Mintuna 24 da suka wuce Lokacin karatu: Minti 2 Ƙungiyar malaman jami'o'i ta Najeriya, ASUU ta ce sun shiga wata sabuwar yarjejeniya da gwamnati, wadda ta ce idan aka ɗabbaƙa, matsalolin da jami'o'in ƙasar suke fuskanta da dama za su kau. ASUU ta bayyana haka ne a wata sanarwa da ta fitar, inda ta ce waɗannan sababbin matakan da suka aminta, gyara ne kan