in nenne da kafa dayake ba nisa
sossai da part din Abban, mamaki take yadda Hamma Abdul ke kokarin fara'a da sake
fuska bayan ta san In har ummu na fushi dashi hankalinshi tashi yake kaman wadda
aka mishi albishir da shiga wuta, Da tunanin ta isa hakan ya sa ta kasa sakewa Iman
duk damuwan Sabon halin ummunsu ya dameta.
GIDAN BOKA
*jama'una Ina jin daad'in comments d'inku da irin soyayyar da kuke nunawa book d'in
nan, waenda na kira da waenda ban kira ba irin khadija salisu, sadiya tijjani da
dai sauranku duk kuna cikin raina ba wai na manta bane, Allah ya bar kauna*
🖤Gureenjo🖤
🥀NOOR IMAN🥀
*029*
"Hahahahahhaa Baku da matsala da wannan, Don ko banyi aiki ba akwai me aiki a kanta
baze ta'ba kusantarta ba inba an karya wanchan alkadarin ba, in ya matsa kuwa komai
ze iya faruwa da shi har ita karan kanta, hahahahhaa" da mamaki Umma tace "wani
irin aiki kenan yake kanta boka? Naka ne?" Wani dariyar ya kumayi yace "ba
huruminku bane kuma In kun matsa komai ka iya faruwa".
Hamna tace "to boka batun mahaifiyarshi naga kaman ta sakankance da maganar auren
ba kaman farko ba" nan ma dariya yayi kan yace "yaro yaro ne, Ai tashin hankalin da
muke kara sa mata akan auren ko uwarki wannan bazata iya d'auka ba se ta tsinewa
d'an, kaman yadda na gayamuku da farko akwai babban al'amari a kanta duk randa ya
karye kuwa ni zan dasa mata nawa, zakuma ki iya tarewa gidansu ba wadda ze ce dake
komai a kai, lokacin ku ya kare ku sallameni maza ku tattara ku bar nan".
Kud'i umma ta zuba mishi kan suka mike suna mishi kirari da munmunar kalamai yana
washe baki har suka fita, a cikin mota se tunanin wani irin al'amari ne boka ke
magana hamna keyi ta kasa Shiru ta fara tambayar umma, umma ce ta hanata tana cewa
"baki ji abinda yace ba kar ki matsa da bincike? Toh kar na kara ji kinyi maganan"
Shiru duk sukayi ba su suka iso masarauta ba se dare basu san me akayi a gidan da
safe ba bare rana.
******
Tunda suka farka daga bacci har sukayi wanka suka zauna karyawa Zarah bata ce komai
ba, abin se ya dami Noor cikin jin wani iri tace "Zarah ko akwai abinda na aikata
gareki ne cikin rashin sani?" Da sauri zarah tace "ko d'aya wallahi ba wani abu"
iman tace "to me yasa kika koma haka? Ko akwai wani abu da ze iya samunki wadda ban
kai In sani ba?" Zarah ta kuma cewa "ko d'aya iman ban son damuwana ya shafeki har
ya 'bata miki mood kinga yau akwai event wadda shine na karshe, sannan damuwar fa
ba wani damuwa bane na azo a gani, in kin koshi tashi mu fara makeup kan waenchan
tsuntsayen suzo su damu mutum".
Murmushi Iman tayi kan ta mike kuyangar dake jiran su gama ci ta tattare ta fara
tatarewa a tsanake har ta gama ta fice da trays d'in, zama sukayi zarah ta janyo
Kit d'inta ta 'bud'e suka fara, ba me cewa komai chan wayan Zarah ya d'auki kara,
kallon fuskan wayan tayi da mamaki ta d'ago wayan ganin Muhammad, akan lips d'inta
ta furta 'hammad!!' Har seda ya kusa tsinkewa kan ta d'aga.
Cikin excitement yace "masha Allah na mata murna sossai, Allah ya basu zaman lafiya
da zuri'a d'ayyiba" Tace "Ameen, se anjima" yace "wait wait madam Ai ban gama
maganan ba" Tace "uhmm" murmushi yayi kan yace "wata biyar aka bani In fidda mata
In ba haka ba Amin auren dole...." katse shi tayi da "Allah sarki se ka fitar ba"
yayi murmushi ya fahimci ta fuskanci abinda yake son fad'i amma take fuskewa yace
"Da farko da naga Iman se zuciyana ya bani duk duniya ba wacce zan iya zaman aure
da ita inba ita ba, bazan boye miki ba sonta lokaci d'aya ya shiga zuciyana kaman
abin asiri se kuma Mom taki auren namu irin kin da banyi zato ba, se kuma nayi sa'a
babba a ranar da na rabu da Iman washegarin na samu wata me irin halayen Iman, duk
kwanakin da suka shud'en nan tana cikin raina daram na kasa fidda ta da tunaninta
nake kwana dashi nake tashi".
Kwa'be fuska tayi tace "congrats to ni me nawa a ciki ko kasa fad'amata kayi shine
zaka wakilceni gani bbc" dariya yayi har Iman seda ta dara dukda ba jin abinda
d'ayar bangaren yake fad'a ba take, on top of that bata ma san wayene ba, cewa yayi
"a'a ko d'aya, tabbas wakiltanki zanyi zuwa ga Zuciyarki ki bata Sakon zuciyata,
zuciyata tace "tana mata so irin na tsakani da Allah" wani irin dariyar rainin
hankali Zarah tayi kan tace "Allah ya baka lafiya" ta kashe wayanta tana tsaki.
Dariya iman tayi tana girgiza kai "Allah ya shiryaki zarah" d'an murmushi zarah
tayi kan tace "Ameen ooo" ci gaba sukayi da makeup d'insu bayan sun gama ta shirya
cikin Sky blue gown da ya matukar Amsanta zarah ta kafa mata head nan ya zauna
d'as, hill ta d'auko mata wadda yasa zarah waro ido tuna fa ya hanata saka hill,
"a'a zarah bazan saka wannan ba samomin flat shoe kafana na ciwo" har zata musa se
kuma ta fasa ta kawo irin half cover na sarauta me lankwasa ta gaba irin ta mata ta
ajiye mata blue.
Alkwabbar da ta sanya ma blue ne me adon fari tayi kyau har ta gaji, hotuna zarah
ta dinga mata tana cewa "yau fah akwai comments insta bakiga yadda aurenku ke
trending ba duk inda kika shiga zaki ga Noorheem" iman tace "dan Allah dae? Ai duk
kece na sani yanzu fisabilillahi se in na koma school ayi ta kallona ana nunani kin
san kowa rayuwar instan nan yake" dariya zarah tayi tana cewa "to se me? Daad'in
abinde matarshi za'a ce ba karuwarshi ba, ke Ai tun randa aka d'aura aure nake
samun followers kaman hauka sbd posts d'in hotunanki da na ango kuma wallahi ya
gani ubana ze ci".
Dariya Iman tayi zatayi magana aka turo kofa aka shigo Anty Rahma ce da Su Teema,
da gudu zarah taje ta rungumeta tana mata oyoyo, "Sannu da dawowa Anty" iman ta
fad'a cikin sanyi, gabanta Anty rahma ta karasa tana cewa "masha Allah,
tabarakallah zarah aikinki na kyau tun daga dubai nake ta kallon hotunan buki a
Instagram gaskiya habeebty kinyi kyau sossai" a kunyace Iman Tace "na gode Anty".
Zarah tace "Anty Ina boxes d'in?" Anty rahma tace "suna Kano chan na sa aka kai
Abban su Halima yaje ya d'auka suna gidana in munje se akai gidansu su gani tukun a
dawo mata dashi gidanta" tura baki Zarah tayi tace "kash na so nan aka kawo na
kashe kwarkwatar idona" teema tace "Allah kuwa da nan aka kawo" Nabeeha Tace "tunda
ana hutu ko zamu roki mommy ta roka mana dad ya barmu mu tafi kanon hutu?" Zee tace
"wallahi kuwa Allah de yasa zasu yadda" a tare suka ce Ameen gabad'aya, teema tace
"Dada fa na jiran amarya tace mu duba ne ko ta gama shiri a fita da ita zasu wuce
filin kilisar" zarah tace "Ai ta gama shiri ku fita da ita zan zo daga baya kinga
ko powder ban shafa ba" Nabeeha ce ta kama hannunta suka mike suka fice, su teema
suka rufa musu baya duk sun ci kwalliya kaman ba gobe.
Zama zarah tayi tana sauke ajiyar zuciya bayan fitansu Anty Rahma tace "Lafiya kuwa
Auta me ke faruwa ne?" Zarah tayi shiru na mintuna kan ta fara bawa Anty rahma
labari tana hawaye bayan ta gama ta d'aura da "Anty bakya zaton asiri akayiwa ummu?
Abin yayi yawa gashi mun rasa mafita" Daga bakin kofa suka ji ance "ba mamaki ze
iya yiwuwa ze kuma iya kasancewa ba haka ba, dama abu irin haka na faruwa shine
Ahmad be fad'amin ba? Me ya d'aukeni?".
Anty rahma tace "ba haka bane nenne be son hankalinku ya tashi ne a fara samun
matsala da ummu bayan tun tashinta ba'a ta'ba samun matsala da ita ba tsakaninku,
amma Ai ya fad'awa su baba galadima" Nenne tace "dukda haka, yau da yamma zamu
zauna gabad'aya aji me matsalar mahaifiyarkun In ba haka ba zata iya tursasa Abdul
ya saki matarshi wadda In hakan ta faru kuwa Za'a samu matsala babba Don wallahi ba
yarda zanyi ba" fita tayi tana me ci gaba da mita.
******
Suna fita aka d'auketa a mota Su Teema suka shiga na baya aka ja suka fice, katon
filin masarautar da ake kilisa nan suka nufa canopy's da aka kakaffa a gefen filin
suka yada zango inda kujerar da aka tanadar mata zama tayi nabeeha ta mayar mata da
hulan baya sossai yadda zata dinga ganin abinda akeyi, mutane ne kad'an ba yawa
iyakaci na cikin masarautar wato family ba'a gayyaci kowa ba bayan haka.
Idon da zata d'aga se ya fad'a cikin nashi ido ya kashe mata guda d'aya yana sakin
wani murmushin iyayi, da sauri ta kau da kanta yayi kyau kuwa cikin bakaken sport
wears da mutanenshi gefenshi duk wurin abokanshi ne family friends 'ya'yan uncles
d'inshi sunyi su goma duk kuma sport wears ne jikinsu ance suyi da kayan sarauta
sunki wai karin nauyi ne ze hanasu gasa me kyau.
Layi sukayi shi yana daga tsakiya, wani abu aka hura da bata san me ba se kawai
taga sun hau gudu da dawakansu, wani irin tsere sukeyi da ya bata tsoro su ko
tsoron fad'owa basayi? Har karshen filin suka je da nisa sossai daga inda suke kan
suka sake juyowa suka dawo zuwa d'aya 'bangaren shima har karshe kan suka sake
kwasowa zuwa tsakiyar filin inda aka fara tseren shine gaba kuma shi ya fara isowa.
Ihu dogaran wurin suka saki suna mishi kirari, murmushi kawai yayi be sauka daga
kan dokin ba ya kar'bi towel da ruwa ya sha ya d'an share gumi kan ya buga kafanshi
dokin ya zabura sukayi gaba ba gudu yakeyi ba yanzu kam idonta na kanshi har ya
kule cikin masarautar ya nufa, sauran ma kowa sauka yayi aka kar'bi dowakan akayi
gaba dasu suma kowanne ya nufi cikin masarauta.
Alqaita da ganga irin ta sarauta aka fara a filin tana son kid'an har ranta shiyasa
ta natsu tana ta aikin kallonsu har mamaki take kumatun masu hura alqaitar nan be
ciwo, ta raja'a da kallonsu da tunani har bata san Ya dawo ba se kamshinshi ne ya
sanar da ita zuwanshi, d'ago kai tayi ta ganshi tsaye yana sake murmushi, Dada ce
ta taso ta zo gabansu tana cewa "Ango ga amaryarka daga nan ka san inda zakayi da
ita Ai" Da mamakin irin wannan tsari nasu take kallon Dada shi ze tafi da ita ba
kaita za'ayi ba?.
Sanye yake cikin bakaken riga da wando masu taushi irin na asalin sarauta, sunsha
ado da zare farare alkyabbar jikinshi ma baki da fararen ado a jiki, takalmin
kafanshima na asalin sarauta ne baki, rawanin nan ya zauna mishi d'as yayi kyau woo
kaman In sato muku shi ku ganshi, ajiyar zuciya ta sauke jin hannunshi cikin nata,
mikewa tayi a zuciyarta kuma tana mamakin me ya hana en uwanta zuwa wannan event
d'in? Bata ga ko d'ayansu ba.
Wata had'ad'iyar mota aka kawo shi ya bud'e mata ta shiga kan ya zagaya aka bud'e
mishi ya shiga, driver yaja part d'in baba yarima suka fara zuwa, suka mika gaisuwa
dattijo me mutunci Haka iyalanshi kowacce seda ta mata kyautar ban girma, kuyangi
na kar'ba suna mika godiyarta, daga nan part d'in baba galadima sukayi shima de the
same thing nasiha me ratsa jiki ya musu kan yayi mata kyautar mota, godiya tayi
sossai har seda tayi hawaye yau itace da mota? Alhamdulillah tayi ta nanatawa
tabbas Abdulraheem Alkhairi ne a rayuwarta daga shi har Zarah sun kasance mata
fitila masu haska mata hanyar duhun rayuwarta.
Nenne petel ma gwal tayi mata kyautarshi kaman ba jikarsu bace kishiyarta ya kamata
daga nan suje wurin ummu ne amma gargad'inta gareshi yasa be ma yi Gigin kaita ba,
suka wuce sashin mai martaba, wai itakam taga karamci dattijo ne me kwarjini da
kamala nasihar da ya musu har kuka seda tayi Allah sarki rayuwa, mutanen nan sun
mata abinda ko da za'ayi duniya sau nawa inde iyayentan nan ne basu isa yi mata ba.
Kyautar shanukai goma, tumakai goma da salwa ashirin, baru irin na turai manyan nan
suma ashirin, se zabbi ashirin da d'awisu guda biyu, qur'ani da sallaya masu
azababben kyau sarki ya mata, godiya ta dinga mishi har seda yace mata ya isa haka,
ficewa sukayi zuwa wurin nenne, itama nasihar ta musu kan tayiwa Iman kyautar wani
Box da bansan menene ciki ba, godiya sukayi kan suka fito zuwa mota kuka ta saka
tana ajiye kanta kan kafad'anshi "Bani da bakin gode maku kai da zarah sede har
abada bazan ta'ba manta abinda kukayimin ba, zaku zauna cikin raina har gaban
abada, kaman yadda bazan ta'ba mancewa da kaina cikin adu'o'i na ba haka kuma bazan
ta'ba mantawa daku ba, In har na manta ku to fa na manta kaina ne, zan yi iya
kokarina wurin ganin nayi zaman amana gidan aurena bazan ta'ba sanadiyar bullowar
wata fitina ba In shaa Allahu".
Kanta ya shafa yace "ya isa haka kukan nan plz, you promised not to cry again
right? So is ok" Shiru tayi bata d'ago daga kafad'anshin ba har suka isa part d'in
mama, iso aka musu sun jima kan aka basu damar shiga, zama sukayi suna gaidata ta
amsawa Abdul kam shima da kyar amma Iman kam kallon wulakanci ta mata taja tsaki,
ta so Abdul ya auri jikarta tun kan hamna amma yaki aka zo aka aura mishi hamna,
bayan duk cikin masarautar ba wadda be san niyyar ta ba shine da ze kara me makon
su neme ta se suka aura mishi wannan bakar yarinyar.
Ganin bata amsawa Iman bane yasa shi mikewa yace "mun barki lafiya" ya taimkaa mata
ta mike ya kama hannunta suka fice tsaki me karfi taja wadda su kansu seda suka ji,
sam bata damu da abinda maman ta mata ba ita tunaninta ma na ga en uwanta ko me ya
hanasu zuwa? Kasa Shiru tayi tace "Su Mama sun tafi ne?" Kaman baze amsa ba se kuma
yace "suna nan" Shiru tayi ganin ya kau da kanshi.
Kenan ba'a gayyacesu event d'in d'azu bane ko basu ga saman zuwa bane, ashe anje
akan su fito su tafi event d'in suka ce sun gaji baza su iya zuwa ba, daga site
d'in mama inda aka sauke en uwanta sukayi ba tare da ta sani ba, kuyangin kofa ne
suka sanar da isowansu kan shigansu ciki, a parlor suka samu familyn baje, murnan
ganin en uwanta ne ya kamata yayinda su kuma suke wani yatsina fuska, har kasa ya
duka ya gaidasu suka amsa kaman basa so musamman inna, itama gaishesu tayi basu
amsa ba se d'aid'aiku karfin hali tayi tace "ina Mama?" Wata daga ciki tace "tana
d'aki bata da lafiya kwa iya shiga" shiga sukayi tana kwance kan gado lullu'be da
blanket.
Da sauri iman ta karasa kanta tana hawaye tace "Mama me ya sameki haka? Me ke
damunki? Mama me yasa baki fad'amin ba?" Murmushi tayi kan tace "Da sauki Iman
karki damu kinji? Zazza'bi ne kawai" Abdul ma gaisheta yayi yana mata Sannu da jiki
ta amsa kan ta d'aura da "Abdulraheem ga amanar Iman na baka duniya da lahira yanzu
bata da kowa sama da kai dan Allah ka riketa amana, kayi mata adalci a rayuwanta ka
zama daban cikin saraun mazanta".
Yace "In shaa Allahu Mama zaki sameni me cika alkawari" godiya ta mishi tana
murmushi Tace "kayya iman me kuma na kukan nan eye? Naji sauki tashi maza kibi
mijinki kiyi mishi biyayya iya iyawarki, ki zama mata ta gari ki tabbatar kinyi
anfani da maganganun da na jima Ina gayamiki akan rayuwar duniya da kuma zaman aure
na Sanki da hakuri ki kara akan na da, kinji? Allah ya miki albarka".
Kuka sossai Iman ke yi ya mike yana cewa "Mama za'azo a kaki asibiti, Allah
ubangiji ya baki lafiya" Da Ameen ta amsa, hannunta ya kama suka fito parlorn tana
me ci gaba da kukanta har sun nufi kofa Inna tace "ke saude dakata" tsayawa sukayi
ta juyo shikam ko motsi be yi ba, goggo saratu tace "Allah sarki bawan Allah abin
tausayi baya cikin hayyacinshi" goggo kamila tace "wallahi kuwa daga gani ka san
aikin asiri ne" inna tace "wani irin boka kike anfani dashi ne Saude? Allah wadaran
naki ya lalace yanzu duk mazan da kika aura kika kashe wasu kika kassara wasu be
isheki ba se kin had'a da wannan kamilallen da bai Dace dake ba?".
Iman zatayi magana kenan taji yace "Allah sarki baby Ashe boka kika samu ya
mallakeni? Da kuwa zan ganshi da na kara mishi kud'i ya kara mallaka miki ni se
yadda kikayi dani" gira ya d'aga mata yana wani murmushi yace "Bazaki san irin son
da nake miki ba Allah, sonki kaman ze huda nan ya fito" ya karasa yana nuna mata
kirjinshi, waro ido tayi ya kashe mata ido yana me jan hannunta jikinshi ya zagaye
kwankwasonta da d'ayan yace "bazan ta'ba iya rayuwa ba ke ba, don't you ever think
of leaving me Ohk?" Tsantsar mamaki ne ya sata d'aga kai bata ma sani ba juyawa
yayi ya sakarwa su inna murmushi kan ya jata sukayi waje wayyo ina wuta Inna ta
saka Abdulraheem🤣🤣🤣, dama zargin dole aka mata sukeyi to gashi ya basu kunya ya
watsa musu tulin kasa a ido.
🖤Gureenjo🖤
🥀NOOR IMAN🥀
*030*
Suna fita ya saketa yana jan karamin tsaki, karamin murmushi tayi se yanzu ta gane
sbd su yayi Don ya nuna musu ba auren tushe aka mishi ba, kuma ba laifi taji
daad'in hakan, mota suka shiga aka wuce da su part d'insu dake kusa sossai da part
d'in su Abba, babban parlor ne irin babban nan, a ciki katon kitchen d'insu yake
guda d'aya se d'akuna guda uku a jere na hagun ya nufa itama tabi bayanshi har
ciki, wow royal set ne a d'akin komai da komai golden, sossai d'akin ya mata kyau
kasancewarta me son royal sets, a tsakiyar d'akin ya dakata kan ya juyo ya kalleta
se ta dukar da kai.
"Ga room d'inki nan Zarah zata kawo miki kayanki gobe in Allah ya kaimu zamu wuce
sbd school d'inki" a hankali tace "Toh na gode" fita yayi itakuma ta zare alkyabbar
jikinta da d'ankwalin kanta tana zama bakin gado, yanzu wai nan ne d'akinta? Na
garin nan kenan da zuwa kawai zasu dingayi Ina kuma na kano da Abba ya d'auki
nauyin yi mata kayan d'aki? Tana nan zaune Zarah ta shigo.
Murmushi suka sakarwa juna kan tace "se yanzu kika gama kwalliyar kenan?" Zarah
tace "bazaki gane bane, yanzu ga Akwatinki nan duk abinda zaki bukata yana ciki,
bari In wuce" hararanta Iman tayi tace "zuwa Ina? Zama zakiyi madam ni kad'ai zaki
bari nan?" Dariya zarah ta saka tana cewa "Lallai matarnan dama tare zamu zauna?
Kinga tafiyata bye bye se mun had'u gobe a kulamin da yayana" da sauri Iman ta
tashi zata riketa da gudu zarah ta fice tana dariya.
Dawowa tayi tana dafe Kai ta zauna bakin gadon again, har Tv me d'auke da receiver
da kuma Fridge akwai a d'akin da kujera dogo royal guda d'aya gabanshi akwai center
table shima de cikin sets d'in royal d'inne, se gadonta da wall to wall drawer
d'inta me madubi tsakiya, d'ayan 'bangaren kuma kusa da wani kofa dressing mirror
ne me azababben kyau.
Ga dukkan alamu kofan na toilet ne, mikewa tayi ta cire kayan jikintan Don ya
isheta akwati ta bud'e ta d'auko towel d'inta da a jiya komai na ciki ta fara
anfani da su, d'aurawa tayi ta nad'e kayan ta ajiye bakin gado ta d'auki sponge da
liquid soap da shima jiya nenne ta had'o mata ta fad'a toilet wanka tayi, dayake a
jiyan Zarah ta nuna mata duk yadda zatayi anfani da irin toilet d'insu, toilet
d'inma kanshi abin kallo ne.
Sanin ita kad'aice kuma ba shigowa ze yi ba yasa ta fito da towel abinta, shafa mai
tayi ta feshe jikinta da turaruka kan ta d'auko wata doguwar rigar atampha straight
gown ta saka ya amshi jikinta sossai ta fito a amaryarta, dayake ta iya d'auri
sossai haka ta kafashi a kanta, wayanta ta d'auka tayi kiran Mama seda ya kusa
katsewa kan taji an d'aga "hello mama ya jikin? An kaiki asibitin" muryanshi taji
yace "an mata allura she's sleeping" da mamakin taya akayi wayan Mama ya shiga
hannunshi tace "kuna asibitin ne?" Yace "yeah but drip d'in da aka sa mata na
karewa zamu taho" Tace "Toh Allah ya kara sauki" Da Ameen ya amsa kan ya kashe
wayan.
So take tace zata zo amma tana tsoro, tv ta kunna ta fara kallo ganin shima be mata
ba yasa ta mike ta fito parlor a kan kujera ta kwanta tana tunanin inda rayuwa ya
kawota, har bata san bacci yayi awon gaba da itaba, se da akayi azahar kan ya nufo
part d'inshi duk a gajiye yake bukin nan ba karamin gajiyar dashi yayi ba gashi har
yanzu be huta ba, tsaki ya ja yana tura kofan parlorn.
Fitowa yayi yana tunanin Ina itakuma tayi har ya wuce ya sake dawowa ya zagayo
cikin parlorn dayake ta bayan kujerun hanyar d'akukansu suke, ganinta yayi tana
baccinta hankali kwance akan doguwar kujera, da ido ya kafeta fuskanta fayau ba ko
d'igon kwalliya se tafi mishi kyau akan da kwalliya, lura yayi da tana jin daad'in
baccinta sossi hakan ya sa yaki tashinta ya juya ze tafi kenan tayi wani irin juyi
saura kad'an ta hantsilo da azama ya tareta chak ya d'agata ba tare da tunanin
komai ba ya kaita d'aki kan gado ya shimfid'eta yana zame mata d'ankwalin kanta.
Ya shafa kan a hankali kan ya mike ya fito yayi tafiyarshi masallaci, daga nan part
d'in me martaba yayi a babban parlornshi ya sameshi zaune bayan an mishi iso, a
kasa ya zauna yana gaida dattijon Amsawa yayi yana tambayarshi Ina amaryarshi
dariya kawai Abdul yayi, suka fara hira da kakan nashi akan matsalan Noor ne duk
hiran ya karkata inda yake fad'amishi yaji labarinta gabad'aya a wurin nenne why
not kan su wuce su je fufore wurin malam.
Abdul yace "mai martaba tafiyarmu fuforen nan da wuya tana makaranta lectures
dayawa zuwa yanzu sun wuceta, and ni a ganina hasashen nenne ne kawai, bawa kaddara
be isa fad'amishi ba seda asiri? Amma In kana ganin muje d'in zamu je idan munzo
sallah karama tunda azumi ya gabato" mai martaba ya d'anyi shiru yana nazari tabbas
maganan nenne ba hasashe bane akwai ayar tambaya akan Matar tashi amma tunda yace
In sun zo azumi zasu je shikenan.
"Toh Allah ya kaimu da rai da lafiya" Abdul ya amsa da ameen ya Allah, Abba ne da
baba yarima da kuma baba galadima suka shigo a tare da sallama, mai martaba da
malabo suka amsa a tare, zama sukayi duk a kasa suna kara gaida mai martaba amsawa
yayi da fara'a, basu jima da zama ba nenne da mama suka shigo, Se ga Nenne petel ma
ta shigo duk gaisuwa suka mikawa mai martaba ummu ce karshen shigowa itada rahama
suka shigo.
Suka gaida iyayensu yayinda Abdul ya gaisheta kaman bata ji ba haka tayi kanshi ya
dukar cikin kunar rai, gyaran murya me martaba yayi kan yace "Ina uwargidan nawa?"
Yayi maganan yana duban Abdul cikin sanyin murya yace "Allah sene banda masaniyar
inda take rabona da ita tunda muka shigo masarautar nan" kwafa nenne tayi baba
galadima ya kalli nenne petel yace "suna ina ne?".
Nenne petel tace "A min aikin gafara mai martaba banda masaniyar bada izinin
mijinta take zaune part d'ina ba, tun safe suka fita da mahaifiyarta akan zasu je
yanzu su dawo har yanzu basu dawo ba kuma wayoyinsu duk basa shiga" girgiza kai mai
martaba yayi kan ya kalli ummu yace "Rashida" d'agowa tayi tana furta "Allah ya
kara tsawon rai" yace "menene matsalarki akan auren Abdulraheem?" Gyara zama tayi
tace "mai martaba yarinyar fa aurenta biyar sannan na samu labarin duk inda ta
zauna se ta raba kan mutane da munafurci irin nata musamman uwar miji da shi mijin
da take aure".
Murmushi irin na manya yayi kan yace "Shine dalilin da yasa kika ce d'anki kar ya
kara nuna miki fuskanshi?" Kai ta gyad'a tana karawa da "mai martaba har fa ciki ta
zubar kwanan nan" Baba galadima yace "Rashida ki kiyayeni kin tabbatar?" Zatayi
magana mai martaba yace "Abdulraheem" Malabo da baba galadima a tare suka d'ago
yana kallon Malabo yace "kirawo matarka" mikewa Abdul yayi ya fita.
Mota ya hau zuwa part din shi don be san ko ta tashi daga baccinta ba In ma ta
tashi be da tabbacin In ya kirata a waya zata iya kawo kanta sashin me martaba, da
sauri ya shiga d'akinta har yanzu bacci takeyi, kanta yayi a hankali yake d'an
bubbuga hanunta yace "Saudah! Saudah!!" Idanunta ta bud'e ta zuba mishi da sauri ya
kawar da nashi jin wani abu ya tsarga mishi sbd ganin sleeping eyes d'inta.
"Tashi me martaba na son ganinki" da sauri ta mike zaune   zatayi mishi tamabaya yace
"ina jiranki parlor" yana kai nan ya fita, bayi ta shiga   ta wanke fuskanta da sauri
ta fito ta d'auki d'ankwalinta ta d'aura tare da d'aukan   alkyabbar d'azu ta saka ta
zuro flat shoe ta fito, dafe da Kai ta ganshi har ta iso   kusa dashi be sani ba seda
tace "hamma muje" kan ya d'ago ya d'an kalleta ya kau da   kai.
Gabanta ne yayi mummunar fad'uwa ganin yadda idonshi yayi ja, be bata daman tambaya
ba har suka iso se sake sake kawai take, a tare suka zauna tana mika gaisuwanta
zuwa ga mai martaba ya amsa da fara'a kan ta gaida sauran mutane parlorn duk sun
amsa banda ummu, mai martaba yace "Saudah zaki iya bamu labarinki?" Ajiyar zuciya
ta sauke kan ta fara bayarwa a hankali tun muryanta na rawa har ta fara Hawaye tun
tana hawaye har ya koma kuka sossai.
Wani irin tsuma jikin malabo ke yi dukda ya ji daga bakin zarah amma se yanzu da
take fad'a da bakinta yaji tafi bashi ainihin tausayi be san sadda ya d'aura hannu
a bayanta yana shafawa a hankali ba, har ta kai aya, matan ma seda suka kuma mata
hawaye banda Ummu da mama da suke ta ta'be baki, mai martaba kanshi ya tausaya
mata, kallon ummu yayi yace "yanzu yarinyar da ta fuskanci irin wannan taskun kike
son kara d'aura mata wani? Kiji tausayinta mana rashida yanzu idan Zarah ce ta
fuskanci irin wannan ibtila'in baza ki so uwar mijinta ta so ta ba?".
Shiru duk sukayi zatayi magana Baba galadima ya daka mata tsawa "Rashida Anya kuwa?
Kina kuwa son gamawa da duniya lafiya? Kar fa ki kasance cikin waenda Allah yayi
maganarsu a hadisi zaki ga suna aikata aiki na gari se mutuwa ya riskesu su aikata
akasin haka su shiga wuta, Toh ki maida hankalinki kiji da kyau Wallahi wallahi
wallahi duk randa kika sa me suna ya rabu da matarshi ki tabbatar kaman kin rabu da
mu ne har abada, kallon Abba yayi yace "Ahmad" Abba ya amsa yana kallon matar tashi
dake kuka tana ganin fa kaman duk baza su fahimci abinda take jiyewa d'anta ba.
Gani take kaman duk labarin da Iman ta bayar karya ne ita ta tsara kayanta ta
fad'a, "For the first time a rayuwana zan rokeka alfarma" Abba yace "baba ka fad'i
duk abinda kake so in Allah ya yarda ni me cika maka umarninka ne" Baba galadima
yace "Ina so ka fad'a da bakinka mu zama sheda duk randa ta sa d'anta sakin
matarshi a bakin aurenta, In ta ga dama kar ta amsa gaisuwarshi har abada".
Iman sossai ta shiga tashin hankali fahimtar abinda ke faruwa anan Ummu bata sonta
bata son aurenta da Abdul, kallonshi tayi kenan shine sanadin damuwanshi
mahaifiyarshi bata amsa mishi magana, cikin rawar murya ta bud'e baki zatayi magana
nenne dake gefenta ta kama hannunta kallonta tayi se ta girgiza mata kai alamun kar
ta ce komai shiru tayi ba don tayi niyya ba, tana ji Abba ya maimaitawa ummu.
Mai martaba ne ya fara mata nasiha da duk ba fahimta take ba itafa Iman ta zama
mata annoba a family d'inta tunda duk sbd ita suka za'ba ba wadda ke goya mata
baya, yana gama nasiharshi ta tashi ta fice ba tare da ta bada hakuri ba bare ta
nuna taji, Nenne petel ce ta share hawayen fuskanta tana gyad'a kai yanzu ta
tabbatar da abinda take zargi In ba aljannu bane suka shigi Rashida to fa asiri ne
a kanta, zata bi duk hanyar da zatabi taga er ta ta koma kanta In shaa Allahu.
Sallamansu me martaba yayi bayan kowa ya d'an kwantarwa da Abdul hankali akan kar
ya damu mahaifiyarshi zata sauko ne da kanta, mikewa yayi Iman ta mike suka fice
har suka isa part d'insu kuka take cikin rud'ani yanzu ta raba shi da
mahaifiyarshi? Duk irin son da zarah ta fad'amata sunayiwa juna tayi ajalinshi
Innalillahi wainna ilaihi rajiun nan kuma matsalar kenan?.
A parlorn ya zube yana kuma dafe kanshi bayan damuwanshi, kukanta yake ji har kasan
zuciyarshi, a gabanshi ta zauna ta ci gaba da kukanta, wani irin tsawa ya dakata
"will you just shut up and leave me alone? Haba da wanne kike so naji?" Me makon
tayi yadda yace se ta fad'a jikinshi ta kuma rushewa da kuka runtse idanunshi yayi
tare da amsanta ya zagayeta a hannayenshi, batayi aune ba taji bakinshi cikin nata,
tsit kakeji kukan ya tsaya se numfashin da take ta ajiyewa, shi kuwa yayi hakanne
don tayi shiru ne amma kuma se yaji abin na neman fin tunaninshi.
🖤Gureenjo🖤
🥀NOOR IMAN🥀
*Wannan page d'in naku ne masoya wannan littafin, Ina godiya kuma Ina jin daad'in
comments d'inku, Allah ya bar kauna*
*031*
A hankali ya d'agota yana kallonta da tsantsar mamaki wai bacci tayi d'an girgizata
yayi yaga fa tsakaninta da Allah bacci tayi a fili ya furta "ikon Allah" kan ya
mike da ita a hannunshi yaje ya kwantar da ita se kuma ya tuna batayi sallahn
azahar ba, fuskanta ya fara shafawa yana kiran sunanta a hankali, da kyar ta bud'e
sexy eyes d'inta ta zuba mishi idanunshi ya kawar yace "tashi kiyi sallah kici
abinci se kiyi baccin" yana kai nan ya mike ya fice, da kyar ta mike tayo alwala
tazo tayi sallah kanta kaman ze tsage haka take jinshi.
Sallama taji anayi wadda hakan yasa ta mike ta fito parlorn ko d'an kwali bata
d'aura ba, kuyangu ne rike da trays sunyi hud'u, kan dining dake gefen parlorn ta
nuna musu suka ajiye, godiya ta musu kan suka fice ta juya da nufin komawa kenan
taji an bud'e kofan dake tsakiya dakatawa tayi se taga shine, juyawa tayi da nufin
komawa taji yace "Ina kuma zaki?" Tsayawa tayi be kara kula ta ba ya nufi dinning.
Abinci ya d'iba da d'an yawa Don ko breakfast be yi ba, ba tare da wani damuwa ba
ya hau cin kayanshi, gajiya tayi da tsayuwar hakan ya sa ta nufi dinning d'in har
ta ja kujera zata zauna yace "koma ki sa d'ankwali" baki ta tura ya d'an kalli lips
d'in kan ya kalleta ya kau da kai, d'aki ta koma ta sanyo d'ankwalin ta zauna ta
d'ibi abincin kad'an ta fara ci tana dafe kai.
Ya jima da gamawa yana zaune ne kawai yana aikin kallon abinda take yi cin abincin
take kaman me cin magani tana 'bata fuska hannunta dafe da kai, mikewa yayi ya
shiga d'akinshi chan ya fito da paracetamol ya ajiye mata a gefenta a hankali tace
"thanks" kan ya juya yayi komawanshi, bayan ta gama cin abincin kuwa ta sha, a
wurin ta bar komai to ko ta tattare bata san inda zata kai sauran abincin ba.
Kwanciya taje tayi bacci ya kuma surarta ba ita ta farka ba se la'asar wasai taji
ta ba ciwon kan kuma, sallah tayi ta zauna danna waya, Instagram ta shiga tana ta
kallon hutunan bukin mutane, wani wadda ta gani nasu da wasu account suka sa ne ya
mata kyau sossai, wadda ya duka a gabanta hannunshi na kan takalminta yana cirewa
ita kuma tana d'an lekan abinda yakeyi hoton yayi kyau sossai dukda sides d'in su
ne ba full ba.
Saving tayi a wayanta ta koma settings ta d'aura shi a wallpaper d'inta yayi kyau
sossai kuwa tunawa tayi da bata mishi godiyan wayan ba, to yanzu ita ta Ina zata
mishi godiyan? Ta'be baki tayi ta ci gaba da danne dannenta gabad'aya ranar zarah
bata shigo mata ba har dare, ba tare da tayi wanka ba ta chanza zuwa kayan bacci,
tayi kwanciyarta bayan ta kira Mama taji jikin da sauki, maman ke fad'a mata gobe
zasu wuce.
Da tunanuka fal ranta tayi bacci, wuraren 10 ya shigo duba ta ya samu kuwa ta jima
da yin bacci, ya jima tsaye yana kallonta kan ya ja mata blanket ya kashe mata wuta
ya fice, kiran sallahn farko ya farka kaman yadda ya saba yayi wanka yayi
nafilfilinshi adu'anshi guda kar fushin Ummu yayi tasiri a kanshi yana rokon Allah
ya sassauta mata jin haushin matarshi, adu'o'i sossai ya musu kan a kira sallah.
Mikewa yayi ya fito d'akinta ya fara lekawa ya ganta tsaye tana mika dayake tana
farkawa ta kunna wuta, da sauri ya kawar da kai yana tsaki ya fice, toilet ta fad'a
tayi alwala tazo tayi raka'atanil fajr tayi sallahn asuba kan ta d'auko wayanta
qur'an app da tayi downloading jiya ta bud'e ta fara karantawa, seda gari yayi
haske kan ta mike ta shiga wanka bayan ta fito ta shafa mai ta d'auko wata atampha
A shape gown anyi ado da pattern d'in rigan red ta sanya.
Katon gyale ta d'auko ta ajiye bakin gado bayan ta kafa d'aurinta, akwatinta take
gyarawa ta fara jin kamshinshi lumshe ido tayi kamshin na shiga har ranta, bata
gama dawowa daga duniyarshi ba taji sallamanshi, amsawa tayi kan ta zame kasa ta
gaidashi, sanye yake cikin kananun kaya bakake as usual kanshi se shekin mai irin
na gyara yakeyi haka sajenshi zuwa gemunshi.
Amsawa yayi yana cewa "ya headache d'in?" Tace "Alhamdulillah yayi sauki" ba
karamin kyau ta mishi a haka ba hakan ya sa ya d'an tsaya yana kallonta, ganin ta
d'ago sun had'a ido yasashi cewa "breakfast" Kai ta gyad'a ya fita tabi bayanshi,
kaman jiya yau ma Shiru Shiru sukayi breakfast d'in bayan sun gama ya dubeta yana
cewa "karfe 9 jirginmu ze d'aga so make sure kin gama duk abinda zakiyi before
8:00" hankalinta na kanshi tace "In shaa Allahu, Dan Allah in su mama basu wuce ba
inje In duba jikinta?" 'Dan Shiru yayi kan yace "saura sun wuce mama kuma da ita
zamu tafi don i don't think zata iya tafiyar mota".
Mikewa yayi ya fice, zama tayi tana aikin sake sake da tunane tunanen yadda ya damu
da en uwanta musamman mama ya d'auketa kamar mahifiyarshi yana darajata fiye da
tunani, har time ya qure se ganin Zarah tayi a kanta duk murmushi suka sakarwa juna
kan Iman tace "nayi missing d'inki wallahi, kika kama kika tafi kika barni ni ka.."
se kuma tayi shiru, hararanta zarah tayi kan tace "karasa mana....." murmushi kawai
Iman tayi kan ta mike suka karasa d'aki suka fiddo akwatin Iman d'in yafa gyalenta
tayi saman ka, ta riko wayanta a hannu suka fito.
Mota suka shiga direct zuwa part d'in nenne, nasiha sossai tsohuwar ta mata kan ta
bata wani leda tana fad'amata duk bayanin yadda za'ayi anfani dasu yana ciki,
sossai tayi mata godiya har da hawaye, zarah ma ta taya ta kan suka fito zuwa
sashen me martaba nan suka samu duka family d'in har da su hamna nasiha sossai
shima ya kuma yi musu yaja hankalinsu akan su zauna lafiya.
Sallama sukayi mishi suka fito, ganin duk su Nabeeha kowacce da akwatinta yasa Iman
jin daad'i, jiransu sukayi har suka karaso kan suka jera, Iman tana murmushi Tace
"masha Allah, baba ya yarda kenan Amma tare zamu zauna ko?" Teema tace "ke rufa
mana asiri, ki bari mu tafasa kan mu kone" kallon mamaki Iman ta musu Ameerah tace
"A to Haka kawai kisa yaya Abdul suburbud'anmu muna zaman zamanmu" Nabeeha tace "In
banda abunki ma Ina mu Ina tarewa gidan Amaryar shekaranjiya" zee zatayi magana
Iman tayi gaba alamun tayi fushi tana cewa "ba se kun min terere ba malamai, In kun
ga dama kar ku zo har ku dawo" dariya suka saka gabad'aya, wadda hakan ya maida
hankalin Hamna kansu, haushi ne ya kamata har wuya.
Tirrr wallahi da rayuwar family d'insu ace tana er uwarsu amma suka wani je suka
makalewa kishiyarta bare a cikinsu, motoci suka shiga tuni akayi dasu Airport,
bayan sun sassauka ne Iman taga Mama wurinta ta karasa tana rike hannunta take cewa
"mama ya jiki?" Tana murmushi tace "naji sauki Ai Iman Alhamdulillah" tura baki
tayi gaba tana Shagwa'ba dama mamance take sakankancewa tayiwa shagwa'ba son ranta,
tace "tun fah Jiya nake ta so in ganki" murmushi Mama tayi kan tace "to ba ga ni
ba" tana kallon fuskan Mama Tace "yanzu In kinje gida mama wa ze kula dake? Pls pls
mama ki rokeshi muje gida tare In kin warke se na bishi".
Mama na hararanta tace "ke rabani wani irin rashin hankali ne wannan? Ke kam se
yaushe ne zakiyi hankali ne wai? Yanzu aka ce ki bi ni se kije?" Rau rau tayi da
ido zatayi kuka se suka had'a ido murmushi ya saki yana girgiza kai tun d'azu yake
kallonta dukda ba jin me suke fad'a yake ba amma yana kallon yadda take zuba ma
mama shagwa'ba se yaji ina ma shi takeyiwa, Allah yayi shi da son mace me shagwa'ba
amma hamna sam bata iya ba itakam wai komai a yi shi classy shagwa'ba kaman zubda
kima ne.
Kau da idanunta tayi zatayi magana se ga Zarah da Hafeez sun iso wurinta tana nuna
ta tace "ka ganta nan Hamma Hafeez itace amaryar yayan" murmushi Hafeez yayi yana
kallonta yace "Anty na barka da safiya" waro ido tayi tana cewa "innalillahi Mama
kiji Hamma Hafeez ni yake gaisarwa harda kirana Anty" tayi maganar kaman zatayi
kuka (karku manta dama chan na gayamuku Iman macece me faran faran da surutu rayuwa
ne ya maidata haka, gashi yanzu ta fara sakewa sbd irin mutanen da take had'uwa
dasu masu sonta tsakani da Allah).
Hafeez na murmushi yace "Mama Ai Anty na ce tunda matar yayana ne" Mama tace "da
hakan ma amma Ai ko matar yayanka ne ka girmeta Don haka be kamata ka kirata Anty
ba, sede ita ta kiraka baba ma" waro gabad'aya idanunshi yayi zarah ta kwashe da
dariya Iman na tayata, "baba kuma" ya fad'a kaman ze yi kuka, Iman na murmushi Tace
"eh mana sunan babana gareka" yace "ahhh nide gaskiya banson wani baba Ina laifin
hamma Hafeez d'in?" Iman tace "a'a da kunya mana gwara de in dinga cewa baban"
zarah na dariya har yanzu Tace "baba hafeez, Tab" d'aga hannu yayi da nufin maketa
da sauri tayi bayan Mama tana dariya.
Isowarshi wurin ne yasata had'iye dariyarta amma har yanzu fuskanta washe, cewa
yayi "Kai wai se yaushe zaka girma ne hafeez? Kana ga mama bata da lafiya amma ka
biyewa yaran nan kuna sakata surutu tuntuni, to ku wuce mu tafi" sum sum suka nufi
shiga cikin Airport d'in har zuwa gaban jirgi Anan ne ma Mama suka had'u da ummu,
gaisheta mama tayi amma ko kallon arziki bata samu ba, sema shigeta da tayi zuwa
cikin jirgi.
Da mamaki mama tabita da kallo, Iman dake bayanta ne tace "mu je Mama" ajiyar
zuciya ta sauke kan ta fara taka matattakalar zuwa ciki Iman ce ta kama hannunta
zuwa sit d'inta se sukayi sa'ar samun sit d'aya da maman, kallon gefe da gefe zuwa
baya tayi a fili Tace "Tab yau en gidan lamid'o sunyiwa masu jirgin nan ciniki"
murmushi Mama tayi gaskiya suna dayawa gayya guda.
Daga inda take zaune tana hango Abdul da suka samu kujera d'aya da Hamna wani iri
takeji a zuciyarta da ta rasa menene ji take kaman ta tashi taje ta finciko hamnan
ta zauna wurin maganan mama ne ya dawo da ita hankalinta "Iman kaman mahaifiyar
Abdul bata sonki?" Ajiyar zuciya ta sauke ba tare da tayi magana ba, "Ina so muyi
magnan anan ne sbd In mun je kano ba lalle mu samu ke'bewa ba" A hankali iman ta
bata labarin abinda ya faru tana hawaye.
Karan text taji a wayanta wadda hakan yasa ta d'ago wayan tana kallon fuskan,
number ne special one, an rubuto "you promised but you failed" ta karanta yafi sau
abinda yafi bata gane ma'anan hakan ba se ta maida hankalinta kan Mama dake cewa
"na sani Iman zama da uwar mijin da bata sonka babban kalubale ne dukda kuwa ba
gida d'aya zaku zauna ba, Ki kiyaye plz na san tarbiyarki amma ki kara ki zama me
hakuri akan duk abinda zata miki, karki kuskura kice zaki bud'i baki ki amsa mata
sbd komin son da mijinki ke miki da zaran kin fara raina mahaifiyarshi darajarki
zubewa ze yi a idanunshi, sannan karki gaji da yi musu alkhairi abinci kowanne
juma'a haka da kyauta, dukda basu rasa ba amma kyauta be kad'an ko da bata kar'ba
ki ci gaba.
Ki zama me mata biyayya fiye da yadda 'ya'yanta suke mata in shaa Allahu zata so ki
watarana" kuka Iman ke yi abinta in fa ta tuna ko gaisuwar mijinta bata amsawa se
taji hankalinta ya tashi tana tsoron kar ta koma mishi irin ummanta, nasiha da ban
baki Mama ta dinga mata akan yadda zata zauna da uwar miji, sossai hankalinshi ya
d'aga ganin irin kukan da takeyi gashi ba halin yi mata text sbd sun tashi, me yasa
ta mishi alkawari ta karya shi da yayi alkawarin baze kara barin hawayenta zuba ba
se gashi tana chan tan kuka shi yana nan yana zaune.
Zafin kukanta yake ji har cikin ranshi, jinginar da kanshi jikin kujera yayi tare
da lumshe ido ko uhm be had'asu da er mulkin nashi ba ita a dole tana fushi dashi
yayinda shi ko iskar da ya kwasota ma be kalla ba, a haka suka sauka Kanon dabo,
drivers kusan biyar da motoci daban daban ne suka zo d'aukansu, Anty rahma da Anty
kalthum kuma mazajensu.
Dayake da 'ya'yan Anty rahma da ta bari gidan Ummu kan ta wuce aka tafi adamawa da
gudu sukayi wurin babansu, sallama tayiwa Abba da ummu akan se anjima da yamma zata
kawo boxes d'in akai gidansu Iman su kalla se a kai mata kayanta daga chan, Anty
kalthum ma sallama ta musu tabi mijinta, Abba ummu da Hafeez suka shiga mota d'aya,
zarah, Nabeeha, Ameera, zee da teema suka shiga d'ayar Picnic d'in, se Mama ta
shiga d'aya da kayanta Abdul yayi ma drivern bayanin unguwarsu Iman d'in ya
tabbatar mishi In sun isa unguwan mama zata mishi kwatance da kyau.
Seda yaga fitansu kan ya shiga gaban d'ayar motanshin, Umma, hamna da Iman suka
shiga baya suka fice, dukda yana mamakin me ze sa umma ta bi su gidansu ba gidan
Ummu ba amma ya kasa magana, ya san biyosu da tayi da biyu akan Iman da har yanzu
take hawaye musamman da mama zata tafi kukanta har da shesheka takeyi ita har ga
Allah tsoron su hamna ne ma ya shigeta.
In shaa Allahu baze bari su kuntata mata ba daga ita har uwarta dalilin da ya hana
manya su haneta tarewa gidanshi shi ko baze ki mata rashin M ba In tace zata hana
Iman zaman lafiya BS BS ne ze zama tsakaninsu, da wannan tunanin suka karasa
gidanshi, fita yayi Iman ma tayi saurin fita tana share Hawaye shi mamakin
hawayenta ma yakeyi ace mutum kullum se yayi kuka?.
Ciki ya nufa tabi bayanshi har sama nan ma kaman Gidan lamid'o d'akuna uku ne a
jere a parlorn saman se babban kitchen d'insu daga gefe, ta lura d'akunan kasa
sunfi na saman yawa sede bata san girmansu ba, Dayake Abba ya fad'amishi anyi mata
furnishing room d'inta da ya kasance daga hagunshi komai na bukata an saka mata,
kitchen kam Dayake guda d'aya su biyu Komai na ciki aka chanza.
Har cikin d'akin ya mata jagora shi karan kanshi d'akin ya burgeshi gashi colors
d'in da yake so, royal sets ne had'add'u black and Ash, dayake duk d'akunan saman
masu Part biyu ne bedroom and parlor amma irin waenda suke a had'en nan kaman yadda
nayi bayanin d'akinshi daga farko, kujerun   ma kad'ai abin kallo ne in taga dama
zata iya kwanaki a d'akin nan bata fita ba   In har ta sa fruits da drinks a fridge
d'inta na ciki, Ac har biyu ne a d'akin ga   katon plasma da decoder d'inshi gaban
had'ad'un kujerun da tsakiyarsu ya kasance   da had'ad'iyar center table me wani
shape na ban mamaki.
Ko tana kwance kan gadonta zata iya kallonta ba tare da wani hijabi ba, wall to
wall wardrobe d'inta ma kad'ai aka bar wani bakyauyen dashi se ya d'auka wata kasa
yake, anyi laying bed nan abin sha'awa, ga dressing mirror d'inta d'an d'as dashi
me full image, kuka ta kuma rushewa dashi wadda ya sa shi dafe kai, daga cewa "ga
d'akinki" se ta sa mishi kuka, Lord have mercy ya furta beneath his breath.
Juyowa yayi ya kalleta yace "Wai ni kam baki tsoron hawayenki su kare ne da kukan
nan? Ayi mutum shi kullum kuka? Saudah bazan iya ba Alkawarin kulawa dake da hanaki
sake kuka na d'auka amma banga kina shirin tayani cika wannan alkawarin ba sema
karyashi da kike ta aikin yi, to bazan iya ba In ke bakya jin zafin kukanki to ni
yana damuna" hawayen ta share cikin rawar voice tace "kayi hakuri, nima ba cikin
son raina nake kukan ba, yanzu kam ma kukan farin ciki ne wai wannan shine d'akina?
Irin d'akin da sede mu kalla a waya ko a tv wadda ko gidajen masu kud'in ma da wuya
ka samu irin wannan wai nice a ciki kuma komai na d'akin mallakina ne? Na gode da
karamcinku gareni, na gode, na gode, bani da abin cewa Abba se Allah ya biyashi da
gidan Aljannah, yaji kanshi kaman yadda yaji kaina, ya saka mishi da d'inbin
alkhairi duniya da lahira, Allah ya biyamishi bukatunshi na alkhairi yaci gaba da
bashi dukiya ta hanyar halal ya kareshi daga sharrin dukkan abin ki ko mutum ko
aljan......"
Kuka ne ya sarke ta hakan yasashi karasawa ya sanyata jikinshi yana shafa bayanta a
hankali yana d'an jujjuya jikinshi alamun rarrashi ko ince irin jijjigan da akeyiwa
yara In sun fara bacci ba'a so su tashi, lub tayi tana sauke numfashi sun jima a
haka kan suka ji an banko kofa
🖤Gureenjo🖤
🥀NOOR IMAN🥀
*I am really really sorry wallahi Ina busy ne kwana biyun nan kuka ji ni Shiru and
har yanzu ban gama abubuwan dake gabana ba In kun samu gobe to In kuwa baku samu ba
kuyi hakuri zuwa jibi, and please ina barar adu'o'inku gobe in Allah ya kaimu zan
d'au hanya tafiyar 12hours A yafi juna*
*032*
Hamna ce tsaye rike da kwankwaso tana watso musu kallon rashin mutunci, cikin
masifa tace "ka kyauta kenan yaya Abdul? Tunda haka ka za'ba shikenan gobe de
kwananta ya kare tunda de bazawara ce" sake Iman yayi yana kallon fuskanta yace
"kiyi wanka ki huta zan fita In na dawo zan ganku" tsintar kanta tayi da cewa "Toh
Allah ya tsare ya kiyaye se ka dawo" wani kallo ya mata yana sake murmushi kan ya
d'an kalli hamna da ta choje bakin kofa kaman d'akinta girgiza kai yayi kan yace
"Ameen thanks dear" ya zagayeta ya wuce.
Bayan fitanshi ta cire gyalen jikinta da d'an kwali itafa a rayuwarta d'ankwali
takura mata yakeyi, d'akin ta bi ko Ina ta karewa kallo tana mamaki, garin ta'be
ta'benta ta ta'bo wani abu kaman button fari se gani tayi wani abu ya sauko daga
sama ihu tayi tana matsawa, labule ne me kauri sossai cotton fari sol gwanin kyau,
ciki ya raba da parlorn, dariya tayi tana kama baki, se taga parlorn ya fita da
kyau babba sossai haka ta bud'e labulen ta shiga d'aki nan ma ya fita kato dashi,
komawa tayi ta kara danna abun labulen ya koma ta kara dannawa ya sauko cikin
nishad'i ta dingayi kaman wata yarinya seda ta gaji ta bari, toilet ta shiga ta
dinga bin komai na ciki shima da ta'be ta'be.
Bayan ta gama ta fito ta fice babban parlorn saman, katuwar plasmar parlorn ta gani
kunne bayan d'azu da suka shigo ba'a kunne ba, boom tv ke kai se wani rawa akeyi
itakam ko kyaun gani be mata ba, hakan ya sa ta nufi gaban tv ta d'auki remote ta
fara chanza tasha, daga bayanta taji ance "eyeee ashe su en kauye kuma talakawa an
san tv tunda har an iya chanza channel" juyowa tayi se taga Hamna, idanunta ta
kawar kan tace "Ina kwana Anty, wai naga abinda ake yi a wanchan tashar ne ba kyaun
ga...." tsawa hamna ta daka mata "ke dallah rufewa mutane wannan kazamammen bakin
ke har kin san abinda yake maras kyau da me kyau? Ni wuce ki 'bace min da gani kan
raina ya 'baci In sa'ba miki kammani yanzun nan".
Umma da yanzu shigowarta ta kalli Iman sama da kasa kan tace "ke kin san ni?" Kai
Iman ta girgiza umma tace "Toh bari In fad'amiki wacece ni, ni kanwar mahaifiyar
Abdulraheem ne kinga kaman mahaifiya nake a gareshi kuma ni mahaifiyar Hamna ce kin
fahimta?" Kai Iman ta d'aga umma ta ci gaba da cewa "so ina da hurumin saki abu
kiyi a matsayina na uwar mijinki, ki wuce ki samamin abinda zanci yunwa nake ji".
Kitchen Iman ta nufa ba tare da tace komai ba, kitchen d'in fes dashi kaman ka
lashe ba datti ko guda d'aya, komai na bukata akwaishi cikin kitchen d'in store ta
bud'e shima akwai kayan abinci jibge se ma suyi shekara suna ci be kare ba, to sede
bata san me zata dafa musun ba ganin safe ne yasa ta d'auko doya ta fere dube dube
tayi tayi har ta samo inda kwai yake ta fasa, ta koma store inda taga an shanya
albasa, garlic, turmeric da ginger d'anye ta d'ibo abinda zata bukata tazo ta had'a
nan take tayi musu yam ball ta juye gabad'aya a cooler, tana fitowa da shi Zarah na
shigowa.
Da mamaki zarah ke kallonta "besty yaya ne yace ki mishi girki?" Kai Iman ta
girgiza itama zarahn ta san baze ta'ba sata ba sede tayi don ra'ayin kanta ko......
se kuma ta waro ido "Hajjiya Umma!!!" Murmushi Sossai Iman tayi ganin yadda tayi
maganan wato irin ta d'ago d'in nan, tace "ke menene don nayi girkin? Muje In ajiye
mu wuce room d'ina kigani, and Yauwa bazaki tafi yanzu ba Allah karma ki fara ce
min zaki tafi waya mutu waya farko".
Kau da sauran maganan Zarah tayi tace "Amma wallahi Iman baki had'u ba, meyasa
kikayi? A garinku ne Amarya ke girki a washegarin tarewarta?" Ta'be baki tayi tana
ajiye tray d'in da ta d'auko kan dinning, sauka tayi ta kama hannun zarah suka nufi
d'akinta tana cewa "wace Amarya? Ni kam ba Amarya bace ban ma san me zan kira kaina
ba, plz mu bar maganan ya kikaga room d'ina?" Santin d'akin zarah ta fara.
Tayi ta zagayawa, bayan ta gama ganin komai ta kunna tv suka zauna kallo, kiran
azahar ne ya d'agasu sukayi sallah, bayan sun idar suka hau hira inda take tambayar
zarah ina su zee, tace mata "sunje yawo ko hutawa basuyi ba ingayamiki haka suke In
sun shigo kano kaman an saki tsuntsu daga keji kin san a fada ba yawo ake barinsu
yi ba".
Dariya Iman tayi tana cewa "Allah sarki, ki sa min numbers d'insu" kar'bar wayar
tayi ta d'auko nata ta saka mata gabad'aya tayi mata saving "Zarah saura ke kizo
kiyi aure mu shaa buki" murmushi tayi tana cewa "ke barni ba yanzu ba, haka kawai
Ina rayuwa freely azo a kulle mutum a gida fita ma se ka roka har ganin Abbana se
ya min wuya" ta karasa tana tura baki, dariya Iman ta saki tana girgiza kai tace
"kema de kin san aure dole ehe yarinya se ki shirya Don kina saken da na san
saurayinki sace wayanki zanyi in turamishi text message baba yace a turo".
********
Gud'ar da ake tayi ne ya cika unguwan har ya sa duk makwabta fita ganin gulma a
daidai lokacin da en yola suka iso, manyan motoci land cruiser ne guda Biyar suka
shigo layin, bayan su inna sun shige, akwatuna aka fara fitarwa d'aya bayan d'aya
ana shigar da shi gidan wow, ko daga nesa ka hangesu zaka san ba harkar yara bane
harkar manya ne Ina tsaye Ina kirge seda aka shigar da guda Goma sha biyu.
Shidda milk color shidda Purple, sakan baki su inna sukayi suna kallon wannan kaya
kap family d'insu gabad'aya ba wacce bukinta ya kai na Noor Iman wasu har Allah ya
isa suke ja se kace ita ta za'bowa kanta mijin, da aka fara bud'e kaya kuwa harda
masu kwallan bakin ciki, kayayyaki ne naji da fad'a waenda baza su ma iya kirguwa
ba, tun suna kirga yawan zannuwan har suka dena manyan zanuwa da manyan laces Anty
rahma ta kwaso mata da d'an kunnaye da sarkoki har da su gold and diamond.
Turaruka kuwa zaka ce karamin perfume store za'a bud'e, umma karan kanta se da ta
jinjina kayan bata karasa kallo ba ta tashi ta shige d'aki kawai, Mama kam harda
kukanta na farin ciki dukda bata jin daad'i har yanzu ita kad'aice ta zage tayi ma
su Anty rahma karamci, Anty rahma ce da kanta ta kasa ta tsare a kan kayan duk
makwabtan da suka shigo kallo seda sukayi dana sani.
Anty rahma tacewa Mama "Am In ba damuwa zaku wakilta mutanenku se a kai mata kayan
daga nan tunda ga motoci" cikin jin daad'i mama tace "to bari In kira babanta yazo
ya ga kayan arziki" mikewa tayi ta fice zuwa d'akinta ta kira baba, mintuna kad'an
se gashi da yake yana kusa, inna da tayi zaman en bori gaban kayan ya duka ya
gaisar bata amsa ba, su goggo saratu ya kalla duk sunyi wani iri da su, Mama ce ta
katse mishi hanzari da rangad'a gud'a kan tace "ka ga kayan d'iyar Albarka" kallon
kayan yayi yace "wace haka?" Mama tace "Noor Iman Mana In ba ita ba waye?" Da wani
irin murna ya nufi akwatinan mama ta fara bud'e mishi yana kallo har kukan daad'i
yayi.
Ba 'bata lokaci bayan ya gama kallo ya cewa su Anty rahama su tattara su kai mata
kar su barshi nan a mata sata Allah yayi mata albarka ya bada zaman lafiya, da
murna Duk suka amsa banda Hajiya inna da su Anty saratu, tattarewa su Anty rahama
sukayi suka fice bayan mama ta d'an had'a kud'ad'en hannunta dubu d'ari ta basu,
godiya suka dingayi Anty rahama na yaba karamci irin na mama.
*********
A nan kuma basu jima suna hira ba su zee suka zo nan aka had'u aka dinga chapter
sossai suka sha hira a cikin irin hirar ta d'ibi experiences dayawa sbd an ta'bo
mutane dayawa waenda zama da kishiya ke basu wahala an ta'bo rayuwar aure sossai,
Anan ne ma teema ta bata sakonnin Nenne tare da yi mata bayani kaman yadda nenne
tayi suna yi suna mata tsiya, kar'ba tayi ta adana a kunyace.
Su sukayi mata shara da mopping na room d'inta da parlorn saman suka shiga kitchen
suka hau girki, 'buruntunsu ne yasa hamna fitowa don ganin waye, da mamaki take
kallonsu basu ta'ba zuwa gidanta wai don sun zo hutu gidan Abba ba, bare kuma har
su mata girki haka zarah, cikin masifa tace "Lallai ma yaran nan yaushe kuka zo?"
Teema tace "tun azahar Anty hamna me ya faru?" Da fad'a tace "ban son munafurci
tambayata kike abinda ya faru? Kuzo tun d'azu ina er uwarku ku kasa shiga d'akina
se d'akin kishiyata? In ni banda darajar hakan goggonku fa?".
Zee Tace "haba Anty hamna Don mun shiga d'akin iman menene ciki sannan itace
sa'armu kuma itace kawarmu" Nabeeha tace "beside kuma ai itama er uwa ce so Don mun
shiga wurinta ba laifi bane" hannu ta sa a baki kawai ta juya d'aki ta d'auki
wayanta ta kira Baba yarima bayan ya d'aga yayi mata ya gajiyan hanya kawai se ta
fashe da kuka cikin tashin hankali yace "lafiya kubra wani abin ne ya faru?" Cikin
kuka tace "Baba su Ameera ne......." "me suka miki?" Ya katse mata hanzari "zuwa
sukayi gidana suka had'u da kishiyata sukayi ta zagina, ashe tun da suka zo nan
suka sauka ko umma basu zo sun gaisar ba".
Cikin fad'a yace "Abinda suka je yi kenan kanon? Suna da hankali kuwa kiyi hakuri
zan kirasu amma bawa uwar taki wayan" bawa umma tayi tana mata magana da hannu
kar'ba tayi ta wani sanyaya murya yace "haba hasfa babba dake kuma kina matsayin
kanwata zakiga yaran nan suna ma yarsu haka baza ki iya magana ba?" Kuka tasa na
munafurci tace "na musu magana Hamma amma ganin suna neman su zageni yasa na fice
na kyalesu" rai 'bace ya kashe wayan ya kira Ameera da yake itace babba.
Suna turara had'ad'en fried rice d'insu zarah na had'a coslow yayinda Iman take
had'a musu zo'bo duk da yadda suka so hanata sa hannu a aikin taki sam, wayan
Ameera da suke jin waka ne ya d'au kara matsawa tayi ta duba tana kallon sunan ta
waro ido ta kalli sauran tace "baba" duk matsowa sukayi ta amsa tare da sanyawa
speaker ko sallamanta be amsa ba ya hau musu fad'a kaman ze ari baki daga karshe
yayi musu rantsuwar ya sake Jin sunje gidan Abdulraheem ma gabad'aya ransu ze 'baci
tunda ba arziki ke kaisu ba, In kuma suka kuskura suka tsallake magananshi ba su ba
kara zuwa kano, Kit ya kashe wayanshi.
Dukkansu a wurin seda ransu ya 'baci Iman har ta fara hawaye Allah sarki yanzu baba
yarima ze na mata kallon maras hankali da tunani, Zarah ce tayi karfin halin karasa
abinda suka bari ta sassaka musu kula dama duk sun kamalla kad'an ya saura rabawa
biyu tayi ta sa musu nasu ta sawa en gidan ma nasu, Duk sun kasa magana daga karshe
Teema ce ta fara magana "Amma matar nan anyi bakar munafuka" Zee tace "daga ita har
mahaifiyarta ban cire kowa ba, In ba munafurci ba yaushe muka mata rashin kunya har
muka zagesu?" Nabeeha tace "ko ganin hajjiya umman munyi ne In ba sharri ba gashi
baba in ya rike abu kullum se ya muku fad'a akai" Ameera ta d'auki wayanta ta danna
kiran Abdulraheem bazasu iya tafiya su bar Iman haka ba duk tayi wani iri cike da
damuwa bata so en uwan mijinta su fara tsananta sam, waennan d'in sune kawayenta
kuma en uwanta tunda duk kannentan mazajensu sun hanasu zuwa aurenta.
Yana d'agawa ta fashe da kuka, Shiru yayi na seconds kan yace "Ameera!!! Lafiya?"
Cikin kuka tace "yaya ba kaga Anty hamna ba Don mun zo taya Anty Iman ayyuka da
gyare gyare shine ta Kira baba ta d'aura mana sharri wai mun zageta gashi Yace kar
mu kara zuwa gidanka tunda abinda ke kaimu kenan se kuka Anty Iman takeyi" Shiru
yayi kaman baze yi magana ba se kuma yace "on my way" ya kashe wayan.
Kusan 30 mins suna zaune jugum jugum se gashi ya shigo Iman kam ma bata nan tana
cikin d'akinta, Zarah ya kalla yace "me ya had'aku da ita?" Bayani tayi masa,
lumshe ido yayi Hamna na so ta kureshi wallahi, wayanshi ya zaro ya kira baba
yarima, bayan sun gaisa yake ce mishi "yanzu baba gidana ne kace kar su Ameera su
kara zuwa? Baba ka fa san hajiya umma kuma ka san irin tarbiyar su Nabeeha baza su
ta'ba iya zaginta ba, kuma ka yarda da maganganunsu?".
Da tunanin hakan yace "me suka ce maka su?" Nan Abdul ya mishi bayani, baba yace
"dukda haka in basu fad'a mata abinda ba shine ba baza ta kirani ba, ba wai na
yarda da maganganunsu duka bane yasa na yanke musu wannan hukuncin, ba ta yadda
za'ayi hamna na er uwarsu suna kawance da kishiyarta dukda hakan shirme ne irin ta
mata but ka duba maganan".
Abdul yace "baba kaji labarin Iman kaima kana son rabata da su Ameera sbd kana
ganin da gaske bata da tarbiya?" Yayi maganan a sanyaye, Auzubillah Baba ya furta,
"shikenan Abdulraheem su dinga zuwan amma dan Allah ka ja musu kunne bana son
fitina" godiya ya mishi sukayi sallama, dayake duk sunji yadda sukayi murna suka
hau yi, zarah ta dube shi da ido ya mata alamun Ina Iman.
'Daki ta nuna mishi da kai ya mike ya nufi room d'in, tana kwance ta kifa kanta kan
pillow daga ita se karamin towel iya cinyarta da alamu wanka ta fito tayi
kwanciyarta ba tare da ta shirya ba, jikinta yabi da wani irin kallo chocolate
fatanta se yalki da sheki yakeyi, a bakin gadon ya zauna kan ya d'aura hannunshi
kan fatar bayanta zabura tayi ta juyo se taga shine, juye juye ta fara Don neman
abinda zata rufe jikinta amma ba komai kusa, hannu tasa tana gyara d'aurin towel
d'in kanta kasa.
Duk ta rud'e wadda hakan yasa shi sake murmushi kunyarta ya mugun burgeshi
muskutawa tayi zata matsa yayi saurin kamo hannunta da karfi batayi balance ba
hakan yasa ta fad'o jikinshi "Ashhh" ya furta yana riketa Don ta buge shi kuma yaji
zafi, da sauri ta d'ago tana shafa kai tace "sorry" karkata wuya yayi yace "kika
karyani se kin biyawa ummuna ni" Siririn dariya ta sake ganin yadda yayin kaman
wani karamin yaro, murmushi ya saki ganin tayi dariya yana cewa "ko ke fa Haka
kawai mutum yayi ta kunci? Ki dena d'aga hankalinki akan abu kalilan haka kin san
ba Lafiya ce ta isheki ba" zatayi magana kenan suka ji gud'a mikewa yayi yace
"tashi ki shirya su Anty rahma ne" mikewa tayi shi kuma ya juya ya nufi akwatinta
dukawa yayi ya 'bude waro ido tayi tana kallon me yake shirin yi, wani orange lace
ya ciro mata riga da skirt da d'an kwalinshi, da karfi ta runtse ido tana danne lip
d'inta na kasa da hakori ganin ya zakulo mata inner wears d'inta duk blacks.
Juyowa yayi ya kalleta yana sake murmushi ya san za'a rina yana mamakin yadda take
abu kaman bata ta'ba rayuwa da maza ba bayan aurenta hud'u, mikewa yayi ya zo dab
ita ya duka ya ajiye mata kayan kumatunshi na gogan nata kuma danne idonta tayi
jikinta na d'aukan rawa girgiza kai yayi yana mikewa murmushi kwance a fuskanshi ya
juya ya nufi kofa seda ya kai dab fita tukun ya had'e rai sbd masu mishi tsiya
irinsu wa'e😜😜 bande kira suna ba.
🖤Gureenjo🖤
🥀NOOR IMAN🥀
*33*
Murmushi yaki barin fuskanta har ta gama shiryawa tare da yafa katon mayafi ta rufe
fuskanta ta zauna kan gado, a parlorn kuwa yana fita kaman ya sani Anty rahma ta
fara mishi tsiya kara had'e rai yayi yana hararanta. Sauran friends d'inta da na
ummu biyu da suka kawo kayan se wasu daga cikin en uwan iman se dariya suke.
'Dakinshi ya shige yana shiga Hamna da Umma na fitowa baki bud'e suke kallon kayan,
har muryar hamna na rawa wurin cewa "wannan kayan fa Anty rahma?" Murmushi Anty
rahma tayi kan tace "na Amaryarki ne mijinku ya mata" bata san sadda ta furta
"kambalastii!! Yanzu duk wannan kayan er kutumar uban chan??? Wai me hamma ke nufi
da ni ne? Wato kaskanci ya shirya nuna min to wallahi Allah ya isa ban yafe ba"
tsabar takaici abinda zata fad'a ma bata sani ba.
Akwati shidda ya mata don bala'i ba irin mitan da batayi ba yayi rantsuwar baze
kara ba amma shine yanzu yayiwa Banzar matarshi goma sha biyu kuma sunfi nata kyau,
da karfi ta fashe da kuka tana kallon ummanta tace "wallahi umma ba zan yarda ba ki
san yadda zakiyi dani Allah bazan yarda ba wani irin cin fuska ne wannan??? Ko fah
kayan fad'ar kishiya be min ba, duk wacce za'ayi sede ayi ni kam se an raba kayan
nan biyu an bani d'aya".
Dafe kai Anty rahma tayi tana kallon umma dake rungume da ita tana buga mata baya
se kace wacce akaywa mutuwa, tana cewa "dole ma hakan za'ayi Ai wallahi duk cikinsu
ba wadda ya isa ya wulakantamin ke ya zauna lafiya har shi Hamma Ahmad d'in, bari
kiga In kira Addan, In ni Abdulraheem ya rainani Ai ita be isa ya rainata ba".
Ummu ta kira cikin masifa tace "Adda zama da d'anki fah ba dole bane ba In bakwa
bukatar mu a family d'inku se mu tattara muyi gaba haba wannan wulakanci da
kaskanci har Ina" ummu tace "me ya faru hafsat?" Umma tace "Ki zo gidanshi yanzu ki
ganewa kanki" ba musu umma ta mike ko sashin Abba bata shiga ta fad'amishi ba ta
fito ta shiga motanta ta ja se gidan.
Nan ta gansu tsaye cirko cirko Anty rahama kam mamakinsu ne ya kusa kasheta taya
za'ayi a raba kayan da akayi Don Amarya a ba kishiyarta Ai Abinda baze ta'ba
sa'buwa ba kenan, bayanin da sukeyiwa ummu ne ya sa ta dawowa tunaninta, bayan sun
gama fad'ar Abinda zasu fad'a ummu ta kalli Anty rahama tace "ke rahama raba
akwatunan biyu, hamna za'bi wadda ya miki" daga bakin kofa sukaji ance "excuse
me!!!" Duk juyawa sukayi se suka ga Abba.
Se a lokacin Abdulraheem ya fito ashe tun fara abin yana jinsu yayi niyyar ya fita
ya sassa'ba ma hamnan se kuma ya fasa jin sun kira ummu kar ta zo taga abinda yayi
niyya laifinshi ya karu a wurinta shi wallahi yanzu har ga Allah tsoron Ummu yake,
mamakin halinta na yanzu kuwa yana ga har kwanan gobe baze dena mamaki ba, the
silent, loving and caring ummunshi ta dawo wuta yanzu, "Am rahama da kud'in wa
kikayo sayayyan nan?" Inji fad'ar Abba, Anty rahama tace "Abba kud'inka" yace
"good, d'auki kayan ku shigar mata" jiki a sanyaye su Anty rahama suka fara
shigarwa.
Juyawa tayi kan Abdulraheem tace "Don ubanka In ni na tsuguna na haifeka kuma Nono
na ka sha kayiwa hamna irin kayannan inga uban da ya isa ya hanaka" kanshi ya dukar
kasa idanunshi na kad'awa a lokaci d'aya cikin sanyin murya yace "In Shaa Allahu"
ya juya kawai ya shige d'akinshi, Abba karan kanshi se da yaji hawaye ya cika
idanunshi me Rashida ta zama ne? Zarah kam kuka ta saka musu, juyawa Abba yayi ya
tafi, ummu ta rufa mishi baya bata so hakan ba ta so Abdul ya ja da ita ta kikkifa
mishi mari ko zata rage abinda ke cinta a rai, su hamnan ma basu so hakan ba haka
dai suka juya suka shige suna kwafa, bayan sun gama shigar da kayan duk suka fice
kowa rai ba daad'i suna kuma jima Iman tausayi Don kiyayyar uwar miji ba karamin
abu bane.
Su zarah ne suka shiga karshe sukayi mata sallama ta kasa kallon zarah kaman yadda
zarah ta kasa kallonta, ita zarah na ganin tsantsar rashin dacewar Iman d'in da
uwar miji, gashi kuma wai mahaifiyarta kunya ya hanata kallon Iman d'in, yayinda
Iman kuma ke jin kaman itace sanadin komai, duk abinda ya faru da family d'insu
itace sila, da kaddararta be bi ta gidansu ba da ummu bata tsani Abdulraheem ba, da
ummu da Abba basu samu matsala for the first time a zamansu ba.
Bayan tafiyan su zarah kukanta ta ci gaba da yi seda taji an kira magariba kan ta
mike ta shige toilet ta wanke fuskanta tazo tayi alwala, daga ka ga fuskanta zaka
san ta sha kuka, ko kayan da suka jere bata kalla ba, ji tayi ta tsani kayan ma da
ya bi ta tata da ya d'iba duka ya bawa Anty hamnan ita kam basu dameta ba sam
wallahi, d'an waenda ya saya mata wurin malabis ma sun isheta rayuwa.
Kasa karasawa yayi ya zauna nan parlorn ya kishingid'a tare da lumshe ido, ita kuma
a 'bangarenta ganin ba wadda ya shigo ya sa ta ci gaba da karatunta hankali kwance
seda aka kira isha ta dakata ta d'aga hannu sama ta dinga kwararo adu'o'i a fili
dukda ciwon da kanta ke tsananin yi hakan be hanata yin adu'anta cikin hawaye da
kaskantar da kai ga mahallicinmu ba.
Duk adu'an da tayi akan Allah ya sasanta tsakanin family d'in mijinta ya kawo musu
karshen wannan tashin hankalin In itace sila Allah ya kawo sanadiyar da zasu rabu
kar wani ciwon ya kamashi sanadin tashin hankalin mahaifiyarshi, rokon Allah tayi
Allah ya hana ta tankawa Hamna da mahaifiyarta ko da kuwa hannu ta d'aga ta mareta,
ta roke Allah ya tsareshi ya kareshi da sharrin masharranci sbd ta san ita kam guba
ke yawo jikinta duk inda ta ratsa se an samu matsala.
Kai ta gyad'a mishi yasa hannu ya share mata Hawayen fuskanta ya ce "ke watarana se
kin nemi hawaye kin rasa a idanun nan naki" ya karasa yana lakace mata hanci
murmushi ta sake tana kau da kanta, shima murmushi yayi yace "ki dena damun kanki
idan kika ci gaba bazamu shirya ba Don ban shirya yin jinya ba, and kiyi hakuri da
ummu ba haka take ba, ban san sadda ta zama haka ba nima..... I'm really confused
and afraid.....".
Ya karasa muryanshi na chanzawa Allah sarki bata san sadda tayi hugging d'inshi ba
tana kuma sa mishi kuka, tausayi yake bata a labarin da zarah ta bata sunfi kowa
kusanci haka tafi sonshi duk cikin 'ya'yanta to me yasa take mishi haka? Bayanta ya
dinga shafawa a hankali yana hura iska daga bakinshi da ze iya da kukan yayi ko ze
ji damuwar dake dankare a zuciyarshi sbd fushin mahaifiyarshi ya sauka.
A hankali yace "me na gama cewa yanzu?" Shiru tayi tana goge hawayenta tare da
mikewa daga jikinshi tace "na dena" yace "good, tashi kiyi sallah In kin idar ki
fito parlor zanyi magana daku" tace "to se ka dawo" ya mike ya fita ta tashi ta
tada sallah, bayan ta idar ta zubawa kayan ido yanzu waennan kayan Allah kad'ai ya
san irin kud'in da suka kashe wurin yinshi gashi ze sake yin wani.
Ajiyar zuciya ta sauke kan ta mike ta fito ba tare da ta Cire hijabin kanta ba,
bata samu kowa a parlorn ba hakan ya sa ta samu kujera ta zauna idanunta suna kan
tv, wani wa'azi ake da ya sata maida hankali kai Shiek Tijjani Ahmad guruntum ke
wa'azin rayuwar aure da yadda mace zata kula da kanta, hankalinta ya tafi gabad'aya
wurin wa'azin se gani tayi tashan ya chanzu ya koma wurin rawa wato boom tv, kallo
d'aya ta mata ta kau da kanta.
Tare da mayar dashi kan yatsun hannunta, ita bata da lokacin tashin hankali wallahi
baza ta iya ba, ita kuwa hamna ta so ta tanka ta yadda zata samu ta ci mata mutunci
son ranta amma se taga bata ce komai ba, kwafa tayi. Da sallama ya hawo saman
idanunshi na sauka kanta sam zuciyarshi baya jin daad'in yadda yake ganinta, yau
gabad'aya yini kuka tayi shi da yayi alqawarin baze kara bari hawayenta ya zuba ba.
Tsakin hamna yasa ya kau da idanunshi ya mayar kanta yana zama, kusa dashi tazo ta
zauna ajiyar zuciya ya sauke ya fara da sallama kan ya musu nasihar zama lafiya, ya
jima yana musu nasiha har seda ya ga Mutuniyarshi ta fara hawaye kan ya dakata,
kallon hamna yayi da hankalinta gabad'aya ke kan tv ko jin abinda yake fad'a be yi
tunanin tanayi ba.
"Hope zaku had'e kanku ku zauna lafiya?" Yayi maganar yana kallonta kallonshi tayi
kan tace "eh in bata shiga harkata ba kenan" kallon Iman yayi ta d'anyi murmushi
kan tace "In Shaa Allahu, Allah ya bamu hakurin zama da juna" yace "Ameen, and
maganan kwana biyu biyu yayi, and batun abinci kowacce ranar girkinta zatayi girki
gida gabad'aya Safe da rana kowa ze iya cin abinshi shi kad'ai amma dole abincin
dare mu ci gabad'ayanmu tare kullum" 'bata rai hamna tayi taya za'ayi ace zata yi
girki da wannan matartashi dukda ba ita zata girka ba amma Ai ita ke biyan kukun.
Zatayi magana ya tari numfashinta da cewa "it's constant ba chanji abinda nayi
niyya kenan, and batun kwana bazan iya dinga bin kowacce d'akinta ba duk wacce ke
da girki dole ta dinga kwana d'akina" hamna tace "Amma Hamma kaima ka san ban iya
kwana d'aki d'aya da kai taya zamu fara Don zuwan wata?" Yace "dole ne shima ba
shawara ba" had'e rai tayi cikin gatse tace "kenan daren yau kwananta ze kare tunda
de BZ ce" d'an kallon Iman yayi se yaga tayi murmushi girgiza kai yayi yace "yes
gobe da yamma zaki kar'ba" wani irin murmushi ta saki kan tace "shikenan ko? Ko
akwai wani abin?" Girgiza mata kai yayi, ta mike ta shige d'akinta se lokacin Iman
tayi mata kallon tsab ashe wata shegiyar night gown ce jikinta dake bayyana komai
na jikinta ko kunyan uwarta bata ji ba yanzu ta fito a haka?.
Allah ya kyauta ta furta tana kawar da kai se suka had'a ido dukar da kai tayi ya
mike ya nufi room d'inshi ba tare da yace komai ba, cikin sanyin murya tace
"Abinci....." tsayawa yayi kan ya juyo ta mayar da kanta kan yatsun hannunta tace
"munyi girki da su Zarah yana kan dining nace ko zaka karasa In zuba maka?"
Murmushi yayi kan yace "kira Hamna and meet me in the dining room" Kai ta gyad'a ya
nufi dining ita kuma ta nufi d'akin zuciyarta na bugawa.
Bata san me kuma ze faru ba ita kam yau ta ga ta kanta da su hamna daga safe zuwa
yanzu sun mata abubuwa kala kala, tana tsoro kar hakurinta ya kare, sallama tayi
yafi sau hud'u basu amsa ba kuma tana jin surutunsu shiga tayi daga bakin kofa ta
tsaya tace "Anty hamna, umma ku fito muyi dinner" hiransu suka ci gaba da yi kuma
zaginta suke fah amma ko a jikinsu murmushi tayi ta juya ta fice.
Yana zaune yana danne danne a wayanshi kallon Ina suke ya mata tace "suna zuwa"
zuba mishi tayi ta tura mishi har zobon, itama ta zuba ma kanta tare da zama suka
fara ci, har suka gama ci ba su hamna ba labarinsu girgiza kai yayi hamna baza ta
ta'ba jin magana ba, be san ya ze yi da ita ba, d'akinshi ya shige ba tare da ya bi
ta kan hamnan ba, bayan ta gama ci ta tattara wurin gabad'aya abinda ta san ze
'baci ta sa duk a fridge.
'Daki ta koma ta tu'be ta sa cotton kayan bacci me kauri riga da wando ta saka hula
tare da kara fesa turare, ta d'auki khimar ta saka tare da jan tunga ta tsaya, se
kuma ta fara safa da marwa ya zatayi taje d'akinshi itakam taga ta kanta, gashi
baza ta iya fara karya mishi doka ba, shahada tayi ta fito tare da jan kofanta ta
rufe ta nufi nashi da wayanta a hannu, ta jima tsaye bakin kofan tana sake sake kan
tayi shahada ta tura kofan da sallama.
🖤Gureenjo🖤
🥀NOOR IMAN🥀
*this page is dedicated to my two beautiful, amazing, caring, loving, and troubles
😏sisters and friends Haneefa Muhammad Gurin(Oda half) and Hauwa Ibrahim
yahaya(Dbestest) kuyi yadda kuke so dashi and plz a sarara min da masifan yin
typing da wuri, Shaa I love you guys so very much🥰🥰 Happy sisters day*
*034*
Tsaye ta hangeshi kan sallaya sanye da Ash jallabiya sallah yake shirin tayarwa da
alamu shafa'i da wutiri, amsa sallamar yayi yana kallonta kanta kasa kaman wata
'barauniya ta lalla'ba ta zauna, se yanzu ya tuna da ashe ana sayawa Amarya kaza,
murmushi yayi tare da nufo parlorn be ce mata komai ba ya wuce ya fita.
Kallon d'akin ta hau yi tana mamakin   irin kud'in da aka zuba don komai na d'akin
kana kallo zaka san ba karamin kud'i   ke gareshi ba, ta kai 1hour zaune a wurin kan
taji bud'e kofa kallon kofar tayi se   suka had'a ido da sauri ta dukar da kanta,
lumshe ido yayi ya bud'e kan ya nufi   cikin room d'in ba tare da ya kalleta ba yace
"ki yi Alwala".
"Ina dashi" ta furta yana ajiye ledojin hannunshi daga gefen sallayan da ya
shimfid'a yace "bismillah" mikewa tayi ta karasa ta tsaya daga bayanshi wani
sallayan ya d'auko ya shimfid'a mata tare da juyawa ya tada sallah, har lumshe ido
takeyi tsabar yadda qira'arshi ke shiganta bata so sam suka gama sallahnan ba
raka'a biyu sau biyu sukayi kan yayi sallama ya fara kwarara musu adu'o'i tana
amsawa.
Bayan ya shafa ya juyo ya dafe kanta yayi mata adu'ar da Allah ya tanadarwa Amarya
ko sabon Abu, ido ya zuba mata bayan sauke hannunshi daga goshinta tunda ya d'aura
hannunshi wurin ta lumshe ido, idanunta da lips d'inta sun d'an kumbura sunyi ja
dukda ba fara bace yana iya ganewa, rawa ta farayi da lashes d'inta hakan yasashi
sa yatsanshi d'aya a hankali ya shafa saman idon, wara idon tayi a kanshi kokari
yayi ya rike idanunta cikin nashi.
Sun jima suna kallon juna kan tayi saurin kau da idanunta lumshe nashi yayi yana
cewa "samo mana plate da cups" har ta mike yace "tsaya, zo ki zauna" komawa tayi ta
zauna shi kuma ya mike ya nufi kofa, yana so ta samu duk wani gata da mace ke samu
a rayuwarta be so tayi missing komai, kowanni miji da ze auri matar da yake matukar
so a daren da zasuyi na farko baze iya bari tayi wani aiki ba gashi be bata gatan
ba tunda yau ma yini aiki tayi.
Kitchen ya shiga ya d'auko plate da cups biyu da spoon and fork ya d'aurasu kan
tray ya fito, karo suka kusa ci da Hamna da matukar mamaki take kallonshi a
zuciyarta tunani take me bawan Allahn nan ze yi da abubuwan nan, ba tare da ya
tanka ta ba ya wuce yayi d'akinshi, inda ya barta nan ya dawo ya sameta a kasan
shima ya zauna ya bud'e ledojin ba tare da ya juye kajin ba ya d'aura haka kan
plate ya san sunci abinci ba lalle taci na kirki ba.
Fresh milk ya bud'e ya zuba musu a cups kan ya sa hannu ya d'auki fork ya yanko
kazar ya kai bakinta kallonshi tayi da ido ya nuna mata bakinta alamun ta bud'e
shagwa'be fuska tayi shima ya shagwa'be nashi murmushi ta saki shima kuwa ya saki
ba tare da ya san ma yayi ba, kad'an ta bud'e ya sanya mata ta fara taunawa a
hankali kallonta ya dingayi yana murmushi har ta gama na bakintan shi kad'ai ya san
manufar kallon da yake mata mussamman lips d'inta dake tauna abinci kaman basa so.
Ya bata kusan sau biyar kan ta kau da kai a na shiddan gira ya d'aga mata alamun
ya? Tace "na koshi" fresh milk d'in ya d'auka ya sa mata a baki da gayya yaki
cirewa seda ta sha rabin cup ya d'an d'aga zatayi magana a shgwa'be ya mayar da cup
d'in be cire ba seda ta shanye ya ajiye yana murmushi fakon idonshi tayi ta zuba
mishi harara kasa kasa tana cewa "wannan gayen ya kware a mugunta wallahi Haka
kawai a saka shan abun dole gashi yanzu cikina kaman ze fashe tsabar koshi shi yana
nan yana dariya" ta karasa tana tura baki.
Be ko kalleta ba seda ya shanye fresh milk d'inshi ba tare da yayi loma ko d'aya na
Kazan ba, yace "me ma kika gama cewa?" Waro ido tayi kan tace "ni?" Ya d'age mata
gira d'aya ta kad'a idanunta kan tace "ba abinda nace" cikin kunkuni shima ya maida
mata abinda ta gama fad'a d'azu, a d'ari ta mike ta sa'bi tray d'in tayi kofa a
kunyace ita kam ta shigesu duk sadda zata yi magananshi se ya ji ta kaman wani
maye.
Tana bud'e kofa suka had'a ido da Hamna da alamun ta jima jikin kofan don ba daga
'bangaren d'akinta take ba ta wurin d'akin Iman take, harara ta sakarwa iman
yayinda ita kuma tayi mata murmushi haushi ne ya zo wa Hamna wuya a take, wato
hamma yarinyar nan ya d'aukowa kwanukan cin abinci Don bala'i shi da ko cup be
ta'ba tace ya mika mata ya mika mata ba sede ya sakar mata harara amma yarinyar nan
har plate da cup fork and spoon ya d'auko mata the biggest issue d'in kuma kaza da
yayi son kai ya sayo musu su kad'ai banda ita da ummanta.
Iman na shiga kitchen ta fara hawaye sossai yanzu kukan takeyi har zuciyarta abin
ya mata zafi ba kad'an ba, jikin umma ta kwanta tana kukan umma dake aikin waya da
en duniyan kawayenta suna fad'a mata wani sabon malamin da suka samo a nijar, da
sauri tayi musu sallama tana kama Hamna tace "lafiya hamna me ya faru?" Cikin kuka
tayiwa umma bayanin abinda ya faru yanzu fitanta d'ibo musu abinci da makalewa da
tayi tana leken abinda sukeyi.
Shiru umma tayi ita karan kanta ta san hamna bata da wuri a zuciyar Abdulraheem
dukda bata tabbatar da ko yana son Iman ko baya sonta ba, har gwara da yana d'an
damuwa da damuwar iman amma tunda ya gane da gangan tsawon shekarun da yayi yana
neman d'a take shan magani ya tattara lamarinta ya watsar, tunanin mafitan 'bata
musu wannan daren ta fara cikin mintunan kad'an ta samo d'aya a zuciyarta tace bari
mu gwada.
A kunne ta rad'awa iman abinda zata je ta fad'o mishi ita kuma ta kwanta tare da
jan blanket ta rufe jikinta Bayan ta cire kowanni abun kwalliya dake jikinta, da
sauri Iman ta tashi ta nufi d'akinshi.
A 'bangaren Iman kuwa Bayan ta ajiye tray d'in d'akinta ta nufa tayo brush tana
tunanin halin hamna how on earth someone could stood so low like that? La'be fah
take musu, Ajiyar zuciya ta sauke tana furta "Allah ya kyauta" Bayan ta gama ta
koma room d'inshi duhu ta gani se blue dim light da ya d'an haska daidai gadon,
bata san ko yana kai ba Don ba sossai take gani ba sbd daga haske ta fito.
Kujera ta samu ta kwanta Bayan ta cire hijabin jikinta kara ta saki jin an d'aga ta
chak tun kan ta gama ajiye hakarkarinta kasa, "hey matsoraciya nine" har ga Allah
ta tsorata ko da yace shinen ma ta kasa natsuwa a gado ya sauketa yana sanyata
jikinshi yace "taya mata zata zo turakar miji ta kwanta kan kujera?" Baki ta turo
kaman ya sani kuwa yace "ci gaba da turo min baki na fara musu hukunci kar a ga
laifina" maida bakin tayi da sauri murmushi ya saki yana hayewa gadon tare da
sanyata jikinshi.
Jikinta yaji da zafi hannunshi yasa a wuyanta zabura tayi sbd sanyin hannun nashi
ga taushi kaman jikin kule, yace "baki da lafiya ne temperature d'inki is not
normal" girgiza kai tayi hannun dake wuyantan ya fara yawo dashi a jikinta a take
jikinta ya hau rawa zuciyarta ya fara bugawa zafin jikinta kuma na karuwa, ci gaba
yayi da binta hankali cikin natsuwa lips d'inta da suke kan rawa ta bud'e da niyyan
mishi magana amma se yayi saurin had'e bakin da nashi, numfashinta yaji ya fara
d'aukewa tana wani irin ja da karfi, da sauri ya d'ago yana kunna hasken d'akin
gabad'aya haske ya gauraye d'akin.
Da mugun sauri har yana had'a steps ya gangara har yanzu tana jan, me gadi da ya
hango fitowarsu da gudu yaje ya bud'e mishi motanshi gidan baya ya kwantar da ita
tana sauka ta sake ajiyar zuciya se suma, da gudu ya zagaya ya shiga driver sit ya
danna button d'in motar ta tashi yaja da mugun gudu ya fice, ko Allah ya kara sauki
da me gadi ke mishi be iya amsawa ba.
A tsiyace ya shiga asibitin, a tsaye yaga wasu nurses da gadon marasa lafiya sauban
na tsaye gefensu, da sauri ya fita ya bud'e ya d'aukota ta farka daga suman da
convulsion d'in again, nurses d'in ne suka matso da niyyar kar'banta ya daka musu
tsawa, "just show me where to take her!!!!!" Gabad'aya ya rikice ya rikita nurses
d'in,Da sauri sauban ya shiga gaba yana nuna mishi hanya da sauri sauri gudu gudu
suka karasa A&E d'in anan suka samu doctor d'in hannunta rike da allura yana
kwantar da ita taja wandon jikinta sama zuwa cinya ta tsikara mata allurar
hannunta.
Wani kara ta sake na azaba da sauri ya kau da kanshi yana ficewa daga d'akin
hankalinshi In yayi dubu to a tashe yake, me ya ja mata convulsion da daren Allahn
nan? Safa da marwa ya dinga yi a kofan d'akin sauban de na tsaye yana kallonshi
mamakin abokin nashi yake shi gabad'aya rayuwansu ze iya cewa be ta'ba gani ya
tashi hankalinshi irin haka ba kuma sunfi shekara goma sha biyar tare, sam shi ba
mutum bane me nuna damuwanshi ta sauki amma yanzu gabad'aya ya rud'e har tsoron
magana sauban d'in ke mishi.
Sunfi 30mins tsaye kan doctor Ameera ta fito tana kallon Malabo da yayi saurin
nufanta yana cewa "ya jikin?" Tace "da sauki ta dena yanzu bacci takeyi, amma kafin
convulsion d'in ba wani rashin lafiya da takeyi? Kaman zazza'bi me zafi?" Girgiza
kai yayi yana cewa "lafiyanta kalau, temperature d'in jikinta ne kawai ya d'an hau"
girgiza kai tayi kan ta nufi office d'inta tana cewa "muje inyi maka prescribing
drugs and injections da zaku kar'bo mata" kai ya gyad'a shi da sauban suka rufa
mata baya se a lokacin sauban ya Samu mishi magana shima cewa kawai yayi "she will
be fine in shaa Allah" Kai kawai Malabo ya d'aga.
A gida kuwa umma na ganin Hamna na tsalle tace "ke plan d'in yaje" cikin farin ciki
hamna tace "umma mike kawai plan nan ya watse yanzu ya fita da ita da gudu rai a
hannun Allah" washes baki umma tayi kan tace "shegiya da ma ta mutu kowa ma ya
huta" murna suka dingayi kaman ance musu zasu shiga Aljanna(Allah ya tsare mana
zukatanmu)
*****
A zaune ya kwana gefenta hannunshi sanye cikin nata yana aikin gadinta har garin
Allah ya waye be rintsa ba, nurses d'in dake shigowa suna dubata mamakin irin son
da yake mata suke har kuskus sukeyi tsakaninsu, da wani namijin ne tun yaushe ya
shantake a gida yana baccinshi cikin kwanciyar hankali, amma wannan ko ruwa suka zo
Chanza mata se ya ce "kuyi a hankali pls" ya dinga 'bata fuska kenan kaman shi ake
cakawa Allura a jiki.
Kiran sallahn asuba da aka kira ne yasashi mikewa ya fid'a toilet d'in d'akin
dayake Sun dawo da ita Amenity, kanshi na tsananin sara mishi alwala yayi ya fito
ya nufi massallaci bayan an idar da sallah ya jima zaune seda rana ya fara fitowa
kan ya mike ya fito, a kasalance ya d'aga waya ya kira Anty Rahama, ta d'aga da
tsokana "shalelen ummu yau kuma da ni aka tashi kenan?" Siririn tsaki ya sake kan
yace "Anty muna hospital Saudah ba lafiya tun jiya".
Cikin mamaki tace "wace kuma saudah??..." da sauri kuma tace "oh oh subhanallah me
ya faru da Iman d'in?" Wani tsakin ya kuma ja kan yace "Asibitin su sauban" ya
kashe wayanshi, d'akin ya koma yana zama sauban na shigowa bargon ya kara ja mata
sama sossai da sauri, murmushi sauban yayi a 'boye kan yace "sannu malabo" yace
"ban son iskanci Sannu se kace wani me ciwon kafa" dariya sauban yayi yayinda
malabo ya banka mishi harara.
"Ya jikintan?" 'Dan fuskan damuwa malabo yayi yace "gashinan dae sauban har yanzu
ko motsi batayi ba" sauban ya d'an duddubata kan yace "everything is normal bacci
takeyi sbd allurar da aka mata karka damu" Kai ya gyad'a yana kamo hannunta, fita
sauban yayi ba jimawa sossai Anty rahama ta iso bata kira malabon ba sauban ta kira
ya kawo ta d'akin yana fad'amata abinda ya faru Don ta san ko zata mutu bazata ji a
bakin malabo ba.
Bayan ta gama ji tayi mata adu'ar samun lafiya, da sallama ta tura d'akin yana nan
zaune ta ganshi gaisawa sukayi sama sama sbd magana ba wahala yake mishi yadda
yaken nan, tace "kaje gida ka huta Abdul zan kula da ita kaji? Na kira kalthum zata
dafo mata abu mai ruwa ruwa ta taho mata dashi kan ta tashi" girgiza kai yayi da
kyar suka lalla'bashi ya yarda ya wuce gida gani yake yana tafiya komai ze iya
faruwa da ita.
                       🖤Gureenjo🖤
🥀NOOR IMAN🥀
*this page is dedicated to yhu Maman Ameer (Amina Ibrahim) ina me tayaki murnan
gama littafinki na zaytoonah wadda be karanta ba yaje ya nema ya karanta kar a
barshi baya, In Ana sallah toh fa ba'a magana littafin zaytoonah me kankat ne ya
ta'bo abubuwa dayawa marar lissafuwa manya manyan kuwa sune Fad'akarwa,
nishad'antarwa, soyayya, ladabi, iya magana da gujewa 'bata daga tafarkin
ubangijinmu, Masha Allah, Masha Allah, mun karu da abubuwa dayawa cikinshi, Allah
ya baki lada. Sannan Ina me tayaki farin cikin fara sabon littafinki "A barwa rai"
Allah ya shigemiki gaba Ina yinki irin over d'innan mutuniyata😘
*035*
Zaune suke a parlorn sama sun kunna waka sun kure kaman gidan rawa, jawahir da
Hamna ke takawa yayinda umma ke zaune tana karasa taune sauran kazan Amarcin Iman
da kukun Hamna ya d'umama musu suka gama breakfast dashi, (ummu Ameer da ummu
haneef😝😝😝😝😜 gashi mutanenku sun cinye basu ragemuku ba🤣🤣🤣) tun shidda jawahir
tazo gidan Don lokacin da akayi bukinsu Iman bata kasar amma tana samun Information
daga wurin ita hamnan.
Tun daga kasa yakejin kid'in ranshi ne yaji ya 'baci ainun ga kanshi dake sarawa ga
damuwan ciwon Iman a hankali ya dinga haurawa har ya isa tsakiyar parlorn ba tare
da ko ya kallesu ba yaje ya kashe kid'an ya nufi hanyar d'akinshi, umma ce ta
dakatar dashi da kiran sunanshi tsayawa yayi ba tare da ya juya ba tace "ya zaka
kashe muna chacewar tayaka murnar Karin aure?" Kuji iskanci🙄 taune lip d'inshi na
kasa yayi na seconds kan ya sake wani munafukin murmushi yace.
"Ai zakuyi hakuri in angwance tukuna, yanzu Ina ango ne, In na angwance I will let
you guys know se kuyi rawar da tushe" Hamna tace "yanzu hamna umma kake gayawa
magana irin wannan? Ko ba kanwar mahaifiyarka bace ba ai ta girme maka har haifanka
zata iya yi, sannan Ina ruwan mu da wani angwancewanka da b.........." hannu ya
d'aga mata "duk babban da be ji kunyar yarda girmanshi ba yaro bazeyi shayin hawa
ya taka ba" yana kaiwa nan ya shige d'akinshi.
Jagwab hamna ta zube kan kujera yanzu take jin tana son mijinta se yanzu takejin
bazata iya rayuwa ba shi ba, ji take ko me yace ta dena baza ta sakeyi ba har
abada, amma yanzu taya zata juyo hankalinshi kanta? Jawahir ce ta dafa ta tace "ke
ki dena d'aga hankalinki plz akan wannan gayen na sha fad'a miki In kina so ki
mallakeshi se kin bi ta masu duniyar wato bokaye(waiyazubillah) sannan ki sake
nairori amma kinki yarda dani" umma tace "Ai yanzu ta yarda tunda munje har sau
biyu, ke wani babban boka kika sani me kankat wadda daga munyi shikenan?" Jawahir
tace "yanzu mu shiga daga ciki muyi magana kar ya ji mu, huuuuuu kawata kice kin
shigo gari wallahi kukanki ya yanke inde wannan mijin naki ne kad'ai matsalarki"
murmushi tayi suka shige ciki suna ta hure mata kunne akan boka shine maganin
komai. (Allah ya shiryemu ya tsare mana imaninmu).
********
A hankali ta fara bud'e idanunta kanta na tsananin sara mata da fankan d'akin dake
juyawa a hankali ta fara cin karo, "Sannu Iman kin tashi?" Taji An fad'a daga
gefenta juyawa tayi a hankali tana d'aga hannunta da taji alamun ba komai a jiki
tana dafe goshinta, Anty rahama ta gani gefenta Anty kalthum da zarah se Hamma
hafeez, murmushi tayi musu tana amsawa da "yauwa" zarah tace "bari In kira ya
sauban.
Fita tayi chan anjima suka dawo da sauban da kuma dr Amira, yana dariya yace "Anty
kuka tura zarah kirana kuna so mutumin yayi kuli kulin kubura da ni ne yau?" Anty
kalthum tace "me yasa ze yi kuli kulin kubura da kai?" Tayi maganan tana dariya tun
kan taji me dalilin. Labarin abinda ya faru jiya ya basu dariya duk suka dingayi
suna mamaki har Doctor Ameera dariya take yayinda kunya ya rufe Iman, Anty rahama
tace "eyeeee malabon ne ya rud'e kan mace aaa Lallai Iman kin taki sa'a".
Anty kalthum tace "sossai ma se ki rikemana d'an uwa da amana Don ko ni yanzu na
tabbatar ba karamin so yake miki ba ko da kuwa be furta ba" Hafeez yace "ke se
yanzu kika gane? Lallai an barki baya ni wallahi tun kan ayi auren na gane yana
mugun sonta, da fa nace ya barni In aureta In yana tsoron fushin ummu bakuga mugun
kallon da ya watsamin ba seda hanjin cikina suka kad'a".
Dariya suka saka har Iman seda tayi murmushi dukda jikintan ba wai sakewa yayi ba
zazza'bin be sauka ba ga ciwon kai da take fama da, dr Ameera ce ta rubuta mata
wasu tests nurse ta d'ibi jininta Hafeez da har lokacin suke hira yana ta aikin
basu dariya ya kar'ba yayi lab Don a gwada a bashi result ya taho dashi, zahra ce
ta taimakawa Iman da silver, brush and macline da ta taho dasu sabbi tayi brush.
Kasa kasa tace mata "kaya fah zahra baza ki iya kije ki kawo min ba?" Cikin jin
jiki tayi maganan, zarah tace "Ohk bari In kar'bi keyn Anty kalthum ko na Anty
rahama inje In d'auko miki" kai Iman ta gyad'a zahra ta tashi tana cewa "A ara min
key in d'aukowa matar yaya kaya a gida" Anty rahamace ta mika mata ta fice, "A sa
miki abinci kici ko kan ta dawo se kiyi wankan" cewar Anty rahama, girgiza kai tayi
tana cewa "A'a Anty in nayi wankan zanfi jin karfin jikina watakila har da apatite
Don yanzu bandashi sam"
Kai Anty kalthum ta gyad'a tace "Anty mu bari zarahn ta dawo" ba Haka Anty rahama
ta so ba Don ba daadi zama da yunwa musamman ita da bata jin daad'i gashi 12 zata
fara shan wasu drugs dole kuma se ta ci abinci, hira suka ci gaba dayi tsakaninsu
suna sanyata ciki amma sede tayi murmushi kawai, da Anty rahama taga har after
1hour da fitar zarah bata dawo ba yasa ta bawa Anty kalthum Umarnin sa mata abinci.
Taimaka mata tayi ta gyara zamanta tare da d'aura mata abincin gabanta 'bata fuska
tayi tana kallon Abincin sam bata da apatite se tsabar headache dake nukurkusarta,
kallon abincin take ta aikinyi sam taki ko gwada kaiwa bakinta gashi de a ido kaman
ka lashe amma sam bata jin ci.
Anty rahama ce ta kula bata ci tace "a'a Iman ya baki fara cin abincin ba? Ko be
miki ba a sake girka miki wani?" Girgiza kai tayi a hankali Tace "zanci Anty" hira
suka ci gaba da yi da Anty kalthum after like 2mins Anty kalthum ta juyo taga har
yanzu bata fara ci ba "ikon Allah Noor Iman kici mana samu kisha drugs da suke
jiranki" hawaye ne ya ciko mata ido ta karkata kai tace "Anty na koshi" Anty rahama
tace "kin me?? Oya gy............" bud'e kofan da akayi da kamshin turaren da ya
bule su ne ya katseta daga maganan da takeyi.
Dukda ta san ba me irin wannan kamshi kaman Abdulraheem aiko shine ya bayyana sanye
da yadin kashmiyya baka d'inkin half jumpha irin na yayi da ya matukar kar'barshi
ba hula a kanshi hakan ya sa gashin da yake matukar ji dashi da asalin gyarashi
bayyana se sheki yake, kallonsu yayi fuskan nan ba fara'a sam Don Allah ya gani ya
tsorata da jikin Iman d'in gashi be samu wani baccin kirki ba, ga asalin damuwan
ummu bayan ya koma ya kwanta ya samu yayi bacci kad'an tashinshi ya gwada kiran
layin ummu, ya Saba kullum safe in be samu ya shiga sun gaisa ba ze kirata a waya.
Sam ya manta da wani bata shirya dashi ba muryarta kawai yake son ji hakan ya sa ya
kirata ya mata miss call yafi biyar amma bata d'aga ba hakan ya kara sanyaya mishi
jiki tabbas ta gani ba wai bata gani ba don da wuya ka ganta ba rike da wayanta ba,
wanka kawai yayi ya fito, daga d'akinshi yake jin dariyar Jawahir da Hamna da tun
dama su suka hana shi bacci musamman wannan figeggiyar yarinyar yanzu be da
lokacinsu ne yasa be bi ta kansu ba bari ya sukliti tukuna.
Basu san fitowanshi ba sbd sun ba kofan shi baya suna facing zarah Hamna tace
"Baiwar Allah kanwar baabarki da kikazo wurinta bata nan" dukda zarah ta kalleshi
hakan be hanata bata amsa ba da "Eyyah ai bata bani labarin ta bar karnuka gida ba"
wucewa tazo yi Hamna ta mike ta tare gabanta "kutt mune karnuka zarah?" Zarah tace
"wadda ya tsargu" jawahir ta d'aga hannu ta kifa mata mari batayi wata wata ba ta
rama kuwa hamna ta d'aga hannu da niyar marin zarahn taji an rike.
Juyawa tayi ta ganshi zatayi magana ya nuna mata d'aki fuskanshi ba ko d'igon
fara'a shakkan magana taji hakan yasa ta kama hannun jawahir zasu wuce yayi saurin
rike hannun hamnan kallonshi tayi idanunshi na kan jawahir yace "would you pls
kindly leave my house and don't you dare step your foots into it again? ever!!!" Ya
maimaita ba wani hayaniya a muryanshi.
A zuciye jawahir ta nufi room d'in Hamna Don d'aukan kayanta se hamna ta rike
hannunta tare da fashewa da kuka daidai lokacin ummu ta shigo gidan umma ma ta fito
tana murmushin mugunta su fah tunda sun san lagwanshi se abinda sukayi tunda baze
Kamu ba Ai me fad'amishi taji ta kamu duk d'aya, "me ya faru?" cewar ummu, Abdul
yace "ummu lafiya kika taho da kanki, ai da kin kirani ni se in zo In sameki"
hararanshi tayi tana cewa "Toh nazo ko korata zakayi ne in sani?" Girgiza kai yayi
yace "kiyi hakuri" tsaki taja tana kallon zarah tace "nace me ya faru? Me ma ya
kawoki gidan nan ke da kikace makaranta zaki?".
Labarin abinda ya faru zarah ta bata tana saukewa taji saukan mari, a razane ta
kalli ummu hannunta dafe da kunci bata ta'ba dukanta ba kafatanin rayuwarta se yau
shi karan kanshi malabo ya kad'u, cikin fad'a ummu tace "idan wanchan uwartaki zata
miki karya nima kenan zan iya miki, sannan yaushe kika fara karya ban sani ba? Wato
kawance da fitsararriyar matar wannan asararren ya fara koyamiki fitsaranci tayi
karyar rashin lafiya ya d'auketa sun tafi hotel ke kuma kika zo har gidan nan da
sunan kin tafi makaranta kike ciwa er uwarki mutunci har da mari wai kina tayata
kishi, to bari In miki me kankat tunda na hana kinki ji, wallahi wallahi Fatima
daga yau kika kara yiwa wanchan munafukar magana Allah ya isa ban yafe ba".
Sossai zarah ke kuka abin tausayi furucin karshen yafi marin d'aga mata hankali,
Abdul ze yi magana ta d'aga mishi hannu tana kallon jawahir tace "kiyi hakuri
d'iyar Albarka ki zo sadda kika ga dama ki fita sadda kika dama inga uban da ya isa
ya hanaki har shi wadda ya gina gidan, In ko ya hanaki kaman nima ya shata min layi
da rayuwarshi ne" kai jawahir ta gyad'a suka juya suka shige d'akin hamna
gabad'ayansu har ummu kan su shige ta nunawa zarah waje tace "wuce kiyi gida
shashasha marar kishin er uwarta".
Fita zarah ta nufi yi tana kuka sossai cikin damuwan da bata san ya zatayi da shi
ba, bayanta ya bi a parlorn kasa ya rike hannunta kawai se ta fad'a jikinshi tare
da kara volume d'in kukanta "Hamma wallahi Allah ummu bata cikin hankalinta, hamma
Noor fa tace kar na karayiwa magana Hamma taya zan iya Noor abin tausayice duk
duniya bata da kawa da ta wuce ni duk waenda suke zagaye da ita Ina zargin ba da
zuciya d'aya suke zaune da ita ba I badly want to help her ko wurin iya zama da
Anty hamna, amma ummu...... sannan mari????" Idanunshi da suka kad'a sossai suka
rine ya bud'e yace "kiyi Shiru ki dena kukan nan watakila mu kuma hakan ne
kaddaranmu, but with time everything will be fine again in Shaa Allah, ohk??" Kai
ta gyad'a mishi yace "me kika zo yi?".
Ta fad'a mishi yace "Ohk ki je gida and karki kara kukan nan zan kai mata kayan"
Kai ta gyad'a ya goge mata fuska tare da kissing forehead d'inta ta juya ta fice
shi kuma ya koma sama se ya rasa me ma ze d'auko shi ba mace ba, shawara kawai ya
yanke ya tafi asibitin ya ba kalthum kud'i taje supermarket ta sayo mata duk abinda
zata bukatan hakan yasa shi juyawa ya fito zuwa hospital d'in, se kuma ya samu suna
fama da ita taci abinci taki.
Gadon kawai ya nufa ya zauna daidai inda kafafunta suke ya rankwafo sossai tare da
d'aukan plate d'in abincin ya sa kan kafanshi ya d'ibo a spoon ya kai mata baki,
ganin fuskanshi ba alamun wargi yasa ta bud'e ya saka mata hawayen idanunta na
gangara, ci gaba da bata yayi hawayenta kuwa kaman an bud'e fanfo, daka mata tsawa
yayi "wani irin iskanci ne wannan? Me aka miki zaki zauna kinawa mutane kuka?" Anty
rahama ce tayi saurin cewa "Abdul kai wai kullum me ke kara hawa kanka ne? Ka shigo
ba sallama sannan ka zauna kana turawa er mutane abinci dole harda tsawa baka ganin
bata da lafiya ne meke damunka ne?" Runtse ido yayi tare da bud'esu cikin nata da
hawayen suka kafe tsoronshi na taso mata sede a take tsoron yayi hanyarshi ganin
shima hawaye ne kwance a kasan idanunshi wadda se ka mishi kallon cikin ido zaka
iya ganewa juna suka kurawa ido.
🖤Gureenjo🖤
🥀NOOR IMAN🥀
*036*
Lumshe idanunshi yayi tare da waresu kan Iman dake kallonshi baya so ya sata kuka
da damuwa haka kuma bayaso a kira zarah don ya Santa sarai ko zuwa yanzu tayi shiru
aka kirata aka tambayeta In har zata bada labari se ta kuma yin kuka, gwara de ita
Iman d'in tana gabanshi ne ze san yadda ze yi ya hanata yin kukan sossai, labarin
Abinda ya faru ya basu dukda ba in details ba don main point d'in kawai ya fad'a.
Salati suka d'auka a tare Anty rahama tace "Allah ya isa fa? Ka gayawa Abba?" Anty
kalthum tace "Toh kwata kwata ma me auta ta sani ina ita ina Allah ya isa?"
Idanunshi na kan Iman da tayi kaman bataji abinda yace ba da mamaki yake kallonta
ganin bata nuna damuwanta ba dukda kuwa shi yana iya ganin tashin hankalinta a
cikin kwayar idanunta, ita kuwa tayi Alkawari bazata kara nuna mishi damuwanta akan
fuskanta ta kara mishi damuwa bayan wadda ya sa kanshi a ciki Don ita ba.
Cewa yayi "Ba zan iya ci gaba da fad'awa Abba komai ba, shi karan kanshi yana cikin
damuwa ummu ta chanza gabad'aya har a yadda take kula da shi da yanzu kwata kwata
batayi, menene kuke ganin ze sauko da ummu ta koma kaman da?" Anty kalthum tace
"Hamma ni kam wallahi ban yarda Haka kawai ummu take ba why not mu nema mata
magani?" Anty rahama Tace "sannan ni inaga fad'an da Abba da kuma su baba galadima
ke mata yake kara tunzurata kan Iman kuma tabbas akwai alamun asiri ko shafan
aljannu jikinta, ummu yanzu ko ni da bama kwana bamuyi waya da juna ba tunda na
kawo kayan auren nan ko na kirata bata d'auka bare har muyi shawarwarin da muka
Saba".
"Ga shawara" duk kallonshi sukayi har malabo, "ina da numbern Baba fufore why not
mu kirashi mu mishi bayanin duk yadda takeyi ko akwai taimakon da ze iya bamu?"
Anty rahama tace "yes hakan yayi ba se mun fad'awa su baba galadima ba kar
hankalinsu ya fi na yanzu tashi" abinci ya kai mata baki se ta shagwa'be fuska da
gira ya mata tambayar ya? A hankali kasa kasa tace "na koshi Allah in na kara amai
zanyi" shi karan kanshi ba don yana kallon bakinta ba da baze ji me ta fad'a ba
murmushi yayi yana ajiye bowl d'in, se suka had'a ido da en uwanshi harara ya
dankara musu kan yace "ban son gulma da sa ido Allah".
Dariya suka saka har Iman seda ta murmusa yadda yayi maganan kaman irin dama wani
gulman suke har had'e rai ya kara yi, kallon Hafeez yayi yace "kirashi mana y ko
credit ne baka da?" Anty kalthum tace "haba ya isa manager guda?" Murmushi hafeez
yayi Yana dialing numbern baban, bappansu ne wato yayan sarki na yanzu, yaki gidan
sarauta Don ko lokacin babansu be rike mukami ba, sede yayi karatun Addini sossai
da sossai, jama'a moddibo suke kiranshi wato malami a hausance amma su Hafeez baba
fufore suke ce mishi Don duk rayuwarshi a fufore yayi wurin en uwan Mamansu da bata
kasance er sarauta ba.
"Assalamu alaikum babban Aboki an tuna da ni kenan?" Murmushi Hafeez yayi yana amsa
sallaman shin kan ya d'aura da "dama chan ana tunawa da kai sati biyu ne fah kawai
nayi ban Kira ba ko ka manta duk juma'a se na kira d'an tsohon?" Dariya yayi yana
cewa "Da gaskiyanka ka fi sauran en uwanka mussamman wannan nasaren" dariya suka
saka Abdul ma seda yayi murmushi ya san da shi yake hakan yasa yace "Allah ya
taimaki moddibo" yana murmushi yace "laaaa ashe Hafeez a handsfree ka sani? Yanzu
yaji na ce mishi nasare baze kaini makka ba bana wayyo ni" duk dariya sukayi.
Su rahma suka gaidashi duk ya amsa yana jansu da wasa kan Hafeez yace "wani
muhimmin magana ke tafe damu baba" yace "to to Allah ya sa lafiya?" Anty rahama
tace "da sauki dae baba, gashi gashi gashi" ta bashi labarin abinda ke faruwa tas,
bayan ta gama ya jima zaune shiru kan yace "Toh Alhamdulillah, tabbas Haka kawai ni
karan kaina na san Rashida bazatayi haka ba sbd sanin halinta tun yaranta amma ance
zato zunubi zan so na ganta Don in tabbatar se a nemi waraka wurin sarki me duka".
Abdul ya sauke ajiyar zuciya yace "moddibo kana ganin zata yarda tahowa ba dalili?"
Yace "zan kirata da kaina in Shaa Allahu sannan kan nan zan sa d'alibaina su fara
yi mata sauka da adu'o'i" godiya suka fara mishi yace "khayya ku nayiwa ko 'yata
nayiwa ban son azar'ba'bi" dariya sukayi duk maganan da sukeyin nan da fulatanci
sukayi sallama ya musu ya kashe wayan.
Duk ajiyar zuciya suka sauke dukda Iman bata ji ko da kalma d'aya da sukayi ba ta
de san in Shaa Allahu anyi nasara daga yanayin fuskansu, hira suka ci gaba dayi su
uku Anty kalthum ta fice sayo mata abubuwan anfanin kaman yadda ya bukata, Amma har
ranta ta rike In ta had'u da Hamna se ta dankara mata zagi ko mari yadda zata huce
takaicin marar musu auta da ta sa akayi.
Hafeez ne ya mishi bayanin ya   kar'bi result na test d'in ya kai office d'in Doctor
Ameerah, da kai kawai ya amsa   sun d'an jima kan kalthum ta dawo da kayyayaki a
hannunta kar'ba yayi duk suka   fice zuwa haraban asibitin Hafeez kam office ya wuce,
murmushi yayi yana tauna lips   very naughty yace "tashi muje In miki wankan tunda
baza ki iya ba" waro ido tayi   a kanshi.
Kau da fuskanshi yayi yana zare mata ruwan hannun hannunshi ta rike idanunta na
cika da hawaye, "menene?" "Kayi hakuri dan Allah" yace "ikon Allah me kikayi?"
Shagwa'bewa tayi tace "wallahi zan iya da kaina" girgiza kai yayi se hawaye sharrr,
murmushi ya saki yana goge mata da d'an yatsanshi yace "to sarauniyar kuka na
duniya, up we go in rakaki toilet d'in but ni zan shiryaki In kin fito" shirin
sauka ta fara ganin tana d'an layi Don jikin ba wai Karfi yayi ba, hakan ya sa ya
d'auketa chak a hannunshi sukayi toilet se da ya ajiyeta ya had'a mata ruwan wanka
ya tabbatar zafin yayi daidai tukun ya juyo kanta se yaga tana kallonshi ido ya
kashe mata da kai ya nuna mata ruwan.
Pouting tayi ta kalli kofa ta kalleshi, juya idanunshi yayi yace "kika sake turomin
bakin nan ko!!!" Gyara bakin tayi tace "kayi hakuri" girgiza kai yayi yace "no ki
sake plz" kanta ta dukar murmushi yayi yana cewa "bazan fad'i me zan miki ba amma
plz ki sake I love it, na san me hali be fasa halinshi, kiyi wanka In kin gama ki
kirani" ya juya ya fice yana murmushi, murmushin itama tayi ta fara wankan a
hankali cikin taka tsantsan Don ji take kaman zata fad'i.
Seda ta gama wankan tukun taga tsiyan da ya mata towel babba da karami Anty ta sayo
tabbas ta gani se ya ajiye mata karamin kawai ya fice abinshi gashi kayan da ta
cire ta zubasu cikin brockets d'in ruwan da ta gama wanka tayi niyyan wankesu ne ma
se taga bazata iya ba, dafe kai tayi tana furta Innalillahi, a razane ta kalli
bakin kofa jin an kwankwasa muryanshi taji yana cewa "are you done?" Shiru tayi
tana hararan kofan kaman shine a jiki kawai se taga ya bud'e da sauri ta juya mishi
baya tana rintse ido.
Bayanta ya kurawa narkakkun idanunshi yana kallo daga kafanta har zuwa saman
cinyoyinta kad'an da suka bayyana zuwa bayanta wuyanta da gashin kanta ke d'igar da
ruwa kad'an kad'an na wanka, da kyar yayi jarumtar fusgo numfashinshi har jikinshi
seda ya d'auki rawa tsabar yadda take half naked ya d'auke mishi hankali.
Ajiyar zuciya ya sauke tare da shigowa ciki yana nad'e hannun riga ya d'auketa chak
zuwa kan gadon asibitin
Mai da dama ya fitar ya bud'e ya sa a hannunshi cikin wani salo ya fara shafa mata
idanunta ta kara runtsewa tsikan jikinta na tashi malami na ba anji jiki me taushi
ba daga shafa mai se aka nemi zarmewa amma sak abinda ya faru ranan shi ya kuma
faruwa yau.
Da sauri ya sa mata doguwar riga me kauri da pant dukda yadda take sumewan tana
farfad'owa tare da jan numfashi kaman asthmatic, da sauri ya fita har yana had'awa
da gudu zuwa office d'in Doctor Ameera yana kwala mata kira su Anty rahama da suka
biyoshi suna tambayarshi menene yayi banza dasu da gudu suka fad'a d'akin ganin
yadda takeyi yasa suma suka rud'e.
Kwantar da kai tayi tace "wallahi Dakta ban sani ba duk wani irin ciwo da nake
tunani an mata tests d'insu babu su a jikinta ciwonta da dama na ga record d'in a
file d'inta high bp and heart attack amma shima taji sauki sossai da sossai, to
wannan kam ban san dalili ba" dafe kai yayi yana cewa "ko waje za'a fita da ita?"
Sauban da tun d'azu ya zo wurin yace "Da waje da nan duk d'aya malabo tests da muka
mata shi zasu mata mu kara hakuri dae muga ko zata sake samun attack d'inshi, se
kuma a kara mata wasu tests d'in da suke da shige da irin ciwon."
Ba don ya so ba ya aminta sbd dama sauban d'inne abokin shawara, su Anty rahama ma
sunyi na'am da zancen sauban d'in, d'akin suka koma suka zauna shi kuma ya zauna
bakin gado tare da kura mata idanu, Abba ne ya shigo da sallama duk mikewa sukayi
"Abba Sannu da zuwa" yace "yauwa ashe duk kuna nan kun barni hangame da baki ban
san daughter na ba lafiya ba" Shafa kai Abdul yayi yace "Abba kayi hakuri na manta
ne wallahi gashi abubuwa sun min yawa".
Abba yace "ba komai Hafeez ya min bayani har abinda ya faru jiya, kunyi kokari
Allah ya ganar da mahaifiyarku" duk suka amsa da Amin ganin yanayin malabon yasashi
tambayar ko ya jikin? Bayani ya mishi akan sake tashin ciwon, shima kwarai yayi
mamaki to wani irin ciwo ne wannan, ya d'an jima dasu kan ya musu sallama ya tafi.
Yini chur Abdul yayi a asibitin duk hankalinshi ba a kwance ba ganin bata farka ba
har yanzu Anty rahama taje gida tayo musu abincin rana yayinda ta taho da mai
aikinta wata tsohuwa akan ta kwana da iman yau kam kar ya kwana asibiti bayan ya
yini zaune, nunawa yayi baze iya ba hankalinshi baze kwanta ba In baya tare da ita,
Shiru kawai Anty rahama ta mishi Anty kalthum tayi musu sallama akan se gobe da
safe ta fice.
Biyar daidai wayanshi ya fara kara dubawa yayi se yaga hamna ajiyewa yayi ba tare
da ya d'auka ba nan ita kuma Tace se ya d'auka a jere a jere ta mishi miscall kusan
goma kan ya d'auka yana tsaki, "kace kai me adalci ne kuma kana adalci amma banga
alamu ba kwanana ya shiga amma har yanzu baka dawo ba" cikin kasan makokoro yace
"kiyi hakuri mana ki bar mata kwanan bata da lafiya she can't sleep all alone" Tace
"wallahi ban bayar ba In baka dawo ba Allah ya isana ban yafe ba Haka kawai In
d'auki kwana In bata, bata isa ba kuwa In taga dama ba rashin lafiya ba ta mu...."
kit ya kashe wayanshi yana d'agowa suka had'a ido da ita.
Murmushi ya sakar mata ita kuma ta mishi yake ita kad'ai ta san abinda take ji
banda ciwon dake damunta, "sannu Bari In kira Doctor" Kai ta gyad'a mishi ya mike
ya fice ba jimawa ya dawo da dr. Ameera ta duddubata komai lafiya se ciwon kan de
da zafin jikin, "dakta a jika towel a ruwa a dinga share mata jiki sbd idan zafin
jikin nan ya fi haka it might be possible ta sake samun wani attack d'in".
Anty rahama ya kalla yace "Anty ki zo ki mata" Tace "aaa ba za ka mata ba?" Ya
girgiza kai "zan tafi gida ne zan dinga kiranta a waya after every 30mins inji
jikin kan inyi bacci hope baaaba zata iya?" Ya karasa yana kallon baaban tace "In
Shaa Allahu Alaji za'a kula" gyad'a kai yayi ya mike se yaji ta rike hannunshi
juyowa yayi dama abinda take so kenan ya kalleta taga yaki kallonta.
"Tafiya zakayi?" Ta furta cikin murayar marasa lafiya, zame hannunshi yayi tare da
maidashi goshinta ya d'an rankwafo kad'an kan yace shima cikin kasa da murya "In
Shaa Allahu gobe da safe zan zo Ina fitowa sallahn asuba, ki kula plz" Kai ta
gyad'a idanunta na cika da hawaye d'an kallon kwayar idanun yayi yace "baki so in
tafi ne?" Girgiza kai tayi, uwargida tayi kira Ai dole ya tafi.
"Allah tashemu lafiya, ka san halin rayuwa ka yafemin In na mu.." "menene haka???
Wa ya gayamiki zaki mutu?" Sassauta murya yayi yace "dan Allah ki dena ambaton
mutuwan nan bana son jinta In de a kanki ne ke se kin haifamin yara dayawa masu
kama dake se kin zagaya duniya har ki ce kin gaji da hawa jirgi, se kinyi rayuwar
farin cikin da ba wacce ta ta'ba samun irinta a fad'in duniyan nan, ki kular min da
kanki wannan alqawari na ne" ya duka yayi mata peck a goshi kan ya juya ya fice.
Su Anty rahama da tun da ta rike mishi hannu suka fice, suka shigo bayan sun mishi
seda safe nan suka dinga hira suna sata nishad'i bayan tayi sallolinta da ake binta
a zaune nan kan gado, dukda tana murmushin hirar tasu amma zuciyarta na wani wuri,
yanzu making love ze je yayi da matarshi ko gashi ita rashin lafiya ya hanata bashi
komai, wasu irin zafafan hawayen kishi ne suka cika idanunta tana da kishi na
bala'i haka Allah ya halicce ta, ya kirata kusan sau uku wani abu a zuciyar na
hanata d'auka dayake wayan a silent yake se ta kifeta kasan pillow tayi
kwanciyarta, se bayan isha Anty rahama ta fara shirin tafiya kaman daga sama suka
ji an banko kofa.
🖤Gureenjo🖤
🥀NOOR IMAN🥀
*037*
Wani wawan ajiyar zuciya ya sauke ganin duk sun zuba mishi ido suna kallonshi yasa
ya juya kawai ya fice a jikin gini ya jingina yana sauke ajiyar zuciya wallahi yayi
mugun tsorata anya hankalinshi ze kwanta har ya samu yin bacci cikin nitsuwa kuwa?
ya yi ta kiranta bata d'aga ba haka ya kira Anty rahama ma bata d'aga ba ya gama
zata ciwonta ne ya sake tashi se kuma ya zo ya gansu suna hira abinsu.
Ita kuma a ciki se bata ji daad'in abinda tayi ba kar ta zama me son kanta dayawa
mana matarshi ce Hamna da ita ta sameshi ba laifi bane don tayi kishin shi amma
babban laifi ne da zata iya ignoring calls d'inshi sbd wani kishi bayan tana gadon
asibiti, Anty rahama ce tace "lafiyan Abdul kuwa? Ina zuwa" ta mike ta fito a nan
ta ganshi tsaye jingine da gini ya d'an Lumshe idanunshi "Abdul" a hankali ya bud'e
idanunshi ya zuba mata.
Tace "menene?" Wani Ajiyar zuciyar ya sauke kan yace "Ina son yarinyar dayawa"
murmushi Anty tayi tare da dafa kafad'arshi "ba wadda ya hanaka sonta ai Abdul ta
chanchanci a so ta" cikin wani irin yanayi yace "ban san sadda sonta ya min Illa ba
Anty yayi yawa sossai a zuciyata wallahi" fad'ad'a murmushi Anty tayi kan tace
"Abinda ya fito dakai kenan?" Murmushi shima yayi yana shafa kanshi yace "I was
calling your phones bakwa picking I thought wani abin ne ya faru" dariya Anty
rahama tayi kan tace "sorry majnun wayata na cikin jaka kuma a silent yake Ina
tunanin wayan Iman d'inma a silent yake Don bamu ji ringing ba".
Hararanta yayi yace "Toh kuma mutum be iya fad'a miki damuwanshi ba me kuma wani
majnun? Mtseww" ya wuce ta zuwa d'akin cikin d'aga murya tace "eh d'in Romeo kawai"
murmushi yayi ya tura d'akin ya shiga dama baza su had'u su wanye Lafiya ba abinka
da sako da sako, kan gadon ya nufa ba tare da ya kalleta ba yace "where is your
phone?" 'Daga pillow tayi ta d'auko ta mika mishi.
Kar'ba yayi ya cire a silent   kan ya mika mata, ba tare da ya kalleta ba ya juya ya
fice, yana cewa baaba "se da   safe" ta Amsa da Allah ya tashemu, Anty rahama ma ta
d'auki jakanta tayi musu sai   da safe ta Bishi da sauri akwai abinda take so suyi
magana akai, babban yatsanta   ta sa akan numbern wayanshi tana shafawa batayi saving
ba kuma ta rasa da me zatayi   saving sede ta haddace numbern tas a kanta.
Daga karshe kawai tayi saving da "Hamma" kawai ta ajiye wayan tare da kwanciya
cikin tunani har bacci yayi awon gaba da ita.
Washegari
Tayi ta zuba ido a kofa ko ze shigo amma be shigo ba kuma be sake kiranta ba taji
rashin daad'in hakan sossai, har Anty kalthum ta zo mata da breakfast suka sata ta
d'anci baaba ta taimaka mata zuwa toilet tayi wanka tazo ta shirya ta sake kwanciya
be shigo ba, Hafeez ma ya shigo ya d'inga tsokananta tana mishi dariyar yake kawai,
ya d'an jima kan ya musu sallama akan office zashi ya biyo duba jikintan, bayan
fitanshi Anty rahama ta shigo.
Nan de suka baje akan taburaman da suka taho dashi suka shimfid'a daga gefen
d'akin, turo kofa akayi da sauri ta d'ago se taga dr Ameera kanta ta sauke a
hankali wai ita yaushe ta fara mishi irin wannan son ne? Ji take kaman zatayi yaya
ba abinda take so illa ta d'aura idanunta kan kamilalliyar fuskanshi, a zuciyarta
kuwa tunani take watakila matarshi ta d'auke mishi hankali har hakan ya sa ya manta
da ita, abinka da mace se taji kaman tayi ta kuka ko zuciyarta ze yi sanyi fata
kawai take Allah ya sanya mishi sonta kwatankwacin wadda take mishi Don tana da
tabbacin ba sonta yake ba ya aureta ne kawai out of pity.
"My patient magana fa nake" firgigit tayi tana kakalo murmushi tace "Ina kwana dr?"
Dr Ameera tace "lafiya kalau tunanin me kike ne haka? Kin san be kamata ki dinga
tunani har kina fita cikin jama'a ba sbd high Bp d'inki tunda an samu heart attack
d'in ya watse" Kai ta gyad'a tare da furta "In Shaa Allahu zan kiyaye, dr yaushe
za'a sallameni? bana jin daad'in zaman asibitin nan gashi lectures na ta wuceni".
Murmushi dr tayi kan tace "za'a sallameki sede ba fa nan kusa ba sbd har yanzu bamu
gane wani irin ciwo ne dake ba" Anty rahama Tace "amma zuwa yanzu ya kamata a gane
tests kusan nawa aka mata" dr Ameera Tace "nima abin na d'auremin kai wallahi duk
irin illness dake kawo convulsion mun mata gwajinsu babu, amma gaskiya In sauran
results d'in da suke lab sun fito bata da d'aya daga cikinsu I will definitely
discharge her ku gwada na gargajiya".
Cikin amincewa da hakan Suka gyad'a kai ta d'an dudduba jikin kan ta fice, wayanta
ta d'auko ta kunna data ajiyewa tayi gefe seda sakon nin gabad'aya suka gama
shigowa kan ta d'auko ta shiga group d'insu na school, waro ido tayi ganin yayi
lectures yau karkata kanta tayi cike da damuwa tana kurawa wayan idanu a yadda take
tunani baze ta'ba raga mata ba kaman yadda taga yakeyi da zarah.
Sunan zarah da ta tuna yasa ta kuma dulmiyawa tunanin zahran Allah sarki aminiyar
kwarai har zuciyarta take kewar zaran, Anty kalthum tace "haba Noor ba yanzu aka
hanaki wannan tunanin ba?" Murmushi tayi kan tace "Anty na daina" Anty rahama tace
"Allah ya sa" dayake tunda ta shigo tayiwa baaba umarnin tafiya se dare kuma Bayan
ta bata kud'in napep.
Mazajen Anty rahama da Anty kalthum duk sun zo sun dubata yayinda Abba ya kira aka
had'asu yayi mata ya jiki, wani irin daad'i take ji idan taga yadda suke nuna
damuwansu a kanta, ba'a ta'ba nuna mata kulawa dayawa haka ba dama mama ce kawai,
murmushi tayi tuna mamanta bata fad'a mata bata da lafiya ba sbd kar hankalinta ya
tashi, amma bari ta kirata yanzu.
Kiranta tayi kusan ringing na karshe tukun taji an d'auka se taji muryan baba
murmushi tayi kan tace "baba mun tashi lafiya?" Ya amsa mata da "Lafiya kalau
Alhamdulillah ya gidan naki?" Tace "mun gode Allah, Mama bata kusa kenan?" Yace
"mamanki Ai ba lafiya ko magana ma bata iyawa yanzu" a rud'e ta furta "innalillahi
wainna ilaihi rajiun jikin ne har yanzu? Me suka ce yana damunta baba? Kuna wani
asibiti ne?".
"Kwantar da hankalinki muna nan FMC female ward jikin ma ai da sauki ba kaman jiya
ba" hawayen da ya gangaro mata ta goge tace "to bari yazo zan shigo In Shaa Allahu
nima Ina asibitin" yace "subhanallah me ke damunki haka?" Tace "zazza'bi ne kawai
baba na warke ma" yace "to Allah ya baki lafiya" ta amsa da "Ameen se na shigo"
sukayi sallama tana share hawaye tana murmushi a lokaci d'aya hawayen rashin
lafiyan mamanta da kuma murmushin sakewar Babanta gareta, ta manta when last baba
ya sake mata sukayi magana haka ba komai a muryanshi na tsana ko ki.
"Me ke faruwa ne Noor?" Anty rahama tayi tambayan tana dafa kafad'anta fad'amusu
tayi mama ce ba Lafiya Adu'ar samun lafiya suka mata suna jajantawa, ita kam
hankalinta na kan waya se kokarin kiranshi take.
********
Kwance yake kan kujeran office d'inshi idanunshi a lumshe kaman me bacci bayan ba
baccin yake ba, hankalinshi da tunanin shi gabad'aya yana kan maganan da sukayi da
Anty rahama, duk da har zuciyarshi kaman be yarda ba amma yanzu da ya zauna ya
nitsar da kwakwalwanshi se kuma ya fara shakar kamshin gaskiya a maganan, amma ze
gwada ya gani tabbas In gaskiya ne ba abinda ze sa shi yin delay akan hakan.
Dukda tana makale a zuciyarshi amma ya kasa tashi zuwa asibitin ya tara abubuwa
dayawa kanshi duk ya tara aiki da kwana biyu baya shiga offices d'inshi, karan
wayanshi ne ya dawo da shi daga tunanin shi, kaman baze d'auka ba se kuma ya sa
hannu a table d'in gefen kujeran ya d'auko "Hayateee💝🔐" ya gani ke yawo jikin
screen d'in, receive ya danna tare da karawa a kunnenshi itace ta fara yin sallama
ya amsa mata tare da d'aurawa da "ya jikin?" Tace "Alhamdulillah" se tayi shiru.
Kallon su Anty tayi ganin suna ta hiransu hankalinsu kwace yasa ta sassauta murya
kasa kasa tace "Hamma shine baka zo ba kuma baka kira ba ko bayan fa ka san bani
lafiya" Tayi maganan har zuciyarta abinda ke ranta kenan, murmushi yayi kan shima
murya kasa yace "sorry dear na d'auka ai ba'a bukatata ne shiyasa" tura baki tayi
tace "ni kam bance ba" murmushi yayi yace "na san baki ce ba ai, office na shigo
abubuwa na min yawa" Tace "Ohk ba matsala ai, plz mama ba lafiya tana nan FMC Ina
so in shiga in ganta" cikin muryan damuwa yace "jikin har yanzu? Subhanallah Allah
ya bata lafiya, ki jirani in zo se mu je tare ohk? And ki kwantar da hankalinki she
will be fine
In shaa Allah".
Kai ta gyad'a hawaye na gangaro mata lumshe ido yayi ko be kalleta ba wallahi
jikinshi ya bashi hawaye takeyi cikin kasa da murya yace "In ba kina son hanani
zaman lafiya ba ki taimaka ki dena hawayen nan yanzu zan taho se muje, kinji?" Tace
"uhmm na dena Allah ya kawoka lafiya" yace "that's my girl thanks" ya kashe yana
mikewa briefcase d'inshi kawai ya d'auka yayi waje dole wanka ze je ya farayi sbd
ya gaji class biyu yayi da safen ya san in yaje asibitin nan se ya jima kuma baze
iya yini da kayan nan ba.
Direct gida yayi yayi wanka tare da shiryawa cikin fararen kananan kaya da sukayi
matukar kar'barshi dukda har ga Allah ba wai so yake ba Don jinshi yake wani iri,
ko ta kan dinning da Peter ya shirya mishi be bi ba ya nufi sauka se ganinta yayi
gabanshi, "Hamna Ina zaka?" Harara ya buga mata kan yace "inda kika aikeni" Sosa
kai tayi kan tace "amm hamma nace ba wata sister d'in babanmuce dake Nijar Allah ya
mata rasuwa Ina so zan bi umma gaisuwa in ba damuwa".
Wani munafukin murmushi ya saki yana mata kallon wonders shall never end kan yace
"Ahhh tooo sabon salo......" abinda ya fad'i kenan kan ya zagayeta ya wuce da
sassarfa ya san iman ta gaji da jiranshi, cikin lokaci kankani ya isa sbd be had'u
da holdup ba seda yayi sallah a masallacin asibitin kan ya karasa amenity, tsaye ya
ganta jikin gadon tana d'aura gyale a kanta yayinda Anty kalthum ke sallah a kan
taburma, Anty rahama na zaune gefenta tana cin abinci.
Cikin fara'a yace "masha Allah jiki yayi kyau kenan?" Juyowa tayi gareshi tana
murmushin ganin fara'a sossai a fuskanshi tace "Ai yanzu ko 'yar tsere aka sanya
min da kai zan wuceka" murmushi yayi yana mamakin ta yaushe ta fara bud'e baki haka
a gabanshi? Dama shi haka yake so ai ya tsani yadda take kin yin magana In ta
ganshin nan, "haka ake so ai Alhamdulillah, kinyi sallah?" Tace "eh kai kawai nake
jira Don Allah muje In ga mamana" hijabinta ta d'auka ta sanya yana kallon Anty
rahama yace "to acici a ci abinci lafiya tunda abinci ya hana a gaidani sbd kar
ince nima zanci" hararanshi tayi tace "ka ji min yaro ni ya kamata In gaisheka ko
kai ya kamata ka gaisheni?" 'Bata fuska yayi yace "nine yaron?" dariya ta fara
mishi ta san abinda ya tsani ace mishi kenan yasa ta fad'i hakan, yana hararanta
yace "kema kin san wuce nan wallahi, yanzu Abba ya kwanta dama nine nan babban
yayan familyn nan har ke" be jira cewarta ba ya ja hannun iman suka fice.
Se mamakin wasanshi take ashe yana sakewa haka sossai ta d'auka ko da en Uwanshin
ma kullum rai a had'e har gwara da zarah ma, ashe ba haka bane, tafiya suke cikin
natsuwa dukda ba wani kayan kirki me tsada ne jikinta ba amma tayi kyau sossai tayi
fayau da ita yadda ya rike hannuntan ko ajikinshi yasa sukayi attracting hankalin
mutanenmu na Nja duk wadda ze wucesu se ya waiwayo ya sake kallonsu gashi sunyi
wani irin dacewa da juna they are just so perfect couples.
Ba wadda yayiwa wani magana har suka karasa female ward kiran baba tayi ta
tambayeshi gadon da suke ya fad'a mata kan suka shiga, gadaje ne a d'akin sunfi
ashirin mutane ko ta Ina ga hayaniya kaman kasuwa dukda wasu securities da nurses
na zuwa akai akai suyi magana akan hakan amma abinka da mata se a hankali, gadon
suka karasa tana kwance oxygen na makale a hancinta ba abinda ke tashi jikin gadon
se saukan numfashinta a hankali.
Baba ne gefenta akan kujera yayinda yayarta matar bappa yushe'u zaune bakin gadon
da alamu ita ke zama da ita, har kasa ya duka ya gaishesu se kallonshi Anty raliya
ke yi tana mamakin wai wannan ne mijin Noor Iman, iman ma gaishesu tayi Bayan ta
duka a hankali garin mikewa jiri ya kwasheta da hanzari ya tareta tare da manna ta
jikinshi bata da option se na tsayawa haka Don In beyi supporting d'inta ba zata
iya fad'uwa any moment.
Baba da ba shine da aikata hakan ba amma shine da kunya mikewa yayi daga kan sit
d'in da yake zaune yace "sannu mamana zo zauna mana ga wuri In ba rashin ji irin
naki ba Ina ke Ina zuwa dubiya bayan ke ya kamata aje dubawa" murmushi Abdul yayi
yana taimaka mata da zaman yana tunanin yaushe kuma bawan Allahn nan ya fara son
ershi?.
Bayan ta zauna yayi excusing kanshi ya fita chan anjima ya dawo da wasu nurses
babbar ciki ce ta dubi baba tace "baba d'anku ya chanza muku d'aki ku tattara
kayanku mu kaiku chan" baba yana kallon Abdul ze yi magana kenan malabo yace "baba
muje zata kuma ganin likita yanzu" Kai baba ya gyad'a speechless ya fara shirin
taya Anty Aliya da sauran flakes d'in.
Iman yazo ya kama abin mamaki nurses d'in na ta'ba gadon da niyyan ja Mama ta
birkice ta fara fisge fisge da sauri suka ja gadon zuwa Emergency d'aya tayi gaba
da gudu zuwa office d'in doctorn da mama ke hannunshi cikin tashin hankali suka bi
bayansu se kuma aka hanasu shiga da sauri doctorn ya zo ya shige yana kokuwan saka
lab coat. Kuka Iman ta fara lumshe ido Abdul yayi ya bud'e kan ya fara shafa
bayanta a hankali basuyi mintuna goma ba doctorn ya fito jiki a sanyaye ya kallesu
yace "sede fah hakuri Allahn da ya bamu ita ya d'auke kayanshi" da karfi Iman tace
"innalillahi wainna ilaihi rajiun" kan ta sulale zata fad'i kuma riketa yayi yana
kwala kiran sunanta, basu ankara ba suka ji fad'uwar baba ma a take nurses maza
sukayi kanshi yayinda Abdul ya sungumi matarshi da sauri ya nufi d'akinta da ita
dayake suna kusa da amenity ba 'bata lokaci suka karasa yana shiga d'akin Anty
kalthum ta fita da gudu zuwa office din dr Ameera se gasu tare a hanzarce umarnin
fita ta basu yayinda ta fara aikinta cikin kwarewa.
"Tooooh Mama fah an tafi, masu zarginta se su dena Allah sa mu cika da imani"
🖤Gureenjo🖤
🥀NOOR IMAN🥀
*038*
"Ba yanzu ba Mama bazaki tafi ki barni ba Mama kece gatana plz karki tafi" abinda
take ta furtawa kenan tun farkawanta daga suman shock d'in abinda doctor ya fad'a,
d'agota yayi ya rungume yana shafa bayanta a kunnenta ya dinga rad'a mata adu'o'in
da zatayi Don samun saukin tashin hankalin da take ciki sbd mutuwar Mama, ta kuwa
kar'ba tayi ta maimaitawa har seda taji ta samu natsuwa kan ta d'ago da sauri
"karfe nawa hamma?" Yace "hud'u saura" Da sauri ta nufi sauka ya riketa "Ina zaki?"
Tace "Hamma baza'a kai Mama bamuyi sallama ba dan Allah ka kaini In ganta" tayi
maganan hawaye na ci gaba da gangara daga idanunta.
Taimaka mata yayi ta sauka sossai tausayinta da sonta suka kara narkewa cikin
zuciyarshi ita kam haka Allah ya so ya ganta, Allah ya bata daman haye waennan
kaddarorin rayuwar, jikinshi ya manna ta har suka isa motanshi ya bud'e mata ta
shiga tana ci gaba da hawaye, shima zagayawa yayi ya shiga se ga Anty rahama itama
ta shige baya suka fice.
Karatun qur'ani yayi playing suratul A'araf sheikh Abdulrahman sudais ke rero
karatun, saurara take tana jin tension d'inta na sanyaya amma fah hawayen be dakata
da zuba ba sede ba magana ko uhm bata iya cewa har suka isa hawaye take, shima
gabad'aya yayi kalan tausayi zafin hawayen yakeji har ranshi amma ya ya iya? Dole
tayi kukan wannan rashi da ze iya da ya tayata.
Mutanen da ta gani jibgi a kofan gidansu yasa kukanta fara fita da shesheka, fita
yayi ya zagaya ya bud'e mata tare da rusunawa kad'an yace "kukan nan be isa haka ba
saudah? Kin san fa ba lafiyace ta isheki ba kema, kiyi hakuri ki kar'bi wannan
jarabawar hannu bibbiyu ko kin manta Allahn da ya bamu ya fi mu sonta? Lokacinta ne
yayi Muma In tamu tazo ko munki ko mun so se mun je gareshi so why not kiyi ta mata
adu'ar dacewa da rahamar ubangiji akan wannan kukan? Ko kin manta kuka karin zunubi
da nauyi ne ga mamaci?".
Tafin hannunta ta sa ta share fuskanta tana gyad'a mishi kai, mikewa yayi ya kama
hannunta Anty rahama da itama hawayen tausayin Iman d'in ya zubo mata ta bi
bayansu, da sannu da sannu suka shige cikin gidan, mata ne ko ta ina hakan ya sa
shi had'a hannunta da Anty rahama shi kuma ya ja baya, en uwa ne ko ta Ina kowa
hawaye da kukan wannan rashi yake Mama mutum ce wacce ta chanchanci ayi kukan
rashinta.
Ana ganin Iman kuwa aka fara Allah sarki Allah sarki wadda hakan ya kara sa Iman
kuka, d'akin baba aka nuna mata alamu chan gawan maman yake, da sassarfa ta karasa
d'akin tare da zubewa gaban gawan da aka mishi komai saura sallah da kaiwa
makwanci, kawai se ta rungumeta ta kuma fashewa da sabon kuka "Mama dan Allah ki
tashi na san baza ki mutu ki barni ni d'aya a duniyar nan ba, mama kin manta kince
In Shaa Allahu se kinga jikokina kan mutuwanki, kin manta kinci burin yi min wankan
jego da alkawarin ko Ina So ko bana so se naci tuwon dawa da kunun tsamiya? Mama
dan Allah ki tashi bazan iya ci gaba da rayuwa ba ke ba In wani abin ya kara faruwa
da ni fah? Mama kina so in mutu nima? Na san bakya so ki tashi dan Allah
mamaaaa.....".
Wani irin kuka me ban tausayi take, Baba dake gefe se share hawaye yake yayinda
Umma tayi saurin ficewa tana ci gaba da kuka, kaman ance saurara taji zuciyar Maman
na bugawa kasa kasa, kunnenta ta kara mannawa Ai ko de ba hasashe bane da gaske ne.
Chak kukanta ya tsaya ta d'ago ta kalli baba tace "baba Mama bata mutu ba wallahi
tana numfashi" girgiza kai baba yayi yace "kiyi hakuri Mamana, ke aka wa rashi dole
hankalinki yafi na kowa d'agawa, na sa...." katseshi tayi tace "baba ba fa wai
rud'ewa bane ko wani abu wallahi naji tana numfashi zo ka sa kunnenka kirjinta kaji
yana bugawa" dukawa Anty rahama tayi ta dafa kafad'anta tana cewa "haba Iman kiyi
tawakkali mana ko kin ta'ba ji Ance wadda ya mutu ya dawo ne?".
Wasu maza ne suka shigo sun kai goma mikewa baba yayi yana cewa "lokacin sallahn
yayi ko?" Kai suka gyad'a, a rud'e Iman ta d'ago tana cewa "baba na rantse ina
cikin hankalina Mama bata mutu ba zuciyarta na bugawa karku kashe min ita dan
Allah".
"Muje kawai gigitan mutuwanne ya sa ta fita hankalinta Allah ya baki hakurin rashi
Don ke aka yiwa" bappa yushe'u ya fad'a, biyo bayansu tayi Anty rahama ta riketa da
karfi ta fisge har tana fad'uwa dayake ita kanta ba wani karfin ne da ita ba, da
gudu ta biyosu tana fitowa tayi wani wawan tuntu'be tare da hantsilawa kad'an ya
rage ta kai kasa taji an riketa.
'Dagowa tayi se taga shine cikin kuka tace "yauwa kai kam na san zaka yarda dani
kazo muje Hamma kaji, wallahi naji zuciyar Mama na bugawa bata mutu ba sukace ta
mutu, ka yarda dani wallahi da kunnena naji" kallonta yayi cikin tausayawa har ze
ce a'a kuma se ya tuna tace ta san shi kad'ai ze yarda da ita idan yaki yarda da
ita fa? She will be shattered amma kuma idan suka je ba gaskiya taji ba fa? Same
thing.
Wani murmushi sauban ya saki yana mikewa yace "da sauran numfashinta lokacinta be
yi ba muna bukatar isa asibiti da gaggawa" zubewa Iman tayi kasa tana mika
godiyarta ga Allah ta hanyar sujudushukur kan ta mike ta rungume Abdul tana ta
maimaita "Alhamdulillah na gode, na gode".
Breaking hug d'in yayi sanin da mutane, a take aka maida Mama cikin gida kowa matan
se tambayar abinda ke faruwa sukeyi baba ne ke basu amsa da "bata mutu ba, ikon
Allah" kawai suna zuwa aka cire mata likkafanin aka sanya mata kaya suka d'auketa
se asibiti, ana isa akayi da ita ICU kaidarshi kuwa ba me shiga kwata kwata se
doctors, hakan ya sa Malabo kama hannun Iman zuwa room d'inta har kan gado ya kai
ta ta kwanta kan ya zauna gefenta yana shafa kumatunta yace "Alhamdulillah Allah
shine abin godiya, lokacin mama be kai ga yi ba tukuna, yanzu hankalinki ya
kwanta?" Kai ta gyad'a tana sake murmushi yace "masha Allah, to yi bacci ko zaki
samu natsuwar hankali Ohk?" Gyad'a kai tayi tare da lumshe ido kumatun ya ci gaba
da shafawa a hankali tun tana jinshi har bacci yayi awon gaba da ita.
Kallon su Anty kalthum yayi yace "sannunku fah" murmushi sukayi Anty rahama tace
"Ai kai ne da sannu da da gaske ne maman ta rasu da Allah kad'ai ya san halin da
Iman Zata shiga ciki idan ta wayi gari taga ba maman" Anty kalthum tace "Ai dole
Anty kin manta shakuwa da son dake tsakaninsu?" Ze yi magana kenan aka turo kofa,
family d'in Iman ne abin mamaki suka dinga shigowa suna dubata duk wadda ya zo da
niyyan duba Mama yaji baza'a barshi shiga ba se baba ya fad'a musu Ai Iman ma ba
lafiya tana asibitin se kuwa kaga sun shigo sun dubata.
Sossai Abin yayiwa Abdul daad'i ba kad'an ba yayi alkawari kuwa tana tashi se ya
fad'a mata waenda suka zo duba ta d'aya bayan d'aya Don kowa seda ya tambayi
sunanshi da alakarsu da Iman sam be manta ba suna cikin kanshi ras abinda be Saba
ba, murmushi ya saki yana furta "Anything for my hayateee" yayi maganan yana kallon
Anty rahama dake mishi kallon yaushe kuma ka zama haka.
Murmushi sukayi, Anty kalthum ta musu sallama ta tafi da tabbacin zata   turo driver
da abincin dare, godiya yayi mata tana dariya tace "haba hamma se kace   bare nayiwa?
Ai ko ba aure tsakaninku Iman matsayin zarah take da shi wurina" ta'be   baki yayi
kan yace "to maganatun ummu ke da Hafeez kam ban san waye gwara ba, na   sallameki se
da safe" Anty rahama tace "Da yake ta gama maka abinda kake bukata yau   ko? Ai dole
ka sallameta" harara ya sakarwa Anty rahama itama kuwa ba 'bata lokaci   ta rama,
ficewa Anty kalthum tayi tana murmushi kaman Anty rahama ta san abinda   ke zuciyarta
kenan tana tsoron furtawa ya ci mata.
Se bayan isha Iman ta farka yana nan zaune gefenta yana aikin kallonta d'akin ba
kowa se su biyu, tun da akayi magrib Anty rahama ta tafi akan bayan isha zata turo
baaaba, lumshe idanunta tayi ta kuma bud'ewa cikin nashi, murmushi ya sakar mata
itama ta mayar mishi "sannu" ya furta, tace "yauwa, wai nayi bacci sossai gashi duk
salloli sun wuceni" yace "dab magrib dr Ameera ta shigo na roke ta ta kara miki
alluran bacci cikin drib da tayi niyan sa miki that's why kikayi baccin sossai".
Kai ta gyad'a tana sauka tace "bari Inyi alwala" da sauri ya mike yana kamata yace
"kula karki illata min kanki plz, muje In raka ki na san jikinki har yanzu beyi
karfi ba" seda suka fara tafiya tace "da kayi zamanka Allah zan iya" yace "you are
welcome" siriryar dariya ta sake wadda ya sakashi murmushi seda ya kaita toilet
d'in kan ya fito ya zauna, bayan tayi abinda zatayi tayo alwala tana fitowa ya mike
ya rike mata hannu suka karasa kan taburma a kan darduma ta tsaya yace "zaki kuwa
iya a tsaye?".
Tayi murmushi tace "na fa ji sauki Hamma zan iya" yana murmushi yace "to
Alhamdulillah" tare da mika mata khimar sakawa tayi ta tada sallah ya koma kujera
ya zauna, la'asar, magrib and isha tayi duk ta gaji ta zauna tana nike kafafunta,
chak ya mike ya nufi basket da tana sallah drivern Anty kalthum ya kawo ya bud'e ya
zuba mata abinci a plate dafaffen doya ne da egg sauce se pepper soup na cow tail,
gyara zama tayi ya d'iba ya fara kai mata ba musu ta bud'e baki ya dinga feeding
d'inta har ta koshi tayi nak.
Ganin ya ajiye spoon d'in Don kau da kanta da tayi yasa tayi saurin d'aukawa ta
d'ibo kallonta yayi ta kauda kai tace "na san baka samu natsuwar cin abinci ba
kaima please bud'e nima inyi feeding d'inka" for the first time tun wayonshi da
wata mace zatayi feeding d'inshi, abinda ya tsana kenan Don yanzu ko ummu be yi
tunanin ze yarda ta bashi abinci a baki ba amma se gashi hankali kwance yake
kar'ban abinci daga hannun hayateenshi.
Kallonta kawai yake kaman ya samu Tv ita kuwa ta ki ko kallonshi abincin kawai take
bashi idanunta na kan plate da spoon d'in hannunta, hannunta ya rike ta kalleshi
yace "Alhamdulillah am full" a tare suka ajiye spoon d'in hannunsu cikin na juna,
cire mata khimar d'in jikinta yayi kan ya mike da ita zuwa kan gadon asibitin
pillow ya sa mata a bayanta ta jingina ya matsa jikinta sossai dukar da kai tayi
zuciyarta na bugawa "kin san yau suwa suka zo dubaki?" Kai ta girgiza mishi, nan ya
fara fad'a mata in ya kira sunan ya manta dangantakarsu se ya wani taune lips yana
buga goshinshi wadda hakan ke matukan burgeta tana murmushi zata tuna mishi se ya
waro ido ya had'a hannu ya buga yace "yesss" se kuma ya shagwa'be mata fuska yace
"ni bana so ki barni In tuna kayana da kaina!!" Murmushi sossai take sakar mishi
har fararan hakwaranta da wushiryanta su bayyana.
Wadda In hakan ya faru shagala yake da kallonta In hakan ya faru, haka sukayi a
karshen lissafin nashi dariya take mishi sossai jin yadda ya kira Nizziya er bappa
yushe'u da Nazza'u ne ko nizzaya wadda hakan ya bata dariya sossai, yadda ma yayi
pronouncing d'in abin dariya ne bare kaga yadda yake wani 'bata fuska kaman an
mishi dole, shagala yayi da kallonta a hankali ya kai hannunshi kan dimple d'inta
ya shafa.
Kallonshi tayi shima kuwa dama ya zuba mata ido, zuciyarshi ne ke luguden bugawa
sbd tunanin maganasu da Anty rahama dake dawo mishi, har kokon ranshi tsoro yake
kar maganan ya tabbatu, yana tsoron sata cikin ciwo da damuwa, amma ya iya dole ya
gwada don kawar da zargin zukatansu dashi da er uwarshi, a hankali yayi leaning
suna kallon juna cikin ido ya d'aura bakinshi kan nata ya fara kissing d'inta a
hankali.
Lumshe ido tayi jin hannunshi jikinta yanayi ne kawai ba Don wai ya ji daad'i ba
a'a sam har rawa jikinshi yake sbd fargaban abinda ze biyo baya, kaman kuwa jira
ciwo yake nan fah ta fara ja tana jan numfashinta sama, da sauri ya d'agota ya
manna ta jikinshi yana jin yadda take kokuwa da numfashinta, zazzafan Hawaye ne ya
gangaro kan kumatunshi kasan makoshi yake furta "innalillahi wainna ilaihi
rajiun!!!!" Hannunshi ya mika ya danna telephone d'in gefen gadon ba'ayi mintuna
uku ba nurses suka shigo ganin halin da take ciki yasa d'aya fita da gudu ta kira
doctor, seda dr. Amira tazo kan yayi karfin halin sa'buleta jikinshi ya d'aura ta
kan gadon jiki a sanyaye ya fita daga d'akin don baze iya jurar ganin irin alluran
da za'a mata ba, jijiyoyin jikinshi gabad'aya sun tashi rad'a rad'a fuskanshi yayi
ja ja jir tsabar 'bacin rai da damuwa, ko had'a ido aka ce kayi dashi baza ka iya
ba, safa da marwa yakeyi a bakin kofan yana tunanin who the hell is after
this!!!!!!!!
🖤Gureenjo🖤
🥀NOOR IMAN🥀
*ban san me zance gareku ba en Annur hausa novels da kuma Noor Iman fans, na gode
sossai da adu'o'inku gareni ga wanna naku ne kuyi yadda kuke so dashi, en Wattpad
Ina me baku hakuri plz ban samu fad'a muku uzurina kan lokaci ba rashin lafiya nayi
ta Ulcer wadda hakan yayi sanadiyar rashin jina kwana biyu, kuyi hakuri.*
                          *039*
Iska me zafi yake aikin fesarwa daga bakinshi yana safa da marwa cikin tsantsan
nazari da tunani, damuwa kuwa har ya rasa adadin da yake jinshi, hankalinshi In
yayi dubu ya tashi bayan duk abinda aka mata a baya ashe har yanzu ba'a barta ba?
Ta Ina ma ze fara da wannan jinyan nata? Fitowar dr Ameerah ne ya maido hankalinshi
kanta tana share gumi tace "Anya dakta?" Murmushin karfin hali yayi yace "kar ki
damu na gano matsalanta zaki iya bamu sallama ko yau In Shaa Allahu ciwon baze sake
tashi ba".
Tace "za'ayi haka kuwa?" Yace "yes of course" Tace "shikenan bari inje office in
rubuto muku" Kai kawai ya iya gyad'a mata yana nan tsaye be motsa ba bare yayi
niyyan shiga d'akin har taje ta kawo musu takardar cikin tausayawa ta kalleshi
zatayi magana yayi saurin sake murmushi yace "dr har kin kawo?" Tace "eh gashinan
plz a kiyaye" dayake ba yarinya bace yasa yace "In Shaa Allahu thanks" ya kar'ba
direct ya wuce yayi Settling bills d'insu na kwanakin da sukayi, daga nan ICU yayi
dr dake duba Mama ya nema.
Aka nuna mishi office d'inshi a bakin kofan suka had'u da sauban da mamaki yace
"har yanzu dama kana nan baka tafi ba?" Sauban yace "a'a na tsaya nan d'inne sbd
hankalinka ya karkata kan Iman ka san itama tana bukatar kulawa sossai" Kai Abdul
ya gyad'a tare da cewa "an ma yi discharging d'inmu yanzu zamu tafi" da mamaki yace
"har ta warke?" Kai kawai Abdul ya gyad'a Don baze iya fad'awa Sauban d'in sirrinsu
ba Don hakan kaman wani Sirri ne na rayuwansu shi da Iman kawai Anty rahama kad'ai
ze iya fad'awa Don suyi shawara.
Murmushi sauban yayi ba Don ya yarda ba yace "Toh Alhamdulillah, dr mukhtar yayiwa
Mama duk tests d'in da ya kamata daga yau har bayan two weeks ba wadda ze iya shiga
kanta se an san wani irin cuta ce da ita" kai Abdul ya gyad'a yace "Ohk yanzu zan
tafi da Iman gida bazan samu zuwa biyan kud'ad'en ba bari In turo maka, ko wani
nurse ne se ka sa ya biya please" sauban yace "Ohk ba matsala" a take Abdul ya
mishi transfern manyan kud'ad'e ya mishi godiya kan sukayi sallama suka yi
hanyoyinsu.
'Dakin da Iman take ya shiga a zaune ya ganta ita kad'ai ta buga tagumi cikin
tunani gadon ya karasa har ya zauna bata sani ba, hannu ya sa ya janye tagumin nata
kallonshi tayi hawayen idanunta ya gangaro hakan ya sashi gane ta fahimci abinda ke
faruwa kenan, matsawa yayi gabanta sossai sai kawai ta kifa kanta jikinshi ta fashe
da kuka mai sauti, lumshe ido yayi yana shafa bayanta a hankali shima kaman yayi
mata kukan.
"Ni kam anya Ina da rabon farin ciki kuwa a rayuwata? Me yasa ne? Upon all people
of this world a rasa wacce za'a sa gaba da mugayen manufa se ni? Me yasa se ni
hamma? Me yasa?" Cikin kasa da murya yace "kaddarace ki daina irin waennan kalaman
kar kije kiyi sa'bo watarana, ko kin manta kar'ban kaddara me kyau ko marar kyau
yana daga cikin cika cikan imani? Kika san ko ta wannan hanyan ki shiga aljannah?
Ki kara hakuri watarana komai me wucewane".
Cikin rawar murya tace "kaima rabuwa zakayi dani ko?.... sbd.. bani da anfani a
gareka... da ni da photo duk d'aya ne macen da baza ta iya ta'bukawa mijinta komai
ba bata da anfani a ga....." tattausan hannunshi ya d'aura kan lips d'inta yace
cikin taushin murya "kinfi kowacce mace yanzu anfani a rayuwata hayatee bayan
ummu...." da sauri ta d'ago tana kallonshi idanunshi ya narkar cikin nata cikin
tabbatarwa yace "yes ina so ki cire ran rabuwar aurenmu hayatee, auren mu yafi na
zo'be karfi ko da bana kallonki muryarki kawai zanji zan iya rayuwa a haka ya
wadaceni har gaban Abada".
Jikinshi ta koma tayi lub ya ci gaba "bare duk wani halin da zaki shiga hayatee se
na fiki tashin hankali sau dubu fiye da naki, zan tsaya miki ko da ba ni zan anfana
da lafiyanki ba har se na tabbatar kin zama cikakkiyar mutum fiye da tunanin me
tunani" hawayen ne ya gangaro mata ta sa hannu ta zagaye bayanshi da kyau yau kam
ta tabbatar ta yi dacen miji, ta samu shouldern da duk wani abinda ze Faru da ita
zata iya kwanciya akai tayi kukanta son ranta, tayi dacen da ba wata mace a duniyar
nan da zata iya katarin samun mijin da zai zauna da ita ko da bazata anfaneshi da
komai ba, tabbas Abdulraheem d'an halak ne wadda ya san hallaci ya kuma gada, ko ba
komai tana sonshi fiye da tunanin me tunani rabuwa dashi shi ze yi ajalinta ta
tabbatar, bata san yaushe ba, bata san ta yaya ba, bata san sa'arda sonshi ya shige
zuciyarta yayi kane kane ba, halaccinshi gareta kuma ya kara fad'ad'a son har ya
rufe duk wani gur'bi lungu da sako na zuciyarta.
Wayanshi dake silent ya fiddo bayan ya bud'e mata Sit ta zauna, wasu nurses en mata
ne suka biyosu da tarkacensu wadda duk daga na Anty rahama se na kalthum se kuma
kayan da aka sayo mata a supermarket, da kanshi ya bud'e musu boot suka saka, cikin
karairaya d'ayar ta ce "kana da kyau, handsome kaji daad'i kai kam" murmushi yayi
sbd kawai kar ya dizga ta taji ba daad'i bayan sun mishi aiki, ba tare da yace
komai ba ya wucesu ya bud'e murfin da niyyan shiga d'ayar tace "pls handsome in ba
damuwa ka bamu number d'inka ma dinga zumunci" had'e gabas da yamma yayi kaman ze
yi magana se kuma yace "excuse me" ya shige motan tare da tayarwa kaman ze buge
d'ayar yayi ficewanshi.
Kaman ance ya kalli Iman tab ta had'e gabas da yamma tare da cunno baki, murmushi
ya saki ya san be wuce kishi ba tunda Lafiya lau suka fito daga cikin asibitin zuwa
mota, yaji daad'in hakan sossai sbd hakan ya sa ya gane tana sonshi ko da kankani
ne tunda ta iya yin kishin shi, tuna daren jiya yayi yadda suka rabu kan tafiyan
shi, bari de ya gwadata ya gani "Hayatee me yasa kika ki d'aga wayana jiya da dare
bayan na san kin gani?" Kallonshi tayi tare da yin raurau da ido tace "kayi hakuri
wallahi sharrin zuciyane nima na san ban kyauta ba" murmushi kawai yayi wani
nishad'i da farin ciki na mamayeshi ya tabbata itama tana sonshi, ganin yayi Shiru
tace "I'm so sorry In Shaa Allahu hakan baze sake faruwa ba" Kai ya gyad'a mata,
hasken wayanshi yasa ya maida hankali kai picking yayi ganin Anty rahama.
"Ayi ta kiranka baza ka d'auka ba kai kam" yace "wayan na silent" tace "wai nace
nazo na samu baaba ma na d'an ciwon ciki da amai shine nayi ta kiranka In fad'a
maka baza ta samu zuwa ba ya za'ayi da kwanan se kuma bakayi picking ba" yace "mind
not an ma yi discharging d'inmu" Tace "what???? Ba de abinda muke zargi ne ya
tabbata ba?" Ajiyar zuciya me nauyi ya sauke kan yace "muyi waya gobe plz" ya kashe
wayanshi.
Ba wadda ya kara magana cikinsu har suka isa gida, zagayawa yayi ze taimaka mata
tace "zan iya fah" yace "na sani madam" a tare suka shiga gidan yana tallafe da ita
har sama, zaune kuwa suka tarar da Hamna a parlorn saman cikin wata arniyar kayan
bacci da ko kunyar idon mahaifiyarta be hana ta sawa ba, tana ganinsu ta mike tsaye
tana rike kwankwaso, ko kallonta duk cikinsu ba wadda yayi ita iman yanzu yadda
take tana jin duk wadda yayi kuskuren shiga gonanta zata koya mishi hankali,
yayinda hamna ke kiyasta yadda zatayi da Iman sbd lokutan da Abdul ya 'bata tare da
ita a ranan girkinta.
"Me kake nufi da ni ne hamma" tayi maganan cikin sanyi wadda hakan ya sa shi jin ba
daad'i, tare da dakatawa fisgewa Iman tayi daga jikinshi ta fad'a d'akinta dama sun
isa kofan, ta rufe kayanta daga ciki, da kallo ya bi kofan kan ya kalli hamna yace
"kaman me fah?" Tace "amma ka san yau kwana na ne ko? Amma se yanzu kake dawowa
kalli time, sannan na tambayeka zuwa nijar kaki bani gamsasshen amsa wai me kake so
in maka ne plz da ze sa ka gane Ina so rayuwanmu ta ingata mu wanxar da farin ciki
tsakaninmu" kuka ta saka tana cewa "ka yarda dani nayi nadamar rayuwar auren da
nayi da kai a baya, zan gyara In Shaa Allahu baza ka sake jin wata matsala daga
gareni ba".
Tausayi ta bashi hakan ya sashi karasawa gareta ya rungumeta "is Ohk, komai ya wuce
muje mu kwanta dare na kara yi" wani shegiyar murmushi ta sake a 'boye plan d'insu
ya tafi yadda suka tsara, hararan kofan Iman tayi tana cewa a kasan makoshinta
'Sannu Sannu dae bata hana zuwa sede a Jima ba'a je ba, muje zuwa wai mahaukaci ya
hau kura, yanzu wasan ya fara' d'aki suka nufa tana manne jikinshi tana mishi wani
salo irin na yaudara da kirsa irin ta mata, nan take ya rufta.
Wanka kawai tayi bayan shiganta d'akin ko kaya bata saka ba tabi lafiyan gado daga
ita se towel, bata iya farkawa ba har se da taji bugun kofa juyi tayi tana mutsike
idanunta a hankali ta sanya kafafunta kasa ganin me knocking baze dena ba, kofa ta
nufa ta ma manta me jikinta kawai ta bud'e kofan, kallonta yayi yadda tayi mishi
wani irin kyau a haka daga ita se towel, fuskanta ya d'an kumbura kad'an idanunta
suna lumshewa da bud'ewa da kansu tsabar baccin be isheta ba aka tashe ta.
Ganin kallon yayi yawa yasa ta shagwa'be fuskanta tare da d'an bubbuga kafanta kasa
tace "dan Allah hamma bacci" yayi murmushi yana me enjoying kallon nata a haka tare
da shagwa'barta yace "kiyi sallah tukuna se ki koma baccin" da mamaki tace "wai har
asuba tayi?" Yace "zauna nan" tare da juyawa ya wuce zuwa room d'inshi, itama
d'akinta ta koma tana shiga bayi ta kalli kanta mirror se ta sake kara tana sake
kallon jikinta, wai haka ta fita ya ganta kaman wata mahaukaciya ga karamin towel
iya cinya, ita kam ta shiga uku gata da Kishiya a haka ne zata karkata hankalin
mijinta kanta.
Dafa goshi tayi cikin kasala tace "ummu plz.... Ina da bukatar zahra ki tausaya"
yanzu ta dawo ta Ina zata fara Don fa bazata zauna hamna da ummanta su mayar da ita
wata bi ta chan ba, hawaye ne ya gangaro mata tuna bata da wani anfani yanzu ga
mijin ma da take Shiri akanshi, sharewa tayi tana nufan basin da wannan tunanin
tayi alwala, ta fito ta sanya doguwar riga tayi sallah da raka'atanil fajir ta fara
kan ta gabatar da na farilla, bayan ta gama bata kwanta ba seda tayi karatun
qur'ani har seda gari ya fara haske kan ta kwanta bacci abinta.
Yana komawa d'akin ya samu wayanshi na neman agaji tunani ya fara waye da asuban
nan haka gabanshi ne ya fad'i ganin Zahra, d'agawa yayi tare da sallama, ta amsa
tana d'aurawa da "hamma Abba ba lafiya ka taimaka ka zo kar ya mutu ya barmu..."
yanke wayan yayi yana zaran keyn da ya ajiye jiya kan dressing mirror, da gudu ya
fita zuwa kasa yana shiga motan ya sakarwa me gadi horn da sauri ya bud'e mishi get
ya fita a guje.
Dayake ba kowa kan titi nan da nan ya isa gidan nasu ko parking me kyau be yi ba ya
fice da gudu Hafeez da yanzu shigowanshi daga masallaci sbd d'an makara da yayi
yana tafiya ne yana mamakin rashin ganin Abba masallaci, dama ya tafi da mamakin
abinda ya hana Abba zuwa buga mishi kaman ko yaushe, ganin Abdul haka ya sa shima
ya rufa mishi baya a tare suka isa part d'in Abban parlor suka sameshi kwance kan
doguwar kujera yana numfashi da kyar yayinda zahra ke zaune kasan kujeran tana
aikin kuka.
A rud'e sukayi kanshi suna kiran sunanshi ganin halin da yake ciki yasa sukayi
saurin sa'barshi zuwa mota zahra tabi bayansu, da mahaukacin gudu Abdul ya ja
motan, wani private hospital dake nan kusa ya kai shi nan take suka amsheshi zuwa
emergency, tunda dr ya shiga ba shi ya fito ba se wuraren 8, kallonsu yayi yadda
duk suka tashi hankalinsu ba me iya magana cikinsu, d'an murmushi yayi kan yace "ku
kwantar da hankalinku mun shawo kan komai Alhamdulillah, jininshi ne yayi mugun
hawa kuma ya jima cikin wannan yanayin ba'a bashi taimakon da ya dace ba hakan ya
sa jikin tsananta amma yanzu komai ya koma normal se kuyi kokarin kwantar mishi da
hankali har jininshi ya sauka gabad'aya yadda ya dace".
Hafeez ne yace "In Shaa Allahu mun gode dr. Zamu iya shiga mu ganshi?" Yace "yes
sure amma plz banda hayaniya" Kai ya gyad'a likitan ya bi gefensu ya wuce, wani
wawan ajiyan zuciya duk suka sauke, cikin karfin Hali Yacewa zahra "me ya sameshi?"
Yana tsoron jin amsanta har ga Allah, kar tace ummu ce sila kuma ta sanadiyarshi da
Iman.
Abinda be so jin bane kuwa yaji "rikici sukayi da ummu akan hanani magana da Iman
da tayi.... Hamma dan Allah kuyi wani Abu maganganun ummu na jiya ga Abba wallahi
sun mugun d'aga min hankali..." ta karasa da kuka sossai, Hafeez ne ya karasa yana
bubbuga mata baya yayinda Abdul ya buga bayanshi da gini yana dafe kanshi ya
tabbata a tsakanin nan aka dubashi shima ba abinda ze hana a ga jininshi yayi
matukar hawa, wani irin Abu ne wai haka? Me mutanen nan suke so yayi ne kam, wani
zuciyar yace Sakin Iman shine solution to all this problems don lokacin da ya auri
hamna ba haka ba, da sauri ya gyad'a kai yana mikewa daga jinginan da yayi ba tare
da ko ya kallesu ba ya nufi hanyar waje.
🖤Gureenjo🖤
🥀NOOR IMAN🥀
*this page is a dedication ga duk wata Nurse me karanta littafina I'm so sorry if
yhu guys feel disappointed, or some kind of disrespect a page d'ina na jiya, ban sa
don cin mutunci ko wani abu ba if yhu noticed and baka ji daad'i ba sorry!!!!!.
*040*
Banko kofan da akayi ne ya sanyata d'ago kai daga kallon jibgin akwatunan dake
gabanta da take shirin fara jerasu cikin wardrobe, kallon Hamna takeyi cikin
mamakin wannan isa haka, ta tashi da wuri sbd bata wani iya baccin safe ba amma
taji daad'in d'an baccin sossai fiye da yadda zatayi na awanni jinta take garau
kaman ba jiya aka sallamota ba hakan yasa ta watsa ruwa kawai ta zura wata cotton
doguwar riga ba tare da ta nemi d'ankwali ba ta janyo akwatunanta da shirin
shiryasu cikin wardrobes d'in.
Cikin ta'be baki take karewa d'akin kallo up and down side by side, daga karshe ta
ja tsaki tana cewa "Eyyah abin kunya da Allah wade na gode Allah da nawa iyayen ne
suka min komai na d'akina basu jira gidan miji ba" ta'be baki tayi tace "Au ashe fa
talakawa ne likis ba sisi bare kobo na taburman kaba" Zatayi wani maganan Iman tayi
saurin cewa "toooh Allah sa de lafiya baiwar Allah se kace ba musulma ba? Ki
shigowa mutum wuri ba sallama sannan ki tsaya kina haushi kaman......" bata karasa
ba ta wani kwa'ba fuska ta maidashi kan kayan.
Cikin 'bacin rai hamna tace "kutumarr ni kike kira karya??" Ko kallonta Iman batayi
ba ta bud'e wardrobe ta fara shirya atamphopin da ta fidda daman, "ke da ke fa nake
magana, don uwa....." "kulll" cewar Iman tana karawa da "Uhmmm uhmm uwata fah ba
sa'an wasan wata uwar bane bare wata yarinya ta samu daman zaginta a kiyaye" cikin
'bacin rai Hamna tayi kanta tare da d'aga hannu da niyyar marinta, hannunta taji an
rike a zuciye ta juya se suka had'a ido yanayin da taga fuskanshi kad'ai yasata
sanyaya nata zuciyar kofa ya nuna mata juyowa tayi ga iman tayi mata wani kallo kan
ta juya ta fice fuuu.
Ajiyar zuciya ya dinga saukewa a jere a jere cikin sanyin murya yace "hayateee
bazan iya rayuwa ba tare da ke ba wallahi Ina sonki sossai, kallonki kawai da nayi
naji rabin damuwana sun yaye" d'agowa tayi ta kalleshi kad'an wani irin sonshi na
kara mamaye mata jiki da jini, hannunshi ta kama be musa ba ya bita har bakin gado
suka zauna kwanciya yayi tare da d'aura kanshi kan cinyarta ita kuma ta sa hannu
cikin sumar kanshi tana wasa da shi.
Cikin taushin murya tace "menene ya faru? Akan matsalata ne ko?" Hannunta d'ayan ya
kama ya d'aura kan kirjinshi tare da d'aura nashi kai idanunshi lumshe yace "Abba
ba lafiya" a rud'e tace "innalillahi wainna ilaihi rajiun me ke damunshi haka??
Yana Ina asibiti ko gida?" Bud'e lumsassun idanunshi yayi ya zuba mata yadda ta
rud'e kawai yasa yaji jikinshi yayi sanyi har hawaye ta fara ko su iya rud'ewar da
zasuyi kenan.
Fridge ta bud'e ganin kaza ya sa ta fiddo shi ta sa mishi ruwan zafi nan da nan ya
narke kan ya narke ta had'a abubuwan da zata bukata ba 'bata lokaci ta had'a pepper
soup na kazan da vegitables ta barshi on low heat, tana aikin ne tana sake murmushi
time to time sbd tuno yadda ya furta yana sonta, bata ta'ba zato ba kuma har yanzu
bata yarda ba taya za'ayi ya so ta cikin lokaci kankani haka, watakila ya fad'a ne
kawai Don yana cikin damuwa amma ko ma menene ta ji daad'i har kasan ranta daad'in
da ta jima bata ji ba a rayuwanta wannan ranar yana d'aya daga cikin waenda bazata
manta ba har Abada.
Irish da plantain ta soya a d'ayar cooker d'in kuma ta dafa white basmati rice,
cikin sabbin coolers d'in kitchen d'in ta shirya komai ta sa a basket tare da
d'aura tumakasa ta rufe saman, a plates ta d'iba musu ita da shi ta zuba p soup
d'in a bowl me d'an girma ta kara zuba plantain and chips d'in wani plate ta
d'aurasu kan tray bata san ko ze sha tea ba, amma de ta dafa ruwan zafi ta juye a
karamin flask ta d'aura gefen tray d'in da cup da kuma spoons, teaspoon and forks,
ta d'auka ta nufi room d'inta da shi a kan center table d'in parlor ta ajiye,
wayanta da ta tuna ta manta shi kitchen ya sa ta koma d'aukowa, daga bakin kitchen
d'in taga umma da plate da serving spoon ta nufi basket d'in da ta shirya don Abba,
da azama ta karasa ta d'auke shi dayake ta fi kusa da basket d'in.
Wani wawan kallo umma ta mata kan tace "ke yaushe na fara wasan haka dake? Kin
ajiye min abinci na d'iba ko se na kutuma miki na maguzawa?" Cikin ladabi tace
"umma Abincin na Abba ne asibiti za'a kai mai" wata uwar harara ta buga mata kan
tace "aaa Baba ne ba Abba ba kin ajiye ko se na sa'bamiki?" Juya kai tayi kan tace
"gaskiya umma kiyi hakuri ba zan iya d'ibar miki ba, In akwai gaskiya ma Ai Anty
hamna ce da girki har mu ya kamata ta bawa amma ana neman 10 ko kitchen d'in bata
shigo ba bare ta d'aura wani abin".
Tana kai nan ta juya ta fice waro ido umma tayi tace "kuttt kan kaza fah ya fara
wayewa ya kamata mu d'auki mataki cikin gaggawa dama ance talaka be iya samun wuri
ba" Shiru tayi cikin nazari in ta barta zata ga kaman bata isa da gidan bane
gabad'aya In ko ta bita zata kawo mata raini tunda taga ta fara gashi abincin ya
shiga ranta. Da karfi ta fara kwala kiran sunanta tana cewa "ke saudatu ne ko wace
uwar tsaya wallahi ko kiyi nadama yanzu In kira wacce ta kawo mijin naki duniya ta
nuna miki Ina da muhimacci sossai a rayuwanku in kuma nuna miki isata".
Da waennan surutan ta karasa ta banke kofar d'akin Iman d'in wadda hakan yayi
sanadiyar tashin Malabo hayaniyarta ta ci gaba dayi har cikin d'akin yayinda iman
ko ta kalleta taje ta ajiye basket d'in gefen gado, kallonshi be sa ta dena
masifanta ba yayinda Iman tayi kaman bada ita take ba shine yayi karfin halin cewa
"umma lafiya?" Tace "Ina fah Lafiya ka kawo fitsararriya marar tarbiyya me
ji......" hannu ya d'aga mata yace "no please go straight to the point" waro ido
tayi tace "aaa ashe ga inda ta gani kaima raina ni kenan zakayi toh shikenan d'an
halak kafasa mu zuba ni da ku" ta fice fuuuu.
Dafe kai yayi kan ya d'aga ya kalleta fuska ta shagwa'be tare da cewa "Allah ni ba
ruwana" girgiza kai yayi yana shirin mikewa fakonta yayi ya fisgo hannunta zuwa
jikinshi yace "bakya ji ko?" Da farko ta tsorata kan ta shagwa'be tace "Da gaske ni
ba ruwana" serious ya ci yace "ki dena neman maganansu pls kinga bana so a ta'bamin
lafiyanki d'azu da ban zo ba fah?" Shiru tayi a zuciyarta tace 'tabbb sun isa ma?
Ni kuma Ina me?' A fili tace "ba abinda ze faru in shaa Allahu, abinci na sanyi
zaka ci ko zaka fara yin wanka?" Murmushi yayi cikin wani yanayi na jin daad'i
abinda ba'a ta'ba yi mishi ba kenan a gidanshi ace wai abinci ne yau ake mishi iso
ya ci kar yayi sanyi ko wanka tukuna, abinda da yayi da ko kar yayi duk d'aya wurin
matarshi.
"Bari In ci kan wankan rabona da sa abu a cikina tun lunch na jiya shima snacks"
d'agowa tayi tace "Eyyah muje to ka ci" gaba tayi yabi bayanta zuwa parlorn kasa ya
zauna ta sauko musu abincin suka fara ci, se santi yake mata tana dariya wallahi
kaman ba shi ba, bata ta'ba ko da hasashen haka yake ba a da yadda ko fara'a bashi
da shi a gaban mutane, shi ya fara ajiye cokalin yace "Alhamdulillah thanks for
this wonderful meal hayatee" murmushi kawai tayi, bayan ta gama ta mike kenan da
nufin zuwa d'akinshi had'a mishi ruwan wanka se kuma ta tuna ashe ba itace da girki
ba, tray d'in ta d'auka ta fito da shi, wani kara ta saki wadda ya sa malabo dake
shirin shiga room d'inshi shigowa kitchen d'in da sauri, da gudu ta 'buya bayanshi
"lafiya me ya sameki?" Ya fad'a yana shirin juyo ta amma sam taki sakinshi ta
makale a bayanshi ga plates d'in duk zube kasa Allah ya sa unbreakable d'in nan ne.
"Innalillahi wainna ilaihi rajiun baka ganshi ba?" Yace "wa?" Tace "wani kato tsaye
yana anfani da kitchen utensils?" Ajiyar zuciya ya sauke yana dafe kai lokaci d'aya
murmushi na su'buce mishi a lokaci d'aya kuma ya had'e rai yace "Peter will yhu
please excuse us?" Peter da ya hangame baki yana kallonsu yace "yes sir" kan ya bi
ta d'ayar kofan ya fita stairs ya gangara kasa ta inda yake bi.
"Cook d'in mu ne fa" ta d'ago da sauri tana cewa "yanzu wannan gardin ke yawo muku
a cikin gida a matsayin kuku? Tabb" ta juya ta fice shima fita yayi zuwa d'akinshi
duk wanka sukayi suka fito kusan a tare a shirye shi sanye da normal kananan
kayanshi bakake ita kuma ta sa wata atampha doguwar riga hijab ta sanya sbd kamata
da kayan sukayi ba komai a fuskanta hannunta rike da wayanta da kuma basket d'in
abincin Abba, sossai ta mishi kyau ba tare da sun nemi mutanen gidan ba suka fice,
Allah kad'ai ya san me suke kullawa sun kule a kuryar d'aki.
Wata BMW d'inshi ya d'auka suka fice zuwa asibitin hira suka dingayi a hankali akan
rayuwanta wadda shi yake d'an tambayanta abinda ya d'aure mishi kai tana bashi amsa
for the first time a rayuwanta da ta ta'ba ba da kad'an daga cikin labarinta batayi
kuka ba, gani take yanzu fah komai ya wuce In Shaa Allahu damuwowinta sun kare
bayan na ummu shi kuma tana sa rai wata rana komai ze wuce.
A jere suka shiga asibitin wani irin kima yake gani yayi da ita sanye da hijab be
ta'ba sanin darajar hijabi ba se yau da ta sa yadda ake kallonsu ma kawai daban ne,
tunawa yayi hamna bata ta'ba sa khimar wai zata fita ba, shi hijabinta ma d'aya ya
sani na sallah wadda bata ma cika anfani da shi ba, da sallama ya tura kofan d'akin
hafeez dake zaune kan plastic chair ya amsa yana d'ago kai murmushi ya saki ganinsu
yace "Masha Allah Amarya anji sauki kenan" murmushi tayi tace "Alhamdulillah
babana, ya jikin Abba?" Yace "ni de ban son wannan babanan, jikin Abba kuma da
sauki bacci yake yi ma d'azu ya farka har magana yayi" murmushi itama tayi tace
"masha Allah" Mikewa Hafeez d'in yayi ya ba matar yayan nashi kujera godiya tayi
kan ta zauna shi kuma ya zauna empty bed d'in d'akin yayinda malabo ya zauna gefen
Abba yana tambayar shi Doctor be kara zuwa ba, yace ya shigo sau d'aya ya kara
dubashi, ze yi magana kenan aka bud'e kofan toilet aka fito duk wurin suka mai da
ido zarah ce, murmushi tayi kan tace "yaya ka dawo?" Yace "eh" Iman tace "Zahra
in......" dakatawa tayi ganin ko kallonta zarah batayi ba hakan ya sa ta tuna
abinda ummu tace cikin sanyin jiki da karayan zuciya ta dukar da kanta tana shafa
fuskan wayanta, zarahn ma jiki a sanyaye ta gyara yafin d'an kwalinta tana kallon
yaya hafeez tace "hamma muje tunda babban yaya ya zo samu inyi wanka se In dawo"
Kai ya gyad'a shima cikin rashin jin daad'i ya mike, malabo ya d'auke idanunshi
daga kan matar tashi yace "kun fad'awa su Anty?" Hafeez yace "a'a ban fad'a musu
ba" Abdul yace "Ohk zan kirasu, sannan ku tabbatar kun fad'awa ummu kuna isa gida"
Kai suka gyad'a suka mishi sallama suka fita.
"Hello baba Ina kwana?" Be ji me aka ce daga d'aya bangaren ba yaji ta kara da "ya
jikin mama?..... Ohk har yanzu ba'a barku kun shiga ba?" Ta kuma yin Shiru kan ta
kara da "amma sun ce da sauki?....... toh Allah ya kara sauki ya bata lafiya ka
gaida su umma" suka kashe wayan kallonshi tayi se ta sakar mishi murmushi shima
murmushin ya mayar mata ganin bata sa abin sossai a ranta ba, wayan shi ya fidda ya
kira Anty rahama da Anty kalthum ya fad'a musu a rud'e duk suka ce gasunan zuwa
dukda ya fad'a musu da sauki.
Yana kashewa aka kirashi d'agawa yayi na mintuna kan ya mike yana ci gaba da amsa
call d'in yace "ganinan zuwa yanzu Ohk Ohk" yana kashewa yace mata "hayatee ana
nemana a office bari inje bani one hour" Tace "Toh Allah ya kiyaye ya tsare" ya
amsa da Amin yana ficewa, da wayanta ta ci gaba da wasa Haka kawai taji tana son
kiran inna ta kuwa kirata suka gaisa cikin mutunci kaman ba inna ba wadda hakan
yayi matukar bata mamaki, har de sukayi sallama bata bar mamaki ba, su Goggo ne ma
suka dinga amsa mata wani iri amma se da ta kirasu tas, tana kashe wayan ta d'ago
se suka had'a ido da Abba.
Murmushi ta saki kan tace "sannu Abba ka farka?" Kai ya gyad'a ta dan zame daga kan
kujeran tace "Ya karfin jikin?" Yace "Alhamdulillah" a hankali ya fara kokarin
mikewa ta karasa ta d'ago mishi pillow ya jingina tana mishi Sannu, toilet ta shiga
ta samo silver ta zo table water ta d'auka ta d'auki sabon brush da ta gani da
alama su hafeez ne suka tanadar mishi ta sa mishi macline ta kawo mishi.
Brush yayi ta tattare kayan ta mayar toilet ta fito ta saka mishi abinci tare da
jan irin abin cin abinci da ake ajiyewa a amenity d'in ta d'aura akai ta ja dayake
me taya ne zuwa gaban gadon kara gyara zaman shi yayi yayi bismillah ya fara ci a
hankali, yana cikin ci Doctor ya shigo da murmushi yace "masha Allah patient d'ina
ya farka" Tace "eh doctor be jima da farkawa ba" yace "haka ake so yanzu zan rubuta
wasu magunguna se a sayo mishi yana gama cin abinci ze sha in an sayo ki sameni
office d'ina In miki prescribing yadda ze na sha Har Allah ya kawo sauki".
Amsa mishi tayi ya karasa ya duba Abban suka gaisa kan ya ja farin plain sheet ya
rubuta magungunan ya bata kar'ba tayi ta mike ta fita Bayan ta cewa Abba bari taje
ta zo, kai kawai ya iya gyad'a mata, seda ta fito har wajen asibitin kan ta samu
POS tayi musu transfer duk kud'in account d'inta dubu goma suka bata cash, asibitin
ta dawo pharmacy d'insu ta sayi maganin kan ta koma cikin asibitin ta nemi office
d'in doctorn yayi mata prescribing kan ta koma d'akin.
Anty rahama da Anty kalthum ta samu har Abba ya gama cin abincin sun tattare
Kwanukan Anty rahama tace "Ina kika shige ne Abba yace kin je Sayan magani tuntuni"
tace "eh wallahi se da na fita POS and kuma pharmacy d'in akwai layi, ga nan
magungunan Doctor yace ya sha yanzu" kar'ba sukayi Abba na yabawa karamci irin nata
abinda 'ya'yan cikinshi zasu mishi ya tabbatar itama abinda zata iyayi kenan
watakila ma har ta fi su, dubi yadda tayi wahalanshi daga zuwa dubiya, ita kuma a
'bangarenta gani take ko me zatayiwa Abba bata fad'i ba tunda har ya fi uban da ya
haifeta ya tsaya mata akan komai har ta samu his handsome, gentle and super loving
son, kofan da aka bud'e ne yasa duk suka maida hankalinsu kan kofan Ummu ce ta
shigo cikin shiganta na yau da kullum wadda basu wuce na alfarma ba.
Cikin isa ta karaso tana kallon Iman ta had'e gabas da yamma "Ina kwana ummu?"
bazata iya shiru ba hakan yasa ko gaida Abban batayi ba tace "tooo su gayyan sod'i
wa ya gayyatoki? Ina ji da cikin ki wallahi ki jira randa zan haifeki kar ki d'auka
duk abinda kike ban sani ba Ina sane d'ana kuma tunda ba ke kika haifarmin shi ba
se kin rabu dashi alakakai wacce tunda ta shigo zuri'ata zuri'ata ya wargaje,
malama kin fita ko se na ci mutuncin waenda suka kawoki duniya?" Mikewa Iman tayi
da sauri kanta kasa ta fice su Anty zasu yi magana tace "duk wacce ta yarda ta min
magana kan wannan watsatsiyar In ranta yayi dubu to se ya 'baci" tana fita hawayen
idanunta suka fara gangara me tayiwa ummu ne da ta tsane ta haka? Wata zuciyar tace
uwar da ta haifeki ma ta tsaneki to waye baze tsaneki ba? Tana tafiya tana share
Hawaye har ta fita get ta tare napep da sauran chanjin hannunta ya kawota gida,
shiga tayi bayan sun gaisa da me gadi bata ko kula su hamna ba da ganinta cikin
kuka yasa suka kwashe da dariya harda tafawa ta fad'a d'aki zuwa gadonta ta fashe
da kuka me sauti.
🖤Gureenjo🖤
🥀NOOR IMAN🥀
*041*
Murmushi yake sakewa akai akai yana sauraran sauban dake zuba mishi surutu akan
Iman, tsaye yake ya d'an jingina bayanshi da gini tare da hard'e kafanshi "khaih
Abokina ka rufta dayawa wallahi wai kaga yadda ka rud'e kuwa akan yarinyar nan?
Allah ban ta'ba zaton zaka so wata mace haka ba duba da yanayinka akan mata" wani
murmushin ya saki yace "Ni Allah ka rabu da ni In ba kana so ka neme ni ka rasa
bane sbd In kana hiranta ji nake kaman inyi tsuntsu In sauka gareta".
Wani irin dariya Sauban ya saki yana cewa "sannu Romeo ko ince majnun kai yanzu ka
zama fah mijin tace" harara ya sakar mishi yana kauda kai yace "Kai ta shafa d'an
sa ido" dariya ya ci gaba dayi har seda Abdul ya buga desk d'in gabanshi yana cewa
"Allah ko ka gayamin abinda ya sa ka juyo dani daga asibiti zuwa office d'inka ko
In maka rashin M" tsagaita dariyar muguntan shin yayi yace "akan maganan mama ne
matar fa tana wahala sossai gashi alamu sun nuna tana kumbura da kad'an da kad'an
why not in da hali ka kaita wani kasan sbd su duba ta da kyau mu iya dubawanmu bamu
gano komai ba dukda sauran results d'in se nan da sati biyu, amma ni a ganina wajen
zasu fi mu kayan gwaje gwaje ingantattu" gyad'a kai yayi kan ya gyara tsayuwarshi
yace "kana ganin wani kasa ya kamata a kai ta?" Sauban yace "I think Miami ko de
Cairo" dafe kai yayi abubuwa na cha'be mishi gabad'aya.
Ga ciwon Abba ga shi an turashi wani aiki New York, ga shi yana so cikin santin nan
su tafi Adamawa wurin baba fufore sbd matsalan hayateenshi da ummunshi, yana so
yaga komai ya tafi smoothly amma be san...... katseshi sauban yayi da cewa "ya y
lafiya kuwa mutumi na?" Ajiyar zuciya ya sauke kan ya fad'a mishi damuwanshi amma
ya 'boye akan me Iman zataje ganin baba fufore, murmushi Sauban yayi yana cewa "Abu
mai sauki ka bar mana Mama a nan zuwa sati biyu in de har zuwa wurin baba fuforen
baze fi haka ba, and Ina ce office se next two weeks suka ce tafiyan? Fine se ka
d'auke matarka ku tafi daga chan ku tafi yawon honeymoon" murmushi Abdul ya sake
yana girgiza kai dama chan yana son zuwa london don duba Company d'inshi.
Ya rasa ya akayi be yi tunanin haka ba seda sauban ya fitar dashi ko Don abubuwan
gabanshin na dayawa, "Allah gayen nan sa idonka yayi yawa se kace haka na sa maka
ido da naka iyalan, mtseww by the way thank yhu" be jira amsan sauban ba ya fice
abinshi yana ji sauban d'in na wasu maganganu cikin dariya girgiza kai kawai yayi
ya karasa motan shi ya tayar ya nufi asibitin da Abba yake, cike ya samu d'akin da
en gidansu gabad'aya kowa da kowa na nan wurin ummu ya nufa ya duka har kasa ya
gaidata a d'age ta amsa.
Ya dawo kusa da Abba ya gaidashi cikin fara'a sossai ya amsa shi, Anty rahama ya
gaisar daga nan itama ta amsa duk yanayinta ba daad'i sbd har lokacin abinda ummu
tayiwa iman na ranta, Anty kalthum, Hafeez da zarah suka gaida shi, amsawa yayi
yana d'an murmushi, sede tunaninshi na Ina Iman tayi be ganta a d'akin ba bayan
yace ta jira shi a nan, be de yi magana ba se mikewa da yayi ya fita yana danna
waya layinta ya ta kira bata d'aga ba.
Dawowa yayi ciki a lokacin umma da Hamna suka shigo cikin fara'a sossai ummu ta
tarbesu yayinda sauran da kyar suka gaisheta duk harara ta zuba musu a fakaice ta
gaida Abba ya amsa ba yabo ba fallasa, Abdul kam ma ko ta inda suke be kalla ba
bare har ya wani gaisheta, Don rashin ta ido a tsayenta yadda take ta gaida Abban
gaisuwan ma ba ladabi bare taushi a harshenta.
Dr. Ne ya shigo da murmushi ya bawa mazan hannu suka gaisa, yace "amm please kuyi
hakuri ku je waje bari In duba shi" duk fita sukayi yayinda Abdul ya mike don fita
kenan Abba ya kira sunanshi, dakatawa yayi, Dr yacewa Abba "hope ka sha magungunan
da 'yar ka ta kawo?" Murmushi Abba yayi yace "na sha tuntuni, yanzu ni Ina ganin
za'a iya sallama na Don bana jin komai jirin ya daina" Doctor yace "ciwon kan fah?"
Abba yace "shima kad'an kawai nakeji" dr yace "masha Allah bari In duba jinin In
har ya sauka sossai za'a iya baka sallama" aikinshi ya fara, Abba na kallon Abdul
yace "mahaifiyarka ta koreta ta tafi" Da sauri ya d'ago zuciyarshi na bashi yanzu
kuka take kenan.
Abba ya d'aura da "Hafeez ya min bayanin komai game da yadda kuka yi da baba fufore
Ina tunanin lokaci yayi da zata wuce yolan nan haka" Abdul yace "Amma Abba jikin ka
fa? Se nake ganin kaman In ba um...." katseshi Abba yayi yace "In ta zauna tana
kara dulmiyar da kanta da jawa kanta raini da tozartani lafiya zata bani? Se de
akasin hakan ni nayi sauki ka kira baba fuforen kuyi magana" Kai ya gyad'a kan yace
"to Abba" daidai lokacin dr ya gama dubashi yana murmushi yace "ka ci gaba da
kwantar da hankalinka Alhaji jinin ya sauka sossai In aka ci sa'a zuwa dare ya koma
normal za'a baka sallama" godiya Abba ya mishi ya juya ya fice su Anty rahama suka
shishigo yayinda umma da ummu suka tsaya daga waje suna magana.
Fita yayi ya nufi hanyar waje yana kallon mahaifiyarshi kewanta na shiganshi wani
iri yake ji har kahon zuciyarshi In yaga irin kallon da take mishi ba so a cikinshi
bare kulawa da damuwa, kau da kanshi yayi be mata magana ba tunda ya san abinda
bata so kenan ya tanka ta, direct gidansu Iman yayi yana ci gaba da gwada number
d'inta amma bata d'aga ba, daga kofa yayi parking tare da bud'ewa ya fito, da gudu
yaga ikhlas zata shiga gida da sauri ya tareta yana cewa "hey kiddo" kallonshi tayi
se ta wangala mishi baki tace "laaaa bature" dariya yayi yace "ke ni ba bature bane
ni mijin Anty Iman ne" Ihu ta saki da karfi tana tsalle kan ta shagwa'be "dan Allah
zaka kaini wurinta? Ai a chan kam Umma baza ta hanamu zuwa wurinta ba ko?" Kai ya
gyad'a yace "zan zo In da'aukeku musamman In kai ku kuyi mata sati biyu" tsalle
tayi cikin jin daad'i, se yaji wani iri da bai sayo musu komai ba.
Yana kallonta yace "ban riko muku komai ba muje se In sayo miki alawa kina so?"
Baya tayi tana kad'a kai tace "Mama ta hanamu shiga motan kowa se na gida" mamakin
wayon yarinyar yake sossai, yace "ni d'an gida ne mana tunda nima mijin Anty Iman
ne" kallonshi takeyi yace "In bazaki ba shikenan shiga kice Ina sallama da baba"
juyawa tayi ta fara tafiya se kuma ta kwasa da gudu daga inda take take ihun "Umma,
baba ga mijin Adda Iman, ikhram zo kiga baturen mijin Adda Iman" murmushi yayi yana
dafe kai ko a wani gari aka ce mata shi bature ne? Kallon fatan jikinshi yayi ya
saki murmushi hmm.
Yana nan tsaye Baba ya fito "a'a Abdulraheem kai bako ne da zaka zo ka tsaya daga
waje? Maza maza karaso ciki" murmushi yayi yabi bayan baban da be tsaya sauraranshi
ba yayi gaba, darduma aka shimfid'a mishi akan taburman dake kasan inuwan Almond
tree d'insu, se da ya zauna tukun suka gaisa da baban, umma ce ta fito sanye da
hijabi itama ya gaisheta yana mamakin kamansu da Iman yadda har ya 'baci kawai de
iman chocolate color ce yayinda Umma fara.
Ba yabo ba fallasa ta amsa ta mike ta koma ciki, bayani yayiwa baba akan abinda ya
kawo shi da maganan da sukayi da sauban ya yanke shawarar ze kaita Miami shine ya
zo kar'ban passport d'inta Don mata shirye shiryen tafiyan, sannan kuma yana so a
had'ata da mutum d'aya da ze na kula da ita, godiya sossai baba ya mishi kan yaje
d'akinta ya d'auko passports d'inta ya kawo mishi seda ya zauna tukun yace "tafiyan
na san ana bukatar mace ne er uwarta ko?" Girgiza kai yayi yace "a'a baba ko namiji
ma ze iya sbd ba'a kwana akan marar lafiya su zasu kula da komai nata, mutum d'ayan
ma munaso ne kawai kar ace an rasa wani nata kusa, ni da Saudah ba zama zamuyi ba
muna ajiyeta wasu kasashen zamu wuce".
Gyad'a kai baba yake cike da al'ajabi wai yau mijin Noor Iman ne ze musu irin
wannan hidimar ba Don shi ba kam sede Mama ta mutu a yadda take dukda ya san mutuwa
da rayuwa duk na Allah ne, har zuciyanshi ya fara da na sanin abinda ya dinga mata
gashi yanzu Allah ya mata za'bi na gari zata huce duk wani takaici da suka kunsa
mata har gwara shi da mahaifiyarta ya rasa dalilin da akayi yasa ya tsangwami ershi
mafi soyuwa cikin yaranshi. Maganan Ikram ne ya dawo dashi daga duniyar tunanin da
ya tafi inda tace "laaaaaa Ashe da gaskiyar Ikhlas bature Adda Iman ta aura???"
Tayi maganan tana kama baki kaman wata babba.
Dariya baba da Abdul sukayi a tare baba yace "haba ikhram ba gaisuwa ba komai?"
Tace "good afternoon" murmushi yayi kan yace "Lafiya kalau ikram ya makaranta?"
Waro ido tayi tana kama ha'ba tace "ashe turawa ma sun iya hausa??" Dariya again
yayi yana kallonta ita ta fi iklas kama da iman amma duk basu da kyaunta, zatayi
magana umma ta kwala mata kira daga d'aki da gudu ta juya tayi d'akin.
Abdulraheem cikin murmushi yace "baba Ina ga ba se an tsaya tunane tunane ba In har
de zaka samu leave a aiki se mu tafi da kai Ina ga ze fi" murmushi baba yayi yana
cewa "za'ayi haka?" Abdul yace "In Shaa Allahu" baba yace "zasu bani In na nema Don
ina jimawa sossai ban nemi wani hutu ba" passport d'inshi yaje ya d'auko mishi yana
ta zuba godiya, Abdul yace "ba komai baba Ai an zama d'aya yadda zan d'auki ummu da
Abbana Haka kuma zan d'aukeku" dukda Haka sossai yayi godiya sukayi sallama ya raka
shi har jikin motanshi ya wuce.
Tsaye take tana kwashe had'ad'en miyan d'anyen ku'bewanta da ta aika Bala me bawa
flowers ruwa ya sayo mata, yaji nama da kifi yayi shar da shi da kaurinshi, har
seda na had'iyi nyau tsabar kyaun miyan, bayan ta gama ta rufe coolern ta d'auka ta
kai dining anan na ga babban na tuwon Don gulma seda na bud'e tuwon semo ne da aka
d'auresu a ledojin d'aura tuwo sun tuku sossai gwanin sha'awa.
Komawa tayi kitchen d'in ta bud'e fridge na ciki ta d'auko babban jug d'in zobonta
ta kai fridge d'in wurin dining sbd a na kitchen ze iya yin kankara, dubawa tayi
komai intact da plates da serving spoon da ruwan wanke hannu duk ta had'a, ajiyar
zuciya ta sauke ta juya d'akinta, tun da ta shigo ta fad'a gado tayi kukanta me
isanta ta mike taje ta wanke fuskanta tayo alwala sbd azahar da taji ake kira Bayan
ta idar ta mike ta fito ganin ba alamun d'aura wani abu a gidan yasata tuna ashe
fah ita zata kar'bi girki so dole ta tar'bi mijinta da yamman nan, komawa d'aki
tayi ta d'auko kud'i tare da sanyo hijabi ta fito har kasa ta aika aka sayo mata
abinda zata bukata ta dawo ta fara tuka tuwonta kan ma ya dawo ta had'a ruwan miya
kawai yanka ku'bewanta tayi ta daka da kanwa, tana gamawa ta had'a zobo.
Wayanta da yake haske tayi saurin nufa ta d'auka ganin baba ya sanya ta zauna tana
cewa "Assalamu alaikum baba Ina yini?" Yace "wa'alaikissalam warahmatullah mun yini
lafiya?" Ta amsa da "Lafiya kalau Alhamdulillah ya su umma da ikhlas?" Yace "suna
nan lafiya mamana yanzu mijinki ya bar nan" wani irin rasss gabanta yayi tana
ambaton Innalillahi wainna ilaihi rajiun a zuciyarta ta d'auka wani abin ne ze faru
da ita se taji baba yana cewa "ki taya mu yi mishi godiya ze fitar da mamanki jinya
wata kasa tare zamuje da ni da ke da kuma shi" wani wawan ajiyar zuciya ta sauke
kan ta sake murmushi tana cewa "Alhamdulillah, Masha Allah" yace "kin samu miji me
hankali da sanin ya kamata fiye da sauran mazajenki dan Allah mamana kiyi iya
kokarinki wajen kulawa da shi ki gani ki ki gani ki ji kiyi kaman baki ji ba se a
zauna lafiya".
Tace "In Shaa Allahu baba bazan baka kunya ba" yace "Toh Allah miki albarka" tare
da kashe wayan amsawa tayi da Ameen tana saukewa daga kunnenta hawaye na silala na
farin ciki, da sauri ta mike tana sake murmushi ta fad'a toilet wanka ta tsalla
tare da alwala bayan ta gabatar da la'asar cikin kayanta ta shiga ta nemi wani riga
da skirt d'in wata maroon and ash atampha ta saka wow zo kuga yadda kayan nan ya
zauna mata kaman a jikinta aka hallicesu tsam skirt d'in ya fito da duk wani shape
na jikinta.
Kallon kanta tayi anya zata iya tsayawa gabanshi haka? Rigan off shoulder ce hakan
ya sa kirjinta ya d'an fito daga sama kunyace ta kamata lumshe ido tayi tana sauke
ajiyar zuciya dole ne kawai a haka zata fita gabanshi sbd tana son bawa kanta wani
gur'bi na musamman a zuciyarshi wadda In ya fita ze ji wajen ya koma mishi kaman
rana yana dawowa gareta ya ji shi kaman a ni'imtaccen inuwa mafi sanyi, daad'i,
kamshi da kayatuwa a duniyarshi.
'Daurinta ta kafa ya kuwa fito d'as dashi dama tun kan su fita ta gyara d'akunansu
gadonta ne ma a d'an 'bace gyarawa tayi ta sanya turaren wuta ta koma nashima ta
saka mishi ta kuma saka a parlorn saman kamshi nan take ya bule ko Ina, hijab ta
sanya tana jin haushin mantawa da tayi bata mikawa su baba mai gadi da kuma bala da
audu driver Abinci ba Bayan ta saka musu.
'Dauka tayi ta fice zuwa kasa daga bakin kofa ta kira bala ya zo ya kar'ba yana ta
zuba godiya, komawa tayi saman ta gyara d'aurinta ta d'an saka powder ta d'auko red
lipstick ta sanya se kwalli a cikin idanunta dayake ita ba me yawan kwalliya bace
amma In tayi d'an kad'an d'in matsanancin kyau yake mata.
Bayan ya bar gidansu ya fara tunanin me ze sayamata tsaraba ya kai mata, shi ba
sanin abinda ta fi so yayi ba har ya wuce wurin masu fruits se ya dawo baya ya saya
fruits d'in da d'an yawa yayi gaba ya sake tsayawa wurin da ake gashin kaza ya sayi
uku manya da su, aka sanya mishi a leda ya wuto be san ko hakan yayi ko be yi ba
haka de ya karasa gida da sake sake horn ya danna aka wangale mishi gate ya shige,
yayi parking ya bud'e baya ya d'auko ledojin da ya taho dasu har ya sa kafa ze
sauka se kuma ya fasa ya gyara zama tare da d'auko wayanshi ya danna kiran baba
fufore bayan ya d'auka suka gaisa cikin raha da dariya kan a natse ya mishi bayanin
abinda yake damun Iman da kuma abinda suka lura dashi sossai ya shiga alhini da
damuwa inda yace duk yadda za'ayi ya kawota wurinshi nan kusa yayi.
Godiya sossai ya mishi kan shima ya fad'amishi d'azu ya bukaci ganin mamansu kuma
ta tabbatar mishi a jibi In Shaa Allahu zata bayyana gidanshi komai ze daidaita In
shaa Allah, godiya ya mishi sukayi sallama kan ya sauka ya nufi cikin gidan tun kan
ya haura saman yake jin wani sassanyar kamshi na tashi lumshe idanunshi yayi ya
bud'e su a hankali ya haura matakalar ya karasa parlorn sanyin ac da kamshin na sa
shi jin wani kasala ya rufe shi.
Direct d'akinta ya nufa tare da tura kofan bayanta kawai ya kalla amma seda gabashi
ya fad'i a natse yake takawa zuwa asalin uwar d'akin, cikin sanyinshi yace "Saudah"
juyowa tayi tana sakar mishi murmushi tare da mikewa wani wawan ajiyar zuciya ya
sauke har be san sadda ya karasa ya rungumeta ba suka sake sake ajiyar zuciya a
tare, Ina ma Ina ma? Ina ma lafiyanta kalau taga ruwan kaunar da yake mata? Wani
'bangare na zuciyarshi yace me kake sauri komai ze daidaita In shaa Allah.
Gyaran murya yayi yace "I've been calling you several times amma baki amsa ba" Tace
"subhanallah I'm so sorry wallahi wayan na silent" sake juna sukayi da sauri ta
d'auki wayan ta duba Ai kuwa six miscalls d'inshi fuskan tausayi tayi ta kalleshi
yace "is Ohk sede please kar ki sake sa wayanki a silent in ba kina so hankali na
ya tashi ba" Tace "Toh" ido ya tsuramata yana aikin kallo har seda matsanancin
kunya ya rufeta kara hugging d'inta yayi yace "you look so cute, beautiful and
super awesome my hayatee" Wani murmushin jin daad'i ta sake tana mikewa tace "thank
yhu" a saman lips d'inta se ji tayi ya had'e bakin da nashi.........
🖤Gureenjo🖤
🥀NOOR IMAN🥀
*042*
Seda yayi kissing d'inta son ranshi kan ya janye jikinshi yana kallon fuskanta,
wani kunya ne ya rufeta hakan ya sa ta mayar da kanta chest d'inshi tana sunne kai,
sossai yayi murmushi tace cikin sanyin muryanta "Na gode kwarai hamma Allah ya
biyaka da mafificin alkhairi" d'agota yayi jin har muryanta ya fara rawa yace "da
akayi me ne hayatee?" Tace "batun jikin Mama b......" katse ta yayi "mama ta wuce
haka a wurina hayatee sbd ita ta kularmin dake ta kuma rainar min ke tun daga
yarintarki har na zo na d'auke kayana so kinga anything for her".
Wani irin blushing take sakewa da ya mugun mishi kyau hakan ya sa shi kama lips
d'inshi na kasa yana tsotsa a hankali yana kallonta se kuma kunya ya kamata tasa
hannu ta rufe fuskanta, murmushi ya saki kan ya 'bata fuska yace "wayyo hayatee
yunwa ze kashe miki ni.." waro ido tayi tace "laaa sorry wallahi na manta shap muje
please inyi serving d'inka" yana taune lips cikin tsokana yace "kina nan kina
soyayyarki Ina zaki tuna" da sassarfa ta fice yana murmushi ya bi bayanta yana mata
wani irin kallo.
Serving d'inshi tayi nan fa ya sa mata darun shi kam hannunshi na ciwo baze iya ci
ba haka ta zage ta bashi da da spoon zata bashi nan ma yace baya so da hannunta
yake so ta bashi a haka ta bashi da ya koshi maimakon ya ce mata ya koshi se In ta
sa mishi ya dinga cizan hannunta kad'an kad'an daga baya kam ma se ya d'an mata da
karfi "Ahhhhsss" tace tana yarfa hannunta kallon sha'awa kawai yake binta dashi
shagwa'bewa tayi tsakani da Allah har da d'an hawayenta.
Da sauri ya rike hannun yasa a bakinshi ya fara tsotse mata razana tayi zata mike
yaki sakinta se ma kafanshi da ya janyo ta, wow sossai yanayin ya ma ko wannensu
daad'i da kyar ya lalla'bata ya bata abincin shima da hannunshi, a nan suka
shantake har aka kira magrib ya mugun kasheta da soyayyarshi me daad'i da sanyaya
rai ba surutu sede kawai actions ita kuwa ta cire kunya ta bashi duk wani irin
kulawan da yake so daga ita har shi ji sukayi kaman su zauna su dawwama haka.
Kan ya fita seda ya gaya mata daga masallaci asibiti ze wuce wurin Abba, ta kuwa
bashi sakon gaisuwa tace ya ce ma Abban se gobe in Shaa Allahu zata zo ta dubashi
seda yayi hugging d'inta again kan ya fice, taji daad'i da bai tambayi abinda ya sa
ta bar asibiti bata jirashi kaman yadda yace ba, kaman yadda shima yaji daad'i
sossai har ranshi da bata nuna mishi komai akan damuwan da mahaifiyarshi ta sanyata
ba, kimarta da darajarta ne suka ninku a ranshi.
Da wannan tunanukan ya karasa asibiti ya samu jikin Abba da sauki sossai su rahama
da kalthum suna nan har zahra da hafeez suna nan umma, ummu da kuma hamna ne basa
nan seda yaji wani iri da a da ne Abba be da Lafiya haka ummu baza ta ta'ba iya
barin kusa da shi ba amma ji bata zo da wuri ba haka tayi tafiyanta, fita yayi ya
samu doctor yace a sallami Abban tunda jinin ya d'an sauka in Shaa Allahu ze samu
kulawa a gida har ya gama warwarewa haka dae ba Don doctorn ya so ba ya bashi
sallama ya kuma tabbatarwa Abdul d'in su tabbatar basu barshi yayi skipping pills
d'inshi ba, godiya ya mishi ya taho.
Yana tahowa ya samu mijin Anty rahama da na Anty kalthum sun zo duba jikin Abban da
sha tara na arziki gaisawa sukayi cikin mutunci kan yayi musu bayanin an ma sallami
Abban ai shi karan kanshi seda yaji daad'i dama ba zaman asibitin yake so ba Hafeez
da Zahra ne sukayi jigilan kai komai d'insu mota daga nan Abba ya sauko yana tafiya
a natsenshi jere suke da Abdul yayinda sauran suka biyo bayansu har motan Abdul
d'in.
Ya bud'e mishi baya ya shiga, su Anty kalthum suka mishi sallama da Allah ya kara
afuwa inda ya gargad'esu kar ya ga kafan ko wacce a gidanshi gobe In ma zasu zo su
bari se zuwa jibi ko gata a haka dae su da mazajensu suka ja motocinsu sukayi gaba,
zahra ta shiga motan hafeez su ma suka nufi gida Abdul a gaba suna binshi a baya,
bayan sun isa sunyi parking suka raka Abban nasu har part d'inshi Abdul na kallon
zarah yace.
"Auta zan baki amanan Abba, ga magungunanshi pls safe, rana dare ki tabbatar ke
kika mishi girki da hannunki kika kawo mishi ya ci ko kad'an ne ki bashi
magungunanshi kar fa ki barshi be sha magani ba kinji?" Murmushi duk sukayi har
Abban seda ma yace "to baba Abdul" duk dariya suka sake har Abdulraheem d'in,
Hafeez ya wuce side d'inshi don hutawa haka ma zarah fita tayi ya saura Abdul da
Abba Anan ne cikin sanyinshi yayiwa Abba bayanin ciwon Iman Don fa shi a rayuwanshi
baya iya 'boyewa Iyayenshi komai irin dae d'abi'ar wadda yayi rayuwar waje fad'awa
iyayinka duk abinda ya shafi rayuwanka ba komai bane, kuma irin ya tashi da hakan
iyayenshi sun d'aukeshi friends akwai tsananin biyayya da shakuwa tsakaninsu.
Sossai Abba yayi jimamin abin, inda ya tambayeshi to yanzu wani irin mataki ya
d'auka, ya sanar dashi ya fad'awa baba fufore yace suyi hanzari zuwa so zasu wuce
jibi Don a gobe ba jirgin yola da ze d'aga, Adu'a sossai Abba yayi mata tausayinta
na kara kamashi anan yayi wa Abdul d'in bayanin hankalinta da yadda ta kula dashi a
jiya, shi be ma san taya akayi ta biya kud'in magungunan ba, amma yana gani aka
koreta be iya cewa komai ba tsabar a lokacin be san yadda ze yi da ummun bane,
sossai ya yabi hankalinta da natsuwarta ya kuma roki Abdul da ko baya sonta ya san
yadda ze yi ya sata a zuciya ya kula da ita fiye da duk wasu mata na duniya bayan
mahaifiyarshi.
Sallama sukayi akan ze kwanta ya huta seda Abdul ya tabbatar ya sha maganinshi ya
kuma sha fruit salad sossai da zahra ta had'o mishi kan ya tafi, da sake saken Ina
su ummu suka tafi ya dawo abin mamaki se ya samesu a parlorn su na sama baje suna
hira kazan da ya kawo d'azu baje suna ci ana hira harda jawahir, kaman wasu friends
se kuma pottage na Irish da ya gaggani a plates d'insu sunci rabi sun babbari gashi
yaji kayan had'i.
Karasawa yayi yana kallon ummu yace "ummu ashe kina nan har an sallami Abba ya koma
gida" tace "au laifine Don na zo nan d'in?" Yace "a'a ko d'aya" kan ya nufi room
d'inshi se kuma yaji ta kira sunanshi tsayawa yayi kan ya juyo ta nuna mishi umma
tace "wannan kam ba uwarka bane da bazaka iya gaidata ba?" Yace "sannu hajiya" ta
amsa a d'age ya juya ya fad'a d'akin Iman zaune take bakin gado ta dafe kai hawaye
na silala a idanunta bata san ya shigo ba seda ya kira sunanta da sauri ta goge
fuskanta tare da kakalo murmushi tace "har ka dawo? Ya jikin Abban?".
Wani irin tausayinta ne ya kuma rufeshi gashi bata so ya san tana cikin damuwa
macen arziki kenan tana iya kokarin ta wurin 'boye damuwanta Don farantawa nata
mijin rai, yace "Abba jiki da sauki hayatee an sallameshi ma" jin daa'inta ta nuna
sossai tace "masha Allah, Allah ya ci gaba da bashi lafiya gobe In Allah ya kaimu
zanje na dubashi pls???" Tayi maganan tana karya wuya.
Yace "to hayatee Allah ya kaimu" tayi murmushi yace "me yasa kikayi wani girkin
bayan naga tuwon d'azu dayawa ze ishesu?" Tayi murmushi tace "ummu ke son Irish
pottage shiyasa kayi hakuri na bawa su bala sauran abincin zasu iya kaiwa iyalansu"
karkata kai yayi kaman yadda takeyi yace "uhm uhm naki hakurin se an biyani" dariya
ne ya kamata ganin da gaske shagwa'ban da takeyi yake kwaikwaya tace "to da me zan
biyaka d'in?" Yana sake wani munafukin murmushi yace "just a kiss" da sauri ta rufe
fuskanta tana dariya sossai tare da yarfe hannu.
Murmushi yakeyi yana kallonta tana matukar burgeshi, tana mishi kyau har na wuce
misali yana sonta fiye da tunanin me tunani, banko kofan da akayi ne ya katse su
daga yanayin da suka fad'a, kallon kofan sukayi ummu ce tsaye tana leke leke dayake
ta sauke labulen da ya raba tsakanin parlor da d'aki hakan ya sa ita bazata iya
kallonsu ba.
Fitowa sukayi suka zura mata ido tace "to romeo and Juliet se a fito haka ko uban
wanke wanke dasu ke tare kitchen d'innan waye bawanki da ze miki? Wato da hajja
umma ta gayamin kuna bar mata duk aikin gidanku ban yarda ba se yanzu, kai kuma
ashe da gaske kai ba ruwanka da er uwarka kuma uwargidanka na lura ko kallonta
bakayi ba d'azu se kuma kazo ka kule wurin wannan munafukan, to ba ita ta haifarmin
kai ba ehe don haka ki raba kanki kan In waiwayo gabad'ayata zuwa kanki na gayamiki
daga ni har d'ana kurwan mu kurrr mayun banza mayun wofi".
Ta fice fuuu da alamu dae su suka zugo ta ta taho ta sauke, a sanyaye ya kalleta ze
yi magana ta sake murmushi tace "bari inyi inzo ina da magana please" Kai kawai ya
iya gyad'a mata ta fice shi kuma ya samu wuri ya zauna, se kuma ya kara mikewa ya
fito ummu ya gani da jakanta alamun tafiya zatayi ya mata sallama tana fita ya
shige kitchen d'in.
Tsaye ya ganta tana wanke wanke, hannu ya sa ya fara d'auraye mata kwanukan ido ta
waro "subhanallah dan Allah ka rufamin asiri ka bari kaji" ba wai ya iya bane Don
abinda ya iya kawai had'a tea, coffee shikenan ko gwada wanke wanke be ta'ba ba
amma baze barta ita kad'ai tayi wahalan ba, yace "asirinki a rufe yake kuma In Shaa
Allahu baze ta'ba bud'uwa ba, so ba ruwanki dani" zatayi magana yace "musu zamu
fara kuma?" Se tayi shiru ta ci gaba da wankewa yana d'aurayewa har suka gama
kowanne da irin tunanin da yake a ranshi.
A tare suka goge kwanukan suka mayar wuraren zamansu, suka fito ko kallon hamna
dake tsaye bakin kitchen d'in tuntuni ba wadda yayi a cikinsu kowa ya shige
d'akinshi a gajiye ta tu'be kayan jikinta ta fad'a wanka, bayan ta fito ta shirya
cikin cotton kayan baccinta masu kauri riga da wando ash ta d'aura hijabinta kai ta
kashe electronics d'in room d'inta gabad'aya kan ta fice tana shiga room d'inshi
yana fitowa wanka daga shi se towel iya kwankwaso duk wani hallita nashi na
murd'add'un maza a bayyane karami a kanshi yana share ruwa, da mugun hanzari ta
juya bayanta.
Murmushi ya saki da d'an d'aga murya sbd tazarar dake tsakaninsu daga arean room
zuwa arean parlorn yace "Allah ya nuna min ranar hayatee" bata amsa ba sbd ta
tabbatar In ta tamabaya amsar ita ze kunyata zama ta yi nan parlorn ta kira Baba
suka gaisa ta tambayi jikin mama ya bata tabbacin da sauki, bayan sun kashe ta
kirasu teema duk su hud'un ta had'asu conference Don ta san d'aya se tayi complain
me yasa aka fara kiran d'aya ba ita ba, bayan sun gaisa sun gama tsokananta tana
musu dariya take tambayarsu ya akayi bata gansu bane a asibiti Abba ba lafiya.
Duk salati sukayi suna tambayar me ya sameshi ta basu amsa anan suka sanar mata Ai
tun ranar da hamna ta had'asu da baba yarima suka tarkata suka koma gidan pendon
zahida wacce suke uwa d'aya da mamanta basu da wani Matsala a gidan kaman nan da
ummu ta fara chanza musu, inda tace ya kamata su zo su dubashi itama gobe zata je
amsawa sukayi kan suka bud'e wani chaptern hiran duk tsokanarta sukeyi itakam ba
amsa se murmushi bata ankara ba taji an fisge wayan ya kashe yana kallonta yace
"yanzu lokacina ne fah hayatee" murmushi tayi kamshinshi na kashe nata duk wani
laka na jikinta yana sa mata kasala.
Sanye yake cikin bakaken pjms masu tsansti rigan upon chest wandon kuma dogo har
kasa farin fatanshi se yalki yake a cikin kayan yana d'aukan ido mikewa tayi suka
karasa bakin gado duk suka zauna shikam aikin kallonta yake yayinda ita kuma
idanunta suke kasa muryanshi ta tsinta yana cewa "Anya bazakiyi deferring semester
d'innan ba hayatee?" Ta d'ago ta kalleshi yace "yes jibi zamuje yola sbd
matsalanki, mun dawo zamuje Miami daga nan New York then London ina so kuma mu kara
wasu kasashen bayan nan ciki harda Saudi Arabia, babban matsalan ma shine gobe
zanyi covering syllables d'ina hayatee be wuce sau uku kika je class d'ina ba, ba
yadda za'ayi kiyi exams ba tare da 75% attendance ba I mean it, kina so kiyi
carrying azo ana cewa matar lecturer da kanshi tayi carrying?"
Kai ta girgiza yace "to please kiyi deferring kar kiyi zaton zan hanaki karatu ne
sam ba haka bane you can read as much as you can ina so inga matata ta tara degrees
dayawa" Tace "to Allah ya sa hakan shi yafi alkhairi" yace "In Shaa Allahu hakan ya
fi, Ina so in bar lecturing ta karfin tuwo sbd stress na min yawa more again bana
so mu dinga samun matsala dake sbd attendance as i know yhu kan kije class se na
shiga and ba ta yadda za'ayi In kasa koranki sbd zanyi sonkai so gwara In dena kan
a fara sa bulala ana Zane ni" bata san sadda tayi dariya ba Tace "ahh na isa?" Yace
"har Kin wuce, d'azu kikace kina so muyi magana uhmmm?" Tace "dama akan school
d'inne...." ringing na wayanta ne ya katseta duk wayan suka kalla "Hamma Muhammad"
kallon sunan yayi se ya kalleta suka had'a ido ya d'an ta'be baki tare da kawar da
nashi a sanyaye ta amsa tare da sawa a speaker.
"Amarya" ya ambata ta d'anyi yake kan tace "Ina yini hamma muhammad?" Yace "kalau
ya gd? Ashe kuma wani yayi sa'ar samunki, bazance kinyi sa'a ba Don shine yayi
dace, Allah ya sanya alkhairi" tace "Ameen" tana kallon Abdul da ya had'e fuskanshi
kaman ba shine ya gama dariya yanzu ba ya koma mata sak kaman randa ta fara
ganinshi.
Har rawa muryanta yake wurin cewa "lafiya kuwa Hamma muhammad?" Yace "kalau
kawarkice ke wainani yasa nace bari In kira inyi kamun kafa dake" ajiyar zuciya ta
sauke tace "ba halin in mata magana Hamma Muhammad" kallonta Abdul yayi se ta kawar
da kai tana ji Muhammad yace "sbd mene?" Abdul na jira yaji tace ummu ta hana se ji
yayi tace "Ai zarah taurin kai ne da ita yanzu na takura mata nima se ta dena min
magana ka san halin ai" sukayi dan dariya a tare, haushin dariyar da Abdul yaji ne
ya sa ya d'aga wayan yace "amm da ni ya kamata ka fara kama kafa ba matata ba so In
kana son zarah da gaske ne ni zaka sama, and please kayi hakuri karka kara kiramin
mata ina da kishi wadda har tsoron kaina nake da kaina sbd abinda zan iyayi akan
iyalina se anjima" ya kashe wayan ya kalleta "ko da kina friendship ko irin wanna
shirmen Besty besty da maza ki dena I hate it zamu iya samun damuwa sbd hakan" yana
kai nan ya kashe wutan d'akin ya hau gadon ya kwanta.
Gadon ta haura itama ta kwanta jikinta a sanyaye sede wani shashin na bata
gaskiyace abinda ya fad'a ba ta yadda za'ayi ta zauna tana hira da wasu mazan bayan
tana da aure sede komai kamawa take, cikin sanyi da shagwa'be murya kaman zatayi
kuka tace "bazan kara ba kayi hakuri" Shiru ya mata se ta sa mishi kukan da ya
d'auka da gaske ne take ya juyo ya janyota kirjinshi ya rungume "is Ohk, sleep
baby, am damn tired and sleepy" Kai ta gyad'a tare da gyara kwanciya bacci me
daad'i da ni'ima ya kwashesu.
*shawara nake nema readers wannan semester d'inmun wuta ne tsakani da Allah ina
wahala sossai daga dawowata zuwa yanzu ban samu hutun da ya kamata bawa ya samu ba,
kullum In na fita school daga 8 se 6, inyi rushing d'in book d'innan a kammalashi
kowa ya hutane ko ko In ci gaba da yadda na tsara a zuciyana sannan In ci gaba da
kokarin ganin na muku kowanni bayan kwana d'aya ne? Me kuke gani??*
                     🖤Gureenjo🖤
                   🥀NOOR IMAN🥀
*wannan page d'in is a dedication to duk wani masoyin littafin nan duk naga
comments d'inku kuma naji daad'i sossai na gode da kulawarku, kaman yadda na fad'a
a shafin da ya wuce shawara nake nema kuma Alhamdulillah kun bani had'in kai wurin
fahimtar junanmu dama ba ta yadda za'ayi ayi tafiya tare ba'a fahimci juna ba, Toh
masu cewa a bi littafi a tsanake kar ayi rushing su sukafi yawa Don hakan shawaran
za'a d'auka zan dingayi ko wani bayan kwana d'aya Allah ya bani iko, Ameen na gode
kwarai love you guys🥰🥰🥰*
*043*
Ita ta fara motsawa da asuba da niyyar tashi wadda hakan yayi sanadiyar tashinsa
bud'e idanunshi yayi yana kallon ta dukda duhun dake d'akin yasa baya iya kallon
fuskanta, a hankali ta zame wai Don kar ya tashi ta sauka bata shiga toilet d'inshi
ba kawai ta nufi room d'inta, seda ta fita tukun shima ya mike ya fad'a toilet
d'inshi wanka yayi kan yayi alwala ya fito bayan ya zura jallabiyarsa milk color
daga cikin bayin.
Massallaci kawai ya fice, bayan ya dawo be duba d'akinta ba kawai ya shige room
d'inshi kwana biyu be yi exercise d'inshi ba har ji yayi ya fara gaining weight
hakan yasashi shiryawa cikin Armani sport wear d'inshi bakake ya d'aura karamin
farin towel a bayan wuyanshi, ya duka ya saka wata adidas black and white canvas
d'inshi kan ya mike ya fito be nufi gym room d'inshi dake kasa ba kawai se ya fice
seda ya hau kan titin unguwan kan ya fara jogging a hankali kaman baya so.
Ta 'bangarenta kuwa Bayan ta idar da sallah tayi azkar d'inta ta mike direct ta
nufi kitchen tunanin me zata girka kawai ta hau yi ita ba wani girkin zamani ta iya
sossai ba zata iya kirga waenda ta iya su ma albarkacin waya, karshe de doya ta
fere tayi musu shi da egg sauce ta had'a musu tea me cike da kayan kamshi ta juye a
flask bata kai ba seda ta fito ta share parlorn duk girman shi tayi mopping ta samu
karamin towel ta goge kan dining da wuraren electronics d'insu, kan ta koma ta
d'auko abincin ta shiryasu kan dining.
'Dakinshi ta nufa ta gyare tas daga ciki har parlorn ta share tayi mopping duk ta
gaji a haka dae ta kunna burner ta sa turarukan wuta daga parlorn har d'akinshi,
Allah ya taimaketa nata d'akin ba dattin da yayi hakan ya sa bata share ba Don ta
gaji wanka kawai ta fad'a tana fitowa ta shirya cikin wata atampha orange color me
ratsin baki da fari d'inkin bubu mai aljihu kad'an ya kamata daga kirjinta amma duk
sauran a sake yake atamphar ta amsheta ba kad'an ba powder ta shafa da lip balm,
d'ankwalin ta d'auko da niyyan d'aurawa d'aga idon da zatayi se suka had'a ido da
mutum.
Da farko razana tayi, da ta tabbatar shine se ta sauke ajiyar zuciya tana dafe
kirji dariya yayi kad'an bottle water dake hannunshi ya karasa shanyewa tare da
jefar da bottle d'in cikin dustbin dake gefen bayin, wurinta ya nufa yana murmushin
shi me kashe zuciyar 'yan mata yace "matsoraciya" shagwa'be fuska tayi tace "to
banji shigowarka ba fa Ai dole In tsorata" murmushi ya kuma yi yana tsayawa dab
bayanta ta cikin madubin ya zura mata ido yana kallo itama shi take kallo da
mamakin yadda akayi yayi zufa haka bayan sanyi akeyi seda ta kalli kayan jikinshi
da kyau tunanin watakila gym ya fito ya fad'o mata.
Ajiye d'an kwalin tayi tana mikewa ta juyo suka had'a ido kawar da nata tayi kan ta
zame kasa tace "mun tashi lafiya?" Yace "lafiya kalau Alhamdulillah hayatee, ya
gajiyan aiki? Naga kin shaa Aiki dayawa haka sannu, Allah yayi miki albarka"
murmushi ta sake tana jin daad'i har kasan ranta mikewa tayi ta kar'bi towel d'in
hannunshi ta matsoshi sossai ta sanya ta fara goge mishi zufan fuskanshi tana cewa
"Ameen hamma, Ai aikin ba wani me yawa bane abinda ya kasance dole ne ga kowacce
matar gida" har lokacin murmushi ne kwance saman fuskanshi yace "hmmm banda kazamai
da malalata" dariya tayi dukda ita har ga Allah bata san da wadda yake ba shi kuwa
da Hamna yake nufi kuma ya fad'i hakan ne sbd ganinta da yayi bayansu ta jikin
madubi tana tsaye parlorn tana watso musu mugun kallo, dayake labulen da ya raba
d'aki da parlorn a d'age yake.
Seda ta share mishi fuska zuwa wuyanshi kan ta sauke hannunta tace "muje Hamma In
had'a ma ruwan wanka kayi samun kayi breakfast na san kila ka fita aiki" cikin jin
shi fa wani ne yanzu me martaba da daraja a gidanshi yace "uhm uhm hayateee sede In
ke zaki min" waro idanunta tayi tana dafa kirji tace "ni??" Dariya hakan ya bashi
sossai be rike ba kuwa ya fara darawa se kuma taji kunya ta juya mishi baya.
Kafad'unta ya kamo ya juyo da ita har lokacin yana dariya yace "yes ke, me sabon
abu a gareki, menene baki gani ba😉" ya karasa da wink, juyawa tayi zata gudu yayi
saurin chabke hannunta yana dariya, wani wawan bugu da akayiwa kofar d'akintan ne
yasa su duk maida hankali kan kofan, murmushi yayi yana kau da kai yace "muje to a
had'amin hakan ma na gode" murmushi tayi ta d'auki d'an kwalin ta yafashi kawai
kanta suka fice zuwa d'akinshi, direct toilet d'inshi tayi ta had'a mishi ruwan
tare da zuba mishi turarukan wanka masu kamshi ta ajiye mishi towel babba da karami
daga gefe kad'an, ta juyo kara ta saki tana rufe idanunta da mamaki yake kallonta
shi kam yana rasa gane kan yarinyar wani lokaci ace aurenta hud'u amma ganin shi da
boxers ze razanata haka?.
Matsawa yayi ya koma bayanta yace "to sarauniyar kunya zaki iya wucewa" da sassarfa
ta wuce tana kau da kai, cikin bakaken kayanshi ta za'bamishi sweatpants da V
shaped shirt me karamin hannu, ta ajiye mishi kan ta fice d'ankwalinta ta d'aura ta
fiddo gyalenta orange da zata yafa, jakanta ta d'auka ta ajiye gefen gyalen, ta
fito ta zauna kujerun main parlor.
"Wallahi umma Hamma Abdul ze kashemiki ni zuciyata ze buga, umma zafi yake min
kaman dutse aka d'aura ya zanyi ne" tayi maganan cikin kuka umma ta rungume d'iyar
tata tace "komai ze yi daidai hamna nan ba da jimawa ba, ki bar maganan se ya
amincen nan kan ki wuce, jibi ko ta yaya ne zamu bar Nigeria bade Nijar bane ko ta
mota se muje" cikin aminta da maganar mahaifiyarnata ta gyad'a kai tare da share
hawaye yayinda uwar ta ci gaba da banbami da fad'an munanan kalamai dake nuna
tsantsar hassada da kyashi ga er uwarta da suka fito ciki guda.
A shirye tsab ya fito se tashin fitinanen kamshinshi me sanyi da ratsa zuciya dake
tashi, kallonshi tayi suka sakarwa juna murmushi ta mike tana cewa "mu karasa
dining d'in ko" bayanta ya bi zuwa dining area da kanta tayi serving d'inshi kan ta
sawa kanta tura mishi tayi seda ya d'auki fork kan ta juya ta nufi d'akin hamna da
kallo ya bi ta be hanata ba har ta shige da sallama, ita hamna na kwance bakin gado
tana danna waya yayinda uwar ke zaune gefenta tana shirya musu kaya a akwati, duk
d'agowa sukayi suka zuba mata mugun kallo, kau da kanta tayi tana ta'be baki kad'an
tace "umma, Anty hamna Breakfast is ready" harara hamna ta zabga mata tace "ummau
nace ummau In uwarkice ita se ki gayamin In banda gulma da kinibibi da son a sani,
wani Umma... Anty Antau" kallon lafiya daga magana? Iman ta mata bata tankata ba
sbd tana son mijinta yaci abinci cikin kwanciyar hankali juyawa tayi zata fice taji
hamna tace "yarinya karama da ita ta iya kinibibi da sa miji a gaba shima In banda
kare ya lashe mishi zuciya me a jikin wannan? Me akayi akayi wannan da yake ta wani
rawar kafa a kanta har da bud'e baki yana mata dariya" cikin takaici ta karasa
maganan.
Murmushi Iman tayi tare da fara waka "Ahayye yaro Ahayee yaro, Ahayye ba yaro ba
iye nanaye....." a hankali take tafiya tana d'an jujjuyawa "a kyau wata tafi wata,
a kyau ko ni nafi...... A kugu wata tafi wata a kugu ko ni nafi...." ta d'an
karkad'a kugun, wani tsalle da Hamna tayi zata chabke ta ne ya sata kwasa da gudu
zuwa waje tana fashewa da dariya sossai, kallonta yayi dama tun d'azu yake kallon
kofan dariyarta sossai ya mishi kyau har be san sadda murmushi ya su'buce mishi ba
dukda ya san wani abin tayo.
Dining d'in ta nufa tana ta dariyarta Don sossai hamnan ta bata dariya se kace wata
er dambe, zama tayi ta fara cin abincinta ba tare da tace mishi komai ba shima be
nemi ba'asi ba ya ci gaba da cin abincin yana kallonta minti minti se tayi murmushi
ta kalli kofan d'akin ta san watakila umma ce ta hana ta fitowa, har suka gama basu
fito ba, plates d'in da suka ci ta had'a ta kai kitchen, se sannan su hamna suka
fito tana lekowa ta gansu tsaye dashi yana gaida umma a d'agen dai yadda ta Saba ta
amsa Don neman tsokana irin nata ta fara wata wakar.
"Anyi sake ga d'an zaki ya girma... wa za ya jaa da ikon Allah.... mu bamu nufin
cuta ga d'an uwa... kowa ya cuce mu mu barshi da Allah......." "Saudah" ya kira
sunanta ta waigo gabanta na fad'uwa Don duk sadda ya kirata da asalin sunanta se
taji tsikar jikinta na tashi "na'am" ta amsa tana dawowa baya dama har ta wucesu
"Kun gaisa da umma?" Tace "eh mun gaisa" wani kallo suka watsa mata, tayi musu
murmushi ta wuce room d'inta.
Murmushi yayi yana girgiza kai, su kuwa dining suka nufa suka zuba abinci ko
waccensu ta fara ci yana nan tsaye ta fito da katuwar gyalenta lullu'be a kanta da
jakanta da kuma wayanta a hannu, kallon yadda kwana biyun nan ta kara kyau da
kyalli se shining fatan jikinta ke yi kawai yake, fararen hakoranta gabad'aya ta
bud'e mishi tana murmushi, yace "je ki side-bed akwai phones d'ina da car key ki
d'aukomin" d'akinshi tayi bayan tayi nodding, da sauri ta d'auko suka fito ba tare
da ta kallesu ba tace "mun fita" .
A mota yake tambayarta waye Muhammad, dukda de taji maganar bazata amma haka ta
danne ta bashi labarin muhammad kaman yadda shi ya fad'a mata da dalilin da ya sa
ya rabu da ita, Shiru yayi bayan gama ji yana tunani kenan In zarah ta aureshi zata
iya fuskantan tsanar uwar miji kaman yadda ita Iman ke fuskanta, Allah ze iya
nunawa ummu iyakarta akan erta da sauri yayi auziyya ya kau da zancen daga
zuciyarshi, a wani babban store yayi parking ya fice mintuna kusan ashirin ya dawo
ya bud'e boot aka zuba mishi wasu manyan ledoji, shiga again yayi yaja bata lura da
inda suke zuwa ba seda yayi parking d'ago kan da zatayi ta ganta kofar gidansu
dukda ta san ba wani tarba zata samu ba amma farin ciki sossai ya nuna akan
fuskanta, se kallonta yake cikin tausayawa cikin rawar murya tace "na gode Hamma
kaman ka san nayi missing su ikhram sossai" yace "zan wuce zuwa azahar zan turo
driver ya d'aukeki se ya kaiki gidan ummu se bayan isha zan taho In d'aukeki" Tace
"to ba matsala na gode kwarai" hararanta yayi tayi murmushi yace "keep smiling
don't cry ohk?" Kai ta gyad'a ta bud'e ta fice tana cewa "Allah ya kiyaye ya tsare"
da Amin ya amsa bayan shiganta gidan ya kira yara ya basu ledojin da kud'i suka
shigar mata. "Adda oyoyo Adda oyoyo" da gudu suka zo suka rungumeta itama cikin
murnan ganinsu ta rungumesu a jikinta.
Hafsy ce ta fito daga d'akin umma itama da gudu tazo ta rungumeta se ta fashe da
kuka tayi kewar yayartata mijinta ya saka numbern iman d'in black list kuma ya
rantse muddin taje gidan Iman a bakin aurenta ta san da ya san zata zo yau da be
barta zuwan ba, baba ne ya fito daga d'akinshi yana cewa "menene haka hafsat? Se
kace wasu yara?" Saketa Iman tayi ta tsuguna "baba Ina kwana?" Yace "Lafiya kalau
mamana ya kika baro gida?" Tace "Alhamdulillah baba" yace "masha Allah tashi a
kasan nan ga key d'in d'akin mamanku ku bud'e ku shiga" kar'ba tayi tana murmushi
yaran da suka shigo da ledojin ta kalla tana murmushi gaskiya mijinta ya cika
jarumi kuma wacce ko wacce mace ke burin samu ji seda ya had'ota da sha tara na
arziki da ita ko tunanin hakan ma be fad'o mata ba d'akin Mama ta bud'e suka ajiye
kayan tsakiyar d'akin.
Suka fice bayan sun nuna mata sabbin Hamsin hamsin d'in da ya ba kowannensu ta
tabbatar yanzu zasu kaiwa iyayensu labari su kuma su shigo ganin gulma girgiza kai
tayi, da sallama ta d'aga labulen umma zaune take kan kujera hannunta rike da
chasbi tana ja hijab sanye jikinta da alamu walaha ta idar kasa Iman ta zauna tace
"sannu umma mun sameku lafiya?" Sau d'aya ta kalleta ta kau da kai cikin kasan
makoshi tace "lafiya" hawaye ne ya cikawa Iman idanu ta mike ta fito da kallo umman
ta bi bayanta hawayenta na zuba akan kuncinta da sauri ta goge tana me ci gaba da
tasbahanta.
Damuwanta ta kawar ganin yadda en uwanta ke murnan ganinta baba da kanshi ya fita
ya sayo mata drinks masu sanyi da ruwa, ita da hafsy suka sharewa Mama d'akinta da
yayi kura suka goge suna hiransu, bayan sun gama suka baje ledojin kayan kwalama ne
a ciki jibgi se frozen chickens guda biyar da wasu turaruka masu kamshi da manyan
turamen atampha super wax guda hud'u.
Da yadin maza gezner wadda se jikin shi Malabon kawai take gani kala uku ta
tabbatar na su baba ne hakan ya sa ta ba Hafsat yaduddukan da turare guda biyu ta
kai mai godiya ya hau yi da zuba mata adu'o'i, har d'akin maman ya zo ya sanya mata
albarka seda tayi hawaye, turamen zannuwan duk uku da turare d'aya ta ba hafsy ta
kaiwa umma, ko kallon kayan batayi ba hafsy de ta ajiye mata ta juya.
Ita hafsyn ta ba d'ayan da turaren da ta ware guda d'aya, ta cewa su ikhram zata
d'inko musu nasu tsalle suka dingayi chocolates da sweets din ta hau rabiya duk
makwabtansu da ta san suna da yara seda ta d'ibar musu ko Ina aka kai musu su
ikhram ke kaiwa bayan sun gama ta had'asu da nasu se ga mata sun fara shigowa wai
sun zo godiya alhali gulma ce ta kawosu, aiko nan suka hau kus kus idan ta wuce
kusa dasu sassanyar kamshinta ya bule su har lumshe ido suke suna jinjina kai
tsabar gulma.
Azahar na yi tayi sallah bata jira abincin umma ba ta shirya, d'akin baba ta koma
suka fara hiran jikin mama da yadda tafiyarsun ze kasance, har kasan ranta girma da
darajar mijinta suka ninku mata, suna hiransu me daad'i da babanta suka jiyo
sallama akan drivern da ze d'auketa ne.
Sallama tayi musu ba yadda baba be yi da ita ta jira taci abinci kan ta tafi ba
tace ita kam a koshe take har mota su ikhram suka rakata kaman zasuyi kuka, haka
suka rabu. Har cikin gidan Abba ya ajiyeta tayi godiya ta fito, direct parlorn
gidan ta nufa gabanta na fad'uwa.
Da sallama ta shiga har ummu ta fara amsawa amma ganin wacece yasa ta karasa
amsawar ciki ciki a kasa ta zauna ta gaida ta ko kallonta batayi ba, zahra dake
zaune kan kujera ta mike zaune tana kallonta itama ita take kallo se sukaji duk
hawaye ya zo musu ga su ga junansu amma ba halin magana gashi seda suka ga juna
tukun kewar da suke binnewa na kwanaki ya bayyana.
Ganin zata iya fashewa da kuka yasa ta tashi ta haura sama, nan Iman ta ci   gaba da
zama tana tsoron tambayar Ina Abba ummu ta masife ta, gajiya tayi da zaman   ta dinga
muskutawa, tsaki ummu tayi ta mike ta hau sama anan ta ci gaba da zama har   la'asar
ga yunwa da ya fara nukurkusanta a zuciyarta da na sanin kin tayin baba na   kamata
sede hausawa sunce da na sani keyace.
Jin har an idar da sallah ya sa ta mike ta nufi waje daga gefe ta d'an bayan ginin
gidan taga pampo da dashi ake bawa flowers ruwa, da tayi niyyar tafiya se kuma ta
fasa anan tayi alwala ta matsa chan gefe inda interlocks ne shimfid'e a wurin daga
inda take tana hangar boys quarters da kuma gidan babban injinsu.
'Dan kwalinta ta zame ta shimfid'a ta gyara gyalenta ta tada sallah, bayan ta idar
tayi zamanta nan, ta danna waya ta gaji tayi game ta gaji ga yunwa da ta fara
tunanin ze mata illa don ulcer d'inta taji ya fara nukurkusanta a kirji. Baiwar
Allah har magrib tana zaune a wurin anan tayi magrib se ta zame ta kwanta idanunta
na fidda hawaye, me ta tarewa ummu ne bata sani ba tana matukar son ganin ummu ta
d'auketa 'ya kaman yadda Abba ya d'auketa tana burin ganin ranar da zata zo ummu na
nan nan da ita cike da so da kulawa amma batayi tunanin mafarkinta ze iya zama
gaskiya ba tunda har yau ummanta ma bata chanza ba.
Zarah dake tsaye tun d'azu a sama tana kallonta tana hawaye ne ta fito ta gangara
zuwa kitchen kallon me aikinsu tayi tace "akwai bakuwa a backyard ki kai mata
abinci" da "to" ta amsa kan ta had'a abincin ta fito ummu da ta kasa ta tsare ne
tace "ke laure Ina zaki da abincin nan?" Laure tace "hajiya zarah ce tace akwai
bakuwa a waje In kai mata" wata uwar harara ummu ta sakar mata daga ita har zarah
dake zaune saman one seater hannu a kan kumatu tace "wuce ki mayar min da abinci
kan In sa'bamiki daga ke har wacce ta aike kin" tana kallon zarah tace "wawiya
kawai marar zuciya ki ci gaba da shiga harkar wanchan karuwar watarana se na
sa'bamiki" mikewa zarah tayi ta haura tana kuka wayanta ta d'auka ta kira Abdul
yana d'auka tace cikin kuka "hamma pls ka zo ka d'auki Iman hakanan" a rud'e yace
"me ya faru? Me ya sameta?" Tace "Kai de dan Allah kayi sauri" kashe wayan yayi ya
mike daga zaunen da yake a company ya fito da sauri ya d'auki mota ya fito.
Gudu ya dingayi yana tunane tunane me ummu zata iya yi wa Iman, kaman an wulloshi
haka ya shigo gidan hasken motarshi da kuma hasken lantarkin da ya haske gidan suka
had'u suka haske mishi figure d'inta wani irin bugawa zuciyarshi yayi.
Da sauri ya fita ko kashe motan be yi ba yayi kanta d'agota yayi a hankali ta bud'e
idanunta kanshi ta kakalo murmushi fuskanta yake shafawa yana duba inda take kwance
a cikin gidan ubanshi amma wai matarshi ke kwance kasa kaman wata almajira rawa
bakinshi ya dingayi yana ta son yin magana ya kasa se shafa fuskanta yake yana duba
jikinta, jikinshi ta shiga cikin rawan murya tace "I'm fine" d'aukarta yayi chak
zuwa mota ba tare da ya kara kallon ko cikin gidan ba ya ja a d'ari suka fice tuki
yake zuciyarshi na mishi tukuki da turirin zafi wani irin wulakanci ne wannan, wani
restaurant ya tsaya ya yi mata takeaway seda hawaye ya cika idanunshi ganin yadda
take ci da sauri sauri alamun taji yunwa watakila tun breakfast da sukayi shima ya
lura ba wani cin kirki tayi ba.
Jiki a sanyaye ya ci gaba da jan motan zuwa gidansu be iya ce mata kanzil ba ya
sauka itama ta fito suka haura sama kowa ya shige d'akinshi wanka tayi kan ta fito
tayi isha anan ta kwanta bacci ya kwasheta, ya jira shigowarta ganin har dare yayi
sossai bata shigo ba yasashi shiga d'akin nata hangota yayi kwance kan sallaya ta
dukunkune tana bacci d'aukanta yayi bayan ya zare mata hijab ya haura da ita kan
gadon ya sanyata jikinshi tare da lumshe ido wani irin haushin duk mutanen da suke
cikin gidansu na ratsashi har zarah me yasa bata kirashi tun farko ba? Kai har shi
karan kanshi haushin kanshi yake ji da ya sa aka kaita bayan ya san halin ummu,
Allah Allah gobe yayi yake ya kaita wurin baba fufore ta samu warakan matsalanta In
ya sa kafa suka bar kasar ze ga me binta ya mata wulaknci chan, da haka bacci ya
d'auke shi.
Washegari kaman yadda jiya ya kasance musu haka yau ma dayake ya fad'amata jirgin
11 zasu bi a tsanake ta shirya musu kayayyakinsu kan tayi wanka bayan gaisuwa ba
wadda ya iya yiwa wani magana a cikinsu kuma sun jima tare tana gyara d'akin yayi
wanka ya fito yana shiryawa tana shirya mishi akwatinshi bayan sun gama suka je
suka ci abinci karfe 10:30 nayi suka fito driver ya d'aukesu se airport anan suka
ga ummu ita bata ma gansu ba kau da kai yayi tace "ga fa ummu chan" yace "na ganta"
Tace "baza mu je mu gaisheta ba? Gashi har Hamma Hafeez da ya kawota ya tafi" Shiru
ya mata tace "kaji" tsawa ya daka mata "wai ke kam baki da zuciya ne? Bazaki nuna
fushinki a fili ba?" Baya ta matsa Allah ya sa ba mutane ta inda suke hawaye ta
taro a cikin idanunta tana kallonshi kanshi ya dafe duk haushin jiyan nan ne de be
bar ranshi ba, hannunshi ta kama cikin sanyin murya Tace "kar de kacemin kana fushi
da ummu Hamma? An ta'ba fushi da iyaye? Kana so Allah ya hukuntamu? Kayi hakuri dan
Allah ni ne tayiwa Abu kuma wallahi na yafe duniya da lahira ban riketa ba sbd uwa
take a gareni mu ci gaba da adu'a in Shaa Allahu zata chanza ko ba haka kake cewa
ba?" Shiru yayi haka ta dinga lalla'bashi da kyar ya sauko seda suka hau jirgin
yaje ya gaisheta ta amsa tana mishi kallo mamaki ganin Iman ya sa bata d'aura da
abinda take son fad'a ba Haka kuma bata amsa gaisuwanta ba hannun ta ya kama suka
koma seat d'insu da kanshi ya sanya mata belt ya kuma rike hannunta ita kuwa ta
kwantar da kanta kafad'anshi tare da lumshe ido har jirgin ya daidaita a sama.
🖤Gureenjo🖤
🥀NOOR IMAN🥀
*044*
Mintuna Arba'in ya kaisu yola daga kano ba wani delay dogarawa da securities da
kuyangi suka zo taransu da motoci na alfarma, ba tare da ya jira wani bushe bushen
algaitarsu ba ya kar'bi key a hannun sarkin dogaran ignoring looks da ummu ke jefa
mishi ya bud'e mata front sit ta shiga ya zagaya ya shiga seda ya jira aka sanya
musu kayansu boot kan ya ja motar da wata matsiyaciyar gudu ya fice daga airport
d'in, Haka kawai yake jin wani irin zafi da kunci a ranshi da ya rasa dalili, yana
d'aukan kwaltar da ze d'auke shi har cikin yola ranshi na kara turara da zafi wata
irin wawan birki ya taka a tsakiyar hanya da ya sa duk ababen hawan kan hanyar
police barrack suka tsaya da tafiya kan kace me wuri ya kacame da masifa sbd ya
tsayarda kowa dake 'barin da suke.
Da mamaki take kallonshi yayinda shima ita yake kallo wasu irin bad thoughts ne
kawai ke yawo a ranshi da ya rasa menene musabbabinshi da kyar ya iya fighting mood
d'in ya juya ga titi ya ja motar bata ce mishi komai ba shima be ce mata ba ya ci
gaba da tafiya abin mamaki shi fa yana ganin gudu yakeyi amma sam kaman a hankali
yake tafiya inda ya kamata ace sun wuce tuni se kuma ya gansu wurin.
Seda suka kusa hour daga jimeta kan suka fara shiga cikin yola abin tafiyan mintuna
goma zuwa sha biyar, kallonta yayi ta kwantar da kanta ta lumshe ido, tsayar da
motan yayi gefen titi ya lumshe idanunshi tabbas akwai abinda ke faruwa sede shi
karan kanshi ya rasa menene, wannan kam kan su isa fuforen se yaushe kenan shi
abinda ya isheshi gashi fa yana gani gudu yake cikin speed amma kuma...... dafe kai
yayi yana ambatar 'Innalillahi' hannunshi ya sa ya kunna qira'a cikin muryan sheikh
Abdulrahman sudais yayi bismillah ya kuma tada motar amma still same thing ke
faruwa.
Da kyar ya samu suka iso ABC se kuma motar ta mutu gangarawa yayi gefen titi ya
tsaya tare da bud'ewa ya fito bayan ya bud'e gaban motan, duddubawa yayi komai
lafiya ba abinda beda lafiya gaban motan dawowa yayi ya tayar mota tace tasheni
muga, hannunta ya kama se yaji hannun sanyi kaman an sa cikin kankara sunanta ya
kira "Saudah! Saudah!! Saudah!!!" Amma shiru ko motsi batayi ba, jijjigata yayi nan
ma fa Shiru kake ji.
Wasu adu'o'i baba yayi ya kai aya tare da salati yace "Abdulraheem ka zama kanka ka
maida hankalinka akan kanka karka yarda wani abu ya shiga tunaninka kana ji na?
Sannan ka dinga maimaita A'uzubikalimatillahi tammati min sharri ma khalaka da
la'ilahaillah anta subhanaka inni kuntu minazzalimeen ka rufe da ayatulkurseeyu
zaku iso lafiya in shaa Allah".
Gyad'a kai Abdul ya dingayi, yana kashe wayan ana Parker wata motar bayanshi fita
kawai yayi ya zagaya ya d'auketa a hannunshi bakinshi na fara adu'o'in da baba ya
fad'a mishi da sauri dogarin da ya janyo motan ya bud'e mishi motan ya sanyata baya
ya kwantar da ita keyn kawai ya kar'ba ya zagaya ya shiga driver sit be iya yiwa
wanchan dogarin magana ba ya ja yana kuma kunna qira'a a motar bakinshi na maimaita
adu'o'in da aka sanyashi.
Tunda ya bar ABC ya fara d'aukan hanyar fufore yake ganin abubuwa kala kala amma be
tsaya ba kuma be dena adu'a ba, a'a tsohuwa tsaye a tsakiyar kwalta, mutum kwance
kasa kaman gawa, jaririn yaro yana kuka, mahaukaciyar mace ta nufi motanshi,
dabbobi kala kala irin su mage, maciji, kare, damisa da zaki, duk be tsayawa second
though yake bin kansu ya wuce   Har akwai inda yazo yaga kwalta ta rabu mishi gida
biyu katon rami tsakiya haka yabi ta kai se kuma yaga normal, kanshi har ciwon yake
tsabar turirin zafin da zuciyarshi keyi amma haka ya daure ya cije yaci gaba da
tafiya be tsaya ba seda ya ganshi cikin fufore wani wawan ajiyar zuciya ya sauke
ganinshi kofan gidan baba.
Unlocking motan yayi ya fito tare da kulle motan da ita a ciki direct babban
parlorn baban bayan ya shige katon iron get na gidan, baba dake safa da marwa a
parlorn yayi saurin nufoshi ya rikeshi "masha Allah, Alhamdulillah Abdulraheem kun
samu isowa lafiya tana Ina?" Lumshe ido yayi ya bud'e baba ya ja shi ya zaunar
dashi kan kujera ya dinga maimaita mishi wasu adu'o'i yanayi bayan ya gama ya mike
ya d'auko wata galon na ruwa ya tsiyaya a cup ya mika mishi kar'ba yayi ya kafa kai
ya shanye yana sauke kofin ya had'a da wata nannauyar ajiyar zuciya.
"Sannu" Kai ya gyad'a baba yace "Ina ita amaryar tawa?" Yace "baba tana cikin mota
bari In d'aukota" mikewa yayi ya fita ya bud'e motar ya d'aukota a hannunshi wani
almajirin baba ne ya zo da sauri ya rufe mishi kofan da dabara ya karasa da ita
parlorn sanyin jikinta har shi karan kanshi ya fara damunshi daga waje zuwa cikin
gidan Allah am ita kuma ya takeji ne? Ya ayyana a ranshi yana kwantar da ita kan
doguwar kujerar parlorn.
Kanta baba ya karaso yana kallonta yace "hasbunallahu wani'imal wakeel, Lahaula
wala quwwata illa billahilaleeyul azeem, Maaarid" ya kira sunan da mamaki,
kallonshi Abdul yayi yace "baba marid kuma sunanta fa Saudah" wani karamin murmushi
ya saki yace "Abdulraheem ba ita nake nufi ba, black demon d'in jikinta sunanshi
kenan" ga wannan d'auketa zuwa d'akin hajja gana (babarbariyar matarshi ta farko
wato uwargidanshi) ka shafa mata don farkawanta ba yanzu ba se in baka labari
cikakke akan marid wani irin bakin mugun Aljanine sannan what he's capable of doing
in dai har ka shiga taskunshi".
Kai Malabo ya gyad'a ya d'auketa ya fice da ita gidan katon family house ne
matanshi hud'u kowacce da sashinta se yaranshi maza hud'u dake rayuwa cikin gidan
suma duk sashinsu a cikin gidan yake, part d'in baba fuforen ne gaba wadda yake
had'e da part d'in baki shima kuma d'akunan daban daban ne akwai waenda ya ware
mussaman don su Abdul d'in da yake Hafeez ya Saba zuwa, part d'in hajja gana ya
shiga da ita don tunda baba yace ya kaita chan ya san ta shirya tarbanta.
Ai kuwa suna shiga tana murmushi tace "lale maraba barkanku da zuwa, Sannu Lamid'o
karasa da ita d'akin chan" murmushi yayi yana karasawa da ita ya shimfid'e ta kan
shimfid'ad'iyar gadon da ya sha gyara ba abinda ke tashi part d'in tsohuwar In ba
kamshin turaren wuta ba, yana murmushi yace "mun sameku lafiya?" Itama cikin fara'a
da jin daad'in ganinshi tace "Alhamdulillah lamid'ona se yau Allah yayi ganinka?"
Murmushi yayi kawai akwai sabo sossai tsakaninshi da ita tun suna yara tana musu so
na tsakani da Allah in kuwa suka taka kafafunsu cikin gidan baba fufore se abinda
suke so za'a yi, tayi ta haba haba dasu shiyasa suma suke sonta ya kai ta makka
kusan sau uku.
Yace "hajja baba yace a shafamata wannan, gashi" ya mika mata mikewa tayi ta kar'ba
ya mike ya fita dama tunanin ta yadda ze fara shafamata yake baze iya ba, baze iya
takalowa kanshi abinda ya fi karfinshi a halin da take cikin nan ba, a duniya be ga
macen da da kallo kawai me kyau In ya mata yanayinshi ke sauyawa ba irin Saudah,
parlorn baba ya koma ya sameshi zaune yana duba wani littafi, gabanshi ya zauna
kallonshi baba yayi yace "bazaka samu cin wani abu ka huta ba kan mu zauna
tattaunawan? Kaga azahar ma tayi muyi sallah tukuna Ohk?" Da "Toh" kawai ya amsa
yana mikewa da kallon tausayi baba ya Bishi yana ganin tsantsar damuwa shimfid'e a
fuskanshi kuma ya tabbatar be wuce ciwon matanshi ba.
'Dakinshi na part d'in baki ya nufa a gyare tsab se tashin kamshin turaren wuta
yake murmushi yayi ya tabbatar aikin hajja ne wannan shi yasa yake son tsohuwar har
ranshi, ruwa ya sakarwa kanshi wani sanyi na ratsa zuciyarshi tausayi da kaunar
matarshi fal ranshi da tunaninta yayi wanka ya fito nan tsakiyar d'akin yaga
akwatinshi ya san baba ya sa aka shigo musu dashi, kananun kaya ya sanya bayan ya
shafa mai turare kawai ya fesa ya fito sallah Don har baba ya tayar da ikama.
Bayan sun idar da sallah suka dawo parlorn shi abinci baba ya had'a musu da kanshi
murmushi yayi ganin favorite d'inshi da ya jima be ci ba, shinkaface da wake da mai
da yaji aka yanka salat da tumatur da albasa da dafaffiyar kwai akai se kifi, ya
kuwa matso ya zauna da kyau ya amshi cokalin da baba ya miko mishi suka fara ci
yana son baba kaman yadda yake son lamid'o dukda yanzu sarauta ya chanza lamid'on
sossai ba kaman da ba, In har ance yau sunzo tare suke komai da tsoffin bacci kawai
ke rabasu.
Sossai yaci abincin dukda tunanin Iman na makale ranshi bayan sun gama wani
almajiri yazo ya d'auke kwanunkan gyara zama sukayi baba yace "Abdulraheem bani
labarin matarka yadda zan iya gane tun wani lokaci marid ke tare da ita" gyaran
murya Abdul yayi kan ya fara bashi labarinta tun daga farko har kawo yau tsoho mai
matukar tausayi da imani se gashi yana hawaye, son Iman na shiganshi Allah sarki
baiwar Allah, Aljani ya dad'e yana cutar da ita ba tare da masaniyarta ba.
Baba yayi gyaran murya bayan gama nazarinshi yace "Abdulraheem Ina tunanin
mahaifiyarta ta San da matsalarta ta kuma san tun yaushene yake tare da ita itama
Ina bukatar ganinta, bazan fara yiwa Saudah magani yau ba har se naji dalilin da
yasa mahaifiyarta ta banzantar da rayuwanta bayan ta san tafi kowa bukatarta" Abdul
yace "baba ba kuma abinda ze faru aka bar ta haka? Sannan baba abubuwan da na
fuskanta yau duk sharrin wannan aljanin ne?" Baba yayi murmushi yace "za'a ci gaba
da shafamata Jan miski da za'afaran me d'auke da adu'o'i wadda na bakan nan kan
isowar iyayentan sede baza ta farka bane sbd an riga anyi noticing d'inshi jikinta
da ba wadda ya gane ne zata ci gaba da rayuwanta normal sede matsalar aure sbd ya
riga ya aureta da jimawa"
Da mamaki Abdul yake kallon baba dama aljani na iya auren mace tun daga yaranta har
zuwa girmanta ba tare da ta sani ko wani nata ya sani ba? Baba ne ya katse mishi
tunanin da cewa "ka dena mamaki sharrin aljani yafi karfin tunaninka musamman marid
da yake na biyun ifrit a karfi da mugunta, sannan abubuwan da ka dinga ji ka dinga
gani a yau kad'an kenan daga cikin sharrinshi Don ya san inda zaka zo, ze iya ci
gaba da tsorata ka da irin muryan matar ka cikin kuka da neman agaji cikin dare ko
ido biyu kuskure kad'an zakayi ta 'bata har buzunta In har ka kuskura ka taimaka
mata wurin barin gidan nan daga yanzu so kayi kokarin ignoring duk wani magiyar me
irin muryanta Don marid ba abinda baya iya zama.
Ka rike adu'a kar bakinka ya rabu da adu'a kaji? Sannan ka tsaya mata cikin dare da
ibada da rokon Allah, Allah ubangiji ya bamu nasara kanshi" Da "Ameen thumma Ameen,
in Shaa Allahu zanyi iya kokarina wurin taimakawa rayuwanta da ganin ta samu lafiya
da dawammamiyar farin ciki dama tun farko abinda ya shigo dani rayuwanta kenan" ya
amsa Shiru ya biyo baya chan dae Abdul ya fiddo wayan shi ya kira baba, kad'an ya
mishi bayanin abinda ke faruwa ya tabbatar mishi su shirya hafeez ze zo ya d'aukesu
ze fad'a musu time in yayi waya dashi, ta waya yayi booking flights biyu ya turawa
Hafeez ta email tukun ya kirashi ya bashi tabbacin yayi booking flight na 10 from
kano to yola gobe ya je gidansu iman ya d'auki iyayenta ya kaisu Airport ya
tabbatar ya nuna musu komai be barsu a duhu ba kan su sauka ze yi magana da sarkin
gida.
Amsawa Hafeez yayi a ladabce, sake kiran baba yayi ya fad'a mishi time da zasu
taso, dukda tambayoyine fal ranshi sbd abinda ya fad'amishin be gamsar dashi ba
amma haka ya amsa yana fatan duk wani abun da ze faru ba kuma mutuwar auren Iman
bane ba, d'akin umma kawai ya Leka yace mata ta shirya zasuyi tafiya na kwana biyu
gobe, dayake ta kasance Shiru shiru marar hayaniya da sawa kai damuwa tace mishi to
kawai.
Anan yola kuwa su nenne Petel sunyi matukar mamakin ganin ummu sede baba galadima
be tanka ba se kallon kin zubar da wayonki da yake mata seda ta musu bayanin Ai da
izinin mijinta tazo baba modibbo ne ya nemi ganinta kan suka sassauta fuska suka
amsa gaisuwarta seda ta mika gaisuwa har wurin mai martaba da nenne kan ta dawo
shashinta tayi wanka ta kwanta tana tunanin me ya kawo Abdulraheem yola? Ba de
karanta ya kawo ba, In ko haka ne zata ci mishi mutunci kuwa amma dae bari ta jira
ta ji da wannan tunanin bacci ya d'auketa.
'Bangaren su hamna kuwa sun gama Shirinsu tsab ganin ba Iman da Abdul ma kwata
kwata be damesu ba a ranar jawahir ta tare gidan suka bararraje koli umma Katuwa da
ita cikinsu kaman wata sa'arsu.
****
Bayan ya gama wayan ya dubi baba yace "dan Allah baba modibbo wanene marid? Ya yake
what is he capable of doing after all what happened today?" Murmushi baba yayi yana
girgiza kai kan yace "maridd! Marid!! Marid!!! Hmm shi dae wani...............
                   🖤Gureenjo🖤
🥀NOOR IMAN🥀
*045*
"Marid ana iya ce musu maradah "rebellious" kaman yadda suka zo a cikin alqur'ani
me girma, cikin sura As-saffat Aya ta 7 (37:7) in da Allah mad'aukakin sarki yace
"And to guard against every rebellious (marid) devil" marid suna ne na larabci ana
iya ce musu giant a turance, suna da karfi they are said to be very arrogant
yawancin rayuwansu sunfi yinshi a ruwa, kogi, fadama da duk wani gulbi ko hanyar
ruwa ko inda ruwa yake, me kyau ko marar kyau, suna da hatsari very dangerous In
aka ta'basu ko mutum ya shiga taskunsu.
Su ba aljanu bane da suke shiga bil Adama domin soyayya kaman jinnul Ashiq sede
suna iya kasacewa jikin mace ba tare da ta sani ba kuma sannan suna hana mace jin
daad'in rayuwa kaman yadda kowa ke yi, wannan na daga cikin hatsarinsu basuyi
rayuwar soyayya ko na aure da mace kaman ashiq ba haka kuma basu barta tayi rayuwan
da kowa ke yi ba, suna iya zama a jikin mutum har ya mutu suna kunta ta mishi ba
tare da ya sani ba duk da wani sa'in laifin mutanen ne.
Marid marada a jimlance suna iya abubuwa dayawa kaman firewa(fly), dive,
destroying abu komai girmanshi, jinsin aljanu ne da suke cikin waenda suka
taimakawa Annabi Sulaiman (A.s) wurin kawo throne na queen of shibah, suna da
kabila wato (tribe) suna da iyalai Don suna auren junansu su hayayyafa kaman mutane
Haka kuma sune na biyun karfi da iko cikin jinsin aljannu In aka cire ifrit. Kaji
yadda marid suke"
Cikin gamsuwa da bayanan baba fufore Malabo yace "Allah ya rabamu da sharrinsu"
baba ya amsa da "Ameen" hira suka d'an ci gaba dayi baban na tambayanshi yanayin
ummu yana bashi amsa anan ne ma ya fitar da abinda ke ranshi ya nuna 'bacin ranshi
sossai akan abinda ummu tayiwa Iman kuma ji yake har lokacin ranshi be yi sanyi ba,
baba ne ya katseshi da nasihohi akan girman iyaye sbd haka duk abinda zasu maka
baka da abinyi se hakuri sede In sun haneka bautawa ubangijinka, "ba'a fushi da
iyaye kaji" baba ya rufe da hakan, Kai ya gyad'a cikin gamsuwa nan suka ji ana
kiran la'asar.
Sallah suka fita sukayi daga nan baba ya zauna rumfarshi na tsakar gida yara suka
fara taruwa Don d'aukan karatu kaman ko yaushe, shi kuwa malabo ciki ya nufa direct
d'akin hajja ya zauna suka fara hirar yaushe gamo dayake d'akin da ta sauke Iman
yayi masauki minti minti se ya kalleta daga karshe ma hannunshi ya sanya ya kama
nata ya riqe dukda sanyin da hannun yayi kaman ya fito daga kankara ko yana ciki.
Tsokananshi hajja ta dingayi wai ita tana kishi gaskiya itace baya sonta, sede yayi
dariya kawai "ka kuwa shiga wurin mutan gidan kun gaisa?" Yace "a'a hajja" Tace "ya
ko kamata ka tashi ka shiga In ba haka ba yanzu se kaji karamin magana ya zama
babba" murmushi yayi yana mikewa yace "bari In gaishesu In zo kar su samin hajjana
gaba" murmushi tayi ya fita me makon ya shiga cikin gidan se ya nufi waje ya d'auki
mota ya shiga cikin gari.
Wurin da ake gashin kaza ya yada zango ya kuwa sayi dayawa har leda takwas ko wani
leda kuwa kaji biyu ne ciki, se godiya me kazan yake cikin jin daad'in wannan
ciniki, murmushi kawai yayi ya ja mota, gidan ya dawo ya dinga shiga part part suna
gaisawa gidan se murnan ganinshi suke don malabo mutum ne me fara'a da son mutane
in kaga yana rashin fara'a to yaga en mata ne musamman na jami'ar bayero. Duk inda
ya shiga suka gaisa se ya ajiye musu leda d'aya, part d'in hajja ya shiga a karshe
ya ajiye mata ledanta.
Godiya tayi mishi sossai, murmushi kawai yayi yace "Hajja ya kamata a cirewa
Hayatee kayan nan a sa mata marar nauyi na san da idonta biyu tayi ta mitan ya
takura mata kenan" murmushi hajja tayi tace "Toh kace mana kawai In baka wuri"
dariya yayi yana dukar da kai fita tayi da ledanta a hannu, kallon iman ya tsaya yi
cikin tausayawa da shaukin so yana sonta har be san adadi ba Haka kuma tausayinta,
kab rayuwanshi be ta'ba tausayin mutum kaman yadda ya tausayawa Iman ba.
Trolley d'inta ya bud'e ya d'auki wani cotton dogon riga me karamin hannu ya nufi
gadon, skirt d'in jikinta ya zame ya saura underskirt d'agota yayi jikinshi ya
sanyata kirjinshi ya lumshe ido na mintuna yana shakan kamshinta me shegen sanyi da
shiga rai.
Ajiyar zuciya ya dinga saukewa akai akai kan ya zuge zip d'in riganta a hankali
tana kan jikinshi ya cire rigan da kuma bra d'inta be d'agota ba seda ya sanyamata
rigan kan ya maidata a hankali yabi bayanta har seda ta kwanta da kyau hancinshi ya
d'aura kan nata ya kuma lumshe ido har yayi kewanta a d'an yinin yau d'innan kawai,
seda ya nisa Don kanshi ya mike ya gyara mata rigan kan ya zame underskirt d'in ya
mike a kasalance ya nad'e mata kayan ya ajiye saman akwatinta, time ya duba shidda
saura ya san zuwa yanzu baba ya sallami almajiranshi fita yayi.
A kuwa kan dardumanshi ya sameshi kishingid'e zama yayi gefenshi yana Jin karatun
qur'anin da yakeyi, seda aka kira magrib suka mike a tare sukayi alwala suka fito
massallaci bayan sun idar da magrib baba ya gyara zama ya fara bawa manya karatun
littatafan da suka saba, murmushi malabo yayi a zuciyarshi yace shiyasa wannan
tsohon be tsufa.
Matsawa yayi ya d'auki alqur'ani ya fara karantawa ba su suka mike ba seda akayi
isha suka gabatar kan suka shige cikin gida suka ci abinci tuwo ne da miyan kuka da
yaji man shanu da kyar ya iya yin loma biyu zuwa uku ba wai Don baya cin tuwo ba se
Don tunanin Iman da baze iya barinshi ci ba, baba da ya fahimci haka se ya fara
janshi da hiran ban dariya da dai wasu abubuwan a haka ya samu yaci kad'an ya wanke
hannu.
Mikewa yayi yana cewa "baba seda safe" baba yace "da wuri Haka Abdulraheem?" Yace
"eh baba Ina so In kwanta da wuri samun In tashi da wuri" baba yace "hakan ma yayi
Allah ya tashemu lafiya" ficewa yayi zuwa cikin gida yayi ma hayateeenshi sallama
kan ya fito yayiwa hajja seda safe ya nufi d'akinshi ya kwanta bayan yayo alwala
Don baya son abinda baba ya fad'a ze iya zuwa mishi, hakan ya sashi saka qira'a a
wayanshi ya kwanta dashi ba don tsoro ba se don za'a iya fooling d'inshi ya
tabbatar In har aka zo maganan da ya shafi hayateenshi.
Washegari
Tun da asuban fari umma ta tashi su hamna da kyar suka tashi daga ita har jawahir,
wanka sukayi suka shirya umma ce ta sama musu abinda zasu ci yayinda hamna tace ita
ba abunda zatayi se mitan rashin zuwan kukunta take na kwana biyu, bayan sun gama
ci suka fito ba tare da ko sun tuna suyi sallahn asuba ba drivern jawahir suka samu
zaune cikin mota suka shige umma ta zauna gaba suka d'auki hanyar katsina, daga nan
zasu shiga nijar abinda ya sa sukayi sammako Don su samu dawowa yau.
'Bangaren baba ma haka ya kasance da wuri ya tada umma ta shirya shima ya shirya me
machine dake kai su ikhram school na zuwa ya d'aurasu kai ya mishi bayanin In an
tashi yayi dasu gidan inna ya fad'a mata zasu d'anyi wata balaguru na kwana biyu,
shi baban be son fad'amata ne sbd tsab zata iya hanashi kwanan nan kullum suka
had'u magananta d'aya akan gidan Iman ya rasa me ta tsare mata yanzu da bata
ganinta.
Karfe goma nayi Hafeez ya iso gidan ya d'aukesu suka fice direct se airport seda
yayi musu komai ya kuma fahimtar dasu yadda zasuyi a cikin jirgi kan ya kyalesu
bayan ya tabbatarwa baba in sun sauka su fito kawai zasuga dogarai sunzo to su musu
magana su fad'amusu su suka zo d'auka, baba na ta mishi godiya ya wuce, baba da
d'an iliminshi ne ya karasa musu abinda ba'a rasa ba cikin ikon Allah suka iso
lafiya aiko suka samu dogarawa biyu tsaye karasawa garesu baba yayi ya musu sallama
suka amsa "ku ne Abdulraheem ya turo d'aukanmu ko?" Nan suka sake musu fuska suna
gyad'a kai da sauri suka bud'e musu mota suka shiga.
Ja sukayi suka fito basu yi fada ba direct fufore sukayi, cikin lokaci kankani suka
isa ita umma gabanta se fad'uwa yake ko me suka zo yi nan ta de san ba lafiya ba ko
magana ta kasa yiwa baba har suka iso, Abdul suka gani tsaye bakin get yana jiransu
da fara'a ya tarbesu dogaran suka d'auki kayan zuwa ciki yayinda ya musu iso zuwa
parlorn baba fufore tsoho me ran karfe.
Suna zama ummu ta shigo   parlorn da sallama tana kallon Abdul ta had'e rai dama ta
san be wuce shi bane ze   kawo kararta har baba ya mata kiran gaggawa haka, a kasa ta
zauna ta gaida baban ya   mata Sannu da zuwa yana kare mata kallo tabbas zargin su
Abdul d'inne ya tabbata   kanta Don daga ganinta ya gane ba cikin natsuwanta take ba,
a mutunce suka gaisa da   su umman iman.
Baba yayi gyaran murya yace "Rashida shiga da bakuwarmu wurin hajja ku ci abinci ku
huta tukun In ganku gabad'aya" amsawa tayi cikin ladabi ta mike umma ma ta mike
suka shige cikin gida, abinci aka kawowa baba shima amma dukkansu suka ci.
Bayan gaisuwa hajja ta gabatar musu da abinci a ciki ma suka ci seda sukayi azahar
kan suka dawo parlorn baba lokacin suma suka dawo daga massallaci, bayan sun zauna
baba ya tsiyaya ruwan galon d'inshi a cup ya mikawa ummu yace "amshi sha rashida"
kar'ba tayi ta Sha tana gama Shaa se murd'awan ciki nan ta kama cikin da karfi se
Amai wani irin bakin amai takeyi cikin azaba da sauri Malabo ya karasa ya kama
kafad'unta a rud'e yana ambatan "ummu" hannunshi ta kama taci gaba da kakari har da
Hawaye tausayin mamanshi yasa idanunshi rinewa a take.
Baba da umma kam se kallon ikon Allah suke, ta kai mintuna biyar tana aman kan ya
tsaya bakin kwayar idanunta suka juya zuwa farare wasu ruwan baba ya kuma d'iba ya
watsa mata tayi firgigit ta mike kasa a sume hawaye ne ya gangarowa malabo akan
kuncinshi da sauri ya share yana kawar da kanshi daga kan mahaifiyarshi ta jima a
haka kan ta bud'e idanunta tana dafe kanta dake sarawa.
A hankali memory d'in abinda ta dingayi ya fara dawo mata tun ma kan auren yadda ta
dingamishi har zuwa rana irin ta yau, hannunta dake rawa sossai ta d'ago ta d'aura
akan bakinta hawaye na kwarara daga cikin idanunta tace "me nayi? Me na aikata
Innalillahi wainna ilaihi rajiun Allah ya Allah" da sauri ta juyo tasa hannayenta
kan cheeks d'in malabo tace "Ina take? Tana ina?" Yace "ummu wace? Hamna?" Tace
"a'a saudah nake magana Noor Iman, wallahi ban san ya akayi ba ban sani ba Allah"
ta fashe da kuka tana jingina da jikinshi kuka sossai tayi har seda umma tayi
hawaye haka Abdul ma duk idanunshi sun rine.
Da kyar ya iya lallashinta tayi shiru baba ya dubi Umma yace "na dawo kanki, Ina so
inji dalilin da yasa kika ki 'yarki kika tsangwami rayuwanta? Bana so ki min karya
waraka zan nemarwa 'yarki daga wurin rabbil izzati, In baki taimaka mata yanzu ba
you will regret it for ever sbd zata iya mutuwa a halin da take ciki yanzu,
taimakonki kawai take bukata a yanzu In har ke kika haifeta da cikinki ki yiwa
Allah ki fad'amin me ya faru?" Kuka umma ta saka Abdul yayi saurin sakin hannun
ummu ya karasa gabanta ya duka yace "ki taimaki rayuwata dan Allah!!!" Ya fad'a
muryanshi na rawa baba yace "dan Allah Aisha" kukanta ta karawa volume cikin rawar
murya ta fara magana "Ina sonta Ina son 'yata dan Allah ka taimakeni kar ta rasa
ranta zan fad'a".
Shesheka ta ja kan taci gaba "lokacin..... lokacin Ina da cikin Iman na wata
shidda.............
🖤Gureenjo🖤
🥀NOOR IMAN🥀
"My Meeroh this is for yhu, I love yhu so much, masoyiyar Stephen, demon da ohooo
sorry fah😅😅 Allah sarki Vampire diaries watcher ya zo please ya tayata kuka😅😅😅*
*046*
 "Akwai wani rana da babanta yayi tafiya bayan wata uku da aurenshi da mamansu
kenan, amma gidanmu ba d'aya ba lokacin ya tafi da safe akan da yamma su hindatu
zasu zo su tayani kwana, yayinda kamila zata je gidan mamansu, ban d'aura abinci ba
se d'an makulashe da nayi taci se chan yamma likis na d'aura mana farar taliya da
miya dama ina da miya na ajiye, bayan na dafa taliyar ta dafu na tsame ta to
tafasashen ruwan ba tare da na tsaya ta huce ba na watsashi gabad'aya kuma da karfi
magudanar ruwanmu da yake me girma sossai Ina watsawa ana kiran magrib so se na
ajiye tukunyar na juya na rufe taliyar na d'au buta na zaga bayi seda na fito nayi
noticing ashe duk abin nan da nakeyi ban rufe kaina ba a haka dae nayi alwala na
shige d'akina ba wuta a d'akin sannan duhun dare be gama shigowa ba amma d'akin
yayi wani irin duhu da ko tafin hannuna bana iya gani.
Lalu'ben inda zan samo torchi nake hannuna ya kai kan keken kwantar da yara da
babanta ya saya don tanadin haihuwa a take na rike keken da kyau se jin kukan
jinjiri nayi yana kuka da iyakar karfinshi kaman kaina ze rabe tsabar karan tayi
yawa, kaman an had'a baki da en nepa suka kawo wuta cikin keken da kukan ke tashi
na kalla, wani irin razanannen ihu na sake ina matsawa baya da sauri hannuna dafe
da cikina, yaro ne a ciki namiji ne ko mace ban sani ba jikinshi daga kai har kafa
kunan wuta ne yayi wani iri ba kyaun gani, idanunshi ba fari se bakin da ya rufe
idanun gabad'aya bakinshi baki kirin har wani hucin bakin hayaki ke fita daga ciki,
gashin kanshi rabi me tsawo baki har kan fuskanshi rabin kuma a aske tal, har Ina
iya ganin karamin kahon dake 'bangare askakken.
Kuka na fara Ina neman kofan fita nan wutan d'akin ya fara d'aukewa da kawowa
tuntu'be naci zan fad'i dafe kujera nayi ina dukawa, kuma d'ago kan da zanyi naga
wata mace zaune akan plastic chair dake d'akin bayanta ta juyamin kanta kasa tana
kuka gashinta a sake dayawa har kugunta faratunta zako zako dogaye bana ganin
fuskanta da sauran jikinta abinda na iya gani kenan na sandara wani ihun kawai na
fad'i sumammiya.
Ban san ya akayi ba nade ji kaman ana kiran sunana cikin mafarki amma da murya me
amo da tsawa a firgice na tashi zaune, se naga wani rabi mutum rabi kwarangwal me
girman jiki sossai da tsawo shima gashinshi kaman na matan nan me kuka a kan kujera
faratunshi har sunfi nata halitta ne shi me muni da tsoratarwa har yau bana fatan
sake ganin wanchan fuskan idanunshi wuta ke ci hancinshi na fitar da hayaki kaman
ana kona karamin bola a take hayaki ya turnuke d'akin cikin tsawa yace "ke biladama
me ya shigar dake gonata? Kin ko san waye ni?".
Cikin kuka nace "ban sani ba amma ko menene dan Allah kayi hakuri kuyi hakuri ban
san me na muku ba" wani irin dariya me rugugi ya sake na minti biyu a take kuma ya
had'e rai yace "tashiii!!!!!!" Jiki na rawa na mike na tsaya ya min nuni da gadon
yaron "jinjirin d'ana me shekaru d'ari da biyar kika kone min da ruwan zafinki ba
tare da kin mana magana mu matsa ko kin ambaci Allah ba da hakan ze hankarar
damu!!! Kinga uwarshi nan Zulhaya'i tunda abin ya faru take kuka ko d'ago ido taki
tayi!!! tun daga Birnin Sin aka tasoni sbd tashin hankali, Me kike tunanin zamu
miki????? Me ya kamata ya zama hukuncinki? Don bazan ta'ba yafemiki ba". Cikin
matsanancin tsawa yake maganan.
Zubewa nayi kasa Don bana fatan sake kallon fuskan wanchan yaron na aljani cikin
kuka nace "ka taimakeni Don girman Allahn da ya hallicemu ka tausayawa d'an cikina
ka yafemin dan Allah, kar ka min komai na tuba" kafewa yayi akan se fa na
fad'amishi hukuncin da ze min cikin tsawa da barazana kawai yake magana, matarshi
dake ta kuka ne ta d'ago ta kira sunanshi da ba zan iya cewa gashi ba, kallonta
nayi da sauri na kawar da kai Ina kuka kawai ba tare da na tuna ambaton Allah ba me
makon ruwan hawayen dake zuba a cikin idanunmu ita na jini takeyi zan iya cewa tafi
mijin munin gabad'aya rayuwa na ranan da bazan ta'ba iya mantawa ba kenan Don naga
tashin hankali iya tashin hankali.
Bud'ar bakin aljanar nan se ji nayi tace "ba zan ta'ba yafe mata ba sede In gindaya
mata sharud'a ta za'ba kuma ta dena had'amu da Allah don bamu sanshi ba" tsawa
mijin ya dakamin "kina ji ko????" Nace "eh naji..... naji" ba tare da aljanar ta
kalli inda nake ba tace "na farko shine ki bani kyautar abinda ke cikinki kina
haihuwa zanzo na d'auke kayana ko na d'aukeshi tun a ciki In raine ko ma menene a
madadin kassara min d'a da kikayi....." Shiru tayi jin na kara karfin kuka na Ina
girgiza kai hannuna dafe da cikina cikin tsawa tace "na biyu!!!!! In kasheki in
kashe d'anki... ko erki, shine ze bawa ruhin d'ana da yanzu ya riga ya mutu salama"
ban san sadda bakina ya furta "innalillahi wainna ilaihi rajiun ba" banga tasowar
ko d'aya daga cikinsu ba se jin saukan mari nayi da yasa na dena ji na wucin gadi
Ina dawowa hankali na naga wani shar'be'biyar wuka na yawo kan cikina kuma rungume
cikin nayi cikin kuka".
Kuka ne yaci karfinta wadda hakan ya sa ta dakatawa Abdul kanshi na kasa ya kasa
d'agowa shi kad'ai ya san me ke yawo kanshi yayinda baba da ummu ke hawaye ba
abinda baba fufore ke yi se gyad'a kai, laifin be wuce na mu mutane bane dama yayi
tunanin hakan Don basu cika shiga mutane ba tare da hujja ko dalili ba, ruwa baba
ya d'auka ya bata ta kur'ba ta ajiye baba fufore kasa hakuri yayi ganin ta kuma yin
Shiru yace "wanne kika za'ba ciki?".
Ci gaba tayi "Akwai na uku wadda shine na za'ba bayan na sha wahalansu, kaman dae
yadda zan muku bayani yanzu... nace "na tuba!! Kuyi hakuri duk ciki ba wadda zan
iya za'ba tsawa ta dakamin "ba'a katseni idan Ina magana..... na uku!!! Shine zaki
haifamana ita bazamu kar'beta ba sannan kuma bazamu rabu da ita ba sede ke zaki
tsaneta ta karfi da yaji se na rabaki da ita ko shi kaman yadda kika rabani da nawa
d'an, kiyi mata tsanar da ze sa ta dinga zargin anya ke uwace? Ki mata tsanar da ko
sau d'aya muka ga so ko tausayi cikin idanunki akanta zamuyi ajalinta har lahira
ina miki rantsuwa da jinin d'ana markuzzz duk randa kika yi magana da ita na
mintuna biyar se na kasheta har lahira da wukan da kike ganinshi gabanki.
Kallon wukan nayi cikin tunani na rashin natsuwa na amince da sharad'inta na uku
dukda na san daga ni har 'yata ko d'ana da zan haifa zamuyi matukar wahala sbd ba
uwar da zata haifi d'a a cikinta tace ta tsaneshi ko me ze mata kuwa, komai na
duniyan nan da dalili sede akwai me karfi akwai kuma marar karfi na tabbatar nawa
me karfin ne sbd ba uwar da zata so a kashe mata d'a ta dalilinta dukda ita tayi
wahalan har zuwa kawowanshi duniya guilt baze barta ba, sannan dan Allah karkuga
laifina a cikin wannan abun ni na san laifina d'aya ne, ba zan iya za'ban sharud'an
farko guda biyun ba sbd duk ba na d'auka haka na d'auki na ukun sbd a ganina shine
gwanda gwanda.
Sallaman su hindatu da saratu yasa aljanun 'bacewa 'bat ajiyar zuciya na sauke ina
mikewa ashe har isha ya wuce da sauri na fito tsakar gidan dayake ba haske sossai
se basu ga fuskana ba sannu da zuwa na musu tare da umartarsu da su isa bari nayo
alwala shigewa sukayi ni kuma na d'au buta nayi alwala na wanke fuskana da kyau na
dawo d'akin hindatu na aika ta had'o mana abincin ni bari inyi sallah, magrib da
isha nayi se lokacin na samu natsuwar kaiwa Allah kuka na ya kawo min d'auki ya
tsaremin abinda ke ciki na laifi kam na san nayi tun farko na kuskuren zubar da
tafasashen ruwa da magriba.
Tun daga ranan ban sake ganinsu ba nayi ta adu'o'i Allah ya sa sun tafi kenan ba
zasu kara shigomana rayuwa ba, kwanan babanta shidda ya dawo a lokacin su hindatu
suka tattara suka koma gidajensu, har ga Allah nayi niyyan fad'awa babanta amma Ina
bud'e baki se inga wannan wukan a daidai cikina yayinda mummunan hallitanta na
tsaye jikin gini tana aikomin da harara me birkitar da hanjin ciki da manyan
idanunta wadda suka fi kama da na ball.
A haka nake Shiru har cikin Iman ya kai haihuwa tun satin da zan haihun waennan
aljanun ke zuwa tunamin da sharad'inmu har a cikin d'akin haihuwa kuwa hakan ya sa
tsoron kar su kashemin ita yasa ko kallonta banyi ba, Allah ya taimakeni taimakon
da har yau bazan ta'ba dena Jin daad'inshi ba kuma har gobe, ya d'aurawa mamansu
sonta wadda nafi kowa jin daad'in hakan don na san ko me zan mata ze zo da sauki In
tana da wata uwa kusa da ita.
Ban ta'ba bata nono ba sede madara da mamansu ke bata tun inna, babanta da kuma
mahaifiyata na sani gaba da fad'a da masifa akan abinda nake mata suna d'auka
alkunyar d'an fari ne har suka dena mamana tayi wa'azin tayi fad'an tayi nasihan
har marina tayi amma ko kallo iman bata isheni ba bawai Don bana sonta ba se Don
tsoron kar su kashemin ita ni kad'ai nake iya kallonsu ni kad'ai na san irin tashin
hankalin da na shiga da barazanarsu akan iman wadda karfi da yaji ya daskarar min
da zuciya na dena kaunarta ko son ganinta sbd su.
Inna da take mata soyayya ta tsakani da Allah da kannen mahaifinta Ina ji Ina gani
a gabana aljanar nan marar imani ta kawo wata mata da tayi zubi da mahaukata kuma
bokayen aljannu tayi surkullenta ta d'iba da kad'an kad'an ta turawa inna, babanta,
hindatu, kamila da saratu a tsakanin zuciyarsu wani abu marar kyaun gani ruwan
ganye shar, ba yadda basuyi ba don su sawa mamansu abin yaki shiga daga yaje kusa
da ita se ya zube shima na tabbatar adu'ar da nake tayi a zuciyata ne Allah ya amsa
min, da kad'an da kad'an su inna suka fara bayyana tsanarsu gareta ba kaman da
farko da sukeji kaman su had'iyeta ba, haka nake shanye duk wani bakin cikin da
zanji akan rayuwan da Iman takeyi da yadda Allah ya d'aura mata kulafucin uwa kaman
me dukda irin soyayyar da take samu wurin mama, kullum baza'a wayi gari a yini
banyi kuka ba kuka sossai cikin nadama da danasanin dafa wannan taliya.
Aurarrakinta da waennan mugayen aljanun ke kashewa sune suka fara min barazana da
lafiyata ba tare da kowa ya sani ba har mahaifinta, kullum cikin dare Haka zan mike
in hau kan sallaya In raba dare Ina mata adu'o'i, banda yadda zanyi inaga Don sun
ga komai ze iya faruwa zuciyata ta fara bushewa da tsoronsu da nake na fara maida
musu magana kuma nake kokarin sanar da babansu yasa sukayi kokarin kasheta a
aurenta na uku ba auren kawai ba har ita sukayi niyyan kashewa amma naji daad'i
sossai da adu'o'ina suka fi karfinsu har yayi tasiri kanta ya kawo mata hamza amma
marasa imanin suka kasheshi.
A lokacin ne nima suka zo da wannan boka suka sa min wannan koren abu a zuciyata
fiye da yawan wadda suka sawa su inna, daga lokacin ne kuma nima naji har zuciyana
bana sonta daga lokacin ne na dakata da mata adu'a daga lokacin ne naji inama banyi
cikinta ba da ban shiga wannan damuwa da tashin hankali na shekaru ba, a lokacin da
na fita harkanta da lamuranta na dena mata adu'a na dena duk wani tsayuwan dare da
nakeyi sbd ita se Allah ya amshi adu'o'ina na baya da na jima ina mata ya kawo mata
Abdulraheem.
Shiru parlorn ya d'auka na fiye da mintuna goma kowa juya labarin yake cikin mamaki
da al'ajabi ajiyar zuciya baba fufore ya sauke yace "menene kike ganin laifinki
guda a cikin labarin nan?" Tace "zubar da ruwan zafi da magrib" yace "tabbas wannan
abinda mutane dayawa suke gani ba laifi bane wallahi wallahi shine abu marar kyau
da ze iya jawo musu nadama na har abada sbd shiga taskun aljannu da suka fimu karfi
da komai da sukayi"
Note:-
(ba wai a littafi ba wannan ba novel bane da kawai na tsara da karan kaina da
zuciyata ba seda aka tayani, ku taimaki kanku en uwana mata in kuna zubar da ruwan
zafi ko da safe ko da rana ko da magrib ko da dare a kasa ku dena ku ajiyeshi se
yayi sanyi inko ya kama dole ku ambaci sunan Allah kan zubarwan, akwai mutane
dayawa da na sani ko naji labari wasu sun haukace, wasu sun mutu, wasu an kassara
su, wasu sun shiga duniya wasu sun zama se adu'a sbd irin wannan dalili, sannan
shiga wanka a lokacin da magrib ta ratso wato lokacinta ta shiga shima ba karamin
hatsari bane ga ke ya ke er uwata mace dan Allah mu kiyaye waennan halittu ba
ganinsu muke ba sannan In sun samu galabar shiga jikin baiwa na Allah ba daad'i
zataji ba, ba kuma daad'i takeji ba bare kuma ace irin su marid, ifrit, duna da
sauransu da sede su nufeka da sharri ba alkhairi kwata kwata a sha'aninsu, ko kuma
Ashiq da ze aureki sbd son da yake miki wadda shi ze hanaki auren wani namiji
jinsinki kaman kowacce mace 'yar uwarki, In basuyi a kanki ba zasu iya yi ga
'ya'yanki don Allah mu kula).
Ihun da sukaji yasasu duk mikewa Abdulraheem baba ya kalla yace "sune sun samu
galabar shigomin cikin gida suna mugaye tabbas wannan shine kuskure mafi girma da
suka aikata gabad'aya rayuwansu, d'aukomin abubuwan nan muje" wasu maguguna da
baban ya mishi nuni da su ya d'iba, bayan shi da kanshi ya d'ibi wasu da sauri suka
fice.
                       🖤Gureenjo🖤
🥀NOOR IMAN🥀
*047*
Daga bakin kofan d'akin ya taka birki yana ambaton Innalillahi wainna ilaihi rajiun
a lokaci d'aya yana lumshe idanunshi he's not that strong In aka zo batun Iman baze
iya ba, baze iya ganin irin wannan azabtarwa da suke mata ba, baba ya mikawa
magungunan ya sa kafanshi da niyyar juyawa baba fufore yace "Abdulraheem" dakatawa
yayi zuciyarshi na tsananta bugawa, "shigo se ka taimaka mini" juyowa yayi ya shigo
yana kau da kai, mama da ummu da kuma hajja gana kuka kawai suke.
Wani irin sauyawa halittarta yayi idanunta sun koma jajajir kaman an zuba musu
ruwan borkono bakin kuma ya koma Ash bakinta baki kirin hannayenta da kafafunta duk
a juye kitson kanta da kanshi ya dinga warwarewa gashin na bazuwa, cikin d'aga
murya baba ya fara magana "Tun muna daad'i daad'i daku ku tattara ku fita harkar
bayin Allah nan laifi ne sun muku amma shekaru ashirin da hud'u yaci ace kun gama
d'aukar fansarku karku shiga hakkinsu kuma, ku fice tun kafin na fara kona ku da
ayoyin Allah" wani irin dariya cikin murya marar daad'i ta sake har tana d'aura
hannu kan baki tsabar dariya gashi muryan a shake kuma na maza.
Murmushi baba ma yayi yace "Ohk fine abinda kuka za'ba kenan? Alright" Wasu adu'o'i
ya fara yana kai aya ya kama ayoyin Allah kaman na cikin suratul baqarah, saffat,
A'araf da jinni da dai sauransu nan fah tun suna dariya har ta fara ihu na fitar
hankali tana d'agawa sama tana fad'owa ita kad'ai In tayi ihu se d'akin yayi wani
girgiza duk wani abu na fashewa seda suka fashe a d'akin komai seda ya juya upside
down, cikin muryan maza me amo da karfi ta fara magana "dakata!!!! ka dakata!!!! Ka
dakata naceee!!!" Kin shiru yayi se ma wani kwal'ba da ya bud'e wadda had'i ne na
abubuwa dayawa irin su za'afaran, zaitun, habbatussauda, khaltuffa, dawa'ujinni da
dai sauransu ya watsa mata wani kara tayi ta d'agu sama ta bugu da gini ta sake
dawowa kan gadon ta fad'i tare da murd'ewa kaman maciji se ga Malabo na hawaye.
Cikin muryanta na asali tace "wayyo hamma" tana mika mishi hannu da sauri ya kama
hannun yace "hayatee kece?" Tace "ka taimakeni ciwo wayyo" baba fufore yace "kauce
Abdulraheem ba ita bace duk cikin munafurcinsu ne yau ko ni ko ku" Abdulraheem ze
yi musu Don ganin yadda take kuka tana ta nanata wayyo wayyo se yaji muryan farko
kaman ta mazan nan tace "ba fa zan barta ba Ina rantsuwa da jinin d'ana da kuma
namijina yadda uwarta ta rabani dasu se na rabata itama da nata, sandin mutuwar
markuzz mijina ma ya mutu Don haka se na ga bayansu".
Baya Abdulraheem ya matsa hawaye na ci gaba da zuba mishi yana gogewa duk wani me
imani baze juri ganin yadda suke mata be zub da hawaye ba gabad'aya ta fice a
hankalinta da kamanninta kaman ba ita ba, artabu aka ci gaba dayi tsakanin baba da
wannan aljana Zulhaya'i seda suka kai ruwa rana gabad'aya ta wahalardasu Don daga
baya neman illata baban ta fara amma dayake yace Allah so ba yadda ta iya dashi
daga karshe ta fara kuka a galabaice tana neman ya tsaya zata fita kar ya gama
koneta ta tuba.
Se sannan ya dakata yace "toh bismillah muna jiranki, ta Ina zaki fita? Tace "zan
fita ta hanci" yace "kiyi alkawari bazaki kara ra'banta ko dawowa inda suke ba"
Tace "nayi.... nayi" yace "ni kuma nayi alkawarin duk radda kika sake kusantar
zuri'ar nan se na kasheki har lahira da ayoyin Allah" Kai ta dinga gyad'awa kan
iman ta saki wani wawan atishawa har sau hud'u a jere kan ta koma ta fad'i kan
gado, zama Malabo yayi bakin gadon tare da kama hannunta yayi kissing wasu Hawayen
tausayinta na sake zuba akan kuncinshi, ajiyar zuciya manyan suka sauke baba ya
kalli baba fufore yace "mun gode Allah ya saka maka ya biyaka da gidan Aljanna"
murmushi yayi yace "kaman yadda Abdulraheem yake jika gareni Haka itama don haka ba
godiya don nayiwa jikata Abu, yanzu shikenan Sun rabu da ita da izinin Allah, kai
Abdulraheem zan baku wasu magunguna ka tabbatar tana anfani dasu zuwa en wasu
lokuta kad'an".
Kai Abdul ya gyad'a Don shi magana ma yanzu ji yake baze iya ba, ficewa baba da
baba modibbo sukayi suka bar matan se Abdul da har yanzu be saki hannun matar tashi
ba, ummu tace "khaih Allah ya mana tsari da irin mugayen nan" umma da hajja sukace
"Ameen" hajja ta fice umma ma tabi bayanta suka zauna a parlor suna ci gaba da
tattaunawa akan matsala irin haka, "Abdulraheem ka yafemin dan Allah" sake hannun
Iman yayi yazo ya kama na mahaifiyarshi yana dukawa gabanta yace "ni ummu baki min
komai ba sema ni da na miki, na kasa nema miki lafiya kan lokaci da na san wani
abin aka miki da tun farko na kawoki nan wurin baba ki yafemin na rashin kula da
hakkinki" kanshi ta shafa tana murmushi Tace "Allah yayi maka albarka yayi muku
gabad'aya, sede Babana kana tunanin waye ze min irin wannan abu akan ku? Me nayiwa
wannan bawan Allahn da ya so sani kassara rayuwan 'ya'yana da na d'iyar wasu?".
Shiru yayi na mintuna kan yace "Allah masani ki dena damuwa akan hakan ummu In Shaa
Allahu Allah ze ci gaba da kareki sannan Ai Allah ba azzalumin bawansa ba baya
barin hakkin wani akan wani shi ze yi mana sakayya, karkiyi zato sbd zato zunubi ne
babba kinji?" Kai ta gyad'a mishi, tace "kaga Ango, daughter na fa ta kular min da
kai kaga yadda kayi wani fresh da kiba?" Mikewa yayi yana murmushi yace "ummu zaki
fara ba" dariya tayi shima ya taya ta kan yace "I miss yhu ummu" Tace "miss yhu
more, uhmm bari Inje In samarwa daughter na abinda zata ci d'azu naji kanacewa tun
jiya bata farka ba ko?" Kai ya gyad'a yace "tunda muka zo ko ruwa bata sha ba"
girgiza kai tayi tana mikewa bayan ta ajiye gyalenta ta fice.
Komawa gefen matanshi yayi ya zauna yana maida hannuwansu cikin na juna idanunshi
akan fuskanta Allah kad'ai yasan abinda yake ji akan yarinyar nan, zuciyarshi kaman
zata fito tsabar yadda take bugawa da sunanta yana mata son da a rayuwanshi be
ta'ba zaton ze yiwa wata halitta ba, wayanshi ya fiddo yana kau da kai daga
kallonta zahra ya fara kira tana d'agawa yace "Albishir Auta" Tace "goro" yace
"ummu ta samu lafiya" wani irin ihu tayi da yasashi saurin kashe waya yana
murmushi, Haka ya kira kalthum da hafeez ya gayamusu rahamace dae suka d'an jima
suna waya har ya bata labarin gabad'aya abinda ya faru yau sossai tayi kuka cikin
tausaya musu, dama idanunshi akan ta yake sede safa da marwa yake so da ya jima ta
bayanta yana kan bawa Anty rahama labari kaman ance ya dawo ta gabanta yaga hawaye
nata gangara daga cikin idanunta da suke a rufe.
Da sauri yace "we talk later sis bye" ya kashe wayan gabanta yaje ya zauna yasa
tattausan tafin hannunshi yana share mata hawaye yace cikin taushin murya "hayatee"
kawai se ta mike kad'an ta rungumeshi zama yayi da kyau yana sanyata jikinshi yana
jin kukan da ta fashe dashi kaman sukan mashi a kirjinshi, jikinta har rawa yake
kab taji labarin da ya ba Anty rahama daga farko har karshe ta tsorata sossai da
lamarin abin ya zo mata bazata dama abunda ya faru kenan? Allah sarki ummanta
sossai take squeezing hannunta a jikinshi tana kuka.
Tsam ya kuma rungumanta yana cewa "is Ohk hayatee, is ohk i got yhu!!" Cikin rawan
murya tace "hamma Ina ummuna? Tana ina don Allah?" Yace "ki dena kukan nan haka se
in kaiki wurinta ok?" Da sauri ta zame daga jikinshi tana share hawayenta hannu
bibbiyu with adoration yake kallonta kaman wata small baby, "kaga na dena" tana
maganan ne wasu hawayen na kuma zuba.
Mikewa yayi yana kama hannunta yace "sauko to muj..." "Ahhhh" da tayi ya katse
mishi magananshi da sauri yace "menene? Me ya sameki?" Ya fad'a a rud'e yana
dubanta, yadda ya rud'e din se ya bata dariya har ta murmusa cikin kuka girgiza kai
yayi yace "ke ko?" Ta shagwa'be tace "hamma jikina ciwo..." yace "sorry dear" ya
tabbatar ko don bubbuguwan da tayi dole jikinta yayi mata ciwo tunda ba sabawa tayi
ba.
Sake hannunta yayi yana dawowa, d'an dukawa yayi ya saka hannunshi yana mayar mata
gashin da ya hauro kan goshinta baya yace "kiyi zamanki anan bari In je In kiramiki
umman from there zan fita In samo miki drugs ohk?" Kai ta gyad'a mishi yayi pecking
goshinta yace "take care and don't cry" murmushi tayi ya juya ya fice, yana fita
parlorn yace "umma hayatee na son ganinki jikinta na ciwo bazata iya fitowa ba" Kai
umma ta dukar a kunyace shi ko ko a jikinshi sema hajja da ya kalla yace "hajja Ina
ummu?" Murmushi tayi tace "tana chan kitchen tana had'awa matarka abinci, se kace
mu en gidan bamu iya girki ba" murmushi yayi yana kashe mata ido yace "Ai kin san
mu na special ne seda haka" Tace "ja'irin yaro ko ba sepecil ba" dariya ya fashe
dashi yana kama baki ze yi magana tace "wuce ka bani wuri bana son ji" kitchen
d'inta ya nufa yana dariya wai sepecil ga mijinta gwani a boko amma ita batayi
karatun ba sbd yanayin wasu iyayen na da da basu yarda da boko ba.
A bayanta ya tsaya yana leka tukunya kaman yadda takeyi juyowan da zatayi kenan
suka kusa cin karo "subhanallah" ta furta a tsorace baya ya matsa yana dariya
ludayin hannunta ta d'aga da nufin kwad'a mishi da sauri ya rike hannunta yana cewa
"sorry ummu, I'm sorry" cikin dariya murmushi tayi tace "Da alamu yau kana cikin
farin ciki" yace "yes sure, I'm the happiest person in the world today, ummuna is
back likewise my hayatee" Tace "tafi marar kunya kawai se na hanaka hayateen naka
inga ta tsiya" shagwa'bewa yayi yace "sorry" murmushi kawai tayi ta juyawa girkinta
da taci karfinshi, yace "ummu zan je dubawa Hayatee maganin ciwon jiki bye" Tace
"Ohk Son, take care" ficewa yayi cikin nishad'i da farin ciki.
Ta 'bangaren umma kuwa seda hajja ta kuma magana kan ta mike ta shige d'akin cikin
zakuwar son rungume 'yarta for the first time a rayuwa tun haihuwarta, iman da ta
lalla'ba ta sauko da kafafunta daga saman gadon ta zauna da kyau tana ganinta ta
mika mata hannu tana cewa "ummaanah" Da sauri umma ta karaso suka rungume juna suna
kuka a tare, d'agowa umma tayi tana shafa fuskanta zuwa kanta cikin kuka tana cewa
"my baby!!!" Se ta kuma rungumeta. (Awwwn so pitiful)
Itama se ta kuma cewa "ummanah" daga karshe ta kwanta a jikinta umman na shafa
gashinta zuwa bayanta wani irin soyayyar uwa da d'iya suke shearing soyayyar da
yafi ko wani irin soyayya a duniya sun jima a haka kowacce na son fara magana amma
this awkward feeling na rashin sabo ya hana, daga karshe umma ta nisa tace "ki
yafemin Saudah" for the very first time a rayuwarta Da taji umma ta kirata da
asalin sunanta se ta kara narkewa hawaye na kuma zubo mata se ta turo baki Don
shine ya fad'o mata yace kar tayi kuka bayan ya San definitely se tayi d'in, a
shagwa'be tace, "Umma ni wallahi ban ta'ba rikeki a zuciyana ba ko shed'an ya
rayamin mummunar abu akanki da sauri nake tuba in nema mana gafarar ubangiji
gabad'ayanmu Don nice ya kamata in nemi yafiyarki ki yafemin umma abubuwa dayawa
sun faru ta sanadiyata" d'agota umma tayi tana kallonta tace "ni ba Abinda kika min
ke 'ya ce ta gari wacce ko wace uwa zatayi alfaharin samu Allah yayi miki albarka"
kuma rungume umman tayi se ji sukayi ance "I'm really jealous here ni baza a
rungumeni ba?" Da sauri Iman ta d'ago tana kallon ummu Allah ya gani tsoronta take
se kuma take ganin abun kaman a mafarki ko de kunnenta ne suka jiye mata ba daidai
ba? Ummu na matsowa tace "com'n come gimme a hug" hannun umma iman ta matse tana
kallonta se ta gyad'a mata kai tana matsawa ummu ta maye gurbinta ta rungumeta tace
"I'm so sorry dear ki yafemin ba laifina bane it was a sihr akan ki da my beloved
son ban san aikin waye ba, kiyi hakuri dan Allah wallahi duk wani mummunan abu da
na ta'ba miki na tuna har kunyar had'a ido dake nake, dan Allah ki yafemin....
d...." da sauri Iman ta katseta tace "ummuuuu....... Alhamdulillah, Alhamdulillah,
Alhamdulillah Allah na gode maka da ka nunamin wannan rana, rana ce da bazan tam'ba
mantawa ba All thanks to Allah he brought all my ummu's back" ta kuma lafewa jikin
ummu murmushi kwance a fuskanta, d'agota ummu tayi tace "banji kince kin yafewa
ummun taki ba to" Tace "ummuna Allah ya yafemana bakimin komai ba wallahi tun da
chan ban rikeki ba, Ai d'a nagari baya ta'ba fushi da iyayenshi" kuma rungumeta
ummu tayi tace "so proud of yhu binty" kan ta mike tana cewa "bari In kawo miki
special dishes da nayi sbd ke na san kina jin yunwa".
Ita ta ma manta da rayuwan cikinta se yanzu da akayi maganan abinci dama tun chan
yake mata kukan yunwa, ummu na fita ta matso gangan umma ta kwanta jikinta nan suka
fara hira a hankali kan kuce kwabo sun sake ana ta shan hira gwanin shawa'a.
************
NIGER
Wani kungurmin daji da suka shigo da seda sukayi tafiyan kusan awa uku a machine
bayan sun ajiye motansu bakin hanya duk sunyi lugub sun gaji kaman waenda aka yi
musu jibgan kare, da kyar suka iya sauka bayan machine d'in ya tsaya dab gidan
bokan sede me............
🖤Gureenjo🖤
🥀NOOR IMAN🥀
*048*
Layi ne a wurin na bala'i abin mamakin kuma matane karankatakap ba namiji ko d'aya
a galabaice Mama ta dubi jawahir tace "ke dama haka ake cin uban wuya kan a samu
ganinshi? Yanzu kina nufin se mun jira duka wannan layin kan mu ganshi?" Murmushi
jawahir tayi tace "no inde da kud'ad'e wannan layin ba komai bane yanzu zamu iya
ganinshi" umma tace "ko nawa ne dan Allah muyi mu hanzarta" Hamna dake ta nyamutsa
fuska tana kallon wurin tace "yanzu anan mutum yake rayuwa? Tabb" ba wadda ya
amsata se d'an waya da jawahir tayi nan da nan wani yazo ya bi dasu ta baya har
bukkan boka.
Wani mummunan bakin kafiri mushriki ne zube a wurin kato irin giant d'innan
shirgege da uban tumbi zaune idanunshi a rufe hannayenshi a bud'e kaman dae yana
wani bautansu dae na shirka, duk zama sukayi cikin dakakkiyar muryanshi yace "me ke
tafe daku?" Umma ce tayi gyaran murya tace "ni dae 'ya'yan 'yar uwata ne nake so
duk su wulakanta su zama abin Allah sarki sbd komai da suka fini, mijinta kuma a
nakastashi, tunda har ya kasa aurena ya aureta se 'yata gatanan tana auren d'aya
daga cikin yaran ne Abdulraheem muna so ya zama a tafin hannunta se yadda ta
juyashi kawai, sannan munafukar d'ayar matarshi a haukata ta haukan da za'a rasa
warakanshi har abada"
Shiru yayi na mintuna akallah talatin har sun kosa duk se kara gyara zama suke kan
ya fad'i wata kalma se ga kwarya a gabansu da wani jan abu ciki wani abin ya kuma
fad'a se ga Iman nan kwance a jikin ummanta tana mata surutu ita umman murmushi
kawai take sakewa, had'e rai Hamna tayi In da itace tayi magana ma wallahi da cewa
zatayi a kasheta har lahira kawai dae tana tsoron wannan gabjejen mutum ne.
Yace "ita?" Umma tayi saurin cewa "kwarai kuwa boka" kai ya gyad'a ya sake fad'an
wata kalma da wani yare da bama su sani ba se ga wani kulli gaban hamna fari da
baki da wasu garin magani gasunan dai kore kore yellow yellow, yace "ba'kin shi
zakiyi wanka dashi a tsakiyar d'akinta ki kirayi sunanta sau ukku a duk inda take
zata haukace tabi duniya, Farin kuma ki sawa shi mijin naki a abinci ko abin sha an
wuce wurin In dae har ya sha ko yaci komai kankartar abin".
Tace "Boka an gode" yace "ki godewa Aljannu" Ai ko ta gode musu ta hanyar cire
makudan kud'i Don har d'akin Abdul ta shiga ta lalu'bo kud'ad'e dayake ta san
ma'ajiyarshi ta zubewa wannan mushriki, kan umma ya koma ya fad'i wasu kalmomi se
ga layu sun bayyana manya guda uku, yace "d'auka" ta d'auka ba ko tsoro yace "ki
binne d'aya bayan d'akin ita 'yar uwartaki, d'aya bayan d'akin shi mijin nata
d'ayan kuma shine ze kasance na yaran ki samu kan bola tsakiyar dare ki binne
shikenan Aljannu zasu karasa aikin ki tabbatar ba wadda ya ganki in sun binnu kuma
ki tabbatar ba wadda ze iya tonowa".
Jawahir ma ta nemi karin shiri akan alhazawanta suka sallameshi da makudan kud'i
suka fito cikin jin daad'i gani suke kaman har sun aikata komai ya faru suna
fantamawa cikin arziki, machine suka samu bayan sunyi tafiyan kafa sossai suka
d'ane ya fito dasu suka hau motansu se Nigeria cikin zakuwa.
*******
"Wannan surutu ya isa hakannan ga abinci sauko kici kan wannan yaron ya dawo miki
da magani kisha ki kwanta ki huta" tray d'in ta ajiye mata umma tace "wai sannu da
kokari" murmushi kawai ummu tayi Iman tace "na gode ummu Allah ya saka da alkhairi"
hancinta kawai ummu ta ja zatayi magana wayanta ya d'au kara dubawa tayi taga zahra
murmushi tayi kan ta d'aga tace "Autana" kawai se zahra ta sa mata kuka ta manta
when last taji ummun ta kirata da haka murmushi ummu tayi tace "ke kam bazaki girma
ba ko? Yanzu me abun kukan?" Tace "ummuna nayi missing d'inki dan Allah yaushe zaki
dawo? Ko In zo?" Ummu Tace "makarantan kuma wa ze je miki zamu dawo ne da daughter
ta samu sauki" zahra tace "ummu zan iya yi mata magana yanzu?" A sanyaye ummu tace
"ga ta".
Ta mikawa Iman wayan kar'ba tayi tace "besty" nan fah zahra ta kuma fara wani sabon
kukan wadda hakan yasa hawaye ya cikawa Iman idanu kan ma ita Iman tayi magana
zahra tace "ki yafemin besty" murmushi Iman tayi tana share hawayen da ya
gangaromata tace "Anki se kin yarda Hamma Muhammad ya turo kin san ina lissafe?
Saura sati date d'in da aka bashi ya cika" a shagwa'be zahra tace "to ya na iya"
dariya Iman tayi tana cewa "masha Allah kice mu shirya shan buki bari inzo In mishi
albishir" murmushi kawai zahra tayi me sauti se kuma tace "innalillahi gaban su
umma kike wannan magana?" Iman tace "kwarai ma kuwa gashi handsfree kike kuma ba"
ihu zahra ta sa zata kashe wayan Iman tayi saurin cewa "ke ke wallahi ba kowa sun
fita" ajiyar zuciya ta sauke tace "amma ke ba!" Sukayi dariya a tare sauka Iman
tayi a hankali sbd jikinta da take jin kaman an mata tsinannen duka a kasa ta zauna
ta sa chokali ta fara cin abincin rice ne da sous d'in hanta se miyan cabbage
girkin da yake kad'an ne ba karamin daad'i ya mata ba, har ta kusa gama ci hira
suke da zahra nan take fad'amata su teema ma sun koma yolan jiya duk wani abin da
basuyi hiran ba seda sukayi, wayan taji an zare daga kunnenta ko bata d'ago ba ta
san waye sbd kamshinshi da ya cika mata hanci.
'Dagowa tayi se tayi saurin ja baya sbd kusancin dake tsakaninsu a duke yake
gefenta wayan ya sakala a kunnenshi yace "ke sarkin surutu ki bar min mata ta huta
haba" dariya tayi tace "hamma dan Allah ku dawo da wuri" yace "yes zamu dawo ne ko
don maneminki da ze turo next week" Da sauri ta kashe wayan shi kuma yayi dariya
'yar kaniya se kace da gaske tana da kunyan dama surutun yake son yankewa don ya
san In ba hakan yace ba se ta dameshi Don ita surutu baya damunta "yarinya se kace
aku mutum ne baya gajiya da surutu" murmushi Iman tayi ta d'ibo abincin a spoon da
take ci ta kai mishi bakinshi bud'ewa yayi ta zuba mishi ya lumshe idanunshi ya
bud'e fes akanta yace "wannan kam daad'in abincin ne ko har da albarkar hannunki
hayatee?".
Siririyar dariya ta sake tana sa hannu a baki tace "a'a nide inaga santin daddad'ar
girkin ummu ne bari In sa maka waigi" ta karasa da janyo pillow ta sa mishi
bayanshi dariya yayi yana gyarawa ya zauna da kyau yana tankwashe kafa yace "I
missed yummy foods d'in ummu wallahi" Tace "Alhamdulillah" shima ya maimaita ta ci
gaba da bashi Don ita ta riga da ta koshi shikam daad'in girkin da kuma soyayya ya
d'ibeshi ya ma manta be jima sossai da cin abinci ba seda yaji cikinshi na shirin
fashewa yace "wayyo hayatee zaki fasamin ciki" dariya tayi tana ajiye spoon d'in
tace "to na bari haka, ga ruwa" ta mika mishi kar'ba yayi ya sha tace "wai da gaske
ne za'a tambayar auren bestyn?" Yace "eh d'azu munyi magana da Muhammad d'in da
kuma Abban na sa an min binciken halinshi be da wani nakasu ko matsala matsalar dai
mahaifiyarshi ce da ta cika matsawa matan 'ya'yanta"
Tace "Toh yanzu haka zata aureshin mahaifiyarshi bata sonta?" Hancinta yaja yace
"me a ciki komai ai lokacine zata dena ne in lokacin hakan yayi sannan yace ma ba
kano zasu zauna ba ya koma aiki Lagos chan zasu zauna" shagwa'bewa tayi tace "Allah
sarki yanzu zan rabu da bestyna kenan" murmushi yayi yace "ga ni se in maye
gurbinta dama chan ni ya Kama ta In zama bestyn" murmushi kawai tayi.
Kwana biyu suka kara a fufore an cika ta da gata da kulawa daga hajja, ummu, umma,
baba fufore da babanta se kuma me gayya me aiki wato malabo sossai taji daad'in
kwana biyun nan fiye da ko wasu kwanaki cikin ranakun ta na duniya duk abinda take
so shi ake yi se abinda take so zata ci, umma ta manta da wani kunyan d'iyar fari
ta rungumi erta don d'aki d'aya ma suke kwana, yayin da gefe d'aya Abdul ya takura
mata Allah Allah yake su tafi ya samu lokacin matarshi seda yayiwa baba fufore
maganan tafiya sau kusan biyar kan baban yace zasu iya tafiya ko washegari ne cikin
murna yazo ya sanar dasu yayinda Iman kam batayi wani farin ciki sossai ba sbd
zatayi missing wannan kulawar da yadda take kwana jikin mamanta kaman wata er goye.
Sede bata nuna a fuska ba don ta san In ta kuskura ta nuna ta shiga uku da rigiman
shi, nan fah aka hau shirin komawa gida, washegarin kuwa suka tafi suka bar su baba
da kewa baki sunyi halinsu, kan su tafi seda baba ya basu wani ruwan magani a half
jarkan da wani mayuka da ya had'a banda na Iman da ya bata wadda zasu zama na
shafawanta har su kare kan taci gaba da shafa duk abinda taga dama, yace a bawa
inna, goggo saratu, goggo hindatu da goggo kamila su sha In sunsha se su shafa
komenene da wannan aljanar ta sa musu ze narke yabi fitsari ko kashi godiya sossai
baba da umma sukayi har da Hawaye shi kam har 'bacin ranshi ya nuna akan godiyan
Don yadda ya d'auki su Abdul Haka ya d'auketa.
A 'bangare d'aya ma Abba da zahra sun matsu sossai su dawo musamman Abba da yake
cikin farin ciki da natsuwa matarshi ta dawo daidai Allah kad'ai ya san irin halin
damuwan da shiga akan halayenta na sihiri, baki bud'e baba da umma ke karewa wannan
masarauta kallo cike da mamakin inda aure ya kawo 'yarsu wannan ba Don aure ba ko
wucewa sun isa yi a kofan masarautar bare su shigo? Khaih gaskiya dukkan godiya ya
tabbata ga Allah mad'aukakin sarki.
Basu kara sakankancewa da al'amuran masarautarba seda suka ga wani tarba na karamci
da suka samu daga wannan gari gaskiya sun jinjinawa karamci da iya tarbar baki irin
na mutanen Adamawa, nenne da kanta ta musu iso ga mai martaba suka mika gaisuwa
inda dama meeting ake na family waenda suke kusa kawai sbd irin abinda ya shafi nan
cikin gida, anan ummu ta wanke kanta ta basu labarin abinda ya faru fufore harda
matsalan Noor Iman gabad'aya kowa a wurin seda ya jinjina wannan al'amari nan mai
martaba ya tofa albarkacin bakinshi inda yayi nasiha sossai akan kula da shiga
harkar aljannu da mutane suke se kuma yayiwa ummu nasihar karta zargi kowa Allah ba
azzalumi akan bayinshi bane da kanshi ze toni asirin mugu daga karshe aka rufe taro
da adu'a.
Gabanta ke luguden bugu jin nenne ta sa kuyangi kai musu kayayyakinsu part d'insu
na gidan shikenan yau kam ta kad'e har buzunta gashi hajja ta sata dole shan wasu
abubuwan da ma bata sansu ba na kwana biyun nan da tayi da ita ga wasu fitinannun
turaruka da ta had'ata dasu, akwai randa ta shafa d'an kad'an wallahi saura kad'an
komai ya faru a d'akin hajja, hajjan ce ta katseshi kunya kaman ya kasheta, to
gashi yanzu part d'insu zasu ware su kad'ai Don har nenne ta ma umma iso d'akin da
zata kwana, ummu kam part d'in iyayenta ta sauka.
Wanka ta farayi bayan shiganta d'akinta ta shirya cikin cotton doguwar riga me
guntun hannu sbd zafin da ake, bayan ta fesa rexona kawai se ta fesa Oud mood spray
kawai ta sa hula akanta, zama tayi bakin gado tana amsa wayan hafsy cikin kuka
hafsyn tace "Adda wallahi muna cikin matsala da damuwa ban dae fad'awa baba ba kar
hankalinsu ya tashi" cikin damuwa Iman tace "me ya faru hafsy?" Tace "mijina ne ya
sayi fili na about 1.5million har ze fara gini se ya shiga kariyar arziki hakan ya
sa ya sayar da filin ga wani mai kud'i ashe tun farko wadda ya sayar mishi da filin
irin 'barayin filin nan ne yanzu asalin mai filin ya kaishi court na sayar mishi da
fili yanzu an nemi ya biya Alhajin da ya sayarwa kud'inshi shi ya d'auki asaran sbd
shine marar karfi cikinsu, shi suke son d'aurawa asaran gashi mun karar da kud'in
da aka saya d'in a jinyar ciwon diabetics na mahaifiyarshi".
Shiru iman tayi cikin nazari da tunani chan tace "Toh Hafsah na san yanzu kika
fad'awa su baba ma d'aga hankalinsu zasu yi kinga ga jinyar mama dukda hamma Abdul
ke yi, gashi nima ba wasu kud'ad'e bane hannuna, sede Zan duba a cikin kayan lefena
In mun dawo gobe akwai d'an kunnayen gwal se In baki ki sayar watakila kud'in su
kai a bawa court d'in" hafsa cikin Hawaye tace "anya kuwa za'ayi haka Adda? Zaki
taimaki mutumin da be ta'ba nuna miki soyayya ba kullum se...." katseta iman tayi
tace "kayya hafsy ban son jin komai gobe in mun iso Zan kiraki, se munyi waya ki
gaida maman nashi da jiki" ta kashe wayanta d'ago kan da zatayi se ta ganshi tsaye
jingine da gini yana kallonta murmushi ta mishi ga mamakinta kai ya kawar ya nufi
ficewa har ta bud'e baki da niyan mishi magana se rufe kofanshi ta gani bata kawo
komai ba ta gyara tayi kwanciyarta tana chat da zahra a haka har tayi bacci bata ji
gogan nata ba gashi ita kunyar zuwa d'akinshi take kar yace wani abu take nema.
*****
Ta 'bangaren su umma da hamna kuwa a lokacin da suka dawo me umma taci ne se Allah
cikinta ya rud'e se gudawa haka ta kwana tanayi daga baya kuma amai ba shiri hamna
ta garzaya da ita asibiti ba tare da ta fad'awa Abba halin da take ciki ba, bayan
an mata komai an bata gado tayi tahowarta ta kira kukunta a waya ta balbaleshi da
masifar me ya hanashi zuwa na kwanaki dayawa nan ya fad'amata ai oga Abdul ya
sallameshi ya Bashi aikin yi a company d'inshi bala'i ta dingayi har seda ya kashe
wayanshi.
Haka take zuwa ta sayi abinci a restaurant ta kai asibitin yau kwananta d'aya kenan
hakan yasa basu aikata ayyukan da boka ya basu ba har yau da ta kai mata abincin
sukayi fad'a sbd mitan da umma ke yi akan bata damu da ita ba bata kwana wurinta
iyakaci ta kawo mata abinci tayi tafiyarta kaman ba mahaifiyarta ba masifa ta hau
yi akan ta zo ta zama mata liability a haka suka rabu tana shigowa gidan kawai ta
ganshi tsaye gaban fridge na parlorn da ruwa rike a hannunshi da sauri ta saki
jakan hannunta ta saka ihu da gudu tayi kanshi ta rungumeshi.
🖤Gureenjo🖤
🥀NOOR IMAN🥀
*049*
Janye jikinshi yayi yana satan kallon inda Iman take bama su take kallo ba tv ta
kurawa ido cikin tunanin laifin da ta mishi da ta gaisheshi da safe be amsa ba Haka
har suka shiga jirgi be tanka mata ba har suka sauko drivers biyu suka zo se Hafeez
da suka zo da zarah, murmushi ta d'anyi tuna irin ihun da Zarah ta yi Don ganinta
da gudu tazo ta rungumeta har seda tayi hawaye Allah kad'ai ya san irin kewar
kawartan nan da tayi, sun so su tsaya hira sede Abba na jira suka d'auki ummu suka
tafi.
'Daya driver ya d'auki su Abba da Umma su kuma d'ayan ya d'aukesu haka sukayi zaman
kurame kaman ba shi ba har gida, zama kawai tayi shi kuma ya nufi fridge shan ruwa
kenan wannan matar tashi ta shigo, su take kallo amma idanunta kan tv yake wani
kullutun bakin ciki ne ya tokareta a kirji ganin ya rungumeta shima yana wani
murmushi wadda shi a wuri shi yake ne don bata haushi amma ita gani take na soyayya
ne.
"Yanzu shigowarka?" Kai ya gyad'a mata yana cewa "kina lafiya?" Tace "kalau wallahi
umma ba lafiya tana hospital" yace "subhanallah shine baki kira kin fad'amin ba?"
Tace "jiya ne kawai fah amma da sauki watakila gobe a sallameta" Kai ya gyad'a tace
"a d'akina zaka sauka ko?" Kai ya kuma gyad'a mata tace "wow I missed you so much
muje In had'ama ruwan wanka" ta ja hannunshi ya kuwa bi ta zuwa d'akinshi.
A zuciye ta mike tayi d'akinta har kwalla tayi tana fad'awa gadonta ita karan kanta
bata ta'ba sanin tana da kishi haka ba kaman yau da wannan tunanin bacci ma ya
d'auketa bata sani ba, se zuhur ta tashi tayi sallah yunwa ne ya fara kwakwalarta
hakan yasa ta mike ta fito kitchen Indomie biyu ta dafa da kwai biyu ta juye a
plate tana fitowa ta ganshi zaune parlor da wasu kayan daban kawar da kai tayi zata
wuce se kuma taga rashin dacewar hakan ta kalleshi ita yake kallo tace "barka da
rana Hamma" yace "yauwa".
Har ta kai kofan room d'inta yace "cikinki kad'ai kika sani kenan?" Yayi tambayar
yana kallonta tace "a'a Hamma wai naga ba nice da girki bane kuma naga Anty hamna
bata fito tayi wani abin ba gashi Ina jin yunwa yasa na dafa, amma In zaka ci
gashinan bari In dafo wani" ta kai gabanshi ta ajiye ta bashi tausayi har ze yi
mata magana se kuma yayi tunanin barinta ta gane kuskurenta.
Itama bata tanka ba ta juya kitchen ta dafo wani tazo ta wuceshi zuwa d'akinta taci
ta koshi tayi tagumi nan gaban plate d'in ko me tayi mishi? Amma in tace a haka
zasu zauna taga ya chanza mata bata iya magana ba zata cutu don tana da saurin
shiga damuwa akan abinda take so, ajiyar zuciya ta sauke tana d'ago kai se ta
ganshi tsaye, idanunta da suka cika da hawaye ta saka cikin nashi tace "hamma ko
akwai wani laifin da na maka ban sani ba?" Gabanta ya karaso ya duka ya rike
hannayenta yace "kin d'aukeni abokin zama?" Kai ta gyad'a yace.
"Toh Ina so daga yau hayatee ina so In zama best friend d'inki, your shoulder to
cry, your favorite person no matter what the situation is, ki dinga sharing
happiness ko sadness d'inki dani kinji?" Kai ta gyad'a yace "words pls" Tace "Toh"
yace "yanzu Hafsat ma ba kanwa bace a wurina?" tace "kanwarkace" yace "to me yasa
in abu ya sameta bazaki iya shawara dani kan ki yanke hukunci ba? Komai nawa naki
ne habeebty kud'i na naki ne base kin sayar da wani abu naki don fitar da
kanwarki/kanwarmu cikin matsala ba, zanyi magana da mijin ohk?" Tace "Ohk kayi
hakuri bazan sake ba In Allah ya yarda".
Murmushi yayi yace "that's my girl" yana lakace mata hanci murmushi tayi itama ta
mike shima ya mike suka fito tare ya shige room d'inshi itakuma ta kai plate
kitchen, aiko chan yamma hafsat ta kirata ta dinga zuba godiya harda kuka, wai har
Abdul yayi settling case d'in, don tun bayan ta dawo da plate taji fitansu da
matarshi, watakila asibiti yaje ya duba umman da taji d'azu tana cewa ba lafiya
daga nan ya wuce gidan hafsan.
Taji daad'i sossai har ranta se ga mijin hafsyn ma ya kirata hakuri ya bata akan
abubuwan da yayi ta mata, bata nuna mishi komai ba tace ita wallahi ta yafe mishi
bata rikeshi a ranta ba, nan ya ba mamanshi itama ta nemi yafiyarta, bayan ta ajiye
wayan take tunanin rayuwanta na baya tabbas zahra da Abdulraheem Alkhairi ne ga
rayuwanta sun shigo mata da haske ya haskake bakin duhun rayuwanta Alhamdulillah ta
furta a fili.
Fita tayi ta d'aura musu abinci sbd tana ganin In batayi ba bata kyauta ba sbd Ai
asibiti hamnan taje so ta lalla'ba ta dafa musu jollof na taliya da yaji veggies da
busashen kifi ta shirya duk kan dining ta koma d'akinta ta watsa ruwa ta murza mai
da turare kan ta nemi wasu English wears marasa nauyi trouser da shirt d'inshi da
ta baya yake dogo kaman jela ta saka, ta saka black hula a kanta se after magrib
taji shigowar mutumin da uwargidan nashi a lokacin ko ba abinda taji.
Mikewa ma tayi ta fito tayi mishi Sannu da dawowa ba ruwanshi gaban hamnan yace
"hayatee sannu kema da gida mun barki ke kad'ai" murmushi tayi tace "ya jikin
umman? Hope taji sauki?" Yace "yes da sauki sossai watakila ma a sallameta gobe in
Allah ya kaimu" tace "to Alhamdulillah, Sannu Anty" ko kallonta hamna batayi ba se
d'akinta da ta fad'a.
Kai iman ta girgiza tana murmushi bata da lokacin wannan shiriritar, kallonshi tayi
shima ita yake jifa da wani irin kallo yana sake murmushi a kunyace ta dukar da
kanta dukda bata saba sa kananan kaya ba amma fah ita yanzu ta shirya zaman aure
daram so ba abunda bazatayi ba don kwato martabarta da dawo da hankalin mijinta
kanta ba, tace "hafsy ta kira Allah ya saka da mafificin alkhairi ya kara bud'i" ya
amsa da "Ameen ya rabbi don adu'ace kawai yasa na amsa" murmushi ta mishi.
Ta juya d'akinta shima room d'inshi ya fad'a se bayan isha suka had'u a dining
sukayi dinner tare godiya ya mata har taji kunya ya kamata, gashi ya dinga santin
abincin ko a jikinshi, hamna kuwa haushi har makokoro gashi bata iya girki ba bare
tace itama zatayi don ta burgeshi be ta'ba mata santi kan abinci ba se yau, dama
ina zai yi tunda abincin gardi ya saba ci.
Washegari da kanshi ya sa ta shirya ya d'auketa suka tafi aka mata passport ya fara
musu chukuchukun tafiya, driver ya kira ya maidata gida shi kuma ya tafi
harkokinshi ta so ta biya asibiti ta kalli Mama sede ya tabbatar mata ko taje
baza'a barta ta ganta ba so haka ta hakura suka koma gida tana shiga ta samu zahra
nan ta sa ihun jin daad'in ganinta a take suka kule d'akinta aka hau hira, chan
yamma se ga kiran muhammad abin mamaki taga zahra ta d'auka harda kashe murya tare
da cewa "boo ya kk?" Duka ta d'aka mata tana dariya tace "lallai zahra yaushe kika
zama munafuka ban sani ba?" Yayinda zahra ta wani shagwa'bewa tana kai karanta
wurin muhammad d'in.
Sossai yinin ya musu daad'i da yamma suka shiga kitchen sukayi girki tare dukda
zahra ta so hanawa tunda ba girkinta bane, seda Iman ta nuna mata be dace ba ai ko
yaya ne mahaifiyarta ce kwance asibiti ba lafiya so Don tayi girki ba matsala,
jollof rice sukayi da salat se zobo suka shirya komai dining kan suka koma d'aki
nan zahra ta fara haramar tafiya Don magrib da ya kawo kai iman bata so ba Don ji
take kaman kar su rabu gashi ita kad'aice gidan kaman rai.
Ba yadda ta iya haka ta rakata har mota ta tafi, itakuma ta dawo sama ta gyara
d'akinta ta share ta kunna turaren wuta kan ta shiga tayi wanka yauma same thing
kananan kaya ta saka bayan ta cire atamphar da suka fita dashi kaman jiya yauma kan
magrib suka shigo gidan tare da matarshi akwai abu d'aya da ta lura dashi daga
gareshi ko yaya idan ba wani abu bane yake dashi me muhimmanci baya wuce magrib be
shigo gidanshi ba.
Haka ta fito ta tarbesu da fara'anta shima a sake ya amsata yana cewa ya gaji sannu
ta mishi ya shige d'akinshi hamna ma tayi nata bayan ta gama watsa mata harara,
murmushi tayi kawai ta koma d'akinta bayan isha suka fito suka ci abinci, nan yake
fad'amata ai gobe za'a iya zuwa duba Mama so ta shirya ze d'auketa ya biya ya
d'auki umma se suje baba yace daga wurin aiki ze wuce, murnanta ya kasa 'boyuwa
sossai ta nuna jin daad'inta.
Washegari kuwa ta shirya cikin wata arniyar orange lace ta tufke kanta yayi kaman
acuci ta kafa d'aurinta da ya rufe mata gabad'aya kan ta saka brown gyale, takalmi
da jaka ta fito d'as da ita gashi fatanta yayi wani fresh da kyau sbd mayukan da
take anfani dasu yanzu na oriflame har wani kumatu tayi na kwanciyar hankali
kunneta da wuyanta siraran d'an kunne da sarka ne na zinari haka zoben hannunta,
shi karan kanshi seda ya 'bata wasu lokauta yana kallonta har seda hamna taja wani
muguwar tsaki kan ya kau da kai daga kallonta ya mayar kan hamnan ta riga ta bud'e
gaba ta shiga tare da buga kofa.
Shiga mazaunin driver yayi yace "wai da wa kike wannan tsakin?" Tace "da kaina
Hamma mantuwa nayi kuma na san bazaka yarda na koma na d'auko ba" sarai ya san
karya take sede a barshi a haka, daidai lokacin Iman ta bud'e baya ta shiga ta
madubi ya kalleta yana sauke ajiyar zuciya yacewa hamna "kije kiyi sauri" ta kuwa
fita kaman gaske ta koma cikin gidan, se lokacin Iman ta kalleshi se suka had'a ido
murmushi tayi yace "kina da kyau hayatee" Tace "waii hamma wannan kam zagi ne ko?
Baka kallon kanka a madubi ne?" Dariya yayi yana d'aga mata gira yace "me kike
tunani ne? Kina zaton na fiki kyau?".
Tace "sossai ma Ina da gami" murmushinshi me narkar mata da zuciya ya saki yace "ni
kam ban gani ba a duniya banga me kyaunki ba hayatee, kin kuwa san kin fi d'awisu?"
Dariya ta saki tana kama baki yace "dariya na miki kyau kiyi tayi please kinji?"
Murmushi tayi tana gyad'a kai daidai lokacin hamna ta shigo motan be kara magana ba
se murmushin da yake sakewa akai akai har suka fice asibitin da umma take ya fara
sauke hamna har ya tada motan iman tace "Hamna please in shiga in gaidata?" Yace
"Ohk bari In gyara parking se mu shiga".
Gyarawa yayi suka sauko suka jera a tare gwanin sha'awa se d'auke idanun Jama'a
suke, bacci ma suka samu takeyi ummu na zaune kan plastic chair da fara'a sossai ta
tarbi Iman har tana cewa tayi fushi shine ko a waya bata nemeta ba tun dawowansu
shine ya bada hakuri ya kuma tabbatar mata yau a gidanta zasuyi dinner don haka ta
tanadarwa daughter d'intan better, cikin jin daad'i tace "aiko ba se ka fad'a ba
daughter yau se abinda kika za'ba" murmushi Kawai iman ke sakewa yayinda hamna tazo
wuya.
Kenan asirin da sukayiwa ummu ya karye garin yaya? Tab dole ko ta wani hali ne yau
a sallami umma su samu su aikata aikin nan in ba haka ba suna gani komai zai ida
chabewa gashi yanzu duk wani so da kulawa da ummu ke bata ya koma kan wannan bakar
munafukar se kwafa take saki minti minti, sallama sukayiwa ummu suka fice dayake
umman na bacci tun shigowansu, suna fita ya rike hannunta lumshe idanu tayi ta
bud'e akanshi suka sakarwa juna murmushi gaskiya he can't wait..... he just can't
wait dare yayi ya nunawa wannan baiwar irin son da Allah ya d'aura mishi nata.
Da wannan tunani suka karasa mota seda ya zagaya ya bud'e mata ta shiga kan ya dawo
ya shiga mazauninshi se gidansu da ihun umma umma ta shiga gidan umman dake zaune
kasan bishiya tana tsince shinkafa tace "ikon Allah menene kuma haka maama?" Dayake
haka take ce mata tun daga fufore, jikinta ta fad'a tana cewa "nayi kewarki ummana"
tureta umma tayi tace "bani son shiririta Ina shi mijin naki kika baroshi?" Tace
"yana waje" karar fad'uwar tray sukaji da sauri suka kallo wurin.
Hafsyce tsaye ga trayn silvern da ta d'auko a kasa, mutsuke idanunta tayi ta kara
bud'ewa umma da ta gane abinda takewa haka ta mike tana cewa "toh maaama ga wata
mashirmaciyar 'yar uwarki" tayi d'aki don nemo hijab, dariya iman tayi tana cewa
"ke ba gizo idanunki ke gane miki ba labarine me tsawo na san kuka dawo umma zata
baki" Da gudu hafsy tazo ta rungumeta tana tayata murna nan umma ta fito da hijab a
hannu tana mitan sun bar mutum a waje.
Hafsy ta mike ta janyo gyalenta daga kan igiya iman ma ta mike suka fito seda umma
ta rufe gidan kan ta karaso Abdul ya duka har kasa ya gaidata ta amsa da fara'a
tana tambayarshi ummunshi baya suka shiga ita da hafsy yayinda iman ta shiga gaba
suna ta aukin surutu ita da hafsyn har asibiti ba abinda ke had'asu da malabo se
kallo don kunyar Umma da yakeji.
Har d'akin da mama take suka shiga wasa wasa kumburintan   yayi yawa wadda hakan ya
bawa iman tsoro da tausayi nan fa ta fara aikin kuka, da   kyar umma ta sata tayi
shiru yayinda malabo ya zuba mata idanu yana kallo adu'a   sossai baba ya mata inda
anan malabo ke fad'amu In one week zasu wuce dukda be so   su kai haka ba sede ba
yadda ya iya dole ya jira visa d'insu.
Sun jima sossai nan kan sauban yazo ya fad'a musu time ya kare yanzu sa iya tafiya,
ba don sun gaji ba suka fito baba ya d'auki su umma da hafsy yayinda Abdul ya
d'auki matarshi sukayi gidan ummu Don su rahama da kalthum sun dameshi da kira akan
suna son ganinta, se a mota hafsat ke bawa su umma labarin irin taimakon da Abdul
ya musu yanzu ya chanzawa mijintan ma wurin aiki zuwa company d'inshi albarka
sukayi ta sa mishi nan umma tayi briefing d'inta kan tafiyansu fufore da nema musu
magani da kakanshi yayi, har suka isa gida labarin kirki, alkhairi, sanin ya kamata
da son mutane irin na Abdul suke.
🖤Gureenjo🖤
                  🥀NOOR IMAN🥀
*Fatima Muhammad Gurin*
           *Gureenjo6763 on wattpad*
*hakika bani da abinda zan ce muku sisters se Allah ya saka da mafificin alkahiri
ya bar kauna, duk naga adu'o'inku gareni na gode kwarai Allah ya amsa ya biya mana
dukkanin bukatunmu na alkhairi ba shaaka wannan page d'in naku ne sadaukarwa ne ga
dukkan waenda suka iya 'bata lokacinsu da data d'insu wajen min adu'a na gode
kwarai na muku wannan page d'inne sbd jin daad'in adu'arku, ranan litini In Allah
ya kaimu zan fara jarabawar na gama tests. Allah ya bamu sa'a gabad'aya a duk
abinda muke.
*050*
Cikin farin ciki da jin daad'in ganinta Anty rahama, Anty kalthum, zahra suka
rungumeta murmushi kawai take musu tana jin daad'in yadda suke kaunarta har kasa ta
duka ta gaida ummu dake "ga daughter, ga daughter" a kunyace ta gaidata ta amsa da
fara'a ta gaida Anty rahama da Anty kalthum duk suka amsa suna mata barka nan fa
hira ya 'barke akan ire iren abubuwa haka da suke faruwa.
Sun jima zaune parlorn ana hira kan Abba, Hafeez da Abdul suka shigo a tare kasa ta
zame ta gaida Abba ya amsa fuska a sake cike da farin cikin ganinta barka ya mata
na shiryawa da ummanta ya sa musu albarka gabad'aya ya wuce parlorn shi, nan Hafeez
ya fara tsokanarta su Anty rahama suna rama mata gogan nata kam zama yayi ya zaro
waya ya fara aikin call idanunshi a kanta wadda hakan ya sa gabad'aya ta takure ta
kasa sakewa kunyan su Anty kalthum na kamata musamman da taga Antyn da zarah na
kuskus.
Dayake tun shigowar Abba ummu ta bi bayanshi, yana gama wayan ya taso yazo inda
take a kasa ya zauna gefenta har cinyansu na gogan juna wayanshi ya dadanna ya fito
da wasu hotuna ya d'an duko gefen kafad'anta yace "duba kiga wanne ne yafi kyau
anan?" Kar'ba tayi ta fara kallo wasu motoci ne masu asalin kyau colors daban daban
daga gani kuma zasuyi tsada akan wata BMW ta tsaya sede colourn Dark blue ne ta san
shi kuma baya son colored car kallonshi tayi shima wayan yake kallo yace "ita tafi
kyau?" Kai ta gyad'a yayi murmushi tare da kar'ban wayan.
Kashe wayan yayi da sauri ganin Anty rahama na leko kai, hararinsu yayi yana mikewa
yace "gulma dae ajali" suka kwashe da dariya gad'aya iman na sakan murmushi, kiran
sallah ne ya katse musu hiran da suka d'auko ana gama kiran Abba na fitowa suka
had'u da mazan sukayi masallaci basu dawo ba seda sukayi Isha, bama su zauna ba
ummu ta nuna hanyar dining tana cewa "bismillahnku dinner is ready" duk dining
sukayi ta d'aga wayanta ta kira zarah tana d'agawa tace "me kukeyi ne har yanzu
baku sauko ba? Kunga In ku bakwa jin yunwa ku turomin 'yata taci abinci" tana kai
nan ta kashe waya.
Zarah ta sauke wayan tana kallonsu Anty cikin muryan shagwa'bewa tace "mu kuma da
bola aka tsinto mu se muyi ta zama da yunwa" dariya suka saka Iman na murmushi ta
mike sbd su Anty ne kawai bata make zarah ba, dama tunda suka shigo take ta
kwaikwayan yadda ummu ke masifa akan Iman se dariya suke, da dariya suka sauko suna
hiransu duk suka zauna se suka bar mata seat d'in dake facing d'inshi.
Zarah ce tayi serving kowa tana bawa Abba labarin itama fah ta kusa zama graduate,
Hafeez yace "a ina d'in ke da yanzu kike level one" Anty rahama tace "kyaleta
shekaru kusan hud'u ke gabanki Don bakiyi komai ba madam" Anty kalthum tace "kila
ma harda spill se ki kara mata shekaru biyu kin san itace Anty olodon gidan nan"
bubbuga kafa ta fara kasa tana cewa a shagwa'be "Abba ka gansu ko?" Yace "Kunga
rahama banaso ku kyale min auta ta sarara, In Shaa Allahu ba spill da zakiyi
kinji?" Kai ta gyad'a tana murmushi a lokaci d'aya tana musu gwalo.
Shifa duk abinda sukeyin nan ba sauraransu yake ba tunaninshi da hankalinshi duk ya
d'auke akan matarshi murmushin da takeyi ji yake kaman fuskanta ya dawwama a haka
har abada, wushiryan tan nan me kyau da one side dimples d'inta da yafi komai
d'auke mishi hankali, dayake saitinshi ta zauna ta d'an mike kafa kanta kasa tana
juya chokali a lokaci d'aya tana murmushin dramar zahra don har time d'in bata gama
ba.
Ita harga Allah matsanancin kunyan cin abinci a haka take surukanta ne fah, wasu
surukan ko kujera ka zauna gabansu ba kasa ba se sunyi mita akan hakan amma su
waennan ba ruwansu en boko ne na gaske yadda suka d'auki su zahra haka suka d'auke
ta, wani irin zabura tayi tana zaro ido da sauri suka maida hankali kanta har suna
had'a baki suka ce "Lafiya??" Cikin In Ina tace "ba komai" satan kallonshi tayi ya
sake wata munafukar murmushi bata san sadda ta harareshi ba ido ya zaro da idanun
ya mata alamun ni?? Bakinta ta d'an turo, kanshi ya gyad'a ya sake kai kafanshi
kaman farko ze mata tafiyar tsutsa a tafin kafa da babbar yatsarshi da sauri ta
mayar da kafan kasan kujera, Abba da ummu da suka fahimci abinda yake faruwa kallon
juna kawai sukayi suna sakan murmushi.
Da kyar taci abinci kad'an shima da takurawar ummu seda duk suka bar dining d'in
kan ta mike ta fara tattare kwanukan ummu daga parlor tace "maza daughter ajiye
kizo akwai waenda zasu tattare ba se kin yi ba" ajiyewa tayi ta je parlorn nan ummu
ta kara basu hakurin abinda tayi musu duka, duk suka ce ba komai wallahi ai sun san
ba yin kanta bane.
Sun mike da niyyar tafiya gida kenan Hamna da umma suka shigo, gaban Iman ne ya
fad'i haka kawai ta rasa dalili wadda hakan ya sata fara ambaton Allah, ummu ta
mike da sauri tana cewa "an sallamekune hamna?" Hamna tace "eh wallahi ummu an bamu
sallama kuma umma tace nan take son sauka In ta kara jin sauki se ta wuce yola" Kai
ummu ta gyad'a tana cewa "to mu karasanku part d'ina, Sannu hajja" Kai kawai umma
ta gyad'a tana hararanta kasa kasa wadda a idanun zahra da hafeez kallon juna
sukayi.
Hamna ta kalli Abdul tace "Hamma gida kukayi In zo muje?" Yace "I thought da car
d'inki kika zo? Besides ba gida mukayi ba, ummu, Abba Allah ya bamu alkhairi" Abba
yace "Ameen ya rabbi Allah tashemu lafiya" ummu da hankalinta ke kan kanwarta tace
"A huta gajiya, se da safenku" suka fice ba jimawa Hamna ma ta fice Anty kalthum da
Anty rahama ma suka tafi, Abba ma yayi part d'inshi, zahra ta kalli Hafeez shima ya
kalleta tace "kana tunanin abinda nake tunani hamma?" Yace "ba alkhairi ya kawota
ba" tace "exactly amma zan sa mata ido baza ta zo ta dinga ruining life d'inmu a
banza da wofi ba".
Suna fita daga gidan ya kama hannunta ya matse cikin nashi yace "ni kike harara
d'azu ko?" Tana karkad'a idanu tace "wayyyo Hamma Allah ba da kai nake ba fa" yace
"to da wa?" Yana kallonta tace "Da kujera fah nake" murmushi yayi yana cewa "amma
kujeran da nake ko?" Tace "dan Allah kayi hakuri hannuna" ta karasa a shagwa'be
murmushi yayi don ya san ba wani rikon arziki ya mata ba shagwa'bace kawai a
lokacin suka isa mota seda ya bud'e mata ta shiga kan ya zagaya ya shiga me makon
ya tayar se ya rankwafa kanta yace "wato don kin rainani har turomin wannan bakin
naki kike ko? To bari su kar'bi hukunci" Kan tayi magana ya had'e bakinsu.
Seda yayi kissing d'inta son ranshi kan ya saketa yace "gobe ki kara turomin wannan
bakin kiga hukunci Ina da hukuncinshi kala kala" Kai ta dukar tana taune lips
d'inta murmushi ya sake yana tada motar cikin nishad'i ganin duk kunya ya hanata
d'ago kai yasa shi sa hannu ya kunna waka abinshi, Yana bi a hankali chan yace
"Hayatee!!" Kallonshi tayi tana amsawa a saman lips d'inta yace "kaman bakici wani
abin kirki ba muje mu samu abinda zakici?".
Tace "a'a na koshi fa" yace "no baki koshi ba oya fad'amin me kike son ci" Tace "da
gaske na koshi" be kara magana ba ya juya kan motar yayi cikin gari chan wurin gasa
nama ya tsaya ya saya gasashen kaza irin me ruwa ruwan nan ya had'a da zallan
gizzard, gaba kad'an ya kara ya kuma tsayawa ya saya fresh milk masu sanyi nan ya
juya motar sukayi gida a hankali yake jan motan yana kara jan lokaci basa magana
sede ya lalu'bo hannunta ya sanya cikin nashi a lokaci d'aya kuma yana bin wakanshi
wadda na larabci ne kad'an kad'an kawai takeji amma ta fahimci na soyayyane.
Se past ten suka shiga gidan sun samu motar hamna da alamu ta shigo a tare suka
sauka suka jera zuwa sama shi ke rike da ledojin a kofan hamna ya tsaya yayi
knocking tana bud'ewa ya mika mata kallonshi tayi ranta na kuna bata so suka shigo
yanzu ba shirin fita d'akin Iman take tayi wankan maganin nan amma sun kwafsa mata
suka dawo da wuri, kar'ba kawai tayi ta juya ciki, d'akinshi ya shiga da d'ayar
itama Iman d'akinta ta shiga ta tu'be kaya ta watsa ruwa tana fitowa ta shirya
cikin kayan baccinta purple masu taushi riga da wando ta saka hula a kanta tare da
sanya hijab.
Fita tayi zuwa kitchen ta san dole ne kawai taci shiyasa gwara ta kawo plates da
cups tun be sata ba, a d'an karamin tray ta shiryasu ta fito zuwa d'akinshi har ta
kai kofa se kuma ta dakata ajiyewa tayi ta nufi d'akinta ta tuna turaren da Nenne
ta bata tace ta tabbatar se zata ke'be dashi zata shafa karkuma ta yarda wani
namiji yaji kamshin a jikinta In ba shi ba Don wani sirri ne ciki.
Direct karamin kit d'inta ta nufa ta d'auko ta bud'e ta d'auko turaren garin
bud'ewa abu kam ya zube kusan kwatanshi a kayanta bayan ance d'an kad'an kawai zata
shafa bayan wuyanta haka ta fasa shafawa ta mike ta fito duk kamshin ya dameta.
Trayn ta d'auka ta shiga d'akin da sallama tsaye yake yana fesa body's pray da
alamu shima wankan ya fito Don sanye yake da bathrobe fara me bud'ad'en kirji
igiyar kawai ya d'aura kuma iyakarshi kasan guiwanshi kafanshi sanye da farar
silifas d'inshi me gashi da a d'akin kawai yake yawo dashi, yana ganinta ya sakar
mata murmushi ta cikin madubin itama ta mayar mishi tana ajiye abubuwan hannunta
kasa gefen dardumanshi inda taga ledojin, zama yayi ya juyawa madubin baya yana
kallonta.
Tana ajiyewa yayi mata hannu akan tazo isa gabanshi tayi a hankali cikin wani irin
tafiya ta Jan hankali wadda bama ta san tanayi ba, tana sa hannunta cikin nashi ya
fisgota kan kafanshi ta zauna lumshe idanunshi yayi na seconds ya bud'e take idanun
suka rine kamshin turarenta yake ji har cikin kwakwalwanshi wani irin kamshi me
fisgar hankali, hijabin jikinta ya cire tare da hulan gashinta ya baje don garin
cire hulan ya zare da band d'inta.
Rud'ewa ta fara jin fuskanshi cikin wuyanta yana shunshunata yana wani lumshe ido
cikin kasa sossai da murya yace "wani irin turare ne wannan hayatee?" Tace cikin
rawar murya "nenne ce ta bani" yace "uhmmm akwai daad'i ki samin kullum kinji?"
Tace "uhm" tana zillewa sede kam ya riketa da kyar ya iya controlling kanshi ya
d'auketa chak zuwa kan darduma shima ya zauna ya sanyata jikinshi da hannu d'aya ya
bud'e kazan ya fara bata da kyar take tauna jikinta na tsananta rawa haka gabanta
na fad'uwa kad'an kawai taci shikam ko loma d'aya be iya yi ba ya tsiyaya mata
fresh milk d'in.
Garin bata ya zube a jikinta sbd yadda jikinshi ke rawa kokarin gogewa take ya rike
hannunta ya kara tsiyayar mata da sauran a fatan jikinta ya d'auketa chak zuwa kan
gado, inda ya zuba ya fara bi yana lashewa yana isa daidai inda turaren nan ya zuba
ai se ya rud'e mata, ya fice hayyacinshi gabad'aya duk yadda take son mai magana ya
hanata se hannunshi da ya mika ya kashe wuta.
****
Salap salap take takawa zuwa tsakiyar d'akin Iman d'in tana ta'ba kofar tajishi a
bud'e murmushi tayi tana tuna yadda umma tace tayi ai wankan magani base ka jika
kanka ba ko shafawa kayi is Ohk, daga ita se towel tana isa tsakiyar d'akin ta
yasar ta fara shafa maganin tana cikin jujjuyawa tanayi kenan tsantsin tiles ya
kwasheta ihu tayi tana ambatan "Umma!! Wayyo Umma na" bata kai kasa ba ta samu ta
rike kujera ajiyar zuciya ta sauke tana karasa shafawa da sauri ta gama ta kira
sunan Iman sau uku ta d'aura towel d'inta ta fito.
A 'bangaren umma kuwa itama seda ta tabbatar kowa yayi bacci kan ta bud'e jakanta
ta d'auko layun ta fito, da sauri zahra dake safa da marwa ta 'buya bayan labule
sadap sadap ta wuce zuwa waje zahra na binta a baya har bayan windown Abba inda
wasu en flowers suke an zagaye da interlocks tonewa tayi sossai ta yi duk wani
abinda boka ya sata tana mikewa kenan taji wani abu ya tsikareta daga kanta zuwa
kafafunta kanta ta Sosa ta juya ta koma d'aki zahra dake la'be ta fiddo wayanta ta
kira Hafeez yana d'agawa tace "sameni bayan windown Abba" a hankali fitowa yayi ta
nuna mishi wurin tare da fad'amishi abinda umma tayi, kallon time yayi wuraren biyu
ya tabbatar baba fufore ya tashi sallah dukda yana jin ba daad'i kira a lokacin kar
ya d'aga mishi hankali amma ba yadda ze yi basu san wani irin mugun illah abinda ta
binnen nan ze musu ba.
Kiranshi yayi a ringing na biyu ya d'aga da sallama kan yace "hafeezu lafiya dae
ko?" Hafeez ya amsa sallaman kan ya mishi bayani abinda ke faruwa sede be
fad'amishi umma bace, salati baba yayi ya sallamar kan ya fad'a mishi wasu adu'o'i
yace ya dinga nanatawa har ya tone layan yana gama tunewa yayi fitsari kai kan ya
kone, nan take sukayi sallama Ai ko ya fiddo zahra ta koma ciki kawo ashana da
kerosine kan ta fito yayi fitsarin suka kone layun tas suka koma d'akunansu.
******
Asubar farko ta farfad'o daga wahalalliyar baccin da ya kwasheta tun cikin daren ba
karamar baqar wuya da azaba tasha hannun mutumin nata ba wadda shi ya tunkaretane
da duk wani karfinshi sbd sanin ita d'in ta sha aure ba ta'bawa ba yaci ace ta san
duk kalan mazan wadda alamarin da ya farun ya zo masa a asalin bazata sbd be zata
ba sam be ta'ba kawo haka a zuciyarshi game da ita ba.
Tunda ya samu kanshi yake aikin gadinta idanunshi a kanta yayin da hannayenshi suke
cikin nata, cike yake da sabuwar soyayya, tausayi, farin ciki da murnan babu wadda
ya ta'ba sanin masa mata, se yanzu ya tabbatar da Don shi kad'ai akayi NOOR IMAN
haka itama Don ita kad'ai aka halliceshi sbd zuciya da gangar jikinshi ita kad'ai
sukewa mahaukaci da fitananniyar soyayya.
🖤Gureenjo🖤
                🥀NOOR IMAN🥀
*Fatima Muhammad Gurin*
          *Gureenjo6763 on wattpad*
*051*
Ganin ta bud'e ido ne yasashi matsawa ganganta sossai yasa hannunshi a kan fuskanta
ya shafa cikin tausayawa yace "I'm so sorry hayatee, ki yafemin kinji?" Shiru ta
mishi se sabon hawaye, lumshe idanunshi yayi yanzu In akwai abinda yake tunanin
yafi komai yi mishi zafi a duniya shine hawayenta, musamman ma In shine sila, cikin
kasa da murya yace "nace I'm sorry kukan har yanzu be isa haka ba? Ko nayi miki
rauni ne?" Nan ma Shiru tayi se mikewan da tayi zaune tare da zame d'ayan hannunta
dake cikin nashi ta zura kafafunta kasa tare da mikewa tana d'aga kafa da sunan
takawa ta sake kara tana dukawa se ta rushe da kuka.
"Ya salaaam" ya furta a hankali kan ya mike ya d'auketa chak yayi toilet da ita
yana ajiyeta ta tubure mishi se ya fita zatayi abinda zatayi ba don ya so ba ya
fito ya kyaleta sede fa a bakin toilet d'in ya tsaya yana safa da marwa, ruwan me
d'an zafi sossai ta had'a ta shiga ciki da kyar da ihu da komai ba yadda ta iya ne
kawai ta san in batayiwa kanta hakan ba ba gata tayiwa kanta ba.
Sau kusan uku tanayi bayan wadda ya mata cikin dare da ko natsuwan sanin ya ruwan
yake batayi ba, bayan ta gama ta d'aura farin towel karami tasa wadda be kaishi ba
a kanta ta d'aure sbd gashinta dake a jike alwala tayi kan ta fara takowa cikin
taka tsantsan dukda yadda zafi ke ratsata har cikin kanta amma aikin d'auke d'auke
ba da ita ba idan bata warke ba har ya koma d'akin Hamna fah.
Tuna hamnan ma se taji wani azababben kishin da bata ta'ba ji ba a ranta se yanzu
da ta gama jin sirrin zuciyarshi da gangan jikinshi ta san menene akeyiwa kishi,
tana bud'e kofan ya dakata chak yana kallonta kauda kai tayi ta nufi kofa hannunta
ya rike yana cewa "Ina zakije?" Kallonshi tayi se ya bata tausayi gabad'aya yadda
take acting bayan tashinta ya sashi shiga wani yanayi da ya kasa 'boyuwa a
fuskanshi.
Cikin kasa da murya tace "room d'ina" ze yi magana ta zame hannunta taci gaba da
tafiyanta a hankali, ajiyar zuciya ya sauke bayan rufo kofanta ya shige toilet yayi
alwala ya fito ya fice masallaci, tana shiga d'akinta ta nemi riga dogo me hannun
vest ta saka dayake straight gown ne kuma bata saka komai jikinta ba yasa ya fiddo
da siffanta sossai hijab ta sanya har kasa ta tada raka'atainil fajr, seda taji an
tada sallah massallaci kan ta mike ta mika nata, tana idarwa ta zare hijab d'in
kwanciya take son yi sede kuma bazata iya wani bacci da jikakken kan nan nata ba
kujeran dressing mirror taja ta zauna ta bud'e a kasalance ta d'auko hand dryer ta
jona tare da kunnawa ta fara busar da kanta.
Tana farawa taji an turo kofa kallon hanyar kofan ta juya tayi don bazata iya gani
ta madubi ba In ba kusanta ya matso ba, had'a idanu sukayi ta kawar tana ci gaba da
abinda take, wurinta ya nufo ya sa hannu a kan nata yana kallon fuskanta ta madubi
sakin dryer d'in tayi ya amsa ya cigaba da mata dukda be ta'ba gwadawa ba sede yana
kallon yadda zahra ke yi wani sa'in In yana gida ta fito parlorn kasa yi sbd kawai
suyi hira.
Tsab ya busar mata dashi ya shafa mata mai se aukin kallo da yake binta dashi wadda
yake sata jin wani uncomfortable feelings, "ashe nayi babban laifi haka da ko
gaisuwa baza'a iya yi min ba? To gimbiya tuba wannan bawan Allahn yake Abdulraheem
be da masaniyar Saudah tashi ce shi kad'ai don shi kawai aka hallici budurcinta".
Ta tsinci magananshi kaman daga sama, da d'an hanzari ta zame ta duka kasa tana
taune baki tace "sorry Ina kwana?" Murmushi yayi duk ta koma wani iri d'agota yayi
ya sanyata jikinshi yace "Lafiya kalau ya jikin?" Tace "Alhamdulillah" kara shiga
jikinta yayi yace "I love yhu more than everything I can love In earth and I don
wanna spend a single day without yhu, ever I will protect you, respect yhu and
cherish you no matter what the situation is, you know I can't dare hurt you
knowingly, I'm sorry once again".
Wuraren karfe tara da rabi yaji ana buga kofa ba Don baccin ya isheshi ba se Don
kawai be son ta tashi baccin be isheta ba yasa ya mike da sauri, ya isa kofan ba
tare da ya sa jallabiyarshi ba, daga shi se three quarter sbd ya san be wuce hamna
ba, aiko ita d'in ce tsaye da waya a hannu kallo d'aya ta mishi ta kau da kai tana
ta'be baki tace "ummu ke son magana da kai" kar'ba yayi ya kara a kunne tare da
sallama tana amsawa bata jira cewarshi ba tace "yi maza kazo babana" Kit ta kashe
kallon wayan yayi ya kalli hamna hannunta ta mika mishi ya d'aura mata wayanta ba
tare da wani magana ya had'asu na gaisuwa a matsayinshi na mijin ta ba ta juya ta
tafi.
'Dakinshi ya shiga sharp sharp ya watsa ruwa ya shirya cikin kananan bakaken kaya
as usual ya zari car key ya fito rike da wayoyinshi da kuma agogonshi a hannu, seda
ya leka d'akin yaga har yanzu bacci take kan ya fito ya fice.
Da hanzari yayi parking yana fitowa sbd horn da ya dingayi ba'a bud'e ba kuma daga
inda yake yana jiyo hayaniya cikin gidan da sauri ya bud'e gidan ya shiga a
tsakiyar compound d'in yaga su mudi driver dasu baba me gadi da duka drivers d'in
gidan suna kokawa da wata ummu na tsaye gefe tana kuka Abba, Hafeez da zahra duk
sunyi cirko cirko, muguwar ajiyar zuciya ya sauke ganin ba ummu bace kuma ba zahra
bace yana d'aga kafa da niyyar karasawa ana bud'e get kusan a tare Kalthum da
rahama suka shigo kana ganinsu zaka san hankalinsu a tashe yake a tare suka karasa
dashi se lokacin ma ya gane umma ce ke ta fisge fisge daga ita se wata doguwar
rigan bacci, gira ya d'age a zuciyarshi yana cewa "ita kuma wannan lafiya?" Be san
a fili yayi maganan ba seda yaga ummu ta mishi dakuwa tana cewa "kanwar tawa ce
wannan d'in? Sannan Lafiya ce ze sa ka ganta haka a....." maganan ummu ne ya makale
ganin umma ta fisge tayi kanshi tana kurma ihun "kaine shege duk kai ne se na kashe
ka yau, me rabani da kai se mutuwa!!!!!! Ihhhhhhuuuu" da hanzari ummu ta riketa
aiko ta bankad'e ta saura kad'an ta kai kasa ba don Abdul yayi hanzarin tare ta ba
da tayi mummunan fad'uwa bayanshi ya bata aiko ta fara yakucinshi tana jan riganshi
Hafeez da su mudi ne suka kuma yin kanta suka kama ta, shikam hankalinshi na kan
mahaifiyarshi.
Maganan Abba ne ya katse tambayar da yake wa ummu "ummu bakiji ciwo ba?" Inda Abba
yace su shigar da ita d'akin da aka sauketa su d'aureta da gado, aiko suka shige da
ita da fad'a da komai hauka fah tuburun gashi bakinta se ashar yake kundumawa,
ajiyar zuciya duk suka sauke bayan an 'bace da ita, Abdul ne yace "wai me ya sameta
ne ummu?" Ummu cikin kuka tace "wallahi ban sani ba Abdulraheem kawai na shiga room
d'inta ganin bata fito ba tunda gari ya waye se gani nayi tana ta soshe soshe tana
ashariya tana ganina kaman an tsikareta ta kurma ihu tayo kaina da sauri na fito
ganin ba hankali ne kaman da ita ba, nan naga su Abbanku da Hafeez suka tareta amma
suma se ta fara ikirarin kashesu, zahra da ta fito ne ta fice ta nemo taimakon su
mudi, me ya sameta haka ni nyasu? Me zan cewa nenne" kawai ta rushe da wani kukan.
Abba yace "kukan nan ya tsaya haka zata samu lafiya in Shaa Allahu, muje ciki muji
shawaran da zamu tsayar" duk parlorn suka shige a lokacin har sun d'aureta sun fito
bayan sun sawa kofan key kururuwanta har inda suke tana furta se ta kashesu
dukkansu wallahi basu isa ba, duk Shiru sukayi shi Abdulraheem kam Allah ya gani
tunaninshi da hankalin shi gabad'aya yana kan matarshi.
Hafeez ne ya katse shirun da gyaran murya tiryan tiryan ya basu labarin abinda ya
faru jiya be gama saukewa ba ummu ta katseshi da "baka da hankali hafeez er uwar
tawa guda?? Yanzu a duniya ka rasa wacce zakayiwa sharri se pendonka? Kar ka manta
mu biyu fa kawai iyayenmu suka haifa?..." duk ta rud'e, kallon zahra tayi tace
"zahra ki fad'i tsakaninki da Allah zaki mutu ki kwanta kabarinki ke kad'ai da
halinki da gaske ne abinda hafeez yake cewa ko karya ne?" Duk ido suka zuba mata
cikin rawar murya da tausayin mahaifiyarsu tace "ummu kiyi hakuri gaskiyace ya
fad'a" kuka ta saka Abdul ya tashi ya koma gefenta aiko ta d'aura kanta kan
kafad'anshi, shi har ga Allah dama ya san zata rina ta riga ta sane mishi tun randa
ta fara taransshi da sukar Iman, duk Shiru sukayi se kukan ummu dake tashi Abba ne
yace "ba fa kukane solution to this problem ba Rashida, bari In kira baba fufore
muji abinda ze ce".
Kiranshi yayi suka gaisa kan ya tamabayeshi abinda hafeez ya fad'a ya kuwa tabbatar
gaskiyace anan ya fad'amishi wacce ta binne asirin gashi yau ta tashi da hauka,
salati yayi ya sallamar ya kara wani cikin alhini yace "kash kash me ya kaita? Me
ta nema ta rasa a duniyan nan me ya kaita kai kanta wuta tun a duniya? Hasbunallahu
wani'imal wakeel, Ahmad ku kawota yola mu had'u fada kuzo dukkanku sbd muji dalilin
asirin In ze yiwu ku taho yau" Abdulraheem be san sadda yayi magana ba yace "nide
bazan samu zuwa ba hayatee ba lafiya bazata iya yin tafiya ba" Dakuwa ummu ta mishi
tace "baba zamu taho In Shaa Allahu".
Sallama sukayi yana me ci gaba da alhinin wannan hali na umma, suna kashewa ummu ta
kalleshi tace "me ke damun daughter?" Kame kame ya fara yana Sosa keya karya ba
d'abiarshi ba ya ma rasa me ze ce chan yace "zazzabine ya kamata da asubar nan"
Anty rahama da kalthum murmushi suka sake suna fahimtar inda maganan ya dosa sede
suna kuma mamakin ya za'ayi tayi ciwo biyan ba buduruwa bace? Oho Allah masani.
Umma tace "ba yadda zamuyi hakanan zaka biya muku flight in yaso mu mu tafi da
umman taku a mota, ban yarda da cewa asiri Hajiya umma zata mana ba watakila ita ma
asirin aka mata ba cikin hankalinta take ba, Allah sarki er uwata" Abba yace
"bazamu tafi da ita a mota ba baze yiwu ba, tabi mota ita kad'ai ko ku had'ata da
d'iyarta bazata cika burinta na kashe min ku ba" ummu zatayi magana ya d'aga mata
hannu yace "this is my final decision so bana son wani objection, Abdul je kula da
Lafiyar matarka, hafeez tafi Airport muga ko za'a samu flight, rahama, kalthum kuje
gida ku shiryo ku kuma tambayi izinin mazajenku zan kirasu waya"
Yana kai nan yayi sama zuwa part d'inshi, duk mikewa sukayi suka tafi cika umarni,
shi Abdul har ga Allah be yi niyyar sake komawa yola ba gashi sati biyun da aka ba
mama a hospital jibi ze cika, tunanin kiran international office yake, kaman kuwa
yana ransu se ga kiransu d'agawa yayi suka gaisa cikin harshen turanci suka fad'a
mishi visa d'insu iman da baba da kuma mama are ready zasu iya tafiya any moment.
Godiya yayi ya kashe wayan ya kira hospital ya tabbatar musu ayi arranging mishi
komai zuwa farkon next week ze fita da ita, sallama sukayi ya shiga motanshi ya
tayar zuwa gidanshi yana isa Abba na kiranshi ya tabbatar mishi ya cewa Hamna ta
shirya maza ta je gidan yanzu da trolley d'inta, yana kuwa shiga d'akinta ya fara
shiga tsaye take tana taka rawa ta Kure Home theater, duk tunaninta komai ya
kammalu ne jin bata ji motsin iman ba tun da garin Allah ya waye.
"Ki shirya zaku wuce yola yanzu da umma" kallon mamaki ta mishi tace "yola?? Sbd
mene?" Yace "when you reach Abba's house you ask him this stupid question, he's
there waiting for you" yana kai nan ya juya ya fita, d'akin Iman ya shiga bata kan
gado se karan ruwa da yaji a bayi kenan wanka take, without second thought ya fad'a
toilet d'in ihu ta kwala tana juye juyen neman towel a rud'e.
🖤Gureenjo🖤
🥀NOOR IMAN🥀
*052*
Da hanzari ya d'auke towel d'in cikin sigan neman tsokana ya d'age hannu sama me
makon ta nemi wani abin se ta fara neman kwace towel d'in hadda tsallenta wadda
hakan ya bashi muguwar dariya aiko be rike ba ya fara yana kuma d'age towel d'in
sama yayin da ya kankance idanunshi yana morewa kallonta hakan, ganin dariyarshi da
kuma kallon da yake mata na kara karfi ne yasa ta hankalta da abinda take aikatawa
da azama ta shige bayanshi ta rungumeshi tare da 'boye fuskanta a cikin bayanshi
tasa hannu biyu ta zagayo cikin shi.
Murmushi ne ya subuce mata jin har yanzu dariyarshi yake, rana na farko kenan da
taga ya jima yana asalin dariya ba murmushi da ya saba ba wadda hakan itama ya sata
jin sanyi har cikin ranta, muryan shi ta tsinta yana cewa "oh hayatee come on zo ki
kwace kayanki mana ko kin hakura..." da wani irin murya yake maganan, cikin
shagwa'ba da bubbuga kafa kasa tace "uhm uhm zaujii bana so" murmushi yayi yace
"Toh zo kici gaba da wankanki" Tace "uhm uhm se ka fita plssss" yace "Toh sakeni In
fita" nan ma ta kuma cewa "uhm uhm sede fa ka juya mu tafi a haka kana fita In rufo
kofa" siririyar dariya ya saki yana cewa "Lallai ma hayatee toh me zaki 'boye min
me ban gani ba? Ko se na siffanta miki yadda duk wani hallita na jikin ki ya....."
katse shi tayi da wata shagwa'ba me kashe zuciya "uhm uhm ni Allah bana so zaujii
ko kayi shiru ko Inyi kuka" Murmushi ya saki yana kama baki yace "errrh Abdulraheem
kama bakinka kan Sarauniyarka ta fara rigima Don bazaka ji da daad'i ba".
Dariya tayi da ita d'in makale bayanshi ya juya suka fara tafiya dariya abinda ta
sa sun ya ke bashi, in ba gulma ba bayan ta gama tsalle yanzu a gabanshi kuma ta
koma bayanshi wai bata so ya ganta, suna isa kofa maimakon ya fita se yayi wuff ya
juyo ta wadda hakan ya sata tsala mishi kara ta kuma shigewa jikinshi dariya ya
kuma saki, ya rungume ta tare da kissing kumatunta yace "can't love you less
hayatee, My drama queen" sakinta yayi zata kuma makaleshi yace "kinga idanuna rufe
suke ba ganinki nake ba" kallon idanun tayi aiko rufe suke a ganinta fa kenan amma
shi fess yake ganinta, murgud'a mishi baki tayi tana d'an hararanshi seda ya fita
ta rufo kofa tukun yace "I see that!!! Kuma se kin gayamin da wa kike Allah ya fito
dake" baki ta kama tana zare idanu tana jinshi yana waka har ya fice.
Murmushi tayi tana sauke ajiyar zuciya kan ta koma ta karasa wankanta ta fito mai
ta shafa tayi feshe feshen turarukanta masu bala'in kamshi da sanyi atampha ta
d'auko zata saka se kuma ta fasa ta d'auko less riga da zani wadda d'inkin rigan ya
had'u karshe leshin ma kana gani zaka san ba karamin kud'i ke gareshi ba, gashi
purple and pink ba karamin amsanta yayi ba, haka nan ta tsinci kanta da shafa
powder ta saka kwalli tare da shafa pink wet lipstick a saman lips d'inta a hakan
ba karamin kyau tayi ba tayi wani fresh da ita kamshinta na amare ya bule ko Ina ya
had'u da na turaren da ta saka bayan ta gyara d'akin kan shiganta wanka, d'aurinta
ta kafa kan ta mike ta fito parlorn saman ba kowa se tvn dake kara.
Kitchen ta nufa Don wani irin yunwa ta tashi dashi don ma ta sha tea cikin dare
had'e da magani, freezer ta bud'e ta fiddo kaza ta ajiye tana kokarin fiddo kayan
miya ne taji an rungumeta ko bata juyo ba ta san waye daga kamshin sassanyar
turarenshi da take bala'in so, juyowa tayi tana murmushi ta sakala hannayenta bisa
bayan wuyanshi tare da karya kai tace "zaujiiii" ta wani ja sunan har cikin ranshi
yake jin amsa kuwwan muryanta me matukar kashe mishi jiki da bud'e mishi duk wata
kofa ta tsikar jikinshi In ta kirashi da zaujiin nan.
Wani irin mahaukacin kaunanta ke kara ninkuwa cikin rai da zuciyarshi, kasa amsa
mata yayi se gira da ya d'age mata yana me kallonta musamman pink lips d'inta,
motsa su tayi tana cewa "yunwa..... bari In girka mana abinda zamu ci" seda ya
tsotse lips d'innan da suka tsone mishi ido kan yace "ummu says karkiyi girki ki
shirya muje gidanta, and am sorry zan sake baki wahala Abba yace mu shirya zamu
tafi yola gabad'aya".
Kallonshi take cikin fara'a da sakin fuska tace "lafiya dae ce ko?" Yace "toh dae
da sauki, je ki shiryo kar yunwa ya illatamin ke In shiga uku" cikin murmushi ta
zame ta koma room d'inta lafaya ta d'auko purple yaji stones ta d'aura kan less
d'in ta d'auki wayanta a hannu ta fito, hannunsu cikin na juna har mota daga ka
gansu zaka san ba karamin soyayya suke wa juna ba gashi sunyi mugun matching dukda
ita chocolate color ce shi kuma asalin fari ke gareshi.
Shi har ya ma manta da wani matsalan umma hiransu suke cikin nishad'i har cikin
parlorn ummu inda suka tarar da en gidan zazzaune ummu de ta buga tagumi yayinda
zahra ke danna waya hafeez ma na kan doguwar kujera kwance ya lumshe ido, ummu na
ganinta ta mike tana cewa "daughter sannu ashe bakiji daad'i ba?" Zubewa kasa Iman
tayi tace "mun tashi lafiya ummu?" Ummu tace "Lafiya kalau ya jikin?" Tace "naji
sauki ummu Alhamdulillah" kallon zahra da ko d'ago kai batayi ba bare ta kalleta
tayi, Abdul na zama gefen ummu ya d'auki trow pillow ya wulla mata a zabure ta mike
tana zare ido se kuma tayi ihu cikin jin daad'i ta fad'a kan Iman wadda har seda
Abdul ya furta "hasbunallahu wani'imal wakeel" shi da ba shi aka fad'a kanshi ba
amma shine da jin zafin.
Cikin fad'a yace "zahra d'agata wani irin sakarci ne wannan? Bakiji nace bata da
lafiya ba?" Turo baki zahra tayi tare da sake Iman d'in da se murmushi kawai take
dukda taji d'an zafi sbd yadda duk jikinta har lokacin be bar ciwo ba, ummu tace
"Ai rashin hankalin zarah!! Allah ya shirya dae kawai azo ayi bukinkin ma ko zan
huta In ba Iskanci ba tun yaushe nake miki magana akan rashin lafiyar ummanku da
yadda babanku ya tsara tafiyan ba daad'i, kikayi kunnen uwar shegu dani ashe
AirPods kika saka kika maida ni mahaukaciya, ya miki kyau".
Mugun kallo Abdul ya mata se idanun ya sauka cikin nata, cikin wani irin sigar
tafiyar da hankali ta karkad'a mishi idanun, taune lips yayi yana jin sakonta har
kwakwalwan kanshi, ajiyar zuciya ya sauke yace "ummu kiyi hakuri kin san har yanzu
yaranta ke cike kanta, wayyo ummu am hungry, yunwa ze kasheni" kallon hafeez da ya
mike zaune yana kallonsu tayi ta banka mishi harara, kan ta dawo kan Abdul tace
"bana son gulma yaushe kuma ka fara kukan yunwa rayuwarka?" Bata jira amsanshi ba
ta d'aura da "bari inyiwa Abbanku magana ko don daughter" ta mike ta Haura, ajiyar
zuciya duk suka sauke hafeez yace "nide na shigesu kunga wani hararan da ummu ke
zuba min minti bayan minti?" Zarah tace "nide ko fa me zatayi sede tayi hakuri na
riga na tsani matar" Abdul ya wani 'bata fuska shima yace "geez hate her tooo"
dariya duk sukayi ganin yadda yayi kaman an ajiye mishi kashi gefenshi.
Shiru sukayi ganin ummu na saukowa batayiwa kowa magana ba se iman tace "daughter
tashi muje kici abinci kar muyi tafiya da yunwa" mikewa tayi tana tafiya a hankali
sbd kar kowa ya fuskanci halin da take ciki gangarowan Abba ne yasa hafeeez da
Zahra kwasa har suna rige rigan hawa dining sbd yanzu ummu bata isa ta korasu ba,
Abdul da Abba sukayi murmushi yayinda Suka samu harara daga ummu sede batace komai
ba. A natse sukaci abinci suka gama.
Abba yace "Toh kun san late flight muka samu Allah ma ya sa ba'a cika ba ku tashi
muyi harama" gangan Iman ya koma kasa kasa yace "ba abinda zaki d'auka?" Tace "eh
na bar wasu kayana chan dawowarmun nan" yace "baby kin tabbatar kin koshi? Ko In
rike miki takeaway?" Da sauri ta girgiza kai yace "you sure??" Ta gyad'a kai yace
"ya jikin kuma naga har yanzu kaman baki tafiya daidai" baki ta zumburo kallon su
Abba yayi ya girgiza kai kawai yana cewa "yarinya kinci sa'an su Abba zamu had'e
ne" gwalo ta mishi ya kuma gyad'a kai yana taune lips.
Zarah dake gefe se dariya take dukda ba jinsu take ba amma soyayyarsu na kasheta,
basu wani 'bata lokaci ba suka wuce Airport duk cikinsu ba wadda ya d'auki komai se
cards d'insu sbd duk suna da kaya chan kuma ba Lallai ne ma su jima ba, a Airport
suka had'u da su Anty rahama kowacce mijinta ya kawo ta, nan da nan suka d'aga
cikin mintuna suka isa yola motocin fada ne suka zo suka tare su da dogarai da
kuyangai, cikin convoy na burgewa suka isa fada sun samu baba fufore ya zo suna
tattaunawa da kannenshi a tsaitsaye suka mika gaisuwa kowa yayi part d'inshi akan
da yamma za'a zauna family meeting.
Suna shiga d'aki ya d'agata sama zuwa kan gado tare da fad'awa jikinta ba ta yadda
zata ji zafi ba yace "baby naga kin warke I need you" waro ido tayi tuna azabar
wuyan da tasha da sauri ta nemi mikewa ya kuma danneta ya sa hannu ya zare lafayan
jikinta kan ya samu fatan cikinta ya fara mata jakulkuli yana cewa "me ma kikamin
d'azu???? Yanzu wa na kama" ihu ta fara da dariya tana "wayyo wayyo ka bari dan
Allah, na tuba" be bari ba seda yaga tana dariya har da hawaye shima murmushi cike
a fuskanshi cikin wani irin salo me wahalar fassaruwa ya fara yawo da hannun nashi
a hankali zuwa lungu da sakon jikinta kan kace kobo zance ya chanza.
Bayan kammaluwan komai ya d'auketa suka shiga wanka tare, duk se murmushi suke
zubawa Don har ga Allah itama fah taji daad'i kasancewa dashi wani irin so da
kulawa ya nuna mata wadda bata tunanin wata mace ta san salon nashi bayan ita, a
wankan ma neman tsokana da ta'be ta'ben da ba'a aikeshi ba kawai yake suna fitowa
suka shirya shi ya wuce massallaci don sallar azahar da aka kira ita kuma tayi a
d'aki bayan ya dawo suka d'an kwanta bacci se la'asar suka tashi inda suka samu
abinci kala kala da aka shirya musu a kan dining sallah kawai sukayi suka fito suka
ci abincin.
Sunayi yana duba time sharp sharp sukayi suka fice babban parlorn me martaba, duk
family an taru waenda duk suke cikin gidan Kwai da kwarkwata sune kusan karshe
shiga, nenne Petel ce tsugune gefe tana aikin kuka yayinda kallon fuskan baba
galadima ze sa ka gane shima yana cikin alhini, umma ce d'aure a gefe se shure
shure take na se ta fice daga gidan tunda aka shigo da ita mijinta wato baban Hamna
na zaune yana karkad'a kafa gyaran murya me martaba yayi kowa ya natsu, yayi umarni
baba modibbo ya bud'e taro da adu'a nan ya zuba musu adu'o'i kan aka shafa.
Ya fara da introducing abinda ya kawosu na Ciwon hajja umma, Hamna ta zama abin
tausayi tayi tsuru tsuru a zabure take sbd saura kiris umma tayi ajalinta sau ba
adadi ana tsayuwa taimakonta duk ta firgice, sunanta mai martaba ya kira ta amsa a
tsorace yace "na san bazaku rasa aikata aikin sirri da mahaifiyarki ba kinga dae
abinda yake samunta bamu da tsimi bamu da dabara se abinda Allah yayi se kuma
abinda zaki fad'a mana na me kike tunani ya jawo hakan, sbd idan ba'a san
musabbabbin Ciwon ba ba ta yadda za'a taimaka mata".
Shiru tayi se kuka tsawa aka daka mata "natsu ki kula ki San wadda ke miki magana"
kukan ta karawa karfi tana zazzare idanu, kaman an mitsini umma ta wani ihu kan ta
fara fad'an abubuwan da ta aikata da irin tsanan da tayiwa ummu da irin tuggun da
ya dinga sakata da iyalanta da wuraren bokayen da tayi ta zuwa haka ta dinga zuba
kaman rediyo lalattacce.
Kukan da Iman ke yi ne ya isheshi wai ita sarkin tausayi dama ga ranshi na mugun
tafasa abubuwan da sukayi mishi tsakaninshi da ummunshi na dawo mishi Sannan
abubuwan da sukayi ta bashi na kazantan boka na sakashi jin wani mugun amai na taso
mishi, ga abinda tayi niyyan yiwa iman da Safen nan da hakan ya faru bata kira
sunan umma ba da shikenan yanzu yana nan hankalinshi In yayi dubu ya tashi, mikewa
yayi ya kama hannunta ta mike itama kallon hamna da ta tsaya kallonshi yayi yace
"na sauwake miki...." nenne tace "Abdulraheem" be kalleta ba ya karasa "igiyoyin
aurena dake kanki guda biyu" ihu ta kurma tayi kanshi kan ta karasa ya daka mata
tsawa azuciye "na rantse da sarkin dake busan numfashi yatsanki d'aya ya ta'ba
jikin rigata se nayi miki muguwar illaar da har abada bazaki manta dashi ba, Sannan
had'ani da mahaifiyata da kuka tayi a baya ban yafe ba Allah ya sakamin da mafi
azabar sakayya" ya fisge hannun iman sukayi waje ana kiranshi Ina yaki tsayuwa se
part d'insu.
Abubuwanshi kawai ya d'auka ya kuma janyo hannunta a parlorn ta tubure tare da cewa
"wai lafiyanka hamma? In fah rai ya 'baci hankali baya gushewa iyayenmu ne chan
suke kiranka....." katseta yayi da cewa "wuce mu tafi Saudah karki kara 'bata min
rai" Tace "amma..." tsawa ya daka mata "shut up!!!! In kema bazaki bini ba fine se
inyi tafiyata dama yanzu mata sun fara bani tsoro" ya juya ya fara tafiya a sanyaye
tabi bayanshi hawaye na zubo mata, mota ya shiga itama tazo ta shiga tunda suka
fara tafiya yake wayoyi kala kala duk cikin harshen turanci kuma a hanzarce har
suka isa Airport bazasu samu jirgin kano ba se na lagos ji yake In ya kwana yola
mutuwa ze yi haka ya biya musu suka wuce.
                   🖤Gureenjo🖤
🥀NOOR IMAN🥀
*053*
Tunda jirgin ya d'aga take zaune shiru gefenshi kanta kasa tana wasa da yatsun
hannunta se yaji wani iri, yaji rashin dacewar tsawan da ya mata ba ita bace da
laifi, hannunshi ya d'aura kan nata ta d'ago ta kalleshi idanunta na cika da hawaye
a hankali yace "sorry" juya kanta tayi yace "am so sorry na d'aga miki murya ba
tare da laifinki ba, I was angry and confused ne how on earth someone can be this
wicked and heartless?".
Had'iye hawayen tayi tace "ba komai, amma duk da haka ai er uwarkace Hamma be
kamata ka saketa ba, tunda har tayi nadama se mu ci gaba da zama da ita da zuciya
d'aya kaman da" hancinta ya dangwale yana murmushi yace "you are so simple hayatii,
wato ma ko kishi na bakyayi? To nayi fushi" yayi maganan yana juya mata keya
kwanciya tayi jikinshi tana murmushi tace "hmmm Hamma duk wadda ya gayamaka hakan
ya kamata yayi istigfari Don yayi babban karya ni kuwa nake kishinka" Da sauri ya
juyo yace "so na fah?" Dariya tayi tana gyara kwanciyanta tace "bacci" ta lumshe
ido murmushi yayi yana shafa fuskan ta yace "I love you" murmushi tayi.
Jirginsu na sauka suka fito suka tari taxi ya fad'i hotel d'in da za'a Kaisu suka
shige tana makale dashi a lokaci d'aya tana kallon garin bata ta'ba zaton lagos ya
had'u haka ba seda tazo kaman wani kasa ta fita, hotel d'in da yace a kaisun ma
abin kallo ne tana ta kalle kallenta har ya sallami me taxi d'in, hannunshi ya
sanya ya kama nata ta d'an kalleshi suka sakarwa juna murmushi.
Seda ya kama musu d'aki tukun suka kuma fitowa zuwa wani boutique dake gefen hotel
d'in trolley ya fara saya musu kan da kanshi ya d'auka mata wasu tsinannun kayan
bacci guda biyu da d'aukan ma seda ya bata kunya bare kuma ace ta saka a jikinta,
ko ya ce mata kala yaja hannunta zuwa wuraren Jeans, bombshell skinny jean ya
d'auka guda d'aya se ya d'auka mata long sleeve carpel outwear duster coat shima
d'aya se tops biyu se wani sakakken English gown longsleeve da scarfs guda biyu.
Daga nan sukayi wuraren kayan maza ya d'auki shirt and jean designer guda se vest
da boxers da turarenshi, seda ya dauki vest da boxers ya tuna be d'auker mata
inners and perfume ba, nuna mata perfumes d'in yayi yace "hayatii d'auki wad'anda
suka miki, one minute" ya juya ya fice wurin inners ya nufa ya d'auka mata bama ta
san ya san sizes d'inta ba se ganinshi da tayi dasu kunya kaman ta nitse hannu ya
sa ya kar'bi perfumes uku da ta d'auko yayi pecking kumatunta yace "thanks let's
go" yayi gaba tabi bayanshi tana kallon ingarman namiji da Allah ya had'ata dashi,
wani irin sonshi na kara huda zuciyarta ya iya kula da ita, ya san duk wani hanya
da ze bi ya sata farin ciki, zata iya buga kirji tace tafi kowacce mace sa'an miji.
Hure idanunta da yayi ne ya sata lumshe idanu kamshin strawberry ya buge hancinta,
cikin kasa da murya yace "ya de?? Ko kin fad'a ne?" Yana wani d'age mata gira, juya
idanunta tayi alamun ban fahimta ba tace "inaa na fad'an?" Seda ya d'an ciza lips
d'inshi tukun yace "kogin love" bata san sadda tayi dariya ba shima ya tayata tana
girgiza kai ta kama hanyar fita Don ganin shi da leda alamun yayi billing, bayanta
yabi da kallo kan a natse shima ya taka yabi bayanta.
Suna komawa hotel d'in ya musu order d'in abinci ya fad'a wanka bayan yayi yayi da
ita su shiga tare taki ta'be baki yayi yace "In ma bakiyi yanzu ba akwai anjima
hayatii" ya juya ya shige, zaune tayi tana ta gwada layin zahra yaki shiga, har ya
fito tana trying layin amma yaki tafiya haka ta hakura ta mike itama tayo wanka
tana fitowa ta samu har abincinsu ya karaso kan sallaya ta ganshi hakan ya sa tayi
saurin saka doguwar rigar nan sakakke tayi tarha da gyalenta wadda ya kasance babba
ta yafashi ne Bayan ta cire lafayan da tasa da safe.
Bayanshi ta tsaya suka rama sallahn da aka biyosu na magrib da isha bayan sun idar
ya mike ya d'auko abincin da kanshi ya kawo gabanta ya tsuguna ya sa mata a plate
shi kuwa coffee ya had'a ya koma bakin katon gadon d'akin ya zauna yana kunna
plasma tv da remote d'in da ya d'auka kan center table, news ya kai dayake karfe
tara yayi ya maida hankali yana kallo yana kur'ban tea, a lokaci d'aya kuma yana
satan kallonta ganin juya abincin kawai take, seda aka gama news tukun ya mike ya
koma kusa da ita ya duka yace "hayatee" kallonshi tayi yace "Lafiya kuwa? Me yasa
bakya cin abinci?" Tace "to kaima Ai baka ci ba" girgiza kai yayi yace "yanzu don
ban ci abinci ba kema ba zaki ci ba? Cikina a cike shine yasa kika ga banci ba, ban
saba cin abinci sau uku ba se biyu that's why".
Kai ta gyad'a kan ta kai Loma bakinta tana kallonshi shima kuma ita yake kallo seda
ta had'iye kan tace "Ina ta gwada layin zahra da ummu baya shiga ko lafiya?"
Shrugging kafad'unshi yayi kan ya mike fuskanshi na nuna alamun da gaske baya son
maganan da ze tuna mishi da hamna ko mahaifiyarta, kayan baccinshi ya saka ya haye
gado ya kwanta.
Seda ta gama cin abincin kan ta mike ta shige toilet tayo brush ta kuma fitowa tana
kallon gadon ganin kaman bacci ya d'aukeshi yasa ta nufi akwatin da ya saya d'azu
ta bud'e ta zaro rigunan baccin da ya sayon ta kafa mishi ido a zuciyarta se masifa
take ta inda zata fara saka waennan kayan duk basu da maraba da babu, kuma kallon
gadon tayi still yana nan yadda yake idanunshi a lumshe, mikewa tayi da guda d'aya
wadda take ganin d'an gara gara red ta shige toilet, sakawa tayi ta kalli kanta da
kyau a door mirror d'in toilet d'in a hankali tace "tabdijam Allah ya kyauta yanzu
fisabilillahi wani irin riga ne mutanen nan sukayi shi kuma yaje ya sayomin? In
fita hakannan mana kawai ba komai jikina, Ai duk d'aya da wannan kam" bakinta ta
turo gaba tana ci gaba da mitan inba asaran kud'i ba me anfanin wannan riga gashi
taga yafi dubu goma.
A haka ta fito sanin yayi bacci ta janyo kofan bayin ta nufi gado ta gefenshi taje
inda lamb switch yake da ma na d'akin gabad'aya da niyyan kashe bulb taje se idonta
ya kyalla kan kamilallen kyakyawan fuskanshi, har bata san ta kura mishi ido tana
kallo ba a hankali ta kai hannu ta shafa sajenshi da ya kwanta lub lub gwanin
sha'awa zuwa kan red lips d'inshi murmushi tayi a hankali tace "you have no idea
how much I love you da kake tambayana d'azu, zaujii am more than madly in love with
you, your handsome face, your attractive red lips, your dark brown eyelids, your
everything zaujii I love you more than anything in this world, more than my life I
can't imagine a life without you" ta duka ta kai mishi peck goshi tana mikewa se
charab suka had'a idanu.
Zaro nata tayi zata mike yasa hannu ya fisgota har seda ta fad'o kanshi ya sa hannu
ya kashe bulb d'in d'akin yana cewa "I love you more hayatee" be jira amsanta ba ya
had'e bakinsu ya fara nuna mata wani hot and dying love.
********
Bayan fitansu daga parlorn Shiru wurin yayi se kukan hamna tana maimaita "na tuba,
na tuba hamma wallahi Ina sonka fiye da kaina" mikewa ummu tayi da niyyan kirawoshi
mai martaba yace "koma zauna rashida" komawa tayi idanunta da har sun kumbura da
kuka na kara tsiyayar da hawaye Unstoppable bata ta'ba zaton haka daga er uwarta
guda da take dashi a duniya ba abin yayi mugun bugar mata zuciya sede ya ta iya?
Abinda ya faru ya riga ya faru gashi tana girban abinda ta shuka.
Bayan ta zauna me martaba yace "kin san Abdulraheem in ranshi ya 'baci ze iya
karasa d'ayan ma gabad'aya kowa ya huta, gwara mu barshi ya huce tukuna se ayi
maganan kubran". Ze kara wani maganan kenan sukaga fad'uwar baba galadima salati
aka d'auka kowa na shirin yin kanshi se nenne petel ma ta zube, a takaice wannan
masarauta sunga tashin hankali Don asibitin masarauta sun kasa yin komai kanshi
seda aka fita dashi FMC nan ma da kyar aka samu ya farfad'o da oxygen a kan
hancinshi neman ganin me martaba da modibbo yayi suna shiga ya kama hannunsu yace
"ku fad'amin yayyuna?? Ku fad'amin ta Ina na gaza da tarbiyar yarinyar nan?"
Modibbo yace "baka Gaza ta ko Ina ba Abdulraheem In kuwa ka Gaza d'in to muma da
iyayenmu mun gaza kenan" mai martaba ma yace "baka Gaza ba galadima ni shaida ne
kayi duk wani abinda ubangiji ya umurta akan renon 'ya'yanka".
Shakuwa yayi da kyar yace "Alhamdulillah Allah kayi shedana ya rabbi in na Gaza ba
tare da sanina ba ka yafemin" ci gaba da shakuwa yayi akai akai, modibbo da hawaye
ya gangaro mishi yace "ka dubi girman ubangiji ka yafemata Abdulraheem ko Allah ze
sa ta samu rahamanshi" girgiza kai yayi yana mai cigaba da shakuwa ganin ba zai iya
wani maganan ba yasa modibbo fara maimaita la'ilaha illallah Muhammadur rasulullah
salallahu alaihi wa sallam. Yana direwa baba galadima ya kar'ba dukkansu uku suka
dire a tare numfashinshi na d'aukewa chak.
Duk karfin zuciya irin na mai martaba se ga hawaye ya fara zuba mishi ba kakkautawa
dama tun chan yana da bala'e'en hawan jini gashi ta sanadiyar d'iyar da ya haifa ya
sota fiye da komai duniya ya kare duk wani hakkinta tayi sanadiyar fad'awarshi ga
ajalinshi ya koma hannun ubangijin talikai da bakin cikinta anya hajja umma anya
zata ga da kyau kuwa a rayuwarta na kabari zuwa har abada?.
(Ya ubangiji ka bamu daman kiyaye duk wani hakki na iyayenmu akanmu yasa mu cika da
imani😭).
Modibbo da mai martaba da kansu suka mishi wanka suka shiryashi aka ajiyeshi dole
yayi kwanan keso sbd daren da yayi, a daren In ka shiga masarautar modibbo Adama
zaka tabbatar da ba lafiya ba tsit ko Ina se karatun alqur'ani da ya karad'e
kafatanin masarautar, ummu wani irin kukan tashin hankali da bata ta'ba yi ba tayi
Abba karan kanshi seda ya girgiza da wannan mutuwa sbd yafi shakuwa da baba
galadima akan ainihin ubanshi, zahra, kalthum, hafeez da rahma ne suka sata a gaba
da lallashi cikin tashin hankali take girgiza musu kai bazasu gane bane ba Allah ya
kar'bi ran mahaifinta Sannan mahaifiyarta na kwance rai hannun Allah er uwarta guda
d'aya gata a haukace Ina ta san zata sa ranta taji sanyi?
A zuciye zahra ta mike ta nufi parlorn me martaba inda hajja umma ke kwance har
yanzu a wurin har yanzu a d'aure sede bakin ya mutu sbd yunwa da ya ci karfinta
Hamna na zaune gefenta se tambayar waye uban ta take yi tuntuni, zahra na isa tace
"bakar munafuka Allah ya isa tsakaninmu dake umma, Allah ya saka mana yayi miki
hukunci akan abinda kika aikata, Kin kashe mahaifinki ga mahaifiyarki chan rai
hannun Allah ki fara kuka tun yanzu umma sbd azabar Allah me tsanani ne akan
bayinsa mushirikai" tana kai nan ta juya ta fice.
Kallon Hamna umma tayi tace "kunceni zan gayamiki" cikin rashin tunani Hamna ta
kwance ta a d'ari ta fice da gudu duk yadda dogarai suka so tareta kasawa sukayi
har ta fice babban titin wajen masarautar a daidai nan wani katuwar tankin mai yayi
kanta ya murkushe har lahira ihu hamna da ta biyota tayi wadda seda ya karad'e
masarautar kan ta zube a nan kasa (Allah kai d'aya ne Allah, ya ubangiji kaine
Allah, ya Allah don girman zatinka ya rabbi ka sa mufi karfin zuciyoyinmu ka hanemu
da bin wani bayan kai, kayi mana tsari da bin wani katon d'an wuta kafiri (boka)
bayan kai, Allah mun gode maka zamu ci gaba da gode maka da duk wani ni'ima taka a
garemu, ya rabbi ka sa mu cika da imani. Ameen ya hayyu ya qayyum).
******
Kwana gabad'aya masarautan nan sukayi ido biyu da safe aka kai Baba galadima
makwancinshi na gaskiya, umma da ta gama zama kwalta aka d'an kalata abinda za'a
kalata aka sallaceta aka kai aka binne, ummu kam seda ta suma sau kusan hud'u kan
wayewar gari da adu'a da komai ta samu d'an natsuwa inda ta Matsa aka kaita wurin
hamna da nenne petel a tare take basu duk wani kulawa.
Ta 'bangaren su Hamna kuwa washegari da safe yayi booking ma mama da Baba flight
zasu tashi da yamma yayinda ya gama magana da sauban kan komai tun jiya har da
asibitin da zasu gani ya gama biyansu komai ta waya daga wannan asibitin zuwa
Airport se sun d'aga kan zasu fita daga hannunsu suna sauka kuma zasu shiga hannun
wanchan asibitin sannan akwai wani d'an gidanshi da ya tura daga london d'in zuwa
Miami akan suna sauka Kamawa Baba hotel kusa da asibitin ya tura mishi kud'i da
komai sbd ance bazasu samu jirgin Miami a yau ba se washegari da safe so be ma yi
booking d'in ba.
Bayan ya gama settling komai ya fara kokarin yi musu nasu booking d'in se kira ya
shigo wayan shi, wani cousin brother d'inshi ne d'an gidan baba yarima d'agawa yayi
suka gaisa kan yace "Abdulraheem kana Ina ne haka baka da labarin abinda yake
faruwa masarauta ne?" Yace "me ya faru?" Yace "Allah yayiwa me sunanka rasuwa jiya
bayan fitanka" a razane yace "innalillahi wainna ilaihi rajiun" ya kuma maimaitawa
kan ya yi baya ze fad'i da sauri Iman da fitowanta toilet yanzu kenan ta rikeshi ya
fad'a kan gado a razane take kiran sunanshi ganin da alamu ya fice hayyacinshi ya
razana ainun ne yasa ta fara kira mishi sunan Allah.
🖤Gureenjo🖤
🥀NOOR IMAN🥀
  *this page is dedicated to you my deedi just want you to know that I love you and
I will always be with you, take your side no matter what the situation is, you are
such a wonderful and strong woman, you should stick in that love🥰🥰, you are the
best sister ever and will always be*
*054*
A cikin kwanaki ukun nan masarautar modibbo Adama ya shiga wani irin yanayi da zasu
ce sun manta rabon da abu makamancin haka ya faru, yau akayi sadakar ukun baba
galadima da umma dukda dae dayawa har an fara mantawa da rasuwan biyu ne ba d'aya
ba, duk wadda ze yi gaisuwa sede yace "Allah yaji kan galadima ya mishi rahama" Tun
dawowan Abdul ya sa aka chanzawa nenne petel d'aki ya kuma janye ummu daga kan
Hamna ta koma kan mahaifiyarta shima kuma anan yake yini yana bata baki Don ya lura
tana cikin damuwa tun bayan da nenne petel ta farka sau d'aya mistakenly wata baiwa
ta kawo musu abinci ta mata gaisuwan baba jikin ya kuma rud'ewa tun jiya da safe
har yanzu bata farka ba.
Abdul yayi masifa kaman ze ari baki, me martaba da modibbo suna zuwa ko wani dare
su dubata yayinda su iman sede suzo fisha su fice, dukda yana bukatan lokaci da
matarshi amma ba yadda ya iya yanzu ummu tafi bukatarshi fiye da kowa se dare ya
tsala yake komawa part d'insu a hakan ya kuwa taimakawa ummun sossai.
Kaman yau bayan sun dawo daga asibitin bayan tayi magrib tana azkar taga kiran
ummanta na shigowa bata d'aga ba seda ta jira ya tsinke tukun ta kirata back tana
d'agawa tace "ummanah Ina kewarku" umma daga 'bangarenta tace "khaih mamana yanzu
sallaman taki kenan?" Baki ta tura gaba tace "ummah Assalamu alaikum" murmushi umma
tayi kan tace "wa'alaikissalam ya kuke? Ya ummunku da hakurin rashi?" Tace
"Alhamdulillah umma d'azu naji kunyi waya ko?" Umma tace "Ina ruwanki" kuma turo
baki gaba tayi cikin shagwa'ba tace "shikenan ummah babu, Ina su ikhram Ina missing
d'insu wallahi, d'azu hafsy take ce min ta shiga satin haihuwanta ko? Ni kam umma
kuna waya da maman Abulkhairi kuwa ya jima ina son tambaya se in sha'afa kullum In
na kira wayanta baya shiga".
Ajiyar zuciya umma ta sauke Tace "yanzu fisabilillahi wanne kike so in amsa miki?
Ni kiran da na miki daban kin wani cika ni da surutu" dariya tayi tace "Toh Ina ji
ummanah me ya faru?" Umma tace "ni kam ko kun ta'ba waya da babanku tunda suka
tafi? In na kira layinshi baya shiga" da mamaki tace "Ina suka tafi?" Umma tace "ee
bakuyi maganan da maigidanki bane? Na zata ya fad'amiki yasa bamuyi maganan ba ai
tun randa akayi rasuwan nan suka wuce da safe zuwa ganin likita da mamanku".
Shiru tayi tana mamaki a hankali tace "bamuyi maganan ba, In ya dawo In Shaa Allahu
zan mishi magana watakila suna waya" Umma tace "Toh shikenan, maman Abulkhairi sun
tafi kauyen su mijinta daga baucin ya d'an kwana biyu sbd rashin lafiyar surukarta,
su ikhram suna gaida ke" Tace "Ina amsawa ummahna itakuma surukarta Allah ya bata
lafiya, se da safe ummah" sukayi sallama ta kashe wayan.
Ta jima zaune tana tunani Allah sarki duk wani ups tackles na rayuwanshi baya
mantawa da ita da family d'inta wani irin sonshi take ji wadda ya wuce misali se
yanzu take gane ashe tun kallon farko da ta mishi ne sonshi ya mata mummunan kamu,
wani irin bukatan mijinta take abinda yayi mugun bata mamaki, a haka ta lalla'ba
tayi isha kan ta kwanta nan kan sallayan ta takure, ita ba bacci ba ita ba ido biyu
ba gashi ta kashe wuta, ta jima sossai kwance d'akin har bata san iya adadin
lokutan da ta d'auka ba se jin motsin kofa tayi alamun za'a shigo bata damu ba
sanin ba me shigowa se shi tana nan kwance bata motsa ba har aka shigo cikin d'akin
tana de kallon inuwan mutum tsaye yana dube dube, murmushi tayi taki magana kaman
kuwa ya san itace nan yayi wurin sallayan sede tun daga tafiyan ta fara kokonton
anya wannan shine? Don tafiyanshi ba haka yake ba, bata gama tunani ba taji ana
shafata kamshin ba namijinta bane da hanzari ta mike tana buge hannun tace
"wayene?" Muryanta na rawa.
Danneta yayi niyyan yi se tayi saurin mikewa tsaye tana lalu'ban inda hasken d'akin
yake amma kan taji har ta kunna ya kama hannayenta ya matse ihu ta kwala cikin
neman agaji tayi karfin halin saka duk karfinta ta bangaje shi tayi kofa da gudu
kan ta isa ya sa mata kafa cikin mugunta se gata a kasa tayi mummunan buguwa ihu
tayi tana ambaton sunan Allah cikin rauni Don ta bugu da tiles d'in sossai.
Danneta yazo yayi a wurin yana shirin shiga gonan da ba nashi ba, da karfi tayi ihu
tana kwala kiran sunanshi "Abdulraheeeeem" kaman kuwa walkiya bulb d'in d'akin ya
kunnu haske ya gauraye d'akin da hanzari ta d'ago Ai kuwa ta Ganshi tsaye ya kura
musu ido yana kallo idanunshi sun wani rine sunyi ja jijiyoyin jikinshi babu wadda
be tashi ba.
Wani irin karfi ne yazo mata lokaci d'aya ta bangajeshi ta mike da gudu tayi wurin
mijinta hijab d'in jikinta da ya rabe biyu ya fad'i kasa daga ita se bakar doguwar
riganta me dogon hannu, hannunshi ya bud'e mata ta fad'a tare da kankameshi kaman
irin jariri ya firgita sossai da sosssi d'innan ta fashe da wani irin kuka a
razane.
Lumshe idanunshi yayi yana jin tafasar zuciyarshi na karuwa sbd sautin kukanta,
jajayen idanunshi ya bud'e akan wadda ya shigo mishi kan mata yayi, gayen na duke a
kasa yana aikin zazzare ido yana neman ta inda ze gudu sede babu tunda tsakiyar
kofan Abdulraheem ke tsaye kallon da yake aika mishi ma kad'ai ya isa ya kasheshi,
da gangan ya matsa gefe Don yaga irin livern da yaron ke dashi aiko ya taso da gudu
ze fice, wani muguwar tad'iya da Abdulraheem yayi mishi seda yayi tumble sau biyu
kan ya fad'a da kai kan tile se ga jini, sakinta yayi yayi kan yaron ya hau duka
kaman an aikoshi seda Iman taga ze yi kisa kan ta dafa kafad'anshi cikin kuka tace
"hamma please ya isa haka" lumshe idanunshi yayi kan yace cikin wani irin murya
"sanya hijab kizo" da sauri ta d'auko wani khimar d'in ta sanya ta biyoshi wani
irin rikon mugunta yayiwa hannun yaron kan ya fara janshi duk jikinsu jini yaron ya
jikkata ainun.
Tana biye dasu a baya suka d'inga ratsa mutane da bayi da dogarai har cikin parlorn
mai martaba yana janye dashi, wani irin wurgi da yayi dashi zuwa jikin gini seda
manyan wurin suka mike banda me martaba, modibbo ne ya fara cewa "Lafiya
Abdulraheem me ke faruwa?" Se wani irin huci yake yana jin ko kwatan 'bacin ranshi
be sauka ba sbd d'an wannan dukan, baba yarima ne ya kuma cewa "Abdulraheem lafiya
me ya maka haka?" Nan ma Shiru yayi se huci kaman wani kumurcin maciji ran maza ya
'baci.
Abbanshi ne yace "wai ba magana ake maka ba?" Yana kallon me martaba yace "shigarwa
matata yayi a cikin masarautar nan ba waje ba" salati duk en wurin suka d'auka
harda me martaba a cikin gidanshi? Matar jikanshi? Tabb Lallai wadda ya aikoshi
dashi kanshi basu nemi zaman lafiya ba, kallon yaron yayi kan ya kalli sarkin
dogarai da mutanenshi dake tsaye, sun san abinda yake nufi dukda be yi magana ba,
bulala suka fara zafga mishi suna tambayar "wa ya aiko ka??" Basa jira yayi ko
kyakyawan numfashi zasu kara lafta mishi seda ya kuma yin tilis kan ya bud'i baki
da kyar yace "sarauniya Mama" Shiru parlorn yayi ran Abdulraheem na kara 'baci ji
yake kaman yayi tsuntsu ya ganshi gaban mama yaji dalilin da yasa ta nemi tozarta
mishi iyali.
Bada umarni me martaba yayi kan a kira meeting d'in gaggawa duk wani jininsu dake
cikin fadan su hallaro, nan take aka fara shela da buga kararrawa cikin mintuna
kad'an aka fara shigowa a tsaye yake duk wadda ya shigo sede ya zagayeshi ya wuce
yayinda ita kuma iman ta tsuguna gaba kad'an dashi kanta kasa seda parlorn ya cika
makil har umma kan me martaba yayi gyaran murya yace "Hauwa kin gane wanchan? Kin
san bana son karya da me yinta" kallon saurayin tayi tana zaro ido tace "a'ah ranka
shi dade, shi yace ya sanni ne?" 'Diyarta karama fatima wacce batayi aure ba har
yanzu amma zata girmi Iman tayi saurin cewa "Abba na sanshi kuma na san itama ta
sanshi Abba sunanshi Ishaq hayanshi tayi yayi blackmailing Matar Abdulraheem samun
ya saketa kaman yadda ya saki hamna se ta chusa mishi Aina'un Anty zulfa'u" kallon
mahaifiyarta tayi tace "dama na gayamiki bazan rufa miki asiri ba muddin akan cutar
da wani d'an uwana ne" zuru zuru tayi ta rasa abin fad'a abin ya zo mata bazata
bata ta'ba tunanin fatima zata tona mata asiri ba, dukda tsanan bakin halinta da
tayi.
Shiru parlorn yayi modibbo ne ya katse shirun da cewa "yanzu fisabilillahi abinda
ya faru da hajja umma be isheki ishara ba? Abinda ya faru be sa kin tuba kin zubar
da makaman yakinki kan ahalin nenne ba?" Wato nenne manga, mai martaba yace
"kyaleta modibbo tunda bazata shiryu Don Allah ba zata shiryu Don wuya, sarkin
dogarai na bada umarnin d'aure yaron nan da giyar kud'i kad'an ya d'ibeshi har yayi
gigin aikata 'barna d'aurin rai da rai da azaba me tsanani, Sannan na yankewa duk
wani jinin Hauwa'u gadon wannan kujeran mulkin nawa ko da ita da 'ya'yanta ne suka
saura daga jinina, hakanan na cireta daga cikin jerin sarauniya na wannan karnin ta
koma kaman kowa a fadan nan, zata koma karshen ginin masarauta da tafi tsana akan
komai a cikin gidan nan da rayuwa ita kad'ai ba baiwa bare kuyanga hakanan fatima
zata koma zama da d'aya mahaifiyarta"
Kau da kai yayi daga kallon da nenne ke mishi na neman afuwa ta kallo kawai ya gane
ya kau da kai ne sbd ya san bazata iya magana nan ba sbd sanin girman sarauta da
izzar basarake da kuma jinin su dake yawo jikinta, nan take aka aiwatar da abinda
yace Mama na kuka na komai aka tusa ta gaba, yace "nayi hakan ne don ya zama ishara
akan duk me shirin cutar da d'an uwanshi yanzu da shi Abdulraheem be gane ba ze iya
sawwakewa matarshi cikin fushi Daga nan duk wani matsala zata iya faruwa, Sannan
nayi hakan sbd na gaji da halin da hauwa ke nunawa sauran 'ya'yan wannan masarauta
tun kan su mallaki hankalin kansu kawo yanzu, kowa ze iya tafiya" mikewa ummu tayi
ta kama hannun iman suka fice bata kai ga kaiwa kofa ba malabo ya rike hannunta
yace.
"Ummu kiyimin aikin gafara bazan iya kara kwana cikin masarautan nan ba kiyi mini
izinin tafiya don Allah" kallonshi tayi zatayi magana suka had'a idanu da Abba ya
girgiza mata kai se ta sake mishi hannun mata tace "shikenan Allah ya kareku a duk
inda zakuje se munyi magana" mai martaba yace "ba de zuciya akayi da masarautarmu
ba ko?" Modibbo yace "aiko dae kar ace baza'a kara shigowa ba don naga alamun hakan
wannan da kishi kaman mazan larabawa" dariya akayi da kyar ya iya yin murmushi yace
"haba na isa?? Ban isa ba ai mai martaba In Shaa Allahu muna dirowa Nigeria nan
zamu fara sauka" ya kalli modibbo yace "malam ai a wurinka muka gado cikin wannan
tauhidin da ka saba koya mana dolen dole" dariya duk akayi ya juya ya fice.
Part d'insu suka fara yi wannan akwatin da ya saya musu a lagos wadda ko bud'ewa
basu kara yi ba tun barowansu ya d'auka da wasu important abubuwanshi ya d'auka
mata wayanta suka fito driver ya d'auka aka kaisu Greenland hotel suka kama room
suka shiga ya rungumeta ya sauke ajiyar zuciya itama rungumeshi tayi cikin sanyin
murya tace "thank you" yace "for??" Tace "na zuwa kan lokaci a sadda na bukace ka"
kuma rumgumeta yayi yace "I'm sorry" Tace "for?" Yace "for leaving you all alone
bayan na san kema kina bukatata" Tace "I love you zaujii, I truly do, I was really
afraid that shikenan rabuwanmu tazo da Allah ya bashi sa'ar shiga gonanka" yace "I
love you too hayatii, god forbid da ko mazan duniya ne suka shiga gonata matukar
bada son ranki bane babu abinda ze sa In rabu dake" had'e bakinsu tayi yayin da ya
d'agata chak zuwa kan gado ya mata runfa da faffad'ar kirjinshi.
A daren ya musu booking flight washegari da safe bayan sun karya sunyi wanka ta
saka waenchan kayan da ya saya mata tayi matukar kyau da shigan shima se yabawa
yake ta lura yana matukar son d'abi'ar turawa inba haka ba Ina ita Ina saka wani
coat da jean se d'an scarf da gashin kanta kawai ya rufe, drivern masarauta ya kira
aka kaisu Airport ba 'bata lokaci jirginsu ya d'aga se Miami.
Suna sauka wannan yaron nashi da ya turo Patrick ya zo ya d'aukesu zuwa suit da ya
kama musu inda suke sama da Baba seda suka kuma hutawa kan suka fito zuwa asibitin
nan suka samu Baba sossai Iman tayi murnan ganinshi haka shima ya kuma yi mishi
gaisuwa Don suna waya kullum da wayan Patrick ya san da rasuwan, shiga wurin doctor
dake in-charge yayi Don jin me suka binciko kan Mama, kai tsaye ya fad'a mishi
abinda ke damunta wato.............
🖤Gureenjo🖤
🥀NOOR IMAN🥀
*055*
“Tumors as you can see here” ya mika mishi wani X-ray “tumors are masses of
abnormal cells in the brain it can be on spinal cord, that have grown out of
control, it can be between benign (non-cancerous) or maligent tumors (cancer) the
main concern about it is:- 1- how fast they grow
2- how readily they spread through the rest of the brain
3- where they are located
4- if they can be removed or destroy and not come back”
Katseshi Iman tayi da cewa “hope hers is non-cancerous” a rud’e cikin taradaddin
amsan da baturen likitan ze bata, murmushi ya mata kan yace “yes hers can be easily
destroy, ur mom will gonna be fine soon don’t worry” kallon Abdul yayi kan yace
“she has small amount of diabetics that’s hyperglycemia, the diabetics met with the
tumors and all are dangerous diseases that lead to coma that’s why it would be
difficult to many doctors to figure out the exact problem” ajiyar zuciya ya sauke
yana kallon iman da ta dafe kanta kallon doctorn ya kuma yi yace “please do
anything that can make her better from those diseases especially the brain tumor”
Kai doctorn ya gyad’a cike da gamsuwa yayi en rubuce rubucenshi ya mika musu wasu
papers ganin akwai sa hannu ya mikawa baba da yaji dukkan bayanan da akayi hannu ya
saka aka ba doctorn ya kuma basu wani abubuwan da zasu bukata daga pharmacy bills
d’in na kasa, ba tare da Malabo ya yarda bappa ya gani ba ya mike yana mikawa
doctorn hannu suka fice.
Duk yadda baba ya so ya biya ko kad’an daga cikin abubuwan da yake kashewa ne
malabo yaki, haka ya biya komai da komai ba ‘bata lokaci aka fara treating mama,
satinsu biyu a miami seda ya tabbatar an gama komai saura jiran farkawan Mama tukun
suka fara shirin wucewa, a sati biyun nan ba wurin shakatawan da basuje ba na cikin
garin miami, Florida state of united state, daga kan Miami Beach, Art deco historic
district, south beach, vizcaya museum and gardens, Everglades national park.
Yininsu chur a bayside market place in da ya kasance large outdoor style mall dake
cikin ruwa with more than 150 shops and restaurants sunyi sayayya har na hauka duk
wani shiga na turawa wadda baze bayyana jiki ba seda ya saya mata da mahaukatan
nighties a sati biyun nan wani irin mahaukacin soyayya sukayi da ya zauna daram a
cikin zukatansu so, shakuwa, kulawa, zallar ruwan kauna shi suka nunawa junansu.
Restaurant yafi kala goma suka je daban daban a areas daban daban wasu a cikin ruwa
kai sune har night club a cikin boat sukayi tasha mamaki taga ikon Allah bata ta’ba
zaton akwai irin wuraren nan a duniya ba, sune har bay-front park suka ga su light
tower da dare, karshen inda suka je shine zoo Miami inda ya ke d’auke da over 3,000
wild animals itade ba dabban ubangiji da bata gani ba, har getto area d’insu da
yake d’auke da wynwood walls street art suka zaga inda taga mutane masu ban mamaki
mata da maza kowa da zane daga kai har kafa na tattoo.
Anan ta samo wani saffron grills inda suke Gasa duk wani abun ruwa wayyo Ai kullum
se sunyi ordern wani abin na ruwa taci, dukda sauran abincinsu ma duk ba laifi taci
a heshi and sushi Asian cuisine, santorini, havana vieja, numfashinta seda ya kusa
d’aukewa ganinta a freedom tower gashi cikin dare wayyo bazata iya fasalta yadda
wurin nan yake ba se wadda yaje, Tabbas ta yarda da inkiyoyin miami da ake ce mishi
“magic city”, “gateway to the Americans”, and “capital of Latin American” Don har
d’an yaren Latin d’in ta koya.
Ya jata har cikin university d’insu inda yayi visiting wani friend d’inshi, in
takaice muku Noor Iman kam ta zama wata baturiya cikin sati biyun nan tayi fresh ta
kara kyau da murjewa wasu wuraren suna d’an zuwa da baba kaman day trip key west
with boat sunje dashi wasu wuraren kuwa kud’i kawai yake bayarwa d’an gidanshin nan
su fice da baba yaje duk inda yake so.
Tun yanawa iman mitan dressing da ta koma yi dukda baya bayyana tsiraici har ya
gaji ya lura yanzu duk abinda mijinta ke so shi takeyi se suyi kwana uku hud’u basu
kwana hotel da suka kama ba sede suyi waya da baba, dasu ummu, da zahra kam kullum
se sunyi waya har an saka ranar bukinta da Muhammad wadda basu da tabbacin zasu
samu zuwa, randa suka cika sati biyu cib ya saya musu ticket to London da train
dukda rabin tafiyar a jirgin ruwa ne rabi a train.
Cikin kewa sukayi sallama da baba inda suka bar mishi patrick da yanzu sun saba
sossai da baban tun baya gane turancinshi har ya fara ganewa sossai, kusan trolley
hud’u sukayi su biyu kuma manya ba kanana tsabar sayayyan da sukayi plus wadda suka
zo dashi biyar, kwanansu biyu a hanya dukda kwata kwata 14 hours ne from miami city
to London amma sun kwana a ruwa inda d’ayan kwanan sukayishi a wani neighborhood to
London.
In ka gansu gwanin sha’awa yadda suke manne da juna suna shan love a inda ba sa
idanawa, abinci ma rabon da d’aya a cikinsu ya ciyar da kanshi sun manta ciyar da
juna sukeyi ko ma menene, da rana suka isa London inda aka zo da wasu zafafan
motoci aka d’aukesu se madaidaicin kyakyawan gidanshi dake nan cikin heart of
London kusa da company d’inshi, fasalta gidan ma aiki ne tsabar kyau da
tsaruwarshi.
A d’aki guda suka sauke kayayyakinsu wadda shine ya nuna be son ra’ayin raba d’aki
a tare sukayi wanka suka shirya cikin normal house wear na shan iska itakam ma
riganta da kad’an ya wuce bombom d’inta gashi me hannun vest peach color, fitowa
sukayi zuwa dining area inda aka jera musu dishes kusan kala shidda a kan kafanshi
ta zauna yayi serving d’insu a plate guda yasa one spoon ta bashi ya bata In ta
‘bata mishi lips ta lashe da tongue d’inta.
Duk yadda zan fasalta muku irin soyayyar su baza ku fahimta ba ku kiyasta kawai a
ranku, ranan yini sukayi bacci da hutawa, se washegari ya fita da ita suka fara
zagaya London kuma bayan ya kaita taga company d’inshi nan ta sha ruwan mamaki
ganin yadda ya san mutane dayawa a London duk wadda ya ganshi ze tsaya su gaisa
yayi musu presenting matarshi, bata tsorata ba seda taga sun shiga kings collage
inda anan ya kuma neman aiki dayake da yayi musu visiting lecturing yadda taga en
mata turawa suke harinshi se abin ya firgitata gasu zafafa masu class, a zuciyarta
take raya yadda zata ci uban duk wacce ta shigar mata hanci akan mijinta dukda
admission ya nemar mata dayake ana ji dashi kuma sananne ne nan da nan suka
tabbatar mishi da ta fara shiri kawai kuma exact course da ta bari shi zatayi Wato
BSC Ed Biology, amma rannan a had’e ta cika tayi tab saura kad’an ta fashe.
Yana driving yana satan kallonta hannunshi da ya sa cikin nata yana murzawa ta cire
ta juya ta cigaba da kallon window, cikin sanyin murya yace “sarauniyata laifin me
na aikata a gareki? Tuba nake tun banji laifi na ba, a fad’amin samun In hukunta
kaina tun kan fushinki ya gama illatani” tura baki gaba tayi cikin kunkuni tace
“haka zaka ce Ai bayan ka gama zagayawa kaga en matanka ka nuna musu ka dawo” yana
shiga manyan offices da anan ne ze kar’ba mata licenses na zama a kasar har iya
yadda ta so yace “en matana kuma hayatee?” Shiru tayi ajiyar zuciya ya sauke bayan
yayi parking ya janyota jikinshi cikin raunin murya yace “ashe zuciyarki bata gama
tabbatar miki da cewa ke kad’aice a cikin birnin Abdulraheem ba? Ashe Abdulraheem
yayi gazawar da har Saudah take ganin kaman ze iya kula wasu en matan bayan ita? Me
zanyi Saudah me kike bukatar inyi daze tabbatar miki da cewa ban ta’ba son wata
hallitar Allah ta jinsin mace ba bayan mahaifiyata se ke? Ina miki son da ban san
adadinshi ba hayatee karki hukunta ni da laifin kallo da shishigemin da en matan
kasan nan zasu min tunda ba ni ke musu ba”
Ajiyar zuciya ya sauke tare da hura mata iska cikin kunneta cikin kuma kasa da
murya yace “hayateee kin kuwa san shekaru na nawa a kasarnan?” Be kula amsanta ba
yace “tun da chan a lokacin da ban samu hasken zuciyata ba ban kula su ba seda na
samu duniyata?” Ze kuma magana ta juyo fuskanta ta had’e bakinsu seda ta mishi wani
fitinannen tongue to tongue kiss kan tace cikin kasa da murya “A gafartamin zaujii,
tsoro nake ina tsoron kar watarana in Gaza ta wani fannin suyi nasaran d’aukemin
kai, god forbid Allah ya sani I can’t imagine a life without you, kaine farin
cikina zaujii kaine haskena, kaine duniyata, kaine murad’in raina, kaine rayuwana
kaine numfashina Ina maka son da bana yiwa raina, kain.....”
Be jira ta karasa ba Don kalamanta saura kad’an su maidashi crazy ya had’e lips
d’insu tare da rungumeta kaman zasu had’iye juna, da kyar suka tsayar da abinda
suka tsokano suka shiga sukayi abinda ya kawosu kan suka koma gida suka d’aura daga
inda suka tsaya, satinsu guda ta samu admission inda da kanshi ya mata komai da
komai sati na zagayowa suka fara fita aiki.
Rayuwa sukeyi cike da ‘yanci da kulawa zata ce tunda tasa kafa ta bar Nigeria ita
de bata ta’ba d’aura wani abu akan gas da sunan girki ba, ko cooku ya dafa ko su ci
a waje In bata da lectures haka zata zauna office d’ishi muddin yana cikin
makaranta ba company ba komai tare sukeyi sun zama jini d’aya kowa ya san irin
soyayyar da suke yiwa juna.
Kwance take rub da ciki tana waya da zahra dake mitan ita ta gaji suyi su dawo
Allah bazata yarda ayi aurenta basa nan ba, kallonshi tayi yana tsaye gabanta rike
da kugu daga shi se boxers jira yake tazo taje ta taje mishi suma Don ba abinda
basa yiwa junansu har shaving, cewa tayi “oh sweetheart Hakuri zakiyi ba yadda muka
iya don ba cikin hutu za’ayi bukinki ba and kinga hammanki yace bazamu koma Nigeria
ba se after five years and he mean it”
Zahra tace “Ai Hamma!! bakiga fad’an da Abba yayi ba da ya samu labarin ajiye
ayyukanshi na Nigeria da yayi amma gayennan ko a jikinshi, ya tsallaka ya barmu da
wahala don tunda nenne ta samu sauki muka tashi dawowa ummu ta d’auko mana hamnan
nan bakiga yadda take kula da ita ba kaman basu mata laifin komai ba” cikin
tausayawa tace “Eyyah Anty Hamna zahra ya kamata ki taya ummu kulawa da ita na san
tana cikin mawuyacin hali” zahra tace “ni dae har tsoro take ban bata cika magana
ba se ido duk abinda zaki mata sede ta biki da ido se aukin ibadah da yanzu naga ta
dage dashi kullum cikin kuka” Iman tace “Allah sarki ya kamata ta dawo nan mu zauna
tare” Da sauri zahra tace “wani irin zama tare Saudah?” Yaune ta farajin zahra ta
kirata da saudah a rud’e kuma a firgice dariya tayi kan Tace “ta koma d’akinta mana
bari zanyiwa ummu magana”.
Katse wayan taga hannunshi yayi da sauri ta kawar da kanta daga fuskanshi ganin
yadda ya had’e rai kaman be ta’ba dariya ba cikin kausasa murya yace “kull karki
soma na gayamiki, karkisa inyi rantsuwa akan abinda ba zan ta’ba yin kaffara ba ki
fita sabgar abinda ban sa ki ba banaso” yana kai nan ya juya ya shige toilet ajiyar
zuciya ta sauke, ko me ze yi sede yayi bazata zama muguwa ba, dole Hamna ta dawo
d’akinta da taimakonta, ta san baze ta’ba iya ‘bata yini yana fushi da ita ba.
Ummanta ta kira Bayan sun gaisa take neman shawaranta akan abinda ta sa gaba sossai
umma ta bata goyon baya ta kuma cikata da adu’a cike da karfin gwiwa ta kira baba
suka gaisa ya bawa mama da yanzu taji sauki sossai sallama kawai suke jira wadda
shima suna zaton nan da sati, yadda ta nemi shawaran umma haka ta nemi na Mama
itama sossai ta bata goyon baya suna waya da maman ya fito ya shirya cikin suit
navy blue masu bala’in kyau da tsada yayi wanka da turare fuskan nan a murtuke da
sauri tayi sallama da mama ganin ya nufi kofa.
Ta sha gabanshi tare da langwa’bar da kai cikin kashe murya tace “zaujiii ka
rufamin asiri kar ka fita kana mai fushi da ni, na tuba” se hawaye sharr abunda ta
san baze ta’ba iya Jura ba kenan, ajiyar zuciya ya sauke kan yace “Hayatii Ai kece”
rungumeshi tayi cikin shesheka tace “don nayi abinda yake daidai? Hamna fah ba ita
tayi maka laifi ba zugawar mahaifiyarta ne da yanzu bata duniyar ma kaga kenan
duniya ba bakin komai yake ba, kuma ba matabbata bane”
Zameta yayi yace “Hayatee bazan iya son wata a yanzu bayan ke ba bazan iya ba,
karkisa na zama cikin masu tashi da shanyayyen ‘barin jiki a ranar gobe kiyama sbd
rashin adalci tsakanin mata na biyu karkiyi please” yana kai nan yayi pecking
d’inta a goshi ya zagayeta ya fice ajiyar zuciya ta sauke hawaye na silalo mata,
Allah ya gani in tace maganan nan kad’ai da yanzu akeyi baya tunzura mata rai da
kishi tayi karya amma ya zatayi? Be dace ba sam ace be mayar da Hamna ba tana er
uwarshi, ko don farin cikin ummu zatayi hakan bare kuma akwai lada na musamman da
ze jiraye ta ranar gobe kiyama.
Lalu’ban numbern Abba tayi ta kira ringing biyu ya d’aga cikin ladabi tace “Abba
barka da rana” yace “yauwa mamana ya kuke ya bakunta?” Tace “Lafiya kalau Abba ya
aiki?” Yace “Alhamdulillah” cikin sanyin murya tace “Abba alfarma nake nema” yace
“tooh Alfarmar mece? Allah ya sa be fi karfina ba” ajiyar zuciya ta sauke muryanta
na rawa tace “Abba Auren Hamma Abdulraheem da Anty Hamna nake so a mayar ba tare da
saninshi ba” Shiru yayi cike da al’ajabi seda ya kwashe mintuna kan yace “me yasa
kike so Hamna ta koma d’akinta saudah?”.
A hankali tace “Abba da hamma da Anty Hamna duk d’aya suke a wurinku na san kuma
baku so sakin da ya mata ba dukda akwai laifinta dayawa a abubuwan da suka faru,
Abba na tabbatar zuwa yanzu tayi nadamar duk wani abinda ta aikata na san ummu zata
fi kowa farin cikin komuwan auren nan, Abba Ina so ya mayar da Hamna ta sanadiyata
watakila Allah ubangiji ya yafe min wasu manyan laifukana da ban san dasu ba”.
Ta karashe tana share hawayen da yake gangaro mata, Shiru Abba yayi Tabbas tayi
gaskiya sun sha zama da modibbo da mai martaba akan yadda zasu sa Abdulraheem ya
maida Hamna tsoro suke sbd baud’add’en halinshi kar ya karasa sakin kowa ya huta,
amma se gashi ita Iman wacce ta gaje sunanta ta nemi komen auren da kanta, cikin
sanyin murya yace “Toh Saudah zan duba lamarin zamuyi shawara da mai martaba, duk
yadda mukayi zakiji”.
Sallama sukayi ta kashe wayan tare da mikewa ta fad’a wanka tana iya yinta don
kokarin kauda wani damuwan kishi a ranta musamman In ta tuna ita fa tazo ta samu
Hamna a gidan be kamata tayi farin ciki ba don sun rabu, tana fitowa ta shirya
cikin high-waist skirt dark blue na kanti me fad’i sossai ta d’auko hill black ta
saka ta saka blue black top me dogon hannu se ta rataya scarf black a saman kanta
bayan tayi parking gashinta pony tail, black handbag karami ta d’auka tana shirin
fita taji wayanta na ringing dubawa tayi seda gabanta ya fad’i ganin me martaba,
komawa tayi a sanyaye ta zauna kan ta d’aga.
Gaisawa sukayi a mutunce cikin yanayinshi na sarauta yace “Saudah babanku ya kirani
yake fad’amin wani magana wadda ya fito daga gareki, kin kuwa tabbatar maganan nan
zaki iya?” Murmushi me ciwo tayi cikin ladabi tace “Allah ya kara tsawon rai, zan
iya In Shaa Allahu kawai a d’aura ta taho zan shawo kanshi In shaa Allah” Ajiyar
zuciya me martaba ya sauke kan yace “toh shikenan za’a mayar da auren tare dana
fatima” dib dib dib haka taji zuciyarta na bugawa ta de daure sukayi sallama kan ta
mike ta fito driver ya d’auketa se cikin makaranta.
Basu had’u ba har ta taso tana shigowa gida wanka tayi ta saka wani sky blue half
gown me hannun vest tana son ire iren shigen sbd ita koyaya tana son ta jita sake
ba nauyin komai, a parlor ta zauna tana gyaran nails d’inta a lokaci d’aya tana jin
karatu a wayanta, ta jima zaune nan kan taji turo kofanshi bakinshi d’auke da
sallama da sauri ta mike ta nufeshi ya bud’e mata hannu ta fad’a suka rungume juna
a tare suka sauke ajiyar zuciya cikin kasa da murya yace “I miss you hayatee” tace
“miss you too zaujii, Sannu da dawowa” jan hannunshi tayi zuwa d’akinsu ta tayashi
cire kaya kan ta jashi zuwa toilet akan yayi wanka karshe tare sukayi wankan bayan
sun gama soyewarsu a toilet d’in.
🖤Gureenjo🖤
🥀NOOR IMAN🥀
*056*
END
Bayan wattanni.
Zuwa yanzu an jima da sallaman mama taji sauki sossai se d’an abinda baza’a rasa ba
na Ciwon sugar da take fama dashi, auren zahra ya kara matsowa Don yanzu haka saura
sati biyu, ta ‘bangaren soyayyarsu da Abdulraheem kuwa ba abinda ya ragu se ma
abinda ya karu sbd bayyanar ciki a jikinta kulan da yake bata na safe daban na rana
daban na dare daban, ta tabbatar da yana da dama ko kuda baze yarda ya sauka a
jikinta ba bare har tayi wani ciwo.
Kaman yau zaune take tayi nare nare tana cin grilled fish hankalinta kwance tanayi
tana kallon wani film a tashar Bollywood, ringing d’in wayanta ne ya d’auke mata
hankali daga kan kallon da takeyi ta duba wayan se taga ummu ce ke kira, da sauri
tayi picking tare da sawa a handsfree cikin sabo da so tace “ummun mu Barka da
warhaka” ummu tace “Yauwa daughter ya kk? Ya jikin?” A kunyace tace “Da sauki ummu
am na warke, ya shirin buki?” Ummu tace “za de ki warke daughter, shirin buki
gashinan munayi zakuyi missing bukin autana” Tace “wallahi kuma banji daad’i ba
dama muna hutu” ummu tace “haka Allah ya kaddaro, kina de cin abinci yadda ya
kamata kam?” Tace “eh......” katseta yayi da cewa “Ina kuwa take ci ummu kullum
abincin kenan gasashen kifi na rasa yadda zanyi da ita ta dinga cin abincin” ta
tsorata Don sam bataji shigowarshi ba hakan yasa ta harareshi.
Murmushi yayi jin ummu na cewa “Ina zata samu abinda zata ci a garin masu jajayen
kunnennan bari ma kaji bazan bari ta haihu chan ba kula ba daga ta shiga watan
haihuwa zata dawo In kaga dama kayi zamanka tunda lokacin Hamna na chan”
murmushinshine ya d’auke jin magannan ummu cikin rashin fahimta yace “wani irin
hamna na nan ummu?” Ya karasa yana kallonta kauda kai tayi cike da rashin gaskiya
ranshi ne yaji ya fara ‘baci, cikin sanyin murya ummu tace “daughter ki kula da
kanki se anjima” ta kashe wayan, duk shiru sukayi na mintuna kan ya daure yace
“Saudah me hakan yake nufi?” Nan ma Shiru tayi cikin d’aga murya yace “dake
nake!!!” Razana tayi don rabon da ya mata tsawa haka tun ranan a masarautar modibbo
Adama.
Cikin sanyin murya tace “I’m sorry za’a mayar da aurenku da Hamna randa za’a d’aura
na zahra” kankance ido yayi yana me mikewa har ze yi magana se kuma ya fasa ya wuce
a zuciye zuwa d’ayan d’akin dake gidan kwanciya yayi ranshi na suya wai sun fishi
sanin abinda yake so ne da zasu yanke mishi hukunci ba tare da saninshi ba? Danne
‘bacin ran yayi ta kokarin yi har bacci yayi awon gaba dashi.
Ranan haka suka yini be ce mata ci kanki ba sede ya fita ya sayo mata gasashen
kifinta me zafi yazo ya ajiye mata, ze fita kenan tayi hanzarin rumgumeshi ta baya
cikin kuka tace “kayi hakuri abinda ya dace ne nayi” in tana bashi hakurin nan
ranshi kara suya yake yadda ya tsani hamna da uwarta ace wai za’a mayar mishi da
aurenta taya ze yi adalci a tsakaninsu? Zame jikinshi yayi cikin son danne ‘bacin
ranshi yace “abinda ya dace? Abinda fah ya dace kikace? Kece zaki zauna da ita In
ta dawon? Kece zaki sauke mata duk wani hakkin da miji ze bata? Me yasa kika aikata
abinda tun farko na haneki akai for the first time a rayuwanmu hayatee kin tsallake
umarni da gargad’in da na miki aka gayamiki don Ina sonki se ya kasance duk abinda
kike so shi zan yi? Bana sonta na gayamiki bana sonta......” Shiru yayi jin kukanta
ya fara hawa kanshi yayi yawan da har numfashinta na fisgewa dama cikin ya bata
wahala sossai.
Kan ya kuma wani maganan ta sume mishi a rud’e ya d’auketa se asibiti da hanzari
aka kar’beta doctors biyu suka rufu kanta shi kuwa se zirga zirga yake yana jin
tsanan hamna na kara yawa a ranshi gashi zata mishi sanadiyar yaro tunda ita duk
zamansu bata bashi ba, wadda zata bashin kuma tana kokarin shiga tsakaninsu awansu
biyu a kanta ta farfad’o likitan ya fito yana fad’an yace cikin nan lalla’bashi ya
kamata ayi Don har yanzu barazanar zubewa yake amma sun ki ji ana barinta shiga
damuwa to ya kuskura ta kuma fad’uwa haka tabbas zasuyi asarar babyn.
Da Ohk kawai ya amsawa dr ya shiga kanta ya zauna tare da rike hannunta bacci take
cikin kwanciyar hankali shima ya kwantar da kanshi daidai cikinta ya jima a haka
kan bacci ya fara fisganshi cikin dare yaji ana shafa kanshi a hankali, d’ago kai
yayi ya kalleta hawaye na gangara a idanunta tace “I’m so sorry zaujii” mikewa yayi
ya hau gadon tare da janyota jikinshi cikin kasa da murya yace “I’m sorry too
hayatee” Tace “ka yafemin kaji ba wai kishinka ne banayi ba hakan shine daidai
shiyasa nake son tayaka abinda yake daidai....” katseta yayi da cewa “shikenan ya
isa maganan nan, na amince ta koma d’akinta sede fa a Nigeria zatayi rayuwanta ban
yadda ta taka kafanta ko wani kasa ba” Shiru iman tayi hawaye na gangaro mata a
haka de ya lalla’bata sukayi bacci.
Washegari aka sallameta satin bukin na zagayowa ya fara had’a kayanshi tsab ya
had’e kayanshi a akwati en daidai tana dawowa daga school ta samu akwatin ajiye da
mamaki ta janye runguman da ya mata tana kallon akwatin tace “wannan akwatinfa
zaujii?” Cikin rashin kula yace “Nigeria zani za’ayi aure ango baya kusa ne?” Dipp
haka fara’arta ya d’auke da kyar ta iya cewa “Yaushe zaka wuce?” Yace “gobe flight
d’in dare zan bi” kai kawai ta gyad’a ta ajiye jakanta ta shige toilet a chan ta
zauna ta sha kuka tana tunanin anya, dama haka maza suke? Ji fah yadda ya nuna mata
baya son auren amma yanzu shine da azar’ba’bin zuwa bayan da na zahra ma be yi
niyyan zuwa ba.
Seda ta gama shan kukanta kan tayi wanka ta fito yana zaune yana danne danne a
system d’inshi hannu ya mika mata cikin sanyi ta make kafad’a juyowa yayi ya zuba
mata ido har ta gama shiryawa cikin kaya marasa nauyi cikinta ya d’an fito a gaban
kayan kad’an Haka, Bayan ta gama fesa turarenshi da yanzu take so bata son nata ta
juyo ta kalleshi tare da murmusawa tace “kallon fah?” Yace “na soyayya ne” yana
d’age mata gira murmushi kawai tayi ta karaso ta kama hannun da yake mika mata ta
fad’a jikinshi ya gyara mata kwanciyan da kyau akan kirjinshi a sanyaye yace “me
yasa kikayi kuka?” Da sauri ta kalleshi yace “yes tun fitowanki hayatee idanunki
suka gayamin haka, ashe har yanzu akwai abinda ze saka ki kuka da damuwa hayatee?
Na d’auka duk matsalanki sun kau da jimawa”.
Tace “Tabbas duk wani matsalan rayuwana ya kau da taimakon ubangiji da kuma naka
ban ta’ba zaton zan yi dariya ko farin ciki na tsawon awanni biyu zuwa uku ba seda
ka shigo rayuwana, Ina sonka Ina kaunarka zaujiii, bani da tamkarka In ka gujemin
wallahi zan illata” rungumeta ya kuma yi yace “har abada bazan iya gujemiki ba don
In na gujemiki kaman na gujewa numfashina ne kiyi hakuri In har action na ya ‘bata
miki rai ba yadda zanyi ne tunda ke kika nuna kina so to dole in sauke duk wani
hakki nawa fara daga tun kan d’aurin aure” Tace “na fahimta zaujii ka taya ni adu’a
please, ka tayani adu’a Allah ubangiji ya sassautamin kishinka nima zan taya kaina
In Shaa Allah” bakinsu ya had’e ya fara sarrafata cikin zallar so da kauna.
Washegarin kuwa ya wuce nigeria sossai tayi kewanshi da kyar ta bar shi ma ya tafin
sbd kukan da take mishi, randa ya isa washegari aka d’aura auren zahra kan aka
mayar da aurensu da Hamna, da dare aka kaita gidanta wato gidanshi na nan kano sede
a kasa yasa aka yi mata nata jeren yace sama na Iman ne kuma be son suyi shearing
komai.
Yana kwance a d’akinshi ta shigo ta duka gabanshi ta fara neman gafararshi cikin
kuka da komai haka de ta samu ya hakura ya yafe mata sede ya fad’a mata gaskiya ko
da ze so ta baze ta’ba iya mata koda rabin so da yake yiwa Iman ba, sun raya sunnah
a daren kaman ko wani ango da amarya, sede kwana yayi be rintsa ba kaman yadda Iman
ma ta kwana ido biyu a kan sallaya shi abinda yafi komai dugunzuma mishi hankali
shine rashin samun layinta yayinda ita kuma tunanin shi da wata macen ya hanata
bacci da gangan ta kashe wayanta Don kar ta shiga hakkinta.
Aiko washegari ya fara shirin barin nigeria sbd har a washegarin bata kunna wayanta
ba, daga ka ganshi zaka san yana cikin damuwa ko breakfast d’in da Hamna ta mishi
be iya ci ba ya wuce gidansu Iman anan ne mama ta matsa mishi yaci kosai yasha
kunu, ya samu kaninta me bin hafsy ya dawo ya kamallah secondary school d’inshi har
ya fara degree a mutunce suka gaisa kaman yadda sukeyi a waya in Iman na waya dashi
tun bayan dawowanshi, sako kowa ya bashi ya kai mata yayinda ikhram da ikhlas ke
jin daad’in tsarabar da ya ciko musu yace inji Iman har su mama ko wacce da nata
tsarabar da baba da su hafsy da umma duk yace Iman ce ta aikoshi dasu ya kuma
tabbatar musu washegari da asuba ze tashi.
Aiko yana dawowa be wani zama da Hamna dake d’an janshi da hira ba ya wuce room
d’inshi ya kwanta zuciyanshi fall kewanta, a daren ma haka ya kwana zaune asubar
fari yayi wanka ya shirya dayake a daren yaje yayiwa ummu da Abba sallama ummu ta
bashi sakon Iman yayin da Abba ya bashi sakon gaisuwa zuwa gareta be fad’awa Hamna
tafiyanshi ba hakan yasa tana bacci ya ajiye mata sakon kud’i da short note akan ya
tafi.
Yana sauka london ya wuce gidanshi a parlor ya ajiye kayanshi ya karasa d’akinta da
sassarfa kwance ya hangeta akan gado tana bacci wani irin wawan runguma ya mata da
seda ya firgitata ganin shine yasa itama ta rungumeshi tana jin daad’in ganinshi
sakinta yayi yana ‘bata fuska kaman ze yi kuka yace “nayi fushi ma kina nan ke
hankalinki kwance kina sharar bacci yayinda ni kuma kika hanani runtsawa”
rungumeshi tayi tana murmushi yace “seriously kin d’aga min hankali please karki
sake haka kinji? Allah ne kad’ai ya san halin da na kwana jiya da shekaranjiya”
bata amsa shi ba se had’e lips d’insu da tayi ta fara aika mishi da zazzafan
sakonni da ya sashi rud’ewa ya manta kowa da komai sakon da shine malamin amma ta
fishi kwarewa a yau wani irin soyayya ta nuna mishi me tsayawa a kahon zuciya,
ranan har rasa kalmar soyayyar da ze mata taji daad’i yayi, washegari motarta da ta
za’ba tun a nigeria ya iso har colorn sossai ta ji daad’i tayi ta mishi adu’a.
Haka rayuwarsu yaci gaba da tafiya har ta shiga watan haihuwanta sau d’aya yaje
nigeria shima da umarnin ummu da Abba don yaki sam hamna ta biyoshi itace me
kokarin kiranshi don in ta biye ta tashi se juma’a juma’a yake d’aga waya ya kirata
yasha fad’amata shi bafulatanin mutum ne yana da yafiya amma baya da mantuwa hakan
yasa har yanzu ya kasa goge bad image d’insu a fuskanshi shiyasa aka ce ka aikata
aiki nagari Don mutane su dinga ganinka dashi ba mummuna da zasu dinga zaginka a
bayanshi ba koda kuwa ka tuba, tana zaune office d’inshi tana duba wasu books na
psychology kawai taji abu ya soketa a baya gyara zama tayi ta ci gaba da karatunta
kaman an tsikareta a lokaci d’aya mararta ya amsa cikin rudewa tace “wayyo Allah
na” da sauri ya kalleta yace “Lafiya Hayatee?” Tace “I think our baby is coming” Da
hanzari ya mike ya kamata suka fito zuwa mota kan su isa asibiti gabad’aya ta rud’e
ta rud’ashi tana kuka yana mata Sannu kaman shima yayi kukan da gudu aka kar’beta
zuwa labour room cikin sa’a bata fi awa ba ta santalo yaranta ‘yan biyu mace da
namiji.
Ranan taga tsantsan farin cikin da bata ta’ba gani ba a rayuwanta a fuskanshi har
kuka yayi adu’a kuwa har ta rasa adadin da ya mata, hotunan yaran na shiga wayanshi
seda duk wadda yake da contact d’inshi ya samu yaran kyawawa kamansu d’aya da
mahaifinsu ba abinda suka d’auko nata, a ranar ummu, mama, zahra, nenne petel da
Anty rahama suka fara shirin tafiya sbd fir yace bazasu nigeria ba.
Hamna ta so zuwa sede In ta tuna yace mata randa ta sa kafanta ta bar nigeria zuwa
wani kasa a bakin sauran igiyanta In ta kuwa had’ashi da mahaifiyarshi nan ma a
bakin igiyanta d’aya dake hannunshi dukda tayi hankali sossai yanzu tana aiki ba
business ba Sannan ta shiga makarantar koyon girke girke ba girkin da bata iya ba
ta kuma nemi yafiyar ubangiji kullum tana kai In ta tuna yanzu Ina abokan sheke
ayarta umma da jawahir? Umma tayi mutuwar wulakanci yayinda jawahir ke chan a kulle
sbd sharrin da wani alhaji ya mata na kashe matarshi Bayan shi ya kashe ta sbd ta
ganshi da jawahir suna aikata masha’a sbd kar ta tonashi ya fad’i a siyasa yasa ya
mayar kan jawahir, ya kuma sa mata miyagun kwayoyi a jaka da bindinga nan take aka
mata d’aurin rai da rai, ita kad’ai ta saura wacce Allah ya nufa da shiriya shiyasa
halinta na yanzu ya zama daban da na da, sede ta kasa daraja a idanun mijinta
kasancewarshi marar mantuwa kuma tun da chan ba wai sonta yake ba asiri ne yasashi
aurenta.
Gidanta ya cika makil da en uwa don musamman nenne ta bada jakadiya aka taho da ita
tace bazata koma ba se tayi arba’in ta had’o ta da duk wani abinda me jego zata
bukata na lafiyanta da dawowar duk wani ni’ima da ta rasa yayin haihuwa mama ma ta
taho da nata haka ummu ma, ta zama wata er gata se shagwa’ba take zubawa son ranta
ranan suna yara suka ci sunan ummu da modibbo, Rashida da Abubakar inda zahra da
take da karamin ciki itama yanzu ta sa musu inkiyan ziyad da ziyadah.
BAYAN WASU SHEKARU
“Ziyadah bance kiyiwa Aaman, Aayan da Asad wanka ba?” Cikin shagwa’ba da harshen
turanci tace “Ammiey please jakadiya should bath them I’m busy with my assignment
now” Iman tace cikin fad’a “Ina wasa dake ne? Jakadiyar sa’arkice? Kin wuce kin
watsa ma yarana ruwa ko se na mareki Sannan In sake miki magana da hausa ki mayar
min da wannan yaren nasaran kiga yadda zanyi dake” mikewa ziyadah tayi tana turo
lips d’inta irin na ubanta ta nufi room d’in yaran tana shiga tace “boyssss” ihu
suka yi suna cewa “yessss sister” tana murmushin son kannen nata tace “it’s time
for bath” ihun first, second and third ne ya cika d’akin girgiza kai Iman dake
saurarensu tayi ziyad dake zaune ta kalla tace “se na ce kaje suna fitowa kana
shirya su ko?” Mikewa yayi ya shige d’akin en mazan shi d’akinshi daban haka
Ziyadah ma, in tayiwa d’aya yana fitowa zai shiryasu ya shafa musu mai da perfume.
Iman bata musu tashin sangarcin kasan waje ba ta musu tarbiyya kaman ba wata kasan
suke na turawa ba Sannan ita a tsarinta bata musu turanci duk wadda ya mata turanci
kuwa ze sani ne, ziyadah da ziyad na shekaru bakwai yanzu yayinda Aayan wadda yaci
sunan me martaba Muhammad ke biyar, Aaman wadda yaci sunan babanta na uku yayinda
Asad wadda shekara d’aya ne kawai tsakaninsu da Aaman wadda yaci sunan baba
galadima Abdulraheem kuma sunan mahaifinsu, a kullum Malabo alfahari yake da sama
musu uwa ta gari me kula da duk wani motsinsu tun haihuwanta na farko suka amshewa
nenne jakadiyarta ta zama nasu har tsawon wannan shekarun bata koma ba.
Su da nigeria sede zuwa a wani zuwan da sukayi ne Allah yayiwa inna rasuwa Bayan ta
roki yafiyar Iman, iman ta yafe musu gabad’ayansu tun da jimawa tunda suma ba yin
kansu bane, har yanzu Allah be ba Hamna haihuwa ba kuma zamansu da Malabo har yanzu
kaman da ba wani soyayya sede zaman hakuri da kyautatawa kaman da se yayi wattani
biyar be je ba, akwai lokacin da Iman tayi niyyan ba Hamna Asad firrrrr Abdulraheem
yaki yayi maganan da ya ‘batawa kowa rai dayake a lokacin sunan zahra ne kowa na
nan har ummu, har seda Iman tayi danasanin fara maganan cewa yayi “Ina me rantsuwa
da mahallicina ba d’ana guda da zan bata saudah a lokacin da nake son ta haihun ba
pills tayi ta sha har ya ‘bata mata mahaifa ba? Aka gayamata anayiwa Allah dabara
ne? Aka gayamata se abinda take so Allah zeyi ne?” Yana kai nan ya juya ya fice
tayi kuka sossai gashi da gaske mahaifarta ya lalace ta tuba ta tuba har ta gaji,
Allah be bata daman haihuwa ba Sannan be had’ata da mahaifinta ba har rana yi tayau
(Allah ka rabamu da aikin nadama, Ya kamata mu fara nazartar abu tun kan aikatashi
wani laifin ko ka tuba waenda suke tare dakai bazasu ta’ba mantawa ba).
“Lalala” ta fad’a tana kama baki kan tace “biyu, karka damu zan rama maka” Aayan ne
ya fito karshe shikam dama baya barin ko ta kwana shiyasa yafi kowa shan duka a
wurin yayyun nashi ga taurin kai, yana fitowa yace “Ammiey am so hungry!!! Wayyo
yunwa ze kasheni” dariya ta ci gaba dayi Allah ya gani tana son yaranta sossai,
ziyad ne da ziyadah suka fito last suna tafiya suna magana suna dariya da alamu
wani gulman suke, kallon Ammieyn sukayi da take cewa “oya a wuce dining it’s time
for dinner”.
Duk dining sukayi ta mike da kyar tana cewa jakadiya “sannu da aiki” tace “khaih
Ammiey se kace wani aikin kirki ne nayi” dariya tayi tana cewa “kema bakin yaran
kika d’auka kenan, bismillah zauna mu ci abinci” zama tayi tana cewa “ba dole ba
yaran da suka koyamin turanci karfi da yaji wai su basa son hausa” iman tace “dole
kuwa su so don ubansu yaren uwarsu kenan” tayi maganan kasa kasa yadda bazasuji ba
daga bayanta taji ance “Allah sarki ubansu de ya shiga uku” ihu sukayi da sunanshi
“Abbieyyyyyy” sukayi kanshi suka rungumeshi yana rungume dasu yace “oyoyo my boys”
tura baki ziyadah tayi kan ta kalli cikin iman tace “lil sis we are mad at Abbiey
right?” Yace “oh my princess what have I done wrong?” Tace “you only know your boys
not us” iman ne ta katseshi da cewa “zaujiii dan Allah ka musu hausa” kallonta yayi
kan ya kashe mata ido d’aya ya juya kan ziyadah yace “so sorry my only princess oya
come and hug daddy” da gudu tazo ta rungumeshi.
Bayan sun gama cin abinci aka dasa kallo chan yaran sukayi bacci ziyad da ziyadah
ne sukayi wahalan kaisu makwancinsu kan kowanne ya wuce d’akinshi dama jakadiya ta
jima a d’akinta, kashe kayan wutan yayi kan ya d’auki matarshi chak se d’aki a gado
ya kwantar da ita fuskanshi cikin wuyanta yana shakan kamshin turarenta me daad’i
yace “ya kamata mu gaisa da lil princess kwana biyu bamu gaisa ba” waro ido tayi
tana salati tace “ohhh Abbieyy fad’i gaskiya dae” yace “karya nayi kenan” tana
dariya tace “na isa?? Ban isa cewa hakan ba amma fah ko ita zata fad’i gaskiya da
safen nan taji d’umin mahaifinta” yace.
“I don't know what would I do without you in my life. Your eyes, se ya shafa
idanuntan, your smile ya shafa lips d’inta da babban yatsanshi and the way you look
at me makes me feel like I am living a sweet dream. Ya fad’a yana kissing eyes
d’inta, I don't want to even imagine living a single moment without you. Kin cika
min rayuwa da soyayyarki you complete the puzzles of my life, Kin ban yara kyawawa
masu sani farin ciki a ko yaushe, banda abinda zan saka miki hayateee, I'm so much
in love with you my dearest wife and I will always be for ever and ever”.
Ajiyar zuciya me nauyi ta sauke kan tayi kissing lips d’inshi kad’an tana kallonshi
da idanunta da ta narkar dasu tace “I wish there was nothing else in the world to
do except for losing myself in your eyes. I could continue doing that for the rest
of my lifetime. You gave me everything I wanted. You taught me everything I needed
to know. You helped me with everything when I was down. What more can I ask for?
I'd rather replace my words of love for you with kisses of love. It's a much better
deal, isn't it?” Ta karasa tana kashe mishi ido.
Wani wawan runguma ya mata har seda tace “washhh my baby” dariya yayi yana cewa
“our baby da....” sailing bakinta da nashi da tayi ne ya hanashi uttering wani word
suka fad’a duniyansu na masoya.
Na gode Na gode Na gode kwarai da kaunarku ga wannan littafin bani da bakin gode
muku sede In ce “JAZAKUMULLAHU BILJANNAH AL-FIRDAUS” musamman:-
ANNUR HAUSA NOVELS
NOOR IMAN FANS
MU KARU DA JUNA GROUP
MY WATTPADIANS🥰🥰
Dama sauran groups da suke karanta Novel d’innan.
Ina kaunarku sossai Allah ya sadamu a wani book d’in da rai da lafiya Son So.
🖤GUREENJO🖤